By Zahra Tabiu
Tsokaci
Wata irin gaba ce tsakanin talaka da mai kudi. Mai kudi yana yiwa talaka kallon nesa-nesa, irinka irin wahala, Allah nagode maka ba ni ba ne. Yakan kara yi masa kallon na fi ka, da gumina na nema kai ma sakacinka da mutuwar zuciya ya hana ka ka samu…ka da ka roke ni don baka nan lokacin da na nema! Talaka na yiwa mai kudi kallon barawo, azzalumi da ya handame dukiyar kasa. Sarkin izza wanda ya ci da rabonmu. Da a ce ni ne ke da kudinka da nayi abinda ka kasa yi, da na taimaki jama’a domin sai nayi yaki da talauci!Amma abin tambaya anan shi ne mai ya sa ba a kallon mutum a matsayinsa na mutum dan adam sai a matsayin tattalin arzikin da ya mallaka ko ya kasa mallaka??? Zahra Tabiu Mai Tafiya
Labarin wasu mata guda uku mabanbanta asali da kaddara ta hada su a yayin da suka dauki aniyar yiwa talauci gudun fanfalaki. Sai suka fada karuwanci..duniya ta zo musu a tafin hannu har suke zaton tafiyar ta kare. Ku biyo su tsakanin Niger da Nigeria mu ga yadda za ta kaya!Mai tafiya..wani guzuri ka tanada?????1.
Kumbar susaKudi kumbar susa, idan ba ka da su sai ya zamto ba ka da murya, ko ka yi magana ba za a ji ba!Kano, NigeriaWai me ya sa mutane ba sa son talaka ne? Har bahaushe ma kan ce wai “talaka ba aboki ba, ko kun shirya ranar biki kwa bata” Irin tunane tunanen da Hindatu ke yi kenen a wata safiyar Laraba.
Ta san an ce wai Laraba ranar sa’a ce, to amma sai ta yi wa wannan Larabar taken ranar bakin ciki, ranar ban haushi. Matsalarta a yanzu bata wuce biyu ba;ta tashi ba ta maganin komai sai naira hamsin! kuma ta wayi gari jinjirinta wanda yayi kwana 40 a duniya yana fama da zazzabi da mura, ciwon da ya kamata ta kai shi asibiti.
‘Ya’yanta biyu Abba da Asiya su suka tsira mata ido suna ma ta kallon gasasshen balangu don yunwar da ke azalzalarsu. Abba dan shekara shida shi ne mai wayo cikinsu ya ce “Mama, in yi gudu in je in siyo kosan”? ta yi sauri ta kawar da idon ta daga kan sa, tausayi yake ba ta. Hamsin din dai ita ta ci wa buri tayi kudin mota ta kai jinjirinta asibitin Murtala tunda ba a biyan kudin kati, idan ya so in aka rubuta magani ta karba a wajen Danladi mai kemis na unguwarsu baga baya ta biya shi a hankali.
To amma ya za ayi ta bar yara da yunwa? Da wannan tunanin da zaro kudin ta ba shi ta ce “yi maza ka je wajen karama ka siyo kosan ashirin ka ce ma ta in ji ni..kar fa ka tsaya wasa” ya fice a guje kafin ta karasa. Ya dawo ya bata canjin suka hau kan dan tsurut din kosan suka cinye har da lashe lashen takarda. Ba ta bi ta kan su ba ta saba jinjirinta a baya agogon bango ya nuna karfe takwas na safe cif.
Ta dauki jinjirin da ta sawa suna muhammadu ba don ta yanka ma sa ragon suna ba ta saba a baya,jikinsa zafi rau! ta tarkato ragowar yaran suka yiwo waje. Ta rufo kofar gami da saqalo ta da wani kara ba don tsoron kar barawo ya shiga ya ma ta sata ba sai don cika ala’da. Ta zunkuda goyon bayanta da ke mutsu mutsu ta ce da Abba ta na nuna makotansu