*_SO DA ZUCIYA!!_*
*_NA_*
*_NANA HAFSAT_*
*_(MX)_*
*_ZAFAFA BIYAR 2022_*
*_SHAFI NA DAYA_*
*_FREE PG: 1_*
___________
*RIMIN KEB’E*
*GADA MAI ‘DOYI*
*GIDAN ARDO BORKINDO*
(AURE-AURE)
“Wahidi…! Sadaka..! Almajiri bara iya, Iya dan Allah dan annabi, Iya yunwa batada hankali, Iya ko ‘kanzo ne ba miya. Ko gaya ne ba miya…Iyaa…wahidin wahidiya..!â€?
Almajirin nata rera baitin barar sa. Dadaa nata ce masa yayi hak’uri, yaki tafiya, Ya rike robar barar sa ahannun hagu, Dayan hannun kuma ya sakashi a hanci yana sakato daskararren tasono yana gogewa a kodaddiyar rigar shaddar jikin sa ruwan bula, Kayan sun fattatake.
**Fatimah-Zahrah (Zaarah) Yar bafulatanar budurwar na kwance akan shamilalliyar katifar kwanciyar ta irin ta boarding school dinnan. ‘Kulaficin nacacciyar baitin rera barar almajirin ce ta tashe ta daga baccin yunwar dole data dauke ta. Ta ja tsaki tana sosa manyan gashin idanun ta da suka jike da ruwan hawayen ta. Ta juya kanta gefe, Ta sauke idanunta akan mahaifiyar ta dake zaune tana yanke faratan hannun ta.
“Dadaa..�
Ta ‘karasa tana rufe bakin ta, Bayan bahaguwar hammar data taho mata.
“Kin tashi?�
“Na tashi Dadaa! Bansan bacci ya dauke ni ba ma.�
“Ai wannan wanki da kika tula dole ki baccin gajiya, Allah ya yi albarka.�
“Aamin Dadaa�
“Ga abinci can cikin kwanon ki. Tun da zafin sa yanzu nasan ya huce.�
Da azama ta janyo kwanon ta bude shi, Dauke yake da danwake da man ‘k’uli da jan yaji.
“Wayyo Allah na! Danwaken Iya fatsuma. Dadaa ina su Hamma Modibbo Da Na’eelah da Raheelah?â€?
“Su Raheelah sun tafi Islamiyya, Hamman ku kuma bai jima da barin nan dinba. Shi ya kawo danwaken nan ma.�
“Allah sarki Hamma, Allah ya kara budi.�
Cikin haka mahaifin su Malam Ardo borkindo ya shigo cikin gidan bakin sa dauke da sallama.
“Atuwaa,Dadaa ku fitoâ€Ya zunduma musu kira yana daidaita zaman da yayi akan wata ‘ballalliyar kujera da ta gaji da lalacewa.
Mama Atuwa ta fito daga cikin d’akinta tana susar kunne da gashin kaza. Ta tsaya ‘kerere akan sa sanye cikin riga da zani kowanne kalar sa daban. Yaja tsaki yana girgiza kai.
Atare Dadaa da Zaraah suka fita tsakar gidan nasu,
“Bappah Barka da dawowa�
Zara ta tsugunna har kasa tana yiwa mahaifin nasu sannu da zuwa. Ya amsa fuskar sa a daure. A ‘darare ta koma cikin da’ki. Don inda sabo ta saba da tsangwama da kyarar mahaifin nasu.
“Sannu da zuwa…â€? Dadaa ta masa sannu ta rakube a gefe ta zauna.
“Ayau yau, Nakeso a share dakin abincin can. Jibi i war haka amarya zata tare.�
Gaba d’aya Dadaa da Mama Atuwa sai suka zube masa idanun su. Kowannen su kallan sa yake cikin tsantsar mamakin kalaman sa. Dai dai lokacin da almajirin nan ya sake dawowa zaure yana kurma barar da yake. Hade da bubbuga ‘kafar sa a kasan fashasshen dab’en da akayi wa zauren.
“Wahidi…! Sadaka..! Almajiri bara iya, Iya dan Allah dan annabi, Iya yunwa batada hankali, Iya ko ‘kanzo ne ba miya. Ko gaya ne ba miya…Iyaa…wahidin wahidiya..!â€?
“Kundugurin uban ka, Nace kaci malafar kan uban ka. Zaka fita ko sai na kirb’a ka anan?� Cewar Mama Atuwa hade da daga hannu ta masa dak’uwa.
Almajirin ya tsaya sararo baisan abinda yasa take masa fada ba Kamar yayi wani lefin? Zara dake daki ta kirawosa ta bashi sauran danwaken da takasa ci. Saboda maganar auren da taji bappan su zai sake karowa a karo na ba adadi. Yayi ya sake su kamar hular sawa.
“Me muka rage ka da shi da zaka sake karo wani auren Ardo? Nace mai ka nema ka rasa agare mu. Allah ya tsinewa dubu goman da ka samu nasan da ita zaka sake karo auren nan.� Cewar Mama atuwa dake huci Kamar tsohuwar zakanya.
“Toh Malam Allah ya sanya alkhairi ya baku zaman lapia.� Dadaa tafad’a tana mikewa tsaye hade da komawa cikin daki.
Mama Atuwa ta buga tsallen albarka tana doddoka hannunta ajikin bango.
“Ardo! Tselen uban can, Abu ta kazar uban can kayya kai, Wabillahil gidan nan zai babbake akan amaryar nan da zakayo. Ke kuma tsohuwar munafuka kina wani dudduk’e kai, Kamar sabuwar amarya, Har da wani yi musu fatan alkhairi. Toh baki d’aya na hadaku nayi Allah ya isa..�
Malam Ardo yamike yana girgiza kai, Zai fuce ta jawo kasan rigar jikin sa yar shara,
‘Yar karamar ‘yarta da ta taso daga bacci alokacin ta tsaya a tsaye ta sau fitsari, Hancin ta dagaje dagaje da majina, Ta riko fatattakakken zanin Mama Atuwa tana cewa,
“Mama yunwa nake ji.�
Atuwa ta sake damk’o kasan rigar Malam Ardo bata ko bi takan Farillatu yar autarta ba, Cikin tsananin takaici hade da kwakwaso rantsuwa ta dire, Da d’oriyar nanawa cinyarta duka tacigaba da cewa,
“Ni da kai sai Allah ya mana hisabi Ardo. Lokacin da kazo neman aure na mekace shekarun baya? Ca kayi da gani babu kari, Matar ka ta farko ma had’aku akayi ba kai ka ganta kana so ba, Kace ni da kai, Bayan aure zamu gwangwaje mu gyagije, Muci duniyar mu da tsinke, Tarin alkawarurrukan da kayi mun sunada yawa Ardo. Harda cewa Kullum zamu dinga shan shayi da buredi mai yanka yanka Ardo, kace da lemon kwalba da shinkafa. Amma tun sati biyu da auren mu ka dena mun komai. Shekaru sha 15 kenan kadena duk wasu hakki na dana yara na dayake akan ka. Aure 8 kayi Ardo, kowacce da tazo tayi yan satinnai Sai ka rabu da ita, Saboda tsabar bakin hali Irin naka. Samun miji Irin ka nayi dana sani, Dana kori manema na a baya, Na bi kyau ba halin kwarai Irin ka, Allah sarki idi mai kifi. Kullum sai ya aika mani da sukunbiya jela…Ranaâ€?
Bata kasara ba Malam Ardo yaja dogon tsaki yana girgiza kai,
“K’ofa abude take, Duk sanda kika shirya fita… A shrye nake na baki takardar sallama.â€?
Mama Atuwa ta wulla masa harara tana tab’e baki,
“Saki? Hohoho ai naga gidan zama Ardo, Na tara yara har 5 kace na fita? Babu inda zani. Na zame maka kadangaren bakin tulu , Akashe ka a fasa tulu a barka ka ‘bata ruwa. Ahayye Atuwa maman sailuba da Sameerah, Uwar Hajaara da Farillatu…â€?
Malam Ardo yaja tsaki hade da bige hannun ta daga rikon rigar sa da tayi, Ya fice yana mita. Ita kuma Mama Atuwa ta figi hannun Farillatu ta goyata tana jera tsaki, Had’i da yadawa Dadaa maganganu. Ranar kaf dangin Malam Ardo na kusa dana nesa sai da Atuwa ta zage su tas kowanne ta kamo sunan sa, Sai ta aibata shi………….
***Ruwan sama tamkar da bakin kwarya. Unguwar rimin kebe ta wanku da ruwan sama. Ko’ina yayi shar. Bishiyu sun ‘kara rinewa sunyi koraye shar da su. Hamamin warin gada mai ‘doyi ya ragu ainun da falalar ruwan sama.
Tun daga nesa Zaarah ke tafe dawowar ta kenan daga makaranta. Yau din an taso su da wuri sakamakon ruwan da akeyi ba winduna a makarntar, Hakan yasanya ruwan zuba ta cikin kwanukan azuzuwan ciki harda na su Zaarah. Shiyasa malaman suka taso su kafin lokaci ya cika. Dubada ruwan ya kanyi gyara sosai duk sanda aka yi. Kwanukan kan rufto ko kuwa wani sashe na azuzuwan ya zaftaro ya fad’o a kasa. Domin makaranta ce ta gwamnati. Wanda duk wani dan adam ya kalla da idanun basira zai iya cewa makarantar gwamnati ta mance da ita. Domin daliban duk tsatson marasa galihu ne. Akan tabarma suke zama. Malaman kuma akan benchi. Sai madaidacin allo da malaman ke bayani ajikin sa. Da ya gaji da gajiya ya karye sai yan chalks (chak) gustsuraru da malaman kan yi musu rubutu.
Ita kadai take tafiya kan hanyar zuwa gidah daga makaranta. Sanye cikin uniform kalar sararin samaniya. Sai yellow (yalo) d’ankwali dake nuna alamar ita din perfect ce. Kayan makarantar sun zauna ‘das a jikin ta. Duk kuwa da sunji jiki ainun, Ga faci nan ajikin kayan an musu dinkin allura da zare, Ta musu ninkin guga kai kace gogewa tayi da dutsen guga. Saboda yadda suka sha kari. K’afafuwanta sun sha sandal takalmi wanda daga gefe gefen takalman an d’inke da zare irin na musu shoe shiner dinnan.
Ta cikin hijabin kana hango tudun yalwataccen gashinta ta d’aure shi da leda. Bayan ta saqale da jakar baya. Wadda aka rubuta da manyan bak’i na foundation/gidahniyar Unicef. Ita kadai ke tafiya tana tafe tana lazumi. Kamar yadda Dadaa ta umarta su dinga yi. Dandazon sauran dalibai na tafe a bayan ta suna shewa da ife-ife. Ita kuwa Zaarah tana tafe Ita kadai abunta. A haka ta karasa shiga tsukukan layin su. Wanda kwalbati ta ruguje gefe da gefenta nata amayar da hamamin kwatar dake zuba ta tsakiyar kwalbatin.
Sakamakon yalwataccen ruwan da akayi, Layin gaba daya ya damule da cakwalin tab’o mai tsananin dank’o. Ta ‘kusa kai tashiga layin nasu. Wanda baya bullewa. Gidan su ne na karshe a layin. Mai dauke da shago a kofar gidan inda Hammah Modibbo ke kwana. Zata shiga gida kenan ta hango su Raheelah da Na’eelah kowannensu dauke da bokiti da yafi karfin su. Zasu tafi ebo ruwa.
“Adda manga (babbar Yaya)Sannu da zuwa.�
Suka hada baki wajen gayshe da ita.
“Sannun ku, Ina zuwa haka? Wannan bokitan waye?�
Ta tambaye su cikin tsananin mamaki , Sanin bata taba ganin bokitan ba agidan.
“Na Aunty amarya ne.�
Cewar Na’eelah.
“Bappah ne yasa mu, Yace mu zuba mata.� Raheelah ta fada tana sosa idon ta na hagu.
Zaarah ta girgiza kai kawai, Tayi Allah ya kyauta azuciar ta. Kafin ta dube su tace,
“Karku dinga ciko ruwan, ku debo iya karfin ku. Sannan banda biyawa wani wajen. Da kun eho ku dawo gidah kai tsaye. Duk wanda zai kiraku kar ku je ku dawo gidah da sauri.�
“Toh Adda Manga…â€?
Suka amsa baki d’aya.
Tukun sannan ta karasa shiga cikin gidan bakinta dauke da sallama. Dadaa na tsakar gidan tana ebe yan kwanukanta da aka fur fito dasu daga dakin girkin da ya zama parlorn amarya a yanzu. Anata yab’e sashen amarya da fenti. Gidane madaidai ci mai dauke da dakuna uku matsakai ta da dakin girki. Sai band’aki daga can ‘kurya. Wanda katangar gefen sa ta zube. An kare da langa langa. Dakuna biyu na kallan gabas d’aya na kallon arewa.
Masu kawo jeran bazawar Malam Ardo tuni sun gama yi mata jere sun tafi. Dakin an saka gado da mudubi. Dakin girkin daya zama madadin parlorn ta sun saka wardrobe din gadon da kuma kujeru guda uku. Sai manya manyan bokiti a gefen dakin. An cire marafan su, Su Na’eelah Da Raheelah na zuba ruwa aciki.
A haka Zaarah ta karasa kalle kallen jeran amaryar mahaifin nasu. Ta shige cikin dan tsukukun dakin su bakin ta dauke da sallama. Dadaa ta amsa ta, Tana kokarin jere yan kwanukan ta da aka furfito musu dasu daga dakin girkin su daya zama mallakin parlorn amaryar malam ardo.
“Yar albarka an dawo?�
“Na dawo Dadaa. Kinsan duk sanda akai ruwa mai nauyi da wuri ake taso mu.�
“Zahiri hakan take, Toh Allah ya temaka ya kuma baku sa’a.�
“Aamin Dadaa. Naga su Raheelah ai awaje.�
“Eh zasu ebo ruwa ba, Baffan kune ya sasu.�
“Amaryar ta taare ne?�
“A’ah, Yan uwanta dai sun zo sun yi j…â€?
Bata karasa ba sakamon fad’owa dakin da Atuwa tayi cikin tsananin furgici da ‘dimuwa.
“Jammu…â€? Ta kira sunan Dadaa cikin rawar baki da dimuwa.
“Na’am Atuwa. Meya faru?� Cewar Dada da hankalin ta gaba d’aya itama ya tashi ganin yanayin na Mama Atuwa.
Atuwa ta yage jemammen hijabin jikin ta, Da yayi du’kun dukun dashi da datti. Ta shiga sosa duddugaggen gashin kanta tana in’ina.
“Kinsan wa Ardo ya auro mana?�
Ta shiga tambayar Dadaa tana nuna yatsanta d’aya ga parlorn amaryar ta Malam Ardo. Dadaa ta girgiza kai alamun a’ah. Zaraah dake gefe ta baje kunne.