Hadin Kai Na Asma Baffa
Official
By
AsmaBaffa
BISMILLAH
Alhmdllh fans Allah ya kawo mu sabon Novel,Allah yasa mu fara lfy mu Gama lfy,Kuma Allah ya bada ikon amfani da fadakarwarsa.
Pls Sharhi nake so da Haka zanfi Jin dadi typing,Kuma zanyi kokarin yiwa kowacce reply inshallah.
Son Kai zanyi wannan page Na ASMABAFFA FANS CLUB ne, ku zan fara bawa.😍😍😍💋💋💋.
Gombe state Kauyen Dingawa Babban kauye ne kusan ma kamar Local Government ne Amma ba a bashi LGA ba, garine na fulanin asali kana Shiga ba sai an fada maka ba.
Fadila Tahir shine cikakken Suna na,Tahir Adam tukur shine Sunan mahaifina,Tahir Adam tukur Asalin fulani ne mu Amma yanzu ba shanu sun Kare,Tahir Su uku ne duk maza iyayensu suka Haifa Wanda har yanzu Suna Raye kakanni na na wajen uwa Dana uba duk ba Wanda ya rasu suna da ransu, Babana shine Babba wajen iyayensa daga shi sai kaninsa kawu Salisu da kawu Usman, gaba daya Allah ya wadatasu Alhmdllh a kauyen Nan Babu masu kudinsu,harkar noma da siyar da kayan masarufi ne sanaarsu,Babana Tahir har mota kurkura da Golf yake dasu duk Ana jigilar Kai Kaya kasuwanni daban daban,Kawu salisu ma Yana da kurkura,Haka Iyayensu Baffa da Yafendo suna Jin dadi ba yunwa ba rashin sutura,sai abinda suke so, daga kakannina har iyayenmu duk sun je aikin Hajji,mune kawai yaran bamu je ba.
Suna da matukar biyayya sai abinda kakanninmu suka tsara shi sukeyi,Tahir da kannensa duk auren zumunci akayi musu,Salisu da Usman matarsu daya Basu Kara aure ba,Salisu Yana da Yara Biyar manya samari guda biyu Mahmoud 28yrs da Umar 26yrs samarine kyawawa farare kasancewar Family dinmu kaf Babu Baki kowa fari ne tas sai dai wasu sunfi wasu fari.
Bayan Umar akwai mace wacce mate Dina ce Saratu18yrs,sai Zainab,da Kuma Abida Yar auta.
Kawu Usman kuwa yaransa biyu Rak Matarsa Bata haihuwa sosai Duk Mata ne Aisha da me Sunan Yafendo Fatima Ana ce Mata Mama.
Babana Wanda shine Babba Tahir Matansa biyu Babata itace ta farko da akayi Masu hadin zumunci Hajiya Hadiza muna kiranta da Hajiyarmu,Bayan Sunyi aure Ta haifi Salman shine 28yrs saurayi saan Mahmood ne Kuma abokai ne,sai kaninsa Musa saan Umar 26yrs, sai Ni Fadila Yar auta a wurin Hajiyarmu Wanda Kuma Ni kadai ce mace a gidanmu,Sai kishiyar Babar mu Haj Balki Amarya tana da Yara hudu Amma duk maza ne Kuma yarana ne kanana Babban 15yrs Abdullahi,Ramadan 12yrs ,Shahid 9yrs sai Ahmad autanta a yanzu 5yrs.
Duk da a kauye muke muna zuwa makarantar Gomnati da Islamiyya,Haka Salman da Musa tare da yaran su Kawu Salisu duk sun Gama HND a garin Gombe Sunyi service Kuma yanzu aiki ake nema musu sannan sai suyi aure Amma har yanzu aiki Bai samu ba sai da hanya Babba.
Ni Kuma na kusa candy muna Ss3 jarabawa zamu zana ta fita,sauran kannena suna secondary wasu primary,muna da kokari gaba daya danginmu Babu dakiki,Sabo da Kawu Usman Yana dauko mana Yan bautar kasa iri iri suna koya Mana turanci karatu da rubutu shi yasa muka iya turanci duk da cewar ba kamar masu yin makarantar kudi ba,ko mutanen birni,iyayenmu suna son juna suna da hadin Kai Amma duk da Haka mu yaransu ba a fiye Zama lfy ba,sabo da munafunce munafunce irin na dangi musamman iyaye Mata su ke haddasa fitina iri iri.
Hajiyarmu Allah yayota Masifaffiya ce number 1 a kaf kauyen Nan an San da zamanta sabo da masifarta,har mu yaranta Bata raga Mana,ita Bata fiye tsokana ba Amma idan aka tabo ta ba mutunci,shima Babanmu Tahir Abbu balainsa yayi yawa Babu Wanda ya kyale Amma Kuma Yana da Dan saukin Kai,ga addini,Kuma Yana da nutsuwa kamar Hajiyarmu matsalarsu rashin Kara da kau da Kai komai masifa.
Karanta Littafin Idan an Cizaa nan
Kishiyar Babarmu wacce muke Kira da Anty ita Kuma tana da hakuri gata Shuru Shuru sai kisan mummuke,a boye take shuka tsiyarta ga tsokana,shi yasa kullum fadansu baya karewa dare da Rana Amma kowa mutan gari laifin Hajiyarmu ake gani Ana tunanin ita take zalintar Anty sabo da ita Bata kyalewa idan anyi mata.
Babanmu kuwa shima yafi ganin laifin Hajiyarmu,shi yasa ya tsaneta ya tsanemu mu yaranta,Yaran Anty da Anty yake kauna.
Matan su Kawu Salisu kuwa magulmata ne su ke haddasa rashin zaman lfy a dangi,Kuma Kakanninmu sunfi kaunar Matan Kawu Salisu da Usman sai Anty da yaransu,basa kaunar Babarmu ko kadan,muma yaranta abin ya shafemu basa kaunarmu,Hajiyarmu Har danginta ba wani sonta suke ba sabo da halinta na Saurin fada da masifa,Bata da kawaici iyayenta kadai ke Dan sonta,muma kakannimu na wajen uwa basa wani sonmu Wai bamu da kunya Yan iska ne mu sabo da kawai muna karatun boko mun Dan waye muna Yar kwalliya mun banbanta da mutanen kauyen shine kawai suka ce mu Yan iska ne Haka mutanen gari ma Ware mu akeyi,kawayena kullum zagina da gulmata sukeyi akan nace zanyi University bazan yi aure ba sai naci da biro, Hajiyarmu tana daura min tallan Dafaffiyar gyada Ina kaiwa makarantar boko da ta yamma,sannan Ina sai da goro da Sassafe kafin na tafi schl sai nayi tallan goro,Sabo da Abbu baya son Hajiyarmu Bai Hana a daura min tallan ba,Amma yaran Anty hanawa yayi a Dora musu talla.
Takaitattun matsalar mu kenan Nan gaba za kuji Wanda baku San dasu bama.
Allah yayi min baiwar hakuri ban gaji iyayena wajen masifa ba,sanyin Hali gareni,ga tsoro,sannan Ina da matukar addini,sannan kaf danginmu Babu me kyauna da kokarina,nafi kowa kyau da fata me kyau kamar jinin balarabiya wasu sun Dan fini haske da kadan duk da cewa Nima farace Amma hancina Bai cika tsini ba Kuma ba gajere ba,sannan Dan bakina karami jajir,gashina Baki sidik ga tsayi ko kitso baya yi,har gadon baya,idona farare tas Dara Dara,tun daga gaban goshina zaka ga gashina yalala ya kwanto, Ni ba rammiya ba ba Kuma me kiba ba,ga shape dirina abin kallo ne duk Wanda yayi tozali Dani sai ya kara, sabo da tsananin kyau na, idan baka sanni ba zaka rantse balarabiya ce ni, Amma duk kyan Nan nawa bani da saurayi bani da mashinshini sabo da halin Hajiyarmu Babu Wanda ke son hada zuria da Tata an Gama yadawa da sharri iri iri ake yi Mana kowa yazo wajena sau daya bazai dawo ba,a cikin dangi za a samu wasu munafukai suje su fada cewar Yar iska ce Ni har cikin shege na taba yi an zubar,sannan suce idan ya aureni zan mallakeshi,ga Masifar uwata,duk kawayena anyi musu aure tuni, sai Ni kadai Wanda a rashin miji ne yasa nake Karasa secondary Amma da ace na Samu miji ko jss1 bazan je ba za ayi min aure,yaran su Kawu Mata du Sunyi aure suna da Yara biyu Kuma mate Dina ne.
Dangi an Kara tsanata Wai ni nake korar samari sai talla da iskanci a garin Ina kwalliya Ina iyayi,Hajiyarmu ma da Abbu laifina suke gani shi yasa suke Kara Jin haushi na,dangi ko biki ko suna bana iya zuwa kullum daga schl sai gida sabo da irin ci min mutunci da akeyi Akan Wai naki aure Nasa yaudara a gaba,dangin uwata ma Haka ga mutan gari,Haka nake Addua Ina kuka kusan kullum Allah ya bani Mijin aure ko wanne irine aura zanyi na huta da bakin cikin da nake kunsa.
Yaya Salman ne kadai da Mahmood suke lallashina sannan suna matukar ji Dani,Mahmood ya taba furtawa zai aureni babarsa Matar Kawu Salisu tace zata tsine Masa shine yasa ma ya hakura Dani.
Takaitaccen tarihina kenan.
Ci gaban labari.
Rataye nake da Yar Jakar makaranta ta wacce Ya Salman ne ya siyo min a garin Kaduna lokacin da suka je service, Uniform dina fes dasu Allah yayoni da Tsafta sosai kullum fes nake ko Ina kungu da sako na jikina,ga Mahmood Yana yawan bani kyautar turaruka masu kamshin gaske dake su Yan gayu ne sun Gama wayewa sabo da karatunsu a birni sukayi.
Ina hanya na mike titi zan dawo gida sai ga motar Abbu Yana tukawa Golf ya rarako wuta kamar zai tashi sama Yana kallona Ina kallonsa Ina daga Masa hannu ko rage min hanya yayi sabo da makarantar Tamu da Nisa sosai ga Rana Amma ta window ya leko sabo da rashin tausayi Yana min Dariya ya wani daga min hannu irin sai na taho,gaba kadan kuma kannena ne su biyu yaran Anty Suma sun taso a gabana ya tsaya ya dauke su a motar suka tafiyarsu tare da bula min kura.
Bansan sanda Hawaye ya tsiyayo min ba,kawai na bawa zuciyata hakuri har na Karasa gida,Ina sallama gida Kuma ko kayana ban cire ba Hajiyarmu ta fara fada uban me kika tsaya yi a hanya banza shashasha kina girma kina hauka,na bude Baki kenan zanyi magana ta dungure min Kai Dalla rufe min Baki sai ki dauki abinci kici kiyi Shirin Islamiyya ga gyada ta tana jiranki ki tabbatar kin siyar, sabo da takaici ban iya cin komai ba wanka kawai nayi tare da Shirin Islamiyya, Ya Salman ne ya shugo tare da kallona yayi Murmushi yace Sister kinci abinci kuwa? Ganin Hajiyarmu zata min fada kawai nayi Murmushin Dole nace sai na dawo bana Jin yunwa, da masifa Hajiyarmu tace me bakin Hali munafuka Wai fushi tayi Akan an Mata fada baza taci ba, Anty uwar tsokana tace kanki kika yiwa cikinki yarinya,gandareriya dake kice baza ayi Miki fada ba,idan Haka kike so ubanwa ya hanaki aure ki tafi dakin mijinki sai kiyi abinda kike so..
Hajiyarmu Bata so wani yayiwa yaranta fada sai ita ko Abbu Nan take ta hayayyakowa Anty da fada yarki ko tawa?,Ina ruwanki,kije kiji da yaranki uwar iya Yar shishigi, Musa ne ya taka musu birki Wai Dan Allah Hajiyarmu me yasa kuke Haka ne why? Kun girma Amma bakwa gani,Ubanka kayiwa turanci ba Ni ba,sabo da kaga bama Jin turanci.
Read Also: Sanyi Da Zafi ANan