Musayar Zuciya Na K.A.S Hajja Ce
A true life story
Na
K.A.S Precious Hajja ceπ
HASKE WRITER’S ASSOCIATIONπ‘
(Home of expert & perfect writer’s)
DEDICATED TO Sanah Isma’il matazu.
Bismillahir Rahmanur Rahimβ¦..
“Hakk’in mallakar Hajja ne, kar wanda yayi min sauyi a cikin sa please.”
Page 1
A makaranta.
“Uwani halilu?”
“Present sir..”
“Baraka lado?”
“Present sir..”
“Sahura Ayuba?”
“Present sir..”
“Indo malam Hamza?”
“Labbaika, present, sir, mah, nazo⦔
Saurin kallon ta malamin yayi jin yauma a yadda ta amsa mai kafin ya zare glass d’in dake manne akan saman idan fuskar shi, ya d’ora dara-daran idanun shi akan nata da nufin ko zata ji tsoron sa sai yaga ta kafeshi da idanuwan ta tamkar zata cinye shi, yayi saurin wurga mata uwar harara ranshi a matuk’ar had’e yace mata cikin tsawa.
“Ke..! Baki da hankali neβ¦?!”
Indo ta mik’e tsaye tana gyaran hijjab d’in ta wanda yayi dikil-dikil da daud’a wuyan ya yage tun daga wuya har zuwa k’irjinta sannan tace,
“Da sauk’i dai malam..!”
“Naga alama ai koma gurinki ki zauna wawuya kawai..”
Ya fad’a ba tare da ya kalleta ba. Komawa tayi ta zauna sai faman soshe-soshe take yi akan ta wanda hakan da alama ba za’a rasa kwaron kwarkwata ba dan yadda take yi ya nuna hakan. sai da ya kammala kiran sunayen su tas! sannan ya mik’e ya fita yana jiran lokaci ya cika sai ya kuma dawowa yayi musu subject d’in turanci wanda aka sari basa fahimtar uban komai a ciki, idan kuwa yana son su fahimta toh sai ya had’a musu da yaren hausa sannan zaiji ruwan amsa da tambayoyi amma idan da turanci zai kwana yana yi sai dai su kafamai idanuwa tamkar zasu cinye shi.
Yana fita wajan mintuna biyar sai gashi ya kuma dawowa hannun shi d’auke da wasu littattafai manya da kananu. yana shiga ya tarar duk sun kaure da surutu yayin da ya kai idanunshi can k’arshen ajin ya hango INdo da wani yaro taci uwar d’amara da hijjabin ta suna dambe. Dorinar hannun shi ya d’akko yayi gurin. sauran yara na ganin shi suka fara watsewa aka bar INdo da lurwanu a gurin. yana zuwa ya fara tsulawa INdo dorinar ganin ita ce me fifik’arewa kafin ya tsulawa lurwanu yana cewa.
“Ke! Sakar mai riga wawuya kawai.”
Axabar bulalar ne yasa ta saki amma da ba tayi niyar sakin shi ba sai ta fasa mai baki kamar yadda ta furta tun farkon fad’an nasu. Malam Sadeeq na kallon su yace.
“Me ya had’a Ku?!”
Idanu kwal-kwal zasu kawo ruwan kuka lurwanu yace.
“Malam itace⦔
Caraf be k’arasa fad’a ba INdo tace,
“Malam wallahi k’arya yake shine ya fara⦔
Shima lurwanu dan kar tamai sharri ya kuma tare zan cen,
“Wallahi malam k’arya take yi kawai na ajiye⦔
“Billahillaxi malam shine ya⦔
“Keep silent or something else’s, sha-sha-shai kawai..”
Babu abin da suka fahimta a cikin abin da yace dasu sai dai yana yin yadda yayi musu maganar da kuma kalaman shi na karshe ya tabbatar musu da cewar fad’a yake musu hakan yasa suka yi shiru suna bin kyakyawan bakin shi da kallo ba kamar INdo da take tunanin ko alawace ji take kamar ta lasa dan yadda ya burgeta.
Komawa yayi wajan teburin shi ya zauna sannan yayi musu alamar suzo baki d’ayan, suka bishi INDO sai faman ture lurwanu take yi a haka suka k’arasa wajan da malam Sadeeq yake jiran su,
“Kai me ya had’a ku da ita?!”
“Malam itace kawai muna zaune sai tazo tana tab’ani da kafa nayi mata magana ta dena takani shine tak’i taci gaba har muka fara fad’a da ita.”
Tun kafin ya bata izinin magana INdo ta fara tana hararar lurwana bakin ta har kumfar yawu yake sabida masifa,
“Kai..Kain uban can..! Na rantse da Allah malam shine ya d’alamin kaure a baya na shine na rama ya kuma yi min kawai muka fara fad’a dan shi masifaffe ne ya raina ni..”
“Ya isah haka kowa yaje ya zauna bana son surutun ban za.”
Tashi suka yi suka tafi dama can karshen aji nan ne wajan zaman INdo dan haka ta tafi malam Sadeeq yayi saurin dawo da ita, tana zuwa yace da ‘yan layin gaba suyi mata guri anan ta zauna cike da jin haushin malamin dan taga alamar baya son ta bare yabi bayan ta a duk cikin al’amarinta.
kararanta Littafin Hadinkai anan Dannan kawai domin karantawa ko dauko akan wayarki
A haka ya kammala musu yabar ajin duk sun gundure shi ga haushin basa ganewa da turanci har sai yayi da Hausa. Ana tashi ya hau mashin d’in sa kai tsaye ya wuce inda ya sauka. Wanka yayi sannan yayi sallar azahar ya koma gefe ya zauna bayan ya janyo wayar shi, laluban d’an uwan shi ya fara yi cikin sa’a ta fara k’ara yana d’agawa yace,
“Hi twins ya gida ya gurin aikin naka?!”
Daga can 6angaran ya amsa cikin sanyin murya kamar yana rad’a,
“Lafiya lau all twins ya student’s da fatan dai kana samun yadda kake so koh?!”
Shafa k’eya yayi tamkar yana ganin shi sannan ya lashi lips d’in shi yace,
“Nop! Twins ga baki d’aya makarantar bata yi ba wallahi, gashi nazo an wani bani formaster teaching kuwa sai dai nayi da hausa wata Kalmar ma ban san yadda zan fassara musu ba wallahi sai dai na barsu a haka.”
Dariya yayi mai sauti ya san dole a bawa d’an uwan shi haushi duba da yadda baya son wasa a harkar karatu gashi an kai shi inda zasu samai hawan jini, cikin basarwa yace.