_Mamuhgee_
#Zafafabiyar
1
Bismillahir Rahmanirraheem
Ina rokon ALLAH Subhanahu wata’ala yanda zan fara littafin nan lafiya cikin aminci da yardarsa ya bani ikon kammalawa cikin kwanciyar hankali da nishadi tareda dacewa lfy Ni da yan uwana gabaki dayanmu.AMIN.
Dan Allah ku kasance masu uzuri idan an samu kuskure ko mantuwa da makamantansu,Thank you.
********
ZADEENs HEALTH CEN/SPEACIALIST,
WEDNESDAY 1:40Am
Tin kafin isowan motocinsu da suka tinakaro babbar gate din asibitin securities na asibitin suka taso kusan a tare suna wangale musu gate din cikin sauri sbd irin gudun da motocin Ahalin ZADEEN’s din suka tinkaro dashi wanda duk wani ma’aikacinsu yasan idan ciwon motacin suka tinkaro asibitin to Hasken idaniyar ahalin ce ba lafiya wadda kullum take cikin ciwo.
Sauran securities din da basu qaraso bude kofar gate din ba kaf dinsu fitowa sukai suka tsatsaya a gate suna bin motocin guda uku da kallan girmamawa duk da tsakar dare ne tareda fatan Allah ya bata lafiya.
Motocin na gama shigewa aka rufe gate din tareda taresa sbd babu wanda yake shiga ta wannan gate din a qaidarsa sai masu asibitin wanda kusan koyaushe suna hanyar zuwanta.
Kafin suyi parking likitoci uku da nurses biyu suka fito ta private kofar da zata kaika kai tsaye zuwa Vip room din dayake sama gaba daya.
A tare duka kofofin motocin suka bude kusan a tare duka suke fitowa babu wanda baa cikin kayan baccinsa yake ba sai DZAD(Dad Zad) wanda shine asalin Zadeens din a yanzu da babu kakansu kuma shine mahaifin marar lafiyar tasu sanye yake da jallabiya da qatuwar rigar sanyi ash sai hula sbd idan ciwon ‘yar dayake gani a matsayin tasa bugawar zuciyar ya tashi saukowa yakeyi gaba daya daga billionaire din da ganinsa ma yake wuya ya koma kaman asalin uban da bayada komai agajin gaske yake nema a gurin Allah.
Gadon da aka tura ta dashi ne komai nata a rufe ko fuskanta baa gani sbd kwata kwata basa bari ana ganinta sosai sai iya likitocin dake kulawa da ita sa ciwonta ne kadai suka san kamanninta sbd tsaro da tsananin rashin wasa da duk abinda ya shafeta.
Suna wucewa ciki sauran familys din suka musu baya babu wanda zuciyarsa bata harbawa da damuwa,
A daidai irin wannan yanayin ne ko lokacin idan suna cikinsa babu abinda bazasu iya kawarwa ba dan biyan buqatansu dan kuwa mantawa suke da komai da kowa sbd JANNAH.
Securities din ZADEEN’s dinne da suka iso asibitin ba tareda kayan securities dinsu a jiki ba sbd basa son asan akwai wani me mahimmanci a asibitin suka zagaye private kofar har ciki batareda alamar da zata nuna securities ne su ba.
A sama kuwa suna isa aka shige da ita inda iya doctors dinne zasu shiga familyn kuwa a nan wani wadataccen palon jira dayake a tsare suka zazzauna cikin yanayi mara dadi wasunsu kuma a tsaye suna kaida kawo cikin rashin sauti ko kadan sbd rashin dadin zuciya.
Mimi data fisu karfin zuciya akan lamarin Jannah din koyaushe itace ta dago idanuwanta da sukai laushi ta kalli Dzad wanda shima juyowa yayi ya kalleta da idanuwansa da sukai jajir kafin ya sauke ajiyar zuciya ahankali yana hade hannuwansa biyu sbd sanyin dayake ratsasa ko zai rage masa wanda kai tsaye zuciyarsa yake jin kaman yana zuwa zai masa illa sbd a wannan lokacin komai zai iya zama ajalinsa dan komai nasa yana gab da mutuwa idan har wani abu ya samu Jannah.
Hannu Mimi ta miqa duka biyu ta dora akan nasa hannuwan tana rufe masa su tareda bude baki cikin tsananin karfin hali da jarumtar da su suke rasawa tace,
“Insha Allah wannan karan zaa dace da zuciyar da zatai mata,
Zaa dace,Jan Zata rayu kaman kowacce ‘ya insha Allah,
Jan zata zama kaman kowanne dan adam,zatai karatu me zurfi ta zama abinda kakeson ta zama insha Allah….
Rawa muryanta tafara yi karfin zuciyarta na neman karyewa dan haka tai shiru tana damqe hannuwan Dad din da dan karfi tana qasa da idanuwanta dake neman cikowa da hawaye.
Dzat din sake kame hannuwanta yayi da nasa yana kasa cewa komai dan irin hakan baya magana kowa ya sani.
Anny matar yayan jannah din wadda ke tsaye gefen mijinta MAHIR ZADEEN riqe da hannunsa tana kokarin kwantar masa da hankali tareda basa kwarin gwiwa dik da itama a sanyayen take sbd duk lokacinda zaa ce jannah ba lafiya a cikin matsanancin tashin hankali take duk da tasan ta riga ta tsira ta fita daga layin wainda zaa iya rabasu da zuciyar dake bugawa a kirjinsu sbd dubawa ko zata daidaita da wadda zata zaunu a kirjin wadda suke son nemowa zuciya kota halin yaya.
Baro gurin Mahir tayi ta dawo gefen Mimi tayi ta zauna ahankali tareda dafata ahankali tana furta mata kalaman kwantar da hankali da fatan ranar warakar jannah taxo.
Mahir zaunawa yayi shima yana dora kafarsa daya akan daya sbd sanyi da shima yake ratsashi wanda yakejin kamar fatar jikinsa ce ta bude kai tsaye sanyin na shigar masa kashi yana daskarar da jininsa gashi kayan bacci ne a jikinsa riga da wando masu tsananin taushi sbd tsadarsu sai jacket daya doro akai.
SALEEM ZADEEN wanda yake bin mahir kuwa kasa zama yayi sbd kansa dayake jin kaman yana motsi dan shi sam dan zafi ne baya da hakurin suspense irin wannan kansa yakejin kaman zai zare.
Shima riga da wando ne a jikinsa na bacci sedai shi hoodie jacket ce a jikinsa sai kai da kawo yakeyi yana kasa dago jajayen idanuwansa da suka sauya.
Kofar palon aka turo da sauri wadda ta saka dukkaninsu dagowa suna kallan Dr AMMAR ZADEEN wanda kai tsaye ya komar da kansa baya ne yayi karatun likitan Zuciya sbd Jannah kadai.
Idanuwansa da sukafi na kowannensu sauyawa ya dago ya kalli kowannensu kafin ya kalli dzat ya basa kwarin gwiwa ya juya ya fice zuwa dakin da jannah din take da doctors sbd shi biyawa yayi inda aka sanar dashi ana tinanin an samu donor kafin ya wuto nan shiyasa suka rigasa isowa.
Zaman kusan awa daya zuwa biyu sukai cikin tsananin daci da damuwar zuciya kafin Ammar ya fito ya shigo dakin yana sauke numfashi me tsananin zafi da huci ya qaraso ya zauna kujeran datake kallan su Dad din ya dago idanuwansa ya kalli dad.
Ajiyar zuciya me sanyi dad din ya sauke a natse yanajin hankalinsa na dawowa jikinsa take yaji dacin zuciyarsa ya ragu sbd yasan Ammar ko zuciya dubu jannah ke buqata zai nemosu ayita gwadawa har a samu wadda zatai daidai a saka mata kota halin yaya ba damuwarsu bane.
Mahir ma ganin hakan ya sauke ajiyar zuciya a boye kafin ya juya ya kalli Anny da kusan itama take ta fahimci akwai wani abin kenan da ido yai mata maganar ta fita da Mimi.
Ajiyar zuciya da numfashi itama ta sauke tareda dafa Mimin cikin kulawa da nuna tausayawa sosai da nutsuwa tace,
“Mimi muje mu duba Jannah din doctors din sun fito”
Dagowa Mimin tayi ta kalli Ammar wanda ya gyada mata kai alamar eh zasu iya zuwan,
Mahir ta kalla shima ya sakar mata murmushin karfin halin alamar insha Allah jannah yanzu zata samu sauki.
Miqewa tayi Anny tabi bayanta suka fice daga gurin Anny taja kofar ta rufe suka nufi dakin da jannah din take.
Suna ficewa Ammar ya sauke numfashi tareda dagowa ya kalli dzad dake jiran bayaninsa ya bude baki yace
“Ansamu donor wanda ta ko ina muke saka ran tayi….
Katsesa DadZad yayi da cewa
“Mene ake jira to?
Saleem da baida hakurin jiran komai batareda sanin abinda Ammar din zai fada ba ya matso gaban Ammar din kai tsaye yace
“Indai ansamu zuciyar da zataiwa Jan ko duka tawa dukiyar dana mallaka akeso zan bayar a karbo heart din ko a inane take kawai ka tabbatarda ka amsota Jan ta sameta”
Yana gama fadar haka ya juya ya nufi kofa ya fice zuwa dakinda jannah din take ya turo musu kofar da karfin daya saka dukkaninsu rintse idanuwansu banda Dad da bai motsaba har lokacin jiran sauran bayanin Ammar din yake wanda daman ba duka zance sukeyi da Saleem ba sbd zafinsa da rashin hakurinsa tareda rashin yadda da raayin kowa wani lokacin sai na kansa.
Ammar takardin dake cikin aljihun jacket dinsa ya fitar ya ajiye akan table din gabansu ya mayar da bayansa jikin kujeran dayake ya jingina yafara cewa
“Daya daga cikin asibitin da muka saka likitocinmu aka samo wadda zatai daidai insha Allah kuma kusan shekarunsu daya da Jannah din sedai matar Aure ce dan tanada tsohon ciki ma sedai batareda saninta ba likitocin sun duba zuciyar komai lafiya kalau.”
Ajiyar zuciya me tattareda samun kwanciyar hankali mahir da dad din suka sauke lokaci daya sbd abinda kawai suke son ji kenan indai komai lafiya kuma ana tinanin zatai to sauran bayanin ba damuwarsu bane sbd sai sun rabata da wannan zuciyar datake bugawa a kirjin ta sun sakawa tasu yar batareda saninta ba sbd itace kusan ta numbar da bazasu iya kirgawa ba sai an cire aga bata daceba.
Dad din a natse yana komawa take Dzad dinsa ya gyara zamansa na asalin Me kudin dayake murza lokacinsa a yanzu ya kalli takardun batareda ya miqa hannunsa ya tabasu ba yace
“Kawai ku saka lokacinda zaayi aikin shine abinda yakeda mahimmanci amma sauran aikin ba buqatan damuwa,
Ku saka likitan datake gani acan asibitin gwamnatin ya turota nan asibitin batareda bata lokaci ba.”
Mahir daya miqa hannu ya dauko takardun ya bude ya zubawa sunan dayake kai idanuwansa tsawon seconds ya duba bayananta da bai fahimci komai a cikinsu ba sbd tin daga sunan da garin datake babu wanda ko a cikin wani yare ya taba ji sbd ba anan suka tashi ba bare susan sunayen garuruwa duka bare qauyuka dayake ganin kamar dabbobine kadai suke iya rayuwa a cikinsu.
Jefa takardun yayi a kan table din kafin ya kalli dad din a natse yace
“Inaga zaifi tinda an samu wanda zatai din and she’s preg abari ayi amfani da tsufan cikin da haihuwansa”
Kallansa Ammar yayi yana tinanin abinda yake fada wanda shi idan tasa zaa bi babu abinda zai tsaya jira bayan cirewa da sakawa Jan.
Dad shiru yayi batareda ya kalli kowannensu ba sbd maganar mahir din dan mahir shine kusan kamar me hangen lamuransu a duk lokacinda zaayi huldan business da irin wannan mummunar ta bayan fagen shine yake aunawa da hangowa ya fada yanda zaayi kuma hakan akeyi a dace sbd yanada ilimin nutsuwar fahimtar komai da mutane,
Hakama yanada wani irin ilimin dayafi duka familyn harshi dad din dan duk da dukkaninsu baa qasar suka taso ba sai yanzu ne da suka zabi dawowa gida sbd nemawa jannah kalbim.
#MAMUH
#ZAFAFABIYAR
#MASTERPIECE
#BESTLOVE #
#BESTSTORY
MASHA ALLAH
idan akwai wanda kuke bukata sai ku fada zamu saka maku