RIKON KAKA
CHAPTER 4
Kaka tai sallama qofar shagon Malam salisu mai
tireda, dattijon mutum mai mutunci ya fito daga
shagon yana fadar.
“A’a Hajiya, sannu da zuwa, yau kece da, kanki?
Ina jikar taki?”
Kaka tace, “‘Yarka tai mata dukan kawo
wuqa, tana can gida a kwance
Mal. Salisu ya dauki salati, kafin ya ce.
“Wacce yar tawa daga ciki Hajiya?”
Ta ce, “Zulai”.
Ya cc, “Don Allah kiyi haquri Hajiya, insha Allah
zan ja mata kunne daga yau ba za’a sake ba,
kiyi-hakuri”. _
‘ Kaka ta cc, “Ainazone don in sanar da kai, don
wallahi kotu zan kai ku, don ni ban hada jika da
kowa ba. don haka duk Wanda ya nrmi takurawa
marainiyar Allah to kotu kawai
za ta raba ni dashi
..Mal Salisu ya ce, “A’a, kar ki haka, don Allah
Hajiya kiyi haquri, insha Allah ba za’a » sake. Ba.
Zanje yanzu ma in sameta, wallahi sainaci
mutuncin ta zanja mata kunne.
‘ Kaka tace To taci, albarkacinka , ”amma wallahi
ka fada‘ mata kada ta sake”. “
Ya ce Insha Allahu”.
Sannan ta juya ta tafi kai tsaye gidan su Rakiya
ta nufa tai sa’ a kuwa Rakiyar na zaune ‘a tsakar
gidan ita da uwarta Kaka tace, “.Suwaiba. wurinki
:naxo ki jawa ‘yarki kunne akan Jikata wallahi
idan har suka Kara dukar min ‘ya to fa kotu ce
zata rabani , da ku don ba zan lamunta ba”. .
‘ Suwaiba ta ce, “Kaka idan kin gadama daganan
ki wuce kotunma, ki tati kon woli, amma.idan
Rukayya ta Kara dukan Rakiya, nace su rama
suyi mata’ dukan tsiya. inga.tsiyar: daure mata
gindin da kike yarinya zata zauna ta addabi
Kowa a gari
‘ Kaka ta ce, “Oh, ashe ma ke kika
’ sa su dakarmin ita kenan. to da kyau ‘ki saurari
_ sammaci
Suwaiba tace ba sammaci ba ‘falwaya ma ubanta
‘
Nimafa da kike ganinanan ba qaramar tantiriyar
‘yar iska bacr, babu wanda nake tsoro duk garin
nan don kiji“. ‘*
Kaka ta’ce, “La ila ha iilallahu! Yanxu suwaiba ni
kike zagi saboda ‘yarki’?”
“Saita fashe da kuka ta fice daga gidan wai an
Zage ta Tun daga daki *Abubakar ya jiyo ta, ya
mike ya fito a hasale sukai karo a zaure, ya ce.
Ya aka yi ne kuma Kaka?“ . Cikin kuka tace,
“Kyale ni Habu, wai ‘ yau ni cc Suwaiba ke zagi‘
Kiri-kiri ba kunya Abubakar ya ce “Suwaibar
Kaka? Anya. kuwa‘?“ ‘ , “Karya nake Habu, ai
dama na saba,to nai maka wadda na saba”.
Yace”Ni fa ba haka nake nufi ba, kaka baki
fahimceni bane” Ta ce; “Gafara can, wallahi idan
baka Je ka ramo min zagin da taiminba allah Ya
isa wallahi” Abubakar yai murmushi kafin yace
“T0 daina kukan haka nan, zan je in ramo miki
yanzu, shige cikin gidan”
Ya samu ya ‘lallaBata ta wucc cikin gidan,
sannan shima ya shige dakinsa. Yana gamawa
ya fito ya kulle dakin ya kwallowa Rukayya kira
yana daga zaure, tana fitowa ya bata Naira darin
kalaci sannanya ficce ya tafi
wurin aikin sa.
::::::::: :::::::::: :::::::::::::
Babbar sallah ta kusa, don haka duk hada-hada
ta koma ta shirye-shiryen sallah, .kowa ka gani
ta yanda zai yi ya samu ya tafiyar‘ da ‘ya’yansa
da iyalinsa yake.
‘ Abubakar tunda wuri ya samu yai musu siye-
siyen sallar su tun daga shi kanshi har‘ Kaka
zuwa’Rukayya, hatta kudin dinkin ya . biya saura
na Rukayya kawai.
, Kullum‘ sai ‘Kaka tai masa mitar dinkin Jika,
tun yana sharewa abin har ya soma isar sa, gashi
yana saura kwana hudu sallah,kuma har yanzu
ba ai masu albashi ba.
Don’ haka Abubakar ya nemi aron Naira dubu
wurin abokinsa, yana dawowa gida k0 dakinsa bai
shiga ba ya nufi dakin Kaka. Tans zaune ita’ da
Rukayya suna cin abinci, Abubakar ya ce
Yau dai’na fita Kaka, ga kudin dinkin wannan
mummunar da ake ta yi min mita kullum, na huta
da ciwon baki_
Kaka ta dauka tana fadar, “To ka kuwa kyauta,
amma da har na fara tunanin k0 in siyar da dan
maraqina in amso mata dinkin nata,dashine don ‘
na dauka baka da niyyar amso mata”.‘
Abubakar yace Hmm! Kaka kenan, ai gashi nan na
ranto nabada, na huta . ’ Ya wuce zaure abinsa
ya shige dakinshi.
Rukayya ta warci dubun tana tsallen’ murna,
tace.
“Kaka baje na karbo?‘
Ta ce, “Jeki ki karb0 abinki kiyi sauri, ko
Yan iskan yaran garin nan sun tsokane ki kar ki
kula su“.
Ta ce, “To kaka”.
Ta dauki hijabinta tana tsallen murna ta fice.
Tana shawo kwanar gidansu ta hango yara sunyi
dandazo ana ta kade kade jikin Rukayya har ciri
yake ta nufi wurin, inda ake_ ta ihu, “Ga ‘yan
kura. ga ‘yan kura masu wasa da kura)” sai a
kwasa aguje ayi nan riii, ayi nan rii
Rukayya ta samu abinda take so, ta ma ~”mance
da aiken da akai mata, ta rufawa sauran yara
baya suka shiga bin masu wasa da kura, sai da
suka zagaye garin kaf.
. Ita da aka aika tun wurin la’asar amma har
duhun magariba ya keto babu ita babu labarinta.
‘
‘Hankalin Kaka ya tash ta leqa dakin Abubakar ta
kwalla mashi ‘kira, ya fito yana fadar.
“To wani abin ne kuma k0?”
Kaka ‘tace tunda fa na bawa Rukayya kudin
dinkin nan taje ta karBo har yanzu bata dawo
ba”. .
Ya ce”To sai me Kaka? Idan ta bata ba mun huta
ba, kema kin zauna bakin ki ya huta”. Cikin
rikicewa ta ce, “a bakin ka ba mara mutunci me
bakin tsiya, bari inje ni na nemota dukma indata
shiga”. _ Tai waje tana mita, Abubakar yai
murmushi wanda iyakar sa saman laBBan sa, ya
koma dakinsa ya sanyo rigar sa ya fita ya ja
gidan ya nufi hanyar neman ta, duk inda ya ga
dandazon yara sai ya je ya duba amma babu ita.
Yana Shawo kwanar gidan Maigari ya hango dan-
dazon yara suna bin ‘yan kura. ‘Tabbas tana nan
ciki”. ‘ _Abinda zuciyar shi ta ce mashi kcnan, ya
shiga kutsawa yana neman ta. Can gaba-gaba ya
hangota ita da wata yarinya suna ta rabzar fada,
sai qokarin raba su ake sunqi rabuwa, da alama
ta sami ‘yar masifa irinta. Abubakar ya kutsa ya
riqo hannunta, tana ganinshi kuwa ‘yan cikinta
suka rikice, idanuwan nan suka yo war waje.
Yanda ya riqo ta haka ya rinwa janta har” gida
ya hankada ta tsakar gidan, Ya dauko igiyar guga
ya shiga zabga .mata tana ihu. . Bai ji shigowar
ta ba sai dai yaji kukanta. “Kashe ta zaka yi?
Jama’a ku taimaka, zai kashe marainiyar Allah”.
Tana ganin kakar ta kwasa aguje ta rugungumeta
tana ihu, kaka tace
“Cewa naika kirata ka duke ta? Ba ‘ccwa nayi ka
nemo min ita ba?” ‘
Cikin takaici Abubakar ya cc, “Duk abinda
yarinyar nan~ke yi duk laifin ki ne, ke ke lalata
ta. Wallahi indai ni zan ci gaba da saka hannuna
a cikin lamarin wannan to wallahi dole ne in
hukunta ta tunda dai ita haka Allah Ya yi ta bata
jin magana k0 miskala . zarratin, kuma harda
hadi da kin shagwaba ta,
kinsa ta raina kowa, bata .ganin kowa da
mutunm, to ni dole na hukunta ta wallahi” “Ina
Naira ta dubu‘?!”. ‘ ‘
Ya daka mata tsawa, tai saurin sakin kaka tana
lalube-lalube a jikinta, har’ da su kwance kallaba
tana dubawa.
Abubakar‘ yai murmushin takaici kafin ya ce, “Kin
yar k0? Da kyau, kinwa kanki don wallahi tallahi
sai dai kiyi sallar haka, fada kuma kar ki fasa, ki
tayi, ban ce ki daina ba”.
‘ Ya yar da igiyar gugan ya wuce dakinshi
abinshi. Rukayya ta kara fashewa da kuka, “Na
‘ yar da kudin Kaka wurin kallon’ yan kura, bari
inje in dubo”. ‘
Kaka ta ce, “Ya za ai ki gansu Jika? Ai ba za ki
gansu ba, kiyi hakuri kawai in lallaBa shi ya Kara
miki”. .
Cikin kuka ta ce, “Ai ba zai Kara min ba”. .
Kakata ce, “Ya. ma isa? Share hawayen ki, ki na_
zaune sai ya kara su k0 da ya rantse sai dai ya
yi azumin kaffara”.
Rukayya ta share ‘hawayénta tabi kaka dakinta
tana fadar.
“Dubi, inda ‘duk ya ji min ciwo, wallahi yana
tafiya sai na rama a wurin ragunan sa”. ‘
Kaka ta ce, “Shcgun ragunan ma da . kullum ke
ke dawainiya da su amma bai gani, kullum ya
kama ki yai ta duka. Wata rana sai na baSu
shinkafar Beta sun Ci sun mutu inga ta tsiya,
kema ki hula. Allah Ya ‘soki ma an kusa kwashe
su ki sami sauki”
Rukayya ta ce”Shinkafar Bera ita ke kashe su
Kaka?”
Ta ce”Sosai ma, ai k0 ke kika ci sai kin . mutu ba
raguna ba”. *
Rukayya tai shiru zuciyarta na saqa da
warwara.
Kaka tace, Tashi ki dauro alwala kiyi sallar
magariba”.’ ‘ ‘
. “Bata ce Kala ba ta miqe ta nufi wurin da . ake
ajiye butoci ta dauka ta nufi kewaye
Ana gobe daren sallah Abubakar ya karbo
dinkunan sa dana Kaka ya kawo mata yana nuna
mata.
Rukayya na kwance saman gado tana kallon su,
dinkunan shi kala uku, na Kaka kala
biyu. .
Sai data gama ganin nata sannan ta ce.
“Ina na Jika?” ‘ .
Ya ce ”Wacce Jika Kaka? Ai na rantse tunda ta
zubar da kudin wurin fada ba zan qara fitar da
wasu in bata ba, wallahi sai dai tai
sallar haka”. _ ‘ Kaka ta jefa mashi nata, “Ai ko
indai ba _zaka amsowa Jika nata ba to nima ban
so, wallahi sai dai ka hada duka ka rike”. ‘
Abubakar ya ninke kayan da ta jefa masa suka
zube qasa, ya ce_
“Ba zan tafi da su ba, sai dai in kinji ‘ haushi ki
kyasta masu ashana su qone, koki bada sadaka
duk daya wai makafi sunyi dare, kinga tafiya ta”.
Ya wuce abinshi ya bar mata kayan
Rukayya ta fashe da kuka tana harbeharbe da ta
tabbatar ya tafi Kaka ta ce, “Ke yi shiru Jika, ai
dama so
yakc ya‘ sa ki_ kuka, idan kika yi ai kinga yai
nasara Ki kyale shi dole ya amso miki dinkin
Inma bai amso ba sai ki saka wadannan nawa
Tana kukan Rukayya ta ce, “Wadanne zan saka?
Wannan dinkin tsaffin su zan saka?
Allah Ya sauwake” . ‘ Kaka ta ce, ”Ba sai ki ba da
su a rage
miki ba?” Ta ce, “Allah Ya sauwake ni dai ban son
su, nawa nakeso”. . Kaka ta ce, “To kiyi shiru
haka nan
muga iya gudun ruwan sa”.
Ta samu da kyar tai shiru,“ amma zuciyarta na
mata sake-sake kala-kala. . ‘ ‘ ‘ Cikin dare duk
sun‘ kwanta barci amma Rukayya ta kasa barci
saboda tunanin rashin kayam sallah, ta tashi
zaune tana tunanin abinda zata yi itama ta‘
guma masa. Can ta tuno’da
shinkafar bera da Kaka ke ajiya a karkashin gado
saboda Beran dake matsa masu.
Ta lallaBa ta dauko ta tamkar wata munafuka, tai
sadaf-sadaf ta fita waje ta sami kwano ta zuba
shinkafar ta zuba ‘ruwa ta lallaba ta nufi wurin
ragunanshi. Duk sun ma yi bacci,‘ ta girgiza
gudayana motsawa .ta miqa mashi. Kamar jira
yake ya kafa kai ya sha sosai.‘
Ta nufo gudan tana girgiza shi, yai kuka
“Beyyy!‘ tai mugun tsorata ta zubar da ruwan. ‘
ta ruga daki aguje ta kudun dine saman gado.
K0 minti biyar batai da kwanciya ba taji ragon ya
soma dire. dire, Abubakar ya fito daga . .dakin shi
hankalin shi tashe, ya kwance ragon yana duba
shi. ‘
Ragon ya fadi yana harbe-harbe, Abubakar ya
rude yai dakin Kaka aguje ya tayar da ita yana
fada mata rago ba lafiya, ta rude sukai waje. .
A lokacin har jikin ragon ya saki, sai kumfa da ke
fitowa daga bakinsa.
Kaka ta ce, “Maza dauko wuqa ka yanka shi,
gazawa zai yi”.
Abubakar ya juya ragon ya kalli gabas, ya ce
“Bismillahi, Allahu Akbar”. Sannan ya yanka. ,
Jikin Abubakar ya mutu saboda gazawar ragon
nasa, duk cikin ragunan yafi kowanne girma, Naira
dubu hamsin sukai cinikin sa gobe za a zo a
dauka. Don haka babu wani kuzari a jikinsa ya
tafi daki ya kwanta, sai dai batun barci babu‘
labarinsa, ita kanta Kaka sai data dau lokaci kafin
baccin ya dauke ta.
Rukayya k0 dadi ne dankare a zuciyarta, tana
labe tana kallon su. Yanda ta ga Abubakar ya
rude sai yai nan aguje ya dawo nan aguje dariya
kawai take masa har da rike cike, ta rufe’ baki
don kar wani yaji ta.
Tunda sanyin safiya Abubakar ya tashi ya tafi, ya
kira mahauci don ‘siyar masa, gashi ranar sallah.
‘
Tare suka dawo da mahaucin, ya duba ragon yai
masa kudi dubu ishirin.
Babu yanda ya iya haka ya ce ya bayar, a take
ya kirga kudin ya bayar sannan Abubakar
ya tafi dakin Kaka ya fada mata yanda aka siya
Kaka ta ce ”Anya Habu ragon nan bai mutu ba
aka yanka?” .
Abubakar ya ce, ”Kai Kaka, Allah Ya sauwake, sai
kace dai ba Musulmi ba zan yanka mushc? To ko
da na yanka shi sai da ya harba, yanzu inda
gabansa kika fadi wannan ai kinga ba zai siya
ba”.
. Kaka tace, ‘A’a, ai nidama ban sone ka aikata
abinda Ubangiji zai yi fushi da kai ne’ .
Abubakar ya ce, “To bai mutu ba na
yanka, yanzu ma buhu zaki ara mana zai fede
anan.
Kaka ta ce, “To bari in duba maka” .
Rukayya ta mike simi-simi ta raba Abubakar ta
wuce tamkar wata tsohuwar munafuka, ta nufi
wurin mahaucin tace masa ‘ “Baba ragon nan sai
da ya mutu aka
‘ yanka shi, kar ka siya”.
Mutumin ya zaro ido yana mamaki, kamin yai
magana tai saurin rugawa daki abinta ta
haye kan gado“ Kaka ta zakullowa Abubakar buhu
a
Qarqashin gado ta bashi, ya fito. “Yauwa ga
buhun Baba Halliru”. Da
yake haka ake kiransa a garin. Ya ce “Riqe shi
nan wurinka Abubakar,
bani kudina”. Gaban Abubakar yai wata irin
faduwa,
ya ce
“Saboda me Baba?” ~
Ya ce “Saboda ni ba mutumin banza bane irinka
da zan siyi mushe in saida wa al’ummar
Musulmai. Ba
“Inna lillahi wa inna ilaihi raji’un! Baba wallahi ba
mushe bane, ni na yanka shi da hannu na
wallahi”. ‘
Ya ce”Kai kaga ni dai ba abokin wasanka bane,
ka bani kudina kawai ban siye na fasa Kanwar ka
da bakinta ta fada mini mushe ne ka yanka. wato
ga mutumin banza ko
Idan bakwason wannan littafin kuyi magana mu
canja
zallah shared a profile .