KWANKWASON JIMINA!!
(MAI WUYAR SHAFAWA)
🦩🦯🦾
✍️: MX
ZAFAFA BIYAR 2024
BOOK TWO
paid page :003
__
“Sunana Imran Abbas… Kuma ni ma dalibi ne kamar ku acikin jami’ar nan.”
“Allah sarki… Imran, Ni sunana Layla wannan cousin sister na ce sunanta Nawraah”
“Nawrah… Layla… Mashaa Allah sweet names” ya fada Yana murmushi dik kuwa da a tsorace yake maganar da yake musu.
Suma murmushin suka masa. Gaba yayi yana mai nuni da wani tankamemen gini me hawa uku yace,
“Nan library ne a first floor… Second floor hawa na biyu kenan shi Kuma gymnasium ne. Sai third ko ince last floor. Shi Kuma cafeteria ne. Amman cafeteria din bata kowa bace”
“Ban fahimci me kake nufi na?” Layla ta tambaye shi tana duban sa da kyau
Nawraah ma idanunta na kasa tana son jin Karin bayani daga gare shi.
Imran ya matsa kusa da su cikin muryar rada yace,
“Jami’ah ce ta yayan masu kudi. Yayan masu hannu da shuni. Duk Wanda kika gani a makatantar nan Wanda badan scholarship ba to ubansa wani ne ko Kuma dangin su sunada hali sosai. Don haka yayan masu kudin sune ke cin abinci a wannan caferia din. Shine Kuma suke amfani da gym din wajen motsa jiki kenan. Sannan sune masu amfani da library din”
“Come again. Bangane me kake nufi ba” Nawraah ta tambaye shi cikin gaskiyar ta
“Shine dai. Nima na kasa ganewa me kake nufi. Na dauka ai makaranta da abubuwan da ke cikin ta mallakar dalibai ce da maluman su da maaikatan dake karkashin su. Me kake nufi?”
Imran ya girgiiza Kai da sauri yana duba bayan sa a tsorace ce ji yake tamkar ana tahowa ta bayan sa. Layla ta dube shi tace,
“Wai wani abunne? Naga tin dazu kaketa dube dube lafiya kuwa? “
Imran ya girgiza musu kai yana ya yafito su da hannu sukayi gaba yace,
“Makaranta ce dake gudanar da karatun ta tsakanin masu hannu da shuni masu kudi kenan da Kuma masu karamin hali Irina kenan marasa gata.”
Layla ta daga Kai tana duban sa tace,
“Na tabbata Kafi mu gata Imran. Amma dik da haka alhamdu Lillahi muna yiwa Allah godia a dukkanin halin da Mika tsinci kanmu…”
“Allah shine ahun godia” Nawraah ta fada tana kada Kai cikin tabbatarwa.
Imran yayi murmushi yace,
“To dika Allah ya bude mana ni da ku din. Don tabbas Dr Bintu tace akwai new students da zasu zo makarantar . Dama weekly ana daukar dalibai goma daga different departments zasuyi activities kala kala zaai grouping dinsu. To ni sai sunana ya fado akan Wanda zai nuna sabbin dalibai gurare na ciki da wajen makarantar . Sunana Imran Abbas kamar yadda na fada a baya. Iyaye na ba kowa bane fyace marasa karfi masu neman abunda zasuci yau da gobe. Na samu scholarship din makarantar nanne shekarun baya tun kan na gama secondary school. Jami’ar nan ta tà saka gasa Wanda yazo na daya zuwa na uku a makarantar sakandire tanan birnin, Amman mallakin gwamnati. Duk daliban da sukaci gasar ta lissafi wato mathematics. Zaa basu gurbin karatun a wannan jamia mai tarin iyalan masu kudi. Ai kuwa sai Allah ya nufa naci. Ni da sauran dalibai hudi da mukayi gasar tare.duk jami’ar tabamu gurbin karatu kyauta ba ko kwandar mu. Sauran dalibai yan ajinmu da mikaci gasar aka kawo mu nan makarantar tare. Dauki da dai sai dukkanin su su hudun suka dena zuwa saboda tsabar mugunta da nuna kyama da kyara da yaran masu kudin ke mana. Dik kuwa da badukan su bane. Amman kaso cassain duk suna lacking manners. Allahul Musta’an.”
“SubhanAllah menene haka suke yi da har daliban da aka kawo na scholarship kyauta suka dai na zuwa?”
Nawraah ta samu kanta da fada masa wannan tambayar…
INA MASOYAN ZAFAFA BIYAR?
KU MARMATSO KUSA…🔊
ZAFAFA BIYAR 2024
ZAFAFA BIYAR!!!
ZAFAFA BIYAR!!
ZAFAFA BIYAR!!
SHIN YAN UWA KUNA DA LABARIN ZAFAFA BIYAR DINKU SUN SAKE ZUWAR MUKU DA WATA TAFIYAR LITTAFAN SU MASU MATUKAR MA’ANA DA ILIMIN DARUSSAN RAYUWA?
YA KE YAR UWA KADA KI BARI A BAKI LABARI… DOMIN DA A BAKI GWARA KI BAYAR…WAI AKACE ZUWA DA KAI YAFU AIKE
GA SUNAYEN LITTATTAFAN WANNAN TAFIYAR… CIKE SUKE DA ILIMIN DARUSSAN RAYUWA KI KOYA KUMA KI GYARA DA KAN KI..CIKI HARDA ZALLAR KAUNA TACACCIYA MARAR GAURAYE
1
AMEENATUH🧕💖: MAMUH GEE
2
TSUTSAR NAMA (ITAMA NAMA CE)🐛👣:BILYN ABDULL
3
GUDUN KADDARA🏃🐾:SAFIYYAH HUGUMA
4
KWANKWASON JIMINA(MAI WUYAR SHAFAWA)🦩🦯:NANA HAFSATU (MX)
K’K’J
(M/W/S)
✍️:MX
4
:::::::::
Imran ya bude baki zai yi magana ke nan sai ga wasu yammata nan su uku sun taho ko wacce sanye cikin manyan kaya Wanda kallo daya zaka yiwa kayan jikin masu ka tabbatar masu tsada ne
Rike kowannen yakeda manyan manyan jakan ku na masu matukar tsada.
“Imraan….”
daya daya cikin yammatan da suka taho ta fada. Tana wani tafiya ahankali tamkar mai tsoron kasa.
“Naam…. Ga ni”
ya amsa da sauri ya rude layla da Nawraah suka hada idanu suna bun Imran da yammatan cike da kallon mamaki daya gauraye fuskokin su
“Ina assignments din? Ka mana kuwa?”
Cewar wata matashiyar budurwa daga gavan sauran tana mai mika masa hannunta alamar ya bata.
Imran ya saka hannunsa a keya yana shafawa muryar sa na rawa. Tamkar zai durkusa alamar ban roko yace,
“Dan Allah kuyi hakuri yau ne ranar aikin volunteer na.”
Dogon tsaki taja tana karkada Kai tace,
“Me kake nufi? Baka yi ba ko Mai?”
Muryar sa na Mai cigaba da rawar da take yace,
“Zanyi zanyi idan na karasa”
“What? Me kake nufi eh? ” ta Kai hannu zata doke shi kenan.
Wata budurwa itama sanye cikin tsadaddun kaya na masu kudi ta karasa wajen tana janye hannun ta tace,
“Calm down….Pele o… Imran” Ta karasa fada tana murmushi
Imran da gaban sa ke dukan uku uku yana harbawa da Sauri ya dubeta da wutsiyar idanunsa ya sauke da sauri yace,
“Kiyi hakuri b…”
“Ssshh ya isa haka Imran. Karka damu kaji?” Ta yi zaurin katse shi tana murmushi
Imran ya sake dagawa da Sauri ya dubeta yana matsa yatsun hannuwan sa yace,
“Dan Allah ni dai kuyi hakuri.musanman ke ma “
“Imran calm down please.kasan dai ba Wanda zan daka ni ko?trust me”
Ya girgiza Kai dasauri yace,
“Zanje nayi yanzu na kawo takardun ma”
“Imran haba mana…. Ah new students dinne wannan?” Ta fada tana duban su
Imran ya daga mata Kai alamar eh sune..Layla da Nawraah sude sun zuba musu ido suna duban su. Baki daya sun daure musu jiki sun kasa gane menene alakar su wadannan yammatan da Imran? Kuma kamar yana shakkar su sosai ganulin yadda jikinsa yake rawa tamkar mazari, Yana Kuma basu hakuri kamar zai musu sujjada. Kana dubansa Kuma kasan Yana cikin firgici Mai tsananin tashin hankali .
Yammatan suka karasa wajen su. Musanman wadda tazo daga haya din ta matsa daf dasu Nawraah tana duban su.
Ta saki wani tattausan murmushi tana gyara zaman jakar jikin Nawraah dake kafafarta tace,
“Sannun ku fa zuwa jamiar mu…. Ko zan san sunayen ku. Forgive my mistakes. Sunana Ilham ana Kirana da Lily wannan course mates na ne Kuma kawaye na ne na amana…. Iman, Inteesar and Nour… Sai Kuma senior na mu na gaba da mu a couch and mentor kenan… Imraan” ta karasa fada tana nuni da su daya bayan daya..
Layla ta kakaro murmushi tana duban ta tace,,
“Sunanta Nawraah, ni Kuma Layla”
“Wow lovely names….mashaa Allah”
“Mungode” Layla ta sake basu amsa.
Nawraah dai baki daya kwakwalwarta ta tafi yi mata nazari akan abunda Imran da yammatan nan suka tattuna akai. Gashi Kuma lily din tazo ta daga karshe ta sake boye lamarin Mai wuyar maanar ta. Amman dai dik da haka tabbas akwai wani boyayyen lamarin a tsakanin su.
“Ka karasa nuna musu koina Imran?”
“A’a da Saura. Amma mungama two third”
“Alright. Nawraah and Layla ku biyoni na nuna muku sauran”
Jan hannun Nawraah tayi tana sake duban kakarta tace,
“Jakan nan ya mun kyau”
“Nagode”
“Woah ko wani brand ne plus year din daya fito?” Wata acikin yammatan ta wullowa Nawraah tambaya..
Nawraah ta dubi lily tana girgiza Kai kawai
“Kaman yvsl… Kaman kuma givenchy”
Cewar daya daga cikin su..
Lily ta riko kafadar Nawraah tana Mai janyo hannun Layla sukayu gaba. Ta juya tana duban kawayen nata tace dasu,
“Karku cikawa kawayena kunne da tambayoyin ku. Mu hadu a cafeteria. Bara na zagaya dasu”
Kawayen suka kada mata Kai suka juya suna duban su kafin su mike su nufi cafeteria
Jikin Imran a sanyaye ya juya library da sauri don hada musu aikin da suka bashi. Wani bangare na zuciyar sa na Masa zugi da radadin abunda zai biyo baya. Ko akansa ko akan su Nawraah. ..
K’K’J
(M/W/S)
✍️:MX
5
:::::::::
Haifa ta shiga nuna musu ko’ina da ko’ina daya dace daga nan ta nufi da su gymnasium inda wasu daga cikin vvip students suke motsa jikin su..
Idanun sa ne ya sauka akanta alokacin da yake kokarin daga wani babban karfe yana motsa jiki da shi..
Ta juya manyan idanun ta tana bin ilahirin babban dakin motsa jikin da kallo…
Bangaren mata na daga can baya wata mata murdaddiyar mata daga gani taci karfe itace ke koya musu
Yayinda mazanma akwai me kula da su shima a murde gabobin jikin sa suke..
“Nan ne gym na Alharamein university….. Amma ba kowane jig and jah bane yake zuwa nan. Free ne for all students a lokacin da aka buda jamiar. Amma da aka samu shareholders da yawa sai aka mayar da shi premium card ne. Kowane student member sai yanada premium membership card sannan zai iya shiga ya motsa jikin sa…”
“Lalle lamarin na manya ne…” Cewar Layla tana jijjuya Kai
Nawraah kuwa bata samu bakin magana ba illa dai ta sauke gauruwar ajiyar zuciya mai tarin ma’anoni…
Juyar da manyan idanunta keda wuta suka sauka akan marwaan daya taso ya kasa cigaba da motsa jikin da yake.yana tafe yana goge fuskar sa da hankici.
Inda suke ya fara dosowa yana murmushi. Iily ta juyar da janta tana kokarin hango anees dake can baya yana motsa jikin sa.
“Dear sis”
“Naam bruh.. Ina yaya Anees?”
“Gashi can yana exercise…. Kinsan su ne?” Ya tanbayeta yana Mai Saka yatsaa yayi nuni da Nawraah.
Iily ta kada masa Kai tana murmushi tace,
“Imran akace yayi volunteering so I lend a helping hand”
Marwaan ya tabe baki yana Mai Karkatar da hankalin sa kacakan kan Nawraah da take saye fuska.don ganin mazan yawanci ba riga suna atisaye ba kadan ba kunya ta cika ta da fargaba.
“Mind to show you gorgeous around?” Ya fada yana kallon Nawraah sosai
Yi yayi tamkar ba tasan yana magana ba. Ta riko hannuwan layla tana janta..
“Ku jirani mana. Kamar kinsan makarantar ne zaku tafi?”
Itadai Nawraah bata tanka musu ba ta janye hannun Layla suka karasa fita .
Marwaan yabi bayan su da sauri har yana hadawa da gudu…
Yana juyawa hango su suna tsaye ita da Layla..
Yayi azamar riko kasan mayafin Nawraah yana jefa mata wani kallo na please ta ba shi lokaci kankani..
“Please …kinji beautiful?”
Ya sake jeho mata tambaya yana danne kasan leben sa
“Same department kuma?”
“Criminology….” Layla ta amsa shi tana dubansa dakyau
Sanye cikin manyan kaya na yadi, kansa ba hula kwantaccen gashin kansa ya kwanta luf
“Mashaa Allah! Allah yabada saa”
“Aameen”
Nawraah ta amsa cikin sunkuyar da kanta a kasa
“Chan swimming pool ne, Da na gefen sa kuma cit, can campus library da sauran su”
“Mungode ..”
Suka hadi baki wajen amsa shi
Gaba suka yi, Nawraah ta dubi Layla,
“Wannan makarantar an hada yayan manyan sosai.”
“Sosai ma. “
Iily na ganinsu tayi sauri ta mayar da wayarta acikin jaka. Ganin tayi message, calls, Whatsapp call, Duk yayi shiru bai ce komai ba”
Ta sake dubawa tana dage ta leka yana kwance akan wani gado na atisaye rike da wayar sa ahannu…
“Muje ko?” Iily ta tanbaye su ranta ba dadi
“Eh tohm”
Rankayawa sukayi gaba daya suka futa daga harabar farfajiyar gymnasium din zuwa main campus central mosque..
“Nan ne masallaci. Idan kuka gama sai lectures block b ne. Auditorium one thousand seaters..”
“Okay elective course ne? Bakya yi?” Nawraah ta tanbayi lily
Lily ta girgiza kanta tana danne hawayen da yake so ya bujere ya zubo mata tace,
“Kai na ke ciwo bazan samu attending ba”
“Allah Allah yakara sauki” suka hada baki wajen yi mata sannu,
“Ameen nagode”
Gaba tayi ta daga musu hannu alamar bye bye..
Masallaci suka shiga suka rage cikin su suka daura alwala. Suka tada sallah sukayi sallar su bayan sun idar ne sun dan huta. Suka nufi cafeteria don cin abinci sannan su biya dakin lakca..
K’K’J
(M/W/S)
✍️:MX
6
:::::::::
Suna dosa kansu wajen babbar kofar da zata sadaaka da cikin wajen cin abincin. Kofar ta bude… Bayan sun shiga ta komai ta rufe da kanta.
Layla ta riko hannun Nawraah tana mata rad’a.
“Kinga kamar a film da ake nunawa chab”
Nawraah tayi murmushi kawai tana duban harabar wajen cin abincin… Baki dayan daliban wajen suka tsaya suna duban su.
Da masu cin abinci da masu shan abin sha. Sun rarraba kansu. Wasu sunyi group iya mata, wasu maza zalla. Wasu mazan da matan duk a hade. Wasu kuma samari ne da yamma ta suke zance..Kowanne dai da abunda yake yi…
“Layla zomu tafi .. Nan wajen anya na talakawa ne kuwa?’ Nawraah ta fada tana duban Layla
“Ke kin cika saurin karaya. Ya zaki ce nan din ba abunda kudin mu zai iya saya? Jami’a ce fa…”
“Shikenan muje…”
A haka suka karasa inda tulin abincin sayarwar yake kala kala gasu nan a jajjere kala kala na gidah dana waje..
Layla ta tabo kafadar Nawraah tana mata nuni da wata stir fry spaghetti sai kamshi ne ke tashi daga cikin ta..
“Nawa ne da ke?” Layla ta radawa Nawraah.
Nawraah ta wulkita idanu tana hararo wajen kwanukan abincin tace,
“Nera dari ce.. ke fa?”
“Nima darin ce sai wata danayi dan taru a asusu na curo”
“How may I help u?” Wani ma’aikacin wajen abincin ya tambaye su yana bude murafen wasu kwanukan dake cike da kaji sun gasu da kifi
Layla ta sa hannu a baki tana cizawa tache,
“Where’s the menu?”
“Here… Ma’am..”
Karba tayi tana nunawa Nawraah. Idanun su suka firfito waje kaman zasu fado saboda tsananin mamakin kudaden abincin da suka girgiza su..
“Karamin abu anan na dubu biyar ne layla shi yasa nace miki anya wajen nan zamu iya shigar sa? Dukan kudin namu idan an hade su dari uku ne fa. Ko ruwan sha ma kina ganin dari takwas ne na roba me sanyi babu ma sachet water..”
Layla ta sauke gauruwar bahaguwar zuciya tana mayar masa da menu din. Nawraah sai janta take subar wajen Layla taki ta sake cewa dashi,
“Ba kuda awara ko gurasa haka?”
“Awara? Gaskia babu… “
“Ba wani abincin me karamin kudi haka daga nera dari?”
“No babu” ya fada yana tamke fuska hade da rufe food flask din wajen da murafen su,
“If u’ll excuse me. I will attend to another next person. Mungode”
Barin wajen yayi ya komai daya bangaren harda gaishe da su yana murmushi .
Yammatan nanne kawayen lily na dazu da suka da kawa imraan tsawa suna masa tsiwa da fada.
ATM card dayar ta zaro ta mikawa waiter din tana duban sauran kawayen nata tace,
“Me kike so kuci?”
Layla ganin tun dazu sun tsaya tare dazu hakan yasanya ta karasa kusa da su tana tambayar su,
“Dan Allah Ina ake sayar da awara ko gurasa haka?”
“Awara? Gurasa? Acikin cafeteria dinnan?” Daya daga ciki ta amsa mata sauran suka fashe da daria.
Hakama sauran daliban baki daya da suka fara babbaka daria. Gashi dakin cin abincin amsawa yake idan ana magana. Daman wajen anyi tsit kowa yana sauraron su.
“Eh ba a sayarwar ne ko yaya? Tambaya ce fa kawai nayi sister” Layla ta sake cewa da su.. Nawraah nata Jan hannunta su bar wajen taki.
“Sis what? Ohh please… Sunana Imaan, Wannan sunanta inteesar waccen Kuma Nour…”
“Okay Allah sarki tohm Imaan Ina zamu samu kenan?”
“Well I dunno … Sai dai ku tanbayi dalibai yan scholarship haka. Dan nan baa sayar da abubuwan da kike fada… “
Bata sake cewar wani abun ba. Tayi gaba sauran na biye da ita.. maaikatan wajen na biye dasu da trays din abincin da sukayi ordering..
Layla ta juya ta dubi Nawraah.
Jikin su a sanyeye suka futa daga cikin cafeteria din sauran daliban ciki suka fashe da dariaa
Suna futa suka hadu da imraan dauke da takardu na a4 a hannun sa. Da alamar aikin da suka bashi ya kammala.
“Ahh” ya fada yana kallon su
‘mun sake haduwa…” Layla ta bashi amsa tana murmushi
Nawraah ma murmushin kawai tayi. Cikinta sai kugin yunwa yake.
“Akwai masu awara kuwa haka ko gurasa anan makarantar mun shiga nan cikin cafeteria dukkanin abincin da suke dashi yafu karfin mu”
Imran take yaji zuciyar sa ta sosu yatabbatar an guma musu wani abun takaicin acikin cafeteria din. Don haka ya dan sauke ajiyar zuciya kamar yana bayani da papers din dake hannun sa yace,
“Masu awara da sauran su an hanasu shigowa cike so kuje ta gate zaku mika kudin ku su baku. Harda me wainar fulawa ma duk akwai. Amman nan cafeteria din bata yayan talakawa bace Irina . Don haka kudin abincin plate daya kadai ya isa ka saya kaya a dinka ma. Haka makarantar take. Sai a hankali. Kudai kawai abunda nake son ku dinga yi shine. Komai rintsi kada ku bari musu ko fada ko cacar baki ta hada ku da sauran dalibai nan. Don harda malaman basu da karfin iKon hukunta daliban don yayan manya ne. Sannan duk wani shirgi da zai hadaku dasu ku tabbatar kunyi nesa da juna. Banda soyayya ko kawance da dalibai yayan masu kudi. Akwai tarin bullies da yawa a makarantar nan lefi kadan zakai akan su sai a koreka, bayan sune da rashin gaskia. Shikenan ruwa ta sha, don haka ku tsaya ku dai ku Saka idanun ku. Ku zama bebaye Kuma makafi masu raunin gani da jin su akan abunda bai shafe su ba Kai har ma da abinda ya shafeku din, ni da kuke gani badan sunkuyar da kan da nake Ina binsu da ladabi ba da tuni nima na dai na zuwa makarantar , Amman dana karance su sai lamarin suke zuwa mun cikin sauki . Sauran abubuwa zan sanar da ku agaba, yanzu kuje bakin gate ku saya abunda zaku saya kuci sai ku tafi inda zakuyi lakca. Allah yasanya albarka a karatun da zakuyi ya kauda duk wani sharri tuggu ko makirci aameen. Bari naje wajen su .. wani abun ya hadaku da sune?”
“A’a komai ya wuce imraan. Mungode maka Allah yasa ka maka da alkhairi ya biyaka Amin “
“Aameen Yaa Rabbi. “
Shigewa yayi cikin cafeteria din yana daga musu hannu. Suka nufi gate din jikin su a sanyaye. Suka siyi awara da gurasa da ruwa pure water kowa daya daya suka koma gefe suka tsakure suka ci suka kora da ruwa sannan suka wuce ajin da zasu dauki darasi na ranar.
To haka rayuwar daukar darasin nasu ya kasance a jami’ar Alharamein university dake yankin naduka crescent.. Suna ganin tarin abubuwa da yawa na kyara da izgilanci amman sai dai su shanye kawai idan an tashi suyi tafiyar su ..
Layla ta tafi gidah Nawraah kuma ta nufi gidan marayun su..
To dama haka rayuwar ta gada. Kowane dan Adam da irin nasa kaddarar.m
Bawa baya tsallake kaddarar sa fyace Allah mahalicci ya Kadarta haka.
::;
Tun asubah data tashi….
K’K’J
(M/W/S)
✍️:MX
7
:::::::::
Tunda ta tashi da asubah bata sake komawa ba. Zuciyar ta baki daya ta mata rauni. Ji take anya ba zata dai na zuwa makarantar nan ba kuwa?
Ta juya ta dubi Amnah da take bacci tana sauke numfashi ahankali. Yayin da take rawar dari na sanyi. Duk kuwa da garin damina ne. An basu sanyi bishiyu nata kadawa. Garin yayi dalam cikin ni’imar Allah..
Nawraah ta kai hannunta akan goshin Amnah ya dau zafi sosai. Hakama jikin nata baki daya ya gauraye da dumi kamar garwashi..
Jikin ta na rawa ta mike ta shiga bandaki ta taro ruwa a roba ta hado da dankwalinta aciki ta nufi wajen gadon Amnah ta saka hannu tana tashin ta ahankali.
“Amnah .. Amnah…” Ta Kira sunanta ahankali tana taba goshin ta.
Faty da Kiran sunan Amnah da Nawraah take tasa ta tashi tana yamutsa fuska. Ta daga hannuwan tana mika hadi da sakin katoton tsaki,
“Meye haka ne saboda Allah ke kullun dan bakin zalinci sai ki dinga tashin mutane suna cikin baccin su kawai don ke bakyaji haba wannan shiga hakki ne” ta karasa fada tana juyawa gefe.
“Kai Faty tsakani da Allah renin hankalin naki yayi yawa. Banda yau yaushe Nawraah ke tashin ki a bacci? Yanzun ma kina ganin Amnah take tashi kekuma kika tashi. Gaskia maganganun da kike suna yin tsauri.” Cewar Raudah wadda gadonta ke gaban na su Nawraah.
“Gaskia dai banga wani abun tada jijiyoyin wiya anan ba Faty. Zancen gaskia fa kenan. Amma kiyi hakuri” wasila ta fada tana zaune akan gado hannunta rike da littafin hisnul Muslim tana karantawa.
Nawraah da jikinta sai rawa yake sahoda batason tashin hankali wani sabanin yazo ya gitta tsakanin su daman fatyn taki jinin su tun sanda aka kawo su gidan marayun akace su zauna a dakin su. Batada aiki sai kyara da tsangwarar su. Tai ta so ta takalo abunda zai sasu fada da Nawraah
Amman tunda Nawraah ta fuskanci irin halayen nata sai ta ke binta sannu ahankali sam bata biye mata. Takanyi shiru aduk sanda fatyn zata yita banbamin fadanta. Sai dai su wasila su shigar wa Nawraah. Sannan fatyn take shiru.
“Kiyi hakuri Faty… Wallahi ba da biyu nayi ba. Amnah ce naji jikinta ya dau zafi zazzabi sosai take. Amma kiyi hakuri. Kinji ko?”
Faty taja digon tsaki ta dauki pillow dinta guda daya daga kan gadon ta mike ta fita tana bugo kofar dakin da karfi tamkar zata ballo..
“Allah ya kyauta. Shareta dan Allah… Karki sake bi takanta. Da kanta zata sakko. Uban me aka mata yarinya kullum cikin nunkufurci. ” Raudah ta fada tana sakin tsaki itama
“Ai faty ni nakan kasa gane kanta Allah” Wasila ta fada tana girgiza kai
“Ku bata hakuri dan Allah…” Nawraah ta fada idanuwanta na tsiyayar da ruwan hawaye…
“Dalla shareta kiyi abunda kika Saka agaba. Zamu mata magana kakki damu”
Nawraah ta katse hawayen da yake zuba. Ta matsa kusa da Amnah da temakon su wasila suka daga jikin Amnah suka kaita bandaki
“Ina ke maki ciwo Amnah?”
Amnah ta kasa magana ta daga hannu dakyar ta nuna cikinta da kanta.
“Sannu kinji zo muje awanke baki kici abinci kinji”
“Na koshi Adda” Amnah ta fadawa Nawraah hadi da zumewaa ta kwanta saboda yadda jikin ta baki daya yake nukurkusar ta.
“A’a ai bazeyiwu ki ki cin abinci ba Amnah. Bazeyiwu ba”
Su wasila ne suka temaka ta daga Amnah suka sake dauraye mata baki da jikinta sannan suka komai farfajiyar daki. Dan flask din da ake duro musu ruwan shayi ta tsitaya da ragowar madarar su ta hada mata shayi ta karyo biredi ta bawa Amnah..Amnahta girgiza Kai bata so.
Nawraah ta shiga tsoma mata buredin a shayin tana bata. Dakyar ta karbi guda uku na tsoman hudun ta amayo komai gaba daya.
Su wasila suka kintsa wurin. Nawraah ta dauki Amnah dakyar suka nufi asibitin dake cikin gidan marayun.
Likita yayi gwaje gwajen sa yace malaria ce. Aka bata maganguna. Ranar Nawraah bata je.. makarantar ba.
Wasa wasa sai datayi kwana uku bataje makarantar ba. Kullun idan Layla ta biyo mata taga jikin Amnan ne dai har yanzu. Itama sahoda tsoron rashin Nawraah a kusa yasa take komawa gidah taki zuwa makarantar.
Ciwon Amnaah meyakwan yayi sauki sai gaba ya sake yi ma. Tayita ramewa a tsaye kamar zaa hureta ta fadi. Asibitkn cikin gidan marayun sunyi iyakar abunda zasu iya since yafu karfin su don haka su dangana da specialist hospital wato asibitin babban na kwararrun likitoci.
Duk inda Nawraah da Ashfeef suka zaga babu way out. Basuda wata madafa da zasu kama suce zasu samu sauki ta bangaren. Ko zaa yaye musu matsalar lalurar da Amnah ke cikin ta rashi lafiya domin kusan cuwonta na baya da aka mata aiki ne yake dawowa
Dakyar take iya cin abinci ruwa ma sai anyi dagaske take iya sha.
Zaune suke a zauren gidan marayun. Amnah na jikin Nawraah dake jingine da bango. Yayinda ashfeef yake daga can gefe ya saka hannu ya tallabe habarsa yana tagumi.
“Nawraah me kikaci karshe cikin naki ya fara miki ciwo. Likita nata tanbayer ki kinki fada ko?”
Amnah tayi rau rau da idanun tana lankwasa yatsun hannuwanta tace,
“Kiyi hakuri Adda…. Hamma ashfeef kayi hakuri Kai ma”
“Hakurin me? Muna sauraron ki…”
Ta Saka hannunta dakyar tana katse hawayen dake zuba mata tache,
“Irin wannan abunda Ammi take kawomun kafin ta mutu dinnan”
Nawraah ta dubi ashfeef shima yana duban ta muryar Nawraah na rawa tace,
“Wane abu eh Amnah? Me kikaci”
“Wannan abun da ake cin su chakulet acikinsa ko Madara me kwakwa”
“Innalillahi Wa inna ilaihi rajiun. Filled doughnut Amnah..ain kika ci?”
“A cikin sharar can suka Saka suna gama ci fa basu cinye ba suka wullar dashi to shine… Shine na dauka na karkade na ci”
Salati Nawraah da Ashfeef suka kamayi. Amnah ta fashe da kuka tana basu hakuri. Da sauri ashfeef ya sungumi Amnah suka nufi asibitkn cikin gidan marayun.
Sunata haki suka sanar da likitan yadda ake ciki. Likitan yayi dube duben sa sai sunje anyi mata scanning awani asibiyin nan baayi acikin saanan zaa gane inda lamarin ya dosa…
Suka dai durkawa amnah allurar bacci akan gadon marasa lafiya daker acikin asibiyin..
Ashfeef da Nawraah suka futa daga ciki suna tunanin yadda zasu samu kudin da zaa yiwa Amnah scanning.
“Kache su bapoah sani kowanne bai ce komai ba ko?”
“Wallahi Nawraah ba abunda kowanne ya ce. Bappah salisu fa cayayi yana meeting ya katse kawai”
“Subhan Allah ya Allah ka kawo kana dauki”
“Aameen Yaa Rabbi”
“Nawraah…”
Da sauri ta juya jin muryoyin su wasila. Daga mata hannu sukayi suka karasa wajen suna tanbayar ya jikin Amnah.
Nawraah ta gaya musu Duk yadda ake cikin. Nan suka yanke shawarar shiga cikin makarantar Alharamein ko zsu dache da wani liititan da zai musu sauki. Ko ayi amfni da record din Nawraah na medical issues.
Ashfeef kuwa ya zagaya wajen gyaran mota shima ko zai samu wani dan kudin da zasu rage
Baki dayan hankulan su baya jikin su. Nawraah tamkar itace marar lafiya yadda baki daya ta zabge ta fice daga hayyacinta. Hakama ashfeef da yaketa kaikawo ganin ya kawo musu dauki ganin shine namiji. Kuma babban yaya daya rage tilo agare su.
*” Yana daga zaune a kujerun waiting sessions yana jiran futowar abokin nasa. Sanye yake cikin kananun kayan da sukayi matukar karbar zatin haibar halittar jikin sa.
Idanuwan sa suka sauka akan kyakkyawar fuskar da ba zai tabe mancewa da itaba a rayuwarsa.
Ya samu kansa da yin kasa da idanu yana binta da wani irin kallo tamkar zai hadiyeta.
Hango su yayi sun nufi kantar wajen neman karin bayanin bude file ko ganin likita da biyan consultation fees. Ya dan matsa gaba dasu yana jiyo abunda suke fada.
Take yaji wani taisayin ga ya sake kama shi. Amma saboda tsoron abunda zai wargaza amintar tsakanin su…
Hakan yasa ya koma ya shiga ta kofar da yake. Ya same shi yana masa bayanin komai.
Bai gama sauraron saba ya futa da sauri yana hangosu ya karasa dauke hannunsa yake da handkerchief din abokin nasa daya kwace da ruwan roba guda day cira a ofishin likitan daya shiga….
Update please…… mungode
Insha Allah
Tsutsar nama book 3 page 53
The story was so amazing
Allah yakara basira