Gidan Gandu Na Sadi Sakana
** ❤ Gargadi❤**
Wannan littafin kirkirarrene,saidai zai iya cin karo da dabi’un wani ko halayyar wata,sannan ba a yarda wani ko wata suyi koyi da mugayen halayyar Wannan littafinba,anyine dan isar da wani sako.
Sannan game da marubuta idan kinga wani abu yayi kama da littafinki toh yanayin tunanine yakawo hakan,dan banida niyyar bata wa kowa rai,burina isar da sakon da littafin ya kunsa,wanda in akayi hakurin bani hadin kai har zuwa karshe toh kowa zai ga mai littafin ya kunsa.
❤Jinjina❤
Babbar jinjina ga proficient writer association,Ina godiya matuka.
❤01❤
………………Gidan gandu,gidane daya kunshi mutane fiye da 300 a muhalli daya banda wanda sukayi aure wasu suka tafi cirani wasu kuma tantirancin su ya hanasu zaman gida,tunda ga baki kofar gidan mutum yasan wane irin gidane saboda yawan kofofinsa tun daga kan kakanni,iyaye,jikoki,tattaba kunne da saurensu.
*
______lokacin safiyace dan baifi 9:30am na safenba,gidaje a kowa yana kokarin aikin gabansa inda masu himma kam yayansu sun dade da tafiya makaranta,maza kuwa wasu sun tafi gona.
Shiru cikin gidan kakeji babu wata hayaniya kowa yatafi harkarsa,bayan yasamu abinda ya sawwaka ya zuba a cikinsa,sai iya kofar kawu shehu wanda dama su kullum cikin fada suke,da inna larai da kuma inna karima.Dakin yan matan gidan ma bakowa sai wata matashiyar budurwa a kwance tana zuba bacci kaman ba gobe,ta dade batayi motsiba can kuma sai ta yi wata mika irin ta wanda ya more da baccinnan,gyara zamanta tayi a bakin katifar tata tana bubbuga kai da kuma jan majina da irin kaman mutum ya shaki kura,
“Kai shiyasa dadina da BURGU yasan DULAH (wiwi),mai kyau yanzu mutum zaiji shi a caji,duk wata gajiyarka saikaji ta tafi,inda ana samun mai kyau haka yaushe mutum zaice yayi asarar kudinsa kuma ai…………”
Katsewa tayi da zancen nata jin wayar ta irin yan nokia dinnan ta dau kara ta cika dakin,juyawa tayi tana yatsina fuska ta dauki wayar kafin ta saka a kunnenta,
“Menene??”
Shine abinda tace tana daga kiran,sai kuma tayi shiru danjin maganar da ake a daya bangaren,
“Hmm indai kaji kira a wajen alhaji sama’ila toh siyasah ce ta kariso yana so ayi masa aiki,toh wallahi kaji na fadamaka inhar ya hau kujerar nan yamanta da mu,to sai yayi dayasanin sanina a cikin rayuwarsa,dan saina masa abinda har ya mutu bazai mantaba,kuma kasan zan aikata,dan haka yanzu ka fada masa,inya amince kazo kadaukeni mutafi a san abin yi,yanzu dama nake maganar ka dan naji dadin dular jiyannan akwai caji baaaba,…………shikenan kazo ka daukeni sannan kace arnan yara su shirya ganinan zuwa yanzunnan”
Fitowa tayi a dakin tana wani garwaya hanya irin na iya shegennan can kuma sai ta dauki bokati dama da ruwa aciki da alama wani ne ya ajiye,
“Keee SAMEEMAH ruwa na ne na ajiye”
Juyawa tayi tana kallon mai maganar cikin daga ido,
“Toh so what dan nakine,ajiyewa zanyi dan naki ne,inkuma kinga a tawani sako na kwakwaiwarki ya nuna miki ina tsoronki ta kizo ki karba,kin manta ina da labarin guntun sabuluna da kikayi wanka dashi?koh an gaya miki bansaniba,dan dai munayin hankali ne kullum shiyasa muke barin koh ta kwana”
“Iyyyeee Ku zo ku jimin wata magana wai sameemah ceh tayi hankali,da kuwa anyi ruwan farin ciki a garinnan,kuma narantse kika shiga wanka da ruwannan saina miki abinda yafi na ruwana,dannima inada wajen zuwa da safennan”
“Keh sameerah ya isheki haka,maida min maganar inbaso kike daga ke har mazinacin bazawarinnaki dazaki wajen sa na juya rayuwarku ba,kuma inkin fasa daukar matakin banza shashasha”
“Kai lallai ma yarinyar nan,a haifeki a gaban mutane amma ki dunga yiwa mutum maganar da uwarsa bata isa yimasa ,shegiya yar daba kawai”
“Hhhhhhh gwanda dakika fadi abinda yake bakinki amma bari na fito nasameki a cikin gidannan yau wallahi mai rabani da ke koh…………..hmmm”
Sauri sameerah tayi tabar wajen dan yanda taga ran sameemah yabaci ba abinda bazata iya mata ba ,na rashin mutunci,takaicinta daya ma,yarinya karama ta takura musu ta addabesu,gashi sunyi waya da bazawarinta Saminu,yace zaizo yadauketa su tafi bikin abokinsa a Kaduna tana ta murna,yanzu tasan dole saidai ta tafi ba wanka, saboda gudun haduwarsu da sameemah a yau,dan tasan in ba hucewa tayiba,tsab zata aikata abinda tace.
Bata dade ba a bandakin ta fito,har yanzu fuskar ta ba fara’a saboda sabanin dasukayi da yayarta sameerah dazu wanda suke uba daya su da itah,dakinnasu ta shige ta nufi hanyar wajen kayanta,dan daki kawai suka hada da yan matan gidan amma kowa shirginsa daban ,gwanda su wani lokacin in wata tayi samuwa ana zama a ci ana dariya da yada zance,amma sameemah in ta shigo da abu a gabansu zata cinye in ya isheta ta bawa karanta BINGO.
Mayuka ta fitar lotion masu gyara fata ta mulke jikinta kafin ta dauko wasu kaya na saki irin na farauta amma anyi musu dikin irin na mata riga da wando.
Bayan ta gama saka kayanne kuma aka shafa hoda kafin aka dauko bakin jambaki wuluk ta shafe karamin bakinta dashi ,ga kuma kwalli da tayi masa saku kasa da sama,dan saida girar ta kusa hadewa da saman ido,juyi tayi a gaban madubinta kafin ta dauki gyalen ta nadeshi a kafada ta fito daga dakin.
A bakin hanyar fitarta daga dakin suka ci karo da wani dan anguwarsu yana rataye da yar gidan inna larai a kafadarsa,yarinyar sai kuka take bazata wuce shekara bakwai ba,Sameemah ce ta fara ganinsa tareda Tambayar “lafiya”
“Ahah seemah jar wuyah(haka kowa ke kiran sameemah a waje)wallahi a hanyar shagon ilu naganta a kwance jini yana binta hine dana tambayeta tacemin wai Labiru ne abokin yayanta Manu yayi mata haka”
“Ayyah Toh sannunka da kokari zaka iyah tafiya”
Bayan ya tafine sameemah ta dauki yarinyar tayi kofar su inna larai din da ita,
“Inna larai! inna larai!! Inna larai!!!”
Suna cikin habaici kowa yana kofar dakinsa ita da inna karima,sai ta zuyo tareda cewa,
“Ke miyene kike ta jundumamin kira kaman zaki cinyeni”
“Iyyeh hakanee abin(sameemah ta fada tana ajiye hanifan a gababan inna larai) toh gashinan,yar tatsitsiyar yar kice wani gardin ya fardeta ,kona ce yabudeta a ledarta,saiki zo ki dundumata da ruwan zafi ba masifa zaki tsaya yiba,itama alamu kwadayinnata ya kaita ta shiga sahu tun lokacin ta ba yiba”
“Lallai sameemah abinda zakice ma kenan,wanne dan tsinanniyar ne wannan?”
“Waye kuwa banda Labiru abokin danki Manu,bake kike manna masa itaba dan kinga yana siya mata shayi da safe,bakuda aiki sai kwadayin tsiya,saiki dundumata ta samu ta ware,ko tayi harkar da kwarin jiki,ni na tafi inna dawo da kaza na dan bata,kota maida jinin da yazuba,in kuma nima bandawo ba tacan tacan,ga wannan kisaya mata ibrofen saboda zafin jiki(tafada tana mikawa inna larai din naira hamsin).
Wani wawan tsalle inna larai din tayi tareda buge kudin dayake hannun sameemah,kafin tabita da wani ashar mai dumi.
Inna karima kuwa tana gefe tana zuba uwar dariya kamar makogaranta zai fito dan mugunta,komawa kanta zagin yayi,cikin haushi inna larai tayi kanta suka rukume da fada,tana zaginta tana kururuwa kan gari ya gari.
Ganin mutanen gidan sun fara sanin abinda yafarune,yasa sameemah zagewa ta fice daga gidan.
Tana fita ta samu Burgu a kan mashin yana jiranta,burgu yana ganin ta fito ya tada mashindin yafara diri,dalewa tayi suka fara tafiya,yana bata labarin yanda sukayi da alhaji Sama’ila,duk zancen dayakeyi bata kulashi ba saima umarni da ta bashi cikin karamar magana,
“Ka saka su dodon dawa su kama Labiru dan malam sule,su kaimin shi gidan karangiya,su dan tabashi kafin naje wanjansa gobe”
“Shugaba reza mai yayi haka?”
“Bai shafeka ba kayi yanda nace kawai”
“Wai yau labiru yaga ta kansa tabbbb”
Da haka har suka isa gidan kungiyar tasu burgu bai sake cewa komai ba saboda yaga yanda shugabar ta murtuke fauska.
Gidane da akayi wajen da langa langa saikuma,dakuna na bulo guda biyu da kuma dakuma dan tsakar gida.
Babu KO sallama haka suka saka kai ,inda kowa yatashi yana yi mata barka da isowa,dakin dayake farko ta shiga,tareda hakimcewa akan wata kujera wadda aka saka tebur a gabanta,sukuma suka zauna a sauran kujerun dakin,
“Uhm uhm,kaman yanda kuka sani wannan kungiya ta kafu bada iya taimakona ba harda naku,sannan muna abune bisa tsari,in munyi abu saida dalili toh dan haka,ba mason katsalandan da yan sanda,alhaji Sama’ila yaba mu aikin ragamar siyasarsa,dan haka zamuje yau ,amma iya mutum shidane zasu biyomu sauran nasaka burgu yabaku aiki,shi zai fadamuku mai na sakashi yasa ku aiwatar kuma kunsan banason ganganci,dan haka k kula,kai kuma ASUSU,(tafada tana nuna wani dan saurayi a gefen burgun a zaune),nawa muke dashi acikin bankinmu na kungiya?”
“Eh shugaba iyah dubu talatinne”
“Toh kabawa dodon dawa dubu goma yah,yasayo mana suyar kaji da lemo,sannan kuma ka tambayi burgu inda ake saida dulah mai caji ka sayo mana,dan wacce ka kawo wancan sati ta asarar kudi ce kawai,inna dawo daga wajen alhaji Sama’ila akwai shagali”
Ihu wajen kowa yadauka mai feduwa sunayi,
“Sai ogah kina abinda kika so,sai shugabar gidan gandu,da girman kujerarki,sai reza ki yanki wanda yasayeki idan ya kuskuren rikeki ba dadaiba,kuma dole ya gyara yayi aiki da ke,ehhhhhhooooool”
“Toh ya isa haka maza ayi haramar fita aiki kuma”
Kowa tashi yayi inda masu kamo labiru suka tafi bayan burgu yayi musu bayani,sannan masubin shugaba seemah jar wuyah kuma suka bita a baya da mashinan su,sai gidan alhaji Sama’ila.
Toh farkon farawa kenan a cikin littafin gidan gandu,daga taskar sady-sakhna,kuci gaba da bibiyar littafin da sannu zamu nishadantar daku yanda yakamata inshaallah,nagoda ga duk daukacin masoyan wannan littafin.