Page 3
……….Zaman duniya da kayan cikinta buƙatar kowacce, amma waɗanda duniya ke buƙata da amfanuwa da kayan cikinta mutanene ƙalilan. A lokacin da wasu mutane ke bushasha da wani yanki na jin daɗin cikinta wasunsu kuka suke da kwankwaɗar ɗacin cikinta.
Yayinda idanun wasu ya bushe da ga kwaranyar ruwa mai amsa sunan hawaye, a lokacinne ijiyar wasu ke ambaliyar zubarwa da buƙatar abin gogewa koda ace ruwan hawayen bazai dakata daga malala ba.
Zuciyoyi duk iri ɗayane a suna, amma a aiyuka kowa da irin tasa. In dai zuciya zata kasance mabanbanta a ƙirazan mutane, to lallai dolene launin halayya da ɗabi’unsu ma ya banbanta. Sai dai wanda ya halicci duniyar da kayan cikinta, ya fika sanin miyasa ya banbanta ma’abota mu’amulantar ta da shawagi a cikinta harma da gudun zukatansu.
Kamar yanda duk ilimin ɗan adam bai isa ƙayyade numfashin da ke fita daga huhunsa zuwa maƙogwaro ya fita ta hanci ba, to lallai babu mai ilimin ƙa’idance ko banbance yawan jinsin ƙabilu da mutanen dake danƙare da duniyar nan sai wanda ya halicceta. A lokacin da fankama da tinƙahonka ke kwarzanta abincin tukunyar gidanka, da zaka leƙa ta gidan wani sai kaga ta fita abin kallo da kayan alfarma masu armashi.
Sai dai duk wannan ba shi bane tushen zancen, ba kuma shi bane abin dubi da hange ko burin riska, tsarin shine waiwaya can bayan bayanka ka hango waɗanda ko tukunyar ɗorawar basu da ita balle tunanin hura wutar da zata dafa musu.