*Shekaru Goma da suka wuce.*
Lokacin sanyi ne, hazo ya lulluɓe garin ruf ta yadda ba zaka ce safiya ce a sannan ba, don hatta motoci da fitilu a kunne suke yawo koina, na ƙasa kuwa baya ganin abinda ke gaba ko yaya tazararsa dashi take.
A cikin motar dake tafiya kan titin expressway na barin gari, Ma’aruf ya zare earpice ɗin dake kunnensa ya sake shi a jikinsa sannan ya juya ya kalli Jamal dake tuƙin motar.
“Let me drive dan Allah.”
Jamal ya girgiza kansa.
“Kaima ka san there’s no way da zan baka motar nan, yaushe kayi ƙwarewar da zaka hau babbar hanya?”
“Kusan shekara daya fa kenan Yaya dana fara koyon tuƙin nan, ko wace irin ƙwaƙwalwa ce dani ai ya isa na iya haka.”
“Da da Muhammad muka zo sai ka gaya masa hakan, amma ni na sanka Ma’aruf babu abinda yake gabanka banda karatun likitan nan, shi yasa kaƙi barin kanka ka koyi komai, ba don wannan babar taka ma ta dage ba ai da yanzu baka ma fara koya ba, something so shameful!”
Ma’aruf yayi dariya yana ɗauke wayarsa daga tsakanin cinyarsa kafin yace.
“Na sha gaya maka makarantar ne ba ƙaramin tsauri ne dasu ba, ƙanwar Havard fa ake ce mata, ba kowa suke ɗauka ba and in my own case da nake baƙar fata dole in dage inyi karatu, babu ruwansu da komai sai abinda ka iya.”
Wani mai mota yazo yasha gabansu a lokacin, Jamal ya kalle shi cikin takaici yana girgiza kai kafin yace.
“Kai kuma ka dage dole sai nan, Universities nawa zaka je ka zama likitan ƙwarai Ma’aruf.”
Ma’aruf yayi dariya yana kallon gefen hanya ta cikin gilashin motar dake ɗaukar ido saboda sabunta, don kwanakin motar biyu kawai da siya bayan Baffa ya gama yi wa Jamal din tsiya akan ya canja tsohuwar motarsa, sai gashi da ya tashi yaje ya siyo wadda tasa kowa gyada kai cikin mamaki.
“Wai likitan ƙwarai, you are too much Yaya, sannan dan Allah sunanta Mami, ba ‘babarka’ ba.”
Jamal ya cije leɓɓensa a wannan lokacin yana kallon gabansa a lokacin da suka gota wani ƙauye suka fara barin gari, yayin da shiru ya ratsa motar kamar yadda hakan ke faruwa a duk lokacin da Ma’aruf ya ƙalubalanci wani abu da Jamal ɗin zai faɗa akan Hajiya Kilishi.
Ba tun yau ba ya sani babu jituwa tsakanin yayan nasa da matar da yake mata kallon mahaifiya akan wani dalili da bai sanshi, don da ace tun daga farko yabi ta Hajiya kilishin ma, baza a taɓa samun shaƙuwa irin haka tsakaninsa da Jamal ba, sai dai soyayyar ƴan uwantakan dake tsakaninsu tafi karfin mizanin yadda yake jin matsayin Mamin a ziciyarsa.
“B… Haka suke maka a makaranta ko?”
Muryar Jamal ta katse shirun motar kamar yadda koyaushe ya saba daidaita al’amura a tsakaninsu. Sai ya juyo da murmushi ya kalle shi.
“Kai a duka friend’s ɗinka ba wanda yake kiranka da Bakori?”
Jamal ya girgiza kansa.
“Man, ni sunana mai daɗi ne babu wanda yake jingina min sunan wani ƙauye.”
Ma’aruf yayi dariya yana sake maida kansa baya, kafin Jamal din ya sake magana.
“Ka gaya min bayan zama likita mai kake son kayi a rayuwarka?”
Ma’aruf bai taso da kansa ba, idanunsa na kallon rufin motar ya cije leɓɓensa alamun tunani, sai kuma ya girgiza kansa yace
“I don’t know, let me just start figuring out that tukunna. (Ban sani ba, bari na dai fara gamawa da hakan tukunna.)”
Jamal ya gyada kansa har yanzu idonsa na manne da titin kafin yace.
“Ina so ka sani Ma’aruf ba kowa zaka dinga yarda dashi a duniyar ba, wani lokacin mutanen dake kusa da kai suna iya zamewa abinda makiyanka, ba a kowacce fuska mai murmushi ake samun so ba, ba a kowanne ido mai kyalli ƙauna take ba, wani zai maka murmushi Ma’aruf amma wuƙa yake caka maka baka sani ba, kuma ba lallai ka gane ba sai a lokacin da komai ya ƙure, ka san irin takun da zaka yi tare kowa. Kar ka tambaye ni me yasa nake gaya maka haka, kawai naji ina so ka sani ne don watakila zai amfane ka a gaba.”
Sai a yanzu Ma’aruf ya sauko da kansa daga kallon saman motar, ya kalle shi sannan ya gyaɗa kansa.
“Its a good advice, (shawara ce mai kyau.) Nagode sosai.”
Shima ya juyo ya kalle shi, wani irin kallo da Ma’aruf yaji kamar yana ratsawa har cikin ruhinsa, kamar bai gama gaya masa komsi ba, kamar akwai sauran wasu bayanan da bai gama kwancewa a cikin kalamansa ba, amma sai kawai shima ya gyaɗa nasa kan sannan ya juya ba tare da yace komai ba. Yawu ya zarce cikin maƙogwaronsa kafin ya juya shima ya kalli titin dake bangarensa.