Idan An Cizaa Complete
Page 1
GOMBE STATE: Jihar Gombe
3rd, FEBUARY 2022: Uku ga watan Fabareru shekara ta dubu biyu da ashirin da Biyu.
DAY: WEDNESDSY: Ranar talata
TIME: 10:30AM, Ƙarfe goma da rabi na Safe
AREA: Wuri: No.442 Karamchi tv. G.R.A state lowcos
PROGRAM: Tare da taurarin Karamchi tv
Sunana FATIMA KABIR SULAIMAN DABO wacce kuka fi sani da (MIMIN KARAMCHI). Ni haifaffiyar jihar Gombe ce a jamhuriyar Nageria. Gombe jiha ce dake Arewa maso gabashin Nageria, ta yi iyaka daga Arewa da Arewa maso gabas da jihohin Barno da Yobe, daga kudu kuwa da jihar Taraba daga kudu maso yamma kuwa da jihar Adamawa sannan daga yamma da jihar Bauchi. Ta samo asalin sunanta ne daga babban birninta, kuma yanki mafi girma a jihar wato babban birnin Gombe. Kuma an ƙirƙire ta ne daga shashin Jihar Bauchi.
Kamar yadda kuka ji sunan Mahaifina Kabir, wato Major Kabir Sulaiman Dabo. Soja ne da ya sha gwagwarmaya a gidan Soja har ya kai matakin Major kafin ya yi Retire(Ritaya), sunan Mahaifiyata Barrister Murjanatu Soron ɗinki. Bakanuwa gaba da bayanta danginta gabaɗaya mazauna soron ɗinki ne da ke babban Jihar Kano.
Lauya ce mai zaman kanta dake aiki a babban kotun Abuja wato Supreme Court Abuja. Mu huɗu cif iyayenmu suka haifa ni Mimi ne ce autar su
Dr. Sulaiman Kabir Dabo shi ne babba a yanzu haka likitan zuciya ne a asibitin Aminu kano.
Sai mai bi masa Madiha kabir sulaiman Dabo, ita yar kasuwa ce ita da mijinta suke da kamfanin sarrafa cafet da jakunkuna tare da takalma suna zaune a garin Lagos.
Sai Khadija Kabir sulaiman Dabo Lectureir ce a Kaduna state University, ita da mijinta dukkan su koyarwa suke yi a jami’ar ta kaduna kuma suna zaune a garin kaduna
Sai ni karamar su FATIMA wacce sunan kakarmu naci wacce ta haifi mahaifinmu wato Hajiyar Shagamu.
Wacce ta samu asalin sunan Hajiyar shagamu dalilin in aka ce mata wani zai je garin lagos a lokacin sai ta ce zai je dai Shagamu shike nan sai sunan Hajiyar Shagamu ya kama sunanta, in ana kiran gata to ni gata ce da kafafunta, na samu sunan Mimi saboda ina da sunan Hajiya yasa Abi ke kirana da Mimi tun ina ƙarama sai kuma sunan ya yi ta bi na har girmana. Iyayena sun yi zama a garuruwa da dama saboda aikin Abi ammh ni na taso na buɗe idanuwana ne a garin Abuja, tare da iyayena da yan’uwa tun da kuma na taso na ke cikin gata mai suna gata, gani ina da sunan Hajiyar shagamu sannan na shiga ran Abi yana kaunata sosai, na yi karatun primary ɗina zuwa matakin Jss3 a wata private school mai suna Regent Collage Abuja, daga nan sai na koma Jihar Gombe wajen kakata Hajiyar Shagamu dake zaune a gidan marigayi Alhaji Sulaiman Dabo da ya kasance fitatten ɗan jarida, kafin rasuwarsa shine shugaban masu yaɗa labarai na gidan gwammatin Jihar Gombe a wancan lokacin baya da ya shuɗe
Tun kafin komawa ta garin Gombe da zama, tun tasowa ta na fahimci ina son tafiye tafiye ina son na ga ina zuwa mabambamtan wurare domin ƙarin ilimi, amma kuma ban san zuwa ko’ina ba sai Gombe duk hutu anan garin gombe na ke yin sa Saboda Hajiyar Shagamu na sona ko da Abi bai so ba ita za ta kira ta ce a saka direba ya kawoni na yi mata hutu, ina son garin Gombe sannan ina son yanayin iskar garin, kuma ina son mutanen garin. ba saboda yana tushe na ba, a’a saboda da garin na saba, kuma asalin kakanin su Abi mutumin AKKO ne. Karamar hukuma karkashin jihar hombe sakamakon fitowa nemen ilimi da kuɗi ya sa suka tarwatsu a cikin jihar Gombe, Kuma duka ƴan’uwan mu da na sani suna cikin garin Gombe ne, tun da Abin mu shine Babba yana da ƙanne guda biyu mace ɗaya namiji ɗaya Alhaji Hamza Sulaiman Dabo, ɗan siyasar da ya yi fice a Jihar Gombe wanda kuma ya riƙe mukamin Senator mai wakiltan mu a majalisa, Sai Hajiya Halima(Yaddiko) itama a garin Gombe ta ke da zama ita da iyalinta, Shi ya sa in za’a ce na zaɓi garin da na fiso da kauna zan zaɓi Jihar Gombe sau shurun masaki ba tare da na sauya ba.
Zama na a garin Gombe ya sa na cigaba da karatuna a makarantar Joy Acadmey Gombe anan nayi candy, Bayan na kamallah sai na bar gaban kakata na yi sallama da Jihar Gombe na koma Abuja da zama daga can na samu gurbin karatu a Univesity of Ibadan in da na zaɓi shashin da nake son na karanta wato Mass Commucation a faculty of Sciences, nan na samu shedar Digirina na farko a bangaren Bechelors of Imformation and Communication Technology. Bayan na gama na koma garin Abuja nayi service ɗina(Bautar kasa) bayan na gama sai na nemi gurbin Master ɗina a jami’ar BAYERO da ke kano BUK.

A gidan yayana na zauna Dr.Sulaiman har na kamallah Master ɗina akan abin da ya shafi harkan Jarida, bayan nan ban koma gida ba sai da na samu Diploma akan abin da ya shafi Brodcasting saboda na karanta aikin jarida ne sakamakon sha’awata ta son karanta labarai a gidan Radio ko Tv. Bayan nan na karanta kwasa kwasai da dama wasu ta online wasu a makarantu dabam dabam sannan na hallaci Seminar kan abin da ya shafi Aikin jarida sosai domin na samu ƙwarewa akan haka, na koma gida ba daɗewa ba Abi ya samu hatsari daga hanyarsa ta zuwa Abuja daga gombe, ya samu tsinkewar Lakkansa ta baya(spinal cord) ayanzu haka baya tafiya sai akan keke yana garin Abuja tare da Brr. Murjanatu ta na kula da shi, ni kuma sai na nemi aiki a jihar Gombe da farko ba awannan gidan Tv na fara aiki ba, na fara aiki da wani gidan Jarida baya nan na bar su na koma nayi aiki da gidan Radion Sarauniya Amina na zama mai karanta musu labarai(News) daga nan ne gidan radion KARAMCHI suka nemeni nayi aiki da su na shekara ɗaya, kafin na samu promotion na dawo shashen telvesion a shashin labarai da al’amuran yau da kullum na gidan karamchi Tv. A takaice wannan shine cikakken Tarihin FATIMA KABIR SULAIMAN DABO.
“Masha Allah kyakyawan tarihi mai cike da darasin rayuwa tambayata ta gaba me ya sa kika zaɓi aikin jarida a matsayin ki ta ƴa mace? tun da na ga kamar mu maza mun fi yawa a wannan bangaran?
Sai da ta yi shuru na wani Lokaci kafin ta saki kayattacen mirmishin da sai da dimples ɗin ta hagu da dama suka loɓa kafin ta gyara zama ta fara faɗin.
Tun farko Burin Abi a kaina shine na zama likita irin yayana, sai dai ni ra’ayi na ba shi anan wajen, ban taɓa tunanin zan iya zamowa yar Jarida watarana ba, sai dai kasan Allah abin da ya kaddaro ma bawa bai isa ya kauce ma wannan bingiren ba.
“Ba ki faɗa min yadda kika tsinci kanki a matsayin yar jarida ba?
Uhm ni ma na tsinci kaina ne a matsayin yar jarida, sai dai akwai wasu kalamai da suka yi tasiri a rayuwata, tun ina yar shekara goma sha biyar wani ya taɓa ce min zan fi dacewa da yar Jarida mai karanto labarai saboda ina da zaƙin da karaɗin murya tun a wanchan lokacin, kenan kuma tun daga lokacin sai naji sha’awar haka ya ɗarsu acikin raina gaskiya wannan shine mafarin komai.
“Dakyau kina ɗaya daga cikin manyan taurarin gidan Tv na karamchi, mutane suna yaba miki sosai sannan kin kasance kamar madubin karamchi wani saƙo gare ki zuwa ga masoyan ki?
Ina godiya sosai da yabawarsu a kaina ina kuma jin daɗin hakan. Saƙon da nake da shi zuwa gare su shi ne su cigaba da kasancewa da gidan talabijin na karamchi domin ganin shirye shiryen mu a ko da yaushe, babu kosawa acikin aikin mu, in sha Allahu ni Fatima Kabir dabo( Mimin karamci) zan cigaba da kawo muku labarai dabam dabam da suke faruwa a jamhuriyarmu ta Nageria cikin Harsuna guda biyu wato turanci da hausa, kudai ka da ku matsa kusa da akwatin talabijin ɗin ku, Mimin karamcinku tana nan tare daku a koda yaushe in sha Allahu
“Ba ki faɗa mana ko shekarun ki nawa ba?
Shekaruna 30 talatin cif a duniya.
“Jikin ki sam bai nuna shekarunki ba. An ya ba kin ƙara ba ne saboda masu kallo su ƙara ganin girman ki ba?
Dariya ta saki da siririyar miryanta kafin Ta ce.
Haba dai Na misau kai ma kasan ba haka tsakanin mu, ƙaramin jiki na ne ke ɓoye shekarun nawa. Ammh tabbas shekarata 30 kamar yadda na faɗa farko
Dariya ya yi mata kafin ya gyaɗa kai yaba faɗin” Na yarda tun da kin dake a hakan ne ammh har yanzu ina da ƴar tamtama to maganar aure fa? Akwai ko an kusa?
Rufe bakinta ta yi da mayafinta kafin ta girgiza kai tana faɗin.
Kowa ya sani ba ni da aure.
“To niyya fa? Ko babu niyyar ne?
Akwai mana in Allah ya kawo wanda ya dace zan yi aure Na misau.
A yadda ta faɗi mganar sai da yanayin muryanta ya sauya, lokaci ɗaaya sai fara’an ta ya ragu kuma an fahimci hakane saboda kowa yasan Mimi mace ce mai fara’a kowa ya ya ta sauya masu kallo suna ganewa. Na misau ya kalleta itama sai ta kallesa
Mirmushi ta yi masa bata ƙara mgana ba shi kuma yace za su buɗe layukan wayarsu domin ba ma masu kallo damar kira, nan da nan ya zayyano lambobin da masu kallo za su kama su kamar yadda suka saba.
Jamilu Adam Na misau kenan mai gabatar da shirin tare da taurarin karamci Tv, sai Kuma bakuwar mako wato Fatima Kabir Sulaiman Dabo(Mimin karamci).
12:40pm.
Laraba.
Wata doguwar mota ce kamar kiran macapolo, sai dai bata kai ta tsawo ba keta sharara gudu a hanyar babban titin shigowa jihar Gombe.
Motar an yi mata kalan fenti yellow da Blue sannan a jikin motar an rubuta GOMBE UNITED da manyan harrufan baki.
Daga cikin motar hayaniya na tashi kaɗan kaɗaan, na hango cikinta kaf matasa ne masu jini ajiki acikin motar. Sannan suna sanye da kaya su ma rigar blue mai ratsin fari haka ma wandunan jikinsu duk kalan blue ne da Fari.
Ba’a jiyo mganganunsu tunda motar tana gudu sosai ga iskar mota, ammh sun yi gungun daga can baya suna kallon wani abu a wayar ɗaya daga cikin su.
Daga farkon kujerun daga na direba sai wasu guda biyu masu zaman mutum ɗai ɗai ta bangaren hannun hagu wani mutum ne ke zaune shima Irin kayan sauran ne ajikinsa, ammh shi ya fi su shekaru zai iya kaiwa hamsin da uku a duniya 53 sannan yana da saurin furfusa, tunda ta saman kansa ga furfura nan sun fara cika masa gashin kansa har wajen tsillin tsillin gemunsa. Waya ya ke yi acikin wayar yana faɗin.
” Eh gamu a hanya mun kusa shigowa Gombe ma.”
“Eh Kano pillars muka je, an tashi 2:01 an je gidansu an ci su wasa ba.”
Ya faɗa ya na sakin karamar dariya kafin ya ce” Shi ya sa nake faɗa maka samun AJI a cikin gombe United alheri ne, gayen ya iya buga kwallo fiye da yadda kake tunani.”
Ya faɗa ya na kallon gefensa kujerun dake hannun damarsa, wani matashi ne yana zaune shima da irin kayan dake jikin sauran sai dai shi ya sanya wata bakar Jaket a saman rigarsa sannan kansa akwai Pcap ya rufe rabin fuskarsa ya kuma lafe ajikin motar kamar mai barci, wata bakar Jaka a gabansa kamar irin ta yan makaranta baka.
Girgiza kai ya yi lokaci ɗaya da yar dariya kafin ya ce” kasan shi ya fi miskili iya miskilanci, tunda muka taso bai yi mgana ba kuma nasan ba barci yake yi ba, Ok zamu yi waya da zaran mun sauka. Yauwa take care.”
Daga haka ya katse kiran yana kallon na gefensa cikin muryansa mai kaushi kaushi ya kira sunanshi.
“Aji..”
“Captain..”
Bai amsa ba, illah motsi da ya yi kaɗan alamun yana jin sa sanin halinsa ya sa ya cigaba da faɗin” Coach na katsina pillars ne ya kirani ka gane shi? Madaki?
Kansa ya ɗan ɗago kaɗaan kafin kuma ya gyaɗa kai kaɗan alamun eh ya gane shi, ba tare da ya jira mganarsa ba sanin da ya yi daman ba mganar zai yi ba, ya sa ya ce” Ya ce na faɗa maka weldone an je kano an ci masu gida.”
Mirmishi kawai ya yi tunda ga saitin yadda bakinsa ya juya nan sai kuma daga karshe ya jinjina kai.
Tun da suka taso idanunsa biyu yana jin hayaniyar da ta fara cika motar, baya jin mgana ne ya so ya tsawartar musu sai kuma ya basar baya so ya zama mai yawan takura gare su, su ɗin Ƴan Team din shi ne a matsayinsa na Captain ɗin su kamar babban Yaya ya ke a garesu yasan suna jin tsoron sa, in ya tsawatar za’a ji kuma za a kiyayewa ammh ya kan zama mai ɗauke kansa akan wasu abubuwa ba saboda komai ba sai saboda tsira da mutumcinsa.
Ya na shirin gyara zamansa daga can baya yaji muryan musa Zinder yana faɗin”Kai jama’a ni dai Allah na gani ina son wannan baiwar Allah nan, tana burgeni, ta iya magana ga iya kwalliya mallam”
Ya faɗa har yana tagumi, Aji ya juya kaɗan yadda ba za su fahimci yana kallonsu ba a nan ya ga sanda Musa ya yi tagumi shi ke da wayar a hannunsa suna kallo.
Koma menene ya ke mgana akai a cikin wayar suke kallo.
Shuru ya yi ya natsu sai yaji ya fara jiyo sautin ta in da ta ke cewa.
Akwai mana in Allah ya kawo wanda ya dace Na misau.
Kamar ɗaukan iska haka yaji muryanta ta shigo jinsa, ita muryan ai bazata ɓoye masa ba, muryan da ya santa tun a zamanin da ba ta kai haka zaƙi da garɗi ba, wani abu ya ji ya daki zuciyarsa har sai da ya runtse idanuwansa saboda yadda yaji jikinsa ya fara rawa.
“Kai fa duk gidan Tv Karamci ba kyakyawa yar gayu irin Mimi wlh”
“Ni Mirmishinta ke burgeni..”
“Ni kuma salon yadda ta ke mgana ke sumar dani Baaba”
“Ni kuma kwalliyarta. Kai matar nan ta san kan kwalliya kowani kaya ta saka sai ya dace da ita.”
“Ni duk ina jin kune, kun ga in tayi mirmishi dimple ɗin ta suka loɓa sai naji kamar zuciyata zata fito waje, ba domin nasan ba za ta so ni ba, ai da tuni na gabatar da kaina wajen Mrs Dimple.”
Gabaɗayansu suka kwashe da dariya Kb ya daki Kafaɗan Sagai yana faɗon” In ma mafarki kake yi sagai gwara ka farka, kana jin tarihinta ubanta soja uwarta lauya ce yan’uwanta kaf masu kusa ne a kasar nan, kai a hakan kaka ke tunanin zata kula ka? Waye kai? Tarihin ka kenan ace kai Sangai ɗan kwallon kafa ne na kungiyar Gombe Untied wato golan su, baya nan ba ka da wani tarihin da wannan yarinyar za ta soka gwara ma ka daina mafarkin da ba zai taɓa zama gaskiya ba.”
KB na dariya yace”Kuma ta girme shi, tace she is 30yrs old sangai wannan uwarka ce ma, tunda in ka yi sauri ne 25 tsawon kafa ne kawai yasa ka ke ma kanka zarra da tusa kanka in da baka da Muhalli.”
Gabaɗayansu suka saka mai dariya suna jan rigan jikinsa, shi kuma sai ya wani warce wayar hannun Musa ya ƙamkame yana faɗin”Age is just a number, ni dai ina sonta in na ganta sai naji kamar zuciyata zata fito waje..” Ya faɗa cike da shaƙiyan da ya saba.
“Ina bukatar sauka a nan.”
Suka ji muryan Captain a kausashe, da ta yi sanadiyar katse musu shagalinsu.
Nan take kowa ya shiga taitayinsa cikin lokaci motar ta natsu kowa kuma ya koma wajen zamansa ya zauna yana zaren ido.
Direba ya juyo yana faɗin”Captain ba mu isa Camp ba fa?
Kai tsaye ya ce”Eh! Anan yau nake da ra’ayin Sauka”
Ya fad’a muryansa na shakewa kamar yana mura. Coach ya juya yana kallon Aji kafin ya koma yana kallon hanya.
Yanzu suka shigo gombe akwai nisa kafin cikin gari.
Da mamaki ya kalleshi kafin ya ce”Aji da nisa da cikin gari fa”
Kai tsaye ya kara faɗin”Ina bukatar sauka anan”
Direba ya juya yana kallon Coach kafin ya yi mgana ya gyaɗa masa kai alamun su tsaya.
motar na tsayawa ya tashi ya ɗauki jakarsa ya rataya ta bangaren hannunsa na hagu ya sauka daga cikin motar kafarsa sanye cikin wani katon booth din takalmi baki mai igoyoyi.
Sai da ya fita sannan ya ɗaga ma Coach ɗin su hannu, su musa sai leke amma ba bakin mgana, Kb ya yi ma Sangai raɗa yana faɗin”Ko surutun mu ne ya damu Captain ya sauka a farkon gari?
Sangai ya yi shuru bai yi mgana ba, amma baya tunanin haka, in da sun dame shi zai yi mgana ya ce su bari ko kuma ya ce za su yi gudun kilomiter 10 in suka koma Studion ammh yanayinsa yanzu ya nuna akwai wani abin da ke damunsa.
Couach ya buɗe window gefensa ya leka yana kiran sunan shi ganin har ya fara tafiya.
“Aji..”
“Coach..”
Ya faɗa lokaci ɗaya yana juyowa, kara kallon hanya Coach ya yi ya ga tafiya mai nisa kafin cikin gari kafin ya maida kallonsa kan Aji cikin lallashi ya ce”Kasan da wahala ka samun abun hawa zuwa cikin gari ko?
“Kafata fa? Miye amfanin ta?
Kai tsaye ya bashi amsar da haka, sannan bai tsaya ba ya juya ya cigaba da tafiya hannunsa daya rataye da jakarsa ɗayan kuma na cikin aljihun wandonsa, yana wannan tafiyar ta sa ta sassarfa ta cikakkun maza masu karfi da kuzari daga yanayin tafiyarsa zaka fahimci yana da zafin nama Zafzaf kamar wani ingarman doki.
Ɗan kwallo ne fa, har za’a nuna masa zafin nqma shi da jikinsa ya gini da komai cikin hanzari. Yana cikin tafiya motar ta zo ta wuce sa yana jin su Musa sun karaɗe da kiran sunan “Captain..”
Ya kuma gan su suna ɗagamai hannu, ammh ko yunkuramin maida musu martani bai yi ba, sai ma cigaba da tafiyarsa da yake yi, yana jin wani irin zafi a karkashin zuciyarsa kishin wani abu mai muhimmanci zai iya sarke masa numfashi in ya cigaba da zama acikin motar nan fitarsa shi ne mafita, adaidaita suna ta tsaya masa ammh bai tsaya ba tafiya kawai yake yi ba tare da ya gaji ba.
Da tafiyar ma taki masa sai ya koma gudu abinsa a saman hanya, zufa ta jika masa rigar jikinsa haka ta ke tsiyayo masa ta saman fuska, ammh bai dakata ba yana wannan gudun yana jin radaɗin dake cikin zuciyarsa yana raguwa tun daga farkon gari da kafarsa ya taka har anguwarsu ta arawa, sai anan ne ya samu abun hawa ya hau zuwa gidansa da ke tunfure, saboda baya so wani daga gidansu su ganshi labari ya kai kunnen Innar mu’azzam ko kuma ya haɗu da Baba.
A bakin kofar gidansa aka sauke shi ya fito da wallet ɗinsa daga cikin aljihunsa ya mika masa 500 ya juya mai adaidaitan na faɗin “Yallaɓai ga chanjin ka.”
Ba juyo ba ya ce”Ka rike chanjin”
Maidaidaita ya fara godiya shi dai bai ko Juyo ba, ya lalubo key din gidansa na karamar Kofa get ɗin milk, ajikin jakar da ke hannunsa ya buɗe gidan.
Ya shiga ya kuma rufe ta ciki, daga waje sai ka raina gidan sai ka shiga zaka fahimci ma mallakin gida baya bukatar kyan gida ta waje ta ciki an zuba aiki na kwararrun magina sannan shi kuma mai gidan ya saki kuɗi.
Gidan akwai fili sosai domin ga wata bakar 4matic nan a haraban gidan sai kuma mashin shima roba roba fara fake a wajen.
Ko da ya isa gabaɗaya jikinsa sharkaf da zuba, Kofar falon ya isa ya saka kafa ya turata sai ta buɗe daman ba a kulleta da makulli ba. Falo ne mai girma ba sosai ba, ba kujeru sai cafet babba da ya malale falon sai Plasma(tv) babba na bango sai dakuna jere guda huɗu rufe suke da Kofofi na farko na ga ya nufa ya saka hannu ya buɗe ya shiga ciki ya rufe.
Shuɗewar nintina talatin sai gashi ya fito ya sauya kayan Jikinsa da alamun har wanka ya yi, tunda ga gashin kansa nan da sanyin ruwa sanye yake da wando three quater, sai farar singileti sai alokacin fuskarsa ta bayyana tarwai.
Baƙi ne shi, mai murɗewan jiki Kana ganinsa ka ga bafullatani ko daga yanayin rsawonsa da Baƙin gashin kansa mai santsi, har ta gashin giransa da na Idanuwansa suna sheki ga shi baki silik, ba shi da saje sai da daga kasan gemunsa yana da gemu kaɗan da ya fito masa shima baki silif da shi gwanin ban sha’awa. Sannan yana cikar sumar kai, mai yawa baƙi silik da ke shan gyara sosai.
Yana da faɗi daga saman sa jikinsa kuma duk a murɗe ne sakamakon training.
baƙinsa mai kyau ne tunda har shining ya ke yi, idanuwansa matsakai ta ne, sai dai yana da karan hanci dogo da bakinsa dai dai misali.
Ƙaramin firizan dake falon ya je ya buɗe ya ɗauki ruwan gora ya kafa kai yasha fin rabi, sai ya rufe firizan ya kuma ijiye ruwan a saman firizan ya Juya yana tafiyarsa na zafzaf ya koma cikin ɗakin da ya fito.
Ya jima aciki kafin ya sake fitowa wannan karon hannunsa ɗauke da wayarsa ya fito ɗayan kuma hannunsa ɗauke da kujera fara ta roba, ya zo ya kafata acikin falon ya zauna yana harɗe kafafunsa waje ɗaya.
Tun yana salla ya ji ana ta kiran wayarsa, tunda ya ji kiran yaƙi ya kare ya zargi mutane guda biyu
Ko Bintu ko Mu’azzam.
Sune suke yi masa mahaukacin kira rututu ko bai so ba sai ya ɗauka in bai ɗuka ba, ba za kuma su fasa kiran ba.
Wannan karon ba Bintu ba ne ɗaan uwanta ne Mu’azzam, sai da yaga kiransa sannan ya tuna ya ce masa sun zo kano buga wasa, kenan yana can yana tunanin in sun gama buga wasa zai shigo wajensa.
Shuru ya yi yana wani tunani, Mu’azzam kamar mai hankali kamar kuma ya girma ammh bai daina abun yarinta ba, shi fa bai ce masa zai zo ba ballantana ya ce yana jiransa ne, kawai daga sun je buga wasa sai a ga ya ce za shi wani waje? Kamar wani yaro ƙarami.
Yana wannan tunanin kiran Mu’azzam GADDAFI DANJUMA ya shigo cikin wayarsa kamar yadda ya yi masa Saving.
Sai da ta kusa katsewa ya ɗaga kiran bai yi mgana ba.
Dagacan bangaram Mu’azzam ya ce”Kana ina ne? Ai kace min tun a jiya za ku gama wasan ko?
Sai da ya lumshe ido sannan ya buɗe kafin cikin muryansa ta kai tsaye ya ce”Eh mun gama.,” Mu’azzam yace”Suwa suka ci?
Kai tsaye ya ce”An ci masu gida.”
Mu’azzam ya ce”Good Ajin Jihata nasan za ka yi musu cin cikin gida ne.”
Mirmishi ya yi ba tare da ya yi mgana,
Mu’azzam ya ce”Yaushe za ka taho?
Yau saboda kai na dawo daga office da wuri fa”
Daman yasan za’a rina cikin dakushe muryansa ya ce”Na taho ina? daman nace maka zan zo ne?
Da sauri Mu’azzam ya ce”Ban gane ba? Kana ina ne?
Kai tsaye ya ce”Ina gida”
Mu’azzam baki ya saki kafin ya ce”Wani gida kuma?
Aji ya ce”Wani gida gare ni?
Mu’azzam ya ce”Mallam sidi ko anguwan Arawa ko Tunfure?
Cikin Kosawa ya ce”Mallam Sidi tushe na ne, anguwan Arawa kuma nan ne gidanmu, Tunfere kuma muhallina ne, ina Tunfere yanzu haka.”
Cikin ƙarin Mamaki Mu’azzam yace”What! Gombe?
Sai ya juya yana kallon matarsa Hibba tana ta kai da kawo tsakanin Kitchen da falo domin shiryama ɗan uwansa abincin tarba ammh wai yana faɗa masa yana Gombe.
cikin jin haushi ya kira sunanshi.
“MANSOOR..!”
“MU’AZZAM.!”
Shima ya ambaci sunan shi, cikin takaici Mu’azzam ya ce”Tun safe da na faɗa ma Hibblove za ka zo wlh ta kasa zama waje ɗaya tayi maka girke girke yafi kala uku, akwai sarewa na faɗ mata ba za ka zo ba? ya za ta ji? Kuma don Allah ya kake son mu yi da abincin?
Kai tsaye ya ce”Ku yi ta ci har sai kun gaji, ni ban ce maka zan zo ba, faɗa maka kawai na yi mun shigo kano buga wasa, wa ya ce ka je ka faɗa ma matarka na ce zan zo? Mun yi haka dakai tsakanin ka da Allah Mu’azzam? sai Mu’azzam ya kasa mgana cikin ajiyar zuciya ya ce.
“Baban Inna.”
“Ɗan inna.”
Read Also: Tsutsar Nama Complete book
Shima ya maida masa, daga haka Mu’azzam ya saki huci kafin ya ce”Ai shike nan.” Sai kuma suka katse kiran a tare, mirmishin gefen baki ya yi kafin ya jinjina kai yasan yanzu za’a kai ƙaransa wajen Inna , yau in ya je anguwan Arawa ya san zai sha faɗan bai kyauta tunda bai je ya ga Mu’azzam ba.
Har zai sauke wayar sai kuma wani tunani ya faɗo masa da sauri ya kunna data ya shiga Facebook searching ya shiga ya saka sunan Karamci Tv.
Sai ga jerin shirye shiryensu ya bayyana, da ga vadion ma kafin ya shiga fuskarta ne cikin mirmishi tare da loɓawar dimple ɗinta Daga kasa ya ga daga ɗora vadeo 1hr ago har an masu kallo 2k comment kuma 1k.
Ƙankancewa Idanuwansa suka yi, ƙaramin tsaki ya ja kafin ya fita daga wajen gabaɗaya, ya koma ya na hura iska daga cikin bakinsa, sai ya ji kamar cikinsa ya ɗauki zafi rau ita kanta isar bakin nasa ma zafi take fitarwa.
Duk iya ƙokarinsa na kar ya kara komawa sai da ya kara shiga ya kuma danna hannunsa ya yi cliking ɗin vedeo.
Daman suna ɗora duka shirye shiryensu ta shafinsu dake facebook wato karamci Tv.
Tausayi ne ya kaishi ko nace rabon yau ya yi kwanan bacin rai da bakinciki, fuskar ta tar take kamar ko yaushe babban abun jan hankali daga gareta zaƙin muryanta.
Iya tsara kwalliya da shiga mai kyau da tsari yanzu ɗin ma wani leshi ne ajikinta mai kalan blue mai duhu da pich, ta yi ɗinkin doguwar riga fitted ta saka mayafi pich mai raga raga na ya yi, sai kuma ɗaurinta mai taken Zahra Buhari, kunnuwanta da hannayenta gold ne hatta ko zabban hannunta ta yi ƙayatacciyar kwalliyarta ta saka kalan jan bakin da ta ke yawan Amfani da shi mai kalan kalan deep blue ja ja kuma, in ta yi dariya sai fararen hakoranta su kara haska kyakyawan farar fuskarta su bayyana tare da hakorin makkanta shima yana kyalli sai ya kara mata kyau da kwarjini.
Fatima Mimi kyakyawa ce ajin farko acikin mata, daga saman kanta kwantattacen gashi da kana gani zaka fahimci tana da sumar cikar gashi.
Hancinta dogo da ƙaramin bakinta wanda saman ya yi tudu kaɗan ga cikar naman lebe, sannan fuskarta tana da ɗan faɗi kaɗan ƙaramin jiki gareta da ya dace da kyakyawan suranta.
Shekarunta ya fi ba ma mutane mamaki, ammh tarihinta bai ba su mamaki ba saboda daga ganinta yar manyan mutane ce, ko daga yanayin shigarta da yadda take hawa kaya masu tsada da yarari.
Tsabar yadda ya ke jin zuciyarsa na wani fat! fat! Kamar zata faso kirjinsa ta fito ya sa ya sauka daga vadeon sai dai rawan da hannunsa ke yi ne ya sa ya faɗa comments section bai sani ba, nan ya ga abin da ya kusa tarwatsa masa tunani da zuciyarsa gabaɗaya.
“Adadin mutane nawa ne suke kallonta?
“Maza nawa ne suke jin ta na burgesu?
“Maza nawa take ba ma sha’awa? Maza nawa take ɗaukan hankalinsu da kyan suranta da kwalliyarta?
Tambayoyin da suka cika masa zuciya kenan, lokacin da ya ga comments ɗin maza rututu.
Yawanci suna faɗin jikinta ya ɓoye shekarunta, sai masu faɗin.
“Mimi mai kyau ki na burgemu”
“Dimple bbym Tauraruwar karamchi”
“Ni dai ina son ki Hajiya Mimi, kin iya kwalliya da ado.”
“Ni kuma ina son yanayin turancin ki, zaƙin muryan ki na tafiya damu.”
“Ina son dariyan ki Mimi,kin haɗu kin haɗu kin ga ji da haɗuwa.”
Gabaɗaya sai yaji jikinsa na rawa jiyoyin kansa suka mike raɗau zufa kawai ke keto masa kamar an watsa masa ruwa, ya dunkule hannunsa na hagu ya ɗaga zai naushi fuskar wayarsa sai wata zuciyr ta ce” Mansoor kana da dalilin yin hakan ne?
Ka manta sharaɗin da iyakar dake tsakanin ka da ita? In ma maza dubu ne zata burge su ji sha’awarta bai kamata ya dame ka ba”
Sai kawai ya koma ya sauke hannunsa ya na sakin huci a fili ya furta.”Hakane bai kamata na damu ba, ita ɗin banza ta je ko mazan duniya za ta aura ma bazai damu MANSOOR AJI ba, ba zai dame ni ba.”
Ya ke faɗa yana kara ma kansa karfin gwiwa, dalilin da yasa wayarsa bata sha naushi ba kenan, sai ma tashi da ya yi ya koma ciki.
Bedroom ne mai ɗauke da cafet da katifa sai kuma hanger mai Dlɗauke da kayansa na sawa, sai takalma ga su nan zube a gefen dakin duk an warwarsa su.
Kwanciya ya yi saman katifar kwanciyar sama ya hard’e hannayensa yana kallon rufin ɗakin wayarsa kuma ya kasheta gabaɗaya.
Vya daɗe yana kwance kafin ya samu barci sai bayan la’asar ya tashi ya yi sallah key ɗn motarsa ya ɗauka ya fita. Sai da ya buɗe get din ya fita da motar sannan ya dawo ya rufe ya koma ya shiga motarsa ya fita.
Abinci ya je restaurant ya siyo da ruwa da lemun maltina kowanne katan, dag anan gida ya dawo ya ci abincin. Farar shinkafa da miyan naman rago. Bayan ya natsa anan tsakiyar falon ya fara training ɗin sa.
Yana sama ya na kasa zufa ya ke yi ammh bai dakata ba har aka kira sallar mangariba.
Sannan ya tsaya ya koma ɗaki ya yi alwala ya sauya kaya zuwa manya kaya na shadda mai ruwan kasa harda hula saboda ya rufe sumar kansa tabbas in Baba ya ganshi da sumar nan sai ya yi masa faɗan rashin yin aski.
A mashin wannan karon ya bar gidan sai anguwam Arawa, a masallacin layinsu ya tsaya ya yi mangariba.
A masallacin ya haɗu da su Baba ɗanlami da Baba Sani. Sun rigashi fita daga waje shi kuma sai da ya gama addu’o’in shi sannan ya fito.
Daga nesa ya hangesu tun da akwai hasken inji a bakin masallaci.
Shi kuma yana fitowa matasan anguwan suka yayyameshi suna masa kirari da sunansa.
Wato Ajin jihata.
Shi kuma ya ba su hannu suna musabaha, suna mgana sai da ya yi mirmishi kuɗi ya lalubo aljihunsa ya diɓo baisan adadin su ba, ya mika ga wani daga cikinsu ya ce su raba a tsakaninsu.
Suka saki Ihu suna faɗin”Allah ya taimaki Ajin jiharmu da ikon Allah sai ka ɗauko mana Kofin duniya.”
Mirmishi kawai ya yi musu ya wuce zuwa in da ya kafe mashin ɗinsa, kusa da mashin din su Baba Ɗanlami ke tsaye suna kuskus.
Suna ganinsa suka fara washe masa baki suna fad’in”A’a Mansoor ne an dawo garin kenan?
Baba Sani ke wannan rawan bakin mganar kallo ɗaya ya yi masu kawai sai ya ɗaaga musu hannu yana Fadin”Barkan ku da dare” Daga haka ya hau mashin ɗin sa ya tada kuma ya bar wajen da sauri.
Baba Ɗanlami ya rike baki yana kallon kaninsa Muhammad Sani.
Kafin ya yi mgana Baba Sani ya kaɗa kai ya ce”Eh lalle wato dai shi wannan Agolan yaron bazai taɓa sauya halinsa ba ko?
Baba D’anlami ya ce”Uhm ka gani dai, yaron nan fa ya raina mu ba mu ci darajan ya zo gabanmu ya gaishemu ba sai dai kawai ya ɗaga mana hannu yana faɗin barkan ku da dare kaamar wasu sa’aninsa”
Ya karishe faɗa yana kwaikwayon yadda Mansoor ya yi musu mgana.
Baba sani ya ji ciwon abu fiye da kullum maganar gaisuwa ba ta dameshi ba daman ai sun saba in dai yaron nan ne bazai taɓa ganinka ya ce maka ina yini ba? Sai dai barka da safiya in da safe ne in kuma da rana ne yace barka da rana.
In kuma da yammah ne yace barka da yammah in dare ne yace barka da dare.
Ba za ka taɓa cin darajan ya ce maka ina yini baba wanne ba? Ai shi bai san wannan tarbiyan ba, ko yara ne suka ce masa ina yini? Sai dai yace barka yaro kamar ya gagari kowa. Shi abin da yafi damunshi suna ganin shi su san za su samu kuɗi sun tsaya ya zo su yi masa maula susan in ya tashi ba ka kuɗi ba kaɗan ya ke ba ka ba babbar kyauta yake yi shi.
Baba Ɗanlami ne ya katse shi da faɗin”Kuma duk Yaya Ɗanjuma ne ya sangarta yaron nan komai akace ya yi sai ya ce ayi hakuri maraya ne, amana ne a hannuna ku tayani rike amanar yaron nan Sani don Allah.”
Baba Ɗanlami ke mgana yana ƙwaikwayon mganar yayan nasu Ɗanjuma.
Baba sani ya yi ajiyar zuciya kafin ya ce”Ai fa ga shi nan Agola yazo yafi masu gida arziki da samun ɗaukaka, kaf ƴaƴanmu ba wanda ya kai yaron nan nan samun duniya.” Baba Ɗanlami ya ce”Kai ina rabaka an ce Ƴan ƙwallo kudi suke samu mahaukata ma kuwa, kai daga yanayin gyaran da ya yi ma gidanmu zaka fahimci yana da kuɗi ga yadda ya gyara ma Meri ɗakinta kamar na wata yar boko, ni fa Auwalu ke gayamin a kungiyar da yake buga kwallo shi ne shugabansu ko Kaftin ne ake kiranshi da turanci na dai manta, ammh maganar gaskiya yaro nan ya sha kwana shi ya sa ya ke mana kallon haɗaarin kaji.”
Baba Ɗanlami ya ja gauran numfashi kafin ya ce”Mu tafi gidan Sani, duk tsiyarsa bai isa ya sallami Yaya Ɗanjuma mu bai sallame mu ba”
Baba sani yace”Kwarai kuwa.”
Haka suka jera suna tafe suna mganganganu Baba sani faɗi yake yi”Har Yaya Danjuma in ka lura ya fara famkama a anguwa shi wai adole Agolan da ya rike ya samu duniya, ba ka ga ko wamzanci yanzu baya zuwa ba sai da ya yi mana mgana ba.”
Ɗablami yace”Wlh na lura ko jiya sai da muka yi mgana da Gaje ta ce sai fankama yaya Danjuma yake yi, Meri kuma daman kasan halinta dariyan hakori ita a dole ɗanta ne mai arziki a gidan Wanzamai gabaɗaya.”
“Ka daina fa danganta shi da gidan Wanzamai, ka ce Agolan gidan wanzamai kuma bai fi ƴayanmu ba sa’an rayuwa kawai ya samu su ba su samu ba, ni fa kamar na ce ko Yaya Danjuma na shige shige ne, ka duba fa duka ya’yansa sun samu duniya yanzu Mu’azzam fa babban Ɗan sanda ne yana kano in ya tashi zuwa kaga motar da yake zuwa da ita da shi da matarsa da ɗansu gwanin sha’awa ga kayan abinci da yake zuwa da shi cikin alfahari Meri ke rabawa sasa sasa ita adole ya’yanta masu arziki.”
Baba sani ya faɗa bayan ya katse Baba ɗanlami.
Dukkansu a tare suka kalli juna kafin su ja gwaron numfashi.
Suka cigaba da tafiya da sauri sauri suna kuma tafe suna zagin Yaya Ɗanjuma da matarsa Meri da ya’yanasu Mansoor da Mu’azzam.
**
Har cikin gida ya shiga da mashin ɗin sa Mariya na cikin ɗakin Magajiya taji karan mashin da sauri ta fito da ya ke Sashen magajiya ke Farko kafin na Inna Merin
sauran sasan kuma da ya gyara gidan sai ya fitar musu da kofar su ta can, shashen iyayen sa kuma ya fitar musu da tasu kofar daga kudu.
Yana kokarin kafe mashin ɗin sa ya ji muryan Mariya ta na faɗin”Yayanmu sannu da zuwa.”
Ta faɗa cikin muryanta mai sanyi, sai da ya kafe mashin ɗin sannan ya dago yana kallonta tana tsaye tana ta yi masa mirmishi.
Akwai wutar nepa hasken farin kwan lantarkin dake waje ya haske masa ƴar farar fuskarta. Cikin rashin sakewa ya ce”Yauwa.”
Daga haka ya wuceta dai dai lokacin da magajiya ta fito daga makewayi da buta a hannunta. Sai ya shigeta zai shige koridon Maman Mu’azzam shi ya sa bashi da mafita sai sun haɗu.
Bai tsaya ba yana gota ta sai ta ji yana faɗin”Barka da dare Magajiya.”
Ta juya ta na kallonsa cikin harzuka da ɗaga murya ta ce”Ji min wulakamci da reni, in ba za ka iya kirana da suna Mama ko Umma ba sai ka sakaya sunana ka ce Maman Auwalu ko maman Mariya ammh ba ka rika kirana da sunana Magajiya gantsal ba, wannan dai sam ba tarbiyan ba ne.”
Ta gama faɗa ta na faman hararan bayanshi, shi dai bai ko juyo ba mamaki ya cikasa to me take son ya kirata?
Ya ga dai ko ƴa’yanta da ta haifa ma tun yana ƙarami ya ji suna gatsa sunanta Magajiya kuma bata damu ba sai shi don yau ya kirata da magajiya sai ta ce ba tarbiya ba ne?
Yana wannan tunanin yaji ta na fadin”Har kina wani fita kina gaishe shi don ubanki to ni nan uwarki ban ci darajan ya ganni ya ce min ina kwana ba, na kara ganin kin gan sa yazo kin fito kina yi masa dariya ki gani in ban falla miki mari ba.”
Bai juyo ba ammh ya san baki Mariya ta tura kafin ta ce”Kai magajiya Baba fa ya ce yayanmu ne.”
Daga murya tayi kafin ta ce”Karya ne wlh, Agola ne ba ɗan gida bane, ba ku haɗa komai da shi ba.”
Ya ji sanda ta furta kalmar agola, adai dai lokacin ya yi sallama ƙofar ɗakin Maman Mu’azzam. Inna Meri uwar Mansoor Innar Mu’azzam.
Idan an Cizaa Part 2
Page 2
A tsakiyar falon ya ci karo da Inna Meri tana tsaye ita da Walida, ya yi sallama suka amsa gabaɗayansu. Tun kafin ya buɗe baki ya fara gaishe da Inna Walida ta yi zaraf ta ce”Yayanmu barka da dare”
Saboda sanin halinsa yanzu tana cewa ina yini sai yace bai ga yinin ba, sai dai ta ce masa barka da dare. Cikin mamakin ganinsu a tsaye ya ce”Barkan mu lafiya na gan ku a tsaye, Innanmu lafiya kuwa?
Inna Meri wata bakar dattijuwa kallon farko za ka yi mata ka fahimci ta fito daga shiyar sokkoto ne, sannan ta haɗa jini da Arawa, saboda gefen bakinta dama da hagu ga zanenta na Arawa nan ɓaro ɓaro ya bayyana duk da ko ta na baƙa na iya ganinsa. Sannan sai alokacin na fahimci in da Mansoor ya ɗauko tsawon sa, Inna Meri doguwa ce sosai mai kaurin jiki kuma.
A shekarunta iyakarta 56 zuwa da bakwai a duniya ba ammh yanayin jikinta bai nuna wahala ba sosai tana sanye da hijabi ne a jikinta hannunta kuma casbaha ne, daga gani ta idar da sallar mangariba ne tana lazimi. Cikin yanayin maganarta ta ce”Tun da naji Kwakwazon Magajiya na ce to Baban Inna ya shigo gidan” Mirmishi ya yi ba tare da ya yi mgana ba, Walida tayi saurin shimfiɗa masa darduma sanin halinsa bai son zaman kujera duk ko da irin tuma tuman kujerun alfarman dake mamaye da falon na inna Meri ko wata amarya albarka. Cikin natsuwarsa ya zauna itama Inna Meri sai ta samu daga gefensa ta zauna saman cafet mai taushi dake malale a cikin ɗakinta.
Cikin yalwataccen fara’an da ba a raba fuskarta da shi ta ce” Tun fa ɗazu muke ta duban hanyan ka ni da Babanku muka ji ka shuru.” Daman yasan tuni labarin dawowarsa ya zo musu tunda Mu’azzam ya ji labari. Kansa na kasa ya ce”Innarmu kun yi mgana da Mu’azzam ne?
Cikin jimami ta ce”Ya kirani kamar ya yi kuka Baban Inna ba ka kyauta ma ɗan Innna ba gaskiya, me ya sa ba ka je ka duba ɗan uwanka ba?
Kai tsaye Ya ce”Inna wasa muka je bugawa kamar kuma wani mace sai a ganni daga zuwa wasa ina faman biye biye
Inna Meri ta ce”To menene? ba wajen ɗan uwanka za ka je ba? ya ce matarsa ta kasa zama waje ɗaya saboda zuwanka maganar gaskiya Baban Inna ba ka kyauta ba.”
Ba ya son jan mganar ya sa Ya ce”Shike nan ki yi hakuri Innarmu, Ina Baba ko a masallaci ban gan sa ba?
Inna Meri tace”Tun ɗazu abokinsa Mallam Hashimu ya kirasa kan dai zaman da ake yi akan auran ƴarsa maigado shi ne ina ga har yanzu ba su kai ga matsaya ba.”
Cikin mamaki Ya ce”Auran ya mutu ne?
Tana gyara zama ta ce”To abin dai nasu sanin gaskiya sai Allah ita ta ce ya saketa shi kuma ya yi rantsuwan bai furta mata saki ba sun dai yi sa’insa har ya dake ta”
Mansoor ya yi shuru bai yi mgana ba, yana ji Inna Meri ta cigaba da ba sa labarin yadda akayi jin ta kawai ya ke yi hankalinsa na wani wajen kuma.
Walida ya ke hangowa ta cikin uwar ɗakin Inna Meri ta na karatu sai dai baisan me ta ke karantawa ba. Ya buɗe baki zai kwala mata kira kenan Inna ta riga sa, tana fitowa ta kalleta tana faɗin”Ke mara wayau baki kawo ma yayan naku ko ruwa ba?
Da sauri Ya ce”Ba na jin kishi Inna”.
Kallonsa ta yi kafin Ta ce”To abinci fa?
Kai tsaye Ya ce”Inna zan ci tuwo ammh ba yanzu ba sai na kusa tafiya.”
Daga haka ta girgiza kanta kafin ta ce”Shike nan kun dawo oafiya ko? Ina fatan an samu nasara? Cikin sakin fuska ya ce”Lafiya lau Innarmu, an samu nasara in sha Allahu.”
Nan Inna ta cigaba da kwararo addu’o’i yana amsa mata da Amin Amin. Walida kuma tsalle ta buga tana faɗin.
“Yayanmu kun ci ƴan kano kenan? eyye na ji daɗi daman yau a makaranta ana ta labarin ƙwallon da aka buga tsakaninku da yan kanon”
Kallonta ya yi lokaci ɗaya yana hararanta kafin ya ce”Ke ba karatu ki ka je yi makaranta ba labarin kwallo yake kai ki kenan ko?
Ta na jin haka ta yi sum sum ta wuce ciki Inna Meri ta ce”A’a ƙyalemin Auta, ita ke bani labaran ƙwallon naku ni kasan ba gane abun na ke yi ba, ranar ma a tibi ta ga an nuno wasu ta ce min Innarmu wata rana za ki kalli Baban Inna acikin tibin na ce Allah ya nuna mana.”
Yana Mirmishi ya amsa ma ta da Amin.
Hira suka cigaba da yi Inna Meri na faɗa msa ta yi waya da mutanen mallam Sidi sun ce ya ji ma bai je ba Goggonsa yalwa har ta yi rashin lafiya kwanaki.
Yana duba agogon fatan da ke hannunsa ya ce”Zan je Inna ba na samun zama ne, ammh zuwa karshen watannan zan ga abin da Allah zai yi.”
Inna Meri ta ce”Ya dai kamata ko ba ka kwana ba, Mu’azzam yafi ka son zumunci yanzu haka duk zuwan da zai yi garin nan sai ya leka wajen yan’uwan mahaifiyarsa ya gaishesu ka ga hakan ai yafi da ace mutum kwata kwata baya zuwa.” Kai tsaye ya ce” Hakane Inna zan kokarta in sha Allahu.”
Wayarsa a ka kira yana ganin Coach ne ke kiransa ya ɗaga suka gaisa nan ya ke faɗa masa gobe da safe suna da morning Training, da kai ya amsa mishi sannan ya sauke wayar dai dai ookacin da ya ji gudu da dariyan yara daga koridon shigowa shashen inna Meri kafin ya yi mgana ya ji Inna na faɗin”To ga shugabanin yan kiriniya nan sun dawo.” Kafin ma ya samu zarafin mganar sun faɗo ɗakin da gudu sauran kaɗan su ture Mansoor dake zaune.
Sai da ya daka musu tsawa sannan suka fahimci yana ɗakin.
Sai suka natsu sum sum suka koma bayan inna Meri suka tsaya suna fiki fiki da ido kamar za su yi kuka.
Inna Meri ta juya ta kallesu kamar tayi dariya sai kuma ba ta yi ba.
Ta jawo Hassan jikinta shi kuma Hussaini ya lafe a bayanta.
Cikin sigar lallashi ta ce”To sojojin Inna ba ku gai da kawun ku ba.”
Daga jikinta suka hadɗa baki wajen faɗin.
“Kawu ina yini.”
Kai tsaye ya ce”Barka da dare ake cewa ina yini ba gaisuwa ba ce kun ji ko?
A tare suka ɗaga masa kai, yan biyu ne masu tsananin kama da juna.
Inna Meri ya kallah kafin ya ce”Daga ina suke Inna? kuma wa ya kawo su?
Inna Meri ta mikar da Hassan ta na ce musu su shiga ciki wajen uwarsu Walida, sum sum suka wuce suna tafe suna taɓa juna ba Halin su yi mugun wasa yanzu kawun su ya za ne musu jiki su san Halinsa ai tunda a ɗakin Inna Meri suka yi yaye, bai damu da kankantarsu a lokacin ba, da sun fara ma Inna kukan banza in da yazo gidan sai ya zane su. Da suka gane shi suna ganinshi suke shiga taitayinsu yara ne yan shekaru biyar zuwa shidda.
Sai da suka Shige Inna Meri ta fara faɗa masa cewa Bintu ce ta kira waya ta ce Walida tazo ta na son ganinta ashe wai faɗa tayi da miji da kishiya shi ne ya sa ta ce Walida ta tattaro yaran ta kawo mata su yi kwana biyu a hannunta
Cikin takaici ya xe”To Inna makarantar su fa? Inna ta ce”Walida ta ce ko an basu hutu, sai ranar litini za su koma, Bintu finitinanniyar yarinya ce Baban Inna ba ta jin mgana tunda Basiru ya aureta wlh bai huta ba, ta addabeshi ta addabi matarsa, kuma shi yana jin kunyar Babanku ne shi ya sa yake raga mata amma al’amarinta sai kara gaba gaba kawai yake yi, Walida ta gaya min ta ce sanda ta shiga gidan Bintu na tsakar gida tana na bala’i uwargidanta na cikin ɗaki ba ta fito ba amma haka Bintu ke zage zage kamar ɗiyar maguzawa.”
Mansoor ya yi shuru na wani lokacin yana jin Inna na faɗin “Ku shiga mganar kai da Mu’azzam Babanku bazai iya da fitinarta ba.” Sai kawai ya jinjina kai kafin ya ce”Ko Bintu ta fara hauka ne ba mu sani ba Inna?
Inna meri kamar tayi kuka ta ce”To ga dai shi, abubuwan da take aikatawa ba na masu hankali ba ne.”
Kai tsaye ya ce”Inna laifin ku ne, kunsan cewa Bintu bata san ilimin zaman aure ba me ya sa kuka aurar da ita? kuma shima Bashir ɗin wawa ne kamar shi yana namiji ashe ban sani ba sakarai ne? ta ya ya yana namiji zai zauna mace ƙarama kamar Bintu na juyasa? Ita ke auransa ko shi ke auranta?
Ya karishe faɗa cikin ɓacin rai, yana jin takaicin yanzu nan in ransa ya ɓaci sai ya ta ka ya je har gidan ya ci mata mutumci tunda ya fahimci ta fara zama mahaukaciya.
Ganin ya fara harzuka ya sa Inna Meri ta sausauta tana faɗin”Ka bari zuwa gobe ka kira shi Bashir ɗin da ita kanta Bintu ka ji abunda ya faru, nima ban ce ka raga mata ba, ka ci min mutumcinta tunda sakara take mara wayau.” Karamin tsaki ya ja kafin ya ƙwalama Walida kira ta fito da sauri tana faɗin gani yayammu. Idanuwansa har sun fara sauya launi ya kalleta yana faɗin”Me kika je kika iske Bintu nayi a gidanta?
Walida ta ce”Sai faɗaa ta ke yi tana zage zage wai duk wanda yaci amanarta ba ta yafe ba tac e na tafi da su Hassan sai Yaya bashir ya gane bashi da wayau.”
Inna Meri tace”Kai Jama’a me Bintu take son zama ne ni Meri?
Shuru ya yi yana wani tunani, bai ɗauka haukan Bintu ya kai haka ba.
Yana ji Inna na faɗin “Fitinar Bintu ya yi yawa, fitannannu biyu Allah ya bani cikin ya’yana da kai da Bintu kai na samu saukin naka Fitinar itace yanzu take son kasheni da bakincikinta.”
Da sauri ya ce”Ki daina haɗaani da ita Inna ni halina ba irin na Bintu ba ne, wannan fa mahaukaciya ce.”
Inna Meri tace”Hmm ka ma fita, yanzu ne ka daina jawo fitinar da ta fi karfinka Baban Inna.”
Ya na jin ta ɗauko wannan mganar ya yi saurin mikewa ya fice yana ce mata an kira sallar Isha’i zai je ya yi sallah ya dawo.
Daman tasan bazai zauna ba, shi da bayason mganar kwata kwata. To kuma gaskiya ne shi ai fitinarsa ba mai iya kwantar da ita sai Allah. Ga bakar Zuciya kamar Kuturi ga kafiyan tsiya ita fa tana ganin Bintu ko kama kafar Baban Inna ba ta yi ba wajen fitina da taurin kai.
Shi zata iya cewa ta wajen dangin Ubansa ya ɗauko wannan hallayar, ita Bintu fa? Ta rasa gidan uban da ta ɗauko hallayan fitina da rashin son zaman lafiya.
Tana jin Walida na faɗa mata ɗakin Bintu duk an fasa kwalaben turaren wuta tana tunanin kila ma dambe tayi da yaya bashir ɗin kafin ya fita. Inna Meri ta mike tana faɗin”To Allah shi ya ye ma Bintu wannan bala’in bani iyawa da halinta ni kam in ya gaji shi basirun ya sakota ta dawo gida ta zauna.” Daga haka ta mike ta shige ciki domin ta da sallah.
Su Hassan sun yi barci ba mugun wasa.
A can masallaci Mansoor ya haɗu da Baba da abokinsa makocinsu Mallam Hashimu, albarkacin Baba yasa suka dawo masallaci tare da su Baba Sani, a kofar gida suka tsaya wannan yace bashi da abinci Baba sani ke faɗin ko ƙwayan hatsi babu a bangaransa Mansoor ya taimaka masa.
Baba Danjuma na gefe kamar ya saka kuka gabaɗaya ƴan uwansa sun zubar da kimarsu da Allah ya basu, sun koma maula wajen wanda ya ke matsayin ɗa a wajensu.
Bai ce bazai ba su ba, kudin da ke Jikinsa duka ya kwashe ya ba su 20k ammh ya ce musu in ya dawo zai ƙara musu, suka karɓa ko Godiya domin sun raina abunda ya ba su. Ko kunya suka wuce bangarensu Baba Ɗanjuma ya sauke Numfashi kafin ya ce”Ka yi hakuri Mansoor kaji ko?
Kansa na kasa ya ce”Haba ba komai Baba suma iyayena ne yadda zan yi maka abu suma suna da haƙƙin na yi musu.”
Jinjina kai kawai Baba Ɗanjuma ya yi yana ta saka albarka. A kofar gidan suka tsaya Mansoor ɗin ya kawo masa mganar Bintu.
Baba Danjuma ya ce”To ni sha’anin Bintu ya fara isata yarinyar nan ba ta jin mgana.”
Mansoor yace”Baba ba ita ta haifi kanta ba. Ubanta zata ci wlh tunda na lura ba ta da hankali.”
Baba Ɗanjuma ya ce”To kila kai in ka yi mata magana ta gyara, ammh ni da Meri har mun gaji da yi mata nasiha mun ƙyaleta, yaro nan kunyata yake ji shi ya sa bai ɗauki wani mataki akanta ba, ammh sha’anin Bintu ya wuce hankali, kwata kwata ba ta daraja mijinta ta zame ma sa fitina a gidansa.” Mansoor jinjina kai kawai yake yi yana tunanin gobe daga studion gidan Bintu zai wuce yana so ya ga Iskancin da aka ce tana aikatawa ne.
Ga shi shegiya bata san komai ba sai hauka, ya’yanta ma ba ta iya kula da su sai dai ta kawo ma Inna ta dinga wahala da su, to a gobe zai saka Walida ta maida mata ya’yanta in bazata zauna da ya’yanta ba to ta aika su wajen kakarsu ta bangaren uba,
Amma ba gidan su ba.
Tare suka shiga gida da Baba Ɗanjuma, ranar Magajiya ke da Miji tana ganinsu tare ta fara masifa tana manganganu ganin haka yasa Mansoor bai tsaya ɗakin Baba Danjuma dake tsakanin Korodon Inna Meri ba, sai ya shiga falon Inna Meri ya zauna Walida ta zuba masa tuwon masara da miyar kuka yana ci suna hira da Inna har ya kamallah yace kuma a ijiye masa ɗumame da safe in ya dawo training zai shigo ya ci.
Karfe goma ya bar gidan ko ɗakin Baba Danjuma bai leka ba tunda Magajiya na ciki yana shiga sai kuma ya jawo tijara, tunda ita kam tun yana ƙarami yasan ta tijararriya ce ba ta raina abun mgana musamman ma shi da ta ke ganin ba ɗan gida ba.
Ya isa gida goma da rabi, da ne ya kan zauna majalisar su matasa a anguwansu amma yanzu majalisar ba kowa, dukkansu sun kama kansu wasu sun yi aure wasu kuma ba ma a garin suke sana’ar su ba ya na jin daga shi sai Nasir sai makama suke garin Gombe. Nasir kuma ya yi aure sannan anguwar da ya ke zaune da matarsa akwai nisa a tsakaninsu sai su jima basu haɗu ba.
Makama ne kaɗai da shi suka rage ba su yi aure ba, ko kuma ya ce shi kaɗai ya rage tun da Makama an kusa bikinsa ma’aikacin bankin First bank ne, shi ya sa in ya shiga anguwan sai dai ya zauna a gida ya yi hira da Inna ko Baba ya ci tuwo ya fito ya koma gida ya kwanta. Shi kanshi yasan rayuwarsa ta sauya, abubuwa masu dama sun sauya daga rayuwarsa. Mafarkinsa, burinsa da komai nashi ya sauya, shi ya sa yake jin kansa kamar bashi ba.
Tabbas Mansoor Ajin yanzu ba shine Mansoor Aji a shekaru goma da suka ga ba ta ba. Wannan wani sabon Mansoor ne, wanda ya rasa mafarkinsa da burinsa wanda rayuwarsa ta juya daga farinciki zuwa baƙinciki.
**
Washegari.
Karamchi Tv
11:30am.
Yau ba ita zata karanta labaran dare fa Salim Bunza ne, shi ya sa bayan ta gama karanta labaran safe ta tattara sauran takardun hannunta zuwa Office ɗin manajansu bangaren labarai da al’amuran yau da kullum na gidan talabijin na karamci.
Mai alhakin editer ɗin su ba musulmi ba ne Peter tare da shi suka je wajen manaja tunda ranar lahadi da safe za su gabatar da shirin sharhin labaran karshen mako ita da Salim.
Ta ji ma a wajen Manaja suna magana har peter ya fito ya barta sai daga baya itama ta baro bangaren zuwa rest room ma’ana ɗakin hutawarsu.
Babban ɗaki ne mai cike da kayan alatu kamar falon wata mace, ga A.c ta ko’ina ga tuma tuman kujeru da suka zagaye wajen ga firiza domin sanyaya makoshin ma’aikata. Sanye ta ke da Abaya mai ruwan ash colur sai ta saka mayafin Abayan ta yi roling ɗin shi a saman kanta.
Kafarta sanye cikin takalmi sahu ciki kafin kaga Mimi da takalmi na sahu waje sai ka ganta da sau ciki sau goma.
Tana son takalma masu rufi sosai, jakarta karama kalan takalminta ash mai duhuwa, a can ta samu debora mai kula da shashen bangaren kula da masu shirye shirye ita da Na Misau suna hira. Zuwan ta ya sa aka cigaba da hiran da ita, duk da jefi jefi hankalinta na kan wayanta Mimi bayan aikinta sai wayarta ta fi ba ma muhimmanci. Chart suke yi da Dr. Sulaiman ya na shaida mata a satin mai shiga shi da iyalansa za su je Abuja saboda duba jikin Abi. Itama sai take faɗa amasa da safen nan sun yi mgana da Mommy tana faɗa mata Abi na a kiran sunanta ya kamata tazo ta ganshi. Sai ya ce mata to ta bari a satin da zai shiga sai ta shigo su haɗu a gida.
Tana can ta na chart ɗinta Debora ta musu sallama ta fita Na Misau ma daya ga yana mgana hankalinta baya kansa sai ya kwashi takardunsa ya fice, suna da shiri shi da abokiyar shirinsan nan da Karfe ɗaya na rana. Sai da ta ji ɗakin ya dauki shuru sannan ta juya ta ga ba kowa sai ita kaɗai sai kawai ta jawo jakarta ta ɗauko Blutooth ɗinta ta maƙala a kunnenta ta kuma yi connacting da wayarta ta sanya wakar da kamar ita kaɗai gareta acikin wayarta.
Tana fara sauraran wakar sai ta koma ta jinginar da kanta jikin Kushin ɗin kujeran da take zaune, Kafarta kuma sai ta ɗora ta saman ɗaya wayarta na saman cikinta ta saka ɗayan hannunta ta dafe jakarta dake gefenta. Cikin zaƙin muryanta kamar ita ta raira wakar ta fara bin karin wakar mai taken lafazina na khairat Abdullahi.
Jarabta da soyayya zafinta na ɗanɗana matuka
Hakika da ƙuna gun kaifi fa ta sha gaban suka
Nayi wutar ciki nayi bakinciki na share kuka na. Ta shiga can ciki takai farmaki ta kama hanjina.
Dakyar na ke fidda numfashi SO ya tushe Kirjina
Wata rana kamar in yi ihu ko wani za ya gano takaicina
Mashi ya soke ni wa za ya dubeni. Raɗadin zafin azaban ya zarce tunanina.
Ta daɗe tsaye tun shigowarta tana kallonta bata ma sani ba, ta yi nisa cikin sauraran waƙan nata da kuma salon yadda ta saba bin karin wakar a koda yaushe, mirmishin gefe baki ta sa ki kafin ta fara takawa zuwa gaban Mimi duk ko da yadda Takalminta mai tsini ke fitar da karamin sauti acikin tayless din dake falon. Sanda ta kariso gabanta dai dai Lokacin da ta ji ta na faɗin
In SO ya doke ka! ƴa’yanka har Jika, ba za ka manta ba ya shiga tarihinka kenan..!
Ba ta bari ta ƙara ɗaukan wani karin ba ta saka hannu ta dauke wayar dake cikinta lokaci ɗaya kuma ta tsaida wakar, cikin kasala Mimi ta buɗe idanuwanta da har sun fara sauya launi ta sauke su fes kan Rukayya Bala(Baby) Ma’aikaciya ce itama a shashin tallace tallace na gidan Talabijin na karamchi. Kuma kawar Mimi ce tare suka yi master ɗin su a Bayero kano sun zama kawaye tun a lokacin da jin sun fito daga jiha ɗaya. Mimi ta fara aiki da gidan Talabijin na Karamchi ita kuma ta kawo Rukayya da suke kira Baby aka ɗauketa wattani kaɗan da suka gabata.
Tana ganin ita ce sai ta yamutsa fuska kafin ta ce”Baby ya za ki kashe min wakata?
Wacce aka kira da Bby gajera mace fara mai dan kaurin jiki, itama wani material ne ajikinta na yadi baki ta yi dinkin Bubu, amma sai ta saka wani karamin hijabi fari daga saman kanta zuwa wuyanta, ta kuma sakalo I.D card ɗinta na wajen aiki ɗauke da sunanta na Rukayya Bala da shashin da ta ke aiki.
Kusa da Mimi ta zauna lokaci ɗaya tana Faɗin “Mimi kamar wannan wakar kaɗai gareki acikin wayarki? Ko da yaushe ita kike saurara kuma ni nasan ba soyayya kike yi ba, ballantana nace wani mara rabon ne ya yi breaking heart dinki, wayarki cike suke da irin waɗaanan wakokin Mimi.”
Ta faɗa ta na mai kureta da ido da kokarinta ta fahimci wani abu, kamar Mimi ta sani sai tayi sauri tashi ta gyara zamanta dakyau lokaci ɗaya tana warce wayarta hannun Rukky ta haɗa Blutooth ɗin da ke kunnenta ta tusa cikin jaka sannan ta kara Juyowa ta na faɗn”Ina jin ki me ma kika ce?
Hararanta Rukky ta yi kafin ta ce”Ke dai kika sani.” Mirmishinta mai kara mata kyau ta yi kafin ta ce”Hajiya Baby mai sunan yan gayu in ji Hajiyar shagamu”
Rukayya ta saka dariya ta na faɗin”Allah Sarki Hajiyarmu na jima ban je ko na dubata ba ko na biki na je yau ne.?
Mimi tace”Oho miki, ko ɗazu sai da ta ce wai ni Binta ina ƙawar nan taki mai sunan yan gayu nace ki nan nan abun ki.”
Rukky tace”Tab yan adawa sun shiga ciki dole yau naje na duba Hajiya, ya ya kin tashi aiki yau ne?
Nima na tashi sai na mu tafi tare”
Mimi tace”Na tashi tun dazu Manaja ne ma ya tsaida ni, amma ba gida zan sauka ba daga nan sai na biya gidan Yaddiko na gaisheta ko da zan fito da safe sai da Hajiya ta rokeni da Allah da Annabi na biya na gaisheta.”
Rukky tace”Ba matsala sai mu fara biyawa ta can, ammh fa da yammah zaki kai ni gida in na gama miki yini.”
Mimi ta mike ta na faɗin”A’a ba wajena kika zo ba, sai dai ki samu adaidaita ba na tuki in yamma ta yi”
Rukky ta mike ta rumgumota ta na mata magiya da fadanci tana faɗin”Haba Hajiyata Mimi, mimi mai kyau da ado.”
Take faɗa da sigar waka, Mimi sai mirmishi ta ke yi, a haka suka fita har main falon na ma’aikatan nasu ga sauran ma’aikata nan a zazzaune suna ganinsu ahaka aka sakar musu dariya.
Na misau da zuwan shi kenan ya kallesu kafin ya ce”Yanzu haka Rukkaya maula ta ke yi tunda naga ta na rage murya”
Hararansa ta yi kafin ta ce”Shisshigi ba kwarjini ina ruwanka da shiga tsakanin ƙawa da ƙawa.”
Sai ya ɗaga hannu yana faɗin”Ba ko ruwana kun fi kusa.”
Mimi na dariya ta ce”Fadanci ta ke yi min Na misau wai dole sai na yi mata lift a motata.”
Dariya ya kwashe dashi lokaci ɗaya yana faɗin”Rukky gaskiya ki rage son kudi ki siya mota ga kudin albashin ki, sannan ga ki lashe money ni kaina kin cuceni kudaɗe sun fi dubu ɗari biyar.”
Jin abin da ya ce ne ya sa Rukkaya ta saki Mimi ta waigo tana kallon Na Misau da ya ɗaga kafaɗa yana fadin”Karya nayi? Ke kika ja har a na fallasa maganar nan, tunda kika ce ba za ki aureni ba.”
Ido ta ke wurga ta na neman abun duka shi kuma Na Misau ya ɓata fuska ya juya yana faɗin “Justice for Na Misau.”
Rukky ta kasa mgana sai kawai ta rarumo laptop din da ke gaban Nura ta bi Na Misau da shi shi kuma ya saka gudu yana fadin to ba gaskiya na faɗa ba.
Suka bar su Mimi da dariya Rukky da Na Misau sun saba rigimansu na fama sai sun saka cikin ka ya kulle.
Manaja ne kaɗai ke iya raba wannan faɗan shima irin su ne shi ya sa yake biye musu.
Sai ɗaya saura na rana suka bar Ma’aikansu Mimi ta ɗauki Rukky a motar ta wata fara ta kamfanin Toyata mai kyau da yarari motar har ɗaukan ido take yi, suna tafe suna hiran bikin kanwar Rukky da za’ayi nan da wattani huɗu.
Mimi ta kalli Rukky, hankalinta na wajen tuki ta ce”Baby wai waye Bibi zata aura ne?
Rukky ta ce”Wani Usman ne ɗan gidan makama yana aiki a bankin First Bank.”
Mimi ta maimaita sunan Usman da Makama acikin ranta sai dai ya bayyana a saman bakinta. Cikin mamaki Baby ta ce”Ko kin san shi ne?
Da sauri Mimi ta girgiza mata kai alamun a’a acikin ranta tana tunanin ko dai Usman ɗin da ta sani ne shekaru masu yawa a baya.
Kai ba shi ba ne, shi wannan da makama ta san shi ba Usman ba.
Saurin kauda wannan tunanin tayi ganin sun shigo yankin fantami in da gidan Yaddiko yake, a kofar gidan Mimi ta faka motar ta saboda gidan na masu karamin karfi ne, tunda Mijin Yaddikk ɗan kasuwa ne mai karamin jari ya’ya ne ma suka taso suka kara gyara gidan ya yi kyau ya koma na zamani.
A kofar gidan sun ga dandalin matasa tunda gidan yana da dakali kuma tun a zamanin baya Mimi tasan kofar gidan Yaddiko baya rabo da matasa.
Suna ganinta sanda suka fito daga motar zuwa kofar da zata sada su da cikin gida.
Suka fara kiran sunanta tunda duk wanda ke garin Gombe ya san fuskar Mimi , tunda gidan Talabijin na Karamci na gaba gaba cikin sahun manyan gidajen talabijin a garin. Fuskarta ba ɓoyayyiya bace a garin.
Hannu ta rika ɗaga musu tana mirmishi Rukky na gefe tana faɗin”Hajiya Mimi kin fa samu ɗaukaka ina ga ko Manaja baya fita ayi masa wannan kiran.”
Ture ta Kaɗan Mimi ta yi ta na hararanta har suka shiga gidan nan wasu ba su daina kiran sunanta ba. Gidan Yadikko cike yake da jikokinta duka ya’yanta ta aurar da su amma tarin Jikokin da suke gidan sun isa gayya duk da Yaddiko na da faɗa jikoki na son zama a gidanta saboda Allah ya dora mata son yara.
Suna shiga aka fara musu oyoyo Anty Mimi, itama ta na son zuwa gidan saboda yaran ammh saboda Yaddiko ya sa ba ta son zuwa duk lokacin da ta zo sai ta yi mata maganar da zai ɓata mata rai.
Rai rai tare da yaran har falon Yaddiko wacce ke zaune a saman cafet tana sakan huluna daman sana’arta kenan tun tana matashiyarta har kuma ta manyanta bata daina ba. An yi an yi ta bari ta ce ba za ta bari ba yana deɓe mata kewan zama ita kaɗai. Har kasa suka zube ita da Baby suna gaishe da yaddiko.
Aneesa daya daga cikin jikokin Yaddiko ta lafe a jikin Mimi saboda yadda take kaunarta sai faman yi mata cancare take yi da Anty mimi na ganki a Tv jiya.
Yadikko ta ijiye julan hannunta tana amsa gaisuwarsu kallon Rukayya ta yi alamun rashin sani da sauri Mimi ta ce”ƙawata ce Rukkaya tare muke aiki da ita.”
Sai ta gyaɗa kai kafin ta ce”Fatima kenan sai yau na ke ganin kafarki , kina garin nan ammh bakya zuwa gaisheni sanda zan je duba Hajiya kuma kina wajen aiki.”
Kan Mimi na kasa ta ce”Ki yi hakuri yaddiko zan gyara in sha Allahu.”
Sai ta taɓe baki, da ka ganta kasan ta haɗaa jini mai karfi tsakaninta da Mimi Saboda suna ɗibar kama.
Mimi Allah Allah ta ke yi su tafi sai ta ji Yaddiko ta ƙwalama ɗaya daga cikin Jikokinta kira tace su kawo ma su Mimi abinci da ruwa. Mimi bakinta na rawa ta ce”Yaddiko gida za mu wuce, Rukky za ta je ta gaida Hajiya.”
Kai tsaye yaddiko ta ce”Eh na sani ku ci abinci ku yi sallah sai ku tafi, ba daga wajen aiki kuke ba?
Rukkaya ce ta amsa mata, ba su da mafita dole Yaddiko ta saka aka shigar musu da abinci wani daki da ke cikin falon nan suka shiga suka cakuli abincin kaɗan Jalop din shinkafa mai Kifi sai zobo mai sanyi.
Bayan sun gama suka shiga tiolet suka yi alwala. A ɗakin akwai dogon hijabi suka yi salla sannan suka gyara fuskarsu suka fito.
Har kasa suka duka suna yi ma Yaddiko sallama Ta ce.
“Har zaku tafi?
Mimi ta gyaɗa kanta sai kawai Yaddiko ta gyara zama tana faɗin”Fatima mganar nan ce da ba ki so wato maganar aure!”
Read Also Gudun kddara Here
Gaban Mimi ya amsa sai ta sadda kanta kasa bata yi mgana ba.
Yaddiko ta cigaba da faɗin”Ya kamata ki manta abin da ya faru a baya ki ba ma manemanki dama ki fito da wani ki yi auranki Fatima shekaru suna ta gudu kuma kinsan dai ba niran ki lokaci zai yi ba.”
Idanuwan Mimi suka tara kwallah ammh ba ta yi mgana ba.
Yaddiko ta cigaba da faɗin” Wannan yaron da kike yi ma wannan kulafacin ba ki da tabbacin yana nan bai yi aure ba, tunda mahaifinki ya yi muku tsakani kika yi alkwarin kin rabu dashi to kuma zaman jiran duk na menene?
“Yaddiko shima bai yi aure ba fa “
Ba ta san lokacin da bakinta ya kuɓce ba sai ji kawai ta yi ta faɗa.
Daga Yaddiko har Rukky suka bi ta da kallon mamaki, ita yaddiko ba ta yi mamaki ba daman ta faɗa maHajiyar shagamu yarinyar nan yaron nan data kwallafarai a kansa ta ke zaman jira shi ya sa ta zaɓi ta zauna ba aure ita kuma Rukky ta na mamakin waye wannan a cikin rayuwar Mimi da ba ta taɓa sani ba?
Sai dai Yaddiko ta katse mata tunani da cewa”Au ko shi kike jira ya zo ya aure ki?
Da sauri Mimi bakinta na rawa ta ce”A’a wlh yaddiko ba shi na ke jira ba, tunda nayi ma Abi alkwari na rabu da shi to da gaske nake yi wlh.” Yaddiko ta kura mata ido cikin nazarinta kafin ta sauke numfashi tana faɗin”Tashi ku je jibi ina nan shigowa na duba Hajiyar ki gaishe ta.”
Daman kamar akan ƙaya Mimi take ,ta mike da sauri Baby ta mara mata baya duk da haka sai da ta tsaida suka karɓi sakon Hajiya dafaffiyar zogale a leda da kuli ta ce a kai mata, Mimi ta karɓa suka yi ma Yaddiko sallama suka fita bayan ta ba ma yaran 2k ta ce su raba.
Mimi bata sauke numfashi ba sai da suka bar layin, sai dai yadda ta ke tukin za ka fahimci Mimi ta rasa natsuwarta sai gudu ta ke yi abin da ba halinta ba ne.
Rukky ta kalleta kafin ta ce”Mimi wannan halin da kika shiga yana da alaqa da mganar Yaddiko ne?
Wane ne na ji tana mgana akan shi?
Da sauri Mimi ta ce”Plz Rukayya ki yi min alfarman toshe kunnuwanki kamar ba ki ji mganar yaddiko ba, wannan mganar ta shuɗe daga tunanina da duniyata ba na son tunawa kwata kwata a rayuwata.”
Tana maganar idanuwanta sun tara kwallah lokacin da ta dire mganarta sai hawaye sharr suka zubo mata kuma ta kasa share su. Yaushe ne zata daina tunanin shi? Sai yaushe ne za ta manta da shi?
Read Also: Idan an ciza Part here
IDAN AN CIZA..! Part 3
Page 3
Hashidu Estate.
Har suka iso anguwan hashidu Estate kuka Mimi tae yi, Rukky kuma tunda ta ce ta kyaleta ba ta ƙara takura mata da mgana ba. Ta dai ba ta hanky acikin karamar jakarta ta tsane hawayen fuskarta da shi.
Ji take yi kamar ta cire zuciyatar acikin gangar jikinta ko za ta daina jin irin abin da take ji, tabbas zuciya itace rayuwar ɗan Adam, in ta samu matsala to dukkan gangan jiki zai raunana. Zuciyar Mimi ta jima cikin ciwo ciwon da kuɗi ko muƙami ba zai iya samar mata da mgani ba, alokacin sai gaybom ya koma ɗanye ciwon ya yi ruwan da kamar a lokacin aka ji sa.
Ko a yadda ta rika sakin hon zaka san ba lafiya megadi ɗan baba tsoho da shekara da shekaru tun marigayi Alhaji Sulaiman Dabo na raye, bayan rasuwarsa ɗansa ya ga ji aikin gadin, shi ya zo jikinsa na rawa ya buɗe mata get ɗin gidan da gudu ta shiga gidan parking ɗin ma ba a natse ta yi shi ba.
Rukky ta kalleta lokacin da ta kashemotar ta cire key din, jakarta ta ɗauka lokaci ɗaya ta buɗe murfin motan ta fice.
Ajiyar zuciya ta sauke kafin itama ta ɗauki jakarta ta buɗe kofar bangaran mai zaman banza ta bi bayan Mimi wacce megadi ke ta yi ma maraba da zuwa da Slsauri take tafiya shi ya sa bata ma ji sa ba, sai Rukky aka bari da amsa masa gaisuwarsa sannan cikin son jin menene ya faru da rayuwar Mimi haka? Sannan wanene wanda maganarsa kaɗaai ke rikita Mimi? duk kokarin Rukky sai da Mimi ta rigata shiga falon Hajiya.
Da Baaba Uwani suka fara cin karo wata mata dake zaune tare da Hajiyar Shagamu.
ƴar’uwansu ce daga can Akko aka zo da ita mijinta ya rasu ƴaƴan ta huɗu kuma suna wajen dangin babansu, ta zauna acan saboda rayuwa ya sa Hajiya ta ɗaukota ta dawo wajenta da zama gabaɗaya shekaru biyar da suka gabata.
Ita ke faɗin “Binta har an dawo? barka da dawowa.” Da yake da Binta kowa na gidan Hajiya ke kiran Mimi, ammh yau kam Binta bata saurareri Baaba Uwani ba a tsakiyar falon ta watsar da jakar hannunta da key ɗin motarta da gudu kuma ta karisa ta shige wani koridon da zai sadata da ɗakinta kamar kuka ta fashe da shi kafin ta karisa cikin ɗakin. Tunda har suna Jiyo gunjinta daga falon.
Baaba Uwani ta kalli Rukky da ta tsaya a tsakiyar falon cikin rashin mafita kafin ta ce”Topa yau kuma me ya samu Binta?
Rukky ta karisa ta kwashe jakar Mimi da key din motartaa, sannan ta kalli Baaba Uwani tana faɗin”Baaba Uwani yadda kika ganta nima haka na ganta, Ina Hajiya?
Baba Uwani tace”Hajiya na cikin ɗaki tunda ta shiga salla bari na yi mata mgana.”
Daga haka ta wuce ta Koridon da Mimi ta shiga Rukky kuma ta samu ɗaya daga cikin Kujerun da suka yi ma Falon kwanya ta zauna. Wani abu ne ya bata mamaki bata taɓa tunanin Mimi ta taɓa yin wani relationship ba, tun suna kano duk wanda ya ce yana sonta kamar makiyinta haka take ɗaukanshi. Ta saka Mimi ckin sahun matan da Soyayya ko aure baya gabansu ta fi ɗaukanta a matsayin macen da take ba ma aikinta muhimmanci fiye da komai a rayuwarta. Sai dai mganar Yaddiko ta sakata shakku da kuma halin da Mimi ta nuna yanzu, abu ɗaya take son sani shi wannan waye shi ake mgana a kan shi? wani matsayi gare shi a wajen Mimi da tuna shi kan ɗaga mata hankali?
Tunaninta ya katse sanda taji sallamar Hajiya da sauri ta mike tana sakin mirmishi. Hajiyar Shagamu kenan tsohuwa lafiyayya da ba ta da irin ƙananun cuwukan zamani na tsoffi da kafafunta da karfinta sannan da idanuwanta da bakinta ras tana gane kowa fara ce sai ɗau duk da ta tsufa sannan gashin kanta duka ya koma fari Saboda furfura, a tsaye take ma’ana tana da kaurin jiki fatar jikinta har wani kwanciya ya yi saboda hutu da jin daɗi kuma a kiyasi za ta kai shekara Saba’in da wani abu a duniya. Amma kana ganinta ka ga Mimi za ka san ita sak mimi ta kwaso kuma zaka so ka ga hotunanta tana matashiyarta Kila sai dai aga Mimi na biyu saboda tsabar kamar su.
Abin da na lura shine gabaɗaya Ahalin Sulaiman Dabo suna ɗiban kamanni da juna.
Hajiya ta na ganin Rukkaya ta washe baki ta na faɗin “A’a mai sunan yan gayu ne yau a gidan?
Rukkaya kanta na kasa ta amsa lokaci ɗaya kuma ta durkushe kasa ta na gaida Hajiya.
Sai ta amsa mata itama ta na zama kan ɗaya daga cikin kujerun falon tana ce ma Rukkaya ta tashi ta koma saman kujera ta zauna. Ba ta yi musu ba ta ta shi ta zauna lokacin kuma Baaba Uwani ta kawo mata ruwa da lemu a wani ƙaramin faranti da ƙaramin Kofin silba.
Bayan gaisuwa da tambayan gida da aiki Hajiya ta kalli Rukkaya kafin ta ce”Ita Bintan tunda ta shige bata fito ba? Hala kun biya wani wajen ne kafin ku kariso nan ko?
Kan Rukkaya na kasa tace”E. mun biya gidan wata Yaddiko.”
Nan da nan fuskar Hajiya ta sauya lokaci ɗaya tana faɗin “Me ya sa Yaddiko ba ta jin magana ne? Ta yi kuma ƙorafin Binta ba ta zuwa gudanta, kuma in ta je bakinta baya iya shuru sai ta ja abin da kafin Binta ta koma gidanta sai an yi ta fama kai jama’a.”
Hajiya ta faɗa ta na mai lokarin bayyana takaicinta kafin ta ce”Allah ya sauwake to.”
Rukayya ta tashi taje gaban Hajiya ta mika mata zogalen da Mimi ta barta da ɗauka lokaci ɗaya da jakar Mimi da key ɗin motarta tana faɗin.
“Hajiya ga sakon zogale Yaddiko ta ce a kawo miki. Wannan kuma jakar Mimi ce da key din motar ta”
Hajiya tace Rukayyan ta ijiye a kan Kujera, sai ta ijiye mata sannan ta tashi ta koma wajen zamanta ba ta jin kishi amma kada Hajiya tayi mganan bata sha komai ba ya sa ta zuba ruwa ta sha kaɗan.
Falon ya yi shuru kowannensu da tunanin da ke cin ransa. Rukayya ce ta kauda shuru bayan ta kalli Hajiya ta ce”Hajiya Mimi kamar kuka take yi acikin ɗakinta fa?
Hajiya ta sauke numfashi kafin ta ce”Shi zata yini yi yau tunda aka famo mata wannan tsohon ciwon, yau kuma kamar gidan makoki haka zai kwana.”
Rukky ta gyara zama kafin ta ce”Hajiya shin wane ne naji yaddiko na mata maganar shi? Domin bayan an yi mganar ne Mimi ta shiga cikin tashin hankali tun muna hanya ta fara Koke koke.” Hajiya ta yi shuru na wani lokaci kafin ta ce”Wani shuɗaɗɗen labari ne Rukayya, shekarun sun daɗe amma In Binta ta tuna kamar yau abun ya faru haka take ji.” Sai kuma ta yi shuru Rukayya kuma ta kosa taji ko waye wannan da tunashi kaɗai kan iya haifar da tashin hankali a rayuwar Mimi
Cikin ƙaguwa Rukayya ta ce”Hajiya to wane ne wannan mutumin da tuna shi kaɗai barazana ne ga kwanciyar hankalin Mimi?
Hajiya ta yi wani iri kafin ta kalli Rukayya ta ce”Wani ne, wani saurayin Binta ne da suka yi soyayya da jimawa.”
Rukky ta ware ido kafin ta ce”To yanzu ya na ina? sun rabu ne ko ya rasu ne?
Hajiya ta girgiza kai kafin ta ce”An ya? Bai rasu ba ya na nan da ransa. Irin soyayyar nan ce tun na tashen balaga Rukayya ya so Binta itama Binta ta so shi kamar ta mutu, amma faruwan wasu abubuwan ya sa suka rabu tun shekaru sama da takwas ina jin.”
Rukayya ta yi jugum kafin ta ce”Me ya hana su aure tun a wanchan pokacin Hajiya? Kuma anan garin ne ko acan Abuja?
Hajiya ta ce”Mahaifinta ya hana al’amarin, A nan garin ne anan kuma suka haɗu lokacin tana zuwa min hutu,”
Rukayya cikin ƙarin mamaki ta ce”Kuma tun bayan rabuwarsu yana nan a nan garin nan?
Hajiya ta yi shuru kafin ta ce”Gaskiya ba na jin ya bar garin nan, tun da tun bayan faruwan lamarin zumunci mu ya yanke tsakanina da mahaifiyarsa ba ni da labarinsu, ba ta zuwa in da nake nima kunya da nauyi sun kasa barina har yau na nemeta. Allah Sarki Inna Meri wata mace kwara ɗaaya da na zauna da ita mai kirki da mutumci mai kawaici da yaƙana mai hakuri da sanin darajan ɗan adam ta zauna dani kamar ni na haifeta daga baya abubuwan da suka faru ba ma su daɗi ba ne shi ya sa sai alaqan da ta haɗamu tun a wanchan lokaci ta jima da lalacewa daga kuma Lokaci ban kara jin labarinsu ba amma ina da tabbacin suna nan a garin nan
Rukayya ta yi tagumi tana jin Hajiya kafin ta ce”To Hajiya me ya sa Abban Mimi ya hana su aure tun da Mimi tana son shi?
Hajiya ta ce”Ai shima ya sota, ya so ta sosai so mai tsanani wallahi. sai dai kinsan komai sai Allah ya yi, alokacin duka an yi abun ne cikin rashin lura da gaba, shi ya sa ake son in mutum ya ciza to ya busa saboda gaba kar ya zo yana nadamar abin da ya aikata, labarin ba shi da daɗin faɗa mai sunan yan gayu ki bar maganar kawai, gwara ki tashi ki karisa gida yau sai sa’a Binta zata fito daga cikin ɗakinta” Ba haka Rukayya ta so ba, ta so ne taji mafarin labarin, ba za ta iya gaddama da Hajiya ba ya sa ta mike ta yi mata sallama ta fita.
Sai da ta taka da kafarta har can babban titi sannan ta samu adaidaita zuwa gida.
Kuma ita duk tunanin ya tafi akan me ya hana wannan auran? Sannan taji Hajiya na faɗin alaqar dake tsakaninsu ta lalace tun daga wancan lokacin, a kuma yadda ta fahimta Hajiyar kanta bata ji daɗin abin da ya faru a wanchan lokacin ba sannan kuma duk yadda akayi Mimi na son wannan mutumin kuma shi ne dalilinta na har yau ba ta yarda ta ba ma wani namiji dama ba, duk ko da tarin masoyanta. Za ta so ta ji oabarin wannan Soyayyar domin kuwa tana da tabbacin akwai abun al’ajabi acikinsa.
Za ta yi ta bin Mimi a sannu sannu har sai ta san komai, ƙarin abun mamaki yadda Mimi tace bai yi aure ba shima a gidan Yaddiko. Kenan tana labarinsa? ta kuma kila san a in da yake rayuwa? Ammh me ya sa bata neme shi ba, tunda dai saboda soyayyarsa ta ki ba ma kowa dama ya kamata ta nemeshi saboda ta ba ma zuciyarta abin da take so.
Har ta isa gida jukinta a sanyaye yake, sai taji Mimi ta ba ta tausayi soyayya ai kamar guba ce, ita kanta da suka rabu da saurayinta faisal ta sha wahala kafin ta farfaɗo balle na Mimi da aka ce sama da shekaru takwas da suka gabata.
7:30Pm
Tun da ta shiga ɗakinta bata fito ba, duk ko da magiyan da Baaba Uwani da Hajiyar da kanta suka zo suna yi mata akan ta fito ta samu wani abu ta saka ma cikinta. Sai ta yi kamar ba ta ji su ba har suka gaji suka kyaleta. Mimi ta yi kuka kukan da sai ta ɗauki lokaci ba ta yi irin shi ba, ammh duk lokacin da tunaninshi ya bijiro cikin duniyarta haka yake maida ta.
Har zuwa yaushe ne zuciyarta za ta daina tunanin sa da begen sa?
Sai yaushe ne za ta iya cire sa a cikin zuciyar ta? yaushe ne za ta sauya rayuwarta ta daina zaman jiran warrabuka?.
Jiran da ta san har gaban abada na cire tsammani ne?
Ita tasan ba zai dawo gareta ba ya tafi kenan kamar yadda ya faɗa da gaske yake sun yi rabuwan Abadan Abadan ne tsakaninta da shi.
Shekaru goma kenan ammh soyayyarsa acikin zuciyarta tana jin ta kamar sabuwa.
Babu abinda bata yi ba saboda ta manta da shi amma ta kasa, babu kalan addu’an da ba ta yi a gaban ka’aba saboda Allah ya cire mata soyayyarsa a cikin zuciyarta ba amma lamarin kamar yana kara nisa ne, ba ta jin ko ɗigon soyayyarsa ta ragu daga zuciyarta sai ma take ji kamar duk ƙarin minti ɗaaya na bugawar numfashinta kara son shi take yi. Ta fara son shi tun bata son menene so ba, ba zata taɓa manta garkon ganinta da shi ba, tana da shekara goma sha shidda a lokacin hatta date ɗin ya kasa ɓace mata a cikin tunaninta.
20 December 2008.
A cikin hutun third tearm da makaranta kan ba su mai tsawo Hajiya ta kira Abi a waya ta ce maza maza ya saka akawo mata Bintu tayi hutu a wajenta, alokacin Abi bai so ba saboda baya so Mimi na yin nesa da shi amma Hajiya ce tanna kaunar Mimi bai isa ya ce mata a’a ba. Ba za ta taɓa mantawa cewa tafiyar Jirgi Abi ya so tayi zuwa Gombe ita kuma ta ce tafi son na mota saboda ta rika ganin gari, direban su Mallam Sale Allah ya jikansa ya rasu a hatsarin da suka samu da Abi shi ya tuko ta tun daga Abuja har gombe. Ba kuma ta yi barcin hanya ba ta yi ta kalle kalle duk abin da ta gani sai tayi tambaya shi kuma Mallam Sale na bata amsa a wannan tafiyar ta haddace sunayen garuruwa da dama kuma tafiyar na ɗaya daga cikin tafiye tafiyen da ba za ta taɓa mantawa da su ba.
Da yammah suka shigo garin ta san tana manne jikin window mota tana kalle kalle har ɗage mata glass din mallam Sale ya yi da suka shigo cikin gari. A kofar gidan Hajiya daga nesa kaɗan ta fara ganinshi.
Sanye cikin riga da wando baki da fari, rigar mai dogon hannu tana da layi layin baki a jikinta ya sanya duka hannayensa cikin aljihun wandonsa. Kansa na ƙasa yana danna karamar wayar dake hannunsa.
Lokacin da Mallam Sale ya yi hon shi kuma sai hankalinsa ya kawo wajen dai dai lokacin da ya ɗago yana kallon motar ita kuma tana kallonshi a a dai dai lokacin suka haɗa ido.
A lokacin ba za ta taɓa mantawa ba, ta yi masa mirmishi har kumatunta suka loɓa sannan ta ɗaga masa hannu.
Shi bai ɗaga mata ba, amma ya maida mata martanin mirmishinta. Wanda in za ta iya tunawa daga wannan mirmishin Allah ya haɗa zukatansu waje ɗaya zata iya rantsewa da Allah ta fara son shi ne daga wannan ganin farko da ta yi masa tana yar shekara goma sha shidda a duniya wacce ta yi jarabawar JSCE.
Tana wannan tunanin ta na tuna shi a can baya acikin idanuwanta, tana wannan kukan ta tashi ta yi sallar la’asar ta yi sujjuda mai tsawo tana rokon Allah ya cire mata soyayyar MANSOOR acikin zuciyarta da tunaninta gabaɗaya, haka da ta yi sallar mangariba tana addu’a tana kuka domin ta gaji ta sare ta na bukatar ta yi rayuwa cikin zuciyarta ba wannan nauyin da wannan ciwon.
Me ya sa ya kasa fita daga cikin zuciyarta?
Me ya sa take ganin duka maza a matsayin mata in har bashi ba?
A wajenta shi kaɗai ne namiji kwara ɗaya da ta yi tunanin zata iya zaman aure da shi, shi kuma rayuwarsa ta yi ma rayuwarta nisa.Babu abin da ke kara sakata kuka in ta tuna RANAR! ranar da ta sanya mata suna bakar rana a wajenta.
Kalamansa har gobe in ta tuna su sai ta ji kamar ta mutu.
In har ni Mansoor na haifu cikin uwata Meri da uba na Ibrahim ƴarka ko ita kaɗai ta rage a duniya nan sai dai ta mutu nima na mutu ban yi ba aure ba
Nayi alkwarin toshe kunnuwana daga jin ta da ganinta na yi alkwarin sauya duniyata daga duniyarta, na yi alkwarin sauya mattacen mafarkina a kanta, na kuma gode maka da ka fahimtar dani darasin rayuwar da na daɗe ana faɗa min ban ɗauka ba, na kuma fahimci akwai tazara mai kimanin kilomita tamanin tsakanina da ƴarka, na kuma fahimci matsiyaci kamata ya yi shisshigi wajen tusa kansa in da bai dace da shi ba. Yadda ka saka iyayena kuka a kaina kai ma wat rrana sai ka yi kuka saboda ƴarka..
Kara tuna hakan da ta yi yasa sai da ta saki kuka ta faɗi nan saman dardunan da ta idar da sallah ta na gunjin kuka, kamar kuma wacce aka tsikari haka ta tashi ta nufi waje makeken Wardrope ɗin dake ɗakin acan kasa ta fara lalubo wani abu.
Wata jaka ta dauko karama daga gani ta jima a boye duk ta yi kura. Sannan ta zo ta zauna ta buɗe jakar ta fito da wata karamar waya kiran Nokia ta da domin an jima da daina ya yin wayar a wannan zamanin.
Ta saka hannunta na rawa ta kunna wayar sai ga shi ta yi kara da wannan yar wakar ta Nokia, yadda hannunta ke rawa haka jikinta ke rawa. Ta gama saituwa wayar ta nufi ma’adanar sakonni.
Tunda hatta layin wayan bata cire ba, sai da jimawar da akayi ba’a yi amfani da layin ba Mtn sun kulle layin gabaɗaya amma abin da ta ijiye wayar saboda shi yana nan aciki. Kuma ta je ta ƙara yin rigister ta sabunta layin, ita duk tunanin ta watan wata rana zai neme ta! Wata ƙila zai tuna da ita. Saƙonsa na karshe ta buɗe kuma ajikin sunan wanda ya turo sakon ne kamar haka.
“Aji Na.!
Kada ki ƙara kirana, ki manta dani daga zuciyarki da duniyarki gabaɗaya. Ki ɗauka bamu taɓa sanin juna ba, soyayyarmu alkwarin mu da mafarkinmu ki saka wuta ki kona su acikin tunaninki, ki kauce ma ganina kamar yadda zan kauce ma ganinki, ki kauce ma jina kamar yadda nima zan kauce daga jin ki gabaɗaya. A da ne na ke hango kaina a matsayin mai sonki ina tunanin wannan soyayyar ta isa komai a wajena ashe na yi kuskure, saboda haka ki ɗauka ma baki taɓa sanina ba kamar yadda nima zan shafe ki daga tunanina da zuciyata gabaɗaya.
Wasu hawaye ne masu zafi ke gudu kan kunci Mimi wasu na koran wasu, har da kwanan watan da sakon ya shigo da kuma lokaci 16 ga watan March 2012, da misalin karfe 9:45pm na dare ranar Laraba.
Ba zata taɓa mantawa da ranar ba, tun bayan tafiyarsu take ta kiran wayarsa ta ji ya suka sauka gida da kuma jikinsa tun da sun fita Mu’azzam na rike dashi yana ɗingisa kafarsa sannan ga raunika a jikinsa.
Ammh wayarsa bata shiga ta kira na Mu’azzam shima baya ɗauka. Wajen kwana uku tsakani sai ta koma tura masa sakon don Allah ya kira ta.
Ba ta so su yi wannan rabuwar ba, ta so ko sallama su yi da juna.
Ammh Mansoor ya tabbatar da kalamansa na shafe ta daga duniyarsa.
A kwana na biyar ne ya tura mata wannan sakon kuma daga kuma ranar ba’a ƙaara amfani da layin ba.
Ita kuma ta kasa daina amfani da nata layin, wayar tafi shekara biyu a kunne kuma a tare da ita, tunani take yi watarana zai iya nemanta abin da bata sani ba, sai daga baya ba ita kaɗai Aji ya shafe daga tunaninsa ba har da dukkan mafarkan rayuwarsa da ya tsara tare da ita.
Lokacin rabuwarsu sai da kamar Depression zai kamata daga baya ta ɗauki dangana dalilinta na yin karatu a ibadan kenan saboda ta tsani Abuja ta kuma tsani Gombe a lokacin. Haka ta rika bin sakonnin nan ɗaya bayan ɗaya tana karantawa, akwai wani sako da har abada ba za ta taɓa mantawa da dalilin turo shi ba.
“Mimi Na nifa na faɗa ma Inna da Baba aure zan yi.”
Inna ta ce da me zan yi aure? ni kuma na ce duk a saida gonakin Baba na mallam Sidi a nema min auran fatima bintuNa”
Ta na karanta sakon tana dariya lokaci ɗaya da kuka, ba za ta manta ookacin suna yin jarabawar fita daga babban Sakandiri ne bayan ta dawo daga makaranta. Hajiya ce ta ɓata mata rai akan sai ta shirya ta je gidan Daddy(Alhaji Hamza) ta kwana ita kuma ba ta son tafiya saboda Mansoor.
Sai kawai ta yafo ɗankwalin doguwar rigan da ke jikinta ta fito haraban gidan tana kunkuni. Ta bar Hajiya aciki ita da Inna Meri ta na ba ma Hajiya Hakuri.
Kamar ba za ta sai ta ganshi a gabanta cikin mamaki da zaro ta ce”Yaushe ka zo ban sani ba? Ba zata manta kayan da ke jikinsa ba alokacin tunda ranar jumma’a ce ya saka farin shadda har da hula.
Yana mata irin kallonsa ya ce”Daga masallacin Jumma’a nake, na ce ba zan koma gida Mimi ba ta ga wankan Ajin ta ba.”
Sai da ya faɗa taga darduma a hannunsa sannan ga kasa nan a saman goshinsa ya kuma bata tabbacin da gaske yake yi daga masallacin jumma’a yake.
Ita fa duk damuwanta in ta gan shi sai ta ji farinciki ya cikata.
Mansoor shine rayuwarta, suka tsaya suna ta hira yana bata labarin irin yadda yake wahala wajen neman makarantar sojoji tunda shi burinsa ya zama Soja saboda haka ma ya ɓata shekaru uku a gida bai shiga makarantar gaba da sakandiri ba.
A lokacin tura bakinta tayi kafin t ace”Aji kabar wannan Sojan nan ka yi karatun ka kawai ai ba ka ta zama ba.”
“Ke bari Kamar yadda ba zan iya barin ki ba.Haka aikin Soja yake a wajena..”
A lokacin fushi ta yi ta juya masa baya tana kunkuni kafin ta ce”To ai shike nan tunda ka fi son soja a kaina.” Ta juya taa masa yar shagwaɓa ya yi ta kiranta ta ruga cikin falon Hajiya da gudu tana dariya.
Shine da daddare ya turo mata wannan sakon na cewa ya faɗa Inna aure yake so. Ta tuna har amsar da ta bashi da cewa ba Soja ka zaɓa ba?
Sakon gaba da ta karanta ne ya saka ta ƙara fashewa da dariya tana kuka, saboda kamar muryansa take ji alokacin yana yi mata mgana.
In ana salla ba’a mgana Mimi Na, sojan banza bari dai na fara samun ki, na tabbata in na same ki a hankali sauran burukana za su tabbata.
Kifa wayar ta yi a saman fuskarta tana raira wani irin kuka, ya za’a yi ma ta manta da shi? Ya haɗa komai na bukatar kowacce mace ya yi mata wani irin son da ya haɗa duka mafarkinsa a kanta.
Kuka ta ke yi kamar ranta zai fita har muryanta ta sauya, sannan ta mike ta kashe wayar ta maida ta ma’adananta.
Ta kuma maidata maboyarta, kuma a wajen ta dauko wani abu a nannade da kyalle ta warware shi. Sai ga hoto ya bayyana na jikin hoton yana tsaye a kamar studion ne akwai mutane a wajen.
Yana sanye da kayan kwallo riga da wando ja da fari da takalmi ja mai igiyoyi.
Ya ɗaga Kofi a sama ya na ɗan mirmishi a kasan hoton an saka.
MANSOOR AJI GOMBE UNITED CAPTAIN!
lokacin da Katsina pillars suka zo suka buga wasan cikin gida suka kuma ci su da bugu uku ba ko ɗaaya kuma duka bugun kwallon nan Aji ne ya buga su a raga.
Rumgume hoton ta yi tana ji zuciyarta na bugawa sama sama. Tunaninta kuma ya tafi akan shin kamar yadda take bibiyan rayuwarsa shima ya na nibiyanta haka?

Tsintar Aji a duniyar kwallon kafa ya sa ta sare ta yarda da mganarsa ya sauya mafarkinsa tuni. Ita ce shaidan yadda Aji ya so zama soja ƙwallo ma ra’ayin Mu’azzam ne ba ra’ayin Mansoor ba, kuma ko a baya ƙwallo bata burgeshi duk ya na buga ƙwallo amma tasan ya na zuwa kallon ƙwallo sosai.
Sai gashi rana tsaka ta ganshi tsamo tsamo acikin ta, duk me ya faru bayan rabuwarsu?
Shi ne ba ta da wannan amsar ta jima Rumgume da hoton tana kuka kafin ta gaji ta nannade hoton ta kuma maida shi ma’ajiyarsa. Sallar isha’i ta yi yunwa take ji har ta fara ganin jiri.
Shi ya sa bayan ta idar da ta ji Baaba Uwani na buga mata Kofa taje ta buɗe
Abinci ta kawo mata sai ta ce ta koma da shi ta haɗo mata tea ne.
Sai ta Juya ta na fadin”Binta ki fito falo Hajiya fa ta damu.”
Cikin dashewar murya ta ce”Ki faɗa mata kar ta damu da ni ina lafiya.”
Daga haka ta juya ciki ta koma ta zauna ta yi tagumi. Tana tunanin makomar rayuwarta anan gaba, ko ta amince ko kar ta amince rabuwarsu da Mansoor ta har Abada ce kuma da gaske yake yi da ya ce zai gogeta daga tunanin sa da mafarkin sa gabaɗaya.
08 Feb 2022.
6:00pm
Yana studio ɗinsu yau sun yi afternoon training ne ya samu wayar mijin Bintu Bashir yana faɗa masa tun safe Bintu ta rufe Kitchen ta kuma ɓoye makulli ta ce ta ga wanda ya isa ya dafa abinci ya ci acikin gidan nan, Bashir ɗin ya ce ya yi ta roƙonta bata saurare shi ba, sai yaji ransa ya ɓaci daman ya na ta so yaje gidan sai kuma wasu abubuwan suka ɗauke masa hankali.
Amma tunda abun har ya kai ga haka ai shike nan zai je gidan yaji ta inda iskancin na Bintu ya fara.
Coach ɗin su ya sanar ma zai je gida ana nemansa daman da mashi ɗinsa yazo sai ya sauya wandonsa jikinsa daga gajere zuwa dogo tunda gidan surukai zai je kuma a matsayin sa na babban yaya ya rike girmansa. Cikin lokaci ƙankani ya iso gidan tun da nan anguwan Arawan ne daga can baya ba su da nisa daga gida.
A kuma Kofar gidan ya ci karo da Bashir ɗin yana jiransa. A yadda ya gansa duk ya yi wani firgai firgai sai ya fahimci Bintu na iskanci kala kala acikin gidan nan tunda har mijinta na tsoronta.
Gaisawa suka yi bayan sun yi musabaha Bashir ɗin ya fara faɗin “Wato yayanmu lamarin ne ya fara fin karfina. Wajen sati ɗaya gidan nan ba ma zaman lafiya.”
Mansoor ya kaɗa kai kafin ya ce”Ka yi min izini mu shiga gidan tare.”
Ya na jin haka ya fara sosa kai yana Faɗin”To to shike nan Yayanmu ammh don Allah kar ka ce za ka yi mata faɗa a bi ta a sannu.” Takaici yasa ya wuce yana faɗin”Kai dai ba ta gagare ka ba? to ni ba za ta gagare ni ba don ubanta.”
Ya na faɗin haka lokaci ɗaya ya yi sallama acikin gidan. Bashir na binsa a baya jikinsa na faman rawa..
Uwar gidan Bintu ce a tsakar gida ita ta amsa masa sallamansa, ba saninsa ta yi ba domin bata ta taɓa ganinsa a gidan ba amman ganin yadda ya shigo gidan ga Bashir a bayansa yana wani sunne kai.
Kafin ma ta yi mgana ya yi saurin tare ta da cewa”Hadiza. Yayan Bintu ne”
Kai tsaye ta kallesa tana faɗin”Ayya ina yini? Bai kalleta ba ya ce”Barkan mu da yamma, ina ne ɗakin Bintun?
Ya faɗa ya ma kallon Bashir saboda shi dai yasan gidan ammh bai taɓa shigowa ba, shima abin da ya sa ya sani saboda Mu’azzam sun ne taɓa wucewa ta kofar gidan ya nuna masa ya ce ga gidan da Bintu ke aure. Da dai Mu’azzam ne shi kam kamar wani mace gida gida na mata ya iya shiga.
Bashir na gaba yana bayansa har ɗakin Bintu Hadiza ta bi su da kallo, ko shi ne yayanta ɗin ɗan ƙwallon kafa wanda a kace zuwa da shi garin aka yi? domin ta san ɗayan yayan nata ɗan sanda ne tun da yana zuwa gidan in yazo garin, kuma ga dukkan alamu wannan bashi da wasa, kuma sai yanzu ta ga kamansu abu ɗaya ne ya bambamta su ita Bintu fara ce shi kuma baƙi ne. Taɓe baki ta yi domin ita abun ya isheta Bashir ya zama sallamame tsoron Bintu yake ji, bai iya wani kuzari in tana wajen shi ya sa take yin abin da ta ga dama.
Ita dai ta faɗa masa ta gaji, ko ya ɗauki mataki ko ta bar masa gidansa ya zauna da yar so Bintu.
Duka duka s haihuwanta ɗaya ne ya karo mata kishiya da fitinanniyar yarinyar nan tunda ta shigo gidan ta daina barin su cikin sukuni. Tana kokarin shiga ɗakinta bata san mai ya faru ba taji muryan yayan Bintu cikin tsawa yana faɗin”Ina za ki je kuma? dawo nan ki zauna munafuka.”
Kuma ta ji ko motsin Bintu bata ji ba, a ranta tace kila dai wannan ne mai maganinta. Tana yar dariya ta shige ɗakinta.
Abin da kuma ya faru shine suna shiga ɗakin nata, Mansoor ya zauna a falo Bashir kuma har ya mike jikinsa na rawa zai je ya kirata sai ga ta fito.
Sai dai jikinta ya yi sanyi da ta ga Baban Inna ai ta shiga uku. Sai ta juya da sauri za ta koma shine ya daka mata tsawo ya ce ta dawo ta zauna. Sai gata ta dawo sumi sumi jikinta na rawa ta zo ta zauna kan kujera ta kuma ga mijinta a ƙasa wani kallon da Baba inna ya yi mata ta bakin ta yasa ta sauko kasa bata shirya ba.
Gyara zamansa ya yi shi cikin kaushin murya da ba wasa ya kalli Bashir yana faɗin”Me ya faru ne? Ka yi mini bayani tun daga farkon rigimar har zuwa yau.
Bashir ya gyara zama ya fara faɗin duk fa rigiman akan less ne da ta gani a jikin Hadiza ne shine ta saka rigiman ya ci amana ya siya ma Hadiza leshi bai siya mata ba, shi kuma ya rantse mata da Allah ba shi ya siya ba da kuɗin adashenta da ta kwasa ta siya saboda ƙaninta zai yi aure.
Shi ne Bintu taki yarda ta rika zage zage tana cewa ya ci amananta shima sai ya siya mata wannan leshin za’a zauna lafiya, ganin abun nata yaƙi wucewa ya sa ya ce in ya samu kuɗi zai siya mata amman ta ce ba ta yarda ba har abun ya kai yau ta rufe kitchen ta ce ta ga mai girki a cikin gidan balle aci abinci.”
“Wlh karya yake yi, shi ya siya mata saboda cin amana..!”
Kafarsa ya saka ya hambareta ya ma manta ba a filin ƙwallo ya ke ba, da ace da karfi ya haureta da sai ta ci haɓo da bakinta.
Cikin tsawa ya ce” Ashe baki da mutumci ban sani ba? mijin naki kike ƙarya ta wa?
Ya faɗa cikin takaicinta yarinyar nan fa ta yi nisa. Ita kuma sai ta koma gefe ta fashe da kuka tana faɗin”Wlh ba gaskiya ya faɗa ba, shi ya siya mata ni dai na ce wanda ya zalunce ni ban yafe ba.”
“In kika ƙara mgana ba tare da nace ki yi ba, na rantse da Allah sai na yi biji biji da rayuwarki anan wajen.”
Ya faɗa mata cikin tsawa ganin yadda yake huci ya sa ta shiga taitayinta kar ya yi ƙwallo da ita ya za ta ko ball ce ya samu, ta kuma san shi da bakar Zuciya kamar Kuturi ya yi zuciya to sai fa ran kowa ya ɓaci.
Shi ya sa ta koma gefe ta yi shuru ta na hararan Bashir kamar Idanuwanta za su faɗo. Ba dai ita zai haɗa da Baban Inna ba, sai ya gane kuransa. Kuma duk yana ganinta ta na harare harare, kuma abun haushi Baahir din na bata hakuri da hannu.
Sai ya ji ba Bintu ba ce abun duka harda Bashir din tunda ya fahimci sakarai ne.
Bai yi mgana ba sai da ya saka Bashir ɗin ya kira matarshi Hadiza.
Ta sako hijabinta tazo ta zauna itama ta tambayeta ta maimaita abin da Mijinta ya ce ta karishe da faɗin “Wlh ni na siya leshin nan da kuɗina, ba Baban Afra ya siyamin ba gaskiyan magana kenan.” Ba domin Baban Inna na wajen ba mikewa za ta yi ta karyata su ammh tasan ta sake magana sai an yi abun kunya a gaban kishiyarta.
Shuru ya yi na wani lokaci kafin ya kalli Bintu ya na faɗin “Ba ki da kaya ne da za ki ta da rigima saboda leshi? Ko a tsirara kike yawo ba mu sani ba?
Bintu ta yi kwalkwal kafin ta ce”Ina da shi, amma Baban Inna.”
A tsawace ya ce”Ke sunan nan ya fita daga Bakin ki ko naci ƙaniyan ki wlh.”
Daga nan ta san kuskuren da tayi da sauri ta gyara da faɗin” Yayanmu shi ya siya mata fa, kuma ai ina da haƙƙin nima ya siyamin tun da adalci aka ce ayi.”
Ta gama faɗa ta na harare harare. Cikin jin haushi ya ce”To na ji ya siya mata ke bai siya miki ba sai aka yi ya ya? uwarsa ce ke da dole sai ya siya miki duk abin da bai yi niyya ba? In ma ya siya mata da ita kika zo gidan kika gansu kuma gidansa ne yana da Ikon ya yi abin da ya ga dama, kin rufe kitchen kin ce ba wanda ya isa ya ci abinci nace abinci daga gidan Wanzamai kika zo da shi?. Na ce daga can kika zo da shi?
Ya karishe faɗa cikin tsawa sai Bintun ta saki kuka za ta sake mgana cikin ƙara daka mata tsawa ya ce”Ba da ke nake mgana ba?
da sauri ta ce”A’a.
Read Also: Sanyi Da zafi Complete Book
Kai tsaye ya ce”To ashe iskanci ne a cikin kanki ban sani ba, ba ki da mutumci na jima ina jin labarin ki kuma daman ina jiran wannan ranar, daga nan wajen wallahi na kashe wannan mganar, ko da wasa kika kara tada mganar leshi na ji labari zan yi miki abin da ba ki yi tsammani ba, sannan ki ɗauko Key din kitchen ki ba ma mijinki ki kuma bashi hakuri, sannan kar na sake jin kin fito kin yi zage zage ko rashin kunya, kin sanni kin san halina ba ni da kyau ko nayi wanka kika bari na kara takowa cikin gidan nan sai nayi miki dukan mutuwa wlh, kuma kinsan ina faɗar abinda zan iya aikatawa ne ba wanda bazan iya ba.”
Ya karishe faɗa lokaci ɗaya yana mike wa Bashir ma ya miƙe shima da sauri yana faɗin “Ai Yaya Mu’azzam ma ya kirani ya ce shi zai siya mata leshin ma.”
Da sauri Mansoor ya ce”Ba zai siya mata ba sai dai ta mutu, hakkinta baya kan mu yanzu ya na kan mijinta ne, abin da ka yi mata ta yi hakuri da shi, zan kira shi Mu’azzam ya siya mata leshinan shima sai na ɓata masa rai.”
Ai daga Bintu har Mijinta ba wanda ya samu bakin mgana Hadiza kuma sai jin daɗi take yi a ranta tana faɗin daman akwai mai maganin Bintu haka aka barta tana iskancinta.
Har sanda zai fita sai da ya juyo ya kalleta yana faɗin”Ki natsu ki zauna lafiya kar ki kara tada ma Inna da Baba hankali in ba haka ba kin fi kowa sani na.”
Daga haka ya fice Bashir ya bisa, Bintu ba ta saki baki tayi ihu ba sai da ta tabbatar da Baban Inna ya bar gidan.
Sannan ta kwanta anan in da ya barta tana kuka Hadiza ta mike ta na yar dariya ta fice daga dakin. Bashir kuma daga raka Mansoor bai dawo ba yana tsoro.
Shi dai Mansoor ya faɗa masa in bai gyara gidansa ba wani na waje ba zai iya zuwa ya gyara masa gidansa ba. Bintu tasan halin Baban Inna wajibi yasa ta fito da key ta mikama Hadiza sannan bakinta gum.
Sai dai Bashir ne ya gane bashi da wayau ta fara gaba da shi, shi kuma yana ta bin ta yana ba ta hakuri, ita bakincikinta ɗaya faɗan da Baban Inma ya yi mata a gaban kishiyarta, Har Mu’azzam ta kira tana kuka ta gaya masa lallashinta ya yi shima yana faɗa mata yadda Yayan nasu ya kirashi ya yi masa faɗaan cewan da ya yi zai raba gardama da siyan leshin. Daman Mu’azzam ne ke biyema iskancin Bintu ya yi ta lallashinta, dole dai ƙanwar naki Bintu ta hakura da maaganar Leshi.
Haka ta je gida tana Inna abunda Baban Inna ya yi bai kyauta mata ba, zaginta ya yi ta yi a gaban kishiyarta.
Inna meri ta ce”Dakyau gwara da ya yi miki haka tunda sakara kike mara wayau.”
Saboda Inna ta goyi bayan ɗanta ya sa bata daɗe ba ta gudu gidan Yaya Amina.
Itama nan ta sanar mata da abin da aka yi mata, itama dai hakuri ta ba ta to wa ya isa ya ce Baban Inna bai kyauta ba?
Ko su Inna bai faɗama ya je gidan ba ammh kowa fa ya ji daɗin haka tunda Bintu ta natsu tana tsoron ta kara wani abu Bashir ya sanar da Baban Inna ta shiga uku.
Wai kura ma tayi lafiya kenan da ace a baya ne kila sai ya barta kwance zai bar gidan.
IDAN AN CIZA..! Part 4
Gidan retire Major Kabir Sulaiman Dabo tun yana cin zamaninsa gida ne da ya amsa sunansa gida, yana cikin garin Abuja sannan a cikin wannan kyakyawar anguwan nan ta samu kusa a gwanmati wato Gwarimpa. Gidan nyana nan da kyansa kamar baya, ko da megidan ke kwance ba shi da lafiya Dr. Sulaiman da Daddy Hamza ba su bari gidan ya bukaci wani abu ba.
Akwai tarin ma’aikata acikin gidan tun daga megadi zuwa masu kula da haraban gidan, ciki kuma masu aikin bangaren share share da girki saboda Barr. ba mazauniya ba ce tana fita kotu in tana da shari’a.
Ammh kafin ta fita sai ta gyara mijinta tsab ta masa duk abin da yake so sannan take fita, in ta na gida ita da kanta ta ke shiga kitchen ta girka masa irin abincin da yake ci saboda yanayin jikinsa.
Major Kabir ba shi da wani aiki daga kwanciya sai ko in ya gaji ta kama shi ta ɗora shi saman Wheelchair da taimakon wani Musa mai kula da fulayoyin gidan tunda ita kaɗaai ba zata iya ba. Duk da kuma tana ma iya bakin ƙokarinta.
ƴayansu suna nesa da su amma suna zuwa ganinsu lokaci bayan lokaci musamman ma Dr. Sulaiman da duk wata shi da iyalansa suna zuwa Mimi kuma sai ta yi wattani uku bata zo ba suna dai magana ta waya.
Wannan watan ba ta kai karshe ba suka haɗu gabaɗayansu a Abuja Saboda jikin Abi da ya motsa, da ya ke akwai likitan na musamman ne daga babban Asibitin Abuja yake zuwa ya na dubashi ko da aka san laluran bata warkewa ba ne, amma zama waje ɗaya dole akwai bukatar tallafawan likitoci da sharwarwari.
Bayan Dr. Sulaiman da iyalansa har da Khadija(Khadi) ta zo itama sai Mimi da Hajiya wacce ta na jin Mimi zabta je ta ce ita ma ba za ta zauna ba, dole Mimi ta yi musu bucking din jirgi suka taho ranar jumma’a da yammah. gidan sai ya yi albarka Sosai Madiha ce kaɗai bata samu zuwa ba ta ce sai karshen wata za ta shigo tayi hutun ta, daga nan har Gombe za ta shiga ta ga dangi kafin ta koma.
Jiya kwana suka yi hira Abi yaji daɗi sai dai yana kwance yana ta faman mirmishi kamar yau ɗin ma da gabaɗayansu suke cikin Bedroom ɗinsu shi da Mommy tunda yace a barshi a kwance yafi jin daɗin kwanciyar. Gabaɗayansu suna ɗakin ƴayan Dr Sulaiman su biyu kacal duka kuma mata da mai sunan Mommy Murjanatu suna kiranta Ummita sai mai sunan Hajiyar Shagamu suna kiranta Momi.
Sune ke tare da Abi suna ta nuna masa abu acikin Kananun tab ɗin su na yara da yake hannunsu. Hajiya na gefen kafafun Abi ta na mgana da Mommy.
Dr.Sulaiman na daga gefe tsaye ya harɗe hannayensa a saman kirjinsa dogon farin Bafullatani mai cike da fara’a da zati.
Matarsa kuma mai suna Jawahir ta na gefen Mimi, ita tana zaune a saman kujerun Dreesing mirro, Mimi kuma tana daga saman madubi sai dai waya ce a hannunta tana ta faman latswa rabi da rabi hankalinta ke wajen Hajiya tana jin hiran da take yi ma Mommy, jefi jefi kuma Big bro na saka musu baki Sisto kuma ta fita ta je za ta yi wanka.
Duk Lokacin da Mimi ta ɗago kanta sai ta ga Abi na kallonta sai ta yi masa mirmishi kawai shima sai ya mai da masa martanin mirmishinsa Allahu Akbar rayuwa kenan Abi na bata tausayi in ta kallesa shi ya sa ka bi rayuwa a sannu in kasan mafarin ka, ba ka san karshen ka ba. Ba za ta manta Rayuwar da suka gudanar a wannan gidan ba shi ya sa har gobe bata kaunar duk wani aiki na kaki saboda gani ta ke yi kamar yadda Abi ya rika tafiyar da rayuwarsa a baya saboda kakin da ke jikinsa ne. Abi ya yi zamanin da duk abin da ya ce ba wanda ya isa ya ta da shi, hatta Hajiya da ta haifesa kuwa, Mommy kuwa da suka yi auran soyayya ba ta isa ya nemi shawaranta ba ra’ayinsa ya ke bi da abunda ya yi masa dai dai shi ya ke aiwatarwa. A zamanin baya mutum ne mai murɗewa da ka’ida mai tsauri, amma sai ga shi rayuwa ta sauya komai yanzu ya yi sanyi Abi ya koma rayuwar kwanciya cikin ibadar Jinyar ta Ubangiji sai ta ga ya yi sanyi rayuwar ma kamar tsoro ta koma ba shi. Duk sanda zata zo ta koma tsakaninsu sai ban hakuri ya rika cewa Ki yi hakuri kin ji ko Mimi?
Sai ta ce bakomai Abi zan cigaba da yi maka biyayya har karshen numfashi na.
Yana so ya yi mata mgana amma kuma har gobe ya kasa iya furta wani abu.
Ko mganar ta ƙi sauraran kowa ake yi a gabansa sai ya ce a kyaleta a daina takura mata, in kuma yan’uwansa suka zo suka fara mganar Mimi taki aure har yanzu kuma shekarunta na tafiya sai ya ce kar da wani a cikinsu ya ce zai takura mata a kyaleta ta yi aure a lokacin da take so da kuma wanda ta ga ya dace da ita. Kowa yasan dalilinsa na cewa a kyale Mimi to bakin alƙalami ya riga da ya bushe abin da ya faru a baya ba wanda ya isa ya iya sauya shi.
“Habibi ko Dr zai ɗaura ka saman Kujeran nan ne, na ga tun jiya fa kake ta kwanciyar nan?
Mommy ta faɗa Lokaci ɗaya tana mikewa Hajiya ta ka da baki ta ce”Gaskiya kwanciya da zama waje ɗaya ba daɗi. Kabiru Allah yasa kaffara ne amma ana ta Ibada Allah ya bamu sa’a kawai.” aka amsa mata da Amin Shi kuma Abi sai ya yi mirmishi kafin ya ce” Honey kyaleni kawai nafi jin daɗin kwanciya in na zauna sai kuguna ya rika min zafi zafi wani lokacin.’
Sulaiman ya kariso yana faɗin “Abi to ai saboda kana jimawa a kwance ne, yawan zaman zai rage lanƙwashewar da jikin ka ya yi a waje ɗaya”
Kwallah suka cika kwarmin Idanuwan Abi ya yi saurin shanyewa yana faɗin”Ku kyaleni kawai, na fi jin daɗin kwanciyar fiye da zama.”
Yadda ya yi mganar ne ya sa sai jikin Kowa ya yi sanyi, Hajiya ta yi tagumi kafin kuma ta fara sharan ƙwallah tana faɗin “Lafiya lau kabiru ya bar wajena ina saka masa albarka, sai ganin Hamza nayi yazo cikin ɗimuwa ya na faɗa min Kabiru sun samu hatsari a hanyarsu ta komawa Habuja, Allah ya jiƙan Mallan Sale ina ganin fuskarsa a cikin Idanuwana har yau wlh.”
Sai ɗakin ya dauki shuru aka koma Jimami, Abi kuma hawaye suke ziraro mai ta gefen kunnuwansa duka biyu Mommy ke saka tissue tana share masa, Mimi ta sauke wayar hannunta ta na sauke numfashi hankalinta duk ya tashi, in ta kalli Abi sai ta ji ta kara tsoron rayuwa gabaɗaya ba Abin da ta sani a baya ba ne jajirtacce namiji wannan Abin a kwance yake yana kokuwa da kaddaran Ubangijinsa.
Sai da Hajiya ta dai na kukan sannan Abi shima ya dai na. Shigowar Sisto Khadi ya sa sai a ka shiga wata hirar na dabam, Jawahir kuma taja ƴayant azuwa Kitchen suna kukan yunwa suke ji, ita kuma Mimi sai ta koma kan wayarta tana karanta sakon Baby Rukayya.
“Don Allah ko sunan shi ki faɗa min Mimi ta”
Charting suke yi tana ta mata magiyan sai ta faɗa mata sunan wanda ta ji yaddiko da Hajiya na mgana ita kuma ta ce mata wannan wani abu ne da ya shuɗe bukatar taso da mganar da ba ta da amfani.
A wajen aiki ma haka Rukky ta rika yi mata magiyan wai sai ta ba ta labarin shi ko wannan mutumin waye shi da Mimi ta kasa mantawa da shi. Ita kuma Mimi ta ce ta bar damunta da wannan mganar, abu ya riga ya wuce ba amfanin ta da maganar yanzu.
“Sunan shi Hayatu..”
Sai ta fara yar dariya saboda yadda Rukky ta turo mata emojin kuka da damuwa, saboda Hayatu sunan saurayin Rukayya ne da suka rabu shi ya sa ta mata shakiyanci.
Tana cikin Mirmishi taji Hajiya na faɗin”Hamza fa ya matsa kan mganar Jaheed da Binta, yaddiko ma ta yi min ƙorafin tunda shi Jaheed ɗin na sonta mai zai hana ayi yar gida?
Mimi ta tsaya cak da abin da take yi tana kallon Hajiya cikin mamaki. Har sau nawa za ta faɗa mata bata son Jaheed amma Hajiya ba za ta fahimci yaren ba kenan
“Mimin ta amimce da shi ne yanzu Hajiya?
Mommy ta katse Hajiya da wannan tambayar Sulaiman ma ya ce”Matsalan har shi Jaheed din ba ka gane in da ya dosa ne.”
Mommy ta ce”To nima shi na gani mai so ai shi ya ke nema ko Hajiya?
Khadija da ta fi kama da Mommy ta gyara zama tana faɗin “Mommy ni ko sai na ga Jaheed ba laifi, Mimi ce matsalan kusan halinta kowa sai ta ce ba ta so kuma in aka biye mata sai dai kila ta mutu ba ta yi aure ba a take taken ta wlh.”
Khadija ta faɗaa lokaci ɗaya ta juya tana mai kallon Mimi ta ke ta hararanta.
Sulaiman ya kalleta ya na yar dariya kafin ya ce”Sisto taho nan naji me ya sa baki son Jaheed din? Mimi ta tura baki kafin ta mike sanye ta ke da doguwar riga mai santsi ta na da buɗewa ta kasanta sannan ba ta kama Jiki sosai ba.
Har gabansa ta zo ta tsaya ya kama hannunta yana faɗin”Me ya sa ba ki ba ma Jaheed dama ba Mimi?
Mimi ta yi shuru ba ta yi mgana ba kuka ke son taso mata sai dai ta danne amma taki mgana.
Khadija ta ce”Ba ta da wani dalili fa, Saboda tasan ba shi da makusa, haka abokin Dee ya ce yana sonta nan ta wulakantashi ni nasan abin da take yi ma ƙulafuci wannan yaro shi ke cikin ranta har yau ta kasa cire shi.”
An so so mata in da ke mata ƙaiƙayi kawai sai ta fashe da kuka har da jiniya, Abi na kwance faɗi yake yi” Dr. Kyaleta ku kyaleta Mimin Abi taho nan taho nan wajena.”
Sa gudu ta haura gadon ta faɗa gefensa ta na kuka shi kuma ya saka hannunsa guda ɗaya yana shafa kanta cikin lallashi yake fadin”Ki daina kuka, ki kwantar da hankalinki tunda baki son shi ba wanda zai ce dole sai kin aure shi Ok?
Sai ta gyaɗa kai kafin cikin kuka ta ce”
Abi ba na son shi, ni wlh ba na son Jaheed”
Ta karishe faɗaa ta na gunjin kuka kamar wacce aka daketa. Mommy da Hajiya suka kalli juna ba su yi magana ba.
Abi ya ɗago idanuwansa ya na kallonsu kafin ya ce”Kar a ƙara takura ma Mimi da mganar kowa tunda ta ce ba ta so a kyaleta, shima Hamzan zan kira shi a bar wannan mganar tunda Mimi ba ta so period.”
Khadija ta buɗe baki ta ce” Amma Abi..'”
“Na ce tunda Mimi bata so a bar mganar nan, abin da Mimi take so ko bayan raina shi za ku yi mata wanda kuma ta ce ba ta so kar ku ce za ku matsa mata don Allah..”
Abi ya katse Khadija, ya na mgana kamar zai saka kuka da sauri Sulaiman ya ce”Abi ba wanda zai takura mata kan abin da ba ta so tunda tace ba ta ra’ayi nima ina goyon bayan a bar mganar.”
Hajiya ta ce” Ni kaina ba zan ce a yi ma Binta fole ba Kabiru, Yaddiko ce da Hamzan suka matsa da zamanta haka ba aure shekaru talatin ai ba kwana talatin ba ne.”
Mommy ta yi shuru ba ta yi mgana ba wani abu da ya faru a shekarun baya suna dawo mata, duk abin da ke faruwa da rayuwar Mimi ba kowa ya ɓata komai ba sai shi.
Ba’a maida hannun agogo baya tasan da ana maidawa da tuni Major Kabir ya maida lokacin ya gyara kuskuren da ya tafka a zamanin baya da ya ke ji da duniyar a saman kansa.
Mimi jin a bar mganar Jaheed sai ta daina kuka ta tashi ta fice daga ‘ɗakin ta koma Bedroom ɗinta na gidan kwanciyarta ta yi ta na sharan kwallah, Jaheed ɗin fa da gaske ba shi da makusambSai dai ita kawai ba ta son shi ne, sannan shagwaɓaɓɓe ne ko ita mace albarka ta zauna tana wannan shagwaɓan Mama boy ne. Jaheed babban yaron Daddy Hamza ne yana Lagoa can ya ke aiki a wani babban kamfanin sarrafa Karafuna.
Sannan kuma a America ya yi karatunsa na Engeniaring har na tswon shekara biyar, yana da wayewa har ta yi masa yawa kuma ita a tunaninta ba sonta yake yi ba kawai yana sonta ne saboda tana aikin gidan Tv asan fuskarta a duniya sannan tana da kyau domin ya sha faɗa mata shi bazai iya auran macen da bata da kyau ba, shi komai nashi ya na son harka da abu mai kyau
Yaddiko ta matsu ta yi aure kamar a saman kanta take zaune shi kuma Daddy saboda Jaheed ne shi ya ke matsa masa tunda ta ki ba shi dama kuma yasan har yanzu bai samu karɓuwa. Ba ko da yaushe take ɗaukan wayansa ba sai ta ga dama, a chart kuma sai ya yi mgana da wajen sati sannan ta ke dubawa. Ita fa Namiji kwara ɗaya ta taɓa so kuma har abada shi kaɗai take so.
Tunda Abi ya ce a bar mganar tasan mganar ta mutu. Saboda a baya ne Abi ke girmama ra’ayinsa saman na kowa, amma yanzu zai iya girmama nata ra’ayin sama da na kowa ba na shi ba ma. Saboda yana tuhumar kanshi da komai ya faru da rayuwar Mami shi ne silar hakan.
Tana jin shigowar Khadija ɗaakin sai ta yi kamar ta yi barci tana jinta ta kira Anty Madiha a waya tana faɗa mata duk abin da ya faru da yadda Abi yace a bar mganar.
Abu ɗaya ya fi bata haushi irin in da Khadijan ta ce”Ni fa nasan me ya sa Mimi ta kin sauraran kowa, wannan yaron ta kwallafara rai akansa wanda ba ta san isalinsa ba, tuni ya yi auransa ma ya manta da ita, itama ai ya kamata ta manta da abin da ya faru a baya ta gina wata sabuwar rayuwar.”
Tana da tabbacin khadija ba ta san menene SO..! Da ace ta taɓa ɗanɗana shi ta ji ya ya raɗaɗinsa yake da ba ta yi wannan mganar ba. Da ace tasan ya ya zafin dafin so ya ke da ta yi mata uzuri, ammh itama ta yi ma lta uzuri saboda wanda take so ba ta sha wahala a kansa ba ta same shi. Shi ya sa ba za ta san zafin dafin ka rasa wanda zuciyarka ta aminta da shi ba, ba ta san ya ya zafi da raɗaɗin raba ka da wanda kake so ba. Duk ba ta san wannan zafin da raɗaɗin ba so khadija tana bukatar a yi mata uziri ko da uzurin ya kai kimanin sau saba’in ne. Saboda wannan dalilin ya sa har suka koma Gombe ita da Hajiya ba ta kara walwala a gidan ba. Haushi Khadija take ji, itama Khadijan haushinta ta ke ji Sulaiman kuma ranar oahadi suka bi jirgi zuwa Kano shi da matarsa da ƴayansa. Mimi kuma sai washegarin litini suka bi jirgi ita da Hajiya zuwa Gombe nan suka bar Khadija tunda ita sai mijinta ya so za su koma tare.
Ko bayan dawowarsu Hajiya ma ba ta kara ta da mganar ba, sai dai kwana uku tsakani ta dawo daga wajen aiki ta iske Yaddiko a gidan ta na ganinta sai da gabanta ya faɗi domin tasan akwai mgana.ilai kuwa kan mganar jaheed ne tana ta ma Mimi faɗan da ta ki ɗan uwanta so take yi ta zauna ta cigaba da fita aiki tana nuna fuskarta a duniya bata da niyar aure.
Daga karshe ta gatsa ma Mimi mgana da cewa” In ma wannan yaron kike ta jira to kin yi a banza, a gabanki a gaban mu mahaifinki ya ce ko bayan ransa kika auri wannan yaron bai yafe miki ba.”
Mimi ta fashe da kuka wiwi Hajiya ta fara yi ma Yaddikon faɗan me ya sa take haka ne? Ita kuma ta ce ai gaskiya gwara ma ta rufa ma kanta asiri ta karɓi ɗan uwanta yadda ma tun lokacin yaron bai kara nemanta ba zata fahimci da gaske yake yi abin da ya faɗa da ya ya ce ko su kaɗai suka rage a duniya sai dai su mutu ba aure ba zai aureta ba.”
Cikin faɗa Hajiya ta ce”To miye na sai kin ta do da abin da ya wuce Yaddiko, ko Kabirun da kike magana ya yi sanyi kuma shi da kansa ya ce tunda Binta bata so a bar mganar ba shi kenan ba.”
Yaddiko ta yi shuru ba ta yi mgana ba sai can ta ce”Ai shike nan ta share kafa ta ci gaba da zama, daga karshe su kansu in da take aiki ta na fara tsufa za su nemo wata domin suma da kyanta da Kuruciyarta suke amfani da zaran shekaru sun ja sai dai kuma ta dawo zaman gida.” Kalaman sun yi ma Hajiya ciwo sai dai bata nuna ba cewa kawai ta yi”To mun gode sosai.”
Alamun ranta ya baci da Yaddikon ta ga haka ne sai ta koma kawo ma Hajiya illar zaman Mimi haka ba aure tunda tana da maneman ba wai babu ba ne.
Hajiya ta yi mata bakam har ta gama maganganunta ta kira Jikanta yazo ya ɗauke ta ya maida ta gida.
Mimi kuma ranar kwana ta yi kuka sai dakyar Hajiya ta lallasheta tasha Tea ta kwantar da kanta a saman cinyar Hajiya tana na hawaye tana faɗin ” Hajiya ko wa ya ƙi ya fahiimceni ko wa yaƙi ya fahimci ta inda na ke jin ciwon abun, Hajiya ta nan ne, anan ne na ke jin wani irin nauyi a kirjina ta nan wajen ne.” Take faɗi tana kai hannun Hajiya saitin wajen zuciyarta.
Cikin damuwa Hajiya ke faɗin “Ki yi hakuri Binta komai mai wucewa ne In sha Allahu.”
Tana kuka Hajiya na share mata hawaye, Kukan da ta yi jiya yasa washegari da safe tana karanta labarai haka ta je wajen aiki fuska duk a kumbure. Ta sha tambayoyi sai dai tace idanuwanta ke ciwo sai aka koma bin ta da sannu Allah ya sauwake.
Rukky ta zo ta sameta a restroom tana hutawa ta riƙa damunta da mgana.
Ta gaji ta kalleta cikin wani yanayi kafin ta ce”Baby ƙyaleni yau bana jin daɗi ne kwata kwata.”
Baby ta kalleta kafin ta ce”Daman tunda na ganki na fahimci haka, ki faɗa ma Manaja sai kije gida ki huta in kin warke sai mu yi mganar bikin Biba ne daman”
Shawaran Rukayya ta bi, taje ta sanar Manaja nan da nan ya ce ta koma gida daman yau da safe duk wanda ya kalli labaran Safe yasan wani abu na damun Mimi. Idanuwanta da fuskarta sun kumbura sannan ba ta da fara’a ko kaɗan shiyasa da ta ce ba ta jin daɗi ba wanda ya karyata hakan. Dakyar ta iya tuka kanta zuwa gida sai dai Hajiya ta ga ta dawo ta ce mata kanta ke ciwo zata huta, Hajiya ta ce Allah ya sauwake ta kwanta zuwa azahar in ta tashi sai taci abinci ta sha mgani.
Ɗakinta ta shige ta kwanta a saman gado ta na sauke numfashi.
Ba kanta ke ciwo ba zuciyarta ne ke ciwo amm tunda zuciyar tana rufe ne ba wanda ya sani ballantana ya fahimci halin da take ciki.
Aji.
Aji.
Aji.
Shi ne ciwonta, shi ne kasarwata shi ne kuma rauninta shi ne ciwon da ya yi shekaru ya na cinta acikin zuciya.
Ta yi addu’an har ta gaji ta bar ma Allah lamarinsa. Wasa wasa sai da shafe kwanaki uku ba ta je wajen aiki ba.
A fuskar labarai Salim Bunza aka yi ta gani ba ita ba sai a ranar na ukun da ta dawo ne ta cigaba da kawo labaranta a yadda ysarin yake tun Farko.
Sai dai kowa in ya kalleta sai ya ce ta rame idanuwanta sun zurma ciki sannan ta rage karsashi da fara’a.
Haka so ya ke ɗiba ya maida kai bawa. Matsayin ka bai dubawa, balle yasan kai waye,ya saka ka yi jinya. Ka sauka kan Hanya ka manta alƙaarya ka yi kalan wawaye.
1rd March 2022
Anguwan Arawa da misalin karfe 8:30pm na daren ranar Alhamis.*
Jiya ya dawo daga can kauyen mahaifin shi wato garin kwami cikin garin hedikwatansu na Mallam Sidi, gajiya ce jiya ta rufe shi ya sa ya wuce gidansa ya kwanta da rana kuma yana camp ɗinsu tunda evening training suka yi. Sai da suka tashi ne ya koma gida ya yi wanka ya ɗauko tsaraban da suka matsa masa sai da ya ɗauko, kifi ne da su dankali doya da sauransu.
Tunda Allah ya albarkaci garin mallam Sidi da amfanin gona da kifin Kifin bushasshe ne, shi ba ya cin kifi tun da ya ji labarin sanadin kayar kifin ne ajalin mahaifinsa ya tsani kifi a rayuwarsa.
A msallacin kusa da gidansu ya yi sallar isha’i yau da Motarsa ya zo shi ya sa matasan anguwa suka ɗauki Ihu ga Aji ya zo, Aji yara da manya sunan Aji na bakinsu.
Tare da su Baba Sani yau ma suka yi sallar har da Baba Ɗanjuma. Tsaraban da ya zo da shi yara ya sauke a kofar gida ya ce su shiga da shi shashen Inna Meri.
Mansoor mutum ne mai kyauta hannunsa ya na sake ne, shi ya sa in dai yazo anguwan nan ya riga ganin mutane kenan. Ta bakin Inna Meri ta ce Baban Inna jama’a fa Rahma ne ka cigaba da aikin alheri wata rana in ka mutu wallahi da wannan shedar za’a tuna ka. Kuma tunda Allah ya rufa mishi asiri ai ya na da halin taimakawa. Bayan ya gama sallaman jama’an garin ya zo ya sallami gidansu.
Tunda tun bayan da ya yi karfi a ƙwallon kafa ko ya ce tun bayan da ya cike takardan Kontiragin ɗin da ya yi da kungiyar ƙwallon kafa ta Gombe United rayuwarsa ta sauya.
Duk watan duniya nan ya na kwasan albashi mai tsoka, sannan kuma ga alawus in sun fita gari sun buga wasa.
Ya fito ma ya faɗi irin kuɗin da yake samu sai ma a karyata sa. Shi ya sa ya ɗauki nauyin abincin gidansu duk wata sannan kuɗin makaranta Mariya da Walida da duk wasu bukatu na shashen su.
Bangaren su Baba sani ma yana siya musu kayan abinci duk wata wani lokacin kudi ya kan ba su, ko kuma ya wakiltan Auwalu tunda in aka ba su kudi sokewa suke yi suki siyan kayan abincin.
Auwalun ma daman ya kirashi tun shekaran jiya yana can kauyensu ya ce ya bari ya dawo, to shima anan gida suka haɗu shima dai yana masa bayanin matarsa ke da tsohon ciki haihuwa ko yau ko gobe ba shi da kuɗin ragon suna ballantana kuɗin hidiman suna. Kuma daman gini yake yi kuma yanzu aikin sai a hankali.
Bai damu ba ya ce zai tura masa kuɗi ta asusun bankinsa ya cire kudin hidimarsa sauran ya siya ma su Baba sani kayan abinci. Anan kuma take ya ba su kowanne dubu ashirin na cefane. Suna ta saka albarka duk da yasan a bayan idon shi sai sun raina.
In da zai rike abin da suka yi masa a baya ko kallo ba su ishe sa ba. Ba zai manta yadda suka ware shi ba, a cewar su shi Agola ne.
Sai dai alherin Baba Ɗanjuma yake kallo a gareshi shi ya sa yake musu komai baya nuna bambamci.
Ko gyaran gidan da ya yi kaf ɗakunan matansu ya sa an sassake an saka musu tayels da kuma fentin zamani.
Dakin Inna Meri da magajiya kuma ya maida musu shi kamar na yaran mata.
Bai nuna bambamci ba duk abin da ya saka ma Inna Meri shi ya saka ma Magajiya.
Amma bata taɓa godewa ba, sai ma masifa da ta ke yi a bar mata ɗakinta ɗan ta Auwalu zai gyara mata, yaron da ke fama da kansa ammh fa da aka gyara ɗakin ta ji daɗi ba ta dai nuna ba har ya’yanta da a shekarun baya sun sha su nuna bambamci kiri Kiri tsakaninsa da Mu’azzam.
Tunda shi sun haɗa uba shi kuma zuwa da shi Inna Meri ta yi agola ne mara galihu.
Tare suka shiga gidan da Auwalu Magajiya na ƙofar ɗakinta tana tatan nikan geron kunun safe da za ta dama suka shigo.
Auwalu ya fara gaisheta ta amsa cikin fara’a amma Mansoor na cewa” Barka da dare Magajiya.” Ƙim amsawa ta yi shi kuma ko ajikinsa ya tsallake zuwa shashen Inna Meri.
Ya bar Auwalu tsaye ya a faɗin “Magajiya kina jin Mansoor na gaishe ki kika amsawa?
Sai ta masifa tana faɗin”Ban amsa ba sai kuma na yi laifi? Ba ka ji irin gaisuwan na shi ba ne wai barka da dare kamar wata sa’arsa ai in uwarsa ce meri ba haka yake gaisheta ba.”
Auwalu yace”Magajiya tsakani ga Allah ko Inna Meri haka yake gaisheta ko Baba ne kuwa shi haka yanayin gaisuwarsa yake”
Sai ta fara balla masa harara ta na faɗin “Ta fi can sakarai mara kishin kai kawai.”
Saboda yadda ya ji tana faɗa yasa ya fasa ma shiga ɗakinta kawai sai ya Juya ya fice.
Tun tasowarsu wannan halin na magajiya da shi suka ganta. Kowa hakuri yake yi da ita musamman ma Baba.
Ba domin yana hakuri ba tuni ya jima da sakinta tunda ta daɗe cikin zamanin rashin mtumci acikin gidan nan ba adadi.
Shi ko Mansoor yana can ɗakin Inna Meri suna ta fira ya na bata sakon gaisuwan mutaanen can da suka ce suna gaisheta.
Ya iske ma Yaya Amina a gidan ta zo tun ɗazu har ta na yi masa tsiyan ta fi wata biyu ba ta ganshi ba. Mirmishi kawai ya yi batare da ya yi mgana ba.
Inna Meri ta kallesa kafin ta ce”Ya ka samu Goggon naka Yalwa? jikinta da sauki ko?
Mansoor yace”Eh ta samu sauki, amma na bar mganar a kaita asibitin cikin gari a dubata, na ba ma jikanta ɗin nan lambata na ce in da wani abu ya kirani.”
Inna Meri tace”Allah Sarki yalwa mace mai son zumumci ba’a wata biyu ba ta zo garin nan ta duba ka ba, sannan ba ta zuwa hakanan mata nan ta na son zumunci kwarai bata manta da ɗan dan uwanta ba.”
Yaya Amina ke faɗin ko itama ta san lokacin da ta ke zuwa ta zo mu su da kifi da dankalin hqusa. Inna Meri na kara faɗa mata kirkin ƴanuwan mahaifin Baban Inna da suka yi mata karamcin da ta kasa mantawa.
Shi dai yana gefe yana jin su ya yi shuru bai saka baki ba. Yana tunanin zuwan da ya yi yadda Yalwa ta matsa masa da mganar aure wai sa’aninsa har da masu mata biyu.
Ya je Bauchi gidan Baba Kabiru ya duba cikin ya’yansa suma yan boko ne irin sa tunda baya son yan kauye.
Sai da ya yi mirmishi shi tun bayan da ya rasa Mimi ko da wasa bai kara kallon wata mace da sunan so ba.
Tun lokacin rayuwarsa ta sauya ya cire babin aure a tunaninsa.
A tunaninsa ba zai iya kallon wata mace da sunan so ba, to so guda ɗayan da kaunar gabaɗaaya ita ya damkawama kuma da ta tashi tafiya sai ta tafi da abin ta gabaɗaya.
Zuciyar Mansoor yanzu babu sararin da zata iya samar ma soyayya matsugguni ba.
Ko Inna ya ka sa faɗa yadda suka yi da Gwggon nasa, ya dai ce mata ta bari in ya kara dawowa sai su yi mgana. Su ma ya yi raban kudi sosai a garin ƴauwansa ne bayan nan Gombe ba shi da kamarsu tunda nan ne tushen mahaifinsa.
Yaya Amina ce zata ta fi mijinta ya dawo daga aiki ya zo ɗaukanta sai Mansoor ya daukan mata kullin buhunta da Inna Meri ta ɗibar mata tsaraba zuwa waje, suna tafe ta na ba shi labarin Bintu ta zo gidanta da yadda ta ce ya je gidanta ya yi mata faɗa gaban Kishiyarta. Mirmishi kawai ya yi bai yi mgana ba ya na can ma ta kirashi suka gaisa kuma yasan ma’anar gaisuwarta daman ya na da tunanin barin mata sako a wajen Inna ko Walida sai ta aika mata da shi. Sai da suka gaisa da mijin nata sannan suka yi sallama ta hau mashin din suka bar Kofar gidan Baba Danjuma kuma na can gefe shi da Mallam Hashimu suna ta mgana, Mansoor ya rasa menene suke tattaunawa haka tun ɗazu suke tsaye suna mgana ba ta kare ba. Har ya Juya zai koma cikin gida saboda tuwon Inna yake son ya ci a camp yau zai kwana gobe suna da morning training.
Read Also: Part and Part 2 here
“Aji.”
Ya ji an kira sunanshi, ya ji muryansa shi ya sa ya juyo yana kallonsa yana karisowa kusa da shi.
Cikin dariya ya ce”Shege Aji motarka na gani sai kuma na hango ka daga nesa.”
Hannu ya bashi suka tafa lokaci ɗaya yana faɗin”Makama ya garin? Kwana da yawa”
Wanda aka kira da Makama ya ce”Aji gaskiya ka sauya rayuwarka, shiken an ka janye jikin ka daga na mutane yaushe rabon da mu haɗu da kai?. Muna gari ɗaaya Aji ammh sai mu yi wattani bamu haɗu ba.”
Mansoor ya ce”Rayuwar ne sai a hankali makama.”karamin tsaki ya ja kafin ya ce”Ba wani rayuwa, Mu’azzam da ba garin nan ya ke aiki ba duk zuwa sai ya kiramu mun haɗu amma kai kana garin nan ko an kira sai ka ce baka da lokaci an ya Aji ba za a manta baya rayuwata ta yi kyau ba”
Mirmishi kawai ya yi bai yi mgana ba Makama ya dafa kafaɗarsa kafin yace” har fa group mu ka buɗe namu mu biyar ko tari baka taɓaa yi ba har abubuwan biki na da ake tattaunawa ba ka ma san halin da ake ciki ba.” Mansoor ya ce”To yanzu tunda ka zo ba sai ka faɗa min ba.”
Makama ya ce” To ya na iya, biki fa ya zo saura wata biyu yanzu.”
Mansoor yace”Allah ya nuna mana.”
Makama ya amsa da Amin Amin.
Tsiya ya fara yi masa wai duk sun yi aure shi ya zauna sai ya zama tuzuru.
Mirmishi ya yi masa bai yi mgana ba shi kuma ya kallesa lokaci ɗaya yana faɗin”Ka ma saki jiki mallam wallahi da kai za’ayi komai a bikina baka isa ka tsame jikin ka ba.” Mansoor ya ce”Allah ya sa muna raye za a yi, kuma ka yi fatan ba ni da wasa a lokacin.”
Makama ya harzuka cikin fusata ya ce”Na bi wasan da gudu na taka da takalmin kafata” Har yana bubbuga kafa da ya sa sai da Mansoor ya yi yar dariya yana faɗin”Makama ba za ka canza ba.”
Cikin yar dariya ya ce”Ina fa zan canza, ni fata na Allah yasa a wajen bikina ka samu cikin ƙawayen amarya wata ta yi wuf da zuciyarka.”
Ido ya saka masa kafin ya ce” kana ganin akwai wacce za ta iya?
Makama ya buga kafaɗarsa lokaci ɗaya yana faɗin”Tsab kuwa mutum ne fa kai ba robot ba.” Sai kawai ya jinjina kai kafin yace”To sai mu gani in za su iya.”
Cigaba da hira suka yi duk dai rabin hira daga bakin makama ne.
Har Baba Danjuma ya kariso suka gaisa ganin haka ya sa ya ce bari ya shiga ciiki ya gaida Inna Meri. Tare suka shiga ya gaida Inna Meri taji daɗi sosai har ta na dibar masa Kifin da Baban Inna yazo da shi ta ce ya kai ma baabarsa.
Da zai tafi ma Mansoor ya rakosa har waje sun ka ɗan jima kafin su yi sallama.
Shi Makama gidansu na can Tudun wada ne yazo Arawa ne gaida wani abokin babansu.
Yadda suke hiran za ka fahimci sun jima da sanin juna.da kuma yadda ya ke labaran wasu abokan na su da Aji ya daɗe bai haɗu da su ba kuma suna gari ɗaya kamar irin su Shamsu, wanda ko a baya ba abokinsu ba ne amman abokin faɗan Aji ne.
Shi fa rayuwarsa gabaɗaya ta sauya ko a baya da yake da miskili ammh yanzu sai ya fi miskili iya miskilanci a baya yana shiga mutane ammh yanzu ya daina shiga jama’a kwata kwata ya koma yin rayuwa shi kaɗai kamar ba shi da kowa abokinsa kawai ƙwallon kafa ne.
IDAN AN CIZA..! Part 5
Page 5
Monday 5rd March, 2022. Gidan Talabijin na Karamchi
10:04am
A shashin al’amuran labarai na yau da kullum na gidan talabijin mai tashe a jihar gombe. Wani shashi ne mai girma a gidan talabijin ɗin mai ɗauke da babban falo tare da ofisoshin manyan ma’aikatan bangaren.
Irin su news manager, editer da sauran su shi kuma babban falo mai ɗauke da kowani rukuni kamar an ƙawayanta ma kowa bangaransa ne. Kowa kuma akwai ƙaramin teburinsa da kayansa a kai sai kujeran inda kake da muhallin ijiye komai naka, daga gefe akwai ɗan aninin da ke nuni da sunan mai wajen. Daga can kusa da office ɗin new manager wajen zaman Broadcaster ɗin gidan talabijin ɗin ne, daga gaba can kuma waje zaman camera man tare da reporters ne, da kuma ɗalibai masu sanin makaman aiki wato yan Intern.
Dole bayan sun haɗa rahottnni da kuma labarai wato bayan camera man da reporter sun gama aikin su kenan akwai bukatar editer ya duba ya kuma ta ce sahihancin labarin. Bayan ya gama dubawa kuma sai news manager ya duba ya cire kalmar da ya ga ba ta dace ba, dole dai sai an bi matakai kafin labarai ya kai ma masu kallo ko masu saurare. Kuma abuin da mutane wasu ba su sani ba, labaran da ake karanta su a gidan talabijin live ne, ko da an mai maitashi to sake karan tashi aka yi ba recording ba ne.
Sannan broadcaster zai iya zama reporter, amma ba kowani reporter ke iya zama Broadcaster ba, kamar yadda Salim Bunza ya kasance a gidan talabijin na karamchi Reporter ne, sannan kuma shi ɗin Broadcaster ne.
Mimi ce kaɗai ce ta kasance Broadcaster kaɗai kuma a tsarin gidan talabijin ɗin su biyu ne Broadcaster ɗin
Kowani na karanta oabarai sau hakwai a sati tunda kwanaki bakwai sai tsarin ya kasance kowa ya na yin adadin rabin kwanakin da zai kasance a sati. Tun da safe da yammah ne, su ma suna shan wahala kwarai tunda suna da tsare tsare kafin ma a fara ɗaukan labaran live a haska ma mai kallo. A kwai bukatar camera man tare da masu makeup tunda abu ne da duniya zata ri ƙa kallo a matsayin majigin gani da ido akwai bukatar gyara ga mai karanta labaran.
A can baya kafin Mimi ta fara aiki da su wata Cindera ce ta yi aiki da su yar Lagos ce, komawa ta yi garin su ya sa ta saki aiki da Karamchi a tsarin su, suke ba da kayan sawa in da zaka karanta labarai amma zuwan Mimi ta ruguza wannan tsarin ta ce ita da kayanta zata rika amfani tunda kuma yar ma su da shi ne daga ganinta kasan ba tsiya a jikinta kuma ta na da kyau ga iya ɗaukan wakan da kwalliya sai suka amince da tsarinta.
Abu ɗaya ake yi mata kafin a fara ɗaukan live shine makeup man ya gyara mata fuskarta ya ɗan kara mata hoda shikenan.
Duk da ba ta daɗe da fara aiki da su ba ta zama tauraruwa a gidan talabijin Karamchi saboda fuskar Mimi, ta kasance mace mai fara’a da farinjini manyan mutane sun sha kawo ziyara suna mai ya ba mata.
Sannan ga zaƙin murya ga turanci da ya zauna a bakinta, wanda in ta juya harshe sai ka rantse bata taɓa jin yaren hausa ba.
Daga office ɗin editor ta fito zuwa mazauninta in da ƙaramin oaptop ɗin ta ya ke da sauran tarkacenta ta ja Kujera ta zauna ita kaɗai ce a bangaren sai daga nesa kuma sauran reporters ɗinsu ne ke nuna ma ƴan inten wasu abubuwan.
Salim Bunza sai dare ya ke da karanta labarai bai riga ya shigo ba tukunnah.
Sanye ta ke da doguwar rigar atamfa mai adon zanen golding a jikinta ta sanya mayafinta mai raga raga a saman wuyanta da ya ji sarka mai kyau da yarari, hannunta sanye da zabbunanta na zinare guda biyu kafarta sanye cikin wani bakin Booth ɗin takalmi kalan na mata. Saukakkiyar kwaliya ce a saman fuskarta amma kallo ɗaaya zaka yi mata kasan ko ba ta yi kwalliya ba ita ɗin mai kyau ce. Ta zauna kenan wata matashiya daga cikin ƴan inten ta zo kusa da ita cikin girmamawa lokaci ɗaya tana faɗin.
“Barka da aiki Anty Mimi.”
Ta juyo Cikin fara’a kafin ta ce”Yauwa Safina kina bukatar wani abu ne?
Safina ta karisa kusa da ita tana nuna mata takardan hannunta lokaci ɗaya tana fadɗn”kan wannan ne, ina bukatar karin bayani.” Cikin kwarwaarta kan abin da ta karanta ta fara mata bayani har sai da ta gamsu. Cikin jin daɗi ta ce”Na gode Sosai Anty Mimi”
Gyaɗa mata kai ta yi cikin irin mirmishinta kafin ta ce”Kar dki damu aikina ne.”
Cikin jin daɗi Safina ta wuce wajen ƴan’uwanta kamar daman ita su ke jira sai aka zagayeta ta fara kora musu bayanin da Mmi ta kora mata yanzu.
Ta na kallonsu a cikin ranta tana jin wani iri, dama ita ce dama dama ace zata iya maida hannun agogo baya. Su ɗin ta san ba su da wata matsala a rayuwarsu ba kamar ita da ciwon dake ckin zuciyata yake taso mata ookaci bayan lokaci ya hanata sukuni ba.
Ajiyar zuciya ta sauke lokaci ɗaya tana buɗe jakarta da ke kan desk ɗin dake gabanta, ta dauko wayarta ta na latsa hasken wayar sai ta ga Missed call har guda uku da sauri ta ja ta duba, sai ta ga Mommy ce ta kirata bata gani ba. Da sauri ta yi kokarin nemanta sai ga kiran Mommy ya shigo kamar yadda ta yi mata saving acikin wayar. Da Sauri ta ɗaga kiran cikin fara’a kafin ta ce” Barrister Murjanatu Soron ɗinki” Mommy daga can bangaren Ta ce.
“Na’am, Fatima kabir Dabo.”
Sai Mimi ta saki dariya kafin ta ce”Mommy mun ta shi lafiya? ya Abi ya tashi?
Annuri na bayyana a saman fuskarta Ita fa Mommy yar ba ruwanta ne.Sunan kowa da sunan uban shi take yi masa saving a wayarta har Korafi ta taɓa yi mata ita kuma ta ce sunan su ne cikakke ko suna kyamatar sunan ne? Mimi tace a’a Mommy ta ce to ba za ta sauya ma kowa ba, to ba ma su kaɗai ba kowa haka ta ke yi masa saving acikin wayarta.
“Lafiya kalau muka ta shi, Habibi ne ma tun jiya ya(e ta kiran sunan ki shi ne nace bari na kira ki na faɗa miki..”
Mimi na dariya ta ce”Allah Sarki Abi Mommy ba shi wayar mu gaisa”
Mommy ta mika ma Abi wayar dake kwance a kan gado sai dai ta saka masa filo ta kara masa daga bayansa kansa ya ɗan ta sa sama. Cikin yanayin Muryan sa da ta sha jinya ya ce”Mimin Abi.”
Da sauri Mimi ta ce”Na’am Abin Mimi ya jikin ka? Abi ya amsa mata da cewa yaji Sauki ya karishe da faɗin “Honey tana kula dani sosai na gode mata Allah ya yi mata albarka.” Mimi ta amsa da Amin Amin.
Sun gaisa cikin fara’a da tambayan aiki ta ce gata ma a wajen aiki.
Cikin yanayin muryansa ya ce”Mimi ki yi hakuri da rayuwar nan kin ji ko?
Mimi ta amsa da cewa” In sha Allahu Abi Allah ya baka Lafiya.”
Abi ya amsa mata da Amin kafin ya ce” yaushe za ki zo?
Da sauri ta ce”Abi kana son ganina ne?
Abi ya gyaɗa mata kai kafin ya ce”Eh ina son ganin ki, ki zo in kin samu dama.”
Mimi ta amsamai da faɗin” In sha Allahu Abi Allah ya kara maka lafiya da tsawon kwana.” Ya amsa mata dai dai ookacin da Mommy ta shigo bedroom ɗin ɗauke da Mug a hannunta damn tana bashi wayar ta fita zuwa Kitchen.
Tana zuwa kusa da shi ta sauke mug ɗin hannunta saman Side drower ɗin gadon dai dai ya na miko mata wayar ta amsa ta na karawa a kunne ookaci ɗaya tana faɗin.
” later lokacin karya wan Habibi ne.”
Mimi ta ce”Mommy sai an juma.”
Daga haka suka yanke kiran a lokaci ɗaya
Mimi ta bi wayarta da kallo tana ɗan Mirmishi, Abi da Mommy kenan sai ta tuna shekaru a can baya in ran Abi ya ɓaci Murjanatu ya ke kiranta kai tsaye Honey sai lokaci bayan lokaci. Amman yanzu komai ya sauya tsarin rayuwar da komai shi ya sa rayuwar nan duk babu tabbas a cikinta.
Yau fari ne gobe kuma baki, in yau ka ji daɗi gobe kuma akasin sa zaka shiga.
Tunani ta shiga yi, tunanin wani irin nema Abi yake yi mata, ko da yaushe tsakaninsu ban hakuri, ita kuma har acikin ranta ba ta taɓa rike Abi acikin ranta ba komai ya yi mata shi uba ne kuma duk abinnda ya yi domin ya inganta rayuwarta ne, ba taɓa fushi da shi Saboda abijbda ya faru a baya ba, Tana kaunar Abi domin mahaifinta ya wuce sauran mahaifa ya kuma yi mata gatan duniya nan, abin da ya faru wani kaddaren al’amari ne daga Ubangiji da bawa bai isa ya kauce ma faruwarsa ba.
Hankalinta ya yi nisa ba ta san Rukky ta shigo ba, sai kawai ji ta yi ta saita dai dai kunnenta ta ƙwala mata kira.
“Mimii..!.”
Firgigit ta yi gabanta na faɗuwa domin ta ji tsoro sai ta ci karo Rukky da ta na mata dariya cikin jin haushi Mimi ta ce”Rukky Why? Kin bani tsoro ba ki ji yadda kirjina ke faɗuwa ba” Rukky na dariya ta zauna saman desk tana kallon Mimi kafin tace”Tunanin wa kike yi ne da ba ki san shigowa ta ba?
Mimi ta lumshe ido kafin ta buɗe tana faɗin” Me ya faru? Domin daga ganin bakin ki akwai mgana.”
Rukky ta ce”Maganar dai da muka fara ta waya, ki zo mu tattauna yadda zamu shirya bikin Bibi.”
Mimi ta kalleta a karkace kafin ta ce”Saboda ita Bibi ba ta da ƙawaye?
mu fa yayye ne Baby ina ruwan mu da tsara biki wannan ai sai ƙawayenta.”
Rukky ta ce” Bibi ta ce mu tsara komai kinsan fa ba ta da wasu kawaye, sai wasu yan makarantar su kuma kinsan yadda zamu tsara al’amarin ba kamar su ba.”
Mimi ta yi shuru kafin ta kara mgana Rukky ta shagwabe fuska ta na faɗin” Haba mana Hajiya Mimi ta.”
Mirmishi ta yi kafin tace”Yaudara! Zan shigo gidan sai mu yi mgana.”
Rukky tace” Yauwa ko ke fa? yaushe to za ki shigo ? Ko yau kawai ki jirani na tashi sai mu tafi tare.” Mimi ta taɓe baki kafin tace”Yau daga nan ina komawa gida zan dauki Hajiya mu je gidan Daddy kinsan Mama ta kwanta asibiti jiya aka sallamo ta sau ɗaya naje na duba ta shi ne yau zan kai Hajiya mu kara dubata.”
Rukky ta jinjina kai kafin tace”Shike nan Allah ya ba ta lafiya.”
Nan suka cigaba da hiran su Rukky na faɗa mata yadda za su tsara Bikin ya yi kyau sosai. Mimi na dariya tac e”Kina ta tsare tsare Baby, shin angon nan zai fitar da kudaɗe ne masu yawa ya baki?
Rukky tace”Ba ma dolen shi ba, ai na yi mgana da shi yace ba matsala akwai abokansa da suke tunanin ɗaukan nauyin yin dinner, mu dai nan kamu kaɗai Ummi tace zata ɗauki nauyi.”
Mimi ta gyaɗa kafin ta ce”Good! Allah ya nuna mana ookacin da rai da lafiya.”
Rukky ta jima har sai da aka kira wayarta sannan ta bar wajen Itama Mimi bata jima ba ta kwashi tarkacenta ta shiga office ɗin manajansu ta kai masa takardun hannunta suka yi mganar da za su yi ta ce mai ita ta tashi sai gobe da yammah tunda sai karfe bakwai din gobe take da karanta labarai amman zata shigo zuwa la’asar. Daga nan ta fito ta yi sallama da sauran ma’aikantan bangaren su. Ta fita zuwa babban falon da ke ma’aikan ana mata mgana ta na amsawa da sakin fuska. Na Misau ta hanga yana ta hira da wani ɗan siyasa acikin shirin Nageria a siyan ce. Daga masa hannu ta yi ta cikin gilashin da ya raba wajen shi kuma sai ya jinjina mata kai.
Ko bangaren su Rukky ba ta biya ta fita zuwa haraban wajen ta kunna motarta bayan ta ijiye jakarta a kujeran mai zaman banza ta zagaya ta shiga bangaren direba ta zauna da bismillah a bakinta. Sannan ta yi ma motar key ta juya ta fice daga gidan talabijin ɗin megadi na faɗin a sauka lafiya Hajiya.” Itama sai ta ɗaga masa hannu cikin fara’an da ke saman fuskarta.
Bata da chanji ne acikin jakarta sai dai gobe in ta dawo. Mimi mai kyauta ce abun hannunta baya rufe mata ido in tana da shi ta ba ka in bata da shi ta ba ka hakuri.
Gida ta koma ta iske Hajiya ta yi barci sai Baaba Uwani kaɗai a gida tana ta zirga zirga sannu da gida ta yi mata sannan itama ta shige cikin ɗakinta. Kaya ta sauya zuwa masu sauki na gida sannan ta haye gado ta kwanta ta na motsa jikinta domin tana jin jikinta duk gajiya ya saukar mata.
Har ta kwanta sai kuma ta mike ta isa kan Dressing mirror ɗin da ke ɗakin ta buɗe jakarta ookaci ɗaya ta ciro wayarta ta koma ta kwanta. Faceebook ta shiga ta sauya Account ɗin ta na Asali na Fatima Kabir sulaimam Dabo(Mimi).Zuwa wanda ta buɗe na sirri da suna MIAJ Kuma account ɗin bai da suna ko wani bayanan da za’a iya gane ko wani jinsi ne. Da ɓoyayyen account take bibiyan Aji kuma da shi ne ta tura masa friend request tun shekaru huɗu da suka gabata kuma ya karɓeta sannan tana following ɗin GOMBE UNITED nan t ke ganin wasu abubuwan
Tun da shi ba chart yake yi ba, ta sha masa sallama bai taɓa buɗewa ba ballantana ya amsa ta ba, sai dai ta na bibiyan shi ta hanyar club ɗin sa. A nan ne ma ta samu hoton sa da ta kai aka yi ma babban elegerment, anan take ganin in suna da wasa da garin da suka je anan kuma take ganin irin cigaban da ya samu bayan rabuwar su. Ba za ta taɓa manta lokacin tana Kano tana Master ɗinta ba , ta taɓa haɗuwa da ɗaya daga cikin abokansa mai suna Nasir. A bakin shi ta fara jin Aji yanzu ƙwallo yake yi, ta daɗe ta na mamaki sai da ta gani sannan ta tabbatar. Shiga ta rika yi hotunan da Club ke ɗorawa yawanci na yan wasan su ne, har akwai hoton da aka ɗauka da Aji tare da Coach ɗin su ookacin da ya yi singing contract da su.
A nan take samun ganin rabin ranta ta kuma kalle shi son ranta, komai nashi na nan a yadda ta san shi sai dai yanzu ya rage fara’a sannan fuskar nan a kimtse kamar wanda ke cikin bacin rai, ya kara dai girma tunda shekaru sun ja, wani hoto da ya yi mata kyau sai da ta ɗauke shi. A Studion ne aka ɗauki hoton yana sanye a blue din kayan kwallo a jikinsa ya duka kamar zai taso daga sujjuda zufa duk ya cika fuskarsa a wannan hoton ta ga dariyan shi.
Har ga fararen hakoransa nan sun bayyana.
Kamar kuma a wani gari ne da suka je kwallo, sai da ta duba rubutun ƙasan Hoton ta ga an saka. Kaduna da date din sannan an Rubuta Captain Aji baka dariya sai ka kada masu gida. Itama sai da ta murmmusa a sanin da ta masa a baya yana dariya.
Sai dai ta san masifaffe ne, abu kaɗaan sai ya harzuƙa sa ya fara masifa. Ga zuciya da kafiya in ya kafe akan abu baya sauya ra’ayi. Tana kai hoton da ta ɗauka wajen da take adana hotunan sirinta ta furta a fili” Ko yanzu ya daina faɗa? Ko wasu hallayansa ne suka sauya bayan mun rabu?
Sai ta kasa ba ma kanta wannan amsar, sai kawai ta kashe data, ta sauka daga kan Account din ta kashe wayarta ta sauke a gefenta ta koma ta kwanta tana sauke numfashi. Ya jima ta na ta tunane tunane kafin barci ya kwasheta. Ba ta tashi ba sai da Hajiya ta shigo tana buga mata kafa da cewa an yi azahar. Sannan ta iya tashi a kasalance ta shiga tiolet tayi alwala ta zo ta yi sallah sannan ta fita fallo ta iske Baaba Uwani da Hajiya suna hira.
Kirchen ta nufa tana faɗin “Baaba me kika girka mana yau?
Baaba Uwani ta ce”Alala Hajiya ta ce tana jin ci yau, shi na yi.”
Mimi ta daka yar tsalle kafin ta ce”Kai Hajiyata Allah ya saka ki a gidan Aljannah, kamar kin shiga raina daman na ce sai weekend na zauna nayi Alala na kwana biyu ban ci ba.” Ta faɗa tana shiga kitchen ɗin cikin farinciki.
Hajiya na mirmishi ta ce”Daman nasan kina so, rashin samun zama ya sa ba ki yi mana mun ci ba, da Uwani take tambayata abin da za a dafa na ce ta yi mana Alala kawai.” Ta na jin maganar Hajiya daga cikin madafin , miyanta har tsinkewa yake yi sanda ta ga alalan gwangwani da manja.
filet ta samu ta zubo guda huɗu ta saka yaji kaɗan mai daɗi da Yaddiko da aiko ma da Hajiya ta kuma tsiyayi soyayyan manja a gefe. Ko da ta fito falo mirmishi kawai take yi cikinta na wani yamutsawa.
Gefe ta samu ta zauna kan cafet ta yi bismillah ta fara ci loma daya biyu ta ɗago tana kallon Hajiya dake kallonta kafin ta ce”Hajiya ke ba za ki ci ba ne?
Hajiya na yar dariya ta ce”Sai ya sha iska zan ci kar na ci da zafi ya lalatamin ciki.”
Mimi ta ce”Hmm hajiya da zafi ya fi daɗi.”
Baaba Uwani ta saka dariya tana faɗin” Binta ko na saka waigi ne?
Mimi ta jinjina kai kafin ta ce”Baaba na manta kafin ki saka waigin haɗomin da ruwa wayyo daɗi Hajiya.”
Ta ke faɗa tana cin alalanta tana santi Hajiya da Baaba Uwani na yi mata dariya.
Baaba Uwani ta tashi ta ɗauko mata ruwa mai sanyi da kofi ta kawo mata.
Mimi na ta buga santi suna ta mata dariya tas ta Cinye ta sha ruwa kafin ta ce”Baaba Uwani Allah ya yi albarka ya sa a gama da duniya lafiya.”
Baaba Uwani na dariya ta ce”Amin Binta.”
ta mike ɗauke da filet ɗin hannunta tana faɗin”Baaba Uwani cikin Albashina na wannan watan kina da dubu goma cash tukwaicin Bintan Hajiya ne.”
Baaba Uwani ta ɗaga hanci ta rangaɗa guɗa kafin ta ce”Ina godiya uwar ɗakina Allah ya saka da alheri Allah ya tsare gaban ki da bayan ki Allah ya rabaki da sharrin makiya da mahassada, Allah kuma ya bama babanki lafiya.” Mimi na gabda shiga madafi ta ce”Amin Amin Baaba Uwani da kika yi min addu’an Allah ya ba ma Abi lafiya kamar na ce na ƙara miki wata duban goman””
Ta faɗa ta na yar dariya Baaba Uwani ta kara karkacewa ta yanka wata guɗaa kafin ta ce”Gaba salamun baya salamun yar lelen Hajiya da ba kamarta Allah ya kara arziki da wadata Na gode kwarai”
Hajiya na gefe da cashaba a hannunta tana ja cikin mirmishi ta ce”Da kin kara da addu’an Allah ya kawo ranar auran Binta da wuri wuri da na cike miki kudin sun zama dubu hamsim”Baaba Uwani na jin haka ta yi zaman dirshan gaban Hajiya tana faɗin”Allahu Akbar Uwar marayu, kin goya na gida kin goya bare, ai ban gama addu’an ba, tana tafe Allah ya nuna mana auran Binta Allah ya bata miji nagari kyakyawan kamarta mai kyan hali da mutumci kamar ita..” Hajiya na dariya ta ce”duk da kin makara na dai ƙara miki dubu goma.”
Baaba Uwani ta ɗaaga hannu alamun jinjina kafin ta ce”Allah ya kara nisan kwana Hajiya, Allah yasa ki dade a duniya kina goya marayu irin mu.”
Hajiya ta ce”Uwani ai duk sona da duniya sai na mutu na barta ballantana ai bazan iya rama shekaruna na baya a duniya ba, ke dai Allah yasa mu cika da kyau da Imani.”
Uwani ta amsa mata da Amin Mimi ta fito ta na taɓa cikinta lokaci daya tana faɗin.
” Hajiya mu bar tafiyar mu gidan Daddy sai anjuma lokacin cikina ya sassaɓe”
Hajiya ta kaɗa kai kafin ta ce”Daman ai sai rana ta yi sanyi.”
Baaba uwani na gefe ta ce”Hajiya nima ina son zuwa na duba mai jikin.”
Hajiya ta ce”Ba matsala duk sai mu tafi tare.
tashi ki zubomin alala ya kara wucewa kafin na gama lazimi.”
Baaba Uwani ta mike ta na faɗin “Angama Uwar marayu.” Mimi kuma dakin Hajiya ta shige ta je ta kunna talabijin. Tunda bayan falo akwai wani talabijin ɗin a ɗakin Hajiya.
Mbc Bollywood ta saka sai ta ga a wani Film ɗin da ta ke matukar so mai suna HIKCHI
FiLM ɗin Rani murkarji ne. Cikin jin daɗi ta gyara zama ta cigaba da kallo.
Ba su samu tafiya gidan Daddy ba sai bayan la’asar, gidansa na anguwan Abubakar Habu Hashidu Estate ne, Hajiya na gidan gaba Mimi na driving Baaba uwani na gidan Baya. Sanda suka je gidan sun iske Jaheed ya zo garin tunda mahaifiyarsa ce Mama sai Amaryanta da suke kira da Anty.
Gidan Alhaji Hamza Sulaiman Dabo gida ne na rayuwar yan boko, kowa kuma abin da ya ga dama shi yake yi shi ba mutum ba ne mai zama ɗan siyasa mai jama’a, kuma ba shi da takura da matsawa rayuwar boko zallah kawai iyalansa ke gudanarwa.
Ko da suka shiga ɗakin Mama Jaheed suka iske kwance kusa da Maman kamar zai koma cikin cikinta. Ga kanwarta nan a cikin ɗaakin amman bai saka shi ya fita ba.
Ya juya yana ta magana a waya sai da yabji mganar Mimi da Hajiya ne ya yanke wayar da ya ke yi ya juyo ya na sakin Mirmishi ya ce”
“Hajiyata Amaryata.”
Hajiya ta balla masa harara tana faɗin”Ni ai ba na mijin da kai, tafi can soloɓiyo kullun kwance ɗakin uwa kamar wani jariri, ke Hansa’u hala nono kike ba shi ne?
Gabaɗayan su ka fashe da dariya shi kuma sai ya hau shafa kansa. Mama ta ba ma Hajiya wajen zama na saman kujera guda ɗaya da ke cikin bedroom ɗin ta.
Kanwarta mai suna Hajiya Turai ta kada baki ta ce”Ai Jaheed jin sa ya ke kamar Yaya bata yaye shi ba.”
Mama ta yi dariya ba ta yi mgana ba, saboda ita macece mai kaunar ya’yanta haka zaka ga ko masu auran in suka zo Jikiko su hau jikinta iyayensu su kwanto kan Jikinta. Ita Anty ma ba ta taɓa haihuwa ba sai dai suna zaune lafiya sai dai kishi na halitta.
Bayan an gaisa da yambayan jki Mama ta ce ta samu sauki, Hajiya ta ce”Sannu! Allah ya kara lafiya.’
Ta amsa da Amin Jaheed kuma kusa da Mimi ya koma ya zauna kamar zai shige jikinta ta yi saurin matsawa kusa da Hajiya Turai daman a gefen gadon ta zauna a kusa da ita. A cikin kunnenta ya yi mata raɗa” Me na yi miki ba ki ɗaukan wayata?
Mimi ta kalleshi ta na masa inkiya da su Mama sai kawai ya ɗaga murya yana faɗin” Mama ga Mmin ba kin ce za ki yi mata mgana ba? Mama ni fa Mimi ta ce ba ta sona me na rasa mene ne bazan yi mata ba in mu ka yi aure?
Ya faɗa cikin yar shagwaɓa Mimi kunya ya kamata sai ta yi saurin tashi, Mama kuma idon Hajiya ya sa ba ta yi magana ba sai Hajiya Turai ce ta kalli Mimi tana faɗin” Mimi miye aibun Son da ba ki son shi? gaye na nunawa daga nan har london?
Ta karishe faɗa cikin zolaya Mimi ta kasa mgana kanta dai na kasa Hajiya sai Mirmishi ta ke yi ba ta ce komai ba.
Baaba Uwani ta ce”Ai daga nan har gaba da london ma Hajiya, wane mutum..”
Mirmishi ya yi kafin ya mike ya na fadin”To na rasa me ya sa ba ta so na”
Yadda ya faɗ kamar zai yi kuka, Hajiya ta taɓe baki kafin ta ce”Ba dole ta ce bata son ka ba, kana mgana kamar wata mace. Ni kuma Binta na namiji take son aura ba yaron mama ba.” Kamar magana ce Hajiya ta sakarma Jaheed ɗin da uwarsa amma sai ba wanda ya nuna
Dariya kawai aka yi, sai ya nufi Hajiya zai mata shagwaɓa ta mike tana faɗin”Ni matsa tafi wurin uwarka ita zata iya da wannan lagen wuya naka kamar wata mace mai laulayi.” Mimi sai da ta saka dariya shi kuma sai ya tura baki.
Hajiya Turai ta ce”Ko dai hajiya na kishi ne.”
Ta karishe faɗa cikin zolaya Hajiya ta wuce gaba tana faɗin”Allah ya tsareni ko tsohon mijina Sulainmnu kafin ya bar duniya duk tsufansa ya fi min wannan lange langen ɗan naku. Allah ya kara lafiya Hansa’u Binta mu je ko? Hajiya ta faɗa tana kallon Mimi daman kamar akan ƙaya take ta yi saurin fita daga ɗakin.
Mama da Jaheed suka biyo bayansu suna faɗin” Tun yanzu za su tafi ba za su bari Alhaji ya dawo ba?
Hajiya na cigaba da tafiya ta ce”Wani Alhajin kuma? Hamza ko da safe ya zo mun gaisa.”
Jin haka suka yi shuru Anty jin tafiyar su, ya sa ta fito suka yi sallama har bakin mota Jaheed ya rakasu.
Ya za ga ya ta bangaren Mimi cikin yar shagwaɓa ya ce,” In zo gobe?
Mimi ta ce”No ina wajen aiki?
Da sauri ya ce” Sai na same ki acan mana.”
Mimi ta yi saurin cewa”A a ka bari in na dawo zan kira ka.”
Karya wuya ya yi kafin ya ce” Jibi zan koma saboda haka promise”
Ya faɗa har ya na mika mata hannu sai taki kamawa sai kawai ta girgiza kai kafin ta ce”In sha Allahu zan kira ka.”
Sai lokacin ya yi mirmishi ya zaga ya wajen da Hajiya ke zaune ya zaro kuɗi Sabbi daga aljihun Jeans ɗin da ke Jikinsa ya ɗorama Hajiya a saman cinyarta, sannan ya sagala Hannu ya mikama Baaba Uwani nata ta karɓa tana masa godiya.
Sai kawai ya ce”Baaba uwani addu’a zaki yi min Allah yasa Mimi ta so ni.”
Baaba Uwani ta ce”Da ikon Allah zata so ka ɗan Alhaji kuma kun bala’in dacewa da juna.” Ta faɗa tana yar dariya, Jin haka ya sa ya kara dumbuza mata kuɗi ya mika mata ta karɓa tana saka albarka da addu’an Allah ya ba shi Binta.
Mimi ta ji hauahi ya isheta ta yi ma motar ta key, ya ɗaga ma Hajiya hannu yana fadin”Amaryata sai na zo, na ba da kudin cefane ba na son gori.”
Hajiya ta ce”Sai ka zo tunda kana yi da ni ai shik enan Allah ya yi albarka.”
Yana ɗaga musu hannu har suka bar haraban gidan.
Sai da suka hau titi Baaba uwani na dariya ta ce”Dubu ashirin ne ɗan Alhaji ya bani Hajiya”
Hajiya ta ce”Kin gode kuwa.”
Mimi na tuki ba ta ce komai ba, Baaba Uwani na soke kudinta a haɓan zaninta ta ce”Binta ina laifin ɗan Alhaji? ga shi ɗan uwanki don Allah ki saurareshi mu yi tuwo na maina”
Mimi na jin ta ba ta yi mgana ba Hajiya ce ta ce”Ai Babanta ma ya ce tunda ba ta so a bar mganar, kuma Ya faɗa ma Hamza, shi dai yaron ne ya kasa hakura.”
Baaba Uwani ta ce”Wayyo wallahi ya na son Bintar ki Hajiya ki saka baki ta saurere shi.”
Hajiya ta ce” Ba ruwana ai ba ni zan zauna ma ta da shi ba, in sun daidaita kansu zan fi kowa murna da haka.”
Mimi na jin haka ta kaɗa kai kafin ta ce”Baaba uwani ni fa Jaheed baya cikin, irin jerin mazan da nake son aura ni da shi ba bambamci ya yi ta wani abu kamar ba namiji ba, ko maganarsa irin na mata ne fa ba ki ji ba?. Ta faɗaa cikin marairacewa, Baaba Uwani ta ce” kuma fa hakane yana abu shima kamar na mata.”
Hajiya na dariya ta ce”Ai na matan ne, ko ba ku ga yadda yake nane da uwarsa ba.”
Daga Mimin har Baaba Uwani sai da suka saka ma mganar Hajiya dariya.
Ita kuma ta ce”To ina mamakin yaran zamanin nan, kamar sun fi kowa sanin darajan Ƴaya mu namu ƴaƴan ba ƴaƴa ba ne.” Mimi na dariya ta ce” Hajiya ta kenan.”
Hajiya ta yi mirmishi ba ta dai yi mgana ba.
Suna tafe suna hira har suka isa gida, ammh sai da suka tsaya a hanya Mimi ta siya kayan marmari saboda na su ya ƙare kuma mai kawo cefanan wannan watan ya yi nuƙusa ni, daga gidan Daddy ne kila gobe ko Jibi za’a kawo kayan abinci da cefane.
Washegari kafin Mimi ta je wajen aiki Rukky ta dameta da kira dole ta shirya ta fita gabaɗaya, ta fara biyawa ta gidan su Rukky sannan da la’asar ta tafi wajen aiki, rigimar Rukky ce da ba ta karewa.
Dole wai sun shiga bikin ƙanwarsu sun yi kane kane, to ya ta iya? In bata saka kanta ba, nacin Rukky kaɗai ya isa ya hanata barci cikin salama.
7rd March, 2022
11:40pm
Ɗakin Inna Meri cike yake da baƙi mutanen Kano ne suka zo garin tn jiya Mu’azzam da matarsa Hibba da ɗansu mai sunan Baba Danjuma suna kiran shi Junoir. Anty Amina itama tun safe ta zo ita da nata gayyar ƴaƴan, sai kuma Bintu tare da ƴan biyunta.
Sai Anty Halima itama da nata gayyar Ƴayan. Sai Hibba da Walida sai Mariya a ɗakin Inna Meri ya cika da hayaniya, ita kuma daman abin da take so kenan..ta yi nan ta yi nan duk domin ta ga ta farantama ƴaƴanta da jikokinta da suke tafe bin ta wannan ya ce Inna zan sha tea sai wannan ya ce Inna zan sha ruwa. Uwayensu na zaune ita ke tsaye kan kafafunta a kansu.
Iyaye nasu na zaune suna hira suna dariya.
Magajiya na tsakar gida tana shanyan yan kayanta da ta wanke sai kwafa take yi, bakin ciki ya kusa kasheta in ta jiyo shewan Ƴaƴan Inna Meri daga bangarenta.
Gaje ce ta shigo daga bangaransu da botiki a hannunta duk da an raba ƙofa amma itama jin hayaniya ya sa ta wanke wasu kaya ta shigo shanya domin ta ji gulma.
Tana ganin Magajiya na shanya sai ta wayance da cewa”Au ke ma wanki kika yi, nima tun safe na ke wanki igiyan can ya cika sai na ce bari nazo na shanya anan.”
Magajiya ta taɓe baki kafin ta ce”Nawa ba su da yawa, ki shanya daga gefe.”
Daga haka ta cigaba da shanyanta tana tsaki ita kaɗai. Gaje ta zo ta fara shanyanta lokaci ɗaaya ta na nazarin Magajiya kafin tace” Hala mariya ba ta gidan ne?
Magajiya kamar ta na jira ta fara faɗin” Ta na nan, ammh ta na ɗakin uwarta Meri tunda taji zuwan su Amina da safe.”.
Gaje ta rike haɓa kafin ta ce”ashe su ne su ka zo shi ya sa na yi ta jin hayaniya, ke ko dan’uwansu ya zo mana jiya mun sha tsaraba an gode Allah ya ba da lada.”
Magajiya ta sake yin kwafa kafin ta sauke ajiyar rai ta na faɗin”Uhm!
Daga nan ba ta kara mgana ba, sai dai jefi jefi ta na ta sakin tsaki ƙananu.
“Salamu Alaimkum..”
Muryan Jummai ya shigo tsakar gidan lokaci ɗaya da bayyanarta a tsakar gidan fakan fakan ta shigo gidan ga goyo ga Ƴaƴanta guda uku kai da kai suna bin ta a baya Magajiya ta dakata da ƙokarin zuba ruwan da take yi za ta yi wanka.
Gaje ce ta tari Jummai da faɗin”A’ a Jummai ce a gidan.” Jummai na zama saman tayels ɗin dake Kofar ɗakin Magajiya lokaci ɗaya tana faɗin “E Gaje, Magajiya ina kwana, wai Mu’azzam ya zo garin nan ƴaron nan munzali ya ke faɗa min ya ce da safe ya ganshi”
Ta faɗa tana nuna ɗan babba ciki ƴaƴanta.
Magajiya bata yi mgana ba Gaje ta ce”Eh ya zo jiya, kin makara har mun cinye tsaraba.”
Jummai tace”Kan uba har kun ma isa, Magajiya ina tsaraban mu?
Magajiya ta kalleta a fusace kafin ta ce”Sai ki shiga ɗakin uwarsa ki tambayeta domin duk abin da ya zo da shi shashenta aka shiga da shi, sai abin da ta ga dama ta aikomin da shi.” Ta faɗa tana nuna bangaren Inna Meri ta na jin wani bakin ciki na yi mata suya acikin ranta.
Jummai ta rufe baki kafin ta ce”Wai kaɗan ta baki magajiya?
Kafin ta yi mgana, Gaje ta yi saurin cewa” To ai daman haka take yi, ta wani tattare komai sai kace agolan ɗan ta ne ya kawo, ai ba ita ta haifi Mu’azzam ɗin ba, balle ta rika tattare komai in adalci zata yi sai ta fito da shi ayi raba dai dai.”.
Ta karishe faɗa a na waige waige na munafunci jummai ta sauke numfashi ta kwanto goyon ƴarta ta buɗe rigarta daman tuni ta cire hijabi, nono ta jawo wani yaraf kamar tsumma a yamushe ta tura ma yarinyar nono a baki Lokaci ɗaya tana faɗin”Ta wani fannin da ƴar gaskiyarta fa gaje, kin manta lokacin da Maman Mu’azzanm ta rasu, Baba ya yi ya yi da Magajiya ta rike su ta ce ba zata rike ɗan kowa ba, bayan ya auro Inna Meri ya ba ta su ta kuma karɓe su ta riƙe su da Amana to anan fa banga laifinta in ta kankane komai ba, da Magajiya ta rike su da yanzu komai suka samu yana bangarenta ne.”
Magajiya kamar ta kai ma Jummai duka haka ta ji, cikin ƙufuluwa da ɗaga murya ta ce”Eh din,na faɗa na kara faɗa bazan riƙe ɗan kowa ba ni ma kaina Ƴaƴana sun ishe ni.” Jummai ta ce”Hmm!
Kafin ta mike yarinyar ko gama shan nono ba ta yi ba, ta warceta ta saba a kafaɗa lokaci ɗaya tana faɗin” Bari naje shashen Inna Meri na samo tsarabata.”
Harara magajiya ta bi ta da shi kamar Idanuwanta za su faɗo ƙasa. Gaje ta rakata da faɗin” Za ki samo kam, domim Meri ba daga nan ba wajen kyauta.”
Magajiya ta kalleta a wulakance kafin tace”Gaje ba kin gama shanyar ba?
Gaje na rawan baki ta ce”Eh dama..!
“To kama gaban ki gaje, kinsan halina bana son Munafunci yanzu sai aji mu da ke.”
Take faɗa lokaci ɗaya tana zuba ruwa a botiki rabi ke shiga ciki rabi na zuɓewa saboda bakincikin an yabi halin kirkin Inna Meri, magajiya mace ce mai bakin kishi da hassada da ƙyashi. Gaje ta ɗauki botikin ta kama hanyar fita tana faɗin”Abun bai kai ha ka ba Magajiya sai an juma.”
Daga haka ta fice ta na taɓe baki.
Read Also: Abban Sodoji Complete Book
Magajiya ta ja tsaki sai a lokacin ta ga munzali yaron jummai.
Tsawa ta daka masa kafin ta ce”Ta shi ka bi uwarka kafin na mare ka.”
Sumu sumi ya mike ya bi bayan uwarsa kamar yadda kakarsa ta faɗa ita kaɗai ta shiga ɗakinta Lokaci ɗaya ta na dage labulen ɗaakin ganin shi kaca kaca.
Kyafci ta yi lokaci ɗaya tana faɗin”Sai na yi ma mariya bugun tsiya, yar iska yarinya kawai.” Take faɗa ta na faman kaye kaye ta na tsaki ita kaɗai.
A shashen Inna Meri kuma ya kacame da hira, Jummai daman akwai zence in ta zauna kaf sai ta zazzage asirin gidanta kullun cikin babu, ba ranar da Jummai za ta zauna ta faɗi alheri a kan mijinta sai dai ta ce ba ta da shi Saboda a taimaka mata.
Mu’azzam in yazo gari haka ya ke fama da babun ƴan’uwansa marasa godiyan Allah, Mansoor dai ba ma ganinsa suke yi ba shi ya fi yi ma mazan matan ma wata sai ta yi shekara bata ganshi ba tunda ya fara harkan ƙwallon nan. Kuma sun fi sakewa da Mu’azzam Mansoor daman shi tuntuni sun ɓata garinsu a wajensa mata ba ta isa ta tare shi da wata mgana ba.
Jummai ke ba da labarin a anguwarsu wani gidan ɗan majalisa yana raba tallafin kayan abinci da suka je bin layi sai da ta yi faɗa da wata mata. Hibba na zaune ta ce”Kai yaya Junmai dambe a titi ba girman ki ba ne.”
Bintu ta yi dariya kafin ta ce”Baki san Yaya Jummai ba ne shi ya sa.”
Hibba sai kawai ta kaɗa kai ta ce Allah ya kyauta wayarta mai tsada ta ɗauka ta tura ma Bobo ɗinta sakon tana Jiran sa zai zo ya kaita gidan su ne yau can zata kwana.
Daman auran zumunci ne tsakaninsu da Mu’azzam ɗiyar kanwar mahaifiyar Mu’azzam ce aka yi haɗin zumumci.
Yanzu can bolari zata fara biyawa babban gidansu kafin ta wuce tudun wada gidansu.
Sai ya ce mata yana tare da Mansoor in sun gama gashi nan zuwa. Amina ta kalleta kafin ta ce”Kun fasa tafiya can tudun wadan ne? Sai ta girgiza kai kafin ta ce”Ya ce yana wajen Yaya Mansoor in sun gama zai taho.”
Bintu na jin an ambaci sunan shi ta yi saurin cewa”Baban Inna, uhm ban faɗa muku abin da ya yi min ba?
Nan ta shiga ba su labarin faɗan da yaje ya yi mata a gaban kishiyarta da mijinta.
Cikin takaici Binta ta ce”Ni ba abin da yafi ban haushi sai cewan da ya yi sai ya yi biji biji da ni na kara mgana a wajen.”
Jummai ta ce “Kan uba, shi fa daman masifaffe ne, har yanzu bai daina masifarsa ba.” Halima ta ce”Ya rage masifa amma ya kara ninka bakar zuciyarsa.”
Hibba na jin su ta na dariya sau ɗaya ya taɓa zuwa gidanta na kano sai dai su hadu in sun zo garin nan. Ta san shi tun suna yanmata tunda suna zuwa gida nan.
Ita dariyansa ne ba ta taɓa gani ba, Kamar baya son zama acikin mutane ne.
Nan aka buɗe caftan Baban Inna ana ta gulmansa.
Hibba na saurare tana dariya farar mace ce doguwa mai kyau da ita ga gashi da ka ganta ka ga bafullatan gombe.
Suna cikin mgana Inna Meri ta leƙo tana faɗin ” Duk ina jin ku, ku gama za ge min Babana na gode.”
Sai gabaɗaya suka saka mata dariya har da Jummai tana faɗin”Ni dai inna ban da ni kar ki hanani tsaraban Mu’azzam”
Domin jummai akwai son abun duniya zata iya kwantar da kanta saboda abun duniya.
IDAN AN CIZA..! Part 6
Page 6
Mu’azzam bai shigo gidan nan ba sai bayan la’asar Hibba har ta gaji da jiransa, sanda ya shigo har lokacin Jummai tana bangaren Inna Meri ba ta tafi ba daman Mu’azzam ɗin take jira ko za ta samu kuɗi a hannunsa.
Tsaraba kuma sauran wanda ya rage na bangaren Inna Meri ta raba gida biyu ta ba ta rabi, daman dankali ne sai wake da garin rogo, sai siga da ya kan zo da shi a raba ma yan gida da makota.
Turamen zani guda biyun da ya zo da shi yace ɗaya Inna Meri ɗaya kuma Magajiya kuma an kai mata nata amman a inda Mariya ta sauke kayan kallon banza ta yi musu ta kauda kanta nan suka kwana kuma ba ta kauda su ba, ballantana ta ga abin da ke ciki. Ita babban bakincikin ta ita ce mace ta farko da ta auri Danjuma a matsayin saurayi da budurwa tun ya na matashin sa, amman yau daga karshe ita ce koma baya a cikin gidansa. A ce har wata banzan bassakwata ta zo ta fita matsayi aciki gidanta da tun tana da kuruciya take cikin shi. Sannan karin takaicinta gabaɗaya inna Meri ta siye kowa na gidan da kirkinta, sannan ƴaƴan gidan masu kuɗin duk ta tattare su a ɗakinta ita sai abin da ta raba ta aiko mata da shi.
Ai in da gaskiya acikin lamarinta Mu’azzam ɗan Danjuma ne, ba ita ta haife shi ba in ta rike kayan da AGOLAN ɗanta ya kawo mata tana kan daidanta, amman na wajen Mu’azzam ko na wajen Amina ko Halima ba ta da hakki a kansu tunda ba ita ce uwar su ba, Magajiya duk ta manta lokacin da uwarsu ta rasu da Ɗanjuma ya ce ta rike su tsalle ta da ka ta ce ba za ta iya rike ƴaƴan wata ba. Itama nata sun isheta duk ba ta duba wannan ba sai yau da suka zama wasu take tunanin ba a yi mata adalci ba.
Tana tsakar gida tana jajjagen kayan miyan abincin dare da za ta ɗora Mu’azzam ya shigo gidan cikin shigan kananun kaya gefe ɗaya key ɗin motarsa wata bakar Jeep katuwa ne a hannunsa yana tafe yana kaɗawa shi fari ne sai dai bai kai Mansoor tsawo ba da ka ganshi ka ga Baba Danjuma saboda suna bala’in ɗibar kama da shi sosai.
Cikin ladabinsa ya gaisheta kamar yadda ya saba shi dai ta na amsa masa cikin sakewa ba kamar ɗan uwansa da ta ce gaisuwan reni yake yi mata. Har ya gota ta zuwa bangaren Inna Meri tana kallonsa ji be sa yadda ya zama kato ya yi kiba saboda ya samu duniya. Kwallah suka cika mata ido, kaf ƴaƴanta ba mai jin daɗi a gidan auran sa, har gwara ma Zuwaira akan Jummai ita Jummai ai kullum a gida a ke ba ta, ba ta kawo ma uwa ba. Sai dai ta bi ta karɓe Auwalu ne Namiji babba shi kuma ya ƙi karatu sai yanzu take jin haushin yadda ta zura masa ido ya ƙi makaranta in da yau ya yi karatu da Meri ba ta isa ta rika mata famkama da kudin su Mu’azzam ba, su ma ai da karatun su ke takama, ba za ta manta yadda Danjuma ya rika fama da shi akan karatu ba ya ki yi, Ita kuma ta ɗaure masa kugun yin abin da ya ga dama ga shi nan daga karshe sai buga bugan gini ga shi ya yi aure ya tara Iyalai shima fama yake yi da kansa. Saddiqu ne bai yi aure ba har yanzu ya na can garin Ikko ya na neman kuɗi amman sai ya shekara bai zo ganin gida ba sai dai a waya sai sako da ya ke yi musu wani lokacin, shima ba sosai ba tunda Auwalu ya fi shi tausayin iyaye shi kawai domin ba shi da shi ne.
Mariya ce ta rage a gabanta ita kuma ai ba ta ɗawainiyarta daga karatu har bangaren Surutu ƴaƴan Meri sun ɗauke mata wannan bangaren kuma duk abin da take so suna yi mata ko jiyan ta ganta da hijabi sabo da takalmi ta zo ta na nuna mata da cewa matar Mu’azzam ta kawo mu su ita da Walida, ta san suna kokari amman bakin cikinta ace ƴaƴan Meri ke taimaka mata to na yaushe kuma in taci ta sha su ne, tunda yanzu Ɗanjuma ba kasafai ya ke wanzanci nashi ba, ba kuma kamar a shekarun baya da ya yi suna tunda abun na su na gada ne ba haya ba.
Duk da tuntuni bala’in magajiya ya sa aka raba girkin bangaren har yau har gobe kayan abinci biyu a ke rabawa, ita rabi Meri rabi ciki har ta san ma sauran ƴaƴanta
Kuma har gobe komai in Inna Meri ta dafa sai ta aika mata da shi sai dai in taki ci, ta bar shi nan Mariya ta ɗauka ta cinye. Har ta gama jajjagen ta tunanin yadda rayuwa ta zo mata ba yadda ta yi tsammani ba da gawayi yanzu suke amfani ta fito da murhun gawayin tana kakkabewa dagacan shashen ta jiyo muryan Inna Meri na faɗin.
“Ɗan Inna ba za ka tsaya ka ci abinci ba?
Ɗanwake Walida ta yi saboda kai.”
Ta na jinsa ya ce”Sai na dawo Inna, in na tsaya yamma za ta yi.”
Ƙaramin tsaki taja. Tana jin wani irin takaici a kasan ranta, Mariya ta ke jira sai ta mata bugun tsiya Jummai ma tunda ta shige har yanzu bata kara lekowa ba kyafci ta yi ita kaɗai ta na girgiza jikinta daga gani za ka san Magajiya ta iya bala’i sannan cutar hassadan dake damunta ne ya sa har gobe ta kasa ganin alherin ƴaƴan Meri ne suka lulluɓe rayuwarta. Ta koma ɗaki kenan taji fitowarsu da mganarsu zuwa shashenta ta ji muryan Jummai na faɗin ” Mu’azzam ka taimaka min yara nan duk ba sa zuwa makaranta daga bokon har islamiyan an kore su.” Ba ta ji dai me ya ce ba ta dai ji Jummai na ta godiya kamar zata kwanta masa, baƙinciki ya kara cikata ita da ya kamata ya’yanta su ba da, su ne yau za su koma yan maula suna roko a na ba suna godiya.
Muryan Hibba taji kamar za ta shigo ɗakinta yasa zaraf ta ɗaga labule ta fito sai suka ci karo da juna cikin shirinta ga Walida rike da ƙaramar akwatinta sai Mariya dake dauke da Junoir, gabaɗayan sune har da Bintu da su Amina suma cikin shirin fita kila duk tare za su tafi ko kafin ta samu damar mgana Hibba ta rankwafa cikin ladabi tana Faɗin ” Sai anjuma Magajiya yau a Tudun wada zan kwana sai jibi in sha Allahu.”
Kadahan kadahan ta ce”Allah ya kaimu, ku gaida gida.”
Mariya ta kallah cikin jin haushinta Mu’azzam kuma ya fice lokaci ɗaya yana fadin”Ku fito mu tafi in na kai ku daga can zan biya wani waje ne.”
Amina ce ta bi shi tana faɗin” Kai Mu’azzam ka ce mu zauna kenan ba za ka dawo da mu ba?. Sun fita can waje suna magana su ma su Binta sai suka rufama musu baya, Mariya ta kallah da ke shirin bin su a fusace ta ce”Ke ina za ki je?
Cikin tura baki ta ce”Za mu raka Anty Hibba can ne, Yaya Mu’azzam zai dawo damu a motar sa.”
Wani irin harara magajiya ta sakar mata kafin ta ce”To ki fita ki gani,wlh sai na yi kasa kasa dake acikin gidan nan”
Daga haka ta duka tana zuba gawayi acikin murhun dake gabanta lokaci ɗaya tana kara sakin tsaki, Mariya ba ta da yadda za ta yi dole ta fita waje ta mika ma Bintu Junior ta ce Magajiya ta hana ta zuwa, ba wanda ya damu sanin halin Magajiya duk wanda ke rayuwa a gidan wanzamai ba ma acikin gidan ba har makota su san wacece ita a haka ma ta rage a shekarun baya in ta fara bala’i da masifa sai makota sun ji acikin gida kuma sai su Gaje sun cika tsakar gida suna bata hakuri, abin da ba a taɓa ji ba shine nuryan Inna Meri tana tanka mata daga ita har Baba Danjuma masu hakuri ne da kau da kai daga sha’aninta.
Da Mariya ta dawo haka ta rika jaraba tana zaginta, Inna Mari na cikin bangarenta ita da Jikokinta ƴaƴansu Amina tunda za su dawo ta nan kafin su wuce gida sai suka bar mata yara a wajen ta, sai ta yi kamar ta leka ta yi mgana sai kuma ta fasa sanin Halin Magajiya yanzu nan sai cibi ya za ma kari, ta kuma san ta na zagin mariyan ne saboda ta zo bangaranta to ta isa ta raba ta da yan’uwanta ne? har ƴaƴan Jummai ta jii an zagi ubansu an ce su da uwarsu marasa zuciya, daga nan Jummai ta tarkata ya’yanta zuwa gida. Sai ta koma kan Mariya har su Mu’azzam suka dawo tana jarabarta.
Inna Meri na bangarenta t na ba ma yan biyun Bintu da suka saka rigiman koko da za su sha, sai da ta mike ta dama musu sannan ta zauna ta a zaman ba su, sauran ma suna gani suka ce suma sai sun sha, gabaɗaya yaran sun zagayeta Sanda suka shigo Bintu da mgana a bakinta faɗi take yi.
“Innarmu wai me aka yi ma magajiya take ta bala’i haka?
Inna Meri ta ce” Ina zan sani? Tun fitan ku ta ke ta yi ta gama zagin Jummai da Jummai ta tafi gida ta koma kan Mariya ina ga bai wuce dai yinin da ta yi a bangarena tare da ku.” Mu’azzam ya samu waje ya zauna yana Faɗin”Har yau dai Magajiya ba ta sauya ba? Wai bakin ta baya ciwo ne?
Walida tace”Inna mariyan ma ta so bin mu Magajiyar ta hana ta zuwa.”
Inna Meri ta ce”Bakomai wata rana sai labari, zata daina.” Yaya Halima ta zauna a kasa kusa da Inna Mari ta bangaren dama Amina ta zauna a bangaren hagu, Bintu kuma ta zauna kusa da Mu’azzam Walida kuma na kofar daki ta yi tsaye ba ta zauna ba. Yaya Amina ce ke faɗin”Inna ai ban tunanin akwai ranar da Magajiya zata sauya. Har Baba dai ya gaji da halinta ya saka mata ido.”
Bintu ta taɓe baki kafin ta ce”Dan dai ta samu daga Baban har Innan salausalau ne da irin mu ne da tuni ta raina kanta”
Inna Mari ta aika mata da dakuwa tana Faɗin”Mungode ja’ira, ai Annabi cewa ya yi duk wawaye ya gani a Aljannah ba masu wayau ba, kum rayuwar nan duka nawa ta ke? hakuri ribar zaman duniya da na biye mata ai ba ta taɓa biyo ni bangarena ta yi min wani abu ba, ai hausawa suka ce kulawa yabawa ni dai Allahu shi ne shaida na tunda aure ya kawo ni gidanan nake zaune da kowa lafiya, Alheri ne tsakanina da kowa acikin zuciya ta ba ni da niyar cutar da kowa, kuma ina so ku saka ranku a duk in da kuke ku rike gaskiya da amana sannan ku nufi wanda ma ya nufe ku da sharri ku saka masa da Alheri, ku ma sai ku cigaba da ganin Alheri a rayuwar ku har bayan ran ku.”
A yadda suka zagayeta za ka fahimci akwai kauna ta uwa da abin da ta haifa a tsakaninsu, Mu’azzam ya yi mirmishi kafin ya ce” Shi ya sa har gobe ba ni da kamar ki Inna ta, Allah ya kara miki lafiya da tsawon kwana.”
Suka amsa da Amin gabaɗayan su, Itama ta amsa da Amin tana faɗin” Nima ai bani da kamar ka ɗan Inna Allah ya cigaba da tsare min kai a duk inda ka sanya kafa Allah ya yi maka jagoranci.’ Cikin bayyana farinciki ya amsa da Amin lokaci ɗaya yana kara faɗin ” Inna in na samu kuɗi zan kai ki Makka kafin ki mutu ke da Baba za ku je ziyara dakin Allah in sha Allahu.”
Gabaɗayansu suka amsa da In sha Allahu Allahu ya sha.
Inna Meri kamar ta yi kuka ta ce”Amin Amin Allah yasa muna da rabon zuwa, Baban Inna shima kullum zencen sa kenan Allah ya cika muku burin ku na Alheri”
Mu’azzam ya ce”Mun fara magana da shi, Inna suprice za mu ba ku in sha Allahu.”
Yan’uwan suka taya Inna da amsawa da cewa Allah ya nuna mana lokacin.
Hira suka cigaba da yi suna hirar su Walida ta je ta zubo ma Mu’azzam ɗanwake ya zauna yana ci lokaci bayan lokaci yana tsoma bakinsa cikin mganar ƴan’uwansa mata. Inna ya kallah sai faman wahala take yi da yara iyayensu na gefe suna hiran su ko ajikinsu.
Cikin faɗa ya kalle su yana faɗin ” Wai don Allah Nanny mai reno kuka mai da inna? tunda kuka zo gida nan ina lura da ku kowacce ta sauke ƴa’yanta sai Inna ke ta faman wahala da su.”
Bintu ta ce”Ai sun fi son renin Innan ne ni fa ba domin Bashir ya ce a’a ba da tuni na dawo da su Hassan wajen Innanmu na gaji wlh.” Hararanta ya yi kafin ya ce”Dole ki kwaso ki kawo mata mana tunda kin samu jaka ko ita ta ce ki je ki haihu.”
rufe baki Bintu ta yi tana dariya Yaya Amina na gefe ta ce” Inna fa ke son kiriniyan yara nan, ko zuwa mu ka yi ba mu zo da su ba sai ka ji ta ce kuka bar ɗiyan ga a gida ba ku zo min da su ba”
Inna na yar dariya ta ce”Kyale su Ɗan Inna rai ne ya kaini, yau in da ba na raye wajen za su je? Wata rana ba za su ganni ba gwara su mori kakar ta su tun yanzu.”
Har suna haɗaa bakin wajen faɗin”Ba yanzu zaki mutu ba Inna.”
Yaya Halima ta karɓe da faɗin”Ita Inna daman akwai kiran mutuwa ana zaune lafiya.”
Mu’azzam kuma ya ce”Inna sai kin ɗauki ɗan Yaya Mansoor ko ƴarsain sha Allahu.”
Inna ta ce”Allah yasa, amman na cire rai da ganin Auran Baban Inna, ganin auransa da ya’yansa ai sai mai yawan rai tunda na ga ba shi da niyyan auran kwata kwata.”
Mu’azzam ya ce”In sha Allahu zai yi Inna mu ta ya sa da addu’a don Allah.”
Inna ta sauke numfashi kafin ta ce”Addua’armu kullum ba ta yankewa a gare ku, Allah ya sausasauta masa wannan zuciyar ya sanya masa salama acikinta.”
Suka amsa da Amin gabaɗayan su Yaya Amina tace”Nifa ina tunanin yarinyar nan ce har yau ya kasa cire ta acikin ransa.”
Yaya Halima ta ce” kike gani? Yarinyar da ya zo ya tsani jin sunanta. Ranar Babansu Khairi na kallon labarai nake gaya masa Mansoor ya sota tun tana matashiyarta a zamanta hannun kakarta sai dai sun rabu da jimawa, itama fa ba ta yi aure ba har yanzu”
Bintu ta ce”Ba ta yi aure ba mana, amman fa tana da kyau ga iya kwalliya ni dai wlh Saboda ita nake kallon tashar su har ga Allah tana burgeni kuma sun bala’in dacewa da Baban Inna.”
Inna na jin su duk ba ta yi mgana ba sai da ta nisa kafin ta ce”Ba wanda yasan abin da ke zuciyarsa, ba na tunanin ita ya ke jira saboda ai shi ya fara yanke alaqa da ita ko bayan dawowarmu Mu’azzam kai ka faɗamin tana ta kiransa a waya ya ƙi ɗauka sannan shi ya yanke sauran alaqan da ta rage tsakanina da kakar yarinyar nan. Tun daga lokacin ban kara taka kafata gidan ba itama Hajiya ba ta kara nema na ba, abu ne ya riga ya faru sai a manta baya a fuskanci gaba kullum ya zo nan babanku zai zaunar da shi yana masa nasihan hakuri da rayuwa sai ya nuna kamar ya ji ammh sam Baban Inna ba’a gane in da ya dosa shi dai ƙwallon nan da ya saka gaba ita ya rike bansan kuma me yake tunanin ya mai da rayuwarsa ba.”
Inna Meri ta ƙarishe faɗa cikin bayyana damuwarta Yaya Amina ta dafa kafaɗarta lokaci ɗaya tana faɗin”Bakomai Inna, zai wuce in sha Allahu Baban inna zai yi aure har ki ga ƴaƴansa” Bintu ta yi karaf ta ce”To ai abun haushin ma ko budurwa ba shi da ita.” Mu’azzam ya yi jim kafin ya ce”Ai ina jin tun bayan rabuwarsa da Fatima Baban Inna bai kara son wata mace ba, ban jin ma mata yanzu suna burgeshi ta sauya shi fa fiye da tunanin ku, yanzu haka abokan mu sun gaji da min korafi sun hakura ana gari ɗaaya sai su yi wattani ba su gan shi ba ya koma rayuwar kaɗaici abin da na fahimta har gobe abun na ranshi ya kasa mantawa ne.”
Yaya Halima ta ce”Nima abin da nake tunani kenan, cire abun a ranshi zai taimaka masa wajen fuskantar wata rayuwar a gaba.” Mu’azzam ya ce”Yau ai wajen sa zan kwana zamu tattauna Allah yasa ya bani damar haka.”
Inna Meri ta amsa da Amin a samam labbanta har aka kira mangariba suna tattauna abubuwan da suka faru a shekarun baya ne.
Kiran sallar Mangariba ya tada su Mu’azzam ya yi alwala zuwa masallaci su kuma matan suka yi na su agidan.
Yaya Amina ta fara tafiya tunda ta fi su nisa, Yaya Halima kuma daga baya Bintu dai har sai bayan Sallar isha’i da Baba Ɗanjuma suka dawo tare da Mu’azzam da Auwalu.
Har ɗakinsa ta bi shi suka gaisa Magajiya ke da miji sai kuma abin da Baba Danjuma ya gani ruwa ma Inna Meri ce ta kawo masa mai sanyi tunda tana da ƙaramin firiza a ɗakinta na Yaya Halima ne da mijinta ya siya mata Babba sai ta kawo mata wannan.
Sai da ya sha ruwan ya ji ka maƙoshi acikin ransa ya yi saka ma matar kirki irin Meri albarka yana tuna karamcinta a garesa tun na tsawon shekarun da suke tare.
ƴan Biyun Bintu suka hau jikinsa suna wasa yana dariya yake faɗin”Ku yi min a hankali kar ku ƙarisa ni domin na ga kuna ji da karfi.” aka saka dariya gabaɗaya, Auwalu yace”In na kalle su sai na tuna yarinyar nan Bintu ai itama ta yi rashin jin mgana, ba domin Mansoor na tsawarta mata ba da sai Allah.”
Bintu ta tura baki kafin ta ce”Haba Yaya Auwalu yaushe na kai yaran nan rashin ji.”
Mu’azzam ya ce”Kin fa yi Bintu ai har gobe baki daina ba sai dai in yan abun naki ba su motsa miki ba.”
Tura baki ta yi tana faɗin”Baba ka gansu ko? Ka yi mu su mgana.”
Baba Damjuma yace”Ku bari mana Fatima Bintu sunanta mai daraja ne babu ruwanta da rashin arziki.”
Nan fa suka yi ta wasa da barkwanci har Bashir ya zo tafiya da Bintu gida Inna Meri tun ɗazu ta yi mata mgana ta tafi gida ta ce ita fa a kusa ta ke daga zuwa gida Inna ta fara cewa ta zo ta tafi, Ahalin tun safe ta zo ta riga kowa ma zuwa shi ne take cewa ba ta daɗe da zuwa ba Inna na koranta gida tunda ta ji haka sai ta kyaleta ta sanya mata ido da kila Baban Inna ya zo ne shi ne dodonta yana cewa me take yi har dare ba ta tafi gida ba? Jikinta na rawa zata haɗa Ƴaƴanta ta wuce tana tura baki iyaka dai ta kwana biyu ba ta zo ba in Inna Meri ta aika walida a duba ta sai ta ce tana nan lafiya ai Baban Inna ne ya koreta kuma a gaban inna ba ta yi mgana ba. Sha’anin Bintu ai sai ita ɓauɗɗiyar mace ce irin Mansoor wasu Lokacin suna da kamceceniya ta bangaren hallaya. Ko domin suna matsayin uwa ɗaya ne?
Mu’azzam sai wajen tara da rabi ya bar gidan nan zuwa Tunfere gidan Mansoor daman ya tura masa sakon in bazai zo ba shi zai je Camp ya kwana gobe suna da morning trainig shi ya sa ya yi ma su Inna sallama da Baba ya wuce tare suka fito da Auwalu ya rage masa hanya ya sauke shi a gidan shi sannan ya wuce.
Lokacin da ya isa wayar Mansoor ya kira ya ce masa ga shi a waje, sai da ya ɗan ɓata lokaci sannan ya fito ya zo ya buɗe masa get ya shiga da motar Ciki ya yi parking ɗin ta kusa da ta mai gidan.
Yana tsaye a bakin falonsa daga shi sai gajerun wando, ba nepa akwai kuma zafi a garin shi ya sa ya zauna haka, bai koma ciki ba har sai da Mu’azzan ya buɗe bayan motarsa ya ɗauko karamar jakarsa ya shiga falon sannan ya maida kofar ya rufe ya bi bayan sa.
Dukkansu sun sake wanka, Mansoor daman baya shiri da zafi sai ya yi wanka sama da sau huɗu a dare ɗaya.
A ƙaramar katifan Mansoor suka kwanta dukkansu, shi Mansoor filo bai dame shi ba sai ya ba ma Mu’azzam ya dora kanshi a saman matashin, daman ya saba kwana in dai ya shigo garin tuni ɗakinsu na samartaka na gida su ka bar ma Saddiqu yanzu shima yana ƙokarin siyan fili ne ya fara ginin muhallin da za su rika sauka shi da Hibba in sun zo garin.
Suna kwance Mu’azzam na ta Juye juye Mansoor ya ce”Kana jin zafi ne? duba bayanka akwai mafita sai ka yi amfani da shi.”
Mu’azzam ya ce”Gaskiya ya kamata ka saka solar tunda wutar nageria ta zama sai Allah ya kyauta.” Kamar bazai yi magana ba sai can ya ce”Zan sa ka in sha Allahu”
Shuru ya kara biyo baya bayan Mu’azzam ya amsa masa da Allah ya sa.
Mansoor ya katse shurun da cewa” Ina Junoir? Mu’azzam ya ce” Suna Tudun wada can za su kwana sai jibi in zamu koma.”
Kai Tsaye yace”Gobe da la’asar zan zo gida ka kawo min shi na gan shi.”
Sai Mu’azzam ya amsa mi shi da toh kawai wayar Mansor din dake gefensa ya laluɓa ya ɗauka yasan password ɗin watan haihuwan Mu’azzam ɗin ne mabuɗin buɗe wayar Mansoor.
Yana buɗewa a fuskar wayar hoton Junior ne ya fara masa maraba wanda aka yi masa ne na cika 2yrs shi ya tura masa ya yi kyau yaron yana ta bangala dariya.
Mu’azzam ya juya ya kalli ɗan uwan da jini bai haɗa su ba amman ya zame masa wani irin ɗan uwan da babu kamarsa.
Cikin yar driya ya ce”Sai aka cire hotona aka sanya na Junoir har an gama ya yi na kenan Baban Inna?
Ya juya masa baya shi ya sa ba zai fahimci yanayin fuskarsa ba.
Kamar baya son mgana ya ce”E, kai ka girma yanzu.”
Mu’azzam ya ce”Ni fa ban yarda ba, dole gobe Inna ta yi alƙalanci.”
Har sai da yaji karan sautin dariyansa Lokaci ɗaaya ya juyo ya yi matashi da duka hannayensa idanuwansa na kallon rufin POP ɗin dakin cikin shakewar muryar da gajiya ta saukar masa ya ce” Hausawa suka ce abun cikin ƙwan ai yafi ƙwan daɗi Mu’azzam”
Mu’azzam ya yi mirmishi bai yi mgana ba ma’adanan hotuna ya shiga yana ta kallo gabaɗaya hotunan shi ne na kwallo sai na yan Club dinsu sai kuma na Mu’azzam da suka cika wayar da Junoir sai hoton Inna Meri da Baba Danjuma da kuma nasu gabadayansu shekara biyu kenan da wata salla shi Mu’azzam ya matsa aka yi saboda tarihi kuma shi ya tura ma Mansoor din hotunan. Ba magajiya domin ta ce ba za ta yi ba, kowa dariya ya ke yi a hoton ban da Mansoor da Mu’azzam ya dafa kafaɗansa ya sunkunya da kansa ta wajen fuskarsa tunda Mansoor din ya fi sa tsawo.
Ya daɗe ya na kallon hotunan yana Mirmishi kafin ya wuce kaf ya bincike hotunan wayar har ya kai kan wani tsohon hoto. Su biyar ne acikin hoton kuma zai kai kimanin shekaru goma sha ɗaaya da ɗaukan hoton.
Mu’azzam bai manta wannan hoton domin hoto ne ma na kati aka yi snaping ɗin sa a waya ina zai manta Shagon Aci kwalba mai hoton yan gayu a anguwansu ta Arawa ya ke. Shi ne a tsakiya sai Ahmad a gefensa na dama hegensa na hagu sannan Nasir.
Makama da Mansoor suna da Tsawo sai suka tsaya agefe da gefe.
Da ka gansu kasan an baya an sha gayu da ji da kai, Mu’azzam ya fashe da dariya shi kaɗai Mansoor ya kallesa kafin ya ce”Daman ka na da wannan hoton?
Ya faɗa ya na nuna masa hoton kansa ya gyaɗa kafin ya ce”Kai ka taɓa turamin shi.”
Mu’azzam ya ce”Bari ko na tura ai na manta na tura maka ina ta neman sa ko wajen su Nasir ban samu ba suma ba su da shi, ina tunanin har na hoton duk sun ɓace mana.”
Mansoor ya ce”Ni ina da su acikin tsoffin takarduna na makaranta”
Mu’azzan ya ce zai kai a wanke masa na Tarihi nan da nan ya ɗauko wayarsa ya tura lokaci ɗaya ya na faɗin” kalli wuyan makama kamar lagwani kyan shi a tura ma yarinyar da zai aura ta gan shi a haka.”
Mansoor na jin sa bai yi mgana ba sai shi Mu’azzam ɗin ya cigaba da faɗin”Bayan sallah da Sati huɗu ne bikin Makama, in na zo sallah na koma sai bikin zan kara dawowa in sha Allahu.”
A shake Mansoor ya ce” Allah ya kai mu.”
Shi kuma Mu’azzam ya cigaba da bashi labarin shirye shiyen biki ya na faɗin su abokai sun ce za su shirya dinner
Mansoor ya ce”Makama ya bar Ustazan cin ne da zai yi bidi’a bikin sa.?
Mu’azzam ya ce”Gidan su yarinyar ke son haka ina ganin.”
Gyaɗa kai kawai ya yi ba tare da ya yi mgana ba, Mu’azzam ke gaya masa za su yanke ko nawa ya kamata kowa ya ba da.
Kai Tsaye Mansoor ya ce”Kar ku fara sani cikin yarintar ku, in na tashi zan turama Makama guddumuwata ba ruwana da wani sha’anin sakarcin banza shima dai kamar wani yaro.”
Mu’azzam ya yi dariya kafin ya ce”To yaro ne mana, tunda yanzu zai yi aure kai ma ka bari ka ga yadda zamu raya bidi’a a naka bikin.”
Wani kallo ya watsa ma Mu:azzam kafin ya kira sunan shi “Mu’azzam..!
Ya amsa da “Na’am'” yana dariya.
Sai kawai ya juya masa baya bai kara magana ba.
Ya bar Mu’azzam na mirmishi ya na tuna shekarun baya akwai wani abu da ya faru da ya kasa mantawa yasa sai da ya kara saka dariya. Da karfi Mansoor yace”Mu’azzam za ka fita falo ka kwana, junior ne kai da za ka rika motsin kwanciya?
Mu’azzam ya tashi zaune yana faɗin”Wani abu na tuna ka tuna muna a yara in su Jummai su ka ganmu tare sai su ƙwace hannuna daga hannunka suna cewa kai mu ne fa yayyenka wannan ba babanmu ya haife shi ba.
Kai kuma sai ka ƙwace hannuna daga wajensu kana faɗin”Eh din ba Babanku ya haife ni ba, amman ai ɗakin Innata yake kwana take kuma bashi abinci saboda haka ya zama ƙanina ka tuna lokacin?
Mansoor ya Juyo ya na mirmishi shima lokacin yana dawo masa girgiza kai kawai ya yi, Allah sarki Kuruci dangin hauka.
Mu’azzam ya koma ya kwanta yana cigaba da duba wayar Mansoor ya na yar dariya.
Sai dai ya bata fuska lokaci ɗaaya da ya gama bincike wayar bai ga hotonsa da uniform ba, kuma tare ya tura masa da hoton Junior cikin kufuluwa ya ce” Baban Inna ina hotuna na a office da na tura maka? Kai tsaye ya ce” Na share su.”
Baki buɗe ya mike zaune yana faɗin “Ka share su kuma? To saboda mene?
Kai tsayen ya kara cewa”Kai ma kasan dalili.”
Mu’azzam ya yi tagumi kafin ya ce”A masu kakin ma har da ƙaninka ka tsana?
Mansoor ya yi masa banza kamar bai ji sa ba sai da Mu’azzan ya kara faɗin” kuma ai tun a wancan Lokacin kai kace na je na zama duk abin da nake son zama.”
Mansoor ya yi shuru kamar ba zai yi mgana ba sai can ya mukusta ya gyara kwanciyarsa Lokaci ɗaya yana faɗin” A lokacin saboda ka matsa ne, amman ni har abada bazan so duk wani aiki mai sanya kaki ba, na tsane su har acikin raina saboda ƙakin su na basu damar cin zarafin mutane yadda suka ga dama.” Mansoor ya faɗa ya na jin wannan abun da ya tokare masa kirji ya taso masa sama duk lokacin da ya tuna sai ya ji kamar ya fama damuwar da ya danne shekara da shekaru ne.
Mu’azzam kuma ajiyar zuciya ya sauke kafin ya ce”A ba duka aka taru aka zama ɗaya ba, a ko’ina akwai na kirki akwai na banza” A tsawace ya ce”Kana gaya amin haka ko Mu’azzam? Ni ban ga na kirkin ba na banzan na gani, kuma da shi zan yi misali.”
Kamar Mu’azzam zai yi kuka ya ce”Ni yanzu na banza ne Yaya Mansoor?
Sai ya kasa bashi amsa sai ma koƙarin mikewa zaune da ya yi ya sauka daga kan katifar ya mike da kafafunsa.
Shi kuma Mu’azzam ya b shi da kallo kafin ya ce”Saboda ita ne ko?
Saboda ita ce ka kasa mantawa da abin da ya faru da daɗewa Baban Inna.”
Har ya kai bakin ƙofar tiolet sai ya Juyo ya na kallonsa cikin kaushin murya Ya ce.
“Saboda ita wa???
Kai Tsaye Mu’azzam ya ce” Saboda FATIMA! Itace silar da ya saka ka tsani masu ƙaki, itace silar rugujewar tuninaninka na zamo wa sojan kasar ka.”
Ƙurama Mu’azzam ido ya yi yana jin wani abu a kirjinsa na wani dif dif, me ya sa zai ce saboda ita ne? Ba saboda ita ba ne.
Cikin ɗaga sauti ya ce”Ba Saboda ita ba ne Mu’azzam.”
Yana direwa ya taso mai da cewa”To in ba saboda ita ba ne, saboda waye da zai saka har ni ba ka iya kallona da ƙakin yan sanda a jikina?
A tsawace ya ce”Saboda mahaifinta ne Saboda shi ne wannan MAJOR KABIR ɗin ne. Saboda shine komai ya ruguje.”
Ya faɗa lokaci ɗaya yana tura kofar tiolet ɗin da ke ɗakin ya shiga da sauri ya kuma maida kofar ya rufe ta da karfi har sai ta yi ƙara bam!!.
Page 7
Kofar ya ƙurama ido wasu shuɗaɗɗun al’amura da suka wuce a baya suna gilma masa, in hasashen sa ya zama gaskiya Mansoor bai manta da Mimi ba har kwanan gobe tana cikin ransa kuma saboda ita ne har gobe ya kasa iya kula kowacce ƴa mace.
Shi da kuma ya yi rantsuwan ko zai mutu bai yi aure ba, ba zai taɓa auranta ba kuma ga shi har gobe yana sonta shi kam ya rasa ta in da zai saka tunanin wannan al’amarin.
Komawa ya yi ya kwanta yana wasu tunane tunane, shima tun bayan abin da ya faru ba su kara haɗuwa ba shi daman ya bar Gombe ya koma Kano. Nasir dai kwanaki can da jimawa ya ce sun taɓa haɗuwa har ta karɓi lambarsa to ba ta taɓa kiransa ba shima kuma daman itace ta karɓi Layin nashi shi bai karɓi nata ba sai dai suna ganinta a akwatin talabijin ɗin, tunda tana aiki a sananniyar gidan talabijin sannan ta yi suna kowa ya santa. Shima dai yana ganinta lokaci bayan Lokaci in yazo garin a tibin Inna in Walida ta kunna, Mansoor ne ba shi da wani masaniya a kanshi sanin shi fa ba ka gane gabansa ballantana bayansa to kila har gwara shi ya kan tsaya su yi magana mai tsawo, wasu tuni ya yanke wannan alaqar a tsakanin su.
Bai taɓa tunanin haka soyayya ke da zafi ba sai akan Mansoor a lokacin ma daga shi har Mimi suna da karancin shekaru shi ya ɗauka a shekarun da suka ɗauka ba sa tare soyayyarsu za ta disashe ashe ba haka ba ne, tana nan ta kara girma ne acikin zukatan su.
Ba zai taɓa man tawa da ciwon da Mansoor ya kwanta a lokacin ba, da kukan da ya riƙe ƙirjinsa yana yi ba, bqasonta yake yi ba kaunarta yake yi sannan sun shaku sosai soyayya ta rufe musu idon da suka kasa gane bambamcin dake tsakaninsu har sai da komai ya kwaɓe sannan Mansoor ya fahimci abin da aka jima ana nuna masa. Tun Mu’azzam na zaman jiransa har barci ya ɗaukesa Mansoor bai fito daga tiolet ba. Sama da awa ɗaya sannan ya fito daga cikin tiolet ɗin jikinsa na faman ɗigan da ruwa. Tsaye kawai ya yi a tsakiyar falon ookaci ɗaya yana mai harɗe hannayensa a saman ƙirjinsa. Mu’azzam yake kallo yana barcin sa cikin salama da kwanciyar hankali ba shi da damuwan komai a cikin zuciyarsa.
Yana jin dama shima haka yake ba shi da wata damuwa. Dama shima zuciyarsa ta sauke wannan nauyin abin da ya tokareta shekaru goma ya yi rayuwarsa cikin salama ba tare da damuwa da tunani ba.
Duk lokacin da ya tuna abun sai ciwon da ke kirjinsa ya dawo sabo, saboda ita ne har gobe ya kasa kallon wata ƴa mace da sunan kallon soyayya. Saboda ita ce ya ji aure ya fita kansa kwata kwata ya ji a duniyan nan ba zai iya zaman aure da wata mace ba.
Saboda ita ne ya sauya rayuwarsa da ga mai yawan hira da son mutane zuwa wani mutum mai son kaɗaici da son zama shuru, Saboda ita ne ya ji ya tsani masu kaki gani ya ke yi dukkansu haka suke marasa adalci da sanin ɗarajan ɗan Adam.
A lokacin baya da ita ya yi mafarkin kasancewa har karshen rayuwarsa.
Shi fa mafarkansa gabaɗaya ko ɗaya bai cika ba, duka ya rasa su sai wasu ya gina sabbi acikin duniyarsa.
Bai tab’a tunanin Soyayyarsa da MIMI akwai wasu tarin bambamce bambancen da mutane ke hango masa wanda shi nashi hangen bai taɓa kawo masa ba. Ya ɗauka ita soyayya babu ruwanta da bambamcin jinsu ko hallita, ba ta kuma duba dukiya ko launin fata, ba ta kallon ilimin mutum ko kuma nasabarsa, ita ba zaɓan chanchanta take yi ba, ba kuma ba tasan ya kamata ba, in da ace Soyayya ta san ya kamata da tun farko yin soyayya da FATIMA SULAIMAN DABO bai kamace sa ba.
A iya hange hangensa bai taɓa hango bingiren rayuwarsa ba tare da Mimi ba, sai ga shi rayuwar ta lula shi wata duniyar da babu Mimi a cikinta ta ɓace daga cikinta, shi ya saba mafarkan ga shi ga Mimi tare da kyakyawan ya’yansu da irin yadda suka gina kyakyawan rayuwarsu, ashe ashe matacaccen mafarki ne ba zai taɓa tabbata ba.Hannunsa da ya kasa CIZAWA shi ya kai sa ga duniyar da ya zama sai shi kaɗai babu MIMI a cikin ta. Ta yi nesa da duniyarsa domin tarin bambamci tare da tazara mai kimanin kilo tamanin da Ahalinta suka hango tsakaninsa da ita wanda shi nashi hangen ya kasa hango masa, saboda tarin soyayya da ta rufe masa jin sa da ganinsa a lokaci ɗaya..
Kirjinsa ya fara tasawa yana faman sama da ƙasa, yaji kamar iskar ɗakin ya fara yi masa kaɗan sai kawai ya buɗe kofa ya fita zuwa falo ya goya hannayensa a bayansa ya fara tafiya yana zagayen falon gaf gaf! ana jin karan takun sa da karfi kamar wani namijin zaki. Zuciyarsa ke zafi tana wani turiri daga ciki iskar bakinsa yake fitarwa ya na jin zafin har a saman fuskarsa. Ba zai taɓa mantawa da tun a lokacin baya Nasir ya taɓa so ya ankarar da shi bai saurareshi ba, ba laifin shi ba ne soyayya ce ta rufe masa ido da ya kasa hango wannan bambamcin dake tsakaninsa da Mimi sai daga baya.
Aji tsakani ga Allah yarinyar nan ta fi ƙarfin ka, naga kana sonta da yawa kar nan gaba iyayenta su hana ka auranta
A lokacin dambe ne kaɗai ne ba su yi da Nasir ba sai da su Makama suka shiga tsakanin su, Shi a lokacin yana ganin ga Hajiya ta ba shi dama har cikin falon gidan yana shiga su yi hiran su da Mimi, ya manta ita kakarta ce sannan ya manta sanadin haɗuwarsa da Mimi sanadin aikatau ɗin da Inna Meri ke yi a gidan Hajiya ne.
“Ni? Kamar ni major Kabir My daughter ta auri yalaka agolan da ubansu har ya mutu a can wani ƙauyen kurmus, uban rikonsa wanzami uwarsa yar aiki? Over my dead body Mimi za ta yi wannan auran ƙasakancin ba ta isa ba, ko za ta Mutu bazan aura mata wannan talakan ba, jinin takalawa wanda bashi da wata kyakyawam makoma ko anan gaba_
Sai da ya saka hannunsa guda ɗaya ya daki bangon falon, yana ji kamar a lokacin ake gaya masa kalaman ta ya ya ake so ya manta da wannan cin mutumcin? a kira sunan mahaifin shi a kabari aci zarafinsa sannan aka kira mahaifiyarsa da yar aiki aka zage ta sannan shima a ka kirasa da mara kyakyawan makoma shi ko zuciyarsa ba ta yi masa adalci ba da har take tunawa da wannan yarinyar da aka gama kare ma zuru’ar sa tanadi a kanta. Shi ba dukan da aka yi masa ke damunsa ba, ya fi jin zafin irin kalaman da Mahaifin Mimi ya jefe shi da shi.wai shi ne mara kyakyawan makoma?
Shi ne saboda shi Inna Meri ta duka ita da Baba Ɗanjuma suna kuka suna roƙon a yi masa afuwa a sake shi.
Ku ja ma ɗan ku kunne, naga alaman Tsageranci na damunsa sannan ku yi masa iyaka da ƴata domin ruwa ba sa’an kwando ba ne, zan sake shi na yanzu amman ko kallon Mimi ya sake yi sai na ɗaure shi da kakin jikina..
Abi ka yi hakuri. Abi ina son shi don Allah kada ka rabamu da juna..
Sai dai ki mutu, amman ba za ki aure wannan talakan yaron ba, ba shi da makoma mai kyau, na tambayi Hajiya kwalin karatun shi tana gayamin iyakarsa Secondary school. Kuma shima soja yake son zama ire iren su ma ba su da wani rabo a duniya.
Abi ina son shi.
Ke yarinya ce Mimi, karatu nake so ki yi ba yanzu zan yi miki aure ba
Abi Ina son shiiiii…!
Murja ki ɗauke min Mimi kar raina ya ɓaci na fasa kanta da bindigata.
Ba zai manta da wannan kukan da ta riƙa yi lokacin da mahaifiyarta ke riketa ba, har gobe yana jin sautin wannan kukan acikin ƙirjinsa. Ya tuna ta na miko hannunta mahaifiyarta da yayarta suka rike ta suka tafi da ita zuwa cikin wani ɗaki
Kafafunsa sun kasa ɗaukansa dole ya koma ya zauna Jagab a tssakiyar Falon yana sauke numfashi sama sama.
Hawaye ya cika kwarmin Idanuwansa, Dakyar kuma siririn hawayen ya gangaro ta wajen idanuwansa hawayen so ne, Hawayen son abin da ka haramta ma kanka har Abada. Zafi ya ji jikinsa duka ya ɗauka kuma yana zufa har ta saman goshinsa.
Shi ya sa ya miƙe yana jan kafa ya koma cikin ɗakin cikin Tiolet ya ƙara komawa ya kara yin wanka. Yana fitowa nepa suka kawo wuta sai ya kure fanka sannan ya kara kunna ta kasa dai dai saitin Mu’azzam ganin kamar yana jin zafi. Gyara masa kwanciya ya yi yana tuna baya yadda ya ke kula da rayuwar ƙaninsa kafa kafa kamar ba shi da wani kani a duniya sai shi.
A fili ya furta” Bani da kamar Mu’azzam bani ni kuma da wami ƙani kamar sa.”
Shima gefensa ya koma ya kwanta bayan ya kashe hasken ɗakin
Ya kuma ɗauki wayar Mu’azzam ya saka masa chaji da chager ɗinsa. Shi kuma wayarsa sai ya sauketa a kasan cafet din da ke cikin ɗakin.
Ya daɗe bai yi barci har biyu na dare barci ma barawo ne ya sace shi. Da asuba da suka dawo daga masallaci Mansoor ya shirya ya tafi camp yace za su haɗu a gida in ya dawo. Mu’azzam sai da ya yi barci ya koshi sannan ya tashi ya yi wanka ya sauya kaya ya ɗauki motarsa ya bar gidan bayan ya kulle gidan tunda ya ga key din gidan anan cikin bedroom din.
A wajen Inna Meri ya je ya karya da waina da Miya Inna Meri da kokari da Safen nan ta toya ta miyar kuma Walida ta yi shi kafin ta ta fi makaranta Mansoor bai zo gidan ba sai da rana sai kuma a lokacin shima ya karya da waina da miya, daga nan Mu’azzam ya je tudun wada ya ga kwanan Hibba daga nan ya taho ma da Mansoor Junior.
Tunda kuma ya ɗauke shi suka fita a mashin sai yamma ya dawo da shi akwai wani team ne da suka gayyace shi kallon wasan su, Bacerlona sunan Team ɗin anguwan Jekadafari ne, can ya je kallon buga wasan su tsakaninsu da Mesi team na anguwan Tudun wada.
A hanya ya ga ana saida kayan wasan yara ya siyan masa jaka guda ya kawo sa wajen Inna Meri, yana ma gidan Mu’azzam ya kira shi ya ce suna tare da Nasir ya ce yana gida su zo su same shi. Sai ga Nasir har ɗakin Inna Meri, daman ai sun saba zuwa lokaci bayan Lokaci ko ba su Mu’azzan suna zuwa gaida Inna Meri. Nasir ya mika ma Mansoor hannu suka tafa lokaci ɗaya yana faɗin “Aji aji manyan gari.” Mansoor ya ce”Nasir kana nan a gari abin ka”
Nasir ya ce”Karyan tsiya kake yi baka neman mutane, ya wasa? Aji ka kusa haurawa waje fa duk garin nan hiran irin taka ledan ka ake yi, ranar muna gaddama da wani a wajen aikinmu na ce ai Aji tun a Nasara Team kowa yasan guru ne a taka leda na gaya masa lamba goma kake bugawa ya ko san duk wanda ke buga lamba goma ya kware a sanin ƙwallo.”
Mirmishi ya yi bai yi mgana ba, sai Mu’azzam da Nasir suka koma hiran ƙwallo Jefi jefi Mansoor na tsoma musu baki.
Daman Mu’azzam mafarkinsa ne kwallo, Shi ma Nasir haka in suka haɗe hiran su kenan ƙwallo.
Sun fi awa a ɗakin Inna Meri sannan suka fito kofar gida sun jima suna hira kafin su yi sallama akan sai sun haɗu da sallah.
Nasir ya tafi ya na yi ma Mansoor tsiyan da azumin nan sai yasa yara sun kiɗaa masa gwuro. Mu’azzam na ta dariya shi kan shi Mansoor din sai da ya yi mirmishi.
Daga Mansoor har Mu’azzam nan suka yi mangariba da isha’i bayan Mu’azzam ya maida Junior wajen maman shi tare kuma da Baba Ɗanjuma suka ci tuwon masaran Inna da miyar kubewa.
Bayan sun gama kuma suka zauma suna ta hira, yau Inna ce ke da turaka shi ya sa suka samu zama da Baba Danjuma sosai.
Sai wajen goma suka baro gidan suka koma gidan Mansoor suka kwana washegari Mu’azzam da iyalansa suka koma kano.
Duka duka sun tafi da kwana goma aka fara azumin Ramadana.
Kamar yadda suka saba haɗaa hannu shi da Mu’azzam duk azumi su siya komai buhu a raba nan cikin gida da kuma makota.
Sannan kowannen su ya aika da kuɗi danginsa, Shi Mansoor ya tura sakon kudi a can kwami shi kuma Mu’azzam nan Anguwan bolari inda aka haifi mahaifiyarsa.
Inna Meri ba ta yi sakacin da suka manta dangin su ba, sannan kaf ƴan’uwansu mata sun samu siga da gero na kayan azumi.
Bintu kuma 50k Mu’azzam ya tura mata Mansoor kuma ya siya mata firiza da ta ce ta na so zata fara saida Zobo da ruwan sanyi da azumi.
Sannan ya ba ta jarin kayan zobon ranar Bintu ta tiki rawa abokiyar zamanta ta sha habaici da Bashir ya yi magana ta ce ya kyaleta itama in taji haushi yayyenta su siya mata.
**
Hajiya da Mimi a na saura kwana huɗu a fara azumi suka ɗaga umra, Hajiya ce daman duk Azumi can ta ke yin azumin ta wannan karon kuma ta matsa tare da Mimi za ta tafi sai Daddy ya niya musu suka tafi tare aka bar ma Baaba Uwani amanar gida.
Hajiya ta je ƙara yi ma ɗanta Kabiru addu’a tare da Binta ita kuma Mimi ta je yin ma Abin addu’an Allah ya bashi lafiya duk da ta taɓa zuwa Umra sau biyu.
Hajji kuma sau ɗaya ta taɓa zuwa lokacin da ta gama bautar kasarta ne kafin ta koma kano ta yi master ɗinta.
Tunda suka je ibada kawai suke yi, kuma daman ba ta da matsala da wajen aikinta tunda Umra ce, ba ma ita kaɗai ta je ba har news manaja din su yaje shi da iyalansa sun haɗu da shi acan, sannan har Madiha sun gani ta je ita da mijinta da ƴaƴanta amman su ba acan suka yi sallah ba.
Tun suna Umra Rukky ke damun Mimi a chart da mganar bikin Bibi sai da Mimi ta yi mata alkwarin in da ta dawo ba zata ja baya ba da ita za’a yi komai a gama in sha Allahu.
Acan kuma ta siya ma Bibi zanin gado mai kyau na guddumwa. Ranar salla ta yi Hoto ta ɗora shi a status ɗin ta mutane suna ta cewa yaushe za ta dawo? Gidan karamchi Talabijin na kewarta. Daman tunda suka tafi ba ta cika amfani da waya ba sai jefi jefi ta dukufa addu’an Allah ya cire mata Soyayyar Mansoor acikin ranta ko zata samu sauki acikin ranta, ba ta san cewa Na Misau ya dauki hoton ta ya je shafinsu na Faceebook ya ɗorata tare da cewa. ” Fatima kabir sulaiman dabo(Mimin karamchi) na yi muku barka da sallah daganan Birnin Madinatul munnahwara.”
Ita ba ta man san ya saka ba sai da daddare da zata kwanta ta buɗe data ta gani ta sha comment har wani na faɗin” Hajiya Mimi Madina ta karɓeki har kin kara jan kumatu.” Sai da kalamansa ya sa ta yi dariya har ta yi masa reply da cewa” Zama waje ɗaya ne, kafin na dawo manaja ya rika sani fitar dafiya.”
Shike nan sai aka fara cecekuce ana ta hira ta jima online ta na yi ma masoyanta reply ita kanta ai ta yi nishadi sai da Mommy ta kirata Vedio call sannan ta koma suna waya da ita tare da Abi da duk ya kara ramewa ya tsufa saboda ciwo. Hajiya har ta fara barci ta tashe ta suka yi mgana da Mommy da Abi. Su ma suna ta shirin dawowa gida nan da sati mai zuwa.
**
Mu’azzam da matarsa da ɗansu duk anan suka yi salla sati ɗaya suka yi suka koma kafin komawarsu sun haɗu kan bikin Makama amman babu Mansoor ba ya nan sun tafi Bauchi buga wasa su kansu ba su damu da shi ba sanin ba zai shiga wannan hurumin ba, ta bakinsa ku riƙa yin abu na masu Aji mana. Tun ana washegarin sallah ya tura ma makama 150k guddumuwa kuma ko da ya kira shi a waya ya yi masa godiya bai ɗauka ba.
A chart kuma ya yi masa mgana bai buɗe sakonsa ba, ya yi ma mu’azzam korafi ya ce kada ya damu ba ya son ya yi masa godiyar ne shi ya sa bai ɗauki kiransa ba.
Sun tattauna yadda za su shirya dinner da sauran bukatun amarya Nasir suka bar ma komai a hannunsa tunda shi ke zaune a gari. Kuma shi ake ba ma jagoran zama da amarya domin ya ji tsarinta.
Bikin zai kama 28 Ga watan April, tunda an ƙara sati ɗaya. Nasir ya je gidan su Bibi sun haɗu da Rukky tunda kamar ita ce ja gaba kan komai sun yi mgana, Nasir irin mutanen nan masu maagana kai tsaye ba su tauna ta
Sai da ya yi ma makama mganar yayar matarsa ce za ta ci ma kanwarta ƙawa ne?
Makama yace to in ma hakane ina ruwansa.
Nasir yace”Shi fa na gani babu ruwana ai da din kallo ne da shi.”
Bayan guddumuwar da suka ba ma Ango sun ba ma Amarya kuɗin gyaran jiki da na abinci ɗinkunan kuma da aka sanya a acikin akwati Ahmad ya ɗinko su duka ya aiko da su da yazo sallah daman ya ce Makaman ya bashi zai ɗinka ma amarya kayan fitan biki.
Kala goma ya ɗinka mata kaya masu kyau da yarari ga su sun haɗu da tela ƙwararre sai kayan suka fita sosai.
Ana saura kwana goma biki aka kawo kayan aure akwati bakwai da ghana Must go. Mimi da Rukky daga wajen aiki suka zo tare ta ga kayan sai dare ma ta koma gida.
A yadda Rukky ke ba ma Mimi labarin abokan angon da Angon kanshi sun yi kokari sosai ba su yi ƙwaron hannu ba.
Dinner daman su suka ce a bar komai a hannunsu za su shirya daga bangarensu.
Saboda Rukky Mimi ta shiga bikin kuma Bibin ma ta ce”Don Allah Anty Mimi kune yan gayu ki tsara min bikina.”
Har sai da tayi dariya, da ta kawo mata zanin gadon da ta siya mata da ta je Umra har Babansu Rukky sai da ya yi mata godiya. Hajiya ma ta ba da 20k ta kaima Mamansu Rukkaya.
Duk Lokacin da Angon da abokonsa za su so Mimi ba ta nan ko suna wajen aiki kuma da daddare sukan zo lokacin ta koma gida.
Ana saura sati ɗaya biki suna mota ita da Rukkya daga wajen aiki za su shiga kasuwa Rukky tana ta mita da tsaki.
Mimi ta ce”Wai me aka yi miki ne? Kin ishe ni da mita”
Rukky ta ce”Ni da abokin Usman ne da suke zuwa tare ba shi da mutumci shekaran jiya kallo na fa ya yi yana cewa wai Amaryan nan ba ta da ƙawaye ne sai ke?
Mimi ta fasjhe da dariya kafin ta ce” Gaskiya ya faɗa kina Yaya kin zama ƙawar ƙanwarki.” Rukky ta ce”To ina Bibi ta ga wasu kawaye Allah na tuba, ai na yi ta jaraba Usman ya bani hakuri da cewa haka yake nace to ya saita bakinsa.”
Mimi ta kara saka dariya kafin ta ce” Baby Rukkaya.” Rukky ta yi dariya kafin tace”Zai ga ƙawaye in ana gobe biki da ranar biki amman yanzu duk mu za mu shirya komai.”
Mimi dai faman dariya take yi sanin halin Rukky ita so ta ke yi a biki na nuna sa’a shi ya sa take so su shiga su shirya komai da kansu.
Sun jima a kasuwa saboda sauran siyayyan kayan kitchen sai Atamfar yinin biki da suka siya tunda Mimi na dinner kaɗai ta turama Rukky kudin ta siya mata less ta ba da ɗinki a waje ɗaya tare da nata.
Na yinin bikin kuma Atamfa ce gold itama Rukky ta ce ɗinki iri ɗaya za su yi saboda haka waje ɗaya za ta kai musu ɗinki.
Mimi ta bar mata, tunda Rukky dai ta dage sai sun zama ƙawayen Bibi.
Satin bikin kaf ba su zauna ba tunda tana da mota mai kawai take sha suna shiga gari. Ko a wajen aiki ma bini bini Rukky ta ja ta sun fita Har Na misau sai da ya yi magana yace” Ke dai Rukky kina da son kuɗi, ki rage ciki ki siya mota ki daina lafe masu mota ana miki ɗani. Rukky ta rika hararan shi Mimi na yi musu dariya.
Sai dai shima yana zolayanta ne, tunda ai su san ƙawaye ne, kuma ga bikin Kanwar Rukkaya da kowa a an bashi katin gayyata. Zirga zirga ya yi musu yawa ba ta komawa gida sai dare har Hajiya sai da ta ce Rukkaya yar gaban goshin Mimi ce da har take iya janta suna faman zirga zirga.
Itama Mimin ta gaida matsayin Rukkaya a zuciyarta ita da ba ta yarda ta je ko’ina daga wajen aiki sai gida fita nan da Rukkaya ta matsa mata suke yi duk jikinta ciwo yake yi. Ana saura kwana uku biki suka je kunshi aka yi ma Mimi lallin Sticker a kafanta ja ya yi maroon a hannun ma an yi mata jan sai aka sirka mata da bakin zane.
Ya yi kyau sosai abun ka ga farar fata a can gidan kunshi ma ana ta santin kunshin saboda Mimi ta manta rabonta da kunshi tun bikin Auran yayarta Khadija in za ta iya tunawa.
Ita kanta haka ta riƙa kallon kunshin tana jin daɗi ana gobe jibi kuma gyaran kai suka je sun yi kuma yamma saboda sai da suka je kasuwa ita da Rukkaya sannan suka tsaya shagon Salloon suka yi gyaran kai Amarya Bibi tana tare da wasu kawayenta guda biyu yan makarantar su sai wata ƴar’uwansu da suka zo daga Bauchi.
Tunda su Rukkaya mamansu ce yar Gombe Babansu kuma ɗan Bauchi ne.
Ranar kuma ita ke da karanta labaran duniya na yamman dole daga Saloon Rukkaya ta wuce gida, ita kuma sai ta koma gida ta shirya ta wuce wajen aiki, ga shi ta zuba kunshinta ga gyaran kai goshi nan ya yi raɗau haka ta rika karanto labarai cikin zaƙin muryanta.
Ranar ta sha magana su kansu ma’aikantan kowa ya ganta sai ya ce ta yi kyau.
A lokacin da ta gama karanta labaran cikin harshen hausa sai ta koma na harshen turanci, a dai dai lokacin Mansoor ya shiga bangaren Inna Meri ba a anguwan ya yi sallar mangariba ba daga Studio yake ya tsaya ya yi sallar acan sai kawai yana shigowa anguwan ya shigo gidan kai tsaye.
Ya ɗaga labulen ɗakin Inna Meri kenan lokaci ɗaya yana faɗin” Innar m…”
Sauran kalamansa sun maƙale a fatar bakinsa lokacin da ya yi arba da ita.
Ba shiga ta yi mara kyau ko wanda ya saɓa mata addini ba, tunda doguwar riga ta saka mai ruwan kasa mai faɗii ba ta ma kama jikinta ba. Sai dai ras kunshinta ya fito tunda hannayen ta suna waje ne.
Kamar ya ga mutuwarsa haka ya ji, gabansa ya faɗi ras!.Haka ya ji kirjinsa na wani irin Dif! Dif! Kamar ya na da ciwon asma.
Inna Meri na ɗakii ta jin muryansa dai dai ta fito tana faɗin “Murya wa nake ji kamar ta Baban Inna”
Sai dai ta hangi bayansa ya na sakin L labulen ɗakinta ya wuce.
Walida ke tsakiyar falon tana sallah inna Meri ta leka daga wajen kofar ɗakin sai ta ga da gasken dai ya fita.
Sai ta dawo dai dai lokacin da Walida ta sallame salla.
Inna Meri ta kalleta tana faɗin”Ba Baban Inna ba ne ya shigo yanzu?
Walida ta ce”Shi ne yana ɗaga labule kuma na ga ya juya da sauri ya fita.”
Inna Meri na gyaran hijabin jikinta rike da casbaha ta koma cikin ɗakinta tana faɗin” Walida ki rage karan talabijin ɗin nan, a haka kika yi salla da shi ƙara ya yi yawa.”
Walida ta juya ta na kallon Mimi tana karanto labarai cikin turancinta mai kyau kamar ba’amurkiya. Sai ta fara tunanin ko ita Baban Inna ya gani ya juya.
Zai iya zama gaskiya saboda akwai wata rana da ya taɓa zuwa yaga sun kamo tashar kuma ita ce ke karanta labarai da safe. Da kanshi ya saka hannu ya tuge soket ɗin talabijin ɗin har ya yi ma Walidan tsawa da cewa su daina barin Tv a kunne in babu kowa a falon.
Ajiyar zuciya ta sauke duk da bata santa ba koma me ya faru ta na ƙarama ya faru.
Amman ta ga dacewar Yayansu da wannan yar gayu. Kuma Inna ta ce gidansu na can cikin Gra, inna ta gaya mata ta yi zaman yi ma kakar mai kyau da iya turancin aiki wacce ake kira da Mimi mimin karamchi.
Shiko iskar bangaren Inna Meri ne ya fara yi masa kaɗan saboda yadda yake jin zuciyar na zafi, ko tunanin tsayawa bai yi ba ya hau mashi dinsa ya bar anguwan.
Yana tafe iska na kaɗashi amman kuma acikin zuciyarsa babu wannan iskar sai wani irin tukikin zafi da yake ji.
Kishi ya ke ji a kasan ranshi, me ya sa ta yi kunshi ta bayyana adon ta a duniya?
Maza nawa suka kalleta? Sannan maza nawa suka yaba da wannan kunshin da ta yi? Yana tafe sai faman sakin huci ta baki ya ke yi, yana tuna shi fa a kwanaki nan yana kai idanuwansa in dai bai kamata ya kai ba.
Sai kwana ya ke yi acikin kuncin zuciya, haka yaje ya ga hotunta a shafin su na Karamchi Tv a Faceebook hotonta na barka da sallah wanda ta yi a madina.
Ta saka bakar Abaya ta yane kanta da mayafi amman gabadaya hakoranta suna waje ne ta yi dariya. Karin bakincikinsa ma yadda ya shiga comments section ya ga ana yabawa da kyan da ta kara ita kuma har ta na ba da amsa tana dariya. Ranar bai iya barci ba saboda bakinciki da Kishi.
Yanzu ma ya ƙara wani mugun gani, saboda haushin da yake ji yasa ya koma gida kuma sun yi waya da Makama ne za su haɗu. Saura kwana biyu bikin sa Mu’azzam sai gobe zai shigo garin.
Yana saman mashin ya ji kiran wayarsa sai da ya isa gida ya duba ya ga makama ne.
Sai ya kirasa daga baya, ce masa ya yi yana anguwan yana jiransa shi kuma ya ce ya koma gida. Makama bai yi fushi ba ya ce zai zo ya same sa su yi mgana.
Page 8
Sai da Makama ya zo ƙofar gidan sannan ya kira Aji ya ce masa gashi ya iso yana wajen get yana jiransa. Ba jimawa ko sai ga shi ya fito har ya sauya kaya zuwa wata jallabiya mai ruwan ƙasa. Hannu ya bashi suka yi musabaha da mirmishi kaɗan a saman fuskar Mansoor ya ce”Makama ango.”
Makama ya fashe da dariyan farincikin da yawanci angawaye a satin bikin su suke kasancewa kafin Ya ce” Aji namu, a waje zamu tsaya ba za a bani izinin shiga cikin gidan ba ne?
Mansoor bai yi masa magana ya wuce gaba Makama ya biyo bayansa duk da ya taɓa zuwa tun ana aikin gidan ba a gama ba.
Ya zagaye haraban gidan sannan ya ci burki a falon gidan yana faɗin.
“Aji gaskiya ka tsara gida komai ya ji ban da abu ɗaya wlh.”
Yasan abin da zai ce shi ya sa ya yi masa banza ya isa ga ƙaramin firizan dake falon ya ɗauko masa ruwan gora guda ɗaya
Sai ya haɗo masa da ƙaramin ƙofin dake saman firizan.
Ya kawo masa har gabansa ya ijiye yana faɗin”Ka sha ruwa Makama.”
Makama da ya yi rashe rashe a zaune ya ce”Zan sha ruwa, Aji ya kamata ace akwai mace a gidan nan gaskiya zai fi kyau.”
Ya kallesa a ɗage bai yi mgana ba sai ma ya kauda kai, shi kuma makama ya sha ruwa ya sauke kofin yana faɗin” Daman alfarma na zo nema a wajen ka.”
Sai ya juyo ya na kallonsa bai yi mgana ba Makama ya gyara zama yana fadin”Ba ku yi mgana da Mu’azzam ko Nasir ba?
Sai ya girgiza kansa kafin ya ce”Ina Studio a gida na bar wayata ban sani ba ko sun kirani.”. Ya faɗaa kai tsaye yana wani tsuke fuska shi fa baya son takura Allah yasa ba wani abu za su ce zai yi a bikin nan ba.
Allah ma ya sani shi har addu’a ya riƙa yi Allah yasa ranar ma suna da wasa a wani garin ya bar garin sai bayan bikin sai ya dawo.
Sai dai addu’arsa ba ta karɓu ba sai ma watan gobe su ke da wasa kuma Kano pillars ne za ta zo wasan cikin gida za a buga, yana wannan tunanin ya ji makama na faɗin ” Dama alfarman wajen kwana nake nema akwai abokai na ko na ce yan’uwa ne daga Zariya za su zo sh ine zan sauke su a gidanka sai sauran dai abokan mu na nan ai duk kasan su.”
Mansoor ya kallesa a karkace kafin ya ce”Ban san su ba.”
Daga haka ya cigaba da faɗin “Su nawa ne? Kasan ba na son takura kuma duk wanda zai zauna a gidana ina da dokoki.”
Makama ya ce” Ba za mu wuce mu goma ba.” Mansoor ya kallesa cikin mamaki kafin ya ce”Ba ni da katifa, kuma ɗakin da nake kwana ne kaɗai a gyare”
Makama ya ce”Bakomai ga falo tunda akwai cafet sai ayi amfani da barguna., Ni da kai da Nasir da Ahmad da Mu’azzam sai mu yi amfani da cikin ɗakin naka.”
“Wani ɗakin kenan?
Har Mansoor na sauri wajen tambaya Makama ya nuna masa ɗakin da hannu kafin ya ce”Nan ciki mana ai muma gobe duk nan zamu kwana Aji.”
Mansoor ya yi shuru bai yi mgana ba yana jin Makama na sanar da shi Ahmad ma gobe zai shigo garin cikin zolaya ya ce”Gobe akwai kwanan hira za mu tuna baya ne Aji.”
Kallon Makama kawai yake yi ya ma kasa magana sai dakyar ya buɗe baki yace” Ni da Mu’azzam kaɗai zan kwana, ku sai dai ku kwana a falo.”
Ya faɗa kai tsaye kuma da gaske yake yi Makama ya kallesa kafin ya ce”Ba ka isa ba, kai ko da yaushe sai ka nuna son kai wato Mu’azzam ƙanin ka ko? Ba ka isa ba Allah tare duk zamu kwana sai dai ka koremu in mu baka son ganin mu.”.
Ya karishe faɗa a kufule, Mansoor ya yi masa banza bai tanka sa ba sai cewar da ya yi” Ahmad da Nasir suna da mata fa to miye haka na wani zuwa su kwana a gida na? Mu fa ba yara ba ne mun girma Makama mu rika abu na masu Aji mana.”
Makama ya fashe da dariya har ya na dafa kafaɗan Aji kafin ya ce”Aji Aji! Aji namu ba zaka taɓa sauyawa ba kai komai sai kace an yi abu na rashin Aji, Ahmad ai ya tafi da matarsa kaduna in da ya ke ɗinki Nasir kuma ya ce gamu za mu kwana waje ɗaya ba zai ware kansa ba”
Mansoor ya yi ƙaramin tsaki ya sauke hannun Makama daga kan kafaɗarsa yana faɗin ” Ka ji ba, to shi yaro ne?
Makama sai faman dariya ya ke yi, Mansoor kuma haushi duk ya kama shi, yaushe ne su Nasir za su girma su daina aikin yara ne?miye wani abun zuwa a cakuɗi a kwana waje ɗaya sai kace masu shiga itfikafi.
Haɗe rai ya yi ba halin ya ce kada su zo ya san su mayu ne domin su kure shi ma Nasir sai ya ce su zo, kuma ya na da tabbacin Mu’azzam ya kasa gaya masa ne ya sa ya ce makaman ya zo da kansa.
A rayuwarsa ta yanzu ya fi son ya zauna shi kaɗai ta fi yi masa daɗi in ka ganshi da mutane yan Club ɗinsu ne ko wani taro na buga wasa ko abin da ya danganci haka.
Ko a baya da yake da sakin jiki da son mutane bai yi aikin yaran da su Nasir ke yi yanzu ba.
Sama sama ya ji Makama na faɗin”To yanzu dai ka amince mu zo ni da baƙina ko?
Mansoor ya kallesa kafin ya ce”Ba na son mata a gidana, ko shaye shaye kai ko sigari na kama mutum na busamin sai na koresa, sannan 9pm nake rufe gidana in suna yawon dare ka faɗa musu su kiyaye sannan kwana nawa za su yi ne?
Makama ya buɗe baki cikin mamaki kafin ya ce”Waɗanan dokikin kamar na shiga Villa? Mansoor yace” Gidan Aji ya fi Villa martaba da matsayi.”
Makama ya jinjina kai kafin ya ce” Ba shakka kar ka damu iyakarsu kwana uku, kuma duk abin da ka zayyano ba sa mu’amala da ko ɗaya mu kuma ka san mu tun muna matasan mu in ma muna da wani halin banza za ka fi kowa sani.”
Kamar magana ce ya gaya masa, shi kuma bai damu ba sai ma kafaɗa da ya ɗaga masa ma’ana is better.
Makama bai ƙara wasu mintina ba, ya ma Aji sallama ya wuce gida saboda ya san ko ya zauna ba biye masa zai yi su tattauna ba tunda yasan hali, shi ko Mansoor Makama na tafiya ya ɗauko wayarsa ya kira Mu’azzam. Yana ɗauka ya fara masifa ta in da yake shiga ba ta nan ya ke fita ba.
Faɗi yake yi” kai ne ka ce su zo su kwana a gidana ko Mu’azzam? ka san me ka jawo ko? Mu’azzanm dai sai cewa ya ke yi”Ni fa ba ruwana ya yi min mgana ne na ce ya je ya same ka ya ji ta bakin ka.”
A Fusace Mansoor ya ce” Mu’azzam ka fara zama mara jin magana yanzu ko? Yaushe ka zama haka? To ka guji haɗuwarmu sai na saɓa maka.” Daga haka ya katse wayarsa ya bar Mu’azzam da dafe kansa dagacan bangaren.
Hibba na gefensa daman suna cin abinci ne kuma a wayar akwai kara taji faɗan da Mijinta ya sha. Cikin kwantar da murya tace”Ka taɓo Baban Inna yau.”
Mu’azzam ya yi shuru kafin ya ce” Na rasa me ya sa ya ke gudun mutane yanzu? Alhalin a baya ba haka Dan’uwana yake ba.” Ya fad’a kamar zai yi kuka, Kansa take shafawa kafin ta ce”Ka yi hakuri mu cigaba da gayama Allah In sha Allahu komai zai wuce” Huci kawai ya saki ta baki wani abu na sukan ranshi.
Hibba ita ta yi ta lallaahinsa har ya samu ya saki ranshi. Shifa Nasir ne ya matsa masa amman yasan haka za ta faru bayan shi Mansoor ba ya son raɓar kowa ciki harda abokan da suka taso tare tun suna yara.
A bangaren Mansoor kuwa kwana ya yi ya na sakawa yana warwara, kamar ya gudu ya je Camp ɗin su ya kwana sai dai kuma ba ma evining training gare su gobe ba Morning ne haka kurum y ji baya son wannan haɗuwar, haɗuwar tana nufin tuna wasu abubuwan da suka shuɗe a baya. Da ace kafin ya sauya rayuwarsa ne ya san zai fi kowa murnan ganin sa a waje ɗaya tare da makama , da Ahmad da Nasir, saboda abokansa ne tun lokacin da Inna Meri aure ya kawo ta Gombe a kuma anguwan Arawa su ya fara sani bayan Mu’azzam. Har gari ya waye bai samu mafita ba hakanan ya shirya ya tafi Studio din su yana shiga wajen daman shi kaɗai ke jira sai ji kawai kake yi ” Barka da safiya Captain” shi kuma yana ɗaga musu hannu dukkansu suna sanye da yellow din riga da ƙannanun wanduna takalman kafarsu ma mai ruwan kwai ne, suna shirye waje ɗaya a layi dukkansu kowa ya harɗe hannayensa a bayan hannunsa sun kame waje ɗaya.
Wajen Cauch ɗin su ya nufa shima yana Shirye da irin kayansu hannun ya bashi suka yi musabaha. Cikin yanayin maganarsa ya ce”Barka da safiya Coach.”
Shima ya amsa masa da cewa” Barka da safiya Captain.”
Nan da nan aka hura usir members suka fara gudanar da training ɗin su.
A gida ya bar wayarsa saboda ya san za a yi ta kiransa a waya sai wajen sha biyu ya koma gida ya yi wanka ya ɗan kwanta kafin azahar sai a lokacin ya duba wayarsa ya ga an kira shi da yawa harda Mu’azzam sai Nasir. Kiran Mu’azzam ya bi, bayan ya dauka sun gaisa yace gashi ya iso yanzu ba da jimawa ba. Shi kuma sai ya ce yana gida zai huta sai zuwa bayan la’asar zai shigo anguwan, ko kiran Nasir bai bi takai ba ya share shi saboda tun a zamanin baya sun fi yawan samun saɓani da Nasir.
Nasir akwai daɓa mgana ko kaji haushi ko ta yi maka daɗi shi kuma Mansoor saurin hasala da zuciya da masifa ko magana za ka iya yi ya ce da shi kake shi ya sa suke saurin samun matsala da Nasir ko a baya.
Bai yarda barci ya daukesa ba sai da ya je ya yi sallar azahar sannan ya dawo ya kwanta kuma ya samu barci sai uku da rabi ya tashi.
Ya ji kuma zuciyarsa ta rage nauyi tunda daman ya daɗe ba ya samun barcin dare sosai.
Wanka ya sake yi ya shirya cikin wata Riga ta kwallo ce an saka MESSI a jikin rigar saboda shi Mansoor allon ƙwaikwayonsa a kwallo tun a zamanin baya Messi ne har kuma yanzu da yake cikin kwallon dumu dumu bai sauya gwani ba, sai ya saka bakin wando mai kamawa ta kasa kaɗan ya yi zanzanro sannan ya saka wani bakin takalmi mai rufi ya kuma gyara gashin kansa da ya tara sai ya ɗora P.Cap saboda ba ya so Inna ko Baba su gani su yi masa faɗan rashin aski.
Ranar har da fesa turare abon da ya jima bai yi ba. Key din mota ya ɗauka da ita yau ya ke fita tunda zai kai ta gareji a yi juyen baƙin mai ya jima bai kaita an duba ta ba. Shifa ba domin Mu’azzam ya matsa masa ba bashi da ra’ayin siyan mota mashin ɗinsa ta ishe sa, farko mashi ɗin da ya siya Baba Danjuma ya ba ma wa, ko wata ba ta yi ba aka tare shi aka karbe mashin ɗin Allah ya sa ba su yi masa rauni ba sun dai dake sa, sai yanzu ya ke tunanin zai ba shi wannan mashin din sai ya siya babba mai kama da mota.
Daga anguwarsa ta Tunfere gareji ya je da yake kanukawan sun waye shi yana zuwa suka fara kiran sunansa “Aji Aji.!
Shi kuma yana ba su hannu suna gaisawa anan ya ɓata lokaci har wajen biyar na yamma Nasir ya kara kiransa ya ki ɗauka sai ga Ahmad ya kirasa shi kam daman sun jima ma ba su yi mgana ba.
Shi ya sa ya ɗauka sun fara gaisawa kenan Nasir ya karɓe wayar yana faɗin “Aji ni kake yi ma wulakanci ko? Duk abin ka dai yau a katifarka zan kwana.”
Bai gama sauraransa ba ya katse wayarsa Nasir dai ba zai taba sauya hali ba.
Sai da aka gama duba motar ya ba su kuɗinsu sannan ya baro garejin zuwa gida, ya je ya iske Inna Meri ita kaɗai a bangarenta Walida ba ta nan ta tafi islamiya. Ya zauna suna gaisawa ta ce masa yanzu su Mu’azzam suka fita suna ta jiransa.
Shuru ya yi bai yi mgana ba, Inna Meri ta je ta kawo masa ruwa da abinci kamar ta san ya na jin yunwa.
Shinkafa da wake ne da manja ya na son dahuwar Inna wake ya dame da shinkafa.
Yadda ta ga yama cin abincin ne ya sa ta san ya daɗe bai ci abinci ba.
Cikin Tausayin shi ta ce” Baban Inna ka rika cin abinci don Allah, zama da yunwa babu amfani ka tattala lafiyarka tun kafin ta kubce maka.” Kai ya gyaɗa mata kafin ya ce'” To inna.”
Daga haka ya cigaba da cin abincin sa, tana lura da shi ana ta kiran wayarsa yana kashewa. Kuma tana jin Nasir kafin su fita dazu yana faɗin baya ɗaga kiransa, sannan Mu’azzam ya ce”Don Allah Inna ki roki Baban Inna kar ya ce zai ja baya a sha’anin nan na Makama kin san halinsa.”
Shiyasa yana gama cin abinci ya sha ruwa ta kalle sa kafin ta ce”Su Nasiru sun fita suna ta neman ka, ka kira su kaji in da suke Baban Inna.”
Ba musu ya ce To Inna ya ɗauko wayarsa ya Kira Mu’azzam sai yace suna kofar gidan su Ahmad. Sai ya ce yana gida su kariso, Bayan sun gama wayar Inna Meri ta kalle shi tana fadin” ka saki jikin ka bikin abokin ka ake yi ba na wani ba, Don Allah ka zama aboki nagari ban san kana zille zille nan.”
Sai da kalaman Inna su ka bashi dariya sai ya girgiza kai kafin ya ce”Mu’azzam ne ya kawo miki ƙara ta ko Inna?
Inna ta ce” ba ruwa Ɗan Inna ni na haife ka ai na san halin ka.”
Mirmishi kawai ya yi bai yi mgana ba Inna Meri ta zauna ta na ta masa nasihanta na kullum ya yi hakuri ya manta baya ya dawo da rayuwarsa kamar ta baya.
Jin ta kawai ya ke yi, shi fa bai ga wani Sauyawar da ya yi ba, ya na dai guje ma wasu abubuwan ne saboda gudun tuno da abjn da ya wuce a baya.
Kiran wayar Mu’azzam ya ƙwace sa ya mike ya ce bari yaje waje suna jiransa.
Yana fita ya gansu gabaɗaya Makama ne kawai babu Ango kenan, yana fitowa Nasir ya ɗauki dutse ya jefe dashi ya caɓe dutsen Ahmad na dariya ya ce”Ka ga Ajin ƙwallon kafa akwai iya kama saiti.”
Mu’azzam na jikin Motar Mansoor ɗin shi da Ahmad suna dariya.
Nasir faɗi ya ke yi” yau fa sai mun raba hali ni da kai Aji.”
Aji ya kallesa kafin ya ce”Nasir ka yi aure ba ka girma ba? Sai yaushe?
Ahmad yace” Sai matarsa ta haihu, daman tsohon ciki gareta.”
Mansoor ya yi mirmishin saman fatar baki bai yi mgana ba, ya isa wajen Ahmad ya bashi hannu suka yi musababa Ahmad ya jinjina hannunsa yana faɗin” Aji an daɗe ba’a haɗu an gaisa ba.”
Aji ya ce”Wallahi ya rayuwa.?
Ya amsa ma sa da Alhamdulillah.
Mu’azzam ya mika masa hannu suka gaisa ya tambaye shi ya hanya? Ina su Junior ya ce duk suna gaishe su.
Nasir ne ya warce hulan kan Mansoor ya ɗora bisa kansa Mansoor ya bisa da kallo kafin ya bata rai lokaci ɗaya yana faɗin. “Nasir ka rika yin abu cikin Aji don Allah mana.”
Gabaɗayansu suka fashe da dariya, Ahmad da Nasir suka haɗa baki wajen faɗiin ” Da girman Kujeran Aji Allah ya kara lafiya.”
Mu’azzam nata dariya, shima Ajin sai da ya Murmusa kafin ya mika hannu ya warce hulansa daga kan Nasir yana faɗin”Kai yaro ne har yanzu Nasir na kara samun tabbacin tsawon kafan ka ne, ya ruɗeka ka yi saurin aure.” Nan ma suka kara kecewa da dariya Mu’azzan na ta mirmishin jin daɗi ganin ɗan uwansa na hira har da mirmishi.
Makama ya tambaya Mu’azzam ya ce ya karbi motarsa ya je ya dawo, suna faɗa masa wai akwai kamu a gidan su Amarya kuma ana bukatar ganin Ango da abokansa. Aji ya kallesu a kaikace kafin ya ce”kamar wasu mata sai ku je kuma?
Ahmad ya ce”Ni kaina na ce ba za mu je ba.”
Aji ya ce”Kana da girman ka Ahmad gwara ka kama kanka da harkan yara.”
Ya faɗaa ya na nuna Nasir, Nasir kuma ya ce shi in ba za su je ba zai raka makama, Mu’azzam ma ya ce shi yanzu Tudun wada zai je ya kai wani sako saboda jibi ya ke so ya koma saboda aikinsa. Nasir kuma ya kira Makama ya ce ya shirya zai raka shi su tafi kamun tare da sauran abokan shi.
Nan ya barsu ya wuce gida su kuma suna nan kofar gidan suna ta hira har aka kira mangariba. Abun mamaki Mansoor ya saki jiki suna ta hira da Ahmad.
Duk dai yawancin hiran ta ƙwallo ce daga nan suka aika cikin gida aka ba su butoci suka yi alwala suka wuce masallaci.
Daga nan Mansoor ya ɗuke su a mota zuwa Tudun wada gidan su Hibba ya kai mata sakon da ta ba da, daga nan dakyar ya roki Mansoor ya biya da su Bolari can gidan su mahaifiyar Mu’azzam kakarsa Innayi ta na nan da ranta da ta ga Mansoor sai da ta ce shiyasa ta ga an sha iskar rahama ashe shi ne zai zo.
Tunda ya daɗe rabon shi da zuwa a baya dai duk zuwa shi da kansa zai raka Mu’azzam gidan ya gaida kakaninsa.
A gidan suka ɗan jima shi ya sa ba su baro anguwan ba sai da suka yi sallar Isha’i.
Daga nan suka koma anguwan Arawa Ahmad ya ce zai ɗauki sako a gida suma sai suka shiga gida suka gaida Baba Danjuma.
Magajiya ba ta nan ta je kauyen su wani kawunta ya rasu. Tare da Mariya ta tafi duk yadda Baba Danjuman ya so ta kyaleta tunda akwai makaranta ta ce da ita za ta tafi. Mariyan ma ba ta so hakanan ta shirya suka tafi. Suna ɗakin Inna Meri tare da Baba Danjuma da Innar suna ta hira Walida ta zuba musu tuwon da Inna ta yi da yamman nan suka ci a kwano ɗaya tare da Baban su.
Ba su bar gidan ba sai goma lokacin da Ahmad ya kira su ya ce yana jiran su a waje, su daga nan suma wuce gidan Mansoor, a nan ne ma Mansoor ya ga kayan da Mu’azzam ya siya musu Shadda mai ruwan kasa su huɗu Ahmad ya dinka musu daman shi ya tura ma kuɗin ya siya musu shaddar. Daman shi ba’a iya masa sai da ya kalli Mu’azzam kafin ya ce” Sai kace wasu yara mu saka anko? Tunaninka ya koma na yara ne Mu’azzam”.
Shi dai dariya kawai ya yi Ahmad ke faɗin. “Haba a baya ai muna ɗinka kaya iri ɗaya Aji ka manta ne”
Kai tsaye ya ce”Yanzu mun girma mun zama magidanta kai da matarka da yarka, Mu’azzam da matarsa da ɗansa Nasir ma haka ga shi Makama zai yi aure ace duk ba ku fita sahun yara kun fara halin manya ba?
Ahmad na yar dariya ya ce”Kuma fa hakane to daga wannan shike nan da bikin ka kowa kalan na shi zai saka.”
Banza ya yi masa kamar bai ji ba suka haɗa ido da Mu’azzam suna dariya.
Su Nasir ne ba su dawo gidan da wuri ba megidan ya riƙa masifa yana faɗin”Ku kira su Nasir ku dawo kar na rufe gidana ya zageni, yana magidanci yana yawon dare”
Ahmad ya ce”Ba sun je kamun Amarya ba.”
Aji ya yi ƙaramin tsaki kafin ya ce” kamun amarya ko kamun shirme.”
Mu’azzam ya kira Nasir a waya ya ce ga su nan a hanya. Sai wajen sha biyu saura suka dawo Mansoor ya yi ta masifa yana cewa da sun kara mintina zai rufe gidansa ne.
Nasir na rungume da katuwar jakar kayansa ya shigo yana fadin”Mun ji to megida mun ji to.”
Ya faɗa yana ture Mansoor ya shige falon.
Makama tare da wasu maza su uku biyun bai san su ba amman yasan ɗayan abokin makama ne Nura suna ga gida ga gida ne.
Hannu suka bashi dukkansu suka yi masabaha, daman da motar Mu’azzam suka dawo sai da ya fita ya rufe get sannan ya dawo. Allah ya taimaka nepa suka kawo wuta sai fanka ta fara kaɗaawa.
Makama da abokinsa Nura da sauran ƴanwansa suka kwana a falo.
Nasir da Ahmad da Mu’azzam da mai gidan suka kwana a ɗakin Mansoor.
Dolensa ya bar katifa nan ya kwana a ƙasa saboda yana kwanciya Nasir yazo ya shige tsakiyar su shi da Mu’azzam yana faɗin
“Ni fa na saba da katifan matata ba zan iya kwanan ƙasa ba.”
Mansoor ya yi ta tsaki ya na faɗin” Nasir sam ba ka da Aji.”
Ya na dariya ya ce”Na ji Aji mai Aji ba.”
Karshe kasa ya kwana shi da Ahmad da Asuba shi ya ta da su suka yi alwala zuwa masallaci daurin auren na safe ne misalin sha ɗaya ne. Shi duk haushin su yake ji wannan abun fa sai ya yi kamceceniya da abin da mata suke yi.
Ko a baya da yake cikin su ba haka halinshi yake ba yana komai da class ne shi ya sa ma a nan ya fara samun ssalin sunansa na AJI
**
SATURDAY, 28 APRIL 2022
8:50PM.
A cikin anguwan Dubai Quaters Usman makama ya kama gidansa mai kyau anan aka saka Amarya.
Tun 7:30pm na yamma aka kawo Amarya gidanta saboda yanayin tsaro, daga nan Amarya da gayyarta za su wuce wajen dinner da abokan Ango suka haɗa. Acikin motocin da suka kwaso Amarya da tawagarta har da motar Aji amman ba shi ya ja motar ba Ahmad ne domin shi ya ce ba zai je ba, Nasir ya ce ya ara masa ya ce bazai ba shi ba sai da ya ba ma Ahmad aro.
Nasir ɗin yana da mota saida ita ya yi daga baya, ana ɗaura aure Aji ya zille musu ko hotunan da aka je gidan Amarya aka yi bai je ba gida ya koma ya kwanta ya juta abun sa.
Sun je dai Reception suka ci abinci daga nan ya hau mashin ya koma gida tunda daman key ɗin motarsa na wajen Ahmad. Dinner dai sun ce ko ya so ko bai so ba sai ya je, ga shi ya yi musu tsiya bai sanya kalan kayansu ba wani farin yadi ya saka mai shara shara. Wai shi ba yaro ba ne ko mace da zai saka anko.
Hakanan suka kyale shi, ya saka nashi dabam a wajen ɗaurin auran ma dakyar ya bari suka yi hoto cewa ya yi wai hoto na yara ne, komai sai ya ce ba aji aikin yara ne.
Sun je gidan su Amarya sun sha hotuna, Mu’azzam ya so ya ga yayar Amaryan da Nasir ya ba su labarin ta kankame komai a sha’anin bikin, sai Makama ya ce Bibi ta ce Anty Baby ta je karɓo ɗinki ita da kawarta Anty Mimi.
Kuma har suka gama hotuna su ka tafi ba su dawo ba, suna tafiya sai ga su sun dawo tella ne ya yi musu tsiya.
Mimi sai masifa ta ke yi tana cewa “Rukky ke kika ja mana da kin bari na kai ma tela na da tuni ya ɗin ka mana.”
Rukky ta ce”Ina na san haka Habu zai yi mana ,ai ya ci taliyan karshe.”
Ko makeup ba su samu yi ba mazan ma’aikansu daga karamchi Talabijin da suka zo musu ɗaurin aure ma ba su haɗu ba sai dai suka yi ma Rukky fatan alheri ta waya. Matan ne kaɗai suka samu tunda su sun jira su, saboda bakin ne yasa ba su samu zuwa kwalliya ba Rukky ta ce su bari anjuma su yi na dinner.
Tun Safe Mimi ta baro gida sai da za’a kai Amarya ta ɗauki Rukky a motar ta suka koma gida ta ɗauki jaka da takalmin da za ta yi amfani dashi tare da ɗan kunne da sarka suka tafi wajen kwalliya daga can za su wuce dinner.
Hajiya ta ga yadda Mimi ta yi kyau cikin Atamfar yinin biki saboda ajikin Atamfar akwai ja, a cikin ranta addu’a take yi mata Allah ya haɗata da wanda zai sauya mata rayuwa a daren nan.
Baaba Uwani kuwa har hqraban gidan ta raka su tana faɗin” Binta Allah ya tsare ya sa a dawo lafiya, Rukkaya Allah yasa a watse taro lafiya.” Suka amsa mata da Amin, sun je shagon kwalliyan daman sun yi booking, Rukky aka fa ra yi mawa.Wacce za ta yi ma Amarya gida suka tura ta. Sai kira Bibi take yi ta na faɗin an gama mata kwalliya ta shirya suna jiran angwaye ne yanzu za su tafi can in da za’ayi Dinner ɗin.
Da za su jira sune, Mimi ta ga yanzu ma aka fara mata nata kwalliyar sai ta ce kawai su tafi in sun gama sai su zo daga baya.
Haka aka yi Amarya Bibi da tawagan ƙawayenta da ƴan’uwa suka yi gaba su Nasir suka zo da motoci suka kwashe su.
Sai wani Hall haɗaɗɗe mai kyau wanda, ya ke tashe a garin Gombe wajen yin bukukuwa. Ko da suka je an gama tsara komai daman kuma sai da Ango ya jira zuwan Amarya sannan tare da ƙawaye da abokan ango suka shiga wajen.
Wajejen goma na dare aka fara gudanar da Dinner ɗin Amarya ta yi shigan Blue ne shima Angon kalar shaddar jikinsa kenan.
Ƙawaye kuma Less ɗin su mai ruwan ash ne da zanen pick, sun yi ɗinkin fitted gown gabadaya sai suka yi amfani da head pick.
Makama ya tambayi Bibi da cewa shi fa yau kwata kwata bai ga Anty Rukky ba
Bibi na danna wayarta ta ce”Suna wajen kwalliya ita da Anty Mimi su nake kira ma yanzu.”
Makama ya ya fito Ahamd da hannu yana faɗin ” Nima wani abokin mu muke jira, bai zo har yanzu.”
Bibi ta kalle shi kafin ta ce” Wai wannan ɗan ƙwallon da kake ba ni labarinsa,?
Sai ya gyaɗa mata kai dai dai karisowan Ahmad yana faɗin” Ango ya aka yi ne?
Makama ya duba agogon fatan hannun shi yana fadin” Aji ba zai zo ba ko?
Ahmad ya ce” Mu’azzam ya je ya ɗauko sa, na kirasa ya ce suna hanya.”
Makama ya sauke Nunfashi kafin ya ce” Allah ya ɗorani akan sa kenan ya ga dama zai zo.” Ahmad na dariya ya ce”Gaskiya ka ci babbar sa’a.”
Ita Bibi rabin hankalinta na kan wayanta sai ji suka yi tana faɗin”Anty Mimi ku yi sauri an fara fa tun ɗazu”
Sai da ta gama wayar ne angonta ya ga duk ta bata rai sai ya ramkwafa ya na lallashinta.
Aji da Mu’azzam sun shigo hall ɗin Sha ɗaya dai dai na dare.
Aji na sanye da wata ɗanyan shadda mai Ruwan ƙasa shi ya na son abu mai ruwan ƙasa da bakin abu da kuma fari.
Hulan kansa dara ce baka, gefe da gefe gashinsa kansa da ya tara ya samu wajen zama a gefe da gefen hulan kansa, kafarsa kuma baƙin takalmi mai rufi na gata mai kyau agogon hannunsa ma baƙi ne na fata.
Suna shigowa Nasir ya je ya yi ma Mc raɗa sai hall ya kaure da muryan Mc da ya ratsa ya shiga kunnuwan mutane da faɗin.
“Kai jama’a ashe dai yau kila sai na tafi gida da kujeran hajji, bikin na masu ƙasa ne yanzu na ke samun ,labarin Aji jiharmu Captain ɗin kwallon kafa na kungiyar Gombe United matashi nan mai tashe MANSOOR AJI aminin Ango ne kuma ya shigo wannan Katafaren ɗakin taro domin taya wannan Ango mai kunya da Amaryarsa mai kyau murnan zamowa ma’aurata kai jama’a don Allah a yi tafi masu garin ne suka shigo.” Sai tafi taf raf! Sannan kallo tuni ya koma wajen Aji da Mu’azzaam shi yasan suna shirya wani abu tunda suka matsa masa sai ya zo, Mu’azzam ya rakasa har wajen zaman su shi da Ahmad da Nasir dai dai Mc na kara faɗin” kai jama’a yau dai gani ga Aji matashin da kaf garin gombe ba wanda ya kaisa iya taka leda ni a nuna min Aji in kai gaisuwa nima ina cikin masoyansa”
Nasir ya nuna Aji Mc ya zo ya duka ya kwashi gaisuwa yana faɗin ” Gari naku ƙasa ma naku sannu da zuwa ɗan ɓaiwa kuma wallah ya ci sunan shi akwai Aji ga shi nan ya bayyana kansa.”
Hall ya ɗauki Ihu, yan mata sai waige suke suna kallon shi ,Aji ya yi tsam ko dariya bai yi ba ya na kallon Nasir ga shi duk kallo ya koma kanshi. Bibi na hightable ita da Angonta ta kalle shi tana faɗin” Wanne ne abokin naka ɗan kwallon?
Sai ya gyaɗa mata kai lokaci ɗaya yana Faɗin”Mansoor Aji ba.”
Sai ta jinjina kai kafin tace”Ya ci sunan shi Aji domin tunda ya shigo wajen bai yi dariya ba.” Dariya ya yi mata kafin ya ce”Haka yake shi” Mc dai ya nace sai zuba kirari yake yi karshe dai mu’azzam aka bari da yi ma Mc likin yan dubi faɗi yake yi” Allahu Akbar an ce ƙanin Aji ne da wannan ban girman, ni fa yau na zo bikin masu jihar da kansu.”
Aji duk ya ji ya takura saboda ƙaran Speeker sun kusa kashe masa dodon kunne, sai kawai ya karɓi ɗin key motar Mu’azzam lokacin ana kokarin fara ciye ciye, ya mike yana faɗin “Zan je gida, hayaniya ya yi yawa a nan.”
Kafin ma su samu zarafin mgana ya kama hanyar fita daga hall ɗin.
Daidai Rukky sun sawo kai ciki ita ce a gaba ta sha kwalliya ta juya baya ta na yi ma Mimi mgana ba ta ga Aji ba. Shi kuma daman yana da tafiya Sassarfa da gaf gaf sai ya yi ƙokarin kauce mata bai san da wata a bayanta ba yana kauce mata sai ya saka kanshi da niyar fita daga wajen sa ji ya yi wani abu kamar mai nauyi ya daki Kirjinsa.
Ƙamshin turarenta mai sanyaya zuciya ya fara yi ma hancinsa maraba
Tsayawa ya yi cak ya na tunanin abin da Ya tokare shi haka, ita ma Rukky sai ta juyo jin shuru sai ta hangi bayan wani dogon mutum baƙi da sauri ta dawo daga baya ta na faɗin”Mimi are u ok?
Ta faɗa ta na kallon Mimi dake faman sosa goshinta.
Ashe kanta ne ya bugi kirjinsa, tana faman gyara hannun doguwar rigarta tunda mai wani zalo zalon igiya ya yi musu ɗayan kuma jakarta ne da wayarta.
Ta ɗago ta na kallon Rukky kafin ta ce”Am fine Rukky Allah yasa ban faɗi ba.”
Rukky ta kalli Aji sai ta ga ya ƙurama Mimi ido idanuwansa sun kankance yana sakin huci kamar zai kai mata duka sai ta yi saurin riko hannun Mimi tana faɗin”Ka yi hakuri ba ta ganka ba ne”
Ko kallon Rukky bai yi ba sai kawai ya kauda kansa ya raɓa ta gefen Mimi zai wuce. Yanayin bugun zuciyarta ta ji ya sauya lokaci ɗaya da ya sa ta kalli mutumin da suka ci karo ya riga ya gifta ta.
Amman ai ta ga gefen fuskarsa sannan ta juya da sauri ta ga bayanshi da yanayin tsawon shi. Tabbas soyayya ba karya ba ce, yau Aji ta gani wlh shi ne ta gani.
Aji ne ajinta ne MANSOOR AJIN Mimi.
Ba ta san lokacin da ta kwace hannunta a na Rukky ba, yana shirin fita daga ɗakin taro ta yi amfani da muryanta mai zaƙi ta kira sunan shi.
“Aji…!
Bai Tsaya ba da karfi ta buɗe murya ta kara kiran sunan shi da sunan da take kiran shi a baya.
“Aji Nah…!!.
“Ajin Mimi..!”
Cak ya tsaya saboda ji ya yi kafafunsa sun kasa cigaba da tafiya duk ko kokarinsa na ya bar wajen kada ta fahimci shine, alokacin hankalinsu Mu’azzan ya kai wajen Bibi ta ga yayarta acan kofar shigowa tana tsaye ga Mimi a tsaye ga abokin su Usman, ko kafin kace me ta baro wajen zamanta ta sauko tana faɗin “Anty Baby me ya faru?
Suma sun Mu’azzam sun taso sun rufa mata baya Ango ma ya Biyo amaryansa Mc na ganin haka ya tsaida sauti shima yana raba ido sauran ƙawayen Amarya da abokan Ango suka bi bayan ayarin masu kallo suma da tamtaman abin da ya faru.
Muryanta da ya ji sai ya ƙara samun tabbacin ita ce, kawai sai ya yunkura da doguwar kafarsa ya taka zai bar cikin hall din, Mimi na ganin haka ta tattare rigarta bayan ta wancakalar da takalmin kafarta mai tsini da jakar hannunta tare da wayarta ta rufa masa baya. Baki buɗe aka bi ta da kallo Rukky ta kwashi gudu ta bi ta tana kiran sunanta ƴan Dinner na ganin haka suka rufa musu baya.
Sunan da Rukky ke kirana ne ya sa Mu’azzam da Nasir suka kalli juna.
“Mimi..”
Ahmad shima ya maimaita sunan
“Mimi.”
Makama ya riko Amaryansa dake shirin bin bayan Yayarta yana faɗin”Mimin mai aikin gidan tibi?
Bibi tace”E, itace ƙawar Anty Baby ce.”
Ai sai makama ya ji ya fara zufa Bibi tabi bayan Yayarta shi kuma ya yi saurin bin bayan su Nasir yana faɗin” Yau fa an haɗe Mimi ce da gaske MIMIN AJI ce.”
A tare suka rumtuma zuwa waje domin ganin abinda ke faruwa, suna fita suka hangi Aji tsaye a haraban wajen Mimi ta sha gabansa sun ƙura ma juna ido.
Akwai hasken farin gulop tar ga shi nan ana ganin komai kamar a magiji.
Shi ya juya baya ba’a ganin fuskar shi ita da ke facing ɗin shi ake iya gani.
Hawaye suna sintiri a saman kyakyawan fuskarta da ta sha kwalliya.
Nasir da Mu’azzam suka kalli juna Ahmad da Makama ma suka kalli juna.
A tare suka furta” inna lillahi wa’inna Ilaihirraju’un..”
Page 9
Gani Mimi take yi kamar a mafarki yau ita ce a gaban Aji tana kallon shi yana kallonta, Yau ita ce ga ta ga shi wanda tazaran dake tsakaninsu bai wuce taku biyu ba, sannan yau ita ce ta ke fitar da numfasshi tare da jin ɗumin numfashin Mansoor a cikin nata numfashin. Farinciki ne ya saka ta kuka yau kimanin shekaru goma rabon da ta saka shi a idanuwanta irin haka. Sai dai ta hangoshi a hoto daman ya ce ta yi nisa da ganinsa shima zai yi nesa da jin ta da ganinta na har abada. Daɗi ne ya cika mata zuciya da ya sa har ta kasa iya rike kanta sai kuka hawaye suna ta faman sintiti saman kyakyawan fuskarta da ta sha kwalliya mai kayatarwa.
Shi kuma so yake yi ya hana idanuwansa kallonta amman sun ƙi bashi haɗin kai kamar an manne masa idanuwansa daga kallon Mimi, ga shi kuma kishi ne da wani irin bakinciki ke yunkuro maasa, in da ya binne tasirin soyayyarta ke kokarin taso masa ya hana tasirin haka bayyana, acikin kirjinsa ya ke jin wani irin zafi zafi iskar wajen ta fara masa kaɗan domin ya ji hucin zafin na fita daga cikin wuyansa zuwa cikin bakinsa, jiyoyin kansa sun mike raɗau kirjinsa na sama da kasa alamun bacin ransa da yanayin da ya ke ciki ya kai makuran kololiya. Bakinsa ya yi wani irin nauyin da ya kasa mgana duk a kokarinsa ya cira kafarsa da sauri ya bar wajen tun kafin Siirin da ke cikin zuciyarsa a kulle a wani bangaren ya fallasa kansa.
Yana ƙokarin dauke kafarsa daga gabanta ya raɓa ta gefenta ya wuce ya ji maganarta cikin zaƙin muryanta da tun asali wannan muryan ce ke kwantar masa da hankali. Sannan ganin mai murya na saka shi cikin farincikin da bai san iyaka ba, amman sanadin abin da ya faru yanzu jin zaƙin muryan yake yi kamar saukar dalma acikin zuciyarsa sannan ganinta na sanya sa bakinciki yana guje ma ganinta ne kamar mutuwarsa.
“Aji Nah..”
Ta ƙara kiransa cikin rawan murya sai kawai ya yi kamar bai ji ya ba, ɗaga kafarsa da sauri zai wuceta ita kuma da azama ta riko gefen hannun rigansa domin ba za ta taɓa bari ya subuce ma ganinta ba, yadda ta rikesa ne ya sa ya tsaya ya na bin hannunta zara zara da yaji kunshi baki da ja da kallo rike da gefen hannun rigansa na hagu sannan ya sauke saman fuskarta kallon da ya yi mata ne ya sa dole ta sake shi wasu hawayen na kara yi mata ambaliya a saman fuskarta. Tana sakin shi ya fara takunsa cikin sassarfa da gifi gif ɗin sa kamar wani Sadauki a fagen yaƙi jii yake yi in bai bar shakan numfashi tare da wannan yarinyar ba za a iya samun matsala.
Kuma cikin su Mu’azzam an rasa mai karisowa kowa ya harɗe hannu a kirji yana kallon ikon Allah. Hatta Rukkaya dake gefe ta kasa karisawa, Tsabar mamaki da Al’ajabi ya hana ta magana ballantana ta karisa wajen tambayoyi biyu ne acikin ranta.
” A ina Mimi ta san wannan baƙin mutumin mai bakin rai haka?
“Me ya sa take kuka saboda ta gan shi?
Wata zuciyar daga can gefen ta gaya mata” ko dai ko dai shi ne?
Shi ne wannan ɗin?
Sai ta kara kallonsu ta na Nazarin wani abu dai dai lokacin da Mimi ta kara tattare riganta ta sha gaban Aji a karo na biyu, wannan karon da karfinta ta tare masa gabansa ta kuma saka hannayenta guda biyu ta tare hanyar tana faɗi da ƙarfi.
“Ba zaka bar nan wajen ba har sai ka yi min mgana, ni ce Mimin ka fa Mansoor?.
Ta faɗa kuka na son ƙwace mata, Mimin ka ce? Kalmar ta fi ɓata masa rai da ya sa a fusace ya kalleta cikin kakkausan murya ya ce”Ni na san ki ne? Kin sanni ne?
Ya faɗa yana nuna kansa. Jikin Mimi ya fara rawa, ta fara nuna kanta ta na rawan baki ta ce” Ni ce fa? ba ka gane ni ba ne?
Kai tsaye ya ce”Ba maganar ganewa ba ne, ban san ki ba, ban kuma taɓa ganinki ba kar ki kara ganina ko a hanya irin haka ki ce kin sanni in ba haka ba zan saka rayuwarki a uku, ni kin ga na yi miki kama da sakaran namijin da ya san shashashan mata irin ku? Iyayena talakawa ne har yanzu muna lallaɓa rayuwarmu ne a inda Allah ya ijyemu ba zamu faɗa inda ya fi karfin mu ba.”
Ya ƙarishe faɗa ya na nuna ta da babban yatsan dake hannunsa zuwa lokacin tuni su Rukkaya sun ɗumgume wajen dai dai lokacin da Mimi ta fashe da kuka tana faɗin”Ko ba domin soyayyarmu ba, na ci arzikin kaunar da ta haɗamu ka tsaya mu yi gaisuwan mutumci Aji.”
Kamar ta yarfa masa ruwan zafi haka ya saka jannu da karfi ya ture hannunta cikin tsautsayi ta yi gefe har sai da ta faɗi bai juyo ba cikin ɗaga murya ya ce” Har Abada babu sauran mutumcin da ya rage tsakanina da ke Fatima Kabir Sulaiman Dabo, har Abada kuwa saboda haka kar ma ki yaudari kanki.” Daga haka ya taka jelan riganta zai wuce ita kuma ta yunkura da niyar tashi kawai sai ji ka ke keeeeee!
Rigar jikinta ta yage ta wajen kugunta da aka saka raga raga a wajen saboda ya taka ita kuma taja sai ya yage ana ganin kaurin cikinta a waje.
Ya ji karan yagan abu sai ya ɗan juya kaɗan yaga kaurin cikinta a waje wani irin hayaki yaji kamar idanuwansa na fita na zafin kishi, yanzu maza nawa ne a wannan wajen? In suka kalle mata jiki fa?
Kawai sai yaji kamar ya mutu.
Ita kuma Mimi kuka ta fashe da shi cikin raunin murya take faɗin “Don Allah don Allah Mansoor.”
Rukkaya ce ta ƙariso wajenta da gudu ta riketa ranta ya baci cikin masifa ta ce”Mimi me ye haka? Ta ya ya za ki
zauna wani wanda bai isa ba yana wulakanta ki haka?.
Ya ji ta saboda har ya fara takawa zuwa wajen Motar Mu’azzam sai kuma ya fasa ya dawo da zafin namansa lokacin Rukkaya da wata kawar Bibi sun tada Mimi tsaye sai ya ga ana ganin jikinta, tuni idanuwansa suka rufe yana tafiya kamar ya ji ya tashi sama.
Tsabar kishi da ya rufe masa ido yasa bai san lokacin da ya daka mata wani irin tsawa ba.
“Ki tsaya anan kar kuskura ki ƙara taku ko ɗaya FATIMA..”
Ya kirata da sunanta da ba kowa ke kiranta da shi ba. Jikinta na rawa ta juya ta lna kallonsa kowa kuma sai ya koma yana kallonsa baki sake hatta ko su Mu’azzam Nasir har sai da ya Murmusa shi fa daman yasan har gobe Aji bai daina son Mimi ba, kuma a kishinta kamar mahaukaci haka ya ke jin kansa. Wajensu ya nuna yana zuwa ya cilla ma Mu’azzam key ɗin motarsa ya caɓe da sauri, shi kuma sai ya mika ma Ahmad hannunsa da sauri ya ɗora masa key ɗin motarsa ya juya kamar wani namijin zaki ya wuce wajen motarsa shi duk saurinsa kar Mimi ta juya baya wajen maza su ga jikinta in hakan ta faru ai sai ya kusa mutuwa saboda bakinciki.
Rukkaya kuma haushi wannan mulkin mallakan ya kamata a fusace ta ce”Dilla mu tafi yanzu ya gama wulakantaki sai kuma ya dawo ya na ba ki umarni? waye shi ɗin?
Mimi na hawaye ga kuka cikin sauri ta ce”Umarninsa kamar dole ne a gare ni na bi Rukkayya”
Rukky ta saki baki galala tana kallon Mimi dai lokacin da Aji ya dawo da wata bakar Jaket baka tana da tsawo nashi ne ta jima acikin motarsa ashe zata yi masa amfani.
A gif gif ɗin sa ya dawo gabansu ya saita rigan ya saka a jikin Mimi bai samu salama ba sai da ya ga jaket ɗin ta sauko har ta rufe in da ya yagen sannan ya sakar mata rigan.
Bai kalleta ba duk kuwa nacin kallon da take yi masa , ga hawaye a saman fuskanta lokaci ɗaya da wani irin mirmishin da ta jima ba ta yi kamar sa ba.
Kamar walkiya ya bar wajen har ya shiga motarsa Rukkaya ta saka hannu za ta warce rigan jikin Mimi tana fadin”Ba za ki saka ba, ya damu da ke ya ture ki, ki ka faɗi a gaban jama’u? Gam ko Mimi ta rike rigan idanuwanta da hankalinta na kan Aji da ya shiga cikin mota. Duk da motar baƙin gilasai ne jikinta na ba ta ita yake kallo, kamkame rigar tayi cikin Mirmishin dake tafe da hawaye Ta ce”Ki bar min Rukky a kallah bayan tsawon shekaru na kara samun tabbacin matsayina bai sauya ba, yana sona har gobe tunda bai daina kishin wasu mazan su ga jikina a buɗe ba”
Rukky ta bi ta da kallo kamar mai taɓin
hankali sakinta ta yi ta so ne ta isa wajen motarsa ta zage shi sai dai kafin ta karisa ya fige motar da gudu ya fice daga haraban wajen Rukky ta ɗaga murya tana fadi’n”Ɗan wulakanci kawai, za ka haɗu da dai dai da kai a gaba kana baƙin mutum sai faɗin rai da nuna isa aikin banza kawai.”.
Ranta ya baci ganin gabaɗaya ya ɓata musu biki ta na juyawa ta nufi wajen su Usman da kamar an da sa su. Bibi kuma da sauran ƙawayenta sun rufe Mimi suna yi mata sannu.
Cikin masifa Rukky ta ce” Usman wannan wani ɗan wulaƙanci ne? A gaban ku ya ci zarafin ƙawata waye shi?
Kai tsaye Nasir ya ce”Aji.. MANSOOR IBRAHIM AJI. Gombe State United Captain”
A fusace ta wurga ma Nasir harara kafin ta ce”Aikin banza shi ne me? don yana ɗan ƙwallo sai ya yi mata wannan tozarcin wallahi ya ci sa’a ya bar wajen nan da sai ya raina kansa wlh.”
Nasir ya ba ta amsa kai tsaye da cewa” Sai dai ki raina kanki, ke ba ki ga abin da ya yi ma ita ƙawar taki ba ne,?
Rukky za ta kara mgana Usman ya tare ta da faɗin”Ki yi hakuri Anty Baby ko an yi miki bayani ba za ki gane ba. Aji abokina ne tare mu ka tashi dukkanmu nan tare muke wannan kuma da kike gani ƙaninsa ne Mu’azzam” Ya faɗa ya na nuna mata Mu’azzam wanda ya yi shuru kamar ruwa ya cisa. Cikin ƙufuluwa Rukky ta kallesa kafin ta ce” Miye haɗin ɗan’uwanka da ƙawata da zai mata wannan wulakanci.?
Sai ya kasa ba ta amsa Nasir ne ya ce” Alaƙace mai karfi a tsakaninsu ke ba ki gane haka ba? To tsohuwar budurwansa ne bayan wasu shekaru yau suka haɗu shike nan kike son ji?
Ya faɗa ya na mai kureta da ido, ta kasa mgana saboda mamaki dai dai lokacin da Mimi ta kariso wajen jikinta kamkame da rigar da Aji ya ba ta kamar wani zai ƙwace mata. Tana zuwa wajen ta saki baki tana kallonsu cikin mamaki ta ce”Su waye na ke gani haka? Ai baza taɓa mantawa da su ba sai ta tuna islamiyan Mallam Dahiru cikin buɗe baki tare da murnan ganinsu ta fara nuna su ɗaya bayan ɗaya.
“Makama..”
Ya amsa mata da” Na’am Mimi”
Sai ta nuna Ahmad tana fadin”Ahmad..”
Shima ya amsa mata da cewa”Na’am Mimi shekarun da yawa”
Sai ta koma ta nuna na kusa da shi “Nasir”
Nasir na dariya ya ce”Na san ai ko ba ki gane Nasir don komai ba kya iya gane ni da kullum sai Aji ya yi faɗa da ni akan ki.
Hajiya Mimi ai ni mun taɓa haduwa shekarun baya.”
“Kin gane wannan?.
Ya faɗa ya na dafa kafaɗan Mu’azzam sai ta kura masa ido kafin ta ce”Laa wai Mu’azzam ne? Ɗan Inna ne ya koma haka?
Ɗan Innan da ta faɗa ya sa suka fashe da dariya shima Mirmishi ya yi kafin ya ce”Anty Mami ashe baki manta da ni ba.”
Saboda tun a baya baya kiranta da Mimi Sai dai ya ce mata Anty Mami. Farinciiki ya kara cika kirjin Mimi cikin fara’a da tuni ta manta da kukan da take yi ta ce” Mu’azzam ina Inna? fatan tana nan cikin koshin lafiya”
Kai tsaye ya ce”Inna na nan lafiya kalau, ina su Hajiya?sai ga shi mun sake haɗuwa bayan wasu shekaru a bikin Makama”
Sai ta nuna Makama kafin ta yi mgana ya yi saurin cewa”Usman ba wanda ya auri ƙanwar Anty Baby.”
Mamaki ya hana Mimi mgana sai faman mirmushi take yi, Rukky ta gaji da ganin abun mamaki ta kalli Mimi tana faɗin ” Duk a ina kikka san su ne wai?
Mimi ta ce”Na san su shekaru da daɗewa Rukky.”Sai ta saki baki tana kallonta ba ta kara mgana ba Dinner ai ta gama rushewa wasu har sun fara tafiya gida tun dare ya yi sha biyu ta wuce. Ita kuma Mimi su Nasir kawai take kallo ta na mamakin yadda duk su ka zama magidanta, tambayansu bayan rabuwa ta fara yi Nasir ke gaya mata dukkansu sun yi aure har Mu’azzam.
ta rike baki tana faɗin”Muzamman ikon Allah” Sai ta bashi kunya Nasir na dariya yace”Ajin ki ne kawai ya rage gauro har mun gaji da biyan yara suna masa kiɗan gauran ci.” Mirmishi kawai ta yi, amman ta kasa mgana sai ta saki mganar ta kama wata in da take gaya ma Nasir a baya da suka haɗu ta karɓi lambarsa ta yar da wayarta ne shi ya sa ta rasa lambarsa.
Shi kuma Usman na wajen Amaryasa tana kunkuni a zo a kai su gida ita kuma Rukky ta koma gefe tana mgana a waya, Dole dai su Nasir ɗin ne za su maida mutane gida ga shi motoci uku ne a hannunsu tunda Aji ya tafi da ta wajen nashi
Mimi ta samu keɓewa da Mu’azzam da Sauri ta ce”Mu’azzam ka bani lambar wayar yayanka mana.”.
Mu’azzam ya yi shuru ya na kallonta ya kasa mgana ita kuma sai ta yi mirmishin karfin hali kafin ta ce”Ba ka son ba ni ne? Kar ka damu ba zan ce a wajen ka na samu ba.”
Ajiyar zuciya ya sauke kafin ya ce”Ina tsoro ne kinsan halinsa fa, ba ya sauya ba ne in ya ji ni na baki lambarsa tamu da shi za ta yi muni.” Da sauri ta ce masa in sha Allahu bazai sani ba.
Jakarta ta karɓo wajen Rukky ta ɗauki wayarta ta kwafe lambar suma dukkansu ta karɓi lambobinsu wannan karon ba za ta kara bari Aji ya suɓuce mata ba.
Ganin dare ya yi ga sauran mutane ya sa Mimi ta ce Rukky ta tuka su da sauran ƙawayen Bibi sai su je ta sauke su, ita sai ta wuce gida domin ba ta gayama Hajiya zata kwana ba.
Tare suka bar wajen ɗaya saura na dare suka maida Amarya da tawaganta zuwa gidanta dag nnan Mimi ta ce za ta tafi gida Rukky ta ce ba za ta bar ta ta tafi ita kaɗai ba. Za ta rakata sai ita ta kwana a wajen Mimi ɗin. Ƙawayen Bibi ma duk nan za su kwana Ango ya yi musu lamuni tunda dare ya yi ga kuma yadda abubuwa suka kasance. Anan suka yi sallama su Mu’azzam ya ɗauke su sauran abokan masu mota kowa ya kama gabanshi, suna tafe a tare motar Mimi na gaba ta su na baya sai da suka zo shatalelen da kowa zai ɗauki anguwar da zai je sannan suka yi ma juna hon su suka ɗauki hanyar anguwan Tunfere su Mimi kuma su dauki hanyar da za ta sada su da GRA.
Lokacin suka isa har Hajiya ta jima da yin barci Baaba Uwani ta ji bugun kofar falo ta zo ta buɗe musu daman Hajiyan ta ce kada ta yi saurin barci Binta ba ta ce za ta kwana acan ba. Sai ko ga su sun dawo, Rukky ta ga abun mamaki Mimi da wannan rigar kamkame ajikinta ta kwaana.
Kamar ta rike Mutum haka ta rika ji sai kuma mirmishi ta ke yi kuma ta yi tambayan duniyan nan waye Aji Mimi ba ta ba ta amsa ba. Sai da safe da Hajiya ta shigo ɗakin Mimi ta mike da gudu ta isa gareta tana rike da rigar ta Rumgume Hajiya lokaci daya t na fadin”Hajiya albishirin ki”
Hajiya na mirmishi ta ce”Gori fari tas Binta.”
Mimi na Dariya ta ce”Hajiya jiya na ga mansoor wlh na ganshi, kalli wannan rigar ma ta shi ce fa.
Hajiya ta yi shuru cikin mamaki tace”Mansoor dai da na sani na wajen Meri.? Mansoor na Binta” Mimi ta gyaɗa kai farinciki ya cika zciyarta Hajiya ta ce”Ikon Allah ya na nan daman? Ubangiji mai yarda ya so. Masha Allah.” Hajiya ta na faɗa lokaci ɗaaya ta na zama gefen gadon Mimi sai a lokacin suka samu gaisawa da Rukkaya.
Rukky tace”Hajiya wai waye wannan Mansoor da tun jiya da Mimi ta ganshi ta ke farinciki duk da wulakancin da ya yi mata?
Hajiya ta yi tsai kafin ta ce”Wulakanci ya yi mata kuma mai sunan yangayu?
Nan Rukky ta zauna ta kwashe komai da ya faru jiya ta gaya ma Hajiya ta karishe da fadlɗin”Masifaffe ne Hajiya wlh bashi mutumci waye shi har da zai saka Mimi kuka? Hajiya ta yi dariyasu na manya kafin ta ce” Ina wanda Yaddiko ta taɓa yi ma Binta zencensa lokacin da kika rakata wajenta?. Da sauri Rukkaya ta gyaɗa kanta ta kosa taji kan zencen.
Hajiya ta gyara zama kafin ta ve” Shi ne kike mganar shi yanzu. Saurayin Binta ne tun tana da kuruciya shima ai yaro ne lokacin shi ne kuma har gobe ta kasa mantawa da shi acikin tunaninta kuma ina da tabbacin saboda shi ta kasa aminta da kowani namiji har yau.”
Mimi ta yi saurin cewa”Ba saboda shi ba ne Hajiya.”
Hajiya ta katse da cewa”,Saboda shi ne mana Binta, kinsan na san ki sarai ko mahaifiyar ki murja ba zata gayamin wacece ke ba.” Sai Mimi ta yi shuru sai ta dukar da kanta tana wasa da Botirin dake jikin rigar Aji da ke hannunta.
Rukkaya ta gyara zama tana faɗin”Hajiya me ya faru ne? Ina so naji labarin wannan Soyayyar? Hajiya ta gyara zama tana faɗin “Yau zan faxamiki komai mai sunan yan gayu” Daga nan Hajiya ta fara bata labarin yaddaa Alaqan ta fara ta dalilin Inna Meri da yadda haɗuwar Mansoor ta kasance da Mimi, da duk soyayyarsu da yadda abubuwa suka faru da kuma yadda alaaqan ta lalace daga karshe.
Hajiya ta karishe da faɗin”Tun daga wannan abun da ya faru iyayensa suka yanke alaaqa damu, tun daga lokacin Meri bata kara zuwa wajena ba nima kunya da nauyi sun hanani na taka shima yaron ban kara jin labarinsa ba, Binta saboda haka ta ta fi can wani gari karatu ko an yi hitu ba ta cika zuwa Gombe ba , itama tun da Mahaifinta ya ce ko bayan ransa bai yarda ta auri wannan yaron ba ta nuna dakiya duk iya tsawon waɗanan shekarun tana nuna bata damu ba ne amman ni nasan ta damu kuma ya na cikin ranta ba ta manta da shi ba, kamar yadda shima bai manta da ita ba, saboda ya ƙaunaci Binta kuma duk da soyayyar dukkansu suna da yarinta ne alokacin sun dauketa da zafi, saboda shi Binta ta zauna a wajena har ta gama babbar Sakandiri, mahaifinta bai so ba, saboda ni na matsa ya sa ya barta Saboda mahaifiyarsa ko da yaushe yana gidanan sun shaku da juna sosai har ta kai su ga aminta da auran juna ni kuma ban hana ba saboda yaron ya fito da gidan mutumci mahaifiyarsa ta zauna da ni har muka rabu ina kewar kyakyawan hallayan ta har gobe in na tuna abinda Kabiru ya yi ma iyayen yaron nan da shi kanshi sai naji ciwo a raina Rukkaya ba ni da yadda zan yi ne kawai.”.
Hajiya ta ƙarishe kamar za ta yi kuka Rukky ta cire tagumin da ta yi ta na kallon Mimi da ke kuka hawaye wasu na koran wasu Ajiyar rai ta sauke kafin ta ce”Ikon Allah, Hajiya ai ba laifin Mimi ba ne bai kamata ya yi mata abin da ya yi mata ba jiya.”
Hajiya tace” Zai iya yi mata ma wanda ya fi shi, tun a lokacin mahaifiyarsa na kuka da shi wajen bakar zuciya da riko, ai daman tun a wajen ya furta ko ita kaɗai ta rage a duniya sai dai ta mutu ya mutu amman ba zai taɓa auranta ba, kila ya kasa manta abin da ya faru ne shi ya sa ya nuna mata haka kuma Kabiru daman ya yi masa tsakani da Binta haka suka yi yarjejeniya da iyayensa.”
Rukkaya ta ji hawaye sun cika mata ido cikin tusayin kawarta ta ce”Hajiya Mimi na son wannan mutumin har gobe kuma nima ma yadda saboda shi ta hana kowa wata damar, me zai hana shi Abi a rokesa ya janye kalamansa saboda farincikin Mimi?
Hajiya ta yi shuru kafin ta ce” Duk da Kabiru ya yi sanyi saboda rayuwa ta sauya masa amman dai bai taba furta haka ba sai dai ya nuna kar a takura mata, Ai an gama lalata alaqar tunda farko yanzu da wuya kalaman baki su iya gyara ta.”
Rukkaya ta ce”Da kuma haka Hajiya, ai shima na ji abokansa na faɗin yanzu ya samu duniya ƙwallo yake yi fa yana babban kungiya a nan garin Gombe ne.”
Hajiya tace”Ba shakka ai yana da zuciya ni dai a sanina burinsa ya zama sojane to ina ga bayan faruwan lamarin komai ya sauya.”
Hajiya ta kalli Mimi dake kuka kafin ta dafa kafaɗaanta tana faɗin” ki kwantar da hankalin ki Binta na sha kuka a gaban Allah ina rokon ya kawo miki abokin rayuwa nagari tunda kika haɗu da Mansoor yau ina ji a jikina kaddaran ku ba ta kare ba, ki yi addu’a sai ki ga komai ya tafi da sauki.”
Sai kawai Mimi ta saki kukanta ta kwantar da kanta saman Cinyar Hajiya tana fadin”Hajiya ta nan anan nake jin wani irin zafi acikin ƙirjina, Ina son Mansoor soyayyarsa ita ce ta cigaba da rike rayuwata Hajiya. Tun da Abi ya raba ni da shi farinciki na ya zama rabi da rabi, ganinsa kuma da na yi yau ya fama min wannan cutar dake cikin zuciyata Hajiya Mansoor na sona har yanzu sai dai ya kasa mantawa da abinda ya faru ne, har yanzu ya na ganin bai cike wannan bambamcin da Abi ya nuna akwai a tsakanina da shi ba shiyasa ya nuna ya manta da ni, in har baya sona me ya sa ya damu saboda rigata ta yage? Hajiya shi ya sakamin wannan da kanshi a jikina.”
Take faɗa ta na gunjin kuka Hajiya na ta faman lallashinta a ɓoye sai da Rukky ta share kwalla. Daman akwai irin wannan soyayyar ta a mutu har yanzu?.
Ƙarshenta dai tafiya ta yi gida saboda Mimi ta yi kuka har ta gaji kanta ya fara ciwo Hajiya ta saka Baaba Uwani ta hada mata Tea ta sha sai ta sha magani ta kwanta.
Tana kwanciya sai barci ta fara barcin kenan Mommy ta kira wayar Mimi sai Hajiya ta kira Baaba Uwani ta ɗaukar mata wayar suka yi mgana
Hajiya ba ta ɓoye mavta komai ba na game da Haɗuwar Mimi da Mansoor ba, da kuma halin da take ciki Hajiya ta ce”Murja ku yi mgana da Kabiru ya janye kudurinsa a kan Binta da yaron nan matukar yana son cigaba da ganin farincikin ƴarsa, in kuma ya na son baƙincikin da ta danne acikin zuciyarta ya yi sanadiyar mutuwarta ai shike nan, amman ki faɗa masa ya sani ya tursasa ma Binta ta yi masa biyayya akan tafarkin sunnar ma’aiki ai aure ta ce za ta yi ba karuwanci ba, sannan da talaka da mai kuɗi duk na Ubangiji ne, yanzu yaron da ya ce ba shi da makoma mai kyau Allah ya ɗaukakasa an ce ƙwallon kafa yake bugawa sannan shi dai wanda ya wulakantan shi ƴar sa ke so har kwanan gobe, ki sanar dashi ni ma uwace a gare shi kuma ya yi ta saɓa umarnina tun a baya kuma na yafe mishi to shima ya yi hakuri ya duba Isharan da Allah ya nuna masa tun a duniya ya Janye kalamansa a kan Binta ya saka baki a nemo wannan yaron da ahalinsa ya roƙesa su gafara ya kuma amince Binta ta aure shi shine kawai masalahan da zamu samu sannan shine farincikin Binta a yanzu.”
Duka mangaganun Hajiya a kunnen Abi tunda a speaker Mommy ta saka wayar ya na kwance ne amman kuka yake yi, ita ma Mommy sai sharan hawaye take yi tana kauda kai ba ta so ya gani.
Ita ya kallo ya na tuna a zamanin baya bai taɓa ba ta damar magana ba, duk abin da ya yanke ko ta na so ko ba ta so haka za ta bi, kuma gaskiya Hajiya ta faɗa shi ya san ya rika take maganar Hajiya a matsayinta na uwa ba ta isa ta ce ya bar abu ya bari ba ya na ganin ya na da kaki sannan ga yadda ya gina rayuwarsa ba wanda ya isa ya rushesa masa. Ya daɗe da yin nadaman abin da ya aikata ma wannan yaron sai dai kunya da tunanin inda ma zai fara ya kasa mgana.
Ya sha kiran Mimi sai ta zo ya kasa magana sai dai ya yi ta lallashinta yana bata Hakuri, ya na so ya samu damar neman gafaran kowa kafin Ajali ya riske shi bakinsa ya yi nauyi amman kalaman Hajiya sun zaburar da shi lokaci ya yi da ya kamata ya gyara abunda ya ɓata shekaru goma da suka gabata. Tabbas Mimi zata samu farinciki ba zai zama uba mai hana ƴarsa nata farincikin a saman na shi ba, kafin ya bar duniya zai yi ma Mimi abinda zata dauwama tana tunawa da shi ko bayan ransa.
Mommy na sharan jawaye a fakaice ta zari tissue ta na goge masa hawayensa cikin karfin Hali ya rike mata jannu da hannunsa na hagu da ya ke motsawa ta kasa kallonsa shi kuma so ya ke ta kallesa amman ta kasa saboda kukan da ke cin ranta.
Kowacce uwa tana son ganin duka rayuwan ƴa’yanta ya inganta, amman ita a cikin Ƴaƴanta akwai wacce ta ke cikin rayuwar rabi farinciki rabi damuwa.
Ta san Mimi ba za ta manta da yaron nan cikin sauki haka ba, ta kuma san shi saboda shi ne ta ke zaune har yau ba ta yi aure ba tunda ba ta rasa manema ba ne.
Tun a lokacin ta san ba’a kyauta ba, amman ba ta da wannan ikon na faɗin haka mutumin da bai ji mganar mahaifiyarsa ba ita din banza ya ji nata.
Cikin ƙaryewan murya ya ce”Murjanatu ki ɗago ki kalleni don Allah.”
Dakyar ta dago ta kallesa sai sharr hawaye shima hawayen ya ke yi da karfi ya kamkame hannunta kafin ya ce”Ki yafe min nasan ke ma na cutar dake, amman ki sani na yi nadama tuntuni nauyi da kunya da rashin sanin ta inda zan fara suka hanani mgana amman tun da Hajiya ta nuna min hanya in sha Allahu zan gyara kuskurena Murja.” Mommy ta kalleshi cikin mamaki kafin ta ce”Da gaske Habibi?
Sai ya jinjina mata kai kafin ya ce”Ki kira Dr ki faɗa masa ya zo ina son ganinshi, zan saka ya san yadda zai yi a tafi dani Gombe zan roki gafaran Hajiya da Mimi sannan zan saka a nemo wannan yaron na rokesa gafara na kuma roke shi ya auri Mimi saboda farincikinta, na kuma yi alkwarin yin azumi uku na kaffaran rantsuwan da na yi.” Da sauri Mommy ta Rumgumeshi tana Fadin”Thank You Habibi Allah ya baka lafiya, yanzu kuwa zan kira Sulaiman Mimi za ta samu farinciki itama.”
Yadda ta ke murna ne yasa ya san ya jima ya na danne mata Hakkinta a matsayinta na uwa.
Ashe abun na damunta acikin ranta ba taa taɓa nuna masa ba.
A gabansa ta kira Dr Sulaiman suka yi mgana ta kuma haɗasu shima ya gayamasa ya yi musu bucking din jirgi zuwa Gombe.
Cikin mamaki ya ce”Me ya faru Abi? Kai da ba ka da lafiya in Hajiya ce sai a kirata ta zo ta ganka.”
Cikin muryan ciwo yace”A a ni zan je da kaina gafaranta zan nema Dr. kuma ina son na gyara kurakuraina na baya.”
Ba shi da abun cewa illah ya amsa da zai yi musu bucking din jirgin Mommy ta ce kar ya damu ba sai yazo ba, ita za ta iya raka Abin har Gonbe kuma ta bashi duk kulawan da ya dace. Ba ta kuma yi maaganar da kowa ba har su Hajiya ba ta kira ta ce ga yadda suka yi da Abi ɗin ba.
Sun dai yi waya da Mimi da ta tashi barci ta ji muryanta duk ya dishe alamun kuka sai ba ta neme ta da mgana ba, ballantana ta nuna mata sun yi mgana da Hajiya
Abi ta tambaya Mommy ta ce mata ya samu barci saboda ba ta so ta haɗasu ya yi mata wata mgana. Farinciki ta ke ji acikin ranta yau ko da ba wani abu a kallah ya sauke nauyin cin zarafin mutanenan da ya yi abu sam bai yi daɗi ba.
***.
Washegari.
8:45pm.
Mu’azzam bai samu tafiya ranar lahadi saboda sanda suka koma gidan Aji a daran jiya baya gidan Allah ya sa Mu’azzan akwai key ɗin gidan ajikinsa da shi suka yi amfani suka buɗe gidan suka shiga suka kwanta..
Har safe suna ta kiran wayarsa bai ɗauka ba sai da rana Mu’azzam ya je Studio ɗin su ya same shi.
A camp ɗin su ya kwana sannan ya ki ba ma kowa damar da zai tattauna abin da ya faru jiya da daddare. Hakanan suka je suka raka Makama ango gidansa Nasir ya wuce gidansa Ahmad ma ya wuce gidansu gobe da Asuba zasu kama hanyar Mu’azzam zai rage masa hanya zuwa Kano daga nan ya samu motar kaduna.
Mu’azzam ya zo ya na ba ma Inna labarin abin da ya faru ta riƙe haɓa tana fadin”Allah Sarki Bintar Hajiya ashe ba ta manta da ni ba”
Mu’azzam yace”Wallahi Inna sai da ta tambaye ki.”
Inna ta yi mirmishi itama tausayin Mansoor da Binta na cika ranta.
Kafin ta ce”Bakomai Ɗan Inna, komai ya yi zafi maganinsa Allah zai huce ka ga ya dawo da kanshi.” Mu’azzam ya ce”Inna har yau Yaya Mansoor na son Anty Mami ni nake faɗa miki haka.”
Inna ta ce” Har gobe ma Mu’azzamu, yana nuna cewa ba ya ta ita ne yanzu amman ƙarya yake yi duk wannan abubuwan da ka yana yi saboda ita ce kuma ina mai rantse maka in ba ita ya aura ba da wahala Baban Inna ya yi aure saboda ba zai iya zama da kowacce mace ba sai ta.”
Mu’azzam yace”To inna ba za a iya yin wani abu ba? Haka za’a barshi ya karar da rayuwarsa cikin kunci?
Inna Meri ta yarfa hannu kafin Ta ce”Me zan iya yi a kai Mu’azzamu ban da addu’a? A gaban ka mahaifin yarinyar nan ya ce mu yi masa tsakanina da iarsa, shima kuma kana ji ya rantse sai dai ya mutu bai yi aure da ya aureta , ni na rasa wannan bakar zuciya irin ta Baban Inna da kafiya da riko, rikon da yake ma abun a ranshi ne yasa ka ga duk ya koma haka” Mu’azzam kamar ya yi y kuka ya ce”Inna ni dai in har ɗan’uwana zai yi rayuwar farinciki zan nemi Anty Mami mu yi magana , zan koma gidansu a Abuja na roki mahaifinta ya bari Yayana ya auri ƴarsa ko da zan mallaka masa duk abin da na mallaka ne.”
Da sauri Inna Meri ta ce”Kul kar ma ka fara, ka san ai kun gwaada haka a baya komai ya lalace. Ko ka je ya amince ya janye maganarsa ya za ka yi da Baban Inna? kana tunanin shi taurin kansa da wannan bakar zuciyar zata barshi ya yafe ne ya amshe ta ko da ya na sonta? Ai ya gwammace ya mutu da wannan bakinciki akan dai ya yafe abunda ya faru ya nuna ya na son yarinyar nan har yanzu, ai gani zai yi kamar ya ragu bakar zuciyarsa ba ta kitsa masa abu mai kyau a kan rayuwarsa addu’ata kullum Allah ya saussauta masa wannan baƙar zuciyar.” Inna Meri ta karishe tana fashewa da kuka Mu’azzam sai ya koma yana ta lallashinta amman shi kanshi kamar ya yi kuka. Allah yasa Walida ba ta nan tana Gidan Bintu can za ta kwana.
Asuban ci zai yi na tafiya shi ya sa ma a gida ya kwana ɗakin Saddiqu, saboda Mansoor dai ya yi ma gidansa ya ji ba zai ji daɗin kwana shi kaɗai ba.
Amman ya kwana tunanin mafita a daran kuma ya kira wayar Anty Mami ba ta ɗauka shi dai zai kara kutsa kansa cikin wata kasadar a karo na biyu mai kamceceniya da kasadar da ɗan’uwansa ya kutsa kanshi a karon farko a shekarun baya.
Ko kaɗan ba su Bari Baba Danjuma ya fahimci akwai matsala ba Saboda kada su ɗaga masa hankali.
Amman fa ya fahimci daga Inna har Mu’azzamu yanayin su ba daɗi sai ya dauka saboda tafiyar Mu’azzamun gobe ne Tunda Ɗan inna ne in ya zo uwar tasa ba ta son ya tafi.
Mu’azzam ya yi ta tufka ya na warwara, sai dai abu ɗaya ya kashe masa gwiwa da ya tuna Nasir ya gayamasa an taba hira da ita acikin labarinta ta ce mahaifinta ya yi hatsari ba shi da lafiya? Abin da bai sani ba shin ya na nan a raye ko ya rasu?
Amsar da ya kasa samu har suka bar garin a mota ma ya ke tambayan Ahmad yace shi ba’a garin ya ke ba wlh bai sani ba sai dai ya Kira Nasir din ya ji ta bakinsa tunda yana garin zai iya sanin wani abu.
30 April 2022
Yasan Mu’azzam ya bar garin duk ba su yi waya ba, saboda yasan yanayin aikinsa ba zai jima ba. Sai da a daran ranar litini ya koma gidansa daman baya son lokacin da zai samu kaɗaicewa wani na gefensa.
Tun haɗuwarsa da Mimi bai ƙara barci cikin salama ba. Ya ji ya tsani kanshi ta yadda har gobe zuciyarsa ba ta daina son wannan yarinyar da yake ganin bakinta fiye da kowa a duniya ba.
In da ya san yadda zai iya ciro zuciyarsa ya ciro son ta ya jefar ya maida zuciyarsa da ya yi haka domin ya cigaba da rayuwa cikin salama.. Tun da alaqan ta yanke bai taɓa kwana ya tashi bai tuna da ita ba, Soyayarta da kishin ta suke kara wahalar da shi.
saboda ita ya kasa kallon ko wa ta ƴa mace da sunan so, saboda ita ya kashe maganar aure acikin zuciyarsa gabaɗaya rayuwarsa ta zama kamar mattaciya saboda cutar da zuciyarsa take ciki.
Kwance ya ke a tsakiyar falon sa, a saman cafet ya y filo da hannayensa idanuwansa suna Rufe ne amman yana fuskantar POP ɗn da ke falon. Bashi da riga daga shi sai ƙaramin wando sannan babu nepa falon ya yi duhu
Tunani yake yi, tunani mai zurfi kamar a lokacin haka ya ke ji amon kukanta na shiga ransa, shi ya yi mata tsawa ya saka ta kuka amman ba ta kaishi shiga bakinciki ba.
Allah kaɗai ne ya kaisa in da za shi lafiya a ranar yana tuna kukan da take yi da yadda ya ture ta.
Saboda haka a daran ranar kusan kwana ya yi ya na gudu a studio sai da ya ji ya gajiyar da kanshi sannan ya sarara.
Muskutawa ya yi ya juya zuwa da jikinsa bangaren dama.
Ya sunan ka?
Ni? Ke ya sunan ki?
Ni sunana Mimi Mimin Abi
Ya tuna mirmishinta da dariyanta tun alokacin sai da kumatunta suka loɓa, ba zai manta amsar da ya ba ta alokaci ba
Sunana Mansoor Aji.”
“Aji ?
Ta faɗa da sigan tambaya alokacin sai da ya yi dariya kafin ya yi magana ta yi zaraf ta ce.
_To wajen wa ka zo?. Wajen Hajiya?
A’a ni wajen Innata na zo
“Inna Mari mai girkin Hajiya?
Dariya ya yi alokacin kafin yac e”Eh ita, ai innata ce.”
Baki ta buɗe tana yar dariya har kayan jikinta bai manta kalansu ba, a lokacin iyakarta shekaru sha shidda kuma wannan shine gani na biyu da ya yi mata kuma maganar su ta farko shi da ita..!
Me ya sa ya kasa mantawa da ita?
Me ya sa ya kasa mantawa da duk abinda ya shafe ta?
“Saboda har yau kana sonta Mansoor.”
Amsar da wata zuciyarsa ta bashi kenan.
Da gaske yama sonta? To me ya sa zai cigaba da sonta ahalin akwai bambanci mai tarin yawa a tsakaninsu?.
Kaddara ba ta haɗa su domin su zauna waje ɗaya ba, ita kaddaran da kanta ta raba tsakanin su.
Page 10
MAFARI.
20 DECEMBER 2008
Anguwar GRA, Gombe.
Hankalinsa na kan ƙaramar wayar dake hannunsa yana yin game ɗin nan mai maciji, tun bayan da suka gaisa da Baba megadi ya koma gefe ya tsaya jefi jefi kuma ya na duba agogon fata irin na matasa a wancan lokacin dake ɗaure a tsitsiyan hannunsa na hagu, gani yake yi kamar yau Inna ta jima ba ta fito ba. Hon ɗin da ya ji an zuba ne har sau uku ya sa ya juyo ta wajen get din sai yaga wata mota mai ruwan toka za ta shiga gidan ba motar ba ne ta bashi mamaki illah daga baya ya hango wata matashiyar yarinya ta jikin window ɗin motar na gidan baya ta lafe sai kalle kalle take yii, da yake lokacin saka ma gilashin mota rufuwa bai zo ba ana iya ganin na ciki, sannan na ciki na iya ganin na waje shi ya sa ya iya hango yarinyar dake cikin motar itama ta samu nasaran ganinsa.
Abun da ya bashi mamaki ganin ta yi masa mirmishi sannan abun burgewa a tare da ita shine loɓawar kumatun ta ma’ana dimple sannan ta ƙara masa da ɗaga hannu, bai maida mata da martanin ɗaga hannun ta ba. Sai dai ya maida mata da martanin mirmishinta a gaban idanuwansa a ka buɗe get motar ta sulala cikin gidan, har kuma suka shige tana kallon shi yana kallonta shima. Sai da motar ta shige cikin gidan sannan ya sauke Ajiyar zuciya shi kaɗai acikin ransa yayi ma kansa tambayar.
“Wacece wannan yarinyar?
A iya sanin shi bai san akwai yara a gidan Hajiya ba, kafaɗa ya ɗaga alamun sanin wacece ita bai dame shi ba, maida hankalinsa ya yi kan wayarsa bai san fitowar Inna Mero ba sai da yaji tana kiransa.
“Baban Inna..”
Da sauri ya ɗaago sai ya ci karo da ita a gabansa ɗauke da wani kwano a hannunta, da hanzari ya saka wayarsa a gaban aljihun rigan dake jikinsa fara mai ratsi ratsin baƙi, sai baƙin wandon dake jikinsa. da sauri kuma ya saka hannu ya karɓi kwanon hannunta yana faɗin” Inna wannan kwanon fa?. Tana mirmishi ta ce”Hajiya ce ta sakani sai da na ɗauko abinci”
Sun fara tafiya a jere da juna ya ke faɗin” Inna ni fa ba na son kina ɗauko abinci daga gidan nan, sai mutane su rika tunanin ko kin raina ƙokarin Baba ne”
Ajiyar zuciya ta sauke kafin ta ce” To ai mutane Allah ne kaɗai da ya hallicesu ke iya musu dai dai, ba ka biye ta mutane ba Baban Inna, kasan ai ba na son ɗaukowa Hajiya ce ke matsamin kuma in ban ɗauko ba sai ta ga kamar ban ji maganarta ba ne.”
Gyaɗa kai ya yi batare da ya yi magana ba sai da suka yi nisa daga fitan layin gidan na masu hannu da shunu suka kama hanyar anguwarsu ta marasa karfi wato Arawa.
“Inna ki sha kurumin ki, in na samu aikin soja za ku huta ke da Baba In sha Allahu, ba za ki ƙara fita wani gida aiki ba.”
Ta na mirmishinta da ba ya ɓacewa a saman fuskarta ta ce”Allahu ya sha Baban Inna Allah ya ida nufi na alheri.”
Kai tsaye kuma ya amsa da Amin kafin ya ce”Inna ni fa ina son na yi aure da wuri, saboda na bar miki matata a nan in na tafi aikin soja ta rika taimaka miki da wasu ayyukan.”
Inna Meri ta yi dariya mai tsawo tana mai bin yaron nata da kallo. Mansoor kenan manyan ƙasa shi kansa tsaye yake faɗin ra’ayinsa. Duka duka shekarunsa ashirin ne a duniya amman ya na da burikan ya zama wani abu saboda iyayensa su ji daɗi.
Tana jin sa ya cigaba da faɗin”Allah Inna da gaske nake yi, ina son na yi auren wuri ina son ganin na haifi ƴayan da zamu zama, muna kamar Yaya da ƙannensa.”
Inna ta kaɗa kai tana dariya kafin ta ce”To Allah ya nuna mana Baban Inna.”
Ya amsa da Amin Innata.
Suna tafe suna hira tunda akwai yar tafiya kafin su isa gida, ya saba kullun zai je kofar gidan da take aiki ya jirata har ta fito su dawo gida tare, Mansoor matashi ne mai ƙulafucin uwa mai kuma son mahaifiyarsa ba shi da mafita ne, da bazai taɓa bari Inna Meri ta yi aikatau a gidan masu kuɗi ba.
“Inna kamar yau kin wuce lokacin tashin ki ko?
Kai tsaye ta ce”Eh Hajiya ce ta tsaida ni na gyara ma jikarta da za ta zo mata hutu ɗaki shi ya sa na ɓata lokaci.”
Kallonta ya yi kafin ya ce”Ko ita ce na gani an kawo ta a mota kafin fitowar ki?
Inna ta ce”Eh ita ce Fatima Hajiya na kiranta Binta mai sunanta ne shiyasa take sonta, yar wajen babban ɗanta ne wani Soja a Abuja.” Yana jin Inna na mgana amman bai tanka mata ba itama sanin halinsa ya sa sai ta saki mganar ta kalleshi tana fadin”An taso islamiyar ne? Na ga kuma ai shidda ba ta yi ba? Kai tsaye ya ce”Ba’a ta shi ba Inna.”
Ba tare da ya gayamata wani abu ya faru ba ta kalleshi lokaci ɗaya tana faɗin”Kai Jama’a yauma faɗan ka je ka yi da wani a makarantan Baban Inna,?
Mirmishi ya yi kafin ya ce” Inna ba faɗa ba ne, kawai dai yar cacan baki ne”
Inna ta ce”Cacan baki ai ƙanin faɗa ne Baban Inna, kullum ina yi maka faɗan shi fa rayuwa da kake gani sai ka yi hakuri in kana so ka ci riban duniya wannan baƙar zuciyar na ka tun yanzu ya kamata ka koyi yaƙi da ita in ba haka ba nan gaba ba za ka iya sarrafa kanka ba.” Da sauri ya ce”Ba faɗa na yi ba fa Inna mgana ya gayamin ni kuma ma maida masa sai mallam Haruna ya koremu daga ajin gabaɗaya, ni kuma ganin an kusa tashi sai na biyo ta nan kawai.”
Inna ta kaɗa kai kafin ta ce”Ai shike nan Allah ya kyauta, nasan dai bai wuce Agola ya kira ka ba, kuma na gaya maka ka daina damuwa da masu kiran ka da sunan nan, ai ba maƙale maka zai yi a jikin ka ba, ina ruwan ka da su ka kyalesu su yi ta kiran ka Agola hakan ba zai rage ka da komai ba kuma ba zai ƙare ka da komai ba”
Mansoor ya yi shuru kafin yace”Ba ma wannan ba ne, Shamsu gidan su man bala ne fa ya ce wai Mu’azzam ba ƙanina ba ne ni kuma nace Innar su ce ta auri Baba ta haife shi? Inna Meri ta fara salati tana tafa Hannu kafin ta ce”Na shige su ni Maryamu, haka ka gaya masa Baban Inna,?
Ko ajikinsa ya ce”To inna maganarsa ce ta ɓatamin rai shi ya sa na tambayesa ko Innar su ce ta haifi Mu’azzam ɗin?
Inna Meri ta kaɗa kai kafin ta ce”Ka bari ba kyau zagin iyayen wasu kaji ko? nima in wani ya zage ni ba za ka ji daɗi ba, duk duniya ba wanda ya isa ya ce Mu’azzamu ba ƙanin ka ba ne ya faɗa ne domin ya tunzara ka.” Suna tafe ta na mgana kuma duk Nasiha take yi masa akan hakuri da kuma daina bakar zuciyan nan nasa nuna masa ta ke yi mai hakuri shi ke da ribar duniya kuma ya ke da ribar lahira.
Suna shawo kwanar layin su suka ci karo da dandalin yara da matasa sun taso daga makarantar islamiyan Mallam Ɗahiru, Mansoor ya hango Mu’azzam tare da su Nasir suna baya suna tafiya suna magana yana jin muryansu a sama gaddama ta sarke su kuma Mansoor na da tabbacin gardaman ƙwallo ce. Su binta kuma suna gaba tare da su Zuwaira amman Bintu na kamkame da hannun Walida da ita ce karama a kaf gidan Wanzamai ita da Mariya.
Bintu ta fara hango inna Meri sai ta saki hannun Walida ta nufi innar da gudu ta faɗa jikinta har garin gudu tana watsa ma Mansoor kasa a kafarsa dake cikin bakin takalminsa. Ransa ya ɓaci tsawa ya da ka mata yana faɗin”Ke zan ba ki wahala, ba ki da natsuwa ko? Sai a lokacin ta ganshi da Sauri ta makale bayan Inna ta na tura baki, dukawa ya yi ya na kakkabe kafarsa itama Walida ta zo da gudu ita a lokacin ko shekara goma ba ta kai ba, Bintu ce ta haura sha amman kuma ba Hankali.
Inna Mari ta tasa ƴaƴanta gaba Mariya da ke tare da su Jummai tana so ta je wajen Inna Meri Zuwaira ta riketa tana mata jan ido, Inna Meri ba ta damu ba ta kallesu tana faɗin”Ƴan makaranta an dawo?
Cikin su ba wanda ya kalleta har da sauran tawagan ƴaƴan su gaje kallonta suka yi suka watsar suka wuce gaba yan matan masu girma irin su Zuwaira suka tasa kannen su gaba sai gidan Wanzamai.
Wanda kaf garin Gombe gidan wanzamai ɗaya aka sani da ya yi shuru gidan da Inna Meri take aure a karo na biyu kenan.
Ba ta damu kanta ba tunda ai ba yau aka fara sai ta rike hannun Bintu da Walida ta bi bayansu, Mansoor kuma ya wuce wajen su Mu’azzam da suka tsaya gaddaman ƙwallon kafa sunan kuma sun dawo islamiya
Mansoor na zuwa wajen ya tankwafi keyar Mu’azzam yana faɗin”Wuce muje gida ka tsaya gaddaman tsiyanku na fama”
Mu’azzam ya dafe kanshi yana yar dariya Nasir ya ce”To mai ƙani ai mu kuma sai mu kwana a hanya.”
Mansoor ya harare shi kafin ya ce”Nasir ka rika yin abubuwan ka cikin Aji don Allah.”
Makama ya ce”Gaya masa ya cika zubar da class.” Ahmad dake gefe ya kwashe da dariya Nasir ya sha mur bai yi mgana ba suna ta hararan juna da Mansoor.
Shi kuma bai damu ba ya tasa ƙaninsa Mu’azzam a gaba yana rike da kwanon da ya karɓa hannun Inna Meri suka wuce gaba su ka bar su Nasir a baya suna kallonsu.
Duka yan nan tsukun anguwan ne, kuma tare suka taso tun suna ƴan yara makaranta boko tare suka yi haka allo da islamiya.
Cikinsu Mansoor da Nasir ne sa’anin juna sai Ahmad sai makama ƙaramin sai Mu’azzam, kuma shima abin da ya sa ya zama tamkar abokinsu duk inda Mansoor ya saka kafa to a bayansa Mu’azzam ne ya na bala’in ji da ƙaninsa, yana kuma kafa kafa da shi to saboda yana shiga cikin su ne ya sa suka haɗe gabaɗaya su biyar ma su mabambamtan hallaya. Kuma duka ana ruƙunun anguwa iyayensu suke sun san juna shiyasa abotan su ta yi tsawon da kowani lokaci suna tare.
Gidansu Mansoor ne a gaba su kuma nasu Nasir sai an yi gaba shi ya sa su suka fara shigewa suka bar su Nasir ya yi tsaki kafin ya ce”Aji ɗan renin wayau ne, ya cika zafi da masifa” sunan Aji da Mansoor ya samu acikin sunan shi su Nasir suka fara saka masa sunan saboda shi mgana ɗaya biyu sai ya ce a riƙa yin abu cikin Aji ko ya ce wane ba ka da Aji tun yana ƙaraminsa Mutun ne shi mai kamewa da son harkan girma ba ya son reni da kuma yin abu na marasa aji. Shiyasa da suka sanya masa sunan suna kiransa har a makaranta wasa wasa yau da gobe har sunan ya bishi acikin anguwa sai an ce Mansoor Aji a ke gane shi.
Tun suna makaranta kuma sunan ya bishi Aji Aji, sannan a filin ball din su ma sunan shi kenan Aji mai Buga lamba goma tunda suna cikin group ɗin matasa anguwan da suke buga kwallo har Team ma garesu mai Suna NASARA TEAM.!
A lokacin da Inna Meri ta shiga cikin gida duka matan gidan suna tsakar gida, tunda gidan na a zamaninsa na baya kafin ya samu gyare gyare Gaje da Harira na tsakar gidan tunda a lokacin suna amfani da tsakar gida ɗaya ne. Dakin Magajiya ne a farko na Inna Meri na daga ɗan wani lungu kaɗan. Ta yi sallama ba wacce ta amsa mata kuma sun ji ta sai ta kada baki ta ƙara kwala sallama wannan karon Harira ce ta amsa sai Inna Meri ta ce”Ina ta sallama ba ku amsa ni ba.”
Sai ma suka yi kamar ba su ji ba kowacce ta na ji da ƴaƴanta suna ta kawo labaran abin da ya faru a makaranta.
Bintu tuni ta warce hannunta ta wuce ɗakin Inna Meri ta na tura baki yunwa take ji ta fara binciken neman abinci, Inna Meri aka bari tsaye da Walida kamar an da sa su.
Magajiya na zaune saman kujera yar tauggono ta na tukin tuwo sai magana take yi da su Jummai kamar ba ta san da wanzuwar Inna Meri a wajen ba.
Inna Meri ta yi mirmishi kafin ta ce”Sannu da gida magajiya, ba ki ji ni ba ina ta sallama ba ne” Kawai sai Magajiya ta fara masifa tana faɗin “To ina ruwana da sallaman ki da za ki zo kaina kina damuna, ni na tura ki gantalinki da sunan aiki da za ki dawo ki shaidamin kin dawo? nifa ba na son munafunci Meri ki yi ta kanki nima na yi ta kaina, ki yi harkarki na yi tawa tunda ba zaman juna muke yi acikin gidan nan ba”
Ta faɗa ta na wani kumfar baki dai dai lokacin da Mu’azzam da Mansor suka shigo gidan. Kuma tun a kofar gida suka fara jiyo jarabarta illai daman su san da uwar su ce tunda ta raina ta daman.
Mansoor da ba shi da hakuri ya ƙariso yana faɗin”Inna me ke faruwa ne?
Tana ganinsu gudun wata fitinar sai ta ja hannun Walida tana faɗin” kun ga ba wani abu ba ne. Mu je ku yi alwala ku tafi masallaci.” Mu’azzam ya yi gaba shi da Walida Mansoor kuma ya tsaya yana kallon Magajiya kallon ki ki yayi kanki
Itama ta kalleshi ta watsar Inna Meri ta turashi gaba ta na faɗin muje Baban Inna an fara kiran salla. Da haka ta ja shi shashenta ta karɓi kwanoon hannunsa ta ce Mu’azzam ya saka masa ruwa a buta su yi alwala. Bintu kuma na tsakar ɗaki tana cin abinci Mansoor ya kalleta kafin ya ce”Ke kafira ce da baki sallah?
Abincin ya kasa shiga cikinta ta damkesa a bakinta ta na girgiza kai, wani kallo yayi mata kafin ya ce”Ki bari na kara kifta idona na ganki a nan wajen sai na wahalar dake.”
Yana gama faɗin haka ya shige ƙaramin makewayin dake bangaren Inna Meri, Bintu kuma na tura baki ta mike Inna ta karɓe kwanon abincin tana faɗin”In ki ka yi sallar sai ki cigaba da ci tunda kin zama acici.”
Mu’azzam na alwala ya na mata dariya sai ta dauko murfin kwano zata je fe shi da shi ya sha mur ya na kallon kofar makewayin kafin Ya ce”Yayanmu ga Bintu..’
Ai kafin ya rufe baki sai ga ta fito da gudu dai dai lokacin da yake fitowa daga makewayin.
Tun kafin ma ya kalleta ta ce”Ba buta ne ina jiran Yaya Mu’azzam ya gama ya bani ne” Dariya ta kusa kama Inna dake duke ta na gyara ma Walida sikat ɗin jikinta Mu’azzam dai sai da ya yi yar dariya yana yi ma Bintu gwalo. Sai da ya jira sa ya gama alwalan sannan suka fita masallacin tare suka bar Inna da su Bintu a gida suna yin nasu.
A can masallaci suka sake haɗuwa da su Nasir , Nasir har ya na ce ma Mansoor ” Su Aji masu ƙani ka wani tasa shi gida, to mu ka ga ba mu je gidan ba.”
Yana jinsa ya yi masa banza daman ai basa zaman lafiya ba su da aiki sai faɗa shi Aji taurin kai da saurin gusata shi kuma Nasir naci da neman mgana.
A kofar masallacin su ka haɗu da shamsu shima matashi ne kamar su ya kalli Masoor kafin ya ce”Ba dai ni ka zaga ba? Wlh sai naci uwarka.”
Mu’azzam na jin haka da sauri ya ce”Kai me yayi maka kake zaginsa?
Nasir da Ahmad suka zagaye shamsu Aji na gefe ya harɗe hannaye a kirji yana jin wani irin zafin zuciya na taso masa wai shi shamsu zai ce zai ci uwarsa.
Su a kokarin su Nasir shamsu ya gaya musu abin da ya faru duk ajinsu ɗaya a islamiyan amman ba su san abin da ya faru ba tunda ba waje ɗaya suke zama ba malaman suna raba musu wajen zama saboda in sun zauna waje ɗaya ba sa karatu.
Mu’azzam kuma ba ajinsu ɗaya ba shi ya na Aji biyar ne su kuma shidda.
Kuma dukkansu wannan shekaran za su gama babban sakandiri illah Mu’azzam da ke aji ɗayan babban sakandiri tunda shekarunsa iyakarsa sha bakwai cikin na takwas ne. Ko kafin shamsu ya gama maida ba’asi Aji ya dunkule hannu ya kai masa naushi saboda yana maida mganar yana ƙara faɗin daga an ce Mu’azzam ba kaninsa ba ne shi ne zai zagar min uwa? Karya a ka yi kanin nashi ne? Ai agola ne zuwa da shi gidan wanzamai Innar sa ta yi.”
Shamsu yaji zafin naushi ganin har jini ya fito shima ya dunkule hannu ya rama ko kafin su Nasir su shiga tsakani sun kaure da dambe dole mutanen dake cikin masallaci da waje suka zo rabon faɗa ciki har da su Baba Ɗanjuma da su Baba Ɗanlami har kuma da mahaifan su Nasir. Shi kan shi Shamsun har da uban sa. Sai da aka samu aka raba fadan amman fa Shamsu ya ci naushi duk bakinsa ya haye ga shi yana fitar da jini.
Mansoor fitinanne ne yana da baƙar zuciya in dai iya fara faɗa ba ya iya bari ana raba su fa domin aji ba’a si yana ƙara kaima Shamsu naushi. Baba sani ya yarfa ma Mansoor mari a gefen fuska yana faɗin”Kai kaci gidanku kai kaɗai ne mai zuciya anan wajen? Ana mgana ka bari kana kara wani hakilo to sai ka daki wanda za ka daka kaji ko? Ya faɗa Saboda ganin yadda Mansoor ɗin ya ke wani huci ya na kallonsa kirjinsa na sama da kasa zufa na keto masa
gashi ya dumkule hannayensa guda biyu ya na jiran ya kai naushi.
Baba Danjuma ya ce”Sani a bi a sannu don Allah.” Baba Ɗanlami ya ce”Yaya Ɗanjuma ka daina saka baki in yaron nan na iskanci, ji abin da yake yi kamar shi kaɗai ne mai zuciya anan wajen” Shi dai Baban Danjuma ƙokarinsa a samu sasanci.
Shamsu aka fara tambaya abinda ya faru ya maimaita karya da gaskiya.
Baba Ɗanlami ya yi ƙaramin tsaki kafin ya ce”To mi ye abun faɗa anan ai ba karya ya yi ba me kuka haɗa da Mu’azzam ɗin? Kowa fa yasan zuwa da kai uwarka ta yi garin nan” Baba sani ya ce”Kuma ban da rashin tarbiya har da ce masa wai uwarsa ce ta auri Yaya Ɗanjuma ta haifi Mu’azzam kaji wani rashin ɗa’a yanzu ya dace aji wannan mganar a bakin yaro kamar Mansoor?
Nasir ya yi karaf ya ce”To amman shi ina ruwansa da cewa Mu’azzam ba kaninsa ba ne, kuma ai yanzu shi ya fara ganinsa ya zage shi.” Su Ahmad ma suka ba da shaidar haka har da Mu’azzam.
Shi ko Mansoor an an yi ya yi mgana bakar zuciya ta hana shi, mahaifin Shamsu Mallam bala ya ba da hakuri ga Baba Danjuma shima ya bashi hakuri suna gayama juna ƴaƴa kowa fa ya haifa sai hakuri.
Su Baba Sani ke ta manganganu suna faɗin”Yaya Ɗanjuma duk kai kake sangarta yaron nan, yana iskancin da ya’yan mu ba sa yin irin shi.” Da an yi mgana sai ka ce maraya ne ai kowa ma marayan ne muma ai marayun ne.” Haka suke cewa sanda suke hanyar komawa gida, su Nasir kowa ya wuce gidan Mansoor kuma Baba Danjuma na rike da shi suna tafiya daga baya faɗi yake yi”Ka rika saka ma zuciyarka salama kaji ko Baban Inna rayuwar nan duka duka nawa take? Cikin jin haushin ya ce”Me ya sa ya ce Mu’azzam ba ƙanina ba ne? Ai ka auri Innata kuma ita ta rike Mu’azzam saboda haka kanina ne”
Baba Ɗanjuma ya ce”Kwarai ma da gaske ba wanda ya isa ya ce kai ba Yayan Mu’azzamu ba ne, suna tafe ya na ta bashi hakuri shi kuma ya na faman saukar da zuciyarsa Mu’azzam shi ya yi saurin yin gaba ya je ya gayama Inna abin da ke faruwa ko kafin su Mansoor su shigo labari ya kawo cikin gida tunda su Baba Sani tun a tsakar gida suka fara mangaganun Yaya Danjuma na ɗaure ma Mansoor kugu yana ma mutane rashin mutumci a gari da ko su ya’yansu ba sa aikata irin shi.
Gaje ta taɓe baki kafin ta ce”Da an yi mgana sai ace ya na da bakar zuciya ga shi ba ka isa ya ganka ya gaisheka ba a wulakance sai dai yace wai barka.”
Suna cikin mganan Baba Ɗanjuma ya shigo rike da Mansoor su Gaje suka gaishe shi ya amsa kai tsaye ɗakin Inna Meri ya wuce da shi ya na kiran ta kamar yadda ya saba.
“Meri meri, ina Merin take ne?
Su Baba Sani da matansu suka bi shi da kallo Baba Ɗanlami ya nuna Yayan nashi lokaci ɗaya yana fadin “Ji be shi, yadda ya ke rawan jiki da yaron nan na tabbata ko Auwalu baya yi ma haka’
Magajiya daman na cikin ɗakinta tana sallah tana sallamewa ta fito tana faɗin” ko Auwalu da ya haifa baya masa son da yake ma agolan nan da Meri ta zo da shi gidan nan Ɗanlami, yanzu haka su yana nan nan da su amman Auwalu bai san ma in da yake ba sai can in ya ga bai ganshi ba ya fara ma mutane faɗan wai Auwalu ya koyi yawon dare, to ai gwara ya koya tunda bai iya jan sa a jiki ba sai Agolan da ba jininsa ba.”
Baba Danlami ya ce”Magajiya lamarin Yaya Danjuma fa akan agolan nan na Meri sai Allah kawai, in muka yi mgana sai ya ga kamar muna nuna ma yaron bambamci ne, kuma mu tsakani ga Allah gaskiya muke gaya masa sai ya rika nuna mu ba mu san girman Amana ba, kuma sai ya rika nuna wai yaron maraya ne.” Magajiya ta taɓe baki kafin ta ce”Ai ga shi nan ya za me ma Agola uba ya kuma maida ƴayan sa marayu”
Duk kuma manganganun da suke yi a kunnen Inna Meri da Baba Ɗanjuma, dake kofar ɗakinta saman tabarma.
Hatta Mansoor ɗin da Mu’azzam suna zaune, Bintu da walida dai suna cikin ɗaki tare da su Amina da ba su jima da dawowa daga gidan ba.
Kan Mansoor na kasa ya na huci Inna Meri ta cire tagumin da ta yi kafin ta ce”Ni na rasa yadda zan yi da yaro nan mallam, nasihan nan ko ɗazu muna tafe a hanya sai da na yi masa, kai dai Baban inna kana son kowa ya rika kama sunanka, to ka sani ba ka san bakin wani ba in wani ya yi maka baki ka lalace ba ruwana.”
Baba Ɗanjuma ya sausaauta murya yana faɗin” ki daina faɗin haka Meri yarinya ta ne in ya ƙara girma zai daina in sha Allahu, ki zuba musu abinci su ci ko sai mun dawo salla ne?. Ya faɗa ya na kallon samarin nasa guda biyu, Mu’azzam ya gyaɗa kai shi ko Mansoor bai yi mgana ba.
Inna Meri tace”Sai kun dawo domin ban jima da yin talge ba.”
Tunda daman tana da sauran miyan kukan jiya sai ta ce bari ta tuka tuwo.
Su Amina sai bayan mangriba suka dawo gidan daga can bolara gidan kakaninsu Mu’azzam bai je ba sai su kaɗai suka je su ka kwana biyu suka dawo. Da suna nan Amina ce babba ita za ta yi mata komai kafin ta dawo, tunda daman ita take bari a gidan in ba ta nan saboda ita Amina ta gama sakandiri ba kudin da za ta cigaba da makarantar.
Duk faɗan da aka yi ma Mansoor bai amsa ko ɗaya ba kansa na kasa yana sakin huci har aka kira sallar isha’i baba Ɗanjuma ya kara saka su suka yi alwala suka koma masallaci. A na idarwa ya taso zuwa gida suna zuwa kofar ɗakin Magajiya suka ga Auwalu na zaune na cin tuwo ya yi butu butu da kayan jikinsa tunda akwai hasken aci bal bal din da Magajiya ta kunna.
Baba Ɗanjuma ya kalle sa kafin ya ce”kai Auwalu yau ina ka je ban gan ka ba.?
Auwalu na sosa kai ya ce”Mun je aiki ne Baba.” Kafin Baba Ɗanjuma ya yi mgana Magajiya ta tare shi da cewa”Ina ruwan ka da in da ya je tunda baka damu da shi ba, ai kana da makwafinsa Meri ta kawo maka Agola sannan Habiba ta mutu ta bar maka ɗan so duk duniya ba ka ganin kowa a gabanka sai yara nan guda biyu, ayi dai mu gani in tusa zata hura wuta.”
Mansoor na ganin haka shi baya juran ganin magajiya ma yi ma Baba tijara ya sa ya tasa Mu’azzam gaba suka shige bangarensu.
Suka bar Baba Ɗanjuma na faɗin “Ki ji tsoron Allah magajiya kin ɗaure ma yaron nan kugu ya ki karatu na bokon tun tuni ya daina zuwa haka na arabin ma, shi zai yi takaici nan gaba ni dai Allah na gani na fita hakkinsa kuma maganar Baban Inna da kike yi ni fa na karɓo shi amana wajen danginsa ba wai domin sun gaza wajen rike shi ba, sai domin ina so na samu ladan rikon maraya. Kuma ni ba na tuna bambamci tsakanin ya’yana duka ɗaya suke a wajena ruwan ki ne, ki saka tunanin haka a ranki ko ki saka ina nuna bambamci Ubangiji na sama na kallon komai.”
Da haka ya juya ya wuce ya barta tana faɗin”In da ka biya mishi kuɗin makarantar me zai hana shi zuwa? Ai ƴaƴan so dai su je su yi karatun mu ga sun zama shuwagabannin ƙasar nan.’
Inna Meri na kofar ɗakinta tana kwashe tuwo sai da ta yi dariya.
Duka ƴaƴan ta makarantar Gwammati suke yi. Su Amina kuma dangin mahaifiyarsu su ke tallafe sda manyan bukatunsu, ita dai ta na ɗauke mu su kananun da ba’a rasa ba da aikin da take yi a gidan Hajiya Fatima Dabo da shi take taimakon kanta da mijinta da ya’yanta amman sai Magajiya da sauran matan gidan su ke ganin kamar a kan ta da Ƴaƴan ta Mallan Ɗanjuma ya tare ita da ɗanta Mansoor da mutuwa ta yi sanadiyar auranta da Danjuma da ko a mafarki ba ta taba tunanin haka ba.
Babu amfanin zama ka yi ma wanda ba zai Fahimce ka bayani ba, tunda aka auro ta tazo garin nan tasan magajiya fitinanniya ce, kuma ba ta da kirki in da tana da kirki ai ba sai an aurota ba za ta iya riƙe ƴaƴan mijinta gam a hannunta ba tare da sai ita an aurota saboda ta zo ta riƙe ƴaƴan matarsa Habiba da Allah ya yi mata rasuwa ba.
Ta rasu ta bar ƙaramin yaro ɗan shekaru uku da wani abu duniya.
“Mu’azzam..”
Page 11
A Jihar Gombe a kafatanin manyan unguwannin da suka zagaye anguwan Arawa da ma nesa da anguwan da kuma waɗanda ke gabas zuwa yamman da su ba wanda bai san da zaman gidan marigayi salihu wanzam ba, wanzancin gidan ba haye ba ne gadon shi suka yi, abun sai yake bin jini, in uba ya gada sai ya gadar ma ɗa, ɗa ya gadar ma jika jika ya gadar ma jikan jikan to a haka tushe da asali gidan Wanzamai ya fara.
Inna Mari ta tsinci kanta da aure a gidan wanzamai mai cike da tsohon tarihi tun bayan rasuwar mijinta na farko, Inna Meri mai suna Maryama ba’arata daga shiyar kasar gida ta Argugun ta fito daga cikin wani yanki na garin Argugun ne, kuma duka danginta da ahalinta arawane sai dai mahaifinta ya rasu sai ta tashi tare da mahaifiyarta wacce a ke kira Inno soro.
Mallam Ibrahim sufi mutumin kwami ne karamar hukumar dake jihar Gombe a arewa maso gabashin Nageria. Mazaunin hedikwatan mallam Sidi dake garin kwami.
Kuma ya kasance manomi ne kuma mai sana’ar kamun kifi, tunda mutanen garin Mallam Sidi sun fi karfi a noma da sana’ar kifi tunda suna da ruwa sosai a garin.
A dalilin sana’arsa ta kifi ya sanya yake da mu’amalan arziki da mutanen argugun kuma yana zuwa garin sosai ta sanadin wannan mu’amalan Allah ya haɗa auran mallam Ibrahim da meri wato Maryama.
Ta baro garinsu shiyar Argugun zuwa garin mallam Sidi yan’uwan Ibrahim suka zame ma Meri uwa da uba da dangi gabaɗaya.
Uwa uba kuma mijinta na sonta kuma ya na tattalinta sannan ita kanta Meri mace ce mai alheri da maida kowa nata shi ya sa ta kasance a bar son kowa suka riketa kamar ƴar su, duk da shima ba shi da iyaye amman yana da kanne da yan’uwa.
Duka duka auransu bai kai shekaru biyu ba ta haihu ta samu ɗa namiji sai aka sanya ma sa sunan mahaifin Meri wato Mansoor, shi ne silan da Meri take kiran Mansoor da suna Baban Inna, a farkon rayuwarta ba ta taɓa tunanin wata rana mutuwa za ta yi sanadin rabata da wannan rayuwar da take ciki ba, ta zama yar garin mallam Sidi sai dai in ta je gida ziyara da ganin ƴan’uwa kowa sha’awarta yake yi ganin ta kowani Fanni ta samu jin daɗin rayuwar da kowacce mace take fatan ta samu.
Sai dai kash ita mutuwa ba ruwanta da jin daɗi da zaran lokacin ka ya yi sai ka tafi.
Mansoor na da shekara biyar a duniya Mallam Ibrahim ya rasu sakamakon kayar kifi da ta makale masa ya yi ta amai dare zuwa safe an yi an gama, Meri ta yi kuka kamar ranta zai fita ba abin da ke kara saka ta kuka sai in ta ɗaga ido ta kalli Mansoor mai kuruciya da kananun shekaru da bai san komai na rayuwa ba har ya zama maraya, yan’uwanta sun zo har akayi bakwai sannan Inno soro ta zauna tare da ita har akayi arba’in ta so ta tafi da Meri can gabanta ta ida sa takabanta sai ƴan’uwan Ibrahim suka hana suna kuka suna rokon Inno soro ka lda ta raba su da Meri da Mansoor su kaɗai suke gani su tuna da ɗan uwansu Ibrahimu.
Sai inno soro ta tausaya musu kuma ganin ba abin da Merin ta nema ta rasa sai ta bar ta a nan ta koma argugun, Allahu akbar Allah mai tsara komai yadda ya so a hanyarta ta komawa gida har ta sauka a garin argugun ta samu a kori kuran dake ɗaukan mutane zuwa cikin kauyakun su to anan ajalinta ya sauka suka samu hatsari nan take Allah ya yi ma Inno soro rasuwa
Meri ta yi kamar ta haukace ga rasuwar miji ga ta uwa abun sai ya yi mata yawa dole ta shirya ita da Mansoor da Yalwar kanwar Ibrahim suka tafi can har aka yi bakwai da farko Meri ta so ta yi zamanta a garinsu ne sai 6an’wan ibrahim suka ce ko bayan kasa ya shafe idanuwan Ibrahim ba za su bari Iyalansa su rasa mafaka ba, da roko da ban baki kawun Meri mai suna Surajo ya amince ya ba su Meri da ɗanta Mansoor suka dawo garin Mallam Sidi da zama a kuma cikin dakin mijinta suka riketa ita da ɗanta. Bayan ta fita takaba saboda halin rayuwa duk da suna kokari a kanta ba za ta ce ta zauna a haka ba.
Sai ta fara sana’ar cikin gida saboda dogara da kai ba domin yan’uwan Ibrahim ba su barta ta neme wani abu ta rasa ba amman ai ba zaka zama a kwance komai sai an dauka an baka ba a kallah dai kai ma a ga kana wani abun domin taimakawa.
Ta zauna da su na tsawon shekara ɗaya har Mansoor ya fara makaranta fimari anan cikin garin Mallam Sidi. Tun tana garin Mallam Sidi a ke kiranta da Inna Meri, saboda ita Innar kowa ne yara da manya kowa nata ne kyauta da Alherinta ya sa ta ke zaune da kowa lafiya
Mansoor kuma ya na ganin gata saboda su na ji da shi suna kallonsa kamar makwafin ɗan uwansu Ibrahimu ne, tun Mansoor ya na ƙaraminsa Inna Meri ta fahimci cewa ya na da bakar zuciya da kafiya ga naci ko faɗa ya haɗasu da yara sai ya yi kwanaki bai bar mganar ba, tun mahaifinsa na da rai in ta yi mgana sai ya ce zai bari yarinta ne.
Ko ita ce ta dakesa sai ya kame a waje ɗaya yana huci da kumburi kamar wani mai Aljanu in za ta kara masa sai ƴan’uwan uban su hana su a tunaninsu yarinta ne ya na girma zai daina sannan ga shi da fitina komai shi a wajensa na fitina ne, saukinta ɗaya suna tare da masu kaunar su shi ya sa abun sai bai cika damunta sosai ba sai da kaddara ta sake jefa ta a wata rayuwar sannan ta san illar halayen Baban Inna a wani muhallin.
Gaddaafi Ɗanjuma wanzan. Ya kasance wanzamin dake yin wazanci a tsakanin kauyen su na karamar hukumar kwami saboda sunan da gidan su ya yi, ya sa duk tsukin nan suna zuwa cire beli ko kaciya ko wani abu da ya shafi kuna suna ba da maganin gargajiya sai a samu dacewa. To Ɗanjuma ya kasance wanzamin gidan su Ibrahim Sufi sannan har shayi ma shi ke yi ma yaran gidan in aka haife su, Mansoor ma shi ya yi masa shayi lokacin da ya cika shekaru uku, sannan akwai abota tsakaninsa da Ibrahim tun ya na raye, ya na siyan Kifi a wajensa akwai dai mu’amala mai kyau domin hatta Inna Meri ta san shi, har bayan rasuwan Marigayi Ibrahim in ya shogi garin yana zuwa ya ganta har ya yi ma Mansoor kyauta baya dai zuwa hannun rabbana.
Tun Meri ba ta fahimci akwai wani abu a zuciyar Ɗanjuma ba har su Yalwa suka fahimta sai ba ta ɗauki abun da gaske ba, tunda ta san matansa biyu a lokacin ashe abunda ba ta sani ba ɗaya daga cikin su Allah ya yi mata rasuwa ta rasu ta bar Ƴaƴa uku mata biyu da ƙaramin yaro namiji.
Kuma ta san hakane bayan Danjuma ya gama zagaye zagayensa ya fito ya sanar da Inna Meri manufarsa na son auranta domin ta taimaka ta riƙe masa yaransa duk da yanzu suna hannun dangin ita matar tashi ne, amman ya fi son shi ya rike ƴaƴansa da kansa.
Bai ɓoye mata komai game da labarin matarsa ba wato uwargidansa Magajiya kenan. Fitinanniya ce mara kirki, ta yi rantsuwan ba za ta rike masa ƴaƴa ba nata sun isheta har ga Allah da farko Inna Meri ba soyayyar Ɗanjuma ya sa ta amince da auransa ba, sai illah tausayin yaran da aka mutu a ka bari tunda yace har da ƙaramin yaro dan shekaru uku da wani abu da ba ya yarda da kowa, Sai ta juya ta ga itama marayan da aka mutu aka bar mata ɗa na kowa ne ba ka san wanda zai rike maka na ka ba watarana bayan kasa ta shafe idanuwanka ba.
Ba ta yanke hukunci ba sai da ta yi shawara da yalwa ita kuma sai ta yi mgana sauran ƙannen Ibrahim wanda acikin su ashe akwai wanda ya so ya auereta sai bai furta ba ganin kamar Inna Meri ta nuna ra’ayinta a kan Ɗanjuma saboda rike marayu sai ba su hanata ba saboda in dai kyawun hali ne da hakuri da kawaici da sanin ya kamata Danjuma ya cancanta tunda sun san shi tun ya na matashinsa kuma gidansu babban gida ne mai kunshe da tarihi. Sai su ka ba ta damar ta yi zaɓi cikin guda biyu ko kanin ibrahimu mai suna Muftahu ko Ɗanjuma ita kuma sai ta bar ma Allah zaɓinsa sai taji tafi natsuwa da auran babba wanda ya mallaki hankalinsa kansa tunda a lokacin Muftahu saurayi ne bai taɓa aure ba, ƙannen nasa maza uku ne Karimu ne babba sai yakubu yalwa sai muftahu shine ƙaramin su daman Ibarahimu ne babban su. Karimu ne ya yi aure da matarsa acikin gida yalwa ma ta yi aure nan makota da su, sai yakubu da shi ba agarin yake kasuwanci ba yana garin bauchi ne kuma shi bai wani damu da zumunci ba sai ya jima bai zo garin ba. Ita kuma Inna Meri sai ta yi duba da gwara ta auri Ɗanjuma ko bakomai Allah zai ba ta ladan rike marayun da suka rasa uwa a ƙananun shekarunsu.
Lokacin da ta gaya musu zaɓinta ba wanda ya nuna bai ji daɗi ba sun yi mata fatan alheri yalwa ce ma ta yi ta kuka tana faɗin za ta yi nesa da su Inna Meri tace suna tare ina nisa tsakanin garin mallam Sidi da Gombe za ta zo itama ai nan gidansu ne zata rika zuwa ta na ganinsu tana kuma kawo musu Mnsoor. Tunda akwai kyakyawan alaaqa da fahimta a tsakaninsu shi ya sa ba za su iya raba ta da Mansoor ba amma sai dai Ɗanjuma ya ba su tabbacin shima Mansoor ɗansa ne kuma yayi alkwarin yadda suka ba shi Amana to zai kula da amanar Mansoor har karshen Numfashin sa, sun kuma aminta da shi sai suka bashi Amanar Inna Meri tare da Mansoor ba daɗewa aka yi auran Inna Meri ta bar garin Mallanm Sidi tana kuka yalwa da Marliya matar karimu suna kuka sula kuma rakata har Gombe a ɗakinta na gidan Wanzamai.
Tun a ranar sula san Meri ta shigo wata rayuwar da ba ta saba gani ba, ba wanda ya karɓe su a gidan nan sai Harira Magajiya kuwa sai bala’i ta ke yi tana zage zage tun a ranar farko Inna Meri ta san sai ta ninka hakurinta kuma ba ta damu ba tunda Danjuma ya gaya mata komai bai rufe ta ba,
Abun bakincikin su ganin Inna Meri ta zo da yaro shikenn Magajiya ta rika sakin habaicin Ɗanjuma da kwashe kwashe ya je ya kwaso wata kuma mai ɗa ta zo musu da Agola acikin gida, kafin su Yalwa su tafi sai dai suka kara jadaddama Inna Meri hakuri da kauda kai ta ce in sha Allahu zata zauna da kowa lafiya suka rabu suna kukan sabo Mansoor kuma sai jin daɗi yake yi a ganinsa kamar irin sun koma sabon gida ne sai da su yalwa za su tafi ya saka kukan sai ya bi su dakyar aka lallashe sa sai da Danjuma ya ja shi shago ya siya masa alawa sannan ya yi shuru amman ya yi ta kuka ya na numfaashin zuciya.
Inna Meri ta shaida ta bangaran Miji ta gama dace sai dai ba za a haɗa samun Ibrahimu da na Danjuma ba acan ita kaɗai ne nan kuma ga magajiya da sauran yara to abubuwan dai sai godiyar Ubangiji kawai, sannan tun ranar farko da ta shigo gidan nan take hakuri da kowa kuma ta ko yi zaman lafiya da kowa in ka yi mata sharri sai ita ta saka maka da Alheri ba mai sonta a gidan hatta kannnen Danjuma su Ɗanlami kenan Mansoor kuma sai suka sanya masa suna Agola ba acikin gida ba har a waje shi kuma sarkin zuciya ko da yaushe cikin fada suke a dake shi kuma ya fara zuciya yana cika ya na batsewa bata mgana sai dai Danjuma duk wanda ya taɓa Mansoor sai inda ƙarfinsa ya ƙare kalamansa kenan yaron nan amana ne a wajena don Allah ku tayani kula da amanarsa.
Tun daga lokacin sai suke ganin kamar ya fifita Agola sama da ƴaƴan sa na cikinsa.
Tunda sanda inna Meri ta zo gidan ya’yan magajiya uku ne, Auwalu ne babba sai Jummai sai Zuwaira ashe ma alokacin tana da wani ƙaramin ciki amman cikin yara nan ba mai kallon Mansoor a komai sai a matsayin Agola, ko waje ya fita sunan da ake kiran shi kenan tunda sun gama gayama kowa shi ba ɗan gidan su ba ne Agola ne.
Ko ya dawo da kuka lallashinsa Inna Meri take yi sai taga ya damu ba shi da wani ɗan uwa na kusa da shi, sai ta yi tunanin gwara ta yi ma Danjuma mgana ya dauko mata yaran marigayiya ta haɗa su da yaronta ta rike kila su su karɓesa a matsayin ɗan uwa.
Yana dawowa ta yi masa mgana sai ya ce daman suna ransa ita ya ke jira kada taga kamar daga zuwanta ya takura mata jin ita da kanta ta ke son a ɗaukosu sai ya ce ta shirya su tafi tare su taho da yaran nan, Haka ko akayi tare su ka je can Bolari gidan su Habiba inda yaran suke, Amina ce babba sai Halima sai ƙaramin yaron Mu’azzamu.
Ganin kirkin Inna Meri da yadda ta nuna zata rike yaran sai Mahaifiyar Habiba ta amince ta ba su yaran tun acan gidan Mansoor ya rike hannun Mu’azzam a fuskarsa kaɗai Inna Meri ta ga ya yi farinciki, sai taji daɗi acikin ranta saboda ita macece mai son yara. Ta dauko su Amina ta rumgumesu kamar itace uwarsu ba su taɓa maraicin wani abu ba, Mu’azzam kuma ya ke ganin gata saboda karami ne shi Inna Mari ta rene shi har ta sanya masa suna wato Ɗn Inna shi kuma Mansoor tana kiran shi Baban inna.
Tunda Magajiya ta ga Inna Meri na riƙe su Amina kamar ita ta haife su sai ta fara bullo da rigima yau ta ce wannan gobe ta ce wannan a irin haka ne ta tada rigima sai da aka raba girki kowacce sai ta koma yin nata saboda a zauna lafiya, Ita a tunaninta kamar Baba Ɗanjuma na cutar da ita ba ta duba da cewa Ƴan uwan Habiba na yi ma yaranta sako itama daga su Yalwa tana samun alherai ma su yawa sai take rage ma Baba Danjuma wasu hidimdimun, sai da aka raba girkin Magajiya ta gane kuranta tunda a baya da girken ke haɗe komai Meri ta barshi a na su gabadaya da aka raba kuma sai ta ja bangarenta ita da ya’yanta.
Ba ta shekara a gidan ba ta samu ciki lokacin Magajiya ta haihu an samu Namiji Saddiqu, ita kuma sai ta haifi mace aka saka mata suna Fatima suna kiranta Bintu, sai ta haɗe kan Ƴaƴanta gabaɗya saboda ba ta nuna bambamci suma kuma yaran ba su da wata uwa da ta wuce Inna Meri.
Ko can gidan kakkaninsu suka je ba su da labari sai Inna ta ma na kaza tana mana kaza sai iyayen Habiba suka samu salama da cewa su Amina sun samu wata uwar kamar Habiba sai su ma suka maida Inna Meri kamar ƴa duk wani abunda za’a yi a gidan tare da ita a ke yi sannan in yaran suka samu hutu suna zuwa can su yi musu Hutu shima Mansoor tana tura shi can wajen su yalwa ya gaishe su.
Tana da cikin walida Muftahu ya rasu har ya yi aure ba jimawa ciwon ciki shima daga dare zuwa Safe, Inna Meri ta yi kuka nata mutuwan mijin kawai take tunawa, duk da shekarun sun ja amman ta kasa mantawa, sannan ga halin rayuwar da suke ciki samun Baba Ɗanjuma ya ragu ga iyalai da hidimdumu Allah ma yasa su Amina suna samun taimako daga dangin Habiba shima Mansoor daga can mallam sidi ana yi masa saƙo Yakubu dake bauchin in ya zo can kwami yana ba da saƙon kayan sawa masu kyau sai Yalwa ta aiko yaronta da shi ko kuma ita ta zo ta kawo masa da kanta.
In kuma aka kawo kayan Mansoor zai ɗauki kaɗan sauran ya ba ma ƙaninsa Mu’azzam in Inna Meri ta ce sun yi masa yawa sai ya ce”In ya ƙara girma sai ya saka Inna.” Tun suna kananunsa kaunar junnasu yake cikin jininsu duk da Mansoor ya girmi Mu’azzam kusan da shekaru biyu da wani abu, amman ji yake yi da shi kamar abokinsa duk abin da ya samu sai ya raba shi biyu ko uku ya ɗauki kashi ɗaya kashi biyu kuma yace na Mu’azzam ne.
Kuma ya na faɗa da duk wanda yace Mu’azzam ba ƙaninsa ba ne, Saboda su Jummai suna yawan gwaba masa magana da cewa Mu’azzam ba ƙaninsa ba ne shi kuma sai ya ce” ƙanina ne saboda innata take ke rike da shi, in ƙanin ku ne me ya sa magajiya ba ta rike shi ba?
Saboda fitinasarsa ya sa suke shayin masa mgana ya ga dama ka zage shi ya rama kuma ba wanda ya isa ya taɓa Mu’azzam ko a makaranta yanzu sai aga tashin hankali.
Yadda ya ke kafa kafa da shi ko su Bintu da ke mace baya yi musu irin haka Baba Ɗanjuma daɗi ya ke ji in ya ga haka sai ya ce ko bayan raina Meri Mu’azzamu da Baban Inna su ne za su rike mini iyalaina.
A can waje kuma bangaren abokai in kana son abota da Mansoor sai ka yi abota da Mu’azzam shi ya sa Mu’azzam ya taso ba shi da abokai sai abokan Mansoor, Mansoor ma ba shi da abokai sai abokan Mu’azzam an sha faɗa da tsiya sai an fara abota abu kaɗan zai haɗasu Mansoor ya watse abotan su Nasir ne abokan gasken da ko an yi faɗa bayan kwana biyu bayan an gama gaba za’a zo a shirya. Sannan islamiyar su ɗaya kuma boko ma duk tare suke sai abotan su ta jima sannan ko an yi tsiya bayan wani lokaci za’a haɗu ko da a filin kwallo ne, da farko Mu’azzam ne ya ke son ƙwallo Mansoor kuma shi kwallo ba ta gabanshi, Saboda Mu’azzam ya fara zuwa kallon ƙwallo har ya fara bugawa duk da shi ra’ayinsa in ya gama makaranta soja yake son zama shi kuma Mu’azzam ya ce yana son ya zama ɗan kwallon kafa.
Amman a fili Aji in yana buga balla sai ya baka mamaki ya ƙware in dai ya na fili sai ya buga kwallo a raga shi yasa lamba goma yake bugawa tun yana matashinsa Mu’azzam kuma dake son ƙwallon har cikin jinin jikinsa bai iya taka kwallon haka ba
Su Nasir su yi ta faɗin “Aji da za ka sanya ra’ayin ka a kwallo da kila kai ma watarana ka iya zama Ahmad musa ko mu ji ka a turai ka koma buga kwallo da irin su Muhammad sala” in suka faɗi haka sai ya gwasale su da cewa”Ina meye wani ƙwallo kuma? Malamai ni fa Soja ne, Sojan kasata in sha Allahu.” Kwatan kwacin yadda Mu’azzan ke son zama ɗan kwallon kafa kwatan kwacin yadda Mansoor ke son zama Soja, kowanne bawa daman yana da na shi burin da mafarki sai dai daman ba duka mafarkan mu ke zama gaskiya ba wasu suna zama a raye wasu kuma har kuma ga Allah suna matsayin mattatu ne.
A komai na Mansoor ya sha bambam da na Mu’azzam a ra’ayi da hallaya Mansoor yana da faɗaa ga zuciya da naci sannan ga riko a cikin kwakwalwarsa har wani waje garesa na musammn kamar blacklist ko sau ɗaya wani abu ya taɓa haɗa ku to ya kulla da kai kenan har gaban Abada. Saɓaanin Mu’azzam ba ruwan shi mai hakuri ne sannan ba shi da fitina shi kuma mai son zaman lafiya ne amman Mansoor bai ƙi gayyar duk ta watse ba, Allah ya sa ma kada a zauna lafiya tun yana ƙaraminsa yan gidan wanzamai suka sa ya fahimci ba nan ne asalinsa ba saboda tun baya gane kalmar agola har ya fara sanin ma’anarta.
Yasan kan tsiyatu kala kala sannan komai na shi na daban ne, gaisawarsa ma ba irin ta kowa ba ce a cewarsa Ina yini ba gaisuwa ba ce sai dai barka da yamma ko barka da safiya in ya gaisheka a haka ruwanka ne ka amsa ko kar ka amsa shi dai ba zai ce ina yini ko ina kwana ba, shi ya sa ake ganinsa wani mara kunya kuma mara tarbiya.
Da gaske ya ci sunan shi na Aji saboda mai Ajin ne ya na da kamewa a kan karan kansa yana yin komai cikin Aji ne da isa, gaye ne da ba ya son reni ko ƙankani. Shi y ssa koda yaushe maganarsa da su Nasir su zama masu aji su rika abun masu Aji duk da yana da son shiga mutane amnan kuma ya iya miskilanci za su yi ta abubuwan su ba ya saka musu baki sai ya ce su na abu kamar marasa aji, sannan shi mai ra’ayin ya yi aure da wuri ne saboda matarsa ta rika taimaka ma Inna sannan yana so ya ga ya taso da ya’yansa kamar matsayin abokan juna sabanin Mu’azzam da yake so sai ya mallaki wani abu da zai rike kansa da iyayensa tukunnah.
Ko magana ake yi sai Mansoor ya ce shi fa yana da gadon gonaki a garin su, su zai saida in ya tashi aure, sai ake ganin kamar abun nashi wasa shirme shirme shi kuma bilhaqqi a kan gaskiyarsa yake yi.
Dukkansu wata makaranatar Gwammati ta cikin gari su ke zuwa rayuwa ta yi wahala tunda Baba Ɗanjuma girma kuma yazo, sai a hankali ba domin Inna Mari macece mai tsayawa ga kanta ba da ai tuni rayuwarsu Mu’azzam ta jima da sauyawa sannan kuma tana samun taimako daga bangarori da dama ko daga can garin su Argugun ana yi mata sako itama ta kan je in wani abu mai bukatar zuwanta ya ta so.
Ko bayan haihuwan Walida ta je gaisuwan Kawu Surajo kuma ta jima acan sai dai ta dawo ta ga Magajiya ta sauka an samu Mariya daman ta bar ta da ciki.
Da ta dawo ne tafara sana’ar cikin gida na saide saide ta na samun rufin asiri to abubuwan sai a hankali da an tarfa jari sai ya darkane, kuma ga shi acikin gida ba zaman lafiya kullum fitinar Magajiya na yau daban na gobe dabam kuma har kwanan gobe ba’a taɓa jin Inna Meri na tanka in tanka da ita ba shi ya sa ba a wajen Baba Danjuma har a makota kowa ya shaida hakuri tsabar shi wajen Inna Meri mace mai kauda kai da yakana babu ruwanta mai rama Alheri ko da mutum ya yi mata sharri.
Bintu ce ta ɗauko irin fitinar Baban Inna itama an sha fama da ita acikin gidan ita da baban Inna ba’a daga musu yatsa su bar shi haka sai sun karya shi, ga su Amina da suke manya amman sai Bintu dake da karancin shekaru ta tare musu mgana acikin gida Inna Meri in abun ya isheta sai ta yi tagumi tana faɗin”Ni wannan fitina na yaran nan na rasa in da suka gado shi, ni dai Allah ya shaida ba ni da fitina amman Allah mai ganin dama ya bani fitinannun ƴaƴa guda biyu Allah dai ya ƙara shiryamin su.”
A koda yaushe kalamanta kenan, to yau da gobe bata bar komai ba dole rayuwar ta yi wahala da ya sa Inna Mari ta nemi shawaran Baba Ɗanjuma ya barta ta nemi aikin da za ta rika yi a cikin gidajen masu kuɗi suna samun abun rufin asiri saboda Aminci da yardan dake tsakaninsu ya sa ya amince mata, Harira ta yi mata hanyar samun aiki gidan wata mata ma’aikaciya ce mijinta ma ma’aikaci ne sai dai aikin kula da yara ne acikin gari gidan su yake, nan Inna Meri ta fara aiki kuma albashin mai tsoka ne sai dai dalilin mazan dake gidan sun yi yawa ya sa ta ijiye aikin gidan tana ganin ita uwa ce bai dace ta zama mai aikin mace ita kaɗai acikin maza ma’aikata sama da biyar ba sai ta ga aikin bai bata sha’awa ba ta ijiye.
Da kamar ma ta hakura tunda tana ta nema ba ta dace ba nan makotan su matar mallam Hashimu Dije ita ta yi mata hanyar aikin da ta ke yi yanzu a gidan Hajiyar shagamu. Tunda a baya kanwar Dijen ke yi sai kuma ta zo ta yi aure sai Hajiya ta ce a samo ma ta wata yar babba haka sai Dije ta yi ma Inna Meri mgana jin Hajiyar ce kaɗai a gidan zata riƙa zuwa da safe ta yi girki da gyaran gida sai kuma zaman kadaicin zata ɗebe ma Hajiyar ai da gudu ta amince
Kuma sai Allah ya haɗa jininta da na Hajiya za ta je da karfe 9 na safe ta yi share share sannan ta dafa ma Hajiya abinci sai kuma su zauna su yi ta hiran duniya da Hajiya.
Inna Meri na jin daɗin zama da Hajiya ba domin alherran da ta ke yi mata ba, a’a sai saboda ita ɗin mai kirki ce da sanin ya kamata, karfe 4:30 da rabi na yi za ta ce Inna Meri ta koma gida ta yi ma yaranta girki sannan kuma in za ta tafi sai ta ce sai ta ɗaukan ma yaranta abinci kuma wani kayan sawa na jikokinta za ta ce su Yadddiko su haɗo mata duk Inna Meri take ba ma wa, ta amince da ita sosai domin ta sha mata jarabawa kuma ta ga ba ta sameta da ko sata ko gulma ko dai wani mugun hali ba, shi ya sa Hajiyar kan zaunar da ita tana gayamata wasu abubuwa da suka danganceta itama Hajiyar tasan labarin Inna Meri da abunda ya barota da garin tsohon mijinta zuwa auranta da Danjuma da kuma ya’yan da take riko.
Tunda wani lokacin kamar asabar da Lahadi su Bintu na biyota in ta kore su sai Hajiya ta ce ta kyalesu mana ai tana son zuwan su saboda suna ɗebe mata kewa sannan ta na jin su sunan Baban Inna da Ɗan Inna Mu’azzam kenan shi ya kan rako Inna Meri kuma ya shigo ya gaida Hajiyar, amman Baban Inna sai dai ya tsaya daga waje, shi ne ma Hajiya ba ta taɓa gani ba.
Kuma Hajiya har gidan wanzamai ta taɓa zuwa Lokacin da Inna Meri ta zame ta faɗi a banɗaki ta samu targaɗe ta saka direba ya kawota har ɗakin Inna Meri ta gaisheta tana da kirki da hakuri ga kyauta fara aikin Inna Meri ba za ta iya kirga alherin Hajiyar Shagamu a gareta ba. Ta san ƴaƴan Hajiya guda uku ne kuma duka masu abun hannunsu Yaddiko dai ta yi aure kuma a babban family ta yi aure sai Alhaji Hamza da ɗan siyasa ne a lokacin ma ya ci sanata, sai wanda Hajiya ke yawan korafi a kan shi kabiru soja da ke garin Abuja.
Hajiya na yawan faɗin halinsa na taurin kai da rashin jin mgana Kakin Sojan dake jikinsa ya sauya masa hallaya ko Hajiya ba ta isa ta ce ya yi abu ko ya bar abu ba yana zuwa amman ba sosai ba sai dai Alhaji Hamza da ya kan zo duk daddare in bai zo yau ba, zai zo gobe Yaddiko ma ko da yaushe ta na tafe kuma suna kula da Hajiya tana da megadi da kuma direba ko da mjinta ya rasu ya’yanta sun ji ƙa rayuwarta da ababen more rayuwa.
Tana kaunar Jikarta Fatima da take kira Binta da sun samu hutu Hajiya na tafe kiran a taho mata da ita ta yi hutu a wajenta. Itama yarinyar na ƙaunar Hajiya shi ya sa ta ke yawan yin hutun ta a gombe tare da Hajiya.
Page 12
28 December, 2008
Da in ya zo a ƙofar gidan ya kan tsaya sai daga baya megadin gida wani Dattijo duk da mgana ba taɓa haɗasu bayan gaisuwa ba. Ranar shi ya leka yana ce ma Mansoor
” Ɗan Samari ai da ka rika shigowa daga ciki, kana jiran babarka taka zai fi da ka yi ta tsayuwa daga waje”
Bai yi masa gaddama ba duk da bai taɓa marmarin shiga gidan ba sai dai ganin yadda dattijon ya yi masa mgana cikin kyautatawa shi ya sa ya kasa ƙin karɓan tayinsa.
Dalilin da ya sa yake shiga daga bakin get wajen zaman megadin nan ya kan zauna ya jira har sai Inna Meri ta fito domin su koma gida tare, Islamiya tunda suka yi wannan tsiyar da Shamsu bai ƙara zuwa ba saboda wani shashi acikin zuciyarsa na gaya masa in har ya koma suka haɗu da Shamsu to ba zai kyalesa ba mafi zaman lafiya shi ne ya yi zaman sa har sai lokacin da ya ji zai iya ganin Shamsu ya wuce ba tare da ya kai masa naushi ba.
Boko ce kaɗai ya ke zuwa itama sabooda sun kusa fara Jarabawar fita ne, in ya dawo da yamman filin ƙwallo suke tafiya daga can nan yake yankowa ta nan. Su Nasir ma ba kullum su ke zuwa islamiyan ba can ya ke ganinsu a filin ƙwallo Mu’azzam kuma tsoron faɗan yayansa ya sa ba ya zuwa sai ranakun da babu makaranta da yamma.
Ko kwanakin karshen mako da suke zuwa da safe.
Yau ma zaune yake a saman bencin katakon da megadi kan zauna a kai ya sha iska yana sanye da wani yadi mai saukakkan kuɗi sai dai a goge suke tas, ya sha karin guga Kallo ɗaya zaka yi ma Aji za ka shaida da gaske ne shi ɗin Aji ne da kansa ba saƙo ba, kuma Ajin na shi ya kama kasa ba, hankalinsa na kan wayarsa ne ƙarama mai tocila ya na faman latsawa, yi yake yi kamar hankalinsa na kan abin da yake yi ne amman kuma ba akan wayar yake ba, yana can gefe in da yake hango yar matashiyar yarinyar nan da Inna Meri ta ce jikar gidan ce. Ta kofar falon da zai sadaka da falon gidan yake ganinta tana lekowa ta na kallonsa sai ta koma in ta ga kamar zai ɗago, ba yau ta fara haka ba tun daa ya fara shiga haraban gidan ya jira fitowar Inna Meri tana yawan leƙosa amman ba ta taɓa fitowa ba. Shima sai ya yi kamar bai ganta ba, alhalin duk lokacin da za ta yi wannan leken shima sai ya tattara hankalinsa a kanta. Yau ɗin ma nunawa ya yi kamar hankalinsa na kan latsa wayarsa sai da ya ji megadi na faɗin.
“Bintar Hajiya ki fito mana, kina leke tun ɗazu.”
Ba ta da yadda za ta yi tunda an ganta kuma har an kira sunanta, sai ta fito tana nokewa tana sanye da doguwar riga na abaya ta yafa mayafin rigar a saman kanta sai faman mirmishi take yi lokaci ɗaya kumatunta na loɓawa. Ta wutsiyar ido yake kallonta a ransa ya ce yarinyar nan akwai arhar fara’a da dariya, Ko ba’a yi mata mgana ba ita kaɗai ma sai ka ga tana mirmishi. Yana jin ta tsaye a kansa tunda ta Ƙariso shi kuma daman Megadi ya shige ɗan ƙaramin ɗakinsa ya barsu, shi kuma sai ya yi kamar bai san da wanzuwar mutum ma a wajen ba. Kamar daga sama ya ji maganarta cikin zaƙin muryanta da ya shaida ta tun a karon farko.
“Ya sunan ka?
Ɗagowa ya yi yana kallonta kamar yadda shima ta ke kallonsa hannayenta na bayanta tana juya jikinta yamma da kudu, lokaci ɗaya kuma ta na jifansa da mirmishinta da har gobe suke da tasiri a rayuwarsa.
“Ni? to ke ya sunan ki?
Cikin karaɗinta ta ce”Ni sunana Mimin Mimin Abi”
“Ni kuma Sunana Mansoor Aji..”
“Aji..?
Ta faɗa da sigan tambaya har ta na saka a yatsa a gefen bakinta, irin sunan ya ba ta mamaki sai da ta saka shi ya yi murmishi ta na da surutu da karaɗin magana kafin ma ya kara magana ta yi zaraf ta kara cewa.
“Wajen wa ka zo? wajen Hajiya?
Sai da ya girgiza mata kai kafin yace” A’a ni wajen Innata na zo.”
Cikin mamaki ta kallesa har da waro ido kafin ta riƙe haɓa ta ce” Inna Meri mai girkin Hajiya.? Sai ya gyaɗa mata kai, kamar wata babba sai ta kama baki tana dariya kafin ta ce”Laa wai daman itace maman ka? Kallonta kawai ya ke yi ba tare da ya yi mgana ba a ransa ya na faɗin yarinyar nan akwai bakin surutu.
faɗi ba’a tambayeka ba kenan shi fa bai tsareta da tambayoyi ba, amman har ta fara fesa masa ita Abuja take suna da Mommy kuma Abi ɗin su soja ne.
Sannan ta gama Jss3 yanzu za ta shiga Ss1 ne, labarai kala kala haka ta na tsaye take gaya masa shi dai ya yi kasaƙe kawai ya na jin ta kuma yana kallon bakinta.
“Kai ina ne gidan ku?
Kansa ya nuna kafin ya ce”Ni? Sai ta gyaɗa masa kai, cikin gajiya da maganar ta ya ce”Gidanmu ya na can da nisa” Ya faɗa lokaci ɗaya yana mikewa sai kawai ta ce”To ina ne ina so na sani ne”
Cikin ƙosawa ya ce”Ke can da nisa ne ba ki san hanyar ba.”
Sai ta rage fara’a sai da ya kalleta sai ya ji bai ji daɗi ba sai ya samu kansa da faɗin” Ba ki san gidan ba yana da nisa daganan”
Sai ta yi zaraf ta ce”Za ka kai ni wata rana na ga gidan ku? Saboda ta kyalesa ya saka ya gyaɗa mata Kai kafin ya ce”How old are u Mimi? Cikin zaƙin muryanta ta ce”I am 16 years old.”
Jinjina kai ya yi aransa ya na faɗin ba Shakka domin ya ga aikin yarinta.
Shima kawai sai ta sauya harshe tana tambayansa “How old are u?
Mamakinta ya kama shi har nuna kansa ya yi ta gyaɗa kanta sai lamarinta ya bashi dariya har sai da ya murmusa kafin ya ce”I am 20 years old.”
Sai ta washe baki kafin ta ce”Ka girme ni ashe.” mamakinta yake yi jin turanci mai kyau a bakinta, bai ɗauka haka Mimi take ba sai da ta dame shi da tambayoyi, har sai da ya gaji ya kalleta yana faɗin ” Kin cika tambaya Mimi, kamata ya yi in kika girma ki karanta aikin jarida.” Bai cika sakewa da wanda bai sani ba sai gashi ya biyema yarinya tana tambayarsa yana amsa mata. A haka har Baba Megadi ya fito ya gansu har sai da ya yi dariya kafin ya ce”Ka haɗu da gidan jarida da kanta, Bintar Hajiya akwai tamboyoyi ita komai so take sai ta sani.”
A ran Mansoor ya ce y gga alama amman bai yi mgana ba. A bakinta ya ke jin izifinta goma sha Bbyar cikin mamaki ya kalleta kafin ya ce”ki na zuwa islamiya ne?
Sai ta washe baki kafin ta ce”Uncle ɗinmu ke zuwa gida ya na koya mana, sannan Mommy tana yi mana karatu da safe kafin mu tafi school.”
Jinjina kai ya yi, shi ya ɗauka yadda take yar gata nan karatun addinin ba zai dameta ba, har fa sunan makarantar bokon da ta yi sai da ta gaya masa da sunan Yayyenta gidansu ya ji dai sunan khadija(Khadi) a bakinta har ya gaji, da labarin Abi ya siya mata kaza ya siya mata kaza kallonta kawai yake yi yana so ya ji ko a cikin ƙasan ran shi ta dame shi amman cikin ikon Allah bai ji ya gundira da jin maganar ta ba.
Har fa turkeshi ta yi wai shi ya sunan makarantar su? Ya faɗa mata bai yi ma ta ba har sai ya gayamata ya iya karatun Qur’ani?
Sai da tambayar ta saka shi dariya dai dai
Lokacin da Inna Meri ta fito cikin shirin tafiya ganin Binta tare da Baban Inna ya sa ta ce” Binta Kina nan ashe? Hajiya na can tana cigiyarki.” Tana ganinta da sauri ta nufeta ta riketa tana faɗin”Inna Meri wai wannan ɗanki ne?
Ta faɗa ta na nuna shi sai da tambayan ya saka Inna Meri dariya. Rike mata hannu ta yi kafin ta ce”Eh mana kuma bashi kaɗai ba ne ina da wasu ƴaƴan a gida.”.
Da sauri ta ce”To ina za ki je yanzu?
Ta ce gida zani Binta, kai tsaye ta ce”To nima zan bi ki ina so na je na ga gidanku ne” Ta faɗa tana kallon Aji da ya yi gim da rai kamar ba yanzu ya gama dariya ba.
Inna Meri ranar ta ga ta kanta, dakyar ta lallashi Mimi ta hakura amman sai da ta ce gobe za ta tafi da ita in dan ta zo, sannan ta yarda Inna Meri ta rakata har bakin kofar falom Hajiya sannan ta juya shi ko Mansoor har ya yi gaba a ranshi yana cewa yarinya nan akwai sai surutu da rigiman tsiya.
A hanya ya ce ma Inna yarinyar akwai surutu Inna Meri ta yi mirmishi kafin ta ce ” In da surutun ta yake burgeni ta bakin Hajiya akwai mgana mai amfani a bakin Binta duk abin da ka ji ta yi tambaya akansa mai amfani ne.
Sai shima ya yarda da maganar Inna Meri ta na tambaya ne a kan gaskiyan duk abin da ba ta sani ba, kuma take son sani har suka isa gida Inna Meri sai labarin jikar Hajiya ta ke bashi. Abun da ya bashi mamaki Inna na gaya masa Hajiya na son a bar mata jikarta amman tana tsoron ta yi magana uban yarinyar ba zai bata ba.
Cikin mamaki ya ce” Saboda mene Inna? Ba ita ta haife shi ba?
Inna Meri tace”Kai ma dai kayi maagana, shine babba ma amman kuma kamar ba shi da sauƙi ko kaɗan na taɓa ganinsa sau ɗaya fusakarsa ba fara’a sannan ya yi ta magana a sama sama ina gidan ya zo Ina cikin madafi ina jin Hajiya na yi masa faɗan kan dai wani abu amman harshensa a saman nata kuma naji ma da kunnena yana mata rantsuwan bazai yi abin da ta saka shi ba.”
Cikin Al’ajabi Mansoor ya girgiza kai bai sami zarafin mgana ba tun kafin ya gansa kawai yaji ya tsane shi me ya sa yana babba kamar sa bai san darajan mahaifiyarsa ba?
Inna Meri sai gaya masa take yi Hajiyar da kanta ta ke mata ƙorafin a cikin ya’yanta yafi ba ta matsala. Shi dai yana jinta amman bai yi magana ba sai dai acikin ransa sai da ya ce kuma ga shi Allah ya basa ƴa mai kyau da kaifin basira.
Tun Mimi na matashiyar yarinya kyanta ya ke a bayyane.
Bai taba tunanin in ta kara ganinsa za ta kama sunan shi ba sai da washegari ma ya koma gidan yana tsaye a haraban gidan ya ji ta ƙwala masa kira.
“Aji..”
Abun ya ɗaure mishi kai, ta kiran sunan shi cikin muryanta mai zaƙi fiye da yadda sauran abokansa ke kiransa.
Shima sai ya samu kansa da amsa mata har kuma itama ya kira sunanta.
“Na’am Mimin Abi ko?
Ta na yar dariya ta Ƙariso gabansa kafin ta ce”A’a MIMIN AJI dai?
Ido ya sakar mata ta na dariya Kumatunta na loɓawa take faɗin “Sunanka ya yi min daɗi ka bar min Please.”.
Ta faɗa cikin yar shagwaɓa har tana buga Ƙafafunta a kasa, a lokacin sai yaji kamar wani abu ya daki zuciyarsa da ya saka sai da ya saka hannunaa ya dafe jikin get ɗin gidan da yake tsaye har bai san bakinsa ya subuce wajen faɗin “Na bar miki daga yau kin zama Mimin Aji.”
Cikin jin daɗi ta ce” Thank you kai ma daga yau ka zama Ajin Mimi.”
Yadda take dariya sai ya ga fuskarta cikin fara’a da annushuwa mai kyau ne sannan ta fi kyau in tana mirmishi ko dariya.
Al’amarin alaƙar Mimi da Aji wani al’amari ne na Ubangiji shi dai kawai ya samu kansa da jin yarinyar a cikin ƙrjinsa sannan saboda ita baya fashin zuwa ya taho da Inna Meri alhalin a baya ba ko da yaushe ya ke zuwa su koma gida tare ba, saboda haka ya ya ye zuwa islamiya ko da yaushe yana hanyar GRA in an yi mgana sai ya ce ya je tahowa da Inna Meri ne. ita kanta Mimi za ta iya cewa Allah ne ya haɗa zukatan su waje ɗaya tunda ga ranar Hajiya har gajiya take yi da labarin Ajin Mimi. Tun Hajiya na ɗaukan abun shirme har dai ranar ta ce”Wai waye ne wannan Ajin ni Binta?
Mimi ta ce”Laa wai hajiya ba ki san shi ba? ɗan Inna Meri ne fa ? me dafa miki abinci.”
Hajiya ta ce”Au shi ne wani Aji? To ai bari Merin ta zo na ji waye wani Aji acikin ƴa’yanta ya na nemen ya ƙwacemin gwamnatina wajen Binta ba ta da magana sai ta shi.”
Haka ko akayi inna Meri na zuwa bayan sun gaisa Hajiya ta ce”Meri wai ni cikin Ƴaƴanki waye wani Aji da Binta ke yawan mganan shi, na ce ina ta san shi ta ce ni bansan shi ba ai yana zuwa gidan nan.”
Inna Meri na dariya ta ce” Mansoor ne Hajiya Baban Inna, bai taba shigowa ya gaishe ki ba ne shi ya sa ba ki san shi ba.”
Hajiya na yar dariya ta ce”To ni dai na ce waye kuma wani Aji? Sai ace masa ya shigo mu gaisa ya daina taremin yar jikata a waje bai zo ciki ya fara ganina ba.”
A lokacin ita Hajiya a wasa take yin maganarta Inna Meri na taya ta da dariya ta ce” Zan gaya masa Hajiya, ai sunan Aji abokansa ne ke kiran shi da shi.”.
Hajiya tace”Sunan banza ba, ga sunan shi mai daɗi.” Mimi na zaune a gefe ta cee”Hajiya Ajin ya fi daɗi wallahi.”
Hajiya tac e”To daman ke me kika sani? Har yanzu yarinya ce ke Binta.”.
Inna Meri na ta dariya Mimi ta tura baki tana faɗin”Ni ba yarinya ba ce.”
Hajiya ta kalleta tana dariya yarinyar da ko nono ba ta da shi sai kirgan dangi da ta fara har kuma yau ba ta fara Jinin al’ada ba, Murja har damuwa ta fara yi Hajiya ta ce ta kwantar da hankalinta wasu matan ba sa farawa sai sun kai sha bakwai kila Binta ta na daga cikin su ne.
A ranar Mansoor bai zo ba, ya je filin ball sun je buga wasa da yan anguwan Tudun wada, Mimi ta riƙa leƙe ba ta ganshi ba Inna Meri na mata dariya ta ce”Baban Inna ba zai zo ba tunda kika ga har yanzu bai zo ba.”
Mimi ta fara fushi har ta na cewa in yazo gobe ba za ta yi masa mgana ba tunda ya ce yau zai zo za ta ba sa wani labari mai daɗi.
Hajiya aka bari da lallashi abun ma sai ya koma ba ma Hajiya mamaki ko abinci ta ƙi ci a daran wai ta yi fushi da Aji.
Da safe da Inna Meri tazo hajiya ta ce”Meri maza ki aika Yaron nan naki yazo ya sakar min jika da ƙwarin da ya yi mata tun jiya nan da kika barta take fushi saboda bai zoaa tun jiya ba ta ci abinci ba.”.
Inna Meri ta rike baki tana faɗin”Ikon Allah.
Sai da Inna Meri ta lallasheta da cewa zai zo sannan Mimi taci abinci ta yi wanka da Hajiya ta so ta saka a kaita gidan Daddy Mimi tace ba inda za ta je sai ta kyaleta.
Hajiya ta yi tagumi kafin ta ce”Ni dai yau ina ganin ikon Allah ni Binta.”
Inna Meri na taya ta da dariya saboda su a tunaninsu yarinta ke damun Mimi a lokacin ba su taɓa tunanin Ubangiji ya ɓoye wani abu a tsakanin su ba. Kamar ko Mansoor ya sani da Yamma sai ga shi tare suka zo da Mu’azzam saboda ba makarantan islamiya daga filin ƙwallo suke yau Mu’azzam ne ya buga ƙwallo shi bai yi ra’ayi ba.
Daman ta yini leƙen waje tana ganinsu ta fita da gudu kamar ta kifa shi dai Aji sai dai ya ganta a gabansu tana haki da sauri yace”Bi a sannu kar ki faɗi ki ji ma kanki rauni.” Sai kawai ta harare shi da fararen idanuwanta
Dariya ma ta bashi da sauri ya ce”Me na yi ni kuma yau”
Cikin yarinyarta ta ce”Ba kai ne ba kai ne jiya ka ce za ka zo ba ka zo ba, sai jiran ka nake ba”
Ta na faɗa sai hawaye sai ya ji ya damu da sauri ya durkusa a gabanta yana faɗin”Afuwan Mimin Aji na je wasa ne jiyan nan.” Tana sharan ƙwallah ta ce”Jiya ma ban ci abinci ba, ko Hajiya ma yau ban yi ma mgana ba saboda ina fushi da kai.”
Mu’azzam na tsaye na kallon wani abu na faruwa kamar a shirin film sai gani ya yi yayansa ya kama kunni yana faɗin “I am so sorry Mimi Mimin Ajii..”
“Kin haƙura?
Sai ta gyaɗa kanta tana mirmishi kafin ta ce”Yau ka zo mu je Hajiya ta ganka sai da ta tambayi Inna Meri wai ba ta san ka ba.”
Dariyan maganarta ya yi sosai ya
na shirin mikewa ya ce”Haka za’ayi ranki ya daɗe tunda Hajiya ta ce ba ta sanni ba, ya zama wajibi ta ganni yau tunda haka Mimi take so.”
“Barkan mu da Yamma Anty Mami.”
Mu’azzam ya faɗa bayan ya duka shima har ƙasa, sai ta fashe da dariya tana rufe baki kafin ta ce”Laa ka girmeni kana ce min Anty? Yana dariya ya ce”Ai abun ba daga nan take ba, girman ne Allah ya baki kar ki damu da ƙananun shekarun ki.”
Ya faɗa yana kallon ɗan uwansa dake masa kallon mamaki.
Mimi kuma ta samu abun yi sai cewa take yi ya maimaita sunan da ya kirata shi kuma ya na ta maimaita Anty Mami, ta saka dariya ta rufe bakinta da tafukan hannunta kafin Ta ce”Aji abokin ka ne?
Kai tsaye ya ce”ƙanina ne Mu’azzam.”
Da sauri ta ce”Laa shima yaron Inna Meri ne?.
Sai ya jinjina mata kai sai ta fara tafa hannu tana faɗin”Kuma ba ku kama, kai baƙi shi kuma fari, kai dogo shi kuma gajere.”
Yadda take lissafin ne tana kwantance ne ya sa dole suka yi dariya gabaɗayan su.
A ranar dai dole Mimi ta yi musu Jagora suka Shiga har falon Hajiya suka iske Inna Meri na yi ma Hajiya kitso tunda ita kan tsefe mata ta yi mata wani in ya tsufa.
Sai Ranar Hajiya ta ga Ajin Mimi, Mu’azzam daman ya sha shigowa wani lokacin ma acan shi kan rako inna Merin da safe kuma ya shiga har cikin falon ya gaida Hajiya.
Hajiya ta kalli Mansoor dake duke gabanta bayan sun gaisa ta kuma kalli jikarta da Mirmishin ya ki barin fuskarta
Kawai sai ta kaɗa kai kafin ta ce”Ai shike nan Aji ko? To ni dai wani ƙwarin ka yi ma jika ta, yau fushinka har shafa ta ya yi aka ƙi yi min mgana.”
Kansa na kasa bai yi mgana ba Hajiya ta cigaba da faɗin “Binta kullum L
labarinta na Aji ne, to ni dai na lura jikata na yi da kai Allah ya haɗa jininku gata nan a kular min da ita Amana domin ina ji da ita ahto, in kuma kana sonta ne sai ka fara biyana kudin toshi har da kudin zence.”
Mansoor a lokacin da sauri ya kalli Hajiya.
So? So kuma? Ita kuma Mimi fuska ta rufe ta kalli Hajiya tana yar dariya Hajiya ta kalli Meri tana yar dariya ta ce”To ke fa Meri kin samu shagwaɓɓiyar Suruka Allah ya tayaki riko.” Abun da ya fallasa abin da ke zuciyar Mimi shi ne sai ta tashi da gudu ta shige ɗakin Hajiya wai ta na jin kunya..Hajiya kuma tun tana ɗaukan abun wasa har dai ta fahimci jikarta da gaske take yi.
Kai Tsaye ta kalli Aji kafin ta ce”Kai Mansoor to jikata da gaske take yi, maza ka fara kawo kuɗin toshi in kana son na shige maka gaba lokacin auran”
Mu’azzam da Inna Meri na ta dariya shi kuma gogan sai mirmishi yake yi abun mamaki. Ba su jima ba suka yi ma Hajiya sallama suka tafi, Mimi kuma ta ki fitowa alamun dai ta na jin kunya Hajiya na dariya tace “Meri ina jin dai Binta kunyar surukanta ya hana ta fitowa.”
Inna Meri tace”Bari naje na lallasota.”
Ƙarshe Inna Meri aka bari da lallaso Mimi sannan ta fito, Shike nan Hajiya ta samu tsokanar Mimi da Binta surukar Meri, Meri na faɗin bakomai itama ai tayi dacen Suruka.
Wani abu ne da ake kira magana daga ƙarami sai ya girmama a zuciyar Mimi da gaske tana son Aji shima acikin zuciyarsa Mimi ce aciki ba tare da tunanin me gobe za ta haifar ba suka kamu da tsananin kaunar juna da ƙananun shekarun su, Saboda Aji Mimi ta buga tsalle lokacin da Abi ya zo da kansa ya dauketa domin ta koma Abuja ta shiga matakin Sakandiri ta saka kuka da rigiman wajen Hajiya za ta zauna, ba za ta iya tafiya ta bar Ajinta a nan ba.
Hajiya kuma ganin yadda Mimi ke kuka ta ce ba inda za ta je ya barta anan Hamza ya saka ta a makarantan da ya’yansa ke zuwa.
Bai so hakan ba amman Hajiya ta ce in har ya matsa sai ya tafi da Mimi za ta ce ba ta bashi har Abada kalaman Hajiya su saka sanya a ka bar mata Mimi a hannunta Alhaji Hamza ya saka ta a makaranta da yaransa ke zuwa kuma Mimi da kanta ta yi ma Hajiya maganar tana so a saka ta a islamiya ita kuma Hajiya ta yi ma Inna Meri mgana, Daga karshe dai Mansoor ya kaita makarantarsu islamiyasu ta mallam Ɗahiru aka jarabata aka ga tana da ƙokari sai aka sanyata a ji huɗu ya so a sakata Ajin su Bintu amman ba zai yuyu ba tunda ta girme ta kuma sannan ta fi ta gaba a karatun.
Saboda ita Mansoor ya koma makaranta lokacin suna rubuta jarabawar fita daga makaranta Sakandiri ne shi da su Nasir.
In bai je makarantar islamiya ba Mu’azzam za’a ja ma kunnen ya Kula da Mimi in aka tashi sai da ya tabbatar da ya rakata har gida. Tun suna Nasir ba su gane ba har suka fahimci wani abu saboda yadda Aji ke kafa kafa da yarinyar masu kuɗin nan suka fahimci yana sonta
Nasir ne ya fara magana, ganin abun na Aji na yin yawa kishin yarinyar yake yi ko miye abun kallo a jikinta Oho. Yana tafe tare tare da ita baya so ta yi ma kowa mgana sai shi in ko ta na yi musu mgana yanzu zai ɓata rai amman in ita da shi ne sai ka ga yana wani annurin farinciki.
Kuma in aka ce wacece ita? Iyaka yace jikar Hajiyar e da Inna ke zuwa mata aiki ce.
Amman Sai ayyukansa suka tona shi ita kanta Mimin ba ta iya ɓoye kaunar da take yi masa ko a gaban waye sai ta kira shi” Aji Nah.” Kuma in yamman ta yi gidan su Mansoor ke wucewa da ita sai an gama sallar mangariba zai rakata gida suna tafe suna hira.
Hajiya kuma hankalinta kwance yadda ta aminta da Meri haka ta aminta da ƴaƴanta
Wata rana ma Mimi har kwana ta ke yi a wajen Inna Meri Hajiya ta ce in duhu ya shiga a daina wahalar da su Mu’azzam ta rika kwanciyar ta nan, ita kanta ta fi son haka acikin gida Magajiya ta rika habaicin kwaɗayi da wahala tunda suna gani kamar kwaɗayi ne yasa Inna Merin da ƴaƴanta ke tafe tarairayan Mimin.
Wata rana sun dawo daga islamiya Mimi na tare da su Binta daman Mansoor ya ba ma su Yaya Amina Amanarta da an tashi za su je su nemeta saboda su kamo hanya tare, ta na hango shi daga nesa tare da su Nasir ta ƙwalamasa kira sannan kuma ta nufosa yana ganin haka ya yi saurin barin su Nasir ya nufeta yana faɗin”Ba na ce ki daina biyo ni cikin maza ba, ba ki ga ke mace ba ce?
Sai ta tura baki kafin ta ce”To ni ai ba ina son ganinka ba ne”
Sai ya ƙarya wuya kafin ya ce” To tunda kin ganni koma wajen su Yaya Amina kin ji ko?.
Kafa kafa ya rakata har wajensu Amina suna gaba su kuma suna bin su a baya Nasir da Makama suna ta haɗa ido suna gulma.
Sai da suka zo layinsu, suna tafiya Mimi ta tsaya ta na waigen Mansoor Nasir kuma ya na tafiya bai ganta ba ya taka mata igiyan takalmi shike nan sai ta faɗi ƙasa goshinta har ya kuje.
Ranar Nasir ya ga masifa haka Aji ya dinga masa masifan yaa gani ya tureta ta faɗi
ran Nasir ya ɓaci cikin ƙufulwa ya ce”Eh ina gani, tunda da gangan ne zan tureta Aji.”
Mansoor ya ce”Wa ya sani ko da gangan ɗin ne? Nasir ya ce”To wai kana ta wani jijiyan wuya Aji anya anya? Ko dai son yarinyar nan kake yi ne?
Da ƙarfi ya ce”Eh INA SONTA ko za ka hana ni ne?
Sai Ahmad da su makama su ka kama baki Mu’azzam daman ya jima da ranfo yayan nasa.
Haka dai aka rabu da faɗa saboda haushi daga nan ya tasa Mimi zuwa anguwansu ko gidan ma bai bari ta shiga ba.
Mu’azzam kuma ya je ya na gayama Inna Meri labarin abin da ya faru.
Ta yi dariya kafin ta ce”Shirmen ne kawai irin na shi, ita da ba yar nan garin ba ko yau mahaifinta ya so zai ɗauketa ta koma wajensa.”
Mu’azzam ya ce”Inna ba fa wasa ba ne Yaya Mansoor na son Anty Mami.”
Inna Meri baa ta ɗauki abun da wani gaske ba tace”To kawai.”
Da irin haka da suke ɗauka ne lamarin ya yi nisa ba su sani ba. Saboda Mansoor na gida tunda suka gama sakandiri bai cigaba da makaranta shi a dole sai ya samu makarantar Sojoji, kuma a lokacin makarantar na wahalan samu shi kuma ya dage in ba nan ba bazai yi wata makaranta ba. A zuwa lokacin komai da ya danganci Mimi Aji ke fara sanin kafin kowa har Jinin al’ada da ta fara shi ta samu tana kuka ta gayamasa yana kunshe dariya ya ce ta je ta samu Hajiya ta sanar da iya, sai da ta je ta gayama Hajiya ta zaunar da ita ta yi mata bayani sai ta dawo tana jin kunya.
Lokacin da ta gayama Hajiya Aji ta fara gayamawa.
Hajiya ta ranƙwasheta akai lokaci ɗaya tana faɗin”Me ya sa kika faɗa masa? Ni kika tsallake ni Binta?.
Ta na tura baki ta ce “Hajiya shi fa zan aura kuma ni to.”
Sai ta kasa ƙarisawa sai ta bar Hajiya da rike baki daga nan Hajiya tasan Binta da gaske ta ke yi ta na son yaron nan tunda har ta iya furtawa. Kuma har zuwan da Mommy ta yi ganinta sai da Mimi ta ba ta labarin Aji.
Mommy ta gaji da jin Labarin Aji ta samu Hajiya tana faɗin “Hajiya wai waye wani Aji ne? Tunda na zo Mimi ke yi min hiran sa,?
Hajiya ta ce”Mijin da za ta aura ne.,”
Mommy ta zaro ido ta na kallon Hajiya Mimi kuma sai ta rufe fuska ta tashi ta bar wajen tana dariya. Nan Hajiya ta zaunar da Mommy ta ba ta labarin tun daga farko sannan ta ƙarishe da faɗin”To kin ji ba sai ki shirya Binta ta samu miji a gombe.”
Mommy ba ta wani ɗauka da gaske ba ne har da Inna Meri ta zo gaisheta ta ce a ce ma Mansoor ya zo ya gaishe da surukarsa.
Ta faɗa cikin Raha saboda ta na kaunar ƴarta kuma abin da yarta take so shi take so. Mansoor ya zo ya gaida Mommy tare su ka zo da Mu’azzam da Nasir makama shi ya fara zuwa jami’a ba ya samun zama sosai. Ahmad kuma babanshi ya kai shi shagon ɗinki. Mommy sai ta ga shi kanshi Mansoor ɗin ai yaro ne sai a ranta ta ce yarinta ne kawai irin na Binta da kuma jaaɗuwar Jini.
Shi kuma Aji in su Nasir suka ce auran Mimi zai yi? Sai yace eh Nasir ya sha faɗa masa wata mgana bai taɓa tsayawa ya duba mganar ya ga ko za ta yi masa amfani tun a wancan lokacin ba, sai daga baya yake ganin gaskiyan Nasir a wancan Lokaci.
Nasir kan cewa Mansoor” Aji gaskiya ka saka kanka a wahala, Yarinyar nan ta fi ƙarfin ka, ba auranta iyayenta za su baka ba, ba ma haka ba kai a yanzu kamata ya yi ka zauna ka yi tunanin makomar rayuwarka ba ka saka kanka a maganar aure da ƙananun shekarunka ba, kai baka tara ba. ba kuma ka ba wani ajiya ba.”.
A lokacin da ya faɗi haka sai da Mu’azzam ya shiga tsakaninsu shi Aji ya na ganin Nasir ya raina shi ina ruwansa da rayuwarsa.

Shi kuma Nasir yana ganin Aji ya shiga inda ƙaren sa bai kai ba ma’ana ya janyo abin da yafi ƙarfinsa.
Saboda Aji ya sa Mimi ba ta son zuwa Abuja in su ka samu hutu sai Abi ya kira waya ya ce Daddy ya sakata a jirgi zuwa Abuja haka zata je ta yi hutuntaduk ba daɗi Mommy dai ke shan labaran Aji har ta gaji, ta taɓa ce mata” Mommy Aji ma fa Soja ya ke son zama ki yi ma Abi mgana ya yi masa hanya, so yake yi in aka yi auran mu sai ya tafi ya barni wajen Inna Meri.”
Daga nan mommy ta fahimci yaron ke kara saka ma Mimi wani tunanin, sai dai alokacin ta yi karaf ta ce mata'” kul na kara jin mgamar auran nan a bakin ki Mimi ga sauran ƴan’uwan ki nan karatu suke yi, ba wacce take mganar aure sai ke in kika bari Abin ku ya ji maganar nan sai ya harbe ki.”
Mimi na tsoron bindiga sai ta fara rawan jiki tana cewa” Mommy shi fa yake cewa zai aureni nima ai ina son shi.”
Mommy ta tsawar ta mata da cewa” To ba na son jin haka, in ya ce miki zai aure ki, ki gayamasa ke ba yanzu za ki yi aure ba sai kin girma kin gama karatu.”
Abin da Mommy ba ta sani ba dukkan abin da ta faɗa Mimi na dawowa Gombe ta kwashe komai ta faɗa ma Hajiya.
Har ta na mata kuka da cewa”Ni hajiya Aji zan aura kuma ya ce in muka yi aure zan yi karatuna.” Jikin Hajiya sai ya yi sanyi wato kenan yan zantukan da suke gudana a tsakaninsu kenan? Lalle yara nan da gaske su ke yi.
Dakyar ta lallashi Mimi ta yi shuru amman Aji na zuwa ta kwashe komai ta sanar masa.
Shi kuma sai ya kalleta yana faɗin”Ki gayama Mommy ba zan hana ki karatun ki ba sannan ni nafi son na aure ki kafin ki kara girma, in kika kara girma zaki iya fin Ƙarfina” Kuma sannan ya fahimci Mimi ba ta son ya ce zai zama soja.
Da ya fara magana sai ta ɓata rai, ranar dai ya tsareta sai da ta gayamasa dalilinta.
Abun ya bashi tsoro tana hawaye ta ce” Abi sai ya yi ta ma mommy tsawa wata rana ma har ya na saka ta kuka, ni ba na son ina ganin bindiga irin ta Abi in muka yi laifi sai ya ce zai harbi kan mutum.”
Daga nan ya fahimci mahaifin Mimi ba Dattijon arziki ba ne amman duk a lokacin bai karaya ba, yana nan akan bakansa na zama soja kuma da gaske yake yi yana son Mimi kuma auranta zai yi in sha Allahu.
Page 13
3rd June, 2011
Suna zaune a ƙofar ɗakin Inna Meri ne gabaɗayan su. Satin da ya wuce a ka yi bikin Yaya Amina tare da Yaya Halima to labarin bikin su Bintu ke ta yi Inna Meri na biye musu. Mansoor da Mu’azzam daga baya su ka shigo gidan tare da Baba Ɗanjuma, sai suka barshi a bangaran Magajiya da tunda aka yi sha’anin nan take ta bala’i da ya da habaici.
A tunaninta Baba Ɗanjuma ya ƙarar da duka abin da ya mallaka a auran Amina da Halima ko a wajen taron bikin sai da suka yi hatsaniya da yayar Mahaifiyarsu Aminan Madina sai da Inna Meri ta shiga tsakani ta ce duk kowa ya yi banza da ita daman abokin yi take nema, kuma daman ita Magajiya burinta shi ne ta watse taron kar a gama lafiya tunda tana da ciwon hassada a cikin ranta ga duk abin da ya shafi rayuwar Inna Meri da ƴaƴanta.
Idanuwanta ya rufe a tunaninta duk kayan da aka yi ma Amina da Halima da abubuwan da akayi na hidimar biki daga aljihun Baba Ɗanjuma ne, abin da ba ta sani ba hatta da abincin da a ka ci a wajen bikin Inna Meri ta yi tanadin shi tuni, sannan game da kayan ɗaki da sauran
hidima dangin mahaifiyarsu sun yi matukar namijin koƙari sannan ita kanta Inna Meri bangaran su tukunya kayan aiki na mata duk ita ta yi su aikin da take fita kullum ba ta bar shi a banza ba duka tattalinta na wajen yara nan mata manya musamman Amina da Halima. Shi Baba Ɗanjuman ma lokacin da maneman auran Aminan suka zo cewa ya yi ba shi da abun aurar da Amina Inna Meri ce ta ce a saka shekara zuwa a ga abunda ubangiji zai yi. To an fa saka na Amina ko wata uku ba’a yi ba Halima ta samu Inna Meri ta ce a haɗa waje ɗaya tunda dangin Habiba sun ce su za su yi komai da yardan Allah.
To da Jajircewanta tare da tsayuwar yan’uwan mahaifiyar su Amina aka samu aka yi auran nan cikin rufin asirin Ubangiji a ka kai kowacce gidanta dake cikin gari, to tun bayan bikin Magajiya ba ta bar su sun zauna lafiya ba sai Allah ya isa take yi in an ci amanarta, ita masifarta ai zuwaira ma ta samu miji Ɗanjuma ya ce ba shi da Kuɗin aurar da ita yanzu sai dai kila zuwa gaba a tunaninta ya ƙi aurar da Zuwaira amman ya buɗe bakin Aljihu ya aurar da yaran da yake so duk ba ta san kokarin na matar kwarai ce irin Inna Meri ba
Suna shigowa lungun ɗakin Inna Meri Mu’azzam ya ce”Inna sai yaushe ne Magajiya za ta hakura da wannan zage zagen ne? Inna Meri na zaune a kofar ɗakinta ƙafafunta na mike, Bintu ta samu kafafun Inna ta yi filo da su, a yayin da kuma Walida ke can daga bayan Inna tana faman zuro kanta. Share tambayar na shi ta yi da kallon zaratan ƴaƴan nata, cikin Yanayin maganarta ta ce”Sai yanzu kuka dawo?
Mu’azzam ne ya samu gefen tabarman da suke zaune ya zauna lokaci ɗaya yana faɗin ” Wlh Inna sai dai har yanzu ba’a dace ba duk inda muka san za mu samu hanya mun bi abun dai sai godiyar Allah kawai.”
Sai inna ta jinjina kai kafin ta kalli Mansoor da ke tsaye ya jingina kansa da garu ga takardu a hannunsa.
Cikin Marairecewa ta ce”An ya Baban Inna ba za ka hakura da neman Sojan nan ba kuwa? Abu kusan shekara uku da gama sakandirin ka, kana zaune gida ba cigaba abokan karatun ka tuni sun san matakin da suka taka, ni tsiyana da kai nacin tsiya ba ka jin shawara ka yi ta kafiya kan abu ɗaya har ga ƙanin ka nan shima ya gama shekeran da ta gabata shima yana so ya biye ma ka da sai ya zama ɗan ƙwallo tunda naku burin Allah bai yarda ya cika ba sai ku watsar da ra’ayin ku, ku nemi zaɓin Allah ku samu in da kuka laɓe domin gyaran goben ku.”
Ta ke faɗa cikin bayyana yadda abun ke damunta Baban Inna fa shekarunsa uku da gama makaranta amman ya ƙi cigaba ya ki kuma zuwa wajen sana’a ya na ce shi sai ya je makarantar Sojoji, kuma an yi nema har an gaji ba sa’a a wanchan shekaran wani kawun su Mu’azzamu har hanya ya yi masa ya je kaduna ya yi jarabawa amman da ta fito sunan shi bai fito ba, duk inda ya san za’a samu yaje amman ba’a dace ba shima Mu’azzam ya gama wanchan shekaran shima ba yadda Alhaji Mustspha matsayin uba yake a wajen mahaifiyarsu bai yi da shi ya nema masa jami’a ya cigaba da makaranta ba ya ce shi Ɗan ƙwallon kafa ya ke son zama yayansa kuma ya ɗaure masa kugun cewa a bar shi ya bi ra’ayinsa.
Abokan da suka tashi tare tuni kowa ya kama kanshi, hatta Nasir ya samu Jami’ar Nasarawa keffi ya na can ya na karatunsa ban da su, kullum sai dai neman yawo da takardu sune gidan ɗan siyasa da gidan wanda suka ji labarin zai taimaka shi kan shi Baba Ɗanjuman ya ɗaure musu kugun a kyalesu Su nemi abunda suke so a dai tayasu da addu’a kawai. Ko uffan Mansoor bai ce ba ko su Binta da suka gaishe shi bai amsa ba, Mu’azzam ne ganin Inna ta fusata tana faɗa ya sassauta murya yana faɗin “Inna ki yi hakuri ki yi mana addu’a amman ni kaina na karaya yanzu haka da kika ganmu daga gidan Couch ɗinmu na Nasara muke Tunda su suna da hanyar da za’a ɗauki mutum daga manyan kungiyoyin kwallon kafa ta Nageria a bashi horo amman duk sanda muka je sai ya ce wai ba kungiyar dake neman ɗan wasa in ana nema zai neme mu, kin san me nema mun koma ne mu kara masa tuni in ana nema kar ya manta damu”
Inna Meri ta kallesa cikin takaici kafin Ta ce”Mu’azzamu ka daina bi ta kan wannan yayan naka, shi kanshi baisan me yake so ya za ma ba. Ka bar batun neman za ma ɗan Ƙwallon nan ka zo ka yi karatunka Allah ya sa maka albarka kana gamawa ka samu aikinka ya fi ye maka wannan zaman da kake yi kana biye ma wannan da bai san ina zai dosa ba.”
Mu’azzam ya ce”Inna ya sani fa, Soja yake son zama.”
Ƙaramin tsaki ta ja kafin ta ce”Ai sai ya zama muna nan muna jira.” Mu’azzam yayi dariya yana kallon Mansoor da hankalinsa ke kan karamar wayarsa ya na ɗan mirmishi
Inna Meri ya kallah kafin ya ce”Hajiya na gaishe ki da gajiyar biki, yanzu daga can mu ke.” Ya lalubo aljihunsa ya ɗauko Sweet da yawa yana mika ma Bintu da har ta zuro kai yana faɗin”Anty Mami ta ce na kawo ma su Bintu.”
Da gudu Bintu ta warce ta na ihun Murna Mansoor ya kalleta a karkace kafin ya ce”Ke ashe wawiya ce bansani ba? tana jin haka ta yi gum da bakinta ta na raba ido.
Walida ta mika hannu ta na faɗin”ki ba ni Nawa ” Bintu ta make kafaɗa kafin ta yi mgana Mu’azzam ya ce”Sai kin bata ko wlh ke ma ya haramta gare ki, yarinyar nan son kai gareta.” Hararansa ta yi kafin ta tura baki shi kuma sai ya mika hannu zai kwace da yasa ta kwashi uku ta mika ma Walida sauran kuma ta tura cikin sikat ɗinta ta mike da gudu zuwa cikin ɗaki.
Mu’azzam ya girgiza kai kafin ya ce”Inna Allah yasa Bintu ta jiƙan ki wata rana.”
Inna na yar dariya ba ta ce komai ba illah kai da ta daga sama tana kallon taurari kafin ta dawo da kallonta kan Mu’azzam ta na fadin”Hajiyar tana lafiya ko? Allah Sarki Hajiya gobe zan shiryar takanas ba domin aiki ba na je na yi mata godiya.”
Mu’azzam ya ce” Ya kamata Inna Hajiya tana da kirki, duk abun Yayanmu sai da ya yabi kirkin Hajiya.” Inna Meri ta yi shuru ba ta yi mgana ba ita fa akwai wani abin da ke ba ta tsoro shakuwar bintar Hajiya da Baban Inna soyayya suke yi, tun tana ganin abun yarinta ne har dai yanzu ta yardan ma kanta da gaske ne. Ban da Baban Inna da rigima ina shi ina ƴar masu kudi, ai wannan jawo ma kai fitina da jidali ne.
Yarinyar nan kunyar surukan take yi mata in dai taje gidan ba ta iya haɗa do da ita, ita kuma Hajiya ba ta damu ba domin ta ce abunda Binta ke so shi ta ke so. Ba za ta taɓa mantawa da sun taɓa maganar da Hajiya saboda Hajiyar da kanta take ce mata yara nan fa da gaske suke son juna su ke yi. A lokacin Dariya Inna Meri ta yi kafin ta ce”Haba Hajiya yarinta ne da shirme irin na Baban Inna sai kuma shakuwa amman ai ruwa ba sa’an kwando ba ne, kuma ina shi ina aure yanzu? Duka duka nawa yake?
A lokacin sai Hajiya ta ce”To ai ko ba yanzu ba Meri sai iyaye su shiga mganar, kamar yadda ya ke son zama Sojan nan ya je can ya na karatunsa itama tana nan ta na yi sanda ya gama ya dawo itama ta gama sai su yi auransu ai ba wani abu, ni fa ba na ƙyamar zuru’arki Meri ke macece mai kirki da mutumci ya’yanki masu tarbiya ne, kuma maganar ruwa ba’a san kwando ba ne bai taso ba abin da Binta ke so shi nake so, matukar kuma ta ce Mansoor ta ke so ni kuma zan shige gaba wajen na ga ta samu abin da take so.”
Tunda lokacin Maganar sai ta fara damunta ta turke Mu’azzam kuma ya tabbatar mata da gaske Baban Inna na son Mimi irin soyayyar da ba zai iya kwantatawa ba, in ba ta manta ba yana da kuma ra’ayin aure tunda ya na da ƙananun shekaru, ita abu daya ke damunta da shi nacin tsiya da kafiya sannan ga ɗauko fitinar da ta fi karfinsa in ba neman jawo zaune tsaye ba ina shi ina Binta yarinyar da Ubanta ma akan dole ya bar ta hannun mahaifiyarsa ita fa tana hango ma Baban Inna nadama kan wannan shegen kafiyar nashi. Kan nacin sa da zama Sojan nan har Mallam Sidi ta shirya ta je bikin yaron yalwa da shi ma taso tafiya ya ce shi ba zai je ba, ta ma ta zencen Babansa yakubu ya kira shi ya je can Bauchi ya same shi ya yi masa faɗa ƙo ya ji Yalwa ta ce to in Yakubun yazo ko in sun yi waya tunda yanzu ya yi ƙarfi kasuwanci yake a Bauchi yana can shi da iyalansa.
To kila dai ba ta samu magana da shi ba ne, bai aiko ba kuma sannan ba ta kara ji daga Yalwa ba, ta so shi Yakubun ya kira shi ya matsa masa kila ya watsar da wannan ra’ayin na sa na zama Soja ya nemi wata hanyar.
“Inna me kika dafa ne?
Mu’azzam ya katse mata tunani sai ta yunkura ta mike tana faɗin “Tuwo ne miyar yauki bari na zubo muku.”
Ta zubo musu kenan sai ga Baba Ɗanjuma ya shigo gabaɗayan su suka yi masa sannu da zuwa ya amsa ya na ƙokarin sakin fuskarsa. Cikin ƴaƴan na shi ya zauna suka ci cin tuwon Mansoor ne ya fara ƙoshi ya tashi Baba Danjuma ya kallesa yana faɗin”Ka ƙosh ne Baban Inna?
Yana nufar randar Inna ya ce”E Baba.!”
ruwa ya diɓa a buta ya shiga makewayi ya kama ruwa sannan ya wanke hannunsa ya kuskure bakinsa. Bayan ya fito sai ya zo ya durkusa gaban Baba Ɗanjuma kansa na kasa, Inna Meri na gefe tana kallonsa kafin ta yi mgana Baba Danjuma ya ce”Ya aka yi ne Baban Inna? da wata matsala ne.”
“Baba Aure nake so na yi..”
Gabaɗayan su suka kalleshi a tare Mu’azzam sai da ya ƙware da tuwo duk da ya san hakan zai iya faruwa amman bai tsammanci maganar da wuri ba, inna Meri ta yi tagumi kawai tana kallon Baban Inna yaro ƙarami na neman saka kanshi a wahala shekararsa fa duka duka ashirin da uku ne tsawon kafa ke jansa yake ganin ya isa ya yi aure har ya riƙe mata yana zaune ba shi da sana’a naira biyar ma na bashi sha’awa. Baba Ɗanjuma sai ya dakata da cin tuwo ya miƙe yana faɗin”Babban mgana, taho ka zuba min ruwa na wanke hannuna sai mu yi maganar sosai”
Haka ko akayi ya zuba masa ruwa a bakin magudanar ruwa ya wanke hannunsa sannan ya koma ya zauna yana kallon Mansoor mirmishi ya suɓuce masa ai shima ya taɓa gaya masa haka tun bai kai haka shekaru ba.
“Baba ni fa ba zan bari sai na fara tsufa zan yi aure ba, da wuri zan yi aure saboda ba na so ya’yana su taso su ganni ƙarfina ya ƙare.”
Ko a lokacin da ya ce masa haka sai da ya yi dariya kuma yana da yaƙinin Baban Inna zai maimaita mganarsa lokaci kaɗan tunda shi baya faɗin abin da ba shi ne acikin ransa ba, Inna Meri ya kallah kafin ya ce”To ke fa Meri kin ji, za ma ai bai gan ki ba Baban Inna Aure yake so yayi”
Inna Meri ta ja katon tsaki Mtsewwww kafin ta ce”Ai sai ya yi auran tunda auran faɗe ne a fatar baki, ban da shegen rigima kana yaron ka da kai ba ka ba wani ajiya ba, kai ba ka ijiye mai ba ka ba sai kawai rana tsaka ka ce wai aure za ka yi? Anya Baban Inna..!”
Ta faɗa tana nuna shi da yatsa kai tsaye ya ɗago yana kallonta kafin ya ce”Inna ina da gado na, a saida gonakin baba na Mallam Sidi ayi min aure da shi.”
Ai sai Inna Meri ta hau tafa hannu tana faɗin” Yai naji sheganta ka, zan ɓace ka Mansoor yanzu nan wlh.”
Baba Ɗanjuma da ya ga ranta ya ɓaci yayi saurin tare ta da faɗin” Kar ki yi masa faɗa ai ba laifi ya yi ba, kuma bai yi ƙanƙanta ba, waɗanda ba su kai shi ba ma su na yin aure yanzu dai mu saurare shi mu fara sanin in da ya samu matar”
Inna Meri gabanta na faɗuwa ba ta son ta ji ya kira sunan da zai ba ta tsoro.
“Mimi ce, jikar Hajiya in da Inna ke zuwa aiki.”
Inna Meri ta ɗora hannu a saman kanta lokaci ɗaya tana faɗin”Na shiga uku ni Merama, da gaske daman son yarinyar nan kake yi baban Inna? Me ya sa ka cika fitina ne? Ina kai ina wannan yarinyar?
Kai tsaye ya ce”Inna tana sona itama, kuma Hajiya ai ta sani kuma ta amince da hakan.”
Inna Meri ta aika masa da dakuwa lokaci ɗaya tana faɗin”Ka ga naka nan, In Hajiya ta sani Hajiya ce ta haifeta, babanta Soja ne kuma ko Hajiyar ba ya jin maaganarta wlh ba zai aura maka ƴarsa kana zaune ba ka da wani tunani ba, ko a addini mai sana’a aka ce ba mai burin banza ba, ka fita idona da wannan mganar na ma gaya maka.”
Daga haka ta tashi ta shige ɗaki tana ta faɗa, shi kuma Mansoor yana gayama Baba Ɗanjuma ai ya na neman karatun Soja in ya samu zai iya rike Mimi, Baba Ɗanjuma ya samu ya lallaɓashi yace za su yi mgana da Safe.
A can ɗakin su ma Mansoor Mimi ya kira a waya yana faɗa mata ya faɗa ma su Inna zai aueta, tunda itama yanzu tana da waya da ta saka Hajiya ta sa Daddy ya siya mata mai kyau da ita yar yayi. Mu’azzam bai isa ya ce ma yayansa wani abu ba, amman shi kanshi ya na hango ma kansa ya yi gaggawa sannan Soyayya ta rufe mishi ido ya kasa gano abunda Inna ke hango masa. A daran shima Baba Ɗanjuma yayi ta fama da Inna Mari ta sauka daga fushinta su yi mgana ta ce in ta sauka sai Baban Inna ya bar maganar Jikar nan ta Hajiya, shi ko Baban Inna ya yi nisa da ba ya jin kira yadda yake jin Mimi a zuciyarsa in ya rasa ta sai ya iya mutuwa. Kuma shi ya gayama Mimi da kansa cewa Inna Meri ta ce ta fi ƙarfin shi.
Kuma su sun tsara rayuwarsu da cewa zai tafi makaranta Sojoji kafin nan za’a ɗaura musu aure sai ya barta wajen Inna ta cigaba da kararunta.
Mmi kuka reras ta riƙa yi ma Hajiya akan abin da Inna Meri ta ce, Hajiya ta ce za ta aika a kira mata Merin ta ji me ya sa ba ta son jikarta ta zama surukan ta? Ba ta ma kai ga aikawa ba sai ga Inna Merin ta zo ma Hajiya Godiya domin 100k ta ba ta da bikin nan bayan ƙananun alherinta a gareta sannan ta bata hutu ta ce har sai gajiyan Biki ya sake ta sannan ta dawo. Tana zuwa da niyar yi ma Hajiya godiya sai tace su shiga cikin ɗakinta ta na son mgana da ita. Tana jin haka tasan kwanan zencen, illai ko Hajiya ta tsareta akan me ya sa ba ta son alaqar Mansoor da Binta?
Inna Meri sai ta saka kuka cikin kukan take faɗin”Haba Hajiya ban da neman rigima ina Baban Inna Ina Bintar ki?
Hajiya tace”To Ubangiji ya haɗa sai mu ce a’a tunda suna son junan su sai kuma mu hana su kudirin alheri.”
Inna Meri ta ce”Hajiya Baban inna yaro ne yarinta ne ke damunsa shekaransa ashirin da uku ne da wattani, da me zai riƙe Binta? Sojan da yake ta ƙulafuci har yanzu bai samu ba kuma ya ki sauya ra’ayinsa don Allah Hajiya a bar mganar nan shakuwa ce kawai ba wai soyayya ba.”
Hajiya ta ce”Duk na fahimci tunaninki, kina da gaskiya abin da za’ayi ai shima kabirun Soja ne zan kira shi mu yi mgana sai a zauna ko shi sai ya ne ma Mansoor ɗin makarantar Sojjojin a yi alkwari in Mimi ta gama karatu su yi auren su ba shike nan ba.”
Inna Meri dai ta kasa mgana amman tana hango wani abu da ba zai tafi dai dai ba amman gudun kar Hajiya ta ga kamar tana gudun maganar sai ta amince da hakan, Kuma Hajiya da kanta ta kira Mansoor ta zaunar da shi ga shi ga Binta ta ce ya faɗa mata gaskiya yana son Binta?
Kai tsaye yake kallon Hajiya kafin ya ce” ba sonta nake yi ba, kaunarta nake yi Hajiya.”
Itama Hajiya ta tambayeta lokacin Mimi an zama yan mata shekaranta sha tara, ta rufe fuska ta ɓoye bayan Hajiya tama yar dariya.
Hajiya ta ce kar su damu za ta yi mgana da baban Binta. A lokacin ita Mimi soyayya ta makantar da ita kamar yadda ya makantar da Mansoor dukkansu suka kasa gano abunda mutane ke hango musu.
Hajiya kuma ta manta waye Kabiru ta ɗauka haihuwarsa da ta yi ya isa ya sa ya bi abin da take so.
Major Kabiru bai san halin da ake ciki ba, Brr Murjanatu kaɗai ta sani tunda ita macece kuma yaran sun fi sabawa da ita shi kullum fuska ba fara’a tsoro tsoron sa ma suke ji, kuma Mimi in ta zo hutu daga baya nan tana yawan kamata suna waya da wannan yaron da ta ce Mimi ta bar maganan sa, ta yi ma Hajiya ƙorafi Hajiya ta ce ta kyaleta tunda har Binta na son wannan yaron to sai a zauna a ga abunda Ubangiji ya tsara, ita ba wai talauci ko yanayin rayuwa ba ɗaaya ba, abu daya take dubawa sun yi yarinta da yawa da maganar aure, sannan ta san waye mahaifin Mimi ba shi da tsarin aurar da ita yanzu to ko Madiha karatu take yi bai saka maganar auranta ba, ballantana Mimi da ta ke just 19 tabbas ta san akwai kura. Ita Hajiya ta fara kira akan maganar Saboda suna da kyakyawan alaqa na mutuntawa a matsayinta na surukarta, Mommy ta ji tsoron da Hajiya ta ce ta fara tuntuɓar Major da mganar cikin firgici ta ce”Hajiya wlh ba zan iya ba, kina ganin ko madiha wani yaron yayata na sonta da Major ya ji ba ki ji yadda yake ta masifa ba ya ce ba yanzu zai aurar da ita ba sai ta gama karatu ta fara aiki.” Hajiya ta yi tsaki kafin ta ce”To ai wannan tsarinsa ne ba tsarin Ubangiji ba, karatun ya fi auren daraja a wajensa ne? ya bar yara sun zama manya bai aurar da su ba da an yi magana sai ya ce ba yanzu ba shi Sulaimanu ai ya na can cikin jajayen fata har yanzu bai dawo kasar ba.” Mommy ta ce” Hajiya karatun likitanci yake yi, sai nan da shekaru biyu zai dawo in sha Allahu.”
Hajiya tace”To dama dama shi tunda namiji ne amman matan ne ya le neman kashe musu rayuwa da tsatauran ra’ayinsa na banza, zan kirasa da kaina na yi masa mganar.”
Ranar a tsure Mommy ta dawo daga wajen aiki, fargaban ta ɗaya ta san komai ya je ya dawo ita zai sauke ma bala’in zai ce tana sane da komai bata gaya masa ba sai da abu ya yi girma. A ranar da dadadde bayan ya dawo daga office Khadija na ɗakinta tunda ita a nan Abujan ta ke karatu Madiha ce ke BUK kano ta na karatun ta acan, Mommy duk jikinta ba daɗi Sai fama take da faɗuwan gaba tana Allah Allah ta ji ya ce Hajiya ta kirashi sai ta ji har sun gama cin abinci bai ce haka ba sai ta samu yar salama.
Sai dai bayan sun koma falo suna hutawa yake ce mata Mimi zata dawo nan ta yi jarabawa so ya ke yi ta ta fi Jami’a mai kyau ta yi karatun likitanci akan abin da ya Shafi mata tunda Sulaiman ya na karantar fannin zuciya, Mommy ta kasa magana sai zufa ke yanko mata duk ko da sanyin Ac dake falon. Kallonta ya yi cikin mamaki kafin ya ce”Honey lafiya? Ko baki da lafiya ne?
Da sauri ta ce”No am fine.”
Saboda ya ga duk ta firgice sai ya yi dariyan basawa kafin ya ce” ko case ɗin dake hanunki ne ya ba ki tsoro.?
Dakyar ta yi yaƙe ta kasa mgana.
Ta fi kowa sanin waye Major ba shi da kyau ko ya yi wanka ko acikin Sojojin shi mugu ne sannan ba shi da uzuri ballantana ragowa ga ra’ayin riƙau ne da shi ita fa yanzu haka ba ta isa ta yi ba dai dai ba sai ya ce da gangan ta yi da farko ba haka yake ba daga baya lamarinsa ya kara ta’azzara.
Daman can halinsa ne sai kuma ya zo ya haɗe da kakin dake jikinsa sai takamarsa ta yi yawa. Daman shi fa ya tsani ace za’a haɗa ƴaƴansa da komai, yadda yake kaunar ƴaƴan to kila sai aikinsa ne za su iya gogawa. kuma ya ci burin akan su da sai ya gina su zai aurar da su ga wanda ya dace in ya ji wannan labarin na Mimi ai sai ya harbeta daga ita har Mimin.
“Kin ga ko na manta Ina Office Hajiya ta kirani ta na son yi mgana dani, na ce ma ta sai na koma gida, miƙo min wayata na kirata in har ma akan Mimi ne sai dai ta yi hakuri zan karɓi ƴata bazan iya kara barin ta a garin nan ba yanzu.”
Can a sama Mommy ta ji Abi na mgana duk sai ta kara ruɗewa, ba ta tashin ba sai da ya ƙara mata mgana sannan ta mike ta ɗauko masa wayar wajen rawan jikin wayar ta faɗi ƙasa haka ta duka Jiki na rawa ta tattaro masa wayar ta mika masa ya karɓa lokaci ɗaya yana faɗin” Murja are u ok?
Sai ta gyaɗa mai kai, kasa tsayawa ta yi da sauri ta shige ɗaki ya bi ta da kallo, bai ɗauka wani abu ba sanin shi da ita akwai ta da saka dmuwar Case in dai ya na hannunta acikin ranta. Lambar Hajiya ya lalubo ya kirata, bayan ta ɗauka sun gaisa ya ce”Hajiya ban jima da dawowa ba, ina fatan lafiya? Hajiya ta gyara zama tana faɗin.
” Lafiya ƙalau, daman akan maganar Binta ne? Kai tsaye ya ce” Eh daman ina shirin miki maganarta nan zata dawo ta yi jarabawa so nake Bintar taki ta zama likitan mata Hajiya.”
Ya faɗa cikin yar dariya Hajiya ta haɗa rai kamar yana ganinta kafin ta ce” Eh to za ta iya zama likita amman daga baya yanzu dai aure take so.”
Ya ɗauka wasa Hajiya take yi sai da ya yi dariya kafin ya ce”Haba Hajiya aure kuma? Mimi ai ba ta san me ake kira aure ba.”
Hajiya ta ce”Ai ba jaririya ba ce shekaranta sha tara da gaske nake yi Akwai wani yaro ɗan wajen Meri dake min aikace aikace sun shaku da Binta kuma yana sonta da gaske itama Bintar na son shi..”
“Wait Hajiya kika ce yaron waye?
Ya katse Hajiya cikin mamaki shi fa gani ya ke yi kamar ta tsuniya Hajiya ke karanta masa
Hajiya tace”Eh yaron Meri ne matar dake taya ni zama.”
Mamaki ya hana shi magana Hajiya na son gayamasa wai yaron ɗan wajen mai aikinta ne ke son Mimi, Shi haka ya yi sakacin da ƴarsa ta za ma a arha da wani yaron talakawa zai ganta ya ce ya na so. Ai bai gama mamaki ba sai da ya ji Hajiya na faɗa masa Mimi na son yaron kuma ta yarda ta aure shi kuma yaron iya sakandiri ya gama ya na son ya zama Soja to shi ya taimaka masa ya samu sojan daga baya komai menene sai ayi.
Huci kawai ya ke yi ya kasa mgana, daman Hajiya ta matsa ya bar mata Mimi ne saboda ta bari wani yaron talakawa mara tarbiya su hore ma ƴarsa kunne lalle ko idon sa idon yaron nan sai ya harbe shi. Kuma sai ya taka wuyan Mimi da har da bakinta take faɗin za ta iya auran wani banzan yaron da bai da wata makomai mai kyau nan gaba.
Kawai amsa ma Hajiya ya yi da Toh ko gama mganar ma ba ta yi ba ya katse wayar Hajiya da sauri ya kira ɗan uwansa Alhaji Hamza.
Cikin masifa ya fara gayamasa yana garin har ahaka ya faru wai Mimi ke faɗin tana son auran wani yaron talakawa?
Alhaji Hamza ya ce bai sani ba nan Major ya sanar dashi abin dHajiya ta ce ya kara da cewa”Hamza ka je ka samu Hajiya ina bukatar sanin tarihin yaron nan tun daga farko har ƙarshe, sai na ji waye mai wannan tsautsayin da zai hure ma ƴata kunni.”
Daga haka ya kashe wayarsa ya miƙe a fusace kamar ya yi bindiga tun daga falo ya ke ƙwalama Mommy kira.
“Murja..”
“Murja..”
Khadija na ɗakinta tana karatu sanda ta ji wannan kiran sai da hantar cikinta ya kaɗa domin a muryan Abi ta fahimci yau akwai bala’i a gidan nan, Mommy kuma tana jin yana kiranta tasan rufa rufa kuma ai ta kare. Shi ya sa ta sadakar ta fito da sauri tana gyara ɗaurin ɗankwalinta lokaci ɗaya tana faɗin”Ga ni nan Habib…’
“Da sanin ki Mimi ta fara soyayya da wani banza yaron talakawa? da sanin ki Murja Mimi take son ta bijirema tunanina? da sanin ki na ce.?
Ya faɗa a fusace kamar ya kai mata duka sai ta kauce cikin rawan jiki ta ce,”Ban ban sani..”
“Sai na harbe shi, ko waye wlh sai na ga da abin da yake takama da shi. Ko madiha ban saka maganar auranta a kaina ba, sai Mimi? Mimi fa? Hajiya ba ta kyautamin ba wlh zan yi abin da zukata ba za su ji daɗi ba.”. Ya ke faɗa ya na huci cikin ƙara daka wata tsawa ya hau kiran sunan Khadija.
“Khadija..”
“Khadija..”
Mommy jikinta na rawa ta ce”Khadija ba ta san komai ba Habibi.”
“Murja zan miki tijara na ce, ƙarya kike yi kin san komai, Hajiya zata gaya miki kuma Mimi yarki ce kina sane da abin da ke faruwa, Wlh tallahi in har da saka hannun ki a abin da ke faruwa zan iya sakin ki a kan haka.” Khadija ta ɗora hannu akanta san da ta fito ta ji maganar Abi Mommy kuma sai kawai ta juya tana kuka ta shige ɗakinta acikin zuciyarta tana fadin” Inna lillahi wa’inna ilaihirraju’un..”
Khadija ya kallah da ke tsaye tsuru tsuru, tsawa ya daka mata kafin ya ce”Ke ma kin fara soyayya ne? za ku tsallake umarnina ne?
Jikin Khadija na rawa ta duka tana faɗin “Abi karatun ka ce za mu yi kuma shi nake yi, wlh ban taɓa soyyayya da kowa ba.”
Yana faman sakin huci ya saka kafa ya daki tuberin gabansa kayan ciki suka watse da karfi yake taku zuwa cikin ɗakinsa Khadija ta zura da gudu zuwa ɗakin Mommy tasan bindiga Abi zai fito da shi ai su yau sun shiga uku.
Page 14
Mommy na zaune a gefen gadota tana sharan hawaye daman abin da take gudu kenan, da gudu Khadija ta faɗo ɗakin tana faɗin “Mommy mun shiga uku bindiga ina ga Abi zai ɗauko.” Ta faɗa lokaci ɗaya tana hawa saman gadon ta lafe a bayan Mommy, tana ta haki tare da sauke numfashi.
Mommy ta yi ajiyar zuciya kafin ta ce”Allah ya duba mu, yau sai abin da Allah ya yi.”
Khadija ta ce”Mommy me ya faru ne? me Mimi ta yi ne?
Nan Mommy ta karanta mata abunda ta sani sai Khadija ta zaro ido kafin ta ce”Mommy ke ma me ya sa ba ki hana ba? Mimi tana hauka ne? Wani yaro ƙarami da bai wuce a wanke masa kashi ba ne za ta jawo ma na bala’i muna zaman zaman mu?
Mommy ta karɓe da faɗin “Hajiya ce ta mara mata baya, me zan ce Khadi?
Khadija ta ce” Mommy ke ma me ya sa kika yi shuru? Kin san fa halin Abi wlh ba Mimi kaɗai ta shiga uku ba har dake har damu gabaɗaya.” Mommy ta yi tagumi kafin ta ce”Khadi addu’a za mu yi Allah ya sausauta zuciyar Habibi.”
Khadija sai ta kasa mgana wayar Mommy dake kan gado ta ɗauka ta kira lambar Madiha tana ɗauka cikin ruɗewa ta fara gayamata abunda ke faruwa. Daga can bangaren Madiha ta ce”Subhanallah Ita Mimin ce ta ce aure take so?
Khadija ta ce”Mommy ma ta ce ta sani tun zuwanta Gombe take tare da yaron, wai kiji ma yaro ƙarami kila ma sa’an Mimin ne.”
Madiha ta ce” Ba su da hankali ne, ita kuma Hajiya ta fara tsufa me ya sa mommy ba ta hana ta kiran Abi ba? Mommy na gefe tana jin khadija na maida ma Madiha zencen bayan Madiha sai da ta kira Sulaiman bai ɗauka ba ta tura mata saƙo.
Ranar a ɗaki ɗaya Khadija suka kwana da Mommy saboda tsoro Abi kuma ko runtsawa bai yi ba bindiga a gabansa yana shan alwashin harbe wannan shegen yaron.
Shi a tsarin rayuwarsa ba tsarin ya aura ma ƴarsa kowani datti, haka kurm rana tsaka wani ɗan talakawa zai zo ya lalata tarbiyan Mimi, duk laifin Hajiya ne ita ce ta matsa sai da ya bar mata Mimi shi ne daga karshe ta yi masa wannan sakayyan.
A washegarin ne kuma Alhaji Hamza ya isa gidan Hajiya ya sameta da maganar, Hajiya ta zauna ta yi masa bayanin komai game da Mansoor har tana gayamasa maraya ne mahaifinsa ya rasu shi ya sa Inna Meri ta yi aure a nan gidan Wanzamai, shi bai gayama Hajiya sun yi waya da Kabiru ba amman shi kanshi sai da ya nuna ma Hajiya abun bai dace ba.
Kai tsaye ya ce”Hajiya kema me ya sa za ki bi ye ma Mimi? Har yaushe take yarinya ƙarama gaskiyan Major ne ta maida hankali a karatunta, shima yaron ya je ya yi fafutar rayuwarsa a gaba in suna da rabon auran juna sai su yi auran lokacin sun san dai dai da rashin sa amman yanzu dai ko ni ban goyi bayan wannan shirmen ba Hajiya.”
Hajiya ta fara faɗa tana faɗin” To ai ba abu mara kyau ba ne, kuma sun yi yarinta da auran ne? ni ban ga illar haka ba ni fa magana na ce ayi ko da ba yanzu za’ayi auran ba ya samu ya taimaki yaron ya cika burinsa daga baya sai ayi auran.”
Alhaji Hamza yace”Hajiya to ai ke ba ki da wannan ikon, magana na wajen Major kuma kinsan yadda ya ke da burin ƴaƴansa su yi karatu.” Hajiya ta fara shiga tana fita Alhaji Hamza ya ga ba za ta gane ba ya yi mata sallama ya fita kuma shima ya saka an yi masa binciken Mansoor abun ka ga ɗan siyasa mai jama’a tuni ya samu cikakken bayani akan Mansoor. Kuma nan take ya kira Major ya zayyana masa.
Amman sai da ya ce”Ka bi komai a hankali Major a lallashi Hajiya a fahimtar da ita illar haka, shi kuma yaron ba sai an yi masa wani abu ba, bakin ka alaikum ka ɗauki ƴarka ta koma hannunka, In ma ta kama sai a sauya ita mahaifiyar yaron da wata mai aikin Hajiyan saboda a samu masalaha.”
Ko alama bai ɗauki wannan shawaran ba, ai sai ya nuna mana wannan yaron ya taɓo tsuliyan dodo ashe ma Agola ne mai tsaurin ido zai gane ya shigo gonar Soja, da wuri ya tashi daga Office ya na komawa gida ya shige ɗaki Mommy ba ta nan tana wajen aiki itama Khadija ce kaɗai acikin gida tun safe ta ke waya da Madiha Sulaiman ma sun yi magana ta gama fesa musu abin da ke faruwa duk da suna can amman a tsorace suke. Khadijan da ta kira Mimi tana mata faɗan abunda ta aikata da cewa”Mimi are u mad? maganar Abi zaki warware? Ko Madiha ba ki ga an mata aure ba sai ke tun baki tafasa ba zaki ƙone?
Mimi ta tura baki kamar tana ganinta kafin ta ce”Ni ai ban ce bazan yi karatu ba, amman bayan mun yi Aure da Aji sai na cigaba da makarantar ko?
Khadija ta zage ta daman ga su saƙo da sakon haihuwa kafin ta ce”Ko ba Aji ba, ai Abi zai Aje miki kanki a kasa da bindiga wawiya kawai.”
Ba wanda yasan abin da Abi ya shirya tunda Mommy da safe ta kira Hajiya sun yi mgana, amman sai ta kasa gayamata abunda ya faru ta dai ce ya yi ta faɗan da ta sani ba ta gaya masa ba, Hajiya ta ce”Kyaleshi dani sai dai in har zai sauya wata uwar ne.” Mommy ta ɗauka kila wannan karon Major zai ji mgamar Hajiya abin da bata sani ba ita kanta Hajiyar tana shakkar abunda zai biyo baya. Bat are da sanin kowa ba ya kira Hajiya a waya suka gaisa ya saki fuskarsa ya ce yana son ganin yaron dake son Mimi acikin satin nan.
Hajiya tana murna ta ce”Ko kaifa sai ku yi mgana ka ga sai ka taimaka masa ai mai son naka mai sonka ne Kabiru.”
Cikin takaici yavce”Haka ne ya zo sai mu ga abin da Allah zai yi.” Amman acikin ransa yana cewa sai ya ga kalan tsaurin idanuwan mara kunyan yaron nan.
Hajiya ba ta san abin da Major ya shirya ba, da kanta ta saka direba ya kaita har gidan Wanzamai a tsakiyar ɗakin Inna Meri ta sanar da ita ta yi mgana da mahaifin Binta ya kuma amince har ya ce a tura masa Mansoor ɗin can Abuja su yi mgana.
Inna Meri sai ta ji yar salama tunda har Hajiya na faɗin”Kin san shima Soja ne, na ce ya yi masa ƙokari yaron dai ya cika Burinsa na zama Soja.” Hajiya ta jima kuma tare da Mimin su ka zo sune har Mangariba daman ranar da wuri Inna Meri ta dawo gidan bayan ta ga ma Hajiya sauran aikace aikacen ta. Mimi sai murna take yi ita ba ta damu ba zata auri Aji ta zauna tare da su Inna Meri da su Binta
Ita ba ta damu ba, ta na son Aji a yadda ya ke kamar yadda shima ya ke sonta.
Ta na son salon soyayyarsa da salon kishinsa a kanta har da Mu’azzam Aji na nuna kishi in yaga ta na hira da shi yanzu sai ya sauya fuska. Hajiya ba ta tafi ba har sai da Baba Ɗanjuma ya dawo suka yi mgansa, Mansoor ya ji kamar an saka shi acikn Aljanna burinsa zai cika zai samu Mimi sannan burinsa zai cika na zama Soja.
Baba Ɗanjuma ya ce bakomai sai Mansoor ya shirya tafiya Mu’azzam ya yi karaf ya ce zai raka shi.
A bakin Bintu labarin abi da ke faruwa ya fita tsakar gida Magajiya da su Gaje suka fara manganganun Kwaɗayi ya sa yaro ya je inda aka fi karfinsa har Magajiya na faɗin da uban me zai yi auran ba shi da komai sai bakar zuciya duk Inna Meri ta toshe kunuwanta in da ace ta san abunda zai faru kenan da ba ta bari Baban Inna ya je Abuja ba da duk abin da ya faru bai faru ba abin da ta yi gudu ne ya zo ya faru a lokacin da ba ta yi tsammani ba. A cikin Satin Inna Meri ta haɗa musu kuɗin mota, shi da Mu’azzam su ka shirya tafiya Abuja ana gobe tafiyar suka haɗu da Nasir a masallaci Mu’azzam ke faɗa masa sai ya ce ai ya ji mgana ta shiga gari ana yawo da cewa Agolan gidan Wanzamai zai auri ƴar yayar Sanata Alhaji Hamza.
Shi a lokacin sai ya ba ma Mansoor shawara da cewa” Aji ni fa in da za ka ji shawarata da na ce ka hakura, domin ni ina ganin yanzu ka yi gaggawa gwara ka tsaya ka fara gina taka rayuwar kada ka manta kana da iyaye da ƴan’uwa, tare fa muka gama makaranta ni yanzu ina ji biyu Makama ma haka Ahmad ya kama sana’ar ɗinki, kai kuma fa? Kana zaune zaman jiran majirata.”
Kai tsaye Aji ya ce masa” Kai dai ba ka gina taka rayuwar ba? to ka yi ta kanka Nasir.”
Daga nan akayi rabuwar baram baram, shi kanshi in da ya san cin zarafin da za’a yi masa a gidansu Mimi kenan har Abada bazai taɓa zuwa ba.
Hajiya ita ta hana su bin motar haya ta saka Alhaji Hamza ya ba da direbansa ya ɗauke su Mansoor da Mu’azzam, sai garin Abuja Aji ya yi shigar manyan kaya shi da Mu’azzam har da hulunu ko alama bai karaya ba.Sun yi kyakyawan sallama irin ta Masoya da Miminsa, sun iso Abuja da yamman saboda tafiyar mota.
Sai dai tun daga bakin get suka fara raina kansu wani makeken gida mai cike da tsaron dakarun Sojoji.
Sannan Sojan dake kofar get ya ce bai san da zuwan wasu baƙi ba saboda haka ba za su shiga ba sai ya samu izini daga cikin gida.
direban ya kalli su Mansoor lokaci ɗaya yana faɗin”To ku kira mana, ina ce asan da zuwan ku.”
Mu’azzam sai ya kasa mgana sai zaren ido yake yi, Mansoor kuma yana shirin kiran Mimi sai ga saƙon ta.
“Aji Nah kun isa?
“Eh mun Iso, amman wani soja ya hana mu shiga ya ce sai ya samu izini daga cikin gida.”
Shima ya maida mata da amsa, tana ganin haka ta yi saurin tashi ta je ɗakin Hajiya ta gayamata, Hajiya tace bari ta kira Kabiru sai dai kuma ta yi ta kiransa bai ɗauka ba alhalin sun yi waya da safe ta gaya masa zuwan su Mansoor. Ganin bai ɗauka ba sai ta Kira Murja itama kiran wajen huɗu sannan ta ɗauka cikin yar damuwa Hajiya tace”Murja kina ina ita faman kira shuru? Baki sun iso suna waje an hana su shiga.”
Mommy na jin wani iri ta ce”Hajiya ba ni da wannan ikon, Major ya ce sai shi da kanshi ya ba su izinin shigowa.”
Hajiya tace”Lafiya me ya faru? Shi kabirun ya ce haka? Mommy ta ce”Hajiya ya hana ni mgana ne, amman na so na kira ki na ce kada yaron nan yazo wlh major ya shirya wulakanta yaron nan ne Hajiya”
Da sauri Hajiya ta ce”Innalillahi wa’inna illahirraju’un..”
Da kuma sauri ta yanke kiran Mimi hankalinta ya tashi ta ce”Hajiya lafiya?
Hajiya ta ce”Maza ki kira Mansoor ki ce direban da yakai su ya juyo da su.”
Mimi ta dafe kirji kafin ta ce”Me ya faru Hajiya? Abi ne ya kore su?
Hajiya ta mike tana faɗin”In ma koran ne da sauki, Kabiru ya rufeni a baibai.”
Hankalin Hajiya duk ya tashi ta kuma ta da hankalin Mimi sai dai Mimi ta yi ta kiran wayar Aji ba ya tafiya, Hajiya ta saka ta kira Alhaji Hamza Daddy shi kuma suna wajen taron siyasa bai ɗaga wayar ba
Hajiya ta kasa zama waje ɗaya faɗi kawai ta ke yi” In har kabiru ya wulakanta yaran nan ba zan yafe masa ba.”
Hankalin Mimi ya tashi ta fara kuka ta yi ta turama Aji sako.
“Aji Nah kun shiga gidan?
“Hajiya ta ce ku juyo Abi ba zai amince ba.”.
Amman ina shuru kuma ko an kira wayar ba ta shiga, su kuma a lokacin suna nan a kofar gida kamar wasu kayan wanki, saboda direban da ya kai su ya ce kai su kawai akace ya yi nan ya zube su ya juya mota ya yi tafiyarsa, abun tausayi Mansoor da Mu’azzam zaune a kofar gidan su Mimi tun karfe biyar har aka yi mangariba, sojan nan ba Imani a ranshi tuni ya shige ciki ya rufe get sai a Aji ne ya gangara can bakin hanya ya siyo musu ruwa suka yi alwala suka yi salla akan dandalin Kofar gidan su Mimi. Mu’azzam ya gaji ga yunwa ga kishi cikin galabaita ya kalli Mansoor dake nuna dakiya ya ce”Yayanmu ka kira Mimi mana, wlh na gaji da zama anan.”
Shuru ya yi ya na wani tunani, da gaske a san da zuwan su amman me ya sa za’a kira su daga wani gari kuma a tozarta su?.
Ƙaramar wayarsa ya duba sai ga layinsa Emergency ba ya iya ma kira sai kawai ya kalli Mu’azzam kafin ya ce”Ba Network, mu kara jira dai mu gani.”
Tun suna ganin abun wasa har dai suka tabbatar da an kira su ne domin aci zarafin su. Sauro sun yagi rabon su ajikinsu, su ne anan kamar wasu almajirai har karfe goman dare. Mu’azzam yunwa ya ke ji kuma gashi anguwan ta masu kuɗi ce babu masu saidae saide a wajen. Mansoor yace bari ya je can bakin titi ya gani ko zai samu ko mai doya ne ya siya musu. Mu’azzam ya rike masa hannu ya na faɗinn”Mu tafi gida, daman an kira mu ne domin a ga an wulakantamu.” Aji ya yi shuru yana kallon ƙaninsa da yunwa ta galabaitar dashi daman a hanya gurasa kaɗai suka siya kuma ba ta da wani yawa..
Shi kan shi ya na yin dauriya ne, amman ya ku sa gazawa. Soyayyar Mimi ta makantar da shi da ganin laifin abin da ke shirin faruwa.
Kafin ma Aji ya samu zarafin mgana sai ga wata katuwar mota ta zo za ta shiga gidan, direban ma soja ne sun ga dai ya tsaya Sojan da ke gadi ya sunkuya ya yi masa mgana su ka ji yana faɗin” Yes Sir..!
Motar na shigewa Sojan ya zo ya ce musu su tashi su shiga ciki in ji Oga.
Jiki duk ya saki Aji ne mai kaurin jiki Mu’azzam duk ya gama laushi.
Ashe ba cikin gida za’a kai su ba nan katon haraban gidan aka ce su zauna su jira tun suna san ran ganin an zo an kira su har suka sare haka Mu’azzam ya fara amai sai ruwa saboda yunwa. Hankalin Mansoor ya tashi saboda Kaninsa na gaba da soyayyar Mimi.
Kokarin fita daga gidan ya ke yi saboda ya je ya samo ma ƙaninsa abunda zai saka a bakinsa. Sojan nan ya ce Oga bai ce su bar shi ya fita ba, ransa ya ɓaci zuciyarsa ta yunkuro daman ga shi ba ta da kyau balle kuma an ɓata mata.
Sai ya yi kokarin fita da karfi wannan Sojan ya saka katon takalmin kafarsa ya shure shi sai da ya faɗi. Mu’azzan na ganin haka ya tashi sai ya ma daina jin jiri ya je ya rike ɗan uwansa yana ba ma Sojan hakuri da har ya fara nuna Mansoor da bindiga.
Dakyar ya hakura sai da wani sojan su masu tsaron kofar shiga gidan ne ya yi masa mgana cikin harshen turanci sannan ya ƙyaleshi.
Shi kuma Mansoor sai faman sakin huci yake ke yi, an riga an yi sara kan gaɓa Kuma a dai dai lokacin megidan ya ce a shigo da su kamar zai ce sun fasa shiga sai kuma wata zuciyar ta ce ya je ya ga waye wannan Mutumin da ya ke da zarran wulakanta shi, sai ya miƙe shi da Mu’azzam sun yi laushi kamar lawashi, Allah yasa daga su sai kayan jikinsu da ai sun rena kansu.
Soja nan na gaba suna bin shi a baya haka suka shiga falon gidan, Ba kowa a falon sai Abi ya na zaune kafa ɗaya kan ɗaya ga bindiga a saman tuburen dake gabanshi suna shigowa ya mike a fusace bayan ya yi ma Sojan da ya rakaso alamun ya bar falon.
Sai da ya fice sannan ya musu wani matsiyancin kallo Mu’azzam ne ya yi saurin zubewa a saman cafet domin ya kasa iya tsayuwa cikin muryan da ta ji jiki ya gaishe da Abi ko kallonsa bai yi ba cikin Ƙaraji ya ce”Wane ne daga cikin ku yake son Mimi?
Ya faɗa kai tsaye cikin takama Mu’azzam ya tsorata domin ko iya kallon Major Kabir bai yi ba saboda ya yi masa kwarjini sannan muryansa ma kaɗai abun tsoro ne.
Mansoor na tsaye ƙi kam ya ce”Ga ni nan..”
Major Kabir ya tako har kusa da shi ya kallesa daga sama har kasa a ransa yana fadin lalle yaga tsaurin idon yaron.
Cikin Yanayin maaganarsa ya ce” Wani zarra gare ka da ya sa har ka iya takowa gidana acikin falona kana gayamin kai ne kake son Mimi? Kai ne ka hure mata kunni take kokarin saɓa ma umarnina miye matakin da ka taka a rayuwa?
Ya faɗa yana kallon Mansoor da ya yi kamar bai ji shi ba, ya dunkule hannunsa kamar zai kai naushi sai faman huci yake saki kamar shi ne Sojan ma.
Major kabir ya kallesa cikin mamaki kafin ya daka masa tsawa yana faɗin” Ina tambayarka kana min shuru? kuma ina mgana kana tsaye? Ka rage tsawon ka a ƙasa na ce.!”
Ya faɗa a tsawace amman goganka ko gezau sai ma Mu’azzam da ya kallah cikin fitar numfashi ya ce”Tashi mu tafi Mu’azzam.”
Major kabir ya ga kamar Mansoor ya raina shi ya zo har gidan shi bayan ya aikata masa wannan laifin kuma yana masa mgana shi zai nuna ma jan wuya lalle bai san me ake kira da Soja ba yau zai sani.
Magana kawai ya yi sai ga sojoji kusan huɗu sun bayyana afalon cikin huci nan da nan ya ba su umarnin su rike masa Mansoor su banƙare shi, Mu’azzam ya fashe da kuka yana faɗiin”Ka yi hakuri don Allah kada ka saka a dake shi.”
Cikin fusata Major kabir ke faɗin “Kamar ni? Kamar ni wani talakan agolan da ubansa har ya mutu a ƙauye, tarihin rayuwarsa kaf babu abun mamora. Yaron da uwarsa ke aiki a karkashin mahaifiyata ba ka da wani Future mai inganci anan gaba, ka yi min laifin ka yi soyayya da ƴata ba da sanina ba ka hure mata kunne ta saɓa ma umarnina maimakon ka nemi afuwata sai ka zo har gabana kana min takama. Who are u.?
“I SAID WHO ARE U…?
Ya ƙara faɗa cikin matsancin tsawa, ya kuma saka kafarsa lokaci ɗaya ya daki kasa sai da suka ji karan bugun takalminsa Mu’azzam tsoro ya kama shi ya fara makyarkyata shi kuma Mansoor Major Kabir ya ce su banƙare masa shi nan da nan ko suka cika aikinsu yana fizge fizge riko ɗaya suka yi masa sai ga shi a hannunsu to in takamarsa zuciya ya zo gidanta.
Mommy dake cikin ɗaki tana jiyo duk abin da ke faruwa ita da Khadija..ta yi kuka har idanuwanta sun sauya oauni
Me ya sa Major zai yi haka? Me ya sa zai saka a kira yaro nan saboda kawai yaci zarafin su?. Tun ɗazu Hajiya da Mimi ke kira ta kasa ɗaga wayarsu. Khadija ce ke leke ta kofa ta dawo da sauri tana faɗin”Mommy Abi kada fa ya yi kisan kai ga shi can ya saka soldeirs sun riƙe shi.”
Mommy na jin haka ta mike jikinta na rawa ta ce” Ba zan bari hakan ta faru ba Khadija yau sai na karya dokar Major.”
Khadija na riketa ta fizge ta fita saboda ji ta ke yi kamar abunda ya ke shirin aikatawa bai kyautu ba. Kuma daman ya ce kada ta sake ta fito in shi bai kirata ba.
Tana fita dai dai lokacin da Major ya ba da umarnin su yi ta dukan Mansoor har sai ya gane kuran shi. Mu’azzam na kuka yana roƙon shi ya daka masa tsawa da cewa ya rufe masa baki ko shi ya tashi kansa da bindiga. Mu’azzam ya koma gefe yana danne bakinsa, ji ya ke yi kamar ya saki fitsari saboda tsoro.
Mommy da gudu ta ƙarisa gaban Major ta duka tana faɗin”Please Habiba ka ce su rabu da shi, na ji bai kyauta ba sai ka gaya masa ba yanzu zaka aurar da ƴarka ba, shike nan ka bar su tafi.”
A fusace ya kalleta kafin ya ce”Wa ya baki izinin fitowa? .How dare are u Murja?
Ya faɗa cikin tsawa sai kawai ta fashe da kuka tana kallon yadda sojojinsa ke dukan bawan Allah da bai ji bai gani ba.
Ta yi rokon duniyan nan ya kauda kai ya ce in har Mansoor ba zai ba da hakuri da bakin shi ba su yi ta dukan shi har gobe da safe.
Mommy na kuka ta ce” To in suka kashe shi fa? Da ƙarfi ya ce”In ya mutu banza ne ya mutu, rayuwarsa ba ta da wani amfani da ni zai yi wasa? Am i his mate? da Major zai yi gogayya yana ɗan talakawa irinsa? Agola yaron mai aiki a ƙarkaahin mahaifiyata , su dake shi in ya mutu zan saka su wurga shi daji namun daji su cinye banza a banza kuma babu abin da zai faru.”
Ya faɗa ko a jikinsa sai ma hannayensa da ya goya a baya ya na jin daɗin a abunda su ke yi. Kukan Mu’azzam da na Mommy ya cika falon a gaban idanuwansu sojoji suka sumar da Mansoor gau saboda duka Sannan kuma anan take ya saka su suka dauke shi yace su je fa shi a cikin kurku zuwa safe. Sannan ya kalli Mu’azzam yanq faɗin”Kai kuma zan baka wajen kwana, da safe ka san in da dare ya yi maka, yaron nan ba zai bar gidan nan ba sai ya gane ya ja da Major Kabir sulaiman Dabo sai na ƙarar da rashin kunyarsa.,”: Mu’azzam ya kwanta a gaban Major yana fadin”Don Allah Sir ka yi mana rai ka yafe masa.”
Mirmishi ya yi irin mirmishin basawa kafin ya ce”Sai na ga waye Boss tsakanin ni da shi.”Daga haka a fusace ya bar falon ya taka zuwa ɗakinsa bayan ya ba ma wani Soja umarnin a kai Mu’azzam ɗaki ya kwana zuwa da safe.
Sai bayan shigewarsa Khadija ta fito ita kanta sai da ta yi kukan tausayin Mansoor da Mu’azzam wanda shima ɗaya daga cikin sojan ya zo ya ja shi sun bar falon Mommy haka ta ke kuka khadija na hawaye.
Dakyar ta iya tashi ta shiga kitchen ta zuba abinci a faranti ta fita kofar falon da kanta ta yi ma shugaban sojojin tsaron gidan mgana ta mika masa abinci ta ce a kaiwa Mu’azzam wanda aka fitar da shi daga baya.
Khadija kuma ta saci wayar Mommy ta kira Hajiya ta na hawaye ta labarta mata abin da ya faru Hankalin Hajiya ya tashi acikin daren ta Kira Alhaji Hamza tace gobe gobe ta ganta a Abuja, Mimi daman ta ji a jikinta tun kafin Hajiya ta sanar mata abunda ya faru ta ke kuka abun tausayi.
Hajiya har kuka sai da ta yi na wannan cin zarafin da Kabiru ya aikata yanzu da wani ido za ta kalli Meri da Baba Ɗanjuma? ta yi nadama in da tasan haka zai faru da ba ta yarda ta tura su ba.
Shima Mu’azzam lokacin da Mansoor ke shan duka wayarsa ta faɗo daga cikin Aljihunsa sai ya yi sauri ya ɗauketa, shima wani ɗaki a ka saka shi amman ba’a kuntace ba ne kuma an kawo masa abinci amman tashin hankali ya sa ya manta da wata yunwa.
Inna Meri ba ta da waya, Baba Ɗanjuma kuma ta shi ta lalace Nasir ya samu nasaran kira Mu’azzam na kuka ya na gaya masa halin da ake ciki da kuma rokonsa ya je ya gayama su Baba ga halin da Mansoor ke ciki yanzu haka bai san inda suka kai shi ba ko ya na da rai Allahu shi ya sani.
Nasir ya shiga ɗimuwa, a daran ya tafi gidan su Mansoor ya iske Inna Meri itama ta kasa barci saboda tunanin halin da ya’yanta ke ciki labarin da Nasir ya gaya mata ya sa ta fasa kuka har yan cikin gida su ka ji.
Baba Ɗanjuma na ɗakin Magajiya ya fito da gudu shi kanshi da ya ji abin da ke faruwa sai da cikinsa ya karta. Inna Meri na salati ta na kuka tana faɗin”Shike nan abinda nake ta gudu ya faru.”
Su Baba Ɗanlami kuma suna ta faɗa suna faɗin yaro zai jawo musu fitinar da ya’yansu ma ba su jawo musu ba.
Nasir shi ya kira Makama yana gaya masa halin da ake ciki su kansu sun shiga tashin hankali daman su san halin taurin kan Aji gashi nan ya kai kansa inda za’a kashe shi.
Saboda dare ya yi ya sa a ka bar ma gobe har da safe sai da Mu’azzam ya sake kiran Nasir ya ce har yanzu bai ga Mansoor ba kuma shi ba zai tafi ya bar ɗan uwansa a wannan bakin gidan ba.
Nasir ya ce ina kada ya je ko’ina bari ya je can gidan ya gani, ai yana zuwa sai ya ji labarin tun safe Inna Meri da Baba Ɗanjuma suna gidan Hajiya shima sai ya Nufi acan, can ɗin ma abun tausayi Mimi ta kwana kuka duk idanuwanta sun kumbura haka Hajiya ya iske Alhaji Hamza ya yi musu Bucking din jirgi zuwa Abuja har da Inna Meri da Baba Ɗanjuma za’a tafi, Inna Meri faɗi take yi”Sai ni naje na duka na bashi hakuri zan roƙe shi Allah ya sakar min Ƴaƴana ba su da kowa Allah ne gatan su.”
Yaddiko na gidan itama duk daga baya take jin labarin abubuwan da suka faru. Amman abunda Yaya Kabiru ya aikata ya yi son rai, ba kyau ka wulakanta mutum.
A ranar suka bi jirgi zuwa Abuja daga filin jirgin suka hau taxi zuwa gidan su Mimi da ke Abuja Mommy ce kawai ta san da zuwan su domin itama ta ce ya kamata su zo gabaɗaya in ba haka Major zai kashe yaron mutane.
Yana Office Alhaji Hamza ya kira shi ya ce ga su sun zo har da Hajiya ma.Shi ya yi tafiyar sa ma ya bar yaron mutane sojoji na yi masa azaba, Mu’azzam kuma ya ƙi tafiya saboda tun jiya bai kara ganin inda a ka kai masa Dan’uwa ba, abinci ko ya kasa saka shi acikin cikinsa shima ya yi kuka ina zai nufa gida cike da sojoji shima yanzu su kamashi su yi ta ta duka Mommy ta aiko masa da abun kari ruwan zafi kawai ya iya sha yana jiran zuwan su Inna Meri tunda Nasir ya sanar da shi tare da su za’a taho.
Mu’azzam na haraban gidan tsaye su Inna Meri suka iso, wajen su ya nufa yana kuka ya rumgume su.
Mimi kuma tana kuka ta kwashi gudu zuwa cikin gida tana kiran sunan Mommy.
Inna Meri sai tambaya take yi Ina Baban Inna? Mu’azzam na kuka yana faɗin”Inna an kai shi wani ɗaki, ban kara ganinsa ba a sume su ka fita da shi. Jini na zuba ajikinsa.”
Mu’azzam ya kara rushewa da kuka Inna Meri na salati da sallallami.
Page 15
Baba Ɗanjuma kuma sai maimaita faɗin” Innalillahi wa’inna ilaihirraju’un” kawai yake yi shi kan shi ba domin yana namiji ba tashin hankalin da suke ciki ba zai saka ya iya mallakan kansa ba. Ba shi ya haifi Mansoor ba amman da gaske yake yi ya karɓo amanarsa kuma yana jin sa kamar Mu’azzam ne shi a wajensa.
Tabbas Baban Inna ya janyo ma kansa fitinar da tafi karfinsa haka Inna Meri da Baba Ɗanjuma ke ta raya acikin ransu saboda ganin samudawan Sojojin dake tsaran gidan Major fuskarsu ba fara’a daga gani ba su san wani abu wai shi Imani ba sun fi gane yaren umarnin wanda ya ijiyesu.
Su kansu kafin Sojan dake tsaren get ya amince su shiga sai da Alhaji Hamza ya kira Yayan na shi da kansa ya yi masa mgana sannan ya kira wayar sojan sannan aka buɗe musu get suka shiga cikin gida.
Har da Yaddiko a ka zo sai ga su kowa ya yi zaman sanyi a cikin falon gidan Major Kabir, Inna Meri tana shan kuka lokaci ɗaya tana riƙe da hannun Mu’azzam, Mimi kuma ma na jikin Mami tana wani irin kuka mai ban tausayi. Hajiya kuwa girgiza jiki kawai take yi ta kasa mgana domin kunyar su Inna Meri take ji, tun bayan gaisawar da suka yi da Mommy ga shi an kawo musu ruwa da lemu amman zullumi ya hana kowa motsi.
Hajiya ta kalli Alhaji Hamza lokaci ɗaya tana faɗin” Wai ba ka ga ya ma Kabiru har da ni aka zo ba ne?.
Cikin ladabi ya ce” Na gaya masa Hajiya, ya ce ga shi nan tahowa.”
Sai kawai ta jinjina kai wani abu na taso mata acikin kirjinta.
Murja ta kalla da ke rike da ƴarta itama daga gani ta sha kuka ba ta cikin natsuwarta. Cikin tsausayi Hajiya ta ce” Murja har ke Kabiru bai saurare ki ba ko? Kuma ba ki san inda ya sa a ka kai yaron mutane ba ko? Mommy ta sauke ajiyar zuciya kafin ta ce” Ba irin rokon da ban yi masa ba Hajiya ɗan uwansa ma yana kuka ya roƙonsa amman bai saurare mu ba, bai sa an fita da shi ba ya na nan acikin Kurkunsa na cikin gida, ba wanda ya isa ya sa su fito da shi sai in har shi ne ya ba su umarni Hajiya.” Yaddiko ta yi kasaƙe kafin ta ce”Kai jama’a kurkuku kuma ?
Mommy ta gyaɗa mata kai kafin ta ce”Eh ya na da wani ƙaramin ɗaki da bai wuce tsawon gajerun mutum ba, sannan ba shi da faɗi kuma a ƙasan yake, akan sanya mutum a ciki in ya yi wani laifi domin a yi masa horo.”
Gabadaya sai Inna Meri da Baba Danjuma su ka kara ruɗewa, Yaddiko ta saka salati Hajiya ta karishe ma ta shi ko Alhaji Hamza kai ya girgiza kafin ya ce” To duk me ya yi zafi? Wannan lamarin da duk an bi shi a hankali da an warware komai cikin sauƙi”
Inna Meri ta zube a kan kafafunta daga saman Kujera ta haɗa hannayenta waje ɗaya tana faɗin”Don girman Allah Hajiya kin yi min rai ki saka a saki Baban Inna wlh na yi miki alkwarin ko hanyar gidan ki bazan kara kallo ba har abada,ni dai ku saka ya sake shi kuma shima in sha Allahu ba zai kara kusantar Inda ƴar ku take ba, laifin yaro ne tunaninsa ba ya ba su abu dai dai in da ace yayi tunanin shi kanshi ba zai janyo ma kansa rigimar da ta fi karfinsa ba.”.
Tana mgana tana kuka Mu’azzam na taya ta sai aka rasa mai lallashinta ballantana ya ce wani abu, Hajiya ke sharan kwalla a ɓoye Mommy kuma na tausayin ƴarta ne.
Ana cikin wannan halin sai ga Major kabir ya shigo cikin kakinsa na aiki wani Soja na mara masa baya. Yana shigowa cikin takunsa na zafin nama na cikakkun mazan jiya, sai ya ɗaga ma Sojan hannu fuskar nan ba rahama shi kuma sai ya juya ya fita bayan ya sara masa.
Baba Ɗanjuma kallo ɗaya ya yi masa shima tsoronsa ya kamasa sai ga shi shima zube kan kafafunsa kusa da Inn Meri ya na rawan jiki da na zuciya.
Ya ga Hajiya a zaune amman bai nufe ta ba sai ya samu wata kujera mai zaman mutum ɗaya ya zauna ya ɗora kafa ɗaaya kan ɗaya ya na ƙare ma mutanen falon kallo har ya sauke kan Hajiya cikin yanayin maganarsa ta Sojoji ya ce” Hajiya duk wannan taron na menene.? da kun yi zaman ku yaro zai yi wasa da gidan Soja ne shi ne nake so na koya masa hankali nan gaba ko sunan Soja ya ji an ambata sai ya yi fitsarin jini acikin Wandonsa.” Kafin Hajiya ta samu zarafin mgana Inna Meri ta rarrafa tsakiyar falon kamar ta kwanta masa, ita ko iya kallonsa ba ta yi saboda firgici cikin roƙo kamar zai yi mata gafara ta fara faɗin”Don Allah ka yi masa aikin gafara ka yi hakuri ka yafe masa yarinta ke damunsa amman ina wuyan Baban Inna ya yi karfin da zai ja da kai? Ka yi masa rai don Allah ka sake shi.”
Take faɗa tana kuka har da majina, A kaikace Major ya kalleta cikin wani irin Murya ya ce”Wace ce ke?
A razane ta ce”Ni ni mahaifiyarsa ce, ga mahaifinsa nan.”
Ta faɗa ta na nuna Baba Ɗanjuma da shima ya ƙariso tsakiyar falon da jan gwiwa Mu’azzam ganin iyayensa duke kamar masu neman gafara ya sa shima ya rarrafa cikin jan gwiwa zuwa kusa da su ya durkusa ba zai bari kimar iyayensa ta zube ba, ko da ba shi da yarda zai yi gwara shima ya yi zaman neman gafaran tare da su. Sai da Major ya gama musu kallon wulaƙanci sannan ya yi wata irin sariya kafin ya ce”Ke ce uwar da kika ki haifi mara kunyar yaron da zai ja da ni? Kai kuma kai ne uban da ke rikon Agolan dake neman ja da Soja?
Ya karishe faɗa yana nuna kansa bayan kuma daga karshe ya nuna su ɗaya bayan ɗaya jikinsu na rawa kansu na kasa kamar sun ga wani mala’ikan mutuwa, kuma kowa ya kasa mgana Hajiya bakinta ne ya yi nauyi? Me za ta ce? Ko ta yi mgana ba zai taɓa Sauraranta ba tunda halinsa ne baya girmama maganarta a matsayinta na uwa a gare shi. Alhaji Hamza ne ya yi gyaran Murya ya fara mgana da cewa” Major..”
Sai kawai ya ɗaga masa hannu cikin kaushin Murya ya ce”Ya raina matsayina, yaron ya yi min tsurin ido bayan ya fara soyayyaa da ƴata ba tare da sanina ba, sannan ya zo har gidana ina mgana yana tsaye ina tsaye sannan wai ni zai nuna ma tsageranci? Sai ni kuma na nuna masa ba’a zuwa gidan Soja a yi taurin kai na ce su yi ta dukansa in har bai yi nadama ya ba da hakuri ba, ka da su barshi ko duka zai kashe shi”
Mimi ta saka wani irin kara ta miƙe tana faɗin” Abi.”
“Ke sai na harbe ki, in kika kara mgana anan wajen nonsess kawai.”
Ya faɗa cikin zafin nama har yana miƙewa da sauri Mommy ta mike da sauri ta maƙale ƴarta a bayanta tana rawan jiki, Hajiya ta yi yunƙurin mikewa dai dai sanda Inna Meri ke dukar da kanta a kasa tana haɗa Major Kabir Allah da Annabi ya saki Mansoor shi kuma ya ce ba yanzu ba sai ya san da wanda ya ke faɗa. Cikin yanayin ba da umarni Hajiya ta ce”Kabiru ni a matsayina na Mahaifiyarka na ce ka saki yaron mutane ka sake shi.”
Cikin kallon Hajiya ya ce”Hajiya kinsan me ya yi min ne? Kama na kamar ni wannan yaron talakawan zai ja da ni?.
Da ƙarfi Hajiya ta ce”Ba na son ji komai, ka sa ka a saki yaron nan yanzun nan ban san zalunci.”
Ta faɗa cikin bayyana bacin ranta har da hawayenta sai ya fara huci yana wani cijewa kamar zai kai duka.
Sai Hajiya ta fara kokarin dukawa tana Fadin” Ko nima sai na duka ne?.
Da sauri Alhaji Hamza ya mike ya isa ga Hajiya ya riƙe ta yana Faɗin” Haba Hajiya ai kin wuce haka a wajen Yaya zai yi abin da kike so yanzu ma kuwa”
Major Kabir ya kallah kafin ya ce” Major ka sa a saki yaron nan don Allah, ka duba darajan Hajiya ga kukan da rokon da iyayen yaron ke yi maka, ka yi masa afuwa ka saka a sake shi.” Yadikko ma ta saka baki, sai da Hajiya ta fashe da kuka tana Fadin”Shike nan kabiru kada ka sake shi. Wlh in har wani abu ya sami yaron mutane ba zan taɓa yafe maka ba.”
Jin haka yasa Alhaji Hamza ya ce” Major ka sarrafa fushinka, Hajiya ke mgana da kai fa.”
Sai da ya fitar da iska daga bakinsa sannan ya ɗaga waya ya kira ɗaya daga cikin Sojojin ya ce a taho da wannan yaron zuwa falonsa ya na jiran su. Cikin lokaci kaɗan da bai gaza mintina goma ba sai ga shi sun shigo da shi kamar sun ɗauko wani cuta suna zuwa tsakiyar falon suka sake shi ya faɗi kasa warwas tunda ba shi wani kuzari, Kamar ma sun watsa masa ruwa ne ya farfaɗo tunda faran rigan jikinsa duk ya baci da jini, fuzkarsa ta kumbura idanuwansa sun shige ciki saboda tsabar duka bakinsa ya sumtuma da goshinsa.
Bai iya kuma motsa hannunsa na dama da kafarsa ta hagu ba, kallo ɗaya zaka yi masa ka san cewa ya bugu buguwa na sosai tunda har kammaninsa ya sauya.
Da wani irin sauri da kuka Inna Meri da Baba Ɗanjuma suka nufi Mansoor Mu’azzam ya tarairayo sa jikinsa yana ta kiran sunan shi amman ko iya buɗe ido ba ya yi saboda tsabar duka, yana so ma ya bude ido ko ya yi mgana ya kasa Allah ne ya yi kwanansa na gaba kwana suka yi suna dukanshi, shi kuma bakar zuciyarsa ta hana shi ya yi nadama. Inna Meri ta riko hannun da na dama da sauri ta ga ya janye hannu ya na cije leɓensa da duk ya fashe saboda duka cikin kuka Mu’azzam ya ce”Inna bar taɓa hannun kila ya samu gocewa ne.”
Baba Ɗanjuma yana share ma Mansoor jinin goshinsa da haɓan rigansa lokaci ɗaya yana kiran sunan shi”Baban Inna buɗe idanuwan ka? Baban Inna, Baban inna” Haka yake ta kiran sunan shi yana jin su amman kuma ya kasa iya buɗe idanuwansa.
Mmi na leƙensa ta bayan Mommy tana kuka ta san in ta ce za ta karisa sai Abi ya saka bindiga ya ɗauke kanta Khadija ma tana falon amman itama ko motsi ta kasa, Hajiya kuwa sai kawai ta dukar da kai tana kuka faɗi ta ke yi
“Kabiru wlh ka ɗauki hakkin wannan yaron kuma in har bai yafe maka ba sai Allah ya isar masa”
Yaddiko sai salati ta ke yi ganin Yadda Sojoji su ka maida hallitar Mansoor.
Alhaji Hamza kuma ya ma kasa magana bai ɗauka rashin imanin Yayan nasa ya kai haka shahara ba, shi ko tsoron ya kashe shi ba ya yi. Hawayen Inna Meri da na Mu’azzamu na ɗiga a saman fuskar Mansoor su suka taimaka har ya iya buɗe likakkun idonsa guda ɗaya ya na kallon iyayensa suna kuka saboda halin da ya saka su, yunkurawa yake yi kamar ya tashi amman kuma ya kasa sai da Mu’azzam ya rike shi sannan ya iya tashi zaune, amman dauriya ce shi kaɗai yasan halin da yake ciki.
Major Kabir kuma sai mirmishin mugunta yake yi kafin ya ce”Zan kyale yaron ku saboda Hajiya amman ba domin haka ba da sai ya raina kansa, amman ko yanzu ya san karo da Soja ba wasa ba. Sannan akwai sharaɗin da zan kafa muku da in har ya tsallake su anan gaba sai dai shi ya mutu wlh.” Inna Meri da Baba Ɗanjuma har suna karo da Juna wajen ƙara dukawa gaban Major Kabir, suna rawan bakin sanar da shi sun amince kuma Mansoor zai yi biyayya ga Sharaɗin sa.
Major Kabir ya nuna Mimi da yatsa kafin ya ce”Ba shi ba ƴa ta, ko kallonta ya kara yi in na sani sai na lalata rayuwarsa, sannan ya sani kada ya kara min wannan tsaurin ido Mimi tafj karfin talaka kamarsa wanda har ubansa ya bar duniya bai shigo birni ba, Kuma ni ba zan iya aura ma ƴata Agolan da rayuwarsa ba ta da wata mamora ba, daga yau sai yau na raba wannan alaqar ba shi ba ƴa ta ba rayuwata in kuma ya ki ji to Wlh a karo na biyu har ku mutu ba za ku kara ganinsa ba domin sai na ɓatar da rayuwarsa, Kuma ba zai bar wajen nan ba sai ya duka ya nemi gafara ta kamar yadda kuka yi yanzu in kuma har yanzu bai yi laushi zan saka shi ya yi laushin.”
Ya faɗa ya na nuna Sojojin da ke baya sun kame, Inna Meri har tana rawan baki riko hannun Mansoor ta kamkame tana fadin”Darajar haihuwar ka da nayi Mansoor ka buɗe baki ka ba shi haƙuri saboda ka tsira da rayuwarka.”
Mansoor kukan zucci ya ke yi zuciyarsa na wani irin suka, yana ji kamar ya zama asarrare mara amfani, duba yadda Mahaifiyarsa da wanda ya zame masa uba da ƙaninsa suke kuka saboda shi, kalli yadda suke duke gaban wani hallita na Ubangiji saboda shi , yau saboda shi an kira sunan mahaifinsa an zage shi da gorin ya mutu a kauye bai taba shiga birni ba, shi ba yana kukan dukan da ya ci ba ne da dai ya ba ma wannan mugun hakuri gwara ya kashe shi, Shi ko da wani suna zai iya kiran kalmar Soyayya? Tun jiya ya ke son yaji ya tsani Mimi acikin ransa amman ya kasa, ji yake yi kamar ya mutu baƙinciki da yake cikin zuciyarsa tunda ya zo duniya bai taɓa tsintar kansa aciki ba. Ba shi da niyar saduda ya so ne su bar shi ya kashe shin in dan har zai iya, Sai dai Kukan Inna Meri da na Baba Ɗanjuma tare da Mu’azzam suna masa magiyan ya bashi hakuri saboda ya tsira Inna Meri ta san halin abin da ta haifa yasa a fusace ta ce”Ko ka bashi Hakuri ko na ce sai ka biyani Nonona da ka sha”
Baba Ɗanjuma ya kira sunanta da karfi cikin tashin hankali.
“Meramu..”
Hajiya ma sai da ta kira sunanta ita kuma ta yi hakane saboda ya ba da hakurin ta san halin Baban Inna da kafiya sai yace sai dai a kashe shi. Kuma hakan da ta yi sai a ka samu masalaha domin Mu’azzam ya rike sa ya durkusa saman gwiwiyonsa tare da Iyayensa kansa na kasa ya na jin taruwan hawaye acikin idanuwansa, ko dukan da aka yi masa bai saka shi kuka irin wannan tozarcin ba muryansa ba ta fita ma sosai Saboda wahala ya furta” Ka yi hakuri..!”
Yana gama faɗin haka sai ya ji wasu hawaye masu zafi sun sauko masa.
Nan Major Kabir ya Koma ya zauna yana Faɗin”Good. za ku iya tafiya da shi amman ya kiyaye sharuɗɗana.
Inna Meri da Baba Ɗanjuma suna rawan jiki masa godiya su ka miƙe jiki na rawa Hajiya nauyi da kunya su ka hanata mgana Alhaji Hamza ne ya ce su tsaya mana a nema musu Jirgin komawa da sauri Baba Ɗanjuma ya ce”Mun gode da karamci ranka ya daɗe ya isa haka.”
Hajiya ta yi saurin kallon Major kafin ta ce”Kabiru ka dubi halin da Binta ke ciki Hausawa su ka ce idan An ciza a hura watarana kada ka zo kana nadamar abunda ka aikata ma wannan yaron”
“Ni? Kamar ni Major Kabir My Daughter ta auri talaka Agolan da ubansu har ya mutu a can wani kauyen kurmus, uban rikonsa wanzami uwarsa yar aiki? Over my dead body Mimi za ta yi wannan auran ƙaskanci ba ta isa ba, ko za ta mutu bazan aura mata wannan talakan ba, jinin takalawa wanda bashi da wata kyakyan makoma ko anan gaba.” Ya karishe faɗa a fusace kamar ba da Hajiya ya ke mgana ba, kawai sai ta girgiza kai kafin ta ce”Shike nan Allah ya hana mu jin kunya watarana.”
Ta faɗa ta na kallon yadda Idanuwan Mimi suka kumbura saboda kuka, Mommy ma sharan kwallan take haka ma Khadija kowa kuma yasan ba’a kyauta ba, amman kowa yana tsoron ya yi mgana wanda bai girmama maganar uwar da ta haifesa ba ai ba wanda kuma ya isa ya yi masa mgana ya saurare shi.
Mu’azzam ya riƙo sa tunda ba ya iya tsayuwa gefe kuma Baba Ɗanjuma ya kama shi za su fita daga falon da gudu Mimi ta ƙwace daga jikin Mommy ta ƙarisa gaban Abi cikin kuka Ta ce.
“Abi ka yi hakuri Abi ina son shi don Allah kada ka raba mu da juna”
Cikin tsawa Ya ce” Sai dai ki mutu, amman Wallahi tallahi ba za ki auri wannan talakan yaron nan ba, ba shi da makoma mai kyau, ina tambayan ƙwalin karatun shi Hajiya na gayamin iyakarsa Secondary school. Soja yake son zama ire iren su ma ba su da wani rabo a duniya.” Mimi ta katse shi cikin gunjin kuka tana kara faɗin.
“Abi ina son shi..”
“Ke yarinya ce Mimi, karatu nake so ki yi ba yanzu zan yi miki aure ba”
Ya faɗa shima bayan ya katseta cikin kaushin Murya.
“Abi Ina son shiiiii…”
Ta faɗa cikin wani irin karyayyen sauti kamar za ta shiɗe.
“Murja ki ɗauke min Mimi kada raina ya ɓaci na fasa kanta da bindigata”
Ya faɗa ya na kokarin sarrafa fushin sa domin ji yake yi kamar ya tokareta ta faɗi in ta na haɗa shi da wannan ƙasƙantaccen yaro nan mara makoma mai kyau.
Ba zai manta da wannan kukan da ta rika yi lokacin da mahaifiyarta ke rike ta ba, har gobe yana jin Sautin wannan kukan acikin kirjinsa. Ya tuna ta na miƙo hannunta Mahaifiyarta da yayarta khadija suka riƙe ta suka tafi da ita zuwa cikin wani ɗaki.
Yayi ƙokarin danne abin da ke taso masa amman sai ya kasa, kafarsa ya makaleta ya kasa tafiya da ya sa su Mu’azzam su ka tsaya su na kallonsa ba su san abin da zai aikata ba da ba su barshi ya kara yin mgana ba.
Sai juyawa kawai su ga ya yi ya na faman ɗingisa kafa idanuwansa a like ga kaya duk sun yage ba hula ba takalmi kamar wani almajiri cikin muryan da ta galabaita ya fara faɗin.
“In har ni Mansoor na haifu cikin uwata Meri da uba na Ibrahim ƴarka ko ita kaɗai ta rage a duniya nan sai dai ta mutu nima na mutu ban yi ba aure ba,”
Ya faɗa ya na sakin numfashi Inna Meri na kokarin toshe masa baki amman sai da ya ida sa faɗin abunda ke ransa a lokacin.
“Nayi alkwarin toshe kunnuwana daga jin ta da ganinta na yi alkwarin sauya duniyata daga duniyar ta na yi alkwarin sauya mattacen mafarkina a kanta, na kuma gode maka da ka fahimtar dani darasin rayuwar dana daɗe ana ga ya min ban ɗauka ba, na kuma fahimci akwai tazara mai kimanin kilomita tamanin tsakanina da ƴarka, na kuma fahimci matsiyaci kamata ya yi shisshigi wajen tusa kansa in da bai dace da shi ba, yadda ka saka iyayena kuka a kaina kai ma watarana sai ka yi kuka saboda ƴarka.”
Yana gama faɗin haka ya juya kamar zai kifa saboda yanayin jikinta Major Kabir ya yi wani kayattacen mirmishi kafin ya ce” Ku ja ma ɗan ku kunne, na ga alaman tsageranci na damunsa sannan ku yi masa iyaka da ƴata domin ruwa ba sa’an kwando ba ne, zan sake shi na yanzu amman ko kallon Mimi ya sake yi sai na ɗaure shi da kakin jikina.” Baba Danjuma bakinsa na rawa ya ce”Ba ma zai kara kallonta ba In sha Allahu ka yi hakuri.”
Haka su ka fita da Mansoor a rirriƙe da shi saboda halin da ya ke ciki, kuma ba wanda ya bi bayan su. Shima Major ɗin mikewa ya yi a fusace ya shige cikin ɗakinsa har yana banko kofa Hajiya ta bi shi da kallo tana Sassauta fushinta domin kada ya zama masifa ga rayuwar Kabiru. Amnan ita ta so da aka Ciza sai a Hura saboda ba’a san abunda gobe za ta haifar ba.
Ko kwana ba su yi a Abuja ba Hajiya ta ce gida zata koma, Mimi kuma ta zauna wajen mahaifinta ba za ta kara amsar ta riko ba tunda ga abunda ya biyo ba, Mommy ta yi tayi Hajiya ta kwana Hajiya ta rantse ba za ta kwana ba. Hajiya na ba ta hakuri Mommy ma na ba ma Hajiya hakuri ta yi mirmishin takaici kafin ta ce”Bakomai Murja wata rana Kabiru zai yi nadama, sai dai ina fatan Lokacin da zai yi nadamar lokaci bai kure masa ba.
Alhaji Hamza a lokacin ya nema musu jirgi suka juya zuwa Gombe kuma har suka bar gidan Major bai fito daga ɗaki ba, Mimi dai kuka ta yi kamar zata ba ma uku lada domin ta so ta bi Hajiya su koma gombe Hajiya ta girgiza kai kafin ta ve”A’a ki zauna ki yi ma mahaifinki biyayya shi ya haife ki ya fini iko da ke, ina miki fatan Allah ya sanya hakan ya zama alheri a rayuwar ki Binta ki yi Hakuri kin ji ko? Mimi tana ji tana gani Hajiya ta tafi ta barta daga nan ta fahimci ta rasa wani hop, domin Mommy ba ta isa da ja da hukuncin Abi abunda ya faɗa tabbas haka din ne zai kasance.
Tun daga wannan daran Mimi ta ke kukan Rashin Aji a rayuwarta kukan da har tsawon shekaru goma ba ta taɓa dainawa ba.
Kuma wannan zafin da kirjinta ya soma tun daga ranar ne, to shi ya haifar mata da ciwon da har gobe bai warke ba.
**
Labarin abin da ya faru da Mansoor ya za ga gari ba wanda bai sani ba. Wani tarihi ne da shi kanshi ba zai taɓa mantawa da shi a rayuwarsa ba, sannan tarihin dafin soyayyar da ba shi da magani.
A ranar kwanan hanya suka yi zuwa Gombe tunda Mota ce ga Mansoor ba lafiya kafin su isa duk jikinss ya kara tsami, Allah ya sa Baba Ɗanjuma ya riko kuɗi a Hannunsa Inna Meri na cikin tashin hankali ba ta tuna da wannan ba.
Motar da su hayo ma daga tasha Sai da Baba sani ya biya, suna ta faɗa da masifan yaro ya jawo musu bala’i, sai dai suna ganin halittar da Mansoor ya koma sai suka yi shuru domin su kansu sun san yaron ya kai kanshi in da ya kusa mutuwa.
Jinya ce sosai Mansoor ya yi domin ya samu targade da gocewar kashi sama da huɗu a jikinsa ga raunika a saman kansa ga tsamin jiki ga raunin dake cikin zuciya wanda ido ba ya iya gani.
Shi kaɗai yasan irin ƙunar da zuciyarsa take ciki, ciwo dai idanuwana ba sa iya gani sai shi kaɗai da zuciyarsa ke cikin kirjinsa ya san halin da ya ke ciki. Makota haka suka yi ta tururuwan zuwa ganinsa wasu duk saboda gulma ne, wasu kuma domin ganin abunda ya faru mata kuma suna ta zuwa yi ma Inna Meri barka da arziki.
Su Baba Sani ke kara ma lamarin magi da gishiri suna ƙara abunda bai faru, har suna cewa shi kanshi Yaya Ɗanjuma da Merin dakyar suka sha domin yaron ya je ya jawo Yar soja an kusa kashe shi fitinarsa ya sa yau ya kusa janyo abin da zai saka har su a kashe su a banza. Nasir da makama kullum suna gidan wajen Mansoor dake kwance ya na jinya, Ahmad kuma sai da ya dawo garin ya zo ya ga yadda Mansoor ya koma shuru shuru ba ya mgana kamar an sauya shi. Baya cin abinci baya mgana ba ya fara’a ko da yaushe ya na kwance yana fama da kuncin zuciya.
Kullim mganar Inna Meri shi ne” Baban Inna ka mike ga kanka wannan kwanciyar ba zai yi maka kyau ba”
Sai kuma ta saka masa kuka, Baba Ɗanjuma shima ko da yaushe cikin yi masa nasiha yake yi.
Su Nasir ma koda wani lokacin cikin faɗin ” Aji ba fa karshen rayuwarka ba ne ya zo, Mimi ba ita kaɗai bace mace a duniya ka mike ka gina rayuwarka zaka samu wacce ta fita a gaba.”
Mu’azzam kuma kamar yafi kowa damuwa maganar kenan” Ka manta da abin da ya faru ka tashi ka kula dani kamar yadda ka saba, ba na jin daɗin ganinka a haka”
Haka su Yaya Amina suna tafe zuwa duba shi kowa na bashi mgana
Har can mallam Sidi inna ta aika Yalwa da ya’yanta sun zo har Baban shi Karimu sai da ya zo duba shi.
Inna Meri ba ta ɓoye musu abunda ya faru ba ta gayamusu komai.
Yalwa na kuka ta ce”Allah ya isar masa ba mu yafe ba.”
Karimu kuma cikin fusata ya ce”Ke sakarai miƙe ga kanka, ubanka har ya bar duniya ba lusarin namiji ba ne ka tashi ka zauna da kafafunka domin gina ma kanka kyakkyawan rayuwa anan gaba.”
Ya san duk abin da su ke faɗa gaskiya ne, amman shi a cikin Kirjinsa wutar ƙiyayya ke bayyana, daddare haka zai kwana bai yi barci ba yana kukan zucci, Auwalu bai taba tausaya masa ba sai dai ya riƙa dariya yana faɗin”Maganin ma su janye janye kenan in ban da karfin hali ina kai ina wannan yarinyar? Tabbas gaskiya ya fada soyayya ta rufe mishi ido da ya sa ya kai kansa inda bai dace ba.
Yana so shima ya manta amman ya kasa ji yayi ya tsani duk abunda ya danganci wani aiki mai kaki burinsa na zama Soja tuni ya za ma mattace acikin zuciyarsa.
So yake yi ya zauna ya yi kuka amman kuma ya kasa sai ranar da Mu’azzam ke masa mgana ya samu ya riko hannunsa ya danna a kirjinsa yana faɗin “Ta nan ne,a nan na ke jin ciwo da zafin abun. Ina so na manta amman na kasa.”
Kawai sai ya fashe da kuka ya dunƙule a jikin Mu’azzam ya na kuka kamar ransa zai fita Mu’azzam bai hana shi ba domin yana so ya samu sukuni. Tun daga wannan kukan da ya samu sararin yi ya samu sauki acikin zuciyarsa, wannan abin da ya faru Shine silar sauya rayuwar Mansoor ya koma rayuwa shi kaɗai ya koma Shuru Shuru sannan mai riko sannan bakar zuciyarsa ta kara ninkuwa sama da sau goma.
Daga lokacin Inna Meri ba ta kara takawa gidan Hajiya ba, Hajiya ma ba ta kara nemanta ba alaqar ta ƙare.
Ana ta masa mganar ya koma makaranta shima sai ya yi tunanin gwara hakan zaman ya ishesa. Da taimakon gonakinsa na gado aka saida ya samu ya fara karatu a gurbin Jami’ar Gombe state University.
Sun ba shi Agric kuma bai sauya ba saboda shi ya riga ya gama sarewa da duk wani burin shi. Da farko tare da Mu’azzam za su shiga sai kuma Alhaji Mustapha ya kawo maganar zuwa Police Acadmy Wudil a matsayin Mansoor ya je tunda shi ke son aikin Kaki, amman ina ya ce har Abada da ya zama ɗan sanda gwara ya mutu.
Sai ko Mu’azzam ya ce zai je tunda Aminin Alhaji Mustpaha ke shugabantar makaranta Kuma shi ya bashi Upper ta mutum ɗaya.
A lokacin tuni shima Mu’azzam ya watsar da mafarkinsa yace shi zai tafi Wudil Mansoor kuma ya ce ƙaninsa ba zai yi aikin kaki ba.
Inna Meri tace bai isa ba sai Mu’azzam ya tafi, Mu’azzam ɗin ma ya nuna ya na son ya je. Kawai sai Mansoor ya ce”Ka je ka je, ka za ma duk abin da kake son zama Mu’azzam amman ka sani har Abada bazan taɓa kaunar wani aikin kaki ba.”
Mu’azzam ya ɗauka zuwa gaba Yayan nashi zai rage wannan kiyayyar sai dai kash kiyayyar ta shi mai girma ce har Mu’azzam ya tafi Wudil bai kaunaci wannan karatun na shi ba, Tafiyar Mu’azzam ta kara saka ya zama ya na son kaɗaici, Saboda zaman shuru in ba shi da karatu sai yake zuwa ya na tsaren wani shago a kasuwa yana samun kudin abun hawa zuwa makaranta, ya daina neman kowa hatta su Nasir ya Guje su. Ko sun neme shi ba ya zama in da za su gan shi, su ma sun gaji da nemansa sun kyale shi a tunaninsu nan gaba zai dawo dai dai. Yana Aji biyu a jami’a Coach na Team ɗinsu na Nasara tare da na Tudun wada Team suka zo nemansa akan suna bukatar wani yaro matashi wanda ya iya buga kwallo za’a bashi horo na shekara biyu wata kungiya zata ɗauke shi. Mansoor suka nema tunda daman tare da shi suka rika bin shugabannin manyan Team ɗin su na yan ƙwallo daga na manyan anguwanni har na ƙananu.
A lokacin sai ya ga ya mu su Mu’azzam ne kuma ya tafi Police Acadmy baya nan, Coach ɗin su na Nasara Team yasan Aji ya iya taka kwallo shi ya matsa akan cewa shi Ajin ya zo a matsayin Mu’azzam ɗin mana.
Da farko yaƙi amincewa sai daga baya ya ga to miye aciki? daman shi tuni mafarkinsa ya daɗe da sauyawa amman bai amince ba sai da ya yi mgana da Inna Meri da Baba Danjuma suka sanya ma lamarin albarka.
Sannan ya amince ba zai taɓa mantawa da Coach din su na nasara Team ba wato Shehu Master Allah ya jikan sa ya rasu shi ya ɗauke shi ya kai shi wajen Coach ɗin su na Gombe United a lokaci suka yi mgana sosai ya jaraba shi ya gani sai ya ce za’a bashi horo na shekara biyu, shi kuma sai ya ga ya masa yana karatu sai ya nuna masa hakan bazai shafi karatunsa ba.
Kwatsam ne fuskar Aji da sunan shi ya bayyana acikin yan kwallon kafa, Ya yi horan shekara biyu sannan aka gabatar da shi a Kungiyar kwallon kafa ta Gombe United lokacin kontiragin Captain ɗin kungiyar saura shekara ɗaya ya kare, tare suka ƙarisa wannan shekaran ɗayan da Aji bayan kuma ya bar Club ɗin ƙokarin Aji ya saka ya samu matsayin Captain saboda daman dalilin da ya sa a ka kawo shi kenan. Shi ne sanadin da ya sa ya zama duk abin da ya zama a ƙwallon kafa, kuma tunda ya riga ya hakura da mafarkinsa sai ya maida kansa ga karatunsa sannan ga wasan kwallon kafa.
Shima ya yi singing kontiragin na shekara goma ne da Gombe United sun kuma fara biyan shi albashi bayan alawun da yake samu in suka fita wasa, da haka ya gama karatun shi ya yi service ɗin sa anan garin Gombe zuwa Lokacin rayuwa ta mika abubuwa da dama sun sauya ciki har da gama makarantar Mu’azzam ya fito da matsayin Assistant superintendent of police ASP, ya kuma samu an ijiyesa a garin kano sai dai ya riƙa zuwa ganin gida.
Kuma har a lokacin Mansoor bai kaunar aikin kaki duk ko da matsayin Mu’azzam na Asp. Ya samu shahara da suna a duniya saboda ƙwallon kafa, sunan Aji ya tashi kan mutane ko da daman ya shiga wasan ƙwallon kafa da sunan shi na Aji sai sunan ya kara ɗaukaka su kansu su Nasir suna mamakin shigar Aji kungiyar kwallon kafa sanin shi ba ya ra’ayin haka sai dai kuma in suka yi duba da rayuwarsa ta sauya sai su daina mamaki.
Acikin Shekaru goma ya taka matsayin da ya taka ya mallaki kwalin Degree sannan ya na shekaru na biyar a kungiyar Gombe United a matsayin Captain mai buga lamba huɗu dan ƙwallon mai sa’a wanda kuma kungiyar ke alfahari da shi saboda yadda ya iya taka leda. Ya yi kudi ko na ce ya samu arzikin da ya gyara gidan su sannan ya fitar ma da Iyayen shi bangaren su, har su Baba Sani suma ya gyara musu bangaren su, ɗawainiyar gidan ya dawo a kansa gabaɗaya sai dai abin da ba’a rasa ba Mu’azzam ya saka Hannu.
Gidan ya rage mutane tunda matan duk sun yi aure mazan kuma sun yi aure wasu kuma suna can wajen sana’arsu da matansu Auwalu ma ya yi aure wahalan rayuwa ya sa Aji ke taimakonsa da Mu’azzam yanzu. Sannan tun daga kan Mimi Aji bai kara neman wata mace ba in aka yi masa mganar aure sai ya sauya fuska gashi ya siya fili ya yi gida ya siya mota ya siya mashin sannan ya siya ma Baba Danjuma ma.
Har aka aka ƙarama Mu’azzam matsayi bayan shekaru uku zuwa superetendant of police SP kuma ya yi aure da yar’uwansa Hibbatu cikin shekara ɗaya ta haiihu aka samu mai sunan Baba Danjuma Gaddafi.
Da ɗaya da ɗaya kuma su Nasir su ma suka samu aiki suka yi auran su, Nasir ya na aiki da Nepa makama kuma aikin banki yake yi , Ahmad kuma yana kaduna yana ɗinki shima ya yi auransa Aji kaɗai ya rage shidin ma yanzu ya sauya ya daina nemansu sai dai in dan su suka nemeshi.
Ya riƙe wannan abun acikin zuciyarsa da ya kasa barinsa ya yi rayuwa irin ta kowa Mimi ita ce sanadin da ya sa rayuwarsa ta sauya zuwa juyin waina daga sama zuwa kasa
tun kuma daga rabuwar sa da Mimi a falon Mahaifinta bai kara ganinta ido na ganin ido ba sai a wajen bikin Makama sai dai can bayan wasu shekaru da suka gabata ya fara ganinta a talabijin a matsayin ma’aikaciya.
Ko rashin lafiyar mahaifinta sai a hirar da aka yi da ita ya sani, domin tun bayan abin da ya faru alaqar gabaɗaya ta lalace ita kanta Inna Meri ba ta da labarin gidan Hajiyar Shagamu a yanzu.
Mafarin Labarin Mimi da Aji.
Page 16
4rd May, 2022.
Abuja, Thursday
03:40Am
Tun ranar mandoy ɗin da ta gabata Mommy ta so su je Gombe kamar yadda Abi ya bukata amman kuma tana jagorantar wani case a kotu sai ta ga gwara ta tsaya ta gama kafin su tafi. Dole ya sanya ta kira Sulaiman tace ya dakata da Bucking ɗin su ya bari sai ranar jumma’a tunda ranar Alhamis ne karshen shari’an nasu.Sun gama tsara na su amman shi Abin da Ubangiji ya tsara ya sha bambam da tunaninsu.
A daran Alhamis duk wani shirin tafiya Brr.Murjantu ta gama yin sa saboda Sulaiman ya kirata ya faɗa ma ta jirgin ƙarfe goman safe za su bi zuwa Gombe in Allah ya yarda shi ya sa tunda ta dawo daga wajen aiki ta kasa zama sai faman shiri take yi musu tunda wannan ne karo na farko tun bayan abin da ya faru da shi da zai kara takawa zuwa jiharsa.
Alhaji Hamza kawai ta kira suka yi mgana Saboda shi zai tura musu motar da za ta ɗauke su daga filin jirgi zuwa gidan Hajiya, Lafiya lau ta gama duka shirinta a daren Abi yace mata ba ya jin daɗin jikinsa yana so ya yi wanka ita ta rarrafa ta ɗora shi saman keke ta kai shi tiolet ta taimaka masa ya yi wanka sannan ta gunguroshi zuwa ɗaki ta shirya shi, sannan ta zo ta yi masa shirin kwanciya a daren sun kwana a jikin juna a baya bata ɗora masa nauyinta saboda yanayin laluransa sai ranar kuma da kansa ya bata umarnin ta matso kusa da shi bayan ta matso sai ya saka hannunsa mai motsi ya jawota gefensa har kanta na matsuwa da ƙirjinsa.
Manganganun da ya yi ta gaya mata sun bata mamaki da tsoro sai dai ba ta taɓa tunanin tafiya Habibi zai yi barta ba. Ya jadaddamata in har bai samu zuwa Gombe da kansa ba ta taya shi neman yafiyar Hajiya sannan ta yi masa alƙwarin neman yaro nan ta bashi hakuri sannan ta yi masa alkwarin samar ma Mimi farinciki da kuma ba ta abin da take so, a lokacin kallonsa ta yi cikin mamaki kafin Ta ce.
“Ka daina faɗin haka Habibi in sha Allahu gobe za mu je Gombe, kuma da kanka za ka samu damar neman gafaran Hajiya, sannan kai da kanka za ka yi magana da Mansoor ka nemi yafiyar sa.”
Mirmishi ya yi mata ba tare da ya yi mgana ba sai dai ta ga ya yi mata wani iri duk ya sauya mata. Ta san ya yi shekaru yana jinya ƴan’uwanta ba duka ba ne su ka bata goyon zaman jinyar Major Kabir ɗin ba, gani suke zata yi wahala da shi tunda ba ranar warkewa. Ita kuma me ya rage mata a duniya ban da ta zauna ta kula da Mijinta uban Ƴaƴanta domin ta samu rabauta ranar gobe kiyama, Shi ya sa ba taɓa nuna masa gajiyawarta ba tana Ƙoƙari a kansa da amanar gidansa da ƴaƴansu
Sun jima kafin su kwanta yana ga ya mata wasu irin mganganu ma su kama da kamar mutum yana barin wasiyya sai hankalinta ya tashi ganin haka ya sa sai ya bar mganar ta rumgumshi ta ce su kwana su yi barci gobe suna da tafiya a gaban su.
Barci ne mai nauyi ya kwasheta acan cikin barcin ta yi mafarkin ta ga an taru gida ya cika ana ta kuka kuma taga wai an saka Habibi a makara za’a fita da shi ita kuma ta rike tana ta kuka.
Kamar an wancakalar da ita haka taji ta a gefe ta bar jikin Kabir, sai da ta tashi a firgice dai dai Lokacin da ta ji ya na tari ba kakkautawa. A firgice ta miƙe ta laluba hannunta ta kunna hasken ɗakin sai ta ganshi kwance in da ta kwantar da shi sai dai kuma tari ya sarƙe shi yana yi kamar numfashinsa zai ɗauke hankalinta ya ta shi sai ta tuna mafarkin da ta yi, ai da gudu ta diro daga kan gado ta isa gare shi tana riƙe shi ƙokarin tarairayosa take yi ta ji yana faɗin”ruwa! ruwa!
Ba tare da tunanin komai ba ta sake shi sai ta kwashi gudu kamar za ta faɗi zuwa falo fridge ta buɗe ta ɗauko masa ruwa mara sanyi tunda Saboda shi ba ta kunna fridge ɗin falo sai dai na Kitchen. Abin da ya sake ba ta tsoro ko da ta koma har ya faɗo daga kan gado ta ruɗe ga ta ita kaɗai ta nufe shi da sauri tana kiran sunan shi.
” Habibi, Subhanallah!”
Haka ta ke faɗi dakyar ta iya ɗago kansa domin sai taji ya kara yi mata nauyi ta kafa masa goran a baki ta na bashi ruwan abin da ya sa ka ta fashewa da kuka shi ne ganin ruwan gefe da gefe sai zubewa yake yi kaɗan ne ma ya ke shiga bakin sa.
Cikin muryan kuka ta ce”Na shiga uku ni Murja me ya same ka haka Habibi?
Shi kuma sai ya kauda kansa ruwan ya suɓuce daga hannunta ya ganganra ƙasa inda su ke zaune gabaɗaya ya jiƙa su ita a koƙarinta ta mikar da shi ta maida shi saman gado kamar yadda ta saba dubarunta. Amman yau sai ya gagareta shi kuma tarin na neman ƙara sarƙe shi cikin muryan da ta fara karyewa ba ta ma wani jin sa sossi ta ji ya kira sunan ta.
“Murjanatu..”
“Murjanatu..”
Da sauri ta amsa da “Na’am Habibi me kake so? Ko na je na kira Megadi ya zo ya taya ni mu ɗora ka saman keken ka?
Sai ta ga ya girgiza mata kai lokaci ɗaya yana riko hannunta cikin sarkewan numfashin da ba ta lura ya fara sama da ƙasa ba ya fara mgana”Murja ki yafe min kin ji? Sannan ki tayani neman gafara Hajiya da kuma afuwar Mimi domin na zalunceta sannan ki yi min alkwarin za ki nemi yaron nan ki ba shi hakuri kuma ki yimin alkwarin yi ma Mimi duk abin da take so saboda farincikinta.” Yana mgana cikin In ina saboda mumfashinsa na sarƙewa Mommy ta fashe da kuka kafin tavce”Ka daina faɗin irin haka sai na ga kamar mutuwa za ka yi ka barni Habibi?
Cikin ƙarfin hali ya ce” Naso na samu damar neman yafiyar su da kaina sai dai lokaci ya kuremin Murja, na amimta dake nasan za ki kula da ƴaƴana ki yi min alkwari guda uku na farko ki tayani neman gafaran Hajiya na biyu ki nemi yaro nan ki tayani neman yafiyarsa, na uku ki yi min alƙwarin yi ma Mimi abin da take so Murja”
Mommy na kuka ta ke ɗaga masa kai lokaci ɗaya tana faɗin”Na ɗauka amman dai in sha Allahu tare za mu je duk ka nemi gafaran su.”
Hawaye ke fita ta gefe da gefen idanuwansa ya ce”Ko bayan raina ban amince ki bar gidan nan ba Murja, ko da aure za ki sake yi ki zauna nan ne gidanki domin ki kula da yaran mu.”
Mommy kuka ta ke yi har da majina ta kasa mgana sai da taji ya kara riƙo ta da karfi lokacin tarin ya kara sarƙeshi faɗi yake yi
” Na yafe miki duka laifin da kika taɓa yi min Murja wanda kika sani da wanda ba ki sani ba , nima ki yafe min duk zaman kuncin da na yi da ke a baya ki yafe min Murj…’
Sai ya kasa karisawa domin tarin ya sarkeshi kuma yana tafiya da numfashinsa yadda Mommy ta ruɗe ne yasa ba ta fahimci lokaci ya kure ba. Domin a lokacin ana kokarin zare ran Abi ne, ita a tunaninta ba ta makara ba ya sa ta sake shi ta mike a guje ta fita haraban gidan tana kururwan kiran ma’aikatan gidan.
Allahu akbar ko da suka taso da gudu suna tambayan ta ko lafiya ta rika nuna musu cikin gida tana faɗin sunan Habibi tana wani irin kuka yasa su ka kwashi gudu zuwa cikin gidan har vikin bedroom ɗin su suka iske Abi kwance a kasa idanuwa sun kafe ba ya motsi. Megadin gidan dattijo ne na yanzu tun bayan yin ritayansa shi ya duba Abi ya tabbatar da rai ya yi halinsa itama kuma a koƙarin Mommy a kama mata shi su je asibiti har ta saka mayafi tana faman kiran can asibitin in da Dr Ashiru ke aiki. Megadi ya kalleta duk ta fita hayyacinta sauran ma’aikatan ma maza tuni sun fara salati matan kuma kuka suke ganin yanayin Hajiya duk ta fita hayyacinta ta ruɗe.
Tsawa ta daka musu lokaci ɗaya tana faɗin”Ku kama min shi mu fita waje,asibiti za mu je a duba shi.”
Kai Baba Megadi ya girgiza kafin ya ce”Hajiya sai dai mu yi hakuri Allah ya yi ma Alhaji rasuwa.”
“Rasuwa? Habibi ne ya rasu?
Ai ba ta san lokacin da ta yi kansa tana kiran sunan shi ba, lokacin har megadin ya saka hannu ya shafe masa idanuwansa, Allahu Akbar Kullu Nafsin Za’ikatul maut kowani rai sai ya ɗanɗani zafin mutuwa Allah ya sa mu dace.
Mommy kamar ta zare ko na ce ta yi hauka haka ta ke rike gawan Abi tana wani irin kuka ta surutai faɗi take yi”Habibi me ya sa ka yi min haka? Ka tafi ka barni Wayyo Allah na shiga uku na lalace.”
Ma’aikatanta mata ne ke tare da ita mazan daman guda uku ne megadi sai direba da mai kula da haraban gidan. Matan kuma mai girki wata bakatafiya ce saira sai mai gyaran gida wata yar matashiyace mai suna Aina’u daga can gidan su kano aka aiko mata da ita saboda su taya ta taimakon gidanta da mijinta. Har gwara Saira da shekarunta ita ke ba ma Hajiya hakuri su kansu ma kukan su ke yi Aina’u kuma sai mutuwar iyayenta suka dawo mata sabuwa itama gefe ta samu ta zauna ta na faman rusa kuka jikinta sai rawa yake tunda take a duniya ba ta taɓa ganin gawa ido na ganin ido ba sai yau.
Abi ya cika misalin 3: 50am na daren ranar Jumma’a ne kuma Mommy ba ta iya kiran kowa ba saboda tashin hankali har aka kira sallar asuba gwan Abi na jikinta ta rumgume ta yi kuka har muryanta ta daina fita tunaninta gabaɗaya ya toshe, da ita da su Sara tare su ka yi wannan zaman acikin ɗaki tana kuka suma suna tayata.
Sai wajen shida saura na safe sannan Megadi da su Habu suka sake shigowa ganin halin da Hajiya ke ciki ya sa Megadi ya durkusa a gabanta yana faɗin” Hajiya ki yi hakuri ki daina kuka don Allah, ya kamata ki kira waya ki sanar da su abin da ya faru ya kamata a suturta Alhaji domin a yi masa gata a kaisa makwancinsa na gaskiya.”
Mommy ta kalleshi da Idanuwanta suka rine saboda kuka sai a lokacin ta fahimci abin da ya kamata ta yi, ta kuma kara samun tabbacin Habibi ya tafi ya barta, Dole ta janye daga gareshi suka kamashi suka matsar gefe suka rufa masa zanin gado suka rufe shi su Sara kuma sai su ka koma falo suka zauna jugum tare da su Habu. Mommy kuma wayarta ta ɗauka amman ta rasa wanda za ta kira a daidai wannan lokacin sai kira ya shigo wayarta ta na dubawa sai ta ga kamar Alhaji Hamza ne saboda ba ta ma wani gani sosai da hanzari ta ɗauka ba ta jira maaganarsa ba ta faahe da kuka tana faɗin
“Abban Jaheed Habibi ya rasu, na shiga uku na lalace Habibi ya tafi ya barni.”
Haka ta ke faɗi muryanta na sarƙewa saboda kuka.
Daga can bangaren Sulaiman ya yi zumbur ya miƙe daga kishigiɗan da ya yi cikin wani irin razana yace”Innalillahi wa’inna ilahirraju’un Mommy Abi ne kika ce ya rasu? Sai a lokacin ta fahimci ba Alhaji Hamza ba ne Sulaiman ne. Sai kawai ta koma ta sulale a kasa ta na kara fashewa da kuka Lokaci ɗaya tana fadin”Sulaiman kun zama marayu yau Abin ku ya tafi ya barmu.”
Ta ma kasa mgana sai wani irin gunjin kuka kawai take yi. Daga can Bangaren Sulaiman ya katse wayarsa da Salati mai ƙarfi a bakinsa wanda ya taho tare da hawaye masu zafi daga kuncinsa.
Matarsa Jawahir na Kitchen tana Koƙarin yi musu abun karyawa tunda zai fita da wuri yana da tiyata karfe takwas ɗin safe sai dai taji salatin mijinta da karfi da yasa ta baro kitchen din da gudu zuwa Bedroom ɗin su nan ta iske shi zaune a kasa dafe da kansa da sauri ta ƙarisa gabansa cikin tashin hankali ta kira shi da sunan da take kiran shi.
“Darling me ya faru na ji kana ta salati haka?
Sai ta ga mijinta uban ya’yanta gwarzon namiji irin Dr.Sulaiman ya ɗago fuskarsa ta yi kaca kaca da hawaye cikin razana ta ce”Innalilllahi Darling me ya faru?
Cikin Wani irin sauti ya ce”Jawahir na rasa mahaifina, Abi ya rasu.”
Cikin wani irin sauti ta furta”Hasbunallahi wa’imal wakeel, Innalillahi wa’inna alaihirraju’un.”
Ta faɗa lokaci ɗaya a na ƙariswa gare shi ta zauna kusa da shi ta rumgumosa sai kawai ya faɗa jikinta ya fashe da kuka yana faɗin “Mommy na can ita kaɗai ba kowa a wajenta, Jawahir na zama maraya Ƙannena sun zama marayu mahaifiyata ta zama bazawara Ƴayana sun rasa kakansu, ki shirya su Momi bari na yi mana bucking ɗin jirgi yanzu nan.”
Da sauri kuma ya mike ya ɗauki wayarsa sai da ya sama musu Jirgin da zai tashi zuwa Abuja da Safa nan sannan ya kira asibitin su ya shaida musu halin da a ke ciki, dole a ka sauya sunan shi da wani Dr Ishaya, sannan daga baya ya kira Alhaji Hamza Saboda Mommy mace ce yadda ma ta ruɗe ya tabbata ba za ta iya kiran kowa ba shima ya tashi yana jin wani irin kasala a jikinsa kiran da ya yi daman ya gaisa da iyayen na shi kamar yadda ya saba duk safiya kafin ya fita aiki.
Alhaji Hamza ya ji mutuwar ɗan uwansa ya na tare da Anty ne lokacin da Sulaiman ya kira shi ya na sanar da shi yayansa Major Kabir ya rasu jiya da daddare.
Salati kawai ya ke ta maimatawa ba shi kaɗai ba duka matansa da ya’yansa sun ruɗe da jin wannan mutuwar daman Sulaiman ya ce ba ya tunanin Mommy ta kira wani shi ya je ya sanar da Hajiya shi kuma yanzu zai kira su Madiha ya sanar da su. Allah ya taimaake shi wayar mijin Madiha ya kira ya sanar da shi abin da ke faruwa shima ya ruɗe yace bari ya nema musu Jirgi.
Dr. Sulaiman cikin wani yanayi ya ce”Ka ga ya ma Madiha cikin hikima saboda kada ta ɗaga hankalinta.”
Cikin tsananin tausayin su ya ce”In sha Allahu Dr, Allah ya jiƙan Abi.”
Ya amsa mata da Amin wayar mijin Khadija ya kira sai kuma kawai ya ji ita ta ɗaga Wayar cikin karaɗinta ta ce”Dr yau ni aka tuna shi ne a ka kira mu da sassafe?
Sai ya kasa gayamata ya ce ta mika ma Mijinta wayar, yanayin muryansa ya sa sai da gabanta ya faɗi cikin in ina ta ce” Dr me ya faru? Jawahir da yara suna lafiya ko?
Kai tsaye ya ce”Ki ba ma Muhammad wayar da shi zan yi mgana.”
Tun daga nan ta san wani abu mara ɗaɗii ya faru sabo ba ta mantawa lokacin da Abi ya samu hatsari Dr Sulaiman ɗin ne ya kira sannan ya ƙi magana da ita sai da Muhammad. Daman ya shiga Tiolet ne ya na fitowa jikinta na rawa ta mika masa wayar ta kuma lafe a kunnensa domin ita jikinta ya bata wani abu ne ya faru.
Sai dai ta yi nadamar yadda ta kara kunnenta ta jiyo ma kanta abunda ya kusa tsaida numfashinta.
Ihu ta rika yi da kuka tana faɗin “Innalillahi Abi ne ya rasu? Na shiga uku na lalace”
Muhammad ke kokarin lallashinta amman kuma taki sauraran shi. Ba su samu jirgi ba sai suka shirya tafiyan mota tunda daga kaduna ne zuwa Abuja. Khadi sun yi mgana da Madiha kowacce murya ta shake suna yi ma juna gaisuwan rashin da suka yi madiha ta ce yanzu za su taso ita kuma Khadija ta ce suma ga su nan a hanya. Khadi ce ta kira wayar Mimi sai dai tana ta ringing ba’a ɗauka ba wayar Hajiya ma haka , sai ta kira wayar Mommy sara ta ɗauka ta ce Mommy na cikin ɗakin da Abi yake, Sai khadija ta kara rushewa da kuka ta kosa su isa Mommy ba za ta iya ɗaukan wannan rashin ba ita kaɗai ba.
Ko kafin takwas na safe a kafafan Sada zumuta duk an saka rasuwar da sauran duk wanda ya kamata yaji rasuwar Major Kabir ya ji, musamman gidan Talabijin na Karamchi a Safiyar ranar suka tashi da wannan alhinin domin ko da Alhaji Hamza ya isa gidan Hajiya Mimi ta bar gida zuwa wajen aiki tunda labaran Safe gareta.
Tana ɗakin Labarai ana gyara mata fuskarta Wayar Daddy ta shigo mata sai da gabanta ya faɗi a lokacin ba ta ji kamar za ta faɗi ba sai da ya ce ta bar komai ta taho gida ita ta sadakar Hajiya ce ta rasu daman ta barta kwance ta na gayamata ba ta jin ɗadin jikinta. Haka ta bar wajen aiki a afujajan sai dai abin da ta je ta ji ne yasa ta ruɗe ta kasa mallakan kanta
Hajiya kuma sai ta yi dauriya ita ke lallashin Mimi Alhaji Hamza kuma ya na amsa wayoyin mutanen domin in za’a saka rasuwar Major Kabir sai an ce Yayan Alhaji Hamza tsohon Sanatan jihar Gombe.
Rukky ne ta yi ta kiran wayar Mimi ba ta ɗauka ba, saboda su san abin da ke faruwa sai Mimin ta rubuta sako ta tura mata.
“Rukayya ki sanar da Manaja Abuja za mu wuce yanzu Allah ya yi ma Abi rasuwa.”
Allahu Akbar zukata sun raunana yawancin mutane ma sanarwa da gidan talabijin na karamci ta yi ne su kasan abunda ya faru ciki har da Inna Meri da ta na ma cikin ɗaki lokacin suna cikin karanta labaran duniya na Safe bayan sun gama suka sanar Walida ce ta rugo ɗaki da guda tana haki ta ce”Inna yanzu nagani a Tibi ana faɗin Allah ya yi ma mahaifin mai karanta labaran na rasuwa Mimi.”
Da Sauri inna Meri ta mike ta fita falo Sai ta ci karo da hoton Major kabir cikin kakinsa Soja ana sanar da rasuwarsa jiya da Daddare za’ayi jana’izarsa yau Jumma’a bayan an sauko daga sallar Jumma’a a gidansa dake Gwarimpa a Abuja.
Ba za ta manta da fuskarsa ba ta gane shi Allah Sarki rai bakon duniya daman ai ƴarsa ta ce ba shi da lafiya duk sai jikin Inna Meri ya yi sanyi a fili ta kaɗa kai kafin ta ce”Allah ya jiƙan sa da Rahama mu kuma Allah ya kyautata ta mu bayan tasu.”
Walida ta amsa da Amin ita ba ta san shi ba amman ai ta san Mimi budurwan yayansu ne a baya kuma Inna Meri ta san su shiyasa ba ta yi mamakin ganin yadda jikin Inna Meri ya yi sanyi ba. Suna zaunen Baba Ɗanjuma ya shigo cikin shirin fita yana ga ya mata shima Jana’iza zai je ƙanin Mallam Hashimu ne ya rasu.
Ta yi salati kafin itama dire da faɗin “Kai Jama’a ana ta tafiya nima yanzu nake ganin sanarwan rasuwan mahaifin yarinyar nan da Baban Inna ya so mai karanta labarai anan yanzu suke faɗi jiya da dddare ya rasu.” Baba Ɗanjuma ya ce”Innalillahi wannan Sojan? Inna Meri ta gyaɗa masa kai sai kawai ya jinjina kai kafin ya ce”Allah ya jiƙan su da rahma Allah yasa Aljanna makoma”
Shima yana tunawa da shekarun baya ne har an zo an gama jin ɗadin duniya kuma an koma. Kai Allah yasa mu dace, Allah ya sa mu mutu muna masu Imani Amin.
**
Kamar yadda aka sanar an yi Jana’izar Marigayi Major Kabir Sulaiman Dabo a gidansa bayan sallar Jumma’a Alhamdulillah ya samu jama’a kama daga yan siyasa abokan hulɗar Daddy tare da Abokan aikin Abi sojoji ritayas kamarsa har da masu kakin a lokacin sannan tare da mazajen yayan shi da kuma sai yan’uwa da abokan arzuka tare da dangin Mommy daga kano aka sallace shi zuwa gidansa na gaskiya. A ka bar mata acikin gida suna kuka sak abin da Mommy ta gani a mafarki shi ya faru ta riƙe gawan mijinta tana wani irin kuka sai da ƙanwarta Zainabu ta zo ta riƙe tare da sauran yan’uwanta da su Mama ko da aka fita da shi sai ta faɗi a sume ita da Mimi. Madiha da Khadi kuma sun kasa mallakan kansu ma.
Alhaji Hamza da Sulaimam suka yi ma Major wanka suka haɗashi saboda nisan makabartan sai bayan la’asar suka dawo daga kaishi. A makabarta Sulaiman ya sha kuka shi da Alhaji Hamza Jaheed ma ya iso da shi akayi jana’iza.
Shi ne ya rike sulaiman ɗin ya tada shi daga gaban kabarin Abi likita ne mai dakiya amman ya yi rashin bangon da har abada ba zai iya maida kamarsa ba.
Suna dawowa aka kafa tantuna a haraban gida domin zaman makoki.
Hajiya kuma ta yi tawakkali tana zaune da hijabi da carbi ko hawayenta ba wanda ya gani Lokacin da aka tafi kai shi bayan Mommy ta farfaɗo ta fara surutai tana faɗin
“Habibi yace na nema masa gafara wajen Hajiya, Hajiya ki yafe masa ya rasu da niyar a yau mu je Gombe ya durkusa ya nemi gafaran ki, ke ma Mimi da ke ya rasu kina bakin shi faɗi yake yi Murjanatu ki yi min alkwarin yi ma Mimi duk abin da zai saka ta farinciki ciki har da neman yaron nan ku rokesa gafaran ya yafe min.”
Sai da Mama ta rufe mata baki sai sakin maganganu take yi kamar ba ta cikin hayyacinta.
Sai a lokacin Hajiya ta yi hawaye cikin kuka ta ce”Na yafe masa duk laifin da ya taɓamin da wanda ya sani da wanda bai sani ba, ina masa fatan salama da aminci da kuma dacewar wannan rana ta Jumma’a mai daraja Allah ya jiƙan ka Kabiru”.
Sai Hajiya ta fashe da kukan da take ta rikewa Mimi ta koma jikinta ta kwanta suka haɗe suna ta gunjin kuka. Mommy faɗi kawai take yi” Habibi ya rasu? Ni murja ina zan sa ka kaina a gabana fa ya rasu Allah ya jiƙan ka Habibi.”
Ƙanwarta Zainabu ta ce”Ki daina kiransa da wani suna in ba sunan shi ba mala’iku da sunan shi suka san shi ba Habibi ba, ai yanzu wani Habibi ya kare Murja gafaran Ubangiji zaki yi ta neman masa shi ne kawai gata da Soyayyar da za ki nuna masa”
In ka kalli Ahalin nan sai ka tausaya musu, duk da yanayin Abi amman fa tsayayyen Uba ne mai yin komai saboda ƴayan shi, shi ya gina su har su ka kawo matsayin da suke a lokacin kowacce ka gani ido ya Kumbura murya ta dishe saboda kuka,
Mutanen arziki daga ko’ina sun zo musu gaisuwa daga Gombe Rukky tare da Salim Bunza da Na Misau da wasu daga cikin ma’aikatansu da aka wakilta ranar biyu sun zo musu gaisuwa, Rukky ma nan ta kwana sai ranar uku ta koma Gombe ita ma Khadi abokan aikinta da na mijinta duk sun zo musu gaisuwa haka Dr. Sulaiman sannan Jawahir ma yan’uwanta suna ta zuwa.Haka dangin Mommy su ma sun yi mata kara kwarai da gaake.
Ana ta zaman gaisuwa manyan manyan mutane nata zuwa gaisuwa su kuma shiga har cikin gida su yi ma Mommy gaisuwa wacce ta za ma abun tausayi.
Mimi ta samu wayoyin mutanen da ba ta san wasu ba ma, a rana ba ta san adadin masu kira su yi mata gaisuwa ba, kaf ma’aikantan su har da masu Inten ba’a bar su a baya ba. Sannan ba ta yi tunanin za ta samu kiran wayar su Nasir ba.
Sai ga shi Mu’azzam ne ya fara kiranta ya yi mata gaisuwa ya ce a kafafen sada zumunta ya gani sai kuma da ga baya Usman ke faɗa masa, sannan Usman ya kirata Ahmad ma tare da Nasir sun yi mata gaisuwa kuma ta ji daɗii kwarai. Sai dai Aji bai kirata ba kuma tana da tabbacin ya sani rashi fa ta yi rashin kuma na Mahaifi, tunda ta karɓi lambarsa ba ta samun kwarin gwiwan kiransa ba. Sai ta ce bari ta gani zai iya yi mata gaisuwa?. Sai ta ɗauki wayarta ta tura masa sako.
“Aji Nah Abi ne ya rasu yau kwana biyar.”
Mimi ce Fatima”
Ita kanta ta san bazai taɓa mata gaisuwa ba, tunda ya kasa mantawa da abin da ya faru a baya, abunda ba ta sani ba tun a ranar yaji rasuwar domin a daren ya je gaida Inna take gaya masa a cikin ransa ko a fili bai ce Allah ya jiƙansa ba.
Sai da Inna ta ce”Kanin ma mallam Hashimu shima ya rasu yau. Allah ya jiƙan su da Rahma.”
Ba saboda shi ya amsa ba sai Saboda ƙanin Mallam Hashimu amman yadda yake jin tsanar wannan mutumin ba zai iya nema masa jinƙai wajen ubangiji ba, ba domin ya na musulmi ba da sai yace Allah ya kara nauyin kasa.
Kuma Mu’azzam ya kira sa ya gaya masa ya ce to ina ruwan sa? Bayan nan har Makama sai da ya kirasa yana gaya masa ya yi tsaki ya kashe wayarsa ya rasa waye ne baban Mimi a wajensu da suka damu da Mutuwarsa. Nasir ne da ya kirasa sai da suka yi faɗa kamar abun arziki Nasir ya ce”Ya ƙarin haƙurin mu kuma Aji?
Aji ya ce”Ni babana ya ji ma da rasuwa, Innata kuma da ranta sannan Babana uban riƙo na yana cikin koshin lafiya.”
Nasir ya yi dariya kafin ya ce” Gaisuwan Major mana baban Mimi, ya kamata ka kirata ka yi mata gaisuwa sanda na kirata sai da ta tambaye ni ka sani kuwa?
A fusace Aji ya ce”Nasir ba domin kai ba ne wallahi da sai na zage ka, kada ku ƙara kirana da irin wannan shirmen na ku”
Nasir ya ce”Aji rasuwa fa aka yi? mutuwa ce fa” ƙaramin tsaki ya ja kafin ya ce”ka bari in ka mutu in ta kirani ta min gaisuwa sai na haɗa na yi mata a lokacin.”
Daga haka katse wayarsa ya bar Nasir da sakin baki, Kuma a daran ta turo masa saƙo. Mamaki ya kama shi wato kenan sun ba ta lambar sa kenan.
Goge saƙon ya yi ya kuma ɗauki lambar ya saka ta a blacklist duk abunda zai haɗasa da abin da zai hana shi barci yana kokarin yin nesa da shi. Ko alama bai ji tausayinta domin wai ta rasa mahaifinta ba, shi a tunaninsa wannan in ya rasu ma abun murna an rage mugun iri a kasa ne, sauran kaɗan ya maida mata amsa da cewa Allah yasa kasa ta kara danne shi sai kuma ya fasa shuru ma ai amsa ce ga mai hankali.
Page 15
Baba Ɗanjuma kuma sai maimaita faɗin” Innalillahi wa’inna ilaihirraju’un” kawai yake yi shi kan shi ba domin yana namiji ba tashin hankalin da suke ciki ba zai saka ya iya mallakan kansa ba. Ba shi ya haifi Mansoor ba amman da gaske yake yi ya karɓo amanarsa kuma yana jin sa kamar Mu’azzam ne shi a wajensa.
Tabbas Baban Inna ya janyo ma kansa fitinar da tafi karfinsa haka Inna Meri da Baba Ɗanjuma ke ta raya acikin ransu saboda ganin samudawan Sojojin dake tsaran gidan Major fuskarsu ba fara’a daga gani ba su san wani abu wai shi Imani ba sun fi gane yaren umarnin wanda ya ijiyesu.
Su kansu kafin Sojan dake tsaren get ya amince su shiga sai da Alhaji Hamza ya kira Yayan na shi da kansa ya yi masa mgana sannan ya kira wayar sojan sannan aka buɗe musu get suka shiga cikin gida.
Har da Yaddiko a ka zo sai ga su kowa ya yi zaman sanyi a cikin falon gidan Major Kabir, Inna Meri tana shan kuka lokaci ɗaya tana riƙe da hannun Mu’azzam, Mimi kuma ma na jikin Mami tana wani irin kuka mai ban tausayi. Hajiya kuwa girgiza jiki kawai take yi ta kasa mgana domin kunyar su Inna Meri take ji, tun bayan gaisawar da suka yi da Mommy ga shi an kawo musu ruwa da lemu amman zullumi ya hana kowa motsi.
Hajiya ta kalli Alhaji Hamza lokaci ɗaya tana faɗin” Wai ba ka ga ya ma Kabiru har da ni aka zo ba ne?.
Cikin ladabi ya ce” Na gaya masa Hajiya, ya ce ga shi nan tahowa.”
Sai kawai ta jinjina kai wani abu na taso mata acikin kirjinta.
Murja ta kalla da ke rike da ƴarta itama daga gani ta sha kuka ba ta cikin natsuwarta. Cikin tsausayi Hajiya ta ce” Murja har ke Kabiru bai saurare ki ba ko? Kuma ba ki san inda ya sa a ka kai yaron mutane ba ko? Mommy ta sauke ajiyar zuciya kafin ta ce” Ba irin rokon da ban yi masa ba Hajiya ɗan uwansa ma yana kuka ya roƙonsa amman bai saurare mu ba, bai sa an fita da shi ba ya na nan acikin Kurkunsa na cikin gida, ba wanda ya isa ya sa su fito da shi sai in har shi ne ya ba su umarni Hajiya.” Yaddiko ta yi kasaƙe kafin ta ce”Kai jama’a kurkuku kuma ?
Mommy ta gyaɗa mata kai kafin ta ce”Eh ya na da wani ƙaramin ɗaki da bai wuce tsawon gajerun mutum ba, sannan ba shi da faɗi kuma a ƙasan yake, akan sanya mutum a ciki in ya yi wani laifi domin a yi masa horo.”
Gabadaya sai Inna Meri da Baba Danjuma su ka kara ruɗewa, Yaddiko ta saka salati Hajiya ta karishe ma ta shi ko Alhaji Hamza kai ya girgiza kafin ya ce” To duk me ya yi zafi? Wannan lamarin da duk an bi shi a hankali da an warware komai cikin sauƙi”
Inna Meri ta zube a kan kafafunta daga saman Kujera ta haɗa hannayenta waje ɗaya tana faɗin”Don girman Allah Hajiya kin yi min rai ki saka a saki Baban Inna wlh na yi miki alkwarin ko hanyar gidan ki bazan kara kallo ba har abada,ni dai ku saka ya sake shi kuma shima in sha Allahu ba zai kara kusantar Inda ƴar ku take ba, laifin yaro ne tunaninsa ba ya ba su abu dai dai in da ace yayi tunanin shi kanshi ba zai janyo ma kansa rigimar da ta fi karfinsa ba.”.
Tana mgana tana kuka Mu’azzam na taya ta sai aka rasa mai lallashinta ballantana ya ce wani abu, Hajiya ke sharan kwalla a ɓoye Mommy kuma na tausayin ƴarta ne.
Ana cikin wannan halin sai ga Major kabir ya shigo cikin kakinsa na aiki wani Soja na mara masa baya. Yana shigowa cikin takunsa na zafin nama na cikakkun mazan jiya, sai ya ɗaga ma Sojan hannu fuskar nan ba rahama shi kuma sai ya juya ya fita bayan ya sara masa.
Baba Ɗanjuma kallo ɗaya ya yi masa shima tsoronsa ya kamasa sai ga shi shima zube kan kafafunsa kusa da Inn Meri ya na rawan jiki da na zuciya.
Ya ga Hajiya a zaune amman bai nufe ta ba sai ya samu wata kujera mai zaman mutum ɗaya ya zauna ya ɗora kafa ɗaaya kan ɗaya ya na ƙare ma mutanen falon kallo har ya sauke kan Hajiya cikin yanayin maganarsa ta Sojoji ya ce” Hajiya duk wannan taron na menene.? da kun yi zaman ku yaro zai yi wasa da gidan Soja ne shi ne nake so na koya masa hankali nan gaba ko sunan Soja ya ji an ambata sai ya yi fitsarin jini acikin Wandonsa.” Kafin Hajiya ta samu zarafin mgana Inna Meri ta rarrafa tsakiyar falon kamar ta kwanta masa, ita ko iya kallonsa ba ta yi saboda firgici cikin roƙo kamar zai yi mata gafara ta fara faɗin”Don Allah ka yi masa aikin gafara ka yi hakuri ka yafe masa yarinta ke damunsa amman ina wuyan Baban Inna ya yi karfin da zai ja da kai? Ka yi masa rai don Allah ka sake shi.”
Take faɗa tana kuka har da majina, A kaikace Major ya kalleta cikin wani irin Murya ya ce”Wace ce ke?
A razane ta ce”Ni ni mahaifiyarsa ce, ga mahaifinsa nan.”
Ta faɗa ta na nuna Baba Ɗanjuma da shima ya ƙariso tsakiyar falon da jan gwiwa Mu’azzam ganin iyayensa duke kamar masu neman gafara ya sa shima ya rarrafa cikin jan gwiwa zuwa kusa da su ya durkusa ba zai bari kimar iyayensa ta zube ba, ko da ba shi da yarda zai yi gwara shima ya yi zaman neman gafaran tare da su. Sai da Major ya gama musu kallon wulaƙanci sannan ya yi wata irin sariya kafin ya ce”Ke ce uwar da kika ki haifi mara kunyar yaron da zai ja da ni? Kai kuma kai ne uban da ke rikon Agolan dake neman ja da Soja?
Ya karishe faɗa yana nuna kansa bayan kuma daga karshe ya nuna su ɗaya bayan ɗaya jikinsu na rawa kansu na kasa kamar sun ga wani mala’ikan mutuwa, kuma kowa ya kasa mgana Hajiya bakinta ne ya yi nauyi? Me za ta ce? Ko ta yi mgana ba zai taɓa Sauraranta ba tunda halinsa ne baya girmama maganarta a matsayinta na uwa a gare shi. Alhaji Hamza ne ya yi gyaran Murya ya fara mgana da cewa” Major..”
Sai kawai ya ɗaga masa hannu cikin kaushin Murya ya ce”Ya raina matsayina, yaron ya yi min tsurin ido bayan ya fara soyayyaa da ƴata ba tare da sanina ba, sannan ya zo har gidana ina mgana yana tsaye ina tsaye sannan wai ni zai nuna ma tsageranci? Sai ni kuma na nuna masa ba’a zuwa gidan Soja a yi taurin kai na ce su yi ta dukansa in har bai yi nadama ya ba da hakuri ba, ka da su barshi ko duka zai kashe shi”
Mimi ta saka wani irin kara ta miƙe tana faɗin” Abi.”
“Ke sai na harbe ki, in kika kara mgana anan wajen nonsess kawai.”
Ya faɗa cikin zafin nama har yana miƙewa da sauri Mommy ta mike da sauri ta maƙale ƴarta a bayanta tana rawan jiki, Hajiya ta yi yunƙurin mikewa dai dai sanda Inna Meri ke dukar da kanta a kasa tana haɗa Major Kabir Allah da Annabi ya saki Mansoor shi kuma ya ce ba yanzu ba sai ya san da wanda ya ke faɗa. Cikin yanayin ba da umarni Hajiya ta ce”Kabiru ni a matsayina na Mahaifiyarka na ce ka saki yaron mutane ka sake shi.”
Cikin kallon Hajiya ya ce”Hajiya kinsan me ya yi min ne? Kama na kamar ni wannan yaron talakawan zai ja da ni?.
Da ƙarfi Hajiya ta ce”Ba na son ji komai, ka sa ka a saki yaron nan yanzun nan ban san zalunci.”
Ta faɗa cikin bayyana bacin ranta har da hawayenta sai ya fara huci yana wani cijewa kamar zai kai duka.
Sai Hajiya ta fara kokarin dukawa tana Fadin” Ko nima sai na duka ne?.
Da sauri Alhaji Hamza ya mike ya isa ga Hajiya ya riƙe ta yana Faɗin” Haba Hajiya ai kin wuce haka a wajen Yaya zai yi abin da kike so yanzu ma kuwa”
Major Kabir ya kallah kafin ya ce” Major ka sa a saki yaron nan don Allah, ka duba darajan Hajiya ga kukan da rokon da iyayen yaron ke yi maka, ka yi masa afuwa ka saka a sake shi.” Yadikko ma ta saka baki, sai da Hajiya ta fashe da kuka tana Fadin”Shike nan kabiru kada ka sake shi. Wlh in har wani abu ya sami yaron mutane ba zan taɓa yafe maka ba.”
Jin haka yasa Alhaji Hamza ya ce” Major ka sarrafa fushinka, Hajiya ke mgana da kai fa.”
Sai da ya fitar da iska daga bakinsa sannan ya ɗaga waya ya kira ɗaya daga cikin Sojojin ya ce a taho da wannan yaron zuwa falonsa ya na jiran su. Cikin lokaci kaɗan da bai gaza mintina goma ba sai ga shi sun shigo da shi kamar sun ɗauko wani cuta suna zuwa tsakiyar falon suka sake shi ya faɗi kasa warwas tunda ba shi wani kuzari, Kamar ma sun watsa masa ruwa ne ya farfaɗo tunda faran rigan jikinsa duk ya baci da jini, fuzkarsa ta kumbura idanuwansa sun shige ciki saboda tsabar duka bakinsa ya sumtuma da goshinsa.
Bai iya kuma motsa hannunsa na dama da kafarsa ta hagu ba, kallo ɗaya zaka yi masa ka san cewa ya bugu buguwa na sosai tunda har kammaninsa ya sauya.
Da wani irin sauri da kuka Inna Meri da Baba Ɗanjuma suka nufi Mansoor Mu’azzam ya tarairayo sa jikinsa yana ta kiran sunan shi amman ko iya buɗe ido ba ya yi saboda tsabar duka, yana so ma ya bude ido ko ya yi mgana ya kasa Allah ne ya yi kwanansa na gaba kwana suka yi suna dukanshi, shi kuma bakar zuciyarsa ta hana shi ya yi nadama. Inna Meri ta riko hannun da na dama da sauri ta ga ya janye hannu ya na cije leɓensa da duk ya fashe saboda duka cikin kuka Mu’azzam ya ce”Inna bar taɓa hannun kila ya samu gocewa ne.”
Baba Ɗanjuma yana share ma Mansoor jinin goshinsa da haɓan rigansa lokaci ɗaya yana kiran sunan shi”Baban Inna buɗe idanuwan ka? Baban Inna, Baban inna” Haka yake ta kiran sunan shi yana jin su amman kuma ya kasa iya buɗe idanuwansa.
Mmi na leƙensa ta bayan Mommy tana kuka ta san in ta ce za ta karisa sai Abi ya saka bindiga ya ɗauke kanta Khadija ma tana falon amman itama ko motsi ta kasa, Hajiya kuwa sai kawai ta dukar da kai tana kuka faɗi ta ke yi
“Kabiru wlh ka ɗauki hakkin wannan yaron kuma in har bai yafe maka ba sai Allah ya isar masa”
Yaddiko sai salati ta ke yi ganin Yadda Sojoji su ka maida hallitar Mansoor.
Alhaji Hamza kuma ya ma kasa magana bai ɗauka rashin imanin Yayan nasa ya kai haka shahara ba, shi ko tsoron ya kashe shi ba ya yi. Hawayen Inna Meri da na Mu’azzamu na ɗiga a saman fuskar Mansoor su suka taimaka har ya iya buɗe likakkun idonsa guda ɗaya ya na kallon iyayensa suna kuka saboda halin da ya saka su, yunkurawa yake yi kamar ya tashi amman kuma ya kasa sai da Mu’azzam ya rike shi sannan ya iya tashi zaune, amman dauriya ce shi kaɗai yasan halin da yake ciki.
Major Kabir kuma sai mirmishin mugunta yake yi kafin ya ce”Zan kyale yaron ku saboda Hajiya amman ba domin haka ba da sai ya raina kansa, amman ko yanzu ya san karo da Soja ba wasa ba. Sannan akwai sharaɗin da zan kafa muku da in har ya tsallake su anan gaba sai dai shi ya mutu wlh.” Inna Meri da Baba Ɗanjuma har suna karo da Juna wajen ƙara dukawa gaban Major Kabir, suna rawan bakin sanar da shi sun amince kuma Mansoor zai yi biyayya ga Sharaɗin sa.
Major Kabir ya nuna Mimi da yatsa kafin ya ce”Ba shi ba ƴa ta, ko kallonta ya kara yi in na sani sai na lalata rayuwarsa, sannan ya sani kada ya kara min wannan tsaurin ido Mimi tafj karfin talaka kamarsa wanda har ubansa ya bar duniya bai shigo birni ba, Kuma ni ba zan iya aura ma ƴata Agolan da rayuwarsa ba ta da wata mamora ba, daga yau sai yau na raba wannan alaqar ba shi ba ƴa ta ba rayuwata in kuma ya ki ji to Wlh a karo na biyu har ku mutu ba za ku kara ganinsa ba domin sai na ɓatar da rayuwarsa, Kuma ba zai bar wajen nan ba sai ya duka ya nemi gafara ta kamar yadda kuka yi yanzu in kuma har yanzu bai yi laushi zan saka shi ya yi laushin.”
Ya faɗa ya na nuna Sojojin da ke baya sun kame, Inna Meri har tana rawan baki riko hannun Mansoor ta kamkame tana fadin”Darajar haihuwar ka da nayi Mansoor ka buɗe baki ka ba shi haƙuri saboda ka tsira da rayuwarka.”
Mansoor kukan zucci ya ke yi zuciyarsa na wani irin suka, yana ji kamar ya zama asarrare mara amfani, duba yadda Mahaifiyarsa da wanda ya zame masa uba da ƙaninsa suke kuka saboda shi, kalli yadda suke duke gaban wani hallita na Ubangiji saboda shi , yau saboda shi an kira sunan mahaifinsa an zage shi da gorin ya mutu a kauye bai taba shiga birni ba, shi ba yana kukan dukan da ya ci ba ne da dai ya ba ma wannan mugun hakuri gwara ya kashe shi, Shi ko da wani suna zai iya kiran kalmar Soyayya? Tun jiya ya ke son yaji ya tsani Mimi acikin ransa amman ya kasa, ji yake yi kamar ya mutu baƙinciki da yake cikin zuciyarsa tunda ya zo duniya bai taɓa tsintar kansa aciki ba. Ba shi da niyar saduda ya so ne su bar shi ya kashe shin in dan har zai iya, Sai dai Kukan Inna Meri da na Baba Ɗanjuma tare da Mu’azzam suna masa magiyan ya bashi hakuri saboda ya tsira Inna Meri ta san halin abin da ta haifa yasa a fusace ta ce”Ko ka bashi Hakuri ko na ce sai ka biyani Nonona da ka sha”
Baba Ɗanjuma ya kira sunanta da karfi cikin tashin hankali.
“Meramu..”
Hajiya ma sai da ta kira sunanta ita kuma ta yi hakane saboda ya ba da hakurin ta san halin Baban Inna da kafiya sai yace sai dai a kashe shi. Kuma hakan da ta yi sai a ka samu masalaha domin Mu’azzam ya rike sa ya durkusa saman gwiwiyonsa tare da Iyayensa kansa na kasa ya na jin taruwan hawaye acikin idanuwansa, ko dukan da aka yi masa bai saka shi kuka irin wannan tozarcin ba muryansa ba ta fita ma sosai Saboda wahala ya furta” Ka yi hakuri..!”
Yana gama faɗin haka sai ya ji wasu hawaye masu zafi sun sauko masa.
Nan Major Kabir ya Koma ya zauna yana Faɗin”Good. za ku iya tafiya da shi amman ya kiyaye sharuɗɗana.
Inna Meri da Baba Ɗanjuma suna rawan jiki masa godiya su ka miƙe jiki na rawa Hajiya nauyi da kunya su ka hanata mgana Alhaji Hamza ne ya ce su tsaya mana a nema musu Jirgin komawa da sauri Baba Ɗanjuma ya ce”Mun gode da karamci ranka ya daɗe ya isa haka.”
Hajiya ta yi saurin kallon Major kafin ta ce”Kabiru ka dubi halin da Binta ke ciki Hausawa su ka ce idan An ciza a hura watarana kada ka zo kana nadamar abunda ka aikata ma wannan yaron”
“Ni? Kamar ni Major Kabir My Daughter ta auri talaka Agolan da ubansu har ya mutu a can wani kauyen kurmus, uban rikonsa wanzami uwarsa yar aiki? Over my dead body Mimi za ta yi wannan auran ƙaskanci ba ta isa ba, ko za ta mutu bazan aura mata wannan talakan ba, jinin takalawa wanda bashi da wata kyakyan makoma ko anan gaba.” Ya karishe faɗa a fusace kamar ba da Hajiya ya ke mgana ba, kawai sai ta girgiza kai kafin ta ce”Shike nan Allah ya hana mu jin kunya watarana.”
Ta faɗa ta na kallon yadda Idanuwan Mimi suka kumbura saboda kuka, Mommy ma sharan kwallan take haka ma Khadija kowa kuma yasan ba’a kyauta ba, amman kowa yana tsoron ya yi mgana wanda bai girmama maganar uwar da ta haifesa ba ai ba wanda kuma ya isa ya yi masa mgana ya saurare shi.
Mu’azzam ya riƙo sa tunda ba ya iya tsayuwa gefe kuma Baba Ɗanjuma ya kama shi za su fita daga falon da gudu Mimi ta ƙwace daga jikin Mommy ta ƙarisa gaban Abi cikin kuka Ta ce.
“Abi ka yi hakuri Abi ina son shi don Allah kada ka raba mu da juna”
Cikin tsawa Ya ce” Sai dai ki mutu, amman Wallahi tallahi ba za ki auri wannan talakan yaron nan ba, ba shi da makoma mai kyau, ina tambayan ƙwalin karatun shi Hajiya na gayamin iyakarsa Secondary school. Soja yake son zama ire iren su ma ba su da wani rabo a duniya.” Mimi ta katse shi cikin gunjin kuka tana kara faɗin.
“Abi ina son shi..”
“Ke yarinya ce Mimi, karatu nake so ki yi ba yanzu zan yi miki aure ba”
Ya faɗa shima bayan ya katseta cikin kaushin Murya.
“Abi Ina son shiiiii…”
Ta faɗa cikin wani irin karyayyen sauti kamar za ta shiɗe.
“Murja ki ɗauke min Mimi kada raina ya ɓaci na fasa kanta da bindigata”
Ya faɗa ya na kokarin sarrafa fushin sa domin ji yake yi kamar ya tokareta ta faɗi in ta na haɗa shi da wannan ƙasƙantaccen yaro nan mara makoma mai kyau.
Ba zai manta da wannan kukan da ta rika yi lokacin da mahaifiyarta ke rike ta ba, har gobe yana jin Sautin wannan kukan acikin kirjinsa. Ya tuna ta na miƙo hannunta Mahaifiyarta da yayarta khadija suka riƙe ta suka tafi da ita zuwa cikin wani ɗaki.
Yayi ƙokarin danne abin da ke taso masa amman sai ya kasa, kafarsa ya makaleta ya kasa tafiya da ya sa su Mu’azzam su ka tsaya su na kallonsa ba su san abin da zai aikata ba da ba su barshi ya kara yin mgana ba.
Sai juyawa kawai su ga ya yi ya na faman ɗingisa kafa idanuwansa a like ga kaya duk sun yage ba hula ba takalmi kamar wani almajiri cikin muryan da ta galabaita ya fara faɗin.
“In har ni Mansoor na haifu cikin uwata Meri da uba na Ibrahim ƴarka ko ita kaɗai ta rage a duniya nan sai dai ta mutu nima na mutu ban yi ba aure ba,”
Ya faɗa ya na sakin numfashi Inna Meri na kokarin toshe masa baki amman sai da ya ida sa faɗin abunda ke ransa a lokacin.
“Nayi alkwarin toshe kunnuwana daga jin ta da ganinta na yi alkwarin sauya duniyata daga duniyar ta na yi alkwarin sauya mattacen mafarkina a kanta, na kuma gode maka da ka fahimtar dani darasin rayuwar dana daɗe ana ga ya min ban ɗauka ba, na kuma fahimci akwai tazara mai kimanin kilomita tamanin tsakanina da ƴarka, na kuma fahimci matsiyaci kamata ya yi shisshigi wajen tusa kansa in da bai dace da shi ba, yadda ka saka iyayena kuka a kaina kai ma watarana sai ka yi kuka saboda ƴarka.”
Yana gama faɗin haka ya juya kamar zai kifa saboda yanayin jikinta Major Kabir ya yi wani kayattacen mirmishi kafin ya ce” Ku ja ma ɗan ku kunne, na ga alaman tsageranci na damunsa sannan ku yi masa iyaka da ƴata domin ruwa ba sa’an kwando ba ne, zan sake shi na yanzu amman ko kallon Mimi ya sake yi sai na ɗaure shi da kakin jikina.” Baba Danjuma bakinsa na rawa ya ce”Ba ma zai kara kallonta ba In sha Allahu ka yi hakuri.”
Haka su ka fita da Mansoor a rirriƙe da shi saboda halin da ya ke ciki, kuma ba wanda ya bi bayan su. Shima Major ɗin mikewa ya yi a fusace ya shige cikin ɗakinsa har yana banko kofa Hajiya ta bi shi da kallo tana Sassauta fushinta domin kada ya zama masifa ga rayuwar Kabiru. Amnan ita ta so da aka Ciza sai a Hura saboda ba’a san abunda gobe za ta haifar ba.
Ko kwana ba su yi a Abuja ba Hajiya ta ce gida zata koma, Mimi kuma ta zauna wajen mahaifinta ba za ta kara amsar ta riko ba tunda ga abunda ya biyo ba, Mommy ta yi tayi Hajiya ta kwana Hajiya ta rantse ba za ta kwana ba. Hajiya na ba ta hakuri Mommy ma na ba ma Hajiya hakuri ta yi mirmishin takaici kafin ta ce”Bakomai Murja wata rana Kabiru zai yi nadama, sai dai ina fatan Lokacin da zai yi nadamar lokaci bai kure masa ba.
Alhaji Hamza a lokacin ya nema musu jirgi suka juya zuwa Gombe kuma har suka bar gidan Major bai fito daga ɗaki ba, Mimi dai kuka ta yi kamar zata ba ma uku lada domin ta so ta bi Hajiya su koma gombe Hajiya ta girgiza kai kafin ta ve”A’a ki zauna ki yi ma mahaifinki biyayya shi ya haife ki ya fini iko da ke, ina miki fatan Allah ya sanya hakan ya zama alheri a rayuwar ki Binta ki yi Hakuri kin ji ko? Mimi tana ji tana gani Hajiya ta tafi ta barta daga nan ta fahimci ta rasa wani hop, domin Mommy ba ta isa da ja da hukuncin Abi abunda ya faɗa tabbas haka din ne zai kasance.
Tun daga wannan daran Mimi ta ke kukan Rashin Aji a rayuwarta kukan da har tsawon shekaru goma ba ta taɓa dainawa ba.
Kuma wannan zafin da kirjinta ya soma tun daga ranar ne, to shi ya haifar mata da ciwon da har gobe bai warke ba.
**
Labarin abin da ya faru da Mansoor ya za ga gari ba wanda bai sani ba. Wani tarihi ne da shi kanshi ba zai taɓa mantawa da shi a rayuwarsa ba, sannan tarihin dafin soyayyar da ba shi da magani.
A ranar kwanan hanya suka yi zuwa Gombe tunda Mota ce ga Mansoor ba lafiya kafin su isa duk jikinss ya kara tsami, Allah ya sa Baba Ɗanjuma ya riko kuɗi a Hannunsa Inna Meri na cikin tashin hankali ba ta tuna da wannan ba.
Motar da su hayo ma daga tasha Sai da Baba sani ya biya, suna ta faɗa da masifan yaro ya jawo musu bala’i, sai dai suna ganin halittar da Mansoor ya koma sai suka yi shuru domin su kansu sun san yaron ya kai kanshi in da ya kusa mutuwa.
Jinya ce sosai Mansoor ya yi domin ya samu targade da gocewar kashi sama da huɗu a jikinsa ga raunika a saman kansa ga tsamin jiki ga raunin dake cikin zuciya wanda ido ba ya iya gani.
Shi kaɗai yasan irin ƙunar da zuciyarsa take ciki, ciwo dai idanuwana ba sa iya gani sai shi kaɗai da zuciyarsa ke cikin kirjinsa ya san halin da ya ke ciki. Makota haka suka yi ta tururuwan zuwa ganinsa wasu duk saboda gulma ne, wasu kuma domin ganin abunda ya faru mata kuma suna ta zuwa yi ma Inna Meri barka da arziki.
Su Baba Sani ke kara ma lamarin magi da gishiri suna ƙara abunda bai faru, har suna cewa shi kanshi Yaya Ɗanjuma da Merin dakyar suka sha domin yaron ya je ya jawo Yar soja an kusa kashe shi fitinarsa ya sa yau ya kusa janyo abin da zai saka har su a kashe su a banza. Nasir da makama kullum suna gidan wajen Mansoor dake kwance ya na jinya, Ahmad kuma sai da ya dawo garin ya zo ya ga yadda Mansoor ya koma shuru shuru ba ya mgana kamar an sauya shi. Baya cin abinci baya mgana ba ya fara’a ko da yaushe ya na kwance yana fama da kuncin zuciya.
Kullim mganar Inna Meri shi ne” Baban Inna ka mike ga kanka wannan kwanciyar ba zai yi maka kyau ba”
Sai kuma ta saka masa kuka, Baba Ɗanjuma shima ko da yaushe cikin yi masa nasiha yake yi.
Su Nasir ma koda wani lokacin cikin faɗin ” Aji ba fa karshen rayuwarka ba ne ya zo, Mimi ba ita kaɗai bace mace a duniya ka mike ka gina rayuwarka zaka samu wacce ta fita a gaba.”
Mu’azzam kuma kamar yafi kowa damuwa maganar kenan” Ka manta da abin da ya faru ka tashi ka kula dani kamar yadda ka saba, ba na jin daɗin ganinka a haka”
Haka su Yaya Amina suna tafe zuwa duba shi kowa na bashi mgana
Har can mallam Sidi inna ta aika Yalwa da ya’yanta sun zo har Baban shi Karimu sai da ya zo duba shi.
Inna Meri ba ta ɓoye musu abunda ya faru ba ta gayamusu komai.
Yalwa na kuka ta ce”Allah ya isar masa ba mu yafe ba.”
Karimu kuma cikin fusata ya ce”Ke sakarai miƙe ga kanka, ubanka har ya bar duniya ba lusarin namiji ba ne ka tashi ka zauna da kafafunka domin gina ma kanka kyakkyawan rayuwa anan gaba.”
Ya san duk abin da su ke faɗa gaskiya ne, amman shi a cikin Kirjinsa wutar ƙiyayya ke bayyana, daddare haka zai kwana bai yi barci ba yana kukan zucci, Auwalu bai taba tausaya masa ba sai dai ya riƙa dariya yana faɗin”Maganin ma su janye janye kenan in ban da karfin hali ina kai ina wannan yarinyar? Tabbas gaskiya ya fada soyayya ta rufe mishi ido da ya sa ya kai kansa inda bai dace ba.
Yana so shima ya manta amman ya kasa ji yayi ya tsani duk abunda ya danganci wani aiki mai kaki burinsa na zama Soja tuni ya za ma mattace acikin zuciyarsa.
So yake yi ya zauna ya yi kuka amman kuma ya kasa sai ranar da Mu’azzam ke masa mgana ya samu ya riko hannunsa ya danna a kirjinsa yana faɗin “Ta nan ne,a nan na ke jin ciwo da zafin abun. Ina so na manta amman na kasa.”
Kawai sai ya fashe da kuka ya dunƙule a jikin Mu’azzam ya na kuka kamar ransa zai fita Mu’azzam bai hana shi ba domin yana so ya samu sukuni. Tun daga wannan kukan da ya samu sararin yi ya samu sauki acikin zuciyarsa, wannan abin da ya faru Shine silar sauya rayuwar Mansoor ya koma rayuwa shi kaɗai ya koma Shuru Shuru sannan mai riko sannan bakar zuciyarsa ta kara ninkuwa sama da sau goma.
Daga lokacin Inna Meri ba ta kara takawa gidan Hajiya ba, Hajiya ma ba ta kara nemanta ba alaqar ta ƙare.
Ana ta masa mganar ya koma makaranta shima sai ya yi tunanin gwara hakan zaman ya ishesa. Da taimakon gonakinsa na gado aka saida ya samu ya fara karatu a gurbin Jami’ar Gombe state University.
Sun ba shi Agric kuma bai sauya ba saboda shi ya riga ya gama sarewa da duk wani burin shi. Da farko tare da Mu’azzam za su shiga sai kuma Alhaji Mustapha ya kawo maganar zuwa Police Acadmy Wudil a matsayin Mansoor ya je tunda shi ke son aikin Kaki, amman ina ya ce har Abada da ya zama ɗan sanda gwara ya mutu.
Sai ko Mu’azzam ya ce zai je tunda Aminin Alhaji Mustpaha ke shugabantar makaranta Kuma shi ya bashi Upper ta mutum ɗaya.
A lokacin tuni shima Mu’azzam ya watsar da mafarkinsa yace shi zai tafi Wudil Mansoor kuma ya ce ƙaninsa ba zai yi aikin kaki ba.
Inna Meri tace bai isa ba sai Mu’azzam ya tafi, Mu’azzam ɗin ma ya nuna ya na son ya je. Kawai sai Mansoor ya ce”Ka je ka je, ka za ma duk abin da kake son zama Mu’azzam amman ka sani har Abada bazan taɓa kaunar wani aikin kaki ba.”
Mu’azzam ya ɗauka zuwa gaba Yayan nashi zai rage wannan kiyayyar sai dai kash kiyayyar ta shi mai girma ce har Mu’azzam ya tafi Wudil bai kaunaci wannan karatun na shi ba, Tafiyar Mu’azzam ta kara saka ya zama ya na son kaɗaici, Saboda zaman shuru in ba shi da karatu sai yake zuwa ya na tsaren wani shago a kasuwa yana samun kudin abun hawa zuwa makaranta, ya daina neman kowa hatta su Nasir ya Guje su. Ko sun neme shi ba ya zama in da za su gan shi, su ma sun gaji da nemansa sun kyale shi a tunaninsu nan gaba zai dawo dai dai. Yana Aji biyu a jami’a Coach na Team ɗinsu na Nasara tare da na Tudun wada Team suka zo nemansa akan suna bukatar wani yaro matashi wanda ya iya buga kwallo za’a bashi horo na shekara biyu wata kungiya zata ɗauke shi. Mansoor suka nema tunda daman tare da shi suka rika bin shugabannin manyan Team ɗin su na yan ƙwallo daga na manyan anguwanni har na ƙananu.
A lokacin sai ya ga ya mu su Mu’azzam ne kuma ya tafi Police Acadmy baya nan, Coach ɗin su na Nasara Team yasan Aji ya iya taka kwallo shi ya matsa akan cewa shi Ajin ya zo a matsayin Mu’azzam ɗin mana.
Da farko yaƙi amincewa sai daga baya ya ga to miye aciki? daman shi tuni mafarkinsa ya daɗe da sauyawa amman bai amince ba sai da ya yi mgana da Inna Meri da Baba Danjuma suka sanya ma lamarin albarka.
Sannan ya amince ba zai taɓa mantawa da Coach din su na nasara Team ba wato Shehu Master Allah ya jikan sa ya rasu shi ya ɗauke shi ya kai shi wajen Coach ɗin su na Gombe United a lokaci suka yi mgana sosai ya jaraba shi ya gani sai ya ce za’a bashi horo na shekara biyu, shi kuma sai ya ga ya masa yana karatu sai ya nuna masa hakan bazai shafi karatunsa ba.
Kwatsam ne fuskar Aji da sunan shi ya bayyana acikin yan kwallon kafa, Ya yi horan shekara biyu sannan aka gabatar da shi a Kungiyar kwallon kafa ta Gombe United lokacin kontiragin Captain ɗin kungiyar saura shekara ɗaya ya kare, tare suka ƙarisa wannan shekaran ɗayan da Aji bayan kuma ya bar Club ɗin ƙokarin Aji ya saka ya samu matsayin Captain saboda daman dalilin da ya sa a ka kawo shi kenan. Shi ne sanadin da ya sa ya zama duk abin da ya zama a ƙwallon kafa, kuma tunda ya riga ya hakura da mafarkinsa sai ya maida kansa ga karatunsa sannan ga wasan kwallon kafa.
Shima ya yi singing kontiragin na shekara goma ne da Gombe United sun kuma fara biyan shi albashi bayan alawun da yake samu in suka fita wasa, da haka ya gama karatun shi ya yi service ɗin sa anan garin Gombe zuwa Lokacin rayuwa ta mika abubuwa da dama sun sauya ciki har da gama makarantar Mu’azzam ya fito da matsayin Assistant superintendent of police ASP, ya kuma samu an ijiyesa a garin kano sai dai ya riƙa zuwa ganin gida.
Kuma har a lokacin Mansoor bai kaunar aikin kaki duk ko da matsayin Mu’azzam na Asp. Ya samu shahara da suna a duniya saboda ƙwallon kafa, sunan Aji ya tashi kan mutane ko da daman ya shiga wasan ƙwallon kafa da sunan shi na Aji sai sunan ya kara ɗaukaka su kansu su Nasir suna mamakin shigar Aji kungiyar kwallon kafa sanin shi ba ya ra’ayin haka sai dai kuma in suka yi duba da rayuwarsa ta sauya sai su daina mamaki.
Acikin Shekaru goma ya taka matsayin da ya taka ya mallaki kwalin Degree sannan ya na shekaru na biyar a kungiyar Gombe United a matsayin Captain mai buga lamba huɗu dan ƙwallon mai sa’a wanda kuma kungiyar ke alfahari da shi saboda yadda ya iya taka leda. Ya yi kudi ko na ce ya samu arzikin da ya gyara gidan su sannan ya fitar ma da Iyayen shi bangaren su, har su Baba Sani suma ya gyara musu bangaren su, ɗawainiyar gidan ya dawo a kansa gabaɗaya sai dai abin da ba’a rasa ba Mu’azzam ya saka Hannu.
Gidan ya rage mutane tunda matan duk sun yi aure mazan kuma sun yi aure wasu kuma suna can wajen sana’arsu da matansu Auwalu ma ya yi aure wahalan rayuwa ya sa Aji ke taimakonsa da Mu’azzam yanzu. Sannan tun daga kan Mimi Aji bai kara neman wata mace ba in aka yi masa mganar aure sai ya sauya fuska gashi ya siya fili ya yi gida ya siya mota ya siya mashin sannan ya siya ma Baba Danjuma ma.
Har aka aka ƙarama Mu’azzam matsayi bayan shekaru uku zuwa superetendant of police SP kuma ya yi aure da yar’uwansa Hibbatu cikin shekara ɗaya ta haiihu aka samu mai sunan Baba Danjuma Gaddafi.
Da ɗaya da ɗaya kuma su Nasir su ma suka samu aiki suka yi auran su, Nasir ya na aiki da Nepa makama kuma aikin banki yake yi , Ahmad kuma yana kaduna yana ɗinki shima ya yi auransa Aji kaɗai ya rage shidin ma yanzu ya sauya ya daina nemansu sai dai in dan su suka nemeshi.
Ya riƙe wannan abun acikin zuciyarsa da ya kasa barinsa ya yi rayuwa irin ta kowa Mimi ita ce sanadin da ya sa rayuwarsa ta sauya zuwa juyin waina daga sama zuwa kasa
tun kuma daga rabuwar sa da Mimi a falon Mahaifinta bai kara ganinta ido na ganin ido ba sai a wajen bikin Makama sai dai can bayan wasu shekaru da suka gabata ya fara ganinta a talabijin a matsayin ma’aikaciya.
Ko rashin lafiyar mahaifinta sai a hirar da aka yi da ita ya sani, domin tun bayan abin da ya faru alaqar gabaɗaya ta lalace ita kanta Inna Meri ba ta da labarin gidan Hajiyar Shagamu a yanzu.
Mafarin Labarin Mimi da Aji.
Page 16
4rd May, 2022.
Abuja, Thursday
03:40Am
Tun ranar mandoy ɗin da ta gabata Mommy ta so su je Gombe kamar yadda Abi ya bukata amman kuma tana jagorantar wani case a kotu sai ta ga gwara ta tsaya ta gama kafin su tafi. Dole ya sanya ta kira Sulaiman tace ya dakata da Bucking ɗin su ya bari sai ranar jumma’a tunda ranar Alhamis ne karshen shari’an nasu.Sun gama tsara na su amman shi Abin da Ubangiji ya tsara ya sha bambam da tunaninsu.
A daran Alhamis duk wani shirin tafiya Brr.Murjantu ta gama yin sa saboda Sulaiman ya kirata ya faɗa ma ta jirgin ƙarfe goman safe za su bi zuwa Gombe in Allah ya yarda shi ya sa tunda ta dawo daga wajen aiki ta kasa zama sai faman shiri take yi musu tunda wannan ne karo na farko tun bayan abin da ya faru da shi da zai kara takawa zuwa jiharsa.
Alhaji Hamza kawai ta kira suka yi mgana Saboda shi zai tura musu motar da za ta ɗauke su daga filin jirgi zuwa gidan Hajiya, Lafiya lau ta gama duka shirinta a daren Abi yace mata ba ya jin daɗin jikinsa yana so ya yi wanka ita ta rarrafa ta ɗora shi saman keke ta kai shi tiolet ta taimaka masa ya yi wanka sannan ta gunguroshi zuwa ɗaki ta shirya shi, sannan ta zo ta yi masa shirin kwanciya a daren sun kwana a jikin juna a baya bata ɗora masa nauyinta saboda yanayin laluransa sai ranar kuma da kansa ya bata umarnin ta matso kusa da shi bayan ta matso sai ya saka hannunsa mai motsi ya jawota gefensa har kanta na matsuwa da ƙirjinsa.
Manganganun da ya yi ta gaya mata sun bata mamaki da tsoro sai dai ba ta taɓa tunanin tafiya Habibi zai yi barta ba. Ya jadaddamata in har bai samu zuwa Gombe da kansa ba ta taya shi neman yafiyar Hajiya sannan ta yi masa alƙwarin neman yaro nan ta bashi hakuri sannan ta yi masa alkwarin samar ma Mimi farinciki da kuma ba ta abin da take so, a lokacin kallonsa ta yi cikin mamaki kafin Ta ce.
“Ka daina faɗin haka Habibi in sha Allahu gobe za mu je Gombe, kuma da kanka za ka samu damar neman gafaran Hajiya, sannan kai da kanka za ka yi magana da Mansoor ka nemi yafiyar sa.”
Mirmishi ya yi mata ba tare da ya yi mgana ba sai dai ta ga ya yi mata wani iri duk ya sauya mata. Ta san ya yi shekaru yana jinya ƴan’uwanta ba duka ba ne su ka bata goyon zaman jinyar Major Kabir ɗin ba, gani suke zata yi wahala da shi tunda ba ranar warkewa. Ita kuma me ya rage mata a duniya ban da ta zauna ta kula da Mijinta uban Ƴaƴanta domin ta samu rabauta ranar gobe kiyama, Shi ya sa ba taɓa nuna masa gajiyawarta ba tana Ƙoƙari a kansa da amanar gidansa da ƴaƴansu
Sun jima kafin su kwanta yana ga ya mata wasu irin mganganu ma su kama da kamar mutum yana barin wasiyya sai hankalinta ya tashi ganin haka ya sa sai ya bar mganar ta rumgumshi ta ce su kwana su yi barci gobe suna da tafiya a gaban su.
Barci ne mai nauyi ya kwasheta acan cikin barcin ta yi mafarkin ta ga an taru gida ya cika ana ta kuka kuma taga wai an saka Habibi a makara za’a fita da shi ita kuma ta rike tana ta kuka.
Kamar an wancakalar da ita haka taji ta a gefe ta bar jikin Kabir, sai da ta tashi a firgice dai dai Lokacin da ta ji ya na tari ba kakkautawa. A firgice ta miƙe ta laluba hannunta ta kunna hasken ɗakin sai ta ganshi kwance in da ta kwantar da shi sai dai kuma tari ya sarƙe shi yana yi kamar numfashinsa zai ɗauke hankalinta ya ta shi sai ta tuna mafarkin da ta yi, ai da gudu ta diro daga kan gado ta isa gare shi tana riƙe shi ƙokarin tarairayosa take yi ta ji yana faɗin”ruwa! ruwa!
Ba tare da tunanin komai ba ta sake shi sai ta kwashi gudu kamar za ta faɗi zuwa falo fridge ta buɗe ta ɗauko masa ruwa mara sanyi tunda Saboda shi ba ta kunna fridge ɗin falo sai dai na Kitchen. Abin da ya sake ba ta tsoro ko da ta koma har ya faɗo daga kan gado ta ruɗe ga ta ita kaɗai ta nufe shi da sauri tana kiran sunan shi.
” Habibi, Subhanallah!”
Haka ta ke faɗi dakyar ta iya ɗago kansa domin sai taji ya kara yi mata nauyi ta kafa masa goran a baki ta na bashi ruwan abin da ya sa ka ta fashewa da kuka shi ne ganin ruwan gefe da gefe sai zubewa yake yi kaɗan ne ma ya ke shiga bakin sa.
Cikin muryan kuka ta ce”Na shiga uku ni Murja me ya same ka haka Habibi?
Shi kuma sai ya kauda kansa ruwan ya suɓuce daga hannunta ya ganganra ƙasa inda su ke zaune gabaɗaya ya jiƙa su ita a koƙarinta ta mikar da shi ta maida shi saman gado kamar yadda ta saba dubarunta. Amman yau sai ya gagareta shi kuma tarin na neman ƙara sarƙe shi cikin muryan da ta fara karyewa ba ta ma wani jin sa sossi ta ji ya kira sunan ta.
“Murjanatu..”
“Murjanatu..”
Da sauri ta amsa da “Na’am Habibi me kake so? Ko na je na kira Megadi ya zo ya taya ni mu ɗora ka saman keken ka?
Sai ta ga ya girgiza mata kai lokaci ɗaya yana riko hannunta cikin sarkewan numfashin da ba ta lura ya fara sama da ƙasa ba ya fara mgana”Murja ki yafe min kin ji? Sannan ki tayani neman gafara Hajiya da kuma afuwar Mimi domin na zalunceta sannan ki yi min alkwarin za ki nemi yaron nan ki ba shi hakuri kuma ki yimin alkwarin yi ma Mimi duk abin da take so saboda farincikinta.” Yana mgana cikin In ina saboda mumfashinsa na sarƙewa Mommy ta fashe da kuka kafin tavce”Ka daina faɗin irin haka sai na ga kamar mutuwa za ka yi ka barni Habibi?
Cikin ƙarfin hali ya ce” Naso na samu damar neman yafiyar su da kaina sai dai lokaci ya kuremin Murja, na amimta dake nasan za ki kula da ƴaƴana ki yi min alkwari guda uku na farko ki tayani neman gafaran Hajiya na biyu ki nemi yaro nan ki tayani neman yafiyarsa, na uku ki yi min alƙwarin yi ma Mimi abin da take so Murja”
Mommy na kuka ta ke ɗaga masa kai lokaci ɗaya tana faɗin”Na ɗauka amman dai in sha Allahu tare za mu je duk ka nemi gafaran su.”
Hawaye ke fita ta gefe da gefen idanuwansa ya ce”Ko bayan raina ban amince ki bar gidan nan ba Murja, ko da aure za ki sake yi ki zauna nan ne gidanki domin ki kula da yaran mu.”
Mommy kuka ta ke yi har da majina ta kasa mgana sai da taji ya kara riƙo ta da karfi lokacin tarin ya kara sarƙeshi faɗi yake yi
” Na yafe miki duka laifin da kika taɓa yi min Murja wanda kika sani da wanda ba ki sani ba , nima ki yafe min duk zaman kuncin da na yi da ke a baya ki yafe min Murj…’
Sai ya kasa karisawa domin tarin ya sarkeshi kuma yana tafiya da numfashinsa yadda Mommy ta ruɗe ne yasa ba ta fahimci lokaci ya kure ba. Domin a lokacin ana kokarin zare ran Abi ne, ita a tunaninta ba ta makara ba ya sa ta sake shi ta mike a guje ta fita haraban gidan tana kururwan kiran ma’aikatan gidan.
Allahu akbar ko da suka taso da gudu suna tambayan ta ko lafiya ta rika nuna musu cikin gida tana faɗin sunan Habibi tana wani irin kuka yasa su ka kwashi gudu zuwa cikin gidan har vikin bedroom ɗin su suka iske Abi kwance a kasa idanuwa sun kafe ba ya motsi. Megadin gidan dattijo ne na yanzu tun bayan yin ritayansa shi ya duba Abi ya tabbatar da rai ya yi halinsa itama kuma a koƙarin Mommy a kama mata shi su je asibiti har ta saka mayafi tana faman kiran can asibitin in da Dr Ashiru ke aiki. Megadi ya kalleta duk ta fita hayyacinta sauran ma’aikatan ma maza tuni sun fara salati matan kuma kuka suke ganin yanayin Hajiya duk ta fita hayyacinta ta ruɗe.
Tsawa ta daka musu lokaci ɗaya tana faɗin”Ku kama min shi mu fita waje,asibiti za mu je a duba shi.”
Kai Baba Megadi ya girgiza kafin ya ce”Hajiya sai dai mu yi hakuri Allah ya yi ma Alhaji rasuwa.”
“Rasuwa? Habibi ne ya rasu?
Ai ba ta san lokacin da ta yi kansa tana kiran sunan shi ba, lokacin har megadin ya saka hannu ya shafe masa idanuwansa, Allahu Akbar Kullu Nafsin Za’ikatul maut kowani rai sai ya ɗanɗani zafin mutuwa Allah ya sa mu dace.
Mommy kamar ta zare ko na ce ta yi hauka haka ta ke rike gawan Abi tana wani irin kuka ta surutai faɗi take yi”Habibi me ya sa ka yi min haka? Ka tafi ka barni Wayyo Allah na shiga uku na lalace.”
Ma’aikatanta mata ne ke tare da ita mazan daman guda uku ne megadi sai direba da mai kula da haraban gidan. Matan kuma mai girki wata bakatafiya ce saira sai mai gyaran gida wata yar matashiyace mai suna Aina’u daga can gidan su kano aka aiko mata da ita saboda su taya ta taimakon gidanta da mijinta. Har gwara Saira da shekarunta ita ke ba ma Hajiya hakuri su kansu ma kukan su ke yi Aina’u kuma sai mutuwar iyayenta suka dawo mata sabuwa itama gefe ta samu ta zauna ta na faman rusa kuka jikinta sai rawa yake tunda take a duniya ba ta taɓa ganin gawa ido na ganin ido ba sai yau.
Abi ya cika misalin 3: 50am na daren ranar Jumma’a ne kuma Mommy ba ta iya kiran kowa ba saboda tashin hankali har aka kira sallar asuba gwan Abi na jikinta ta rumgume ta yi kuka har muryanta ta daina fita tunaninta gabaɗaya ya toshe, da ita da su Sara tare su ka yi wannan zaman acikin ɗaki tana kuka suma suna tayata.
Sai wajen shida saura na safe sannan Megadi da su Habu suka sake shigowa ganin halin da Hajiya ke ciki ya sa Megadi ya durkusa a gabanta yana faɗin” Hajiya ki yi hakuri ki daina kuka don Allah, ya kamata ki kira waya ki sanar da su abin da ya faru ya kamata a suturta Alhaji domin a yi masa gata a kaisa makwancinsa na gaskiya.”
Mommy ta kalleshi da Idanuwanta suka rine saboda kuka sai a lokacin ta fahimci abin da ya kamata ta yi, ta kuma kara samun tabbacin Habibi ya tafi ya barta, Dole ta janye daga gareshi suka kamashi suka matsar gefe suka rufa masa zanin gado suka rufe shi su Sara kuma sai su ka koma falo suka zauna jugum tare da su Habu. Mommy kuma wayarta ta ɗauka amman ta rasa wanda za ta kira a daidai wannan lokacin sai kira ya shigo wayarta ta na dubawa sai ta ga kamar Alhaji Hamza ne saboda ba ta ma wani gani sosai da hanzari ta ɗauka ba ta jira maaganarsa ba ta faahe da kuka tana faɗin
“Abban Jaheed Habibi ya rasu, na shiga uku na lalace Habibi ya tafi ya barni.”
Haka ta ke faɗi muryanta na sarƙewa saboda kuka.
Daga can bangaren Sulaiman ya yi zumbur ya miƙe daga kishigiɗan da ya yi cikin wani irin razana yace”Innalillahi wa’inna ilahirraju’un Mommy Abi ne kika ce ya rasu? Sai a lokacin ta fahimci ba Alhaji Hamza ba ne Sulaiman ne. Sai kawai ta koma ta sulale a kasa ta na kara fashewa da kuka Lokaci ɗaya tana fadin”Sulaiman kun zama marayu yau Abin ku ya tafi ya barmu.”
Ta ma kasa mgana sai wani irin gunjin kuka kawai take yi. Daga can Bangaren Sulaiman ya katse wayarsa da Salati mai ƙarfi a bakinsa wanda ya taho tare da hawaye masu zafi daga kuncinsa.
Matarsa Jawahir na Kitchen tana Koƙarin yi musu abun karyawa tunda zai fita da wuri yana da tiyata karfe takwas ɗin safe sai dai taji salatin mijinta da karfi da yasa ta baro kitchen din da gudu zuwa Bedroom ɗin su nan ta iske shi zaune a kasa dafe da kansa da sauri ta ƙarisa gabansa cikin tashin hankali ta kira shi da sunan da take kiran shi.
“Darling me ya faru na ji kana ta salati haka?
Sai ta ga mijinta uban ya’yanta gwarzon namiji irin Dr.Sulaiman ya ɗago fuskarsa ta yi kaca kaca da hawaye cikin razana ta ce”Innalilllahi Darling me ya faru?
Cikin Wani irin sauti ya ce”Jawahir na rasa mahaifina, Abi ya rasu.”
Cikin wani irin sauti ta furta”Hasbunallahi wa’imal wakeel, Innalillahi wa’inna alaihirraju’un.”
Ta faɗa lokaci ɗaya a na ƙariswa gare shi ta zauna kusa da shi ta rumgumosa sai kawai ya faɗa jikinta ya fashe da kuka yana faɗin “Mommy na can ita kaɗai ba kowa a wajenta, Jawahir na zama maraya Ƙannena sun zama marayu mahaifiyata ta zama bazawara Ƴayana sun rasa kakansu, ki shirya su Momi bari na yi mana bucking ɗin jirgi yanzu nan.”
Da sauri kuma ya mike ya ɗauki wayarsa sai da ya sama musu Jirgin da zai tashi zuwa Abuja da Safa nan sannan ya kira asibitin su ya shaida musu halin da a ke ciki, dole a ka sauya sunan shi da wani Dr Ishaya, sannan daga baya ya kira Alhaji Hamza Saboda Mommy mace ce yadda ma ta ruɗe ya tabbata ba za ta iya kiran kowa ba shima ya tashi yana jin wani irin kasala a jikinsa kiran da ya yi daman ya gaisa da iyayen na shi kamar yadda ya saba duk safiya kafin ya fita aiki.
Alhaji Hamza ya ji mutuwar ɗan uwansa ya na tare da Anty ne lokacin da Sulaiman ya kira shi ya na sanar da shi yayansa Major Kabir ya rasu jiya da daddare.
Salati kawai ya ke ta maimatawa ba shi kaɗai ba duka matansa da ya’yansa sun ruɗe da jin wannan mutuwar daman Sulaiman ya ce ba ya tunanin Mommy ta kira wani shi ya je ya sanar da Hajiya shi kuma yanzu zai kira su Madiha ya sanar da su. Allah ya taimaake shi wayar mijin Madiha ya kira ya sanar da shi abin da ke faruwa shima ya ruɗe yace bari ya nema musu Jirgi.
Dr. Sulaiman cikin wani yanayi ya ce”Ka ga ya ma Madiha cikin hikima saboda kada ta ɗaga hankalinta.”
Cikin tsananin tausayin su ya ce”In sha Allahu Dr, Allah ya jiƙan Abi.”
Ya amsa mata da Amin wayar mijin Khadija ya kira sai kuma kawai ya ji ita ta ɗaga Wayar cikin karaɗinta ta ce”Dr yau ni aka tuna shi ne a ka kira mu da sassafe?
Sai ya kasa gayamata ya ce ta mika ma Mijinta wayar, yanayin muryansa ya sa sai da gabanta ya faɗi cikin in ina ta ce” Dr me ya faru? Jawahir da yara suna lafiya ko?
Kai tsaye ya ce”Ki ba ma Muhammad wayar da shi zan yi mgana.”
Tun daga nan ta san wani abu mara ɗaɗii ya faru sabo ba ta mantawa lokacin da Abi ya samu hatsari Dr Sulaiman ɗin ne ya kira sannan ya ƙi magana da ita sai da Muhammad. Daman ya shiga Tiolet ne ya na fitowa jikinta na rawa ta mika masa wayar ta kuma lafe a kunnensa domin ita jikinta ya bata wani abu ne ya faru.
Sai dai ta yi nadamar yadda ta kara kunnenta ta jiyo ma kanta abunda ya kusa tsaida numfashinta.
Ihu ta rika yi da kuka tana faɗin “Innalillahi Abi ne ya rasu? Na shiga uku na lalace”
Muhammad ke kokarin lallashinta amman kuma taki sauraran shi. Ba su samu jirgi ba sai suka shirya tafiyan mota tunda daga kaduna ne zuwa Abuja. Khadi sun yi mgana da Madiha kowacce murya ta shake suna yi ma juna gaisuwan rashin da suka yi madiha ta ce yanzu za su taso ita kuma Khadija ta ce suma ga su nan a hanya. Khadi ce ta kira wayar Mimi sai dai tana ta ringing ba’a ɗauka ba wayar Hajiya ma haka , sai ta kira wayar Mommy sara ta ɗauka ta ce Mommy na cikin ɗakin da Abi yake, Sai khadija ta kara rushewa da kuka ta kosa su isa Mommy ba za ta iya ɗaukan wannan rashin ba ita kaɗai ba.
Ko kafin takwas na safe a kafafan Sada zumuta duk an saka rasuwar da sauran duk wanda ya kamata yaji rasuwar Major Kabir ya ji, musamman gidan Talabijin na Karamchi a Safiyar ranar suka tashi da wannan alhinin domin ko da Alhaji Hamza ya isa gidan Hajiya Mimi ta bar gida zuwa wajen aiki tunda labaran Safe gareta.
Tana ɗakin Labarai ana gyara mata fuskarta Wayar Daddy ta shigo mata sai da gabanta ya faɗi a lokacin ba ta ji kamar za ta faɗi ba sai da ya ce ta bar komai ta taho gida ita ta sadakar Hajiya ce ta rasu daman ta barta kwance ta na gayamata ba ta jin ɗadin jikinta. Haka ta bar wajen aiki a afujajan sai dai abin da ta je ta ji ne yasa ta ruɗe ta kasa mallakan kanta
Hajiya kuma sai ta yi dauriya ita ke lallashin Mimi Alhaji Hamza kuma ya na amsa wayoyin mutanen domin in za’a saka rasuwar Major Kabir sai an ce Yayan Alhaji Hamza tsohon Sanatan jihar Gombe.
Rukky ne ta yi ta kiran wayar Mimi ba ta ɗauka ba, saboda su san abin da ke faruwa sai Mimin ta rubuta sako ta tura mata.
“Rukayya ki sanar da Manaja Abuja za mu wuce yanzu Allah ya yi ma Abi rasuwa.”
Allahu Akbar zukata sun raunana yawancin mutane ma sanarwa da gidan talabijin na karamci ta yi ne su kasan abunda ya faru ciki har da Inna Meri da ta na ma cikin ɗaki lokacin suna cikin karanta labaran duniya na Safe bayan sun gama suka sanar Walida ce ta rugo ɗaki da guda tana haki ta ce”Inna yanzu nagani a Tibi ana faɗin Allah ya yi ma mahaifin mai karanta labaran na rasuwa Mimi.”
Da Sauri inna Meri ta mike ta fita falo Sai ta ci karo da hoton Major kabir cikin kakinsa Soja ana sanar da rasuwarsa jiya da Daddare za’ayi jana’izarsa yau Jumma’a bayan an sauko daga sallar Jumma’a a gidansa dake Gwarimpa a Abuja.
Ba za ta manta da fuskarsa ba ta gane shi Allah Sarki rai bakon duniya daman ai ƴarsa ta ce ba shi da lafiya duk sai jikin Inna Meri ya yi sanyi a fili ta kaɗa kai kafin ta ce”Allah ya jiƙan sa da Rahama mu kuma Allah ya kyautata ta mu bayan tasu.”
Walida ta amsa da Amin ita ba ta san shi ba amman ai ta san Mimi budurwan yayansu ne a baya kuma Inna Meri ta san su shiyasa ba ta yi mamakin ganin yadda jikin Inna Meri ya yi sanyi ba. Suna zaunen Baba Ɗanjuma ya shigo cikin shirin fita yana ga ya mata shima Jana’iza zai je ƙanin Mallam Hashimu ne ya rasu.
Ta yi salati kafin itama dire da faɗin “Kai Jama’a ana ta tafiya nima yanzu nake ganin sanarwan rasuwan mahaifin yarinyar nan da Baban Inna ya so mai karanta labarai anan yanzu suke faɗi jiya da dddare ya rasu.” Baba Ɗanjuma ya ce”Innalillahi wannan Sojan? Inna Meri ta gyaɗa masa kai sai kawai ya jinjina kai kafin ya ce”Allah ya jiƙan su da rahma Allah yasa Aljanna makoma”
Shima yana tunawa da shekarun baya ne har an zo an gama jin ɗadin duniya kuma an koma. Kai Allah yasa mu dace, Allah ya sa mu mutu muna masu Imani Amin.
**
Kamar yadda aka sanar an yi Jana’izar Marigayi Major Kabir Sulaiman Dabo a gidansa bayan sallar Jumma’a Alhamdulillah ya samu jama’a kama daga yan siyasa abokan hulɗar Daddy tare da Abokan aikin Abi sojoji ritayas kamarsa har da masu kakin a lokacin sannan tare da mazajen yayan shi da kuma sai yan’uwa da abokan arzuka tare da dangin Mommy daga kano aka sallace shi zuwa gidansa na gaskiya. A ka bar mata acikin gida suna kuka sak abin da Mommy ta gani a mafarki shi ya faru ta riƙe gawan mijinta tana wani irin kuka sai da ƙanwarta Zainabu ta zo ta riƙe tare da sauran yan’uwanta da su Mama ko da aka fita da shi sai ta faɗi a sume ita da Mimi. Madiha da Khadi kuma sun kasa mallakan kansu ma.
Alhaji Hamza da Sulaimam suka yi ma Major wanka suka haɗashi saboda nisan makabartan sai bayan la’asar suka dawo daga kaishi. A makabarta Sulaiman ya sha kuka shi da Alhaji Hamza Jaheed ma ya iso da shi akayi jana’iza.
Shi ne ya rike sulaiman ɗin ya tada shi daga gaban kabarin Abi likita ne mai dakiya amman ya yi rashin bangon da har abada ba zai iya maida kamarsa ba.
Suna dawowa aka kafa tantuna a haraban gida domin zaman makoki.
Hajiya kuma ta yi tawakkali tana zaune da hijabi da carbi ko hawayenta ba wanda ya gani Lokacin da aka tafi kai shi bayan Mommy ta farfaɗo ta fara surutai tana faɗin
“Habibi yace na nema masa gafara wajen Hajiya, Hajiya ki yafe masa ya rasu da niyar a yau mu je Gombe ya durkusa ya nemi gafaran ki, ke ma Mimi da ke ya rasu kina bakin shi faɗi yake yi Murjanatu ki yi min alkwarin yi ma Mimi duk abin da zai saka ta farinciki ciki har da neman yaron nan ku rokesa gafaran ya yafe min.”
Sai da Mama ta rufe mata baki sai sakin maganganu take yi kamar ba ta cikin hayyacinta.
Sai a lokacin Hajiya ta yi hawaye cikin kuka ta ce”Na yafe masa duk laifin da ya taɓamin da wanda ya sani da wanda bai sani ba, ina masa fatan salama da aminci da kuma dacewar wannan rana ta Jumma’a mai daraja Allah ya jiƙan ka Kabiru”.
Sai Hajiya ta fashe da kukan da take ta rikewa Mimi ta koma jikinta ta kwanta suka haɗe suna ta gunjin kuka. Mommy faɗi kawai take yi” Habibi ya rasu? Ni murja ina zan sa ka kaina a gabana fa ya rasu Allah ya jiƙan ka Habibi.”
Ƙanwarta Zainabu ta ce”Ki daina kiransa da wani suna in ba sunan shi ba mala’iku da sunan shi suka san shi ba Habibi ba, ai yanzu wani Habibi ya kare Murja gafaran Ubangiji zaki yi ta neman masa shi ne kawai gata da Soyayyar da za ki nuna masa”
In ka kalli Ahalin nan sai ka tausaya musu, duk da yanayin Abi amman fa tsayayyen Uba ne mai yin komai saboda ƴayan shi, shi ya gina su har su ka kawo matsayin da suke a lokacin kowacce ka gani ido ya Kumbura murya ta dishe saboda kuka,
Mutanen arziki daga ko’ina sun zo musu gaisuwa daga Gombe Rukky tare da Salim Bunza da Na Misau da wasu daga cikin ma’aikatansu da aka wakilta ranar biyu sun zo musu gaisuwa, Rukky ma nan ta kwana sai ranar uku ta koma Gombe ita ma Khadi abokan aikinta da na mijinta duk sun zo musu gaisuwa haka Dr. Sulaiman sannan Jawahir ma yan’uwanta suna ta zuwa.Haka dangin Mommy su ma sun yi mata kara kwarai da gaake.
Ana ta zaman gaisuwa manyan manyan mutane nata zuwa gaisuwa su kuma shiga har cikin gida su yi ma Mommy gaisuwa wacce ta za ma abun tausayi.
Mimi ta samu wayoyin mutanen da ba ta san wasu ba ma, a rana ba ta san adadin masu kira su yi mata gaisuwa ba, kaf ma’aikantan su har da masu Inten ba’a bar su a baya ba. Sannan ba ta yi tunanin za ta samu kiran wayar su Nasir ba.
Sai ga shi Mu’azzam ne ya fara kiranta ya yi mata gaisuwa ya ce a kafafen sada zumunta ya gani sai kuma da ga baya Usman ke faɗa masa, sannan Usman ya kirata Ahmad ma tare da Nasir sun yi mata gaisuwa kuma ta ji daɗii kwarai. Sai dai Aji bai kirata ba kuma tana da tabbacin ya sani rashi fa ta yi rashin kuma na Mahaifi, tunda ta karɓi lambarsa ba ta samun kwarin gwiwan kiransa ba. Sai ta ce bari ta gani zai iya yi mata gaisuwa?. Sai ta ɗauki wayarta ta tura masa sako.
“Aji Nah Abi ne ya rasu yau kwana biyar.”
Mimi ce Fatima”
Ita kanta ta san bazai taɓa mata gaisuwa ba, tunda ya kasa mantawa da abin da ya faru a baya, abunda ba ta sani ba tun a ranar yaji rasuwar domin a daren ya je gaida Inna take gaya masa a cikin ransa ko a fili bai ce Allah ya jiƙansa ba.
Sai da Inna ta ce”Kanin ma mallam Hashimu shima ya rasu yau. Allah ya jiƙan su da Rahma.”
Ba saboda shi ya amsa ba sai Saboda ƙanin Mallam Hashimu amman yadda yake jin tsanar wannan mutumin ba zai iya nema masa jinƙai wajen ubangiji ba, ba domin ya na musulmi ba da sai yace Allah ya kara nauyin kasa.
Kuma Mu’azzam ya kira sa ya gaya masa ya ce to ina ruwan sa? Bayan nan har Makama sai da ya kirasa yana gaya masa ya yi tsaki ya kashe wayarsa ya rasa waye ne baban Mimi a wajensu da suka damu da Mutuwarsa. Nasir ne da ya kirasa sai da suka yi faɗa kamar abun arziki Nasir ya ce”Ya ƙarin haƙurin mu kuma Aji?
Aji ya ce”Ni babana ya ji ma da rasuwa, Innata kuma da ranta sannan Babana uban riƙo na yana cikin koshin lafiya.”
Nasir ya yi dariya kafin ya ce” Gaisuwan Major mana baban Mimi, ya kamata ka kirata ka yi mata gaisuwa sanda na kirata sai da ta tambaye ni ka sani kuwa?
A fusace Aji ya ce”Nasir ba domin kai ba ne wallahi da sai na zage ka, kada ku ƙara kirana da irin wannan shirmen na ku”
Nasir ya ce”Aji rasuwa fa aka yi? mutuwa ce fa” ƙaramin tsaki ya ja kafin ya ce”ka bari in ka mutu in ta kirani ta min gaisuwa sai na haɗa na yi mata a lokacin.”
Daga haka katse wayarsa ya bar Nasir da sakin baki, Kuma a daran ta turo masa saƙo. Mamaki ya kama shi wato kenan sun ba ta lambar sa kenan.
Goge saƙon ya yi ya kuma ɗauki lambar ya saka ta a blacklist duk abunda zai haɗasa da abin da zai hana shi barci yana kokarin yin nesa da shi. Ko alama bai ji tausayinta domin wai ta rasa mahaifinta ba, shi a tunaninsa wannan in ya rasu ma abun murna an rage mugun iri a kasa ne, sauran kaɗan ya maida mata amsa da cewa Allah yasa kasa ta kara danne shi sai kuma ya fasa shuru ma ai amsa ce ga mai hankali.
Page 17
Kimanin sati uku kenan da rasuwar Major Kabir Sulaiman Dabo, zukata sun fara ɗaukan dangana tuni baki na nesa da na kusa sun gama zaman makoki sun koma gidajen su. Ciki harda Dr. Sulaiman da iyalansa sai Madiha wanda daman mijinta ana yin bakwai ya koma da yara ita kuma sai da akayi kwana goma sannan ta koma.
Khadija kuma sati biyu ta yi sannan itama ta koma, itama dai kamar mijin Madiha ranar bakwai mijinta ya koma tare da yara, sai a ka bar Mimi da Hajiya sai Inna Zainaba sai kuma Inna Ladidi wacce take autarsu mahaifiyar Mommy mai rasuwa ita kaɗai ta rage musu a raye a ɗakin su.
Hatta iyalan Alhaji Hamza sun dawo Gombe Hajiya kuma da Mimi sai da aka yi sati uku sannan suka yi shirin dawowa saboda ita Mimi aikinta, ita kuma Hajiya saboda makota suna ta zuwa mata gaisuwa ba ta nan. Mommy dai ta ɗauki dangana amman fa sai ana yi ana lallashi duk sanda ta tuna sai kuka rana ba ta taɓa fitowa ta faɗi ba tare da ta tuna da yau ta yi rashin miji ba. Ranar da su Hajiya su ka koma sai mutuwar ta dawo musu sabuwa Hajiya ta yi kuka, kukan da ba ta yi ba lokacin da aka yi mutuwar sai yanzu Mimi ma kamar ita kaɗai aka yi ma mutuwar duk ta rame kamar ba ita ba, itama ta kasa gasgasta yau babu Abi gani take yi kamar in ta shiga Bedroom din Mommy za ta ganshi. Sai dai ina wanda ya mutu ba ya dawowa tafiya ce ta har abada sai dai fatan Allah ya haɗamu a darussalam.
Mommy ma ai ta ga kara daga abokan aikinta Saboda macece mai kirki da fara’a ita Mimi ta ɗauko wajen fara’a da iya mu’amala. Haka su Hajiya suka dawo suka bar Mommy cikin kewa Allah yasa ma ga Inna Zainabu da Inna Ladidi, ita dai Inna Zainabu ana yin arba’in za ta koma kano Inna Ladidin ne za ta zauna da Mommy har ta fita takaba. Tun da suka dawo daga Abuja yan anguwa da makota su ka ji Labarin Hajiya ta dawo a ke ta shigowa yi mata gaisuwa daga bangaran abokan siyasar Daddy ma suna ta zuwa waɗanda ba su samu zuwa can Abujan ba, har da yan’uwan su Anty da Mama da suma ba su samu zuwa can ba duk jin Hajiya ta dawo ya sa suke ta zuwa yi mata gaisuwa tare da yan’uwan mijin Yaddiko da sauran mazajen ya’yanta da ba su zuwa can Abuja ba, daman ita saboda ba ta jin daɗi kwana takwas ta yi ta biyo Alhaji Hamza suka dawo gida.
Ita Mimi ana zuwa mata gaisuwa daga wajen aikinta harda wasu mutanen da ba ta taɓa sani ba kiranta kawai a ke yi ace ta ba da address, ita kam ai ta ga kara kuma har acikin ranta taji daɗii Rukayya kaf da iyayenta sun zo mata gaisuwa har Bibi sun zo tare da Usman kamar ta yi masa maganar Aji amman sai ta fasa. Saboda ta na da tabbacin ya ji labarin babu amfani ta ci gaba da bibiyar ya sani ko bai sani ba tunda ita da ta tura masa sako da hannunta tana da tabbacin ya sani. Tun da suka dawo ba ta koma ma wajen aiki ba so take yi sai ta samu yar natsuwa.
A halin da ta ke jin zuciyarta a lokacin ba za ta iya samun wani sukunin komawa wajen aiki ba. Sai dai ta yi ta kwanciya a gida da kumburarrun idanuwana ba ta da aiki sai tunani Hajiya kuma kullum da carbi tana falo ita da Baaba Uwani, ita da ba ta nan ma aka yi rasuwar ta je kumo.
Hajiya ce ta koma ma lallashin Mimi in ta ganta cikin damuwa ta kan ce ma ta”Binta ba kuka ko damuwa Kabiru ke bukata yanzu daga garemu ba, addu’armu ita ya fi bukata shi ya sa na ce gwara ki koma wajen aiki zai rage miki zaman kaɗaici da tunane tunanen rayuwa.”
Jin Hajiya kawai ta ke yi ai ita duniyarta cike take da abun tunani saboda haka ya zame mata dole ta yi kuka sannan kuma ta yi tunani. Ko bayan dawowarsu Mu’azzam ya sake kiranta ya yi mata gaisuwa sai take gaya masa sun baro Abuja suna gida ita da Hajiya, nan ya yi mata alkwarin zuwa ya yi mata gaisuwa in sha Allahu in ya shigo garin. Yadda ba ta yi ma Makama maganar Aji ba shima ba ta yi masa ba, ita a tunanin nutuwa ta kore komai, abin da ba ta sani ba mutuwa ba ta kore ko da kankanin tsanar da Aji ya yi ma mahaifinta ba.
**
Saturday 27 March, 2022
GRA.
11:16am.
Yau gidan Hajiya na cike da baki ƴaƴan Yaddiko guda biyu mata da ƴaƴans suka kara zuwa yi ma Hajiya haisuwa, sai kuma baki daga can kumo suma mota guda da suka zo yi ma Hajiya gaisuwa.
Mimi na cikin ɗaki tare da Rukky da ta zo ɗazu daga wajen aiki Hajiya na falo tare da baƙinta, kamar ita take yin takaban ko da yaushe da hijabi da carbi.
A dai dai lokacin Inna Meri tare da Bintu da Walida sai yan biyun Bintu Hassan da Husaini suka shigo gidan, kuma har a ran Inna Meri sai da ta ce gidan ya na nan a yadda ta san shi sai dai ya samu gyare gyare da ba’a rasa ba. Da ya ke tun a baya ta san kan gidan ita ce a gaba suna bin ta a baya har cikin falon Hajiya da farko Hajiya ba ta gane Inna Meri ba saboda yanzu jikinta ba wahala tana samun hutu da jin daɗin rayuwa.
Sai bayan da ta yi mata gaisuwa ta ga ba ta gane ta ba sai ta gyara zama tana mirmishi kafin ta ce”Ba ki gane ni ba ko Hajiya?.
Hajiya ta kalli Inna Meri da kyau kafin ta yi salati ta dire tana faɗin “Kai jama’a kada ki ce min Meri ce maman baban inna.”
Inna Meri na dariya ta ce”Ni ce Hajiya.”
Nan fa Hajiya ta rasa ina za ta saka kanta saboda farinciki, bakinta yaki rufuwa ta rike hannayen Inna Meri duka biyu tana fadin”Allah Sarki Meri ashe rai zai kara ganin rai? Ki yi hakuri Meri kunya da nauyi sun hanani na kara neman ki, ki yafeni”
Ta faɗa lokaci ɗaya tana yi kamar ta fashe da kuka da sauri Inna Meri ta ce”Haba Hajiya bakomai, nima ki yafemin ai nima ban kara neman ki ba ookacin ina cikin ruɗu ne shi ya sa amman naji rasuwar a gidan tibi kuma jiya ɗan Inna da muka yi waya yake faɗamin kun dawo nace daman na yi alkwarin sai na zo na yi miki gaisuwa in sha Allahu”
Hajiya ta ji daɗi har cikin ranta sai mirmishi take yi Walida da Binta da kalla kafin ta ce” Meri kada dai kice min yan matan nan naki ne suka girma haka?
Bintu ce ta fara sakin dariya ta rufe fuska kafin ta ce”Hajiya Bintu ce fa, ga Walida.”
Ta faɗa ta na nuna Walida Hajiya ta rike baki cikin mamaki kafin ta ce”Ikon Rabbi. Bintu ke ce haka? Sai kuma ta kalli Walida lokaci ɗaya ta na faɗin”Ba shakka shekarun da yawa Walida an zama yan mata, to waɗannan yaran fa?
Inna Meri ta tura mata su Husaaini gabanta tana fadin”Jikokin ki ne Hajiya, yaran wajen Bintu ne yan biyu ne ga su nan Hassan da Husaini.”
Hajiya ta riƙesu kusa da ita ta na faɗin”Ba shakka , yara nan Allah ya raya ku kun ji ko?
Ta fada ta na shafa kawunan su duka biyu, su kuma suna ta kallonta.
Kara gaisawa suka yi Inna Meri ta kara yi mata gaisuwa Hajiya ta ce”Uhm ke dai bari Meri Kabiru ashe ba’a deɓo da yawa ba.”
Inna Meri ta ce”Allah ya sa an huta Allah ya kyautata tamu bayan ta su.”.
Hajiya ta yi ta amsa da Amin Amin, ganin mutane sun yi yawa a falon ya sa Hajiya ta kalli Inna Meri lokaci daya tana faɗin”Meri ko za ku shiga ciki ku jirani na sallami baki na? Daman ina neman ki kuma ko ke ba ki neme ni ba wannan karon ni zan neme ki.” Inna Meri ta yi mirmishi kafin ta ce”To bakomai Hajiya, Ina Binta ne? Ina so itama na yi mata gaisuwa su Bintu ma suna son su ma su yi mata gaisuwa.”
Hajiya ta ce bari ta saka a kaisu ɗakin Binta
Baaba Uwani da ke kitchen ta ƙwalama Kira ta na zuwa tace ta raka su Inna Meri ɗakin Binta itama ga ta nan zuwa duk da ita Baaba Uwanin ba ta taɓa ganin Inna Meri ba tunda lokacin da ta zo gidan tuni Inna Meri ta daina zuwa shi ya sa ba su san juna ba Amman da Hajiya ta ambaci Meri sai da ta so ta ɗauki sauna tunda in dai suna hiira da Hajiya tana yawan ambaton sunan Meri din da kuma irin kyautatawar da ta yi mata lokacin da ta yi aiki a gidanta.
Har ɗakin Mimi Baaba Uwani ta raka su, Mimi na kwance saman gadonta da ya sha shimfiɗar alfarma da kyakyawan zanin gado na kamfanin FHB CLOTHING Phone no 08034109622
Wtsapp no.08080266674 Zannuwan gadon su masu kyau ne da inganci ka daɗe kana mora kamar yau ka siye shi.
Ta yi kwamciyar ruf da ciki Rukky ne ke zaune a gefen gadon tana laatsa wayarta jefi jefi suna hira da Mimin da ba’a jin muryanta sanda ma Baaba Uwani ta shigo ta ce baƙi ne Hajiya ta ce a shigo da su Mimin ba ta iya tashi zaune ba a tunaninta tunda ta ji Hajiya ta ce a shigo da su har cikin ɗakinta sai ta yi tunanin kila bakin na gida ne.
Dukkansu a tsaye suka tsaya tunda mai ɗakin ba ta ko tashi ba, Rukky ce ta kallesu lokaci ɗaya tana faɗin ” Sannun ku, Mimi ki tashi an zo miki gaisuwa.”
Sai Mimi ta yunkura ta mike tana gyara zaman rigan jikinta wata doguwa mai ruwan hoda kanta ba ɗankwali tunda daman hula ce ta kuma saɓule kanta, har ga Allah ba ta gane Inna Meri da farko kamar Hajiya ba, ta ji sanda ta yi mata sannu sai ta ce cikin dashewar murya”Ku kariso ku zauna mana, Rukky hayo gadon ki ba su waje” Sai Inna Meri ta ce”Bari mu zauna anan ya isa.” Ta faɗa tana zama saman cafet din da ke makeken bedroom din Mimi. A cikin ran Inna Meri tana faɗin an sauya komai na ɗakin da ba haka ta san shi ba yanzu ko cike yake da kayan alatu na more rayuwa kamar ba ɗakin budurwa ba, to budurwa ce yar gata wacce ta san kanta Dole ɗakinta ya kasance abun kallo haka Bintu ke ta sakawa a cikin ranta nan da nan taji makeken gadon Mimi ya gama tafiya da Imaninta taji kamar ita ce ita, a cikin ranta taji in sha Allahu sai ta yi irin gadon nan itama.
Inna Meri ta san Mimi ba ta gane ta ba har suka yi mata gaisuwa kuma har su Bintu ba ta gane ba, ta dai kallesu kamar tana so ta ji ta san fuskarsu amman halin da take ciki ya hana ta tsayawa ta gane su, sai ta koma ta kishigiɗa kawai tana jin Rukky na faɗin”An zo miki gaisuwa kina ta kwanciya kuma? Cikin wani yanayi ta ce”Na amsa su Rukky ki barni kaina ke ciwo.”
Inna Meri ta bi Mimi da kallo wato a kwalban nan ta zamani ana rage mata ma kyau a fili tafi haka kyau da hasken fata.
Inna Meri ganin kawar Mimi na ta kallonsu ga su Hassan sun fara kiriniya ya sa ta ce”Hajiya ta ce mu jira ta gata nan zuwa.”
Sai Mimi ta muskuta kafin ta ce”Laa bakomai ku jira ta ɗin.” Sai ta koma tana kallon yan biyun Bintu da suke neman yin wasa Walida ta yi musu jan ido, sai suka burgeta da ganinsu yan biyu ne kuma ma su kama sosai sannan sun ci gayunsu da kaya iri ɗaya.
Rukky ma su take kallo acikin ranta ta ji ta na sha’awar yan biyu, amman wahalansu ne ke ba ma mutane tsoro Walida kuma Bintu ta ke yi ma raɗa da cewa”Gaskiya Anty Mimi ta fi kyau a fili.”
Bintu ta yi dariya kafin ta ce”Gaskiya kam.”
Dai dai Lokacin da Hassan ya ture Hussaini ya kusa faɗuwa sai da Rukky ta mike ta rike shi da Sauri Bintu ta daka ma Hassan tsawa Lokaci daya tana faɗin”Kai ba na son mugunta, in ka turesa ya ji rauni fa?
Kawai sai ya saka kuka Inna Meri ta kirasa da hannu tana faɗin “Taho nan kyale Mamanka kai da kake da ni ina kai ina kuka Megidana”. Take faɗa tana masa dariya jikinta ko ya zo ya lafe yana sharen kwallah Hussaini kuma na ganin haka shima sai ya kwace daga rikon Rukky ya dawo ya kwanto a jikin Inna Meri wai shima sai an ɗauke shi.
Rukky ta fashe da dariya Mimi na taya ta ganin Inna Meri ta haɗa duka ta ɗauka saman jikinta tana faɗin “Ya na iya? Ni mai mazaje har guda biyu.”
Rukky ta koma ta zauna tana faɗin “Ina jin ana yawan labarin suna da kishi sai yau na gani, wace ce mamansu hala.?
Ta faɗa ta na kallon su Bintu sai Walida ta nuna ta, Rukky ta ce”Ma sha Allah Allah ya raya miki su, Sun samu jikin kaka sun yi luf Allah dai ya kara tsawon kwana.”
Kafin Inna ta samu zarafin Magana Hajiya ta shigo dakin ganin su Inna Meri zaune a kasa ya sa ta kalli Mimi tana faɗin”Ba ki gane su ba ne hala Binta?
Mimi da kanta ke Sara mata ta dafe shi tana yamutsa fuska kafin ta yi mgana Hajiya ta yi saurin cewa”inna Meri ce fa, tare da Bintu da Walida fa, ni kaina ban ganeta da farko ba sai daga baya.”
Mimi ta yi kasaƙe tana kama sunan da Hajiya ta ambata ai sai ga ta ta zaro ido da sauri ta diro daga kan gadon ta tsaya kan kafafunta tana kallon Inna Meri da su Bintu sai a lokacin ta shaida su ɗazun ba ta wani kallesu sosai ba duk da dai suka sauya mata gaskiya, kunya ta kamata Inna Meri na yar dariya ta ce”Shekarun da yawa Hajiya ba lalle ta shaidamu kai tsaye ba.”
Jikin Mimi sai ya fara rawa sai ta rarumi mayafin Rukky ta saka sai gata gaban Inna Meri ta durkusa tana faɗin”Inna Meri ki yi hakuri wlh ban gane ki ba ne”
Inna Meri ta yi mirmishi kafin ta ce”Bakomai Binta ya ƙarin hakuri kuma? Allah ya jikansa da Rahma.”. Mimi ta amsa kanta na kasa tana jin wani irin kunya na kamata. Mamaki ya kama Rukky ta kalli Hajiya tana so ta yi mgana sai ta fasa jin Mimi na faɗin”Bintu. lalle Bintu an zama uwa ke ce haka?.
Bintu ta saka dariya kafin ta ce” Auran wuri su Inna su ka yi min, amman har gobe Bintu na nan da yan matan cinta.”
Ba Mimi ba har Hajiya da Rukky sai da su ka yi dariya, Mimi ta ce”Kai Bintu kina nan dai da halin ki” inna ta ce”Wannan ai ba za ta taɓa sauyawa ba.”
Mimi tace”Walida an zama yan mata Eyee, Ina su Yaya Amina da Yaya Halima?
Walida tace” Suna gidajen su, da Inna ta ce zata aika musu su zo mu zo nan gaisuwa tare sai kuma ta sha’afa.”
Mimi ta kaɗaa kai kafin ta ce”Allah Sarki ki ce don Allah ina gaishe su.”
Walida ta amsa ma ta da in sha Allahu za ta gaya musu , Yan biyun Bintu Mimi ta kira abun mamaki ba su yi mata kiyuwa ba, Hajiya kuma ta kara ficewa ta ce bari ta sallami bakin Kumo za su tafi.
Rukky kuma ta ga Mimi ta manta da ita sai hiran ta ta ke yi, amman tun ɗazu da ta zo kwance ta yi mata tana mgana dakyar ba ta kawo komai ba ta ɗauka kila cikin yan’uwansu ne, ganin haka ya sa ta yi shirin tafiya tace Mimi ta ba ta mayafinta za ta wuce gida. Sai ta ba ta nata ta ɗauko wani karamin hijabinta iya gwiwa ta saka ta ce ma su Inna Meri bari ta raka kawarta, su ma su ka yi sallama da Rukky har 500 500 hundred ta ba ma su Hassan su ka karɓa suna faɗin sun gode ko domin hararan da suke sha a wajen uwar ta su.
Sai da su ka fito haraban gidan sannan Rukky ta kalli Mimi kafin ta ce”Wai su waye waɗanan da kina ganinsu kika mike tsaye? Ko ƴan’uwan ku ne? Mimi ta yi mirmishi kafin ta ce” Surukata ne da ƙannen saurayina.” Rukky ta saki baki tana kallonta kafin can ta ce”U Mean maman Aji ne da ƙannensa?
Mimi ta lumshe ido jin sunan rabin ranta da aka kira kafin ta buɗe su akan na Rukky sannan ta jinjina mata kai alamun hakane.
Rukky ta riƙe baki ta ce”Ikon Allah dalilin mutuwa yau sai ga shi sun zo, ko da yake ai kin ce ƙaninsa ɗin nan ya yi miki gaisuwa da sauran abokan su Usman to shi baƙin masifaffan Ajin ya kira ki ya yi miki gaisuwan kuwa? na ga mahaifiyarsa da ƙannensa babu ruwansu amman shi kam wlh ba shi da mutumci ai ko Allah ma gafurin Rahimunun ballantana shi ɗan Adam ba kowa ba.”
Mimi ta rausayar da kai kafin ta juya tana faɗin” Sai anjuma Rukky ki gaida Mama.”
Rukky ta taɓe baki tana faɗin “Uhm Mimi Allah ya yaye miki wannan makahon son da kike yi ma wannan gayen.”
Mimi na jin ta amman ba ta tsaya ba ta yi shigewarta cikin gida, itama Rukky ta juya ta fice daga gidan ta na tunanin ita ba ta ga abulin da zai saka har a wannan lokacin Mimi ba ta daina son wannan masifaffan gayen ba, ga bakin fuska ga bakin rai da faɗin rai Allah dai ya sauwake.
Ko da Mimi ta koma a falo ta tsaya saboda Anty Sadiya babbar ɗiyar yaddiko ta ja ta da hira daga ita har Hajiya ba su samu kansu ba sai da bakin Kumo suka tafi sannan su ma su Anty Sadiya suka tafi.
Sannan Hajiya ta koma wajen Inna Meri Baaba Uwani ta sako abinci sai Hajiya ta saka a kai ma Inna Meri na ta a ɗakin Hajiyar daman tana so su yi mgana, Hajiya dai ta saka a gidan su ka yi sallar azahar kuma ta matsa ma Inna Meri sai da ta ci abincin da aka kawo mata.
Lokacin da ta ce a ƙoshe take sai da Hajiya ta ce mata” Nan fa gida ne Meri, kar ki manta har abincin nakan saka ki ɗaukan ma yara kada rayuwa ta sa ki sauyamin don Allah.” Jin haka ya sa ta saki jiki ta ci doya da miyar ƙwai ɗin da Baaba Uwani ta yi bayan ta gama ta sha ruwa. Hajiya ta zaunar da ita su ka fara labarin bayan rabuwa da rayuwa.
Hajiya ta kalli Inna Meri tana faɗin “Meri ina ɗan Inna? Ina shi Baban Inna? Ina fatan duk suna nan lafiya”
Inna Meri tace”Suna nan lafiya, ɗan inna na kano yana aiki ɗan Sanda ne yanzu. Ya yi aure da matarsa Hibba da ɗansu mai sunan Mallam, Baban Inna dai bai yi aure ba yana nan yana buga ƙwallon kafa auren dai har yanzu lokaci bai yi ba.”
Hajiya tace”Allah Sarki haka Binta ta gaya min kila ki kinsan kwanaki sun haɗu wajen bikin ƙanwar ƙawarta ɗin nan Rukayya da ta fita ko?
Inna Meri tace” Ɗan Inna ya gaya min kinsan dai uban gayyar ba zai taɓa faɗa min ba.”
Hajiya na dariya ta ce”Ikon Allah Mansoor manya hali dai na nan an girman ma ba’a daina ba.”
Inna Meri ta yi wani mirmishi kafin ta ce” Wasu abubuwan sun ragu amman wasu kam kamar an kara ingiza su ne, fatan mu dai Allah ya shirya mana gabaɗaya.”
Hajiya ta amsa da Amin Amin, tana so ta dauko mganar amman kuma kunya da nauyi sun hana ta fara maganar sai kame kame take yi. Dakyar ta iya karfin halin cewa” Meri ki yafe ni don girman Allah ni nasan mai laifi ce a gare ki tun akan abin da ya faru a baya”
Inna Meri ta yi saurin cewa” Ba komai Hajiya ni ban rike ki a raina ba, ko yanke hulɗa da na yi dake na yi hakan ne saboda samun mafita ba domin ina jin haushin ki acikin raina ba.”
Sai kawai Hajiya ta fashe da kuka cikin kukan take faɗin “Wlh Allah ɗaya ko Meri tun bayan abib da ya faru yaro nan Mansoor ke raina ina ta so na zo na duba shi amman kunya da nauyi suka hana ni, har ga Allah ban san abunda Kabiru ya shirya ba kenan da ban yarda na tura su wajensa ba, ki yafe min shima Kabirun ku yafe masa Wallahi tallahi kafin rauwarsa ya yi nadaman abin da ya aikata muku.”
nna Meri ta riƙe hannayen Hajiya da sauri tana faɗin ” Da gaske na ke Hajiya ban riƙe ki a raina ba wlh, kuma komai ya wuce tun a wanchan lokaci maganar kuma wanda ya rasu ai ba komai tsakanimu sai fatan Allah ya sa ya huta.”
Hajiya na jan majina ta ce”Amin Amin Meri na gode. Wlh ina gaya miki ana gobe za su taho nan shi da Murja a daran ya rasu, kuma da niyar yazo ya roke ku gafara tare da neman afuwan Mansoor sai dai Allah bai nufa ba, bai wayi gari da rai ba.”
Inna Meri ta hi tausayin Hajiya Itama kamar ta yi kuka ta ce”Allah Sarki ai Allah ya ga niyarsa, bakomai wlh Allah ya jiƙan sa da Rahma daman can Allah ya kaddara sai hakan ya faru.”
Hajiya ta saki hannun Inna Meri ta na tsane hawayenta da hannu ta ce” Kabiru ya rasu da sunan Binta a bakinsa ya na matukar tausaya mata tun bayan abin da ya faru Binta ba ta kara ba ma wani namiji dama ba, da gaske ya ke yi kafin rasuwarsa Murja ta ce ya ce har azumin kaffara zai yi in har Mimi na son Mansoor har yanzu to shi ya saki ya kuma ba ma Mimi dukkan daman rayuwa da wanda take so.”
Hajiya ta karishe faɗa tana kallon yanayin Inna Meri wacce ta yi jim kaɗan tana nazari, ita fa ta ga ya ma Hajiya komai ya wuce Baban Bintu ma haka amman babban matsalan shi ne uban tafiyar duk da itama za ta iya rantsuwa ta ba da shaidan har gobe ya na son Binta kuma dalilinta ne yaki ba ma rayuwarsa haske ko kaɗan sai dai in ina ita ina taran Baban inna da wannan maganar? Ai wannan bakar zuciyar tasa kamar ta kafuran farko ba za ta barshi ya baiwa zuciyarsa abin da take so ba.
“Kin yi shuru Meri, ko kina ganin da matsala ne?
Hajiya ta faɗa ta na kallon Inna Meri, ita kuma sai ta rausayar da kai kafin Ta ce” Hajiya da gaske nake yi da nace komai ya wuce kuma har abada bazan ƙi Binta a matsayin Surukata ba, sai dai abu ɗaya ne matsalan Baban Inna a gaban ku ya yi rantsuwan ko zai mutu bai yi aure ba ba zai iya auranta ba, Hajiya kin san wasu daga cikin hallayarsa kafiya da naci ga zuciya da riko har gobe Baban Inna ya kasa manta abunda ya faru tun daga lokacin rayuwarsa ta sauya ya daina shiga mutane ya koma rayuwa shi kaɗai, ya daina nuna ya na jin daɗin duniyar nan ma Hajiya mun yi mun yi akan ya daina tuna baya ya fuskanci gaba amman har gobe ya kasa gina ma kansa wata rayuwar, kina ganin a wannan halin da ya ke ciki zai karɓi maganar Binta a karo na biyu.?
Inna Meri ta karishe faɗa tana kallon Hajiya itama sai ta kalleta cikin tunani da nazari, Inna Meri ta yi ajiyar zuciya kafin ta ce”Shi ne hanzarina Hajiya, da kamar wuya gurguwa da auren nesa wannan zuciyar ta Baban Inna ni kaina ta na bani tsoro bansan adadin sallar daren da na yi a kan sa ba, ina rokon Allah ya ya ye masa wannan bakar zuciyar ko ya samu shima ya yi rayuwa irin ta kowa” Yadda Inna Meri ta karishe a raunane ya sa Hajiya taji itama jikinta ya yi sanyi sai ta kasa mgana.
Illah kai da ta kaɗa tana faɗin “Kafin rasuwar Kabiru Murja ta jaddaddamin ya ce a yi ma Binta duk abunda ta ke so, ni kuma nan duniya ban ga abunda Binta ta jima ta na so da kauna tare da bege irin Mansoor ba.”
inna Meri ta ce”Ikon Allah! A cikin ranta kuma sai tace ai shima har gobe bai daina begenta ba, Hajiya duk sai gwiwanta ya yi sanyi sai dai ta cigaba da gaya ma Inna Meri irin wasiyar da Kabiru ya bari kafin ya rasu har acikin ran Inna Meri ta tausaya kuma ita ba ta da matsala mai yin shine matsalan da kansa. Sai ga Inna Meri sai a’asar su ka bar gidan Hajiya shima Baban Inna ke ta faman kiran wayar Inna Walida ta ɗauka cikin muryansa ta koda yaushe ya ce”Ina Innar ? Lokacin tana ɗakin Hajiya sai ta yi masa ƙaryan tana sallah.
Cikin yanayin maganarsa Ya ce”Ina kuka je na zo bakwa nan gabaɗaya.?
Sai Walida ta rasa bakin mgana Binta na yi mata raɗan ta ce sun je gaisuwa dakyar ta iya ce masa suna cikin gari sun raka Inna gaisuwa amman ga su nan zuwa.
Lokacin Mimi na ɗakin amman hankalinta na kan waya ne, Walida na sauke wayar Bintu ta ce”Da kin sake kin gaya masa in da mu ka je da yau sai yayi biji biji dake.”
Walida tace”Ina sane shi ya sa na rasa abin da zan ce.”
Allah ya taimaka sai ga Inna Merin ta ce su zo su tafi, Hajiya ta ji daɗi ita da Mimi har bakin get suka rakasu Hajiya na jadaddama Inna Meri sai ta zo da kanta har gida in sha Allahu. Sai a hanya ne suke faɗama Inna Meri Baban Inna ya kira.
Cikin faɗuwar gaba ta ce”Allah ya sa dai ba ku ga ya ma sa in da mu ka zo ba ko?.
Bintu ta ce”Wa zai je ya yi karo da Kura? Ce ma sa walida ta yi muna cikin gari gaisuwa.”
Inna Meri ta ce”To gwara hakan, ba na son fitinarsa da yamman nan.”
Adaidaita suka hau saboda su Hassan suna zuwa Kofar gidan Wanzamai suka ci karo da shi tare da Baba Danjuma sun fito sallah. Suna ko ƙarisowa wajen su su Bintu na rige rigen gaishe da Mansoor ita da Walida sau ɗaya ya amsa, yana sanye da riga da wando baki da fari a jikinsa. Kansa da Pcap kamar ko da yaushe.
Shi Baba Danjuma bai san Mansoor bai san inda su Inna suka je ba kawai sai ya kalli Inna yana faɗin”Na ga kun jima ne? Ko Hajiyar ce ta tsaida ku? Inna Meri ba ta kawo zai iya cewa wani abu ba kawai sai ta ce”Eh wlh shiyasa mu ka jima.” Mansoor ke yi ma Inna barka da zuwa, Sai kawai Baba Ɗanjuma ya kallesa yana faɗin”Daga gidan Marigayi sulaiman Dabo su ke, da yake Mu’azzamu ya yi waya da ita Innar taku ya ce sun dawo shi ne ta ce za ta je ta yi musu gaisuwa na ce hakan na da kyau an yi zaman amana a baya Allah dai ya jikan sa.”
Ba su Bintu kaɗai suka tsure ba har Inna Meri, shi ko tun kafin Baba Ɗanjuma ya gama mgana sauran rahaman dake saman fuskarsa ta gushe bai kara mgana ba.
Inna Meri ta tasa jikokinta gaba za su shiga gida da sauri Bintu ta ce”Inna bari kawai mu wuce yamma ta yi”
Sai da dariya ta kusa kama walida wato ta san abin a zai biyo baya dole ta gudu in gari banza ne Bintu sai Inna ta yi mata jan ido take tafiya.
Ita kanta Inna Merin a sanyaye ta shiga gidan suna shiga da Magajiya suka fara cin karo, Mariya ba ta nan ta na gidan Zuwaira, Inna na yi mata sannu da gida dakyar ta amsa Ita walida ma wucewarta ta yi, ita kanta Innar yau ba tsaya bin Magajiyar kamar uwarta ba ta biyo bayan Walida.
Suna shiga ɗakin Walida ta juyo tana faɗin”Inna yau mun shige su mun yi ma Baban ki laifi”
Inna Meri na rataye hijabinta saman Kofa ta ce”An yi masa laifin sai ya zo ya dake ni.”
Innar ta faɗa a kufule sai Walida ta ja bakinta ta yi shuru ta yi ciki ita kuma Inna sai ta fara zuba ruwa a buta ta shiga ta kama ruwa daman Hajiya ta yi ta yi su tsaya su yi sallar la’asar Inna Meri ta ce sun sai sun isa gida. Ta fito kenan ta fara alwala sai gashi ya shigo da gif gif da ɗin tafiyarsa kafin ma ta ɗago kanta ta ji maganarsa a masifan ce a saman kanta.
“Inna fisabillahi me kuka je yi gidan nan?
Tana shafan kai ta ce”Gaisuwar mutuwa.”
Ta faɗa itama kai tsaye, wani abu ne ya ji ya taso mai cikin kokarin danne abun ya ce”Inna har za ki iya zuwa gaisuwar wannan mutumin?
Inna ta ce”Eh mana ai musulmi ne ɗan uwana ko?
Ta katse shi cikin gajiya da maganarsa zai kara mgana ta ɗaga masa hannu cikin kosawa kafin ta ce”Ka ga na je gaisuwa gidan maƙiyanka sai ka dakeni Mansoor haba don Allah, kai kenan shigen bakar zuciya ko a baya da ka ga na daina hulɗa da Hajiya wlh ba saboda abin da ya faru ba ne, saboda kai ne ba na so in dawo maka da abin da ya wuce ne amman ba domin tsoron fininarka ba.”
Ta faɗa kai tsaye kafin ta juya ta cigaba da wanke kafarta, shi kuma takaici ya hana shi mgana. Kirjinsa ke wani suya yana jin hucinsa na fita ta bakin hancinsa.
Sai kawai ya juya yana faɗin”Shike nan Inna ai shike nan kawai.”
Gif Gif kamar wani damisa haka ya juya ya fice Inna ta rakasa da harara Ina dalili da sanyin la’asar zai zo ya tada mata da hankali. Ta kuma san tunda ya fusata ya fita an yi yaji sai ranar da kuma aka huce.
Tsab ta idar da alolanta ta shiga ɗaki tana kiran sunan Walida wacce ta leko tana faɗin “Ya ta fi ne Inna?
Ƙaramin tsaki ta ja kafin ta ce” Lokacin sallah ya kure Walida ki fita zuwa alola.”
Daga haka ta shimfiɗa sallaya nan tsakar falon ta tada sallah.
Janafty
Page 18
Huci kawai ya ke saki shi kaɗai ransa in ya kai dubu ya ɓaci Inna ba ta kyauta masa ba, ba domin Baba Ɗanjuma ya ga fitowarsa ba, da anguwan zai bari dole ya yi alwala suka tafi masallaci tare ana idarwa saboda kada ma su Baba Sani su tare shi ya yi saurin tashi yana kara waya a kunne kamar yana waya Baba Ɗanjuma yana can yana musabaha da mutane Baba Sani da Baba Ɗanlami kuma ganinsa ya sa suke Allah Allah su fito domin su haɗu amman ko da suka fito ya bar haraban masallacin ma gabaɗaya.
Baba Sani ya jinjina kai kafin Ya ce
“Ɗanlami wai ka lura yaro nan yana gudun mu ne yanzu? Baba Danlami ya yi kayfci kafin ya ce”Wlh nima na lura, ka bar mutum kawai saboda kuɗin da yake ba mu ne duk wata sai ɗan taimako in ya taso, ba dole ya ganmu ya yi wucewarsa ba tunda ga yan maula.” Baba sani ya yi shuru kafin ya ce”Laifin duk na Yaya Ɗanjuma ne, in da amana muma fa muna da hakki akan dukiyar yaron nan tunda ai gidan uban mu aka riƙe shi, amma ya tattare komai ko nuna masa matsayin mu ba ya yi yadda ake ba ni labarin kuɗin yan ƙwallon kafa wlh zai iya kai mu saudiya ma sannan ya siya mana manyan gidaje a garin Abuja da motoci.”
Baba Ɗanlami sai da ya yi wata yar dariya kafin ya ce”Haba! to ai naga shi ma Yaya Ɗanjuma bai kai shi Saudiyan ba ma sannan bao sai siya masa mota ba, ya dai gyara gidan ya siya masa mashin itama tunda aka sace ai bai kara siya masa ba, kai ko uwarsa Meri ai ba kai saudiya ba mu kuma a suwa? Karan kaɗa miya.”
Baba Sani zai yi mgana kenan sai ga Baba Ɗanjuma ya zo wajen sai ya yi shuru hannu ya ba suka yi yi musabaha daman tunda ya gan su yasan da wata mgana.
Baba Ɗanlami ne ya fara faɗin.
“Yaya Danjuma gaskiya ka yi ma yaron nan Mansoor mgana, kamar mu zai gani ya rika wulakantawa? Baba Ɗanjuma ya yi saurin cewa”Anya? Ko dai bai gan ku ba ne?
Baba Sani ya ce” Zencen kake so, ya fa ganmu amma sai ya ɗauke kai ya yi wucewarsa in ma saboda ɗan abin da yake ba mu ne ya ke ganin kamar ya na yi mana alfarma gwara ka gaya masa gaskiya muma muna da hakki a kansa tunda ya tashi a ƙarkashin mu, duk tsiya dai a gidan Wanzamai ya tashi kuma da gidan zai yi tutiya yau ko saudiya ya kaimu bai biyamu rikon da mu ka yi masa ba ahto.”
Baba Ɗanlami ya ƙarishe da faɗin”Ka ji zencen gaskiya.” Baba Ɗanjuma bai yi mamaki ba sanin halin ƴan uwan nashi kamar waɗanda suka taɓa tsinana ma Mansoor ɗin wani abu suna ta kumfar baki, baya son nana ta mgana ɗaya ya sa ya ba su hakuri yace zai yi masa mgana.
Ashe korafin na su ba ɗaya ba ne nan take Baba Ɗanlami ya kalli Yayan na shi yana faɗin” Shi kuma Mu’azzamu dai ya manta damu? Ko wancan zuwa ma bai bari mun haɗu ba, ina ga ko ya yi saƙo iya kai da Meri saƙon ke zuwa gare ku, domin ba na jin ko Magajiya tana samun wani abu aciki.”
Sai alokacin ya buɗe musu ido cikin gargaɗi ya ce”Ko ni da na haifesu ban kwanta a gida na dogara da su ba, suma ai suna da na su uzurin rayuwar duk abin da kuka ga ba’a baku ba ba’a kawo ba ne, wani abun ma ba na sanin da shi ake ɗauka a baku ba yaran nan duka biyu daga Mu’azzamu har Mansoor ɗin ba sa yi min abu ba su yi muku ba ko da ɗinki ne na kaya domin ɗaya suke ɗaukan mu, kune da shigen zarge zarge da tsegumin ku da ya sa kuka kasa fahimtar komai ballantana ku godema Allah Bisa ni’imar da ubangiji ya yi muku.”
Yana gama faɗin haka ya yi wucewarsa ya bar su su na raka shi da harara Baba Sani har ya na kwaikwayon maganar Yayan na shi Baba Ɗanlami ya ce”Dankari! Mgana fa ya faɗa mana wato ba ma gode ma Allah kuma sannan mu zuciyarmu ta mutu sannan har da gorim mu ƴaƴanmu su yi mana ɗin ” Baba Sani ya yi tsaki kafin ya ce. “Kyaleshi akwai ranar maida martani.”
Suna tafe suna ta faɗin mganganu.Suna zagin ɗan uwansu uwa ɗaya uba ɗaya da suke tunanin ya samu duniya zai wulakantasu Ahalin duk tarin alherin da sanadin su Mu’azzam suke samu har gobe ba su gani ba Ƴaƴan na su kowa na fama da rayuwa wasu ma ga iyalai ba aikin yi, shi fa babban yaron Baba Sani Direba ne yau ya na da mota gobe bai da shi, bai da ma takamammen mai gidan da zai ba shi mota saboda tsabar rigime rigimensa, sauran mazan na shi kuma duk ba wani mai ƙwakwaran Sana’a sai Hayatu kaɗai da ya ke sana’ar fenti amman kuma shi kanshi ya sani da iyalansa ko kaɗan ba shi da zuciyan taimakon iyayayensa da ga shi sai matar shi sai ƴaƴansa dangin matarsa kawai da ita suke shanawarsu.
Sauran matan kuma suna gidajen mazajensu suna ji da kansu, wasu ma suna nema ne, shi ko Baba Ɗanlami duk wannan Kumfar bakin da ya ke yi ya na da ya’yan amman ba su iya taimakonsa da komai, tunda Abdurrahim ɗinsa ya na sana’ar sai da kayan wuta, sannan ƴarsa Bara’atu tana auran mai kuɗi sai dai irin makokan nan ne, ita kanta ba ta ci ba ballatana ta kawo gida. Amman ba’a taɓa jin suna mgana kan ƴa’ƴansu ko samu suka yi ba su taɓa nunawa a gani bar su dai ko da yaushe idanuwansu na kan Mu’azzam da Mansoor gani su ke yi kamar suna kawo ma Baba Ɗanjuma wani duniyar ne su ba ya ba su, ko kuma suna ware su ba sa ba su kuɗi tunda su gani suke yi wani duniya Mansoor da Mu’azzam suka tara.
Da bacin rai ya isa gidansa, daman kuma a mashin ɗin haya ya zo, motarsa ya kunna ta sai ta fara wani hayaki sai kawai ya barta sai ya kira bakanike mashin ɗin sa kuma ta yi kura sai ya kai wanki kuma yana jin kasalar zuwa sai kawai ya hau mashi ɗin haya zuwa can anguwar. Sai ga shi ya je ya ji abin da ya kusa saka shi kamar ya mutu saboda Haushi shiyasa ko jimawar da ya so ya yi bai yi ba ya yi tafiyarsa dalilin da yasa yana ganin su Baba Sani suna jiran sa kuma in ya tsaya a yadda ya ke jin ɓacin rai zai iya yi musu ba dai dai ba, in kuma ya yi musu mgana yana cikin fushi ya faɗi abunda bai dace ba sai su ji haushin shi shi ya sa ya yi tafiyarsa kawai.
Takaicinsa ɗaya wai Inna har da gayya ta yi na zuwa gidan to ina abun zuwa Allah ya jiƙan rai ga wanda ya kusa kashe miki ɗa Mu’azzam ya faɗo masa a rai daman ya san duk yana sane da duk abunda ke faruwa aiko sai ya ci masa mutumci. Sallar Isha’a a gida ma ya yi yunwa ya ke ji amman ɓacin ran da yake ciki ya hana shi ya sama ma kansa mafita. Mu’azzam ya doka ma kira ya na faman huci fushinsa tsab yake son ya huce a kansa.
Mu’azzam na tare da Matarsa Hibba suna yin Dinner sai ga kiran Mansoor ya ɗauka da zumuɗin sa sai dai zumuɗin ya koma ciki domin cikin faɗa da masifa Mansoor ya fara faɗin” Mu’azzam !Mu’azzam! Mu’azzam! Sau nawa na kira ka?
Yana jin haka ya san yau shi kuma sai ya sha masifa. Cikin sanyin murya ya ce.
“Sau uku.”
“To ka kiyayeni wlh in ba haka ba sai na ɓata maka rai, bar ganin kana da kaki, kakin ka banza ne ni awajena ba ka wuce ƙanina da nake yi ma hukunci in ya yi ba dai dai ba.”
Mu’azzam na shafa keyarsa yace”Me na yi ne yau kuma? Cikin kufuluwa Aji ya ce”Abunda ka san ka aikata ashe ba ka da kishin kai ban sani ba? Kai ne ka kira Inna ka na gaya mata wai su Mimi sun dawo ka sakata ta ɗauki su Walida suka tafi gidan wai sun je gaisuwa me ye haka? Me ye alaqar mu da su da har kake wani yaɗa sun dawo? Ba na son wawanci fa Mu’azzam ka sanni sarai.” Mu’azzam ya yi shuru ya rasa na cewa in ya yi mgana sai maganarsa ta yi zafi sai kawai ya zaɓi da ya yi shuru haka ya zauna sai da Mansoor ya gama masa masifa da faɗa sannan cikin ladabi ya ce”Allah ya baka hakuri ba da wata manufa na faɗa ma Innar ba, kuma har ga Allah ni ban ma san za ta je ba domin ba ta faɗa min ba.”
Mansoor ya yi ƙaramin tsaki kafin ya ce”Ni fa na daina yarda da kai, kai ma ka koma layinsu Nasir, nan ba har lambata ka ba ta ba? Mu’azzamu kada ka bari mu haɗu domin haɗuwarmu ba za ta yi mana kyau ni da kai ba.” Daga haka ya katse wayar ya bar shi sagale da ita a kunne kafin shima ya sauke yana faɗin”Ikon Allah!
Ajiyar zuciya ya sauke kawai ya Cigaba da cin abincinsa Hibba ba ta yi mgana ba tana fama da Junoir ne ma a lokacin to ita ai ba ta isa ba wannan faɗan tsakanin Yaya da ƙaninsane, sai dai in bai yi masa wani abun da ya baɓa masa rai ba haka zai kirashi ya yi mishi faɗa ko Inna da Baba albarka.
Har mamakin masifar Yaya Mansoor take yi, shi abu kaɗan a wajensa na faɗa ne. Tana ta nazarin mijin nata ya na cin abinci yana mirmishi shi kaɗai, cikin mirmishin itama Ta ce.
“Me ya faru ne.? Na ga kana ta mirmishi kai kaɗai”
Kai ya kaɗa kafin ya ce”Ina son yayana, na tabbata duk duniya ba wanda zai kai sa kaunata wani abu na tuna kawai da ya sa naji zuciyata ta yi sanyi. Fata na nima wata rana na saka shi farinciki kamar yadda yake sakani.” Ba ta matsa sai ta ji me ya tuna ba ta amsa da Amin Amin, sai da ya gama cin abincin sa sannan ya kira Inna bayan ta ɗauka sun gaisa ya faɗa mata yadda suka yi da yayan na shi cikin yar dariya Inna Meri ta ce”Kyale shi ɗan inna faɗan da ba zai iya yi min ba ne ya sauke maka, rabu da shi kada ya saurara ma kansa ya je bakar zuciyarsa ta hana shi zama lafiya da kowa.”
Sun ji ma suna ta mgana da Inna, tana bashi labarin yadda Hajiya ta yi ta murna da ganinta amman ba ta faɗa masa mganar Mimin da Hajiya ta yi mata ba, amman ta faɗa masa Hajiya ta ba ta labarin Major ya so ya zo ya nemi gafaran Baban Inna kan lamarin da ya faru a baya sai dai Allah bai yi ba lokaci ya ƙare. Mu’azzam ya ce”Mu ai ba mu da matsala Inna, tuni mun yafe abunda ya faru matsalan daga Yaya Mansoor ne shi fa kamar ba ya iya yafiya ga wanda ya ɓata masa Inna.”
Inna Meri tace”Allah shi ya ye masa wannan cutar, domin cuta ne ta bala’i da ya kamata a nema masa tsari wajen Ubangiji.”
Mu’azzam sai da ya yi dariya jin abunda Inna ta ce itama sai ta biye mishi suna dariya ƙarshenta dai kafin su yi sallama sai da ya ba ma Hibba wayar suka gaisa da Inna Meri ta na tambayan Megidan ta Hibba ta ce ga shi a jikinta ya yi barci sannan suka yi ma juna sallama.
Yaya Amina washegari da ta zo gidan ta ji abin da ya faru ta yi ta dariyan Bintu da ta gudu cikin dariyan ta ce”Bintu ga tsoro ga ban tsoro.”
Inna Meri ta ce”Ina za ta tsaya jiya nan ya warwareta, ɗan inna dai aka kira jiya aka yi ma borin.” Walida ta ce”Inna ke ma fa jiya kin yi ma Yayanmu tsawa.”
Inna Meri ta ce”Da ban yi mishi haka ba, da ba zai bar mganar ba, ni kaɗai nasan fitinar za ta faru ƙarkashin wannan maganar.”
Yaya Amina ta ce”Gaskiya tunda shi dai ba zai gane abunda aka yi ba, Allah Sarki ashe ba ta manta damu ba.”
Walida tace”Wlh ta ce duk a gaishe ku.”
Yaya Amina ta ce”Mu na amsawa da Inna ta min mgana ai da tare za mu je.”
Walida na riƙe dariyanta ta ce”To yanzu ma ba ta ɓaci ba, in za ki je ne ai gidan ba ɓoyayye ba ne.”
Ita Kuma Yaya Amina sai ta ce sai dai in Walida za ta raka ta ita kuma ta ce ba da ita ba ya zo Baban Inna ya ji labari ya yi biji biji da ita. Inna na gefe ta na yi musu dariya kafin ta ce”Sai dai ya yi muku amman ni ai na kuna ba na tashin ƙauri ba yadda za’a yi dani sai hakuri.”
Yaya Amina ta ce”Inna ke sha kumdun ne, ni kuwa sai ki sa ya kulla dani mu na yar mutumci da ɗan ƙanina,Halima har mamaki take yi in taga muna hira na kan ce ma ta tun tuni daman tamu ta zo ɗaya da Baban Inna” knna Meri na sakacen hakorinta ta ce”Ke ku rabani da halin Baban Inna, zuciyarsa har wani zaɓan wanda za ta yi mu’amala take yi, Allah dai ya ye mishi wannan cutar.” Walida na kwasan dariya ta ce “Inna ba shi da lafiya ne?
Kai tsaye ta ce”Eh mana ai ciwo ne babba ma kuwa, ku yi ta masa addu’an Allah ya ye masa.” Suna ta dariya Inna Meri na faɗin su daina dariya ba abun dariya ba ne.
Yaya Amina na gidan har bayan la’asar sai da su ka yi sallar sannan Amina ta ce Walida ta raka ta su je gidan Bintu.
Walida ta ce ita makaranta za ta je Yaya Amina ta ce to su je in ta rakata sai ta wuce makaranta daga nan.
Inna Meri na zaune ta na jan casbaha tace”Ku gaishemin da Bintu, ku ce mata nan fa ba gidan Baba Inna ba ne ta kwantar da hankalinta ya yi mana ma yaji.”
Dariya ta kara ka ma su Walida su ka fita suna yi Inna na gimtse fuska,.Da ya ke yau Yaya Amina ita kaɗai tazo yara duk suna makaranta har sun fita Inna ta kira su, bayan sun dawo ta kalli Amina tana fadin”Amina ki shiga bangaren su Gaje ki gaishe su, sannan ki shiga ɗakin Magajiya itama ki gaisheta ba ta jin daɗi.”
Yaya Amina ta amsa da toh Inna sannan su ka fita ɗakin Magajiyan su ka fara shiga ta na kwance Jummai ta zo gidan ashe tana ganin Amina ta washe mata baki su ka gaisa
Aminan ta gaida Magajiya ta amsa mata fuska ba fara’a Walida ma duk da ta shigo da Safe sai da ta kara yi mata ya jiki ta amsa ta na wani haɗe rai ita dai Magajiya ba ta san zaman lafiya ciwo ya rafketa Mariya na gidan Zuwaira ba ta dawo ba Inna Meri ke yin abinci yanzu ta ke ba ta kuma safe da rana da yamma Inna Meri za ta shiga ta duba ta amman ko da rana ɗaya ba ta taɓa gode mata ba. ita dai Inna Meri komai take yi domin Allah ne.
Hiran da Walida da Yaya Amina suka riƙa yi kenan a kan hanyarsu ta zuwa gidan Bintu, da suka shiga shashen su Gaje ma har ana faɗa musu mgana kiri kiri Gaje ta ce ma Amina ba’a ganinsu ko sun zo suna ɗakin uwarsu Meri to ka da su manta suma ɗaya suke da Meri a wajen su.
Walida ko ta bata rai a ranta ta ce ba ɗaya ba ne, Amina kuma sai ta ba ta hakuri Harira ce ma yar ba ruwanta ba kamar Gaje da kamar halinsu ya zo ɗaya da mijinta wajen kallon rayuwar wani.
Sun je sun iske Bintu ita kaɗai a gida su Hassan sun bi babansu gidansu, abokiyar zamanta ba ta nan suna biki a gidanu, ta yi murna da ta gansu sai ga shi ta kawo musu ruwa da zoɓo daman ta na saida wa.
Ta zauna kusa da Yaya Amina tana faɗin”ki ce yau a gida kika yini”
Yaya Amina na shan ruwa ba ta amsa ta ba, sai Walida ne ta ce”E, ke ai kin gudu jiya.”
Bintu ta ce”Uhm na yi gudun gara ne Walida yau da safe Baban inna ya kirani a waya ya zazzageni Walida.”
Walida ta zaro ido Yaya Amina kaɗan ta ƙware da ruwa ta ɗago tana faɗin”Kai! me ya ce miki kuma?
Bintu ta yi tagumi kafin ta ce”Kawai da safe muna cikin karyawa da Bashir sai ga kiransa ni fa tunda na ga kiran Baban Inna nasan ba na alheri ba ne na tashi na yi ciki ina ɗaukan waya ko gaisuwata bai amsa ba ya fara min masifa wai mu munafukai ne ni da Walida me ya sa da Inna ta ce ga inda za mu rakata ba mu kirasa a waya a ɓoye mun faɗa masa ba? da ina masa rantsuwan ni ma ban san inda za mu je ba ya dakamin tsawa yana faɗin duk sai yaci ubanmu me ya sa da ta ce mu rakata ba mu ce ba za mu je ba? Kuma sannan mun yi masa ƙarya da ya kira mu ka ƙi gaya masa in da mu ka je, yace wlh wannan ƙaryan da munafuncin da mu ka yi masa sai mun raina kanmu.”
Walida ta yi fiki fiki da ido ta kasa mgana Yaya Amina ta ce”To ke ba ki ba sa hakuri ba ne?. Bintu ta ce” Wani hakurin? Ya tsaya ne ma ina cikin mgana ya yi tsaki ya kashe wayarsa walh Baban Inna ya cika masifa”
Yaya Amina ta ce”To ai jiya ma yazo zai yi ma Inna ta balbaleshi da masifa shi ne ya koma gida ya kira Mu’azzam ya sauke a kan shi.”
Bintu ta ce”Kai jqma’a shi ya yi hakuri da rayuwa mana, ni fa ban ga wani abu acikin zuwa gaisuwan da muka yi ba”
Walida ta ce”To ni ma dai shi nagani.”
Yaya Amina ta ce”To shi gani zai yi ba kwa kishinsa ban da abunsa da mai rai ake fushi ba da wanda ya mutu ba.”
Nan su ka cigaba da tattaunawa Walida ta shantake ba ta je islamiyan ba Bintu na ba ma Amina labarin yadda Hajiya da Mimi da su ka yi ta rawan jiki da su ka gan su.
Yaya Amina ta ce”Allah Sarki Itama kila har yanzu ta na son shi.”
Bintu tace”To daman mana, shi ma duk wannan kumfar bakin na Soyayar ne.”
Gabaɗaya suka saka dariya ba su suka baro gidan ba sai shidda saura na yamma.
Suna komawa gida Inna ta ga Walida ta dawo da wuri cikin faɗa ta ce” Amman dai ba ki je makarantan ba ko?
Walida ta sosa kai ba ta yi magana ba Inna tace “Ya yi miki kyau.”
Yaya Amina ke labartama Inna yadda Baban Inna su ka yi da Bintu sai da Inna ta yi dariya amman ba ta ce komai ba acikin ranta tana son ganin yadda lamarin zai kasance. Shi dai kahaifin Mimi da ya fara ja Ubangiji ya karɓi kayanshi sauran Baban Inna shi kuma sai ta tsaya ta ga ina wannan bakar zuciyar za ta kaisa.
Kamar Inna ta sani yaji ya yi musu sai da ya kusan kwana goma sannan ya zo gidan Sun dai ji kabarin ya na kaduna sun je buga wasa daga bakin Mu’azzam shi tuni har sun shirya kansu. Sai da ya dawo ya zo gidan shima bai daɗe ba, Walida daman tana nemansa nan ta gaya masa an fara biyan Jamb ta na so ta biya nan ta ke ya ba ta kuɗin har da na abun hawa ya ce kuma in akwai wata matsalar ta kirashi ta wayar Inna ta gaya masa.
Duk kuma wannan abun bai zauna ba ya na tsaye a kofar ɗakin Inna Meri.
Ita ko ta yi masa banza kamar ba ta gansa ba, har ya tafi kuma sai ya dawo ya kira Walida yana tambayanta ina Mariya? Ita ba za ta yi jamb ɗin ba ne? Domin suna aji daya ne SS3 Kuma tare aka biya musu kuɗin jarabawar fita.
Sai take faɗa masa Mariya ta daɗe ba ta nan ta na gidan Yaya Zuwaira, Inna ya kalla kafin yavce”Inna me ta je yi can kuma?
Inna na tankaɗen garin tuwo ta juyar da kai kafin Ta ce”Ina zan sani, shiga ɗakin Magajiya sai ta faɗa maka”
Cikin Kallonta ya ce” Innarmu.”
Ko kara kallonsa ba ta yi ba sai kawai ya kaɗa kai ya fice bai kara magana ba ta bishi da kallon tausayi a ranta ta na masa fatan Allah ya yaye masa wannan bakar zuciyar.
Da daddare Mu’azzam ya kira wayarta yana faɗa mata Babanta ya kawo masa ƙaranta.
Tana mirmishi ta ce”Me kuma na yi ɗan Inna? Ckin dariyan shima ya ce” Ya ce ya zo kin yi kamar baki gan shi ba ,yana mgana kika yi banza da shi sannan ko abinci bavki ba shi ba.” Inna Meri ta ce”Ban ba shi ba sai ya zo ya ƙwata, ko auransa na ke yi da zai zo ya tsaya a saman kaina yana min wani cin magani? Ɗan Inna rabani da Baban Inna ba na iyawa da fitinarsa.”
Cikin magiya ya ce”Haba Innarmu maganin kukan mu, a yi masa afuwa in kina fushi da shi ina zai saka kansa Inna?
Ya faɗa cikin wani yanayi sai ta ji tausayin duka ya’yan nata ya kamata amman ba ta huce ba cikin gatse ta ce”To shi ba shi da bakin da zai zo ya ce in yi hakurin ne?
Mu’azzam sai da ya yi dariya kafin ya ce”Allah ya huci zuciyarki Inna”
Ta amsa mai da Amin bayan sun yi sallama ba jimawa Baba Ɗanjuma ya shigo.
Shima sai da ya yi mata mganar cikin Lallashi ya ce”Meri fushi da Baban Inna ba naki ba ne a wannan lokacin, ki yi hakuri ki fahimce sa don Allah.”
Inna ta gyara zama kafin ta ce”Au kai ma ƙaran nawa ya kawo maka?
Kai tsaye ya ce”Ko ɗaya ni na fahimci yau ya na cikin bacin rai ya shigo gida ya fito ban gansa cikin yanayi mai daɗi ba, ki yi hakuri tunda har mu fahimcesa sai mu yi ma rayuwarsa uzuri kin ji ko?
Ba za ta iya yi ma mallam gaddama ba sai ta amsa masa. Shi ya sa bayan kwana biyu da ya zo Innar ta sakar masa amman ba sosai ba da kanta ta kawo masa abinci ya zauna yaci sosai tausayinshi ya kama inna har sai da ta ji taruwan kwalla acikin kwarmin Idanuwanta. Bai yi wani doguwar mgana ba da zai ta fi ya ijiye mata kuɗi yana faɗin “ki yi hakuri Inna.”
Daga haka bai kara cewa komai ba sai ta ɗauki kuɗin tana saka albarka kafin ta ce”Ka leka ka duba Magajiya ba ta ji daɗi ba kwana biyu.”
Sai ya amsa mata da to, yana fita sai ya ganta nan kofar ɗakinta kamar ta fito daga makewayi ne. Mariya na cikin ɗaki ta dawo shekaranjiya ta na jin muryansa yana faɗin” Magajiya ya jiki?
Dakyar ta amsa shi kuma cikin yanayinsa ya ce”Allah ya kara lafiya”
Bai ji ta amsa ba Mariya ce ta leko tana gaishe shi ya amsa yana kallonta har ya wuce sai ya sake dawowa yan faɗin”Ke me ya sa kika tafi wani waje kika bar zuwa makaranta? Kafin ta yi mgana Magajiya ta yi zaraf ta ce”Ba wani waje ta je ba gidan ƴar’uwanta ne ko za ka hana ta ne? Ko bangaran magajiya bai kalla ba ya cigaba da faɗin “Walida ta biya Jamb ke me ya sa ba za ki yi ba?
Da sauri ta ce”Ina son na yi Yayanmu Baba ne ya ce ba shi da kuɗi Yaya Auwalu ma na yi masa mgana ya ce ba shi da kudi.”
Hararanta ya yi kafin ya ce”Daman su suka saba ɗawaniyar makarantar ki? biyo ni ki karbi saƙo a waje.” Ya wuce cikin takunsa na gif gif Magajiya sai ta kasa mgana saboda ya lna mata ƙwarjini wani lokaci.
Jiki na rawa mariya ta zari hijabin Magajiya da ke saman kofa ta bi bayanshi da mota ya zo sai da ya shiga ciki ya ɗauko kuɗi ya bata na farko ya ce ta biya Jamb ta yi ma Walida magana ta rakata. Ta karɓa da sauri tana godiya sai ya mika mata wani kuɗin yana faɗin”Ki kaiwa Magajiya.”
Har sai da ta ramkwafa wajen amsa masa acikin zuciyarta ta na jin wani iri, gida ya ce ta shiga sai ta shige ta laɓe sai da ta ga shigarsa mota da tafiyarsa sannan ta koma tana dafe kirji ita fa tun ba ta gane ba har ta zo ta gane cewa tun tuni ashe son Yaya Mansoor take yi ba ta sani ba.
Jiki na rawa ta je ta na nuna ma Magajiya kuɗin ta ba ta nata tana faɗin “Ya ce in ba ki” Magajiya ta taɓe baki ba ta ko karɓi kuɗin ba ta shige cikin ɗakinta lokaci ɗaya tana faɗin” Shi ne kike ta wani rawan jiki kamar ya ba ki wata duniya”
Kuma acikin ranta ta ji daɗi bashi ake bin ta ko ta samu ta biya daman in ba shi ko Mu’azzamu ba ina take samun kuɗi? Sai dai fa taƙi godema Allah.
Page 19
Bayan Wata Ɗaya
Bayan wata ɗaya da ya yi dai dai da kimamin wattani biyu da kwanaki da rasuwar Abi, kuma wata ɗaya tsakani da zencen da Hajiya ta yi da Inna Meri sai dai tun bayan lokacin ba su ƙara haɗuwa ba, Inna Meri ba ta koma ba itama Hajiyan ba ta dawo ba saboda sun kara komawa Abuja da aka yi arba’in ita da Mimi suka kwana biyu suka dawo. Gidan can na Abuja ya rage daga Mommy sai Inna Ladidi ita Inna Zainaba bayan arba’in ta koma gida, sai kuma yan aikin Mommy na amana, duk da gidan ya yi rashin megidan amman Dr. Sulaiman da Alhaji Hamza ba su bar shi ya yi kewa ba komai da ake bukata har da wanda ba’a bukata ma suna tana dar da shi. Mommy dai duk wannan bai dame ta ba, ita dai kukanta ta yi rashi rashin da har da har abada ba za ta mai da makwafinsa ba.
Sannan ta kuduri niyar cika wasiyyan mijinta shi ya sa zuwan da su Hajiya suka yi ta yi mata mganar Mimi da Mansoor Hajiya ta zayyane mata abunda ya gudana a tattaunawar da suka yi da Inna Meri, Mommy cikin wani yanayi ta ce” Hajiya ni zan je da kaina mu yi mgana, ba zan iya sukuni ba tare da na cika wasiyar Habibi ba, ya rasu da Mimi a bakinsa da kuma ƙudurin nemansa ya nemi gafaransa tunda shi bai samu wannan damar ba, ni ina raye Hajiya in sha Allahu da zaran na fita takaba batun zan fara tunkara in sha Allahu.”
Hajiya tace”Shike nan Allah ya fitar dake lafiya.” Ta amsa mata da Amin suka cigaba da tattaunawa, duk akan mganar Mimin ne wacce duk ta yi sanyi ta koma wata iri, sannan kowa ya gan ta ya san tana da damuwa ga rashin mahaifi ga ciwon da ya jima a zuciyarta. Har su Khadija sun zo addu’an arba’in su kan su, suna ta korafin ganin Mimi ta rame kuma wani abu da kowa bai sani ba tun daga ranar da Aji ya saka mata wannan rigar da ita take kwana da ita take ta shi, in ta na jin kewarsa sai ta rumgume rigar ta yi ta kuka. Ba kowa ba ne zai iya fahimtar Halin da ta ke ciki ba sai ita kanta da ubangijin da ya halliceta.
Kwanansu biyar suka dawo gombe lokacin tuni daman Mimi ta koma bakin aikinta ko a can ma ana ta ƙorafin ta sauya sai dai ana tausaya mata sanin ta yi rashin uba musamman ma Rukky da suke tare ta fi kowa sanin Mimi ta rage karsaahi da fara’a
ko labarai take karantawa za’a ganta irin so cool haka kamar wata mara lafiya.
Sai dai ana yi mata uziri saboda ta yi rashi kuma dole daman sai a hankali.
Hajiya ba ta taɓa mganar da kowa ba amman Mommy ta yi mgana da Dr Sulaiman shi kuma sai yake ganin abun wani iri har yana cewa”Mommy to tunda Hajiya ta ce ta yi mgana da mahaifiyar shi ta kuma ba ta tabbacin sun yafe ai ina ga shike nan ba lalle sai kin je da kanki ba.”
Mommy ta ce a lokacin”A’a ai shi yaron aka saɓamawa kuma shi Habibi ya jadadda neman gafaransa sannan kuma ya ce ya janye kalamansa kan Mimi in har tana son shi har yanzu da amincewarsa mu aura mata shi.” Kai tsaye ya ce”Haba Mommy wannan fa wani abu ne da ya shuɗe shekaru sama da takwas, ki ƙyale wannan mganar.”
Sai ta ga kamar bai fahimceta ba, sai da Alhaji Hamza ya zo shima ta yi masa mganar shima dai irin ta Sulaiman ɗin ne ya ce tunda Hajiya ta yi mgana da Inna Meri ta ce komai ya wuce ba kuma amfanin kara nemansu wanda ma ya yi abun nan yau ba shi a duniya kowa sai ya yi hakuri.
Da ta yi masa mganar ita Mimi har gobe ta na son yaron tunda har ya amince kafin ya rasu me zai hana a nemi shi yaron a dai dai ta a ji in har har yanzu yana ra’ayin Mimi sai a yi mgana saboda farincikin Mimin.
Kai Tsaye Alhaji Hamza ya ce”Wannan maganar banza ce, muke da mace in har ya na sonta har yanzu shi zai neme mu ba mu za mu neme sa ba, mganar Mimi na son shi har yanzu ba magana ba ce tunda ta iya rabuwa da shi a baya a yanzu ma ba wata tsiya ba ce ta samu miji ta yi auranta ta manta da shi lokaci ne kawai bai yi ba.”.
daga nan sai ta fahimci dukkansu ba su gane in da ta dosa ba, ita kuma wasiyyan mijinta take son tabbatarwa shi ya sa ta kara kiran Hajiya ta faɗa mata yadda suka yi da su sai Hajiya ta ce”Rabu da su ba za su gane ba ne, ina son na je har gida na samu Meri da megidan nata amman kafin nan zan aika Binta gidan ta amso lambar wayarta mu yi mgana kafin na je.”
Da haka su ka rabu da Mommy wacce ta ce ita fa alƙawari ta yi ma Habibi na cewa In sha Allahu za ta yi kokarin ganin Mimi ta samu abin da take so itama ta yi farinciki kamar kowa nan kuma duniya yaro nan shine cikon farincikin Mimi kuma dalilin shi ne har yau ta kasa ba ma wani namiji dama ciki har da ɗan uwanta Jaheed. Duk kuma bikin da a ke yi Mimi ba ta sani ba har ta su Khadi ba wanda Mommy ta yi mgana da shi Saboda kamar Sulaiman suma suna ganin ba wani soyayyar da ta hana Mimi aure kawai dai kila na ta ra’ayin ne amman su a ganinsu tunda sun rabu tun a baya kowa ya kama gaban shi ina abun cewa mutum na nan yana fama da dakon wahala.
Hajiya kuma ta na goyon bayan Murja Saboda ita take zaune da Binta ita kaɗai ta san yanayin da yarinyar take ciki so take kafin ta bar duniya ta ga Mimi na cikin farinciki a kuma ɗakin auranta kamar ko wata mace.
Tuesday 04 May, 2022
Mimi na wajen aiki ta samu wayar Hajiya sai dai in da ta aiken ta ne ya ba ta mamaki, cikin ƙarin mamaki a muryanta da fuskarta ta ce”Hajiya wai gidan su Aji kike nufi na je?.
Kai tsaye Hajiya ta ce”Eh don Allah ki je ki karɓon min lambar wayar Meri ina son na yi mgana da ita, ga shi ni kuma ban samu zuwa ba.” Cikin wani mamakin ta ce” Hajiya zan iya gane gidan kuwa? Kuma in kina son zuwa direba ba sai ya kai ki ba, ai ba sai kin aike ni ba” Da sauri Hajiya ta ce”Kafin na samu lokacin zuwa ina bukatar lambar wayarta ne da gaggawa.”
Ba ta kawo komai a ranta ba ta amsa ma Hajiya, sai dai ta na tunanin me ya sa Hajiya ta ce sai ita ta je da kanta. Alhalin in tana son zuwa ba wahala ba ne hakan.
Tunanin hanyar gidan ma take yi shekarun da ya wa rabonta da gidan nan, ta so ma ta kira Rukky ta rakata sai dai ta na da aiki shi ya sa kawai ta kyaleta ba ta yi mata mgana ba. News ɗin da za ta karanta gobe da safe na wajen Editer in ya gama dubawa zai kai ma Manaja ya duba shima, shi ya sa sai kawai ta yi musu sallama ta wuce da cewar sai gobe da safe.
Ta baro gidan Talabijin ɗin cikin zullumi da misalin biyar na yamma a can ta yi yininta yau saboda in ta koma gidan ma sai dai ta yi ta zaman tunani kuma ita kanta ta gaji da tunanin, tana tafe a motar ta har anguwan Arawa a ranta tana tunanin ashe za ta gane anguwan, sai dai anguwan ta samu sauye sauyen gine gine sai ga ta har kofar makaranta mallam Ɗahiru ta kalli makaranta abubuwan da suka faru a baya suna gilma mata sai da ta yi mirmishi a saman lebenta kafin ta furta a fili” Allah Sarki ashe makaranta Mallam Ɗahiru ta nan nan”
Makaranta ba kowa tunda ranar alhamis ne ba islamiya daga nan tana tafe a sannu sannu tana kallon gidajen har wajen kofar gidan Wanzamai sai dai abun ya ba ta mamaki Saboda a yadda ta san gidan ba haka ta gan shi ba wannan ya koma na zamani sannan ya samu bangare biyu kuma kowanne da kofar shigarsa, ta jima a cikin mota tana kallon gidajen har gaba ta yi ta kuma dawo baya in da ta tabbatar da kanta nan ne,saboda masallacin dake kallon gidan da ta sani har gobe ya na nan, Sannan akwai wasu gidajen da ba su sauya ba suna nan a yadda ta san su tun da farko.
Kofar gidan ba kowa tsit sai jefa jefa mutane na wucewa, ta kasa fitowa daga cikin motar ta sama da minti sha biyar sai da ta duba agogon fatan dake hannunta ta ga har shidda saura duhu zai fara shiga sai ta yi gundunbala buɗe murfin motarta ta fito daman tana sanye da doguwar rigan wani material mai kalan ratsin pick sai ta yi amfani da pick ɗin mayafi mai roba ta yi Rolling da shi fuskarta sanye da wani siririn gilashi na ado kafarta sanye da bakin takalmi mai tudu kaɗan wanda ya yi maching da bakar karamar jakar dake hannunta. rufe motar ta yi sannan ta riko key ɗin motar a hannunta tare da wayarta hannunta na hagu kuma ta rike jakarta sai ta ɗan haɗa da rike gefen rigarta daga kasa tunda ta na ɗan sharan kasa, rasa kofar da zata nufa ta yi yasa ta yi kumdubalan faɗawa na gabanta lokaci ɗaya da sallama a bakinta.
Gaje ke cikin madafi ta na kaɗa miya Harira kuma ta na tsakar gida ta na wanki suna Hira ita da Gaje su ka tsinkayi sallama cikin wata murya kamar ta yan gayu.
Gabaɗayansu suka ɗago suna kallon Mimi da ta kariso tsakiyar tsakar gidan na su da Mansoor ya simince shi ya yi kyau sai dai ba gyara daga gani yau ma gidan bai ga shara ba. Mamaki ganin ta suke yi shi ya sa har Gaje sai da ta fito daga cikin madafi tana kallon Mimi cikin mamaki. Itama kallon mamaki ta ke yi musu saboda sai taga kamar ta gane su amman ta manta sunayensu. Rankwafawa ta yi cikin ladabi bayan sun amsa mata sallamar ta, ta gaishe su a tare su ka amsa har suna haɗa baki.
Cikin yanayin maganarta ta ce”Ina neman Inna Meri ne, don Allah ina ne ɗakinta?
Saboda ta ga gidan kamar ya sauya mata, Harira ta kalli Gaje itama ta kalleta suma su na mata kallon sani amman sun rasa in da suka santa.
Harira ce ta ce”Ai ba nan ne bangaren su Merin ba hala kin jima ba ki zo gidan ba ne ? Ai an fi shekara da raba mana kofa.”
Mimi ta kalleta sai ta yi mirmishi kafin ta ce”Allah Sarki! Gaskiya na ɗan jima ban zo ba shi yavsa yanayin gidan ya ɓace min.”
Gaje ta ce”Ƙofar su tana gaban namu da kin fita za ki ganta tana kallon garun nan, in kika shiga sai ki yi tambaya a nuna miki bangaren Merin.”
Mimi ta yi musu godiya har ta Juya sai Gaje ta ce”Baiwar Allah.!
Sai ta juyo ta na kallonta kai tsaye ta ce”Kamar na sanki wlh, ko ke ƙawar Walida ko Bintu ce?
Mimi ta yi mirmishi ba ta yi mamaki ba saboda mutane na yawan ganinta su ce kamar sun santa fuskarta ba ɓoyayiya ba ce ba lalle su iya ganeta a baya ba amman ta na da tabbacin fuskar Mimin karamci suka sani. Ba ta samu zarafin mgana ba sai ga Mariya ta shigo shanya sai ta ga su Gaje cirko cirko ga kuma wata yar gayu a tsaye daman ta ga mota a kofar gida tana ta mamakin motar waye tunda ba ta Yaya Mansoor ba ce.
Kafin ma ta yi mgana Harira ta ce”To ai ga ma Mariya nan, ke mariya raka ta wannan bakuwar Inna Meri ce kai ta bangarenta.”
Mariya ta kura ma Mimi ido kamar za ta yi magana sai ta fasa sai tace toh ta ijiye botikin shanyar ta wuce gaba Mimi ta bi bayanta bayan ta yi ma su Gaje godiya suna fita Harira ta kalli Gaje kafin ta ce”Ni fa ina ji a jikina kamar na san yarinyar nan”
Gaje ta yi shuru tana tunani kafin ta ce”Nima wlh kuma ba ƴan’uwan Meri na can garin su ba ne, da kin ji hausan su, amman tabbas na san fuskarta sai dai na rasa a inda na santa.”
Sai su ka shiga tunanin in da su ka taɓa ganin Mimi sun manta da a kwatin talabijin ɗin ɗakin Gaje su ke ganinta tunda tana da wani tsohon tibi da ɗiyarta ta sauya nata ta kawo mata tunda a gidan nan ba wanda bai san mai aikin gidan tibin nan ita ce wacce Mansoor ya so a baya babanta Soja ya sa a ka yi ta dukansa ya kusa mutuwa ba.
Ita kuma Mimi suna fita kofar gida Mariya na gaba tana binta a baya sai dai tana ta juyowa ta na kallonta Mimi kuma sai ma ta mirmishi ta ke yi ta na mamakin girman Mariya ai ta santa mana ko da ya ke ga Walida ma ta zama yan mata.
Sun zo kofar shiga gidan Mariya ta juyo da sauri tana nuna Mimi da yatsa kafin ta ce”Laa ina ganinki a talabijin ɗin Magajiya ke ce ko? Mimi ko?
Mimi ta yi mata mirmishi hakoranta farare har su ka bayyana a waje kafin ta ce” Mariya a she za ki gane ni?
Mariya ta ji muryan Mimi ta fi ma zaƙi a sarari sai kawai ta daka tsalle ta shige cikin gida ta bar Mimi na bin bayanta da dariya, ita Mariya daɗi ta ke ji ta kama sunanta kuma sannan ta ganta a fili ba’a talabijin ba wanda sau tari ma Magajiya na ganin ana nuno ta za ta fara maasifa sai an sauya mata tasha tunda gidan tibin na su babba ne ya na kan babban recodan da ake kama sauran manyan manyan tasoshi.
Magajiya na bakin kofar ɗakinta tana tuka tuwo Mariya ta shigo ta na tsalle tana shirin mata mgana ta ga ta wuceta zuwa bangaren Meri ba ta samu sauke numfashi ba ta ji Mimi na gaisheta ta amsa kai tsaye tana kallonta, ita ma sai ta kalleta ta gane ta Magajiya kai lalle rayuwa gidan duk ya sauya mata ganin Mariya ta yi gaba ya sa itama ta bi bayanta cikin irin yanayin takunta. Magajiya ta bi ta da kallon mamaki tana tunanin itama a inda ta san fuskar, Sai abun ya kasa barin ta, ta yi sukuni a gurguje ta gama kwashe tuwo sai ta hau ƙwalama Mariya kira sai da ta fito tana zuwa ta kalleta kafin ta ce”Wannan wace ce na ga kun shigo tare? Kusa da ita ta matsa kafin ta ce”Laa ba ki gane ta ba? Ina wannan da ake nunota a talabijin wanda har Walida ta taɓa faɗamin wai budurwan Yaya Mansoor ce to ita ce fa Magajiya leka waje ki ga wata hadaɗɗiyar motar da ta zo da ita”
“Ke Dilla rufemin baki sakara kawai, ina botiki na.?
Mariya na tura baki an katseta ta ce”Ban shanya ba fa” Kamar za ta mareta haka ta kai mata hannu kafin ta ce”Wuce ki je ki shanya ki ɗaukomin botikina.”
Ba yadda ta iya haka ta wuceta fita amman sai da ta gama tsayawa wajen Motar Mimi da ta koma su gaje su ka turketa da tambayan ko ta san wace ce? Kamar yadda ta gaya ma Magajiya haka ta gaya musu sai Gaje da Harira su ka haɗa baki wajen faɗin “Haba shiyasa mu ka ga kamar mun santa, ikon Allah to me ta zo yi?
Mariya tace ita dai ba ta sani ba sai kawai ta fara Shanyarta ta bar su da rike baki suna faman tunanin me ke shirin faruwa kenan?
Bayan fitan Mariya har leke su ka yi waje domin ganin Motar da Mariya ta zuzu ta su ma kan su sun shaida kyanta Har Harira na fadin”To me ya kawo ta? daman suna hulda da su ne har yanzu?
Gaje ta ce”Ni dai Mallam ya faɗa min ba wannan alaqar daman Merin ce kuma tuni ta daina aiki a gidan shi kan shi Mansoor ɗin ya kama kan shi ke ko karo da Soja wasa ne, sai dai fa kinsan ni dake muka ga sanarwan rasuwan uban nata ko kila shi ne ya ba su lasisin sake dawowa har kuma ta ke zuwa wajen Meri?
Harira ta ce”To wa ya sani?
Gabaɗaya sai su ka rasa sukuni kamar yadda Itama Magajiya a na ta bangaren ta saka sukuni ba tunanin da ba ta yi ba.
Yau sai ga shi da kanta ta tura Mariya ɗakin Inna Meri saboda ta na so ta san abunda ya ke faruwa a cikin gidan.
Ita kanta ta kasa shiga ɗaki sai faman zagaye take yi ta na kasa kunni sai dai ko Minti ashirin Mimi ba ta yi da shiga bangaren Meri ba, sai ga shi ta fito Inna Meri iya kofar ɗakinta ta rakata tana ba ta sakon ta gaida Hajiya Mariya da Walida ne su ka rakota har waje, Walida sai wani ji da Mimi take yi mariya kuma sai faman washe baki take yi. Ta buɗe motarta ta shiga sannan ta buɗe dirowan motar ta ɗauko kuɗi ta mika ma walida ta ce su raba Walida ta ce ba za ta amsa ba. Sai ta harare ta kafin ta ce”In Mu’azzam ko Mansoor suka baki kyauta kina maida musu ne?..
Sai ta ji kunya ta kasa magana sai Mimi ta ce to kamar hakane in dai za su baku abu ku karɓa ku yi godiya nima wajibi ne ku karɓa. Dole Walida ta karɓa Ita da Mariya suna ta kwarara mata godiya. Suna wajen har ta tada motar ta yi ribas ta bar anguwan sannan su ka koma cikin gida.
Abib da ba su sani ba Aji na daga nesa ya na kallon su a saman mashin ɗin sa daga gidan su Musa Zinder suke yaron dake cikin United ɗin su jiya wajen evening traning ya samu rauni sai aka maida shi gida to da yamman nan ne ya fita ya je ya ɗauki Coach daga gidansa suka je su ka duba shi daganan ya mai da Coach gida shi kuma sai ya gangaro ta anguwar tunda yau wajen kwana uku bai leko ba sun yi kuma waya da Inna akan za ta je biki can bauchi tana son ganinsa. Mamaki da wani irin takaici ya sandaran da shi a inda yake, me wannan yarinyar ta zo yi musu kuma a gida? Yanzu Ita Inna abin da take yi dai dai ne? Ina ruwanta da waɗanan mutane da ba rayuwarsu ɗaya ba yanzu in ya yi mgana sai a ga laifinsa ransa ya ɓaci har wani duhu ya ke gani da ya sa ya fasa ma ƙarisowa kofar gidan daga nan ya juya kan mashi ɗinsa ya koma ta anguwar tunfere amman yana tafe yana sakin huci Inna gaskiya ba ta yi masa adalci ba wlh kamar ya koma ya ji dalilinta amman a yadda ransa yake ɓace Inna ba za ta fahimce sa ba shima ba zai fahimceta ba.
Bangaren Inna Meri kuwa har Walida ta shigo da murnan kuɗin da Mimi ta ba su dubu goma su ka raba ita biyar Mariya biyar, tana nuna ma Inna Meri cikin murna tana faɗin” Inna na samu na siyan ankon Bahijja” Inna ta kalleta kafin ta ce” Kun gode Allah ya saka mata da alheri.”
Har Walida ta shiga cikin ɗaki ita tana tsaye ta na wani tunani, a ba za ta ta ga Mimi, tunda taji Hajiya na neman lambar wayarta jikinta ya ba ta maganar da su ka taɓa yi ne, ita kam ai ta gama mgana, fitinar Baban inna ta ke tsoro kuma an ce in ba ka san karshen fitina ba kada ta ɗukota daga fari ita fa ba wanda ma ta yi ma wannan mganar ko Mallam ba ta yi ma mganar ba ashe ita Hajiya da gaske take yi.
Har dare abun na sukan ranta, sai ga shi Baba Ɗanjuma na dawowa tun a waje su Baba sani su turkeshi da mganar matan su sun tsegunta musu, shi fa kai tsaye suka ce me Mimi ta zo yi? Gwara dai su dawo cikin Hayyacin su in sun manta abin da ya faru a shekarun baya ne wato ya na ganin yanzu ya isa ko? Vwara ya faɗa masa in ya kara ɗauko wata fitinar ba dai gidansu ba.
Shi da bai san kan mganar ba sai ya yi Shuru har sai da ya zo ya tambayi Inna Meri itama ta kaɗu da jin har labari ya fita waje cikin mamaki ta dhiga warware masa abunda ya faru, Shi kan shi sai da ya yi shuru kafin ya ce”Dankari! Babban mgana shi Baban Inna ya san da mganar?
Inna Meri ta ce”Ina zan bari ya sani kasan halin shi da bakar zuciya.”
Baba Ɗanjuma ya ce”To ka da ki yi masa zencen, mu bari mu ga abin da ubangiji ya tsara a tsakanin su.”
Inna Meri ta ce daman shi yasa ta ki yin zebcen da kowa. Baba Ɗanjuma kuma har Magajiya sai da ta sakar masa mganar Agolan gidansa zai kara jawo masa wani rigiman shi dai bai ce mata komai ba ta yi ta faɗa da bala’a akan abunda ya wuce tuntuni.
Shi ko a bangaren Mansoor ya kasa sukuni sai da ya kira Mu’azzam yana tambayansa ko sun yi waya da Inna? Mu’azzam yace”Eh jiya ma daddare mun yi mgana har ta ce min kwana biyu ba ka zo ba.”
Cikin son kara samun tabbaci ya ce” Bayan nan ba ta yi maka wata mgana ba?
Mu’azzam ya ce”Ta yi ta faɗa ne kan bikin da za ta tafi Bauchi ta ce kuma ka zo amman ba ka zo ba.”
Aji ya sauke Numfashi kafin ya ce”Daga nan ba ta ce wani abu ba?
Sai Mu’azzam ya fara mamaki kafin ya ce” Shike nan mana.”
Aji ya sake cewa”Ka tabbata shike nan? ba ta ce maka ko ta yi wata bakuwa ba?
Mu’azzam ya yi shuru kafin ya ce” A’a gaskiya ba ta faɗa min ba, ko ka ji labarin ta yi wata baƙuwa ne?
Sai kawai Aji yace shikenan daganan ya kashe wayarsa Mu’azzam ya yi ta mamaki tunda kuma ya ji haka a ransa yasan akwai wani abu a kasa ya so ma ya kira Inna ya tambayeta ko ta yi bakuwa ne sai kuma ya sha’afa.
**
Da Sassafe kamar wanda a ka koro sai ga shi ya zo gidan daga morning training yake har kayan ma bai sauya ba tunda dai bai koma gida ba. Sai dai Inna Meri ta gan shi kamar daga sama suna cikin karyawa ita da Walida sai ga shi ya ɗago labule ya shigo.
Dukawa ya yi a kasa ya gaida Inna Meri ta amsa tana faɗin “Idon ka kenan Baban Inna? Sai ya dukar da kai yana faɗin” Inna wasa gare mu, muna ta shiri ne.”
Walida ta gaisheshi ya amsa sai ta tashi ta shiga ciki tunda yau ɗin ba su da jarabawa.
Inna ta kalle shi kafin Ta ce”Wasa ai yafi maka sada zumumci Baban Inna.”
Kai tsaye ya ce” To ki yi hakuri Inna.”
Ta yunkura ta mike tana faɗin”Koko da kosai muka yi bari na zuɓo maka”
Dama yunwa ya ke ji nan ya gyara zama Inna Meri ta zubo masa ya sha Sosai sai da ya ji cikinsa ya cika. Inna Meri na kallansa ta na tausaya masa magidanci kamarsa abinci ma ba ya samun ci sai raɓe raɓe.
Shikuma yana ta jira ya ji ko Inna zw ta yi masa zencen zuwan Mimi sai ya ji ba ta yi ba sai ma ta fara masa faɗan ta gaya masa Babansa yakubu zai aurar da yara har biyu tana so ya shirya su tafi tare, kai tsaye ya ce”Inna ina naga wani lokacin zuwa biki kamar wani mace? Zan dai baki gudummuwa kikai musu Allah ya ba da zaman lafiya in kina neman ɗan rakiya ne ki tafi da Walida mana.”
Inna Meri ta aika masa da dakuwa kafin ta ce”Ai ba ka yi kuɗin da za kaki zumunci da dangin Babanka ba, zuwan ka yafi kuɗin da za ka aika muhimmamci.”
Cikin shafa sumar kansa da ta taru ya ce”Inna ki yi hakuri na je na gaba tunda shi naga duk kusan sati sai an ce ƴarsa za ta yi aure.”
Inna Meri ta girgiza kai tana yar dariya kafin ta ce”Allah ya shirye ka Baban Inna, yana da ƴaƴa mata ne da yawa kuma baya barin su tsawaita karatu shi ya sa yake yawan sha’ani kuma ko wancan sha’anin sai da ya yi min zencen ka ni fa ina jin kunyarsu domin sun nuna min kara su ka bar min kai ka girma a hannuna. Gwggon ka ma yalwa ba ka kara zuwa ka duba ta ba sai dai ka yi musu saƙo Babanka Karimu har hatsari ya samu na yi na yi da kai amman ba ka je ka duba shi rana ɗaya dai Haba”
Kansa na ƙasa ya ce”Inna ban samu zuwa ba a wanchan lokacin ba, amman in sha Allahu zan samu lokaci na leƙa”
Kai tsaye tace” Bauchin fa?
Shima kai tsayen ya ce”Har can zan je Inna ba shike nan ba,”
Inna Meri ta ce”Ba shike nan ba ai ba sau ɗaya ba zumunci za ka riƙe domin su ne makwafin mahaifinka shi ya sa ko yaran nan su Amina ba na barinsu haka ko da yaushe ina tunasar da su su yi zumunci da dangin mahaifiyarasu Mu’azzamu dai ba shi da matsala yana zuwa sosai kaine dai sai a hankali, ina kuma maka faɗan ka gyara domin Allah da kanshi ya tanadi Aljanna ga ma su sada zumumci.”
Shi fa ai tunda ya kawo kansa shike nan Sai da Inna ta gama mai wa’azi sannan shi ma ɗin Baba Ɗanjuma ne ya cece shi da ya shigo ɗakin a ranar da yamma ya dawo ya kawo ma Inna kuɗin gudummuwa da kuɗin mota ita kaɗai za ta tafi ta mallam Sidi za ta biya su tafi da yalwa tunda taji sauki sai ya ba ta ishaahen guzuri har Mu’azzam ma ba’a bar shi a baya ba Inna na ya bari Baban Inna ya ba ta kuɗi ya ce shima ya na neman albarka ne.
Walida ta so zuwa suna da jarabawa ita kuma Bintu ranar kanwar Mijinta na aure ta so ta gudu ta bi Inna, Inna Meri ta ce ba in da za ta bi ta ita ba Merin mahaukata ba ne.
Ranar alhamia ta tafi mallam Sidi ta kwana washegari suka tafi Bauchi suna can garin Hajiya ta kirata sai ta gaya mata ba ta gida ta bari in ta dawo sai ta zo har gida ta sameta. Su ba can ciki garin Bauchi Alhaji Yakubu ke zaune da iyalansa yana da rufin asiri tunda yana kasuwancin ne.
Ko a wannan zuwan sai da ya tambayi Mansoor ta ce ya ce yana da buga wasa.
Yana dariya ya ce”Dakyau ai ina bibiyan wasannin shi, wata rana a kasuwa wani abokin kasuwancina Alhaji Ubale na zencensa na ce masa ɗana ne ɗan yayana mai rasuwa ne yana ta mamaki nace masa ya daina mamaki da ya ke ba’a wajen mu ya tashi ba ya na tare dake ne, amman na masa alkwarin duk ranar da ya zo zan kira shi ya gan shi shima yana bibiyan wassanin shi sosai.” Inna Meri ta yi saurin cewa”Ai ya ce zai zo in sha Allahu.”
Alhaji Yakubu ya ce” Ya kamata saboda yara nan duk ba su san shi ba daga masu auran har ƴan matan” Da ya ke matansa biyu ne kuma suna yawan haihuwan kai da kai kuma Allah bai ba shi ɗa namiji ba sai mata sun kai goma bayan waɗanda ma ya aurar.
Inna Meri na Bauchi aka kirata daga can Argungun aka faɗa mata wani kawunta ya rasu da ke zaune a jega ba ta ko gama cin biki ba ta dawo Gombe ta fara Shirin tafiya Argugun daman Mu’azzam na son garin nan domin Inna Meri ta sha zuwa da shi tun yana yaro yanzu kuma yana son komawa sai dai ba lokaci ga aiki ya sa bai samu zuwa ba, Mansoor shi ya nema ma Inna tashar Golf Yaya Halima ta ce za ta rakata Walida kuma jarabawa Bintu kuma ta kara ɗaura ɗamara Baban Inna na ji ya ce ta zo taje ɗin in ta isa ai ta na jin haka ko sallama ba ta zo ma Inna ba. Amman ta tafi da yan biyunta tunda sun saamu hutu suma ɗin Aji sai da yace ba’a za je da su ba Inna Meri ta ce ita ta ce a haɗo kayansu za ta je da su.
Tafiyar Inna shiyar gida ya sa Hajiya ba ta ganta ba har ƙara kiranta ta yi sai ta gaya mata an mata rashi ta na gida sai dai idan ta dawo, sun rabu akan ta na dawowa za ta neme ta Inna Meri da niyar Sati biyu za ta yi su dawo sai ga shi su ne har wata daya yan’uwa sun hanata dawowa Yaya Halima taji daɗin garin ta share kafa ta bar miji da yara Inna Meri kuma duk da ba ta da ƙananan yara hankalinta ya koma gida, ga Halima tare da ita da su Hussaini su da ba su damu ba dakyar su ka bari ta dawo sai da ta yi kwana talatin da biyar.
Bayan ta dawo hutawa kawai ta yi na kwana biyu ta raba tsaraba ta shirya ta je gidan Hajiya Saboda kada ta ɗauka da gangan taki zuwa sai ta iske ba kowa a gidan Hajiya suna Abuja matar marigayi ta fita takaba Mommy kenan.
Haka ta dawo ba ta ganta ba sai ta yi Tunanin kiranta a waya kuma wayar ba ta shiga ba, ashe a gida Hajiya ta manta wayar ta mace ba chaji tunda har da Baaba Uwani suka tafi wajen kwanansu uku acan za’a yi mganar rabon gado ya sa suka ɓata lokaci ma ma ba su dawo ba.
Janafty
Page 20
An raba iya ada din dukiyar da Abi ya mutu ya bari, an kuma raba shi dai dai yadda addini ya hukunta. Tare kuma da malamai da alkalai aka yi rabon a gaban Daddy da yaran duka sai Hajiya har da Yaddiko. Hajiya ma ta samu gida tunda ya bar gidaje da motoci da kuɗi ma su yawa a cikin banki, sannan gidan da Mommy ke ciki ita da Sulaiman suka ci gidan shi kuma ya ce ya bar mata halak malak domin ta cika wasiyar mijinta ta ce za ta cigaba da zama a gidan tun da ga aikinta sannan gefe ɗaya ta ce za ta je kano ta ɗauko ƴaƴan ƴan’uwanta saboda su taya ta zama tunda Inna Ladidi za ta koma gida bayan ta fita takaba.
Kwanan su huɗu ne su ka dawo, Mommy kuma washegari ta bi Jirgi zuwa kano ita da Inna Ladidi za ta raka ta sannan itama ta je gida ta gaida ƴan’uwa da iyaye. Rana ɗaya su ka tafi da Khadi ita ta yi kaduna ita kuma Madiha kwananta uku ne ta bi Jirgi ta koma Lagos Mimi da Hajiya da Daddy da Yaddiko tare sua je kuma tare su ka dawo Gombe gabaɗaya. Ko bayan an gama rabon gadon Mommy ta so ta yi mganar Mimi sai kuma ta fasa a cikin ranta ta kuduri niyar daga kano Gombe za ta sauka sai an san yadda za’ayi daga can. Ba ta ɗauka ma za ta jima a kanon ba sai ga shi ta yi sati biyu daga kanon ne ta biyo Gombe Hajiya ma ba ta san tana tafe ba, tunda ba ta faɗa mata ba ta dai san sun rabu akan cewa daga kanon za ta biyo nan. Mimi kuma ba ta ɗauka zuwan Mommy da wani abu ba,ta ɗauka dai ta biyo ne kafin ta koma Abuja ta kuma ji daɗin zuwan Mommy domin hakan ya bayyana har saman fuskarta.
Zuwan Mommy ya sa Hajiya ta ƙara kiran Inna Meri a waya a nan ne ma take jin labarin ashe ta zo ba su nan Hajiya ta ba ta hakuri ta ce ta bar wayar a gida ne, ba ta je da ita ba amman in ta na gida za ta shigo ko yau da yamman ko zuwa gobe. Ita kuma Inna Meri surutun mutane ne ba ta so sai ta ce ma Hajiya ta bari ita za ta zo, Amman Mommy ta nuna gwara su je da kansu su suke nema bai kamata su tsaya jiran sai ta zo ba. Da haka suka tsara zuwa gidan Wanzamai ba tare da kowa ya sani ba ita kanta Mimi ba su yi mgana da ita ba, ba kuma ta san abin da suke shiryawa ba.
**
WednesDay 24 May, 2022
10:54am.
Gidan Wanzamai.
Inna Meri na cikin uwar ɗakinta zaune saman sallaya ta idar da sallar Walha sai barci ya kwasheta ba ta sani ba sai dai ta ji muryan Walida na ƙwala mata kira da karfi da yasa ta mike a firgice har wuyan hijabin jikinta na shaketa tunda ta taka shi wajen saurin ta miƙe Cikin tashin hankali Ta ce
“Me ya faru Walida? domin ta ɗauka wani mummunan abu ne ya faru ganin Walida a gabanta tana haki sama sama.
Cikin leken falo ta matso Kusa da Inna Meri Lokaci ɗaya tana faɗin”Inna Bali kika yi Inna” Inna Meri ta maimaita” Baƙi kuma?
Da sigar tambaya sai Walida ta karkace kai kafin ta ce”Hajiya ce fa da wata mata suka zo ga su nan a falo suna jiran ki.”
Inna Meri ta yi shuru ta na tunanin wata Hajiyar ce kafin tunaninta ya ba ta Hajiyar Shagamu ce. Ƙirjinta ya amsa ji kake Ras! amman sai ba ta nuna ba illah kallon Walida da ta yi kafin ta ce” Ki kawo musu ruwa.” daga haka ta gyara zaman hijabin jikinta ta fita falo, abun ya kara ɗaure mata kai ganin Hajiya da wata mata ƴar gayu sai da ta zauna anan kasan Cafet suka gaisa da Hajiya da matar sannan Hajiya ta kalleta tana faaɗin “Sai kika gan mu ko? Murja ce ta ce gwara mu zo kawai, mahaifiyar Binta ce matar marigayi.”
Sai da Hajiyar ta faɗa sannan ta gane ta gani ɗaya ta taɓa yi mata kuma ganin ba na cikin kwanciyar hankali ba ne. Cikin gyaɗa kai ta kalleta kafin ta ce”Allah Sarki Hajiya ya karin hakuri? Allah ya jikan sa da rahma.”
Mommy ta amsa da Amin Amin ta na ƙare ma falon kallon tsab tsab daman Walida tun safe ta gyara shi ta share Inna Meri na cikin faɗin da basu wahalar da kansu ba,da ita ta zo gidan Hajiya. Mommy ta yi mirmishi kafin ta ce”A’a ai muke so gwara mu bi yo sahu, ni na ce ma Hajiya ta bari mu za mu zo da kanmu.”
Inna Meri ba ta ce komai ba, tunanin ta ɗaya yanzu magana zai yaɗu acikin gidan da zuwan su Hajiya ba ta son abun mgana.
Walida ta kawo musu Pure water a filet Hajiya ta yi mata sannu ta na tambayan Bintu tace ta na gidanta, daganan ba ta zauna ba sai ta zari hijabi ta fita. Tana fita da ga shashen Magajiya su Gaje da Harira sun yi zaman dirshan suna kuskus suna ganinta sai su ka yi shuru sai ta yi kamar ba ta gansu ba, ta yi ficewarta daga gidan gidan Dije mai waina ta shiga wajen ƙawarta Bahijja.
Mommy ce ta sha ruwa Hajiya kuma ta ce cikinta ya cika sai dai kafin su tashi tafiya, Hajiya mike kafarta ta yi tana faɗin”Meri haka waje ya sauya,gabaɗaya na kasa gane gidan sai da muka yi tambaya bayan kuma mun shigo shima dai gidan duk ya sauya.”
Inna Meri ta ce”Eh an yi gyara sosai an raba mana bangare da su Gaje mun koma farko, nan ma ciki an raba bangarena da na Magajiya aikin duk na Baban Inna ne.”
Hajiya ta washe baki kafin Ta ce” Masha Allah Allah ya sa albarka.” Inna Meri ta amsa da Amin. Kafin shuru na wani lokaci sai can Hajiya ta muskuta kafin Ta ce.
“Meri magana ce mai muhimmanci ke tafe damu, ina fatan megidan na nan?
Inna Meri Ta ce”Gaskiya ya fita amman dai ba nisa ya yi ba ina kyauta ta zaton yana kan hanyar dawowa.”
Sai Hajiya ta kalli Mommy kafin ta ce” kin ji Murja, ko za mu jira har ya dawon ne?
Sai Mommy ta ce”Hajiya shi yaron fa?
Sai Hajiya ta kalli Inna Meri lokaci ɗaya tana faɗin”Meri har da shi Mansoor ɗin Murja ke son gani za ta sauke nauyin marigayi ne da ta ɗauka.”
Inna Meri ta yi kasaƙe kafin ta ja gauran numfashi Ta ce”To sai dai na kirasa a waya Allah yasa yana kusa.” Ta faɗa lokaci ɗaya tana miƙewa Walida ta ke kira sai taji Shuru sai Mommy ta ce in wayarta taje nema gata nan saman Kujera. Sai ta ɗauka ta shiga ciki da yake Inna Meri ba ta da duhun kai ta iya dubo suna ta yi kira.
Baba Ɗanjuma ta fara kira ta tambaye shi ko yana ina ne? ya ce ga shi ma a kofar gida sai ta ce ya kariso suna da baƙi.
Baban Inna kuma kira byu ta yi masa bai dauƙa ba tana shirin ijiye wayar ta fito sai ga kiran shi Muryan shi a Cunkushe ya ce mata ya ɗan kwanta ne, ba ji kiranta daga farko ba Itama Innan muryanta a cushe ta ce ya zo gida tana son ganin shi, bai kawo komai ba ya ɗauka ko wani abu ne ya taso, bai taɓa tunanin wani abu daya danganci yarinyar da sanadinta mafarkinsa ya ruguje ba.
Inna Meri na dawowa falon ta faɗa musu Hajiya ta kira su a waya sai ga Baba Ɗanjuma shi tun a waje ma ya ga mota, Gaje ce ta shigo samun ruwa wajen Magajiya ta ga shigowar su Hajiya shi ne ta je ta kira Harira suna ta tsegumin son sanin su waye suka zo wajen Meri masu kudi haka sun tambayi Magajiya ta ce ita bata sani ba, Walida kuma da ta fito sanin halinta yasa ba su tambayeta ba domin su san ba za ta gaya musu ba. Kuma ganin Baba Ɗanjuma ya shigo kuma ya wuce bangaren Inna Merin da sauri ya sa su ka san tabbas da wani abu. Kuma suna son sanin abin da ke faruwa amman ba hali ita kanta Magajiya sai tunane tunane take yi Hajiyar ne take ganin kamar ta taɓa ganin ta sai dai ta rasa in da ta santa amman acikin ranta tana tunanin kamar akwai wani abu daya danganci zuwan da yarinyar nan mai aiki a gidan tibi ta yi, jikinta na bata kamar taron ya na da alaqa da ita.
Cikin girma da arziki Hajiya suka gaisa da Baba Ɗanjuma yana zauna a kasa kusa da Inna Meri Mommy ma ta sauko ƙasa ta zauna lokaci ɗaya ta gyara zama Inna Meri ce ta faɗa masa matar Marigayi ce shima nan take ya yi mata gaisuwa ta amsa kafin ta ɗora da faɗin” Bisa abin da ya faru shekarun da su ka gabata ne tsakanin yaron ku da ƴar mu Mimi wanda har ya jawo rashin fahimta abubuwa suka faru da ba su yi ma kowa daɗi ba, dalilin haka ya sa sai zumunci ma ya yanke gabaɗaya, saboda kalaman major a kan yaron wajen ku sai dai wallahi tallahi kun ji rantsuwan Musulami Habibi ya rasu ana gobe za mu zo Gambe da niyar ya zo ya baku hakuri ya kuma jemi gafaran Mansoor sai dai Ubangiji bai amince ba yana gangaran mutuwa yana jaddamin wasiyar na nema masa gafara a wajen sa daku iyayensa shi ne naga ya dace na tako da kafata na zo na wakilce sa don girman Allah ku yi hakuri, ku yafe abunda ya faru kuskure ne kuma kowani ɗan adam ba ya wuce kuskuren sa domin tara yake ba mu cika goma ba. Ku duba Allah ku yafe masa tunda ba shi a duniya nan kuma kafin rasuwarsa ya yi nadama matuka har ya so ya nemi gafaran abin da ya faru da kansa.”
Mommy ta dakata tana sharan ƙwalla da gefen mayafinta kafin ta cigaba da faɗin.
“Habiba ya cika a gabana sannan da Mimi a bakinsa ku yi hakuri ku yafe masa.”
Baba Ɗanjuma ya yi saurin tare ta da faɗin”Haba Hajiya ki daina kuka, wallahi ba komai tun a lokacin mu ba mu riƙe ku a ranmu ba mun yafe Allah ya yafe mana gabaɗaya, shi kuma Allah ya jiƙan sa da rahma ya sa ya huta.”
Gabaɗaya su ka amsa da Amin Inna Meri Ta ce”Ai na gaya ma Hajiya tuni wannan ya wuce a wajen mu tuntuni.”
Baba Ɗanjuma Ya ce”Kwarai ma kuwa kuskure duka aka samu tun a wancan lokacin, rayuwar duka nawa take ma Allah na tuba? Allah dai ya sa mu dace ko da ba ku zo ba ma Hajiya babu komai.”
Hajiya tace”Hakane mun gode kwarai Allah ya bar zumunci Amin.”
Mommy kuma kanta na ƙasa Ta ce” Ina son ganin Mansoor domin shima na bashi hakuri.” Inna Meri tabce” Yana hanya zai zo in sha Allahu.”
Sun yi shuru na wani lokaci sai Baba Ɗanjuma ya miƙe da niyar fita sai Hajiya ta kira shi ya dawo ya zauna.
Mommy ta kallah ta ga kuka take yi sai ta girgiza kai kafin ta ce”Meri tun kwanaki na faɗa miki kafin rasuwar Kabiru ya janye kalamansa kan Mimi ya ce ya amince in har ta na son Mansoor to a aura mata shi saboda farincikinta”
Inna Meri ta yi shuru kafin Ta ce”E, kuma ai tun a lokacin na gaya miki ni ba ni da matsala, in ma da matsala yana wajen Baban inna ne”
Baba Ɗanjuma Ya ce”Gasikiya sai dai a jira a ji ta bakinsa ko ba haka ba Hajiya?
Hajiya tace to shike nan sai a jira ɗin, nan Hajiya ta cigaba da ga ya musu saboda Mansoor har yau Mimi ta kasa kula kowa kuma har gobe yana ranta shi take so farincikinta na tare da Mansoor.
Inna Meri ta yi shuru ba ta yi mgana ba domin ta san halin abin da ta haifa shi kuma Baba Ɗamjuma kai tsaye Ya ce”Dama mu ba muki ta ba, matsalan daga bangaren kune amman tunda ku da kanku kun amince sai ayi mgana da shi Mansoor ɗin sai muji ko yana ra’ayinta har yanzu, mu namu fatan alheri ne kawai.”
“Assalamu Alakaimu.”
Muryan Mansoor ta katse Baba Ɗajuma da zence da ya kwararo, gabaɗayansu suka ɗaga kai ya na tsaye a kofar ɗakin bayan ya ɗaga labulen ɗakin, sai dai fuskokin da ya gani ne ya sa bai shigo ba.
Biri daman ai ya yi kama da mutum, ya ga mota a kofar gida sannan ya shigo ya ga su Magajiya na binsa da wani kallo ya zo kuma ya yi mummunan gani. Da ga Hajiyar har Mommy ba wacce bai gane ba, shi ya sa ya wani ƙara haɗe rai kamar an aiko masa da sakon mutuwa. Ƙokarin ma komawa da baya ya ke yi Baba Ɗanjuma ya kira sunanshi ya amsa ya kuma ba shi Umarnin Shigowa.
Kamar ma ba zai shigo ba ya na ta tukubiri ya cire takalmin kafarsa ya shigo daga barci ya tashi daga shi sai jallabiya mai ruwan kasa da dogon wando. A kofar ɗakin ya durkusa yana gaida su Inna da kwana bangaren su Hajiya kuma ko kallo kamar ya ga kashi. Su kuma suna ta kallonsa da mamakin sauyawarsa ya kara girma fiye da tunaninsu Hajiya ma ta fi mamakinsa duk ko a baya ta san shi da tsawo amman bai kai haka buɗewa da kiba ba, ita kuma Mommy daman ba wani ganinsa ta yi sama da sau uku ba, ta dai san ya samu bambamci mai yawa tsakanin baya da yanzu.
Inna Meri ce ta kalle shi kafin Ta ce”Ba ka ga baƙi bane? Ko ba ka gane su ba ne?
Kai tsaye ya ce”Na gansu Inna, kuma na gane su.” Ya faɗa cikin saka mamaki a cikin ganin nasu a gidansu kafin ya cigaba da faɗin”Naga kakar Mimi naga mahaifiyarta abun mamaki me ya kawo su? ko sun manta cewa babu sauran wata alaqa a tsakaninmu ne?
Ya faɗaa ya na mai kallon fuskokinsu ɗaya bayan ɗaya sai kuma a cikin su aka rasa wanda zai fara magana daga Hajiyar har Mommy ya yi musu ƙwarjini.
Sai Baba Ɗanjuma aka bari da rattaba masa bayanin da Mommy ta yi musu bai ko gama saurara ba ya kausasa murya Ya ce.
“Baba.”
Baba Ɗanjuma ya amsa da na’am domin shi kanshi yasan akwai rigima. Cikin shan alwashi ya cigaba da faɗin” Na rantse da wanda raina ke hannunsa ba zan iya yafe masa. Shari’a da ni da shi sai a gaban Ubangiji.” Ya karishe faɗa ya na jin wani irin nauyi acikin ƙirjinsa an ma raina masa wayau bayan an gama tozarta shi an lalata masa rayuwa shi ne za’a zo ana gaya masa mganar banza.
Uban kuturu to ya yi kaɗan ma yana jin Hajiya ta fara masa nasiha tana faɗin “Shi kabirun ma ya rasu ba za ka yi hakuri ba?
Kai tsaye Ya ce”Kowani mai rai ai mamaci ne, nima wata rana zan mutu za muje gaban Ubangijin da ya yi talaka da mai kuɗi a gabansa sai ya fitar min da haƙƙina”
Daga nan sai jikinsu ya yi Sanyi Mommy na jin haka sai ta fashe da kuka tana faɗin”Wlh ya yi nadama don Allah ka bar komai ya wuce.” Kamar a fusace Ya ce” Ba komai ba ne ballantana na bar shi ya wuce, rayuwata gabaɗaya ne aka lalatamin kinga kuwa ba kamar a bar shi ya wuce ba ne. Akwai hisabi tsakanina da wannan mutumin kuma yadda ya sha alwshin yarsa ta fi karfina nima yanzu na fi karfinta da duk abin da ya ke takaman tana da shi.”
Hajiya ta ce”Ka yi hakuri ba laifin Binta ba ne, har gobe tana sonka ka amince ka aureta sai ku manta baya ku fuskanci gaba.”
“Ni ba ni da kudin auranta. Har yanzu ni talaka ne, sannan mahaifina har ya mutu a kauye ne kuma har gobe ni agola ne a gidan nan kinga kuwa har gobe ban chanchanta ba.”
Ya ba ma Hajiya amsarta sai su ka kasa mgana Baba Damjuma ne ya ce” Mansoor ka yi hakuri ka ji ko! Ko Allah muna yi masa laifi ya yafe mana.”
Inna Meri ta amsa da cewa”Kuma ba’a son kafiya ba a son a yi ta ba ma musulmi hakuri ya nuna kafiyarsa.”
Kansa na kasa ya na jin wani iri zuciyarsa na wani irin zafi sai yaji kamar a yanzu komai ke faruwa. Taruwa suka yi da na su iyayen da na shi suna ta ba shi mgana.
Mommy na kukan ta na fadin farincikin Mimi ya na tare da shi ne ya taimaka mata don Allah. Inna Meri na ta faman fadin ya Sausaauta ma kamsa in kuma ya ciza ya hura saboda kada ya zo ya yi nadama.
“Inna na yi rantsuwa, kina so na yi azumin kaffara ne?
Ya faɗa yana kokarin saka wani tunani acikin ranshi, shi ya kasa ma sarrafa yanayin da yake ciki a lokacin Mommy kuma ta tare shi da faɗin”Shima har azumin kaffaran ya so ya yi Allah bai amince ba.”
Mirmishi ya yi mirmishin da ko inna da Baba sun jima ba su gan shi cikin wannan Mirmishin ba.
“Na amince zan yi azumin kaffara a kanta, zan aure ta.”
Hajiya da Mommy su ka haɗa baki wajen fadin”Alhamdulillah.”
Inna Meri kuma kallonsa take yi domin a jikinta taji ba ta yarda da maganarsa ba.
Baba Damjuma kuma na ta saka albarka ya na fadi “Ko kai fa? Ai gwara ka manta komai.” Mommy ta rike Hannun Hajiya tana fadin”Habibi zai yi farinciki yau ya ga Mimi ta samu abin da take so.”
Munafukin mirmishi ya yi kafin ya ce”Kafin nan ina da wasu sharuɗɗa guda huɗu, biyu zan faɗe su kafin aure. Biyu kuma zan kafa su bayan auran.”
Ba tare da tunanin komai ba Mommy ta ce ba komai sun amince nan take Aji y ace zai tura ma Mimi sharudɗan ta wayarta da amincewarta zai yi amfani daga nan ya tashi ya fice kuma bai nuna alamun wasa yake yi ba kuma bai nuna alamun ya yafe ba.
Inna Meri sai ta rasa gane in da ya dosa a jikinta taji kamar ya na shirya wani abu.
Hajiya da Mommy suna ta godiya,Inna Meri ta rakasu har wajen mota jikinta duk ya yi sanyi Magajiya da su Gaje kamar za su rasu saboda son jin gulma ai tunda suka ga Mansoor suka san babban abu ne ke faruwa ita kuma magajiya ta so ta gane Hajiya Shiyasa Inna Meri na dawowa daga rakasu ta tare ta da Fadin”Ikon Allah wannan kamar Hajiyar da kika yi aiki a gidanta ko?
Inna Meri ba ta iya karya ba sai tace mata Eh ita ce. Daga haka ta wuce bangarenta Magajiya ta yi wani munafukin dariya kafin ta ce”A yi dai mu gani.”
Gaje kuma fadi take yi”Kwanaki yar ta zo yau kuma kakar da kanta anya lafiya kuwa?
Harira ta ce”Da fa wata mgana, duk boyen su dai ai za ta bayyana har mu sani.”
Duk Inna Meri na bangaranta ta na jinsu ta ma rasa abunda ke yi mata daɗi.
Baban Inna yafi ba ta mamaki wai ya amince cikin sauki haka?.
Ko da ta san shima ya na sonta ba ta ɗauka lamarin na shi zai zo da sauki haka ba.
Baba Danjuma daganan masallaci ya tafi saboda ana ta kiran sallah itama daga wajen ta ɗauro alwala ta shiga daki ta yi nata sallar.
Mimi ta dawo wajen aiki ta ga Hajiya da Mommy ba sa gidan da ta yi ma baaba uwani mgana sai ta ce sun fita har ga Allah ta ɗauka suna gidan Daddy ne yasa ba ta Damu ba. Sai kawai ta kwabe kaya zafi ya isheta ta koma ta kwanta tana duba wayarta kuma Hoton Aji ta ke kallo har barci ya ɗauketa. Sai da taji muryan Mommy na kiran sunanta sannan ta farka.
Ta ga Mommy na ta fara’a amman ba ta ɗauka wani abu ne ya faru ba.
Ce mata ta yi ta tashi ta yi sallah tana tashi ta shiga tiolet wajen Mommy ta gyara mata wayarta sai ta ga Hoton da take kallo tunda wayar nata ba tsaro.
Mirmishi ta yi kafin ta ce afili”Kin kusa samun abin da kike so ƴata.”
Daga haka ta ijiye mata wayarta ta fita zuwa ɗakin da ta sauka itama kwabe kaya tayi sai da ta yi wanka sannan ta yi sallah.
Dukkansu suka hadu afalo su ka ci abinci har da Mimi sai bayan sun gama ne Mimi ta kalle su kafin ta ce”Mommy ina kuka je ne?
Mommy ta yi mirmishi kafin ta ce”Gidan surukan ki mana”
Cikin mamaki Mimi tace”Gidan surukai na kuma? Ta faɗa da sigan tambaya.
Mommy ta kalli Hajiya suka yi dariya kafin Hajiya ta maida kallonta wajen Mimi dake musu kallon tuhuma da mamaki.
Cikin tausasa murya Hajiya ta ce” Eh mana mun je neman gafara abin da ya faru ne a baya.” Mimi ta yi wani iri da fuska kafin tace”Ban gane ba”
Saboda ita dai ba ta san da mganar ba.
Nan Hajiya ta zayyana mata komai sai ta tuna lokacin rasuwar Abi Mommy ta yi ta jadadda cewa kafin rasuwar Abi ya so ya zo gombe ya nemi gafaran Hajiya ashe ciki har da Ajinta a ranta sai taji wani irin sanyi da Sauri tace”To shi ya ce yafe din Hajiya?
Hajiya tace”Bai yi mgana ba amman mun fahimci yafiyar sa tunda ya karɓi tayin mu ya amince zai AURE KI.!”
Mimi ta waro ido cikin mamaki kafin tace”Aure kuma?
Cikin matukar mamaki da kaɗuwa ta yi tambayan.
Wannan karon Mommy ce ta ja ƴarta Jikinta tana lallashinta lokaci ɗaya tana warware mata yadda komai ya fara ta karishe da Flfadin”Habibi kafin ya rasu ya yi ta nanata min mi yi miki abunda kike so, ni kuma nan duniya na tabbatar da yaron nan shine farincikin ki Hajiya ma ta tabbatar min da haka, kuma silan shi ne kika sa ba ma kowani namiji dama ciki har da ɗan uwanki Jaheed kina son shi kina kaunarshi tunda kuma har ya janye kalamansa kafin rasuwar shi kina da damar ki yi rayuwar farinciki” Kafin Mommy ta gama mgana ta fashe da kuka kamar wata karamar yarinya sai ta ji kamar a mafarki.
Cikin kuka take kallon Mommy Lokaci ɗaya tana faɗin”Aure fa Mommy? Kuma Aji ya ce ya amince da bakinsa?
Mommy ta gyaɗa mata kai kafin ta ce” Eh duk da yace ya na da Sharuddansa bai faɗa mana ba ya ce zai tura miki da kan shi in kin amince shike nan zai yi azumin kaffara.”
Mimi ta ji kamar numfashinta zai ɗauke cikin wata irin murya ta ce” Mommy ni fa na hakura tun lokacin nan da kin faɗa min da ban barku kun je gidan ba.” Hajiya na yar dariya ta ce”Ba ki son shi ne? In ba ki so ba shike nan ba ko ba haka ba Murja”
Mommy na taya ta dariya ta ce”To tunda ba ta so miye amfani Hajiya? daman daboda farincikinta ne” Mimi na jin haka ta yi saurin cewa”Mommy…!
Sai kuma ta kasa mgana sai kawai ta tashi da gudu ta shige koradin in da ɗakinta yake ta na Rufe fuska jinta ta ke yi kamar tana yawo a saman iska. Ta shiga ɗakinta tayi tsaye zuru ta na tunanin ko dai mafarki ne har marin kanta sai da ta yi. Ashe ashe burinta zai cika? Ashe ashe za su iya zama ma’aurata ita da Aji.
Tsalle ta buga lokaci ɗaya ta haye gadonta tana birgima nauyin da ke saman Kirjinta ya na sauka a hankali farincikin da take ji ya sa ta manta ma a inda take.
Mikewa ta yi ta fara uban tsalle asaman gado ta na cilli da fillows ɗin kan gado, ji take yi kamar ta kurma ihu duniya su san yau ta na cikin farinciki.
Ita kaɗai sai dariya ga hawaye sannan ta koma ta rufe fuskarta da bakinta tana yar dariya ta yarda farinciki na saka mutum ya yi hauka bai sani ba.
A falo kuma bayan fitan Mimi Mommy ta ce”Mimi na son yaro nan Hajiya, ni kuma sai naga kamar shi ya daina sonta ko abunda Habibi ya yi masa ya shafe kaunarta a cikin zuciyarsa ne? Hajiya ta ce”Ba na jin haka, ina da kyakyawan yakinin kamar yadda ba ta manta da shi, shima bai manta da ita i ba, in har ya daina sonta me yasa ya kasa aure? Sannan me yasa ya amince da bukatar mu a karon farko? Mommy ta yi shuru kafin ta ce”Haka ne to ya zamu bullo ma Alhaji Hamza da sauran ƴan’uwanta?
Hajiya ta ce”Ki bar ni da shi Hamza su kuma yan’uwanta in mgana ta tabbatar sai ki faɗa musu iyaka dai su kawo dogon turancin su na yaran zamani kada ki sauresu tunda dai Binta na son wannan yaron da ikon Allah sai ta samu abin da take so.”
Da haka su ka cigaba da tattaunawa su tunaninsu bai kai ga in da tunanin Mansoor ya kai ba, a ran Mommy sai da ta jinjina zafin kan Mansoor ba ta ɗauka haka yake ba.
Mimi ranar kasa barci ta yi sai dai barawo kila ya sace ta, washegari haka ta tashi cikin annushuwan da ta jima ba ta aciki, Mommy da Hajiya su ka fara tsokanarta da Amarya tana jin kunya Baaba Uwani na wajen ta gyara zama ta na fadin”Wai ni Hajiya kun bar ni cikin duhu, Aure Hajiya binta za ta yi ne ban sani ba? Hajiya na yar dariya ta ce”Mu na saka ran haka”
Tuni Baba Uwani ta saki guɗa sai da ta rangaɗa guda uku Mimi na jin haka tayi waje tana dariya daman a shirye take wajen aiki za ta je. Baaba Uwani har haraba ta bi ta tana yi mata kirari da Amarya hak nnan ta zazzage mata sauran kuɗin jakarta Baaba Uwani faɗi take yi” Ko waye wannan ya yi farar sa’a, ya tsinci dami acikin akala kyakyawan mace a jari ce ballantana Binta Fatima take uwar ado da kwalliya”
Mimi farinciki ya sa ta kasa rufe baki haka taja motar ta zuwa wajen aiki ranar duk wanda ya ga Mimi sai yace me ya faru da ita bakinta yaƙi rufuwa ko a wajen karanta labarai haka ta ke ta washe baki kamar gonar auduga in kuma akace me ya faru sai ta kara sakin dariya ta kasa cewa komai.
Amman yini ta yi sadaka bakin Jakarta ta ɓude, daman can ba ta da rowa amman kyauta ranar na musamman ne gabaɗaya dalibai yan Inteen sai da ta saka musu Data ma’aikatan kuma ta bi su 2k kafin kuma ta kariso daman ta tsaya a banki ta cire kudi ta yi ta ba da sadaka a hanya kafin ta karisa wajen aiki. Rukky na bangaren su taji Labarin Hajiya Mimi na ta rabon kuɗi sai ga shi ta garzayo, ita kanta yanayin da ta Mimi sai da ta rike baki tana faɗin”Faɗa min me muka samu ne? Mimi ta saki kayattaciyar dariya kafin ta ce”Za ki ji in lokaci jin ya yi.”
Yadda ta faɗi mganar muryanta cikin annushuwa ya sa Rukky ta zargi wani abu.
Cikin juya ido ta ce”Ko dai ko dai, kun daidaita da Jaheed an saka rana, aure kawai mu ke jira.” Mimi na yar dariya ta ce”Kin faɗo kasa warwars kinsan ai ba zan iya auran Jaheed ba.”
Rukky ta ce”Ke ce dai da Iyayin ki, ina laifinsa Allah na tuba.”
Mimi na jinta sai ta yi mata shuru Saboda ba ta san mganar Jaheed wanda har yanzu bai daina damunta da magiyan ta amince masa su yi aure. Dannan duk da bakinta na rawan ta yi ma Rukky zencen sai ta kasa saboda ba ta san matsayinta ba an ce ya ce sai ya ba da sharuɗɗa kuma ya ce ita zai turo mawa, to a ina zai samu lambar wayarta? Shiyasa ta yini duba wayarta amman ba wani sakon da ya shigo, Haka ta koma gida ta na wannan annushuwan ta iske ma Yaddiko a gidan ta zo, Hajiya da Mommy sun fi kowa sanin sirrin annushuwanta da walwalanta sai da Yaddiko ta tafi Hajiya ta tasa ta da tsiya kala kala tana tsokanarta Mommy kuma na gefe Flfarinciki ya cikata har kwallah Sai da ta share tana faɗin”Allah ya jikan ka Habibi, ga Mimi yau tana cikin farinciki.”
Har washegari ba ta ga kira ko saƙo ba sai ma Jaheed dake damunta da kira da turo saƙo, ko da wani lokaci taji karanta wayanta jikinta na rawa take dubawa sai ta ga ba wanda ta ke tunani ba ne, ganin an kwarari sati sai jikinta ya fara yin sanyi kada ya zo murnanta ya koma ciki.
A daran ta kusa kai ɗayan dare ba ta yi barci ba, da ta gaji ta ta shi ta yi salla raka’a huɗu sannan ta koma ta kwana da asuba da ta tashi ta yi sallah sai ta jawo wayarta za ta yi karatu nan ta ga an tura mata da saƙo
gabanta sai da ya faɗi ganin sunan shi domin ta yi saving din lambar shi.
“Aji Nah”
Hannunta na rawa zuciyanta na bugawa Fat! Fat! ta buɗe saƙon tana karantawa sama da kasa ta na ma kuskure wajen karatun, abunda ya rubuta ne bai wani ba ta mamaki ba sanin halinsa a wajenta Sharuɗɗan nasa ba su yi mata tsauri ba.
Da sauri ta mike ta fita daga ɗakin zuwa ɗakin da Mommy ta sauka ta isketa ta idar da sallah ta na Lazimi. Gabanta ta karisa ta zauna tana faɗin”Gud Morning Mommy.”
Mommy ta amsa mata da gyaɗa kanta Mimi sai ta mika ma ta wayar tana faɗin “Aji ya turo min saƙo” Da Sauri Mommy ta karɓi wayar a hannun Mimi ta danna wayar haske ya kawo sai ta shiga ta karanta saƙon kamar haka.
“Sharaɗi na farko bayan sadaki da ɗaurin aure aba za’a yi wata bidi’a da auran mu ba, sannan sharaɗina na biyu shi ne a cikin gidanmu za ki zauna tare da mahaifiyata domin har gobe ba ni da kuɗin da zan iya siyan gidan da ƴar Major kamar ki za ta zauna ba”
Ina jiran Amsar ki, domin da amincewarki zan yi amfani.
“Mansoor Aji.”
Mommy ta ɗago tana kallon Mimi kafin ta ce”Ban gane ba shi da gidan da za ki zauna ba? Ba ƙwallon kafa kika ce yana yi ba?
Mimi ta gyaɗa mata ai kafin ma ta dire mgana Mommy ta mika mata wayarta lokaci daya tana faɗin” Ban yarda ba, ko da Habibi ya amince da auran nan kafin ya rasu bai ce ki je in da zaki wulakanta ba farincikin ji yake so Mimi, ki amsa masa da cewa ba ki amince ba, kin dai amimce da sharaɗin farko amman na biyu ya sauya tunani” Mommy na ta faɗa Mimi ta dukar da kai ta na tubutu a wayarta sai da ta gama sannan ta ɗago tana faɗin “Mommy mi ye ciki? Ai ba daji zai kai ni ba, tare da mahaifiyarsa zan zauna ba matsala Mommy.” Baki sake Mommy ke kallonta kafin ta ce” A ina za ki zauna a wannan gidan? To ni dai ban ga wajen zama ba.”
Cikin yar shagwaɓa Mimi ta nuna ma Mommy fuskar wayarta kafin ta ce”Ni fa na tura masa na Amince.”
Mommy ta warce wayar tana gani kafin ta waro mata ido tana faɗin” Ba ki da hankali ne? Ta fada cikin Faɗa sai kawai Mimi ta kwantar da kanta a saman cinyarta tana faɗin” Mommy ba farincikina kike so ba? Mommy ta gyaɗa kanta kafin ta samu zarafin mgana Mimi ta yi saurin cewa”To ki amince, zan iya za ma a ko’ina in dai zan samu abin da nake so abin da na ke so Aji ne, ba wani abu na shi nake bukata ba shi ɗin nake so.” Sai Mommy ta kasa mgana amman ta na hasko in da Mimi za ta zauna a wannan gidan ne, amman kalamanta ya sa bakinta ya mutu.
Hajiya ma da ta ji abin da Mansoor ya ce sai ta nuna ba komai duk in da yake son ya ijiyeta hakkinsa ne kuma ta da tabbacin Meri za ta yi ma Binta rikon ƴa ce ba suruka ba.
ƙarshen littafi na ɗaya.
Janafty
Wed Aug 14 2024