MAI IDO A TSAKAR KA
(DUNIYA)
GAWURTATTU UKU
BADI’AT IBRAHIM MRS BUKHARI B4B ( GIDAN ƘAMSHI)
ƊANƊANO! ƊANƊANO!! ƊANƊANO!!!
1
DAMATURU
Hadarine gagarumin gaske a garin namu na Damaturu, misalin ƙarfe huɗun yamma ne, amman yanayin duhun garin in ka kalla, zakayi tunanin asubane, ga wata sassanyar iska dake busawa tare da ƙananun yayyafin afumangai da aka soma yanzu. Jama’a sai gudu suke yi, yayin da da dama suka ƙara sauri.
YAHANASU:
Sauri_sauri gudu_gudu nake tafiya, bana fatan shan dukan ruwa. Hijabin dake jikina harya soma jiƙewa, dan yayyafin ya ƙaru sosai. Da sauri nasha kwanar lungun bayan layinmu, wanda inna ɓulla zai kaini, kusa da gida. A cikin lungun akwai wani tsohon kango, wanda ya kasance matattarar ƴan shaye_shaye. Zaman su a anguwar yana cima mazauna wannan anguwa tuwo a ƙwarya. Gashi matasan daga can wata anguwa suke zuwa. A guje nazo zan wuce wannan kangon. Banyi aune ba naji an fisgoni da matsiyacin ƙarfi. Ihun tsoro nayi, amman kafin in gama wangale bakina, naji an cusamun tsumma a bakin nawa. Jikina sai rawa yake yi kawai, ga kangon akwai duhu bana ganin mutanen dake ciki sosai. Ga wani irin mugun warin sigari dake tashi a wajan. Ban gama tantance fari da baƙiba, naji hannun wani matashi a jikina ya fisge hijabin dake jikina. Tare da daƙumo mun ƙirjina. Fitsarine ya soma zubowa a ƙasana, hawaye ya gama wanke mun fuskata. Kokawar ceton kaina na soma yi da wannan matashi, nice naushi, da yakushi, abun takaicin bakina a toshe yake. Ina cikin wannan dambarwa, naji an daddanne mun hannayena, cike da rashin imani wannan matashin yai mun mummunan fyaɗe. Zafin yagani da yayi ne, yasa na fisge hannayena a hannun matasan da suka daddanneni. Dutsen dake kusa da kaina na ɗauka da zafin nama, na rotsama wannan matashin a kai. Take kanshi ya fashe, jini ya wanke mun fuskata.
“Ta kashe Tijjani, kai mu ware tun kafin asirinmu ya tonu” Cewar matasan samarin. A guje suka fice a cikin kangon. Ruwa ake zubawa kamar da bakin ƙwarya. Jikina sai kakkarwa yake yi, da ƙyar nasa hannu biyu na ture wannan tsinannen matashin wanda tunda na buga mishi dutse bai motsa ba,. Da sauri na rarumi Hijabina na mayar jikina, da ƙyar na miƙe tsaye, raɗaɗi da yaji_yaji nake ji a ƙasana, zuchiyata kuwa dan tsoro kamar zata faso ƙirjina ta fito. Cikin jan ƙafa na fice a kangon. Bana ko ganin hanya sosai, sabida ɗimuwa, ga ruwa da akeyi, harda ƙanƙara, sai dukana ruwannan yake yi. Amman bana jin dukan ruwan sam, damuwata shine, darajata da wani tsinanne ya keta mun, shikenan nasan na shiga ƙuncin rayuwa da tasku kenan. Da ƙyar nasa hannu na tura get ɗin gidanmu na shiga. Babban gidane mai cike da jama’a sosai. Sai jan ƙafata nake yi kawai, da ƙyar na iso ƙofar ɗakinmu. Suna zaune suna kallo na faɗo ɗakin a jiƙe sharab, jikina sai ɓari yakeyi, idanuwana kuwa kamar garwashin wuta.
“Yahanasu lafiya kike kuwa da zaki tawo a cikin irin wannan ruwan mai ƙarfi?” Mahaifiyata ce ke magana, amman in buɗe baki nayi magana na kasa. Hannu na saka a ka, na shiga runtuma kuka mai tsuma zuchiya. Gabaki ɗaya na tashi hankalin ƴan uwana, duk sun miƙe tsaye suna kallona.
” Ya Innana jini a ƙafar Yahanasu” Cewar Fanda. Wakil Yayana ya dubeni yace.
“Yahanasu kiyi magana dan Allah kin tayar mana da hankali, meke faruwa, meya sameki?” Ya Innana mahaifiyarmu ta iso kusa dani, bata ce komai ba, taja hannuna zuwa uwar ɗakinta. Akan gadonta ta zaunar dani.”
“Yahanasu ki cire kayan jikinki tukunna, koma menene ya sameki ki kasance mai juriya mana, kin ɗaga mana hankali ainun” Tausayina dana mahaifiyata yaimun dirar mikiya a zuchiyata, jikina ya tsananta rawa ainun, idanuna suka shiga kakkafewa. A gaggauce Ya Innana ta zare mun hijabina, ganin rigata a kekkece da tayi , ya tashi hankalinta sosai. Da sauri hannu na rawa ta ɗaga mun zanina. Matsawa baya tayi da sauri hannunta dafe a ƙirjinta, tana zubar hawaye. Jikinta ya mace mus tama rasa me zata yi mun dan ta bani kulawa. Duk girmana sai Innana ta dena ganinshi. Tana hawaye ta cire mun kayan jikina tas, bargo ta yafa mun. Sai naga ta rungumeni tana kuka mai fitar da wani irin sauti, mai tada hankali.
” Ya Innana, ku buɗe ƙofar dan Allah” Wakil ne yake magana. Maganar Wakil ita tasa Innana dakatawa da kukanta. Ban ɗakin ɗakinta ta shiga, bata jima ba ta fito, hannuna ta kama ta ɗagani tsaye. Rungumeta nayi ina kuka. Ni kaɗai da ire_iren waɗanda suka shiga ƙangin fyaɗene zasu gane irin raɗaɗi da azabar da nake ji.” Mun kasa magana daga ni har Ya Innana, an rasa wanda zaice da wani kar yayi kuka. Har cikin bayan gidanta ta kaini, ta tara mun ruwa a bokiti, wanda take ta sawa a kittle.
“Ki gargasa jikinki, saimu tafi asibiti. Amman garin yaya hakan ta faru dake?” Firgicewa taga nayi, har ina zabura. Ba shiri tace.
“Shikenan ya’isa. Koma waye yai miki wannan aikin, wallahi kotu ita zata shiga tsakaninmu, wallahilƙudrat da zan ganshi saina kasheshi, sai dai aimun duk abinda za’ayi mun.” Fita tayi fuu, ni kuwa sam na kasa yin wankan, asalima wani irin zazzaɓine yake shirin halakani
Ya In na na” Na ambaci sunanta a wawware. Ba shiri ta dawo har tana tuntuɓe”
Mutuwa zanyi Innana, zafi zai kasheni” Hannuna yana cikin nata, tana ɗigar hawaye tace.
“Bazaki mutu ba.” Wanka ta soma yi muni, tana daddannamun jikina da tawul, saida tazo yimun tsarkine, hankalinta ya kuma tashi. Gashi jikina ya saki kamar zan sume mata. Da ƙyar muka fito a bayan gidan, doguwar rigarta ta buɗe durowa ta zura mun. Ta samun suwaita da hular sanyi, fita tayi da sauri.
Innana:
Tana fitowa yaranta suka baibayeta da tambayoyi.
“Wakil kayi maza kaje ka sanarma Ba Bakuri, za’a kaimu asibiti tunda Babanku baya gida, ko Bulama ƙarami sai ya kaimu” Kafin yace wani abu sai suka jiyo sallamar mahaifinsu Ba Modu a ƙofar ɗakin. Fanda ce ta amsa mishi a raunace. Shigowa yayi da fara’a kamar yadda yake a kullum, dan Ba Modu ma’abocin far’a ne sosai. Ganin iyalenshi a wani irin hali da rabon da ya gansu a halin, tun rasuwar Mahaifiyarsu Hajja Yahanasu wacce ta kasance kaka ga yaran gidan. Innana ya kalla hawayenta bai tsaya ba, daga kallonta kasan cewar tayi kuka ta ƙoshi, ga tashin hankali sosai a fuskata.
“Innana Lafiya kuwa ki ke zubar da hawayenki a gaban yara, meke faruwa?” Cikin muryar kuka tace.
“Ba Modu Yahanasu ce wani azzalumin yai mata fyaɗe, tana ɗakina a cikin mawuyacin hali, har firgita take yi” Tana kaiwa nan ta sake fashewa da kuka mai zafi” Tashin hankalin da iyalan ɗakinnan suka shiga ba’a magana. A tare suka shiga ɗakin dan ganin Yahanasu.”
Yahanasu:
Ihu na ƙwalla mai ƙarfin gaske, ina yunƙurin tashi, dan ba ƙaramin firgitani shigowarsu tayi ba. Muna haɗa idanu da Wakil na sanƙare a wajen, numfashina ya ɗauke”
Innana:
“Innalillahiwainnailaihilrajiun innalillahiwainnailaihilrajiun innalillahiwainnailaihilrajiun. Allah ka tsinema wanda yaci mutuncin yarinyarnan ya keta mata haddinta. Ya Allah ita kuma ka rufa mata asirinta ka bata miji na gari” Kuka take yi mai zafi. Da sauri Ba Modu ya isa kan Yahanasu, shima hawayen yake fitarwa, taɓata yayi, tabbas babu sauran rai a jikinta. Da sauri ya fice a ɗakin ya nufi shashen babban wansu Bakura a firgice.
Sallama ya shiga yi, da kiɗimammiyar murya, hawaye bai dena gudana a idanunshi ba har sanda matar wanshi Hajja Gana ta fito. Ganinshi a wannan mawuyacin yanayinne yasa ta koma da sauri ta kirawo wan nashi. A hanzarce ya fito, tabarau ɗinshi a hannu, ganin ɗan uwan nashi na kuka ya gigita mishi duniya ainun.
“Modu menene ya saka zubar hawaye duk jarumtarka?”
“BaKura, Yahanasu akaima mugun aika_aika fyaɗe akai mata. Tana ɗakin Uwarta a sume” Sun kiɗima sun razana ainun, Hajja Gana kuwa, fashewa tayi da kuka, abunka da mace, kuma uwa. A gaggauce suka nufi ɗakin Innana dukkansu.
“Wakil maza ka samu Bulama a kawo mota ƙofar ɗakinnan, a ɗauki Yahanasu” Baice komai ba ya fita. Cikin ƙanƙanin lokaci gafatanin ƴan gidan suka san halin da ake ciki. Cirko cirko suka yi a tsakar gidan ko wacce fuskarta cike da alhini. Bulama da Wakil ne suka saka Yahanasu a mota, a gidan baya suka shinfiɗeta. Baguji kishiyar Innana ta shiga gidan bayan tana kuka, taima Yahanasu matashin kai da cinyarta. Bakura ya shiga gaban mota, shi da Bulama ƙarami. Da sauri motar ta fice. Modu ya dubi mata da yaran gidan yace.
“Kuyi haƙuri, kuma ku sata a adda’a kawai. Innana ki shige muje Wakil ya kaimu asibitin. Fanda ke kuma ki shiga cikin gida. Jiki a mace suka wuce garejin mota.
A bakin titi suka hango dandazon jama’a yara dama manya. Har babu hanyar wucewa a ƙafa ma, balle kuma ababen hawa. Bakura ne ya sauke glass ɗin motar ya yafito wani matashi da hannu, matashin ya iso wajan.
“Lafiya meke faruwa ne haka”
“Wallahi Baba wani ɗan shaye_shaye ne, aka ciro gawarshi a cikin kangon lungun gidan lado, shine jama’a suka taru” Jinjina kai Bakura yayi yace.
“Allah ya kyauta. Taimaka yaro ka buɗa mana hanya, mara lafiya ne damu” Da sauri matashinnan ya kutsa kai cikin dandazon mutanennan yasa aka bubbuɗa musu, suka wuce. Specialist (General Hospital damaturu suka shiga da sauri, dan anan suke ganin likita. Cikin gaggawa, ma’aikatan kiwon lafiya suka fito da gadon tura marasa lafiya, aka ɗaura Yahanasu akai. Dai_dai shigowar motar su Wakil. Gudu_gudu Nurses suka shige da Yahanasu ɗakin jinya na mata, Dr Zangina yana biye dasu a baya.
Baka jin maganar kowa a wajan, sai amon kukan Baguji da Hajja Gana, Innana kuwa, bata da kuzarin yin kuka mai sauti, hawayene kawai ke gudana a kumatunta. Wakil yana gefe yayi jigum, Bakura da Ba Modu kuwa, sai ajjiyar zuchiya kawai suke ta yawaita saukewa, iya tashin hankali suna cikinshi sosai.
“Wai a cikin ruwan da akeyi ɗazu ta shigo gidanne, a ina abun ya sameta, kuma tasan su waye, a cikinku Modu wa yarinyarnan taima wani bayani ?” Bakura ne yake musu wannan tambayoyin a jere. Ba Modu yace.
“Bakura ni kaina banda masaniya akan komai gaskiya,shigata gidan na tarar dasu a falo cikin damuwa. Innana ta faɗa miki wani abune?” Ajjiyar zuchiya Innana ta sauke sannan tace.
“Nayi yinƙurin tambayarta, amman a ɗimauce take ainun bata iya bani amsar komai ba, sai firgitata dana kuma yi” Bakura yace.
“Bulama Ƙarami a nemi ofishin ƴan sanda mafi kusa ayi report maza. Shi Wakil ya tsaya ko za’a buƙaci wani abun.
“To Ba BaKura” Sa kai yayi, ya fice da hanzari. Yana fita sai ga wata tawagar. Bagulaji da Ahmada wan Yahanasu, da Dala tafe suma a kiɗime, nan duk aka haɗu akai tsattsaye ana jiran fitowar likita. Matan suka rufu akan Innana wacce take ta faman hawaye, sai rarrashinta suke yi. Bakura yace.
“Za’ayi duk wani bincike daya kamata ayi. Wannan abun baza mu barshi ba, duk wanda aka kama da yin wannan aika_aikar wallahi bazan raga mishi ba. Maman nawa za’aima wannan cin zarafin?” Yana cikin sababin Dr Zangina ya fito.
“Amm mutum ɗaya zata iya shiga ta zauna da’ita. Anyi mata allurar bacci mai ƙarfi, sai gobe da rana zata farfaɗo. Sannan dan Allah a kiyaye yin motsi da wani abu mai ƙara, dan gudun firgitata. Bakura ku same ni a office da Modu” Bakura ya dubi Innana yace.
“Innana ke da su Baguji duk kubi Dala ya mayar daku gida. Hajja Gana ke ki shiga ki zauna da Yahanasun, in yaso saiki kwana da’ita. Mu kuma zamu je a soma bincike.” Harga Allah Innana ranta baiso hukuncin Bakura ba sam. Gani take yi a irin wannan lokacin bai kamata ace za’ayi mata wata kara ba. Ya kamata a barta kusa da ɗiyarta, wala Allah ta samu sassaucin zugin zuchiya. Ko da ta koma gidanma, me zata yi acan? Ita dai ba bacci zata yi ba, ba iya cin abinci zata yi ba. Amman tasan Bakura shine uba, Babban wa dake zartar da ko wanne irin hukunci akan kowa, kuma dole kabi ko baiyi maka ba. Duk da dai ya kasance adali mai ƙaunar ganin farin cikin kowa. Da jan ƙafa tabi ayarin su Baguji suka tafi. Hajja Gana kuma ta shiga ɗakin majinyatan jikinta a mace.
“A gaskiya wanda yai ma yarinyarnan fyaɗen azzalumine sosai, dan yayi mata muguwar illa. Sai da nayi mata ɗinki uku, ga raunuka wanda suke buƙatar kulawa, shi yasa take cikin firgici. Bacci take amman tana firgita, duk ƙarfin allurar da akayi mata. Fatanmu shine inta farfaɗo ta dawo dai_dai. Dan akwai yiwuwar ƙwaƙwalwarta ta taɓu. Amma zuwa gobe likitan kwakwalwa in yazo, za’a kaita gwajin ƙwaƙwalwa. Allah ya bada haƙuri. A wannan karon sai da Bakura ya zubar da hawayenshi sosai. Ba Modu kuwa sai cizan leɓe kawai yake yi, zuchiyarshi na tafarfasa. Babu wanda yace da kowa komai, Bakura na gaba. Ba modu na bayanshi, duk sun goya hannayensu a baya. Suna fitowa farfajiyar babban asibitin, motar ƴan sanda ta shigo, motar Bulama na gaba. Bakura yaja tunga ya tsaya, jirine ke shirin jefar dashi, da sauri Ba modu ya riƙeshi.
“Bakura kayi a hankali, kayi haƙuri ƙaddara ta riga fata, adda’ar samun lafiya zamu yi mata. Shi kuma Naseer ba lallai bane ya aureta, dan wannan lamarin babbane, ni tunda abun ya faru nake hasaso fuskar iyayen yaronnan.” Bakura bai iya tankawa ba, har ƴan sandannan suka iso garesu.
“Ba Bakura ga ƴan sandan sun iso, suna buƙatar ganin Yahanasun, kuma suna son ganin likitan daya dubata. Kuma zasu gudanar da bincike, da zaran Yahanasu ta samu damar yin magana. A wannan karon Ba modu har yafi Bakura dauriya. Wucewa suka yi ciki, su kuma su Bakura suna tsaye a wajan, har suka fito, Bulama ya mayar dasu gida. Gidan a hargitse yake sosai, duk wanda ka gani a cikin damuwa da taraddin halin da Yahanasu take ciki yake. Bakura ya wuce ɓarayinshi, Ba modu kuma ya shiga ɗakin Ya Innana. A falo ya tarad da Fanda, da Fanna data tawo gada gidan mijinta a kiɗime, sakamakon kiranta da Bulama ƙarami yayi, ya sanar da’ita halin da ake ciki.
“Fanna kece a tafe, sai kika ji abunda ya faru da ƴar uwar taki ko?” Fanna tace.
“Bawa (Baba) Naji amman a wanne halin take ne?” Zama yayi ya dubesu yace.
“Adda’arku take buƙata kawai, zata samu lafiya da izinin Allah. Sannan ƴan sanda zasu yi duk binciken daya dace, dan zaƙulo duk masu ruwa da tsaki a cikin wannan mummumunar aika_aikar. Ki daure ki koma ɗakinki, gobe saiki wuce asibitin daga can gidan naki. Gobe ƴan gidannan ma zasu je. Ina Innana?” Fanda tace.
“Tunda ta shigo ta shige ciki, ta kulle ƙofar, munyi bugun duniya taƙi ko da kulamu ne, Yaya Ahmada ma ya shigo ya ganta, amman bata bashi dama ba”
“Kuyi mata uziri kunsan a kiɗime take, dole a bita da laluma, bari in sameta.” Wucewa yayi ya barsu a falon. Kwankwasa ƙofa yayi tare da kiran sunanta. Jin muryarshi yasa ta taso da wuri ta buɗe. Hijabine a jikinta, idar da sallahnta kenan. Hannunta ya riƙe suka koma ciki, a bakin gado yai mata masauki, ya zauna dab da’ita, hannunshi a cikin nata.
“Innana nasan kwatanta tashin hankali da damuwar da kike ciki ɓata lokacine. Amman muyi haƙuri dukkanmu mu tungumi ƙaddarar data faɗa kan Yahanasu. Muyi mata adda’ar samun lafiya, da rayuwa mai ɗaurewa a gaba, kuma duk abinda ya kama na bincike, zamu gudanar dashi da izinin Allah” Cikin rauni tace.
“Yara suka ce, anga jakar Yahanasu a cikin kangon gidan Lado. Harda ƙyallen atampar dake jikinta. Dala yace kar a taɓa har sai hukuma tazo” Gabanshi ya faɗi da ƙarfi, hawayen dake shirin zubo mishi ne, ya haɗiye, yace.
“A kangon lungun gidan Lado? Kaddai wannan yaron da aka tsinci gawarshi yana ɗaya daga cikin waɗanda suka keta ma Yahanasuna haddi? Ina zuwa bari in samu Bakura, muje mu samu Dala a wajan, kafin ƴan sandan su zo” Da sauri ya fita a shashen, harda gudu_gudu yake haɗawa. Da Ba Bakura da Baana ƙaninsu, sai Ahmada, da Ba’a kaka, sai Bulama Fari. Ko wanne ɗaki suna da Bulama, ko wanne Bulama da inkiyarshi. Tare duk suka ɗunguma zuwa kangon lungun gidan na Lado. A wajan suka samu Dala, da Abokinshi Mustapha suna tsaye. Shiga cikin kangon suka yi. Ga jakarta a yashe a ƙasa, ga kyallen rigarta yagagge a ƙasa, ga tsumman da aka rufe bakinta dashi, sai jini malala a ƙasa. Suna cikin kangon, sai ga ƴan sanda da Bulama Ƙarami sun shigo. Motar ƴan sandance, ta jawo hankalin mutanen anguwa, har suka soma fitowa, sabida a tunaninsu wannan matashin daya mutu a kangonne ƴan sanda suka zo dan ganin kangon. Malam Mato ne ya shigo cikin kangon, ya dubi Ba Bakura yace.
“Alh Bakura, ashe kaima kaji abinda ya faru a wannan anguwa? Yanzu haka gawar tana gidana, yara sunje kiran ƴan sanda, ina cikin gida, Mata suka ce sunji motar hukuma ta shigo” Ɗan sanda da jin haka yace.
“Alh muna son a nuna mana gawarnan, dan akwai binciken da zamu gudanar akan gawar. Kai kuma Ayuba, a ɗauki jaka da ƙyallen kayan asa a mota.” Umarnin mai gidanshi Ayuba yabi. Daga kangon kuma, suka rankaya gidan Alh Mato dan ganin wannan gawar. Yarone saurayi santalele a kwance, kanshi a tsage, har zuwa lokacin jini na ɗan zuba, kanshi wani irin askine mara daraja, ga zip ɗin wandonshi a zuge. Wannan Kofur ya zuba ma gawarnan idanu ƙur, sannan yace.
“Alh Zamu tafi da gawarnan asibiti, in an samu iyayenshi, sai ai musu kwatance ofishinmu akwai binciken da za’a gudanar mai zafi akanshi. Ayuba a ɗauki gawarnan asa a mota.” Gawar aka ɗauka zuwa cikin mota, al’umma sun haɗu a layin anyi cirko _cirko. Suna fitowa motar ƴan sandan da Alh Mato yasa a kira suka iso suma. Kofur Madaki yai magana dasu, suka juya. Kallon su Ba Bakura yayi yace.
“Alh a lokacin da abun ya faru, Yahanasun waya soma ganinta?” Ba Modu yace.
“Mahaifiyarta ce ta ganta”
“Good, ina buƙatar ganin mahaifiyar tata, ku kuma Ayuba ku jirani a wajan motarnan. Kai Kofur madaki wajan Innana akayi, yai mata tambaoyi da dama, daga ƙarshe ya karɓi riga da hijabin jikin Yahanasu, yai musu sallama ya tafi. Ko da dare yayi, gari yayi tsit, idanuwa da dama bacci sam ya gagari idanuwansu. Ba Bakura, Innana, Ba Modu, kusan akan sallaya suka raba darensu, suna roƙon Allah kan Allah ya toni asirin duk wanda ke da sa hannu a cikin wannan lamarin. Innana a kan sallaya ta kwana, kuka kuwa tayi shi, har fuskata ta kumbura tayi suntum da’ita gwanin tausayi.” Tun sassafe, gidan ya tashi da kaya_kaya kamar yadda ake tashi a kullum. Mata da yaran gidan, sai zuwa ɗakinsu Yahanasu suke, suna sake jajantama Innana halin da Yahanasu take ciki. Da misalin goman safe sai ga Mama Gana ita da ɗanta Ya Ari, sun iso daga Yobe. Ƙanwace ga Ba Bakura, Ya ga Ba Modu, ita ta cika nono ya karɓa. A ɓanrayin Ba Bakura ta sauka. A falonshi ta yada zango sai sharar hawaye take ta faman yi.
“Yanzu Ba Bakura ashe abunda ya faru kenan? Oh na tausayama wannan yarinya.” Ba Bakura yace.
“Waya faɗa miki Mama Gana?” Cikin kuka tace.
“Bulama Fari ne ya faɗamun a waya, shine fa nace bari in tawo, ayi komai dani zaifi. Ina shi Modu ɗin?”
“Modu yana cikin gida, gara da kika zo ma. Dan inason in Yahanasu Allah ya bata lafiya akwai taron da nake son haɗawa a gidannan, akan ita Yahanasunne kuma, kinga gara da kika tawo” Tana share Hawaye tace.
“Ina Hajja Gana banji ɗuriyarta ba. Kafin ya bata amsa, matan ƙannen nata suka shigo da sallama dan su kwashi gaisuwa. Mama Gana macece mai zafi da saurin fishi, gata da hargowa, haƙuri kowa yake yi da’ita. Dan inta zo daga Yobe saita gundiri kowa a gidan da jarabarta. Sai dai tana da kirki, gata da son sada zumunci. Shi yasa ko aure ne ya taso a gidan, ita ke shigema matan ƙannen nata gaba. Gaggaisawa akayi, aka shiga jajantawa juna.
“Ohh Innana dare ɗaya harkin faɗa wallahi. Ki dinga sassauta ma kanki, adda’a zamu bita dashi, Allah ya toni asirin duk wanda ke da sa hannu a wannan lamari. Ƙannen nata ne suka yo sallama suka shigo. Da yara mazan gidan. Duk ɗaya bayan ɗaya tai ta tambayar yaran iyalansu. Daga baya matan ƴaƴan nata suka shigo su uku suka gaisheta. Su Dala basu yi aure ba tukunna. Amman an tsaida lokacin dama harda su Fanda, da Yahanasu a cikin waɗanda za aima auren, yara kusan goma za’a aurar. Ba Bakura yace.
“Modu ai saimu hanzarta muje asibitin sha ɗayan rana tayi. Wakil yana can ya kai musu abinci.” Shisshiryawa suka yi, mota uku suka nufi asibitin. A hakanma, sai da aka ba ƴan matan gidan Haƙuri kan cewa inta dawo gida sa ganta.”
ZURIYAR GIDAN BULAMA BUKAR BULAMA…….✍🏻
[26/07, 2:34 p.m.] +234 806 874 8984: MAI IDO A TSAKAR KA
( DUNIYA)
GAWURTATTU UKU
BADI’AT IBRAHIM MRS BUKHARI ( B4B)
2
Wannan labarin ya faru a gaske. Babu wani abu dana ƙara, saima waɗanda na ɗan sakayesu, dan gudun ɗaga ma masoyana hankali.
Sadaukarwa garuku iyaye mata. Duk wata uwa ta duniya wannan littafin sadaukarwa ne a gareta.
Gargaɗi.
Ban yarda a sarrafamun littafina ta ko wacce siga ba. Yin hakan take dokace, a kiyaye.
Nasiha. ( Mu guji ta’amali da miyakun ƙwayoyi domun kare lafiyarmu. Wannan saƙone daga hukumar yaƙi da sha da fataucin miyagun kwayoyi)
Saƙon gaisuwata
Zuwa gareku
Maman Khairat
Ummu Nabeela
Maman Yasser
Maman inteesar
Jinjinar ban girma a gareki.(Ambassador)Rashida Adamu Abdullahi mai sa’a, kuma women lida ta ƙungiyar 13_13, bugu da ƙari ƴar gwagwarmayar ƙwato hakkin mata, ƴar siyasa, kuma ƴar kasuwa. Shugabar ƙungiyar Mata Jarumai Association of kannywood atis
ZURIYYAR GIDAN MARIGAYI BULAMA BUKAR BULAMA.
Shine mahaifinsu Ba Bakura. Shi cikakken Babarbarene ( Kanuri) Gaba da bayanshi, mazauna Damaturu. Auren zumunci suka yi shi da Matarshi mai suna Yahanasu. Kasancewar Baburawa akwaisu da ƙabilanci, aurensu kuma da tsauri, hakan yasa wasu yaruka basu fiye aurensu ba,.Su da Shuwa arab, banbancin al’adunsu kaɗanne, sunyi matuƙar kama a al’adance sosai.Bulama ɗan boko ne sosai, manajer ne a bankin first bank dake garin DamaturuYaranshi Biyar huɗu maza sai ɗaya mace. Bakura shine babban ɗan Bulama, wanda ake kira da Ba Bakura, Ba ko Bawa yana nufin ( Baba a yaren Kanuri. Matarshi ɗaya itace Hajja Gana. Mata mai sauƙin kai da son mutane. Itace suruka ta farko a cikin gidan Marigayi Bulama. Yaran Ba Bakura biyar. Bulama Babba shine ɗanshi na farko, Ma’aikacin banki ne shima, ya gado takwaran nashi. Yana zaune a garin Kaduna da matarshi mai suna kofur Zubaina, sai yaranshi biyu mace da namiji. Macen sunanta Maryam taci sunan mahaifiyar matarshi Zubaina. Namijin kuma sunanshi Bakura suna kiranshi da Bawa. Bulama Babba shine kaɗai yake auren bahaushiya, kuma shine kaɗai yabar garin Damaturu da zama, sai dai ya shigo ziyara. Daga baya ma ziyarar ta gagara, ko waya saiya shafe fin wata biyu bai ɗaga waya ya kira iyayenshi ba. Aike kuwa da duk wata sai yayo aiken kuɗi masu tsoka, duk iyayenshi sai an bibbisu da kuɗinnan, ba dan basu dashi ba, sai dan biɗar albarkar iyaye, kuma shike riƙe da gidan ada, kasancewarshi babban ɗa a gidan. Ya taso cike da soyayyar ƴan uwanshi sosai. Amman matarshi ta shiga ta fita ta raba shi da kab ƴan uwanshi, babu mai zuwa gidanshi, tunda baya neman mutane, kuma ko an kirashi sai yayi ra’ayi yake ɗauka. Ko da yaushe Hajja Gana a cikin damuwa da ƙunar zuchiya take, bata jin daɗi sam yanda mace ta rabata da ɗanta data reni cikinshi harna tsawon wata goma sha biyu, yaron da sai tiyata akayi mata aka cireshi a jikinta, ta kuma sha baƙar azabar jinya. Ko da yaushe a cikin hawaye take. Ba Bakura shi kuma ko da yaushe a cikin bata haƙuri da tausarta yake. Wannan kenan.
Sai mai bi ma Bulama Gunsum, matarshi ɗaya mai suna Yalewa, sai ɗiyarsu ɗaya mai sunan mahaifiyarsu, suna kiranta da Ba gana. Lauyan gwamnati ne shi. Sai mai bin Gunsum. Bukar, Shi bashi da aure, yanzu ne dai ake shirin yin gagarumin bikinsu, shi ɗan kasuwane babba a babbar kasuwa, yana da shagunan suturu, yana da shagon kayan ƙwaliya da shafe shafe na mata, kasancewar fannin kasuwanci ya karanta. Sai bai binshi itace Fandau Babba, tana gidan mijinta tana aure a Yobe, ita kuma malamar makarantar sakandare ce. Sai ƴar Auta Aisa ita kuma a wani kamfani take aiki, itama kasuwancin ta karanta, tana aure a Damaturu, soja ne mijinta, suna zaune a barrak.
Sai mai bin Ba Bakura itace Mama Gana. Tana aure a Yobe itama, yaranta Huɗu dukka maza. Yurom ne babba, sai Ya Ari, sai Mainam, sai Bulamanta. Principal ce a Babbar makarantar mata dake Yobe. Masifaffiyace ta bugawa a Jarida ( maman Yaseer kanta ta sara mata) Sai dai tana da kirki da son ƴan uwa sosai, kuma kasancewarta ita kaɗaice mace a cikin ƴan uwanta, sai suka ɗaurata take jan ragamar auren yaran gidan, itace haɗa akwatuna, itace gyaran Amare, da siyan kayan ɗakin amaren. Maza kuma ita ke haɗama matansu akwati, sannan da ita ake komai dai.
Sai mai bi mata Ba Modu. Yaranshi Takwas, matanshi biyu Innana itace uwar gida. Yaranta biyar. Bulama Baƙi shine Babba a ɗakinta. Likitan ƙashine a wani asibiti mai zaman kanshi, sai Wakil, shi kuma nurse ne a wani asibitin shima mai zaman kanshi sai Yahanasu, ita kuma ƴar jarida ce, tana aiki a gidan talabijin dake kan tauraruwar ɗan adam, lamta ta ɗari da tamanin da biyu. Fandau ƙarama, malamar makaranta ce itama, tana da aure. Sai Fanna Wacce bata soma aikin ba tukunna, kammala karatun nata kenan. Wakil da Yahanasu, da Fanna ne basui aure ba a ɗakin. Kuma suna daga cikin waɗanda za’a haɗa a aurar dasu. Surukan gidan duk suna cikin gidan, gidane mai bala’in girma wannan kenan.
Sai kishiyar Innana mai suna Bugulaji, ita yaranda uku maza mace ɗaya. Ahmada shine babba, shike taimakon mahaifinsu da kula da gidan gonarshi, yana riƙe da ɓangaren masu gasa kifi su jera a kwali, shike kula da kifayen da ake kiwatawa, shi ya zaɓi taimakon mahaifinsu, amman yana da kwalin digri ɗinshi a fannin kanikanci, yana ɗaukar albashi mai tsokar gaske daga wajan mahaifin nashi, kasancewar kamfanin bushasshen kifin Ba Modu babba ne sosai. Ya na da mata da yaro ɗaya. sai mai bi mishi Dala, shi kuma likitan idanune, baida aure, suna daga cikin waɗanda za’a aurar, shi da Autarsu. sai autarsu Yabulu, ita kuma yanzu take kan haɗe digri ɗinta a fannin Jarida.
Sai mai bin Ba Modu, Baana, matanshi biyu, Baguji, da Yana. Yaransu bawai. Mata huɗu maza uku. Ya Sufaim itace babba, sai mai bi mata, Aisa, Bulama ƙarami, Ba’a Kaka, Ya gana, ya gaji. Dukkansu suma ma’aikatan gwamnati ne. Tsabar son bokon wannan familyn ba’a aurar da yarinya har sai ta kammala digrinta na farko, ta soma aiki sannan sai tayi aure. Kuma basa bada auren ƴaƴansu mata a waje, mazan ma a cikin family suke zaɓa. Family ne mai kyau, da daɗi, ko wanne a waye yake. Basu da tarin dukiya mai yawa, amman suna da rufin asiri sosai. Kab matan yaran gidan suna cikin gidan tare da yaransu suma, waɗanda za’a kuma aurowar ma anan gidan zata zauna. Suna da tarbiya sosai yaran gidan, cikinsu ba wanda baiyi saukar Qur’ani ba, gasu da girmama juna sosai, ko wanne ɗaki akwai Bulama, kuma ko wanne Bulama yana da inkiya. Ba Bakura shine jagora kuma jaraba, shike riƙe da ikon gidan, sai umarnin da ya bayar ake zartarwa. Wannan kenan”
Dawowa labari:
Yahanasu.
Da kuka na farka da safennan, banda firgita da iface ifacen dana dinga yi cikin dare. Da dama jama’ar dake ɗakin suna jinyar marasa lafiya, gani suke kamar makarai ke damuna. Tsabar ɗimuwace, da raɗaɗi, ko ina ciwo yake yi mini. Hajja Gana tayi kuka harta gaji, ko rintsawa ban barta tayi ba.
“Yahanasu wannan kukan ya’isa haka zaki iya jama kanki wani ciwon kuma a ɓata goma ɗaya bata gyaru ba. Ga Ya Hajja Gana kin hanata cin abinci, kema babu abunda kika saka a bakinki.” Wakil ne yake mun Magana cikin sigar rarrashi da kwantar da kai. Hajja Gana tace.
“A’a Wakil batta ta koka, ni kaina kwana nayi ina faman kukan tausayin Yahanasu. In sha Allah za’a gano wanda yai mata wannan aika_aikar. Ƴan sandan kace suna hanyar zuwa ko?” Ta tambayeshi cikin sigar taushi. Kai ya ɗaga mata halamar “E” Ni dai sai faman kuka nake yi kamar wata ƙaramar yarinya”
Hango su Mama Gana nayi, da su Ba Bakura, da sauran ƴan gidanmu. Wani irin yam_yam nake ji a jikina, takurewa nayi waje guda, na harhaɗe ƙafafuna. Ji nayi na muzanta, ina jin kamar tsirara kowa ke kallona, ina ganin kamar suna ganin mikin dake ƙasanane. Su kansu ganin yanayin kunya da tsarguwar da nayi, ya kaɗasu, sai sharar hawaye matan suke yi. Ba Bakura sai ajjiyar zuchiya kawai yake faman yi, idanunshi sun kaɗa sunyi jawur. Ya Innana ta matso kusa dani tana rarrashina da muryarta wacce take ƙarfafani. Take wani dangana da tawakkili ya saukarmun, hawayena na dinga ƙoƙarin sharewa, amman sai sabunta kansu suke yi.
“Hajja Gana kunci abinci kuwa?” Ba Bakura ke tambayarta.
“Babu wanda yaci abinci, ko runtsawa banyi ba. Yahanasu firgita tai ta yi da daddare, har daddanneta ma’aikatan jinyar suka yi, da ƙyar ta dawo nutsuwarta da naita tofeta da adda’a.” Mama Gana ce ta matso gadon da nake kwance ina sauke ajjiyar zuchiya, na kasa ɗagowa in kalli kowa dan wata kunyace take kamani.
“Taimaka mun Innana ki ɗagata ta jingina, tasha tea. Sai a nemo ruwan zafi ta gaggasa jikin nata” Ya Innana ta zaunar dani, ta jingina matashi a bayana. Mama Gana da kanta ta bani tea nasha, badan inason in sha ba, sai dan ganin na rage ma iyayena damuwar da suke ciki a kaina. Ƙwaƙwalwata ce, ta haskomon sanda wanna matashin ya keta rigata, yake shan ƙirjina.
Ahhhhhh” Na saka ƙara mai doɗe dodon kunnuwa, ƙoƙarin durowa na ya soma yi. Su Bulama baƙi ne suka daddanneni, inata fisge fisge. Ma’aikatan kiwon lafiyane suka rufu a kaina. Allurar bacci suka zurkuɗa mun, luu naji bacci na ɗibana, dishi dishi nake ganin dangina.”
Ba Bukura:
“Modu muje gida dukka maza mazan mu sauke ma Yahanasu Qur’ani mai girma, muyi addu’o’i ayi sadaka, mu yi tawassali da wannan aiyukan Allah ya dawo mata da nutsuwarta. Wakil kai kuma na wakiltaka kaji da ɓangaren ƴan sanda. Hajja Gana da Innana ku ku zauna da’ita. Bugulaji ku kuma a koma gida aita taya Yahanasu da Adda’a. Zanga likita kafin mu tafi” Yana gama magana yayi gaba, Ƙannenshi suka bi bayanshi, saida suka bar ɗakin matan suka fita su kuma.
“Dr yaya halin da yarinyarnan take cikine? Hankula duk sun tashi” Dr ya dubi Ba Bakura yace.
“A taya ta da adda’a. Ƙwaƙwalwarta babu wata matsala. Dan jiya dole likitan ƙwaƙwalwa saida yazo ya dubata. Ɗimaucewa tayi, wani sa’in yana iya fin hauka ma, sannan a tsorace take, tsoronne ya sanyata cikin ɗimuwa, a sakamakon abunda ya faru da’ita. Sabida ƙwaƙwalwar tata, tana hasko mata abunda ya faru da’ita, shi yake haddasa mata wannan firgita da ihun. Sannan daɗin daɗawa tana cikin zafin ciwo sosai, dan taji raunuka manya. Sai dai muna iyakar ƙoƙarinmu wajan bata kulawa.” Jikinsu a mace mus suka bar asibitin. Gabaki ɗaya manya da yara, maza da mata, Ba Bakura yace su je falonsu ayi saukar tare. Kasancewar suna da yawa, yasa nan da nan suka sauke Qur’ani mai girma. Sukaita ma Yahanasu adda’a. Ba Bakura yayi tofi a ruwa a kofi, ya zuba a cikin gora, yace akai Asibiti, in Yahanasu ta farka a bata ta sha, a shafe mata jikinta da ruwan tofin. Sannan ya wakilta Bulama ƙarami a yanka rago, ayi sadaka, sannan a nemi miskinai a basu sadakar kuɗi. Duk yasa aka harhaɗa kuɗaɗen sadakar. Zukatan ƴan gidan duk a jagule. A cikin wannan yanayin na damuwa, gidansu Nasiru mai shirin auren Yahanasu suka ji abunda ya faru da Yahanasu. Ba shiri mahaifin Nasiru ya wakilta mahaifiyar Nasirun akan taje gidan taji me ake ciki. A kunyace Bagulaji tayi ma mahaifiyar Nasiru bayanin halin da Yahanasu take ciki. Kuma tace zasu je asibitin zuwa dare su dubo Yahanasun. Lokaci ɗaya zancen Anyi ma Yahanasu fyaɗe ya bazu a anguwa, labari har ma’aikatar su Yahanasu sunji labari. Zuga guda suka je dubiya asibiti. Amman sun tarar da su Hajja Gana a waje, a zazzaune, dan ba lokacin dubiya bane lokacin, jajanta musu sukayi, suka ajjiye ledar lemo da ayabar da suka harhaɗa kuɗi suka sai mata.
Ofishin ƴan doka:
Wasu Tsofaffi mata da miji na gani zaune a ofishin D p o matar sai matsar hawaye take yi. Shi kuma namijin sai ajjiyar zuchiya yake saukewa.
“Kuka ba naki bane, yin wannan kukan yana nuni da cewar kina bin bayan mummunan aikin da ɗanki ya aikata ko? Fyaɗe yayi mata fa, ita kuma zafin keta mata haddi da yayi yasa ta kwaɗa mishi dutse ya mutu. Ai yafi mishi sauƙi daya mutu, dan da iyayen yarinyar daya ma ɗanyan aikinnan sun kama shi da rai, da ɗanye zasu cinyeshi.” Mahaifin matashin da yayi ma Yahanasu fyaɗe yace.
“Ranka shi daɗe, maganar gawar yaron, a taimaka mana muje asibiti mu ɗauka, ayima yaronnan sutura. Ko a yanzu yaga aya, tunda da yanzu yana cikin makwancinshi, mutuwar wulaƙqnci da ƙasƙancin da yayi ma ya’isa, mu kammu dama ya riga ya zame mana ƙarfen ƙafane, ni bana jin takaicin mutuwarshi sam, na dai fi son ayi mana alfarma a bamu gawar mu binneta, abunda ya shuka shi zai girba ba, kuma duk tsuntsun da ya ja ruwa shi ruwa kan doka.” D P O yace.
“Zaku iya ɗaukar gawar ɗanku, tunda likitoci sun gama bincike, maniyyin da aka samu a jikin yaron, maniyyin ita yarinyar da yaima fyaɗene, ƙwararru sun auna. Da ƙyar aka samu yarinyar ta tabbatar ma mai jinyarta, cewar ita ta kashe yaron. Babu wata doka da zata yi aiki akai, sabida a cikin ɗimuwa da fitar hayyaci take, babu wata doka da zata hau kanta, domun a hanyar ceton nata ran ne ta kashe taƙadarin ɗanku dake neman tata rayuwar, kuma duk mutumin da yayi kisa domun kuɓutar da kanshi daga kisa, bashi da laifi, kamar yadda ba’a shari’a da mahaukaci, haka ba’a zartar da hukunci akan ire_iren su Yahanasu. In kuma kuna ganin a turaku kotu to” Cikin sauri iyayen wannan mamaci suka ce, babu wani kotu da zasu je, su sun yafe, kuma a ta ya su roƙon gafarar iyayen Yahanasu. Haka suka fita harda godiya a hakanma.Da haka wannan zancan ya mutu mus, ba’a ƙara tado dashi ba. Lokaci yaita tafiya cikin damuwa da zulumi. Babu laifi Yahanasu tana samun sauƙi, kuma ta dawo cikin hayyacinta. Sai dai ta zama shiru_shiru bata son magana sam. Ranar da iyayen Nasiru suka zo dubata, kasa magana tayi dasu sai hawaye, Nasiru ya tausaya mata ganin yanda tai wata iriyar muguwar rama, kamar ba Yahanasu ba. Kwananta goma a asibiti aka sallameta, suka dawo gida, da jikin nata ya ɗan yi ƙwaɓi sai ta soma yin azumin daya wajabta a kanta na kisan kai da tayi.
Wannan kenan.
YAHANASU:
Ina kwance akan gadon Ya Innana ina karanta littafin addu’o’i, Ya Innana ta shigo da sallama, ita da Fanna. Waje ta samu ta zauna a kan gadon, Fanna kuma ta zauna a kujerar dake cikin uwar ɗakin.
“Yahanasu, abunda zan sake somawa dashi shine. Haƙuri da yarda da ƙaddara. Bana jin daɗin ganinki a cikin wannan yanayin. Sai ciwon damuwa ya kamaki ai. Jiya Yaguji har ɗakinnan ta shigo ta sameki, amman kinƙi ce mata komai. Kiyi haƙuri abunda zai faru ya riga ya faru, saimu rungumi ƙaddara baki ɗayanmu, ni na fiki jin zafin yadda rayuwa tayi dake, amman ki sani hakan ba wai yana nufin ƙarshen rayuwarki ba ne. Jibi akwai taro da Ba Bakura ya tara, duk ƴan uwa za’a taru. Abunda ya tsayar da Mama Gana kenan bata koma ba. Maganar janye aure da iyayen Nasiru suka yi, suka ce a dakace su kuma. Karya baki tsoro, rayuwarnan cike take tab da ƙalubale, kiyi haƙuri, hakan karya dame ki, in ma rasa Nasirun ki ka yi, Allah zai ɓullo miki da mafiyinshi, kuma in dai har ya gujeki, ki sani dama ba masoyinki bane, sai ki gode ma Allah da ya sa akai walƙiya.” Murmusawa nayi na dubi Ya Innana. Ni dama aure da sha’anin maza duk ya fice mun a raina. Inason ni kaina a bani lokaci in samu cikakkiyar nutsuwa tukunna. Mikin dake zuchiyata dai har abada bazai gogu ba nasan wannan.
Ya Innana, na karɓi dukkan ƙaddarar da rayuwa zata zo mun dashi a gaba ma. Allah shike tsara mana rayuwa ba mu ba. Duk yanda kuke so haka zanyi. Maganar dakatar da maganar biki da iyayen Nasiru suka yo aike kuma. Ya Innana, ni a tawa fahimtar iyayen Nasiru basa son ya Aureni ne, shima kanshi ya dena sona, ƙila dama ba son gaskiya yake yi mun ba, gangar jikina kawai yake so. Sun mance cewar babu wani bawa dazai iya tsallake wani abun da kanshi, face wanda ubangiji buwayi gagara misali ya tsallakar dashi ba. Ni a sanar da iyayen Nasiru cewar na haƙura na janye gabaki ɗaya. Tun kafin su su ce muku hakan, dan nasan zaku ji ciwo gaya. Ku taya ni da adda’a Ya Innana, ina cikin damuwa mai yawan gaske, zuchiyata zafi take yi mun” Ya Innana ta dubeni da kyau tace
“Naji daɗi da kika fahimci inda surukanki suka dosa, janyewarki, da danganarki ta matuƙar faranta mun. Kuma nasan lallai turbar haƙuri da juriyar dana ɗauraku akai, lallai kun hau. Na sani na baku tartibiyar tarbiyya da akeson ko wacce uwa ta baiwa ƴaƴanta. Mun baku ilimin Arabi da Boko. Yahanasu ni kaina zanfi son ki manta da Nasiru ki shiga sabuwar rayuwa. Allah yayi muku albarka duka” Da Ameen” muka amsa ni da Fanna. Haka dai lamurana suka ci gaba da tafiya. Duk wani jin daɗi da ake ganin jin daɗine, ni bana sonshi, bana kallonshi ma a matsayin jin daɗi. Bana son hayaniyar kowa, kuma ban cika son fitowa in haɗu da jama’a ba, tsoron kowa nake ji, gabana faɗuwa yake yi, ko da ƙaramin ƙara naji a gefena, ko wata sowa. Wayata ma kashewa nayi, na tura a jakata. Yau gidan namu an tashi da shirin gudanar da taron da Ba Bakura ya haɗa. Har munyi wanka, mun karya Ba Modu kawai muke jira.”
Ba Bakura:
Waya ce a hannunshi, yana ta faman kiran wayar Bulama Babba. Amman tana ringin ba’a ɗagawa. Sunturi ya shiga yi a babban falon nashi. Idanunshi sun kaɗa sunyi jawur. Ya rasa meya canja mai tunanin ɗanshi, da har ya gujesu haka. Aita kiran wayarshi bazai ɗaga ba, kuma shi bazai kira ba. Zuwa duba iyaye da dangima sai ya bushi iska yake yi. Zama yayi akan kujera, yana kallon lokacin da Bulama Babba yake rarrafenshi a falon. Da kuma lokacin da yake raba dare yana aiki a falon. Yarone mai ƙulafacin iyaye da ƴan uwa sosai. Ko lokacin da ya tafi Kaduna karatu, ba’ayi tunanin zai iyaba ma. Amman a haka ya daure, sai dai fa kullum sai yayi kiran waya. Lokacin da ya soma ɗaukar albashi kuwa, ƙannenshi mata sunji daɗi sosai, mutum ne wanda abun hannunshi sam basu dameshi ba. Wani irin jiri Ba Bakura yake ji daga zaune, sanadiyyar damuwar juya musu baya da Bulama Babba yayi hawan jini ya dokeshi, ko da yaushe a cikin shan magani yake. Sabida shaƙuwarshi da Bulama Babba ta dabance, dan aboki ya ɗaukeshi ba ɗa ba. Hajja Gana ce ta shigo cike da sallama, tana sanye da lafaya mai kalar baƙi da fari, tasha ƙunshi baƙi, ga ƙamshi na tashi ta ko ta ko ina a jikinta. ( Kunsan kanuri ma ba baya ba wajan ƙamshi da ƙunshi) Kallon me gidan nata tayi, kallon shari’a, kawar da damuwarta tayi ta nemi waje ta zauna, sannan tace.
“Bulama ya ɗauki wayarka kuwa, ko har yanzu matarshi bata bashi izinin ɗaukar wayarmu bane?” A raunace take maganar muryarta tana rawa tamkar mazari. Kallonta Ba Bakura yayi, yace.
“Tun jiya nake faman kiran wayarshi, har yau bai ɗaga ba, yanzu na gama kiranshi amma ina. Bana neman dukiya a wajan Bulama Babba dan da dukiyata yaci yasha, yai karatu, har ya zama mutum, yayi aure. Tunda matarshi da yaranshi yana ganin sun isheshi rayuwa, ai shikenan. Bazan sake ɗaga waya in kira Bulama ba, ko zuwa yayi karki sake ki kawoshi gareni, in kuwa ki ka yi Hajja Gana zaki ga fishin Bakura. Duniya ce ai mai ido a tsakar ka, akwai ranar da zai gane babu abunda yakai Ahali daɗi.” Tari ne yaci ƙarfinshi. Hajja Gana kuwa, sai haɗiɗiyar zuchiya kawai take yi, ta rasa me zata ce. Iya damuwa da tunani, harma da kukan babu wanda bata gaji dayi ba. Tana ji tana gani, ɗanta data ɗauki ragamar kula da rayuwarta, yau an wayi gari ya fifita wata mace sama da’ita mahaifiyarshi. Sallamar Ba Modu da iyalanshi ne ya katse musu damuwar da suke ciki. Sun zauna ba’a jima ba, Mama Gana ta shigo. Ba Baana da nashi iyalan suma sun shigo. Falo ya cika dam da iyaye da yara. Kowa ya saurara yana jiran Ba Bakura.
Ba Bakura:
“Modu ka buɗe mana wannan taron da adda’a domun kawar da shaiɗan, da naiman albarka.” Ba Modu ya tashi tsaye ya gabatar da adda’a mai tsayin gaske, aka shafa ya zauna. Falon ya sake ɗaukar shiru na wasu daɗiɗu kowa da tunanin dake cikin zuchiyarshi. Ba Bakura kawai ake saurare ya soma magana……✍🏻
Mrs Bukhari ce