قصة حزينة جدا عن السجناء🥺💔
*E7*
Su na Cikin Maganar nan, Su ka ji yo wani irin gurnani, A ruɗe su ka ɗago suna kallon su,
Wannan dattijon ne Ya rikiɗa nan take ya zama wata halitta mai matuƙar tsoratarwa, Ya shiga girgiza jikin shi Yana wani irin gurnani,
Tashin hankalin da ba’a sama shi date, Wani irin tsoro ne ya bayyana a kan fuskokin su, Tuni zufa ta wanke su sharkaf, Don tunda Allah ya halicce su basu ta6a ganin mutun ya rikiɗa ya koma dabba ba, duk da suna Jin labarin Matsafan dake rikiɗa suna canza halittar su,
Ja da baya halittar nan tayi, Kafin Ya daka suka, Kaitsaye Ya faɗa kan Ƴa’ƴan malamin nan, Ya shiga yagar Naman Jikin su Yana ci, malamin na kuka yana ƙoƙarin ceton ran ƴa’ƴan shi da jini Ya wanke fuskokin su, Aikuwa nan take sauran Alhazawan guda biyar dake a kewaye da su, suka rikiɗa, gaba ɗayan su ka canza halittar su, Cikin lokaci ƙanƙani su ka handame malamin nan da ya’yan shi,
In taƙaice maku zance, Sai da Suka cinye namansu tass, Ko ƙashi basu bari ba, Tukunna Suka rikiɗa a lokaci ɗaya suka koma Mutane, Bakin kowannan su, Da6a da6a da jini,
A hanzarce bodyguards ɗinnan suka zura hannayen su Cikin aljihunan wandunansu kowannansu ya zaro Hanky mai girma. suka shiga goge masu jinin da ya 6ata bakunan su, Bayan sun kammala suka jefar da hanky ɗin Cikin ƙoramar dake a gabansu,
Batare da 6ata lokaci ba, suka koma Cikin motocin su, a guje suka bar cikin dajin 6aaat suka 6ace,
Jikin Taj na kerma Ya kalli Uzair wanda tuni ya jima da ƙamewa a tsaye kamar saƙago, Idanuwanshi sun firfito waje tamkar zasu faɗo ƙasa,Wani irin matsanancin tsoro ne ya ziyar shi zuciyoyin su, hankalin su ya tashi matuƙa,
A ruɗe Taj ya fisgi hannun Uzair suka Koma Cikin motar su, Aka rasa wanda zaiyi driving ɗin su, tsakanin su biyu, jikinsu duk yayi sanyi ga wata uwar zufa dake tsatstsafo masu, tamkar waɗanda aka tsamo su daga cikin ruwa sun haɗa uban gumi, daƙyar Taj ya iya tada motar, ya samu ya karya kwana da wani irin speed ya fusgi motar tamkar zasu tashi sama, Duk tsoro ya kama su ga tausayin malamin nan da ƴa’ƴanshi, abun ya yi matuƙar girgiza su,
A can gida kuwa, Sam bacci ya ƙaurace wa idanuwansu, Daga angel ɗin har aneelerh, Sun yi zugudum saman Gado, kowa da abunda yake ayyanawa a ran shi, Ganin har ƙarfe 12 ta buga amma ba su dawo ba,
“Aunty aneelerh, ni tsoro nake ji kada a ce wani abu ya faru da su daddy” Janyo ta Jikinta aneelerh ta yi Tare da shafa sumar kanta tace”in sha Allah ba a bunda zai faru da su, zasu dawo ne nan bada jimawa ba, ni inaji a raina”
“Allah bazan ƙara bari ya tafi ya barni ba, duk inda zai je ƙafata ƙafar shi, idan ba haka ba zan sa ce tayar motor shi kowa ya rasa” aɗan shagawa6e tayi maganar, tamkar zata fashe da kuka,
Fashewa aneelerh tayi da dariya daƙyar ta tsagaita da yin dariyar tace”Idan ki ka sa ce tayar motar shi ae yana da ƙafafu ko suma zaki guntule su ne? Kuma in banda abun ki, idan kika sa ce tayar motar shi, ae a kwai ta Uzair zasu fita a cikin ta shi ne,”
Tur6une fuska tayi, ba halin tace zata sa ce tayar motar uzair,
Suna Cikin tattaunawar nan, Suka jiyo hon ɗin motar su, Da gudu Angel ta zabura Zata sauko daga saman gadon, Aneelerh ta ruƙo hannunta”ki bari su ƙaraso Ciki mana”
Komawa tayi ta zauna jikinta har wani rawa yake yi duk ta ƙagara taga daddynta,
Baba maigadi na buɗe masu ƙopar, A tsiyace suka shigo da motar bayan sunyi parking ɗinta Taj ya kashe motar,
Uzair ya kalli shi ganin yadda zufa keta tsatstsafo mashi ya haɗa uban gumi”banaso su gane wani abu ya faru pls, Ka daidaita natsuwar ka”
Kallon shi taj ya yi “natsuwa fa ka ce?tayaya kenan? akan idona fa mutane suka rikiɗa suka canza halittarsu, kuma akan idona suka handame mutun da ya’yan shi, wlh ko a film naga hakan saina girgiza ballantana kuma a zahiri, ni wlh ka cuce ni, danasani tunfarko ban biye maka ba, da duk banga wannan tashin hankalin ba” ranshi duk ajagule ya yi maganar,
“Amma ae koba komai, mun ƙaru ko?tun da kaga yanzu mun samu a bunda zamu taimaki al’umma,”uzair ne yayi maganar,
Wani kallo Taj ya jefa mashi”mu taimaki al’umma, ka yi hauka ne”?
Bai ba shi amsa ba, sai ma ya fito daga motar, ya nufi cikin gidan, Jiki a sanyaye taj ya fito daga motar yabi bayan Uzair suka nufi cikin palourn,
Kusan atare suka haɗa baki wurin yin sallama, jin muryoyin su yasa Angel da aneeleeh suka fito daga ɗakin, da gudu angel taje ta faɗa ma daddynta,
“Nayi fushi sai yanzu zaka dawo,duk ka tayar mun da hankali, ko bacci na kasa yi”
Zuƙunnawa yayi saman gwiwowin sa, yadda tsawon shi zaizo dai dai da nata,
Sosai yayi hugginta ɗinta”Am sorry angel, Nasan nayi laifi, ayi mun afwa,”aɗan shagwa6e tace”shikenan amma kada ka ƙara,” amsa mata ya yi da toh batare daya rabata da jikin shi ba, sam baiso ta gane halin da yake ciki, hawaye ne cike tab da idanuwan shi, tamkar ya rushe da kuka haka yake ji bakomai yafi tsaya ma shi a raiba fa ce yacce waɗannan Mutannan marasa imani suka fatattaki malamin nan da kuma ƴa’ƴan shi, Yanzu shikenan sun kashe su, Babu su a doran duniya, tabbas waɗannan mutanan sun san me suka taka,
Aneelerh da uzair tuni sun shige ɗaki,
“Sannu da dawowa” batare da ya kalle ta ba, ya nufi toilet zai shiga,
“Wai meke faruwa ne? Nayi maka magana baka amsa min ba,”
Juyo wa ya ɗanyi Yana kallonta a lokacin ya ruƙe handle ɗin ƙopar toilet zai shiga, “To matar ɗan jarida, ba za ki bari na samu natsuwa ba” cikin zolaya ya yi mata maganar,
Murmu shi taɗan saki, shima ya mayar mata da martanin murmushin kafin ya shige cikin toilet ɗin.
Tunawa da taj yasa Aneelerh miƙe wa Ta fito falon, Bata same su a nan ba hakan na nufin ya ɗauki angel sun tafi gida.
Ta so ace tayi ma shi sannu dawowa, ga shi kuma Ya tafi, Ta wani 6angaren kuma ji take kamar wani abu Ya faru ba daidai ba, Tun daga kan yanayin Uzair, da kuma shi taj ɗin.
Hakanan taji hankalin ta bai kwanta dasu ba, sam babu natsuwa a tattare da su, Juyawa ta yi zuwa cikin ɗakin a lokacin uzair Ya fito daga toilet ɗin, da alama Ruwa yaɗan watsa ma jikin shi, short ne kawai ya bari ajikin shi,
“Sannu da fitowa” ta faɗi tana kallon shi,
“Yawwa madam,”
“Bari na kawo maka dinner ɗin ka, nasan ka kwaso yunwa,”
Da sauri ya dakatar da ita “No bana jin yunwa, bacci nake ji” yakai ƙarshen maganar tare da nufar Cikin ɗakin wurin Closet ɗin shi, Ya buɗe cikin jerin jallabiyoyinshi ya ɗauko ɗaya Ya zurata ajikin shi,
Juyawa yai Still aneelerh tana a tsaye tana kallon shi, Ta gefenta yabi ya wuce ya kwanta,
“Nayi tunanin zaka yi missing ɗina,” tayi maganar tare da takawa Ta koma gefen gadon,
“Kodai wani abu ya faru ne? naga duk ka sauyamun, Shima taj ko sallama banyi ma shi ba, Ya ɗauki angel sun tafi gida”
Ganin zata takura mashi da surutu ne yasa shi yin saurin janyota jikin shi, wata irin runguma yayi mata, sai ga shi tayi tsit bata ƙara cewa uffan ba,
Taj kuwa bayan Sun koma gidan, Upstairs Ya wuce da angel, Yakaita bedroom ɗinta, Yasan aneelerh bazata barta da yunwa ba,
Dawowa down Yayi a hanzar ce ya shiga bedroom ɗin shi Ya faɗa toilet, shaf shaf yayi wanka ya fito, wuri ya samu saman kujerar gaban mirror ya xauna, wasu zafafan hawaye ne su ka soma yin zarya akan fuskar shi, Uban tagumi ya zabga tamkar marayan da ba shi da ma fadi aduniya,
“Daddy”muryar angel ce ta katse shi, ta cikin madubin yake hangenta, tana a tsaye bakin ƙopar,
Da sauri ya share hawayen dake a kan fuskashi cikin sanyin murya yace”Ba ki yi bacci ba?
Ƙarasa shiga cikin ɗakin tayi”daddyna ba ka da lafiya ne?
“Lafiyata ƙalou me kika gani ne”?yayi tambayar tare da ɗan juyawa yana kallon ta, a lokacin ta ƙaraso in da yake zaune,
“Ni dai inaji araina, baka da lafiya,”
daƙyar ya ƙaƙaro murmushi yace “Waya faɗa maki bani da lafiya?
“Naji a jikina” ta yi maganar tana ƙare mashi kallo,
“Bana hana ki yawo da daddare ba kallabi ba”? da biyu ya yi mata maganar don ya mantar da ita wancen zancen,
“Mantawa nayi,”
Nuna mata hanyar fita yayi da hannun shi”Oya go back to ur room ki ɗaure kanki da kallabi, before ki kwanta”
Maƙe mashi kafaɗa tayi”Ni dai zan kwana anan, muyi bacci a tare”
Ɗaure mata fuska ya yi”Za ki wuce ko sai nayi ball dake” a faɗa ce ya yi mata maganar,nan da nan yanayin fuskarta ya canza, ƙwalla ta ciko tab a cikin idanuwanta, cikin shessheƙar kuka tace
“Dan Allah daddy ka bari in kwana anan yau kawai” ta ƙarasa maganar tana matsar ƙwalla,
Gyaɗa kai yayi”Shikenan Ki fita waje Ki jirani zan kira ki” juyawa tayi da sauri ta koma daga waje, ta jingina bayanta jikin wall,
Miƙewa ya yi jiki ba ƙwari ya nufi wardrobe ya ɗauko kayan baccin shi, ya soma sanya su a jikin shi,
“Daddy in shigo” jin muryarta ya sa shi yin murmushi tare da cewa”ban kammala ba”
Sai daya ƙarasa zura kayan a jikin shi, tukunna Ya kira Sunanta Angel, Shigo wa tayi cikin ɗakin A kwance ta same shi saman gado, Ƙarasawa tayi ta haye saman gadon, Can kusa da shi ta kwanta,
Addu’a ya shiga jerowa yana tofa masu, Kafin Ya janyo ta jikin shi, a daren ranar da ƙyar ya samu bacci Ya ɗauke shi,
****Boss Bature****
A washe garin Ranar, Angel ta farka bata same shi a saman gadon su ba, Tunda ya tafi sallar a suba bai dawowa ba.
Ita kaɗai acikin gidan, Ga yunwa tana ji, fito wa ta yi daga bedroom ta sauko down kaitsaye ta nufi cikin falo, Fridge ta buɗe ta ɗauko Fura a cikin roba, Ta koma saman sofa Tana sha, duk in taji kamar motsin mutun saita kalli ƙopar taga idan shi ne Ya shigo,
Wuraren ƙarfe tara na safe Ya shigo Cikin falon, A kwance ya sameta, Tana ta bacci, ga robar furar data sha a jiye saman table,
Ƙarasawa yayi a gabanta ya zuƙunna tare dakai hannu yana shafa gefen fuskarta, Yasan tayi neman shi har ta gaji, Shi kan shi baisan ya akai bacci ya ɗauke shi a masallaci ba, Kodan jiya bai samu isasshen bacci ba ne,
Kasa janye eye ɗinshi ya yi daga kan fuskarta, hakanan ya dinga jin bugun zuciyarshi na ƙaruwa, sallamar uzair ce ta katse mashi kallon nata da ya ke yi, Miƙewa taj ya yi tare da juyawa Yana kallon shi,
Gaisawa suka fara yi, kafin suka rungume juna kamar yadda suka saba,
“Inason magana dakai” acewar uzair,”
Nuna mashi wuri yayi saman sofa”bismillah”
Zama Yayi saman 2 seater, taj kuma ya zauna a saman 1 seater, kallon kallo su kayi ma junansu na tsawon mintuna biyar batare da wani daga cikin su yace ƙala ba, Sai da taj ya gaji da zaman tukunna yace
“Ina sauraronka”?
A tsanake uzair ya soma magana”game da waɗannan mutanan da muka gani jiya”
“Suwa kenan”? yadda yayi tambayar tamkar baisan komai ba,
“Ina nufin waɗannan Miyagun da suka Kashe malamin nan da ƴa’ƴan shi,
Wani irin kallo Taj ya yi ma shi”Wai dama ba mafarki bane”?
Harara uzair ya ɗan jefa ma shi”take it serious pls, Banason wasa so nake muyi magana a kansu,’
Girgiza kai taj yayi”badani ba wlh, Na riga da nabar komai a matsayin mafarki, Bana so kasa ke tunamun a bunda ya faru jiya,”
“Kana nufin xamu ƙyalesu ne suna aikata 6arna acikin ƙasarmu”?acewar uzair ,A harzuƙe taj yace”ƙwarai kuwa, tunda bamu da yadda zamu yi da su, sunfi ƙarfin mu, mubar su da Allah shi kaɗai ne zai yi mana maganin su,
Uzair yace”Ba haka na sanka ba taj, Nayi tunanin zamu haɗa hannu a matsayin mu na ƴan jarida wurin ganin mun fallasa su, don a ɗauki mataki a kansu,”
Taj yace”Allah ya taimaka, Amma ni dai babu hannuna a ciki, kaima kuma ina gargaɗin ka akan ka manta da su, tamkar baka ta6a sanin su ba, In ba haka ba zaka jefa kanka cikin matsala ne , domin kuwa waɗannan mutanan da kake gani Shaiɗanu ne, sunfi ƙarfin hukuma ita kanta ballantana kuma mu da muke ƴan jarida”
Abu kamar wasa, suka soma gaya ma juna magana, Shi uzair yasa kafiya a kan saiya bi ƙwaƙƙwafinsu don ya tona masu asiri, Shi kuma taj yana ƙoƙarin fahimtar da shi irin haɗarin da zasu jefa kan su, a ƙarshe dai Uzair Ya miƙe rai a6ace yace”idan har ban tona masu asiri ba,tabbas zan ajiye aikina na ɗan jarida ne, domin ban cancance shi ba” yana kai ƙarshen maganar shi ya fuce, Taj dai yana a tsaye ya yi kasaƙe yana kallon bayan shi, har ya 6ace ma ganin shi,
Duk wannan surutun da su ke yi akan kunnan angel tun ɗazu ta farka daga bacci, duk da bata fahimci me suka tattaunawa ba,
“Daddy faɗa kuke da Daddy uzair?” a ɗan ruɗe Ya kalleta, da sauri yace”a’a, muna tattaunawa ne, game da zuwan Uncle abdallah, na faɗa mashi cewa Ya bari mu fara zuwa buzaye shi kuma yace dole mu jira su dawo Sai mu tafi atare”
Murmushi tasa ki”Nima nafi so mu tafi tare da su mommy adama”
“Me zaki Ci in kawo maki”?
“Komai zaka ci nima zanci” miƙewa ya yi tare da juyawa Ya nufi kitchen, don yau ba aikin safe gare shi, Sai wurin mare ce zai fita.
Zama tayi tana Jiran dawowar shi, almost 15 mins Ya fito hannun shi ɗauke da plate, indomie ce daga sama Kuma wainar ƙwaice, Asaman table ya ajiye masu,Kafin Ya koma kitchen ɗin Ya haɗo masu tea a cup biyu,Yazo ya ajiye gefen plate din
tare suka zauna Suna ci, still zuciyarshi a cunkushe take, Yana so ya taimaka ma uzair wurin fallasa asirin waɗannan mutanan ta wani 6angaren kuma Yana jin tsoran su jefa kan su Cikin masifa, tunda mutanannan sunfi karfinsu nesa ba kusa ba, Allah ne kaɗai zai Iya dasu, ga kuma angle din shi bayaso wani abu ya faru da ita ta sanadiyar shi gaskia yana cikin tsaka mai wuya
Ya yi zurfi cikin tunani, muryar Angel ce ta katse shi, “Daddy!”
Firgigit ya yi tare da kallon ta, “Na’am!”
Fuskarta da alamun damuwa ta ce, “Tun ɗazu ina ta kiran ka amma ba ka amsa mini ba. Daddy kamar kana cikin damuwa.”
Girgiza mata kai ya yi, “Am ok, ba wani abu. Kawai ina tunanin rayuwar duniya ne mai ban al’ajabi, rashin tsoron Allah ya yi ƙaranci a zukatan wasu mutanen. ban sani ba neman duniya ne koko mene ne yake jan hankalin su har su manta cewa wata rana za su mutu? Kuma za su koma ga Allah, sannan duk wani abu da suka mallaka ba za a ta6a binne su da shi ba, a gidan duniya za su bar shi.”
Tun da ya fara magana Angel ta ƙura masa ido tana kallon shi, sam ba ta fahimtar kan me yake magana. Shi kansa ya manta da wa yake magana? Abin ne ya dame shi yasa yake ta sambatu ko ya samu ya rage raɗaɗin dake cikin zuciyarsa.
Haɗa ido sukayi da ita, lokaci ɗaya yaja bakin shi ya yi shiru, da mamaki akan fuskarta take kallonshi, can dai tace”Daddy, Meya faru”?
Ƙaƙaro murmu shi ya yi”halan kinji inata zuba ko? wani programme ne da zamu gabatar a gidan radion mu shine nake tsara yadda zanyi shi”
Murmushi tasa ki”Allah ya taimaka daddy, I wish u all the best’ ya amsa mata da ameen,
*ANEELER*
A zaune su ke ita da uzair saman dining chairs suna fuskantar Juna, gaba ɗaya hankalinta na akan fuskar Uxair tunda ya ruƙe spoon yake ta jujjuyashi Cikin abincin da ta zuba ma shi a plate sam ya kasa cin shi sai kacaccala shi yake yi kamar ƙaramin yaro, ta lura da canzawar da yayi daga daren jiya zuwa yau kamar wani abu na damun shi bama kama bace tabbas akwai abinda ke damun shi.
Gyaran murya ta ɗanyi ma shi, Ya ɗago suka haɗa ido tace”My man, kaƙi faɗamun abunda ke damunka, tun ɗazu nake kallon ka, sam ka kasa Cin abinci why pls”?
Daƙyar ya iya bude baki yace”don’t worry ur self am ok, just bana jin daɗin zuciyata ne,”
“daka daure ka faɗamun may be in sama mana solution”
Murmu shi ya ɗansaki cikin zolaya yace”Matsalar bata asibiti bace balle kice za ki yi mun allura inji sauƙi”
Ta6e baki ta ɗanyi tare da mayar mashi da martanin murmushin “kana nufin matsalar data shafi asibiti kaɗai zan iya magani”?
Girgiza kai yayi”karfa ki dauka da zafi, It was a joke”
Kallon shi kawai tayi kafin ta mayar da eyes ɗinta akan abincin dake gabanta,
Wuraren ƙarfe shida na marece, taj, Yana daga kishingiɗe saman Sofa, jikin shi na sanye Cikin jeans da white shirt, a lokacin angel tana can cikin ɗakinta,
Ƙwanƙwasa ƙopar falon shi a kayi daga waje, A hakanlali ya ɗan buɗe i danuwans hi tare da tambayar wanene, Ba abashi amsa ba aka turo kopar ɗakin, uzair ya gani a tsaye Sanye da jallabiya, fuskar shi babu walwala, miƙewa zaune taj yayi yana kallonshi yace”Shigo ciki mana”
Ƙarasa shigowa Cikin falon yae tare da samun wuri saman Sofa ya zauna, batare da ya furta mashi komai ba,
“Meke damun ka ne aminina? naga sauyi sosai akan fuskarka”
harara ya dan jefa mashi tare da cewa”Kaine damuwata Taj, saboda kaƙi bani haɗin kai akan abunda nakeson Cimmawa”
Murmushin takaici taj yayi”cos You wanna get yourself into trouble shiyasa naƙi goya maka baya, Idan suka kama mu munayi masu leƙen asiri what do you think will happen next? They will kill us as soon as they find out that we are investigating them,”
Jinjina kai Uzair yayi”Yanzu haka zamu zuba ido ana aikata 6arna batare da Mun hana ba”?
“Ƙwarai kuwa, Saboda bamu da yadda zamuyi,illa iyaka Muyi addu’ar Allah ya kawo mana ƙarshen su, that’s the only solution”
Jiki a sanyaye Uzair ya miƙe ya soma tafiya har yakai bakin fita daga Falon ya ɗan dakata
“Ka manta alƙawarin da mu ka yi ma juna tun kafin mu fara aiki’? shiru taj ya yi yana kallon bayansa,
Cigaba da magana uzair yayi” duk runtsi duk wuya zamu ƙarfafa ma juna gwiwa wurin ganin mun taimaki ƙasar mu, amma sai gashi kaine na farko daka fara sare mun gwiwata, Narasa goyon baya daga gareka, ji nake tamkar narasa wani sashe na jikina,”
Miƙewa tsaye taj yayi tare da nufar inda Uzair yake atsaye Ya soma magana”Ina jiye mana tsoron abunda zai biyo baya ne, akan idon mu suka kashe mutun da ƴa’ƴansa, a haka kuma ka ke so Mu yi bincike akansu?wannan fa ba aikin mu bane, shin wai kai baka tsoron asirin mu ya tonu su gane cewa muna bibiyar su?ko ba don saboda mu ba, ka tuna kana da mata ni kuma inada ƴa, So ka ke Mu jefa su cikin masifa ne? Yana kai ƙarshen maganar shi uzair yace”In sha Allah hakan bazata ta6a faruwa ba, Nidai inaso ka bani haɗin kai kawai”
Duk yadda Taj yaso ya fahimtar dashi amma Yaƙi ya gane, ba don yaso ba, Ya amince mashi akan suyi Bincike akansu, don su samu hujjojin da zasu fallasa su, har hukuma ta ɗauki mataki a kansu, Tun daga wannan Lokacin Suka soma tunanin ta ina zasu fara neman su, A ƙarshe Uzair ne ya ba shi shawarar su koma inda suka fara ganinsu acikin dajin nan, Cikin sa’a ranar da suka je again suka sake ganin miyagun mutanan nan sun kamo wani mutumin, kamar yadda suka kamo malamin nan, da alama Leƙen asiri shima Yayi masu, Akan idonsu suka koneshi, ranar Taj hankalin shi ya tashi matuƙa har yace ma Uzair shidai zai Cire hannun shi, kusan faɗa sukayi da uzair akan hakan, daƙyar suka sasanta kansu, kuma suka Cigaba da bibiyan Alhazawan nan, Sai dai duk wannan tsawon lokacin da suka ɗauka suna Bibiyarsu Allah bai basu damar sanin kosu wanene su ba, daidai da fuskokin su ba su sani ba, Abu ɗaya kawai suka sani inda suke yankewa mutum hukunci wato Cikin dajin nan a bakin ƙorama, Abunda su taj basu sani ba, duk wani motsinsu akan idanuwansu suke yin shi, Sunsan komai game da bibiyar su da su ke yi zuba masu ido kawai su kayi, yayin da su basu san da hakan ba, Lalube kawai su ke yi acikin duhu…………
Ganin babu Riba a bindiddingin su da sukeyi ne yasa Taj ya cire hannun shi, uzair kuma yasa naci Akan binciken shi, duk yadda taj ya gargaɗeshi amma Ya sanya kafiya, ashe ajaline ke kiran shi.
*************************
A daren Ranar Alhamis ne Wannan mummunan ƙaddarar ta riskesu wadda tayi silar rasa rayukan su,
Wuraren ƙarfe 9 na dare, Taj na zaune tsakiyar gadon shi, ya tasa laptop ɗinshi agaba yana ta ƴan danne danne acikin, har ma ya yi shirin kwanciya singlet ce ajikin shi tare da short, wani aiki ne ya tsayar da shi, Allah Allah ya ke yi ya gama aikin ya je ya kwanta, sai hamma yake yi, ba zato ba tsammani yajiyo bugun ƙopar falo,
Agogo ya kalle, Cike da mamaki Ya sauko daga saman Gadon ya fito ɗakin ya nufi cikin falon, a baƙin ƙopar ɗakin ya tsaya tare da tambayar wanene? Daga waje yajiyo muryar aneeleerh,ka bude mun kopa nice” muryarta Cikin shessheƙar yaji sautinta, jiki na rawa ya buɗe mata ƙopar har saida gaban shi ya faɗi ganin Yadda fuskar ta tayi jawur saboda kukan da ta sha, kayan Bacci ne ajikinta riga da wando sai mayafin data yafa akanta, gefen goshinta kwantaccen gashin kanta,
Aruɗe yace”Aneelerh? Lafiya? me meya faru ne? Ya akai naganki acikin daren nan’?
Daƙyar take iya kallonshi, da runannun idanuwanta wadanda suka yi jawur da su,
“Uzair ya fita bansan inda yaje ba Cikin daren nan, na farka bangan shi ba, hankalina bai kwanta ba, na je wurin baba mai gadi don in tambaye shi ko sun yi magana da uzair kafin fitar shi, yace mun eh sunyi magana da shi kafin ya fita amma bai faɗa ma shi inda zaije ba,……” tunda ta soma magana hankalin taj ya ɗungunzuma, jikin shi ya soma kakarwa, fargabar shi kada ace uzair ya tafi Wurin mutanan nan, dama yace mashi bazai fasa bindiddiginsu ba, idan kuwa hakane to kuwa tabbas yaje yi masu leƙen asiri ne,
Jin yayi shiru bai ce mata komai ba yasa tace”ko kasan inda ya tafi ne”? girgiza mata kai yayi alamar a’a, saboda bai son ya tayar mata da hankalinta,
“Kin kira layin shi”? ya yi tambayar yana kallonta,
“Na kira shi har bansan adadi ba, Amma bai ɗaga ba, kuma kiran yana shiga”jinjina kai yayi” Bari na jaraba kiranshi, ki shigo Ciki ki zauna” yakai ƙarshen maganar yana nuna mata sofa,
Cikin sanyin murya tace”bazan Iya zama ba,” tausayinta duk ya kamashi, bedroom dinshi ya koma a hanzarce Ya kai hannu ya ɗauki wayar shi dake a jiye gefen laptop ɗin shi, Ya shiga call logs, ya danna ma uzair kira, tana fara ringing, uzair yayi picking call ɗin,
Rufe shi da faɗa yayi ta inda ya ke shiga bata nan yake fita ba,
“Duk inda kake ka dawo gida yanzu yanzu, kasa baiwar Allah sai kuka take yi, Saboda rashin hankali, Ka kama hanya ƙarfe tara na dare ka tafi ka barta batare da ka sanar da ita inda kaje ba, Anya kuwa kasan me ka ke yi? wai shin ina kaje ne ma…….? duk wannan suratan da taj ke yi uzair baice mashi uffan ba, A ƙarshe ma saiya yan ke kiran gaba ɗaya, jikin taj ba ƙaramin sanyi ba, tunani ya shiga yi wai shin dawa ma yake waya? idan uzair ne meyasa bai yi ma shi magana ba? kuma ya ɗaga kiran Anya kuwa ba’a samu matsala ba, sake kiran Layin ya yi a switched off ya samu wayar, Nan fa jikin shi ya mutu, hankalinshi Ya tashi
Saman bedside drawer Ya ɗaura wayar, ya fito daga ɗakin ya koma falon, Cike da zullumin amsar da zai ba aneelerh,
Lokacin da ya shigo falon ya ƙaraso inda take tsaye, sai ya shiga Yin ƴan kame kame,
“Bai ɗaga kiran ba ko” ta yi tambayar a ƙagare,
Muryarshi na inda inda yace”Am..um..kingane..eh..muyi waya dashi, ki kwantar da hankalin ki, Yana kan hanyar dawowa gida, yanzu ki koma ki kwanta, kada ki takura kan ki,”
Wani irin kallo yaga tana yi ma shi kallon ban yadda dakai ba, da sauri yace”kiyi hakuri ki koma gida, nan badajimawa ba zai dawo”
Jiki asanyaye Ta juya ta fuce daga falon, Ko bayan tafiyarta saida ya kuma kiranta awaya, Ya ƙara kwantar mata da hankalinta,
Kasa zama ya yi, zarya ya shiga yi tsakanin ɗakin shi zuwa palour, ya rasa meke yi ma shi daɗi duniyar nan, duk bayan ƴan mintuna sai ya jaraba kiran Layin Uzair don yaji in ya bude wayar amma a kashe yake samun ta,
Bawan Allah ya rasa ta zama, duk ya shiga damuwar rashin amininsa, juyawa ya yi da sauri Ya haye upstairs ɗakin angel, ya tura ƙopar ɗakin a hankali, ko’ina duhu, ya lalauba jikin bangon ya kunna switch, tare dakai idanuwanshi kanta, Sai bacci take yi, ta ƙudundune Cikin bargo, murmushi ya ɗan saki kafin ya ɗauke i danuwan shi daga kanta, ya mayar dasu kan wall ɗin dakinta, Zanunnukan da tayi ne tare da kalaman da ta rubuta ma shi, a kullum ya kallesu sai yaji farin Ciki acikin zuciyar shi, duk mun baƙin Cikin da yake ciki,
A hankali Yake tafiya cikin ɗakin nata, ta 6angaren hagu ya zagaya saitin inda take kwance saman gadon, Kneel down Yayi tare dakai hannu Ya yaye blanket ɗin data rufa da shi, rigar bacci ce ajikinta,
Kyakkyawar fuskarta Ya ƙurawa ido yana kallonta, Hakanan ya dinga jin bugun zuciyar shi na ƙaruwa, wani irin matsanancin faduwar gaba, a cikin zuciyarshi ya shiga ambaton Innalillahi wa’inna ilaihirraji’un” ya ambaci hakan ba iyaka,
“Daddy” muryar ta ce ta katse shi, kallonta yayi ganin ta buɗe manyan idanuwanta a kan fuskar shi,
“Dama bakiyi bacci ba”? murmushi ta sakar mashi tare cewa”Nayi mana, yanzu na farka” hands ɗinshi ya sanya ya tallabo fuskarta”ƴar kyakkyawata, Allah yabar mun ke,”
“Ameen daddy, gobe uncle da aunty zasu dawo ko sai mu tafi buzaye ? tayi tambayar tana ƙoƙarin mikewa zaune,
Girgiza mata kai yayi”Till next week nake tsammani”
Ta6e baki ta ɗanyi”daddy ka kwana ɗakina yau”yatsina fuska yayi”Gadonki yayi mun ƙanƙanta” cikin zolaya ya yi mata maganar,
Turo mashi baki tayi”To muje ɗakin ka mu kwana” maƙe mata kafaɗa yayi”A’a, kowa ya kwana a ɗakinsa,” shagwa6a ta soma yi mashi, sosai ta ba shi dariya, suna Cikin Yin fira, Ya tuna da uzair, Rass yaji gaban shi Ya faɗi, Da sauri ya kali agogo, Ƙarge goma da rabi mayar da idanuwanshi kan angel yayi” ki koma ki kwanta, Sai da safe” yana ƙoƙarin mikewa tayi saurin ruƙo hannunshi da sauri kallonta ya yi idanuwanshi sun taunta sosai, ƙaƙaro murmushi ya yi don ya gane me take nufi, Kiss ya mannata mata a saman forehead ɗinta, Yasa hannu ya kwantar da ita tare da lullu6e mata jikinta da bargo, addu’a ya yi mata, kafin ya kashe hasken ɗakin,
Lokacin daya fuce daga ɗakin yana jiyo sautin muryata tana faɗin”I love u so much daddy, Allah yabar mun kai, ina matuƙar ƙaunar ka habibi” murmushi yasaki A hanzarce Ya sauko down stairs, ya faɗa ɗakin shi, daga gefen gadon shi Ya zauna tare da ɗaukar wayar shi, ya ci gaba da jaraba layin Uzair, still a kashe yake samun ta, Zuciyar shi tajima da karaya, A sukwane ya ɗaura wayar saman bedside drawer, a wannan yanayin ne Bacci ya yi awon gaba da shi, sama sama yake yin baccin na shi, 🥺🥺🥺
Sannu a hankali agogon bangon ke harbawa, yana ba da sauti tik-tik-tik. Sakamakon dare da ya tsala don time din karfe ɗaya da rabi na dare, wayar da ke ajiye saman bed side drawer ƙirar Samsung Galaxy ta soma ruri da ƙarfi gaske. A lokacin ya yi nisa a cikin barcin nasa, kusan sau uku kiran na shigowa yana katsewa. A kira na huɗu ne, sautin ya daki dodon kunnansa, a firgice ya farka yana faman ambaton sunan Allah,
Kafin ya zame hannunsa daga kan fuskarsa wani kiran ya sake shigowa wayarsa a hanzarce ya mika hannu saman drawer ɗin ya ɗauki wayar,
Lokacin daya kalli screen ɗin wayar Sunan Aminina ne Ya bayyana, ajiyar zuciya ya ɗan sauke dama jiran kiran shi ya ke yi, A tunanin shi ya dawo gida ne, Shiyasa ya kira shi dan ya sanar ma shi game da dawowar shi, picking call ɗin yayi tare da manna wayar a kunnansa tun kafin ya yi sallama, kunnuwansa suka jiyo masa sautin harbin bindugu. A gigice ya furta, “Aminina!” Kafin Ya ƙarasa rufe bakinsa, muryar Aminin nasa ta katse masa hanzari, a ruɗe yake faɗin,”Na ba ni na lalace, shikenan tawa ta ƙare.”
A firgice ya dakatar da shi, “Ka nutsu ka yi mini bayanin me yake faruwa ne?”
“Sun kama ni ina yi musu leƙen asiri, yanzu haka sun biyo motata, na san kashe ni za su yi, kai ma kuma ba za su ƙyale ka ba. ba zan so ka yi irin mutuwar wulakancin da zan yi ba, don Allah na roke ka, ka gudu kai da Angel, ba na fatan laifina ya shafe ka Abokina. Bayanan sirrin da na ɗauka a wurinsu, yana a cikin memory ɗina, ita kaɗai ce hujjar da asirinsu zai tonu…” Bai kai ƙarshen maganar ba, ɗif ya ji kiran ya katse.
A gigice yake kwaɗa masa kira na fitar hayyaci sam ya manta da cewar wayar ta katse, sake kiran layin nasa ya yi cikin sa’a aka ɗaga kiran, abin da bai ta6a tsammani ba, sautin kururuwa ya ji a cikin kunnansa mai matuƙar razanarwa, wata kausasshiyar murya ya jiyo tana magana ta cikin wayar, “Idan kana son sanin meke faruwa, ka kalli screen din wayarka.” Jiki na rawa ya ɗago da wayar yana kallon screen ɗin yayin da suka canza kiran zuwa Video Call.
Saboda tsabar firgita, a ruɗe ya diro daga saman gadon, Idanuwansa sun firfiro waje tamkar ƙwayar idon za ta faɗo kasa. Ba komai ne yasa shi firgita ba, face motar Amininsa dake ci da wuta, akan idonsa suka zazzaga wa motar fetur, yana hango yatsun hannun amininsa ta tagar motar, wuta sai cin naman jikinsa take yi. Wata irin zufa ce ta wanke masa fuskarsa, a kiɗime ya shiga furta, “No, no!” Duk ya firgice, rejecting call din suka yi.
Wani irin matsanancin ciwon kai ne ya far masa, ba arziƙi ya zube gefen gadon a zaune yayin da jikinsa ke kyarma sosai, ku san minti goma shabiyar baya a cikin hayyacinsa, ya rasa ma me yake yi masa daɗi duniyar nan.
Yana cikin wannan halin ha’ula’in, muryar amininsa ta soma dawo masa a cikin kunnansa, “Ka gudu kai da Angel ba na so laifina ya shafe ku.” Tabbas kuwa za su dawo kansa ne, domin su kashe shi kamar yarda suka kashe amininsa, ba komai ya fi ji ba face ƴarsa ɗaya tilo da ya mallaka wato Angel.
A matuƙar ruɗe ya miƙe, ko jallabiya bai zura a jikinsa ba, iya key ɗin motarsa ya ɗauko saboda tsabar ruɗu wardrobe ya dosa zai buɗe a matsayin kofar dakin, har sai da kansa ya bugu tukunna ya ankare, ya nufi ainihin ƙofar, da sauri-sauri ya fito daga bedroom ɗinsa da ke a downstairs ya nufi cikin babban falon, kai tsaye Upstairs Ya haye. A kiɗime yake tattaka staircases din benen, bai nufi ko’ina ba sai ɗakin Angel, bugu ɗaya ya yi ma ƙofar ta buɗe, ko’ina duhu, kunna hasken ɗakin ya yi, nan take haske ya gauraye ko’ina, wurga kwayar idonsa ya yi kan Angel da ke ƙunshe cikin lallausan bargo, a hanzarce ya ƙarasa shiga ɗakin, tare da hawa saman gadon yana kwala mata kira, “Angel, Angle my daughter!Azeezaty!” Babu alamun za ta farka, a hautsine ya cakume ta ya saba ta saman kafaɗarsa. Da sauri ya fito daga bedroom din nata, ya sauko downstairs, Sam baya a cikin hayyacin shi, balle ya iya tunawa da aneelerh dake a cikin mawuyacin halin na rashin dawowar mijin ta gida,
kai tsaye ya fito waje wurin da motocinsu suke, ɗaya daga cikinsu ya buɗe ƙirar Range Rover, back seat ya buɗe ya kwantar da Angel tukunna ya buɗe diver seat ya shige ciki, a gaggauce ya yi wa motar key, a daidai bakin gate ya tsayar da motar, a hanzarce ya fito ya buɗe gate ɗin, kafin ya koma cikin motar ya fusgeta da gudun gaske. Fitar motarsa ke da wuya, wasu danƙara-danƙaran motoci gudan shida suka nufo shantalelen titin da zai sada ka daga gidansa da alama sun hango motarsa hakan yasa suka bi bayan motar da wani irin matsiyacin gudu. Hankalinsa ba ƙaramin tashi ya yi ba, saboda ya hangi motocin da ke biye da motarsa ta cikin mirror ɗin motar, hakan yasa shi ƙara gudun motar. La66ansa na kyarma yake ambaton La’ila’ha’illa anta subhanaka inni kuntu minazzalimin! Shi kansa bai san inda zai dosa ba, driving kawai yake yi a makance, shessheƙar kukan Angel ce ta fara dawo dashi cikin hayyacinshi, da alama ta farka sakamakon gudun ceton ran da yake yi da su, yasa kanta ya dinga buguwa jikin motar, har hancinta ya fashe jini ya soma zuba.
A ruɗe take furta,”Daddy…What’s happening, where are u going in this darkness night?”
Karamar yarinya ce da ba za ta wuce 11 years a duniya ba, maganarta ma daƙyar take fita saboda halin da take ciki, hawaye ne suka wanke masa fuska yana mai dana-sanin yin aikin jarida fiye da tunanin mai tunanin, saboda shi ne silar shigar shi cikin wannan tashin hankali.
“Angel am really sorry! Na cuci rayuwarki, a yau daddynki ba zai iya ceton ki ba, Angel ba zan jure rashin ki ba, ba zan so laifina ya shafe ki ba.” Yana magana cikin kuka, tafin hannunta ta sanya ta dafe hancinta dake bleeding, jini duk ya 6ata fuskarta, cikin shassheƙar kuka ta kuma cewa, “Dad! My nose is bleeding, zan mutu, gabaɗaya ya rikice ya rasa inda zai tsoma rayuwarsa ya ji daɗi. Bai san amsar da zai ba ta ba, iya sorry kawai yake iya furta mata.
Har yanzu motocin nan na biye da motarsu, lokacin da ya fara jin saukar alburushin bindiga a bayan motar a gigice ya karya kwana ya faɗa wani kurmin daji, mai duhun gaske, shi kansa bai san ina zai dosa ba, ga manya-manyan bishiyoyi da suka cunkushe hanyar, a ruɗe ya yi parking ɗin motar ya zagaya ta back seat din motar jiki na kyarma ya zura hannu ya ɗauko Angel, daga ita sai rigar barci a jikinta, sumar kanta duk ta rufe fuskarta, da gudun gaske yavyi cikin dajin da ita yayin da take sa6e avsaman kafaɗarshi. Hasken motarsa ne da ya bari a kunne yake haskaka masa gabansa, yana cikin gudun nan ba tare davya ankara ba, ya ɗaura kafarsa saman wani ƙarfe mai tsatsa, wanda ke a tsire cikin ƙasa, kaifinsa tamkar na wuƙa, zuruf karfen ya shiga ta cikin tafin ƙafar ya 6ulo ta sama, wani irin raɗaɗin azaba ne ya kai masa ziyara, tsikar jikinsa duk ta tashi, tuni jini ya wanke ƙafarsa, sam ya kasa motsawa daga tsayen da yake a hankali ya shiga furta, “Innalallahi wa’inna ilaihir raji’un.” Cikin kyarma yake ambaton hakan, muryar Angel ce ta katse shi, “Dad let’s go home, nan fa daji ne, akwai kura da zagi za su cinye mu. Daddy ko dai mafarki muke yi ne?” Ta yi tambayar still tana shassheƙar kuka.
Cikin sanyin murya ya ba ta amsa, “Mafarki ne Angel, ba gaskiya ba ne.” Hannayenta ta sanya tare da zagayo da su ta wuyansa, ta manna masa kiss a gefen fuskarsa, “Daddy, to mu tashi daga mafarkin, Angel tsoro take ji.” Tamkar ya fashe mata da kuka haka yake ji,
A tsiyace suka kwararo da gudu cikin dajin da ya shigo da motar, ai ko da jin sautin shigowarsu, bai san lokacin davya fisgi ƙafarsa ba, ya ɗago da ita daga jikin ƙarfen, jini ya dinga kwaranya. A haka ya dinga jan ƙafar har ya karaso daidai wani uban rami mai zurfi wanda kasansa tafkeken ruwa ne ke gudana, tsayawa ya yi zuciyarsa na raya masa cewar ya jefar da Angel cikin ruwan, ya ƙwammace ta mutu a cikin ruwan dacta yi mutuwar wulakanta a hannun mutanen da suka biyo su, don babu ɗigon imani a kansu, in suka kama mutun fetur suke zazzaga masa su ƙona shi har lahira. Ya yi zurfi a cikin tunanin Angel sai kuka take yi, sautin motocin miyagun da suka biyo shi ne yasa shi dawowa cikin hayyacinsa, Allah Sarki yana ji yana gani haka ya ɗaga Angel sama ya yi wurgi da ita, tsulundum ta faɗa cikin tafkeken ruwan mai zurfin gaske yana jiyo sautin kururuwarta.
Ba ƙaramin tashin hankali ba ne zai sa uba ya yi silar mutuwar ɗiyarsa.
Saboda tsabar kuka jikinsa har jijjiga yake yi, duk ya ji ya tsani kansa. Don tuni ya fitar da rai da rayuwa a cikin duniyar nan, domin kuwa Angel tamkar numfashi take a gare shi, jiki a mace ya zube saman guiwowinsa a gaban ramin wani irin jiri ne ya soma kwasar shi, nan take ya yanke jiki ya faɗi a mace.
A daidai lokacin suka ƙaraso da motocinsu, bayan sun yi parking sun kewaye shi, wasu gabza-gabzan samari ne suka fito, ƙirar Samudawa, baƙake wulik! Babu ɗigon imani a kan fuskokinsu, sun yi shigar bakaken kaya da alama bodyguards ne, a tare suka buɗe wa iyayen gidan nasu murfin motocin don su fito.
Abin ban mamaki, manyan mutanane dattawa, suna sanye cikin shiga ta mutunci wato shigar Hausawa, shadda har da malun-malun kai ka ce mutanen arziƙi ne. Koda fitowar su, ba su dora idonsu a kan komai ba sai a kan gawar Taj dake yashe cikin ciyayi.
Guntun tsaki ɗaya daga cikinsu ya ja, “Mala’ika ya riga mu ɗaukar ransa, ba haka na so ba.”
Na gefensa ya ce, “Ban so ya yi salahar mutuwa irin wannan ba, amma duk da haka ba mu makaro ba, tun a nan za mu fara azabtar da shi kafin mu mika shi hannun Munkar da Nakir.”
Tuntsirewa suka yi da wata irin mahaukaciyar dariya, lokaci guda kuma suka ɗaure fuskokinsu. Ɗaya daga cikin manyan mutanen ne ya juya tare da kallan ɗaya daga cikin miyagun da suka zo da su, cike da ba da umarni ya ce, “Miƙo mini galon ɗin fetur tare da lighter.” A hanzarce wanda ya yi wa magana ya nufi motocinsu.
“Maganin masu kunnen kashi ke nan, an gaya musu shiga gonarmu abuvne mai sauƙi.” Bai kai ƙarshen maganar ba, aka miƙo masa galon din fetur yasa hannu ya kar6a, cire murfin ya yi tare da zazzage masa fetur ɗin a jikin rigarsa, sharkaf suka wanke shi.
Dalilin da yasa za mu ƙona shi, saboda gudun mu bar wata hujja da zai sa a zarge mu.
Ba su ƙyasta lighter ɗin ba, har sai da suka kusa shiga motocinsu tukunna ya ƙyasta ya jefe saman ciyayin dake a kewaye da shi. Da gudu wutar ta shiga cinye ciyayin har ta hau saman jikinsa. A lokacin sun shige cikin motocinsu, da gudu suka fisge su tare da barin cikin dajin. Cikin ƙanƙanin lokaci, wutar tacinye shi ƙurmus.
*To Jama’a Zaku ga nasanya Farkon labarin nayi hakan ne don in tariyo maku daga inda zamu tashi fatan an waye ni*
*waɗan da su ka shirya yin payment zasu iya farawa, 08103884440 cikin wata mai zuwa free pages book one zai ƙare, Ina yi ma kowa fatan alkhairi, sai mun haɗu a next page in Allah yakai mu da rai da lafiya*
*💋Boss Bature✍️💋**💋KURKUKUN ƘADDARA💋*
_daga alƙalamin Boss Bature✍️_
*Dedicated To Aunty Kubra❤*
*E8*
Hasken rana ne ya haske fuskarta, sakamakon windown bedroom ɗinta da ta bari a buɗe, dogon numfashi ta ja tare da buɗe kumburarrun idanuwanta waɗanda suka yi luhu-luhu da su sun ƙanƙance saboda kukan da ta sha a daren Jiya. Kwance take a saman gadonsu, jikinta duk ya yi nauyi sam ta kasa motsawa, gefe da gefe na gadon ta kalla don ta ga ko Uzair ya dawo. Ras ta ji gabanta ya faɗi ganin still bai dawo gidan ba, hankali a tashe ta yunƙura ta miƙe zaune tare da wurga idanuwanta kan agogon bangon, ƙarfe tara na safe ko sallar Asubahi ba ta samu ta yi ba, saboda nauyin barcin da ya ɗauke ta.
Siraran hawaye ne suka gangaro daga cikin kwarmin idanuwanta har izuwa saman kuncinta, masu ɗumi, harshenta ta sanya ta ɗan lashi gefen bakinta inda ruwan hawayen ya gifta.
Daƙyar ta samu ta lalla6a ta sauko daga saman gadon, still riga da wandon jiya ne a jikinta, kanta babu mayafi, sumar kanta ce da ta zubo mata ta ko’ina ta yamutse.
A hankali take tafiya harta shige toilet, after some minutes ta fito daga cikin toilet ɗinta, da alama alwala ta yi, lemar ruwa ce a fuskarta da hannayenta.
Cikin wani irin yanayi na jin faduwar gaba, da tsinkewar zuciya, ta nufi closet ɗin kayan su, buɗewa ta yi tare da zura hannu ta ɗauki hijab ɗinta, ta sanya a jikinta.
Saman dardumar dake shimfiɗe ta tsaya, a tsanake ta kabbara sallah, cikin nutsuwa ta soma yin ibadarta.
Bayan ta kammala, zama tayi saman dardumar tare da ɗaga hannayenta Cikin harshen larabci ta soma yin addu’o’inta daga ƙarshe ta rushe da matsanancin kuka tana faɗin. “Ya Allah Ka dawo mun da mijina lafiya,Ya Allah ka karemun shi aduk inda yake! inaji araina kamar wani mummunan abu ne ya faru da shi, Uzair bai ta6a tafiya batare da sanina ba. Amma jiya ya tafi ya barni in the midnight without my knowledge,” Sosai take yin kukan ta jima, kafin ta yanke shawarar zuwa Wurin taj donta tambaye shi idan Sunyi waya da Uzair.”
Miƙewa tayi da sauri, ta fito daga Cikin bedroom ɗinta, ta nufi hanyar fita daga falon, a bakin gate ta samu maigadin gidanta zaune saman benci yana sauraron radio.
Tunda ya hango ta ya yi saurin ajiye radio ɗin saman bencin ya mike ya tunkare ta, “Barka da safiya hajiya, kun tashi lafiya.”Ba ta amsa mashi sallamarshi ba, saboda ba ta acikin natsuwarta,
“Inaso zanje wurin taj ne, may be sunyi waya da uzair, wlh nadamu sosai nakasa samun natsuwa baba, inaji kamar wani abu ya faru da shi,” Tana magana hawaye na fita daga cikin idanuwanta.
Tsananin tausayinta ya kama baba maigadi, tunda yake bai ta6a ganin hawayen Aneelerh ba, sai a daren jiya da kuma yau, ya lura da tashin hankalin dake akan fuskarta.
Cikin sanyin murya yace”Kiyi haƙuri ki kwantar da hankalinki, in sha Allah uzair yana cikin ƙoshin lafiya, babu abin da zai faru da shi.”
Gyaɗa mashi kai ta yi tare da wuce shi ta nufi gate ɗin, Hannu tasa ta buɗe ƙopar jikin shi ta fuce daga cikin gidan.
Girgiza kai maigadi ya yi ji yake da a ce yana da halin da zai iya taimakon Aneelerh a yau daya taimaketa, abin da ciwo ka ga mutumin daya saba kyautata maka a cikin wani ƙunci na rayuwa kuma baka da yadda za ka iya taimakon shi, komawa yayi jiki asanyaye ya zauna saman bencin.
Bayan fitar Aneelerh, kai tsaye ta nufi gidan Taj dake a jikin gidansu, tun abakin gate ta hango maigadin gidanshi a tsaye ya jingina bayan shi jikin gate ɗin, fuskar shi duk a harmutse da alamun damuwa atattare da shi, hakanan taji gabanta yayi wani irin mugun bugu ras!
Ƙarasawa inda yake tsaye tayi muryarta da fargaba atattare da ita ta ce, “Assalamu alaikum”
Tunkan takai ƙarshen maganar taga ya ɗan firgita, sai daya kalleta tukunna Yaɗan saki fuskarshi yace”wa’alaikum salam, malama Aneelerh, in ce ko lafiya?”
Hawaye ne suka sake wanke fuskarta, cikin shessheƙar kuka ta ce, “Har yanzu uzair bai dawo ba, yanzu ma zuwa nayi wurin taj, don inji idan ya kira shi awaya,” Tana kai ƙarshen maganarta baba maigadi ya ce, “Innallahi Wa’inna Ilaihir raji’un!”
A ruɗe ta ce, “Baba lafiya?” Cikin tashin hankali ya ce, “ƴar nan tun jiya na gaza samun kwanciya hankali, ko runtsawa ban yi ba, saboda damuwa, jiya bayan kin zo neman Taj, kin tafi na shiga daga Cikin ɗakina na kwanta, har bacci na fara bacci sama sama, can cikin dare wuraren ƙarfe ɗaya da rabi, ina kwance na ji fitar mota daga cikin gidan nan. A firgice na farka na fito daga ɗakina, koda na fito naga gate a wangale, na leƙe banga komai ba, na dawo na duba naga babu motar taj da yake yawan fita da ita, a nan na gane cewa shine ya fita cikin motarshi.”
Tunda ya soma magana Aneelerh ta dafe ƙirjinta da tafin hannunta, ta zazzare ido tana kallon shi,
“Na yi mamakin ina Taj ya tafi batare daya sanar dani ba! domin kuwa tunda nake aiki a ƙarkashin shi bai ta6a lekawa koda ƙofar gida batare da sanina ba, amma sai gashi jiya tsakar dare ya fuce, kuma abun da ya ɗaure mun kai, ba shi kaɗai ya tafi ba. Hada ANGEL!” A gigice Aneelerh ta shiga ambaton Innallahi Wa’inna Ilahir raji’in! Na shiga Uku! Wai meke faruwa ne? Wayyo Allahna!” Gabaɗaya ta bi ta ruɗe, shi kan shi baba maigadi da ya sanar mata, sai da yayi danasani ganin yadda ta daura hannayenta a saman kanta tana zabga salati.
Juyawa tayi da gudun gaske Ta koma Cikin gidanta, A lokacin malam Garba maigadinta Yana zaune saman bencin yaga shigowarta a guje, har yana tambayarta lafiya, amma bata saurare shi ba.
Hankalinshi ya ƙi kwanciya, Miƙewa ya yi da nufin yaje su yi magana da tajo,yana ƙokarin fita daga cikin gidan, baba maigadin gidan Tajo, ya tura kofar gate ɗin, suka yi kicibus da juna.
“Wai meke faruwane ɗan ladi”malam garbane yayi mashi tambayar fuskarshi a yamutse.
Baba maigadi ya ce, “Tun ɗazu naso in zo mu yi magana. Amma damuwa ta hana ni, lamarin dai babu daɗin ji.” Nan ya kwashe duk abin da ya faru na tafiyar Tajo tsakar dare ya sanar da shi.”
Malam Garba ya hauyin sallallami, hankalinshi duk ya tashi a rude ya ce, “Indai kuwa haka ne akwai matsala. Ya kamata a sanar ma Ƴan sanda don a san abin yi tun kafin lokaci ya ƙure mana”!!
Jinjina kai baba maigadi ya yi” ni ma abun da nake tunani kenan, amma mu ɗan ƙara jira kaɗan zuwa anjima”
“Shikenan zan koma bakin aikina, zuwa anjima idan ba wani labari game dasu sai muje police station ɗin” a cewar ɗan ladi, daga haka suka yi sallama da juna. Ya koma gidan da sauri don ya barshi a buɗe bakowa
Aneelerh kuwa bayan shigarta Cikin gidan. Afujajen ta nufi bedroom ɗinta ta shige, jikinta na kerma ta ɗauki wayarta dake ajiye saman bedside drawer,
Call logs ta shiga ta dannawa numbar da tayi saving da Abie kira,Tana fara Ringing, Aka ɗaga wayar, muryar babban mutuncine mai cike da kamala Ta karade kunnuwanta, “Assslamu Alaikum daughter…” Tun kafin ya kai ƙarshen maganar, Aneelerh ta rushe da matsanancin kuka tamkar ranta zai fita…”
Muryar Abie a ruɗe ya shiga kwala mata kira.” Aneelerh lafiya kike kuka meya faru? Waya ta6a mun ke? ki buɗe baki ki yi mun magana!”
Sai da ta yi kukan mai isarta, sannan ta soma magana cikin shessheƙar kuka”a…Abie..Uzair da Taj..” katse ta ya yi da cewa.”me ya faru dasu? Wani ya rasu ne’
“A’a, tun daren jiya Uzair ya bar gida wuraren ƙarfe tara, shi kuma Taj ya bar gidansa karfe ɗaya da rabi na dare, kuma ya tafi tare da Angel. Babu wanda yasan meya faru dasu, kuma dukansu layinkan wayoyinsu akashe, Abie ina cikin matsanancin tashin hankali.”
Lamarin ya girgiza abie sosai,”
Muryarshi cikin sigar lallashi ya ce, “ki kwantar da hankalin ki aneelerh, In sha Allah babu abun da ya faru da su, yanzu zan yi waya da uncle ɗinki, ki ɗan ƙara haƙuri.” Cikin shessheƙar kuka ta ce”To Daddy, saina jika “ya ce” ki daure ki ci abinci, na san ba ki ci komai ba” Amsa mashi ta yi da to kafin suka yi sallama ta kashe wayar. Saman gado ta koma ta zauna zugudun cikin zullumi, salla kadai ke tada ta.
Wuraren ƙarfe huɗu na marece, tana kwance magashiyan fuskarta ta kumbura tayi suntum, tunda tayi sallar la’asar bata cire hijabin jikinta ba,
jiniyar motor ƴan sanda tajiyo daga waje Wii! wiii! ras! taji gabanta ya faɗi, fargabarta kada ace gawar Uzair kota taj suka kawo Cikin gidan,
A hanzarce ta miƙe, da gudu ta fito daga cikin bedroom tana sauko ƙafarta cikin falon, adai dai wannan Lokacin mahaifinta Alhaji Muhammad falgore ya doko sallama, Yana sanye Cikin shiga ta alfarma, Shaddace fara tass taji guga, tare da malun malun, kanshi Na sanye Cikin hula, Bayan shi kuma Ƴan sanda ne su huɗu sanye cikin kakin su, ɗaya daga Cikinsu Uncle dinta ne kaninta mahaifinta me ruƙe da muƙamin dco(Divisional Crime Officer),Atare dashi akwai Ic (inspector crime) sai kuma Ipo(Investigation Police Officers) Su biyu ne ɗaya mace ɗaya Namiji masu tsayi da jiki ba laifi a launin fata baƙake ne,
Zuba masu ido aneelerh tayi tana kallonsu batare da kiftawa ba, tasan aikin mahaifinta ne, mutunne mai ɗaukar abu da mahimmanci babu wasa a lamarinshi, Sam ba ta yi tsammanin zai yi report din case din wurin ƴan sanda ba, Sai gashi ɗungurugum ya taho dasu Gidan,
Ganin ta yi tsaye tana kallonsu yasa Shi yi mata gyaran murya yace”Daughter Kece kika koma haka”? jin haka yasa ta nufe shi da sauri, tunkafin ta ƙaraso ya buɗe mata hannayen shi ta faɗa a kirjin shi, ta fashe ma shi da kuka, duk jikinsu yayi sanyi, Hannu yasa yana shafa bayanta cikin sigar lallashi, kafin ya kalli uncle din nata yace dashi Bismillah su zauna”wuri suka samu kowa ya zauna saman sofa, Bayan ya raba jikinshi daga na aneelerh yace itama ta zauna, atare dashi suka zauna,
Uncle Bash ƙusa yace”Aneelerh Why tun daren jiya daya fita baki sanar damu ba”?
Cikin shessheƙar tace”Ae nayi tunanin zai dawo kafin da safe”
Jinjina kai yayi”okey, yanzu ki natsu ki faɗa mana taya akai yabar gidan without your knowledge”?
Ƙoƙarin buɗe baki tayi donta kora masu jawabi kamar yadda suka buƙata, nan take Wani irin yunƙurin amai yazo mata, da sauri ta miƙe daga saman sofa din ta watsa aguje zuwa bedroom ɗinta,
Dco ya kalli Ramlat Jami’ar binciken da suka zo da ita yace da ita tabi bayan aneelerh, amsa mashi tayi da Okey sir, Kafin ta miƙe ta bi bayan aneelerh cikin bedroom ɗinta,
Tana shiga tajiyo Sautin ƙaƙarin aman da aneelerh keyi acikin toilet, kaitsaye ta taka izuwa cikin toilet ɗin, Agaban Sink ta samu aneelerh tana ta kwara amai tamkar ƴar hanjin cikinta zasu fito waje,
Ƙarasawa tayi har zuwa bayanta, ta sanya hannunta tana ɗan bubbuga bayanta, Tana yi mata sannu,
Bayan ta kammala yin aman, Ramlat ta kunna mata fanfo, ta wanke bakinta tass, Takai hannu jikin tissue holder ta yago kaɗan ta miƙa ma aneelerh ta goge mouth ɗinta, daga haka ta ruƙo hannunta suka fito daga Cikin toilet ɗinta
“Sorry dear ki kwantar da hankalinki, in sha Allah we will try our very best wurin ganin mun gano inda mijinki ya ke,”acewar Jami’ar binciken,
Aneelerh dake ta faman fitar da numfashi mai ɗumi tace”Bana jin daɗin jikina, tun jiya banci komai ba, kuma bana jin zan iya cin wani abu,”
Ramlat tace”Ki daure kici, lafiyar ki muke buƙata, domin kuwa idan ba lafiya atare dake taya zamu iya samun haɗin kanki wurin yin investigation ɗinmu”?
Takai ƙarshen maganar a lokacin sun dawo Cikin falon, Hankalin Dco da na sauran jami’an ya dawo kansu, mahaifinta kuwa jikinshi ba ƙaramin sanyi yayi ba, ganin yadda ɗiyar shi ta rame, tamkar ba neelerh ɗinsa ba,
A gefen abie ta zauna tare da kwantar da kanta saman kafaɗar shi, Ramlat Ta kalli dco tace”Sir, bata da koshin lpy, kuma ta sanar dani cewa tun jiya bata Ci komai ba,”
Uncle bash yace”Idan har bata ci abinci ba, ba zamu iya samun bayanan da muke bukata ba awurinta,” Yayi maganar eyes dinshi akan Abie, kafin ya mayar dasu kan Ramlat yace”ki duba frigde nasan baza a rasa abunsha ba, Ki ɗauko mata tare da ruwa me sanyi”Amsa mashi tayi”okey sir” kafin ta juya ta nufi fridge ɗin dake A falon”
Hanmu tasa ta buɗe frigde din, Lemuka ne a jere masu sanyi, hada fura da youghurt, fresh milk ta dauko mata tare da ruwa”ta ruƙo bottles din a hannunta ta dawo ta ɗaura su asaman C table din dake agaban sofa din da aneelerh take,
Uncle bash yace”Aneelerh ta shi kisha,”batare da musu ba, Aneelerh ta mike zaune, Takai hannu ta ɗauki milk ɗin ta buɗe ta kwafa abakinta, ta shiga ɗaɗɗakarta, makoshinta har wani sauti yake badawa kwat kwat!!
Abie yace”Ki sha a hankali, kada ki shaƙe” janye bottle din tayi daga bakinta tana faman sauke ajiyar zuciya, lallai ba ƙaramar yunwa take ji ba, bayan ta ajiye milk din Abie ya dauki bottle water me sanyi ya mika mata, hannunta na kerma ta buɗe mufin ta kwafa abakinta, A hankali take shan ruwan harta kammala, Sai gashi ta ɗan samu natsuwa,
Uncle bash yace”Aneelerh kiyi mana bayanin yadda komai ya faru a daren jiya, muna sauraronki”
Ganin yadda zufa ke keto mata, abie yace ta cire hijabinta”hannu tasa ta ɗebe hijabin, dama akwai Kallabin data ɗaure kanta da shi,
A tsanake ta soma Yi masu Bayani tiryan tiryan
“Ji wuraren ƙarfe tara, nafarka ban samu uzair a saman gado ba, nayi tsammanin ko ya shiga toilet ne amma ko da na duba baya a ciki, na yanke shawarar zuwa na tambayi megadi,koda naje wurinshi yace mun Yaga lokacin da Uzair ya fita acikin motarshi, kuma har magana sunyi da shi kafin tafiyar shi, koda jin haka na dawo cikin gida na ɗauki wayata na kira layin uzair tana ringing amma uzair bai ɗaga ba, a ruɗe na ajiye wayar na fito na nufi gidan taj, ina zuwa na shiga gidan, A falo nayi mashi sallama, ya fito daga ɗakin shi, harma yayi shirin kwaciya, nake faɗa mashi Game da tafiyar uzair ƙarfe 9 na dare na farka banganshi ba, Nayi tunanin ko ya kirashi awaya, saboda kusancinsu dana sani, Uzair zai iya 6oye mun abun amma bazai iya 6oyema Taj ba, Shiyasa na tambaye shi,A wannan lokacin taj yace na jirashi ,Zaije room dinshi ya kira shi awaya, na tsaya ina jiranshi, koda ya dawo na tambaye shi ya kirashi,yace mun in kwantar da hankalina duk inda yake ayanzu yasan yana akan hanyar dawowa ne, ba don na yadda da kalamanshi ba, na dawo gida zuciyata duk a harmutse na kwanta, Ko a daren sai da taj ya kira layina, ya ƙara kwantar mun da hankalina, a wannan yanayin bacci yayi awon gaba dani,
Shiru ta ɗanyi tana mayar da numfashi, kafin taci gaba da cewa”da safe na farka wuraren ƙarfe tara, still uzair bai dawo ba, Nan ma hankalina ya ƙara tashi, Na yanke shawarar zuwa Wurin taj don inji idan sunyi waya da uzair, koda ace ya kirashi tsakar daren jiya, Ina fita daga gida na nufi gidan taj, tunkafin ma naƙarasa naga baba maigadin gidan atsaye ya jingina bayanshi jikin Gate din gidan fuskarshi da alamun damuwa atattare da ita……………”Komai daya faru saida aneelerh ta sanar dasu, lokacin da aneelerh ta kammala zayyana masu komai, Lamarin yayi matuƙar girgizasu, ipo Yace”akwai matsala, Uzair ya fita gida ƙarfe 9 na dare, Shi kuma taj ya fita tare da ƴarshi ƙarfe ɗaya da rabi nadare? tabbas wani Babban al’amarine ya afku”
Ramlat tace”Kuma dukansu atare da wayoyinsu suka fita”?
Aneelerh tace”Shi uzair da wayarshi ya fita, Amma shi Taj banda masaniya akan hakan”
Dco yace”Aneelerh zaki yi mana jagora zuwa gidan Taj don mu fara gudanar da binciken mu”Amsa mashi tayi”toh” kafin suka miƙe gaba ɗayansu suka ɗunguma zuwa gidan Tajuddeen, A bakin gate Dco Yace ma malam Garba yabi bayansu, Don shima zasu buƙaci jin ƙarin bayani awurin shi, Lokacin da suka ƙaraso bakin gate ɗin gidan Tajo, Baba maigadi Na zaune saman benci cikin zullumi, Dco yace shima Yabiyosu Cikin gidan,Ya miƙe yabi bayansu,
A falon Gida Taj, Abie ya zauna, baba maigadi da malam garba suka zauna saman Carpet suna jiran tambayoyin da za’ayi masu,
Aneelerh ce ta yi masu jagora zuwa bedroom ɗin taj, A bude suka samu ɗakin, Da sallama tashiga ciki, Dco da ic da ipo suka mara mata baya,
A tsakiyar Dakin suka tsaya suna bin ko’ina da kallo, Karaf idanuwan Aneeleeh suka sauka akan wayar Taj dake yashe ƙasan tiles, A ruɗe tace”Uncle ga wayar shi anan” A tare police men din suka kai idanuwansu kan abunda aneelerh ke nuna masu,
Hanky Ic ya curo daga cikin aljihun shi, a hankali ya taka zuwa inda wayar take a ƙasan tiles,ya zuƙunna tare da ɗaukota,Ya dago da ita ya juyo da ita, Screeen ɗin wayar ya fashe, sakamakon Bugun tiles da Tayi,
Juyowa Yayi tare da kallon Dco yace”Sir, A hasashe na, Jiya Bayan aneelerh tabar gidan nan, Tajo Ya dawo Ya kwanta har bacci ya ɗauko shi, Wuraren ƙarfe ɗaya da rabi na dare, An kira wayar shi, kuma ya ɗaga kiran, tabbas an gaya mashi wani abu daya ɗaga mashi hankali, wanda yayi matuƙar razanar da shi, har baisan lokacin da yayi wurgi da wayarshi ba, Ya fito daga ɗakinshi Yaje ya ɗauki ɗiyarshi ya gudu da ita,tabbas anyi mashi barazanane, kuma zai iyayiyuwa anyi amfani da uzair wajen razanar da shi”
Jinjina kai dco yayi”tabbas akwai wani 6oyayyen Al’amari, daya faru a daren Jiya, taya za’ae mu gano ainihin meya faru?
Ipo yace”Abu na farko daya kamata muyi shine, mu fara tambayar masu gadin gidajensu A wani yanayi sukayi rabuwar ƙarshe dasu, sannan Wayar taj, Yakamata A gyarata, kodan mu samu damar bincikar last Call da yayi recieving awannan daren! Sannan zamu duba messages ɗin wayarshi, koda ace sun tattauna game da wani sirri dake atsakaninsu shida uzair”
Gaba ɗaya sunyi amanna da maganar ipo, aneelerh dae Jikin ta ƙaura yayi la’asar,Tunda taji hasashen Ic gabanta Ya dinga faɗuwa rass rasss! Daurewa kawai take yi,
Cikin falon suka dawo Kowa ya zauna, Ipo Ya kalli ɗan ladi baba maigadi na gidan tajo, yace”lokacin da taj zai fita A daren Jiya! Kaine ka buɗe mashi gate”Da sauri baba maigadi ya girgiza kai”a’a yalla6ai, Wlh ni bansan ma Ya fita ba, Kwatsam Ina Cikin Bacci sama sama Naji alamun buɗe gate, kafin inyi wani yunƙuri in miƙe inzo in duba,Tuni Ya fuce, Babu shi babu alamar shi, har waje na leƙa banga komai ba, na dawo cikin don in duba wurin ajiye motocin shi anan naga ya fita da ɗaya daga cikin su, Bayan haka kuma na shiga cikin gidan don inga ko ƴar shi angela na nan, sai naga babu ita, nan na gane cewa da ita ya tafi, Wannan shine iya abunda nasani,
Jinjina kai Ipo ya yi kafin Ya mayar da idanuwanshi kan Malam garba me gadin gidan Uzairu,Yace”kaifa?Me ka sani game da tafiyar Uzair”?
Malam Garba yace”Naga lokacin da uzair ya fita, har magana mun yi da shi, Abunda ya faru ina zaune saman benci ina sauraron radio, Sai ga Uzair ya fito daga Cikin gidan, Sai faman sauri yake yi, Ya buɗe mota ya shiga yayi mata key,Ya ƙaraso da motar Yana yi mun hon in buɗe mashi gate, Na taso Na buɗe mashi, har ina tambayarshi ko lafiya, naga zai fita a lokacin da bansaba ganin ya fita ba, ya ce mun babu komai, bazai jimaba yanzu zai dawo, Nayi ma shi Allah ya kiyaye hanya, wannan shine maganarmu ta ƙarshe da shi,’
Jinjina kai ipo yayi”bayan wannan ko akwai Wani wanda ke yawan zuwa gidajensu?
Har suna haɗa baki wurin cewa a’a,
Dco yace”Yanzu Idan munason ganawa da iyayen kowannansu taya zamu same su”? ya yi tambayar yana kallon aneelerh,
Cikin sanyin murya tace”surukaina basa ƙasar nan tun da jimawa suka tafi suwa south korea amma kwanan nan zasu dawo, Shi kuma taj Iyayen shi Suna zaune a Buzaye, Sun tsufa sosai, Ni aganina baikamata asanar dasu ba, Hankalin su zai tashi sosai,’
“Bazamu sanar dasu ba, Amma Shi taj ina matar shi? Ipo ne yayi mata tambayar,
Abie yace”ae shi Taj tunda matarshi ta haifi ƴarshi ta fari, ta gudu tabar gidan, Kamar yadda aneelerh ta sanar dani, Acikin bathtub tabar mashi jinjirar,Itace ANGEL yarinyarshi,”
Dco yace”Okey, Shine Yake auran ƴar gidan tsohon gomna, Alhaji Ubaid Sani wadata” Jinjina kai abie yayi eh shine,
Ipo yace”Abunda za’ae yanzu, zamu fara bincikar wayar taj, wata’ƙil asamu wata shaida, Sannan zuwa gobe in Allah yakai mu, Zamu Kira Surukanki, don yakamata asanar dasu halin da ake Ciki, Shima Alhaji ubaid Zamu tuntu6e shi, Sannan Zamu Je gidan Radion da suke aiki, Dole mu binciki kowa dake atare dasu, idan Akayi sati ɗaya ba’aji ɗuriyarsu ba,Za’a Yaɗa labarin 6acewar su ta kafafan sada zumunta, Wata’ƙil adace”
Sun jima suna tattaunawa Da ƴan sandan kafin su tashi tafiya, Sai da suka ƙara kwantarma Aneelerh hankalinta, Sukayi mata alkawarin zasuyi iyakar bakin ƙoƙarinsu, sosai suka bata baki, kafin Ƴan sandan suka tafi, Ya rage gidan daga ita sai Abie sai su baba maigadi, Umarni abie Ya basu dasu Cigaba da kula da gidajen, Kafin a ƙare Binciken,
Ita kuma aneelerh yace Ta tashi su tafi gida, don bazai barta ita kaɗai agidan ba, ba don taso ba tabi bayanshi, A motarshi suka tafi,drivern gidansu ne ke tukasu,
Tsawon One Week Ƴan sanda suna Bincike akan case ɗin, Basu samu komai ba,Har gidan radion su taj sukaje,Ɗaya bayan ɗaya Aka fiddo da ma’aikatan gidan radion suka yi masu tambayoyi,
A Ƙarshen Satin Cikin Weekend Uncle abdallah Ya dawo ƙasar tare da Hajiya adama, duk arana ɗaya Suka shigo garin tare da Alhaji ubaid,
Sun girgiza da jin abunda ya faru na 6acewar Su tajudeen Hajiya adama tasha kuka tamkar ranta zaifita, Haka Alhaji ubaid ya shiga matsananciyar damuwa Musamma da ya ji cewa tare da jikar shi Taj ya tafi adaren Ranar, yarinyar da yake gani tamkar ƴarsa benazir data gudu tabarshi tsawon shekaru, kasancewar shi babban mutun Wanda yasan mutane da dama, tun ranar daya shigo ƙasar Ya kira Cp(Commisioner Of Police)Sukayi zama na musamman Akan case ɗin 6acewar Su tajo,
Gaba ɗaya Cp ya tattara Jami’an da suke akan aikin Binciken case ɗin, don yaji bayani daga garesu, Bakomai yafi ɗaure ma kowa kaiba, face Yadda aka rasa samun wata hujja da zata tona asirin abunda ya faru dasu adaren ranar,
Wayar Taj da suke tunanin zasu samu Wata shaida atare da ita, koda Akaba me gyaran waya ya canza screen ɗin, Cikin rashin sa’a suka samu komai na wayar Ya goge, Duk zurfin binciken da Jami’an sukayi, Basu samu koda motocinsu ba, Saƙo da lungu na garin da bayan garin dare da rana haka sukayi binciken amma basu samu wata shaida ba, A ƙarshe binciken ya koma CID,
Labarin 6acewar Su taj ya karaɗe social media, Ta ko’ina zancen 6acewarsu a keyi, Mafi rinjayen mutane sunfi tunanin An kashesu ne a 6oye, Tunda kowa yasan su da son fiddo da gaskiya, kota halin ƙaƙa, Wannan yasa mutane su ke Hasashen kodai an kashesu a 6oye ne Allah shine mafi sanin dai dai!!!
Rayuwar Aneelerh gwanin ban tausayi baiwar Allah, Ta jigata sosai, ta shiga mawuyacin hali na rayuwa, ta rame sosai ta ƙanjame hatta aiki Abie ya hanata zuwa tunda ba ƙoshin lafiya gareta ba, Rashin Uzair da taj da kuma ANGEL ba ƙaramin nakasa rayuwarta yayi ba,Tayi kewarsu sosai,a kullum addu’arta Allah ya bayyanar dasu aduk inda suke, saboda su takan tashi tsakar dare tayi nafilfili, tayi masu addu’a Tana kuka,Haka rayuwarta taci gaba da kasancewa, Abinci kanshi sai abie da mami sun tasata gaba tukunna take Cinshi, a karshe da ciwon nata yayi yawa, Dr ya duba ta, Ashe hada laulayin Ciki, Allahu akhbar Abunda suka jima suna rokon Allah ya basu ita da uzair, Ga shi Yau Allah ya kar6i addu’arsu a lokacin da shi uzair ɗin Bayanan, Allah sarki rayuwa kenan.
A 6angarensu Hajiya adama kuwa, basu koma south korea ba, Anan suka Ci gaba da zama, saboda halin da ake Ciki na 6atan Ya’yansu ,kullum Cikin zullumi suke,
Akwana Atashi Yau wata ɗaya cuff da 6atansu tajuddeen, A lokacin Kowa ya fara sarewa, Tuni ƴan sanda sun sallami su baba maigadi, makullan gidajensu Yana a hannun jami’an CID, sun ruƙe su har zuwa lokacin da zasu kammala bincikensu,
Tun Uncle abdallah Yana 6oye wa Mutanan Buzaye game da 6atansu Tajo, harya yanke shawarar zuwa buzaye don ya sanar dasu halin da ake Ciki,
A ranar da suka shirya tafiya tare da hajiya adama suka Bi jirgin asubahi zuwa katsina state, A hotel suka sauka, A washe gari su ka wuce zuwa buzaye, Lokacin da suka isa garin da safe, a ƙopar gidansu Malam zahiru suka risƙi mutane zazzaune saman tabarma, nan fa hankalinsu ya tashi, Sunzo da mummunan labari Sun riski labarin dayafi nasu ɗaga hankali .
Mutanan da suka samu a ƙopar gidan, Ƴan zaman makoki ne, Allah ya yi ma iyayen tajuddeen rasuwa su duka Biyun, Malam Zahiru ne Ya fara Rasuwa sakamakon Hatsarin Da yayi, Yana Cikin tafiya gefen titi ya dawo daga gona zashi gida, Wata mota ƙirar dab,Ta biyo ta titin da gudun gaske kaitsaye tabi takanshi, Ashe burkin motar ne Ya samu matsala, Duk yadda drivern dake tuƙa ta yaso Ya yi control ɗinta abun Yaci tura,Gaba ɗayansu suka mutu a wannan lokacin,
Tunda labarin mutuwar shi ta riski Yahanasu mahaifiyar tajuddeen taji mummunar mutuwar da Mijinta yayi,nan take Zuciyarta ta buga ko shurawa batayi ba, innalallahi’wa’inna ilahirraji’un!!!Uncle abdallah yaji mutuwar ɗan uwansa,duk yadda yaso ya jure hakan ya faskara tamkar ƙaramin yaro haka ya dinga kuka,mutane suna lallashinshi,
Hajiya adama saboda tsabar kiɗima har suma saida tayi, Ciwo gadan gadan Ya taso mata, A nan gidan deeje suka xauna mahaifiyarsu Uncle abdallah, ita kanta deeje batasan inda kanta yake ba Tun bayan rasuwar malam Zahiru Ta kamu da ciwon paralyse, Laraba ƙanwar yahana su Ce ke yin jinyarta, da wasu daga cikin ƴan uwansu na nan buzayen, Kafin Barin su uncle abdallah buzaye, Itama deeje Allah yayi mata rasu wa, Wa’iyazubillah Babu wanda bai tausaya ma Uncle abdallah ba, lokaci ɗaya ya rasa ya’yan shi da suka 6ace,Ya rasa ya’yan shi da matar sa yanzu kuma Yayi babban rashi na mahaifiyarsu deeje, Lamarin dai babu daɗin ji!
Kusan wata ɗaya su ka yi A buzaye kafin suka tattara yanasu yanasu suka koma Jos,
Zaman ƙasar gaba ɗaya ya gagaresu, Babu wani Labari me daɗi, a ƙarshe suka tattara suka koma south korea, Cike da zullumin Me zai biyo baya, Don sunyi magana da Ipo, ya yi masu alƙwarin duk halin da ake Ciki game da bincikensu taj zai kira su awaya ya sanar dasu, Shima Alhaji Ubaid, Sun ƙare magana da Jami’an dake bincike a kan case ɗinsu Tajuddeen, sun yi mashi alƙwarin zasu yi iyakar bakin ƙoƙarinsu,wurin Bincikar ainihin abunda ya faru da su,kuma zasu binciko su aduk inda suke muddin suna a doron duniyar nan!,kuma duk halin da ake aciki zasu dunga tuntu6arshi akai kai,
A 6angaren Aneelerh kuwa,Komai Ya hargitse mata baiwar Allah, Ga rashin da ta yi Ga kuma Laulayin Ciki da take fama dashi, kullum cikin yin kuka take, tsananin tausayinta ya kama su Abie, Kowa lallashinta yake yi, Akan tayi hakuri tabarma Allah komai, tun daga wannan lokacin ta hana idonta bacci,Takan tashi tsakar dare tayi nafilfili duk don saboda su Angel,idan tafara nafilfili har sai kafafunta sun fara yi mata zogi tukunna take dakatawa, idan kaga aneelerh tayi bacci to da rana ne, domin kuwa ta maida dare lokacin yin ibadarta, kullum rana ta Allah sai ta yi masu sadaka, bayan haka ta yi magana da abie akan A nemo manyan malamai su taya su da addu’a kuma ayi masu sauka, batare da 6ata lokaci ba, Abie Ya aiwatar da duk wani abu da Aneelerh ta bashi shawara akai,
Ƴan sanda Sun Dage damtse wurin Yin Bincike,Yayin da malamai suka Bada himma Wurin taya su addu’a da kuma yi masu sauka, Haka zalika su aneelerh Sun taka rawa wurin Yi masu addu’a, da sadaka, akan Allah ya bayyanar dasu,wannan kenan..
Shin ya rayuwar Angel ta ƙare a cikin ruwan da mahaifinta ya jefa ta? Ta rayu ko ta mutu?
Bayan wasu ƴan kwanaki da Tajuddeen ya jefa ta a cikin ruwa, hadari ne Ya haɗu bakikkirin a sararin samaniya, kafin wani lokaci yayyafi Ya soma sauka a doran ƙasa. Daji ne mai manya manyan bishiyoyi da tsirrai, kowane ganye ka kalla yayi kore shar da shi, gwanin ban sha’awa, musamman ciyayin da ke cikin dajin masu tsayi da cukowa, a daidai wannan lokacin garken shanu suka shigo cikin dajin. Aƙalla sun kai talatin da biyar, suna tafe suna Cin ciyawa.
Wucewarsu keda wuya cikin dajin,Wata kyakkyawar bafullatanar daji, fara tass Jawur da ita, sanye cikin kayansu na al’ada, Ta bayyana hannunta ruƙe da sanda, siririyace Bata da ƙiba ko misƙala zarratin gata doguwa sam6al, Amma akwai dukiyar fulani cike tab da ƙirjinta, ga yalwataccen gashin kai dake gareta mai tsayin gaske, anyi mata kitson kalaba,Wanda yasha ado da duwatsu,wutsiyoyin gashin sun sauka har tsakiyar bayanta, ga wasu da suka zubo ta gefe da gefe na fuskarta,
Tabarakallahu ahsanul khaliqin,Wasu dara daran idanuwa gareta Farare Ƙal kamar fatar farin Cikin kwai, Launin Idon nata Brown Colour ce, tana da kwarin ido sosai,Ga ziraran Eyelashes, Jagirarta tamkar anzanata saboda tsaruwarta, Ga wani dogon hanci da Allah yayi mata, siraran la66anta jawur dasu, Akwai kwalliyar ɗige ɗige asaman fuskarta har goshinta, Wuyanta na sanye da sarkoki, Haka hannunta ma akwai awarwaro,Tana da hujen hanci mai shegen kyau, idan tayi dariya kuwa wayyo Allah madarar kyau, Kai kace gonar audugace, Saboda kyan fararen hakoranta masu tsari, wani ƙarin kyan dimple biyu gareta wanda ko magana take yi, sai sun lotsa,A ƙalla Bazata Wuce shekara Goma sha Shida ba,
Tafiya take Yi a bayan shanayen tana Korasu da sandar hannunta, Wani Lokacin Har rawa take Yi tana jujjuya Jikinta, Da alama ba ƙaramin daɗin yanayin garin take ji ba, ko kusa bata jin Sanyi, Burinta A ruwan sama ya sauka sosai don tayi rawa acikinsa, kamar yadda ta saba,
Fararen kafafuwanta na sanye Cikin takalma, Cikin harshen fulatanci ta soma raira waƙa,
Tana cikin yin waƙar ruwan sama ya soma sauka tamkar da bakin kwarya, Wani irin farin Cikine Ya lullu6eta, Cikin harshen fulatanci tace”Ni ɗin Jinin nasara ce, Mai nema mai samu,Mai nasara mai sa’a, Daga Yin magana Gashi ruwa ya sauka wuhuhu Sai ni DANEJO”
Rawa Tashiga Yi acikin ruwan Yayin da shayenta suka duƙufa Cikin dajin suna kiwo,
Juyi ta dinga yi tana karkaɗa qugu, ruwan saman duk ya jiƙe kayan jikinta sharkaf, sun manne mata,Ƴar rigar jikinta bata rufe Cibinta ba, Sai ɗan zanin data ɗaura, kallabin kuma taci ɗamara dashi,
Tana Cikin Yin rawar nan Cikin rashin sa’a ta ɗaura ƙafarta saman wani dutse dake a bakin Ramin da wannan tafkeken ruwan yake, Gaba ɗaya Dutse ya jirkice, A gigice Ta fasa Uwar ƙara, duk yadda taso Ta hana kanta faɗawa Cikin ramin amma hakan ya faskara, Domin kuwa gaba ɗaya Ta rufza Cikin Ramin, Tsulum Ta nutse Cikin ruwan,
Within Seconds Ta fiddo da kanta daga Cikin ruwan Tana faman haki kamar wadda tasha gudu, Gaba ɗaya gangar jikinta tana acikin ruwan, Iya kafaɗarta Ya tsaya, Idanuwanta sunyi luhu luhu dasu, Ƴan hanjin cikinta sun kaɗa, Hankalinta ya ɗunguzuma, Ba ruwan bane damuwarta, don tun tana ƴar ƙarama Baffanta Ya koya mata Ruwa, Babbar damuwarta shine taya za’ae Ta fito daga Cikin Ramin?
Rushewa tayi da kuka cikin harshen fulatanci ta soma Kiraye Kirayen Sunayen Ƴan uwanta donsu kawo mata ɗauki,
“Inna wuro,Adda!Nanne!bawuro!Wayyo Allah Na babu wani akusa da zai kawo mun ɗauki”? tana Cikin wannan yanayin Shanayen ta Suka Leƙo Cikin Ramin Kamar sunji abunda take cewa, sun kewaye ramin suna ta kuka Emmoh !emmoh!
Nuna su Tayi da yatsan hannunta”Banga amfaninku ba, Ciyawa kaɗai kuka Iyaci,”cike da takaici tayi maganar,Tana Cikin sambatun nan, Aka kwatsa Tsawa mai sautin gaske a gigice Ta nutsar da kanta Cikin ruwan don ba ƙaramin tsorata tayi ba
sosai ruwan saman Ke safka da ƙarfinshi,
Lokacin da danejo ta nutsa kanta Cikin ruwan a tsorace sakamakon Tsawar da aka kwatsa, Ba zato Ba tsammani idanuwanta suka sauka akan Kyakkyawar Yarinyar dake kwance saman dutsen dake a ƙasan ruwan mai girma da faɗi, sumar kanta duk ta rufe fuskarta, rigar Jikinta duk ta nannaɗe ta manne mata, biji biji take iya hangenta saboda ƙasan Ruwane
Waro ido waje daneju tayi a matuƙar tsorace take kallon Yarinyar, Shin mutunce ko aljan, Abunda ta fara sakawa aranta kenan, tunawa da wata tatsuniya da Nannensu ke basu, Akan macen kifi, nan da nan tsoro ya ɗarsu acikin zuciyarta, A gaggauce ta fiddo da kanta daga Cikin ruwan Tana faman Mayar da numfashi,
Waswasi ta shiga yi acikin zuciyarta,Anya Yarinyar data gani Acikin Ruwan Mutunce? kodai ta macen kifi ce ko ɗan ruwa? ta jima tana wannan zancen Zucin Kafin Ta kuma nutsa kanta Cikin ruwan, Cike da fargaba ta nufi inda Yarinyar take saman dutse har Allah ya kawota Saitin Inda yarinyar take, Hannu biyu tasa Ta ɗaukota, Sama tadinga yi Har ta fiddo da kanta daga Cikin ruwan, Natsuwa tayi tana kallon kyakkyawar yarinyar, Daga gani ba ƙaramin Jiki taji ba, Allah kaɗai yasan Tun wani lokaci take kwance a ƙasan ruwan, Cikinta yayi 6ul6ul dashi,Da alama Ta shaƙi ruwa sosai,
Mu haɗu a next Page don jin yadda zata kaya, Jama’a an rasa shaidar da zata bayyana abunda ya faru? taya kenan za’a san meya faru dasu Taj?Su wanene waɗannan Mutanan masu haɗarin gaske? shin danejo zata taimaki angel? Idan ta taimake ta kuna tunanin angel yarinya mai ƙiriniya zata juri zama a hannun fulanin daji? ya zata rayu batare da mahaifinta ba? Duk dai acikin littafin kurkukun ƙaddara zaku samu amsoshin tambayoyinku, Tafiyar ta dabance salon ma na daban ne, a kullun burina in kawo sabon salo wanda ba’a ta6a ganin irin shi ba, Allah dai ya taimaka, Waɗanda suka shirya yin payment na kurkukun ƙaddara 500 ne, Suyi mun magana ta layi na 08103884440.*💋KURKUKUN ƘADDARA💋*
*dedicated to Aunty kubra❤*
_Daga alƙalamin Boss Bature✍️_
*E9*
At first sight da Danejo ta kalli fuskar yarinyar, sai taji tsananin tausayinta, Kuma nan take taji tana son ta taimaki rayuwarta.
Tunda ta ayyana hakan azuciyarta sai taji ta daina Jin tsoron tafkeken ramin Ramin, kodan saboda Yarinyar zata yi iyakar bakin ƙoƙarinta wurin ganin ta ceci rayuwarta.
Dabarace ta fado mata aranta, Da sauri ta sanya hannu ɗaya, ta Kwance kallabinta data ɗaura ɗamara dashi, Ɗayan hannun kuma na dafe da yarinyar,
a saman bayanta ta goyata, kafin a hankali ta cigaba da matsawa cikin ruwan harta ƙaraso jikin gwamagwaman duwatsunan dake kewaye da wurin, jikinsu akwai hudoji, tsaf mutun zai iya daddafawa ya haura sama, Sai dai yana da matuƙar hatsari idan Duwatsunan Jiki suka 6allo, mutun zai iya jin mummunan rauni ga shi ita harda goyo.
Cike da fargaba danejo ta sanya hannayenta, ta dafa jikin dutsen A haka tadin ta tafiya tana bin jikinsu, Har Allah ya taimaketa ta hauro sama, tana faman Mayar da numfashi, da sauri ta sanya hannayen ta tare da warware goyon da tayi mata, ta sauko da ita a hankali ta kwantar da ita saman ciyayin, ɗagowa tayi tare da kallon shanayenta dake ta kuka, Ta wurga masu harara don ba ƙaramin haushin su take ji, daga gani dai akwai ƙuruciya atattare da ita.
Mayar da idanuwanta ta yi akan fuskar yarinyar, ta sanya hannu tana yaye sumar kanta data rufe fuskarta.
Tayi wani irin haske, ƙananun la66anta sunyi pink sosai suka ciza, duk irin kyan danejo saida tayi mamakin Tsantsar kyawun yarinyar data tsinto acikin ruwa.
Hannayenta ta ɗaura Asaman ƙirjinta tashiga dannashi, Nan take ruwa ya sona fesowa Ta bakinta da hancinta, cigaba da dannawa tayi har saida ruwa Ya daina zubowa, natsuwa Tayi tana kallonta, ta yi tunanin zata farka amma sai taga ko motsi ba ta yi ba, Da sauri ta jogana kunnanta saitin Zuciyarta don taji, idan tana harbawa a razane ta ɗago, ranta duk ajagule fargabarta kada ace yarinyar tarasa ranta.
Tunawa tayi da saman dutsen da ta ganta akwance, hannu tasa ta juyo da bayanta, ta cusa yatsun hannunta acikin sumar kanta data cukurkuɗe, har saida ta taddo fatar kanta fara sol, Anan taga Raunin data ji, ashe kantane ya ɗan fashe daga baya, sakamakon buguwa da kanta yayi jikin dutsen, A ruɗe danejo ta miƙe tare da daukarta, ta sa6eta saman kafadarta, Sam ta manta da shanayensu, hankalinta na akan Yarinyar dake Cikin mawuyacin Hali, Watsawa Tayi da gudun gaske tamkar zata tashi sama,
Tana Cikin gudun nan, wani bafullatanin Sanye cikin kayan fulani, da ƴar hularshi, Hannunshi ruƙe da sanda zai gifta, Karaf idanuwan shi sauka sauka a kan danejo dake ta tsala gudu,
Mamaki ne ya kama shi, ɗaga murya ya yi tare da kwala mata kira, har cikin kanta tajiyo kiran da ya yi mata, Batare da ta juyo ta kalleshi ba ta amsa mashi da na’am,
Cikin harshen fulatanci Yace inata baro masu shanayen su kuma menene ta dauko a hannunta, tace ma shi suna can suna kiwo, Yaje ya cigaba da kula dasu,”daga haka bata ƙara cewa uffan ba,
Girgiza kai Bawuro yayi a ranshi yace bazata ta6a canzawa ba, daga haka ya nufi Cikin dajin inda shanayen su suke,
Danejo kuwa bata nufi ko’ina ba, Sai wuraren wasu Bukkoki rukuni rukuni a ƙalla sunyi Shida, A gefen ɗaya daga Cikin bukkokin wani tsohone tukuf zaune cikin kayan fulani, daga gefe kuma Wasu Manyan matane, Sun kwan biyu aduniya, Sai sussukar gero sukeyi, ga wasu kuma Ƴan mata su biyu matasa Suna 6arar masara,
Tundaga nesa Tsohon Ya hangota, da ƙarfi ya ambaci sunanta DANEJO, lokaci ɗaya sauran Mutanan suka ɗago suna kallonta, Ganin yadda take ta gudu yasa duk sukayi tunanin ko wani mugun abunne yabiyo ta, aikuwa aguje Suka nufi Cikin bukkokinsu kowa ya ɗauko makaminshi, Shima tsohon ya miƙe yana ɗangyale ƙafa ya shige cikin bukkar gefen shi, Sai ga shi ya fito hannun shi ruƙe da Ma shi, (to fa yaƙi ya ta shi)
Ƙarasowa tayi tana ta faman haki, lokacin da suka lura da abinda ke ruke a hannunta sai kowa ya ajiye makaman yaƙinsa, suka tattara hankulansu akan yarinyar data ɗauko, A saman Shimfiɗar kakansu ta sauke yarinyar, tare da ɗagowa ta kalli kakansu cikin harshen fulatanci tayi mashi bayanin inda ta tsinceta, koda jin hakan Jiki Na rawa Ya koma Cikin bukkarshi, Sai ga shi ya fito hannun shi ruƙe da ƴar jakkar fata, a gefen shimfiɗar ya sauke jakkar, Yace ma danejo ta nuna mashi inda taji ciwon, rubda ciki ta kwantar da ita, tasa hannu ta yaye sumar kanta, nan suka ga raunin da taji, Bude jakar yayi ya curo wasu magunguna nasu na gargajiya, wanda suke Yi ma mutun treatment dasu idan yaji ciwo,
Matsowa sauran Fulanin sukayi Gaba daya sukayi masu Danejo ƙawanya, Duk sun baza idanuwansu akan yarinyar, Cikin ƙanƙanin Lokaci ya kammala Yi mata treatment ɗin Raunin nata, Sannan Ya kalli Danejo yace ta dauketa takaita Cikin bukkarsu, ta kar6o bargunan da suke lullu6a dasu, A rufa mata ajikinta, sannan a hado garwashin wuta, A sanya mata a cikin ɗakin don ya ɗumama.
Bayan danejo ta dauketa, takaita Cikin bukkar su Saman shimfidar da suke kwana ta kwantar da ita, ta fita zuwa sauran bukkokin ta kar6o bargunansu, da zannuwa duka Ta haɗosu a hannunta, ta shigo cikin bukkar ta lullu6a mata su, kamar yadda kakansu yace ta yi mata, tana Cikin nannaɗeta cikin bargunan, Adda ta shigo hannunta ruƙe da murfi na karfe, Garwashin wutane jawur a saman shi, A gefe ɗaya ta ajiye garwashin wutar,
Kafin ta samu wuri ta zauna gefen danejo, magana suka soma Yi cikin fulatancinsu,
“Tausayinta nake ji, ƙaramar yarinya da ita, ko ya akai ta faɗa Cikin ruwa? Shin ina iyayenta suke ne? taya akai ta shigo Cikin kurmin dajin nan”? danejo ce ta yi maganar fuskarta da alamun tausayinta,
Adda tace”Nikaina nakamu da tausayinta, Allah kaɗai yasan daga wata uwa duniyar take, har na ƙosa tafarka, duk da nasan zaiyi wuya ace tana jin yarenmu, baiwar Allah gata kyakkyawa da ita kamar ta macen aljanna da kaka yake bamu labarinta”
Murmushi danejo ta ɗanyi kafin tace”Tunkafin ma tafarka Na ji nakamu da sonta sosai, kamar ni na haifeta” wani irin kallo Adda tayi mata”Ke da ko aure baki da shi,” danejo tace”Ae ba laifi bane don na kirata da ƴata, balle kuma ni dana Tsinceta cikin ruwa kinga kuwa, a yanzu bata da wani makusanci daya wuce ni jinjina kai adda tayi “bazan biye maki ba, sarkin surutu” ta miƙe tare da fucewa daga Cikin bukkar.
_Taƙaitaccen tarihin danejo, Fulanin dajine, Masu yaɗa zango acikin daji wurin da ke da yalwataccen Abincin da dabbobin su zasu ci, kuma Su yi kiwo su yi noma, fulanine dake rayuwa acikin daji, babu wayewa attare dasu, kuma suna da ƙarancin ilmin addini, a wannan Lokacin saboda su kadai suke rayuwar su a daji,_
Family din danejo basu dayawa, Saboda yawancinsu ba’a wuri ɗaya suke ba, Kowa Ya kama gabansa, Kaɗan ne suka rage, Ita dai takasance marainiyace, Iyayenta sun rasu tun kafin ta mallaki hankalinta, kuma ita kaɗai suka haifa, ta taso A hannun ƙanwar mahaifiyarta wadda suke kira da inna wuro, ƴa’ƴanta huɗu bawuro shine babban ɗanta,Yana da mata Ɗaya Haulatu, ɗansu ɗaya wanda suke kira da cubaɗo, bayan shi sai Adda itace ta biyu, sai gidaɗo sai kuma ƙanwarsu hasiya, Kakanninsu duk sun rasu, Ɗaya kaɗai ya rage masu na 6angaren Mahaifiyarsu, sukaɗai suke rayuwarsu a wuri ɗaya.
Yinin ranar Danejo bata motsa ba, ta kasa ta tsare sai Yarinyar ta farka, saboda ta ƙwallafa rai akanta sosai, tunkafin ma tafarka tasan wacece ita, Allah ya jarabceta da son yarinyar,
Tun tana sa ran zata farka, har dare ya yi bata farka ba, har sun fara fidda rai, Su uku ne acikin bukkar, Danejo da kuma Hasiya, suna ta zaman jiran tafarka har bacci ya yi awon gaba da su.
Tsakar dare lokacin kowa Yayi bacci Cikin ƴar bukkarsa, ta soma mutsu mutsun buɗe idanuwanta, ƙoƙarin motsa Jikinta tayi sai dai ina sam takasa,tamkar an ɗaureta da igiyoyi haka take ji, ga wani irin zafi da take ji ajikinta, sautin muryarta sam baya fita, Can ƙasan maƙo shi take sambatu,
“Daddy mu koma gida, tsoro nake ji,”tun sautin baya fita harya fara fita da ƙarfi, da iya ƙarfinta na ƙarshe Ta yaye bargunan da suka lullu6a mata, buɗe idanuwanta tayi sosai tana kallon Bukkar, Wasu jerin kwaryoyi tagani a jere, da wani akwatin karfe da sauran tarkacensu na fulanin daji, Wurga eyes dinta tayi akan Fitilar kwan dake Ajiye a ƙasa wadda ta haskaka Cikin bukkar, kafin takai idanuwanta kansu Danejo dake ta bacci daga zauna suna gadinta,
Wani irin tsorone Ya ziyarci zuciyarta, hankalinta ya tashi matuƙa, ganin baƙin fuskoki, Ga kuma wani wuri mai kama da A kurkukin kaji, rushewa tayi da matsanacin kuka, a firgice Danejo da hasiya suka farka jin sautin kukan Mutun, Tsareta da ido su ka yi suna kallonta kamar yadda take kallon su, Cikin harshen fulatanci suka soma ƙoƙarin rarrashinta, Ta wawware masu gray eyes ɗinta, jin suna yi mata gwaranci,
Cigaba da kuka tayi tana faɗi”Daddy! wayyo Allah na!! Ina daddyna ya ke!! Su wanene ku! A ina nake ne!!” miƙewa Ta yi da ƙyar saboda ba isasshiyar lafiya gare ta ba, Jikinta sai kerma yake yi, Ga uwar zufa data wanke mata jikin nata, ganin tana ƙokarin neman hanyar fita daga Cikin bukkar yasa suka miƙe da sauri Suka nufe ta zasu ruƙeta, watsawa ta yi da gudu tana bin jikin bukkar a ƙokarinta nata gano hanyar da zata fuce, su kuwa sun dage sai haƙuri suke bata”kiyi hakuri ki zauna baki da lafiya, muma mutane ne kamar ke kada kiji tsoron mu baza mu cutar dake ba” tunda suka soma magana take ta faman zazzare masu idanuwanta, saboda bata fahimtar yaren da su ke yi mata magana da shi, ballantana kuma harta fahimci cewa lallashin da suke Yi mata,
“Wayyo Allah daddyna, Ni ku maida ni wurin daddyna, Inaso nagan shi,” sosai take Yi masu kuka, mai tsiwar gaske, gaba daya sautin kukan nata ya karaɗe kunnuwan duk wani mai yin Bacci acikin bukkokin,
Kukanta Ya ishesu, ɗaya bayan ɗaya suka soma fitowa daga cikin bukkokinsu, kowa yana ta faman Yin hamma, A haka suka nufi bukkarsu danejo, inda suke Ji yo sautin kukan nata.
Inna wuro ce ta shigo ciki, tare da su haulatu, gaba daya suka ɗaura idanuwansu Kan ANGEL, dake ta kuka, tambayar su Danejo su ka yi meke faruwa?Suma su ka ce basu sani ba, ta tashi tana ta kuka, kuma su basu san harshen da take yi masu magana da shi ba” adaren ranar babu wanda ya runtsa Cikinsu, taruwa sukayi akanta sunata aikin lallashi, ta burkuce masu sam bata fahimtarsu, kamar yadda suma basu fahimtarta, sunan Daddynta kawai take kira,
Koya rayuwar Angel zata kasance acikin fulanin daji? Yarinyar da ta taso Cikin kulawa da soyayyar mahaifinta, batasan rashi ba, batasan maraici ba, Ta saba da rayuwar gatanci sai abunda takeso daddynta yake yi mata, Yau gata a ƙurmin daji, Cikin fulanin daji mutanan da basu Jin harshen hausa Sai fulatanci, ita kuma bata Jin fulatanci daga hausa sai turanci, Sai kuma larabcin data koya a makarantar islamiyar da take zuwa, Taya zata Iya jure zama dasu? Abincinsu yanayin rayuwarsu sam ta banbanta da ta mutanan dake rayuwa Cikin gari,
Kafin safiya tayi Angel ta galabaita sosai, Idanuwanta sun kunbura saboda rashin bacci da kuma kukan data sha, sun ƙanƙance, jijiyoyin wuyanta duk sun firfito rudu ruɗu jikin fatarta, le6enta ya faffashe hada busasshen jini, ga wani irin zazza6i na tashin hankali daya rufarmata, a ƙarshe yanke jiki tayi ta faɗi asume, Jinya ta koma sabuwa, magunguna suka shiga haɗa mata nagargajiya ƴan dabarunsu da ba’a rasa ba, Hada wasu ganyayyaki suka jiƙa mata acikin gora, suna bata tasha, Allah ya haɗa jininsu da ita, musamman Danejo kullum A tare da ita take kwana, Ba ƙaramin tausayinta suke Ji ba, Saboda ko magana bata Iya furtawa, Jikinta yayi tsauri sosai, Babu sauƙi tamkar zata rasa ranta, ga shi ko a bincinsu bata Iya ci, Furace kaɗai itama ɗin sai sun ɗura mata abaki tukunna take wucewa ta makoshinta daƙyar, angel ta wahala sosai, ta rame ta bushe ta ƙanjame tayi duhu tamkar ba yarinyar nan mai ƙiriniya ba,
Kusan Wata Uku ta yi Acikin wannan mawuyacin halin, kafin Allah ya kawo mata sauƙi, tafara buɗe baki tayi magana, Sai dai subi ta da ido don basu fahimtar me take cewa, kullum saita yi masu sambatu akan su nemo mata daddynta, daga baya da ta fahimci basu gane yaren da take yi masu, Saita Zuƙunna ta sanya yatsanta a kasar wurin da ruwa ya jiƙa,ta soma Zana fuskar mutun Asaman ƙasar, data kammala zanen ta kirasu tana nuna masu zanen, Suka zuba ido suna kallon jagwalgwalon zanan fuskar da ta zana, Kallon juna su ka yi Alamar basu fahimta ba, fashewa tayi da matsanancin ku ka, Ta watsa da gudu Tabar wurin bukkokinsu, Suma suka bi bayanta a guje, suna ƙokarin kamota gudun kada wata muguwar dabbar daji ta halakar da ita,
Cikin ƙurmin dajin ta nutsa, har tazo inda wannan ruwan Yake inda Taj ya jefa ta ciki, Juyo wa Tayi tare da kallonsu, sai faman haki suke yi sun sha uban gudu, da hannu ta dinga nuna masu cikin ruwan Saboda ta gane cewa a nan ne inda daddyn ta Yazo da ita Ya wurgata ciki,
Duk yadda taso ta fahimtar dasu, Sam sun gaza fahimta, dunƙule hannayenta tayi tare da murzasu, tana kwatanta masu a cikin mota suka zo dajin, Nan ma still basu gane me take nufi ba, Zuƙunnawa tayi agaban ruwan, ta rushe da matsanancin kuka, duk jikinsu yayi sanyi,
Babu yadda angel ta iya adole ta haƙura taci gaba da rayuwa acikin fulanin daji, tun bata saba ba da su ba, har ta fara sakin jiki da su, Bata da abincin daya wuce fura da nono, da kuma Gasassar masara, Sai kuma nama idan sunyi farauta, shigarta ta koma ta fulanin daji, Danejo ce tayi mata kyautar kayanta, Wanda tun tana yarinya kayan suke ajiye cikin akwatin ƙarfenta, Zuwan Angel Cikin rayuwarsu Ta fiddo da kayan, Ta bata su ta sanya,
Duk rana ta Allah sai angel da danejo sunje Bakin ruwan nan, Kullum ne wani lokacin har dare suke kaiwa abakin ruwan, atare suke fita kiwon shanu, hatta tatsar nono sai da danejo ta koya mata, da wasu abubuwan nasu na fulanin dajin, baiwar Allah ba yadda za ta yi don dole take rayuwa a cikinsu, Allah ne kaɗai yasan halin da Zuciyarta take aciki, a kullum idan suka kwanta suna Bacci, tare da su danejo da hasiya, bata iya runtsawa, Zama take yi tsakar dare, tadinga kukan zuci tana roƙon Allah yasa daddynta yana A raye, ta karaya sosai, wani sashe na zuciyarta yana raya mata cewar Waɗannan mutanan da suka Biyo su suna harbin motarsu sun kashe mata daddynta, amma kuma har cikin ranta tana jin cewa Yana A raye, taya zata tabbar da hakan? Ita dai bata ga gawar mahaifinta ba, balle tashai da yabar duniya, A ƙalla Angel tayi shekara Biyu A hannun fulanin dajin nan, A lokacin Tafara Jin fulatanci sama sama saboda xama da tayi da su,
duk da sabon da tayi da su hakan bai sa ta fasa ƙudirinta na guduwa daga Cikin dajin ba, duk don saboda taje neman Mahaifinta, abunka ga Yaro ga kuruciya, zuciyarta saita dinga raya mata cewa ta gudu taje gidan su, zata samu mahaifinta agida.
A ranar data shirya guduwa daga Cikin dajin, Sai da tabari kowa Ya yi bacci, batare da jin tsoro ba ta fito daga Cikin bukkar, Ko’ina duhu kasancewar darene sosai, Cikin sanɗa take tafiya Tana nufar cikin dajin, duk in taji kukan shanayensu saita firgita, gani take kamar zasu farka daga bacci ne su hana ta guduwa
Ganin tayi nisa daga inda bukkokinsu suke, ta soma tunanin wace hanya zata bi don ta fita daga cikin dajin, ga duhu ko’ina, sai ɗan hasken farin watan da ba’a rasa ba, tana cikin wannan tunanin ta jiyo muryar mutun a bayanta, A firgice ta juya don taga wanene, Hasken fitila tagani amma ba ta iya tantance wanda ya biyota ba, duk da taso ta ɗauki murya,
Tattare zanin jikinta tayi na kayan fulanin da suka bata sune sanye ajikinta, ta watsa aguje cikin dajin tamkar zata tashi sama, tana gudu tana tuntu6e wani lokacin har faɗuwa kasa take yi a haka za ta daure ta miƙe taciga ba da gudu tana waiwayan mutumin daya biyo ta, ganin shi ma yana gudu, nan fa ta ƙara gudun nata, tsawon lokaci suna wannan ƴar guje-gujen cikin dajin ita da mutumin daya biyo ta har Allah Ya kawo ta bakin titi a galabaice ta haye saman titin, wani irin jirine ya soma ɗibar ta. Ta fara tangal tangal za ta faɗi ƙasa, a haka ta jure taciga ba da gudu, ba zato ba tsammani sai ga wata zungureriyar mota baka ta yi parking a inda take a tsaye, A slow murfin motar ya zuge,
Zuro Hannu aka yi daga cikin motar aka ɗauke ta, murfin motar ya koma ya zuge da kanshi, da gudu motar ta miƙi titin.
A daidai wannan lokacin Danejo ta faɗo saman titin a galabaice hannunta riƙe da ƴar filita. Ashe ita ce ta biyo Angel, don ta ga lokacin da za ta gudu daga Cikin bukkarsu.
Waro ido waje ta yi ganin dankareriyar motar da ta ɗauki Angel, tunda take a rayuwarta wannan ne karo na farko da ta fara yin tozali Mota, Tsoro duk ya cika ta, hankalinta ya yi matuƙar tashi, ganin an raba ta da Angel. A gefen titin ta tsugunna tana kuka tamkar ranta zai fita. Wannan shi ne silar rabuwar Angel da Fulanin Daji.
A nan gefen titin Danejo ta yanke jiki ta faɗi a sume, a washe garin ranar ƴan uwanta suka farka daga barci, ba su ga Angel da Danejo ba, hankalinsu ya tashi gabaɗaya suka bazama cikin dajin neman su. Har Allah Ya sa Su Bawuro suka tarar da ita a gefen titi ita kadai a kwance ba numfashi, lamarin ya yi matuƙar girgiza su, tunda suke da Danejo ba ta ta6a yin nisan kiwo irin na yau ba, sun yi mamakin ganin ta ita kaɗai ba tare da Angel ba.
Bayan komawarsu cikin rigarsu, Suka yayyafa ma danejo ruwa ta farfaɗo, fashewa ta yi da matsanancin kuka tana faɗa masu yadda suka rabu da Angel. Duk jikinsu ya yi mugun sanyi, kowa bai ji daɗin lamarin ba, sai dai ba su da yadda za su yi. Da ma tsintacciya ce duk da sun yi sabo da ita, zuwan Angel cikinsu ba ƙaramin farinciki ta samar masu ba. Sun ji takaici da baƙin cikin ɗauke tan da aka yi, to ya za su yi? Allah Ya riga da ya ƙaddara faruwar hakan.
Da daɗi da ba daɗi haka Danejo ta ci gaba da rayuwa cikin ƙunci da takaicin rashin Angel, ta rame ta ƙanjame tamkar ba Bafullatanar nan ba mai yawan fara’a mai son yin rawa, yanzu ta koma salihar ƙarfi da yaji. Kullum cikin yin zazza6i take, kuma kullum tana akan hanyar zuwa bakin ruwan nan inda suke yawan zuwa ita da Angel su zauna. Kafin tafiyar Angel ta ba su labarin mahaifinta daya gudo da ita cikin daji, a lokacin ta fara jin Harshensu na Fulatanci, ta kwashe duk abin da ya faru ta sanar da su.
*ANEELERH*
Kwance take saman haɗaɗɗen gadonta na gidan su, A gefenta ƙaramin yaronta ne wanda bai wuci shekara ɗaya da ƴan watanni, Jikin shi na a sanye da overall pink colour, Kyakkyawan yaro rainon madara, fari tass kamannin shi sak na mahaifiyar shi, tamkar ta yi kakin shi, kan shi a cike yake da kwantacciyar suma mai laushin gaske, mommyn ta shi dake kwance gefen shi tana ta sharar bacci Rigar bacci ce a jikinta launin sky blue,
Wata irin zufa ce ta soma wanke mata fuskarta, ta ko’ina zufar take tsastsafo mata, rurruƙe bedsheet ɗin tayi da hannayenta da ke ta kerma, sambatu ta soma yi tana ambaton sunan ANGEL, still idanuwanta suna a rufe da alama mafarki take yi, Cikin shesshekar kuka take faɗin”Angel meyasa nake ganin cikin mawuyacin hali? Waya ta6amun ke? Angel kiyi magana meyasa ki ke kuka? Dan Allah ki faɗamun angel,” Ciccije lips ɗinta take yi sosai take ƙara sautin kukan nata,
A dai dai lokacin mami ta fito daga ɗakinsu, itama kayan baccin ne a jikinta doguwar riga, sai hamma take yi da alama daga bacci ta farka, ɗakin Aneelerh ta nufa tunkafin ta shiga ta soma jiyo sautin muryarta, ta cikin ɗakin tana kuka,
Da sauri mami ta faɗa cikin ɗakin babu wadataccen haske sun kashe Kwan ɗakin kafin su kwanta, bedside lamp ce kaɗai take a kunne ta ɗan haskaka ɗakin,
Ƙarasawa tayi daga gefen gadonta, takai hannu tana ɗan bubbuga shoulder ɗinta”Aneelerh! Aneelerh! Lafiyar ki kuwa? Kike ta ku ka”? Muryar mami ce ta farkar da ita, lokaci ɗaya ta zabura zata sauko daga saman gadon, damƙo damtsen hannunta mami tayi’ke lafiya? Bakya ji ina magana”?
“Mami ki barni in tafi, tana buƙatar taimako na,” la66anta na kerma tayi maganar,
Fuskar mami da alamun ruɗi tace”wai wacece kike magana akai”? Juyowa tayi suna kallon juna, idanuwanta sunyi jawur tace”ANGEL “
Sakin hannunta mami ta yi ta dafa kafaɗunta, cikin natsuwa ta soma magana” ki kwantar da hankalin ki, ki faɗamun meya faru da angel, kinyi mafarki ne akanta”?
Jinjina kai tayi cikin shessheƙar kuka tace”Mommy, I had a really scary nightmare about angel, tana a cikin mawuyacin hali, yanayin da nake ganin angel abun ya ta6a zuciyata……” takai ƙarshen maganar hawaye na bin fuskarta
Shiru mami ta yi idonta akan fuskar aneelerh, Kafin tace”addu’a yakamata ki yi,”
Cikin disasshiyar miryarta, ta ambaci “أَعُوذُ بِاللَّهِ مِنَ الشَّيْطَانِ الرَّجِيمِ وَمِنْ شَرِّ هَذِهِ الرُّؤْيَا”
Kusa sau uku tana ambaton addu’ar,
“Aneelerh mafarki ba gaskiya bane, Shaiɗan ne kawai yake son rikitar dake” girgixa kai aneelerh tayi”mami wannan mafarkin ya wuce a ce shaiɗan ne, ba yau ne rana ta farko da nafara yin shi ba mami, kuma a duk lokacin da zanyi shi, angel nake gani ita kaɗai tana kuka jikinta sanye da yagaggun kaya kamar Almajira,”
“A kowani lokaci, ki ka yi mummunan mafarki akan angel, you should pray for her, alama ce da ke nuna cewa tana buƙatar addu’ar ki, duk da ki nayi saiki ninka akan wadda kike yi masu, muma kuma in sha Allah zamu dage” miryar abie ce, sam basu ji alamar shigowar shi ba, a tare suka Kai idanuwansu kan shi,
A tsaye yake bakin ƙopar ɗakin jallabiya ce a jikin shi, yayi shirin zuwa masallacin domin yin sallar asubahi da ake ta kira,
Tafiya yaci gaba da yi cikin ɗakin yana nufar su,
“Wipe ur tears aneelerh, bana so na sake ganin hawayen ki, ” cikin sanyin murya ta amsa mashi da “toh”
“That’s good, Jiya munyi waya da uncle abdallah” ya dakata da maganar, a ƙagare suke kallon shi, sun ƙosa su ji mai zaice,
“Yayi mun magana akan BABY JUNAID, nasan aneelerh bazata ji daɗin maganar ba, shiyasa tun jiya ban sanar maki ba,” tunkafin ma yakai ƙarshen maganar aneelerh ta ɗaure fuskarta walwalarta gaba ɗaya ta ɗauke,
Ita kanta mami yanayinta ya canza, don tunkafin ma ya ƙarasa sunsan inda zancen nashi ya dosa,
“Suna so A basu shi, ya koma hannun su da zama, da zarar kin yaye shi,…..’ girgiza kai aneelerh ta shiga yi tana faɗin”Haba abie, idan aka raba ni da shi ya ake so inyi da raina? Yaron nan fa shi nake gani inji daɗi araina, ina kallon shi amatsayin kyautar Allah, inaji araina Allah yabani shi ne saboda rashin da na…..” ƙasa ƙarasa maganar tayi saboda kukan da ya ciyota, da sauri ta kifa kanta saman pillow,
Dariya sosai abie ya yi, ganin yadda ta harzuƙa jin za’a rabata da gudan jininta,
Kallon juna su kayi shi da mami, “meyasa? Kana ganin halin da take ciki, kuma ka ke son ƙara tayar mata da hankali, dagaske ka ke ko wasa? Nasan ka da son zolaya”
Bai bata amsa ba, Ya juya ya nufi ƙopar fita yana faɗin”Idan na dawo daga masallaci zamu yi magana” daga haka ya fuce daga cikin ɗakin,
Shafa bayan aneeleeh mami tayi”ke ki kwantar da hankalin ki, ae wlh ba wanda ya isa ya raba ki da ɗanki, Sai Allah nasan aikin hajiya adama ne, ita zata tunzura shi akan su ɗauko yaro, in banda ma abunsu ae yaron bai kai shekarun da zasu ɗauke shi ba, koda kuwa an yaye shi, nifa ko ya cika shekarun da zasu ɗauke shi bazan bari su rabaki da shi ba, idan suna son ɗa su haifi wani mana, wannan dai naki ne ke kaɗai……..”
Jin kalaman mami yasa aneelerh ta tsagaita da yin kukan, ba ƙaramin daɗi taji ba, ɗagowa tayi daga kan pillow ta kwantar da kanta saman kafaɗar mami,
“Mami karki bari araba ni da baby junaid ɗina, wlh zuciyata zata iya bugawa” shafa sumar kanta mami tayi”ae me raba ki da shi sai ya shirya, Idan ma suka matsa number zanyi wa lawyer na magana,” murmushi aneelerh ta saki saboda jin daɗin maganar, tasan mami tana son farin cikin ta, bazata so a bunda zai6a ta mata ranta ba
“Kada mu makara, ta shi kije kiyi sallah, shime babyn naki ki tada shi yaje ya yi sallah,” dariya aneelerh tayi tare da saukowa daga saman gadon ta nufi toilet, mami nata kallonta har ta shige ta rufe ƙofar, ajiyar zuciya taɗan sauke dama ta faɗi hakan ne donta kwantar mata da hankalinta,
Juyawa ta yi tana kallon Junaid dake kwance sai sharar baccinsa yake yi, hannu takai ta shafa sumar kanshi” Grandson, Allah yabar mana kai,” bargo taja ta lullu6e mashi jikin shi, yaron ba ruwanshi sam baida damuwa, ga nauyin bacci da Allah ya yi mashi, shifa ba ƙaramin abu ke tada shi daga bacci ba,
Saukowa mami ta yi daga saman gadon ta fuce daga ɗakin zuwa nata ɗakin domin tayi sallah,
Fitarta keda wuya aneelerh ta fito daga toilet, shaf shaf ta canza rigar baccin jikinta zuwa Jallabiya, ta ɗauko hijabi ta zura a jikinta, ta koma saman darduma ta kabbara sallah a tsanake ta shiga yin ibadarta,
Bayan ta kammala yin sallar saman darduma ta zauna tana yin tasbihi, hannunta ɗaya ruƙe da cazbaha, bayan ta kammala tayi azkhar, kafin ta ɗaga hannayenta sama ta soma yi masu Angel addu’a, Yayin da hawaye ke bin fuskarta,
“Ya Allah kafi kowa sanin a wani hali waɗannan bayin naka suke ciki, ya Allah ka tsare su da tsarewarka, Ya Allah ka kare su daga sharrin mutun sharrin aljan da sharrin duk wani abin cutarwa, Ya Allah idan har suna araye ya Allah ka bayyanar mana da su, idan kuma……kasa ƙarasa addu’ar ta yi, sam bata so ta ambaci mutuwa, tuni idanuwanta sun cicciko tab da kwalla, lumshe idanuwa ta ɗanyi yayin da kwakwalwarta ke tariyo mata fuskokinsu, Uzair taj da kuma Angel,
Ta yi nisa acikin tunaninta, Sautin kukan Junaid ya farkar da ita, ajiye cazbahar tayi saman dardumar ta miƙe da sauri ta nufi saman gadon, yana ganinta ya dakata da yin kukan ya tsareta da manyan idanuwanshi, murmushi tasakar mashi sai gashi shima ya sakar mata murmushi,
Cire hijabin jikinta tayi tare da ninketa ta ɗaura saman mattress ɗin, hawa saman gadon tayi tare da kai hannu ta ɗauke shi jan hancin shi tayi”i know u are not hungry rigima ce kawai ko”? ta6e tausasa la66ansa yayi alamar zaiyi kuka, dariya tasaki tare da cewa”stop crying my baby boy, shagwa6a66an yaro na” a gefen gado ta zauna tana shayar da shi, bayan ta kammala ta zaunar da shi, takai hannu ta ɗauko hoton su angel dake ajiye saman drawer,
Su haɗu ne a haton ranar birthday ɗin Angel a kayi masu hoton, sunyi matuƙar yin kukan, kowannansu fuskar shi ɗauke da dariya ga cake duk ya 6ata fuskarsu, yatsun hannunta ta ɗaura saman hoton tana shafa fuskokin su, tun daga face ɗin Uzair zuwa ta taj, kafin ta tsayar da hannunta a kan hoton Angel, murmushin takaici ta ɗan saki, ta ɗago ta kalli junaid, ya tsareta da ido yana kallonta ko ƙyaftawa baiyi, gefen shi ta matsa ta zauna, ta saita hoton saitin fuskarshi, magana ta soma yi mashi saitin kunnanshi,
“Ka ga wannan shi ne daddyn ka, sunanshi Uzair, wannan kuma Taj, shi aminine kuma ɗan uwa ga mahaifinka, ita kuma wannan she’s ur elder sister Sunanta ANGEL” tana rufe baki taji ya maimaita sunan Angel, murmushi tasaki dama wani lokacin duk in tayi magana saiya maimaita,
“Da ace tana nan, da yanzu ita zata dinga goya mun kai abayanta, Allah sarki Angel tayi jiran zuwanka na tsawon lokaci kullum tana tambaya aunty aneelerh wai ke bazaki haifa mun ƙani ba, ni na ƙosa naga ɗan yaron ki, sai ga shi na same ka a lokacin da angel bata nan, tana a raye kota mutu bani da masaniya akan hakan,” duk wannan surutun da Aneelerh ke yi, Ya natsu yana sauraronta kamar yana fahimtar me take cewa”
“KANA NAKA ALLAH NA NA SHI wa ya yi tunanin ma za’a wayi gari babu su a lokaci ɗaya? Ban ta6a kawo hakan araina ba, kaima kuma ban sanya ran zan same ka ba, sai gashi Allah ya bani kai, ina matuƙar sonka my baby boy,” takai ƙarshen maganar tare da manna mashi kiss saman forehead ɗinsa, kafin ta ɗaura hoton saman side drawer,
Rungumoshi ta yi a jikinta, wani baccin ne ya kuma ɗaukarsu,
Wuraren ƙarfe tara na safe, Mami ta shigo ɗakin nata, har ta kimtsa kanta Cikin Atampa,
Ganinsu rungume da juna ita da junaid, yasa ta saki murmushi, baƙaramin ƙaunar yaron take ji ba, ita kanta mamin saboda sunan yaron yaci Sunan marigayi mahaifinta Alhaji Junaid Shuwa, tun lokacin da mami ta auri Mahaifin Aneelerh Alhaji Muhammad falgore ta ƙwallafa rai akan ta samu ɗa namiji don ta sanya ma shi sunan mahaifinta, Allah bai nufa ba, ƴa ta samu mace kuma daga ita bata ƙara haihuwa ba, Aneelerh tasan da wannan burin na mahaifiyarta, shiyasa ta sanyawa yaron Suna Junaid, kuma aka amince mata da sunan, ko lokacin da su Uncle abdallah suka zo Nigeria don su ga jikan su, basu yi gaddama ba da aka faɗa masu sunan yaron, saima farin Ciki da su kayi An haifa masu ɗan kyakkyawan Saurayi.
Ƙarasawa gaban gadon tayi ta kira sunanta”Aneelerh wake up, lokacin yin breakfast ya yi, abie na son magana dake,”
Buɗe ido aneelerh tayi akan mami, biji biji take ganinta kafin idon ya washe,
“Mami,” ta ambaci sunanta muryarta da alamun bacci,
“Muna jiran ki a dining area,” mami ce ta yi maganar, tare da juyawa ta fuce daga ɗakin,
A lalace Aneelerh ta miƙe ta sauko daga saman gadon, toilet ta nufe ta shige, bayan ta fito daga wankan, bata canza jallabiyar jikinta ba, mayafi kaɗai ta dauko cikin closet, tayi rolling ɗin shi a saman kanta,
Fitowa daga ɗakin tayi ta nufi dining area, A saman dining chairs ta iske su zaune su biyu, sai Ana mai aikin gidan Aneelerh dake tsaye tana yin serving ɗinsu,
Tana ƙarasowa Ana ta soma gaishe da ita cikin girmamawa”good morning madam, how was ur night” murmushi Aneelerh ta sakar mata”Alhamdulillah, ina fata kema haka,” jinjina mata kai ta yi alamar eh,
Mayar da idanuwanta tayi kan iyayen nata, gaba ɗaya ita suke kallo, da sauri ta gaishe da su, su ka amsa mata fuskokin su a sake,
Kujera taja ta zauna, Ana tace” me zan zuba maki”?
“Cup of tea, ki haɗa mun da noodles,” amsa mata tayi da toh, ta ɗauki serving spoon da plate ta soma zuba mata noodles ɗin, bayan ta gama haɗa mata ta tura mata gabanta, tare da kofin tea,
Har ta ɗauki fork zata fara cin abincin ta ɗago ta saci kallon iyayen nata, da yake suna fuskantar juna,
Ganin suna kallonta yasa ta sunnar dakai ƙasa, murmushi su ka sakar mata, mami tace” Ina kika baro mana baby junaid ɗin mu”?
“Bacci yake yi,”
“Ya cika bacci anya kuwa lafiya”?
Abie yace”lafiyar ce ta kawo haka ae, yaron fa ɗan hutu ne, ” da zolaya ya yi maganar, murmushin gefen fuska aneelerh tasaki”mami ae ya farka ɗazu, daga baya ne ya koma bacci” mami tace”Okey, ki ci abincin ki, yana huce wa” kallon abie ta yi tare da cewa”abie da gaske ne uncel abdallah ya kira akan zasu kar6i baby junaid”? yanayin yadda tayi maganar a ɗan tsorace take da jin amsar da zai bata,
“Dagaske na, Amma ki kwantar da
hankalin ki, bawan da zai raba ki da babynki, mutu ka raba takalmin kaza” dariyar farin ciki ta saki, hatta Ana dake a tsaye saida ta murmusa,
“Ci ki ƙoshi daughter, farin cikinki ae shi ne namu,” yakai karshen maganar tare da kallon Ana dake a tsaye”Nayi magana da drivern da zai kai ki garin ku, ki kasance a cikin shiri a kowani lokaci zai iya zuwa ku tafi” jin wannan maganar yasa yanayin fuskarta ya canza ta shiga yarfa hannu, cike da mamaki suke kallonta, tattara skirt ɗin jikinta tayi tare da zuƙunnawa saman guiwowinta, tana faɗin
“Allaji ayi haƙuri abarni anan tunda har nakai wannan lokacin, wlh kona koma ƙauyanmu wahala zanci, Noman doya za’a sanya ni, dan Allah Alaji a taimaka, ƴan uwana duk suna a cikin garin nan suna aiki, dama mu uku ne marayu iyayen mu sun rasu,” tuni hawaye sun wanke fuskarta, kallon aneelerh tayi a marairaice tace”madan ki taimaka, abarni anan wlh noman doya da wahala”, duk wannan ƙibar da nayi idan har na kuskura na koma ƙauyan mu, Cikin kwana uku zan sace,” mami dai dariya ce ke son kufce mata, amma ta gumtse ta cikin baki, shi kanshi abie taso ta ba shi dariya, musamman hausarta da bata fita sosai,
“Abie, tunda tana taimaka ma Inna hauwa wurin yin girki, da aikace aikacen gida ni ina ganin barta kawai,”
Mami ma tace”Nima na goyi bayan haka, saboda ta nuna bata son noman doya…..”takai ƙarshen maganar tana ƴar dariya,
“Yanzu ina ƴan uwan naki”? Abie ne yae mata tambatar,
Hannu tasa tana matse ƙwallar dake akan fuskarta,
“Esther tana aiki a restaurant itace take aiki gidan Iyayen Sir uzair, Tun bayan barin su ƙasar ta koma restaurant da aiki, ita kuma janet, tun lokacin da madam Benazir ta koreta, ta samu aiki a hotel,”
Ajiyar zuciya abie ya sauke, kafin yace”Shikenan zaki zauna anan, amma fa zan sa maki ido, duk ranar da kika aikata badaidai ba, zan turo ki ƙauyan ku, aje can ayi noman doya,”
Gaba ɗaya suka saki dariya, miƙewa tayi muryar na rawa ta shiga faɗin”thank u sir, thank u madam ngde ngde,” tsantsar farin ciki ne akan fuskarta,
“Ki koma wurin Inna hauwa, ku yi breakfast ɗin ku,” mami ce ta yi mata maganar, da sauri ta juya ta nufi part ɗinsu,
A tsanake suka cigaba da yin breakfast ɗinsu, sai da suka kusa kammalawa, aneelerh ta mike mami tace ina zuwa,
“Inaji araina kamar Junaid ya farka, bari naje na duba shi,” da sauri ta wuce ɗakinta,
Kallon Juna abie da mami su kayi,
“Namanta ban faɗa maki ba, Munyi waya da ɗan Iya, wai yana so Aneelerh ta koma hannun shi da zama, Zai sama mata aiki a Asibitin *CHIEF OBINNA* ” rass Mami taji gabanta ya faɗi, can kuma ta ɗan saki murmushi,
“Ka daina yarda da maganar ɗan Iya, kasan halin shi, Ya iya shirga ƙarya in banda abunka taya za’ae ya iya sama mata aiki A wannan katafaren asibitin wanda ma’aikatan cikinsa ma fa, ɗai ɗai ku ne ƴan ƙasar nan, amma fa in ta samu aiki acan zan fi kowa mafarin ciki, don naji ance ƙaramin ma’aikaci na asibitin just cleaner kawai albashin shi yakai Dubu ɗari da hamsin,
Abie yace”nima nayi mamaki da yace haka amma kuma kinsan shi, mutunne na jama’a, duk wani politician daya shahara yasan shi, to ba abun mamaki bane don yace zai iya sama mata aiki acan, Ni abunda yasa ma na yi mata sha’awarar zama can abujan, zata fi samun kwanciya hankali akan nan, yau fa tsawon shekara biyu da watanni, rabon aneelerh da taje aiki, badan Dr Aisha ta kar6i ragamar kula da asibitin ba, da yanzu komai ya durƙushe”
Shiru mami tayi na wani lokaci, aranta ta ayyana cewa in kuwa har Aneelerh ta samu aiki a asibitin *CHIEF OBINNA* tabbas cikin ƙankanin Lokaci zata zama hamshaƙiyar mai kuɗi, kuma zata ji daɗin rayuwa agidan ɗan Iya, saboda barkwancin shi dana matar shi, ƴan sharholiya ne ana shan drama a gidansu, sai dai kafin Ashawo kan Aneeelerh ta zauna acan ɗin shine abu mai wuya, kuma suma kansu baza su so tayi nesa da su ba, duk da shima abie Suna hasashen zai samu ƙarin matsayi a wurin aikin shi, nan badajimawa ba za’ayi mashi transfer zuwa Ministry of finance dake abuja,
Sun jima suna tattaunawa da abie kafin Yayi mata sallama, Ya tafi zuwa wurin aikin shi, ita kuma Mami ta koma falo, a lokacin aneelerh ta dawo falon hannunta ɗauke da juanid, fira suka zauna sunayi yayin da plasma tv ke a kunne suna kallon tashar arewa 24,
*To fa😳Su Angel An yi gudun gara An faɗo gidan zago, ko ina ne Wurin nan? Lamarin ya ɗaure mun kaina, To dai mu haɗu a next page gobe in Allah yakainu da rai da lafiya, don jin yadda zata kaya, kada ku manta friday da weekend ba posting, Amma zanyi ƙoƙari in dinga yi maku Long pages, Ga waɗan da suka shirya yin payment ƙopa a buɗe take su yi mun magana (08103884440)**💋KURKUKUN ƘADDARA💋*
*Boss Bature ✍️*
dedicated to Aunty kubra❤
*E10*
_Kamar yadda na fara littafin nan ina rokon Allah Subhanahu wata’ala da ya ba ni ikon kammala shi lafiya, alfarmar Annabi Muhammad(SAW). Allah Ya ba ni ikon faɗakarwa da kuma ilmantarwa harma da nishaɗantarwa, Ubangiji Allah ya kare ni daga rubutu abin da ba zai amfani al’ummar Annabi ba.✍️_
Gargarɗi
_Ban amince wani ko wata ya yi amfani da wani sashe na book din nan ba ta kowace siga, ko a karanta mini shi a Youtube don already na siyar da littafin, Ko a haɗa mini document, idan kunne ya ji jiki ya tsira, ko da Allah na bar mutun zai bi mini haƙƙina!👌_
*South Korea*
Seoul City-Gangnam-Gu
Hamshaƙiyar Unguwace ta Attajiran masu kuɗi dake zaune a Seoul, Babban birnin korea ta kudu, babban birni ne mai manyan-manyan gine-ginen gargajiya dana zama ni masu matuƙar ƙayatarwa, ga manyan hanyoyin jiragen karkashin kasa da kuma Wuraren shaƙatawa, masu matuƙar jan hankali, A ɗaya daga Cikin jerin Modern apartments din dake a Gangnam-Gu Haɗaɗɗen masaukin Uncle abdallah ya ke, inda suke sauka duk in suka zo ƙasar.
tafi ƙarfin awa ɗaya a tsaye Tana Kallon hotonsu dake a manne Jikin bangon bedroom ɗinsu, Idanuwanta Sun Cicciko tab da ƙwalla, Har yau she ne wannan baƙin Cikin zai gushe acikin zuciyarta? taya zata Iya sakin jiki tayi rayuwa acikin duniyar nan batare da Ya’yanta ba? tabbas ta yi babban rashin, A kullum ta kali hoton su, sai ta zubar masu da hawaye, Almost 2 years kenan babu su babu labarin su, itace kullum Cikin zullumi da zarar wayarta tayi ringing, jikinta har 6ari ya ke yi don ta ɗauka taga ko Jami’an dake bincike kan case ɗin su tajuddeen ne suka kirata don su sanar da ita ko an gano inda suke,
Tun lokacin da suka dawo Seoul hajiya adama Bata ƙara samun kwanciyar hankali ba, Gangar jikinta gaba ɗaya tana a nigeria, Sunan tana zaune a korea ne, duk irin Sabon da tayi da ƙasar hakan baisa ta gundure ta ba, duk don saboda Abunda ya faru na 6acewarsu tajudden, Ita fa a ayanzu Tafi sha’awar su koma nigeria, Hankalinta sai yafi kwanciya koba komai Zata dinga ganin ƴan uwanta,
Tsadadden leshi ne a jikinta, launin silver yabi shape ɗin jikinta, Ta kashe ɗaurin ɗan kwali, Yayin da ta goya hannayenta a saman ƙirjinta,
Sam ta kasa janye idanuwanta daga Kallon hoton nasu da take yi, bakowa tafi ji ba, face Angle ƙaramar yarinyar da bata mallaki hankalinta ba, taso ace tuntuni rainon yarinyar ya dawo hanninta da yanzu suna atare, Sai dai kash Ƙaddara ta riga fata,
Ziraran hawaye ne suka soma saukowa kan kuncinta,
Muryar me aikinta ce Ajumma ta katse mata Tunanin nata
Cikin harshen su na korea take sanar da ita cewa Saƙon ta ya iso, Share hawayen fuskarta ta yi, kafin tace”A shigo mun da su ciki,” itama da harshen nasu take magana, don tana ji ba laifi,
Turo ƙopar ɗakin ajumma tayi, Babbar macace ta kwana biyu aduniya tsufa ya fara kamata, fara ce sol gashin kanta iya kafaɗarta ya tsaya, Jikinta na sanye da ƴar riga da gajeran skirt, Faffaɗan tray ne a hannunta, Saman shi kwalaban Soju ne (Giya) sun kusa Uku, tare da glass cup guda ɗaya,
A saman Round table ɗin dake a kusa da gadon hajiya adama, ta ɗaura tray ɗin, Ta juya zata fita, har ta kusa kaiwa bakin ƙopar fita muryar hajiya adama ta katse ta”Idan mutun yana so ya bugu sosai, har ya manta wanene shi, kamar yaya ya kamata yasha” shiru ajumma tayi tana tuna gargaɗin da Abdallah ya yi mata akan karta kuskura ta ƙara ba matar shi soju tasha, idan ba haka sai ya kore ta daga aiki, Yau ɗunma don Abdalla baya a gari ne, Shiyasa ta kawo mata soju ɗin,
“Kin yi shiru baki amsa mun ba”? Muryar na kerma tace”Kwalba ɗaya, Amma ran ki shidaɗe ina jin tsoro, kada yalla6ai ya ritsa ki a lokacin da kika sha kika bugu, Zai iya korata daga aiki”
“Kada ki damu, Bazan faɗa ma shi cewa ke kika kawo mun giyar ba, Zance ni na fita na siyo ta, hakan yayi maki” jinjina kai ajumma tayi kafin ta ruƙe handle ɗin ƙopar ta fuce,
Zama Hajiya adama tayi a gefen katafaren gadonta, takai hannu ta Ɗauki kwalbar Soju Ta cire mufin, Abaki ta kwafata Cikin ƙanƙanin Lokaci ta shanye duka, wani irin biji biji tafara gani a cikin idanuwanta, Ajiye kwalbar tayi, tare da kai hannu ta ƙara ɗaukar wata kwalbar ta shanye duka, sauke kwalbar tayi saman table, Ta yunƙura zata miƙe duniyar ta soma juya mata, sha tara sha takwas ta dinga gani acikin idanuwanta, wani irin nauyi Jikinta yayi mata, Tangal tangal ta soma yi tana tafiya ta nufi hoton dake manne jikin bangon ɗakinsu, Ta curo hoton ta ƙura mashi ido tana kallon shi, har wani girgiza kai take yi,
Can dai ta rushe da wata irin mahaukaciyar dariya tamkar zararra, muryarta ashaƙe ta soma magana”Duniya juyi juyi, wohoho Kai ya ɗau zafi, In ban da ta6ara da ɗamsil basira Ta ya za’ace mutun ya 6ace tun 1960 Amma An gaza gano inda yake? Ƴan sandan nan basu san ciwon kansu ba, Gashin Hammata ma yafi su Amfani, Nayi fushi Allah Ni da kaina zan nemo abuna ahe, Ku zuba ido ku gani yanzun nan zan gano su,’ takai ƙarshen maganar tare da ajiye hoton ƙasa, tattare Zanin leshin jikinta tayi, ta zuƙunna ƙasa tana rarrafe, Saƙo da lungu na ɗakin ta shiga Bi tana sambatu Tana faɗin”Gasu Can sun 6oye, kamo su nan kamaso Sunan, Zo nan ɗan ɗana Uzairu Yaron mamansa, kaima zo Tajuddeen ɗina, Kai na manta da Angela ta Yarinyata zonan in raira maki waƙa, Wacece Kumatu Angel ce kumatu, kumatutu kumatu, kumatutun mama, kumatutun baba……” tana raira waƙar tana kuka, zama tayi tare da cewa”Yauwa, Ga abinci Nan Shekaran jiya na girka maku shi, nasan kuna jin yunwa, banda wawaso, duk wanda ka samu rabon ka ne,,” gaba ɗaya ta haukace ita kaɗai take ta sambatu, giya takai mata karo, ita fa ala dole su take gani acikin idanuwanta, tana magana tana sakin gyatsa,
Yunƙurawa tayi ta miƙe tsaye tana faɗin”Zan Binciko ku duk inda kuka 6oye ja’iran yaran, harni zan girka maku abinci ku ƙi ci? Kai tajo hada cewa ba daɗi? Ni da ku ne” hannu tasa ta zuge zip ɗin rigarta, Ta cire rigar tare da yin wurgi da ita ƙasa, Ta warware zanin shima ta jefar da shi ƙasa, ya rage daga ita sai undy, Ƴar duma duma da ita, ga uban tumbi, wurgi tayi da kallabi leshin kanta, Ta koma mahaukaciyar ƙarfi da yaji, dambe ta shiga yi ita kaɗai, sai da ta Tarwatsa komai na ɗakin, da sunan tana neman Su Uzairu, itace har cikin toilet, gaban toilet seat taje tana leƙawa, Hankali Ya gushe,
A karshe ta zube ƙasa tana birgima tana faɗin”Ya Allah kota sama ne, A jeho mini su, Nasan kasan inda su ke, tunda kai kana ganin komai, ko karkashin ƙasa mutun ya 6oye…….”
Ta jima tana sambatu, kafin Allah ya kawo bacci ya yi awon gaba da ita, Lokacin da Uncle abdallah ya shigo Cikin gidan, Jikinshi sanye Cikin Suit sun zauna ma shi,
Tun a palour suka yi kici6us da Ajumma, Sam ba ta yi tsammanin Aranar zasu dawo ba, A tsorace ta gaishe dashi muryarta na kerma, Kota kanta bai bi, kaitsaye ya nufi bedroom ɗinsu Ya tura ƙopar ya shiga, tun daga kan Kayan Hajiya adama data tube ya fara Cin karo da su yashe a ƙasan tiles, Ko’ina na ɗakin ta hargitsa shi, tsayar da idanuwan shi yayi akan hajiya adama da ke kwance ƙasa ta baje sai sharar bacci take yi hada minshari, Ga kwalaban Soju ɗin da tasha nan Ajiye saman table,
“YA SALAM” rai a6ace ya ambaci hakan, kutsa kai yae cikin ɗakin A ƙasa yayi toxali da hotonsu Uzair, wanda hajiya adama ta jefar ƙasa, zuƙunnawa yayi tare dakai hannu ya ɗauki hoton nasu yana kallo,
Nan take ya gane dalilin shan giyar nata, in har zata cigaba da kallon hotonsu uzair, to kuwa bazata ta6a daina shaye shaye ba, ba irin faɗan da baiyi mata ba akan tadaina amma taƙiya,
Takawa yayi zuwa jikin bangon ya liƙa hoton, kafin Ya nufi inda take a kwance ya zuƙunna, ya jima yana kallonta, hannu yakai saman ƙafarta yaɗan bubbuga, Shiru bata farka ba, Sai da yayi dagaske Sannan Ta buɗe idanuwanta waɗanda sukayi jawur dasu, Tana kallon shi,
“Get up, Ina son magana da ke” da alama har yanzu wine ɗin bata sake ta ba, daƙyar ta lalla6a ta miƙe zaune tana faman yin hamma,
“Waya kawo wannan abun Cikin gidan nan”? Ya yi tambayar yana nuna kwalaban Soju ɗin da ta sha, fuskar shi a murtuke,
“Ni na kawo su, don su ɗebe mini kewa,”
“Narasa gane meke damunki? Meyasa kullum burinki ki 6atamun rai? Kin manta sharuɗɗan da dr park ya gindaya maki akan lafiyarki? Kina tunanin shan wine ɗin da kike yi shi ne mafita agare ki? Yakai ƙarshen maganar yana kallonta,
Sai faman lumshe ido take yi,”magana fa nake yi maki? Harara ta wurga mashi”To Ubana Alhaji Adamu, Zaka fara faɗan naka ko? nasan bai wuci kace haramin bane shan giya, Zan illata lafiyata, bayan shi sai kuma me”? A harzuƙe tayi maganar tana kallon shi, har saida gabanshi ya faɗi ras! Saboda yadda ta rufe ido tana gaya mashi magana, lallai har yanzu bata dawo Cikin hayyacin ta ba,
Sassauta muryarshi yae, Cikin sigar lallashi yace”Allah ya huci zuciyarki, ni ba faɗa nace zanyi maki ba, Amma dan Allah kidaina shaye shayen nan baida amfani, idan damuwa ce tayi maki yawa Ki ɗauko qur’ani ki karanta mana”
“Ka yanke shawara game da komawarmu nigeria? nifa na lura kamar baka damu da 6acewarsu ba, harkokin kasuwancinka kawai kasa agaba, Nikaɗai ce nasanya damuwa akansu, almost 2 years ban ta6a ganin ka tashi tsakar dare kayi Nafila a kansu ba,
Jinjina kanshi yae”Adama kenan, Ae duk cikakken musulmi wanda yayi imani da Allah, ya kuma yi imani da ƙaddara mai kyau ko mara kyau, Bazai ta6a zama ya ƙuntata kan shi ba don Allah ya jarabce shi, Nasan cewa aduk inda suke Allah yana atare dasu, Kuma inayi masu addu’a, wannan ma ya wadatar ba dole saina tashi tsakar dare ba, bansani ba ko so kike in ajiye harkokin kasuwancina, In sanya damuwa araina a ƙarshe Nima in koma ɗan giya,’ hannu tasa ta dafe gefen kanta, hawaye masu ɗumi suka soma shararowa mata,
Ruƙo hannayenta ya yi Cikin nashi”Ki faɗamun kome kike so zanyi maki, Amma dan Allah kidaina shaye shayen nan kodan saboda lafiyarki, bana so kema in rasa ki kamar yadda narasa iyaye na, da kuma ya’yana,” cikin shessheƙar kuka tace”Mu koma Nigeri, Nagaji da zama a ƙasar nan, ƙwara idan ina acan zanfi samun kwanciyar hankali,”
“Shikenan, Zanyi abunda kike so amma ki ɗan bani lokaci, In kammala wani aiki da nake yi, da zarar na gama zamu koma can ɗin kamar yadda kikeso,”
Gyaɗa kai tayi”wannan karan idan har baka Cika min alƙawarina ba, sai dai kawai kaji labarin Na tafi,”
“In sha Allah hakan bazata faruwa,” sosai ya kwantar mata da hankalinta, Har ya samu Ta shiga toilet tayi wanka ta canza kaya, Da kanshi ya gyara masu ɗakin, ya tattara kwalaban Soju ɗin ya fita yaje ya jefar dasu, Sannan hankalin shi ya kwanta,
*UAE*
Haɗaɗdiyar Daular Larabawa
Abu dhabi,
Alhaji Ubaid ne zaune A cikin Hamshaƙin falon gidansa, Wanda yaji Hadaddun furniture tsadaddun gaske, ga wani sanyin A.c dake ratsa sassan Jikin mutun,
Ya ɗau wankan Shadda, Ya hakimce saman 3 seater, Hannun shi na ruƙe da jarida, A gaban shi table ne mai ɗauke da mug na coffee,
Ya natsu yana Karanta Jaridar, kamar daga sama yaji An fisgeta, kafin ya ɗago ya kalli wanda ya kwaci jaridar daga hannun shi, tuni tayi tearing ɗinta into pieces,
Bakowa bace face Laila, Mahaifiyar Benazir, doguwar balarabiya tasha wankan Abaya launin royal blue, yalwataccen gashin kanta har tsakiyar bayanta, Ƙafafunta na sanye da High heels,
Zuba mata ido yayi batare daya ce mata ƙala ba,
“Idan har zaka cigaba da kallon waɗannan gantalallun Ni kuma bazan gaji da yage duk wata jarida da zaka kawo A cikin gidan nan ba, tunda na lura bakasan ciwon kanka ba, Menene alaƙarka da su? Ga ƴarka ta cikin ka da ta 6ata shekara da shekaru Baka damu da ita ba, sai wasu can rainon talauci,” rai a6ace takai ƙarshen maganar, tare da juyawa ta nufi bedroom ɗinta, Sai gata ta dawo hannunta ruƙe da newspaper me ɗauke da sunan khaleej times, ta wurga mashi saman fuskar shi”Ita ce jaridar dana amince maka ka karanta, tun da karantun jaridar ya zamar maka dole”
Hannu yasa ya janye jaridar daga saman fuskar shi, still idonshi na akan fuskarta,
“Mutanan da kika kira da gantalallu, Sunfi ki daraja da ƙima a idona, dake da ƴar taki, Saboda bakusan ciwon kanku ba, in banda rashin ɗa’a, da rashin sanin darajar miji har kin isa Ina karanta abu kinzo ki fisge ki yayyaga, Haka aka koya maki tarbiya a gidan ku,”?
Wuri ta samu saman Sofa ta zauna tare da ɗaura ƙafa ɗaya bisa ɗaya, batare da tace mashi ƙala ba,
Sai da ta mula tasha iska tukunna tace”bansan meke damunka, duk kabi ka sanya damuwa kan wasu kucakai, ga wadda take jinin ka, Amma sam Baka damu da ita ba,”
Murmushin takaici yasaki kafin yace” Benzir don son ranta ta gudu kuma tana a raye tunda har ta iya ta turo mun saƙo a duk lokacin da taga dama, Su kuwa waɗannan bayin Allahn, Rana ɗaya aka neme su aka rasa, Har yau babu labari a kansu, taya bazan damu da su ba? Jikata ɗaya da nake da ita kwallin kwal, Narasa ta, ƙaramar yarinyar da bata mallaki hankalin ta ba, Wayasan a wani hali suke ciki”?
Ta6e baki Laila tayi”Laifinsu ne ae, kasan ƴan jarida da kafiya, ga shegen naci da bin ƙwaƙƙwafi, acan wurin neman labari suka tsokano abunda yafi ƙarfinsu gayanan ae yanzu wa gari ya waya,”? Yadda tayi maganar ko ajikinta,
Girgiza kai Alhaji ubaid yayi yayin da yake kallonta”Hada jikarki fa a cikinsu,”
“Jikarka dai, Ni ban haɗa komai da su ba, Auran benzir da yaron nan ƙaddara ce, kai ka sani nesa ba kusa ba, benazir tafi ƙarfin shi, Ni nayi tunanin ma ɗan Abdallan ne shima ashe ɗan wani faƙirin mutunne dake zaune a karkara…..” rai a6ace Alhaji ubaid ya dakatar da ita”Cin mutuncin ya isa haka, Kuma ki iya bakin ki, mutumin da kike kira fakiri a yanzu haka baya a raye ya riga mu gidan gaskiya, ke wai baki tsoron Allah? Mace har mace ba kyan hali, silar ki ga shi nan duk narasa ya’yana saboda gur6ata masu tarbiyar da kike yi,”
Murmushi tasaki tana kallon shi,”Nifa komai zaka faɗi akaina bazan ta6a jin haushi ba, Ga Coffee ɗinka nan Yana huce wa yakamata ka sha” tayi maganar tana nuna mashi Mug ɗin dake ajiye saman table,
Banza yayi da ita batare daya furta mata komai ba,
Kashe murya tayi tare da cewa”Habibi fushi ka ke da Nooril ƙalbin taka”? Dariya taga ya saki kamar wani zautacce, mamaki ya kamata, ta ƙura mashi ido tana kallon shi,
Wayar shi dake ajiye saman sofa hand ta soma ringing,
Hannu ya miƙa ya ɗauki wayar tare da miƙe wa, still da dariya akan fuskarshi ya fuce daga Cikin gidan,
Girgiza kai lailah tayi”ɗan siyasa kenan, Jibi yadda ya mayar dani shashasha, Ina tunanin na harzuƙa shi ga shi nan ya fuce yana yi mun dariya wato nice mahaukaciyar, Allah ya kyauta, Ni ya dawo ma muyi magana ta fahimta, Tunda ciwon ƙafar ta shi yayi sauƙi, zan tunzura shi ya nemi takarar shugaban ƙasa, Wannan shi ne burin da nake da shi,’ takai ƙarshen maganar tare da kwalawa mai aikinta Zainab kira, da sauri ta fito daga Cikin kitchen ta nufe ta, Balarabiya ce a ƙalla takai shekara arba’en, jikinta na sanye da kayan aiki,
Cikin harshen labaraci tace”ki sanar ma Sauran maids ɗin Gobe A shirya Abinci kala kala na gargajiya dana zamani, Dr Shureim zai kawo mana ziyara daga egypt”
Jinjina kai zainab tayi cikin ladabi ta amsa mata da”Toh, in sha Allah za’a shirya komai, Allah ya kawo shi lafiya,”
Laila ta amsa mata “ameen”
Bayan fitar Alhaji Ubaid, A entry hall na gidan ya tsaya ya amsa Kiran da akayi ma shi daga gida Nigeria, Yana waya idonshi na akan Masu aikin gidanshi, dake ta aikace aikacansu,
“Ka kwantar da hankalin ka, Lokaci kawai nake jira, Ina nan ina shirye shirye dawowa Nigeria, Siyasa fa yanzu muka sanya ƙafa ba gudu baja da baya, Namiji da jarumta aka sanshi bada ragwanci ba, Wannan karan babbar kujera nake hari, Zanyi duk iyakar bakin ƙoƙarina wurin ganin Na siye zuciyar Dattijon nan, Kona samu ya sanya mun albarka Cikin lamurrana,”
On the other hand muryar Babban mutumin Da yake waya da shi ce ta soma bayyana” Da kamar wuya fa, kasan halin shi Kaifi ɗaya ne, wani irin bauɗaɗɗan mutunne abunda ya yi niya shi yake aiwatarwa, Amma zamu yi kokarin shawo kanshi, Ko dan muyi nasara akan abunda muke son Cimmawa, yanzu dai dawowarka Nigeria shiya fi komai mahimmanci,”
“zan dawo In sha Allah, Kodan saboda Yaran nan da suka 6ace, Sunan ina zaune ne a Ƙasar nan amma tunanina gaba ɗaya yana a nigeria, nadamu da su,” fuskarshi ɗauke da matsananciyar damuwa yakai ƙarshen maganar, abokin nashi da suke waya yace”Wai har yansu babu labarin su? Ae ni da naji shiru nayi tunanin an same su ne,” muryarshi da alamun mamaki
“kusan shekara biyu fa kenan babu su babu alamarsu, Ni tsorona ma kada ace abokan hamayyata ne suka Farmake su, kasan mutanan nan ba imani ne da su ba, Komai zasu iya aikatawa indai akan siyasar su ce,”
Jajanta ma shi abokin na shi ya yi, da ga haka su kayi ma Juna Sallama, Har ya juya zai koma Cikin falon, Yaji ƙarar shigowar mota, juyawa yayi yana kallon Motar da ta shigo, Danƙareriya mota mai numfashi, da alama Baki ya yi,
Bodyguard ne Ya fita daga Driver seat na motar, Ya zagaya ya buɗe mashi mota, Wata irin dariya Alhaji ubaid ya saki lokacin da yayi tozali da Alhaji badamasi, Mataimakinsa Lokacin da yana gomna a jihar jos, da sauri ya nufe shi yana faɗin”Marhaban bika Mutumina, Irin wannan zuwan bazata haka, Yaushe ka shigo ƙasar” Alhaji badamasi sai faman washe baki yake yi, yayi shigar larabawa, Ga wani ƙamshi dake fita a jikinshi,
Rungume juna su kayi kamar zasu haɗiye juna, A tsaitsaye suka fara gaisawa kafin Suka Nufi Cikin garden ɗin gidan, A waya ya kira lailah yace Ayi ma mai aiki magana ta kawo masu kayan marmari su sha, A garden a kayi masu Shimfiɗa Saman Lallausar darduma suka zauna domin tattaunawa a tsakanin su,
Shin Ya rayuwar Angel ta kasance bayan An sace ta Cikin Mota?
Sambatu take ta faman yi, Cikin fitar hayyaci, tarasa gane inda take, Ko’ina duhu, babu haske ko misƙala Zarratin, jikinta yayi mata wani irin nauyi tamkar an ɗaura mata dutse a samanta, Ko yatsan ta ta gaza ɗagawa, Wani baƙon yanayi da bata ta6a jin kanta acikin shi ba, ga zafi ta ko’ina, numfashin ta kanshi daƙyar take fitar dashi, atakure take jin kanta, tun tana kukan a bayyana har ta koma tanayin na zuci, Cikin disasshiyar muryarta ta soma ambaton duk wata addu’a da tazo bakin ta,
Tsawon mintuna talatin kenan, tana acikin wannan yanayin ta haɗa uban gumi, duk ta cicci je la66an ta sun faffashe, Saboda ƙuncin da take Ciki, takaici ya isheta, ta kuma rushewa da kuka tana faɗin”Wai ba kowa ne a kusa, Ku faɗamun ina ne nan! Wayyo Allah na! Danejo! daddy Can you hear me! its me ur angel, pls if u are hearing my voice, Answer me, Am really scared of being alone in this darkness……” cikin shessheƙar kuka takai ƙarshen maganar,
Wani irin raɗaɗi maƙoshin keyi mata hada ƙaiƙayi,Tana Cikin buƙatar ruwa, throat ɗinta ya bushe ƙamas,
Ƙoƙin motsa lips ɗinta tayi da niyar ta ƙara magana, Ba zato ba tsammani, haske ya soma bayyana Acikin wurin da take, nan take ta dakata da yin kuka biji biji ta fara gani kafin idanuwan nata su ka washe ta ƙura ido tana Kallon Ceiling ɗin da take fuskanta,
Dogon Ginin dutse ne mai matuƙar Girma da faɗi da tsayi, Ceilling ɗin Yayi uban soro daga inda take daƙyar ta ke iya hango ƙarshen shi, wasu fitilu ne jere can saman ceilling ɗin, hasken su ne ya gauraye Cikin ɗakin da ta ke, sauke idanuwanta tayi tare da yin ƙoƙarin miƙewa zaune, don ta samu damar ƙarewa baƙon wurin kallo,
tamkar hostel na kwanan ɗalibai haka wurin ya ke, daga 6angaren da take kwance 6angaren yamma ne tana fuskantar gabas akwai jerin gada je da a ka yi su da Metal(ƙarfe) A ƙalla sun kai goma sha biyar, single bed ne na mutun ɗaya kowane gado yana da lallausar mattress a saman shi, tare da matashin kai (pillow) da kuma duvet, launin farare, a ɗaya daga Cikin gadajen ANGEL take a zaune, tana bin kowace kusurwa ta ɗakin da kallo, akwai wasu kujeru da a kayi su da Katako zubin armchairs guda biyu dake ajiye, agaban kujerun there’s a table an ɗaura wasu fitilun kusan uku a saman shi, daga tsakiyar ɗakin akwai shimfiɗaɗɗen red carpet,
Saukowa Tayi daga saman gadon Cike da fargaba take kallon baƙon wurin da ta tsinci kanta a cikin shi, juyawa tayi tana kallon bayanta bene ne madaidaici, da alama akwai ƙopa a can saman stairs ɗin, Amma daga inda take tsaye bata iya hangen ƙopar ta yi lungu,
Lumshe idanuwanta ta ɗanyi tare da buɗe su akan ƙopar dake a rufe, saman ƙopar taga an rubuta “Toilet” nan take ta gane makewayi ne, ɗakin yana da tagogi both left and right na jikin bango amma an garƙame su, ginin da alama tsohon gini ne aka sabunta shi,
A ruɗe take zazzare gray eyes ɗinta da suka jiƙe sharkaf da ruwan hawaye, long eye lashes ɗinta duk sun cukurkuɗe, dogon hancinta yayi jawur da shi saboda matsar da ya sha lokacin da take ku ka, heart shaped lips ɗinta sunyi light pink sun bushe ƙamas, gaba ɗaya ta rikice musamman da ta shafa jikin ta, a hautsine ta kalli uniform ɗin da aka sanya mata, launin baƙaƙe zaro ido tayi ganin an canza mata kaya ita a iya saninta kayan fulani ne ajikin ta lokacin da ta gudo daga hannun fulanin daji, hatta kanta kitson kalaba ne da danejo ta yi mata amma yanzu an warware mata kitson an sakar mata gashin ga shi nan a haukace har kusan waist ɗinta ya yi mata tamkar hijabi, uniform ɗin jikinta riga ce me dogon hannu takai mata har guiwarta, sai dogon wando har kasa, a bayan rigar an rubuta no 1,
Juyawa ta yi da gudun gaske ta nufi benan nan, a zafafe take tattaka matattakalar har takai bakin ƙopar sai dai a garƙame take an rufe ta,
Hankali a matuƙar tashe ta dunga bubbuga ƙopar tuntana yi a hankali tana tambayar bakowa ne anan har takai ga kai ma ƙopar naushi ta ƙafa ta hannu, tamkar ƴar dambe duk ta raunata jikin ta, Saboda ƙopar ta metal ce,
Jiri ta fara gani acikin idanuwanta ba arziƙi ta dakata tana fama mayar da numfashi, zufa ta ko’ina a kan fuskarta,
Jingina bayanta ta yi a jikin hand rail ɗin benan a galabaice, ga uwar yunwa tana ji kamar tacin ye ƴan hanjin cikinta,
Tana cikin wannan yanayin ta jiyo motsin tafiyar mutane can kuma taji alamun ana buɗe ƙopar ɗakin da take ciki, a hanzarce ta wurga eye balls ɗin ta kan ƙopar tana jira taga wata ja’irar ce ko wani ja’irin ne xai shigo, domin kuwa ta ɗaura ɗamarar yin yaƙi da duk wanda ya yi silar ɗauko ta daga saman titi ya kawota wannan wurin mai kama da prison.
Cikin ƙanƙanin lokaci aka buɗe ƙopar tare da turo ta, awani slow angel ke kallon ƙafar mutanan da suke ƙoƙarin shigowa ciki, wasu gabza gabza Mutanene masu tsayi da faffaɗan ƙirji, Wata kalar ƙira gare su mai ban tsoro kowannan su na a cikin Shiga ta baƙaƙen kaya long coat har guiwa sai dogon wando, sunyi 6adda kama ta yadda ko akaifar hannunsu baka iya gani, sun sanya mask a fuskokin su, Sun 6oye ainihin halittar su, ƙafafuwansu kuwa Army boots ne suka sanya, kawunansu na sanye da cowboy hat, dai dai da ziririn gashin kansu baka iya gani ko’ina arufe ya ke, motsa lips ɗinta ta soma yi da niyar ta yi magana sai dai kafin ta yi yunƙurin furta wani a bu, idanuwanta suka sauka akan ƙafar matashin saurayin da ke ƙoƙarin shigowa, kalar uniform ɗinta ne ajikinshi baƙaƙe masu ɗauke da No 1 A halitta dogo ne fari sol da shi, kyakkyawan gaske, Droopy eyes ɗin shi farare ƙyal da su, Yana da dogon hanci, full lip ɗinsa red colour ne, yana da dimple ɗaya a gefen fuskar shi wanda ko motsa lips ɗinsa ya yi sai ya lotsa, Yana da yalwatacciyar sumar kai, ta kwanta luf har mid back ɗinsa dark brown saboda tsabar kyanshi sai ka rantse da Allah maca ce ba namiji ba,
ta yi tunanin shi kaɗai ne wuce warshi ke da wuya, sai ga wata matashiyar budurwa me sanye da black uniform no 2, itama fara ce sosai doguwa kamar angel tana da manyan idanuwa ga dogon hanci, soft lips ɗinta brownish colour ne, tana da yawan gashi ya cika kanta kamar an kifa mata kwando, tsayin shi ya haura kafadarta,
Tana ƙarasa saukowa sai ga wasu matasan ƴan mata masu sanye da red uniform kowanne da numbers a bayan rigar shi, gasu nan kala kala wasu baƙake wasu farare wasu wankan tarwaɗa, kamar yadda angel ke kallonsu haka suma suke binta dana mujiya,
A kalla mata sunkai goma acikinsu maxa kuma biyar, sai da suka kammala shigowa tukunna waɗannan GIANTS ɗin su ka fuce daga ɗakin bayan sunyi locking ƙopar,
Cikin tashin hankali angel ke bin kowannan su da kallo, can dai tace”wai uban wanene ya kawo ni wannan wurin! Menene alaƙata da ku!”nuna matasan ƴan matan ta yi da yatsan hannunta “ku faɗamun su wanene ku?kuma ina ne wurin nan? kun wani tsare ni da ido kuna kallo na” a harzuƙe ta yi maganar,
ɗaya daga cikinsu ce wannan me black uniform no 3 ta soma magana cikin harshen turanci”kamar yadda kika tsinci kanki a cikinsa batare da sanin ki ba, mu ma haka muka tsinci kan mu, abu ɗaya na sani shi ne, kurkukun ƙaddara gida ne na marayu wanda basu da gata,’
girgiza kai angel ta yi’ae ni ba marainiya ba ce, iyaye na suna araye wlh bazan zauna acikin kurkukun nan ba, i must find away to leave……..” kafin takai ƙarshen xancen nata wata matashiya me ɗauke da uniform jajaye no 4 baƙa siririya tace”ba gidan cutarwa bane, gidan taimakon marayu ne zasu tallafi rayuwarki, dayawa ma anan aka rainesu tunkafin su mallaki hankalinsu, xamu samu kulawa tunda bamu da kowa kurkukun ƙaddara shi ne gidanmu”
Uwar harara angel ta wurga mata”prison will neve be a home for me, ba zan ta6a lamunta ba, taya za’a sato mutun akawo shi wani baƙon wuri sannan ace gidan marayu ne? Ta gidan ubanwa aka gaya masu cewa ni marainiya ce, da uwata da ubana kuma da dangina, ba daga sama na faɗo ba,” yadda take magana rai a6ace har wani huci ke fita daga cikin bakinta,
Takun tafiya suka jiyo daga cikin ɗakin muryar wata tsohuwa tukuf suka jiyo tana faɗin”Ina Magana”da hanzari dukansu suka sauka daga saman benan xuwa cikin ɗakin hada angel,
Tsayawa su kayi idanuwansu akan tsohuwar, a tsaye take jikinta na sanye da doguwar riga mai gashi gashi ajikinta, launin ja hannunta na ruƙe da sanda fara ce tass ta tsufa tukuf idanuwanta duk sun zurma, fuskarta ta yi uban tamoji tamoji, kanta babu gashi ko ɗaya da yake baƙi, gaba ɗaya uwar hurhurace hatta jagirarta hurhura duk ta kamata, hada gemu gare ta fari fatt yadda kasan namiji, ga wani katon hanci dake gare ta, uban gi6in dake abakinta yadda kasan ƙogon dutse, haƙora huɗu kaɗai suka rage abakinta na sama dana ƙasa, can cikin kursurwar bakinta, dogayen haƙora ne ko ta rufe baki sai na saman sun leƙo waje, hannayenta kuwa xaƙo zaƙon akaifu ne haka ƙafafuwanta wasu tsoffin takalma ne launi rigarta jajaye, kunnuwanta falo falo an manna masu bari ma,
Mamaki ne ƙarara akan fuskan angel, ta ya akai tsohuwar ta shigo cikin ɗakin batare da ta biyo ta ainihin ƙopar shigowa cikinsa ba? To kodai ta saman rufi ta duro ne ?ko kuwa bango ta tsaga ta shigo?
Kamar daga sama angel ta ji tsohuwar tace”ko ɗaya! ta ƙopa na shigo ciki” ta yi maganar tare da juyawa tana nuna mata wata ƙopa dake a ɗaya daga cikin kusurwowin ɗakin,
“Nan ɗaki na ya ke, Ni tamkar uwa nake awurin ku, dayawa sunsan wacece ni saboda na shayar da wasun ku, wasu kuma na rainesu kamar DANISH da BATOOL!” ta kai ƙarshen maganar tana nuna wannan mai kyakkyawar matashin nan da sandar hannunta tare da wannan matashiyar mai kama da larabawan, sunayen su ne ta faɗi, masu kalar uniform ɗin angel,”
Angel dai wani irin kallo take binta da shi, mamakin ta ke taya akai tsohuwar take karantar abunda mutun ke saƙawa acikin zuciyarshi”?
“Ni duk ba wannan ba! Meyasa aka kawo ni gidan nan? Nifa ba marainiya bace, Ko da ace ni marainiya ce taya za’a sato mutun akawo shi cikin wannan munafukin ginin ace wai gidan marayu ne? Taya akai ku ka san cewa ni marainiya ce? That means ku ne ku ka kashe mun mahaifina kenan? Sannan ku ka raba ni da mahaifiyata itama ku ka kashe ta ko? Dama can kuna bibiyar rayuwata in ba haka ba ta ya akai ku ka san ina a hannun fulanin daji? Har ku ka tura aka ɗauko ni? wai menene manufar ku tayin hakan huh?
“Gidan kurkukun ƙaddara Gidan Marayu ne wanda suka rasa gatansu, duk yaron da ki ka gani acikin prison ɗin nan to ba shi da iyaye! Zai iyayiyuwa iyayenki sun mutu batare da sanin ki ba, sa’annan duk wanda ki ka gani acikin kurkun nan na jininsa ne ya sadaukar dashi zuwa gare mu don mu gatanta shi har zuwa lokacin da zai mallaki hankalin shi” tsohuwa ce ta kora mata wannan jawabin,
Still angel ta gaza fahimtar inda zancen ta ya dosa cikin ɗaga murya tace”If it’s an orphanage, then why is it called a prison? You just wanna mislead me with your lies, I won’t believe you, idan har kuna son zaman lafiya ku mayar dani inda ku ka ɗauko ni cikin salama in ba haka ba zan addabi rayuwar ku” takai ƙarshen maganar tana haki ta harzuƙa sosai,
Sauran prisoners ɗin duk suna a tsaitsaye cirko cirko suna sauraran tattaunawar baƙuwar yarinyar da su kayi tare da tsohuwa, tun da suke a gidan prison ɗin ba’a ta6a samun yarinyar me taurin kai da kafiya ba irin baƙuwar da suka tsinta yau acikin su,
“Bansan wacece ke ba, amma na lura kamar kina son wuce gona da iri, yakamata ki kiyaye harshen ki, wannan tsohuwar da ki ke gani tamkar uwa take agare mu, tun da mu ke da ita bata ta6a cutar damu ba, muna samun kyakkyawar kulawa daga gare ta, don haka bazamu bari zuwan ki ya zama silar tarwatsewar farin cikin mu ba hope u understand me!”
A wani slow angel ta juya don taga wani isasshe ne ya yi mata magana, sauke idanuwanta ta yi akan kyakkyawar fuskarshi sai ka rantse da Allah bashi bane ya yi maganar, daga ganin shi akwai izza atattare da shi,”
“Sannu isasshen me walkin sa! Kai kuma a suwa ɗan wake a hotel? am talking you are talking? duk wanda ke son zaman lafiya acikin ku, kada ya kuskura ya shiga gona ta, domin ni ba irin ku bace! Wlh uban mutun zanci kuma a zauna lafiya!”
Tana huci takai ƙarshen maganar tare da ɗauke idanuwanta daga kan shi ta mayar dasu kan tsohuwar” ke kuma tsohuwa na dawo gare ki! Ku maida ni inda ku ka ɗauko ni, Kuma a faɗa mun uban wanene ya sadaukar dani xuwa gidan nan! Saboda idan na samu damar fita daga cikin sa inje in naƙasa rayuwar shi”
Lallai angel ba sauƙi a zafafe take magana tana huci yadda kasan mayunwaciyar zakanya,
Sassauta murya ta yi”idan kun saba rainawa mutane hankali kuna ɗaukosu ku kawo su cikin gidan nan da sunan zaku gatanta su, to ni ba kalar su bace, ni ba marainiya bace kuma ni bana buƙatar gatanci daga wurin ku, Gata na shi ne Allah koda kuwa bani da kowa a duniyar nan ina da Allah,”
Murmushi tsohuwar tasa ki yayin da take kallonta tace”buri ya yi kama da mutun, da ace baki yi wannan haukan ba, da bazan tabbatar da cewa ke ɗiya ce ga Zaheer tajuddeen ba, hatsabibiyar yarinyar da ta addabi mahaifinta ina da labarin ki tunkafin zuwan ki duniya”
Ruƙe qugu angel ta yi yayin da take kallonta, jin wani soki burutsi da tsohuwar ta yi mata,
“Bazan yi jayayya dake ba, saboda nasan wacece ke! abu ɗaya nake so in tunasar maki shi ne, ke marainiya ce mahaifin ki ya rasu babu shi a doron duniyar nan mahaifiyar ki ma ta rasu babu ita, danginki kuma su ne suka damƙa mana ke don mu raine ki wannan dalilin ne yasa kika kasance acikin Gidan kurkuku saboda mu ne gatan ki, kuma muke da alhaƙin ɗaukar responsibilities na rayuwarki, kama daga cin ki shan ki da sauransu….idan ki kayi biyayya mu kuma zamu sama maki farin ciki,”
Hawaye ne suka wanke fuskar angel jin cewa mahaifinta ya rasu duk da bata gasgata maganar dattijuwar ba cikin shessheƙar kuka tace”kiji tsoron Allah ki fada mun gaskiya daddy na bai mutu ba! Kuma ƙarya ki ke yi mun na cewa dangina ne suka kawo ni cikin wannan kurkukun,”
Matsawa tsohuwar ta yi zuwa inda angel take atsaye, ta tausasa murya tare da cewa”ƴar nan ki kalle ni tsofe tsofe dani da ace na ta6a aure da yanzu nayi tatta6a kunne dake, amma har kika iya buɗe baki ki kace mun ƙarya nake yi? Lallai babu tarbiya atare dake shiyasa ƴan uwanki suka kawo ki prison don mu koya maku ladubban rayuwa, sa’annan ina mai ƙara tabbatar maki da cewa mahaifin ki ya rasu babu shi a doron duniyar nan, nasan ke bakisan da hakan ba saboda ya jefa ki acikin ruwa shiyasa baki ga lokacin da ya rasu ba, idan har kina son sanin komai game da mutuwar mahaifin ki, zan fada maki hatta wanda su kayi silar mutuwar shi, amma fa ba yanzu ba sai naga hankalin ki”
Tana kai ƙarshen maganarta, bata jira angel ta bata amsa ba, ta juya tana dogara sandarta a daddafe ta nufi ƙopar shiga ɗan ɗakinta,
Zubewa angel ta yi saman guiwowinta tare da fashewa da matsanancin kuka tamkar ranta zai fita, gaba ɗaya ta ji ta tsani kanta, komai ya sire mata zuciyarta ta karaya dama saida ranta ya bata cewar kodai daddynta ya mutu ne, dama yasan mutuwa zai yi shiyasa ya jefa ta acikin ruwa shi kuma ya tsaya waɗannan mutanan da suka biyo su da mota suna harbinsu suka kashe mata daddynta,
Ƙara sautin kukan nata ta yi tana ambaton”Innallahi wa’inna ilahirraji’un! Wayyo Allah na daddy na! Sun kashe mun daddyna shikenan sun raba ni da farin ciki na, sun raba ni da Mahaifina sun naqasa mun rayuwata, ya Allah ka ɗauki raina nima in huta………”sosai take kuka fuskarta ta yi jawur jaga jaga da hawaye hada majina,
Duk suna tsaye suna kallonta, an rasa wanda zai lallashe ta, saboda basu saba da ita ba, wasu kuma shakkar ta suke ji yayin da wasu kuma suke jin haushinta saboda ta zagi tsohuwa wadda suka ruƙa amatsayin mahaifiyarsu,
Tuntana yin kukan nata da sauti har takai ga kakarewa muryarta ta dissashe ta, anan ta yanke jiki ta faɗi a sume.
Guntun tsoki matashin saurayin nan yaja, tare da ta6e lips ɗinsa ya yi gaba abun shi ya nufi gadon shi me ɗauke da no 2 haka kowani gado yake da number,
Suma sauran matasan suka wuce zuwa saman gadajen su, mutun ɗaya ce ta kasa tafiya saboda tsananin tausayinta da take ji, kuma ita har ga Allah yarinyar ta kwanta mata aranta,
Hannayenta bibbiyu ta sanya tare da tallabo kan angel dake a ƙasa ta ɗaura shi saman cinyarta, juyawa ta ɗanyi tare da kallon kowannan su dake kishingiɗe saman gadonshi, tsayar da ƙwayar idonta ta yi akan Hannah ta ɗan ɗaga murya tare da cewa”abunda ku kayi ba ku kyauta ba, kuna ganin halin da take aciki na rashin mahaifinta amma kowa ya yi shiru ya wuce ta babu me lallashinta?
Ta6e baki hanna ta yi”rashin mahaifi akanta aka fara rashi? tafi mu gata fa dayawan mu nan tun muna jarirai aka kawo mu kurkukun nan, mun ta shi ba mu san kowa namu ba, bamu da wanda ya damu damu tsohuwace kaɗai gatan mu, kuma agaban mu ta zageta tass ba ta ga girman gemun ta ba, saboda rashin kunya irin ta ta,” Hanna na rufe baki, wani saurayi dake a cikinsu tuttu6e6e me suna haris yace”nifa bata kwanta mun araina ba, kyau kamar aljanna, kuma daga gani ma duk mun girme ta, “yana rufe baki mubeen ya kar6e da cewa”bazata wuce shekara takwas ba wannan jibi yadda take raira mana kuka kamar ba’a gama rainon ta ba,”
Gaba ɗaya suka sanya dariya, ran batool ya 6aci,
“Is enough, kunsan bana son hayani ya” wannan kyakkyawar saurayin ne da tsohuwa ta kira da sunan DANISH ya yi maganar tare da lumshe idanuwanshi ya kwantar da kanshi saman pillow,
Jinjina kai batool tayi, jiki asanyaye ta sauke kan angel a ƙasa, ta miƙe da hanzari ta nufi toilet ɗinsu, jim kadan ta fito hannunta ɗauke da ruwa sai sauri take yi saboda zubar da yake yi, adai dai saitin fuskar angel ta yarfar da ruwan, nan take taja dogon numfashi batare da ta buɗe idanuwanta ba, yatsun hannunta ne kaɗai suke kerma, miryarta adisashe take faɗin daddyna bai mutu ba, he is still alive ina ji araina sai sambatu take yi, ga wani irin matsanancin ciwon kai daya far mata ga yunwa da ƙishir ruwa duk ita kaɗai,
Cikin sanyin murya batool ta yi mata magana”SISTER” har cikin kunnanta taji sautin kiran yadda kasan wadda aka tsokano a hargitse ta buɗe idanuwanta da suka kada su kayi jawur da su, yunkurawa ta yi da hanzari ta ɗauke kanta daga kan cinyar batool, ta jefa mata uwar harara tare da cewa”bana son ganin kowa a kusa dani, bana son kowa,”
❤dedicated to Aunty kubra❤
*Daga alƙalamin Boss Bature✍️*
*E11
Tuntsirewa su hanna su kayi da dariya jin yadda ta gwasale Batool,
“Bai kamata ki yi mun haka ba, kowa yaƙi kula ki a lokacin da ki ka suma ni ce kaɗai na damu da ke amma shi ne kika watsa mun ƙasa a ido”?
Cigaba da kuka angel ta yi ba tare da tace mata uffan ba, ita kaɗai tasan raɗaɗin da take ji,
Zuba mata ido Batool ta yi batare da ƙyaftawa ba,
Adai dai wannan lokacin suka soma jiyo motsin buɗe ƙopa, gaba ɗaya suka kai idanuwansu bakin benan
Turo ƙopar a kayi waɗannan Giants ɗin ne su uku masu sanye da baƙaken kaya su ka shigo hannayen su ɗauke da Faffaɗan wooden trays masu ɗauke da kayan abincin su, kowanne na a ruƙe da faranti ɗaya,
Bayan sun ƙarasa sauko wa kai tsaye su ka nufi jan carpet din nan, a saman shi su ka sauke farantan, kafin suka ja gefe ɗaya suka goya hannayen su asaman ƙirjinsu, dama ƙa’idar aikin su ce idan suka kawo masu abinci ba su tafiya tsayawa suke yi har sai sun kammala tukunna su kwashe kayan abincin su tafi, kuma basa magana sai in ta kama dole,
one by one su ka soma saukowa daga saman gadajen su, izuwa gaban kayan abincin kowa ya samu wuri ya zauna, ruƙo hannun angel batool ta yi tare da cewa”ki taso muje mu ci abinci,” fusge hannu angel ta yi” bazan ci ba, ni kawai a mayar dani inda aka ɗauko ni,”
“This is the only chance u ave to eat, we get food once a day, if u don’t eat it now, u will lose ur food,” cikin sigar lallashi batool ke yi mata magana, ita kuwa ta kangare akan baza taje taci abincin ba.
Miƙewa batool ta yi duk bata ji daɗi ba, taso ace yarinyar ta saki jiki da ita amma ta nuna kafiya, wuri ta samu saman carpet ɗin ta zauna,
faranti na farko Grilled Chicken wraps ne guda goma sha biyar a jere, iya adadin su, faranti na biyu kayan marmari ne nunannu an yayyanka su, a faranti na uku wooden cups ne guda goma sha ɗaya, sai jugs guda biyu ɗaya na ruwa me sanye ɗaya kuma na Lemu ne da aka hada da nau’ikan kayan marmari,
A tsanake kowa yakai hannu ya ɗauki chicken wraps ɗinsa, suna Ci suna satar kallon angel, batool dai bata ji daɗi ba, ganin taƙi tasowa taci, ga nata nan ajiye shi kaɗai, idan wani ya cinye tayi asara, in kuma ba’a samu wanda yaci ba, zasu tafi da shi ne.
baiwar Allah ta galabaita sosai, ga jaraba nacin ta ga yunwa ga kuma abinci amma taƙi ta shi taje ta xauna cikin su ta ci, wani irin ƙululun baƙin ciki ne acan ƙasan zuciyarta, eyes ɗinta a rufe hawaye ke gangarowa saman kuncinta,
Ƙasa ƙasa da murya batool ke yi mata magana”ki taso ko ci,” maƙe kafaɗa angel ta yi, alamar baza ta zo ba,
A ƙarshe ma sai ta miƙe tana tangal tangal zata faɗi amma ta jure a haka ta taka izuwa gaban waɗannan Giants ɗin ta ci burki ta tsaya,
“Ku maida ni inda ku ka ɗauko ni, bansan zunubin dana aikata ba, da har za’a sato ni izuwa cikin wannan kurkukun,” magana take yi masu amma ko uffan basu ce mata ba, domin kuwa a tsarin aikinsu basa magana da prisoners,
“Dama kin daina wahalar da kanki, domin kuwa waɗannan da kike gani basa ji basa gani, idan kuma kika ce xaki matsa masu jikin ki ne zai gaya maki”
Juyawa angel ta yi da sauri don taga wani ja’irin ne ya tsoma mata baki, ɗaya daga cikin matasan ne me suna naufal,
Nuna shi ta yi da yatsan hannunta”karka kuskura ka ƙara shiga hurumina, ba ruwan kowa da rayuwata,” juyawa ta kuma yi kansu cikin xafin rai tace”magana nake yi maku, ku faɗamun wanene ya bada umarnin a kawo ni wurin nan? Shiru basu tanka mata ba ga shi bata iya ganin koda ƙwayar idonsu ce balle tasan ko suna kallon ta,
Zubewa tayi saman guiwowinta tana raira masu kuka tamkar ranta zai fita,
tana ji tana gani suka kammala cin abincin, Giants ɗin nan suka tattara kayan abincin suka kama hanyar fita daga ɗakin, ranta ya 6aci ta dunga ɗura masu ashar kamar ɗiyar maguzawa,
Da gudu tabi bayansu tana kuka tana zagin su, ƙopa suka buɗe suka fuce, ƙopar ta datse, ta dinga bugun ƙopar tana kuka, silalewa tayi bakin kopar ta kwantar da kanta, tako ina babu sauƙi,
“Idan kina jin bacci, gadon ki shi ne no 1 zaki iya zuwa kije ki kwanta” batool ce ta yi mata maganar, tana a tsaye saman matattakalar benan, buɗe idanuwanta tayi waɗanda suka kaɗa su kayi jawur, ta watsa mata harara muryarta a disashe tace”wai ke mayyace? Ki rabu dani mana kamar yadda sauran ƴan uwanki suka yi,” jinjina kai batool ta yi,” I worry about you but you don’t worry about yourself, i won’t disturb u again tun da kin buƙaci hakan, just whenever u change ur mind, za ki iya yi mun magana,’ jiki a sanyaye batool ta juya ta koma cikin ɗakin,
Tuni kowa ya koma saman gadon shi ya zauna, wasu suka kama bacci wasu kuma suna zaune suna fira,
Yinin ranar angel a galabaice ta yi shi, sai da takai ga bata gane komai idanuwanta sun rufe saboda tsabar jin yunwa, ga raɗaɗin da zuciyarta ke yi mata, wani irin matsanancin ciwon kai ne ya far mata, a nan saman benan ta zube rai hannun Allah,
lokacin da dare ya yi, hasken ɗakin da kan shi ya ɗauke, dama ƙa’ida ne idan dare ya yi gaba ɗaya hasken wurin yake kashe kan shi, sai dai mutun in yana buƙatar haske ya yi amfani da fitilun da ke ajiye saman table,
Duhu ya mamaye idanuwanta, ta ƙuntata sosai ji ta ke kamar ta haɗiyi zuciya ta mutu, wannan wata irin rayuwa ce me cike da ruɗa ni? taya zata ci gaba da rayuwa acikin kurkukun nan? ta gaza gane sarƙaƙiyar da ke acikin rayuwarta, shin wanene a cikin danginta ya kawo ta cikin gidan kurkuku da sunan araine ta? Anya kuwa wannan ba ƙanzon kurege bane? tabbas akwai mata maƙarƙashi a cikin gidan kurkukun nan,
A cikin zuciyarta take wannan tunane tunanen,
Saboda tsabar yunwa ko yatsanta, bata iya ɗagawa,
Batool sam ta kasa runtsawa saboda halin da yarinyar take ciki, ta damu da ita sosai ga shi ita kuma bata so ta kusanto ta, kowa ya yi bacci ban da ita,
Saukowa ta yi daga saman gadonta cikin duhu ta shiga laluban inda fitilun suke, har Allah yasa ta gano table ɗin takai hannu ta ruƙe handle ɗin fitilar bayan ta kunnata, tafiya ta soma yi Cikin ɗakin har zuwa saman benan anan ta samu angel cikin mawuyacin hali, zuƙunnawa ta yi agabanta, muryarta ƙasa ƙasa tace”Yar uwa” angel bata iya amsa mata ba, domin kuwa takai mataki na ƙarshe wanda ko la66anta bata iya motsawa, a lokacin jikinta ya yi mugun yin sanyi ta fidda rai da rayuwa, cikin zuciya ta dinga yi furta kalmar”ruwa! ƙishi nake ji! A taimaka mun,” batool batasan me take cewa ba, saboda a cikin zuciya ta yi maganar, Allah dai ne kawai ya taimake ta, batool ta yi tunanin ko tana buƙatar ruwa, dama ɗazu ta 6oye mata chicken wraps ɗinta, tun ɗazu taso ta bata taci sai dai taƙi bata fuska, shiyasa ta ajiye mata zuwa lokacin da zata neme ta,
Miƙewa ta yi da sauri ta nufi ƙarƙashin gadonta inda take ajiyar ruwa acikin bottle water, ta zuƙunna tana haskawa da fitilar hannunta, kwando ne ajiye a karkashin gadon, a cikin shi take 6oye abinci idan ta rage saboda gudun yunwa, zura hannu tayi ciki ta ɗauko Chicken wrap ɗin, Ta tura cikin aljihunta, sannan ta ɗauki robar ruwan ta ruƙo a hannu ɗaya, ɗayan hannun kuma yana a ruƙe da fitila, da sauri ta koma saman benan saitin inda angel take ta zuƙunna, ta sauke fitilar ƙasa, tare da bottle ɗin, hannu tasa ta tallabo kan angel ta jingina shi gefen shoulder ɗinta,
Sannan ta ɗauki bottle din ta buɗe murfin ta kafa mata bakin robar,
yadda kasan mafaraucin da yayi rashin ruwan sha na tsawon sati ɗaya haka angel ta shiga ɗaɗɗakar ruwan, maƙoshinta har wani sauti yake badawa, kwat kwat!
Murmushi batool ta saki ba ƙaramin daɗi taji ba ganin yadda take shan ruwan,, Yarinya taji ƙamshin mutuwa,
Sai da ta shanye ruwan nan tass tamkar xata haɗa da robar ruwan duka ta shanye,
Janye bottle ɗin ruwan ta yi daga bakinta, ta ajiye ta saman matakalar, ta mayar da murfin a mazauninsa,
Hannu ta zura cikin aljihun ta, ta ciro chicken wrap ɗin duk ta rugurguje, a haka ta dinga tura mata abaki, la66anta har kerma suke yi wurin ci, kuma har lokacin kanta yana asaman ƙirjin batool, sai da ta cinye tass ta soma jin wani irin tashin zuciya, yunƙurin amai ta soma yi, a ruɗe batool ta shiga bubbuga bayanta tana faɗin”Sorry sis, bari na raka ki toilet” kafin batool ta miƙe ta yi yunkurin tallabota, tuni Ta saki aman anan saman benan, ta dinga kwararo shi gaba ɗaya ya 6ata hada jikin rigarta, baiwar Allah taji jiki, saboda tsabar tausayinta da batool take ji, batasan lokacin da ta fashe da kuka ba, duka chicken wrap ɗin da taci sai da ta amayar da ita, tun ruwa na fita abakin ta, har yakai ga babu komai sai dai kawai kakarin aman da take yi,
Ganin mawuyacin halin da ta shiga ne yasa batool ta miƙe tare da ɗaukar fitilar, ta ruga da gudu zuwa ƙopar ɗakin tsohuwa, knocking ƙopar ta soma yi tamkar zata 6alleta,
Mutun uku dake bacci saida su ka farka, Danish da ya kasance baisan hayaniya ko misƙala zarratin, Sai hanna da kuma Haris, Har suna haɗa baki wurin tambayar Batool lafiya take neman tsohuwa, ko ta kansu bata bi ba, har saida tsohuwa ta buɗe ƙopar, Hannunta ruƙe da sanda ta fito, batool na kokarin buɗe baki ta yi mata jawabi, tariga ta cewa”Kada ki damu, ki koma wurinta zata dawo dai dai, nayi mata addu’a daga cikin ɗaki,” tana faɗin hakan ta juya ta koma cikin ɗakinta, tare da jan ƙopa ta rufe,
Jikinta asanyaye ta juya sam ba haka taso ba, taso ace tsohuwa tazo ta duba jikinta, saboda halin da yarinyar take ciki, muryar Haris ce ta ratsa kunnanta”Just because her duk kin damu kanki, kin hana idonki bacci, meye alaƙarki da ita”?
Hanna tace”tambayar da nake so na yi mata kenan, shi dai danish baice komai ba, bacci ne dai an hana shi yi, ya takure saman gadon shi, sai faman lumshe ido yake yi,
Batool ku wa Ko kallo basu ishe ta ba, lokacin da ta koma wurin angel, wani abun mamaki a zaune ta same ta, ta jingina kanta jikin bango, shanyayyun idanuwanta a buɗe sun kaɗa sunyi jawur, Sumar kanta duk ta barbazo mata har saman fuskarta, la66anta na kerma take ambaton”rabbi yassir wala tu’asir watammim bil khairi” wani irin farin ciki ne ya lullu6e batool, har batasan lokacin da ta saki murmushi ba, maganar tsohuwa ta tabbata ga shi ta farka har tana magana, duk da batasan me take cewa ba,
“Yar uwa” ta ambaci sunanta, idanuwanta Jiƙe sharkaf da hawaye ta ɗago ta kalle ta, wato duk irin korar da take yi mata hakan baisa ta guje taba, lallai ba ƙaramin so take yi mata ba, batool ba tayi tsammanin zatayi mata magana ba, sai ji tayi tace”Ina so in wanke jiki na, bana jin daɗi,”
Miƙa mata hannu batool tayi”ki taso na raka ki toilet” miƙa mata hannu angel tayi, ta ruƙo nata daƙyar ta samu ta miƙe, ita kanta ta yi mamakin yadda ta rayu don ba ƙaramar azaba tasha ba, taji jiki sosai, amma yanzu ko yunwa bata ji, jikinta ba wani ciwo, sai dai ciwon dake a cikin zuciyarta dake tafarfasa,
Har toilet batool ta rakata, da yake babu wadataccen haske bata iya kallace shi da kyau, A bakin fanfo suka tsaya ta wanke mata gaban rigarta daya 6aci da kuma wandonta, wani irin sanyi jikinta, tuni ta soma kerma,
Fitowa su ka yi daga Cikin toilet ɗin hannunsu cikin na juna, batool ta kai ta har saman gadonta mai ɗauke da no 1 kusa dana danish na shi no 2 ne, sai na batool no 3, hawa saman gadon ta yi batool ta lullu6a mata bargo asaman jikinta, sosai ta ƙudundune,
Komawa batool tayi ta gyara inda angel ta 6ata da aman, ta goge ko’ina duk ita kadai baiwar Allah, bayan ta kammala ta dawo Cikin ɗakin ta ajiye fitilar saman table ɗin, ta kukkuna sauran fitilun ɗakin ya yi haske, danish da bai koma bacci ba ya lafe saman mattress ɗinshi, yana fuskantar angel dake ƙudundune cikin bargo, babu tazara tsakanin gadajensu gab su ke da juna, idan har mutun zai iya miƙa hannu to xai iya ta6o gadon dake a kusa da nashi, shi dai hakanan sam yarinyar bata kwanta ma shi ba, ji yake kamar an kawo masu monster acikin ɗakin su, bargo yasa ya lullu6e fuskarshi,
Dawowa batool ta yi wurin angel don taji idan ta yi bacci, a gefen gadonta ta zauna, Cikin sanyin murya tace”sister kinyi bacci”
Hannu angel tasa ta yaye bargon da ta lullu6e kanta da shi, fuskar nan tayi jawur ta kumbura, daƙyar take iya kallon fuskar batool,
Hannu batool takai tare da shafa fuskarta, Cikin sanyin murya ta soma magana” i know we don’t know each other that well, but i’m still worried about you, nasan irin raɗaɗin da kike ji acikin zuciyar ki, bazan iya yaye maki shi ba, amma abu ɗaya nake so in tunasar da ke, duk abunda haƙuri bai baka ba, to rashin haƙuri bazai ta6a baka shi ba, tsohuwa ce ta ta6a faɗa mana haka,” shiru ta ɗanyi na wani lokaci, angel na sauraronta kafin taci gaba da cewa” yau kika tsinci kanki acikin kurkukun nan ni kuwa tun ban mallaki hankali na ba nake acikinsa, bansan kowa nawa ba abun da nasani kawai tsohuwa ce ta raine mu……..” bata kai ƙarshen maganar ba, cikin shessheƙar kuka angel tace”bazan iya jure zama acikinsa ba, cewa fa ta yi daddy na ya mutu, yanzu ni marainiya ce amma ae ina da dangi masu ƙaunata aunty aneelerh tana so, mommyna adama tana so na, don me za’a kawo ni gidan marayu”? daƙyar take magana saboda yanayin da take ciki,
“bazan iya amsa tambayarki ba, amma shawarar da zan ba ki shi ne ki bi komai a sannu, idan kika ce zaki bi ta ƙarfi da yaji don ki bar cikinsa to kuwa kece a wuya domin kuwa ni tun da na taso a cikin GIDAN KURKUKUN ƘADDARA yau tsawon shekara da shekaru banta6a ganin hanyar fita daga cikinsa ba, babu wanda yasan ta hanyar da aka shigo da shi, balle kuma yasan hanyar da zai fita daga cikin sa, sa’annan duk wani motsin mu a tafin hannunsu yake suna kallon mu, kewaye ne kaɗai idan kika shiga basa iya ganin ki……..”
Cikin rashin fahimta angel tace”Idan har dagaske orphanage home ne meyasa xasu ƙuntata rayuwar mutun babu shige babu fuce kenan ko makaranta mutun baida ikon zuwa? Gaskiya bazan ta6a yarda da gidan nan ba…….”
Batool tace”bana son muja zancan nan da tsayi, kamar yadda ba zaki fahimce ni ba, nima bazan iya fahimtar ki ba, saboda dukkan mu cikin ruɗani mu ke, abu ɗaya zan sanar dake GIDAN KURKUKUN ƘADDARA ba gidan cutarwa bane, saboda ni tunda na taso a cikinsa ba’a ta6a cutar dani ba kuma banga an cutar da wani ba, sai dai abu ɗaya ne da ya ke ci mun tuwo a kwarya shi ne kullan da a ke yi mana, ba ko’ina bane muke da ikon taka ƙafarmu ba acikinsa, najima ina tunanin ya wajen sa yake? Saboda ni ban ta6a fita daga cikinsa ba,”
Shiru angel ta yi batare da ta kuma cewa wani abu ba, saboda har yanzu tana ɗan jin jikinta ba daɗi, amma tabbas tana da tambayoyi dayawa da suka cunkushe zuciyarta, Dama gidan marayu bibiyar rayuwar mutun suke yi idan suka ga iyayen shi sun mutu sai su sato shi zuwa cikinsu? Meyasa batool tace sau ɗaya ake basu abinci a rana kamar yadda ta faɗa mata ɗazu! Meyasa za’a haɗa maza da mata a ɗaki ɗaya? Meyasa mutanan dake kawo masu abinci su ka yi 6adda kama!? Meyasa ba’a shige da fuce acikinsa? saboda me a ka yi masu iyaka da komai na cikinsa? Tabbas kuwa akwai wata maƙarƙashiya da ake shiryawa acikinsa, kodan saboda wannan tambayoyin da suka toshe kwakwalwarta, dole ta sanya nutsuwa don ta gano komai dake wakana,
“Zanje na kwanta, Amma kafin nan i naso ki faɗa mun sunan ki, duk da naji ɗazu kamar tsohuwa ta ambace shi, sai dai ban ruƙe ba,” muryar batool ce ta katse mata zancen zucin nata,
Ajiyar zuciya angel ta sauke kafin tace”Sunana ANGEL ke fa?” batool ta bata amsa da cewa”Ni sunana BATOOL inaso ki ɗauke ni tamkar ƴar uwarki, kuma ina so ki saki jikin ki acikin mu, ta hakanne zaki samu duk abunda ki ke so,”
“Kin wahaltu sosai yau, ki samu ki yi bacci, takai ƙarshen maganar tare da jan bargo ta lullu6e fuskar angel da shi,
“Sleep well my lovely sister” ƙasa ƙasa da murya angel ta furta mata”thank u, Sister” murmu shi batool tasaki ba ƙaramin daɗi taji ba, da angel ta kira sunanta da sister, wuce wa tayi zuwa nata gadon ta kwanta, kamar daga sama ta jiyo muryar hannah”kin gama kula da jinjirar ta ki? Tsoki batool taja” mind ur own business” tana faɗin hakan bata ƙara tanka mata ba,
Kowa ya runtsa a daren ranar banda mutun ɗaya! Dama taya zata iya bacci? ya yin da zuciyarta ke a cunkushe a ƙuntace da rashin mahaifinta, duk da har yanzu bata gasgata kalaman dattijuwar nan ba, ita dai tana ji aranta daddyn ta he’s still alive! kuma taci alwashin duk runtsi duk wuya sai ta nemi hanyar guduwa daga cikin kurkukun ƙaddara, ni dai nace Allah ya ba mai rabo sa’a,
Ataƙaice cikin ƴan kwanakin nan ba irin haukan da angel ba ta yi masu ba akan su fitar da ita daga cikin kurkukun amma duk a banza, babu mai saurarenta acikinsu batool ce kaɗai ke lallashinta, duk ta bushe ta rame dama ba ƙiba gare ta ba, yadda kasan ɗiyar roba haka ta koma cikin sati ɗaya kawai, duk ta fita hayyaci kuma taƙi sakin jiki da su, musamman mazan haushin su take ji, saboda wannan Danish ɗin da basa jituwa da shi, ta tsane shi kamar mutuwarta shima haka ya tsaneta ko kallon arziƙi bai haɗa ta da shi, ko fira suke yi ta sanya masu baki to ya gama magana, ita kallan ɗan iska ta ke yi ma shi saboda doguwar sumar dake akan shi ita a ganinta ta ya yana namiji xai tara suma? tsayin sumar shi har ya kusa taddo nata, gaba ɗaya dai haushin mazan take ji saboda an haɗa su rayuwa a wuri ɗaya sam bata so ko kallonta su na yi ae ita a wurinta iskanci ne hakan, abunda bata sani kwata kwata basu da feelings a tare da su, suna ɗaukar kansu tamkar jinsi ɗaya da matan, ita ce kawai ta sanyawa ranta hakan, bakomai ya ƙara ɗaure mata kai ba fa ce rashin barin su yin ibada, batool ta sanar da ita cewa basu da addini, duk wanda ke rayuwa acikin kurkukun ƙaddara baida addini, rayuwa kawai suke yi tamkar arnaku ko sunan Allah basu ambato acikin maganar su, ba sallah ba sallati, bama su san yadda akeyin ta ba, dokar prison ɗin ce ba’a ibada acikinsa, wani irin kurman kurkuku ne, baka sanin lokaci dare ne kaɗai idan ya yi suke ankara saboda hasken ɗakinsu da ake ɗaukewa sai kuma idan safiya ta yi sun ta shi daga bacci, ita kanta angel ɗin ta ta6a gigin yin sallah, duk da basu da hijabi, ranar da tayi alwala ta yafa bargon lullu6arta da sunan za ta yi sallah, zagaye ta su ka yi suna kallonta da mamaki don basu san menene take yi ba, da zarar ta ɗaura niyya zata kabbara, sai ta dinga jin kukan mahaifinta, idanuwanta su dinga nuna mata fuskar tajuddeen wuta na ƙone jikin shi, gaba ɗaya take rikicewa ta gigice ta dinga kuka ire iren irin wannan gane gane da take yi yasa ta daina yunƙurin yin sallar, abun yana affecting ɗin ta
Yanzu dai ta zubawa sarautar Allah ido, ta daina haukan guduwa daga cikinsa tun da ta ga babu hanya, amma fa bawai hakan yana nufin ta haƙura ba, tana nan akan bakanta! ta lura cewa idan har zata cigaba da borin haukan da take yi masu tofa bazata ta6a samun nasara ba, wannan dalilin ne yasa ta nema ma kanta maslaha, tayin rayuwa cikin salama don ta samu damar yin bincike ta gano ainihin sarƙaƙiyar dake acikin Kurkukun ƙaddara, don tun daga kan ma’anar Sunan kurkukun fassara ce me zaman kanta, Kuma kullum tana cikin yin azhkar na safe dana mare ce, wanda daddynta ya koya mata, har tsakar dare bata runtsawa xama take yi tsakiyar gadonta, ta ɗaga hannayenta sama tana jera addu’o’i akan Allah ya kawo mata mafita acikin rayuwarta,
*Boss Bature✍️💋*
*After some weeks*
Zaune take a tsakiyar gadonta, ta jingina bayanta jikin bango, idanuwanta suna arufe fuskar nan ta yi jawur idanuwan sun kumbura, ga busassun hawaye duk akan fuskarta,
Kasancewar safiya ce ba su jima da farkawa daga bacci ba,
Sautin dariya taji ƙasa ƙasa taji muryoyinsu suna yin gulmarta “Wari take yi, tun da tazo bata yi wanka ba daga gani dai ƙazama ce,” can ta ji muryar wani ya kuma cewa”idan muka ƙyale ta mu zamu cutu, jiya fa daƙyar nayi bacci saboda warin jikinta gaba ɗaya ya cika ɗakin nan,” tuntsure wa su ka yi da dariyar shaƙiyanci,
“Ku ta shi muje muyi mata magana, ta je ta yi wanka, in ba haka ba mu zamu yi mata da kan mu,” haris ne ya bada wannan shawarar,
Angel dai ta natsu tana sauraronsu, dama mugun haushin su take ji, tana jiyo sautin tafiyar su a bakin gadonta suka tsaya kusan su shida,
Gyaran murya ɗaya daga cikin su yai mata”ke tashi ki je ki yi wanka” a hankali ta ɗan buɗe idanuwanta da suka kumbura ta ɗan kalle su, wanda ya yi magana shi ne Haris, a halitta baƙi ne yana da jiki,
“Ba zamu zuba maki ido kina cutar damu ba, jiya nan daƙyar mu ka yi bacci saboda warin jikin ki, don haka ki tashi kije ki yi wanka ko mu yi maki da kanmu” cike da ƙwarin gwiwa javed ya yi maganar, dogo ne launin fatarsa chocolate,
Jin ta yi banxa ta ƙyale su yasa Mubeen jinjina kai ya kalli naufal dake a gefen shi yace “je ka cika mana bokiti da ruwa,” ya yi maganar yana naɗe hannun rigar shi,
Danish da ke a kishingiɗe saman gadon shi bai tanka masu ba, yasan suna yi duk don su ƙuntata mata ne saboda tsanarshi da ta yi,
ƴan matan dake a tare da su Deeja da yasmeen, sun ruqe qugu suna sakin murmushin mugunta,
Da alama dai hada ƙuruciya ke damun su, don dukan su gaba ɗayan su baza su wuce shekara shabiyar ba, mazan cikinsu ne ke akwai ƴan shekara sha bakwai, kamar danish dasu haris,
“Bakya ji ana maki magana”? muryarta na kerma tace” duk wanda ya yi gigin ta6a ni, zanyi mashi illah, babu ruwanku da rayuwata,” tamkar xata fashe da kuka ta yi maganar,
“Sarkin yawa yafi sarkin ƙarfi, zamu gani mu dake wazai ma wani illah,” haris ne ya yi maganar, tare da naɗe hannun rigarshi yace dasu Naufal su ɗauko mashi ita, akaita toilet su yi mata wankan tsarki,
Jin haka yasa ta durowa daga saman gadon, Duk da jikinta ba ƙwari daure wa kawai take yi, hannu haris yakai zai ruƙo kwalar rigarta, aikuwa ta daddage ta ɗaga kafarta tare da kai mashi naushi tsakiyar cikin shi, azabar zafi yasa ya yi saurin dafe cikin shi, rai a6ace javed ya kai mata bugu aikuwa ta damƙi ƙafar shi ta hagu ta dinga janta har saida ta yarfar dashi ƙasa, faɗa ne ya kaure a tsakaninsu, bugu tadinga kai masu da naushi, dama ta ƙware wurin iya cixo da yaku shi, duk sai da ta raunata su, sai faman nishi suke yi, da taga ta gama da mazan ta koma kan matan,
Haɗe kawunan su tayi, ta ruƙo gashin kansu, tadinga ja tamkar xata tsunka su, kuka hada majina suka dinga yi,
koken koken da suke yi ne ya farkar da su Batool da sauran ƴan uwan nasu dake bacci, ganin yadda Angel take Mazgarsu yasa suka sauko daga saman gadon suka nufeta suna ƙoƙarin rabata da su, daƙyar suka samu nasarar janye Angel gefe ɗaya, sai huci take yi kamar kuranya, Su deeja da yasmin suna zuƙunne ƙasa, dafe da kawunansu sai kuka suke yi,
Duk wannan abun dake faruwa tsohuwa tana a tsaye baƙin ƙopar ɗakinta, hannunta ruƙe da sanda, ta yi tsaye tana kallon sabuwar ƴar wasan damben da suka samu,
Danish kuwa dake kishingiɗe saman gadon shi, hankalin shi kwance dama yasan za’a rina, shiyasa bai shiga cikinsu ba, koda suke xancan zasu je suyi mata magana akan wanka, don ya lura ƙarfi ne da ita, gashi duk cikinsu itace ƙarama amma tafi su ƙarfi,
Gyaran murya tsohuwa ta yi, da sauri angel ta ɗago tana haki, suka haɗa ido da ita,
“Aikin ki ya yi kyau, tsanar da ki ka yi masu har takai ga bugunsu so ki ke ki kashe su?”
Rai amatuƙar 6ace tace” bugun su yanzu na fara idan har ba su daina shiga gona ta ba, kuma wlh idan har baku fitar dani daga cikin kurkukun nan ba, zan addabi rayuwar kowa ne, nace banaso ku ƙyale ni inyi rayuwata na tsani gidan nan, Natsani kowa dake acikinsa, kince nan gidan marayu ne kuma za’a gatanta mu but why kuka killace mu sai ka ce dabbobi? haka ne gatancin Abinci sau ɗaya a rana? Kun hana mun yin ibada, uwa uba kun haɗa mu rayuwa da maza a ɗaki ɗaya? Me hakan yake nufi iye”? Idanuwanta azazzare ta yi maganar, tamkar ta sanya hannu ta shaƙo wuyan tsohuwar hake take ji,
Maimakon tsohuwar ta bata amsoshin tambayoyinta sai ta kece da wata irin mahaukaciyar dariya,
Runtse ido angel ta yi cikin jin zafin dariyar tsohuwar, cije lips ɗinta ta ɗanyi kafin ta buɗe eyes ɗin nata,
“Wlh ban yadda dake ba, saboda gaba ɗaya babu gaskiya acikin kurkukun nan, idan kun 6oye mana manufarku ta killace mu anan baku isa ku 6oyewa Allah ba, yana ganinku kuma asannu Allah zai warware mana komai, ni nasani zuwana gidan kurkukun nan jarabawa ce ta ubangiji………”daƙyar takai ƙarshen maganar saboda hawayen da suka cika mata idanuwanta,
“Dabbar dake yawo a daji, tafi mu gata tafi mu ƴan ci, idan su basu damu ba, zai iyayiyuwa don sun taso rayuwarsu acikin kurkukun ne, kuma sunsan basu da kowa, amma nifa ina da dangina masu sona, hakanan anje an sato ni an kawo ni cikin wannan munafukin ƙaddararran kurkukun mara kan gado,”
“Angel” muryar batool ce ta ambaci sunanta, a harzuƙe angel ta juya baya tana kallon batool tace,
“Nasan bai wuci ki ce xaki bani hakuri ba, akan inja bakina inyi shiru, Batool bazan Iya ba, narasa gane meyasa bakwa fahimtata ne, iya cutuwa an cutar da rayuwata, tun ina jinjirata mahaifiyata ta gudu tabarni a wulaƙance cikin kwamin wanka, nata so cikin so da ƙauna na mahaifina, An raba ni da shi, An kashe mun shi duk da har yanzu ban gasgata hakan ba, sannan na faɗa hannun fulanin daji, na rayu acikin daji tare dasu a matsayin tsintacciya, wai ni Angel ƴar gidan daddynta, na shiga mawuyacin hali na rashin mahaifina atare dani, na saba dashi mun shaƙu sosai, komai shi yake yi mun wanka, ya gyara mun gashin kaina mu kwana rungume da juna, dama haka rayuwa take? Lokaci ɗaya narasa gatancin nan, na dawo ina kwana a saman tabar ma cikin bukka, bani da abinci daya wuce gasassar masara da fura, yanzu kuma gashi na tsinci kaina acikin GIDAN KURKUKUN ƘADDARA, ya a ke so inyi da raina? Wlh da rayuwa acikin kurkukun nan kwara na ƙare rayuwata a hannun fulani daji, koba komai zan sha iskar duniya, in yawata inda nakeso, inyi rayuwar ƴan ci, Amma nan fa? Ta karfi ta tsiya aka kawo ni cikin shi banma san ta ina aka shigo dani cikin gidan kurkukun nan ba, don kuwa sai da aka fara gusar mini da hankalina tukunna, in banda munafurci taya xa’ace gidan marayu ne? Meyasa da za’a kawo ni cikinsa ba’a barni cikin hayyaci na ba? Meyasa za’a hana mu shige da fice, An tauye mana haƙkin mu na rayuwa an hana mu sakat wai da sunan za’a gatanta mu………………….’
(SHIN ME KU KE TUNANI AGAME DA GIDAN KURKUKUN ƘADDARA? MU HAƊU A NEXT PAGE IN ALLAH YAKAI MU DA RAI DA LAFIYA, HAR YANZU FREE PAGES NE WANDA YA SHIRYA BIYA ZAI IYA YI MUN MAGANA 08103884440, WASAN FA YANZU AKA SOMA BUGA SHI, DOMIN KUWA BAMU NUTSA CIKIN LABARIN BA, YANZU AKA FARA)*💋KURKUKUN ƘADDARA💋*
Daga alƙalamin Boss Bature✍️
Cikin shessheƙar kuka takai ƙarshen maganar, hawaye ta ko’ina akan fuskarta, tabbas jikin kowannan su ya yi sanyi, banda mutun biyu, danish dake kwance saman gadon shi sai Haris dake zaune ƙasa ya dafe cikin shi,
Saukowa batool ta yi tare nufar inda angel take tsaye agaban tsohuwa, ta dafa shoulder ɗinta”I feel ur pain angel, abun da ciwo labarin ki akwai ta6a zuciya, dole kiji ɗaci aran ki, kuma dole ki ƙuntata acikin kurkukun nan, abunda yasa kika ga mu ba mu damu ba saboda bamu da wanda zai yi kukan rashin mu! Mu matattu ne a idon jama’a kamar yadda tsohuwa ta faɗa mana, a gidan nan aka raine mu agidan nan muka taso, tunda mu ke bamu ta6a yin tozali da hasken daya fito daga wajen kurkukun nan ba, ina yawan tambayar kaina koya wajen kurkukun nan zai kasance? Ya mutanan dake rayuwa a wajen sa su ke? Bani da amsar tambayata amma ina fata wata rana nima wata rana in fita daga cikin sa, sai dai nasan abune mai wuya……” cikin sanyin murya takai ƙarshen maganarta,
“Zan iya zuƙunnawa saman gwiwowina in roƙe ki akan ku fitar dani daga cikin kurkukun nan, inaso na rayu cikin ƴan uwana” angel ce ta yi maganar muryarta a rauna ce,
Jinjina kai tsohuwa ta yi a yayin da take binsu da kallo da waɗannan kwarkwararrun idanuwan nata, tsawon mintuna kafin tace”koda ace kin zuƙunna saman gwiwowin ki don ki roƙe ni akan in fitar dake daga cikin prison ɗin nan, hakan bazaiyi aiki ba idan ku ka yi haƙuri a sannu zaku fahimci manufar wannan kurkukun na tara ku acikinsa, Amma a yanzu shawarar da zan baku shi ne, ku so junan ku tun da baku da kowa ku xama naku ku kaɗai, ku kasance masu faranta ma juna” daga haka bata ƙare cewa komai ba, ta dogara sandarta tare da juyawa tana ɗangyala ƙafa ta nufi cikin ɗakinta, tana shiga taja ƙopa ta datse,
Zubewa angel ta yi saman gwiwowinta, tare da fashewa da matsancin kuka mai cin rai tamkar ranta zai fita,
Rankwafawa batool ta yi tare da ruƙo hannayen angel cikin nata, ta miƙar da ita tsaye, ta rungumeta ajikinta tana lallashin ta, sun ɗauki tsawon mintuna, kafin ta raba jikinsu,
Kallon sauran ƴan uwan nasu ta yi, kowa yana a tsaye banda Danish dake kwance
Ɗaya bayan ɗaya ta shiga kiran sunayen su”Hannah, Hibba, deeja parveen, Eve, yasmin, rubina, Aziza” kowa ya kasa kunne yana sauraron abunda zata ce masu, juyawa tayi kan mazan dake acikinsu ta ambaci sunayen su one by one”Danish, javed Haris, mubeen, naufal” sai faman huci haris yake yi saboda haushin bugun da angel ta yi masu,
Calmly ta soma magana cikin sanyin murya”kamar yadda tsohuwa tace mu so junan mu, Let’s consider ourselves as blood relatives, inaso mu yi ma juna alƙawarin duk runtsi duk wuya zamu kasance a tare, Sa’annan bana jin daɗin yadda ku ke ware angel acikin mu, i thought we are all the same, bamu da banbanci jinsi ɗaya ne mu da ita duk abu ɗaya ne, idan ba mu so juna ba, wa zamu so? Nasan kuna jin haushin angel ne saboda abubuwan da take yi wanda bakomai ya jawo hakan ba face ƙuntata rayuwarta da a ka yi, taya mutumin da ya saba rayuwar shi a sake rana ɗaya a tsamo shi daga cikin danginshi a kawo cikin GIDAN KURKUKUN ƘADDARA! taya bazai ƙuntata ba”? dakatawa ta ɗanyi da yin maganar tana bin fuskokin su da kallo,
“Batool ni dai inason Angel, kuma bazan ta6a faɗa da ita ba, zan ɗauke ta tamkar yadda na ɗauki kowannan ku,” bakowa bace ta yi maganar fa ce AZIZA, yarinya ce me ƙarami jiki fara ce sosai duk cikin su babu me gajartar ta,
ɗaƙyar angel ta iya buɗe idanuwanta da suka kumbura ta ɗaura su akan fuskar aziza da ta yi maganar, ba ƙaramin son yarinyar ta ji ba, saboda ita kullum a cikin fara take baka ta6a ganin fuskarta a ɗaure,
“batool, nima xan ɗauke ta tamkar yar uwata,” kallon wadda ta kuma yi magana angel ta yi, hibba ce ta yi maganar fuskarta ɗauke da murmushi,
Lumshe ido angel ta ɗanyi tare da buɗe su tana ci gaba da kallon su,
“Nima na goyi bayan Batool, angel tamkar ƴar uwa take acikin mu” acewar Parveen
Murmushi batool ta ɗan saki, har cikin zuciyarta ba ƙaramin daɗi taji ba,
Miƙa hannunta na dama tayi saman iska tare da kallonsu tace”ina so muyi wa juna alƙwarin kasancewa atare, zamu so juna kuma zamu taimaki juna, sannan babu faɗa atsakaninmu kuma babu nuna wariya, duk wanda ya amince ya ɗaure tafin hannun shi a saman nawa,”
Angel ce ta fara ɗaura tafin hannunta saman na batool, matsawa aziza ta yi itama ta ɗaura nata hannun, Hibba ta ɗaura nata parveen ma ta ɗaura nata, kallon sauran Batool ta yi ganin sun ƙi matsowa su ɗaura nasu hannuwan,
“Duk wanda bazai so zaman lafiya a cikin mu ba, babu ruwan mu da shi domin kuwa baya atare da mu”
Jin wannan maganar da batool ta yi yasa Eve ta matsa ta ɗaura nata hannun, rubina ma ta sanya nata, mutun biyu suka rage Cikin mata basu sanya hannayensu ba, deeja da yasmin Sai kuma mazan su, don shi danish har yanzu bai motsa daga saman gadon shi ba,
Zuba masu ido batool ta yi tana bin sauran da su ka rage da kallo, Masu girman kan Cikin su,
“Idan har baku ɗaura hannayen ku ba, kada ku yi tsammanin idan wani abu ya faru da ɗaya daga cikin ku, xamu share mashi hawayen shi,”
Gyaɗa kai Javed ya yi tare da kallon su haris, kafin ya wuce su zuwa inda su batool su ke A tsaye shima ya ɗaura hannun shi fuskar shi ɗauke da murmushi ya ce”Nima ina goyon bayan ki batool, kuma ina ba angel haƙuri akan irin wariyar da muka nuna mata” yakai ƙarshen maganar idanuwan shi akan fuskar angel, itama kallon nashi ta ke yi, har cikin ranta taji daɗin waɗanda suka nuna suna sonta,
Matsowa kusa Yasmin ta yi, “idan muka yarda da junanmu, muka so junanmu tabbas xamu cimma nasara, nima ina goyon bayan batool,” takai ƙarshen maganarta tare da ɗaura hannunta saman nasu,
Kallon deeja su ka yi dake a tsaye ta toge saboda haushin angel take ji,
Matsawa mubeen ya yi da sauri haris ya ruƙo hannun shi”badai zuwa zaka yi ba”? Jinjina mashi kai ya yi”zuwa zanyi, saboda inason mu samu maslaha a tsakaninmu,” ya janye hannun shi daga ruƙo da ya yi mashi, ya wuce wurin su shima ya ɗaura hannun shi, murmushi batool ta saki tana kallon shi,
Kallon haris naufal ya yi tare da cewa” am sorry bro but am not supporting, also am advising u, ka aje makaman yaƙin ka kazo mu rungumi junanmu,” yana kai ƙarshen maganar shi yaje wurin su, sai da ya fara kallon angel ya sakar mata murmushi kafin ya sanya nashi hannun, kallon kallon aka koma yi a tsakanin Deeja da haris da kuma mr arrogant dake kwance saman gadon shi, ganin suna kallon shi yasa shi rufe eyes ɗinshi tamkar mai yin bacci, tasan indai ba sanya hannun shi yayi ba, haris bazai ta6a supporting ɗinsu ba, gyaɗa kai ta yi tare da kallon deeja tace”ke baza ki goyi bayan mu ba? Bana so ki yi abunda zaki yi danasani, duk wanda bai sanya hannun shi ba, to baya a tare mu”
Kallon harris tayi ganin yana maƙe mata wuya alamar karta shiga cikin ku, ta ɗauke idonta daga kanshi ta mayar dasu kan fuskar batool, ganin ba ta da mafita yasa ta shiga cikin su, itama ta sanya nata hannun
Murmushi batool ta saki, kafin ta ce su maimaita duk abunda tace, suka amsa mata da toh, alƙawari ne suka ɗaukarwa juna,
Banda mutun biyu Haris da Danish, bayan sun kammala yi ma juna alƙawari gaba ɗaga suka shiga rungume junansu, a yau suna jin kansu tamkar ciki ɗaya suka fito,
Bayan kowannan su ya samu natsuwa, Batool da angel su ka kalli juna, lokaci ɗaya suka sakar ma juna murmushi,
“Idan zaki shiga toilet, muje tare nima ina so zanyi wanka,”
Gaba ta yi angel tabi bayan ta, har zuwa ƙopar shiga toilet ɗinsu hannu batool ta sanya tare da tura ƙopar suka shiga daga ciki, ƙofofi ne kusan guda uku kowanne a rufe ya ke, ɗaya daga ciki angel ta shiga, itama batool ta buɗe ɗayan toilet ɗin ta shige ciki,
Sai yau ta samu damar ƙarewa toilet ɗin kallo na ƙurulla, ko’ina a tsaftace ya ke, sai dai babu wadatattu kayan amfani, akwai dai toilet seat, sai shower ta tsaye wani ajiyayye bucket, kwandon wanka me ɗauke da soap and sponge, a kwai cabinet dake ɗauke da sabulai da hada ledar detergent da kuma Shampoo ɗaya, saman ceilling ta wurga idonta, wasu munafukan tagogi ne kusan uku, masu murfin ƙarfe an garƙame su da kwaɗo jikin su har ya yi tsatsa, mayar da idanuwanta ta yi akan tagar jigin bango guda ɗaya jikinta wani tsohon glass ne duk yayi ƙura, tunani ta shiga yi idan har zata iya samun makamin da zata iya fasa glass ɗin jikin glass ɗin da shi tabbas zata iya kutsawa ta cikin tagar ta dira ta baya, daga nan zata samu damar shiga cikin kurkukun taga me ke wakana, jinjina kai ta yi tare da cewa”I will try”, sauke idanuwanta ta yi akan tukunyar fular dake ajiye daga ƙasa jikin bango tana da girma, fulawar cikinta duk ta yagalgale saboda rashin kulawa, ta6e bakinta ta yi kafin ta mayar da idonta kan igiyar da ke a ciki da a lama ta sagala kaya ce,
tafiya ta soma yi tana bin kowace kusurwa ta makewayin da kallo, bakin magudajin da ruwa ke bi ta tsaya wasu ƙananun hudoji ne da basu fi shida ba, tanan ruwa yake bi ya wuce, akwai wasu fanfuna guda biyu da su ke a kashe,
Sai da ta kammala bin ko’ina da kallo tukunna ta sanya hannayenta ta kamo ƙasan rigarta, ta cireta tare da rataya ta saman igiyar,
“Ko madubi babu da mutun zai kalli fuskarsa, ta ya zan gane ina ƙara kyau ko muni nake yi”? tayi maganar acikin zuciyarta,
Bokitin nan ta janyo tare da tara shi gaban fanfon ta kunna, ruwa ya soma bulbulowa daga cikinsa, tafi sha’awar ta yi da bokin akan ta kunna shower,
Zuƙunnawa ta yi tana jiran ruwan ya cika, kamar daga sama taji an banko ƙopar toilet ɗin da ta ke ciki, A gigice ta ɗago tare da wurga idonta kan door ɗin don taga wanene ya shigo,
*DANISH* ne a tsaye hannun shi ruƙe da rigar shi, tun daga ƙasa har sama take kallon shi, kamar wani bugagge sai faman lumshe eyes ɗin shi yake yi, shafaffan cikin shi tamkar wanda bai ta6a cin abinci ba, ranta a matuƙar 6ace ta miƙe saboda tsabar fusata bata ɗauki rigarta ta sanya ba, ta rufe shi da faɗa” kai wani irin jaki ne ba ka da hankali za ka faɗo cikin kewaye batare da ka nemi izni ba? saboda daƙikanci da dabbanci dama da biyu ka shigo don ka ganni babu kaya ko?
Tunda ta soma balbale shi da masifa bai yi yunƙirin tanka mata ba, kuma bai motsa ba ya dai yi kasaƙe yana kallonta, sai da takai ƙarshen maganar tana haƙi cikin sanyin murya yace”Duk kin wani ta shi hankalin ki, to me zan gani a jikin na ki? Ƙirjin naki ma ashafe ya ke kamar bangon ɗakin mu, kwarama tsohuwa tafi ki abun kir…….”kafin ya kai ƙarshen maganar, ta sunkucin bokitin ruwan da ta tarba, gaba ɗaya ta sheƙa mashi ruwan a jikin shi, sharkaf ta jiƙa shi,
Runtse idanuwan shi ya ɗanyi saboda ruwan daya shiga ciki, long eye lashes ɗinshi sun jiƙe sharkaf, hannu ya sanya tare da share ruwan dake akan fuskarshi, kafin ya buɗe idanuwan shi, ta yi saurin ɗaukar rigarta da ke a saman igiyar ta zurata a jikinta,
Tana huci ta ci gaba da kallon shi tana fadin”Zaka fita ko saina ƙara watsa maka wani ruwan? Ƙaton banza kawai matsalar ace mutun baida addini kenan, ko dabba tafi shi kan gado,”
A lokacin ya ƙarasa buɗe idanuwan shi, jinjina kan shi ya yi still bai tanka mata ba, ya juya ya fita daga cikin toilet ɗin,
Lamarin ya ɗaure mata kai, har ta soma tunanin kodai yana da ta6in hankali ne? In ba haka ba taya zai faɗo mata bagatatan Cikin toilet batare da ya tambayi ko akwai mutun aciki ba, idan ma ya yi tunanin babu kowa ne why bazai yi knocking ba? Guntun tsoki taja, aranta tace”Amma dai wannan anyi sullu6iyo, Shashasha sauna, next time idan ya kuskura ya ƙara faɗo mun irin haka, saina koya ma shi hankali,” takai ƙarshen maganar tare da nufar ƙopar toilet ɗin da nufin ta rufe, hannunta ta ɗaura saman handle ɗin ƙopar, shiru ta ɗanyi jin alamun bai tafi ba, zurfi tunani ta shiga lokacin da ta shiga cikin toilet ɗin ta manta bata yi locking ɗinta ba, kodai ya yi tunanin babu mutun ne shiyasa ya faɗo ciki? Don ta lura Haka suke yi idan suka ga ƙopa ba a datse ba, shi ne babu mutun a ciki, idan kuma suka ganta a datse to shi ne ke da akwai mutun, kenan itace ta yi ba dai dai ba? Da ace ta rufe ƙopar danish bazai iya shigowa ciki ba,
Ta6e baki ta yi, ta tura ƙopar ta rufe, ta koma ciki domin yin wanka,
Cikin ƙanƙanin lokaci ta kammala yin wankan, ta mayar da kayan jikinta, ita kanta ba ƙaramin daɗin jikinta taji ba, tana buɗe ƙopar ta same shi a tsaye ya jingina bayan shi jikin bangon toilet ɗin, da alama jira yake ta fito ya shiga,
Wuce shi tayi zuwa cikin ɗakin,
A tsaitsaye ta same su, banda mutun biyu Batool da Aziza,
“angel” hannah ce ta kira sunanta, ƙarasawa ta yi kusa da ita ta tsaya,
Fuskarta ɗauke da murmushi tace”kin fito kenan, nima wankan nake so inyi ina jira su batool su fito sai in shiga,”
“Idan ku kayi wanka babu wani abu da ku ke shafa ma jikin ku”? Angel ce ta yi mata tambayar,
girgiza mata kai ta yi tare da cewa babu, mu ma haka muke zama duk in mu ka yi wanka,
“Comb fa? Ina so in taje gashin kaina”,
“Guda ɗaya ne muke da shi, kuma yana a wurin danish, da shi muke amfani in kina so sai in aro maki,” da sauri tace”a’a na fasa” aranta kuma tace komai danish danish sai na koya mashi hankali, sullu6uyo kawai,
Tafiya ta yi zuwa gefen gadonta, ta zauna tana bin kowannan su da kallo,
Motsi buɗe ƙopa su ka jiyo daga can kusurwar da benan ya ke,
Nan fa su Hannah suka fara murna sunsan abinci ne za’a kawo masu,
Takun tafiyarsu tamkar na dawakai, saukowa su kayi daga saman matattakalar benan, Giants ne
Hannayen su ɗauke da farantai, shiga ciki su ka yi a dai dai saitin carpet ɗin nan suka ɗaura sauke tray ɗin,
Kafin su ka ja baya tare da goya hannayen su saman ƙirjin su,
Fuska a ɗaure angel ke kallonsu, ko gunki bazai nuna masu iya tsayuwa ba, abun na ci mata tuwo a kwarya, wai su waɗannan mutanan su wanene? Basa ji basa magana, kullum kuma cikin shiga iri ɗaya kuma sun 6oye ainihin suffar su,
Jin jina kai ta ɗan yi aranta tace”A sannu zan gano ko su wanene ku,”
“Angel ki taso mu ci” Hibba ce ta kirata ganin ta yi zugudum saman gadon,
Saukowa ta yi tare da tunkarar inda suke zaune itama ta zauna gaban farantan, ta lanƙwashe ƙafafunta, mutun uku suka rage basu ƙaraso ba,
Javed yace”wai ina danish ya ke ne? da su batool, wani yaje ya yi masu magana su zo mu ci,” yunƙurawa haris ya yi da niyar yaje ya kirasu sai gasu sun fito daga cikin ƙopar shiga toilet ɗin a tare, komawa ya yi ya zauna, gefen angel batool da aziza su ka zauna, danish kuma ya zauna gefen javed, yana fuskantar angel tun da suka haɗa ido, ta wurga mashi harara tare da murguɗa ma shi small mouth ɗinta,
Bin ta ido kawai ya yi, don baima san menene ta ke yi ba, haushin shi take ji ta ƙara jin tsanar shi saboda sharrin da yayi mata, da ya ce ƙirjinta kamar bangon ɗakin su, tsohuwa ma tafi ta abun kirki, kalaman nan sun baƙanta mata rai, kuma taci alwashin sai ya ɗanɗani kuɗar shi,
Batool ce ta ya ye jan ƙyallen da aka rufe saman trays ɗin, Hamburger suka samu tare da chicken legs na ƙosassun kaji anyi masu jar suya har wani maiƙo suke yi, kowa zai samu burger ɗaya da kuma Chicken leg ɗaya, a tray na biyu Tea pot ne sai jerin wooden Cups, faranti na ƙarshe basket ne mai ɗauke da kayan marmari, a gefe ɗaya kuma bottle waters ne’ fuskar kowannan su awashe, baƙaramin daɗi suka ji ba, duk da sau ɗaya ake a basu abinci arana, Amma suna Ci su ƙoshi wani lokacin ne ba’a basu abun da zai ƙosar dasu, amma yau kam ba laifi, kowannan su Tunanin wanda zai rage yaci da anjima yake yi,
Batool ce ta zuzzuba masu kakkauran tea a kowani Cup, ta miƙa masu ɗaya bayan ɗaya, kusan atare suka kai baki suna sha, Idonta idon danish Sun hana juna sakat, gani take kamar wani abun yake ayyanawa aranshi tun da ya ganta babu riga a jikinta, nan take ta murtuƙe fuska, a ƙule tace”Stop looking at me”
“Ae bani ke kallon ki ba, ke kike kallona,” amsar daya bata kenan, daga haka ya ɗauke idonshi daga kanta, ya kai hannu ya ɗauki burger ɗinshi yana ci,
Yunƙurawa tayi tare da miƙewa, kowa yabi ta ido, batool tace”Har kin ƙoshi”? Fuskarta a hautsine tace”Zan ajiye ne da anjima inci” takai ƙarshen maganar tare da kai hannu ta ɗauki Chiken leg ɗinta, ta ɗibi fruits, ta kuma ɗaukar bottle water ɗaya,’ duk fa don saboda danish tabar wurin, Saman gadonta ta koma ta zauna, kuma still bata daina kallon shi ba, lamarin ya ɗaure ma shi kai, shi dai baisan zunubin daya aikata mata ba, sam ta tsani ganin shi, abunda bata sani ba danish mugun shakkarta yake ji, shifa har yanzu kallon monster yake yi mata, bai yarda cewa itama mutun ce kamar su, saukowa ta yi daga saman gadon ta nufi gadon batool, ta zuƙunna bakin gadon ta zura hannu a ƙarƙashi ta janyo kwandon da batool ke ajiye ragowar abincin ta, a ciki itama ta ajiye Fruits ɗinta, apple uku sai ayaba guda biyu, ta raba cinyar kazar biyu ta tura rabi aciki, rabin kuma anan zuƙunne ta cinye ta, tana kammala ci ta buɗe murfin robar ruwan tasha rabi, bayan ta gama ta rufe kwandon, ta tura shi Ciki, kafin ta miƙe hannunta ruƙe da bottle water ɗinta, ta koma saman gadonta, daga ƙasa ta ajiye bottle ɗin,
a lokacin suma sun kammala cin nasu abincin, wasu sun rage cinyar kazarsu, wasu kayan marmari suka rage, kowa dai ya ɗauki robar ruwanshi don ya ajiye zuwa anjima,
Tattara kayan abincin giants su kayi, A jere suka fuce daga cikin ɗakin, prisoners kowa Ya koma saman gadon shi, Anci an ƙoshi saura bacci, aikin su kenan Abun ba ƙaramin ɗaure wa angel kai yake yi ba, wai su kwata-kwata basa gajiya da rayuwar kulle? Daga ɗaki sai toilet, daga anci abinci kuma sai hawa gado ayi bacci, anya kuwa suna da lafiyar kwakwalwa?
Ganin da gaske bacci za suyi yasa tayi saurin cewa””Wai ku baku tunanin fita daga cikin kurkukun nan? Ko baku da ra’ayin yin rayuwar ƴan ci ne, Cikin mutane?
“Ta ya zamu sanyawa ranmu fita daga cikinsa, bayan tsohuwa ta faɗa mana cewa mutanan dake awajen kurkukun nan baza su ta6a ƙaunar mu ba, wahala zamu sha tunda bamu da kowa a ƙarshe ma akashe mu da ranmu,” yasmin ce ta bata amsa,
Rubina tace” bamu da kowa tsohuwa itace gatan mu, taya zamu yi tunanin barin kurkuku bayan babu ƙofar fita daga cikin shi? idan mun fita wurin wa zamu je”?
Guntun tsoki angel taja”daga anyi magana sai kuce tsohuwa, bansan me ta jiƙa ta baku kuka sha ba, wanda har ya gusar maku da tunanin ku, Amma ni inada tabbacin ba hakanan aka ƙyale ku ba, saboda babu mutumin da zai juri a kulle shi, tamkar yadda ake kulle dabba,”
Harara danish ya jefa mata, dama haushin ta yake ji, bai dai ce komai ba haris ne yace”yanzu kina so mu yadda dake mubar 6angaren tsohuwa? Wai ke da me kike taƙama ne? idan bakisan wacece tsohuwa ba, bari in ƙara tunasar dake, itace ta raine mu ta kuma gatanta mu, bamu da tamkarta a duniyar nan,’
Cike da takaici angel tace”dukkan ku baku da tunani, bakusan ciwon kan ku ba, Ni bansan taya zan fahimtar daku ba, gidan kurkukun nan ba alkhairi bane, gatan da kuke faɗin tsohuwa ta baku, ba gata bane gata shine abar mutun ya yi rayuwar ƴanci, amma ku an killace ku, an hana ku ganin hasken rana, acikin kurkukun ma an yi maku iyaka da shiga ko’ina, a rana sau ɗaya kuke samun abinci, an haɗa maza da mata ɗaki ɗaya suna kwana shin wannan gata ne? Kullin mu ne yawo cikin uniform kala ɗaya, wai ku baku gajiya da rayuwa a kulle ne? Kuyi tunani mana babu alkhairi atattare da kurkukun nan”
Murmushi Batool ta ɗan saki, kafin tace”angel, dama kin daina wahalar da kanki, domin kuwa indai akan tsohuwa za ki yi magana babu wanda zai ta6a fahimtar ki, its better ki yi shiru da bakin ki, yadda kika ganmu kibar mu kawai mu haka ƙaddarar tamu rayuwar take a cikin kurkuku”
Shiru angel ta ɗanyi, sai lokacin ta ƙara tabbatarwa kanta cewa An gama dasu tabbas ba hakanan tsohuwa ta ƙyale su ba, batasan wata irin huɗu ba ta yi masu ba, da har suka gaza fahimtar dai dai, taso ace sun yarda da maganarta ta hakan ne zasu haɗa hannu wurin nema ma kansu mafita, sai dai kash sunƙi bata haɗin kai,
“Ina son fita daga cikin kurkukun nan, amma bansan meyasa ba, bana jin zan iya rayuwa awajensa, a duk lokacin da nayi tunanin fita daga cikinsa sai inji ƙunci da raɗadi suna taso mun acikin zuciyata” javed ne ya yi maganar,
“Nikaina ina sha’awar wata rana in ganni awajen kurkukun nan, but i don’t know why bana jin zan iya fita daga cikinsa koda na samu damar yin hakan”
Kasa kunne angel ta yi tana sauraron su kowa yana tofa albarkacin bakinsa, banda Danish, da ya lumshe idanuwan shi tamkar mai yin bacci,
“Tsohuwa ba gaskiya take faɗa maku ba, nasan zaiyi wuya ku fahimce ni, amma kuyi tunani mana, Kowani ɗan adam Da Allah ya halitta A duniyar nan, ba daga sama ya faɗo ba, shin kun ta6a tunanin Ina iyayen ku su ke? Meyasa kuka kasance marayu? Idan iyayen ku sun rasu ina danginku su ke? Idan na baku labarin rayuwata ina da tabbacin zaku fara kwaɗayin yin rayuwa a wajen kurkukun nan, kuma zakuyi tunanin Ina iyayen ku da dangin ku su ke…….” muryar Deeja ce ta katse mata xancen nata da cewa,
“Kince kowani ɗan adam da Allah ya halitta? Waye ɗan adam ɗin kuma wanene Allahn da kike magana akai”
Mamaki ƙarara akan fuskar angel ta ɗago tana kallon deeja dake zaune can saman gadonta, fuskarta babu alamun wasa ta yi tambayar,
Speechless sam ta kashe mata baki, tsabar mamakin tambayar da Deeja ta yi mata, har wani shock taji, sai lokacin ma ta tuna dasu wa take magana, ta jima tana mamakin wannan ikon Allahn, Gaskiya yaran nan an cuci rayuwar su, basu san komai ba game da wanda ya halicce su, wato su kawai rayuwa suke yi kara zube,
“Kinyi shiru baki ce komai ba”? Deeja ce ta yi maganar, jin tayi shiru bata ce komai ba, buɗe baki angel ta yi da niyar ta bata amsar tambayarta, ba zato ba tsammani taji an daki kokwan kanta, wani irin duhu cikin idanuwanta, da sauri ta sanya hannu ta dafe kanta dake yi mata raɗaɗi muryarta na kerma ta shiga ambaton”LA’ILA HA’ILLA ANTA SUBHANAKA INNI KUNTU MINAZZALIMIN!!” gaba ɗaya suka tsareta da ido ganin ta runtse idanuwanta, Jikinta na kerma, da sauri batool da su hanna suka sauko daga saman gadajensu suke nufi gadon angel, Suna tambayarta lafiya meya faru, bata basu amsa ba, jiki ba ƙwari ta sulale saman mattress ɗinta ta kwanta,
Kallon juna su ka yi cike da tsantsar mamaki,
Hanna tace”Anya kuwa lafiya? Kodai bata jin daɗin jikin ta ne” miƙa hannu batool ta yi saman wuyan angel ta shafa shi, Sanyi taji sosai ” kallon su tayi”lafiyarta qalou, bacci ta ke yi,”
Sautin dariyar Haris suka ji, a tare suka juya suna kallon shi, hannun shi rungume da pillow,
“Dama karta farka, kowa ya huta”
Hararar shi batool ta yi, tare da kawar dakanta, Cigaba da magana Haris ya yi”Saboda ita duk kun ta shi hankalin ku, yarinyar nan fa ba son mu take yi ba, saboda bata son tsohuwa…..” kafin yakai ƙarshen maganar shi, Danish yace”haris, pls stop talking about her,’ shiru haris ya yi saboda Danish ya nuna baya son yana maganarta,
A gefen gadon angel su batool suka zazzauna suna jiran ta farka, hankalansu sam bai kwanta da irin baccin da angel ta yi ba, shiyasa suka gaza komawa saman beds ɗinsu,
Lamarin ya ɗaure masu kai, tsawon awanni tana bacci, Tun suna sanya ran zata farka har suka fara fidda rai,
“Kodai inje in faɗa ma Tsohuwa ne? Acewar Hibba, Batool tace”Mu ɗan ƙara jira mu gani, wata’ƙil kafin dare ta farka,’ Azeeza duk tafi shiga yanayi saboda ita tausayi gareta ga tsoro, muryata a sanyaye tace”Ni bana so wani abu ya samu angel, saboda ina sonta,’
Haris dake sauraron su, kamar ya miƙe yaje ya rufe su da bugu haka yake ji, don shi ya tsani ya ji suna damuwa da ita,
Saukowa javed yai daga saman gadon shi, hannyen shi Cikin Aljihun wandonshi ya nufi gadon angel, inda suke a zazzaune, a tsaye ya tsaya yana kallon su”ku kwantar da hankalin ku, zata farka ne, zaman ku anan yana ƙara takura mata”
“To kai meye ruwanka da ita’? Haris ne yai maganar, Kallon shi javed yai tare da cewa”Cos she’s my sis, i must worry about her, ” yakai ƙarshen maganar shi, tare da janye idon shi daga kan haris Ya mayar da shi kan su batool da har yanzu basu matsa daga saman gadonta ba,
Dogon tsoki Haris Yaja rai aɗan 6ace yace”daga zuwanta har ta fara canza maku tunanin ku,” Mubeen yace”Ka fa iya bakin ka, halan ka manta bugun da muka sha a hannunta ɗazu da safe, kodan kaga tana bacci ne”? Cike da zolaya yakai ƙarshen maganar yana dariya, Janyo pillow haris Yayi tare wurga ma mubeen saman fuskar shi, Cafke pillown mubeen ya yi a hannun shi still da dariya akan fuskar shi yace”Yarinyar fa akwai ƙarfi, Na lura gaba ɗaya tsoranta ku ke ji, duk masu nuna basu sonta sunfi kowa jin shakkarta,’ wannan maganar da mubeen ya yi ce tasa Danish satar kallon shi ta wutsiyar idonshi, yadda mubeen ya yi maganar kamar ya karanci abunda ke a cikin zuciyoyonsu, shifa a halin yanzu bai ƙi angel taƙi farkawa ba, saboda ko motsi ta yi sai yaji gaban shi ya faɗi, Ya tsani mutun mai tsiwa ita kuma taci ka kwakwazo, ɗazu a cikin toilet ɗinnan da ta rufe shi da faɗa har zazza6i ya ji a jikin shi, dauriya kawai ya yi wurin mayar mata da martani, don baiso ta gane yana jin shakkarta,
“Zan koya mata hankali ne, ai ba ƙyale ta nayi ba,” haris ne yayi maganar fuska a ɗaure,
Javed yace”Zaka koya mata hankali ko zata koya maka hankali? Nakasa fahimta,’ shiru haris yae bai tanka ma shi ba,
“Yarinyar nan fa duk cikin mu babu tsaranta, saboda ƙarama ce, amma sai shegen wayau ga ƙarfi, Ni har tsoro take bani in tana magana, ƙwayar idonta ma tsoro take bani, Ita sam bata jin shakkar kowa” Deeja ce ta yi maganar,
Naufal yace”Ni kuma ba ƙaramin burgeni take yi ba, yanayin rayuwarta ya banbanta da namu, tana da ƙwarin gwiwa sosai, babu tsoro acikin lamuranta,”
Naufal nakai ƙarshen maganar shi, Batool tace”Ni ina ji araina zuwanta cikin rayuwar mu, tamkar bayyanar haske ne acikin duhu, idan har zamu zauna da ita cikin lalama zata koya mana abubuwa da dama waɗanda bamu sani ba, saboda ita ta yi rayuwa A wajen kurkukun nan, muna buƙatar neman ƙarin haske dangane da rayuwar mutanan dake a wajensa”
Jinjina kai eve ta yi tare da cewa”Kalamanta na ɗazu sun tsaya mun araina, har na fara tunanin Ina iyayen mu su ke waɗanda suka haife mu? Ina dangin mu? Nafara doubting akan wani abu, Amma kafin nan, inaso angel ta farka ta bamu labarin rayuwarta, Inaso inji, kuma inaso ta faɗa mana wanene Ya halicci kowa, kuma wanene ɗan adam da ta take magana akai,”
Maganganun da su ke yi ba ƙaramin ƙona ma haris rai su ke yi ba, ganin Yarinyar ta fara cin galaba akansu, taya wata can baƙuwa zata shigo cikinsu, ta soma kokarin canza masu tunanin su’
A harzuƙe ya daka masu tsawa, har saida Danish ya firgita, don baisan Tsawa ko kaɗan, Jikin shi har kerma yake yi, idon shi akan Haris dake ta faman huci,
Nuna su ya yi da yatsan hannun shi “kada wanda ya kuskura ya ƙara magana makamanciyar wannan acikin ku, ban ta6a sanin baku da hankali ba, sai yau, taya zaku fara ɗaukar maganganun ƙaryar da take faɗa maku? Yarinyar na fa bata da cikakken hankali, batasan me take yi ba……” muryar shi a disashe yakai ƙarshen maganar idon shi akan danish daya daddafe kanshi da hannayenshi biyu, jikinshi nata kerma
Gaba ɗaya hankalinsu Ya koma akan Danish, Sun san lalurar shi ta rashin son hayaniya, idan abun ya motsa kusan burkice masu yake yi,
Sassauta murya haris Yayi”danish am really sorry, raina ne ya 6aci sam na shafa’a,” ya yi maganar yayin da yake saukowa daga saman gadonshi, ya nufi gadon danish ya zauna daga gefe yana lallashin shi,
“Pls kada wanda ya ƙara magana a cikin ku, kowa ya koma gadon shi ya kwanta” acewar javed, Miƙewa su batool su kayi kowa ya nufi gadonshi, Ya zauna,
Shima javed ɗin Ya koma nashi gadon Ya zauna, ya rage saura haris dake aikin lallashin Danish, daƙyar ya samu ya shawo kanshi, ya saki kanshi daya tallabe da hannayen shi, bai ta shi daga wurin shi ba har saida yaga ya kwanta tukunna ya miƙe ya koma nashi gadon,
Lokacin da dare Ya tsala, hasken ɗakinsu ya ɗauke gaba ɗaya, kowannansu Ya nutsa Cikin bacci, a wannan lokacin ne ta soma mutsu mutsun buɗe idanuwanta da su ka yi mata nauyi, jikinta duk ba da daɗi ga zufa,
Ambaton sunan Allah ta cigaba da yi har ta samu ta buɗe idanuwanta, duhu ko’ina saboda basu kunna fitilun ɗakin ba kafin su kwanta,
Lalla6awa ta yi ta miƙe zaune tare da jingina bayanta jikin bango, Sam ta manta abunda ya faru da ita, hatta maganganun da su ka yi kafin ta kwanta baccin duk ta manta su,
Wata irin matsiyacin yunwa ta soma ji, ga ƙishin ruwa, tunawa da ragowar naman kazarta da ta jiye yasa ta saurin saukowa daga saman gadon, cikin duhu ta dinga laluban hanya, har Allah ya kawo ta saitin inda table ɗinsu yake, hannu takai ta ruƙo handle ɗin fitila, ta kunnata tare da ɗago da ita, da sauri ta tunkari wurin gadajen su, ɗaya bayan ɗaya ta shiga haska fuskokinsu, wasu sun ƙudundune cikin bargo wasu kuma basu lullu6e jikin su ba, adai dai bakin gadon Batool ta tsaya tare da zuƙunnawa daga gefen gadon, ta zura hannu ta janyo kwandon, tana hamma ta buɗe shi, shiru ta ɗanyi tana kallon Ikon Allah, An samu wani ya gwaigwaye tsokar jikin naman sai ya bar mata ƙashin kaɗai, Apples ɗinta guda uku anciye biyu, sai ɗaya aka bar mata shima ɗayan saida aka Cinye kusan rabin shi, sam bata yarda da abunda idanuwanta suka nuna mata ba, hannu ɗaya ta sanya tana murza idanuwanta, don ta ƙara tabbatar da abunda suke gane mata,
Dagaske dai an cinye mata Abincin da ta ajiye, a ruɗe ta ruƙo hannun kwandon, tare da jijjiga shi taga dai ba komai sai wannan guntun apple ɗin da aka rage mata,
Ranta yayi bugun 6aci har wani jiri take gani acikin idanuwanta, tsabar takaici tuni idanuwanta sun cicciko da kwalla,
Ta rasa wa zata zarga acikinsu, tasan dai batool bazata iya cinye mata abinci ba, sai dai Cikin sauran ƴan uwan nasu,
Cikin shessheƙar kuka tace”Wlh tun da aka cinye mun Cinyar kaza ta saina hana kowa bacci a adaren yau,”
Runtse ido tayi tare da kwatsa wata irin gigitacciyar ƙara mai matuƙar tsiwar gaske, Har Cikin kokwan kansu, kusan atare Suka farka Sai faman zare ido suke yi, kowa yana tambayar lafiya wanene? Duk sun bi sun ruɗe, batool ce ta lura da angel dake atsaye, yaye bargon jikinta tayi tare da saukowa daga saman gadonta, ta nufi angel tana faɗin”Sister kin farka, Meya faru? Lafiyarki kuwa? a jere ta jefa mata tambayoyin, Su hanna ma duk suka shiga tambayarta lafiya meya faru,
Zuciyarta na tafarfasa tace”Uban wanene ya cinye mun tsokar namana yabar mun ƙashi? Wlh kodai ku faɗa mun ko kuma in hana kowa runtsawa acikin daren nan,’
A ruɗe Batool tace”A ina kika a jiye ne”?
“Cikin kwandon da kike ajiye ragowar abinci, anan ciki nasaka, an samu wani mara imanin ya cinye mun kaya na”
Parveen tace”Zai iyayiyuwa 6era ne ya cinye shi,”
“Dama kuna da 6eraye”? Jinjina kai parveen tayi alamar eh,”Muna dasu kuma duk in muka ajiye abinci, suna bi su cinye”
Wata irin dariya angel tasaki”wannan dai ba 6era bane ya ci shi ba, Sai dai 6eranya, ku faɗa mun wanene ya cinye mun abuna idan har kuna saman lafiya”
Guntun tsoki Haris Yaja”Wannan wani irin rainin wayau ne? Munyi maki kama da 6arayi ne? Saboda kin raina ma mutane wayau, ” yana rufe baki deeja tace”wama ya sani, ko ke ce kika cinye abunki cikin magagin bacci shi ne xaki zo ki ishi mutane da tsiwa, muna yin baccin mu mai daɗi kin katse mana shi,”
Jinjina kai angel tayi”Shikenan tun da bazaku faɗi mini wanene ya cinye mun tsokar kaza ta ba, da apple ɗina guda biyu, Zaku ga abunda zai biyo baya, Bakusan wacece ni ba, Kafin zuwana kurkukun nan, Duk wanda ya 6ata mun rai, idan har na karanta mashi Carman dudu, Bai ƙara kwana ɗaya yake mutuwa, Cikin shi zai kumbura, ya fashe daga nan shikenan tashi ta ƙare” In a serious matter ta yi maganar, da yake ta raina musu wayau, Ta riga ta gane cewa basu san komai ba, Shiyasa tace musu haka,
Kallon kallo suka soma yi a tsakaninsu, kowa da abunda yake saƙawa acikin ranshi, ruƙo hannunta batool tayi”Pls Angel kada ki karanta mana wannan abun, daga ji wani mugun abunne, nidai nasan bani naci ba, amma ina tsoro ace wani ne yaci acikin ƴan uwanmu kinga zai cutu,” Ta6e baki angel ta yi”nidai nace a faɗamun wanene yaci mun abuna, in ba haka ba zan karanta ne”
Fashewa da kuka azeeza tayi tana faɗin” Wai bazaku faɗa mata wanene ya cinye mata abinci ba,”
Shidai haris yayi zuru da ido yana jira yaga me zata yi musu,
“Angel, kiyi haƙuri kada ki karanta mana, kinga mu nan duk ƴan uwanki ne. Ke kanki ba zaki so wani ya cutu ba” acewar javed,
Girgiza kai angel ta yi”Ba kunce akwai 6eraye ba? To ai su zan karantamawa, tun da su suka cinye mun Abuna, meye naku na damuwa ne”? Shiru su kayi suna kallonta kowa yasha jinin jikin shi,
Zuƙunnawa tayi a ƙasa ta ajiye fitilar hannunta, kafin ta runtse idanuwanta, motsa lips ɗinta ta soma yi tana karanta Carman dudu, batare da sautin yana fita ba,
Cikin shessheƙar kuka Parveen tace”ba ni kaɗai na ci ba,” angel bata buɗe idanuwanta ba, taci gaba da karantawa, a gigice parveen ta duro daga saman gadonta, Ta zube agaban angel tana kuka, ta ruƙe kafafunta, gaba ɗaya ido ya dawo kan parveen, Dariya ƙunshe abakin angel ta buɗe idonta,
“An samu 6eran kenan”? Murya na kerma parveen tace”Eh ni ce,” ɗagowa ta yi da idanuwanta waɗanda suka kaɗa su kayi jawur tace
“Bani kaɗai bace, Hada yasmin da deeja, Su suka cinye maki apples, ni kuma naci naman, ki yafe mana bazamu ƙara ba”
Jinjina angel tayi”tun da ke kin bani haƙuri, Na yafe maki, amma su kuwa zasu Gane kuren su,” tana kai ƙarshen maganar, ta rufe idanuwanta kamar wata bokanya ta ɗaga hannanyenta sama, taci gaba da sambatu,
Kallon Juna deeja da yasmin su kayi, idanuwan su cike tab da kwalla, Batool tace”ku bazaku je ku bata haƙuri ba? So ku ke Cikin ku ya kumbura,”
Saukowa su kayi daga saman gadajensu, da rarrafe suka ƙarasa inda angel take zaune, Har suna haɗa baki wurin bata haƙuri, batare da ta buɗe ido ba, tace”Kun yi jinkirin tuba, Don haka zaku yi tsallan kwaɗi, duk idan ku kayi tsalle ɗaya zaku ce Aunty angel kiyi haƙuri bazamu ƙara ba, bayan haka kuma gobe idan aka kawo mana abinci, Zaku raba shi biyu kuban rabi, kun amince? Murya na kerma suka ce Eh,
Fuska a ɗaure ta buɗe idanuwanta, tana kallon su”nan gaba idan kuka ƙara satar mun abinci na, kada kuyi tsammanin zan yafe maku, ” atare suka ce bazamu ƙara ba,
Gyaɗa kai tayi tare dakai hannu ta ɗauki filitar data ajiye a ƙasa, ta yunkura ta miƙe tsaye”Oya ku fara tsallan kwaɗi, “
“Ae bamu san yadda ake yi ba” deeja ce ta yi maganar, kallon su tayi ganin yadda jikinsu keta kerma, sai taji tausayinsu ya kamata,
Ta6e baki ta ɗanyi”Kada ku ƙara na yafe maku, Abunda kuka aikata baida kyau, domin kuwa sata ce, kuma haramun ne mutun ya ɗauki abunda ba na shi ba, babu daɗi ni yanzu baku kyauta mun ba, yunwa nake ji sosai, banci haƙƙin wani ba, nawa ne na ajiye saboda gudun yunwa amma kunbi kun cinye mun kaya ne, wannan ba adalci bane, idan naku aka ɗauka zaku ji daɗi” girgiza mata kai su kayi alamar a’a,
“Kada ku ƙara, ko ba nawa ba kada ku ƙara ɗaukar abunda ba naku ba,” amsa mata su kayi da toh,
“Ina danish ya ke”? Haris ne ya yi tambayar ganin gadon shi wayam babu kowa” sai lokacin su ka lura da babu danish A cikin shi, Nan fa hankulansu suka ta shi,
“Wai dama tun ɗazu Danish baya acikin mu? Amma kafin mu kwanta danish yana atare damu” Rubina ce ta yi maganar fuskarta da alamun ruɗu,
Da sauri Javed Ya sauko daga saman gadon shi, yaje saman table ya ɗauki fitila ɗaya, batool ma ta ɗauki ɗayar fitilar duk suka kunna su don ɗakin ya yi haske,
“Ku duba ko’ina, Allah yasa dai ba wani abunne ya faru da shi ba,” haris ne yai maganar, gaba ɗaya sauran dake asaman gadajen su duk sun sauko, sai zagaye cikin ɗakin suke yi suna neman Danish, Saƙo da lungu ko’ina suka shiga dubawa amma babu shi, lamarin yayi matuƙar ɗaure masu kai,
“Yakamata mu sanar ma tsohuwa halin da ake ciku” Acewar Mubeen,
Deeja tace”bari naje na kirata,” tana kokarin zuwa taje ta sanar da ita, Batool tayi saurin cewa”ku dakata” gaba ɗaya suka Juyo suna kallonta,
Haris yace”kin gano inda ya ke ne?
Girgiza kai tayi”a’a, ” kafin ta kalli angel da ke a tsaye tace”lokacin da kika saki ƙarar nan, baki ga gifcin mutun ba”?
Shiru angel tayi tana ƙoƙarin tariyo abunda ya faru,
“Gaskiya ni banga gifcin kowa ba, amma meyasa kika tambaye ni”?
“Saboda danish baya son tsawa, zai iyayiyuwa lokacin da kika saki ƙarar nan. Har muka farka daga bacci, a wannan lokacin danish ya rikice ya sauko daga saman gadon shi ya faɗa wani wurin”
Sakin baki angel tayi galala tana kallon batool, da mamaki akan fuskarta tace”saboda kawai nayi ihu sai ya 6ace a neme shi arasa, ko dai yana da ta6in hankali ne”? Tayi tambayar tana kallon batool,
Kafin batool ta bata amsa, Haris yace “yanzu ba lokacin yin magana bane, bamusan awani hali ɗan uwanmu yake ciki ba, yamakata muyi hanzarin nemo shi”
Ya kai ƙarshen maganar, tare da kai hannu ya kar6e fitilar dake a hannun batool, ya yi gaba suma suka bi bayan shi,
Ko’ina kaf sai da suka duba, Basu ga danish ba, a gajiye suka koma saman gadajensu, kowa ya zauna cike da jimamin rashin ganin danish,
Deeja tace”ni dai bari naje na kira tsohuwa,” haris ya dakatar da ita” dare yayi sosai, kada mu takura mata, mu jira zuwa gobe da safe, nasan kafin lokacin duk inda yaje zai dawo ne”
Angel dai duk ta rasa sukuni, aranta tace No wonder dama ni nasani, ba cikakken hankali gare shi ba, “
Bacci ne ya fara ɗaukar wasu daga Cikin su, Mutun uku ne suka gaza runtsawa, Haris da Batool sai Angel, kuma dukansu idanuwansu acike suke da bacci,
Fitsari ne ya matse ta, da sauri ta sauko daga saman gadonta, hannunta ruƙe da fitila, ta nufi first door ta toilets ɗinsu,
Bayan ta buɗe ƙopar ta shiga ɗaya daga cikin toilet ɗin, ajiye fitilar ta yi a ƙasa, ta sanya hannu ta tu6e wandon jikinta ta zuƙunna tana fitsari, har wani lumshe ido take yi, saboda daɗin da taji, sai da ta kammala yin fitsarin tayi tsarki, tana ƙoƙarin mayar da wandonta, taji mutsu mutsun mutun, Hankalin ta yayi matuƙar ta shi, Kasa juyawa tayi la66anta sai kerma su ke yi, tsananin tsoro ne bayyane acikin idanuwanta, Ta wutsiyar idonta take hangen shi biji biji, koma wanene dai a zaune yake, ya jingina bayan shi jikin bango, Gefen tukunyar fulawar dake ajiye cikin toilet ɗin su,
Tafi ƙarfin minti goma a tsaye batare da ta juya ba, zuciyarta a cunkushe da tunanin wanene Acikin toilet ɗin? Mutun ko Aljan? Kenan koma wanene ya gama ganin budurcin ta,” ta ambaci hakan acikin zuciyarta, tunma kafin taga wanene Ranta ya 6aci ta harzuƙa sosai, ko aljani ne wannan ɗan tahalikin sai ya ɗanɗani kuɗarsa,
Daurewa ta yi ta cije, a wani slow ta ɗan juya tana kallon wurin,
Har saida ta zabura lokacin da tayi arba da Danish, a matuƙar ruɗe take kallon shi,
Ya ƙanƙame Jikin shi da ke ta kerma, ya saki dogayen ƙafafuwanshi ƙasa, ya jingina bayan shi jikin bango, Gaba ɗaya sumar kanshi ta rufe mashi fuskarshi,
Runtse ido ta ɗanyi tare da biting lower lip ɗinta, Har ta kai hannu zata rarumi bucket ta kwaɗa ma shi akai, sai kuma ta fasa ganin da alama bai ganin ta, saboda sumar kanshi data lullu6e eyes ɗinshi,
cikin sanɗa ta soma tafiya tana tunkararshi, a saitin inda yake zaune ta zuƙunna, tana kallon shi,
Abunda ya faru lokacin da angel takwatsa ƙarar nan, ya farka a firgice ya duro daga saman gadonshi tamkar walƙiya yabar cikin ɗakin saboda tsabar rikitar da ya yi ashe cikin toilet ya faɗo,
Tagumi ta zabga tana kallon ikon Allah, ta sauke ajiyar zuciya yafi sau uku, da ace yau ta kama shi yana kallonta lokacin da take Cikin yin fitsarin nan, da kuwa ya gane kuransa, Allah ne ya taimake shi saboda sam baya a hayyacinsa, baisan ma ta shigo cikin toilet ɗin ba,
Miƙa hannu tayi da niyar ta janye sumar dake akan fuskarshi, sai kuma ta fasa ta miƙe, taje ta ɗauki fitilarta, kafin ta kama hanyar fita daga cikin toilet ɗin, Bayan ta fito ta nufi cikin ɗakin kamar yadda ta tafi tabar batool da haris xaune saman beds ɗinsu a haka ta same su,
Gefen gadon batool ta tsaya tare da ɗan ranƙwafawa saitin kunnanta tace”Danish yana a toilet, ki faɗa ma haris kuje ku ɗauko shi, Amma kada ki ce ni na faɗa maki”
Buɗe ido batool tayi jin maganar Angel a cikin kunnanta”are u serious danish yana acikin toilet”
“Eh, yanzu na ganshi aciki, amma kamar baya a hayyacinsa”
Jiki na rawa Batool ta sauko daga saman gadonta, Sai da tafara gaya ma Haris cewa Danish Yana acikin toilet, tukunna tayi gaba shima yabi bayanta,
Ajiyar zuciya angel ta sauke, tare da ajiye fitilar ƙasan gadonta, Ta haura daman gadon ta kwanta, tana jiran taga sun shigo da shi, Zuciyarta a cike take da tunanin meke damun shi? yanayin abubuwan da yake yi kamar akwai wani abu dake damun shi, ‘ can kuma saita ja guntun tsoki aranta tace”Ko ina ruwana da shi, matsalar shi ce,”
Jin takun tafiyarsu yasa ta ɗan saci kallonsu, Batool ce da haris sun ruƙoshi daƙyar yake tafiya, A saman gadonshi suka sake shi, ya haye saman mattress ɗinshi ya kwanta, Haris ya janyo mashi duvet ɗinsa ya lullu6a mashi har zuwa chest ɗinsa,
Kafin suka koma saman beds ɗinsu domin yin bacci,
Juyowa tayi da niyar ta saci kallon shi, karaf suka haɗa ido da shi, Harara ta jefa mashi, tare da juya ma shi baya ta kalli 6angaren hagu,
Tunani ta shiga yi acikin zuciyarta, anya kuwa ɗazu bai kalle ta ba, lokacin da take yin fitsarin nan ba? Idan kuwa haka ne tabbas ya gama da ita, shikenan Ya gama ganin tsiraicinta, ranta ne ya bata cewa ta ƙara juya taga idan ya yi bacci, a hankali ta sake waiwayowa, karaf suka haɗa ido da shi, Ɗaure mashi fuska tayi tare da zare ma shi gray eyes ɗinta”Kallon ya isa, Ka juya ka kalli can mana, bakasan ba’a son ana bacci ta 6angaren Hagu ba,”
Yadda kasan tayi magana da gunki, Ko motsa lips ɗinsa, baiyi ba balle ma tayi tunanin zai tanka mata,
“Can’t u hear me”? a ɗan tsawace tayi ma shi maganar, jin yaƙi tanka mata kuma yaƙi daina kallon nata, yasa ta ruƙo pillownta, Ta daddage ta jefa ma shi saman fuskarshi, Salon Jan faɗa,
A hankali ya ɗaura dogayen yatsun hannunshi saman pillown ya janye shi daga kan fuskarshi, Ya ɗaura shi saman nashi pillow ɗin ya haɗa biyu kenan, ya ɗaura kan shi asama,
Rai a6ace tace”ka dawo mun da pillow ɗina, ko ranka ya 6aci,” banza ya yi mata,
“Magana fa nake maka”
Sai lokacin ya ɗan buɗe baki yace”Zo ki ɗauka, ae bani na kawo shi nan ba” shiru ta yi tana cigaba da kallon shi, ganin ta tsare shi da ido, yasa shi juya mata ƙeya,
Cike da takaici ta koma ta kwanta, tare da jan bargo ta lullu6e fuskarta, sai da tayi addu’a tukunna ta samu bacci ya yi awon gaba da ita,
In the morning,
Kasancewar Jiya basu samu isasshen bacci ba, Babu wanda ya farka,
Cikin bacci angel ta yi Kakkauran Juyi da niyar ta gyara kwanciyarta, kwatsam idanuwanta suka sauka akan fuskar tsohuwa dake a tsaye bakin gadon ta, hannunta na ruƙe da sanda, mamaki ne ya kamata har ta soma tunanin kodai mafarki take yi, ƙura mata ta yi tana kallonta, itama kuma tsohuwar ita take kallon,
Ƙasa ƙasa da murya angel ta ambaci”A’uzu billahi minasshaiɗanin Rajim”
Fuskar tsohuwa ɗauke da murmushi tace”Ni ce shaiɗanin”?
Bata amsa mata tambayarta ba, har saida ta yunƙura ta miƙe zaune ta jingina bayanta jikin bango, tukunna tace “Ai kin wuce nan, idan akwai na gaba da shaiɗan to ke ce tsohuwa”
Baki asake tsohuwa ke kallonta,
“Meyasa kika zo kika tsaya a bakin gado na”? Ta yi tambayar fuska a ɗaure take kallonta,
“Zuwa nayi don in tashe ku daga bacci, naga har gari ya waye baku farka ba……” tunkan takai ƙarshen maganarta, Angel ta katse ta da cewa”Ƙarya kike yi, Idan tashin mu kika zo yi daga bacci why baki bi kowani gado ba, Sai kika zo kan gadona kika tsaya kina kallo na, wlh kiji tsoron Allah, tsofe tsofe dake kina ƙarya,” ta ƙarasa maganar tana sakar mata harara,
Jinjina kai tsohuwa tayi”Ke wai baki jin tsoro na? Meyasa baki jin shakkar yi mini magana ne?
“Inji tsorin ki akan me? Ni da nake neman hanyar da zan tarwatsa shirin ku taya kike tunanin zan ji tsorin ki? Idan ma kina tunanin hakan acikin ranki to ki daina, suma waɗanda suke jin shakkar taki don kin juya masu tunaninsu ne, Amma asannu zan dawo da su Cikin hayyacin su, “
Shiru tsohuwa tayi tana kallonta batare data ce komai ba.
Angel taci gaba da cewa” ina zargin jiya ke ce kika kwaɗe mun kaina da sandar hannun ki, Saboda kinga ina ƙoƙarin kwance shirinki, wato so ki kayi nima ki ɗaure mun kaina ta yadda zan manta da komai, tabbas kinso ki yi nasara sai dai Allah bai baki ikon yin hakan ba, farkawar dana yi daga bacci komai dana manta sai da ya dawo cikin kaina, Kuma bazan fasa faɗa masu Allah ba, har sai na fargar da su,
“Taya kenan zaki iya aiwatar da hakan? Ko kina tunanin zaki iya sarrafa tunaninsu ne? Yaran da ni na raine su da hannu na, na gatanta su, tun da suke basu ta6a shan wahalar rayuwa ba, komai suna samu ba’a abunda ban yi masu ba, matsayin uwa nake a wurinsu, a haka kike tunanin zasu ji maganarki fiye da tawa”? Tsohuce ta yi maganar yayin da take sakin wani irin bazawarin murmushi,
Wani irin kallon rainin wayau angel tayi mata”Wlh tun da nake arayuwata ban ta6a ganin Muguwar maca ba, Azzaluma kuma macuciya irin ki ba!”
Yadda tayi magana batare da jin ɗar ba, ya yi matuƙar girgiza tsohuwa,
“Wai ke baki jin tsoron Allah? Ki tuna fa komai kike yi Allah yana kallon ki, har kina da bakin da zakice kin basu gata? Kin raine su? Kuma har kike kiran kanki a matsayin uwarsu? Tirr wlh ji nake kamar inyi kakin majina in watsa maki akan fuskarki saboda natsane ki, Wlh nafi son mutuwa ta so dubu dake!” Zuba mata ido tsohuwa tayi tana kallon Ikon Allah,
Sassauta murya angel tayi Idanuwanta cike tab da ƙwalla tace”Kin cuci rayuwarsu, kin gama dasu, ni banmasan ya zan kwatanta irin cin zalinsu da ki kayi ba, kuma ga dukkan alamu kin sani kike take sani, dan baki yi kama da jahila ba, Kawai salon tsabar mugunta ne, Yaran nan ko nonon raƙuma suka sha iya abunda zasu yi kenan, Ga sunan Wasu kala da su they don’t even know anything about the one who created them because you never told them, cos of your wickedness Kin barsu a cikin duhu, sun zo duniya a wahalce kuma zasu koma a wahalce, Idan yau ɗayansu ya faɗi ya mutu menene makomarshi dan Allah meyasa ki ka yi musu haka? Meyasa?……….” kasa ƙarasa maganar angel tayi saboda wani irin ƙuntataccen kuka daya kubce mata, kuka sosai ta fashe da shi,
Tsohuwa kuwa ta kafe ta da waɗannan Kwala kwalan idanuwanta nata, masu kama dana ƴan ƙwaya,
Cigaba da magana ta yi”Idan wani zunubi suka aikata maki, bai kamata ki ɗauki fansa ta wannan hanyar ba, balle ma nasan basu aikata maki komai ba, To kodai cikin danginsu wani ya yi maki badaidai ba, shiyasa kike ɗaukar fansa akansu” ta yi tambayar idanuwanta jawur hawaye duk sun wanke fuskarta,
Tun da suka soma magana babu wanda ya farka daga cikin masu yin baccin, tamkar wasu matattu,
Jinjina kai angel tayi”dama nasani bazaki bani amsar tambayata ba, sai dai ki kafe ni da ido kina kallo,” ta yi maganar cikin sanyin murya tare da sanya hannunta da dama tana share hawayen dake silalowa,
Kafin ta ɗaura da cewa”Allah ba azzalimin bawansa bane, Allah zai bi masu haƙƙinsu, inda na gode ma Allah, Mutuwa tana akan kowa, Walau mutun walau aljan, akwai kwanciyar ƙabari akwai kuma hisabi, Ina fata duk kin shirya ma wannan……..” Muryar Batool ce ta katse ta ta hanyar kiran sunanta”ANGEL” koda tsohuwa taji muryar batool, Sai ta juya da sauri tana dogara sanda ta nufi ƙopar shiga ɗakinta,
Har ta kusa shiga ciki muryar angel ta sake katse ta da cewa”Baki san Su ji me muke tattaunawa ne shiyasa kika nemi hanyar guduwa? Allah dai yana a madakata yana jiranmu, kuma inaso ki sani Zanyi amfani da ilmin da nake da shi, da kaifin basirar da nake da shi wurin Sarrafa tunaninsu, Kuma zansa su kar6i addinin musulunci, after that I will fight for our freedom, because no one deserves to live a locked up life!
Tsawon mintuna tsohuwa bata motsa ba, kuma bata juyo ta kalli inda angel take ba, can dai taci gaba da dogara sandar, har samu ta shige cikin ɗakinta taja ƙopa ta rufe,
Fashewa da wani sabon kukan angel ta yi, da sauri batool ta sauko daga saman gadonta, tazo gaban gadon angel ta zauna daga gefenta,
Muryarta aruɗe take faɗin”Sister what’s wrong with u? and why are u crying”? Kallonta angel tayi da idanuwanta da suka rune, muryarta a karye tace”Batool ina kuka ne saboda ku”
“But why”?
“it will be hard for you to understand me, even if i tell you, so just forget about it,” cikin shessheƙar kuka ta yi maganar,
Dafa shoulder ɗinta batool tayi”Pls ki faɗa mun meyasa kike kuka sabo da mu”?
“Baki ga tsohuwa ba”? Angel ce ta yi mata tambayar, girgixa kai batool ta yi”Banganta ba, tazo ne? Ita ce ta saki kuka”?
Girgiza kai tayi”A’a, Mubar maganar, inaso zan shiga toilet,” daga haka ta zuro da ƙafarta daga saman gadon ta sauko, ta nufi toilet ɗinsu, Ta tafi tabar batool da tunanin dalilin kukanta, meyasa ta ke yin kuka saboda mu? ta yi ma kanta tambayar da bata da amsarta,
Tunda ta shiga Cikin toilet ɗin taci burki ta tsaya Idonta na akan Window nan dake a jikin bango, wadda ta ƙwallafa ma rai akan son Fasa glass ɗin jikinta, don ta samu damar dura wa Cikin kurkukun.
Hannu tasa ta share hawayen dake akan fuskarta, Cikin zuciyarta ta soma yin magana”rana ta farko dana tsinci kaina cikin gidan kurkukun nan, A ƙagare nake dana nemi hanyar da zan fita daga Cikinsa, Amma Ayanzu bana sha’awar Barinsa batare da waɗannan bayin Allahn ba, Kuma batare da ƙwaƙƙwarar hujja da zan yin amfani ba, wurin ganin na tarwatsa duk wani shirinsu, Zanbi komai asannu domin Cimma nasara, Bi’iznillahi,’
Angel yarinya ce mai kaifin basira Fiye da tunanin mai tunani, wayan dake gare ta yafi ƙarfin shekarunta, wasu ɗabi’un nata da halayanta sam ba irin na yara bane, she’s genius”
Lokacin da ta fito daga wankan, A tsaye ta samu Batool tana jiran na ciki ya fito ta samu ta shiga itama tayi wankan” Kallon juna su ka yi,
Murmushi Batool ta sakar mata tare da cewa”tun ɗazu nake jira na ciki ya fito in samu nima in shiga in yi wanka,
Angel tace”Wani ya shiga sauran toilets ɗinne”?
Jinjina kai batool tayi”Eh, Hanna ce ta shiga ɗaya, ɗayan kuma Danish ne da deeja suka shiga Ciki,” Har wata zabura angel ta yi jin abunda batool tace”What! danish da deeja ne suka shiga atare? Saboda me”?
Fuskar batool asake tace”Dama idan babu wuri kuma uziri ya kama mu, mutun biyu suna amfani da toilet ɗaya…….”
tunkafin Batool takai ƙarshen maganarta, Angel ta yi gaba zuwa ƙopar sauran makewayin, Rai a matuƙar 6ace takai hannu tana Bubbuga ƙofofin tamkar zata Fasa su,
“zaku fito ko saina 6alle ƙopar”? Tana huci ta yi maganar, Bama tasan wanne suke a ciki ba,
Kusan atare suka buɗe ƙofofin toilets ɗin, na biyun Hanna ce ta leƙo kai, Na ƙarshen ne Deeja da danish suka fito, wani matsiyacin kallo Angel ta shiga binsu da shi from head to toe, hannun shi na a ruƙe da rigarshi, ita kuma iya rigarce har guiwarta, wandonta na hannunta,
“lafiya kike bubbuga mana ƙopa”? Fuska aɗaure deeja ta yi mata tambayar”
Dakuwa angel ta sakar mata”Ungo nan, Ku dukanku ku kar6a ku raba,”
Kallon juna su ka yi don basu fahimci me take nufi ba, Runtse ido tayi zuciyarta na tafarfasa ta ambaci”Allahu ajirni fil musibati……
Batool sai faman tamyarta take yi lafiya? Meya faru”? Ware idanuwanta ta yi akan fuskar deeja da ta danish, sae faman lumshe eyes ɗin shi yake yi, da alama bacci bai ishe shi ba, Sam tarasa ta ina zata fara, wato su awurinsu ba laifi bane idan mace da namiji sun shiga toilet ɗaya, tun zuwanta bata ta6a sanin suna yin hakan ba, Sai yau da take ji awurin batool ta kuma gani da idanuwanta,
Cizon lips ɗinta tayi tamkar zata fasa su, Cikin fusata ta nuna Deeja da hannu”Zoki wuce, Ki jira idan ya gama ki shiga” maƙe kafaɗa deeja tayi”babu inda zanja, meye naki aciki?
Wata irin gigitacciyar tsawa angel ta daka mata, Saboda tsabar ruɗi a firgice danish Ya koma Cikin toilet din,”
Da gudu Sauran Ƴan uwansu dake acikin ɗakin suka faɗo Toilet area ɗin, Haris da su aziza,
“Meke faruwa ne”? Javed ne yae tambayar, Batool tace”Nima bansani ba, ranta ya 6aci ne saboda na faɗa mata cewa idan uziri ya kama mu kuma babu wuri mutun biyu suna shiga toilet ɗaya shine take fushi,”
Harara haris ya watsa mata tare da cewa”To ke meye naki aciki da har zaki nuna 6acin ranki akai”?
Matsawa angel tayi Saitin inda haris yake a tsaye, Kafin ta soma magana atsanake,
“Saboda hakan bai dace ba, Koda kuwa Namiji da namiji ne su shiga toilet ɗaya balle kuma Mace da namiji, bazan bari ana aikata 6arna batare dana hana ba, don haka daga rana irin ta yau, idan har na ƙara kama mutun biyu acikin toilet ɗaya, Saina Karanta ma shi charman dudu Cikin shi ya kumbura ya mutu kowa ya huta”
Jin wannan maganar ta angel yasa hankalin kowannansu ya tashi, musamman deeeja tuni idanuwanta sun cicciko tan da ƙwalla,
“Ya kike so muyi idan uziri ya kama mu, a lokaci ɗaya”? Hanna ce tayi mata tambayar,
“Sai ku matse koma menene ku ke ji, idan na ciki suka kammala suka fito sai mutun ya shiga”
“Ammaaaa…….”kasa ƙarasa maganar haris yayi ganin tana nannaɗe hannun rigarta alamar za ta yi dambe,
“Abi Umarni na azauna lafiya, Shine kawai idan kuma mutun yace zaiyi mun gardama, yasan me zai biyo baya,”
Gaba ɗaya duk suka sha jinin jikinsu, juyawa tayi tare da kallon deeja”Ke kuma Munafuka, zoki wuce ki jira idan ya kammala ki shiga, ni dama sam ban yarda dake ba, da wasu idanuwanki tubarkalla kamar na kwartan mazuru, idan shi yana da ta6in hankali ai ke da hankalinki, Sullu6iyo kawai, zaki wuce kosaina Zubar maki da haƙoran gaba”? Jiki na rawa deeja ta ƙarasa fitowa daga cikin toilet ɗin Taja ƙopar ta rufe,
Kallon sauran ta yi”Kowa Ya kama harkar gabansa, kuma Allah yasa wani yayi gulmata acikin ku, Aljanata kamila zata faɗa mun ne, daga nan ni kuma zan tofa ma mutun charman dudu” takai ƙarshen maganarta tare da sa kai ta wuce su tamkar damisa, Ta nufi Cikin ɗakin sai da ta shiga ta zauna gefen gadonta, Taci gaba da tiƙar dariya, can kuma ta dakata da yin dariyar hawaye suka soma shararowa daga cikin idanuwanta,
Hannu biyu tasa ta dafe kanta, wani irin tsananin tausayinsu take ji, har cikin ranta take jin tsananin sonsu da ƙaunarsu, a halin yanzu babu wanda bata so acikinsu, saboda tausayinsu da take ji, ashirye take data taimaka masu wurin gyara rayuwarsu,
Jin motsin shigowar su Cikin ɗakin Yasa ta yi saurin share hawayen dake akan fuskarta, ta kishingiɗa saman gadonta,
A jere suka shigo kowa sai satar kallon Angel yake yi, cike da jin tsoronta, Ko zama ba suyi ba, Giants suka turo ƙopa suka shigo Hannunsu ruƙe da kayan breakfast ɗinsu, ba ƙaramin daɗi angel taji ba dama daren Jiya da wata irin matsiyaciyar yunwa ta kwana,
Bayan sun ajiye Masu farantan, kamar kullum Jiki na rawa suka Nufi saman Carpet ɗin kowa yayi zaman Cin tuwo, Suka zagaye trays ɗin,
Sai da duk suka hallara, Hada danish wanda tunda ya zauna Jikin shi keta kerma sam babu natsuwa attare da shi, Gaba ɗaya tsawar da angel ta daka masu ɗazu ta gama gigita shi,
Tun da suka fara Cin abinci, Wurin ya yi tsit baka jin sautin komai saina taunar abincin da suke yi, ganin nata ya kusa ƙarewa yasa ta fara tsantsani, can data lura danish ba wani cin abuncin yake yi ba, tsakurarsa kawai yake yi kamar baisan ci, da yake suna Fuskantar Juna, ta faki idon sauran ƴan uwan nasu, tayi musayar plate dana danish, ko da taga yana kallonta, saita zazzare mashi ido don kar yace zai anshe kayan shi,’ lamarin yayi matuƙar ɗaure ma shi kai, yana ji yana gani tayi mashi musayar plate, ta ajiye ma shi nata data kusa Cunye, na shi kuwa a cike yake da abinci, bai dai ce komai ba, Yaci gaba da cin nata abincin data tura mashi,
Bayan sun kammala, Giants suka tafi da kayan abincin, Ganin Kowa ya nufi gado zai kwanta yasa tayi saurin cewa”Ku dakata” Tsayawa su ka yi tare da juyowa suna kallonta,
“From now on, when you finish eating food, no one will lie down and sleep, you have to exercise, doka ta ce duk wanda yaƙi bi kuma yasan me zai biyo baya,’
Natsuwa su kayi suna sauraronta, Haris ne yai kokarin cewa”Saboda me”?
“Saboda lalacin ku yayi yawa, idan kuna motsa Jiki zaku yi ƙarfi, “
“So kike kiyi iko damu”? Kafin ta bashi amsa aziza tayi saurin cewa”pls haris kayi shiru, kada ta karanta mana charman dudu, nidai zanyi abunda kike so angel,”
Murmushin gefen fuska angel tasaki tare da kallon su batool tace”what about u guys? Zaku yi ko kuwa”? Har suna haɗa baki wurin cewa”eh zamuyi komai kikeso” Kallon haris tayi”kaima dole kayi idan har kana son zaman lafiya, idan ba hakan ba ta kanka zan fara aiwatar da aikina, tare da aljanata kamila,”
Haɗe girarsa yai fuska a tur6une yace”Ae bance bazan yi ba”
Ƙumshe dariya tayi abakinta, daƙyar ta samu ta basar da dariyar, ta ɗaure fuska tana hura hanci,
“Sister ya ake yi toh baki faɗa mana yadda zamu motsa jikin ba”
“U will start running from wall to wall, untill i command you to stop, Idan aka kammala sai ayi Jumping,”
Amsa mata su ka yi da toh, jikin bango suka koma suka tsaya a jere, Kowa ya naɗe hannun rigarshi,
Komawa tayi daga bakin gadonta, ta zauna tare da ɗaura ƙafa ɗaya bisa ɗaya, Cike da bada Umarni Tace”Idan Na ƙirga uku Sai ku fara” su ka amsa mata”Toh”
“1,2,3, Oya start” Da gudun gaske suka tafi Bayin Allah, Idan suka kai karshen bango sai su dawo sai su koma, har saida su ka yi kusan sau talatin tukunna ta basu hutu, zuƙunnawa su kayi a ƙasa, zufa ta ko’ina ajikinsu, Musamman danish kamar an tsamo shi daga Cikin ruwa, sae nishi suke yi,
“Lokacin yin jumping ya yi, Maza kowa ya miƙe afara tsalle sau talatin kowa zaiyi duk wanda ya kammala sai yaje toilet ya watsa ruwa,” amsa mata su ka yi da toh, ta tsaresu da ido har saida kowa ya kammala tsallan nashi, sannan ta ƙyale su tace kowa ya watsa ruwa azo ayi fira,
Anan ta zauna tana jiransu, Bayan sun kammala, Jiki amace suka dawo cikin ɗakin Kowa Ya zauna saman gadon shi,
“Yau kin bamu wahala sister, amma naji daɗin Jiki na” batool ce ta yi maganar, Haris da deeeja sunfi kowa Jin haushin angel, saboda ta sanyasu aikin wahala, danish kuwa tuni bacci ya yi awon gaba da shi, sam basu saba da wahala ba,
Kallon su ta yi ɗaya bayan ɗaya tun daga kan danish dake bacci har zuwa sauran dake ta faman yin gyangyaɗi,
Gyaran murya ta yi masu gaba ɗaya hankalinsu ya dawo kanta,
” Jiya kamar Kunyi mun wata tambaya ko’? har suna haɗa baki wurin cewa”tambaya akan me kanan”? Ta gefe ta kalle su “Kun manta? Ku tuna kun tambaye ni wani abu jiya,”
“Eh, muna so Ki bamu labarin rayuwarki,” azeeza ce ta yi maganar,
“Gobe zan baku labarin rayuwata, Yau inaso Mu tattauna dangane da addini ne, Kallon juna su ka yi kafin suka dawo da hankalinsu kanta,
“Addini kuma? Menene ma’anar hakan”? Da ruɗi akan fuskar hibba ta yi mata tambayar,
Tana kokarin buɗe baki taci gaba da magana, Danish dake bacci ya kwatsa wata irin razananniyar Ƙara mai firgitarwa, ” gaba ɗaya Hankalinsu Ya koma kanshi,
A zubure ya miƙe zaune Ya sanya hannayenshi Biyu ya daddafe kanshi, yaci gaba da fasa gigitacciyar ƙara, Da gudun gaske su haris suka sauko daga saman gadajensu. suka nufi gadon danish, Kowa ya shiga Lallashin shi suna bashi baki,
Angel kuwa sakin baki tayi tana kallon ikon Allah. lokaci ɗaya ranta ya bata cewar tabbas Danish ba shi kaɗai bane, Meyasa sai lokacin da take ƙoƙarin yin magana kan addini zai farka yana fasa masu ƙara? Da alama anyi hakan ne don a ɗauke masu hankalinsu daga kanta, gashi yanzu gaba ɗaya sun rasa samun natsuwa sun duƙufa suna lallashin shi,
Wani irin wahalallan murmushi angel tasaki tana kallon ikon Allah, wato da tsiya dai sai an dakatar da ita, jiya an kwaɗe mata kai da sanda yau kuma ta 6angaren danish aka biyo mata,
“Danish Pls can u talk to me? kana ganin fuskokin mu? Meya faru dakai? Atare suke jefa mashi tambayoyin nan, Angel ta kasa kunne tana sauraronsu,
“Danish ka yi mun magana meke damunka? haris ne yae tambayar yana shafa dogon wuyanshi, Sae faman kerma jikin shi yake yi, ga wata irin zufa dake tsastsafowa daga Cikin sumar kanshi, ya runtse idanuwanshi sosai, duk ya ciccije lips ɗinsa,
Zurfin tunani ta shiga yi, shin wata hanya zata 6ullo masu, tun da nan an toshe ta, sai yanzu ta ƙara yarda cewa akwai wata maƙarƙashiya, bakomai take tunawa ba face Wani American film da ta ta6a kallo na Magicians, a gidan aunty aneelerh, A cikin Film ɗin matsafa ne suke canza ma mutun tunaninshi su sarrafa shi, ko su sanya mashi tsafi a jikin shi, ko kuma suyi amfani da shi,’ Jiya daga za ta yi magana an kwaɗe mata kai, kuma bata ga kowa ba, hakanan ta ke zargin tsohuwace kuma ga dukkan alamu zarginta ya tabbata tsohuwarce, sanan meyasa Basa son duk wani abu daya shafi Addini? A lokacin da ta kalli film ɗin ta ɗan shiga ruɗu harta tambayi aneelerh,
“Su matsafan ba’a iya yin maganinsu”? aneelerh tace”Allah shi ne maganinsu, idan yaso duk wannan 6acewar da suke yi sai kiga an kama su har an ɗauki mataki kansu, shiyasa ake so mutun ya kiyaye kuma ya dage da neman tsari awurin Allah, saboda su mutanene masu hatsarin gaske, ta kowace hanya zasu iya 6ullo maka,” aneelerh tayi mata bayani akansu sosai, Natsuwa tayi tana bin ko’ina na ɗakinsu da kallo, tana ji acan ƙasan Zuciyarta kamar ta manta da wani abu, wanda ta gaza tunawa acikin kwakwalwarta, Aranta tana ji kamar ta ta6a kasance acikin gidan kurkukun ƙaddara, tsayar da idanuwanta ta yi akan red carpet ɗin da suke zama Su ci abinci kanshi, tunawa tayi da maganar aneelerh a inda tace”ɗaya daga Cikin alamomin matsafa, shi ne launin Ja, suna sanya jajayen kaya ko kuma A gidansu suna yawan amfani da jan abu kamar labule haka da sauransu,
Jinjina kai angel tayi tare da cewa”Tsohuwa tana sanya jajayen kayan, Kuma carpet ɗin ɗakin mu Shima ja ne, kuma duk in aka kawo mana abinci, a saman trays ɗin ana sanya janƙyalle a rufe shi, Menene ma’anar launin jan nan na gidan kurkukun ƙaddara? su Giants suna sanya Baƙaƙen kaya shima launin baƙi bako da yaushe yake kasancewa abu mai kyau ba, dole nayi kokari wurin gano ma’anar waɗannan kalolin guda biyu Black and Red, kuma dole Nayi bincike akan lalurar dake damun danish domin kuwa wannan ciwon nashi Ba Misophonia bace, Kirkirarta a ka yi domin shi kawai,
Hankalin angel fa yaƙi kwanciya, Saima ƙara ta shi da yake yi, Babban abunda take ji ma tsoro, Abunda take hasashe ya zamo gaskiya, saboda taji ance matsafa idan suka ɗauki mutun suna amfani da shi ne, Ko su cire sassan jikinshi, Ko su ɗibi jinin jikin shi, idan kuwa har hakane, To kuwa bata ga ta zama ba, duk da tana kokwanto akan hakan saboda su Batool sun faɗa mata cewa ba’a ta6a cutar da su ba, Kuma suna samun abinci, Matsafa ina suka ga lokacin ba mutun abinci, da zarar sun kamo shi kashe shi suke yi bayan sun gama kwashe amfanin jikin shi,
Duk ba wannan ba, tambayoyi da yawa da take neman amsarsu WACECE TSOHUWA? SU WANENE GIANTS DAKE ZUWA KAWO MA SU ABINCI? A INA GIDAN KURKUKUN ƘADDARA YAKE? TA FARA HASASHEN GIDAN KURKUKUN BA’A CIKIN NIGERIA YAKE BA, ZAIYI WUYA MA ACE ACIKIN GARI YAKE, SHIN SU KAƊAI NE ACIKIN GIDAN KURKUKUN KO KUWA AKWAI WASU MUTANAN? MEYASA AKA HANASU SHIGA CIKIN SHI”?
ta yi zurfi a cikin tunaninta muryar batool ta katse ta da cewa”Angel har yanzu baki yi bacci ba”! Firgigit tayi tare da kallon batool dake a zaune gefen gadonta hannun ruƙe da fitila, tsananin mamaki ne ya kamata, ganin duk sunyi bacci, ita kaɗaice zaune saman gadonta, batasan tsawon lokacin da ta ɗauka ba, Sai da batool ta fargar da ita, ashe dare ya yi har sun kwanta, ita a yadda tabarsu suna akan danish dake ta fasa ƙara, Yanzu ga danish ɗin nan kwance cikin bargonshi sai bacci yake yi, su azeeza ma duk sun kwanta,
“Yansu na farka zan shiga toilet shine na hango ki a zaune, nayi mamaki” murmushin yaƙe angel ta sakar mata tare da cewa”Bana jin bacci ne, ya jikin danish”?
“Ya ji sauƙi, baki ga ma har yayi bacci ba” tayi maganar tana haska gadon danish ,
Gyaɗa kai angel tayi”Nima yanzu zan kwanta, kije ki shiga toilet ɗin,”
Batool tace”ae har na shiga na fito, zan wuce ne na lura dake a zaune”
Shiru angel ta ɗanyi, ganin kamar tana acikin damuwa yasa batool tace,”Baki da lafiya ne? Ko wani abu na damunki”?
da sauri angel tace”bakomai, kawai ina tunanin rayuwar duniya ne”
“Yau da kika samu motsa jiki, ga6o6in jikina sai ciwo suke yi mun, amma yanzu dana ta shi daga bacci sai naji daɗin jiki na,”
Angel tace”idan kuka saba kullum zaku ji dadin jikin ku, zai saki sosai ba’a son mutun daga yaci abinci ya kwanta, anfi son kadan motsa jikinka, “bayani tayi mata dangane da amfanin motsa jiki, batool tace”Daga yanzu duk in muka ci, abinci zamu dinga yi, bari naje na kwanta” tana kokarin miƙewa angel ta yi saurin ruƙo hannunta, kallonta batool tayi tare da cewa”Lafiya”?
“So nake na tambaye ki, A gidan kurkukun nan Ana kiwon kaji ne”? Cikin rashin fahimtar zancanta, batool tace”Kiwon Kaji kuma? Meye ma’anar hakan”
Dafe kai angel tayi”Ina Nufin kaji da ake kawo mana muna ci kusan kullum, Ana kiwonsu ne a gidan nan ne? Still batool bata fahimci zancenta ba, ta dai san kaza da ake kawo masu a soye suci, amma batasan ma’anar kiwon ba,
“Shikenan tunda baki sani, Amma kin ta6a shiga cikin kurkukun nan? Naga ranar da aka kawo ni, Ni kaɗai nafarka acikin ɗakin nan, Ku kuma daga waje kuka shigo Ciki, Ina kuka je ne”? Ta yi tambayar tana kallonta”
“Bazan iya tuna komai ba,” cike da takaici angel tace”Komai baki sani ba ke, to faɗa mun a gidan kurkukun nan ku kaɗai ne kuke rayuwa a cikinsa”?
Girgiza kai tayi”A’a bamu kaɗai bane, Kinga wannan numbobin na bayan rigunan mu, akwai me 400,” waro ido waje angel tayi muryarta har shaƙewa take yi wurun cewa”Are u serious”? Ɗaga mata kai batool tayi alamar Eh, taci gaba da cewa”idan zan iya tunawa kafin zuwanki, Munyi rayuwa acikin wasu Prisoners ɗin waɗanda Ke rayuwa a killace cikin kurkukun nan, bamu kaɗai bane, muna da yawa,” mamaki ƙarara akan fuskar angel ta kuma cewa”Amma ku meyasa aka ware ku daga Cikinsu”? Batool tace”nima bansani ba,”
“Yanzu faɗa mun, duk wani abu da kika sani game da kurkukun nan,”
“Bansan komai ba”
“Ke dai ki tuna” shiru batool tayi tana kokarin tunano abunda ta sani, tsawon lokaci kafin ta soma magana
“Idan aka ɗauki mutun ba’a dawo wa da shi, idan muka tambayi tsohuwa ina ƴan uwanmu suke waɗanda aka ɗauka daga Cikinmu, sai tace mana mu kwantar da hankalin mu, Suna nan cikin ƙoshin lafiya wata rana zasu da…..” bata kai karshen maganarba, ta miƙe da sauri ta dauki fitilarta, ko kallon angel ba ta yi ba ta wuce saman gadonta ta kwanta,
Zuba mata ido angel tayi Cike da mamakin yadda ta miƙe zumbur ta tafi batare da ta ƙarasa maganarta ba, kodai itama an zungureta ne? Ta yi tambayar a cikin Zuciyarta,
Kafin ta yi Shirin kwanciya, kamar kullum ta ɗaga hannayenta sama tana yi masu addu’o’i, Hada daddynta kullum ne bata mantawa da shi, Yana acikin ranta……….🥺
*ANEELERH*
Mami ce zaune gefen gadonta har ta yi shirin kwanciya, jikinta na sanye da Sleeping gown, ta ƙura wa screen ɗin wayarta ido,
fitowa abie Yayi daga Cikin toilet yana gyara wuyan jallabiyar jikin shi,
gyaran murya yayi mata ta ɗago tana kallon shi, fuskarta da alamun damuwa tace”Ina ta kiran aneelerh bata ɗaga ba, “
“Bansan meyasa kika tashi hankalin ki ba, sai kace wadda ta tafi wata uwa duniya,”
“Dole na damuwa, saboda ni bata faɗamun cewa a can xata kwana ba, kuma na kira layin Uncle bash ɗin tana ta ringing bai ɗaga ba, itama dr Aisha na kira layinta bata ɗaga ba, idan acan zata kwana ae yakamata su kira su sanar dani,”
Murmushi abie ya saki”Na lura ba ƙaramin ji kike da ƴar nan taki ba, Ko da yake nasan saboda wa kika hana idonki bacci,”
“Bai wuci kace saboda baby junaid ba, ae dole na damu da jika na, shi kaɗai fa nake da shi kwallin kwal an tafin mu da shi, sai da nace tabarmun shi a wurina, amma ta kafe akan saita je can da shi,”
“In banda abunki, taya zata tafi tabar maki shi, bayan ba’a yaye shi ba, idan ya yi kuka ya zakiyi da shi”?
“Nima ae macace, Kaima kasan ina da abunda zan bashi” Dariya abie yayi a lokacin ya dawo gefenta ya zauna,
“Yanzu dai ki kwanta kiyi bacci, zuwa gobe da safe, zasu dawo kiga jikanki,”
Ba don taso ba, ta ajiye wayar Suka kwanta bacci atare,
A 6angaren Aneelerh Kuwa, tun Bayan magbrib suka baro gidan Uncle bash, Drivern gidansu Musa ne ke yin driving ɗinta, Tana a zaune Cikin back seat na motar, Jikinta na sanye da Arab gown ta yafa mayafi akanta, Baby junaid na rungume saman kirjinta, Yasha kayan sanyi ajikin shi,
“Ba gida zamuje ba, Gidana nake so ka kaini akwai wasu kaya da zan ɗauka”musa dake driving yace”Amma Ba mu yi da Alhaji cewa zan kaiki gidanki ba,”
“Eh na manta ban faɗa ma shi ba, ka kaini ba matsala,” acewar aneelerh,
Shi dai hankalin shi bai kwanta da su je gidan nan ba, ganin dare yayi kuma gidan yana a karkashin Binciken ƴan sanda bai son wani abu ya faru,
“Amm hajiya naga dare yayi yanzu, me xai hana mu bari sai gobe da safe in kaiki gidan’?
ɗaure fuska aneelerh tayi sam batasan gaddama”meyasa ka ke yi mun magana sai kace wata ƙaramar yarinya? Bani nace ka kaini ba? Ae ba jimawa zanyi ba, akwai abunda nake so in dauko ne Ko minti biyar bazan yi acikin gidan ba,’
Muryar shi na inda inda yace”Zan kai ki mana kawai dai naga dare yayi ga kuma yaro ahannunki,’
“Muje kawai nidai” Amsa mata yayi da toh, ya juya sitiyarin motar ya haura saman titin da zai sada shi da unguwarsu Uzair,
Lokacin da suka ƙaraso unguwar tsit babu hayaniya ko gifcin mutun baka gani, kowa ya shige gidanshi, akwai hasken street light ta ko’ina,
A bakin gate ɗin Gidan, Musa yayi parking ɗin motar, ya fito da sauri ya buɗe ma aneelerh murfin motar, Fitowa tayi hannunta rungume da junaid, Key ɗin gidan yana a hannunta, Dama biyu gare su ɗaya na uzair ɗaya nata, wanda ke a hannun jami’an dake bincike na Uzair ne,
“Madam kodai in bi ki mu shiga Ciki”? Kallon shi tayi ganin duk ya tsorata”Motar fa wa zaka barma gadinta”? Muryarshi a sanyaye yace”hakane kuma bari na koma Ciki na jira ki, dan Allah Aunty kiyi sauri” murmushi tasaki jin ya canza mata suna, ya kirata da madam ya kuma kirata da aunty, Maimakon sunan da yake kiranta da shi Hajiya,
Wuce wa ta yi zuwa bakin ƙopar dake a jikin gate ɗin gidan, ta sanya key ta buɗe ta, ta shiga daga Ciki, duk akan idon musa dake a tsaye ya jingina bayan shi jikin motar,
A tsanake take tafiya Cikin Gidan wani irin yanayi take ji atattare da ita, Ko’ina ta shiga bi da kallo, tun daga kan inda suke ajiye motocinsu har zuwa ƙopar shiga falonsu, Bakomai take tunawa ba face rayuwarsu da Uzair, tuni taji hawaye sun wanke mata fuskarta, yau tsawon shekara biyu da watanni kenan, babu su babu alamarsu,
Hasken electric bulbs ne Ya gauraye gidan, tamkar da rana,
Lokacin da tazo bakin ƙopar falon, ta sanya key ta buɗe ƙopar ta shiga daga Ciki, Ko’ina a gyare yadda kasan mutane na rayuwa acikin gidan,
A saman Sofa ta kwantar da baby junaid dake ta bacci, ita kuma ta shige Cikin bedroom ɗinsu, tsayawa tayi tana bin ɗakin nasu da kallo, sai ta dinga ganin kamar fuskar uzair yana sakar mata murmushi,
Girgiza kai kawai ta yi yayin da hawaye ke cigaba da sauka saman fuskarta, Hotonsu na aure dake manne jikin bango ta ƙurawa ido, Sunyi matuƙar yin kyau, kusan minti biyar kafin ta Hau saman gadonsu ta kwanta tana shessheƙar kuka,
Dama babu abunda ya kawota Cikin gidan tazo ne kawai don ta ƙare mashi kallo saboda kewar Mijinta da tayi,,
Bubbuga mattress din ta dinga yi da hannunta tana kuka tana faɗin Wai ina kaje uzair? Meyasa ka tafi kabarni cikin maraicin rashinka, bayan kasan bana iya rayuwa da wani ɗa namiji idan ba kai ba, dan Allah mijina ka dawo gareni wlh ban gaji dakai ba, ina matuƙar ƙaunarka, kazo kaga Babynmu kyakkyawa da shi, so kake ya taso amatsayin maraya wanda bai da uba? Why uzair? Wata amsa kake so na bashi idan ya tambaye ni dangane da Mahaifinsa? Sai sambatu take yi ita kaɗai tana kuka, sam ta manta da Musa driver dake jiranta, ga kuma Yaro da ta bari a palour shi kadai saman Sofa yana bacci,
Kusan awa ɗaya aneeelerh bata motsa ba, wani irin yanayi mara misaltuwa take jin kanta a ciki, sai faman shessheƙar kuka take yi,
Lokaci ɗaya taji mummunar faɗuwar gaba ras! Tamkar ƙirjinta zai dare biyu, bugun zuciyarta ya ƙaru, Jiki na rawa ta sauko daga Saman gadon muryarta na kerma take ambaton sunan Junaid,
Da gudun gaske Ta faɗo Cikin Falon, Tana ɗaura kanta saman Sofa ɗin data kwantar da junaid, taga wayam babu shi sai dai towel ɗin data nannaɗe shi aciki, A ƙasa aka jefar da shi,
Kamar afarmaki take ganin lamarin, Tsabar ruɗi tarasa me zatayi, Tsananin tsoro ne bayyane akan fuskarta, Ƙarasawa tayi gaban sofa ɗin ta sanya hannu tana shafa Saman kujerarar, ta tabbatar cewa an ɗauke Mata Yaronta, tunani tayi kodai Musa ya shigo ya ɗauke shi ne? da gudu ta zabura Ta fito daga cikin falon, Har ta kusa kaiwa Bakin gate ta juyo kukan baby junaid ɗinta, a matuƙar gigice ta juya ta koma Cikin gidan, duk inda ta nufa sai taga babu shi, Rushewa tayi da matsanancin kuka tana faɗin”Innallalahi wa’innna ilaihirraji’un! Wayyo Allah na! dan Allah wanene ya shigo? kada ku cutar mun da yarona na roƙe ku, ku ƙyale mun shi, ‘ tana Cikin maganar nan tajiyo takun tafiyar mutun a firgice ta juya bayanta, gifcin shi ta gani koma wanene yana a sanye Cikin bakaken Kaya, Fuskar shi tana sanye da face mask, Hannunshi na ruƙe da Baby Junaid, Da gudun gaske Aneeelerh tabi bayanshi, sai dai kafin ta ƙarasa tuni ya 6ace ma ganinta,
Gaba ɗaya ta haukace Jikinta sai tsuma yake yi ga wata uwar zufa data tsastsafo mata, ita ba kanta take ji mawa ba, Ɗanta take jimawa ba, shida bai mallaki hankalin shi ba,
“Dan Allah na roƙe ka ka dawo mun da ɗana, Kome kakeso zan baka, Amma kada ka cutar mun shi, idan ma ni kakeso ka dauke ni ka ƙyale mun shi pls,” cikin shessheƙar kuka tayi maganar,
Motsi ta kuma Ji daga can saman stairs ɗin gidan, A hautsine ta ɗaga ido tana kallon mutun dake atsaye, Hannun shi ruƙe da baby junaid, ƙarfin hali hada ɗaura shi saman kafadarshi, yana shafa bayanshi, kuma yaron yayi shiru,
Zuba ma shi ido tayi tana kallon shi batare da ƙyaftawar ido ba, Koma wanene wannan mutumin ba ƙaramin karkarfa bane, Yana da tsayi da kuma faffaɗan Ƙirji, ta ko’ina ya rufe jikin shi, ta yadda mutun bazai iya shaida shi ba,
Muryarta na kerma tace”Dan Allah kada ka cutar mun da shi, kome kakeso zan baka,” ta yi maganar tana kallon shi, zufa ta ko’ina saman fuskarta,
Gani take kamar zai jefo shi ta saman bene ne ya faɗo kasa kanshi ya fashe,
Fashewa ta kuma yi da wani sabon Kukan, Tunawa tayi da musa driver da gudu ta juya ta nufi hanyar fita don taje ta sanar da shi abunda ke faru,
Harta ruƙe handle ɗin ƙopar, Muryar mutumin ta ratsa kunnnuwanta,
Cikin harshen Turanci yace”idan kika kuskura kika fita, zan wurgo da shi ƙasa,” Ras Taji gabanta ya faɗi, Kamar gunƙi haka ta ƙame, zuciyarta a cunkushe Ta juyo tana kallon shi, Har lokacin Yana a can sama,
Muryarta na kerma tace”Na fasa bazanje ba, wlh bazanje ba, dan Allah ka bani ɗana, wlh nayi maka alƙawari bazan ƙara zuwa gidan ba,”
Dawowa cikin Falon Ta yi, A bakin stairs ɗin ta tsaya, fuskarta jaga jaga da hawaye, Bata ta6a ganin tashin hankali ba irin na yau, Ko wanene wannan mutumin? Taya akai ya shigo Cikin gidan? Bayan makullan gidan Suna a hannun jami’an ƴan sanda? Anya kuwa mutunne kodai ta bango ya ratsa Ya shigo?
“Ka faɗamun ko nawa kakeso zan baka ina da kuɗi, Ni dai kawai burina ka bani Yarona,”
Tana magana tana taka staircases ɗin, a kokarin ta nata haura inda yake,
“Hajiya” Muryar Musa driver ce, A firgice aneelerh ta juya tana kallon musa, Ai koda musa yayi arba da mutumin dake A can saman stairs sanye da bakaken kaya, Nan take jikin shi ya hau yin kerma, Ya shiga ambaton”Ƙalu Innallahi wa’inna ilaihirraji’un hajiya wannan kuma daga ina”?
Cikin muryar kuka aneelerh tace”Nima bansani ba, Daga shiga Cikin ɗaki na dawo na taras ya dauke mun baby junaid ɗina, dan Allah kataimaka ka sanya baki mu bashi haƙuri ya bamu junaid mu tafi mubar masa gidan,”
Kallon shi musa Ya kuma yi”Bawan Allah, Don son da kake ma iyayenka Ka taimaka ka bamu yaron nan, Wlh tsautsayi da ƙaddara ne ya kawo mu Cikin gidan nan, dama saida na gargaɗi hajiya nace mata kada mu zo, Amma ta sanya naci akan sai mun zo yanzu ga irinta nan”
Roƙonshi suka dinga yi ko tanka masu baiyi ba, tamkar baijin me suke cewa, Ya ƙanƙame Yaro a hannunshi sai shafa sumar kanshi yake yi,
“Hajiya wannan mutumin fa, ba bamu yaron nan zaiyi ba, Kizo muyi ta kanmu kawai, Allah zai baki wani ɗan, idan ba haka ba mu duka zamu rasa ranmu,”
“Wlh ba inda Zanje sai ya bani yarona, saboda bakasan ciwon haihuwa ba shiyasa zaka ce mu tafi mubar ma shi yaro a hannu, ” rai a6ace takai ƙarshen maganar, Duk yana atsaye yana sauraron su,
Suna Cikin yin maganar nan, gaba ɗaya hasken gidan ya ɗauke, duhu ya mamaye ko’ina,
Aneelerh ta shiga matsanancin tashin hankali, Cikin duhu taci gaba da tattaka matattakalar benan, Tana jiyo muryar musa yana kwala mata kira, amma ina kota kanshi bata bi ba, lokacin da ta ƙarasa hawa benan, Muryarta na rawa take faɗin”Bawan Allah, ka bani yaro na in tafi, nasan kana jina, dan Allah kada ka cutar mun shi,” tana magana tana lalube Cikin duhu,
Motsin shi ta dinga Ji acikin kunnuwanta, alamun yana a kusa da ita, Kamar ma zagayeta yake yi, Jikinta sai kerma yake yi, ga wata uwar zufa dake tsastsafo mata, mugun tsoro take ji, amma saboda soyayyar dake a tsakanin uwa da ɗa, ta kasa guduwa ta kwammace komai zai faru ya faru, koda zata rasa ɗanta ne,
Wani irin daddaɗan ƙamshin turare ta soma shaƙa Cikin hancinta, koma wanene wannan Ba 6arawo bane, Kuma ba da niyar mugunta yazo ba, Lamarin ya rikitar da ita,
Cikin sanyin murya tace”Dan Allah ka bani shi in tafi, wlh bazan faɗi ma kowa naga mutun acikin gidan ba,”
Hannunta taji ya ruƙo, ras taji gabanta ya faɗi, ɗaura mata baby junaid yayi asaman ƙirjinta, da sauri ta tallebe shi, ta rungume abunta ajikinta, Natsuwa tayi tana jiran jin ya furta wata magana sai dai baice komai ba,
Lokacin da ta daina jin motsinshi a kusa da ita, a dai dai wannan lokacin hasken Gidan Ya dawo gaba ɗaya ya gauraye ko’ina,
Nauyayyiyar ajiyar zuciya ta sauke, tare da ɗaura idanuwanta kan baby junaid dake ta sharar bacci, saman ƙirjinta,
Ƙara ƙanƙame shi tayi ajikinta, kamar zata mayar dashi Cikin cikinta, Yau da ace ɗan tahalinkin nan ya kashe mata shi, da kuwa har ranta zata iya rasawa,
“Hajiya zamu iya tafiya yanzu”? Musa ne yayi maganar jikinshi sai kerma yake yi, yana daga can down stairs, Harara ta wurga mashi,
“Ka bani key ɗin motar, ka kama gabanka, Sakaran Namiji kawai, hada cewa in bar mashi yarona in Zo mu tafi, ban ta6a ganin ragwon namiji irin ka ba, duk macan da ta aure ka tayi asara, ” zuru musa yayi mata da ido,”
Saukowa down stairs tayi tare da miƙa mashi hannu”bani key ɗin motar”
Cikin sanyin murya yace”ayi haƙuri hajiya ruɗu ne ya jawo hakan”
A fadace tace”dalla ni bani key,”
Zaro key ɗin motar yayi daga Cikin aljihun shi ya miƙa mata, tasa hannu ta fusge shi, Cikin fushi ta fuce daga cikin falon,
Da gudu musa yabi bayanta yana lallashinta.
Bayan ta rufe gidan da key ta buɗe mota zata shiga driver seat, da sauri musa Yayi hanzarin cewa”Dan Allah aunty aneelerh kiyi hakuri wlh bana Cikin hayyacina ne, su6ul da baka nayi wurin furta maganar, ban kaiga tace ta ba,”
Daƙyar musa ya samu aneelerh ta haƙura ta miƙa mashi key din motar, ta shiga passenger front seat ta zauna shi kuma ya zauna a driver seat,”
Da gudun gaske ya fusgi motar, kafin su ƙarasa gida saida ta gargaɗe shi akan karya kuskura ya faɗa ma su abie dangane da mutumin da suka gani Cikin gidan, yaja bakin shi yayi shiru tun da bai cutar dasu ba, su ɗauka tamkar mafarki su kayi, Yace mata toh,
Lokacin da suka ƙaraso Cikin gidan, A parking space Musa ya yi parking ɗin motar, ya fito ya zagaya ta other side ɗin ya buɗe ma Aneelerh mota,
Fitowa tayi hannunta rungume da baby junaid, Har lokacin Jikinta kerma yake yi, ta tsorata sosai da wannan tahalikin da ya kai masu farmaki,
Kallon musa tayi shima kallon nata yake yi, harara ta jefa mashi ya sunnar da kan shi ƙasa, Ni zan wuce ciki, “
“To hajiya sai Allah yakaimu, Allah ya kyauta gaba,” bata amsa ma shi ba ta nufi Cikin gidan,
Da alama duk sunyi bacci, bata nufi ko’ina ba, Sai Cikin Bedroom ɗinta, a saman gado ta kwantar da junaid, sai baccin shi yake yi hankali kwance,
Rage kayan jikinta ta yi, ta shiga toilet domin yin wanka, after 15 mins ta fito waist ɗinta ɗaure da towel fari,
Walking slowly ta nufi Saman mirror chair ta zauna, tare da ɗaura gwiwar hannunta gaban madubin, ta zabga uban ta gumi,
Zuciyarta a cike take da tunanin mutumin nan, ko wanene shi? Taya akai ya samu damar shiga Cikin gidan dake a garƙame? Kodai bayan shigarsu ciki shima Ya samu damar shiga Cikin gidan? Shin me yaje yi acikin gidan, gaba ɗaya ta burkita ma kanta lissafi, kusan raba dare ta yi azaune tana tunani akan shi, bata iya gano komai ba, a ƙarshe ta miƙe taje gaban closet, ta buɗe ta curo kayan baccinta, Ta sanya su ajikinta,
Komawa saman gadon tayi, ta kwanta tare da janyo junaid ta rungume shi ajikinta, Cikin ƙanƙanin Lokaci bacci yae awon gaba da ita, Ko da gari ya waye Aneelerh bata sanar da kowa game da mutumin da suka gani acikin gidan Uzair ba, ita kanta tarasa gane dalilin dayasa ta kasa buɗe baki ta faɗa masu cewa wani ya shiga gidan, wata’ƙil ta hanyar hakan asamu wata evidence da zata bayyana ainihin meya faru da su tajo, kuma tun daga ranar bata ƙara gigin zuwa gidan ba, gani take kamar mutumin yana bibiyar rayuwarta, kodan kada ta tona ma shi asiri dole ya bibiyeta, shiyasa take tsoran fallasawa,
Back To prison🌷
A kwana a tashi ba wuya wurin Allah A yau angel ta cika shekara 1 da rabi A gidan KURKUKUN ƘADDARA, tun daga ranar da tayi ma batool tambayoyin nan bata ƙara tambayarta wani abu dangane da gidan kurkukun ba, dalili kuwa shine a duk lokacin da zata tambayi batool game da prison ɗin, Sai wani abu ya faru, wanda zai ɗauke masu hankali, Haka xalika a duk lokacin da ta yi yunƙurin sanar dasu wani abu game da addinin musulunci sai wani abu ya faru wanda zai dakatar da ita, ta ko’ina an toshe mata hanya,
Abu ɗaya ne take kokarin Koyar da su shine yawan ambaton sunan Allah acikin maganarsu, saboda kwata kwata basa furta sunan Allah, zuwan angel cikin rayuwarsu sun fara koyan wasu abubuwan wanda basu iya ba, salon maganarsu ya fara komawa irin na angel, ta zama tamkar malama acikinsu, Idan suka kammala Cin abinci, bata bari su koma bacci, motsa jiki take sanya su suna yi, Ko kuma suyi wasa a tsakaninsu, bakomai yasa suke jin shakkarta ba, face rashin tsoranta, da kuma wannan kalmar ta charman dudu da take yi masu barazana da ita, shiyasa a kullum take Cin galaba a kansu, duk wannan tsawon lokacin da angel ta ɗauka acikin gidan kurkukun ƙaddara, har yau babu jituwa tsakaninta da Haris da kuma mr sound hater wato DANISH, su biyun nan sunƙi yarda da ita, duk da sunfi kowa jin shakkarta, kuma in ta bada umarni dole kowa yabi hada su ɗin,
Zaune suke gaba ɗayansu sun kewaye Kayan abincin da aka kawo masu, giants suna a tsaye sun kasa sun tsare suna jiran su kammala Ci su kwashe Kayan su tafi,
Hanna ce ta ya ye jan kyallen da aka rufe saman trays ɗin, tray na farko fried meat ne, sai faffadan plate me ɗauke da Snacks a tray na ƙarshe kuma jug ɗin ruwa ne, sai kofuna Bayan su kuma sai kwandon dake ɗauke da kayan marmari da ƴar ƙaramar wuƙa, wadda zasu yi amfani da ita su yanka fruits ɗin,
Kowa yakai hannu ya dauki fried meat yana Ci,
Gaba ɗaya hankalin angel na akan wuƙar da aka sako Cikin kwandon kayan marmarinsu Cin naman take yi kamar zata shaƙe, so take ta sace wuƙar batare da sun gani ba, ɗagowa ta ɗanyi tana kallon Su Giants dake a tsaye, abinci ma baza a bar mutun yaci a tsanake ba sai an tsare mutun da ido, a cikin zuciyarta ta yi maganar don tasan suna kallon su,
Cikin ƙankanin lokaci ta cinye nata abincin, miƙa hannu ta yi tana nuna jerin Cups ɗin dake a jiye Javed yace”ruwa zaki sha”? Ta ɗaga mashi kai alamar eh,
Da kanshi ya zuba mata ruwan ya miƙa mata, ta kar6a tana yi mashi godiya, bayan ta shanye ruwan ta ajiye kofin, xama ta yi tana jira sauran su kammala cinye nasu, ko ta samu a zo kan fruit ɗin yadda zata ji daɗin sace wuƙar,
Sun ɗauki tsawon mintuna kafin suka kammala, kowa ya sha ruwa Kafin suka kai hannu suna ɗaukar kayan marmarin, ganin basu yi amfani da wuƙar ba, yasa tace ma batool” ba zasu yanka ba” batool tace mata”A jiyewa zamuyi sai anjima mu sha,” yatsina fuska angel ta yi ganin zata rasa damar da take da ita, ta ɗaukar wukar,
Dabara ce ta faɗo mata aranta, miƙewa ta yi tsaye tamkar zata bar wuri, ta ɗan ɗaga kafarta alamar za ta yi tafiya, gaba ɗaya ta yanke jiki ta faɗa saman kayan abincin, aruɗe su hannah suka kewaye ta suna jijjiga jikinta, hankalinsu a tashe suke ambaton sunanta,
Ganin sunyi mata rumfa ta yadda waɗannan Giants ɗin bazasu iya ganin meke wakana ba, a hanzarce ta yi wuf ta zura hannu ta ɗauke wuƙar tare da saƙe ta gefen qugunta, mutun ɗaya ne ya ga lokacin da ta ɗauki wuqar don ta fakaici idon su ne,
Miƙewa ta yi tana faman haki tace su bata ruwa tasha, jiri ne ya kwashe ta,
Da sauri Hibba ta cika mata kofi da ruwa ta miƙa mata, kaɗan tasha ruwan don bata jin ƙishir ruwa duk cikin plan ne,
Ganin sun kammala cin abincin yasa Giants matsowa suka tattara komai da suka yi amfani da shi, har fa sun Kama hanyar fita, danish ya ɗaga murya tare da cewa”She took a knife” tashin sense a razane angel ke kallon shi, kafin ta ɗaura idonta akan giants gani ta yi sunja burki sun tsaya cak, ɗaya daga cikin ne ya jiyo tare da nufar inda suke, tamkar zaki
Saboda tsabar ruɗi tunkafin ya ƙaraso angel ta curo wuƙar ta miƙa mashi yasa hannu ya kar6a, ƙiris ya rage ta fashe da kuka kamar jira take su fita, ta yi wani irin kukan kura ta daka tsalle ta faɗama danish, kokawa ta 6arke a tsakaninsu bugu ta shiga kai mashi, ta yakushe shi da akaifun hannunta, hada cizo ta gartsa mashi gefen wuyan shi,
Su batool suna ta ƙoƙarin rabata da jikin shi, amma ina duk wanda ya yi gigin ta6a ta wurgi take yi da shi, daƙyar haris ya cakumota, rai a 6ace ya yi wurgi da ita gaba ɗaya ta kife ƙasa kanta ya bugu sosai,
Zuƙunnawa su kayi agaban danish dake yashe ƙasa yana fitar da numfashi sama sama, farar fatar wuyan shi tayi jawur ga sahun haƙoran angen nan tamkar an zana su, duk ta 6ata ma shi wuya da yakushi red marks ta ko’ina,
Ran kowannan su sai da ya 6aci, musamman haris, rai a 6ace ya ke faɗin
“Dama ae ba sonshi ki ke yi ba, shiyasa ki ke son kashe mana shi, na rasa me danish ya yi maki, bafa shi bane ya yi silar zuwanki prison ɗin nan ba, ballanta na kice xaki ɗauki fansa a kanshi, ki bar ganin ana jin tsoronki, Allah daga yau idan kika kuskura kika ƙara ta6a fatar jikinshi saina karairayaki,
ɗagowa angel tayi idanuwanta sunyi jawur, batool da aziza suna a 6angarenta,
Cikin shessheƙar kuka tace”Idan ka ta shi ka kashe ni dan Allah, kada ka barni da rai na, meyasa zai ce na ɗauki wuƙa? Ina ruwan shi? Idan har bai shiga hurumina ba ni zan shiga nashi ne”? Ta yi tambayar a ƙule,
Batool tace”ban goyi bayan wani a cikin ku ba, Amma laifin danish nafi gani, meyasa za ka tona mata asiri don ta ɗauki wuƙa? Menene naka aciki? Juyawa ta yi kan angel’ke kuma angel baki kyauta ba, kalli yadda kika raunta shi, sai kace ba ɗan uwanki ba….”tunkafin takai ƙarshen maganar angel tace”danish bazai ta6a zama ɗan uwana ba, bana son shi bana ƙaunar ganin shi,”
Jinjina kai batool ta yi”its okey, daga yanzu zan shiga tsakanin ku, kada wanda ya ƙara shiga hurumin wani ina fata hakan ya yi,”
Javed yace”idan ma suka ƙara ni da kaina zan sanar ma tsohuwa a ɗauki mataki akansu,”
daga haka Haris da su mubeen suka kama hannun danish su kayi mashi jagora zuwa saman gadonshi, kwanciya saman gadon ya yi bawan Allah har wani jiri yake gani acikin idanuwanshi, shifa bakomai yasa ya tona ma angel a sirin ta ɗauki wuƙa ba, face sanin irin tsanar da tayi mashi, tsoron shi kada ace shi zata yanka da wuƙar wannan dalilin ne yasa shi tona mata asiri, ashe da rabon yaci na jaki a hannunta,
Miƙa mata hannu azeeza ta yi”ki tashi muke ki kwanta, ki huta” sai da ta ɗanyi jim kafin ta ruƙo hannun azeeza ta miƙe, saman gado ta koma ta zauna, hawaye sha6a sha6a akan fuskarta, danish ya tarwatsa mata plan ɗinta, taji takaici kamar ta sanya pillow ta taushe ma shi fuska haka take ji,
“Angel me zaki yi da wuƙa”? batool ce ta yi mata tambayar, ɗagowa angel ta yi tare da kallonta, tana a tsaye gefen gadonta,
Girgiza kai ta ɗanyi”babu komai, kawai inaso na mallake ta ne,” ɗan zaro ido batool ta yi”karfa ace wani kike harin kashewa a cikin mu” cikin zolaya ta yi mata maganar,
Cikin sanyin murya angel tace”a’a batool bazan iya kisan kai ba, ni kawai naso ace na mallaki wuƙar,”
“Da ace kina shiri da danish, da ya aro maki wuƙar shi,” da mamaki angel ta kalle ta tare da cewa”yana da wuƙa”? Jinjina mata kai ta yi eh, akwai wata ƙaramar wuƙa da yake amfani da ita wurin datse gashin kan shi, tsohuwa ce ta bashi wuƙar lokacin da ya ta6a tambayarta yana so ya rage tsayin sumar kanshi, shi ne ta ba shi wuƙar to bai mayar mata da ita ba, har yau tana nan a wurin shi,”
Dafe kai angel ta yi tare da satar kallon danish dake a kwance saman gadonshi, da alama bacci ya yi awon gaba dashi, yadai sha wahala,
“Ga samu ga rashi” ta ambaci hakan acikin azuciyarta, tasan koda me take yawo danish bazai ta6a ara mata wuƙar shi ba
Kallon batool ta yi”kinsan inda yake 6oye wuƙar” kallon sama batool ta ɗanyi da alama tunani take yi, can tace”a ƙarƙashin katifar gadonshi naga yana 6oye ta,
Angel tace”ki taimaka kice ya ara maki ita a matsayin ke zakiyi amfani da ita,
Ɗan zaro ido batool ta yi”ae bai yadda ya fiddo da wuƙar nan, kaifi ne da ita tana da haɗarin gaske, kona tambaye shi bazai bani ba, saboda yasan ba abun da zan yi da ita,”
Jinjina kai angel ta yi”shikenan na haƙura” daga haka bata kuma cewa komai ba, ta koma ta kwanta amma fa bawai ta haƙura bane, a can cikin zuciyarta tana shirya yadda zata sace wuƙar danish batare da sanin shi ba, da wannan tunanin ta yini da shi kuma ta kwana,
A daren yau ta kammala shirya yadda zata ɗauke wuƙar, kowa ya yi bacci saman gadonshi, duk sun lullu6e da bargunansu, angel ce kaɗai idonta biyu tana kwance idonta na fuskantar ceilling duk da duhu babu wadataccen haske saina fitilun ɗakinsu da suka kunna,
“Lokaci ya yi da zan tashi inje saman gadon danish in ɗauke wuƙar sa,” acikin zuciyarta ta yi maganar, tana ƙoƙarin miƙewa tajiyo takun tafiyar mutun acikin ɗakin nasu, da sauri ta koma ta kwanta cike da fargabar wanene a dai dai wannan lokacin ya faɗo masu ɗaki,
Ƙyalla ido ta yi daga kwancen da take tana satar kallon inda take jiyo sautin tafiyar, kaskon turaren wuta ta hango a hannun mutumin dake zarya cikin ɗakin nasu, wani irin baƙin hayaki ke tashi daga cikin kaskon, kamar ana turara turaren wuta,
Mutumin dake ruƙe da kaskon turaren wutar, jikin shi na a sanye cikin doguwar riga me hula launin ja, rigar har ja take ƙasa,
Kasa kunne angel tayi tana sauraron muryar mutumin dake magana, kamar muryar tsohuwa sai dai bata iya tantance da wani yare ake magana ba, wani irin gu6ataccem yare mara daɗin ji,
Nan fa hankalin angel ya ɗan tashi, xufa ta wanke fuskarta, duk ta sha jinin jikinta, tsoro take ji kada ace wani mugun ne yazo cutar da su,
Bata kai ƙarshen zancem zucin nata ba, ta hango mutun yana tafiya a bakin gadajen su Hannah, yana tafiya yana hura masu hayaƙin zuwa saman jikin su,
Da sauri angel taja bargo ta lullu6e fuskarta, acikin zuciyarta tana ambaton la’ila ha’illa anta subhanaka inni kuntu minazzalamin,” lokacin da mutumin yazo saitin gadonta, da sauri ta sanya tafin hannayenta duka biyun ta toshe bakinta da hancinta, duk don saboda kada hayaƙin ya samu damar shiga jikin ta,
Tana jiyo takun tafiyar mutumin yadda kasan takun tafiyar jaki,
Lokaci ɗaya tadaina jin takun tafiyar da kuma surutan da mutumin ya ke yi, da sauri ta ya ye bargonta, tabi ko’ina da kallo bata ga kowa ba, alamar mutumin ya tafi, sai dai hayaƙin daya turara masu har yanzu bai gushe ba,
Saukowa angel tayi daga saman gadonta, Zuciyarta cike da ruɗani, ko wanene mutun nan daya zo masu a tsakiyar dare, sanye da jajayen kaya? Turaren menene yake hayaƙa masu a cikin ɗakinsu da kuma saman jikin su? sam bata yadda da hayaƙin nan ba, tafi tunanin wani mugun abunne aka turara masu,
Tunawa ta yi da surori da kuma addu’o’in da malaminsu na makatantar islamiyya ya ta6a koya masu yace su yawaita karansu domin neman kariya daga sharrin mutun sharrin aljan da duk wani abun cutarwa,
“Zan tai taimaka masu, saboda basu da maiyi masu addu’a, a kullum in na kwanta ina bacci, daddyna yana yi mun addu’a, su kuwa basu da iyayen da zasu yi masu addu’a” acikin ranta tayi maganar
Kamar yadda mutumin nan yabi ko’ina na ɗakin yana turara Masu baƙin hayaƙin nan, itama haka ta soma bin kowace kusurwa ta ɗakin nasu tana karanta Ayatul kursiyyu, da amanar rasuli, Suratul mulk, Suratul kafiroon, Suratul ikhlas, falaqi da nasi, duk in ta karanta kowannan su Saita maimaita, daga bisani tabi kowani gado tana tottofa masu addu’oin saman bargunan da suka lullu6a da shi, daga kan gadon hanna ta faro xuwa gadon mubeen har zuwa gadajen su batool, tana zuwa kan gadon danish taja guntun tsoki zata wuce, sai kuma taji aranta kamar bata kyauta ba, don me zata yi ma kowannan su addu’a amma shi ta kasa yi ma shi saboda me? Lafin me ya yi mata? shiru ta yi tana tunani, menene ribar ta idan taƙi yi mashi addu’a,
Har ta kusa wuce gadon shi taja da baya ta koma tare da shiga daga gefen gadon, ranƙwafawa ta ɗanyi saitin fuskarshi ta soma karanto addu’o’in bayan ta kamalla ta tottofa mashi saman fuskarshi, kamar daga sama taji an damƙi hannunta, a razane ta kalle shi ashe ya farka, muryar shi a disashe yace”tsanar takai har ki zo kan gadona kina tofa mun miyau asaman fuskata”? Zuba ma shi ido angel ta yi batare da tace Furta komai ba, tama rasa bakin magana, yadda ya yi mata maganar ita kanta ta yi mamaki sai kace ba wannan mai jin shakkartata ba, bakomai yake jima tsoro ba, face wannan kalmar da take faɗi na cewa zata tofa ma mutun charman dudu Cikin shi ya kumbura, tuna wannan yasa shi ƙara tsorata, shi kanshi baisan yana da ƙwarin gwiwar yi mata magana irin haka ba,
tsawa ya ɗanyi mata tare da cewa”Ba ki ji ina magana ba”? Still ta yi ma shi shiru saboda bata jin zata iya faɗa mashi cewa addu’a take yi mashi, don ma kada yaji kamar tana ƙaunarsa ne,
Ganin ta yi mashi shiru ya ƙara har zuƙa, A tsananin tsorace Ya damƙo ƙasan rigarta da ƙarfi da niyar ya goge abunda ta tofa ma shi asaman fuskar shi, Cikin rashin sa’a ya janyota gaba ɗaya ta faɗa saman jikin shi………………🥱
*❤❤❤PRISONERS❤❤❤*
dukkan ilahirin jikin shi rawa yake yi, kusan suman kwance ya yi saboda tsabar tsoratar da ya yi jin Angel saman jikin shi ɗungurugum, zuciyarta har wani tafarfasa take yi saboda tsabar fusata, a rayuwarta ta tsani jikinta ya haɗu dana ɗa namijin da ba daddynta ba, kamar ta haɗiyi zuciya take ji, tayi Niyar idan ta ɗago ta kwashe shi da zazzafan mari, Sai dai wani yanayi da ta tsinkaye shi a ciki ya yi silar dakatar da ita, lokacin da jikinta ya haɗe da nashi wani irin zafi taji rau tamkar hucin garwashin wuta, lamarin yayi matuƙar ɗaure mata kai, ta fahimci cewa baida ƙoshin lafiya, da alamun zazza6i attare dashi numfashinsa kanshi da hucin zafi yake fita, gaba ɗaya jikin nashi a raunace yake, Ga fargabar angel dake a kwance saman shi, yasha jinin jikinshi a tsorace yake da tsiwatarwa, baiso ta tayar mashi da lalurarshi
daddagewa tayi tare da yunƙurawa ta ɗago daga jikin shi, tarwatsastsiyar sumar kanta ta sauka har saman wuyan shi, a raunace ta kalli kyakkyawar fuskarshi, sama sama yake numfashi ya lumshe sexy eyes ɗin shi bai kai ga datse su ba, shima ɗin ita yake kallo, farar fatar wuyan shi tabi da kallo, ta ko’ina Jan tabon yakushin da ta yi ma shi ne,
Sun ɗauki tsawon lokaci A saman gadon Batare da wani ya furta wata kalma ba, idanuwansu acikin na juna, Jira yake ya ga wani Irin hukunci zata yanke mashi don yasan ba ƙyale shi za ta yi ba, tana iya cewa xata karanta mashi charman dudu, Cikin shi ya kumbura,
saukowa ta yi daga saman gadon nashi jikin ta duk ba daɗi, Sai yanzu ta lura da irin illar da ta yi ma shi, tana zargin kanta da alhakin Ciwon nashi, Ji take kamar taje ta faɗa ma tsohuwa cewa baida lafiya, amma ta kasa sam ba ta so yasan ta damu dashi, kuma ba ta son taje wurin tsohuwa saboda tsanar matar da ta yi,
zuciyarta a karaye ta koma saman gadonta ta kwanta, Ita kanta tasan bazata Iya runtsawa ba, Saboda zullumin rashin lafiyar danish, gani take kamar idon ta rufe idanuwanta zata farka ta taras da gawarshi ne, tana da hanyoyin da zata iya taimaka mashi sai dai bazata iya ba, saboda batason Raini ya fara shiga a tsakaninsu,
“I don’t know why I’m worried about him,” ta ambaci hakan acikin zuciyarta tare da juyawa don ta saci kallon shi, a kwance yake kanshi saman fillow, idon shi biyu ya yi lamo yana kallonta,
Gyara kwanciya tayi Ita ma ta fuskance shi, don yau taci alwashin bazata bari ya runtsa ba, kodan kada yayi bacci daga nan ya zarce zuwa barzahu, zullumin da take yi kenan,
Ganin yaƙi daina kallonta yasa ta ɗan ɗaure mashi fuska tare da cije lower lip ɗinta, ƙasa ƙasa da murya tace”Stop looking at me or else i will poke ur eyes” ta yi maganar tana kwatanta mashi yadda zata zungure ma shi idonshi da yatsan hannunta, har wani lumshe ido ya yi, tamkar yaji saukar yatsan nata acikinsu,
Slowly ya kuma ware manyan idanuwan nashi akan fuskarta,
Ƙura ma juna ido su kayi kallo na ƙurulla, ta jima tana mamakin wani abu atattare da prisoners ɗin da take atare dasu, gaba ɗayansu babu mummuna acikinsu, sam ba su yi kama da ƴa’ƴan malam shehu ba, sunfi kama da rainon madara, ƴan gidan Mommy da daddy, Expecially danish da Batool da Azeeza Hasken fatarsu sam bana baƙar fata bane, Kamar dai ita da take half cast, Launin fatar Su Hanna da su javed Dukansu irin na ya’yan Hutun nan ne, Ko’ina Aka samu kyawawan yaran nan? Zaiyi wuya su kasance ya’yan talakawa ne , Sai dai irin ƴa’ƴan hamshaƙan masu kuɗin nan, wannan ɗan shilan da take kallo, Yanayin shi tamkar akwai jinin sarauta atattare da shi, Baisan magana baisan hayaniya, kullum yana naɗe saman gado yadda kasan ɗan wani basarake, idan ka kalli soft skin ɗinshi ko tabo babu, fari ne sol, ga kyan ido ga kuma kyan sumar kai, Anya wannan ba ɗan wani shegen bane, ta yi tambayar acikin zuciyarta,
Bawan Allah, duk ya tsargu da irin kallon da angel ke yi mashi, Ga bacci yana ji amma yaƙi yarda baccin ya ɗauke shi saboda gudun kada ta yi ma shi wani abu, yasan dole ta hukunta shi,
kallon juna suka cigaba da yi da zarar taga ya fara lumshe ido zai yi bacci sai ta Ambaci kalmar charman dudu, a firgice yake ware idanuwanshi , ta hana shi runtsawa gashi in bai samu isasshen bacci ba, yana samun matsala, kusan raba dare su ka yi ita da danish, sai da Allah ya taimake shi bacci ya fara ɗaukarta tukunna ya samu shima ya runtsa_
In the morning🌹
Mutsu mutsun farkawa daga bacci ta soma yi, a cikin zuciyarta tana karanto addu’ar ta shi daga bacci, tunawa da danish yasa tayi hanzarin buɗe idanuwanta A hanzarce ta yi wuff ta miƙe zaune tana kallon shimfiɗarshi, babu kowa asaman mattaress ɗin sai Bargonsa da pillow dinsa, hankalin ta ya yi matuƙar tashi, ta shiga tambayar kanta Ina danish ya shiga? Meyasa kowa yana a kwance saman gadon shi, sai shi kaɗai ke babu? Ko dai ya shiga toilet ne?
Ta ƙarasa zancen zucin a lokacin da take sauko daga saman gadonta, cikin takun sauri ta nufi ƙofar shige toilets ɗinsu, hannu tasa ta tura ƙofar ta shiga daga Ciki, sai da tabi kowani toilet ta bincika amma babu danish,
Dawowa tayi da sauri taje gaban gadon batool,
Bubbuga ƙafarta tayi tare da Kiran sunanta”Batool! Sister!” saboda tsiwar muryar angel hatta su Azeeza sai da su ka farka,
“Meya faru sister” muryar batool a disasashe tayi mata maganar, tashin ta kenan daga bacci, idanuwanta sun ɗanyi ja saboda bacci,
“Na duba ko’ina banga danish ba, Jiya ya kwana da zazza6i yanzu kuma na farka ban same shi ba,”
“What? Danish bai da lafiya”? Haris ne ya yi maganar tashin shi kenan shima daga bacci, Fuskarshi da alamun ruɗi don ba ƙaramin Jin danish yake ba acikin zuciyarshi,
Jinjina kai angel tayi alamar eh kafin tace”Bansan inda ya shiga ba, tun ɗazu nake neman shi” Ta shi xaune batool ta yi, idonta akan angel tace”meya faru da danish ɗin mu”? Ina ya shiga”? Ta yi tambayar tana faman yin hamma,
Javed yace”Ni dama tun jiya na lura bai da ƙoshin lafiya, kunsan halin shi idan baya da lafiya yana da juriya baya bari mu sani kodan kada mu tashi hankalin mu akanshi, Amma nasan yanzu duk inda yake yana a tare da GIANTS, zai iya yiyuwa sune suka so su ka ɗauke shi”
Batool tace”taya zamu iya tabbatar da hakan”?
Hibba tace”Idan mu ka tambayi tsohuwa zata faɗa mana inda ɗan uwan mu yake, Bari naje na sanar mata,” Ta karasa maganar tare da saukowa daga saman gadon nata, da azama ta nufi ƙopar ɗakin tsohuwa,
Kowa yayi zugudum yana jiran tsammani, Knocking ƙopar Hibba ta yi, Almost 3 times, suka soma jin mutsu mutsun buɗe ƙopa ta cikin ɗakin,
Fitowa tsohuwa ta yi hannunta ruƙe da sanda kamar kullum dai Cikin shigar nan tata, ta gado, wato doguwar riga launin Ja,
Haɗa ido su ka yi da hibba, Cikin girmamawa hibba ta gaishe da ita, ta amsa mata gaisuwar ta ta, tare da cewa”Zan iya sanin meke faru”?
“Dama danish ne, Angel tace jiya taji zazza6i a jikin shi, yanzu kuma mun farka bamu ga ɗan uwan mu acikin mu ba, bamu san inda ya tafi ba” Hibba ce ke magana amma idon tsohuwa yana akan angel dake daga can cikin ɗakin tsaye ta ruƙe qugu a bakin gadon batool, wani irin kallo take yi mata, murguɗa mata baki angel tayi tare da galla mata harara,
Ƙayataccen murmushi tsohuwa ta saki wanda bai kai zuci ba, ta ɗauke idonta daga kan angel ta mayar dasu kan Hibba,
“Giant ne yazo ya ɗauke shi, yanzu haka danish yana a treatment room, da zarar yaji sauƙi za’a dawo maku da ɗan uwanku,” tana kai ƙarshen maganarta, ta juyawa ta koma cikin ɗakin nata, taja ƙopa ta rufe,
Kowa ya ji Amsar da tsohuwa ta ba hibba, hankalin su duk bai kwanta ba, Mamaki ƙarara akan fuskar angel tace”dama har treatment room ke akwai a Cikin prison ɗin nan”
Batool ce ta bata amsa da cewa”Eh, amma bakowa ne idan baida lafiya, ake kai shi can ba, Tsohuwa ce take duba lafiyar jikin mu,’
Yau tsawon shekara ɗaya da rabi, bata ta6a jin Zancan wani treatment room ba, sai yau, kuma tun da take da su, da wuya wani acikin su ya yi koda Ciwon kai ne, wani iko na Allah, Lafiyarsu ta banbanta dana sauran Jinsin bil’adaman da ta sani, ita dai hankalin bai kwanta da Treatment room ɗin nan ba, saboda me za’a ɗauke shi daga Cikin su, maimakon tsohuwa ta bincika lafiyar jikin, Shi ne sai an wani ɗauke shi daga cikin su,
Zuciyarta duk ta karaya, Batasan a wani hali yake ciki ba, juyawa tayi tare da nufar toilet ɗinsu, Tana ƙoƙarin shiga ta jiyo muryar haris yana cewa”Ke ce silar Ciwon Danish, saboda jahilin bugun da ki kayi ma shi jiya, idan har muka rasa ɗan uwanmu, kema ki fidda rai da rayuwa” Kasa buɗe ƙopar toilet ɗin tayi Kamar wadda aka dasa ma aya
Muryar batool ta kuma ji tana cewa”Haris dan Allah kadaina wannan maganar, Angel ba ita bace silar rashin lafiyar shi ba, lafiya lou muka wuni da danish, daga baya ne Ciwon ya same shi”
Tsawa haris ya daka mata”Shut up! Dama ae kina bayanta, wa kika fara sani acikinsu? Danish tun kafin ki mallaki hankalin ki kike a tare da shi, amma saboda wata can wadda bamusan da zamanta ba, gaba ɗaya kin kwaye mana baya,” yana huci yakai ƙarshen maganar,
“Dama ba ƙaunarsa take yi ba, shiyasa take son raunata shi,” acewar deeja,
Ta yi niyar ta juya taje ta nakaɗa masu bugu, amma saita fasa, saboda a halin yanzu ita kanta zuciyarta ta karaya,
Buɗe ƙopar ta yi tare da shigewa Ciki, Ta jingina bayanta Jikin bango, siraran hawaye masu ɗumi suka soma gangarowa saman kuncinta,
Ta ɗauki tsawon lokaci bata motsa ba, har saida Taji motsin shigowar mutun a toilet area ɗin, Firgit ta ɗanyi tare da kai idonta kan wanda ya shiga, Batool ce a tsaye tana kallonta,
“Angel meyasa kike kuka? Ko dan saboda abunda suka ce? Bafa laifin ki bane,”
Cikin sanyin murya tace”Ba saboda su nake zubar da hawaye na ba, idan naso zanje in bubbuge su ne, Kawai ina jin ba daɗi, saboda bugun da nayi ma danish jiya, baki ji jikin shi ba jiya yayi zafi sosai, yana a cikin wani hali, kuma nasan Nice silah,”
Dafa kafadarta batool tayi”Dan Allah ki kwantar da hankalin, ki daina zubar da hawayenki, danish fa zai dawo cikin ƙoshin lafiya, tsautsayi ne kuma ya riga da ya faru,’
Murmushin takaici angel ta yi withouth sayin anything,
Saukar tafin hannun batool taji a saman fuskarta, tears ɗin da take zubarwa ta shiga goge mata,
“Ina da saurin kuka, abu kaɗan yake harzuƙa ni,” angel ce ta yi maganar cikin ƙunar rai,
“Koda ace kowa zai juya maki baya, Ki sani Ina atare dake, a koda yaushe zan kasance a hannun damanki,” da ƙwarin gwiwa batool tayi maganar,
Wani irin kallo angel ta ke yi mata mai nuna tsantsar so da ƙauna,
“Da ace mu tagwaye ne Iyaye na suka haifa da sai ince ke ce twin sister ɗina, saboda yadda kika damu dani, kika mayar da damuwarki tawa, Idan ina farin ciki kema kina farin Ciki, haka zalika idan ina baƙin ciki kema kina baƙin ciki, Batool you’re so special, Ina roƙon Allah ya bani damar taimaka ma rayuwarku,’
Ƙayataccen murmushi batool ta ɗan saki,
Kafin tace”Muje muyi wanka, idan muka fito, zan gyara maki gashin kanki, naga duk ya hargitse,” tayi maganar tana ruƙo doguwar sumar kanta, Gashin yayi tsayi sosai har ya zarce waist ɗinta ga uban yawa, yayi datti babu gyara har tashi yake yi, ita fa mantawa take yi da wani gashi akanta, Tun zuwanta kurkukun sau biyar ta ta6a wanke shi,
Cikin shessheƙar kuka tace “Na saba daddyna yake wanke mun kaina, shiyasa nake jin wahalar wanke shi da kaina, ya saba mun da komai, yanzu gashi bamu atare da shi,” zuƙunnawa ƙasa tayi tare da fashewa da matsanancin kuka, da sauri batool ta zuƙunna agabanta, tana lallashinta
“Ashe dama haka rayuwar duniyar take? ni ban ta6a tunanin akwai wani lokaci da zaizo ba, wanda zanyi rayuwa ni kaɗai batare da daddy na ba, kuma ba’a cikin gidan mu ba, sai gashi yau na tsinci kaina a wata sabuwar rayuwa Cikin mutanan da banta6a yin tozali ba, duk yadda naso in jure nakasa, ina kewarka daddyna, inason naganka, nasan bada son ranka ka jefa ni cikin ruwa ba, kayi hakan ne donka ceci rayuwata, meyasa baka bini cikin ruwan ba? Ka tsaya har saida suka kashe ka’?
Natsuwa batool ta yi tana sauraron sambatun da angel take yi, da alama tafara fita hayyacinta,
Mahaifina shine sanyin idaniyata, shine komai nawa, ya gatanta ni tamkar sarauniya, Ya Allah duk wanda yayi silar tarwatsa ƙaunar dake a tsakanin zuciyoyin nan guda biyu, Ya Allah ka ƙasƙantar da rayuwarshi, ka haɗa shi da bala’e da masifa, wanda zasu hana shi runtsawa,’
Duk da batool batasan kan zancen ba, hakan bai hana zuciyarta yin sanyi ba, hawaye suka soma sintiri saman fuskarta,
Girgixa kai ta shiga yi, idanuwanta cike tab da kwalla, fuskarta tayi jawur da ita,
Kallon batool tayi Jin shessheƙar kukanta, ƙaƙaro murmushi angel tayi”meyasa kike kuka”?
Cikin muryar kuka batool tace”Saboda ke angel, ina tausayin rayuwarki”
Itama Cikin muryar kuka tace”Bani bace abun tausayi ba, kune abun tausayi, Nifa na taso ta tare da iyaye na, nasan dangina, Naje makaranta, kuma nayi rayuwar ƴan ci, Ina sanya sutura mai tsada, Inci abinci fiye da sau uku arana, Daddyna yana ɗaukata a cikin motarsa yakaini duk inda nake so, Amma kufa?….daƙyar takai ƙarshen maganar saboda kukan daya ciyota,
“Ba…tool, An cuci rayuwarku, An ƙuntata ku, an hana ku duk wani jin daɗi na duniyar nan, tun kuna yara kuka tsinci kanku acikin gidan kurkukun nan, Bakusan komai game da rayuwar duniyar nan ba, bakusan su wanene Iyayen ku ba, ku kanku bakusan suwaye ku ba, rayuwar kawai kuke yi a kurmance, mutumin da baisan mahaliccinshi ba, idan ya faɗi ya mutu yau, ya farka ya same shi acikin ƙabari Ya zaiyi? A lokacin da yasan gaskiya bayan lokaci ya qure masa, Wlh an cuci rayuwarku, ni kuma indai ina araye duk runtsu duk wuya bazan ta6a bari rayuwarku ta qare ahaka ba, koda kuwa zan rasa raina ne wurin ceton rayuwarku, xan roƙi Allah ya bani tsawon rai saboda ku…………’
tana kai ƙarshen maganarta, ta kifa kanta saman gwiwowin ta, taci gaba da yin kuka kamar ranta xai fita, itama batool ɗin kukan take yi har yanzu hawayenta basu daina zuba ba
Ƙara matsawa tayi tare da ɗaura kanta saman bayan angel, su ka cigaba da yin kukan atare, sun ɗauki tsawon lokaci, kafin batool ta ɗago da kanta daga saman bayan angel,
Calmy ta furta Sunanta”Angel” a hankali ta ɗago tana ƙoƙarin buɗe idanuwanta da suka raunata sosai saboda kukan da ta sha,_
“Batool kinsan komai game da gidan kurkukun nan saboda acikin shi aka raine ki, meyasa ba zaki iya yi mun bayani yadda zan fahimta ba”? Muryarta a sanyaye tayi maganar,
Girgiza kai Batool tayi tare da cewa”Angel bansan komai ba, da ace na sani, bazan iya 6oye maki ba, Ni dai tunda na taso acikinsa, a killace nake bama zuwa ko’ina, bamu san komai ba”
Jinjina kai angel ta ɗanyi tana faman matse hancinta da ya yi jawur,
“Yanzu duk acikin ku, babu wanda yasan wani abu dangane da prison ɗin nan duk irin tsawon shekarun da ku kayi acikin shi”?
Zurfin tunani batool ta shiga, ƙasa ƙasa da murya ta furta sunan”DANISH”
A ruɗe angel ta maimaita sunan”Danish? Ya san wani abu? Ki yi mun bayani pls……’
Cigaba da magana batool ta yi” Idan ma akwai wanda yasan wani abu, To shi ne, danish ne, duk da bani da tabbaci, ” a matuƙar ruɗe angel ke kallonta,
“Sai dai danish bazai ta6a baki haɗin kai ba, saboda yana da wuyar sha’ani fiye da tunaninki, baida yarda, tun fil’azal balle kuma yanzu daya samu lalurar rashin son hayaniya, sai ya ƙara burkicewa,’
“Kina nufin lokacin baya Danish ba haka yake ba’?
Jinjina kai batool ta yi”Eh, daga baya ne ya koma haka, lokaci ɗaya muka rasa gane kan shi, ko bacci yake yi ya dinga furgita kenan yana sambatu, yanzu ne abun ma ya ɗanyi sauƙi,
Dafe kai angel tayi”Ni nasan koda me nake yawo danish bazai ta6a sakewa dani ba saboda ya tsane ni,”
“yana da sauƙin kai angel, sai dai yarda ce baida ita, bai yarda da kowa ba a cikin mu, tsohuwace kaɗai ya yarda da ita,”
Wani wahalallan Murmushi angel ta saki wanda bai kai zuci ba, dafa kafadar batool ta yi”ngde ssai batool, muje mu shiga wankan, idan muka fito sai ki gyara mun gashin kaina,” amsa mata tayi da toh, Atare suka miƙe kowa ya shige cikin toilet,’
Bayan wasu ƴan mintuna kusan atare suka fito daga Cikin toilet ɗin lemar ruwa kwance saman sumar kansu da suka wanke, Lokacin da suka shigo cikin ɗakin a zaune suka samu kowannan su Saman Red Carpet ga kayan breakfast ɗinsu nan an kawo masu,
Giants Suna a tsaye Sun goya hannayensu saman ƙirjinsu,
Yau fa ta 6aci saboda rashin danish, Sun gaza sakin Jiki su ci abinci, Ji su ke kamar ɗan uwansu bazai dawo Cikin su ba, sanin cewa a lokacin baya duk wanda aka ɗauka zaiyi wuya adawo da shi,
babu irin lallashin da Batool batayi masu ba akan suci abinci amma sunƙi Ci, kowa sai dai ya tsakuri kaɗan kamar anyi ma su dole, ganin zasu wulaƙanta abincin yasa ta ɗauko kwandon da take ajiye abinci a cikin shi, ta kwashe rabi da kwata aciki, Ta ajiye masu shi tasan da anjima dole su 6uƙaci cin abinci, idan yunwa ta addabe su,
Bayan tafiyar su Giants, Batool ta ɗauko Comb, ta zauna saman gadonta daga gefe, tace ma angel ta zo ta zauna ta gyara mata gashin kanta,
Angel kaɗai tayi niyar gyarawa gashi, sai gasu rubina dasu Hanna, Sun jera layi suna jira ta kammala gyara mata ga shi, Suma ta gyara masu nasu gashin,
Baƙamar wahala batool tasha ba, Wurin taje masu sumar kawunan su, kowa cikinsu tubarkallah Yawan gashi gare su ga tsayi, In ka cire deeja ita kaɗaice keda gajeran gashi, amma yana da yawa cike da kanta,
Mutum biyar ta yi mawa, ta miƙa ma angel comb ɗin tace Ta gyara ma sauran Huɗun gashi idan ta kammala itama ta gyara mata nata gashin, yinin ranar abunda su ka yi ta yi kenan, hada mazan suma duk saida suka sharce sumar kawunansu, su kansu ba ƙaramin daɗi su kaji ba, da su ka gyara Sumar kawunansu.
*Boss Bature🌷✍️*
Wasa wasa Har dare ya yi ba’a dawo da danish ba, duk sun damu, kowa yana zaune saman gadon shi, ita kanta angel da bata shiri da shi saida ta damu da son sanin a wani hali ya ke ciki, kallon kowannan su ta yi”me zai hana ku kwanta ku yi bacci nasan cikin dare zasu dawo maku da ɗan uwanku,”
Batool tace”angel bazamu iya runtsawa ba, mun saba kwana atare idan har danish bai dawo ba, a zaune zamu kwana”
Ba haka angel taso taji daga gare su ba, taso ace sun kwanta bacci ya ɗauke su, ko dan ta samu damar Bincikar inda danish ya 6oye wuƙar shi,
Takun tafiya suka jiyo da sauri suka kai idanuwansu kan mutumin dake fitowa, tsohuwace ta shigo cikin ɗakin hannunta ruƙe da sanda, ta tsaya tana binsu da kallo,
Da sauri haris dasu Hannah suka sauko daga saman gadajensu su ka nufi wurinta har suna haɗa baki wurin gaishe ta, ta amsa masu fuskarta asake, kafin tace”me ya hana ku yin bacci ne”?
Atare suka haɗa baki wurin furta sunanshi” Danish, har yanzu ba’a dawo mana da shi ba, muna ta jira” ta lura da irin halin da suka shiga,
“Kamar yadda kuke kewarshi shima haka yake kewarku, kuna aranshi,”
“Amma jikin na shi da sauƙi”? Haris ne ya yi tambayar a ƙagare,
Kafin tsohuwa ta basu amsa angel ta sauko daga saman gadonta, ta nufi inda suke a tsaye ido cikin ido suke kallon kallo tsakaninta da tsohuwa,
“Muna so mu gan shi, mu kuma yi mashi ya jiki,” Acewar angel
“Kada ku damu kanku, zuwa gobe danish zai dawo cikin ku,” acewar tsohuwa
“Me zai hana akai mu treatment room ɗin mu duba lafiyar jikin shi”? cike da tuhuma angel ta kuma yi mata tambayar,
“Ba’a bada iznin zuwa inda danish yake ba, saboda ciwon nashi baya son hayaniya”
“Idan muka je ba zamu yi surutu ba, kawai muna so mu ganshi ne” angel ta kuma tambayarta, Hannah tace”pls tsohuwa kibari muje mu duba shi, we really missed our brother”
Girgixa kai ta kuma yi”dare yayi yanzu zuwa gobe zai dawo”
“A yanzu muke son ganin shi, kibar mu muje mana ko akwai wani dalili dayasa baki so muje ne”
“Ke da baki jituwa da shi, meyasa kika damu dashi ne”? Tsohuwace ta jefa mata tambayar, fuskarta ɗauke da wani shu’umin murmushi,
Tur6une fuska angel tayi tare da haɗe rai tace”wannan bai shafe ki ba, wai taya ma akai kikasan cewa bana jituwa da danish? Bayan wannan taya akai kikasan Halin da danish yake ciki, ta wace ƙopa kike bi ki fita daga Cikin ɗakin nan ne? Don ni bana ganin gifcinki, bansani ba ko bangon ɗakinki, kike ratsawa ki wuce, ko kuma layar zane kike yi ki 6ace,
Matashin murmushi tsohuwa ta saki, Yayin da idonta ke akan angel tace”duk yadda kika ɗauka haka ne,” ta6e baki angel ta yi, su haris duk suna sauraronsu batare da wani ya sanya baki ba,
“Danish zai dawo zuwa gobe, iya amsar da zan iya baku kenan, kowa yaje ya kwanta” tana kar ƙarshen maganarta, ta juya tana dogara sanda ta shige ɗakinta tare da jan ƙopa ta datse,
“Wannan munafukin ɗakin ko menene acikinsa, wata rana saina san yadda nayi na kutsa kai cikinsa,” angel ce ta yi maganar acikin zuciyarta, kafin ta kalli su hanna tace”har yanzu kun yadda da matar nan”?
Jinjina kai su kayi alamar eh, harish yace”Tsohuwa bazata ta6a yi mana ƙarya ba, danish yana kar6ar treatment ne, Idan ma akwai wanda ya kamata mu ga laifin shi to ke ce Angel, jiya kamar xaki kashe shi duk Kika yakushe wuyan shi hada cizo saboda tsanar da ki ka yi ma shi” rai a6ace haris ya yi maganar tare da jefa mata harara,
Ya yi tunanin zata mayar mashi da martani, amma sai yaga tana nannaɗe hannun rigarta, tuni yasha jinin jikin shi
“Wlh duk wanda ya kuskura ya ƙara ɗauramun alhakin ciwon danish, Sai na yi mashi jahilin Bugun da zai gaza ta shi” A harzuƙe ta yi maganar, nan da nan kowa yasha jinin jikin shi,
Murya na kerma azeeza tace”dan Allah kowa ya yi haƙuri, nidai bana son tashin hankali, tun da tsohuwa tace mana gobe zai dawo to mu haƙura muje mu kwanta mana”
Sai da batool ta lalla6a kowannan su kafin ta samu, Suka nufi gadajensu kowa ya haye sama ya kwanta
Ya rage saura angel kaɗai a tsaye tana binsu da kallo, Yayin da tunaninta gaba ɗaya yana akan Danish,
Gyaɗa kai tayi tare da juyawa ta koma saman gadonta, har dare ya tsala bata runtsa ba, Allah na gani ta damu da rashin danish acikin su, tana ji aranta kamar wani abun ne zai faru da shi, ko a wani hali yake a yanzu oho Allah wa’alamu,
Lokacin da kowannan su ya yi bacci, tana cikin saƙe saƙe acikin zuciyarta, tajiyo motsin mutun, da sauri ta ƙyalla idonta don taga wanene
Wannan mutumin ne me jajayen kaya har ƙasa, hannun shi ruƙe da kaskon turaren wuta, sai yawo yake yi acikin ɗakin su, yana tafiya yana karanto wasu ɗalasimai, hannun shi ɗaya ruƙe da kaskon turaren wutar ɗayan hannun kuma yana amfani da shi wurin kora hayaƙin zuwa kowani sashe na cikin ɗakin,
Mamaki ne ƙarara akan fuskar angel ga tsoro tana ji, da sauri ta ƙudundune cikin bargonta, ta sanya tafin hannayenta ta toshe hancinta da bakinta kamar yadda ta yi jiya. Aranta tace”Yau ma ya dawo kenan”
Ya jima acikin ɗakin nasu yana turara masu hayaƙin, kafin taji tsit alamar ya tafi, da sauri ta yaye bargon tana faman sauke ajiyar zuciya,
Saukowa ta yi daga saman gadon jikinta na kerma, hasken fitilun nan guda uku ne ya ɗan haskaka Cikin ɗakin, fitila ta ruƙo a hannunta tana haska wurin gadajensu,
Kamar yadda tabi kowanansu jiya har gadon shi ta tottofe shi da addu’a, haka yau ma tabi gadajen su ta yi masu addu’o’i,
A daidai bakin gadon danish ta tsaya tana kallon shimfiɗarshi, bakomai ya faɗo mata aranta ba face jiya da tazo yi ma shi addu’a, ya damƙo hannunta yayi tunanin wani mugun abunne take yi mashi, ɗan abunda ya faru jiya atsakaninsu ya tsaya mata arai, matsawa tayi zuwa gefen gadon ta tsugunna tare da leƙa ƙarƙashin gadon tana haskawa da fitila, ganin babu wuƙar anan, yasa tayi tunanin ɗaga katifarshi,
koda ta ɗaga ƙarƙashin Katifar bata samu wuƙar anan ba, ba ƙaramin takaici taji ba, taso ace Ta gano inda wuƙar take kota samu ta lalata glass ɗin dake ajikin windon toilet ɗinsu,
Allah kaɗai yasan inda ya jefa wuƙar, wata’ƙil ma, ya maida ma tsohowa ita, guntun tsoki taja, yanzu shikenan narasa damar da nake ita? Babu wani makami da zan iya yin amfani dashi wurin rotsa gilashin, kodai naje toilet ɗin In ƙara dubawa? tana yin wannan tunanin ta miƙe da sauri ta nufi Cikin toilet ɗin, Ta tura ƙopar ta shiga daga Ciki, tana haska ko’ina da fitilar hannunta,
Abu biyu ne Yazo mata aranta, na farko Bokitin da ke acikin toilet ɗinsu Na ƙarfe ne, Na biyu kuma wannan tukunyar fulawar dake ajiye Jikin bango, waswasi ta shiga yi kodai tayi amfani da bokitin? ƙwara shi akan tukunyar fulawar, saboda Zata Iya rugujewa azo kuma buƙata bata biya ba, Anyi asara kenan,
Bata kaiga yanke shawarar dame zata yi amfani ba, ba zato ba tsammani Taji saukar hannun Mutun saman kafadarta, awani irin Firgice tayi kwakkwaran juyi Ta daddage ta ɗaga fitilar hannunta zata kwaɗawa mutun daya dafa kafaɗarta, wani irin ihu batool tasaki a tsorace take faɗin”wayyo! Ke ni ce fa, batool ce,’
Nauyayoyar ajiyar zuciya angel ta sauke, Tare da janye fitilar, ta daidai ta natsuwarta, ba ƙaramin dariya batool ta bata ba, ganin yadda ta gigice,
“Allah ya taimake yau, da kin kwanta jinya,”
Dariya batool tayi”Kin ban tsoro me kike yi acikin toilet ne”?
“Ke zan tambaya, dama baki yi bacci ba,? Taya akai kika faɗo mun Cikin toilet batare da neman izni ba, yanzu da ace wani uzirin nake yi fa?
Hannu batool ta sanya tana sosa kai, tace”raina ya bani cewa ba abunda kike yi ne, shiyasa na shigo Ciki, Kuma na ganki Ɗazu zuƙunne agaban gadon Danish bansan me kikeyi ba, Amma ina hasashen wuƙar shi kika je nema halan”
Yatsina fuska angel tayi”I don’t know why kin sa mun ido, ” ta yi maganar da zolaya,
Batool tace”saboda na damu dake”
Ruƙo hannunta angel tayi tare da janta suka fito daga Cikin toilet ɗin, a bakin ƙopar fita daga area ɗin suka ɗan tsaya suna magana,
“Na duba ko’ina batool banga wuƙar ba, kodai ya maida ma tsohuwa ne?”
Girgiza kai batool ta yi “I don’t think so, nafi tunanin yayi mata wani mugun 6oyan ne, shiyasa na baki shawarar ki shirya dashi, Ku samu kusanci sosai, ta hakanne zaki samu damar sanin inda ya ajiye wuƙar,’
Tur6une fuska angel tayi”Anya zan samu yardar danish, Kin fa ce yana da wuyar yarda da mutane, balle ni kuma daya ɗaurawa karan tsana,”
“Ki jaraba ke dai, Danish yana da sauƙin kai sosai, ya danganta da yarda kika tafiyar dashi, amma wani hanzari ba gudu ba, har yau baki faɗa mini me zaki yi da wuƙar Ba!? I ave to know,’
Ta tsareta da ido tana jiran jin amsar da zata bata, ƴan kame kame angel ta shiga yi don batasan batool ta gane ainihin abunda zata aikata, tasan bazata bari ba, zata yi kokarin dakatar da ita ne
Ganin tana ƙoƙarin ƙara tambayarta yasa tayin saurin katse mata hanzarinta da cewa
“Ko kinsan akwai wani mutumi da ke zuwa ɗakin mu tsakar dare yana yawo da kaskon turaren wuta a hannunshi?
Tayi maganar a kokarin ta nata gusar mata da zancen wuƙa,
“Yaushe kika ganshi”? Angel tace”ko yau yazo, jiya ma na ganshi, idan yazo Sai yaita yin magana cikin wani irin yare mara daɗin ji, sannan yana bin kowani gado yana kora hayaƙin zuwa kowani sashe na ɗakin mu,”
Maimakon taga mamaki akan fuskar Batool, sai taga ta saki murmushi tare da cewa” kada ki damu kanki angel, tsohuwace ae kullum idan dare ya tsala sai ta shigo ɗakin mu, ta turara mana hayaƙin Kariya,”
Maimaitawa angel tayi’hayaƙin kariya kuma? Jinjina kai batool tayi eh, mun ta6a tambayarta hayaƙin menene tace mana hayaƙin kariya ne daga sharrin baƙaƙen aljanu domin kuwa akwai su acikin kurkukun nan, kuma hayaƙin yana da waraka acikin shi, shiyasa zaki ga ko ciwo bamu cika yi ba”
Angel tace”Ni a iya sani na, idan har za’a ba mutun kariya ba hayaƙi yakamata ayi mashi ba, addu’a ya kamata ayi ma shi, sam ni ban yarda cewa hayaƙin kariya bane, dole akwai wani 6oyayyan sirrin a tattare da shi,”
Kafin batool ta kuma cewa wani abu, suka jiyo sautin shessheƙar kuka daga can cikin ɗakin su,
“Wanene ke kuka”? Angel ce tayi tambayar tana kallon batool,
Batool tace “Muje mu duba, ina tunanin Aziza ce, “
da sauri suka fito daga area ɗin toilet, suka faɗo cikin ɗakin, haskata Angel ta yi da fitilar hannunta, a tsaye suka ganta tsakiyar ɗakin sai kuka take yi tana laluban hanya saboda lalurar da take fama da ita, ta makantar dare (nyctalopia) bata iya gani idan dare yayi, ko kuma idan babu wadataccen haske, haka suke fama da ita, in ta farka zata shiga Cikin toilet, sai ta dinga kuka tana ambaton sunayensu har sai wani ya farka acikinsu ya rakata,
Tun lokacin da angel tayi noticing lalurar yarinyar, sai da tayi ma batool magana ta tambayeta tun yaushe take fama da ita? Batool ta bata amsa da cewa”tsohuwa tace haka aka halicce ta, da zarar dare yayi ganin ta ya ke ɗauke wa, koda an kunna hasken fitila biji biji take gani” tun daga wannan lokacin angel take jin tsananin tausayinta, tana matuƙar jin yarinyar acikin zuciyarta,
*❤❤❤PRISONERS❤❤❤*
Ƙarasawa suka yi inda aziza taka a tsaye Angel ta ruƙo hannunta,
“Its ok stop crying muna atare dake, Ina zaki je ne”?
Cikin shessheƙar kuka tace”Fitsari nake ji ya matse ni,”
Bari naje na rakata, takai ƙarshen maganar tare da ruƙo hannun azeeza, suka nufi toilet, gefen gado batool ta koma ta zauna tana jiran fitowarsu, badajimawa ba Angel ta fito hannunta ruƙe dana azeeza, har saman gadonta takaita sai da taga ta kwanta, ta janyo mata duvet ɗinta ta lullu6a mata shi saman jikinta, tana jiyo muryar azeeza ta cikin bargon tana faɗin”I luv u so much angel,” murmushi angel ta saki tare da cewa”Luv u too my sister, Allah ya kare mun ke, ki amsa da ameen” tana jiyo muryarta tana faɗin”Amen” ba ƙaramin daɗi taji ba, wuce wa tayi zuwa nata gadon ta haye ta zauna tare da jingina bayanta,
“Ba zaki kwanta ki yi bacci ba”? Batool ce ta yi mata tambayar,
“Zan kwanta, Ina yin addu’a ne ko baki gani ba” kallonta batool tayi ganin ta ɗaga hannayenta biyu sama tana magana cikin harshen da bata sani ba, da larabci take yin addu’ar,
“Nima kiyi mun addu’ar, inaso,”
Angel tace”Toh, ki kwanta kiyi bacci, zanyi maki addu’a,” amsa mata tayi da toh , kafin ta kwanta,
Bayan angel ta kammala yin addu’ar ta ta sauko daga saman gadonta, tabi kowani gado ta tottofe su da addu’a, bayan ta kammala ta koma saman nata bed ɗin ta kwanta,
Daƙyar ta samu bacci ya yi awon gaba da ita, har mafarkin danish sai da ta yi saboda ta sanya wa ranta shi sosai,
Slowly ta soma ƙoƙarin buɗe idanuwanta, dishi dishi ta dinga ganin mutane kewaye da gadonta, sanya cikin baƙaƙen kaya hannunsu zaƙo zaƙo da dogayen akaifu, Kowanne ya ɗaga gudumar dake hannunshi da niyar rotsa mata kanta, A gigice angel ta zabura tana faɗin”Innallallahi wa’inna ilaihirraji’un” sautin dariya taji ta ko’ina acikin kunnanta, hannu tasa ta murza idanuwanta, tare da ware su akan mutanan da take gani, Su batool ne a jere, Sun nannaɗe hannayen rigunansu, Sai faman haki suke yi suna nishi kamar waɗanda suka sha gudu
“angel tun ɗazu muke jira ki bamu wani training ɗin, duk mun iya wanda kika koya mana” rubina ce tayi maganar,
Nauyayyiyar ajiyar Zuciya angel ta sauke, Ashe idanuwanta badai dai suke nuna mata ba, tayi tunanin wasu shaiɗanun aljanune suka kawo mata ziyara,
“Ki tashi Muje mu motsa jikin mu atare” Acewar batool,
Muryarta a disashe tace”Kun takuramun, ba haka ake ta shin mutun daga bacci ba, duk kun tsoratar dani” taƙarasa maganar tana jifarsu da harara hada murguɗa masu baki, gaba ɗaya suka tuntsire da dariya,
Muryar javed taji yana faɗin”Zata taso ko sai munzo mun cuccu6eta”? ya yi maganar yana naɗe hannun rigarshi, ɗaya bayan ɗaya take kallon fuskokinsu, zufa sai tsastsafowa take yi daga jikin su,
Ba ƙaramin burgeta su kayi ba, fuskarta ɗauke da murmushi tace”me yayi zafi javed, yanzu zan taso amma fa saina fara shiga toilet, “
Har suna haɗa baki wurin cewa”To kiyi sauri ki fito, muna jiran ki,” ƙarasa janye bargon Jikinta tayi tare da saukowa daga saman gadon, Suka matsa mata hanya tabi ta wuce,
Walking slowly ta nufi ƙopar shiga makewayinsu, Harta ruƙe handle ɗin ƙopar da niyar ta buɗe sai kuma ta ɗan dakata tare da juyawa tana kallon Haris dake kwance daman gadonshi, idanuwanshi na fuskantar ceilling, da alamun damu atattare dashi, tasan bakomai ya jawo hakan ba, face rashin ɗan uwanshi danish don ta lura ba ƙaramin ƙaunarsa yake yi ba, Yau ce rana ta farka da tafara Jin tausayin haris, duk yabi ya ƙuntata kan shi saboda rashin danish, Allah sarki danish kowa Jikin nashi yake”?
Janye idanuwanta tayi daga kan haris ta mayar dasu kansu Parveen dake a tsastsaye, Tace”Har yanzu ba wani labari game da dawowar danish”?
Jinjina kai su kayi”eh, mu ma munyi expecting ɗin idan muka farka daga bacci zamu same shi kwance a cikin mu, ashe ba’a dawo mana da shi ba”
In brittle voice Azeeza tace”nadamu da rashin ɗan uwanmu, Jiya har mafarkin danish nayi, Allah yasa su dawo mana da shi, idan ba haka ba ni ko abinci bazan Iya ci ba” muryarta tamkar zata fashe da kuka,
Mubeen yace”nikaina daurewa kawai nake yi amma gaba ɗaya zuciyata a raunace take da rashin danish” yana rufe baki, Naufal yace”idan har jikin danish baiyi sauƙi ba, Zaiyi wuya su dawo mana da shi yau” zuciyarshi a karaye yae maganar,
“Ni abunda nake jima tsoro ma, kada a ƙi dawo mana dashi, kamar yarda ake yi mana a lokacin baya” Da sauri angel ta kalli fuskar batool da ta yi maganar, a yanayi na jin farga ba, tunawa tayi da tattaunawarsu da ita jiya a cikin toilet area, Inda batool take faɗa mata cewa”A lokacin baya duk wanda aka ɗauko acikinsu ba’a dawo dashi, He has gone forever,” da sauri ta shiga girgiza kai tana faɗin”that’s impossible, danish must be back, ku kwantar da hankalinku, babu abunda zai same shi, bana so inji kuna xancen cewa ba lallai danish ya dawo cikin mu ba, ‘ a harzuƙe takai ƙarshen maganar tare da buɗe ƙopar ta shige ciki, Koda ta shiga cikin toilet ɗin a jikin bango ta jingina bayanta, Idonta akan windown nan data kwallafawa ran son fasa ta,
“Da ace xan iya samun damar rotsa gilashin nan, dana yi ƙoƙarin binciko inda treatment room ɗin nan yake, kodan saboda inga danish, bawan Allah, ni tsorona ma kada ya rasa ranshi batare da ya kar6i kalmatusshahada ba, banaso ɗaya daga cikin su ya rasa ranshi batare da na musuluntar da shi ba, idan har hakan ta faru i won’t forgive my self, tabbas zanyi asarar jinkirin da nayi,’ cikin shessheƙar ku ka tayi maganar tuni hawaye sun soma sintiri akan fuskarta, ta ɗauki tsawn lokaci a tsaye batare da ta ta6uka komai ba, Har sai da tajiyo muryar Batul daga waje tana kwala mata kira”Angel! Angel! Kixo mu yi breakfast giants sun zo, ke kaɗai muke jira” Daƙyar ta iya ɗaga murya tace”Kada ku jira ni, ku fara kawai,”
Takai ƙarshen maganar tare da sanya hannayenta biyu Ta tu6e kayan jikinta asaman igiya ta ɗaura su, wanka ta samu tayi bayan takammmala ta mayar da kayan Jikinta,
Lokacin da ta fito daga Cikin toilet ɗin, A zazzaune ta same su saman red Carpet, a tsakiyarsu wooden trays ne na kayan abincinsu, kowa ya hallara banda mutun biyu ita da kuma Haris dake kwance yana kallon ceilling, yadda tabarshi haka ta same shi,
Ba irin lallashin da batool ba tayi mashi ba akan ya taso yaci abinci amma ya kafe akan sai an dawo mashi da ɗan uwanshi, a dole suka ƙyale shi,
A hankali angel ta ɗaura idanuwanta akan su giants dake a tsaye kamar gumaka sun goya hannayensu saman ƙirjinsu,
Maimakon taje ta zauna taci abincin, sai gani su kayi ta nufi Inda su giants suke a tsaye, A ruɗe batool ta shiga kiran sunanta tana faɗin”Angel where are u goinig? Ki zo muyi breakfast” ko kallon inda batool take ba tayi ba, Tana ƙarasawa gaban giants, taci burki ta tsaya tana ƙare masu kallo, ga tsoronsu tana ji haka nan ta daure ta cije, ganin kanta take yi wata ƴar ƙaramar halitta agabansu, saboda a Halittar jikinsu, Gabza gabza ne ga ƙirar jiki mai matuƙar razanarwa,
“Pls angel kada kija mana muna zaman lpy, ki dawo ki zauna acikin mu muci abinci” hanna ce tayi maganar,
Yasmin ma tace”Angel, giants basa ji basa gani, Kada ki ce zaki tanka masu, suna iya yi maki illa” Kowa yasha Jinin Jikin shi, duk tana sauraron magiyar da suke Yi mata, amma taƙi koda juyawa ta kalle su, hatta haris dake acan kwance saman gadonshi, Ganin angel agaban giants Yasa shi yin zumbur ya miƙe zaune yana kallon Ikon Allah, Azeeza har ta fara kuka saboda tsabar tsoron kada su cutar da angel,
Sai da angel ta gama kalle su daga ƙasa har sama, Kafin tace”Ko dabba idan a ka yi mata magana tana responding ballanta kuma ku da kuke Jinsin bil’adama, Meyasa a koda yaushe Kuke yin 6adda kama idan zaku zo wurin mu? Why? u can’t even talk to us? Saboda rashin gaskiya wato kuna tsoron muga fuskokin ku saboda gudun kada mu tona maku asiri nan gaba idan Allah ya ku6utar damu ko? Tayi tambayar cike da tuhuma tana kallon su, Ko motsi wannan ba suyi ba, Balle ma ta gane cewa suna sauraronta,
“Ko gunki bazai nuna maku yadda ake tsayuwa ba, agoya hannu saman ƙirji, ku dai ga ku nan wasu hamagawa da ku, to kodai ba mutane bane ku? Nafi zargin cewa ku ɗin Robot ne, wato sarrafa ku akeyi daga Can sama, ta yadda baku iya furta komai sai an baku izni koba haka ba”? Tayi tambayar a harzuƙe tana kallonsu,
Su batool sai faman lalla6a angel suke yi akan ta daina yi masu magana tazo suci abinci, amma ƴar tahalikar nan ko kallon inda su ke ba ta yi ba, sai ma cewa tayi”Su rabu da ita, Suci abincin su, Yau sai taga abunda ya turewa buzu naɗi, a tsakanin da giants dole suyi mata magana,
Atsiwace tace”Ba zakuyi mun magana ba? wlh duk ranar da wani ya kuskura acikin ku, Ya furta koda kalmar A ce, zan gano ko wanene shi koda bansan shi ba, idan har naji muryarshi awani wuri zan shaida shi ne, saboda Allah yayi mun baiwar tantance muryar mutane,” A zafafe takai karshen maganar, ga yunwa tana ji amma taƙi zuwa taje taci abinci,
Ruƙe qugu tayi”meyasa baku dawo mana da danish ɗin mu ba? ina kuka kai mana ɗan uwan mu? Tsohuwa tace kune kuka zo kuka ɗauke shi”? Tayi maganar tana faman haɗiyar yawu,
Aiki fa ya ga angel , ita kaɗai sai sambatu take yi kamar wata zautacciya,
Ganin taƙi zuwa taci abinci Yasa batool taje ƙarƙashin gadonta, ta ɗauko kwandonta, ta kwashe ragowar sauran abincin da suka Ci, da niyar ta ajiye ma angel da haris,
“Giants we are done,” Javed ne ya sanar dasu, yayi hakan ne don su samu su tafi, kafin angel takaiga ƙure su, don in suka fusata, komai zasu iya aikatawa,
Ta gefen angel suka bi suka wuce, Tattara kayan Abincin su kayi a jera suka nufi benan, Ganin zasu tafi basu bata amsar tambayarta ba, yasa ta watsa da gudu ta riga su hayewa saman benen, a jikin ƙofar ta jingina bayanta tare da ware hannyenta, wato ta toshe masu hanyar sa zasu bi su fuce,
Tsayawa su ka yi a tsaye saman matattakalar benan, tunda suke aiki a prison ɗin, basu ta6a ganin hatsabibiyar yarinya irin wannan da take agabansu ba, da ace tasan irin hatsarin dake gare su da bata yi gigin shiga huruminsu ba,
Kallon kallon aka soma Yi atsakaninta angel dasu giants, Hankalin su Batool yayi matuƙar tashi, duk suna a tsaye bakin benan sai roƙon angel su ke yi akan ta matsa ta basu hanya su wuce, ba iri magiyar da basuyi mata ba, amma angel ta maƙe kafaɗa akan bazata matsa ta basu hanya ba, Ita so take taga ikon Allah Shin giants zasu Yi mata magana akan ta basu hanya su wuce ko kuwa”?
Cikin muryar fushi haris Yace”wai ke baki da hankali ne? Ba zaki matsa ki basu wuri su wuce ba? an faɗa maki basa magana, idan ma abunda kike ma hari kenan,” rai a6ace tace”babu ruwan kowa dani, ku kama harkar gaban…….”
bata kai ƙarshen maganar ba, Taga ɗaya daga Cikin giants ɗin ya miƙa ma na gefenshi Kayan abincin dake a hannunshi, Ya kar6a ya haɗa dana hannunshi, Zuba ido tayi tana jira taga me zasu Yi mata, wani irin zazzafan taku giant ɗin yayi yadda kasan Zaki Ya nufi abun harinsa, tuni jikin angel ya soma kerma, ta ƙanƙame jikinta tana girgiza mashi kai, muryarta na kerme ta shiga faɗin”wlh kada ka kuskura ka ta6a…..”bata kai ƙarshen maganar ba, Taji ya damƙi qugunta ya ɗaga ta sama, yadda kasan ƴar tsana, ta dinga ihu tana kuka tamkar ranta zai fita, saukowa da iya yayi daga saman benan, Su batool duk sunyi tsuru tsuru suna kallon shi,
Daga inda yake yayi wurgi da angel Wani iko na Allah, Saboda tsabar iya saitinsu, bata faɗa ko’ina ba sai saman gadonta, gaba ɗaya ta kife sumar kanta duk ta tarwatse saman mattress ɗin, Juyawa Giant ɗin Yayi ya koma inda sauran ƴan uwan nashi suke, buɗe ƙopar su kayi suka fuce tare da datseta,
Kusan atare su Azeeza suka sauke ajiyar zuciya, jiki na rawa suka nufi angel, wadda tunda giant ya wurgar da ita saman gado bata ƙara motsi ba,
Jikinta gaba ɗaya ya mutu, tamkar wadda aka zarewa laka, Ta furgita sosai lokacin Daya jefar da ita, har wasu baƙaƙem turari masu wutsiya ta dinga gani acikin idanuwanta,
Hayewa saman gadonta, Batool hanna da azeeza sukayi, Sai kokari suke yi wurin ɗago da ita,
Su javed mubeen da Su Deeja duk suna a kewaye da gadon,
“Angel,angel.pls wake up! dan Allah ki tashi angel, Muna atare dake Kinji?
Suna magana suna jijiga jikinta, Haris yace”laifinta ne, tun farko saida muka gargaɗeta amma saboda taurin kai irin nata taƙijin maganarmu, yanzu wa gari ya waya ” yayi maganar Cikin halin ko’in kula,
Eve tace”bari naje na fada ma tsohuwa, azo a duba lafiyar jikinta” da hanzari ta juya ta nufi ƙopar ɗakin tsohuwa, Kafin ta kwankwasa ƙopar ɗakin sai ga tsohuwa ta buɗe ta fito hannunta ruƙe da sanda,
“Meke faru wa ne yara”? Her voice was shaking tace”an…gel…ce
…..bata motsi…’
“Keep calm and tell me what’s wrong, with her? is she not feeling well?
Jinjina kai Eve tayi”Giant ne ya wurgar da ita, Tun ɗazu muke akanta, bata farka ba, ko motsi ba ta yi”
Gaba ɗaya hankalinsu ya dawo kan tsohuwa suna jira suji amsar da zata basu,
Jinjina kai tsohuwa ta ɗanyi tare da cewa”Yarinyar ce taci ka kafiya, sam bata jin magana, shiyasa bana so kuna yin koyi da ita, domin kuwa zata 6ata maku tarbiya ne, tun tana yarinya ba ƙaramar hatsabibiya bace…….” gaba ɗaya tsohuwa ta takwashe tarihin rayuwar angel ta sanar dasu, hatta bugun da tasa ƴan ƙato da gora su kayi ma Mahaifinta, kuma a ƙarshe tace masu itace silar da mahaifinta ya rasa ranshi,’ da alama tsohuwa tana ƙoƙarin dasa masu kiyayyar angel acikin zuciyoyinsu ne, gaba ɗaya sun saki baki galala suna kallonta,
Batool ce tayi kokarin cewa”Amma angel ta faɗa mun cewa daddynta wasu ne suka kashe shi, kuma shine ya jefa ta Cikin ruwa, ” bazawarin murmushi tsohuwa tasaki tare da girgiza kai tace”Ƙarya take yi maku, muguwar makirace, Ta faɗa maku hakanne don ku tausaya mata ba”
Aruɗe azeeza tace”amma angel bazata ta6a yi mana ƙarya ba, saboda tana son mu dagaske, Kuma idan bazan manta ba, lokacin da aka kawo ta kurkukun nan, kefa da kanki kika ce zaki faɗa mata waɗanda suka kashe mahaifinta, meyasa yanzu kuma zaki ce mana itace tayi silar mutuwar shi!”? Cike da tuhuma azeeza ta jefa mata tambayar, sam tsohuwa batayi tsammani wani daga Cikinsu zai iya yi mata gaddama ba, tabbas an fara samun matsala,
“Kinyi shiru baki bamu amsa ba tsohuwa? Kodai azeeza tayi gaskiya ne?
Lamarin yayi matuƙar ɗaurewa tsohuwa kai,
Javed yace”Nima idan zan Iya tunawa keda kanki tsohuwa kika ce Iyayenta sun rasu, hakan na nufin ita kanta angel ɗin batasan cewa iyayen nata sun rasu ba, sai a bakin ki taji hakan, But why kike kokarin ɗaura mata laifin kashe Daddynta? anya kuwa tsohuwa?ya kai ƙarshen maganar da alamun kokwanto,
Haris dai ya rasa bakin magana ba, hatta sauran duk sun natsu suna jiran amsar da tsohuwa zata basu,
Rai amatuƙar 6ace, tsohuwa ta buga sandar hannunta kasa, Nan take kowannan su ya toshe kunnuwanshi, sakamakon sautin buga sandar daya doki dodon kunnuwansu,
Da kakkausar murya tace”Zan sake maimaita maku, Kudaina yarda da maganarta, Ni kaɗai ce na isa da ku, Babu wani mahaluƙin daya isa ya sarrafa tunaninku, Ina fata an fahimce ni” Da sauri suka amsa mata da toh,
Cigaba da magana tayi”Angel ba sonku take yi ba, sam bata ƙaunarku, tana so ta shiga tsakanina daku ne, Ni kuma bazan bari hakan ta faru ba, saboda bana so ta gur6ata ku kamar yadda take gur6atacciya” A ladabce suke amsa mata da toh, deeja tace”Amma idan muka ce zamu ƙi bin Umarninta, Zata karanta mana charman dudu ne Cikinmu ya kumbura, shiyasa muke jin shakkarta”,
Wata irin mahaukaciyar dariya tsohuwa ta saki aranta tace”Yarinya sai ɗan banzan wayau uwa dila agari” a fili kuma tace masu”Charman dudu ba wani mummunan abu ne, Angel tayi maku wayau ne don ta tsoratar daku, Saboda ta lura bakusan ainihin ma’anar kalmar ba” cike da mamaki suke kallon Juna, Jin abunda tace, Batool tace”zamu iya sanin ma’anar Kalmar”?
Jinjina kai tsohuwa tayi, Cikun hikma ta fayyace masu komai game da asalin kalmar charman dudu, har waƙar ta raira masu, ‘ ransu ya 6aci sosai, irin yadda angel ta azabtar dasu da kalmar ashe ma waƙa ce ba abun cutarwa ba, sunji haushi sunji takaici, musaman haris da Deeja,
“Daga yanzu, Ku daina yarda da duk wani abu da zata faɗa maku, saboda wayau ne da ita, so take ta burkita maku lissafi” acewar tsohuwa,
Parveen tace”Amma tsohuwa menene ma’anar Sunan Allah dakuma Bil’adama? Angel tace mana Allah shine Ya halicce mu dagaske ne”?
Har saida tsohuwa ta zabura jin tambayar da parveen tayi mata, Lokaci ɗaya kuma ta murtuƙa fuskarta tare da cewa”Shima duk ƙarya take Yi maku, babu wani Allah, idan harta ƙara matsa maku akan Ku yarda cewa akwai Allah, Ku sanar da ita cewa Ta kira maku shi ku ganshi da idonku, Kafin Ku yarda dashi anan zaku tabbatar da cewa ita ɗin babbar maƙaryaciya ce,” takai ƙarshen maganar fuskarta ɗauke da wani irin munafukin shu’umin murmushi, irin na tantiran ƴan duniyar nan waɗanda suka ga jiya suka ga yau,
Aka ce rashin sani yafi dare duhu, gaba ɗaya sunyi amanna da maganar tsohuwa,
Ganin taci galaba akansu yasa ta Juya tana dogara sanda ta koma Cikin ɗakinta, Tare da jan ƙopa ta datse,
Abunda ya faru tun lokacin da tsohuwa ta buga sandar hannunta, gaba ɗaya Tunaninsu ya canza, daga gardamar da suke yi mata zuwa bin umarninta, yanzu gaba ɗaya sun ɗauki maganarta, aransu duk sunji sun tsani angel saboda ta kashe mahaifinta, tsoronta ma suke Ji yanzu kada suma ta kashe su, ga haushin ƙaryar da tayi masu na Kalmar Charman dudu da take yi masu barazana da ita, jira suke tafarka suci ubanta, Bayan wannan kuma tayi masu ƙaryar cewa akwai wanda ya halicce su, lallai angel tana a tsaka mai wuya fidda ta sai ALLAH,
Ta yi matuƙar karya masu zuciya, Jikin su duk yayi lakwas tamkar an zare masu laka, tafiya suke yi kamar mashayan giya, Idon kowa na akan gadon angel dake kwance magashiyan rai hannun Allah, Ji suke kamar su rufe ta da bugu har saita gaza tashi,
Komawa su kayi saman gadajensu Zuciyoyinsu sai tafarfasa suke yi saboda tsabar 6acin rai, Kowa ya shiga faɗin Laifin da angel ta aikata mashi da kuma irin fansar da zasu ɗauka akanta idan ta farfaɗo, don sunci alwashin sai sun raunata Sassan Jikinta,
Tsawon awanni angel ta ɗauka, Ba ita ta ta shi farkawa ba, Sai Wuraren marece, Da wani irin yunƙurin amai ta farka, da gudun gaske ta duro daga saman gadonta, idanuwansu akanta babu wanda yayi yunkurin zuwa ya taimaka mata,
Toilet ta shige a galabaice Ta zuƙunna gaban tap tana kwarara amai, bakomai ke fitowa daga Cikin bakinta ba, face xallar ruwa, Cikinta sai tuƙuƙun azaba yake yi mata, har wani jiri take Gani, Cikin shessheƙar kuka take ambaton sunan Batool don tazo ta taimaka mata,
Batool tana jin muryar angel cikin mawuyacin hali amma zuciyarta ta hanata zuwa inda take, Kowa haushinta yake ji, An canza masu tunaninsu, hatta azeeza da tafin kowa jin tausayi ayau itama ta juya ma angel baya,
Koda taji batool bata amsa mata ba, sai ta shiga kiran sunayensu ɗaya bayan ɗaya, suna jinta amma su kayi kunnan uwar shegu da ita,
Numfashinta sama sama yake fita da hucin zafi, bugun zuciyarta ya ƙaru sosai, hakanan ta dinga jin kamar wani abu zai faru da ita, dakyar ta samu aman ya dakata da zubowa, ta kunna tap ruwa ya shiga kwararowa, Ta tarba tafin hannayenta, ruwa ya taru acikinsu, ta kuskure bakinta tare da wanke fuskarta,
Sam takasa ta6uka komai, saboda tashin zuciyar da take ji, Ga jiri da take gani acikin idanuwanta, temperature ɗin Jikinta yayi zafi sosai da alama zazza6i ne ke shirin yi mata mugun kamu, tana ƙoƙarin miƙewa amma ta kasa cos she’s feeling dizzy idan ta yi attempting miƙewa tsaye,
Bata fasa neman ɗauki daga wurinsu ba, Taci gaba da ambaton sunayensu”Batool! Azeeza! hibba” muryarta a disashe take maganar daƙyar ma take ƙoƙarin ɗaga muryarta, Jin basu amsa mata ba, yasa ta soma kiran sunayen mazan dake acikinsu
“Javed! Mubeen! Naufal!’ nan ma taji shiru basu amsa mata ba, lumshe runannun idanuwanta tayi tare da cizon lower lip ɗinta,
Daga Can Cikin ɗakin kuwa, Hankalin batool yaƙi kwanciyar, tana so taje ta taimaka mata amma zuciyarta taƙi bata haɗin kai, Idan ma tayi motsi kamar zata sauko daga saman gadonta, sai haris ya dakatar da ita tare da cewa”duk wanda ya kuskura yaje da niyar taimakata, babu ruwan mu da shi,” tunzurasu yake yi duk don saboda kada suje su taimaki angel
In taƙaice maku zance, A gajarcanshi Har dare yayi babu wanda ya motsa daga Cikin su, Sun bar angel acikin toilet ita kaɗai, tun tana kiran sunayensu har tagaji tadaina, baiwar Allah ta shiga mawuyacin hali, anan cikin cikin toilet ɗin ta kwanta saman floor ɗin, abu uku suka haɗe mata a lokaci ɗaya, Ciwon kai, raɗaɗi da Cikinta ke yi mata da kuma matsiyaciyar yunwar data addabe ta, yinin ranar ko ruwa bata kora ma maƙoshinta ba, ya bushe ƙamas har wani ƙaiƙayin azaba yake yi mata,
Kafin su kwanta bacci, sai da suka cinye abincin angel da batool ta ajiye masu ita da haris, Koda su ka kammala cin abincin, Zaman jiran dawowar Danish Suka tsaya yi, har saida tsohuwa ta fito daga Cikin ɗakinta ta same su a zazzaune saman gadajensu, ganin damuwa akan fuskokinsu yasa tace”Akan danish ne”? Har suna haɗa baki wurin amsa mata da eh, Shiru ta ɗanyi tana kallonsu kafin tace”ku ƙara haƙuri, danish bazai samu damar dawowa yau ba, jikin nashi yayi tsauri sakamon Illar da ƴar uwarku angel tayi mashi, akwai wani dafi a hannunta wanda ku baku sani ba, idan har ta yakushi mutun kota gartsa mashi cizo, ya ɗauki tsawon lokaci ba’a bashi emmergency treatment ba, Dafin yana Illata sassan jikin shi ne, kuskuren da mu kayi shi ne, da bamu yi gaggawar miƙa dashi zuwa treatment room ba, lokacim da Angel tayi mashi wannan jahilin bugun, Shiyasa har Dafin yayi mashi illa ajikinshi………” dakatawa ta yi da yin maganar fuskarta duk a harmutse duk don su yarda da abunda take faɗa masu, Cikin jin ƙunar rai haris yace ” idan har ɗan uwanmu ya rasa ranshi saboda ita, bazamu ƙyale ta ba, ita ma sai mun kashe ta” yana rufe baki deeja tace”Ae dama ba son shi take yi ba, muguwa kawai, tun da tazo gidan kurkukun nan, ta ɗaura mashi karan tsana ni bansan me danish ya tsare mata ba, ” takai kai karshen maganar tana huci,
Haris Yace” Yadda tayi ma danish Jahilin bugu, muma sai mun rama mashi, In yaso suyi jinyar atare”
Yasmin tace”ƙwarai kuwa, Muje mu same ta har inda take, mu nakaɗa mata bugu har sai ta kasa tashi,”
Tsohuwa ta fakaici idonsu ta saki wani irin kafin murmushi, hanya mafi sauƙi da zata koya ma angel hankali, saboda rashin kunyar da take yi mata,
Cikin sanyin murya batool tace”Bai kamata mu ce zamu bugeta ba, wannan ba dai dai bane, saboda ita ɗin yarinya ce duk mun girmeta, bugu bashi zaisa ta gane kuskurenta ba, idan muka daina shiga sabgarta ma ya wadatar, daga yanzu babu ruwanmu da ita, har sai danish yaji sauƙi ya dawo cikinmu tukunna zamu waiwayeta,”
Azeeza tace”na goyi bayan shawarar da batool ta bada,” suma sauran su ka ce duk sun goyi bayanta, banda haris da deeja,
“Tsohuwa yanzu Sai yaushe kenan zamu sake ganin ɗan uwanmi? Idanuwanmu sun yi maraicin rashin ganin shi” javed ne yayi maganar muryarshi a sanyaye,
Tsohuwa tace” A yadda mu ka tattauna da giant, Ya sanar dani cewa”Danish zai ɗauki Tsawon kwana Biyar Kafin ya dawo cikin ku,”
Ransu ya ƙara 6aci jin cewa sai ya ɗauki tsawon kwana biyar kafin ya samu sauƙi, Kamar su ɗaura hannayensu saman kawunansu su fasa ihu, haka suke ji saboda tsabar takaici, tsanar da su kayi ma angel ta ƙara ninkuwa acikin zuciyarsu,
“Kowa ya je ya kwanta, Mu kwana lafiya Yara na” takai ƙarshen maganar tare da juyawa tana dogara sanda Ta nufi ɗakinta, ta shige tare da jan ƙopa ta datse,
Kallonsu batool tayi”Mu yi haƙuri muje mu kwanta,” gyaɗa kai su kayi kowa Ya wuce zuwa saman gadon shi Ya kwanta,
Gaba ɗaya duk tattaunawar da su batool su kayi tare da tsohuwa akan kunnan angel, baiwar Allah da rarrafe ta fito daga Cikin toilet, ɗin abakin ƙopar shiga ɗakinsu, Ta zauna tare da jingina bayanta, saboda takasa ƙarasa tafiya cikin ɗakin, Kaf taji irin ƙalin sharrin da tsohuwa tayi mata, sai yanzu ta gane dalilin dayasa suka juya mata ba, Lokacin ta take ta kiransu acikin toilet don su kawo mata agaji, ashe sun jita suka ƙi zuwa, saboda tuggun da tsohuwa ta ƙulla mata,
Jikinta duk yayi sanyi, zuciyarta ta karaya, Don sun ɗauki gaba da ita wannan ba damuwarta bace, ta yi masu uziri saboda jahilcin dake ɗawainiya dasu, ita tausayinsu ma take ji, yadda ake ta juya masu tunaninsu, wanda da ace suna da wayau babu wanda ya isa yayi masu haka,
Abu uku ne yafi tsaya mata arai, na farko shine Batool, bata ta6a tsammanin batool zata Juya mata baya ba, Tunanowa tayi da maganarsu ta jiya da kanta take faɗa mata cewa”Koda ace kowa zai juya mata, Ita tana atare da ita, kuma a koda yaushe zata kasance a hannun damanta, amma sai gashi yau ba irin kiran sunan batool da batayi ba aka tazo ta taimake ta amma taƙi zuwa, Abu na Biyu kuwa meyasa tsohuwa take Yi masu ƘARYA? da girmanta tsofe tsofe da ita? ƙaryafa alamace dake nuna cewa mutun baida gaskiya, lallai wannan matar ba ƙaramar makira bace, abu na ƙarshe daya tsaya mata aranta shi ne DANISH! A wani hali yake ciki? Meke faruwa da shi? meyasa baza’a dawo da shi cikinsu ba? Jiyafa tsohuwa da kanta tace masu yau zai dawo, amma kuma yau sai gashi ta canza magana, meyasa❓❓❓
Ta jefa ma kanta tambayar da bata da amsarta,
A hankali ta kifa kanta saman gwiwowinta, yalwatacciyar sumar kanta ta yi mata rumfa tamkar hijabi, shessheƙar kuka taci gaba da yi ita kanɗai a cikin toilet area, tarasa ina zata tsoma ranta taji daɗi, gaba ɗaya ta tsani Gidan Kurkukun ƙaddara, A yanzu bata ƙi ta samu hanyar da zata gudu daga Cikin shi ba koda kuwa ita kaɗai ce, tunda ta lura Yaran da take son taimaka ma rayuwarsu, Zaiyi wuya taci galaba akansu, saboda already an juye masu tunaninsu,
Dare yayi sosai, duhu ya mamaye Cikin idanuwanta, ƙasa ƙasa da murya take ambaton sunan daddynta, wata magana ce ta faɗo mata acikin ranta wanda daddynta ne ya ta6a faɗa mata ita
_Ki sama ranki cewa ko babu ni zaki iya rayuwa, nasan cewa ƴata jaruma ce, mutane suna yabonki saboda ƙwarin gwiwar dake gare ki, Angel bana so rashina yayi silar canzawarki_ a lokacin da taj yayi mata wannan maganar saita fashe da kuka tana faɗin”Nidai daddy kada kayi mun maganar mutuwa bana so,” murmushi taj yayi idanuwanshi cike tab da kwalla yace”daughter mutuwa dole ce, ni dai kawai alƙawarin da nake so kiyi mini, shi ne, ki kasance a yadda kike ko bayan raina, kada ki bari wani abu ya canzaki, kada kiyi tunanin idan kika rasa ni xaki rasa gatanki, Domin kuwa Allah yana atare dake, kuma shine gatan kowani bawa, idan kika shiga hali na ƙunci Allah zaki kaima kukanki, In sha Allah zaki samu mafita_
Sosai angel ta fashe da kuka tunawa da wannan maganar ta mahaifinta, wani irin yanayi ta shiga mara misaltuwa, kusan raba dare Tayi acikin toilet area ɗinsu, batare da ta motsa ba Jikinta duk yayi tsami babu daɗi, ga kaɗaici dake damunta, ga yunwa da ciwon da take fama dashi duk ita kaɗai,
Ɗagowa ta yi da fuskarta wadda ta kumbura suntum tayi jawur, Tsinin hancinta yayi Ja, saboda matsar daya sha, Idanuwanta sun kumbura sun ƙanƙance, daƙyar take iya buɗe su, dogayen yatsun Hannayenta sai kerma suke Yi, wani irin matsanancin sanyi ne ya mamaye Jikinta, ta ko’ina babu sauƙi,
Daƙyar ta samu ta lalla6a Jikinta, Ta buɗe kofar da rarrafe Ta shiga Cikin ɗakin, tana tafiya tana kallon gadajensu duk sun kwanta sun lullu6e da bargo, hankalinsu kwance sai sharar bacci suke yi, adai dai bakin gadonta, Ta yunƙura ta miƙe ta haye sama ta kwanta, ta janyo bargo ta ƙudundune jikinta,
Acikin Ƴan kwanakin Nan angel ta fuskanci Mawuyacin Hali, saboda juya mata bayan da su kayi, Haris Ya samu damar fanshe haushin shi akanta saboda sunga bata da ƙoshin lafiya, wani sabon wulaƙancin, Sai haris yaga tana bacci, Ya je toilet ya Ciko bokiti da ruwa ya sheƙa mata ajikinta, Idan aka kawo masu abinci tana bacci, babu me tashinta daga Bacci, Haɗuwa suke su cinye mata abincinta, Sai da ta jera kwana Uku bata Ci abinci ba, Ta rame ta ƙanjame, Ta zama abun tausayi, ko magana daƙyar take iya furtata, yanzu takai ga ita ke ji shakkarsu, saboda Rashin lafiyar da take ɗawainiya da ita, bata son abunda suke Yi mata, duk Cikinsu mutun uku ne basu ta6a yi mata wulakanci ba, Batool Azeeza da Javed, basu atare da ita amma kuma ko kallon banza bai ta6a haɗa su da ita ba, kawai dai sun janye jikinsu daga nata ne, ita kanta angel ta lura da wani abu agame dasu, Sam wani abun bada son ransu suke yi ba, kamar ana tunzurasu ne, Shiyasa take Yi masu uziri, Duk wani plan ɗinta a yanzu ya tarwatse, Saboda juya mata bayan da su ka yi, Yanzu takaiga Ko sunan Allah da suke fadi sun daina, taya zata fahimtar dasu Cewa Akwai wanda ya halicce su, Bayan Sun ƙureta akan sai ta Kira masu Allah yazo sun ganshi tukunna zasuyi Imani dashi? Wa’iyazubillahi, Tsohuwa ta gama da rayuwar bayin Allahn nan, suna A cikin duhun jahilci, zaiyi wuya ta shawo kansu Cikin sauƙi, Saboda tsanarta da su kayi ayanzu tafi sha’awar zama Cikin toilet, akan ta zauna Cikin ɗakinsu suna yi mata gal6anci da rashin wayau ba, Sun kasa banbance tsakanin gaskiya da ƙarya, Duk da ba laifin su bane,
*Boss Bature🌷✍️*
Runtse idanuwanta ta ɗanyi tare da buɗe su, ita kaɗai zaune Cikin duhu, Ta gaza runtsawa,
Shessheƙar Kukan Azeeza Taji, Tasan bai wuci fitsari take Ji ba, ganin ita kaɗaice idonta biyu Yasa ta sauko daga saman gadon, Ta je inda fitilun ɗakinsu suke tabi kowacce ta kunna ta, kafin ta ɗauko ɗaya tana haska Cikin ɗakin, A tsaye ta hango azeeza ta matse idanuwanta, hawaye sharkaf, ƙarasawa tayi da sauri ta ruƙo hannunta,
Ta rakata Cikin Toilet, Tayi fitsarin A bakin fita daga Cikin toilet area ɗinsu, Angel ta tsaya tana haska fuskar azeeza,
“Angel” taji ta ambaci sunanta, ba ta yi tsammanin zata Shaida ta ba,
“Taya akai kika gane ni ce”? tayi tambayar tana kallonta,
“Naji ajikina cewa ke ce, ” shiru angel tayi na ɗan wani lokaci suna fuskantar juna kafin tace”Azeeza kema kin tsane ni ko? Baki son ganina ? Shiyasa ko magana ba kuyi mun,’ idanuwanta acike tab da kwalla tayi maganar,
Girgiza kai azeeza tayi fuskarta da alamun rauni attare da ita tace”ba haka bane angel, dai dai da rana ɗaya ban ta6a jin tsanarki acikin zuciyata ba, kawai ba yadda zamuyi ne, sai kina yi mana uziri, mu kanmu bamu jin daɗin abunda ke faru atsakaninmu, ” takai ƙarshen maganarta, tare da rungume angel a jikinta, kusan atare suka fashe da kuka,
Cikin shessheƙar kuka azeeza take faɗin”ni nasan cewa angel ba cutar mu kike yi ba, kamar yadda tsohuwa take faɗa mana, ke mai son mu ce, kina ƙaunar mu, kamar yadda kikayi niyar taimakon mu, kada ki fasa angel,”
Kalaman azeeza ba ƙaramin sanyaya mata zuciya su ka yi ba, sosai ta ƙara huggin dinta tightly a jikinta,
Suna Cikin wannan yanayin su ka ji sautin shessheƙar kukan mutun, da sauri angel ta saki azeeza, ta wurga idonta kan mutumin dake tsaye abakin ƙopa, Da fitilar hannunta ta yi amfani wurin haska fuskarta, bakowa bace face batool, fuskarta sharkaf da hawaye Allah kaɗai yasan tun lokacin da take atsaye tana sauraronsu,
Muryarta adisashe tace “Ki yafe mun angel, nayi kuskuran juya maki baya dana yi, bada son raina hakan ta faru ba, Na zauna nayi tunani duk irin ƙuntata maki da su haris su kayi dai dai da rana ɗaya baki fasa tashi tsakar dare Kinyi mana addu’a ba, saboda ƙaunar mu da kike Yi……..” dakatawa tayi da yin maganar tana sauke ajiyar zuciya, kafin taci gaba da cewa”Bana so kiyi kokwanto akaina angel, nasan abunda ya faru cikin ƴan kwanakin nan zaisa Kiji aranki kamar bana ƙaunarki ne, ko kusa angel, har yanzu kina nan yadda kike acikin zuciyata,’
Saboda Jin daɗin maganar Batool batasan Lokacin da ta fashe da wani sabon kukan ba, Matsawa batool tayi inda suke Ta janyo Angel ajikinta ta rungumeta sosai, Ta mika hannu ta ruƙo azeeza itama ta rungumota, atare suka cigaba da yin kukan,
*❤❤❤PRISONERS❤❤❤*
Muryar Javed su ka ji yo daga bayansu
“Nima ina neman yafiyarki angel, duk da bana ɗaya daga cikin masu ƙuntata maki” raba jikinsu su ka yi daga cikin na juna, kowannansu idanuwanshi ya kaɗa yayi ja saboda kukan da suka sha, still hawayen basu daina sintiri saman faces ɗinsu ba,
Kallon javed su ka yi dake a tsaye, Shima da alamun nadama atattare da shi, cikin sanyin murya angel tace”basai kun nemi yafiya ta ba, saboda ba laifinku bane, nayi maku uziri tuntuni’
Ƙarasa shigowa Cikin toilet area ɗin yayi ya tsaya a kusa da su, sannan yace”Angel, muna so mu tabbatar da gaskiya, a tsakanin ki da tsohuwa, sai dai babu wata ƙwaƙƙwarar hujja da zamu shaida hakan,” yakai ƙarshen maganar idon shi akan fuskarta,
“Ku bani lokaci, bi’iznillahi Zan kawo maku ƙwaƙƙwarar hujjar da zan wanke kaina, ZAN TABBATAR MAKU DA CEWA GIDAN KURKUKUN ƘADDARA BA GIDAN MARAYU BANE, SANNAN ZAN TABBATAR MAKU DA CEWA AKWAI ALLAH WANDA YA HALICCE KU, BA DAGA SAMA KUKA FAƊO BA,”
Baƙaramin daɗin maganarta su ka ji ba, batool ta ruƙo hannayen angel biyu acikin nata, cikin natsuwa ta soma magana”Ina yi maki fatan nasara Angel, muna atare dake,”
Angel tace”Bana so ku nuna mun shirya agaban tsohuwa, Ku cigaba da pretending cewa Kuna goyan bayanta baku atare dani, ta hakanne zan samu damar bayyanar maku da gaskiya,’
Atare suka haɗa baki wurin amsa mata da toh, Kallon azeeza ta yi wadda ke atsaye tana jinsu amma bata iya ganinsu,
“Mu koma Ciki mu kwanta, Azeeza ta gaji da tsayuwa” ta ruƙo hannun azeeza, Batool da javed su ka yi gaba a cikin ɗakin suka yi ma juna sallama, Kowa ya wuce gadonshi, sai da tafara kai azeeza saman gadonta ta kwanta ta lullu6eta da bargo, kafin Ta koma nata gadon, daga ƙasa ta ajiye fitilar hannunta, ta haye saman mattress ɗin taja bargo ta lullu6e jikinta zuwa saitin neck ɗinta, kasa runtsawa tayi, ɗan juyawa ta ɗanyi tare dakai idanuwanta saman shimfiɗar Danish, why Har yanzu ba a dawo da shi ba? Allah yasa dai ba jikin nashi bane yayi tsauri sosai ba, duk da babu sabo a tsakanin mu, naji na yi kewarsa sosai, inaso na sake ganin danish, Fatana Allah yasa adawo dashi, kada maganar batool ta tabbata na cewa duk wanda aka ɗauka ba’a dawowa da shi ya tafi kenan har abada! To wai ina ake kai su? Idan suna araye meyasa ba a ta6a dawo da su ba? Ni dai a iya sanina mutuwa ce kaɗai idan akayi ta ba’a dawowa!!!!!
Ɗaura hannunta na dama tayi asaman goshin ta zagoyo da shi, idanuwanta na fuskantar ceilling,
“Menene ma’anar Gidan Kurkukun ƙaddara? A iya sanina Gidan Kurkuku Yana nufin Gidan Gyara hali, Amma wannan kurkukun meyasa last name ɗinshi Ya ƙare da ƙaddara! Dole ya kasance ɗaya Cikin biyu, Kodai kyakkyawar ƙaddara ko kuma mummuna, ‘ lumshe idanuwanta ta yi a hankali ta ware su, Zuciyarta Cike fal da tunani, Tun lokacin da daddynta ya gudo da ita daga Gidansu, Take lissafin kwanaki, bata ta6a bari lissafi ya kwace mata ba, ko babu calender tana iya hasashen Yau nawa ga wata, ku ma ta canka dai dai,
Tana Cikin Yin tufka da warwara, Tajiyo Takun Tafiyar Mutun, Tunkafin ma takai idonta kan wanda ya shigo ɗakin nasu, Ta yi hasashen tsohuwa ce, daga kwance ta wurga eye balls dinta kan tsohuwa dake shigowa Cikin ɗakin, Sanye cikin shigarta, ta gado jar doguwar riga me hula, hannunta ruƙe da kaskon turaren wuta, zagaye ɗakin ta soma Yi tana kora hayaƙin ta ko’ina, murmushin takaici angel ta saki, yau ta ƙudiri aniyar sai tayi mata magana ga da ga, batare da jin tsoro ba, ta mike tare da saukowa daga saman gadonta, Cikin sanɗa take tafiya har ta ƙaraso bayan tsohuwa ta Cigaba da binta suna tafiya atare, batare da tsohuwa ta ankara ba, kasa kunne angel tayi tana sauraran ɗalasiman da take karantawa, kai daga jin yadda take Karanto su zaka shaida cewa ba abun arziƙi bane, wani mugun abunne take ƙulla masu,
“ƴar nan Kina tunanin bansan Kina bin bayana bane”? Tsohuwace tayi maganar, batare da ta juyo ta kalli bayanta,
Koda angel taji maganarta, bata ji wani fargaba ba, saima ƙwarin gwiwa da ta samu na cewa” nasan kinsan ina bin bayanki mana, Taya ki aiki nake yi, naga kina ta wahala ke kaɗai, Me zai hana yau Ki bani Kaskon turaren wutar In rage maki aiki”? juyowa tsohuwa tayi suka fuskanci juna ita da angel, Wani irin balagaggen murmushi ne ɗauke akan fuskarta tsohuwa,
Ɗaure fuska angel tayi tamau ba fara’a ko misƙala zarratin,
“Bibiyata kike Yi kenan? Da alama har yanzu baki daddara ba, Ina mai baki shawarar Ki ajiye makaman yaƙin ki, Ki yi rayuwarki tamkar salihar dabba, ki ajiye wannan Girman kan naki, da taurin kan nan da kafiya, Muyi rayuwa Cikin salama,’ takai ƙarshen maganar tana washe wawulan bakinta,
Still angel bata tanka mata ba, Jira take ta kammala Suratan nata marasa kan gado,
“Ƴata faɗa da aljani ba riba, Ko har yanzu Kina tunanin zaki Ci galaba akaina ne eye? Tsabar takaici Ji take kamar ta shaƙo wuyan matar, mummunar banxa kawai, ta ambaci hakan acikim zuciyarta, a fili kuma tace”tun yaushe kuma? Cin galaba akanki tuni na fara, bari na faɗa maki abunda kike tunanin bansani ba,’ ƙura mata kwarkwararrun idanuwanta tsohuwa tayi tana jiran jin me zata ce,
“Kafin na faɗa maki irin nasarar dana fara samu akanki, zan fara faɗa maki babban kuskuran da kuka tabka,” fuskarta ɗauke da murmushi takai ƙarshen maganar, Tsohuwa dai tayi kasaƙe tana kallonta,
A tsanake angel taci gaba da cewa”Kuskuren kuwa shine, ɗauko ni da ku kayi zuwa Cikin gidan Kurkukun nan, ganganci ne mutun ya ɗauko ajalinsa ya raine shi da hannunsa, ada ina tunanin meyasa na kasance acikin gidan kurkukun ƙaddara? Amma yanzu na samu amsar tambayata, inaji araina Ba hakanan Allah ya ƙaddara mun rayuwa acikin gidan kurkukun nan ba, babu shakka Nice zanyi silar tarwatsewar……..” bata kai ƙarshen maganar ba, Sakamakon wata ƴar iskar dariya da tsohuwa ta fashe da ita, Ta wage wawake bakinta, Haƙoran nan jawur dasu, kasancewar angel na a kusa da ita, Da sauri ta kawar da kanta gefe Jin ƙarnin Jini na fita daga cikin bakin tsohuwa, lamarin yayi matuƙar ɗaure mata kai zuciyarta ta shiga ruɗani, gaba ɗaya ta rikice tana zare ido, fuskarta ɗauke da tsantsar mamaki da aljabi ta ɗago tana kallon tsohuwa a lokacin ta dakata da yin dariyar,
Da shaƙaƙƙiyar Miryarta ta tsoffi tace”Your dream will neva come true angel, Wasiƙar jaki ce kike saƙawa aranki, wadda bazata ta6a zama gaskiya ba, har yanzu akwai sauran kuruciya atattare dake, shiyasa nake yi maki uziri, bakisan komai game da gidan kurkukun ƙaddara ba, ki kalli ginin da kyau, Tsohon ginine wanda tun kafin zuwana duniya aka ƙirƙire shi,”
Angel fa ta shiga ruɗani, Idanuwanta azazzare take kallon tsohuwa, sama sama take fahimtar zancenta, wata irin narkakkiyar zufa ce ta shiga tsastsafo mata ta ko’ina ajikinta, saman goshinta duk ya jiƙe da zufa, bakomai ya tsara mata arai ba, face wannan ƙarnin Jinin da taji abakin tsohuwa,
“Gidan Kurkukun ƙaddara, Baida ƙopa a lokacin da aka Ginasa, Kurman ginine, Ke Ko mutuwa bata isa ta fidda gawar mutun daga Cikinsa ba idan har ya shiga Cikinsa, Duk wanda muka ƙaddara ma rayuwa acikinsa, Anan zai rayu Anan kuma zai mutu, Ƴar nan ta ina kike tunanin zaki iya tarwatsa Gidan kurkukun ƙaddara? Ta yi mata tambayar tana sakin shu’umin murmushi,
Tuntsirewa Angel tayi da dariyar yaƙe, tana girgiza kai, hada dafe Ciki, tsohuwa ta zuba mata ido Itama da murmushi akan fuskarta,
“Halan wani shaƙiyancin ne zaki yi mun shine kike dariya” ? Tayi tambayar tana kallon angel,
Dakatawa tayi da yin dariyar, Tare da sanya hannu tana kore hayaƙin kaskon turaren wutar dake a hannun tsohuwa daya takura mata,
Sai da ta daidaita natsuwarta tukunna tace”Ubangijin mu Allah subhanahu wata’ala, mamallakin Komai da kowa, mahaliccin Maginin gidan kurkukun ƙaddara da kuma tsohuwa ita kanta dake agabana, da iznin shi komai ke wakana, wanda idan yaso a yanzu haka da muke atsaye sai ki fadi ki mace shikenan, An shafe babinki rayuwarki, duk wani ƙarfin iko da kike taƙama dashi kinga ya qare, Zaki je ki fuskanci reality, Allah kenan da shi na dogara, Kuma shi zai bani Ikon tarwatsa ku, wai ke har kina da bakin cewa duk wanda kuka kaddara ma rayuwa acikinsa Bai isa ya fita ba? Anan zaiyi rayuwa anan zai mutu? Ke wacece? Kin manta ta ƙofar da kika bi kika zo duniya? Kin manta yadda aka halicce ki tun daga ɗigon maniya har zuwa gudan jini? Ke kanki fa baiwace ta Allah ƙasƙantacciya butulu, waɗanda ma suka fiki hatsabibanci irinsu fir’auna Yanzu suna Ina?
Jin wannan tambayar ta angel yasa Walwalar dake akan fuskar tsohuwa ta gushe zuwa tsananin fushi da 6acin rai,
“Dama nasan bazaki bani amsa ba, ƙarya ta ƙare, Idan Allah yaso arana ɗaya dake da kurkukun duka zai shafe babinku, Shi kaɗai yake da iko akan komai, Bansan A ina kika samu kwarin gwiwar Yin magana a gadarance ba, akwai fa ranar da wannan sihirin naki bazai ta6a taimakon ki ba,
Zaro ido tsohuwa ta yi tana kallonta, Cike da mamakin Jin ta ambaci cewa tana da sihiri taya akai tasan hakan? Bata kai karshen zancen zucin nata ba Angel tace”Kina mamaki ne? Ta yi tambayar fuskarta ɗauke da murmushi, Kafin taci gaba da cewa”Ɗaya daga Cikin nasarorin da na fara samu kenan, Kina amfani da sihiri wurin sarrafa Tunanin waɗannan bayin Allah, Kun Hana ayi ibada acikin gidan kurkukun ƙaddara saboda Itace Lagwanku, wannan dalilin yasa Duk wani prisoner dake rayuwa acikinsa, kuka hana shi yin addini, Hakan na nufin ku kanku Kuna tsoron Allah saboda kunsan cewa shi kaɗaine zai Iya kawo ƙarshen ku, shiyasa kuke gudun dun wani abu daya shafi addini musulunci, sai dai kunyi abanza, domin kuwa kome kuke Yi Allah yana kallonku, dama ce na ɗan lokaci ƙanƙani, “
Ajiyar zuciya ta sauke kafin taci gaba da cewa”Ke kanki kin fara Jin shakkata, dalilin dayasa kuwa nace haka, Saboda kinga addu’ar da nake Yi masu tafara tasiri ajikinsu, Har sun fara gaddama dake, Wannan dalilin ne yasa Kika Koma Yi masu hayaƙin sihiri domin juye tunaninsu, sai dai kash aduk Lokacin da ki ka turara masu hayaƙin sihiri ni kuma ina bin kowani gado In tottofe su da addu’a, wannan yasa kike jin haushina saboda ina ruguza maki shiri, sabo tsabar makirci kikayi ƙokarin cusa masu tsanata acikin zuciyoyinsu, duk don saboda kisa in karaya, shima kinyi abanza,”
yadda take magana babu tsoro tamkar zata shaƙo wuyan tsohuwa, daurewa kawai take yi tana yin magana da ita, saboda munin fuskar matar, Ƙyamarta take Ji, fuska duk ta lalace ta ta6ar6are,
“I ave alot to say, Amma bazan Iya jure Yin magana mai tsayi dake ba, saboda 6ata lokacine yin magana da matacciyar zuciya,” fuskar tsohuwa babu annuri take kallon angel, Kaskon turaren wutar dake a hannunta tuni garwashin ya mutu, hayaƙin ya daina wanzuwa
Dogon tsoki Angel taja, tare da juyawa zata je ta kwanta, har ta kusa kaiwa bakin gadonta, ta ɗan dakata da yin tafiyar ta waiwayo ta kalli tsohuwa dake a tsaye ƙiƙam uwa saƙago, ta kafe ta da waɗannan kwartayen idanuwan nata,
“A’uzubillahi minasshaiɗanirra’jim, Aniyarki ta biki, Kuma ina nan ina zuba ido, Gobe adawo mana da ɗan uwan mu danish, idan ba haka ba komai zan iya aikatawa wlh, zan nuna maki hatsabibanci na, zan addabi rayuwarki,
“takai ƙarshen maganar tare da jefa mata harara ta murguɗa mata baki, gyaɗa kai tsohuwa tayi Batare da ta furta wata kalma ba, ta dogara sandarta zuwa kopar ɗakinta, ta buɗe ta shige tare da jan ƙopa, tafiyarta keda wuya angel tabi kowani sashe na ɗakin ta tottofe shi da addu’o’in neman tsari kamar yadda ta saba, ta kuma bi kowani gado tun daga kan gadon su Hanna duk ta wanke su da addu’a, bayan ta kammata ta koma saman gadonta, A tsakiyar gadon ta zauna tare da ɗaga hannayenta tana addu’a, akan Allah yabata Ikon yin nasara akan miyagun mutanan nan, Allah kuma Ya tsare mata daddynta aduk inda yake, idan kuma Ya mutu Allah ya kai rahama ƙabarinshi, Hatta danish sai da ta yi ma shi addu’a, Ta kuma roƙi Allah daya kawo masu ɗaukin fita daga Cikin Gidan kurkukun ƙaddara, Ta jima tana yin addu’o’i kafin daga ƙarshen ta janyo bargonta, ta lullu6a ma Jikinta,
Cikin ƙanƙanin Lokaci Bacci Yayi awon gaba da ita, can cikin dare wata irin zufa ta soma wanke fuskarta, wani irin matsanancin zafi ta ko’ina ajikinta, mutsu mutsu ta dinga yi tana matse idanuwanta, yayin da ta dunƙule hannayenta, tamkar ƴar dabbe, duk ta hargitsa shimfiɗarta, da alama mafarki take yi, ciccije la66anta tayi har sai da ta fasa su, ƙasa ƙasa take karanta duk wata addu’a da tazo mata a cikin kanta, a daren ranar bata yi bacci mai daɗi ba,
Tun daga saman gado Ta mirgino ta ƙundumo ƙasa ta daki floor ɗin sosai, har cikin kanta taji zafin buguwar da ta yi, Lokaci ɗaya ta farka kamar wadda Aka tsakura ta ware manyan gray eyes ɗinta tana kallon ceilling, Sai faman haki take yi kamar wadda ta yi gudun famfalaƙi,
Ƙoƙarin tariyo abunda tayi mafarki akanshi tayi, A cikin mafarkinta wasu baƙaƙen Maguna Guda uku sun farmake ta asaman gadonta, Faɗa ya kaure a tsakaninsu, Ta dinga yakushinsu tana kai masu cizo suma suna kokarin yakushinta sai dai Allah bai basu nasara ba, a ƙarshen itace taci galaba akansu ta yi masu jina jina sukai ta kuka, har suka sauko daga saman gadonta suka watsa aguje,
Nauyayyiyar ajiyar zuciya ta sauke, wani irin sanyi ya ratsa zuciyarta, lokaci ɗaya ta saki murmushi har dimples ɗinta suka lotsa, da alama taji daɗin damben da tayi acikin mafarkinta, bata motsa daga kwancen da take a ƙasa ba, hada bargonta da pillow ɗinta duka suna rungume a hannuwanta, Suma hadasu akayi artabun,
“Gidan kurkukun ƙaddara Ba gidan marayu bane Gidan Matsafa ne” yanzu ta ƙara tabbatar da zarginta akan cewa Gidan Mallakin Matsafa ne, Sai dai batasan wasu kalar matsafa bane, masu shan Jini, ko kuwa masu Cin naman mutun, akwai sauran rina akaba, dole sai ta bi asannu tukunna zata gano ainihin me waɗannan matsafan suke aiwatarwa da mutane ,
Ta yi zurfin acikin tunaninta muryar batool ta katse ta”Sister lafiya? Me kike yi a ƙasa”? Wurga idonta tayi akan batool dake A zuƙunne gabanta, ba tasan Lokacin da tazo wurinta ba,
“Sai faman sakin murmushi kike Yi kamar wadda akayiwa albishir da mukullin fita daga Cikin Gidan kurkukun ƙaddara” fashewa angel tayi da dariya Jin abunda batool tace, haƙiƙa maganarta ba ƙaramin daɗi tayi mata ba, wannan babban albishiri ne kuwa mutun ya mallaki mukullin fita daga kurkukun ƙaddara, Har tafara ayyana irin shagalin da zatayi aranar da tabar gidan kurkukun nan, zatayi farin Cikin da bazata Iya misalta shi ba,
“Faɗamun me kike ma dariya? Wata’ƙil nima ya sanya ni farin Ciki”acewar batool fuskarta ɗauke da murmushi tayi maganar,
Mikewa zaune angel tayi still pillown ta na rungume a hannunta, sumar kanta duk ta tarwatse saman bayanta, hada side by side na fuskarta, hannu batool takai tare da ruƙo gashin kanta tana fadin”yakamata In rage maki sumar kannan naki, idan ba haka ba nan gaba idan kina tafiya sumar zata dinga taɗiyo ƙafarki ne,” dariya suka saki atare,
Angel tace”baki lura gashin ki yafi nawa yawa ba? Kalli Fa yadda sumar kanki ta Cika ko’ina kamar kin kifa kwando asaman kan naki, Gashin duk ya nannaɗe kamar taliyar indomie,”
Ta6e Baki batool tayi ta ɗan kai idonta kan sumar kannata, ita kanta tsoron kallon yawan sumar ta take Yi, saboda yadda take ha66aka,
“Kwanan nan zan samu abunda zan datse ta, Don ni banga amfani gashin kaina ba,” acewar batool,
Angel tace”da ace a waje kike rayuwa da baki faɗi hakan ba, saboda gashi abun ado ne ga ƴa mace, yana ƙara ƙawata kyan mace sosai, kuma yana jan hankali mutane, idan Allah yasa muna da rabon fita daga Cikin kurkukun nan, ke da kanki zaki shaida abunda nake faɗa maki, mutane ma rububinki zasu dinga yi saboda kyanki,”
Duk wannan maganganun da angel ke yi batool fa bata fahimtarta, domin kuwa batasan Ya kyan fuskarta ya ke ba, tun da Allah ya halicce ta Bata ta6a kallon madubi ba, tadai san kyau a fuskar danish da kuma fuskokin su Azeeza, Amma Ita batasan Ya kamanninta suke ba, kamar yarda suma su Azeezan basu ta6a kallon madubi ba, Basusan Ya suffarsu take ba, Sai an kwatanta masu,
“Angel nifa bansan Ya ake ganin kyau na ba, Saboda bansan ta wace hanya zan ga fuska ta ba,” tayi maganar tana kallon angel,
Tuntsirewa angel tayi da dariya Hada dafe Ciki, Batool ta daure fuska”stop laughing at me bana son wasa fa ” daƙyar angel ta samu ta dakata da yin dariyar, A tsanake Ta kalli batool tana zayyana mata kyawun fuskarta,
“Farko dai ke doguwace, fara sol son kowa ƙin wanda ya rasa, idanuwanki Dara dara dasu manya farare ƙyal launin su brown colour, ga dogon hanci, tausasan la66anki brownish colour ne yadda kasan yankan tumatur saboda tsabar kyansu, ke fa ɗin kyakkyawa ce ajin farko, tun da angel ta soma magana batool ta saki baki galala tana kallonta, Tsabar farin Ciki ya hana ta furta komai, Daɗi take Ji ana zayyana mata irin kyanta,
Wani abu da angel bata sani ba, tun lokacin da Ta soma zayyana kyan fuskar Batool, Gaba ɗaya su Hanna dasu azeeza, rubina Hibba, eve, yasmin, da deeja da parveen Kaf ɗinsu Suna a zuƙunna kewaye dasu, Jira suke ta kammala Zayyana ma Batool kyawun fuskarta suma ta faɗa masu Ya nasu Kyan yake, Tofa angel ta zama Mirror,
Baƙaramin wahalar da ita su ka yi ba, Sai da tagama da matan sai ga Javed da mubeen, hada naufal suma suka tasa ta gaba sai ta faɗa masu Ya kyawun fuskarsu yake, har wani jiri take gani acikin idanuwanta saboda tsabar gajiya, Ga gunwa tana ji sunƙi bari ko toilet ta shiga ta watsa ruwa ajikinta, sai daɗi suke ji an faɗa masu cewa su kyawawane, Sai da ta kammala Javed Yace”Yanzu ki faɗa mana waye yafi kowa kyau acikin mu”? Suka tsareta da ido suna jira su ji amsar da zata basu, Kowa sai gyara sumar kanshi yake yi don ta ce shine yafi kyau,
“Zan fada maku tsakani da Allah, wanda yafi kowa kyau acikin ku, Baya atare daku yanzu haka,” gaba ɗaya taga sun kwashe da dariya, Da mamaki akan fuskarta tace”meya baku dariya” Mubeen yace”saboda Kin canka dai dai, Wannan wanda baya atare damu shine yafi kowa kyau acikin mu,”
Murmushin gefen fuska angel tasaki tare da ɗaura idonta kan batool tace”Amma duk da kyanshi, Batool itace zata zo na ɗaya saboda Ita macace, bayan batool kuma sai Azeeza kodan saboda wannan kyakkyawan murmushin nata, Daga azeeza kuma sai Javed….” duk wanda ta ambaci sunanshi sai taga yanata washe baki
“To ki faɗa mana wanene Yafi kowa muni Acikin mu”?
Batare data yanke shawara da zuciyarta ta basu amsa da cewa”Haris ne, Cikin mata Kuma deeja ce”
Deeja dake atsaye Ta ruƙe qugu tuni ta tur6une fuska, jin an kirata da mummuna, dama a ƙule take da angel ganin yadda sauran Ƴan uwanta duk suka Saki jiki da ita, bayan irin Ƙarairakin da tayi masu, ita kanta angel tayi mamakin zuwan da su ka yi wurinta, bayan Irin juya mata bayan da su kayi amma yau sai gashi sun sake da ita, duk da tasan Zaiyi wuya ayanzu su yarda da ita, kamar yadda suka yarda da ita a lokacin Baya,
Duk wannan abun dake faruwa Haris Baya acikin ɗakin bai jima da farkawa ba, Ya wuce Toilet, baisan wainar da suke toyawa ba,
“Kowa ya ta shi yaje ya shiga wanka, ya tsarkake jikin shi, kafin giants su kawo mana breakfast ɗin mu,” batool ce tayi masu magana, ɗaya bayan ɗaya kowa ya mike Ya nufi Toilet,
Lokacin da suka kammala Yin wanka, bada jimawa ba, Giants Suka kawo masu Abinci, Yau Hada Chocolate Cake aka kawo masu Kowa ɗaya, ba ƙaramin dadi suka ji ba, Saboda suna matuƙar son cake,
Yanzu sun saba da zarar Sun kammala Cin abinci, Sai a haɗu a motsa Jiki, Bayan sun gama, Kowa zai zauna ya huta ne, Yau fa tun da aka ta shi basu ga walwalar haris ba, Hatta angel tayi mamakin halin daya shiga yau, ya saba kullum sai ya ƙunsa mata baƙin Ciki, amma Yau kota kanta baibi ba, ko abincin shi bai ci ba, kamar wanda ɗan kanoma Ya kama haka ya dinga yi masu safa da marwa acikin ɗakin, idan ya gaji da yin zarya ƙafafuwanshi suka soma yi ma shi raɗaɗi sai ya koma saman gadonshi ya kwanta ya kalli ceilling, damuwace ta ishe shi ya rasa ina zai tsoma ranshi yaji daɗi, Ya gaza samun kwanciyar hankali, kowa ya kasa gane kanshi,
A lokacin suna zazzaune Saman gadajen su suna hutawa, Haris Ya sauko daga saman nashi gadon, Buguzun buguzun yake tafiya har zuwa bakin kopar ɗakin tsohuwa yaci burki ya tsaya tare da kai hannu ya kwankwasa ƙopar, Duk suka zuba mashi ido suna kallon shi, kusan sau uku yana buga kopar kafin, Ya soma jin alamun ana buɗe kopar ta Ciki,
Tsohuwa Ce ta fito hannu ruƙe da sanda, tun daga kan yanayin yadda ta ganshi ta tabbatar da cewar ba a hayyacin shi yake ba, ya haɗe rai zuciyarshi har wani tafarfasa take Yi,
“Harisu Lafiya ka ke buga mun ƙopa”? Yana huci yace”Nagaji da jiran dawowar danish, So nake naganshi, ko bai warke ba adawo mana shi cikin mu mu cigaba da yin jinyarshi, hankalin mu sai yafi kwanciya,” tunkan haris yakai ƙarshen maganarshi, Sauran ƴan uwan nashi duk suka sauko daga sama beds ɗinsu suka nufi inda tsohuwa da haris suke atsaye, banda angel dake hakimce saman gadonta, tana kallonsu,
Marairaice mata fuska Azeeza ta yi, Cikin sanyin murya ta wanda ya karaya tace”Idan har dagaske Kina son Mu, adawo mana da danish ɗinmu mu cigaba da yin jinyarshi acikin mu, mun yi maraicin rashin shi acikin mu,”
Ɗaya bayan ɗaya suka shiga Yi mata magiya akan adawo masu da danish ɗinsu, Su suke Yi mata magana amma idonta na akan angel, dake kallonta fuskarta ɗauke da kayataccen murmushi, aranta tace”nasan yanzu zata ƙara jin haushina saboda sun fara tuhumarta akan bazata dawo masu da ɗan uwansu ba, Yanzu ya rage naki tsohuwa kodai ki dawo da danish ko kuwa sufara zarginki,”
Gyaɗa kai tsohuwa tayi fuskarta a tur6une tace”Ku kwantar da hankalin ku, Yau danish zai dawo Cikin ku, Kuje ku xauna,” Takai ƙarshen Maganar tare da juyawa ta shige Cikin ɗakinta,
A bakin ƙopar ɗakinta, suka Zazzauna don yau sunci alwashin indai Danish bai dawo ba anan zasu kwana, angel dai na can kwance daman gadonta bata motsa ba, ta zuba ido tana jira taga ta wace ƙopa za’a shigo masu da danish, Dagaske zai dawo yau ko kuwa? Lumshe idanuwanta ta ɗanyi tana jin bacci sama sama,
Har wuraren marece ba’a dawo masu da ɗan uwansu danish ba, sai da kowa ya fidda rai da dawowarshi aranar
Kwatsam Ba zato ba tsammani, suna zazaune a bakin kopar ɗakin tsohuwa wasu har sun fara gyangyaɗin Bacci, Suka soma Jin motsi buɗe ƙopa, zumbur kowan nan su Ya miƙe Cike da sa ran Ganin danish, sun tabbatar shi ne saboda yanzu ba lokacin kawo masu abinci bane sun riga sunci tun ɗazu da safe,
takun Tafiyar Giant suka Jiyo daga Can kusurwar Benan, Jiki na Rawa suka Watsa da gudu Xuwa bakin stairs ɗin Kowa Ya ci burki yana faman Baza Idanuwanshi, Tuni Giant ɗin daya kawo shi Ya juya ya fuce Ya datse door,
Tun daga ƙasa suka soma Kallon shi, doguwar ƙafarshi sai kerma take yatsun ƙafar duk sun manne ma juna, jikin shi sai rawa yake yi idanuwanshi sun zazzaro tamkar ƙwayar idonshi zata faɗo ƙasa, jijiyoyin wuyanshi duk sun fito ruɗu ruɗu saman farar fatarshi,
Kayan jikinshi duk sunyi uban squeezing, sumar kanshi ta hargitse duk ta cukuikuiye
Lamarin ya yi matuƙar ta6a zuciyoyinsu, Duk sun gaza yi mashi magana, haris ne ya yi ƙoƙarin furta sunan shi”DANISH lafiyarka kuwa? Ko har yanzu jikin ne”? Ya yi tambayar yana ƙoƙarin matsawa kusa danish,
Dafe kai suka ga yayi da hannuwanshi, Ya fasa wata irin gigitacciyar ƙara, wadda ta razanar dasu, Angel dake niyar nutsawa Cikin baccin ta, Sautin ƙarar danish ya farkar da ita, a firgice ta ware idanuwanta tare da kallon inda suke a tsaitsaye Cirko cirko abakin Benan, Da sauri ta sauko daga saman gadon Jikinta har 6ari yake yi, ta cikinsu ta ratsa ta tsaya Dab dashi tana kallon shi,
Ya ƙanƙame Jikinshi yana Girgiza masu kai, la66anshi na kerma ya soma faɗin kada su matso kusa da shi, baison ganin kowa, ya tsani kowa” yana kai ƙarshe maganar shi, da gudun gaske ya bi ta tsakiyarsu ya bangaje su bai nufi ko’ina ba sai Cikin toilet area ɗinsu Ya shige ɗaya daga Cikin toilet ɗin Yaja ƙopa ya datse yadda baza su iya shiga ba,
Fashewa da kuka Aziza tayi saboda tsoran da taji,
Da gudu suka ɗunguma zuwa bakin ƙopar ta farko, Haris ne ya shiga bin ƙofofin toilets ɗin yana kwala mashi kira”Danish! danish! Baka ji ina kiran ka? Wai meke faru ne? Pls ka buɗe mana ƙopa, Munyi kewarka sosai,” a ƙopar toilet na ƙarshe yaje ya bubbuga ta yaji ta a garƙame alamar Nan ciki danish ya shiga,
A ruɗe rubina tace”Bari naje na faɗa ma tsohuwa tazo taga halin da ɗan uwanmu yake ciki, kada mu rasa shi” ta yi maganar tare da juyawa da gudu ta fuce,
Cikin shessheƙar kuka aziza tace”Wayyo Allah danish meya ke faru dakai ne? Dan Allah ka buɗe ƙopar,”
Hawaye ne acike da idanuwansu Javed, Eve tace”Ban ta6a ganin shi cikin wannan mawuyacin halin ba, sam danish baya a hayyacin shi,” tana rufe baki deeja tace”Ai duk laifin Angel ne, itace sila da ace bata ta6a lafiyar jikin shi ba, da duk hakanbata faru ba,”
Cike da takaici Angel tace”Nifa bani ce silar shigar shi cikin halin nan ba, koda ace ni ce amma ae an kai shi treatment room ko? meyasa daya dawo babu sauƙi ajikin shi? Kenan ba duba lafiyar jikin shi akayi ba, Wani abunne daban su ka yi mashi……..”tsawa Haris ya daka mata”Idan har Danish ya rasa ranshi, ke ma ki shirya binshi, ƙafarshi kafarki, muguwa kawai,”
Fashewa angel tayi da matsanancin kuka tana faɗin ita ba ita bace sila,
Faɗo wa cikin wurin rubina tayi har suna haɗa baki wurin tambayarta ina tsohuwar take, idonta cike tab da kwalla tace”Na kwankwasa ƙofar ɗakinta, bata buɗe ba”
Guntun tsoki Haris yaja, Yaci gaba da bugun ƙopar yana kiran sunan danish amma shiru bai amsa masu ba,
Gaba ɗaya sun taru agaban toilet ɗin Sai faman ƙwala mashi kira suke yi ya yi shiru babu magana,
“Me zai hana mu sanya ƙarfi mu buge ƙopar wata’ƙil ta buɗe,” batool ce ta kawo wannan shawarar, gaba ɗaya suka shiga bugun ƙopar, idan wannan yayi ya gaji sai wannan ya jaraba, duk anan ƙarfinsu ya ƙare dama ya lafiyar gwiwa, abinci sau ɗaya arana,
Gaba ɗaya sun fidda rai da fitowar danish, duk jikin su ya yi sanyi, ransu yana basu cewar danish ya mutu acikin kewayan,
Ransu duk a jagule suka fito daga wurin toilet din, suka koma cikin ɗakinsu a ƙasa kowa ya zauna, angel tana a tsaye bakin ƙofar farko ta shiga toilets ɗinsu,
Idanuwanta sun Cicciko tab da kwalla, zuciyarta acike take fal da tunanin Meya faru da danish? Yau 5 days kenan Yana a treatment room meyasa baiji sauƙi ba? Anya kuwa duba lafiyar jikin shi akayi ko kuwa ƙara mashi ciwon akayi? Duk yadda ta ƙagara ta yi toxali da danish sai da taji ƙuncin halin da ta ganshi aciki, kwata kwata Baya a hayyacinshi tamkar an canza shi, runtse idanuwanta tayi tana tuna Yanayin da tayi arba dashi, gwanin ban tsauyi kamar wanda aka zaƙulo daga bakin kura,
“Yanzu ya zamuyi? Munbar shi acan ciki, Allah kaɗai yasan halin da yake Ciki” mubeen ne ya yi maganar fuskarshi jaga jaga da hawaye,
Naufal yace”muna ji muna gani zamu rasa ɗan uwanmu, Wai meke faruwa da danish? tsohuwa tace an kaishi treatment room, ana duba lafiyar jikin shi but why danish baiji sauƙi ba”? Ya yi ma kanshi tambayar da baida amsarta,
hibba tace” ga shi tsohuwa bata nan, nasan da ita zata ceto rayuwarshi” daga inda angel take tana iya juyo maganganun su, ta tsani taji sun ambaci sunan tsohuwa, kuma har suna da yaƙinin itace kaɗai zata iya ceton rayuwarshi,
Aziza sai kuka take yi tamkar ranta zai fita, shi haris Yama rasa ta cewa saboda tsabar ƙululun baƙin Cikin daya tokare mashi maƙoshin shi, zuciyoyinsu sun karaya, ba haka su kayi tsammanin zasu ga ɗan uwansu ba, ba ƙaramin sage masu gwiwa akayi ba, sun rasa yadda zasu yi danish Ya buɗe masu ƙopa, Ko magana baiyi balle ma su sanya ran yana araye,
Gaza jurewa angel tayi, Juyawa tayi tare da komawa cikin toilet area ɗin, A bakin ƙopar toilet ɗin da yake aciki ta tsaya tare da kai hannu ta ruƙe handle ɗinta, Zurfin tunani ta shiga yi akan yadda zata samu Ta 6alle ƙopar, sam babu wani makami dazata yi amfani da shi, ƴan dabaru ta shiga yi na yadda zata 6alle ƙopar, Allah ne ya taimake Cikin sa’a, Sakatar ta saki, Ƙopar ta buɗe batare da tasha wahala ba, ajiyar zuciya ta sauke tare da tura ƙopa ta shiga ciki tana faman wurwurga idanuwanta, tun abakin kopar tayi arba da wandonshi yashe a ƙasa, ras! Taji gabanta ya faɗi, cigaba da tafiya tayi tana bin ƙasan da kallo, rigarshi ta gani a ƙasa itama ya yi wurgi da shi, tsayawa tayi a tsaye cike da fargabar halin da zata yi tozali dashi,
Yana acan Gefen tukunyar fulawar nan, anan ya zauna, daga inda take tana iya hangen fuskarshi, wuyanshi har zuwa ƙirjin shi, sai kuma ƙafafuwanshi daya zuro dasu ta ƙasa,
Ya lumshe idanuwanshi sai nishi yake yi tamkar wanda yasha gudu,
Muryarta na kerma ta ambaci sunanshi”DANISH”
buɗe idanuwanshi ya ɗanyi Sunyi jawur dasu daga gani yana acikin mawuyacin hali, jikin shi duk zufa ta wanke shi kamar wanda aka tsamo daga cikin kogon ruwa
Ta wutsiyar idonshi yake kallonta, juyawa tayi da sauri ta ɗauko mashi rigarshi da wandonshi,
Matsawa ta ɗanyi nesa da shi, yadda bazata iya ganin tsiraicin shi ba
Cikin sanyi murya tace”bansan me yake damunka ba, amma ina zargin kaina akan halin da ka ke ciki, dan Allah ka yafe mun ka yi haƙuri,” har lokacin bai motsa lips ɗinsa ba, balle ta yi tsammanin zaiyi magana magana,
Miƙa mashi kayan shi tayi”dan Allah ka mayar da kayan ka, bazan so ƴan uwanka su ganka a haka ba, hankalin su ba a kwance ya ke ba, duk sun damu dakai”
Wurga mashi kayan tayi a saman fuskarshi suka sauka,
“Dan Allah ka sanya kayan ka,” ta kuma maimaita mashi, cikin sigar lallashi,
Gani tayi ya runtse idanuwan shi sosai, ya ciccije soft lips ɗinshi duk ya fasa su, wata irin gigitacciyar ƙara ya saki,
Afirgice angel ke kallonshi, Su Batool dake acan cikin ɗakin Jin sautin ƙarar Danish Yasa suka Watso a guje, kafin su ƙaraso angel ta yi saurin juyawa zuwa bakin ƙopar ta datse ta,
Tana jiyo sautin bugun ƙopar da suke yi suna ambaton Sunan danish, tayi masu hakanne don bazata so sugan shi tsirara babu kaya ba,
Kafin ta dawo inda yake, tuni Yayi watsi da kayanshi data wurgo mashi, kwance ƙasa ta hangoshi sai burgima yake yi wannan karan hada hawaye akan fuskar shi lamarin ya yi matuƙar ɗaure mata kai, tana so ta taimaka mashi amma tana jin tsoron kallon tsiraicin shi
Rufe idanuwanta ta yi, amma bata rufe su sosai ba, tana gani biji biji a ahaka ta lalla6awa ta cigaba da tafiya zuwa inda yake kwance ta lalubo Wandonshi, ta soma kiciniyar mayar mashi a jikin shi, daƙyar ta samu ta zura mashi, Ajiyar zuciya ta saki tare da buɗe idanuwanta akan fuskarshi,
Sai faman nishi yake yi, idanuwanshi suna arufe, long eye lashes ɗin shi duk sun jiƙe,
calmly ta furta sunanshi”Danish are u ok”
Jin muryar angel acikin kewayan yasa suka gane cewa tana a ciki, sunyi mamaki yadda akai ta buɗe kopar, nan fa suka shiga kwala mata kira suna fadin ta bude masu ƙopa
Ɗaga murya ta yi tare da ce Masu Bazata buɗe ƙofar ba, saboda sun ƙala mata sharrin cewa itace silar jefa shi cikin halin da yake Ciki, don haka idan har sunga ta buɗe masu ƙopa, danish ya samu sauƙi ne”
Bugun ƙopar haris yake yi tamkar zai 6alleta” Bazaki zo ki buɗe mana ƙopar ba? a harzuƙe tace”Bazan buɗe ba,”
Sassauta murya haris ya yi”pls angel ki buɗe mana ƙopa, nasan bakya son danish kada kice zaki ƙarasa shi,”
Girgiza kai ta ɗanyi cike da jin takaicin maganar haris,
Tafin hannunta takai saman fuskar Danish ta shafa a hankali tare da ambaton sunanshi”Danish”
Dogon numfashi taga yaja gami dasauke ajiyar zuciya, yana so ya buɗe idanuwanshi amma ya kasa, sai lumshewa eyes ɗin nashi suke,
“Danish pls try to open ur eyes,”
Sama sama numfashinsa ke fita da hucin zafi, hannayenta ta sanya tare da tallabo kanshi ta ɗaura saman laps ɗinta,
Shafa gefen fuskarshi taci gaba dayi, yayin da ta soma karanto addu’o’i acikin zuciyarta, tana ɗan tottofa mashi saman fuskarshi,
Ba’a ɗauki tsawon lokaci ba, ya fara dawowa cikin hayyacin shi,
Lokacin dare ya fara yi, su biyu acikin toilet, ya yin da su batool ke zazzaune bakin ƙopar shiga toilet ɗin, sun galabaita har sun gaji da bugun ƙopar suna yi mata magiya akan ta bude masu, suga a wani hali ɗan uwansu yake ciki, wasu har sun fara gyangyaɗin bacci,
Itama angel ɗin baccin ta soma ji a cikin idanuwanta,
A lokacin da bata yi tsammani ba, taji ya ruƙo hannunta a cikin nashi sosai ya damƙe mata hannu, firgigit tayi tana kallon shi,
Lumshe idanuwanshi suke bai kaiga ƙarasa rufe su ba, He was calmly looking at her face without blinking his eyes,
Furta sunanshi tayi”danish” muryar shi so cool ya ambaci sunanta “angel” for the first time da danish ya ta6a ambaton sunanta,
“Are u ok,”? Ta kuma tambayarshi, bai amsa mata ba, ƙoƙarin miƙewa zaune yayi amma jikin nashi yaƙi bashi haɗin kai, da sauri ta taimaka mashi wurin tallabo shi ya miƙe zaune, tare da kwantar da kanshi saman kafadarta, still numfashin shi da huci yake fita, tana jin shi saman fatar wuyanta, saitin inda dogon hancin ya shafa,
*❤❤❤PRISONERS❤❤❤*
Sam bata ji komai ba, daya kwantar da kanshi saman kafadarta, sai taji tamkar ɗan uwanta ne na jini, ƙurawa sumar kanshi ido tayi, doguwa har saman bayan shi, kamar ta sanya hannu ta shafa sumar haka zuciyarta ke raya mata,
‘Pls angel open the door for us, mun ƙagara mu ga ɗan uwanmu,” muryar hannah ce take yi mata magiya,
Hannu tasa ta dafa kafaɗar shi”danish suna son ganin ka, mu koma ɗaki,” kusan minti biyar da yin maganar, ya ɗan dago da kan shi, still jikin shi ba kwari kerma yake yi,
Rarrafawa tayi ta ruƙo rigarshi ta miƙa mashi, yasa hannu ya kar6a ya zurata ajikin shi, Sai da ta taimaka ma shi wurin ruƙo shi tukunna ya samu ya miƙe, a haka suka soma tafiya har suka ƙaraso bakin ƙofar ta buɗe ta fito da shi, gaba ɗaya suka miƙe tsaye zasu rungumo shi,
Da sauri batool ta ware hannayenta wurin kare shi”Jikin shi ba ƙwari, danish yana buƙatar hutu,” A jiyar zuciya kowa ya sauke, wuce wa angel ta yi Cikin ɗakin, Su Batool suka Bi bayan su, ya rurruƙeta ji yake kamar zai faɗi ƙasa, wani irin jiri jiri yake gani a Cikin idanuwanshi, a saman gadonshi ta tsaya tare da taimaka mashi ya kwanta sama,
“Sannu danish, Allah ya baka lafiya,” batool ce ta yi maganar, su haris ma duk su kayi mashi ya jiki, sam ya kasa amsa masu amma duk yana jinsu,
Sunyi tsaitsaye cirko ciko a gefen da gefen gadonshi, hasken ɗakin ya yi duhu, alamar dare yayi lokacin bacci ne, da sauri Javed yaje gaban table ya kunna masu sauran fitilun, ɗakin yayi haske ya ɗauko ɗaya daga Cikin fitilun ya ajiye ta daga gefen gadon Danish,
Motsin buɗe ƙofa suka jiyo, da sauri kowannan su Ya juyo yana jiran ganin wanene zai 6ullo daga saman benan
Biyu ne daga Cikin Giants dake kawo masu abinci, Abun mamaki ɗaya daga Cikin su hannun shi na ɗauke da wooden tray, samanshi an rufe da jan ƙyalle, da alama kayan abinci ne, ɗayan Giant ɗin kuma Syringe ne a hannun shi, already an zuba ruwan allurar a ciki,
Me ruƙe da syringe ɗin ne ya yi masu nuni da hannunshi su matsa su basu wuri, da sauri suka ja baya, me ruƙe da tray ɗin ya sauke shi ƙasa gefen gadon danish, Kafin ya matsa zuwa saman gadon, wata irin zabura danish ya yi, ya daddafe kanshi yana faɗin baya so kada su matso kusa da shi, ya dinga ambaton sunayen su haris yana faɗin ba zasu taimake shi ba? Suna ganin za’a cutar da shi,
Tsananin tsauyin shi ne ya kama su batool, idanuwan kowannan su ya ciko tab da kwalla,
Ruƙe shi sosai Giant ɗin ya yi, shi kuma ɗayan Ya daddage ya caka mashi allurar a wuyanshi, nan take jikin shi ya saki, ya sulale saman katifar idanuwanshi a rufe,
Sakin shi su ka yi, a tare suka juya cikin takun nan nasu, suka fuce daga cikin ɗakin,
Fitar su keda wuya Su hannah suka yi mashi rumfa suna ambaton Sunanshi, danish danish
Haris yace subar shi ya huta zai ji sauƙi tunda anyi mashi allura,
Angel tace”Wai kun yadda allurar magani ce su kayi ma shi? Meyasa danish yake kuka yana faɗin bayaso sai kace ƙaramin yaro? Kuma har yana faɗin mu taimake shi, u ave to think about it, ni sam ban yarda da waɗannam mutanan ba, Allah kaɗai yasan me su kayi ma shi”
Yatsina fuska deeja tayi cike da jin haushin angel ta soma magana”babu abunda su ka yi ma shi, tun da muke dasu basu ta6a cutar da wani daga cikin mu, koma meye kece kike da alhakin ciwon da…….’ Bata kai ƙarshen maganarta ba, sakamakon naushin da angel ta sakar mata a saman fuskarta, tsabar raɗadi yasa Deeja ta dafe kuncinta,
“Ni kika buga”? Harara angel ta jefa mata”kaɗan kika gani, in har kika ci gaba da faɗin cewa ni ce silar da danish yake a wannan halin saina zubar maki da haƙoran gaba, wawuya kawai, don kinga kwanakin nan nayi sanyi shiyasa har kika samu damar gaya mun magana”
Ganin sun harzuƙa yasa javed yin saurin shiga tsakaninsu, cikin sanyin mirya yace” kodan saboda danish, kuyi haƙuri kuyi shiru,” jinjina kai deeja ta yi”na ƙyale ki a yanzu, amma wlh saina rama naushin da ki kayi mun” Tsoki angel taja”duk lokacin da kika shirya nima a shirye nake, mai rabon shan duka,”
Daga haka su ka yi shiru, Can Haris ya hango parveen zuƙunne gaban Kayan abincin da aka kawo, sai faman shinshina su take yi, hannu yakai tare da ruƙo wuyan rigarta, ya ɗago da ita tsaye ta maƙe wuya
“Abincin Mara lafiya ne, Kada ma mutun ya sanya rai,” harara parveen ta ɗan jafe mashi”Amma ae muna jin yunwa sosai, wannan dama ce a gare mu, kuzo kawai mu zauna muci mu ƙoshi, in yaso sai mu rage mashi kaɗan, bama lallai ya iya cin abincin ba”
Wani kallo Hannah tayi mata” ke fa dama indai kan abinci ne, Ba imani kika cika ba, Kinsan dai sau ɗaya ake kawo mana abinci, wannan kuma da kika ga an kawo na danish ne, ina ma laifin kice idan yaci ya ƙoshi ya rage sai muci kingin”?
Murmushin yaƙe parveen ta saki”Ae naga bacci yake yi, zamuyi ta jiran shi ne har saiya farka yaci ya rage tukunna muci”? ta yi tambayar tana ƙyafƙyafta ido, yadda tayi ba ƙaramin dariya ya basu ba,
Mubeen yace”Ni kaina yunwa nake ji, Don ba yadda zanyi ne Allah,” yana rufe baki naufal yace”ae ba kai kaɗai ba, ina ɗazu ɗinnan da muka dinga bugun ƙopa, to anan duka abincin da muka ci ya zube,”
Murmushi haris ya ɗan saki tare da cewa”duk bala’in ku dai bazaku ta6a abincin ɗan uwana ba, har saiya ci ya rage” dariya su kayi gaba ɗayansu, da alama suna farin cikin dawowar ɗan uwansu,
Dare fa ya yi sosai, yakamata kowa yaje ya kwanta, acewar yasmin, juyawa su kayi kowa ya nufi gadonshi, Banda mutun ɗaya Parveen ta yi tsaye agaban gadon danish
Dawowa Haris ya yi tare da kai hannu ya ruƙo wuyan rigarta” muje ki kwanta” bubbuga ƙafa ta yi tare da cewa”Mara lafiya ne fa shi, taya zamu barshi shi kaɗai, Ni inaso Inyi jinyarshi ne”,
“Saboda shi kaɗai ne a ɗakin ko”? Ya yi tambayar yana kallonta, shiru tayi tana faman tur6une fuska,
“Oya muje ki kwanta, sarkin wayau” ya ambaci hakan tare da janta, sai da yakai ta har saman gadonta, tukunna shima ya wuce nashi gadon ya kwanta,
Gaba ɗaya sun kasa runtsawa, bakomai suke jira ba, face farfaɗowar Danish,
“Kinyi bacci”? Muryar haris ce, yana daga kwance yayi maganar yana kallon Parveen dake a kwance saman gadon ta dake a kusa da nashi
“Taya zan iya bacci da ƙamshin abinci a hanci na,” dariya haris yayi,
“Amma Haris baka ganin abincin zai iya lalace wa, tunda shi danish ba’asan lokacin da zai farka ba,”
“Calm down ur mind, tun da ki ka ga sun ajiye abincin nan, sunsan zai farka ne, Giants ne fa Sunsan me suke yi,” sun jima suna tattaunawa, da haris before bacci yayi awon gaba da parveen,
Tsakiyar dare lokacin rabi da kwatarsu sunyi bacci, banda mutun ukun, Angel data ɗaurawa kanta alhakin ciwon danish, sai kuma Haris da yake na hannun damarshi, bayan su sai Batool, kowannansu yana kwance sunyi likimo tamkar masu yin bacci,
Ashe zuƙunne bata ƙare ba Kamar daga sama su ka ji danish ya fasa gigitacciyar ƙara mai matuƙar firgitarwa, farfaɗowarshi kenan, ya ta shi da wani sabon Ciwon, a matuƙar gigice angel ta yaye bargonta haris da batool duk suka cire bargunansu, hatta masu bacci sai da suka farka sakamakon Ƙarar danish data karaɗe Cikin ɗakin,
Gaba ɗaya hankalin su yae matuƙar tashi, ganin Danish Zaune saman gadonshi sai ƙara yake saki, ya daddafe kanshi da dukkan hannayenshi, tamkar wanda ake cikin zare ranshi saboda tsabar yarda yake fitar da sautin ƙarar har wani jijjiga muscles ɗin Jikin shi ke yi,
Durowa su ka yi daga saman gadajensu, jikinsu har kerma yake yi wurin tunkarar shi, Haris ne ya hau saman gadon, Javed da Mubeen hada naufal da sauran Ƴan matan duk Suna a tsaitsaye fuskokinsu da alamun ruɗu,
“Danish meya faru? meke damunka? dan Allah kayi mana bayani, ” magana suke yi mashi amma sam baya sauraronsu ihu kawai yake yi, shi kaɗai yasan Raɗaɗin da yake ji bawan Allah,
“Bari naje na kira tsohuwa” Acewar Batool, juyawa ta yi da niyar taje ƙopar ɗakin tsohuwa, Angel tayi wuff ta ruƙo hannunta, tsayawa tayi tare da waigo wa ta kalli hannun angel da ta ruƙe ta, suka haɗa ido da juna”Ki jira akwai abunda nake so, in jaraba yi mashi idan bai ji sauƙi ba sai kije ki faɗa mata,”. Rai a6ace haris yace”don me zaki hana ta zuwa ta kira ta? So kike mu rasa ɗan uwanmu? Baki ga halin da yake Ciki bane? Yana rufe baki Deeja tace”Da alama so take ta ƙarasa kashe shi, dama ni ban yarda da ita ba, ko me take da shi da zata iya taimakon shi?
angel bata tsaya sauraronsu ba. Kota kansu bata bi ba, batool ta kuma kallo tare da cewa”Ku bani dama,” jinjina kai batool ta yi tare da kallon su haris tace”Tun da ta nemi alfarma, mu barta ta jaraba, amma kuma komai ya biyo baya, ke kija tun da kin hana a kira tsohuwa” gyaɗa kai angel ta yi, tare da matsawa ta haye saman gadon danish, ya kakkame Jikinshi sai kerma yake yi, yana sakin ihu ga zufa duk ta wanke jikin shi, duk da weather ɗin prison mai sanyi ce,
Miƙa hannu ta yi da niyar ta ruƙo shi, Ya buge hannun nata alamar baiso, duk yabi ya birkice masu,
Ganin yaƙi bata damar ruƙe shi yasa haris jan dogon tsoki tare da cewa”U just wanna waste our time, pls batool go and call her” tafiya batool ta soma yi ta nufi ƙopar ɗakin tsohuwa,
Rufe ido angel tayi, Cikin sanyin murya mai tattare da natsuwa da cikar kamala, ta soma raira qira’ar karatun alqur’ani mai girma,
Gaba ɗaya suka bita da kallo, sam basu san me take karantawa ba, amma tunda suke basu ta6a jin sautin abu mai daɗi ba, irin wanda angel take Rairawa ba, hatta batool dake ƙokarin kwankwasa ƙopar ɗakin tsohuwa, tana fara jiyo sautin karatun da angel keyi nan take ta dakata, tamkar an dasa mata aya, da matuƙar mamaki ta juyo tana kallon inda suke.
Bakomai yafi ɗaure masu kai ba, Fa ce yadda danish ya yi shiru, yadaina ihun da yake yi, kuma jikin shi ya daina yin kerma,
A hankali angel ta buɗe idanuwanta, ta ɗaurasu akan fuskar Danish still bai buɗe idanuwanshi ba, matasawa ta ƙarayi kusa dashi sosai, ta sanya hannayenta biyu tare da ruƙo doguwar sumar kanshi, ta tattare ta zuwa bayanshi, moving lips ɗinta ta yi xuwa saitin kunnanshi na dama, sosai taci gaba da raira mashi karatun har cikin kanshi yake jin wani irin baƙon yanayi mara misaltuwa, zuciyarshi tayi sanyi, kasala ta baibaye shi,
,
Haƙiƙa Angel tabar ƴan kallo, Su haris sun saki baki kamar lehen sakarai sai kallonta suke yi, ta kawo masu wani baƙon abu da basu ta6a ji ba,
He slowly wrapped his arms around her waist and squeezed her tightly tamkar zai shige cikinta, sai faman nishi yake yi yana fitar da numfashi da sauri da sauri, tana jin zafin jikin shi sosai ajikin nata, saboda matsewar da suka yi ajikin juna, tana jin yadda heart ɗinsa ke beating very fast, ƙasa ƙasa da murya yake furta mata, kada tadaina, taci gaba yi mashi yana samun sauƙi,” kamar yadda ya buƙata haka taci gaba dayi mashi karatun, har sai da taji tempreture ɗin jikin shi ya dawo normal, numfashinsa da natsuwarshi sun daidaita tukunna ta dakata da yi mashi karatun acikin kunnuwanshi, zame jikinta ta yi daga nashi, tare da sanya hannayenta ta dafa shoulders ɗinshi, eyes ɗinta na kallon Fuskarshi, idanuwanshi tamkar na mashayin giya,
“Danish can u see my face” tayi maganar tana nuna mashi fuskarta, jinjina mata kai yayi alamar eh, ɗagowa ta yi tare da kallon su Haris dake a tsaitaye, Yadda kasan ƙerarrun gumaka, tsabar mamaki yasa sun kasa rufe bakunansu, Kowa zuciyarshi acike take fal da tunanin menene angel ta karantawa ɗan uwansu danish harya dawo cikin hayyacin shi,
“Angel kinyi matuƙar bamu mamaki” batool ce tayi maganar a lokacin ta dawo inda suke.
“Duk da bamusan menene kika karanta ma danish a kunnanshi ba, amma nayi matuƙar jin wani irin sanyi da daɗi acikin zuciyata, sai naji dama baki daina ba, kin cigaba da yi,”
Batool nakai ƙarshen maganarta, Javed yace”Nikaina naji wani irin daɗi mara misaltuwa, nayi mamaki kuma ganin yadda danish ya samu natsuwa yadaina haukan da yake yi,” yakai ƙarshen maganar idonshi akan danish,
Hanna tace”i feel the same, zanso nasan menene angel kika karanta mashi me daɗi,” tayi maganar fuskarta ɗauke da murmushi,
“Zanyi maku bayani, amma yanzu danish yana buƙatar kulawarmu,” tayi maganar tana kallonsu,
Haris dai yayi shiru shi da deeja kowa na tofa albarkacin bakinsa kan irin dadin da suka ji amma banda su, saboda tsabar kunyar da suka ji,
“Ga abincinsa kar ya lalace, aba shi yaci” parveen ce tayi maganar, tare da rankwafawa ta ɗauko tray din ta miƙa ma Angel, hannu biyu angel tasa ta ruƙe handle ɗin tray ɗin a tsakiyarsu ta sanya tray din, ta cire jan ƙyallen, waro ido parveen tayi ganin Roasted Chicken guda ɗaya sai maiƙo take yi ga wani irin ƙamshi, gefe kuma Milk ce a cikin bottle me sanyi, sai wooden bowl mai ɗauke da Fruits salad,’
“Zaka iya ci”? Ta yi tambayar tana kallon danish, wata irin narkakkiyar zufa ta gani tana gangarowa ta cikin yalwatacciyar suman kanshi, bai iya bata amsa ba, sai dai kallon ta da yake yi,
Sai lokacin harisun tsohuwa ya samu damar buɗe baki yace”Bari na taimaka ma shi ya watsa ruwa ajikin shi,” yakai ƙarshen maganar, Tare da ruƙo danish, Javed ya taimaka shi suka yi mashi jagora zuwa Cikin toilet ɗinsu,
Bayan tafiyarsu batool ta kalli sauran ƴan uwan nasu”tun da jikin nashi da sauƙi, ku je ku kwanta,” Yadda kasan ƴan gudun hijra haka suka tafi sharaf sharaf kowa Ya hau saman gadonshi Ya kwanta,
Ganin parveen taƙi tafiya yasa tace”ke fa” Hannu tasa tana ɗan sosa keyarta “Jira nake Su haris su dawo da danish yaci abincin shi, idan ya rage nima in samu in ɗan ci…..” wani kallon rainin wayau batool tayi mata wanda yasa ta kasa ƙarasa maganar,
“Sai kace kinfi kowa Jin yunwa, Allah yasa idan ya fito ya cinye abincin duka sai muga ya za ki yi” angel dake zaune saman gadon danish ta yi zurfi Cikin tunaninta, bakomai ya ɗaure mata kai ba, face yadda ta iya yin karatun qur’ani tiryan tiryan tun zuwanta gidan kurkukun tasha Yin attempting karatun qur’ani tana gazawa, sai ta dinga jin raɗaɗi a maƙoshinta, A yau dai kamar umarni aka bata tayi karatun haka tadinga ji, Kuma taji kwarin guiwar yin qira’ar, kenan nan gaba zata Iya samun damar yin ibada, mamaki take yi ya akai take samun nasara akan wasu abubuwan? Tabbas Allah yana atare da ita saboda kyakkyawar niyar dake gareta, kuma tana ji aranta cewa Akwai masu yi mata addu’a, fatanta Allah yasa dadynta idan yana araye ya kasance ɗaya daga Cikin masu Yi mata addu’a, Saboda ita addu’ar Iyaye kar6a66iyace akan ƴa’ƴansu kamar yadda hadisa ya tabbatar da hakan,
Shigowarsu haris Cikin ɗakin ne ya katse mata zancen zucin nata, ta ɗago tana kallonsu, Hannayensu ruƙe dana danish, jikin shi duk lemar ruwa, Hada sumar kanshi suka wanke mashi, duk ta manne mashi saman fatar wuyanshi, Lokacin da suka ƙaraso, Saman gadon ya haye ya ɗan kishingiɗa kan shi saman pillow, jikin shi duk ya saki babu ƙwari, idanuwanshi na a lumshe,
“Abincin fa”? Angel ce tayi ma shi maganar, slowly ya dan buɗe idonshi akan fuskarta, in a throaty voice ya furta mata”I can’t eat anything now, u can share it,” voice ɗinshi yayi low sosai, daƙyar ta iya jin me yake cewa,’
Cikin rashin jin ɗaɗin maganar shi haris yace”Ko madarar ce ka ɗaure ka sha, nasan kana jin yunwa,” girgiza ma shi kai ya yi”bazan iya ba, kada ku damu kanku am ok,”
Babu wanda yaji daɗi Acikinsu, Sun so koda milk ɗin ce yasha, amma ya nuna masu cewa babu yunwa attare dashi, Su parveen abun nema ya samu, zama su kayi a kasa Kowa Ya shiga kai hannu yana yagar naman kazar yana Ci, Komai saida suka Bi suka lamushe, bayan sun kammala, Haris Ya zauna gefen gadon Danish, sauran suka wuce saman beds ɗinsu suka kwanta, Angel ma tuni ta koma nata gadon, hankalinta ba ƙaramin kwanciya yayi ba, danish ya dawo Cikin su, sai da dare ya nutsa, tukunna haris yabar gefen gadon danish ya koma nashi gadon ya kwanta,
Zuciyarta ce ta dinga tunzurata akan ta juya ta saci kallon shimfiɗarshi, yayi bacci ko baiyi bacci ba?, kasa jurewa tayi a hankali ta dan mirgina ta juya ta 6angaren da yake fuskanta, bayan shi kaɗai take iya gani, jikinshi na lulu6e da bargon da haris ya rufa mashi har zuwa kafaɗarshi,
tana kokari rufe idanuwanta, taga yana mutsu mutsu, ƙoƙarin juyowa ya yi, da sauri ta rufe idanuwanta, don kar ya gane shi take kallo, natsuwa ya yi a yayin da yake kallonta, zuciyarshi cike fal da mamakin canza mashi da tayi, yafi tunanin taji tausayin shi ne saboda halin daya shiga, wata zuciyar kuma tana saƙa mashi cewa kada ka yarda da ita, so take ka saki jiki da ita, ta samu damar kashe ka cikin sauƙi, ta wani 6angaren kuma ba ƙaramin sanyi yaji ba, tun da ta karanta mashi wannan abun da baisan menene ba, Sai yaji duk duniya babu abunda yake kwaɗayin ya kasance yana sauraro acikin kunnanshi idan ba shi ba,
Tunani tayi ko yayi bacci yanzu, tana mutsu mutsun buɗe idanuwanta, yayi saurin rufe nashi eyes, shima baiso ta gane cewa Ita yake Kallo, ta jima tana kallon shi, da zarar taga xai buɗe ido sai ta rufe nata idon, shima haka idon yaga zata buɗe idonta sai yayi saurin rufe nashi, Sai da suka raba da dare suna wannan wasan, Kafin Allah ya kawo bacci 6arawo yayi awon gaba dasu
*ANEELERH*
A tsaye Take saman darduma ta kabbara sallah, Jikinta sanye da dogon Hijabi maroon colour har ƙasa ta sauko, tana ƙoƙarin yin sujjada Taji mutun saman bayanta Ya haye, Kasa ɗagowa tayi saboda gudun kada ya faɗo tasan bai wuci junaid bane, ba yau ya saba yi mata haka ba, a bedroom ɗin Mami ya kwana, har yasan ya tako daga ɗakin mami zuwa ɗakinta, a duk inda ya kwanta bacci ya ɗauke shi ko mun tsakiyar dare ne idan ya farka sai ya nemota duk inda ta shiga, Yadda kasan malamin duba,
Bubbuga bayanta taji yana yi tare da ambaton “Doki sukuta sukuta, doki sukuta sukuta!, yana magana yana sukuwa hada cewa Mommy, Ki tashi mu tafi yawo,’ a hankali ta miƙa hannu ta ruƙo shi tare da janye shi daga saman bayanta, Ya faɗo daga gefe saman dardumar, bubbuga ƙafafunshi ya shiga yi, yana raira mata kuka, daurewa kawai take yi sam bata so taji yaron yana kuka, Tsananin tausayin shi taje ji,
Hannu ya miƙa ya ruko cazbaharta dake ajiye saman darduman, Ya miƙe zaune ya zura cazbahar saman wuyanshi, Allah Allah take ta kammala sallar kafin yayi tunanin ɗaukar qur’aninta da ta ajiye wurin daya ɗauki cazbahar, kura mata ido yayi jin taƙi tanka mashi ashagwa6e yake kiran sunanta”mommy! Ni ki tashi muyi wasan doki” yayi maganar da hausarshi da bata ƙarasa nuna ba, ya hanata sakat, daƙyar ta samu ta kammala yin sallar ta zauna zaman tahiya, Ya ɗaura kanshi saman laps ɗinta, Yana cigaba da yi mata shagwa6a, bayan sallame sallar ne ta samu damar kallon shi,
“Bansan meyasa kake yi mini haka ba junaid why? Bakaga sallah nake yi ba, bana hanaka in ina sallah kana hawar min bayana ba”? Wani kallo taga yana binta dashi, kamar wani mai hankali, a yanzu fa shekararshi biyu da rabi,
Sai daga baya ma ta lura da rigar dake ajikinshi, Singlet ce ta abie ya sanya, ta yi mashi yawa har ƙasan ƙafafun shi takai, cike da mamaki tace”kai! Waya sanya maka rigar abie”? Fuskarshi a tur6une yace”Ni na ta” hararar shi tayi”you’re lying, ina kaga wayan da zaka iya ɗauko rigarshi ka sanya? tayi maganar tare da kai hannu tana jan kumatun shi,
“Faɗa mun gaskiya My baby boy, ko mamie ce ta sanya maka ita”? Girgiza mata kai yayi”kintan Allah wlh ni nata, in na miki ƙarya Allah ya ƙona……” bata bari yakai ƙarshen maganr ba, ta ɗan hambare bakinshi” Bana haka irin wannan rantsuwar ba?ba’ajin magana ta ko”? ashagwa6e yace”Ae ae nima musha naji yana yi,” tsoki taja, shiyasa batason Junaid Yana zuwa wurin shi, duk a wurin shi yake koyan wannan rantse rantsen marasa kan gado, dole sai ta ja mashi kunne, Ya daina Yi agaban ɗanta, tun da yaron wayau ne dashi komai ɗauka yake yi acikin kanshi,
“Kadaina kaji babu kyau,” amsa mata yae”Toh, in na daina zaki kai ni wurin Angela”? Murmushi tasaki tare da cewa”Da alama kana son ƴar uwar nan taka junaid, sai dai bansan ya za’ae in kaika wurinta ba, Nima nemanta nake yi….” cikin sanyin murya takai ƙarshen maganar, duk inta tuna su sai taji zuciyarta ta karaya, Almost 4 years kenan babu su babu labarinsu, ‘
Ɗaukar Junaid ta yi a hannunta ta miƙe ta ɗaura shi saman gadonsu, tana fadin”ka koma bacci dan Allah my baby boy, bana so kayi ta 6arna pls,” amsa mata yayi”to” ya lumshe idanuwanshi alamar bacci zaiyi, ƙura mashi ido tayi tana kallonshi batare da ƙyaftawa ba,
Shafa fuskarshi tayi da hannunta, kafin ta zauna daga gefen gadon, takai hannu ta ɗauki wayarta dake ajiye saman bedside drawer,
Gallery ta shiga, ta lalubo tsoffin hotunansu tana kallo, Wani hoto ta buɗo wanda suka yi su uku, Ranar graduation ɗinsu akayi masu hoton a University of Hagen, dake a ƙasar germany, su uku su kayi hoton kowannasu yana asanye Cikin Graduation gown sunyi matuƙar yin kyau, Allah yayi halitta ta farko Aneelerh ce, A tsakiyarsu Benazir ce kyakkyawar balarabiya, Ta ƙarshe kuma wata aminiyarsu ce masha Allah, Matar akwai diri kamar ita ta ƙera kanta, kowacce da irin baiwar kyan da Allah yayi masu, sai dai kash gaba ɗayansu a halin yanzu ƙaddarar rayuwa tayi silar tarwatsewarsu,
A tsanake take kallon hotunan nasu, tayi matuƙar yin kewar aminnanta, bazata ta6a manta irin shaƙuwar da su kayi da juna ba, runtse idanuwanta tayi tana tuna wasu maganganun da suka jima suna yi mata yawo acikin kanta, ɗaya daga Cikin aminnan nata ne ta furta su a cikin text message da ta ta6a tura mata lokacin da take Cikin tashin hankali tace”Aneelerh bazan Iya jurewa ba, ko gaisuwata bai amsawa, bansan shi wani irin uba bane, ni dai banyi dacen iyaye ba, Yanzu haka da nake rubuta maki text ɗin nan, Ina akan hanyar zuwa airport wlh idan nabar ƙasar nan bazan sake dawowa Cikinta ba, tun da yace baison gani na, aneelerh agaban kowa Yaci mutunci na, agaban maids ɗin gidanmu, yayi mun korar kare hada tsine mun yayi kamar wani jahili shi baisan ƙaddara ba ne? Idan har na biyewa zuciya zansha poison ne in mutu……..”
Sosai aneelerh ta fashe da kuka, lokacin da ta kammala tariyo abunda ya faru, A fili tace”Allah sarki Aisha! Bansan A ina zan ƙara ganinta ba, Allah ya kare ki aduk inda kike, ni shaida ce akanki, Ke mutuniyar kirkice, bana fata, ƙaddarar rayuwa tayi silar canzaki daga yadda nasanki, ‘
Cikin shessheƙar kuka aneelerh tace”Narasa Aisha saboda korar karan da mahaifinta yayi mata, na kuma zo narasa Benazir, duk da ita don san ranta ta gudu, daga baya kuma Narasa Mutun uku masu mahimmanci acikin rayuwata, ” jefar da wayarta tayi saman mattress, Ta kifa kanta Jikin pillow, junaid tuni ya jima da komawa bacci,
Tasha kuka kafin bacci yayi awon gaba da ita, Wuraren ƙarfe 9 na safe, Mami ta shigo ɗakin Jikinta sanye da atampa , murmushi ta saki ganin yadda uwa da ɗanta suke ta sharar bacci, Girgiza kai ta ɗanyi “Jikana mai abun ban mamaki, dama nasan bai wuci nan ka gudo ba, wurin mommyn taka, bayan ka sace mun rigar mijina, Allah dai ya shirya mun kai,’ Takai ƙarshen maganar, tare da ƙarasawa Cikin ɗakin agaban gadon aneeleerh ta tsaya tare dakai hannu tana ɗan bubbuga kafarta” Daughter baccin ya isa haka, Ki tashi muje muyi breakfast,”
Buɗe ido aneelerh tayi sun ɗan kumbura saboda kukan da tasha, koda ganin busassun hawaye akan fuskarta, sai mami ta ɗaure fuska”aneelerh when zaki daina kuka? Sai kace wata ƙaramar yarinya? Abu kaɗan sai kuka duk kin maida kanki wata sauna,” rai aɗan 6ace tayi maganar, yayin da take zama gefen gadon idonta akan fuskar aneelerh,
Miƙewa zaune aneelerh ta yi, batare da tace komai ba,
“Fada mun me kuma ya saki kuka”? Muryarta a disashe tace”Mami kiyi hakuri idan kukana ya 6ata maki rai, nasan bakya son ganin zubar hawaye na, nima ba so nake yi ba, sai dai wani abunne ko nayi kokarin na danne saina kasa, idan ba hawayen na zubar ba, bana jin daɗi,” yanayin yadda tayi maganar ba ƙaramin kashe ma mami jiki tayi ba ,
Ruƙo hannayen aneelerh tayi acikin nata”Aneelerh, kodai zaki ɗauki shawarar mahaifinki ne, ki koma abuja gidan Uncle ɗinki da zama? ina ganin kamar in kina acan zaki fi samun sauƙi acikin zuciyarki, amma zamanki anan sam babu cigaba,” girgiza kai aneelerh tayi yi”Mami dan Allah kudaina yi mun maganar komawa gidan uncle da zama, ya kuke so nayi da rai na? A halin da nake Ciki, ku kaɗai nake gani inji sanyi acikin raina, indai nayi nesa da ku, bazan ta6a samun natsuwa ba” takai karshen maganar fuskarta a yamutse,
Mami ta fahimci halin da aneelerh take Ciki, dama tasan zaiyi wuya ta amince tayi nesa da su,
“Shikenan, bazan ƙara yi maki zancen komawa can ɗin ba, ina fata hakan yayi maki” jinjina kai aneelerh tayi alamar eh,
“Yanzu ki tashi ki shiga toilet ki wanke fuskarki sarkin kuka, Allah idan baki daina ba sai yaronki ya raina ki, ga shi nan yanzu shima ya fara zama irin ki, ko kallon banza mutun yayi mashi sai ya fara ta6e baki zaiyi ma mutane kuka,” murmushi gefen fuska aneelerh ta saki, tare da juyawa tana kallon junaid dake kwance, har lokacin wuyanshi na sanye da cazbaharta daya sanya,
Dariya mami tayi don ita sai lokacin ta lura da cazbahar da ke sanye a wuyan junaid,
“Wayaga ɗan Sarkin malamai,” dariya sukayi atare, gwanin ban sha’awa,
Miƙewa mommy tayi”xan koma dining ki same ni acan ina jiranku,”
Amsa mata tayi da toh mami, kafin ta sauko daga saman gadon ta shige toilet, after some minutes ta fito tana gyara doguwar rigar material ɗin dake ajikinta,’
Har lokacin Junaid Bai farka ba, tasan dole yana jin yunwa, hannu takai tare da ɗauko shi, aikuwa kamar ta tsunkule shi, Yaita kuka yana fadin shi bai gaji da baccin ba, tana dariya tace”Am sorry My baby Boy, breakfast zamuyi da zarar mun kammala, Sai ka koma baccin ka, daƙyar ta samu ta shawo kanshi Ya daina kuka, Toilet ta shiga da shi, ta yi mashi wanka, ta fito dashi sa6e saman kafaɗarta, ta nado shi Cikin towel, Gyara mashi Jikin shi tayi kafin ta sanya mashi riga da wando, rungume dashi ta fito ta nufi dining table, Mami ta hango a zaune tana Shan tea, Kujera taja ta zauna suna fuskantar juna da mami tace”ɗazu ban gaishe ki ba, My first love, Ina kwana mamina, ina fata kin tashi cikin koshin lpy,” fuskar mami dauke da murmushi ta amsa mata da cewa”Alhamdulillah, my lovely daughter, Ya grand son ɗin nawa naga yana ta tur6une fuska uwa alkubus, halan tashinsa ki kayi daga bacci”? Takai ƙarshen maganar idonta akan junaid, dake zaune saman cinyar mommynsa, sai shan mur yake yi, yana hura hanci, Shi an takura mashi,
“Mami saboda fa ya ci abinci na tada shi, amma da yake shi baisan abun arziki ba, shine yake ta hura mun hanci,”
Mami tace”kwantar da hankalin ki, ae da zarar yayi arba da noodles zai wartsake” hannu mami takai tare da ruƙo plate ɗin dake shaƙe da noodles ta tura ma aneelerh agabanta,
Hannunshi har kerma yake yi wurin kokarin tsoma shi Cikin taliyar, da sauri aneeleerh ta damƙi hannun nashi tare da cewa”Baka ga akwai zafi ba? So kake bakin ka ya ƙone”? ta6e baki ya soma yi alamar zaiyi kuka, lallashin shi ta shiga yi”haba my baby boy, Fushi ba naka bane bari na baka da hannu na” hannu ta sanya ta soma ɗibowa tana bashi abaki yana Ci,
“Mami Ina abie? Ko har sun tafi”? Jinjina kai mamie tayi”tun yaushe kuma, tun bayan sallar asuba yace mun bazai dawo gida ba, daga can zasu wuce, “
“Shi ne ko ya jira muyi sallama dashi” rai adan 6ace tayi maganar, mami tace”sauri yake yi ne, idan mun kammala cin abinci sai ki kira shi awaya ki yi mashi Allah ya kiyaye hanya,” amsa mata tayi da toh, daga haka suka Cigaba da cin abincin su,
*south korea🌹*
Seoul City,
Hajiya adama ce zaune saman Sofa mai mazaunin mutun uku, A cikin katafaren Palourn gidansu, jikinta na sanye da doguwar cord lace milk colour, idanuwanta na a manne da farin glass medicated, Ta natsuwa tana daddana laptop ɗinta dake asaman Table ɗin gabanta, da alama Komai ya daidaita don yanayinta bai nuna tana acikin damuwa ba,
Gaba ɗaya ta tattara kwandon hankalinta akan aikin da take yi acikin laptop ɗinta,
Sautin Dirar motoci ta juyo acikin Apartment din nasu, dakatawa ta ɗanyi da daddana laptop din ta ɗago tana kallon bakin kofar shigowa falon, duk da tasan ba lallai In baƙin su bane tun da basu kaɗai bane akwai sauran mutanan dake Haya Acikin Ginin,
*❤❤❤PRISONERS❤❤❤*
Uncel abdallah ne Ya shigo Falon, Hannun shi ruƙe da key ɗin motarshi, Suit ne ajikin shi, Miƙe wa Hajiya adama tayi fuskarta asake tace “Welcome back dear, I heard the sound of cars Coming in ko munyi baƙi ne”? sai da ya samu wuri ya zauna tukunna ya kalle ta fuskarshi ɗauke da murmushi yace”Ni ne baƙon ae, fatan na same ki lafiya, Yau naga walwala atattare dake, Ga shi kin ɗau wanka kinyi kyau abunki,”
Ta6e baki ta yi “Ae tun da kayi mun albishir game da komawarmu gida, Nake ta sakin fara’a ni kaɗai abuna, Yanzu haka ma da kaganni a zaune, Ina duba kayayyakin da zan siyane na tsaraba da zanyiwa mutanan gida,” takai ƙarshen maganar tare da kama hanyar zuwa kitchen tace”Bari na kawo maka Ruwa mai sanyi kasha”
“Da kanki Hajiyata? Ina mai aikin gidan take ne”? A sukwane ta Juyo tana bin shi da kallon bansan rainin wayau,
“Oh kamanta irin Korar da kayi ma Ajumma daga gidan nan, Saboda laifin da ba nata ba, ƴar baiwar Allah, dama burinka kaga ina shiga kitchen da girmana, ae yanzu hankalin ka ya kwanta, Hajiya adama ta zama kukun mijinta” Dariya Uncle abdalla Yayi”Matar nan kina sani nishaɗi, Abun alfahari ne mace ta girka ma mijinta abinci da hannunta yaci ya sanya mata albarka, Ta samu lada, Ni ae naga Cigaba sosai, da na kori wannan tsohuwar matar, Tun barinta gidan, kika daina shan Soju, gashi yanzu kin samu natsuwa kin dawo Hajiya adamar dana sani,”
Hararar wasa ta jefa mashi daga inda take a tsaye” korar ajumma da kayi ba shi ne yasa na daina shaye shaye ba, Da naso zan fita inje in siyo da kaina ne, Allah ne yayi silar shiryuwata, dama ba halina bane, tsautsayine da ƙaddara, da kuma damuwar da na shiga na rashin mutun uku masu mahimmanci acikin rayuwata……….” muryarta a karye takai ƙarshen maganar, da sauri tajuya ta shige Cikin kitchen,
Jingina bayan shi Yayi a jikin Sofa ɗin da yake zaune, Har ga Allah Shi kanshi yana acikin matsanaciyar damuwa na rashin ya’yan shi da ya yi, Yaji raɗaɗi sosai, sai dai ba yadda zai yi, daure wa kawai ya ke yi, A duk lokacin daya tuna rashin Da yayi, Na ɗan uwansa, Kuma yayansa Malam zahiru, da mahafiyarsu deeja, Sai ya dinga Jin kanshi tamkar marayan da baida mafaɗi aduniya, Dama wake gaya mashi gaskiya idan yay badai dai ba? malam zahiru ne, tun yana yaro shi yake zaunar dashi yayi mashi nasiha game da rayuwar duniyar nan, kalmar da yafi faɗa mashi itace “ABDALLAH KAJI TSORON ALLAH, ‘ tuna wannan yasa shi kai hannu ya dafe goshinsa, Idanuwanshi suka Cicciko tab da kwalla, haƙika yaji mutuwarsu, Hatta yahana su Mahaifiyar Tajuddeen, Yaji mutuwarta sosai, Mutanan kirkiki, Mutane masu ƙima da daraja,
Ajiyar zuciya ya sauke, tare da lumshe idanuwanshi, Bakomai yake tunawa ba face Tajudeen lokacin da zai raba shi da iyayenshi, Suna kuka yana kuka saboda basu son rabuwa da juna, Suna matuƙar ƙaunar ɗansu, Amma saboda son zuciya yabi ta ƙarfi da yaji don yana da arziƙi, ya ba mahaifiyarsu Cin hanci, aka damƙa mashi yaro, tun da yake bai ta6a danasanin raba tajudeen da iyayenshi ba, Sai bayan rasuwarsu, tsawon shekaru basu yi tozali da dansu ba, har sun koma ga mahaliccin su, Shi ma kuma ɗan nasu An neme shi ƙasa ko sama babu shi, Wannan wata irin ƙaddarar rayuwace? Yanzu idan Allah yasa aka ga su tajudden Taya zai Iya Sanar dashi game da mutuwar Iyayenshi!!? innallahi wa’inna ilaihirraji’un…………
Tun ɗazu Hajiya adama ta fito daga cikin kitchen, hannunta ruƙe da plate mai ɗauke da glass cup na ruwa mai sanyi tare da snacks, ta jima a tsaye tana kallon Mijinta nata da ya yi zurfin Cikin tunani, Hawaye ta gani kwance a cikin idanuwanshi, Da alamun damuwa attare da shi ba kamar yadda ya shigo mata ba, A saman C table ta ɗaura plate ɗin dake hannunta,
Kwala mashi kira Tayi A firgice yakai idanuwanshi akanta yana kallonta
“wai lafiya dear, Ina ta kiran sunanka Amma hankalinka sam baya atare dakai, Meya faru ne? Yanzu fa nabarka fuskarka asake, amma kuma na dawo na taras dakai cikin damuwa” tayi maganar tare da kai hannu ta ɗauki Cup ɗin ruwan ta miƙa mashi,
Hannu yasa ya kar6a, tare da kaishi saitin bakinshi yana sha, Zama hajiya adama tayi tana fuskantar shi, Jira take yi ya gama sha yayi mata bayanin dalilin shiga damuwarshi,
A hankali ya sauke Cup ɗin saman table, ya zura hannu Cikin trouser pocket ɗinshi ya zaro hanky ya goge fuskarshi, sai da ya daidaita natsuwar shi tukunna ya kalle ta, gaba ɗaya hankalinta na akanshi, sam baison ya faɗa mata dalilin shiga damuwar tashi, don yasan halitta, Yanzu ta kama yi mashi kuka, shiyasa ko zancen su Taj bai cika son yi mata ba, Rauni ne da ita,
Gudun kada ta ƙara tambayar shi meke damunshi, yasa shi yin saurin canza zancen ta hanyar cewa”Yawwa, Yanzu wani shirye shirye yakamata muyi na komawa Ƙasar mu? Naji kince zaki yi siyayyar kayan tsaraba da zaki yi ma mutanan gida,”
Jinjina kai Hajiya adama tayi tare da cewa”eh, idan ya rage kamar saura 4 weeks Mu tafi, Inaso zamuje Shopping mall atare, Akwai kayayyakin da nake so Na Siyawa ƙanne na, kasan su mayun kallon korean drama ne, suna san suturarsu ba ƙaramin burgesu yake yi ba, inaso na siya masu, hada Jikana zan siyawa kayan wasan yara, da kayansu na al’ada suna burgeni, ita Fatima ma hada cewa in yi masu tsarabar abincinsu, In banda shiririyata, zan dai siya masu chocolates ɗinsu kalar wanda bamu dasu a gida, ” magana take yi mashi amma hankalin shi gaba ɗaya baya akanta, har saida Tace”Kai fa? Me zaka yi tsaraba da shi
Murmushin yaƙe ya yi mata, muryarshi a karye yace”Wa nake da shi da zanyi ma tsaraba? Dama ƴa’ƴana ne, yanzu kuma babu su, amma duk da haka zan siyawa Angel kalar suturarsu, a ƙiyashin da nayi yanzu takai 15years a duniya, Zan yi mata siyayya sosai in ajiye mata, hada bags and shoes da teddys, komai ma zan siya mata, duk ranar da Allah ya bayyanar dasu, sai in damƙa mata abunta,’ yakai ƙarshen maganar, tare da duƙar da kanshi ƙasa, Shi kanshi baisan yayi waɗannan Zantuttukan ba, Saboda su ne aranshi shiyasa yayi maganar, Shessheƙar Kukan Hajiya adama yajiyo acikin kunnanshi, Kafin ya ɗago da kanshi tuni ta miƙe da sauri ta wuce zuwa bedroom ɗinsu, Binta yayi da kallo har saida ta 6ace ma ganinshi,
Girgiza kai kawai yayi, kafin ya miƙe ya nufi ɗakin, Don ya samu yayi wanka Ya canza kayan jikinshi,
*Back To Prison🥺*
Mutsu mutsun farkawa daga bacci ta ke yi, eye lashes ɗinta sun manne ma juna, daƙyar ta samu ta ware idanuwanta basu sauka akan kowa ba, sai akan fine face ɗin Danish dake ta sharar bacci, kasalalliyar ajiyar zuciya ta sauke a yayin da take kallon shi cikin natsuwa, kamar wani baby ya naɗe Jikinshi cikin bargo, fuskarshi kaɗai ce awaje, tun daga kan yadda yake fitar da numfashin shi, zaka shaida yana acikin kwanciyar hankali, baƙaramin daɗi taji ba, tana fatan Allah ya yaye mashi lalurar dake damunshi,
Almost 15 mins tana kallon shimfiɗarshi, kafin ta yunƙura ta miƙe zaune ta jingina bayanta a jikin bango, gadajensu batool tabi da kallo, Tayi mamakin ganin basu farka ba, Kamar wasu matattu sai sharar bacci suke yi, kowa ya kudundune jikinshi cikin bargo, sunyi matuƙar burgeta sai ta dinga jin inama ace Acikin Gidan Mahaifinta suke ba’a Cikin Gidan Kurkukun ba, da sun more rayuwarsu, tasan cewa Danginta zasu kar6esu hannu bibbiyu, musamman aunty aneelerh, da hajiya adama suna son yara sosai, taci alwashin idan Allah ya bata Ikon musuluntar dasu, Zata nema masu hanyar da zasu gudu daga Cikin Gidan kurkukun ƙaddara, Sai dai babban abunda take yi ma fargaba shine, Taya za’ae Su fita daga Cikin kurkukun da ransu da lafiyarsu? Idan Allah yasa sun samu ƙopar fita kenan, Bayan wannan abunda take matuƙar jimawa Anya kuwa GIDAN KURKUKUN ƘADDARA A cikin ƙasar Nigeria yake!? idan har ba’a Nigeria yake to kuwa dai suna acikin tsaka mai wuya! Fatanta Allah yasa ba awani ƙurmin dajin ginin yake ba, Don kuwa akan hanyar guduwa ma wata dabbatar na iya kai masu hari ta Cinye Naman Jikinsu…….”
Tana Cikin yin wannan Zancen Zucin nata, Karaf idanuwanta suka sauka akan danish dake ƙoƙarin faɗowa daga saman gadonshi, Cikin magagin bacci, A hanzarce ta duro daga saman gadonta tayi gaggawar tarbe shi, ƙiris Ya rage ya tiƙo ƙasa, ba don Allah yasa tayi saurin zuwa ba, da kanshi yayi mugun buguwa,
Nannaɗeshi tayi tare da turashi saman gadon, Ya koma yadda yake, Ajiyar zuciya ta sauke yayin da take kallonshi, Soft red lips ɗinsa ta gani suna motsi, alamar yana sambatu, miƙewa tayi ta hau saman gadon, ta duƙar da kanta saitin la66ansa, ta natsu tana sauraron me yake cewa,
_the sounds is soothing me, I can’t stop listening to ur voice, pls keep reading it in my ears, am really enjoying it_
Murmushi ne ya bayyana akan fuskarta, jin sambatun da danish yake yi, duk akan Karatun kur’anin da tayi mashi jiya ne, ta fahimci cewa ba ƙaramin daɗi yaji ba, shiyasa ma har yake sambatu acikin Baccinsa,
Whispering tayi mashi acikin ear ɗin nashi tace”Kana so In koya maka”? sam batayi tunanin zai amsa bata, sai ji tayi yace”yeah,” da sauri ta kalle fuskarshi, Abun mamaki Bacci yake yi bai farka ba, amma yana magana, ƙumshe dariya tayi kafin ta ƙara cewa”Dame zaka biya ni idan na koya maka”? Tayi tambayar Tana sauraron amsar da zai bata,
Cikin muryar bacci yace”I ave nothing to pay you, but I can promise you myself if you want” Cikin nishaɗi angel take dariya, A maganar da yayi mata idan har zata fassarata a matsayinta na wadda tayi rayuwa awajen kurkuku, Tamkar kalaman soyayya ne, Amma shi awurin shi bakomai bane, ya faɗi mata hakan ne saboda baida abunda zai iya biyanta da shi, idan ba kan nashi ba,
“does that mean you will be my slave? If I give you an order, will you follow?”
Amsa mata yayi”yeah” koda wankin Uniform ɗina ne? Tayi tambayar tana kallon fuskarshi, idanuwanshi na arufe gam, wannan karan bai bata amsar tambayarta ba, da alama ya kuma yin nisa Cikin baccin sa,
Ruƙo bargon shi ta yi tare da ƙara janshi ta rufe mashi har zuwa saman fuskarshi, Tana ƙoƙarin saukowa daga saman gadon danish, Ta ji yo motsin buɗe ƙopa, da alama giants ne suka ƙaraso, Yau Abinci ya riga masu Cin shi, ƙarasowa,
Ƙarasa saukowa tayi daga kan gadon nashi, ta tsaya a tsaye tana Jiran su ƙarasa shigowa Ciki, Takun tafiyarsu ta soma jiyowa, kafin su bayyana su ukun nan hannayensu a ruƙe da wooden trays, mai ɗauke da kayan Kalacinsu,
Akan idonta suka wuce zuwa saman dining carpet ɗinsu, Kowa ya sauke Farantin dake a hannunshi, Ja da baya su kayi atare suka ƙame kamar yadda suka saba, tunani ta shiga yi Kowanene acikinsu Ya damƙeta aranar nan har yayi wurgi da ita, bazata ta6a manta azabar da tasha ba, Ta tsani giants a rayuwarta, ko son ganinsu bata yi, Saboda basu da Imani, Ga ƙarfi kamar na dawakai, ta jima tana kokwanto akansu Anya kuwa Cikakkun mutanene? Kodai half jins ne?
Ta yi zurfi Acikin tunaninta, taji motsinsu, Ras taji gabanta ya faɗi ganin suna tattara kayan abincin da suka ajiye masu, aruɗe tace” ina zaku tafi da abincin mu? Bayan bamu Ci ba” babu alamun suna sauraronta,
“Magana fa nake Yi maku, idan saboda suna yin bacci ne yanzu zan tashe su, pls kada ku tafi” ko waiwaye wannan basuyi mata ba, Tana ji tana gani suka haura saman bene da abincin suka fuce daga Cikin ɗakin, Tana Jiyo sautin garkame ƙopa da su kayi,
“Ya salam” ta ambaci hakan tare da dafe kanta, muryar batool ce ta katse ta da cewa”Angel lafiya naji kina sambatu ke kaɗai”? Da sauri angel ta juya baya tana kallon batool dake kwance saman gadonta, farkawarta kenan daga bacci,
“Giants ne, Sun kawo abinci kuma sun tafi dashi bansan meyasa ba”?
Waro ido waje batool tayi fuskarta da alamun tashin hankali tace”mun shiga uku! Shikenan yau mun rasa abincin da zamu ci, angel meyasa baki tada mu daga bacci ba lokacin da suka zo”? Fuskarta a hargitse tayi maganar,
“Ina fa kokarin in tada ku daga bacci, sai naga suna tattara kayan abincin, kuma har roƙonsu nayi su tsaya amma basu saurare ni ba…..” tunkan takai ƙarshen maganarta, suka soma Jin shessheƙar kukan Parveen, gaba ɗaya suka kai idanuwansu akanta, zaune take saman gadonta, ta wage baki tana ta kuka, Jin cewa Giants sun zo sun tafi da abincinsu,
Sautin Kukan Parveen ne ya farkar da sauran Ƴan uwan nasu, Hanna tana hamma tace”wai meke faruwa ne? Me akayi ma Parveen take kuka”
Javed yace”Yanzu haka rigimartace kawai, duk tabi ta tashi mutane daga bacci, saboda tsabar jarabarta,
Hannu danish ya sanya tare da zame bargon da ke lullu6e a jikin shi, idanuwanshi sun ƙanƙance daƙyar yake iya ware su, saboda baccin bai ishe shi ba,
Haris dake faman yin miƙa yace”kun yi shiru baku bamu amsa ba, Meyasa take kuka”?
Batool ce ta bashi amsa da cewa”Saboda giants sun kawo abinci, Angel bata samu damar tada mu daga bacci ba, har suka tafi da kayan abincin shine take ma kuka”
saboda tsabar tashin hankali Har suna haɗa baki wurin cewa”What? giants sunxo sun tafi da abincin mu”? Amatuƙar ruɗe kowannasu yake faman baza ido,
Dafe kai javed yayi”ae shikenan mun rasa abinci yau, Mu da ganinsu kuma sai gobe, kafin lokacin mun gama jigata,”
Yana rufe baki Rubina tace”Wlh bazan iya jurewa ba, da matsiyaciyar yunwa na farka yau….” mubeen yace”ae ba ke kaɗai ba, Cikina har wani kukan yunwa yake yi” yayi maganar yana shafa stomach ɗinshi,
“Yanzu ya zamu yi kenan”? Naufal ne yayi tambayar yana kallonsu,
Azeeza tace”Mu ci hakuri kawai, Idan munji ƙishi musha ruwa sai mu kwanta muyita bacci har gobe tayi, Harara Hibba ta jefa mata daga inda take zaune saman gadonta”Wannan fa ba abun wasa bane azeeza, magana ake ta babu abincin da zamuci yau, ” azeeza tace”idan bamuyi haƙuri ba, to ya zamuyi” tayi maganar tana watsa hannayenta,
Da buɗar bakin deeja sai cewa tayi”bakowa bane ya jamana xama da yunwa ba face angel, meyasa da suka zo baki tashe mu daga bacci ba? Saboda tsabar mugunta,’
Shiru angel tayi don bazata biye mata su yi cece kuce ba, tun da ita halinta ne bata gajiya da shiga sabgar mutane,
“Kodai naje na faɗa ma tsohuwa, ta taimaka tayi magana, su giants su dawo mana da abincin mu,” fuska amarairaice parveen tayi maganar, tagama shan kukan nata, taga babu mai lallashinta ta haƙura don kanta,
“Koda kinje babu abunda tsohuwa zata iya yi mana, kema kinsani” yasmin ce tayi maganar, fuskarta a hade, shi dai danish yayi lamo saman gadonshi yana bin bakunansu da kallo, sam baison hayaniyar da suke yi, don ba yadda ya iya ne daya dakatarsu,
Bakowa Angel tafi jima tausayi ba, Sai danish sanin cewa Jiya baici abincin shi ba, ya basu suka cinye, yanzu ga shi sun rasa abincin yau, dole yafi kowa jin yunwa bawan Allah,
Yau fa ba kanta, Duk jikinsu yayi laushi, Ko toilet babu wanda ya shiga don yin wanka ko wanke fuska, damuwarsu Yunwar da zasu kwasa yau, an sanyasu yin azumin dole batare da sunyi niya ba,
Saukowa haris yayi daga saman gadonshi, Ya wuce gadon danish, daga ƙasa ya zuƙunna tare da ruƙo hannun danish acikin nashi, idonsu cikin na juna, yace”ɗan uwana, ya jikin naka”? Cikin sanyin murya ya amsa mashi da cewa”da sauƙi sosai,” murmushin haris yayi”Am glad to hear that, Nayi kewarka sosai na tsawon kwana biyar din nan, saina ji kamar na rasa wani sashe na jikina ne” wannan maganar ta haris ba ƙaramin faranta mashi rai tayi ba, shi kanshi ya shaida irin ƙaunar da haris ke yi mashi aduk duniya bai da tamkar shi,
“Haris, nima nayi missing ɗinku sosai, har bazan iya misaltawa ba………” dakatawa ya ɗanyi da yin maganar, ya juya bayan shi yana kallonsu batool,
“Can i talk to u”? Danish ne yayi tambayar yana kallon kowannnsu, Jin haka yasa suka sauko daga saman beds ɗinsu, suka Nufi gadon danish, a kewaye da gadon suka tsaya curko cirko suna yi mashi Yaji ki, ƙasa ƙasa da murya yake amsa masu, yayin da idanuwanshi ke akan fuskar angel dake a tsaye can nesa da su, Batool ce ta lura da kallon angel da yake yi, ta fahimci yana son itama tazo ne, amma tasan bazai iya kiranta ba, hakan yasa ita ta kira ta da kanta tace”Ki zo mana, danish yana son yin magana damu” tafiya ta soma yi xuwa bakin gadonshi ta tsaya a gefensu tare da goya hannayenta saman kirjinta,
Calmly yaci gaba da cewa”dama inaso nayi maku godiya ne, bisa irin nuna kulawarku agare ni, kun damu dani sosai, nasan kunyi missing ɗina na tsawon 5 days da bana acikin ku, nima kuma duk da bana atare daku kuna araina, i luv u so much guys……” tun da ya soma magana suka natsu suna sauraronshi, Yaushe rabon da suji danish yayi magana mai tsayi irin wannan har sun manta, lallai jiki yayi sauƙi suka ayyana hakan acikin ransu,
still bai janye idanuwanshi daga kan fuskar angel ba, itama shi ɗin take kallo, So yake yayi mata godiya amma ya kasa, ita kanta angel ɗin ta lura da hakan amma saita basar, Jira take taga idan zaiyi mata magana,
Muryar javed ce ta janyo hankalinta wurin kallonshi” Angel Amadadin danish, muna matuƙar yi maki godiya, bamu ta6a tsammanin zaki iya taimakon shi ba, a lokacin da kika nemi alfarmar mu baki dama, Sai gashi kin bamu mamaki, Ta silarki danish ya fara wartsakewa, tabbas ke ɗin alkhairi ce agare mu, Kuma yakamata Gaba ɗayanmu mu fahimci cewa angel masoyiyarmu ce ba maƙiyiyar mu ba” ya ɗan dakata da yin maganar yana kallon fuskokin sauran ƴan uwan nashi, kafin yaci gaba da cewa”Idan har muka yi ma angel biyayya zamu koyi abubuwa da dama awurinta wanda bamu Iya ba, zata wayar mana da kanmu, kuma zata ɗaura mu akan hanyar dai dai, Amma fa shawara ce nake bamu muyi tunani,” yakai ƙarshen maganar yana jira yaji amsar da zasu ba shi,
Deeja ce tace”Amma ae tsohuwa tace mana kada mu yarda da ita, mu daina sakewa da ita, zata gur6ata mana tarbiyarmu ne, kuma tana yi mana ƙarya nidai gaskiya bazan yarda da angel ba, ” tayi maganar tana maƙe kafaɗarta, maimakon angel taji haushin maganar deeja, Saima ta saki murmushi saboda ta lura hada quruciya ke ɗawainiya da ita,
“maganar da Javed ya faɗa gaskiya ne, Angel masoyiyarmu ce, kuma komai take yi mana tana ƙoƙarine don taga mun dawo akan hanyar dai dai, Ina roƙon duk wani dake ƙyararta acikinmu ya ajiye makaman yaƙin shi, yazo mu rungumi juna, faɗa ba namu bane,” a tsanake batool takai karshen maganarta,
“Silar angel, danish ya samu sauƙi, bashi kaɗai ba, Tun jiya da angel ta raira mana waƙar nan mai daɗi da sanyaya zuciya, gaba ɗaya jikin kowannanmu yayi sanyi,……” dariya angel tayi jin abunda azeeza tace,
“Ba waƙa bace, Karatun al’qur’ni ne mai girma, ” cike da mamaki suka maimaita kalmar”Karatun al’qur’ani mai girma” Hanna tace”menene ma’anar hakan? Ko zaki iya fahimtar damu”? Tayi maganar a ƙagare da son Jin amsar da angel zata basu,
Ƙoƙarin buɗe baki tayi da niyar ta ba Hanna amsar tambayarta, Sai dai kafin tayi yunƙurin yin hakan, Suka Jiyo Motsin buɗe ƙopar ɗakin tsohuwa, Nan fa hankalinsu gaba ɗaya ya koma akan ƙopar ɗakin,
Fitowa tayi daga Cikin ɗakin tana dogara sanda, Fuskarnan a tur6une babu walwala acikinta, da sauri Su hanna suka Nufe ta, Cikin girmamawa suka gaishe da ita, babu yabo babu fallasa ta amsa masu,
Parveen tace”tsohuwa Yunwa muke ji, Giants sun kawo mana abinci, A lokacin bamu farka daga bacci ba, har suka tafi da shi”
Jinjina kai tsohuwa ta ɗanyi tana bin fuskokinsu da kallo, Su kansu sun lura da canjin dake atattare da ita, kamar wani abu na damunta, Hanna tace”tsohuwa Baki da lafiya ne? Naga kamar bakya Acikin walwala,” sai lokacin tsohuwa ta buɗe baki tace” kunyi kuskure da ku ka bari giants suka juya da abincin nan, ai kunsan basa wasa da lokaci, meyasa baku farka daga bacci ba har suka tafi? Bayan kunsan cewa Ba dawowa zasuyi ba, idan har suka tafi dashi”!
Muryar Parveen tamkar zata fashe da kuka tace”yanzu shikenan bazamu samu abinci ba yau”? Idanuwanta suka cicciko da ƙwalla,
angel dake acan tsaye ruƙe da qugu, ta tunkari inda suke, agaban tsohuwa ta tsaya tare dacewa”Irin ƙaunar da kike masu kenan? ashe uwa zata Iya barin ƴa’ƴanta da yunwa? Alhalin ita tacika cikinta ta ƙoshi! Waye bai kuskure rayuwa? Yin bacci ya zama laifi kenan? Inbanda rashin lissafi taya mutumin dake bacci zai zama mai laifi? Meyasa su giants ɗin da suka zo basu ajiye mana farantan abincin ba, su sai su tafi idan yaso aduk lokacin da muka farka sai mu ci, Amma saboda tsabar zalunci shine suka tattara kayan abincin suka tafi dashi, Anya kuwa tsohuwa? Cike da tuhuma takai ƙarshen maganar tana kallon fuskar tsohuwa, ta tsareta da waɗannan Jagwalallun idanuwan nata,
Daƙyar ta iya buɗe baki tace”Haka dokar Aikin Giants suke! Lokaci gare su, basa wasa da aikinsu, idan suka kawo abinci suka ga babu wanda yazo yaci zasu kwashe ne su tafi dashi,” wannan itace amsar da tsohuwa taba angel,
Mamaki akan fuskar angel tace”Wannan wata irin dokace mara kan gado mara tsari? Wannan ae horo da yunwa ne! Abincin ma da sau ɗaya ake bamu shi a rana, mun ƙoshi bamu koshi ba wannan ba damuwarku bace, Shine kuma harda wata dokar in an kawo abinci bamu hallara ba, za’a juya dashi? Me hakan ke nufi? Wai mu me kuka ɗauke mu dabbobi ko me? A harzuƙe angel tayi maganar,
Wata irin gigitacciyar tsawa Batool ta daka ma angel, gaba ɗaya saida kowa ya razana hatta danish dake a kishingiɗe saman gadonshi saida ya firgita ya nemi zaucewa,
A matuƙar ruɗe Angel ke kallon batool, ta ɗaure fuska tamkar ba ita ba, Cikin fushi ta soma magana
“Yakamata ki kiyaye harshenki aduk lokacin da zakiyi magana da tsohuwa, don me zaki dinga yi mata magana a gadarance? Babu tausasa harshe? Idan ma kina son shiga tsakaninmu da ita ne, Inaso ki sani bazaki ta6a yin nasara ba, ita ɗin uwace agare mu kuma bazata ta6a iya cutar damu ba……” ba angel ba, hatta su haris sai da suka sha Jinin jikinsu, Jin yadda Batool ke magana a faɗace abunda bata ta6a yi ba,
Muryar angel adisashe tace”Batool! Yau keda kanki kike Yi mini tsawa! Saboda kawai ina son ƙwato maku haƙƙinku da aka tauye…..” kafin takai ƙarshen maganarta, Javed ya dakatar da angel ta hanyar ɗaga mata hannunshi”Is enough! Kawai kiyi mana shiru, Kina so ne, Ki shiga tsakaninmu da ita, babu ruwanki da rayuwarmu, Ki barmu a yadda kika ganmu, haka muka saba rayuwa, bin dokar kurkuku wajibi ne agare mu prisoners” wani irin shu’umin murmushi tsohuwa ta shiga saki Nan da nan walwalar fuskarta ta dawo Jin yadda Suke Goyan bayanta, ashe har yanzu Hayaƙin sihirinta na aiki yadda ya dace, ta ambaci hakan acikin zuciyarta,
Tuni idanuwan angel sun Ciko tab da kwalla, tsabar baƙin Ciki Ya hana ta ƙara cewa komai, Juyawa tayi a fusace ta koma saman gadonta, Ta zauna tare da ruƙo pillow ta rungume a kirjinta,
Kallonsu tsohuwa tayi da alamun farin Ciki akan fuskarta tace”Ku cigaba da yi mun biyayya ƴa’ƴana, albarka zata tabbata akanku, ” muryar parveen a ƙule tace”Abincin fa”?
Tsohuwa ta bata amsa da cewa”Ku jira ni, Ina zuwa” ta ambaci hakan tare da juyawa ta shige Cikin ɗakinta, baka iya hangen komai ko ka leƙa sai duhu,
Badajimawa, Sai ga tsohuwa ta fito hannunta ɗaya a ruƙe da Kwandon kayan marmari, Miƙa ma Su tayi” Ku je kusha, Kafin zuwa gobe zaku samu abinci” Hannunsu har kerma yake yi wurin kar6ar Kwandon daga hannunta,’ Juyawa tayi tana dogara sanda ta koma Cikin ɗakinta, tare da jan kopa ta datse,
Ita dai angel sam bata yarda da kayan marmarin da tsohuwa ta basu ba, Cike fa da kwando, manyan apples ne tare da damin ayaba,” a kalla kowa zai samu apples uku, da Ayaba Uku, Batool ce ta rarraba masu kayan marmarin kowa ya kar6a yana sha, koda ta miƙa ma angel hannu tasa takar6a amma bata sha ba, A ƙarƙashin pillow ɗinta ta 6oye su, tana jira taga idan sun kammala sha batare da wani abu ya faru dasu ba, itama sai tasha, Har batool sai da tayi mata magana akan bazata sha ba, tace mata ba yanzu zata sha ba, Sai zuwa anjima,
Tun da suka kammala Cin apples ɗinnan da ayaba, wani irin matsiyacin bacci ne yazo masu, lamarin ya ɗaurewa angel kai, Ganin su kwakkwance A ƙasa suna bacci, kamar waɗanda suka Sha kayan maye, Juyawa tayi da sauri tana kallon gadon danish, cike da fargabar kada ace shima baccin ya ɗauke shi, idonshi biyu ta same shi, ya kwantar da kanshi saman pillow, babu alamun bacci attare dashi, Su biyu suka rage idonsu biyu,
Tabbas tafara zargin Kayan marmarin da tsohuwa ta basu ne ya sanya su yin bacci, da yake ita da danish basu sha ba, shiyasa bacci bai ɗauke su ba, ko meyasa tayi masu haka? Kodan kada su ji yunwa ne”?
“Meyasa ba zaka sha ba”? Tayi tambayar tana kallon danish, ganin ya ajiye nashi apples ɗin a gefenshi,
Cikin sanyin murya ya amsa mata da cewa”bana ra’ayi, zuwa anjima xansha” ya ƙarasa maganar, tare da miƙewa zaune, ya zuro da dogayen ƙafafuwanshi ƙasan gadon kafin ya yunƙura ya miƙe tsaye, Har yanzu jikin nashi babu ƙwari, shiyasa tun ɗazu ya gaza saukowa daga saman gadon,
Daƙyar yake ɗaga ƙafar yana tafiya, Ji take kamar taje ta taimaka mashi sai dai batasan tana kusanta kanta dashi,
Tafiya yake yi yana waiwayon su Haris dake baje a ƙasa suna sharar bacci, sam bai kawo komai aranshi ba, Shigewa Ƙopar toilet ɗinsu yayi, Sai da ya 6ace ma ganinta tukunna ta ɗauke idonta daga kanshi, Cike da fargabar kada ya raunata kanshi, tun da ba ƙoshin lafiya gare shi ba,
Tsawon lokaci da shigarshi cikin toilet ɗin, ta Lumshe idanuwanta tare da kishingiɗawa, da niyar ta ɗan runtsa itama, Takun tafiyar mutun tajiyo acikin kunnata, tana buɗe ido ta fasa wata irin gigitaciyar ƙara tare da sanya hannu ta rufe idanuwanta, Jikinta na kerma, A matuƙar ruɗe Ya koma Cikin 6angaren toilet ɗin nasu, Ya la6e abakin ƙopa yana leƙen ta,
Abunda ya faru Lokacin data buɗe ido, Karaf idanuwanta suka sauka akan Surar danish, Ya fito naked babu sutura ajikinshi, Wannan ne yasa tayi matuƙar firgita, Jikinta ya hau kerma, dole ta ruɗe saboda halittar dake gare shi, Dogone sosai komai Na jikinshi ba ƙarami bane, shi kuma tsawar da tayi ne yasa shi gigicewa ya juya aruɗe ya koma sashen toilet ɗin, Yana leƙenta,
Ƙanƙame jikinta tayi ta gaza motsawa, tayi matuƙar tsorata, ranta ya 6aci sosai batare data buɗe idanuwanta ba, taci gaba da surfa mashi masifa ta inda take shiga bata nan take fita ba, sai da ta gaji da zazzaga mashi masifa tukunna ta yi shiru tana faman huci har lokacin bata buɗe idanuwanta ba,
Jin yayi shiru bai ce mata komai ba, yasa ta sassauta muryarta tare da cewa”Go back, I don’t wanna see you naked, if you need something, you should ask me to give it to you”
a ƙule tayi maganar, don ba ƙaramin haushin sa taji ba, ƙato da shi zai fito babu kaya ajikinshi, yanzu da ace idonsu Batool biyu ba bacci suke yi ba, duk haka zasu ganshi, tarasa gane wani irin mutunne shi, duk da tana yi mashi uziri na halin da yake Ciki na rashin lafiyar da take tunanin ɗaura mashi ita akayi, shiyasa ya zama wani sauna dashi,
Kasa kunne tayi sosai don ta samu damar jin me yake ce mata, magana yake yi mata akan ta miƙo mashi bargonshi, yana so zai lullu6e jikinshi,
Sai lokacin ta fahimci cewa, Ya wanke kayanshi, dama haka suke Yi idan suka wanke kayansu, sai su sanya bargo su lullu6e jikinsu, maimakon tunkafin ya shiga cikin toilet ɗin ya tafi da bargon shine bai tsaya ya ɗauka ba, yanzu gashi yasata kallon haramun, ta ambaci hakan acikin zuciyarta,
“wait, I will hand it to you ka koma toilet” amsa mata yayi da toh, bayan wasu daƙiƙai, ta ɗan zame tafin hannunta daga kan fuskarta, ta saci kallon Hanyar toilet ɗin, Ganin babu shi yasa ta yi saurin saukowa daga saman gadonta, takai hannu saman nashi gadon ta ɗauko bargonshi, Ta nufi bakin door ɗin farko ta tsaya tare da ɗaga murya tace”Ga bargon” zuro mata da hannun shi yayi, maimakon ta miƙa mashi bargon saita tsaya tana kallon kyawawan yatsun hannunshi, sai kace bana ɗan bil’adama ba, saboda tsabar kyau, matsalarsu ɗaya basu yanke akaifa, yadda kasan hannun shaiɗanu, Ƙumba zaƙo zaƙo,
“Bring me am waiting” figigit tayi jin muryarshi, harya gaji da miƙa hannu, da sauri ta damƙa mashi bargon, ya kar6a,
Abakin ƙofar ta tsaya tana jiran ya kammala sanya bargon ya fito itama ta samu ta shiga wankan,
Tana Cikin tsawuwar nan, Taji takun tafiyarshi, bin ƙopar tayi da kallo, Fitowa yayi, Jikinshi ɗaure da bargon daya sanya, har zuwa chest ɗinshi,
Bata bari sun haɗa ido ba, Ya wuce ya nufi gefen gadonshi Ya zauna, tare da jingina bayanshi a jikin bango,
Tunani tayi kodai itama ta wanke kayanta ne ? Domin kuwa tajima bata wanke su ba, har tsami suke Yi mata,
Komawa tayi ta dauko bargonta dake yashe saman gadonta, da sauri ta nufi toilet ta shige, tsawon lokaci tana aciki, sai da ta kammala wanke kayan ta ta shanyasu, bayan tayi wanka ta ɗaura bargon a ƙirjinta, A bakin ƙofar fitowa daga sashen makewayin nasu ta la6e tana satar kallon danish, Sam bata so ya ganta in zata wuce,
Ganin ya lumshe idanuwanshi ne, yasa ta yi tunanin yin sauri ta wuce, Cikin sanɗa take tafiya, har ta samu takai bakin gadonta ta haye ta kwanta, yinin ranar su biyu suka yi shi, ita da danish, lokacin da kayansu suka bushe ita taje ta dauko masu uniform ɗinsu, ganin ya fara bacci yasa tayi saurin warware bargon dake ajikinta, ta xura uniform ɗinta, sai daga bisani taje bakin gadon danish ta tada shi daga bacci, ta miƙa mashi nashi unifom ɗin yasa hannu ya kar6a,
Ta juya ta koma gadonta, ta zauna daga gefe, idonta akansu batool dake ta sharar bacci, koda taga yana kokarin zame bargonsa don ya zura kayanshi da sauri ta kifa kanta saman pillow, ba ita ta ɗago ba har saida ya kammala sanya kayan ajikin shi, tukunna ta ɗago da kanta,
Abu kamar wasa har dare yayi su batool basu farka daga bacci ba, Hankalin angel yaƙi kwanciya shi kanshi danish jikin shi duk yayi sanyi, har sauko yayi daga saman gadonshi yaje ya duƙa agabansu yana tatta6a su, wannan wani irin dogon bacci ne da mutun zai kwashe yini guda tun safe har dare? Anya kuwa tsohuwa abunda tayi ta kyauta masu? Sai kace wasu matattu,
*❤❤❤PRISONERS❤❤❤*
“Danish Ko dai inzo in kama maka, Mu mayar dasu saman beds ɗinsu? Ta yi tambayar tana kallon danish dake zuƙunne agaban Haris dake ta bacci, batare daya juyo ya kalle ta ba, yace mata eh, saukowa tayi daga saman gadon ta ƙarasa inda danish yake, yasa hannu ya ruƙe ƙafafuwan Haris ita kuma ta ruƙe hannayenshi Suka ɗaga shi zuwa saman gadonshi suka kwantar da shi, Haka suka bi kowannansu ɗaya bayan ɗaya suka ɗauko shi daga ƙasa suka mayar dashi saman gadonshi, suna ajiye batool saman gadonta, gaba ɗaya hasken ɗakin ya ɗauke duhu ya mamaye idanuwansu, basa iya ganin juna,
“Bari naje na kunna fitilun ɗakin, kada ka motsa” ta faɗa mashi hakanne don tasa halin shi da ruɗu, yanzu ya rikice mata, tafiya take yi cikin ɗakin tana laluban hanya har Allah yasa taci karo da table ɗin da fitilun suke, takai hannu ta kukkuna su, ɗakin yayi haske sosai, ta ɗauko ɗaya daga Cikin fitilun ta juyo tana hasko inda danish yake a tsaye, Ya goya hannayenshi saman chest ɗinshi ya ɗan jingina bayanshi jikin bango, tunkararshi tayi adai dai inda yake ta tsaya, Da sauri ya rufe idanuwanshi saboda hasken fitilar dake a hannunta, ba ƙaramin cika mashi ido yayi ba, ganin haka yasa ta kawar da fitilar gefe,
“Muje mu kwanta ko”? tayi tambayar tana kallonshi, babu musu ya amsa mata da toh, juyawa tayi gaba ta wuce nata gadon shima Ya wuce gadonshi, a tsakankanin beds ɗinsu ta ajiye fitilar, kusan atare suka haura saman gadonsu suka kwanta suna fuskantar juna, ya tsareta da sexy eyes ɗinshi yana kallonta without blinking, ganin kallon yayi yawane yasa tace”ba zaka yi bacci ba”? Wit low voice ya amsa mata da cewa”bana jin bacci,” yatsina fuska tayi sam ba haka taso ba, saboda ta shirya yin amfani da wannan damar da take da ita,
“Danish Baka jin yunwa? Naga jiya baka ci komai ba, yau ma kuma babu abinci, why bazaka Ci apples ɗinka ba? Sai in haɗa maka da nawa ka ci”? Angel sarkin wayau, so take yaci don shima yayi bacci mai nauyi irin nasu batool, ko ta samu ta shige toilet ɗin can ta fara gudanar da aikinta na fasa Glass window ɗin nan domin Shiga Cikin gidan Kurkukun ƙaddara,
“Bana jin yunwa” shine amsar da yabata, tunani ta shiga yi ta wace hanya zata yi mashi wayau don ya yi bacci,
“Tunda ba zaka yi bacci ba, to ka daina kallona mana, Ni inaso nayi bacci bana iya bacci idan ana kallona” jin abunda tace ne yasa shi yin saurin rufe idanuwanshi,
Tsawon mintuna angel tana kallon shi, tunanin kiranshi tayi don taji idan yayi bacci” Danish” amsa mata yayi”yeah” wai bazaka runtsa ba, da buɗar bakin sa sai cewa yayi”If you don’t sleep, nima bazanyi ba.” serious yae maganar, rufe idanuwanta tayi”its okey, ga shi nan zanyi baccin kaima kayi” Ya amsa mata da toh, daga haka kowa yayi tsit acikinsu,
A lokacin da tayi tunanin ya nutsa cikin Baccin shi, ta sauko daga saman gadonta, takai hannu ta ɗauki fitilar da ta ajiye a tsakankanin beds ɗinsu, cikin sanɗa take tafiya tana tunkarar sashen toilet ɗinsu, duk taku ɗaya saita waiwo ta saci kallon Shimfiɗar danish,
Tana kawowa bakin ƙopar shiga sashen ta afka ciki, ta buɗe toilet ɗin ta shige taja ƙopa ta garƙame ta,
A ƙasa ta sauke fitilar, ta taka zuwa gaban bokitin ƙarfen nan ta ɗauke shi, tsayinta bazai kai ga tagar ba, dole sai ta ƙara da tsalle, cike da ƙwarin gwiwa ta daddage ta daka uban tsalle ta ɗaga Bukitin ta bugashi jikin glass ɗin da iya ƙarfinta na ƙarshe, sai dai wani abun mamaki glass ɗin Ko zagewa baiyi ba, Kamar ta daki ƙarfe ashe abun bana wasan yara bane, Tsalle taci gaba dayi tana kwaɗa bokitin jikin glass ɗin a ƙalla tayi kusan sau Talatin amma glass ɗin Ko yaƙi tsagewa, jikinta duk ya saki ga uwar zufa dake tsastsafo mata, sai faman haki take yi kamar wadda tasha uban gudu, ta galabaita sosai, sauke bokitin tayi ƙasa, ta zukunna tana mayar da numfashi, hatta idanuwanta sai da suka Canza launi,
Idan tahuta ta dawo normal saita kuma mikewa ta ɗauki bokitin Ta cigaba da buga shi jikin Windon, Har saita galabaita tukunna saita koma ta zukunna tana haki,
A wannan Karan Da azama ta miƙe ta ɗauki Bokitin ta daddage ta ɗaga shi da niyar ta kwaɗa shi jikin glass ɗin, kwatsam Taji motsin mutun acikin Makewayin, Ras gabanta yayi wani irin mugun bugu, tsananin tsoro ya bayyana akan fuskarta, batasan Lokacin data jefar da bokitin hannunta ba, Sam ta kasa juyawa taga wanene Ya shigo Cikin toilet ɗin, Bayan kafin ta shiga sai da ta garƙame ƙopar ta ciki ta sanya jam lock, ta yadda ba wanda zai iya shigowa, tabbas kuwa wannan ko wanene to ba mutun bane sai dai aljani, tuni tasha Jinin jikinta, Zufa ta ko’ina ta shiga wanko mata,
Takun tafiya taci gaba da ji ana tunkaro inda take, wani irin wahalallan yawu ta haɗiya, kafin tayi tunanin juyawa baya taga wanene taji an rungumeta, sai da ya zagayo da hannayenshi saitin shafaffan cikinta tukunna ta gane wanene, tsabar ruɗi takasa furta komai, muryarshi ta juyo ƙasa ƙasa yana faɗin”mu koma ɗaki, i was scared of being alone, kin tafi kin barni ni kaɗai,” tashin hankalin da ba’a dama shi date! Kwanto da kanshi yayi ta gefen wuyanta, tsigar jikinta duk ta tashi, domin kuwa wannan daƙyar ya kasance danish ne! Taya akai ya shigo toilet ɗin bayan tayi locking ƙopar, saukar numshinsa taji asaman skin ɗinta, sai ƙara ƙanƙameta yake yi yana faɗin su koma ɗaki,” acikin zuciyarta ta shiga ambaton”La’ila ha’illah anta subhanaka inni kuntu minazzalimin,” Daƙyar ta samu ta daure ta cije Takai hannu ta raba hannayenshi daya tamke cikinta dasu, a ruɗe ta juya tana kallon fuskarshi, dagaske dai shi din dai ne, danish da ta bari akwance yana bacci, da sauri takai idonta kan ƙopar toilet ɗin don taga idan ta nan ya biyo, wani abun al’ajabi, ƙopar a datse take da jam lock ɗin kamar yadda ta barta, kallonshi tayi sai faman lumshe idanuwanshi yake yi,
“Ki wuce mu tafi, bacci nake ji” yadda yayi mgnr voice dinshi a raunace,
Babu musu ta yi gaba yabi bayanta, abakin ƙopar ta tsaya ta cire jam lock ɗin, tasa kai ta fuce yana abiye da ita, ta yi tsammanin Idan aljani ne zai 6ace na aihin kuma ta ganshi kwance saman shimfiɗarshi sai da ba haka ta gani ba, Shi ɗin daine da kanshi ya taso, Tabɗi akwai gwarama domin kuwa dole ɗaya ya kasance gaskiya, Danish Ana sarrafa shi? Ko kuwa yana da sihiri ne ajikinshi ne? Ita damuwarta ba faɗo mata da yayi cikin toilet ba, a’a Taya akai ya shiga bayan ta sanya jam lock ta Ciki? Ta ina ya shigo?
Takai ƙarshen zancen zucin nata tare da haye wa saman gadonta, shima ya hau nashi gadon ya kwanta, yana fuskantar inda take kallo,
Zuba mashi ido tayi cike da tuhuma, shi kuwa ya lumshe ido alamar bacci zaiyi, ta jima tana kallonshi kanta ya gama ɗaure wa, daga bisani ne bacci yae awon gaba da ita, tsakar dare ta farka ta miƙe tabi kowani gado ta tofe su da addu’a, Bayan ta kammala ta koma ta kwanta wani sabon baccin ya kuma ɗaukarta,
*in the morning🌹✍️*
A washe garin ranar, tun kafin ta farka ta soma Jin hayaniyar su Batool, tsabar farin ciki yasa tayi saurin kai hannu ta zame bargon jikinta, ta ware round eyes ɗinta tare da kallon gadajensu, a zazzaune ta same su sai surutu suke yi kamar ba waɗan da suka sha uban baccin nan ba, na yini guda,
Miƙewa tayi zaune ta sauko daga saman gadonta, a hankali take tafiya tana binsu da kallo, a lokacin danish bai farka ba, yana naɗe Cikin bargonshi,
Abakin gadon Batool ta tsaya tare da kasa kunne tana sauraron firar da suke Yi
“ko wanka bansamu nayi ba, Jikina duk tsami yake yi mini, tun ɗazu da muka ci apples ɗin nan bacci ya ɗauke mu bansamu nayi ba” azeeza ce tayi maganar,
Batool tace”Nifa nayi mamaki, ya akai mu kayi bacci daga Cin tufa da ayaba, kuma ba’a floor muka kwanta ba, to waye ya dawo damu saman gado”? Fuskarta da alamun ruɗi tayi maganar,
“i was confused, na kasa gane tsawon wani lokaci muka ɗauka muna yin bacci, amma gani nake kamar bamu daɗe ba, tun da har yanzu safiya ce”
Ƙumshe dariya angel tayi jin abunda suke tattaunawa, wai su duk a tunaninsu suna a jiya ne, basu san cewa sun ɗauki tsawon rana ɗaya suna bacci ba, har wata ranar ta shigo, kamar waɗan da a kayiwa wahayin surutu, Sumar kawunansu duk ta cukurkurɗe, Bakunansu hada yawun bacci,
“Yanzu haka zamu yini kenan muna jin yunwa babu abinci’? Nifa apples ɗin da tsohuwa ta bani ba abunda ya tsinana mini saboda wata irin matsiyaciyar yunwa nake ji” acewar parveen, duk fa wannan surutun da suke yi basu san cewa angel tana atsaye ta ruƙe ha6a tana kallonsu,
“Yanzu ya zamuyi kenan? Sam lokacin baya tafiya yadda ya dace, Nayi expecting ɗin ma idan muka farka daga bacci zamu ga marece yayi amma sai naga wai har yanzu muna a safiya” baki a kumbure Hanna tayi magana, Ita dai deeja sai buga tsoki take yi, abun ya motsa, haris na kwance saman gadonshi idonshi na fuskantar ceilling,
Juyawa angel tayi tare da kallon shimfiɗar Danish, samun shi tayi a kishingiɗe, For the first time da ta ta6a yin tozali da Kyakkyawan murmushin akan fuskarshi, masha Allah, Waya ga zumar kyau, Dimples ɗin shi biyu sun lotsa sosai, yadda kasan kanshi farau kyau, ɗan zaro ido tayi tana kallon fuskarshi, farkawarshi kenan daga bacci, gaba ɗaya hankalinshi na akan su batool dake ta faman yin sambatu, Su yake yi ma murmushi jin wata shiririta, Su ɗauki tsawon Yini ɗaya suna bacci, Su kwana suna bacci amma suna faɗin cewa Basu son komai ba, Rashin ma bugi ne ke damunsu
Ɗauke idonshi yayi daga kansu batool, ta wutsiyar ido ya hangi angel tsaye tana kallonshi, da sauri ya kalleta suna haɗa ido, ya ɗauke murmushin dake akan fuskarshi, Can kuma ya kifa kanshi saman pillow, girgixa kai tayi fuskarta dauke da murmushi aranta tace”Ka gama rowar murmushin naka, wata rana abanza xaka dinga yi mini shi batare dana roka ba,”
Gyaran murya tayi masu Batool, kamar masu jira kusan atare suka ɗago suna kallonta, har suna haɗa baki wurin ambaton sunanta”ANGEL”!
saukowa Batool da azeeza su ka yi daga saman gadonsu suka nufi inda take a tsaye, rungumeta azeeza tayi tana faɗin”Angel kema kinyi bacci da kika ci apples,”
Bata bata amsa ba, sai da tafara zagayo da hannayenta saman bayan azeeza tukunna tace”Ae ni banci appales ɗina ba, Ni da danish, Ku da kuka Ci ku kayi bacci, gaya nan yanzu kun wartsake,” ɗagowa azeeza tayi daga kan Jikin angel tace”Amma ae lokaci bai motsa ba, har yanzu fa safiya ne, yau zamu yini muna jin yunwa” aɗan shagwa6e tayi maganar, hakan ba ƙaramin dariya yaba angel ba,
“Sister”! Batool ce ta ambaci sunanta, tana atsaye kusa dasu, ruƙo hannunta Angel tayi acikin nata tace”My other half, nayi missing dinki, ina fata kin tashi lafiya, an sha bacci” lumshe ido batool tayi fuskarta a yamutse tace”am not feeling well, sai nake ji kamar wani abu ya faru da muna bacci, na shiga ruɗu,” janyota angel tayi zuwa jikinta, ta rungume ta, batool ta kwantar da kanta saman kafaɗar angel, hannu tasa tana shafa bayanta tace”Ki kwantar da hankalin ki, ba abunda ya faru, bacci kawai kuka sha,” ajiyar zuciya batool ta sauke tare da raba jikinta daga na angel, still idonsu acikin na juna
“Yakamata Ku je ku yi wanka, bazan 6oye maku ba, tsami ku ke yi, daurewa kawai nake Yi ina yin magana daku” cikin zolaya tayi maganar, gani tayi suna shinshina Jikinsu, harara batool ta jefa mata”Sister kinyi wanka shine baki tada mu daga bacci ba, Munyi wanka mu ma,”? Fuskarta akwa6e tayi maganar,
“Ae ni bana tada mutun idan yana bacci, yanzu tun da kun farka, sai kuje ku yi,”
Juyawa batool tayi tare da kallonsu Hibba dake zaune saman gadajensu, Ko motsawa basuyi ba,
“Ku tashi muje mu yi wanka,” saukowa Kowannan su yayi daga saman gadon shi,
“Jiya nida danish mun wanke hada uniform ɗinmu,” su6uce mata maganar tayi
Cike da mamaki batool tace”Jiya kuma”? Da sauri angel tace”Ina nufin ɗazu da safe, lokacin da kuna bacci, ae na fada maki ni da shi bamu Ci namu apples dinba,” takai ƙarshen maganar tana ƴan kame kame, Batool kamar bata yarda da maganarta ba, gyaɗa kai kawai ta yi tare da wuce ta nufi toilet,
Batool ce tabasu shawarar suma su wanke nasu Uniform ɗin, Sai da kowa ya cire uniform ɗinshi, Suka yi ɗaurin gaba da Bargunansu, Hada maxan su, tattara Uniform ɗin Batool tayi ita da Angel da Hanna, Suka shiga toilet sec ɗinsu, Anan Suka tara kayan wankin, Azeeza da javed ne suka ɗebo ruwa a buckets, rubina ta ɗauko masu detergent, Su Uku Suke wankin kayan suna yi suna fira, Sauran ƴan uwan nasu ba wanda ya taya su dama su suka sanya kansu zasu wanke masu kayan, don sunce su baza su yi wanki ba kada ƙarfinsu ya qare, Gashi yau babu abinci, angel dai jinsu kawai take yi, ta ƙosa taga reactions ɗinsu idan su giants suka zo kawo masu abinci, zasu sha ruwan mamakin sanin cewa Sunyi baccin kwana ɗaya,
Angel ta dage sai Cuɗa kayan take yi, Koda tazo kan Uniform ɗin haris saita yatsina fuska, Ta ɗago su tana shinshina su, A karshe ta wurga ma batool saman fuskarta tace”ki wanke su, Ni bazan wanke ma ƙato kaya ba”
Dariya su kayi gaba ɗayansu, azeeza tace”Amma kuma kike wanke ma Mubeen dasu javed? Su ba ƙattan bane”? Girgiza kai angel tayi a yayin da take matse rigar data kammala Cuɗawa, tace”Idan kika lura Haris duk yafi su girman Jiki, shifa tuttu6e6ene ga Tumbi, Kuma mummuna……” bata ƙarasa maganar ba, karaf idanuwanta suka sauka akan haris dake atsaye bakin ƙofar toilet ɗinsu, Fitowarshi kenan daga wanka, ya ruƙe qugu jikinshi na sanye da bargon daya lullu6a, fuskarnan babu walwala attare da ita, harara angel ta watsa mashi, ita fa idan ta ɗauko magana ba wanda ya isa ya hana ta ƙarasawa, don haka taci gaba da cewa”sam baida kyau, Hancinshi gajere ne, gashi baƙi, idanuwanshi mitsi mitsi,” tayi maganar tana murguɗa mashi baki,
Tayi tunanin haris zai tanka mata, amma sai taga ya girgiza kai kawai, Ya wuce cikin ɗakinsu,
Batool tace”Na lura angel baki son haris, bansan meyasa ba,” takai karshen maganar tana kallonta,
“batool, he hates me for no reason, that’s why I don’t like him” takai ƙarshen maganar, a yayin da take kai hannu ta ɗauki Bucket ɗinta, da niyar taje cikin toilet ta zumar da ruwan kumfar ta ɗebo wani ruwan da zasuyi ɗauraya da shi,
A bakin fanfo, ta tsaya ta tura bokitin ta kunna tap din ruwa ya shiga kwararowa, zuƙunnawa tayi tana jiran bokitin ya cika,
Bakomai ya faɗo mata arai ba, face Lokacin da Tana agida Tare da daddynta, Ita ko hanyar laundry bata sani ba, daddynta da kanshi yake zuwa ya wanke mata uniform ɗinta na makaranta, Yayi goge mata su, duk wannan wahalar bata san da ita ba, shi ne yi mata wanka ya zura mata kayan ajikinta, Allah sarki rayuwa kenan,
Ganin ruwan ya Cika bokitin, yasa takai hannu ta kashe fanfon, ta miƙe ta ruƙo handle ɗin bokitin ta fuce dashi, a lokacin har su Batool sun kammala Yin nasu sa6in, saura ɗauraya, atare suka dinga ɗauraye kayan, Azeeza ce take zuwa ta shanya su asaman igiyar dake a cikin toilet ɗinsu,
Suna dab da zasu kammala, Sai ga Yasmin ta faɗo Cikin toilet sec din Fuskarta aɗauke da murmushi sai faman washe baki take yi
“Lafiyarki kuwa kike ta faman zabga murmushi”? Batool ce tayi mata tambayar,
Daƙyar ta samu natsuwar cewa”Giants ne suka zo kawo mana abinci, “
Da mamaki akan fuskar batool tace”are u serious? Jinjina kai Yasmin tayi”Ku dai kuzo muje mu ci abinci,” azeeza tace”amma nayi mamaki, yau ba rabon mu kwana da yunwa,” angel dai sai murmushi take saki tana kallonsu, ganin har yanzu basu gane cewa wata ranar bace ta zagayo,
“Bari mu mayar da buckets din Gamu nan zuwa, Allah yasa dai ba wasa kike yi mana ba,” acewar azeeza,
Yasmin tace”Am serious ku dai kuyi sauri kuzo, ” ta juya cike da zumuɗi ta fuce,”
Da sauri suka ƙarasa shanyar kayan nasu, hannayensu a ruƙe dana Juna suka Faɗo Cikin ɗakin, A tsaye suka samu Giants Sun ƙame, Ga kayan abinci nan saman dining carpet ɗinsu, A shaƙe, Su Mubeen duk suna a zazaune Kowa Ya natsu Jikinsu sai kerma yake Yi saboda tsabar yunwar da suke Ji,
Ƙarasa shiga Cikin Ɗakin su ka yi, a gefen ƴan uwansu suka zauna a jere, Batool, azeeza da angel,
Parveen ce ta yaye masu jan ƙyallen tray na farko, waro ido tayi tare da wage baki ganin Tsiren nama A shaƙe Da tray din, saboda yawanshi har suci su rage da anjima su ci, Wani irin maiƙo tsiren ke yi, yaji kayan ƙamshi hada su albasa da tumatur, batare da 6ata Lokaci ba, kowa ya zura hannu yana ɗaukar tsiren naman yana Ci, yadda kasa akuyoyi haka suke taunarshi, mutun ɗaya ne yake Ci atsanake tamkar baison ci, sam baison Cin abinci, karasa uban me yake ci ya ƙoshi, ranshi ne ya bashi cewar ana kallonshi, slowly ya ɗago da idonshi, da sauri angel ta duƙar da nata idon don kada ya gane shi take kallo,
“Kinsa min ido sosai,” ya ambaci hakan acikin zuciyarshi,
“Saboda ban yarda dakai ba, kai ɗin abin tuhuma ne, dole na sanya maka ido, duk wani motsinka akan idona,” acikin zuciyarta tayi maganar, tamkar ta bashi amsar maganarshi alhalin kuwa batasan me yake saƙawa aranshi ba,
“Bansan meyasa kike tuhumata ba, laifin me nayi maki ne? Yayi tambayar acikin zuciyarshi,
Itama tabashi amsa acikin zuciyarta”baka yi mun laifin komai ba, sai dai Ina zarginka, taya akai jiya ka faɗo mini cikin toilet? Bayan na datse ƙopa ta ciki? Taya akai ka shigo? ……….” bata kai ƙarshen zancen zucin nata ba, muryar rubina ta katse mata hanzarinta,
“Kuna ta Cin nama kun manta da shan ruwa”
Tayi maganar tana kallon kowannan su, dakatawa su kayi da Cin naman, Hibba tace bari ta zuba masu ruwan, Bottle water ta ɗauka me sanyi, Ta tsirara masu ruwan acikin Wooden cups ɗin dake a jere, Kowa Ya mika hannu ya ɗauka yana sha, Saboda tsabar kallon angel da yake yi har sai da ya shaƙe ya hau yin tari, da sauri haris ya ɗaura hannunshi akan bayan danish yana ɗan bubbugawa, sai da ya daina yin tarin tukunna ya zame hannunshi,
Dariyar gefen fuska angel tayi saboda ta gane itace silar daya shaƙe, Ta san ya tsargune da irin kallom da tayi mashi ɗazu, abunda ke faruwa su duka biyun basu yarda da Junansu ba, Shi yana kokwanton canzawarta, ita kuma tana zarginshi da ba cikakken mutun bane, tun Daren jiya daya faɗo mata toilet batare da ya kwankwasa ta cire jam lock ya shigo ciki ba, ta ina ya shigo? Shine abunda ya sanya mata ruɗi agame da shi,
Bayan sun kammala Cin abincin, Sauran da suka rage, Hada kayan marmarin da aka kawo masu da kuma snacks, Batool ta tattarasu ta kwashe acikin kwandonta, takai karkashin gadonta ta 6oye masu,
Tattara Kayan abincin giants su kayi, Javed Ya ɗauko masu Na shekaran Jiya da suka kawo ma danish Ya miƙa masu suka kar6a, kafin suka fuce daga Cikin ɗakin,
Lokacin da Uniform ɗinsu suka bushe Kowa Ya ɗauko Ya sanya kayanshi ajikin shi,
Saboda tsabar Jin daɗin da su ka yi, Hanna ta basu shawarar suyi wasa,
Gaba ɗayansu suka taru, a tsakiyar ɗakin nasu, raba kansu su kayi gida Biyu, mutun bakwai bakwai, sai mutun ɗaya ya rage, itace me gabatar da wasan, wato hanna, bayani ta soma Yi masu akan yadda zasu gudanar da wasan,
“Duk wanda na canko acikin ku, zan rufe ma shi ido da tafin hannaye na, in matse su, zan ba shi sunan wanda zai gano mana, idan har ya kuskura bai canka dai da ba, da shi da wanda ya canko, kowa zaiyi masu dundu ɗaya abayansu, kun amince” Haɗa baki su kayi wurin cewa Eh mun amince,”
Duk wannan abun da suke Yi tsohuwa tana atsaye bakin ƙopar ɗakinta tana kallonsu, hannunta ruƙe da sanda, fuskarta ɗauke da wadataccen murmushi,
“Haris come out dakai zan fara, zaka gano mini deeja,” fitowa haris yayi daga Jerin layin da yake yaje gabanta ya tsaya yana fuskantar sauran ƴan wasan, Hanna ta tsaya daga bayan shi ta zagayo da hannayenta saitin fuskarshi ta rufe mashi idanuwanshi da tafin hannayen ta,
Tafiya su ka yi agaban layin na farko, Kowa yasha Jinin jikinshi, daga haris yakai hannu zai canko mutun, sai kaga suna girgiza kai, gudun kada yaja masu dundu, Cikin rashin sa’a haris Ya ruƙo hannun mubeen yace Itace, aikuwa gaba ɗaya suka fashe da dariya, mubeen kuwa rai a6ace yace”amma dai haris anyi hamago, kai baka gane hannun mace da namiji ne? Deeja ce fa akace ka kamo ba ni ba,” Maganarshi tayi matuƙar basu dariya, hatta tsohuwa saida ta murmusa,
“Kamar yarda nace a dokar wasa, Idan mutun ya canko ba dai dai ba, Da shi da wanda ya canka kowa xaiyi masu dundune, don haka Mubeen da haris ku zuƙunna ku bamu bayanku,,
Mubeen yana Cika yana batsewa ya fito daga cikin layi, ya Duka shima Haris Ya duƙa, kowa ya naɗe hannun rigarshi, babu tausayi babu imani, haka suka jera layi, suka dinga kai masu dunduna abayansu, koda akazo kan angel dama haushin haris take ji, Muguwar da gwiwar hannunta ta daddage ta buga mashi ƙulli a baya, har wani sauti ya bata durum! nan take ya kife ƙasa, dama shi mubeen tuni ya zube yana mayar da numfashi ido sun ciko tab da kwalla, koba a faɗa mashi ba yasan wacece tayi mashi wannan dundun, idanuwanshi akan fuskar angel yaci alwashin sai ya rama idan idan aka zo kanta,
Hanna tace”the next person is, ” kowa ya kasa kunne yana jira yaji su wanene,
Murmushin mugunta ta saki kafin tace”Batool! Ki gano mana Javed,” Jiki ba ƙwari Batool ta fito daga Ciki layinta, Hanna ta rufe mata ido da tafin hannunta, suka soma tafiya suna Bin layin na farko, Duk wanda ta ruƙo hannunshi saita saki, harfa ta ruƙe hannun javed ta murza shi kamar tace shine sai kuma ranta ya bata cewar bashi bane, ƙasa ƙasa da murya yake ce mata ke ni ne, ki ce ni ne,’ amma ina batool sai ta tsalleke shi ta ruƙo hannun Parveen, wadda tuni fitsari ya kamata, motsa lips ɗinta tayi tare da cewa”He is the one”
Hanna tace”you’re wrong” tayi maganar tare da zame hannunta daga kan fuskar batool,
Waro ido tayi ganin parveen, gaba ɗaya suka fashe da dariya, Cikin shessheƙar kuka parveen tace”Ban yafe ba, Kinja min bala’e, “
Janyo kwalar rigarta batool tayi’hakuri zakiyi, dama kinfi kowa Cin abinci yau, Kizo kawai mu basu baya suyi mana dunduna, ba yadda ta iya haka suka duƙa, kowa yayi masu dundu abaya, parveen tasha kuka, ita kanta batool saida ta matse ƴar kwalla, don da mugunta suke yin dundun,
Komawa su kayi Cikin layi, next person da aka kirawo, Azeeza ce aka ce ta Canko masu Naufal, hanna ta rufe mata idanuwanta, Da yake Allah yayi mata baiwa, duk wanda ta ruƙe hannunshi saita shinshina kamar mayya, wai da ƙamshin jikinsu take amfani, tana zuwa kan hannun naufal ta shinshina, sai ce wa tayi”Shi ne” gaba ɗaya suka sanya sowa, ” tsohuwa fa yau ta samu abun nishaɗi, sai faman murmushi take yi, har lokacin basu son cewa tana atsaye bakin ƙopar ɗakinta ba, tana kallonsu,
Babu rabon azeeza tasha dundu, angel dai sai fargaba take yi, ta ƙosa layi yazo kanta taji wa za’ace ta canko, Har Allah Allah take Yi acikin zuciyarta,
Mutane na gaba da aka kira, Deeja ce akace ta gano Danish!!, hanna ta rufe mata idanuwanta suka tafi suna bin layi, duk wanda ta ruƙe hannunshi saita saki tace bashi bane, hankalin angel yayi matuƙar tashi, fargabarta kada Deeja ta cankota, taja mata bugu, aikuwa dai deeja tana zuwa gaban angel ta damƙi hannunta, har kusan fitsari saida angel tayi, aruɗe take girgiza mata kai kamar tana ganinta, har ta buɗe baki zatace shi ne, sai kuma ta saki hannun angel ta ƙara gaba, nauyayiyar ajiyar zuciya angel ta sauke hada sanya hannu ta shafa ƙirjinta, taji daɗi,
Cikin rashin sa’a deeja ta canko Rubina tace shi ne” rubina taji haushi, shaƙo wuyan Deeja tayi tana jijjigata tace”saboda ke shashasha ce, ta ina hannuna yakai na danish tsayi? Ba ki ga yatsun hannayena guntaye bane? Ke baki banbancewa ne? Gaba ɗaya suka fashe da dariya, hatta danish dake a tsaye saida ya ɗan saki murmushin gefen fuska,
Hanna tana dariya tace”Ba faɗa bane wasa ne, Kuyi haƙuri kuzo ku xuƙunna, Ku kar6i la’adarku” rai a6ace Rubina ta fito daga Cikin layi, takai hannu ta jan yo wuyan rigar Deeja, suka shiga tsakiya, Suka duƙa, ɗaya bayan ɗaya kowa yazo yana yi masu dundu abaya, koda aka zo kan angel, saida ta naɗe hannun rigarta, dama haushin deeja take ji, ta daddage da iya ƙarfinta na ƙarshe ta Buga mata dundu abaya, har saida deeja ta kife ƙasa tana kuka,
Girgiza kai tsohuwa tayi ganin irin muguntar da angel ke yi masu wurin Yin dundu, ta kosa layi yazo kanta taga idan ita zata Iya tsira🤣
“Tun da naga mutane sun ragu, saura mutun huɗu suka rage, bazai yiyu abaku za6i ku canka ba, Sabo da za ku yi nasara Cikin sauki, don haka gaba ɗaya ƴan wasa su dawo Kan layi,” hanna ce tayi maganar idonta akan su Haris dake zuƙunne suna jinyar bayansu,
Miƙewa su kayi kowa yana hura hanci, Suka Koma Kan Layi, Tofa su angel murna ta koma Ciki, ganin sun koma su goma sha huɗu,
“Adai dai ta natsuwa, Last 4 person da suka rage, zan fadi sunayensu, akwai Eve, Angel, danish and hibba, sai kuma Ni hanna cikon ta Biyar, Yanzu Zan koma Cikin ƴan wasa, Batool ke ce zaki wakilce ni, A matsayin alƙalin wasa, a dokar wasan Sabon alƙali zai Iya faɗin nashi sabbin dokokin,”
murmushin mugunta batool tasaki, harta hango haɗin da za ta yi, Fitowa ta yi daga kan layi, Ta koma ta tsaya a inda hanna take, Ita kuma hanna ta koma Kan layi ta jera da sauran ƴan wasa
Idon kowa ya koma kan alƙalin wasa Wato batool, a tsanake ta soma magana” A matsayina na sabon alƙalin wasa, Ina da tawa sabuwar dokar, Mutane biyar da suka rage idan har na canko ɗaya daga Cikinsu, na bashi sunan wanda zai za6o mini, idan ya kuskura ya canko ba dai dai ba, dashi da wanda aka bashi sunan shi ya gano kowa Zai yi masu dundu A bayansu, Sa’an nan babu su babu Cin sauran abincin da muka rage, kason su za’a raba ma sauran Ƴan wasa ne su Cinye” tun da batool ta soma kora jawabi, hankalin angel ya ɗunguzuma, ba ita kadai ba hatta hibba da eve da hanna sai da hankalinsu ya tashi, Jin wannan Dokar ta batool, taya za’a raba ma sauran ƴan wasa abincinsu idan suka yi failing, akwai matsala babba,
Idon batool akan Na Angel data cika ta batse, murmushi ɗauke akan fuskar batoo tace”Next person Is…….” Gaba ɗaya sun baza ido suna sauraronta, hatta tsohuwa a ƙagare take da taji wa batool zata Canko,
“Danish! ” a hankali ya ɗago da lumsassun idanuwanshi ya ɗaurasu kan batool, Yana jiran Jin wa zata ce ya canko,
Tunkafin batool ta ƙarasa maganarta, angel ta shiga girgiza mata kai daga inda take a tsaye Cikin layi, Alamar kada tace ya gano ta, don tasan halin danish zaiyi wuya ya iya canko ta, ita da take da tarin maƙiya acikin wasan kowa so yake tayi failing don tasha dundun, expecially haris da Deeja, a ƙule suke da ita, don har yanzu basu daina jin raɗadin dundun da tayi masu ba,
“Danish zaka Canko mana ANGEL, kafin mu fara zan ƙara tunasar dakai dokar wasa, idan har kayi kuskuran canko wadda ba ita ba, Kowa zaiyi maku dundu, sa’annan babu ku babu Cin abinci an jima, za’a raba ma sauran ƴan wasa naku” wani irin murmushin mugunta haris da deeja suke saki, daɗi kamar ya kashe su, don sunsan cewa Danish bazai iya canko daidai ba, saboda halinshi da suka sani,
Cike da shaƙiyanci deeja tace”Ina fata Danish Ya gaza canko ki, Na rantse hatta spinal cord ɗinki sai ya amsa idan nayi maki wani mugun ƙulli” tayi maganar tana kwatanta yadda zata bugu bayan angel da hannunta, gaba ɗaya suka sanya dariya, angel kuwa ta ɗaure fuska babu walwala kwata kwata, duk tasha jinin jikinta,
Haris yace”ni kuwa Da gwiwar hannuna zan daki bayanta har sai ya 6urma, In yaso su Giants sunyi jinyarta a treatment room,” gaba ɗaya suka sanya dariya cikin nishaɗi, idanuwan angel tuni sun cicciko tab da kwalla, tabbas ta gama karaya domin kuwa tasan danish bazai ta6a iya gano ta ba acikinsu,
“Danish come forward” Batool ce ta yi maganar tana nuna shi, fitowa yayi daga Cikin layi, ya ƙarasa gaban Batool ya tsaya, saboda tsabar mugunta haris hada cewa ajira ya cire rigarshi, a ɗaure ma danish fuska da ita, don yasan tsayin Batool bazai kai na danish ba, hakan na nufin bazata Iya datse mashi ido da tafin hannayenta ba, batare daya samu ƙofar da zai iya kallonsu ba, jama’a kowa fa yaci burin bugun angela,
Hannu haris ya sanya tare da tu6e rigarshi, Ya wurga ma batool ta sanya hannu biyu ta ca6eta, idon danish akan na angel da tabi ta kame kanta, kamar ta fashe da kuka,
Ɗaure mashi fuska batool tayi da rigar haris, ta matse mashi ido sosai har saida yaji zafi,
“U can Start” ta ambaci hakan tana kallon shi, tafiya ya soma Yi yana lalubansu, ya ruƙo hannun rubina ya saki, ya ruko na azeeza ya saki, ya ruƙo na eve ya saki, ya kuma ruƙo na parveen ya saki, Kowa ya zuba ido yana kallon shi, ya cafko hannun javed ya murza shi, Kowa yayi tunanin shi zai canka amma sai suka ga ya saki hannun,
“A ƙa’idar wasan, Ba’a magana, idan na kama mutun yayi magana, kowa zaiyi mashi dunduna Biyu, sannan ya rasa abincin shi, Bayan wannan kuma Zai wanke mana uniform ɗinmu idan su ka yi ɗauɗa, zai kuma wanke toilets ɗinmu, Bayan wannan kuma ɗan wasa yana da damar da zai iya ta6a ko’ina ajikin sauran ƴan wasa domin ya samu damar canko wanda akace ya za6a, wannan ba laifi bane” alƙaliyar wasa ce ta kora masu wannan jawabin, tayi hakanne don tasan halin angel da shegen wayau, tana iya cewa zata yi ma danish raɗa don ya gano ta,
Cigaba da tafiya Danish Yayi yana ruƙo hannayensu, yana zuwa kan saitin angel ƴan hanjin cikinta suka kaɗa, kowa ya tsaresu da ido, jira kawai suke su ga idan danish zai iya gano ta,
Ruƙo hannunta na dama yayi da hannayenshi biyu, ya shafa su ya matsasu sosai, runtse idanuwanta ta yi jikinta na kerma, ba halin tace mashi itace, saboda idon kowa dake akansu,
Sakin hannunta ya yi, nan take su deeja suka soma Sakin murmushin mugunta, wani irin wahalallan yawu ta haɗiya, A wani slow danish Ya ɗaga ƙafarshi har zai wuce sai kuma ya ɗan dakata, kowa ya baza ido yana kallon ikon Allah,
Komawa ya yi gabanta ya tsaya tare da miƙa hannu tamkar zai kamo hannunta, sai kuma ya kauce hannunshi ya cafko sumar kanta, ƙayataccen murmushi ne ya bayyana akan fuskarshi, cikin sanyin murya yace”she’s the one, am i right? Gaba ɗaya su Azeeza suka Daka sowa suna Tafa mashi hannu, hatta tsohuwa saida Ta ɗanyi murmushi duk da ba haka taso ba, amma Abunda ya burgeta kaifin basira irin na danish, yayi wayau, saboda yayi amfani da yanayin kakarwar da jikinta keyi, da ya ruƙo hannunta da farko ya fuskanci hakan, shiyasa ya sake dawowa ya kai hannu kamar zai damƙi hannunta, sai yayi wayan kaucewa ya damƙi gashin kanta, saboda yasan idan itace, zai samu gashin kanta har wurin qugunta, wato danish yayi amfani da kwakwalwarshi,
Wata irin nauyayyiyar ajiyar zuciya angel ta sauke, lokaci ɗaya kuma ta fashe da wata irin mahaukaciyar dariya hada dafe ciki, Taji daɗi data tsalleke tarkonsu Haris da deeja, kamar su fashe da kuka saboda tsabar 6acin rai da takaici, plan ɗinsu ya rushe,
Sai da ta kammala shan dariyar, tukunna ta sanya hannayenta biyu ta warware ma danish ɗaurin da akayi mashi akan fuska, bayan ta kammala ta xame rigar tare da wurga ma haris ita saman fuskarshi, rai a6ace haris ya ca6e rigarshi yana faman kumbura baki
Natsuwa tayi tana kallon danish dake ta faman ƙoƙarin bude idanuwanshi, eyes lashes ɗinshi sun cukurkuɗe sun hana shi buɗe ido, matsawa tayi kusa dashi sosai, ta sanya yatsun hannunta wurin buɗe mashi idanuwan, yadda zai gani da kawai,
Fuskarta ɗauke da murmushi tace mashi”thank u so much danish, ka taimake ni, da yau an karya mini spinal cord ɗi na, gaba ɗaya suka saki dariya, banda haris da deeja,
Ruƙo hannunta danish yayi acikin na shi, ya jata suka koma gefe ɗaya, aka cigaba da buga wasa, juyawa tsohuwa tayi batare da kowa ya ganta ba, ta koma Cikin ɗakinta, taja ƙopa ta rufe,
Lokacin da suka kammala wasan, Saman gadajensu suka koma, waɗanda suka sha bugu sai faman jinyar kansu suke yi, rabi da kwatarsu ba’a ɗauko tsawon lokaci ba suka kama baccin wahala,
In the night 🌌
Lokacin da dare yayi hasken ɗakin ya ɗauke, suka ɗauko fitilun ɗakin suka kunna su Saman Dining carpet ɗin su, Dakin yayi haske sosai, Kowa ya samu wuri saman Carpet ɗin ya zauna, Batool taje ƙarƙashin gadonta ta ɗauko masu Kingin Tsiren namansu, Ta rarraba masu Kowa Ya kar6a Yana ci, da suka kammala Suka ci snacks ɗinsu da Sauran kayan marmarinsu, Suna Ci suna fira gwanin ban sha’awa,
Bayan sun kammala Ci, Kowa ya kasa runtsawa, dama angel tayi tunanin daƙyar su iya yin bacci saboda baccin da suka sha A jiya, idanuwansu sunyi wuƙi wuƙi, babu alamun bacci,
Duk suna a zaune saman gadajensu, Tunani ta soma yi kodai taje toilet ta ƙara jaraba fasa glass window ɗin nan? Wata’ƙil idan ta dage kullum tana zuwa tana Bugun jikinshi, Allah ya taimaketa ya fara tsagewa, juyawa ta ɗanyi tare da kallonsu, kowa ya kishingiɗa saman gadon shi, kallon shimfiɗar danish tayi ya kifa kanshi saman Pillow, Aranta tace Allah yasa yayi bacci, kada yayi mini irin na jiya, don na lura akwai almatsutsai akanshi, ba shi kaɗai bane,
Zuro ƙafarta ƙasa tayi daga saman gadon, ganin sun rufe idanuwansu yasa ta lalla6a cikin sanɗa taje gaban Carpet ta ɗauki fitila, da sauri ta wuce ta shiga sashen toilet ɗinsu, Taja ƙopa ta garƙame ta, ajiyar zuciya ta sauke yayin da bayanta ke ajingine da ƙopar,
Glass window ɗin ta ƙurawa ido daga inda take a tsaye, tana ƙoƙarin motsawa da nufin taje ta fara aiwatar da aikin fasa shi, kwatsam Tajiyo shessheƙar kuka tare da Iface iface daga Can Cikin ɗakinsu, A matuƙar kiɗime ta juya takai hannu ɗaya ta Zare jam lock ɗin kopar, da gudun gaske ta faɗo Cikin Ɗakin, Tunkafin ta ƙarasa Ciki, Ta hango su batool da hanna, agaban gadon Deeja, su javed kuma suna a tsaitsaye gaban gadon parveen, ga kuma haris da danish agaban gadon Rubina, Hankalinta yayi matuƙar tashi, Iskokai ne suka tashi Ko kuwa menene? Karasawa ciki ta yi da sauri taci burki agaban Gadon Parveen, Idonta akanta, Ta daddafe Cikinta sai juyi take yi tana kuka tana fadin Cikinta Ciwo zata mutu su taimaka mata,
Arude ta kalli fuskokinsu Batool, Bakomai ta gani ba face tsantsar tashin hankali, sun rasa ya zasu yi mata, da sauri angel ta matsa gadon Deeja dake ta ihu tana fadin Cikinta ciwo yake yi mata, wuce wa tayi zuwa gadon rubina ta tsaya tana kallonta itama ta daddafe Ciki sai kuka take yi tana matse idanuwanta, fuskarta tayi jaga jaga da kwalla,
Kallon Su haris Tayi muryarta na kerma tace”MEKE FARU WA NE’?_
Fuskar Haris a hargitse ya bata amsa da cewa”mu ma bamu sani ba, muna a kwance muka Ji sautin kukansu, mun rasa ya zamuyi da su”
Shiru angel ta ɗanyi ta ruɗe ta rasa madafa, Komawa Tayi bakin gadon Parveen, su batool duk suna a tsaitsaye cirko cirko, a ƙasa ta sauke fitilar hannunta, kafin ta ɗago takai hannu ta janyo Parveen zuwa Jikinta, ƙanƙameta praveen ta yi sosai tana kuka tana faɗin” angel ki taimaka mun ciki na, bana jin daɗi, xafi yake yi mini raɗaɗi nake ji,
Ƙura ido angel tayi tana kallon ɗigon Jinin dake ajikin wandon Parveen Nan take ta gane cewa Jinin al’ada ne, a karo na farko kenan da ta ta6a ganin sunyi jini, ta jima tana mamakin ya akai basu fara ba, saboda a shekarunsu ya isa ace sun fara Shi tuntuni saboda sun girmeta, abun ya ɗaure mata kai,’ shessheƙar kukan Parveen ne Ya dawo da ita Cikin hayyacin ta,
Ɗago da kanta tayi daga Jikinta, ta dafa kafaɗunta”Kiyi haƙuri kiyi shiru parveen zanje in faɗa ma tsohuwa,” takai ƙarshen maganar tare da saukowa daga saman gadon, ta kalli su batool dake atsaye Cikin yanayi na damuwa,
“Ku kula da su, Bari nayi mata magana tazo ta duba su, in yaso sai tayi maku bayanin Abunda ke damun su,” amsa mata su kayi da toh, da sauri ta nufi ƙopar ɗakin tsohuwa takai hannu ta bubbuga ƙopar, almost 3 times tana knocking ƙopar, Kafin tajiyo motsinta,
Buɗe ƙopar tayi tare da fitowa Hannunta ruƙe da sanda,
“Meke faruwa ne nake Jin koke koke” tayi tambayar tana kallon Wurin gadajensu,
Muryar angel na rawa ta bata amsa da cewa”ciwon Ciki suke yi Ina tunanin menstruation ne, suna buƙatar magani da kuma pads ɗin da zasu sanya”
Maimakon taga damuwa akan fuskar tsohuwa sai taga ta duƙar dakai ƙasa tana sakin wani irin shu’umin murmushi, ran angel ya 6aci sosai,
“Magana fa nake yi maki akan lalurar dake damunsu, don me xaki 6uge da yi mun murmushi? Maimakon Inga damuwa akan fuskarki? Kina ji suna kuka suna ihu amma ke ko ajikin ki? Ba zaki je ki duba lafiyar Jikin su ba”?
Ɗagowa tsohuwa tayi tare da kallonta, da wannan Shaƙaƙƙiyar muryartata ta tsoffi ta soma magana
“I ave no responsibility to check their health, the giants will come and take them to the treatment room” har saida angel ta zabura jin abunda tace, Can kuma ta wurga mata harara,
“Amma dai baki da Tausayi kuma baki da Imani, taya zaki ce za’a zo a ɗauke su? bayan kina da halin da zaki iya duba su da kanki? Kenan Giants su zasu duba Lafiyar su, Ke fa yakamata ace Kin duba su, Ba wani ƙato ba,” zuciyarta a harzuƙe takai ƙarshen maganar, Kafin tsohuwa ta mayar mata da martani, Suka Soma Jin motsi buɗe ƙopa daga can saman benan…………………….
*❤❤❤PRISONERS❤❤❤*
A matuƙar kiɗime angel ta juya tana kallon stairs ɗin, hatta su Batool a ruɗe suka kai idanuwansu kan benan, tunkafin ma su ƙarasa saukowa sautin takalmansu ya karaɗe kunnuwansu, Cikin takun nan nasu na majiya ƙarfi suke tafiya bakowa bane face GIANTS, a jere suka sauko daga saman Stair cases ɗin, haƙiƙa hankalin angel yayi matuƙar ta shi, Jikinta har tsuma yake yi, juyawa tayi tare da kallon tsohuwa, Cikin karyayyiyar murya tace” na roƙe ki dan Allah Ki taimaka, kada ki bari a tafi dasu parveen, abar mana su acikin mu, Ni nayi alƙawarin zan kula dasu,” idanuwanta cike tab da ƙwalla takai ƙarshen maganar,
Girgiza kai tsohuwa ta yi babu alamun sassauci akan fuskarta tace”Ba hurumina bane shiga abunda ba ruwana, Dokar Prison ce, Wadda bani na tsarata ba, duk wani mara lafiya za’a zo a ɗauke shi akai shi inda za’a duba lafiyar shi, idan kinga na duba mutun to ciwon bai yi tsauri bane, Giants da ki ke gani basa sauraron kowa, Koda kuwa nice, saboda ba a ƙarƙashina suke ba, dukan mu Ma’akaita ne dake aiki gidan kurkukun ƙaddara, Kuma a ƙa’ida wani baya shiga hurumin wani………”
kalaman tsohuwa sunyi matuƙar girgiza angel, kafin ta yi yunƙurin buɗe baki ta furta wata kalma, tajiyo muryar parveen tana kuka tana faɗin Kada su bari a tafi da ita, mutuwa zata yi, ita bazata bi su ba ‘ a hargitse angel ta juya tana kallonsu, Kusan atare giants suka kai hannuwansu saman gadajensu Deeja da rubina da parveen, Wata irin ɗauka su kayi masu ta hanyar ruƙe waist ɗinsu suka yarfa su saman faffaɗan kafaɗunsu, bayin Allah Sai kuka suke Yi suna Bugun bayan giants da hannayen su, Nan take zuciyoyinsu Batool suka karaya Jikin kowan nan su yayi sanyi, har ma basu san lokacin da suka fashe da matsanancin kuka ba, Juyawa giants su kayi atare suka soma tafiya dasu ɗauke saman kafaɗunsu suka nufi stairs ɗin,
Da gudun gasken Angel ta tunkaresu Tana ƙarasawa bayansu Ta cafko hannayen parveen dake abayan giant ɗin dake ɗauke da ita, da iya ƙarfinta na ƙarshen ta janyota gaba ɗaya ta faɗo ta baya, baiwar Allah jikinta sai 6ari yake yi, ɗagowa tayi tare da rungume angel ta ƙanƙameta tana kuka tana faɗin”dan Allah angel kada ki bari su tafi dani, saboda basu dawowa da mu, bana so nabar Cikin ƴan uwana bansan inda zasu kai mu ba, Ina ji araina kamar na tafi kenan…….” Giant ɗin dake a ɗauke da Parveen Ya tsaya Tsak wanda ko ba’a faɗa maka ba, zaka shaida cewar A fusace yake, domin su ba’a katse masu aiki, Da gudun gaske su Hanna da su Javed suka ƙaraso Inda su angel ke a zaune ƙasa suna kuka,
Kallonsu kawai take yi idanuwanta sun rune ita kaɗai tasan irin tashin hankalin da take ci, Na raba ta da ƴan uwanta da ake ƙoƙarin yi,
Cikin shessheƙar kuka Batool tace” Dan Allah ki daina kuka Parveen, tsohuwa ta faɗa mana cewa Cuta ba mutuwa bace, Sai in kwanan mutun ya qare, Zasu yi maki magani ne zuwa gobe idan ku ka ji sauƙi zasu dawo mana da ku,” Ita kanta batool ta karaya sosai ta yi maganar ne kawai donta ƙarfafa mata gwiwa,
Zufa ta ko’ina Ajikin Parveen Muryarta na kerma tace”Koda ace ban dawo ba, Idan an kawo abinci, ku dinga ajiye mini nawa” Hawaye sharkaf akan fuskarta tayi maganar, angel dai takasa cewa komai, Zuciyarta ta gama karaya,
Kafin wani ya kuma cewa wani abu, Giant ɗin yakai Hannu da niyar ya ɗauki parveen, a tsorace ta ƙankame jikin angel tana faɗin” kada ki bari su tafi dani, bazasu dawo dani ba, idan har kuna sona dagaske ku taimake ni, kada ku bari araba ni daku……” ƙanƙameta angel tayi ajikinta, Giant ɗin ya damƙi qugun Parveen, ta ƙarfi ya fisgeta daga Jikin angel ya ɗaura ta saman kafadarshi Ya juya Cikin zafin nama Ya haura saman benan, Sauran Giants ɗin guda Biyu dake a ɗauke da rubina da Deeja suna abakin ƙofar fita suna jiran ƙarasowar shi, yana daga cikin dokar aikinsu Basa tafiya dole sai suna atare da juna, wani irin jiri ne Ya rufe idanuwan angel, anan ƙasa ta kwanta idanuwanta na zubar da hawaye, Suna Jiyo sautin muryar parveen cikin shessheƙar kuka take faɗin cewa”Angel dan Allah kiyi mini addu’a, Kuma idan gobe ba’a dawo dani ba, ku ajiye mini abinci na”
Wannan maganar ta parveen ta yi matuƙar kashe masu sassan Jikinsu, A nan suka wuni zuƙunne suna kuka, Mutun biyu ne acikinsu basu zubar da kwalla ba, Danish da Haris Saboda sun sa ma ransu cewa Za’a dawo masu da ƴan uwansu ne, duk da haka sun yi matuƙar damuwa da halin da su Parveen suka shiga, Na raɗaɗin ciwo ga kuma maraicin da zasu Yi na raba su da ƴan uwansu,
Tsohuwa dake a tsaye Bakin ƙopar ɗakinta, Ko a ha6ar xaninta bata sanya damuwar Halin da yaran suka shiga ba, Sai da taga Sun sassauta da yin kukan tukunna Ta dogara sanda ta nufi inda suke a zuƙunne ta tsaya tana kallon fuskokinsu da suka jiƙe sharkaf da hawaye
“Idan ku ka yi haƙuri, Za’a dawo maku da ƴan uwanku ne da zarar sun samu warakar Lalurar dake damun su, Kuka bazai ta6a yi maku maganin komai ba, Illa iyaka ya ƙara haddasa maku wata damuwar, Shawarar da zan baku shi ne, Ku sanyawa zuciyar ku haƙuri da juriyar rashin ƴan uwanku, kada ku cusawa kanku damu…….” bata ƙarasa maganar ba angel ta yunƙura ta miƙe zaune idanuwanta sunyi jawur gwanin ban tsoro, muryarta a zafafe ta soma magana
“Har kina da bakin zuwa ki bamu haƙuri akan mu yi shiru mu daina kuka? Wlh tun da nake 6anta6a ganin Muguwar mace azzaluma irinki ba!
Ɗan zaro ido tsohuwa tayi da kwala kwalan idanuwanta tamkar ƙwayar idanuwan zasu faɗo ƙasa,
“Kince ke uwa ce agare su, meyasa da naje na faɗa maki cewa Cikinsu na ciwo, baki zo kin duba jikin su ba? Koda sannu ne kiyi masu Amatsayinki na mahaifiyarsu, Amma bakiyi hakan ba, sai dai wasu ƙattai suka zo suka ɗauke su da sunan zasu duba lafiyarsu, bayan ke ya dace kiyi hakan a matsayinki na Ƴa mace, duk da bani da ilmi akan abun amma auntyna ta ta6a faɗa mini cewa Menstruation lalura ce ta mata da suke yi a kowani wata, zaki iya taimaka masu idan kinso basai an kaisu wani wuri ba……” cikin shessheƙar kuka takai ƙarshen maganar, Su batul duk sunyi zugudum suna sauraronsu,
“Banta6a jin tausayin wani ɗan adam ba aduniyar nan ba, kamar wadannan bayin Allah, wai su haka rayuwarsu zata ƙare? A tagayyare basu da me share masu hawayensu, basu da kafaɗar da zasu ɗaura kansu akai suyi kuka a lallashe su, Wannan wata irin Makauniyar ƙaddara ce? Tayi tambayar idonta akan tsohuwa dake a tsaye ruƙe da sanda, baka Iya gane awani hali take Ciki, domin kuwa fuskarta a haushine take, tsufanta da muninta sun ƙara bayyana
Juyawa tayi da sauri tana dogara sanda ta nufi ƙopar ɗakinta, tana ƙoƙarin kai hannu ta buɗe ƙopar muryar angel ta katse mata hanzarinta
“Ba zaki ce komai ba? Saboda rashin gaskiya? Zuciyarki ta bushe baki ji baki gani zalunci kaɗai kika sa agaba, wlh rantsuwar ɗan musulmi idan har ba’a dawo mana da ƴan uwanmu ba, SAI NA KASSARA RAYUWAKI, koda kuwa zan rasa raina ne’
Girgiza kai tsohuwa tayi batare data waiwayo ta kalleta ba ta soma magana
“Zaki Iya zagina ki ci mutuncina son ranki, saboda a yanzu ni kike ganin laifina, Unaisah ga shawara….” a ruɗe angel ke kallon bayan tsohuwa, Jin yau ta ambaci asalin sunanta,
Cigaba da magana tsohuwa tayi”ME ZAI HANA KIYI TUNANI AKAN WAƊANƊA SUKA SADAUKAR DAKU A GIDAN KURKUKIN ƘADDARA? mutun baya ta6a kasancewa acikin gidan kurkukun ƙaddara dole sai in Na JININSA NE YA SADAUKAR DASHI!!, nifa ba kowa bace agidan kurkukun nan face Ƴar Aiki me rainon Yara,” tsohuwa nakai karshen maganarta, ta yi saurin tura ƙofar ɗakinta ta shige taja ƙopa ta garƙame, ta tafi tabar angel da tunani, Zuciyarta ta shiga ruɗani, Kenan dama Tsohuwa bakowa bace Agidan kurkukun ƙaddara? Su kuma prisoners dake rayuwa acikinshi na Jininsu ne suka sadaukar dasu?tayaya kenan? Wata irin sadaukarwace wannan? Meyasa aka sadaukar dasu? Me za’ayi dasu? danginsu basa ƙaunarsu ne shiyasa suka sadaukar dasu ko kuwa?
Wani irin matsanancin ciwon kai ne Ya taso mata, me raɗaɗin gaske, da sauri ta sanya hannu ta dafe kanta, Ɗaƙyar ta iya ɗaga kafarta ta juya tana kallonsu Batul, waɗanda ke zazzaune Cikin jimamin rashin ƴan uwansu, da alama Basu ji komai ba game da abunda tsohuwa ta tattauna da angel,
“Wa suke dashi A duniyar nan? Zuciyarta ce ta bata amsa da cewa “ALLAH”
biji biji take gani acikin idanuwanta, daƙyar ta samu ta iya zuƙunna agabansu, Muryarta a disashe tace”kuyi haƙuri dare yayi sosai, Ku zo muje mu kwanta, ” miƙewa kowannansu Yayi, Suna jan ƙafa suka Nufi gadajensu Kowa Ya haye ya kwanta, sai da tabi su ɗaya bayan ɗaya tayi masu addu’a, taja masu bargunansu ta lullu6e masu Jikinsu, koda tazo saitin gadon Parveen sai da ta matse kwalla, bakomai take tunawa ba face kukan parveen da kuma kalamanta na karshe da take cewa Tayi mata addu’a kuma idan an kawo abinci su ajiye mata, angel tasha kuka kamar ba gobe, lokacin data zo kan gadon Deeja, tuni jikinta yayi sanyi tunawa da irin muguntar da tayi mata ɗazu da suna wasa, ta sanya gwiwar hannu ta daki bayanta harta kife ƙasa, cikin shessheƙar kuka angel ta furta “NAYI DANA SANI” Wuce wa tayi zuwa bakin gadon Rubina, Ta jima tana kallon shimfiɗarta, Kafin ta nufi gadonta ta hau sama ta zauna daga tsakiya, Hannayenta ta ɗaga sama Ta soma yi masu addu’o’i, Yayin da hawaye ke fita acikin idanuwanta, wasu na bin wasu,
A daren Ranar Kowa Ya runtsa banda Angel, Ta dage sai addu’a take yi masu ta hana idonta bacci duk don saboda su Parveen,
A washe garin ranar, dayawansu basu farka daga bacci ba, har lokacin tana a zaune tsakiyar gadonta, ta jingina bayanta jikin bango, fuskarta ta kumbura sumtun, tayi ja sosai, ga jirwayen hawaye,
Mutsu mutsun da taji ne yasa ta soma ƙoƙarin buɗe idanuwanta Sun kumbura ga raɗadi da suke yi mata, daƙyar ta samu ta ware idanuwan sosai, gefenta ta ɗan kalla don ganin wanene ya motsa, Danish ne ta gani zaune saman gadonshi, ya lumshe idanuwanshi fuskarshi babu alamun damuwa atattare da ita,
Zuro da ƙafafuwanta ƙasan gadon ta yi tare da gyara zama daga gefen gadon tana fuskantar danish,
Cikin sanyin murya ta ambaci sunan shi”Danish” a hankali ya buɗe idanuwanshi ya juyo yana fuskantarta,
“Ka tashi lafiya”? Jinjina mata kai yayi alamar eh, ajiyar zuciya ta ɗan sauke kafin tace” Inaso na tambaye ka wani abu idan ba damuwa” ya amsa mata da toh,
Saukowa tayi daga saman gadon, taje bakin gadonshi ta ɗan zuƙunna daga ƙasa, ta ɗago tana kallonshi idonsu acikin na juna tace
“Shekaran jiya da daddare, lokacin da na shiga cikin toilet ka biyo ni, Taya akai ka shigo bayan na datse ƙopa ta ciki na sanya jam lock”? ta tsare shi da ido tana jiran jin amsar da zai bata, ɗan tahalikin nan yayi shiru yana binta da ido batare daya motsa lips ɗinsa ba balle ma tayi tunanin zai bata amsa,
“Ba ka yi mini kama da maƙaryaci ba, duk da bana yarda da mutun ta yanayinsa, pls tell me the truth kawai inaso na sani ne, saboda kafin na shiga toilet ɗin sai da na tabbatar na barka a kwance kana bacci kafin na shiga ciki, Kuma ko bayan dana shiga saida na Haska ko’ina babu mutun, amma wani abun mamaki sai gaka acikin toilet ɗin, wanda nayi Imanin bata ainihin ƙopar ka shigo ba, Kuma baka Biyoni abaya ba” Cikin tuhuma take yi mashi maganar,
muryar shi a sanyaye yace” Bazan iya baki amsa ba, saboda ni kaina bansan ta ina na shiga ba, abunda na sani shine Na sanyawa raina inason nabi bayanki ne, kuma na samu kaina Acikin toilet ɗin shine kaɗai abunda zan Iya tunawa amma bayan wannan bansan komai ba”
Zuba mashi ido tayi tana kallonshi, har cikin ranta ta yarda da maganarshi, domin kuwa babu alamun wasa a fuskarshi ya bata amsar, kwara tabi komai asannu wurin yin bincike, Idan ba haka ba, zata iya tarwatsa lissafin kwakwalwarta ne,
Ƙaƙaro murmushi ta yi akan fuskarta, yayin da take kallon shi,
Mayar mata da martanin murmushin yayi Calmly yace” kin sanya damuwa aranki, Jiya kinyi kuka kuma baki yi bacci ba Why? Akan su Parveen ne”?
Jinjina mashi kai tayi alamar eh, ta ƙara da cewa”na damu dasu sosai, Ina ji araina kamar baza a dawo mana dasu ba, shiyasa zuciyata ta karaya har nagaza runtsawa”
Duƙowa taga ya yi saitin fuskarta, har saida ta ɗan tsorata, Zuciya da saƙe saƙe sai tayi tunanin ko kiss zaiyi mata, ƙiris ya rage tsinin hancinshi ya gogi nata, runtse ido tayi tana jin me zai mata
“Ki kwantar da hankalin ki, Zasu dawo na yi maki alƙwarin hakan,” ɗagowa tayi tare da kallon shi,
“Taya akai kasan cewa zasu dawo”? Tayi tambayar tana kallon cikin idanuwanshi,
Murmushin gefen fuska ya ɗanyi, Can kuma yace”Kin manta anzo an ɗauke ni, Kuma an dawo dani, Suma zasu dawo ne”
Girgiza kai angel tayi”amma koda aka dawo dakai, baka Acikin hayyacin ka, kamar an ƙara maka Ciwon Ajikin ka, danish zaka Iya tuna ina aka kai ka bayan an ɗauke ka daga Cikin mu”? ta jefa mashi tambayar,
“Angel, ba zan iya tuna komai ba, tun bayan da giants suka ɗauke ni bansan meya faru ba, har sai ranar da suka dawo dani cikinku tukunna na iya tuna wanene,”
Shiru angel ta yi bata kuma cewa komai ba, Lamarin ne yafi ƙarfin tunaninta, Wata irin Murɗaɗɗiyar sarƙaƙiyace Acikin Kurkukun mai wuyar fassaruwa,
Miƙa hannu danish yayi tare da ruƙo nata hannun acikin na shi, Magana ya soma yi idonshi acikin nata”angel, ina neman yafiyarki, for everything that happened because of our misunderstanding, I hate you for no reason, but now I can say that I love you more than anyone……..” kalaman shi ba ƙaramin sanyaya mata zuciya su ka yi ba, sai taji tamkar an yaye mata damuwarta na ɗan wani lokaci,
ƙayataccen murmushi ta saki tana motsa lips ɗinta, alamar tana so tace wani abu amma ta kasa furtawa, sam batayi tsammanin jin hakan daga gare shi ba, ta yi farin Ciki saboda yana ɗaya daga Cikin nasarar da take so ta samu na Jituwa atsakaninta da kowannan su, tana so ta shiga cikin zuciyoyinsu sosai ta yarda zata samu damar janyo ra’ayinsu, yanzu saura mutun biyu ya rage mata haris da deeja, taci alwashin Idan aka dawo da deeja bazata ƙara bari faɗa ya haɗa su ba, Shi ma haris ɗin bazata biye mashi ba, xata jasu ajikinta,
“What are u thinking about”? Jin voice ɗin danish yasa ta ɗanyi firgit ta kalle shi, still idanuwanshi na akan fuskarta,
” baki bani amsa ba,” ya tambaya yana sauraranta,
“Dama ni ban ruƙe ka azuciyata ba, Ni baka yi mini laifin komai ba, dani dakai tamkar ƴan uwana ne jini,” ba ƙaramin daɗin kalamanta yaji ba, har cikin zuciyarshi yaji sanyi, zame hannunshi yayi daga Cikin nata, ganin ya lumshe eyes ɗinshi yasa tayi tunanin ko bacci zai koma ne,
Yunƙurawa tayi tare da miƙewa daga gaban gadon shi, A dai dai Lokacin Batool ta fito daga sashen makewayinsu, itama fuskarta a kumbure, suna haɗa ido da angel ta nufeta, rungume juna su kayi kowa yayi shiru, batare da sunyi magana ba,
Azeeza dake zaune saman gadonta, farkawarta kenan idanuwanta na akansu,
Sun ɗauki lokaci kafin suka raba Jikinsu daga na Juna,”
“Idanuwanki sun nuna alamun baki yi bacci ba jiya, meyasa”? Batool ce tayi mata tambayar,
“Taya xan iya runtsawa, alhalin ƴan uwana suna Acikin mawuyacin hali, anzo an raba ni dasu, an kaisu wani wurin, dole na damu, Nayi kewarsu sosai, Na gaza jurewa ne…..” kukane ya ciyota, da sauri ta duƙar da kanta ƙasa, sam bataso ta nuna rauninta agabansu, saboda zata ƙara karya masu zuciya ne, sai dai duk ƙoƙarinta na hana kanta yin kukan hakann ya faskara, ita dai sam hankalinta bai kwanta da ɗaukar su parveen da akayi ba,
Dafa kafaɗunta Batool ta yi da hannayenta biyu, Cikin sigar lallashi tace”pls angel, u should stop shedding your tears, kina ƙara sanya mana damuwa ne, ke da kike ƙarfafa mana gwiwa yau ke ce da kanki ki ke zubar da hawaye to mu me zamu yi kenan”? Idon batul cike tab da kwalla tayi maganar,
Ta wutsiyar idonta ta hangi azeeza dake a zaune ta kasa kunne tana sauraronsu, da alama baccin bai sake ta ba, bata fahimtar me suke tattaunawa,
Sanin raunin azeeza yasa tayi saurin sanya tafukan hannayenta, ta share hawayen da suka wanke fuskarta, murmushi tayi wanda kai zuci ba takalli batool dake kallonta tace “Nadaina batool, bazan ƙara ba, kema kada kiyi kuka” jinjina kai batool tayi”Nima bazan bari hawaye na su zuba ba, Angel inaso mu haɗa hannu wurin taimaka ma sauran ƴan uwanmu, mu dinga lallashinsu muna basu baki har Allah yasa adawo dasu Parveen, Inaso mu sama ma junan mu farin ciki koda kuwa babu wani acikin mu, kamar ke da kika jure rayuwa batare da Mahaifinki ba, haka nakeso muma mu ƙarfafa zuciyoyin mu, mu yi rayuwa da sanin cewa wata rana samu iya rasa wani,
Tun da batool ta soma magana angel ta natsu tana kallonta, acikin zuciyarta tana Jinjina Ma batool, Yarinyar akwai tawakalli, Tana da hankali da tunani, Allah yayi mata baiwar iya sarrafa harshe wurin tsara kalamai masu kwantar da hankali, Haƙiƙa Iyayensu sunyi babbar asara Na rashin ya’ya kamar su,
“Angel kinyi shiru baki ce Komai ba, Ina ta surutu Ni kaɗai,” ajiyar zuciya angel ta sauke tare da kallon Batool tace”Am sorry Sister, naji maganganunki, sunyi mini daɗi sosai kuma in sha Allahu, zamu yi hakan, Zamu haɗa hannu wurin sama ma kanmu farin ciki,”
Muryar azeeza ce ta katse su da cewa”Wai har yanzu ba’a dawo mana dasu parveen ba? Jiya har mafarkinsu nayi,” saukowa tayi daga saman gadon ta nufi su angel dake a tsaye ta ruƙe qugu tana kallonsu,
“Ba’a dawo dasu ba Azeeza, Mu ƙara haƙuri zuwa anjima may be Giants su kawo mana su” Batool ce ta bata amsar tambayarta,
Ta6e baki azeeza tayi tare da cewa”Ni dai indai ba’a dawo mana dasu ba, Bazan ƙara Cin abinci ba” maganartace ta basu dariya,
Sauran ƴan uwansu dake bacci ɗaya bayan ɗaya suka dinga farkawa, duk wanda ya buɗe ido saiya tambayi su deeja, Angel da batool ne ke kwantar masu Da hankalinsu akan su ƙara haƙuri zuwa anjima, lokacin da kowa Yayi wanka, Suna a zazzaune saman gadajensu, Sai ga giants sun shigo kawo masu abinci, Bayin Allah duk sunyi tsammani za’a zo masu da ƴan uwansu amma sai suka ga akasin,
Koda suka koma saman dining carpet domin Cin abinci, saboda damuwa, kaɗan suke tsakura suna ci ba don suna jin daɗin abincin ba, Angel hada ƙoƙarin mikewa taje karkashin gadon batool ta ɗauko kwando, tazo tana kwashe kingin abincinta, Yasmin tace”meyasa ba zaki ci ba? Bafa Ki ci dayawa ba’? Angel tace”su parveen zan ajiye mawa, kada su dawo da yunwa anjima, Jin abunda tace ne yasa suma suka rage sauran nasu abincin don a ajiye ma su parveen, angel ta kwashe duka cikin kwandon, Taje ta 6oye a karkashin gadon batool,
Bayan tafiyarsu Giants, Hanna ta basu shawarar su motsa Jiki Ko sun samu Lokaci yayi saurin wuce wa duk don saboda tsammanin za’a dawo masu da ƴan uwansu yau, bayan sun kammala motsa Jikin nasu Kowa Ya gaji sai uwar xufa ke tsastsafo masu, A dole suka je toilet kowa ya watsa ruwa a jikin shi, ba ƙaramin ɗaɗi suka Ji ba, saman gadajensu suka koma kowa Ya hau ya zauna fira suka soma yi atsakanin su, wani irin bacci ne yazo ma angel batare data shirya mashi ba, dama jiya ana binta bashin baccin da batayi ba, gyara kwanciyarta tayi asaman gadonta, tare da jan bargo ta lullu6e kanta, Cikin ƙanƙanin lokaci bacci yayi awon gaba da ita,
*ANEELERH*
Almajirai ne daddabe a gaban motarta, sunyi dandazo suna jiran Ta basu sadakar kuɗi kamar yadda ta saba basu a duk lokacin da tazo zata wuce ta wurin makarantar allonsu, Sai faman zumuɗu almajiran suke Yi, Kayan Jikinsu duk sun yayyage, kowannan su na aruƙe da kokwan bararsa,
Zuge glass ɗin motar ta yi, almajiran sai kallonta suke yi, tana a zaune saman driver seat, Jikinta na asanye da atampa, riga da skirt sunbi shape ɗin jikinta, Ta yafa mayafi akanta, ba ƙaramin kyau ta yi ba, Yayin da baby junaid ke akwance saman passenger front seat, Kayan sanyi ne ajikinshi sunyi matuƙar yi mashi kyau, baccin shi yake yi hankali kwance, ga wani irin ƙamshi dake fita ajikin shi,
Ƙoƙarin Zaro kuɗi take Yi acikin ƴar purse ɗinta Bendir guda ta ciro na ƴan ɗari biyar biyar, zarowa ta dinga yi tana miƙa ma almajiran, Sai murna suke yi, suna kai hannu suna karba tare da yi mata addu’o’e Sai da ta kammala raba masu, tana yunƙurin Zuge glass ɗin motar, taga an zuro mata hannu, ras taji gabanta ya faɗi ganin hannun babban mutun sanye cikin baƙar safa,
Da sauri ta kalli fuskar mutumin, ya sanya Mask a fuskarshi, Baƙaƙen kaya ne ajikinshi, bakomai ya faɗo mata araiba face mutumin da ya Ɗauke mata baby junaid ɗinta lokacin da taje gidanta, nan take gabanta yyi mugun bugu, A tsananin tsorace ta shiga kiciniyar zuge glass ɗin motar, ganin zata datse mashi hannu yasashi yin saurin zame hannunshi
Key tayi ma motan hannunta na kerma ta ruƙe steering da wani irin speed ta fusgi motar da gudu ta haura saman titi tana ambaton”La’ila ha illa anta subhanaka inni kuntu minazzalimin” tarasa ina zata dosa, saboda tsabar ruɗi, Gani take kamar mutumin yana abiye da ita, ashe dama bibiyar rayuwarta yake yi? Tayi tambayar acikin zuciyarta, Marece ne sosai Tana kokarin shan kwana, muryarshi ta ratsa kunnata”Baki bani sadakar ba” a gigice taja burki ta tsayar da motar, idanuwanta azazzare ta ɗago tana kallon shi ta cikin Rear view mirror ɗin motar,
Mutumin Yana a zaune Cikin back seat na motar, a hakimce,
Tayi matuƙar razana ganin shi acikin motarta, taya akai ya shigo bayan ta rufe motar, Anya kuwa mutunne ba aljani ba? muryarta na rawa tace”dan..dan Allah na roƙe ka, kada ka cutar damu, bansan wanene kai ba, ban kuma san laifin da nayi maka ba, ka faɗi kome kake so zanyi maka shi” idanuwanta cike tab da kwalla tayi maganar,
“Kome nake so zaki yi mini”? Ya yi tambayar yana kallonta, a tsorace tace”Eh, wlh zanyi”
Ya amsa da “Okey, ” hannu taga ya zura cikin aljihun wandon Jikin shi ya lalubo wayarshi, Ya ɗan daddana ta kafin ya miƙa mata wayar”Location ɗin nan zaki bi, ” batare da musu ba ta kar6i wayar tashi, idonta akan google map ɗin daya buɗo mata, daga gefenta ta ɗaura wayar, Ta ci gaba da driving tana bin location ɗin, yayin da zufa ke tsastsafo mata, zuciyarta a firgice take da tsoron inda zai kai su, Wayar shi kanta abun tsoro ce saboda ta banbanta da sauran wayoyin da ta saba gani, Babu sunan Company ajikin wayar,
Dogon titi suka Miƙa sham6al har zuwa cikin wata area, Ta jigunannun masu kuɗi, Manya manyan gine gine, Unguwar shiru babu yawaitar mutane acikinta, a bakin wani katafaren Gida ta ƙaraso da motar, yace tayi horn ta danna horn nan take Wagegen gate ɗin gidan Ya zuge awani slow, kutsa motar tayi acikin gidan, har saida ya bata umarnin ta tsayar da motar tukunna ta tsaidata,
Buɗe murfin motar yayi tare da fitowa ya zagaya other side ɗin da junaid yake a kwance, Ya buɗe motar ya zura hannu ya ɗauke shi, Aruɗe aneelerh take kallon shi, ganin ya ɗaukar mata yaro,
“Let’s go in” yayi maganar yana nuna mata hanyar zuwa cikin gidan, Jiki asanyaye ta buɗe motar ta fito tabi bayanshi, Wa’iya zubilla Ta yi matuƙar girgiza da ganin kyawun gidan ya tsaru iya tsaruwa kai kace ba’a 9ja yake ba, Duk da a tsorace take hakan bai hanata bin ko’ina da kallo ba, suna ƙarasowa bakin glass door ta falon gidan, Muryar na’ura ta karaɗe kunnuwansu, wani abun mamaki daya ɗaure mata kai, na’urar da ta soma magana tana sanar da zuwan su, sai da ta faɗi Cikakken sunan aneelerh, wato Aneelerh muhammad falgore, Ras taji gabanta ya faɗi, a karshe na’urar tace”you’re permitted to come in” nan take ƙopar glass ɗin ta zuge,
Mutumin yace mata su shiga Ciki, ta zura kafarta acikin katafaren falon, Tsayawa faɗar irin kyawunshi 6ata baki ne sai wanda ya gani, wani irin sanyin a.c ne ta ko’ina, Komai na Cikin falon White Colour ne atsaftace yadda kasan ba’a ta6a amfani dashi ba, saboda kyawunshi da sabuntakar furniture ɗin dake acikin shi,
Miƙa mata Junaid Ya yi, da sauri ta sanya hannu ta kar6eshi, ta rungume shi ajikinta, A saman Sofa 3 seater Ya bata Umarnin ta zauna, xama tayi tana faman baza ido, Jira take taga me za ayi mata, Acikin zuciyarta sai addu’o’in neman tsari take karantowa,
Takun takalma ta soma ji daga can saman twin stairs ɗin dake a falon, a hanzarce takai idanuwanta wurin tana kallonsu, waro ido waje tayi Jikinta ya shiga 6ari ganin Gabza gabzan Mazan dake saukowa saman benan, kowannansu na asanye Cikin shiga ta baƙaƙen kaya, A ƙalla sunkai su takwas, bakwai Suna a left hand na benan, Yayin da mutun ɗaya ke tafiya atsanake ta right hand ɗin stairs ɗin
Kusan atare suka sauko daga saman benan, Aneelerh bata Iya ganin komai na Jikinsu ba, Gaba ɗaya sun rufe kansu daga ƙasa har sama Cikin black dress, Dogayen riguna na maza masu haɗe da huluna kamar alkebba, Guda bakwai ɗin suka Ƙame a tsaye tare da goya hannayensu saman ƙirjinsu, shima wanda ya kawota gidan Yana a tsaye gefen hand sofa ɗin da take a zaune Ya ƙame kamar yadda sauran su ka yi
Mutum ɗayan nan daya rage, shine Ya zauna saman sofa 2 seater, Ya ɗaura ƙafarshi ɗaya bisa ɗaya, aneelerh fa tasha jinin jikinta, sai faman ƙanƙame junaid ta ke yi ajikinta, Yaro sai bacci yake yi baisan halin da Mommynsa ke ciki ba,
“Ki natsu Ki saurari maganganun da zamu tattauna dake, mintina ƙalilan zamu salleme ki ki tafi” Na gefenta ne yayi maganar, wanda suka zo tare da shi,
Jin haka yasa ta daidaita natsuwarta, ta kasa kunne tana jiran Jin me zasu Ce, wanda take tunanin shine team leader ɗinsu, wanda ke zaune saman Sofa 2 seater akanshi ta tsayar da idanuwanta, wata irin ƙirar ƙarfi ce gare shi, taban al’ajabi, mai matuƙar jan hankali da tsoratarwa, kai daga ganin wannan babu wasa acikin lamuranshi, baƙaƙen kayan sun zauna mashi sosai, sun bayyanar da zazzafar surarshi, tayi tunanin shi zai yi mata magana amma sai taji yayi shiru,
Takun tafiya ta kuma jiyowa ta can 6angaren, Wani ƙaton ne Ya fito sanye da bakaken Kaya, Hannunshi a ruƙe da plate me ɗauke da Glass Cup, ruwan sanyi ne aciki, a saman table ɗin dake a kusa da sofa ɗin da aneelerh ke a zaune ya ɗaura plate ɗin, Cikin girmamawa yace mata”Zata iya sha” ya ambaci hakan tare da juyawa Ya bar falon, duk fa waɗannan Garadan mazan na a kewaye da ita, Da farko taji tsoron tasha kada ace An sanya mata wani abu, amma daga baya saita kai hannu ta ɗauka ta ɗan kur6i ruwan, sanyi gare shi ga daɗi, bayan ta ajiye Glass ɗin, Sai ga wannan katon daya kawo mata ruwa, Ya dawo Cikin falon hannunshi ruƙe da Laptop Tsadaddan gaske, Adai dai gaban aneelerh Ya ajiye laptop ɗin saman table gefen plate ɗin da ya kawo mata ruwa,
Daddana laptop ɗin Ya shiga yi Cikin ƙwarewa, Aneeelrh dai ta zuba ido tana jiran ganin me za’a nuna mata,
Bakomai bane Ya bayyana akan screen ɗin Laptop ɗin nasu, Face Hotonsu da su kayi ranar birthday ɗin Angel, Su Huɗu, Angel ce a tsakiyarsu, Taj yana agefenta ya zuƙunna, Aneelerh da Uzair Suna atsaye fuskokinsu ɗauke da murmushi,
Tsananin mamaki ne ya kama Aneelerh ganin wannan hoton, duk da tasan Zasu Iya samun shi a social media, saboda sunyi share ɗinshi a insta da Facebook, twitter da tiktok, hada videos na birthday ɗin angel,
“Kin gane su”? Muryar mutumin ce ta katse mata tunaninta, da sauri tace”Eh, ƴan uwana ne,” ya nemi ta yi masu bayanin menene alaƙarta da su” da hannu ta nuna mashi hotonta dana uzair tace mijina ne, wannan kuma ɗan uncle ɗin shi ne, Sunan shi Tajuddeen, Ita kuma yarinyar Ɗiyarshi ce, sunanta Unaisa amma muna kiranta da Angel,’
Jinjina kai ya yi tare da cewa”Mu jami’ae ne masu zaman kansu, muna da interest akan case ɗin 6acewarsu, that’s the reason why muke Bibiyarki, saboda sanin cewa ke kaɗaice zaki Iya bamu bayanan da muke so, Zamuyi maki tambayoyi, da zarar kin amsa mana zamu sallame ki ki tafi, kuma bazaki sake ganin mu ba,” ta amsa ma shi da toh,
Tambayoyi suka shiga yi mata, tun daga kan alaƙar dake tsakanin su tajuddeen da Uncle abdallah har izuwa kan Alhaji ubaid, da ita kanta hada iyayenta duka saida su ka yi mata tambayoyi a dangane dasu, hatta Benazir sai da suka yi mata tambayoyi akanta, duk ta amsa masu wanda ta sani, abunda ya ɗaure mata kai hada ƙawarta Aisha suka Yi mata tambayoyi akanta, game da yarda akai mahaifinta yayi mata korar kare daga gidan shi, Lamarin ya ɗaure ma aneelerh kai, taya akai suka san kowa da take atare da shi? Su wanene waɗannan jami’an masu Uniform baƙaƙen Kaya, Taso ta tambayesu daga ina suke, amma sai suka ce mata, basu bata iznin tambayar komai agame dasu ba, Sannan suka ce ta sawa ranta cewa a mafarkine Ta haɗu dasu, kada tayi tunaninsu kuma kada ta kuskura ta yi gigin faɗa ma wani agame da su,
bayan sun kammala Yi mata tambayoyin har bakin motarta suka rakota, ta buɗe ta shiga, suka yi mata godiya taja motar ta fuce daga Cikin gidan, Tana cikin yin driving saman titi Junaid Ya farka yana ta tsala kuka, a dole ta kashe motar daga gefe ɗaya ta rumgumo shi ajikinta tana lallashinshi, yace mata Yunwa yake Ji, ta bashi abinci yaci,” tunawa da madararsa da ta ajiye mashi a backseat na motar yasa ta juya ta kai hannu ta ɗauko mashi ita, acikin bottle take, ta cire murfin ta kafa mashi abaki yana sha, yayin da ta shiga zurfin tunani, abun ya tsaya mata aranta, ita gaba ɗaya rayuwar duniyar tsoronta take ji, meya faru dasu uzair? Shiru ba labarinsu kusan shekara huɗu? Sannan ga wasu mutane suna Bibiyar rayuwarta da sunan jami’ae ne, Anya kuwa bazata gudu tabar ƙasar nan ba, na wani lokaci? Gani take kamar zata rasa ɗanta ne, kamar yadda ta rasa mutun ukun nan masu mahimmanci, tana cikin yin wannan xancen zucin junaid ya fashe da kuka yana faɗin”tasa mashi madara a hanci,” da sauri takai idonta kanshi, fuskarshi ta 6aci da madarar, batasan ya akai ta janye robar daga bakinshi ba ta kwafa mashi a hancin shi, rufe bottle ɗin tayi tare da ajiyeta gefe ɗaya, ta zaro hanky cikin ƴar purse ɗinta ta shiga goge mashi madarar, bayan ta kammala ta maida hanky a cikin purse ɗin, Ta rungumeshi ajikinta tana lallashinshi, har saida yayi shiru lamo ajikinta tukunna ta tashi motar ta miƙi hanya ta nufi gida,
Lokacin da ta koma Gida, a palour ta taras da Mami da wasu ƙawayenta suna fira, sai da ta fara gaishe su, suka amsa mata, tare da miƙa mata hannu ta basu junaid, Ita kuma ta wuce cikin ɗakinta, tana shiga ta rage kayan jikinta ta faɗa toilet tayi wanka, ta fito waist ɗinta a ɗaure da towel tana kokarin zama saman mirror chair, alert ya shigo Cikin wayarta dake ajiye saman mattress, da sauri takai hannu ta ɗauki wayar, kamar a mafarki take ganin credit alert ɗin da aka turo mata via dollar account ɗinta, wanda a kuɗinmu na nigeria kuɗi ne bana wasa ba, har saida ta dafe ƙirjinta da hannu ɗaya, ta shiga ruɗu akan wannan kuɗin da aka turo mata, bayan ita ba wanda ta ba acct number ɗinta, Shi kanshi dollar account ɗin ta jima bata yi amfani dashi ba,
Komawa ta yi gefen gadonta ta zauna hannunta ruƙe da wayar tana kallonta, wani saƙonne ya kuma shigowa cikin wayarta, cikin harshen turanci aka rubuto shi, karantawa tayi kamar haka
_mun gode da haɗin kan da kika bamu_
Nan take ta gane cewa Jami’an nan ne suka Turo mata da kuɗin, ajiyar zuciya ta sauke tare da jefar da wayar saman pillow, Ta gyara kwanciyarta saman mattress ɗin, Yayin da idanuwanta ke fuskantar ceilling, zuciyarta a cunkushe take da tunani kala kala duk akan Jami’an nan, Su kuma ko daga ina suke? Waye ya sanya su bibiyar case ɗin su tajuddeen? amma tasha ruwan mamakin Irin Ƙirar jikinsu, especially wannan ɗayan daya zauna saman sofa wanda take tunanin shi ne team leader ɗinsu, Kamar shi ya ƙera kanshi, daga gani dai jami’ae ne su bana wasa ba, ita dai fatanta Allah ya tabbatar da alkhairi akan bincikensu dana su Uncle bash,
Ta yi zurfi acikin tunaninta, tajiyo muryar baby junaid yana faɗin”Mommy kizo inji mami, ” daga kwancen da take ta juya tana kallonshi, ya ruƙe qugu abakin ƙopar ɗakin, yana ta faman zumbura baki yace”Bake kika sanya mun madara a hanci ba, ae na faɗa mata, tace zata rama mini”
Yadda yayi maganar ne ya bata dariya, har fararen haƙoranta suka bayyana, Miƙa mashi hannu tayi”zo nan My baby boy” maƙe kafa ɗa yayi”Ae baki sona, Tunda kika sanya mun madara a hanci,” saukowa tayi daga saman gadon ta wuce wurin closet ɗinta, Jallabiya ta ɗauko ta zura ta ajikinta, kafin ta dawo ta nufi inda yake a tsaye, ta zuqunna agabanshi tare da kai hannu tana shafa sumar kanshi tace”My baby boy, nifa mommynka ce, ni na haife ka, bani da tamkarka aduniyar nan inasonka fiye da kaina, jinka nake kamar bugun zuciyata,’ takarasa maganar tare da sanya hannu ta ɗauke shi, kafin ta mike ta wuce cikin falon,
A lokacin ƙawayen Mami sun tafi, A zaune ta same ta saman Sofa, Riga bubu ce a jikinta, idonta na akan plasma tv, tashar arewa 24 take kallo
Takun tafiyar aneelerh ne ya janyo hankalinta, ta juyo tare da kallonta, fuskarta asake tace”My daughter Kinyi mana laifi, Junaid ya faɗa mini abunda kika yi mashi acikin mota, ashe dama shirin kashe shi ki kayi”? cikin zolaya tayi maganar, Fuskar aneelerh ɗauke da murmushi tace”Kuskure ne mami bansan nayi mashi haka ba, kuma fa har hakuri na bashi amma shine bai kar6i uzirina ba,” takai karshen maganar a yayin da take zama saman Sofa tare da junaid, Ya manne ma jikinta,
Kallon shi mami tayi”ka yafe mata ko in rama maka”? Ashagwa6e yace”nayi mata amma idan ta ƙara, afaɗa ma uncle bash ya sanya gun ya harbe mata kai,” gaba ɗaya suka kwashe da dariya aneelerh tace”amma baka da mutunci junaid, uwar taka zaka sa a harba da bindinga? Idan na mutu ya zaka yi”? Watsa hannu yayi tare da cewa”Shikenan, sai aje kasuwa asiyo wata uwar” tuntsirewa su kayi da dariya, mami tace”Aku sarkin ɗumi, Kwanan nan xan sanyaka makaranta, tun da bakinka ya buɗe, ga surutu” Aneelerh tace”nima tunanin da nake yi kenan, ko islamiyace a fara sanya shi yana zuwa kafin asanya shi ta bokan,” fira suka cigaba da yi har baby junaid yayi bacci a jikinta, aneelerh bata fada ma mami game da abunda ya faru da ita ba, kamar yadda jami’an suka gargaɗeta akan ta manta da komai nasu ta ɗauka tamkar mafarki tayi shiyasa taja bakinta tayi shiru gudun kada taja ma kanta,
*Back to Prison*
After One Day👌
Wani irin narkakken Jini ne mai kauri da ƙarni yake gangarowa ta cikin ƙoramar ruwan dake Gudana, Sassan Jikin mutun ta gani gunduwa gunduwa tsulundum acikin Jinin, Hannu tasa ta dafe kanta tare da fashewa da matsancin kuka na fitar hayyaci,
A firgice ta farka daga baccin da take yi sakamakon bugun ƙafarta da aka yi, wata irin Zabura Ta yi tare da miƙe wa zaune, Tana binsu Da Kallo, ɗaya Bayan ɗaya, Suna a kewaye da gadonta, Batool Hanna hibba, Azeeza, yasmin, eve, javed Sai kiran sunanta suke Yi suna tambayarta lafiya? Me take ma kuka? Abunda ya faru suna a kwance saman gadajensu suka soma Jin shessheƙar kukan angel, Hakan yasa suka yi gaggawar zuwa gaban gadonta don suji dalilin yin kukan nata,
“Angel meya faru ne? Duk kin bi kin ruɗe? ko kinyi mummunan mafarki ne”? batool ce ta jefa mata tambayoyin,
Ƙanƙame Jikinta Ta yi da hannayenta, wata irin zufa Ce ke tsastsafo mata ajikin fatarta, Sai faman zazzare Manyan idanuwanta take Yi, gaba ɗaya bata Acikin hayyacinta, tayi matuƙar tsorata da mafarkin da tayi, muryarta na kerma ta soma Magana”Ina parveen? ina rubina da Deeja an dawo dasu? Ko kuwa har yanzu? Takai ƙarshen maganar tana kallonsu Batool,
*❤❤❤PRISONERS❤❤❤*
“Angel Still ba’a dawo dasu ba, Abincin da muka rage musu tun jiya ya riga da ya lalace, da mun sani mun cinye shi,” Hanna ce ta bata amsa, Azeeza tace”Yanzu shikenan baza adawo mana da su Parveenar mu ba? sun tafi kenan”? Muryarta a sanyaye tayi maganar, Hibba tace”Pls Azeeza stop sayin that bana jin daɗi, kuna karya mana zuciya, Tsohuwa fa tace za’a dawo dasu da zarar Sun samu lafiya,” Eve ce ta kalli Hibba da tayi maganar tace”Hib kin manta lokacin baya? Ƴan uwanmu da muke atare dasu? Wasu in an ɗauke su ba’a dawowa dasu sun tafi kenan”? Idon angel akansu tana sauraronsu, kwata kwata bata acikin natsuwarta, tana matuƙar jin tsoron ta yi mummunan mafarki, saboda Xaiyi wuya mafarkinta yaƙi xama gaskiya, kafin zuwanta gidan kurkukun ƙaddara saida tafara mafarkin kasancewa acikin shi kuma sai ga shi ta tabbata, ta tsinci kanta acikin shi,
“Yakamata mu daina wannan maganar, Muna ƙara tayar wa junan mu hankali, Idan muka kwantar da hankalin mu, za’a dawo dasu ne,” acewar Javed, yasmin tace”Yanzu me zamuyi toh? Ni nagaji da zama zugudum, ” fuskarta a yamutse Tayi maganar,
Azeeza tace”Muna da abunyi mana, Angel zata Wanke mana gashin kanmu, ta kuma gyara mana shi, ” tunkan takai karshen maganar, yasmin ta harare ta”Kefa matsalarki kenan, Sai ana magana ta hankali ki wani soko wa mutane Shiririta aciki,” zum6ura baki Azeeza Ta yi tare da murguɗawa mata shi tace”To me kike so Muyi? Wanka ko motsa Jiki? Ko kuma bacci? Ko giants xamu Jira su kawo mana abinci”?
Banza yasmin tayi da ita, Zama batool tayi a gefen gadon angel, ta ruƙo hannun angel acikin nata tace”Sister, na lura sam bakya acikin hayyacin ki, Ki faɗa mini, me kika gani acikin baccin ki wanda ya tsoratar dake”? Idanuwan angel cike tab da ƙwalla ta ɗago ta kalli fuskar batool, bazata Iya faɗa mata ainihin abunda ta gani acikin mafarkin ta ba, Saboda Bata son ta tayar mata da hankali, Kuma faɗin baida amfani, sannan ma babu kyau mutun yayi mummunan mafarki ya faɗi ma wasu,
Don haka tace mata”bakomai batool Just bana Jin daɗin Jikina ne,”
“Ko zakiyi wanka ne? May be kiji daɗin Jikin ki,” cikin sanyin murya tace”eh, xanyi, ” tana rufe baki Azeeza tace”Angel me zamuyi yau”? Murmushi angel ta ƙaƙalo, yayin da take kallonta tace”Little Kome kike so Shi za’ayi, ” ashagwa6e Azeeza ta bubbuga ƙafar tare da cewa”Ni kidaina ce mun little bana so,” gaba ɗaya su kayi dariya, Hanna tace”Ae gaskiya ta faɗi, kallarki fa? Wata ƴar ƙarama dake, Ko kafaɗarmu baki kai ba, banta6a ganin wadda bata cigaba ba acikinmu irin ki, Duk yawan abincin da kike Ci sam baki ƙara auki, ba ƙiba ba tsawo,” dariya suka saki gaba ɗayansu, Rai a6ace Azeeza Ta zuƙunna kasa tana yin kukan ƙarya, Angel tace”pls kudaina janta, Nima na faɗi ne kawai don ayi nishaɗi, amma azeeza ae itace babbarmu,” ta yi maganar tana ƙyaftawa musu ido, atare suka haɗa baki wurin cewa”hakane Azeeza itace babbarmu, muma wasa muke Yi mata, don kawai ayi raha ne” Sunsan azeeza da son girma, jin wannan maganar tasu yasa ta miƙe tana gumtse dariya abaki,
Angel tace mata”Me kike so Muyi yanzu?
“Ki wanke mana gashin kanmu, Kuma ki gyara mana, keda batool kamar yadda ku kayi mana ran nan kin tuna’? Zaro ido angel tayi”Azeeza Baki ga yadda na farka ba yau, sam babu natsuwa atare dani, Taya zamu Iya wanke maku wannan uban gashin kan naku, Kuma mu gyara shi,? Ta6e baki azeeza ta yi, Itafa in taso abu to ayi mata kawai, idan ba haka ba yini zatayi tana faman tur6une musu fuska duk da tana da yawan fara’a kamar Gonar auduga,
“Kada Ki damu sister azeeza, Koda angel bata samu damar tayani ba, Ni xan gyara maku gashin kanku, Mu barta ta huta, tun da bata Jin daɗi, Kuxo muje toilet,” Batool ce ta yi maganar, Ta juya ta nufi toilet suka bi bayanta,
Bayan tafiyarsu Cikin toilet, Angel ta sauke ajiyar zuciya, tare da jingina bayanta Jikin bango, Gefe ta juyar da kanta tana kallon Gadon danish, kamar dai kullum yana a kudundune Cikin bargo, Haris da mubeen da Javed hada naufal duk basu farka daga Bacci ba, sakamon daren da su kayi jiya batare da sun runtsa ba, Suna Xaman Jiran adawo musu ƴan uwansu,
Saƙe saƙe ta shiga Yi acikin zuciyarta, game da wasu tambayoyi da suka cunkushe mata kwakwalwarta, sun hanata sakat, idan ta takura kanta akan tunaninsu Har wani matsanancin ciwon kai take ji, tabbas tana son Yin magana da tsohuwa duk da tasan zaiyi wuya tsohuwa ta amsa mata tambayoyinta, amma zata jaraba tunkararta, Yau ɗin nan,
A6angaren su Batool, sai da tabi kowannan su ɗaya bayan ɗaya ta wanke musu sumar kawunansu, Baƙaramar wahala tasha ba, domin kuwa Dukansu tsayin gashinsu Ya zarce midback ɗinsu, Ga uban yawa dake gare shi, bayan ta kammala wanke musu gashin, Sai da kowannan su Yayi wanka, Kafin suka dawo Cikin ɗakin, Kamar yarda suka bar angel zaune saman gadonta haka suka sameta, ganin sun fito daga wankan Yasa itama ta miƙe domin zuwa yin wankan, Shigarta da ƴan mintuna ta fito, A lokacin Danish dasu Mubeen duk sun farka daga bacci, saukowa su ka yi daga saman gadajen su, Atare suka Nufi Toilet domin suma suyi wankan ko sunji daɗin Jikin su.
A zaune ta samu batool gefen gado ta ruƙe Comb, Zata Gyara musu gashin kansu, hakanan taji tana sha’awar Tayi musu Kitson kalaba Guda Biyu akansu don ta Iyata, Kallon batool tayi tare da cewa”Ki bari In yi musu kitson Kalaba, Nasan ba’ata6a Yi maku ba, Yau zan jaraba mu gani idan zan iya” Cike da Jin daɗi Batool ta mika mata Comb ɗin, Tasa hannu ta kar6a, tare da samun wuri gefen gadon batul ta xauna, Ta ɗago ta kalli su Azeeza dake ta murna za’a gyara musu gashi tace Su zazzauna a ƙasa, zata fara gyarawa azeeza nata idan ta kammala mata zata Kira ta gaba da zata yi mawa,
A ƙasan gadon azeeza ta zauna tsakankanin ƙafafuwan angel, Hannu angel ta sanya tare da Ruƙo sumar kan Azeeza, Launin gashin kanta Dark blonde, mostly Turawa ne suke da irin wannan gashin kan, sharce sumar kan angel tayi, Kafin Ta raba gashin zuwa gida Biyu, a tsanake Ta soma yi mata kalaba, Tunkafin ta kammala su Hanna sai santin kalabar suke yi, duk sun ƙagara a kammala Yima azeeza suma ayi musu, Guda Biyu tayi mata shima daƙyar ta samu Tayi su saboda santsin gashin Ga tsayi da yawa, Tun da aka kammala Yima azeeza kitson, ta miƙe ta koma gefe tana ruƙe wutsiyoyin kalabar da hannayenta, Sai tsalle Take yi Wutsiyoyin kalabar suna yin sama da ƙasa, ita fa yau ta samu abun wasa,
Ɗaya Bayan ɗaya saida angel tayi musu kitson kalaba guda Biyu, Koda akazo kan Batool sai cewa tayi ta gaji bazata Iya ba, bakomai yasa tace haka ba face Fargabar Ta yadda zata Iya kama Gashin batool, Baƙar wahala zata Ci saboda yawan dake gare shi gashi kamar roba kuma Curly irin nata, a dole batool ta haƙura badan taso ba,
Danish Basu Jima da fitowa daga wanka ba, Giants suka zo Kawo musu abinci, Kamar Jiya haka Yau ma suka ɗibarwa Su Parveen Abincin acikin kwandonsu, Da niyar idan Allah yasa Aka dawo dasu Yau sai su basu su ci, gudun kada adawo dasu Da yunwa,
Bayan sun Kammala Cin abincin, Giants suka tattara Farantan suka Fuce daga Cikin ɗakin,
Duk sun damu da rashin ƴan uwansu, hakan yasa suka kasa samun natsuwa especially angel, Zarya ta soma Yi acikin aɗakin, idan takai ƙarshen bango saita dawo ta sake zagayowa, Har saida ƙafafuwanta suka soma Yi mata raɗadi tukunna ta dakata da yin zirga zirgar, Ta nufi gadonta da niyar ta huta, gefen gadon ta zauna Zugudum, Zuciyarta acike fal da tunanin duniya, wuraren marece su ka Jiyo alamun motsin buɗe ƙopar ɗakin tsohuwa, Bayin Allah da gudu suka duro daga saman gadajensu, Jikinsu na 6ari suka ƙarasa ƙopar ɗakin nata suna jira ta fito,
Sandar hannunta ce ta fara leƙowa, Kafin ta zuro kai ta fito waje, Jikinta sanye da jan doguwar rigar nan ta gado,
Kusan atare suka haɗa baki Wurin gaishe da ita, Ta amsa masu fuskarta asake, Sai faman mamular baki take Yi kamar me cin goro, fuskarnan a jagwale saboda tsabar tsufa ta koma kamar aljana, hurhura ta ko’ina,
“Tsohuwa Ya jikinsu Deeja? Tun jiya muke ta tsammanin jiran dawowarsu amma shiru ba’a dawo mana dasu ba, Munyi kewarsu sosai, Bacci ma daƙyar muka Yi shi, Ko abinci bama Jin daɗin Cin shi saboda rashin ƴan uwanmu” yasmin ce tayi maganar cikin nuna damuwarta,
Mubeen Yace”tun daga Lokacin da aka ɗaukesu har zuwa Yau, kullum Cikin zullumi muke,” Angel dai ta tsareta da ido kamar yarda itama tsohuwar idonta ke akan angel, Kowa da abunda yake saƙawa aranshi,
“Kinyi shiru baki bamu amsa ba? Yaushe za’a dawo mana da ƴan uwanmu? Idan mensturation ne Yanzu ya isa ace jikinsu Yayi sauƙi,” Fuska aɗaure angel ta yi mata maganar,
Jinjina kai tsohuwa Tayi, Sai da ta mula tasha Iska Tukunna tace”Ƴan uwanku suna acikin koshin Lafiya, Bazan Iya sanar daku lokacin da za’a dawo dasu ba, Saboda bani da masaniya, amma nasan bazasu wuce Cikin week ɗin nan ba,” A ƙagare Azeeza tace”Dagaske Su parveen Sun Ji sauƙi? Kuma Suna tambayar mu? Suma sunyi kewarmu”? Murmushi tsohuwa ta sakar mata tare da cewa”Eh mana, sun damu daku sosai, Kuma suna tambayarku, da zarar Sun ƙarasa Jin sauƙi za’a dawo maku da su” wani irin murmushin farin Ciki ne Ya bayyana akan fuskokinsu, In ka cire mutun Huɗu Batool Angel da javed sam babu walwala akan fuskokinsu, Baka iya tantance awani yanayi suke ciki, da alama suna kokwanton kalaman Tsohuwa, sun dai yi shiru ne kawai,
“Just for today, Ki kaimu inda suke domin muyi musu Ya jiki, Tunda Kince Suma sun Yi kewar mu, hakan zai rage musu damuwa” angel ce tayi maganar
Girgiza kai tsohuwa Tayi tare da cewa”Ba’a bada iznin ɗaya daga Cikin ku, Yaje inda suke ba, Idan Ku ka yi hakuri zasu dawo ne” batare da angel ta yi mata musu ba tace”Shikenan zamu zuba ido mu gani idan za’a dawo mana dasu”
Kallon su Batool angel tayi tare da cewa”Ku koma kuje ku zauna, inaso zanyi magana da tsohuwa” Jin wannan maganar yasa tsohuwa tayi saurin kallon angel fuskarta da alamun mamaki,
Juyawa su batool suka Yi atare suka tafi izuwa saman gadajensu, duk wannan abun dake faruwa danish Yana a kwance saman shimfiɗarshi, ko sarki bazai nuna mashi Jin daɗin gado ba, Ya cancanci da akirashi da MAJI DAƊIN GADO,
“Ƴar nan ina sauraron ki, wata Irin magana ce ki ke son Yi dani kuma? Yau ke da kanki”? tsohuwace tayi maganar, fuskarta akwa6e,
cikin sanyin murya angel tace”Inaso mu shiga daga Cikin ɗakin ki, Muyi magana” zaro ido waje tsohuwa tayi jin abunda angel tace, Can kuma saita yamutsa fuska tace”Ba dole sai mun shiga daga Ciki ba, Kome Ki ke son tattaunawa dani, Kiyi mini magana anan ya wadatar”
“Meyasa baki son in shiga ɗakin ki”? Ko akwai wani abu da bakya son in gani ne? Da tuhuma angel tayi mata maganar, girgiza kai tsohuwa ta yi tare da cewa”Babu abunda nake 6oyewa kawai dai bana bada iznin A shiga ɗakina, idan magana zakiyi dani to mu yi ta anan, babu wanda zai ji mu,”
Ta6e baki angel ta ɗanyi still idanuwanta akan tsohuwa tace”yau tsawon shekarata Biyu agidan kurkukun ƙaddara, Ban ta6a ganin wani ya shiga Cikin ɗakin ki ba, Bansan me kike 6oye mana ba, Amatsayinki na uwa agare su, meyasa baki bari muna leƙawa cikin ɗakin ki? Kuma bakya zama acikin mu domin Yin fira, Ko hakan ya sa6awa dokar prison ne”?
Bazawarin murmushi tsohuwa tasaki kafin ta Juya Tana dogara sanda tace da angel”Ki shigo daga Ciki,” tsananin mamaki ne Ya kama angel, Jin ta amince mata akan ta shiga Cikin ɗakin nata,
Sai da angel ta fara juyawa ta kalli su batool, ganin hankalinsu gaba ɗaya baya akansu Yasa ta bi bayan tsohuwa, Kafin ta shiga ɗakin tsohuwa Sai da takaranta addu’o’in neman tsari, sannan ta zura ƙafarta Cikin ɗakin, bakinta ɗauke da sallama,
A tsakiyar ɗakin Angel Ta tsaya tana bin Ɗakin tsohuwa da kallo, Abun mamaki abun al’ajabi, Bakomai bane aciki face Shufke sufken fulawowi,Ta ko’ina tamkar ɗan garde, Sai wasu tsoffin Kujeru guda Biyu suna fuskantar Juna, tsakiyarsu table ne mai ɗauke da Tea pot, da ƙananun Kofina guda Biyu, bayansu babu wani abu na furniture, Gado ko katifa,
Bayan ta kammala Kallon Cikin ɗakin na tsohuwa, Ta wurga idanuwanta kan tsohuwa dake yunƙurin zama saman ɗaya daga Cikin kujerun guda biyu dake fuskantar juna,
Muryarta angel ce ta katse mata hanzarinta da cewa”ina kayan ɗakin suke? Naga babu gado ko katifa? A ina kike kwana”?
Wata irin mahaukaciyar dariya tsohuwa tasaki, Mai matuƙar sautin gaske, Angel tuni tasha jinin jikinta, Muryar tsohuwa ashaƙe tace”Ƴar nan Badai Iya tambaya ba, Dama ganin kwakwaf kika zo Yi mini acikin ɗakin nawa? Keda kika ce Magana zamuyi ae kamata Yayi ki zo ki zauna ga kujera har ma da shayinmu na tsoffi in zuba maki musha don muji daɗin tattaunawa” Takai ƙarshen maganar tana nunawa angel kujerar da hannunta,
Jikinta tamkar na wadda aka zarewa Laka haka Taci gaba da tafiya Ta nufi kujerun Ta shiga Ciki ta zauna, tana Bin tsohuwa da kallon Ban yarda dake ba,
Ƙarasa xama saman kujerar tsohuwa Tayi, a yayin da suke fuskantar Juna ita da angel, Ido cikin ido suke Kallon juna,
“Ina sauraronki wata magana ce kikeson tattaunawa dani”? Ta yi tambayar a ƙagare da son ji,
Angel da ƙarfin hali tace”Tambayoyi ne nake son Yi maki, Ina fata zaki amsa mani” Wani irin kallo tsohuwa ta jefa mata, da mitsi mitsin idanuwanta,
Cigaba da magana angel tayi”Badan Hali na ba, Alfarmace nake nema awurinki, duk da nasan zaiyi wuya ki amsa mini tambayoyina, bansani ba ko yin hakan ya sa6awa dokar Prison”
Gajeren murmushi tsohuwa ta saki, kafin tace”A dokar gidan kurkukun ƙaddara, Ba’a ba mu damar Yin magana da prisoner ba dangane da abunda ya shafi Kurkukun, Yin hakan babban laifina wanda hukuncinsa mutuwa ne……….” aruɗe angel ta ɗan zaro ido tana kallonta, Tsohuwa tace”Kinga kuwa babu ta yadda za’ai In iya amsa maki tambayoyinki kodan saboda in tsira da raina”
Angel tace”Amma ae babu mai ganin mu, Daga Ni sai ke ne acikin ɗakin nan, Babu wanda zai san anyi” Cikin sigar wayau angel ta yi maganar, hakan ba ƙaramin dariya yaba tsohuwa ba, ganin ƙaramar yarinya na neman raina mata hankali, su da suka ga jiya suka yau
“Mu sha Tea mana, ” tayi maganar tare da kai hannu ta ɗauki tea pot, tana tsirara musu ruwan tea Acikin Cups,
“Ko kin zuba bazan Sha ba,” acewar angel, kallonta tsohuwa tayi”saboda me”?
“Ban yarda da duk wani abu da zai fito daga gare ki ba,”
“Amma meyasa ƴar nan”?
“Saboda Ina kokwanto Akan shayin da da zaki bani, Shekaran Jiya da kika ba su batool apples Sunyi bacci Na tsawon yini guda batare da sun farka ba, Har safiya tayi, ina da tabbacin cewa silar apples ɗin da kika basu ne, Shiyasa nake tsoron in sha tea ɗin nan, wata’ƙil kinsa Poison aciki,”
Fuskar tsohuwa ɗauke da murmushi tace”Da ace naso kashe ki da tuni na aiwatar da hakan, kada ki manta kina acikin ɗakina ke kaɗai, Koda sandar hannu zan Iya cutar dake, ƴan uwanki kuma dana bawa Apples Taimakonsu Nayi saboda bani da ikon da zansa Giants su dawo masu da abinci, Shiyasa na baku Apples ɗinmu na gidan kurkukun ƙaddara, Domin kuyi bacci Har gobe Ta yi saurin zagayowa ko kun samu Ku ci abinci” dariya angel ta ɗanyi Tare da cewa”Hakan Yayi kyau, yanzu dai tun da bakyaso In tambayeki agame da kurkukun ƙaddara, Inaso Nayi maki tambaya biyu bata Cikin kurkukun bace….”tsohuwa tace “ina sauraronki”
“Gidan Kurkukun ƙaddara A Cikin Nigeria Yake? Sa’an nan kince Mutum baya ta6a kasance Acikin kurkukun nan dole sai in na Jininsa ne Ya sadaukar da shi, Abunda da nake so In sani, Na jinin naka daya sadaukar dakai Kamar wa kenan”?
“Kin manta abunda na faɗa maki kenan? kiyi mini ko wace irin tambaya amma kada Ki tambayeni game da gidan kurkukun nan…..” tunkan takai karshen maganar angel ta katse ta da cewa”Amma ae ba’a Cikin kurkukun Nayi maki tambayar ba, Kawai ni inaso insan a wace nahiya Yake, Sannan Na jininka da zai Iya sadaukar dakai Kamar wa kenan”?
Tsohuwa bata amsa mata tambayarta ba, sai da ta fara miƙa hannu ta ɗauki kofin da ta zuba shayi acikin shi, takai bakinta tana kur6arshi kusan sau uku, Angel dai ta zuba mata ido, bayan ta Ajiye kofin saman table ɗin, Tana faman mulmula baki tace”Shayin da daɗi, Ki jaraba sha mana” girgiza kai angel tayi”Na ƙoshi, ni dai kawai ki amsa mini tambayata” dariya tsohuwa tayi”Ban ta6a ganin yarinya mai wayau da kaifin basira ba irin naki, Gaskiya Iyayenki Sun Iya haihuwa gaki Kyakkyawa Kamar ke kika ƙera Kyanki,..” ɗaure fuska angel tayi ganin tsohuwa Na ƙoƙarin Kaucewa Tambayarta, ta hanyar canza wani zancen,
Rai a6ace tace”ba wannan na tambayeki ba, Ki bani amsar tambayarta,”
Jinjina kai tsohuwa Ta yi idonta acikin na angel tace”idan na baki amsar tambayarki, Ni kuma me xaki bani? Kinsan ance gwammanti bata aikin banza” kallon rainin wayau angel tayi mata”Amma ae kinsan bani da abunda zan Iya biyanki da shi ko?, Ni dai kawai ki amsa mini tambayata”
Tea pot tsohuwa Ta ɗauka ta ƙara tsirara ruwan tea ɗin acikin cup ɗin gabanta, kafin ta ajiye pot ɗin ta ɗauki kofin takai baki tana sha” Sai da ta kur6e shi duka ta sauke kofin saman table, Tukunna tace”Tambaya ta farko, Gidan kurkukun ƙaddara Ni kaina bansan awace Nahiya yake ba, Abunda na sani shi ne ba’a Cikin kowace ƙasa Yake ba, mashin ko mota bazasu Iya kawo ki cikin kurkukun nan ba”
aruɗe angel ke kallonta, sai da takai karshen maganarta angel tace”Amma Ni lokacin da za’a kawo ni acikin mota aka ɗauko Ni, idan har zan Iya tunawa” dariya tsohuwa Ta saki,
“iya saninki kenan, A mota aka Cafko ki, Amma Bayan nan bazaki Iya tuna Ta Cikin ina aka ƙaraso dake nan ba,” shiru angel ta yi Zuciyarta cike da was wasin maganar tsohuwa, Gani take kamar ƙarya take Yi mata,
Muryar tsohuwa ce ta katse mata Zancen nata da cewa”Tambaya ta biyu, Na jinin ka da zai Iya sadaukar dakai, Mafi rinjayen sadaukarwa Iyayene waɗanda suka Yi silar zuwan ka duniya sune suke sacrificing ɗin ɗansu, Uwa Ko Uba, Bayansu Kuma sai Cikin Blood relatives ɗinka, Domin kuwa Bare bazai ta6a Iya sadaukar dakai ba”
A matuƙar kiɗime angel ke kallon tsohuwa, Muryarta har rawa take yi wurin furta”Iyayen mutun? uwa ko Uba? Anya kuwa zan Iya yarda da maganarki? Duk irin ƙaunar dake a tsakanin Iyaye da ɗansu Zasu Iya sadaukar dashi zuwa ga wannan ƙuntatacciyar rayuwar? To Meyasa zasu Yi hakan?
Fuskar tsohuwa ɗauke da murmushi tace”Kina mamaki ne?, dama nasan zaiyi wuya ki yarda da magana ta, Yanzu dai Ina sauraronki, Idan akwai tambayar da kike da ita, Ki faɗa mini kafin in tafi”
Angel dai ta jinjina maganar tsohuwa abun Ya tsaya mata arai, ya cunkushe kwakwalwarta, Daƙyar ta iya buɗe baki tace”Tambaya Ta ƙarshe da nake so Inyi maki, Mu prisoners dake rayuwa a gidan Kurkukun ƙaddara, Jinsi ɗaya ne? Dukanmu ƴan nigeria ne? Naga da yawan mu kamar fararen fata ne,
Tsohuwa tace”meyasa Ki kece haka”?
Angel tace”saboda Sam babu kamanceceniyar Jinsin baƙar fata atare da mafi rinjayenmu, Misali Kamar danish da Parveen da Javed Sun fi kama da ƴan ƴankin Asia, Azeeza Kuma kamanninta sak da European, Ita kuma batool tafi kama da Jinsin Larabawa, idan muka koma 6angaren Hanna da Hibba, sun fi kama da buzaye Ƴan ƙasar niger…..” ɗaya bayan ɗaya saida angel ta korawa tsohuwa Bayani adangane da Jinsin da kowannan su take hasashen yana kama da shi, takai ƙarshen maganar, a ƙagare da son jin amsar da tsohuwa zata bata,
“Lokacin da kina atare da Iyayenki, Mutane da wani jinsi suke kwatantaki”? Tsohuwace ta jefa mata tambayar yayin da take sakin murmushi,
Yatsina fuska angel ta yi tare da cewa”Sun fi tsammanin Ni balarabiyace wasu kuma baturiya, amma asalin mahaifiyata half cast ce, auntyna ce ta faɗa mini cewa kakata mace balarabiyar ƙasar egypt ce”
Tsohuwa tace”Kinyi kyan kai, Wannan tambayar da kikayi mini, Kina da amsarta ahannunki, ina fata zaki tashi ki tafi Cikin ƴan uwanki tunda na amsa miki tambayoyinki,” maƙe kafaɗa Angel tayi alamar bazata tafi ba
“Korata kike Yi daga ɗakin ki? Tsohuwa tace”a’a kawai dai Akwai inda nake son xuwa ne” Mamaki akan fuskar angel tace”ta ina xaki bi ki fita daga Cikin ɗakin nan naki bayan naga babu ƙopa, Koda yake ba abun mamaki bane, ae naga kafin ma in shigo Ciki, Kincanzawa ɗakin suffarshi duk don kada In yi maki leƙen asiri” tuntsirewa tsohuwa tayi da dariya, Itama angel ɗin dariyar tayi, sai da suka kammala shan dariyarsu kamar wasu ta6a66u, bayan sun tsagaita da yin dariyar angel tace
“Na jima inaso in tambayeki, Ya akai kika san Tarihin rayuwata? Kinsan komai dangane dani, Bayan haka kuma inaso insan asalin sunanki, Daga kin amsa mini waɗan nan tambayoyin xan Tashi intafi Cikin ƴan uwana”
Tsohuwa bata amsa tambayar ba, har sai da ta ɗauki tea pot ta ƙara zuba ruwan shayi a kofi ta kur6a sau biyu, Sannan ta ajiye kofin ta soma magana atsanake,
“Amsar tambaya ta farko, Duk yaron da aka sadaukar agidan kurkukun ƙaddara, Muna bibiyar rayuwarshi ne tun Yana acikin Cikin mahaifiyarshi, Har zuwa lokacin da zata haife shi, zamuyita bibiyar rayuwarshi da zarar yakai shekarun da muƙe buƙatarsa To babu makawa xamu ɗauke shi ne….”
“hakan na nufin tun ina jaririya kuna atare dani? Kenan kune kuke sanyani duk wani mugunta da nake Yiwa daddyna”? Da ruɗu akan fuskarta tayi tambayar, tsohuwa tace”A’a, bamu bane, baƙin aljanine dake atare da mahaifiyarki, Yana matuƙar sonta, Kuma yana da zafin kishi, shine maƙasudin rashin jituwar Iyayenki, Ya tsani Mahaifinki tajudden yaso ya tarwatsa shi, Amma hakan ya faskara saboda Daddnyki mutunne maison yin ibada, bai wasa da azkhar, kuma yana yawan yin sadaka, sannan babbar kariyar dake atare dashi, Yana Yin nafilfilin tsakar dare, A lokacin da benazir ta haifeki, Baƙin Aljani Ya fita daga jikinta ya koma a jikin ki, domin ɗaukar fansa akan mahaifinki, yayi amfani dake wurin ƙuntata mishi, Amma A yanzu Baƙin Aljanin baya atare dake,
Angel fa ta shiga ruɗu, duk da tana kokwanton maganar tsohuwa, Bakasafai Take yarda da zantuttukan ta ba saboda sanin Cewa Ita ɗin Babbar maƙaryaciya ce,
“Kin tambayi sunana, Zaki iya kirana Da TAMIRA Shine Asalin sunana,” Tsohuwa Na kai ƙarshen maganarta, Ta yunƙura ta miƙe daga saman Kujerarar, Da sandar hannunta ta nuna ma angel hanyar fita daga ɗakin, batare da musu ba, Angel ta miƙe ta nufi hanyar fita daga Cikin ɗakin Har takai bakin ƙopat fita, Muryar tsohuwa ta dakatar da ita,
“Shawarar Da nake so Na baki, Kada ki kuskura kice zaki Sanya naci akan sai kin gano ainihin ma’anar Kurkukun ƙaddara, domin kuwa daga ranar da kikasan ma’anarshi, Bazaki sake runtsawa ba, Kuma ba zaki sake Jin daɗin abinci ba, duk wani kingin jin daɗi da ya yi saura acikin rayuwarki, Zaki rasa shi ne! Wani irin mummunan faɗuwar gaba angel taji, Har saida ta dafe kinjinta saboda bugun da zuciyarta tayi mai sautin gaske,
Tsohuwa taci gaba da cewa”Ƴan uwanki suna farin Cikin kasancewarki acikinsu, Saboda Kin kawo musu canji acikin rayuwarsu, Ina fata zaki mayar da hankali wurin faranta musu rai, Amma fa kinsan da sanin duk ranar da kika Binciko ma’anar The destined prison, daga ranar daga ke har su, Zaku fuskanci matsanancin tashin hankali, Kuma daga wannan Lokacin bazaku ƙara Yin tozali da TSOHUWA TAMIRA ba, Zaku yi ta yin gwagwarmayar rayuwa ne atsakaninku, na gargaɗe ki ne saboda Ina sane da duk wani ƙudurinki nasan bin kwakkwafin Gidan kurkukun ƙaddara, Shiyasa na sanar dake irin matsalar da zaki jefa kanki da kuma ƴan uwanki” angel na ƙoƙarin Waiwayowa baya ta kalli tsohuwa taji an ingizata waje, Ƙopar ɗakin ta rufe,
Kamar an jehota ta faɗo ƙasa, Cikin ɗakinsu, har kanta saida Ya bugu,
Tun daga wannan Ranar Angel tashiga ruɗani, Kalaman tsohuwa sunyi matuƙar ɗaure mata kai, Tarasa Ina zata tsoma ranta taji daɗi, Kowa Saida Ya lura da canzawar da tayi, Sam tadaina shiga cikinsu, Gani take kamar Dukansu mutuwa zasuyi shiyasa take janye jikinta gudun kada sabon Yayi yawa ta yadda zata rasa kanta idan ta rasa wani acikinsu, Su batool duk sunyi tsammanin rashinsu Parveen Ne yasa ta canza ta shiga damuwa, Kullum cikin Lallashinta suke yi, Akan tayi haƙuri su koma kamar yadda suka ada, Daƙyar suka samu angel ta koma Yi musu wasa da dariya, Harma tana koya musu wasu wasanni donsu farantawa junansu,
Akwana a tashi Yau tsawon Sati Biyu kenan, Ba’a dawo musu da ƴan uwansu ba Har sun fidda rai da sake ganinsu, tun suna tambayar tsohuwa har sun gaji sun daina, kowa ya zubawa sarautar Allah Ido👀
Yau Tun da Suka tashi daga bacci suke ta jiran a kawo musu abincinsu suci amma shiru giants basu zo ba, Tun safe Har marece, Jikinsu duk Ya yi laushi, azeeza tuni ta fara Yi musu kukan yunwa, Lokacin da dare Ya ratsa hasken ɗakin Yayi duhu, Nan fa suka ƙara shiga tashin hankali ganin zasu kwana basu Ci abinci ba, la66ansu duk sun bushe, Ruwa kaɗai suke tasha tun safe, Cikinsu harya ɗaure, wasu daga Cikinsu hada amanshi su ka yi,
a ƙarshe suka haƙura Da abincin, Kowa Ya hau saman gadonshi ya kwanta, Cikin sa’a bacci ya ɗauke su, Ganin sun nutsa acikin baccin su yasa angel ta sanya hannu ta yaye bargon data lullu6e fuskarta da shi, Saukowa ta yi daga saman gadonta, Sumar kanta duk ta cukurkuɗe kamar ƴar mahaukaciya saboda rashin gyara, Cikin duhu take tafiya tana laluban hanya, Fitila taje ta ɗauko ta kunnata, Tana haske Saitin gadajensu Hannah, ganin babu mai motsi acikinsu Yasa tayi sauri Cikin sanɗa ta nufi sashen toilet ɗinsu, har yanzu bata haƙura da Ƙudirinta ba, Nason fasa gilashin nan, Alwashi ne ta ɗaukarwa kanta Koda zata rasa ranta saita Ga uban me ake aikatawa acikin gidan kurkukun, Duk da tana Jin fargaba akan irin gargaɗin da tsohuwa tayi mata, don a lokacin harta fara tunanin ajiye makaman yaƙinta, amma daga baya sai ta dinga jin tamkar ana tunzurata akan taje taci gaba da jaraba fasa gilashin zata Ci nasara, Zuciya da saƙe saƙe, gani take kamar idan ta fasa gilashin ta dira ta cikin tagar, zata samu damar zuwa wurinsu deeja ne, Harma ta dawo dasu Cikin ɗakin, Da yake sune damuwarta,
Tana shiga Cikin toilet ɗin, Taja ƙopa ta garƙameta da jamlock, A ƙasa ta sauke fitilar, ta ɗaga hannayenta Sama tana roƙon Allah Ya bata Ikon Fasa Glass ɗin a karo na karshe don daga yau ta sanyawa ranta cewa idan har bata fasa shi ba, ta gama zuwa tana shan wahala, zata haƙura ne,
Bayan ta kammala yin addu’ar, Da ƙwarin gwiwarta ta kai hannu ta rarumi bokitin ƙarfen, Sai da taja da baya ta watsa dagudu ta buga tsalle ta daki glass ɗin Da iya ƙarfinta na karshe, Amma wani abun takaici ko tsagewa Baiyi ba, kamar dai kullum haka taci gaba da bugun glass ɗin da bokitin amma Yaƙi nuna alamar ana bugunsa, saboda tsabar zufar dake tsastsafo mata ajikinta Tamkar wadda aka tsamo daga Cikin teku, Idanuwanta sun rune saboda wahala, Hannunta sai zogi yake yi mata, ga wani irin fitsari daya Matseta, da sauri ta jefar da bokitin gefe ɗaya ya gangara ƙasa, Tasanya hannu ta kwale wandon jikinta, Zuƙunnawa tayi a bakin magudaji tana fitsari, sai da ta kammala taje gaban fanfo tayi tsaki, tana kokarin miƙewa kwatam ta hango mutumin jingine da bango, Ya goya hannayen shi saman ƙirjinshi, Tun kafin ma ta ƙarasa juyawa ta gane kowanene, Sakamakon doguwar sumar kanshi data hango,
Muryarshi ce ta ratsa kunnuwanta,
“Can I give u a hand”? ras taji gabanta ya faɗi, azuciyarta tace”Danishi! Nashiga uku, kada ace ya ga abunda nake ƙoƙarin Yi, wayyo Allah na” rai a6ace ta ƙarasa juyowa tana fuskantar 6angaren da yake atsaye ya jingina bayan shi jikin bango, Rai a6ace ta nuna shi da yatsa”Wannan wani irin shashanci ne danish? Why zaka dinga faɗo mini Cikin toilet? yanzu da ace na tu6e kaya ina wanka ko ina wani uzirin Shikenan ka gane mini tsiraci na, Wlh bazan ƙyale ka ba” A fusace ta nufi bokitin data jefar ƙasa tasa hannu ta ɗaukeshi Ta daddage ta wurga mashi bokitin, Da sauri danish ya sanya hannayen shi biyu ya cafke bokitin a hannunshi, ɗagowa yayi da lumsassun idanuwanshi ya ɗaurasu akan fuskantar,
“Raunata ni kike so Ki yi? A ƙule tace”kashe ka zanyi ” Cikin sanyin murya yace”Am really sorry, na kar6i laifina, kada ranki ya 6aci, daga yau bazan sake ba faɗo maki cikin toilet ba,” yakai ƙarshen maganar a yayin da ya ajiye bokitin ƙasa, ya ɗago idonshi Yana kallon Tagar da angel ke ƙoƙarin fasawa,
Zaro idanuwanta ta yi ganin yana kallon glass window ɗin da alama yaga abunda take Yi, muryarta na kerma tace”Nasan kaga abunda nake kokarin yi, So nake in fasa gilashin tagar nan, Saboda Ina da matsalar kwakwalwa, Tun lokacin da ina agidan daddyna kafin zuwana kurkukun nan, Na fasa gilassai bila adadin saboda Ni idan nayi tozali da gilas tsoro Yake bani, kuma hakan yana jaza mini matsala, Likita ma yace Idan ina yawan zama inda ke akwai glass zan Iya mutuwa” angel sarkin wayau, idanuwanta cike tab da kwalla takai karshen maganar, hada marairaice mishi fuska don Yaji tausayinta, ya kuma yarda da maganarta,
Danish bai kawo komai aranshi ba, har cikin zuciyarshi ya yarda da kalamanta, matsawa yayi kusa da ita, Ya sanya hannayenshi biyu ya tallabo fuskarta, Idanuwan su acikin na juna, Cikin sigar lallashi yace”Am sorry angel, don’t cry pls, da kin faɗa mini tuntuni da na jima da sauke miki gilashin,” ta6e baki tayi tare da cewa”Ae bazaka Iya ba, ko Ni nasha gwada cirewa amma na kasa, kullum saina sha wahalar,” ta fadi hakanne don tasan Cewa danish bazai Iya ba, ita kanta da take da ƙarfi ta jaraba ta kasa balle shi da yake sai a hankali ba ƙoshin lafiya ba,
“xan jaraba in gani idan zan iya,” yakai karshen maganar yana tattara hannun rigarshi, da sauri angel ta ɗauko mashi bokitin ta miƙa mashi, bakinta ƙumshe da dariya So take yasha wahala kamar yarda ta sha, Shima Yaji ajikinshi,
Girgiza mata kai yayi”bana buƙatar yin amfani da bucket, I will use my hands” dariyar rainin wayau angel tayi mashi”wlh bazaka Iya ba, Da hannu fa ka ce, haba dai, kai dai ka kar6i Bokitin inga iya ƙarfin ka,” Bai saurareta ba, Ya tunkari Glass window din, Da yake Allah yayi shi da tsawo, Yafi angel tsayi ba sai yasha Wahalar yin tsalle ba kamar yarda take yi, Agaban tagar ya tsaya yana kallonta,
Angel ta ruƙe qugu, Tana jiran ganin Ikon Allah, Fuskarta ɗauke da dariyar mugunta,
hannayen shi biyu ya sanya yana shafa Jikin glass ɗin da ya yi uwar ƙura, ƙasan glass ɗin Ya ruƙo da yatsunshi, Ƙura ido angel tayi ganin glass ɗin kamar ya fara motsi, Gabanta ne ya faɗi ganin Danish ya daddage Ya 6a66ako glass ɗin tun daga tushen shi can cikin ginin dutsen da aka zura shi, Haka ya zaƙulo shi gaba ɗaya ya curo faskeken glass ɗin, Tashin hankalin da ba’a sama shi date,
Kanta Ya gama ɗaurewa, Ta zazzaro idanuwanta waje, kwayar idon kamar zata faɗo ƙasa saboda tsabar mamaki, Gaba daya tabi ta ruɗe ta rikice, Tarasa bakin magana sai bin shi da ido take yi kamar wadda aka dasa ma Aya,
A ƙasa Ya jingine glass ɗin Jikin bango, Ya ɗago yana kakka6e tafin Hannayenshi da ƙura ta buɗe su, A wani slow Ya juya bayan shi Yana kallon angel dake atsaye Ko motsi bata Yi, Ta ƙame kamar abun bautar ƙasar india wato kirishna,
Cikin sanyin mirya ya ambaci sunanta”Angel”? Shiru bata amsa mashi ba, domin kuwa sam bata acikin hayyacinta, matsawa yayi kusa da ita, Ya sanya hannayenshi biyu ya dafa kafaɗunta,
“Meke faru ne? Maimakon inga farin Ciki akan fuskarki, Ko baki ji daɗi bane? Na sauke maki glass ɗin, daga yanzu kin daina shan wahalar bugun shi da bokiti” shi kaɗai yake ta maganarshi, kwata kwata bata a hayyacinta, hura mata iska Yayi asaman fuskarta da bakinshi, Amma ƴar tahalikar nan ko ƙyata idonta bata yi ba, Janyota yayi zuwa jikinshi Ya kwantar da kanta saman chest ɗinshi, Ya sanya hannunshi abayanta yana shafa sumar kanta, kafin ya matso da lips ɗinshi saitin kunnanta yayi mata raɗa”angel, faɗa mini meya faru? Ko kina so in kawar da glass ɗin daga Cikin toilet ɗin gaba ɗaya, yadda bazaki sake ganin shi ba? Jin taƙi yi mishi magana, ya raba jikin shi daga nata, Ya nufi gaban fanfo Ya kunna ruwa ya ɗebo a tafin hannunshi, Ya dawo inda take atsaye kamar gunki, Ya watsa mata ruwan saman fuskarta, Nan take Taja dogon numfashi, har wani zabura tayi ganin shi agabanta, a ruɗe ta wurga idanuwanta kan tagar, Tayi tsammanin ko mafarki take Yi, amma sai taga akasin Hakan dagaske dai Danish Ya cire Glass ɗin tagar da take ta shan wahalar son fasa shi, Tsawon kwanaki, Lamarin Yayi matuƙar ɗaure mata kai, yadda har ya iya 6a66ako shi tun daga tushen shi ya zaro shi, Wanda Tayi imanin Babu wani mahaluƙin da zai Iyayin wannan aikin hakanan siddan ragadan batare da Akwai wani shiri atare da shi ba, Tsohon ginine fa kuma na dutse, A yanayin fuskarta baka iya gane halin da take Ciki, Ta yi farin Ciki da cire glass din da Danish Yayi ko kuwa batayi ba? Tabbas tayi fari ciki mara misaltuwa sai dai mamaki Ya hana ta nuna wannan farin Ciki, Ayanzu ta ƙara zargin cewa danish Ba shi kaɗai bane, Kuma ba wani ke sarrafa shi ba, tunda da ace wani ke sarrafa shi da baza a bari Ya cire glass ɗin nan ba, ganin irin kallon da take Yi mashi ne yasa shi ruƙo hannunta acikin nashi yace”Angel baki bani amsa ba, kina so in kawar da glass ɗin daga Cikin toilet din”? kamar wata sakarya haka take binshi da ido, sai da ya sake maimaita maganar tukunna ta iya bashi amsa da cewa”Inaso ka maida shi yadda ka ciro shi, Kaga duk lokacin dana shigo cikin toilet ɗin sai in zaro shi in kawar dashi wani wurin yadda bazai iya yin affecting ɗina ba” amsa mata yayi da toh, Ya juyawa ya nufi inda ya ajiye glass ɗin Ya ruƙo shi ya shiga kiciniyar mayar dashi, Bayan Ya kammala Ya juyo yana kallonta a lokacin Ta juya baya tare da ranƙwafawa Ta ruƙo hannun fitilar da tazo da ita, ɗagowa tayi suka haɗa ido da shi, Daƙyar ta ƙaƙaro murmushi tasakar mishi, muryarta na rawa tace
“Nagode sosai danish, you’re so kind, ka damu dani kuma kana bani kulawa, miƙa mashi hannunta tayi”Zo mu koma ɗaki mu kwanta, Dare yayi sosai,” ƙarasawa danish yayi inda take atsaye ya zura hannunshi acikin nata, ta ruƙe sosai tana faɗin”pls keep it under wraps, saboda bana so kowa Yasan cewa Mun cire glass ɗin nan kaga tsohuwa za ta yi mana faɗa idan taji awurin wani, koba haka ba” ɗaga mata kai yayi alamar eh, tare da cewa”I will zip my lips, daga ni sai ke,” Cike da jin daɗi tace”Mu biyu kaɗai muka sani, Idan naji maganar awurin wani To kaine, duk da nasan bazaka faɗa ma kowa ba,” Ba ƙaramin daɗi danish yaji ba ganin yadda take ta fara’a saboda Ya cire mata gilashin dake Sanya mata jin tsoro, yayin da ita kuma angel ɗin Shine abun tsoro awurinta, don kuwa ga dukkan alamu Akwai wani abun al’ajabi attare dashi,
Kusan atare suka duro da ƙafafuwansu Cikin ɗakin nasu, Adai dai Lokacin kunnuwansu suka soma Jiyo musu motsin buɗe ƙopar ɗakinsu, Mamaki ƙarara akan fuskarsu suka kai idanuwansu saitin benan dake a ɗakin, daga saman matattakalar benan suka Fara kallon ƙafafuwan Mutun Uku dake saukowa, masu sanye da jajayen Uniform, daga bayansu Kuma Giants ne Hannayensu a ruƙe Da Kayan abinci……shin su wanene?
*❤❤❤PRISONERS❤❤❤*
Tun daga ƙasa har sama su Angel ke binsu da kallo, Yayin da giants suka Wuce Cikin ɗakin zuwa Inda Dining carpet ɗinsu Yake, Bayan sun ajiye masu dinner ɗinsu, Batare da 6ata lokaci ba, Suka fuce daga Cikin ɗakin,
Atare Suka kalli juna ita da danish fuskokin su da alamaun mamaki, ga dukkan alamu basu gane su wanene ba, duk sunyi tsammanin Ko sabbin ɗauka ne aka kawo musu acikin kurkukun,
“Danish su wanene ko ka gane su”? Girgixa mata kai Yayi alamar a’a, Jan hannunshi Tayi”muje mu gani,” Tayi gaba Yabi Bayanta, Suna ƙarasowa bakin benan Inda suke atsaye, Ta haska fuskokinsu da fitilar Hannunta, Ras taji gabanta ya faɗi, da ƙarfi ta ambaci sunayensu”PARVEEN! RUBINA! DEEJA” sai da ta kira sunayen su Tukunna danish Ya gane cewa sune, Sunyi matuƙar girgiza da yanayin da suka Yi tozali da ƴan uwan nasu, Sam sun kasa Yi masu magana, Fatar Jikinsu Tayi haske sosai, Fuskarsu tayi jawur abunka ga farar fata, Idanuwansu duk sun kumbra suntum ga dukkan alamu ba ƙaramin kuka su kayi ba, Kayan jikinsu sun yi uban squeezing Kamar waɗanda aka kwato daga Bakin kura, Sumar Kansu Kuwa Ta hargitse ta fita hayyacinta, kai kace sabbin mahaukata ne, Kwata kwata babu natsuwa atare dasu, Yatsun hannayensu dana ƙafafuwansu sae kerma suke Yi, kamar waɗanda sanyi yayi ma mugun kamu, Tsabar ruɗu Ya hana Angel da danish su furta wani abu, Duk irin Zumuɗin da suke Yi nasan adawo musu Da ƴan uwansu Jikinsu Yayi laƙwas, domin kuwa ba haka suka tsammaci ganinsu ba, wani tashin hankalin ma La66ansu dake a bushe sun faffashe, hada busasshen jini ajikinsu,
Muryar angel cikin damuwa ta ambaci “Innalallahi wa’inna ilaihirraji”un! Parveen! Deeja! Rubina! Meya faru daku? Meyasa kuka canza har haka? Dan Allah kuyi mini magana, Me akayi maku? Duk kun canza kun rame kun fita hayyacin ku,” Idanuwanta acike tab da kwalla ta yi maganar, hawaye ne masu ɗumi suka soma gangarowa akan fuskokinsu, Lokaci ɗaya suka fashe da matsanancin kuka mai tsuma Zuciya, hankalinsu danish Yayi matuƙar tashi, Koke koken Da suke Yi ne Ya yi silar farkawar su Batool, har cikin kunnuwansu sautin kukansu parveen ke kai musu, Aikuwa Jiki na rawa suka Yaye bargunan da suka lullu6a dashi, Da gudun gaske Suka nufi wurin su ɗaya bayan ɗaya suka ƙaraso bakin stairs ɗin banda mutun ɗaya, Azeeza dake fama da lalurar makarantar dare, Ta farka daga bacci amma bazata Iya kawo kanta inda suke ba,
Koda su Batool Suka ɗaura idanuwansu akan fuskokinsu Parveen, wani irin farin Ciki ne Ya bayyana akan fuskokinsu, Sam basu Lura da yanayin da suke Ciki ba, Saboda tsabar murna Batool ta cakumo deeja da niyar ta rungumeta aikuwa Ta fasa wata irin gigitacciyar ƙara, wadda tayi matuƙar girgizasu, da sauri Danish ya sanya hannayenshi Saman Ears ɗinshi Ya toshe su gudun kada lalurar shi ta motsa, aruɗe suka haɗa baki suna tambayar lafiya meya faru dasu? Meyasa su ke Kuka? maimakon suga farin Ciki akan fuskokinsu,
Muryar batool a sanyaye tace”deeja meyasa kika saki ƙara saboda ina ƙoƙarin Rungumarki ajikina? Ba ku yi farin Ciki da dawowa Cikin Mu bane”? shiru babu wanda ya amsa mata acikinsu sai kuka suke Yi, Yasmin tace”Na lura gaba ɗaya ma basa acikin hayyacinsu zaiyi wuya ace sun gane mu” javed yace”pls Stop shedding ur tears kuna ƙara tayar mana da hankali, meyasa duk kuka canza? Tsohuwa ta faɗa mana cewa kuna acikin ƙoshin lafiya, Har ma tace mana kuna kewarmu, amma sai gashi Yadda muka ganku a yanzu ba haka mukayi tsammani ba, why pls”? Zuciyarshi a hautsine ya ƙarasa maganar,
“Angel Ki yi mana bayani? Yaushe aka dawo dasu? Meyasa kuma basa Iya magana” Cikin shessheƙar kuka Batool Ta jefa mata tambayar, Itama angel ɗin kukan take Yi, daƙyar ta iya tsagaitawa ta bata amsa da cewa”Kamar yarda kuka gansu haka muma muka gansu, Giants ne suka shigo tare dasu, Hada abincin ma suka kawo mana gashi can sun ajiye farantan saman dining carpet, Dukkan mu mun shiga ruɗanin halin da muka riskesu, Ko magana ma sunƙi yi mana”
Matsawa haris yayi tare da kai hannu Ya ruƙo yatsun hannun Rubina, afirgice ta zame hannunta daga nashi, ta runtse idanuwanta tana faɗin”Zafi nake ji ku daina ta6ani bana so, Ku ƙyale ni ku rabu dani, bana son ganinku” lallashinta hannah tayi”Shikenan tunda bakya so ba zamu ƙara ta6aki ba, Kiyi shiru kinji” Tayi maganar tana leƙen fuskarta,
Angel tace”Ni dama nasan za’a rina, Mutanan nan raina mana wayau suke yi, Tsohuwa tayi mana ƙaryar cewa An kaisu treatment room inda za’a duba lafiyarsu, tsawon 2 weeks kenan, Ga shi yau an dawo dasu babu alamun sauƙi ajikin su, ga dukkan alamu ma wani sabon Ciwon aka jaza musu ” rai amatuƙar 6ace angel tayi maganar tana huci, Mubeen yace”pls Mubi komai a hankali, ko dan saboda su Deeja, Ni inaga yakamata aje a sanarma tsohuwa tazo ta duba halin da suke aciki….”tun kafin mubeen yakai karshen maganar shi angel ta wurga mashi uwar harara, kamar zata rufe shi da bugu tace”Amma baka da hankali wlh, wai har yaushe ne zaku fahimci cewa matar nan Muguwace ba sonki take Yi ba, Kuma babbar maƙaryaciya ce! Tayi mana ƙaryar cewa A cikin satin da aka ɗauki su parveen za’a dawo dasu, Sai gashi yau tsawon 2 weeks kenan, Sannan bayan haka ta sanar damu cewa Su parveen sun samu lafiya harma suna tambayarmu, To yau gashi dai an dawo dasu Ba kamar yarda aka ɗauke su ba, kwata kwata babu cikakkiyar lafiya atare da su, ku baku lura da canzawar da su kayi bane? Muryarta a harzuƙe tayi maganar, Jijiyoyin wuyanta duk sun bayyana jikin fatarta saboda tsabar masifa, Kowa yayi shiru yana sauraronta, Cigaba da magana tayi”Kun maida kanku kamar gumaka, Ana cutarku baku ganewa, Yanzu ku kalli fuskokinsu deeja da la66ansu, wlh ko makaho ya shafa jikinsu sai yaji ajikinshi cewa basu da ƙoshin lafiya, Balle ku da kuke Mutane, Su parveen ba Maganin ciwonsu akayi musu ba, Ƙara musu wani ciwon akayi bisa wanda suke dashi”
Wannan bayanin Da angel ta kora musu Yasa sun fara Kokwanton Kalaman tsohuwa, Sun kuma fara yarda da ita,
Muryar hibba asanyaye tace”angel ae mu bamu san komai ba, Rayuwa kawai muke Yi acikin duhu, ba lallai mu iya fahimtarki ba,” Haris Yace”Tun da kike atare damu ban ta6a Yarda dake ba, Saboda ina zargin ke ɗin Kamar babu gaskiya acikin lamurranki, Yau ce rana ta farko Da kika fara sanya mini kokwanton wani abu acikin raina, Sai dai bazan ta6a Yarda dake ba har sai kin bani kwakkwaran Hujja da zata tabbatar mani cewa Cutar da rayuwarmu ake Yi,’ haris na kai karshen maganar shi, Batool tace”Muna goyan bayan haris, Idan har dagaske Ana Cutarmu a gidan kurkukun nan, To kiyi ƙoƙari ki bayyanar mana da kwakkwarar hujjar da zamu aminta dake, Ɗaya bayan ɗaya Angel ke binsu da kallo, wai wace irin hujja ce suke so Ta kawo musu? Bayan ga abu nan zahiri sun gani, acikin zuciyarta tayi tambayar, Tunawa da irin rayuwar da suka taso suna yi yasa ta Yi musu uziri, dole suna da ƙarancin fahimta, kansu Yana acikin duhun Jahilci, idan har bata lalubo hujjar da zasu Gasgata maganarta ba, to kuwa bazasu ta6a yarda da kalamanta ba, taya za’ae ta samo hujja bayan tsohuwa ta gargaɗe ta akan kada ta kuskura Tace zata Zurfafa bincike akan Gidan kurkukun, har ga Allah tana matuƙar fargabar Abunda zai biyo baya idan har tace zata Kawo musu hujja,
Sautin kukan Azeeza ne Ya jawo hankulansu, kusan atare suka Waiwaya baya suna kallonta, Har ta sauko daga saman gadonta, Sai faman laluban hanya take Yi tana faɗin” Wai bakowa ne akusa, Ni baza’a nuna mini su parveenar mu ba, dagaske an dawo mana dasu? Ina ta magana tun ɗazu babu mai ji na,”
Kallon Naufal Haris yayi tare da cewa”Kaje ka ruƙo ta kada ta faɗi” Naufal ya amsa mashi da toh, Da hanzari Ya tunkari parveen, Yana ƙarasawa gabanta, Ya ruƙo hannunta acikin nashi, Ya janyota zuwa inda suke abakin benan, “to ina su parveenar suke Ae ban ganinsu” Tsoki Haris Ya ɗan ja”kefa matsalarki kenan abu kaɗan sai kuka, Kamar kinfi kowa baki, Ki barmu muji da abunda Ya ishe mu,” a ƙule yayi maganar, cikin sanyin murya danish yace”haris ka bi ta a hankali, banaso kana yi mata magana irin haka” jinjina kai haris yayi tare da cewa na daina, kawai bana son yawan kukanta ne,”
“Ni dai ku nuna mini Su, kuma kuka bazan daina ba, Yanzu na fara sai dai ka buge ni” rai a6ace azeeza tayi maganar, mutumin dake fama da kanshi, kwata kwata bata iya ganin fuskokinsu, Biji biji take gani,
Matsar da ita naufal Yayi zuwa gabansu deeja da suka ƙame Sai shessheƙar kuka suke yi, ko gajiya basa yi,
“Gasu nan Agabanki Kiyi musu magana” naufal ne yae maganar, Hannayenta ta ɗaura asaman kirjin deeja tana shafata, Harta samu ta ruƙo hannunta ta ɗago shi zuwa saitin hancinta ta shinshina shi, duk suna kallonta, farin Ciki ne ya bayyana akan fuskarta, rungumeta tayi tana faɗin”Deeja Ashe kune dagaske, Nayi farin Ciki da aka dawo mana da ku, yanzu shikenan kunji sauƙi baza’a ƙara raba mu daku ba, Ni dai na roƙe ku kada ku ƙara Yin rashin lafiya, Kodan saboda kada araba mu daku, Saboda bamu jin daɗin rashin ganinku acikinmu” ita kaɗai take ta sambatunta, Javed ya kira sunanta”Azeeza Kiyi hakuri ki ƙyaleta, Basu son ana ta6a su, Har yanzu da sauran Jikin nasu” Cikin shessheƙar kuka tace”meyasa toh basu son ana ta6a su? Basuyi farin Ciki da dawowa Cikin mu bane? Duk irin kewarsu da muka Yi,” babu alamun zata fahimce su, angel ce tace”Javed ka barta, tun da naga yanzu Deeja bata Yi ƙara ba kamar yarda tayi ɗazu da batool ta ruƙota,” Eve tace”Nima na lura da hakan”
“Nidai kuyi mini magana, Wai sai kace baku Ji na, ko fushi kuke Yi damu ne”? matsawa tayi gaban Rubina Ta ruƙo hannayenta takaisu saitin hancinta ta shinshinasu, kafin ta faɗa jikinta ta rungumeta tana faɗin rubina, Kema bazaki Yi mini magana ba? Duk kun shareni,” jin shiru bata amsa mata ba, yasa ta janye jikinta daga na rubuna, da alama Jikinta yayi sanyi, Ruƙo hannun Parveen Tayi, batare data shinshina shi ba tace”parveen, Ke ma ba za kiyi mini magana ba? Meyasa bakwa farin ciki da dawowarku Cikinmu ne? Duk irin kewarku damu kayi, Munji raɗaɗin rashinku acikinmu, Tun ranar da Giants suka zo suka tafi daku, Kusan kullum ne sai Mun ajiye maku abinci, amma abanza yake lalacewa, mun yi maraicinku sosai” takai kai karshen maganar tare da ɗaura kanta saman kirjin parveen, hada ƙoƙarin zagayo da hannayenta zuwa bayan parveen ta ƙanƙameta,
“Yanzu ya zamuyi da su? nifa nagaji da tsayuwa ƙafafuwana har sun fara Yi mini zogi, Yakamata Mu koma Cikin ɗaki Mu xauna, yasmin ce tayi maganar,
Kallonsu Deeja Angel ta yi tare da cewa”Ku zo mu shiga Cikin ɗaki, Nasan Kuma kun gaji da tsayuwa” pls ku wuce mu tafi dare yayi sosai” ta karasa maganar tare da nuna musu Hanya, sai lokacin deeja ta iya buɗe baki tace dasu”Ni bazan Iya tafiya ba, ƙafafuwana zafi suke Yi mini,” Kallon Juna su ka yi, Hatta muryarta ta canza, kamar ba deeja da suka sani ba, Muryar parveen na rawa tace”Nima Bazan Iya tafiya ba, raɗaɗi nake Ji,” daƙyar tayi maganar saboda raɗaɗin da bakinta ke Yi mata, wanda shi ya hana su yin magana tun ɗazu amma duk suna jin me suke cewa kuma suna fahimta,
Rubina tace”nima bazan Iya ba,” lamarin yayi matuƙar ɗaure musu kai, Haris yace abunda za’ae yanzu, Zan Goya deeja abayana, danish ka goya rubina ita kuma angel ta goya parveen kai kuma naufal Ka taimaka Ma Azeeza ku shigo ciki, Zuƙunnawa su ka yi agabansu Deeja, Suka haye saman bayansu, Atare suka miƙe suka nufi Cikin ɗakin dasu, Sauran ƴan uwan nasu duk suna abiye dasu, A saman gadajensu suka sauke su, angel ta tambayesu ko suna jin yunwa, suka ce mata a’a, bacci suke so suyi sun gaji,” acikin zuciyarta ta kudiri aniyar idan Suka farka gobe zata Tambaye su game da abunda ya faru dasu, duk da tasan zaiyi wuya su iya tunawa,
Basu kwanta bacci ba har sai da suka Ci abincin da giants suka kawo musu, bayan sun kammala ci suka koma saman gadajensu suka kwanta zuciyar kowannan su acukunshe take Da tunanin halin da suka riski ƴan uwansu,
A daren ranar bayan kowa Ya koma saman gadonshi Ya kwanta, Angel tabi su ɗaya bayan ɗaya Ta tottofe su da addu’a, Ta lullu6e musu jikinsu da bargunansu, Wani abu daya ƙara ɗaure mata kai, A lokacin harta koma saman gadonta ta zauna ta ɗaga hannayenta sama tana Yin addu’o’i kamar yadda ta saba, Kwatsam Taji shessheƙar kukan Deeja, ga dukkan alamu mafarki take Yi, da hanzari angel ta sauko daga saman gadonta taje bakin gadon deeja ta ɗan ranƙwafa tare da kasa kunne tana sauraron me take cewa, Kuka take Yi tana faɗin bana so ku daina kuna cutar dani, zafi nake ji, kashe ni kuke Yi, Ni ku ƙyaleni ku rabu dani” Ciccije la66ata tayi tare da kai hannayenta saman mattress ɗinta tana damkar jikin katifar, Idanuwanta na fitar da ruwan hawaye, Can kuma sai taga deeja ta kai hannu tana sosa gaban wandonta, tana faɗin ƙaiƙayi take ji, zafi yake yi mata, mutuwa zatayi,” Daga bisani ne Deeja tadaina sambatun da take Yi, taci gaba da yin baccinta
Haƙika angel tayi matuƙar girgiza duk da bata Iya gano komai game da sambatun deeja ba, amma Jikinta yayi mugun yin sanyi, tabbas tana hasashen An yi masu wani mugun abunne kuma agabansu a Kayi musu, tun da gashi nan ta gani da idonta deeja na sosa wurin tana faɗin cewa ƙaiƙayi yake Yi mata,
Ikon Allah kenan, An juya musu tunaninsu don kada su Iya tuna komai Da akayi musu, Amma sai gashi Allah Ya haska mata wani abu ta cikin mafarkin da deeja ta yi, yanzu ya rage nata tayi ƙoƙari ta gano me akayi musu,
Kasa kwanciya tayi Domin kuwa baccin ya qauracewa idanuwanta, damuwa ce cunkushe acikin zuciyarta, safa da marwa ta shiga Yi acikin ɗakin yayin da zuciyarta ke tariyo mata abubuwan da suka faru ɗazu, na farko tana so Ta yi bincike akan danish, Taya akai yake Iya shiga cikin wurin dake a kulle, 6acewa yake Yi ne ko kuwa bango yake ratsawa ya shigo? Dole ne ɗaya ya kasance Cikin Biyun nan, Bayan wannan Kuma Ta yi matuƙar girgiza lokacin daya shafa glass Ya ruƙo ƙasan shi Ya 6a66ako shi tun daga tushen shi, to wai shi ɗin Aljani ne Ko mutun? Ko kuwa shigarshi A kayi? Ta rasa gane dawa zata Yarda,
Lokaci ɗaya kuma Ta fara tunanin meyasa Uniform ɗinsu Ya banbanta dana sauran ƴan uwansu? Su Uku ita da danish da batool su kaɗai suke da baƙaƙen Kaya, Yayin da Su Azeeza nasu Uniform ɗin Jajaye ne dukansu, Tabbas akwai dalilin dayasa aka Banbanta masu launin uniform ɗinsu, don me nasu zai kasance launi ɗaya dana GIANTS? Ta sanya alamar tambaya, ranta ne ya bata cewar bazata ta6a Iya gano menene atattare da danish ba, Har sai ta fara gano Dalilin banbance Uniform ɗinsu dana sauran Ƴan uwansu prisoners!!!
Nauyayiyar Azuciyar zuciya ta sauke, saboda yawan tunanin da take Yi da sanya damuwa aranta, Zuciyarta har wani nauyi take Yi mata a ƙirjinta, ita kanta tarasa Ya zatayi wurin rage ɗaura ma kanta damuwa akan hakan Ya faska,
Canza akalar tunanin nata Ta yi zuwa gasu Parveen, a yayin da take Cigaba da yin zirga zirga acikin ɗakin nasu, Tana zargin ana cutar dasu ne sai dai takasa gane wata irin cutarwa ce a ke yi musu, Ɗaukarsu da ake da sunan za’a je a duba lafiyarsu, Ga dukkan alamu Ba Lafiyarsu ake dubawa ba, Wani ciwon ake ƙara Danƙara musu ajikinsu, Shiyasa idan aka ɗaukesu daga Cikinsu Ba’a barinsu Cikin hayyacin su, har sai time da aka dawo da su, Tun akan danish ta lura da hakan, sannan kuma Lokacin da giants suka Shigo cikin ɗakin nasu atare da su parveen, da ƙafafuwansu suka tako, Amma daga baya suka ce baza su Iya tafiya ba, Hakan na nufin adai dai lokacin da suka sauke ƙafafuwansu acikin ɗakin daga nan sihirin da akayi musu ajikinsu Ya warware, Suka dawo hayyacinsu har suka gaza taƙa ƙafafuwansu,’
Jinjina kai angel ta yi a fili tace”Sannu ahankali zan binciko koma menene, babu fashi domin kuwa Alwashi ne na ɗaukarwa kaina Koda Kuwa zan rasa raina saina gano uban me ake aikatawa A Gidan kurkukun ƙaddara,!
Komawa tayi saman gadonta ta kwanta, tare da jan bargo ta lullu6e jikinta, Cikin ƙanƙanin Lokaci Bacci yayi awon gaba da ita,
A washe garin ranar, babu wanda Ya farka daga bacci acikinsu, Saboda daren jiya basu kwanta da wuri ba,
A firgice ta farka sakamakon sautin shessheƙar kukan parveen daya karaɗe kunnuwanta, ware manyan idanuwanta tayi tare da kai hannu ta zame bargon jikinta, Saukowa tayi daga saman gadon ta nufi gadon parveen a zaune ta same ta tsakiyar gadon, fuskarta ta ƙara kumbura sumar kanta duk ta hargitse, Jikinta hada zufa,
Da sauri ta ƙarasa daga gefen gadon ta zaune, tare da kallon fuskar parveen tace”Sister are u ok? Why are u crying? Ko jikin ne”? Daƙyar parveen ta ɗago ta kalli Cikin idanuwan angel, batare da tace komai ba, angel ta kuma cewa”Dan Allah ki faɗa mini meyasa ki kuka? May be Ina da abunda zan iya taimaka maki” cikin nuna damuwa tayi maganar, muryar parveen a disashe tace”bana Jin daɗin Jikina, ƙaiƙayi nake ji, kuma ina so Inyi wanka amma na kasa miƙewa saboda bazan Iya tafiya ba, wahala nake sha” tsananin tausayinta ne ya kama angel, Cikin muryar lallashi tace”shikenan ki daina kuka, kada wannan ya dame ki, Ni zan Iya yi maki komai, Yanzu zan Goya ki in kaiki toilet, idan ma kina so har wankan sai inyi maki”
“Nagode sosai Angel,” saukowa Angel tayi daga saman gadon nata, ta juya tare da zuƙunnawa tace da parveen ta hau bayanta, Matsawo Parveen Tayi ta lalla6a ta haye bayan Angel, hannayenta ta sanya ta ruƙe parveen, Ta daddage ta miƙe ta wuce toilet ɗauke da ita abayanta, Shigarsu toilet keda Wuya acan Cikin ɗakin Deeja da Rubina suka farka da wani irin sautin kuka mai razanarwa, Duk wani mai bacci saida Ya farka sakamakon Kukan nasu daya karaɗe Cikin ɗakin,
Jiki na 6ari suka sassauko daga saman gadajensu, Banda Danish Yana kishingiɗe saman gadonshi, Ya farka amma bai buɗe idanuwanshi ba, da alama baccin bai ishe shi ba, ko kuma tsiwar tasu ce ta addabe shi,
Agaban Gadon deeja Haris da Batool, da hibba hada hanna Suka tsaitsaya suna kallonta Fuskokinsu ɗauke da damuwa,
Su javed da sauran ƴan uwan nasu suna a zuƙunne gaban gadon Rubina,
Duk sun ƙanƙame Jikinsu Dake ta kerma, Sun rasa gane masu, gaba ɗaya sun canza, xama batool tayi daga gefen gadon Deeja, muryarta a sanyaye tace”Deeja, Meya ke faru dake ne? Jikin ki Yana yi maki ciwo ne? Ɗaga mata kai ta yi alamar eh, Haris yace”Ni narasa gane wannan ciwon naku, ance Ana baku treatment amma ya akaiba wani sauƙi atattare daku? Kun wani fige kun fita hayyacin ku,” aruɗe yakai karshen maganar, Hanna tace”Deeja zaki Iya faɗa mana inda aka kai ku? Da kuma abunda aka Yi maku? Girgiza kai deeja tayi har lokacin hawaye basu daina zuba kan fuskarta ba,
“Bazan Iya tuna komai ba, tun lokacin da aka ɗauke Ni daga Cikin ku, sai Jiya da aka dawo dani Tukunna Na Iya tuna wacece Ni!” Kaitsaye maganar deeja taje kunnan Angel dake Kokarin Fitowa daga sashen toilet ɗinsu, Bayanta ɗauke da parveen data goyo, ta taimaka mata tayi wanka hada sumar kanta ta wanke mata, Kasa Cigaba da tafiya tayi, ta kasa kunne tana sauraronsu
Hibba tace”Abun da ɗaure kai, Ni fa gani nake kamar an ƙara musu Ciwon ma, To inba haka ba Kallarsu fa ku gani, sati biyu da suka wuce kafin azo a ɗauke su daga Cikin mu, Da ƙibarsu jikinsu da auki amma Yanzu Kamar an ɗibi naman jikinsu,” Kowa fa ya fara Kokwanton wani abu aranshi, Hakan ba ƙaramin daɗi Yayi ma angel ba, saboda sun fara tunani na hankali,
Jin muryoyinsu javed dake a zuƙunne gaban Gadon Rubina. yasa takai idonta kansu, Ta kasa kunne don taji su me suke tattaunawa
“Rubina Acan inda aka kai ku suna baku abinci? Naga duk kun rame kamar akwai Yunwa attatare daku, Sa’an nan Ya akai la66anku suka faffashe wani Ya cije ku ne? Eve ce tayi mata tambayar. idanuwan rubina cike tab da kwalla tace”A’a ni bazan Iya tuna komai ba, ku daina Yi mini tambayoyi dangane da inda aka kaini saboda bansani ba ni kaina” Mamaki ne ya kamasu, Jin tace batasan komai ba, yasmin tace”Nayi matuƙar damuwa da hankalin da kuke Ciki, bamu yi tsammanin Zamu ganku haka ba a wulaƙance, kwata kwata Jikinku babu alamun sauƙi, saima abunda yayi gaba, Gaskiya nidai ban yarda da wannan treatment room ɗin ba, Yakamata mu yi ma tsohuwa magana, idan wani bai da lafiya acikinmu kada a ɗaukar mana shi, abar mana shi acikinmu muyi jinyarshi”
Naufal yace”Wai Ina parveen ne? Naga babu ita asaman gadonta”? A hanzarce suka juya suna kallon Gadon Parveen,
Muryar angel ce ta janyo hankalinsu zura gareta,
“Gata nan abayana, Ta farka tana buƙatar Yin wanka shine na taimaka mata Tayi, Yakamata suma su deejan su yi wanka, Ko sunji daɗin Jikinsu” Ajiyar zuciya kowannan su ya sauke, Wuce wa angel tayi zuwa cikin ɗakin Abakin Gadon parveen Ta ɗan rankwafa tare da kwantar da ita saman mattress ɗin, Da gudu Azeeza ta nufo gadon parveen ta haye gefenta, fuskarta ɗauke da murmushi tace”Ƴar uwa ya Jikin naki? Daƙyar parveen ta ƙaƙalo murmushi tare da cewa”Da sauƙi sister, Nayi missing dinku sosai Ƴan uwana, Ina abincin da nace ku ajiye mini”? Fuskarta aɗaure tayi maganar tana kallonsu,
Azeeza tace”Ki tambayi angel kiji, tun ranar da aka ɗauke Ku daga Cikin mu, Kullum sai mun ajiye maku abinci yana lalacewa, Har mun fidda rai da za’a dawo mana da ku ashe da rabon Mu sake sanya ku acikin idanuwanmu,” tana kai karshen maganar ta kifa kanta saman mattress tana kukan karya, murmushi parveen tasaki, tare da miƙa hannunta saman kan azeeza ta ruƙo kalabar da akayi mata,
“Azeeza wa yayi maki wannan”? ɗagowa azeeza tayi tare da kallon kalabarta da parveen ta ruƙe a hannunta tace”Angel ce tayi mini, kema in kina so sai tayi maki idan kika ji sauƙi”
“Batool da Hannah, Ku taimaka masu deeja suyi wanka, ” Angel ce tayi musu magana,
Batare da 6ata Lokaci ba, Batool Da Hanna suka Goya su deeja da rubina asaman bayansu, suka nufi toilet da su,
Ataƙaice Yau dai kusan Sati ɗaya da aka dawo dasu parveen, Jikinsu Yaƙi sauƙi Lafiya ta yi ƙaranci A jikinsu, basu Iya tafiya sai an taimaka musu, ko sunyi yunƙurin miƙewa da niyar su taka ƙafafuwansu Sai kaga ƙafar ta gurɗe, ko daga baya da suka fara Jin sauƙin jikinsu, sai tafiyarsu ta koma irin ta gwami, basu Iyayin tafiya lafiya lou batare da ƙafarsu ta gwame ba, Hankalinsu Batool Yaki kwanciya, Har zuwa bakin kopar ɗakin tsohuwa su kayi domin Su sanar da ita halin da ƴan uwansu suke aciki, Koda suka kwankwasa ƙopar ɗakin tsohuwa ta fito, Suka sanar da ita abunda ke faruwa dasu Parveen Na rashin Iya tafiyarsu, Sai cewa tayi su cigaba da basu kulawa, Zasu dawo dai dai, tana faɗi musu haka Ta juya ta koma ɗakinta tare da jan ƙopa ta rufe, Babu yadda suka Iya haka suka Cigaba da kulawa dasu, Idan zasu Yi wanka Dole sai An taimaka musu, Batool da angel sune ke ɗawainiya dasu, Hatta wankin Uniform ɗinsu sune suke Yi musu, Hakan ba ƙaramin daɗi yake yi musu ba, Hankalinsu Ya kwanta ganin irin soyayyar da ƴan uwansu ke nuna masu,
Da taimakon Allah, jikinsu Yayi sauƙi sosai suka koma yadda suke ada, Tafiyarsu ta dawo dai, Ranar Har wasa su batool suka yi saboda murnar samun sauƙin su deeja, Yanzu babu faɗa a tsakanin Deeja da angel sun daina ƙin junansu, Tun lokacin da aka dawo dasu, angel ta lura da irin canzawar da deeja ta yi, Bata jan kowa faɗa, babu ruwanta da kowa, Sai In ana wasa ne zaka ga ta sanya baki itama ayi da ita, hatta haris Yanzu sun samu jituwa atsakaninshi Da angel, Suna yin rayuwarsu Cikin so da ƙaunar juna, Tsawon kwanaki, Sun samu kwanciyar hankali,
A daren Wata rane ne, Angel Ta kawo masu shawarar su yi wasan Ƴar 6urun 6urun, ta gabatar musu da yarda zasuyi wasan, Gaba ɗayansu suka hallara atsakiyar ɗakinsu, mubeen Ne ya cire rigarshi Ya miƙa ma angel, ta kar6a ta ɗaurewa batool idanuwanta da rigar, Da gudu kowanansu Ya ruga zuwa ma6oyarsa, Wasu suka shige ƙarƙashin gado, wasu suka Nufi Cikin toilet suka 6oye, Hada wanda ya 6oye Ƙarkashin table ɗin da suke ɗaura fitilinsu, Batool taci gaba da bin hanya tana lalubensu tana fadin”6urun 6urun ku 6oye ku 6oye da nisa, Garin gudu ku faɗi ku gurje abanza, Kun 6oye” suka ce a’a, Kusan sau uku Tana tambayarsu sun 6oye sai suce a’a, Ana huɗun ne suka ce mata Eh sun 6oye, nemansu ta dinga Yi acikin dakin, Tarasa ina suka 6oye, ga shi sun ɗaure mata idanuwanta sosai bata Iya gani,
Angel da azeeza Suna a rungume da juna ƙarƙashin Gadon Batool ɗin, Sai tiƙar dariya suke Yi, Danish kuma Yana a karkashin gadonshi tare da parveen, Haris da deeja suna a Karkashin gadon angel, Naufal da Mubeen Sun 6oye kasan table, hanna da hibba hada javed suna a la6e Cikin toilet, kamar aljanu ko tsoro basa Ji, Su rubina da yasmin hada Eve, A jikin bango suka la6e, Don sunsan bazata iya gano su ba, tunda an kulle mata idanuwanta, Sai wahala take sha sunƙi bari ta kamasu, na cikin toilet ne Suka Ji motsi aikuwa gaba ɗaya suka watso da gudu waje cikin sa’a ta cafki wuyan rigar Javed, Ta dinga tsalle tana faɗin ta kama ta kama, Jin haka yasa sauran ƴan uwan nasu suka firfito daga ma6oyarsu, angel ta warware mata ɗaurin dake akan fuskarta, ta ɗaure ma Javed idanuwanshi, Da gudu kowa Ya rugo Zuwa wurin 6oyenshi, wannan karan Azeeza ta tona musu asiri, fitsari ya matse ta, tace ma angel ta rakata suje toilet tayi, angel tace mata ta jira akama wani acikinsu sai su fita, Aikuwa ta fashe mata da kuka tana faɗin ta taso su tafi ya matseta kada tayi shi awando , Maganar azeeza tayi matuƙar basu dariya, Javed najin muryoyinsu ya dinga laluban hanya Cikin sa’a Ya kamo rigar azeeza a lokacin ta fito daga karkashin gadon, ta buge mashi hannu tana fadin Ita fitsari take Ji, fitowa daga karkashin gadon angel tayi Tace da danish”Ya jira ta rakata tayo fitsarin, Idan suka dawo ita zata Yi wasan amadadin Azeeza” Yace mata toh , Bayan sunje toilet ɗin sun dawo, Sauran ƴan wasan duk suka fito daga wurin 6oyansu, Batool ta kar6i rigar hannun javed ta ɗaure ma angel idanuwanta sosai, wannan karan basu 6oye ba, Raina mata wayau suka dinga Yi suna zagayeta, daga ta miƙa hannu za ta cafkosu sai suyi sauri suja da baya, baƙaramar wahala tasha ba, Daƙyar ta samu ta ruƙo wandon Hibba, Ta dinga murna tana faɗin ta kama,
Daren Ranar Ba ƙaramin nishaɗi suka yi ba, Sai da dare ya ratsa tukunna suka kwanta domin Yin bacci,
A washe garin da su ka yi wasan ne ta farka fuskarta dauke da murmushi, ta miƙe zaune saman gadonta, Babu wanda ya tashi daga bacci sai ita, Saukowa tayi daga saman gadonta, da sauri ta nufi toilet, da niyar yin wanka, Tana shiga Ciki, taja kopa ta datse, Tsayawa tayi atsaye tana kallon glass din jikin tagar, abunda yasa har yau bata dura ta cikin windown ba, Saboda fargabar maganar da tsohuwa ta faɗa mata na cewa Zata ja musu bala’e, A yanzu bata son duk wani abu da zai tashi hankalinsu, tafi son su kasance Cikin farin Ciki, har zuwa lokacin da Allah Zai Taƙaita zamansu agidan kurkukun idan suna da rabon fita, idan kuma Anan ƙaddarar rayuwasa ta tsaya tana yi musu fatan da cewa,
Hannayenta ta sanya tare da kamo ƙasan rigarta, tana yunƙurin tu6e rigar, Hancinta ya shaƙo mata ƙarnin Jini, Nan take gabanta Yayi wani irin mugun bugu, A matuƙar ruɗe ta saki rigar ta fasa cireta, ta soma bin ko’ina na jikinta tana shinshinawa a ƙoƙarinta nata gano Inda ƙarnin jikin ke fitowa, Hatta wandonta saida ta ɗaga ta leƙe ciki don taga idan itama tafara Period ɗin, amma koda ta bincika bata ga Jinin ba, Sai da ta gama shan wahalar duba Jikinta a karshe idanuwanta suka sauka akan busasshen jinin dake a saman tafin hannunta, waro ido waje tayi tana kallon Jinin, tarasa a ina ta same shi, tun da ta duba ko’ina na jikinta bata ga ciwo ba, a kalla ta kwashe fiye da awa acikin toilet din Cikin yanayi na jin fargaba, Ta shiga ruɗani sosai,
Da gudun gaske ta fito daga Cikin toilet ɗin, bata nufi ko’ina ba sai bakin gadon azeeza, Saboda itace Jiya suka 6oye a karkashin gadon batool atare, Tabbas kuwa tana hasashen Jinin daga Jikinta yake, bubbuga ƙafar azeeza tayi da hannunta tare da ambaton sunanta”Azeeza”! Har cikin kunnan ta tajiyo kiran da angel ke yi mata, rai a6ace ta farka tana faman mutsustuke idanuwanta, muryarta adisashe tace”Wai lafiya? Wanene ke kirana, Hakanan mutun na yin baccin shi an wani katse mishi” angel na yunƙurin buɗe baki tayi mata magana tajiyo muryar hanna tana fadin”Nashiga Uku, Jini A jikina! Wanene Ya goga mini jini” afirgice angel ta juya tana kallon hannah dake zaune saman gadonta, Bata gama ruɗewa ba, Suka juyo muryar Eve tana fadin itama Jini ajikinta, hankalin fa angel yayi mugun tashi ganin kusan mutun huɗu acikinsu sun fara Jinin al’ada, da ace tana da halin da zata dakatar da jinin da tayi hakan saboda ta fuskanci ba ƙaramin barazana bane Yin Jinin Agidan kurkukun ƙaddara
Sai kuka suke ta Yi sunga Jini Ajikinsu, Da yake basu da ilmi akan Jinin, Ita kuma angel ɗin Tagaza buɗe baki tayi musu bayani saboda ruɗun da kwakwalwarta ta shiga, koke koken da suke Yi ne ya farkar da Batool daga bacci, aruɗe ta sauko daga saman gadonta tana tambayarsu lafiya koda itama tayi tozali da jinin daya 6ata wandonsu a firgice ta ɗaura hannayenta asaman kanta tana faɗin mun shiga uku, hibba Hanna yasmin Jinin menene ajikin ku? kodai Ciwo kukaji wurin Wasan Ƴar 6oyen da mukayi Jiya”? har suna haɗa baki wurin bata amsa da cewa”Suma basu sani ba, kawai sun farka sun ganshi ajikinsu ne,” Lamarin ya ɗaga musu hankali ba matan kaɗai ba, hatta mazan da suka farka daga bacci suka ga abunda ke faruwa da ƴan uwansu jikinsu duk Yayi sanyi, don sun san cewa huɗun ɗin nan duka xa’a zo akwashe su da sunan za’a bincika lafiyar jikinsu daga nan kuma su da ganinsu sai In Allah Ya nufa za’a dawo dasu Cikinsu, kafin su yanke shawarar zuwa su faɗa ma tsohuwa, sai ga giants sun shigo Cikin ɗakin wannan karan ba Su uku suka zo ba, wani iko na Allah Su huɗu suka shigo giants ɗin, Iya adadin marasa Lafiyan dake akwai, Abun ya basu mamaki matuƙa, ka rasa wake sanar dasu game da duk wani abu dake faru atsakaninsu,
Babu irin haukan da angel batayi musu ba akan bazasu Ɗaukar musu ƴan uwansu ba, Amma duk abanza, Ba ita kadai ba wannan karan hada su deeja suna kuka suna faɗin Kada su bari a ɗauki ƴan uwansu, Ba duba lafiyarsu xa’ayi ba ƙara musu Ciwon za’ayi, Wani abun ban tausayin ma. lokacin da giants suka ɗauki su Hanna, Suka nufi kopa zasu fita dasu, Da gudu Azeexa da batool da su deeja suka bi bayan giants abunda basu ta6a yunƙurin Yi ba, Aikuwa sunyi danasanin Binsu da sukayi da niyar su ƙwaci ƴan uwansu domin kuwa, Wurgi giants su kayi dasu, gaba ɗaya suka kife saman benan kansu Ya bugu sosai, Kuka hada majina, danish bai ta6a sanya kokwanto akan Giants ba, Sai yau da suka jefar da su Angel yaga rashin Imani tsantsa atattare dasu, kuma ranshi yayi mugun 6aci, zuciyarshi ta hasala, bashi kaɗai ba Hatta haris da naufal da mubeen Sun fusata sosai,
*❤❤❤PRISONERS❤❤❤*
Saboda tsabar buguwar da su ka yi, ga6o6in jikinsu sun jigata sosai, Angel tana yashe saman last step na benan, Azeeza da batool sun yi gefen dama atare aka wurgar dasu kamar kayan wanki, Deeja da Parveen da rubina suna ata 6angaren hagu, kowa Ya tarwatse, Sun yi kuka har sun gaji ga takaicin ƴan uwansu da aka tafi dasu ta ƙarfi da yaji, ga kuma takaicin wurgin da akayi dasu kamar wasu dabbobi marasa Ƴanci, ita angel ma hancinta har ya fara bleeding sakamakon bugun ƙasan da yayi, hakan ba ƙaramin tayar masu danish da hankali Ya yi ba, haris Yana zuƙunne gabansu azeeza dake a kwance ƙasa sunata kuka Yana lallashin su, Mubeen da naufal suna a 6angaren da aka wurgar dasu deeja, suna ta aikin lallashi,
Danish ke a zuƙunne Inda angel take kwance ƙasa, ya rasa ya zaiyi da ita saboda sautin kukanta dake neman hargitsa mishi lissafi, yana so ya lallashe Amma ya kasa, Yanke shawarar ɗaukarta yayi zuwa toilet don ya samu ya wanke mata fuskarta ko jinin ya daina zuba, Hannayenshi Ya sanya duka biyun Ya ruƙo waist ɗinta Ya ɗago da ita zuwa saman kafaɗarshi, Ya yunƙura ya miƙe ɗauke da ita Ya nufi sashen toilet ɗinsu,
A bakin fanfo Ya sauketa, Ta zuƙunna saman ƙafafuwanta, idanuwanta sunyi jawur launinsu Ya ciza sun koma kamar na zombie, hawaye duk sun wanke fuskarta sharkaf, Jikinta har kerma Yake yi, Giants bala’e ne, duk yadda suka ta6a mutun sai yaji jiki,
“Am sorry angel” ya furta hakan Yayin da idanuwanshi ke akan fuskarta, a raunace ta ɗago tana kallon shi without saying anything, ita kaɗai tasan Azabar da take ji ajikinta, Zuciyarta ta hasala, har wani tafarfasa take yi,
Janye idanuwanshi yayi daga kan fuskarta, Yakai hannu saman tap ɗin ya kunna shi, Ruwa ya soma kwararowa, Da tafin hannayenshi Ya dinga tarbo ruwan yana wanke mata fuskarta, Ba ƙaramin sanyi taji ba lokacin daya watsa mata ruwan a fuskarta, har saida ta lumshe idanuwanta, Bayan ya kammala Ya kashe tap ɗin, Ya ɗan juyo yana kallonta,
Cikin sanyin murya yace”zaki sha ruwa? Girgiza mashi kai tayi dakyar ta iya buɗe baki tace”bana jin ƙishi, wanka nake so In yi, U can wait for me out side,” amsa mata Yae da okey, kafin ya miƙe Ya fito daga Cikin toilet ɗin Ya tsaya Abakin ƙopar Yana jira ta kammala, lalla6awa tayi ta miƙe taje bakin ƙopar toilet ɗin ta datse ƙopar ta koma ciki, tsawon mintuna bata fara wankan ba, takaicin duniya ya isheta, tarasa ina zata tsoma ranta taji daɗi, yanzu shikenan an ɗauke su hanna? Suma za’aje a cutar da rayuwarsu kamar yarda aka cutar da su parveen, Ya salam, fashewa tayi da wani sabon kukan mai cin rai, Tana jiyo cool voice ɗin danish daga bakin door ɗin yana yi mata magana,
“Angel stop crying, its hurting me, idan ba haka zan shigo daga ciki,” tana Jin yace haka da sauri ta taja baki tayi shiru don tasa halin shi, Yanzu ya faɗo mata Cikin toilet, Miƙewa Tayi jiki duk ba ƙwari ta zame kayan jikinta ta ɗaura su saman igiya, Ta cika ruwa abokiti Ta soma Yin wankan,
Yana a tsaye Bakin door ɗin ya jingina bayanshi, fararen idanuwanshi na fuskantar ceilling, Yayin da zuciyar shi ta yi nisan kiwo Cikin tunanin Abunda Ya faru ɗazu Zuwansu Giants, tambayoyi ya shiga jefa ma kan shi wata irin lalura ce ke damunsu Hannah? Jinin menene Yake fita ajikinsu? And why tsohuwa bata nuna damuwa a kansu ba? Bakomai yafi ɗaure mashi kai ba, face yarda giants suka nuna rashin tausayi wurin yin wurgi dasu azeeza, don kawai suna ƙoƙarin hana atafi da ƴan uwansu,
Yayi zurfi acikin tunaninshi, kunnuwanshi suka soma Jiyo mashi muryar haris a kausashe yana magana daga Can Cikin ɗakinsu, Da sauri Ya bar ƙopar toilet ɗin Ya shigo ɗakin nasu, kaitsaye Eyes ɗinshi suka sauka akan tsohuwa dake A tsakiyar ɗakinsu Hannunta ruƙe da sanda haris ne agabanta Ya ruƙe qugu, Yana mata maganaTamkar zai rufe ta bugu,
“Saboda me zasu yi wurgi da su? Saboda rashin tausayi da mugunta suka jefar dasu, kamar wasu barguna, gasu nan kina gani da idanuwanki ko tashi sun gaza yi saboda raɗaɗin da jikinsu yake Yi musu, wai mu me aka maida mu ne eye? nifa nafara kokwanto akan kowa ma dake atare damu, ” Yana magana yana watsa hannayenshi kamar zai buge tsohuwa dama fa shi haris akwai zuciya, Idan ya fusata Ya isa masifa,
Tun da haris Ya soma magana, Tsohuwa ta zazzaro kwarkwararrun idanuwanta waje, Kwayar idon kamar zasu rubzo ƙasa saboda tsabar zaro su da ta yi, Bakomai bane yasa tayin hakan face Mamaki da al’ajabin daya kamata, karo nafarko kenan da aka fara samun wani acikin su Ya ɗaga mata murya, haƙika tayi matuƙar girgixa, sai da yakai karshen maganarshi Ya juya mata ƙeya yana ƙunƙuni,
Ruƙe ha6arta tayi idonta akan keyarshi, Muryarta Na rawa tace”HARISU!! yau ni kake gaya ma magana babu tausasa harshe? A ina ka samu wannan ƙwarin gwiwar? Kamanta matsayina ne awurinku? Wato ina can ina tufka ana nan anayi mini warwara,” a wani sukwane Haris Ya juyo Yabi ta da wani irin kallo Yace”Indai akan ƴan uwana ne fiye da haka ma zan Iya fada maki, Wannan matsayin da kike dashi awurin mu kina dab da rasa shi, Saboda Na fara zargin ba ƙaunar mu kike Yi ba,” kasa karasa maganar haris yayi idanuwanshi cike tab da kwalla, tsohuwa sai faman gyaɗa kai take Yi kamar wata ƙadangaruwa,
Ganin tana ƙoƙarin juyawa ta koma Cikin dakinta Ne yasa Danish Yin saurin dakatar da ita, ta hanyar yi mata magana” meyasa a koda yaushe muka sanar dake agame da rashin lafiyar ɗaya daga Cikin mu baki nuna damuwarki? jin muryar danish Yasa tayi saurin Juyowa tare da kallonshi, A tsanake Yake tafiya yana tunkarar inda take atsaye, Duk wannan abun dake faru Su azeeza sun natsu suna sauraronsu, a lokacin sun dakata da yin kukan sai dai har yanzu basu iya miƙewa daga kwacen da suke a kasa ba,
A gefen haris Danish Ya tsaya tare da ɗaura hannunshi na hagu saman kafadar haris, still idanuwanshi akan tsohuwa Yana jiran Jin amsar da zata basu, Sai faman zare ƙwalaƙwalan idanuwanta take yi, Da alama zuciyarta ta shiga ruɗani,
Bata gama kiɗima ba, zazzaƙar muryar angel ta ratsa kunnuwanta da cewa”Ki basu amsar tambayarsu mana? Daga anyi magana kaɗan sai ki dogara sanda Ki koma ɗaki, saboda rashin gaskiya, Meyasa kike 6oye mana gaskiya ne? Tun rana ta farko dana tsinci kaina acikin kurkukun nan raina ya bani cewa ba abun arziƙi ake aikatawa acikin shi ba, saboda bai kwanta mini araina ba, Kina yawan yi mana ƙarya, wanda bani kaɗai ba hatta su kansu yanzu sun fara kokwanto akanki, kince mana ana kaisu treatment room domin duba lafiyarsu, to meyasa ake dawo mana dasu a haukace? Maimakon Muga sauƙi ajikinsu saima dai muka ga tashin hankalin akan fuskokinsu, Da jikinsu, mutumin dake yin jinin al’ada meya haɗa shi da ƙaiƙayin gaba? Da kuma gwamewar ƙafafuwa? Uwa uba da fashewar le6e, ga rama, Wannan wani irin treatment ne tsohuwa”! Tayi tambayar tana kallonta, Tsohuwa dai tarasa bakin magana, sai faman gyaɗa kanta take yi,
Angel taci gaba da cewa”Allah dai ba Azzalumin bawansa bane, idan ma cutar mu ku keyi, To ku sani Allah Yana kallonku, Kuma akwai ranar hisabi, ranar da duk wani abu da kuke taƙama dashi aduniyar nan bazai ta6a taimakonku ba…….” Angel bata kai ƙarshen maganarta ba, Tsohuwa ta buga sandar hannunta, Cikin nuna 6acin ranta, Da sauri danish ya dafe kanshi da hanneyenshi,
Ranta amatuƙar 6ace tace”Kin manta abunda na faɗa maki? Nifa bakowa bace agidan kurkukun ƙaddarar nan? Don me zaki titsaye ni kina gaya mini magana yadda kika dama? Meyasa bazaki tuhumi Iyayenku da suka sadaukar daku ba sai ni? Da bani da wata alaƙa ta jini da ku? Ga dukkan alamu baki Ji gargaɗin da nayi maki ba, Ina matuƙar Tausayawa rayuwarku! Domin kuwa duk ranar da kika kuskura Kika bari Ƴan uwanki prisoners suka gasgata maganarki akan tawa, to daga wannan ranar ba zaku ƙara Yin tozali da ni ba, Zan barki dasu ne, Kiga idan zaki iya taimakon rayuwarsu,” Tsohuwa Nakai karshen maganarta, Ta Juya fuu kamar zata tashi sama Ta nufi dakinta, Ta shige taja kopa ta rufe,
Sai lokacin danish Ya zame hannayenshi daga saman kanshi, Wato a lokacin da tsohuwa ta buga sandar hannunta, basu ƙara fahimtar me take cewa ba, tamkar ta wanke masu tunaninsu na tuhumar da su ke yi mata, ita kanta angel ta lura da hakan, Sai dai ko kaɗan hankalinta bai tashi ba, Domin kuwa tasan dole su cigaba da tuhumarta, da zarar an dawo musu da ƴan uwansu da aka ɗauka,
Kallon juna su kayi ita da danish, Kafin ta ɗauke idonta daga kanshi ta mayar dasu kansu Batool, tafiya tayi zuwa inda take a kwance, Ta zuƙunna tare da kai hannayenta saman kafaɗun batool ta ɗago da ita tare da kwantar da kanta saman kafaɗunta,
“Sister, yanzu Haka zamu zuba ido muna ji muna gani, Ana raba mu da ƴan uwanmu”? Cikin shessheƙar kuka batool ta yi maganar, kafin angel ta bata amsar tambayarta, Naufal ya rigata cewa”Haƙuri zamuyi, Giants sunfi ƙarfin mu, Ni dai na roƙe ku nan gaba kada ku ƙara gigin shiga huruminsu, Ina gargaɗinku, Idan ku ka yi haƙuri za’a dawo mana da su ne, kamar yarda aka dawo mana dasu Parveena,
Mubeen yace”Nima abunda nake so naja musu kunne akai kenan, Mutanan nan ƙarfi ne da su, They are extremely dangerous! Da ace tun farko baku Yi yunƙurin tunkararsu ba da duk hakan bata faru ba, kun riga da kunsan halinsu, Basa ji basa gani, duk wani koke koken da za ku yi musu abanza, ba saurarar ku zasu Yi ba”
Danish yace”pls let it be past, tunda sun riga sun tafi dasu, Koke koken Ya tsaya iya haka, “
Jinjina kai Angel ta yi tare da binsu Azeeza da kallo tace”Ku daure ku tashi, ku je toilet ku wanke fuskokin ku,” amsa mata Su ka yi da toh, daƙyar suka iya miƙewa tsaye a daddafe suka Nufi toilet,
“Batool kema kije Ki wanke fuskarki, koma Kiyi wanka” amsa mata tayi da toh, Ta ɗago da kanta daga saman kafaɗar angel, Hannunta adafe da sumar kanta, ta miƙe ta wuce cikin toilet,
Ba Iya wanke fuska Su kayi ba, Hada wanka su Kayi, Time da suka fito, mazan gaba ɗaya sun koma saman gadajensu, Angel ma tana zaune daga gefen gadonta, Kowa da abunda yake saƙawa acikin zuciyarshi,
Lokacin da giants suka zo kawo musu abinci, Fushi suka Yi, suka ƙi zuwa su Ci, naufal yace”da rabon muyi ma kanmu asara, domin kuwa su basu san bihim ba, ko ajikinsu, Mu zamu Ji jiki,” wannan maganar da naufal yayi ce tasa parveen ta sauko daga saman gadonta, Ta nufi saman dining carpet ta samu wuri ta zauna, Ɗaya bayan ɗaya suma sauran suka sauko daga saman beds ɗinsu, Suka Nufi Carpet ɗin suka zazzauna,
Lafiyayyan abinci aka kawo musu, ba don suna jin daɗinshi ba suke Cin shi, Kamar waɗanda aka Yi ma dole, In ka cire parveen dake ta zuba loma, dama ita bata wasa da abinci,
Abinci take Ci amma hankalinta na akan giants dake a tsaye sun ƙame, Harara ta dinga jefa musu tamkar ƙwayar idonta zata faɗo kasa, ita kaɗai take haukanta domin kuwa babu tabbacin ko suna kallonta, Bayan sun kammala Cin abincin, Sauran daya rage Batool ta 6oye musu shi acikin kwandonsu, saboda su samu wanda zasu Ci da anjima,
Bayan tafiyar giants, Safa da marwa suka shiga Yi acikin ɗakin duk babu daɗi saboda rashin ƴan uwansu, an rairaye su yanzu sun koma su goma sha ɗaya, Babu mutun Huɗu acikinsu, dole suyi maraicin rashinsu atare dasu, ga zullumin da suke Yi da fargabar ko awani hali suke Ciki?
Idan suka gaji da zagaye ɗakin sai su koma saman gadajensu su zauna, a haka har dare ya rutsa dasu, Ɗakin Ya yi duhu, Rubina ce ta kunna musu fitilun Ɗakinsu Haske Ya gauraye ko’ina, Kowa Ya kishingiɗa saman gadonshi,
Ta yi tsammanin sunyi bacci Jin ɗakin Yayi tsit, Juyawa tayi tare da fuskantar gadon danish, idonshi biyu Ya kwantar da kanshi saman pillow,
“Meya hana ka bacci”? Amsa ya bata da cewa”ke zan tambaya, me kike Yi har yanzu baki runtsa ba”? Ta6e baki ta ɗanyi”Damuwace ta hana ni bacci, ina jin duk babu daɗi zuciyata”
Shiru baice mata komai ba, sai dai kallonta da yake yi, kamar yadda itama take kallonshi, Gani yayi ta miƙe ta sauko daga saman gadonta, a bakin gadonshi ta zuƙunna tare da ɗaura hannayenta saman mattress ɗinshi
Da ɗan mamaki yace”lafiya”? Murmushi ta ɗansaki kafin tace”Bakomai kawai ina so Muyi fira ne,” mayar mata da martanin murmushin yayi, har dimples ɗin shi ya lotsa,
“Ai ni ban Iya fira ba, in fact ko surutu ban iya ba, sai in ta kama dole,” tace” toh ka ƙaddara ta kama dolen ne, tambaya ce nake so In yi maka hope zaka amsa mini” ɗaga mata gira yayi tare da cewa” Am all ears”
Kame kame ta shiga Yi, abun ma sai yaso ya ba shi dariya, hannun shi yakai saman sumar kanta ya ruƙo gashinta tare da cewa”Faɗa mini mana, indai nasan amsa zan baki,” tace”Dama nayi mafarki ne, kana da wuƙa, shin dagaske ne”? Da budar bakinshi sai ce mata yayi”you’re trying to be smart, tell me the truth waya faɗa maki cewa ina da wuƙa? Nasan ba mafarki ki kayi ba,”
Hararar shi Tayi jin ya ganota, taso tayi mishi wayau,
“Na ta6a tambayar batool, cewa Inaso zanyi amfani da wuƙa, shine take faɗa mini cewa Akwai wadda tsohuwa ta baka lokacin da kace mata kana so ka rage yawan sumar kanka,” Wani kallo taga yana binta dashi, Can kuma yace”me zakiyi da ita”? Dariya tayi tare da cewa”bafa kai zan kashe ba, Nasan abunda kake tunani kenan, ni kawai inaso In rage sumar kaina ne, bama ni kadai ba hada batool itama Gashin kanta yayi yawa yana takura mana” tayi maganar tana yamutsa fuska,
Ta6e mata baki yayi”Nima namanta inda na ajiye ta, ko na mayar mata da ita ko ban mayar mata ba, namanta, “
A ƙagare tace”pls ka daure ka tuna, Zata yi mana amfani,”
“Angel idan Kina son In rage maki gashin kanki ne, Ba buƙatar Yin amfani da knife, i can use my nails to cut it for u” zaro ido ta ɗanyi da mamaki tace”taya zaka Iya amfani da akaifa wurin rage yawan gashin kaina, baka ga yawanshi ba ne”
“Idan kin bani dama zan Jaraba” girgiza mashi kai tayi”a’a, Ni dai nafi so Inyi amfani da wuƙar, Idan Allah yasa ka tuna inda ka ajiyeta sai ka ɗauko mini” ta faɗi hakanne saboda ba gashin take so ta rage ba, Wuƙar take buƙata saboda tsaro,
“Its Okey, Kije ki kwanta, duk time dana tuna i will let u know” ya karasa maganar tashi tare da jan bargo ya lullu6e jikinshi har zuwa kanshi, Miƙewa Ta yi tare da juya ta koma saman gadonta ta kwanta, A daren ranar saida ta roƙi Allah Akan Yasa itama ta fara Menstruation kodan saboda giants su ɗauketa sukaita ɗakin nan taga uban me suke aikatawa, Idan Allah yasa Hankalinta bai gushe ba kenan,
Wasa wasa Yau har tsawon One week kenan ba’a dawo dasu Hannah ba, Tun suna sanya damuwa aransu har suka haƙura suna zaman jiran tammani, Tun daga ranar da aka ɗaukesu Kullum sai ta roƙi Allah tsakar dare Akan Ya karesu aduk inda suke, Bayan haka kuma Tana yawan yin addu’ar akan Allah yasa ta fara jinin itama, duk don saboda da taga me ake yi musu,
Yanzu ta kaiga ko tsohuwa basu tambaya dangane da ƴan uwansu, saboda sun fahimci cewa ita ɗin bata da banbanci da totan masara awurinsu, bi ma’ana bata da amfani duk wani magiyar da zasu Yi mata bazata iya Sanyawa adawo masu da ƴan uwansu ba, sai da ta gaya musu ƙarairakinta,
Yau tsawon 3 weeks kenan Suna ta baza ido suga an dawo musu Da ƴan uwansu, Sai acikin satin karshe na watan da suka shiga, Aranar da daddare suna zaune saman carpet Suna fira sun kunna fitilun ɗakinsu, Ba zato ba tsammani sai ga giants Huɗu sun shigo cikin ɗakin nasu Kafaɗunsu Ɗauke dasu Hannah, A wani irin zabure suka miƙe suna kallonsu, wuce wa cikin ɗakin giants su ka yi adai dai bakin gadajensu hannah masu ɗauke da numbobinsu suka kwantar da kowannansu, Atare suka juya suka fuce daga cikin ɗakin,
Azeeza sai tsalleta take Yi tana murna an dawo musu da ƴan uwansu, Su batool kuwa Kallon Kallon suka shiga Yi atsakaninsu, sun rasa gane farin Ciki zasu Yi ko baƙin Ciki? Ga shi dai an dawo musu da ƴan uwansu da suka daɗe suna jimamin rashinsu, Sai dai ga dukkan alamu Basu acikin hayyacinshi, Har ƙwarama lokacin da aka dawo dasu parveen sunyi magana, Amma waɗannan bayin Allahn, Idanuwansu ne kaɗai suke motsi, Numfashin su da hucin zafi yake fita, ƙafafuwansu duk sun tale, Wani abun tashin hankalin ma, Hada Yakushin akaifa asaman wuyansu, fatar wurin tayi jawur, jini ya kwanta, La66ansu sun faffashe, Hankalinsu danish ba ƙaramin tashi yayi ba, Matan kuwa Sun sha kuka kamar ransu zai fita, Angel tace Yanzu babu buƙatar saita yi musu bayani game da cewar cutar dasu ake yi yau dai gashi nan zahiri idanuwansu sun gane masu, Sahun yakushin akaifar dake asaman wuyansu, Haƙiƙa sun yi matuƙar girgiza, hatta mazan saida suka zubar musu da hawaye saboda tsabar tausayinsu daya kama su, daren ranar basu Iya runtsawa ba, A gefen gadajensu Hanna suka zaune suna Jimami, har garin Allah Ya waye, Koda suka je bakin ƙopar ɗakin tsohuwa suka kwankwasa mata, Munafukar bata fito ba, Hakan ya ƙara tabbatar musu da cewa Bata da gaskiya,
Haƙiƙa sunsha wahala wurin Yin jinyarsu Hannah, kamar bazasu Rayu ba, jikinsu yayi tsauri sosai, babu sauƙi saima abunda ya qara gaba, sai da takai ga Komai daga kwance suke yin shi, fitsari kashi, duka dai, a ƙalla sun ɗauki tsawon one month suna yin jinyarsu kafin Allah yasa suka samu sauƙi Jikinsu ya warware, Suka koma kamar yarda suke da, Sai dai babu wani walwala atattare dasu, Suna yawan firgita, Ko kiran sunansu Kayi sai kaga sun ɗan zabura, Idan suna bacci kuma Sun dinga sambatu suna koke koke, Ahaka ahaka dai da taimakon Allah angel Tana yi musu addu’a duk rana ta Allah, Sai gashi sun wartsake, Sun dawo normal, Bayan sunji sauƙi, Sai ga tsohuwa ta shigo ɗakinsu, Wani irin mugun kallo da suka dinga jefa mata, ba arziƙi taja sandarta ta koma Cikin ɗakinta, Angel taso ace su hanna sun Iya tuna abunda ya faru dasu amma sun kasa, kwata kwata basu Iya tuna komai, Da ace sun tuna koda kaɗan ne to kuwa tabbas sauran ƴan uwan nasu zasu Ƙara gasgata maganarta, duk da ayanzun ma ta fara cin nasara saboda kokwanton su Ya ninku akan gidan kurkukun, Sun sha jinin jikinsu, Sun fara tsorata da lamarin, Haris har alƙawari ya ɗauka akan bazai ƙara bari giants su ta6a wani acikin su ba, Sai dai in bayan babu ranshi, danish dai bamu san matsayarshi ba, Shi dai baice komai ba, Iya nuna 6acin ranshi akan fuskarshi ne, Amma su naufal mubeen da javed duk sun ɗauki wannan alƙawarin na hana atafi da ƴan uwansu idan basu da lafiya! Kallonsu kawai angel take Yi domin kuwa tasan babu abunda zasu Iya yi, ba wani ƙarfi gare su ba, balle suce zasu Iya ja da giants, Mutanan da take tunanin Ba cikakkun mutane bane, Ƙarfinsu bana jinsin bil’adama bane,
Bayan komai Ya lafa tsawon Watanni uku wani iko na Allah, cikin matan ba wanda ya ƙara Yin Menstruation, kamar an ɗauke musu da jinin, Hakan ba ƙaramin daɗi yayi ma angel ba, Yanzu hakalinsu ya ɗan kwanta,
Ganin sun samu natsuwa yasa Ta fara jan hankalinsu zuwa ga addinin musulunci, Idan dare Yayi bata barinsu Yin bacci, Tarihin annabawa take basu tun daga kan tarihin Annabi Muhammad (SAW) Cikin hikma take Basu tarihin, Kuma ga dukkan alamu ba ƙaramin daɗin shi suke Ji ba, domin kuwa idan ta fara basu tarihin, Ko fitsari mutun ke ji sai kaji yace a jira ya dawo sai acigaba, idan kuwa tace ta gaji abari gobe zata ƙarasa musu kamar su yi mata hauka, Taci wahala sosai Wurin janyo hankalinsu duk da bata ci nasara ba saboda duhun jahilcin dake akansu, Suna Yi mata tambayoyin ƙural da suka fi ƙarfinta musamman haris, Da yace idan har akwai Allah wanda ya halicce su to meyasa bai ta6a zuwa ya kawo musu ziyara ba? Ire iren irin waɗannan tambayoyin sune kesa tana karaya wani lokacin, Ita dai tayi iyakar bakin ƙoƙarinta wurin sanar dasu gaskiya, Sauran kuma tabar ma Allah domin kuwa shi kaɗai ne zai basu ikon musulunta idan yaso, mutun huɗu ne acikinsu ta lura da suna matuƙar son Addinin, Batool, Azeeza da Javed, sai kuma parveen, sauran kuwa kokwanto ne Ya hana su yarda da ita saboda wasu tambayoyin su da ta gaza amsa musu, shi danish bama tasan a wata matsaya yake ba, Yana dai son tarihin annabawan da take basu, Sai dai Babu alamar yana da niyar kar6ar addinin nata, mutun huɗun nan da suka nuna suna da interest sune suka fara kar6ar addinin musulunci acikinsu, Ta biya musu kalmar shahada, Kusan Yini guda suka ɗauka tana ta fama dasu akan su maimaita sun kasa furta ta, Sai cikin dare Wani iko na Allah tana sake biya musu sai gashi sun maimaita lafiya lou batare da inda inda ba, Tayi farin Ciki sosai kamar ta zuba ruwa a ƙasa tasha, Duk da farin Cikin nata ragagge ne tun da sauran basu kar6a ba, Tafi damuwa akan danish saboda tana ji aranta idan har ya kar6i addinin zai taimaka ma sauran ƴan uwan nashi saboda suna jin maganarshi sosai, duk da haka bata ƙyale shi ba, ta addabi rayuwarshi ta hana shi sakat, Sai yana tsaka da yin bacci ya dinga jin muryarta acikin kunnanshi tana karanta mashi kalmatusshahada, wato da tsiya sai ya kar6i addinin, babu yarda batayi dashi ba, Amma Yaƙi bata haɗin kai a ƙarshe da ta gaji ta ƙyale shi badan ta haƙura ba, Ta dai bashi lokaci ne ya ɗan sarara, duk da haka bata yi fushi dashi ba, Sai ma ƙara janshi da take yi ajikinta, saboda sanin mahimmanci da yake da shi, dole saida shi wasu abubuwan zasu tafi dai dai, a 6angaren su batool da suka musulunta, tafara ƙoƙarin Koya musu addu’o’i da karatun kur’ani, sai dai wani abu dake ɗaure mata kai, Wahalar da suke sha wurin furtawa, Ita parveen ma hada amai take Yi idan angel ta matsa mata akan ta furta karatun kur’ani, ita kuma azeeza daga anfara sai ta kama bacci, ba ƙaramin takaici angel ke ji ba, daga bisani tayi wani zazzafan nazari, Acikin kwanakin kowani sati akwai wace rana da idan dare yayi tayi musu karatu suke amsawa lafiya lou batare da sun kakare ba, a irin ranar ne ta ta6a yi ma danish karatun kur’ani da daddare lokacin da giants suka dawo dashi kuma dai dai lokacin ne take basu tarihin annabawa batare da ta samu targaɗe ba, Kuma a irin lokacin ne su batool suka furta kalmatusshahada batare da sun yi inda inda ba, duk irin lissafin kwanakin da take yi Tun lokacin da daddynta Ya gudu da ita bata ta6a bari lissafin kwanakin wata sun ku6uce mata ba, Sai dai wannan karan ta kasa gane wace rana ce wannan mai tarin albarka? Meyasa take samun dama A ranar? Bata iya hasashen wace rana bace sai dai tana ganeta ne da alamominta, duk irin ranar ta zagayo bata bari ta tafi abanza, kusan kwana suke Yi da daddare tana Koya musu karatu tare da yi ma sauran ƴan uwan nasu da’awa kota samu suma Su kar6i addinin, Allah mai yarda yaso, Sai gashi ɗaya bayan ɗaya suna zuwa wurinta suna cewa suma zasu musulunta, cikin waɗan da suka kar6i addinin musulunci akwai, batool, azeeza, Hannah, Hibba, deeja, parveen, Eve, yasmin, Angel, Batool, rubina, Cikin maza mutun uku, Javed, Naufal da Mubeen, yanxu mutun biyu ya rage mata acikinsu, Haris da danish, Su kaɗai suka yi mata cikas, Duk da Tayi matuƙar yin farin Ciki, Da Allah ya bata ikon musuluntar dasu Hanna, Ranar da suka kar6i shahadar ko bacci bata yi ba, A tsakiyar gadonta ta zauna tana kukan farin ciki tare da Yi ma Allah godiya, daya bata wannan damar, Nima dai Na matse kwallata kuma na tayasu murna koba komai sun tsira da imanin da su ka yi, Allah zaiji ƙansu,
A wani dare Ne, dukkansu Sun kwanta bacci, Angel tana a kudundune cikin bargonta, kwatsam ta soma Jin shessheƙar kukan mutun acikin kunnuwanta, tun bata ɗauki abun serious ba har sautin kukan ya fara disturbing ɗinta, Sai kuma ta dinga jin hannun mutun asaman jikinta kamar ana bubbuga ƙafarta ƙasa ƙasa ta jiyo miryar mutun yana yi mata magana, A hanzarce ta yaye bargon jikinta ta ɗago da idanuwanta masu ɗauke da bacci biji biji take Iya ganin fuskarta, tana a zuƙunne gaban gadonta, fuskarta sharkaf da hawaye,
Mutsustsuke idanuwanta ta yi da yatsun hannunta don ta samu damar ganin kowacece, koda tayi arba da deeja sai taji gabanta ya faɗi rass! Tun kafin ma takai ga faɗa mata abunda ya kawo ta,
“Angel Jinin nan ne ya dawo mini, Na shiga toilet in yi fitsari shine naganshi, hankalina Ya tashi sosai bansan Ya zanyi ba,” fuskarta a yamutse tayi maganar, dafe kai angel tayi tare da ambaton”INALALLAHI WA’INNA ILAIHIRRAJI’UN! wannan wata irin masifa ce, mun shiga uku! Ni nayi tunanin Kun daina gaba ɗaya, ashe da sauranshi,” idanuwanta cike tab da kwalla tayi maganar,
Ruƙo hannunta deeja tayi acikin nata”Dan Allah angel, Ki san yadda za’ae ki hana atafi dani, wlh gani nake kamar idan aka ɗauke ni wannan karan baza’a dawo dani ba,” tana kuka ta yi maganar, Hankalin angel ya tashi matuƙa, Saukowa Tayi daga saman gadon ta nufi gadon Danish, Hannu takai ta ruƙo bargon daya lullu6a dashi ta yaye shi, Bubbuga ƙafadarshi tayi tare da ambaton sunashi”Danishi!danish!” daƙyar ta samu ya farka, Yana faman yamutsa fuska Yace”menene”?
“Pls ka tashi deeja bata da lafiya, Menstruation ne Yazo mata” ware idanuwanshi ya yi jin abunda tace, Saboda ya gane me take nufi, tun da tayi musu bayanin komai dangane da jinin,
“Dan Allah Danish kada ku bari Giants su ɗauke ta, mu taimaka mata,” yunƙurawa yayi tare miƙewa ya zauna saman mattress ya jingina bayanshi jikin bango, batare daya ce komai ba, idanuwanshi na akan deeja dake a zauƙunne sai kuka take Yi,
Ganin baida niyar tanka mata yasa ta wuce gadon haris, ta tada shi, daya farka ta sanar dashi abunda ke faru wa, Jikinshi har 6ari yake Yi, duk yabi ya ruɗe ya sauko daga saman gadonshi, Yana tambayarta Ina deejan take, Tun kafin ma ta bashi amsa sai ga deeja ta nufo su, Tana karasawa gabanshi ta fashe da kuka, Ruƙo hannunta yayi acikin nashi Ya janyota jikinshi Yana lallashin ta yana faɗin”ta kwantar da hankalinta, Ba wanda ya isa ya tafi da ita sai dai ahaɗa dashi atafi amma bazai ta6a bari giants su ɗauke ta ba, muddin Yana numfashi” Angel taji daɗin kalaman da haris yayi duk da tasan zaiyi wuya ya iya hana su tafiya da ita, Ga wanda taso Ya harzuƙa can saman gado Amma Yaƙi cewa komai, Haushin shi duk ya cikata, ta tsani halayyarshi ta lalaci da rashin son ta6uka komai,
“Haris Bari in tada su Naufal, In yaso sai mu haɗu mu duka mu hana su tafi da ita” Yace mata”toh” ɗaya bayan ɗaya tabi kowannan su saman gadanshi ta tada shi, duk wanda ya farka, Yaji abunda ke faruwa sai gaka ya zare ido saboda fargaba da tashin hankali, A tsakiyar ɗakin suka hallara su goma sha huɗu, sun sanya deeja a tsakankanin su suna jiran giants su ƙaraso, da alama yau sun shirya yin faɗa da Giants,
Motsin buɗe ƙopar ɗakin tsohuwa suka Jiyo, Da sauri suka kai idanuwansu kanta, a lokacin ta ƙarasa fitowa daga Cikin ɗakin Hannunta ruƙe da sanda, fuskarta a yamutse babu annuri babu walwala, Ɗagowa tayi tare da kallonsu
Babu wanda yayi yunƙurin yi mata magana, Sun ɗaure fuskokinsu, Saboda mugun haushinta da suke Ji,
Azeeza ce tace”ni dai bari in je in roƙeta kada ta bari atafi da deejan mu” har ta ɗaga ƙafa zata je wurin ta, Haris Ya damƙi hannunta tare da cewa”Ashe baki da hankali? Idan kinje kin roƙe ta me zata Iyayi mana? In banda ƙarya”? Wannan maganar ta haris tayi matuƙar girgiza tsohuwa,
Angel tace”Allah ya kamata ki roƙa ba ita ba, saboda shi kaɗai ne zai Iya taimakon mu amma waccan matar, Ba abunda zata yi mana,” takai karshen maganar idonta akan tsohuwa,
Jinjina kai tsohuwa ta yi jin abunda haris yace, daga bisani ta Dogara sandarta zuwa inda suke atsaye taci burki ta tsaya, ɗaya bayan ɗaya ta shiga binsu da wani irin kallo, sun rasa gane kallon menene take Yi musu, Juyawa tayi tare da kallon danish dake zaune saman gadonshi, Dama shi kaɗaine baiyi yunƙurin miƙewa ba, da alama baya goyon bayan abunda suke shirin aikatawa,
“Saboda shi yafi ku wayau da hankali shiyasa bai biye maku ba,” tsohuwa ce tayi maganar a lokacin da ta janye idanuwanta daga kan danish ta mayar dasu kan angel, Ido cikin ido suke kallon juna,
Murmushin takaici ne ya bayyana akan fuskar tsohuwa,
“Koda gigin wasa kada ku kuskura kuce zaku Hana giants tafiya da deeja!! ina gargaɗinku idan har kuna son zaman lafiya to ku daina yunƙurin shiga huruminsu…..” Haris ne ya dakatar da ita ta hanyar daka mata tsawa yace”Wai ina ruwanki da rayuwarmu ne? Bakin nuna baki damu da mu ba? To ki fita sabgarmu mana? Idan ke bazaki Iya hana su tafi da ita ba, to mu ki barmu muyi da kanmu” rai a6ace yai maganar,
Muryar danish ce ta ratsa kunnuwansu, a yayin da yake saukowa daga saman gadonshi yace”Haris ka sassauta kalamanka, Abunda tsohuwa ta faɗi gaskiya ne, Baza ku Iya ja da giants ba, Kuna Yunƙurin jefa rayuwarku cikin hatsari ne, Na rasa ya zanyi in fahimtar daku,” wani irin mugun kallo haris ya jefa mashi,
“Danish kana goyan bayanta ne? Bayan duk irin ƙarairakin da take yi mana, da kuma Nuna rashin damuwarta akanmu , Sannan da ita fa ake haɗa baki ana cutar da rayuwar ƴan uwanmu amma duk ahaka kake binta”? Zuciyarshi a hasale yayi maganar, sam baiyi tsammanin danish zai mara mata baya ba,
“Haris u ave to understand me, Bazamu iya yin komai ba, saboda mu ba komai bane, Ni bana so na rasa wani acikin ku…….” Kasa karasa maganar yayi ganin irin kallon hararar da angel ke jefa mashi, shiru yayi tare da duƙar da kanshi ƙasa,
Tsohuwa ta dasa da cewa”Bawai bana son taimakon ku bane, kawai ba yadda zanyi ne, Ni kaina giants sunfi ƙarfi na, matsayinsu da nawa ba ɗaya bane, sunfi ni ƙarfin iko, Idan nace zan hanasu tafiya da wani daga Cikin ku zan rasa raina ne……” Angel tace”Oh ashe ta ranki kike Yi? Su baki damu da rayuwarsu ba, Ae ni nayi tsammanin har rayuwarki zaki iya sadaukarwa akansu ashe ba haka bane, ƙaunar da kike yi musu ta bogi ce, Ni na tabbata da ace ƴa’ƴan da kika zuƙunna kika haifa ne da baki faɗa musu wannan maganar ba”
Girgiza kai tsohuwa tayi wannan karan idanuwanta hada farin ruwa kwance acikinsu tace”Bazaki ta6a fahimtata ba, Koda ace na sadaukar da rayuwata akansu nayi abanza, saboda yin hakan bazai canza komai ba, Ae ƙwarama Ni dana 6ata tsawon shekaru ina rainansu, Iyayensu fa da suka sadaukar dasu? Suna can suna sharholiyarsu sun ma manta da suna da wasu ƴa’ƴa da suka sadaukar, Nifa kaɗaice na damu daku, Ni da ban haɗa alaƙar komai daku ba, ae na cancanci a jinjina mini”
Maganar tsohuwa ta yi matuƙar girgizasu, Kallon kallo suka shiga yi atsakaninsu, batare da wani ya kuma Yin magana ba,
“zan Koma ɗakina, Amma kafin nan zan ƙara ja maku kunne, Kada Ku kuskura ku shiga hurumin giants, Idan Kunne Yaji Jiki ya tsira” tsohuwa na kammala maganarta, Ta juya tana dogara sanda ta shige Cikin ɗakinta, Idanuwansu akan abayanta har saida ta 6ace ma ganinsu….
*❤❤❤PRISONERS❤❤❤*
Haƙiƙa maganar tsohuwa ta yi matuƙar ta6a zuciyoyinsu, Jin cewa Iyayen su suna can suna sharholiyarsu sun manta da suna da wasu ƴa’ƴa da su ka sadaukar, Wai ashe dama su ba Marayu bane marasa Iyaye! ? Jikin su ya yi mugun sanyi, kamar waɗanda aka zarewa laka, ita dama angel ta san da wannan shiyasa ta ƙudiri aniyar idan har Allah yasa tayi nasarar fita daga Cikin kurkukun, Kaitsaye zata fara neman Azzalumin da ya yi sacrificing ɗinta acikin danginta, don a halin yanzu kowa suspect ne awurinta, Mahaifinta da aunty aneelerh kaɗai ta cire aciki, Amma sauran dangin nata da wanda ta sani dama wanda bata sani ba, Kaf ɗinsu she’s suspecting them,
ɗakin nasu ya yi shiru babu mai magana saboda ruɗanin da tsohuwa ta jefa su aciki, Kowa da abunda yake saƙawa aran shi, kuma har lokacin suna atsaitsaye kewaye da deeja, babu wanda Ya motsa, danish Yana a gefe ɗaya ya goya hannayenshi saman ƙirjinshi,
Lokaci ɗaya kamar an zungure su gaba ɗaya suka ɗago da idanuwansu suna kallon saman benan Jin motsin buɗe ƙopa, Hankalin deeja yabi ya tashi haiƙam Jikinta ya soma kerma ta ƙanƙame Jikin haris tana kuka tana faɗin kada su bari atafi da ita, duk ta cukuikuye mashi rigarshi, Hankalinsu ba ƙaramin tashi yayi ba,
“Pls kada wanda yayi yunƙurin dakatar dasu, am warning u,” danish ne ya gargaɗe su,
Babu wanda Ya kalli inda yake sai dai duk sun sare zuciyoyin su sun karaya,
Takun tafiyar giant ne Ya ja hankalinsu zuwa ga kallon staircase ɗin dayake saukowa, Shi ɗaya yazo musu wani gabjejen ƙato dashi a bubbuɗe yake tafiya, Ganin Yana tunkarosu gadan gadan Yasa duk suka watse saboda tsoratar da suka Yi, batool taja hannun azeeza duk suka ja gefe, Ya rage daga angel sai haris daya fusata Yana jiran shi ya ƙaraso, da sauri danish ya sanya hannyenshi biyu ya ruƙo wuyan rigar haris dana angel da ƙarfi Ya janyesu gefe ɗaya batare daya saki wuyan rigarsu ba, duk yadda suka so su kwace daga ruƙon da yayi musu sun kasa, Angel hada yakushin shi tadinga yi da hannayenta amma ko ajikinshi,
Giant ɗin na ƙarasowa Ya sanya hannayenshi biyu ya ɗauki deeja saman kafaɗarshi tana ta kuka baiwar Allah, a haka Ya juya da ita ya fuce daga Cikin ɗakin, suna ganin an tafi da ita, su ka fashe da kuka kamar ransu zai fita,
Kamar Jira take Giant ɗin Ya fita, Danish na sakin wuyar rigarta, Awani fusace Ta juya ta fuskance shi ta ware yatsun hannayenta biyar cuf, ta wanke shi da zazzafan mari ji kake tasss, Har saida kanshi yayi gefe ɗaya,
Ranta amatuƙar 6ace tace”Banza daƙiƙa, ban ta6a sanin kai wawa bane dolo sai yau, Kana ji kana gani za’a tafi da ita baka iya ta6uka komai ba, don me zaka hana mu taimakonta? Ta yi maganar tana ciccije le6enta, ɗagowa yayi da fuskarshi, tafin hannunshi dafe da inda ta mara, wurin yayi ja saboda hasken fatarshi ga sahun dogayen yatsun hannunta nan ruɗu ruɗu asaman fatar, wani irin raunataccen kallo yake binta dashi batare daya furta komai ba, Sauran ƴan uwan nasu duk suna a tsaye cirko cirko suna kallonsu, Haris dai baice komai ba, duk da baiji daɗin marin da angel ta yi ma danish ba, Sai dai shi kanshi yaji haushin yadda danish yaƙi nuna fusatarshi akan tafiyar da aka yi da deeja,
“Angel meyasa kika mare shi? Kalli yadda kika raunata mashi fuska! shi fa bashi da laifi, yana ƙoƙarine Ya dakatar da ku gudun kada ku jefa rayuwarku cikin hatsari, saboda Lafiyarku yayi hakan, taya zamu Iya ja da giants? Kin manta irin wurgin da su ka yi damu lokacin da muka yi yunƙurin hana atafi dasu Hannah”? Juyawa angel tayi tare da kallon batool da ke magana, nuna danish tayi ta yatsan hannunta tace”batool kina supporting ɗinshi? duk irin halin ko in kulan da ya nuna akan deeja? Kowa ya nuna tausaya agareta ganin irin halin da take ciki tana kuka tana roƙonmu akan kada mu bari atafi da ita, Amma wannan Kwankon ashanan Koda naje na faɗa mishi Ba abunda yace saima ya share ni kamar wata ƴar iska, ni shi ne abunda yafi ƙona mini rai” azafafe ta ƙarasa maganar tana jifarshi da harara, duk ya sha jinin jikin shi,
Muryar azeeza kamar zata fashe da kuka tace”Ni dai dan Allah kowa yayi haƙuri, tun da an riga an tafi da deejan mu, Muje mu kwanta dare yayi sosai,” harara haris ya wurga ma azeeza duk da bata iya ganinshi yace”Baki da ƙafa ne? Ki wuce kije ki kwanta ko wani ya ruƙe ki ne”? Da alama dai duk sun fusata,
Jikin danish a sanyaye Ya juya ya nufi azeeza ya ruƙo hannunta yaja ta har zuwa saman gadonta ta hau ta kwanta ya sanya mata bargo ya lullu6e mata Jikinta, kafin Ya koma Saman gadonshi Ya kwanta idanuwanshi na fuskarta ceilling, Angel itace mutun ta farko da ta ta6a bugunshi, karo na biyu kenan tana ta6a lafiyar jikin shi, abun ya tsaya mashi arai,
Ɗaya bayan ɗaya suka nufi gadajensu kowa Ya haye ya kwanta, Ya rage saura angel ita kaɗai a tsaye, tsabar baƙin Ciki Ya hana taje ta kwanta, saboda mugun haushin danish da take ji, ga zarginshi da take Yi, gani take kamar shi ɗin secret Giant ne acikinsu,
Sai da ta bari Kowa Yayi bacci, Ta haura saman gadonta ta janyo pillow ta ɗaura kanta akai, Yau ta juya ma danish baya, ada kullum Juna suke fuskanta idan zasu yi bacci,
Sam ta kasa runtsawa tunanin deeja ya hanata sakat, tarasa ina zata tsoma ranta taji daɗi,
Muryar danish ce ta ratsa kunnata,
“Angel” Ya kira sunanta, Yana daga kwance saman gadonshi, tana ji tayi banza ta ƙyale shi, ya kasa bacci saboda fushin da take yi da shi, Sake kiran sunanta ya yi”Angel” kusan sau Biyar amma bata amsa ma shi ba, miƙewa yayi tare da saukowa daga saman bed ɗinshi, Ya matsa daga gefen gadonta ya zauna, hakan ba ƙaramin ƙona mata rai yayi ba, duk da bata waigo ta kalle shi ba amma taji alamar yana akusa da ita,
Cool voice dinshi ce ta kara ratsa kunnanta, “Am really sorry, I don’t mean to hurt u, just bana son Su cutar da ku ne that’s the reason why na hana ku abunda ku ke ƙoƙarin yi, Giants sunfi ƙarfin ku, ba zaku iya ja dasu ba…..”kamar an katse shi ya dakata da yin maganar yana kallon gefen fuskarta, pillow yaga ta sanya saman kanta ta toshe kunnanta, don ma yasan ba sauraronshi take yi ba, duk sai yaji ba daɗi, Gaba ɗaya ya rasa sukuni, shi dai bai ƙaunar yaga wani na fushi da shi, ko zafin marin da ta yi mashi ɗazu baiji ba, da ace wani ne tayi ma marin nan ko bai rama ba sai ya fusa ta,
“Angel pls talk to me. i realized my mistake, and I regret it, ba zan sake ba” shiru bata tanka mashi ba, ” wannan karan muryarshi tayi zaƙi da sanyi kamar zaiyi kuka, Miƙa hannunshi yayi tare da ruƙo doguwar sumar kanta, aikuwa a fusace ta sanya hannunta da ƙarfi ta ka6e mashi hannunshi,’ batare da ta yi magana ba,
Still baiyi fushi ba ya kuma cewa”Angel if you don’t talk to me, I won’t sleep, I will spend the whole night here” babu wasa a fuskarshi yayi maganar,
Ji take gaba ɗaya ya takura mata, zaman shi agefen gadonta kamar saman kanta take jin shi, Tasan halin shi Ba cikakken hankali ne dashi ba, Yana iya aiwatar da abunda ya fada, Tuna wannan yasa ta miƙe xaune har ya fara sauke ajiyar zuciya atunaninshi ta yafe mashi ne, ashe masifa ta tashi ta zazzage mashi,
Cakumar wuyan rigarshi tayi da hannayenta biyu, ta zazzare mashi manyan gray eyes ɗinta Ta jijjiga wuyan rigar tashi, Saboda masu bayyaci yasa ta sassauta muryarta,
“Wai menene alaƙata dakai ne? Ka addabi rayuwata ka hanani sakat, kai nifa bansan ganin wannan mummunar fuskar taka, na tsani ragon namiji irin ka, pls na roƙe ka ka tashi kabar gefen gadona ko na samu inyi bacci” Takai karshen maganar tare da ture shi gefe, ko motsi baiyi ba, kallonta kawai yake yi da lumsassun idanuwanshi,
A hasale tace”idan har bazaka sauko daga saman gadon ba, Ni zan tashi in baka wuri,” ganin tana ƙoƙarin saukowa daga saman gadon yasa shi yin saurin damƙar hannunta, wani irin mugun kallo ta jefa mashi”sakar mini hannu na,” ba musu ya saki hannun. ta sauko daga saman gadon, Ta dauƙi bargonta da pillow, Ta juya ta nufi tsakiyar ɗakinsu Ta shimfiɗa bargon ta jefa pillown saman shi, Ta haye ta kwanta, duk yana a zaune gefen gadonta yana kallonta,
Lumshe idanuwanta ta yi da niyar bacci ya ɗauketa, kamar daga sama taji an sanya hannu an ɗauketa da ita da bargon da pillown duka ya tattare su ya ɗaga sama Ya nufi gadonta, Yana zuwa ya jefe ta saman gadonta, aɗan tsorace ta ware idanuwanta tare da wurgasu kan fuskarshi Yana atsaye ya kafe ta da ido, Tsabar mamaki ya hana ta furta komai, kamar walƙiya haka Yaje ya daukota,
Cikin nuna jin takaici tace”Nashiga uku! Wai ina ruwanka dani ne? idan na kwana a ƙasa matsalarka ce ko tawa”? Ya bata amsa da cewa”tamu” guntun tsoki taja, bata ƙara furta mashi komai ba, tana jin motsin shi abayanta, haukanshi na matuƙar ɗaure mata kai, Lokacin da bacci yayi awon gaba da ita, A zaune ya fara gyangyaɗi, A ƙarshe da baccin yafi ƙarfinshi a bayanta ya kwanta saman gadonta, lallai ya taro march,
*ANEELAH*
Wuraren ƙarfe 12 na safe, Tana a ƙudundune Cikin bargonta, Tun bayan sallar asuba data kwanta bacci bata farka ba, wani irin nauyin bacci ne ya ɗauketa, Hada ƙarin maganin muran da tasha a daren Jiya,
Baby junaid ne ya shigo cikin ɗakin yana azaune Cikin motar shi ta wasan yara, Da hannu Yake juya streering wheel ɗin motar, Ba ƙaramin kyau yayi ba, jump suit ne a jikinshi launinsu ɗaya da ƴar motar wasan shi, Army green, da alama ba ƙaramin daɗin motar yake ji ba, daga ya juya steering saita tafi da gudu, agaban gadon Mommynshi Ya tsaya, tare da kai hannu ya danna wani maddani A jikin motar, nan take motar ta soma yin Jiniya, Afirgice aneelerh Ta farka tare da yaye bargon data lullu6a dashi hannunta dafe da ƙirjinta, jallabiya ce a jikinta, Muryarta na kerma take ambaton” Innallahi wa’inna ilaihirraji’un”
tayi matuƙar tsorata, Duk a tunanin ta ƴan sanda ne suka zo gidan ashe motar wasan junaid ce, Fuskarta a yamutse take kallon shi, ya wage baki yana dariya fararen hakoranshi tar dasu, Dimples ɗinshi biyu sun lotsa sosai, a fusace ta miƙa hannu ta ɗauki pillow ta wurga mashi saman fuskarshi, nan take ya kwa6e fuska zai yi kuka,
Cikin nuna 6acin ranta ta soma Yi mashi magana”Karka kuskura kace zaka yi mini kuka stupid, Wlh nayi regretting dana fidda kuɗina na siya maka motar nan ashe kaina abun zai ƙare!, bazaiyiyu ba ka hanani kwanciyar hankali, zan 6a66alla motar In jefata cikin bola kowa ya huta” Jin wannan maganar yasa shi ƙara sautin kukan nashi, Ganin tana yunƙurin saukowa daga saman gadon yasa jin tsoro, gudun kada ta 6alla mashi motarshi kamar yadda tace, aikuwa da sauri yaja streering Ya juya motar da gudu yajata ya nufu ƙopa, Murmushi ta saki tana bin bayanshi da kallo, aranta tace”Allah kaɗai yasan irin ƙalin sharrin da zaije yayi mini a wurin mami, yau nifa na shiga uku, Wata’ƙil ma yaja a hanani Yin breakfast, ” takai karshen maganar tare da saukowa daga saman gadon takai hannu ta ɗauko filon data jefa mashi a ƙasa ta wurgo shi saman gadon, miƙa tayi tare da yin hamma ta wuce toilet, after some minutes ta fito tana tafiya a slow ta nufi gaban mirror ta zauna, wata irin yunwa take ji kamar taci ƴan hanjin cikinta, wayarta ta ɗauka dake ajiye gaban mirror, ta danna power hasken screen ɗin ya kawo, hoton angel ne a matsayin wallpaper ɗinta, ta yi mata hoton ne saman gado tana bacci ta saki baki, Tana matuƙar son angel, Tayi missing ɗinta sosai, duk rana ta Allah idan tafarka daga bacci ta ɗauki wayarta saita sumbaci hoton, Yanzu ma kiss ta manna mashi, aranta tace”I really missed u angel, kamar in yi hauka, Allah ya kare mini ke aduk inda kike, Inaji araina cewa Kina araye kuma kina tunani na, I luv u so much” tuni hawaye sun Cika idonta,
Tana yunƙurin miƙewa daga saman mirror chair ɗin, Sai ga Ana Mai aikin gidansu ta faɗo Cikin ɗakin tana Haki hannunta ruƙe da wayarta, Jikinta sanye da Riga da skirt, Sun matseta, Hankalin aneelerh ba ƙaramin tashi yae ba, Ta cikin mirror ta hangota, da sauri ta ƙarasa Juyawa Baya tana kallonta tace”Ana lafiyarki kuwa? Babu neman excuse kin faɗo mini ɗaki? Kamar wadda tasha ƙwaya”? Tayi maganar tana tunkararta, Duƙar dakai ƙasa ana tayi Muryarta na ɗan rawa tace”Am sorry madam, Wani abune na gani daya bani mamaki, shi ne nazo in nuna maki,”
Matsawa aneelerh tayi kusa da ita, Tare da miƙa hannu ta kar6i wayar Ana, tana ɗaura idanuwanta kan screen ɗin, Ras taji gabanta ya faɗi waro ido waje tayi tana kallonta, mamaki ƙarara akan fuskarta tace”Abun mamaki! ana a ina kika samu hoton nan? Kuma daga gani sabuwar ɗauka ce!” murmushi ana ta ɗan saki kafin tace”Yanzun nan Na ganshi A instagram, shafin twins Na Family ɗin Obinna, Zayn da zaid pravin Obinna, Su ne su ka yi posting ɗin a page ɗinsu na insta, madam i was shocked da naga pic ɗin nan nace ashe matar nan tana araye da ranta da lafiyarta! ” jinjina kai aneelerh tayi da alama tayi matuƙar girgiza tace”Wonders shall neva end” kallon Ana tayi tare da cewa”Ki jira ni ina zuwa, dole mami taga hoton nan, amma dai matar nan ta bani mamaki matuƙa” Jiki na rawa aneeleh ta fuce daga Cikin ɗakin, gudu gudu sauri sauri ta nufi bedroom ɗin mami, bayan tafiyarta ana ta fito ta tsaya a falo tana jiran dawowarta,
Aneelerh Na yunƙurin yin sallama a ƙopar ɗakin Mami, sai ga mamin ta fito Jikinta sanye da riga da zani na atampa, Ƙiris Ya rage su bangaji juna ita da aneelerh, Sakin baki mami tayi tana kallonta,
Da sauri aneelerh tace”Am sorry mami, a ruɗe nake ne, wani abun mamaki ne Ana ta gwada mini acikin wayarta, Shi ne na kawo maki kema ki gani” tana inda inda tayi maganar, tare da miƙa ma mami wayar hannunta, tasa hannu ta kar6a, koda mami ta kalli hoton saita ruƙe ha6arta da hannu ɗaya, ta ɗan zaro ido da mamaki akan fuskarta tace”Kai! Wa nake gani kamar BENAZIR”! aneelerh tace”Mami itace, Kalli dakyau ki gani, ba’a jima da yin posting ɗin ba, ” Mami tasha ruwan mamaki, Sai ƙarewa hoton kallo take yi, dagaske ɗin dai benazir ce, Daga gani hoton batasan an yi mata shi ba, tana a tsaye, hannunta ɗaya ta dafa murfin danƙareriyar motarta, tsadaddiyar gaske, jikinta na sanye da business suit black colour sunbi shape ɗinta sun zauna mata cuf cuf, kamar don ita aka ƙera kayan, hips ɗinta sun fito sosai, hannunta ruƙe da wayarta ƙirar i phone 15 pro, kanta babu hula ko ɗan kwali, Zallar gashin kanta ne daya sha gyara Har midback dinta, idanuwanta na manne da glass, idan ka ganta a hoton ba zaka ta6a yarda cewa ta ta6a aure ba, Ko tana da ƴa, saboda tsabar haɗuwarta, Jikinta Badai kyau ba, agogon diamond ɗin dake sanye a hannunta, a ƙalla Price ɗinta yakai 100m,
Kallon Juna mami da aneelerh su ka yi kowa Fuskarshi ɗauke da al’ajabi, mami tace”Abun mamaki baya ta6a ƙarewa, Wai dama ƴar nan tana nan da ranta da lafiyarta? Hankalinta kwance tsawon shekara da shekaru bata ta6a waiwayar ƴarta da mijinta ba, Anya kuwa benazir ce aneelerh? Kodai watace me kama da ita? to ae abunne da ɗaure kai wlh, ‘
Murmushin takaici aneelerh ta saki tare da cewa”wlh mami itace! Babu shakka benazir ce, ae ina ganin hoton ko doubting ban yi ba, na shaida itace, Kinsan dama ita tun fil’azal wayayyiyar macace akwai son gayu, Kuma tafi sha’awar rayuwar ƴanci, ” mami tace”Haka fa take, Oh Ni ƴarsu, duniya da abun tsoro take, Anya kuwa Benazir tasan ciwon kanta”? aneelerh tace”Ina fa, ae babu alama, Yanzu haka ko Iyayenta basu da masaniya akan inda take rayuwa, Duk da Naga kamar Ƙasar waje ne, idan kika ƙura ido a jikin Ginin dake a bayan hoton an rubuta Rbc (Royal bank of canada) dake acikin toronto, Kuma ga dukkan alamu mami hoton bada saninta aka ɗauke shi ba, don da ace ta sani da bata bari an ɗauke shi ba, kodan kada asirinta ya tonu agane inda take, tun da ko Iyayenta basu son awace nahiya take zaune ba suma nemanta suke Yi ruwa ajallo,”
Mami tace”Nama rasa me xance, kawai dai Allah ya shiryeta in me shiryuwace, amma dai wannan rayuwar da ta ɗaukarwa kanta bamai 6ullewa bace, Wlh zata yi danasanin mara amfani, kwata kwata benazir bata yi wayau ba, Allah kanta tayi mawa, Ace da ranka da lafiyarka, Ka gudu kabar Jinjira acikin kwamin wanka, da mijinka batare da ka waiwaye su ba almost 4 years, Saboda shafewar basira da rashin hankali, tana can tana yawon biɗiɗi,” takarasa maganar tare da jan dogon tsoki Ranta ya 6aci ta miƙe ma aneelerh wayar”kar6i nan nagaji da ganin kayan takaici,” kar6ar wayar aneelerh Tayi, Har ta juya zata Bar ƙopar ɗakin mami sai kuma ta ɗan dawo baya tace”mami Baby junaid fa”?
“Yana aciki kwance saman gado yana bacci, Yazo yana kuka ya faɗa min wai kin ce zaki 6alla mashi mota, Daƙyar na samu na lallashe ya daina kuka ya kwanta,” dariya aneelerh tasaki tare da cewa”Ya takura mun ne mami, ina tsaka da yin bacci na ya daddage ya danna jiniyar motar, baki ga yarda na zabura ba, Ni nayi tunanin ƴan sanda ne suka zo ashe shine” Dariya mami tayi tana girgiza kai tace”Allah ya shirya min jikana, ” aneelerh ta amsa da amin, kafin Ta juya ta nufi falo, Agaban dining ta hango ana tana jera kayan breakfast ɗinsu, Ƙarasawa tayi inda take atsaye ta miƙa mata wayar tare da yi mata godiya, don ba ƙaramin daɗi taji ba, atlease tasan benazir tana araye, Idan Allah yasa suna da tsawaicin kwana wata rana Allah zai haɗa su ne, ta wani 6angaren kuma Abun ya tsaya mata acikin zuciyarta, Irin yadda taga benazir a hoton hankalinta kwance babu wata damuwa akan fuskarta,
Yinin ranar da tunanin benazir tayi shi, Da rana ne Abie Ya dawo daga wurin aikinshi, Yazo musu da babban albishir Na ƙara mashi matsayi da akayi zasu koma Abuja da zama, mami tayi farin ciki, aneelerh kuwa sam bataso haka ba, Ita fa duk wani abu da zai rabata da jos ba son shi take Yi ba, gani take kamar idan ta ɗaga ƙafa tabar garin shikenan ba zata ƙara ganin mutanan nan ukun da ta rasa ba, waɗanda a koda yaushe take Addu’ar Allah ya Bayyanar mata dasu, babu yarda ta iya yanzu dole tabi iyayenta don bata son rabuwa dasu, tafi so duk Inda zasu je ƙafarta ƙafarsu,
*Back To prison*
Ƙwaƙƙwaran Juyi angel tayi da niyar ta gyara kwanciyarta, sai ji tayi an tokare bayanta, A matuƙar ruɗe ta juyo tana kallonshi, waro ido waje tayi ganin danish saman gadonta, Aikuwa rai a6ace ta sanya ƙafarta da ƙarfi ta ture shi gaba ɗaya ya gangara ƙasa Kanshi Ya bugu sosai har saida yafirta”ash!!” saboda zafin da ya ji, Zazzaga mashi masifa ta soma Yi ta inda ta shiga bata nan take fita ba, sautin muryarta ya karaɗe Kunnuwan masu bacci ɗaya bayan ɗaya su batool suka dinga farkawa Suna tambayar lafiya me ya faru?
Nuna danish ta yi da yatsan Hannunta tace”wlh kaɗan ka gani, Idan har baka fita sabgata ba, Ina mace kana namiji Ka kwana a gadona, Salon kawai kaja mini zunibi,” Tun da ta fara Yi mashi faɗa, bai motsa daga kwancen da yake a ƙasa ba, ya dafe gefen goshin shi da hannu, Yaji zafin buguwar da kanshi yayi,
Saukowa su batool su Ka yi daga saman beds ɗinsu, fuskokinsu duk A yamutse idanuwansu sun kumbura sakamakon kukan da suka sha Jiya da za’a tafi da deeja,
Abakin gadon angel suka tsaya suna kallonsu ita da danish, Ta rufe ido sai faɗa take mashi hada pillow ta jefe mashi saman fuska, Ya rasa ina zai tsoma ranshi yaji daɗi, shouting ɗin da take yi mashi ba ƙaramin gigita shi yake yi, daurewa kawai yake yi,
“Pls angel, Ki yi haƙuri Ki ƙyale shi hakanan, kodan saboda lallurarshi ta rashin son hayaniya zai iya rikicewa, Hanna ce tayi maganar, angel ta watsa hannu tare da cewa”Idan ya tashi ya haukace ƙarewa ma, wlh ko ajikina, tun farko saida naja mashi kunne akan ya ni santa kanshi dani amma yaƙiya, saboda head fish ne dashi”
Girgiza kai batool ta ɗanyi idonta akan angel tace”Sister badan halina ba, Pls Ki bar maganar nan, Ki barshi yaji da kanshi, Nasan kina fushi dashi ne saboda abunda ya faru jiya, Ki yi haƙuri ki manta komai, kuma ki daina fushi dashi saboda Baya ƙaunar yaga ana share shi, Yana shiga damuwa” daƙyar batool takarasa maganar ganin irin kallon da angel ke jefa mata,
Gyaɗa kai tayi tare da jinjina kai tace”Shikenan zan ƙyale shi amma babu ruwanshi dani! Ni kawai bana son Yana kallona ko Yana yi mini magana, ” Tana kammala maganar ta sauko daga saman gadonta ta bi ta gefensu Ta shige toilet,
Zuƙunnawa batool tayi agaban Danish Ta ruƙo hannunshi acikin nata, Ba ƙaramin tausayin shi taji ba, ganin sahun marin da angel tayi mashi asaman fuskarshi har yau bai disashe ba,
Cikin sanyin murya tace”Am sorry danish, Kamar yarda tace ka ƙyale ta, to ka rabu da ita har zuwa time da zata huce, if not zata cigaba da Ƙyararka ne, Nasan zata dawo da kanta ne ta nemi yi maka magana,” sai lokacin ya samu ya miƙe zaune, ya jingina bayanshi jikin bango, ɗaya bayan ɗaya ya shiga binsu azeeza dake atsaye da kallo, matan ne gaba ɗayansu, Sai daga bisani Haris da su naufal Suka Sauko daga saman gadajensu, A inda yake zaune suka tsaya cirko cirko suna kallon shi,
“Kuma fushi ku ke yi da ni? Kamar yadda take fushi dani”? Yayi masu tambayar idonshi akansu, atare suka haɗa baki wurin cewa a’a, Kallon haris yayi tunkafin yayi mashi magana haris yai saurin cewa”am not angry with u, kaima ka sani bazan iya fushi dakai ba, just banji daɗin abunda ya faru ba jiya, amma komai ya riga daya wuce” jinjina kai danish yayi kafin ya kuma cewa”komi nake yi ina yi ne saboda ku, amma nasan zaiyi wuya ku fahimci hakan, sai nan gaba”
Naufal yace”Pls danish, mu komai ya wuce awurinmu, abunda ya faru ya riga daya faru ba wanda ya isa ya dawo dashi baya, so pls mu manta kawai, baida amfani tuna baya,” Danish yace”idan ku kun fahimce ni, ita taƙi ta fahimce ni, tun daren jiya nake bata hakuri amma taƙi ta saurare ni,” sai lokacin suka gane inda damuwarshi ta dosa, dama shi haka yake sam baya son wani yana fushi dashi tun fil azal, gaba ɗaya yake rasa sukuni,
“Danish kada ka damu kanka, In dai angel ce Zata kula ka, Ae bata iya fushi ba, tana da saurin hawa da kuma saurin sauka,” acewar javed,
Ta6e baki yai tare da cewa”Its okey, ngde da kulawarku agare ni, ” daga haka Ya miƙe jiki ba ƙwari Ya Nufi toilet, domin yin wanka,
Kafin Giants su kawo musu Breakfast ɗinsu, Sai da kowannan su Ya yi wanka, Basu jima da hallara A cikin ɗakin nasu ba, Sai ga Giants ɗin sun shigo ɗauke da kayan abincinsu, bayan sun ajiye musu saman dining carpet, duk suka zazzauna kewaye da farantan, Yau farfesun naman kaza aka kawo musu da zafinshi hada tiriri Yaji kayan ƙamshi, ga kuma dambun nama da aka haɗo musu dashi, sai Kayan marmari kamar kullum da kuma soft drinks, Abun na ɗaurewa angel kai, ganin irin badagon da ake yi da nama agidan kurkukun, sam bata yarda da irin wannan Lafiyayyar cimar da ake kawo musu ba, kullum basu da abinci sai nama kala kala! Na kaza na shanu na rago, wani naman ma batasan na wace dabbar bane, tana yawan tambayar kanta ko su wanene ke girka abincin kurkukun daga gani ƙwararru ne a 6angaren catering, sun iya sarrafa abinci, wani naman saboda tsabar dahuwar shi kana jefa shi abaki tunkafin ka taune da haƙori zai dagargaje da kanshi, ita dai fargabarta kada ace abincin da ake basu su naci, da ransu za’a fanshe, duk in zuciyarta ta saƙa mata hakan sai taji gabanta ya faɗi rasss! Don kuwa ko gwamnati bata aikin banza, balle kuma mutanan da Ba Allah ne aransu ba, Sunsan dalilin dayasa suke basu lafiyayyan abinci wata’ƙil kodan suna amfani dasu ne, Allah wa’alamu
kafin su fara Shan farfesun saida ta tunasar dasu akan su yi bismilla, Kullum ne sai ta tuna musu, hatta haris yau da tace su yi bismillah sai da yayi duk da bai musulunta ba, danish ne kawai baiyi ba, Ta lura dashi duk wani abu daya ƙunshi sunan Allah aciki bai furta shi, hakan ba ƙaramin ƙona mata rai yake yi ba, Har suka kammala cin abinci, da zarar sun haɗa ido dashi sai ta dinga jefa mashi harara, duk yabi ya tsargu ya hana zuciyarshi sakat, farfesun ma ba’a cikin kwanciyar hankali yasha shi ba,
Bayan sun kammala Cin abincin, Giants suka tattara farantan Suka fuce daga Cikin ɗakin,
Ganin suna yunkurin zuwa saman gado su kwanta ne, yasa angel ta dakatar dasu, tace su motsa jikinsu, Idan sun kammala su watsa ruwa ajikinsu, Sannan Sun kwanta su huta, babu musu suka amsa mata da toh, banda danish da haris, tuni sun haye saman gadajensu, Shi haris damuwar rashin deeja ne yasa shi ƙin ta6uka komai, tunanin abunda ya faru daren jiya kafin atafi da ita ya tsaya mashi arai, Yaji tausayinta sosai, su kansu sauran ƴan uwan nasu sun damu da deeja, Ba yadda zasu yi ne shiyasa suka barma Allah komai,
A tsakiyar ɗakin suka Jera layi suna yin exercise, kamar wasan ƴar tseral haka suka dinga zubawa da gudu idan suka kai ƙarshen bango sai su dawo su sake komawa, Sai da suka tara uwar zufa ajikinsu tukunna kowa Ya nufi toilet domin watsa ruwa, Bayan sun fito ne, parveen ta matsa ma angel akan tayi mata irin kalabar da tayi ma su azeeza, Dama tun ranar da ta ganta ta kwallafa rai akan tana so itama, kafin marece yayi angel tayi ma parveen kalaba biyu akanta, ba ita kaɗai ba hada rubina tayi mawa, Bayan ta kammala musu kitson, Kowa Ya koma saman gadonshi ya zauna, Fira suka soma yi atsakaninsu acikin firar ne, suka tambaye ta, wai da tace musu wata rana zasu fita idan suka fita ina zasu je? Su da basu san komai na wajen kurkuku ba, murmushi tayi tare da cewa su kwantar da hankalinsu, Gaba ɗayansu zasu yi rayuwa agidan daddynta, Tace daddyna yana da gida, kuma gidanmu ɗaki Shida ne, Akwai palour ɗaya, dani da azeeza da batool zamu ware ɗaki ɗaya, Parveen da deeja da hanna zasu ware nasu ɗakin ɗaya, sai Eve da hibba da rubina suma zasu ɗauki ɗaya, nawa kenan? Suka ce mata Uku, tace toh, sauran ɗakunan guda uku, Javed da Naufal tare da Mubeen zasu ɗauki ɗaya, sai Haris shi da wancan Maji daɗin gadon suma zasu ɗauki ɗaki ɗaya,” da ta ambaci maji daɗin gado hada harara ta wurga ma danish, ya lumshe idanuwanshi tamkar baiji me tace ba,
Azeeza tace”Saura ɗaki ɗaya ya rage, wa za’a bamawa” angel tace”Na daddyna ne idan Allah yasa yana araye, ko ince daddynmu” gaba ɗaya suka saki murmushin farin ciki, parveen tace”amma kina ganin daddynki zai so mu,” angel tace sosai ma, In ma daddyn nawa baya araye, zamu zauna wurin auntyna adama ne, Ko gidansu aunty aneelerh na, zasu ɗauki nauyin duk wani abu da zamu buƙata, Cin mu shan mu da suturarmu, kuma zamu yi rayuwar ƴanci, Zamu je inda muke so, Muje shan ice cream, muje cinema kallo, hada shopping mall zamu dinga zuwa kowa ya za6i abunda yake so, ” parveen na murmushi tace”Zamu dinga samun abinci akai akai”? Dariya angel tayi tare da cewa”Sau uku arana, za’a bamu breakfast, lunch and dinner, Idan ma kinga dama tsakar dare kika farga da yunwa zaki Iya zuwa kitchen ki girka abunda ranki yayi maki, ” Gaba ɗaya suka sanya ihu suna murna jin tace zasu Iya girki da kansu, Ga kuma abinci available, A lokacin jikin angel yayi mugun sanyi, ganin yadda suke ta farin Ciki, gani take kamar bazasu rayu ba, balle aje ga maganar fita daga Cikin wannan Kurman kurkukun ƙaddarar,
Batool tace”wlh angel baki ji irin daɗin da naji ba, sai naji dama ace yau mu fita daga kurkukun nan, muje gidanku, kinga shikenan mun rabu da giants, bazasu ƙara zuwa su ɗauki wani acikin mu ba, balle har su cutar dashi,”
Azeeza tace”Nima na ƙosa inga ranar da zamu fita daga prison ɗin nan, wlh Ina so inyi rayuwa irin wadda ki kayi tare da daddynki, ae kince mana zai so mu, muma zai maida mu kamar ya’yanshi, zai dinga zuwa damu yawo yakaimu wuraren da kika bamu labari ko”? Angel tace”Eh, kuma koda ace babu daddyna, akwai sauran dangina duk zasu so ku, kuma zasu gatanta ku kamar ya’yansu ku,” acikin zuciyarta tace”sai dai fitar ce keda wuya, bansan ya zamuyi ba, gidan kurkukun nan yafi ƙarfi na, sai dai bai fi ƙarfin mahaliccin mu ba,
Har dare Yayi suna fira Gwanin ban sha’awa, ta faranta musu sosai, Bayin Allah sun ƙwallafa rai da son yin irin rayuwar da tayi, wato rayuwar ƴan ci, yanzu a shirye suke da zarar sun samu hanyar fita zasu bita ne, hmmmmmm
*❤❤❤PRISONERS❤❤❤*
Saboda daɗin fira yasa suka dawo bakin gadon angel kowa ya samu wuri a gefe da gefen gadon suka zauna waɗanda basu samu wuri ba daga ƙasa suka zauna, Javed hada ƙoƙarin ɗauko fitilun ɗakin guda uku Ya kunna a ƙasa ya ajiye su, ɗakin ya yi haske, sun ɗauki tsawon lokaci, sai da angel taga sun fara gyangyaɗin bacci, ta Katse masu firar tare da cewa”its time to sleep, Kowa Yaje ya kwanta, gobe in Allah ya kai mu da rai da lafiya zan ƙarasa baku labarin” suka amsa mata da toh, ɗaya bayan ɗaya kowa Ya miƙe suna tafiya suna bangaje juna a haka suka nufi gadajen su, har sun kwakkwanta Muryar angel suka ji yo tana cewa”Su yi addu’a kafin su kwanta” suka amsa mata da toh,
Danish yana lafe saman gadonshi, ya lumshe idanuwanshi, amma babu alamun bacci yake yi, Gyara kwanciyarta ta yi, yau bata ju ya ma shi baya ba, suna fuskantar Juna,
Ganin yana mutsu mutsun buɗe idanuwanshi yasa tayi saurin Fuskantar ceilling, tare da rufe idanuwanta, Sam bata ji lokacin daya sauko daga saman gadonshi ba, sai dai taji hucin numfashin mutun yana kokawa da Nata numfashin, da sauri ta buɗe idanuwanta, Tsabar firgitar da ta yi ne yasa ta zare ido, Ganin fuskarshi a kusa da ta ta, Saman gadonta Ya hau Ya yi mata rumfa da ƙirjinshi, ƙiris Ya rage tsinin hancin shi ya gogi nata, Tsananin mamaki ne Ya kamata, Tuni ta shiga ruɗanin kome zai yi mata, Gashi ya tsareta da idanuwanshi ko ƙyaftawa babu, muryarta na inda inda tace”La..fi..ya”!? Yace”haƙuri nazo na baki, ki daina fushi dani, tun jiya baki yi mini magana ba, Idan muka haɗa ido sai ki ta harare na,” daƙyar yakai ƙarshen maganar throat dinsa na moving kamar yana swallowing ɗin wani abu, yana ganin ta fara yunƙurin motsa la66anta alamar zata yi magana da sauri ya ɗaura dogon yatsan shi saman ƙaramin bakinta, Cikin sanyin murya yace”Pls don’t shout at me, Idan kinsan ba me daɗi zaki faɗa mini ba, Kiyi shiru kawai, nafa baki haƙuri, Kuma na gane kuskure na,”
Hawayen da ta gani kwance a cikin fararen idanuwanshi ne yasa taji zuciyarta ta karaya, sai ma taji tausayin shi yakamata, Shi dai haka rayuwarshi take, Yana da matuƙar saukin kai, ga haƙuri matsalar shi ɗaya ragwanci, hannu tasa ta kawar da yatsanshi daga saman bakinta,
Sai da ta fara jefa mashi harara, kafin tace”Zan yafe maka amma sai ka yi mini alƙawarin wani abu” yace”komene ne zanyi” ɗan ta6a baki tayi tare da cewa”kada ka ƙara bari a ɗauki wani daga Cikin mu, Saboda nasan kana da ƙarfin da zaka Iya hana wa” tunkafin ta karasa maganar, Yae saurin girgiza kai yana faɗin”That’s impossible, ki fahimce ni, Ni ba kowa bane face prisoner, bani da ƙarfin da zan Iya yin fighting da giants, sunfi ƙarfina, idan ba so kike in rasa raina ba”
tsoki taja”hmmm dama nasan haka zaka ce, Idan har dagaske baka da ƙarfi, to ta ya akai ka ke Iya shiga toilet bayan na datse ƙopa ta Ciki? Kuma ya akai ka iya 6a66ako glass door ɗin dake acikin toilet, tun daga tushen shi, taya zan yarda da maganganunka? Ta yi tambayar tana kallon cikin idanuwanshi, Har lokacin yana a yadda yake bai ɗago ba,
Runtse idanuwanshi ya yi, tare da biting lower lip ɗinshi, A hankali ya ɗan ware su akan fuskarta, Muryar shi arauna ce ya soma magana”Bansan ya zanyi in fahimtar dake ba Angel, Ni kaina bansan Ya akai nake iya shiga wurin dake a rufe ba, Also ƙarfin da yazo mini time dana cire glashin nan yanzu babu shi ajikinta….” kawar da kanta gefe tayi tare da cewa”Ban yarda dakai ba, danish Ina zargin kai ma Giant ne, kamai da mu shashasha kana 6oye mana ainihin wanene kai, Sannan kuma kasan Komai game da kurkukun nan, Amma kaƙi ka sanar damu, kafi so mu yi ta shan wahala har mu rasa rayukan mu, Kana ji kana gani ana cutar da rayuwar ƴan uwan mu amma kai hankalin ka kwance, Ko ajikinka…..’ Kafin ta rufe bakinta, Taji saukar ɗigon ruwan acikinsu, da sauri ta kalle shi, Hawayen shi ne suka sauka cikin bakin ta, Yana girgiza kai yace”angel stop accusing me, am not a giant, Bana jin daɗin maganganun da kike gaya mini, its hurting my heart,” Daƙyar Ya kai karshen maganar, wani irin raɗadi zuciyarshi ke Yi mishi, idan akwai abunda ya tsana Ya biyo bayan Giant, Yaji zafin Kalaman angel fiye da zafin marin da ta yi mi shi, ita kanta angel da ta yi maganar sai daga baya ta yi danasanin furta mashi zargin da take yi akanshi, bata ta6a ganin fushi akan fuskar danish ba, sai yau, Jikin shi har kerma yake Yi, wurin saukowa daga saman gadonta, da sauri ta mike xaune tana kallon shi, Ji take kamar ta kira shi ta lallashe shi, girman kai ya hana tayi hakan, Ta yi tsammanin zai kwanta asaman gadon shi ne, amma sai taga ya ɗauki pillown shi tare da bargonshi, bai nufi ko’ina ba sai cikin toilet area ɗinsu, duk sai taji ba daɗi, Ya rasa ina zai kwanta sai cikin toilet, In da madaddalar shaiɗanu suke? Dama Ya lafiyar giwa, har ta koma ta kwanta da niyar tayi bacci amma sai ta gaza runtsawa, Damuwa duk ta cika ta, a ƙarshe dai ta ji bazata Iya jurewa ba, ta miƙe Ta sauko daga saman gadonta, sai da ta fara zuwa gaban table ta ɗauko fitila ta nufi cikin sashen toilet ɗin, Tana zura ƙafarta Ciki, ta same shi a kwance saman shimfidar da yayi, hawaye ta ko’ina asaman face ɗinshi, ya lumshe idanuwan shi jin motsin mutun yasa shi ɗan buɗe idanuwan da suka canza launi, koda ya yi arba da ita sai ya ju ya mata baya, A ƙasa ta ajiye fitilar ta zauna gefen shimfiɗar tashi, Kusan mintuna tana kallon gefen fuskarshi, Daƙyar ta iya buɗe baki ta soma magana,
“Danish fushi ka ke yi dani? nayi nadama, da nasan kalamaina zasu 6ata maka ranka, da ban furta maka su ba, nima na faɗi ne kawai badan ina nufin hakan ba, ” Babu irin lallashin da bata yi mishi ba, amma ɗan tahalikin nan yaƙi tanka mata, Muryarta a karye tace”Nagaji da lallashinka, Kaga Idan ma bazaka haƙura ba, to ka tashi mu koma ɗaki ka kwanta, Amma kwana a wurin toilet ɗin nan sam bai dace ba, Akwai shaiɗanun aljanu zasu iya cutar dakai,’ sai lokacin yace”Meye damuwarki idan sun cutar dani? Jikin ki ko nawa”? Ta bashi amsa da cewa”Namu, saboda na damu dakai, dani dakai abu ɗaya ne, jinin dake yawo ajikin ka shi yake yawo ajikina, taya ɗan uwa zai share ɗan uwansa? Duk da nasan laifina ne amma na gane kuskure na na yin fushi dakai bazan ƙara ba,” Bai ƙara tanka mata ba,
“Pls danish, mu koma ɗaki, ” magiya ta dinga yi mashi amma yaƙi tanka mata, har ta fara tunanin ko ya yi bacci ne jin shiru, matsawa ta yi sosai kusa dashi, ta ɗan kwanto saman jikin shi tana leƙen fuskarshi, ya rufe eyes ɗinshi, kamar ya fara bacci, yanke shawarar ɗaukar shi ta yi kamar yarda ya ɗauketa jiya da ta yi fushi ta kwanta a ƙasa tsakiyar ɗakin su, Murmushi ta saki yayin da take nannaɗe hannun rigarta, tana kammalawa, ta soma kiciniyar ɗaukar shi, duk yana jin motsin hannayenta a bayanshi, wani irin nauyi ne dashi yadda kasan dutse, Ta tattara Iya ƙarfinta na ƙarshe ta ɗaɗɗago dashi, ta samu ta raba shi da saman bargon, tana ƙoƙarin Juyawa don ta nufi ɗaki dashi, wani irin nauyi Ya fisgeta, ba arziƙi ta sake shi ta rubza saman jikinshi, tana faman haki hana nishi kamar wadda tayi uban gudu, bawan Allah, kanshi ya bugu sosai, ba yadda ya iya, Jarabar angel tafi ƙarfin shi, har time ɗin bai buɗe idanuwanshi ba, bai kuma motsa ba, saboda nauyin jikinta dake asaman nashi, Babu alamun zata ɗaga shi, ta kifa kanta saman kirjinshi, sumar kanta duk ta tarwatse, slowly ya ɗan ware idanuwan shi, ya ɗaurasu akan sumar kanta, Muryarshi na ɗan rawa ya ambaci sunanta””An..gel” Ƙasa ƙasa ya furta sunan, bata amsa mashi ba. Kuma bata ɗago ba, ranshi ne ya bashi cewar kodai tayi bacci ne
Zagayo da hannayen shi yae saman bayanta, a wannan yanayin bacci ya yi awon gaba su, manne da juna,
A washe gari
Haris ne ya fara farkawa daga Bacci, Cikin buƙatar zuwa toilet, Saukowa Ya yi daga saman gadonshi ya nufi toilet yana hamma tare da yin miƙa duk a lokaci ɗaya, Zura ƙafar shi keda wuya ya yi arba da su angel dake a kwance saman bargon danish, sun ƙanƙame juna suna bacci, Yadda kasan tip da tyre, Tsabar mamaki ne ya kama dashi, har wani leƙen su yake yi don ya gane ma idonshi da kyau, hada sanya hannu ya ruƙe ha6arshi, can kuma sai ya saki murmushi, Mutumin da ke jin fitsari maimakon ya shiga toilet, Sai ya juya saboda gulmar data ciyo shi, Jikin shi har rawa yake Yi, wurin komawa cikin ɗakin, agaban gadajensu Javed, Yaje yana tashin su daga bacci, ɗaya baya ɗaya ya dinga tada su, Kowa Ya mike yana miƙa da hamma tare da tambayar shi lafiya? Yace musu Su zo suga wani abun ban mamaki, Koda jin haka jiki na rawa, Kusan atare suka sauko daga saman beds ɗinsu, lokacin da su batool suka shiga, Suna Yin arba dasu Danish manne da juna, Kowa Ya buɗe baki haɗi da zare ido, Kamar sun samu tv, A kewaye da shimfidar Suka zuƙunna suna kallonsu, Yayin da su masu baccin basu san wainar da ake toya ba,
Angel ce ta fara farkawa, A hankali ta ɗago da kanta daga saman ƙirjinshi, ras taji gaban ta ya faɗi ganinta ajikin danish, sam ta manta meya faru jiya, waro ido ta ɗanyi tare da sanya tafin hannunta ta rufe bakinta, Gyaran miryar Da haris yai mata ne yasa tayi wuff ta sauka daga saman jikin danish ta koma gefe ɗaya, Ta yi tunanin zata ga haris shi kaɗai amma sai ta gansu kaf ɗinsu kewaye dasu, Tawaga guda, sun baza na mazurinsu suna kallon Ikon Allah, Muryarta na in ina tace”Am..kun..gane..jiya..um” bata ƙarasa maganar ba, Batool tace”Ai mun riga mun gane komai ba sai kin yi mana bayani ba,” azeeza tace”ƙwarai kuwa, Aljanu ne suka kawo ku nan, koba haka ba”? Ta yi tambayar tana kallon faces ɗinsu Hannah, har suna haɗa baki wurin cewa eh, wani kallon rainin wayau taga suna Yi mata, Kafin ta ƙara furta wani abu, danish ya farka yana kokarin buɗe idanuwanshi, Biji biji yake iya ganinsu, Haris yakai hannu ya bugi ƙafarshi”tashi ka yi mana bayani, meya faru a daren jiya,” gaba ɗaya jikin shi kasala yake Ji, Yunƙurawa Yayi tare da miƙe wa zaune, a lokacin idanuwan nashi sun washe yana ganinsu, One by one ya dinga binsu da kallo, sai wani sakin murmushi suke Yi kamar sabbin mahaukata, ɗauke eyes ɗinshi yae daga kan fuskokinsu, Ya mayar dasu kan angel da tayi wuƙi wuƙi da ido, Suna haɗa ido dashi, ta fara zazzaga mashi masifa”Duk kai kaja mini ina zaman zaman lafiyata, Tun farko basai da nace Ka koma ɗaki ka kwanta ba amma saboda kafiya irin naka kaƙi jin maganata, Ka nace saika kwana anan, Ni banma yarda dakai ba, kaine ka janyo ni jikinka, har bacci ya ɗauke ni, saboda rashin tsoron Allah, gashi kaja min zunubi,” tun da tafara faɗa suka zuba mata ido suna kallonta, Ita fa gani take kamar suna zargin wani abu, yayin da su kuma basu kawo komai aransu ba, saboda ilminsu bai kai nan ba, Abun ma burgesu Yayi, don su a wurinsu ba wani bane don mace ta haɗa jikinta dana namiji, sun saba ba tun yanzu ba, saboda haka suka taso suna rungumar junansu, abu ɗaya ne basu yi neman junansu, shima saboda basu da shauƙin sha’awa kwata kwata, an cire masu shi, amma fa suna ƙaunar junansu sosai, sai ma mutun ya yi tsammanin akwai soyayya asakaninsu, Alhalin nan kowa babu wannan aransu, Kawai ƙaunar juna ce,
“Angel ki daina ƴan kame kame, Mun riga mun san komai,” harara ta jefa ma hanna da ta yi maganar tace”Me kuka sani? Idan ma wani abu ku ke zargi to shine ke da laifi ku tambaye shi ku ji,”a ƙule tayi maganar, shi dai baice komai ba, idonshi na akan fuskarta,
Parveen tace”danish ka faɗa mana gaskiyar abunda ya faru? Dagaske ne Kaine silar komai? Ɗaga mata kai yayi alamar eh, saboda gudun jarabar angel,
Javed yace”Ni ban yarda ba, Nafi zargin Angel, Cos danish bazai ta6a kawo ki nan ba, sai dai ko kece kika biyo shi, wama ya sani ko faɗa ne ya haɗa ku, ” miƙewa tsaye angel tayi”Ni kun ga tafiya, Ina da abun yi” Takai karshen maganar tare da Juyawa ta Nufi toilet ta buɗe ta shige, Jamlock ta sanya ta datse ƙopar, kafin ta le6e tana sauraron me suke cewa,
“Danish faɗa mana gaskiya, Meya faru daren Jiya a tsakaninku? Ya akai kuka baro ɗaki kuka dawo nan”? Batool ce ta jera mashi tambayoyin, angel dake la6e ta yatsina fuska aranta tace”Wannan batool ɗin sai kace ƴar jarida, ko ina ruwansu da abunda ya faru adaren jiya in ban da gulma da son jin kwakwaf mtsww”taja tsaki daga ƙarshe,
Tana Jinsu suna ta tambayarshi ya faɗa musu, Amma yaƙi basu amsa sai dai ce musu ya yi, ya manta komai, bazai iya tunawa ba, dole suka haƙura da tambayarshi, Ajiyar zuciya angel ta sauke, a fili tace yayi ma kanshi ƙiyamul laili, dama Bata son ya faɗi ne don kada ajinta ya zube, su ji cewa itace ta biyo shi don ta ba shi haƙuri,
Bata fito daga Cikin toilet ɗin ba, sai da ta yi wanka, A waje ta samu Su haris suna Jiran Na cikin toilets ɗin su fito su ma su shiga ko sun samu su yi wanka, Wuce su ta yi zuwa Cikin ɗakin, Babu kowa duk suna a can sai ita kaɗai, daga gefen gadonta ta zauna, bakomai ya faɗo mata acikin ranta ba face Deeja, Ko awani hali take ciki yanzu Allah wa’alamu, ɗaga hannayenta sama tayi cikin harshen labarabci ta soma jero addu’o’i tana karanto da niyar Allah ya tsare musu ƴar uwarsu, tana Cikin Yin addu’ar taji yo motsin buɗe ƙopar ɗakin tsohuwa, da sauri takarasa shafa addu’ar, Ta juya tana kallon ƙopar, tsohuwa ta fito daga cikin ɗakin, hannunta ruƙe da sanda, fuskarta a harmutse baka Iya gane awani yanayi take, haɗa ido su ka yi da angel, da buɗar bakinta sai cewa ta yi”Ba zaki zo ki gaishe ni ba”? Murguɗa mata baki angel ta yi tare da cewa”Mutanan kirki nake gaisarwa, ba masu matattar zuciya ba” bazawarin murmushi tsohuwa tasaki, haɗi da girgixa kai tace”kin tsane ni kamar mutuwarki” angel tace”fiye da haka” dariya tsohuwa tayi,
“Idan ba ki son ganina to ki kwantar da hankalinki, nan badajimwa ba, Zaku daina gani na,” babu yabo ba fallasa angel tace”Da munji daɗi wlh, kwara mu daina ganinki, tun da dama babu amfanin da kike yi mana, sai sai kawai kullum ki leƙo da ƴar sanda a hannu,” wannan maganar ta angel ba ƙaramar dariya ta bata ba, Musamman data kwatanta yadda tsohuwa ke leƙo wa da kanta,
“Ba zaki yi kewata ba”? Ta jefa mata tambaya, angel tace”Kin ta6a ganin anyi kewar maƙiyi? To idan ma ana yi ni bansani ba, Ni dai burina shine ki fita arayuwar mu, saboda baki da amfani, ” hannu takai ta ɗauki pillow Ta ɗago dashi tana nuna ma tsohuwa tace”Kinga wannan matashin kan na hannu na? wlh yafi ki amfani yafi ki daraja da ƙima a wurin mu, ai ke dake da waccan tukunyar fulawar ta Cikin toilet ɗin mu baku da banbanci,”
Tuntsirewa tsohuwa ta yi da wata irin mahaukaciyar dariya hhhhhhhh, da gudu su Hannah suka shigo cikin ɗakin sakamon Jin sautin dariyar tsohuwa wanda yajawo hankalinsu, A tsakiyar ɗakin suka tsaitsaya suna Kallonta, Ɗauke ido tsohuwa tayi daga kan angel ta mayar dasu kansu Batool tace”Kuma bazaku gaishe ni ba”? Maimakon su gaishe ta, Sai suka juya suna kallon angel, Tsohuwa tace”ba shakka, Uwarku kuke Jira ta baku Umarni kenan”? Shiru suka Yi basu ce mata komai ba, Still idonsu na akan angel data maƙe musu kafaɗa alamar kada su gaishe da ta ita, Shigowa cikin ɗakin mazan su ka yi gaba ɗayansu duk sun yi wanka, Suna ƙarasowa inda tsohuwa take, cikin girmamawa Danish Ya ɗan russuna tare da gaishe da ita, hakan ba ƙaramin fusata Angel yayi ba, har saida taja dogon tsoki,
Dogara sanda tsohuwa ta yi zuwa inda danish yake a tsaye, Ta miƙa hannunta ɗaya ta shafa sumar kanshi tace”Albarka zata tabbata akanka, Yarona, ina matuƙar alfahari dakai, Saboda kai na musamman ne, Zan yi kewarka sosai” Cikin sanyin murya danish yace”meyasa kika ce haka”? gajeran murmushi tsohuwa tasaki kafin tace”Bakomai,” ta ambaci hakan tare da kallon su Batool dake a tsaitsaye cirko cirko tace”Ko kaɗan banji haushi ba da kuka ƙi gaishe ni, Saboda bancancanci hakan ba, Naji daɗi da ku ka nuna min cewa Kun girma kun mallaki hankalin ku, zaku iya tafiyar da rayuwarki even without me,” tana kai karshen maganarta, A sukwane ta juya tana dogara sanda ta nufi ɗakinta, Har ta kusa shiga sai kuma taci burki, kamar an dakatar da ita, a hankali ta waiwayo baya ta kalli angel dake zaune tana hura hanci, tace”me ma ki kace? Dani da tukunyar fulawar dake acikin makewayin ku bamu da banbanci”? Ɗaga mata gira angel tayi alamar eh, dariya tasaki tana girgiza kai tace”Tukunya fulawar dake a makewayinku tafi ni mahimmanci Angel, Ku dage da bata ruwa akai akai, Furannin dake Acikinta zasu Yi tsuro su girma, gwanin ban sha’awa,” tana faɗin hakan ta juya ta karasa shigewa cikin ɗakinta, taja ƙopa ta rufe,
Ta6e baki angel ta yi tare da watsa hannayenta tace”Abanza” batool tace”bansan meyasa naji jiki na yayi sanyi ba, sai naga kamar bamu kyauta ba da muka ƙi gaishe da tsohuwa” Harara angel ta watsa mata”Ae sai ki bita cikin ɗakin ki gaishe da ita, Ni ko me matar can zata yi wlh bazan ta6a girmamata ba, muguwa azzaluma macuciya kawai da ita,” Cikin sanyin murya danish yace”Ki daina angel badai dai bane, ita tamkar mahaifiya ce agare mu, koda ace kuwa muguwace ita, saboda tafi iyayen mu, idan har dagaske suna araye kuma su ne suka yi silar zuwan mu nan” daƙyar ya kai ƙarshen maganar, ganin tana nuna shi da yatsan hannunta”Kai ka kiyaye ni! Wato raini ya fara shiga tsakanina dakai saboda jiya mun kwana a shimfiɗa ɗaya ko”? yadda tayi maganar ba ƙaramin dariya taba su batool ba, Haris yace”Da alama Jiya kunji daɗin baccin nan, shiyasa muka taras daku a manne da juna, Yadda kasan ANTA da JINI,’ dariya su hanna suka saki, Angel kuwa tasha mur, tana jifar danish da harara, murmushi ne ya bayyana akan fuskar danish, tana ƙunƙuni tace”zamu haɗu” juya mata ƙeya ya yi, batare da ya tanka mata ba,
Azeeza tace”Ni dai bari naje toilet, In zuba ma fulawar nan ruwa, Saboda tsohuwa tace mana tana da amfani” ruƙo wuyan rigar azeeza haris Yayi”Zo nan Sullu6iyo, Ke har kin yarda da maganar ta? Bayan irin ƙarairakin da take gaya mana? Shin idan kin bama fulawar ruwa ta girma, wani amfani zata yi mana? Ko ɗibarta zamu dinga yi muna ci ne”? Yayi tambayar yana Leƙen fuskarta, Gatsina mashi hanci ta yi, tare da cewa”Oho, Nima bansani ba,” ta faɗi hakan tare da buge hannunshi, Ya zame daga ruƙon da yayi mata, Hanna tace”Dama ita mashiririciya ce narasa me ke damun azeeza, Kwakwalwarta gaba ɗaya shirme ne acikinta, saboda rashin aikin yi flower zaki je ki zuba ma ruwa? bubbuga ƙafa azeeza tayi rai a6ace tace”To wai ina ruwanku dani ne? Bani naji zan iya ba, Sai ku ƙyale ni,” Da ɗan tsoki ta ƙarasa maganar,
Parveen dake ta faman Yin hammar yunwa tace”Dan Allah ku yi shiru, Surutunku Yana ƙara Harzuƙa Yunwar Ciki na,”
Rubina tace”damuwarki kenan, abinci abinci, Kowa dai da abunda ya ishe shi,” Haris yace”Ni kuma damuwata deeja, ” Yana faɗin hakan gaba ɗaya walwalar dake akan fuskar kowannan su ta canza zuwa damuwa,
“Ba kai kaɗai ba haris, Gaba ɗayan mu mun damu da deeja, tana acikin ran mu, Mun yi shiru ne saboda bamu da yarda zamu yi, damuwa ko yin kuka bazasu ta6a dawo mana da ita ba, Haƙuri Shi ne yakamata mu yi, Sai kuma mu bi ta da addu’a, Allah Ya tsare mana ita aduk in da take” Angel ce tayi maganar a yayin da ta miƙe daga saman gadonta, walking Slowly Ta nufi inda suke a tsaitsaye itama ta tsaya, Jikin kowannan su Ya yi sanyi, shessheƙar kuka azeeza ta fara, aikuwa haris ya daka mata tsawa tare da cewa”Zaki yi shiru ko saina buge maki baki? Ƴar rainin wayau, yanzu kika gama zancen bama flower ruwa amma daga jin anyi maganar Deeja kin wani 6are baki zaki ma mutane kuka ke da kika fi kowa ƙaton baki acikin mu” idamuwanta cike tab da kwalla take kallon haris, sai kuma ta duƙa ƙasa ta ɗaura kanta saman guiwowinta ta fashe da kuka, girgiza kai danish yai idonshi akan na haris, Shi ma haris din kallon nashi yake yi, don yasan dole ya tanka mashi, Saboda sanin halin shi na rashin son ana 6ata musu rai, musamman azeeza kodan yana ganinta ƴar ƙarama ne acikinsu,
Tunkafin danish yace wani abu haris ya riga shi cewa”Its ok Bazan ƙara ba, amma itama ta daina Yi mana kuka” Azeeza dake a tsugunne tana kuka ta ɗago da kai Cikin shessheƙa tace”Bazan daina ba, In ka tashi ka kashe ni, Kuka yanzu na fara” yanayin yadda ta yi maganar taso basu dariya,
Matsawa angel tayi kusa da azeeza, Ta sanya hannayenta biyu ta ɗago da ita, tare da rungumeta ajikinta, tana lallashinta, Cikin ƙanƙanin lokaci azeeza ta yi shiru, kamar wadda ta samu jikin mahaifiyarta, ta lafe ma angel, hada zagayo da hannayenta biyu abayan angel ta ƙanƙame, Batool dake kallonsu ta saki murmushi, tare da cewa”gwanin ban sha’awa,” angel tace”kema idan kinaso kizo in rungumeki” kafin batool ta bata amsa, Hanna tace”Ni baki ta6a rungume ni ba ajikin ki” Tun da hanna tace haka gaba ɗaya sauran Ƴan matan suka ce suma bata ta6a yin hugging ɗinsu ba, Lokaci ɗaya ta ji gabanta ya faɗi rass! Da sauri ta sanya hannayenta Biyu ta janye azeeza daga Jikinta, Hannunta na dama ta ɗaura saman ƙirjinta a saitin zuciyarta, Yayin da la66anta suke kerma, Hankalin su Hanna ba ƙaramin tashi ya yi ba ganin irin canzawar da angel ta yi, Ji su ka yi ta fara ambaton”Innalallahi wa’inna ilaihirraji’un”! har suna haɗa baki wurin tambayarta lafiya, Girgiza kai ta ɗanyi tare da cewa”Bakomai kawai bana Jin daɗi,” Tana kai karshen maganarta, Jiki na kerma ta koma gefen gadonta, duk sunata kallonta,
Haris yace”Yakamata Mu je mu zauna, kafin giants su kawo mana abinci,” hibba tace”Yau bazamu motsa jiki ba”? Parveen tace”Sai mun ci abinci tukunna,” Basu kai ga zuwa sun zauna ba, Sai ga Giants sun shigo kawo musu abinci, Bayan sun sauke abincin Jiki na rawa kowannansu Ya samu wuri ya zauna saman dining carpet, Suna tsaka da cin abincin Angel ta miƙe suka tambayeta Harta ƙoshi sun ga bata Ci dayawa ba, tace masu ta ƙoshi, gaba ɗaya sun lura da yanayinta, kamar bata Jin daɗi, ko bayan da suka kammala Cin abincin giants suka tafi, Agaban Gadon angel suka je suka tsaitsaya Suna kallonta, Ta kwanta idanuwanta na fuskantar ceilling, cikin nuna damuwa suka tambayeta ko lafiya tace musu babu komai su kwantar da hankalinsu, Badan sun yarda da maganarta ba suka ƙyaleta kowa ya koma saman gadon shi ya zauna, Yau ko motsa jikin basu samu sun yi ba, saboda canzawar da angel ta yi musu, tana daga kwance ta kasa kunne tana jin muryoyinsu suna fira, parveen tace”idan angel ta gudu damu, zuwa gidansu, Shikenan mun huta da ganin giants, Zamu sakata mu wahala, Kuma zamu dinga fita yawo, Wlh ni duk na ƙosa inga ya wajen kurkukun nan yake, Nasan zaiyi kyau sosai, kuma zaifi daɗi,” Azeeza tace”kuma ta faɗa mana cewa daddynta zaiso mu kamar ya’yanshi, hada sauran ƴan uwanta ma, mu ma zamuyi rayuwa kamar kowa, ” can kuma tajiyo muryar javed yana cewa”dama kun daina wannan mafarkin da bazai ta6a zama gaskiya ba, In banda abunku taya za’ai ku fita daga Cikin kurkukun nan? kuna tunanin Giants zasu Barku? haris yace”faɗa musu dai, Nima jinsu nake kawai, Ni bana so ma suna ƙwallafa rai akan son Yin rayuwa awaje, saboda suna wahalar da zuciyoyinsu ne, ita kanta angel ɗin da take Sanya musu rai, bata da hanyar da zata Iya ku6utar dasu” Hanna tace”Amma ae ta faɗa mana cewa, Idan muka dage da addu’a, muna kai kukan mu wurin Allah, Zai ji ƙanmu ya taimake mu, Mu fita cikin kurkukun” koda tayi wannan maganar sai haris Ya tuntsire da dariya tare da cewa”Taya kenan hakan zata Iya faruwa? Wannan fa ba gaskiya bane…..” Bai ƙarasa maganar ba, sakamakon Tsawar da angel ta daka mashi, a yayin da take ƙoƙarin miƙewa daga saman gadonta, Hankalinsu duk ya dawo kanta, Harara ta wurga mashi tamkar ƙwayar idanuwanta zasu faɗo ƙasa, Muryarta da rauni tace”Ya isa haka haris! Bana so kana shiga hurumina, kuma Ka daina ƙaryata magana ta! Idan kai baka Yi imani da Allah ba, Su sunyi, Kuma in sha Allahu zamu samu mafita ne bi’iznillahi, ka zuba ido ka gani” Jinjina kai haris yae fuskarshi ɗauke da murmushin rainin wayau, yaso ya mayar mata da martani, Amma danish ya dakatar dashi ta hanyar yi mashi magana, gyaɗa kai ya yi tare da jan baki Ya yi shiru,
Ɗakin Ya yi tsit babu mai magana, wuraren marece, Duk sun kwanta saman gadajensu, wasu sun fara bacci, yayin da wasu kuma sun lumshe idanuwansu ne badan suna jin bacci ba,
Damuwar duniya ta ishi angel, Ga wani irin faɗuwar gaba da take ji, tarasa gane dalilin hakan, addu’o’i kawai take janyowa Acikin zuciyarta, Tana ji aranta kamar wani abune zai faru, wasa wasa suna kwancen nan har dare Ya ratsa hasken ɗakin Ya yi duhu, tun tana iya jiyo hirarsu suna faɗin har yanzu ba’a dawo da deeja ba, har tadaina Jin surutunsu alamun sunyi bacci, Aranta tace”ita kuma wannan Makauniyar rayuwar haka zata ƙare? Kullum muna ƙunshe a ɗaki Ɗaya tsawon shekara da shekaru, Gaskiya bazai yiyu ba, Nifa ina da burikan da nake son Cimmawa don haka bazan zauna in zuba ido ba, dole in nema ma kaina mafita, tana karasa zancen zucin nata, ta yunƙura ta sauko daga saman gadonta, Cikin duhu ta shiga laluban Fitilun ɗakin su, ko da ta ɗauko fitilar bata kunnata ba, saboda gudun kada Danish ya farka daga bacci Ya bi bayanta, Cikin sanɗa taci gaba da tafiya ko sautin tafiyarta baka Iya ji, tana shiga sashen toilet ɗin Abakin door ta kunna fitilar, Ta buɗe toilet ta shiga ta zura jamlock, A ƙasa ta sauke fitilar, Ta ɗauko bokitin ƙarfen nan, ta Ajiye shi jikin bangon da tagar Nan take, saboda ta sa mu tsawonta yakai, Daddagewa ta yi tare da haye saman bokitin, tana yunƙurin kai hannu ta zame glass ɗin muryar danish Ta ratsa kunnata
“Angel!” ras taji gabanta Ya faɗi, gaba ɗaya jikinta ya hau kerma, tsantsar 6acin rai ne ya bayyana akan fuskarta, a tsiyace ta juya saitin Da yake tana kallonshi, A tsakiyar toilet ɗin taganshi A tsaye, tun kafin yai magana ta riga shi cewa”kai nifa nagaji, Don me zaka dinga faɗo mini cikin toilet? Bayan ka yi mini alƙawarin cewa bazaka ƙara shigowa ba?
Cikin sanyin murya yace”Ina Bibiyarki ne saboda sanin ƙudirin da kike dashi na son shiga Cikin prison, wanda yin hakan zai iya haddasa mana shiga mummunan haɗari, ” Har saida taji gabanta Ya faɗi, jin abunda yace, Da mamaki tace”Oh dama kasan abunda nake son yi kenan? Taya akai ka sani?
“kawai naji araina ne, kina son ki dura ta tagar, ko last time dana Sauke maki glass, Ban yarda da abunda kika faɗa mini ba, na cewa bakya son kallon glass yana affecting ɗinki, da ace dagaske ki ke, to da tun lokacin kin kawar da shi daga Cikin toilet ɗin amma sai baki yi hakan ba, ” Ya ƙarasa maganar a yayin da yake tunkararta, Runtse ido ta ɗanyi tare da cizon lips ɗinta, Rai a6ace tace”wlh duk bala’in ka baka isa ka hana Ni yin abunda nayi niya ba, kada ka kuskura kace zaka ma dakatar dani, idan har ba so kake In yi maka Illa ba”
“Angel Na roƙe ki kada ki je, Zaki jefa rayuwarki da tamu Cikin hatsari, Ba’ayi musu leƙen asiri, Ki fahimce, yafi muyi rayuwarmu Cikin duhu akan musan ainihin abunda ke faruwa acikin prison, amma daga ranar da kika haura tagar nan, xaki ja mana ne gaba ɗayan mu ne”… Tamkar zai fashe da kuka Yake yi mata magiya akan karta dura, A ƙarshe daya ga ta kafe tasa naci akan saita dura, ai kuwa da ƙarfi Ya sanya hannu ya janye bokitin da tahau sama, Gaba ɗaya ta tafi zata kife ƙasa da sauri ya sanya hannayenshi biyu Ya tarbo ta, ta faɗo saman jikin shi, Suka rubza ƙasa atare, kanshi ba ƙaramar buguwa yai ba, ita kuwa kamar jira take yi su faɗo aikuwa ta daddage ta dunƙule hannayenta, Ta shiga kai mashi bugu a ƙirjinshi, Ya yi shiru batare daya dakatar da ita ba, zuciya ce ta fusgeta, a karshe ta kifa kanta saman ƙirjinshi tana kuka tana faɗin”Ya rabu da ita taje, Ita ta gaji da rayuwar kulle, Bazata Iya jure azabtar da ƴan uwansu da ake Yi ba, ” Haƙiƙa Danish yaji tausayinta, Sai dai bazai Iya barinta taje yin leƙen asirin ba, saboda shi ya fita wayau da hankali, Ya kuma san Abunda sai biyo baya, Idan har ta dura ta tagar nan,
Tuntana yin kukan har tagaji tadaina muryarta ta disashe, Sai lokacin ya samu damar yunƙurawa Ya ɗago da ita a jikinshi, A saman kafaɗarshi ya kwanto da ita, ranƙwafa yayi tare dakai hannu ya ɗauki fitilar da tazo da ita, Ya juya ya fuce daga cikin toilet ɗin, Yana shiga ɗakinsu Ya kwantar da ita saman gadonta, Daga ƙasa ya ajiye fitilar hannun shi, Ya zauna daga gefenta yana kallon fuskarta, Wadda ta yi jaga jaga da hawaye, hannayenta ya ruƙo acikin nashi, ya soma lallashinta, ya ɗauki tsawon lokaci Amma ko kallo bai isheta ba, Sai da ya gaji don kanshi tukunna Ya ƙyaleta, Ya koma nashi gadon Ya kwanta, A daren ranar daƙyar bacci ya ɗauki angel,
Ranar da Deeja ta Cika 4 days da aka ɗauketa, A daren Ranar Giant Ya dawo da ita, Babu wanda ya sani duk sunyi nisa a cikin baccin su, A tsakiyar ɗakinsu Giant Ya sauke ta, Baiwar Allah duk ta fita hayyacinta ta rame ta fige, kamar wadda aka ɗibi naman jikinta, kasancewar sun kunna fitilun ɗakin su, Hakan ya bata damar bin Cikin ɗakin, Bata nufi ko’ina ba sai bakin gadon angel, a gefe gadon ta zauna, fuskarta sharkaf da hawaye, hannu takai saman shimfiɗar angel ta ɗan bubbuga kafadarta, Ƙasa kasa da murya take ambaton sunanta don kada ta takura ma masu yin bacci, koda angel taji muryar deeja acikin baccinta, a matuƙar ruɗe ta yaye bargonta, muryarta na kerma tace”deeja! Dagaske kece? Ko dai mafarki nake yi,” jinjina kai deeja tayi cikin shessheƙar kuka tace”its me angle, am back, Giant ne ya dawo dani, na same ku kuna bacci, bana so na tashi kowa shiyasa nazo wurinki, saboda akwai abunda nake son faɗa miki,” Tun da angel taji haka, Sai ta yaye bargon dake a jikinta, Ta kalli fuskar deeja da kyau, Gaba ɗaya ta zabge Duk ta bushe, janyota tayi zuwa jikinta ta rungumeta sosai, kamar zata maida ta cikin cikinta, Tayi matuƙar yin kewarta, Sun ɗauki tsawon lokaci, Kafin angel ta raba jikinta daga na deeja tace”Ki faɗa mini menene? Deeja tace”za’a iya jin mu idan muka Yi magana anan, amma zan shiga toitet, sai ki biyo ni” angel ta amsa mata da toh, Miƙewa deeja ta yi jiki duk ba ƙwari ta shige toilet, angel ta miƙe ta bi bayanta, bayan sun shiga, deeja ta sanya jamlock ta datse ƙopar, ta juyo suka fuskanci juna ita da angel,
“Faɗa mini menene kikeson Gaya mini? Duk na ƙagara inji” Cikin shessheƙar kuka deeja tace”Angel yanzu na ƙara yarda da maganarki na cewa ana cutar da rayuwar mu, wani iko na angel, Duk da bakomai zan iya tunawa ba, Amma lokacin da giant ya tafi dani, ina Cikin hayyacina, Inata karanta addu’ar nan da kika koya mana acikin zuciyata, Har yakai ni wani part inda wasu jerin daƙuna suke, Bayan ya shiga dani ɗaya daga cikin su, duhu ya mamaye idanuwana, ban iya ganin komai sai dai biji biji nake gani, Har lokacin ban fita hayyaci na ba, Sai dai bana iya gani da kyau, Naga mutun shida wanda ba baƙaƙen kaya bane ajikinsu kalar na giants, naga launin Ja a ƙugunsu, angel daga nan ne na fita hayyacina, bansan me akayi mani ba, Sai dai naji ajikina an cutar da rayuwata, nayi kukan mutuwa, Na azabtu iya azabtuwa, ” Deeja nakai karshen maganarta, Ta zube saman gwiwowinta, tare da fashewa da matsanancin kuka, kamar ranta zai fita, Hankalin angel yayi matuƙar tashi, duk da bata ji me mutun shiddan nan suka Yi mata ba, amma tana ji aranta cewa Lalata suke yi dasu, idan har zata iya tunawa, can lokacin baya,Ta ta6a yunƙurin guduwa daga islamiya zata je gida, Tazo giftawa ta ofishin head master ɗinsu, Tajiyo shessheƙar kuka, da kuma maganganun mutane, duk da ƙarancin shekarunta a time ɗin tana dab da shiga 11 years, Har zata wuce ta la6e ta kasa kunne tana sauraronsu, ɗaya daga Cikin ɗaliban makarantar ne aka samu wani malami yayi ma fyaɗe ya kuma cigaba da lalata da yarinyar da bazata wuci shekara sha bakwai ba batare da sanin kowa ba, idan tazo islamiya aka tashi sai ya ɗauketa saman mashine ɗinshi zuwa gidanshi da ya gina da niyar yin aure, amma sai ya 6uge dakai yara yana 6ata musu rayuwa tare da yi musu barazana, Mahafiyar yarinyar ce ta fara lura da canzawarta, Bata iya tafiya ƙafafuwanta sun gwame, ga yawan yin amai, da su ka kaita asibiti likita ya tabbatar musu cewa ƴarsu Cikine da ita, iyayen yarinyar sun shiga damuwa, bayan sun baro asibiti sun dawo gida, mahaifiyar yarinyar ta ɗauko wuƙa ta ɗaura akan wuyan yarinyar tayi mata barazana akan ta faɗa musu wa yake yin lalata da ita har ta samu ciki, in ba haka ba zata kashe ta, atsananin tsorace yarinyar ta faɗa musu cewa malaninsu ne na islamiya, Koda jin haka sai suka tasa ƙeyarta gaba suka zo makarantar don su tabbatar da abunda ta faɗa musu, A lokacin angel bata fahimci komai ba, amma ta naɗi komai a acikin kanta, sai yanzu da Deeja ke faɗa mata wannan maganar ta soma tariyo abunda ya faru da ɗalibar nan ta makarantar islamiyarsu, duk da bata da tabbaci akan hakan amma tana zargin Suma lalatar ake yi dasu, ‘ Zuƙunnawa ta yi agaban deeja, Ta sanya hannayenta biyu ta rungumota ajikinta, Lokaci ɗaya ta fashe da matsanancin kuka tamkar ranta zai fita, itama deejan kuka take yi sosai, ta ƙanƙame angel da hannayenta, Abun da ciwo idan har ya tabbata cewa lalata ake yi dasu saboda rashin imani kuma a lokacin da suke Yi jinin al’ada, 😭😭😭
*❤❤❤PRISONERS❤❤❤*
Sun ɗauki tsawon lokaci rungume da juna suna ta kuka, Sai da suka yi mai isar su tukunna kowa Ya yi shiru, ba tare da sun raba jikinsu daga na juna ba, Muryar deeja a disashe tace”Na gaji da irin wannan rayuwar angel, bazan iya jure ganin ƴan uwana suna shan wahala ba, tun da ba yanzu suka fara ba, zasu ci gaba da zuwa suna ɗaukar mu ne ɗaya bayan ɗaya har sai sun ƙarar damu, nayi tunanin cewa gata ne ake nuna mana acikin kurkukun nan ashe ba haka bane, tsohuwa ta yi mana ƙarya da tace mana gidan marayu ne, za’a gatanta rayuwarmu, ta yaudare mu ta cuce mu, ba zamu ta6a yafe ma duk wanda yayi silar sadaukar damu zuwa cikin kurkukun nan ba…….”
katse maganar ta yi, batare da ta kaiga ƙarasa ta ba, saboda wani irin ƙululun baƙin ciki da ya tokare mata maƙoshinta, Sai lokacin angel ta iya buɗe baki tace”Dama ni nasani tun farkon zuwana kurkukun nan na gane cewa Ba orphanage home bane, Tun daga kan sunanshi, shiyasa nayi ta ƙoƙarin in fahimtar daku, saboda ni nayi rayuwar ƴanci da hankalina da wayau na, sihirin tsohuwa tamira bai yi tasiri a Jikina ba, shiyasa Tunina bai gushe ba, dama taya za’ae Gidan marayu ya kasance Kurkuku? Kuma ba shige ba fuce, Abinci sau ɗaya arana! Uniform kala ɗaya, sai dai idan munyi wanka mu cire mu wanke mu maida a jikin mu? Ga shi babu wani mai kula damu, Rayuwa muke yi kara zube, wlh ko dabbobin dake garari acikin daji sun fi mu ƴan ci, koba komai zasu yawata inda suke so, Kai ni da irin rayuwar nan ma ƙwara mutuwa, saboda ɗaci ne da ita, rayuwar kulle, babu wanda zaiso ya kasance cikin irin wannan makauniyar rayuwar, Ai ko maƙiyi na bazan yi ma fatan shigarta ba…..” Sai lokacin angel ta raba jikinta daga na deeja, Idanuwan kowannan su ya yi jawur saboda tsabar kukan da suka sha, Cikin karyayyiyar murya deeja tace”Ni bana Jin ma zanyi tsawaicin kwana, Gani nake kamar nice gawar fari acikin mu….” kafin ta karasa maganar angel ta yi saurin sanya tafin hannunta ta toshe mata baki, tana girgira kai, Hawaye na bin fuskarta tace”in sha Allah ba ke bace gawar fari, wlh bana Yi mana fatan mu rasa rayuwar mu acikin kurkukun nan, ina matuƙar so inga kuma kunyi rayuwa kamar kowa, Idan ma mutuwar ce na ƙwammace ni in fara yinta, saboda bazan Juri rashin wani acikin ku ba, bakisan yarda nake jinku ba, akan ku bana jin tausayin kaina, saboda ku ne abun tausayi” Daƙyar takai ƙarshen maganarta, hawayen deeja duk sun wanke hannunta data rufe mata baki dashi,
“Kowani ɗan adam da irin tashi ƙaddarar rayuwar, kowani bawa da irin ƙalubalan da yake fuskanta acikin rayuwarshi, Allah yana jarabtar bayin shi ba dan baya sonsu ba, face don ya jaraba imaninsu, babu wanda zaice maka 100% yana rayuwa Cikin jin daɗi, dole akwai ranakun farin ciki da kuma na baƙin Ciki, wani farkon rayuwarshi Jin daɗi ne, tsakiyar rayuwarshi wahala ce har zuwa ƙarshenta, wani kuma da farko zai ci baƙar wahala amma daga ƙarshe sai kaga Ya samu farin Ciki, Akwai wanda kuma Kaf rayuwar shi tun daga zuwanshi duniya Allah zai fara jarabtar shi, har zuwa ƙarshen rayuwar shi bazai ta6a jin daɗin duniya ba, zai fuskanci ƙalubale iri iri wanda idan Baida ƙarfin imani da tawakkali zai fidda rai da rahamar ubangiji ne, Zaiyi tunanin cewa ko Allah baiso na ne? At end har yakai ga tunanin salwantar da rayuwarshi don ya huta, wanda yin hakan kuma zai ƙara Jefa kanshi Cikin matsala ne, Kazo duniya a wahalce kuma ka koma a matsayin zero duka kayi asara, Amma idan kayi haƙuri ka miƙa lamurranka ga Allah subhana’hu wata’ala Koda baka ji daɗi anan ba, acan ana kyautata zaton zaka dace, akwai wanda kuma bai ta6a shan wahalar duniya ba, gatanci ta ko’ina, wahalarta kaɗan ya sani, in kaga 6acin ranshi to wani Ya rasa na kusa dashi, aduk halin da bawa ya tsinci kanshi Ya kasance mai godiyar Allah, Kafi wani, wani yafi ka, yanzu kamar rayuwar waɗannan bayin Allah, tunda suka zo duniya A garƙame suke kamar dabbobi, An tauye musu duk wani haƙƙinsu na rayuwa, basu son komai game da jin daɗin duniya ba, sun yi rayuwa acikin duhun jahilci, Basu son iyayensu ba, Basu son danginsu ba, su kansu basu Su wanene su ba, Haba jama’a, wannan rashin imanin har ina? A haka ake so su mutu su fuskanci mahaliccinsu, ai ƙwara wanda ke rayuwa acikin mutane yana fuskantar jarabawar rayuwa, Amma akwai imani azuciyarshi, Atlease Ya tsira da wannan idan yayi tawakkali, amma waɗannan bayin Allahn fa? Ba don zuwan angel acikin rayuwarsu ba da shikenan An kashe su da ransu an gama dasu, yakamata mu ƙara jin tsoron Allah acikin zukatanmu, mu kasance masu tawakkali, kuma mu kasance masu godiya ga Allah aduk halin da muka tsinci kanmu, tun da bamu rasa komai na rayuwa ba, ka kwana ka tashi da ranka da lafiyarka, ka je inda kake so, Ka ci mai kyau kasha mai kyau, ka sanya sutura mai kyau, kana a tare da iyayen ka ko babu su akwai danginka, kai idan ma babu dangin naka Allah Yana atare dakai, Zaka Iya rayuwa ko babu su, da daɗi da ba daɗi, Allah ya baka rai da lafiya, Amma sai kaga bawa yana Ƙorafi don ya rasa wani abu ƙalilan, ko angaza biya mashi buƙatarshi, dayawa gajan haƙuri kesa wasu harsu fara neman duniya ido rufe, Allah dai yasa mu dace, Shiyasa ake so mutun ya dinga ziyarta asibitoci da wuraren da faƙiran talakawa suke yin rayuwa, Kodan ya ƙara imani, Allah dai ya tsare mu ya kare mu daga faɗawa tarkon halaka, kada amanta adunga taya ƴan uwan mu addu’a waɗanda ke a hannun kidnappers da kuma ƴan boko haram, da matsafa, muna roƙon Allah ya kawo mana ƙarshen wannan masifar da muke fama da ita a ƙasarmu badan halin mu ba, Alfarmar Annabi muhammad (SAW) addu’a takobin mumini ce da ita ne kaɗai zamu Iya yaƙar su, tun da mu bamu da yadda zamuyi, waɗanda keda ikon Yin sun gaza, saboda rayuwar mu bata da mahimmanci awurinsu, takansu suke yi, wanda nayi imanin da ace yau hada ƴa’ƴansu aka ɗauka da anga tashin hankali, cikin ƴan awanni sai sun san yadda zasuyi an dawo musu dasu, Akwai dai ranar ƙin dillaci, ranar da dukiya ko ya’ya ko wani muƙami na duniya bazai amfane su da komai ba, A ranar zasu shaida cewa ALLAH ƊAYA NE.
A hankali angel ta zame hannunta daga saman bakin deeja,
“Deeja kodai in taimaka maki ki yi wanka? Naji jikin ki wani iri, daga gani baki jin daɗin shi” girgiza kai deeja tayi”a’a, bazan Iya yin wanka da ruwan sanyi ba, Jikina zai ƙara tsauri, ki barni kawai ahaka, ” tsananin tausayinta ne ya ƙara kama angel.
“To Mu je mu kwanta, ko kin samu ki yi bacci ki huta” shiru deeja ta ɗan yi batare data amsa mata ba, har sai da angel ta ƙara maimaita mata, tukunna ta buɗe baki tace”bazan iya tashi ba, ki kije ki tada su daga bacci, ki faɗa musu cewa an dawo dani, su zo mu gaisa,” maganar deeja ta yi matuƙar girgiza angel sai taga kamar bankwana ne take so ta yi dasu, muryarta na kerma tace”amma meyasa? Idan baki iya tafiya ne, ni sai in ɗauke ki abayana in kai ki cikin ɗakin ki kwanta, In yaso gobe da safe sai ku gaisa da su” idanuwan deeja a marairaice take kallon fuskar angel, da wata irin raunatacciyar murya tace”dan Allah ki kira mini su in gansu, kada na mutu batare da nayi tozali da ƴan uwana ba,” girgiza kai angel tayi cikin shessheƙar kuka tace”In..sha.. Allah ba zaki mutu ba, har sai mun fita daga cikin kurkukun nan, Na roƙe ki ki daina Yi mini maganar mutuwa, kina karya mini zuciyata, Kinsa Jikina duk ya yi sanyi” hawaye ne masu ɗumi suka wanke fuskar deeja, idanuwanta sunyi jawur sosai, la66anta na kerma tace”dan Allah ki kira mini su mu gaisa, inaso inga ƴan uwana.”
Juya mata baya angel ta yi tare da cewa”Ki hau in kai ki cikin ɗakin, Sai in tada maki su ku yi magana” fashewa deeja tayi da kuka tana faɗin”bana ce maki bazan Iya miƙewa ba, Kije ki kira mini su ko so kike saina mutu ne batare da nayi bankwana dasu ba”? Yanayin da tayi maganar yayi matuƙar girgiza angel, Hatta muryar deeja ta canza sosai, a ƙarshe ta sassauta muryarta tana yi mata magiya akan ta kira mata su, Muryar angel na rawa tace”shikenan ki jira dan Allah, yanzu zanje in tada su daga bacci kinji,” Aruɗe ta yi maganar, ta miƙe da sauri tana tafiya tana waiwayon deeja, fargabarta kada ta mutu kafin ta dawo daga kiran nasu, bayan ta cire jamlock ɗin ƙopar da gudun gaske ta faɗo Cikin ɗakin har kusan tuntu6e ta yi, tun kafin ta ƙarasa cikin ɗakin ta dinga kwala musu kira, Haris danish, naufal hanna hibba batool yasmin ku tashi an dawo da deeja, da alama sunyi nauyin bacci babu wanda ya motsa, gaban gadajensu taje tana bubbuga ƙafafuwansu tare da cire musu bargunan da suka lullu6a dasu, Wannan karan muryarta da sauti mai ƙarfi take kwala musu kira, a matuƙar firgice kowannansu ya farka Yana faman Yin hama, Ba ta bari sun wartsake ba, tace musu”ku tashi muje toilet, deeja tana aciki, An dawo da ita, amma bata da ƙoshin lafiya, ita ce tace in kira mata ku, tana son ganinku” Jiki na rawa suka sauko daga saman gadajensu, Haris yafi kowa zumuɗi, shine agaba sai naufal da mubeen da danish, tare da javed, Matan kuma batool ce agaba sai su hanna hibba eve da su Parveen, Mutun ɗaya ce bata sauko daga saman gadonta ba, Azeeza amma ta farka tana ta kuka tana faɗin ita ba wanda zai kai ta wurin deeja, saboda anga bata da ido, har angel ta juya zata bi bayansu Batool sai kuma ta fasa jin muryar azeeza da sauri taje bakin gadonta ta ruƙo hannunta, tare da taimaka mata ta sauko daga saman gadonta, suka nufi toilet section ɗinsu, lokacin da kowannansu ya hallara acikin toilet ɗin da deeja take, hankalinsu Yayi matuƙar tashi, Ganin yadda jikinta ke ta kerma, wata irin zufa ce ke tsastsafo mata a jikinta, gaba ɗaya ta jiƙe sharkaf, a sukwane suka zuƙunna gabanta suka kewayeta, suna ambaton sunanta, hannu biyu haris ya sanya tare da tallabo fuskarta, daƙyar take iya buɗe idanuwanta da suka rune tana kallonsu, ita kaɗai tasan irin raɗaɗin azabar da take ji ajikinta, muryar haris a ruɗe ya ambaci sunanta”deeja! ke ce kika koma haka? me ke damunki? kina iya ganinmu”? jinjina ma shi kai ta yi alamar eh, Azeeza dake ta kuka tana faɗin su nuna mata deeja, angel ta zuƙunnar da ita agaban deeja, Ta haɗa hannun azeeza dana deeja, Sosai deeja ta ƙanƙame hannun azeeza dake acikin nata, Cikin sanyin murya ta ambaci sunanta”Azeeza”! Amsa mata tayi”na’am, deeja ashe an dawo mana dake muna ta bacci bamu sani ba, Mun yi missing ɗinki sosai, ” shafa fuskar azeeza ta yi da hannunta, nan take azeeza ta ɗan zabura tana faɗin”Zafi hannunki deeja, baki da lafiya ko”? Bata amsa mata ba, sai dai binsu da take yi da kallo, matsawa batool ta yi daga gefenta ta ɗaura hannunta saman wuyan deeja, da sauri ta zame shi, jin wani irin zafi na fitar hayyaci, hankalin ta ya yi matukar tashi tace”Yakamata mu kira tsohuwa ta duba jikinta, kwata kwata babu alamun lafiya atattare da ita” haris yace”me tsohuwa zata Iya yi mata? Ai kawai ku taimaka mata ta watsa ruwa ajikinta, zata ji sauƙi,” girgiza kai batool ta yi tare da cewa”bazaka gane ba, kwara a kira ta, tun da ita tafi mu sanin meke damunta” Angel ta lura dasu kowa yana tofa albarkacin bakin shi, amma banda Danish tunda suka shigo ya zuƙunna na ɗan wani lokaci sai kuma taga ya miƙe ya jingina bayanshi jikin bangon da deeja take a zukunne, ya goya hannayen shi saman ƙirjinshi, ya ɗaga kanshi sama idanuwanshi na fuskantar ceilling, tsabar haushin shi ne ya kamata, shi da yake amatsayin babba acikinsu yaƙi buɗe baki ya yi magana, Koda lallashin deeja ne yayi duba da irin halin da take aciki,’
“Ko da ace kun kira tsohuwa, ba abunda zata Iya yi mini, nidai tunda na gan ku Alhamdulillah hakan ma ya wadatar” Deeja ce ta yi maganar, Hanna tace”pls ki tashi mu koma ɗaki ki kwanta,” kallon hanna deeja ta yi, ƙarfin hali kawai take yi wurin yi musu magana”Ae bazan iya miƙewa ba, ƙafafuwana sun ruƙe,” Juya mata baya haris yai tare da cewa”ki hau in goya ki, mu shiga” nan ma tace mishi bazata Iya motsawa ba,’ lamarin yayi matuƙar girgiza su, jikinsu yayi mugun yin sanyi, Rubina tace”nidai zanje na kira tsohuwa ne” tana kai karshen maganarta, da sauri ta juya ta buɗe kopar toilet ɗin ta fuce, gudu gudu sauri sauri ta ƙarasa bakin ƙopar ɗakin tsohuwa, Tasa hannu ta kwankwasa ƙopar, kusan sau uku tana yin knocking, kafin ta samu tsohuwa ta buɗe mata ƙopar ɗakin, fitowa daga Ciki tayi hannunta ruƙe da sanda, ta ɗago da ido tana kallon rubina, Muryarta na rawa tace”dan Allah kizo ki taimaka mana an dawo da deeja amma jikinta babu sauƙi, ko iya miƙewa bata Yi,” duƙar dakai ƙasa tsohuwa ta ɗanyi batare da tace komai ba, “dan Allah ki taimaka badan halinmu ba, kada mu rasa ƴar uwarmu,” kafin tsohuwa ta ɗago da kanta sai ga su Javed da hibba hada yasmin sun fito daga Cikin sashen toilet dinsu, Hankalinsu duk atashe, ɗaya bayan ɗaya tsohuwa take binsu da kallo, Gaba ɗaya suka haɗa baki wurin yi mata magiya akan tazo ta duba jikin deeja bata da lafiya, duk sun ruɗe bayin Allah, Girgiza kai tsohuwa ta ɗanyi fuskarta babu yabo ba fallasa tace”Ni da bani da amfani awurin ku?me kuma zan Iya yi maku? Ita uwar ta ku bata iya duba mata jikin nata ne”? Duk sun gane akan wa take magana wato angel, hibba tace”pls ki taimaka mana mu dai, ki manta da komai kizo ki duba Jikinta, mun gane kuskuren mu, bazamu ƙara ba” suna kai karshen maganarsu gaba ɗaya suka zube saman gwiwowinsu, suna roƙonta, Da buɗar bakinta sai cewa ta yi”zan iya taimakon ku, bisa sharaɗi ɗaya”! A ƙagare suka tambayeta menene tace”Su je su kira babarsu angel, tazo ta durƙusa agabanta ta roƙe ta, idan har ta yi hakan ita kuma zata duba lafiyar deejan su,” da sauri suka miƙe da gudu suka nufi cikin toilet ɗin, a lokacin Deeja tana kwance saman ƙirjin haris, ya ƙanƙameta da hannayenshi, su angel duk suna a kewaye da ita, banda Maji daɗin gado daya ke atsaye kamar gunki, Yadda suka banko ƙopar toilet ɗinne yaja hankalinsu angel zuwa ga kallonsu, a fujajen suka faɗo, kusan atare suka haɗa murya wurin cewa”Ki zo angel, tsohuwa tace zata duba jikin deejan mu, amma dole sai kin durƙusa agabanta kin roƙe ta,” Waro ido waje angel ta yi bakinta asake galala take kallonsu, lallai wannan tsohuwar ta ɗauko ta da zafi, taya zata ce saita durƙusa mata sannan zata duba lafiyar deeja? Mamaki ya hana ta motsa, magiya su javed suka dinga yi mata akan tazo suje ta duƙama tsohuwa, ko sun samu ta duba Jikin deeja” kasa tanka musu ta yi, Har saida batool tace”Angel ki taimaka ma rayuwar deeja, dan Allah badan halin mu ba, Kije ki roƙeta, wannan ce kaɗai damar da muke da ita, idan ba haka ba, deeja zata Iya mutuwa ki kalli yadda jikinta keta kerma yana zufa, duk ta fita hayyacinta” Batool na rufe baki azeeza ta fashe da kuka tana faɗin”Dan Allah angel kije kada mu rasa deejan mu, muna son ƴar uwar mu,” ɗaya bayan ɗaya angel take kallonsu, a karshen ta tsayar da idanuwanta kan fuskar deeja dake kwance saman kirjin haris, la66anta sai kerma suke Yi, ” ganin zata 6ata musu lokaci yasa suka nannaɗe hannuwan rigunansu, batayi wani aune ba, taji sun sunkuceta gaba ɗaya suka cuccu6ota suka juya da ita zuwa cikin ɗakin, tana ta kiciniyar ƙwace kanta amma sunƙi bari ta kubce musu, a haka suka shigo da ita cikin ɗakin, Tsohuwa na ganinsu ta saki wani irin bazawarin murmushi, dama tasan taurin kan angel da kafiyarta baza su ta6a bari ta tako da ƙafafunta zuwa gabanta ba, su javed na ƙarasowa inda tsohuwa take a tsaye suka saki angel ta faɗi ƙasa, Idon tsohuwa na akanta, ɗagowa ta yi fuskarta a hargitse, saboda tsabar masifa ta rufe idanuwanta tana zazzaga masu masifa tana faɗin don me zasu je su ɗauko ta? Ita fa bazata ta6a duƙama wannan tsohuwar najadun ba, mai kafirar zuciya wadda batasan Allah ba, ‘ta inda take shiga bata nan take fita ba, Hankalinsu Rubina ya ƙara tashi ganin tana ƙoƙarin 6ata musu lokaci, ga deeja can tana jin jiki ita kuma da suka ɗauko donta taimaka masu gashi tazo tana ƙara Kwafsa musu, Zuƙunnawa su ka yi gaba ɗayansu saman gwiwowinsu suna roƙon angel akan ta taimake su badan su zata yi ba, ta dubi girman Allah ta roƙi tsohuwa taje ta duba lafiyar deejansu, ” tsananin tausayinsu ne ya kama angel ganin hada hawaye akan fuskokinsu, saboda tsabar jaraba da jin takaici ta fashe da kuka tana faɗin”wayyo Allah na na shiga uku, yau zan aikata babban zunubi arayuwata, wlh na tsane ki kamar mutuwa ta, bansan ganinki, muguwa azzaluma, mai zuciya irinta kafiran farko, ke daga ganinki kin hada iri da jinsin fir’auna, saboda rashin imani taimakon ne bazaki iya yi mana ba, dole saina roƙe ki…..” Bata ƙarasa maganar ba, yasmin ta sanya hannu biyu ta toshe mata baki, Cikin shessheƙar kuka tace”dan Allah angel kidaina, idan baxaki Iya ceton ran ƴar uwarmu ba, bai kamata kina ƙara fusata tsohuwa ba, so kike ta fasa taimakon mu” A tsiyace angel ta buge hannun yasmin data toshe mata baki dashi, idanuwanta sun yi jawur tamkar garwashin wuta, kallon kallon suka shiga yi ita da tsohuwa,
“Lokaci Yana ƙure maki, idan har kika bari na juya na dogara sandata na koma Cikin ɗakina, To ku fidda rai da zan sake fitowa, wannan ce kaɗai damar da kuke da ita” tsohuwace tayi maganar, fuskarta ɗauke da shu’umin murmushi, mai nuna tsantsar farin Ciki, bata ta6a jin nishaɗi ba irin na yau, a hankali angel ta kawar da idonta daga kan fuskar tsohuwa ta mayar dasu kan fuskokinsu Javed da yasmin da hibba dake a zuƙunne saman gwiwowinsu, fuskarsu sharkaf da hawaye, gyaɗa kai kawai tayi Jiki ba kwari ta maida idonta ga tsohuwa, murya na kerma tace”zan roƙe ki ne bada son raina ba, dan haka kada ki yi tunanin kin ƙasƙantar dani ne, zanyi ne saboda waɗannan bayin Allahn, da kuma ƴar uwata dake acikin mawuyacin hali, Sannan kada ki yi tunanin kece zaki bata lafiya, Allah subhanahu wata’ala shine ya baki ikon yin hakan, domin kuwa saida yardar shi ne komai yake wakana” daƙyar takai karshen maganar ganin tsohuwa na ƙoƙarin juyawa ta koma Cikin ɗakinta, aikuwa da sauri angel ta ɗago ta zuƙunna saman gwiwowinta, Muryarta a disashe tace”Na roƙe ki dan Allah badan Ni ba, kije ki duba lafiyar Deeja” Wata irin mahaukaciyar dariya tsohuwa ta fashe da ita, tamoji tamojin fuskarta har rawa suke yi, saboda tsabar yarda jikinta ke jijjiga, Angel kuwa wani irin ƙululun baƙin Cikine ya Turniƙe zuciyarta, har wani zazza6i taji ajikinta, Kusan atare su javed suka sauke ajiyar zuciya, saboda tsabar mugunta saida tsohuwa tasa angel ta maimaita maganar da tayi kusan sau uku tukunna tace”hakan ya yi mini, haƙiƙa yau na shaida irin ƙaunar da kike yi musu, ke ɗin uwace ta gari agare su, Ina ji araina cewa nan gaba har rayuwarki zaki Iya sadaukarwa akansu, don ba ƙaramin mamaki nayi ba ganin irin yadda kika sauke duk wani girman kai naki da kafiyarki wurin roƙo na akan lafiyar ƴarki deeja, Naji daɗi sosai Albarka zata tabbata akanki, ni kuma yau ta kasance ranar tarihi arayuwata, wato ranar da the most arrogant young lady in the world ta zuƙunna saman gwiwowinta domin ta roƙe ni……”Tsohuwa bata karasa maganarta ba, muryar angel Cikin fushi tace”Kinga surutun ya isa haka, tunda nayi maki abunda kike so, kema saiki biya ni” cike da shaƙiyanci tsohuwa tace”To gimbiya sarautar mata, Ai ko me kike so yau zanyi maki shi” Harara angel ta watsa mata kamar kwayar idanuwanta zasu faɗo kasa,
Juyawa tsohuwa tayi zata koma cikin ɗakinta, muryar javed ta katse ta”deeja fa? Naga zaki koma Cikin ɗaki” batare da ta juyo ta kalle shi ba tace”Ku jira ni yanzu zan fito,” Tsayawa su kayi suna jiran ta, Badajimawa ba sai ga tsohuwa ta fito hannunta ɗaya ruƙe da gorar ruwa ta gargajiya, miƙa ma javed tayi”Ruƙe mun nan, Mu je ciki ka nuna mini ita” da sauri javed ya sanya hannu biyu ya kar6i gorar ruwan, Suka shiga gaba tabi bayansu, angel dai bata bi su ba, A nan ƙasa ta kwanta zuciyarta na tafarfasa, Ji take yau ta bata kanta, tun da harta durƙusawa tsohuwa,
Lokacin da suka shiga Cikin toilet ɗin, Tsohuwa ta basu umarnin su fita waje su jirata, haris dai bai yarda da ita ba, ya ƙyaleta ne kawai yaga iya gudun ruwanta, ɗaya bayan ɗaya suka fuce daga Cikin toilet ɗin, kafin javed ya fita sai da ya fara ajiye mata gorar ruwan a kasa, Tukunna yasa kai ya fuce, Cikin ɗakinsu suka koma Kowa zuciyarshi cike da zullumi, daga Cikin toilet ɗin suka soma Jin kukan deeja yadda kasan ana zare ranta, hankalinsu yai matuƙar tashi, gaba ɗaya suka gaza jurewa, Komawa su kayi Cikin sashen toilet, Koda suka je bakin ƙopar toilet ɗin a datse suka same shi, A dole suka zauna ƙasa zaman jiran fitowar tsohuwa, danish dai yana acikin ɗakinsu, bai bi bayansu ba, Saman gadonshi ya koma ya zauna, yana satar kallon angel dake kwance a ƙasa, Yana so yaje ya lallashe ta amma yana tsoron masifarta, don kuwa yau sai Allah, Taci ka ta batse, jira take kawai ta samu wanda zata huce haushinta akanshi,’ wannan dalilin ne ya hana shi tunkararta, gudun kada yasha mari,
Yau fa babu bacci, Dare ya koma musu tamkar rana, azeeza ce kaɗai take gyangyaɗin bacci, tana atsakankanin Batool da naufal, ta ɗan ɗaura kanta saman kafadar batool, ga dukkan alamu bacci take so ta yi, Naufal ne ya lura da ita, ruƙo hannunta yayi acikin nashi yace”azeeza tashi muje in raka ki cikin ɗaki ki kwanta, kada ki yi bacci anan” maƙe mashi kafaɗa tayi muryarta adisashe tace”ba yanzu zan kwanta ba, sai na jira an fito da deeja” Haris dake sauraronsu yace”naufal, Kada ka biye mata, pls ka ɗauke ta, ka kaita cikin ɗaki,” rigima ta sanya musu, akan ita bazata je ta kwanta ba, sai ta ga deeja” Naufal bai tsaya sauraronta ba, ya sanya hannayenshi biyu ya sa6e ta, kamar wata ƴar baby haka ya ruƙota ya nufi Cikin ɗakin da ita, A saman gadonta ya kwantar da ita, tare da janyo bargonta dake a nannaɗe ya lullu6e mata jikinta, sai gashi ta yi shiru alamar bacci yai awon gaba da ita, ajiyar zuciya naufal ya sauke sai da ya fara ɗagowa ya kalli danish dake kishingiɗe saman gadonshi, Ya kuma kallon angel dake kwance a ƙasa, Ya ɗan girgiza kai, kafin Ya juya ya nufi Cikin sashen toilet ɗin, Lokacin da naufal ya shiga Ciki, Ya yi dai dai da buɗe ƙopar toilet da tsohuwa ta yi, aikuwa Jikinsu har 6ari yake yi wurin miƙewa tsaye idon kowa akan Ta, fitowa tayi hannunta ruƙe da sanda, Ta ɗago ta kallesu tace”Ina babar taku take Ne”? Suka haɗa baki wurin cewa”Tana acikin ɗaki” tsohuwa tace”Ku je kuce mata ta ɗauko bargo tazo, ta ɗauki diyarta, ” amsa mata suka Yi da toh, Batool ce taje cikin ɗakin ta isar da saƙon zuwa ga angel, atare suka dawo hannun angel ruƙe da bargo, fuskarta a kumbure take hararar tsohuwa,
Matsa mata Hanya tsohuwa tayi”Ki shiga Ki lullu6a mata shi ajikinta, ki fito da ita, ” batare da ta amsa mata ba ta nufi ƙopar toilet ɗin ta shige Ciki, tsohuwa ta kalli javed tare da cewa”idan sun fito ka ɗauko mini gorar ruwan nan, ka biyo ni da ita” ya amsa mata da toh,’. Har ta fara tafiya ta dan juyo tana kallon fuskokinsu tace”Yakamata kuje ku kwanta, duk da ma naga kamar Lokacin ya ƙure garin ya waye” bata rufe baki ba, sai ga hasken ɗakin su Ya gauraye ko’ina, sun yi matuƙar yin mamaki, maganar tsohuwa ta tabbata, har gari ya waye basu sani ba, Atare suka haɗa baki wurin yi mata godiya, bata amsa musu ba sai cewa tayi”bani yakamata ku yi ma godiya ba, Babarku ce ta cancanci hakan,” Fuskarta ɗauke da murmushi tayi maganar, tare da juyawa ta fuce daga cikin sashen toilet ɗin ta nufi dakinta,
Fitar tsohuwa keda wuya, Sai ga angel ta fito hannunta ɗaya talla6e da deeja, da alama hada wanka tsohuwa tayi mata, uniform dinta na sanye a jikinta, Daga sama kuma bargon da angel ta lullu6a mata ne,” wani irin farin Ciki ne Ya lullu6esu, Ganin ƴar uwarsu ta wartsake har tana iya taka kafarta, Sai faman sauke ajiyar zuciya suke Yi, wuce wa gaba angel ta yi suka bi bayansu, a bakin gadon deeja suka tsaitsaya, angel ta taimaka mata ta kwantar da ita saman gadonta, muryar deeja na ɗan kerma tace”Sanyi nake ji, ku ƙara mun wasu bargunan akaina, Ko jikina ya yi ɗumi,” Da sauri kowannan su ya nufi gadon shi suka ɗauko bargunansu suka lullu6a mata ajikinta, Cikin ƙanƙanin Lokaci bacci ya yi awon gaba da ita, duƙawa angel tayi agaban gadon deeja daga gefe, ta soma karanto addu’o’i tana tottofa mata, bayan ta kammala ta ɗago da idanuwanta ta kalli su Batool dake a kewaye da ita, tace dasu suyi mata addu’a suma, kowa ya ɗan zuƙunno da kanshi saitin gadon, suka karanta abun da taɗan koya musu suka tofa mata, daga bisani haris yace dasu, Su koma su kwanta, ganin jiya basu samu isasshen bacci ba, ba musu suka amsa mashi da toh, kowannan su Ya wuce saman gadon shi, suka kwakkwanta, Ya rage saura haris dake a tsaye sai angel dake zuƙunne agaban gadon deeja, wuri ya samu gefen gadon deeja ya zauna, ba laifi yanzu hankalin shi ya ɗan kwanta, kallon angel yae tare da cewa”Ke fa? Baki jin bacci”? daƙyar ta iya ɗago da ido ta kalle shi, baiwar Allah damuwar duniya ta isheta, maganganun da deeja ta faɗa mata sune suke ta yi mata yawo a cikin kanta,
“Dake nake magana” muryar haris ce ta kuma katse ta, batare data amsa mashi ba, ta yunƙura ta miƙe ta nufi gadonta, tana isa ta haye sama ta kwanta, koda suka haɗa ido da danish dake kishingiɗe saman gadon shi, harara ta watsa mashi, kafin ta juya mashi baya, lumshe idanuwanshi yayi, zuciyarshi duk ba daɗi, saboda ya gane dalilin dayasa ta harare shi, dole taji haushin shi, saboda rashin ta6uka komai, shi kuma aganinshi indai baida maganin abu to baida amfani ya tsoma baki, shiyasa yake yin shiru, Amma har ga Allah yana matuƙar damuwa dasu, Yana jin tausayin ƴan uwanshi, Yana matuƙar ƙaunarsu fiye da kan shi,
Rabi da kwatarsu tuni bacci Ya yi awon gaba dasu, mutun uku ne suka rage, Haris da tuni ya jima da komawa saman gadonshi, damuwar halin da deeja ke aciki ce ta hana shi runtsawa, Sai kuma Parveen da Yunwa ta addabe ta, ta lafe kwance saman gadonta sai juyi take yi, bayan ita kuma sai Angel wadda babu alamun zata runtsa, ita fa babban abunda ke damunta, irin takurawa rayuwarsu da ake yi, da kuma cutar dasu da ake yi, tana matuƙar jin tsoran tarasa wani acikinsu, tabbas zata ji raɗaɗin da yafi wanda taji a lokacin da ƙaddara ta rabata da daddynta, a yanzu tafi jinsu acikin zuciyarta fiye da kowa ma nata, yanzu bakomai yafi tsaya mata arai ba, face mutun shiddan nan da Deeja ta faɗa mata cewa ta gansu akanta, Shin su wanene su? Uban me suka aikata mata? Kodai su duka suka afka mata a lokaci ɗaya suka lalata rayuwarta? Innallahi wa’inna ilaihirraji’un, Allahumma Ajirni fil musibati…… wani irin ɗaci take ji acikin zuciyarta, idanuwanta suka cuccuko tab da ƙwalla, ta tausaya ma rayuwarsu, Idan har suka cigaba da kasancewa acikin kurkukun nan tabbas kuwa wata rana za’a nemi koda gawawwakinsu ne arasa, Ita dai bata fatan tarasa ranta acikinsa, kodan saboda ta gano su wanene suka assasa ƙungiyar da kuma waɗanda suka sadaukar dasu, Wannan alƙawarine ta ɗaukarwa kanta, sai sun ɗanɗani kuɗarsu, sai sunyi danasanin haihuwarsu da uwarsu ta yi acikin duniyar nan!!! Acikin zancen zucin da take yi, kwata kwata bata sanya tsohuwa aciki ba, duk da itama taji haushin abunda tayi mata ayau, amma ta ajiyeta gefe ɗaya, saboda ba ita bace agabanta, masu ƙungiyar kurkukun ƙaddara sune agabanta, da kuma waɗanda suka yi sacrificing ɗinsu.
Lokacin da giants suka shigo kawo musu abinci, Mutun ɗaya ce ta Iya miƙewa, har zata tada su daga bacci, Haris yace ta ƙyalesu, taje ƙarƙashin gadon batool ta ɗauko kwandon da suke ajiye abinci, ta kwaso musu aciki, idan suka farka zasu Ci, ta amsa mashi da toh, Bayan ta ɗauko food basket ɗin taje gaban jerin farantan da giants suka sauke musu, Ta zuƙunna ta ajiye kwandon gefe, ta sanya hannu ta yaye jan ƙyallen dake akan farantin farko, Steak and onions ne, Yankan nama manya manya sunji albasa da kayan ƙamshi, Hannu tasa ta dinga ɗebowa tana zubawa cikin kwandon, duka ta kwashe, Ta kuma buɗe faranti na biyu dake ɗauke da Snacks tare da madaidaicin bowl Na kayan marmari ta kwashe komai ta ɗaura akan naman, Faranti na ƙarshe Bottles waters ne, Miƙewa tayi tare da sanya hannu biyu ta ɗauke kwandon, Yayi nauyi, A agaban gadonta ta ajiye shi, ta koma domin kwaso robobin ruwa, dake a jere saman faranti na ƙarshe, Ta ruƙo su a hannayenta, Bayan ta kammala giants dake a tsaye suka raƙwafa atare suka ɗauke farantan, Tare da kama hanya suka fuce daga Cikin ɗakin, Zama parveen tayi agaban gadonta, ta ɗago ta kalli haris dake kallonta tace”Ba yanzu zaka Ci ba? Yana daga kwance saman gadonshi, Yace mata”sai sun farka zai ci” tace”Nima in jira sai sun farka”? Ba don taso ba ta faɗi hakan, Girgiza mata kai yai alamar a’a kafin yace”zaki iya ci mana, kici iya cinki, sauran da kika rage sai muci, ae nasan duk haɗamarki ba zaki iya lamushe abincin duka ba, ko rabi ma ba zaki iya tadawa ba” murmushine ya bayyana akan fuskar Parveen, jin abunda yace, bata ƙara tanka mashi ba, takai hannu tana zakulo naman tana turawa abaki, Sai da taci iya cinta, ta haɗa da snacks ɗin duka, har saida cikinta yayi ƙato, tukunna ta dakata da ci tana faman shafa ciki, bottle water ta ɗauka ta buɗe tasha ruwan, Data kammala ta tura kwandon ƙarƙashin gadonta, Haris yace”Salon da anjima idan kinga muna cin namu, kice kema zaki ci,” dariya ta ɗanyi har dimple ɗinta na saman chin ɗinta ya lotsa, komawa saman gadonta ta yi tare da hayewa, da niyar itama ta samu baccin ya ɗauke ta,
Basu suka tashi farkawa ba, sai da suka kwashe tsawon awanni suna bacci, daga bisani yunwa ta fara farkar dasu, ɗaya bayan ɗaya, kowa ya miƙe yana hamma, Haris yace suje su wanko bakinsu suzo suci abinci, Suka amsa mashi da toh, Kowa ya nufi toilet, bayan sun kammala wanke fuskokin suka zo suka zazzauna ya dauko musu kwandon abincin dake a karkashin gadon parveen, Ya ajiye musu atsakiyarsu, ba yadda baiyi da angel ba akan tazo taci abinci amma taƙiya saima ce mashi tayi ita bata jin yunwa su dai su ci, Komawa yayi bakin gadon danish a lokacin ya ɗan fara bacci, ya tada shi tare da cewa” ka taso mu ci abinci,” danish yace”suje su ci baijin yunwa” lamarin yai mutuƙar ɗaurewa haris kai, su biyu sunce basu jin yunwa, Anya kuwa lafiya? Ko dai duk don saboda rashin lafiyar deeja ne yasa suka ƙi Cin abinci? A ƙarshe daya gaji dayi musu magana akan su taso sai ya ƙyale su, ya koma wurin dasu batool suke a zazzaune shima ya zauna, Suka tsoma hannayansu suna Cin abincin, Ba duka suka cinye ba, Sai da yace su rage ma Deeja idan ta farka, Sai kuma Angel da danish, Yankan nama shida shida suka ajiye ma kowannan su, Sai fruits, banda snacks duka suka cinye shi, Sun dai ajiye musu bottle water Biyu, bayan sun kammala suka ajiye musu nasu a karkashin gadon batool,
Wuraren marece, Deeja ta farka muryar ta a disashe take faɗin, Ruwa zata sha, ƙishi take ji, da sauri haris Yaje ya ɗauko robar ruwa cikin wanda suka ajiye musu, Ya koma gefen gadonta ya zauna yana kallonta a lokacin ta yaye bargunan da suka lullu6a mata, daƙyar ta yunƙura ta miƙe zaune ta ɗan jingina bayanta jikin bango, Yadda kasan fatalwa, tayi haske ga rama, ƙashin wuyanta duk ya fito 6aro 6aro jikin fatarta, Gashin kanta kuwa duk ya hargitse, Baiwar Allah daga gani ba ƙaramin Jiki taji ba.
*❤❤❤PRISONERS❤❤❤*
“Sannu deeja ya jikin naki” ya yi maganar tare da buɗe murfin robar ruwan ya kwafa mata baki, Hannu bibbiyu tasa ta tallabe hannanyenshi dake a ruƙe da robar, saboda tsabar yadda take shan ruwa kana Iya jin sautin throat ɗinta kwat kwat! Har sai da yace mata tasha a hankali kada ta shaƙe, janye robar ta yi da hannunta alamar ta ƙoshi, Sai lokacin ta samu damar ƙare mashi kallo, su batool dake a zazzaune saman gadajensu suna yin fira, Ganin deeja ta farka yasa suka dawo bakin gadonta, wasu suka zauna wasu kuma suka tsaya atsaye, A hankali take binsu da kallo ɗaya bayan ɗaya, Ba ƙaramin daɗi taji ba, irin yadda suka nuna mata kulawa, sai dai a yayin da take kallonsu, wani irin tausayin kansu ne ya kamata, domin kuwa tasan ƙarshen su yana dab da zuwa, a yanzu bakowa tafi jimawa ba face waɗanda ba’a ta6a ɗauka acikinsu ba, musamman azeeza da tafi kowa rauni acikinsu, gata ƴar ƙarama duk da ba shekaru suka fita ba, amma babu alamun girma atattare da ita, saboda rashin tsawonta, idan suka miƙe tsaye ko kafaɗarsu bata kai ba, farat ɗaya ka kalleta sai ka yi hasashen shekararta Goma, saboda ƙarantar jikinta,
tana Cikin yin zancen zucin nan muryar batool ta katse ta da cewa”deeja me kike tunani muna ta yi maki magana tun ɗazu amma kin yi shiru baki ce komai ba, ina fata kina lapiya,” ajiyar zuciya ta ɗan sauke, still idonta na akan azeeza data zauna gefen gadonta ita dasu Yasmin, haɗa baki suka yi wurin yi mata ya jiki ta amsa musu da cewa”Alhamdulillah Jiki da sauƙi, Naji daɗi sosai da irin kulawar da kuka bani, Ina matuƙar alfahari da ku ƴan uwana nakaina” Murmushi suka saki gaba ɗayansu, ta mayar da idonta kan haris dake kallonta, ta lura da irin damuwar da ya yi akanta,
“Lokacin da aka tafi dani, haris ya iya Cin abinci kuwa”? da zolaya tayi maganar, gaba ɗaya suka yi dariya, yasmin tace”ae tunda aka ɗauke ki, ya gaza samun natsuwa, idan ya kwanta saman gadonshi idanuwanshi na fuskantar ceilling sai ya ɗauki tsawon lokaci bai tashi ba, wata’ƙil hoton fuskarki yake gani” Harara haris ya watsa ma yasmin da tayi maganar,
Kafin yace “Abunda ta faɗa ba ƙarya bane, Na damu dake sosai, Ko bacci nake yi sai nayi mafarkin ki, Bani kaɗai ba Kowa ya damu dake” duƙar dakai deeja ta yi hawaye suka cicciko idanuwanta, muryar azeeza ce ta ratsa kunnan ta”Sister deeja pls don’t cry, muna cikin farin cikin samun sauƙin ki, kada ki karya mana zuciyoyin mu,” azeeza na rufe baki, deeja ta karasa kifa kanta saman gwiwowin ƙafarta, sosai ta fashe da kuka, Sai faman lallashinta suke yi, ita bakomai ne yafi damunta ba, face tuna cewa wata rana fa dole wani ya mutu a cikin su, gashi sun shaƙu da juna, Allah kaɗai yasan raɗaɗin da zasu ji aranar da suka rasa wani acikin su,
Haris ne yace dasu”kubarta ta huta, kowa yaje yayi wanka, zan kula da ita” kasa tafiya suka yi har saida ya maimaita musu maganar tukunna suka miƙe, azeeza hada bubbuga ƙafarta tana faɗin”wai shi yacika takura, yana ganin kamar yafi kowa girma, shine zai wani kore su” murmushi haris ya saki batare da ya mayar mata da martanin ba, bayan sun bar bakin gadon deeja, suka nufi toilets domin yin wanka, hannunshi ɗaya ya ɗaura asaman bayan deeja yana ɗan bubbuga shi cikin sigar lallashi yake yi mata magana”its ok my lovely sis, kukan ya isa haka, ki daina pls kina ƙara ma kanki ciwo, kuma kina sanya mu cikin damuwa” Sai lokacin deeja ta ɗago da idanuwanta sunyi jawur da su, yadda kasan na mashayin giya, kallon shi kawai take yi kamar yarda shima yake kallonta, matsawa yaɗan yi dab da ita, ya sanya hannunshi ya ruƙo arm ɗinta tare da janyo da ita, ta kwanto saman kafaɗarshi, lallashinta yaci gaba da yi har saida ta daina yin kukan, Cikin sanyin murya tace”Danish baizo ya duba jiki na ba, naga fuskar kowa amma banda tashi, meyasa”? Girgiza kai haris ya ɗanyi dama saida ranshi ya bashi cewar saita yi magana akan danish, Yaji haushi da takaicin irin halin ko’in kulan da danish yake nuna musu, duk da yasan yana yi badan baya ƙaunarsu ba ne, Amma aduk lokacin da basu jin daɗi zaiyi wuya yaja su ajiki, har ƙwara Azeeza, itama ɗin ya lura don yana mata kallon ƙaramar halitta ne shiyasa yake damuwa da ita sosai, muryar deeja ce ta kuma katse shi”haris naji ka yi shiru? Ko dai danish bai yi farin ciki da dawowata ba ne?”da sauri yace”A’a, Ke ce baki ganshi ba, danish ya damu dake, ko adaren jiya da angel tazo tada mu daga bacci, hada shi muka shigo cikin toilet ɗin,” Deeja tace”Amma shi bai jani ajiki ba, kamar yadda kayi” runtse ido haris ya ɗanyi kafin ya buɗesu a hankali yace”ki yi haƙuri yanzu bacci yake yi, amma ina da tabbacin zuwa anjima idan ya farka zaizo da kanshi ya duba jikin ƴar uwarshi” ta6e baki ta ɗanyi tare da cewa”da kamar wuya” ruƙe hannunta haris yai acikin nashi yace”Akwai steak da muka ajiye maku tare da fruits in ɗauko maki ki ci” yayi mata maganar ne don ya kawar mata da zancen danish, ɗago da kanta ta ɗanyi daga saman kafaɗarshi tace”Anya zan iya ci, baki na babu daɗi, amma ina jin yunwa aciki na”
“Don’t worry ur self xan taimaka maki ki ci shi” yakai karshen maganar, tare da miƙewa daga saman gadonta, Ya juya ya nufi gadon batool dake gefen na Danish, yana kwance sai baccin shi yake sha hankali kwance, guntun tsoki haris yaja ji yake kamar yaje saman gadonshi ya shaƙon wuyanshi, Bayan ya ɗauko kwandon ƙarƙarshen gadon batool, Ya juya ya koma gefen gadon deeja, a tsakankaninsu ya ɗaura basket ɗin, Deeja sai kallon shi take yi don ba ƙaramin burgeta yake yi ba, saboda irin yarda yake nuna damuwarshi akanta,
“Angel ta yi bacci ne”? Yace”I don’t think so, Kinsan jiya ranta ya 6aci sosai, saboda tsohuwa tace bazata duba lafiyar jikin ki ba, har sai ta durƙusa agabanta ta roƙe ta, Inaga shiyasa ta lafe saman gado ta rufe ido, amma ba bacci take yi ba” juyawa deeja tayi tare da kallon gadon danish dana angel, duk suna kwance abunsu, kafin ta juyo da kanta tana fuskantar haris dake miƙo mata yankan Nama, buɗe baki tayi ya tura mata aciki, tasa hannu ta dafe tana Ci, sai da ta kammala taunewa tace”Haris, naji daɗin abunda angel tayi saboda Ni, farkon zuwanta prison din nan, Nayi tsammanin bata ƙaunata, duk da a lokacin Mune muka fara nuna mata ƙiyayya, Amma yanzu na gane kuskure na, domin kuwa angel tana matuƙar son mu sosai, kuma ita ɗin Alkhairi ce agare mu,” jinjina kai haris ya ɗanyi, tare da cewa”Nima na fahimci hakan, yanzu dai ki maida hankali ki ƙarasa cinye naman kisha fruit ɗin sai ki kwanta, ki ƙara hutawa” murmushi tasakar mashi, shima ya mayar mata da martani, A tsanake yaci gaba da bata Naman tana ci, bayan ta kammala tasha fruit ɗin ta kwanta saman mattress ɗin, Ya lullu6a mata bargo ajikinta, baisan ya zai ƙare dasu angel ba idan suka farka suna Jin yunwa, ganin deeja tana Ci yasa ya ƙara yankan nama Shida Cikin nasu Ya haɗa mata, kuma duka ta cinye shi, wanda ya rage acikin kwandon yanka shida ne na mutun ɗaya sai dai su raba uku uku ita da danish, Sai apple guda ɗaya, ayaba biyu, ɗauke basket ɗin yae daga saman gadon deeja, Yaje ya tura shi ƙarƙashin gadon batool, A lokacin duk sun fito daga wanka, ba ƙaramin daɗin jikinsu suka Ji ba, a tsakiyar ɗakin nasu suka hallara, Hannah ce ta shirya musu wasan da zasu Yi,
Angel dake kwance sautin hayaniyarsu duk ya cika mata kunnuwanta, pillow ta sanya saman kanta ta toshe kunnuwanta, Ƙasa ƙasa take jin hayaniyar ta ɗan ragu, wani irin baccine yayi awon gaba da ita batare da ta shirya yin shi ba, su batool sunsha wasansu, har sai da dare yayi hasken ɗakin ya ɗauke sannan kowa ya koma saman gadonshi ya kwanta,
Batare da sun kunna fitilun ɗakinsu ba, yayi duhu sosai, Har time ɗin bacci bai ɗauke su ba, fira suka soma yi a tsakaninsu kowa yana daga kwance saman gadon shi, Batool ce ta fara cewa”kun lura da angel duk yinin yau bata sauko daga saman gadonta ba” Haris yace”Kije ki tada ta mana” muryarta ƙasa ƙasa tace”So kake in jama kaina, ae tun ɗazu naso inje in lallashe ta, amma fargaba ta hana ni, kasan halinta, zata iya sauke fushinta akaina”Hanna tace”nima abunda ya hanani tunkararta kenan, kada in sha mari” Gaba ɗaya suka tuntsire da dariya, Javed yace”gaskiya banji daɗin abunda tsohuwa ta sanyata tayi ba, kawai don ba yadda zamuyi ne shiyasa muka tursasa mata akan ta durƙusa mata” Haris yace”nifa Haushin tsohuwa nake ji, don me zata ce dole sai angel ta durƙusa mata tukunna zata duba lafiyar deejan mu? Kenan koda ace mutuwa za ta yi bata iya duba ta ba, in har angel bata bi umarnin taba, sai dai tarasa ranta?Anya kuwa tsohuwa tana son mu? Eve tace”nima nafara kokwanto akanta, ae bata ƙaunar mu, shiyasa ran nan naƙi gaishe da ita,” eve na rufe baki hibba tace”kuma hada cewa wai angel ce babar mu, baku ji me tace ba ɗazu ba da muna a wurin toilets, ” waɗanda basu sani ba, suka tambayeta me tsohuwa tace, Nan hibba ta kwashe maganganun da su ka yi da ita, ta sanar musu, aikuwa sunsha dariya, batool tace”oh shiyasa naji tace aje akira babar mu tazo ta ɗauki ƴar ta, tsohuwa ta iya zolaya, gashi yau ta fusata mana Mamanmu,’ rubina tace”Abunda ta faɗa gaskiya ne, angel itace babar mu, saboda tafi kowa damuwa da mu, bazan ta6a manta irin wahalar da ku kasha ba, ita dake batool wurin yin jinyarmu lokacin da giants suka dawo damu, kun nuna mana ƙauna, muna matuƙar alfahari daku,’ azeeza tace”Da Batool da angel sune zasu zama iyayen mu idan muka fita daga Cikin prison ɗin nan, zasu bamu kyakkyawar kulawa” eve tace”Nifa ina tsoran ranar da zamu fita, mutanan dake awajen kurkukun nan zasu Iya su cutar damu, ko su kashe mu ma,” parveen tace”waya faɗa maki? Ba angel tace mana gidan daddynta zamu zauna ba, ina ruwan mu da wasu mutane, ae ba akansu zamu zauna ba, dangin angel ne zasu taimake mu”da ƙwarin gwiwa parveen tayi maganar, Haris dai sai dariya yake yi musu, jin irin wasiƙar jakin da suke saƙawa, wadda bazata ta6a zama gaskiya ba, azeeza tace”Na ƙosa Allah, zamu ji daɗin rayuwar mu, kowa zai sakata ya wala, muje inda muke so, ni dai kawai burina inga ga gidansu angel da kuma daddynta,”
“Amma fa ita kanta angel ɗin bata da tabbacin cewa daddyn nata yana araye koya mutu,” acewar Batool, azeeza tace”Ae ko baya araye akwai auntynta aneelerh, da mommynta adama tace duk danginta ne kuma zasu ɗaukin nauyin ɗawainiya damu” sai lokacin javed ya tsoma baki, muryarshi da alamun bacci yace”pls, surutun ya isa haka, kun takura mana, dare fa yayi sosai, yakamata kowa yaja baki yayi shiru ku kwanta ku yi bacci, kun zauna kuna ta tsara shirme da shiririta, kuda fita daga Cikin kurkukun nan sai dai ata mafarki, amma badai zahiri ba” a ƙule ya ƙarasa maganar, shi kanshi javed ɗin da yayi maganar ba ƙaramin buri yake dashi ba akan su fita, kawai dai baison suna ƙwallafa rai ne, tun da babu ƙopar da zasu Iya guduwa acikin kurkukun, tun da javed yai musu magana babu wanda ya kuma cewa wani abu, tuni bacci ya fara ɗaukarsu, mutun ɗaya ce bata runtsa ba, Jira take suyi nisa dayin bacci ko ta samu ta lalla6a taje ƙarƙashin gadon batool ta ɗauko Yankan naman da aka ajiye masu danish ta cinye, dama ta ƙware wurin iya satar ragowar abinci,
lokacin da parveen ta tabbatar da cewar sun nutsa Cikin baccin su, Cikin sanɗa ta sauko daga saman gadonta, duk da duhun dake akwai hakan bai hanata gano inda gadon batool ya ke ba, daga gefen gadon ta zaƙunna tare da zura hannu cikin ƙarƙashin gadon ta janyo kwandon, har wani lumshe idanuwanta take yi tana shaƙar ƙamshin naman, tana yunƙurin tsoma hannu da niyar ta ɗauki tsoka ɗaya, kwatsam taji an damƙi wuyan rigarta ta baya, A matuƙar tsorace ta wage baki zata fasa ƙara, yayi saurin sanya tafin hannunshi ya toshe mata baki, ta yadda bazata iya yin ihun ba, Saboda tsabar tsoratar da tayi har saida ƴan hanjin Cikinta suka kaɗa, Jikinta sai kerma yake yi, shegen tsoro ne da ita, duk a tunaninta ɗaya daga Cikin aljanun da tsohuwa ta basu labarin akwaisu agidan kurkukun ne yazo ya damƙeta, zazzaro idanuwanta tayi waje, jikinta ya ɗau zafi,
Cool voice ɗinshi ce ta ratsa kunnanta”its me, me kike yi agaban gadon batool? Ko kinzo ne ki sace mana steak ɗin mu da aka ajiye mana ne? wata irin nauyayyiyar ajiyar zuciya ta sauke jin muryar danish, Ta harzuƙa sosai ashe shine ya firgitar da ita, tayi matuƙar yin mamakin taya akai ya iya ganinta Cikin duhu? Kuma har yasan cewa tazo satar naman da aka ajiye musu ne, bayan basu da masaniyar sun ajiye musu,
“Am talking to u, ki amsa mini, dama har yanzu baki daina bin abincin mutane kina satar musu ba”? Yawu ta haɗiya, tare da sanya hannayenta ta zame mashi hannunshi daya toshe mata baki dashi” ta juyo tana fuskantar inda yake atsaye, duhu ya hana ta ganshi dakyau,
Muryarta kamar zata fashe da kuka tace”Ae zuwa nayi inga idan ya lalace, in zubda, tunda naga tun ɗazu da safe aka ajiye maku amma baku ci ba” muryarshi asake yace”A cikin Cikin ki zaki zubda shi ko?” shiru tayi bata bashi amsa mishi ba,
“Maza ki wuce kije ki kwanta, tunkafin in yi wurgi dake” tana ƙunƙuni ta juya tana laluban hanya harta gano gadonta ta haye ta kwanta, zuciyarta duk ajagule, taso ace tacinye naman duka, ita uwar haɗama, kuma ba yunwa take ji ba,
Bayan tafiyar parveen, danish ya duƙa inda ta ajiye kwandon, yana ƙoƙarin ruƙe handle ɗin yaji an damƙi hannunshi, har sai da ya ɗan ji bugun zuciya, duk da bai iya gane wacece ba, amma yaji aikin shi cewa ANGEL ce, itama parveen ɗazu daya Canko sunanta, saboda yasan halinta ne, Ya farka yana Jin yunwa, ɗazu yaji haris yana cewa arage musu nasu naman shiyasa ya yi tunanin akwai saura, wannan dalilin ne yasa shi saukowa daga saman gadon shi, ya nufi gadon batool donya duba yaga idan an rage musu nasu, Yana tunkaro bakin gadon yaji motsin mutun, nan take ranshi ya bashi cewar itace, dama halinta ne,
Kusan atare zuciyoyinsu ke bugawa, gashi dai basu ganin juna dakyau, saboda duhun da ya mamaye idanuwansu, muryarshi na ɗan rawa ya ambaci sunanta”Angel” Muryarta a kausashe tace”Ni ce, sai me? Idan ma yankan naman nan kazo ka ɗauka sai dai ka haƙura kabar mini saboda nafi ka jin yunwa ” yadda tai maganar babu sassauci, dagaske yunwa take ji sosai, kamar ta cinye ƴan hanjin Cikinta, shima kuma yunwar yake ji, cikin sanyin murya yace”me zai hana mu ci atare, sai mu raba” kamar tana ganin shi tace”A’a, kawai dai ka haƙura kabar mini, saboda ba isata zaiyi ba”
“but why ɗazu baki ci ba? Da haris ya yi maki magana”? A harzuƙe tace”Saboda bana jin yunwa a lokacin yanzu kuma ina jinta, meyasa ma ka tambayeni? bata jira yabata amsa ba, ta kuma cewa”To kai meya hana ka cin naman ɗazu”? Tayi tambayar tana jiran jin amsarshi, sai da ya ɗanyi jim before yace”saboda ke, na damu da halin da kika shiga, naji kince ba zaki ci abinci ba, shiyasa nima naƙi ci, saboda bana so ki ji yunwar ke kaɗai,” sam bata ji ɗaɗin maganarshi ba, saima haushin shi data ƙara ji, muryarta ƙasa ƙasa tace”Nifa baka burgeni komai zaka Yi, ko son ganinka ma bana yi, wlh haushinka nake ji kamar in nannaushi fuskarka, ka 6ata mini rai sosai, Kana nuna ka damu dani wannan duk abanza ne, tun da baka iya nuna damuwarka akan deeja, da aka dawo da ita daren jiya, kowa yana tofa albarkacin bakinsa amma kai kaja baki kayi shiru amatsayinka na babba acikin mu, har haris ma yafi ka sanin yakamata,” Tana kai ƙarshen maganar, ta fusge kwandon daga hannunshi ta miƙe, cikin duhu ta nufi table dinsu ta ɗauko fitila ɗaya ta kunnata, A saman dining Carpet ta zauna, Ta ajiye kwandon agabanta, ita kuma fitilar ta ajiyeta a gefe, Zuciyarta duk ba daɗi, ita kanta bada son ranta take gaya mashi magana ba, daurewa kawai take yi,
Daga inda yake a zuƙunne bakin gadon batool yana hangenta, jikin shi yayi mugun yin sanyi, duk sai yaji ya rasa kuzarinshi, tamkar ya fashe da kuka haka yake ji, baya son angel tana yin fushi da shi, hatta faɗan da take yi mashi baya so, dan ba yadda zai da ita ne, kasa jurewa yai ya yunƙura ya miƙe ya nufi saman dining carpet ɗin, Yana ƙarasawa ya zauna tare da lanƙwashe ƙafafuwanshi Yayi zaman cin tuwo kamar yadda tayi, Ya kasance suna fuskantar juna ita dashi, Ko kallo bai ishe ta ba, bakinta acunkushe da yankar naman data tura sai tauna take yi, duk in suka haɗa ido saita jefa mashi harara, bawan Allah miyan sai tsinkewa yake yi,
yana so ya ɗauki naman yaci, sai dai ya kasa saboda gudun faɗan ta, Muryarshi arauna ce yace”pls angel, ki bari na ɗauka naci nima, koda fruit ɗinne, am serious yunwa nake ji” sai da ta kammala taunar naman dake abakinta tukunna tace”baka da ƙarfin da zaka ƙwata ne? Wai kai wani irin namiji ne? Mace kake marairaice ma fuska? duƙar da idanuwanshi ƙasa ya yi batare daya tanka mata ba, dogon tsoki taja, takai hannu ta ƙara ɗaukar yankan naman ta tura abaki tana ci, Sai da ya rage saura biyu, tace mashi”in kaga dama ka ɗauka kaci,” tayi maganar tana daukar fruits din ciki tana sha” muryarshi na rawa yace”bazan ci ba, saboda me zaki dinga yi mini faɗa? Nifa haka rayuwata take, ki ƙyale ni mana, bana jin daɗin yadda kike kushe ni,” Ranshi amatuƙar 6ace ya miƙe, Ya juya ya nufi gadonshi ya haye ya kwanta,
Sai bayan daya tafi, Jikinta yayi sanyi, daƙyar ta iya shan fruits ɗin, idanuwanta suka Cicciko tab kwalla, yunƙura ta yi tare da miƙewa ta ɗan ranƙwafa ta ɗauki fitilar ahannu ɗaya, yayin da ɗayan hannun kuma ta ruƙe handle na kwandon, wurin gadon shi ta nufa, daga gefe ta ajiye fitilar tare da kwandon, idanuwanta na akan gefen fuskarshi, ya ƙanƙame pillow aƙirjinshi, jikin shi har wani kerma yake yi saboda tsabar 6acin ran da yake ciki, Zuciyarta ce ta dinga tunzurata akan kada ta kuskura tace zata lallashe shi ta ƙyale shi wata’kil yayi hankali, gani take ma idan taci gaba da lallashin shi zai ƙara lalacewa ne, ƙwara ta koya mishi hankali, jinjina kai ta ɗanyi alamar gamsuwa da shawarar da zuciyarta ta bata,
“Idan kaga dama ka tashi ka ɗauki naman kaci, idan kuma baka ci ba, matsalarka ce” Takarasa maganar tare da watsa hannayenta, Irin bata damu din nan ba, wuce wa tayi zawa gaban table ta ƙara ɗauko wata fitilar ta kunna ta, kaitsaye ta nufi gadon deeja, domin ta yi mata yaji ƙi, tun ɗazu da safe take ta son taje wurinta amma damuwa ta hanata, zuciyarta tayi mata nauyi a ƙirjinta, shiyasa ta tagaza tashi daga saman gadon ta yi kwanciyarta,
Daga gefen gadon deeja ta zauna, tana haska fuskarta da fitilar hannunta, da alama tayi nisa acikin baccinta, har cikin zuciyarta taji daɗin yadda deeja ta samu sauƙi, don jiyan nan zuciyarta ba ƙaramar karaya tayi ba, harta fara fidda ran da zata rayu, sai gashi Allah ya taimake su, deeja ta wartsake, a hankali ta ɗaura yatsun hannunta saman fuskar deeja ta ɗan shafata, kafin ta soma karanto addu’o’i tana tottofa mata,
“Bazan tashe ki daga bacci ba My lovely sis, gobe in sha Allah, idan kika farka daga bacci zanzo in yi maki ya jiki, Allah ya ƙara maki Lafiya, ” janye hannunta tayi daga kan fuskar deeja ta mayar dashi saman sumar kanta, dake a hargitse duk ta yamutse babu gyara, aranta ta ayyana cewa, idan deeja ta samu lafiya sosai jikinta yae kyau zata gyara mata gashin kanta, ta kuma yi mata kalaba, kalar tasu azeeza, sauƙin ma ita gashin nata bai kai nasu tsayi da yawa ba, ya dai sauko har saman kafaɗarta, baƙi wulik, kamar na ɗiyar roba, Ta jima zaune tana kallon deeja, daga bisani ta miƙe hannunta ruƙe da fitilar tabi gadon kowannan su ta tottofesu da addu’o’i, lokacin da ta dawo zata wuce gadonta, Sai da ta saci kallon shimfiɗar danish, Still bai ɗauki naman shi yaci ba, duk sai taji ba daɗi, Duk yinin yau baici komai ba, ko ruwa bata tunanin yasha mutun sai kace aljani, anya kuwa zata biye mashi, kodai taje ta lallashe shi ya tashi yaci?
A ƙasan gadonta ta ajiye fitilar hannunta, wurin ya ɗanyi haske hada ƙarin ɗayar fitilar dake a kusa da gadon danish,
daga Gefen gadonta ta zauna tana kallon bayanshi, still babu alamun yayi bacci, yatsun ƙafarshi basu daina yin kerma ba, Zuciyar imani ce ta zo mata, ta miƙe taku ɗaya biyu, ta zuƙunna abankin gadon shi, Cikin sanyin murya ta ambaci sunanshi”Danish” shiru bai amsa mata ba,
“Fushi kake yi da ni, saboda kawai na faɗi gaskiya,” ta ɗanyi maganar tana hararar bayanshi,
“Its ok komai ya wuce, bazan ƙara ba, pls ka tashi ka ci naman nan kasha fruit din idan ma baka Iya Ci da hannunka sai in baka abaki, ba wani abu bane, ni kawai bana so ne ka kwana da yunwa, dama ka faɗa mini cewa saboda ni ne baka Ci abinci ba, To yanzu ni naci kaima saika tashi kaci, ko ba haka ba My man”? Bakinta ƙumshe da dariya tayi maganar, babu alamun zai tanka mata,
Cikin zolaya tace”dama ance mutun mai haƙuri bai iya zuciya ba, yau na tabbatar da hakan, danish yayi fushi da angelar shi,” babu irin lallashin da bata yi mashi ba, amma yaƙi tanka mata a ƙarshe ranta ya 6aci a fusace tace”Kai ni fa ko daddyna bana zama in lallashe shi kamar yadda nake yi maka, don ma ka samu ina kula ka shine kake wani shamin ƙamshi, to shikenan, Nasan me zanyi, Zanje ne kawai in dura tagar nan ta cikin toilet, kome zai faru ya faru, ” tana kai ƙarshen maganar, ta miƙe da sauri ta ɗauki fitilar dage ƙasa gefen gadonshi, Ta nufi sashen makewayinsu har ta kusa kaiwa bakin ƙopar shiga, Kamar walƙiya taganshi agabanta tsaye yana faman lumshe idanuwanshi, doguwar sumar kanshi duk ta yamutse, Tsananin mamaki ne ya kamata, da sauri ta ɗan juya ta kalli gadon shi donta tabbatar idan shine dagaske, bata ga kowa ba, sai taga kamar 6acewa ya yi daga saman gadonshi ya faɗo gabanta,
Kafin ta yi mashi magana ya riga ta cewa”zan ci shi kenan ko”? Ɗaga kai tayi alamar eh, ya ruko hannunta acikin nashi yaja ta suka koma Cikin ɗakin, a gefen gadonshi ya zauna, Suna fuskantar juna shi da angel, tana azaune saman nata gadon, ta tsareshi da ido tana jiranshi ya kammala Ci, kwandon Ya dauka ya ɗaura shi saman laps dinshi, A tsanake ya kai hannu ciki ya ɗauki yankan nama yana ci, Bayan ya gama taune shi duka, Ya ɗauki sauran 6allin apple data rage mashi yakai baki yana gatsa, jefi jefi yakan ɗan ɗago ya saci kallonta, Ko uwarsa Albarka yadda ta tsare shi da ido,
“Zaka sha ruwa”? Ɗaga mata kai yayi alamar eh, ta miƙe tsaye sai da tafara ɗaukar kwandon, Kafin ta nufi gadon batool, A ƙarƙashi ta tura kwandon ta ɗauko mishi robar ruwa guda ɗaya, Ta dawo ta miƙa mashi, yasa hannu ya kar6a ta koma saman gadonta ta kwanta tana facing ɗinshi, Buɗe murfin bottle ɗin yayi tare da kwafata abakin sa, kusan rabi ya sha, bayan ya gama shan ruwan, ya maida murfin bottle ɗin ya ajiye ta daga ƙasa, Sannan ya gyara kwanciyarshi, suna fuskantar juna, kallan ƙurulla suka shiga yi ma junansu, bakomai take tunawa ba, face yadda ya sha gabanta ɗazu saboda tace zata dura tagar nan, tarasa gane dalilin dayasa baison tasan komai dangane da kurkukun, Ta fahimci cewa danish yasan komai, shiyasa yake lalla6ata don kada ta gani taja musu wata matsalar, Abunda kuma bazai ta6a yiyiyuwa bane,
Da wannan zancen zucin bacci yayi awon gaba da ita, shima danish ɗin tuni bacci ya ɗauke shi,
A washe garin ranar, kafin kowa ya farka daga bacci, batool ce tafara tashi tana miƙa tare da Yin hamma, ta sauko daga saman gadonta, cikin sauri ta nufi toilet saboda wani irin fitsari daya matseta, Ya ɗaure mata mararta, hada ɗan gudunta wurin shiga toilet, batare data yi locking door din ba, hannayenta ta sanya wurin zame wandon jikinta ta zuƙunna tana Yin shi, bayan ta kammala ta kunna fanfo ta yi tsarki, Ajiyar zuciya ta sauke tare da miƙewa tsaye tana gyara wandon Jikinta, kafin ta nufi ƙopar fita, harta miƙa hannu zata buɗe sai ga azeeza ta faɗo cikin toilet ɗin. jikinta sai kerma yake yi, batool tace”lafiyarki kuwa kika faɗo mini Cikin toilet ba neman excuse? Batare da azeeza ta kalli batool ba tace”ke dallah fitsari ne ya matse ni, ni ina nasan da mutun a ciki, ” tana faɗin hakan ta wuce cikin toilet ɗin, girgiza kai batool tayi fuskarta ɗauke da murmushi ta fito daga waje, taja mata ƙopar ta rufe, tana ƙoƙarin shiga cikin ɗakinsu, Tajiyo muryar azeeza daga Cikin toilet tana kwala mata kira na fitar hayyaci, da sauri ta koma ta nufi ƙopar toilet ɗin, Fitowa daga Ciki azeeza tayi idanuwanta azazzare hannunta dafe da saitin ƙirjinta tace”Batool, naga ɗigon jini a cikin toilet wurin magudaji ke ce kika zubda shi”? Wata irin mummunar faɗuwar gaba ce tazo ma batool, nan da nan walwalar fuskarta ta ɗauke, amatuƙar ruɗe tace”Bani bace, sai dai ko kece da kika shiga ciki yanzu, saboda ni har na fito banga wani ɗigon jini ba”aruɗe azeeza tace”Wlh bani bace, Ae ni yanzu na shiga, Ko tsugunnawa ban kaiga yi ba, naga jinin, hakan na nufin daga Jikin ki yake, ” a tsiwace batool tace”Nifa bani bace na zubda shi ba, wlh bani bace” tuni hawaye sun wanke fuskarta, Azeeza ta fashe da kuka tana faɗin”Wlh kece, Ae ni ban kaiga yin fitsarin ba, Ki yadda ko karki yadda naki ne daga Jikin ki ya fito,” shaƙo wuyan rigar azeeza batool tayi da hannunta biyu ta jijiigata, cikin shessheƙar kuka tace”You’re lying to me azeeza, Kina so ki ƙala min sharri ne, Kiji tsoron Allah, ki faɗi gaskiya,” Hankalinsu yayi matuƙar tashi, Kowa Ya haƙiƙance Yana ƙoƙarin kare kanshi,
*Jinin wanene AZEEZA OR BATOOL ❓❓❓*
*❤❤❤PRISONERS❤❤❤*
Saboda tsabar firgicin da azeeza ta shiga nan take ta saki fitsarin da take ji ya soma gangarowa ta cikin wandonta, an rasa me lallashin wani acikin su, kowa sai kuka yake yi, Kuma har lokacin Batool bata saki wuyan rigar azeeza da ta shaƙe ba, bayin Allah su kaɗai suka san Fargabar da suke aciki, babban abunda suke jima tsoro shi ne azo araba su da ƴan uwansu, Basu da tabbacin za’a dawo dasu ko baza a dawo dasu ba,
Cikin shessheƙar kuka ta wanda ya galabaita azeeza ta kware maki tana faɗin”Wayyo Allah na, Na shiga uku, batool kin shaƙe min wuyan rigata, Ki sake Ni, inji da abunda ke damu na…..”daƙyar ta kai ƙarshen maganar, tana kiciniyar ƙwace wuyan rigarta da ga ruƙon da batool tayi mata, wata irin zufa ce ta wanke fuskokin su, Sun yi jawur, idanuwansu sun kumbura luhu luhu saboda tsabar tashin hankalin da suke aciki.
Waɗan da ke acikin ɗaki basu san meke faruwa ba, babu alamun zasu farka daga bacci, Wata irin gigitacciyar ƙara batool ta saki sakamakon Cizon da Azeeza ta gartsa mata a hannunta, kaitsaye sautin ƙarar ya daki dodon kunnuwan su, Aikuwa a firgice kowannan su Ya farka, at same time suka ya ye bargunansu tare da yin wurgi dasu, Kowa yana faman zazzare ido, fuskokin su da alamun ruɗani, lokacin da suka ankara daga inda sautin ke fitowa, Jiki Na rawa kowannan su Ya sauko daga saman gadonshi, da gudun gaske suka nufi sashen toilet ɗinsu, kamar an jeho su suka faɗo Ciki, Kowa yana faman baza na muzurinsa, Angel ce farko sai Hanna da hibba, kaf matan da mazansu hada danish da haris,
Hankalin su yai matuƙar tashi, ganin Jinin dake ɗigowa daga hannun batool sai yarfa shi take Yi, ta runtse idanuwanta sai kuka take yi kamar ranta zai fita, Tun da suke a rayuwar su basu ta6a ganin batool tana kuka mai sauti ba irin na yau, saboda tsabar hakurinta da juriyarta, Ita kanta azeeza data gartsa mata Cizon, duk tabi ta ruɗe jikinta sai kerma yake yi, ta manne jikin bango, Sai zazzare idanuwanta take yi fuskarta sharkaf da hawaye,
“Innallallahi wa’inna ilaihirraji’un! Batool meya faru dake? Me kuke yi anan keda azeeza? Badai faɗa kuke yi ba”? Angel ce ta jefa musu tambayar, a yayin da take matsawa kusa da batool, takai hannunta tare da ruƙo hannun batool dake bleeding, Hanna tace”ashe dama kune kuke faɗa? Tun ina bacci nake ta jin hayaniya cikin kunne na, amma kun bani mamaki, yanzu batool ki rasa da wa za ki yi faɗa sai azeeza”? Hannah na rufe baki haris yace”Ku faɗa mana meya haɗa ku da har kuke ƙokarin illata junan ku, wannan wani irin abun kunya ne, ” Lamarin duk bai yi musu daɗi ba, sai tambayar su suke yi akan su faɗa musu dalilin yin faɗan na su amma sun kasa tanka musu, saboda kukan da suke yi.
“Hannunta yana zubar da jini, Ya zamu yi? Ko dai muje mu faɗa ma tsohuwa”? Mubeen ne yai maganar, muryar danish da alamun bacci bai ishe shi ba yace”Basai an faɗa mata ba,” ya ƙarasa maganar tare da matsawa ya tsaya gefen angel dake a tsaye gaban batool, ya miƙa hannu ɗaya ya damƙo hannun batool dake zubar da jini, tare da kaishi saitin bakinshi tamkar zai gartsa mata cizo, ya kama wurin, kamar yana tsotsar jinin, duk suna kallon shi, Musamman angel da mamaki ya kamata ganin wani sabon salon treatment da bata ta6a gani ba,
Sosai batool ta runtse idanuwanta, tana faman cizon brownish lips ɗinta, a hankali danish ya zame bakinsa daga saman hannun batool, wani iko na Allah jinin ya tsaya da zuba, sai dai a bunda ya ɗaure ma angel kai, ganin bai zubar da jinin daya sha ƙasa ba, A ruɗe take bin fuskarshi da kallo batare daya lura da ita ba, Sauran ƴan uwan babu wanda Ya kawo komai aranshi sai ita data ankara da abunda ya yi, zuciyarta ta shiga ruɗanin, taya akai ya ke iya swallowing ɗin jini!?
Muryar azeeza cikin shessheƙar kuka tace”Dan Allah batool ki yafe ni wlh bada son raina na gartsa maki cizo ba, ke ce kika shaƙe mini wuyan rigata har naji zafi na cije ki,” wani irin jiri batool take gani acikin idanuwanta, biji biji take bin kowannan su da kallo, Angel tace”Batool meke damunki? Wai baza ku faɗa mana me ya haɗa ku ba? Meyasa ku ke yin kuka? Ga zufa duk ta wanke jikin ku,” matsawa batool ta yi kusa da angel ta kwantar da kanta saman kafaɗarta, da sauri angel ta sanya hannayenta biyu ta rungumeta sosai ajikinta, cikin muryar kuka batool ta zayyane musu abunda ke faruwa, Hankalinsu yayi matuƙar tashi, deeja dake a gefen haris ta fashe da kuka tana faɗin”mun shiga uku, abunda nake gudu sai da ya faru, wannan wace irin masiface? Fuskarta a yamutse takai kai ƙarshen maganar, haris yace”gaskiya bazaiyiyuwa ba, nidai bazan bari atafi da wani daga Cikin ku ba, sai dai a haɗa dani,” cigaba da magana deeja tayi yayin da hawaye ke bin fuskarta tace”Dan Allah mu hada kanmu, wannan karan kada mu bari atafi da ƴan uwan mu, ina matuƙar tausayin azeeza da batool, bazan so su ɗanɗani irin raɗaɗin azabar da muka sha ba, musamman azeeza zamu iya rasata,” maganar deeja ba ƙaramin tsorata azeeza ta yi ba, jikinta ya hau 6ari, haƙoranta har kakarwa suke yi kamar wadda sanyi ya kamata, da sauri javed ya janyota jikinshi, kamar jira take yi dama ta ƙanƙame shi tana cigaba da yin kuka, lallashinta ya shiga yi, yana ɗan bubbuga bayanta da hannun shi,
Zuciyoyinsu duk sun karaya, Fuskar Rubina ɗauke da matsananciyar damuwa tace”Wai shin Jinin wanene acikin su? Ta ya zamu iya ganewa? ɗagowa azeeza ta yi daga jikin javed tana faɗin”I just know it’s not my blood, wlh ba jini na ba ne, sai da na faɗa ma batool cewa banawa bane, Saboda ni ko da na shiga toilet ɗin ban kai ga cire wandona ba, na yi tozali da shi”
cikin shessheƙar kuka batool tace”Nima banawa bane, ba daga jikina yake ba, har na shiga na fito daga Cikin toilet ɗin ban ganshi ba” koda batool tae maganar bata raba jikinta daga na angel ba, ta ƙanƙameta, ji take kamar in ta raba jikinta daga nata za’a zo arabasu ne,
Hawaye ne masu ɗumi suka wanke fuskar angel. Har cikin zuciyarta tana jin wani irin mummunan faɗuwar gaba, muryar na ɗan rawa ta ambaci sunayensu Batool azeeza, “duk suka natsu, suna jiran jin me zata ce musu,
“Since we were all confused, we couldn’t figure out whose blood was in the toilet, abunda yakamata muyi zamu shiga toilet ɗin mu duba jinin da kyau, idan muka tabbatar jini ne, Azeeza da batool kowannan ku zai shiga cikin toilet ya bincika jikin shi, ta hakanne kaɗai zamu Iya gane daga jikin wa jinin ya ɗigo” gaba ɗaya kowa yayi amanna da maganar angel, koda suka shiga toilet ɗin suka duba dakyau, jini suka gani har ya ɗan bushe a ƙasa, Hankalinsu ya ƙara tashi, angel tace abunda ya rage yanzu, su shiga su duba jikinsu, Batare da 6ata lokaci ba, azeeza da batool suka shiga cikin toilet, kusan atare suka fito daga Ciki, Har suna haɗa baki wurin faɗi “Ba daga jiki na yake ba” Lamarin yae matuƙar ɗaure musu kai, To wai jinin wanene toh? dole dai acikinsu ne wani ya zubar dashi, kuma azeeza ta tabbatar musu da cewa sabon Jini ne, domin kuwa lokacin da ta shiga cikin toilet ɗin, da ruwa ruwa jikinshi, kafin yakai ga bushewa,
Kowannan su ya shiga ruɗani, in a low voice danish yace”ku daina wahalar da kanku, Idan ma dagaske jinin ne, Giants ne zasu banbance wanene acikin su,” harara angel ta watsa mashi tare da cewa”danish har fata kake yi azo a ɗauke su”? duƙar da kanshi ƙasa yai batare daya bata amsa ba, haris yace”yanzu duk ba wannan ba, ku zo mu koma ɗaki mu jira mu gani me zai biyo baya” muryar azeeza a rauna ce take fadin”Ni wlh bazan fita daga nan ba, ku rufa mana asiri mu yi zaman mu acikin toilet mu datse ƙopar, ta yadda ba zasu Iya shigo wa su ɗauke mu ba” la66anta har shaking suke yi saboda tsabar firgici.
Tsananin tausayin su ne ya kama ƴan uwansu, haris yace”Azeeza ta kawo shawara mai kyau, mu rufe su kawai acikin toilet, kun ga shikenan munyi maganin Giants ba zasu Iya shiga su ɗauke su ba” Jinjina kai angel ta ɗanyi alamar gamsuwa da bayanin Haris, ta ƙara da cewa”Ni zan zauna a atare dasu cikin toilet ɗin”
Girgiza kai danish yayi yana binsu da wani irin kallo mai wuyar fassaruwa yace”that cannot be possible, if you say you will stop the giant from taking her you’ll bite off more than u can chew………” daƙyar ya ƙarasa maganar ganin irin kallon da suke watsa mashi asaman fuskarshi, Tsabar takaici ya hana Haris furta komai, Sai angel ce tai ƙoƙarin cewa”Kome zamu yi be shafe ka ba danish, u should stay away from us, tun da ba ka supporting ɗin mu that’s mean baka da amfani awurin mu, ka koma saman gado ka kwanta zai fi maka kwanciyar hankali. If not wlh zan yi maka abunda baka tsammani,” angel na rufe baki deeja tace”Danish baya atare damu, na fara zargin cewa Yana atare dasu, shiyasa ko jiya da aka dawo dani duk irin baƙar wahala dana sha, Kowa Yana yi mini sannu duk da bata maganin ciwo amma ina ji daɗi, atlease ƴan uwana sun nuna sun damu dani sun yi kewata, amma danish ko kusa dani baizo ba, sai kace wata maƙiyiyar shi.
hawaye na bin fuskar deeja takarasa maganar, Ran haris ya 6aci sosai, a fusace ya kai hannun shi ya damƙi damtsen hannun danish ya fusgo shi ya ja shi da ƙarfi ya fitar dashi daga cikin sashen toilet din. har cikin ɗakin su bakin gadon shi ya kawo shi, anan ya dakata Ya ɗago suna kallon juna ido cikin ido shi da danish,
“Ba ka da amfani a wurin mu, duk da haka bawai ina gudun ka bane, ko Ina fushi dakai a’a ko ɗaya, har yanzu kana nan a yadda kake cikin zuciyata, sai dai bama buƙatar ka a halin da muke ciki yanzu, Gado shi ne ya dace dakai ka hau ka kwanta” ya ƙarasa maganar tare da jan dogon tsoki, kafin Ya juya ya nufi sashen toilet ɗin. Jikin danish ya yi sanyi, slowly ya ɗan juya baya yana kallon haris dake ta sauri har sai da ya shiga ƙopar tukunna danish ya ɗauke idonshi daga kallon bayan nashi da yake yi,
Kamar yadda suka ce ya hau saman gado, aikuwa gadon ya haye ya kwantar da kanshi saman pillow, shi kaɗai yasan irin raɗaɗin da yake ji acikin zuciyarshi, ganin yadda ƴan uwanshi suke nuna rashin amfanin shi acikin su, abun yana mishi ciwo acikin zuciyarshi. Daurewa kawai yake yi dan ba yadda zaiyi,
Bayan haris Ya koma cikin toilet ɗin, atare da angel suka tsara yadda zasu shirya ma Giants don su hana atafi da ƴan uwansu, Bayin Allah sun damu da ƴan uwansu sosai, babu mai tunanin abinci acikinsu ba don basu jin yunwa ba, sai dan damuwar da suka shiga, na fargabar kada azo a ɗaukar musu ƴan uwansu,
Haris ne yace da angel ta shiga Cikin toilet ita da batool su datse ƙopar ta yadda giant ba zasu Iya shiga Ciki ba. ita kuma azeeza a ƙarƙashin gado zasu 6oye ta, hanna tace ae zasu Iya gano azeeza tunda suna kallon komai suke Yi, amma ita a ganinta, abar azeeza ta shiga cikin toilet ɗin tare dasu angel, Haris yace su yi hakan kawai, toilet ɗin ƙarshe suka buɗe angel da su azeeza suka shiga Ciki, kafin su rufe ƙofa haris yace”su kwantar da hankalin su, idan an kawo abinci zasu kawo musu nasu su ci,” suka amsa mashi da toh, daga bisani angel ta datse ƙopar da Jam lock,
Kallon juna suka shiga yi atsakaninta dasu azeeza dake a tsaitsaye, fuskokinsu sharkaf da hawaye, sam babu kwanciyar hankali atare dasu,
Tsananin tausayinsu ne ya kamata, gaba ɗaya ta sanya hannayenta biyu ta rungumesu ajikinta, Cikin sigar lallashi take Yi musu magana,
“In sha Allah giants bazasu raba mu da ku ba, bazan bari a cutar mini da ku ba, ina ji ina gani, wlh sai inda ƙarfi na ya ƙare, koda kuwa zan rasa raina ne, amma wannan karan ashirye nake dana fuskanci kowani irin tashin hankali ne” with Confidence angel tayi maganar, babu wasa akan fuskarta.
Hankalin su batool ya ɗan kwanta, saboda jin abunda tace, ɗagowa batool tayi daga jikin angel, idanuwanta sun ɗan kumbura saboda kukan da tasha, cikin sanyin murya tace”Angel, bana so wani ya cutu acikin ku ta dalilin mu, idan har giants sun zo zasu tafi damu, kada kuce zaku shiga huruminsu, ” girgiza kai angel ta ɗanyi tare da cewa”ki daina faɗin hakan, batool da ace kinsan me suke Yi maku idan suka ɗauke ku, da baki ce haka ba, ke kanki bazaki so atafi dake ba, mutanan nan basu da imani basu da tausayi, kashe mana rayuwa suke son yi ta yadda ba zamu ta6a amfanuwa ba, burinsu shine su ƙarar damu,” tamkar zata fashe da kuka ta kai ƙarshen maganar, azeeza dake kwance jikin angel, taƙi ɗagowa baiwar Allah, Jikinta sai kerma yake yi, ta ƙanƙameta tamkar zata koma cikin cikinta, wani irin faɗuwar gaba take ji, ita kanta angel tana iya jiyo sautin bugun zuciyar azeeza, fargabatar kada tsoro yasa zuciyar azeeza ta buga harta mace kafin ma su ƙaraso,
“Mu samu wuri mu zauna, nasan kun gaji da tsayuwa” daga jikin bango suka zauna, still azeeza bata saki jikin angel ba, hannu bibbiyu ta ƙanƙameta koda suka zauna, itama batool ta ɗan kwantar da kanta saman kafaɗar angel, toilet ɗin yai tsit ba ka jin hayaniyar komai, tsawon lokaci kafin angel ta fara faɗa musu addu’o’in da zasu karanta na neman tsari, saboda tsaro,
Lokacin da angel ta datse ƙopar toilet ɗin, Ajiyar zuciya kowannan su Ya sauke, Haris yace dasu su koma ɗaki su zauna su jira su ga waye zaizo ɗaukarsu azeeza, Hada ja musu kunne akan karsu kuskura su bari tsoro yasa su faɗa ma giants inda suka 6oye su azeeza, duk runtsi duk wuya suja bakinsu su yi shiru, Suga iya gudun ruwansu, suka amsa mashi da toh,
atare suka nufi cikin ɗakin, Idanuwansu akan danish dake kwance saman gadonshi, haushin shi duk ya kama su, wani sullu6iyo dashi,
Suna yunƙurin haurawa su zauna saman gadajenshi, kwatsam suka soma Jin motsin buɗe kofa tacen saman bene, wa’Iya zubillahi zoka ga tsantsar tashin hankali akan fuskokinsu, A matuƙar ruɗe suke kallon matattalar benan ,
Takun tafiyar giants suka soma Jiyo wa acikin kunnuwansu, kafin su bayyana su uku masu kawo musu abinci hannayen su ruƙe da farantai, wata irin nauyayyiyar ajiyar zuciya suka sauke ganin basu zo da shirin tafiya da wani ba, Bayin Allah hada murmushin su, saboda sun sa ma ransu cewa baza a ɗaukar musu ƴan uwansu ba,
Da ido suka bi giants da kallo har suka sauke musu farantan abincin, da sauri suka nufi saman dining carpet ɗin suka zazzauna, babu wanda yae tunanin yayi ma danish magana akan yazo yaci abinci, sai ma ta ƴan uwansu suke yi dake acikin toilet, ƙasa ƙasa da murya suke yin magana don kada giants su ji su,
“A ina zamu ɗibar musu abincin mu kai musu”? hibba ce tai maganar, hannah tace”ku daina magana kada Giants su ji mu, abunda za’ae mu ɗauko kwandon batool mu ɗibi abinci, sai mu ajiye, bayan sun tafi sai muje mu kai musu acikin toilet ɗin,” haris yace”kin kawo shawara mai kyau,” batare da 6ata lokaci ba, hanna ta miƙe taje ta ɗauko kwandon daga ƙarƙashin gadon batool ta dawo ta zuƙunna gaban farantan, ta yaye jan ƙyallan da aka rufe faranti na farko dashi, fried fishes ne aka kawo musu, manya manya sun soyu sai maiƙo suke Yi, a ƙalla kowa zai samu ɗaya, Kifin akwai tsoka jikinshi sosai, A hankali take kai hannu tana ɗaukar kifin tana ajiyewa acikin kwandon, ganin ta ɗauki uku, yasa haris yace”Ki ƙara ɗaya kodan saboda danish” duk da fushi da yake yi dashi hakan bai hana shi jin damuwa dashi ba, Hanna tace toh, tasa hannu ta ƙara ɗaukar ɗaya ta ajiye, Ta ɗibar musu fruits tare da robar ruwa guda uku ta ɗauka, miƙewa tayi hannunta ruƙe da kwandon taje bakin gadon batool ta ajiye shi ta dawo ta zauna, a tsanake suke Cin nasu fried fish ɗin, Suna ci suna satar kallon giants dake atsaye sun goya hannayen su saman ƙirjinsu yadda kasan Gumaka, ko gajiya da tsayuwa basa yi,
A 6angaren su angel dake acikin toilet, Tuni bacci yai awon gaba da azeeza da batool, duk suna akwance saman jikinta, itama angel ɗin wani irin bacci take ji ga yunwa dake addabarta, sai faman lumshe idanuwanta take yi,
Daga wajen ƙopar toilet ɗin ta soma Jin ana yi musu knocking ras taji gabanta ya faɗi, hatta su azeeza dake baccin jin bugun ƙopar yasa suka farka a firgice suna faman zazzare idanuwan su,
Muryar hanna suka jiyo tana faɗin”Ni ce angel, ku buɗe mini kopa, breakfast ne na kawo maku” Kusan atare suka sauke ajiyar zuciya, duk sunyi tsammanin ko Giants ɗin ne suka zo tafiya dasu,
“Ku jira na amso mana abincin” tai maganar tare da zame jikinta daga nasu ta miƙe ta nufi ƙopar, ta cire jam lock ɗin, ta janyo ƙopar tare da leƙo da kanta waje,
Hanna ta gani atsaye ita da haris, kwandon Yana a hannun hanna ta ruƙo shi,
“Angel Giants sun zo kuma sun tafi, Ni ina ganin kamar ɗigon jinin nan ba jini bane. Tunda da ace shine, Giants zasu tafi da su azeeza ne, Amma kinga har sun kawo mana abinci sun tafi” shiru angel ta ɗanyi tana nazarin maganar Hanna. Ita gani take kamar jini fa ne, kawai dai bai kai ga zuwa bane gaba daya shiyasa basu zo sun ɗauke su ba
Muryar haris ce ta dawo da ita daga zancen zucin da take yi,
“Nima ina tunanin ba jini bane gaskiya, tun da ga shi har zunzo sun tafi batare da sun buƙaci tafiya dasu ba” abunda za’ae yanzu ku fito mu koma cikin ɗakin ku zauna ku yi breakfast ɗinku” Gyaɗa kai angel tayi badan taso ba tace”Allah yasa abunda muke hasashe ya zama gaskiya, bari nayi musu magana su fito mu koma daki amma kafin nan, zan taimaka musu su wanke fuskokinsu,” haris ya amsa mata da toh .kafin ya kalli hanna yace”Mu jira su acikin ɗaki” juyawa suka yi atare suka koma ɗaki,
Badajimawa ba, Sai ga angel ta fito hannayenta ruƙe da nasu azeeza, Bayin Allah har faɗa wa sun ɗan yi saboda damuwa, Ƴan uwansu ba ƙaramin daɗi suka ji ba, da su kayi tozali dasu,
A saman dining carpet suka zauna su uku, Hanna ta ajiye musu kwandon. Angel da azeeza suka ɗauki fried fish ɗinsu A hankali suke Ci, Sauran ƴan uwansu duk suna a kewaye dasu suna kallonsu, ganin batool ta kasa ci ne yasa haris yi mata magana yace”batool meyasa baki ci? Muryarta na ɗan kerma tace”Hannuna Zafi yake yi mini” sai lokacin suka tuna da cizon da azeeza ta gartsa mata, Zuƙunnawa haris yai agabansu, ya kai hannu cikin kwandon ya gutsiri tsokar kifin ya mika mata abaki, ta ɗan buɗe shi tana Ci, sai ƙara kwantar musu da hankali ƴan uwan nasu suke Yi, bayan sun kammala Ci, suka sha fruit ɗinsu, tare da ruwa,
Angel tace yakamata suje suyi wanka, jikinsu duk zufa, suka amsa mata da toh, har tana cewa idan bazasu iya yin wankan ba zata taimaka musu suyi, batool tace ita zata Iya, azeeza kuma tace tafi son angel tayi mata wankan, hannun su aruke dana juna suka nufi toilet, bayan tafiyarsu, Haris ya ɗauki kwandon yana kallon sauran Fried fish din daya rage na danish tare da Rabin gwanda, Ta6e baki ya ɗanyi kafin ya nufi gadon danish, Ya ajiye mishi kwandon daga gefen shi yace”Idan kaga dama ka ɗauka ka ci, breakfast ɗin ka ne” ko motsi danish bai yi ba, ya runtse idanuwanshi, kuma ga dukkan alamu idonshi biyu ba bacci yake yi ba,
Watsa hannu haris yai alamar bai damu ba, Ya wuce abunshi, bayan wani lokaci, angel tafito daga Cikin toilet tare dasu azeeza, Wani irin sanyi suke Ji, asaman gadajensu suka kwanta, angel ta lullu6esu da bargunansu, Cikin ƙanƙanin lokaci bacci yai awon gaba dasu,
Ajiyar zuciya kowannan su ya sauke, yanzu sun ƙara tabbatar da cewa ba jinin gaske bane suka gani acikin toilet tunda har marece ya doso amma ba’a zo an ɗauki wani daga Cikin su ba,
Ita dai angel ta kasa samun natsuwa acikin zuciyarta, abu biyu ne ya dameta, na farko Jinin batool da danish yasha da niyar ya taimaka mata wurin dakatar da bleeding ɗin da yake yi, amma wani abun mamaki bai zubda jinin ba sai ya shanye shi, hankalinta bai kwanta da hakan ba, abu na biyu daya tsaya mata arai shi ne wannan ɗigon jinin dake acikin toilet na wanene? Dole akwai wanda ya zubar dashi,
Zuciyarta cike fal da tunani ta ɗan kishingiɗa saman gadonta, da niyar ta samu ta runtsa, juyawa ta ɗanyi tana satar kallon danish dake kwance saman gadonshi, yatsun hannunshi dana ƙafarshi sai kerma suke Yi, hakan ya tabbatar mata da cewa idonshi biyu, ta6a baki ta ɗanyi aranta tace”Haka zaka ƙare, mutun sam baya gajiya da hawan gado, mai matacciyar zuciya kawai” takarasa xancen zucin tana mai jan tsoki, ta ɗauke idanuwanta daga kan jikin shi, ta mayar dasu kan kwandon da haris ya ajiye mashi daga gefen gadonshi, yau kuma kowa zai lallashe shi yaci abincin shi? murmushin takaici ta dan saki, wani lokacin in yana abu kamar ƙaramin yaro, har mamaki yake Ba ta
*after some hours💔*
Kafin marece ya yi sai da kowan nan su ya yi wanka, Suka koma saman gadajensu suka kwanta, har lokacin danish bai motsa ba, Yana ayadda yake lafe saman gado,
Angel tana ƙoƙarin nutsawa cikin baccinta, ta soma jin motsin mutun a jikinta, aɗan firgice ta ware manyan idanuwanta akan fuskar wanda ke zaune saman gadonta, Tayi mamakin ganin batool, fuskarta duk a yamutse. Idanuwanta sun ƙanƙance, tunkafin ma batool tayi mata magana taji wani irin faɗuwar gaba,
Muryarta na ɗan rawa tace”Lafiya? Batool meke damunki”? Cikin sanyin murya ta soma magana”Bana jin ɗaɗin jikina angel, gaba na sai faɗuwa yake yi, na gaza jurewa, shiyasa nazo wurinki, don kiyi mini addu’a, ko na samu naji sanyi araina” ajiyar zuciya angel ta sauke a yayin da take yunƙurin mikewa xaune tace”Wlh har gabana ya faɗi dana ganki nayi tunanin ko jinin ne kika gani yazo miki ashe bashi bane” jinjina kai batool ta ɗanyi alamar eh, tace”Bashi bane, bana jin daɗi ne kawai”
“Tun da nake dake batool ban ta6a ganin ki cikin damuwa ba, irin na yau, kin canza sosai, duk sai naji ba daɗi jikina,” daƙyar batool ta ɗan ƙaƙalo murmushin dole akan fuskarta tace”kada ki damu sister, zan dawo dai dai ne, just fargabar abunda ya faru ɗazu ce tasa duk na canza, Amma yanzu da ɗan sauki”
Ido cikin ido suke kallon juna. angel ta ruƙo hannayenta acikin nata tare da cewa
“Zanyi maki addu’a, amma nafi so naji ki ajiki na, don naji daɗin kwantar miki da hankali kamar yadda kika saba yi mini” murmushi suka sakar ma juna atare,
A saman chest din angel batool ta kwantar da kanta, tare da sanya hannayenta, ta zagayo dasu ta bayanta, sosai tayi tighting ɗinta, wani irin tsananin ƙaunarta take ji, suna matuƙar son junansu fiye da tunanin mai tunani, addu’o’i angel ta soma karantowa tana tottofa mata asaman kanta, har cikin zuciyarta take jin wani irin daɗi yana ratsata, har tana fadin”sister kada ki daina yi mini addu’ar nan, ki cigaba, ina jin wani irin sanyi acikin raina,” murmushi angel tasaki, tare da ɗaura hannayenta saman sumar kan batool dake a dumbuje babu gyara, ta shiga shafata tana faɗin”indai akanki ne, zan iya kwana batare dana runtsa ba, wurin yi miki addu’a, ina matuƙar ƙaunarki my batool, ” muryarta asanyaye ta karasa maganar,
“Mu kwanta mu yi bacci, mu ma, ” acewar batool, a manne da juna suka kwanta saman mattress ɗin, angel taci gaba da yi mata addu’a har sai da bacci ya ɗauke su gaba ɗayansu,”
To jama’a, ɗaki fa ya yi shiru baka jin hayaniyar komai, hankalinsu kwance sai sharar baccinsu suke yi, kamar waɗanda aka yanka mutuwa agabansu,
Lokacin da marece Ya nutsa, deeja tafarka daga bacci ta miƙe ta zauna saman gadonta, hannunta rungume da pillow, ɗaya bayan ɗaya take bin gadajensu da kallo, kafin ta tsayar da idonta akan shimfidar haris, ta jima tana kallon shi, kafin ta ɗauke idanuwanta, hakanan taji tana ra’ayin tabi kowani gado ta kalli fuskokin ƴan uwanta,
Don haka ta sauko daga saman gadonta, Still jikinta ba ƙwari sosai, kamar ɗiyar roba hake take yin tafiya, tun daga kan gadon su hanna taso ma bi tana kallonsu har zuwa gadon azeeza, Ta ɗan dakata da tafiya tana kallonta, wani abu daya ɗaure mata kai bacci take yi amma sai firgita take Yi, numfashinta kuma a hargitse take fitarshi, matsawa ta ɗanyi tare da samun wuri gefen gadon azeeza ta zauna, hannunta ta ɗan ɗaura bayanta ta ɗan bubbugata, aikuwa a firgice azeeza ta farka tana faman zazzare idanuwanta, lokaci ɗaya kuma ta dafe kanta da hannu ɗaya tana faman sauke ajiyar zuciya ganin deeja ce,
“Azeeza lafiya kike ta firgita kina bacci? Ko dai baki da lafiya ne”? Tayi mata tambayar cikin nuna damuwarta,
Muryar azeeza adisashe tace”Hankalina ba a kwance yake ba, deeja bana jin daɗi, baccin nan da kika ga ya ɗauke ni har mafarkin Giants sai da nayi” idanuwanta acike tab da kwalla takai ƙarshen maganar,
Janyota deeja tayi zuwa jikinta ta dan rungumeta da hannu ɗaya, tana lallashinta,
“Ki kwantar da hankalin ki My little sis, muna atare dake, babu abunda zai faru daku,”
Azeeza tace ina jin ƙishin ruwa,” da sauri deeja ta raba azeeza daga jikinta, ta sauko daga saman gadon ta nufi gadon batool ta zuƙunna ta tura hannu ƙarƙashi ta ɗauko robar ruwa, Ta miƙe ta koma gadon azeeza, ta zauna tare da cire murfin ta kwafa mata ita abaki, sosai ta shiga shan ruwan,
A wani irin firgice Azeeza Ta jefar da robar ruwan dake ahannun deeja. Ta zabura ta yunƙura ta duro daga saman gadonta ta faɗo ƙasa, Ta shige ƙarƙashin gadonta, Jikinta sai kerma yake yi, Lamarin yae matuƙar ɗagawa deeja hankali, muryarta da alamun ruɗu take kwala ma azeeza kira tana tambayarta lafiya? Meyasa ta jefar da ruwan! Kafin deeja tayi yunƙurin saukowa daga saman gadon azeeza da niyar ta duƙa ƙarƙashin gadon ta janyota, kwatsam ba zato ba tsammani taji motsin buɗe ƙopar ɗakin su hankalinta a matukar tashe ta ɗago tana kallon Benan, Ba ita ba hatta masu bacci sai da suka farka jin sautin buɗe ƙopar, wani gabjejen Giant na ya faɗo Cikin ɗakin, mai faffaɗan ƙirji bayyanar shi tamkar baiyanar mutuwa ne agaresu, Wani abun ɗaure kai ma Giant ɗin daya shigo yasha banban da waɗanda suka saba zuwa kawo musu abinci, domin kuwa shi hada Star ɗaya a jikin baƙar rigar jikinshi daga gefen hannun hagu, sai lokacin deeja ta gane dalilin dayasa azeeza ta gudu ta 6oye ƙarƙashin gado, Wata irin faɗuwa gaba ce tazo ma deeja, lokaci ɗaya ta fasa ƙara mai matuƙar firgitarwa muryarta na rawa take ambaton”Innallahi wa’inna ilaihirraji’un! wayyo Allahna mun shiga uku! Mun bani!’ wannan maganar da deeja tayi ce tasa duk wani mai bacci ya ƙarasa wartsakewa, Hankalin angel da batool yai matuƙar tashi, a matuƙar ruɗe angel ta ruƙo hannun batool suka sauko daga saman gadonta, da gudun gaske taja ta suka faɗa cikin sashen toilet ɗinsu, Suna shiga ɗaya daga cikin makewayin, Angel ta zura jam lock ta datse ƙopar, tana juyowa batool ta faɗa jikinta tana kuka take faɗin”Angel tafiya za’ayi dani, naji ajikina nice aka zo ɗauka, shikenan za’a raba ni da farin Ciki na ina ji ina gani, za’a ɗauke ni a tafi dani inda za’a cutar da rayuwata, Ba lallaima ne a dawo dani Cikin ku ba” Fashewa da kuka angel tayi Cikin shessheƙa tace” wlh bazaiyiyu ba, haƙurina ya ƙare, komai xai faru sai dai ya faru amma wlh bazan bari atafi dake ba, duk runtsi duk wuya ina atare dake, Sai dai su kashe ni” gaba ɗaya sun shiga matsanancin tashin hankali, su biyu acikin toilet sun ƙanƙame juna
A hankali giant ɗin yake saukowa daga saman staircases ɗin, haris yai matuƙar harzuƙa, Su rubina duk sun zazzare idanuwansu, damuwace ƙarara kwance akan fuskokinsu. Wasu har sun fara kuka, tun kafin ma a ɗauki ƴan uwan nasu, Duk wannan budurin da akeyi danish bai motsa ba, haka zalika Azeeza bata fito daga inda ta 6oye ba, domin kuwa tuni ta jima da sumewa,
Yadda kasan zaki Haka giant ɗin nan Ya tunkaro wurin gadajensu, Yana zuwa tsakiyar ɗakin Yaja burki ya tsaya ga dukkan alamu kamar kallonsu yake yi duk da basu Iya gane hakan. Tunda jikinsu gaba ɗaya a lullu6e yake da baƙaƙen kaya, hatta idanuwansu
Ƙasa ƙasa da murya haris yace”ku ƙyale shege kada ku faɗa mishi inda suke muga ya zaiyi, Na rantse yau sai dai ayi duk wacce za’ae amma bazan Bari wannan ƙaton Ya ɗauki ɗaya daga Cikin mu ba”
Muryar Hanna Cikin shessheƙar kuka take take roƙon giant ɗin tana faɗin”Dan Allah kada ku raba mu da ƴan uwanmu, Idan ma ɗaukar ta zama dole to ni ku ɗauke ni ku tafi dani amma na roƙe ka ka ƙyalesu, sun tsorata sosai zasu Iya rasa ransu, “
hannah na rufe baki, sauran matan suka fashe da kuka suna roƙonshi, bayin Allah hada ƙoƙarin saukowa daga saman gadajensu suna yi mashi magiya akan ya ƙyale musu ƴan uwansu, su sun amince ya ɗauke su amma kada ya ta6a musu Azeeza da batool, tabɗijancan Iska na wahalar da me kayan kara, sufa duk atunaninsu zai ji tausayinsu Ya ƙyalesu, Sai dai abunda basu sani ba, Zuciyar giant tamkar dutse take. basu da tausayi ko misƙala zarratin, babu ɗigon Imani akansu, Su fa kawai Umarni suke bi daga sama, haris da ranshi ke a6ace yace”Ku daina wahalar da kanku, babu alamun zai saurareku, tun da ba tausayi ne dasu ba, Ae mun riga da mun 6oye su, kuma babu wanda zai nuna mishi inda suke idan yaga dama yai ta tsayuwa daga yau har jibi, idan ya gaji ya kama hanya ya koma,” haris fa ya ɗauko ta da zafi,
Tunda suka fara magana, gabjejen giant ɗin nan baiko motsa ba, Kamar yana sauraron me suke tattaunawa,
Da mamaki su ke kallon Giant ɗin, ganin ya ɗaga hannayen shi biyu yai clapping ɗinsu, Cikin rashin fahimtar me yake nufi yasa suka zazzare ido suna kallon Juna,
Danish ne ya fara motsawa daga saman gadonshi, Ya miƙe ya sauko da ƙafafuwanshi ƙasa, ya ɗan ɗago ya kalli giant ɗin dake a tsaye na wani lokaci kafin ya ƙarasa saukowa daga saman gadon, Yaje gaban giant ɗin ya sara mashi, a matuƙar ruɗe suke kallon danish, abun mamaki abun al’ajabi
Daga bisa ni, su ka ga danish ya juya Ya nufi sashen toilet ɗinsu, gaba ɗaya suka bi shi da ido, Batare da wani ya motsa ba, Zuciyoyinsu cike da fargabar me danish zaije yi acikin sashen toilet ɗinsu,
A lokacin batool da angel suna a zuƙunne jikin bangon toilet, sun ƙanƙame juna, Unexpected Angel tajiyo motsin buɗe kopa, tashin hankalin da ba’a sama shi date, Ƙopar dake a rufe kafin su shigo ta ciki ta sanya jamlock ta garkame ta, A matuƙar ruɗe take kallon Jikin ƙopar ganin jam lock ɗin yana motsi da kanshi ya zame kanshi, ƙopar ta buɗe, saboda tsabar tsoron da taji tuni zufa ta wanke fuskarta, batool kuwa tuni jikinta ya ɗauki wani irin zafi na fitar hayyaci,
Duk a tunaninsu giant ne zai shigo wani abun al’ajabi sai ganin danish su ka yi ya faɗo Cikin toilet din, yana ƙarasa shigowa, Ya miƙa ma Batool hannu yace ta taso su tafi, wani irin kallon tashin hankali angel da batool suke binshi dashi, Ganin taƙi miƙa mashi hannunta yasa shi yin saurin damƙo damtsen hannunta ya janyota ta ƙarfi ya fiddo da ita daga Cikin toilet ɗin, da gudu angel tabiyo bayanshi, ta cafko hannun batool tana ƙoƙarin ƙwato ta, amma abun ya faskara domin kuwa ba ruƙon wasa yai mata ba, Adai dai lokacin da danish ya fado Cikin ɗakin, su haris suka ga ya ruƙo batool, zuciyarsu tai matuƙar karaya, lamarin yai matuƙar girgixasu, tsabar ruɗanin da suka shiga yasa suka gaza ta6uka komai,
Kafin su yi wani yunƙuri, Danish Ya ƙarasa gaban Giant ɗin tare da batool Ya damƙa mashi ita, Giant ɗin ya sanya hannu biyu ya ɗauki batool saman kafaɗar shi batare da 6ata lokaci ba. ya juya ya nufi hanyar fita daga ɗakin, Al’ajabi ya hana su motsa, Suna ji suna gani giant ya tafi da batool tana ta kuka tamkar ranta zai fita,
Nan take angel ta yanke jiki ta faɗi ƙasa asume, kamar jira suke Yi giant ɗin Ya fita, Haris yai wani irin kukan kura ya duro daga saman gadonshi, Ya kai ma Danish farmaki, kwalar rigarshi ya damƙa ya jijjiga shi, Hawaye na fita Cikin idanuwanshi yace”Ka kashe mu danish! Ashe dama baka da hankali? Kai wani irin wawan mutun ne sakarai soko maloho, wanda baisan Ciwon kanshi ba, wlh ka karya mini zuciyata ko a mafarki ban ta6a tunanin zaka Iya ruƙo hannun batool ka damƙa ma giant ita, don aje acutar da rayuwarta, ashe na yaudari kaina bansani ba, mugu azzalumi, wawa daƙiƙi….” Kafin haris ya ƙarasa maganar shi, Gaba ɗaya sauran ƴan uwan nasu suka tarar ma danish, bugu ta ko’ina suka shiga kai mashi, Kamar sun samu jaki, Hada matan duka suka nannaɗe hannayen rigunansu suka dunga bugunshi, amma ko gizau baiyi ba. Har saida suka fasa mishi hancin shi da bakin shi jini ya soma zuba, tukunna suka sake shi, anan ƙasa ya kife idanuwanshi sunyi jawur tamkar garwashin wuta, wani irin jiri yake gani, ya rasa meke yi mishi daɗi, ta ko’ina ga6o6in jikinshi raɗaɗi suke yi mishi domin kuwa ba ƙaramin bugu suka yi mashi ba, sun haɗa mishi Jini da majina sun xautar dashi,
Kowa sai faman haki yake yi, Kuma babu wanda yaji tausayin shi, suna a tsaitsaye cirko cirko suna kallonshi, sai faman juyi yake yi, tun da suke dashi basu ta6a jin tsanar danish ba sai yau daya nuna musu true colour dinshi, mugun zargin shi suke yi, tabbas shima yana atare da giant shiyasa yake goya musu bayan duk abunda suke yi. Ɗan jakar uba,
Haƙiƙa Danish ya yi breaking heart dinsu, hawaye ta ko’ina akan fuskokinsu, Ji suke kamar su tattake shi ya mutu su huta, tun da baida amfani acikinsu, tare da shi ake haɗa baki a cutar da ƴan uwansu,
“Daga rana irin ta yau kada ka ƙara kiran mu da sunan ƴan uwanka, mugu azzalumi” Javed ne yai maganar, deeja tace”dama tun jiya da aka dawo dani, naga sauyi atare dashi, ko sannu baiyi mini ba, ashe hada shi ake haɗa baki a cutar damu,”
Mubeen yace”ae ni banso muka barshi da rai ba, wlh da mun sani mun karkarya ƙasusuwan Jikin shi, ” yana magana yana cije le6e,
“Danish baida tausayi baida imani, yau ya tabbatar mana da hakan, shi ɗin ba jinin mu bane, don haka ya tattara ya san inda dare yai mishi tun kafin muyi silar mutuwarshi,”
Duk wannan suratan da suke Yi, danish yana kwance, numfashinsa na fita sama sama, daga gani yana acikin mawuyacin halin da shi kanshi baisan Ina zai tsoma ranshi ba,
Hancin shi dake bleeding jini duk ya wanke farar fatar fuskarshi, muryarshi adisashe yake faɗin “ku taimaka mun da ruwa in sha” wani irin kallo mai kama da harara suka shiga jefa mishi, haris yace koba ruwa ba? Ka jira ka gani, don ubanka, ” rai a6ace yaje ya ɗauko robar ruwan dake a ƙarƙashin gadon Batool ya dawo ya tsaya agaban danish, Ya buɗe murfin robar ya watsa mashi ruwan duka akan fuskarshi, yana gamawa ya jefar da robar ruwa aƙasa yace”Iya taimakon da zamu Iya yi maka kenan, ni banga ma amfanin kallonka da muke Yi ba, ku wuce muje mu xauna. Mubar shege ya ji ajikin shi”. Yana ji yana gani ƴan uwanshi suka juya mishi baya, Suka nufi gadajensu su ka zazzauna, zuciyoyin su acike da alhinin rashin Batool da suka Yi,
Hanna ce ta lura babu angel acikinsu, babu wanda ya lura da cewar ta sume a bakin ƙopar shiga sashen toilet dinsu.da sauri ta miƙe daga zaunan da take a gefen gadonta, sai da ta fara zuwa karkashin gadon batool ta ɗauko wata robar ruwan, Ta nufi inda angel take kwance ƙasa, Ta buɗe murfin robar ta ɗan ɗebo ruwan a tafin hannunta ta watsa mata saman fuskarta, nan take angel taja dogon numfashi ta fatser dashi, muryar ta cikin shessheƙar kuka take ambaton sunan batool tana faɗin An raba ni da ƴar uwata, innallahi’wa’ inna ilaihirraji’un! Wannan wata irin rayuwace
“Angel ki tashi xaune,” muryar hanna ce ta katse ta, jikinta duk ba daɗi, daƙyar ta samu ta yunƙura ta miƙe xaune tana faman huci sumar kanta duk ta tarwatse har tana kokarin rufe mata idanuwanta, bakowa ta ke kallo ba face danish dake kwance a ƙasa yana juyi, hannayenshi dafe da forehead ɗinshi,
Da buɗar bakinta sai cewa tayi”me danish yake yi araye batare da kun kashe shi ba”? Fuskarta babu wasa tai maganar, haris yace”munso muyi hakan amma sai muka ƙyale shi, bawai don mun haƙura ba ne, Xamu jira ne har time da za’a dawo mana da batool muga awani yanayi take ciki, idan ta tsira shima xai tsira da ranshi, muddin kuwa batool tarasa ranta a silar shi, wlh shima sai yabi bayanta, duk irin ƙaunar da nake yi mishi, xan rufe ido ne da hannu na zan kashe shi. Inya so nima daga bisani in haɗiyi zuciya in mutu”
Zuciyar angel har wani tafarfasa take Yi, sam ba haka taso ba, ta yi niyar tayi mishi bugun mutuwa har saiya haukace, Amma sai ta haƙura ta ƙyale shi ganin irin yadda jini ya wanke fuskarshi, koba komai Ya ɗanɗani irin zafin da suka ji acikin zuciyoyinsu,
“Angel, ki tashi muje saman gado ki kwanta” girgixa kai angel tayi tare da cewa”Kibarni anan kawai, ba inda zanje yau sai naga abunda ya ture ma buzu naɗi,” gyaɗa kai hanna tayi tare da miƙewa ta juya ta koma saman gadonta ta zauna,..
Duk sunyi zugudum cike da zullumin awani hali batool take aciki, a lokacin da ba su yi tsammani ba, suka ga hasken ɗakinsu ya ɗauke, duhu ya mamaye idanuwansu, Da sauri javed Ya miƙe ya lalubo fitilunsu Ya kunna su, ɗakin yayi haske, yau fa ba bacci dare ya koma tamkar da rana, Jimamin rashin ƴar uwarsu suke ta yi, ba wanda ya damu da danish, gaba ɗaya sun manta da azeeza dake a sume Cikin ƙarƙashin gado,
Har dare ya tsala, babu wanda ya runtsa acikinsu, sai daga bisani ne, Haris ya lallashe su, har ya samu suka kwanta, shima ya kwanta zuciyarshi duk ba daɗi, yana matuƙar jin tausayin danish, amma haushin shi ya hana ya taimake shi, bashi kaɗai ba. Hatta sauran ƴan uwan nashi, duk sun damu. Da danish, tsoransu kada ya rasa ranshi,
Ganin sunyi tsit Yasa ta fara tunanin ko sunyi bacci ne, duk da tasan zaiyi wuya yau su iya runtsawa, sai dai su yi likimo, amma wannan duk bai dame ta ba, Don yau taci alwashin saita dura tagar nan kodan taje ta taimaki rayuwar ƴar uwarta, kamar yadda tayi alƙawari, bazata bari a lalata mata rayuwar ƴar uwarta ba, yunƙurawa tayi tare da miƙewa, taje saman table ɗinsu ta ɗauko fitila, Ta juya ta nufi cikin toilet ta buɗe ta shiga ciki, wannan karan ko jam lock bata sanya ba, a buɗe tabar ƙofar, domin kuwa jininta akan akaifa yake, Komai zai faru sai dai ya faru ko a mutu ko arayu,, tsakanin ita da danish, yau saita dura tagar nan, Ita kaɗai tasan irin ƙuncin da take ji acikin zuciyarta, bayan ta ajiye fitilar a ƙasa, da ƙarfi ta janyo bokitin ƙarfen ta jingina shi jikin bangon tagar, tana ƙoƙarin hawa taji motsin mutun ya shigo Cikin toilet ɗin, a waske ta juyo baya don taga wanene, Bata yi mamaki ganin shi ba, ai yanzu ta daina ganin shi a matsayin mutun, ita da taga zahiran ɗazu da jam lock ya cire kanshi,
A tsaye yake jikin shi duk ba ƙwari, wani abu daya ɗan ɗaure mata kai, Jini daya 6ata fuskarshi yanzu babu shi, aranta tace”nasan bai wuci shi ne ya lashe shi ba, tun da ɗazu ma naga yasha na batool, Maye kawai, “
Yadda suke fuskantar juna, kamar abokan gaba ne suka haɗu a filin daga, banbancin kawai babu makami ahannun su,
Cikin muryar fushi tace”kada ka kuskura ka matso ku sa dani, because I can harm you, I hate you Danish, I don’t wanna see you, you are a bad person without faith and compassion,”
Muryarshi tamkar zai fashe da kuka yace”You should understand me, I am innocent, I am doing what is right……..” wata irin tsawa ta daka mashi yayin da take nuna shi da index finger ɗinta tace”ban damu da duk wani abu da zaka ce ba, wawa daƙiƙi, wlh rantsuwar ɗan musulmi, idan har ka kuskura kace zaka hana In dura tagar nan sai na yi maka mummunar illar da zata sa ka gaza takawa da ƙafafuwanka,”
A matuƙar ruɗe danish yake kallonta, baisan ya zai yi ya fahimtar da ita ba,
Ganin yana yunƙurin taka ƙafarshi xai tunkarota yasa ta takai hannu ta fusgi bokitin data ajiye ta ɗaga shi sama tana faɗin”Idan ka kuskura ka ƙara taku ɗaya, I will drop this bucket on your head idiot,” a wani irin raunace yake binta da kallo, duk da irin gargaɗin da take yi mishi hakan baisa ya dakata da yin tafiyar ba, yana tunkararta, ganin dai dagaske so yake ya hanata, aikuwa da sauri ta ajiye bokitin ta haye tare dakai hannu ta ɗaɗɗago da glass ɗin, Ta dure shi ƙasa, Tana yunƙurin hawa bisa tagar, Taji ya damƙi ƙafafuwanta daƙarfi, a ƙoƙarin ya janyota ta faɗo Cikin rashin sa’a ya zame wandon Jikinta gaba ɗaya ya sabule ƴan fararen cinyoyinta santala santala suka bayyana a suffarsu, saboda tsabar jaraba ko waiwayon wandonta bata yi ba, A haka ta dire tagar ta faɗa ta baya………………”
Ta tafi tabar danish a tsaye hannun shi ruƙe da wandonta, don ma Allah yasa rigar uniform ɗinsu tana da ɗan tsayi ta rufe ass ɗinta duka,
*❤❤❤PRISONERS❤❤❤*
Tun da ta dure tagar nan , danish ya kasa motsawa tamkar an ruƙe ƙafafuwan shi, Jikin shi yai mugun sanyi tamkar wanda aka zarewa laka, idanuwan shi na akan wandonta data bar mishi ruƙe a hannun shi, Kallon shi yake yi batare da ƙyaftawar ido ba, tsabar tashin hankali ne ƙarara akan fuskarshi , babban abunda yake jima tsoro Hannun da Angel zata faɗa, ba lallai ta Iya ganewa Ginin kurkukun ba. Domin kuwa a birkice yake. Idan har ba ka da ilmi akan shi, har ta6in hankali zaka iya samu saboda ruɗanin da zaka shiga,
Muryar shi na rawa ya furta”bazan ƙyale ta ba, why angel? Dole na bi bayanki, ” Yana yunƙurin haura tagar, kunnuwan shi suka jiyo mishi sautin muryar haris dake ta ƙwala ma shi kira daga can cikin ɗakin su, Aikuwa a matuƙar ruɗe Ya fasa Yunƙurin dura tagar, da sauri Ya nannaɗe wandon angel. Ya wurga shi saman tukunyar fulawar nan ta Cikin toilet ɗin, kafin ya miƙa hannu ya ɗauki fitilar da angel ta ajiye acikin toilet ɗin, Ya juya ya nufi hanyar fita, buɗe ƙopar shi keda wuya, Sai ga haris ya faɗo sashen toilet ɗin hannun shi ruƙe da fitila, Haska fuskar danish yai, ganin shi ne yasa shi sauke ajiyar zuciya, sam ya gaza runtsawa saboda tunanin mutun biyun nan batool da kuma danish, fargabar Halin da suke aciki Ya hana shi sakat.
danish ya yi mamaki zuwan haris nemanshi , bai ta6a tsammanin wani daga Cikin su zai waiwaye shi ba. Duba da irin aika aikar da ya yi musu.
Sun ɗauki tsawon mintuna suna kallon Juna, sai daga bisani haris ya jefa mashi harara tare da cewa”Ya jikin naka”? daƙyar danish ya samu ya dai daita natsuwarshi, Cikin sanyin murya yace”Da sauƙi” ta6e baki haris yae kafin ya kuma cewa”ka zo mu koma ɗaki, naga baka ci breakfast ɗinka dana ajiye maka ba, kuma nasan kana jin yunwa, tun safe har dare ko ruwa baka sha ba,” yana magana yana wurga mashi harara dake nuni da cewa ba don yaso yake yi mishi maganar ba, har yanzu akwai sauran haushin shi da yake ji acikin zuciyar shi,
Danish bai motsa ba, kallon haris kawai yake yi, shi damuwarshi akan angel ne, Baya jin zai Iya bin haris su koma ɗaki,
Jin yayi shiru yasa haris sake cewa”magana fa nake yi maka”? Fuskarshi a yamutse ya soma magana,
“Meyasa ka damu da ni? Duk irin abunda na aikata mu ku? Rai a6ace haris yace”ba wannan na tambaye ka ba, abinci nake magana, kazo muje ka ci” girgixa kai danish yai alamar a’a yace”Na ƙoshi, ka ƙyale ni koda yunwa zata kashe ni, bai shafe ka ba, lokacin dana buƙaci taimako awurinku, akan ku bani ruwa in sha, ka tuna abunda ka yi mani?
A fusace haris yaja dogon tsoki tare da matsawa ciki ya ruƙo hannun danish da niyar ya fusgoshi su tafi, da sauri danish ya ƙwace hannun shi, cikin kakkausar murya yace”Nace maka bazanci ba! Ka rabu dani! Babu ruwan kowa da rayuwata, tun da kun nuna cewa bani da amfani acikin ku,” wani irin kallo haris yake bin shi da shi, kowannan su sai faman huci yake yi,
Shi burin shi haris ya tafi ya bashi wuri ko ya samu yaje ya taimaki angel, don yasan yanzu haka tana can tana neman ɗauki ta gama furgicewa,
Haris Na ƙoƙarin buɗe baki don Ya mayar mishi da martani, Muryar Deeja Ta katse mishi Hanzarin shi, daga can cikin ɗaki Ya jiyota tana ƙwala mishi Kira, don dole ya saki hannun Danish Ya juya da gudu ya koma Cikin ɗakin,
Shigar shi ke da wuya, Ya yi arba dasu deeja gaba ɗayansu agaban gadon Azeeza, tunkafin ma ya ƙarasa shiga hankalin shi yai matuƙar tashi, Ganin azeeza rungume jikin deeja, babu numfashi, kamar matatta, Su parveen sun tasa ta gaba sai kuka suke Yi,
A bunda ya faru, Tun lokacin da azeeza ta 6oye ƙarƙashin gado ta 6oye don kada giant ya ɗauke ta, gaba ɗaya sun manta da azeeza, da ta 6oye a ƙarƙashin gadon ta, Har suka kwanta basu tuna da ita ba, sai daga baya ne deeja tana kwance saman gadonta, ta yi zurfi acikin tunaninta, kwakwalwata ta soma tariyo mata abunda ya faru kafin atafi da Batool, Nan take ta dafe ƙirji, ta miƙe zaune tana Ambaton sunan azeeza, Koda sauran ƴan uwan nasu suka ji tana kiran sunan azeeza, suma sai suka wartsake kowa Ya sauko daga saman gadon shi, A gaggauce Deeja ta ɗauko dayar fitilar data rage a ɗakin, Ta ajiye ta daga ƙasa gefen gadon Azeeza, Ta zuƙunna tana leƙa kanta ciki, Anan ne taganta xaune Kamar gunki babu abunda ke motsi ajikinta, Ta fashe da kuka Tare da kai hannu ta 6an6arota daga Jikin bangon data jingina, ta janyota wajen gadon, ta kwantar da ita saman jikinta, Su Hanna duk suka kewayesu, kowa ya zuƙunna suna ta kuka suna ambaton Sunan Azeeza, Zuciyoyinsu duk sun karaya, ganin yadda jikinta ya sandare, Cikin shessheƙar kuka hibba tace su jira ta dauko ruwa a yayyafa mata wata’ƙil su samu ta farka, tana karasa yin maganar ta miƙe ta ɗauki fitilar ta nufi gadon batool, tana laluban robobin ruwan da suka ajiye, sai dai bata samu ko ɗaya ba, duk sun ƙare, Jiki amace hibba ta dawo tana haska su da fitilar hannunta tace babu ruwa, bari naje toilet na ɗebo, har ta juya zata nufi toilet ɗin, Muryar deeja ta katse ta da cewa”Ina haris yake? Naji motsin shi ɗazu, Ya sauko daga saman gadon shi, ina tunanin toilet ya shiga, Bari na kwala mishi kira yazo,” Batare da6ata lokaci ba, deeja ta shiga kwala mishi kira, Sai gashi ya faɗo Cikin ɗaki,
Haris na ƙarasawa kusa dasu, Muryarshi na ɗan rawa ya ambaci sunan azeeza tare da cewa Meya faru da ita? Nan suka sanar dashi komai, tun daga zuwan Giant, dafe kanshi yai da hannu ɗaya, idanuwanshi sunyi jajur, zuciyarshi duk ba daɗi, Yau dai gaba ɗaya basu ji daɗin ranar ba, sun yini da baƙin Ciki acikin ransu,
Kallonsu parveen yae ganin yadda suke ta yin kuka babu ƙaƙƙautawa, Cikin sigar lallashi yace”Ku kwantar da hankalin ku, azeeza zata farka suma ne tayi, bari naje na ɗebo ruwa a yayyafa mata” yakai karshen maganar tare da juyawa Ya nufi cikin ɗakin, Yana laluban Inda ya jefar da robar ruwan daya watsa ma danish ɗazu, Cikin sa’a yaci karo da ita can gefen dining carpet ɗinsu, Da azama ya je ya ɗauko bottle water ɗin Ya juya ya nufi sashen toilet ɗin su.
Lokacin daya shiga, baiga danish ba, babu shi babu alamarshi, Sai dai bai kawo komai aranshi ba, ganin ɗaya daga Cikin ƙopar toilets ɗin nasu a garƙame, sai yayi tsammanin ko yana aciki ne, ɗayan toilet ɗin ya shiga ya kunna fanfo ya tarba robar ruwan, sai da ta Cika tab, kafin Ya kashe fanfon Ya fito daga Cikin toilet ɗin Ya koma inda su deeja suke a zazzaune, Zuƙunnawa yai, bayan ya ajiye fitilar hannunshi, Ya tarba ruwan a tafin hannun shi ɗaya, Ya watsa ma azeeza saman fuskarta, Kowa ya baza ido yana jiran ganin ta farka, amma shiru ko motsi bata Yi ba, Nan fa hankulan su suka ƙara tashi matuƙa,
Cikin shessheƙar kuka suka haɗa baki suna roƙon azeeza akan ta taimaka musu ta farka, Haris dasu Javed sai lallashinsu suke Yi, ganin yadda duk suka shiga damuwa, parveen na kuka tace”tun da muke arayuwar mu ba mu ta6a fuskantar tashin hankali, irin na yau ba, An ɗauke mana batool, ga azeeza kuma taƙi farkawa, Ni tsorona ma kada ace ta mutu…..” kasa ƙarasa maganar ta yi saboda kukan daya ciyota, ta kifa kanta saman gwiwarta, muryar deeja adisashe tace”dan Allah ku daina maganar mutuwa, wlh bana sonji, in sha Allah azeezan mu zata farka, babu abunda zai same ta, addu’a ya kamata muyi mata,” Haris yace”wace irin addu’a? Babu abunda zata yi mana, kawai dai mu jira zuwa lokacin da zata farka,” idanuwanta cike tab take ƙwalla take kallon shi,
Tsananin tausayinsu ne ya kamata haris, bayin Allah, tun safe hankalin su ba’a kwance yake ba, ga shi har dare ya ratsa basu runtsa ba,
Kusan sau uku haris yana yayyafa ma azeeza ruwa akan fuskarta amma taƙi farkawa, Jikinsu duk yai sanyi, haka suka zauna a kewaye da ita, suna kallonta yayin da hawaye ke cigaba da sauka a kan fuskar kowannan su.
“To ko dai mu yi ma tsohuwa magana tazo ta duba ta kada ta mutu” acewar yasmin, har suna haɗa baki wurin cewa”Taje ta kirawo ta,” Da sauri yasmin ta miƙe ta dauki fitila ta wuce ɗakin tsohuwa, lokacin da yasmin ta bubbuga ƙopar ɗakin tsohuwa bata buɗe mata ba, kusan sau takwas tana yin knocking kamar zata 6alle ƙopar har saida haris yace mata ta dawo zai iyayiyuwa bata nan,Tukunna ta ƙyale ƙopar ta dawo wurinsu ta zuƙunna,
Magiya suka soma Yi mata akan tafarka
“Azeezan mu ki tashi dan Allah, Badan halin mu ba, wlh ba mu gaji dake ba Muna matuƙar ƙaunarki ƙaramar mu kuma babbar mu, pls wake up, kome kike so zamuyi maki, bazamu ƙara 6ata maki rai ba, kuma ba zamu bari giants su ɗaukar mana ke ba” kamar wasu sabbin mahaukata haka suka dinga yi mata sambatu akan tafarka, tun sunayin maganar da ƙwarinsu har ta kai ga muryoyinsu sun disashe, kowa yaja gefe suna matsar ƙwalla, idanuwansu duk sun kumbura saboda tsabar kukan da suka sha,
“Wai ina angel take ne!? Nifa banganta acikin mu ba? Yakamata wani yayi mata magana tazo taga halin da azeezan mu take aciki, tayi mata addu’a ko mun samu tafarka” Kallo kallo suka shiga yi a tsakaninsu, Jin abunda deeja tace, gaba ɗaya sun manta da babu angel acikinsu sai da tayi wannan maganar su ka tuna da ita, Hanna tace”ɗazu acan nabarta zaune bakin ƙopar shiga sashen toilets dinmu,” tayi maganar tare da juyawa tana nuna musu wurin, Basu ga komai ba, naufal yace”kodai tayi bacci ne”? Haris ya bashi amsa da cewa”ae bata a saman gadonta, ɗazu da zan shiga toilet na duba naga babu ita” a matuƙar ruɗe suke kallon juna, Eve tace”kodai ta shiga toilet ne? Bari inje in dubo ta”
da sauri haris ya dakatar da ita tare da cewa”Ni zan dubo ta” Ya miƙe tare da kai hannu ya ɗauki fitila Ya juya ya nufi sashen toilet ɗinsu, yana gab da zai shiga, ba zato ba tsammani sai ga danish Ya faɗo hannayenshi biyu suna rungume da angel, ya tallabota a jikinshi, babu alamun tana motsi, A wani irin yanayi Su Hanna suka mimmiƙe tsaye suna kallon shi, mamaki ƙarara akan fuskokinsu, Yayin da zuciyoyinsu ke acunkushe da tambayoyi dangane da abunda ya faru da ita da har ta sume bata motsi,
An rasa me buɗe baki yayi mishi magana A cikinsu, ko kallo basu ishe shi ba, kaitsaye Ya wuce da ita saman gadonta Ya kwantar da ita, sumar kanta duk ta hargitse, Fuskarta tayi jawur, musamman tsinin hancinta, hada ɗigon Jini, daga gani ba ƙaramar wahala tasha ba, hawayene ta ko’ina akan fuskarta, kayan Jikinta sunyi uban squeezing, Hada wandonta Daya maida mata ajikinta, Da gudu Su Hanna suka Tunkaro gadon suna tambayarshi Meya faru da angel a ina ya ɗaukota? bai tanka musu ba, Domin kuwa A yanzu baya atare dasu, itace A gabanshi, zuciyarshi sai harbawa take yi da sauri sauri, numfashin sa da hucin zafi yake fita, a wani irin yanayi yake bin fuskarta da kallo………………..”
“Shin meya faru da angel Bayan ta dura tagar nan”?
Lokacin da Angel ta haura tagar nan, ta faɗo ta baya wani irin duhu ne ya mamaye idanuwanta, kanta ya soma juyawa, Ta sanya hannayenta bibbiyu ta dafe kanta, Jikinta ya soma kerma a hanzarce ta fara ƙoƙarin kamo sunan Allah acikin bakinta, sai dai abun ya faskara, sautin shessheƙar kuka ta dinga Ji acikin kunnuwanta, ranta ya dinga bata cewar batool ce take kuka, Cikin duhunnan, ta miƙi hanya gudu gudu sauri sauri hada tuntu6e, ita kanta batasan ina zata dosa ba, domin kuwa notikan kwanta sun kwance, bata ji bata gani, a makance take tafiya burinta takai ga inda take jiyo sautin shessheƙar kukan nan, Haske ta fara hangowa a ƙarshen hanyar data biyo, da gudu ta nufi inda take hango hasken nan, tana faɗowa cikin wurin, Idanuwanta suka sauka akan katafaren filin dake da manya manyan benaye, a ƙalla sun kai Shida benayen kuma kowane matakalarshi ta haura goma sha, don akwai wanda matattakalarshi takai talatin shine wanda idan ka hau zai kai ka har third floor na ginin, Ginin yana da tsayi da faɗi, Daga sama wasu irin manya manyan fitilune da suke haskaka wurin, idan ka kalli kowani hawa na benan zakaga Wasu Tagogi wadanda glass din Jikinsu launin Ja ne, Masu girma, Babu ƙofofin ɗakuna Sai dai da alama za’a Iya samun ƙofofinsu ta can cikin hanyoyin dake akwai, wani irin kurman Ginine, Mai matuƙar ruɗarwa, wani irin fargaba ne ya ɗarsu acikin zuciyarta lokacin da tafara Jin wani irin gurnani, Ginin Ya dinga juya mata, benayen suka dinga motsi Suna Yin ƙasa da sama, Waro ido waje angel tayi Jikinta na 6ari, Ta zabura zata Juya ta koma Inda ta fito, sai dai ina babu hanya, tama rasa gane ta inda ta faɗo Cikin wurin, Tsabar ruɗi yasa ta baza da gudu ta faɗa tsakiyar wurin, hannayenta dafe da kanta saboda wani irin firgici da take aciki, tuni zufa ta wanke Jikinta sharkaf, Bata gama rikicewa ba, Daga can saman hawa na uku ta soma Jin muryar mahaifinta tajudden Yana kuka yana kwala mata gira, A matuƙar ruɗe ta juya ta baya tare da ɗaga kanta saman benan, A tsaye ta hango shi, tare da Wasu irin haluttu masu gashi gashi ajikinsu, Jibga jigba, Sun kewaye shi, Sai Cuzgar naman Jikin shi suke yi, Wata irin gigitacciyar ƙara angel tasaki, mai kuwar gaske, Ta fashe da matsanancin Kuka tana fadin”Daddy! wayyo Allah na daddyna! Shikenan sun kashe mini daddyna!! nashiga uku, Dan Allah ku ƙyale mini daddyna” Tana kuka ta watsa da gudu ta nufi ɗaya daga Cikin benayen da nufin taje ta taimaki daddynta, tana gudu ana maida ta baya, Da zarar takusa kaiwa saman benan sai taga Sun juya mata, Benan yaja da baya, Ya koma can Ciki, Haka ta dinga bin benayen tana ƙoƙarin hawa samansu, Amma wani abun ruɗarwa benayen tamkar masu Rai, sosai suke motsawa wurin yin ƙasa da sama, Jikinta duk zufa ta galabaita sosai, idanuwanta sunyi jawur, Jijiyoyin wuyanta duk sun fito ruɗu ruɗu Jikin fatarta, Muryarta har ta disashe, Duk da mawuyacin halin da tashiga na tsoro da firgici hakan baisa ta fasa yunƙurin hawa benan ba, Bakomai take ji ba face mahaifinta da take hangowa can saman waɗannan halittun suna Cin naman jikinshi, sai kuka yake Yi yana miƙa mata hannu akan tazo ta taimake shi, Akan idonta halittun suka gutsire ƙafafuwanshi, Jini ya dinga tartsatsi yana gangarowa ta saman benan, Angel tashiga ruɗani, addu’a ta kubce mata, gaba ɗaya tunanin ta ya gushe, Tun tana yin kuka har ta koma tana yin na zuci, Ƙafafuwanta sai zogin azaba suke yi mata, saboda zarya da tadinga Yi, Lokacin da benayen suka gama yi mata wasa da hankali, Suka koma yadda suke, waɗannan halittun suka 6ace ma ganinta, sai dai gangar jikin mahaifin ta dake a yashe saman hawa na uku, Da gudu ta haura saman dogon benan nan wanda ya ke da matattakala Talatin, Tana tafiya tana zamewa, a haka harta samu ta haura saman shi, Tana ƙarasawa inda gangar jikin tajudden take, ta zuƙunna saman gwiwowinta, ta dinga kuka hada majina tana ambaton sunan shi tana faɗin sun kashe mini daddyna, sun rabani da farin Cikina, Wayyo Allah na, Ya Allah ka ɗauki raina nima in huta, yatsun hannunta na kerma ta ɗaga su da nufin ta shafa gangar jikinshi, nan take gangar jikin ta 6ace 6aat, a matuƙar gigice ta zazzare idanuwanta eye lashes ɗinta suka bubbuɗe, tsigar jikinta ta dinga tashi, zufa ta ko’ina, kwakwalwarta ta burkice, kafin ta yi wani yunƙurin motsawa ta soma Jin motsin tafiyar wasu abubuwa ta ko’ina, a firgice ta ɗan juya baya tana kallon Jikin wata taga dake a datse, Ras taji gabanta yai wani irin mugin bugu, Bakomai bane angel ta gani face wasu irin manyan kunamu sun ɗaga ƙarin su, Yayin da suke gangarowa daga Jikin bangon suna tunkaro inda take zuƙunne, wa’iyazubillah, ƙiris ya rage zuciyarta ta buga, saboda tsabar razanar da ta yi, ga shi jikinta babu ƙwarin da zata Iya saukowa daga saman benan, Jikinta na 6ari ta soma rarrafawa tana tunkarar banen dan ta sauko ƙasa, tana kuka tana waiwayon kunamun dake tunkarota, a wannan lokaci ta dinga kwala ma danish kira na fitar hayyaci tana faɗin yazo ya taimake ta, zasu kashe ta, ta mutu ta bani ta lalace ƙarshenta yazo,
Adai dai wannan Lokacin Danish Ya faɗo Cikin wurin, Hannun shi ruƙe da wandonta, sai faman waige waige yake yi, karaf idanuwanshi suka sauko akan angel da ke yin rarrafe tana saukowa daga saman benan, Hankalinshi yai matuƙar tashi, da ƙarfi ya ambaci sunanta yana faɗin ta tsaya kada ta motsa ba abunda zasuyi mata, sai dai kash angel bata Iya fahimtar maganar shi, saboda bata acikin hayyacinta, Da gudu ya nufi benan da niyar yaje ya taimaka mata, kafin ya ƙarasa gwiwowin ƙafarta suka sage, Tun daga kan matattakalan farko Angel ta burki ce ta dinga mirginowa tana gangarowa ƙarshen stair ɗin, kanta da hancinta duk suka fashe suna bleeding, kafin ta faɗo ƙasa, sai da ta fita hayyacinta, Jini ya wanke fuskarta, har saman wuyanta, hatta knuckles ɗinta saida suka gurguje, A ƙarshe ta ƙundumo kan ground floor ɗin, kanta ya dake shi, goshin ya fashe, ƴar rigar uniform ɗin dake ajikinta, tuni ta yaye ta nannaɗe ta dawo saman Cikinta, tsiraicin ya bayyana sosai, gashi ko pant babu ajikinta, Wasu irin zafafan hawaye ne suke wanke fuskar danish time ɗin daya ƙarasa ya zube agabanta saman gwiwowinshi, yayin da numfashin shi ke fita a wahalce, A wani irin yanayi mara misaltuwa yake kallonta, dama abunda yake guje mata kenan, Amma ta ƙi jin maganarshi, hannunshi na kerma ya ruƙo rigarta data nannaɗe, ya janyota ya rufe mazaunanta, a saman laps ɗinshi ya ɗaura wadonta, kafin ya sanya hannayenshi biyu ya ɗago da ita, zuciyarshi ta ƙara karaya ganin irin mummunan raunin da taji akan fuskarta, idanuwanshi ba zasu juri ganin angel cikin mawuyacin hali ba,
da sauri ya kwantar da ita saman ƙirjinshi, ya matseta da hannayenshi biyu, ya kwanto da kanshi saman sumar kanta dake a yamutse, ya ɗan lumshe idanuwanshi, saboda tsabar zafin jikinta har a jikinshi yana ji, cikin wata irin raunatacciyar murya ta wanda ya galabaita ya jigata ya fita hayyacinsa ta dinga kira mishi sunan daddynta, ta zagayo da hannayenta zuwa bayanshi, ta cakumi rigarshi tana yamutsa ta, babu alamun hankali atattare da ita, santala santalan cinyoyinta sun fito farare sol dasu, sai faman motsa su take yi, tana harɗesu jikin juna, ganin rigarta na ƙoƙarin kwarewa ta ƙara nannaɗewa yasa shi yin saurin kai hannu ya damƙi ƙasan rigar ya gyara mata ita,
A hankali Ya sanya hannayenshi biyu ya ɗago da kanta daga saman ƙirjinshi, Jininta duk ya 6ata mishi gaba rigarshi, ya tallabo fuskarta, Yana ƙare mata kallo, Idanuwanta sun ƙanƙance, tausasan la66anta sun kumbura sun ciza launinsu, tsinin hancinta yai ja sosai, jinin ne ke gangarowa ta cikin ƙofofin hancinta, Cikin karyayyiyar murya ya ambaci sunanta Angel, bata amsa mashi ba, don a halin da take aciki batasan wanene akanta ba, sunan daddynta kawai take iya ambato,
Cikin harshen turanci yaci gaba da cewa “Angel, kinga abunda kika ja ma kanki ko? Yanzu da ace banzo ba ya zaki yi? Kalli yadda kika raunata kanki, ta ko’ina babu lafiya a jikinki, saboda kafiya irin taki na gargaɗe ki amma kika ƙi jin magana ta, saboda baki ɗauke ni abakin komai ba, kin ɗauka cewa shiga cikin prison abune mai sauƙi, yanzu gashi nan kin ja ma kanki yin jinya, nasan ko gobe aka nuna maki hanya fita ba zaki ƙara gigin binta ba” shi kaɗai yake ta sambatun shi, baiwar Allah, sai nishi take yi, ita kaɗai tasan irin raɗaɗin da take ji ajikinta,
Haɗe fuskokinsu yai wuri ɗaya, ya mayar da hands ɗinshi Tsakanin sumar kanta da wuyanta, harshen shi ya ɗaura saman fuskarta, a hankali ya soma lashe jinin dake zuba, har sai da yaga babu sauran jinin dake ɗiga tukunna ya zame tongue ɗinshi, idanuwanta sai rurrufewa suke Yi, biji biji take ganin shi, tun tana yin numfashi daƙyar daƙyar har ta kai ga sumewa saman jikinshi, da dabara ya samu ya zame wandon unform ɗinta daga saman laps ɗin shi, Ya damƙo dogayen ƙafafuwanta, Ya shiga kiciniyar sanya mata shi, daƙyar ya zura mata wandon yaja shi har saman waist ɗinta, bayan ya kammala, Ya ɗaɗɗago da ita, ya yarfata saman kafaɗarshi Ya miƙe Ya juya Ya nufi hanyar komawa ɗakin su, sai dai da alama danish bata taga ya koma Cikin ɗakinsu ba, 6acewa yai ya faɗo Cikin toilet ɗinsu ɗauke da ita a hannunshi, a lokacin Har ya gyara ɗaukar da ya yi mata, ya sauko ta daga saman kafaɗar shi, Ya yi mata irin ɗaukar da ake yi ma jariri, Yana kan hanyar fitowa daga Cikin toilet ɗin, Yaji motsin mutun Yana tunkaro ɗakin Da wani irin sauri Ya faɗo bakin ƙopar sashensu, Kunji yadda akai danish Ya ɗauko angel,
*PRISONERS💔*
hankalinsu yaƙi kwanciya, Ganin irin raunatar da angel tayi, masu karyayyiyar zuciya acikinsu tuni sun fashe da kuka, Hibba tace”wannan wata irin rayuwace, daga wannan sai wannan, yau dai bata yi mana daɗi ba, muna fama da azeeza data sume ga kuma Angel itama asume jikinta duk ciwuka, wai dan Allah meya faru da ita ne? Tana rufe baki hanna tace”pls danish ka faɗa mana a ina kaga angel, can fa nabarta a zaune, Yanzu kuma sai gashi ka shigo da ita daga Cikin toilet, yaushe ta shiga ciki? A matuƙar ruɗe tayi mashi tambayar, haris yace”Allah yasa ba wani mugun abun ka yi mata ba, Wama ya sani ko bugunta ka yi don ka huce haushin abunda muka yi maka,” da sauri danish ya ɗago da idanuwanshi ya ɗaurasu kan fuskar haris da ya yi maganar, wani irin raɗaɗi yake ji acikin zuciyar shi, ƴan uwanshi suna yi mishi kallon mugu mara tausayi mara imani, duk sai yaji ya tsani kanshi, sam ya kasa furta komai, duk da ya ɗago ne da niyar ya mayar mishi da martanin maganar shi amma sai ya kasa,
“Yakamata muyi ƙoƙarin wurin ceto rayuwan ƴan uwanmu bawai mu tsaya muna surutu mara amfani ba” Acewar Mubeen,
Cikin fushi haris yace”Ka faɗa mana me ka yi ma angel da har ta suma? Hawaye ne suka cika idanuwanshi, Cikin sanyin murya yace”ka bari tafarka sai ka tambaye ta me nayi mata, idan har ni na zalunce ta, kuna da right da xaku iya rama mata, amma bai kamata ace kuna tuhumata ba”
Naufal yace”zamu zuba ido mu gani har zuwa lokacin da zata farka wlh idan har ta fada mana cewa kaine silar halin da tashi ga, to ka kwana da sanin cewa ba zamu ƙyale ka ba,” Yana magana yana galla mishi harara, Girgiza kai danish ya ɗanyi batare daya tanka ma naufal ba, ya lura gaba ɗaya shi suke zargi akan halin da angel ta shiga, basu son cewa itace ta ja ma kanta ba,
“Ina azeeza take”? Yayi tambayar yana bin fuskokinsu da kallo, kusan atare suka haɗa baki wurin cewa”Ina ruwanka da ita? Ka damu dasu ne”? Girgixa kai ya ɗanyi tare da cewa’taya bazan damu dasu ba, ƴan uwanane su, baku isa ku hanani tambayarsu ba”
Javed yace”Har kana da bakin cewa su ɗin ƴan uwanka ne? Mugu dakai saboda rashin imani ka damƙi hannun batool ka miƙa ma wani ƙato ya ɗauke ta don aje acutar da ita, a haka har kake kiransu da ƴan uwan ka”? Tuni idanuwanshi sun cicciko tab da kwalla, tunawa da rashin imanin da ɗan uwansu danish yayi musu, jikin shi duk yayi sanyi, har lokacin yana zaune gefen gadon angel, daƙyar yake kallonsu saboda nauyin haɗa ido da su ya ke ji.
“Ka faɗa mana wanene kai!” har saida gabanshi ya faɗi jin tambayar da haris ya jefa mishi, muryarshi na kerma yace”wha..what u mean? Haris ni kake tambaya wanene Ni”? jinjina kai haris yai tare da cewa”Eh, so nake insan wanene kai! Danish bani kaɗai ba gaba ɗayan mu nan zargin ka muke Yi, Kawai ka faɗa mana gaskiyar wanene kai, meyasa kake atare damu” a ruɗe danish yake kallonsu,
Naufal yace”bana tunanin danish cikakken mutun ne, Saboda babu zuciya a ƙarjinshi, Haba rashin imanin yayi yawa, ka duba kaga yau tsawon shekara nawa, danish yana atare da batool, tun kafin mu mallaki hankalin mu yake atare da ita, baida wani makusancin daya wuce ita, in ka cire haris, amma yau rana ɗaya ka gaza ceton rayuwarta, sai ma ka taimaka wurin miƙa ta ga azzaluman da zasu azabtar da rayuwarta……” wani irin kukane yazo ma naufal ba arxiƙi ya katse maganar, hawaye suka soma bin fuskarshi,
Haris ya ɗaura da cewa”ba zamu ta6a mantawa da wannan ranar ba, danish ka cika butulu, mara imani da tausayi, Yarinyar nan babu irin ciwon kan da batayi ba akanmu, tana matuƙar son ƴan uwanta, idan wani baya lafiya acikinmu, batool ko bacci bata iya yi har sai yaji sauƙi, ka cuce mu danish, kuma ka karya mata zuciya, nasan batul bazata ƙara yarda dakai ba, saboda kaine silar duk wani hali da zata tsinci kanta,”
Tun da suka soma yi mishi magana, yayi shiru yana binsu da kallo bai ko tanka musu ba, duk yadda zaiyi musu bayani yasan ba lallaine su fahimce shi ba, amma yafi su jin raɗaɗin rabuwa da batool, shi kaɗai yasan irin ƙuncin daya shiga lokacin daya janyota ya miƙa ma giant,
Sun tasa shi gaba suna jiran jin amsar dai basu, bai bi ta kansu na, ya miƙa ya tunkari inda su deeja suke zuƙunne, yana yunƙurin zuƙunnawa don ya duba lafiyar azeeza, naufal ya damƙi hannun shi tare da cewa”kada ka kuskura ka ta6a ta, babu ruwanka da rayuwarmu” murmushin takaici danish ya sakar mashi, batare daya mayar da martanin maganar shi ba, ya fusge hannun shi daga ruƙon da yae mishi, Ya zuƙunna agabansu deeja, wani irin haushin shi take ji kamar ta shaƙe wuyan shi, Tun da ya zuƙunna take ta aika mishi da harara kamar ƙwayar idanuwan zasu faɗo ƙasa, wanda ake yin hararar domin shi baima san tana Yi ba, hankalin shi gaba ɗaya yana akan azeeza, dake rungume jikin deeja,
Robar ruwan da haris ya ajiye a ƙasa, Danish Ya miƙa hannu ya ɗauko ta, A baki ya kur6i ruwan, duk suna a tsaye suna kallonshi, A saman fuskar azeeza ya watsa ruwan, Wani iko na Allah nan ta ke azeeza taja dogon numfashi, Jikinta ya soma kakarwa, Cike da mamaki suka dinga kallon danish da kuma azeeza, ganin yadda yai nasarar watsa mata ruwa ta farfaɗo,
Hannayenshi biyu ya sanya ya tallabo fuskar azeeza yana kallonta, muryarta adisashe take faɗin dan Alah kada ku bari su ɗauke ni, wlh mutuwa zanyi, ni bazan bi su ba, “
“Azeeza”! Muryar danish ce ta dawo da ita cikin hayyacinta, ta ɗan buɗe idanuwanta tana kallon shi biji biji saboda matsalar idanuwanta, da sauri su haris dasu hanna duk suka zuƙunno agabanta, suna ambaton sunanta, ɗaya bayan ɗaya take binsu da kallo, badan tana gane su ba, yayin da idanuwanta ke lumshewa, muryarta na ɗan rawa tace”Dagaske ba’a tafi dani ba, ina atare da ƴan uwana”? Atare suka haɗa baki wurin bata amsa da cewa”Eh, muna atare dake” har xatayi murmushi sai kuma ta fasa, tunawa da batool, nan da nan walwalar fuskarta ta ɗauke. A tsorace tace dasu”Ina Batool take” nan fa kowa yai shiru, hakan yasa ta fahimci cewa An ɗauke batool, shessheƙar kuka ta fara yi musu, Danish yace”its okey azeeza, ba lafiya gare ki ba, kina buƙatar ki huta” girgixa mashi kai tayi hawaye ta ko’ina akan fuskarta tace”Yanzu shikenan an ɗauke mana batool dinmu, an tafi da ita, baiwar Allah, nayi danasanin cizon ta da nayi, dame xata ji”? Fashewa tayi da kuka, Cikin sanyin murya haris yace”Pls azeeza stop shedding ur tears, Ya riga daya faru babu wanda ya isa ya dawo dashi baya, abunda nake so daku shine muyi haƙuri mu rungumi ƙaddararmu, idan da rabon za’a dawo mana da batool, Ko min daran daɗewa, ƴar uwarmu zata dawo cikinmu ne”
Sosai haris ya shiga kwantar musu da hankalinsu, sai gashi kowa daga Cikinsu yaja baki yae shiru, danish yace”Yakamata kuje ku kwanta…..” daƙyar ya ƙarasa maganar, ganin irin kallon da suke watsa mishi, Haris yace”Itafa angel? Kaƙi faɗa mana meya faru da ita, a ina ka ɗauko ta? Me kuma ya haɗa ka da ita da har kayi mata wancan jahilin bugun,”
“Haris, bani da amsar da zan baka, amma idan tafarka, zaka Iya tambayarta, ” yana kai karshen maganar, Ya miƙe tare da ɗaukar robar ruwan Ya nufi gadon angel, Bai kai ga ƙarasawa ba, Ya ɗan dakata da yin tafiyar, Batare daya juyo ya kalle su ba, da wata irin kakkausar murya yace”ku wuce ku je ku kwanta,” Tun da ya ambaci hakan suka fara Jin wani irin matsiyacin bacci yana niyar dauƙarsu, A daddafe kowannansu Ya miƙe Deeja ta ruko hannun azeeza a saman gadonta suka kwanta su biyu ta rungumeta ajikinta, Cikin ƙanƙanin lokaci ɗakin yai tsit Baka jin hayaniyar komai bacci duk yae awon gaba dasu,
Ajiyar zuciya yaɗan sauke, Aranshi yace”nasan da hakanan nace su kwanta bazasu bi umarni na ba”
Daga gefen gadon angel ya zauna, Yana binta da kallo, sai yaji sam baya son ya tada ta daga bacci, saboda sanin tsiwarta, Its better ya ƙyale ta zuwa wani lokaci, A hankali Ya ajiye robar ruwan daga ƙasa, ya haura saman gadon, ya sanya hannayen shi biyu ya damƙi ƙafafuwanta, A tsanake Yake daddana mata su, Yana yi mata tausarsu, duk inda ya ta6a sai kaji ya bata sauti ƙass, daga bisa ni ya ruƙo yatsun hannayenta, Ya dinga jansu, bayan ya kammala, Ya kwanta daga gefenta, idanuwanshi akan fuskarta,
“Idan tana bacci tafi kyau, da sanya zuciya natsuwa, amma idan tafarka, tsiwarta tafi komai ɗaga hankali,” da wannan zancen zucin bacci yayi awon gaba dashi,
Daƙin yai tsit, Ba ka Jin sautin komai saina minsharinsu,
Bayan wani lokaci, Hasken fitilun saman ɗakinsu Ya gaure ko’ina, wanda ke nuni da cewa gari ya waye, babu alamun masu bacci zasu farka,
Motsin buɗe ƙopa ne Ya karaɗe kunnuwan danish, A hankali Ya ɗan ware sexy eyes ɗinshi, ya yunƙura ya miƙe daga zaune ya jingina bayan shi da bango, Angel na a kwance gefenshi, idanuwanshi sai faman lumshewa suke Yi, da alama baccin bai ishe shi ba, jikinshi duk ba daɗi, A buƙace yake da son Yin wanka, gaba ɗaya hankalin shi ya koma kan staircases jin Sautin tafiyar mutane.
Giants ne suke shigowa hannayensu ɗauke da sabbin gadaje kalar nasu, duk mutun ɗaya yana ruƙe da gado ɗaya, A jere suke saukowa daga saman benan, kusan su Goma sha biyar, Kaitsaye suka wuce can Cikin ɗakin, 6angaren da gadajensu danish suke fuskanta, A nan suka jera sabbin metal beds ɗin da suka shigo dasu,
Duk akan idonshi, Bayan sun kammala jera gadajen, Sai ga Wani giant ɗin Ya shigo Hannun shi ruƙe da doguwar ledar kaya, mai ɗauke da sunan Prison, Bargunane acikinta tare da bedsheets da kuma pillow, Yana ƙarasowa Ciki, Batare da 6ata Lokaci ba, suka curo da zannuwan gadon suka shimfiɗa ma kowani gado, daga bisani suka ɗaura bargunan, tare da pillow, Bayan sun Kammala A jere suka Juya suka fuce daga Cikin ɗakin,
Mamaki ne ya kama danish, yayin da yake saukowa daga saman gadonshi, Ya nufi inda gadajen suke a jere, Yana ƙare musu kallo,
aranshi yace sabbin prisoners za’a kawo mana, Har mutun goma sha biyar? Mun cika talatin kenan,” ta6e baki ya ɗanyi, Shi dai fatan shi Allah yasa kar akawo musu masu ɗan banzan surutu da tsiwa, Sai da yabi kowani gado ya ƙare ma numbobin jikinsu kallo, sun fara daga no16 har izuwa No30, Jinji na kai yai kafin Ya juya ya nufi gadon angel, daga gefe ya zauna, tare da kai hannu daga ƙasa gefen gadon, Ya ruƙo bottle water ɗin daya ajiye, har ya tarba hannu zai ɗibi ruwa ya watsa mata, Yaji motsin buɗe ƙopa, dakatawa ya ɗanyi yana jiran ganin wanene zai shigo, Yayi tsammanin xaiga new prisoners ɗin da za’a kawo musu, amma sai yaga Giants suna shigowa, Ukun farkon masu kawo musu abinci ne, Hannayensu ruƙe da wooden trays, Na bayansu kuma su biyu ne hannayensu ruƙe da wasu jibga jibgan akwatuna kusan guda biyu masu girma, Suna da tayoyi daga ƙasan su, daga bayan masu ruƙe da akwaitin, akwai wani Giant ɗin kuma hannun shi ruƙe da Floor laps Masu girma, daga gani zasu yi haske sosai idan aka kunnasu, Danish dai ya zubawa sarautar Allah ido, sai kallonsu yake yi,
A saman dining Carpet ɗinsu, Giants ɗin suka sauke kayan breakfast ɗin nasu, waɗanda ke a ruƙe da akwatin nan, a tsakiyar ɗakin suka ajiyesu, Saura Giant ɗin dake ɗauke da floor lamps a hannun shi, Daga ƙasa Ya ɗaura su, Atare suka juya hada masu kawo musu abincin suka fuce daga Cikin ɗakin, Fitarsu keda wuya, Danish ya soma Jin takun tafiyar wani kuma again yana saukowa daga saman benan, da sauri yakai idonshi kan me shigowa, Gaba ɗaya Jajayen kayane ajikin mutumin, doguwar riga ce bazai Iya tantance macace ko Namiji ba, gaban rigarsa taurari ne guda uku, hannunshi na dama yana a ruƙe da sanda Golden colour, daga gani tsohone, hatta takalmin shi jajaye ne, a bayanshi wasu Giants ne su Huɗu, kowanne hannayenshi na a ruƙe da kayan amfani na toilet, A tsakiyar ɗakin Mai sanye da jajayen kayan ya tsaya, Ganin haka yasa danish ya miƙe ya ɗan sara mashi, Da hannu yai mishi alamar Jinjina, kafin Ya juya ya kalli giants da suka zo atare, Da hannu yayi musu nuni da sashen shiga toilet ɗinsu, suka nufi Ciki suka shige, kusan Minti talatin Suna aciki, Kafin daga bisani suka shigo cikin ɗakin, Babu kayan da suka zo dasu a hannunsu, sun barsu acikin makewayin nasu,
Tamkar sojoji haka suke ƙame abayan Wannan ɗan tahalikin mai sanye da jajayen kaya,
Danish Yana a tsaye yana binsu da kallon mamaki,
Ware ido yayi ganin mutumin ya ɗaga hannun shi ɗaya ya ɗaura shi saman fuskarshi, nan take ya zame mask ɗin da ya 6oye ainihin fuskarshi, dattijuwace fara tass, launin idanuwanta blue ne, daga gani baturiyace, tana da dogon hanci, gaban kanta hurhurace,
Ƙayataccen murmushi tasakar ma danish tare da cewa”Ƴan uwan naka bacci suke Yi? Muryarshi na ɗan rawa yace”eh” lumshe idanuwanta tayi yayin da take kallonsu tace”gwanin ban sha’awa, tunkafin in fara zama acikin ku har naji kun kwanta mini araina,
aɗan ruɗe danish yake kallonta, kai daga ganinta kasan babu wasa atare da ita, Sam batayi kama da masu Imani ba.
“Zan tafi but I will come back. When they wake up, tell them that their new guardian has come to visit them,” fuskarta asake tayi maganar,
Ya amsa mata da toh, Har ta ɗaga ƙafa zata juya sai kuma ta dan dakata, yayin da idanuwanta suka sauka akan Angel dake kwance saman gadonta, Shu’umin murmushi ne ya bayyana akan fuskarta tsohuwar, A hankali ta furta sunan ta
*Unaisa zaheer tajudeen Our destiny*
Ta ambaci hakan tare da juyawa ta nufi hanyar fita daga Cikin dakin,da sauri Giants ɗin suka Bi bayanta, bayan tafiyarsu danish ya maimaita kalmar ƙarshe da tsohuwar ta furta *Our destiny* kalmar ta tsaya mashi arai, yayi mamakin jinta, shin meyasa ta kalli angel ta ambaci sunanta a amtsayin ƙaddararsu? ta6e lips ɗinshi ya ɗanyi tare da komawa saman gadon angel ya zauna, A tsanake yake kallon fine face ɗinta, soft lips ɗinta sun bushe sosai, robar ruwan dake a hannun shi ya kai saitin bakinsa ya kur6i ruwan tare da watsa mata shi saman fuskarta………………
*❤❤❤PRISONERS❤❤❤*
Ruwan na sauka saman fuskarta, awani irin firgice ta farfaɗo ta zabura zata miƙe, ga6o6in jikinta suka ƙi bata haɗin kai, wani irin raɗaɗin azaba taji a jikin ta, ba arziƙi Ta koma ta kwanta, Cikin shessheƙar ku ka take ambaton sunan daddynta bakomai idanuwanta su ke hango mata ba face waɗannan halittun da ta gani suna cuzgar naman Jikin daddayn, abun ya tsaya mata aranta, daƙyar ma sautin muryar ke fita saboda raunatar da la66anta suka yi, ga maƙoshinta dake abushe ƙamas tana cikin buƙatar ruwan sha, jikinta sai kerma yakeyi, a hankali danish ya ajiye bottle water ɗin daga ƙasa gadon, rumfa ya yi mata da ƙirjinshi yana jiran ta ƙarasa dawowa cikin hayyacinta, yana ganin ta fara ƙoƙarin buɗe idanuwanta, ya yi saurin sanya tafin hannun shi ya toshe mata ƙaramin bakinta, saboda gudun tsiwarta, yasan muddin ta haɗa ido dashi sai ta zazzaga mishi masifa, jin hannun mutun saman fuskarta yasa ta ƙara firgita, da ƙarfi ta buɗe idanuwanta tana faman zazzare su, launin gray ɗinsu ya ciza, eye lashes ɗin sun cukurkuɗe Cikin juna, kaitsaye eye balls ɗinta suka sauka akan fuskar danish, biji biji take iya ganin shi,
Muryarshi na ɗan rawa ya fara yi mata magana
“Angel…..ki natsu ba ki da ƙoshin lafiya” a dabarbarce yayi maganar ganin irin kallon da take watsa mishi, wanda ke nuni da tsantsar ƙiyayyarshi da take ji,
Sassauta muryar shi yai batare da ya zame tafin hannun shi daga saman fuskarta ba, yaci gaba da cewa”Nasan yanzu bani da sauran mutunci a wurin ki, kin gaya mini cewa kin tsane ni, baki son gani na, Angel Ni mai laifi ne a wurinki, duk yadda xanyi maki bayani ba lallai ne ki fahimce ni ba, Amma bazan takura maki ba, idan har da akwai abunda za ki yi mini wanda zaisa ki huce haushinki a kaina, Ni na amince ki yi mini shi, amma kada kice xaki ƙaurace mini, zuciyata zata iya bugawa……..” bai kai ga ƙarasa yin maganar ba, Sakamakon damƙar hannun shi da angel tayi, Cikin fushi ta janye shi daga saman bakinta, batare da ta tanka mishi ba, da yasan yadda take jin tsanar shi a halin yanzu da bai wahalar da kanshi ba wurin neman yafiya agare ta, ji take kamar ta shaƙe wuyanshi ta jijjiga shi ta buga kanshi jikin bango har sai ya sheƙe tukunna ta ƙyale shi, Ba don Allah yasa jikin nata ba isasshen lafiyace dashi ba, da ba abunda zai hana yau ta Illata shi,
Tuni yasha jinin jikinshi, domin kuwa yana ji a jikin shi irin tsanar shi da take Ji, wasu irin zafafan hawaye ne suka cika idanuwan shi, muryar shi tamkar zai fashe da kuka yace”Ki bani dama ta ƙarshe xan gyara kuskure na,” lumshe idanuwanta ta yi, Yayin da maƙoshinta ke motsi tamkar tana haɗiyar wani abu, sam bata jin zata Iya tanka mishi gani take kamar in yaji muryarta zai ji sanyi acikin zuciyarshi, that’s the reason why taƙi yi mishi magana, tafi son Yaji a jikin shi irin halin da ya jefasu, har abada baxata ta6a mantawa da abunda ya faru Jiya ba, duk irin alƙawarin da ta ɗaukar wa batul akan zata taimaki rayuwarta, bazata ta6a bari a cutar da ita ba. Yanzu ya tashi abanza kenan? taya hankalin ta zai kwanta? Bayan batasan awani hali batool take aciki ba, tana can hannun waɗannan azzaluman mutanan da deeja ta bata labarin ta gansu akanta, suna Cutar da rayuwarta, Sai ta dinga imagining ga batul can itama sun danneta tana ta kuka tana buge buge.
Lokaci ɗaya angel ta fashe da kuka mai sautin gaske, Hankalin danish ya tashi matuƙa, duk yabi ya ruɗe, yana so ya lallashe ta, Sai dai yana jin shakkar ta6ata,
“Am sorry angel….ni ne silar komai, pls stop crying it’s hurting my heart, bazan juri ganin ki, cikin wannan Yanayin ba……” Wani irin matsiyacin kallo ta jefa mishi, idanuwanta sunyi jawur gwanin ban tsoro, dama tunda ta farfaɗo daga suman da ta yi fuskarta take a kumbure, cheeks ɗinta sunyi ja, La66anta sunyi luhu luhu ,
Duk da irin kallon da take wurga mishi hakan baisa shi ya dakata da yin maganar shi ba,
“Angel, nima bada son raina ba, Na miƙa batul ba, bana tunanin akwai wanda yakai ni ƙaunarta acikin ku, Batul tamkar jinin dake yawo ajikina take, Na rayu da ita tun ban mallaki hankali ba, mun shaƙu da juna, kusan komai atare da ita muke yi, a duk lokacin da lalurata ta tashi ta rashin son hayaniya, ita ce take jana ajikinta, ta rungume ni har sai taji na samu natsuwa tukunna take saki na, Meyasa ba zaku fahimce ni ba? Ku yi tunani mana, Ni har raina zan iya sadaukarwa akanta….” daƙyar ya ƙarasa magnar tare da kifa kanshi saman katifar gadonta, da alama kuka yake yi,
Gaba ɗayan su kuka suke yi babu mai lallashin wani acikin su, duk wannan budurin da ake yi ƴan uwansu dake ta sharar bacci babu wanda Ya motsa acikinsu, kamar matattu, idan har ba danish Yaje ya tashe su ba, zaiyi wuya su farka da kansu, In ba wani iko na Allah ba, saboda baccin nasu bana Allah da annabi bane, shi kaɗai yasan mai ya yi musu da har suka kama yin shi, duk da yai hakan ne don ya kawar musu da damuwar dake acikin zuciyarsu,
a hankali ya ɗago da kanshi daga saman mattress ɗin, idanuwanshi sunyi jawur dasu, launinsu ya ciza sosai, fuskarshi tayi jawur da ita, Cikin sanyin murya yace”dame xanji? Idan har kuka juya mini baya zan shiga damuwa, Ni bazan hana Ku tsane ni ba, idan ma takama ku buge ni son ranku, but please don’t say that you’ll cutt me off from u, abun zaiyi mini yawa, ga rashin batool ga kuma rashin ƴan uwana,”
Tun da ya soma yin maganar, ta tsagaita da yin kukan idanuwanta na fuskantar ceilling, Haƙiƙa kalaman danish sun kashe mata jiki, sun so suyi tasiri akanta, Sai dai a duk lokacin da ta tuna da irin yadda ya damƙo hannun batul Ya rabata da ita, Yaje ya miƙa ma Giant, Sai ta ji tsanarshi Ta ƙara ninkuwa acikin zuciyarta,
Ɗauke eyes ɗinta tayi daga kallon ceilling da take Yi, ta tsayar dasu akan fuskarshi, bakomai take gani ba acikin idanuwanshi face tsantsar nadama.
Sun ɗauki tsawon lokaci suna kallon juna batare da wani daga Cikin su Ya ƙyafta idanuwan shi ba, Kowa Da abunda zuciyarshi take raya mishi, ganin ta fara motsa la66anta alamar za ta yi magana, sai yaji sanyi acikin ranshi, yayi tsammanin zata yafe mishi ne, amma sai yaji tace”inaso ka yi mini alƙawari…” a ƙagare yake kallonta cike da son jin wani alƙawari ne takeso Ya ɗaukar mata, Don a shirye yake daya bi umarninta.
Muryarta adisashe taci gaba da cewa”idan ka yi mini wannan alƙawarin zanyi farin Ciki, kuma zan tabbatar da cewa Kai ɗin mai ƙaunata ne,” aɗan ruɗe yake kallonta, shi dai fatan shi Kada tasa yayi mata alƙawarin da ba zai Iya cika mata shi ba.
Calmly ya furta”Ki faɗa mini menene kike son in ɗaukar miki alƙawari akanshi? Girgixa kai ta ɗanyi, Still hawaye na bin kuncin tace”Ka fara ɗaukar alƙawarin kafin na faɗa maka akan menene”
Hawaye wasu nabin wasu akan fuskarshi Yace”I can’t, saboda nasan ba alkhairi xaki faɗa mini ba,” Saukowa yai daga saman gadonta, Ya zuƙunna saman gwiwowinsa, a ƙoƙarinsa naya nemi yafiyarta, don shi har ga Allah baison tayi fushi dashi, Yana matuƙar Jin ƙaunar angel acikin zuciyarshi,
“Nasan idan nace ka dawo mini da batool bazaka Iya ba, Haka zalika idan nace Ka faɗa mini wanene kai? Still amsa ɗaya zaka bani shi ne baka sani ba, kaga kuwa baka da amfanin da zaka Iya mini….” bai bari ta karasa maganar ba, yai saurin katse mata hanzarinta da cewa”I know bani da amfani awurinki, amma ki tuna abunda ya faru jiya, may be kin manta, ni ne naje na ceci rayuwarki, na faɗa miki ne badan Ina tunƙaho da hakan ba, sai dan kisan cewa ni ɗin mai ƙaunarki ne kuma ina da amfani awurinki,” awahalce yai maganar, daga shi har ita babu mai ƙoshin lafiya acikinsu, Daƙyar suke magana kamar anyi musu dole, kayan jikinsu ba ƙaramin tsami suke yi ba, hada ƙarnin jininta da yai bleeding jiya,
Fuskarta a yamutse tace”danish, ban damu da duk wani abu da zaka faɗa mini ba, alƙawarin da nake so ka ɗaukar mini shi ne, Ka nesanta kan ka dani! Ras! Yaji gabanshi ya faɗi, tun kafin ma yaji ƙarshen xancen nata, Ya soma girgiza kai alamar bazai Iya ba,
“Bana son ka ƙara kusanto ni, balle ma har kayi tunanin zuwa wurina, koda gigin wasa kada ka kuskura ka bari mu haɗa ido da juna, ya zamar maka dole ka janye jikinka daga nawa, idan har kana son zaman lafiya acikin kurkukun nan…….”
Bawan Allah ya rasa ina zai tsoma ranshi yaji dadi, ya riga dayasan Halinta, tana da wuyar sha’ani, ga kafiya idan ta furta magana zai yi wuya ta canza ta, duk da wani lokacin tana da saurin sauka idan tayi fushi sai dai wannan karan babu sassauci akan fuskarta,
“Har tsawon wani lokaci kike so in janye jikina daga naki”? Idanuwanshi cike tab da kwalla yayi mata maganar,”
“Har zuwa lokacin da za’a dawo da batool, Idan tace ta yafe maka shikenan nima zan yafe maka mu cigaba da yin rayuwar mu kamar yarda muka saba, idan kuma har ba’a dawo da ita ba, hmmmmm…..” ta ambaci hakan saboda tagaza idasa maganar, sai faman taunar la66anta take yi, har sun ɗan ƙara fashewa dama abushe suke.
Ba ta yi tsammanin zai ɗaukar mata alƙawarin ba, sai ji tayi yace”I promised u angel, bazan sake koda kallon ki ba, ballantana har inyi miki magana, Inaso in tabbatar maki da cewa ni mai ƙaunarki ne, Kuma inason farin Cikin ki,…….” dakatawa ya ɗanyi da yin maganar, yana bin fuskarta da kallo, tun yanzu ya fara jin kewarta a tare da shi, wahalallan murmushi ya sakar mata har dimples ɗinshi suka lotsa sosai, da sauri ta kawar da fuskarta gefe ɗaya, saboda wani irin shock da taji, Kyanshi na ƙoƙarin jan hankalinta, idan har taci gaba da kallonshi zata fara danasanin janye jiki dashi,
“Angel zan tafi, Amma kafin nan, ina neman alfarma a wurinki, ina fata zaki yi mini abunda nakeso a ƙaro na karshe, Muryarta ƙasa ƙasa tace”menene”?
“Ki kula mini da kanki, sannan an kawo mana breakfast ɗin mu, kada damuwa ta sanya ki gaza cin abinci nasan kina jin yunwa, ki samu wanda zai taimaka miki acikinsu wurin yin tafiya saboda ƙafafuwanki sun raunata sosai, ba zaki Iya taka su ba, bayan haka Jiya na same ki acikin mawuyacin hali kina ambaton sunan daddynki, zai iya yiyuwa kinyi ƴan gane gane da suka shafi mahaifinki, wanda ba gaskiya bane, inaso ki kwantar da hankalin ki, akan wannan, after that, akwai taimakon da zan Iya yi maki, ta yadda zaki gane cewa, mahaifinki da batool awani hali suke ciki, idan har kin amince mini zan nuna maki,” wani irin kallo angel take binshi dashi na rainin wayau, sai kace wani malamin duba, da alama yana ƙoƙarin yi mata wasa da hankaline,
“Nasan zaiyi wuya ki yarda dani, but pls Ki bani dama”muryarshi ce ta katse mata zancen zucinta da take Yi, shiru ta ɗanyi tana was wasin kalaman shi acikin zuciyarta, kafin ta ɗan yamutsa fuska tace”its ok, ka nuna mini ta wace hanya zan iya gane a wani hali suke Ciki,”
Ba ƙaramin daɗi yaji ba, da sauri ya Juya mata bayan shi tare da cewa”Ki hau in goya ki,” fuskarta a ɗaure tace”Ina zaka kaini”? Ya bata amsa da cewa”Cikin toilet ɗin mu,” ba don taso ba, ta yunƙura daƙyar ta miƙe xaune tana faman cizon la66anta, ta sanya hannayenta biyu ta ruƙoshi, Ta hau saman bayan shi, ya miƙe ya nufi sashen toilet ɗinsu ɗauke da ita a bayan shi, Sam bata lura da sabbin gadajen da aka kawo musu acikin ɗakinsu ba, Saboda ta lumshe idanuwanta, yayin da yake wucewa da ita cikin toilet ɗin, Bayan ya shiga cikin makewayin nasu, wanda keda glass window ɗin nan, Yayi mamakin ganin Kayan amfanin da aka zuba musu sababbi acikin toilet ɗin su, An gyara shi tsaf komai a tsaftace, An ajiye musu trash can mai girma, Daga can sama Jikin bango inda cabinet dinsu Yake, Care product ne a jere tun daga kan hair gel, shower gel, conditioner, komai ma aka tarkata musu hada Toothbrushes da aka ajiye musu acikin holder dinsu, tare da toothpaste, Kuma kowani product yana ɗauke da sunan kurkukun ƙaddara, hakan na nufin ma’aikatan Prison ɗinne suka haɗa su, Ya yi farin Cikin ganin sabbin kayan amfanin da aka sanya musu acikin toilet, ta wani 6angaren kuma sam Bai ji sun kwanta mishi a ranshi ba, tun da ba dawwama zasu yi cikin farin ba,
Jin yaƙi cigaba da tafiya yasa ta ɗan ɗago da kanta daga saman kafaɗar shi, Ta cunkuli fatar cikinshi da hannunta, Har saida ya ɗan ciji la66ansa saboda zafin daya ji, Muryarta a kausasace tace”Idan ba zaka nuna mini ba, ka sauke ni in koma ɗaki,” Muryarshi a sanyaye ya furta mata am sorry, Taja tsoki, tafiya yaci gaba da yi cikin toilet ɗin ya nufi ƙatuwar tukunyar fulawar nan dake a killace Jikin bango, Anan ya ɗan zuƙunna ya sauke Angel, ta xauna a ƙasa tana faman lumshe idanuwanta, ta ko’ina raɗaɗi take ji ajikinta, sai lokacin ta lura da sabbin kayan dake a cikin toilet dinsu, da mamaki akan fuskarta take binsu da kallon ƙurulla, Sai ta dinga gani kamar ba gaskiya idanuwanta suke nuna mata ba,
“Lokacin da kuna bacci, Giants suka shigo da su, hada new metal beds da boxes guda biyu, ina expecting din sabbin prisoners xa’a kawo mana” Danish ne ya kora mata bayani, Ganin yadda take bin ko’ina na toilet din da kallo yasan dole ta buƙaci jin daga ina aka same su,
Ko kaɗan bata yi farin Ciki da ganinsu ba, Ita fa a halin yanzu komai na kurkukun ta tsane shi, abu ɗaya ne idan aka daina Yi musu xata so shi harma ta haƙura ta rungumi ƙaddararta, su cigaba da yin rayuwarsu Har Illah masha Allahu, shine a daina ɗaukar ƴan uwansu ana lalata rayuwarsu, sai dai tasan abune mai wuya, wannan dalilin ne ma yasa zata cigaba da neman hanyar da zata ku6utar dasu, domin kuwa babu fashi, Shiga Cikin kurkuku yanzu ta fara, Babu gudu babu ja da baya! ba’a halicce ta don ta zama raguwa ba, ita ɗin Jinin jarumai ce, masu dakakkiyar zuciya, waɗanda suka Yi imani da Allah batare da was wasi ba! duk da abunda ya faru da ita jiya, hakan baisa zuciyarta ta karaya ba, Sai ma taji kamar ana ƙara encouraging ɗinta akan taci gaba da bibiyarsu, a mutu ko ae rai, Kuma taci alwashin daga rana irin ta yau bazata ƙara sakin baki tayi bacci ba, Zata dinga raba dare biyu, kodan ta dinga kai kukanta wurin Allah, akan halin da suke aciki da kuma ƴar uwarsu batool!……..” Ya jima yana kallonta ganin yadda numfashinta ke fita, ta ciccije la66anta, bakomai yajawo hakan ba face zancen zucin da take Yi, daga cikin zuciyarta,
“Angel!!” Firgigit tayi Jin muryarshi acikin kunnuwanta, wani irin kallo ta jefa mishi, da sauri yace”Ki ɗan jira ni, Yanzu xan dawo” Bata amsa mishi ba, dama bai sanya ran zata tanka mishi ba, don ya lura yau mulki take ji.
Miƙewa Yayi da sauri Ya juya ya fuce daga Cikin toilet ɗin, badajimawa ba sai gashi Ya shigo ciki hannun shi ruƙe da robar ruwan daya yayyafa mata afuskarta ɗazu Cikin ɗaki, Bin shi da kallo tayi har ya ƙarasa gaban fanfo. ya zuƙunna Ya kunna shi, ruwa ya shiga kwararowa ya tarba robar, saida taci ka tukunna ya miƙe da azama ya dawo inda take zaune jikin bango, Ya zuƙunna agaban tukunyar fulawar,
ya ɗan saci kallonta ta wutsiyar idanuwanshi, harara yaga tana jefa mishi, ƙayataccen murmushi ya saki tare da cewa”Idanuwanki basu gajiya da yin harara”? Murguɗa mashi ƙaramin bakinta ta yi, tana faman hura hanci tace
“Bai shafe ka ba” Yace “its ok am sorry, abunda zan nuna maki ayanzu, sharaɗin shine, Koda ace zuciyarki ta ƙaryata hakan to kada ki amince just ki yarda kawai da duk wani abu da zan faɗi batare da kokwanto ba,” bata amsa mishi ba, sai ma ta juya mishi ƙeya,
Bai damu ba, yaci gaba da cewa”yanzu inaso ki rufe idanuwanki”, rai a6ace tace”saboda me xan rufe idanuwana”? Yatsina fuska yayi don tafara hayaƙa shi da tsiwarta,
“Kiyi kawai abunda nace miki, asannu zaki fahimce ni” Sai da taja guntun tsoki mai sauti, kafin ta runtse idanuwa nta, tana faman murga baki,
Bai san ya akai ya tsinci kanshi da kallon kyakkyawar fuskarta ba, sai yaga tafi yi mishi kyau a haka, duk da raunin dake akan fuskarta, sai ma suka ƙara mata kyau especially heart shaped lips ɗinta da suke abushe sun faffashe, kamar ta shafa musu jan baki pink, bakomai ya ƙara ƙawata fuskarta ba face gashin jagirarta masu tsayi dark brown dasu.
Jin shiru Danish baice ta buɗe idanuwanta ba, yasa ta harzuƙa ta yunƙuro zata wage baki ta zazzaga mishi masifa, Yai saurin cewa”Saura kaɗan” ajiyar zuciya ta ɗan sauke Cikin ƙagara da son jin me zai ce next,
“Ki buɗe idanuwanki a hankali,” mutsu mutsu ta soma yi cikin wani irin yanayi ta ɗan waresu ta ƙara buɗesu kafin ta zarosu tana ƙarewa tukunyar fulawar kallo, abun mamaki abun al’ajabi, yauƙanannun fulawowin dake acikinta waɗanda sun jima da bushewa duk sun yagalgale sun lafe cikin ƙasar dake acikinta, ɗaya daga Cikinsu tagani ta miƙe ta bubbuɗe ganyayyakin jikinta sun wawware tayi matuƙar ɗaukar hankalinta, musamman launin Jikinta Ja da ya ciza, tsabar mamaki ya hana ta rufe bakinta, Idan ta kalli furan sai kuma ta kalli fuskar Danish,
Har dai tagaza jurewa tace”taya akai kayi hakan? Kamar a mafarki,”
“Ba shi yakamata ki tambayeni ba, wannan furen da kika gani ki ɗauka cewa ran mutun ne mai numfashi a jikin shi ” Ya ƙarasa maganar tare dakai hannu ya shafa ganyen shi tare da cewa”Batool ɗinki ce, Our lovely sister, idan kika kalli furan da kyau, zaki ga yana da cikakkiyar lafiya ajikinshi, Launin shi ya ciza, hakan na nufin batul aduk inda take a yanzu tana acikin ƙoshin lafiya, Idan kuma ki gaka ganyen jikin furan Yana fitar da ruwa kamar zufa batare da an yayyafa mashi ruwa ba, that mean batool kuka take yi tana kewan ƴan uwanta, idan kuma ganyen ya kwanta jikin ƙasar dake acikin fulawar, to batool bacci take yi……..” tunda ya soma kora bata jawabi, take kallonshi babu wasa a fuskarshi, Yadda kasan irin malamin duban nan, sai da yakai ƙarshen maganarshi tukunna tace”to idan furan ya mutu fa me hakan yake nufi? Maimakon ya bata amsa sai ya sadda kanshi ƙasa, tuni ta gane me hakan ke nufi wato mamallakin furan ya mutu kenan,
“Baka amsa mini tambayata ba,” ɗagowa yai da kanshi ya ɗaura idanuwanshi akan fuskarta yace”idan ganyen dake ajikin furan Ya bushe ƙamas Ya tsotse ko ya fiffige, Hakan yana nufin mamallakinsa yana acikin mawuyacin hali, Idan kuma ganyen furan ya mutu, ko ansa mishi ruwa bazai tashi ba, ma’anar hakan mamallakinsa ya mutu baya araye” duk da bata gasgata maganarshi ba, amma sai da taji gabanta ya faɗi ras, muryarta na ɗan rawa tace”Shi…shi fa daddyna? Ina nashi furan yake? Taya za’ae in iya gane cewa yana a raye ko ya mutu?” aruɗe take jera mashi tambayoyin,
Kwantar mata da hankali yayi, “Ki natsu yanzu xan duba maki na daddyn ki amma kafin nan Kiyi mini alƙawarin cewa komai ki ka gani ba zaki yi kuka ba, idan kuma muka yi nasarar ganin furan daddynki Cikin ƙoshin lafiya, zaki bani abinci abaki. Nima in baki, a karo na ƙarshe kafin mu ƙauracewa juna,”
da yake a ƙagare take da son gani, da sauri tace mashi eh ta amince, yace to ta rufe idanuwanta, Bayan ta rufe su, Na ɗan wani lokaci, Yace ta buɗesu a hankali, Kamar wata sakarya haka take bin umarninshi, tunkafin ta ƙarasa buɗe idanuwanta ta soma hango fure Launin Kore, a gaggauce ta zare eyes ɗinta akan furan har zata fara Farin ciki sai kuma ta lura da naƙasar dake a ƙasan furen ya ɗan lanƙwashe alamar ba lafiya atattare da shi.
Wasu irin zafafan hawayene suka wanke fuskarta, Har wani zazza6i taji ajikinta, muryarta adabarbarce take faɗin” Danish Ya mutu ko? Naga ganyen kamar ya karye, Dan Allah ka faɗa mini, zuciyata zata Iya bugawa….” tsananin tausayinta ne ya kama shi ganin yadda tabi ta ruɗe, bakomai yake tunani ba face Iyayen shi, Shi da bai rayu dasu ba, kuma ba shi da tabbacin Suna araye ko sun mutu, shin dagaske sune suka sadaukar dashi? Anya kuwa shima yana da iyaye kamar kowa? A lokacin baya kafin zuwan angel bai ta6a tunanin wasu iyaye ba, gani suke Yi kamar tsohuwa itace komai na rayuwarsu, zuwan angel ne yasa suka fara tunanin suma ina iyayen su suke? Idan tana basu labarin irin ƙaunar da daddynta yake yi mata sai suji inama ace suma sunyi rayuwa da nasu Iyayen………”
Sautin kukan angel daya ƙaru ne yasa shi Barin yin zancen zucin nashi ya ɗago ya kalleta, ta wage baki sai kuka take Yi, baisan time daya saki murmushi ba, bai ta6a ganin ƙuruciyarta ba sai yau, da ta gasgata abunda shi kanshi baida tabbaci akanshi, kawai yana nuna mata ne don ya samu ya kwantar mata da hankalinta,
Ahankali ya sanya hannayenshi biyu Ya tallabo fuskarta, Yana ƙare mata kallo, hawaye ta ko’ina, Cikin sanyin murya yace”kin manta bayanin da nayi maki? Idan har furan bai bushe ba ko ya fiffige ya mutu, to mamallakinsa yana araye,” Cikin shessheƙar kuka tace”Am…amma ae ya naƙasa, kai ba ka ga Ciwo a jikin iccen shi ba” Da lumsassun idanuwanshi ya ɗan kalli furan kafin yace”na gani, sai dai ba hakan yana nufin mamallakinsa ya mutu ba, sai dai ko karyewa ƙafarshi tayi sakamakon wani rauni daya ji, ko kuma wani ciwonne na daban ya same shi a ƙafar shi, kinji ma’anar raunin dake ajikin furen” hannu tasa tana share hawayenta hankalinta har ya ɗan kwanta,
“Kuma Allah idan har na gane cewa ƙarya kake Yi mini, to ka sani har bada babu ni babu kai, kuma kullum xan dinga zuwa ina duba furennin ina basu ruwa akai akai. Kodan kada su mutu, hakan kuma ba yana nufin na yarda da maganganun ka bane kawai dai zanyi amfani dasu ne” ƙiris ya rage ya saki dariya, jin wautarta, Ta wani 6angaren kuma yaji daɗi sosai, koba komai yasanyata farin Ciki, ya kuma bata aikin yi, duk da shima yana jin fargabar ranar da zata gane cewa ƙarya yake yi mata,
Taso ta tambaye shi furan aunty aneelerh kodan tasan awani hali take aciki, amma sai ta fasa don ta gaji da zama Acikin toilet ɗin, Gashi tana buƙatar Yin wanka sai dai tasan bazata Iya ba saboda ga6o6in jikinta dake yi mata ciwo,
“Muje mu ci abinci, Ko xaki yi wanka in taimaka maki”? Sakin baki tayi tana kallon shi jin abunda yace,
“Yanzu idan nace ka taimaka min inyi wanka? Kuma saika amince”? Fuskarta a ɗaure tayi mishi maganar, baisan sadda ya furta”ae naga komai jiya so ba wani abu bane, nima ae kin ta6a gani na naked, bai kamata ki damu ba, har wankan ma sai mu yi atare,”
ras taji gabanta Ya faɗi, Ta zazzare gray eyes dinta tana kallonshi, Da sauri ya sanya tafin hannayenshi biyu ya toshe kunnuwanshi, saboda gudun tsiwar da zatayi mashi, shi kanshi baisan Ya furta maganar ba, su6ul da baka yai,
sosai ta runtse idanuwanta, tana ƙoƙarin tariyo abunda ya faru jiya, saboda lokacin data dura tagar nan, batasan cewa Ya zame wandon jikinta ba, Ita dai kawai tasan ta dura ta miƙi hanya, sai yanzu da ya yi wannan maganar ya tuna mata da komai, aikuwa ta daddage ta fasa wata irin gigitacciyar ƙara, Jikinshi ya kama rawa, saboda sautin daya fita hatta masu bacci na Cikin ɗaki saida suka farka, Kusan atare suka yaye bargunansu, agaggauce suka dudduro daga saman gadajensu, da gudun gaske suka nufi sashen toilets dinsu hada masu Yin tuntu6e garin sauri, Haris ne agaba su Hanna na abiye dashi, kamar wasu sabbin mahaukata haka suka faɗo Cikin toilet ɗin, Gaba ɗayansu ne suka shugo ciki, Sai faman haki suke yi, a matuƙar ruɗe suke kallon angel da danish, ta runtse idanuwanta jikinta har wani jijjiga yake yi kamar mai iskokai, muryarsu da alamun baccin bai ishe su ba, suka shiga tambayarsu lafiya, azeeza tuni ta nufi angel ita da parveen suka zukunna suna shafa fuskarta tare da tambayarta lafiya meya faru da ita? Meyasa take kuka, Hanna dasu rubina suka karasa suma suka zuƙunna agabanta, Mazan da suka rage a tsaye sai aika mishi da harara suke Yi, gani suke kamar wani mugun abun yayi mata, dama tun Juya suke zargin shine yayi mata bugun tsiya da har ta raunata,
Haris yana huci yace”wato saboda kaga muna bacci shine ka ɗaukota daga saman gadonta ka kawo ta cikin toilet ka naɗe hannun rigarka ka nannausheta saboda bugun da ka yi mata jiya bai ishe ka ba, Wai danish me kake so ka zama ne? Slowly Ya xame hands dinshi daga saman ears ɗin shi daya toshe, hawaye ne kwance acikin fararen idanuwanshi, Tsawar angel tayi matuƙar ta6a kanshi ta tsokano mishi da lalurarshi, shiyasa jikinshi ya kama kakarwa,
Javed yace”Ae bazai ta6a buɗe baki ya bamu amsa ba, mugu kawai, yanzu xamu ji komai abakinta tunda ta farfaɗo, serious idan har tace kaine ka dake ta, zaka ji a jikinka ne,”
Mubeen dai bai ce komai ba, Ya jingina bayanshi Jikin bango yana kallonsu, Gaba ɗayansu babu wanda Ya lura da sabbin kayan da aka sanya musu acikin toilet ɗinsu, saboda hankalin su ba a kwance yake ba,
Su Deeja sai faman lallashinta suke Yi, Ganin yadda take ta kuka, Tana faɗin Wlh ka cuce ni, Na tsane ka Danish, ashe kai ɗan iska ne ban sani ba, Allah ya isa bazan ta6a yafe maka ba, tun da ka gane min budurci na…..” muryarta ashaƙe ta ƙarasa maganar, ita kanta batasan menene ma’anar budurci ba, tadai san kalmar acikin kanta, azeeza ta janyota ajikinta ta rungumeta tare da zagayo da hannayenta saman bayanta, tana ɗan bubbugashi, Hankalinsu Haris yai matukar tashi jin abunda tace har suna haɗa baki wurin maimaita kalmar budurci, basu ta6a ji ba sai abakinta, Amma sai suka ɗauka cewa wurin bugunta ne Ya ta6a wani organ na jikinta, Shi take kira da budurci, nan fa suka harzuƙu, Naufal Ya shaƙo wuyan rigar Danish Ya ɗago dashi Yana huci yace”ka faɗa mana uban me kayi mata? Taya akai ka gane mata budurcinta? Saboda baƙin hali irin naka”! bawan Allah ya rasa ya zaiyi, hayaniyar su ba ƙaramin tafasa zuciyarshi take yi ba, Ga wani irin zafi da jikinshi ya ɗauka, haris ne ya lura da yadda yake lumshe idanuwanshi, Da sauri ya ƙarasa gabansu Ya ruƙo hannun naufal ya janye shi daga jikinshi, wani irin jiri ne ya kwashi danish Ya tafi xai faɗi ƙasa sai dai bai kaiga ƙarasawa ba, haris Ya tallaboshi da hannu biyu, ya ruƙo shi zuwa saman jikinshi, Ya rungume shi sosai, yana ambaton sunanshi, duk da ƙarnin Jinin da ke a jikinshi hakan baisa haris Ya guji ta6a shi ba, kallonsu mubben yai tare da cewa”Pls ku taimaka mini, mu kai shi daki” Turo baki Javed, Naufal kuma ya juya mishi ƙeya, mubeen Ya ɗaga kai ya kalli ceilling ɗin toilet, alamar bazasu ta6a shi ba,
“Ka bani mamaki haris, Kafi kowa nuna 6acin rai akan abunda Danish yayi mana, amma sai gashi yanzu nema ka ke yi ka taimake shi” Rai a6ace naufal yai maganar,
Fuskar haris ɗauke da matsananciyar damuwa yace”bazan iya jure ganin shi acikin mawuyacin hali ba, Shi ɗan uwanmu ne, tabbas yayi mana kuskure amma abunda nake so ku fahimta, koda ace danish Bai miƙa ma giant batool ba, to xasu ɗaukota ne da kansu, don su tafi da ita, baida za6ine,”
Sunyi mamakin canzawar da haris yai lokaci ɗaya, duk dan sunsan irin ƙaunar dake a tsakanin shi da Danish, dole yaji tausayin shi a halin dayake ciki,
Ganin sunƙi taimaka shi yasa shi yin fushi, Yaja danish shi kaɗai ya shiga dashi cikin ɗaki ya kwantar dashi saman gadon shi, idonshi biyu sai dai jikin nashi ne ba ƙwari,
Shigowa cikin ɗakin Hanna da deeja su kayi angel tana a goye bayan hannah, Ta rurruƙeta da hannu biyu. A saman gadonta hanna ta kwantar da ita, sai faman sauke ajiyar zuciya take yi, a can ƙasan zuciyarta wani irin ƙunci ne ya cunkushe mata, danish yaga tsiraicinta, Babu sauran kwanciyar hankali, yanzu shikenan zai dinga ganinta tsirara koda ace da kaya ajikinta, tuna wannan yasa ta ƙara fashewa da wani sabon kukan, gaba ɗaya hankalinsu Ya dawo kanta, baiwar Allah bakinta duk ciwo amma ahaka take riskar kuka,
“Dan Allah angel ki daina kuka, Kiyi haƙuri, Ki faɗa mana me danish yayi maki? Hibbe ce tai mata magana, duk sun shiga damuwa, Azeeza tace”ina matuƙar jin tausayin angel, taji jiki ba kaɗan ba, danish bai kyauta mana ba Allah,” Kowa yana tofa albarkacin bakinsa, danish dai duk yana sauraronsu ya lumshe idanuwanshi yayin da hannayen shi biyu ya rungume pillow dasu,
sai da Angel ta gama shan kukanta mai isarta, tukunna tace musu ita fa bashi bane Yayi silar halin da tashiga ba, hasalima taimakon ta yayi a jiyan nan, a dole ta ƙirƙiro ƙarya ta fada musu cewa, Ta fita hayyacinta ne Saboda ɗauke batool da akayi shine ta fada toilet ta ɗauki bokitin nan na ƙarfe ta bubbuge jikinta dashi, da ta galabaita shine ta faɗi ta sume cikin toilet ɗin, ta faɗa musu hakan ne badan tana so ta kare shi ba, face don ta kwantar musu da hankalinsu,
Gaba ɗaya sunyi amanna da abunda ta fada musu, har suka ɗanyi danasanin maganganun da suka gaya mishi duk da haushin sa da suke ji, Duk wannan abunda dake faruwa babu wanda ya ankara da sabbin gadajen da aka sanya musu acikin dakinsu, Har sai da suka fara Jin yunwa, Parveen tana hamma tare da kai hannu ta shafa cikinta ta soma ambaton Yunwa take ji,
Tana rufe baki Danish yace “An kawo mana breakfast tun ɗazu da safe, time da kuna bacci,” batare daya buɗe idanuwanshi ba, yayi maganar,
Atare suka Juya baya don suka ga In dagaske ne an kawo musu abinci, duk da sun cewa danish baya ƙarya…..
*❤❤❤PRISONERS❤❤❤*
Kaitsaye idanuwansu suka sauka akan sabbin gadajen da aka jera a cikin ɗakin nasu, gaba ɗaya suka zazzare idanuwansu saboda tsabar mamaki duk suka bi suka ruɗe, Sun saki baki suna kallon Ikon Allah saboda ba su yi tsammanin zasu yi arba da wani baƙon abu a cikin ɗakin su ba, da mamaki akan fuskar parveen Tace”Kuna ganin abunda nake gani kuwa? ko dai idanuwana ne suke nuna min ba dai dai ba”? Azeeza tace”Ae duk mun gani sabbin gadaje ne har kusan goma sha biyar tare da Akwatuna Biyu, ko a ina aka same su”? Danish ne ya basu amsa da cewa Ɗazu da safe kuna bacci giants suka kawo su, akwai ma kayan amfani da aka sanya mana a toilets” deeja tace”hakan na nufin zamu kar6i baƙuncin wasu prisoners ɗin”? Tai tambayar fuskarta babu walwala, domin kuwa ba abun farin ciki bane agare su, da duk wani mai hankali ba zai so wani bawa ya ɗanɗani irin rayuwar ƙuncin da suke yi ba.
“Innalallahi wa’inna ilaihirraji’un! Ni dai har ga Allah bana farin ciki da zuwan waɗannan Sabbin prisoners ɗin, Saboda bana so suma su ɗanɗani irin rayuwar da muke Yi acikin kurkukun nan” Deeja ce tai maganar, Haris yace”ni kaina bana son mu ƙara yawa, muna fama da kanmu xa’a ƙaro mana wani ciwon kan” hibba tace” ni babban baƙin ciki na, Mu da muke fatan wata rana mubar kurkukun nan, sai gashi ana ƙoƙarin kawo mana wasu har mutum goma sha biyar zamu ƙara cunkushewa, tashin hankali kuma zai ƙaru” hannah tace mu je mu duba gadajen ni sunyi mini kyau, Dama mu ma a canza mana sababbin,” wani kallon harara deeja tai mata “Wato ke ta gado kike yi, to Allah yasa acanza miki gadon kiyi ta zama cikin prison ɗin, mu kuma Allah ya bamu sa’ar fita daga cikinsa” hanna tana ƴar dariya tace ba amin ba, Aniyarki tabi ki,”
Agaban gadajen suka tsaitsaya cirko cirko suna ƙare musu kallo, Sabbi gal dasu sunyi matuƙar yin kyau, Azeeza da parveen hada ƙoƙarin hawa saman wasu daga Cikinsu suna faɗin Bari su ɗana kafin baƙi su ƙaraso, azeeza tace ita yau ma asaman sabon gado xata kwana, suma sauran su ka ce duk anan zasu kwana su sha lagwada,
sai da suka gama kallon gadajen kafin suka koma kan akwatunan suna kallonsu tare da Floor laps ɗin da aka ajiye musu, ba ƙaramin daɗi suka ji ba, dama fitilun dake gare su sunyi kaɗan, Idan dare yayi sai dai mutun yai ta yawo da fitila zuwa toilet, amma yanzu sun yanke shawarar zasu ɗauki ƙananun fitilun guda uku, su ajiye su a kowani toilet, don su sawwaƙawa kansu.
a cikinsu an rasa wanda zai buɗe boxes ɗin nan, duk sunyi tsammanin Ba mallakin su bane, na sabbin prisoners ne da za’a kawo shiyasa basu ta6a su ba, saima suka kawar dasu zuwa bakin gadajen, bayan sun gama da ɗaki, eve tace”su je su duba toilets suga sabbin kayan da aka sanya musu, Parveen ta bubbuga ƙafa tare da cewa”Mu fara Cin abinci tukunna idan ku ba ku jin yunwa ni ina ji” sai da ta yi maganar suka tuna da cikinsu, hankalinsu gaba ɗaya yana akan Kayan da aka kawo musu,
Atare suka nufi dining carpet ɗinsu suka zazzauna, Kowa ya natsu zasu fara Cin abinci,
Duk wannan abun dake faruwa angel da danish suna kishingiɗe saman gadajensu, sun Juyawa juna baya babu mai fuskantar wani, kowa da abunda yake saƙawa acikin zuciyarshi, ita dai damuwarta batool ɗinta, ko awani hali take ciki? Fatanta Allah yasa maganar da danish ya faɗa mata akan furen nan ta zama gaskiya,
Bayan su parveeen sun kammala Cin abinci. Sauran da suka rage ma angel da danish, Haris yace su je su ɗauko kwandon batool a kwashe musu nasu aciki, Nan fa duk jikinsu yae sanyi tunawa da batool ɗinsu, duk da dama tana acikin ransu ba yadda za su yi ne, tsakaninsu da ita addu’a ce kawai.
Hanna ce taje ta ɗauko kwandon batool dake a kusa da gadon danish Kifin da suka ajiye mishi tun jiya duk ya bushe jikinshi, hada ƴar rabin gwandar da baici ba, nuna musu kwandon tai tare da cewa”Fried fish din ma ya lalace bari naje na zubar dashi, in wanko basket din sai asanya musu abincin aciki…..” tunkan ta ƙarasa maganar parveen tai wuf ta sanya hannu ta kar6e kwandon tana faɗin”Inji wa yace maki ya lalace, bani nan ki gani, yanzu nan zan sanya shi a hanya…” Murmushi suka saki gaba ɗayan su yayin da suke kallonta, A ƙasa ta zuƙunna ta ajiye kwandon tare da kai hannu Ciki tana tatta6a Jikin kifin, azeeza tace”amma parveen baki da hankali, tun jiya fa yake a buɗe cututtuka duk sun hau jikin shi a haka zaki ce? Salon Cikin ki ya 6aci,” Harara parveen ta watsa mata tare da cewa”Bai shafe ki ba ae cikina ne ba na ki ba” duk yadda suka so su hanata Cin fried fish din nan taƙi ji, tai kunnan uwar shegu dasu, Zama tayi na musamman tacinye shi tass bayan ta gama da kanta taje toilet ta wanko kwandon tass ta shigo dashi Cikin ɗakin ta miƙa ma Hanna kwandon, tasa hannu ta kar6a ta zuƙunna gaban farantin da niyar ta ɗibar musu wanda suka rage musu, Muryar Angel ta dakatar da ita,
“Kada ki haɗa mini abinci dashi, Ki ware mini nawa daban” idanuwanta arufe tai maganar, batare data motsa daga kwancen da take asaman gadonta ba, Haris yace ki ɗibar mata nata ki je ki taimaka mata taci, Ni kuma zan kaima Danish nashi, ta amsa mashi da toh,
Kafin marece yayi saida suka shiga cikin kowani toilet suka dudduba sabbin kayan da aka sanya musu, bakomai yafi burgesu ba face Hair gel kodan sabo da gashin kansu, sun samu na gyara shi, basu fara amfani dasu aranar ba, saboda sunfi so sai angel ta samu sauƙi ta taimaka masu wurin gyarawa.
A daren ranar Saman Sababbin gadajen nan kowannansu ya kwanta, in ka cire mutun biyun nan, Angel da kuma danish suna asaman gadajen su, jiki duk ba daɗi da ga ita har shi, ko wanka sun kasa tashi su yi, room ɗinsu yayi wani irin haske tamkar da rana saboda sabbin fitilun nan da suka kunna hasken su ya gauraye ko’ina gwanin ban sha’awa, Cikin nishaɗi suke ta wasa da pillows, Idan wannan ya jefa ma wannan sai shima yaɗauko pillow Ya jefa ma na kusa dashi, yadda kasan basu da wata damuwa bayin Allah, Angel tana jiyo hayaniyar su suna yin fira bayan sun gama wasa da pillown deeja tace”Nifa gani nake kamar zamu dawwama acikin kurkukun nan, tunda ga wasu ma za’a ƙaro mana” Parveen tace”ai kwara su zo suma su ɗanɗani irin zaman da muke yi, su ji in akwai daɗi,” Azeeza tace muguwa parveen yanzu har wasu kike yi ma fatan suyi irin rayuwar da muke yi”? Parveen tana dariya tace”Nifa na faɗi hakanne kodan mu samu a ƙyale mu adaina ɗaukarmu mu tsaffin prisoners, su kuma sabbin sai acigaba da ɗaukarsu, Kunga mun hutu ko ba haka ba,’
Murmushi angel ta ɗan saki, yayin da idanuwanta suke fuskantar ceilling, ta ɗan ɗaga murya tana faɗin”parveen maganar da ki kayi sam ba ta yi mini daɗi ba bai kamata kina yi musu mummunan fata ba, tun kafin zuwansu ma, Ni tausayinsu ma nake ji, su da basu san komai ba, wlh ko maƙiyina bana yi mishi fatan shiga wannan kurkukun ƙaddarar, ballanta su da za’a kawo mana, musamman in ya kasance daga waje za’a kawo su, Ba ƴan asalin cikin kurkukun bane”
jin wannan magnar ta angel yasa parveen tace”patient Ashe baki yi bacci ba, da ace nasan idonki biyu da ban furtata ba,” dariya su kayi gaba ɗayansu, Angel tace”Oh, wato ni sarkin yin wa’azi ko? Kiji tsoron Allah parveen, Nidai komai na faɗi inayi ne don in taimaka muku wurin gyara rayuwarku,” hanna tace”ai kina ƙoƙari kuma muna jin dadi sosai, muna fatan Allah yabarmu tare dake har bada, har mu shiga aljanna,” murmushi angel ta ɗan saki, tare da yunƙurawa ta miƙe zaune saman gadonta ta jingina bayanta jikin bango, ta wutsiyar idonta take satar kallon danish, Ya rungume pillow sai bacci yake yi, aranta tace shi ko tsamin jikinshi baiji, ” can kuma ta ta6e baki tana faɗin to ni meye ruwana dashi, ” ta ambaci hakan tare da jan tsoki, Muryar Javed ta jiyo daga inda take fuskantarsu Yana ta yi musu faɗa akan su yi musu shiru sun hanasu runtsawa, su kuma sun dage sai zuba suke yi kamar kanyar da bata da daɗi,
kasa kunne ta yi tana sauraron firar da suke Yi, sai taji akan gidan daddynta su ke magana, lamarin ya ɗan bata mamaki, jin parveen tana faɗin ai wlh idan suka gudu daga Cikin kurkukun suka koma gidansu angel ita acikin kitchen zata dinga kwana, ko dan ta dinga dafa abunda take so”
Sakin baki angel tai tana sauraron ikon Allah, aranta tace wato ita parveen burinta na duniya shine abinci, taci abinci bata gajiya, mai iya rainonta sai manomi, amma wannan in baka da ƙarfin jari saita naƙasa ka,” bata kammala zancen zucin nata ba, ta jiyo muryar azeeza tana faɗin”Ni dai ba ruwana da wani abinci, Idan Allah yasa muka bar kurkukun nan muka koma gidansu angel, A ɗakin daddynta zan dinga kwanta, nima ya rungumeni kamar yadda yake yi ma angel suna kwana tare,” Haris yace”Sannu uwar son banza, menene alaƙarki dashi da har xaki kwana a ɗakinshi Ya rungume ki,” zum6ura baki tae ashagwa6e ta bashi amsa da cewa”Ae ta faɗa mana cewa, Daddynta yana son ƴa’ƴa, Kaga kenan muma zamu zama kamar angel awurinshi” naufal yace”Kuna yaudarar kan ku dayawa, ku ɗan sarara mana, kada wata rana zuciyarku ta karaya, a garin sanyawa rai abunda bazai ta6a yiyuwa ba,”
Kafin wani ya kuma cewa wani abu angel tace”Inji wa ya faɗa maka cewa bazai ta6a yiwuwa ba? Ƙarancin imanin ku shine zaisa mu dawwama acikin kurkukun nan, bai kamata kuna sage musu gwiwa ba, Idan Allah yaso a yau ɗin nan zamu iya barin kurkukun nan wannan ba abun mamaki bane, amma nasan zaiyi wuya ku yarda da maganata har sai ranar da Allah yasa muka ku6uta inda rai da lafiya, tukunna zaku tuna da wannan maganar dana faɗa maku!!!”
Haris yace”kada ki damu, Ni zan tuna maki, wannan ba wani abu bane” yana magana yana dariya kamar wani zautacce, Ya raina maganarta, ba ƙaramin haushi taji ba, tadai yi shiru ne ta ƙyale shi saboda sanin irin jahilcin dake ɗawainiya dashi.
Lokacin da bacci yai awon gaba dasu ita kaɗai ta rage bata kwanta ba, kamar yadda tai alƙawarin xata dinga raba dare biyu domin ta samu damar yin addu’o’inta, tana Cikin yin addu’oin hawaye ta ko’ina akan fuskarta, danish ya farka ya ɗan miƙe xaune saman gadonshi yana kallonta, ganin tana ƙoƙarin juyowa ta kalli inda yake yasa shi yin saurin kawar da kanshi gefe, gudun kada ya sa6a alƙawarin daya ɗaukar mata, saukowa yai daga saman bed din shi Ya janyo bargonshi Ya nufi Cikin toilet dashi, Tana ta bin bayan shi da kallo Cike da mamakin me zai yi a irin wannan lokacin, tsawon mintuna sai gashi ya shigo ɗakin chest ɗin shi ɗaure da bargon, Alamar ya wanke uniform ɗin, Sun ishe shi da tsami, Sai lokacin ta tuna da yadda jikinta yake, ta dage tana ta yin addu’o’i batare data tsarkake shi ba, Yanke shawarar zuwa toilet din tayi don ta wanke kayanta ta samu tayi wanka, tana ƙoƙarin saukowa daga saman gadon ƙasusuwan jikinta suka rurruƙe har wani sauti suke badawa ƙas! ƙaƙas!! wani irin raɗaɗi taji ajikinta, ta ɗan cije la66anta tana faman ambaton wash Allah na, duk akan kunnan danish dake zaune saman gadonshi, Ya lumshe idanuwanshi, Tun da yai wanka sai yaji daɗin jikinshi, wata irin ni’ima ta saukar mishi, yaso ace suna shiri da juna daya taimaka mata wurin yin tafiya don ya fahimci cewa so take itama ta yi wankan,
Ba yadda ta iya dole ta haƙura da yin wankan tayi zamanta tsakiyar gadon, a haka baccin yai awon gaba dasu,
A kwana atashi ba wuya wurin Allah, Yau tsawon Sati biyu kenan ba’a dawo musu da batool ba, babu ita babu alamarta, Kullum sai sun sanya ran zasu ga an shigo da ita amma sai suji shiru, hatta sababbin prisoners da suke tsammanin za’a kawo musu har yau ba azo dasu ba, rashin dawo musu da batool yafi komai ɗaga musu da hankali, ganin sun sanya damuwa sosai yasa angel ta faɗa musu maganar da suka ta6a yi ita da batool, a inda take ce mata, tana so su haɗa hannu wurin sama ma junan su farin Ciki koda kuwa babu wani acikinsu, wannan maganar tayi matuƙar karya musu zuciya, domin kuwa ranar da angel ta faɗa musu ita, kusan kwana su ka yi a zaune suna jimamin rashin ta, sunyi matuƙar yin kewar ƴan uwarsu fiye da tunanin mai tunani, a ƙarshe da suka rasa abunyi sai suka koma suna biye ma angel, atare da ita suka zuwa toilet wurin tukunyar fulawar nan don suga awani hali batool take aciki, tun da ta basu labarin Abunda danish ya faɗa mata na cewa batool ɗinsu ce a jikin Jan furen nan shi kuma koren Na daddynta ne, abun ka ga masu ƙarancin hankali ga kuma ƙuruciyar dake ɗawainiya dasu duk sai suka yarda da zancen danish, a rana sau uku suke zuwa wurin furannin nan domin su basu ruwa, da safe da rana da daddare, wani lokacin har tsakar dare suna zuwa duba furen suga a wani yanayi yake, idan suka samu furen batool yana tsastsafo da ruwa ajikinshi, haka zasu zauna sunata kuka suna lallashin furen amatsayin batool suna yi mashi magiya akan yayi haƙuri ya daina kuka, Suna atare dashi, Idan kuma suka samu furen ya kwanta cikin ƙasar dake a ruƙe dashi, sai su yi ta jin daɗi suna faɗin batool bacci take yi, kada su takura mata su tafi su barta ta huta, duk wannan haukan da suke yi danish yana kallonsu, Ya rasa gane wani irin kaine dasu, shi yayi abu don ya faranta ma angel rai, su kuma sun ɗauka dagaske ne, gashi har suna ƙoƙarin zautar da kansu akan furennin bogi.
A kowace rana idan dare yai kafin su kwanta bacci sai sunyi ma batool addu’a Akan Allah ya kare musu ita aduk inda take, tsawon kwanakin nan sunƙi sakewa da Danish suna atare dashi ne, badan sun yarda dashi ba, musamman angel ko kallo bai haɗa ta da shi, bawan Allah duk ya shiga damuwa daurewa kawai yake yi, amma rashin tanka mashi da take yi ba ƙaramin illata zuciyarshi take yi ba, yanzu takai ga ko wasa suke yi da zarar ya tsoma baki, to zata zame hannunta ne tace ta fasa, ƙiri ƙiri ta guje shi ta maida shi abokin gabanta, a ƙarshe daya gaji da irin wulaƙancin da take yi mishi, aikuwa ya janye jikin shi daga gare ta, Ya nisanta kanshi da duk wani abu da zai haɗa shi da ita, hakan ba ƙaramin takurata yai ba, itafa tafi son yai ta binta tana yakice shi, sai gashi reshe na neman ya juye da mujiya.
*PRISONERS❤*
A wata rana suna kwakkwance saman sabbin gadajen da suka gaje na baƙin prisoners sai sharar baccinsu suke yi, babu wanda ya farka acikin su, Gari tuni Ya jima da wayewa, A wannan lokacin ne motsun buɗe dakin tsohuwa Ya karaɗe Cikin ɗakin, A hankali ta buɗe ƙopar Hannunta ruƙe da sanda kamar kullum, fuskarta babu walwala, tsufanta ya fito sosai, jikinta na sanye Cikin rigar ta, Ta gado Launin Ja, Cigaba da dogara sandar tayi yayin da take tun karar Cikin dakin, Tayi mamakin ganinsu kwance saman sabbin gadajen da aka kawo maimakon ta gansu A saman nasu beds ɗin, Murmushi ne ya bayyana akan fuskarta, a fili tace”Zaman Prison yayi maku daɗi Jikokina, Kuna hutawarku Cikin walwala, Sai dai kun manta da Tsohuwa Tamira,”
Sai da tabi kowani gado ɗaya bayan ɗaya tana binsu da kallo, tun daga kan gadon haris da deeja, zuwa nasu Javed da rubina, a bakin gadon da angel take kwance ta ɗan dakata tana kallonta, ganin wani irin sabon salon kwanciya, ta wawware ƙafafuwanta, har sun sauko daga ƙasan gadon, gashin kanta duk ya tarwatse ya barbazo saman mattress ɗinta, fuskar tsohuwa asake tace”Unaisah mutuniyata sarkin tsiwa Ina matuƙar yinki,” tana ambaton hakan taɗan ja da baya kaɗan, ta daddage ta buga sandar hannunta a ƙasa, Nan take ta bada wani irin sauti kamar fashewar bomb, agigice suka farka suna faman zazzare idanuwansu, saboda tsabar ruɗu parveen da rubina suka sauko daga saman gadajensu, Da gudun gaske suka nufi toilet zasu shige su 6oye, azeeza da tafi kowa jin tsoro tuni ta jima da shigewa ƙarƙashin gadonta, tsohuwa ta rikitar dasu, babu wanda ya lura da ita, sai da suka gama tsorata, Tukunna Ta soma Yi musu gyaran murya, Nan fa Hankalin kowa Ya dawo kanta, sai faman mutsustsuka idanuwansu suke yi, Na cikin toilet da suka 6oye sai gasu sun fito hannunsu ruƙe cikin na juna, azeeza ta leƙo daga ƙarƙashin gado don ta ga wanene yai musu gyaran murya tana yin tozali da fuskar tsohuwa sai gata ta fito tana faman sauke ajiyar zuciya,
Da alama ta nishaɗantu da abunda ta yi musu, Sai tiƙar dariya take Yi, su kuwa sai faman sauke ajiyar zuciya suke yi hada masu dafe ƙirjinsu, hanna tace”Tsohuwa kin bamu tsoro, ƙiris ya rage in saki fitsari a wando,”
Dakatawa ta ɗanyi da yin dariyar da take yi, Ta dago tana kallonsu tace” Naji daɗin ganin ku cikin ƙoshin lafiya, Ina fata baku da wata damuwa”? Tai tambayar tana jiran amsarsu, atare suka haɗa baki wurin cewa”Ƴar uwarmu batool ba a dawo mana da ita ba, almost 2 weeks kenan, bamu san awani hali take ciki ba,” shiru tsohuwa ta ɗanyi na wani lokaci kafin tace”ku ƙara haƙuri idan da rabon za’a dawo da ita, to za ku ganta ne, amma abunda nake so daku, ku daina sanya damuwa aranku” tsohuwa na rufe baki muryar Danish ta ratsa kunnanta,
“Long time, ba mu ganki ba, kin daina zuwa wurin mu” Murmushi tayi tare da nuna shi da sandar hannunta tace”Shikaɗai ya damu dani, dama nasan babu wanda zaiyi kewata acikin ku idan bashi ɗin ba, maimakon da kuka ganni ku tambayeni lafiya na ɗauki tsawon lokaci banzo wurinku ba, amma babu wanda yae tunanin hakan,” ta karasa maganar tana kwa6e fuskarta, hada jefa musu harara tana murguɗa musu baki, gaba ɗaya suka kama tiƙar dariya ganin yadda take murmura idanuwanta yadda kasan na gwaggwon buri, da alama yau wasa tazo tayi musu,
“Kodan bani da amfani awurinku ne shiyasa kuka ƙi damuwa da rashina” shiru suka ɗanyi, angel dai tana zaune ta jingina bayanta jikin bango,
Haris ne yai ƙoƙarin cewa”taya za’ae mu ƙi yin kewarki tsohuwa? ae munji daɗin irin taimakon da kika yi ma deeja, gashi ta samu sauƙi sosai ta wartsake,” yakai karshen maganar tare da ɗan juyawa yana kallon deeja dake zaune gefen gadonta dake kusa da nashi, muryarta aɗan disashe tace”Nima inata so inyi maki godiya amma ban samu damar ganin ki ba, ranar da aka ɗauki batool, azeeza ta sume muka rasa ya zamuyi da ita, mun yayyafa mata ruwa ajikinta amma bata farka ba, Har ƙopar ɗakinki muka ƙwanƙwasa don kizo ki duba jikinta baki buɗe ba, shiyasa muka yi tsammanin ko baki nan ne,”
Jinjina kai ta ɗanyi tare da cewa”Hakane na ɗanyi nisan kiwo, Yanzu ma zuwa nayi don In duba ku ko akwai wani abu da kuke buƙata kafin in tafi” Basu fahimci me take nufi ba
“Mu ba abunda muke buƙata, Batool kawai muke so a dawo mana da ita” acewarsu parveen,
Tsohuwa tace”zata dawo ne, yanzu dai ku faɗa mini me ku ke so kafin in tafi, inji idan zan Iya yi maku shi”
Ta6e baki angel tai tare da cewa”kamar dagaske, nasan ko mun nemi taimako awurinki bazaki Iya yi mana shi ba” Kallonta tsohuwa tay, kafin tace”Me ki ke so Unaisah”? Yadda tayi maganar ba bu wasa akan fuskarta,
“Ki nuna mana hanyar da zamu fita daga Cikin kurkukun nan” shi ne abunda muke so” maimakon tsohuwa ta bata amsa saita fashe da dariya tana ɗan girgiza kai, daga bisani da ta tsagaita da yin dariyar tace”Kin buƙaci abunda bazan Iya yi maku shi ba, saboda yafi ƙarfina, Abunda nake so ki fahimta shine, Ni bakowa bace a gidan kurkukun nan, tun ban mallaki hankalina ba nake acikinsa, tsawon shekara da shekaru na rayu acikin kurkukun nan a matsayin prisoner kamar dai ku din nan, Nima tun ina ƙarama na taso acikinsa, Na jure duk wata gwagwarmayar dake acikinsa kafin na kawo wannan matsayin da nake dashi acikin kurkukun, ba lallai bane ku yarda dani ba, amma zan fada muku gaskiyata, Ni ban ta6a fita daga Cikinsa ba, Anan aka haifeni anan na rayu acikinsa nayi aure har na hayayyafa, akwai ya’yana da jikokina acikin kurkukun nan suna rayuwa”. Tunda ta soma kora musu jawabi, angel take binta da wani irin kallon rainin wayau har sai da takai ƙarshen maganarta, sannan angel ta soma magana
“Idan har dagaske bakisan Hanyar fita daga Cikin kurkukun nan ba, to taya akai kikasan tarihin rayuwata? Kinsan komai agame dani, bayan haka ke da kanki kika faɗa mini cewa Mashine ko mota bazasu ta6a Iya kawo mutun Cikin kurkukun nan ba, kenan ƙarya kike yi mini”?
Dogon numfashi tsohuwa taja kafin tace”banyi maki ƙarya ba, tabbas hakane, Duk da bana fita daga cikinsa amma ina iya sanin meke wakana awajen kurkukun nan,” lamarin yayi matuƙar ɗaurema angel kai, Wannan wata irin baƙar ƙaddarace? Kenan itama tsohuwa tun tana kamarsu ta ke rayuwa agidan kurkuku matsayin prisoner? Itama batasan kowa nata ba? anya kuwa zata Yadda da maganarta? Kafin angel tayi yunƙurin ƙara tambayarta wani abu, muryar naufal ta katse mata hanzarinta,
“Tsohuwa mun ga canji sosai, ga sabbin gadaje an kawo ga kuma akwatuna guda biyu, bayan haka kuma acikin toilets ɗinmu an zuba kayan amfani acikinsu, mun yi mamakin ganin sauye sauyen nan, kamar zamu dawwama acikin farin ciki ne “
Tuntsirewa tsohuwa tayi da dariya tana faɗin”Ae ba’a dawwama cikin farin Ciki a gidan kurkukun ƙaddara, Waɗannan sabbin gadajen da ku ka gani, Ƴan uwanku ne za’a kawo, Nan badajimawa ba, daga yau zuwa gobe zaku Iya ganinsu, Sa’annan kayan amfanin da aka zuba muku acikin makewayinku, Nice nayi fafutuka wurin ganin an sanya muku su…..” dakatawa ta ɗanyi da yin maganar, haƙiƙa sun ji dadin jin cewa itace ta sanya aka kawo musu kayan amfanin, a karo na farko kenan da tayi musu abun kirki, gani suke kamar akwai wani abu da take so ta fada musu, wanda ba lallai bane yayi musu daɗi ba,
Duƙar da kai ƙasa tsohuwa tayi na wani lokaci, suna ta kallonta, kafin ta ɗago idanuwanta akan fuskokinsu, sai suka ga kamar ruwan hawayene kwance acikinsu.
Kafin su yi yunkurin yi mata magana ta riga su cewa”Ku ɗauko mini akwatin nan da aka kawo muku” da sauri naufal da haris suka je suka janyosu agabanta suka kwantar da akwatin nan,
“Kunsan menene aciki”? Suka haɗa baki wurin cewa a’a, murmushi ta saki tare da cewa”Sabbin Uniform ɗinku ne masu kyan gaske, tare da takalma, da sauran abubuwan da nasan zaku buƙata, Zaku Iya buɗewa ku gani”
Wani irin farin Ciki ne ya bayyana akan fuskokinsu, Jiki na rawa suka zuƙunna agaban akwatunan haris ne jagaba wurin buɗe akwatin farko, Kaya ne danƙare acikinshi, A ninke suke an jera su, uniform ɗin farko Launin baƙaƙe ne sun sha banban da kalar style din na jikinsu,
“Mutun Uku, Su fiddo da kayan a hankali sai ku dudduba a tsanake” acewar tsohuwa,
Suka amsa mata da toh, haris da deeja ne sai angel suka sanya hannayensu cikin akwatin suna zaro kayan tare da ɗago dasu suna warware ninkin da aka yi musu, haɗaɗɗun riguna ne masu kyan gaske, basu da banbanci da Wrap coat, suna da igiyoyi guda biyu a jikinsu, tsayin su zai kai har gwiwowinsu, sannan suna da dogon hannu, gefe da gefe akwai aljihu ajikin rigunan, yadin jikinsu mai matuƙar kyau da ɗaukar ido, kowace shirt tana da ƴar vest launin red acikinta, Uniform ɗin farko masu launin Black, Mallakin angel da batool ne tare da Danish, Numbobinsu ne akai no 1 no 2 zuwa 3, A bayan rigunan, wani abun mamaki daga ƙasan numbers na jikin uniform ɗinsu, Kowa da sunan da aka sanya mishi su ukun nan, da turanci aka rubuta sunayen anyi amfani da launin Ja, A bayan rigar Batool an rubuta
*HEART BEAT*(Bugun Zuciya) rigar danish an rubuta *PRISON SHIELD* (Garkuwar kurkuku) yayin da ita kuma Angel abayan rigarta aka rubuta *DESTINY* Wannan suna dai ya ɗaure musu kai, Har tsohuwa su ka tambaya menene ma’anar sunayen tace masu kada su damu, suna ne kawai, Angel bata yadda da sunayen ba, basu kwanta mata aranta ba, tabbas akwai dalilin dayasa aka rubuta musu sunayen abayan rigunansu, su ukun nan, Ita dai fatanta Allah yasa ba wani mugun abun bane.
kowace riga tana da dogon wadonta masu kyan gaske, Uniform dinsu azeeza sunyi kyau sosai launin Ja, iri ɗaya ne dana su Danish banbancin kala ne kawai, Sai kuma rubutun dake abayan rigunansu Angel, babu anasu rigunan sai dai numbobinsu, abun burgewa kowace riga tana da cotton scarves, Irin ɗan mayafin nan da mazan indiya suke ɗaurawa asaman wuyan su.
*❤❤❤PRISONERS❤❤❤*
Launin ja, tun daga kan fuskokinsu zaka shaida irin tsantsar farin cikin da suke aciki, tun kafin ma su sanya kayan ajikinsu har sun fara Imagining irin kyan da zasu yi musu, tsohuwa dai sai murmushi take yi tana kallonsu, daga ƙasan Uniform ɗin nasu, wasu haɗaɗɗun rigunan sanyi ne masu dan banzan kyau, launin bright rust red da kuma dark brown, sai faman ɗaɗɗaga rigunan suke yi suna kallonsu, sun rasa bakin magana saboda tsabar murna, ga wasu hats haɗaɗɗun hulunan gayu na mata dana maza masu kyan gaske, Ƙasan akwatin gaba ɗaya sabbin takalmansu ne kala bibbiyu, zubin anckle boots da kuma slippers, Yara fa sun zama ƴan gayu, kaf saida suka zazzage kayan akwatin suna ta kallonsu suna yaba kyawunsu haɗi da nuna irin farin cikin da su ka yi.
Tsohuwa tace su buɗe ɗayan kwatin su duba kayan dake acikin shi, tasan zasu Yi farin ciki, akwai wata ƴar kyauta data sanya musu aciki, taban mamaki, Jin wannan maganar yasa suka tattara uniforms din da komai na akwatin farko suka maidasu ciki suka datse shi, cike da zumuɗi Angel ta buɗe musu akwati na biyu, a danƙare yake da kaya, abu na farko da suka fara Cin karo dashi, hankys ne launin ja da baƙi, mai ɗauke da sunayen kowannan su, sun yi matuƙar Yi musu kyau, Hada mayukan gyaran Jiki dana gyaran gashi, da Set na kayan gyaran akaifa, ga wasu ribboms na ɗaure gashi, Yawanci duk basu san yadda zasu yi amfani dasu ba, amma tunda ga angel sunsan zata Yi musu bayanin komai.
“Tsohuwa, kince akwai gift da kika sanya mana, Ta na ina? Ko su ne waɗannan kayan”? Angel ce tai mata tambayar tana kallonta,
Tsohuwa tace”Ku duba daga can ƙasan akwatin zaku same ta” Jiki na rawa suka ɗaɗɗaga kayan har suka taddo wrapping sheet ɗin dake nannade da wani abu, wanda shape ɗinshi daga sama round ne mai faɗi, ƙasa kuma ya ɗan tsuke, kallon juna suka yi cikin ƙagara da son ganin menene aka nannaɗe haka, kowa ya baza ido suna jiran ganin menene, A tsanake angel ta soma warware wrapping sheet ɗin awani slow, Sai da ta taddo ƙarshen shi ta yakice paper ɗin da aka nannaɗe shi, A hankali take bin shi da kallo, Su azeeza duk suka zazzaro idanuwansu ganin wani abun ban mamaki da basu ta6a gani ba, shin kunsan menene? Nasan Kun ƙosa kuji, To ba komai bane face*MADUBI,*
wani irin farin Cikine ya bayyana akan fuskar angel da ƙarfi ta ambaci sunanshi MIRROR, yayin da take kallon kyakkyawar fuskarta wadda yaushe rabon da taga suffar face dinta tun tana atare da daddynta tsawon shekara huɗu da watanni yama kusa ci ka 5yrs,
Ya burge ta sosai, madubin Round shaped ne mai matuƙar ɗaukar ido, Yadda kasan ƴan ƙauyen ido sama, Haka suka kewaye madubin Suna Kallon fuskokinsu, sun saki baki kamar lehen sakarai, In ka cire mutun ɗaya wanda Yaja gefe ɗaya kamar baya maraba da ganin sabon abunda basu ta6a gani ba, su kuwa sai ihu suke Yi suna Murnar ganin fuskokinsu kamar suyi hauka, Ɗakin nasu ya cika da Hayaniyar su, abun nema ya samu, Tsohuwa dai sai murmushi take yi tana kallonsu, Sun tasa madubin gaba Na tsawon lokaci, sai faɗi suke wai dama haka fuskokinmu suke? azeeza tace Wai Allah na, dama haka nake da kyau? Komai na fuskata ɗan ƙarami mai kyau, Hanna tace”Nima fa kyakkyawace, Idanuwana farare ƙyal, ga dogon hanci, ” deeja tace”duk da ban kai ku kyau ba, amma Nima ba daga baya ba, Manyan kyau ne dani,” tana rufe baki yasmin tace”ni matsalata idanuwana ƴan mitsi mitsi kamar zasu shige ciki, hancina luluyayye, har ƙwara bakina ma, ” gaba ɗaya suka kwashe da dariya hada tsohuwa, parveen dai ta ƙura wa madubin ido ita da Rubina sai kallon fuskokinsu suke yi kamar zasu lashe su, har sai da haris Yakai hannu ya danƙwashi kawunansu tukunna suka zabura, suna faman wurga mashi harara,
“Idan kun gama kallon ƙurallan ku bamu abun muma mu duba kyawun fuskokinmu” Wani irin kallo parveen tai mishi tare da cewa”shawara kyauta haris, Ka haƙura da duba abun nan, saboda Ina jiye maka tsoron munin fuskarka da zaka gani, zai iya sawa zuciyarka ta buga” kafin haris ya bata amsa deeja ta riga shi cewa”Ki Iya bakin ki Parveen, Ƙarya kike kice wai haris bai da kyau, don kawai yana da duhun fata ne, kuma ahakan Ba ƙaramin kyakkyawa bane, kawai kina yi mishi baƙin Ciki ne,” takai ƙarshen maganar tana jifarta da harara, hakan ba ƙaramin daɗi yayi ma haris ba, koba komai deeja ta yabe shi, abunda ma ya ƙara burgeshi, da kanta ta ruƙo madubin daga hannun angel ta kanga mashi saitin fuskarshi, Atare suka haɗa faces ɗinsu suna kallon juna ta cikin madubin sai dariya suke saki,
Satar kallon danish angel tai don taga a wani yanayi yake ciki, Yana zuƙunne a tsakaninsu javed da mubeen, yaɗan duƙar da kanshi ƙas, Yayin da idanuwanshi suke akan yatsun hannun shi, Aranta tace Shi kuma haka zai ƙare! Kowa Yana kallon fuskarshi acikin mirror, banda shi, wama ya sani ko aljani ne, shiyasa yake tsoron Ya haska fuskar shi Cikin madubi, Amma dai zanso Ya kar6i mirror ɗin nan kodan yaga irin baiwar kyan da Allah yae mishi…….” kasa ƙarasa maganar tai ganin yana ƙoƙarin ɗago da kanshi da alama yaji ajikinshi ana kallonshi,
da sauri ta duƙar da nata kan ƙasa tana faman tsuke baki, koda ya ɗago Bai ci sa’ar haɗa ido da ita ba, Sai suka haɗa ido da Haris Ya sakar mishi murmushi yana faɗin” Deeja bani abun nan in haska ma Sarkin kyau fuskarshi, Nasan yau danish ko bacci bazai iya yi ba idan har yayi tozali da kyakkyawar fuskarshi,” Ya ƙarasa maganar tare da sanya hannu Ya ruƙo madubin, Ya ɗan yunƙura ya miƙe ya nufi danish, sai dai kafin ya ƙarasa danish yae saurin kifa kanshi saman gwiwarshi, bubbuga bayanshi haris yae tare da cewa
“Kar ka bani kunya mana, Kowa ya share ka sai ni na damu dakai, pls bro Ka ɗago ka kalli fuskarka,” batare daya ɗago da kanshi ba yace”Haris i can’t bana son ganin shi, pls ka janye shi daga saiti na, zai iya affecting lafiyata,”
jin wannan maganar ta Danish yasa duk suka ɗago da idanuwansu suna kallon shi, Lamarin ya ɗaure musu kai,
Deeja tace”But why danish? Kowa fa ya duba fuskarshi Kuma lafiya lou ba wani abu daya cutar damu, sai kai zaka ƙi kallon fuskarka? Javed yace “Haba danish idan ma saboda abunda ya faru a tsakanin mu dakai ne yasa kace ba za ka duba abun nan ba, Ina mai baka haƙuri just for today a matsayin mu na ƴan uwa mu kalli fuskokinmu acikin baƙon abun nan,”
Lamarin yae matuƙar ɗaure musu kai, sai roƙonshi suke yi suna yi mishi magiya akan ya kalli madubi amma ɗan tahalikin nan yaƙi ɗagowa, rai aɗan 6ace Haris Ya damƙi sumar kanshi da niyar ya ɗago da kanshi Ya tursasa mishi akan ya kalli madubin, aikuwa rai a6ace danish ya bangaje haris Madubin dake hannun shi ya kubce zai kife ƙasa, Jiki Na kerma Ƴan matan su kayi sauri ruƙo shi, Ran haris ya ƙara 6aci ya shiga zazzaga mishi masifa, deeja tace”Su rabu da shi, dama baya atare dasu, Shi kaɗai yasan dalilin shi na ƙin kallon madubin, danish ba abun yarda bane, Tsohuwa dai tana atsaye tana binsu da kallo bata tanka musu ba, duk wanda yai magana idonta na akan la66ansa.
Naufal yace” Ku ku ka damu da shi, ae gaya nan ya baku kunya, Kar Allah yasa ya kalli madubin, don ma ya samu ana lalla6a shi ne, Kuma wlh da ace Madubin nan ya fashe silar hankaɗe haris da kayi, Da ka ji ajikinka, shashasha” yana huci yai maganar,
“Ni dai A iya sani na, Aljanu ne basu son kallon madubi ko su gifta Ta wurin da aka ajiye shi, idan su ka yi suffar mutane saboda baya 6oye ainihin suffarsu ta jinni, na ta6a kallon wani film da irin hakan ta faru, ina da tabbacin cewa danish Ba cikakken mutun bane, Yana da alaƙa da aljanu,” Angel ce tai wannan tunanin acikin ranta,
Gyaran muryar da tsohuwa tayi musu ne yasa suka ɗago suna kallonta, Banda Danish daya kifa kanshi saman gwiwowinsa.
“Ku ƙyale shi, Idan ya nu na baya son abu to ku daina ƙoƙarin tursasa shi, kuma kada hakan yasa ku zarge shi, Danish ɗan uwan ku ne, tamkar uba yake agare ku shi da Haris, Tun ɗazu Na lura da irin wariyar da ku ke ɗan nuna mishi, shin meya faru atsakaninku ne? Ko wani zai iya faɗa mini”? Tai tambayar tana bin faces ɗinsu da kallo, Deeja ce ta kwashe duk abunda ya faru tsakaninsu tun daga kan batool daya bi cikin toilet ya ruƙo hannunta ya damƙa ma giant ita, har izuwa irin bugun da suka yi mishi, da kuma yanke alaƙar da suka yi da shi” tun kafin deeja takai ƙarshen maganarta, tsohuwa ta soma girgiza kanta, Yayin da idanuwanta ke akan Danish daya kifa kanshi, duk sun lura da irin damuwar dake akan fuskar tsohuwa, magana ta soma yi cikin nuna 6acin ranta ga abunda suka yi mishi
“Kada ku kuskura ku ƙara ɗaga hannu kuce zaku ta6a lafiyar jikin shi, bama shi kaɗai ba, Kowa ma, Nayi mamakin jin cewa kun haɗa kai kun bugeshi sai kace wani jaki, ko a shekaru Danish Ya ɗare maku amma ahaka kuka rufe ido kuka jibge shi kamar bawan ku, ina hankalin ku ya tafi ne? Musamman ke angel,” tai maganar tana nuna angel da sandar hannunta, Yatsina fuska angel tae tare da cewa”Ae ni ban ta6a shi ba, lokacin da suka jibge shi, Na suma bana ahayyacina kuma da ace idona biyu saina 6alla hannun shi daya ruƙe batool, saboda baida tausayi mugu ne shi, inaji ina gani Ya raba ni da batool ɗita, tana kuka ina kuka” daƙyar angel ta karasa maganar tare da ɗaura kanta saman laps ɗinta tana shessheƙar kuka tunawa da irin abunda ya faru aranar, gashi har yau babu alamun za’a dawo musu da ƴar uwarsu,
Deeja tace”Har ga Allah danish ya ƙona mana rai, yayi mana abunda bazamu ta6a mantawa ba, tabbas shi dan uwanmu ne amma baya atare damu, akwai wata mummunar manufa atare dashi, In ba haka ba meyasa duk irin shaƙuwar dake a tsakanin shi da batool bai duba wannan ba, ya rasa dame zai saka mata saida sharri, ae wlh duk abunda ya faru da batool alhakinta na akan wuyanshi, Kuma jira muke ta dawo muga awani hali take aciki, kafin mu ƙarasa yanke mishi hukunci” Daga cikin zuciyarta take magana, fuskarta babu alamun wasa, tsohuwa sai jinjina kai take yi, Tana kallonta, sai da takai ƙarshen maganarta tukunna tace”Aikuwa indai kuka ce zaku Cigaba da ta6a lafiyar jikin shi da rabon wata rana ku rasa madafarku, nayi mamaki da Danish ya ƙyale ku har kuka jibgeshi, bayan yana da ƙarfin da zai Iya rama abunda ku ka yi mishi, amma saboda ƙaunar da yake yi maku sai baiyi hakan ba, Saboda baya son wani acikin ku ya cutu, baku da masoyi a duniyar nan daya wuce Danish, shi tamkar jagora ne acikin rayuwarku, ku daina raina shi, akwai ranar da zaiyi maku amfani, amma muddin kuka ce zaku cigaba da nuna mashi wariya acikunku, to tabbas kuwa xakuyi danasani mara amfani…….” Tunda tsohuwa ta soma kora musu jawabi, suka kasa kunne suna sauraronta, batare da suna fahimtar taƙameman abunda take son ganar dasu ba, donsu ana su tunanin basu ga amfanin da zai iya yi musu ba, in banda ya hau gado ya naɗe kamar wani basarake,
“Ba lallai ne ku fahimce ni ba, saboda na karanci hakan akan fuskokinku, Shawarace nake baku kyauta, Bana so ku yi danasani Anan gaba, ” har suna haɗa baki wurin furta Kalmar danasani, deeja tace akan me zamu yi danasani? Bata bata amsa ba, tace”Ku tattara kayayyakin nan ku maidasu cikin akwatin, Ku rufe shi, sannan Ku kawar dasu gefe inaso muyi magana daku kafin in tafi” da sauri Su haris suka mayar da kayan da suka curo cikin akwatin suka datse shi, tare da jansu gefe ɗaya suka jingine su jikin table ɗin dakinsu,
bayan sun dawo Tsohuwa ta basu umarnin su miƙe tsaye, Gaba ɗayansu suka yunƙura tare da miƙewa suna kallonta, duk sun ƙagara da suji me take son faɗa musu,
Ɗaya bayan ɗaya take binsu da kallo na ɗan wani lokaci kafin ta soma magana cikin muryarta ta tsoffi,
“Tsawon shekara da shekaru Ina Rainon Yara agidan kurkukun ƙaddara, Ban ta6a samun Yaran da suka kwanta min araina ba naji ina ƙaunarsu har cikin zuciyata irin ku ɗin nan ba, Kun ciri tuta, domin kuwa kun kafa tarihi acikin rayuwar tsohuwa tamira…….” murmushi ne ya bayyana akan fuskokinsu, Inka cire mutun huɗu, Angel, deeja, Haris da Danish, Babu walwala attare dasu,
“Naso ace ina da hanyar da zan Iya taimaka maku, saboda ƙaunarku da nake yi sai dai kash bani da damar yin hakan, Amma ina fatan nan gaba idan muna da tsawaicin kwana mu sake haɗuwa daku, duk da nasan zaiyi wuya ………” Kallon kallo suka shiga yiwa junansu, Kamar sun fara fahimtar inda zancenta ya dosa,
“Tsawon lokaci Ina atare daku, Duk da ban amfane ku da komai ba, Amma nafi waɗanda su ka yi silar zuwan ku kurkukun nan, Na raini wasunku tun suna ƙanana tun basusan kansu ba, har suka fara tasawa suna rarrafawa yanzu gasunan sun girma gwanin ban sha’awa, wannan abun farin Ciki ne kuma abun ayaba mini ne, ga wanda yasan ya dace” tai maganar fuskarta ɗauke da murmushi, bayin Allah duk jikinsu yai sanyi, Sai kallon suke yi,
“Acikin ku akwai waɗanda suke Yi mini kallon muguwa maƙaryaciya, Mara amfani, Akwai ma wadda tace dani da tukunyar fulawar dake acikin toilet dinku bamu da banbanci, ” duƙar da kai ƙasa angel tai, Cikin jin Nauyin maganar da tsohuwa tayi,
“Ba za ku ta6a sanin amfani na ba, sai ranar da bana atare daku, A ranar zaku tuna da irin mahimmancin da nake dashi acikin rayuwarku, kuma a wannan lokacin zaku yi danasanin rashina atare daku, Amma bana son hakan ya karya zuciyoyinku, Inaso ku ƙarfafa ma juna gwiwa kusanwa ranku cewa, ko babu ni, ko babu wani acikin ƴan uwanku xaku Iya rayuwa! Domin kuwa ba’a halicci duniya don mu dawwama acikinta ba, dole ne akwai ranar da kowa zai barta, ko muna so ko bama so…….” dakatawa ta ɗanyi da yin maganar idanuwanta sunyi jawur a yayin da take kallonsu.
“Abunda yasa na buƙaci abaku waɗannan sabbin kayan saboda Inaso nima wata rana ku tuna dani acikin rayuwarku, A ƙalla dai nayi muku abun kirki……..” bata ƙarasa maganar ba, sakamakon shessheƙar kukan da suka fara, Batasan ya akai suka ɗagota ba tunkafin ma takarasa zance, girgiza kai ta ɗanyi tana murmushi tace”Jikokina kenan, meyasa zaku karaya tun yanzu? Haba Kar muyi haka daku, kada ku bari hawayen ku su xuba, akwai ranar da zasu yi maku amfani,”
“Dan Allah ki fahimtar damu me kike son faɗa mana? Gaba ɗaya kin jefa mu acikin ruɗani” azeeza ce tayi magana,
“Bankwana nake Yi muku! ” wani irin bugu zuciyarsu tayi, Tsabar tashin hankali ne ya bayyana akan fuskokinsu, Sam sun kasa furta komai,
“Dama na faɗa maku cewa, Ni mai raino ce, a ƙa’idar aikin masu raino na gidan kurkukun ƙaddara, da zarar yaran da yake raino sun mallakin hankalinsu, to za’a canza wanda zai dinga kula da su ne,”
A matuƙar ruɗe suke kallonta, Wasu har sun fara matse ƙwaalla, ashe basu ji komai ba,
“Zanje naci gaba da rainon ƙannanku masu taso wa, Ku kuma Za’a canza muku sabuwar da zata cigaba da jagorantar rayuwarku, sai dai fa zaku ga banbancin domin kuwa, Ni ba komai bace akanta, bansani ba kota kawo muku ziyara…..” Cikin sanyin murya danish ya bata amsa da cewa”tazo, namanta ban fada musu bane”
Tsohuwa tace”Bakowa bace face TSOHUWA ZAFREEN! Ita ɗin takasance ɗaya daga Cikin shuwagabannin dake ruƙe da gidan kurkukun ƙaddara! Kaifi ɗaya ce, zuciyarta bata da banbanci da dutse, a rashin tausayi Cikin kaso ɗari tana da casa’in da tara…..” tashin hankalin da ba’a sama shi date!! Tuni gwiwowinsu sun jima da sagewa, Zuciyarsu ta tsorata sosai, tunkafin ma suyi toxali da tsohuwa zafreen, Kusan atare ƴan matan suka zube saman gwiwowinsu, banda angel da mazan,
Sai kuka suke yi suna rokonta akan karta bari akawo musu tsohuwa zafreen, Idan ma yazama dole ta rabu dasu to ta taimaka ta hana akawo musu ita, abarsu suyi rayuwarsu batare da kowa ba, zasu Iya kula da kansu,”
Cikin raunin murya tsohuwa tace”Ae ni bani da ikon da zan hana tsohuwa zafreen zuwa wurinku, Saboda A matsayi ko ƙafarta ban kama ba, wani abun ɗaure kai ma, Ita da kanta ta nemi da abata sashen ku don taci gaba da kula daku, saboda ita ba cikin ma’aikata take ba, Shugaba ce Ra’ayin kanta ne zuwa wurinku, kai Danish ae ka ganta, Tana da babban muƙami, agaban rigarta taurari uku ne, idan baku san ma’anarsu ba, bari in sanar maku, duk wanda kuka gani da Star uku agaban rigarshi To shugabane na gidan kurkuku, A mataki na ma’aikatan prison daga star ɗaya yake farawa zuwa star biyu kafin ka samu taurari ukun nan, Idan kuka duba Jikin rigata babu star ko ɗaya saboda bani da wani matsayi agidan kurkukun ƙaddara, Raino kawai nake yi”
Cikin shesshekar kuka su parveen suke faɗin wayyo Allah mun shiga uku mun bani mun lalace, tsohuwa dan Allah kada ki rabu damu wlh zamuyi biyayya, zamu biki sau da ƙafa, Tun yanzu mun gane kuskuranmu…..”
haƙiƙa sunyi matuƙar bata tausayi sai dai ba yadda zatayi, haka Allah ya riga daya ƙaddara musu rayuwarsu, amma fa zasu ci baƙar wahalar da ba lallai bane su Iya rayuwa, Angel duk tafi su shiga damuwa, ita gani take hada ƙarin donta ƙetare Iyakar data faɗa mata na cewa duk ranar da ta kuskura ta yi leƙan asiri to bazasu sake ganinta ba, amma kuma ae koda ta dura tagar bata ga komai ba, sai ma wahalar da tasha, sai dai idan ko dama ƙarya tayi mata data faɗi hakan tun da ta saba canza magana,” numfasawa tayi tare da kallon tsohuwa tace.
“Idan ma saboda sa’in sar da muke Yi atsakanina dake ne yasa zaki tafi ki barmu, ina mai baki haƙuri, zan ma iya zuƙunnawa saman gwiwowina akan in roke ki, dan Allah badan halin mu ba, kiyi haƙuri ki cigaba da zama damu…..” da sauri tsohuwa ta ɗaura idanuwanta kan wadda tayi maganar, tayi mamaki ganin angel ce, idanuwanta sun Cicciko tab da kwalla duk da basu zuba ba,
Wata irin mahaukaciyar dariya tsohuwa ta tuntsire da ita, Jikinta har jijjiga yake yi saboda tsabar yadda take yin dariya kamar zata kife ƙasa, Duk suka ƙura mata luhu luhun idanuwansu da suka canza launi saboda kukan da suka sha,
Daga bisani tsohuwa ta dakata da yin dariyar tana kallon angel tace”Unaisa kenan, Ban ta6a tunanin zaki Iya furta hakan da kanki ba, lallai kun tsorata da tsohuwa zafreen tunkafin zuwanta, to agaskiya dai ba taimakon da zan Iya yi maku, shawarar da zan baku shine, koda gigin wasa kada ku kuskura tana magana kuna kallon cikin idanuwanta, na farko kenan, sa’an nan, ba’a sa’insa da ita, musamman ke unaisa, Kina da gangancin ya6awa mutun magana, ina mai gargaɗin ki da ki kiyayi harshenki, wurin Yi mata magana, abu na ƙarshe da zan fada maku, idan tana awuri ba’a tsegumi, ko ƙyafcen ido, da yafu ce, Har kisa tana iya yi, idan har akai hakan agabanta, idan har kuna son ku ci ribar zaba da zafreen, to kuyi mata biyayya tamkar zaku bauta mata, idan ta bada Umarni, Jiki na rawa kuyi gaggawar yi mata shi, babu musu, idan har baku kiyayi abunda na fada muku ba, tabbas zaku yiwa mutuwar ku kutse tunkafin lokacinku yayi, ” wani irin wahalallan yawu kowannan su Ya haɗiya, wasu har sun fara jin zazza6i ajikinsu, sun tsorata da tsohuwar nan da za’a kawo musu,
“Ba lallai bane, kullum ku dinga ganinta, kamar yadda kuka saba ganina jefi jefi, saboda ita ɗaya ce daga Cikin shuwagabannin kurkukun, zaima yi wuya a sati ku ganta, Zata iya ɗaukar tsawon kwanaki bata leƙo ku ba, Ta inda zaku samu sauki kenan, domin kuwa baiyanarta ba alkhairi bane……”
Muryar su azeeza ce ta katse mata hanzarinta,
“Tsohuwa yanzu shikenan tafiya zakiyi kibarmu? Fuskokinsu sharkaf da hawaye hada majina,
Daƙyar ta ƙaƙalo murmushi akan fuskarta tace”ƙwarai kuwa tafiya zan yi in barku, babu tabbacin zamu ƙara haɗuwa, ni dai shawarata agare ku shine, Ku daina gaba da junanku, ku hada kanku, kuma ku kawar da idon ku ga duk wani abu da ɗan uwanku Danish zaiyi, ku daina fushi dashi, hakan zai iya haddasa mashi matsala acikin zuciyarshi,” ajiyar zuciya ta ɗan sauke kafin ta ɗago suka haɗa ido da angel,
“Jikata unaisa, Baki ya mutu, tsohuwa zata tafi ki huta da ganin mummunar fuskarta, meyasa banga kina farin Ciki ba”? Tai tambayar tana sakin ƴar dariya, angel kuwa fuskarta aɗaure take, ta tsuke baki, baiwar Allah damuwa ce danƙare akan fuskarta, ” a hankali tsohuwa take buga sandar hannunta, wanda ke nuni da cewa akwai wani abu da hakan ke nufi, sai dai basu fahimci dalilin dayasa take bubbuga sandar ba, dakatawa ta ɗanyi still idonta na akan angel taci gaba da cewa
“Ƙaramarsu babbarsu, ki cigaba da taimakon su kamar yadda kika saba, Inajin daɗin hakan sosai, haƙika zuwanki cikin rayuwarsu tamkar bayyanar haske ne acikin duhu, ki haɗa ka ƴan uwanki, kada ki bari wani abu ƙalilan ya shiga tsakaninki da waninsu, kuso junanku, ku sama ma kanku farin ciki, duk runtsi duk wuya kada kuyi kuskuren da zaisa ku raba kawunanku, idan har kuna son cimma burinku, Inaso ku ɗauka cewa ku kamar
*MUKULLAI NE NA MABUƊIN WATA ƘOFA GUDA ƊAYA WADDA ZATA SAMA MAKU FARIN CIKI ACIKIN RAYUWARKU, TABBAS KUNA DA DAMA*
Amma fa dole sai kun yarda da kanku, kun haɗa hannu, domin kuwa Ƙofar farin cikin nan tana atare daku, Sa’annan
*KU NE MAKULLAN DA ZAKU BUƊE TA*
Nasan a yanzu bazaku ta6a fahimtar kalamaina ba, sai nan da wani lokaci, Aranar da kuka fita hayyacinku, wasu ma basa araye, To awannan lokacin ne zaku gane me nake nufi…………”
Tunkafin ta ƙarasa maganarta, Da ƙarfi Ta buga sandar hannunta, wata irin ƙura ta mamaye idanuwansu, Kafin wani lokaci hayaƙin ya washe, Sai dai koda suka buɗe idanuwansu, ba su yi nasarar samun TSOHUWA TAMIRA ba, Ta riga da ta tafi, ta barsu da kewarta, sun shiga ruɗanin maganganun data faɗa musu, ga fargabar da suke aciki na baƙuncin TSOHUWA ZAFREEN, Lamarin yayi matuƙar gigitasu, yinin ranar da jimamin rashinta suka Yi shi, babu wanda bai matse kwalla ba acikinsu, Sunyi kuka tamkar ransu zai fita, sunyi danasanin duk wani abu da ya shiga atsakaninsu da ita, dama ance sabo turken wawa, hatta angel da tafi kowa tsanar tsohuwa a yau Saman gado ta haye ta rungume pillow tana matsar kwalla, fuskokinsu sunyi jawur gwanin ban tausayi, babu wanda yai kwakkwaran motsi acikinsu, kowa yana tuna irin rayuwar da suka yi da tsohuwa Tamira, Har giants suka kawo musu abinci basu motsa ba, badan Allah yasa parveen tayi tunanin kwashe musu abincin Cikin kwando ta ajiye musu shi ba, da sun yi asarar shi, duk irin zumuɗin da suke yi na sabbin kayan da aka kawo musu babu wanda Ya ta6a su, Kai hatta akwati nan basu ishe su kallo ba.
Sai da yunwa ta fara kai musu karo tukunna suka fara neman abinci, A lokacin dare ya nutsa Haka suka zazzauna saman dining carpet dinsu, parveen ta ɗauko musu abincinsu, Yadda kasan waɗanda akayiwa dole, Suna cin abincin suna matsar kwalla, Musamman parveen idan ta cunkusa Naman abaki, tana tauna Tana ambaton sunan tsohuwa, shikenan ta tafi tabarsu, Yanzu ya zasuyi, Bayan sun kammala cin abincin, babu wanda yai tunanin yin wanka, ga jikinsu sai tsami yake yi, ahaka suka haura saman sabbin gadajen nan kowa ya kwanta, zuciyoyinsu cike fal da jimamin rashin tsohuwa Tamira, da kuma fargabar irin rayuwar da za su yi da tsohuwa Zafreen, ɗaya daga Cikin shuwagabannin kurkukun ƙaddara, suna daga kwance suke Yin fira, Haris yace daga Jin sunanta babu imani atattare da ita, Ni inaga toilet zan koma da kwana, zaifi mini kwanciyar Hankali, ashagwa6e azeeza tace Ni dai Allah ƙarƙashin gado zan dinga 6oyewa duk idan naji takun tafiyarta”
parveen tace nidai in har bazata hanani cin abinci ba, babu ruwana da shiga huruminta, zanyi mata biyayya kodan in tsira da Ciki na,” deeja kuma tace”Allah ya jiƙanmu badan mun mutu ba,” rubina tace”Ai kawai mu ɗauki shawarar tsohuwa mu bita sau da ƙafa, Har Allah ya kawo lokacin da zamu Rabu da ita,” dogon tsoki javed yaja mai sautin gaske kafin yace”Kunga surutun ya isa haka, pls kowa ya lallashi zuciyarshi, Ku rungumi pillows dinku, aja bargo a lullu6e jiki, kowa Yae bacci, zuwan tsohuwa Zafreen ba fashi,” Sai da duk suka gama surutansu, tukunna Angel ta soma magana muryarta adisashe tace”In sha Allah, babu abunda zai faru, koda tazo bazata Iya cutar damu ba, Ni babu bawan da nake jin tsoronshi aduniyar nan, In ba mahalicci na ba, saboda nasan babu wanda ya isa ya cutar dani face da izninsa, Allah shine maganin duk wani mugu mai kafirar zuciya, kafin ayi azzaluman kurkukun kaddara Anyi waɗanda suka fisu, irinsu fir’auna yanzu duk babu su a doron duniyar nan sai dai kajisu a tarihi,’ Tunda angel ta ambaci sunan fir’auna, nan fa suka addabeta akan ta basu tarihinshi suna son Sanin wanene shi, tace musu su yi haƙuri yanzu kanta ke yi mata ciwo, amma ta yi musu alƙawarin idan taji sauƙi zata basu tarihin Annabi musa (AS), bayan haka saida ta kwantar musu da hankulan su, kafin ta samu bacci ya ɗauke su,
Lokacin da dare Ya ratsa, Angel ta sauko daga saman gadonta, zuciyarta duk ba daɗi, ahaka ta lalla6a ta nufi toilet ɗinsu, ba don komai ba, sai don ta duba awani hali furen batool yake aciki, Tana sanya ƙafarta Cikin toilet din ta hango furen batool da alamun lemar ruwa ajikinshi, kamar zufa haka ya tsastsafo ajikin ganyen shi, nan fa hankalinta ya ɗan tashi, da sauri ta ƙarasa inda tukunyar fulawar take, Ta zuƙunna tare dakai hannu tana shafa Jikin ganyen shi, sosai ruwan ke tsastsafowa, Duk saita rasa sukuni, ta shiga damuwa, muryarta na ɗan rawa ta soma faɗin”dan Allah batool ki daina kuka, Ina atare dake, ban manta dake ba, kina araina, kullum ina yi maki addu’a, Duk da nagaza zuwa in taimake ki amma nasan cewa Allah yana atare dake kuma zai kare ki ne,”
cikin shessheƙar kuka angel take lallashin Furen, Batasan cewa Danish Yana tsaye bakin ƙopar toilet ɗin ya la6e yana kallonta, tsananin tausayinta ne ya kama shi, sai dai baijin zai iya zuwa ya lallashe ta, saboda alƙawarin daya ɗaukar mata, abunda baisani ba ita kanta, A halin yanzu a matuƙar ƙagare take da son su shirya da juna don ba ƙaramin azabtuwa take yi ba,
Shiru ta ɗanyi tana ƙarewa furen kallon, ganin Ya daina tsastsafo da ruwa ajikinshi, wani iko na Allah sai taga furen ya kwanta cikin ƙasar tukunyar, alamar mamallakin shi bacci yake yi, murmushi ne ya bayyana akan fuskarta, aranta ta raya cewa Batool taji lallashin da take yi mata shiyasa tayi shiru ta kwanta tana bacci, A hankali ta mayar da idanuwanta kan furen daddynta, tafi yarda dana batool akan nashi, saboda shi bata da tabbacin yana raye koya mutu, Jikin furen yayi kore shar dashi, kuma iccen yaɗan miƙe ba kamar lokacin farko da ya fito a lanƙwashe ba, Ziraran yatsun hannunta ta ɗaura asaman furen daddynta tare da shafa ganyen shi, a fili ta furta I wish kana araye daddyna, har yanzun kana nan acikin zuciyata, ba abinda ya sauya daga ƙaunar da nake yi maka, I luv u so much, zan cigaba dayi maka addu’a kaida batool ɗina da kuma ƴan uwana prisoners, Alƙawarine na ɗaukarwa kaina,”
murmushi tasaki tana faɗin”Har na tuna lokacin da na ƙala maka sharrin cewa kai ba mahaifina bane, ɗan yankar kaine, aranar kasha bugu wurin ƴan ƙato da gora, kuma duk da abunda nayi maka hakan baisa ka guje ni ba, saima ka ƙara ƙaunata, ashe babu rabon xamu ƙare rayuwarmu atare…..haka na dinga burin in zama house wife, ashe da rabon in zama prison wife, Gidan hutun da nake burin inyi aure, har ina faɗa ma aunty aneelerh zan auri hamshaƙin mai kuɗi saboda masu aiki su dinga yi mini hidima ina daga kwance, sai gashi na ƙare agidan kurkukun ƙaddara, wayyo Allah na, babu daddyna babu aunty aneelerh da uncle uzair, babu mommy adamana da uncle abdallah, babu makaranta, babu house wife, duk waɗannan burinkan sun tashi a tutar babu…..”
daƙyar ta ƙarasa yin maganar saboda kukan da yafi karfinta, ta kifa kanta saman gwiwowinta taci gaba da kuka, tana fadin nayi danasani daddyna ka yafe mini, wlh ina matuƙar ƙaunarka, dama saida ka fada mini cewa bani da tamkarka a duniyar nan yanzu na shida hakan…..’
Duk wannan suratan da take yi akan kunnan Danish, Ya ɗan jingina kanshi jikin ƙopar toilet ɗin, Ya natsu yana sauraronta, Hakanan taji aranta kamar akwai mutun abayan ta, a hankali ta ɗan dago da kanta, tana ƙoƙarin juyawa ta kalli bayanta danish yai saurin fita daga Cikin toilet din ya tsaya daga waje, Yana faman sauke ajiyar zuciya,
Baiyi tsammanin ta biyo shi ba, Sai dai yaji ta ambaci sunan shi,
“Danish”! Kasa juyawa baya yae don ya kalleta, duk yabi ya kama kanshi,
“Shine kana ji inata kuka ko kazo ka lallashe ni” Yayi mamakin jin abunda ta ce, cije lips ɗinsa yae kafin yace”Saboda me zanzo in lallashe ki? Ko kin manta alƙawarin dana ɗaukar miki? Batare daya juyo ya kalleta ba, yayi maganar,
“Meyasa kake bibiyata? Nasan saboda ni kazo bakin ƙopar toilet din nan ka tsaya, Allah kaɗai yasan tun lokacin da kake kallona, kaga kuwa Alƙawarin Ya jima da karyewa,”
girgiza kanshi ya ɗan yi tare da cewa”bana sa6a alƙawari, idan kin manta bari in tuna maki, kin ce kada na kurkura na ƙara hada ido dake kinaso in nisanta kaina agare ki, Tabbas nazo bakin ƙopar toilet din kuma na kalle ki amma ban bari mun hada ido ba. Hope kin fahimta yanzu ban karya miki alƙawarinki ba, Tun da bamu haɗa ido da juna ba kuma banzo kusa dake ba,”
Harara ta shiga jefa ma bayan shi, kamar ƙwayar idanuwan zasu faɗo ƙasa, wani irin kewarshi take ji kamar tae hauka, tayi danasanin sanya shi ya ɗaukar mata alƙawarin nan, ta manta cewa Prisoners basu Iya karya alƙawari ba, ta inda suka banbanta da mutanan dake rayuwa awaje kenan, majority dinsu basa ƙarya kuma basu Iya gulma ba, musamman DANISH!
Takaici ne ya isheta, Can dai tace”Idan nace na fasa alƙawarin fa”? Danish ya bata amsa da cewa”Idan kin fasa Ni bansa fa, bazai ta6a yiyuwa ba” yana faɗin hakan Ya wuce cikin dakinsu yabarta a tsaye tana faman cizon le6enta,
Daga bisani ta gyaɗa kai tare da wuce wa ta nufi cikin dakin, a kwance ta same shi saman gadon shi ya rungume pillow, ta6e baki tayi kafi ta nufi nata gadon ta haye ta zauna daga tsakiyarshi ta ɗaga hannayenta sama tana jera addu’o’i, Cikin harshen larabci,
ta ɗauki tsawon lokaci daga bisani ta shafa hannayenta saman fuskarta, kafin ta gyara kwanciyarta, Sai da ta lumshe idanuwanta, Zuciyarta ta soma tariyo mata maganganun da tsohuwa ta faɗa musu kafin tafiyarta, tabbas akwai wasu kalamai da tayi aciki waɗanda suka ɗaure mata kanta, ta kasa fahimtar inda suka dosa, Duk irin kaifin basirarta, ta gaza gano menene tsohuwa take nufi, da tace musu su dauka cewa su makullaine da zasu Iya buɗewa kansu ƙopar farin ciki, tayaya kenan? daƙyar ta samu bacci ya ɗauketa a daren ranar,!
Ko a washe garin ranar babu wanda ya sanya sabon uniform ɗinshi acikinsu, damuwar rashin tsohuwa ta hanasu sukuni, ga fargabar zuwan tsohuwa Zafreen, da kuma new prisoners, daga Sunji motsin ƙopa a firgice suke kallon ƙopar, don suga wanane, a ƙarshe sai su ga bakowa, Kunnuwansu ne kawai suke Jiyo musu hakan, sakamakon sanya rai da suka yi, wasa wasa yau har tsawon 2 weeks da tafiyar tsohuwa babu wani sabon Labari, ta ko’ina shiru kake ji, su kaɗai suke rayuwarsu, hankalinsu har ya ɗan kwanta don a tunaninsu, An ƙyalesu ne su yi rayuwarsu su kaɗai, Bakomai yafi ɗaga musu hankali ba, face rashin batool don a lissafinsu yau Wata ɗaya kenan babu Ƴar uwarsu acikinsu, Ba’a dawo musu da ita, har sun fara fidda rai da sake ganinta 🥺
*PRISONERS💔*
Yau tun da sassafe Angel da hanna suka taimaka ma ƴan uwansu mata wurin gyara sumar kansu, gwanin ban sha’awa kowa saida suka wanke mashi sumar kanshi, suka gyara musu ita, su kansu ba ƙaramin daɗi suka ji ba, ganin yadda sumar kansu tayi kyau ga laushi da kyan gani a ido, ga wani irin ƙamshi da gashin nasu yake fitarwa mai daɗin shaƙa, Bayan Sun kammala gyara ma su azeeza, Hanna da angel suke koma toilet, saboda su wanke nasu gashin kan, sai da angel ta kammala wanke ma hanna, ya rage saura ita, duk yadda hanna taso ta wanke mata gashin kanta, hakan ya faskara, saboda uban yawan dake gare shi, Gashi ya nannaɗe yadda kasan taliyar indomi, Tun tana nish tana ƙoƙarin tattaro gashin kan Angel, kamar hannunta zasu 6alle, a ƙarshe data ga abun yafi ƙarfinta, sai ta fita tabar angel acikin toilet ɗin, sai gasu sun shigo kusan su Shida hada su javed da naufal, wai sun zo wanke mata kai, ashe bayan da hannah ta fita daga cikin toilet ɗin, ɗakinsu ta shiga taje ta kira su, donsu taimaka mata, mamaki Ya kama angel, ganin sun shigo suna nannaɗe hannuwan rigunansu, Kusan dambe akayi acikin toilet din, tana faɗin ita bata so su barshi ta haƙura da wanke gashin, Su kuma suka ce bata isa ba, Yadda aka wanke ma kowa gashi, Itama sai sun wanke mata nata, ko tana ko bata so, A lokacin Danish Yana la6e bakin ƙopar toilet din yana kallonsu, don ba ƙaramin nishaɗi ya samu ba, ganin yadda suke ta yawo acikin toilet din sai zagaye shi suke yi, Ita tana gudu su kuma suna bin bayanta hannayensu ruƙe da shower gel da comb, da sauran abubuwan da zasu yi amfani dasu wurin wanke mata gashin su gyara mata shi, Sai da kowannansu Ya gama galabaita, tukunna suka samu ta basu haɗin kai, Su shida suka wanke mata gashin kanta, tadaici azaba, har wani jiri take gani acikin idanuwanta, saboda yadda suke ja mata gashin, Bayan sun kammala wanke mata shi, waɗanda ke ruƙe da combs, suka soma sharce mata shi, daga bisani suka bi da mayukan gyaran gashi suka shasshafa mata, ‘ Lokacin da suka kammala, Sunyi mamaki Ganin irin yadda gashin kanta ke ta ɗaukar ido, yayi dark brown dashi ya warware tamkar hijabi yayi mata abayanta, ta yi farin Ciki sosai da suka taimaka mata wurin gyara mata gashin kanta, ta ƙara jin ƙaunarsu acikin zuciyarta,
Kafin marece ya doso, ɗaya bayan ɗaya suka soma shiga toilet suna Yin wanka, saboda yau sun shirya canza Uniform dinsu, sai ɗauki suke Yi zasu sanya sabbin kaya, Bayan sun kammala Yin wankan, Ya rage saura Danish Yaƙi zuwa yai wanka, Hatta mazan sun wanke sumar kansu, amma shi duk ya takure kanshi, Ya hana kanshi sukuni acikinsu, duk da ayanzu babu wanda yake nuna mishi wariya, tun ranar da tsohuwa tayi musu faɗa akan su daina ware shi acikinsu, tun daga ranar suka daina gaba da shi, Shi ɗin ne dai kamar baison suna kusanto shi, Kuma bakowa yaja hakan ba face Angel, ita ɗin dai ce da baya son ya karya mata alƙawari.
Ganin baida niyar tsohuwa ya wanke sumar kanshi Yasa haris zuwa har saman gadonshi, Ya damƙo hannun shi ya janyoshi, Har saida ya sauko daga saman gadonshi suka nufi toilet, Yana fadin Allah idan bakai wanka ba, Ni zanyi maka da kaina, kowa yana nishaɗi sai kai kaɗai duk kabi ka takura rayuwarka sai kace wani bare, Idanma don abunda ya faru ne ae mun yafe maka komai ya wuce mana, tun da ya riga daya faru,” Kamar wani ubanshi haka haris ya dage yana tayi mishi faɗa, har suka shiga cikin toilet din, bawan Allah yai shiru bai tanka mishi ba, haris bai fito daga cikin toilet din ba sai da ya taimaka mashi ya wanke sumar kanshi, Kafin Ya fito yabarshi aciki, don yayi wankan,
Kafin wani lokaci, duk suka hallara acikin ɗakinsu, Angel ta janyo musu akwatin kayansu Ta bude shi, a hankali take zaro uniforms ɗin tana miƙa musu, da yake tasan numbers ɗinsu, shiyasa ba ta sha wahala wurin banbanta na kowa ba, Bayan kowa ya kar6i nashi, nan fa suka soma sanya su ajikinsu, Cikin dabara, Idan suka cire tsohon wandon, sai su zura sabon a jikinsu ta yadda tsiraicinsu bazai fita ba, kafin ma su sanya kayan ajikinsu saida angel ta biya musu addu’ar sanya sabbin tufafi, duk suka yi banda Danish, Ya ruƙe kayan a hannunshi yana zaune gefen gadonshi, babu alamun zai zurasu ajikinshi,
Uniform din sunyi bala’in yi musu kyau, yadda kasan ɗaliban high school na ƙasar Korea, Tabarakallahu ahsanul khalikin, Kyau ne ya haɗu da kyau, abunka ga farare kayan sun fiddo da hasken fatarsu, Sun bi shape din jikinsu sun zauna musu cuf cuf, Especially angel, Wow abun ba’a magana, Yarinyar dama can kalar kyau ce, Ƙarshe ce afagen kyau, Hatta ƴan uwanta su azeeza sai santin kyanta suke Yi, duk da irin kyan da su kayi don itama azeeza ba daga baya ba, jajayen kayanta sun mayar da ita tamkar fure awurin kyau, musamman in tayi dariya fararen hakoran nan suka bayyana ajere kamar gonar auduga, tubarkalla,
Danish fa sai satar kallon angel yake yi da zarar Ta juyo zata fuskanci inda yake sai yae saurin kawar da kanshi gefe, baisan cewa ta lura da irin satar kallon da yake yi mata ba, hakan ba ƙaramin dadi ya yi mata ba,
bakomai Yafi ƙawata kyan uniform ɗinsu ba face Cotton scarves din da suka daura awuyansu, da kuma igiyar wrap coat dinsu da suka daure, Sai takalmansu, da kuma ribbom da matan suka ɗaure Sumar kansu dashi, Banda angel saboda sanin yawan gashinta shiyasa bata yi gigin sanya ribbon ta daure shi ba, don zai iya tsinkewa, hatta giants da suka zo kawo musu abinci, sai da suka yi musu wani abu daya basu mamaki, da hannu suka yi musu thumbs up, wato alamar jinjina, wannan abun dai ya gigitasu, basu ta6a yi musu hakan ba sai yau da suka ga sun ɗauki wanka, angel dai bataji dadi ba, saboda tasan ƙarshe duk wannan gayun da suke Yi, abanza zai tashi, tun da ba fasa daukarsu za’ayi ba, sai daga baya tadinga danasanin Gyaran gashin da su kayi da sabbin uniform ɗin da suka sanya ajikinsu, don ba ƙaramin fiddo da kyawun surar jikinsu kayan su kayi ba, hakan zai ƙara ma ƴan iskan ƙaimi wurin biyan buƙatarsu da su, zasu ji daɗin gur6ata musu rayuwa, in ba haka ba taya akai giants da basu magana Yau kawai don sunga sunyi kyau shine suka yi musu alamar jinjina wato sun burgesu da suka yi gayu, aiko dai akwai matsala babba!!
*❤❤❤PRISONERS❤❤❤*