Page 1 & 2
__ababban filin jirgin saman mlm aminu Kano fasin jojine ke saukowa daga jirgin kowanne jayeda jakkar kasanya..daga gefe nahango wasu jibga jibgan sojojine tsaitsaye kowanne da bindigarsa Kamar masu jiran yak’i.
Wani natashin saurayine kesaukowa cikin isa da tak’ama tafiya yakeyi cikin takon irinna k’ak’k’arfan namuji farineshi tassss gashi kyakkyawa nagaban kwatance Dan karamun bakinsa yamotsa tareda yamutsa kyakkyawar fuskarsa yace Ahmad kunkiyi magana da Abba kuwa ? Yafada cikin sweet voice dinsa.. no shinake k’ok’arin Kira tin d’azu Amma baya tafiya bansan miye matsalar ba..jiyowanayi Dan ganin Waye Wannan Ahmad d’in domin kodajin yadda yake fidda zance cikin kalama da nutsuwa abun gwanin Sha,awa.
Masha Allah nafada alokacin Dana ganshi domin shima d’in kyakkyawa ne ba garya sedai shi Ahmad ba fari bane Kuma baza,a kirashi bak’i ba fatarsa Kuma wani irin shek’i takeyi na ban mmki.
Takowa yayi har inda Wannan saurayin yake tareda dafa kafadarsa Yana fad’in yawwa Yama shiga tareda Kara wayar akunne. Cikin sauri d’aya saurayin yakarbe wayar tareda fadar hello abbahhh yaja sunnan cikin shauk’i dafarin cikin shakar iskar kasarsa ta haihuwa…d’aya bangaren Abba ya,amsa tareda fad’in SADEEQ gamasu d’aukarkunan sunzo munyi magana da YAZEED kaji son.
Lunshe fararen idanuwansa yayi kana yace ok Abba tareda yanke wayar Yana mikawa Ahmad abarsa kana yajuya yana fuskantar jirgin bega kowaba numfasawa yayi kamun yadube Ahmad yace miyasa be fitoba? Kamun Ahmad yayi magana sukaga yasawo kafa d’aya awajen matakalar jirgin kamun yasauko data biyu yafito gaba daya Yana tako cikin kuzari da izza.
Kallo duk suka bishi dashi kamun ya,Ida k’arasowa kawai suka rankaya zuwa inda sukaga dandazon sojoji na dunfarosu motoci akalla sunkai 15 sukazo d’aukarsu Amma mota daya suka shiga suduka ukku saurankuma sojojin suka shiga sukad’au hanya.
Seda suka d’au hanya kamun sadeeq yakallin wannan daya fito daga baya yace yoshe kakira Abba YAZEED? D’agowa yayi yakalli sadeeq da mayatattun idanuwansa yawatsamai su kana yamayardasu ya lumshe batareda yace komaiba.
Nikam ai dask’arewa nayi Ina kallan kyau zaharaninshi domun kuwa tsakanin SADEEQ, AHMAD, YAZEED narasa wanne yafi wani kyau aji izza tak’ama hutu dakuma jarumta.
Asalinsu
Family d’aya ne gabaki d’ayansu yarane sa,annin juna Wanda bazasu wuce shekaru 28 ba zuwa 30 Kuma akwai shakuwa me tarin yawa tsakaninsu
Iyayensu su hudu ne agun nasu iyayen ALH.ALI shene babba wato Abba Kuma shine mahaifin AHMAD y’ay’ansa 4 ne akwai Sameer da Salman se auta fauza..se ALH.AMINU shike binsa Kuma shine mahaifin YAZEED shine kawai d’ansa dagashi bekara haihuwaba..se ummyy itace kanwarsu Kuma itace mahai fiyar SADEEQ itama yaranta 2 sadeeq da siyamah.. se auta ALH.ZAYYAN shiko yaranshi ukku duka Mata. Anty khadi anty lele se sumayya
Sadeeq shine aka farahaifa a family yanada kwana 8 aduniya aka haifi YAZEED shiko yanada wata daya aka haifi AHMAD dukansu suntaso cikin soyayyar iyayensu da kaunar junansu basasan abunda ze taba wani daga cikinsu.
Ahmad mutinne me hakuri da nutsuwa idan kaga Ahmad na fada to d’aya daga cikin yan,uwansa aka tab’a… sadeeq kuwa mutinne mesan Wasa da raha barkwanci da sauransu..Sabanin YAZEED da yakeda zuciya da zafin Rai Kuma bayasan raini ko kad’an.
Dukansu miskilaine Amma Ahmad da yazeed sufi zama asalin miskilai musamman yazeed…ahakan sukayi karatunsu harsuka Gama sa,annanne kowanne yazab’i karatun dayakeso Amma ganinn cewa yazeed soja yakeso yasa dukansu suka karanci sojan tareda goyon bayan iyayensu inda sadeeq dakesan yayi Dr seya fito a Dr cikin sojojin..
Cigaban lbr.