GARGADAN SO NA MSHAKUR
DA SUNAN ALLAH MAI RAHAMA MAI JINKAI
ANCE MONEY IS POWER! Shin kun
yarda? Ance kudi kan iya maganin komi har cuta da bakin ciki kun yarda? Ance
kudi na kankaro mutunci sannan kudi kan iya siyan kowa shin kun yarda? KU
BIYONI A WANNAN SABON LABARIN MAI SUNA GARGADAN SO DAN WARWARE MUKU ZAREN
EPISODE
Dankareren kerarren falo ne dazaka dauka acikin presidential villa kake sabida kyawunshi, wani Babban attajiri ne adakin yana sanye da manyan kaya da akalla zaikai 68-69yrs hakan nan yana sanye da manyan kaya dake walkiya kaman da duwatsun diamond aka kera shaddan, sai gani attajiri a gefensa shima yana sanye da manyan kaya ya kafa hula aka, sai kuma wasu mataye guda biyu suma da zasukai kaman 49 ko 50yrs haka duk zazzaune cikin shiga ta alfarma shigan da kudi ke ihu suna screaming, duk wanda ka kalla cikin falon kana iya ganin tsananin tashin hankali dasuke ciki, kap mutanen nan babu mai magana, sai zancen zuci da kowa keyi, agogon dake daure a wrist din attajirin ne yayi kara hakan yasa yadago kanshi yakalli sauran mutanen dake dakin da duk sun dagokai suna kallonshi sabida karan da agogon hannunsa yayi yabude zaiyi magana amman ba murya dan gyaran murya yayi. “Uhmm uh’umm” sannan yace “this is 72hours daidai kenan tun bayan munkai kudin dasuka bukace mu damukai amman shiru, basu saki yarinya ba, basu kiranmu ba” saikuma ya zauna da sauri kan kujera yana kallon attajiran matan da ke kuka dudda bata bari hawaye ya taba fuskanta dan tarike tissue tana mammannawa dayan matan dake kusada ita dake nuna kaman kawarta ce sabida yanda take bubbuga bayanta yace “Noor is just 4yrs, yau kwananta 5 in captivity” sai kawai yatashi kaman wanda aka tsikara da saurin gaske yayi wajen kofa dayan Alhajin yabishi da dan gudu yasa hannu yabude kofa yafice wasu manya manyan security dake sanye da kayan sojoji ne kusan su 10 gaban dakin sunyi layi biyar na kallon biyar.
Babban Riganshi ya shiga tattarewa yana sauri dayan na binshi da sauri shima yace “ina zaka Your Excellency?” Cikeda tashin hankali yana tafiya still batare daya tsayaba yace “I’m going to see Khaleelu” daidai wasu securities na budemai wani babban kofa ya shiga cikin wani lafiyayyen falo dayay mahaukacin haduwa ga duhu ya cikashi, hannu yasa ya kunna wutan dakin yayi haske dau, yawuce wajen lift dake falon ya shiga yakaisa sama babu komi dake aiki adakin banda AC, wani kofa yabude dakin shima duhu dasauri ya kunna wuta, ya Allah! Kyan dakin is worth rubutawa a littafin world record, wani matashi ne kadai zaune adakin akasa kan wani lallausan fur carpet dagashi sai joggers na aritza ash color da rigansa farin t-shirt, yabama kofan baya hakan yasa bayansa kadai zaka iya gani that’s huge and full da gashin kansa dakeda dan yawa and it’s kind of coily kaman na dan fulani baki kirin.
Dasauri attajirin yayi wajen da yaron yake ya zaga ta gabanshi yaduka cikeda damuwa yace “Khaleely, Khaleel, Son!”
Ko motsi yaron da ake kira baiyiba dayan Alhajin dai ya tsaya wajen kofa yana kallonsu, dasauri attajirin yakai hannayenshi biyu yakai wajen habansa yadago kan matashin cikin tattausan murya yace “Khaleel” ahankali matashin yabude idanunshi dakenan manya manya sannan dara dara kaman idanun yar budurwa wanda suke cike da dogayen black eyelash hakama giranshi yanada gashi sosai and giranshi is very thick gakuma fadi zaikai ahada giran wani guda biyu waje daya shine fadin nasa gashi kuma gashi ya cikasu tam, gashin kansa ma yafi na wata, bawai yatara gashi chanchan bane kawai dai akwai gashin and sunyi coils, lips dinshi are pinkinsh but ba chanchan ba, but yanada plumpy lips that’s so masculine in nature and sexy, ga dogon hanci kaman jijiyan tattasai, yanda ya zubama mutumin da kana ganinshi kasan mahaifinshi ne idanu yasa mutumin yayi kaman zaiyi kuka yakai hannunshi kan wuyanshi yace “jibi yanda yarona ya rame eh, look at you Khaleelu you don’t eat anything saidai ruwa yau day 6 babu proper meal in this ur tummy, da wanne zanji eh”? Saikuma yakai hannunshi yakama kafadanshi yace “i come to tell you I will not sit still naki komi sabida this takadiran kidnappers dinnan sunce kada muyi involving police then sainai folding hannu inbar wani abu yasameka and jikata”sai alokacin ya iya bude baki shima kana gani kasan karfin haline kawai ahankali yace “Pops if anything should happen to Noor I don’t know wat will become of me” Dasauri Baban yace “I know Khaleel, nima idan abu yasameka I don’t know what will become of me da mahaifiyarka, tsaya kaji Khaleely” ture hannunshi Khaleel yayi daga kafadanshi yace “Pops banso naji, don’t involve police! I don’t care idanma wani kudin sukeso they should keep calling zanta basu koda duka abinda na mallaka zai karene i just want my daughter back Dad” baki baban yabude zaiyi magana Khaleel yatashi azafafe ya tsaya tareda pointing door wai yanada tsawo and cikakken huge man ne, kai tsaye yace “leave my room Pops I wanna be alone!” Baban zai sake magana ya kara nunamai kofa cikeda karfin hali yace “nace kafita, leave Pops i want to be alone idan sun sake kira” kallonshi babban yayi irin kallon tsantsan soyayya dakuma kauna da tausayi da damuwa duka dinnan sannan yatashi yana gyara babban rigan yace “muje Musbahu” wucewa sukayi suka fice, suna fitowa Abba yace “get me DIG awaya kahadani dashi” dasauri Musbahu ya tsaya yana kallonshi cikin damuwa yace “I know abinda nakeyi I will never put my granddaughter in danger but this nonesense have to end, muje office dina” office nashi suka wuce nan ma bude musu kofa akayi suka shiga ciki Babban office ne dakana gani zaka gane kaman na yan siyasa ne dan ga hotonshi an rubuta Senate President Alhassan Mangal, zama yayi kan kujera yana kallon Musbahu dake waya sai chan yamikomai wayan karban wayan yayi yasa a speaker kai tsaye cikeda isa irin yanda manyan mutane ke magana yace “abinda nakeso nafada maka yanzu is something da banso yabi gari hartakai media dan it has to do with jikata that is just 4yrs old” yayi shiru chan yace “On 21st of this month kwana biyar dasuka wuce kenan ranan asabar ankai Noor park, it’s her usual thing weekend ana kaita park, she has 2 International nannies da kuma 1 Nigerian, dakuma 2 securities nata wanda 1 happens to be driver, 5 people accompanied her to the park but right under their nose aka saceta Noor tabace bata ba alamunta kidnappers sun kira sunyi demanding for 100M munkai exact location 2days ago sun karba but shiru basu saketa ba” yadanyi shiru yace “I thought we can handle everything on our own tunda kudi ne but mun bayar but still shiru Noor is a baby, sunyi warning namu not to involve police ko bazamu sake ganinta ba forever, my son is looking miserable I need your help DIG, I need your best team that can save jikata without a scratch and wayanda zasu iya aikin discretely konawa kuke bukata I will pay”.GARGADAN SO
M SHAKUR
EPISODE
Cikin muryan jinjinan ban girma DIG yace “I feel honored your excellency dahar kai tunani na in this difficult time, I have the best task force that can save Granddaughter ka Allah taimaki excellency, team of 3 ne, the tech genius, the powerhouse, saikuma the criminologist dakeda highest record na decoding, encoding, profiling and tracking kidnappers, trust me your Excellency this case is a piece of cake for Miss Hawwa!” Dasauri Dad yace “I think I’ve heard of this name Hawwa” dasauri DIG yace “you will definitely cus she’s a government asset, somehow somehow maybe takardunta ko work dinta yazo gabanka, thanks to her akai rescuing almost all our kidnapped victims dasuka zo Ecowas summit daga Washington DC” dasauri Dad yace “tabbas yanzu natuna sunan” DIG yace “yanzu dai wat will happen is, i need to bring them over suyi proper investigation and ask you people lot of questions and watch how they save Noor, 24hrs yamusu kadan inhar they gather information” dasauri Dad yace “okay but kuzo without uniform, and karkuzo da office car cus I think the kidnappers are watching movement na gidana” dasauri DIG yace “wannan ba matsala bane we will be there in an hour” ya katse wayan ijiye wayan Dad yayi kan table ya sauke ijiyan zuciya Musbahu yace “Khaleel zai yarda kuwa?” Anatse Dad yace “zaima yarda ne baida wani option, bazan folding hands ina kallonshi in pains ba”.
Wayanshi yadaga yakara a kunne babu wasa akan fuskanshi yace “come to my office now” wasu maza guda biyu suna sanye da riguna da wando da tie kaman masu aikin bank sukazo wajen wani office sukai knocking kofan, suka shiga sannan aka sake knocking kofan DIG yace “come in” ahankali aka turo kofar office din, kafafunta ne suka fara lekowa cikin office din dake sanye cikin wani black cover shoe dakeda dan tudu zuwa dogon navy blue wando normal trouser length material dake jikinta zuwa wata shirt mai dogon hannu sky blue dake da stripes na white lines wanda shima bai kamata ba yakuma sauka dan yarufe bombom dinta yasauka kan cinyanta daidai tsakiya, saikuma gyale datai rolling na kashka navy blue dashi ma ya sauka yarufe kirjinta sai igiyan ID card nata data saka a wuya ID card din yasauka akan kirjinta wanda fuskanta da sunanta ke jiki, fuskanta babu kwalliya ko guda daya banda milky skin nata that is light brown in color dake sheki, ita ba fara ba and ba baka ba, sannan ba coffee ba, very light brown skin fata gareta da saura kadan yakoma fari, she’s tall about 6’0, tanada round eyes dasuke nan farare fattt ba manya ba kuma, sunada shape kaman na kifi da abun yakarama fuskanta classic v and symmetrical shape, tanada dogon karami hanci dan dass dashi, tanada small lips that are full and very pink, tanada gashin gira baki but baida fadi looking kaman tayi carving and tinting nasu nan ko batayi ba, akalla zatai 29 ko 30yrs hakanan cus she looks matured and calm, bin yan office din tayi da kallo ba yabo ba fallasa ta maida kofan tarufe sannan tazo gaban table din da DIG ke zaune yana kallonta ta saramai cikin zakakkiyar muryanta dake da dadi tace “Sir!” Dan murmushi yamata kadan yace “ease Hawwa” sauke hannun tayi tana kallonshi binsu duka ukun yayi da kallo yace “Hayatu, Abraham and Hawwa, the 3 of you are my biggest asset! I take joy and proud cewa ninai training naku kawowa this stage da kasarmu gabaki daya ke alfahari daku, they can never talk about crime solving batare da an ambato sunayenku ba sabida yanda kuke samawa kasa lafiya a sirrance, yanzu ma lokaci yazo dazaku kara baje bajintarku” yayi shiru duk suma sukai shiru suna kallonshi jan kujeran dayake kai baya yayi yamike tsaye yazagayo ta gaba inda suke yazauna akan table duk yana kallonsu yace “anyi kidnapping jikar Senate president dinmu Alhassan Mangal, yau is the 6th day datake hannu abductors dinta and she’s just 4yrs” dukansu kallonshi suke yadan sauke ijiyan zuciya yace “I don’t have full information na case din dan yanzu yanzun nan case din yazo table dina basuso suyi involving force sabida kidnappers din warned them not to kosu kashe yarinyar, but bayan sunkai 100M 2days ago har yau shiru ba kira ba yarinya yasa Excellency yabani kiran sirri” yadan sauko daga kujeran standing straight yace “team!” Atare sukace “yes Sir!” Yakallesu duka yace “you have just 24hrs to rescue that little innocent girl, Hawwa!” Anatse Hawwa tace “Yes Sir!” Yace “I trust you! But ayau I just want you to make me extremely proud banso Excellency yayi nadaman kiransu dan haka saving that little gurl is a must! Am I clear”?
Dan allah gargadar so page 79