Search
You have no alerts.

    Samrin Bana Chapter 5

    05

    [3:01PM, 17/11/2016] Rahamat Nalele 👯:

    Suna tafiyar cikin nutsuwa RAMADAN ya kalli SAILUBAH ka’dan Yace Auntyna ki dinga gyara abu pls kidena  6atawa

    Tayaya xa’ayi Ki gaya mata tashare mijinta.

    SAILUBAH Tayi mai banxa

    Shi kuma yanace sai tayi magana ya qara kallanta

    Haba mana dan Allah Auntyna ki dinga gyara ki dena 6atawa ki dena xiga mutum yanxu kin xigata akan ta yaudari ‘Yar uwarta inkece aka xoma ta wannan hanyar……

    Da fusata ta katseshi da cewa. Waiwa ya gayama ni xugata nayi shawara na bata wacce ta dace da ita. Tafa’da da 6acin rai

    Shuru yayi mata dama so yake tayi magana kuma tayi

    Har suka qaraso gida bai qara magana ba

    Yana parking tafuta daga motar da xafin rai. Yabita da kallo yayi Murmushi

    itako tana xuwa ‘daki tasaka key dan tasan ba barinta xaiyi ba

    KHAMIS da XEE ko shuru kakeji acikin motar bamai magana acikinsu

    Saima XEE ce da lokaci lokaci takan kalli KHAMIS ‘din dan xuciyar tata hanata daurema kallansa

    Da yayi parking a ‘kofar gidansu ya kalleta cikin wani yanayi ya sanyaya murya Yace my Aunty mun’iso

    Duk da XEE tasan sun iso hakan bai hanata kallansa cikin sauri ba. Dan muryar da yayi amfani da ita wajan yi mata maganar ta shigeta ba’dan ka’dan ba. Ya lura da hakan sarai. saiya futa daga motar yaxo ya bu’de mata motar kamar yanda masoyi yake yima masoyiyarsa

    Tafi toh xata ‘dau jakarta sai kawai yayi saurin ‘dauka yana cewa da alamun gajiya atare dake my Aunty xanso in kai miki har gida idan kin amince min. Yafa’da da jifanta da wani kallo mesaka Sarki yayima Bawansa ladabi.

    Da sauri Tace na amince. Ya qura mata ido

    Tace lafiya kike kallona haka

    Yayi Murmushi yace Wlhi wani tunani na shiga. Tunda nake dake Aunty XEE ban ta6a jin da’din muryarki irin tayau bah…….

    Da’di kamar ya kashe XEE Tace sai yau ka ta6aji

    Ya waro ido Yace kinga xan ‘daure Kaina. Ai Kullun muryarki acikin da’din sauraro take

    Tace toh Nagode

    Ta shige gaba yana binta abaya yana qare mata kallo har suka iso falan gidan Yace mamah bata nan ne. Tace gashi dai daga dukkan alamu

    Ta ibo drink taxuba mai a cup itama tasaka ma kanta kana Tace xanso kasha Qanina

    Ya kar6a da Murmushi Yace banso shaba dan banajin shan Komai saboda damuwa Amma tunda kinaso nasha ba’abin da xai hanani Sha

    Sanda ya Sha ka’dan Tace meya sakaka cikin damuwa Yace Wlhi Aunty wata nake So❤ saidai ta girmeni ban san ya xanyi bah

    Da sauri ta furzar da drink ‘din da yake bakinta ha’de da sakin cup ‘din ya fa’di qasa……

     jikake tass ya fashe

    Tayi saurin xamowa daga kan kujerar da take cikin tashin hankali Tace wa kakeso kuma

    Da sauri ya matso  kusa da ita da ciro hankicif ‘dinsa cikin nuna tsoro ya kama hannunta taji wani shock shima yaji Amma ya share ya  fara goge mata hannun nata da gefan bakinta Yana cewa am sorry Aunty XEE na tada miki da hankali ko. Karki damu nasan baxata soni bah. Sai dai Wlhi baxan ta6a Auran wata mace ba in ba ita ba. Ya qarashe maganar da sake mata hannun nata

    Aiko saiga hawaye ya xubo mata cikin kuka Tatashi xata bar falan.

    Yace baxan ta6a yafema kaina ba idan har kika tafi cikin kukan nan kika barni  batare da kin gayamin dalilinki nayin shiba

    Juyowa tayi ahankali Tace KHAMIS nakamu tasan wani yaro wanda na girme masa gashi kaima kakamu dasan wacce ka girma. Ganin da nayi matsalarmu ‘dayace shi yasani rikicewa har nayi wannan kukan

    KHAMIS yajah numfashi ha’de da lumshe idansa yanajin kukanta har cikin ransa kana ya bu’de idan

    Yace ki dena bana so bana san jin kukanki yana damun xuciyata pls kitsai dashi karci sakani cikin wani dan Allah

    Ahankali XEE ta qaraso gabansa Tace shin abinda kafa’da haka yake

    Yace akan me xan miki qarya. Yafa’da yana mai goge mata hawayan

    Kawai ki share my Aunty xan kiraki anjima kiban shawa’a akan ya xan 6ulloma da ita budurwar tawa. Sannan kema kinemi shawarata akan wanda kikeso. Tunsa kinga mu SAMAREEN BANAH ne xan iya baki shawara yanda xakiyi dashi kema Kinga kyabani shawarar yanda xanyi da ita

    Shuru tayi masa

    Shiko har yakai ‘Kofa ya juyo ya dawo dan yana so ya hanata bacci

    Ya shafi gefan fuskarta Yace kimin alqawarin xaki cire damuwa aranki my Aunty

    Tace idan na iya cire ko wacce damuwa araina ai baxan iya cire damuwar SO ba

    Ya lakuce mata hanci Yace insha Allah xaki kasance da wanda kikeso dan shima yana MASEEFAR SONKI

    Tace ya akayi kasan hakan bayan…..

    Ya katseta da cewa saboda ko makawone yaji wuccewarki kawai yanasan Allah yayi halittar kyakkyawar mace anan

    Tayi Murmushi Tace yanxu kai ka tabbatar da hakan

    Yace Wlhi ayanxu bawanda ya kaini tabbatar da hakan koda ko Ya Surajo ne

    Ta ‘daure fuska xatayi magana Yace bye bye sai munyi waya Ya fitta

    Tabishi da kallo

    Sallar magriba  SAILUBAH tayi tafa’da tunanin wani Alhaji Aliyu da ya kirata ‘daxo wai abikin Saudat ya ganta dan Allah dan annabi tabashi dama yaxo gareta. Yanda yake rokwanta ne yasata bashi ixinin yaxo

    Tana tunaninsa ne zaizo bayan Isha’i ne ko xaixo gobe bata sani ba

    To ganin yanxu mah  taji wayanta na ringing sai tayi  tunanin shine

    Ashe bashi bane wanine kuma wai Alhaji Aminu

    Duk dai abikin Saudat ne suka ganta. Yana gaya mata dan Allah taso shi Yana Santa  yana garin Abuja da xama. Baida mata. Kuma da maganar Aure xaixo gareta dan Allah tabashi dama yaxo gareta

    Dan yanxu haka yana Cikin garin kano dan gobe yake san komawa Abuja

    Toh fah😳 kunsan SAILUBAH da Alhazawan garin abuja ba qaramin so take musu ba dan ku’dinsu nan take taji ya wanta mata arai dan muryarshi nada da’di

    Amma danta gwada shi sai Tace hmm banajin yau xaka ganni dan nagaji da yawo sai gobe

    Kamar xai mata kuka yake mata magiyar tayi hakuri ya ganta dan Allah Tace toh kaxo Amma kasani minti biyar kacal xan baka

    Yace angama ranki ya da’de

    Bayan tayi sallar isha’i. Kyalliya tayi Sosai RAMADAN Yace Auntyna wannan kwalliya haka. Sam ta manta sunyi fa’da ‘daxo taje takama hannunsa ta sakarmai kiss a kumatu  Tace yau burina ya fara cika nayi saurayi ‘dan abuja anjima xaixo

    Da tsoro RAMADAN ya waro ido cikin wani yanayi Yace pls Auntyna Karki soshi dan Allah

    Ta galla mai harara tare da sake hannunsa tana ta6e baki Tace Wlhi saina so shi

    Kuma na ranshe da Allah kakorar min shi saina maka dukan tsiya

    Yayi Murmushi Yace wasa nake miki baxan koreshi ba

    Sam SAILUBAH bata yarda da murmushin da yayi ba. Dan tasan halinsa sarai fa’danta da cika bakinta baya hanashi korar mata su. Dan haka sai Tace suje ‘dakin shi xata gaya mishi wani Abu

    Haka ko sukayi gidansu dayin part ‘dinshi

    Suna shiga ‘dakin tacire key ‘din ‘dakin nashi tafita da gudu ta kulle shi ta baya tana ai nasan maganinka

    Ta window ta leqo tasheqe mishi da dariya Tace in yaxo ya tafi xan dawo in bu’deka. tana fa’din hakan tabar gun

    Shuru RAMADAN yayi yana tunani

    Gaskiya ta shamma ceshi dan yasa aransa ko ganinsa baxatayi ba xai koreshi Ashe ta ankare dashi

    Yayi kwafah da fa’din ni da ke har abada muna tare da juna Auntyna

    SAILUBAH na shiga gidansu saiga Alhaji Aminun yaxo

    Sanda tashafe minti goma Sha biyar Sannan taje gareshi

    Yace ina wini tauraruwa me haskake taurari

    Tace lafiya da fatan kaxo lafiya Yace lpy lau

    Tace toh Madallah

    Nan ya qara fa’da mata shi ko Waye

    Wai yana Saida ‘dan kunne da tsarqa na xinare ne a Abuja iyayansa ‘yan nan kanone sana’ar tasa ce takaisa Abuja

    Sosai mutumin ya tafi da imanin SAILUBAH dan ganinshi da tayi kyak kyawa ga  xaxxafar motar da yaxo da ita

    Ta’dan dai bashi dama haka

    Yace Yaji da’di xai turo iyayansa suxo dan bai ta6a SOYAYYA ba bayasan yaudarar mata

    Kuma komai xa’ayi shi da sauri

    Tace toh itadai saita xanta da mahaifinta tabashi labarin yanda sukayi Yace duk da haka xai turo iyayansa gobe

    Daxai tafi saiya bu’de mata wani qaramin akwati Yace ta ibi iya adadin ku’din da takeso

    Nan cikin SAILUBAH ya mun’da dan ganin yawan ku’din kuma duk ‘yan dubu dabu ne a ciki

    cikin wani yanayi Tace ka barshi Nagode

    Yace aa fah ina San Ki ‘dauka ko ku’din xai sami farin jini aguna kisa mai albarka dan Allah

    Tace aa dai ka barshi

    ‘Daukar wata leda yayi yasaka mata bandir ‘din ku’dinnan guda goma😳 miliyon ‘daya kenan a ha’duwar farko.

    Ya saka mata akan cinyarta Yace nasanki da temako duk xaki iya bayar da wa’yan nan Amma dan Allah ko naira biyar CE kici aciki

    hakan xaisa inji da’di. Ga wannan cikakken bayanai ne akaina kiba Abbanki nasan mah xaisan mahaifina

    Shuru SAILUBAH tayi tafuta daga motan da ku’din a hannunta.

    Tana kallansa yafita da motar tashi  yana ‘daga mata hannu

    Bayan 6ace warsa tayi cikin gidansu da gudu tayi ‘dakinta ta xaxxage ku’din a gado. tana murna sai watsa ku’din take sama tana ta dariya

    Can ta tuna da RAMADAN. Aiko da gudu ta’dau kin ‘dakin nasa tafitoh xuwa Gidansu ko gyale babu ajikinta sai ‘dan kwalinta data rufe kanta dashi xuwa kafa’darta

    Da sauri take bu’de ‘dakin tana bu’dewa takama hannun RAMADAN tana jansa har cikin gidan

    Sanda sukaxo ‘dakinta taja musu burki Tace kalli gadona

    RAMADAN ya xaro ido cikin tsoro Yace Auntyna wannan ku’dinfah

         Tayi dariya ta ‘dane gadan ta watsa ku’din sama Tace aikin Alhaji Aminu ne

    Sai kuma tasauko ta ta tsaya agabansa

    Kaga burina xai cika xan xama matar Babban mutum. xan mallaki ku’da’de masu yawa. xanje gidan marayu inbata tallafi. xanje asibitoci nakai xiyara………

    Ya isa da Allah Ki mayar masa da ku’dinsa

    Cak ko ta tsaya da maganar tata

    Tace kut……

    Na lura ba qaramin Baqin ciki kake yimin bah. Wlhi inxaka mutu baxan mayar da wannan ku’din bah

    Ban da haka me xaisa na mayar masa da ku’dinsa

    Tambayarka nake kaban amsa.

    RAMADAN yaja numfashi Yace saboda ba sanshi kike ba ku’dinsa kike so

    Yanxu ya dace Ki yaudare shi

    Tace eh ai rayuwace

    Qila indan na Auresa naji ina sansa

    Yayi Murmushi Yace toh Allah ya tabbatar da alkairi

    Tace AmEEn Amma kadena min baqin ciki Sannan inaso gobe kaxo ka rakani gidan marayu da wajan almajirai

    Kamar ya tsinka mata mari haka yaji Yace gaskiya baxan ‘dauke ki da wannan qaxan taccan ku’din ba, ma’ana baxanje ba

    Tace toh shi kenan karka kar kaje. Ainima nakusa yin mota xanje ko ina da kaina basai nane mi ka kaini ba jeka nagode…….

    Da mugun kallo yabita kana Yajuya ya futa xuciyarsa nayi masa xafi

    SAILUBAH ta bishi da kallan harara. Kana ta ha’de ku’da’danta tanemi guri ta adana Sannan tanemi kiran XEE.

    RAMADAN juyi ya dinga yi akan makeken gadansa duk ya rasa nutsuwarsa

    Can yatashi yana safah da marwah yana tunanin ta inda xai biyoma Auntyn tasa

    Yasan tashiga da yawa. Da gaske wannan karan saiya bita ahankali

    Yana cikin tunaninne FAWAS ya shigo ‘dakin nasa shi da KHAMIS

    FAWAS Yace lafiya naganka Cikin damuwa

    Yace Auntyna ce ta jefani cikin damuwar kun santa da ku’di

    yanxu tayi wani tsinanne wai daga Abuja.

    Ni damuwata yanxu na sanshi.

    FAWAS Yace tokai mexai dameka

    Yace kun kasa ganewa har yanxu

    KHAMIS yayi Murmushi Yace hmm Aunty LUUVAH kenan

    Ni dai tana burgeni Sosai. Tana burin ta mallaki ku’di masu yawan gaske. Kuma ta temakama marasa shi

    Wannan burin nata yaba tsumani ba’dan ka’dan ba

    FAWAS Yace toh wai me xai dameka akan hakan Bayan kafi kowa sanin wannan burinta ne

    RAMADAN Yace dole Komai ya dameni akanta.

    xaku gane ne nan gaba. Ya dafe kansa na mintunoni

    Can ya saki murmushin mugunta dan tuno da wani abu wanda in yayi mata xai bala’in 6ata mata rai har Tace ta hakura da Alhaji Aminun

    ya kalli KHAMIS ya ‘dora da fa’din ya Aunty XEE…

    KHAMIS yayi dariya Yace tana nan qalau na burkitata kamar yanda tayi nasarar burkitanin daga ankarewa da ita.

    Wlhi RAMADAN banajin ko wacce mace arai ayanxu kamar Aunty XEEE

    Ya abin xai kasance idan kunya ta hanata furtamin Kalmar SO

    Ha’da ido FAWAS da RAMADAN sukayi atare kuma suka saki Murmushi

    Shege yaga cikakkiyar mace

    Ai dole kaso ta. Dan ta ha’du tako ta’ina

    Kagaya mata pls karki dinga hargitsata. dan nasan ka’dan da aikinka ka tarwatsa mata kwanya…….    Cewar FAWAS

    KHAMIS yayi dariya Yace aina rigada na tarwatsa mata kwanyar dan Wlhi yau nayi alqawarin saina hanata bacci

    Yanxu haka nasan tana cikin damuwa dan na jefata cikinta

    RAMADAN Yace ya isa haka dan Allah

    Pls karka wahalar da ita da yawa

    Dan bana san tashiga damuwar da har tasata jefamin Auntyna aciki.

    KHAMIS ya tashi yana dariya Yace Aunty LUUVAH ka sani kawai. Itace damuwarka karka damu baxan bari she’daniyar xuciyata ta wahalar da Masoyiyata ba. Bare ta shafama Auntynmu

    FAWAS Yace lokaci yayi ya kamata muje ko

    KHAMIS Yace ina😳

    Ai yau ba xuwa xance bare club dan wannan daran na Aunty XEE ne xanje gida ina buqatar kwantawa in tsara mata kalamai. Na barku lafiya (ya fita) cikin nisha’di

    FAWAS Yace naso naga Aymana Wlhi

    RAMADAN yayi Murmushi Yace kanajin wani filing kenan dan baka xuwan axxiqi

    Yace hmm watoh RAMADAN ina San Aymana Amma banajin xan Aureta Gaskiya. Kuma abin mamaki ta tsaya min arai kamar maiya

    RAMADAN yayi Murmushi Yace har yanxu dai kana tana tare da wannan burin naka

    Yace sosai ma kuwa

    Damuwata ‘daya a ina  xan sami ‘Yar Qauyan

    Yace hmm yanxu dai muje in rakaka gun Aymanan Amma dan Allah karka matse musu ‘ya dan abinda kayi shi xa’ama ‘ya’yanka

    Yace kada’de kana fa’da mana wannan Kalmar inda karatune nasan ni xanxo na ‘daya pls muje dan Allah karkace komai

    RAMADAN ya ta6e baki Yace toh Allah ya ganar daku……

    Qawata nashigo babbar harka fah😀

    Gaskiya arxiqi da’dine dashi. Na samu wani Alhajin Abujah Wanda ya rikitani yan xunnan da tsabar ku’di har nera million ‘daya………

    XEEE wacce take kwance tana jinyar xuciyarta da tatafi da tunanin KHAMIS Wanda ya hanata nutsuwa Sam…..

    Aiko tanajin furucin SAILUBAH tadiro daga gado Tace what one million naira 😳

    SAILUBAH tayi Murmushi Tace kema abin yabaki mamaki ko. Karya tsoratar dake dan yanxu aka fara wasan

    Inaso gobe kixo gida ki gani ganin idanki

    idan kuma kintashi xuwa kixo da Wannan qaramar jakar taki dan ki sami rabanki

    XEEE Tace abin mamaki dama nasan burinki xai cika. Xaki ganni qarfe tara gobe yanxu ma dan dare yayine

    SAILUBAH ta kwashe da dariya Tace shegiya XEEE taji maganar nera aiko goban xaki wanke idanki dasu

    Tace na sani aminiyata idan ina tare dake ban wanke idona da naira ba ai babu ranar daxan wanke idan dasu

    SAILUBAH tajah numfashi Tace ya kikayi da qaramin yaran naki

    Tace hmm ina sane ai naqi kiranki dan ya burkitani

    SAILUBAH Wlhi Wlhi Wlhi ina MASEEFAR SON KHAMIS Ya Xanyi

    Nan takwashe Komai tagaya ma SAILUBAH.

    SAILUBAH tayi mata dariyar rainin hankali Tace karkiyi yunqurin ki ransa. ki bari har sai shi yane meki akan ki bashi shawarar imba haka bah Wlhi ina tabbatar miki saiya baki wahala  yadinga garaki

    Tace Kinga ko kiran shi ya shigo a qaramar wayata kamar yasan hirarshi muke

    SAILUBAH Tace yauwa. Na sanki da rikicewa kinutsu karya rainaki da yawa pls

    Tace hmm SAILUBAH kenan bakiji yanda jikina yake rawa ba.

    SAILUBAH tajah tsaki Tace Gaskiya kinada matsala XEEE da Takaici

    XEEE tayi dariya Tace hmm Allah ya jarrabeki dasan qaramin yaro kiji fiye da yanda nakeji……….

    Cikin maseefa Tace ba AmEEn ba ‘yar is…….

    XEEE ta katseta da cewa saida safe ta tsinke hirar tasu

    SAILUBAH Tace tajah tsaki Tace Allah ya rabani da soyayyar qaramin yaro……..

    XEEE ko bajewa tayi agado tatattara nutsuwarta cikin bugun xuciya ta’dauki wayan KHAMIS Wanda saura ka’dan tayanke a karo na biyu

    Tace hello

    Yace inata kira Aunty. Allah yasa jin da’dine da lafiya da kwanciyar hankali ya hanaki ‘dauka

    Tayi murmushi Tace toh bansan me xance maka ba KHAMIS Amma ina cikin lafiya da kwanciyar hankali musamman mah yanxu

    Yace toh madallah dama nakiraki ne akan………

    Sai kuma yayi shuru

    Cikin sanyi XEEE Tace akan nabaka shawara kan budurwarka ko

    Tace eh Aunty Allah yasa baxan takura miki ba. Wlhi xuciyata CE take san xuwa gareta yanxu gashi kuma idan naje bansan me zance mata ba

    Shuru XEEE tayi kishi nacin xuciyarta.

    Dama ace ina tare dake tana shafi gefan fuskarki na dawo dake daga tunanin da kika fa’da

    KHAMIS ya fa’da Cikin sanyin murya….

    Join Us on WhatsApp Here

    0 Comments

    Heads up! Your comment will be invisible to other guests and subscribers (except for replies), including you after a grace period.
    Note
    error: Content is protected !!