Search
You have no alerts.

    Kangin Bauta Na Mansur sufi

    Kanagin Bauta Na Mansur sufi

    Kangin Bauta 1
    Littafin yaki
    Rubuta labari
    Mansur Usman Sufi

    Kyawawan samari ne majiya karfin damtse su uku, mai matukar kwarjini da ban tsoro. Na
    farkonsu yana rataye da waɗansu zaratan takubba guda biyu a gadon bayanshi kuma ya
    kasance mai matuƙar kaurin jiki fiye da ‘yan uwanshi.
    Saurayi na biyu yana dauke da wani irin KWARI DA BAKA mai daukar hankali,jikinsa a murde
    yake ya tara kwanji,
    kallo daya zakayi masa kafahimci cewa ya fi sauran yan uwansa kirar sadaukantaka.
    Na ukun kuwa yana ɗauke da dauke da dogon nashi mai baki biyu,
    bakin yakasance daga farkon sa yayi fadi daga karshe yayi tsini ya fitar da baki biyu.
    Babu abin da zai burge ka ga samarin sama da yadda suka yi shigar yaƙi iri daya sak,
    kuma suna zaune abisa jajayen dawakai ingarmu.
    Samarin uku suna tafiya ne acikin wani daji ma,abincin dogayen bishiyoyi,koramu,
    tare da kwazazzabai.gaba daya yanayin dajin ya banbanta da sauran dazuzzukan da idanuwa
    suka saba gani.
    Domin hatta kwari da tsuntsayen dake cikin sa abin tsoro ne.awasu lokutan sai kaga tsuntsaye
    na dauke da fuskokin bil,adama,hatta bishiyoyin dajin suna canza launi zuwa launi,
    Tabbas dajin yana da matukar kwarjini ga duk jarumin daya tsinci kansa acikin sa dolane ya
    razana
    Haka dai zaratan samarin uku suka cigaba da tafiya adajin Babu alamun razani atattare da
    fuskokinsu Lokacin da suka shafe tsawon sa,a daya da dakika talatin suna tafiya acikin dajin,a
    dai dai wannan lokaci ne suka fara hango wani katafaren gida kwaya daya jal adajin,
    Al,amarin da yayi matukar basu mamaki kenan suka ce acikin zukatan su.taya za,ace wannan kasurgumin daji ace an gina wannan kerarrran gida a cikinsa.Amsar tambayoyin da suka kasa bawa kansu kenan, suka cigaba da tafiya,
    Da isar su bakin gidan suka tarar da gidan ya kasance tankameme Tamkar gari guda.gaba daya
    ginin anyi shine da waɗansu manyan duwatsun wuta wadanda ido bai taba gani ba,
    Katangun gidan sun kasance masu tsawon gaske.akwai ƙatuwar kofa guda daya jal mai tsawo
    da kauri inda za,a sanya karti majiya karfi mutum hamsin bazasu iya ture ta.
    Nanfa samarin suka yi cirko-cirko suna nazarin kofar tsawon dakika arba,in dayansu bai ce
    uffan ba.
    Daga can sai daya daga cikin su wanda ake kira da suna Hilwas yayi gyaran murya yace “yaku
    ‘yan uwana yanzu mene ne abinyi?
    Gashi yanzu mun iso gidan boka kimraz,naji ajiki na cewa dukkan baiwar da muke da ita bazata
    yi mana wani amfani ba face muyi Amfani da fasahar da muke da ita.”
    Koda jin wannan batu sai sharwas yayi caraf ya tari numfashin Hilwasa
    yace”Ni shawarar dazan bamu muyi tunanin hanyar da zamu bude Wannan kofa,

    Karanta Littafin Karshen Zalunci Anan

    0 Comments

    Heads up! Your comment will be invisible to other guests and subscribers (except for replies), including you after a grace period.
    Note
    error: Content is protected !!