Iyabo
NAMA YA DAHU…
ROMO ƊANYE
LITTAFI NA BIYU
1
Motarmu na dira a tsaha idanuna su kai tozali da kyakkyawar fuskar Yaya Hamma. Yana jingine a jikin wata Bus ya ƙurama motarmu idanu bai ƙibtaba, bai kawar da kanshi daidai da na sakan guda ba, har sai da yaga na fito a cikin motar. Da sauri ya nufoni fuskarshi ɗauke da yalwataccen murmushi, murnarshi ta kasa ɓuya. Yasa hannu ya karɓi ledar kayana.
“Jabu tunda na shigo tasharnan zuchiyata bata dena dokawa ba har sai da na ga sakkowarki a cikin motarnan. Wata zuchiyarma ce mun take yi baza ki dawo garemu ba kwata_kwata” Ɗan murmusawa nayi kawai nace.
Yaya Hamma kenan, na gode da kulawa, amman kafin ma in tafi na sanar maka zan dawo.” A jere muka fito daga cikin tashar, a bakin titi muka samu motar Girai muka shiga, wata kwaraɓaɓɓiyar Bus mara gudu muka samu. Bayan tafiyarmu ta ɗan yi nisa sai nace dashi.
Ni ko ya jikin Dada Yaya Hamma?”
Wannan tambaya tawa farad ɗaya saita sauya fuskarshi, daga farin ciki izuwa ɗaurewar fuska, harma da alhini. Lamarin daya dagula jinin jikina kenan, ruɗewar da nayi da yawa ne yasa yace dani.
“.Ki kwantar da hankalinki Jabu. Bawa baya iya tsara ma kanshi yadda zai rayu. Nayi imani da hakan na faruwa Al’umma babu mai zubar da hawaye. Bayan tafiyarki abubbuwa manya sun faffaru marasa daɗin labari. Amman bazan baki labarin komai a cikin motar haya ba. Kiyi haƙuri in mun je gida zaki ji komai”
Bai daina rarrashina ba har muka iso Girai. Ni dai ko da muka shiga akori kura bana iya ko magana sai fargaba da nake cikinta. Jikina sai bani yake yi Dada ta haɗiyi zuchiya ta mutu ne ƙila bayan tafiyata, ko kuma maƙetacin mijinta ya kasheta. Da waɗannan tunane_tunanen muka shiga cikin Jaɓɓi lamba. Sai gamuwa da mata masu tallar nono muke yi
Yaya Hamma gidan su Dada zaka kaini, zan tsaya a ƙofar gida sai kai ka shiga” Ƙuramun idanu yayi, sai naji idanun nashi sun yi mun kaifi ba shiri nayi ƙasa da nawa idon, tare da sauraren amsar da zai bani.
“Dada bata gidanta, tana gidan Baffa Musa, ki bini kawai in kai ki”
Ai jin haka yasa na kuma tsurewa har hawaye sai da ya zubo a idona. Tafiya muke babu mai cewa da ɗan uwansa ci kanka har muka isa gidan Baffa Musa, tafiyar ƙafa ce mai mugun nisan gaske. A ƙofar shiga gidan naci karo da Burodami Debisi shi da Jatau. Sai nayi turus ina dubanshi cike da maɗaukakin mamaki. Shi kuma cikin sanyi yake kallona irin kallon da naso in samu irinshi daga gareshi a shekarun da suka shuɗe, shekarun da wutar sonshi ta kusan ƙone mun rayuwata. Sai a yanzu da bana buƙatar kowa a cikin rayuwata ne, zai dinga jifana da irin wannan kallon? Ko zan iya ba maza wata damar, babu Burodami Debisi a cikinsu, zaifi mutumci ya riƙe matsayinshi na wa gareni
“Iyabu Ekabo ( Sannu da Zuwa)
Burodami Debisi yaushe a gari?” Na tambayeshi da yaren hausa, babu yabo babu fallasa a fuskata. Jatau yace.
“Ai tun ranar da kika yi tafiya shima ranar yazo. Tare muke ta zuwa kiwon shanu” Da mamaki na dubeshi, kuma na yaba ƙoƙarinshi daya iya har kwana biyu a ƙauyenmu.
“Mu je ciki Jabu, ki ga halin da Dada take ciki, naga kamar kin sha’afa” Cewar Yaya Hamma da muryarshi a kausashe har ɗan rawa take. Wucewa nayi cikin gidan, Yaya Hamma na biye dani a baya, su Burodami Debisi na biye dashi har zuwa cikin bukkar Goggo matar Baffa Musa.
A kwance na tarar da Dada kanta naɗe da bandeji, sai kuma hannun damanta dana ga an ƙulle da tsumma, ga kara an jera mata kamar mai karaya. Sai numfarfashi take fitarwa, Boɗɗo na gefenta a zaune, su Yusufu, da Cubu duk suna kewaye da’ita, harda yaran Baffa Musa waɗanda suke gidan miji, Yafendonmu Jabu, da Yafendo kaɓoji mahaifiyar su Yaya Hamma, da Yafendo A’i suna wajen duka.
Kuka kawai na fashe dashi domin na rasa ma abinda zance, bansan wa zan tambaya ya bani amsa ba, kowa a cikin damuwa yake. Boɗɗo ce ta dawo kusa daf dani ta riƙe hannayena biyu.
Meke faruwa da Dada Boɗɗo, naga hannunta kamar karayace ma?” Baffa Musa ne yace.
“Abinda ya faru kusan sanadiyyarki ne Jabu. Wannan ƙiyayyar da mijin Daso yake yi miki abune daɗaɗɗe sosai. Kuskuren da ita Daso tayi shine data yarda da sharaɗinshi kafin ya aureta. A lokacin da mahaifinmu Allah ya jiƙan rai ya matsa ma da Daso kan a cikin gwarazan samarin da suke neman aurenta za’a saka shaɗi, a lokacin shaɗi gwarazan mazan fulani suke yi su auri mace, dole sai namiji ya nuna jarumtarshi. Aka saka ranar shaɗi, Allah cikin ikonshi sai mai nagge yai nasarar cinye wannan gasa ta neman auren Daso. Gashi matashi mai dukiya, dan Allah ya albarkaceshi da tarin shanu a lokacin. Amman mutumne shi mai zuchiya da kafiya akan ra’ayinshi ko mai muninshi. Duk da wannan kusan ɗabi’ace dake gudana a jinin ko wanne bafulatani, amman na mai nagge yayi yawa. Bayan anyi aure kafin ta tare sai yake sanar mata shi mutumne mai tsananin kishi shi baya son ya saka ɗiyarta ƴar margayi a idanunshi sam, ta yi mai alƙawarin zata kiyaye mishi hakan, amman bazai hanata zuwa ganinki ba, bai kuma yarda yaranshi suyi zumunci dake ba. Ita kuma Daso cikin rashin sanin girman furucinshi sai ta amince mishi da duk abinda ya gindaya. Duk da dai ba’a musu dashi.
Jabu daga ranar da yar mahaifnki Toyosi ta ɗakkoki ta kawoki garinnan dan kiga dangin mahaifiyarki, bayan tafiyarku sai da igiyar auren Daso ya kutsure, ta fuskanci tashin hankali, da faɗa sosai harda duka ma a wajen mai Nagge kafin ya korota gida.
To shekaran jiya kinje mishi gida, a gabanku ke da Daso ya fashe mata kai. Bayan ya rakaku da gudu sai ya rufeta da duka. Ana cikin wannan hali ranar ko tallar Nono ta kasa zuwa. Sai ga Debisi shima da yamma lis. Zuwanshi ne yai silar da kika ga Daso a kwance tana jinya. Hamma gashi shi yaita kai kawo akan nema mata lafiyarta. Debisi kuma da Jatau suka kaita asibitin Girai aka duba lafiyarta. Wai hawan jinine ma da’ita a yanda su suka ce. Kinji abunda ya faru, amman kuyi hakuri wata rana fa sai labari, masu ba da labarin ma wata rana basu. Haka zamu shuɗe kamar yadda magabatanmu suka shuɗe.
Kuka mai taɓa zuchiya na fashe dashi kawai. Wannan zalunci da mai yayi kama, yama za’ayo a raba uwa da ɗiyarta ɗiyar ma ta fari marainiya bugu da ƙari.
Tsit ɗakinnan yayi bakwa jin komai sai sautin kukanmu ni da ƙannena da suka kewayeni suna rarrashina.
“Jabu ki dena wannan kukan. Ki yafe mini kinji? Yarintace tasa bansan girman sharaɗin da mai nagge ya gindayamun ba, ba dan bana sonki bane na amince mishi ba. A cikin yarana kab nafi jinki fiye da kowa, kasancewarki marainiyar yarinyar da bata taso a gaban mahaifanta ba. Bugu da ƙari soyayyar Toye kanki ta koma kacokam.”
Hannunta nayi carab na kama, idanu ta lumshe wasu hawayen nadama suka gangaro mata. Mayafina nasa na goge mata. Baffa Musa ne yace.
“Daso baki da lafiya bai kamata ki yawaita magana ba. Hutu kike buƙata. Na faɗa ma Jabu wannan labarinne domun tasan abinda ke gudana, ba dan in tashi hankalinki ba. Kai kuma Debisi duk sanda zaka zo wajen Jabu, ka sameta a gidan Yafendonta, ka sanarma Toyosi itama. Jabu ku tashi ku koma can gidan Yafendonku, ki samu ki huta”
Ba haka naso ba, so nayi su barni in yi ma Dada jinya. Amman Baffa Musa yaƙi fur sai cewa yayi ma dinga zuwa dubata, matanshi zasu kula da’ita.
Muna tafe a hanya amman tunani ya cika kaina, damuwa tayi ma zuchiyata yawa, ina neman wanda zan kwanta a kafaɗarshi in ci kuka ko zan samu salama. Gwadabe ne ya faɗo mun, tunashi kawai da nayi wallahi sai na tsinci kaina ina murmushi kawai.
Tare duka muka shiga gida. Ni da su Daso wacce tunda na dawo naga ta fita sha’anina. bukkarmu muka shiga, na nemi waje na zauna jigum. Yaya Hamma ne ya shigo hannunshi riƙe da kayana. Yana shigowa sai naji Daso ta sau siririn tsakin da ba kowa ne zai ji ba.
“Ga kayanki Jabu. Ku kuma ku bamu waje zan yi Magana da Jabu” Su Cubu duk suka miƙe suka fita, banda Daso wacce kwanciya take shirin yi. Sai da ya yareta kuma da faɗa naga yana magana. Kuka kawai naga Daso ta fashe dashi ta fice fuu.
Ni dai ba ta fishin Daso ma nake ba, ta kaina nake yi. Zama yayi a ƙasa yana fuskantata. Idanu ya zubamun yaƙi cewa dani komai, yaƙi kuma ya dena kallona. Ni kuma duk sai na tsargu. Jatau ne ya leƙo.
“Jabu ki zo Debisi yana son zaku yi Magana, yana gindin bishiya, ki je da tabarma, ga fura Hari ta dama sai ki tafi mishi dashi”
To” kawai na iya cewa, ya saki asabarin yayi tafiyarshi. Yaya Hamma kuma naga yayi ƙasa da kanshi kawai yana wasa da layar dake ɗaure a tsintsiyar hannunshi”
Yaya Hamma bari in je in dawo, tunda naga kamar baka son yin maganar da kace zamu yi” Ɗagowar da zaiyi sai naga idanunshi sun rine, jijiyoyin fuskarshi sun yi burɗun_burɗun. Gabana ya yanke ya faɗi ganin yanda cikin ƙanƙanin lokaci na ganshi a cikin wani irin yanayi. Cikin kaurin murya mai cike da karaya yace.
“Shikenan gobe zan dawo, nima zanje gida in kwanta jiri nake ji” Haka kurum sai banji daɗin ganin shi a sabon kamanni ba. Kafin in gama tubkewa ya fice bankai ga warwarewa ba. Jikina a mace na fito tsakar gidan. Tabarma da damammiya fura Hari ta miƙo mun nasa hannu na karɓa. Har na kai ƙofar fita na juyo na kalli Boɗɗo nace.
Boɗɗo ku jirani in je in dawo. Inaso zamu je gidanki akwai muhimmiyar maganar da nake son mu tauna” Ina faɗan haka sai naga Daso ta zare idanunta, firgici ya bayyana karara a fuskarta”
Ficewa nayi waje. A tsaye a gindin bishiya na hango Debisi yana kallon garken shanun da suke wucewa. Kurama juna idanu muka yi, ina daga tsallake ina jiran shanun su gama wucewa”
Zuchiyata ce naji tana bugawa da ƙarfi, idanun Debisi naji sunyi mun kaifi. Na so Debisi so na haƙiƙa, soyayyarshi ta wahalar da rayuwata, dan zuchiyata bata iya son abu ba, in zata so abu da gaske take sonshi, haka kuma ban iya ƙin mutum ba” Bamu dena kallon ƙudan da muke ma juna ba har sai da garken shanunnan suka gama wucewa. A hankali na isa ƙarƙashin bishiyar. Carab ya amshe ƙwaryar damammiyar furar dake hannuna. Na shimfiɗa tabarmar dana fito da’ita, tare da cewa.
Bismillahi Buradomi ka zauna”
Murmushi yayi mun, irin wanda ada nake mafarkin ganin yanai mun. Banda a yanzu dan tuƙuƙi naji zuchiyata nayi mun. Kuma ina fatan ba cewa zaiyi sona yake yi ba, dan zan iya zaginshi tsab, laifinshi mai girmane a gareni, babu abinda zai iya faɗamun in yarda ba yaudara bace”
Waje na samu na zauna kamar yadda yai mun izini.
Shiru ne ya biyo baya na tsawon minti shida kafin yace
“Bansan ta inda zan soma ba Iyabo. Gashi zuwan nawa ya haifar da matsala mai girma, ina mai neman gafararku baki ɗaya. Amman kafinnan me kika je yi a Kano, sannan wannan ramar duk ta rabuwa da Gwadaben ce, ko kuna cikin wata damuwane?” A jijjere yayi mun tambayoyin da na yi jim, ina cinka cinkar wanda zan sona amsawa a cikin zuchiyata. Sai na sake jin amon muryarshi yana cewa
“Da zan baki shawara, da nace ki shirya ki bini mu koma Kano. Tunda kika baro Kano kika barmu cikin kewa da alhinin rashinki. Nawa kuwa yafi na kowa. Kuma a kwana biyu kacal da nayi a rugarnan na tabbatarma kaina rayuwarki ba zata taɓa yi miki daɗi ba. Ke da kika taso a maraya, ga hasken lantarki, ga ruwan famfo, ga makarantu, ga titina, ga_ga_ga. Amman anan fa babu abunda suka sani sai kiwo da tallar nono, ace kamar Dada tallar Nono itama take zuwa yi, su Ɓodɗo ma tallar suke ɗauka fa” katseshi nayi ta hanyar cewa.
Tambayarka ta farko gareni shine. Naje Kano ne nayi fasfo zan tafi ƙasa mai tsarki da izinin Allah neman kuɗi. Tambaya ta biyu kuma. Ciwo nayi mai tsayi shi yasa na rame. Gwadabe kuma yana ɗamfare a raina tsaiwar numfashinane kaɗai ka iya kawo ƙarshen soyayyar Gwadabe.
Batun rashin iya zaman rugarnan kuma. Zan iya ko dan Dada, da ƙannena. Bana jin komai na dangane da kewar birni, ko ƙyale_ƙyalen dake cikinta. Ni babu abinda a halin yanzu yake burgeni. Nafi samun nutsuwa a haka” Ashe ni na kasheshi da namaki ban sani ba. Sai da na juyo naga bakinshi a hangame yana kallona, da halama ya ɗan jima yana kallon nawa
“Saudiyya fa kika ce zaki je neman kuɗi Iyabo?” Ya faɗa a ƙagauce da son jin amsata.
E Saudiyya da izinin Allah, Lokaci kawai zamu jira.”
” Da izinin wa zaki tafi Iyabo, me yasa Kano bata isheki neman kuɗi ba har sai kin dangana da ƙasa mai tsarki, sannan me yasa baki yi tunanin Aure, ko komawa makaranta wanda nasan yana daga cikin burukanki na rrayuwa ba?” Ya sake jejjero mun wannan tambayoyi cikin ɓacin rai a wannan karon. Baki na tsuke bance mishi komai ba. Tsawa ya daka mun wacce tasa ƴan hanjina kaɗawa.
“Ba dake nake yi ba kin mun banza ba?”
To ni kam Burodami me zance maka? A halin yanzu babu wani karatu, ko aure a gabana. Rayuwar mahaifiyata kawai nake dubawa, da mafarkin samar mata da sauƙin rayuwa. Ka dai taya ni da adda’a zaifi. Dan babu makawa zanyi tafiyarnan. In kaga banje ba Allah ne baiyi ba. Kayi haƙuri kar kace na bijire maka”
Sai yayi shiru na wasu daƙiƙu kana yace.
“Amman ba kya ganin in kika tsallake ƙasarki Najeriya, kika tafi wata ƙasar neman kudi. Ba kya ganin wasu zasu yi miki kallon da bai dace ba? Ballantana kinga ke bazawarace kina da ƴaƴa. Acan kuma baki san hannun waɗanda zaki faɗa ba”
Hannu na gari zan faɗa da izinin Allah. Kuma wama zai san na tafi Burodami Debisi?. Kaga Dada tana cikin halin da ya kamata a taimaka mata. Kuma ni bazan wuce shekara uku ba zan dawo. Kafin in dawo amman sai na tabbatar da na samu dukkan abunda naje nema.” Ajjiyar zuchiya ya sauke, yayi shiru yana kallona, ni kuma nayi ƙasa da kaina.
“To batun aurenmu sai kin dawo za’ayi kenan. Ko kuwa zaki amince a ɗaura kafin ki tafi? Dan ni harna sanarma Baffa Musa sababin zuwan nawa. Yayi murna matuƙa da jin hakan” Wani kallo nayi mishi, wanda ko a mafarki banyi tunanin akwai ranar da zata zo da zan yi mishi wannan kallo ba.
Aure a tsakaninnu babu shi har gaba da abada. Har gobe nice Iyabo mai ƙibarnan, wannan wacce sai da ka kwanta jinyar ƙiyayyarta. In ma mafarki kake yi ka farka” Ina dasa aya sai kawai na miƙe hawaye fal Idanuna. Takalmaa nake shirin sawa yayi maza ya miƙe shina.
“Iyabo”
Ya kirani da sauri. Cak na tsaya. Ban tafi ba, ban kuma juyo ba. Ina jiyo takunshi har izuwa daf dani.
“Nasan kina sona Iyabo kar ki soma yaudarar zuchiyarki. A rashinane kika auri Gwadabe. Iyabo zan baki farin ciki irin wanda mafarki da hasashe ba zasu iya hasko miki ba. Duk duniya ba wanda zai soki sama dani, sai dai ya biyo bayana.” Hawayena na share, tare da lumshe idanuna, zuchiyata kuwa sai aikin turiri take. Da ƙyar na haɗiyi miyau nace.
Iyabonnance dai wannan mai ƙibar da kaƙi aurenta sabida wannan halitta tata. Ba canjawa nayi ba. Duk da nasan na zabge rabi da kwatan ƙibata, a sanadiyyar halin yau da gobe Ka sani kibata zata iya nunkuwa da kaso sama da hamsin akan na da wanda ka guje ni dominta. Debisi ina mugun girmamaka ne ma yasa harna tsaya saurarenka. Amman da ba dan haka ba ko kusa dani baka isa kazo ba. Maganar soyayya ko aure babu ita, dalilin da yasa ka barni ina budurwa. Dalilin ne dai yasa na barka bayan na zama bazawara” Ina dasa aya nayi shigewata cikin gidan. Duk a tsakar gida na tarar dasu, amman banda Daso.
“Adda Jabu Yaya Debisi ya kawo miki wata ƙatuwar leda, tana wajen Adda Daso. Muma duk yayo mana tsaraba mai yawa” Ɗan murmushi na ƙaƙaro nace.
Ayya. Ai Burodami Debisi ba daga nan ba ta wajen kyauta. Boɗɗo ku taso muje gidanki, dan acan nake son mu tattauna kamar yadda na faɗa miki ina da Magana da zamu tattauna daku. Ina zuwa bari in samu Daso in sanar mata” A cikin bukkarmu na sameta tayi tagumi sai aikin tunani take faman yi, dan bata san ma na shigo ba har sai da nazo daf da’ita. Ta ɗago fararen idanunta ta zuba mun su. Akwai damuwa sosai a tattare da’ita, wanda a tunanina baya rasa nasaba da kewar tsohon mijinta marigayi.
Daso wai me ke damunki ne, ni tunda na dawo na ganki wani sukuku. Ko duk rashin lafiyar Dada ne?” Na jefeta da tambaya, tare da kafeta da idanu domin karantar yanayinta.
“Ba komai abubbuwane sukai ma zuchiyata nauyi Jabu. Amman zamu tattauna zuwa dare” kai na gyaɗa mata kawai.
To ni zanje gidan Ɓoɗɗo akwai maganar da zamu yi dasu duka” Kur ta mun da idanunta kamar mai karantar wani abun a fuskata, sai kuma ta ja numfashi tace.
“Bari in zo muje, inaso dama inje wajen Hama, in yaso in kun gana tattaunawar sai ki same ni a ɗakinta”
Hakan ko akayi, a hanya ne take labartamun Debisi ya kawo mun wata ƙatuwar leda, ta adana mun ita. Ni dai kai kawai na gyaɗa. Mun ci tafiya sosai kafin muka iso gidan. Matan gidan duk suna tsakar gida anata tuwon dare, wasu kuma suna wanke ƙoren tallar nononsu, Yafendnmu bata nan bata dawo daga can gidan Baffa Musa ba. Daso ta ya da burki a ƙofar bukkar Hama, tana zaune tana tuƙin tuwon masara, masararnan fara tas gwanin ban sha’awa. Da dariya da haba_haba muka kaisa da Hama kafin muka shige bukkar Boɗɗo. Bayan kowa ya nemi waje ya zauna, sai na yi gyaran murya na soma da cewa.”
Dukkanku kun fini sanin irin halin da Dada take ciki a gidan aurenta. Da irin matsalolin duka, da tsangwamar da Baffa yake yi mata. Ku yi haƙuri Baffa mahaifinku ne, amman nasan ku kan ku kunsan yana zaluntar Dada. A shekaru irin na Dada ai yaci ace ko da an daketa a baya, a yanzu a barta ta huta ko dan kaifin idanunku. Ga yawon talla, duk rauni da da gajiyar dake jikinta tana talle. Amman anan naga ku kamar talla wani abune na dole.” Boɗɗo ta tari numfashina da cewa.
“Talla tana cikin sharaɗin aurenmu mu kam. Domin da kuɗin nononnan zaki ɗauke nauyin ci da sha na gidanki, harma ki yi ma kan ki sutura da dukkan buƙatu. Su kuma maza aka barsu da kiwo. Sai dai wasu matanma suna fita kiwon su dawo lafiya. Dukan da Baffa yake ma Dada ni shine damuwata. Anan ɗakin mun sha zama domin tattauna wannan matsalar, rashin mafita ke sa mu yi haƙuri kawai. Amman zukatanmu na sosuwa ainun, hakan ya zabtare kima da darajar Baffa ta Uba a garemu. Domin mun fi son Dada sama dashi sai dubu babu haɗi”
To ni dai ina da shawara, so nake zan tafi saudiyya neman kuɗi. In na tara kuɗi zan dawo, inaso Baffa ya saki Dada ne kawai. Ni kuma zan ɗauketa harda su Yusufu in sai mata gid, ta zauna ta ci moriyar haihuwa ko wanke_wanke ni zan dinga yi mata ko da nayi aure. Amman meye shawararku kune ƴan uwana?” Boɗɗo tace.
“Da hakan zai faru wallahi Adda sai mun fi kowa farin cikin faruwar hakan. Ni da Amaduyal mu muka san irin wuya da dukan da Baffa ya dinga yi ma Dada. Har ɗaureta yake yi a jikin gadonta ya daketa ciki da waje.” Anan suka sake fayyace mun halin da Dada take ciki a gidan aurenta. Kuma duk suka bani haɗin kai akan suma sun amince a saki Dada. Sai dai wani hanzari ba gudu ba, duk yawan shanayen Dada dake hannun Baffa bazai yarda ya bayar ba. Ni kuma a wannan lokacin sakin kawai nake buƙata ba shanayen banza ba. Sai da mu kai sallar isha a gidan. A ɗakin Yafendo muka haɗu mu ka ci abinci anata hira, maza kuma suna waje suna shan iska.
“Cubu je ki kira Hamma a waje ya raka su Daso guda, kuma sai ku kama hanya tunda ga Yusufu sai yai muku jagora” fitar Cubu ke da wuya sai gata Yaya Hamma na biye da’ita.
“Dada gani” Ya faɗa da murya mai kauri. Yarinyarshi dake hannun uwarshi sai ɗaga mishi hannayenta take yi halamar ya dauketa Hama ta miƙa mishi yarinyar ya ratayeta a kafaɗarshi.
“Su Daso zaka raka gida tunda dare yayi .” Ɗan murmushi yayi kawai kafin yace.
“To Dada su sameni a waje sai mu je. ” A tsaye ya ɗan yi ma ƴar tashi wasa ya miƙa ta hannun uwarta ya fita. Muma mu kai ma Yafendo sallama muka fito, suma su Yusufu suka nufi hanyar komawa gida.
Shiru_shiru mukaita tafiyar. Duk cikin mu ukun kowa da abinda ke azalzalar zuchiyarshi. Abun mamaki har muka isa gida ba wanda yayi ko tari.
A ƙofar gidan muka haɗu da Jatau da Burodami Debisi sun kafa sun tsare suna jiranmu.
“” Ƴar halak ta ƙi ambato ka ganta ma. Jabu mun fi mintu talatin muna jiranki anan wajen” Hannu Yaya Hamma ya miƙa musu suka gaggaisa, sai naga ya kuma haɗe ranshi. Ni da Daso dai muna tsaye, Allah cikin ikonshi sai ga Manga shima ya tawo taɗi shi da abokinshi. Yaya Hamma ne yai ma Daso jan ido ta je wajensu.
“Jabu ki je ki saurareshi, ni zan jiraki a wancan wajen itaciyar, inason mu yi magana ne” Yaya Hamma ya faɗa a sanyaye.
To Yaya Hamma” Iyakar abinda na faɗa kenan. Burodami Debisi yaima Hamma godiya, ni dai na bi bayanshi dai muka matsa gefe haka.
MRS BUKHARI B4B GIDAN ƘAMSHI CE
Ina miƙa saƙon gaisuwa ga masoyana.
Sister Khadija maidoki ina godiya.
Part 2
NAMA YA DAHU..
ROMO ƊANYE
LITTAFI NA BIYU
2
“Gimbiya Iyabo sai wahalar da zuchiyata sonki yake ta yi. Ni na ɗauka dake zan koma Kano a matsayin matata fa, ashe abun ba haka bane. Ki tausayama masoyinki ki tsamoni daga cikin halin da kika sanyani, kaina bisa wuya, banda tuno baya. Kuma nayi imanin su Iyaa da Burodami kokodeen zasu yi alfahari da aurenmu Iyabo “
Duk wannan maganar yana yinta ne cikin kyakkyawan lafazi mai taushi. Maganganunshi babu inda basa ratsawa a jikina. Sai dai kash ya makaro, dan banga abinda zai iya cemun in yarda dashi ba.
Ina Mai baka hakuri ka fitar dani a zuchiyarka dan Allah. Nayi imanin a rashin samun yadda kake so a wajen matarka soja ne yasa kake son ni ka aureni” Da sauri ya fuskanceni sosai cikin kidima yace.
“Wallahi bazan iya ba. Baki san irin azabtuwar da ruhina da gangar jikina suke yi bane shi yasa. Ki dena tunanin dan ban samu yadda nake so a wajen Yemisi bane na dawo gareki. Iyabo ina sonki”
Ɗan guntun murmushine ya sufce mun ba tare da na shirya ma hakan ba.
Zaka iya, tunda har na iya cire sonka a zuchiyata. Na rungumi soyayyar Gwadabe har kuma ya samu matsayin da babu wani ɗa namiji da zan iya bashi wannan matsayin. Kaga kuwa zaka iya, dan a baya sonka ya rufe mun idanu ta yadda bana ji bana gani. Ido da addini kaƙi fur a haɗa mu aure. Kaje ka auri sojar matarka siririya irin samburin matan da suke burgeka. Na roƙeka ka barni in auri namijin da yasan darajar ƙiba irin Gwadabe. Wanda zai dinga kammamani yana kuranta kyauna”
Baki na tsuke nayi kicin_kicin. Daya isheni ma da magiya sai kawai na fashe mishi da kuka. Da ƙyar ya rarrasheni nayi shiru.
“Shikenan Iyabo, zan sake baki lokaci. Ni gobe zan koma asubanci zanyi. Amman fa ki sani zan jiraki kije ki dawo sai muyi auren”
Allah ya tsare ka gaishe mun da kowa da kowa. Banda matarka Yemisi, dan nayi imani batasan wajena ka tawo ba” Bai iya ce mun komai ba na yi tafiyata na barshi a wajen. Yaya Hamma kuma yana daga can gefe can gaba da inda su Daso suke tsaye. Dole ta gabansu zan wuce, hakan yasa saida na tsaya aka gaggaisa kana na Isa wajen Yaya Hamma Daso ta bini da idanu kawai. Zama nayi a gefen itacen da yake zaune, muka ƙurama juna idanu ƙur kamar zamu haɗiye junanmu. Idanunshi jawur harda kwantaccen hawaye marar yawa a cikin idanun nashi. Lumshe idanu yayi, yaja wani numfashi marar fassara a gareni, yai amfani da murya mai salon taushi da sanyi tarara wajen cewa.
“Me yasaki kuka, kuma me Debisi yake nema a wajenki ne Jabu, na fahimci akwai babban sababin daya kawoshi rugarnan?” Ƙireni da idanu yayi.
Nima ajjiyar zuchiyar na sauke. Na fayyace mishi ƙudurin Burodami Debisi a kaina. Na tsokata mishi ɗan labari akan cewar iyaye a baya sun haɗamu aure amman sai ya nuna baya ra’ayina. Amman na ɓoye mishi dalilin shi na ƙin nawa. Murmushi naga yayi har yanayin fuskarshi sai da ta sake. Gyara zama yayi yace.
“To cika mun alƙawarina da kika ɗaukarmun akan kina dawowa zaki sanar dani dalilin zuwanki birni”
Dariya na kwashe dashi, shima dariyar yake yi. Kwashe labari nayi na bashi. Da kuma dalilin da yasa zan tafi ɗin. Tashi ɗaya ya birkice har yana tsugunnawa akan guiwowinsa a gabana. Idanunshi suka cika fal da hawayen da suka kasa gangarowa.
“Na roƙeki kar ki tafi Jabu ki barni. Shekara uku ban saki a idanuna ba, ai abune wanda ka iya kwantar dani. Ni zan siyar da saniyata in baki kudin a hannunki ki siya ma Dada gida, kiyi sana’arki da sauran kuɗin ki yi haquri ki janye wannan tafiyar dake shirin rabamu. In kuma ni kike so in mata duk abinda kike so a shirye nake. Yafendo uwatace, ina jin motsin sonta da tausayinta a raina. Jabu na roƙeƙi kar kiyi nisa damu, rayuka da yawane zasu jikkata”
Mamaki ya kamani, to me Yaya Hamma yake nufi da wadannan kalami nashi? Ni ba yarinya bace na lura sarai tun zuwana yana ra’ayina. Amman ban tabbatarba sai jiya dana ga kishin Debisi ƙarara a idanunshi. Wannan kalamai nashi na yanzu sun ƙara tabbatarmun Yaya Hamma rainon sona yake yi. Kuma na fahimci Daso na tsantsar sonshi, Yafendo ma ta sani kuma tana fatan faruwar hakan. A duk sanda Yaya Hamma zai zo gida, sai Yafendona ta alaƙanta zuwan da Daso. Gashi matarshi ƙawarmu ce, mutuniyar kirki mai son jama’a.
Kayi haƙuri ka tashi dan Allah yaya Hamma mu yi magana ta fahimta dan Allah ” A tsugunne a gabana Daso ta iso ta sameshi. Numfashi ta ja tare da saurin yin turus, ganinta ne yasa ya tashi ya zauna.
“Ki shiga gida Daso, ban gama magana da’ita ba. In muka gama zan rakota, ina buƙatarta tare dani”
Fuu ta wuce har tana haɗawa da gudu. Tausayinta ya kamani, dan babu son da ya kai son maso wani ciwo, zafi ne dashi kamar zafin fitar rai daga gangar jiki.
Mun fi awa ɗaya da rabi muna tababa tsakanina da yaya Hamma akan tafiyata. Bamu cimma matsaya ba Baffa ya fito ya korani ciki dan gaskiya dare yayi har ƙafa ta ɗauke magiya kawai Yaya Hamma yake yi tare da tambayata shanu nawa zai siyar ya bani kuɗin.
Ko da na shiga bukkarmu a zaune ƙiƙam na samu Daso ta kurama aci bal_bal idanunta. Ledar gabanta ta turo gabana ina tsaye.
“Ga saƙonki na wajen ɗan uwanki” Murya ba daɗi ta yi maganar. Ledar na ɗauka na zauna. A hankali na zazzaro kayan dake ciki. Kayan tea na gani, da macline da brosh, sai mayafai biyu, takalmi biyu da atampa ɗaya leshi ɗaya, sai zungureriyar wasiƙar da bani da niyyar karantawa. Biyu na raba kayannan cib na ba Daso, kayan tea ɗin kuma na ajjiye mana.
“Ki riƙe abunki ni bana so”
Wai Daso na yi miki laifine kike fushi dani. In akwai matsala ki sanar mun mana?” Na jefeta da tambayar ina ɗaga murya dan ta mugun ɓata mun raina ainun.
“Hmmm”
Shine iyakar abinda tace dani. Kayana na kwashe na mayar ko da na ɗane gado na kwanta Amman me? Sai bacci yace bani bashi. Tunanin Dada ya cakuɗe mun da tunanin furucin Yaya Hamma na ɗazu, da irin yanda duk ya kiɗime. Hasko mun da hoton Gwadabe da zuchiyata tayi sai hawaye ya soma tsiyayomun masu zafin gaske. Babala ta zalunci zukatanmu data ƙi amincewa mu rayu a tare. Nasan duk inda Gwadabe yake kuwa yana can zuchiyarshi a batse da kewata. A tsakanin ni da Daso babu wanda ya runta
Washe gari sassafe ni da Hari muka gama duk aikin gida. Ina gama karyawa nai ma Yafendo sallamar ni zani gidan Baffa Musa.
Acan na tarar mijin Dada yazo ɗaukarta, kuma abun haushin harta fito daga ɗaki ma suna tsakar gida. Da ƙyar na danne zuchiyata na bashi girmanshi albarkacin uwata da yake aure. Shi kuwa banza ya ba ajiyata, in kun tanka ya tanka. Har a kan fuskar Dada banga tayi farin cikin zuwan mijinta ba, fuskarta ma cike take da tsoro. Amman haka ya tusata a gaba suka tafi, ni ko da kuka na fice a gidan na dawo gida. Na tarar da su Yafendo sai dafa madara suke yi, taga na shigo da kuka kamar karamar yarinya dai.
“Jabu lafiya kaddai Adda Daso mutuwa tayi?” Ganin yanda duk suka ruɗe suka yo kaina yasa na yi musu bayanin dalilin kukana. Yafendo da Hari ne su kaita rarrashina dai haka.
Gaga_gaga haka rayuwa tai ta tafiya. Ko wacce rana kafin faɗuwarta sai hawayena ya zuba. Dada jikinta ya warware har ta soma fita tallar Nono. Sabida tsananin tausayinta yasa nake binta wajen sana’ar nonon nata. Sai tayi zamanta a gefen rumfa. Ni kuma ni zan zuba Nono in kai, in je in kwaso ƙworena. Munayin hakan ina jin daɗi itama tana jin daɗin hakan, dan karayar tata bawai ta warke sumul bane. Ƴan tsegumi suka sanarma da Mijin Dada ai ana ganinmu tare. Kwatsam muna kan siyar da Nono sai gashi ya zo dan ya zama ganau ba jiyau ba. Da ganinshi Dada jikinta ya soma mazari. Kwafa yayi kawai yaa bar tashar fu. Ranar dai haka muka ƙarashe kasuwarnan cikin taraddadi. Wannan shine silar da na dena bin Dada wajen sana’ar tata.
Ta ɓangaren Hamma kuma shaƙuwar data shiga tsakaninmu shakuwace ta ban mamaki. Banda Dada da ƙannena,shi kaɗai nake gani ya yaye mun damuwata da kalamanshi masu sanya kuzari, gashi kullum sai naci tsire da lemun kwalba, Abunka da ƙauye tuni ƴan tsegumi suka tseguntama Hama ana ganin Hamma kullum da wata mace har dandali. Dan babu ranar da bama zuwa dandali, da Hama ta gane ai nice mijinta ke ƙwaƙwa, duk wannan far’a da haba_haba da take yi muni sai du ta dena. Har ta kai ta kawo ta dena kulani, ko na gaisheta ma da kyar take ka da baki ta amsa, harma abu ya zame musu rigima a tsakaninta da Boɗɗo. Daso kuwa tsakanina da’ita takun saƙane, taƙi ta yarda ba soyayya muke yi da Hamma ba. Tunda duk shakuwarnan bai taɓa cewa yana sona ko zai aureni ba. Ita kuma ma a lokacin har Baffa ya san da zaman Manga. Dan ance mishi zuwa kaka ya turo manya a gama komai. Ita kuma tayi tsalle ta dure kan cewar Allah ya kasheta bata son Manga. Baffa kuma yace ya bata kwana talatin ta fito da mijin aure in ba hakan ba ya aura mata Manga. Ni dai sai shirin tafiyata na sanya a gabana, nayi watsi da iskantakun Daso. Lokacin da labarin tafiyata ya shiga kunnen Dada bata ja ba, sai ma fatan samun nasara da tai mun. Baffa Musa ne yaso ya turje, amman su Dada suka haɗu suka tausheshi. Yaya Hamma dai ko hirar tafiyar tawa nayi mishi sai ya gimtse fuskarshi shi yasa ko zancan ma ni bana yi mishi, shima baya so, yayi juyin duniya in janye wannan tafiya. Ni kuma fur naƙi amincewa, har shanu biyu ya siyar da daddare sai ga kuɗi dumus nera na gugar nera har nera dubu ɗari cib
Miƙo mun yayi nasa hannu na amsa sai naga kuɗine.
Bayani yaimun akan siyar da shanunshi da yayi, duk dan kada in tafi. Ni kuma naƙi karɓa fur, na bashi hakuri tare da yi mishi bayanin na riga nasa Hajiya Salamatu ta kashe kudinta da ɓata lokaci. In nayi mata haka ban kyauta ba. Dole babu yanda ya iya haka ya mayar da kuɗin aljihun ƴar shararshi, tare da sauke kanshi ƙasa kawai. To ya akayi_ya akayi labarinnan ya je kunnen matar Yaya Hamma sai Allah. Nan ta da bori Boɗɗo na bani labarin irin rikicin da su ka yi ita da Yaya Hamma. Har sai da Yafendo ta shiga cikin lamarrin. Kuma jin abinda Yaya Hamma ya aikata yasa Yafendo ta fusata itama. Kun dai san fulani da maganar Shanu, dan tsabar ɓacin ran da Yafendo tayi ƙwace kuɗin tayi a hannun shi Yaya Hamman, tare da gargaɗin koma me zaiyi mun yayi mun ni ƴar uwarshi ce. Amman bata yadda ya sake taɓa shanu ba, waɗannan shanu gadon_gadone da suke fatan ƴaƴansu Hamman da jikokinsu, da haularsu masu zuwa suita gadansu.
. Ana saura sati guda in tafi, sai Yaya Hamma ya soma rashin lafiya. Abu kamar wasa ƙaramar magana ta zama babba. Tun yana zuwa kiwo har dai ya dena. To dake a ɗakin Yafendo yake jinyar tashi, ana saura kwana biyu in tafi sai na je dubashi. Ina shiga sai Hama ta bar duk abinda take yi ta dawo ɗakin Yafendo ta zauna. Harma tana shafan sumarshi a gabana dan inji haushi, shi kuma kunyata tasa ya ture hsnnunta. Ai ko abun ya mugun sokar zuchiyata ta yadda ni kaina sai da nayi mamakin yanda naji sautin kishin mutumin da bai buɗe baki ya furta mun kalamin so ba. Sai dai iya so da kulawa a aikace yana nuna mun. A furucine bai furta ba, kuma na fahimci nauyi abun yake yi mishi. Kunya da kawaici irin na fulanine ya hanashi furta mun yana sona. Shigowar Yafendo da fura a hannunta ne yasa Hama tashi ta dawo ƙasa ta zauna.
“Jabu ga fura ki sha” Ta miƙo mun. Hannu biyu nasa na amsa nace.
Use Yafendo.
“Hama kin baro aikin ki kin dawo kin zauna? Maza tashi ki koma kan aikin ki, kinsan zaki je tallan nono fa” Har cikin ranta bata jin daɗin wannan katsalandan da Yafendo tayi mata ba. Amman ni kuma kamar in goya yafendo haka naji” Tare suka fice ɗaki ya rage daga ni sai Yaya Hamma. Shi kuma fishi sosai yake yi dani duk fa akan tafiyar tawa ne. Ni sai tafiyar ta fitar mun akai, kuma nayi mishi rantsuwar da ace da kuɗina akayi mun komai da tuni na fasa. Amman yanzu in nace na fasa hajiya Salamatu ba ƙaramin bacin rai zata nuna ba, kuma ƙila ita kanta uwani in ja mata.
Yaya Hamma ya jikin naka?”
“Da mutuwa ma zanyi kila hankalinki sai yafi kwanciya ko?” Sai naji faɗuwar gaba har idanuna suka kawo ruwa. Cikin rawar murya nace.
Ko kusa bazan ji daɗi ba. Kayi haƙuri tafiyar da zanyi ta dole ce, kuma bazan shige shekaru uku ba zan dawo. Kuma ina fatan in dawo in sameka a cikin aminci. Ɗan murmushin gefen baki kawai yayi mun.
“To ki shirya tare zamu tafi kanon. Bazan dawo ba har sai jirginku ya tashi. Idanu na zaro nace.
Ka rufa mun asiri kar kasa matarka ta bindigeni. Kai da baka da lafiya kuma sai in ɗaura maka wahala? Wallahi ka barshi. Hararata yayi mai cike da tsantsar so.
“Ai ratayayyen hakkine a kaina inga tafiyarki.” Shiru nayi zuchiyata na doka mun tambura.
To Allah ya baka lafiyar Yaya Hamma. Ni zan zo in wuce” Sallama nayi mishi na fito da furata a hannuna a ɗakin Boɗɗo na shanye furata.
Washe gari Dada ta kawo mana ziyara da su Cubu dan muyi sallama. Tayi mun nasiha mai ratsa zuchiya sosai. Nayi kuka kamar raina zai fita. A daren na kasa baccin kirki. Ina kwance Daso ta shigo ta tsaya a kaina.
“Sai ki tashi Yaya Hamma na kiranki. Jabu wallahi kiji tsoron Allah kinzo kin samu mutum da ƴar matarshi suna soyayyarsu gwanin sha’awa. Amman kinzo kin raba wannan soyayyar da shaƙuwa, kin hana Yaya Hamma ya samu lokacin kan shi balle ita Matarshi ta samu lokacin shi itama” Tashi tsaye nayi ina jujjuya maganganun da Daso ta fesomun. Kai kawai na girgiza tare da cin alwashin sai na jero mata waɗanda suka fi wanda ta faɗa mun zafi. Ficewa nayi na barta da ƙunan zuchiya. A zaune na sameshi yana zane a ƙasa da tsinke. Zama nayi a gefe nace.
Barka da zuwa Yaya Hamma. Yaya jikin naka amman?”
“Jiki da sauƙi Jabu. Ya shirin tafiya? Nasan dai an gama komai ba tun yau ba. Ke naga zumuɗin tafiya ki barni kike yi” Sai naji duk jikina ya mutu. Shine yake ganin kamar ina zumuɗin in tafi in barshi. Amman har cikin jikina inajin zafin kewarshi tun yanzu, bansan kuma ya abun zai zama in na tafi ba.
A ranar dai hirar batai armashi ba jikkunanmu a mace mu kai sallama. Harna taka zan shiga gida ya kira sunana.
“Jabu” Cak na tsaya. A hankali na juyo muka zuba ma juna idanu na mintunan da bazan iya faɗar adadinsu ba. Ya kasa ce mun uffan. Fitowar Jatau ce ta katse komai. Bai samu damar faɗa mun abinda yasa ya kirayi sunana ba, Jatau ya tareshi da zantuttuka. Cikin na shige na barsu nan.
Ina shiga na harari Daso nace.
Gobe zan bar garin. Kinga hakan zai baki damar cusa kan ki a wajen Hamma. Kinga in da rabo sai in dawo in sameki kina goyon ɗanku na biyu ke da shi.” Ina faɗin haka ta kalleni tace..”haka kika ce mun Jabu?”
Ƙwarai kuwa haka nace. In kin isa ki maye gurbina a zuchiyarshi in zaki iya Ni kin ganni nan tafiyata tafi komai mahimmanci a wajena” Kwafa tayi tace dani.
“Zan baki mamaki Jabu, zaki san nima macace wacce Allah ya horema duk abun alfahari kinsan dai na fiki kyau nesa ba kusa ba, in banda ma namiji da gane_gane ko me ya gani a jikinki oho”
Ni ban ma sake bi ta kanta ba. Itako sai mita take yi da fillanci. Ina kwance shiru duk kewan yarana ya kamani, dama Baban yaran. Can kuma sai Hamma ya fado mun, da kuma alwashin da Daso taci mun. Da irin wannan tunani bacci yayi awon gaba dani. Asubar fari na yi wanka tsab. Ana fitowa masallaci na suri kayana a jakar leda na fito.
Na yi sallama da kowa da kowa. Ana cikin haka Yaya Hamma ma ya shigo. Muna fitowa Boɗɗo da mijinta na isowa suma. Sai da suka rakamu fa har Girai kana suka dawo mu kuma muka shiga cikin gari, Yaya Hamma ya samu a motar Kano. Sassafe motarmu ta hau kwalta. Sai da tafiya tayi nisa Yaya Hamma yace.
“Inaso ki mun wani alƙawari Jabu. Nasan kina da riƙon alƙawari na san hakan silar shaƙuwarmu. To ki mun alƙawarin da kika tabbatar zaki cika mun shi. Kar ki yaudareni in yayi miki tsauri ki ce mun ba zaki iyaba” A sanyaye nace dashi.
Faɗi alkawarinka a shirye nake da in cika shi. Matsayinka ya wuce hasashenka” Daɗi yaji sosai.
“Ki mun alƙawarin ba zaki wuce shekaru ukunnan da kika ɗebarma kanki ba. sannan ki mun alkawarin ba zaki kula samari ba dan Allah. Sannan ki mun alƙawarin ba zaki dawo kiji ke kinfi ƙarfin zama tare damu ba. Bi ma’ana kar ki sake halayyarki, sannan ki mun alƙawarin riƙe mutuncinki” Shiru nayi mishi ina murmushi kaina na ƙasa.
“Au ke dariya ma na baki ko? Kin kyauta ai” Ɗago kaina nayi na kalleshi.
Yaya Hamma na karɓi duk alƙawarurrukanka. Allah yai riƙo da hannayena in cika maka alkawarurrukanka. Amman ina da taambaya…”
“A’a Jabu “.. yayi saurin dakatar dani ta hanyar ɗaga hannayenshi. Ba shiri na yi shiru da bakina.
“Ni dai tunda kin ɗaukii dakon alkawarina ai Shikenan. Ni kuma zan yi zaman jiran dawowarki, tare da miki fatan samun nasara kuma” Daga haka kuma mu ka ɓige da hirarraki, ya dinga bani labarai dangane da al’adun Fulani. Ni kuma dama na kasance ma’abociyar son tarihi ce da duk abinda ya shafi gargajiya ta ko wanne ƙabila.
Allah cikin ikonshi da amincewarshi muka isa garin Kano. Kai tsaye gidan Uwani muka ya da zango. A gidanta muka ci abinci. Yaya Hamma ya fita zuwa masallaci dan rama sallolinshi, nima na rama nawa sallolin.
“Baki ga yanda kuka dace ba wallahi. Ashe kyakkyawane Yaya Hamman naki. Kuma na lura gaskiya yana tsantsar sonki. Munafuka kema fa kin soma sonshi. Ni dai amman bana bayan wannan soyayyar ruga ba wajen zamanki bane” Dariya mu ka yi dukka.
Hakane Uwani wallahi na tsunduma cikin sonshi. Shi kuwa dama ba’a magana dan shi ya koya mun yanda zan so shi. Sai dai fa akwai kura Uwani”
Sai da ta gama dariyarta tas kana tace mun.
“Ƙurar me kuma Iyabo, akwai wata matsalar ne?” Nace da’ita.
E to akwai matsala ta ɓangaren matarshi, da ɓangaren yarinyar ƙanwar Dadanmu Daso wacce nake gidansu a zaune. Matsalolin du manya ne daka iya dakile soyayyarmu. Matarshi tunda aka kai mata gulmar ana ganin mijinta a wajena, sai ta tayar da ƙayar baya, kullum cikin fitina dashi take. Ke har shanunshi daya siyar ya bani kuɗin ban karɓaba sai da su kai rikicin da har mahaifiyarshi ce ta shiga. Ƙanwata tana Aure a gidan Uwani tana auren ƙanin shi hamma ɗin. Sai suka tsiri zaman doya da manja. Ita kuma Daso ko tsaiwa da zaurawa bata son yi kwata kwata duk sabida da shi. Akwaifa wani abokin mijinta mai rasuwa da yake tsantsar sonta. Yarinyarnan fur ta dire wai bata sonshi. Ni kumaa a jiya ta caccakamun magana akan wai Hamma na zaman soyayya da matarshi ni nazo shiga tsakani na hana aci soyayyarnan yadda ya dace. To kinsan mu mata, saina caccaka mata nawa maganganun nace ta aurshi in dawo in samu tana goyon ɗansu na biyu. Ita ma cikin fishi sai tace zan gani. To jiya da ƙyar nayi bacci Uwani ” Dariya muka dinga yi ni da Uwani.
“Ni dai shawarar da zan baki wallahi ki raba kanki da wani auren ruga, kiyi fatali da wani Hamma. Kinga ƙasar zamu bari Iyabo soyayya ba taki bace. Shigowar Yaya Hamma da Hafizu ne ya dakatar da tattaunawar tamu. Sun zauna babu daɗewa nace.
Uwani Hafizu mu kam zamu tafi gida. Sai gobe kuma in Allah ya nuna mana.” Tare su kai mana rakiya izuwa titi har sai da Bus ɗinmu ta tashi sannan suka juyo. Kwatsam su Iyaa suna tsakar gida suna wannan hira tasu mai kamar faɗa muka shigo.
“Ah Ah ah ah Iyabo. Ikabo ( sannu da zuwa)” Nan ta miƙe ta soma rawa harda guntuwar waƙarta su Iyaa Beji na mata dariya. Dukkansu saida na bisu ɗaya bayan ɗaya na dinga zubewa a gabansu ina kwasar gaisuwa bisa ga al’adarmu. Yaya Hamma dai duk abinda yaga nayi shi yake maimaitawa.
“Lekan, Lekan woo ah” Lekan ya amsa da karfi sai gashi harda gudu.
“Ahh Antimi Iyabo Ikabo o ti dara osale ( Anti Iyabo Sannu da zuwa Ina wuni?)”
Owo bawo ni o se n se? ( Yaya kake Lekan)? Nima na tambayeshi da yarenmu. Hannu ya miƙa suka gaisa da Yaya Hamma kana yace mun.
“Owo mo dara Antimi ( Ina lafiya Anti)
“Mu u lo si yara re ( Kai shi ɗakun ku) Cewar Iyaa. Ni kuma ta jaye hannuna muka shige ciki.
“Ashe dai zaki zo Iyabo? Nayi kewarki sosai. Sai inta mafarkin ki. Har sai da Debisi yaje ya dawo ya tabbatar mun kina lafiya sannan na samu nutsuwa. Sai kika ga Debisi ko?” Murmushi nayi mata nace.
Sai gashi Iyaa babu zato” Dariya tayi kawai kana tace.
“Duk abinda babba ya hango yaro ko ya hau bishiyar rimi ba zai hango ba. Dama dan ya samu nutsuwa ne yasa na ce ya aureki dan zaki fi ganin darajarshi da kimarshi sama da ko wacce mace. Amman sai ya nuna shi baya so. To wacce yake so din gasu can kullum cikin faɗa, ko jiya uwar haka suna gidannan anata shari’ar da ni na gaji da’ita. Yanzu dan Allah da ke ya aura hankalinshi ba kwance ba?” Kasa amsata nayi, dan da kunya Debisi dai ita ta tsugunna ta haifeshi.
“Shi wannan ɗin da ya rakoki ko shine oko omo obirin ɗin nawa? (Sirikina). Kai na sauke ƙasa nace.
A’a yaron Ƙanwar Dada ne. Dama zan tafi saudiyya aikataune shine ya biyoni in mun tashi sai ya koma shi kuma”
“Ah Ah orira ( abun mamaki) Saudiyya fa kika ce?” Sai ta miƙe ta shiga rawa tana jero mun waƙoƙin sanya albarka. Har sai da ta tara mun matan gidan. Nan take kowa yaji abinda ke faruwa. Nan gidan ya kacame da waƙoƙi da murna. Bayan sun tafi ne Iyaa ta bani Amala tace.
“Ki kaima Ɗan uwanki amala yaci abincin yarbawa” mayafina nasa na ɗauki kwanon na fice zuwa ɗakin lekan. Da sallama na shiga na samu yana kallon wani film na yarbawa. Shi kaɗaine a ɗakin sai lemun kwalba na limca dake gabanshi.
*Ƴar uwa ina fatan baki mance da kayan ƙamshin Mrs Bukhari gidan ƙamshi ba ko? Ƴar na gata ba take haye ba, Kanuri gidan ƙamshi. Matso kusa ƴar uwa ina da turarukan wuta nau’i daban_daban. Turaren kaya da zaki turare gidanki ƙamshi ya riƙe miki surura, sannan inada kabbasiyya turaren ruwane da ake fesama sutura a yayin da ake turara kaya a kabbasa, kana inada turaren wadrop da ake saƙawa a tsakankanin kaya.
Turarukan wutana kuwa in kika turara gidanki yana sati guda yana ƙamshi. Inada turaren turara jiki gangariya wanda yake kama fata.
Akwai kulaccam ta matan aure mai sirrin rikita maigida, ga gyaran fata. Akwai kuma kulaccam ta gashi, haɗe da turaren fesawa a gashi.
Mai gayya mai aiki humrata ta matan Aure mai sirrin ƙara dankon soyayya, kiga oga na shinshinarki kamar mage taji ƙamshin kifi ɗanye.
Inada humrori kala_kala.
Ina da room freshener, da mopping mix mai sirrin ƙamshi.
Kar in ta lissafo muku duk wani nau’in ƙamshin da kikeso in kika samu Mrs Bukhari ƴar mutan Maiduguri kin samu ƙamshi.
( Albishirinku akwai package na musamman dana tanadarma masoya wannan littafi nawa. Package ne mai ɗauke da abubuwa huɗu manya kuma a kan kuɗi ƙalilan karki bari garaɓasarnan ta wuceki zaki ciji yatsa kwasha_kwasha nayi da kayana domunku)*
Part 3
NAMA YA DAHU….
ROMO ƊANYE….
LITTAFI NA BIYU
3
A hankali na isa na zauna a gefenshi. Idanu kawai ya zuba mun sai naga yana kaɗa kai.. Kwanon abincin na tura mishi gabanshi.
Ga Amala abincin bugun gaban yarbawa da fatan kana iya ci” Dariya yayi mun yace.
“Tun kafin ki zo duniya nake cin Amala. Ai nayi zaman oghomosho, sarkin garin Oghomoshon ma bafulatanine. Kinsan tun shekaru aru aru yarbawa suke a matsayin bayin Fulani. Hakanne yasa auratayya tayi ƙarfi a tsakanin Yarbawa da Fulani. Sai kiga bafulatani sak amman sai kiji bai iya ko fillancin ba sai yarbancin. Haka sai kiga beyerabiya na zagargaza fullanci. Ki duba Dada yanda naga da yarbanci zalla take magana dake.” Ajjiyar zuchiya na sauke nayi dariya. Shima dariyar yayi ya soma kantara lomar Amala miyar ewedu sai dalali take yi a hannunshi. Sai da ya cika bakinshi da ( phomo) ganda kana yace.
“Ni ko kibar matan yarbawa na birgeni, kuma Allah ya zuba musu sura masha Allah .” Dariya nayi sosai nace.
Ku da kuke da farare kuma siraran mata masu gashi” Dariyar shima yake yi mun.
“Jabu kenan. Ai cikakkiyar mace ƴar duma_duma daban take da siririya. Shi kyau a sura yake ba’a fuska ba ai. Bance sirara basu da kyau ba. Kuma bance yarbawa sun fi filani kyau bane. So nake ki fahimta, wani namijin mai sha’awar haɗa shinkafa da doya ne. Wani kuma taliya kaɗai ta wadatar dashi” Cikin karantar yanayinshi nace dashi.
To kai a wacce matsayar kake ne?”
“Koma a wacce nake zaki sani ne” Cikin raha dai mu kaita hirarmu har ya kammala cin abincin nashi. Kana nayi mishi sallama na tafi.
Sai zuwa washe gari na haɗu da su Burodami kokodeen da su Burodami Debisi. Kuma na zagaya gidajen nasu naga yaransu, na gaisa da matansu. Yemisi dai babu yabo ba fallasa, dama ya lafiyar kura ballantana tayi hauka. Haka dai akaita mana shirin tafiya, dan har munje anyi mana gwaje_gwaje iri da kala a asibiti. Ana washe gari zamu tafi ko bacci na kasa yi dan dadi, da kuma wata fargaba data lulluɓeni. Burodami Debisi, da Yaya Hamma, da Hafizu sune abokan rakiyar tamu har zuwa filin jirgi, ko ince ɗakin jira. Gefe guda muka keɓe da Yaya Hamma da jikinshi naga har rawa yake yi, idanuna a cike da ruwan hawaye. Naso Yaya Hamma ya furta mun kalmar so kafin in tafi ya jaddadamun matsayina a zuchiyarshi. Amman kunya da ƙauyanci ya danneshi. Haka dole mu kai sallama ba tare da naji inda soyayyarmu ta kwana ba. Ko da muka shiga cikin Bus ɗin da zata kaimu gaban jirgi ai sai na sake fashewa da kuka, ina tunano fuskar Yaya Hamma, da yanda yake ta aukin jaddadamun alƙawarinmu. Burodami Debisi kuwa kamar ya shaƙo Yaya Hamma ya rufeshi da duka haka yake ji. Gurin dake ɗaure a shintsiyar hannunshi daya bani na sake damƙewa a hannuna.
Yau ni Iyabo gani a cikin jirgin sama zai tashi damu zuwa ƙasa mai tsarki. . Hukunci sai mai tsaga idanu. Allah sarkin girma in ji kishiyar mai duwawu.
Maraɗi
Gwadabe:.
Auwala bai dire Sabitu a ko ina ba sai a gaban malam, ga almjirai cike da wajen. Tun kafin Malam yayi magana. Baba Asshi ta fito babu ko mayafi a jikinta. Kallon da taga gardawan Malam Magaji na yi mata ne yasa ta koma daga zaure.
“Auwala wannan wanne irin riƙo kayi mishi kamar ka kamo barawo” Malam ya girgiza kanshi yana bin ƙofar zauren da kallon baƙin ciki. Baba Fhatsima ce ta fito saye da katon mayafinta ta jaye Hadiza tare da cewa.
“Koma me ya faru a barshi a tattauna a cikin gida. Auwala cikashi, kai kuma Sabitu jeka abinka. Allah yayi muku albarka baki ɗaya. Hadiza ta jawo suka shigo zauren Baba Asshi ta harareta sama da ƙasa tace.
“Ni nawa yaran sai ki tsine musu ai, tunda naki kika sama albarka. Ni na ji jaraba fa, kun bi kun sani a gaba Fhatsima kin hana mun jin daɗin aure” Baba Fhatsima Taso tsaiwa ko wacce zata hanata bacci ta feso mata. Auwala sai ya kama hannunta suka shige. Su kuma su Gwadabe suka wuce barayinsu dan watsa ruwa su ji daɗin jukkunan nasu. Gwadabe yana wankannan yana tunanin me yasa gida in da mace sama da ɗaya ake yawan samun rabewar kai ne. Ta ina kuma matsalar tafi rinjaye tsakanin matan, ko uba da yake zama majingina a wajen mata da yaran gida.?
Da wannan tunanin ya fito. Fitowarshi ke da wuya Ine tazo ta yi kiransu gabaki ɗaya harda Gwadabe izuwa turakar Malam. A babban falonshi duk suka gurfana Malam ya soma magana da cewa.
“A wannan karon duk macen data nuna zata kawo mun rabewar kan ƴaƴa ni zan iya sallamarta ta tafi gidansu. Allah yana gani daidayya ina bakin ƙoƙarina dan ganin nayi adalci a tsakanin matana harma da su yaran nawa. Ke Fhatsima kece Babba a gidannan na faɗa ba tun yanzu ba zan haɗe kan yarana da matansu dukka a gida ɗaya dan su rayu tare yaransu su cuɗu da juna ta yadda zasu shaƙu da junansu. Wannan magana tamkar a rubuce take ba fashi. Duk da Asshi ta nuna ita bata bukatar a haɗe yaranta dana Fhatsima. Harma Jamilu ya goyi bayanta a kan hakan. Rikicin Sabitu da Hadiza ne yasa na dawo da wannan maganar baya. Nasan ko wacce nayi mata bayani ita kaɗai Amarya malam uwar kissa ta dubeshi da taushin murya tace.
“Allah shi gafarta malam ni nawa yaran da suka kasance ƙananu ya za’ayi dasu to?” Dariya malam yayi cikin so yace.
“Amarya harda su Rabi’u za’ayi wannan ginin. Su kuma mata _matan da zasu yi aure ko wacce zan bata kadara a matsayin kyauta, kanana marasa aure kuma sai in ajjiye musu zuwa lokacin da Allah zai ƙadarta su yi aure. In kuma ta Allah ta kasance a kaina sai a danƙa musu baya cikin gado na basu halak malak, hatta ginin da Shi Tasi’u zai musu baya cikin gado na mallakawa kowa halak malak harda Gwadabe dan gudun kar in kwanta dama tashin tashina ta tashi. Dan kuna ganinane kuke samun damar faɗace_faɗacen nan da kuke yi. Wallahi duk ranar da za’a wayi gari bana doron ƙasa zaku yi dana sani, za kuma kusan mahimmancina. Zaku iya tafiya” A lokacin dai jikkunansu duk ya mutu, amman kowacce tana jaye ƴaƴanta suka shige ƙurya sai labari yasha banban. Wannan kyauta da malam ya furta bata cikin gado itace ta tayar da ƙayar baya, baƙin ciki da hassada ya shigo, musamman ga wadanda basu da damar cin tudu biyu. Haka bikin yaran gidan yaci gaba da matsowa, sai shirye_shirye aketa ta faman yi kowa ta ciki na cikinta. Yaya Tasi’u da matarshi Anty Badi’at ba zama, dan ita ta shiga cikin nijer ta siyo kayan gadajen Amare da kayan kitchen ita da Amaryar Malam. Kwana bakwai da Baba Magaji ya ba Gwadabe ta cika, Baba Magaji baice komai ba, shima Gwadabe yaƙi cewa komai, zuchiyarshi kullum cikin taraddadi take kawai, har aka tsunduma sha’anin biki dai Baba Magaji na kallon Gwadabe ya zuba mishi idanu.
To al’adar auren Maradi ya banbanta da al’adar aure a Najeriya ƙasar hausa. Su yanda suke bikinsu shine.
KAN GORO
Shi yanda ake yinshi shine. Iyayen Ango zasu tawo da goronsu a jarka za’a daddaleshi, yana danganta da yanayin karfin miji. Zasu tawo da balis ( Akwati) wasu suna zuba kaya a ciki, wasu kuma basa zubawa, zasu tawo da kuɗin sadaki, da hidimar girke_girke rigi_rigi.
Iyayen Amarya maza su kuma zasu zauna a manyan taburmai domin tarbar iyayen ango da wannan kaya. Iyaye mata a gida kuma zasu yi girki na alfarma a fito dashi. Anan za’a tsayar da lokacin Aure da bai haura wata guda ba, wasu ma sati guda ya danganta. To su dangin Ango zasu tafi da wannan gara ta dafaffen abinci tare da tsayayyen lokacin Aure.
LIFARAN
shi kuma lifaran ( Anko) ake nufi. Daga kawo wannan kayan aure da kuɗi. Dangin Ango, da dangin Amarya sai su fidda Ankon biki.
LALLE
Amarya zasu zauna zaman lalle na kwana biyu ita da ƙawayenta.
KUƊIN SIGA
Shi kuma kuɗin siga kuɗine da dangin Amarya suke hidima dashi ma dangin ango. Akwai kuɗi uwa ko kuma ai mata kaya, da su saitin bahuna, da turmin zani na goyo. Shi wannan setin bahunan da turmin zani ana bayarwane a matsayin an mayarma da uwa zanin goyo da bahunan wankan Ango lokacin da yake jariri, da sontolon tsaba duk na uwar miji.
Sai buhunhuna hatsi na gara bana wasa ba. Hatta facala in amarya na da shi akwai kudinta, kudin abokan ango na zirga_zirgar biki, sai buta da Dadduma, da jikka biyu na kudi na uban miji. Baki ƴan nesa kuma da suka tawo biki, ana zuba tsaba a roba da turamen zannuwa a basu. Su kuma sai su ba da jikka goma na uwar Amarya a matsayin tukuicin wannan hidima
ƊAURIN AURE.
Su kuma da safe akeyin ɗauri in dai na budurwane. Sannan ana fitarma da maza ƴan ɗaurin aure abinci waje aci asha a goge wuya.
WATSI
Wannan ɓangaren gidan ango ke yi.
Bayan isha ko bayan magriba za’a shinfiɗa tabarma a zaunar da ango a tsakiya. Ai ta mishi watsin cingom da kudi shima ya danganta da ƙarfin dangin ango, amman a wannan watsin ango na samun kudi ainun.
ƊAUKO AMARYA
Bayan an gama watsi kuma dangin Ango zasu je su ɗauko Amarya a kaita ɗakin mijinta.
Iyaye suna yin hidimar kayan ɗaki sosai, gado biyu suke yi, banda kafet_kafet da manyan daddumai.
YININ BIKI
Shima bikine rigi_rigi ake yinshi, sannan a yinin bikinnan suke sa anko dangin ango dana Amarya. Ayi yinin biki a watse shikenan biki kuma ya ƙare.
Daga cikin wannan sha’ani na biki babu wanda aka raga. A zahirin gaskiya an kashe kuɗaɗe sosai, duk wata hidima da akayi Tasi’u da matarshi ce suka gudanar da duk wani kashe kuɗi.
Gwadabe kuma a lokacin sha’anin bikinne ya karema ragowar ƴan matan gidan kallo tsab. A tsahirance sunfi Hadiza kyau ta fuskokinsu, sai dai ita kuma Hadiza ta fisu diri da kiba, dan shi kuma baya sha’awar mata sirara sam. Da wannan dalili nashi ne ya ƙudurce a ranshi da zaran an watse biiki zai tunkari Baba Magaji da batun Amincewarshi ga Hadiza. Ga Tamu ko da yaushe su kai waya yakan yi mishi tuni da batun ƙanwarshi da take zaman jiran Gwadaben. Harma sun yi waya sau biyu haka. Yanda ya ɗan taɓa hira da’ita sai yaji babu dai wata matsala a tattare da’ita ko na rashin tarbiyya, ko na fitsara irin ta wasu matan. Ƙarshen wayarshi da Tamu a cikin hidimar bikinnan yake cewa da Gwadabe.
“Gwadabe duk ɗan abinda ka rarumo na kudin moya kazo ayi aurennan kowa ya huta. Bara’u yace ya ɗauke maka sadaki. Ni kuma zanyi mata akwati da kaina. Aure kawai zaka zo a ɗaura, sabida manema sun soma damunta, duk da dai bata ƙarashe karatun ba amman ƙiris ya rage’ Jin wannan batu ne yasa Gwadabe kiran Bara’u yai mishi bayanin halin da yake ciki akan ɗiya da Baba Magaji ya bashi harma da kyautar wajen zama. Bara’u shi kuma ya tafi kafa da ƙafa har Habuja su kai magana da Tamu. Ya nuna ai wannan ba komai bane, Gwadabe mijin mace huɗu ne bama biyu ba. A take suka kirashi suka tsaida magana kan da zaran yarinyar ta gama karatunta za’ayi auren. Ƴan biyu dake hannun Tamu sai wayau suke yi, suna karatunsu hankali kwance. Ayashe tana riƙe dasu da amana ta game yaran da nata ta maishesu tamkar yaran data tsugunna ta haifa. Haka ma Toye yana zuwa makarantar boko data allo, suna zuwa gona yin noma. Dan Bara’u ya siya musu ƴar ƙaramar gona da yaron wajenshi, harma bana sun noma gyaɗa na kwano uku, da taimakon Sakina dake rakasu gona tana kuyi wannan ku bar wancan
Amare sun tare a gidajen mazajensu lafiya, hankalin iyaye ya dawo jikinsu kuma kowa ya ci gaba da sha’anin gabanshi. Wata ranar talata da daddare bayan su Gwadabe sun gama karatun dare sai ya nemi ganawa da Baba Magaji kan batun Hadiza. Dan yaga tun bayan da aka yi bikin gidan. Sai zawarawa suka shiga zurubtu akanta, suka shiga hidimar kashe mata kudi. Dan samarin nijar jaruman gaske ne akan matansu.
“Baba Magaji dama akan maganarmu ne da kai. Shine nace na zaɓi Hadiza kamar yadda kaima ka zaɓa mun tun farko. Sai dai akwai ƙanwar abokina Tamu da shi Tamun ya bani tun kafin in tawo nan ɗin. Shine nake tunanin in ka amince sai a haɗa tare ayi bikin lokaci guda. Tunda ita yarinyar kafin lokacin da aka kintata na bikin zata kammala karatun da take yi.” Ƙur Baba Magaji yayi yana kallonshi ya jima baice komai ba yanata jujjuya maganar Gwadabe a kanshi. Yana kuma hango irin gagarumar matsalar da ka iya bullowa. Wanda ada ita ya guda, sai gashi ta kuma biyoshi.
Bayan dogon nazari da Baba Magaji yayi sai yace.
“To Gwadabe naji duk bayaninka. Kuma na gode da nuna sonka da auren Hadiza. Wani hanzari ba gudu ba Gwadabe. Hadiza macace mai ɗan banzan kishi ainun. Kaga kishi? Shi ya hallaka igiyoyin aurenta na baya. Abinda yasa na soka da Hadiza, yarinyace mai biyayya batta da kishi dai. Nayi tunanin kuma ba lallai ka rakito wani auren nan kusa ba, duba da sana’ar taka ma da kake yi har yanzu baka da ido akanta. Kila ko da zaka yi auren sai nan gaba, kila a lokacin Hadiza ta zama babbar mace ka samu sassauci. Kaga mahaifiyarta ko? A lokacin dana auro Asshi sai da muka shafe tsawon shekaru biyu da rabi bata haɗa shinfiɗa dani ba. Kai ƙafarta bata sake taka turakata ba, har sai da santa yaimun lahanin da ya kusan rabani da rayuwata kafin. Gwadabe ina son Fhatsima fiye da yadda kake tunani, kuma ina matukar girmama duk lamarinta. Bata taɓa yin hayaniya ko musu dani ba.
Shawarar da zan baka shine. Kaje ka auri ƙanwar Tamu ɗin, ita kuma Hadiza Allah ya fito mata da wani mijin. Gudun kar zumunci ya taɓu dukkanku ƴaƴanane. Tashi kaje Allah yai maka albarka”.
Gwadabe yaso Baba Magaji ya bashi dama yace ko da wani abune. Amman sai ya ki bashi wannan damar haka dole ya tashi ya tafi. Kuma tsakani da Allah Hadiza ta kwanta mishi fiye da yanda ƙanwar Tamu ta kwanta mishi. Dukkansu a cikinsu baiga na ajjiyewa ba, abu suka haɗe mishi goma da ashirin, ga tunanin Iyabo wanda yake ɗamfare a zuchiyarshi babu dare bare rana. Da Hadiza yaci karo a zaure zata fita taci kwalliya da bakar lafaya ta zubo gashinta gaba. Murmushi ta sakar mishi da ganinshi. Shima yai mata murmushin tare da cewa.
“Sai ina da wannan kwalliyar kamar zaki gasar sarauniyar kyau?” Dariya kalaminshi suka bata, sai da ta dara kana tace.
“Sallama akeyi dani a waje Yaya. Bansan ma ko waye ba” Sai yaji nan nake kishi ya lulluɓeshi dan ai Gwadabe gwanine na ƴan kishi mun sani tun a baya. Ƙin magana yayi da yaga tana shirin wuceshi ne yace.
“Ke daga an aiko ana kiranki sai ki fito harda caɓa kwalliya haka? To maza ki koma Baba batai miki bayanin suna son haɗamu aure bane, ko ni dinne bakya so talaka?” A zabure ta ɗago ta kalleshi cikin maɗaukakin mamaki. Shi kuma yai tsai yana karantarta. A madadin yaga damuwa sai yaga akasin hakan. Dan bata san sanda ta kwashe da dariya ba, ta juya ta shige gida da sauri halamar dai itama fa tana ra’ayinshi yayi mata.
Kanshi ya dafe tare da jin haushin kanshi kan furta wannan kalma mai nauyi. Tsoronshi Allah, tsoronshi kar sanadiyyar aurensu zumunci ya taɓu. Dan ƙasan zuchiyarshi gurbin son iyabo ne, tsakiyar zuchiyarshi kuma na ƴaƴanta ne. Ko wacce irin macece zata rayu dashi sai dai ta rayu dashi a saman zuchiyarshi. Yana tsoron rashin adalci, yana tsoron fitinar mata biyu da rabe_raben kan ƴaƴa irin na gidan Baba Magaji. To wacece ta cancanta Gwadabe ya aura a cikin mata biyunnan? Wani shashe na zuchiyarshi yace.
“Ka ba ko wacce daga ciki lokaci ta fayyace maka irin sonta, a ciki sai ka zabi guda, guda kuma ka bata haƙuri. Cikin rashin tunanin abinda hakan ka iya haifarma ɗaya daga cikin matar da za’a ba hakuri Gwadabe yai na’am da shawarar zuchiyarshi ba tare da yayi hangen nesa ba. Wannan shi ake kira nama ya dahu romo ɗanye.
Nan Gwadabe ya raba lokacin shi ta hanyar rabashi a tsakanin Hadiza, da Shafa, Hadiza suna keɓewa suyi zance, yayin da Shafa kuma yake kiran wayarta su sha hira. Yana auna kalaman ko wacce a zuchiyarshi, yana nazari dan gano wacce tafi sonshi da nuna tausayinshi. Tun Baba Magaji bai san Gwadabe na zance da Hadiza ba har mata suka tsegunta mishi. Kuma Baba Fhatsima, da yaya Tasi’u, harma da su Auwala sun aminta da wannan haɗin kuma sun yi farin ciki sosai. Baba Magaji ranar yaso su tattauna da Baba Fhatsima akan batun Hadizan da Gwadabe, kasancewar ranar ita ke da miji.
“Fhatsima naga kamar Hadiza ta amince da soyayyar Gwadabe ko?” Ya jefo mata tambayar yana daga kwance, ita kuma tana kasa a zaune tana dama mishi furar da duk daren duniya sai ya sha kafin ya kwanta.
” Kwarai ko. Nima kuma na daɗa ƙarfafarta naga Gwadabe yana da hankali.” Kai Baba Magaji ya gyaɗa yace.
“Hmm Hadiza kenan. To abinda ta guda a gidan uban yaranta shine ya sake biyota. Kishiya ba? Dan abokin Gwadabe Tamu ya riga ni ba Gwadabe ƙaunarshi, kuma ya riga ya karɓa tun kafin yazoshi. Ni da naso dakatar dashi neman Hadiza dan harna sanar dashi dalilin mutuwar aurenta na baya. Amman bamu san me Allah yake son nunawa ba akan hakan, ƙila wata ayar zai saukarma mata masu kaso aurensu sabida kishiya. Allah ya daidaita tsakaninsu” Shiru Baba Fhatsima tayi kawai. Furar da take damawa ta dakatar da damata. Lokaci guda ta jagule. Hakan yai sababin sawa Baba Magaji ya mike zaune ya sakko ƙasa daf da’ita. Yayi ƙasa da muryarshi yace.
“Fhatsima kiyi haƙuri a bisa kalamina. Allah ya sani ba dake nake yi ba, da ita Hadiza nake yi. Amman kiyi haƙuri”
“Hmm Malam kenan. Ashe nuna kishi ga abinda kake so matsalane a wajen maza mu bamu sani ba? Tunda nake kishina a gidannan tsawon shekaru fin talatin ka taɓa kamani ina shirka, ko na taɓa tayar maka da hankali ne?
Ai ko Hadiza batai kishi na hauka a gidan mijinta ba. Allah yayi ƙarewar aurenne dan ku maza in kuka auro wata macen kukan juyama wata baya na wani lokaci kafin ku gama shan romonta. Abunda Hadiza bata da ilimi akai kenan shi yasa aurenta ya mutu a wannan gaɓar. Amman Nagode da wannan furuci naka” Ta ƙarashe maganar tana shessheƙar kuka mikewa tsaye tayi tana shirin barin ɗakin. Malam yayi carab ya cafe hannunta. Tayi sauri ta runtse idanunta tare da fashewa da wani irin kuka mai ɗaci. A wannan daren Baba Magaji ya sha rarrashi da ban baki. Dan har kuɗi ya debo da baisan iyakarshi ba ya bata da safe kafin ta koma ɓarayinta.
A haka soyayyar Gwadabe da ƴan matanshi biyu taci gaba da kasancewa. Ko wacce cikinsu na ƙoƙarin ganin ta nuna bajintarta. Danma ba wacce ta san da zaman ƴar uwarta, iyaye sun bar zancan a tsakaninsu. Domin shi Baba Magaji a ganinshi Gwadabe ai bazai haɗe mata biyu a lokacin guda ya aura ba, dole da ɗaya za’a soma.
Ta ɓangaren neman Gwadabe kuwa, Allah yasanya mishi albarka a harkar neman. Dan yana da ido sosai na ganin zinariya. A zuwanshi har ya samu zinariya sau biyu, kuma ba laifi madaidaita ne. Hakanne ya bashi damar yi ma Babala aike, ita da Bara’u abokinshi na amana.
Da yamma lis yau su Gwadabe suka shigo gidan, sun shawo gajiya sosai. Harda ƴar ledar kayan kwalliya a hannun Gwadabe. Ɓarayinsu suka wuce dai kamar kullum, sai da su kai wanka suka sake kayan jikinsu. Yayi daidai da lokacin Sallah sai suka wuce kofar gida dan gabatar da sallah.
Ta ɓangaren Hadiza kuma tayi kwalliyarta me ƙayatarwa sai ƙamshi take faman zabgawa, ga abinci ta ajjiye da kwanukan zubawa, shigowar su Gwadabe kawai take jira. Baba Fhatsima kuma tana zaune daga gefe tana jin wani shiri da ake gabatarwa a gidan rediyo hankalinta yana wajen shirin. Amman idanunta na kan Hadiza wacce tun ɗazu sai gyare_gyaren gashin kanta data bazoshi ya sauka kafaɗarta take yi. Irin wannan ganɗoki ko a aurenta na fari ma bata yishi ba, duk da shima wancan auren Malam ne ya haɗashi almajirinshi ne mijin.
“Hadiza sai nake ganin kamar kin zafafa soyayyar da kike ma Gwadabe. Kibi a hankali kinsan halin maza da karya ma mace zuchiya. Ƙila ma bake kaɗai bace a ranshi” Ƙur ta zuba mata idanu tana karantar yanayinta, dama ta soko zancanne taji irin amsar da zata bata. Dan tana son auna kishinta da Malam yake ta ikirarin ita ta biyo”
Ƙasa tayi da kanta, lokaci guda sai ta jagule har idanunta ya kawo ruwan hawaye.
“Baba abinda ya faru a baya kuskurene wanda bana mafarkin ya sake faruwa dani a gaba. Nasan an yi mun laifi, amman nima na nuna rashin hakurina ƙarara. Wallahi a lokacin da Tsalha ya dinga nuna mun ni ba cikakkiyar mace bace, sai da yayi amarya ya gane kanshi. Banyi tunanin a daren zan rayu ba, wani abune yake dannemun harshena izuwa moƙoshina. Baba ina da kishi mai yawa, anata cewa wai ke na biyo. Ni kuma in sha Allah zanyi koyi da salon kishinki, da dabarun kissarki ta hanyar gina babban matsayi a zuchiyar Gwadabe. Ta yadda ko mata ɗari zai auro bai isa ya haɗemu a matsayin abu guda ba” Kuka ta fashe dashi mai ciwo.
MRS BUKHARI
Part 4

NAMA YA DAHU…
ROMO ƊANYE
LITTAFI NA BIYU
4
Baba Fhatsima ta dubeta a tsanake tace.
“Shikenan ni da kaina zan kwatanta miki yada zaki zauna daram ki wuce wulaƙanci a zuchiyar ɗa namiji. Hadiza a lokacin da Malam yace zai ƙaro aure sai da na kwanta jinya. Amman sabida kirsa irin tamu ta mata ni na haɗa akwatin da Malam ya kaima Asshi. Kuɗin dana samu a hannun malam bana wasa bane. Zuchiya kullum ciwo da zafi suke yi mun Hadiza. Wallahi inna kalli Malam sai inji kamar in ɗura mishi zagi. Amman wallahi ko ɓacin rai baya iya ganewa a fuskata. Horon da nayi mishi na ƙauracema shinfiɗarshine, tunda ya raina iyawata, sai da nasa da kanshi ya gane mahimmancina da kuma banbancina. Duk da ina fishi dashi, saina dukufa shan magunguna ingantattu, musamman tukuɗi da gumbar matan Kanuri da tsuminsu, da shayin su na musamman. Na dinga gyaran kaina dan sake kankaro mutuncin kaina. Ni kishina bana ayi zagi ko bankaura bane. Da duk tsufana Malam har gobe yana mararina Hadiza.
Sallamar su Gwadabe ce ta katse wannan tattaunawa wanda nasan ba Hadiza kaɗai ke karuwa da’ita ba, harda masu karatu. Saurin share hawayenta tayi, wanda karab a idanun Gwadabe.
“Baba yinwa” Cewar Auwala wanda baya jurar yinwa. Dariya duk aka saka mishi. Baba Fhatsima tace.
“Ai kai wacce zata aureka ba zaka barta ta huta da ɗaura sanwa ba” Saida ya cusa tuwo loma babba a bakinshi, tun kafin Mammada ya gama zuba musu, kana yace.
“Tabb ai ni tun da jimawa tasan Yaya nake. Kullum naje saita kawo mun shayi da cukui, wataran harda abinci fa.” Mammada yace.
“Bayan uban abincin da kake take cikinka dashi kafin ka tafi? Shi yasa cikinka kullum yake ƙara girma. Baba yau daya zarme rijiyar haƙon zinariya da ƙyar aka zaroshi tsabar ƙiba fa” Duka Auwala ya kai mishi, yai maza ya matsa kusa da Gwadabe wanda shi kuma hankalinshi na kan gimbiya Hadiza da yaga tana cikin rashin walwala. Baba Fhatsima tayi Dariya tace.
“Duk ai ya kusa karewa gini kam gobe za’a soma an kawo bulo da yashi, an yi ginshiƙi. Aikin ba wani daɗewa zaiyi ba tunda an riga da an tanaji kudin aikin. Duk kuyi aurenku nima na huta” Gwadabe yace.
“Ai Baba kila fa Auwala ya dinga zamowa cin abinci ɗakinki, baya zage ya kwashi girki a gaban Amarya haka ba” haka dai sukaita raha a tsakaninsu kamar yadda suka saba a koda yaushe. Ana cikin haka Yaya Tasi’u shima ya shigo akayi hirar dashi. Kiran sallar isha ne ya fasa taron. Da Gwadabe ya tashi fita sai ya ajjiye ledar kayan kwalliyar da ya siyo ma Hadiza a gefen ƙafarta ya fita.
“Tashi kiyi Sallah kafin Gwadabe ya kiraki zance, dan zancanku ba ɗaga ƙafa. Yaran zamani kome kuke cewa in kunje wajen zancen oho. Zance ai sai su Ine yanzu dai duk ya ƙare.” Hadiza tayi murmushi tace.
“Gobe ma mu kayi da Anty Badi’a zamu je gidajensu mu ganosu, tun bayan biki mu ta ɓangarenmu babu wanda yaje. Shekaran jiya Sauma’iyya suka je gidan Hafsatu.”
“Daga gidan mijinta taje, ke yaya akayi kika san taje? Tsegumi” Dariya Hadiza tayi tace.
“Baba asshi ce naji tana faɗama Amaryar Malam. Wai Hafsatu ta aiko mata da kuɗi harda soyayyun zabbi” Harara Baba Fhatsima ta doka ma Hadiza ba shiri ta tada kabbarar sallah. Dan babu abinda Baba Fhatsima ta tsana irin gutsiri tsoma” Hadiza tana kan sallayar bata tashi ba Gwadabe ya aiki yaron Amaryar Malam yayi kiranta. Sai da ta kuma gyare_gyaren kwalliyarta kafin ta fita. Baba Fhatsima tana jimantama Hadiza ranar da zata ji labarin bada ita kaɗai Gwadabe yake soyayya ba, kuma akwai yiwuwar ba ma ita kaɗai zai aura ba. Ko da ba’a hade bikin ba, tasan babu wani nisa a tsakani.
Fitowa tayi tsakar gidan tana busa ƙamshi. Amaryar Malam da taci kwalliyarta na zuwa turaka ta bushe da dariya, dama can basa shiri sam da Hadiza. Dan bama su wuce sa’anni ba. Ko kallonsu batayi ba. Harfa ta sha kwanar ɓarayin su Gwadabe ta jiyo Baba Asshi na cewa da Suwaiba.
“Sabida tsabar tayi bandarine fa Malam ya tafi ya ɗauko ɗan ƙanwarshi dan ya haɗasu. Ƙanwar tashi ma da bata da mutunci. Ni dai na gode Allah in Fhatsima ta fini da soyayyar miji, da ɗa mai arziki. Bata fini a surukai ba. Dan masu arzikin gaske ƴaƴana suke aure. Itako Hadiza gidan da za’a sakata ubanta nema ya bayar” karab a kunnen Hadiza, karab kuma a kunnen Baba Fhatsima. Dukkansu kai suka girgiza kawai. Hadiza tayi shigewarta ciki. A bakin dakalin ƙofar ɗakinsu yake zaune. Ga hasken lantarki tanwar ya haske ko’ina. Gardawan malam su biyar suna wajen suna wankin suturunsu, sai Sabitu dake tsaye a ƙofar ɗakinsu kawai dan babu dai Abinda yake yi. Kwana biyunanne ya tsiri yin hakan a daidai lokacin da Gwadabe zai fito ya zauna domun ganawa da Hadiza. Tun daga nesa Gwadabe yake ƙarema Hadiza kallo. Zani daya gani ɗaure a jikinta sai yake ganin kamar iyabo ce ke tawowa, dan Iyabo ta ƙware wajen iya ɗaurin zani sosai, takanyi matuƙar kyau da zani, ƙibarta na daga cikin abinda ke sa ruhinshi ke fisgarshi akan son Iyabo. Isowar Hadiza ce tasa ya dawo hayyacinshi. Zama tayi gefenshi sosai.
“Barkanka da wannan lokacin angon Hadiza mujin mace ɗaya tilo.” Murmushi yayi mata kawai, a kullum in ta kirashi da mijin mace ɗaya tilo sai yaji faɗuwar gaba, haka ƙanwar tamu take yawan ce mishi.
“Mijina ni ni kaɗai. Babu wata mace data isa ta rabeka” Da sunyi mishi irin furucinnan sai yaji hankalinshi ya tashi a madadin ya samu nutsuwar kalaminsu. Anya bai cutar da zukatan ƴan matan ba kuwa, lokaci baiyi da zai bayyana musu gaskiya ba kuwa? To wai in ya zayyana musu gaskiya du suka gujeshi ya zaiyi da kunyar waɗanda yake ganin darajarsu a jikin ƴan matan? In kuma suka ritsashi suka ce sai dai ya zaɓi ɗaya, Yaya wacce aka ce tayi haƙuri zata yi? Haƙiƙa yayi kuskure mafi girma da rinjaye, awannan tunanin kamata yayi tun farko zaiyi shi, ba yanzu da wankin hula ya riga ya kaishi dare ba.”
“Wai tunanin me kake yi ne Yaya tun ɗazu inata magana fa, bakace komai ba” Ya tsinkayi shagwaɓaɓɓiyar Muryar Hadiza, wanda tasa saida tsigar jikinshi ta tashi, dan wannan yana daga cikin sabon salon da take son fitowa dashi dan mallakar zuchiyar Gwadabe.
“Akwai muhimmiyar maganar da nake son mu yi ni dake. Hadiza banaso ki fassarani da ko wacce iriyar mummunar fassara, ina cikin tsaka mai wuyar fita ne, abinda yasa abinda ya faru ya farun kenan.” Shiru tayi tana kallonshi da ƙananun idanunta waɗanda gashi sukaima rumfa. Bayan ta ja numfashi na daƙiƙa sai tace.
“Ina saurarenka, zanyi maka shari’ar gaskiya da gaskiya. Faɗamun matsalar dan tuni fuskarka ta nuna matsala zaka faɗa mun” Shiru yayi yana shafan sumarshi kanshi.
“Hadiza ba da ke kaɗai nake soyayya ba. Akwai ƙanwar abokina Tamu da ya bani tun kafin in tawo Nijer ” Darara dam_dam_dam gabanta yai mummunan tsinkewar daya tunkudo ruwan hawaye nan take suka soma shatata a idanunta. Duk da haka tace.
“Dan Allah kace dani wasane, kar kayi amfani da kishin da akace maka shi yai sanadiyyar mutuwan aurena ya zamema logo. Na roƙeka karka yaudari zuchiyar data saba da rayuwa da sonka.” Take hankalin Gwadabe ya kai ƙololuwar tashi, dan bai taɓa tunanin Hadiza zata ɗauki wannan lamarin a yanda ta ɗauka yanzu ba. Da ƙyar ya samu kuzarin ce Mata.
“Wallahi da gaske nake yi Hadiza. Kafin in tawo nan na riga dana amshi soyayyarta. To kuma da nazo nan sai Baba Magaji yace in zaɓi mace a cikin ƴaƴanshi in aura, amman sai yace yafi mun sha’awarki”
“Kenan ba sona kake yi ba, Malam kai ma biyayya? Shikenan ni na hakura kaje ka aureta” Tana gama faɗar haka ta mike fu ta bar barayin. Yayi yinƙurin tareta sai Auwala da shigowarshi barayin kenan ta gefenshi ma Hadiza ta raba ya dakatar da Gwadabe bisa dole ya tsaya.”
“Koma me ya haɗaku kyaleta ta huce, su mata a cikin irin wannan halin baka iyawa dasu sam.” Ajjiyar zuchiya Gwadabe ya sauke tare da lumshe idanunshi.
“Auwala laifi nayi mata. Tana da dalilin yin fishi dani. Laifinane, dan Allah ka bita ka bata baki a madadina”
“To wannan ma dabarace. Kai jeka bari in shawo maka kanta ka koma ciki ka jirani.”
Gwadabe na shiga ɗaki kiran Shafa na shigowa wayarshi. Jiki a mace ya ɗaga wayar, itama yayi mata duk bayanin da yaima Hadiza. Ƙit ta kashe wayarta, ko da ya kuma kira sai yaji a kashe ma wayar baki ɗaya. Dafe kanshi yayi bakinshi na ɗaci, damuwa duk ta haɗu ta dameshi.
Hadiza.
Da sauri ta shiga ɗakinsu har tana cin karo da Ine wacce suke shirin fita ita da mijinta sun kawo ma Baba Fhatsima ziyara irin ta godiya da angwaye suke yi.
Ganin mijin ƙanwarta yasa tai saurin share hawayen dake bin gefen fuskarta.
“Ango ka sha ƙamshi kune a tafe da daddarennan? Mu da muke shirin kawo muku ziyara”
A ladabce ya gaishe da Hadiza yana yi yana sosa kanshi.
“In kin gama kya same ni a waje ni kam” Yace da Ine wanda hankalinta yake kan Hadiza.
“Yaya Hadiza nifa fishi nake yi wallahi. Tunda kuka kaini ba wanda ya sake leƙoni ma” Ta faɗa a karaye yayinda Hadiza take kallonta da halamar tuhuma. Ganin hawaye na neman ɓallewa a idanun ƙanwar tata ne ya tabbbatar mata tana cikin damuwa, ko kuma kewar gida.”
“Ki sha kuruminki dama gobe zamu je gidanki ni da Anty Badi’a. Yanzu dai kije ki samu mijinki karki barshi yaita jira” Ine tace.
“Bamu shiga cikin gidanba ma, yanzu dai zamu zazzagaya, amman munje ɓarayin su Yaya Tasi’u.” Fitarta shigowar Auwala yana kwaɗama Hadiza dake shirin zama kira.
Shigowa yayi ranshi a matuƙar ɓace.
“Ke meye ya haɗaki da Gwadabe, da har yake kiranki kina ƙin tsaiwa? Ki sani wanki ne Gwadabe, kuma mahaifiyarshi ƙauna take ga Malam.” Hadiza najin wannan sababi na Auwala sai ta saki rushin kuka tana faɗin
“Ni wallahi na fasa auren. Yaje can ya auri ƙanwar abokinshi. Ai ba sona yake yi ba. Malam ne ya cusani wajenshi” Duka Auwala ya kawo mata. Baba Fhatsima dake zaune tana kallonsu tace.
“Bita a hankali Auwala. Zo zauna inji meke faruwa haka uhm?” Zama Auwala yayi a ƙasa, yana dokama Hafiza harara.
“Ki buɗe baki kiyi mun bayani Hadiza. Menene ya haɗaki da yaiyen naki?” Hadiza ta kwashe yanda Gwadabe ya faɗa mata ta sanar ma Baba Fhatsima. Tsaki dogo Auwala ya ja yace.
“Ni nama ɗauka wani muhimmin abune yanda naga Gwadabe duk ya damu. To sai me dan ba da ke kaɗai yake soyayya ba, dama cewa akayi dan ke aka halicci Gwadabe ke ke kaɗai?
Baba kinji fa abinda take cewa, wannan baƙin kishin nata ne yasa ta tsallake yaranta ta dawo gida. Tana da aiki ja matsawar irin wannan ƙazamin kishin bai fita a ranta ba.” Shiru Baba Fhatsima tayi, tana sauraren ɓaɓatun Auwala, da sautin kukan Hadiza. Ajjiyar zuchiya ta sauke kana tace.
“Hadiza kina nufin ba zaki taɓa zama da kishiya ba ko me kike nufi? Bar ganin ina goyon bayanki Hadiza, ai in dai wai ke bazaki zauna da kishiya bane, to ya fiye miki sauƙi ki ƙare rayuwarki a gidan mahaifinki. Dani da Malam mun san bake kaɗai Gwadabe yake nema ba, kuma a haka muka ji yafi miki ki aureshi. Dan Gwadabe yarone mai hankali da kunya. Ke dai kiyi fatan kasancewa uwar gida a gidanshi kawai. Kai Auwala tashi yi tafiyarka, ka kuma cema Gwadabe ya kwantar da hankalinshi Hadiza mu muka bashi ita, duk duniya in banda ƙaddara babu wanda ya isa soke batun aurennan. ” Tashi Auwala yayi ya dubi Hadiza yace.
“Yara basu ajjiye komai ba sai sakarci. Ni zan so ma Malam ya soma aura mishi waccan ɗin kafin ita. Gashi ita ƴar birni wayayya da’ita, kuma hankalinshi take janyewa sosai. Maza ki tsaya kallon ruwa kwaɗo yayi miki ƙafa” Baba Fhatsima ta daki ƙafafun Auwala dake son tunzura Hadiza.
“Ja’irin yaro, fice ka bamu waje” Ta faɗa cikin sigar wasa, fita yayi yana sake kambaba yanda budurwar Gwadabe take kulawa dashi a waya. Kuma duk dan ya tunzura zuchiyar Hadiza ne. Ai kuwa yaci nasara dan take zazzaɓi me zafi ya luluɓeta, sai hawaye idanunta yake fitarwa” Harara Baba Fhatsima ta doka mata tare da cewa.
“Shashasha maza dai ya gane kishi shine logonki kiga in baki faɗi ƙasa warwas ba. Ba’a ƙarin aure ni Malam yayi mun har kishiyoyi uku? Da banyi haƙuri ba ke kina ganin zan kai haka ne? Ai mace a gidan aure da jarumta akeson ganinta Hadiza. Dan Gwadabe ba ke kaɗai yake nema ba, ba hujja bace na cewa ke kin fasa aurenshi ba. Ai kina gani a cikin gidannan dama dariya suke yi ta mana. Ko baki ji Abinda suke cewa bane ɗazu da zaki je wajen Gwadaben? Ai kinji sarai. Maza dai ki ma kan ki shaidar da babu me iya goge miki ita na zafin kishi. Ni kinga tafiyata Malam na son ganinmu dukka a turakarshi, Allah dai yasa lafiya. Dan malam bai fiye haɗe kan matanshi ya tattauna dasu baki ɗaya ba, yafi gane ya tattauna da kowacce ranar girkinta” Tana gama faɗar haka ta sa kai ta fice ta bar Hadiza da jinyar zuchiya. Yayinda maganganun Auwala suka shiga yi mata amsa kuuwa.
“Ni inata wahalar da kaina na son ganin na burgeshi. Sai gashi ashe wata a waya kawai take jaye mai hankalinshi. Ni Hadiza zan iya zaman kishi a karo na biyu kuwa? Wallahi nasan mata ƴan uwana da yawa ba zasui mun uziri ba
Wasu ma zagina zasu yi. Amman Ubangijin da yayi ni, ya yiku. Shi ya banbanta zuchiyiyoyinmu. Wata abinda tata zuchiyar ta ɗauke, wata in akace sai zuchiyarta ta ɗauke wallahi mutuwa za tayi. Ni Hadiza macece mai mugun kishi mai zafi, nifa ko baiwace na fi son ace tawace ni kaɗai babu mai irinta. Kishi ni shine raunina nasan ko wacce mace da irin rauninta.”
Baba Fhatsima”
Lallai hausawa sun yi gaskiya da suke cewa magaji mafiyi. Ita kanta Baba Fhatsima tana mamakin yanda Hadiza ta xama kwafinta a kishi. Komansu iri ɗaya ne ta ɓangaren kishi babu inda ta barota saima finta da tayi. Ita kanta da ba dan ta kai zuchiyarta nesa ba, da kuma tunanin goben yaranta ba, da a lokacin da malam zai ƙaro Aure da tuni ta bar auren kwata_kwata. Har gobe zuchiyata tana azabtuwa ainun da zaman kishin da Malam ya haɗata yi da sauran matanshi. Duk da tasan cewar ita da Tasi’u sune fitulun dake haska gidan malam, hakan bai hanata kishi ba. Iya rigima Malam yake kiranta a duk sanda ta murɗa kambun kishinta ta juya mishi baya.
Ajjiyar zuchiya ta sauke a daidai shigarta ɓarayin da turakar Malam take. A zuchiyarta take roƙama Hadiza Allah ya bata haƙuri da juriya. Ɗayar zuchiyar tata tana cike da tausayin Hadiza a bisa dakon nauyin kishi da zata ɗauka na iya tsawon rayuwar duniyarta.
Da sallama ta shiga falon na malam, yana zaune a kujera mai cin mutum uku Amaryar Malam tana gefenshi tana kiciniyar cire mishi babbar rigarshi. Baba Fhatsima ta haɗiye wani yawu mai kauri, tare da yin wuf ta yi ƙasa da idandunanta. Kunya da nauyin Fhatsima suka kama malam. Cikin dibibicewar data mugun ƙular da Amaryar Malam yace.
“Uwar gida sarautar mata, farar mace alkyabbar mata, zo ki zauna Fatsima” Ɗan siririn ɓoyayyen tsakin da a iya kunnen Baba Fhatsima ya sauka Amaryar Malam tayi. Kujerar gabaki ɗaya ta sauka ta barma malam da Baba Fhatsima, ta koma kujera mai cin mutum guda ta kumbura tai suntum. Murmushin takaici Baba Fhatsima tayi, a zuchiyarta tace.
“In banda maza da faɗuwar girma ni Fatsima da yaushe zan haɗa gado da yarinya ƴar cikina? Amman su maza basa ko jin kunya, da nauyin manyan yaransu. Wacce iriyar taɓarace Malam bai yi ba lokacin da ludayin Amaryarshi ke kan dawo? Murmushi ta kuma yi mai cike da fassarori da dama.
“amarya ina ganin sai kin tashi kin kirawo mun Asshi, da Suwaiba Lokaci yana ƙurewa ya kamata ace sun hallara” Ba dan ranta yaso ba ta fita ta bar Malam daga shi sai Baba Fhatsima ba. Tana fita Malam ya dubeta yace.
“Fatsima bakya tsufa ke dai. Wazai ga Tasi’u yace ke kika haifeshi?”
“Hmm Malam Baka rabo da daɗin baki, koma kince borin kunya” Da Malam da ita da tai maganar suka kwashe da Dariya. Shi yana dariyar yanda akayi ta ɗagoshi. Ita tana mai dariyar kaji kunya. A haka matan Malam suka shigo suka iskesu.
“Au aini naga kamar Amaryar Malam itace da girki ko? In ba ɓatan lissafi nayi ba. Ta faɗa tana kallon Amaryar Malam data cika tana shirin fashewa. Suwaiba ta taɓe bakinta tace.
“Girkinta ne, kin mance ita ta wuni tana hidimar yara?” Malam ne ya dakatar dasu ta hanyar cewa.
“Yanzu zaku zauna kuji dalilin kiranne ko kuwa zaku tsaya bin ƙididdigar waye me kwana waye marar kwana ne. Wai shin me yasa ke Asshi baki da aikin daya shige na ta da tarzoma ko da yaushe?” Zama ko wacce tayi a kujera. Amaryar Malam ta je ta zauna a kusa daf da Malam. Bai dai ce da’ita uffan ba. Takaddu dunkulallu ya ciro daga aljihun rigarshi ya zube a ƙasa.
“Ko wacce ta ɗauki ɗaya ta riƙe a hannunta kafin in gama bayani sai ku buɗe. Sai da kowacce cikinsu ta ɗauka sannan Baba Fhatsima ta ɗauka a ƙarshe. Malam yace.
“To wannan ƙuri’ace nayi muku kamar dai yadda nake yi a ko wacce tafiya in ta taso mun. Kuma tunda nake yin wannan ƙuri’ar duk wacce ta ɗauki tafiya bana sakewa da’ita nake tafiya. To a wannan karonma wata tafiyace ta taso babba a gabana ta banbanta da duk tafiye_tafiyen dana saba yi a baya. Naba ko wacce dama ta buɗe takaddarta duk wacce ta ɗauki tafiya to Allah ya ciyar da’ita. Sannan ku sani babu zalunci ko son kai a cikin wannan lamarin Allah shine shaidata. Bismillah ko wacce ta buɗe.
Nan da nan ko wacce ta shiga kiciniyar buɗe takaddarta tare da zabarin ganin ta ɗauki tafiya
Domin tafiya da malam ana samu alkhairi sosai, kuma macce tana samun lokacin kanta dana mijin nata, soyayya ake darza tsantsa. Cikin sa’a Baba Fhatsima ta samu tafiya. Har cikin ƙasan ranta tayi farin ciki sosai, dan ta jima sosai rabon da ta samu damar tafiya tare da Malam. Kuma a halin yanzu tana cikin yarda dashi. Baba Asshi tafiyar da yayi na ƙarshe wacce ba’ayi wata ba sai yanzu, tare da’ita akaje. Amaryar Malam kuwa sai da ta samu takaddar tafiya sau huɗu a jere ras, Suwaiba ta samu sau biyu a tare. Wannan karon kuma Allah ya ciyar da Baba Fhatsima.
“Malam nice na samu tafiya” Bai san sanda murmushi ya subce mishi, farin ciki ya bayyana s fuskarshi ba. Malam har tsaiwar dare yayi kan Allah ya dafa mishi Baba Fhatsima ta samu wannan takadda ta aminci. Kawar da kai Baba Asshi tayi gefe, tare da taɓe bakinta. Malam kuwa yace.
“Masha Allah dama kina da paspo ta kwana gidan sauƙi sabida haka ki soma shirin keta hazo” murmushi Baba Fhatsima tayi mai cike da danƙararriyar soyayyar Malam da take ta farfaɗowa.
“Allah ya nuna mana lokacin malam. In ka bani dama sai in koma ɓarayina” Kai ya gyaɗa.
“Ki isa cikin aminci Fatsima uwar gida ran gida” Ai fitar Baba Fhatsima sai tarzoma ta tashi, daga ƙarshe dai fatattakarsu Malam yayi. Amaryar Malam dake da kwana itama ta bisu tana kuka wai ta yafe kwanan ma baki ɗaya.
A wannan daren zukata da yawa a cikin tunani suka kwana, ko wanne da abunda yake tubkewa da warwarewa haka garin ya waye kamar yadda aka saba.
Gwadabe:.
Tun asuba yake kiran wayar Shafa amman wayar har zuwa lokacin a rufe take. Gashi yana son zuwa ganin Hadiza yaga ya ta kwana. Duk da Auwala ya kwantar mishi da hankali a daren jiya.
Tashi yayi jiki a saɓule ya nufi cikin gidan. Yau matan Malam babu wanda ya amsa gaisuwar su Auwala ma balle kuma Gwadabe wanda yazo dandalar arziki. Sai Baba Fhatsima ce dake zaune a dokin ƙofa tana siyan lalle da gishirin lalle akan wata yarinya tace.
“Gwadabe yau makara kayi ne sai yanzu ka samu shigowa?” Da biyayya ya zube ya gaisheta, ta amsa cike da fara’a.
“Ka shiga Hadiza na ciki, da zazzaɓi ta kwana, likita ma Matar wanku zata kaita” Kai ya kuma saukewa harda sosa kanshi.
“Subhanallaah Allah ya bata lafiya, bari in dubata” Ya faɗa da kunya. Shiga yayi ya samu Hadiza a zaune tana shan kunu. Ƙurama juna idanu su kayi na daƙiƙu. Ita ta rigashi sauke ido.
“Ina kwana Yaya Gwadabe?” Bai samu damar amsawa ba, waje ya samu ya zauna a ƙasa ƙur idanshi a kanta.
“Ina roƙon Allah yasa ba maganata ta jiya bace sanadiyyar ciwonnan naki ba Hadiza?” Bai jira ta amsa shi ba dan bai tambayeta yana nufin saita amsaba ya ɗaura da faɗin.
“Wallahi ba dan Baba magaji ya tozartaki ko ya ƙasƙantar da darajarki bane yasa yai miki zaɓin Gwadabe ba. Nima ba dan tayin da yaimun bane yasa na amsheki ba face kin yi mun kuma naji zan iya rayuwar aure dake. Yanayinki da zubinki yana mun kama da na matata Iyabo sosai. Ki fahimceni auren zumunci cike yake da tarin hikimomi.
Itama fa bawai ina nufin bana sonta bane A’a itama inai mata kalar nata son daban. Hatta tsohuwar matata gurbinta shine a ƙasan zuchiyata. Ki kwantar da hankalinki kinji?” Tunda ya soma magana zuchiyarta ke lugude. Musamman da taji matsayin da Iyabo ta wawashe a rayuwar Gwadabe.
Sai Allah ya sadamu ranar Monday da izinin Allah danjin yadda zata kaya.
Ki faɗi abinda kika ɗauka na darasi a wannan labarin duk da bamu yi nisa ba.
Part 5
NAMA YA DAHU..
ROMO ƊANYE
BOOK 2
5
Assalamu Alaikum barkanmu da juma’a. Iyabo tana godiya a bisa karɓar labarinta da kukayi hannu bibbiyu
Lokaci ɗaya taji kishin Iyabo ya soki murfin zuchiyarta fiye da kishin wacce za a haɗasu zaman kishin na gasken_gasken.
Bata sami zarafin furta mishi kalma ba Auwala da Anty Badi’a suka shigo a tare.
“Hadiza in kin shirya muje Yayanku ya rage mana hanya ko?.”
” to”
Ta furta tana kallon Gwadabe, wani irin kallo daya kasa fahimtar fassararshi.
A kunyace ya gaishe da Anty Badi’a, ta amsa cike da kulawa.
“Gwadabe maza muje Mammada na jiranmu kasan fa yau muna da aiki.” Cewar Auwala kenan. Kafin ma ya miƙe Malam Magaji ya iso dokin kofar yana faɗin.
“Yarannan har yanzu basu wuce aikin ba, Auwala me kuke yi a ƙunshe a ƙurya haka?” Da sauri suka fito, sumi_sumi sukai ma iyayen sallama suka fice a gidan. Cikin sa’a Gwadabe ya gwada sake kiran layin Shafa ya samu a buɗe. Sai dai harta gama kuka ta tsinke ba a ɗaga ba. Yana sauke wayar a kunnenshi sai ga kiran Tamu ya shigo.
“Abokina yau kaine da kira sassafe haka, ya kwanan iyalin kuma?’ Cewar Gwadabe daya tari numfashin abokin nashi ta hanyar rigashi magana. Ajjiyar zuchiya ya sauke yace.
“Tun jiya Ayashe ta sanar dani Shafa nata faman kuka ta kulle kanta a ɗaki. Ko da aka wayi safiyar yau taƙi cin abinci, taƙi zuwa wajen aiki. Shine nasa ita Ayashe tai kiranta dan inji menene. To ta dai ƙi yin magana ma, bansan ko kana da masaniya akan kukan ba, kasan yarannan fa da zafafawa akan soyayya, dan naga ta ɗauki lamarinka da girma. Kasan mata da surutu ina jin labaranka sosai ta bakin Ayashe” Jim Gwadabe yayi kawai yana mamakin halin da Shafa da Hadiza suka shiga a kanshi, ya ɗan shafo ɗan siririn hancinshi tare da shiga zancan zuchi.
“Ohh ni Gwadabe ni ba kyau mai suna kyau ba, ni ba tsayi ba, ga tumbi, ga ƙaton kai. Amman akaina waɗannan matan suke shiga damuwa haka? Dama_dama Iyabo na cancanci ta soni, duba da yanda tasha naci a wajena, da irin yanda na jajirce kan soyayyarta. Amman waɗannan haɗani dasu dukka akayi, bawai ni nace ina sonsu ba.”
“Kana jina kayi banza dani Gwadabe ko network ne, ko ko dai wani rashin kunya Shafa tayi maka?” Tamu ya tsinke mishi zaren zantuttukam zuchin shi. Da sauri yace.
“Kai kasan komai Tamu akan Hadiza da Baba Magaji ya bani bayan na baro najeriyane. To ita Hadiza bata san da zaman Shafa ba, kamar yadda Shafa bata san da zaman Hadiza ba.” Nan dai ya kwashe labarin duk yadda ta kasance musu a jiyan. Tsaki Tamu yayi kawai tare da cewar.
“Shirmen banza harma ka tunzurani ƙila saina zaneta ma. Yanzu akan wannan maganar ne duk ta takure kanta?”
“Kul wallahi kar ka soma dukan mun mata ni dai na faɗa maka dan ubanka” Dariya suka yi Tamu yace.
“Wannan siriki kwai fitsararren maras kunya” Dariya suka sake sawa, kafin Tamu yace.
“Yaushe zaka shigo mana najeriyar ne Gwadabe, ka gujemu. Ko dai har yanzu damuwar rashin Iyabo ne ya hanaka zuwa? Mu kuma cike muke da kewarka, ko babu komai ya kamata kazo kaga yara” Gwadabe yaji wata kewa ta kamashi, take yaji yana sha’awa da son ganin abokan nashi da ma yaranshi.
“Tamu zan zo zuwa ƙarshen wannan watan da muke ciki, kaga yau wata yayi goma biyar, yana kaiwa ƙarshe zan zo in duba ku. Ya yaran?”
“Yara kowa lafiya lau sunata karatunsu hankali kwance. Toye ma dana shiga ƙauye naga yayi noman masara shi da yaron Bara’u baka ga yanda masarar tai kyau ba. Na lura yaron yana da mai da kai akan abinda yake gabanshi, shi kanshi Bara’u ya yaba” Sun jima suna hirarsu ta abokai kafin daga bisani su kai sallama. Ko da yaje wajen aiki daya fito cikin ramin haƙar zinariyar dan hutu sai ya kira lambar Shafa, bata shiga ma baki ɗaya. Da ƙyar ya samu dai ta shiga, kuma yaci sa’a aka ɗauka. Daga nan zancan fishi ya ƙare, bayan ƴan bayanai daya yi mata, da kuma kalamin kwantar da rai, sai suka balle da hirar soyayya, wanda rabi da kwatan hirar Shafa ke yinta, shi dai yana dai ƙarfafa mata guiwa ne. Bayan sun yi sallama ya kira Hadiza ma yaji yaya jikin nata tare da ɗan taɓa hirar da rabinta da kwatanta labarin zafin da taji a zuchiyarta ne, shi dai aka barshi da aikin rarrashi.
Jigum ya zauna yayi tagumi bayan gama wayarshi da Hadiza. Kanshi ya ɗauki caji ainun. Harga Allah shi dai bazai iya gane yana son su Hadiza ne, ko kuma yana kallon darajar waɗanda sukai mishi tayinsu ne ba. Domin mace ɗaya tilo Iyabo itace a zuchiyarshi abadan. Yasan abune mai wuya dawowar Iyabo cikin rayuwarshi. Yana fatan inya shiga Najeriya Allah ya haɗa fuskokinsu ko da a hanya ne. Yana kuma da burin son ƴaƴanshi su yi rayuwa a gefenshi damin ya ɗauke musu raɗaɗin maraicin uwa a rayuwarsu. Mammada ne ya dafa kafaɗarshi, yana zaune a gefenshi shi bai ko ji tawowar tashi bama. Abinci ya miƙa mishi, garau_garau irinta leburori irinsu, yasa hannu ya amsa.
“Menene Gwadabe, kaddai batun Hadiza ne duk yabi ya dameka?”
“A’a wallahi Mammada tunanin rayuwa kawai nake yi da rashin daɗin aikinnan, tare da tunanin yarana da basa kusa dani anan” Ɗan murmusawa yayi, sai da ya ciko garsu_garau a cokali ya danna a bakinshi dam kafin yace.
“Wannan ai mai sauƙine Gwadabe, kai da kake jarumi me auren mata biyu, ai zasu riƙe maka yaranka wannan bama wata matsala bace” Abincinshi yaci gaba da dannawa a baki bashi da damuwar komai. Sai Gwadabe yaji dama ace shine Mammada da yaji daɗi. Wunin wannan rana da tunanin Iyabo da yaransu Gwadabe ya wuni. Yayi ƙoƙarin samun layin Bara’u ma dan ya sanar mishi da batun zuwanshi, amman dai basu sami damar jin juna ba. Kamar dai yadda aka saba bayan isha Gwadabe ya aiki yara su kai mishi kiran Hadiza. Yana zaune a saman dakali tazo ta sameshi, bayan sun gaisa yayi mata ya jiki, sai shiru ya biyo baya. Dukkansu a cikin tarawa da ɗabewa suke. Sai dai tunaninsu ya sha banban dana juna.
“Menene ya dameka wanda harya kasa ɓoyuwa akan fuskar taka, ko baka samu damar jin muryar Shafa bane?” Ɗagowa yayi suka haɗa idanu. Ɗan gajeren murmushi yayi mata tare da cewa.
“Babu mamaki dan naji sunan Shafa raɗau a bakin ki, tunda Malam yasan sunan. Yaya jikin naki da sauƙi, kuma kinsha magungunan da suka baki? Ya jero mata tambayoyin da yake tunanin zasu jaye hankalinta daga barin batun Shafa. Amman sai ta jefo mishi wata tambayar da cewa.
“Ni ko zan so ganin tsohuwar matarka ko da a hotone domin inga da abinda tafi sauran mata” Ta ƙarashe maganar da taɓe bakinta. Anan ne taga ya gintse fuskarshi dukkan annurunshi ya dakata.
“Kar ki kuma kawo maganar Iyabo anan wajen. Ki tsaya dai iyakar matsayinki da kike dashi a zuchiyata. Batun ita kanta Shafa ki shafe shi a kan ki, ni dake mu tattauna akan iyakar abinda yake gabanmu. Kuma ko ita Shafa in tayi mun magana a kan ki, ko Iyabo, dakatar mata zanyi domin babu abinda zaku ji daga gareni. Dukkanninku kuna da matsayi na musamman a zuchiyata” Ajjiyar zuchiya ta sauke. Ranta yayi matuƙar ɓaci ainun, idanunta kuma sun rufe da kishi. Amman a zuchiyarta tasan ita ke da laifi da bata cakalo zancan ba da ba’ayi ba ma balle har ya tsayar mata.
“Karshen watannan inaso zan leƙa Najeriya in dubo su Babala da yaran wajena in Allah ya nuna mana da rai da Lafiya.” Cikin dakiya tace.
“Allah ya nuna mana lokacin” Ya amsa mata da “Ameen” Shiru ya sake wanzuwa a tsakaninsu na kusan minti biyar cur, Gwadabe ne ya daure yace.
“Kishi yau ya hanaki yin magana ko Hadiza? Bansan me yasa kike damun zuchiyarki har haka ba wallahi. Mata ku dinga sassautama rayukanku akan kishi ko a zauna lafiya ” Kallonshi tayi ido a cikin ido tace.
“Ashe kishin abinda kake so yana iya zama illa ni ban sani ba? Ai na ɗauka wanda yake da girman daraja ake kishi ba wanda bai isa ba” Kai ya dafe tare da lumshe idanunshi.
“Yi haƙuri Hadiza kinji. Bance laifi bane dan kin nuna kishinki a gareni ba. Amman tunda lamarinnan ya faru baki bar zuchiyata ta zauna lafiya ba. Kinga na dawo a mugun gajiye yau. Hira dake yana warware dukkan gajiyar dana kwaso. Amman yau ke da kan ki kike shirin labto mun wata gajiyar ta daban ma” Yayi maganar da irin sigar daɗin bakin maza mai zurma matan da basu gane kan rijalu ba ( Ummu nabeeha ana magana) Jin ya faɗi haka ne yasa ta ɗan sassauto har suka taɓa hirar dai ba wani armashi.
Haka kwanaki sukaita tafiya dare ya shigo, haske ya maye gurbinshi. Gwadabe sai ɗan siyan tsaraba yake yi yana adanawa kafin zuwan lokacin tafiyarshi. Baba Fhatsima itama sai shirin tafiya take ta tayi. Matan gidan kuwa sai tashin hankali ya ƙaru a garesu. Cikin kwana goma suka shirya tsab da yamma Tasi’u ya ɗaukesu izuwa Airport. Al’amarin daya mugun tada tarzoma mai girma a gidan bayan tafiyarsu Malam. Dan Baba Asshi tana kuka a tsakar gida ta dinga kiran iyayen Baba Fhatsima tana kunduma musu ashariya. Hakanne ya tunzura Hadiza da su Auwala da shigowarsu kenan. Al’amarin dai baiyi daɗi ba sam, Yaya Tasi’u ne ya dakatar da faɗan ta hanyar yin hargagi ga ƙannen nashi akan kowa ya kama gabanshi. Dan samarin ɗakin Baba Asshi ma sun shiga rikicin.
“Ku yi haƙuri Baba. A dai dinga kai zuchiya nesa. Ya kamata ace yanzu maƙota sun dena jiyo sautin faɗa da ashariya daga gidan Malam. Wannan al’amarin tun muna yara aketa faman yinshi har yanzu tsugunne bata ƙareba. Ya kamata ace mun haɗe kawunanmu tun kafin wankin hula ya kaimu ga dare”
Cewar Yaya Tasi’u kenan cikin takaici da baƙin cikin irin rarrabuwar kawunan dake cikin gidansu. Inama zasu yadda a haɗe a zama abu guda. Amman kash an bar kari tun ran tubani. Malam shi ke da sa sannu a faruwar komai, kuma yafi kowa da kowa son ganin ya haɗe kan ahalinshi sun dawo abun sha’awa a yanzu da yake ganin kamar wankin hula na shirin kaishi dare fa”
BABA FHATSIMA
A hotel ɗin dake bayan harami aka sauke Malaman da aka zaɓe aka biya ma aikin umara su da iyalinsu. A baya malam ya samu ire_iren kyautuka irin wannan, kujerar aikin Hajj ma da suka yi da Baba Fhatsima na farko wani ɗan siyasa ne Babba ya bashi, a sakamakon adda’a da malam yake taimaka mishi dashi, kuma yana ganin buɗin haka. Sun je umara da dama, gashi a wannan karon ma Allah ya nufa da’itan za’a sake komawa.
Zaune take akan kujerar dake ɗakin hotel ɗin. Tana jiyo zubar ruwan wankan malam a ƙasa. Zuchiyarta sai take jinta fes Kamar babu wata damuwa dake ƙunshe a cikinta tsawon shekaru. Tunani ta faɗa mai zurfi. Tana tuno lokacin da suka sauka a wannan hotel da suke ciki a shekarun baya. A lokacin Malam yana ji da’ita yana girmamata fiye da tunanin me tunani. Bata mance wasu kalamai da malam ya faɗa mata a ranar da suka shigo makkah da daddare bayan sun gabatar da mu’amalar aure ba.
“Fhatsima samunki nasarane babba a cikin rayuwata. Wallahi Fatsima jina nake yi tamkar wawa soko muddin bana tare dake. A duk lokacin dana kalli ƙwayar idanunki su kaɗai ka iya sauke mun dukkannin damuwata, duk girman matsalar da nake ciki. Ƴan siyasar da muke mu’amala dasu da dama sun sha bani ɗiyoyinsu in aura. Amman Fhatsima nasan ni naki ne ke kaɗai bazan iya haɗa soyayyarki da ko wacce mace ba a faɗin duniyarnan da muke ciki ba.”
Fitowar Malam ita ta katse mata zaren tunaninta ta dawo duniyar mutane. Ido malam ya zuba mata ƙur, jin kaifin idanunshi yasa ta ɗago kai suka haɗa idanu. Amman me sai malam yaga kwantaccen hawaye a guraben idanun Fhatsima. Zama yayi a kusa da’ita ya kama hannunta dukka biyu, ɗumin tafukan hannun juna ya ratsasu sosai. Ƙunshinta yake bi da kallo yanda aka jera salateb ( suffa,) akayi ado dashi cikin hikima, lallen ya sake fito da kyawu da hasken hannun nata.
“Fhatsima wannan lallen nawa ne akayi mun?” Ya faɗa a mugun raunace dan ji yake kamar yayi kuka. Shi kaɗai yasan irin gasuwar da ruhinshi da gangar jikinshi take yi. Itama a sanyaye tace.
“In ba kai ba Magaji wa zanyi ma lalle uban ƴaƴana?” A sanyaye cike da kunya yace da mamaki ya dubeta dan yasan in tana cikin yarda dashine har take iya kiranshi da Magaji a keɓe, amman dama a cikin mutane da cikin fishi Malam duk take kiranshi.”
“Fhatsima yau ni kika kira da uban ƴaƴanki, kuma kikace domina kikai wannan lallen?” Murmushi tayi tace.
“Magaji ai har yau har gobe ruwa na maganin dauɗa” Farin cikine marar misaltuwa ya lulluɓeshi.
“Fhatsima nayi kewar kasancewa tare dake, nayi kewar rashin samun cikakken lokaci kamar yadda kika sabarmun, nayi kewar kulawarki, nayi kewar tausasamun da kike yi Fhatsima. Na sani ni nayi kuskuren ruguza amincin dake tsakanina dake. Wanda in kin tambayeni dalili bani dashi wallahi. Nayi nadamar komai, ina takaicin faruwar komai Fhatsima. Hawayene tab a guraben idanunshi, yana ta girgiza kai irin na kaico.
“Magaji cutuwa iya cutuwa nayi, tun daga lokacin da abubbuwa sukaita faffaruwa dauriyaa kawai nake yi, da ba a iya hawan jini abun zai tsaya ba, numfashina zai rabani dashi, in Barka a duniya da matan naka na so” Ɗan murmusawa yayi kawai. Baice komaiba ta ɗaura da cewar.
“Na fuskanci wulaƙanci da matsi wanda ni kaina bansan ina da irin wannan haƙurin ba. Soyayyarka data yaranmu ce kaɗai tasa naci gaba da rayuwa da matanka. Burina shine ace da kaina naba ɗiyoyinmu tarbiyya a bisa doron alƙawarin da nayi maka tun kafin aurenmu. To Alhamdulillah na sauke nauyi”
“Gashi ƴaƴan da suka fito a ɗakinki sun kasance sanyi da hasken idaniyata Fhatsima. Sun kasance abun alfahari kuma jagorori. Wannan kaɗai wata babbar nasarace a gareki, kuma hakan ya ƙara tabbatar dake a matsayin shugaba kuma uwar gida a gidan Magaji. Ko wacce mace da ƴaƴanta, dani kaina Magaji a cikin rigar alfarmarki nake Fhatsima ” Idanu ta ƙura mishi tana mishi dariya shima dariyar yake yi.
“Magaji kai da kaya mallakar wuya ne. Kuma ba’a hana ma ba da rago fata, tuwo baya canja sunanshi. Yarannan baka ragesu da komai ba tun yarintarsu har zuwa yanzu da nake wannan maganar.
Fatana Allah ya haɗe kan iyalin naka baki ɗaya. Duk da kai da kan ka ka farraƙa haular gidanka, kasan…..”
“Ya isa Fhatsima kar ki rusamun farin cikin dake ƙunshe a raina” Ya katseta da hanzari.
“Inaso ki tsaya mun kuma ki taimaka mun ke da Tasi’u da Jamila mu haɗu mu haɗa kan iyalinmu. Abinda ya wuce ya wuce, kece zaki taimaka komai ya gudana. Sannan haɗe yaran da matansu ni inata jaddadawa kamar zai iya gyara lamarin. In kan yaran ya haɗe, dole iyayen su shafa ma kansu ruwa. Asshi ce dai nasan zata ba da wahala. Ammam fa a shirye nake tsab da in rabu da duk matar da zata kawo mun taurin kai. So nake in gyara abinda na ɓata tun da rayuwata kar in bar baya da ƙura.” Ajjiyar zuchiya Baba Fhatsima ta sauke. Yayin da take hasko abubbuwan da suka zama sune sababin faruwar waɗannan matsaltsalu na gidan Malam. Gani take yi kamar yanzu suke faruwa.
“Baki ce uffan ba Fhatsima” Ya jefeta da tambayar.
“Malam a ɗayan biyu ne wannan haɗe yaran da kai da Tasi’u kuke ganin zai yi tasiri wajen kawo soyayya da shaƙuwa a tsakankanin yaranka. Hakan zai iya faruwa, ko kuma hakan ya sake farraƙa kan yaran, ko da ta Hanyar matayensu, ko ƴaƴan da zasu hayayyafa. Malam wannan lamarin babbane. Amman mu dage da roƙon rabbil izzatu. Gamu a ƙasa mai tsarki mu dage da adda’a Allah yasa hakan ya zama matattakalar da zamu hau tsanin da zai wanzar da farin ciki a tsakanin Ahalinka. Sannan sai ka sanya dokoki masu tsanani, kayi ƙoƙarin dogewa akan dokokin. Kar ka faɗesu ba tare da ka basu mahimmanci ba, wannan raunin naka yana ɗaya daga cikin abinda ya soma kawo rarrabuwar kai a tsakankanin Ahalinka.”
A taƙaice dai sun jima sunata tattauna yanda za’a ɓullo ma lamarin. Sun yi adda’a sosai. Malam da Baba Fhatsima sun sasanta kansu sai ɓarzar Amarci ma suke yi abinsu. Sai yanzu ne Malam ya dawo cikin nutsuwa da hayyacinshi. Ya saki ajjihu wajen ganin ya kyautatama Baba Fhatsima, duk da ragowar mata da ƴaƴanshi ma bai barsu a baya ba.
Gwadabe.
Ana gobe Gwadabe zai kama hanyar Najeriya. Sun sha hira ainun da Hadiza da ƙyar ta barshi ya samu ya shiga ciki yaci gaba da shirya kayan tafiya. Kishine ɗamfare a ƙirjin Hadiza dan ita gabaki ɗaya a tunaninta Gwadabe baibai kawai ya ninketa amman wajen Shafa yake son zuwa. Shadda dalleliya da ƴan kunne Hadiza ta bayar a kaima Babala, ta bada agogo mai kyau tace ya kaima Shafa. Anty Badi’a kuma ta ba da takalmi da mayafi tace akaima Babala. Yaya Tasi’u kuma kuɗi ya bayar akai mata, sai ƙarin guziri da yaba Gwadabe. Sassafe kuwa Mammada ya rakashi tashar mota. Motarsu ta ɗaga zuwa Najeriya. A garin Kano ta dabo tumbin giwa Gwadabe ya sauka. Misalin ƙarfe tara na dare dake motarsu ta samu matsala a hanya sun daɗe a yashe a titi sosai.
Sakkowarshi daga mota ita ta kara mishi damuwar rasa Iyabo da yayi a rayuwarshi. Gashi dare yayi, kuma bazai taɓa iya taka kafarshi zuwa gidan Yaya Hambali ba. Bashi da zaɓin daya wuce ya nemi gidan kwana a tasha, gobe sassafe yana son ya leƙa gidansu Iyabo ko Allah zai yi ko juna su gani, su gaisa kafin ya tafi.
“Malam muna da ɗakin saukar baƙi in kana da buƙata. In kuma a Kano tafiyarka ta ƙare akwai tasi da Bus a bakin tasha zata kai ka duk inda kake buƙata. Cewar wani ɗan yuniyon.
“Inada buƙatar ɗakin, Takai zan wuce zuwa gobe da safe dan Allah”
“Nera hamsin kuɗin kwana, in bawali zaka yi a banɗaki kuma nera biyar, ba haya nera goma, wanka nera ashirin, ruwan zafi ma ashirin.” Wani ɗan yuniyon dinne yace.
“Haruna ka fiye surutu, ka ɗauki jakarshi dallah ka rakashi masauki” Wanda aka kira Haruna ya tuntsure da dariya yace.
“Ai gara muyi gwari_gwari dai.” Jakar kayan Gwadabe ya saɓa a bayanshi yace.
“Biyoni muje in kai ka” A baya Gwadabe ya bishi zuwa can cikin tashar, wani gida mai kama dana masu zaman banza suka shiga. Maza da mata, da ƴan daudu ne a cakuɗe suna caca, masu ƙidan garaya kuma sai kiɗa suke yi, ga masu shan tabar sigari, ga masu cin goro da tomtom kowa dai da abinda yakeyi. Ƙyauran wani ɗaki Haruna ya buɗe suka shiga. Matasane a ciki fin su takwas, wasu sunyi bacci, wasu na bacci, wasu abinci suke ci. Tabarmace malala a ɗakin, sai kayi matashin kai da buhun kayanka. Gwadabe bai gama ƙarema dakin kallo ba Haruna ya miƙo mishi hannunshi. Nera hamsin ya bashi.
“To ka raɓa ta can lungun ka kwanta. Kana buƙatar abinci ne?’
“E ina buƙata, amman tuwo nake so” Haruna yace.
“Tuwo miyar kukace kaɗai tayi ragowa. Ko wacce malmala nera ashirin ce, nama kuma ko wanne tsoka nera goma, man shanu ko wanne cokali nera biyar” Dariya Gwadabe yayi, duk da damuwar da yake ciki. Shima harunan dariya yayi. Nera ɗari ya miƙa mishi.
“To a haɗa komai da komai na ɗari harda ruwan sha”
Zaman Gwadabe ke da wuya sai ga kiran wayar Shafa.
“Assalamu alaikum Shafa barka da dare, har izuwa irin wannan lokacin baki yi bacci ba?” Ɗan murmusawa tayi, cikin taushi da zaƙin murya tace.
“Na kasa baccin inata jiran kiranka kace mun ka isa Takai in samu nutsuwar ruhi tukunna. Jin shiru ne yasa nace dai bari in nemeka”
Ɗan murmushin wahala yayi mata yace.
“Ayya. Kin ganni a Kano bamu daɗe da shigowa ba ma. Sai zuwa gobe in Allah ya kaimu zan karasa takai ɗin.” Iska ta fesar daga bakinta.
“To Allah ya nuna mana. Bari in barka ka samu ka huta, zuwa safiya in ka isa Takai mayi waya” Bai bata amsaba ƙit wayar ta ɗauke chaji ya ƙare, a ajjihu ya wurga wayar ya samu ya gyara zaman ƙatuwar jakar buhunshi. Wata budurwace ta shigo mishi da tuwo. Bayan ya gama ci kuma sai yayi jigum a zaune yanata faman tunanin yadda za’ayi gobe kafin tafiyarshi yaga Iyabo ko da basu yi magana ba. Wata zuchiyar tace dashi.”ƙila ma tana can gidan mijinta ta mance dakai” take gabanshi ya tattake ya faɗi. Da wannan zulumin ya kwana. Sassafe bayan sallar asuba ya fice a tashar bayan yaba Haruna ajjiyar jakar kayanshi. Kai tsaye motar layin su Iyabo ya shiga. Tun daga hango gidan damuwarshi ta sake yin tsanani, bugun zuchiyarshi yaci gaba da ƙarfi. Iyaa Debisi ya hango tana ma yara masu kawo niƙa niƙan wani abu haka kamar gero, kamar dawa. Yana isa wajen ta kalleshi ta zuba mishi harara harda tsaƙi, ta mayar da hankali a kan niƙanta. Shi ko ƙiƙam yayi yana jiran ta kashe injin ɗin su gaisa. Amman bayan fa gaisuwar baisan me zai soma cewa ba. Ya