Idan Ba Keba Complete Book
🌈 IDAN BA KE 🌈
True Life story
Nimcyluv sarauta
1.
Jimeta/Yola
Njoɓoli Rugar Rome
Gudu Saniyar take tana bin ta a baya itama, hannunta riÆ™e da sanda na korar Nagge, tamkar wanda suke wasan tsere haka Saniyar ke gudu a cikin jejin ita ma bata fasa bin ta ba, sauran Naggen suna gefe guda ko wacce na cin ciyayi wanda bisa kuskure tana can tana bin Saniya É—aya tilo, sauran Naggen suka faÉ—a cikin gonar wani manomi, a yunwace suka rufarwa albarkatun gonar. Cikin siririyar muryarta mai nuni da Yarintar ta, da kuma nuna cewa ita É—in zallar bafullatanar Yola ce Æ´ar Usul. “Waru! Waru! Waru” shi ne abin da yarinyar ke ta nanatawa cikin hausarta ta Fulani, yayinda Saniyar tuni tai mata nisa cikin gajiya wa da bin Saniyar ta tsaya a wajan wata gaÉ“ar ruwa tana riÆ™e Æ™ugunta ta ce “Bone, lalashewa ta samu Nagge Aradu” da sauri kuma ta É—auki sandar tana Æ™ara yin kan Saniyar ganin ta tsaya da gudun da take, cikin sa’a ta cimmata tana zuwa ta kama Æ™ahonta tare da Æ™ifÆ™ifta idanunta alamar zallar fitsarar dake tattare da ita “d’ume ngid’d’a?” Ma’ana “me kake so?” Kallon ta Saniyar ta yi sai kuma ta kaÉ—a jela tare da zubewa a wajan ta shiga shura Æ™afafuwa kamar zata mutu, cikin tsoro haÉ—i da razani HALISA ta ce “Jomirawo ka taimakeni” ta faÉ—a tana kallon Saniyar wacce tai male-male a Æ™asa ga wani ruwa mai kama da jini na fitowa ta Æ™asanta, kuka Halisa ta sanya domin idan Saniyar ta mutu a nan wajan ta shiga uku, itama watan mutuwarta ya kama. Tsayar da kukan tai kafin ta fara duba cikin jeji babu kowa sai ita, ga wani kwantaccen baÆ™in hadari dake Æ™asa wanda a koda yaushe zai iya tashi.
Juyawa tayi ta nufi wajan wata bishiya inda ta hangi Æ™aramar igiya a jiki, tana zuwa jikin bishiyar ta zame hular Fulanin dake kanta, nan da nan sumar kanta ta sauka wacce take jajir babu alamar baÆ™i ko É—aya, gashin ba wani cika ne dashi ba, kawai tsayin gashi gareta, domin har fatar tsakiyar kanta ana iya ganowa. cikin sayin jikinta ta fara jan igiyar tana Æ™oÆ™arin kunce igiyar gaba É—aya daga jikin reshen bishiyar, kamar daga sama taji saukar wani abu mai sanyin gaske zuwa kafaÉ—unta. Cak ta tsaya tana sauraren yadda abin ke tafiya sululuuuu a jikinta har ya gama sauka, hannunta ta miÆ™a da nufin kama abin da ya sakko mata domin bata da tsoro ko kaÉ—an, cikin rashin sa’a hannunta ya sauka saman Æ™aton kan maciji wanda yake kwance a jikinta, wani santsi-santsi ta ji a jikin macijin ga wani sanyi sosai dake ratsa fatar jikinta, bata gama yadda da abin da zuciyarta ke ayyana mata ba, a hankali ta juya wani ihu ta kurma wanda ya yi daidai da É—aukewar numfashinta, baya tayi zata faÉ—i kafin ta kai zuwa Æ™asa macijin ya yi wata girgiza cikin sakanni ya juye zuwa wani saurayi wanda jikinsa ya ke sanye da wasu haÉ—aÉ—É—un kayan sarauta na farin saÆ™i, fari ne tas amma kamar Fatar mace haka fatar hannunsa da sauran jikinsa suke gaba É—aya gashi ya kwanta luff. Zubewa ya yi a Æ™asa ta faÉ—o jikinsa idanunsa a kan fuskarta, ya jima yana kallonta kafin cikin izza da nutsuwa ya ce “kin tsoratani, kin tsorata kanki Danejo, banyi niyyar zuwar maki ba yanzu” Danejo sunan da Æ´an rugar Rome suke faÉ—awa Halisa ke nan. Sai da ya gama Kallon ta sosai, kallon da ya jima bai mata ba tun tana zanin goyo matsayin Jaririya. ÆŠaukanta ya yi ya nufi inda Naggen suke yana zuwa ya tarar da wannan Saniyar dake Shure Shure ta haihu, ashe daman ciwon haihuwa ke damunta. Halisa ya kalla yana sakin Murmushi kafin ya zaro harshesa waje sai ga wani zobe ya bayyana, cikin sauri ya saka mata zoben mai É—auke da tambarin wata masarauta, kafin ya yi Girgiza sai ga shi ya sauya kama, kamarsa a fuska na nan, amma kayan jikinsa sun sauya sun koma irin kayan Fulani sak komai da komai, goya Danejo ya yi a bayansa, ya É—auki jaririn Saniyar cikin nutsuwa ya fara kaÉ—a Naggen zuwa Rugar Rome. Kamar Æ™ifatawar idanu haka ya Æ™araso Rugar..

0 Comments