NA GA TA KAINA
*NA SADNAF*🌸🌸🌸🌸🌸
®️ *_PURE MOMENT OF LIFE WRITERS_*
{We Don’t just entertain nd educate we also touch the heat of readers P.M.L}💪🏻_
*Free Novel*
*Tun kafin nayi nisa a rubutu nake da burin rubuta wanan labari Allah bai nufa ba sai yanzu labarin Nan ya faru a gaske tun 19’s wahalar rubuta shi nake gani Sabida yanda xan na had’a present da past Amma a yanzu Allah ya nufa zanyi insha Allah zai na zuwar muku sau uku a sati idan na samu sarari ma zaku iya samun pages fiye da haka labarin Nan ya bambanta da sauran novels Dina na baya za’a ga abubuwa da za’a ga Anya dagaske zai faru kuwa ya faru dagaske zaka iya aikata Abu da baka d’aukeshi a bakin komai ba sai bayan shekara da shekaru sai abun ya dawo maka Allah ya tsare mu da tsarewarsa ya tsaremu da imanninsa Ameen*
*Page 1*
*1992*Da Sauri na shige d’akina na rufo k’ofa a lokacin da Umma ta hangoni ta biyoni a guje ko nauyin cikin dake jikina banji ba sabida tsabar tsoronta da nakeji.Jingina nayi da k’ofar d’akin Ina sauke numfashi Umma kuwa sai tura k’ofar take Tana auna min zagi iyayena da kasa ta Dade da rufe musu Ido da take ta Kiran sunansu Tana zaga yasa naji wani irin hawaye na zubomin Sanin na riga da na kulle k’ofar yasa naja k’afana na nufi Kan gadona Sabida kaina danaji Yana neman fad’owa sabida tsananin ciwo rabona da abinci har na manta lemon kwalba da bredi su kawai suka zama abincina a matsayina na Mai tsohon ciki nida gidana ban Isa na fita ba sai uwar mijina ta nada min duka bredin ma da lemo sai na fakaici Bata palon nake fita na siya kamar yanda yanzu na faki idonta na fita Ina dawowa ta gani ta biyoni a guje sabida kawai na fita siyan abinda zan sawa cikina.Dan cikina dake ta mutsu mutsu yasa na tuna da yunwar da nakeji na tashi na mik’e dak’yar na jawo ledar bredi da lemo Dana siyo na fara tusa bredin Ina hawaye Dan ko kad’an ba dadinsa nakeji ba ci kawai nake.Abban Zahira daya fad’omin a Raina yasa naji na k’asa ma had’iyar bredin bansan lokacin da kuka ya k’wacemin ba na fara magana a fili cikin tsananin kuka”Nasiru Mai nayi maka haka Dana cancanci haka daga wajen Kai da mahaifiyarka?laifine Dan na zab’eka a cikin dumbin masoyana na aureka ka raboni da dangina da kowa nawa ka kawoni wani garin kana wulakantani Mai nayi Dana cancanci haka daga wajenka”?Kukan dayaci k’arfina yasa na kasa cigaba da maganar da nake a fili na koma na kwanta sabida rawar da jikina keyi na cigaba da kukan da ya zame min jiki ko da ba’a min komai ba fuskata Bata rabo da hawaye sosai nake k’ewan yarana Amma uwar mijina ta hanani ganinsu Mahaifinsu kansa sai dai na jiyo muryarsa rabon Dana saka shi a idona wata hud’u kenan da sunan muna gida daya.Mahaifiyarsa ta zama tamkar itace matarsa Dan komai ita ke masa kwana ne kawai Bata yi a d’akinsa.”Mommy Mommy”Naji siririn muryar Zahira Tana tab’a k’ofata Zumbur na mik’e nayi hanyar k’ofa har Ina cin tuntub’e rabon dana ga ita da Nadiya har na manta Dan k’arfi da yaji Umma ta hanani ganinsu a d’akinta suke kwana ko d’akinsa da ta ga sun nufo d’akina zata daka musu tsawa tasa kanwar Nasiru Safiyya ta d’aukesu ta maidasu daki ta kulle tun yaran Ina jin suna kukan hanasu da akayi su zo wajena har suka zo suka SabaIdona ya rufe sosai da San ganin yarana hakane yasa ko kad’an ban tuna da wata Umma na palon ba Dan inajin tashin muryar ita da Safiyya da kanwar Safiyya Lami a palon suna Hira.Da Sauri na bud’e k’ofar banyi wata wata ba na d’aga ta Sama na rungume ta a jikina inajin wani irin Sanyi a zuciyata Wai ace Kai da danka karfi da yaji a nemi rabaku itama zahiran lamo tayi a jikina Tana sauke ajiyar zuciya ko damuwa banyi da yanda naji cikina ya dunkulle ba sabida yanda na Dora Zahira a jikina wuwurga Ido na fara yi ko zan hango Nadiya Amma Banga alamarta ba da Sauri na sauke Zahira na ruk’o hannayenta nace Mata “Ina Nadiya”?