Saifudeen by billy giro a complete hausa noevel
Bismillahi rahamanir rahim
.
Zan fara da sunan Allah ina kuma fatar na kammala da yardar shi.
Allah yasa haka amin.
Baya Kafin faruwar hakan.
Tsaye yake gaban mirror d’aure da farin towel a qugunsa yana taje sumar kanshi,wanda kallo d’aya zaka mishi kasan cewa hadadden guy ne shi,first class da sam bai aje kanshi kusa ba.
Sosai yake matuqar ji da kanshi sbd Allah yayi shi me tsananin kyau tamkar shi yayi kan shi.
Shiyasa sosai kyawawan en mata ke rubibi akan sa amma sam baya kula su,mace d’aya kawai yake kulawa wato “Sophie”wata classmate d’isshi da sukayi karatu tare a London wacce yanzu haka tana nn Nigeria ta biyoshi.
Bayan ya gama taje sumar kanshi ne ya tafi da cumb d’in yana qara kwantar da sajen fuskar shi dake kwance luf kan farar fatar shi tas wacce tamkar ka kwanta jini ya fito.
Sai da ya feshe jikin sa da body spray snn ya nufi kan bed inda ya ajiye kayan sawar shi da ya ciro,ya zauna tare da cire towel d’in jikinsa ya cillar gefe,ya janyo guntun wandon sa fari qal ya saka snn ya saka dogon wandon sa na suit silk fari,rigar ciki baqa yayi stocking da black belt,ya saka necktie fari,sucks baqaqe da takalmi baqaqe snn ya saka er samar shi fara,ya fesa turare kana ya d’auki briefcase d’issa ya fito bai zarce koina ba se 6angaren iyayen shi.
Ya sami mahaifiyar tashi ta fito daga kitchen tana jera breakfast kan dinning.
A natse ya gaida ta fuskar sa ba yabo ba fallasa,byn ta amsa yace am going.
Da sauri ta kalle shi tace”breakfast fa gashi har na kammala had’a komai ka d’an tsaya mana kaci ko kad’an ne”
Yace”No umma ina sauri ne”
Ba tare da ya jira me zata ce ba yasa qafa ya fita abin shi.
Ta bisa da kallo kawai tana mamakin yau ko Abban sa bai je ya gaida ba ko lafiya,nan se ga Abban na shi ya fito cikin shirin sa tsaf na fita,ta kalle sa tace kaddai kaima fita zakayi hakan nn baza ka ci komai ba kmr yanda saifuddeen ya fita.
Komai be ce da ita ba se d’an murmushi yayi had’e da girgiza kansa a lokacin da yaji tashin motar saifuddeen,kana ya qarasa gun dinning yaja kujera ya zauna yana fad’in”Halan me saifuddeen yace maki da zai fita?
Umma da ta janyo plate zata fara serving nashi tace”ce min yayi sauri yake”
Abba yace”haka dai ya gaya miki amma ba wani sauri da yake da akwai dalilin da yasa baya so mu had’u”
Umma tace”shi saifuddeen d’in?
Yace”shi d’in yaron da ko kad’an baya so in masa zancen aure amma jiya se gashi na ganshi da wata baturiya a office d’inshi yanda na gansu abun takaici matsayin sa na musulmi yana biye mata kan lalaci irin nasu na turawa.
Numfashi umma ta fitar snn ta zauna a hankli tana kallon Abba wacce da alama tasan saifuddeen na tare da Sophie ba yau ba amma se tace “kana nufin yanzu saifuddeen duk jiji da kanshi yana kula en mata.
Abba yace”Hm Mamn yusra knn ae duk namijin da kika ga baya kula mace to ba lafiyar sa qalau ba,amma irin kulawar da ake so shine namiji ya nemi mace da son aure ba irin shirritar da naga saifuddeen ya d’auko da wacce sam aure bazai ta6a shiga a tsakanin su ba,dan haka wlh sam bazan yarje masa wnn shashan cin ba,ni aure zan masa ko yana so ko baya so!
Yana kaiwa nn ya fara cin abincin da umma ta zuba mishi.
Umma dake kallon sa tayi shiru bata sake cewa komai ba,se abinci ta zubawa kanta ta fara ci cike da tunanin yanda zata shawo kan saifuddeen ya rabu da Sophie,dan ko kad’an bata son huld’ar sa da ita shiyasa ma bata so Abba yasan da ita ba.
Se da yamma liqis saifuddeen ya sake dawowa 6angaren su umma,sanye da qananun kaya a jikin sa,rigar fara ce tas me guntun hannu,rubutun jikinta baqi ne manya da aka rubuta Being human,wandon kuma fari ne tas tree quarter wanda duk da cewa fuskar sa ba annuri amma yayi matuqar kyau se qamshi ke fita a jikin shi sbd mutum ne shi da sam baya wasa da turare yana son qamshi sosai a rayuwar shi,shiyasa jinin sa ya had’u da Sophie dan haka take itama ko yaushe cikin qamshi take.
Umma dake zaune kan doguwar kujera hannun ta riqe da littafin addu’o’i ta kafe idon ta a kansa har ya qaraso ya zauna a kusa da kujerar da take zaune,still fuskar nn tasa ba annuri ya kalle ta yace”umma i will back to England”
Umma tace”meyasa?
Yace”kmr yanda suke buqata”
Tace”kmr ya u mean zaka kar6i tayin su ka koma can da aiki ka bar asibitin mahaifinka saifuddeen?
Yace”eh”
Da mamaki tace”why?