*Mrs Bukhari ce*
*GISHIRIN*
*ZAMAN*
*DUNIYA*
_Daga Al’kalamin_
_Badi’at Ibrahim_
( Mrs Bukhari Ibrahim B4B)
GAWURTATTU BIYAR π€π»
Labari wanda yai duba kan gwagwarmayar mata a duniya. Da irin gudummawar da ilimin mace ya ke bayarwa ga al’umma. Da kuma rawar da ilimin mata ke takawa a cikin gidajen Aure.
True life story
Kashi na 1
Babi na 7~8
Shiga ‘d’akin da su Jamila su ke na yi. Nan fa su ka soma yi mun gu’da tamkar za su tsinke hancinsu. Sister Murja ta ce.
“Sadiya gaskiya za mu yi matu’kar kewar ki a Asibiti. Kafin ki gama cin amarci ki dawo.” Dariya na k’wak’wulo cike da far’a na ce.
“Ni kuwa ba kewar da zan yi. Bazan so ma hutun nawa ya k’are in dawo ba, na fi so in ta zama wajan angona. Sister Jamila ta sa ka shewa ta ce.
” lallai Ahmad ya sa mu babban rabo da ya same ki a matsayin umman ‘ya’yanshi. Zai yi alfahari da kasancewarki matar shi. Uwa uba ga ki da tsoron Allah, kin kuma kasance mai alkhairi, da son taimako. Sadiya ba ki ci ka duba kan ki ba, hankalinki ya fi ta’allak’a ne akan ganin ko wacce mace ina ma ace ta samu ilimi , da duniya za ta yi alfahari da ita. Ina ji a jikina wata rana za ki zama wata.” Kokawa na ke ta yi da hawaye na kar ya zubo, dan gudun kar ya fallasani. Amma sai da ya ci amana ta ya zubo da gudu. Kukan kawai na shiga rerawa a hankali, ina tuno yaya rayuwa za ta kasance mun a kauye, kuma a k’ark’ashin namijin da na ba shi shekara biyar, wai me ya sa ba’a cika bai ma mace dama bane? Bayan addinin musulunci ya fa’di girma da daraja, da ma baiwar da Allah yai ma mace. Rarrashina su ka shiga yi, a na su tunanin kukan rabuwa da gida ne. Dan har Jamila ta na yi mun tsiya da cewa. “Sai kace wata karamar yarinya, har da kukan zuwa gidan miji?” Ni dai ban da kuzarin da zan ci gaba da biye ma cece ku ce d’in su.
Sha d’aya na yi, Goggo Mariya ta shigo har d’akin da na ke ta ja hannuna, zuwa d’akin Mama na. Mun yi kuka ni da Mama tamkar rabuwar da baza mu sa ke ha’duwa ba. Jaka ta Mama ta zuge ta sa ka mun wani abu. Da kyar ala zare ni a jikin Mama a ka yi waje da ni. Kowa ya shiga mota. Ina zaune a bayan mota kusa da maman su Amina, wacce ta kasance aminiya ga mahaifiyata. A kusa da ita Goggo Mariya ta zauna, sannan Goggo Asabe. A gaban mota kuma Kawu Sulaiman ne zaune bangaren me zaman banza. D’ayar motar kuma su kawu Bala ne da sauran matan da aka tawo da su. Mama na hango a k’ofar gida, ta na d’aga mun hannu. Nutsa kai na, na yi a tsakankanin cinya ta. Na fi awa hu’du ina kuka mai ta’ba zuchiya, abubbuwa da yawa ne a kar’kashin wannan kukan nawa. Zazzab’i da wani irin jahilin ciwon kai ne, su ka rabke ni. Awa takwas mu ka yi a titi mu na zirara gudu. Kauyan mafara mu ka tsaya a ka yi sallar azahar da la’asar. Daga nan kuma mu ka sa ke mi’kar hanya. Su Goggo Asabe sai hira da dariya su ke yi abinsu. Ni kuwa ina zaune na yi tsuru tsuru, ko k’wakk’waran motsi ba na iya yi. Maman Amina takan sa musu baki a cikin firar ta su jefi jefi. A. Haka har mu ka iso bus top. Babura aka tarar mana. Hawaye sai sabunta kansu su ke ta yi a kumatu na. Kowa ya hau Babur dinshi, ga kaya ni’ki ni’ki a hannun ko wacce daga cikin mu, kaya har a gaba aka saka masu Baburan su ka ta ya mu rik’ewa. Gudu akeyi cikin ciyayi da kaucina, Hankalina baya tare da ni sam. Gani na ke yi wani nannauyan bacci ne na ke yi, mai cike da muggan mafarkai kawai, tunda uwata ta haife ni ban ta’ba ganin k’ungurmin k’auye irin wannan ba. Domun ban ta’ba zuwa da wayo na ba. Sai lokacin ina k’arama Mama ta na zuwa da ni, a lokacin bansan komai ba.”
Gidan Amarya
Goggo Hansatu na hango a tsaye a dan k’aramin tsakar gidan da ke b’arayin Sadiya hannunta ri’ke da k’ugunta ta tusa kayan kitchen d’in Sadiya a gaba, ta na ta tunani. Amina ta ce.
“Goggo me zai hana mu yi ma yayan shi Angon magana, ko da kafinta ne a nemo mana wanda zai buga mata kitchen ko da na langa langa ne, kamar yanda aka yi mata bayan gida da langa langa. In ba hakan mu ka yi ba, sai dai in da kayan za mu koma. Goggo Hansatu ta zare idanu ta ce.
” mu koma da me? ‘Yannan ni kai na da taimakon Allah na iso lafiya a Babur. Ni ka’dai ma kenan balle kuma ace da kaya. Shawarar da ki ka bayar ta yi kyau sosai. Bari in je wajan matar Anas d’in, ko Allah zai sa mu dace a samu kafintan.” Goggo Hansatu da kanta tayi tattaki har zuwa b’arayin Matar Anas. Bilkisu na tsugunne ta na ta kici kicin hura kara ta na son d’aura d’umame. Shi kuma Anas d’in fitowarshi daga d’aki kenan zai fita waje, Goggo Hansatu ta shigo.
“Ahh Goggo Hansatu, ai da kin aiko ni nazo, da ba ki wahal da kan ki ba.” Cewar Anas. Bayan Goggo Hansatu sun gama gaisawa da Bilkisu. Sai ta ce da Anas.
“Babu komai ‘dannan. Ka ga kafinta na ke so ka ne mo mana. Zai buga mana madafi ne da langa langa, kamar yanda aka buga ban d’akin na Sadiya. Na ga wajan ba madafi. Shiru Anas ya yi, sannan ya ce.
” toh bari zan fita yanzu, in je gidan mai gari, yaron wajan shi shine kafinta, sai mu zo da shi ya ga wajan.” Godiya Goggo Hansatu ta yi mishi ta fita, ta koma b’arayin Sadiya. Amina ta ce.
“Andace kuwa Goggo?” Zama Goggo Hansatu ta yi tukunna, sannan ta ce.
“Za dai a dace. Ya ta fi kiran kafintan sai ya zo ma ji ta bakinshi. Ba ma wannan ba Hadiza, ina ganin dole ku zan aika zuwa cikin garin Zamfara. Yarinyar nan a siyo mata tocila irin wanda su ke yin chaji da hasken rana. Wannan duhu ya yi yawa, damuwar za tai mata yawa, a siyo mata kalanzir shima, ta ‘danyi amfani da shi, kafin ta ko yi kunna kara kuma, abun tuwo na buhu ma, a k’aro mata kamar buhu hud’u. Da tarkacen da kuka san zata sha wuya kafin ta sameshi a wannan kufan.” Bilkisu, da matar Dauda Hasiya ne, su ka shigo hannayensu rike da kwanukan abinci. ‘Dakin amarya su ka wuce dan ajjiye kwanukan. Tsurewa su ka yi dan ganin ha’duwar d’akin. Bilkisu tace.
“Hasiya ji d’aki, komai a tsare kuma babu kaloli barkatai. Baki Hasiya ta tab’e tace.
” d’akin ‘yar boko ba. Wallahi ni sai na ji na tsane ta tun kafin ta zo. Kishin balbali sai tafarfasamun ruhina yake yi. Goggo ma ta ce babbace Amaryar ta fi k’arfin Aliyun fa. Kuma kwantai ta yi a burnin shine aka k’ak’aba mishi ita.” Bilkisu tace.
“Haka na ji a wajan Anas, sai dai Baaba ta ce, auran shi ya na nan daram da khadija, daya dawo da wata guda. Tun yarinyar ta na k’arama aka ba shi ita.Ni ai na fiki jin kishin balbali a kanta, da d’akina yafi na kowa tsaruwa a kab surukan gidannan, yanzu an kawo kishiyar da d’akinta ya fi nawa hmm.” Hasiya ta ce.
” mu lek’a k’uryar d’akin mu ga ni. Bilkisu ta ri’ke hannunta tace.
“Alkur’an ba ruwa na. Ki zo mu fita.” Fitowa su ka yi.
“Goggo ga karin kumallo mun shigar muku. Goggo Hansatu ta ce.
” An gode” bayan su Goggo Hansatu sun gama tattaunawa. D’akin su ka koma. Dumamen tuwon jiya ne da ruwan kokkon gero wanda babu sikarin arziki, shine kumallon. Kokkon kawai su ka sha, tuwon kuma su ka mayar musu da shi. Hadiza da Amina, Goggo Hansatu ta ba su wadataccen ku’di, su ka tafi dan hawa Babur ya fita da su zuwa bus top. Daga nan kuma sai su hau motar da za ta shiga da su, cikin garin Zamfara. Jama’ar gidan Malam mai Hula kuwa, a na ta hidima da shirye shiryen tarbar Amarya, dan Goggo Safiya ta sanar mu su da cewar yau za’a kawo amarya kuma za su yi bu’dar kai. Duk an shisshiga mak’ota an sanar musu. Dan haka gidan ya kasance a cike fam. Sai tsegumi da gulme gulme ne ya ke ta shi a gidan. Wasu su na ganin ba’a kyauta ma Khadija ba, ita data ta so cikin so da begen Aliyu. Mari mai dawo tace.
“Ance tun jiya Khadija ta ke ta faman kuka ko abinci ta kasa ci. Hasiya matar Dauda ta ce.
” wannan yarinya abun a tausaya mata ne, za’a hadata kishi da ‘yar boko, ‘yar bariki, ga ta rayayyar maraya, kuma ance Babba ce, dan ta girmi Aliyun.” Nan fa tsegumi ya ci gaba, kaya kaya kawai ka ke ji.
Duk wannan surutun bai hana su aikin su ba. Wainar gero su ke toyawa. Bisa al’adar kauyan RAQUMA, wainar gero ana yin ta ne in ana wani sha’ani. Kamar bikin Sallah, bikin Aure, da bikin haihuwa. Sun k’ware sosai wajan iya wainar gero. Wasu kuma suna gaban turmi suna daka dawo ( fura) ma su curata daban, masu sa ta a cikin gari daban. Kowa dai ka ganshi, a cikin aiki ya ke.” K’auyan raquma ta gama d’aukar harami, gida a cike yake tab da mata, abokan Ango ma suna waje, suna jira amaryarsu ta iso, su tarbeta.”
*Mrs Bukhari Ibrahim*
*GAWURTATTU BIYAR,5π€TAFIYAR TA MUSAMANCE*
1, *MU GANI A ΖASA..π₯*
_Ummu Affan_
2, *ABIN CIKIN ΖWAI..π₯*
_Ummu Maher_
3, *GUNTUN GORO..*π₯
_Mom Islam_
4, *GISHIRIN ZAMAN DUNIYA*π
_Mrs Bukhari_
5_ *AUREN WATA TARAπ©ββ€οΈβπ¨*
_Miss Hajo_
………..π₯π©ββ€οΈβπ¨π₯π….