BAHAGON RAYUWA BISSIMILLAHI RAHAMANIN RAHIM DUK KAN GODIYA YA TABBATA GA UBANGIJIN MU SARKIN TALIKAI DA YA KAWO MU WANAN LOKACIN TARE DA BAMU LAFIYA INGANTTACIYA A RAYUWAN MU, YABO DA GODIYA YA TABBATA GA ALLAH WANDA YAI MUNA NUNFASHI TARE DA MA ABUBUWAN RAYUWA ACIKIN HIKIMOMIN SA YA ALLAH MUNA MASU ROKONKA DAKA BAMU IKON GODE MAKA AKODA YAUSHE MU KASANCE CIKIN BAYI MASU TSORON KA MASU MAKA BAUTA TSARKAKKE A RAYUWAN MU, WANNAN RABARI NE MAY DAN TABA ZUCIYAR MAY KARATU TA DA WASU SAKWANI A CIKIN SAI DAI BAIDA YAWA SOSAI DON BUKATAN MAKARANTA NAYI TARE DA FATAN ZAMU AMFANA DA DAN SAKON DAKE CIKIN SA , NAGODE TAKU HAR KULLUN ZAINAB IDRIS MAKAWA SEENABU GA MASU SON JIN KARSHE ZASU IYA KIRANA DA WANAN NUMBER DIN KAMAR HAKA 08036959257 DOMIN YIN REGISTER, , , , BAHAGON, , , , , , ⚓1⃣ Gidane ginan kasa wanda da ganin sa kasan akwai talauci da kauyanci a cikin sa sai dai duk da kasancewar gidan karami akwai tarin jama, a a cikin sa sosai. Gida ne wanda ya kumshi matan aure guda uku ko wace da nata zurian don dama irin wanan gida babu komai a cikin sa sai gasar haihuwa a tsakanin matan dake gidajen. Ba wai damuwa da rayuwa akayi ba banda bakin kishi da hassada juna a tsakani, abinda ba kai tsanmani ba shine mutum yakan riska a cikin irin wanan gidajen. Sai dai kuma tallakawa ne fitik din su don abinda zasuci ma watarana aiki ne a gare su sai dai kowa taiwa rayuwan ta dana yayan ta dabara su sami dan abinda zasu aikawa cikin su. Ga ko wani daki a cike da yara bi da bi irin haihuwan nan na kafin ka yaye ka samu wani. Sai dai su matan gidan hakan ba takura bane a garesu sai dai ma jin dadin rayuwa don babu wacce aka bari a baya daga cikin su wurin saka nata irin. Duk da uwargidan da may bi mata sunfi yawan iyali a gidan amma kuma suna kyashi da hassadan ganin Rabi amaryan su itama da ba ta dade ba da shigowa cikin su tana kokarin cin masu ga haihuwa. Gsshi dai ba wani tallafi suke samu ba daga mijin nasu wanda zasu taimakawa rayuwan su dana yayan amma kuma kullun zance ya tashi sai su manta da nasu su shiga sake mata magana a tsakar gida. Sai idan ta gaji ne takan mayar masu da martani da cewa haihuwa aina Allah ne kuma yaya arzikine kowa kuma na dashi batai bakin ciki da nasu ba ai. Duk hakkurin irin na Rabi, sau da yawa takan shanye ta take irin abinda akewa diyan ta a gidan tayi kamar bata gani ba. Sai dai tana mai bawa yayan nata shidda tarbiya sosai fiye da sauran yaran dake gidan da tarbiyan su sai a hankali. Abu daya ne talaucin su bai hana yaran gidan yin karatun boko ba har ma da na addini wanda diyan Rabin sun fi maida hankali ga kowani fanni na karatun nasu. Gashi bata shiga tsabaga kowa haka ma yayan nata suke a gidan zata iya zama a daki ida ba wani abin bane zai fito da ita waje. A haka dai suke zaune a gidan da dadi ba dadi watarana aci watarana kuma a hakkura asawa sarautar Allah ido a gani. Uwar gidan da suke kira da mama tana da diya tara mata bakwai maza biyu, sai may bi mata inna tana da diya takwas maza uku mata biyar. Sai ita Rabi dake da diya shidda maza hudu mata biyu yar ta ta fari mace ce ana kiran ta da safiya may bi mata kuma Aisha, sai mazan issah dauda, aminu da shaibu sai karamin da take goyo da suke kira da abu. Duk inda zaka nemi yan uwan da ke son jinunan su to yaran Rabi sun kai can don suna balain kaunar junan su sosai a rayuwan su. Allah may rufin asirin bawan sa dan karfin da Safiya ta fara kawowa ne ya ragewa Rabi wani wahala a gidan da take fuskanta na rayuwa. Don safiya yarinya ce mai hazaka ta dauko yan kule, kulen dan abin makulasan yara tana zuwa makatan ta dashi wanda ta hakane uwar ke dan samun na sabulu daga ciki da sauran abubuwab rayuwan yau da kullun. Wanan dan walwalan da ubangiji yai masu sai kuma hassada da kyashi yazo ya shiga cikin zukatan sauran matan gidan. ************ ************ Tun dawowan su daga makaranta ta dan tsaya shago ta sayo dan madara da suga wanda take ganin zai isheta yin dan gulusuwan da zatayi gobe na zuwa makaranta dashi ta shigo ta samu kamar kullun sauran mutanen gidan suna tsakar gida suna harkokin su na yau da kullun kamar yadda suka saba. Bata shiga dakin su ba tabi iyayyen gidsn da wasu daga cikin yayyen ta tana masu sannu da gida. Ba wai amsawan dadi ake mata ba amma hakan bai hana ta gaida su kamar yadda ta saba a kullun suna amsa mata cikin gajewa da halinta. Idan kuma da zata wuce bata gaidasu ba wani matsala ne hakan don har rankwashi sai tasha a gun wata a gidan ranan. Da sallama ta shiga dakin mahaifiyar ta tana zaune ninke kayan wankin da tayi na kanne ta tun safe ta samu tanayi a dakin. Uwar ta amsa mata sallaman ta cikin mutunci tare da fadin kun dawo tace eh tare da kokarin sauke dan jakar makaranta dake makale a kafadan ta. Bata zauna ba ta fara kokarin ciro dan sayayyan da tayo a hanyar dawowan ta tare da ciro sauran dan kudin da ya rage tana kokarin yiwa uwar bayanin komai. Haba yar nan bayyani kuma namay fa cire jakar ki zauna ki huta ga dan ganye nan dana gyara maku da garin rago kici kisha ruwa ki huta kafin lokacin zuwa islamiya yayi maku. Ta zauna ke nan da niyar ta cire safan dake a kafan ta taji ana kwala mata kira a tsakar gidan da Safiya safiya da karfi. Cikin takaici da bacin rai uwar tace dama na sani ai ba za a bari ki zauna kici dan abincin ba ma yanzu za, a nemay ki da wani aikin kuma. Taja guntun tsaki tana cewa yar tashi kije idan kin dawo kyaci ai, cikin takaici Safiyan ta ture kwanon data bude. Cikin ranta tana fadin kamar ni kadaice yarinya a gidan daga dawowanabza a fara kwala min kira da bakin aike ko aiki, komai sai dai a kirani ace nice zanyi ni kadai. Kafin ta kai ga fita ta sake jin muryan Inna tana fadin wai Safiyan bata jinane ko may wai ? Da sauri ta amsa da naam Inna gani tafe ina daura zani ne dama tafita waje tana karasa daura zanin da takeyi din. Cikin takaici Rabi ta jawo marfin kwanon data bude don cin abincin data aje mata ta rufe tana fadi a ranta, in dai don aji ta bakinane ake wanan halin bazaku taba jina ba a kan hakan. Duk yaran dake gidan nan wasu ma basuje ko ina ba tun safe amma ba a aike su ba sai wacce ta biyo rana ta shigo yanzu ake kwalawa kira haka. Ko sai yaushe zasu daina wanan halin hassadan nasu a gidan nan haka oho don dai wani abin da gaiyya ma suke masu shi. Jin muryan Inna tayi daga waje tanawa yar nata fada aka may take kiranta ta shige daki taki fitowa tun dazun. Tace inna ina cire uniform ne a jikina dama ba kin fitowa nayi ba sai inna din tace ai dolen ki ma ki fito ga tatsin kamu can a roba yana jiran ki tun dazun har ya fara kumbura. Safiya takai kallon ta ga inda kammun yake a bude fam ga roba sai kudajen da suka mutu a saman shi ba ako dan sakaya shi da wani abu ba. Ta sauke ajiyan zuciya tare da cewa Inna don in dan ci abinci kafin na fara don banci komai ba tun safe dana fita gida. Wani irin tsawa ta daka mata tace kai amma lalai safiyan nan wuyar ki ya isa yanka yanzu ni zan saki aiki har ki tsaya kina cewa wai na bari ki dan ci abinci. To ki zauna kada ki tatse idan ya gama yoyewa sai ki fito kina ca kin shige daki kuna gulman da kuka saba dake da munafukar uwar ki ko. Haba inna gulma kuma dani da ummi ta ake bude baki zatai magana taji saukan mari a fuskan ta kayauuu, . Daidai lokacin kuma mahaifin su da ya dawo daga wurin aikin jiman shi ya shigo gidan yana ganin ta dafe kumcin ta bai tsaya bin ba asi ba yace ke Safiya ungo nan yai mata dakuwa yana fadin. Ashe rashin kunyar da ake fadi kina dashi yakai haka ban sani ba uwar taki ne zaki tsaya kinawa musawa a gaban ta. Inna tace gara dai da kagani da idon ka yau idan an fadi ace an sakawa yarinya tsana don ba a kaunar su a gidan. Safiya tana share hawaye ta wuce ta fara gyara inda zatai tatsin kullun don duk kwanonin da akaci abincin daren jiyane a gurin ba a wanke ba har lokacin. Wanda tasan kuma karshen ta itace zata wannke su idan ta gama don haka ta mayar da hankalinta sosai ga abinda takeyi. Sai dai har lokacin Inna na tsaye da baba suna kare mata zagi har da mama dake gefe tana kashewa yarta karama kwarkwata a kai. Hakan bai ishi baba ba sai da yakai kofan Ummi dake ci gaba da gyaran dakin ta ya daga raggan labulen ta da ya dafe saboda dauda da tsufa dayayi. Zagin Ummin yake sosai a kaina ina jin shi sai sharan hawaye nake ina aikin dake a gabana mai yawa ban dai san may ummi tace dashi ba naji yace da ita da karfi akan yar taki har kike son ki mun rashin kunya Rabi ? Ban yi aune ba naji ya fada dakin ya fara dukan ummi sai ihu take kamar yadda ta saba idan yana dukan ta din don yau bashine karo na farko da naga yana dukan ta ba. Aiki nake jikina sai tsuma yake saboda muryan ummi dake ratsa kunnuwa na a lokacin da ina da hali ko karfi a ranan babu abinda zai hana na kwatar mata hakkin ta a gidan nan. Tun ina iya kuka ciki ciki har takai na bude murya na sosai ina fitar da sautin kukan nawa a fili kowa najiyoni a gidan . Sai da ya gaji ya fito daga dakin yana haki ya kara nufa na da zagi da baki irin wanda bai dace mahaifi yana wa yar tashi ba. Ina jin ya nufo ni na mike da gudu na bar wurin don nasan idan na tsaya zan sha na jaki ranan ba bisa laifin komai ba. Sai da naga ya shige na fito inda na labe baci gaba da aikina da nakeyi inayi ina kallon kofan mu ko zanga fitowar ummina daga dakin ta amma naji shiru. Sai da na karasa har wanke wanke na na samu daman shiga dakin namu inda na samu ummi kwance saman matatan katifan ta daya sude ta kifa ciki tana sharban hawaye. A hankali nakai tsugunne daidai kan ta ina fadin ummi sannu kiyi hakkuri ummi nice naja maki hakan. Ta sa hannun ta share hawayen da ya fito daga idanuwan ta ta dago da kyat ta dan motsa tana fadin ba komai yar nan akwai Allah yana kuma tare da mai gaskiya. Tace jeki ki shirin makaranta kada ki rasa haddan na yau a wuce ki ga abincin nan ki dauka ki ci ya dai bushe ko. Na koshi nace da ita abu ga mahaifiya sai ta manta da nata damuwan naji tace dani da sauri may kikaci maza dauki ki ci ki wuce don kin makara ko. Ban ki ba ina ci ina shan maji har nagama na shirya a gurguje na bar gidan da sauri sai dai duk abinda nake ina tuna irin wanan cin zarafin da baban mukewa mahaifiyana. Ina jin matan gidan na faman sakin magana a kan mu suna fadin ai kadan ma muka gani don sai mun raina kan mu a gidan. Ban tsaya ta kan su ba nafice abina don inda sabo na saba jin wannan kalaman a gun su tun ina yar ficiciyata har zuwa yanzu. Mun dawo daga islamiya banga Ummina a gidan ba gashi babu halin na tambayi wani inda ta tafi a lokacin. Waje na fita na yayo dan kirorin da zan hura wutan da zan yi madarana dashi har lokacin ummi bata dawo ba gidan. Na hada ina kokarin tukawa ne naji mama ta kwala min kira nasan ba komai bane abincin dakin mu take kirana na dauka gashi idan na bar madaran zai iya konewa. Ba yadda na iya dole na sauke shi a hakana na tafi bata barni na dawo gurin aikina ba sai dana kawar wa kowa da abincin shi na koma lokacin har ya sandare ko a haka rai a bace na juye ina nifin dakin mu naji sallaman ummina ta dawo gidan. Sai dai fuskanta yana a kumbure har lokacin sannu da zuwa nake mata a cikin zakuwa da ganin ta ta amsa min a dararare ta shiga dakin gidan ba wanda yai mata kin dawo. Itace ta fara shiga daki nabi baya ta kofi na dauko na dibar mata ruwan sha don ban tsanmanin ta sha ko ruwa har wanan lokaci nan naji matan gidan suna dariya suna fadin. Mutum ma da wani gata gare shi da har zaiyi yaji don baisan kunya ba ya juyo babu ko dan rakiya zikau ya dawo shi kadai. In mutum ya isa ya nuna shi din dan gatane mana muga tsomamun iyayyen mutum sun dawo dashi. A haka dai za a kare uwa lalace diyan ma haka na sai bakar wahalan banza kawai a duniya. Ban tsaya karasa sauraren su ba na debi ruwana na shige na sake fitowa na hada kan nannena suje suci abincin da aka samu dafawa a ranan don ranan girkin Inna ce ranan da wuya a rasa dan abin tsakurawa idan tana girki a gidan. Ni dai ina zaune ina zubawa yan kannena abinda zasu ci ina jiyo dariyan su da yaran su wanda nasan akan zance guda suke yin sa. Ranan dai a haka muka kwana da ummi ba tako iya magana sai idan ya kama nice nai ta controling din kanne na har sukai barci. Fita nayi duk da dare ya soma na karbo mata magani a gurin mai shagon uguwar mu ta hadein. Zan shigo gida na hade da uwale yar wurin mama take cewa ke kuma daga ina haka ko har kin fara fitan dare ne bamu sani ba. Nace a marairaice haba uwale sheri kuma zaki min daga ganina najuya naji ta shako bayana tana fadin wake sherin yar iskan banza kawai dake. Nace to yanzu may nai maki kuma tace ko zaki zage ni ne yanzu ki koma daki irin na uwarki jiki yai tsami. Nace saukin abin dai ai ba uwata kawai ake duka a gidan ba sai ko naji ta shake ni da karfi tana fadin da uwar wa ake duka in ba uwar ki ba kawai. Ta fara duka na sai ga dan wurin inna ya zai shigo yaya haruna don shi ba ruwan shi da harkan kishin gidan mu duk daukan kanne yake muna gaba dayan mu bai biyo sauran yaran gidan ba. Yace ke sake ta mana may tai maki tace dashi cikin hasala wai fa uwata take zagi don kawai nai mata magana daga ina take yanzu. Yace ke din daga ina kike ko wani ya baki gadin ta ne a gidan ku dai wanan bakin dan ubancin naku shi zai cuce ku wata ranna a gidan nan. Ta ture ni da karfi sai da na bugu ga rubaben bangon katangar gidan mu na dafe goshina ina kuka na shige ciki. Ina mamaki irin wanan bakar tsanar da mutanen gidan mu sukai muna mu da mahaifiyar mu. Wanda har hakan ya shafi wasu daga cikin dangin mahaifina suma basu kaunar mu ko kadan magana kadan in dai ya shafe mu yanzu zagi ko duka ne zai biyo baya. A yadda na samu ummi ta zauna daga kofa nasan duk abin da muke yana a kunnen ta kasancewar gidan namu ba wani babba bane a haka muke rayuwa a matse a cikin sa. Nabawa ummi maganin ta tare da debo ruwan da zata sha dashi na jawo dan keson tabar man roban da nake kwana a sama na kwanta daga gefen yan kanne na wanda kafin gari ya waye duk sun jika ni da bolin su. Sai idan babana yana dakin ummi ne nakan je dakin mama na kwanta daga kofa makure babu wuri a kasa wai babu inda zan saka mata tabar ma a dakin ta. ********* ********* ********* Gidan mu ana kiran shi da gidan Jima don duk wani nau,in fata zaka samay shi a gun baba wanda yake sarafawa ya mayar dashi fata. Mahaifin mu ya gaji wanan sanan ne a gun mahaifin shi shima mahaifina kamar yadda na fada maki a baya mata uku ke gareshi irin auren karfin hali na malam bahaushe. Mama itace ta wanke shi suna da shekara uku da aure ya auri inna wacce dama da ita yai samartakan shi tana budurwa tai aure ta fito ya aureta. Sai inna ta daya aura daga baya a wani kauye tazo gun yan uwan ta ya ganta ya shiga nema da yake Allah yayi dashi rabon zuria a tsakani kuma. Don saida yan suka suka dinga suka amma ummi tace sai shi take so tun wannan lokacin da aka kawo ummi gidan matan gidan suka dauki tsana da tsangwana suka saka mata tun abin na dan dadi har takai zama ya koma zaman hakkuri kamar yadda matan hausawa da yawa suke zaman yi a gidajen su. Idan ka dan yunkura daukan mataki sai ace kayi hakkuri don iyali sin taru suma matan abinda suke duba ke nan wani lokaci akan idan sun bar diyan su may yai makomar su kuma gidan gun matan dake gidan. Suma kan su kishiyoyin ummi din ba barin junar su sukayi ba don zakaji fada ya gaure a tsakanin ko kan diya ko kuma kayan abinci idan wata zata karbi girki a cikin su. Wanan halin da wuya ai kwana biyu cikakke basu samu baraka ba irin hakan wanda sai mutane sun shigo rabo daga waje. Haka yasa gidan namu ya kara suna gun mutanen uguwar mu gashi yaran gidan ba tarbiya ko kadan komai girman mutum zasu iya ci masa mutunci don samun daurin gindi a gun uwayen su da sukayi. Ba yabon kai ba don ina dakin ummi a gaskiya ko kwatance za a yi da dakin mu ake kwatancen masu daman gidan na mu a unguwa. Da wanan rayuwan muke zama a unguwar mu hakana yau da dadi gobe ba dadi don dai an fimu karfi ta ko ina a gidan dole sai zama na hakkuri kawai a tsakani tunda Allah ya riga ya hada zaman mu a cikin su. Bawai iya mu ba har wani wanda ya rabe mu haka nan suke hassada dashi da bakin ciki . Yadda duk ake son tarbiya muna samun shi a gun uwar mu don duk da matsin kishiyoyin da take ciki batai sake dabawa diyan ta tarbiya ba wanan fannin sai dai kawai talaucin da rayuwa na kakanakayi da muke a gidan. Allah ya taimake ni duk diyan dakin namu muna da dan kokarin mu a fannin karatun mu ba wanda baida kokari a cikin mu. Wanan ne daman da muka samu zance na rayuwa don da wuya ai hutu wani cikin mu bai dan samu kyauta ba nabajin ta muna dan samun abin dan more rayuwa a hankali. Ga irin dan kyaututukan da muke ciyowa a wurin musabika da kuma quzee din mukeyi a makarantar boko. Maimakon a taya mu murna a gida sai tarin takaici ko a ce an dai bamu ne kawai don bakin iya yin mu. A haka zamu wuni ranan cikin bacin rai a gidan saboda hattara da tsangwaman da zamu shiga gun mutanen gidan mu. ZAINAB IDRIS MAKAWA SEENABU 8/14/20, 7:10 PM - Ummi Tandama: BAHAGON, , , , , , , 🧕🏿2⃣🧕🏿 FREE PAGE SEENABU MAKAWA MAISON WANNAN NOVEL ZATA IYA KIRANA DA WANNAN LAYIN DON YIN REGISTER 300 TA BANK KO RECHARGE CARD NA 400 ZAINAB IDRIS MAKAWA ZENITH BANK 2253380105 SAINAJI KU MASOYA AI HAKKURI DA MU WRITERS YANAYI NE YA KAWO HAKAN DA FATAN ZAKU FAHINCE MU, , , , , Sauri nake ina shirin tafiya makaranta kasancewa yau monday don nasan akwai dogon assembly da wasu bayanai a irin wanan ranan. Socks na jawo na fara sakawa a kafana daya yayin da na ji an fara kwala min kira a tsakar gida. Haushi da takaici ne ya rufe ni a lokaci daya don nasan wani sabon fitina ina zata dora min duk wanan saurin da nakeyi zai tashi a zero ke nan bazan samu assemby din da nakewa kwadayin samu ba kuma wata kila aike ne ko wani aikin zanyi. Na aje socks din ban saka ba don karba kiran inna din samun ta nayi tana kokarin dama kunun koko take cewa dani na kwaso kayan zuba kunun ko wani daki na kawo mata. Na juya rai bace naje karbo kayan na kawo ina kokarin ajewa ne takai idon ta akan roban dakin mu sai kawai naga tai cilli dashi a gefe daya. Ni dai ina tsaye ina kallon ikon Allah ta fara zubawa sai data gama zubawa kowa ta jawo roban ta dan yafuta ta dan zuba muna rabin abinda take awo dashi ta dangwara mun sai na dauka na nufi daki ina juyawa a hankali ina kallon kunun da rai bakwai zasu sha su rayu a gidan. Ina kokarin rufe roban ne naji ummina tana cewa babu kunun ne ko don naga kin dawo da roban hakana ba komai a cikin sa. A sanyaye na ce akwai ima anzuba muna ta mike ta jawo roban tana kdllon kunnun dake a cikin sa sai naga ta dauki roban zata fita. Da sauri na tare ta nace ummi kiyi hakkuri kusha hakana may duniya don Allah bata saurare ni ba ranta ya baci tafita. Ba wai wanan ne karo na farko da Inna ke muna haka ba a gidan koda yaushe in dai ita zata raba abinci to na dakin mu kan kankare ne kuma ko mutum biyu baya isa a dakin namu. Ina ga yau ta gaji ne gashi kuma mun kwana babu ko kwandala a dakin balle ta dan sai garin kwaki ko kanzo tabawa yara dan abin dake gare mu munyi kitso da wanki dashi a cikin sati. Muryan Ummi naji tana fadin haba yaya wanan koko aiko su shaibu ba zai isa ba balle sauran yaran har akai ni. Sai naji Inna tace da ita au da kika fito kikai min tsaye a kai zikau dake tsoron ki zanji na kara maku babu ko may ? Ummi tace kawowa nayi ki duba ki gani ga sauran roban nagani duk a cike amma ki duba abinda kika zuba muna don Allsh dai. Tabe baki tayi tare da fadin yanzu aike akeji kunu ne shi naga daman zubawa idan kin isa ki diba ki kara maku tunda keda diyan ki kune yan gwal a gidan ku kadai akaiwa bakin cin abinci cikin mu. Ummi tace ba sai na diba ba ai idan bazaki kara ba abarshi don ban san wa zanbawa ba wazan hanawa ba, cikin yaran. Eyye lalai ma Rabi wuyan ki ya isa yan ka wallahi to bara kiji ke din nan dai da nake gani baki kai min can ba kunu ne ba zan kara ba sai kiyi abinda zakiyi dama naga tun da na zuba munafukar yar ki take bin kunnun da kallo tana min wani tsiwa a kai. Nifa din nan kujera ce daidai da zaman kowa idan wani abu kike ji da safe nan daidai nake dake yanzin nan don ban daukan raini da wullakancin kowa. Don idan mutum yai min tsiya yanzun nan na nada mai dukan tsiya inbuge shi in bugi banza naga wanda zai rama mai kuma. Ummi dai bata tanka taba ta duka tana kokarin juye kunun a roba da sauri inna ta tare tana fadin kada ki lalata muna kunu da wanan kazamin roban naku daya dafe don tsufa. Muryan babana naji ya fito daga dakin inna yana fadin wai may nene ya akayi ne kuma da farar safiyan nan haka ? Wani irin harara ta watso mashi tace wanan yar kauyen matar taka ke son shiga mun hanci da kudundune da safen nan akan kunun dana dama na basu. Niko idan ta kawo rainin da sukewa mutane kaina yanzu zata sha na jaki wanan iskancin ta tsaya iya kai tai maka shi can bani ba. Baba yace muga kunun sai ummi ta nuna mai ya kada kai yace haba Rakiya yanzu wanan dan kunun ace rai bakwai zasu sha shi ai babu gaskiya ga wannan zance yakai ido ga sauran robobin da aka cika yake cewa wanan nasu waye haka shi ? Tace ko zaka shigar mata ne naga daga jin muna zancen mu na mata kayi wuf kafito kana kokarin saka bakin ka ciki. Fitowan ka ba zai hana ni yin abinda nai niyar yi ba akai don ba wani yai wahalan dama min ba. Ita har waye da zata fito tace min wai banyi daidai ba ko iskancin nasu ne zai kawo gare ni yau kuma ? Ummi ta wufta da kunun a roban dake gaban inna ta juye tace ga kunun ki nan ki barshi Allah da ya halice mu ba zai barmu da yunwa ba yana sama yana ganin mu. Tace da baba kagani ko kaga irin cin kashin da tai min dai a gaban ka ko ita wacece da zanyi wahala dama kunu ta fito tai min wullakanci dashi. Ummi ta juya bata ce da ita tak ba ta nufi dakin ta inna ke fadin samun wuri banza diyan masiyata yar kauye wanda bata da tarbiya ta uwa ta uba. Ummi ta ce a, a yaya maganan nan iya ni dake ne baikai na iyayye ba fa don haka ki daina zaga min iyayyena da basu ji basu gani ba da safen nan. Don ni iyayena ba mutanen banza bane ko da suke kauye ba wanda ya taba ganin su suna roko a wurin wani. Dama mahaifin inna maroki ne ya tsufa amma har yanzu yana roko a cikin gari kowa yasan shi sai inna ta fusata da maganan ummi din. Tai wuf ta kamo hijjabin dake wuyan ummi ta shake ta har idanuwan ta suka firfito waje tana fadin rokon sata ne ko maita da zaki min gori dashi. Bata bata amsa ba ta sake sabon shake ta daga inda baba yake yana karasowa yana fadin sake ta mana Rakiya kasheta zakiyi ne ko may ? Kafin ya karaso ta kaita kasa ta danne tana duka tana fadin gobe ki kara zagin ubana don yana roko roko ai ba sata bane duniya. Jin sun kicimay yasani fitowa da sauri ga ummi a kasa inna ta haye tana duka mahaifin mu na kokarin banbareta daga saman ta. Ihu na saka da karfi har yasa mutanen gidan gaba daya fitowa dama wanda bai tashi daga barci ba ya falka. Ya banbareta saman ta shi da mama tana huci tana fafin gobe kice zaki kara zagina yar iska don an kyale ki har zaki kaiga zagin iyayye na. Haka kawai don samun wuri yar kauyen banza a kauyen may kuke sha banda ruwan kasari da gwabe da safe. Mama tace don dama sunyi hayaniya da yamman jiya a, a Rakiya baki da gsskiya ni kaina na san baki basu abinci yadda ya dace ba yau ba. Ta juya kan mama tana fadin bani bayarwa kedin daban ne wurin basu wake kwashe abincin bakeda yara ki ba ku goma a daki daya katan banza kin tarasu ba moriya. Daga can Nura dan mama daya taso daga barci ihu na ya tayar dasu yace kada kice zaki zagi maman mu yanzu rayuka su baci wallahi. Su dai da kika raina don basu kawo karfi ba ki tsaya a kansu amma mu kan idan kokai wa maman mu yanzu zaki ji mu don kin dai san mun fiku karfi da yawa kuma. Da sauri na karasa na daga ummi ina gurza kuka ina mata sannu ummi a cikin kuka itama din kukan take sharba a lokacin. Tsawa baba ya daka min wai na raba su da ihu kada na tara mashi mutane a gida a dauka ko anyi mutuwa ne a gidan tun da safe haka. Yaya Sani dan wurin Inna din ne mai dan dama a gidan mu yace a, a baba ai dole ne Safiya ta kuka irin wanan wullakancin haka a daki uwarta a gaban ta don basu da karfi kuma a hanata kuka ai cin zalun yayi yawa mana. Ya juya gare ni yana fadin ke ba makaranta zaki ba maza kije ki shirya ki tafi kada ku makara bar su da Allah kowa ya zalunci wani Allah na gani ai don ba anan duniya zata tabbata ba ai. Na dago kai nabi babana da kallo na sake kallon yaya sani din na juya nabi bayan ummi muka shiga daki. Sai naji Inna na fadin kaikan sani anyi hasara wallahi yanzu akan kishiya da yan uba kake fafin wanan maganan haka to tunda kaji haushi sai kazo ka rama masu nasan ka isa wawa kawai wanda bai san ciwon kan shi ba. Banji may ce da ita don rashin kunya a gidan mu ba sai na tsaya fadi ba ba abin kunya bane da yaci wa uwar shi mutunci a bainan jama, a. Ina kokarin daukan dan tsunman jakan makaran ta ina goge hawaye ummi ke fadin kuyi hakkuri yar nan mu kuma namu rayun a haka yazo muna gidan nan Bahagon rayuwan Allah ya nufe mu da gani cikin su. Yaya sani ne ya dago labulen dakin yana fadin ke Safiya miko min roban kunun naku naku nan ya dauke da katon roban da inna ta dama kunu a cikin sa gaba daya. Uwar na daga wurin madafa tana fadin wai ko dan nan ka ka daya kuwa ko an hada dakaine an mallake min ban sani ba wai ? Jikina na rawa na dauko roban dake gefe na mika mai ya raba kunun biyu ya juye muna a roban mu yana fadin maza ku sha ku tafi kada ku makara. Da sauri na dauka na ciki na fara zubawa yan kanne na don ina gudun inna ta shigo ta hana mu sha kuma. Har muka gama inna bata bar zagin Sani ba zagi irin wanda ba a son uwa taiwa diyan ta shi take faman zuba mashi. ********* ********* ********* Ko da muka shiga school ranan mun makara sosai nasha bulala na na wuce aji raina a bace ba don bugu ba sai dai abinda na bari a gidan mu na cin kashin da akewa mahaifiyan mu. Don ni a iya sani na banga wani hslin rashi biyayyan da take nuna masu ba a gidan don ko aiki yai masu yawa watarana sai ta taya su idan kuma diyan su ko sune basu da lafiya zakace wani nata ne ba lafiya ta shiga sintiri gaida mashi ke nan a cikin su. Ita ranan da duk wani yaron ta zai kwanta ciwo babu mai lekashi har ya ji sauki ya mike ba su gaida mutum. Don Allah maijin kan bawan sa ne da wuya dan dakin mu ya kwanta ciwo a gidan mu sai can ba a rasa ba zakaji wani cikin mu ba lafiya. Zan dai iya cewa ummin mu mace da bata da kyashi ko hassada kuma mu kan mu ta koya muna wanan akidar nata na matukar hakkuri tare da sanin ya kamata . Ba don halin nan nata ba na irin rayuwan da kishiyoyi da miji suke mata a gidan na wullakanci amma daidai da rana daya bata mayar da martani irin wanda bai dace ba a kan su. Ni na rasa may ke jawo wanan kiyayyan haka akan mu da uwar mu sai yanzu da wayo ya fara zo min ne na fahinci ba komai bane illa zalar kishi irin na macen bahaushe kawai. Don ummin mu yarinya ce a cikin su kuma har yawan haihuwar da tayi bai sa kyaun ta da dirin ta ya gushe ba gare ta wanda su sauran sai dai kawai zaman rayuwa. Zan iya cewa a gun mahaifiyan mu yan dakin mu maka kwaso dirin mu mazan mu da matan mu ba laifi uban mu ma dogo ne sai dai shi baki ne amma baya ga tsayin nashi komai na mahaifiyar mu muke debowa. Daga hasken fata tsayin don itama tana dashi zuwa suma hanci da idanuwa manya masu fari kal dasu. Don idan zagi ya tashi dashi matan gidan mu ke zagin mu ko yaushe sai suce damu shegu masu zubin uwar su. Sai kaji guda ta karbe da cewa ba dole ba tunda tafi miji jaraba dama ai ance wanda yafi jaraba a wurin saduwa shi da ke biyowa a duniya. Tun ban san kallaman ba har na fara fahintar ma anan shi idan sun fadi na turo baki ina maijin haushin kalamin su gare mu. Ranan dai sunan naje makaran ta ne amma babu wani abinda na iya tsinanawa a karatuna na dawo gida da bacin rai na samu ummi ta dan gyagiji tana aiyukan ta a tsakar gida. Uniform din kannena kwaso duk da tsofi ne amma bana taba barin su da dauda kullun na dawo sai na wanke muna su na sha idan sun bushe na buge nakai daki kafin mu wuce islamiya. Do ba halin na barsu nazo na iske an masu ba daidai ba ko tukunya za a sauke dasu ake saukewa idan an tashi aiki in suna shanye a waje. Mun gama shirin mu muka shirya zuwa islamiya mun fito ke nan yaya sani yana zaune a daban su na yan matasa yace dani ke Safiya zo nan. Jiki na min bari na nufe shi sai naji yace dani kunci abinci nace eh yaya munci yace to ki saurareni kiji daga yau duk wanda kika ga zai daki ummin ki ki nemo sanda kema ki buga mashi ninace a mutu har liman. Da sauri na dago kai ina mamakin kalamin shi yace eh don abin yai yawa daga magana sai duka irin haka itama Rabin na fada mata ta daina zama ana mata wanan cin fuskan tun bakuyi wayo ba har gashi kun tasa ana bu daya a gidan. Yace baki ji may Nura ya fada bane kowa ma ai uwarshi ya sani don haka ninace ki rotsa mutum koma waye. Yace maza ku tafi kada ku makara zance a gun yaya sani muka samu sauki dakin mu don yafi kowa zama tantiri a gidan mu. Sai gashi kuma Allah ya dora mu a kan shi yana jin mu a gidan ko dan ladabin da muke mashi ne oho ? Don zamu ganshi komai yawan abokan shi sai mun duka mun gaida shi idan kaya muka gani a hannun shi zamu karba a hannun shi mukai dakin su. Shima idan yar dahuwar shi ya samo ni zai nema na dafa mai kuma ko ya bani bana karba nace ya bar shi, sai idan ya zare min ido zan karba naci ko na bawa kan ne na suci. Tun wanan fadan da akayi gidsn mu ummin mu ta dan samu baki idan ana mata wanin abin cin fuska zata zage ta mayar da martani kamar yadda akai mata ba dadi din itama. Abin dake ci mun rai shine irin yadda gamu da yawa a gidan mu amma kowa a ware yake ba mai hurda da wanin shi dan dama tsakanin yaran dakin mama dana Inna akwai dan shiri a tsakanin su. Nice dai babu halin idan suna zaune ko suna wanin abin da ya shafe yara mata nace zanzo wurin yanzu zakaji sun fara hattarana. Suna fadin ke kuma may kika zo yi nan munafuka kawai sai wata tace muguwa mai irin halin uwar ta kawai in ba gulma ba may kika zo saurare nan. Dole zan bar wurin don zagi da hattara irin haka yasa ko suna abin su bana shiga shirgin su ina daki da ummi na ko ina wani aikin a waje sai dai abinka da yaro inayi ina sauraren su sai na manta na saka baki wata rana su kyale ni wata rana kuma nasha ba dadi garesu. In kaji dariya na ko farin cikina muna tare da kanne na ko kuma na fita zuwa makaranta ne. Idan baba ya shigo yaga bana cikin su yanzu zai fara fada dani wai ina tsabbare kaina a cikin yan uwana. Sai kaji Inna tace mugun hali ya ci may idan batai hakan ba ko uwarta baka ganin komai nata a makidance takeyi shi don dai kawai duniya ta zage mu. Ace muna gallaza mata ita da uwarta a gidan kasan mutum baida gadon ka amma yana da na maganan ka yanzu. Sai kaji baba ya amsa da naga alama ai an koya mata halin tsiya ta iya itama. To ba dole ba kullun suna daki ana mata hudubar tsiya a kai dabiar da ba zai amfane ka ba ko yau tana tsabbare sun hada kai da uwar ta a daki suna wance tayi min abu kaza don may bazata tashi da mugun hali ba kuwa ? Abin yana ban mamaki don sai inga ai komai a baiyyane yake ai a gidan ni dai a iya sani wani fitina bai tasowa ace da Safiya a cikin sa. Ko wani ya kawo kara daga waje yace ai Safiya tai mun wani abin suko ko yaushe cikin sallama mashi ake ana kawo karan su gun shi. Sai dai abin mamaki wanan bai sa yayyena maza su kini ba a gidan namu don su basu matsa min kuma ba su yarda ai min sheri a gaban su yanzu zasu ce zasu daki yarinya idan tai masu tsiya tun dai yaya sani. Kuma duk wanan abin idan sun dan samo kudin su gun Ummina zasu nufo dashi ta baye masu har ya kare. Da haka har ummi ke dan samu tana basu shawaran abinda zasu yi wanda zai amfane su a rayuwan su, sai kuma iyayyen nasu suka koma cewa. Wani sallon yaudara ne don ta raba su da yayan su ummi ta dauko sukai mata ahir da yaran su shikan yaya sani da ya samu labari tun a nan yau zaune tsakar gida yana fadin. Oho wai ni za aiwa yau don a raba ni da mai taimaka min a dinga kwace min kudi to ban yarda ba babu wanda zai hanani bawa maman safiya a jiyan kudi na a gidan nan. Ke mama da kike fadin haka ba nan Nura ya sayo akuya ba ku kai masa sheri aka sayar da akuyan akace mai ya bata. Cikin tsawa mama tace dashi kai kada ka kawo min diban albarka idan kaje kayo shaye shayen kane kake son saukewa a kaina bazaka sha da dadi ba yanzu na saka yara na suyi maka tsinanen duka a gidan nan. Wuf daya yayi ya yanko reshen darbejiyan dake baya gidan mu yana fadin yau naga shegen dan ki daya isa ya tabani a gidan nan idan ba a kwashi gawan shi ba shege nake. Yau kuwa zan gwada maki halin mashayan da kika kira min aiko yai cikin su a kofan dakin ta da take tsaye da diyan ta a take suka watse. Suna rige rigen shiga daki wani na ture wani daga kofan dakin wurin shiga dakin don yai masu mai ka uwa da wabi baki daya. Ashe fadan bai kare ba sai ga Inna ta na cewa idan har yaron na yana shaye shaye ke ko diyan ki barayin kororo ne da karuwai, waye bai san abin da suke a gari ba har akuyan da kike fadin an sace dake da diyan ki kuka sace shi ai. Nan fada ya kaure tsakanin ranan dai gidan mu babu dadi tonon asiri zalla suka dinga yiwa junan su har abin dake a boye saida kowa yaji shi gare su. Baba na kasuwa dole aka kirashi shi yazo ya kashe wanan wutar fitinar da ya ruru a gidan don gaba daya yaya Sani ya haukace masu a gidan. Iyakarmu kallo da saure sai washe gari da baba ya kira sulhu da safe kuma suka so su dora laifin gun ummi na mai farin jini a gare su. A nan ma yaya Sani baiyi shiru ba yace may ye laifin ta a ciki kudi dai ne har gobe ko kaya ita zanbawa a jiya ni babu ruwa na da zancen kishin ku. Dole inna tana ji tana gani suka saka mashi ido don ya riga da ya kangare ba mai iya lankwasa shi a halin yanzu. Idan ya shigo gida har da gaiyya yake jan ummi na da hira a cewan shi haushin mama yake ji don itace ke kulla duk wani makirci a gidan. Ita ko Inna bata tsayawa saurare sai ta hau ta zauna a kai daga baya kuma mama ta zamay jikin ta ta nuna bada ita akayi zancen ba ta bar Inna a ciki. Mu dai a gun mu har gobe gaba dayan su a yan uwa muka dauke su ba mu banbanta a tsakanin mu dukkan su a yan uwa muke daukan su. Sai dai su a gun su ba wani canji a gare mu dasu har gobe halin yana nan na yan ubanci da suke nuna muna a gidan. Mun zama su shanun ware ko bare da suke kyankyamin mu daga cikin su suna bakin ciki su bude ido su ga dan dakin mu na wani abin ci gaban rayuwa yanzu sheri zai tashi a tsakani sai anga bayan abin an durkusa. ZAINAB IDRIS MAKAWA SEENABU 8/14/20, 7:10 PM - Ummi Tandama: BAHAGON, , , , , , , , 🧕🏿3️⃣ 🧕🏿 FREE PAGE, , , SEENABU MAKAWA, , , NA ROKE KI DAN ALLAH DON SON MANZON RAHAMA IDAN DA ZUCIYA BIYU ZAKI SHIGO GROUP DIN KADA KI SHIGA DON ALLAH DON BAZAN YAFE MAKI BA WANDA KIKA TURAWA HAKKIN YANA AKAN KI YAR UWA DON ALLAH KI HAKKURI DA DAUKAN HAKKI AKAN NOVEL DON BA A YAFE BA ONLINE NOVEL NE KIN SANI BA PUBLISH NOVEL BANE DA KI KE FADI KIN BIYA NE DON ALLAH MU SAHIRCE WA JUNA AKAN HAKA YAR UWA KAN ABINDUNIYA DAFATAN ZAKI KU FAHINCE NI. Yau alhamis bamu shiga islamiya don haka na ke son zuwa ziyara gidan yan uwan mahaifiyar mu dake a cikin gari. Zaune nake ina kwaliya a kofan dakin mu yayin da mutane gidan mu ke ta aiyu kan su na yau da kullu a cikin su har da ummi na wacce ke wanke kofi. Sallama aka shigo dashi gidan dashi shi ne ya dauki hankalin kowa a gidan baki daya tare da amsawa. A, a mutanen lagos yau she agarin abinda su maman mu ke fada ke nan mu yara muka shiga sannu da zuwa. Ta dan tsaya a tsakar gida suna gaisawa sama sama da mutanen gidan da ga nan ta kwasa tai dakin mama, Daya bayan daya ake shiga gaida ita tana amsawa don sanin muhinmanci ta ga iyayye mu baki daya. Gwago kulu ke nan kauna ne ga mama kuma yar uwa ga mahaifin mu don mama da mahaifin mu yan uwane dukkan su auren gida ne sukayi irin matar fari zabin iyayye din nan. Haka yasa mama ke shimfida mulkin ta yadda taso a cikin gidan daga ita har yaran ta ko magana ake a gidan wanda ya shafi gida zakiji mama tace mu din kujera ne dole a bi mu. Don da mijina aka samay ni ko anki ko an so dole ne a gan mu a gidan babu yadda za yi damu dan mu yandagi ne. Watarana idan tana irin wannan habaicin Inna takan biye mata suyi tayi sai sun gaji har ta kan ce ban ga macen da zato tace zata shifida min doka ba a gida na. Sai dai duk wannan haukan ga may wayau da hankali yasan Inna ce ke shimfida mulkin ta a gidan don baba a can hankalin shi yafi karkata. Ni dai nakan ce tsoro ne don wani lokaci zaka ga ya juya gun wata da zaran inna taga haka yau zata birkice mashi da masifan dare daban na rana daban saiya dawo a kan ta. Duk wani dan uwan mahaifin mu da zai za gidan wirin mama zai yadda zangon shi ba zai tafi wani daki ba sai in wani dalili ya kawo mai shi. Wannan abin yana kona wa inna rai don ita mace ce mai son taga komai ita ne a kan gaba a gidan namu. Saida na kanmala kwaliyana na saka hijjab dina na karasa kofan mama ina fadin sannu da zuwa gwago alokacin sun hade kai da mama suna magana a hankali kasancewan su biyu ne a dakin ki. Cikin dan hanzari ta amsa min da yawwa na juya zan tafi sai take cewa wa nake gani kamar sai tai shiru can tace ba yar wurin Rabi bane ? Mama tace itace tace, mana tace ikon Allah girman dan mutum baida wuya har yaushe yaushe aka haifi yarinya nan diba yanzu yadda takai da girma. Sai naji mama tace ta biyo tsawon kafan uwar tane kisan Rabi ba baya ba wurin tsawo shine suka kwaso ai duk haka yaran suke in kin gansu. Nidai na tafi ba abina ban tsaya jin sauran abinda zasu fada ba don dai zancen bai kare ba na bar su akai. Dariya naji sun kwashe dashi wanda nasan wani sheri aka fada wanda yai dadi har sukayi hakan . Mu Huda muka fita da kannena gidan gwagon mahaifiyar mu muka fara zuwa inda muka samu taro na arziki ta rasa ida zata saka mu. Haka mu ke gani idan munje gun ta muna samun taro yadda ya kamata sabanin dagin mahaifin mu, wanda basu ma san da zaman mu ba nake gani. A binci ta shiga girka wa don idan muje wuni muke a gidan ta, nafito na kama mata aiki yadda ya kama ta har muka kan mala yin komai. Abinda bamu saba ba gidan mu an cika muna kwano da shinkfa da mai da yaji sai ci muke yi hannu baka hannu akushi. Ga zobo mai sayi data sayo muna mu sha dashi mun kai kat na kwashe kayan da mukai aiki da amfani dasu da wanda mukaci abin ci akin sa. Na gyara mata gida sai nace da ita zamu mu gaida su mama watau diyan ta ke nan dake aure a cikin uguwa. Tace kada mu dade don mu koma gida da wuri mun tafi inda can ma muka samu taro yadda ya kama ta sun bamu alheri su man shafi da sabulu da omo da dan kudi muna ta murna mun samu kyau ta . Gwago ma tai muna abin arziki muka dawo gida bayan sallah la, asar cike da zudin kyautan bajin ta da muka samu. Muna tajin dadi muka nuna wa ummi alherin da tan uwanta suka kai muna ta sani tare da fadin shine abin dayasa bani son kuna zuwa gidan su don dawai niya kuke kai masu. Kani yai caraf yace ummi cewa sukayi fa mu dinga zuwa ko yaushe kuma kikece damu kada mu koma abamu . Gaba daya dariya muka sa mai ummi tace damu tare da dubana nida nake da wayo a cikin su yawan zuwa zai sa su gaji daku ne ku zauna matsayin da Allah aje ku Allah zai dube mu. Jikina yai sanyi don na fahinci may ummi take nufi din a sanyaye na ce in sha Allahu ummi baza kara zuwa mu kai masu nauyi ba haka. Dan abinda muka samu ummi ta ware min wani abu acikin sa waina kara jari dashi na sana, a na da nakeyi kada mu kashe a baki daya. Wanan kudin shine sillar da har takai mun da samun sauki a dakin mu don a hankali na fara sarrafa kudin biyar na kamowa goma gama na zama ashirin ashirin ya koma wazo har zuwa sama. Idan baka raina sana, a tau watarana sai ya koma maka babba don tun ina dan madara har na koma ina soya ruwa ana saye a gida. Sai gashi har nawaje suna shigowa saye na hada da aya da sauran makulasa sai sanaa ya koma na ummi na. Sannu sannu ina sana,ar har muka koma mangyada da sauran abin amfani kudi na shigo muna. Sai hassada da kyashi ya shigo a cikin wa yan gidan mu nan kuma bamu da sauran shakat gare su zasu ce damu ganin muna dan sana,an dake kawo mu kudi ya muke son yi masu gani gani. Sai suka da habaici ya tashi har zance yakai gun baba na magana kadan yanzu zai yo cikin ummi da zagi yace wai mutane suna shigo mai gida don su din ga lekan may asirin gida suna fita waje suna fadi. Nan mama ta turza don kan taki yarda da zancen baba na wanga karon ta ko hankace mashi da fitina tana cewa ai da takoma in irin halin da ta fito gara ta hankura dashi ta tafi inda ake son cigaban ta yafi mata don ta ganne cigaban ta akewa hassada bakomai ba. Inda watane ke wanan sana, ar aiba za hana ba amma don anga tana samu za ai mata bakin ciki ga sana,an ta, kowa na dan sana,an shi cikin gida bai yi magana ba, sai nata ne za ia wa bakin ciki. Da haka zancen ya mutu karshe mama ta ce ya kyale ta taita sana an ta tunda kowa na saman sanaar ashi badon aina tasa ba dole ta kyale ummi ta ci gaba da sana, an ta tana na kallo ba yarda zata yi a gidan. Wanan ke nan ya wuce saura wani kama don ummi ta kyatare wanan karon daga kaidin ta. Wanan abin da akeyi ina yar shekara goma sha uku da haihuwa amma duk idon gidan mu na ga kaina gaba dayan su kamai yan yazu ace safiya ce. Koban ji ban gani ba don dai kawai ai min fada suji dadi yanzo zasu jawo abinda za ai min fadi din . Duk wani aiki aike yi mai dadi da akasin sa duk ni zan yi amma duk wanan ban tsira akan shi ba don cewa suke wai lalaci da raggaci yai min yawa. A haka jebawan mu shiga secondary yafito inda naci makarantan kwana aiko take yan gidan mu suka nuna bakin cikin su ka zancen. Suke cewa makaratan kwana ko lalacewa may zaki koyo banda lalacewa a makarantan kwana bokon diya mace ko lalacewa. Kai komai sun fada akan wanan zuwa karatun nawa karshe dai baba sha zuga sai cewa yayi abar zancen karatu don shi bai ga amfanin yin karatu ga ya mace ba. Ina ji ina gani aka watsar da zancen karatu na ganin da gaske baba keyi na sulale jiki na tafi wurin gwago na fada mata komai. Batai sanyi ga gwiwa ba ta sami babana a kasuwa don magana bai yi a gida nan dai gwago ta shawo kan shi har ya yarda amma da sharadin . Baba hannun shi a ciki ko kwadalan shi ciki gwago tace taji ta dauka akwai Allah zakawo mafita. Amma yace ba zai yarda da batun zuwa makarantan kwana ba gwago tace taji zasu samo jeka ka dawo na tafi. Wannan shine dalilin zuwa na makaranta da nayi mutane gidan mu dai sun ga ina shirin ba su san komai ba. Ranan da zan fara zuwa hankalin kowa a gidan ya tashi don sai suke zargin mahaifin mu ne yai min ko mai. Nan ko ina ta saka shi a gaba da cewa munafucin banza da wofi idan an tanbaye shi kudin yace bai dashi amma ya dau ki yar gwal ya saka a makaranta don ran uwar ta yai dadi. Ba dole ba yana gudun bacin ran uwar ta kada ta hana shi kwana da ita ya rasa jin dadin shi. Da abin ya ishi baba yai ratsuwa har ya gaji shi ba dasanin shi bane baiba ma san wanda yai samo min makaranta ba amma nasu yarda ba. Sai cewa yayi ya biya min din suda yake wa dayan su lalurori fa saiko fada dashi da inna har takai ga yin ya ji a gidan. Yaya sani yace safiya ki shirya da kaina zan kaiki in ga wanda ya isa ya hana ki zuwa na gane yan bakin ciki ne mutanen gidan nan. Da yaya sani muka tafi makaranta sai da yaga komai ya kamala ya dawo gida. Tun wanan lokacin aiki ya rage man agidan namu saboda ban da lokacin zama a gida har su ganni suce in ma su aikin. Sannu a hankali girma ya shi gana yanzu na fara ganewa bawai son ummi ne mahaifin mu ba yayi ba kawai dai shakun matan shine yake ji. Na gane hakane ta yadda idan ya fakaici idon matan shi yake nuna kulawan shi kan ta har nama yakan dan ja ta da wasa ko da ba, a. Sai dai idan matan shi sun gani ya kan dan yi kamay kamay kamar bashi ne daga karshe dai ya koma fada kamar bashi ba. Kadai muke zaman mu da dadi ba dadin a gidan watarana mu kwana da farin ciki watarana akasin sa. Sannu tashi na kamal aji uku zan shiga babba ajin aga da secondary sai ga gwago tazo daga lagos nan mukai ta murna da zuwan ta sai awan kararon bata ita kadai tazo muna ba. Ita da zurian ta da maigidan tazo ganin mu nan aka shiga ina aka saka da ita da diya ta da maigidan ta don dai ba karamin son ta yan uwa keyi ba, in zata zo takan sayo abubuwan anfani tajo ma iyayyen mu da shi. Nikan ina saurin naje makaranta don haka tsayawa nayi daga kofa na gaida su dan suna dakin mama ne zaune har mijin nata da yaran ta. Take cewa wanagani kamar yar wurin Rabi haka koyaushe za a gan ki kamar ke kadai ke kiwo a gidan gaki tsatsab dake kamar wata wayyayiya. Murmushi kawai nayi zantafi sai naji tace wanan ai takar ita koke kiyawu agidan. Ta juya tana magana da mama bandaiji abin da suka fada ba nai tafiyana don ina saurin in tafi makaranta. A kofan gida muka tarar da wani matashi yana shan taba zaune saman mota kallo daya nai mashi na kawar da kaina daga gareshi. Sauri nake na wuce don da gani tare suke da gwago mu sai naji yace ke shiga ciki ki dabo min ruwa nasha. Na dauka badani yake ba ina kokarin wuce wa naji ya sake cewa dake nake fa na juya baya na ko zanga wace yake magana da ita. Sai naga babu kowa a tare dani na dan tsaya kadan yace ruwa nace ki debo min a ciki. Juyawa nayi nakoma na debo mashi ruwan nakawo mashi ya kurba sau daya yake cewa wanan wani irin ruwa ne mara dadi. Nace shi muke sha a gidan mu don haka shi ke gare mu, oho i see waya kaleni sama da kasa yake cewa karbi ki mayar . Haushin sa ne yakama ni lokaci guda don ya rena muna wayau da arzikin gidan a haka dai na karba na wuce shi don warin taba duk ya isheni da hamami. Na dawo zan wuce yake cewa dani ke yana kokarin kuna wani taban a bakin shi shigo kice wa su mum sufito haka nan dan Allah. Kamar nace bazan tafi ba sai dai na juya zantafi sai gasu sun fito daga cikin uban na gaba suna biye a bayan su. Nikan nawuce abina ban tsaya kara sauraren su ba don dama nakara zuwa islamiya duk da nasan bawai buguna za ayi ba amma ya kamata ace na isa a cikin lokaci. Har na isa makaranta ban dana jin warin taban da aka sha a jiki na ba gani nake duk jikina warin taba yake kamar nice nashi taba din . Mun dawo na debi kayan mu na wanke don ban samu wanke wa da rana ba aka raba tsaraban gwago ko wani daki aka bamu. Saida na shigo dakin mune na samu tsaraban da gagwo ta kawo muna a gefe, na samu wuri na zauna gefe ina cewa da ummi. Wanan mutumin dasu gwago suka zo dashi dazun baida tarbiya zama fa yayi kofar gida yana shan taba a gaban ko wa. Ummi tace dani wa kina nufin ubale aishine dan gwago kuna fari duk sain an ni shi sunyi aure amma shi, shashanci ya na shi yi wai shi dan fari yana takama da zama cikin kabilu ya saje dasu. Nace Allah ya kyauta amma kan wallahi bai yi ba wallahi mutun sakace wani ibom can. Muna cikin magana mukaji fada ya kaule a tsakanin mama da inna kan kayan da gwagon mu ta kawo tsaraba inna ke cewa da mama wai tarage kayan ta basu abin da taga dama. Mama ta bata amsa da cewa yar uwarki konawa ina yar uwa nane dai ko kaya kuma abinda naga dama kenan na bayar inkina so ki karba inbaki so zaki iya mayar. Mama tace idai kayane je ki ta ci saukin abindai muma muna da yan uwa bake kadai keda su ba balla ki kawo muna bakar magana. Muna daki da ummi muna sauraren su har suka sude bamu leko ba sukayi suka kare ba mu leka waje ba. Washe gari kuma da safe suka aza sabon fitina a gidan baba na dakin inna ya fito yake cewa daga yanzu indai rabo zai kawo fitina kowa ya rike abin sa a zauna lafiya. Da haka karshen fitinan ya mutu kowa in yaga dama ya rike kayan shi ba dole araba wa saura inna tace yafi nono fari. Mu dai namu dasu ido don sun fi kusa wanda yace zai shiga fadan su a ciki zai kwana minti goma yai kadan aga sun shirya tsakanin su. A yau asabar bamu zuwa makaranta don haka na shirya cikin kayan da mama lami ta ba ina son zuwa gaida kawata da bata da lafiya. Wanan ne karo na farko da na sa kayan a gidan mu don basu san ni da kayan ba nan sukayo mani ca da idanuwan su naji mama tana fadin. A yau kwaliya akaci haka yau sai ina da wanan adon nai murmushi kawai ba tare da na bata ansa ba sai naji inna na fadin ke ma dai yaya da wani zance ki. Yarinya kekaga tana wanan irn kwalliya haka ai kin san abinda take yi inba mashin shine ai banza ya kai zomo suwa ke ma kin san aida wallakin wai goro cikin miya. Muka hada ido da ummi na sai taimin da alama da ido na kyaleta na kara shiryawa nake cewa zan tafi tare da yi masu sallama. Inna tace dama diya mace inta dadani namiji ai ba tafiba hankalinta bai taba kwanciya yawon gantalin za, a ake sallaman mu. Kai akwai ki da wani zance wallahi ina safiya da ga wani saurayi kyalle ta dai da nacin son karatu a rayuwan ta inji mama ke fada mata haka na. Ta ja tsaki tace ai ku ke kara zugata wanda baida lokacin kan shi a gida kulun boka watafi son karatu adaiyi shaani kawai wai an cuci na kauye. Na fito gida ina tunanen kallamin inna ba zaka taba jin kalman alheri abakin ta ba in ba yayan ta bane sai na sheri. Ita da bakin ta take fadi wata rana yarinya ga kyau ga wanka amma babu saurayi yau kuma ta can za ta kuma ce maza naka bi. Naje gidan su Amina na samu bata da lafiya sosai amma ta samu sauki na dan zauna da ita mukai hira nawani lakaci na mike zani gida don kar na dade Inna tace sai da ta zubar nadawo kuma. Mun fito tare da Amina donta dan taka ta walwale jikin ta muna tafe muna hira inda muke tafiya a hankali ina bata labarin text din da kayi muna, bata nan yadda ya kaya. Hon din motane ya damay mu daga bayan mu da kara daga ni har ita ba wanda ya juya dan gani ko wa nene mai mator kuma bai daina hon din ba. Ganin ba zamu tsaya ba yasa shi fito wa a motar ya biyo mu, sallama yai muna duk muka juya a lokaci daya muna kallon shi. Nikan a zato na sun san juna ne sai kawai na fara tafiya na barsu tare ban tsaya ba kada naja wa kaina magana ban yiba ance nayi ina ga na tsaya. Sai naji yace don Allah malama ko zaki taimaka taimaka min da yar uwar ki ta saurare ni min ti biyu in ba damuwa. Safiya dake ake magana inji Amina, na juyo nace wani a cikin mamaki yace nasan badaidai ba ne na tare ku a hanya. Amma kuma dole yasa na tsada ku a hanya yanzu don idan kun tafi ban san ina zan kara haduwa daku ba. Nace gaskiya bazan tsaya ba sunana ya baci ga ban za a saman hanya sai yai murmushi yace naga alama ai amma don Allah kibani dan lokaci nasan wani abu gare ki. Allah daya ke hada mu dashi har da Amina din yasa na tsaya badon na so ba ya ce sunana sulaiman ni dan garin nan ne saidai ba anan nake ba. Ina fatan zaki bani amsa ga tambaya a wurin ki don Allah ida bazaki damu ba zan so nasan gidan ku don na gabatar da kaina. Gaskiya malam kayi hakkuri saboda karatu nake yi sai an jima nan nabar su tsaye awurin na wuce. Ya dan rintse idanuwa shi tare da sauka da ajiya zuciya yana mai sauke num fashi , ya dan yi murmushi tare da duban Amina dake gefen shi tsaye yace. Idan ba damuwa ki tai makeni da noba ta kokuma gidan su zai fi sauki a gare ni nan dai yabawa Amina tausayi tabashi addresen gida yai mata godiya ta tafi. Ban da lafiya da fatan zakuyi hakuri da mistake din kuka gani anan kwana uku ina typing ban iya hadawa ba. ZAINAB IDRIS MAKAWA SEENABU 8/14/20, 7:10 PM - Ummi Tandama: BAHAGON, , , , , 🧕🏿4️⃣ 🧕🏿 SEENABU MAKAWA DON ALLAH NAMIJI KAYA SHIGA DON MATAN MUTANE MUKA KA TARA ANAN INKA KA SHIGA ALLAH YA SAKA MU NA DON ALLAH YAR UWA ABIN DUNIYA KAR YA JAKI GA HALAKA IN KI BIYA KADA KI TURAWA WANDA BAI BIYABA DON BAZAN YAFE MAKI HAKKI NABA, , , , Dare ne kowa na zaune a tsakar gida saboda zafi da duhu da akwai yaro ya shigo yana kwala sallama a kofa. Baba na gida ya amsa yaron yace wai ana sallama a waje sai baba yace yaya Nura ya duba yagani. Zuwa can ya dawo yace wai wani wai wurin Safiya yazo amma ya ba son ganin ka. Inna tai caraf tace Safiya kodai Ainau, Safiya ina taga saurayin da zai mata sallama, ga wayannen ta tanan wake maganan ta. Yace nidai abinda ya fada min kenan na fada yasamu wuri ya zauna yaci gaba dacin abincin sa. Inna tace tashi maza Ainau jeki ki gani wake sallama dacewan Ainau yar wurin Mama taje ta ga ba wurin ta bane tadawo kafin Ainau ta dawo ta shige da yar ta mairo daki. Sukayi ku ku ku da ita saiga Aina tadawo tana fadin Inna ba wurina bane wannan fa dangaye ne ke sallama a waje. Saiga Mairo ta fito zata har takai kofa taji ance ke dakata wurin ki aka zo ko kuwa tace zan duba na gani ne. Maza koma ki zauna yaya sani ne ke wannan maganan da mairo daga dakin Inna ta daka mashi tsawa tace kabari tafita ta duba mana ko ita akewa sallama. Ya ce yaushe mairo ta koma Safiya a gidan nan ne ke bana son rainin woyo maza kidawo wurin nan tun ranki bai baci ba. Sanin hali yasa ta juwoyo simi simi ta da dawo cikin gida ta zauna ya mike ya fita zuwa kofan gida wurin bakon da kansa. Duk wanan kace nacen magana da suke faman yi kunnen mu nida ummi sukeyin sa, kallo daya zai kayi min kagane a rikice nake. Ummi dai batai min magana ba don tsaban tsoro duk jikina ya dauki rawa a lokaci daya can najiyo muryan yaya sani yana kwala min kira. A rikice na fito daga dakin na rabe gefe guda a tsugunne lokaci guda yake cewa dani, akwai wanda kukai magana dashi zai zo gida ne ? Gaba daya hankalin yan gidan mu ya dawo gare mu suna sauraren mu a hankali na bude bakina zanyi magana . Naji Inna tace dani ke yan zuwa har da masu mota kike tsayawa don tsaban miskilan da munafunci irin naki na gado. Nasoma rantsuwa baki na rawa ina fadi wallahi tallahi na rantse da Allah inna bantaba magana dakowa waye ba Ji nayi yaya sani yace Safiya na amsa da sauri da naam ya ce tashi kije inda ake maki sallama waje. Ai gara dake daza ki jawa mai mata kika jawo muna su diyan su da kara da doki duk zuwa yake wurin su fa. Maza tashi tafi kada yaga an tsaida shi kin dade baki fito ba ya dauka bakya nan ne. Na mike gwaiwa da sanyi da ce tau yaya nufi kofar gidan wurin wanda aka ce din yana min sallama wanda yaja min zagi da zargi agida uwurin mutanen gidan mu. A kofan gida nahango shi tsaye ya jingina jiki da mota hannu daya kuma ya dafa motar shi dashi ya tsura wa kofar gidan mu ido. Yana gani na ya dan muskuta tsayin shi yagyara da kyau har na iso kusa dashi. Fuskana kamar zanyi kuka a lokacin nazo na tsaya sai yace dani ba gaisuwa yan mata kamar baki na na ciwo nace dashi Ina wuni ? Shima cike da yanga yace min lafiya lau yan mata, Wai halan ba ke kadai bane Safiya a gidan naku sai naga wasu yan mata nata fitowa da sunan safiya mana. Saida na dan bata lokaci kafin nace ni kadai ne mana kawai da sun fito ne sun dauka wiri su aka zo yaron yai matuwa yace safiya don sun ga ba wanda ke aikowa kirana sai yau. Ya nisa tare da cewa "kai, kice ni din nazo a sa, a ke nan nine zan bude fage in bar tarihi. To amma naso naga baba ne da kaina koda yake ai naga yayan mu ya bani go ahead naci gaba da zuwa . Kallon sa nakeyi ta gefen ido ya yagyara tsayuwar shi da kya yace na samu goyon baya kai tsaye ke na kinga duk lokacin da nake son ganin ki ina iya zuwa. Na turo baki ina cewa indai na amince da hakan ko nifa na fada maka karatu nake son yi ban da lokacin tsayawa soyayya. Ba zabin ki nake son ba illa yaka ki bani hadin kai shikaratu nufi ne na Allah. Don haka ki bar Allah yai maki zabi kar ki raja, a a bangare daya don kinfi son karatu kice gareshi zaki tsaya. Kunya bakin ciki da takaici suka sauka min a lokaci daya na rasa amsa da zanbashi kawai sai hawaye suka dinga zubo min . Ganim ina kuka yasa shi cewa subbahanallahi ko ban fadi daidai bane ga magana na kike kuka. Ganin bazan yi shiru yace Allah ya naki hankuri idan kin huce na dawo mu gaisa watarana dama yan yanzu zuwa nayi wurin baba don neman izini ban samay shi ba naga yayan ki. Ya bude motar shi ya dauko leda cike dakaya ya miko min nace yabarsu na gade yake cewa Safiya nadai gane bakiyi naam dani ba ne. Nace ba hakana bane in son samu ne nafison saina gama karatuna tukun yace wanan baida matsala mudai samu fahintar juna tukun shi yafi. Nan nabarshi da kayan naki karba ashe ya samu dan makwabtan mu yace ya biyo ni da kayan ciki. A Cikin gida kuwa tun fitana mutan gidan suka kasa suka tsare suga yadda za a yi yayin da inna take ta masifa da yaya sani akan wai nata mata shiga hanci da kudundune kan ala, amarin ta inda take shiga ba nan take fita ba. Shigowa na kenan yaron da ya biyo ni da kaya ya shigo gidan shima inda na nufa can yaron ya nufa da kaya niki niki. Yaya Nura ne yake tambayan yaron maynene yadauko a hannu shi haka sai yaron kewa Safiya ace nadauko mawa . Gaba daya suka sako ido suga kamay nene a cikin ledan saidai bazasu iya ganin ko may a ciki ba saboda duhun dakeyi. Inda da hali dazasuce akawo ledan suka abinda ke cikin sa sai dai hakan bazai yuyu ba don yaya sani na gida alokacin. Dole da ido suka koma yin magana ba halin su maganta yai cikin su da rashin kunya. Har washe gari kayan na nan a jiye ba a taba ba ba a kuma bude ba a cewar umma in yazo na mayar mai da kayan sa kada na nadauko mata wahala tana zaune kalau. Daga ni jar ummi tsoron taba kayan muke ja agidan bamu yarda nun taba komai ba daga ciki Ummi tai mashi dogon ajiya. Abim duniya ya isheni a raina ga kayan mutumi a je a gidan mu ina tsoron tabawa a tsakar gidan mu sai habaici ake min cewa a samu a hanawa dangi. Amina na samu a school nake fada mata halin da nake ciki don dai gaskiya ni sulaiman yafi karfina da soyyaya. Dariya Amina ta soma yi min tana cewa safiya kenan ina kika taba jin haka kedai kawai kice matsayin ku ba guda ba. Amma zancen yafi karfinki bai taso ba don dai sulaiman mijin da mata da yawa zasu so ne. Balle mutumin daya nemi izzini ta gidan ku ai zance ya kare iyaka muyi fatan alherin ga hakan, nisawa nayi nace da ita Amina nifa in son samu ne nafi son sai na gama karatu kafin na fara zance da wani namiji . Safiya kin kwantar da hankalin ki bafacewa akayi zaki aure shi ba dole, abune nufin Allah . Nace haka ne amma ni sherin mutanen gidan mu nake jiwa don masheran tane na karshe sun sa yadda zasu kulla wa mutam sheri ya zama gaskiya . Da dai zai jaye ya je gaba yane mi wata zai fi sauki don ina gudun jefa shi a cikin zargin mutamen gidan mu. Ba tadai yarda sai bani karfin gwiwar da tayi akan na hakkura naga ya gudun shi in yasu sai nayanke hukunci akai. Sulaiman mutumin kirki ne sosai a yadda na fahinci shi ba a garin yake zama ba zuwa yake duk karshen wata kokuma farkon wata. Idan zaizo yakan yo muna sayayya yadda ya kamata ya zo muna dashi har kullun yazo bani sakewa dashi amma shi sai yake daukan hakan da kurciyane kawai. Tun yana zuwa ban sauraren shi har yakai na fara sauraren shi ina dan bashi lokaci sannu sannu har kowa ya fara sanin shi a gidan mu. Dan idan yazo zai ba da kudi da kayan rabo irin su sabulu da manshafi a rabawa mutanen gidan mu, inda ni kuma yakan kawo min kayan provition na amfanina. Wannan abin shiya tsone idon mutanen gidan mu don walwalan da suke ganin mun samu a gidan. Tsegumi da kazafi yaki karewa a gidan sai cewa suke wai babana yaga kudi shiyasa idon shi ya rufe bai iya magana wai har cewa sukeyi . Sulaiman na dauka na da mota muna fita yana yawo a cikin gari maganganu dai marasa dadi suke kai da kawo akan zancen. Sai dai ummi na hankalinta yakan tashi dajin wannan zancen sai da dare tan tayar dani daga barci ta sakani a gaba da cewa. Yar nan kirufa min asiri ki kamaka kan ki karki tona min asiri a cikin abokan zama abin na da suke fada gamay dake Allah yasa ba gaskiya bane kodai daya ke nasan ki nasan halin ki. Nasan abin da zaki iya da wanda bazaki iya ba amma dai dolene na kara tsawata maki akan hakan. Don Allah ki kafa mutuncin ki ki rufa muna asiri yar nan bani kadai ba har da mahaifin ki nakan son rantse mata cewa ba gaskiya bane sai ta dakatar dani da cewa bar ni na fada maki yar nan. Nice mai fada maki gaskiya duk duniyan nan ku nake da ku nake gani ina alfahari a duniyan. Idan ummi tafadi haka nakan ji wani irin tausayin ta a raina wana abin yasa sulaiman ya rage zuwa gidan mu wanda Hakan kuma suma ya shafe su don dan abin da suke samu ya daina zuwa yana basu sai kuma suka koma cewa . Ya gama dani ya gudu suna dariya suna fadin na goga masu tsiya a ranan da sukai dariya a ranan kuma yan uwan sukaima suka zo wurin babana da kaya niki niki na nema wa sulaiman aure na. Amsan da baba ya basu shine sai yayi shawara da matan shi don ina da yanne har hudu a gaba na .. Yara suka shigo da kaya ciki niki niki kowa ya fito yana gani ana sake magana nidai muna daki da mahaifiya na ba wanda yaleko daga cikin mu. Ana cikin wanan haya niyar gwago lagos ta bugowa mama waya ta layin Nura yana bawa mama ba, a jin abinda take fada sai da mama ta shiga daki. Tace wai hayaniyar may kuke yi a gidan ku ne haka ina jin na hayaniya kamar mutane da yawa wurin. Mama ta ba ta amsa da muna kallon kayan da aka kawowa Safiya ne shi meke ta surutu. Gwago tace wacce safiya ba dai safoyan naku da nake son naiwa yaya magana ba a kanta. Mama tace Safiya dai yar wirin Rabi na nan gidan nake maki magana sai gwago tace kaya kayan fa?. Akwai matsala ne inji mama take tamabayan ta akwa matsala kan don dama ina son nemawa yaron nan auren ta ne yanzu kuma naji wani magana can. A, a ta yaya za ayi gida bai koshiba akaiwa daji dole asan nayi dai akan haka amma dai zan fadawa malam di don ya sani a san abin yi. Nan dai sukayi kulle kullen su da mama har suka gama mama ta kashe wayan tun da mama ta fito take anna shuwa da guda a tsakar gadan karshen ta suka shige daki da inna. Shiru shiru basu fito ba sai wani lokaci mai tsawo suka fito suna murna suna dariya tun nan Ummi na tasha jinin jikin ta. Washegari da safe magana ya fara fitowa a gidan mu cewa wai dan gwago na lagos za a bani da farko jin su mukeyi sai ranan da sulaiman yazo zan fita babana ya dakatar dani. Ya tashi ya fita zuwa wurin shi bansan may ya fada mashi ba sai tashin motan sulaiman kawai naji ya tafi. Baba yana dawowa cikin gida ya kwala min kira da sauri nafito daga dakin mu yake cewa dani . Safiya wanan yaron dake zuwa wurin ki na dakatar dashi don zan hadaki da dan wurin gwogon ki na lagos ne. Saboda haka daga yau bani sin jin zancen wanan yaron a gidan nan duk abin da kuka san kunci na shi ku tattara mashi a mayar mashi da abin shi. Gaba na ne ya fadi na dago kai a razane na kalli babana zan yi magana sai hawaye ya hana ni fadin komai muryan baba ne ke cewa kin dai ji abanda na fada maki. Nace a sanyayye naji baba ina mikewa ya kwala wa ummi kira yana cewa ina rabin take ne kizo kiji ke ma hukuncin da na yankewa yar ki. Ummi ta fito duk jamaan gidan sukayi tsit suna sauraren shi yace yar daga yau ban son na kara ganin wani yazo gun ta. Kuma ku hada nashi i nashi tun wuri ku mayar shi da kayan sa kinji magana na ya karasa kamar mai fada. Daga kofan inna inda take zaune tace, hum,in a, she akwaita kuwa a gidan nan, yo wasu kaya kayan kayan da ake shigewa dasu daki muku,muku a cinye ina za a samay su ai yau ga ranan ta. Ummi ta kada kai kawai ta wuce zuwa dakin ta koda ta shiga ta samu na kifa kai a gwiwa na ina kuka. Cikin kuka nace ummi kin ji abinda baba yace, Naji amma yaya zamuyi kin san halinsa baban naku sarai balle maganan da aka shirya yin shi akan mu. Dom haka kar ma kisaka wa ranki damuwa akan abinda ki kasan bamai hanawa sai Allah Tace dani ba kuka zakiyi ba don kuka bashine mafita ga wanan zancen ba samun mafita shine abin yi. Da yake cewa dan gwagon ki zai hada ku dashi shidin ma ya san ki ne ko kuwa dai wani irin hadi zaiyi. Nace ummi Allah yasa dai ba wanan mai shan taban bana yake nufi ba zai hada ni dashi aure. Yanzu dai ki bari kisamu gwago da safe ki sanar da ita halin da ake ciki don mu san mafita. Nace ummi kina ganin baba zai yarda da maganan gwago har ya yarda yajanye maganan shi . Tace sai mun jeraba mun gani tukun don a gaskiya in dai yaran laraba ne ban ga mai tarbiyan da zace zaki aura a cikin su ba. Yaran da idon su ya bude da duniya basu kallon kowa da daraja a idon su kowa a hankade suke ganin shi. Kuka na saka wa ummi a cikin daki tu tana saurare na har tagaji ta kwanta ta bar ni nasan itama dai ta kwanta ne ba wai barci ta samu yi ba. Da safe ban shiga makaranta ba gidan gwagon ummi naje na saka ta gaba ina ta kuka da kallamai masu tsuma zuciya. Gwago tai rarashin duniya ta ga ina batan shiga cikin wani hal dole ta aikwa diyan ta suzo tana neman su. Sin zo sun samay ni take mayar masu da abin da ke faruwa kowan su yace gaskiya takuran yai yawa har da auren ma baza a bari inyi wanda nake so ba. Sun yake magana cewa zasu je su sami babana akan zancen don su dauki matakin da ya dace. Sai dai baba bai saurara masu ba ko kadan inda yake shiga ba nan yake fita ba yana cewa wa ya haifa mashi yar da zai fada mai yadda zai yi da ita. Karshe dai aka tashi baran baran dasu da shi kowa na kunfan baki ran su ya baci suka tafi. Bayan tafiyan su ya kira mahifiyana ya sauke mata kwadon balai har t yake ikirarin cewa kan zancen nan sai ummi na tabar mashi gidan shi. Ga zaton shi ummi zatai shi amma ga mamakin shi sai yaji tace da yafi nono fari wallahi indai kagani haka shi yafi maka to ka matsa. Ta shige dakin ta tana bakar magana wanda sai yaune take mayar mashi da ansa a tsakar gida. Su ko inna dadi suka ji yadda baba yake muzanta ummi dani a tsakar gida suna jin dadi sai cewa sukay mai abu ja mara abu ja. Samun wurin mahaifi ya ya yanke sha wara kan diyar shi amma don karfin hali za a zo a ce ga yadda zai yi. Bani ci bani sha nabi na ramay dana fito tsakar gida yanzu zakiji su inna na cewa yarinya an cuce ki an hadaki da tsoho wai a cewan su Ahmed ya tsufa baiyi aure ba za a daukeni yarinya karama a bashi. Su dinga fadin wai ai karyan kilibibi ya kara min don ban ga wurin yi ba a gidan gwago don bazan kawo mata haka ba gida. Daga ummi har ni bamu jin dadin mutanen gidan mu habaici da yaben magana bamu da shakat a gidan ko kadan. Har takai rainin wayon yana son taba mutuncin ummi hakan yasa ranan nai magana wa mutan gidan . Dan wurin inna ya dauki roban ummi yai wanki dashi maimakon ya mayar ida ya dauka sai ya barshi a tsakan gida ummi tai magana ya taso kamar zai duke ta uwar na gani bata tsawata mashi ba. Bansan lokacin da nasa baki ba ga maganan fadan ya koma nawa duk da nasan ba iyawa zanyi ba. Uwar tace ina na fito takama mu tai muna tas ni da ummi da sauran yaran dakin mu. Baba ya dawo inna ta kwashi karya da gaskiya ta fada mashi inda yake shi banan yake fita ba a gidan. Ga inna irin matan nan ne dabasu so a taba su diyan su amma suna iya yiwa dan wani ka mita magana daya sai anyi kwana barkatai ana maimaita shi. Fitina ya ishi ummi tace kai yaya ina dai anyi wanan zancen ya wuce aiko ta hayayyako wa ummi da masifa da jidali . Wanan abin ya kara jefa ummi cikin damuwa da kuci da takurawan ta kasance cikin tashin hankali haka yasa na kara shiga damuwa da halin da mahifiya na ke ciki. Damuwa yayi min yawa ga auren da akeson min na dole a kaina ga halin da ummin mu take ciki da mutanen gidan. Ranan itace da girkin gida girkin da ba komai ake kawo masu nahadi cikkake ba sai mutum yayi dabaran da kan sa. Da taimakona ummi ta samu ta kammal aikin ta na dauka nakaiwa kowa nashi dakin su na koma dakin mu na zauna sai dai na kasa aiwata komi akaina na rasa manene abinyi don kawo sassuci na alamarin namu a gidan. Haka na kwana da wanan damuwar a raina ban samu barcin kirki ba tara dani dama tun da wanan zancen ya fara bani barcin kirki a tare dani. Kuyi hakkuri please kadan kuka samu ZAINAB IDRIS MAKAWA SEENABU 8/14/20, 7:10 PM - Ummi Tandama: BAHAGON , , , , , 🧕🏿5️⃣🧕🏿 DON ALLAH YAR UWA IDAN BAKI IYA HAKKURI DA YANAYI, NA ROKEKI KI AMSHI KUDIN KI TUN RAYUKAN MU BAI BACI BA DA JUNA , KOMAI NA RAYUWA ALLAH KE BADA IKON YIN SA DON HAKA MUYI HAKKURI DA JUNA, , , , , IDAN BAKI BIYA BA KADA KI KARANTA HAKKIN WASU PLEASE DON BA A YAFE BA. IDAN KIN FITAR MIN DA NOVEL ALLAH ZAI KARBAN MIN BASHI NA A WURIN KI Da asuba na fito tsakar gida ina shara don kasancewan ummi ca mai girki ranan. Ummi na gani ta fito daga dakin ta cikin zumbulelen hijjabin ta na sallah idanuwanta na zubar da hawaye. Kai tsaye ta nufi hanyar kofar gida tsatsiyar dake hannuna na aje na nifi wurin ta da sauri tare da riko hijjabin ta nace. Ummin mu ina zaki ? Tajuyo hawaye na zuba a idon ta cikin raunaniyar murya tace dani. Gidan mu zan tafi . Take nawa idanuwan suka ciko da kwalla don nasan wannan tafiyan da zatayi bana lafiya bane cikin rudani nace mata. Ummi may yasa zaki tafi kibarmu cikin gidan nan ? Batayi magana ba sai hawayen daya karu a idon ta ta juya taci gaba da tafiya atake na fashe da kuka mai tsuma rai. Na bita muka fita waje ina cewa ummi hakkuri zakiyi dan tafiya kibar mu a haka cikin wannan gida ba shine mafitaba. Tace dani gidan mu zan tafi na gaji da wannan zaman na kunci da bakin ciki. Na sake cewa da ita kiyi hakkuri ummi watarana sai labari, sai ta dan kalle ni tace dani . Haba yarinya da ace za a daina ai da an daina shekara nawa ana bu daya shikenan mutum tsakanin ka da mutane babu zaman lafiya . Duk gida an tsane ka har ku yashafe ku sai yaushe wanan halin zai kawu. Ina shirin bata amsa baba ya fito don zuwa sallah yana ganin mu har yaso cewa su waye a nan ? Ko ya gane mune sai yaja tsuki ya ce ai ki kyale ta tafi tunda har yanzo ita bata san tai hakkiri ba sai ya wuce. Nace da ita ummi ki daure don darajan mu ki koma tace yaya basu hana na kwatar wa kaina yanci ba. Dakyat ta yarda muka koma ciki munyi arziki mutanen gidan basu fito ba har ta koma ta shiga dakin ta. Shi kan shi baba da yaga bata tafi ba da alama yaji dadin hakan don yasan abune mawuyaci ta tafi gidan su su kyale ta ta dawo din. Hakana muka wuni agidan cikin bacin rai sai dai ina yi ina kara kwantar wa ummi din da rai. Da dadare baba ya dawo baiga dan dakin mu a waje ba ya shigo dakin namu ganin ya shigo yasa mu fita dakin na shimfida mu tabarma a waje muka zauna. Ummi na zaune a bakin gadon ta ya samu wuri ya zauna a kusa da ita yace Rabi niban san ina hakkirin ki yaje ba yan zu. Har yarinya karama zatafiki tunane, ina iya hakkuri na gurin naga na kyautata maku amma hakan ya gaza samuwa. Kiyi hakkuri don Allah ki yafe min ba laifina bane nakan rasa may ke yawan kawo maku wanna matsalan. Ummi dai bata tanka shiba ta kawar da kan ta gefe daya don bata son ko kallon shi balle ganin shi. Ganin haka yasa shi mikewa yabar mata dakin yana cewa a bani abinci na ci ya fice. Ya nufi hanyan fita ta bishi da hararan tsana don kwata kwata ta gaji da shi zaman auren dai sukeyi ita bata ga wani amfanin hakan ba. Ta mike tana jin wani tukukin bakin ciki a ranta ta rasa yaya zatayi ta magance matsalar dake damun ta a ranta batare da wani yaji ba. Matsawan tana son kawa karshen auren nan sai dai idan nata auren zai tabo ne hakan kuma tonon asiri ne gurin yayanta ********* ********* ********* A gurin mutanen gidan mu muke jin wai su gwago zasu zo ai maganan auren mu da dan ta . Zan iya cewa kowa a gidan mu bai san wanan mijin da ake cewa anyi min ba a cikin yara don haka aka matsu da su zo din . Ba wani yi gyara ba balle kwalliya don taron bakin da zasu zo, ranan weeken ne don haka kowa yana gida bamu fita ba. Muna zaune a cikin dakin hira muke da ummi na ina dariya mukaji ana masu sannu da zuwa da bakin lagas. Gwago ce ta fara shigowa gidan ita daya mutanen gidan mu sai raba ido suke suga mikin nawa. Suka kwasa sukayi dakin mama a ca aka shiga zuwa gaida ita dakin na mama Ummi ce ta fara zuwa cikin mu taron ta gidan yawa da gulma nan aka saka ido akan ta. Ta gaida gwago bata tsaya ba ta dawo dakin ta ta umurceni da naje na gaida ita din , na saka wani tsohun hijjabi a jiki na fita. Daga kofa na tsaya nake cewa gwago sannu da zuwa ta juyo da sauri tana cewa karaso mana ciki Safiya. A hankali na taka na shiga dakin na tsugun na kasa take cewa dani a a baki san yau zamu zo bane banga kiyi kwalliyan taron mijin naki ba. Na dukar da kai na kasa take cewa dani tare muke suna nan kofar gida kin san shi ba mai son shiga mutane bane. Haka yake tun yana karami da gudun mutane amma yi saa ya yarda ya biyo mu ne. Sai mama tace ai shi hali shi tun na kurciya yana nan mashi ke nan baya son hayaniyan nan dai kamar yadda na san shi ashe ? Ina suke ban dago ba take cewa dani maza ki shirya ki samay su a kofar gida. Na tashi simi simi na fita daga dakin na koma dakin mu na zauna ban fadawa ummi abin da tace dani ba. Sun dade da mama daki sun kashe murya sai zuwa can mama ke cewa safiyan tana can waje ne har yanzu. Yar wurin mama ta amshe da cewa bata fita ba tana nan gida sai mama din ta taso tazo har dakin mu da kan ta tana min fada. Hijjab din ummi na salla na zura a jikina na fita idanuwan yan gidan mu caaa a kaina Na samay su su biyu a waje na karasa wurin su da sallama a bakina ko wanin su ya kunna taba yana zuka. Jin sallama na da sukayi dayan yai saurin kashe taban hannun shi shiko dayan ko a jikin shi bai masan na zo ba. Sun saka kida na tashi kamar gidan dj mutum ya shiga da kyat na bude bakina saboda warin taban da yacika wurin ina jin kamar zan yi amai. Na kara gaidasu cikin murya a sanyayye sai gudan ya amsa min dayan wanda nake ganin shine dan gwagon mu yana dai zaune. Sai can gudan yace dani a, a ko ke ce Safiyan a hakalin na bashi amsa da eh da sauri ya dago kai ya kalle ni, na sake cewa kunzo lafiya. Mai maganan ya bani ansa da lafiya kalau mun samay ku lafiya ya karatu nace Alhamdullahi sai nai shiru. Jefi jefi can yace barin dan taka wurin mai shagon can na sayo abu nasan yayi haka ne don ya dan bamu wuri. Tafiyan shi ke da wuya shiru ya biyo baya har na wani lokaci sai naji yace barka da fitowa. Nace barka mu da wuni. Yace ya kike lafiya na bashi amsa. Na jingina jikina da motar su don na gaji da tsayuwa yace da fatan anyi maki bayani a gida. Sai na girgiza kaina nace ba wanda yai min baya ni an dai ce nazo na gaishe ku. Ya ce Ok in kin koma za suyi maki yace ina dai fatan kin san abu ga makaranta don naga kamar har yanzu da saura. Ko da yake wannan matsalar gwagon ki ne nace dashi namu dai. Yadda na fadi maganan sai ya fahinci ko ban gane dukkan abin da yake fadi ba. Yace ina baki fahinci magana ba cewa nayi iyayyen mu sun yi cewa zasu hada a tsakanin mu sai dai ni a tsarin rayina nafison macen da ta mallaki hankalin ta . Macen data waye tasan duniya ya nunani yace dube ki ina ganin duk baki fi shekar sha hudu ba in ma kin kai. Na yi wani gajeren murmushi nace to yaya na iya da zabin a kaina babu komai sai dai nima in son samu na samu yaro sauriyi mai shekaru kalilan wanda zai rike ni tsakani da Allah. Amma tunda iyayye suka sani babu komai Allah ya tabbatar da alheri a tsakani. Yaji haushin amsan da na bashi yace ba laifi nima hakan zan daure nai maneji dake kafin kan ki ya waye. Nace abin na da sauki tunda kaima da wayewar iyayye kake kuri tunda sun sani nasan da sannu zai waye din kaga ba maganar na waye ko ban waye ba dole ne nayi biyyaya ga magabata na. Tun da sune masu iko dani banice ke da ikon kaina ba zanyi biyyaya a gare su. Ya sake jin haushin magana na amma a fili yacewa yayi ashe ra, ayin mu yazo daya kenan kan biyyaya ga magaba tan mu sai ki shirya zaman ukuba a tare dani. Nace insha Allahu in yin hakan shine farin cikin mahaifi na a shirye nake da na rugumi duk wani ukuba da zan sama a gidan ka. Sai ki shirya ke nan yarinya don ba zan yi renon banza a rayuwa na nace dashi Allah ya shige muna gaba. Nace idan ka gama zan koma ciki hanya a bude take maki zaki iya tafiya sai dai kina da daman fadawa iyayyen naki irin ra,ayin . Na dan yi jim na wani lokaci sannan nace dashi idan son samu ne kaine babba kai ya kamata ka tun kare su da zancen. Saboda kai zasu fi daukan zancen ka da muhinmanci ya ce yin hakan ba zai yuyu a gare ni ba amma ba matsala. Ya fara dube dube a cikin motan nidai duk warin taba ya ishe ne a wurin gani nake kamar a kamfanin taba na shiga. Sai naji yace dani ga wannan kya kara kisai littafi da biro, sai na girgiza kaina ba tare da nakarba ba nace ka barsu na gode ina da wadatar littafi da biron. Ya langabar da kai tare da karya harshe acikin turanci yace you will regret later sai kuma a harshen hausa yace ai ba cewa nayi kina da matsalar su ba, Nace to na gode ban karba ba na fara tafiya yace to shike nan, na soma takawa a hankali shi kuma ya bini da kallon tsana. Bayan na ahiga gida dakin mu na nufa yayin da masu gulma an zuba ido a ga abin da zan shigo dashi. Tun shigana gida san bani da natsuwa ziciya ta kwata kwata bata natsu da wanan hadin ba ko banza bai a cikin tsarin mazan da nake so. Wayewan shi yayi yawa bai laifi yana da tsarin maza amma dai tsarin dan maciji don farine dogo ga iya gaye komai nasa karfafa ne amma ziciyan sa da jikin shi babu tarbiya a ciki. Sai dai ban da zabi akan haka don bani da ikon bijirewa maganan mahaifina don haka naci alwashin tursasa zuciya na da hakkuri koda kuwa yin hakan zai rasa farin cikina. Sai da gwago ta gama abin da takeyi ta fita zuwa waje zuwa can ta dawo ciki da wasu ledaji a hannun ta. Ta nacewa ga wannan na sarakkuwa nane kayan mun gani muna sone muka zo dashi zan dawo idan yaya ya dawo gida mu gana kafin mu tafi. Har suka tafi ban sake ganin shi ba nadai ji labari cewa sun tafi an tsaida bukin mu da zaran na gama karatuna wanda yazo saura wata uku mu kanmala. Ba waya ke gare ni ba balle ya dinga kirana haka yasa ban ji daga gare shi shima baiji a wurina. Na dan kwatar da hankalina don na fuskaci jerabawan dake tafe min na final exam da zamuyi duk da ban sa rai ga cewa zan samu ci gaban karatun nawa. Kulliyomin ba wani kwaciyan hankali a tare dani gashi duk biyayya da nake keyi ba gani akeyi ba don saida yakai an hada gwago fada da baba na da ummi wanda nasan bakowa yai wanan hadin ba sai mutanen gidan mu. Har yakai ummi na ta kasa hakkuri tai tafiyan ta gidan su sai suka koma fadin cewa don tagacewa buki na ya taso ne ba ta aje komai ba yasa ta tafi gidan su wai. Wanan tafiyan na ummi shi ya rage muna walwala sosai dani da kan ne na a gidan ko yaushe ina daki ina barzan kuka. Yan kane na sukan damay ni da tambayan yaushe ummi zata dawo idan nace ta tafi gidan su kila ba zata dawo ba sai su fashe da kuka. Na rasa mai ke mun dadi gashi nima dake dan kula dasu ana ahirin yi min aure a lokacin duk da ba wani alaman shirin aure da akeyi a gidan namu . Don ban gani a kasa ba kamar yadda idan za ai buki ake ta faman shirye shiryen buki agidan namu. Ban san may mama tagani ba ta sako dama sherin na wurin inna don ita ce tace wai ummi na na fadin sai da gwago tasan cewa dan ta bai da tarbiya zata ce a hada shi da diyar ta. Ta fadi maganan wurin yan uwan su mama da suka kawo kaya gidan mu su kuma suka kwasa suka je suka fadawa gwago maganan . Nan gwago ta shiga fada tana zagin ummi wai damay diyan ummi sukafi diyan ta don ma za a rufa mata asiri a auri yar ta. Ta aikowa baba magana akan cewa ya ja wa ummi kune ga baganan da take sake mata shi kuma baba bai tsaya binke ba yai cikin ummi da masifa har yana cewa tana bakin ciki da hurdan da yake yi da yan uwan shi. Shine akan wawiyar yar ta take son hada shi da yan uwan shi ta bata isa ba wallahi idan bata iya ganin auren haya a bude yake mata ta tafi gidan su. Ita kuma ummi ta kasa hakkuri ta mayar mashi da ansa cewa ba tai bakin ciki da su ba sai yan zu inma tayi bakin cikin ai dole ne don ba aiwa yar ta adalci ba ai ga yannan ta agidan abadasu mana. Rikici yai rikici don itama ummi ba raga masu ba wannan karon ta rufi idon tamayar masu da mai zafi. A karshe sika kwasa da baba har yakai tabar gidan cikin dare duk magiyan da nake mata bata tsaya ba. Mama ta sulce jiki ta samu wani wan baba ta fada mashi halin da ake ciki ta kuma ce a gaskiya ita bata taba jin ummi tai wannan maganan ba. Baba musa ya samu babana sai cewa baba yayi dashi ta tafi mana idan hakan yafi mata alheri. Baba musa yace dashi matsala gidan ka baka bincike baka kuma son a fada maka gaskiya kun samu boyar Allah kuna cuta mata ita da diya ta cikin gida. An tabbatar min da cewa bata fadi wanan maganan ba yau kake da Rabi a gidan nan ya kamata kasan abida zata iya aikatawa da wanda bata iyawa. Nan dai suka rabu da shi babu dadi ranan da yamma da baba ya dawo gida yana ta fada da baba musa. Mama tace dashi ai bai fadi karya ba gaskiya ya fada wa ya taba ji a gidan nan lokacin da Raba ta fadi hakan. Sai inna ta caraf tace kina nufin ke nan karya ne sheri akai mata ai idan bata fada anji ba alama ya nuna hakan. Yace kin ga idan ke zaki je ki dawo da ita ban hanaki ba ai bani na kore ta ba sherin ta ne yakore ta balle ku matsa min. Yaya sani na gida zaune yana cin abinci yace baba a gaskiya maganan gaskiya kuna cin amanan boyar Allah nan ga mama ta fadi gaskiya tace bata ce ba ai shike nan . Ke inna in kina rage sheri ki rage don ke ma diya mata ke gare ki gasu nan har guda biyar maki. Tace to ubana baki zakai muna ko may yace ni gaskiya nake fada maki tace bako haka ba. Ya mike yabar abincin da yake ci yace to tabar maku gidan sai kuyi yadda zakuyi da diyan nata. Ya shura takalman shi ya bar gidan. Sai fada ya koma tsakanin inna da mama tonon asiri ya tashi baba yana zaune yana jin komai. Dole gidan ya koma babu armashi kowa na cikin damuwaidan ka cire inna da diyan ta suke an shuwa a gidan kawai. ********* ********* ********* Kwana uku shiru babu wani motsi a gidan kwakwara mama ta kara samun baba a kan zan cen. Ta nuna mashi damuwar ta tana cewa malam ka dubi Allah kaje kadawo da matar ka ta dubi yaran ta yara sun koma kamar marayu a gidan. Yace ina son zuwa sai dai ban san da wani ido zan kalli Rabi da shi ba don don iyayyen ta sun mani mutunci amma ni na kasa rike masu ya. Gobe zan sami malam lawal ya rakani muje ko zata dawo in kuma ahi zai tafi wala ba a sa. Mama cikin nuna damuwa sosai ta ce dashi da haka yafi don ace anyi buki yar ta bata gida gara dai ayi hakkuri. Washe gari ana gama sallah asuba baba ya samu malam lawal da maganan yai mashi bayanin komai bai boye mashi ba. Malam lawal yace a gaskiya baka kyauta ba da baka bincike a gidan ka ai yaron ka gaskiya ya fada a tare ake hade kai dakai ana cuta wa Rabi. Sannan fa ka sani yanzu ba aiwa yaro dole samu da wayawan kai da aka samu ita yar uwar naka ta nuna dan ta tasani. Gashi an fara samun haka tun ba a yi auren ba idan anyi akazo aka samu matsala wa aka cuta yar ka da uwarta. Daga karshe dai baba ya nuna su tafi su kadai don shi yana jin nauyi da kunya zuwa ya tun kari iyayyen ta. Sun isa garin da sanyin safiya sai dai basu samu mahaifin nata ba a gida amma yayan ta da kannen ta suna gida. Bayan sun gaisa malam lawal yace dama mun biyo sawun Rabi ne don Allah ayi hakkuri ta koma tsakanin harshe da hakori ma ana samun matsala bare mutum da mutum balle zaman aure da ya gaji hakan. Yayan nata yace haka ne amma naso ace shi malam Audu yazo da kan shi don ko mu a kauye mun daina wa yaran mu auren dole. Bayan haka duk hakkurin da Rabi ke yi ita da yar ta baya gani sai da ya kora muna ita gida dom ya nuna muna ya gaji dasu. To idan shi ya gaji dasu da ai har diyan nata ya koro muna mu bamu gazawa da su. Malam lawal ya jijiga kai yace ai dai yi hakkuri a madadi na abokin sa ina bada hakkuri koma may nene ya hada su tsakanin miji da mata ne. Hakan ba zai sake faruwa ba tunda idan mukayi laakari ai hakan bai taba faruwa tsakanin su ba tun suna zamanin kurciya yanzu da aka tara iyali. Yayan ummi yace eh saboda hakkurin irin nata ba shine zaa ce bai taba faruwa ba amma ia duk halin da take ciki muna da labari. Yanzu ko da anin ya isheta ai da kan ta ta ne may mu dama ranan muke jira don duk abin da yasa kaga Rabi ta bar diyan ta to abin yaya kamari. Malam lawal bai gaji da bada hakkuri ba har mahaifin ummi din ya dawo gida ya samay su. Nan su malam lawal aka shiga gaisuwa dashi nan dai malam lawal ya gabatar da bukatan su na bikon ummi din. Tsohon yai shiru can yace a gaskiya Rabi bata taba yaji ba nasan halin Rabi da hakkuri abu daya zaisa na yarda na mayar da ita dakin ta shine. Bukin yar ta da yataso amma idan ba haka ba Rabi bata komawa gida nan ya isa haka na. Ya dubi dan shi daya yace shi ga ka kira min Rabi, kanin ummi ya shiga kiran ta ta shirya tafito don amsa kiran mahaifin nata. Sai fitowanta ne ta ga su malam lawal ta durkusa a gaban mahaifin nata cikin ladabi tsoho ya dube ta yace. Rabi ga abokin mijin ki sun zo bikon auren ki don haka maza ki shirya ki bisu. Take idanuwan ummi ya ciko da hawaye zata yi magana tsohon ya daga mata hannun tare da cewa. Haba Rabi ban sanki da mussu ba, ita rayuwa hakkuri akeyi da komai ki yi hakkuri ki koma daki mijinki ko domin yayan ki . Tabude baki zatai magana tace baba amma, , , , , Ya koma katseta cikin tsawa yace kin san ni sarai bani son mussu aiko ? Tashi ki je ki shiryo ku tafi. Badon ummi ta soba haka ta shiga ta shirya tana shiri tana kuka ta fito da lulubin ta suka nufi tasha da su baba lawal. ZAINAB IDRIS MAKAWA SEENABU 8/14/20, 7:10 PM - Ummi Tandama: BAHAGGON , , , , , 🧕🏿6️⃣🧕🏿 INDAN BAKI BIYA BA KADA KI KARANTA HAKKIN WASU PLEASE DON BA A YAFE BA ONLINE NOVEL NE, , , Lokacin da suka dawa bata zo gida ba wurin gwago ta nufa malam lawal ya je ya dauko baba yazo dashi gidan gwago. Gwago da malam lawal suka su gaba da nasiha akan a zauna lafiya arike hakkin iyalin abawa kowa hakkin ta yadda ya dace. Baba yace insha Allahu komai ya wuce zaa gyara da yarddan Allah zai kulla da hakkin iyalin shi Da daddare su gwago suka rakota gida ta dawo dakin ta tare da kara mata nasiha a zauna lafiya ta kyale kowa da halin sa. Lokacin da suka shigo gidan mutanen gidan suna waje zaune mu kuma muna daga cikin dakin mu sai naji murya kamar na yar uwar mama na sallama. Hakan yasa ni mikewa in leka aikuwa nahango tafe da ummi na buga tsale ina cewa lah ga ummi mu ta dawo. Mukayo kanta da murna suka shiga dakin komai yana nan tsab yadda ta barshi dakin ba laifi suka samu wuri suka zauna. Zauna na durkusa ina gaida su kaunan ummi ke cewa dani wanan wata irin amaryane ba kwalliya ko kadan. Na turo baki gaba take cewa ai ko bakya son mijin a dan yi maki gyaran irin na amare ko ? Wannan wani gyara zata samu babu kwaciyan hankali ahaka suke ahirin kai ta gashiko ance mijin nata dan duniya ne inji kaunan ummi gudan. Aiko ba komai a dan gyara ta in ba haka suke so su kwashe ta sukai ba akara samun abin fada masu nan gaba. Take cewa dani washe gari ki same ni gidana da safe da dan abin da zan maki koda yake ma an makara duk da haka dai hakan za a yi. Sun dan zauna nan nake basu labarin irin yadda mama tai ta matsa mashi akan ya dawo da ummi dakin ta da kuma yadda tai ta dan taimaka muna da ummi bata gidan. Nan da zasu fita suke gaida mama din suna fadin ga Rabi nan ta dawo Allah kauda tautsayi tsakani. Mama tace ba komai zama tare ke kawo wani abin amma in an ciza aka hura sai ya wuce. Har suna shirin fita daga gidan sai inna tace muda ba a gayar wa sai ace mu mutu. Baku duk mutuwa ai amma dai baku so ganin hakan ba anso ace bata dawo ba sai gashi ta dawo din bakin cikin haka zai kashe mutum. Inna tace bakin ciki ya kashe wa matar da baa bi bayan ta ba ta wanke kafa ta dawo don kwakwa irin naku. Tace wa ke nan zaune gida kamar kayan wanki tun yaushe mijin naki ke bin sawo har kauye. Abun da yaba inna haushi ke nan tace ke kinyi kadan ki shigo kice zaki zage ni har dakina. Mama lami tayi zaton dukan ta inna zatayi kafin inna ta karasa daga hannu taji an kwashe ta da mari tajuyo a cikin mamaki taji an sake sauke mata wani marin . Aiko danbe ya kicimay masu take gida ya rude sai ga inna a kasa mama tabita ta haye da duka da yakusa. Ganin inna bata diban komai a jikin mama lami yasa hausi yar inna dauko faskaren icce ta nufi mama dashi sauran ma suka dauko tadai samu mama dashi sau daya zata kara buga mata ne mama ta kauce iccen hau kan jikin inna. Sai ga jini tarrrr yana zuba daga goshin inna din yaran suka kara fasa kururuwa mutane suka fara shigowa har da su yaya sani da abokan shi. Yaya sani har ya dauko icce zai shiga dukan su dashi sai yaji mama na fadin yanzo kin ga abin da kika jawa kan ki in da suka shigo basu tan ka ki ba kin kyale sune sun tafi da baa kai ga haka ba. Amma kin bisu da zagi da gori yanzu gashi har kin jawo yar ki tai maki rotse akai. Sai jikin shi yayyai sanyi ya yarda iccen da ya dauka kasa yana cewa ashe inna ke kika ja wa kan ki gashi yanzu an barki da jinyan jiki. Baba ya shigo gidan ya samu gidan a har gitse da kyat ya samu mama ta mayar mai da abin da ya faru yake cewa shi ba ruwan shi ta dauki mataki da kan ta in zata iya don shi bai sata ba. Nan inna tashiga balle ballen bagana ida take shiga banan take fita ba wai baba an je an hada shi da boka da malam kan shi ya zare. Baba ya shigo dakin mu don ya gaida ummi zamu fita yace mu zauna yake cewa ummi kin dawo lafiya ya mutanen gida. Ta amsa shi da kyat da suna lafiya. Yace don Allah Rabi kiyi hakkuri da halin inna kin saba da halin ta kiyi hakkuri a zauna lafiya. Bata tankashi ba ta kawar da kai daga duban sa ma sam bata son ganin shi. Shima yace da mu da ita sai da safen ku. Allah yakai mu ta bashi amsa dashi. Yana fita na sauke ajiyan zuciya nace ummi kiyi hakkiri tun da ya gane laifin sa abin ya wuce. Ya gane ko yana shirin ganewa ai da sauran sa duk wanda yace ya karkata wuri daya a gidan sa ai kullun yana tare da tashin hankali. Don dai yanzu in suyi min ba kyale su zanyi ba sai dai duk adauke mu masu fitinan don kyaluwa bai yi. Abin da na lura dashi da baba da mama ke aiwatar da shirin bukin su sai ko gwagon ummi da suke dan jefawa ciki wani lakaci. Mun kara jerabawan mu na karshe kowa na farin ciki da hakan a ban gare na bakin ciki ne tar ga zuciya na . Sai dai ba wanda zan fadawa naji sanyi sallama muke da junan mu na samu Amina bakin get tana jira na mu tafi. A kasa muke tafiya don bamu son mu rabu Amina ke cewa mun yi barka da saka uniform yanzu muna da freedom din kan mu ba mai takurawa rayuwan mu. Take naji wani iri a raina tace ni dai nursing school nake son zuwa idanuwana suka ciko da hawayen bakin ciki lokaci guda don a da tare muke wanan burin kowa ya fadi abin da rayuwan shi ke so. Nin nayi shiru tana ta magana take cewa dani bakiji bane Safiya, cikin raunaniyar murya nake ce mata ina jin ki ni nasan wana daman ya wuce ni ke nan a rayuwa na. Tace saboda may zakice hakan wanda zaki aura din ba dan birni bane zai iya barin ki kici gaba da karatun ki bayan kuyi aure. Na hade wasu yawun bakin ciki nace da ita kayya Amina wanan auren da za ai min takar bauta zan tafi yi wanda yafi wanda nake yi a gidan mu. Da sauri tace saboda may kika ce haka nan nake koro mata da yadda mukayi ranan da suka zo da mahaifiyar shi. Na kara dace Amina ke kin taba ganin anyi aure mijin bai ma san da zaman matar da za a aura mashi ba. Na kara sa cikin kuka da fadin zan yi biyayya ga mahaifina shi dake gurin yaganni cikin irin wannan rayuwa. Zan zauna na rugumi kaddaran da ubangiji ya aiko min dashi amma ni nasan babu komai cikin yin hakan da suke son yi sai hada zumunci fada. Tace matsalan Safiya shi baba yaki gane gaskiyan magana wa yan nan matan na zugashi in gaskiya ne ai suna da diya mata suba dasu ma ai sun fi kusa da gwago din. Nace da ita ai fakewa sukayi da cewa wai ni nayi karatun boko suko saura basu yi ba don haka ni ce na dace dashi. Tun ban da wayyo nake jin irin wayyewar su da kuma irin tarbiyan su ba daya ba da namu amma mama cewa tayi wai zaman birni ne kawai. Har muka kai gidan su Amina maganan muke muna tafiya ganin yadda na bata fuska da kuka yasa ta cewa dani na shiga gidan su na wanke fuskana. Mahaifiyar ta na tsakar gida taga shigowan mu take cewa damu yaudai kunyi barka sai kuma a fada wani. Ganin yanayi na yasa ta katse maganan nata ta biyomu cikin dakin ta da muka shiga. Ta samay ni zaune Amina a gefe na ina kuka wiwi tace may zan gani wai haka yau duk kukan karasa makaranta ne haka ? Amina ne ta iya bata amsa da cewa mama matsalar auren ta ne take wa kuka. Sai mahaifiyar ta tace yanzu yaushe raban naji an tursasawa yarinya auren dole can. Irin wanan ma mijin ai ba zaiga darajan su ba bare kuma ke. Cikin kuka nake sanar mata da yadda mukayi dashi din duk abin da ya fada min da suka zo. Taja gwaron numfashi tace shi baban naki ne bamai saukin kai ba, bai san yanzu an bar irin wanan auren hadin ba ne. Ai lokaci ya shude na irin haka sai dai kiyi hakkuri Allah yana sane dake yi addua idan akwai alheri ya tabbatar muna. Nace Mama wallahi shima mutumin bai ko san suna yi ba don kwatakwata yace ni ba tsarin shi bane yadda na lura shima umurnin mahaifiyar shi yake bi don nagane so yake ni na fitar da rashin amincewa ga iyayyen mu a fili san nan gashi miti biyu yai yawa bai kuna taba ya zukaba. Kaini ban ma taba ganin mai sha irisa ba wata kilama ba iya taba yake shaba. Don ranan da na fara ganin sa tare fa suke da iyayyen shi amma babu kunya yanata zukar tabanshi in na tunashi a raina duk hankalina sai ya tashi. Nayi hakkuri na jure wai don na farantawa baba rai amma na gaza sakewa a raina. Ba wani soyayya tsakani na dashi saima munanan halayyanshi da yake nunawa a fili. Nakara fadi cikin wani irin kuka saboda Allah mama ta ya ya zan samu natsuwa har nai farin ciki ga auren da na san bubu komai cikin sa sai tarin kaskanci. Mama ta girgiza kai cikin damuwa tace kidaiyi hakkuri don bamu da wata zabbi sai abin da Allah yayi. Ta dan tsagai ta tana mai matukar tausaya mani tace gaki yarinua mai hankali ace za a hada ki aure da mara tarbiya mara mutunci. Da sun bar sulaiman ya ci gaba da neman ki aiko su da sun dara amma a kai bakin ciki da kasancewan ku tare. Yanzu ina mutunci ga irin hakan da ake shirin yi nace mama don ma baki shiga gidan mu kin gani bane ummina fa bata dade da dawowa gidan ba duk akan maganan. Maman Amina tai salati ta sanar da ubangij tace badai ta dawo gidan ba ko ? A hankali na share hawayen dake fuskana nace tadawo amma dai har yanzu cikin fitina suke din inna ba barin halinta zatayi ba. Tace kin ga Safiya ki tsayar da hankalin ki debi kwanaki uku zuwa bakwai duk abin da ya sauwaka daga biyu zuwa uku dare. Kirinka nafila ko wani raka,a ko wani raka,a ki karanta kulhuwallahu kafa goma sha biyu a bayan fatiha. Idan ki idar ki zauna ki yi yabo gun mahallicin mu sai ki hada da istigfar duk abin da ya sauwaka kar ya gaza kafa dari, sai ki kara karata kulhuwallahu kafa goma sha biyu ko wani da bisimillah shi safiya muddin kika rike wanan zaki ga abin mamaki idan har ba a fasa auren ba to mukkadarine daga Allah Allah ba zai barki ki tabe haka na ba. Cike da gansuwa da maganan ta nace nagode mama insha Allahu zandage dayi yau din nan zan fara basai gobe ba. Amina ta tashi ta debo min ruwa a buta na wanke fuska na dashi bayan na wanke maman ta tayi tayi in ci abinci naki sai da zuciyana ya samu natsuwa. ********* ********* ********* Bike ya rage saura sati biyu duk nabi na ramay kulliyomin bani da kwaciya hankali tare dani yan gida mu sai shirin buki suke yi. Ranan ina zaune sai ga yaya Nura da wayan shi har dakin mu wai ana magana dani a waya na karaba ina mamakin waye zai kirani da wayan shi. Na karba da sallama na amma sai naji muryan wanda naki jini a wayan yana cewa ke yar kauye watau kina nan ga bakan ki ko. Nagane shime a layin duk da gabana ya fadi amma a fili sai nace muna dai a bakan mu ko don kaina mayen da ka dafe min kana son shiga cikin rayuwana. Yace ke manya na san bakomi kikewa ba sai son ace kina lagos kina aure ko ? Nace wanan ba shine matsalan ba don ba nice farko shiga lagos daga kauye ba kafin ni wasu sun rigani. Yace a harzuke suwa kenan kike nufi oho mahaifana kike son ki zaga ko may ? A yadda ka dauki maganan nawa hakan nan amsa yake don bani ce farkon shiga birni ba. Avikin tsawa yace ke dakata kiji kiyiwa bakin ki waigi ki san wanda kike magana dashi, ke har wata mace ce da zan tsaya ina bata lokacina a gare ki. Yan mata wani iri ne ban gani ba ke har kinada abu yiwa maza feleke ne yaja tsuki yace a fusace. To ki sani ba irin Ahmed akewa irin feleken nan ba don ni baki cikin tsarina kin sani bakuma zaki taba samu ba. Daga kawai ana son rufa iyayyen ki asiri a taimake su da har ina macen take nan. Nace a rifa wa iyayyena asiri taimake so ko a rufawa naka kai da ka tsufe masu awaje kar akai ga abin kunya duk barinki ya kare babu maija. Ya kut nasan ran shi yakai kololowar baci ne da magana yace zan gwada maki yanzu nake a cikin bariki kuwa. Kinga ni dama kiran ki nayi gwagon ki ta damay ni in akwai event din zakuyi na sani. Nace akan wanu aure zayi event badai wanan auren kaddaran ba naka zan tsaya bata lokacina akan sa. What ever you take it duk daya gare ni sai dai in ke baki so nasan wa yan nan mastiyatan yan uwan ki na su. Nace dadin abin dai ba a taba canza ma tuwo suna sai dai a kira shi da tuwon abu kaza. Au aikin banza bade za a iya saka mai suna ba ya kashe wayan shi yana jan tsuki. Wasu zafafan hawaye ne suka zubo a idona nace wannan wani irin tarbiya ya samu ko kadan muddin ba zai ragawa iyayye na bazan raga mashi ba. Duk da kalaman da yake fada min suna da zafi kalamai ne na cin zarafin iyayye don haka na kara tsanar shi a raina. Haka ummi ta shigo ta samay ni a cikin damuwa yanayina kadai ummi ta duba tasan raina a matukar bace yake cikin sallon hikima irin manya ta tuhumi abin dake faruwa. Tace dani kina nan kina bata ranki ga abin da kika san ba zai hannu ba sai nace da ita ummi wannan mutumin ne baida mutunci . Ko yaushe sai so ya zageni da iyayye na har da aibatani bai dauke shi a bakin komai ba don shi bai san darajan iyayyen shi ba. Ummi ta jijiga kai sannan tace, abinda nake so dake yi hakkuri yi kuma tawassali da Allah in sha Allahu aniyar sa tabi shi baji a gare ki sai dai a gurin sa. Abin da nake so dake shine kibi umurnin mahaifin ki koma maynene tsakanin shi da yar uwan shi ne bai shafe ki ba ke dai ki zage ki neme aljannan ki a gurin mijin ki zai fita masu ai in dai halin sa ne. Kibar biye mashi ranku na baci ko banza ba saan yiki bane shi don ya girmay ki balle kuma ga aure zai shiga tsakanin ku. Wanan magana na ummi su suka sanyaya min zuciyana take naji komai ya kawu min a rai na samu karfin gwiwan rake mashi abinda na kulla yi duk da manufar sa akaina na kuntata min. Kamar yadda su gwago sukace basu son akaini da tarkace duk da haka an yi min kokarin wasu abubuwa wanda sam mutanen gidan mu basu zaci hakan ba. Don ko yan uwan ummi sun hada kudi cas suka kawo mata tare da sauran tarkace na amfani gida. Yayan da abokan arziki na cikin gari suma suka kawo nasu gudun mawan take kaya ya hadu ayadda baa zata ba. Inna da ke cewa suga yaidda za ai buki uwa bata aje komai ba ta manta abin daga Allah yake don Allah shikewa bawan sa budi yadda yawo. Yan uwan ummi sun yake shawara a tafi da kudin asai mun abin daya kamata a can idan an tafi kayan lafen dasu gwago suka kawo sai da inna tasa aka bude shi ita da diyan ta duk suka wawashe abin da suke so ciki. Ina zaune a dakin mu don cikin gidan baimin dadin fita ina ummi sai shige da fice sukeyi na hada hada buki ni dai abin mamaki yake bani a raina. Muryan yaya Sani naji a tsakar gidan namu yana kwala min kira na fito da sauri ina amsa kiran nashi. Ya na kallona ganan sa ya fadi ya tsorata ainun da irin rama da ya gani tare da ni. Ya ke Safiya lafiya irin wanan zabgewa da kikayi haka, keda ya kamata murna zakiyi aure ki huta da halin gidan nan . Take idanuwa na suka ya kawo kwalla na dan sake mashi murmushin yake nace gani yaya. Sai naga jikin shi yai sanyi da leda a hannun shi nasan abu yake son in dafa mashi a lokacin. Sai ya juya dashi yana fadin barshi dai har ya taka yace dani Safiya zo nan sai nabi bayan shi muka fita. Jikin bango na rabe a lokacin ne kuma kwalla ke zubo min a idanuwana babu kakautawa. Na sa gefen hijjabi na ina shrewa sai naji ya sauke ajiyan zuciya dan kalle ni tausayina ya kara kama shi. Ganin dagani sai shi a wurin kuma shi kadai ne mutum a gidan mu bayan ummi na dazan fadawa damuwa na. Nace yaya Sani ina cikin wani hali wanda ba mai iya fitar da ni sai Allah dakuma baba. Yace na sani Safiya karatu kike so amma baba yanuna karfin haihuwa a kan ki zai maki auren hadi na katse shi da cewa auren dole dai yaya. Don wanda zaa bani ba ao na yakeyi baba kuma darajan iyayyen mu yake gani ba. Ya zaro idanun shi waje alaman mamaki fa abin da na fadi din yace wa ne shi don uban shi. Na girgiza kaina nace ko kadan baida mutunci yaya gashi kuma mashayin ne sosaiyace dani kuma baba ya san da haka din nace ban sani ba yaya. Ki kwantar da hankalin ki zan yi bincike akai inna gane gaskiya kika fada min zan yi duk abin da zanyi in ga an fasa auren nan . Maganan yaya sani shi kwantar min da zuciya har na dan ji sanyi a raina sai ya miko min leda da imdomei a ciki yace jeki ki dafa kici kafin in dawo. Naji dadi a raina na ahiga nayi yadda yace na dafa indomei na shiga dakin mu muka ci da kan ne na. Yaya sani kuma tafiya ya bincika inda yajiyo halin Ahmed babu dadi ko kadan a wurin yan uwa dake zuwa. Yaya sani yace wanan abin duk sherin su inna ne ba komai ba nai mamaki ga su hausi yannen ta ne amma ce wai za ai mata aure ita. Nan ya dawo gida ya ta yar da haukan shi ya kira yan uwan baba mu suka hadu ya fada masu halin da ake ciki. Suka taru da dare akan baban mu suna fadin wanan baiyuyuwa ba ai muna auren dole ba bamuyiwa diyan mu. Baba yai wuf yace babu mai hana wanan auren sai Allah yadda lanto ta nemi arziki a gidana haka nima zan mata shi da cewan wai gwago. Sabada haka yadda nayi niyya haka zan yi saidai idan na kaita ta fito matsalar ta ne wannan. ZAINAB IDRIS MAKAWA SEENABU 8/14/20, 7:10 PM - Ummi Tandama: BAHAGGON, , , , , , , 🧕🏿 8️⃣ 🧕🏿 YAR UWA IDAN AKWAI MASU NEMAN ACCOUNT NOBA DONA TA WURIN KI GA NOBA NA NAN SHINE 2254380105 ZAINAB IDRIS MAKAWA ZINETH BANK KO NOBAN WAYANA DON ALLAH KU TAIMAKA MIN. AKWAI MASU KARBAN KUDI SUCE ZASU TURO MIN AMMA BASU BANI SAI SU RIKE A HANNUN SU IDAN NA TURA SU TURA WA MAI SHI NOVEL DON ALLAH KUJI TSORON ALLAH YAN UWA. MASU CEWA BAN MAGANA YAUSHE ZAN TSAYA HIRA YAUSHE ZANYI TYPING SAI DAI INDAN ZAMU CIRE KWANA BIYU BA TYPING NE SAI HIRA SAI KUZABA MIN. NAGODE NAGODE DA KASANCEWA KU TARE DANI KAUNA NE YA JAWO HAKAN SAI KUYI HAKKURI DANI YAN UWA Ina zaune bayan na gama gyan gida tare da dan dafa abin da zanci tunda shi ba damuwa yayi da abincin dare ba sai dare sosai yake dawa kuma a buge. Kofa naji a na murdawa sai na tashi na bude ban yi tsan manin shi bane a lokacin. Shine tsaye bakin kofan ya kara daure rain shi naja baya tare da mashi sannu da zuwa tun da yau ya shigo cikin dan hankalin shi gidan. Bai ko kalleni ba ya shige ciki da hanzarin shi nikan na koma na zauna inda nake da farko . Sai zuwa can ya fito yana saye da gajeren wando da yar faran singlet ajikin shi ya samu kujera ya haye yana kokarin kuna taba. A kawo ma abincine nagama nace dashi sai yai wani dagowa ya kalle ni a hankade yaci gaba da abin da yakeyi. Na ja gafe daya na kama kaina na natsu ga kallon tv da nakeyi saboda yin hakan shine alheri a gare ni tunda naga yana jin tsiya yau din. Haka muka zauna zugun zugun sai busar taban shi yake yi wanda warin ya cika falon ya hana ni sukuni gaba daya a wurin. Nake zan shige ciki naji yana cewa ke kawo min abinci in ci zan fita , koda na kawo mai abincin ko cibi uku baiyi ba dan dama yaci dan doyan da na hada wurin girkin dashi. Ya tsamay hannuwan shi ya ture plate din gefe daya kasa daurewa nayi nace cikin damuwa abincin bai maka bane in dafa ma wani. Kamar dama jira yake tsutsayi yaja ni nai mai magana sai ko ya mike da sababi kamar wanda naiwa bakar magana yana cewa. Ke kada ki kuskura ki nemi takura min da tambayan banza da wofi ke zaki sani cin abincin dole ne kokuwa da zaki damay ni da nacin tsiya. Jikina yai sanyi na tsaya kawai ina kallon shi a cikin mamaki karo na biyu na sake tambayan shi cikin girmamawa may kuma nai maka daga tambaya kawai . A fusace ya jefamin wani irin harara tare da cewa ke wai baki da hankaline ki barni mana kon zauna kina damuwa na kawai da bakin nacin ki. Na dago idona cike da damuwa ina kallon shi daga abin arziki kawai sai hattara irin haka sai dai a fili fadi nayi Allah baka hakkuri na ga bakaci abincin bane. Sai ya zubo min wani irin kallo na fushi yace a hasale ke don Allah ki wuce dakin ki, ki bani wuri kaganin ki ma kara tada min da hankali yake yi. Zanyi magana yace waike wata irin yarinya ne mara hankali sai ya dakatar dani da hannun shi na dama cikin wani irin murya mai cike da tsawa yace nace ki wuce ki bani wuri in ba haka ba zan yi maganin ki yanzu nan. Na juya zuwa ciki hawaye na zuba min na fada saman gado na ina bakin ciki da dana sanin wanan zaman kaddaran da na samu kaina a cikin sa zama da mashayi mara tarbiya. Zuwa can naji ya fita yabar gidan na sauke a jiyan zuciya a hankali na mike na fito do in yi sallah. Bai shigo gidan ba sai wajajen karfe goma lokacin har na kwanta sai dai ban yi barci ba ko da alama yau baya a cikin maye do banji yana haukan nashi ba. Ban fito ba shi ma bai nemay ni ba don haka sai da gari ya waye na fito a falo naga ledan daya shigo na kayan break fast da su sabulu da omo da maclean da sauran su. Ban taba nadai kaqar na fara gyaran gidan ina tsaka da gyaran falon gidan ya fito da jallabiya a jikin shi. Tsaida abin da nakeyi nay na gaida shi da ina kwana yaya ? Sai ya jefe ni da kallon nan da na tsana bai ce uffan ba ya dauke kan shi gefe guda. Dukawa nayi naci gaba da aiki na sai da na gama naje na duba abinci na samu ya dahu na zuzuba a cikin plate nadawo na sama shi falon nace. Ga abin karyawa nan na gama a saman table bani bukata ya bani amsa dashi a fusace . Da mamaki nake kallon shi idona ya ciko da hawaye nadake nace don Allah yaya idan laifi nai maka laifine ka fada min abin da nayi sai in gyara don gaba. Wai ke wata irin yarinyace idan gidan kike son na bar maki zan iya bar maki kin isheni nida gidana kin hana ni shakat wallahi. Wanan ai takurawa rayuwa ne an daukoki kin zo kin zauna wa mutum a gida kin hanani shakat dani da gidana . Da mamaki nake kallon shi nace nima bayin kaina bane zama a gidan ka umurnin iyayyene nake bi hakana. Ya fadi a fusace da cewa very good dama zaman umurnin naki iyayyen kike bi , ni sai kiyi kokarin hadani da nawa yan uwan da iyayye ko ?. Da sauri na kalle shi ina cewa ai iyayyen ka da yan uwanka duk nawa ne hannu ya daga min yana cewa ba yan uwanki bane kan, don da basu zo gidan nan kin yi masu wullakanci ba sun koma rai bace. Na soma kallon shi baki bude ina fadi cikin mama ki da cewa ni har yaushe wani dan uwa na zai shigo na wullakan tashi ina nima su nake gani a matsayin nawa yan uwan a nan garin. Kai ya girgiza min yana cewa ba gaskiya bane hakan don da basu gidan nan kin masu taron wullakanci ba. Kin raina masu wayau ko bari su zauna bakiyi ba kike cewa wai bana gida kina kokarin rufe kofa su fita kullun suka shigo abinda kike masu ke nan. Da sauri nake kallon shi cikin mamaki baki bude nace har yaushe suka shigo gidan nan in ba jiya ba kuma nan suke zaune suna tanbayan ka nace baka nan ruwan ma da na kawo masu basu sha ba nan suka tafi suka barni dashi basu ko sha ba. Yace kenan dai sun zo din ko tabbacin cewa sun shigo kenan gidan kin masu wullakancin ko ? Gabana yai mugun faduwa sosai ni? Dama sherin da sukai min kenan to wallahi wallahi ban masu wullakanci ba a gidan nan yan uwana ne fa su dan may zanyi masu haka. Wani harara ya watso min yace da yan uwanki ne aida baki wullakan ta su ba harkina fadin magana a kaina , nace ba haka bane ya daga min hannu yana fadin ya isa haka maganan ya isheni ji ki sani kuma ba zan dauki raini ga yan uwa na ba a gidan nan. Ya juya ya shige dakin shi can ya fito ya dauki key din motar shi ya fice a hasale yabarni tsaye in da nike. Kwana uku cur muka dauka bai damuwa da harkana a gidan haka muke zaune dashi ba dadi ta ko ina saukin abin yana barmin abinci inci wanda raina yake so. Sai dai na fahinci akwai matsala a tsakanina da yan uwan shi ke nan amma na rasa gane ta ina wanan matsala ya ke tsakani da su. Haka muke zama har na tsawon kwanaki ranan ko may ya gani oho sai naga ya fito yana bude kulan abincin da nayi da safe don yanzu yakai nabar gaidashi don ko na gaida shi baya karbawa tun ranan da na gaishe shi yace dani Ke wata irin yariya ce wai mara zuciya gaisuwan na dole ne ko an baki ajiyana ne wai tun wanan ranan ban kara gigin gaida shi ba a gidan kowa harkan gaban shi yake yi. Bayan ya gama ina saurare fita shi sai naji shiru alaman bai fita ba ke nan agidan. Wuraren shadayan rana na fito a zotona yana dakin shi ne ashe yana falo kwance ban sani ba. Gashi ba daman in koma yace dani munafuka sai na daure na wuce shi zuwa kitchen. Dole hakana nake aiki duk na daburce na gama abin da nakeyi a kitchen nafito na nufi hanyan daki sai naji yace dani zo nan. Gabana ya yanke ya fadi a sanyaye na iso gabanshi nace gani sai dai ban yarda na kalle shi ba shima din ta gefen ido yake kallona. Yace dani ke baki iya gaisuwa bane ko may ? Na nisa tare da cewa gaisuwan nawa ne naga baka so shiyasa tun da ba ajiyan ka aka bani ba. Sai naga yayi tsam ya mike yayi amfani da hanayen shi biyu ya rike min hannu da karfin tsiya saida na sake kara. Sai da yaga na jirkita don kan shi yadan sasauta rikon dayai min din yana kallon fuskana dake fitar da hawayen wahala. Jinayi gaba daya jikina ya hau rawa don kusantan juna da mukayi a lokacin. Hakanan gabana banda bugawa ba abin da yakeyi ba bata lokaci ya shiga kokarin manna bakin shi a nawa, nayi kokarin kwacewa shi kuma yai amfani da karfin shi ya hanani kwacewa . Abin da ya kama daga bakina zuwa wuyana babu inda bai mana bakin shi ba da kiss ban yarda mun kalli juna ba sai ruwa hawaye dake zuba min nace cikin karfin hali don Allah yaya kayi hakkuri ka kyale ni. Kamar hadiyeni zaiyi yace ina bakin naki mai fadar bakar magana ya shiga zan kyale ki amma ki sani duk kika kara min rashin kuya a gidan nan nasan maganin ki. Don kawai ya kyale ni warin taba ya isheni tankar zan yi amai nake ji na amsa mashi da uhm mhm. Ya sake ni da karfi har ina gauruwa da kushin da sauri na shige daki na na barshi wurin tsaye. Jikina na rawa na fada daki ban daki na nufa naje kamar zanyi mai ina ta jakarjn amai bai fito ba na wanke bakina nafito duk jikina ya mutu.. Ban fito ba sai da naji yabar gidan na fito ina kallon wurin da yasha taba duk ga guntun taba a yashe a kasa. Tsaki nayi na dauko perker na kwashe tare da gyara falon ina jan tsuki hawayen ta kaici na zuba min ko nace zan ja Allah ya isa gawa zan ja shi. Ga mahaifina daya sani dole ko ga gwagona ta jawo min haka gashi har yau ban saka ta a idona ba. Ban may su sadiya suka ce ainihin nai masu ba a gidan wanda har ya hasala ta da diyan ta gaba ki daya sun dauke kafan su da zuwa wurina. ********* ********* ********* Tun wanan rana na koma jin tsoron shi zan tashi da wuri inyi aiyunakana na shige ban fitowa sai ya fita zan fito falo in zauna. Kaina ya isheni da kaikayi don haka naji ina son yin kitso na rasa yadda zanyi dashi gashi yana damu na. Don haka ranan zai fita da safe na samay shi yana cin abinci na dan tsuguna nace da shi don Allah ina son in fita zuwa gyaran kai don kaina na bukatan gyara. Baiyi magana saima nuna yayi kamar baijini ba na kara maimaita abinda na fada da farko ya dago ya kalle ni a lalace yace umurnina kike jira komay ? Nace bakyau mace ta fita bada imurnin mijin ta ba yagama ya mike yana ce min kin san garin ne da zaki fita idan kin shirya na saukrle ki wani wuri a nan cikin unguwa. Da sauri nace na shirya na shiga daki na sauko hijjabi na saka da man kitso nafito ya bini da kallon kamar zai yi magana sai kuma yaja tsuki kawai ya fita. Na bishi baya ya juyo cikin tsawa yana fadim ni zan rufe maki gida ko may sai na juya da sauri na tafi rufe gidan kafin in zo har ya tayar da mota ko ina shiga ya fisgi motar da kar fin tsiya dan can kasan lalayin mu ya kaini ina sauka ya mika man kudin kitson na karba yaja motar shi ya tafi. Ni na kai kaina wuein mai kitson nai komai nan na hadu da wata mata bahausa muna dan hira da ita harna sake jikina sai nake cewa idan zatai kitso wani karon tazo zan mata. Ita kuma ta fara tallanta min kitson wurin matan hausan dake kusa sukai aman, na da zancen kitson nawa., Na dawo gida cikin walwala da dan sakin jiki koba komai yau na hadu da hausawa yan uwa na mun taba hira duk da dai ba a jaha daya muka fito dasu ba amma naji dadin hakan ayau. Sai dare ya dawo banfito ba balle in gan shi sai da safe ko da na tashi na samu har da abinci yaci sosai. Na hada breakfast na aje mashi komai da zai bukata na wuce daki abina zaune nake na kunna kira, a ina bi a hankali. Ya shigo dakin sai ganin shi nayi a kofan dakin daga shi sai gajeren wando babu ko riga ajikin hannun shi rike da taba yana busawa. Shi kan shiyagane dan firgita danayi a wannan lokacin da gani shi sai kawai ya sai ya kyalkyale da dariya. Ya lura da taban da nake kallo sai naga ya kalla ya dan girgiza kan shi saiya kashe taban gaba daya a dakin. Kusa dani yazo ya zauna yana bare tomtom ya jefa a baki yana tsotso a hankali. Kusa dani yazo ya zauna ya shiga neman hannu na sai nai tsam na mike tsaye na koma can kusa da window na tsaya na bashi baya sai tuna nake koma na barmai dakin ne sam ban san ya baro gado ba yazo inda nake. Sai ji nayi ya zagaye man kuguna da hannayen shi biyu yana fadin yau zan cire wanan jin kai da kike min a gidan nan. Take na zazzaro idanuwa na don tsoron abinda naji ya fada sai yace may kike nufi dama yana kokarin rungumoni na shiga kokarin kwatar kaina yace dama kiwon ki nake yi da nufin ki kina cinye min abinci ga bazane. Ko kina nufin baki san abida aka kawo ki yi nan bane sai girki da shara ki kwanta kawai ko nufi kike baki san matsayina a wurin ki bane yanzu. Rokon shi na shiga yi ina fadin kayi wa Allah ya Ahmed ka kyale ni don Allah, na samu na kwace kaina gare shi zan gudu naji ya kara fisgoni tare da zaro min ido wanda tuni sun juye sun koma wani launi. Yace don't be stupid baki da hankaline kike jayayya dani koke mahaukaciyane kina nufin haka zan zauna dake ina kallon ki. A sanyayye na sunne kaina idanuwa sai kwalla ke fita nace don Allah kayi hakkuri har na shirya sai ya watso min wani kallo na bai amin ce ba. Ya kara juyani a hankali muna fuskanta juna kaina yana kallon kasa na ji ya kara dagoni tuni naji ya hada bakina da nashi irin na jiya. Ya rinka aikawa da wasu iron dabaru na salo salon na saukan hankali masu kama da siddabaru da gusar da hankalin matum. Tsaye nake kikau kamar dutse na rasa sanin dadin da yake ji har yake lumshe idanuwan shi har takai yana fitar da wani sautin nunfashi. Jikina har lokacin rawa yake yi zuciya sai bugawa yake yi uku uku sai da ya gaji da jagula na dan kan shi ya janye daga gare ni yana kallona ido cikin ido ina share hawaye yace bakauyiya kawai ashe ma kodan kiss din nan baki iya ba. Bakina yana rawa nace kaina kasa dan kuya nace ban iya iskaci ba don ni ba yar iska bace yace ok ashe bakin naki bai mutu ba ke nan . Zan ko gwada maki kin hadu da dan iska yau don sau kinyi regreting din fadar baka ga abinda zai maishe ki mace. Dago ido nayi na kalle shi tare da shiga firgicin kallaman da naji ya fito bakin shi sai dai babu komai a idon nashi sai tsaban fitina irin wanda katattare da lafiyyen tazurun gaye da ya dade baiji mace a tare dashi ba. Kai tsaye ya shiga rabani da kayan jikina tare da yi min gargadin kar in kuskura in motsa sai faman rokon shi nake yi har da hawaye da majina . Amma bai saya fasa abinda yake yi ba saida ya barni daga ni sai under wear kadai ya tsaya yana kallon na daga sama har kasa har yatsun kafana. Ya tabbatar da duk abinda yake so da kwaydayi gun mace ya samu a jikina ashe kallon da yake min na yariya don ina cikin hijjab na ko yaushe. Azahiri ba hakan abinyake ba don na zarta tunanen sa fiyye da yadda yake tsamani . Take kirjin shi ya shiga bugawa da karfin gaske yayarda mahaifiyar shi tai mashi zabin daya dace dashi yau. Lallai zai more a gun wanan yarinyan duk wani lafiyayyen nami ya gani dole ne ya kyasa can yace cikin tsawa me , , kukan may kikeyi haka ? Naji muryan shi ya juye kamar batashi ba don maganan ya juye kamar wanda ya damu da ni . Da kyat na daure na bude bakina mace don Allah yaya kayi hakkuri kada ka taba ni. Ya nisa yace in nai hakkuri may zaki bani da zakice nayi hakkuri kafin in yi magana sai ji nayi ya ratsa hannayen shi a saman kirjina yana barazanan soma murza su hakan ya sani firgici. Na soma wash innallilahi kayi hakkuri don Allah yaya idaniwan shi a lumshe yake fadin tsaya kin san bana wasa dake ko? Na gaya maki ki daina jayayya dani ko, in ba hakaba wallahi yau sai na sumar da ke gidan nan fuska a murtuke yake magana. Hawaye masu zafi suka yi min kwale a fuskana na nasan yau nawa ya samay ni mai kwatana a wurin shi sai Allah. Ban fasa zubar da hawayen da nakeyi ba naji ya kamo ni ya manna a jikin shi yana wani nishi yana fadin ki saki jikin ki karki tsorata dani zan yi ne kawai na bar ki. Duk wandan nab sabatun da yakeyi yana yin sune hade da lasan kumcina da fatanjikina da jin maganan shi kasan ba a cikin hayacin shi yake ba. Ranan kan ban san ida nake ba azaba yasa na kasa motsawa sai kuka da nakeyi wiwi harda karkadawa shiko ya kasa saurara min ya kasa yi min komai a hankali haka kuma yaki saurara min tsawon lokaci tun ina kuka da hawaye har suka kafe suka daina fitowa. Ganun da yayi na zama kamar somamiya don tsaban wahala sannan ya saurara min ya matse ni cikin gamsuwa yana fidda sambatu kamar mara hankali yana fadin thank you mum, i love you pretty, I love you so much hold me now hald me, please. Da kyat na samu ya mike ya barmin dakin ya barni kwance cikin galabai ta da wahala babu mai tai maka min. Sai da na dan samu natsuwa na rarafa zuwa ban dakin dake dakin na wa na dade zaune ina kuka ina kiran suna mahaifiya ta har na gaji na daina hawaye suka kafe min da kyat na samu nai wanka na fito ko mai ban shafa ba nakai kwance. Barcin wahala ne ya dauke ni har ya shirya ya fice gidan ban sani ba sai wurin karfe uku na rana na falka koshi yun wa ne ya tayar dani. Da kyat na taka naje falon cikin sanda don ban sani ba ko yana falo lakacin don tsoron shi nakeji tsoron mu hadu dashi yanzu nake ji a raina. Nayi arziki baya nan har na gama abinda zanci na shige daki dakyat nai sallah na koma na kwanta zazzabi ya rufe ni. Ban falka ba sai dare natashi don inyi sallah har yanzzu jikin nawa ba karfi sosai kwana biyu haka nai ta fama a gidan ni kadai shi kuma bamu kara haduwa da shi ba. Sanu a hankali na soma samun natsuwa a gidan sai ranan gashi ya dawo a cikin mayen shi duk da na rufe kofa haka yazo yana dukan kofan dole na bude mashi. Baai tsaya jiran komai ba haka ya afkamin nan na shiga dukan shi da yakusa amma bai hana ahi cin ma bukatan shi ba. Ya fita ya barni ina kuka ni daya a daki babu wanda zai lalashe ni kan haka na gaji nai shiru ina jan Allah ya isa. Bamu hadu dashi ba sai wani safiya na fito ashe bai fita ba mukai kicibis dashi a falo da sauri cikin kaduwa naja baya yace ke may nene haka wai halan ni dodone da zaki kama guda na. Bari kiji in ke manya ne baki cina don kawaii na taimaka maki zaki hauni da cizo da yakusa banza dake ma. Jikina na rawa amma na dake nace dashi ko gobe kazo min a cikin maye haka zan yi ma tunda ni ina tsoron Allah . Yace waye bai tsoron Allah nace kai mana sai ko ya biyoni a guje na kwasa nai daki nai sa a kafin ya iso na sakey. ZAINAB IDRIS MAKAWA SEENABU 8/14/20, 7:11 PM - Ummi Tandama: BAHAGGON, , , , , , , 🧕🏿🧕🏿7️⃣ YAR UWA KADA KI KARANTA IDAN BAKI BIYA DON BAA YAFE BA ONLINE NOVEL NE NA KUDI, Yaya Sani bai da karfin da zaitare baba ya hana ai bukin nan gida ya cika da yan buki yan uwan ummi suzo sun mata kara na rufin asiri yadda ya kamata don kowa bai tsanmaci hakan ba. An daura aure bayan sallah azahar duk masu cewa basu san angon ba sun san shi ranan. Kowa sai albarkacin bakin sa yake fadi walima akai mun na sauka shine zance event din da akayi kawai. Nan gidan mu na kwana acewan su washe gari run da safe zamu kama hanya zuwa ida suke. Hakan akayi washe gari muka kama hanya bisa rakiyan mama da mama lami su kadai zaa tafi da su sai so da suka zo wurin daurin aure daga can. Sai dare muka shiga garin don haka bazan iya cewa ga yadda garin yake ba don da dare muka shiga. Gidan gwagona muka fara tsayawa nai mamakon ganin gidan da suke zaune ciki ana cewa suna lagas sai mitum ya dauka a cikin wani daulan duniya suke da zama ashe abin ba haka yake ba. Dan gidane tsohon gina suke zaune ciki mai dakuna hudu gidan duk ya gage saboda tsufa. Ashe sana, a take sosai irin na arewa irin su kamu, hura kunu mai zafi da kosai da kayan amfamin na arewa da sauran tarkace da matan hausawa za su bukata. Kazab tan gidan kawai ya ishi mutum ya raina masu mama lami tace cikin rada lagas din kega in kaji ance mutum na kudu sai ka dauka wani dadin duniya yake can ciki. Washe gari aka kaimu gidan da zamu zauna shi wanan gidan ba laifi don gida ne dan matsakaici dashi da daki biyu da falo ya dan sha kayan zamani an zuba ya kara haska wurin . Muka kebe ni da mama lami tana bani shawara da cewa kin safiya ga komai a gidan mun sama don haka yan may zakiyi da su. Nace mama ki koma dasu kawai ba abin da zan yi da sunan ni. Tace a, a ba haka za a yi ba zan raba biyu in baki rabi ki boye in kin san gari sai ki samu dan sana a kinayi kin dai ga sarakuwa taki ita ma ba zaune take ba nema take yi. Don yanzu bida na kai yafi komai dadi ina kin iya kitso da sannu sai ki fara dan yi sai kuma dan abin da kika ga yana karbuwa anan din. Mama lami bata boye ma su mama yadda mukayi ba sai mama ta bada shawaran cewa ai dabaran ba ma gwogo na wani abu ace in samu sanaa na rike. Kashi daya a bani a hannu na sauran a koma dashi gida da kudin dari biyu ne da hamsin da dan kai. Duk da an kawoni da kayan abinci mai dan dama sai sukace mu dauka muyi amfani dashi sun kara jamin kunne a kan zaman aure mukai sallama dasu akan washe gari zasu tafi don baba yace kada su wuce kwana biyu a can. Aka barina ni daya a gidan a garin da ban san kowa ba shiru banga shigowan shi ba gidan har bar ci ya dauke ni. A tsorace nake sai haushin karnuka dake tashi unguwan da karan motoci jefi jefi. Dayan dakin dake bude na shiga na rufe kaina a ciki har barci ya fara dauka na naji ana bugun gidan da karfi. Tsoro ya kami sai da naji yana antaya min zagi na taso a tsorace daidai lokacin da aka turo kofan da karfi dama ba a rufe kofan yake ba . Yasha yayi tatil dashi sai rangaji yake yi a tsakiyan falon na rakube gefe daya ina kallon ikon Allah yau ni safiyane a gaban dan giya. Magana yake son yi amma layi ya hana maganan fita ya kwasa da tangadi ya shige daki da kyat ya iya bude kofan. Shiru shiru banji ya fito ba na tashi na dan leka dakin da ya shiga kwance yake rub da ciki har takalman shi yana nasari da karfi. Na sauke ajiyan zuciya na juya zuwa kofan na rufe da key na kashe wutan falon na dawo na takure a wuri daya a falon. Inata tunanen wani irin zama zamuyi dashi a gidan haka a cikin maye duk jikin shi ya baci farin kayan dake jikinshi na jeans da farar tieshirt duk sun baci da laka. Nasan yasha faduwa ba iyaka a hanya ne yafi a kirga kafin ya iso gidan cikin maye. Washe gari da asuba na tashi ina jin kiran sallah can nesa da mu yana tashi don haka nasan asuba yayi ke nan. Na idar da sallah gabana sai faduwa yake yi don far gaba da tsoron shi don ban san mene zai wakana ba in mun hadu. Na mike da kyat na fito falo na fara gyan wurin koba a fada ba kin san may zai tashi gida akan warin taba. Ina tunanen may zan girka na shiga kitchen tsaye nayi ina kallon komai a hankali don komai akwai a kitchen din na fanin girki. Dabara ya fado min na nagirka abu maidan ruwa ruwa tun da safiya ne yanzu. Nan na zage na dora faten dan kali da turawa sai kunun custad dana gani na dama har na gama babu motsin shi. Na kara gyara ko ina na shiga dayan dakin da na mayar nawa wanda babu komai sai dan gado da katifa sai yan kayana dake a gefe daya. Na gama zan fito na debi abincin da na girkana muka gwabza karo dashi zai shiga kitchien din shima. Ya sauya kayan jikin shi zuwa dogon jellabiya mara hannu hannushi rike da taban da ta kusa kare waba. A tsorace naja baya kadan na rabe tare da dan tsugun nawa nace dashi ina kwana. Kallona kawai yayi ba tare da ya amsa min ba yana zukan taban shi wanda warin shi ya banbanta da wanda na sani. Na raba shi na wuce zuwa falon sai naji yace uban wa yace ki rufe min kofa daren jiya dana fita. Kallon shi na dan yi nace uban wa ya rufe ma kofan har ka bude ka shigo din in an rufe ne. Ya dauki kallon na daga sama har kasa gaba daya na rufe jikina cikin hijjabi babba har kasa. Yace dube ki yar iska kucakan baza sai iya bakar magawa wa babba zanyi maganin ki gidan nan. Zanyi magana kenan aka buga kofa gidan har sau biyu ya nufi kofan yana fadin who's on the door tare da bude kofan kadan. Lokacin na samu daman shigewa da abincin dake hannu na daki ashe kanin shi ne ya kawo muna abin karyawa daga wurin gwago. Kiran da yake min ne nasan cewa shine ya shigo gidan ina daki na karba mashi na fito saye da hijjab dina ina gaida shi cikin ladabi naci yaya sa,adu ina kwana. Da fara,a a fuskan shi ya amsa min tare ta zolayana na wasan tobasai yana cewa yau ga bakauya a lagos. Murmushi nayi ina jin kunyan mayar mashi da mashi da magana. Shiko gogan ya zauna ya harde kafa har ya kara kunna taba yana zuka a hankali sai naga annuri dan uwan yarage fara a a fuskan shi. Da harshen turanci yake ce mashi baidace yana sha a cikin gida ba haka ko banza yaga ni karamar yarinya ce fa. Mind your business please, don't boader me, is my house ina da right din abin da nake so in bata so ta fita waje. Sai ya kada kanshi yace ni zan tafi dama mummy ne tace na kawo maku breakfast nace ai muna godiya wurin gwago amma dan tsaya in zuba maka abinci mana. Baiki ba yake cewa tou har amarya ta fara girki ashe sai ya mike yana cewa dan uwa ai dole taga kayan banza mana. Uhmmm uhmmm naji dan uwan yace dashi da yake fadan haka ya shige yana ce ma kanin zan dan watsa ruwa ni. Shigewan shi na kawo mama yaya saadu abincin yace tun banci ba kamshi ya buge ni da alama amaryan namu ta iya girki. Dan murmushi nayi kawai na juya zan tafi yace ji mana sai na dawo na zauna a kujeran dake dan nisa dashi. Ina wasa dan yatsun hannu na a hankali yace Safiya nasan cewa ba, a kyauta maki ba don baki san ko waye Ahmed ba kosu kan su iyayyen namu basu sani ba ne. Nai dan murmushi nace na sani yaya saadu yace kin sani fa nace eh don shi ya fada min komai kuma gashi ina gani a zahiri. Ya ce Allah sarki safiya kiyi hakkuri karki biye mashi ku zauna lafiya duk abinda yake yi ki barshi da Allah tsakanin shi ne da mahaliccen mu. Ke dai abinda kawai zan fada maki shi kiji ki ki jini dan ko ita mahaifiyar tamu sai hakkuri don son da take mashi yayi yawa har yakai bata iya tsayawa tai masa fada. Don haka kar ma kice zaki dinga kai kara wurin ta don bata so, wanan zai iya kawo tsana a tsakanin ku. Nace nagode yaya saadu yace zan dan rika lekoki jefi jefi ina duban lafiyan ki kinji ko kedai ki kula da hakkinshi da ya rataya a wuyan ki. Godiya na kara yi mai ya mike bayan ya gama cin abincin ya tafi ya barni a cike da tunane a raina. Ina zau ne a dakin ni daya sai gashi ya fado min kwatsan a dakin yana faman kale kalen dakin kamar bakon shi. Hijjabi na dake gefe daya namika hannuna na dauko yace kada ki sama ki saka wanan tsunman a jiki ki yar kauye kawai. Sai ya ja tsuki gefen gadon da na ke zaune ya samu ya zauna kadan yana may bin dakin da kallo har lokacin. Kwata kwata na kasa sakewa a dakin don ban taba zama da namiji hana ba a rayuwana. Sai naji yace ke baki iya gaisuwa bane ko a gidan ku ba a gaisuwa safe ne nace ai da zun na gaishe ka a falo. Sai naji yace may kuke magana a kai da Saadu naji ya dade bai tafi ba nace abinci ya ke ci. Ido ya kafa min bai yi magana ba na wani lokaci saidai bina da yaya da ido yana mun kallon kurulla do bai taba ganina haka babu hijjab ba sai yau. Yace koma may ye shiya sani nida gidana ba wanda ya isa ya hanani abin da nake son yi don kawai wani yaji dadi. Na dukar da kaina kasa idanuwa na suka kawo ruwa ya mike yana cewa common abincin ma ba a koya maki yadda zaki ba mutum shi ba. Ya fice na sauke ajiyan zuciya a hankali tare da mikewa nabi baya shi ya zauna wurin cin abincin da aka tanadar a gidan. Abincin da gwago ta aiko na fara budewa sai naga kosai ne da kunu mai zafi yace rufe shi wanda kika girka zaki bani nasan girki ba wani dadi sai maneji kawai. Shi na zuba mashi na juya na dauko mashi ruwa ga kwalabe nan barkatai a cikin fridge din wanda ban san kasu ba . Kafin wani lokaci har ya tashi da abincin a binka da mashayi dama cikin na rurin neman abin da yaci duk ya cin ye duka. Na kwashe kayan a raina nace ka kaishi in dai gulma ne abincin da yace ba dadi gashi ya lashe duka bai bar komai a kwanon ba. Don gatse nace ko in karo ma ne? Ciki daka tsawa yace dani don Allah ban wuri kin ce ko dadi abincin yayi ne kawai dai don ba abin da zan ci ne shiya sa. Kayan na kwashe na wanke na koma daki na dan kwanta do in huta saboda gajiya a jikina. Na dan kwanta sai barci ya dauke ni ban falka ba sai wani lokaci can a cikin barci nake jin kida na tashi a gidan. Na bude idanuwa da kyat kallon lokaci nayi idan ba ai sallah ba naga lokaci da saura don haka nace barin dan samu abin da naci don wanda na diba da safe ban ci ba sabo zuwan yaya saadu yazo gidan. Na fito falo a zatona ya fitane yabar gidan na tashi kwatsan sai na gan shi kwace rigingine saman three seater dagashi sai gajeren wando yana busa taba sigari yana busa hayaki cike da yanga da gwanewa. Tsoro da firgici ne suka dira min a zuciyana don ban taba ganin namiji a haka ba da sauri na juya zan koma daki naji yace ke bani son shashanci fa. Nace may nayi kuma ? Ya dago ya dan harareni ya koma ya kwanta yana cewa may kike nufi ne nufin ki ni zan dafa muna abinci da kika shiga daki kika kwanta. Kallon wurin da kulla yake nayi sai naga alaman an cinye abincin nace ba akwai abinci ba a kulla. Ba surutu na tsai da ke ki min ba abinci na ce ki dafa muna, ban tsaya magana ba na wuce zuwa kitchien din. Tsaye nayi ina tunane yadda ya dora abincin nan shi kadai a cikin shi kuma wai yana neman kari. Aiki nakeyi amma karan kidan da yasaka ya damay ni gashi babu hali nace ya dan rage ya sauke min kwandon balai a kaina. Sai da na hada komai na fito zuwa sallah don lokaci yayi na a zahar na shiga bandaki na dauro alwala nafito na tayar da sallah. Na koma kitchean di bayan na idar na karasa aiki na daya rage min kafin wani lokaci na hada abinci ko na aje mashi a falo nai shigewa na ciki. Ina gama ci sai gashi cikin shirin shi do lokacin karfe biyar na yamma ya kusayi ko gabana ban da bugawa ba abin da yake yi. Naji yace abincin fa nace dashi an gama ya dan harare ni tare da fadin ni kenan zan zubawa kai na ko. Mikewa nayi nabi bayan shi zuwa falon yana zaune na zuzuba mai komai harda gaiyya nayi wurin zubawan amma duk haka sai da ya lasheshe kaf. Ya mike ya dan shiga daki zuwa can ya fito ina jin lokacin da ya fita ya bar gidan. Fitan shi gidan yasa ni sauke ajiyan zuciya namile nafito na fara dan gyaran gidan na murda kofan dakin shi na jita a kulle nace kai ka sani. Naga komai na dawo falo na zauna ga tv amma inajin tsoron kunnawa yazo yace wayace in taba mai kaya. Kewan gida ya dawo min a rai na zauna ina tunane ina kukan rashin yan uwana da nayi kusa dani. Na saba a gidan mu in gari ya waye hayaniya kawai ya isheka tun safe har dare ihun yara ne zai tare ka a gidan. Gashi yanzu nazo nan garin da bansan kowa ba ina zaman kadaici duk da unguwa guda muke dasu gwago na sin amma har dare yayi babu wanda ya sake zuwa wurina bayan yaya saad duk da kuwa tana da yara yan mata zasu girmay ni ga shekaru. Ko da yake nasan wanan sana, a da takeyi bazai basu lokacin samun zuwa yawo ba ko wani lokaci. In gari ya waye tun karfe hudu idan ta tashi bata da lokacin komawa kuma yi wanan sauke wancen har dare . Jama, a sai shige da fice suke a gidan wanda akasarin su hausawa mazauna lagos da ke zuwa sayen kayan iri na arewa da babu shi a can. Yaran ta mata ko wace nada aikin da zatayi nata cikin sana,a da take suna taimaka wa uwarsu dashi. Suma mazan kakani ba a barsu a baya ba wurin bada nasu taimakon in ba haka ba yaro ya gane kuren sa ta hana mai kudi. Yau ma kamar jiya bai dawo ba ina jin barci na ja kofan dakin da nake ciki na rufe kwantawa nayi na makure a wuri daya cikin tsoro. Karfe biyu saura naji ya dawo gidan a cikin mayen shi da yasaba ina jin shi yana ta surutain shi da banke banken kaya ban dai fito ba balle. Can nabar jin motsi haka yasani n yayi barci kenan Allah ya kyauta nace tare da gyara kwanciyana dakyau sai dai babu barcin kwarai gare ni. Da asuba na fito in yi gyaran falo sai ganin shi nayi tirim kwace tsakiyan falon yayi amai da fitsari ya bata wurin dashi. Take idanuwa na suka kawo hawaye nasihan da akai min ne yazo min a rai a hankali na juya zuwa ciki na dauko abin kwashewa na fara gyara wurin da ya bata nai nisa da gyara motsina ya tayar dashi. Daga barcin naga ya mike kata kata zuwa ciki nan naji dadin tsabtace wurin da kyau ina yi ina kuka da addua a cikin bakina hawaye nata zuba min. Nagama na shiga na dora girki abin da zamuci don nasan da ya tashi abinci zai nema in banyi kuma iyayyena su sha zagi. Har nayi na gama ban ji motsin shi ba na shige nai wanka na fito bayan na gama gyaran jikina na fito do in debi abinci in ci ga dai abincin na diba sai na tasa shi a gaba na kasa cin koda cibi daya ne. Nai zurfi ga tunane najiyo motsin shi daga dakin shi lokacin har karfe takwas da rabi saura na safe rana ya soma fitowa a gurguje ya fito yana sauri. Ina kwana nai mashi ya amsa a dakile kamar wanda baya son amsawa bani abinci na yace dani ya nufi wurin cin abincin kai tsaye a ranan nasan wai ashe yana aiki ya makara saboda ya bugu a daren jiya. Nidai na zuba mai na koma daki yana ci ya fice a gidan ban sake jin duriyan shiba kuma har rana ina zaune ni kadai a gidan nace barin leka waje inga yanayin uguwan. Uguwa ne irin mai jamma, a din nan da yawa kowa na harkan gaban shi ba ruwan wani da wani kowa tashi ta fisshe shi din nan. Na dan duba yanayin na koma ciki tare da jan kofa na rufe kwantawa nayi sai barci ban tashi ba sai biyu da rabi. Na tashi ina salati don makaran da nayi wurin yin sallah na dade zaune ina adduoi na neman tsari da mafita ga Allah. Na tashi nafito duk da akwai dan sauran abinci amma sai da na girka wani na rufe. Don ina gudun ya dawo ya hauni da masifan don ni yanzu tsoranshi nake ji sosai gani nake zai zo ya samay ni da duka idan ya je ya shawo. Na gyara gida na dawo falo na zauna can dai nace barin kuna tv in kallo ina kunnawa yana a wani tasha da aka badala iskancin filin Allah maza da mata. Da sauri na kashe karshe ma a mike daga falon na koma daki na zauna ba wani aiki a gareni sai na tunane. Sati na guda a kidan muna wanan zaman in ya fita run safe baya dawo gida sai dara ya raba idan zai shigo kuma a buge zai dawo gidan. Tun ina tsoro har na fara sakin jikin na na saba da zaman kadaci ba mashigowa nima bana zuwa wurin kowa. Duk da zaman da muke yi dashi tun ranan da yai mai da fitsari nakwashe ta rage zagina da tattara sai dai ba sakin fuska ko kadan a wurin shi. Nima dai hakan ne a wurina daga gaisuwan safe zan ja bakina na tsuka sai kuma wata goben in Allah ya kamu lafiya. Yau ma zai fita na gyara gidan nake rokon shi da ya kunna min tv zaman kadaici ya isheni har zai yi magana komay ya tuna sai da ya gama jan rai ya hada ya nuna min yadda zanyi. Ya fita ina zaune ko ina zaune ni daya kallo ya dauke min hankali wani indiya ake yi mai ban tausayi kofa naji ana bugawa. Nai mamakin jin bugun kofa a lokacin na tashi na saurara kofan ake bugu a hankali na bude kofan. Sisters din shine su biyu tsaye a kofan na tare su da mutunci sai naga suna amsawa dakyat suna wani yamutse fuska. Nace sai yau anty ? Naji sadiya tace min tauuu, Na sake cewa ina su gwago suna lafiya ? Ta amsa da lafiya kalau. Nace dasu ku zauna mana. Sai naga sun kalli junna su kamar ba zasu zauna ba sai dai suka zauna din kitchean na wuce na fito da cups da goran ruwa na kawo masu. Ita dai habiban ko magana bata son yimin nace dasu bissimillah ga ruwa sai naga sun kalli juna sun tabe fuska . Sadiyan tace bar ruwanki dama mu hanya ya biyu damu nan muka ce bari mu biyu magani ko yaya yana gida mu gaisheshi. Nace yana wurin aiki sai daren ya shigowa habiban tace ke sadiya mu tafi don Allah hakan haka auka fice nabisu da idanuwa cike da mamaki yan uwan nawa kenan kuma yan uwan miji na. Da wani zanji a raina wai da nashi ko da nasu tsiyar da naga sun fara nuna min ina ce wurin su zan ji dadi ashe abin ba hakana yake ba. ZAINAB IDRIS MAKAWA SEENABU 8/14/20, 7:11 PM - Ummi Tandama: BAHAGGON , , , , , 🧕🏿9️⃣🧕🏿 DON ALLAH YAR UWA KADA KI KARANTA IDAN BAKI BIYA BA DON BA A YAFE BA DON ALLAH KI YI HAKKURI DA HAKKIN WASU, , , A kwana a tashi zama yai tafiya saida babu wani jin dadin aure a gare ni kullun zaman hakkuri nake yi garama da zaman gidan mu mai wahala da wanan zaman ukuban da nake cikin sa yazu. Ko ba komai a gidan mu ina ganin iyayyena ina jin dadi da yan uwa na nan ko haka zan wuni banyi magana da kowa ba na tsawon kwanaki. Sai da na cika wata biyu cur a gidan ranan yace in shirya zamu tafi gidan su da farko murnan zuwa nayi sai kuma na tuna da abinda yan uwan shi sukai min sai murnan ya koma ciki. Don yanzu ma ban san abinda zanje na sama a gidan sai dai nasa a raina cewa zan kama kaina da sha, anin su a rayuwa na. Na shirya cikin cotton lace light green mai yan duwatsu kanana sai hijjab dina da na saka a falo na samay shi yana jiran fitowa na. Simi simi na fito tare da cewa gani yaya mikewa yayi yana mai kare min kallon muka fita nasan kwalliya na ne bai kashi ba. Don shi indon ta nashi ne baiki ace na fita ba hijjab a jikina ba ko na yafa dan gyale a kafada na mu fita yafi son na fito yar bariki sahihiyar ta amma ni na kasa yin hakana. Mun shiga kwanan gidan tun daga nesa muka hango jama , a masu sayen abinci sun cika wurin sai ya dan ja ya mota ya tsaya nesa da gidan na su. Yace cikin wani murya ke ki saurare ni kiji may zan fada maki dakyau hakan danaji yasa na natsu ina sauraren shi. Yace bani son naga kin fito waje inda suke sana a ar su din nan kuma ki tabbatar kina saye da wanan abin har mu fito cewa hijjabin kenan. Duk kika yarda na ganki wurin wanan sana an ran ki zai baci ki kama kan ki da dabiun wurin nan a sanyaye na amsa da to yata da mota muka karasa gidan. Maza da mata a waje sai cin abinci suke yi tuwon shinkafa miyar ganye da agushi sai kamshi ke tashi. Tunda muka tsayar da motar mu yan wurin suka sako muna idanuwan su da kallo maza da mata yan duniya. Nan aka fara yi mai kirari da sunan shi na tan bariki nidai daga kafa nakeyi amma ji nake kamar zaa ce ke in sheka da gudu. Wani rumfa muka nufa inda gwagon nawa take ciki ga yan matan ta nan gefe daya suna kidayan kudi sunci kwalliya sun kure adaka. Duk yawan taron nan dake ciki bai hana ni zuwa gaban ta na durkusa ba in gaishe ta sai cewa tayi yau kun ga daman zuwa ku gaida ni koda yake baki da laifi ai ga mai lefin nan gaban ki. Bai bata amsa ba wata maidan buje tazo ta run gumay shi sai yaja hannun ta sukai waje suna rike da junan su. Nauyi da kunya suka kamani tace tashi ki zauna dan duniya ya hadu da mashiririta yan uwan shi. Na juya inda sadiya take ina gaishe su don ko banza sun girmay ni ga shekaru. A dakile ta amsa mim gaisuwa sai ga wata yar fara mai dan buje tazo da hausa ta gwargwari tana cewa a wanan ne amaryan tamu. A gaskiya hardguy ya iya zabe mace Allah yasa a zauna lafiya amarya sai hakkuri da mutumin fa don naganki yarinya karama shiko gashi tsohon tazuru. Cikin wani murya gwago tace da ita salima me i no wan dat wooo sai salima tace sorry ma. Nace ashe su gwago tsofin bariki ne har da turancin go and come an iya a raina nake fadar hakan wata yar baka mace tazo ta katse min tunane da cewa. Wai ki shiga ciki inji hardguy saina rashi na bi bayan ta ina jin habiba na mata magana sai dai ban fahinci may take fadi ba. Ina nan zaune sai gata ta dawo tana cewa may za a kawo maki ne murmushi nayi nace a a barshi na gode a koshe nake ai. Sai mamakin wanan rayuwan nake mace da auren ta tara kananan yaran mata a gida ana shar holiya wai da suna neman kudi. Zuwa can ta dawo dauke da abinci a cikin tire tana cewa yace in kawo maki wai kin dade baki ci abincin hausawa ba ta sauke tire din naga tuwon shikafa ne da miyan alaiyahu ya ji agusi da naman shanu tace dani ko baki sin wanan akawo maki na yauki. Murmushi nai mata nace a, a barshi kawai ko wanan ma na gode ai sai ta kashe murya tana dan waige waige tace mijin kine ya saya maki indon hajiya ne har kizo ki tafi bazakici komai ba a nan. Kin santa da shegen son kudi koda yake ke bakuwa ne a gidan baki san komai ba tukun tun tafiyan ta ina zaune ni kadai ban kuma taba abincin ba duk da ina son ci. Can sai gata ta dawo dauke da kwalban coke a hannuta mai sanyi ta dire min tace kina nan zaune ke kadai ba, yi hakkuri dan Allah hajiya bata tasowa yanzu sai ta rarage cinikin ta. Ina nan zaune sai ga sadiya ta fara shigowa gidan cikim gidan daga wurin sanaar su tace a, a kina nam zaune na ashe. Murmushi nai mata kawai sai ta dan fara rage kayan jikin ta zuwa can ta kai kallo ga abincin dake aje a wurin sai take cewa a, a baki ci abincin bane. Aikoda kin ci abincin ki don mijiki yau yana can ya samu yan matan club suna sharholiyan su dama ya dade baizo ba sai yau. Wani irin naji a raina amma na dake a fili cewa nayi abin da suka sabayi ne yin hankan ya zamay masu jiki ko. Ko bata fahinci may nake nufi bane sai naji tace min bari in debo mai zafi nazo muci tare tunda naga kina jin kunyan ci. Nace aida kin bari naci wanan din bata saurare na ba ta fita sai gata ta dawo da wani abincin wanan karon miyar danyan kubewa ne ta debo muna. Tare muka zauna muna cin abincin muna hira sai na fahinci bata da matsala ita har take cewa dani tankan so zuwa gidan mu amma sai take tsaro kamar nace mata tsaron mai sai dai na kyale ta kawai. Nan na taya ta sance kanta da ya tsufa da kitsu nai mata wani kitsun duk wace ta shigo ta samu muna kitsun sai ta yaba da kyan kitsun da nai mata. Nan sukai ta fadan zasu zo in masu kitsu a gidan suma habiba dai ko kallo ban isheta ba sai A wurin ta nake jin wai yaya saadu yai tafiya dama shi ba mazauni gida bane yana zuwa kasa ibom neman kudi ne a can. zuwa can gwago na tashigo daka ciki lokacin ina masu shara son ko lokacin gyaran wuri basu dashi. Kullun ana aikin naiman kudi a waje koma nasu kaca kaca a gidan yake nai ma wurin tas na kama na wanke wa na wanke. Saida ta samu wuri ta zauna a dakin nata wanda na share kale kale take bin dakin dashi ta kwala min kira ina bakin famfo na amsa nazo. Nazo na durkusa gabanta sai tace dani kwanaki na aika yaran nan gida ku kikai masu rashin mutunci su da gidan dan uwan su. Ni har na aika a dibo min dana kice wai barci yake baki tashe shi ke har yaushe kika san dadin miji kega mai miji. Sai sadiya tace mama na fada maki fa ba haka tace ba tace da sadiya ke rufa min baki yar uwar takine zatai mata karya ko may ? In dai zurian Rabi ne wani irin tuggu ne basu iya ba matar da kullun cikin kullin sheri takewa kishiyoyin ta ta hana su shakat a gidan. Na dago kai na kalle ta don jin kallaman da ta fadi gamay da mahaifiyana sai tace eh mana. Ko kina nufin bansan shirin da kukayi akaina bane dashi kan cewa zaki shigo ki mallake min da sai a baninda kuka ce da ke da uwarki a kan shi. Na dukar da kaona hawaye na tsiyayo min a fuskana ganin ina kuka tace a hasale karya na fada ke nan ko kina nufin nai maku sheri. Nace haba gwago wallahi tallahi bansan komai ba akan haka, sai habiba tace wallahi karya kike yi an ina jin ki ranan daurim auren ku wai suna maki huduba Ita ta fada habiban ta fada haka suka sani a gaba da zagi kamar ba yar dan uwan ta nake ba shi babana yai mata halarci ita kuma tai mai son ranta Kwasan ya fado dakin kamar wanda aka turo ganin yadda nake nake kuka da rantsuwa a gaban mahaifiyar shi da habiba nata yanka min zagi. Cikin mamaki yake kallon su ya kalle ni yana son jin abinda ya faru haka suke min masifa ina kwasan kuka. Sadiyana ta fara mashi bayani sai uwar ta katse ta jikin shi yai sanyi ganin yadda nake kukan da rantsuwa sai zagi suke zubamin. Ke tashi muje hakana yace dani ya dubi uwar yace muzamu tafi don banga amfanin yin hakan da kuke yi ba . Simi simi na miki na jawo hijjab dina dake rataye ga igiya na saka ina fadin sai amjiman ku itako gwago sai faman fada takeyi tana cika tana batsewa. Nan ya biyo ni baya ranshi yana mai suya yasani sarai safiya ba zatai wa yan uwan shi haka ba sheri yaran suka kulla min wurin uwar su tun ranan da yazo ta fada mai ya samani da maganan nai mashi bayanin komai ya yarda Nika sai faman kuka nake ina tunane a raina wanan wace irin kiyayya ne haka may ne mata a rayuwan ta take shirin nakasa ni. Har muka isa gida tunanen maganganun su nake akaina may nai mata a rayuwa na take son gani na a cikin ukuba can na nisa nace Allah ya fata duk abinda ya shirya zai samay ni babu makawa sai ya faru dani . Na share hawaye na na mike zan shiga wanka ya shigo dakin yana fadin may ya hadaki da su habiba ne na ce babu komai nidai a rayuwa na. Sai yai min wani kallon na sama da kasa yace zanbin cika idan kice baki da gaskiya zaki gane kuren ki. Yana fita gidan nasu ya koma gwago najin dawowan shi ta samay ta ta cika fam har lokacin don yar ta habiba ta zugata ta zugu akaina. Yace mummy may ke faruwa ne tsakanin ku da yarinyar nan ina ke kika hada wanan abin bai dace ba kuma ace akwai matsala a atsakanin ku yanzu. Tace cikin fada kaga rufe min baki don wa nake wanan fadan duk mugun nufinta akan mu dakai mun sani duk sherin da aka kulla azo ai muna gashinan yana fita fili muna gani. Mummy har wani hali ke gareta wanda baku sani ba tace kai ina zaka sani tunda a boye akeyi don a mallake ka da yan uwanka. Niko kowaci tuwo dani miya yasha munafuka sai ta dinga yin abu simi simi da ita wai ita ta kwara mugun halin na nan tattare da ita na ta shiga dura mai akidar banza daiyi min wai mun zo da nufin raba shi da kowa kuma nu cinye dan abin hannun shi na gudu. Tun bai dauka ba har ya fara dauka yana cewa aiko zata gamu dani dama ni ba yarda nayi da wanan yarinyar ba sam. Sai da ya biya wurin abokan shi ya dawo gida misalin karfe tara na dare ya tarar dani na fito bandaki daure da tawul ya fado min dakin da masifa. Ke mara mutunci dama na fada maki in na bincika naji baki da gaskitya zan dauki mumunan mataki a kanki watau kun hada baki da iyayyen ki kizo ki haince mu ko. Idanuwa na suka kada sukayi jawur mamaki da takaici suka rufe min zuciya yace an turo ki anga kudi banza anzo aci ko har a kashe ni. A hasale na bashi amsa da cewa kai dan Allah har ina kudin yake da za, a turoni tun daga arewa har nan ci ku kudi ya rufe wa ido kudin da ana nema kamar ba neman su akeyi ba. Kafin in karasa magana na sai naji yakaiwa bakin nawa naushi saida naga wani wuta ya gitta min na duka tare da dafe fuska na. Nadago nace ka dukeni akan gaskiyata ban karasa ba ya shiga duka na har tawul din dana daura yana sancewa. Baisa ya daina ba sai da ya barni kwance a dakin ya fito yana maida numfashi daya baya daya ya nufi dakin shi. Kuka ma kin zuwa yayi min a idona na dade duke a wurin da kyat na daga nakai bakin gado a haka na haye gadon na kwanta cikin dare zazzabi ne ya rufe ni mai karfi saboda zafin bugun da na sha. Da safe har ya fito ban fito daga dakina ba ya leka ko na gama abin karyawa sai dai babu alaman ko fitiwa banyi ba lokacin. Ya shigo dakin da niyar yai min fada nan ya samay ni cikin bargo ina rawan sanyi zazzabi mai karfi ya rufe ni. Da zumar yai min fada ya shigo dakin sai ya samay ni a haka kwance cikin bargo ina makerketa yadan ja ya tsaya. Ya dade tsaye yana kallona sai ya juya ya fita zuwa can sai gashi da paracitamal da goran ruwa ya kawo min da kyat na tashi ina sha na koma na kwanta. Wasa wasa sai da na kai kwana uku kwance ina jiyan dukan dayai min tun wanan lakacin gaba daya zaman ya karasa jagulemuna a gidan. ZAINAB IDRIS MAKAWA SEENABU 8/14/20, 7:11 PM - Ummi Tandama: BAHAGGON, , , , , , 🧕🏿🔟🧕🏿 NAGODE DA KUWALAWAN KU GARENI YAN UWA DA BAZAR KU MUKE RAWA IDAN BAKI BIYA BA DON ALLAH KARKI KARANTA YAR UWA DON A KWAI NAUYI A KANKI. Nazama sha tikan duk dare yaje yawon shi ya dawo, acikin maye zai nemay ni idan nakiya kuma zai min mugun bugu ya biya bukatan shi. Gari kuma ya waye in tashi in girka mashi abinda zai ci don ciki ya kwakware mai da ruwan giya. Daya tashi babu abin da yake nema sai abinci mai dan nauyi da zai cika ciki dashi idan ya gama wani bi ya kara nema na koda karfin tsiya ya biya bukatan shi. Acikin irin haka na ranan yana tsaka da buguna, sai ga yaya saadu ya shigo gidan namu yayi sallama har ya gaji amma yana jiwo ihuna daga ciki. Kai tsaye ya fado cikin gidan ya samu ya danne ni ya ta bugu a kasa da karfi ya tire shi samana daga ni sai underwear a jikina. Ya na ganin na haka nan ya juya baya da saurin shi shiko gogan sai mazurai yake da idon yana mai mai da numfashi . Sai ya hau zage zage yana fadin sai ya halakani a gidan nan wani tsawa saadun ya daka ma wan nashi daidai na samu na daura zani a jikina ta dawo ciki yana cewa . Amma bros baka kyauta ba wallahi ina yarinyar ga taga karfin ka da zaka dinga dukanta haka yace dakata mallam kada kazo min gida kace zakai min nasiha kan wanan bazan yarinyar mara mutunci. Yace haba bros matar kace fa ta sunna kake zagi haka ya kamata ace yanzu ka daina abubuwa da daba ka kama kanka. Ya juya wurin ina ta faman kuka yace kin ga Safiya ya isa haka shiga ciki ki kitsa kan ki kizo haka bakyau wallahi. Nasamu naja kafana zuwa daki wanda da kyat nake dagata don wallah ina shiga naji yana cewa dan uwan nashi wanan abin baiyi ba wallahi. Na dawo sadiya ke fada min irin sherin da habiba ta kulla mata wurin mummy a gaskiya abinda kuke yi baku rike amana ba. Yace wani amana can dama waya ce yana son ta ko waya nemota sai dan uwan yace mummy kuma hakan da akai maka bakaji dadi ba yanzu ji yadda ka koma kaima kasan akwai banbanci da yadda ke da a watse. Ashe ko aure dadi gare shi ko ba a fada ba yarinyan nan tana fa da hakkuri har yakai ka kure hakkurin nata ta soma mayar maka da martani kana babban kanka. Nan dai yake cewa yarinyar baza ne kana ganin ta wurin nan munafukane ta kware bata da kunya sai na gwada mata ba irin mu akewa haka ba a tashi lafiya. Yaya saadun yace baka ko kyauta ba wata mace zaka samu ta zauna tana hakkurin da irin halin ka nan dai sukai ta kwasan dashi. Daga karshe ya shige dakin shi ya barshi a zaune a wurin ya kwala min kira na fito ina kuka ina share hawaye da habar zani na. Nazp na durkusa kasa gefen kujera ina cewa gani yaya ya dago yana cewa a haba dai hau kujera ki zauna mana na girgiza kaina nace nan ma yayi min. Yace Safiya msi yasa bakiyi wa mijin ki biyayya har kika bari yana dukan ki haka kamar wata mara gata eyeh. Kuka yaki tsaya min nace yaya bana mashi komai haka dai ya daukan wa ran shi yai ta dukana do ban da daraja a idon shi. Don kawai yana ikirarin da cewa bashi ni akayi ya tare ni da cewa a haba kibar fadin haka mana ke fa kaunar shine ko banza. Yadai bani hakkuri ya lalashe ni da kuma nasiha har zuciya na tayi sanyi da zai tafi ya kawo duba goma ya ce na rike a hannuna zan samu na kashi. Nai mai godiya ya taka har kofan dakin shi yana fadin bros ni zan tafi sai na saike lekowa kenan sai ya amsa mashi daga ciki da yaushe zaka koma. Yace ina nan har kwana biyu sai yace sai mun hadu ke nan ya saadin yace don Allah aita hakuri yace is ok ai. Ina shiga daki na raba kudin da yaya Saadu ya bani biyu na boye rabi kamar nasan zai karba sai ko gashi ya shigo yana ce min . Ke bani kudin da saadu ya baki nan ashe wurin rabawa ban raba daidai ba bakwai din na boye na bashi ukun sai ya kalla yai tsaki yace munafuka kawai. Ya fice gidan na harare shi ina cewa a fili mugu kawai ashe baiyi nisa ba ya juyo yana fadin may kika ce nace ni badakai nakeyi ba. Yafice yana kutawa tare da gaura kofar gidan da karfi na sauke ajiyan zuciya ina mai kallon jikina inda na ji ciwo tare da dan tabawa. Fitowa nayi na kara gyara wurin da ya bata nagama nai wanka na gyara jikina ina shirin dan kwatawa na mike naji nocking din kofan gida. Na fito don ina ga kowa nene akofan sai ganin yarinyar aikin gwago da tai alkawarin zuwa kitso wurina a kofan nai mata sanu da zuwa tare da sake mata fuska tashigo ciki. Baya mun gaisa da itane take cewa dani kitso tazo in mata na ji dadin koba komai zandan sake yau a gidan a wurin ta nike jin wasu halaiyan shi da ban sani ba da farko take cewa amma ke ba yar uwar su hajiya bane. Nace may kika gani tace gani nayi dai bata kaunar ki koda yake hajiya ai da kowa zata kwasa indan ya taba mata dan lelenta. Murmushi nayi mata kawai tace tana masifan son shi cikin yaran ta gashi dai yana aiki kuma yana samu amma bata jin kyashin kashe mai kudi. Nace aidon su take nema ko tace wallahi yana da hanyan samu sosai amma yan matan shi basu bari ko wanan gidan da mota da ya saya sai da dabara ya saye su. Na dauka da yai aure zai daina amma da yake dan duniya sai abin da yai gaba ga abinda yake yi. Nan nake ji wai ai da dawata yake zaune a gidan sai da hajiyan tayi da kyat ta raba su da kamar sun rabu yanzu kuma sun dawo sun dinke wuri guda da ita. Nan tashiga bani hiran abokiyar shashan shi din da irin rayuwan da sukayi a baya dama wanda suke yi yanzu din har nagama mata kitsa tana min hiran shi ne. Mun gama ta ciro kudi ta bani ban karba nace ta barshi sai idan ta sake dawowa tace a, a karba wallahi idan kika soma da haka zakita aikin banzane wa mutane nan garin neman kudine ba a wasa da neman kudi. Naimata godiya taimin alkwarin zata sake dawo idan an kwana biyu na rakata ta tafi sai da ta wuce na duba kudin nayi mamaki don har dubu daya tabani. Ina ta murna na shiga daki naje hadawa da wanda na boye sai naga ashe dubu uku na bashi na boye bakwai. Yanzu ga shi taban daya sun tashi takwas taban shawara na sayo kayan yin kitso don akwai wa yanda zata turo min. Tun ranan da tazo kamar ta buda min hanyane na yin kitson na dinga samun customers mssu zuwa ganin haka ina yi a boye sai na sheda mashi don karya zo ya sani ya hauni da jidali. Baice komai ba sai ke kika sani kardai ki bata min gidana kan wani kitso naki na banza can. Don haka idan sun zo muke fita ta waje muyi kitson basai mace ta shigo gidana ba mun bata mai gida. Wata rana wata mace tazo da diyan ta sai suna neman ruwa sai da aka tafi wani gu aka sayo mata sai take ban shawara na dinga saida abin sanyi mana. Wanan shawaran yai min dadi sosai tun wanan ranan na fara sayar da ruwa sai nai shawaran ko na dinga zobo sai inayi dashi da wasu yan kakanan drinks ina sayar wa. Aiko sai abin ya karbe ni matan hausawa harda kumshi nake masu mai zane take sunana ya fara dagawa. Hankalina ya dan fara kwantawa koba komai dai ina samun abokan hira har ina dariya sai dai in sun tafi na koma dip. Wata rana na gama kitso na gyara gida na dora girki gap da zan gama na shiga wanka koda nafito abinci yayi na kwashe. Ina zaune a falo ina cin abinci sai gashi ya shigo ina gaida shi da dawowa ya amsa ciki ciki ya wuce dakin shi. Ya fito ya zauna kenan wayan shi yai kara ya dauka zaune nake a takure a falon ina gudun in daga yace min munafuka. Sai na dake na zauna a takure a yadda na fahinci wayan da yake da mace yake magana amma ko yaji darr dan ina zaune a wurin. Daji lalashinta yake yi don a yadda suke magana hakkuri yake bata ita kuma sai masifa take mai a wayan. Zuwa can ya mike zai fita sai na sasauta murya na nake cewa kayan miya sun kare a gidan na gobe ya rage kawai da zanyi. Ya juyo a wullakance ya dube ni yana cewa ina kudin da kike samu a wurin kitson naki ki fitar ki saya mana. Ya fice ya barni ina mai binshi da kallon mamaki don tunda kayan da nazo gidan na sama ya kare idan nai mashi magana sai ya hauni da fada. Gashi kuma ance kudi yake samu sosai a wurin aikin shi amma baya nuna yana dashi sai yaga dama yayi. Nidai na fahinci anyi sallah na mike zuwa yin sallah nabar falon ban fito ba ina shirin kwaciya ne naji dawo wan shi gidan. Na dan tsaya inga da may ya dawo min a cikin mayen ne ko a birkice naji shigowan shi na mike na fito falon inda yake sai naga yana shigowa yana dariya. A zatona waya yake yi sai naga ashe ba waya bane yana magana ne da wata da suka shigo gidan tare. Yana dago kai ya ganin ya hade fuska tare da cewa a fusace ke kuma may kikeyi anan baki kwanta ba ? Yarinyar da suka shigo da ita gidan tana wani taunan chewgun kas kas tana harare hararen ko ina na gidan. Naji tace wanan ne dama matar taka ashe karamar yarinyace haka no warder kake gudun mutane yanzu Ta kalle ni sama da kasa sai tace dashi muje don Allah karma ta kwanta mana ita ta sani tai gaba ya juya ya bita a baya. Suka barni tsaye a wurin imani ya kashe ni may yake nufi kenan karuwa ya dauko min a gidan ko may ? Jin sun rufo kofan daki ne nadan zabura na dawo cikin hankalina dakyat naja kafana na koma daki. Tunane nakeyi wanan wani irin bariki ne haka karuwa har cikin gidan tazo ta wuce ni ta shige daki ita da mijina ina tsaye. Da kyat naga safe don banyi barcin kirkiba a gidan da safe ban fitoba don haka ban dora girki ba a gida ko gyaran gida ban fito nayi ba. Sai zuwa can ya kwala min kira daga falo saida ya kirani sau uku na amsa mai na fito falon ina saye da hijjab dina har kasa. Ya kalle ni a wullakance yace dani ina abin karyawan mu banga kin aje min ba nace a sanyaye banyi ba. What ya fadi da karfi nace banyi na sake fada mai saboda may zaki ce baki dafa min abinda zanci ba. Cikin dakewa nace ita wanda ta kwana gidan bata dafa maka bane koba mace bace da baza ta dafa ma ba. Ban san ya iso inda nake tsaye ba sai ji nayi ya buge min baki kub da nashi basan lokacin da na dafe wurin ba. Ya daga hannu zai kara kai min wani marin sai ga ta ta fito daure da tawul a jikin ta iya cinya tace a, a marta koma ta dafa ba iya ci zanyi ba wanan kazaman yarinyar ba zan iya cin girkin ta ba. Ta jashi zuwa cikin daki tana wani kariraya tana kwanta mai ajiki suka rufe kofa dakin garam ina wurin a tsaye. Na sauke ajiyan zuciya a raina nace lalle yau na ga iyakar barikin da nake ji ana fada anayi a lagos na ganshi a wurin wanan bawa shine giya shine taba gashi kuma ya buga ga dauko karuwa kwana a gidan mu na sunna. Ina jin sun gama watse war su suka fice a gidan da ihuce ihucen su da tafawa a tsakanin su. Nace shashu banza kawai a haka zaka kare ba aga farar ka a gida ba sai gun matan bazan za suna fita sai ga yaya saadu ya shigo gida. Natare shi da mutunci muka gaisa dashi yake tambaya na yaya gidan na amsa mai da lafiya kalau. Sai yake tambaya na yanzu abubuwa sun yi sauki a tsakanin mu ko sai nai murmushi kawai nake cewa dashi babu komai yaya. Ya ce a, a Safiya kada ki biye min komai ni dan uwanki ne nasan kuma halin mijin ki sarai da rashin mutunci do haka in baki fada min ba wa zaki fadawa. Sai idanuwa na suka ciko da hawaye a lokaci guda nace yaya komai na nan a yadda ka san shi saima abinda ya karu. Yau ma da wata mace suka kwana gidan a gaban ta yai min rashin mutunci don naki dafa masu abin karyawa. Hakkuri ya bani ya dade yana mun na siha ina ta fada mai irin matsalolin da muke samu dashi a gidan. Yana bani hakkuri tare da fadin sai na hada dayi mashi addua don addua baibar komai ba in kuma yi kokari in kawar da idona ga abin da yake yin don ko na ce zan fada wa iyayyen mu ba yarda zasuyi da ni ba. Da zai tafi yakawo kudi ya bani yana cewa na rika in dinga sayen abinda zanci basai na tambaye shiba kar yaita duka na a banza. Nace mai akwai kudi wanda na tara do yanzu kitso nake ina samun kudi yace tona kara kawai dasu. Yai min alkawarin zai saya min fridge don sana,an zobon da nakeyi ya bunkasa sosai naji dadi ina ta zuba mai godiya mukai sallama ya wace. Da ya tafi na kirga kudin sai naga har sha biyar ne cif din su banyi sanyi a kafa ba na shirya na shiga yar kasuwar uguwar mu na sai kayan amfani na dasu da abinda zan dan rika ci da rana. Ashe da yabar gidan gidan su ya koma wurin mahaifiyar su ya ke fada mata duk irin abubuwan da dan uwan nashi yake min. Sai ko ta hau fada da cewa dama tsiyan dan tallaka keman bai iya samun wuri ba ta tsamoni cikin wahala tasani ga rigan mutunci ina bidan in tona masu asiri. Da nake cewa yana sha, shan ya hana ya kyautata min ne duka kuma in banyi mashi laifi ba ai ba zai duke ni ba , a gidan mu wani irin wahala ne bana sha nazo nan a saka ni cikin rigar mutunci shi zai ma danta sheri. Yace mummy yarinya ga fa diyan dan uwanki ne halal malan aka dauka aka baki badon taso ba ko uwar ta taso ai kama yayi ki tsawata mashi yadaina shigo mata da maye da matan banza baki goyi bayan shi ba haka. In tana ahan wuya a gidan su nan ai aurene ya kawo ta kamata yayi ta samu sayin rawa ta huta ba wahala irin haka ba. Tace to ubana dama ai ka saba min fada sai kayi ita kuma ta zuba ruwa a kasa tasha tunda ta hada ni da diyana fada. Sadiya dake gefe tana saurare tace mummy ai gaskiya yaya ya fada gaskiya abinda yayan ke wa Safiya baya kyautawa idan mu akaiwa haka bafa zaki ji dadi ba. Harara ta watsawa Sadiya din tana cewa ai duk kuna da bakuson dan uwan ku da alheri daga yarinya taimai kake kun dauka kun haye ke nan kun yarda da abinda ta fada. Saadun yace mainene daga ciki kake wanda ba halinsa ba cikin abinda ta fada din ina duk halin da ta fada kin sani yana yin su sarai. Nan dai yaran suka barta tana ta fada tana fadin ai zata je gidan zamu hadu gobe bazan kara fadawa wani sirin mijina ba. ZAINAB IDRIS MAKAWA SEENABU 8/14/20, 7:11 PM - Ummi Tandama: BAHAGGON , , , , , 🧕🏿🧕🏿1️⃣1️⃣ INA MAI BAKU HAKKURIN RASHIN JINA KWANA BIYU WUTAN MU YA LALACE YAR UWA IDAN KIN FITAR MIN DA NOVEL DON KAN KI KE KI SANI DON KIN SAN DAI HAKKIN WASU NE. Ina duke ina wanki bansan hawa ban san sauka ba sai jin bugu nayi daga baya na sai da na kife a jikin roban da nake wanki din. Bai hakkura ba ganin na fadi kasa ya kara kai min duka bazan iya kare kaina ba na fadi kasa gaba daya yana ta duka da zagi. Sai da ya gaji don kanshi ya barni nayi ligis a kasa yashe ban ko motsi ruwan da nake wanki duk ya zube min a jiki na yana huce yake fadin. Baki ga komai ba idan kin ce magana zaki dinga dauka kina kaiwa gidan mu shi wanda kika fadawa yazo yai maki maganin abin na gani mana. Mata yanzu ma na fara shigowa dasu gidan nan gidan ubanki ne ko gidana da zaki kafa min doka akai. Yar iska jiki matan da nake bi din basu fi min ke ba, ke har mace ce may za a samu a gare ki banda wahala. Har ya shige ciki ya fito yace ban ga daman kawo abinci ba ki aika wa uban ki mai dakunanen hula ya kawo maki in ya mayar dake wata tsiya. Yar iska nida gidana har kina sin kafa min doka nakawo mace ki hanani naji dadin da nake so idan kin isa. Nikan zafin bugu sai wani gumzi nake yi kamar raina zai fita ya shige na dade wurin ko kafana bana iya dagawa a lokacin. Da kyat naja kafa na shiga dakina ko ina sai ciwo yake min don zafi da cowo kuka nake ina tunanen rashin imani irin na yaya Ahmed. Bai kara bi ta kaina ba sai shaye shayen shi yake a cikin falo ina jin shi warin giya da taba har dakin da nake ciki. Sai dare naji yana rufe gida ya fita da kyat na ja kafana zuwa falo nan na samu yai baja baja da kayan da yai shaye shayen wurin. Kitchen na nufa na dan hada ruwan liptop na don a lokacin shi kadai nake iya saqa cikina ga wani irin zazzabi ya na neman rufe ni. Ranan tunane kala kala nayi gadai kudi a jiki ina son gudu in koma gida don dai na san motan zuwa arewa bai gagara na zuwa. Amma kuma nasihan Ummi yana min yawo a raina da tace dani yar nan komai wuya komai dadi ki natsa kafan ki a dakin ki wuya baya kashin bawa. To amma kuma a haka ake son na zauna cikin wanan irin ukuban babu dadin rai ko yaushe sai fitina kamar ankawo mai jaka. Nidai tun zuwa na gida ba zan ce ga rana daya wanda naji dadin zama da shi ba daga ni har shi zamane na dole muke yi da junan mu. Washe gari abin yafi na gare ne duk fuskana ya kumbure ga hannu da kafa ban iya daga wa ko kadan don ciwo. Ina cikin wanan halin amma ya saka kida yana tashi ina jin sautin na shiga min har cikin rai na ba halin in magan ta. Ganin da yayi kayan wankin da na jika ya kwana ya wuni yasa shi shigowa dakina a fusace yana cewa ke don ubanki kayan nan da kika jika suna wa mutane wari baki kwashe su wurin nan ne. Sai ya samay ni cikin wani hali banko san ya shigo dakin ba lokacin tsayawa yayi a kaina yana kare min kallo sai kuma ya juya ya fita. Ko ina nawa ya hakke ya kumbura dan bugu da ciwa gashi ba mataimaki yan kitso na sai zuwa suke suna tafiya. Wata boyar Allah da nake kira mama biyu don tana da tagwaye tana kawo su kitso wuri na tai karfin halin fadowa har cikin daki na. Sai da ta dan yi ihu don ganin halin da nake ciki tace dani amarya waya maki haka ko hatsari kika yine wai. Na bude idona da kyat ina kallonta dishi dishi nace buguna yayi tace amma mijin nan naki baida imani ita na samu ta taimaka min har na da wanka . Ta dan sayo min abinda zanci da dan magani na sha tai ta jamashi Allah ya isa yafi a kirga ta shirin tafiya ne sai ga yaya saadu ya shigo gidan yace yazo ya sallamay ni nao zai tafi. Hankali yace bai kwanta ba ga yadda ya barni ranan sai kuma yazo ya tarar da abinda ya faru dani. Matar take kara yi mashi bayanin halin da ta samay ciki aikuwa bai tsaya ba ya juya zuwa gidan su kai tsaye wurin mahaifiyar su. Ya je ya sameta yake fada mata irin taasan da yayan nashi yai min maimakon tai fada sai cewa tayi fada kota tausaya mashi sai ta fara fada dani tana cewa. Ai maganin ta kenan yarinya bata da kunya sam ga sa ido ga abin da bai shafe ta, gunma da yai mata dukan tsiya goma bata karawa ai. Ya ce mummy na fada maki yarinyan nan tana cekin wani halin a yanzu idan ba zaki dauki mataki ba ni zan dauka don wallahi zanyi karashin gurin yan sanda akan zai kashe yarinyar mutane. Da sauri tace dashi dan uwan naka zakai kara har kana fadi da bakin ka akan wata Safiyan ce ? Yace ita din ba yar uwar mu bace mummy da zaki ce hakan wa take dashi a garin nan bayan mu ka wata sani in bamu ba. Waya ta jawo ta kira wayan Ahmed din ya amsa mata a kadarance da cewa mummy aiki nake yi fa banson kira yanzu. Tace kazo ga Saadu nan ya zo ya tayar min da hankali akan makiran yarinyar nan safiya wai ka mata duka har ta kwanta kuma baka kaita asibiti ba. A cikin fada ya na daga sautin muryan shi yace wai ina ruwan shi da matana ne wai May yasa yake son shiga harkan gidana ne matar shi ko mata na don haka babu ruwan shi ko kashe ta nayi. Yana tsaye yana huci ya ansa a fusace da haka kace to wallahi jira kaga matakin da zan dauka a kanka ai akwai hukuma a kasan ko sai ya fita a fusace uwar na kwala mashi kira amma bai dawo ba. Mike tayi a firgice tana fada tana shiryawa tabi bayan shi tare da kiran habiba ta raka ta. Ina kwance bayan na samu taimakon daga maman biyu tadan bani dan ruwan tea na sha nakoma na kwanta sai dai hannu na ba dama na daga da kafa. Tana tsaye a kaina suka shigo gidan tun daga kofa take kwala min kira a gigice tana cewa fito muna fukar banza da wufi kawai ganin ban fito ba yasa suka nufi hanyan dakin. Sai sukai kocibis da maman biyu a kofan dakin kallon kallon sukai wa juna sai gwago din tai karfin halin fadin ina ita Safiyan take ne. Dan jan jikinta tayi a kofan shiga dakin sai suka samu wurin shiga dakin a kwance suka samay ni sharkaf jiki ba dadi gaba daya na sundule saboda bugu. Sai ta sasauta fadan da takeyi ta fara cewa uhmm uhmmm aishe abin yayi muni ne haka ban sani ba. Maman biyu da bata san ko su waye suba sai tace wanan tsinanen mijin nata mara mutunci da tarbiya an baka diya amana don rashin mutunci kai mata wanan dukan kamar zaka kashe ta. Sai habiba tadan juyo tace mata ai mijin ta ne sai dai itama tabar mai shigan tsagal ga alamarin shi. Matar tace haba yar uwa ko ke ce ai ba zaki dauki hakan ba mace banza har cikin gidan ki don rashin tarbiya da tsoron Allah. Tana kokarin cewa na tashi na zauna ta gani sai maman biyun tace ina ga kamar fa ta gwauce ne ko tayi tarmashe. Don bata iya daga wa sai an kamata maman biyu din ke magana cikin tsigar tausaya wa. Sai gwagon take cewa na daga ta gani mana. Habiba tace in ko don taji ana karawa abin gishiri bazata daga ba yanzu. Aiko maman biyu tai kanta da sabon fitina tana cewa amma dai ke baki da tausayi idan da yar uwar ki ce aikaiwa haka abinda zaki fada ke nan. Wanan ai rashin tausayawa ne ke fa mace ce kin san zafin wanan abin mutum kobaida tausayi dole ya tausaya mata. Ta neme fada mata maganan banza tace kama kanki kin kuwa san ko ni wace ce yan zan saka dake da mijin nata a kulle min ku baki daya don kashin kai ya so yi anan. Sai da taga da gaske maman biyu keyi kuma ta kalleta taga ba raini a jikin ta da gani watace ko matar wani a garin hakan yasa taja bakin ta tai shiru, gwago sai fadi take . Kaddarane ai ya kawo hakan fada tsakanin mata da miji ba a shiga sai mutun yayi kunya idan ya shiga. Maman biyu tace amma dai irin wannan abin dole a tausaya wa mutum bari ai ya dawo zan tsawa ta mashi. Tace yanzu a taimaka akaita asibiti kada yarinyar mutane ta halaka ga banza don shi na mijin kawai na ta yaya kai kaiwa yarinya sanadin haka. Amma kana ganin ta cikin wani hali ace koda dan paracitamal wanan bazaka iya saya mata ba don tsaban iskanci wallahi ni sai nasaka a adana mun shi bawani abu bane. Gwago tace a dai yi hakkuri a dan sawo mata dan magani tasha ko zata samu sauki. Tace What da karfi wanan case din fa ba avin a zauna da ita gida bane. Sai ga yaya Saadu ya shigo yana fadin a fito da ita mu tafi asibiti fa mota nan na samo a waje gwago tace har asibiti za aika bari a bata magani kawai. Don kar aje suce sai an kira mijin nata maganan ta zama babban case kuma . Yace ya zama mana waje ya zama don may zai duketa kuma ya kawo ido yana kallon ta haka kwance a gida. Maman biyu dake tsaye a kaina tace asibiti kan sai an kaita don wanan bana zama gida bane mutafi tare zan san abinda na fada masu. An kama ni an fito waje sai maman biyu taga motar hayace suke nufin a shiga tace dasu sallami mai motar ga motar na nan mutafi. Da motar ta muka tafi ta kaimu wani asibiti na kudi da farko sunce idan duka ne sai anzo da yan sanda sai maman biyu ta dauko id card din ta ta nuna masu sai suka yarda zasu dubani. Nan aka dubani ni ansamu nayi tarmashe da kuma raune a hakarkarina suka ce dole sai sun bani gado. Duk maganin da aka rubuta da awo da sauran su itace ta bayar da komai aka bani gado a wani daki ni kadai a ciki. Nan yaya saadu ya daga wayan shi ya kirashi yake sheda mai yazo an bani gado a asibiti ya fada mai sunan wurin. Nan ya iso yana mazurai da ido yana kamay kamay sai fadi yake waya kawota asibiti nan na kudi kun san dai bazan kashe kudina ga wanan mara mutuncin ba ga banza. Maman biyu da take gefe tana kokarin hada min maganin da aka bani insha tun shigowan shi take hararan shi. Ta dago kai ta harare shi tace amma dai kai ka kai mara mutuncin gaske wallahi ma jin dadin naka yayi yawa da har zaka kashe yar mutane so ba a hukunta ka ba zaka zo kana muna maganan banza a nan. Ya bita da kallon kallamin ta zuwa gare shi daidai lokacin da take dago ni daga kwance tana bani magani, Sai faman murde murde nake yi saboda zafin da ciwo da nake ji a jikina ya tsura min ido yana kallon yadda na koma ga ciwo a fuka da hannu duk na goge wurin bugu. Likita ma ya shigo yana dudubani sai da ya dan bata lokacin shi sosai a kaina ga dan karen tambayoyi da suke min duk yabi ya tsargu sai dai na boye wanda yai min haka don cewa nayi a duhu ne ban san su ba. Nan nadama yazo mashi gwago ce taja shi zuwa waje ta fara yi mai fada akan ya rage wanan zafin rai don kar yaje ya kashe yar mutane yajawo masu magana. Idan ma tai maka laifi ne ai basai kai mata mugun duka ba haka har yakai taji rauni maganar yaya Saadu ne suka ji a bayan su yana fadin. Amma mummy bai kamata ki na haka ba fada ya kamata ki masa kin san fa girman abinda yayi badon wanan matar yau ba abinda zai hana ba adaure shi ba. Idan ba a daure ni ba sai kai kaje kasa a daure ni mana wai may ye dalilin ka na min shishigi a gidana irin haka matar ka ce ko mata na. Yaya Saadu yace kauna tace kaga ashe ina da right din da zanga ana cutan ta in saka baki na akai. Ya zaburo mai shima ya zabura mashi kamar zasu buga gwago taga suna batun tara mata mutane sai ga maman biyu ta fito tace wanan wani rashin mutunci ne haka. Wallahi in bakai hankali ba sai na sa an daure mun kai yau don baka da tausayi mutumin da ya cece matar ka har zaka zo kana son mai rashi mutunci. Ta harare shi ta wuce zuwa wurin motar ta sai da ta dan gwauta ya juya yake tambayan su wacece wanan matar ne. Gwago tace a tare muka samay ta da Safiya a gidan ku ya bita da kallon mamaki har ta dauko abinda zata dauka ta koma ciki koda ta dawo ta sallamay ni nayi barci. Don haka tafito tana gyara gyalen dake jikin ta tana cewa waye zai zauna da ita a nan don ni zan tafi gida sai suka fara gardama tsakanin gwago da Habiba din. Taja tsaki ta wuce tana mai jin haushi da Allah waddai da rayuwan su gasunan da ganin su marasa tarbiya dasu kawai ta dan tsaya tana cewa gwago kizo na maidake gida ita yarinyar sai ta zauna. Ya zama dole subi umurnin ta don sun hango ita din wata ce shiyasa suke kyale ta suna binta a sannu. A hanya su da gwago take dan binciken ta tana jin wani abu a gamay dani sai take lurar da gwago din nauyin amanan dake kanta na tare da fada mata cewa idan ya kara min irin dukan nan zata sa a daure mata shi. Gwago ta tsora ta tace insha Allahu ba za a sake ba wanan ma akasi aka samu ayi hakkuri dai zata sauka takawo kudi taba ta tana ta godiya. Yaya Saadu yace zai tafi wani wuri ya dawo sai ya bar yaya Ahmed da habiba zata fara mashi tsegumi ya katse ta da cewa ke raba ni dan Allah da anyi an ce. Sai taja bakin ta tai shiru ta tsargu ta koma gefe daya ta rakube wuri daya tana harare harare wa mutanen dake sintiri a haraban asibitin. Ya fita ya dawo dauke da leda da lemo da ayaba a ciki ya nufo dakin ya shigo ya samu na farka. Ina zaune ina dan matsa kafana a hankali don haka likita yace dani nayi sai gashi ya shigo dakin babu kunya babu alamunta ya samu wuri ya aje ledan dake a hannun shi. Yazo ya zauna a kusa dani ga mamakina sai naga ya fara wade ayaba a hankali ya miko min sai na girza kaina alaman a a yace likita yace abaki abin gina jiki saboda haka kici wanan nan. Yayi niyar wai bani har a baki don yaudara sai na ki karba sai dai ya wade min na karba nakai a baki da kyat. Naci kamar kwaya uku da kyat don bakina bai da dadi nace ya ishe ni sai ya mayar da ledan ya aje gefe daya ina zaune na langabe kaina a karfen gadon da nake kwance. Sai naji ya kamo hannun da yafi mun ciwo na dan matsawa a hankali sai da nai kara, yana fadin ai sannu zai warke ya bar ciwo da yake na zugi. Ban kai ga bashi amsa ba sai ga matar da nake cewa maman biyu mutumiyar kirki ta dawo niki niki da su flask da ledoji da wata yar budurwa bayan ta. Suka samu wuri gefen gado na suna aje kayan da suka shigo dashi din tana cewa a she kin falka sannu yaya jikin ina sauri karki falka babu abinda zaki ci anan. Yana zaune ya dukar da kanshi kamar maijin nauyi da kunyan ta sai can tace wanan ne mijin naki ko sai lokacin ya dago yake cewa da ita sannu da zuwa. Yana kokarin mikewa tsaye ya fita tace dashi No zauna abinka ai tafiya zanyi don ba dadewa zanyi ba dama wanan kayan na kawo sai yarinya da zata dan zauna da ita don naga kaunar bata son zama da ita. Ya dai mike yana cewa zan dan tafi nan bakin get ne na sayo abu sai ya fice tabishi da harara tana cewa mara mutunci kawai sai ta ja tsuki nasan haushin sa take ji har cikin ranta. Tace wa yarinya Nafisa dan zauna anan bakin gadon barin zuba mata abincin nan kadan ta danci. A sanyaye nace nakoshi maman biyu tace da sauri may kika ci da kyat na bude baki nace ayaba naci sai ta kalli wurin ledan ayaban da ya aje tace ina wanan bawan da nagani shi kika ci. Na kada mata kai alaman eh, Sai take cewa idan kika biyewa wanan mijin naki mara mutunci kina tunane sai ranki yai ta baci ga banza. Nan ta zuba min ta jawo kujera a gabana ta zauna ta debo min zanyi gardama tai min jan ido dole na karba. Ina ci ta jefo min tabaya akan auren mu ina bata amsa a hankali har na dan ci abincin kamar spoon biyar zata karo nace na koshi. Bata ce dani uffan ba ta aje plate din tare da mikewa tana gyara gyalen kan ta tana cewa barin koma yara suna gida na barsu. Sallama tai muna ina mata godiya ina share hawayen dake zuba a idanuwa don tun tana tambaya nake kuka. Ta fice tare da jawa yarinyan kuna akan ta kula sosai idan da matsala ta kirata a waya. Tai muna sai da safe ta fice daga dakin na dade ina kuka bayan fitan ta dakin. ZAINAB IDRIS MAKAWA SEENABU 8/14/20, 7:11 PM - Ummi Tandama: BAHAGGON , , , , , , , , , , 🧕🏿1️⃣2️⃣🧕🏿 INA MAI GODIYA GARE KU YAN UWA NA GODE DA KAUNAR KU A GARENI ALLAH YABA HAKKURIN ZAMA DA JUNA NAGODE. YAR UWA NOVEL DAI NA KUDI NE BA YARDA KI KARANTA BA INDAN BAKI BIYA BA DON BA A YAFE BA, , , , Tsaye yake ya jingina jikin shi da motan shi yana busa cigari sai busar da hayaki yake sama da alaman tunane yake yi a lokacin. Har ta tako zuwa inda yake tsaye yana shagalin shi bai farga da zuwan ta ba sai da tai magana ya dawo cikin hankalin sa. Tace dashi wanan abinda kake yi ba dabian diyan hausawa bane komai na ba haushe ansa shi ne a cikin kawaici da alkunya. Murmushi yayi ya jefar da taban dake hannun shi kasa yana takewa a cikin kasa. Yace hajiya har kin fito kenan tace eh dama na kawo abinci ne da yarinya da zata zauna min da ita don na lura yan uwan nata basu san zama anan gashi tana bukatan mai taimaka mata wani fannin. Angode yace da ita har ta juya zata fara tafiya sai kuma ta juyu tace dashi a gaskiya wanan dukan yayi muni kwarai da an kai ka ga hukuma ba abin da zai hana su kulle ka wurin su . Ya kamata ace ka godewa Allah da yabaka mace irin wanan yarinyar dan babu macen da zaka doka a yanzu irin wanan batai karan ka ba. Yace sherin shedan ne akasi akasamu haka bazai sake faruwa ba in Allah ya yarda. Taima shi sallama ta yafi bayan ta bashi dan shawarwarin da ya dace na zaman takewa a tsakanin zama ta tafi sai sauke ajiyan zuciya yayi kawai koba komai dai ta rufa mai asiri. Don irin wanan wayyayun mata ba a shansu a banza amma ita gashi ta rufa mai asiri. Sai wani tunane yazo mashi a rai a ina safiya tasan wanan mace ne haka da har take mata irin wanan taimakon dole ya sani don gaba. Sai da na kwashe kwaki sati a sibitin san nan suka sallamay ni kudi dai ya sha kashi sosai na dawo gida har lokacin dari dari nake dashi don nasan mai hali baya fasa halin shi. Zaune muke a falon da Maman biyu ta wade min lemon da zan sha sai ta tambaya labarin auren mu dashi Ban boye mata komai daga ciki ba na labarta mata sai tace barin fada maki idan sun tambaye ki ko yaya nake dake ki fada masu cewa ni yar uwan mahaifiyan ki ce tun a gida akace ki nemay ni idan kinzo nan don zan kula da almarinki kamar yar uwata ta jini kike a guri na don muna garin da dan uwa ke bukatan taimako juna. Tace idan Allah ya hada ki zama da miji dan iska sai hakkuri don gaskiya mijin nan naki yayi nisa da harkan bariki duk na miji da zai iya dauko macen banza zuwa gidan shi tantiri ne. Don gaskiya sai kin kwantar da hankalinki sosai kin bi halin shi a sannu ki guji duk wani abinda kika san zai jawo maku matsala a tsaka don shi zai iya yi bai zama komai ba amma idan ke kin yi zai iya komawa fitina. Ki bishi sau da kafa ki guji saka ma alamarisa ido koda yaushe kina jina ko sai na gyada mata kai alaman eh. Nace cikin murya mai rauni tare da hade miyau bakin cikina a wuyana nace ina iya kokarina don ganin na kyautata mashi. Amma da yake shi wani irin mutum ne mai hali na daban duk abinda nayi baya gode min. Sannan abun bakin ciki shine yadda yan uwanshi suka tsane ni sun sani a gaba kamar ba yar uwan su nake ba sam babu kauna a tsakani na da su . Sanan shi ya kasa fahintar makircinsu na san ba wani abu yasa suke min haka ba sai don sun dauki iyayyena tallaka ni ban kai sa,an auren shi ba ga rayuwan da suke yi a nan don ya banbanta da namu. Ta katse ni da cewa duk ki manta da wanan yanzu ki kama Allah Allah yana tare da mai hakkuri ko yaushe. Za a zo ya wayi gari ya gane gaskiya ya daina su kuma zai fahinci kutungwila da suke shirya wa a kanki. Nace mhm anty kenan sai dai don kin ce Allah ya fasan gaskiya wani abin da biyu yake min shi don kawai ya kuntata ma rayuwa na. Tunda dagani har iyayyena babu wanda yake shakkan zagi yadda rashi yaso idan yana jin tsiyan mutumin da kullun a buge yake in baisha da safe ba da dare zai sha. Amma nai hakkuri da hakan ina zaune shi don bin maganan iyayye in yai amai na kwashe anty in yasha giya anan inda kike zaune zai bar kofi ko kwalban in dauke. Haka zai shigo cikin mayen shi yai ta surfa min a shar ya danne ni da karfin tsiya yayi abinda yake so dani na karasa fadi cikin kuka. Maman biyu tai tagumi tana saurare na cikin jimamay abinda nake fadi ina kuka. Zuwa can ta nisa tace sai hakkuri Safiya don zaman aure a yanzu hakana ya kunsa ko wani gida da tasu lalurar idan kuma kin ga zaman wasu sai ki daga hannu kiwa Allah godiya ke. Nace a hakan maman biyu har akwai macen da tafini wahalan aure a duniyan nan tace naki kika sani safiya Allah daiya kyauta zamanin nan. Nace ni maganan mahaifina da yace idan na neme saki a gunshi da bakina bai yafa ma haihuwan da yai min ba. Tace to kin gani ko sai hakkuri karki gaji da hakkuri kuma ki rike ibadan ki kina yin adduoin da hannun ki bibiyu bada wasa ba. Ina kuka ina mata godiya tace zata tafi amma zata dawo kwana biyu ta duba ni in Allah ya yarda. Nai mata godiya ta tafi ta barni ni kadai a cikin damuwa da tunanen rayuwa mai kunci da nake ci a gidan. ********* ********* ********* Na mike na shiga daki dakin duk yayi kura na rashin mutum a cikin sa duk da jikuna da dan sauran tsami amma haka na daure na gyara shi har zuwa falon gidan da duk yai kura nasan ko sau daya bai taba gyarawa da ban nan. Sai zuwa marance na gama har da girki da na dora na shiga nai wanka na fito na gyara jiki na sai yamma lis ya dawo gidan daidai lokacin da nake fitowa cikin daki ya shigo. Cike da girmamawa irin na macen da tasan darajan wanda take aure na gaida shi da dawowa bai takan ni ba sai umhum din da yace dani. Nan ya zauna saman kujera yana debe takalman kafan shi da safa sai na je fridge na dauko mashi ruwan sha ban kai ga kawowa ba ya dakatar dani fuska daure yace ni bance maki ina bukatan ruwa ba. Da sauri na kalli idanuwan shi kamar zanyi magana amma kuma sai na juyana mayar da ruwan ida na dauko da farko. Ya na cire takalman ya shige dakin shi baiyi magana ba nidai ina tsaye daga kofan kitchen na bishi da kallo kawai. Abinci na dauko na jera mai saman dan taburin cin abincin dake falon na juya na shige ciki abina tare da turo kofan dakin. Can bayan kamar awa daya naji yana turo kofan dakina ya shigo yace ke nazo in maki kashedine akan fada wa Saadu sirin gidana da kike yi. Ban taba zaton munafuncin da mummy ke fadin uwarki nadashi ya shafe ki haka ba sai yanzu. Da sauri na dago kai don jin abinda ya fada gamay da ummina ina kallon shi cikin mamaki. Nace ita gwago tace ummina muna fukane ita yaya akayi ta sani ko ta taba yi mata munafuncin ne . Yace karya mummy zatai mata kike nufi komay ? Nace wai may yasa iyayyena basu da daraja a idon ka baka jin nauyin fada min magana a gamay da su. Ya a cikin tsawa wanan ke ya shafa kin dai ji na fada maki in ba haka ba daga ke har saadun zaiyi karanku ina ce tare kuke kuna cin amana na. Da sauri na sake dago kai na kalle shi a cikin mamaki abinda ya fada na wai zai muna kazafi dani da yaya saadu akan muna tare . Ya ce eh muddin baki daina jawo mani shi a gida ba abinda zanyi maku kenan a gidan nan ya juya ya fara takawa sai kuma ya juya yana cewa uhmhum dama ina son in tanbaye ki Ina son insan wanan matar mai zuwa a inakika santa ne uta din wacece may ye alakarki da ita da take taimaka maki haka. Nai shiru ban bashi amsa ba saida ya sake maimaitawa na ce yar uwar ummi na ce ita a kano take acan tai auri wani babban sojja ita din kuma custom ce. Da sauri yace mayne ita din da nake gani custom ne ashe no warder take abu a gadaran ce don tasan abinda ta taka. Nidai ban tanka shi ba sai shirun da nayi kawai yai huce ya fice daga dakin na sauke ajiyan zuciya tare da fadin Allah ya sauwa ka. Kwana biyu ba wani fitina a gidan idan ma zaiyi shedan shi bai yi min a falo saidai ya shige daka cikin dakin shi ya dadaki giyan shi yayi talil ya lamay a wurin. Dan kwana biyu jani shakat a raina ga maman biyu tazo ta kawomin abinci na boye a dakina duk da shima ya sayo koma amma bata yarda tuban mazuru ba tace indai boye wanan. Na kwasa nakai dakina na boye tana shirin wacewa ne ya shigo gidan basu hadu ba tun ina aaibiti sai yau din nan suka sake haduwa dashi. Ya shigo yana ganin ta yadan sake fuskanshi suka gaisa sai a lokacin ya samu yi mata godiyan dawainiyar da tayi damu a asibiti. Ta katse shi da haba babu komai ai, adaiyi ta hakkuri koda yake nasan kana yi sai ka kara kasan safiya yarince karama bazaka hada hankalinta da naka ba. Ya dan sosa kai yace ba komai komai ya wuce ai na gode kwarai ta mike tana saka hannu a jakar ta kamar yanzu ne zata sallame ni tace ke kuma karbi wanan kyadan rike karki dami mijin ki da bani bani. Zai shige ciki tace ya tsaya shima ta debo ta bashi yana aaa amma ta matsa mashi ya karba na rakata har waje ta tafi na shigo ciki. A falo na samay shi tsaye yana jirana ina shigowa ya miko min hannu da cewa na kawo kudin nan da ta baki nan na dago da mamaki ina kallon shi. Ya sake fadar miko min su nan nace kuma idan kika kuskura kika fada mata cewa na karba sai na lalatsaki a gidan nan. Jiki na rawa na mika maisu ya shiga kirgawa yaga dubu biyar ne nashi kuma goma ya hada yace sha biyar kenan. Ya tura a aljihun ya shige dakin shi ya dade da shiga ina kitchen naji muryan shi yana cewa ni zan fita idan kinga nakai sha daya ki rufe gida bazan dawo ba a xan zan kwana. Nace dashi to kawai ya fita ya sha kananan kaya sai kamshi yake nace a raina yau an samu kudin sheke aya ke nan. Kamar yadda ya fada bai dawo gidan ba sai safe ko safen sai wuraren sha dayan rana shigo man har zuwa lokacin bai gama warwarewa ba daga mayen shi. Ya shigo ido yai mai ja sai zage zage yake zubawa ni dai ina daki ban fito ba har ya gama ya fada dakin shi ya bingire sai barci. Bashi ya falka ba sai karfe hudu na rana koshi yunwa ta tayar dashi ba ibada ba ko wani abu don daren jiyan da yake jin kudi a aljihun shi club yaje suka kwashi rawan su suka sha giya da matan banza su gama suka shiga sheda da matan a wurin. Ya fito ya samay ni zaune ina kallon wani film din magic ya samu wuri ya zauna fuska daure yake tanbayana abinci fa. Na dago nace dashi babu nama ya kare hakana na dafa abincin don shi baicin abinci ba abin miya a ciki. Har zaiyi magana sai yai shiru ya ja tsuki yana fadin zubamin hakana don yunwa nake ji haka na zubo mashi ya lashe daki ya koma ya kwanta. Babu batun cika ibada gare shi don ba zance yana cika sallah shi ba don ko da safe sai ta hantse mashi zai tashi haka kuma da rana ko yana zaune akai sallah baya tashi yayi sai jefi jefi yakan yi. Yau ma shirin fita yake a gidan sai naji sallaman yaya saad ya shigo har na taso da yar fara a ta zan tare shi sai na tuna kashedin da yai min a kansa. Haka na tare shi kadaran kadaham nai mashi sannu da zuwa yake cewa lalai kauna ta jiki yai dama ya zauna a saman kujera yana cewa ashe kana ciki a dadaure ya bashi amsa umhum. Shika yaya saadu ya share shi ya shiga tambaya na yana kuma min hiran tafiyan su har kasan togo suka tafi. Ganin ban saka ba kamar yadda ya sanni sai ya dan shiga tsarguwa a take ya fara tambayan make faruwa ne Safiya ki fada min ni yayanki ne fa. Na share kwalla dake fuskana nace dashi ba komai yaya saadu ya mayar da duban shi a kan dan uwanshi da ya mayar da hankalin shi ga abin da yake yi da waya shi yace . May ke faruwa ne bros. Sai yace ai gata nan ka tamabaye ta kaji abin da ya samay ta din ya matsa min da tambaya nace don Allah yaya Saadu ka bar zuwa don yaya yace zai kulla muna sheri ni dakai wai tare muke a gidan nan. Mikewa naga yaya saadu yayi yana huci yake fadin kaika dade baka kulla muna sheri ba. Ban san rashin mutuncin ka ya kai hakka ba sai yanzu don ta na yar uwa nace kaga ina kula mata inda wata ne can bare ka dauko ba abin da ya damay ni da ita. Wanan wani sallon yaudara ne ka dauko kaika dade bakai muna sheri ba cike da tsoro na ke magana a, a yaya na fada mane don kawai ka dauke kafan ka. Na sake cewa cike da tsoro na dan kalle shi nace na fada ma a gaban shi ne don ka san gaskiya nake fada don ka kiyaye. Ya dago jajayen idonuwan shi ya ce dani indan baibar shiga maganan ki dani ba a gidan nan zan iya mashi komai tunda bai da mutunci. Bai kai aya ga maganan shiba saiko yaya saadun ya taso mashi kamar zai dake shi da kyat na samu suka hankura ya fice gidan a fusace. Ranan nasha duka sosai a wurin shi sai dai bai yarda ya kaini kwance ba amma na zagu a gurin shi . Ban damu ba don zargi da sherin da yake son muna da yaya saadu shine abin da ya tsaya min raina tun lokacin da ya fadi hakan. Amma yau sai naji na samu sukuni akan wanan maganan na gyagije naci gaba da har kokina kamar kullan. Na koma yin kitso idan yakawo in dafa muna kowa ya ci indan bai kawo ba kuma na dan jawo kayan abincin da maman biyu ta kawo min na hada wani abu na ci. Wani lokaci haka zai dawo gidan da abin amfanin gida duk ranan da naga ya shigo haka nan nasan yar arzikin na a kai. Zai zauna baisha min taba a falo ko giya ba sai dai yai ta yawan waya da matan banza ranan kuma duk matar da tazo kitsu ranan sai dai ta koma bakitso don bai bari nayi . Yakan zauna ranan mace nake yakan wuni darza na sai ya gaji ya kyaleni don kan shi indan yai haka yakan dade bai neme ni ba kuma sai lakacin da yai mashi dadi a rashi zai kara kusanta ta. Ranan da naje gaida gwago dakuka na dawo gidan mu don tun case din da na fada ma yaya saadu abinda ya fada ashe sun je can gabanta suyi kaca kaca da juna su a gaban ta. Tun wanan lokacin taka nema na ta fada min kada inyi sanadin raba kan diyan ta da munafunci na dana iya a tare na gansu kuma tare zan barsu. Idan na kara hada diyanta fada sai daukeni ta mayar dani gidan matsiyacin ubana naje can mu karata can dasu. Zagi ta ida take shiga ba nan take fita na har cewa tayi wanan kaddararen aure nawa da ta tauye ma danta jin dadi dashi. Ban wani dade ba don ko ruwa ban sha ba a gidan na juyo na dawo gida ina kuka a idanuwa na, Nazo kofan gida na samu maman biyu tazo gidan bata samay ni ba tana shirin wuce wa sai gani tafe ina sharan kwalla a idona. Ta tsaya da mamaki tana kare min kallo tare da tambaya na ke lafiya kike tafe kina kula haka . Nan nake fada mata duk abin da ya faru a bayan ta har dukan da yai min tace wanan mijin naki ya zama abinda ya zama sai addua kawai gare shi. Ina kuka nake cewa da ita ni gaskiya gidan mu zan koma na gaji da wannan halin baida ranan gyara halinsa sai dai gaba gaba dakeyi. Tace kada ki fara cewa zaki gidan ku don mahaifin bazai barki ba ba kuma zai goyi bayan kiba don haka gara ki zauna kiyi hakkurri da halinsa tunda kin saba yanzu. Mutun sai kace mara imani komai a ziciya har yanzu fa bai daina abin da yake yi ba yanzu har rashin kwana a gida ya tsiro dashi. Tace kardai ince wurin matan banza yake kwana ta fiddo ido waje don mamaki tace wanan kuma sabon sirfan da ya dauko don mugunta fa. Nan na soma kuka ina fadin san anty ba sona suke yi ba sin cuce ni sun cuci iyayye na, sun muna rufa rufa an hada ni da alkakai na soma kuka wiwi. Tace meye haka kuma Safiya so kike ki tayar min da hankali nima cikin kuka nace da ita ba haka bane anty. Wallahi ni kadai nasan halin da nake ciki yanzu haka abinci sai yaga daman bani zai kawa a gidan nan ga uwar shi har fadi tayi wai ina mashi wayo ina karbe mai kudi. Kenan ashe tasan dan ta yadda yake amma taiwa mahaifina rufa rufa ta aura wa danta ni hakana. Hakkuri tai ta bani kan indan kara bashi lokaci idan bai daina ba zata bani kudin mota in koma gidan iyayyena da zama. Ranan bamu rabu ba sai da ta kaini har gidan ta na gani kamar ba a kasan nan suke zaune ba mutum zai dauka a Amerika yake don kyawon shi. Naci na sha ta bani kyautan suturu masu kyau da tsada dama tun da nazo ko kyale bai taba hada ni dashi ba. ZAINAB IDRIS MAKAWA SEENABU 8/14/20, 7:11 PM - Ummi Tandama: BAHAGGO, , , , , , , , 🧕🏿 1️⃣4️⃣ 🧕🏿 YAR UWA WANAN NOVEL NA KUDINE IDAN BAKI BIYA BA KADA KI KARANTA HAKKIN WASU PLEASE, , , , , Tafiyan dare mukayi sai wajajen sha daya da wani abu na rana muka isa garin mu duk jikin yai min tsami dama yaya jikin yake balle an tabashi kuma. Mun sauka yaya ya nema muna mashin muka hau zuwa gidan mu tare da kaya na niki niki shi yai wahalan daukan kayan da kansa. Suna hada hadan su na safe sai jin sallama na kawai sukayi yara suka dauka ga Safiya ga safiya tazo. Da gudu kanena suka sheko suka rungumay ni suko su mama sun fito da mamaki suna kallona mama ne tace safiya kuna tafe ashe ke daya ne take sai idanuwa suka ciko da kwalla. Na shige dakin mu ina kuka shigowan yaya Sani da kayana niki niki ya na kokuwa dashi yasa aka samu masu taimaka mashi daukowa. Kowa sai mamaki yakeyi sunyi tsaye cirko cirko suna mamaki Inna tace babu lafiya kan gaskiya. Wanan tafiya da gani bana dadin rai bane sai aka fara lekowa don gulma wai ana gaishe ni da zuwa sai a fita ana dariya waje don sheri. Inna ta koma kan yaya sani wanda ya gama aje kaya a wahalce dashi ta tsare shi da idanuwan ta tana cewa daga ina ka tsinto Safiya kai kuma. Baiyi magana ba sai samun wuri da yayi ya zauna yana neman ruwan sha yana jin inna ta matsa tambayan shi saida ya gama kwakwadan ruwan shi ya sauke numfashi. Ya dago kan shi yana fadan can lagos mana inna sai ya mayar da kan shi a kwanon da yake shan ruwan. Cikin mamaki da dafe kirjin ta tace har lagos katafi ka dauko ta dakin mijin ta kana ko da hankali kuwa. Sunyi tsaye akanshi cirko cirko suna sauraren shi maimakon ya yi magana sai ya mike kawai ya fita daga gida batare da ya tankasu ba. Can waje ya samu yan uwanshi su yaya Nura yana basu labarin rashin mutuncinn da ya samu mijin nawakeyi don haka ya hade kan su akan suyi wa baba tawaye ga zancen. Don gulma baba har ya fita kasuwa sai inna ta tura yaro ya kirashi a kasuwan don tasan bazasu ji komai a wurin yaya Sani din ba. Tun shiga na dakin ummi kuka nake yi ban iya magana ba har da ruwa da kunun da ta aje mun ban iya shan ko daya ba a ciki. Kanina ta tura ya kira mata gwagonta da sauri a gidan su don tasan ba lafiya ba wanan zuwan nawa kan. Ta fita ta kira su mama da inna kafin gwago din ta zo nan suka sakani gaba da tambaya amma basu samu amsa komai ba ban da aukin kuka da nakeyi. Gwago ta taso hankali a tashe tazo gidan namu cikin tashin hankali da son ganina kamar karta shigo na kara sautin kuka na ina fadin ban komawa wallahi gwago kasheni zai yi kinga duka, Na shiga bude jikina ina nuna mashu ga tabo nan ko ina a jikin nawa ba iya ka take ummina ta fashe da kuka inna ne kawai batai kuka a wurin . Sai ga baba da yaron da ya tafi kiranshi sun dawo tun a kofan yake fadin ina Safiyan take ne lafiya ko tare suke da mijin nata Nan take gidan yai tsi kowa na sauraren abinda zai fito bakin na amma sai kara sautin kuka na da nakeyi kawai. Tsawa ya dakamin tare da tambaya na dacewa ke ki ba mutane amsa kin tsaya sai kuka kike zubawa mutane, kukan ne zai fishe ki. Daga kofa suka tsinkayo muryan yaya Nura da yaya sani suna cewa baba mijin nan ta dan iska ne wallahi da ce anan arewa yake zaune ba abinda zai hana mu casa shi wallahi. Baba ya daka may tsawa da kai rufe muna baki don Allah yanzun dai may ya kawo nan a wani dalili tazo . Yaya Sani ya karbe zance cikin dakewa yace a dalili na tazo don ni naje har lagos na dauko ta na zo da ita gida kar ya kashe ta ga banza kar mara galihu da gata . Wani kallo baba yake mashi ya ci gaba da cewa diba baba ka gani yadda duka ya mayar da yariyan ga duk ta koma kamar wata ta baba wallahi. Baba ya daka mai tsawa da kai dakata kaina ubanta ko kaine uwar ta ya girgiza kai alaman a a baba yace to kada hurumin dauko ta ka dawo gida ita . Baba ta yaya zanje na samu yana dukanta da zagi akan taki dafa masu abinci shida karuwan shi ya doke ta yana zagi na fitan arziki. Ina ruwan ka baba ya firfito da indo waje ya sake cewa nace ina na ruwan ka wa ya aike ka zuwa dauko ta idan ya ga dama ya kashe ta mana ai mijinta ne kuma dan uwantw. Gwagon Ummi tace a a malam wanan ba hujja bane gaskiya kace fa ya kashe idan yaga dama da yar uwar shi ce aiba zai mata wanan tsinanen duka haka ba. Baba yace cikin daure fuskan karki saka bakinki ga zancen nan don ba maganan ki bace diya dai diyatace kuma dan yar uwana na bawa ita. Don haka ko yanka ta yake yi gunduwa gunduwa sai ta koma gidan nan shidin da yaje ya dauko ta shi zai mai da ita dakin ta ta zauna ai kowa hakkuri yake a dakin shi. Mama tace bako da duka ba har da su tarmashe da sauran su sai dai wani abin kadai tsaya ai bincike kada a dauki yarinya a mayar wani abu yaje ya samay ta ta halaka fa. Baba ya amshe zancen nata da cewa idan ta halaka aure ya halaka ta nace aure ya halakata sai ummi na ta fashe da kukan bakin ciki yace sai kiyi amma komawa sai ta koma wanan gidan ba fashi . Ya juya ya fice gidan da banbami shiko yaya sani fadi yake yi ba inda zan tafi wallahi abar shi yaje ya kashe ta din ba shike nan ba ai yar shi ne yace. Wanan kalamai na yaya sani suka tayar min da hankali ina ihu ina fadin yaya Sani kataimake ni bana komawa gidan nan kashe ni zaiyi wallahi. ********* ********* ********* A can lagos din bayan tafiya na bai tafi gidan su ba har tsawon kwana biyar yana hadiyan bacin rai shi kadai. Da farko ya dauka wasa ne yana cewa in tafi mana ya huta da wahala da yar kauye maganganu dai na batacin yake fada gamay da ni din. Sai yazo ina dan ya dawo zaiga gidan yai mashi girma ga wani irin duhu ba gyara shi kuma bashi da time din zama yai gyaran. Don haka ya bugo waya gidan su kannen shi suje su gyara mai gida basu so zuwa ba suka tafi dole. Sun dawo suna kwarara amai da zubar da miyau na kazantan da suka gani a gidan amai ne ragowan giya ne kai komai sun gani a gidan. Suna fadawa uwar su kan cewa basu kara zuwa gyara mai gida sai ta hausu da fada inda take shiga ba nan take fita ba. Idan ya rasa kudi babu mai bashi yadda yake samu ya amshe dan kudin da nake samu ga maman biyu ko wurin kitso. Yanzu babu inda yake samu sai dai ya arro ko kuma asai mai giyan kyata don mashaya akwai su da wanan kara. Sai ya kara sanin ashe ba karamin karya nake mashi a gidan ba gaskiya ne da aka ce mutum dan adam yana da rana. Ga yariyar da ya raina yaga ranan ta tun ba, aje ko ina ba gashi yasan muhinmacina a gidan yasan ina hakkuri dashi to amma kuma shidin ya kasa kyautata min ne bai san dalili ba. Ina da matukar mahinmaci sai yanzu da ban gidan ya gane hakan duk da bakwa yake dani ba sai ya ga dama amma sai tafiya ya zamay mashi yashin hankali da rashin kwaciyan hankali , ya rasa may ke kawo mai jin yawan tsana na a rashi. Kodon yawan zagina da mahaifiyan shi keyi ne a gaban take fadin kwadayin mahaifina ya jawo min haka yana gani ita sakarai ne don kawai ya bata diya sai ta bude mashi bakin aljihun ta na kashe mai kudin ta, ba dai a kan wanan diyar tashi ba dai. Wani yammaci sai gashi yazo gidan su dayamma nan mahaifiyar ta tare shi da zance na tana zagi tana aibanta ni tare da zagin iyayye na kamar yadda ta saba yi idan yazo. Yai shiru yana sauraren ta sai can da abin ya isheshi yace mummy zuwa zakiyi fa, ki dawo da ita don ba zan sake taba . Uwar dago cikin mamaki tace haka zaka ce ni ina ganin bata dace da kai ba sam, Yace mummy idan ba ita ba da iyayyen ta wata mace ne zatai hakkuri damu gaba daya duk abinda muke mata tana zaune tana hakkuri sai zuwan dan uwata ya gudu da ita. Ke kanki kin san cewa indan yar ki akewa hakan bazaki taba lamunta haka ba . Don haka ki kama hanya zuwa arewa ki dauko ta kidawo da ita nan shine saukin mu bai kamata ace don ki aka dauki yarinya nan aka bani ita. Don kwai ina danki ace baki kaunan ta ai gaskiya saadu ne da yake fadi da taimakon ki muke wani abin. Duk ke ke kara lalatamu muke abin da muka ga dama abin da bai dace ba idan munyi sai baki iya hana mu , sai muga cewa shine daidai don bamu da masu yi muna fada a rayuwan mu. Shi wanan tsohon ya na shagamu can yake sha a nin shi bai damu ba da halin da muke ciki a garin na babu ci babu shan shi. Nan dai ya takewa uwa gidan wuta akan sai taje ta dawo mashi da matar shi ya zube mata kudin mota anan ya fice yabarta tana tunane akai. Yaushe yaran nan ya fara son Safiya hakan nan ban sani ba kodai shima sun magance shine yadda suka magance yaya a gidan shi. Yanzi ni idan naje da wani ido zan kalli mahaifin yarinya nan dashi nace na rike mai ya amana ko mai. ********* ********* ********* Acan gida bayan baba ya kare fadan shi ya kare da cewa zai hada kudin mota da zaran sun cika bani kara kwana mashi gidan shi. Bayan fitan shi ne gwagon ummi ta rarashe ni da mama na samu na danci abinci da aka aje mun sai dai ban iya cin komai ba ruwan kunu kawai na iya sha. Dana dan gyagije namike naje nai wanka na fito har lokacin gwago tana nan zaune na sa kaya a jikina, Sai lokacin na fara ciro masu tsaraban da nazo dashi da wanda na sara ina gwadawa mahaifiya ta nan dai muka cire ma kowa tsaraban shi. Na fitar wa aka fitar ana tallata min ne diban ma maman Amina kawata aka kai mata take tambayan nazo ne yaron ke fada mata cewa nazo tun jiya ina nan gidan mu. Nan da nan aka saye kayan don na sake su da sauki sai gulma ya fara tashi a gidan mu daga dakin inna suke fadin ai gwai dama sun san cewa yaran gwago ba su da kamun kai. Sundai yi shiru ne naje na dan dano ai maganin mu kenan uwa cikin ukuba diya ma haka ai kadan muka gani. Na dan samu sukuni don har na fara maida jikina da haske naje na gaida maman Amina kawata mun dade muna hira da ita na dawo gida kada baba ya dawo bai samay ni a gida ba don satan hanya nayi nazo gidan su. Wai duk da halin da nadawo gidan mu ciki Inna sai da tai bakin ciki da gani na haka na kodan dan kayan da na saro ne ake saida min ban sani ba. Wani lokaci taimin gori akan rashin dace miji wana sain kuma ai min habaici wai ina wa mutane takama natafi birni na waye. Don dan kayan da nake sai daiwa yasa mutane na ribibin zuwa sayan unders na yara da yan dogon riga na mata nashan iska da sauran tarkace. Shine dalilin da inna ta rasa sukuni a cikin zuciyar ta tace wai ai gara na koma akarasa ni can ko yaushe cikin ba babana mugun shawara take a gida. Ina da sati uku da zuwa gida ne safiyan wata asabar sai ga gwago ta sauka a garin direct gidan mu ta yo sun tare ta kamar yadda suka saba mata idan tazo har da ummi na bata nuna mata komai ba a zuciyar ta. Hakan yasa gwagon dan sake jiki bayan sun gama gaisawa da mama sai gwago tace dada wanan yaron haka yaje yai muna, ya dauko kaunan shi ya zoda ita gida bada sanin mu ba. Sai mama din tai murmushi tace muma haka dai muka gansu kwatsan a gari sai dai a gaskiya abin baiyi dadi yadda suka zo muna da labari . Anyi abu don dadin rai kuma sai abu nason ya koma tsiya haka don ma malam daya tare maganan ya hana kowa ya fadi yace yana tara kudin mota ne , ta koma dakin ta. Gwago taji sanyi a ranta sai dai taji mama tace a gaskiya dake har wanan yaron baku rike amana ba sam abin baiyi dadi ba wallahi don ma dai anyi kawaici andubi baya . Gwago tace to ai dada yanzu dai kuyi hakkuri kamai aka ce munyi mun dauka sai dai muba da hakkuri kawai. Mama ta sake cewa ki sani diyar malam diyar ki ce ba sai an fada ba don in anyi laakari da irin diyaucin da ya nuna tun daga kan auren har kawo yanzu amma sai ga labari mara dadin ji ya samay mu kuma mun ga alama don ga shedan bugu nan da tazo muna. Yadda duk akeyi mama tayi don ta fadi gaskiya yadda ya dace har da zancen kudin da suka bar ma gwago ta ja min jari sukayi tace wai mijina ya karbi kudin Amma zatai mai magana ya dawo min da kudina na dinga juyawa da kaina zaifi tana ta ban hakkuri can dai ta tashi zuwa dakin mama ne tayo mata rakiya wurin ummina. Nan ma hakkuri ta bayar suna cikin dakin ne baba ya shigo gidan wanda inna ta aika a kira shi yazo wai ga gwago tazo. Yana shigowa yai dakin mama aka ce suna dakin ummi sai ya kama fada yin may ina ruwan ta da ita aiba ita taba ki dayin ba. Nan dai yake ta sababi irin na maza da iyalin su basu da tacewa sai su kaida ke kafa dokan su a gidan yadda ransu yaso. Bai tsaya sauren ta ba yace binta kinzo dama ina son zuwa wani sati in mayar maki da yarinyanan . Sai hakkuri yake bata abin ya bani mamaki naidai tuna yadda take zama ta kare mashi zagi da yankar kauna . Amma shi yana nufanta da alheri ya kuma bata go ahead akaina yace tana da iko akaina ta tsawa ta min ba sai nazo gida ba. Hannu na sa akai ina ihu baba yace indan ban rufe masu baki ba yanzu zai debe min albarka dole mama tasani yin shiru mama tana fadin adai tsaya abin abin a sannu ba a hakana, Tsawa ya daka ma mama tare da cewa indan bata kama mashi baki ba yanzu zai da ita dani mu bar mashi gidan shi. Duk yadda akeyi mama tayi amma ita inna cewa tayi indan ma na zauna gidan may zan yi ai kawai gara na koma daki na, na zauna shiyafi. Baba ka taimake ni karka mayar dani idan ka mayar dani kashe ni zasuyi wallahi wayyo baba ka taimake ni yace idan ban isa gare ki ba sai dai kibi duniya. Ummi na saboda kawai ci kala bata ce dashi ba amma zuciyar ta kamar zai tsage take jin shi ansa rana, ranan labara zamu tafi. Don gwago zatai dan sayayya da zata tafi dashi na sana an ta can sai wani nan nan dani takeyi don ganin idon mahaifana. ZAINAB IDRIS MAKAWA SEENABU 8/14/20, 7:11 PM - Ummi Tandama: BAHAGGON , , , , , , 🧕🏿1️⃣3️⃣🧕🏿 IDAN BAKI BIYA BA KADA KI KARANTA HAKKIN WASU PLEASE DON WANAN NOVEL DIN KUDI NE. Ummina dake barci ta falka cikin matsanacin firgici daga barcin da takeyi wanda kwana uku kenan a jare ta mafalki dani. Kuma mafalki mara dadin takeyi a gamay dani din wani lokaci sai taga na gwauce zan fada rami ko tagan ni a ruwa mai zurfi ina iyo. Ina gudu ana bina zaa kashe ni da wani guduma a hannun mai shi ire iren wanan mafalkin takeyi koda yaushe hakan ya tayar mata da hankali. Ta shiga cikin damuwa sosai ta dan saka abin a ranta don haka yau ta kudiri aniyar fadawa baba na idan ya dawo dakin ta. Haka akayi sai da yagama sauren ta kaf yaji abinda take fada bai bari takai aya ga zancen ta ba ya ko hauta da sababi har yana daga murya sauran mutanen gidan suna jin shi. Mama ce da taji fadan yayi yawa hakana ta tako zuwa kofan dakin tana cewa haba malam ayi hakkuri koma may nene tunda ka taba fada ai ya isa ko. Yace a hasale bari matar nan da abin haushi auren yariyar take son kashe wa don rashin sanin ciwon kai. Yariya na gidan mijin ta zaune lafiya hankali kwance zaki tsiro da wani tsurku wai kila ba lafiya take ba ke kina yawan mafalkin ta ke kila wani abu zai samu yar ki. To Wallahi ahir din ki da zancen Safiya a gidan nan idan ba haka ba rayuka zasu baci sosai akan haka don sam ba zan lamunta ba. Har yayi ya kare bata ce dashi uffan ba da safiya kuma ya tusa jidali inda yake shiga ba nan yake fita ba. Sai inna ce ta sa mashi baki tana fadin ai kasan dan tallaka bai iya samun wuri ba in bashi ba abin farin ciki yar ki na can lagas tana aure amma ke bakin ciki ya hanaki ki gane haka ki kwantar da kai kici arziki. Mutum mai bakin ciki da hassada ai har kanshi yake yi saboda mugun hassada daya huda jiki na sheri, har taci ta sude ummi bata tankasu ba sai share su da tayi tana aikin ta a cikin gida. Kwana biyu hakana suke da baba sama sama sai da taga ya dan fara mantawa da zance ta roki fita unguwa gidan gwagon ta. Bai hana ta ba illa cewa da yayi a gaishe ta ta gama abinda takeyi ta shirya ta tafi gidan nasu kamar yadda muke kiran gidan gwagon nasu. Bayan sun gaisa da gwago tana tambayan ta yara da sauran muta ne gidan take cewa gwago dama nazo in fada maki ne kwanan duk na kwanta barci farkin yar nan nake yi ba dadi wallahi. Nan de ta kwashe yadda take mafalkin ta fada ma ta shiru gwagon nata tayi sai zuwa can tace wuri ne bakusa ba in ba haka ba da sai a shirya aje a gane ta. Sai dai addua duk inda take Allah ya tsare muna ita kawai zamuce wanan shawara na gwago ta dauka har tadan ji saukin abinda take ji gamay da ni a zuciyar ta. A hanya tana dawowa tafe take tana tunanen ko a wani hali nake sai Allah kawai ya sani don yanzu kusan shekara daya ke nan da tafiya na amma babu wanda ke da labarin halin da nake ciki. Yaya sani zaune yake gaishe ta amma bataji shi ba har sau uku yana mata magana tayi nisa a cikin tunane. Sai da ya kara kiran sunanta da karfi taji shi ta sauke wani ajiyan zuciya da karfi take amsa mashi gaisuwan da yake mata din. Yake tambayan ta lafiya dai na ganki a cikin damuwa tai murmushi kamar kada ta fada mai sai take cewa babu komai. Yace wani matsalane kuma ya taso ki fada min, sai ta fara haye take fada mai yawan ma falkin da take yi dani ta kara da fadin gashi tun tafiyan ta babu wanda ya ji labarin su itama gwagon naku ta bar zuwa yanzu kamar da datake zuwa akai akai. Shiru yayi yana tunane sai can yace lafiya take ummi mafalkine kawai ke zuwa haka na amma bari nayi maki alkwarin zan bincika inji. ********* ********* ********* Na samu masu kitso na yawan zuwa neman kitso a wurina da kuma sayen kayan sanyi da nake sayarwa a gidan. Haka ya hana ni shiga damuwa da halin da nake ciki don yanzu takai bai bani abinci sai dai inyi dabara inci wa cikina. Dan neman kudin da nakeyi Allah yai ma abin albarka sai gashi ina samu sosai duk abin da na taba da sunan kudi sai Allah ya sama abin albarka . Ga anty maman biyu yanzu ta mayar dani kamar wata yar uwata na jiki nakan dauki lakaci naje nai mata gyaran gida da sauran aikin da shafi na mata dai. Wanan ya kara kawo muna shakuwa a tsakanin mu har yakai ta tutube da zancen karo karatu tunda taga takarduna suna da kyau. Murmushi nayi kawai nake cewa Anty nasan ko nai mashi magana ba bari zai yi ba koma ya bari ita mahaifiyar shi ba bari zatayi ba. Don haka na hakkura da wanan zance zan tsaya inda Allah ya ajeni Allah bai manta da kowa ba ina ji ina gani na koma dani da wanda baiyi karatu ba duk daya. Tai shiru tana kallona can ta nisa take cewa yanzu idan zaki iya sana,a sai mu duba muga yadda za a yi don dai wanan kitso Safiya bazai fishe ki ba. Nai murshi nake cewa zan iya mana anty tunda ba wani abu nake yi ba tace to za a diba a ga binda ya dace dani. Nai shirin komawa gida don karfe biyu ya wuce ta hada min goma na arziki kamar kullun na nufi hanyar gida ina sauri don in koma inyi abinci. Bai bani kuma indan bayin ba fada ne idan na dafa kuma ya lashe, sai dai ashe na makara don na samu ya dawo gidan ko. Ina kokarin shiga ne naji an shako ni ta baya sai da idanuwa suka firfito don wahala yana fadin yar iska ina kika fito kin fito wurin biyar mazan ki. Gaba na ya fadi don jin sabon sherin da ya kulla min kuma nai karfin halin fadin Allah yai min tsari ga shiga halaka da duk wani muslimi mai imani. Nace ni wurin maman biyu na fito don ina mata aiki tana dan bani abinda zanci yanzu can na fito zaka iya binkawa kaji gaskiyan abin. Yana huci yakai idon shi ga dan jakar kayan da na shigo dashi gidan sai ya fisge jakar ya shiga bincike nasan dama kudi yake nema ba wani abu ba yana ganin dubu biyar ya saurin dauka yana huce yana muzurai da idanuwan shi ya hankadani gefe daya ya fice gidan. Nakai kallona ga kayan da ya wawatsar min a kasa na duka na fara kwashewa tare da ajiya zuciya idanuwa na zubar da hawaye. A hankali na zare hijjab din dake jikina na shiga adana kaya inda ya dace da komai a cikin shinkafa naga wani leda an dukule abu ina budewa na ga kudani da takarda a ciki da sauri na dauka ina karantawa kamar haka. Nasan mijin ki ba zai barki da kudin motan dana baki ba shiyasa na saka maki wanan a cikin nan don in kin gani ki boye ki samu na amfani dashi. Safiya ki ci abincin da na baki idan ya kare kada kiji kunyan dawowa ki fada min a shirye nake da in taimaki don rayuwan ki na bukatan taimako. Ina hawaye nake karantawa nagama ina mata addua nasan Allah ne ya turo wanan matan a rayuwa na don ta taimaka min. Idan badon Allah da ita ba da ban san yadda rayuna zai kasan ce ba a garin da bani da kowa sai Allah amma gashi ta rike ni tankar jinin ta tana taimaka min. Da safe da wanki na tashi a gidan da gyaran gida komai na gyara na dora girki dayake ina da komai a hannu na girki nayi lafiyayye na zauna naci. Na shiga wanka na fito ina shiryawa naji shigowan shi sai dai kamar ba shi kadai bane tashi nayi na leka tare yake da wata mace mai siffan kabila da dan riga karmi ajikin ta wata yankwamama da ita ta sa gashin doki akan ta. Baka ce bata da wani kyau na ga ya rungumo ta yana tsotson sassan jikin ta da sauri na sake labulen ina runtse idona. Wani irin kuna nake ji a raina har na koma na zauna sai wata zuciya tace dani na fita na yi masu magana. Koda nafito sun shagala a cikin abinda suke yi basuji fitowa na ba daga dakin har naje gurin fridge na dauko goran ruwa mai sanyi ban tsaya jiran komai ba na bude goran na kwarara masu ruwan akai. Wani irin zabura sukayi da karfi yace kina hauka ne zuciyana ya dake nace yanzu dai na fara haukan . Zan kara zuba masu ruwan ya daga hannu ya sharara min mari sai da na gigice na dako nai kan yankwamaman da duka sai shi kuma ya shiga duka na sai da yai min lis . Da kyat na kwaci kaina a hannun shi na bude kofa a gigice na fito gidan haka nabi hanya ba komai a jikina sai gidan gwagon mu. Na isa da kukana tana gani na ta zabura tsaye tana fadin ke lafiya may ya faru da Amadun ne yayi hatsari ne komay ? Duk suna tsaye a kaina sai faman rusa ihu nake yi da kyat na tsagaita kukan da nake yi nake cewa duka na yayi gwago don ya shigo da mace gidan nai magana. Sai bude baki tayi tace ke mai ya kaiki yi mashi magana gidan shi ko naki har wani dadi ki yaji da zaki ce kar ya nemi matan da yake so. Dakatar da kukan da nakeyi nayi ina kallon ta cikin mama tace kin ga bazan hana shi jin dadin rayuwan shi a kan ki ke ma in kina iyawa jiki kiyi shaanin gaban ki lagos bariki ne kazo na zo ba mai shiga shanin wani anan. Yo wanan wani abu ne da kullun zai zama abin masifa a kanki kin hana yaro shakat a ruyuwan shi. Habiba tace mummy ai duk laifin ki ne da kika hada shi da wanan kucakar yarin sam bata dace da zama matar shi mutum kamar doluwa gata nan. Sukai min kaca kaca suka korani haka na fito ina kuka na nufi gidan don ban son in tafi gidan mama biyu saboda gidan zumu ba kasuwa bane. Na dawo na samu sunyi shaye shayen su a gidan sun bar baje kwalaben giya sun shige daki sai kida ke tashi daga ciki. Hakana na shige tare da bakin ciki a raina ranan dai yadda naga dare haka naga safiya. ********* ********* ********* Yaya sani yazo ya sallami ummi da dare da cewa zai yi tafiya kamar yadda ya sallamay ta haka ma ya sallami kowa a gida ba tare da wani yasan idan zai tafi ba. A cikin daren nan yabi mota sai garin lagos shigan safe yai wa lagos din bai sha wahala ya samu motar zuwa unguwar mu. Gidan gwago ya nema ya samu suna cinikin safiya mutane da yawa a wurin ta masu karya wa sai ganin shi tayi kwatsan. Da mamaki take maimaita sunan shi tana cewa sanu kaine a garin namu injin dai lafiya yace lafiya lau ta saka a kawo mai abin karyawa ya karya dama tun abincin da yaci a gida bai sake karya ba har lokacin. Bayan ya karya ya bukaci a kaishi wuri na sai ta fara yi mai kwana kwana don tasan cewa daren jiya nasha duka wata kila ina can ina jinya jiki na. Da dai ya matsa Sadiya tace bari ta kai shi gwagon bata so haka ba tare da Sadiyan suka zo gidan mu, Daidai lokacin ya tsaye yana surfa min zagi wai naki fitowa in dafa masu abin karyawa yana cewa don ubanki ki fito nace dakin nan tun ban biyo ki na kara maki ba. Aka turo kofan shigowa gidan na fito karuwan ta fito daga ita sai dan tawul iya cinyan ta tana cewa wai may ke faruwa ne sai ma a lokacin nasan wai bahausa ne ita don hausan da tayi. Kallon kallon akeyi wa juna kamar daga sama na ga yaya sani a gidan ban san lokacin da nayi ihun murna ba na rugumay shi sai kuma na fashe da kuka don murna . Shikan Ahmed shiru yayi don ya san duk banbamin da yake a kaina yaya Sani yaji shi ga kuma karuwan shi a tsaye da dan tawul tana cewa wai bazata dafa muna bane komay ko lalatsa muna yar iska. Wani tsawa ya daka mata sai da ta zabura ta kama kanta tare da mashi wani irin kallon ko ta fahinci abinda yake nufi ne sai tai shiru. Yaya Sani yace bari kuka Safiya yau Allah ya gwada min abin da ummin ki kata mafalki a kai. Lalai ba gidan uban ta bane ashe kai baka da mutunci baka da kima ga kwalaben giyan su nan a zube da suka sha daren a jiya ba a kawar ba. Na shiga rawan jiki da yaya na ina ce mashi ya zauna a baude nake tafiya ga kumburi a fuska na baki ya sundule min. Shigewa yayi baya yagama hararn Sadiya da ta kawo shi gidan yaya Sani bai iya kara furta komai ba yai shiru yana bin gidan da kallo. Nace yaya bari na hada ma abinci kaci yace ki barshi kawai na ci a wurin gwago zama nayi a kusa dashi ina tambayan mutanem gida. Sai ga su sun fito daga dakin suka fice gidan sadiya ma tace ita zata tafi tabar aikin ta ne a gida yana jiran ta. Bayan fitan su ne duka na fashe da kuka mai tsuma zuciya tamayoyi yake mim iin bashi amsa a hankali. Ya nisa tare da fadi ashe dama haka yake kuma aka aura maki shi ba zan barki garin nan ba Safiya cikin wanan halin kafana kafan ki. Naji dadi nace yaya sani ka taimake indan ka barni kashe ni zaiyi wallahi baya da imani ko kadan. Muna nan har na gama shiri na kwatsam sai ga gwago na tashigo gidan tana wani haba haba da mutane, Ya nuna mata ban fada mashi komao ba gamay da zama na a wurin su ta tafi tana cewa sai ya dawo akwai dakin su yaya saadu ta gyara mashi. Yace ba zai dade ba zamu dawo gwogo na fita daga gidan ya dube ni yace akwai kudi hannunki da zai ishemu tafiya gida. Nace eh yaya akwai yace don shima dakyat ya hada kudin da ya biyo babban mota yazo don ya ga ummi ta damu. Mun tafi har gidan maman biyi dashi taji dadi tai murna taba lamban waya akan idan naje sai in kirata don yaji saukan mu. Takawo kudin mota ta bamu harda na guzuri wanda zai ishemu nai mata godiya ta kaimu na dan yi tsara ba na saro lace da yan dogayen riguna takai mu garejin kananan motaci muka kama hanya sai arewa. Tafe muke zuciya ta babu abin daka cikin sa sai yawan tunane fan ban san irin tarbon da zamu samu wurin mahaifin mu ba idan mun isa. Can lagos shishiru gwago bata ga ya sani yazo gidan ta ba ta tayar da habiba taje tazo mata da shi. Zuwan ta yayi daidai da dawowan shi gidan da dan ledan chefane a ciki don ya san yaya sani na gari yai wanan. Sai dai babu kowa a gidan sai ga habiba yake tambayan ta tace bata san inda muka tafi ba itama zuanta kenan mummy ta turo ni in kira wanan bakon. Dakyat ya bude gidan ya samu ya shiga sai bayan ya bude ne wata makwaciyar mu takawo mao key tace nace a bashi yace ni ina inane da zan bata key din gidan. Taga dai na dauki jakkana da wasu kaya mun tafi idon ya fitar waje acikin mamaki yace What. Eyyeh ta tafi tace damu har mun mata rakakiya yayi wani dan fito a bakin shi irin na yan daba ya shige ciki ita ko habiba komawa tayi gida ta fadawa mahaifiyar ai gwago naji tace dama ban yarda da zuwan dan iskan yaron nan ba. Kana ganin shi kaga dan tantiri dan duniya ko ina babu mai zuwa daga ma yayi barka ya rabu da kaya gidan shi shegiya banda taulali mai aka kawo min dama su karata can. ZAINAB IDRIS MAKAWA SEENABU 8/14/20, 7:11 PM - Ummi Tandama: BAHAGGON, , , , , , , , , , 🧕🏿1️⃣5️⃣🧕🏿 YAR UWA WANAN NOVEL NA KUDI NE IDAN BAKI BIYA BA KADA KI KARANTA HAKKIN WASU PLEASE, , , , , , Kamar yadda baba yace haka din ne ya faru gwago ta daukeni zuwa lagos ita kadai kamar mara gata ta, tafi dani. Mama ta ance an samu wacce ta raka ni muka tafi tare amma sam baba yaki yarda da hakan yace wai ai gwago uwata kuma gwago na. Su yaya sani sun so siyi ma baba dan banga banga amma yaki yarda yai masu tijaran tsakar gida. Wanan abin shiya tunzura ummina tabar gidan baba yan uwanta kuma suka kama mata suna cewa su dai basu ga amfanin auren da babu yanci cikin sa ba. Da farko baba bai damu da tafiyan ta ba sai daga baya ya damu a kan yara don yanzu dole ya bada komai na anfanin su. Wanan abin ne ya fara damun shi taje bikon ummi mahaifinta yace badai gida shi ba yaje yayi iko da yar shi shi kuma yai iko da tashi don da baifi daba amma ummi ta gama auren gidan shi. Ya dauka wasane sai da yaga yannen ta sun kaishi kara kotu akan ya bata takardan sakin ta yasan da gaske suke wanan karon. Aka shiga kotu suka kora wa alkali halin da yake mata da rashin bata yancin ta alkali yace zai daure shi don sai ya fadi gaskiya indan ba sayar dani yayi ga gwago na ba yake kamay kamay. Yai ta rantsuwa akan wallahi bai sayar dani ba zumunci dai ne tsakanin shi da gwago na Alkali yace zumuncin zamanin nan zakai wa haka. Daga Allah ya taimake ka yar ka ta dawo gida wurin ka lafiya ba tare da wata matsala mai karfi ba don rashin sanin zafin kai zaka maida ta gidan wahala watau taje a kashe ta da kurciyan ta ko. Yace ba haka na bane alkali yace haka ne mana sai ta zama mara anfamni zaka dawo uwar ta da ita ko yana dai ta bada hakkuri alkali yace ya basu sati biyu su shirya in ba shiri tazo ta karbi takardan ta. Da haka suka wuce aka rabu baran baran baba hankalin shi yai matukar tashi mama tace na fada maka kabi abin nan sannu kaki . Safiya ba irin sauran yara bane yarinya ne mai biyayya da sanin ya kama ta amma har kaga ta kasa hakkuri a wanan halin ta akwai magana da anyi bincike tare da kafa hujja mai kar fi. Amma kaki tsayawa ai komai a hankali ka dauki yarinya kamayar da ita ba wani binciki kwakwara yanzu duk abin da ya faru da ita sai ka kuka da kan ka. Nan suka taru da shi da Inna suka mai mama caa a kai wai tana dai su agoya mani baya ne in kashe aure yasa take fadan haka amma wani wahala nake ciki. Nan dai itama tai masu nasu borin ta ce aidon ba diyar Inna bane a wanan halin da duk gari kowa ya gama jin wanan zancen ko. ********* ********* ********* Daga ni sai gwago da wasu mutane a bayan babban motar traller da zasu kai kaya kurmi don son mallaha ta kasa biya muna dubu hudu zuwa lagos. Ina rakube a wuri daya a cikin mota duk inda mota ta tsaya sai ta sai abin kwalam taci bata ko kallona ni ko ta bani baya gama na ina tunanen halin da na baro ummi na ciki. Sai wani awara data saye tun a arewa taci ta raga yai tsami ta jehomani kaina girgiza mata alamar a a bana ci har muka kai sai ruwa da nasha ina da muka sauka mukai sallah. Anan na kulla ko sallah ba bata yi daidai irin sallah yan kasuwan kauye ne a gagauce ake yin sa ba cikawa. Mun sauka lagos da dayan rana don motar bata sauri maimakon mu tafi gidan ta ta hada mu tai muns fada sai kawai tace a kaimu gida na bata ko shiga ba ta saukemin kayana tana ta masifa wai ban da kama jiki. Ni dai na fita suka ja mota suka tafi suka barni nan tsaye ina mamakin ta a raina sai da motar ta bace na juyo ina kallon gida tare da sauke ajiyan zuciya na fara takawa zuciya na fal da mamaki gwago da alaman sam bata da digon amana a rayuwan ta. A hankali na tura kofan gidan ga mamakina sai naga gidan a bude na shiga da addua na ga baki da alama akwai mutum gidan. Warin taba da tsamin giya ne sukai min maraba ga hanci na take wani irin bakin ciki ya lulube ni na rintse idanuwa na don takai ci. Dakina na nufa da buhun kayana ina ja don ba zan iya dauka ba don nauyi saboda nayo yan sare sare a arewa na je da shi. Dakin yana nan kamar yadda na barshi babu sauyin komai a cikin sai dai kuran da yayi kawai na rashin mutum a cikin sa. Zama nayi nai tagumi hannu bibiyu idanuwa na suna fitar da hawaye takaici don gwago takai katuntumar yar cin amna. Koda yake bata da laifi duk wullancin da na gani mahaifina ne ya ja min shi don jajircewa shi a kan gwago wai shi zumunci . Ina ga motsi suka ji ya fito kofan gidan a bude yake sai kuma ya kalli kofan dakina shima a bude yake dakin. Da sauri ya tako zuwa kofa ya daga labulen dakin ina zaune shabe shabe sai hawayen da nake zubarwa a idanuwa na. Kamar daga sama naji shigowan shi dakin babu annuri fuskanshi ko kadan sai dai ya dan nuna mamakin gani na a wanan lokacin. A take na razana yayin da nai kwali dashi tsaye kofan dakin ya rike labulen dakin. Fara takowa yayi zuwa inda nake zaune gabana ya fara faduwa da tsoro yazo daidai kaina ya tsaya na cewa. Ciki buga tsawa yace dani tun yaushe kika dawo gidan nan ban sani ba yana ma dakin yan dube dube can ya juyo ya tsare ni da idanuwan shin jajjaye. Ya sake maimata tambayan shi gare ni da yaushe kika dawo nace ? Na dan kalle shi nace yanzun gwago ta sauke ni ta wuce sai ya watso min mugun kallo kamar zai make ni, yace waye ya baki izzinin wucewa garin ku. Ban bashi amsa ba sai ma kawar da kai danayi daga kallon shi don wani irin tsanan shi nake ji da haushi yana shigata da zaran na ganshi. Ya harare ni yana cewa wanan ya zama maki na farko da na karshe a gidan nan don ba zaki maishe ni yaro ba . Banko san yana tsaye ba haushi da takaici sun cikani na shi caraf na jiyo muryan mace na magana daga falo ya juya da sauri ya fita zuwa falon . Daidai wanan lokacin naja tsaki tare da fadin ai guma yaro da halin ka Allah dai ya sauwa ka gashi dai mutum a ido amma a ina halin shi na kamala baikai ba. Can naji sun fice daga gidan na fito na kalli gidan a kazance da kyama hawaye ya zobo min na takaici da bakin ciki suka rufe min zuciya. Yanzu ni haka zan zauna a mara gata kamar wata mara asali in zauna da mijin da bai san tsoron Allah ba a zuciyar shi. Bazan iya zama cikin wanan jassabab in yi ibada dole na shiga aikin gidan duk da gajiyan da na dibo din a motar. Kafin wani lakaci na gama gyaran gidan na dora girki abincin da zanci na shiga wanka daidai lokacin da na fito bandakin ne sai gashi ya dawo gidan da ledoji niki niki kamar da gaske. Tsaye yake a tsakar falo yana kwala min kira da ke wai kina inna ne nake kira baki karba min yazo ya bankado labulen dakin ina ciki ina sallah sai ya juya yakoma dakin shi. Sai da na idar nafito falon baya nan na taka zuwa kofan dakin nashi na tsaya daga kofa don tun ranan da yace karna kara shiga mai daki ban sake ko taka kofan shi ba. Nace mai gani daga kofan har ya tube ya kuna taba ga kida na tashi daga cikin dakin nai magana naga kamar bai jiba na juya abina zan shige ne ga kayan da ya shigo dasu gidan. Nasan kiran da yake min kenan don haka na tsaya ina duba kayan, kayan miya ne sai maclean da sabulun wanka dana wanki sai madara da ovaltine da sugar. Ina duke ina cire komai ina kaiwa inda muke ajewa ya fito falon daga shi sai gajeren wando jikin shi ba rika sai hayaki da yake busawa. Take falon ya karade da warin taban ba dadin ji, ya zama min dole na mika al, amura gaba daya ga Allah don shine kawai zaimin mafita saboda yadda naje gida baba ya wulkantani a gaban yan uwa na da su inna ummi na tana kumsan bakin ciki gaba daya naji duniyan ta fice min a rai duk kuwa da shedan da yaya sani yayi dakuma wanda suka gani a jiki na baisa baba ya sassauta min ba ga halin da nake ciki . Ko gaida shi nayi da kwana baya karba min itama ummi na abin ya shafe ta. Yanzu dai gani na dawo a turke na mai cabo haka zan daure in ta hakkuri don kada fushin iyayyena na hau kaina. Dama ance sabo turken wawa inda sabo ai yanzu na saba da wahalan gidan shi musamman idan yana jin fitanan shi anan falo zai min shaye shayen shi. Haka kuma idan yaga dama ya afka min duk rokon da zan mai bai sai ya kyale ni, har sai ya ji ya samu yadda yake so da kansa. Na nisa tare da fadin akwai Allah sai naji yana fadin in akwai sauran abinda ban sayo ba ki fada kada kuma kice na barki da yunwa. Dajin haka nasan ya tafi gidan gwago ta kwashe karya da gaskiya ta fada mashi kenan shine yazo da wanan sayayyan. A sanyaya na bashi amsa da sai man miya ba a sayo ba man miya ki saye mana iyakar kudina kenan na kashe. Na dago ina kallonshi nai karfin halin fadin ai ba hakki na bane saye da sai in saye din. Yaci gaba da busar taban shi bai tanka min ba can naji yace tsiyan ki kenan ke ba ai maki daidai . Na dago zanyi magana naga yana min wani irin kallo kamar tsohun maye sai nabar maganan da zan yi a lokacin na gagauta kawar da kayan don bai mashi wuya ya afka min a nan wurin mutum kamar hariji bai gajiya da kwana da mata. Ranan dai bai barni ba tun karfe takwas da na sallame sallah insha,i yana nan yana sintiri a falon. Ina addua ya shigo min daki muryan shi naji a tsakiyan kunne yana cewa yau ki tabbatar da cewa zaki biya bashin kwanakin da kika dauka agida . Na dago kai na dan kalle shi naga idanuwan shi jajaye akaina babu ko alaman kuya a tare dashi nace banci bashi kowa a kaina ba don ma ko nace ai akwai masu biya da suka fini daraja da kima. Ban gama rufe baki ba nagan shi a gaba na dauka daya yai min sai saman gadon dakin nawa . Ba bata lokaci ya shiga kiciniyar cire min hijjabin da nai sallah ya rake daga ni sai zani Allah ya tai make ni tun da na fito daga wanka na dan kintsa jikina. Ba ta lokaci ya shiga sinsina na wuya na da na shafe da hummura da alama yaji dadin kan shi naga yana wani shakan ko ina daga bisani ya shiga watsa min kiss irin nasu na yan duniya. Yakai tsawon minti uku yana abu guda ajikina zuwa bakina ina kokarin janyewa ne daga gare ya da kata daga abinda yake yi yace. Wanan abinda kike yi shi ke yawan bata min rai dake a koda yaushe mutum zaizo gare ki sai anyi rigima. Ba tare da jin tsoron shi ba nace dole ayi rigima don ba a zuwa ma mutum ta tsigar da ya dace sai a cikin may ko najasa. Shiru yayi na wani dan lokaci yana kallona ido da ido yace nine najasan ke nan ma ko. Gabana ya fadi naga yadda idanuwan shi suka kara kadawa sukai ja jawur dasu a lokaci daya nai saurin dauke idona gare shi. Yayi amfani da hannushi ya sake juyo fuskana muna fuskantan juna yace come on so nake ki kalli idanuwa ki gayamin cewa wani najasa kike magana ko ysushe. Na dai gane yau yana son mutunci ne don ko magana da yake yi a cikin karamin murya yake yin sa tankar yana tsoron wani yaji mu ne. Kawai sai ji nayi hawaye sun soma cika min idona na cije fatar bakina sai can nace yaya ka bani daman in fada maka abinda ke zuciyana tsakani da Allah. Sai na ji yace ke nake saurare ai gaba daya ya tsare ni da idanuwan shi sai na dan yi shiru zuwa wani lokaci. Sai na soma magana da cewa yaya ka yarda dani tun da nazo gidan ka na zo da shirin maka bibyaya a duk yadda kake. Amma sai ka dauke ni daukar mace biya a gare ka yau koda ace sayoni kayi a matsayin boya baka san asalina ba ban cancanci irin abinda kake min ba. Kadoke ni, ka zagi iyayyena, ka dauko min karuwan ka har gida uwa uba ka zauna kayi shaye shayen ka har mai na gyara wurin duk ina hakkuri da hakan don biyayya ga iyayye. Amma hakan bai maka ba sai ka yi kokarin tozar tani a gaban karuwan ka akan dole nai mata abin karyawa. Yaya ina zaka da wanan alhakin a kan ka kai kadai bafa ban iya dauka mataki bane ina dai hakkuri ne don daraja aure dana iyayye amma duk wana bai isa ba sai ka , , , , Kuka ne yaci karfina na kasa karasa abinda zan, fada mashi din , irin rikon da naji yayi min shiya tabbatar da magana na yadan shige shi a lokacin. Anan nayi kokarin kwace jikina daga ga gare shi amma sai naji ya kara matse ni daga jikin shi, ya shiga yin wasu irin magan gannu wanda na kasa fahintar may maganan nashi ke nufi don acikin harshen turanci irin nasu na wayyayu yake yi. Acikin wani irin yanayi naji yana kokarin shiga na a lokacin fadi nake don Allah yaya ka barni amma bai kulani ba. Naci gaba da magiya ba tare da yasan ina yi ba har sai da yacin ma manufan sa gare ni. Ya gama ya mike kamar wanda aka tsikara yana mai daukan wando shi yt a bar dakin ina kukan takaici na bishi da kallo har ya bace min. Nan naci kuka na ya isheni na tashi nai wanka ina tausayin kaina ni kadai a dakin . Washe gari koda na tashi duk jikina yai tsami haka na daure na sama muna abin karyawa na gama na jera mashi a taburi. Kwana biyu zaka ce ya daina halin shi ne don da yadawo aiki yana gida sai dai shan giya yabar yi a falo amma taba kan sai abinda ya karu. Na shiri ranan wani jumma a na tafi gidan maman biyu tayi mamaki kwarai data ganni take tambaya na yaushe na dawo . Na koro mata labari duk yadda zuwana gida ya kaya da kuma dawona da gwago nan garin sai da ta gama saurare na ta nisa tana cewa. A gaskiya mahaifin ki yana da taurin rai Safiya ya kuma tafka babban kuskure da bai tsaya binke ba ya dauki mataki yadda ya dace. Sai ya koro ki babu wani bincike da yayi wai duk karan zumunci yake yi alhalin yanzu zamani ya canza mutane basu da gaskiya ko kadan kowa nasa ya sani. Takare da cewa babu komai yadda kikayi kin kyauta Safiya kibar wa Allah alamarin sa Allah yana tare da mai gaskiya. Nan take tambaya da na dawo yaya halin nasa ya sauya ko kuwa yana nan kamar kullun nake cewa da ita ya sauya halin shan giya a falo kuma tun ranan da na dawo na samay shi da mace har yau banga ya dauko wata a gidan ba. Tace Allah yasa ya daina indai ba tuban mazuru bane yai maki amma ga yadda na fahinta yana san son ki iskan cin dai ne ya sha gaban shi. An sauko jumma a nai shirin komawa gida ta dan hado min dan abinda ta saba yi min tasa driver gidan su ya kawoni gida. Sanin halin shi da nayi yasa nace drivern ya sauke ni tun a farkon layin mu na karasa da kafa. ZAINAB IDRIS MAKAWA SEENABU 8/14/20, 7:11 PM - Ummi Tandama: BAHAGGAN, , , , , , 🧕🏿1️⃣6️⃣🧕🏿 YAR UEA WANAN NOVEL DIN NA KUDINE IDAN BAKI BIYA BA KADA KI KARANTA HAKKIN WASU PLEASE, , , , , , , Yau nayi yamman yin kitso saura kadan na karasa wa wata mata kitso ta dawo daganin shi a gajiya yake lis,. Nai mai sannu da zuwa ya amsa min ciki ciki ya shige ciki nai sauri karasa ma matan kitso na sallamayta na shiga ciki. Na samu yana dakin shi don haka ban tsaya jiran komai ba na dauki tsintsiya na shiga gyaran gidan a gagauce ko da dai bai datti amma kaida ne nayi gyaran saubiyu nan. Ya fito daga daki rai a bace ya wuce zuwa wurin three seater yana tsuki ya zauna nayi saurin dagowa ina duke na sake gaida shi cike da girmamawa. Bai amsa min ba sai gyara kwanciyan da yayi rai a bace mashi yace wai ke wata irin doluwar yarinya ce . Da mamaki nake kallon shi don basan laifin da nayi mai ba yake ce min doluwa kuma na ina kallon shi da mamaki. Ya katse ni da cewa in ba dolewa kike ba yaushe har zaki tsaya uin wani kitso can kin san lokacin dawowa na gida yayi. Kamar zan yi magana sai na duka naci gaba da sharana ban ce dashi uffan ba, wai ashe yin haka dana yi yaji haushi na. Dole dama yaji haushina mana sabda tun da na dawo na hanashi shakat a gidan badai magana nake masa ba amma yana dan daga kafa ga haliyyan shi na banza a gidan. Yau kwana uku kena da naga ya tsiri daukan zafi dani abu ba abu ba zai hauni da fada. Kamar daga sama naji saukan mari a fuskana ina duke sai da na gigice na dago ina dafe da fuskan da har idanuwa na sun fara fitar da hawaye don zafin marin. Fuskan shi babu annuri a cikin sa yace don ubanki ina magana zaki banza dani kici gaba da shara don kin mayar dani dan iska . Na sake kallon fuskan shi tare da nuna razana shi kanshi sai da ya fahinci razana nawa na goge wahayen dake zubo min cikin takaici. Nace yaya may kake son nace maka bance ba ma ka mareni har da zagin ubana balle na tsaya baka amsa. Baiko numfasawa yake fadin na zagi ubanki ko zaki rama ne ya wani zazzaro ido waje. Oh na zaci ai zaki rama ne yar iska kawai mara kunya banza munafuka in anyi magana kice wai ke ta Allah ce ina sanin Allah yake a nan. Cike da tsoro nace dashi Allah ya baka hakkuri, ya buga min tsawa da fadin rufe mun baki mara kunya kawai. Ya harare ni sama da kasa a karo na biyu kamar zai kara buguna sai dai na samu ya hakada ni gefe har ina gwauruwa da bango. Ban sake magana ba na dadafa bango na shige kitchen ina jin shi yana dura min zagi yana fadin duk rana da ya dawo ya samay ni ina shegen kitson nan a gidan nan sai ya balbalani har da mai kitson Ya gaji da fadan shi ya suri key din motar shi ya fita waje tare da banko min kofan gidan a fusace. Na nisa a hankali dana ji fitar shi gidan naceai hali baya barin halin sa kwana biyu bai dake ni ba hannusa na masa kai kayi dana tanka ya samay ni yai ta jigga kamar an turo shi. Na kamala aiki na cikin baci rai kaina namin ciwa kamar zai tsage ina ji ranan ya dawo a buge yana hauka shi ban fito ba karya hada dani. Kwana ki muka dauka a haka a gidan yana faman daukan fushi dani a gidan da zaran ya shigo gidan zai kuna kida na tashi sama kamar kune na zai tsage. Da zara na shigo falon idan yana ciki yanzu zai dauko taba ya kunna yana busa hayakin sama yana tashi ya gauraye falon. Da sauri zan bar abin da nake yi na shige don jin warin nake kamar zan amaye hanjin ciki na kaina ya dinga sarawa. Yauma bai fita ba tun safe yana gida kuma a falo yake zaune bai shiga ciki ba dole na fito hakana ina aiki na. Na gama hada abinci na aje mashi nai wuf zan koma daki na yace ka dakata naja na tsaya. Yana zaune yana ya mutsan fuska yana kallon abincin da na aje a gaban shi kaikace mugun abu na kawo mashi. Ya wani harde kafa yayi kutun kutun da rai yana busa hayaki sama a zuciya ta nace dan isaka ka fada ma Allah ai. Ina tsaye har wani lokaci a wurin amma hakan baisa ya dago ya kalle ni ba duk da cewa ni gyara tsayuwa don ya san dani a wurin tsaye. Dole na gaji na dan yi mai magana dacewa gani yaya gani kamar bada shi nake yi ba shiru yayi yana kallon tv da ke aiki wasu fitsararu na rawa. Na kara cewa yaya gani don Allah kafada min abinda zan wanka nake som naje nayi nai sallah don lokaci yayi. Yayi wuf ya mike tsaye yana nunani tare da daka min tsawa ya sake nuni da hunnu yace ke yarinya baki fini sanin Allah ba don ba ke kadai bace yar musulmai. Idan baki san abinda kike yiba nina san abinda nakeyi kada ki cika min kunnuwa da surutun ki na bashi na dakar dake inji ba. Shiru nayi ina mamakin wanan mulkin malkan da yake min kamar ya sai boya a gidan zuwa ca na nisa nace a hankali yi hakkuri yaya. Ya koma ya zauna yana kokarin bude abincin dake gaban shi , can ya dago yana cewa uban wa zai ci maki faten doya da rana. Tsaye nayi kawai ina kallon shi da mamaki zuciyana yana tafarfasa zangan min uba da yake yi ba gaira ba dalili. Yace a fusace ba tambayan ki nake ba kinyi shiru kin kyale ni, nace nafada maka bamu da koma a gidan ya kare tun kwana biyu da ya wuce.. Wani kallon sama da kasa yai min ya watsar yana cewa wanda na kawo maki kikai barna yanzu ki barnatar da wanda kika gani. Bazan sake sayen koma a gidan nan ba sai wata ya kare don bake nake yiwa aiki ba da zaki ta cinye min kudi a banza. Ikon Allah nace a raina amma a fili cewa nayi dashi yaya ban barnan abinci don ma karya kare ban yin dahuwar rana sai da dare nake dafawa. Yace ke kika sani ni ba ruwa na kin dai ji abinda na fadi kuma ba zan fasa ba don haka ki bace min da gani. Har na juya naji yace dauko min ruwa mai sanyi wanan yayi zafi ya fara cin abincin wayan shi yai kara ya dauka tare da fadin kin dawo kenan don naga nomban nigeria. Ban san may wada yake wayan da ita ta fadi ba naga ya kalli a gogon hannun shi sai yace yau dai duk yadda za ayi zamu hadu. Yana sauraren ta yana murmushi a fuskan shi abin da ban taba ganin yayin ba a matsayina na matar shi. Can yace alrigt sai nazo din amma fa kada in samu baki nan ya aje wayan yana ci gaba da cin abincin sa daya gama kushewa. Ya dago yana kallona nai kicin kicin da rai saurin dauke fuskanshi yayi ya dauki ruwan ya kora ya aje ya mike ya dauke key din shi ya fice daga gidan. Shiru nayi ina mamaki wanan hali na shi na rashin tsoron Allah a gadarance komai yake sam bai tunawa a akwai Allah. Kusan karfe daya dare ina kwance har nayi barci na falka naji dawowan shi gidan ya shigo yana may sai dai bai bugu sosai ba. Don baji yana min haukashi na zagi ba ina jin yana buruntu a falo can naji ya bari nasan ya kwanta ne. Barci bai kara dauka na ba na shiga tunanen wanan halin nashi shine giya shine taba uwa uba neman mata. May zai je ya gayawa Allah tsiyan abin kuma baida mafadi da zai tsaya yai mashi fada da nasiha yaji. Duk iyayyen sun watsar dasu suma suna nasu sharholiyan da muamula da yan iska ta yaya zasu gyara tarbiyan diyan su. Gaba daya ba na gari dan dama dama yaya saadu koshi ban tabatar da halin shi ba tunda bana shedar shi. Ina kwance naji hawaye nabin kuncina zuciya na cike da tausayin kaina ga wanan rayuwan da mahaifina ya zabar min yi . Na tabbatar da i zuwa yanzu baba yana da labarin halin da nake ciki sai dai karfin hali ne kawai irin nasa na jajircewa. Na nisa tare da gyara kwanciya na tsoro da fargabane ta sauka min a zuciya ta anya ko nima bazan kwashi zunibi a wanan zaman ba. Washe gari ba abin da zan dafa mu na a gidan don komai ya kare har wurin sha daya rana can naji motsin shi yafito daga dakin shi. Fita yayi daga gidan na dauke ya shiga gari ne zuwa wani lokaci sai gashi ya dawo da ledan take away a hannun shi. Lokacin ina folo ina tsaka da gyaran gidan babu kunya ya samu wuri ya zauna tare da cewa in miko mashi goran ruwa. Nabar abinda nake yi na shiga na dauko kofi tare da goran ruwan na kawo mashi daidai ya bude take away din nasa. Tozali nayi da rabin kaza sai dan shinkafa a ciki na friderice da aka zuba yasha hadi launin kore shar. Nan ya zauna babu tsoron Allah ta cinye tas ya wurga min roban a kasa yai zaune yana sakatan hakori da tsike yagama ya jawo taba ya aza. Sai da na gama abinda nake yi har sha biyu ya gwauta lokacin ana neman karfe daya na rana. Na fito saye da hijjab dina ina saka takalmi na ya juya a fusace yana fadin ina zaki ? Ban ko numfasa ba nace neman abinda zanci tunda safe banci komai a ciki na ba yayi saurin cewa to wa ya hanaki kice barnan ki ya kaiki ga karar da abincin da na kawo maki ai. Nace abincin da ka kawo min yaushe nake barnan shi gidan nan dudu fa kwano biyu ne na shinkafa kuma ko kazon shi baka taba gani a kasa ba. Kwano biyun ai nayi kokari daso kikeyi na kawo maki buhu komay ai a gida ku ko kwano biyun ana cine na shinkafa. Daya ke nan kon samu banza shine kike barnatar wa ko ta yanzu kici kuma wallahi in kika kuskura kika fita yau sai na balbala ki a gidan nan. Alokaci guda jikina yai sanyi nace kayi ma Allah yaya kayi hakkuri in nemi abinda naci kar yunwa ya illanta ni. Yace bazaki fita ba nace a hankali na matsa wajen shi nadan fara magana a sanyaye cikin kamala nace yaya nasan ka isa ka hana ni fita amma ka tausaya min in samo abinda naci tun da ranan jita wallahi banci komai ba a gidan nan. Yace ke na fada maki don ba zan yarda ki rika zubar min da kima a waje ba a ganki kinje sayen abu ga hannu. Da mamaki na dago ina kallon shi bakunya ya fadi haka kamar ince kaida ka sayo abinda kaci fa yanzu. Nace ya kamata ka tauna maganan ka kafin ka fadi indan ban sayo naci ba may zanci a gidan nan kenan. Yace ke kika sani gobe in na kawo abinci zaki koyi tatalin shi dakyau ya tashi ya shige dakin shi ya barni tsaye a wurin na bishi da kallon mamaki. Ina cikin daki na idar da sallah azahar naji fitan shi daga gidan nan na fito falo na zauna sai ga makwaciyana ta shigo wurina bahausa ce akwai dan nisa a tsakanin mu. Bayan mun gaisa take cewa dani ai tun dazu naso shigowa nasan wanan miskilin mijin naki na gida don naga motar shi a waje . Nace yanzu ya fita bai dade da fits ba ta na bude hijjib din tace ga dan wake nayi damai da yaji nasan zaki so don nan ba arewa bane na kawo maki na karba ina godiya. A zuciya na sai kabbara nakewa Allah da yai min mafitan abinci ts ida ban zata ba bata dade ba ta fice tare da min sallama tace tana da aiki gida. Nai mata godiya na dan raka ta bakin kofa ts fita na koma a sukwa ne daki na hauci hannu baka hannu akushi naci sai da na cinye shi tas na kora da ruwa mai sanyi. Nai hamdala gs Allah da ya bani abin da zanci shi mugun baiga karshe na ba na bude window dakin da sake fanka kamshin ya fita. Bai dawo ba sai bayan karfe tara na dare yazo da ledan shi na abinci da na dan wani bussashe burodi ya wuga min daki na ya zauna nan yaci abincin shi ya koshi ya fice gidan tare kulle ni ta baya. Bai dawo ba sai safe lis koshi don ranan aiki ne nasan zai tafi wurin aiki ya dawo da wuri don kada ya makara. Ya fice baiko bi ta kaina ba na sauke ajiyan zuciya na mike da sauri na shirya zuwa gidan maman biyu don na samay ta gida kada ta fita office. Nayi arziki tana shirin fita na iso gidan tana ganina ta aa Safiya yau da safe haka kika bugo sammako. Maimakon in bata amsa sai kuka bata hanani ba ta zauna tana tare da harde hanneyen ta saman kirjin ta. Sai da nayi mai isata ta miko min ruwa tace jeki ban daki ki wanke idon ki dashi mikewa nayi ta bini da kallo a ranta tace wake da laifi mahaifina ko mijin koko ni. Fitowa na ya katse mata tunanen tace zauna a kawo maki abinci kici nasan baki karya ba wanan sammakon da kika bugo haka. Mai aikin ta ta kwala wa kira tazo tace akawo min abin karyawa aka cika min gaba na da abinci fal na kasa cin komai duk da ina so din amma kincin zuciya ba zai barni naci komai a lokacin. Ta mike zuwa ciki can ta fito ta samu ban taba komai ba daga cikin abin da aka aje min din. Tace aa anty yan biyu bakici bama na lafiya dai zan fara kuka tace dani dakata banson yawan kukan nan ki fada min binda ke faruwa. Dama nasan wanan mijin naka dan iska tuban mazuru yayi ba tuban Allah da annabi yayi ba. Nace wallahi anty dama kin fada ai nace wallahi anty da yunwa yake horoa na yanzu nan na kwashe komai na fada mata . Tace dan iska wai ashe bazan sa a kama min dan iskam mijin nan naki ba aimin maganin sa matsalan kawai mahaifin ki da idan yaji zai tsitsine ki a banza. Anya safiya wana mijin naki kuwa yana cika sallah shi don bai abinda masu imani keyi a rayuwan su. Nace ina fa yake cika sallah anty ibandam dai gashinan ne daga jumma, a sai jumma,a ake yinta . Tace kin ga yanzu aiki zani bari na saka a samo maki abinda zaki ci kiyi ki koma gida don yana iya maki tako yaje ya dawo ya gani ko zaki fita. Tace ki dai kara hakkuri mu gani indan bai daina ba wallahi ni da kaina zanyi karansa a raba wana kaddararen auren naki. Komai aka hado min mai yawa babu abunda babu na fannin girki da ba a hada min ba niki niki na dawo gida da kayana. Taimin alkawarin zata dinga zagayowa akai akai tana dubani nai msta godiya ina kuka tace nayi hakkuri ta kawo kudin ta kara min ta wuce zuwa wurin aikin ta. Ban bata lokaci ba na shiga kawar da kayan kafin mugun ya dawo gidan ya tar dasu ya samu na min iya shege a kan su. Komai na adana su tsab ba abin da na bari a fili na dawo falo na zauna can ko kamar ta san zai dawo sai gashi ya shigo gidan ina zaune a falo. Ko kallo ban ishe shi ba ya shige dakin shi fuskan murtun kamar na yan high killer marasa imani dasu jin kadan ya fito ta sake fice wa na nisa tare da fadin macuci azzalumi kawai ta Allah bataka ba. Kashi dai karfafa ne gashi da tsayi da saje ya kewaye masa fuska a ido kamar kamili idan ka gashi amma duka halinsa ba na saye. ZAINAB IDRIS MAKAWA SEENABU 8/14/20, 7:11 PM - Ummi Tandama: BAHAGGON , , , , , 🧕🏿1️⃣7️⃣🧕🏿 YAR UWA WANAN NOVEL DIN NA KUDI NE IDAN BAKI BIYA BA KADA KI KARANTA HAKKIN WASU PLEASE, , Gani ina gida ya sa ya juya ya fita nasan ba komai ya dawo yi gidan ba abincin da na dauko tun na safe gidan maman biyu shina yini ci a cikina. Mugun bai dawo gida ba sai da magariba ya shigo da leda biyu a hannun shi na dauka wani abu ya sayo ashe wai garin kwaki ne. Dayan ledan kuma kayan break fast din safe da zai karya dashi ne ya sayo ce na dauki garin ni ya sayowa na aje mai kayan tea din shi da safe zai karya dashi. Na dauka nakai saman fridge na aje ashe yana kula dani ban sha ba yace ke garin bazaki sha bane a dakile nace na koshi a harzuke yace kin koshi may kika ci ?. Nace komai atakaice. Kamar zaiyi magana sai ya fasa ya sai ya mike zuwa dakina yana bincike baiga komai ba a dakin ya fito yana kutawa. Yace idan ma baki sha ba ke kika sani ni dai hakkina zaki bani ba ruwa na da rashin cin ki wanan ke ya shafa. Banko dago kai na kalle shi ba na kurama tv da ta shigo ya samu ina kallon super story. Tashi nayi zuwa sallah inshai don lokaci yayi ban fito ba ina gurin da na sallama sallah zaune sai gashi ya shigo daga shi sai gajeren wandon boxes a jikin shi. Kallo daya nai mashi na kawar da kaina don bani son ganin shi a irin siffan nan yace ke bake nake jira bane. Nai dabur dabur na rasa abinda zanyi gashi ya tsure ni da idanuwan shi jajaye kamar garwashi wuta. Yace a dake ki samay ni a dakina ina jiran ki gabana ne ya fadi badai wanan dakin matataran karuwan shi da mashayan giya yau zai ce na samay shi ciki. Dan jin nayi na dan wanj lokaci tunane ya hana zuciya na shakat a lokacin ta shi nayi na bude kaya na na ciro turaren jiki duk na mulke jikina dashi hijjab dina na sallah na cire na nike a saman gado na canza zanin jikina. Ina tsaye ina kara kintsawa sai gashi ya dawo kamar maye yaso kurwa yace yana zazzare ido wai ashe bake nake jiraba ne. Tare da tsura min ido kamar zai cinye ni danya nace gani zuwa ina gyarawa ne yaja tsuki ya fice daga dakin nace kaji dashi dai kazami ko wanka baiyi idan za a kwanta dashi. Na shiga dakin da sallama na yana kwace dadaya saman gadon dakin ga abin taba nan ko ina sakin birjit warwatse a kasa sai kwalaben dake wani gafe a ajiye. Ina shiga ya kalle ni sama da kasa yace mallama dallah zo konji ina da abin yi tun dazu kin shanya ni ina jiran ki. Dan matsawa ni bakin gadon zan zauna sai ko naji ya sa hannuwan shi masu kama da na karfe ya hankado ni saman gadon sai na kai kwance. Tun takwas da wani abu nake dakin bani na fito ba sai daya da wani abu na dare ya koro ni koshi nasan giya zai hada dashi. Ina fita ruwan zafi na samu nai wanka tare da gassa jikina dashi san nan na samu barci sai dai barcin sama sama nake yin sa. Da safe na tashi duk jikina yana min ciwo amma don rashi imani sai da yasa na dafa mai ruwa tea ya zauna yasha ya sha ya koshi bai ko kalli gefen da nake ba. Nima sai harkan gaba make yi ban kula abinda yake sha ba a lokacin har ya gama ya fice na sauke ajiyan zuciya. Golden morn na hada na karya dashi na mayar maboya na boye sauran inda bai gani na sama yan kitso sun zo min don haka nake busy da jamma, a wata mata ce ta gwada min inda ake sayar da wake da bread a area namu. Shi na sayo na ci abanicin rana na sai shan ruwa ya biyu bayan har na gama ma mutun biyar kitso bai dawo gida ba na lissafe in kudina na na soke na gyara wurin kamar banyi ba. Bai ma dawo gidan ba sai dare koda zai shigo a buge ya shigo gidan ranan ko matsin haukan shi baiyi ba. Washe gari sai karfe goma saura ya tashi sai ya hauni da fada wai yaya akayi ban tashe shi ba har yakai rana. Badon na gudu ba da ya dake ni son ranshi da naga yana da niyar bugu na bude gida na gudu sai da ya fita na dawo gidan. Na samu yai baja naja da kaya na yana neman kudi a ciki bai samu komai ba sai dari biyar da na aje canji ya gani ya dauke . Nagyara kayana tare da mayar da komai inda yake ma dafa abinci naci na koshi na dan kwanta falo in huta sai barci masu kitso suka tayar dani kai biyu na kama ranan kawai. ********* ********* ********* Ina sauri in shirya in tafi gidan su gaida gwago na dake fama da kafa kwana biyu bata ko iya tashi. Tsaida ni yayi wai sai na dafa mashi ruwan zafi a gurguje na dafa mashi don an dauke wuta na zube mai ya kewa ya na fito kada ya hana ni in yi laifi gun ta. Yau basu sana a duk yan matan gidan su nan kowa da abinda take yi sai dai masu hira da maza cikin su sunfi yawa. Na shiga duk suka bini da idoban kula su ba na shiga dakin gwago din na bada baya naji sun kwashe da dariya. Na shiga naga gwagon nai mata sannu da jiki tana amsa min da kyat inda ciwo har da hali kamar bata son ansa min. Muka dan zauna tsawon wani lokaci a dakin shiru itace ta kawar da shirun da fadin shi yana gida ne ko ya fita aiki ? Nace yana gida na barshi zai fita yanzu kaita kada min can ta sake cewa ke har yanzu babu ko batar wata sai aukin akawo maki ki juye a masai. Shiru nayi ina wasa da yatsun kafana ta sake cewa idan har kin san wani abu kike yin don karki samu ciki idan na gane ki bazaki sha da dadi ba gare ni. Teema tashigo dakin wanan yarinyar da muka taba haduwa da ita a gidan farin zuwa na tana gani na sai ta washe baki tana min dariya. Duk naje gidan mukan dan kebe da ita muyi hira wani lokaci takan ziyarce ni ko taje nai mata kitso a sace. Yau ma mun samu mun killance take cewa dani ashe kin zo nace eh kwana biyu ban ganki ba tace kin san mutanen namu sai a hankali. Kwana ki hajiya taji natafi wurin ki taita sababi dani ta kar na sake zuwa gidan ku idan na koma duk abinda tai min nina ja wa kaina. Nace o o zuwan kuma da kike yi an maishe shi tsegumi tace ai basa so na je ba don suna ganin zan fada maki abubuwa gamay da mijin ki. Tsaki nayi nace in dai wanan mijin nawa ne mai zaki fada mi wanda ban sani ba tai saurin jiyowa gareni tace akwai shi amarya kedai baki sani ba kawai. Wata sabuwar fuska naga ta fito daga wani daki tana wani shan kamshi tana wani yamutse fuska ta dube mu a wulkance tafita daga gidan. Da ganin ta goggace takwarai yar barikin gaske ce don basai an fada maka ba tafiya ma tana wani girgiza jiki goggagan karuwa da ita. Sai naga teema tayi dariya tace dani kinga ta nan nace da ita eh sai kuma tace bari dai zanzo har gida in fada maki magana baiyi a nan an saka muna ido da yawa. Ban damu da naji komay zata fada min ba muka dauki wani zancen zuwa can naji gaba na yana faduwa da farko na zo da suna yini ne a gidan sai kuma naji bazan iya ba. Nace zan koma gida na leka gwago tana barci don haka na tafi ban sallamay ta ba Sadiya kawai na sama a gidan mukai sallama na tafi. Na murda kofan gidan najishi a bude nai mamaki da har lokacin bai fita ba zuwa aiki ba na tura kofa a sannu na shiga gidan. Gaba daya baka jin komai sai nishin su a falon basu masan na shigo ba sai ihun da suka ji na kurma don gigicewa. Da sauri ya tashi yana fadin ke ke ke may ye haka maynene zaki tara muna mutane akai kamar kin ga wani mugun abu. Ban tsaya saurare shi ba sai na shiga kitchen na dauko yuka na nufo su dashi suna kokarin shigewa daki na nufosu da yuka gadan gadan nai kan yarinyar da yuka sai ya tare ni. Nai cikin su gaba daya suka shige dakin sai da ya kimtsa yafito yaso ya jibge ni nai tsaye nace wallahi yau idan ka dake ni akan wata mace a gida nan sai nayi karan ka wajen yan sanda. Fadin da nayi bai yarda ba sai da taji nace dama maman biyu tace ko harara na ka sake yi na fada mata ai karan ka. Jin na ambaci maman biyu yasa ya dakata dako har yana nade belt zai shirin jibgana dashi yaga banza. Amma duk da haka sai da ya tureni na fadi gefe na shiga bakina ni kaina naji mamakin kaina da na dake nai masu yankar kauna a gidan. Ta fita tana wani taunan chewagun sai lokacin ma na gane ashe wanan yarinyar mai sallon da na gani gidan su ne wurin gwago. Ta kalle ni a wullakance tace kin dauki bashi in dai wanan ne a tare kika samay mu tare kuma zaki barmu. Ta wuce gaba yaba binta baya suka fice a gidan nasa hannu a kai nace ba shiga uku nikan nawa ya samay ni. Dama abinda teema tai niyar fadamin kenan ta fasa naji dai tsna cewa ki tafi gida yanzu kada ki wuni a nan . Naso na tambaye ta sai na share kuma don ban gane manufanta ba don tace magana baiyi a gidan sai dai tazo. Wanan karon na turza na kafa mashi cin mutunci banji tsoron shi ba yace ke ki rufe min baki Liliya ta fiki komai ke inba kaddaraba may zai kaini aure ki. Nace kamar yadda ka zamu min mijin kaddara a rayuwana in badon darajan iyayye ba mai zanyi da dan giya mazinaci a rayuw, , , , Marin da ya kwashe ni dashi yahanani karasa abinda zan fadi ya samay ni ya mamara awurin yakuma ce. Auren Liliya zaiyi ko da ita taki shiyasa uwarshi ta aura mashi ni don ya manta da Liliya. Nace auren ku bai damay ni ba zina daine bazan yarda ashigo har cikin gida ai min ba yace tunda gidan ki ne sai ki hanani abinda nake so yi. Ranan dai munyi shi ba dadi yafice yabar min gidan bai kwana a gida ba washe gari na shirya zuwa gidan maman biyu. Na samayta a gida bata fita aiki ranan na bata labarin tace ni wanan mijin naki na rasa wani iri dan iska ne safiya ai mashaya giya wasun su basu damu da mata ba. Nace anty shi fa tatirin dan iska ne na gaske tace aiko ba irin ki ya kamata ya aura ba daidai dashi ya kamata ya samu yar iska irin shi su saje. Amma ke ai cutar ki zai ta yi a banza don baki saba da abin yan bariki ba ni fa ina jin tsoron kar ya kwaso maki karuwa su halaka ki. Nace nima anty abinda nakewa gudu kenan wallahi yau wanan tazo gobe ma wata zai kwaso duk a mutum daya. Tace Allah dai ya kyauta ban dawo gida ba sai yamma lis koda na dawo gidan yana nan kamar yadda na samay shi alamu sun nuna bai dawo ba har lokacin. Na kule gidan na shige dakina bayan na gama abinda nakeyi ne na kwanta can cikin dare naji dawowan shi na fito na bude kofan ya shiga ciki. Fuska a daure babu walwala nima haka na daure fuska na ina budewa na wuce zuwa ciki abina na kwanta. Da safe kafin na fito yayi sakkon barin gidan duk da yake weekend ne a lokacin amma sai da ya fita gidan . Can yan iska irin shi fada ya hada su sukai mashi dukan tsiya akan Liliyan Allah ya rama min ya dawo gida jina jina dashi. Nan ya zube min a falo yana kwala min kira na fito da sauri yace taimaka min da ruwan zafi na gasa kafa na. Nai kamar kada insa sai na tuna da hadisin da kecewa Aljanan ku na karkashin kafan majajen ku. Da taimakona ya samu ya gagasa jikin shi da kyan ya samu barci koshi sama sama da safe jikin yai masa tsami sosai. Kwana biyu bai iya ko dagawa nan yan iska suka shiga shigowa gida maza da matan su wai sun zo gaida shi. Naga mutane iri iri a gidan wurin dubiya sai na kara tsunke ma alamarin shi a raina nasan ba karamin dan duniya bane ashe nake zaune dashi . Harda maza masu kitso mata masu dan buje iya cinya da sauran su inaji harda shugaban yan giyan lagos yazo gaida shi wasu in sun zo su bani alheri in sun tarar dani a falon wurin shi don boyewa yake cewa nayi kada su ganni wai yana jin kunya ace nice matar shi. Gashi ina jinya shi amma sai zagina yake ba kakautawa ranan sai ga mahaifiyar shi tazo ankawo ta ta gaida shi nan na dan ji abinda ya faru da kyau wurin ta. Sun sha sun bugu ne sai wani yazo yaja liliya sai ya hana su kuma suka tarar mashi sukai mai dukan tsiya sai da aka kwace su. Abinda yasa bai je asibiti ba yan sanda zasu cisu kudi sosai ne shine akai rufa rufa yake jinya a gida. Bayan su gwago sun tafi daki na shige naki fitowa yai kira kamar may naki fitowa waje da ya matsa min sai na leko nace kira karuwan ka tai jinyar ka mana . Ita da kaje fada don ta da ya dauka baza iya ba sai yaga na koma daki na rufo kofana nabarshi zaune a falon. Zagi kan na sha shi a wurin shi amma baisa na fito ba sai da safe na fito yana zaune yana gyan gyadi saman kujera yana jin motsina ya bude idon shi da sukai ja yace don Allah taimaka min nai brushe kafan nan ya matsamin da ciwo. Nace karuwan da kai fada a kanta bazata tai maka ma bane ai ita ya kamata tai jinyar ka ba ni ba. Ya marairaice yana cewa don Allah taimaka min asibiti zan koma a duba min kafar kamar zan share shi sai dai na taimaka mashi yai wanka. Ranan harda sallah akayi amma saidai a zaune ya ban kudi wai a sayo abin karyawa na safe na hada yace na taimaka mashi yaci sai wani cika nake da batsewa. Yadawa asibiti da rana sai ga yar iskan ta shigo muna gida da kawayen ta nan suka zube falo ana ta tafka iskanci da iya shege a folon namu. ZAINAB IDRIS MAKAWA SEENABU 8/14/20, 7:11 PM - Ummi Tandama: BAHAGGON , , , , , , 🧕🏿1️⃣8️⃣🧕🏿 YAR UWA NOVEL NA KUDI NE IDAN BAKI BIYA BA KAR KI KARANTA HAKKIN WASU PLEASE, , , Satin shi guda cur a gidan yana zaune yana jin ya Lilliya takar itake jinyan shi kusan ma a gidan take kwana nai magana ya zundumi ubana tun lokacin ban sake kallon su ba. Idan dai gari ya waye zan masa ina kwana da yaya jikin idan tana kusa zai amsa min da kyat kamar baya son gaisuwan nawa. Sai in bata kusa zan samu ya dan amsa min har yasani wani abin in mashi ranan maman biyu tazo duba shi ta samu Lillya mane dashi. Ya dan ji nauyin hakan amma abin su na yan duniya sai bai nuna a fili ba ya basar ta kasa yin shiru tace wanan fa da take manne dakai haka. Matar kace ko mai, sai yadan yunkura yana cewa No kawatace take dubani. Kallon mamaki taimai tace amma kasan hakan ba daidai bane agidan ka wata karuwa zata shigo ga matar ka na sunna da sunan wai tana duban ka ai duk abinda zakuyi ku tsaya iya waje ku yi shi. Lilliya ta dago kai tai mata wani kallon banza tace ke wacece da zaki zage ni da sunan karuwa ai karuwancin ma isa ne ko. Tace OK yanzu zaki san ni ko wacece ya dago da sauri yana ce mata will you keep quite. Take ta har zugo mashi maman biyu batai mata magana ba ta mike zuwa kofa ta sa mashi key ta rike ke din a hannun ta. Waya ta dauko tai kira dashi aka amsa mata sai lokacin suka kulla da ita Lilliya ta dago tana cewa may zaki yi in bariki ne nafiki iya wa tace bissimillah ina son yau inga iya barikin naki. Taso taja da ita jacket din dake jikin ta tacire sai uniform din ta ya baiyyana dakatar da abinda tai niyar yi mata tayi tana cewa haka kawai zaki zageni. Karyan bariki kike yau zan gwada maki akwai wa yanda suka fiki suka riga ki shiga bariki da lasisi. Mari takai mata naji dadin hakan daga inda nake tsaye a rakube jikin kujera. Taso turzawa amma karfi ba guda ba take ta murde ta kafin tai wani abu aka fara dukan kofan ta je ta bude sai ga kartan sojojin tsaye a kofa ko wani a cikin shirin shi. Hakkuri ta fara badawa harda shi munafukin yana cewa madam don Allah ayi hakkuri rashin sanin ke wacece yasa tai maki haka. Arest her tace da su take ko suka kamata saura shi tace shima a tafi dashi fuskata babu burbushin rahama take maganan. An fice har dashi a gidan wani dadi ya kamani sai hawaye bata ko tsaya ta kaina ba ta fice gidan itama ta bisu. Daga inda nake tsaye a cikin fargaba da tsoro na mara masu baya ina tsaye motocin su suka wuce dasu. Ko ba koma yau maman biyu ta daukan min fansan wullakacin da ake min a gidan don ya gama zagine ke nan a kanta ta shigo gidan ta samay ni daki ina kuka nasan abinda ya kara harzuka ta kenan. Ina zaune takure a cikin damuwa sai gashi ya dawo duk ya jirkita azotana da yadawo zai hauni da duka da zagi yadda ya saba ne. Sai gashi naga sabanin hakanan ya dawo ya bukaci ruwa masu zafi zai gasa jikin shi dashi sai kuma dan abinda zaici. Yana zaune bayan ya fito wanka ga abinci a gaban shi yace Safiya ina daki na amsa masa na fito kujera ya nuna min da hannu alaman wai na zauna. Sannu a hankali na kai zaune saman kujeran ina fuskantar shi tare da sauraren abinda zai fada min a lokacin. Yace kin dai ga yanda wanan matar suka yi a gidan nan ko na dago kaina a hankali ns dubeshi ya tsare ni da idawan shi. Na sake dukar da kaina kasa ba tare da na amsa mashi ba yace yanzu dai ba wanan ba abinda nake so dake shine. Kiwa ita madam din nan magana a sake Lilliya don ba karamin tsaro sukai mata ba yau kawai duk ta jemay saboda tsaro da horo irin nasu na sojoji. Ban san cewa girman ta da kimarta yakai haka ba sai yau din nan da na gani ke kaidace zakiyi magana a saki Liliya da sauri inba haka ba abin zai jawo min matsala sosai gani zaune gida banda lafiya. Banyi magana ba naji yana cewa umurni na baki ba son jin raayin nake so ba ki mata magana a sake ta. Na nisa nace shike nan kiran yace eh shike nan nake so ki fada mata a sake ta. Na mike ina ce mai ai da kai kai mata magana zai fi don zata fi jin maganan ka sama da nawa do ni ban san ta inda zan dauko mata zancen ba. Rashin mutunci tai mata ta dauki mataki ta dauka irina ne da kuke wa son ranku a gidan ku taka ni iya son ranku a zauna lafiya. Ni banga laifin maman biyu ba da ta dauki mataki ga marasa mutunci irin ku wayan da basu san darajan aure ba. Ke ya isa ya dakatar dani ta hanyan daga min hannu shi yace umurni fa na baki in kina son kanki da lafiya gidan nan kiyi abinda na umurce ki da shi. Fuskan shi babu alaman sauki gare shi don haka na juya na tafi kawai ba tare da nai wani magana ba. Da safe nai sammakon zuwa gidan maman biyu nayi sa a tana gida kasa na zube ina mata godiya ga hawaye na zuba a idona. Ta ce assha safiya tashi tashi don Allah may ye hakan ai dole a tausaya maki don kinyi karanta da irin wanan rayuwan. Dudu fa baki kai ashirin ba amma kike fuskantar wanan bahangon mijin naki mai rayuwan kazan ta. A gaskiya dani wata ce a cikin zurian ku da sai ince a raba wanan auren don baida alaman nadama ko gaba duk kaga namiji yakai haka alamarin akwai ban tsoro cikin sa. Nace yanzu ma shi ya turo ni akan nazo na baki hakkluri a sake ta wai idan ba haka ba zan gane kurena gare shi. Tace da sauri kinji ba na fada maki ai baida nadama ko kadan ai dana sani abarshi can shima amma sai na tausayama luluran da yake ciki. Gaskiya naso yin wani abu akan zaman nan naku amma sai ina ganin kamar ciki ne dake . Nai saurin dagowa ina duban ta a gidimay nace ciki kuma anty tace tabbas indan ba hasashe nake yi ba kina da shigan ciki. Gabana yai mugun faduwa tace yaushe ne rabon dakiyi jini a tare dake ? Nai shiru ina nazari can nace gaskiya wata uku kenan tun da nayi ina gida ba sake yi ba. Tace shit, Zargina ya tabbata gaskiya akanki na dade dama ina zargin hakan amma zan sa aimaki test a gani. Yanzu ki ci abinci zanyi waya a sake ta don ba imani ke ga irin su ba tare suke da yan daba sai dai da yake zamu kafa hujja akan in wani abu ya samay ki nan da shekara biyar itace. Naga tasa akawo mata abinyin test ta auna fitsari na ya nuna positive alaman ina dauke da cikin wata ukun. Nai bakin ciki da jin wanan labari kwarai da gaske munyi sallama zan tafi take cewa in kwantar da hankalina killa sanadiyar cikin nan in samu sauki a gurin shi don wasu maza nason yara. Ta dan bani shawarwari masu mana ta cika ni da abin arziki na bar wurinta zuwa gida zuviya ciki da bakin cikin labarin cikin dake jikina. Yana zaune ya kura ma tv ido na shigo bako kin dawo sai cewa yayi yaya kin samay ta a gida ? Nace eh na samu dama zata sa a sake ta saboda kai koda banje ba din tace abin da tayi matane ya bata mata rai ai. Bai yi magana ba kuma naji ta yadauki waya kowa yake sanar ma zancen sakin nata oho nadai ji ya dade yana waya din. Nikan abinda ya damay ni ya damay ni zancen cikin dake jiki nakewa bakin da nadama ina tausayawa rayuwan da abin cikin cikin nawa zai taso ya ga ubanshi nayi a duniya. A haka ma ba tarbiya yaya za a ce aiwa yara tarbiyan rayu kirikiri bani shiga mutane duk da bariki ana cewa ba ruwan wani da wani . Ina ganin barikin dane bana yanzu ba don wata mace da tazo kitso ya dawo ya shigo murtun compound din tace . Na dis yeye man you marry , . Dis man too dey follow women . Murmushi nayi mata kawai ban bata amsa ba sai wata da take zaune ne tayi mata magana da cewa hakana fa ba kyau. Sai tayi shiru damuwa ya isheni da fargaban halin da zan shiga nan gaba a garin mutane . Sai wuraren sha dayan rana aka sako lilliya daga hannun sojoji bayan tasha dan banzan wahala. Haka ya daure ya fara fita tun wanan ranan baya zama gida yana wurinta acan kafar ta karasa warkewa a hanya. ********* ********* ********* Yau na tashi jikin ba dadi ga damuwa dana sawa raina ga kuma halin maigidan ba sauki akan komai. Kwace nake a falo saman dogon kujera nayi da daya da kafana ko zan ji dadi jikina misalin karfe biyar na yamma. Can na fara barci naji dawowan shi gidan yana gauran kofan shigowa gidan gabana ne ya fadi don ganin shi a murtuke da fuska. Innalillah wa,inna ilaihi rajiun Allahuma Ajirni min musibati waakhimi min kharir minha na anbato a raina. Ya shigo yana ta faman kalle kalle har ya kai zaune saman kujera tsoro ya kamani don ban an damay ya shigo ba. Na dago cike da natsuwa da girmamawa na furta sannu da dawowa bai amsa min ba sai taba da ya ciro cikin aljihun shi yana kokarin kunawa warin taban ya gauraye falon lokaci guda. Na mike da sauri zan bar falon sai lokacin yai magana yace ke mayye haka kuma ? Ina kokarin tare aman da yazo min a baki nace zan zan zan sai na mike da gudu na fada dakina direct makewayi na shiga nai ta shega amai aciki. Bina yayi da kallon mamaki bai yarda dani ba, ya mike ya bini yana tsaye nake ta aman sai da nagama na mike zan fito naganshi a tsaye ya rike kugun shi. Gabana ya sake faduwa yana min wani irin kallo na tuhuma mai kama da bai yarda dani ba yace ke mai ke samun ki ke amai haka. Na amsa dakyat da cewa ban da lafiyane . May ke damun ki koma may nene ke kika sani don ni banda lokacin ki ya juya har ya fara tafiya ya juyo yana ce mun ki sani ban son kazanta a gidana. Na yamutsa fuska nace kona bata ma aini ke gyarawa ba wani ba ya juyo yace may kika ce ne ? Nace bada kai nake ba ai yace shgiya naga randa bakin nan naki zai mutu da bakar magana dibi yadda kika murje kikai wani bulbul dake duk abincina kike cinyewa ga banza. Yafice na sauke ajiyan zuciya na zauna nadan huta na fito kai tsaye kitchen na fada don girka abinci don nasan a gida zai kai dare tunda ya dawo da wuri. Na gama aiki da kyat na shiga na watsa ruwa don lokacin sallah ya gabato ina zaune ina lazimi naji ya kwala min kira. Na taso dagani sai yar doguwar rigan da anty ta bani ranan da naje gurin ta tace ta gani ne dataje sayayya ta sayo min shi. Na fito abincin da na aje mai yana bude na sauke idanuwana akan abincin dake gaban shi din. Ya watso min harara yana cewa wani irin abinci kika dafa haka nace shi kadai ya saura muna a gidan shiyasa na dafa taliya ne nai jelop din shi. A fusace yace what, what are you saying ? Kina nufin har abincin da na sayo yakare komay ? Na girgiza kai nace yaushe rabon da ka sayo abinci a gidan nan wanda ka sayo din ai shi na dafa lokacin da bakada lafiya masu jiyan ka suka cinye. Ya dakatar dani da hannu yana fadin ya isa haka maganan ya isheni sai ki zauna ki cinye dama haka kike so ai. Ya dauke makulin motar shi dake saman tabur yabar gidan yana faman huci. Sai da muka share kwana uku cur ban da lafiya kuma ba a girka komai a gidan. Ina kwance daki ina fama da kai na nidai kamar kar maman biyu ta ambaci cikin nan wahala ya soma zuwa min. Sai kawai gashi ya shigo min daki misalin goma na dare don rashin imani irin nashi sai ji nayi ya afka min . Na soma kuka ya gama ya daga yana cewa may ye haka tsiyan azo wurin ki kenan walahi ki damu mutum da munafukin kukan ki. Na dago ina cewa azo min haka kamar wata karya ni kadai nasan abinda nake ji a jiki na yanzu haka ji nake kamar baya na zai tsage san nan ban ci komai ba tun safe ga yunwa na damuna. Yakai kofa ya juyo yana cewa ai sai ki samu abinda kikaci ko kije asibiti adubaki nace da nawa zan tafi asibitin yace ke kika sani. Washe gari ma da ciwon na tashi don da dare banyi barci ba ciwon mara ya hanani shakat a rayuwa na. Ban fito ba har ya gama shirin shi zai fita komay ya gani sai ya leka dakin nawa. Ina kwance ina faman murde murde a saman gado ni kadai a dakin ya leko yadan dade tsaye akaina sai ya karaso bakin gadon yana cewa. Wai ke may ke damuwan ki ne haka kike faman murde mude a gado ke kadai a dakin ? Da kyat na bude bakina nace cikina ke ciwo sai kaina dake sarawa kamar zai balle min nake ji. Ya fita da zai dawo sai gashi da magani da maltina da peak milk mai sanyi a leda da kayan abinci ya sayo. Ya samay ni a falo na yi laga laga dani ya miko min maganin da maltina yana cewa ga magani ki sha. Nai mamaki ganin magani harda maltina ya sayo min babu kunya babu alamanta ya zauna yana cemin tashi ki sha. Da taimakon shi na hadiye maganin sannan ya hada min maltina da madara yace in shanye kafin ya fito. Bayan kaman minti shirin sai gashi ya fito ya dubeni yace yanzu ya fada maki ko yana nan ? Nayi ajiyan zuciya nace ya fada min nace na gode yace na taimaka maki ne don nima kin taimaka min da banda lafiya don haka arama ma kura aniyan ta. Na ciza baki na yunkura ina cewa aiko kura ta gode in don Allah akai mata. Ya harare ni yace gunma ki wartsake don ba zan dauki nadewa a gado ba tunda kun hanani hurda da yan mata na yanzu. Na saurin kallon shi ina cewa wa ya isa ya hanaka da abinka muka ganka mu mun isa wanan sai Allah daya hallice ka ai. Sai kawai naji ya kyalkyale da dariya sai nai saurin dago kai na kalle shi cike da mamaki yau shike dariya haka kamar ba shi ba. Yace ashe kun san da haka da baki wahalan hada baki da matar sojs tashigo abin da bai shafe ta ba. Ya fice ban sake jin duriyan shi ba sai dare sai gashi ya dawo min a cikin maye yana ta tsuki burutsun shi a gidan. Ina daki ya samay ni a haka na dan dago ina kallon shi naga ya nufo ni gadan gadan sai na fashe mai da kuka don na san halin fitinar shi sarai ba imani ne dashi ba. Yace a cikin maye ke ke may nene haka ? Na yun kura na tashi da kyat ina cewa don Allah yaya kayi hakkuri wallahi ban iyawa banda lafiya ne. Na gaya maki zan maki wani abune kawai kawai yana inda inda ya kasa fadin abinda zai fada din ya juya yana suruntun abinda banji ba ya fice dakin. Na lumshe idanuwa na a hankali ina sauke ajiyan zuciya ganin ya fita natashi na rufe kofan dakin nawa. ZAINAB IDRIS MAKAWA SEENABU 8/14/20, 7:11 PM - Ummi Tandama: BAHAGGON , , , , , , 🧕🏿1️⃣9️⃣🧕🏿 YAR UWA NOVEL DIN NAN NA KUDINE IDAN BAKI BA KADA KI KARANTA HAKKIN WASU PLEASE. Kwanaki goma sha uku da aukuwan wanan lamari yana zaune a falo ya harde kafa yana shan ruwan kwalba da sigari yana sha yana yamutsan fuska kamar an sashi dole ya sha. Na fito daga daki rike da cup a hannu na ban san yana zaune wurin ba sai ganin shi nayi yana korawa. Da sauri na wulkita zan juya dakin da nafito ganin haka yasa shi mike a ida yake zaune din ya nuna ni da hannu. Ke ban san sau nawa zan fada maki cewa idan ina zaune kika gani ki daina gudu kamar wata mara gaskiya dake. Nikan ban masan yana yi ba don na dafe bakina da hannu daya kar amai danake ji ya fito mun a falon. Ganin yanayin da nake ya dakatar dashi ga fadan da yakeyi din ya kafa min idanu yana kallona a cikin zargi. Yace Safiya ciki gare ki ne ko may ban sani ba don tun ga kwanaki naga kina wanan aman na tsiya. Nikan ban ma san yanayi ba ina tsugune na dafe kaina sai kakarin amai da nakeyi a ban dakin . Hakkali a tashe ya sake magana da cewa kefa nake tambaya na dago da kyat ina cewa cikin yanayin ciwo warin taban nan ne ke wahal dani. Ya ja tsuki ya juya yabar wurin dakin shi ya shige da bacin rai bai fito ba haka nima ban fito ba na kara dunkulewa cikin dakina. Kwana biyu baya gidan ban san ina ya shiga ba ga komai ya kare min don haka na shirya zuwa gidan maman biyu. Yanayi na kawai ta kalla tasan ban jin dadin jikina yace wai ko kunje asibiti kaina girgizamata kawai alaman a a. Safiya kamata yayi ki fito ki sanar dashi zancen cikin nan amma ba wai ki boye ba don ba zai yuyu kibar ciwo a jikin ki ba don ciki ciwone. Nace to Anti shidin ne almarin shi har yanzu ba canji kin ga tun kwanaki ya gane bana jin dadin jikina amma don rashi imani yau kwana biyu kenan baya gidan kuma ban san ida ya shiga ba. Idan ma yana nan ba wai kyaleni zai ba don banda lafiya haka zai afka min kamar dabba don rashi imani irin nasa. Tace ke Safiya kar in sake jin kalman dabban nan a bakin ki, karki manta shifa mijin ki ne na sunna. Nace anty ai ba fadina bane, Annabi nefa ya siffanta duk mai irin wanan dabian da daba, sannan sai kinga irin wahalan da yake bani abin har da mugun ta yake hadawa. Wai in mun hana shi bin mata banza waje ni zanji a jikina tunda nace ina iyawa. Sai na soma mata kuka tai saurin cewa may ye haka kuma safiya ko so kike ki tada min hankali ? Ina kuka nace wallahi anty ba haka bane wallahi ni kadai nasan abinda nake ji ajikina yanzu haka idan indan ina tafiya jire nake gani marana kuma kamar zai tsage min biyu nake jinsa sanan na kasa sa komai a baki na komai naci sai ya dawo min. Tace ya zama dole ki dada masa idan bai dauki wani mataki ba ki zo kifada min kina jina ko don ba a zama a duhu haka kina jina ko. Nace naji zandan kwanta kozan samu barci yanzu haka jiri nake gani tace inshiga daga ciki don kar a dameni nan falo na kasa barci. Na samu nayi barci sosai sai wajen uku na rana na farka daga barcin naji dadin jikina matuka don naji kaina yabar sarawa. Nai sallah naci abinci sannan na fara shirin komawa gida ta harhado min komai da zan bukata zakace ko uwatace ko wata yar uwana ta jini abinda take min. Kusan karfe hudu da rabi na dawo gidan na danji saukin jikina ko banza nadan samu warwarewan zuciya na dana dan samu idan da na tsiyaye. Har na dawo na dan gyara gida tunda na samu karfin jikina bayan nai sallah ishai ina kwace saman carpet ina kallo ya dawo gidan. Kai tsaye dakin shi ya wuce bai fito ba yan yai wanka ya fito saye da guntun wando da singlet sai taba a hannun shi. Bai same ni a falo ba yayi zaton ina dakin girki ne sai da ya saurara sannan yajiyo kakarin amai daga daki na ina cikin ban daki. Ya mike da sauri zai bini sai gani na fito ina tafiya kamar wacce tayi makwanni cikin ciwo ya dinga sata kallona har na dawo inda na tashi saman carpet na kara kwantawa. Na daure na dago kai a hankali nace dazun ka dawo ina gaisheka baka amsa min ba ido kawai ya tsura min baiyi magana ba. Sai cewa yayi tashi muje chemist a duba min ke ban yarda wanan uban amai da kike min haka ba cikin gida in an yi magana kice babu komai. Ban mussaba na yunkura na tashi daki na shiga na dauko hijjab dina na fito ya kulle gidan muka wuce chemist din da yace. Sai daya bata lokaci sosai yana dudubani don har fitsari yasa nayi ya auna ni ga dan karen tambayoyi da yake min har na gaji da amsawa daga karshe dai ya bashi tabbacin ina da ciki wata hudu da kwanaki. Ya bani magunguna da zanyi amfani dasu don taimaka min wurin rage aman da nakeyi don acewa mai chemist din yawan kakarin da nakeyi yasa cikina kullewa . Amma ba ciwo bane mai tsanani don haka mu kwantar da hankali mu tunda ya fara magana yake gum baiyi magana ba sai mur din da yasha. Hakan da yayi yasa nasan akwai magana fan a zuciyar shi dama kuma abinda nake gudu ke nan ban yi saurin fada mashi ba. Ya sallami mai shagon muka kamo hanyan gida har lokacin yana gum da bakin shi sai da muka shiga gida na yi hanyan daki na sai kawai naji ya shakoni ta baya. Idanuwa suka firfito waje kamar zan shude yace a hasale uban wa yai maki cikin da kike dauke dashi nace . A lokacin da yasan bakin cikin da nake ciki nafi bukatan ya kashe ni in huta da wanna rayuwan wahala da na samu kaina a cikin sa. Jin kaifin shakan yai yawa nace uban da yake matseni duk dare yai min dole ka taba kwana dani a cikin yarda nane a gidan nan. Ya kara shako ni yana fadin yar iska sai ki san yadda zakiyi da cikin nan inba haka ba na lahira sai ya fiki jin dadi. Nace cikin karfin hali amma kadai san ba yar iska ka samay ni ba ko bantaba kwana da wani namiji ba bayan kai a rayuwa na da zakai min wanan tambayan yan iska. Yace good sai ki san yarda zakiyi da cikin nan a gidan nan don ni ban shirya haihuwa ba yanzu yara su hanani shakat a rayuwa na. Ras naji gabana ya fadi nace wata sabuwa kenan kuma inji yan caca wani sabon fitina kuma zai kawo min yanzu. Hakana mukai ta jidali a gidab dagani sai shi daga karshe dai ya kaini kara wurin ma haifiyar shi akan lalelale sai na zubar da cikin nan in ina son a zauna lafiya. Babu kunya ta kirani nazo gidan ta ta tare ni da maganan cikin har tana cewa nafison in cika gida da yara miji baida wadata. Nace Allah daya bani shi zai dubeni da abinda ke cikin cikin nawa don haka na san zunubin da ke ga wanda yai kashin kai ni ba zan zubar ba. Tace tunda haka kiks zaba duk abinda yai maki ke kika jiyo baruwa na karma kice kin sanni. Ranan ban kwana ba sai da yai min dan karen dukan tsiya har ya barni kwace da kyat na lalaba naja jikina zuwa dakina. Washe gari jikin yai min tsami na lalaba nai wanka na lalubo sauran magani na hade na koma na dun kule. Waya naji yana yi da wani likita akan zubar da cikin koda ya leko dakina na lafe kamar mai barci sai ya fice gidan. Ina nan ina sake zuci sai sallaman maman biyu naji gidan don tun ranan da suka samu matsala akan lilliya bata dawo gidan ba. Yau tazo taji yadda mukayi dashi ne akan zancen cikin na tare da murna na abinka da wanda ta rigaka kwana sai ya rigaka tashi. A take ta gane yanayin da nake ciki na bugun da yai min a daren jiya kan naki yarda a zubar da cikin cikin sauki. Tace dani kunyi halin naku ko, ? Kin sha dukan ko badai duk akan cikin bane wannan dukan haka ? Idana sun ciko da hawayen na dama nace anty cewa yayi wai a zubar da cikin shi bai shirya haihuwa yanzu ba. Tace a cikin mama what ? Na hade wasu yawun bakin ciki nace har da maman shi abinda tace dani kenan wai idan ban zubar ba duk abinda ya samay ni ba ruwan ta. Kai ta dafe tai shiru na wani lokaci can tace wai wa yan nan mutane kuwa musulmai ne kuwa ? Na murmusa nace wai musulmai ne kuwa anty babu dai tauhidi a zukatan su ne kawai. Ta mike ta fice gidan kai tsaye ashe wurin aikin su ta tafi don ta bincika tasan komai akan shi. Can ta samay shi tace su hadu gidan shi yanzu sanin halin shi da tayi yasa baiyi gardama ba ta riga shi isa gidan ya samu tana jiran shi. Yana shigowa tace zauna shagon mata don ka zama shagon mata baka da aiki sai dukan mace macen ma karamar alhaki irin wannan. Dadin may kake ji cikin dukan da kake mata ne wai, kai bama wanan ba cikin dake jikin ta waye mata shi ? Ya dago ya kalle ta don jin abinda ta fada tace eh ina son inji ko ba naka bane don musan abin yi. Yace kin gane madam nasan ciki nawa ne to amma ni gaskiya ban shirya, , , , Sai yai shuru tace, go on, baka shirya may ba dama ka auro tane kawai don ka more rayuwan ka da ita ko may ? Tace tirr da hali irin naka tirr da rayuwan kafiran farko kai acikin su ma kana kasa da fir,auna. Ashe kai ba abin farin ciki ne ya samay ka ba maimakon ka godewa Allah da baiwan da yai maka sai kawai kai halin ku na yan duniya. Ba a haihuwa kai aka haife ka, dama kenan ka auro tane don kawai kaji dadin rayuwa da ita ko may tun wuri ka gyara halin ka tun duniya nayi dakai. Tai mashi kaca kaca yana saurare ta kamar wani salihi can dashi ni nasan jin ta kawai yake yi badon nasihan ta shige shi ba. Ta nisa tace dashi haba dai kamar wanda baida tausayi katuna fa kaima kana da kanai kuma haihuwa zakayi indan anyiwa taka haka yaya zakaji. Sannan ina son ka sani idan wani abu ya samay ta, ko cikin dake jiki ta sai nasa an daure kowa naka a duk inda suke a garin nan sai antona man su. Kuma ka tabbatar da kana bata abincin daya dace mace mai ciki taci dan lafiyan jikin ta dana baby dake cikin ta. Duk ta baibaye shi ta ko ina baida halin motsawa ta mike tana gyara gyalen jikin ta, ta wuce ko kallona batayi ba ina kuka da mahaifina da ya jefani wanan halin. Ya dinga sintiri a cikin falo yaje ya dawo har na wani lokaci ya dawo inda nake rakube yace ke ki fada min may ye hadin ki da wanan matar. Nai shiru ya kara daka min tsawa yace ba zaki fada min ba, nace yar uwan mahaifiyata ce na fada maka tun farko sai ya ja tsuki ya fice gidan. Tun wanan lokacin bai ce min ban ce mai zaman doya da manja muke yi dashi a gidan sai ya kwashe kwanaki bai gidan sai yaga dama zai dawo bai dadewa kuma ya fice. Nima haka ya fiye min dadi don ba matsi ba tsagwama ba warin taba da giya sai in yini falo gidan hankalina kwance. Abinci dai da maman biyu tasa mai doka ina samu sai dai bamai dadi ba amma ina ci in koshi ko ba dadi yafi babu. Ranan ina zaune a falo ina kallo sai gashi da liliya yana gaba tana binshi a baya da katon akwatin ta, suna kokarin shigowa dashi. Wai ashe auren bariki sukayi, yan giya yan uwan su suka daura masu aure acan mashaya su. Ko kallona basuyi ba suna kokarin shigewa da kayan nata, ina zaune ina kallon ikon Allah, suka shige dakin shi da kayan can sai gata ta fito ta bude munafukin gyalen da ta rufe fuskan ta dashi tace. Ke wa kike da suna ina son fada maki ban son ganin ki a falon nan indan maigidan na gida in ba kiran ki akayi ba. Nace ke kuma a suwa dan wake a hotel, tace ni a su matar gidan, inda ance min karuwa yanzu na zama matar gidan sai a nemi wani suna a canza min. Ya wuce a kiraki da kilaki ko mai dadiro don sunan da ya dace dake kena don kin fi cancan ta dashi. Shine ya fito yana cewa baby na fada maki bani son kina shiga tsabgan yarinyar nan, da ita da babu duk daya a gare ni tana zaman cikin ta ne da tace taji ta gani dashi. Kema kin san wanan ba ajina bace kawai dai matsala aka samu aka aura min ita amma wanan abar ai da gidan aiki ya kamata ta a danganta ta. Nace andai ji kunya wallahi tunda dadiro aka fake aiko anci baya wallahi ya balla min harara da jajayen idon shi. Yaja ta suka shige ina jin suna dariya dariyen su a dakin ga kida na tashi ina daga dakina bakin ciki ya cika ni. Haka dai muke zaune a gidan ba ruwan shi dani ina kallo zasu sayo abu su zauna a falo su baje suci inya rage a zubar ga abin shara. Ko ta dafa da kanta a gidan kanshi yana tashi gidan haka zanta juye da cikina su gama su cinye su hana min ina kallon su ko kallo ban ishe su ba. Ranan suna zaune suna ta shakiyancin su a falo na samay shi a falon suna gani na, ta wani shige mai jiki . Shi kuma sai ya daure fuska murtuk nace dashi yaya abincin da ka saya min ya kare tun kwana biyu da ya wuce. Sai cewa yayi kije gidan ku a baki don ni ba dole bane sai na baki tunda baki jin magana na. Ita kuma ta dago kai ta wani harareni tace ke bana fada maki kada ki kara kula min miji in yana nan ba shine don maita irin naki kikai mai magana yanzu wai manyar ina ce halan. Nace ke tsohuwar kilaki rufe min bakin ki da ke nakeyi balle ki samun baki ga zance na. Tsawa ya daka min yace duk ranan da na sake jin kin kira min mata da kilaki sai na halaka ki a gidan nan. Kallon mamaki nabi shi dashi ina cewa ai akwai Allah yana sane da komai da ka ke yi shi zai saka min. Ban karasa ba ya buge min baki gau da mari sai da wani wuta ya gittamin gaba na. ZAINAB IDRIS MAKAWA SEENABU 8/14/20, 7:11 PM - Ummi Tandama: BAHAGGON , , , , , 🧕🏿2️⃣1️⃣🧕🏿 YAR UWA NOVEL DIN NAN NA KUDI NE IDAN BAKI BIYA BA KADA KI KARANTA HAKKIN WASU PLEASE, , , , , Tun muna jiyo maganan su sannu sannu har suka fara daga murya mudai har barci ya kwashe mu bamu san lokacin da suka kwanta ba. Shiko yaya saadu gida ya tafi ya samu mahaifiyar da yanzu jikin sai a hankali sun kammala cinikin dare habiba na kirga kudi da sukai ciniki. Dinban habiba yaya yace munafukan banza da wofi kizo ki zauna da yar uwar ki kikace baki da lafiya ne. Yanzu may kike yi anan zatai magana ya dago kamar zai make ta yana cewa duk dai abinda kawa wani kasani sai an rama mashi. Mahaifiyar su tace kai kada kazo fa kace zaka samin yara gaba da hitina kan safiya. Idanuwan shi sukai jawur ya kalleta yace mummy halinda yariyan nan ke ciki ba wanda ya ja mata sai ke saboda son kai, Kin san danki yafi karfin ki kema da kika haifeshi baki iya shi rayuwan mu ba daya ba da tashin arewa amma kika rufe ido kika nace sai anyi. Mummy ansan mukadari ne ba wanda ya isa ya goge shi amma kuma sai ki saka ido a kanshi aike kika haifi abin ki. Ajiyan zuciya tayi wani bakin ciki ya tokare mata zuciya, tace Saadu, nayi kuskure da na dauka Safiya idan ta auri yayan ku zata gyara rayuwansa na jefa rayuwan yarinya cikin kunci da wahala. Ni kaina nasan ba aiwa yarinyan nan adalci ba amma ba yadda na iya dashi sai ya ce zai dauki mata akan magana na. Gashi mahaifinta dan uwa na gari ya dauki amana ya damka a hannu na don ba da halin zuwa gidan su gun mahaifanta takai kara uba yace bai yafe mata ba. Yaya saadu ya katse ta da cewa safiya tana cikin kunci da bakin ciki wanda duk wanda ya ganta yana da imani dole ya tausaya mata ace ana horon mutum yunwa saboda Allah fa. Sannan mummy keda kanki kika bashi goyon bayan a fitar da cikin da jikinta keda kanki mummy mu mai yasa baki fitar da cikin mu ba da kika samu. Wani kallo ta watso mai bai damu ba ganina acikin kunci da bakin ciki yafi komai bata mashi rai yace yanzu gashi tace zubar da cikin zatayi ta huta da wahala. A razane tace zata zubar kuma da cikin yace eh to ba abinda kuka zaba kenan ba dama itama yanzu shiyafi mata sauki zubar da cikin. Mummy zan inya hana wani abu mummuna da zai faru nan gaba kema kiyi abinda abin da ya dace akan zaman nan nasu amatsayinki na uwa gare shi. Don sai karuwan nan ta bar gidan nan wallahi ko ta halin yaya, ya juya zai fita daga dakin a hasale tace saureren nan Saadu kaji. Ban son kana shiga harkan gidan dan uwanka haka nan kabarshi shike da gidab shi da su. Ya zamana na karshe kada ka sake zuwa mai gida katayar mashi da hankalin iyalin shi. Ya juyo ya kalle ta yayi dariyan takaici yace mummy da kun hana ni na yarda nabar zuwa don biyyaya a gare ku. Amma yanzu na fahince ku bakin ku daya ne akan yar uwata muddin Safiya tana gidan shi bazan taba fasa zuwa gidan nan ba. A wane dalili zan nisanta kaina da yar uwana saboda karuwa ko may, zanyi haka wanan karon ba zan sake dauke kafana a gidan ba indai safiya tana ciki. Muddin ina raye ina numfashi ba zan sake bari a kuntatawa rayuwan safiya ba, danki yana danne mata hakkin ta batada matsayi da yancin a gidan shi amma duk baiyi laifi ba Mummy kin dauki yariya karama kamar safiya kin aura ma mutun irin Ahmed, ya dauko karuwa mata karuwa a gida ya hada tada ita sun taru suna kuntata mata kice wai baki sani ba. Duk kece sillan lalacewa rayuwan rayuwan mu haka mummy yarinya na zaman ukuba a hannun danki kice wai kada a taimaka mata, duk kece mai kawo matsala a tsakanin mu mama. Yana gama fadi ya juya ya fita yabar gwago cikin kunan rai ta bishi da kallo har ya kule tace Saadu kao baka san uwa da soyayyan dan ta ba. Inda zaka bincika kaga yadda nake cikin damuwa da bacin rai akan yaran nan da baka furta hakan ba inda kasan nauyin da maihaifin yarinyar nan ya danka min banda yadda na iya ne. Baka san nauyi da rikon amana kedashiba da matukar wahala duk abin nan ina sane dasu amma son dana ya rufe mun ido. Shiko dan waje ya koma yana jigina jikin shi ga mota yana tunane ya dinga kuna wiwi yana zuka yana wa kwakwalwan sa caji tare da neman mafita akan matsalar mu. Ya nisa yana cewa a ranshi hakika Safiya ke yar uwata ce ta jini kuma mata ga dan uwa na zan tabbatarb kin kasance cikin farin ciki zan fuskaci duk wanda ya nemi ya kawo maki kunci a rayuwan ki. Burin mahaifinki akan hadin auren ki shine da dan uwana yaga an hada zuria mai dorewa a tsakanin shi da yar uwar shi amma dan uwana yana son yaga rushewan wanan alakan saboda rayuwan duniyanci daya dauka. Ya Allah ka tabbatar da farinciki da kwanciyan hankali a rayuwan ku kar zumunta ya baci a sanadin auren ku. Iya sani na mummy bata da gidan zuwa a arewa wanda ya wuce gidan mahaifin Safiya don ko sako ne ta gareshi take turawa a sayo mata abu a aiko dashi nan. Haka dai ya kwana yana yawan tunane barkatai da samo fita ga matsalar mu . ********* ********* ********* Fitanan sune ya farka damu daga barcin safe da muka samu mukeyi a gidan nida Sadiya. Fada suke yi sosai shida ita hakan yasa mu fitowa da sauri dakin mu danbe suke yi a tsakanin su. Suna ta faman fashe fashen kayan falon da suke fadawa da gani har sadiya ba mai iya raba su don sun fimu karfi. Sun dauki lokaci suna abu guda saida sadiya takira yaya saadu yazo ya raba su ta kwashe kayan ta tana mai zagin kaskanci irin na yan duniya. Wani magana da ta fada sai da yaya saadu ya kadu bayan tafiyanta ne sadiya ta taimaka min don mu gyara gidan mu mai da komai inda yake. Kuka nake ban iya aiwatar da komai ba a lokacin sai gasu sun shigo gidan da shida dan uwanshi. Sun zauna suna fuskantar juna yaya saadu yace dashi matan bariki dama haka suke su raba ka da ta kwarai su kuma daga karshe su guje maka. Kamayi arziki bata kai ga kore maka mata ba ta tafi ya dago ya kalli dan uwan nashi ai ba tafiya tayi ba barazana ne kawai. Yaya Saadu yace yar bariki ne zata iya dawo ma rayuwana in yau ta ga dama ko gobe sai dai ka sani. Yarinyar na Safiya yar uwan muce jinin mu ne ita kamar yar cikin mummy take a wurin mu infact dai kasan wanan auren naku anyi shine don kara zumunci. A ganina bai kamata ace abinda iyayye sukai maka gata akan saba shikake wullakantawa. Na tabbatar da mahaifin yarinyar nan na kusa ko yasan halin da yarsa take ciki da tuni ya raban auren ku da ita. Ya kamata ace Safiya ta samu kulawan ka fiya da komai a gidan ka bata isa ta hanaka barikin kaba amma kabata kullawa yadda ya dace don kauce ma shiga hakki. Nasan da mahaifinta yasan halin da yarsa ke ciki a gidan ka da duk wanan abin bakai ga yinsa ba. Don basu san halinka na boye ba mummy ta rufe massu kokai waye ta aura maka karamar yarinya da yaci ace yanzun tana karatu ne. Please Ahmed ka gyara rayuwan ka duk wani abinda kasan yana kawo nakasan rayuwan ka nesance shi. Ba abinda ya zamo ma dan adam dole a rayuwa mussamman abinda zai nesantakan da ubangijin ka yazama dole ka yakeshi a ranka. Musamma giya da mata ba alheri bane ga rayuwan dan adam ba dole bane ba kuma inda yazama ma dole sai kayi shi. Don Allah bros ka rabu da wanan rayuwan ka rugumi matarka ka rike yarinyan nan amana zaka ga yadda rayuwan ka zai canza duk wanda ya samu mace kamar safiya yayi saa a rayuwa shi ga tsabata ga hakkuri da biyyaya. Ya sa hannu ya dafe kanshi kamar maganan yana shiga zuciyar shi can ya lumshe idanuwan shi yana hango kyakkyawan fuskan na da suran da Allah yaimin da natsuwa da hakkuri. Yace kai baka ko gudun ka dauko maku cuta ka manna wa yar mutane matar nan fa baka san iya mutanen da take hurda dasu ba har wata kasa take zuwa. Yaji zuciyar shi da jikin shi yai sanyi saboda maganan da dan uwanshi ke fadi gaskiya ne ko abokan shi sun sha fada mashi hakan. Gaba daya jikin shi yaji yai sanyi amma kuma yasan abu mai wuyane ya iya rabuwa da lilliya ko ya rabu da kowa bai iya rabuwa da ita wasan dadi. Ya kalli yaya Saadu yace na gode daka tunarta dani wasu abubuwan da na manta dasu a rayuwa. Yaya saadu bai tafi ba sai da ya tabbatar da ya daidata komai a tsakanin mu yabar gidan . Abinda bai sani ba shine na kudiri aniyar kwatar kaina daga gare su bazan kara yarda da irin cin fuskan da yake min ba agaban matan bazan shi da yake kwasowa. Kwana biyu kamar komai ya lafa sai dai a raina nasan kwanton bauna yayi kawai na kwana biyu. Yana kawo min abinci kai da kai kuma idan zai fita zai sallamay ni kuma idan ya dawo nakan taso daga dakina ko nabar abinda nake yi nazo na gaida shi da dawowa. Wata rana zai fita na tambaye shi zuwa wurin maman biyu indubata kamar ba zai barni in tafi ba sai dai kuma yace kada in dade. Na gama shiryawa na rufe gidan na kama hanyan gidan ta nayi saa ta dawo wai ashe bata garin duk wanan dadewan da tayi. Take tambaya na ko nazo bata nan ne sai nake fada mata irin kullen da yasani da dauko Lilliya da yayi ya kawo gidan. Da irin horon da na sha a wurin su har yaya Saadu yazo ya kwace ni a hannun su daidai lokacin da nake ganuwan shan wahalan su. Ta nisa tare dacewa safiya wanan mijin naki bariki ta aure shi rashin sani yasa mahaifinki ya nace da ki zauna dashi hakana. Amma wanan da kike gani tuban mazuru yai maku kawai may yuyuwa ya canza mata gidana suna haduwa baki sani ba. Nace inma gida ya canza mata baida may ni ba don ban gani ba abinda sukeyi bisa ga yadda suka zauna min gida ana iya shege a gabana. Nifa anty yanzu cikin nan ne kawai matsalata badon ciki ba da duk abinda baba zai mun sai dai yai min ba zan zauna ba. Sai dai nakan tuna furucin baba sai jikina yai sanyi da yake cewa indan aurena ya mutu in tabbatar da zaman ummina ma ya kare a gidan shi. In badon wanan ba aida tuni na gudu na koma ga iyayyena ko don maganar kine wallahi don da dan uwanshi kemai magana ya rabu da Lilliya cewa yayi. Wai abinda yasa ba zai rabuda itama ba sun jima tare ni tun baida komai suke tare tabar maza da yawa take zaman shi shi kadai. Wai cewa yayi har musulunta tayi saboda shi saida sukai alkawari da ita cewa bazai wullakantataba kuma ba zai taba rabuwa da ita ba shi dalilin da yake duba. Sai dan uwan ke tamabayan shi yana ganin Lilliya ta musulunts ne matar da ko shiga irin na musulmai batayi kuma ita bata daina hurda da wasu mazan banza ba har yanzu. Kai amma mijin nan naki wani irin soko ne wallahi indan ka gan shi a fuska kamar mutumin kwairai inji anty. Tace yanzu shi baiji kunyan fadar wanan dalilin nashi na bazan ba shi watau baiyi tunanen harcin da iyayyen ki sukai mashi ba sai na wata matar banza can. Nace ai haka dan uwan ya fada mai idan yana son zaman lafiya da kwanciya hakali sai ya rabu da matan bariki. Sai cewa yai mai wai bayajin zai iya rabuwa da lilliya ko ya rabu da kowa don baida matsala da ita tana binshi shi sau da kafa tana mashi komai ko wanan akasi aka samu suka sami matsala. Kanin yace mai aiko ya zama dole ya rabu da ita don farin cikin gidan shi nace kin san may ya cewa kanin ? Wai mau zai sa kanin na shiga mai harkan shi wai ai lilliya ma tarsa ce don haka zai zauna da wacce ya ga dama a cikin mu ya saki wacce yake son saki ko kuma ya zauna da mu dukkan mu. Sai cewa yayi dan uwan ya rabu dashi kar ya caja mashi kwakwalwa don yana bukatan hutu tare dashi. Na kinga kenan bazai iya rabuwa da ita ba ni ko yana iya rabuwa da ni inya so. Haka dai dan uwan ya lalaba shi har suka samu suka rabu lafiya dashi ya wuce in ba haka ba ranan nasan ba karamin tashin hankali za a yi ba a tsakanin su. Tace kin ga ni yanzu so nake ki kwantar da hankalin ki ga komai ki kula da kanki sosai don ki haihu lafiya. A hankali na daga mata kai alaman na gane ta kawo kudi masu yawa ta bani da zan koma tare da kwantar min da hankali. ZAINAB IDRIS MAKAWA SEENABU 8/14/20, 7:11 PM - Ummi Tandama: BAHAGGON, , , , , 🧕🏿2️⃣0️⃣🧕🏿 YAR UWAN NOVEL DIN NAN NA KUDI NE IDAN BAKI BIYA BA KADA KI KARANTA HAKKIN WASU PLEASE, , , , , , Abin yai min yawa a tare da ni ga yunwa ga ciwo ga ciki sai yar dadiron gida da tazo ta kakace gidan da zama . Ga miji dani da babu duk daya a gare shi bai san cina ba bai san sha na ba ko ciwo gashi har wanan lokacin maman biyu bata zo gidan mu ni kuma ban fita ba. Don da zaran nafita da ya dawo fada mai take yi ya samay ni yaita jibgana sai ya ga dama ya yabar ni. Suna zaune falo sun sayo kaji gassasu suna ci ga kayan shaye shaye nan mai sanyi agaban su wasu ansha wasu ba a taba ba. Kayan abincin da maman biyu ta bani duk sun kare banda komai da zanyi dabara dan kitson da nakeyi ya hanani wai ana cika masa gida. Jin motsin su a falo da dariye dariyen su yasa ni fitowa na samay shi, da farko da nai magana tankar bai jini ba. Sai da na kara cewa yaya wurin ka fa nazo tun jiya ban ci komai ba a gidan nan sai ya dago ya dubeni wani irin yai karfin halin daga Lilliya daga jikin shi. Ido ya zubamin na sake cewa tun jiya da safe banci komai ba a gidan nan, Lilliya ce ta sake kwanta mai a jiki tana wani iri da idanuwanta. Yai karfin halin sake daga ta daga jikin nashi again yace baki ci abinci ba mai kike jira da baki dafa ba. Nace wanda ka saya min ya kare sai ya juya ida take zaune yana kallonta ya zuba mata ido yana kallon ta. Yace baby kin san ba a horo da yunwa a bari ta dinga dafa abinci tunda akwai shi kuma ke ba damuwa da dafawa kikayi ba. Ta wani ya mutsa fuska tace abata badon halin ta ba don albarkacin wanan baby dake jikin ta. Tsayawa nayi ina masu kallon mamaki abincin ma da zanci wai sai ya nemi yardan karuwasa idan ta yarda a bani indafa. Ganin ban wuce ba yasa yace bakiji ba abinda tace kinci albarkacin cikin jikin ki tace eh don kuwa babyn dear na ne kinga kuwa bazamu barshi da yunwa ba. Kije mana ya daka min tsawa yana harara na wai na wuce mana tunda an bani na kalle shi nace haba yaya kaji tsaro Allah. Yanzu cikin daren nan karfe goma ya wuce wani abinci kake son na dafa inci a wannan lokacin. Ya zuba min ido yana kallona da idanuwan shi da sukai ja amma ya kasa fadin koma sai bina da kallo da yake yi. Sai a lokacin Lilliya da ke jin mu ta dago jajayen idanuwanta da suka rine tace wannan abinda muke ci kike so komay Kasan mai ciki da gwada zai yiyu kamshin shi taji tafito daga dakin ta, idan har shi ko kika biyu wallahi kwalelen ki idai wannan ne. Kofan da aka turo ne yasani juyawa bani ba harsu din suna diban kofan don suga mai shigowa lokacin. Bakowa bane illa yaya saadu ya shigo gidan fuskan shi a daure da alaman har yanzu yana cikin zafi da maigidan. Tunda yai sallama ya shigo gidan jikin shi ya bashi cewa akwai wani tsiyan da aka shukawa a gidan. A hankali murya a sanyaye na gaida shi da zuwa sabanin yadda na saba gaida shi abaya idan ya zo. Tambaya na yake a gagauce yana yi yana kallon inda suke zaune a ciken hasala maynene matsalan safiya may sukai maki nace , ? Ganin shi yasa kuka da banyi niyar yiba yazo min a lokaci guda . Durkusawa nayi a gaban su ina tsananin kuka kamar na fita yacina Yaya Ahmed ya daga zaune ya zuba min idonsa da suke jawur , ya kasa fadin komai, . Kumshin naman kazan daya rage guda daya basu taba ledan shi ba shi ya dauka ya miko min yana fadin. Indai wanan ne kikewa kuka don ba a baki ba gashin nan kije kicke baby bari zan saya maki wani kafin mu kwanta. Ban karba ba kuka kawai nake yi ya sake cewa karbi mana kibani wuri da kukan nan naki hakanan. Yaya Saadune yace safiya in nama kikewa ki karba gashinan ya baki sai na dan tsagaita kukan da nake yi nace yaya tun jiya ban ci komai ba a gidan nan . Na fada mashi yace wai wanan ta bani indafa yanzu yaya yaushe zan dafa har inci da daren nan . Na juya ina fuskatan shi nace yaya ina cikin wani babban matsala da tashin hankali da ban taba tunane ko tsanmanin zan shige shi ba. Yaya Saadu ka mai dani gida inyakani baba zai yi kan naki zama gidan dan yar uwanshi sai dai ya yankani a kan hakan ko dabba aka daure a gida ana bata abinci taci balle mutum. Yaya saadu kai kadai nake jin saukim rayuwa a wurin ka sai kuma maman biyu da tai min tsaye, . Ita ma bakin ciki da takaici ya sa ta dauke kafanta da zuwa dubana bani da kowa dake zuwa dibani sai kai da kazo yau din nan. Ya tausaya min sosai yace kinyi hakkuri safiya tun jiya na dawo motana ne keda matsala sai na tsaya gyara da na dowa nike tambayan mummy ke sai take fada min wai kina nan da ciki kuma kuna samun matsala. Ya juya wurin dan uwanshi yana cewa yanzu kai rayuwar daka zabawa kanka ke ga ka dauko karuwa har cikin gidan kana sunna kana fifita ta sama ga matar ka. Yaushe zaka girma kasan ana mutuwa ayi hissabi wai har ace kace matar ka ta zubar da cikin da kuka samu wai har ka tsaya kana mata wullakanci akan hakan. Wanan matar banzan daka dauko ka kawo mata gida fa a matsayin may take ita in ma har zakuyi abin ku , ku tsaya can kuyi inda bata ji balle ta gani. Yanzu bakajin nauyi da kunya kana ciyar da matar banza abinda kake so ka kasa ciyar da matarka ta sunna ga ciki ga bakin cikin ka da yunwa yaya kake son tayi. Tsawa ya daka mai yace ya isheka Saadu ya isa haka gidan ka ko gidana ka sani matar da kake kira da matar banza matatace. Mata mata fakace yai masu wani kallo yana tafa hannun shi yace dakyau wanan ce matar kake nufi ko may . Tun wuri idon ka ya bude akan wanan ya nuna Lilliya yace wan yan kaddangarun bariki masu ma mutum shigo shigo ba zurfi. Yanzu ka dubi wanan yarinya wata take dashi garin nan bayan mu bata da kowa Allah ne gatan ta kaine gatan ta amma ga ciki jikin ta kuma ga horo da yunwa. Nice na katse su nace yaya bansan yaya zanyi da matsala ta ba ya zama wajibi na zubar da cikin nan dake jiki na. Gaba daya suka dubo ni nace shine kwanciyan hakalina a yanzu ina ni kadai ban san yaya zanyi da kaina ba ina ga mun zama mu biyu nan gaba. Na san idan na zubar ina da daman yin wasu abubuwa , ban kai ga fadin abinda zan fada ma sai naji yaya Ahmed yace duk kika taba cikin nan a yanzu bakin auren ki. Nai mai wani irin kallo na juya ina fuskantar shi nace tsaron mutuwar aure na shine zai hana ni fitarwa ba, indai zubarwa zai kawo min kwaciyan hankali.. Matsala ta guda shine baba don nasan bazai barni in zauna mai gida ba don ya rantse kan haka. Tausayina ya kama shi baisan lokacin da idanuwan shi suka kawo hawaye ba ya kalli wan nashi da yake hassale shima yana sauraren mu . Wani kallon yake min ga alaman yunwa a tare dani da rashin kwaciyan hankali, kai bashi ba ma duk wanda ya ganni sai ya tausaya min saboda nayi kankanta da shiga irin rayuwan nan. Shi kanshi lokaci na farko da yadan tausaya min kenan a gidan don wanan shine lokaci na farko a rayuwan shi da yaji ya tausaya min ya sake kallona ina cikin kun ci da tashin hankali. Shiko yaya Saadu wani irin radadi da bacin rai ya dinga ji a zuciyar ji yake kamar ya samay su yai ta dukan su a lokacin. Do yana tausaya min ya son abani kulawa yadda ya dace amma wan nashi yaki ya saurare shi. Ganina da tayi cikin wanan halin kuncin fa ciwo ga yunwa da bakin ciki ya fi komai bata mashi rai. Ya kasa jure gani na cikin wanan halin ya fita waje ya barmu a yadda ya samay mu shiko gogan harara ya watsa min yace. Ban san abinda yasa kike son hadani da dan uwa na ba a dalilin ki bamu shiri yanzu da shi. Sai liliya tace munafunci mana munafuka wai harda cewa zata zubar da cikin jikin ta da da akace ki zubar uban wa ya hanaki zubarwa. Ke kilaki rufe ma mutane baki don ba a kasa dake ba a zancen nan kibar masu magana suyi. Nan cacan baki ya kaure tsakanin mu don bazan in mata bane ko banza tafini karfi ga tsayi ga komai turwa kawai nakeyi ina maida mata martani ganin shi zaune. Shiko gogan taba ya jawo ya dinga kunnawa yana zukewa yana fesar da hayaki sama kwakwalwan shi ta dinga caji yana neman mafita. Yaya Saadune ya dawo ya samay mu a haka da kayan abinci niki niki ya jani zuwa dakina ya bani magana da kalamai masu kwatar da hankali. Yace safiya na fahinci matsalar ku muddin bai daina hurda da matan bariki ba zaku samu zaman lafiya ba. Nai maki alkawri zan kula dake da abincikin cikin ki har ki haihu bazan taba batin ki kwana da yunwa ko kishin ruwa ba. Safiya ban san abin ya kai maku haka dashi ba har yana horon ki da yunwa ga kuma karuwa ya dauko maki a gida. Nan dai ya sani gaba har saida yaga na ci abincin da ya sayo min din saidai na kasa cin abin kwarai a lokacin don ciki na ya kulle sosai. Ya rasa abinda zai yi ya fice ya daho ruwan zafi tea ya hada min mai zafi shina samu na dan sha a lokacin sai kuma na fara shega amai. Yana ta faman yi min sannu waya ya dauka ya kira habiba da safiya suzo su kwana dani . Shedaniyar ko bata san yana kulle da ita ba jira yake yaga hankalina ya kwanta ya koma kansu. Sai cewa tayi amma wanan abin da kake mata baiyi ba wallahi kune ke kara shagwabata takeyin abinda taga dama. Sadiya kawai tazo habiba tace wai kanta ke ciwo itama ta tausaya ma halin da nake ciki sosai tace bakida lafiya har haka amma bamu sani ba kuma gashi yaya suna zuwa gidan mu shida lilliya. Suna nan zaune inda suke yaya saadu ya fito yabar ni da sadiya ta taimaka min ya dawo wurinsu falo. Lilliya tasa halin shi sosai bai daukan raini tun farko ya tsane ta sosai don baison taraiyan ta da dan uwanshi . Ahmed har yaushe zaka zauna macen banza tana dinga juya ka a gidan ka tana yiwa mutane iko haka, na tausaya wa rayuwanka da ka kare a gidin wanan matar da duniya ta gama yayinta. Tasan halin sa sarai tana son magana tana gudun jibga yace idan matar nan bata bar gidan nan ba sai na sa andaure min ita a garin nan. Fada yake yana zare idanu halinshi ba dama dai tai magana tasha na jiki a gurin shi da daren nan mikewa tayi ta shige daki. Nan ya zauna yana suna magana nasiha nasiha fada fada dashi karshe dai yace wai yayi kuskure zai gyara . Amma zancen Lilliya tabar gida bai taso ba shi kanshi ba fa dadin ta yake ji ba don ta gama isarsa dan kwanakin da sukayi tare amma kamar jaraba bai iya rabuwa da ita. Shi kuma yaua ya kafe akan lalai sai tabar gidan tunda ba auren kwarai sukayi da ita ba. Lalai kuwa Safiya ba zata zauna da wanan yar duniya a gidan nan ba kaji na fada maka tun wuri kasan abinyi. Yasan yaya saadu ya fishi zama dan duniya sai ya dafe kai ya rasa abinyi do maganan shi ta girgiza shi ainun . Muna daki muna jin badakalar da suke kwasa tsakanin su jikina yai sanyi don kirikiri ya fifita da ni yadda yake maganan aibanci gamay dani. Jiki na yai sanyi sosai tsananin tausayin kaina ya kama ni na tuna yadda nake cikin yan uwana yau gashi an kawo ni dani da tutu duk daya. Hawaye ne ya wanke min fuska itama sadiya dake jin fadan da sukeyi kuka takeyi karshe dai shigewa yayi yabar kanin nashi a falon yana fada. Dakin ya shigo wurin mu ya kalle ni tausayina ya kama shi yasan duk mahaifiyar suce ta jefa ni wanan halin . Don tasan halin data sarai amma ta nace sai yayi aure a zurian ta wai ko zai daina abinda yake yi wanan yarinyar haka ina zata iya shirya wanda ya haura talantin da wani abu can. Yace Safiya ni zan tafi dare yayi nai maki alkawrin da sannu zan dinga warware ko wace irin matsala a rayuwan ku muddin ina raye. Ko ina gari ko bana nan tankar kauna na da muka fito ciki guda nake jin ki mijin ki yayi nisa sosai da bariki sai addua lamarin sa. Yai muna sai da safe yana ma sadiya tuni da ta tabbatar da naci abinci da safe na sha magani na. Bayan tafiyan shi munajin suna hayaniya a dakin su nan sadiya ke kara fada min ko wacece lilliya da halayen yayan nasu da abin da yasa uwarsu ta auro mashi ni din. ZAINAB IDRIS MAKAWA SEENABU 8/14/20, 7:11 PM - Ummi Tandama: BAHAGGON, , , , , , , , 🧕🏿2️⃣2️⃣🧕🏿 YAR UWA NOVEL DIN NAN NA KUDI NE IDAN BAKI BIYA BA KADA KI KARANTA HAKKIN SU PLEASE, , , , , A can gida sani Allah sani annabi aka samu ummi ta dawo dakin ta amma har ta dawo tana nan akan bakan ta na bata zama gidan da bata da yancin kanta balle diya. Inda ba a san darajan mace ba da yara ake masu mulkin kama karya a gidan baka da wani tacewa sai yadda akayi dakai. Yan uwanta kuma suka mara mata baya sai da baba ya koma yana karamin murya da sani Allah sani Annabi mahaifinta ya kara tursasamata ta dawo gidan. Sai dai dawowan a tsatsaye ta dawo masu gidan bata shayin kowa da anmata abu yanzu ne zata maida martani akai. Hakan ya dan saman mata sauki a gidan gashi tun bayan ni da nai aure ba wanda ta kara aure a gidan mu nima din danayi sunan nayi ne kawai. Yanzun dai suke fitar da mazajen auren don haka kowa shirin aurar da yar shi yake yi a gidan in ka debe ummi na daga cikin wacce ke kumsan bakin cikin yarta. ********* ********* ********* Zaune nake a kasa saman dan center carpet din falon abinci a gaba na sai kira,an dana kunna ina saurare ina bi a hankali. Nayi wani irin fari duk wanda ya ganni sai yai maganan farin dana kara cikin jikina ya turo sosai don ya girma yanzu. Banji shigowan shi falon ba sai ganin shi nayi a tsakiyan falon yana ce min wanan wani irin abune kin ruda gida haka da karan karatu idan bi kike baki rage karan yadda zaki ji mai shigowa gidan. Ban kula shi ba sai dai ina mamaki a raina shida yake sake kida ya kure karan kamar gidan zai tashi don kara baac mai komai ba sai ni yau da na saka kira,a gidan yake fada Ban saure shi ba ya dauki remote ya rage karan ya juya ya shige dakin shi kai tsaye. Kiran sallah magariba akayi don haka na mike zuwa daki na don yin sallah har na idar banji motsin shi ya fito daga dakin ba. Don haka na mike na leka dakin kwance yake yana sharar barci ko kaya bai cire ba yadda ya saba yi indan yadawo gidan. Muryana ya dinga ji a tsakiyar barcin shi ina tada ya tashi yau sallah bai saurare ni ba ya gyara kwanciya yaci gaba da barcin shi. Saida yaga dama ya tashi don kanshi yai abinda zai yi ya dan fita nasan giyan shi ya je ya dirka sai dai bai bugu ba ya dawo da ledodi da yasayo abin breakfast din mu. Na kashe wutan daki na kwanta ina jin motsin shi a falon barci ya daukeni motsin shi da naji a dakina ne ya tayar dani daga barcin da na fara yi. Yace na kasa barcine shiyasa nazo taya ki hira namiji baida ta ido ko kadan nida yace ban iya komai ba yake fadawa wanan maganan haka. Nidai na matsa mai ya hawo ya kwanta daf dani naji ya fara shafana a hankali. Idona na lumshe ina maijin tsanar shi a raina don ban iya mantawa da cin fuskan da sukai min gidan shida lilliya. Ya juyo gareni yana cewa may ye azuciyar ki may yake yawo a kwakwalwar ki gamay dani. Nace kai dan uwa na ne na jini kuma mijin da mahaifina ya zaba min dole komai yai zafi ina tare da kai duk rintsi komai wuya komai dadi ina tare da kai a gidan nan amatsayin matar ka kar kayi tunanen daukan fansa a gare ni don kai dan uwana ne kuma mijina. Wani iri yaji har acikin zuciyar shi don yasan ya cuta min ta ko ina harda ma inda ban sani ba sai dai kawai ayi hakkuri da juna. Nisawa yayi tare da gyara kwanciyar shi yace to ki daiyi hakkuri da komai. Nace hakkuri kan na yi amma yaya bazan sake irin hakkurin da nayi a baya ba amma zama kan yamin dole a gidan ka. Shiru yayi ya kasa barci yana ta juye juye ya tsinci kansa a wani yaniyi tabbas ya san ya zulunce ni tako ina duk kokarin da nakeyi baisan may yasa ba ya gani ba. Yarinya ba inda ta gaza dashi tsabta da girki da kula da kayan gida da kokartawa da bashi hakkin shi duk ta yanda yazo mata amma shi ya kasa daina barikin shi a zauna lafiya. Ga saadu kanin shine na baya amma har ya fishi hangen nesa ya hanngo mai abinda bai taba tunanen hangowa ba a rayuwan shi. Ya tashi ya yai zaune yana maici gaba da tunanen abubuwan rayuwa a ran shi. Har barci ya fara dauka na naji matsin shi yai yawa na haska hasken tocina don in ga may yake yi a lokaci tare da cewa ba kayi barci bane ? Yace yau na kasa barci ne ban san abinda ke damuna ba haka nace Allah ya kyauta ko may nene amma da zaka koma dakin ka ka barni zaifi min in samu barci. Ban dauki lokaci barci mai nauyi ya dauke ni ya lumshe idon shi yana mai kare min kallo na dunkule a wuri daya ina barcina hankali kwance. Sai wuraren asuba ya samu barci ya dauke shi bai wani dade kwarai yana barcin ba ya dinga jin murya na ina tadashi yai sallah. Bai saure ni ba sai barcin shi yake yi nan na barshi a kwance na wuce nai wanka tare da dauro alwala har na fito bai falka ba. Nata da sallah na harna idar sai nasari yake kwasa a cikin barci duk ya wani rudamin daki dashi. Na idar ina addua na sake ta dashi da yaga kamar damun shi nakeyi sai ya dauki filo ya danne kanshi dashi. Har na gama anbinda nakeyi yana nan a kwace min dirin a daki yana barci matsa mai nayi sai ya tashi. Nan ya mike a harzuke ya hauni da masifa meye damuwan ki da rashin tashina kibarni lokacin da duk na tashi zan iya yin sallah na. Ban samu barci da wuriba jiya da kyat na samu barcin ya dauke ni yanzu kuma kinzo zaki matsamin ki kyale ni nai barci na karki sake tasheni. Nan nima nace a harzuke zan tashe ka dole in tashe ka ko sau nawa zaka koma barci muddin bakayi sallah ba sai na ta dakai. Haka kawai ana sallah kana kwance kana barci katashi in kayi sallah sai ka koma ka kwanta yafi, magana da nakeyi na damay shi. Ya mike a hasale zai koma dakin shi ya kwanta yana fama dani na daure nace yanzu kai bakajin, kunya ko tsaron Allah kaine fa yakamata ace ka data dani nayi sallah amatsayi na kaunan ka ko matan ka. Amma ana sallah asuba kai kullun kana kwance kana barci a daidai lokacin da Allah yake sauke rahamarsa ga bayin sa. Yana kuma yi ma bayin sa gaffara yana raba alheri ga masu rabon samu ya sa imani azuciyar masu imani, amma kai sai dai ka kwanta kawai kana barci ko yaushe. Bai kula ni ba ya shige dakin shi ya kyaleni ina wa,azina koda ya shiga ya koma barcin shi bai damu da surutun da nai mashi ba. Sai wajajen takwas saura ya falka yai wanka tare da yin sallah ya fito da shirin zuwa aiki a falo ya samay ni zaune. Ina ganinya fito na mike zuwa hado mai abin karyawan shi dama na gama yana aje. Na tsugun na gaban shi na aje tare da mashi ina kwana ya amsa min adakile, ban daga ba daga wurin ba nace dashi. Yaya don Allah ka daure da yin ibada bai kamata ba magidanci da kai kana wasa da addinin ka, may yasa kuna diyan musulmai kuke sakaci da ibada. Hannu ya daga min ya dakatar dani daga maganan da nakeyi yayi da hannuwa don haka naja bakina nai shiru tare da komawa gefe na zauna. Yagama ya fice abinshi lokacin naji gidan kamar an debe min kaya da nauyi akaina na mike na shiga gyaran gida dakyat na samu na gama . ********* ********* ********* Kwana biyu banda matsalan komai da shi a gidan sai dai ba sakin fuska akaina wanan bai damay ni ba indai hat zaibar zuciya ta ta samu saida. Ranan na samay shi zancen zuwa asibiti a duba ni don ina fama da ciwon mara idan dare yayi bana barci da dadi. Ya kawo kudin zuwa ya bani yace na shirya ya sauke ni indan zai fita nako shirya da wuri na zauna jiran shi. Sai da ya gama abinda yake yi ya fito muka kama hanya a can wani unguwa ya kaini wani asibiti mai kyau na kudi . Yace idan zan dawo ga yadda zanyi ga yadda zanyi nace na gane na yanki kati nabi sahun masu ganin likita a wurin. Can layi ya kawo kaina aka ce nai fitsari aka kuma debi jina na dan aunawa an gama na koma na zauna sai da layi ya sake kawo kaina na shiga. Ba matsalan komai ba likita yai min yan tambayoyi irin na likita karshe sai ya rubuta min magani sai kuma yadan dubeni yace dani idan ba damuwa yana son nazo da mijina yana son ganin shi gobe. Banji komai a raina ba nace zan fada mai ya bani wani dan note yace dashi zai zo idan zaizo din na karba nai mashi godiya na fice. Na dawo gida a gajiye na samu bai dawo ba na kwanta na dan huta don na sayo abinda zanci a hanya da zan dawo. Ban tashi ba sai wajajen karfe uku na tashi a gagauce nai sallah najira akai la,asar na hada nayi sai na mike na dora girki dare. Har na gama bai dawo ba lokacin da ya saba dawowa kafin magariba na shige sallah na gama ina sauraren dawowan shi, naji shiru nan na fara tunanen ko ina ya tsaya. Shiru bai shigo ba har nagaji na kashe kayan kallo na kwanta sai wuraren sha dayan dare naji ya shigo gidan a cikin maye. Inna lillilahi nayi a raina ina jinshi yana ta hauragiyan shi shi kadai a falon na tashi na kargamay kofan dakina don ma kada ya shigo min dakina. Haka na kwana ga ciwo ga bacin rai nasan mairaba shi da wanan halin sai Allah duk wani wa a zi da sauransu bai shigan shi don yayi nisa. Gari ya waye ban fito da wuri ba sai wuraren takwas na fito ina yan aikace aikace na duk da nayi nauyi ban iya dukawa sosai yanzu. Ya fito yana wani murzan idanu kamar wanda barci bai isheshi ba, ashe shi din ne kuwa don ya na cikin sauran maye har yanzu, . Dan juyowa nayi na kalleshi na mayar dakaina naci gaba da abinda nakeyi nace mai ina kwana a takaice ba tare da na fuskace shi ba. Shima yai mamakin a yadda na gaida shi don ba haka nake gaida shiba din yadai amsa min ne kawai don yasan wai fushi nakeyi ke nan. Ya zauna yana tambaya na abin karyanwanshi na ba shi amsa dacewa dashi ban yi ba har zai yi magana sai kuma ya tuna bai sayowa ba daren jiya da zai dawo gida don a buge yake lokacin kuma masu kaya sun kwashe. Zama ya dan yi na wani lokaci yai shiru sai can ya furzo iska daga bakin shi yana mikewa yake tambayana jiya kin samu ganin likitan ? A takaice nace mai eh nagan shi yama bani takarda wai yana son ganin ka asibitin sai ya dago da sauri yana kallona yace. May zanmai ba ya dubaki ba shine kuma zai ce sai na je ya ganni ni ban iya lalurar su na likitoci don Allah. Nace to kasani ko wani abin ne yake neman ka din kamaf tai magana sai kuma ya fasa ya karbi takardan dake hannuna yana cewa idan na fita zan biya nagan shi. Tun wanan lokacin bai kara min magana ba nice ma dana tambaye shi yake cewa yaje yace ya dinga sai min kayan karin jini ne. Da alama yanzu ya koma ruwa sosai don sai dare yake dawowa indan kuma bai zuwa aiki ya zauna min falo yaita bakin rai a falo yana jin fada. Zai sha abinda yaga dama a wurin da nai magana yanzu zaiyi cikina da cin mutunci da tonan asiri sai ya gaji ya kyale don kan sa. Wata rana na tafi gaida mahaifiyar shi gwago na mun gaisa dadi dadi da ita sai kowa yai shiru zuwa can tace dani yanzu komai yai daidai tsakanin ku ko an daina jin korafin ki. Nai mamaki dajin wanan magana nata datai min nace da ita dama ai ba korafi bane fahinta ne akan addini don akwai karancin illimin addini a kan shi. Nan ta haye tace wai ita nake fadawa magana akan dan ta nihar yaushe aka haife ni da zan ce zan koya masu addini. Nidai nai shiru ina sauraren ta har ta gama dama da wuya nazo gidan bamu samu matsala akan dan ta ba bata kaunar a fadi magana gamay dashi ko kadan . Ban dade ba nai sallama dasu na juyo zuwa gida da kafa na tako nan na hadu da wata yar unguwar mu a hanya muka jera da ita muna tafe muna zuba bayeraba na amma kano aka haife ta ta iya hausa sosao don haka in taga bahaushe take matukar jin dadi a ranta. Tafe muke muna hira tana tambaya na yaji da kuka take so nake cewa da ita ina dashi ai tazo zan bata taji dadi tana ta min godiya. Tun daga nesa na hango motar shi nasan cewa yana gida sai dai nayi mamakin may yake yi a gida wanan lokacin haka mun dan tsaya da wata makwabciyar mu suna magana da Mujida har take ce min yanzu na yi nauyi nabar kitso ko ? Nai dariya nake cewa da ita na daina ma don maigidan ne ya hana nai mai kitso a gida . Ta rike baki tana mamakin halin maza tace shi bai ganin baiwa ne daga Allah na hanyan samu yai maki zai hanaki samu nan dai muka wasan ce muka wuce ita kuma ta kama gaban ta. Mun zo kofan gidan na tura kofan yana bude sai nace ta jira ni a kofa na dauko mata don kada na shiga da ita kuma ya zama min fitina wurin shi . Sai ta tsaya a waje tana jirana tana ce min karfa ki shiga mai gida ya rike ki ki manta dani a waje. Kunsan yare idan yana jin hausa iya yin gare su shi sai ya nuna yafi bahaushen iya hausan ma ga kuma mutane suna kallon mu tana jin dadi. Nidai na wuce ta ina dariyan abinda naji ta fada zuciyana cike da mamakin abinda ya dawo yi gida da ranan nan haka. Don dama da sunan zan wuni gida gwago na tafi sai yamma zan dawo ta ban samu fuskaba do haka nai shawara indawo gida kawai in nemi abinda naci don har na fara jin yunwa ko. ZAINABU IDRIS MAKAWA SEENABU 8/14/20, 7:11 PM - Ummi Tandama: BAHAGGON, , , , , , , 🧕🏿2️⃣4️⃣🧕🏿 YAR UWA NOVEL DIN NAN NA KUDI NE IDAN BAKI BIYA BA KADA KI KARANTA HAKKIN WASU PLEASE, , , , , , , , , Mun isa garin mu garin mu an shiga sallah magariba kafan mutane ya dauke sosai mota ya tsaya dani kofan gidan gwagon ummi na. A nan aka sauke min kayana kaf sai faman tabayana takeyi lafiya kuwa nakai ma driver ruwa nan dai na fada mata tsaye muka wuce gidan mu. Nan aka karasa sauke min kayana nai sallama da drever na shiga gida tunda yaran gidan suka kyala ido suka ganni suka ce ga Safiya nan da nan na cikin daki suka firfito waje suna min sannu da zuwa. Dakin Ummina na nufa yayin da aka shigo min da kayan da nazo dashi ciki yar jakar kayana da tsaraban da nazo masu dashi. Ni bani sanin cewa na sake masu amma su suna ganin wai na zama wata yar birni dani take inna wani kishi ya tarsu a zuciyar ta na yadda na canza. Lafiya kalau suka tare ni sabanin ummina da ta shiga zargin zuwana gani da juna biyu a jikina kuma. Mama tazao muka gaisa take tambaya na kowa nace duk suna lafiya take cewa ashe da sai dai muji haihuwan ki kawai don bamu ma san kina da ciki ba. Murmushi nai mata kawai muka gaisa ta fita daga dakin ta koma ta aiko min da abinci daga wurin mama din. Ban iya cin komai ba sai kunu da na nema don ummina bata rasa kunu a dakin ta. Baba ya shigo gida daga masallaci yara suka tare shi da cewa safiya tazo baba cikin mamaki yake tambaya da cewa Safiya ? Ya nufi daki Ummi yana tambayana nazo lafiya nace Alhamdullahi sai da ya tambayi kowa har Ahmed din da kan nesa. Sai kuma ya dakatar yana tabmbaya na da lafiya dai na ganki ke kadai ina mijin naki yake ne? Ban ji tsoro shi ba nace dashi yana gida baba ni kadai nazo, kamar zaiyi magana sai ya juya ya fice dakin na mu. Yan gidan mu suna baibaiye dani har wani lokaci sannan suka dauke kafan su. Nasan ba komai yasa sukai min haka sai tsaraban da nazo masu dashi wancan zuwa da ni tare da yaya sani. Har lokacin da suka barni dakin ummina na min kallon zargi sai dai batai min magana ba sai da na dan kimtsa na samu wuri na kwanta don a gajiye nake sosai. Ban falka ba sai cikin dare na falka da tunane a raina barkatai na yadda zamu kwashe da mahaifina gashi daga zuwa ba abinda ya fara tambayana sai Ahmed din da mahaifiyar shi. Na dade a haka ina tunane sai zuwa asuba wani barcin ya dauke ni kuma har na makara da sallah sai da ummi na ta ta tadani. Nayi sallah na fito na gaida iyayyena na koma daki don baba bai shigowa gida sai hantsi ya fito yake dawowa daga masallaci. Ummi na samu tayi zaune tana tunane ita kadai a dakin na samu wuri na zauna sai tace min yar nan lafiya kika zo gida a haka yadda kike nan ? Kuma ba a samu wani ya biyo ki ba kika biyo hanya ke kadai haka gari ba kusa ba ? Kafinta gama maganan ta hawaye ne ya cika min ido na cikin kuka nace mata ummi saki na yayi yau kwana hudu kenan yace na bar mashi gidan shi . Salati ta saka tare da dafe gaban ta tace yasake ki ka ce fa za tai magana sai kuma naga ta mike kawai ta fita dakin. Na bita da kallon tausayi har ta bace min ashe dakin mama ta tafi ta kirata sai gasu sun dawo dakin cikin rudewa. Mama a rude take tambayana Safiya may ke faruwa ne wai ni dama tun jiya da kika zo nake zargin wani abu. Ban boye masu komai ba duk yadda mukayi na kwashe na fada masu da abinda gwagona tai min duk ban boye masu ba. Salati mama ta saka itako ummi na sai kuka takeyi ba tsagai tawa mama ne ta samu bakin cewa amma in haka Asiya tai muna taci amanan zumunci wallahi sai Allah ya saka maki. Inna da yarta ta fadawa taji ummi na kuka kuma mama na dakin mu ta kasa gidin zama taje ta dawo a tsakar gida don taji may akeyi. Mama ne ta kirata sai ko gata tazo nan suke fada mata abinda ya faru dani ummi dai bats samu bakin magana ba sai inna ne tace adai binkita aji gaskiyan maganan. Tunda naji ta fadi haka nasan zata iya zuga baba a kan maganan don ta wuce nan kadan ne daga cikin sherin ta. Shigowan baba gidan yasa suka fito daga dakin mu dakin Inna yake ta bishi dakin ko may ta fada mashi sai gashi ya fito yana cewa ina Safiyan take. Nan ya fado dakin mu ya samay mu da ummi na a dakin yace ki fada min gaskiya may ke faruwa dake ? Yadda na fada masu mama haka na mayar mashi da maganan tiryan tiryan yana saurare na har na gama fada mashi komai. Yace cikin tsawa ke safiya badai gidan nan ba ai na fada maki tun farko kada ki dawo min gida. Sai lokacin ummi tai magana tace idan bata dawo ba duniya kake son ta shiga ya koreta akan karuwa tabar mai gida ina yake son ta tafi garin mutane kai bakai tunanen haka ba baka gode ma Allah da ya kawo muna ita gida lafiya ba. Ke Rabi kifita a idona tun muna sheda juna nida ke ke tsaya kiji bazaki zauna min a gida ba muddin kika kashe auren nan kiji na fada maki. Ya tashi ya fita yana fada yaya sani ne yashigo gidan yace yaji ance nazo jiya da dare sai kuma ya samu labarin abinda ke faruwa. Nan yace ai dama nasan haka zai faru ko ta koma da idona fa na samu ya dauko karuwa a gidan kuma yaiwa safiya dan banzan duka. Amma baba ya hana aiyi magana to ai ga irints nan yanzu cikin kuka nace yaya Sani wanan ba wacce ka sani bane nan na shiga basu labarin abinda suke mun yaya sani yace kai ina wallahi bai yuyuwa gaskiya. Dole baba ya canza maganan shi na komawa n ki gidan nan sai dai in yasa yaci kudin sune yake kamay kamay. Daganan Inna ta kirashi dakin da yazo, to to ita kuma Inna zata fara abinta kenan baije ba saida ta sake daga murya ta kirashi ya tafi. Fada tai mai sosai akan ya canza hali yafita batuna da uwana don ba ysn goyo muke ba yace ni Inna baruwa na da harkanku na kishi, ni kaunata nake tausayawa. Fita yayi ya tara kan yan uwan baba suka hada mai mitin din kashi akan ya fada masu gaskiya in ya karbe kudi wurin gwagona ne yasa bai iya raba aure na da Ahmed. Nan baba ya kara yin fushi ranshi ya baci sosai ya kumbura sosai yahau yace diyar su ko diyar shi da zasu tsure shi akaina. Yamike yana fadin yau yau din nan zan bar shi gidan shi in koma gidan mijina ko mu bashi gidan shi nida uwata. Allah ya taimake ni yazo gida sai ga su yaya sani sun shigo yace infito da kaya na inbar mashi gidan shi in kuma ban komawa gidan mijina mu fita mai gida dani da ummi. Fitina ya tashi si yaya sani suka ce mu zauna kada muje ko ina ya shigo har dakin mu zai doke ni mama da ummi suka taso mai sukace idan ka dake ta da tsoho ciki haka wani abu ya samay ta sai an daure ka a garin nan. Sai jikin shi yai sanyi ya dauki kayana dake gefe yafita dasu waje gidan ya watsar yaya Nura ya kwaso ya dawo dashi ciki yace haba baba wai kodai Safiya ba diya cikin ka bane ? Yaringa fa tun tasowan ta bata da gata a cikin gidan nan kamar kowa kun tsane ta ita da uwar ta may yasa baba kake mata haka kai kayi su İnna suyi ? Sai jikin shi yai sanyi yabi yaranda da kallon mamaki Yaya Sani ya karasa kwaso min kayan ya shigo dasu gida. Ya rasa abinda zai yi ya fice yana fadin sai sun bar min gida yau ita da uwar ta kowa yai mata tsaye a garin nan. Nan ne gidan ubanta basu zuwa ko ina inji yaya sani haka kawai ka bayar da yarinya ana mata wullakancin da aka ga dama amma kamar bakai ka haifeta ba. Sai ga yan uwan shi sun shigo maza da mata nan suka taru sukai mai tas a kan mu suka ce sai sunyi karan shi ga hukuma idan ya kore mu ni da ummi gidan nan ai ba kaina aka fara aure ya mutu ba. Nan ya fice gidab yana banbami kowa na mai tirda halin shi itako ummi ta hada kaya wai zata bargidan aka taru har gwagon ta da ta shigo akace ina zata tabar yar ta da tsohon ciki haka ? İna waje tsugune a ina kuka mama ta fito tace a hasale tashi ki shiga ciki kin zauna waje kina kuka ba inda zaki tafi. İnna sai wani kallon banza take min ita da diyan ta don ba haka suka so ba sun so baba ya kora mu ne yadda yai niya. Muna sauraren dawo wan baba muji may zaice sai muka ga ya dawo bai ce komai ba ashe maigari ya samu labari ne yai mashi tas gwagon ummina ta kai karan shi wurin shi. Sai dai bana fitowa waje in kuma gari ya waye na gaida shi da kwana baya amsa min sai ya kawar da kanshi yaki kulani wanan abin ya matukar tayar min da hankali a gida. İnna ta shiga sake maganganu a gidan wai sai bakin ciki na ya kashe masu miji inda basuyi hankali ba. Sai yarta ta karbe da cewa wallahi sai dai ta kashe uwarta ba mahaifin mu ba ita da ta hana ta zaman aure, ai da har wani jin kai ake muna an auri dan birni za a tafi birni. Ban saurare su ba don ina sharan kofan mune mama ce tace sai ko makiyin Allah bai fadin haka ga Rabi. Don kowa yasan yadda ta nuna kin ta ga auren nan abu dai ne in an fi karfin ka baka da yadda zakayi sai hakkuri amma zancen ta wa mutane hawan kai karya ne. Nan dai fada ya kaure a tsakanin su koma sai da suka dauki lokaci suna yi suka dakatar don kan su. ********* ********* ********* Tunda hakan ya faru na samu dan sa ida a gidan sai dai ba wani dadi ga zaman gidan yayana nan a yadda yake baya komai ya lafa ne na kwaso kaya dake gidan gwagon ummi. Wanda maman biyu ta hada min kan kudi na taimin kari ta saro min kaya dasu wai na juya kar nai zaman banza haka na. Sai lokacin su inna yan sin banza suka dan sake min fuska don ana son banza nadai basu wanda na yo tsara a kyauta sauran kuma na shiga lodawa kanne na suna fita min da su. Kafin wani lokaci mutuwan aure na ya ba gari mu kowa ya sani ana tir da halun baba kowa sai cewa yake yaci kudin su ne in ba kudin su yaci ba may ya kawo haka gare shi. Ana dukan yar ka a wullakanta ta har tazo ma gidan da rauni kace wai sai ta koma gidan mijin nan da zama. Wurin yanne na maza nake samun gata sosai don zasu sayo min abin kwalama da yan abubuwa idan sun fita. İtako ummi har lokacin ba dadi tsakanin ta da baba zaman dai akeyi amma kullun sai masifa a tsakanin su. Gashi shiru tunda na zo baba baiji wani labari daga wurin su gwago ba ita bata zo ba dan ta bai zo ba sai jikin baba ya fara sanyi . Gashi yai masu aike yafi a kirga amma sun ki bashi amsa balle ya san abinda yake ciki din yana a kan bakan shi sai na koma gidan dole. Ranan kwatsam sai ga yaya Saadu ya dira gari wai sun shigo arewa ne yace zai karaso ya dubani. Yana zaune dakin mama naje gaishe shi da zuwa sai ga baba yazo shima anyi sa a yana gida bai fita ba bsyan sun gaisa sai ya dube ni yace ke kuma ashe haka abin yakai. Baba sai dai kai hakkuri don maman mu da dan uwana basu rike amana ba ba gwama ma da auren na ya mutu tun baika ga kasheta ba a rasata. Akai tsit ana sauraren shi ya shiga lissafo masu irin rayuwan da nayi a can harda wanda ban fada ba na yunwa da irin zagin da yake min na cin fuska. Yace baba wallahi Ahmed da wuya ya sauya halin shi don yayi nisa da duniya yaudaran ku dai mummy mu tayi bata fada maku halinshi ba na gaskiya. Amma baba yarinyar nan tasha matukar wuya a han shi yai amai ta kwashe ya shawo giya yazo yai mats dukan tsiya a gidan sai ya barta kwance. Ya kwaso mata tana zaune suna cin abu ya hana mata ga ciki a jikin ta, kai abin ma baya faduwa wallahi sai dai Allah ya saka mata ka wai za a ce. Jikin baba ne yai sanyi ga bayanin da yake masu nauyi da kunya suka rufe shi don har su yaya Sani suna a tsaye wurin suna sauraren baiyanin shi. Zai tafi ya kawo kudi yaba baba yaba su mama da yaran gida ni kuma ya rubuta lanba ya bani ya bani karamar wayan shi yace inda wani abu a kirashi insha Allah zai taimaka ya kawo kyautan kudi masu yawa ya bani. Yace idan aiki ya sake kawo shi arewa zai dawo ya duba mu lokacin yasan na haihu yace kiyi hakkuri Safiya tun yazu Allah ya fara saka maki ai don ya fara ganun abinshi. Nai murmushi nace yaya banda abinda zance sai godiya gare ka don ka fitar dani zargi a gurin baba. Don ni na kasa mai bayani yadda kai masu saboda ina jin kunya fadi amma yanzu sunji nagode maka da Allah ya kawo ka zo kai masu bayani. Ya tafi yabar zukata da magana da kiyastawa na abubuwan da ya fada baba kan nauyi da kunya sun hana shi shakat a rayuwan shi. Mahaifina ya dan sasauta min don tun da yaya Saadu yazo yana amsa min gaisuwa indan na gaida shi sabanin da da yake kyale ni. Ranan wata jumma,a ya dawo daga kasuwa ya shigo da leda a hannun shi ashe rogo ke ciki mai zafi da zogala ya sayo min. İnna zata karbi ledan yace a a barshi kayan safiya ne sai ya kwala min kira ina daga dakin mu najib sai na fito. Ya miko min ledan dake hannun nasa yace karbi jeki ki gyara ki ci inna na tsaye har lokacin tana son tasan may a cikin ledan. Na duka na karba a cikin ladabi nai mashi godiya sai naji inna na cewa wata sabuwa ke nan kuma. Ban dai kula ta ba na wuce dakin mu sai da nashiga na bude naga ashe rogo ne daffafa da zogale. Jikina rawa na shiga gyarawa sai da na gyara na kasa naba kowa na gidan mu ba wanda ban ba na zauna na dan ciyen sauran na kora da ruwa. Tun wanan ranan idan zai dawo gida yakan dan riko min dan abin kwadai irin cimar kauye na gyara naci duk da ina ba kowa isan na gyara amma sai da hakan ya zama tsegumi a wurin İnna. Don da ta tayar da fitina ta kaca kaca taiwa baba ranan kan haka yace shi yana sayo min ne don ya ga ina cikin lalura na ciki. Gashi kuma ban da miji kusa yasa yake sawo min amma duk da haka bata yarda ba tana ta faman fada. Sai mama ne ta dakatar da ita tace haba haba wanan abin da kikeyi bai kawo kallo ba wallahi abinda ba ita kadai take zama taci ba kowa sai ta ba gidan nan. Shine kuma har ya zama abin fitina haka yarinyar nan koke kike dashi ai kina mata basai malam yayi ba. Nan ta juya kan mama da fitinar ta tana ce mata munafuka ai da ita ake kulla komai da akeyi a gidan. Bata kare fadan taba sai ga Yaya Sani ya shigo min da kade a leda yana kwala min kira na fito in karba. Mama tace ta kin gani yanzu kuma may zaki ce duk wanda ke da imani dole ne ya tausayawa safiya halin da take ciki a gidan nan. Tace ai bani na aike ta da ba ana yi muna rawan kai an tafi birni ba diyan mu suna nan sai da dubu ya cika za a zo a zauna muna gida dan kudin da za a yo muna cefane a kwashi ana sayo mata gaye dashi. Mama tace dubu bai cika ba don iyayyen kirki duk basu rushe gidan yar su sai dai su gina shi don haka ki natsu kisan may kike fadi idan da yar ki ne haka ya cika da ita yaya zaki yi. Tai wani iri shewa tace can dai gasu gada diyana basu ciki wallahi tace amma kin zuga na wasu sun shiga ai. Tace muka dai zuga tare karki debe kan ki ciki wayai ruwa yai tsaki cikin wanan hadin , tunda kin sai tun ba a yi auren ba watsetse ne shi. Mama tace sanin haka danayi yasa ai nake tausaya ma yarinyar don kar abin yai min yawa. Kuma sa bakin da nayi ayi bawai na sheri bane don a hada zumun ta ne nayi badon wani abuba kedai kika yi don sheri kije kitayi ai. Ummi tana jin su tace wanda duk ya cuci wani dai Allah yana ganin sa shine Alkalin mu daku. Baba ne ya sake shigowa gidan ya iske suna rigiman har lokacin ya ce wanan wani irin rigima haka kuke yi. Kun ishi mutane da hayaniya haka yaci gaba da fadin dame kuke son muji da tashin hankalin ku koda halin da yariya ke ciki. Yanzu ba lokacin hayaniya bane abinda ya faru ba za a canza shi ba ku barmu muji da abinda zuka tanmu ke ciki mana. Yarinyar nan tana bukatan kwanciyan hakali amma kun tsaya kuna tonon asiri irin haka yarinyar nan fa ba ita ta saka kan ta ba. ZAİNAB İDRİS MAKAWA SEENABU 8/14/20, 7:11 PM - Ummi Tandama: BAHAGGON, , , , , , , , , 🧕🏿2️⃣2️⃣🧕🏿 YAR UWA NOVEL DIN NAN NA KUDI NE IDAN BAKI BIYA KADA KI KARANTA HAKKIN WASU PLEASE, , , , , , Na tura kofan na shiga da sallama yana kwance saman dogon kujera daga shi sai kajeren wanda ga taba rike a hannushi yana zukawa. Daidai lokacin da Lilliya ta fito daga dakin tana waya gaisuwar da nai niyar yimai ban samu yi ba na shige kitchen abina kai tsaye ina tsuki. Shiko yana ganin na gani na sai ya dan zabura alaman rashin gaskiya a tare da shi. Ina fitowa da ledan da na hadawa Mujida kayan miyan da tarokeni ci ta gama wayan ta juya gare shi tana cewa. Ahmed kayi gagawan yi ma wana yarinyar waigi kaina, kai mata magana ka tsawata mata don bazan lamunci batacin ta gare ni ba. Wai kaima kamar ka, ke zama da wanan karamar yarinyar mara kunya banza zata shigo tasamu mutane tana masu tsuki kamar wacce ta samu dabbobi, karamar mara kunya kawai. Har zan wuce banyi niyar kula suba jin tace dani mara kunya sai na juyo gare ta na fasa fita daga gidan. Nai mata wani irin kallo sama da kasa a wullakance nace kar ki dauki alhakin dabba kici mai mutunci, don ko dabban ma ya fiki mutunci da daraja a idon jama a. Don da dabba yana da baki aikai mai sallama da zai amsa sallaman kai tsaye kin ko kaga ashe sunfiki darajja kenan daidai nan mujida ta shigo gidan ta tsaya tana sauraren mu. Nace ke dani yanzu waye mara kunya da zaki zo har cikin gidana duk da na kyale ki ki nemi ki kirani wai mara kunya ni yar kice ko may ? Mujida ne ta katse ni da cewa towai ita din waye nace ban san ko ita din waye ba na dai dawo na same ta a cikin gida na tana shige da fice min a gida ai yanzu dai muka shigo dake gidan ko ? Na tambayi mujida ta amsa min da eh wallahi nima naji shiru baki fito ba shine naji muryan ki na leko. To ta tare ni da suratai tana fada dani amasifance ni kuma bansan da watake yi ba ma, a gidan sai dai ko idan mahaukaciya ce ita din don in ba hauka ba ba yadda za ayi ta shigo min gida ki tube haka zindir don daga ita sai breziya da gajeren wando a jikinta. Mujida ta kalli Lilliya ta sake kallo na taga ban da inda nake da hadi da ita na kinga ina da hadi da ita ne mujida ? Sai Mujida tace kai dis one na ashawo, Wanan ai karuwan titi ne ta shigo maki gida taci maki miji ne , "na so dem dey do ehhuu ashawo ta shiga mata ihu da sowa akai tana batun tara mata mutane. Lokacin ya zabura zaune kamar zai yi magana Mujida ta juya gare shi tace Oga barin fada maka gaskiya zama da irin wa yan nan shedanun yana jawowa mutum babban asara a rayuwa. Ka gansu nan guba ne irin su don a take sun nakasa wa mutum rayuwa ko ta jama hasara babba. Da mamaki suka tsaya suna kallon mujida don bata da alaman tsoro ko kadan irin matan nan ne da suka san kan lagos ciki da bai dinta. Fada ba nata ba ta saye zancen haka, wai ko ina Safiya take haduwa da irin goggagun mata haka yan duniya dasu oho. Itako Lilliya zuciyar ta ji take yi kamar zai fashe don bakin ci, kalaman da muke fada mata sun mata muni sosai. Shiko maigidan da mamaki a fuskan shi ya ke kallon mu yana son yai magana sai dai bai iya cacan bakin mata ne dai kawai. Zan sake yin magana sai ya daga min hannu da cewa dakata, min don Allah, shin munyi dake cewa gidan kine ke kadai. Yadda gidan nan yake gidan mijin ki, na fada maki itama gidan mijin ta ne, tana da daman shigowa duk lokacin da take so. Sai Lilliya ta karbe da ai wanan cin mutumtuci ne kamar wanan zan zauna gida daya da ita tana min rashin kuya don bata da tarbiya, wanan yar kauyen da ita may ta sani banda jarabar maza iri naka har da zuwa mata ciki don kwakwa. Wanan ga kankanta ga jahilci Mujida ta cabe da cewa yi muna shiru munafuka masu yawon kwantan mijin mutane kawai ashawon banza ai gara da ita an sheda daurin auren ta kefa a bariki ne aka dauro naku. Na ce kin taba ganin karuwa tayi aure ne ai sai zaman banza dai, sai na hada da cewa karuwan titi anzo za a samu wurin fake wa. A hasale ya dani ki iya bakin ki Safiya kiyi hankali dani wanan dakike gani, ni a wurina tafiki tunda tasan mutinci da daraja a idota. Don kana dan bariki irin ta ba muje ne ya tadda mutafi kai da ita duk ruwan bariki na cinku kaga dole kasan ta fini, tafini iya shan giya da karuwanci ba. Fayau fayau ya kwashe ni da mari biyu masu kyau a fuska na yace ba nace ki iya bakin ki ba wanan da kike gani tashigo gidan nan ke nan bata sake fita ko ina. Na dade a duke tare da dafe kumci na inda ya mare ni , inajin mujida na ta mai ruwan balai akai ta hadu su ta zage tas yace shi ba zai mata komai ba ni dai dana jawo ta gidan zaiyi wa. Don haka in zaki zauna ki zauna in ba zaki iya zama da ita ba ga hanya nan ki fice min gida na fada maki sai lokacin na samu baki magana. Nace zan fice amma sai ka bani shedan ficewa karna je gida ace zaa sake dawowa dani gidan ka kuma don da in dawo gidan nan gwama muta. Yace abu mai sauki kenan wai takarda kike nufi komay nace dashi eh a hasale. Mujida dajin haka ta fara fadin a, aa kada kayi mata haka mana, ga ciki ajikinta ga kurciya kace zaka saketa don wanan ashawon matar ta nuna Lilliya a wullakance. Wallahi na fada ma wanan da kake gani poison ne sai ta halaka ka, har dukiya ka da komai naka, daga karshe ta gudu ta barka da wahala. Indan taga sakin yafi mata sauki ai a shirye nake da yin sakin kalman sun ban mamaki wai a kan karuwa yake maganan sakina. To ko na zauna may zan tsinta ga mutumin da ya furta hakan banda tarin takaici da bakin ciki da sune na ke gani a koda yaushe na dago kai na kalli Lilliya wace ke tsaye tana wani muzurai da ido don jin abin da ke wakana tsakanin mu. Bata da wani abinda za a so daga gare ta haka take kamar kato yai shirin mata da ita, sai farin na mai data shafa ke aiki jikin ta kawai. Muryan Lilliya ne ke fadin dama ai karanbani ne da kwadayi ya shigo da ita ba komai ba may zaka deba a jikin wanan yarinya nema wai. Na ce ai shi yasan abinda yake diba gare ni kullun in ba kaddaraba may zai shigo dani cikin fasikai irin ku. Ta tafa hannu da min tsowa miji dai ya dawo hannun na dama nawane ba naki ba, dama matsala aka samu ya aure ki dan wani dalili yanzu ya dawo hannuna kenan . Lilliya ya ambaci sunan ta cikin tsawa ta bar maganan da take yi din yace kyale ta ni ma nagaji da wannan yarinyar mara tarbiya haka. Nace dashi kayya amma kai kan anyi hasarare baka ko jin kunyan kiran wanan a matsayi matar ka. Wallahi kaban mamaki wai da hankalin ka da ilimim ka namiji kamar ka, zaka kar awanan matar titin fuska a kone yasha mai, ga kai kamar iccen kwakwa, Abu haka a tsaye kamar kato, mace ba addini ba al,ada ba dabia na kwarai, mutum irin ka maijin duniya da hayaki bai kamata ya buge a wannan abin banzan ba . Dama wata mai surar kwarai ce sai kai min gadara a dajin kai a kanta dan wanan dai kake cewa wai tafini tafini iya shedana ko. Wallahi na tausaya maka yaya kayi hasara namijin duniya kamar ka ya kare a dadiro da wannan abu da bata cikin tsarin mata. Ai gara dani da kankantana da rashin ilimina ko ba komai ina da addinina kuma a gaban iyayyena ka dauko ni ba bariki na biyo ba In dai wanan matar ne gatanan ga ka ba zan zauna ku kashe ni da bakin hali irin na kuba kai da ita , da yarinta na tsohuwar banza ta zo ta zauna min gida tsofai tsofai da ita wai kuna dadiro dadiron na kuma na iya shege ne. Banji tsoron su ba haka na tsaya gaban su nai masu tasa yana tsaye kamar wani soko a buge yake har lokacin. Ya kalle mu nida mujida rai bace yace ku fice ku bani gidana, sannan ki tatara yau yau ki bar min gida na ki bar garin nan ki koma gida uban ki na sake ki saki daya. Mujida zatai magana ya daka mata tsawa yace na fada maku kubar min gidana haka na. Nasan halin shi sarai don haka na dakatar da mujida nai mata godiya tare da bata abinda ta bukata gareni, ta fice tana tausaya min. Dakina na shiga wurin da nake boye kudi na daga na kwashi kudina da takarduna na fito ba tare da na sake waigen su ba yana zaune yayi tagumi kamar wanda abin ya dama. Koda na fita waje tsayawa nayi ina tunanen inda zan nufa araina ko inje gidan gwago na don kartace ban fada mata ba na wuce. Sai kuma nace banzan tafi ba gidan anty zan nufa maman biyu sai na tare taxi na tafi, ina tafe ina tunane idanuwa na suka yi jawur ina jin zuciyana yana min zafi da wani irin kuna da zugi. Ina tuno irin cin mutuncin da nai ta fuskanta a gida duk hakkurina sai da haka ta kasan ce dani yanzu in naje gida a haka ko wani iri hukunci zan fuskan ta gun mahaifina kuma. Wasu hawaye suka zubo min ina jin tsanar shi ya kara shiga min rai na har na kai gidan maman biyu ina tunane a zuciya na. Na samu ta dawo aiki kenan tana zaune yaran ta sun zagaye ta suna mata hira sai gani na shigo. A yadda ta ganni ta fahinci ba lafiya yaran suka rugumay ni suna min oyoyo da ganina tace oya ku shiga ku cire uniform a huta . Duk suka shige suka barmu da ita sai a lokacin ta dago kai ta dibeni take cewa Safiya nayi mamakin ganin ki yanzu da yamman nan . Dukar da kai nayi bance da ita komai ba nace anty yuwa nake ji murmushi tayi tace yunwan ne kike ji yasa ki kuka don ga alaman kuka nan tare da ke. Ban samu cewa komai ba takira yar aikin ta tace ta kawo min abinci da zai isheni wai yunwa nake ji kin san abu gamai ciki. An kawo abinci sai dai ban iya ci ba tana lura dani tana waya sai ta katse waya tace a, a Safiya bakici abincin ba mana ko baiyi maki dadin ci bane. Maimakon in yi magana sai ga hawaye yana zubo min a idona nace a hankali anty gida zan tafi yau. Ta dago da sauri tace wani gidan dai kike magana zuwa nace garin mu. Tace kina ko da hankali kuwa yau din nan kina haka kice zaki tafi arewa may zaki tafi yi arewa kina cikin wanan condition din. A hankali nace da ita ya sake ni ne zan koma garin mu ne. Ya may kika ce ta fada a razane . Na sake cewa anty ya sake ni akan wanan karuwan tashi yaban saki ya zabi zama da ita sama da ni ne. Innalillahi take maimaitawa da karfi a bakin ta tace Safiya da gaskiya kike ko wasa wai? Nan na fara bata labarin abinda ya faru a gidan tun fitana har dawowa na gidan da nazo na samay a cikin gidan. Tace yanzu abin nashi har yakai can ya sake ki da tsohon ciki a jikin ki babu ko tausayi hakan . Anya wanan mijin naki ko yana da imani ya bata maki kurciyan ki ga banza ya cuci rayuwan ki. Kin ga hakkuri zaki duk abinda ya samu bawa mukkadari na daga ubangiji bai cuciki ba kanshi ya cuta da yardan ubangiji zai girbi abin sa. Amma uwarshi ta sani kuwa na girgiza mata kai alaman aa na hada da cewa ban tafi can ba nan nayo. Tace ya kamata muje mu sanar da ita karta ce baki fada mata ba don mutum abin tsoro ne yanzu balle tana gani itace makusanciyar ki a garin nan. Nan dai ta yanke shawaran mu tafi mu sanar da ita ko banza dai gwago nace ita din . Mun tafi mun samay ta tana cika tana batsewa dakyat take karba muna gaisuwan da muke mata, bayan mun zauna ne tace kun kai ga yadda kuke so kedashi. Yanzu may kika zo yin mun sai da kuka bata abu zaki taso ki zo min may kike son na aiwatar yanzu din. Gidan shi ne shike da iko da abinshi ki kyale shi mana yayi yadda yake son da gida shi kema ba kawo ki akayi ba acikin gidan. Anty ne ta katse ta da cewa kai kai wanan magana taki baiyi ba a saki yarinya sai kuma ki bita da wanan irin maganan . Yanzu in yarki ce ta samu wanan matsalar abinda zaki ce da ita kenan, karuwa fa zaman dadiro a cikin gidan ta haba hajiya kiyi tunane mana. Tace haka zan fada mana to waya ja wanan matsalar haka karamar yarinya da ita ta iya kishin tsiya. Yanzu ai sai ki koma gida kuje kuyi ta zaman gida ai kin san abinda kika baro gidan naku ba wani abu ya canza ba. Tsam anty ta mike tace dani tashi muje Safiya akwai Allah duk wanda ya cuci wani a cikin ku Allah yana ganin sa ai. Haka na muka fice gidan muka barta nan tana ta faman fada abin dai zabar kunya don bai ma faduwa . Gidan mama biyu nai kwana biyu ta rakani gidan na dauko abinda nake so cikin kayana washe gari na kama hanyan arewa acikin motar da akai min shata sai gida. Asubanci mukayi amma sai dare muka kai garin mu lokacin da mota ya tsaya kofan gidan mu an shiga sallah isha,i . ZAINAB IDRIS MAKAWA SEENABU 8/14/20, 7:11 PM - Ummi Tandama: BAHAGGON, , , , , , , , 🧕🏿2️⃣5️⃣🧕🏿 YAR UWA NOVEL DIN NAN NA KUDINE IDAN BAKI BIYA BA KADA KI KARANTA HAKKIN WASU PLEASE, , , , , Cikin wata daya da nayi a gidan mu cikina ya karasa shiga wata na tara duk da nace ma ummi da mama bansan ko wata nawa cikin yake ba. Amma su daya ke manya ne sun gane na shiga watan tara nan aka shiga min jikile jike ana bani. Don samun saukin haihuwa wai idan haihuwa yazo vazan wahala ba sosai indan ina shan abin karya zaki. Watarana da dadare ina cikin barci na farka da matsanacin ciwon mara da ban taba jin irin sa ba, wai ashe nakuda ya kamani . Cikin barci na dinga tada ummi na daga barci ina fadi wayyo ummi bayana marata ciwo kamar zai fashe min nake jin shi. Ummi ta tashi a rude take tambayana ya nake ji na fada mata, fita tayi daga dakin taje ta tada mama sai gasu sun dawo a tare da mama din dakin. Nan suka fara bani abinda ya dace da akewa mai na kuda da fada min yadda zanyi abin yazo min da sauki. Abu wasa wasa har wuraren karfe sha biyu na rana ba labarin haihuwa gashi ina dan banzan wahala. Don haka suka yanke shawaran su kaini asibiti don ina wahala sosai na gala baita matuka na wahala a gida. Mun isa asibiti aka duba ni suka ce haihuwa ne sai dai bazan iya da kaina ba don haka za ai min theater ne. Bani dake wahala ba harda su mama da suka kawoni sai da hankalin su yai matukar tashi, aka rubuta masu abinda za a sayo kafin theater din. Baba ya fara fadi tashin neman kudi don ya sayo maganin da sauran kayan aikin don baida kudin a hannunshi. A cikin karfin hali na daure nace baba akwai kudi a hannuna a tambayi ummi na agida ta duba zata gansu. Allah da ikon shi anshiga dani dakin theater sai Allah ya kawo min saukin haihuwa na nisa sai abin cikin cikin nawa ya fito. Ashe abin da matsala ne shiya sa na wahala diya ce mace sai dai tazo da wani irin halitta na daban likitoci suka taru akan mu suna dibata. Daga karshe dai hakana dai aka sallamay mu muka koma gida da ita cikin yanayin da tazo. Sai dai mama ta hana abawa kowa yar ya gani tana dunkule a raggan zani duk wanda yaga abinda yarinyar keyi dole ya tausaya mata. Karamar yarinya da bata dauki alhakin kowa ba a kanta tana bautar Allah cikin wani yanayi na ban tausayi. Amma ita inna har kiran mutane take su zo su aga abinda na haifa mutane ko sai suka fara tururuwan zuwa ganin halittan yar. Kwana daya da haihuwa Baba ya shigo gida da dadare yake ce min yaya za a yi a samu su gwago can lagos a fada masu zancen haihuwan nawa. Na lumshe ido nace baba aida a kyale su kawai, yace aa baki da hankaline yarsu ce fa suna da hakkin a fada masu ai. Sai nace sai dai yaya saadu don shi kawai nake da nomban shi wayan shi cikin su bayan shi ban da lanban kowa cikin su. Ko shi da yazo ne yaban wayan da zo dashi shine har na samu namban shi din, da ban da layin kowa a cikin su. Yaya sani ne yakirashi sai baba ya karba yana fadama mashi zancen haihuwan yayi murna sosai dajin na haihu lafiya da Allah ya saukeni lafiya ba tare da anmin aiki ba. Sun gama da baba yace a bani wayan yai min barka na karba cikin jin kuya nake karba mai yace da ya kashe zai kira mummy da Ahmed ya fada masu na sauka lafiya. Hakan ko akayi nan ya kirsu ya sheda masu zancen haihuwan nawa sai dai ba wanda yai farin ciki da jin haihuwan daga cikin su. Shima gogan daya kira shi cewa yayi and so what idan ta haihu may kake son nayi mata yanzu kuma ? Ashe lokacin suna tare da Liliya ne ya kirashi don haka baida halin nuna farin ciki da haihuwan nawa. Nan dai dan uwan yai mashi tas yakuma ce indan baiyi hankali ba sai ya hada shi da hukuma akan wanan case din. A haifa ma ya kace min and so what kai wani irin jahilin mutum ne wai kana koda inmani kuwa kai ? A cikin fushi ya nufi gidan su yana fada ma mahaifiyar su yadda sukayi da saadu din wai ya kira shi da jahili. Tace ai gaskiya ya fada maka dole ne ai a fada muna san nan ai wani abu daga nan wurin mu kuma ya zama dole mu tafi yace wa ? Cikin hasala shi ba inda zan tafi indai ke zaki tafi ban hanaki ba amma nikan ba inda zan tafi tun wuri . Don nasan a jirace suke damu yanzu kuma sun samu kafar samun mu ke nan don haka ni ba inda zan tafi final. Saadu yazo yasa uwar a gaba son su hada abinda zasu sai mu na kayan suna suzo muna dashi, mahaifiyar nasu tace bata da kudi yanzu a dai tambayi Ahmed din. Gogan da aka tambaye shi dubu goma kawai suka samu a wurin shi wai baida kudi duk karuwai sun cinye kudin shi da giya dole yaya saadin ne ya fitar da kudi ya sai muna abinda za a zo dashi din. Sun saka ranan tafiya saura kwana biyu suna munyi waya dashi nai mashi kwatancen gidan maman biyu don yaje ya fada mata. Ya ko je tayi murna dajin na haihu din ta karbi lanba na a wirin shi ta bashi abinda zai kawo min sai dai bai gwadawa mahaifiyar ta suba. Da dare ina zaune a dakin mama don anan nake jegona sai naji wayana na tsuwa alaman kira ya shigo min . Na dauka da sallama muryan wace najine ko a barci na falka ina sheda shi maman biyu ce ta kirani, na dan kwala ihu do jin muryan ta, tace dani. Ai nayi fushi dake nace anty ba hakana bane wallahi kullun kina a raina ban san yadda zanyi in kiraki bane. Don lanban da kika bani ya bata nan dai muka taba hira da ita take tambayana yadda muka kwasa da mahaifin mu da nazo gida ? Ta fada mata komai harda zuwan yaya Saadu wurin mu da yadda ya wanke ni a gaban su baba da sauran yan uwana. A karshe mukai sallama da ita tace zan ga sako wurin yaya saadu idan ya zo nai mata godiya na kashe wayan. Idan na kalli yarinyar tausayi take ban don yadda take wahala matuka taita murde murde da hannu idanuwa warwaje tana wani irin numfashi a wahalce kace ko zaka je kadawo kasamu bata da rai. Mama ce ke kwana wahalce da ita har safe sai a kama mata tadan kwanta da rana ta runtsa barcin ba wani barci ba take tashi. Da aka ga wahalan yai ma yarinya yawa aka koma asibiti da ita likita ya tambaye ni idan na taba mugun faduwa da ciki. Nace a a yace duka fa kowani buguwa mai karfi sai nai shiru mama tace mijin da ta aura yake dukan ta da ciki likita yace wanan abun ne ya taba yarinyan tun a cikin ciki yasa tazo kamar jujartata. Hawaye na fara yi ina tausayin yarinyar da kaina, magani aka rubuta muna muka dawo gida rai baci tun a mota mama ke ta zabga fada tana cewa mutane ba imani haka ?. Yanzu gashi ke ke wahala shi yana can yana barikin shi hankali kwance abinshi. Mun iso gida mama tana kuka tana ma mutanen gida mu bayani komai da likita ya fadi. Allah ya isa yaya sani suke ta ja baba baki ya mutu da har ya fara cewa in gwago tazo sai in hakkuri in koma dakina. Wai kada yarinya ta tashi ba uba tare da ita maganin da likita ya bayar a bata shi ake bata kai da kai sai numfashin ya fara ragewa ya dan fara komawa nomal. Su yaya Saadu sun taso kamar yadda suka shirya ba isoba sai da safe don tafiyan dare sukayi. Tun da ya shigo yagga yadda yarinyar take hankalin shi yai matukar tashi sosai gwago tun taron da yan gidam mu sukai mata ta shiga tsarguwa. Mama na kuka take fada masu abinda likita yace a gamay da yarinyar yaya yace komai akace ya faru ne ba a kyauta ba gaskiya amma ayi hakkuri. Suka bayar da abinda suka zo dashi wanda ni nasan yaya saadu ne yayi shi don nidai duk zama na gidan bai taba yin min sutura ba. An karba da godiya sai gwago tace adai yi hakkuri dashi mama tace ba a dai kyauta ba gaskiya malam ya bada yarinyar don zumunci ya dore gashi abin kuma baiyi dadi ba. Baba sun zauna da gwago ya nuna mata bacin ran shi sosai ga irin rikon da dan ta yai min acan har da nata laifin ma, sai ta kama kukan munafunci wai yara zasu bata masu zumuncin su. Baba yace basu bata muna zumunta don ba su suka hada mu ba balle su yanke muna zumuncin mu. Nan ta danji sauki har ta fara aibanta ni wai ban da kirki banda tatali banda sanin ya kamata ko ita rashin kunya nake mata.. Sai da yaya saadu ya bari ta gama ya kawo matsalnta duk ya fada ma baba da yadda tabar tarbiyan su ya lalace komai ya fadi. Sun dade suna magana baba ya san yi mata nasiha har da alkwarin wai zai mayar dani dakina yace dasu. Ana gobe sunane sun zo washe gari da safe yarinyar ta koma Allah ya gani banji bacin rai da rashin ta ba don a halin da tazo da ta rayu wani gwamma ta koma yafi. Nan dai aka kawar da ita yan uwana sun tausaya min sosai nidai abu ga kurciya ga bacin rai banji komai ba a lokacin. Sai gwago ta kebe da yaya saadu da mama wai a rage abinda suka zo dashi tunda yarinya ta koma nan yaya saadu yai cikin ta. Yace indon dubu goman da Ahmed ya bayar kike jin zafi ga dubu goma ki mayar mai da abinshi ban iya abin kunyan da kike shirin yi. Mama tace wai ko Rakiya kan ki daya kuwa may yasa abin duniya yake rufe maki ido haka ita yarinyar da tai wahalan haihuwa fa ? Nan dai suka yi shi baran baran sai da rayuka suka baci masu, washe gari suka daga suka koma inda suka fito. Bayan wucewar sune mama ke mayar da yadda suka kwashe da gwago kan kayan nace mama aida kun mayar masu da abinsu ma. Don ni bani son komai da ya fito daga wurin Ahmed sai mama tace ai ai a she shi dubu goma kawai ya basu su kara. Duk kanin ne yai sauran kayan da kuka gani uwar bata sako komai ba ni bansan inda Rakiya zata kai son kudin ta ba wallahi. Nan nake basu labari ai ko zuwa nayi gaida ita bata bani abinci sayarwan ta sai ansaya mun zan ci. Kowa yai tir da irin hali nata na son kudi da rashin taimakawa uwan uwa kullun tazo sai kukan babu takeyi. Maman biyu ta bugo min waya da dare tana min barka da taro ya watse lafiya ? Murmushi nace anty ai yarinyar ta koma jiya nan dai nake fada mata yadda akayi da abinda likita ya fada akan ta. Tace kin ma huta wallahi Allah ta baki lafiya yasa ita kuma ta huta nace amin nan dai mukai hira tana tambayana yadda aka kwashe da gwago tazo nake fada mata komai karshe nai mata godiyan sakon da ta aiko min mukai sallama da ita. Tun da akai sati na dan watsake ina yin komai sannu a hankali ina mai da jiki na ina harkokina na yau da kullun sai dai ban fita ko ina ina gida koda yaushe. Dan dama dama naka dan dauki lokaci in fita ziyaran yan uwa ban dadewa in dawo gida don ko na fita sai na tsargi kaina don ban son a dauko min maganan zama lagos. Sana a nake gadan gadan kanena ke fita mun dashi don haka hankali na yadan kwanta har nakan manta da rayuwan gidan Ahmed din da nayi a baya. Zan tura kudina wa maman biyu da kudi sai ta sayo kaya ta turo min dashi ta motar haya a kawo min. Haka nake har na dan samu nawa sai kuma kyashi da hassada ya shiga zukatan Inna da wasu yaran gidan namu zaka ji ana sake magana akan sanaa nawa a tsakar gida koda yaushe. ********* ********** ********* Hai huwana da wata uku na dan fara ciwon kai sakuma yawan zazzabi da yake biyowa akai akai. Ranan ina kwance yaya saadu ya bugo min waya na mike da kyat na dauki wayan tare da sallama yanayin murya na da yaji yasa yace baki da lafiya ne Safiya. A hankali na bashi amsa da wallahi yaya kwanan nan duk kai da zazzabi ke yawan damu na na rasa gane kan jikin nawa. Yace subbahanallahi kin kuwa je asibiti nace ban je asobiti ba ina dai shan magani a gida ne yana min sauki in na sha magani ai. Yace No kije asibiti a duba lafiyan ki asan may ke damuwan ki yafi sauki da shan maganin nan da kike yi nace naji yaya zan tafi. Mukai sallama yace dama ya bugo ne yaji lafiyana tunda suka koma bai samu kirana ba sai yau nayi hakkuri nace nagode kwara muka sallama yana kara jaddada min akan in tafi asibiti fa nace zan tafi ai. Kwana biyu na ji sauki nikan na manta da zuwa asibitin da mukayi dashi naci gaba da harkokina kawai. Kamar naji sauki da jikin zai tashi mun sai yakaini kwace kasa nai ta faman jiya a gida ina zuwa chemist ina karbo magani na dan ji sauki. Ban san yaya akayi yaya saadu ya samu lanban yaya Sani ba ya buga mai yana cewa ya kirani wayana a kashe. Sai yaya sani yake ce mai ai banda lafiya ne kwana biyu kila na kashe wayan ne . Yace subbahanal lahi kon ka kaita asibiti andubata yace dashi a a ina ganin bataje asibiti ba yace da yaya sani don Allah akaini a dubani. Shi zai turo da kudin zuwa asibitin haka ko akayi amma da yaya sani yai magana gida akace mai dahuwan kassa nakeyi tunda banyi ba da na haihu sai yanzu nakeyi. Sunyi waya dashi yaya sani ke fada mai abinda akace ya matsa wa yaya sani aka ya kaini asibiti fa yanzu ba a wasa da ciwo gida. Har na dan ji sauki kwana biyu kuma sai jikin nawa dawo fiye da farko dole muka kwasa sai asibiti. ZAINAB IDRIS MAKAWA SEENABU 8/14/20, 7:11 PM - Ummi Tandama: BAHAGGON, , , , , , , 🧕🏿2️⃣6️⃣🧕🏿 YAR UWA NOVEL DIN NA KUDI NE IDAN BAKI BIYA BA KADA KI KARANTA HAKKIN WASU PLESASE, , , , , , , , , , Mun yanki kati muka bi layin ganin likita a tare da sauran jamma a da muka samu a wurin. Sannu sannu har layi ya kawo gare mu muka shiga wurin likitan bayan yan tambayoyi sai ya tura mu wurin yin test. A can ma mun dan bata lokacin mu a wurin don mutane da sukai yawa masu son ai masu test din. Mundan jira suka bamu sakamakon mu koma wurin likita dashi muna zaune a gaban likita dani da baban mu da yaya sani. Munyi zaune shiru ya gama rubutun da zai yi ya dago kai yace baba wanan yar kace ? Baba ya gyara zama yace kwarai kuwa yata ce wanan kuma wan ta, sai likitan ya sake tambaya tana da aure ? Baba ya dan kara gyara zaman shi yace eh to ta dai taba auren yanzu wata hudu kenan da mijin ya sakota da ciki ta dawo gida wata uku kenan da ta haihu goyon ta koma. Sai likitan ya girgiza kanshi alaman tausayawa gare ni ya sake tambayan baba yanzu ina mijin nata yake muna son ganin shi, shi mijin nata. Baba yace ayya ai ba nan yake ba can Lagos yake da zama da iyayyen shi shiru likitan yayi yasa biro da yake rubutu a bakin shi kamar mai nazari. Ya dago yace baba indan ba damuwa su fita waje muyi magana dakai sai baba yace ai ba damuwa likita duk diyana ne indan kaga wani matsala ne kafadi muji. Sai likitan yai shiru can kuma ya dan dago kai ya kalli baba din yace a gaskiya ba yar ka tana dauke da cutan tsida mai karya garkuwan jikin dan adam. Baba yace ban fahince kaba hawanjini komay kace likitan ya girgiza kai yace gwaji ya nuna muna tana dauke da cuta mai karya garkuwa jikin dan adam watau HIV. Ban san lokacin da na yanka ihu ba baba yace ke may ye haka kuma daga bayani ki yanka muna ihu tashin hankali. Likita yace tana da right din yin haka don ba karamin masifa bane ya samay ta. Baba tace likita may kace yace ina nufin ciwon da ya samay ta yana da wuyan sha ani sai ya fara yiwa baba bayani yace. Sai da ya kawo wiri aure ya ce mace na dauka ta mijin ta idan mijin ba mai tsayawa ga matar sa bane yana neman mata a waje shine dalili daya na tambaye ku mijin nata yana ina? Da sai mu ga gwada shi mugani shike da ciwon ko ita anan zamu fahinci wanda ya sawa wani ciwon a cikin su. Baba ya miki yace ke tashi muje kin ji ai ba nan kawai bane asibiti akwai wasu guraren zuwa bayan nan. Da kyat na miki don duk illahirin jikina yai sanyi baba na ta faman fada niko tunane nake yi ko shiyasa yaya saadu ya matsa in je asibiti. Yasan dan uwan shi nada ciwon ne yasa ya damu da zancen azo dani asibiti a duna dai aga may ke damuna ne. Mun shiga gida ana fadin kun dawo baba ya na fada kaji min dan iskan likita kawai ka rasa abin dafa mata sai mugun ciwon da kowa ke guda. Nan da nan aka firfito waje don saure inna ce tace may akace yana damun tane wai ? Yace bar mugun liki wai wai Safiya na dauke da wani ciwo ko tsida ko may tace badai kanjamau ba yace wai shi . Nan da nan Inna ta dafe gaban ta munshiga uku mun lalace a gidan nan muke zaune da mai kanjamau sai ya dakata fadan yana kallon inna din da ta rikice. Yace ke kuma may nene duk kin bi kin wani rude dake ? Tace malam kanjamau fa akace irin ciwon da ya kashe dan gidan malam sahabi kwana ki har akaki taba gawan sa. Nan jikin baba ya fara sanyi yace don Allah ki bari ke ma kin yarda ke nan tana da wanan ciwon ? Tace bani yarda tunda mijin ta karuwai ne abokan hurdan shi ko yaushe cikin su yake yana like a gidin su yaya bazan yarda da maganan likita ba. Ummi na tasaka kuka mai tsuma zuciya mai sauren ta tana cewa na shiga uku na lalace yau ni Rabi may zan gani a rayauwa. Tayi dakin ta tana kuka cikin dakin ta samay ni nima kukan nakeyi in cewa ummi yaya Ahmed ya cuci rayuwa na. Ummina na mutuwa zanyi in barki in barki da yan uwana da kowa naki ni safiya na shiga uku. Yar nan Ahmed bai cuce ki ba malam ya cuce ki shida ya bashike duk da yasan halin yaron ya kuma amince da ya hadaku. Kuka muke yi nida ummi da kanne na adakin baji ba gani sai baba ya tsaya daga kofa yana cewa wai baku barin kukan nan ba a fa sheda cewa shine abinda ke damun ki ba kun aza ma mutane kuka haka a gida. Dole mukai shiru irin yadda yake ta faman fada sai dai ummi bata tsagaita nata kukan ba da take yi gwanin van tausayi ance uwa uwace bakowa ke karba sunan ba. Baba ta samu an tsagaita kukan ya kwantar masu da hankali dan kwana biyu ga damuwa ga ciwo naci na baba ya ki kwantar da hankali ya fahinci komai. Wanan karon an jijigani sosai Yaya sani sukai waya da yaya saadu yana tambayan shi yaya jikin nawa ? Ya fada mashi ina jin jiki anje asibiti ga abinda likita ya fada innalillahi yake maimaitawa yace dama ina tuhumar haka ya faru . Don shima Ahmed din tun fitan Safiya baida cikakan lafiya tare dashi yace a kaiwa baba waya su yi magana. Bayan ankai sun gaisa da baba yake cewa baba naji ance kun kai Safiya asibiti likita ya fadi abinda ke damun ta kun karyata. Baba yace gaskiya ne haka akayi wani likitane mai mugun nufi ya zarga mata wanan sherin don kazafi irin na likitoci. Yaya Saadu yace baba ka saurare ni kaji yace ina jinka yace don Allah don Allah kukai yarinyar nan asibiti ta karbi magani in ba so kuke mu rasata ba gaba daya. Abinda likita ya fada ba karya bane haka ne don na dade ina zargin haka shi ya da ita don mijin ta ma nemin mata ne ga shan giya idan ya sha baya laakari da irin matan da yake hurda dasu. Baba kukai ta asibiti a san abinda ake ciki su dora ta ga maganin da ya dace tasha tin bai mata nisa ba. Baba yai mashi godiya sama sama sukai sallama ya dukar dakai yana kukan nadama ya cuce ni ya cuci mahaifiya ta dashi kan shi. Tun wanan lokacin ya koma kamar baida lafiya a gidan washe gari ma bai tafi wurin bidan kudin shi ba. Ina daki mun bana fitowa don da na fito yanzu kowa zai kama kan shi babu mai zama dani balle idan na taba abu wani ya taba. Daga ni sai yan dakimu nake hurda kawai a gidan suma kamar ana kyanaman su din kamar ni. Abinda yasa na fara ganewa yadda mama ta dauke kafanta ga sha,ani na agidan ba ruwanta dani yanzu. Ba may son ace yana hurda dani kamar zan lika masu cutan a jikin su koda yaushe ina daki ga jikin ba dadi min. Shi baba har lokacin bai yarda ba saidai nadama ya shige shi sosai na yadda yaba da ni ga dan gwago duk da yasan bana kwarai bane shi. Ya dinga tuna irin badakalar da suka kwasa da ummi a gidan kan aure na , ashe tafishi gaskiya da ta nuna rashin yardan ta da aure. Ashe mafalkin da tace tayi dani mara dadi nada na saba da abinda zai faru da nine gaskiya idan haka ne gwago taci amanan zumunci. Ga ciwo ga saki ga haihuwa ba yar tazo a wani irin yanayi takoma ni ina zan kai alhakin wanan yarinyar a kaina. Sai hawayen nadama da dana sani suka fara zubo mai yana fadin Safiya ni na cuce ki da kaina da na tursasa maki auren wanan yaro akan ki. Kwana biyu baba yayi cikin wani irin yana yi ga ummi na kullun tana faman kuka a daki gwagon ma haka. Kwana bakwai da faruwan wanan maganan sai ga yaya saadu ya dira garin da dare mun dai ji zuwan shi amma bai shigo ba don dare yayi lokacin. Da safe ya shigo gidan ba wani taron arzikin da ya samu gun mutanen gidan mu sai a wurina da ummi na da bata gwada mashi komai ba. Don ni nasan irin taimakon dayai wa rayuwa na a likacin da nake bukatan taimako ba kowa a kusa dani. Ya gaisa dasu ya shigo har dakin mu ina kwance na mike da kyat da kwance da nake ina mashi sannu da zuwa. Yace dani sannu Safiya ashe kuma haka abin ya kasance ban iya bashi amsa ba sai hawayen da ke zuba min a idon . Ummina ma kukan takeyi yana share hawaye yace dani bari kuka Allah na sane dake safiya kowani mai rai da irin tashi jerabawan. Allah yasa mu iya cinye jerabawan mu ummi tace dashi amin mun gode da kulawan ka gare mu yace nazo ne mu kaiki babban asibiti ki karbi magani da ya dace. In Allah ya yarda zaki samu lafiya in dai kina shan magani Allah da yai cuta shi keda maganin sa. Sai ga baba ya shigo dakin namu ya kalle ni yace sannu safiya yaya jikin na amsa dakyat da da sauki baba. Daga inda yake tsaye hawaye ya fara zuba mishi yace haka Allah ya nufa dake zumunci nai wa suka ci amanan ki. Yaya yace ayi hakkuri baba in Allah yaso zata samu lafiya indai tana shan magani ai yanzu an samu maganin cutar. Yanzu baba asibitin birni zamu da ita inda zamu ji mafanin da ya dace a bata tana amfani da shi. Ikon Allah kana ganin zata samu lafiya idan ana shan maganin yace kwarai kuwa don ai mutane da yawa na dashi amma saboda suna amfani da maganin ba a ganewa. Yace a shirya ta sai in san da suwa zamu tafi mota na nan da nazo dashi dashi zamu tafi. Abin mamaki da baba ya fita ya lalubo mama don tafiyan sai cewa tayi gaskiya bazata samu zuwa ba adaije da wani. Muna jin ta daga dakin mu ina kuka ummi na kuka tace oh Allah mutum da ranshi ya koma abin gudu. Yaya saadu yace babu komai mama insha Allahu zata samu lafiya tace baka san halin mutanen gidan nan ba. Tun yanzu sin tsane mu sun tsagwamay ta kyama da tsoron mu suke ji wai zamu saka masu cuta mu halakasu. Yace babu komai mama a dai bari ta fara sha maganin a gani suda kansu zasu daina ai sai dai ta kiyayye rezan da take amfani dashi kada ta bari jinin ta ya fita wani ya taba. Da wanan masullan kitson naku na mata idan an kiyayye hakan ba abin da zai faru da kowa duk fadan mutane ne kawai amma banda haka ana mua mullar komai da mutum kamar kowa. Tace kayya yarinya dai ai ta nakasa yanzu ba zancen aure a gare ta ke nan har abada ko samun zuria a gare ta. Yace aa mama duk dai wanan a barshi har Allah ya bata lafiya yace mama ki shirya mu tafi dake kawai ina jin rikicin wanda zai tafi akeyi a waje da baba. Mama ki rungumi yar ki kar ki yarda ki biyewa mutane ki kyamace ta sai kowa ya ji dadin kayamatar ta a gidan. Ummi ta share hawaye tace babu komai ai idan na kyamace ta wa zai duba min ita ya riga da ya cuce ta yariyar nan ta bisa bakin ta da cewa baida tarbiya . Amma malam ya rufe ido yaci muna mutunci a gidan nan har yana ikirarin korana a gidan. Yazu da haka ya cika da ita wake wahala dani da ita a daki kawai ke wahala ba wanda ya damu da mu a gidan nan har da wa yanda ke zuga shi kan zancen. Baba ne ya shigo rai a bace yace duk sun ce bazasu tafi ba sai ummi tace ni zan kai ta da kaina barin tashi na shirya. Suka fita shida yaya saadu suka bar mu ummi na shirin tafiya sai ga gwagon ta ta shigo gidan nan ta samu ummi na shiri take fada mata abin dake faruwa a gidan. Gwagon tace baki zuwa zauna ki fake yaran ki ni aiki may nake da sai kin je da kan ki kamar baki da kowa duniya. Ta juya zuwa gida din ta shirya tai sallama da yan uwan ta bata dauki lokaci ba ta dawo dama yaya yana waje suna jiran a fito dani. Ummi na da gwago suka tallaboni zuwa wajen mota duk yan gidan mu sun zubo muna ido wasu na ce muna sannu wasu kuma sai kallon tsoro suke min. Mama ne take tambaya dawa zamu tafi gwago tace da ita za ai tafiyan sukai mata Allah ya bada lafiya. Aka kamani na shiga mota na zauna da kyat gwago ta shiga suna tsatsaye suna kallon mu yaya sani yai magana da cewa A a bada mama za a tafi bane gwago tace ai sun gama nasu ranan wuya sai naka ai sai kawai yace ina zuwa barin zo dani za a tafi. Ya shiga gida da sauri sai gashi ya fito da shirin shi uwarshi na kwala mashi kira yace sai ta dawo zan raka safiya asibiti ne. Nan tashiga da fada wai sai yaje an halaka shi ya mai she ta baya amma una baiji ba mota ya daga yaya saadu yaja babana yana gaba mu muna baya muka tafi. Mun bar ummi da jin bakar magana a gidan mussanman inna da ke ta zage zage dan ta daya bi. Har saida ummi ta gaji ta bata amsa tace ai itama ba saye tayi ba kuma ba qurin yawon banza ta kwaso shi ba. Yanzu kuce haka amma lokacin da kuke zuga baba a kan auren baku nuna bacin rai ba sai yanzu da ta baci kowa ya zamau jikin shi ya na nuna mata kyama. Allah da ya jarebeta dashi bai manta da ita ba yana sane da halin da take ciki kuma kowan ku bai wuce nan ba ai. Sai mama tace Rabi bai kamata ki fadi haka ba kuwa yaya zamu kyamace ta ai mun san ba ita ta dorawa kanta ba. Sun dai cuce ta kuma sai Allah ya saka mata don Rakiya da danta ba suyi ba wallahi abaku yarinya da lafiyan ta ku illanta yar mutane ko waiwaye babu. Yadda sukai wa yarinyan nan sai ubangiji ya saka mata ummi tace ai ba Rakiya kawai da duk wanda ke da hannu a ciki ubangiji ba zai barshi ba da yarda Allah. Mama ta shiga damuwa da maganan ummi ummi ta shiga daki tana kuka tabi ta tana bata hakkuri ummi tace wallahi ba zan taba yafe wa ba yaya. Kiyi hakkuri Rabi komai da kika gani ya faru da bawa Allah na sane dashi ummi tace amna yaya ya dace yadda kuke kyamatar yarinyar nan abin har mu ya shafa. Wanan maganan na ummi shi ya kawo laushi ga mama har ta tsawaci yayan ta a daki kan su daina guduna haka bai da kyau su kyale inna dama haka take son gani fa kowa a gida burin tane taga an koma baya. ZAINAB IDRIS MAKAWA SEENABU 8/14/20, 7:11 PM - Ummi Tandama: BAHAGGON, , , , , , , , , 🧕🏿2️⃣7️⃣🧕🏿 YAR UWA NOVEL DIN NA KUDI NE IDAN BAKI BIYA BA KADA KI KARANTA HAKKIN WASU PLEASE, , , , , , , , , , Yaya Saadu yana tuki yana min sannu yana jin wani tukuki a zuciyar shi gamay dani, yana ji kamar ya rabani da wanan ciwon gaba daya a jikina. Tausayi nake bashi jina yake tankar yar uwar shi da suka fito ciki daya ba komai ya yasa yake ji dani ba sai irin girmama shi da nakeyi. Wanda ko wayanda suka fito ciki daya basuyi mai yadda nake mai ya lumshe idon shi tare da nisawa. Yace a ranshi Safiya nai maki alkawari zan dinga kula dake muddin ina raye insha Allahu zan baki kulawa daya dace. Baba ne ke magana dashi amma baiji shi ba sai da baba ya sake maimaita maganan shi yaji shi. Saadu kayi hakkuri kasa imani da addua a a ranka nima abinda nayi nayi nadamar shi ban wa yarinyar nan adalci ba. Wallahi ban san abinda dan uwanka da mahaifiyar ku kuntatawan da suke wa yarinyar nan yakai yakai haka ba. Ya nisa yace baba abinda ya faru ba wanda ya isa ya goge shi sai dai tabbas tun farko anyi kuskuren aura mata shi don sanin ko waye Ahmed din sam bai dace da kamilar yarinya irin Safiya ba don sani ko shi waye da akayi. Yace yanzun haka karuwan da ya saki Safiya a kan ta ta gudu ta barshi bayan ta gama yashe shi kaf bata barshi da komai ba. Shima yanzun haka din ya fara jinya don ciwon nasa ya fi na Safiyan nisa sai yanzu ne wai mummy take data sani dashi. Bayan a lokacin da yake miyagun halayensa ta kasa tankwara shi ta dauki son duniya ta dora a kan shi. Itama karuwan naji ance takai kwance a inda take tana bukatan taimako. Ina zaune a bayan mota ina jin su na lumshe idona don bakin ciki sun cuce ni sun illanta min rayuwa na. Mun isa garin muka nufi asibitin direct nan ya bar mu cikin mota suka fita dashi da yaya sani zuwa ganin likita. Gwago ta ga mai ruwa ta kirashi ta saye muna tabani nasha baba na kallon yadda nake shan ruwan da kyat yana min sannu Safiya. Gwago ne tace Allah ya isar maki yar nan ya saka maki da gagawa sim cuce ki sun illanta rayuwanki ga banza. Baba yana jin ta hawaye yake na nadama yana gogewa yace gwago banyi wanan hadin da wata manufa ba a rayuwa na. Sai don zumunci ya kara karfi a ysakanin mu iyayyen mu duk abu guda suke ta uwa ta uba shine da tazo da wanan zancen naga dacewan shi nayi. Yaya Saadune suka dawo dauke da keken da ake sa maralafiya yace a kamani asa sama yaya sani ya ciciboni ina wai ya dora a keken. Wani daki ne muka nufa ashe likita ke ciki ya dan yi min tambayoyi su yaya da baba ke amsa mai yai rubutu ya bayar yace zasu dan kwantar dani inda masu irin case dina suke in sha magani na kwana biyu a gani. Aduniya ban san irin godiyan da zan ma bawan Allah nan ba sai dai ince Allah ya biya shi da alherin sa. Nan take ya sayo magani da ruwan da za a kara min da abubuwan gina jiki kuma yace ba zai tafi ba sai yaga yadda jikin nawa ya kasance. Baba kuka yake yana mashi godiya yace baba komai nai wa Safiya kaina nai wa don yar uwata ce ta jini. Na samu kulawan da ya dace dani ashe ciwo in ba a dace da magani ba sai ai ta wahala dashi. Don yanzu na rage yawa jin abinda nake ji a jiki na so sai sannu a hankali nake jin sauki yana shiga na. Kwana biyar suka sallamay mu daga asibitin, har lokacin muna asibitin da yaya Saadu da yaya sani. Sun bani magani amin register zan dunga zuwa ansan magani a wurin su tare da fada min mata kan da zan bi don kare kaina da sauran alumma da nake zama da su. Aka bamu sallama na dawo gida da dan karfin jiki na sai da yaya ya sawo min abubuwan bukata na rayuwa yai muna sallama ana ta yi mashi godiya ya kama hanya. Yan gidan mu na dan ga dan canji a wurin su yaran mama sun rage tsanar da suke min amma dai suna kyamana don in na taba abu sai an wake ko a yar a bayan idona. Kauna tace ta fada min haka sai dai nai murmushi kawai na ware kayan amfanina a gidan ban amfani da kayan kowa har da na su ummi na don na nema masu mafita. Da sannu ina warware wa na fara harkan kasuwanci na da mutane da farko suna kyamar saye daga baya kuma suka fara saya. ********* ********* ********* Yaya Saadu daya bar wurin mu gida ya koma direct tun da ya iso jikin su ya basu cewa bai cikin dadin rai. Sai da ya huta yai wanka yadan taba abinci kadan ya tashi ya fice gidan yaya Ahmed ya nufa. Ba kalman dake mai yawo arai sai da ya shigo dakin ummi ina kwance na dago nace dashi yaya ya Ahmed ya cuce ni Ya illanta min rayuwa ya kashe ni da yarinta na ya mai dani abin tsoro a cikin yan uwana da gari sai ya runtse idanuwan shi. Yai sallama yana ciki kwance ya taso da kyat ya bude kofan gida yaya saadu ya shigo ciki yana mai wani irin kallo. Zama yayi yai shiru ba tare da yai magana ba shima wuri ya samu ya zauna yana kallon shi don yasan magana ya kawa shi . Don tun da na bar gidan ba sake zuwa gidan ba sai yau da yazo ya tunkare shi akan magana na. Ya dan dago ya gyara zaman shi dakyau baiyi magana ba saida ya dan furzo da iska daga bakin shi ya numfasa yace. Kana da labarin Safiya bata da lafiya har ciwon yai tsanani sai da naje na kaita asibiti, yace dashi ban sani ba, banda labarin ta tun tafiyan ta inbada ta haihu kazo kafada muna ba, sai yace dashi Ahmed ka cuci Safiya ka illanta rayuwan karaman yarinya a banza saboda son kai irin nata ka zuba mata kanjamau tana ta wahala a rayuwan ta. Ahmed din yai mai wani kallo na tambaya sai yace dashi na illanta ta kamar yaya ? Yace kasan Safiya tana dauke da HIV kuma kaika saka mata shi don dai kai kafi kowa sanin kamilar yarinya ce ita. Ahmed din yace tasan dai inda ta samo abinta don dai ni banda komai normal nake kowa ya sani. Saadu yai saurin cewa normal kake kamar yaya aiko makaho ya lalaba yasan may kake ciki. Sai yace dashi sheri zakai min ko may ? Babu sheri anan . Don mummy da mahaifin safiya sunyi kuskuren aure maka kamilar yarinya kamar safiya don sun san halinka na boye suka aure maka ita hakana. In ma shi mahaifin nata bai sani ba ita mummy mu ta sani saidai ta boye masu ne. Ahmed ba yadda ban yi da kai ba ns baka shawara ka gyara rayuwan ka ka nisan ta kanka da fasikanci. Ba abinda ya zama ma dan adam dole may kake nema gun mace kai da Allah ya hore ma mace yarinya karama a gida. Sai da na fada ma wanan matar da ka aje a gida ba alheri bace gare ka amma kaki ji yanzu gata ta sa ka cuci yar mutane. Ya dafe kai gami da lumshe idanu yana tunane a ran shi yana hango irin wahalan da nake yi da ciwon a ranshi. Ya hango surana da muryana da irin karfin halin da nake dashi wurin turzawa sai kuma muryana idan ina son abu da tsabta na. A take ya ji jikin shi ya mace wani na dama da tsoro ya shige shi amma sai ya dake yace wa kanin nashi. Wai may ya damay ka da nine rayuwan ka ko nawa kuje can kai da ita ku nemi inda ta kwaso cutan ta. Please ka rabu dani don Allah da zancen wata safiya can kwakwalwata yana son hutu dan Allah kazo min da wani zancen ka na bazanza. Yace okay haka kace ya mike ya fita zuciyar shi kamar wuta yake jin shi ba abinda yake tunawa sai halin da ya barni ciki. Gidan su ya koma inda ya samu mahaifiyarsu da zancen, tun shigowan shi ta sha jinin jikin ta don tasan da abinda ke damun shi. Sai daya zauna take cewa dashi ina kafito ne aikai ma abin kari baka nan ka fita. Ya nisa yace da ita daga wurin Ahmed nake mummy kin san Ahmed ya cuci yarinyar nan safiya a rayuwan ta . Tace may ya faru kuma da Safiya din zancen wai har yanzu bai kare ba a gare ka kana bin dan uwanka da maganan ta rayukan ku na baci ga banza kasan fa yace bai mai da ita. Mummy yazu wake batun komawan ta bayan ya illanta ma yarinyar mutane rayuwa har abada. Wani kallo taimai nason jin ba a sin maganan shi yace Safiya fa HIV ne gare ta kuma ba kowa ya samata ba shine. Innallilahi ta furta da karfi tace H may yanzu kana nufin har shi Ahmed din yana dashi komay ? Yace ai yasan yana dashi mugu shiyasa ya sake masu ya don kar asirin shi ya tonu. Hannu ta fara tafawa tana salalami tana cewa wai ta shiga uku ta lalace Ahmed na da kanjamau ko may ? Yace mummy Ahmed kawai kike ji mawa ita diyan mutane da kuka cuta fa ita ba abin tausayawa bane ? Sai ta kama inda inda tana cewa ai dukkan su abin tausayawa ne itama ai dole a tausaya mata. Yace mummy dake da mahaifin yarinyar nan kuna da kamisho cikin ciwon yarinyar nan. Amma shi mahaifin da yasan kun cuce ta ai kuka yake kuma yana nadaman abinda kuka kulla sai dai ko kadan bai kufulece kiba. Amma ke gaki yanzu dan ki kawai kika sani kika damu da damuwar shi ita ko ko oho ? Idan zaki kirashi ki masa magana yaje ya duba diyar mutane tun wuri ki masa. Ahmed din bai shigo ba saida yamma ya shigo rai a bace shi aladole an bata mashi rai. Nan ya zauna da uwar ta dauko mai zancen da cewa abinda naji da gaske ne ko karya ne yazo ya fada min. Nan ya shiga fada wai Saadu na binshi da mugun nufi har yana lakaka mashi mugun ciwo. Tai ajiya zuciya tace yanzu naji magana amma yazo ya tayar min da hankali ga banza ya hanani sukuni a rayuwana duk yinin yau ko ruwa ban sha ba. Mummy kazafi yake min ta san ida ta dauko cutan ta can ni bani da masaniya akan haka. Uwar ta hau ta yarda da maganan shi nan ta shika fadin mugun zance akaina da mahaifana yana tayata fadi. Sun yanke yiwa yaya Saadu kaca kaca kan maganan da yake so ya dora wa dan uwan nashi wai yana son ya bata mashi suna ga banza. Ya shigo sunyi kaca kaca dashi a gaban mahaifiyar tasu tana tayashi zagin shi yace dasu OK haka kukace . Time will soon come da gaskiya zata bayyana kan ta indai ana boyon komai ba a boyon ciwo ai muje zuwa ni daku. Macucin banza da wofi kawai kawai ka cuci yar mutane kazo kana wani kamay kamay azzalumi banza da wofi sai Allah ya tona maka asiri ai. Yace dai naji kuje can ku nemi wanda yasa mata cuta idan ma kaine ka fito fili kafadi yafi don naga zakewan ka yayi yawa akan ta dama. Wani irin shock ya kama shi ta juyo yana duban dan uwan da mamaki sai kuma yai murmushi yace ni ba dan akuya bane irin ka. Ina dai kokarin sauke hakkin da kai ka kasa saukewa ne akan ta amma baku ganewa sai lokacin ku gane gaskiya inyayi. Ya fice ya basu wuri bai kara shigowa gidan ba har ya tafi bai koma wurin aikin shi ba sai da yaje gidan maman biyu ya sanar da ita halin da nake ciki. Da taji hankalin ta ya tashi sosai ya kwantar mata da hankali da cewa ya kaini asibiti yanzu ina samun sauki an daiyi arziki cutan baiyi nisa sosai ba aka tare shi. Ranan haka ta wuni a cikin bacin rai tana ta tsine ma Ahmed din da uwar shi ta ma kasa kirana don in ta kirani ma may zata fada min banda karin tashin hankali. Sai dai ta kasa daurewa bayan kwana biyu ina zaune daki da ummi wayana yai kara na dauka na ga itace take kirana. Na dauka tare da fadin Anty kwana biyu kina a raina ban samu kiran ki ba banda lafiya ne. Asanyaye tace safiya naji komai yayan ki yazo nan ya fada min halin da kike ciki Allah ubangiji ya isar maki. Sai na kama kuka tace bari kuka haka Allah ya kaddara da rayuwanki Allah ya nufe ki da rayuwan BAHAGGON AURE. Komai da bawa ya gani yana cikin littafin sa rubuttace ne ga ubangiji dama sai dai muyi fatan Allah ya baki lafiya. Nace amin anty tace ki kwantar da hankalin ki ki sha magani kada kiyi wasa da sha magani sosai don kada cutar yayi galaba a kanki. Nan nake jin yadda yaya Saadu suka kwashe da yaya Ahmed din da uwar su tace min barsu ai Allah ba azalumin kowa bane. Da sannu gaskiya zatai halinta in sun ce su mahainta ne ciwo ai ba a boyon sa shi zai baiyana kasa agani watarana. Ta dade tana lalashina ina kuka tace ina ummi nace gata a kusa dani tace inba ummi waya su gaisa. Nabata wayan suka gaisa tai mata jajen akan abinda ke faruwa tare da kwantar mata da hankalin ta takumace duk lokacin da muke da damuwa mu tutube ta zata taimaka muna. Nai sallama da ita har take tambaya na sana, a ta nace yana nan ina yi tace to karki daina shine zai tallafa maki kina samun dan kudin sayen abinda zai gina maki jiki kiji ko nace na gode kuka ne yaci karfina na kasa magana na kashe wayan ina tunane a raina. Bayan mun gama wayan na dade ina kuka ina tunane a raina karshe na hakkura na kyale na barwa Allah komai shi zai mun mafita da yardan ubangiji. ZAINAB IDRIS MAKAWA SEENABU 8/14/20, 7:11 PM - Ummi Tandama: BAHAGGON , , , , , , , , , , 🧕🏿2️⃣9️⃣🧕🏿 YAR UWA NOVEL DIN NAN NA KUDINE IDAN BAKI BIYA BA KADA KI KARANTA HAKKIN WASU PLEASE, , , , , Wurin motar muka nufa gaba dayan mu saadatu na kwace a ciki sheme kamar bata numfashi kuka muka saka a lokaci daya. Dayan dan sanda ke fadi ba kuka zakuyi ba ayi niya akaita asibiti tun lokaci bai kure ba a take baba da yaya sani suka fada motar da inna. Suka nufi asibiti da ita har lokacin mu ba mu san may ya samay taba asuban fari baba ya dawo gida rai a bace. Da mukaji shigowan shi lokacin mun tashi muka firfito waje mama ne ke cewa malam lafiya may ya faru da Saaden ne ? Cikin takaici yake fadin fyade akai mata wai kuma bata san ko su waye ba tadai ce sunkan zo cin kasuwa su sai sana ar ta. Kowa ya dafe kirji da firgici a cikin mu ta sake tambayan shi da ta farfado dai ko yace a takaice da ta falka yanzu sai dai bata san inda take ba. Nan ya shige ya barmu a cikin tashin hankali ba kwanta ba da mukai sallah cikin kayan abinci na na diba na hada masu abin karyawa. Na gama da wuri muka isa asibitin tana kwance sharkaf kamar bata da rai Inna na zaune a gefen ta cikin tashin hankali. Munyi mata sannu da yaya mai jikin tace da sauki na bata abinda nazo dashi nace su mama suna nan tafe. Maganin da likita ya rubuta ake neman kudin saye baba yace baida shi inna kuma tace dama dan abinda ke gare ta ne nan ta juya dashi sukai sana a. Na bude post dina na kirga kudin na bayar sai lokacin aka sawo magani da ruwan da za a karamata. Anyi mata allurai da sauran abinda ya dace a taimaka mata dashi bayan kamar awa daya ta farfado da kuwan wayyo inna zasu kashe ni. Tana fisge fisge nan dai muka taru muka taushe ta nurse tazo ta kara ba ta allura sai aka samu tayi barci. Ranan dai asibiti muka wuni ba dadi kafin wani lokaci labari yabi gari mutane sai shigowa suke yi dubata. Suna asbitin kafin a sallamota sai ga yan gidan mijin da zata aura wai a basu kayan su yace ya fasa dama itace ta biyu zata shiga. Wani sabon tashin hankali kuma nan suka shiga hayaniya da su mama tace aiko baku da imani kwa tsaya har a sallameta dai ko koma may ye sai ayi shi hankali kwance. Nan dai aka samu suka tafi suna bakaken magana wai dama ai shi yaji yagani a kanta ina ba haka ba me zaiyi da ita ma. Andai samu an lalaba su suka tafi baba ya shigo gidan ake mayar mashi ranshi ya baci yace ai sai su bari inda ta dawo ita data karbi kayan su sai ta mayar masu da abinsu. Inna na can labari ya samay ta nan ta sa hannu akai tana kuka wai so suke su tozarta ta in bashi ba ai wanan abindaya faru da yar ta kaddara ne kwai. Ji fa inna na kalleta a raina nace ashe tasan akwai kaddara shine ni taki yarda da nawa kaddaran da yazo min. Na yar tane abin yarda ke nan mu dai hakkuri muka bata kawai muka bar dakin muka koma waje muka zauna. Washe gari aka sallamo su suka dawo gida an basu wata uku su koma ai mata awon ciki dana HIV nan hankalin inna ya sake tashi sosai tana kuka tana fasin Alah ya tsine ma wa yanda sukaiwa yarta fyade. Da yamma bayan sun dawo gida tana cikin jimamay maganan likita sai ga ya gidan mijin na saade sun dawo wai sun samu labarin an sallamata ta dawo gida shine suka zo karban kayan su. Nan suka hau da inna tace baza ta bayar ba aiba ita tace ta fasa ba don haka bata yarda shi mijin yace bai yi ba sai dai in sherin yan uwan shine. Suka tafi basu gane komai ba nan suka barta ta na halakatai a tsakar gida wai basu da imani yarinya na fama da abinda ya samay ta zasu zo masu da wani fitina kuma. Mu dai muna daki muna sauraren ta sai baba ne ya shigo yace da ita don may bazata basu kayan su ba tun da sunce sun fasa. Nan ta shiga kamay kamay Ummi tace dani wasu kaya kayan da ta sayar wasu kuma yarinya ta sa ajikin ta. Nace ashe akwai cakwakiya don naga mutanen basu da alaman mutunci tare dasu. Ummi tace na dai kallo kawai ai mun yi imani da mukai mata jajen abinda ya faru in wasu ne aiko kallo bata ushesu ba. Da itace ba abin da zai sa ta kalle mu dama haka Allah yake ai yanzu in tana da imani tayi ai ta daina aibanta kin da takeyi a gidan. Murmushin takaici nayi nace badai inna ba ai laifi tudu ne katake naka ka hango na wani watarama kiji tayi min fade in halin ta ya tashi. Ummi tace dako tajini don yanzu nima Allah ya bani abin fada mata ai kowa ya ji da nasa abin fade. Kwana biyu Saade bata ko iya fito tsakar gida koda yaushe tana daki ranan mukaji Inna na mata fada wai ta fito ta kunkumay acikin daki. Mai ciwo ma ta fito tana walawa sai ita zata tsiri zaman daki muna jin ta ummi tace anzo wurin . Sai ko ummi tai wuf tafita waje tace may zaki fada min bayan Allah ya nuna maki bakin halin ki tun a nan duniya. Ai ni gara tawa ansan gidan miji ta kwaso shi ke ko fa daba a ko san suwaye sukai mata kaca kaca ba a gari. Baba yana jin sun fara ya fito tare da daka masu tsawa yace ke Rakiya yaushe ne zaki hankali yanzu duk wanan isharan da Allah ya gwada maki bai isheki ba sai kin tsaya jan magana. Sai cewa Inna tayi Allah ne ya nufe ta da ganin haka a rayuwan ta kuma ba zai zama abin fade ba ai. Yace ita ko itace ta saya da kudin ta ko ke in kina da kunya har zaki kawo irin wanan magana haka wanan abin bai isheki ba. Ko tafiya nake na koma ana gwada ni a gari banda sukuni a cikin mutane gida kuma babu dadi. Wanan karon bazan lamunce ki ba duk kika haddasa min fitina a gida zan dauki mata mumuna akan ki ne. Jin abin daya ambata yasa tai sanyi don ta zaburo wa ummina sosai kamar zata cinye ta danya ya kara da fadin . Ke wata irin mace ce wata ukun da aka bamu mu koma baiti ba har kin shiga goranta ma wata halin da take ciki ki bari a san makomar yar taki tukun san nan ki samu abin fadi. Dama Inna bata son zancen komawa asibitin nan don ko yaushe tsinewa likitan takeyi akan yace su koma a sake auna ta. Nan ta shiga cewa insha Allahu babu abinda zai faru da ita sai alheri na gane kaima so kake wani sheri ya faru da ita a gidan nan su zama daya da yar ka. Tai ta sababi ba wanda ya sake kulata har tayi ta gaji ta koma dakin ta tana mai zuba mugun addua ga masu fyaden da masu zagin yar ta. ********* ********** ********* Ranan ina waki tufafin mu da rana naji anyi sallama muryan dai ta wace na sani ne amma kuma may zai kawo ta nan. Naji tana tambayan ina nan da sauri na dauraye hannuwa na fito daga inda nake wanki mama biyu ne tare da yan tagwayen ta. Sun girma sun kara wanj irin kyau dasu da uwar su baki daya ban san lokacin da nai cikin suba da murna na sai fadi take alhamdullah. Naji dasin yadda na samay ki alamu ya nuna min kina ahan maganin ki ke nan mun shiga dakin mu na rasa ina zan sakata. Na fara gabatar ma mutanen gidan mu da ita suka shiga gaisawa da ita suna tambayaan ta yara da maigida nan na fito na aika a sayo masu fanta kwalba da ruwa mai sanyi. Tace no ki barshi ashe garin naku yana da nisa haka ne yanzu zamu wuce dama nayi alkwarin zanzo na duba ki ne tunda ke kin yada mu. A kunyace nace ban yada kuba anty yanayi dai ne yazo da hakan mun dan taba hira tamike tace zasu wuce don dare yayi yau zasu koma dama buki tazo yi arewa shine tace bari tazo ta gane ni. Ina ta rawan jiki na rasa may zan basu tace huta abinki bashi ya kawo ni ba tunda nagan ki alhamdullahi. Ta kawo kudi tace in bawa ummi na ga tsaraba mai yawa da ta kawo muna a cikin buhu ta fito tsakar gida taba su inna dubu ashirin su raba. Takawo wani tace aba baba in ya dawo nafita na rakata bakin motar ta anan take cewa dani idan na samu lokaci indan leko wuein su ina kuka ta rungumay ni tana share min hawaye. Nan dai suka tafi suka barni cike da kewar au gani nike abun kamar a mafalki wai anty ce a garin mu yau. Mun koma naji inna na fadin tunda nike ban taba rike ko dubu biyar ba na kaina a rayuwana yau ga bakuwar arziki ta zo mun dashi. Ban tsaya ba na shiga dakin mu na bude tsaraban da ta kawo min turmin zani guda uku da sauran tarkace ne a ciki nai murna sosai tare da yin hamdala. Mun dade muna hiran ta ina fadawa ummi irin taimakon da tai tayi min acan lokacin da nake cikin bukatan aimin din. Ummi tace Allah ya saka mata da alheri daga waje naji mama na fadin mukan ai Safiya kin jawo muna arziki har gida wannan abin arzikin da may yai kama. Baba ya dawo gida ummi ta bashi kudi da akace a bashi din ya shiga murna da saka mata albarka. Yana ta godiya yace haka Allah ke ikon sa yau na tashi tun shekaran jiya banda ko kobo a aljihun nan yazu ga kyauta na samu daga sama. Kwana biyu ana facali a gidan mu kafin su kare nidai ina kallon su kawai ba kunya ba tsoron Allah a tare dasu. Haka rayuwan yake gudana dan dama yanzu bakin Inna ya mutu ko tayi ma sai a bayan mu don da ta fadi ummi take mayar mata. Sai dai indan wani abin can na kishi ya hadasu daban amma dai ba gori ba don yar ta na gida kamar mujiya da ta fita sai a kama nuna ta. Wasu ma harda kari wurin bada labari zancen nata suke karawa don maganan yai dadin fada shiyasa Saaden bata son fita ko ina koda yaushe tana gida zaune. Yaya Saadu yazo diba mu bayan kamar wata shida da tafiyan maman biyu shima yazo muna da abin arziki kamar yadda ya saba kawo muna idan zai zo. Sai dai wanan karon da wata yazo yarece dai amma yace matar sa ce da ya aura ya kawo muna ita taga gida. Baba yace ikon Allah kayi aure bamu sani ba a gurina matar tashi ta sauka don bata jin hausa munyi dan hira da ita kwanan su biyu damu sukai muna sallama suka koma. Kafin ya tafi yake min maganan aure wani iri naji don bayi zaton zai min wanan maganan ba ya kula da kaduwan da nayi sai yace. Safiya ki daure ki samu wani mai irin matsalar ki ki aura hakkuri zaki yi bawai don kina so ba sai dai don kare mutuncin ki. Nai shiru na dago kaina idona na zubar da hawaye nace ni yanzu yaya ina zan samu miji a haka yadda nake kowa fa garin nan ya san zance na ba inda inna bata kaini ba . Yace ai kinji abinda na fada mai irin matsalar ki zaki aura acan gurin ansan maganin zasu iya hada ki da wani mai wanan lalurar idan hakakin ki ya kwanta sai ki daure ki aure shi. Hakkuri zaki yi da almarin kaddarane kuma yadda kikai tawakkali yana dakyau sosai haka ake son musulumi dayi. Shima Ahmed yana can ciwon yakai shi kwance sosai sai da nazo ne na kaishi asibiti da yana gida kwance yana karyan wai sammu ne. Nai dariya nace shida yace baida shi yaya akayi haka kuma yace kyale su don Allah wai saida muka je asibiti ya baiyana yanzu ne mummy ke fadin an cuce ki. Da wani ido zata kalli baba dashi bayan duk wahalan da kika yi bata zo ta dubaki ba har yau yanzu dai suna can na barta dashi ban san yadda zasu karata ba nidai na kaishi asibiti yadan samu sauki yanzu yana nan gida. Allah ya sauwa ka nace yace ko zaki hakkura ki koma mai kiyi hakkuri ku zauna hakana. Nai saurin cewa Allah ya sauwa ka yaya ida bakai ka fada min haka ba yau da sai an raba mu amma kaine ban cewa komai. Yai dariya yace Allah da zaki hakkura ki koma yanzu ai yayi nadaman abinda yai maki ya koma yana daya sani ita ma Lilliya naji ance an kwashe ta zuwa garin su okene. Nace yaya don Allah mu bar hiran su kazo zamu rabu da dadin rai kuma kana son ka bata tsarin nace ai zan shigo lagos indan anyi daidai kana nan sai na karasa wurin ku naga mazaunin ku. Yace yaushe kenan nace idan baba ya barni sabin wata nake son zuwa nake fada mai zuwan maman biyu da tace in dai je in mata kwana biyu yace idan zaki zo sai ki sanar dani tunda ga waya. Nan suka kama hanya suka tafi ya barmu cike da kewar shi yaya Saadu mutum ne wanda yasan kan sa yasan hakkin zumunci. Yanzu fa zuwa yayi ya kawo muna matar da ya aura wai taga garin su da yan uwan shi don tasan yana da asali. Rayuwa yaci gaba muna a gidan dadi ba dadi haka muke hakkuri mu zauna a cikin sa anyi bukin yar wurin mama salin alin mun sha buki inna na kallo ita da tasha alwashin yar ta zatayi aure. Sai gashi Allah yai nashi ikon a kan ta ba maganan aure gare ta sai in Allah ya kawo mijin nasan dai ba a karkaran mu ba kan don ba inda zancen ta bai kaiba har da makwabtan garin mu. Dole muka koma fita tare da ita tun uwar na fada har ta gaji ta saka muna ido don yanzu haka muka koma kamar aminai da ita. Sai dai ban yarda tasan sirina don su ba abin yarda bane ga mutane sherin su yawa gareshi don ta gado uwar ta da hassada sosai. Idan wata ya zagayo sai in tafi amsan magani acan wani ya leke min wai shi sona yake yi har da zuwa gidan mu. Ranan da ya fara zuwa kin fita nayi sai da yaya sani ya shigo na fita bayan wuce wanshi nace da yaya sani ni ban yarda da shi bane. Don da ganin shi manemin mata ne sosai don tsarin shi ya tabbatar da hakan yana magana yana wani iri. Niko yanzu ba zan yarda na koma wa wala ba bayan na fito gare shi yace ki dai kwantar da hankalin ki ki bishi sannu mu gani. Ni dai a raina nasan abinda na yanke shawara a kai so nake baba ya yarde min in tafi wurin maman biyu sai ranan da suka gane ni. Amma ban fadawa ko ummi na ba na bar zancen a raina don naga ko ita tayi aman na da zuwan mutumin wuri na su ala dole na samu mai sona da halin da nake ciki in dai yi aure ko yaya ne su nasu kawai kenan garesu. Basu tunanen hali na gari ko wani irin rayuwa zan je kuma na tarar ga ciwo ga taulalin miji a kaina. Shi yasa na yanke wa kaina shawaran barin gari salin alin batare da kowa yasan manufana ba a gidan. Don in sun sani ba zasu yarda in yi nesa da suba ko kadan shiyasa na bar abin a raina ni kadai. Sai in lokaci yayi su san manufana idan kuma basu gane ba a tafi a hakana duk inda nake sarin kaya a birni tare da kanina nake zuwa don ya iya ya saba dasu don ko na tafi bazai sha wani wahala ba ya iya. Harkan kasuwan ci na tare dashi muke yi yasan kan komai da yadda muke aje uwar kudi mu fidda riba daban duk ya iya. ZAINAB IDRIS MAKAWA SEENABU 8/14/20, 7:11 PM - Ummi Tandama: BAHAGGON, , , , , , , , 🧕🏿2️⃣8️⃣🧕🏿 YAR UWA NOVEL DIN NAN NA KUDI NE IDAN BAKI BIYA BA KADA KI KARANTA HAKKIN WASU PLEASE.......... Matsala na yanzu Inna ce tabi gari tana bada labari a kaina wasu har zuwa suke yi ganina a gidan mu. A cikin gida kuma ita da yaran ta ne suka tsan gwamay ni a gidan ko zama nayi a wurin sai sun share ko su goge zasu zauna. Idan na taba ubu bazasu taba ba koda sunyi niyar taba abin sai su fasa. Ga sake habaici a tsakar gida wai an kwaso cuta an zo za a lakaka masu sudai an cuci rayuwan su wallahi. In naji su na kan yi murmushi kai a fili amma cikin raina nakan ji zafi da dacin zuciya ya kama ni. Wani lokaci kuma idan sunyi man nakan shige daki inyi ta kuka sai ummi na tai min nasiha nakan yin shiru ko inji dan dama da sanyi. Har aikin da kan taya ummi sai suka tsani cin abinta idan na dan taba wani abu daga ciki ko ta gama ta basu sai kaji ana kiran almajiri a juye mashi. Da na gane hakan sai inyi zamana kawai a daki bana fitowa taya ta aikin ita ummi ta fahinci manufa na sai tace min ki zaman ki a daki yafi maki har kiji sauki. Ranan ina daki kwance ina karatu akai sallama ina jin bakuwar suna gaisawa da mutanen gidan mu. Sai take tambayan Safiya tana nan kuwa aka nuna mata dakin mu ta nufi can suka bita da kallon mamaki yar gayu da ita zata zo wuri. Jin ta ambaci suna na yasa ni saurin tashi ina da sauri ina daga labulen dakin mu don in ga ko wacece take nema na din . Bakowa bace sai Amina kawa na da mukayi karatu tare da sauri na sake labule na nufo ta muka rungumay nuna da ita sai yan gidan mu sukai tsaye cirko cirko suna kallon mu. Na san ba komai bane suke ma mamaki sai yadda ta rugumay ni ne su gashi suna gudu na agidan suna gwada min kyama a fili. Muka shiga dakin mu nan na aika ka sayo mata pure wata mai sanyi tana cewa a a nace ta dai bari a sayo mata bayan yaron ya fice sayen ruwan ne. Tace dani ashe kuma haka abin ya kasan ce dake alamarin yazo da matsala haka Allah ya nufa Safiya kiyi hakkuri nima da na shigo jiya mama na ke fadamin abindake faruwa. Safiya jiya da naji maganan nan ban iya barci ba amma kuma danaga masu shi yanzu ba a gane su a fuska sai na barwa Allah alamari . Gaskiya naji dadi yadda nazo na samay ki baki gala baita ba gaki har jikin ki na dawo naji dadin haka kwarai da gaske. Nan na fara bata labarin abinda ya faru tun farko sai cewa take subbahanallahi amma wanan mutum baida tausayi baida imani ko kadan. Tana share hawaye tana fadin Safiya Allah ya duba maki alamarin ki ya tausaya maki wanan BAHAGGON rayuwan da kika taso a cikin shi. Nace da ita amin don yanzu idona ya kyan kyashe da kukan nayi nayi nagaji sai dai na kasa daurewa ganin tana kukan nima kukan nake yi. Sai ummi ne take bamu hakkuri tana cewa haka Allah ya nufa ba yadda banki auren nan ba amma mahaifinta da matan shi suka nace da sai tayi. Yanzu da wahala ya cika da ita duk sun watse din sa muna ido da ni da ita a daki sun koma suna kyamatar ta a gidan. Safiya tace ai wanan jahilci ne ba a gudun mutum sai dai ayi taka tsantsan wurin yana yin zaman takewa. Amma in ana gudun mutum tunane sai ya shiga maishi sai ciwon ya samu galaban samun wurin yin barna da kyau. Mun dade da ita a gidan nan ta wuni wurina nai mata dahuwa taci zata tafi na rakata bakin kofan gidan mu. Zan shigo gida na hadu da Inna ta yafa zata fita ta wuce na shiga gida ashe tabi bayan Aminan ne ta tsaida ita. Tace keko yar nan baki san may ke faruwa da Safiya bane nagan ki wurin ta har da cin girkin da tai maki. Amina tai murmushi tace kwarai kuwa na sani shine ma ya kawo ni wurin ta ai don in mata jajen abinda ya faru da ita. Inna tace baki gudun ki dauki wanan cutar kema a wurin ta don ance saurin yadduwa ne dashi. Amina ta girgiza kai tace ba haka bane gaskiya a samun sa ta hanyar saduwa kamar yadda ita Safiya ta samu daga mijinta. Sai kuma ta wurin amfani da zera ko masilar kitso ko allura idan jinin maishi ya shiga jikin ka to kaima kana iya samun wanan cutar bayan haka zaku iya hurda ko wani iri da mai wanan cutar kamar kowa. Inna tai mata wani irin kallon rashin gamsuwa da maganan ta tace ni dai na fada maki gaskiya don naga kamar baki sani bane. Ashe kin san komai idan iye iyen ki ya kai ki kika dauko ma kanki cuta ke kika sani ninayi nan. Amina tace da ita dakata inna sai ta juyo ta tsaya tace da ita wanan abinda kuke yi ya kamata ku dai na wanan halin da kuke nunawa safiya. Inna ki sani idan yarki ce ta shiga irin wanan halin yaya zakiyi sai ta tofar da miyau tace bakin ki ya sari dutse Allah yai ma diyana tsari. Tace kin gani itama fa ba da son ranta ta samay shi ba kin sani ya kamata ku jawo ta a jiki kuna kwantar mata da hankali ba ku dinga aibanta ta kuna hattaran ta ba haka. Don Allah Inna ku daina wanan abin da keyi sai ta tare ta dacewa mugun halin uwarta ce ya bisu ai kadan ma suka gani ai. Allah ya kyauta Amina tace da ita ta wuce tana bakaken magana Amina dai tabita da kallo tare da girgiza kanta kawai ta wuce. Inna ta dawo ido mirsisi tana zage zage a fakaice sai kuma ta shige daki suna magana da diyan ta kus kus kus. ********* ********* ********* Ina zaune a dakin ummi tun safe da na fito van sake leko waje ba ina dai jin hayaniyar mutanen gidan mu daga waje suna harkokin su na yau da kullum. Ba abinda nakeyi sai tunane abu biyu ne ya tsaya min a raina na farko in na tuna muamula na da mutane yadda ya ja baya yanzu. Sai na biyu yaya rayuwa ta zata kasance a haka zan zauna dakin uwa ta in kare rayuwa na ba wani abin ci gaba da zanyi wa rayuwana. Na lumshe idanuwa na cike da takaici take naji hawaye na zubo min ashe ummi ta shigo dakin ban sani ba tana tsaye a kaina nadan wani lokaci. Muryan tane yasani bude idanuwa tana tsaye a kaina tana kallo na cikin bacin rai da ya baiyyana a fuskan ta. Ta lumshe idanuwan ta cikin takaici ta juya tana neman abinda tazo dauka a dakin lokacin muryan ta yayi rauni ta fara magana ba tare da ta dubeni ba. Watau so kike kuma ki jawa kanki sabon matsala a rayuwa baki san ciwon kan ki ba ana fada maki ko yaushe kiyi hakkuri kibar wa Allah almarin ki. Amma sai ki zauna a daki ki ta kuka kina tunane ke kadai ana fada maki gaskiya baki dauka to maye amfanin zama na a gidan kina kara min bakin ciki ? Ki rungumi kaddaran da ubangiji ya jarabe mu dashi sai Allah ya tausaya maki yai maki mafita ta inda baki zata ba. Kuka nake yi sosai nace ummi ba hakana bane in na tuna da irin zaluncin da sukai min ne sai na kasa hakkuri a raina. Tace sai kin fitar dasu a ranki ki rungumi kaddara ki mai da alamarin ki ga ubangiji kamar yadda kowa ke fada maki a kullun duk masoyin ki abinda kawai zai fada maki kenan a yanzu. Don kaddara ya riga fata gare ki ki dinga fita kina mu amula yadda kowa keyi a gidan gida na ubanki ne babu mai koran ki cikin sa koshi bau isa ya kore ki ba tunda shi ya jefa ki a wanan halin. Da sannu zasu janye manufarsu a gare ki kowa a dawo daidai dama zaman gashi nan dai ne anayi har duniyan ma nawa take ga dan adam. Ba abin mamaki bane ki mara lafiya ki rayu mai lafiyan ya mace ga Allah duk wanan sau nawa yana faruwa ga dan adam. Don haka har kulun nake godewa Allah da ba wurin wani hanya mara kyau kika kwaso wanan cutan ba . Har kulun ina godewa Allah daya bani yayan da suke da hankali da hangen nesa Allah ya kara shirya min ku sak na amsa mata da Amin. Naji dadin wanan nasihan sosai na ummi kiran da a kai mata a waje ne yasata fita dakin lokacin na sauke ajiyan zuciya na mike tsaye. Washe gari tun da safe da nai sallah ban kwanta ba na fito na share tsakar gidan mu tas baba da ya dawo massalaci ya gani ina wanke wanke yake min sannu. Ya zuba min ido cike da tausayi ya wuce dakin shi yana tunanen a ran shi yana daya sani ya barni na auri zabi na gashi yanzu yaron ya zama wani abu a gari lokaci guda ya samu wurin aiki mai kyau yayi aure shi anan garin. Haka naci gaba da rayuwa zaune a gida in lokacin karban magani yayi in shiga mota in je in karbo idan zan dawo na dan riko ma yaran gidan mu tsaraba. Sai kaji suna cewa yaushe ne zan tafi birni in sayo masu abu kaza dana taba sayo masu acan. Yanzu hankalina ya kwanta ina samun walwala sannu a hankali har nakan fita zuwa gidan gwago da yan uwan mahaifiya ta da kawaye na don sun gaji sun daina gudana. Masu son kaya har gida sukan biyo ni don saya ko ba da sautu a sayo masu wani abin idan suna so. Haka sai mu a mula na ya dawo daidai da mu tane ina hurda da kowa babu tsangwama ko hattaran da suke min da farko. Na tayar da sana a ta zanga zanga dashi nake samun ina juya rayuwan mu harda na kanne a gidan don haka muka koma bamu da wata damuwa a tare damu. Sai dai har yanzu wanan muguwar akidar ta inna nan a ranta da wasu diyanta abin yana damu na sosai yadda suke nuna min tsana a hili tundai babban yar ta da ake shirin yiwa aure. Don da dan abu ya hada mu da ita yanzu zatai min gori da ciwon dake jiki na zata tsaya tai muna tas a tsakar gida babu kunya ko jin tausayi na ga halin da na tsinci kaina a ciki. Yau kasuwan garin mu yaran gidan mu masu sana a suna ta sha anin sana an su da zasu fita dashi cin kasuwan. Maganan yara ya taso sai rikici ya hada su da yaran dakin mu dana Inna da diyan dakin mu subbahanallahi ranan naji tonon asiri da ban taba ji ba a wurin inna kamar dai ta dade tana shirya muna ne. Abin da yafi kona min rai shine irin zagin da take min da cewa naje na debo cuta don mugunta ina son in yada ma gida kowa ya samu. Haihuwana ya zame masu bakar haihuwa a gidan da barnan suna ko fita sukayi sai ai ta nuna su basuci ba basu shaba Wai tun auro ummi gidan ya juye masu da tsiya basu kara gane gidan nasu ba. Tai ta fadan maganganun har tayi ta gaji karshe ta juya ga ummimu nan sukai tayi tace itama ai ba sayen shi tayi ba aure ne yaci ta . Inna tace oho dai da ana muna sallo wai itace mai karatun boko a gidan nan anyi aure a birni, to yanzu ina bokon yake ? Wai ina zaune a gida haka zan tabbata ina kallo yan uwanta na aure ni ko ba halin yin aure a rayuwan na. Ummi tace Allah ya fi mu sanin daidai don yana sane da komai da kowa a rayuwa sai da baba ya shigo gidan san nan suka daina. Watau a gaskiya tunda inna ke fada min bakar magana akan ciwon nan bai taba kona min rai irin na yau da tai min ba ni dai ina zaune ina kallon ta ina aiki na banko tanka mata ba har taci ta sude ita kadai. Sai dai ance ko shiru magana ne don haka shirun da nayi sai yaci mata rai kuma wai na mayar da ita mahaukaciyan tsakar gida don nasan abinda na jajibo gidan. Mama ne tai magana da cewa haba dai ya kamata ki tauayawa yarinyar nan kin dai yi fadan nan bata tankaki ba baki bari hakana. Ta koma kan mama kuma wai ai ta san mama bakin ciki take da mijin da yarta tasamu don yafi na yar ta shiyasa take kyashi yar nata. Mama tai dariya tace kuma dai an ba a san maci tuwo ba sai miya ya kare . Tace ai tun yanzu Allah ya baiyyana an sani in bashiba da ita ake zancen da zata saye ya zama nata nan dai baba ya kara shigowa ya raba su fadan. Yaran suka fita da sanaa su gidan ya koma shiru ina kwance a dakin ummi na sai ga kanina ya dawo daga kasuwa tare da sakon dana bashi ya sayo min idan zai dawo gida. Ina waje ina aikin miyan danyen kifi ne sai ganyen zogale na gyara ban hada ba yar wurin mama da ta dawo talla nace ta hada muna nabata kayan hadin ta gyara muna ta raba taba kowa nasa. Na gama na shiga daki na dibarwa kowa miyan na aika masu dashi sai Inna tace a dawo min dashi. Yaya Sani yana gida lokacin yace mata saboda may za a mayar mata ya ansa hannun yaron da na aika dashi yana ma uwar nasiha. Shiru shiru kowa ya dawo sai yar wurin ta babban da ake shirin yiwa aure ne bata shigo ba . Ina jin mama na tambayan ta har yanzu Saadatu bata shigo bane tace kila ta tsaya amsan kudin ta ne. Har magariba shiru bata dawo ba nan hankalin uwar ya tashi ta yafa ta fita bata gane ta ba. Can sai gata ta dawo tana fadin ban san ida yarinyar nan ta shiga ba na duba har layin da suke aje sana ar su ban ganta ba. Shiru shiru an baza yara ko ina ba a gane taba nace wa ummi na bari na fita in duba ko Allah zai sa a dace. Tace dani ki zamawa agun uwar su indai wanan matar ce barta inda kika ganta nace wa ummi aini ba don ta zani ba. Don yar uwata ne da baba don naga hankalin shi ya tashi sosai tace sai na dawo . Har goma da wani abu na dare muna yawon bidan ta babu labarin ta hankalin gidan mu duk ya tashi. Muna tsaye kofan gida cirko cirko da wasu yan uguwan mu cikin zulumin ina ta shiga baban mu hankalin shi duk ya tashi na bada shawaran aje gun yan sanda a sanar dasu. Baba da yaya sani suka nufi wurin yan sanda da daren nan suka sanar dasu abin da ake ciki har daya da wani abu na dare dole muka hakkura muka shiga gida hankali tashe. A cikin gidan ma ba kwantawa mukayi don babu mai hankalin kwanciya sai yara kanana kawai sukai barci. Dole baba ya hakkura suka shigo gida bayan duk an bincika gidan yan uwa da abokan arziki ba a samay ta nan ba. Wani irin ihu da kururuwa Inna tasa da daren nan tabamu tausayi muka koma bata hakkuri amma ina bata ko sauraren mu. Can wuraren biyu da rabi na dare mota ya tsaya kofan gidan mu da sauri baba ya bude dakin shi shi da su yaya sani suka fita don ganin ko nan ne motar ta tsaya. Kafin sukai ma har an fara dokan kofan gidan namu da sauri baba ya bude tare da tabayan ko waye ? Suka ce yan sandane ya bude kofan suka fice nan muka fara bude kofunan dakunan mu muna fitowa don jin may ke faruwa yan sanda gidan na mu da dare haka. Sun ja baba gefe suna mashi bayani muna tsaye cirko cirko cikin jimay abinda ke shirin faruwa Inna baba ya kira inda suka karasa bakin motan muna biye dasu a bayan su. Wani irin ihu Inna ta saka duk sai da muka firgice mun zaci ko gawan Saadatu inna tagani a motan. ZAINAB IDRIS MAKAWA SEENABU 8/14/20, 7:11 PM - Ummi Tandama: BAHAGGON, , , , , , , , , , , , , 🧕🏿3️⃣0️⃣🧕🏿 YAR UWA NOVEL DON NAN NA KUDI NE IDAN BAKI BIYA BA KADA KI KARANTA HAKKIN WASU PLEASE, , , , , Idan nace zaman danakeyi gidan mu akwai dadi nayi karya zama dai nake yi na wacce ta rasa gatan ta da madafa saidai dadin . Abin ban dogara da sai abin gida ba ina tsaye ina nemawa kaina mafita ga rayuwa shiya sa abin yazo min a cikin sauke, Don ban kallon abin wani sai ma su su kalla a wuri na a nema in bayar akuma yi min gori daga karshe. Gidan da sai an nema aci ai kin san gida ne na mawuyacin rayuwa ga bawa don ranan da bai suma ba kowa tashi fisshe shi da yaran ta. Duk da yake mahaifi mu mutum ne mai zafin nemawa kansa bai dogara ga sana a daya ba buga nan buga can yake yi har a samu ubangiji ya rufa asiri. Yau ma mun wayi gari baba ya wuni bai samu kudin da za ai muna girki ba har kwana biyu ga kuma Inna bakin halin nata ya motsa sosai. Don da yar ta ta fara a daki ta nemi kudin a gunta ta rasa dan sana, an mai da takeyi jarin yana kokarin karye mata sai inna tace ta basu su sayo abinci da zasu ci tace bata da kudi. Nan take ta fada tun tana yi a daki har ta fito waje da jidalin a bakin ta ganin ta shiga daki yasa na fito don dora muna girkin abinda zamuci a dakin mu. Ba wani abin tsone ido nayi ba dafaduka ne na taliyan da make sayar wa na dauki biyu in dafa muna adan kau da miyau sai da dare nake son in muna tiwon masara. Tunda ta kyala ido ta ganin a bakin murhu ta fara irin maganan ta da cewa gida ya koma muna wurin gwada tsara muda diya. Mun koma kamar kishiyoyi a gida da mu da ku ai gara ma ke Saadatu ba a debe tsamanin aure a gare ki ba do baki da cuta amma wata kan ai haka zamu zauna muna nuna hali da mu da ita. Tafito ba komai takeyi ba amma taje ta dawo a tsakar gida tana dauke dauke a tsakar gida kamar mai sabon hauka. Da ummi taji abin yayi yawa sai gata ta fito waje da sauri na dago don jin motsinta nace da ita don Allah ummi kada kice zaki tanka mata. Tai tsaye tai shiru sai taka koma daki ko ba a fada ba maganganun na Inna sun bata wa ummi rai sosai. Yar ta Saadatu ne tafito daga dakin su tace da ita wai ke inna akan naki taba kudin mutane ne kike wanan magana har kina hadawa da Safiya may tai maki yanzu ? Mafarin kija fitina ku kama fada da tononasiri da ummi a gidan nan ke baki taba fadan gaskiya sai ayita akare kece baki da gaskiya kulun. Nan kuma ta juya akan Saade din tunda bata samu wace zatayi da itaba tace ke gara can shanyayya kawai an hada dake an shanye keda dan uwanki. Nidai nagama aikina na shige dakin mu na raba na aikawa kowa gidan da nasa, muka zauna nida kanne mukaci namu. Bayan mun gama cine nace wa ummi da take zaune tayi shiru a dakin namu tana kallon mu. Ummi gaskiya barin gidan nan zanyi na dan kwana biyu, da sauri tace dani ina zaki tafi inda yafi maki nan din ? Nace ba wani wuri zan tafi ba gun maman biyu zani in dan kwana biyu a can kin gama zata tace ban yada ita ba ai. Tace dani kina ganin magafinki zai barki ki tafi kada ma ki soma wanan magana rayuka su zo su baci ga banza tsakanin mu da shi. Nace ummi don Allah kiyi hakkuri kibar ki barni in gwada sa ata na gani ko zai yarda in tafi wallahi idan ban gusa naba inna wuri ba wata raba ana abinda ba daidai ba a gidan nan. Ummi tace ai saidai kada akara amma kan Allah dai ya sauwaka kawai za a ce ma zancen nace amin. Ummi na dauka nabar zancen ne niko iya gaskiya na kenan na fada bayan kamar kwana biyu na samu baba a kofan shi zaune bayan ya gama cin abincin dare nake fada maishi kudirina nason yin tafiya zuwa wirin maman biyu. Sai da ya kurkure baki ya watar da ruwan da ya gunda a baki yace dani anyya Safiya ba zaki hakkuri ki zauna nan ba ki barwa Allah alamarin sa yafi. Gyara tsuguni nayi da kyau nace dashi baba ai ba zama zanje nayi ba zuwa zanyi na ganta kwana biyu sai na dawo gida. Yace safiya bawai naki tafiyan ki bane ai wanan matar tana da mutunci da zaa gunta amma kinsan halin da kike ciki yanzu Yan uwan ki ma da kuka fito ciki guda dasu suna nuna maki kyama balle wata can da girma da arziki ne ya hada ku kawai. Nace baba ba haka na bane ita ta bukaci da naje gun ta, na dan kwana biyu sai in dawo don kawai nai mata alkwari ne zan zo nake son zuwa ai. Yace Allah ya kaiki lafiya nace amin baba na gode baba yace ba koma har na mikr tsaye naji yace dake dawa zaku tafi sai na danyi shiru sai kuma nace ni kadai zan tafi baba. Yace tau Allah ya kyauta agaida su Inna na kofar ta bata san maganan may mukeyi da baba haka hankain ta yana gurin mu . No juya na nufi daki naji tana cewa a yanazu kuma mai cuta a jiki tafi ko wani da gidan nan samun ido , nidai wuce wa niyi ban kula taba sai magana take tana dariya. Tun ranan da mukai magana da baba na fara shirin tafiya zuwa lagos gun mama biyu sai da na shirya tsaba na fitar da zancen tafiyan gun mutanen gidan mu. Aiko a take inna ta kasa boye jan halinta tace zaki koma a dora daga inda aka tsaya ne na hadi wasu yawin bakin ciki nace niba wurin gwagona zan tafi ba. Naji tana son daukan zancen da zafi daga zan tafi lagos gobe mata take ta kasa boye min bakin cikin ta a fili ta nuna hassada akan tafiyan ban tsaya kula taba washe gari na dauki hayan zuwa garin lagos. ********* ********* ********* Ban isa ba sai dare sosai na iso garin lokacin ya fara yin shiru don haka ban sha wahalan zuwa unguwar su maman biyun ba da ba don dare ne abin hawa sun rage zirga zirga a hanya lokacin . Nazo na samu sun rufe gida sun kuma canza mai gadi kusan ma,aikatan gida duk an canza su an kawo wasu. Don haka basu gane ni ba araina nace kodai ba gidan bane nazo sai mai gadin ne ke tambayana wurin wa nazo nace dashi madam Hauwa sai naga ya juya zuwa ciki na dan lokaci ya dawo yana tanbayan daga ina nake na fada mai sai gasu tare sun fito da ita. Tana farin ciki da murnan gani na muka kwasa zuwa cikin gida tare farin ciki gani na duk ya cika mata zuciya. A raina nace ikon Allah gidan mu suna kyama na wasu kuma bare na farin ciki da zuwana cikin su haka duniya ta gada. Naga halarci agun mutanen gidan na samu kaunata tazo da kuma yar uwar mijin ta suna zaune da ita sai kuma gani na zo. Amma duk da haka basu nuna min rashin jin dadin zuwa na ba sai ma taro na arziki da na samu a guri su. An cika min gaba da abinci ban iya ci sosai ba don nisan tafiyan da na kwaso sai dai ina kallon abincin ina tuna su ummi da kanne na ko yanzu wani hali suke ciki oho ? Da zan bar gida na mikawa ummi na waya na kwashe nombobi na akan idan na zo ja samu yar karamar waya in saye don wanan ta ji jiki sosai. Ban dade zaune ba sai gata ta fito daga dakin ta dake sama take cewa dani Safiya taso akaiki dakin da zaki zauna don ki huta naga kin gaji da yawa. Na mike tare da daukan hand bag dina muka nufi dakin daki ne babba wanda ya kumshi gado da mirro da ban daki da tv da AC acikin sa. Bata dade ba tafita na sauke ajiyan zuciya tare da bin dakin da kallo ina mamaki ban bata lokaci ba na fada bandakin na watso ruwa tare da dauro alwala nafito na rama sallolin da ake bina . Daga nan na kwanta ban dade ba abu ga wanda ya gaji barci ya kwashe bani na falka sai da asuba don na saba tashi a wanan lokacin. Na shiga ban dakin na dauro alwala nafito nai sallah ban kwanta ba na dade zaune ina addua kamar yadda na saba yi duk safe sai da gari ya haska na fito daga dakin bayan na gyara na samu mai aiki tana ta gyaran wuri sai na so taya ta amma sai ta hana. Nan dai na taya ta aiki mikayi tare sai tabar min ta tafi hada abin karyawa muna gab da gama aikin anty tafito daga dakin ta tana cewa. Dama nayi tuna nen hakan dake Safiya may yasa ba zaki huta ki natsu ba sai ki fito ki kama aiki. Murmushi nayi nace da ita ai wanan duk ba aiki bane a gida duk nike wa ummina aikin da ya dace inyi na. Murmushi tayi tace yanzu dai ki dan huta tukun kafin na san abinyi a kan ki nafi son naga kin huta kin kwantar da hankali kafin mu san abinyi a kanki. Bayan mun yi wanka ne an fito karyawa take gabatar min da yar uwar mijin ta dake zama dasu sai kaunan ta da ke zaune dasu wai tana karatu naga tana min wani kallo na rainin wayo. Ni dai ban kulata ba muka ci abinci inda duk hiran da ni maman biyu keyin shi akan yanayin garin mu da ta gani ina bata labarin garin namu da abubuwan da muke shukawa a karlaran mu din. Mun gama na mike don kwashe kayan tace in barshi mai aiki ta kwashe nace haba anty kamar dai ba mata ba na kwashe naje na wanke ban dawo inda suke ba na shige don yin sallah walha. Dana gama na dan mike don har yanzu akwai gajiya tare dani sai barci ashe ta leko dakin ta samu ina barci a inda na idar da sallah na. Ta juya ta koma tare da jawo min kofan ban farka ba sai sha biyu da wani abu na gyara jikina na fito nan falo na same su da kauna tana mata fada ko da ban sani ba nasan a kaina don naji tana fadin. Na dai gaya maki karki yarda ki sawa yarinyar na ido a gidan nan don ba wurin ki tazo ba indan ma tayi wani abinda ba daidaiba just ki fada min. Don ban son abinda ya faru da dake da faiza ya kara faruwa akanta don duka daya na dauke ku don ko ita din ma ni na kawo ta nan din. A take sai naji kuka yazo min a hankali na juya zuwa dakina da na fito din ba zan iya rike kukan ba a lokaci kuma gashi ban son suji na ji maganan su. Sai dai a raina nasa duk yadda kaunan nata take zan iya hade bacin ran da zan gani a gurin ta don mu rabu lafiya ni da nazo cin arziki ina ni ina fada da masu gida. Ina daki dunkule ban fito ba suma basu nemay ni ba ashrle ta fita ne gida sai shidda na yamma ta dawo gidan nan ta zube a falo inda ta samay su suna kallo. Nan na fito cikin su tare da gaida su na samu wuri na zauna ta dago kai tana cewa Safiya kin tashi ai na leka ki har sau biyu na samu kina barci. Nace wallahi anty sai yanzu na fito nima ban san barci ya kwashe ni ba sai tace tare da nuna kaunan mijita dake zaune ban gabatar maki da wa yan nan ba bayan tafiyan ki ne suma suka zo anan suke zaune tare damu yanzu. Wanan ita ce faiza kaunar maigidan ne auren ta ya mutu ne tadawo nan da zama wirin mu. Sai wanan yar uwatace itace autar mu itama anan take zaune yanzu tare dani da fatan zaku zauna a cikin aminci har kowa ta samu miji tayi auren ta. Tace kuma wanan itace safiyan da kuke ji ina fadin zata iya zuwa ko wani lokaci yar uwata ce itama zata zauna damu anan na dan wani lokaci da fatan zaku rike juna da amana. Sai naga Fatin ta dago ta kalle ta don jin ta kirani da yar uwa nima ban san dalilin anty na fada masu haka ba. Faizan ne tai murmushi tace kai anty lallai kina ji da wanan safiyan ai kin fada muna zuwan ta tuntuni kuma insha Allahu zaki samay mu yadda kike so a cikin amana. Sai ta juyo gare ni tana cewa ki saki jikin ki kuma ki ja kowa ajiki saboda yanzu mun zama daya da junar mu ga gidan gidan Jamma a ne. Wa yanda ma bamu san inda suka fito ba suna zuwa suci arziki su tafi ni dai abu daya ne ko kadan bana kaunar rashin gaskiya duk abinda zamuyi mu yi shi a cikin gaskiya da amana. Murmushi maman biyu tayi tace indai Safiya ce to kar kiji komai a kanta, saboda komai daidai gwagwado Allah ya wadatar da ita da natsuwa da sanin ya kama ta daidai misali. Ta nisa tace tare da cewa ai shekenan Allah ya zaunar da mu lafiya da junan mu tace aini naji dadin zuwan ta kwara don in kun watse nakan ji gidan ya koma min shiru wallahi. Ita dai fatin tana ta charting din ta ba dago kai ta kalle mu ba balle tasan may muke fadi ma. Na ce a raina wanan da gani zamu kwasa da ita sai dai duk abinda zata zo min da shi zan yi kokarin kawar da kaina akanta. Muryan maman biyu ya katse min tunane na take tambaya na ko nayi waya da mutanen gida da nazo nace da ita banda waya a hannu na don wayan da zanzo na barwa su ummi shi acan don su samay ni. Tace a a ke ko ana haka ai ya kamata ki kirasu su san kin iso lafiya yafi ke fati je daki ki dauko min wanan wayan dake saman mirro na ki kawo. Kamar bataji yar nata ba sai da ta kara maimaita maganan nata ne ta mike zuwa dauko wayan a dakin ta. Ta bita da kallo tare da firgiza kan ta tace kai Faiza akwai matsala wallahi sai kun ta hakkuri da ita don Allah. Faiza tace aini yanzu nasan halin ta ba abinda zata yi ya dakay ni kuma sai dai ita Safiya da bata saba da halin ta ba. Ta kawo wayan tana mikawa yar nata ba tare da ta kalli kowa a wurin ba ta karba tana ce min ina sim din ki yake na tashi zuwa daukowa. Ashe bayan na tashi yar take mata fada sai tai hushi tabar falon gaba daya ta koma daki. Koda na fito ban gane ta ba na mika wa anty sim din na samu harta cire nata dake ciki tana cewa ki fara amfani da wanan har in sayo maki naki wayan . Ta saka min sim din tace karbi ki kirasu su san kin sauka lafiya ko hankalinsu ya kwanta idan sun jiki. Faiza tace lalai kan do irin haka hakali baya kwanci sai kaji mutum balle lagos garin ne mai tare da hatsari sosai. Na karba kira biyu sai kaunata dake bi mun ta dauki wayan nan dai muka gaisa nace tabawa ummi wayan muka gaisa na fada masu na iso lafiya nace ga anty. Ta karbi wayan sun gaisa sosai ummi tai mata godiya tare da cewa don Allah don ma aikin Allah ki rike min ita amana don gidan nan ba dadi shiya sa ta zabi zuwa wirin ki ta zauna. Tace ummi kada kiji komai zaman Safiya a guri na tankar a gida take daku saboda Allah kadai yasan abinda ke zuciya ta kuma shi ya san yadda nake jin Safiya a raina. Ummi tai mata godiya ta bani wayan ina tambayanta sauran mutanen gidan mu tace duk suna lafiya. Lokacin sallah da ya gabayo ne yasamu watsewa inda na kula da kowa dakin ta daban ashe a gidan sai dai duk kan mu ukun a kasa muke sai masu gidan ne ke sama da yaran su. Yanzu yar uwa kin kwamace in barki da Allah da kike fitar min da novel waje kiba rabawa group group ki tuna duniya ba matabbata bane. Akwai ranan hisabi tsakanin mu dake ban san kin shigo da fuska biyu bane amma idan baki iya rikon amana ki magana na baki kudin ki don bazan taba yafe kaki ba ko wace ce ke ubangiji yai gagawan isar min a gare ki idan kika kara fitar min da novel ga wanda bai biya ba. Allah yai min sakayya a gare ki ko wacece ke. ZAINAB IDRIS MAKAWA SEENABU 8/14/20, 7:11 PM - Ummi Tandama: BAHAGGON , , , , , , , 🧕🏿3️⃣1️⃣🧕🏿 YAR UWA NOVEL NAN NA KUDI NE IDAN BAKI BIYA BA KADA KI KARANTA HAKKIN WASU DON BA ZAN YAFE MAKI BA IDAN KUMA KIKA FITAR MIN DA NOVEL UBANGIJI YABI MIN HAKKINA A KAN KI, , , Washegari misalin karfe goma na safe ina zaune a daki sai ga dayan yan biyu ta ta shigo dakina tace dani mumm is calling you. Ban bata lokaci ba na mike nabi bayan ta zuwa amsa kiran sama naga ta nufa don haka nabi baya yarinyan nata can . Wanan ne karo na farko dana taba haurawa wa sama dakunan gidan koda muka hau sai naga saman ashe babba ne da dakunoni kamar kasan. Ina mamakin girman gidan yarinyar ta tura kofa ta shiga nima na mara mata baya tare da sallama na shiga. Na samu tana tsaye tana gyara rigar uniform din ta a jikin ta ta dauko abaya ta dagwara a sama fara gaida ita nayi nace anty ina kwana ta juyo tana fuskanta na fuskanta dauke da murmushi tace Safiya an tashi lafiya. Nace Alhamdullahi ta sake tambayana da kin ko yi break fast don yau banda time din fita ina shirin zuwa office ne. Nai murmushi nace yanzu zanyi anty tai saaurin ce aa kada kiyi wasa da karyawa keda kike shan magani zaki tsaya biye muna kada ki bari tara yayi baki karya ba a kullum. Kai na gyada mata kawai alaman to tace dama na ce akira min ke na kara fada maki don fita zanyi don Allah a kada kishiga shirgin su faiza ki zauna da kowa da zuciya daya. Fati ba kirki ne da ita ba don bata da kunya koma kisan hiran da zaki yi dasu don inda halima ina son ki kama bakin ki akansu maana sirin ki kibar wa cikin ki shiya sama ban hada kowa a daki daya ba nabawa kowa nata dakin daban. Tace da fatan zaki fahince ni na ce a sanyaye da eh anty nagode ta sake cewa idan kina son wani abu ki tambayi mai aiki ko Faiza su baki nace to ta juya saman gadon ta tace kwashi wayan nan kayan ki fara amfani dasu kafin na dinka maki naki. Na fara mata godiya sai ta dago min hannu alaman in bari duk da haka sai da na gode mata din. Daki na koma batare da na hadu da kowa a falon ba har na shige na aje kayan yadda na dauko su da zata fita saida ta leka kowan mu sannan ta fice gidan. Na gyara dakin sai lokacin na bude kayan don in kaisu a wardrabe din kayana kaya ne masu kyau har kala biyar sai dogon riga daya cikon na shidda kenan. Na gwargwada sai naga size dina ne ma nasan ta dade dayin su ba yanzu da ta kara jikin girma ba dai. Nai murna a raina ranan doguwar rigar na sa don yaba kyauta kenan maishi ya ji dadi indan ya ganka da abinda ya baka a jiki. Shiru yai yawa a daki na fito waje anan na samu yaran zaune suna kallo su kadai suna gani na suka nufoni nan muka zauna ina biye ma shirmay su suna bani labari wai uncle yace zai zo ya kaisu birch zan bisu ko muje tare eh kawai nace dasu. Ganin kan su ya tsufa da kitson dake kansu yasa nai shawaran sance masu nai masu wani mai kyau na hannu don dai indai kitsone Allah ya hore min iyawa ko wani iri. Faiza ce ta fito ta samu muna kitson karshe dagani daga barci ta tashi tace wai ashe kuna nan na saba ba in fito ba kowa a falon dole nima na koyi zaman daki ta kai zaune tana yaba kitson da mukeyi tare da cewa ashe kin iya kitso ne haka ? Na dai yi mata murmushi a raina nace ai kitson ne ya jawo min wanan alherin da nake ciki don lokacin da ta fara kawo su har sau biyu tana zuwa amma bana karban kudin su sai ince su din ai yara nane. Haka yasa uwar ta daina kawo min kudi a lokacin sai dai wani abin da tafiya yai tafiya kuma ta fahinci halin da nake ciki ta shiga taimaka min. Jefi jefi muke hira da ita na gama tare da daura masu ribon don shuku biyu nai mako waccen su sai take cewa nima gobe zan sance kaina ki mun ghana wiving don shi nake so nace da ita Allah ya kaimu kawai. Fati ne ta fito daga dakin ta ko kallo inda muke bamu ishe ta ba zata wuce mu nace mata anty Fati ina kwana cikinciki ta amsa min gaisuwan ita ko Faiza ta ja wani tsaki tare da kawar da kanta. Dining ta wuce ta bubude kulolin dake wurin ta wani tabe baki tace duk ma an jagule abincin ambar jagwalgwale. Ba wanda ya kulata sai kuma naga ta zauna tana diba nan ta zauna taci ba tare da kula mu ba sai dai tana yi tana satan kallon mu a fakaice. Ni dai ina mamakin ta a raina dayar yan biyun ta nufeta take cewa ta dubi kitson da Anty tai masu korar yarinyan tayi daga wurin ta ta wuto tana yi tana waigen ta kamar zatai kuka ganin haka yasa nace zo nan kada ki kuka kyale anty. Ke naji ta fada kamar wacce ta samu diyarta don haka ban dauka da ni takeyi ba sai da ta sake fadin ke Safiya bakiji bane san nan na dago kai ina kallon ta. Tace ban faye son ana shiga harkata ba don haka ki kiyayye yar kice ko yar yar uwata koda yake ma kalan dagi ce ke don naji anty na fadin wai kema kauna tace ko a ina ta samay ki oho ? Ko da yake kila ta wurin mamanta kika fito ban sani ba nan na fahinci ba uwarsu daya ba ashe kila uba suka hada. Ni dai ban ce da ita komai ba sai Faiza ce tace mata amma dai kin san ba girmuwanta kikayi ba da zaki fada mata haka. Koda yake baki da laifi don ita ta fara kiran ki wai da anty shiyasa kan ki ya fasu haka kike jin kanki wata babba can. Ya ishe ki gida dai ne baki iya korana don nima gidan yar uwata ce dariya naji tayi tace yar uwa ko muna yar uwa ai da yar uwan kwarai ce da kin so abinda take so ke yanzu baki ji kuyar korar wanan yarinyar a gurin ki. Nan dai sukai ta cacan baki wanda nake gani ba yau suka fara irin haka a tsakanin su ba da naji abin yai yawa nace da ita ta kyale ta don Allah maganan ya kare ai mutum guda bai fada. Sai kuma ta juya kaina tace wai ai dama taga zubina na munafukai ne don haka sai dai hassada ya kashe mu don ita ta wuce ajin muko. A raina nace wata sabuwa kenan kuma nayi gudun gara na fada ma zago in na gudo gidan mu don inna ga wata kuma na samu a nan yan kuwa zamana nan mai dorewa ne kuwa. Maigidan bata dawo ba sai hudu na marance daya bayan daya muke shiga muna gaida ita da dawowa koshi ban san ta dawo ba sai da Faiza ta fada min sannan na tafi. Dama yaran na wuri na sun rigani isa don sai da na tsaya nai sallah na fita zuwa gaida ita din da dawowa. Zaune take kasa yayin da diyan nata suke saman jikin ta ta mimike kafa suna zuba mata surutu saman jikin ta na gaida ita ta dago har kullun fuskan ta a cikin murmushi tace dani safiya yaya muka wuni nace lafiya kalau anty kin dawo lafiya ta amsa a sake da lafiya. Sai na juya tace kin ga Safiya debo min abinci na nan don ban iya saukowa kasan nan yanzu na gaji yau da yawa. Na juya zuwa dauko mata abincin ashe baya wucewa na sai yar tace mummy kin san may yau da baki nan mummy fati tana ta fada su Anty tana ta zagin su . Sai dayar tace sai da wanan anty tai kuka ita gwagon mu batai kuka ba tana bata amsa sukayi ta fada sosai. Na shigo dauke da ture tace dani ashe kunsha kitso ne haka sannu da kokari murmushi kawai nayi na aje mata tana cewa yauwa sannu yar gidan anty na gode. Na juya na fita dakin har nakai kofa tace don Allah yimin magana da Faiza idan kin fita nace to anty. Ina fita na nufi dakin faizan tana zaune tana waya na isar mata da sakon anty na fito daga dakin. Sai da ta gama ta fita daki na koma na kira ummi na don jin lafiyan su da sauran mutanen gida . Nan take fada min bayan wuce wana ai anyi fada da baba da inna har don bata san inda naje ba sai daga baya da taji take zage zage wai naje yawon dandi zanbarbada wa maza cuta. Shikuma baba ya kasa kyale ta nan dai abin ya kaisu har da duka abin da bai taba yi wa wata mace ba a gidan nan. Nace ni kuwa ummi may na tsare ma inna ne a gidan tafi dason in zauna in wulkanta tana min gori ko yaushe a gida ? Yanzu dai ai ya dauki mataki a kanta don da wuya ta sake maganan ki kuma ai a gidan nan yadda suka kwasa dashi abin ba dadi wallahi. Nan dai muka sha hiran mu kan matsalan gidan namu da ita karshe nai mata sallama na tashi don gyaran daki sam bani barin dakin da kazanta ko kadan. ********* ********* ********* Faiza na shiga dakin anty tace ta samu wuri ta zauna sai da ta kai zaune tace da ita yanzu yaran nan ke fada min abinda ya faru da bana nan. Shi nake son ki fada min komai nan ta fara fadi yaran na tuna mata wani abin har ta kai karshen zancen ta. Tace wanan yarinyar sai na fito mata ta bayan gida zamu zauna lafiya bata kara furta wani abin ba sai faiza da ta mike ta fice daga dakin tana masu yan biyu wasa. Hankalina yanzu akwace yake babu abinda ke damuna araina Fati ce kawai matsalata ban kuma kulata bayan gaisuwa da yama kamar na dole a tsakanin mu babu abinda ke hada mu da ita. Nayi wani haske na kara kyau sakamakon mayuyukan da Anty ta sayo min in dinga amfani dasu a maimakon vesiline da nake shafawa da. Wanda ko vaseline din ban damu da shafawa da don oilyskine din da nake dashi sai dai ina da dry face amma haka nake barinsa ba gyara. Nan ko anty ta maysa min son ita yar son kwaliyane taki jinin taga mace bata gyara fuska ba ko jikin ta tun ban iya ba dole na kowa duk kowa da ba inda nake zuwa daga gida sai gida. Duk wanan halin da nake ciki nakan tuna da halin da rayuwa na yake ciki zamana kenan ba karatu ba aure tare da ni. Duk da anty na iya bakin kokarin ta wajen ko dayaushe takan muna nasiha da gargadin mai kyau da nagarta . Babu irin wanda batai muna badon komai ba ba sai don jin tsoron Allah takance ku kama kan ku daga duk wani nauin shiga tarkon shedan Takance duk kanku amma kuke a wurina don haka ba zan yi sakaci da tarbiyan ku ba don baku gaban iyayyen ku. Ta kuwa sa a don duk kan mu babu wanda baya daukan nasihan ta dan dama Fati wani lokaci sukan kwasa wajen saka tufafi sai taso tace zata saka irin na kabilu nan sukan kwasa da yar nata. Bayan ita bata da wani matsala da kowan mu gashi yanzu zuwa na zatafi hankalin ta kwace don tasan yaran ta zasu samu kulawan da ya dace ko bata gida. Don ni dama haka nake dayara kona waye sai kaga atake yaro ya lake min a jiki bai damu da uwarsa ba koda na zauna gida akwai yar makwaciyar mu data lake mun duk safe da an mata wanka zata zo gidan mu sai da yamma indan dare yayi zan maida ita gida. Amma naiyyanar ciwon dake jikina sai uwar ta hana yarinyar zuwa wanda nasan aikin Inna ne don dama tana jin haushin hurdana da matar. Dadine gashinan sai abinda mutum bai so a gidan anty mijin ta kuma baya kasan tun zuwa na wai yaje US wani aikin suna sojoji amma kwanan nan naji antyn tana maganan dawowan shi kasan. Don haka muke yi yadda muka ga dama a gidan babu mai takura muna amma naji Faiza na fadin yanzu yaya zai dawo gidan zai koma ba dadi don in yana nan babu wali a gare mu. Ni dai dama ba sanin shi nayi ba don haka ban damu ba don koda yana nan ba ruwa na sai in fake ma daki inda har yana gida baiko ganin giccina a gidan nace a raina. Muna zaune falo da anty take cewa wani sati maigidan zai dawo kuma tana ganin shida sulaiman zasu dawo. Faiza tai saurin cewa harda shi zai dawo anty tace ba dole ba yana zuwa ya zauna a kasar mutane gashi arzikin shi sai kara habbaka yake yi yanzu ai gara dai ya dawo gida asan abin yi kan case din shi. Kamar yadda anty ta fada hakane satin da muka shiga bamu da hutu a gidan don shirye shiryen taron maigidan da kanin sa da zasu dawo kasan. Kusan aikin nice a gaba don banda kasala akan aiki duk yadda yake kuwa kafin wani lokaci mun hada komai yadda ya kamata muyi. Sai a wanan lokacin naga Fati na rawan kafa don har takan dan saka hannun ta ga aikin da mukeyi ayi tare da ita. Tai ta faman murna tace ance harda Uncle sulaiman zai dawo ashe gidan namu zai cika ke nan kwanan nan. Da yake ba hira muka saba yi da ita ba babu wanda ke kulata har tayi ta gama sukiburutsun ta ta bar wurin. Don ba sabawa tayi da irin haka ba don haka bata da jimirin dade wa tare damu a falon ranan da zasu dawo kuwa tun safe muke murzan aiki sai yamma muka gama kowa yaje yai wanka kafin shigowan shi. Tun da nai wanka na jawo dogon rigata na saka a jikina na koma nabi gado na haye don dama a gajiye nake don mun sha aiki sosai. Ban fito ba ina jin ana ta hayaniya a gidan nasan matafiyan namu sun iso kenan zuwa dare anty ta leko daki na tana cewa najiki shiru ga bakin mu sun iso gida lafiya har sunci abinci baki fito ba ke . Nai murmushi nace sun iso lafiya anty tace kalau suka iso nace da safe indan sun huta mu gaisa dasu ai wani kallo tai min. Tace amma Safiya baki ko kyau ta min ba in kin ce sai gobe mutum ya kwaso gajiya na mike zubur nace tuba nake anty ta dan harare ni tace ke kika sani ai. Tace ai har uncle din yara ya tafi abishi don shi dama bai son yawan magana na fita da zumbulelen hijabina yana shirin tashi sai gani shi kadai na gani a wurin sai anty da yaran ta har kasa na kai ina cewa daddy barka da dawowa. Ya juyo da sauri tare da amsawa yana kallo na yace Safiyar taki ke nan ashe ma karamar yarinya ce haka yace mun samay ku lafiya nace lafiya kalau. To yaya hakkurin abinda ya faru aita hakkuri haka duniya yake dama ba komai ne ke zuwa wa mutun daidai ba a sanyayye nace nagode a huta gajiya don har idona ya kawo kwalla ko. Na juya zan tafi naji anty tace dani Safiya a rage kayan nan daga wurin nan na juyo na fara kwasan kayan ida ba wani cin abincin sukayi ba sosai dan tabawa sukayi suka barshi duk uban wahalan da mukaci na aikin yin shi. Na saka na fridge a cikin sauran kuma na adana su inda ya dace a jiye su san nan na koma dakina na rufo Asuba ta gari indan tunane ya barni nai barci yadda ya kamata Yar uwa ina zaki da hakki a kan ki na mutane ance ba a yafe ba baki barin turawa kina daukan nauyi a kan ki, Karatun nan fa ba dole bane kiba kanki lafiya mana da daukan nauyi don neman suna kike turawa ko don kina ganin haka ba komai bane. To nace Allah yai min gagawan isa ga mai fitar min da novel waje . ZAINAB IDRIS MAKAWA SEENABU 8/14/20, 7:11 PM - Ummi Tandama: BAHAGGON , , , , , , 🧕🏿3️⃣2️⃣🧕🏿 YAR UWA NOVEL DIN NAN NA KUDI NE IDAN BAKI BIYA BA KADA KI KARANTA HAKKIN WASU PLEASE, , , , , Washegari muka hade a falo duk kan mu sai anty dake wurin mijin ta Fati sai faman murna take yi uncle Sulaiman ya dawo, Hararan gefen ido Faiza tabita dashi tace wai kina ta murnan dawowan Sulaiman wanan dan bakin rai jiya kin ga ya dubemu ne ma. Kai wallahi turai ya karbeshi kin ko ga yadda ya kara girma yai wani fresh dashi kamar bashi ba don Allah. Faiza ta watsa mata dan harara tace yanzu ai kanki ake ji shi baki ko isheshi kallo ba, ta bata rai tana fadin oho dai ko bai san ina yi ba wata rana zai sani ai. Mako uku cur da dawon su amma sau biyu naga daddy a gidan haka wanda Fati ke maganan shi ko yaushe ban taba ganin shi ba kuma sunce yakan shigo gidan wani lokaci amma Allah bai taba sawa mun hadu da shi ba. Yau ya shigo gidan anty tai mai tayin abinci yace bai jin cin komai a lokacin kai ta girgiza tace wai kai har yanzu kana nufin baka fitar da zancan Samira a rayuwan ka bane ? Yai murmushi yace kai samiran may can ai ni yanzu in ba lokaci ba ban faye kawo ta a raina ba sai dai ai kin san yazama dole ba zan taba mantawa da ita bane. Anty ta nisa tacd dashi Allah ya sauwaka amma don Allah ka rage yawan tunane ka koma alamarin ka kamar kowa ita fa har naji ance tayi wani aure ko. Yace nima haka naji gun wani dan uwan su can. Ta dade tana dan kallon shi sanan ta gyara zama tace na cewa dashi ya kamata ka manta da komai hakana ka samu wata wace kake zuwa wurin ta ku shirya. Sai yaneme ya katse zancen sai ta hana shi samun damar yin hakan tace kyale ni har in gama tukun yanzu sulaiman da hankalinka da ilimin ka da komai kaifa ka iya sa wani agaba kai mai fada idan kaga zai kauce irin haka. To yaya za a ce kai da kan ka ke irin haka kuma. Kar fa ka manta Allah yana sane da komai na bawan sa shekara biyar kenan ka kasa cire hafsat a ranka sau kace ba musulmi ba ? Haba sulaiman shi fa musulmi da tawali,u aka san shi saboda hadisi ne ingantacce daya tabatar muna da hakan imanin dayan ku baya kammala har sai yayi imani da kaddara mai kyau da kuma akasin hakan. To what come over you ? Sulaiman Da zaka manta da duk wanan a ranka ? Gaba da daya lamannin shi suka sauya a lokaci guda ciwon da dade yana cin zurciulyar shi ya dawo mashi sabo fil, wanan dalilin ne yasa dama yake gudun gida don kowa na shakkun fada mai zancen aure. Ko ita kanta anty sai daga baya taji dama bata dauko mai zancen ba don kawai ganin yadda ya sauya alokaci guda. Ta kalle shi a sanyayye tace sulaiman ban dauko wanan maganar ba don in tayar maka da hankali amma kayi hakkuri kayi tunane akai. Kar kaga na dauko ma maganan da kowa yake gudun fada maka nayi hakane amatsayi na wacce muka shaku dakai don zaman ka a haka yana damun kowa. Ya mike don bai son maganan yai nisa yace zan fita sai na dawo sai dai ba lalle ne in dawo kusa ba don ina son in leka bauchi kwanan nan. Ba damuwa haka na da kyau ai aje gida adubasu yafi amma kayi tunane aka magana na don Allah shi yafi. Ya sauke ajiyan zuciya tare da karfin halin fidda murmushi a fuskan shi yace zan diba madam ni zan tafi tace aiko danafi kowa jin dadi wallahi. Ta sake cewa yau dai kaki taba abincin gidan na mu ya dan yi murmushi yace mata yau bana jin yunwa ne shiyasa. Ya fice a sanyayye tabishi da kallo tausaya mashi daidai lokacin Fati tashigo get din gidan bai ko kalli inda take tana gaidashi ba yaja motar shi zuwa wurin da ake masa aiki. Ta shi go da yar fara an ta a fuskan ta tana cewa ashe uncle yazo gidan sai dai kuma bai dade ba ya wuce kuma ? Anty ta kalle ta fuska daure tace ke Fati ki saurare ni dakyau kiji may zan fada maki naga kina wani rawan kai tun zuwan Sulaima. To ki kama kan ki don sulaiman ba ajinki bane ya wauce sanin ki ki tsaya a matsayin ki idan kina son mu rabu lafiya dake ke ina ma kika ga haka zai yuyu dube ki ki dubeshi ina zaki hada kan ki dashi. Kuma ni ina auren dan uwan shi ina kika taba ganin an yi hakan sai ta turi baki gaba tana cewa damay yafini kuma ni ba mace bane halan ? Ta shige tana kumkumi ta bita da harara har ta bace mata dagani tana sauke ajiyan zuciya ina fitowa daga daki na. Nace anty ashe kina zaune nan ban sani ba dana fito na taya ki hira ai tun dazu. Ta kara sauke ajiyan zuciya tace ai bani kadai bane nida uncle din yara ne yanzu ya fita daga nan . Nace ayya aiko da na ganshi kullun muna samun sabani sai ya tafi nake fitowa har yau ban sanshi ba . Tace aikuwa da kinga shi yaro mai taken zamani don Sulaiman abin son a san shine bari rana da ya shigo zan kiraki ku gaisa don yace zai tafi gida ya duba su ya dade rabon shi da gida. Nace Allah sarki dan uwanki ne anty ? Tace a a dan uwan mai gidan ne iyayyen su guda sai dai tasu tazo daya da manjor ne kawai sai muke dasawa da shi sosai. Bai iya boye min komai nasa nima haka shiyasa nake son shi da komai nasa don shawaran shi baya wuce ni shima. Nan muka zauna tana ta bani labari da irin arzikin da yan gidan su daddy ke dashi da sauran su har Faiza tafito ta samay mu anan itama ta zauna. Fati bata fito ba sai da yamma lis ta fito tana jan kamshi Faiza ne tace yau may ke faruwa da yar mulki ne naga tun dazun take fushi a gidan ? Anty ta ja tsaki tace rabu da mara wayau kawai bata san abinda take yi bane shiya sa sai gata ta fito a fusace tana fada wai waya shiga dakin ta da batanan ya dauko mata hand dryer din ta. Faiza tace itace don Safiya ta karbi nawa kuma bata bude kofa ba lokacin shiya sa na dauko naki din. Nan ko ta shiga fada ta inda take shiga ba nan take fita ba sai da anty ta dakatar da ita da cewa. Ke Fati kin ishe ni wallahi haba ke kika saye shi ko ni da zaki saka mutane a gaba kina masu fada haifan su kikayi komay ? Don haka ki shirya kayan ki gida zan maida ke nagaji wallahi duk naji abinda kikewa Safiya tun zuwan ta garin nan ido kawai nasa maki inga gudun ki. Tun farko ina sai da na hada ku nai maku nasiha amma kika shure magana kina yadda ran ki yaso dasu a gidan nan. Wai halan kikai Faiza matsayi ne agidan da zaki dinga hura ma mutane hanci yadda kike so ya zama dole in mai dake gida don ban iya zama da wanan iskacin naki haka . Jin anty na ambato gida yasa ta sausauta maganan ta ita ko faiza kai ya fasu jin ance tafi kowa matsayi a cikin mu sai wani budawa take yi. Nan dai anty ta kafe akan lallai ta shirya ta maida ta gida sai na shiga ba anty hakkuri tana ta faman fada da ita. Ds kyat na samu ta hakkura da zance sai dai tace wallahi ta shiga hankali ta don ta gaji da ita a gidan Tun wanan lokacin ta shiga hankalin ta da kowa dama ba mai shiga tsabgan ta cikin mu don haka bamu damu da ita ba. Da anty zata dawo ranan sai ta sayo min nawa in huta da aron nasu da nakeyi tare da yan sayayyen kayan makeup dina. Zama na a gidan yasa yanzu zaka ga komai a gidan tsab don kai aiki iyakan ta girki nice ke tsabatace gida kafin duk su tashi na gama komai har in kama mata yin girkin kuma. Wanan abinda nakeyi shiya na kara shiga ran anty sosai tana tausaya ma halin da nake ciki takan kaini amsan magani secretly ba tare da kowa ya sani ba a gidan. Kuma ban taba jin wani ko ganin an kyan kyankyamayni ba a gidan zama suke dani ba wani nuna rashin yarda dani gashi bata rage ni da komai ba na fannin rayuwa kuma. Sati uku da maganan mu ina daki kwance yan biyu ta tashigo da gudu tace wai inji mummy su inzo . Na dauki dan kwalina dake saman gado nai rolling din kaina dashi tare da dan gyara fuskana kartai min kwankwami rashin gyara. Na fito su biyu na samu a fali sai dai may shi ya hada baya ban iya ganin fuskan shi a lokacin. Gasu yan biyu sun na wasa da hannuwan shi sai dai mai shi fari ne soll da ganin shi yan biyu tana ta jan yatsun hannun shi na iso wurin tace yauwa Safiya ga uncle yau a gidan. Sai ya juyo da sauri yana kallon wace akace ma safiya din don bai taba jin sunan a gidan ba sai yanzu. Juyo wan shi mukai ido biyu dashi sai da gabana ya fadi don ban taba ganin namiji hadade irin shi ba nan dai na gaisheshi ciki kunya kunya. Ya amsa min da lafiya lau kawai ya juya yaci gaba da wasa da yaran dake damun shi nace anty gani. Tace shike nan dama kiran ki nayi ku gaisa da uncle din yara da baki sani ba sai nai murmushi na juya na barsu wurin daya fahinci na wuce. Sai yace ita kuma wanan din wacece ita anan gidan take itama da zama ? Tace budurwan da nai maka kamay ke nan yace kai haba madam kikan fara maganan ki don ki koreni ko. Tace daga maganan mace zan koreka wai ko sai mun kaika mararaba mun ma wanka ne zaka daina tsaron mata. Yace kai don Allah bari wanan ma ta gama secondry ne tace tun yau she ta kare Allah da gaske nake yi inda kana ciki sai in kama ma kawai musha buki. Take ya daure fuskan shi alaman ba wasa a tare da shi tace kai ke nan da an maganan aure sai ka bata rai may kake nufi ne wai ? Bai bata amsa ba sai ci gaba da yayi da hira da yaran dake gaban shi sai da ta kawo mai zancen aikin da akeyi mai ta samu ya sake fuskan shi. Ni ko tunda na juya na wuce ina ta mamakin haduwan wanan mutumin da anty tace dan uwan daddy ne mijin ta kuma wai may kudi naji anty na cewa. Na gaji da tunane na watsar da zancen na kama sha anin gabana daya damay ni kwai sai ga fati ta shigo dakina abinda ban taba gani ba tun zuwa na gidan. Tana shigowa ta fada saman gadon dakin nawa da yasha gyara sai kamshi ke tashi a dakin tako ina na dakin. Safiya kin san kowa yau ina cikin farin ciki ga uncle can a falo yazo tun dazun yazo yana falo na dade dakina ina leken shi ta fada saman gadon tana wani irin dariya. Nikan kallon mamaki kawai nake binta dashi don abin ya daure mun kai sosai tace wai kin san wani abune safiya na gyara zama tare da cewa aa. Tace wallahi anty tana kawo min kubsawa don sam bata son zance da guy din nan ni kuwa duk yadda zanyi in ga yaso ni sai nayi kin san abinka da yan uba. Sai nai saurin kallon ta don jin kalamin ta gamay da anty duk wanan halarcin da take mata amma wai tana kiranta da yan uba. Ta kara lumshe ido tana ce min guy din ya hadu ne sai ma in kin ganshi wallahi yanzu tashi zan yi in dake kawai in je mu gaisa dashi ko bata so ni ban damu in dai bukatana zai biya. Nace haka za a yi kije ku gaisa ko ki samu shiga ai ba a bori da sanyin gwiwa tace ai shi na gani wallahi. Ta mike tana wani juye juye tace yaya kika gani na hadu ko da gyara nace cikin daga kai komai tsab wallahi. Ta fice daga dakin na bita da kallon mamaki nace oho zamani ina zaki damu mata cusa kai ga maza haka ? Acan falo tun da anty taga ta tun karo wurin su tace kin ga Fati kira min safiya ta hada ma uncle fruit salad wai abinda yake so ke nan. Tace anty bagani ba zan iya hada mashi ai tace don Allah ki raba ni da shirmay ki ranan da ta hada masu bacewa kikayi ke baki iyaba. Sai tace ai naga yadda ta hada din kin ga kira min Safiya nace don Allah ban son shirmay ki hakan nan. Ta wuce tana mai jin haushi yar uwar nata data kwabsa mata a gaban shi sai gata dakina tana cika tana batsewa tace tana kiran ki . Niko ina cewa yaya anyi nasara dai ko kin samu magana dashi tace ina yar bakin cikin zata bari ai komawa zanyi ko bata so. Nace antyn ne yar bakin ciki tace to in ba bakin ciki ba ko zama bata bari nayi ba ta koreni da karfi da yaji ban san abinda take nufi da hakan ba. Mikewa nayi zuwa amsa kiran anty na je da sallama na ce anty ance kina kirana tace eh kin ga don Allah wanan gwauron zaki hada ma fruit salad wai yake son sha yau. Ban tsaya ba na juya zuwa kitchen din ya dan kalle ni ta witsiyar ido a ranshi yace ba laifi yarinyan sai dai akwai shamaki a tsakanin mu. Ban dauki wani lokaci ba wurin hadawa don akwai komai na bukata kankara na jefa yadda zai yi saurin yin sanyi bayan na hada din. Na nufo dashi nan na tsikayi Fati zaune tare da su tana wani kwarkwasa yar nata nata hararan ta bata damu ba nazo gaban shi na aje yace dani thanks kawai na juya zan wuce.. Anty tace dan tsaya ki zuba mashi nima ki zubo min karya shanye ba sha ba nan na juya na sake dukawa gaban shi ina diban mata kamshin turaren madina dana shafa ya dokan hancin shi sai lumshe ido yake yi cikin sytle. Na diba na bata na dago muka hada ido da Fati sai naga tana harara na ni dai na wuce abina ban kara juyowa ba. Sai gata dakin ban bari tayi magana ba nace kai amma Fati kunyi balain dacewa da wanan mutumin gaskiya. Da da fushi ta shigo amma jin abinda nace yasa ta washe baki tana fadin gaski Safiya nace kwarai kuwa kiyi kokari anty tafahinci ki . Tace haka za ayi ai don haka sai na zauna ki fada min ta inda zamu bullo mata nace niwa aini yar kauye ce ban san komai ba wallahi.. Da yamma muna falo gaba dayan mu Faiza ke cewa wai ni yaushe Yaya sulaiman ya wuce dazu ne ? Kafin anty ta bada amsa Fati tai carab tace ai kedai yau ya dade gidan nan sai anty ta balla mata harara tace ke aka tambaya ko kin san wucewar shine. Wai ke may yasa baki da hankali ne Fati sai tai wani turo baki kamar karamar yarinya nace anty kin sani ko za ayi yar gida ne. Tai saurin cewa haba Safiya don Allah kibar wanan zance ki kyale ta da shirmay ta can so take mukai ga yadda ba a so. Ita ke haukan ta nan shi yana da wace zai aura ko ina ma zai kai ki haka kazama dake sai tai fushi ta daga wurin Faiza tace da gaske anty ya samu mata. Tace insha Allahu muna fatan hakan amma sai komai ya kankama zamu je ayi magana don ba yar kasan nan bace yace. Nan ta hau murna don jin dan uwan nata ya samu wace zai aura ashe maganan ya fada kunnen Fati dake wuce wa. Sai da na dawo daki ta samay ni da maganan nace tayi kokarin cusa kan ta dai in Allah yayi ai ba wanda ya isa ya hana ta sauke ajiyan zuciya tace shiyasa nake son ki wallahi don fadin gaskiya. Ni dai na samu ta fita na rufe kofa na asuba ta gari sai kuma in Allah ya kaimu lafiya muji da wace zata zo min kuma a gidan. ZAINAB IDRIS MAKAWA SEENABU 8/14/20, 7:12 PM - Ummi Tandama: BAHAGGON , , , , , , , , , , 🧕🏿3️⃣3️⃣🧕🏿 YAR UWA NOVEL DIN NAN NA KUDINE IDAN BAKI BIYA BA KADA KI KARANTA HAKKIN WASU PLEASE DON BAN YAFE BA IDAN KON FITAR MIN DA NOVEL UBANGIJI YA SAKA MIN A KANKI CIKIN GAGAWA. Wanan abin yasa yanzun muke shiri da Fati don ko yaushe tana dakina muna hira abu daya kullun na yadda zata shawo kan shine a gidan. Zata shigo ta fadi nidai ina ta mata dariya indan ta gaji ta fice ta koma dakin ta, sai dai abu daya ne wanda ban yarda da shi ba. Irin yadda take kushe maganan anty ko take sukan ta da munana kalamai marasa dadin saurare. Don haka sai na dakatar da ita nace idan zamuyi hiran mu mubar saka sunan kowa mudai nemi mafita akan yadda zamu fito mazancen ta da sulaiman din. Taso tai hushi alokacin amma sai tai tunanen ba ida take kai maganan ta ba tare da wani yaji ba sai gurina, sai gashi ta dawo da kanta. Ina kwance daki sai gata ta fado min daki tana dariyan jin dadi nace halan mutumin ya shigo ne. Tai wani far da idanuwa tace dani bai shigo ba tukun amma naji mijin anty na waya dashi wai su hadu karfe hudu nan gidan. Nan dai mukai shawaran abinda ya dace tayi tabar dakin tana ta murna nikan fitan ta dakin na kwanta abina don ina fashin yin sallah a lokacin ban son shiga mutane. Kamar yadda Fati ta fada hakan ne yazo gidan bayan hudu ya dan gwauta kadan yana falo da anty daya sama a falon ita da yaran ta. Tun shigowan shi take faman sake murmushi a fuskanta kamar yadda ta saba indan sun hadu. Ya zauna suna gaisawa da ita yace komao lafiya ko ta amsa mai da lafiya kalau muke, tace yaya aiki kuma?, ya lumshe idon shi yana cire hular kan shi . Yace aiki muna kai wallahi yai ajiyam zuciya yace yanzu ma mijin ki ne ya kirani koda yake dama yau ina da niyar shigowa gidan naku. Sai ga mijinki ya kirani kuma tace ka kwana biyu baka shigo nan din bane ya sake cewa wallahi yau nake da niyar shigowa don ina son in baki wani aiki ne. Ta nisa tare dacewa tau fa, ina jinka rankaya dade, See you nine ranka ya dade kuma ni dai kisa a hada min wanan abin don yau dashi zan tafi don ina son shi sosai wallahi. Mikewa tayi don yaran sun shige don bude tsaraban da ya shigo masu dashi da zaizo don haka babu yaro kusa sai anty taje kirana da kanta. Tana wucewa Fati ta fito acikin wani irin kwaliya tana kashe ido wai tana mai sannu da zuwa takai zaune a dayan kujeran falon. Niko ina daki na kwanta wuri daya na dunkule wani iri kamar maijin sanyi idan ka ga yadda na kwanta. Tabani, tayi tana kiran sunana a hankali, inda na bude ido na sauke a fauskanta ina mai kallonta cikin magagin barci sai naji ta tambaye ni dacewa lafiya kike kuwa kike ta barci haka ? Na murza idona tare da cemata anty barci ne kawai ya dauke ni tun dazun tace to tashi don Allah aiki zan saka ki don wanan bakin batauren ya shigo wai fruit salad yake son aimashi. Na sake murza idona nace to anty barin tashi yanzu zan fito ta mike don barin dakin nawa har takai kofa nace ina mike wa Fati na nan ne muyi tare. Tace Fati ko mashiririciya may zata iya wanan don Allah fito ki hada mashi tunda har yai magana kada ya tafi ba a hada mai ba kuma. Hankalin shi naga wayan shi baiko san tana zaune a wurin ba ita kuma sai wani gyare gyare take yi daga zaune kamar wacce ake tsunkulan ta. Anty ne ta iso gurin tun da ta ganta ta daure fuskan ta har tazo ta zauna ba walwala a fuskan ta. Ta zauna tare da cewa ke kuma may kike anan din kije safiya na jiranki ki kama mata aiki. Ta juya inda yake tana murmushi tace ina jinka sakon may kake magana akai ne wai ? Ok dama account dinki nake so inyi amfani dashi in tura ma wani kudi miliyan hamsin mun sai injin ne a gurin sa . Sai bayan sati biyu zaa fitar da kudin kinga kenan kema zaki iya samun wani abu daga yin hakan . Tace sulaima ba matsala gayin hakan dagowa yayi yana mata dariya yace idan da matsala ai ba zan saki a ciki ba kedai ki bayar zaki gane abinda nake nufi. Sai ya fara mata bayani a takwaice yace ashe ke matsoraciya ne kina tsoron kada a yaudare ki ko da irin haka yawancin mutane suke dagawa ina son inga account dinki yana motsine. Nan ta shiga dariya don ta gane mafusa arlallan business yake son sakata ciki itama nan ta shiga yi mashi godiya daga mata hannu yayi yace haba madam ya idan ban maku ba suwa zan taimakawa ? Yace sai dai gida da fili danake son saya a Abuja ta saki baki tana kallon shi don jin irin bayani da yake mata na gida da filin da yake so. Ta sake cewa yanzu sulaiman ga gida ga fili kake shirin saya haka yace ai wanan ba komai bane sai tai wani irin shewa. Tace iyyye tun yanzu ashe bari mu fara shirin buki ashe, Dariya ya fara mata yace ba a sayen gida sai za ai aure ki rufa min asiri tun dawowan mu kudin nan nake son in sai gida da fili dasu, don ina yin wani aiki acan Abujan kuma dai ina ganin anan zan zauna don nafi son zama arewa da nan din. Tace kayi dabara wallahi shawaran da nake ba daddy su kenan ko yaushe amma naga shi ra, ayin shi baison zama arewa sam. Yace arewan ne babu dadin zama saboda mutane yan sa ido ga abin da bai shafe su ba sai suyi tama zargin banza ba gaira ba dalili kai kana neman nakan ka amma mutane idon su na kanka. Mijin anty ne yashigo sai suka can za firan suka fara gaisawa dashi a daidai lokacin da na fito dauke da tiren a hannu na da na shiryo mashi. Daddy din na fara gyarwa sai shi sai daddyn yace Safiya kike ko kina gidan nan ban gani ki sai nike tsamanin ko kin koma ne ban sani ba. Murmushi nayi kawai sai anty ne ke cewa ita wanan ai in ka ganta waje su yan biyu ne suka fitar da ita dole zaman daki baya isan ta ko yaushe tana ciki kumshe. Na gama jerawa zan wuce sai naji tace yauwa daddy shine nace ma mutumi na ko zai fada neman Safiya ne ya tsaya yana min kwana kwana. Don Allah ba sai yar gida gida ba kawai ga mata har gida ya samu ba niba har mijin nata wani irin kallo yai mata nidai na wuce na barsu nan. Ina ganin sun dade a wurin sai dai ban san maganan da sukeyi ba dagani dai maganan tana da muhinmanci a gare su. Sai can naji fitan mazan daga gidan wanda ban debe tsamani sallah suka fita yi don lokaci da yayi yan biyu ne tazo take ce min mummy su na kiran su. Ban tsaya ba na jawo dankwali na dora a kaina muka fito tare da yarinyar da tazo kirana din . Tana zaune tana hada wasu takardu dake saman table din gaban ta tace kinga bai ko sami tafiya dashi ba yadda yace anan suka shanye abinsu shida major. Ina kwasan kayan nake jin yadda anty ke ta faman yabon sulaiman din har take ce min wallahi safiya idan na samu nai wanan hadin a tsakanin ku kowa naki ya huta indai Sulaiman ne don bai da matse na tare dashi balle matar shi mutum ne mai sakin aljihun shi sosai wallahi. Nidai abinda na saba nai mata watau murmushi sai dai a raina nace kardai anty ta zamo cikin masu rufe ido ayi cuta da ita kan abin duniya. Ni dake da lalura har take zancen hadani da wani wanda baida matsala irin nawa ni yanzu aiko mai irin matsalata banda lokacin shi balle mai lafiya in cuta mai. Na kwashe kayan zuwa kitchen da zan fito ma ban dawo wurin ta ba sai nai hanyan dakin na don zancen ta ba abin saurare bane a wurina. ********* ********* ********* A can gida kuwa ummi da kanina shafiu sun rike sanaar da na bar masu dakyau don takar ina gari ne don yaron bai da wasa ko kadan. Saadatu inna ta kwaso ciki tun ba a gane ba har mutanen gidan mu suka gane ana ta kumbiya kumbiyar zubarwa sai dai Saadatun taki ba Inna hadin kai a zubar da cikin tace tsoro take ji. A wani dare basu san baba yana waje yana alwala ba rikici kan azubar da cikin ya hada ta da inna a dakin su tun bai sauraren su har takai baba ya saka kunne ga maganan su. Nan yaji abinda ya tayar mashi da hankali ya koma dakin shi sai kuka koda gari ya waye bai fito ba har wani lokaci. Mama ne ta shiga dakin shi don taga may ya samay shi ta samay shi a cikin wani hali take hankalin ta ya tashi. Zata tara mashi jamma a yace taje dai ta kira mai inna da su ummi da yaya Sani su zo. Kowa ya taru suna jiran suji may zai fada masu sai can yace ma mama yanzu har da ke ashe za a hada kai a cuta min gidan nan. Abu na faruwa haka amma an rasa wanda zai iya fada min sai da Allah ya sanar dani jiya da dare nan ya kwashe abin da yaji tsakanin inna da Saadatu yake fada masu. Nan Inna ta kama fadan karya wai baidai ji da kyau ba mama ne tace haba Rakiya ko makaho ya lalube saadatu ai yasan halin da take ciki. Don baki samu bane shiyasa muka kawo ido muka saka maku kawai amma batu duk ya gama bin gari ai. Shiru wurin yayi sai yaya Sani ne ya kawar da shirun da cewa Inna kin kai ga yadda kike so ba abin da baki fada akan matsalan Safiya agidan nan. Yanzu gashi ke Allah ya nuna maki nashi isharan sai ku san yadda zakuyi da ciki ai maza basu son ta da aure amma suna son ta da lalata. Baba yai magana karo na biyu yace ba mai zubar da cikin nan a gidan nan don bani kunya biyu abarshi ta haifi abinta kuma duk wanda yace zai yi yunkurin zubar da cikin nan sharia ce zata raba mu dashi. Nan ko inna ta aza hannu akai wai dama ta sani baba bai kaunar ta da diyan ta ai yafi son yaga sun lalace a gidan. Yace yadai ji amma ba mai zubar mai da ciki a gidan shi sai inna tace zata kaita wurin yan uwanta a wani kauye a zubar can. Amma ba yace bai yarda ba da kuyan lahira ya kwmmace yai na lahira don zunubin shi bai kona shiba na yar shi ba zai kona shi ba. Haka dai aka watse baram baram a wurin inna ta shige dakin ta tana kuka diyan ta ma suka bita kukan sukeyi suma. Gidan dai ya koma masu ba dadi na kira ummi da safe don inji lafiyan su take fada min halin da ake ciki nan ko na tausaya masu sosai. Ummi tace min abinta ne Allah ya mayar mata ta gani ko tafiyan nan ba abinda bata fada ba wai karuwanci kika je yi acan. Yanzu gashi taga abinta har a kuryan dakin ta ta koma mujiya a gidan don ko fitowa bata son yi tsakar gida. Abin su na kishi a yadda ummi ke magana sam bata tausaya ma inna da Saadatun ba sai nine nace ummi wanan abin fa ba inna kadai ya shafa ba har daku dake da diya a gidan. Don suna gidan mu ne zai lalace ga banza sai ai muna bugun dan kadanya gaba dayan mu ba wai za a ware ta ita kadai bane a zaga. Sai naji tayi lau shi tace abin tane ai da ban haushi wallahi nace hakkuri za a yi a rungumi kaddara tun da baba yace ba a taba cikin. Nan dai na bata shawara nakuma ga ta dauka san nan mukai sallama na kashe wayan cike da jimay abunda naji din. Banyi niyan kiran saadatun a yanzu ba sai hankali ya kwanta zan kirata in kwantar mata da hankali don nasan bayin ta bane sherin uwar ta ne Allah yake nuna mata abin ta tun a duniya. Sai dai kwana biyu na shiga damuwa sosai har anty ta fahinci haka ranan ta kirani dakin ta dama nasan kira dakin ta magana ne na muhinmanci. Nan ta shiga tsoratani da nasihohi iri iri na ban tsoro don ita tana zaton halin da nake ciki ne nasa damuwa akan shi. Nan dai nace mata anty bashine ke damuna ba yar uwata ce ta shiga wani hali abin yake damuna arai. Ba abin da zan iya boye mata yanzu sai na kwashe komai dake faruwa na fada mata sai da ta bari na gama fada mata komai sai tace dani. Lallai Safiya kina da imani a zuciyar ki in bashi ba matar da take son taga bayanki zaki dauki damuwar ta ki saka a ranki karfa ki jawa kan ki wani sabon lalura gaki yarinya karama dake. Addua zakiyi mata kawai shiya fi nace anty ban taba jin tsanar diyan Inna araina ba don itace maisa suke min abinda sukeyi din tace ai shi nace kiwa yar uwar ki addua Allah ya rabata lafiya don aikin gama ya gama ko. Nai mata godiya zan fita tacevin dakata ledan dake gefen ta ta miko min nasa hannu biyu na karba ina godiya tace bani zaki godewa Sulaiman ne ya saya maku. Yaji ina maganan saya maki waya yace in bari zai kawo maku waya yau ina office sai gashi dasu guda uku shi na zaba maki wanan farin ga sauran nan zan ba su faiza nasu ita da fati . Nan shiga mashi godiya da addua ita ko sai dariya ta min tace ai wanan karamin aikin shine wallahi . Ranan haka muka kwana da murna tare da mu kowa yana farin cikin rike babban waya a cikin mu wanda kudin shi zai iya kai dari da hamsi. Ranan ina kwace falo saman doguwar kujera kasalance sanyi da iskan dake fitowa daga naoran sanyayya falon na barazanan saukar min da barcin marance. Sai ga Fati ta fito falon daga dakin ta take cewa dani wai dama dakina zata ashe ina nan zama tayi gap da kaina tace . Dama wani abu nake son kin min Safiya sai na dago ina kallon ta don jin may take so na dashi. Ta dan nisa take cewa ba wani abu bane nake so sai ki dauko min lamban mutumi na a wayan anty idan kin samu hali don bata yarda in dauki wayan ta sam. Ke naga kuna dasawa da ita don jiya naga ta baki wai ki tura abubuwa a cikin wayan ki. Ban kai ga bata amsa ba sai muka ji sallaman shi a kofan falo ya karasa shigowa yana rike da brief case din shi tare da su yan biyu a bayan shi ga katuwan leda da ya riko a dayan hannun shi wanda nasan tsaraban su yan biyu ne a ciki. Daga inda nake kwance mukayi arba dashi ban riga na kai ga tashi zaune ba. Har suka karaso inda nake yaran suka fado min suna cewa yau uncle ya kaisu yawo birch sun ga ruwa da kifi . Na yun kura na tashi zaune ina kamo dan kwalin kaina da ya zamay min don a kwance nake. Ita ko Fati duk ta rude da ganin shi zuciyar ta ya rinka saka mata tunane daban daban ba gaira ba dalili na samu na kai zaune ina mashi sannu da zuwa. Bai dago ya kalle ni ba sai dai a ranshi yana nasawa tabbas yarinyar kyakyawa ce mai cike da kwarjini da kamala ya fadi a zuciyar shi. Sai naji Fati cikin rudewa tana cewa gashi ko anty ta fita har yanzu bata dawo ba kamar bai son magana naji ya bata amsa da tana tafe sunyi waya da ita ai. Mikewa nayi zuwa kicthen na hado mai abin sha da ruwa na kawo mashi sai ga anty ta dawo har fati ta zauna tana mashi zuba a gaban shi. Nan mukai mata sannu da dawowa nikan na bar wurin sai yaran suka biyu ni suna bani labarin fitan su da uncle din. ZAINAB IDRIS MAKAWA SEENABU 8/14/20, 7:12 PM - Ummi Tandama: BAHAGGON , , , , , , 🧕🏿3️⃣4️⃣🧕🏿 YAR UWA NOVEL DIN NAN NA KUDI NE IDAN BAKI BIYA BA KADA KI KARANTA HAKKIN WASU DON BA A YAFE BA, , , , Anty ce ta shigo gida da karfe shidda na yammaci duk muna a falo zaune sannu da zuwa muke faman yima ta tana amsawa a gajiye takai saman kujara ta zauna tare da fadi wassh Allah yau na gaji sosai ga shi kuma gobe zan bi hanya da safe. Gaba dayan mu maida mata hankali mukayi don jin ina zata tafi kuma da safe da tace din, mike kafa tayi saman dan stole din da ke gaban ta tana gyara zama take fadin . Gobe tafiya zamuyi da uncle Sulaiman zuwa abuja zamu tafi muga wurin da yake son saya ya matsa sai baban su yan biyu yaje yaga wurin dani kafin ya saya. Faiza ne tace ai hakan nada kyau mutum ya dinga sa ba gabatan shi gaba kafin yaya abu sai anty tace wanan ai halin Sulaiman ne. Har sukaci suka sude ban saka masu baki ba ina daga kwance ina sauraren hiran tasu anan na dan fahinci wani abu a tsakanin su. Tun da asuba ta shirya wai ashe ta jirgi zasuyi tafiyan bakwai yai masu a airport jirgin su bai dade ba ya daga zuwa abuja. Muna gida zaune ni da faiza ita kuma fati tun tafiyan su ta fita daga sunan baza ta dade ba sai gashi har hudu na yamma yanzu. Hudu ya gwauta sai gata hurjanjan ta shigo gidan bata ko kalle mu ba ta shige dakin ta Faiza ta kalle ta ta tabe baki. Nidai na mayar da hankali ga tv don karamin aikin faiza ne yanzu ta dauko topic din fati aduniya taki jinin Fati da komai nata. Itama fatin na kula da haka bata kaunar Faiza don takance min munafukace wai don haka zama a taka tsantsan ya kamani a cikin su sai bani yarda daya yayi da daya a bayan shi. Ban jima ba a wurin na mike na shige daki da yan biyu don bada su aka tafi ba na zata kwana zasuyi sai gashi sun dawo da yamma . Tana da gajiya don haka bata zauna da mu ba tayi dakin ta don sauke gajiya a jikinta lokacin ne fati ra samu daman shigowa dakina. Ni sai da naji tsoro lokacin dana ganta tace ke matsoraciya nice na sauke ajiyan zuciya . Nace may ke faruwa ne Fati na ganki da daren nan haka, ta dai ce uhumm kawai ba tare da tai magana ba takai zaune a wurin . Tace aike dai baki sani ba yau naje wurin wani mai magani ne a wani kauye wani irin kallo nai mata na dafe kirjina nace maigani kuma ? May kika tafi nema gun mai magani ko baki da lafiya ne ban sani ba sai naga ta girgiza kai tana cewa haba dai kamar ba mace kike ba . Zuwa nayi a samo min kan madam din gida da kuma mutumin nawa gaba nane ya fadi ras taci gaba da yi min bayanin abinda ya kaita . Ban iya karasa sauraren ta ba sakamakon fadawa tunanen danayi mai zurfi a raina nace tabas inda akwai abinda na tsana shine inga mace tana biyan bokaye da malamai a rayuwanta. Balle fati da ko aure batayi ba ta fada wanan akidar sanan babu kunya babu tsoron Allah ko nauyi bata ji har tana fada min inda ta tafi da yadda akayi. Wanan abin ba karamin tashin hankali bane musanman ma da tace takai har da anty gun mai magani to aima yar uwar nata may can. Ida babu kuya babu tsoron Allah take fada muna yadda suka kwashe da boka a take na suma jin hawaye masu dumi na bin kuncina bata farga da hankan ba sai daga baya. Maganan da tai min ne ya dawo dani hayaci na kallona take yi da wani irin mamaki baiyyane a fuskan ta ta ce dani Safiya may ke faruwa ne naga kina kuka daga ina baki labari. Girgiza kai nayi cikin takaici nace Fati waya baki wanan shawaran na zuwa wurin boka at dis age da kike har kin san hanya bin bokaye. Abin haushi da takaici kuma kirasa wacce zaki kai sai yar uwar haihuwar ki wace ta zamay maki uwa da uba ga komai naki. May kike nema wanda wanan boyar Allah batai maki ba a rayuwan ki muma da ba uba daya muke ba may ta rage mu dashi a rayuwan mu. Kafin in fadi wani abu sai ta katseni da cewa bafa wani abu nake so gare ta ba kawai yardan ta nake so ga bukata na akan sulaiman kawai. Na girgiza kai har wanan lokacin fuskana yana dauke da guntun hawaye wani irin kallo nake binta da shi mai nuna tsanan abinda ta fada min. Sai ta hau cewa ni fa yarda da amincewa yasa na fada maki da ace nasan ke ba yar hannu bace ga wanan harkan ba abinda zai kaini fada maki . Nisawa nayi nace wallahi zan fada maki gaskiya tun wuri ki daina wanan halin tun bai zama maki jiki ba ko. Ta mike tana cewa yau hiran namu dake ba zai yi ba do bani son mutum mai kara min zuciya akan abin da na saka gabana. Tamike tare da nuna ni da yatsa tace i hope wanan maganan ya tsaya iya ni dake kawai a gidan nan idan naji shi a waje zamu samu matsala dani dake sai ta fice. Kallon mamaki na rakata da shi ta buga min kofan daki garau ta fita na sauke ajiyan zuciya ina mamaki halin matan yanzu har da macen da batai aure ba ta iya zuwa gurin boka don kawai a asirirce mata yar uwar ta ina ga in ta samu kishiya kuma ? Tun wanan lokacin mukai sanyi ni da Fati Faiza tayi tayi tasan may ya hada mu bamu kaman da amma naki fada mata sai ce mata nake yi kila ta samu wata kawar ne a waje. Yanzu anty bata faye zama a gida ba suna aiki sosai a wurin aikin su don haka sai kula da gidan ya dawo hannun mu. Duk da dai sauran ba wani abu sukeyi ba sai ni da mai aiki zamu aiwatar da komai kafin masu gidab su dawo Faiza irin mutanen ne masu fuska biyu. Amma bayan haka ta na da kirki sosai amma sai na fahinci akwaita da aikin ganin ido abinda bata sani komai da muke a gidan yana kunnen anty. Ta san yadda kowa ke rayuwan shi a gidan ido kawai ta saka muna tana kallon kowa da halin sa ranan da rana anty tai muna dawowan bazata a gidan . Ina daga ni sai mai aiki dake wankin kayan ta nikuma ina muna girki da zamuci ga yaran ta zaune suna kallo a falo na dafa masu indomie kafin an gama hada abincin gida. Su ko faiza tana barci a dakin ta tayi dadaya a saman gadon ta Fati kuma ta fita yawan ta sai in yai mata dadi kafin yar ta dawo aiki take dawowa gida. Tana shigowa ta samu yaran na cin abincin da na aje masu suke ci take tambayan su suka ce anty safiya ne ta dafa muna. Jin motsi yasani fitowa ina yarfe ruwan da na daureye hannu a hankali naga itace ashe ta dawo nake mata sannu da zuwa. Tace sannu da aiki safiya shiya yanzu sai in fita gidan nan hankalina kwace ba tare da fargaban wani abu ba ga yaran nan dako ban da kwanciya hankali idan na barsu a gida don kamar ban barsu da kowa bane saboda basu samun kulawa yadda ya dace.. Har na gama girki na kawo ma anty nata sai mai aiki ta shigo ta samay ta a zaune falo ta fara gaisheta da dawowa. Tace yanzu na gane zuwan safiya gidan nan yai maki dadi don duk kin tatara aiki kin bar matayi daidai ina kawowa anty ruwan sha naji tana fadin haka sai nace a a anty tare, , , , Hannu ta daga mi alaman in shiru naja bakina naci gaba da jera mata abincin tana may ci gaba da fadan da takewa funke mai aikin ta. Sai ga Fati ta dawo nan tabita da harara simi simi ta shigo tana kamay kamay fada tai mata sosai ranan har ni din bata bari ba. Bayan kamar kwana hudu dayin haka kowa a cikin mu ya shiga taitayin shi don gudun laife gare ta daga ni sai Faiza dake charting a wayan ta. Sai gata ta shigo gidan sun dawo unguwa da yaran zaune nake zugun nayi tagumi nayi zurfi acikin tunanen duniya. Sai muryan ta naji daga sama a kaina tana fadin Safiya wallahi zamu bata dake a gidan nan matukar baki daina damun rayuwanki da tune tunen marasa tushe ba ke kadai ke gidan nan ne da kika kasa sake ranki cikin yan uwa kiyi walwala. Na dago kai da sauri ina kallon ta a lokacin ya shigo da kaya niki niki da suka sayo ashe tare dashi suka fita unguwan . Nisawa nayi ina mata sannu da zuwa sai dai bata amsa ba sai ci gaba da fadan da takeyi min kamar ba magana yake yi ba don hausa shi da baya fita da kyau yace. Bata da lafiya ne ko may ke damun ta haka din ? May kuwa uncle na rasa gane hankalin yarinyar nan tun da tazo gidan nan taki ta sake jikin ta kamar kowa sai zama tana yawan tunanen banza da wofi ita kadai. Zaune yakai saman kujeran da fuskantar mu tare da aje kayan da suka shigo dashi din tace kamar wanan yarinyar da bata wuce 19 years ba zata saka ma kanta tune haka. Jinayi yace keko may yasa kike haka din tunda antyn ki bata son yadda take ganin ki ba kamar kowa ba a gidan yana magana yana kallo na . Yaci gaba da cewa don Allah ki kwantar da hankalin ki ki daina damun kanki koma may ye a ranki ki fitar dashi don tunane yana iya kawo maki illa a lafiyar ki. Ya maida kallon shi ga anty yace bata dade da zuwa nan din bane ko may ko gida take tunane haka ? Tsaki tayi tace wani irin dadewa kuma ai duk ta rigasu zuwa nan halintane hakana din kawai dason shiga damuwa. Shi ya kawar da maganan da dauko maganan bude gidan shi da suke shirin yi yace sai in an gama tsarawa zai zo mata da yadda akayi ya mike yana shirin wucewa sai lokacin tace dashi ba zaka tsaya ta hada maka fruit din ba. Yace no barshi kawai zan tafi don naga mai hadawan bata cikin hayacin ta mikewa nayi da sauri nace barin hada zan iya ai. Ban dauki lokaci ba na hado mai nakawo yace dashi zai tafi don baida lokacin tsayawa yasha a nan din, har waje suka fita da anty sun dade sai gata ta dawo ciki. Lokacin muna zaune da diyan ta da Faiza tace in bude ledan da suka shigo dashi gidan in fitar da kayan dake ciki. Nan Faiza ta tayani fitarwa muka fitar da kayan wanda yawanci duk na twins din tane tufafi da kayan makulashen yara tace mu diba in kai saura dakin su. Bata barni haka ba dana dawo na zauna sai da ta bini da nasiha kan in cire damuwa a raina Faiza ke cewa ta rasa may nake wa yawan tunane hakana. Ba laifi nayi korin ganin na fitar da komai a raina sai dai ba abinda zan iya fitarwa kai tsaye bane yadda take nufi amma na dan rage yawan sa ma kaina damuwan da nakeyi din. Mako biyu tsakani ranan muna zaune dukkan a falo sai ga ta ta sauko daga sama ta zauna take cewa Fati ta shirya mata kayan su yan biyu zata Abuja gobe tafiya ya kamata. Sai ta juya gareni tana cewa ke ma Safiya ki shirya don dake zan tafi saboda yaran nan ba zasu barni ba inyi abinda ya kaimu da sauri Fati tace anty nima in shirya ina sin zuwa Abuja wallahi. Tace da Safiya zan tafi ko ita don yara zan tafi da ita Sulaiman zai yi bukin bude company a can da gidan da ya saya a take fati ta shiga rokon ta wai taje da ita. Tace karatun ki fa fati kina fa wasa da karatu gashi kun kusa rubuta jerabawan fita ke bakiyi ma kanki fada ne wai kamarki har yanzu a secondry school ? Nan ta turo baki gaba tana fadin na dai gane kin fi son safiya damu a gidan nan komai sai kice safiya ita kadai. Tace dole ne in ce safiya don tafiku hankali da tunanen abinda ya kamata ko ruwa kuna iya ba mutum ne in ba ya kama maku dole ba. Faiza ma ta marairaice mata saida tace duk su shirya mu tafi tare sannan aka samu lafiya don da Fati ta hau sosai ga maganan. Kowa ya shiga shirin tafiya don tace sako zamuyi mu tafi kala uku kawai na dauka koshi dogayen riguna ne kawai na zaba. Tun da safe muka kama hanyan abuja a mota mukai tafiyan don mijin ta baya nan suna ruwa wurin aikin shi basu fitowa sai bayan watanni a ruwan shiyasa ma bai faye zama a gidan ba. Gidan su na abuja muka sauka wanda shi mijin tane wai yake dashi don harda funke mukayi tafiyan bamu bar kowa a gida ba. Gidane mai dauke da dakuna hudu da falo daya na maigidan inda ta zauna a ciki sai dayan wanda fati da Faiza zasu zauna ni da yara tace mu shiga guda sai mu bar ma funke na farin shigowa wanda dama saboda masu aiki akayi shi. Ba wani hira don kowa na da gajiya tare dashi wanka kawai mukayi sai abincin da aka kawo muna daga wani gidan abinci ina jin Faiza da fati na ta santin abincin don dadin shi niko takura bai bari naci sosai ba don na lura dukkan su biyu kamar yanzu sun tsane ni a gidan don yawan nuna mani kulan da maigidan namu takeyi ko a gaban kowa. Na riga kowa shigewa ashe sulaiman din yazo gidan bayan na shiga barci nan Fati ta kama rawan kai saida anty ta tura ta ciki ta basu wuri. Washe gari tun da safe da ta fita bata dawo ba sai wurare karfe hudu ta dawo gidan nan ma bata huta ba don wasu suka zo suna tsarare dasu. Har na kwanta sai ga anty dakin na mu hannuta rike da tasbaha tana ja shiyasa nake son ta don wayen wata da tsabgogin gabanta bai hanata yin ibadan ta sam. Mikewa nayi zaune daga kwanciyan da nake ta kalle ni tace wai ko kin dauko kayan kwarai kuwa Safiya don taro ne na masu hannu da shuni za a yi. Nace anty na dauko wanan riga ne da kika sayo muna ranan na fadi tare da kallon ta don jin may zata fada gamay da shi. Cike da tsukana tace min Safiya ai da kin tona min asiri a cikin taro da sai in nuna ba tare dani kike ba a wurin kawai kisa mutane su raina min da wayo ? Dariya nayi itama abin ya bata dariya don jin nace anty wanan riga mai balain kyau. Tace kin ga ni yanzu ma fita nazo kirakani muyi dama nayi tunanen hakan ki shirya ina fitowa yanzu zamu fita da faiza ba zan je da wanan mai rawan kan tsiya ba ta bani kunya. Ashe harta fada ma Faiza ko koda na fito faiza na falo zaune tana kallo hijjab da dogon riga nasa ta kalleni ta wani kwashe da dariya . Sai kuma tace min mutumiyar na ciki tana fushi wai za a fita damu bada itaba kafin in magana sai ga ta tafito tana saka ma kofa key tare da kiran Funke tana cewa ta kula mata da yara da sukai barci tun da magariba. Na muka fita tare da rufo kofan gidan mukai ma Funke sai mun dawo wata mota baka muka samu waje a kunne yana jiran fitowan mu. Baya muka zauna inda sai wani kamshi da ban taba ji ba ya daki hancina ga sanyi AC mota suka hade suna bada wani irin yanayi a motar, ita ta zauna gaba tare da driver muka kama hanya fita daga gidan kallon titi nakeyi inda naji Faiza tace ina wuni yaya Sulaiman . Sai lokacin na dawo daga tunanena nace dashi ina wuni ya amsa muna a tare lokaci guda anty ke ta hira sai eh ko aa yake ce mata. Tafiya mukayi mai nisa sai gamu bakin wani shago maigirma anan muka firfito inda muka barshi a cikin motar zaune muka fara shiga mu da anty. ZAINAB IDRIS MAKAWA SEENABU 8/14/20, 7:12 PM - Ummi Tandama: BAHAGGON, , , , , , , , , , 🧕🏿3️⃣5️⃣🧕🏿 YAR UWA NOVEL DIN NAN NA KUDI NE IDAN BAKI BIYA BA KADA KI KARANTA DON BA A YAFE MAKI BA HAKKIN KARANTAWA BA BIYA. Tunda nake ban taba zuwa wuri irin wannan ba a rayuwa na sai dai ban nuna ba saboda natsuwan da Allah yai min. Sune a gaba ina binsu baya a hankali anty tace mu diba mu gani sai ban tafiba nabi bayan anty din wasu jakka da ta kalma take dubawa bata san ina bayanta ba. Sai nace kai anty wanan kayan zaiwa su yan biyu kyawo sosai ta juyo da sauri tana cemin har kin duba ne? Jin nai shiru yasa ta juyowa tana fuskanta tana tare da cewa mai kika zaba ne nace ban dauki komai ba kai ta girgiza kawai taci gaba da daukan abinda take so. Tafiya takeyi tana fadin sai ki zabar ma diyan naki kayan a tare mukaje wurin kayan yara na fara duba masu sai kuma na gaza itace tai ta zama musu kalloli masu kyau. Batai min magana ba sai wucewa da tayi layin riguna ina biye da ita can ma zaban taitayi tare da atamfofi. Ni dai har muka gama a shagon banga sulaiman din ba sai nai zaton ya ajemu ya tafi ne to wa zai mai damu gida daren nan haka. Acan wurin biyan kudi muka hade dashi bai sai komai ba sai turare guda biyu ya dauka bazaka ce tare muke dashi ba yadda ya nuna a wurin. Ni dai kafana ya gaji da tsayawa sai na fita daga shago na samu bayan wani mota na jigina jikina dashi. Sun gama suka kwaso kaya niki niki suka fito zuwa motar na tako inda suke na samay su ta dago tana ceman yayi da ake sakayan a both din motan da muka zo dashi. May yasa kika fito daga ciki nace na zata magana zasuyi ai shine na basu wuri tsaki taja kwai tana bude kofan motan muma muka nufu motar muna budewa. Har muka iso gida ba wanda yai magana a tsakanin ni da Faiza sai da motar ta tsaya ne muka fito nan muka fara jidan kayan zuwa ciki dasu sai a lokacin naga ashe ba karamin sayaya mukayi ba . Dakin anty muka nufa dan kai kayan can amma sai tace mu zube su a falo na ta zauna tare da jawo wani laida sai naga ashe nama ne gadade suka saya a wurin . Tana fitar da kayan tana cin nama hankali kwance ta miko min wani laida shake da kaya tana cewa ungo naki matsoraciya kawai ta kuma mika min wani karamin laida da kayan sanyi da naman ciki faiza kuma ta dauki nata zuwa dakin su kowa ya shige muka kashe wuta muka watse wurin. Da safe kowan mu ya makara don haka bamu fito da wuri ba ni dai ina kwance bayan nayi sallah sai na koma barci. Banyi nisa da barcin ba sai ga anty ta shigo daki da hijjab din ta tayar dani tayi na mike zaune tare da gaisheta da kwana takalleni tace safiya kinyi sallah kuwa ? A girmamay nace nayi sallah anty tun dazun sai tace madalla tashi mu fita gidan nan tun yan bakin nan basu tashi ba mu fita daga gidan nan maza ki tayar min da wa yan nan sarakunan barcin yanzu mu tafi. Har muka gama muka fice daga gidan basu sani ba wurin gyaran gashi suka tafi don har dani anyi mawa ina ban so amma sai da anty tasa akaimin gyaran na koma kamar bani ba. Ni kaina nasan gyaran ya fitar min da kyaun surar fuskana don ban taba gyara irin haka ba bamu dawo gida ba sai shabiyu da rabi muka shigo gidan. Mun samu sun cika fam sai dai ba mai iya yin magana a cikin su dole kuma suke gyashe mu da dawowa . Nan muka zube a falo tare da muna neman abinci ina yawan mamakin yadda sam anty bata kyaman mu,amula dani kamar yadda gidan mu suke gwada min. Sai da muka gama ne sai Faiza ta kula da gyaran gashin da akai mun din tace wai dama anty wurin gyaran kai kuka tafi ba tare da muba. Tace fuska gimtse eh idan kun shirya driver yana waje sai ya kai ku kuma bata da daman da zatai mata wani korafi ba. Sai harare harare suke aikamin a fakaice bandai kula suba anty ta shige dakin ta sai lokacin Faiza ta samu yi min magana akan fitan mu nace nine nace zan bita da zata fita tace idan kun tashi zaku tafi. Fitowan anty ne ya hana maganan yayi nisa sosai ta fito tana cewa da au baku tashi kun shirya bane ke kuma Safiya tashi zakiyi ki sallah sai mu fara hada kayan gift din nan tun ba ai yawa ba ki kira funke ta taimaka maki hadawa. Su idan sun dawo sai su karasa a inda kuka tsaya din don takwas za a fara program din ban son a samu matsala a wurin mu ko kadan. Mikewa nayi din zuwa sallah nake cewa da su idan sun wuce sai sun dawo ni zan shiga in sallah faiza ne kawai ta amsa min ciki ciki na shige abina. Sallah nayi na fito anty bata falo don haka na bita dakin ta a inda na samay ta zaune a kasa inda ta idar da sallah tace yauwa Safiya kin ga dauko wancan buhun ki miko min. Koma da yake ai shi uban gayyan yace ba zai gayyaci mutane dayawa ba a gurin sai nine ma na gayyato mai abokaina da mazan su sai abokan mai gidan da suke garin nan. Nace haka nake ganin sa kamar baida rigima ai tace haka yake sai kuma wanan kaddara da samay shi ya kara sawa yana gudun mutane yanzu. Kamar ince wani kaddarane anty sai naga ni may ya shafe ni kuma da zan je wani tambayan abinda bai shafe ni ba can. Na miko mata inda na aje a gabanta sai tace ai ma mu tafi falo kwaso su duka ki fito min dasu tamike tana cewa ko dai in tai maka maki ne da kwasa. Ida da sauri nace haba anty barshi kawai zan iya ai basu da wani yawa ta fice inda na fara kin kimo wa zuwa falon inda har ta zauna ko kasa saman center carpet. Na dauko sauran na samu sufi na farkon nauyi haka dai na ta kwasowa zuwa falon har na gama. Ba bata lokaci muka fara hadawa dani da funke tana directing din mu ina mamaki a raina wai bukin bude gida da company akewa wanan gift din kamar na wani buki can da ya shahara nace kai masu kudi na shagalin su. Anty ne ke fadin ko basu yi ba a kara ne safiya naga abin bai wani cika ido ba sosai nace wai anty duk wanan za a ace bai cika ido ba tace kin ko san wa yanda muka gaiyata a wurin ne. Jakka ne dan na tafiya sai towel da sabule da turare da man shafi da su drinks da snack muke zubawa ako wani bag. Tsab muka shirya komai yadda ya dace sai tace funke tai ta kwasa zuwa mota inda driver da ya kai su faiza yadawo yana waje sai da aka gama kwasa ta ce in fito mu tafi inda za a kai. Na gaji amma babu halin in nuna mata gajiya na don ban so ta fahinci hakan daga gare ni a tare muka fito inda yaran har sun fice waje ko. Nan mu ka kama hanya sai wani unguwa mai nisa tsarin unguwar yafi na su anty haduwa sosai don ginane sai kace a kasan turai mutum yake ga ba yawan hayani ya a wurin ko wani gida a rufe yake. Wani tsararen gida muka shiga da motan mu tace bude ido da kyau kiga gidan da sulaiman ya kera dan dawowan nan nasu kai kudi suna aiki wallahi. Nai mamakin jin kalaman anty tace wallahi sulaiman mutum ne dake tsaya ga neman na kasa yaro ne wanda tun farko bai tsaya jiran sai ambashi ba haka ya taso da neman na kansa. Gashi maraya ne bai tashi da mahaifin shi ba don tun yana matakin karatun shi na farko mahaifin shi ya rasu sanadiyan hatsarin mota. Dan dukiyan da aka raba masu ne a wanan lokacin ya fara juyawa shine Allah yasa masa albarka har yakai haka yanzu sai dai ya taba aure duka duka watan su shida suka rabu da matar. Motan mu ne ya tsaya a ciki gidan koma suna tsaye a waje da wasu abokan shi shi ya dakatar da labarin shi da take bani a motan . Shi da kansa ne yazo ya bude mata motar muka firfito nan abokan shi suka shiga gaida ita wanda da gani sun san ta dama. Ciki muka shiga nikan ba boyo dama bakauya nake nan ko nai ta zuba kauyan ci wurin kalle kallen gidan. Nayi mamaki wai wanan dai sulaiman din ne mai wanan gidan haka dana gani mun shiga mun fita ko ina sai faman yaba mai anty keyi. Niko duk na takura a wurin don ban saba hurda da maza irin hakaba don yawan kalon da suke min din yayi wa a gani na. Nuna mata nayi na gaji sai tace inje in zauna a mamakeken falon in jira su a nan tare da twins din ta muka zauna a falon nan na ci gaba da ba ido abinci don in samu na karaswa. Wayana ne yai tsuwa na dako da sauri inda naga ummi na ce ke kirana a lokacin nace Allah sarki ummi taji shiru yau shine ta kira ni don kaida ne a rana sai na kirasu kusan sau biyu ko uku inji lafiyan su. Nan nake fada mata bamu lagos mun zo Abuja ne da anty wurin bukin bude company kanin mijin ta da za a yi yau tace shi gidan harda wani buki ake mai kuma ? Dariya ummi ta bani ban san lokacin da na bude baki ina kwasan dariya ba a daidai nan suka fito daga daki shine agaba sauran na bin shi a baya. Nan nai saurin gimtsewa kamar bani bace mai yin dariyan a farko muna ta magana da ummi inda suka zauna sai na kasa sakewa a wurin. Karshe dai don in fitar da zargi sai nace wa anty ga ummina su gaisa da ita ta karbi wayan tana murmushi nan suka gaisa ina jin anty nace mata gata nan ina ta bata wahala bamu zauna ba yau tun safe ai Safiya tana da kokari wallahi naji dadin zama da ita sosai ummi. Sun gama gaisawa ta bani wayan nai mata sallama tare da kashe wayan nawa nan na zauna a takure a cikin su inda anty ta umurce ni da in bude jaka guda suga yadda muka hada kayan ciki. Mikewa nayi ina gyara gulyalena dake zamewa akaina na dauko jakka guda tare da bude masu sai naji sulaiman din yace kai basuyi kadan ba. Ban san lokacin da na dago na dan kalle shi ba sai naji anty din tace gata nan ai nace a kara don nasan halinka tace wai ya isa hakana. Yace No if possible don Allah a kara mana why not na mata a saka zanuwa a cikin sa na maza ku saka masu shadda a ciki kai hamza kaje ka dauko su a cikin dakin nan a zuba. Daga haka suka fice aka barmu nan muka ci gaba da aikin kara kayan bamu dawo ba sai shida na yamma don mu shirya. Mun dawo mun samu su Fati na gida itakan anty dakin ta shige tana cewa mu shirya bakwai zamu bar gidan. A kusan tare suke tambaya na ina muka tafi haka nace mun je inda za ai event din ne don hada wurin sai ita Fati tai tsaki tace to mu wai may ya kawo mune tunda ba a yi damu. Faiza ne tace a a zaki iya wanan jigilan da Safiya keyi haka ba gajiya tace wane ni kuwa sai fatin tace wai mun ga sulaiman a wurin nace a a bamu ganshi ba ai. Tace ai gara ma da ban tafi ba don ni shi kadai nake son gani dama ban damu da wasu can ba. Sai faizan ta harare ta tace hum,umm ashe kina da aiki indai wanan miskilin ne mai yi kamar yana jin warin mata tace wasu matan ba. Ni dai ban zauna ba shiga nayi sai na samu kaina da dan kwantawa don a gajiye nake so sai yaran ne da suka shigo na tashi dole na fara shirya su. Ina cikin shirya sune anty ta leko tace da ni aa kunanan da mutanen naki kuna ta fama yauwa safiya sannu da kokari kiyi ki gama sai kema ki shirya. Tace karbi nan nasan ki da sin dogon riga shiyasa na sayo maki ban baki bane don wa yan nan yan sa idon kada su damay ni da korafin banza. Na amsa hannu bibiyu ina godiya tace kin ga don Allah ni kuyi sauri bamu da lokaci ban so ma in kai yanzu ba a nan bamu tafi ba. Nan tafita ta barni ina duba kyawon rigan data bani rigan yakai riga wurin haduwa sosai na ce a raina wai na ko gode ashe idan na koma gida inna sai bakin ciki ya kashe ta. Tsab muka fito bani ba ba yaran ba ban bari anty ta jiramu ba don a gagauce na shirya simple makeup nayi a fuska na duk da hakan ba karamin kyau nayi ba sosai. Duk sun fito nice karshen fito wa a tare da su yan biyu muka fito kowan mu in ka gan mu basai an fada ma cewa ga inda zamu ba a lokacin. Nan ko su Fati aka sako min ido take kowan su ya daure fuskan su, don basu san da rigan da na saba na gani amma nai kamar ban gan su ba. Nan dai babu tsatsayawa muka fice gidan har da funke gaba dayan mu ba a bar kowa a gidan ba mota biyu mukai tafiya dasu inda nida yara da fati muka shiga mota guda sai anty da faiza da funke a dayar motar. Da kamar ba za tai min magana ba sai naji tace wai yaya kika ga shiga na ne Safiya na fito kuwa ? Nace kai ai duk kin fimu haduwa wallahi kin ko ga yadda ki ke wani haskawa wurin nan ashe akwai wanda zai kai ki haduwa a wurin. Taji dadi ta washe baki tace ina yinki safiya wancan yar bakin cikin cewa tayi wai in saka dayan rigan nan don ta san baikai wanan din haduwa don ta fini fitowa. Nace ke kyale ta don Allah ita Faiza bata taba fadawa mutum gaskiya ai tace da sauri ashe kema kin gane ta yanzu ni shiya bani shiga harkanta . Mun isa wurin ba kowa sai anty damu muka karasa duba aikin da akayi bayan wuce wan mu nan muka shige wani daki muka kara gyarawa kafin a fara. Ni dai kwance nake sai su ke ta heleke su da gwale junan su kamar wasu kishiyoyi can nidai murmushi kawai nake ta masu sai anty ne ta shigo dakin take cewa ai an bude wurin yanzu za a fara don Allah tana son kowan mu ya natsu muyi abu a hankali kada mu bada ita. Bamu fito ba sai da taro yai taro muka fito muna mara ma anty baya tare da wasu yan uwan su da suka zo daga bauchi sai yanzu na gansu. Sulaiman din ya fito tare da abokan nan nashi na dazu wanda na fahinci sune dai abokan shi na shakiki na kusa. Mun fito wurin ya dauki tafi don mc na bayani akan Sulaiman din da dalilin haduwan a nan wurin ni dai biye kawai nake dasu kamar ace in sheka in ruga da gudu. Don yawan mutanen dake wurin naga anty ba abinda ya damay ta sai walwala take tana ta gaisawa da mutanen wurinta saka wasu matarial sai walkiya take yi a gurin. Ana ta bayanai akan ki shi din wanene tare da manufar shi na bude company da yayi nan wuri ya dauki tafi rafrafraf . Sulalewa nayi na fice daga dakin taron na fita waje wani iska mai sanyi ya dake ni na shaka sai naji ina son in dan kadaice ni kadai a wuri daya. Wani dakali na hango a gefen don haka na nufi wurin na zauna ina kallon masu shige da ficen wurin. Nace a raina idan mutum na cikin wayan nan har sai ya manta da halin da yake ciki ya shagala da rudin duniya dan dai ma ita anty mace ce mai kula da addinin ta. ZAINAB IDRIS MAKAWA SEENABU 8/14/20, 7:12 PM - Ummi Tandama: BAHAGGON , , , , , , , , 🧕🏿3️⃣6️⃣🧕🏿 YAR UWA NOVEL DIN NAN NA KUDINE IDAN BAKI BIYA BA KADA KI KARANTA HAKKIN WASU PLEASE DON BA A YAFE BA DAKE DAKE TURAWA MUTANA DA SU DAKE KANRATAWA DUK ALLAH ZAI KARBAN MIN HAKKINA A GUN KU, , , , Hankali na ya tafi ga kallon yadda wani miji da mata suka shigo ririke da junan su a wurin har zuwa cikin holl din dadin kallon su yasa ban dago kai inga ko waye a kusa dani ba yana waya. Gama wayan shi yayi daidai da kare kallona don sun zo sun shige har ina ajiyan zuciya naga mai shi ya zauna a saman abinda nake zaune. Sai na dago da sauri ina kallon shi yace dani sun baki shaawane daidai da yake zama sai a lokacin na gane shi, yinayi kamar banji abinda yake fadi ba don yadda yai maganan baiyi shi akan zan iya jiba. Da sauri na matsa mai sai dai ban tashi ba don wurin nada girma ko mutum huda zasu iya zama akai ya sake cewa hayaniya yayi yawa a ciki ko ? Kai kawai na kada mai alaman eh sai yake cewa dani yana kallon wayan dake hannun shi Bana son yawan hayaniya don haka na fito waje na sa driver yazo ya dauke ni yanzu zan tafi . Saurin kallon shi nayi sai naga shi bai ko kallon inda nake gashi dan zaman da yayi kusa danu duk a takure nake a wurin. Yana yi yana kallon agogon hannun shi akai akai nasan lokaci yake diba na zuwan driver shi nace sai naji yace bakiji tsoron zama a nan ke kadai ? Karamar dariya nayi sai wanda ya saurara zai iya jina tare da nuna alaman ina jin nauyin sa wanda hakan ya zamay nin jiki ga kowa indan muna magana. Sai kuma naji ya sauke wani murmushi shi ma yace koda yake bai kamata na katse maki yanayin da kike ciki ba na son ki kadaita kan ki ga mutane, Kin san ku mayya sai a hankali bai kamata na katse maki jin dadin din ki ba wa wanan lokacin yar gajeran murmushi na sauke har yanzu akwai alaman jin kunya a tare dani. Shiru ya biyo baya na runtse idona ina dan fidda ajiyan , gabana yaci gaba da bugawa don gani nake kamar a mafalki na shiga tambayan kaina shin may ya fito dashi waje a wanan lokacin da aka hadu don shi a kumayace zai wuce ya barsu Sauke ajiyan zuciya na yi don ina mamaki hali iri na uncle sulaiman da ga mutum shiru shiru mai kyakyawan halitta da kyakyawan hali. Jin shi da nayi yana jan dan tsiki akai akai kuma yana yi yana kallon agogo har yanzu lokaci zuwa lokaci. Dagani ba sai an tambaya ba don mutum zai fahinci a gajiye yake a lokacin gana haka sai kawai na miko mai goran ruwan faro dage gefena ajiye wanda na fito dashi. Nai mamaki dana ga ya amsa yana min godiya tare da kafa kai bai sauke ba sai da ya zuke ruwan goran duka. Ya wurgga da goran yana kara min godiya dai dai nan abokin shi hamza ya isa wurin yana fadin kai ana can ana neman ka kuyi photo ashe kana nan ka boye. Sai lokacin ya farga dani a wurin nima sai tsarguwa nayi a yadda ya samay mu kamar masu wani hira. Saurin gaida shi nayi don kada ya zargi komai a tsakanin mu sai ya dago yana ma sulaiman din wani kallo mai kama da zargi yaya haka kuma ? Baka da hankali yai mashi alama tare da mikewa yana shirin barin wurin nidai gyara zama na yi ba tare da na kalle su ba sai naji hamza yace a a zaka tafi kabar ta kuma a nan kawai barin koma dama bamu gan ka bane shine na fito in dubaka. Yama rasa abinda zaicewa hamza din sai sauran biyun sun fito suna cewa hamza yaya sai hamza din yace yeh na gangashi ashe yana nan ne. Dukkan su suka karaso ida muke, naji dayan na cewa kai muna can muna neman ka harda madam ashe kai kana nan hamza ne yai masu nuni da hannu cewa su duba sugani. Sai duk suka juyo inda nake zaune wani dariyan shakiyan ci gudan ya dauka yace i see mutafi kawai inda ka gama mutane na jiranka kuyi photo a ciki . Basu tsaya ba suka wuce suna ce mai sai ka shigo kenan girgiza kai yayi tare dadan jan tsuki ya juya yana dubam ida na tare da cewa ba zaki shiga daki ciki ba ? Nace nan di yafi mun dadin zama akwai isaka mai dadi a wurin, shigewa yayi ba tare ya sake juyu ba yabar ni zaune na sauke ajiyan zuciya tare da lumshe idona. Na dan dade zaune a wurin babu abinda nakeyi sai tunanen abubuwan da nake gani sai ga funke an aikota ta kirani ban dauki lokaci ba na koma ciki tare da ita take ce min mu fara ba mutane abin gift din kamar yadda aka tsara fon uban gaiyyan kan shi yace ya gaji sai da aka nemo muna shi waje , Wai da wata yarinya tana fadi batare da ta kalle ni ba take naji gabana ya yanke ya fadi ya kuma ci gaba da bugu uku uku don kada anty ta gane nice muke waje ince mata may . A tare muka je dakin da kayan suke sai da muka shiga ta fara bayani san nan na sauke ajiyan zuciya tana mun bayani gabana yaci gaba da fadu. Munyi yadda ya dace haka mutane sukai ta watsewa don komawa gidajen su don dare yayi sai mu yan gida kawai aka bari nan wata doguwar mota ta kwaso mu zuwa gida gaba dayan mu a gidan anty aka sauka. Sai mazan ne suka sauka gidan sulaima din haka wuri yayi kada dole nida yara muka koma dakin anty sukuma bakin suka sauka a dakin mu. Ni dai bayan na tube har nayi barcin na falka anty tana gun bakin suna hira ko tashi nawa yan biyu ce ta falka da ni wai zata yi fitsari. Na dawo kaita sai ga anty ta shigo dakin take cewa bumuyi barci bane idona da sauran barci nake cewa yan husna zatai fisari natashi. Tace kin ganni sai yanzu muna can muna fira yaushe rabo a kasa na kwanta su suka hau gado sai da ta fito han daki ta ganni kasa take cewa haba dai Safiya ku kwanta mana saman gadon da yara nace kasa ma yai min don na sa bargo. Tace kedai kin huta wallahi shiya sa nake ma Sulaiman gwadayin ya aure ki ai don rayuwan ki ke simple ne kamar nashi. Ai yanzu dole in matsa mashi don an fara kawo mai mata wai ya aura ko da kuwa bai so haka za saka shi a gaba sai ya yarda. Jin abinda ta fada yasani kallon ta da mamaki tace kina ganin wautana ko kan abinda nake kokarin hadawa da hankalina Safiya. Sulaima mutum ne da ko wacce ke mafalkin auren shi kyakyawa mai kyauwon siffa da hali na gari ga wadatan zuci da Allah ya bashi dana Aljihu mai tattare da illimi addini da na zamani uwa uba dan karen tsoron Allah kamar yana ganin sa. Abin da na fadi shu ya dakatar da ita da yabon da take fadi nasa don cewa nayi anty ni ina ni ina Sulaiman gashi dan masu arziki niko yar tallakawa. Dama dai Fati dake mutuwan son shi kikai kokarin hadawa dashi don ita yar uwar kine gashi tana mutuwan sin shi sosai , , , , Ke dan Allah rabani da abin haushi koda sulaiman zai iya auren ta ba zan yarda in hada shi da fati ba don bata da tarbiyan da ya dace da mutum kamar sulaiman a tare da ita. Balle aure ita dashi ya haramta gare su don dai sulaiman shima victim ne irin ki matsalan ku daya dashi. Da sauri na dago kai na kalleta nace nace a razane HIV anty ? Tace wallahi Safiya tana hawa gado take cewa matsalan ku daya dashi shima wata ya aura maishi suka munafunce shi basu fada mai ba sai bayan aure ya baiyyana mata koda akaje aka duba akaga shike gare ta har yai nisa da aka auna shi aka samu shima ya samu daga gare ta. Wallahi safiya daya kiramu yana kuka kamar karamin yaro yake fada muna ranan mun shiga tashin hankali ba karami ba a gidan nan . Allah yasa daddy yana nan shi ya shiga jirgi yaje can South African ya samay su inda ya samu ya shawo kan shi sai dai kafin yaje har ya saketa ko. Daga baya daddy yayi yayi dashi ya maida ita amma yace ya gama auren ta karshe ma yace shi ba zai kara aure ba a rayunwan shi. Daga baya muke jin wai ta gaji da bin shi ta auri wanda yasa mata cutan yanzu shine kika ga sam baya son ai mashi maganan aure kuma ya koma gudun mata. Dama can ba damuwa yayi da matan ba sai abin yazo mashi da sauki dalili kenan kika ga ina son in hada ku don ko banza halin ku zai zo daya dashi. Yanzu haka yan uwa basu san halin da yake ciki ba don ba afitar da zancen waje wani yaji ba. Shine ita mahaukaciyar kika ga tana wanan haukan haka shi yasa ma kika ga bai son zuwa kasan nan don matsin da iyayyen shi ke mai akan ya kara aure. Kafin taga bani labarin fuskana har yacika da hawaye fam taji ina kuka tace ke ko saurin karaya gare ki ai hakkuri za a yi haka wani rayuwa yakan zo wa ba ya zama BAHAGGON RAYUWA . Amma in ai yi hakkuri aka rungumi kaddara sai Allah ya duba ma mutum Allah mai tausayin bayin sa ne akoda yaushe yana ma mutum mafita ta hanyar da bai zata ba. Nasan labarin nan da kika ji ya sa kin tuna da naki matsalan ya dawo maki da shi sabo sai hakkuri abin ba dadi gaskiya. Ta haye gado ta kanta tare da kashe wutan dakin ya koma duhu ta barni cike da tausayin kan mu da ma sairan uan uwa musulmai da suka tsinci kansu a wanan halin irin namu. Tabbas Sulaiman idan ya zama mijina zan yi kokari inga na bashi kwanciyan hankalin da ya dace dashi naji zuciya na ya sami karbuwa dashi dari bisa dari bawai don kudin shi ba don ni basu gaba na yanzu don ina ganin kwana nawa ma yarage min a duniyan. Saboda na sha zama inyi ta nacin rokon Allah da yai min mafita ga matsala ta in samu miji wanda zan masa biyayya kuma yasan ina yi. In har abin ya tabbata zan fi ko wata mace sa a a rayuwana amma kuma ban taba tunanen samun haka ba. Sai gashi kwatsam Allah na baiyyana min ansan addua na yana batun bani uncle Sulaiman a matsayin miji a gare ni. Nasan anty da naci kan abinda take so wanan abinda take shirin hada min da wani irin godiya zan saka mata dashi don tsabar girman shi da daraja a a gare ni. Sai dai kuma kash nace a raina anys kuwa shi uncle sulaiman din zai soni kuwa ga yadda yake baya kallon ko wata mace. Kuma ma yasan cewa na taba aure har da haihuwa indan bai taba sani ba anya zai so bazawara kamata kuma yar talakalis. Wanan sune tambayoyin dana rika yiwa kaina kawai sai jin hawaye masu dumi nayi sun soma bin kuncina a karo na farko da na furta Allah ya isa ga Ahmed kenan. Don shi ya jefa rayuwa na a wanan hali dan ma taimakon Allah ya kawo min sanadin sanin anty a rayuwa na har take kokarin mantar dani halin da nake ciki yanzu. Na sake fadi Allah ya isa aure na da Ahmed cikin sanyin jiki na gyara kwanciya na ina ci gaba da tuna ne wanda ban san iya wanda nayi ba a lokacin. Washe gari mun tashi da baki a gidan don haka tunda nai sallah muka fada kitchen dani da funke don hada masu abin karyawa. Koda anty ta tashi har mun gyara gida mun gama hada breakfast din na shiga wanka ina jin tana fadin yau na shiga uku wani irin barci ne nayi haka mai nauyi. Na fito ina mata ina kwana tace safiya ai yau kan ban san irinbarcin da nayi ba ga baki gida ban shirya masu abin karyawa ba har wanan lokaci. Nace anty fita falo kiga abinda muka shirya masu ko yayi na dai hada ban san ko zaki soshi na tace kai Safiya ubangiji Allah yai maki albarka yasa mu raka da junan mu. Har kin hada abinci ina daki kwance ban sani ba shiyasa nake son kada ki kubcewa Sulaiman don shi kadai ya dace dake. Shima kene kika dace dashi sai ku taru ku rufawa junan ku asiri a zauna lafiya. Murmushi nayi nace kai anty dai kina dai son musa kafan wando guda da fati a gidan nan don ta mutu akan so uncle din sosai wallahi. Wai ba zaki rabani da wata Fati can ba ana maganan mutanen kwarai kina kawo min fati ciki wanan kazama may ta iya banda rashin kunya ita kuma Faiza ragguwa ce ta karshe bata iya aiwata komai banda kallo da kwanciya ai dai za a yita ta kare ga yan uwan haihuwan shi ai sunzo Sai da mukai wanka muka fito falon a lokacin har bakin suma sun fito ko take cewa kun gani sai yanzu na tashi ba sukace suma basu dade da tashi daga barci ba ai. Dayan tace gashi har an hada abin karyawa ko tace aikin sarakuwan ku ne wallahi sai duk suka kalleta matar take cewa sarakuwan mu ta ina tace Sulaiman mana. Nan suka shi murna da sa albarka ga abin nidai kunya duk ya rufe ni dago kan da zanyi sai ga fuskan fati tana tsaye kamar ruwa yaci ta. Uncle ne sukai sallama da sauran mazan da suka kwana gidansa suka shigo da murnan su sai ya samu suna zuba abinci yace a a madam baku gaji ba har kun iya tashi kunyi wanan aiki haka. Bata kai ga bashi amsa ba sai wata tace kaidai ai kayi dace wallahi ga yarinya da kirki ga kunya Allah dai yasa ayi damu. Kallon mamaki yake aikwa anty sai tace Safiya na fada masu nufinka akan ta shine suke ta murna da abin. Ajiyan zuciya yayi ya gyada kai yana cewa kai madam baki da dama wallahi sai matar tace wallahi mukan munyi murna don wallahi zaben yayu kun dace kwarai . Gashi muna barci an hada muna abin karyawa irin haka may ake nema gun mace dama tasan darajan yan uwaka an kuma samu tunda anty ta yaba da hankali ta may za a jira banda musha buki. Ni dai duk na kasa sukuni a wurin don haka na mike da sauri na shige daki cikin kunya duk suka bini da dariya banda shi da yake jin wani iri a zuciyar shi. Don may anty take son ta yaudari yar mutane gata karama zata cuta ma rayuwan ta bayan tasan halin da yake ciki. Idan wani ma bai sani ba yasa take fadin haka ai shi da ita sun san matsalar shi ta rasa wanda zata cuta sai wanan yarinyar dake kokari da ita haka a gidan. Shi har naka bashi tausayi idan yazo bai taba samun Faiza ko fati na kau da kara a gidan ba komai ni zai samu ina yi ko yara ke son abu sai dai yaji sunce anty Safiya. Har suka gama karya da yan uwa yana cikin wanan tunanen yace su tashi yakai su su zaga gari don washe gari zasu koma gida don haka yake son ya fita dasu. Har sun fita ya juyo yace madam idan na gama dasu kila zan dawo don akwai maganan da nake son yi dake idan mun samu time. ZAINAB IDRIS MAKAWA SEENABU 8/14/20, 7:12 PM - Ummi Tandama: BAHAGGON , , , , , 🧕🏿3️⃣7️⃣🧕🏿 INA ROKON ALLAH DA YA SADA MU DA RAHAMOMIN DAKE CIKIN WANAN WATA MAI ALBARKA YAN UWA, YASA MUNA CIKIN YANTATTUN BAYIN SHI, , , Bayan komawa yan bauchine gida sai muka fara shirin tafi muma don sam ba mu san zamuyi wanan kwanakin haka ba a abujan. Har lokacin Fati bata sake min fuska ba cikin ma bataji kan maganan sosai ba don dukkan su basu kusa dan haka basu ji maganan da akayi da kyau ba rana. Mun fara shirin komawa lagos sai dai har lokacin bamuga Sulaiman din a cewan anty tafiya ya kama shi ya tafi gida. Shiri sosai mukeyi dole a mota mukai tafiyan don kayan da muka loda na amfanin gida a Abujan dama wasu tarkace can. Mun dawo da kwana biyu mun warwale gajiya a jikin mu yau anty ta fita aiki Fati tafita zuwa makaranta sai Ni da Faiza kawai a gida. Na gaji da kwaciya dan haka na fito falo muyi hira da Funke sai na samu Faiza ta rigani fitowa tana gani na take cewa kema kin fito shiru yai yawa a gidan. Nan na zauna muna hira har funke din sai dai matasalan Faiza shine son ayi da wani a bayan shi wanda ni kuma ban lamunci haka ba sam. Take fadi wai dama tana son mu samu lokaci ne ta fada min Fati fa ta fara zargina akan ina shishiwa don in fi kowa gun anty dama haka muke da bin bokaye ai duk inda bakauye yake ya san inda bokan kwarai yake ko malam. Murmushi nayi nace aiko ba boka da malam idan ka gyara alakarka da mutane sai a soka ita tasan wanan don haka take zargin kowa da wanan halin. Duk hiran da ta dauko sai in kawar dashi don mafi munin sabo shine giba amma ita shine sana,anta yi da wani idan baya kusa. Munyi gyaran gidan nida Funke kamar ba tafiya muka yi ba munn maida gidan tsab gwanin ban shaawa na koma daki na kwanta ban falka ba sai da maigidan ta dawo ta turo yaran su kirani. Ckin barci naji suna tadani wai mummy su na kira na, mika kawai nayii na sauko muka fice dakin zuwa falo tana tsaye a tsakar falon da waya a hannun ta. Wuri na samu naja na tsaya ina jiran ta gama sai na zo na fahinci sa mijinta take waya sai da ta gama ne ta kashe wayan ta maida hankali gare ni.. Anty sannu da dawo wa nai mata ta amsa tare daga mun hannu tace yawa safiya zozozo nan kin ji tana mika hannu wai in zo kusa da ita haka take yi idan abu ya dan ruda ta ko ya bata mata rai. Banyi nawa wurin karasawa inda take ba ta riko hannu bibiyu tana cewa Safiya kiji min daddy da rigima wai bai fada min zai fito ruwa ba mu shirya mai sai yazu da suka fito wai yake sanar dani sun fito. Jimun daddy da neman rigima fa safiya ni kaina ma ya kulle ban san may nake ciki ba wallahi yanzu in an gama masu clearing za a kawo shi gida. Nace anty ba daddy yafi son tuwo ba tace shi ne ai safiya nace akwai komai hade tuwon kawai zan tuka bani minti ashirin yanzu sai inyi warming din biya don dama jiya na hada su. Tace kai Safiya sai ta rungumoni zuwa jikin ta tana cewa yarinyar nan basan godiyan da zan maki ba amma dai bari komai nake dabban zan fitar maki in daddy ya dawo. Haka take dason abin ban dariya sai dai kuma indan ta tashi daure fuska ba mai gane kanta kuma sai taga daman saukowa dan kanta da kanta. Kafin daddy ya iso gida mun hada mai table lafiyayyen abincin irin wanda yake so namu na gargaji na shirya mai tuwon semo sai miyar kubewa danya sai stwee din cow tail dashi zai hada ya ci simple. Sai abin sha suma na jera su yadda ya kamata da kunun samiya da yake son sha sai kamshi kayan yaji yake yi. Wanka na shige ina ciki naji jiniyan su ta aiki ta shigo gidan haka yasani sanin ya dawo take gida ya rude da murna don shima daddy kamar matar shi yake bai da matsala ko kadan da kowa a gidan. Matsala daya ne ba a ganin shi sosai kullon yana ruwa kasancewa shi na sojan ruwa indan ma yana tudu aikin gaban shi ya shamai kai. Ban fito ba sai da na shirya mai kawai na shafa na zura rigana na fito tari yan shi na samu kowa a falo security din shi na ta shige da fice nace aifa bissimillahi a raina yanzu zamu fara ganin kattan sojoji a gidan ba da dare ba rana. Can na hango shi yana ta yanka loman tuwo yana kaiwa baki na karasa da sauri ina fadin daddy sannu da zuwa ya dago yana kokarin hade loman tuwon da ya cusa a baki yace. Yace yanzu nake tambayan ki naga kowa ban ganki ba na dauka kin koma gida ne sai anty dake gefen shi tace ai yau da ta wuce da bakaci wanan tuwon ba aiki ta tsaya yi sai ta shiga wanka kafin ka iso. Nan dai na gaida shi nai mashi sannu da zuwa da yaya aiki da hanya ya amsa a takaice yana mai ci gaba da cin tuwon dake gaban shi alama ya nuna yana jun dadin kasancewan shi a gida. Tunda suka shige bai kara fitowa ba daga shi har matar nasa su yan biyun su suna tare dani ranan a wurina suka kwana basu koma dakin su ba. Duk da daddy ya dawo bai hana anty fita aiki ba da safe sai da daddy ya tashi yai breakfast shi kadai nace a raina mijin ma,aikaciya kenan. Bai fita ko ina ba muke ta fama da dauwainiyar shi a gida har zuwa lokacin da ta dawo don bata dade a wurin aikin ba ranan. Da yamma aka fitar da tsaraban da yazo dashi wanda tufafi ne sai kayan ciye ciye irin na kasa shen ketara yazo dasu wannan kan an zube su ne kowa ya ci ya sha iya shan shi da ci. Daki na koma ina kallon tsaraban ina mamaki dan zuwa na gidan su na karu da abubuwa da dama na rayuwa. Na tuna da iyayyena da yan uwana dake zaman ukuba saboda talauci kullun ana ganin laifin juna a tsakanin zama tausayin halin da gidan mu ke ciki ya kamani. Na wani fitina nan har da talauci ke kawo shi ma in kowa na dashi ai ba mai kallon halin da dan uwa ke ciki kowa tashi ta isheshi ma. Daddy ne ya tsure anty a daki yana tambayan ta game da hadin daya samu labari tana batun hadawa a tsakani na da sulaiman. Kin fi kowa sanin halin da yaron nan yake ciki amma shine zaki dauki yar mutane ki hadata dashi don kwadayi komai yaushe kika fara wanan halin na marasa imani ban sani ba. Idan yarinyar ta gane an cuce ta kina ganin ba zatayi kuka dake ba kai har ma da mu duk abin zai iya shafa nan gaba. Haba dai daddy may zai sa da hankalina nayi irin haka ga yar mutane may tai min yarinyar nan ai in babu godiya to kuma babu fallasa. Ta sauke ajiyan zuciya tana cewa dashi matsalar su daya da sulaiman domin ita ma Safiya postive ce da sauri yace may ne ? Tace wallahi kamar yadda shima ya samu ta sanidan aure haka itama ta samu gun mijin da aka aura mata dan uwanta nan dai ta shiga bashi labarina yana fadin subbahanallah. Yanzu wanan yarinyar mai hankali haka aka dauka akabawa mashayi ya cutawa rayuwanta subbahanallahi wallahi dai ana cuta a duniyan nan. Yana kada kai yana fadin wallahi ta ban tausayi gaske nake ganin ta shiru shiru ashe da abinda ke damunta a rayuwan ta. Ya kara nisa yace yanzu na fahunce ki idan kinyi hankan kin taimaka masu sosai don sulaiman idan a biye masa baiki ya zauna a haka ba ba aure. Tace ai shi na gani don haka kamar yadda kowa bai san da halin da suke ciki ba sai muyi rufa rufa a daura kawai ta tare an wuce wurin Allah kadai yasan gawan fari tsakanin mu da su. Nan dai suka kara tatauna yadda zasu fitowa zance don kada a samu matsala a wani bangaren a taru a rufawa juna asiri. Mako shi kusan uku tun a abuja daya bar mu ya tafi bai zo gidan ba wai ashe tafiya ta kamashi ya ketara waje sai yanzu ya samu kan shi ya dawo nigeria din. Ranan jumma daidai an sauko daga sallah sai gashi gidan ya shigo babu kowa a falon gidan sai nauran kallo da yake aiki shi kadai a falon. Goran ruwa yaje da kansa ya dauko a fridge ya dawo ya zauna yana sha sai ga funke ta fito ta ganshi a zaune da sauri ta gaida shi don tana son zuwan shi don dan abinda yake bayarwa a bamu bayan tafiyan shi. Ta juya bayan ta gaida shi zuwa kiran Anty a sama dakin ta sai gata da saurin ta tana fadin oyoyo da karamin mai gida. Yace ai nayi fushi tun yaushe nake nan zaune sai ni da kaina na dauko ruwan da zansha gaskiya gidan nan yana bukatan kari don gidan yai maki girma ke kadai dole yaya ya kara wata. Tai wani dafe kirji tana cewa waini dakaina kawa Allah ka huce ina ni ina amarya yanzu a gidan nan. Nan fa nabar su Faiza ashe duk sun shige subar falin ba kowa a wurin wane ni in kyale ka haka koda yake zuwa bazata kai ma kai muna ai yaudin. Yace kuma hakane fa to na dai huce tunda anfini gaskiya ya nisa yana gyara zama dakyau yace wallahi nima dai haka tafiyan ya kama ni gashi tun a abuja bamu hadu ba sai naga ban kyauta ba ko ban gajiya ban samu yi maki ba . Tace kai haba dai ai nasan yadda harkan naku yake bawani lokacin kanku kuke dashi ba sosai mu dai tunda kana lafiya ai shike nan. Ya sake mika hannu yana daukan ruwa gami da bude roban ruwan yace wallahi lafiya nake sai dai abinda ba a rasa ba dai. Tace bari a kawo maka abinci shima captain tunda suka tafi masallaci bai dawo ba shida twins yace ashe suna can yau ya dauki rigima . Tace wallahi rankai dade abincin fa your fovourite akayi yau fa a gidan don nasan kaima kaman dan uwanka ne kana son cin tuwo shi Safiya ta girka mashi. Dam gaba shi yai mugun bugawa jin ta ambaci suna na take yawan mafalkin da yake akaina ya fado mashi a rai don bai ko son ya ganni don bai son zuciyar shi yana fada mashi karya a kaina. Ban san da shi ba a wurin don anty ta kirani na fito da dan kwalina a hannu ina kokarin daurawa akaina sai ganin su nayi tare zaune suna kwasan dariya. Gaba yai mugun faduwa dan ban san da zuwan shiba gidan kuma ban tsamani anty ta sani ba don baji tana magana ba. Ban yar da mun hada ido ba sai gasheshi nayi da cewa sannu da zuwa uncle, ya amsa da yauwa mun samay ku lafiya. Tuni har anty ta lura da yadda na daburce ko sai tace safiya ga bako mun samu yau girkin ki ko saura bai ragewa don maciya biyu sun hade a gidan jeki zubo mai abincin kafin daddy ya dawo. Sai yace ai da a bari ya dawo muci tare don tunda ya fita da su yan biyu bai nisa da gida yanzu tunda an sauko tun dazun. Na kalli anty tace barshi kin ji bai jin yunwane sai dan uwanshi ya dawo kin san haka suke kamar tasbaha wajen zumunci. Ya kalleta yai murmushi yace in dai an matsa muna sai mu kawo wa mutum kishi ya yanzu don na gane tako yanzu baki son zancen kishiyan nan. Dariya suka kwashe dashi tace mu ai yanzu ba batun mu akeyi ba kai dai ne gwaro zamuwa aure don zaman nan naka haka yana bata min rai wallahi. Ya kwar da maganan da cewa kin ga ke ne mai sin cin naman Turkey yana mota na sayo maki ki tura a kwaso maki da sauran tsaraban ki har na fara tafiya zuwa dakina don jin topic din da suka dauko. Sai naji tana cewa kai safiya don Allah dawo kin ji ki dauko min a saka a fridge tun bai lalace ba kace gobe akwai harka a gidan nan ke nan komai bazan ci ba sai shi gobe in Allah ya kaimu . Juyowa nayi na dawo inda suke na dan tsaya dan nisa kadan dasu tace taya ni murna maigidana ya sayo muna naman Turkey wai yana a motan shi waje. Dan murmushi nayi kadan yasa hannu a aljihu yana ciro key din motar shi yace anya kuwa zata iya kwaso kayan ita daya ? Tace ai shine kuma fa kodai ba ka son ta wahala ne tun yanzu yace kai madam baki da dama wallahi aidai yanzu nasan takonki in kin yi wasa sai kiji ayyururi a gidan. Tace gaba dai ba nan ba ai anyi tun 1900 dariya yayi yana miko min key din tace nifa da gaske nakeyi wallahi ba wasa ga magana na tace kira funke ta taya ki kwaso kayan don waya nan mashiriritan nan san sun kwanta ne. Funke na kira muka fita tare a daidai lokacin da motan daddy yake shigowa ge din gidan tun mota bai tsaya ba su yan biyu suke kwala min kira. Sun fito suka nufo mu suna cewa daddy ya kaisu shopping da zasu dawo mosque nace kaga yan gata daddy kenan daddy ya fito muna mashi sanu da zuwa ya amsa tare da cewa motar waye anan ? Funke ne da sauri tace uncle ne yazo aisai yaran suka kwasa da gudu ciki suna fadin uncle oyoyyo nan suka barmu muna dariya shima daddy ya bisu ba tare da ya kara fadin komai ba. Nace a raina ko yaro yasan mai kyautata mashi ke nan muka bude buth din da kyar don dagani har ita ba wanda ya iya saida security din kofan ya taimaka muna budewa. Mun shigo da kayan da kyat muka koma kwasowa mun samay su na ta murnan ganin juna shi da daddy sun zauna kamar abokai sun rungumay junan su. Mun gama kwasowa muka zube su nan a inda suke zaune anty sai cewa take a a a Sulaiman duk may ka kwaso muna haka ? Yace well yanzu dai ai ki buda ki gani don ni yarana na yowa sayayya bake ba tace aina sanj indai sin kaine akwai ku dashi ba a magana. Nace daddy a kawo abinci ne yanzu ? Na fada tare da dan kallon shi yace haka ya kamata yar albarka ke kan ai mijin ki ya huta wallahi. Jeki ki bamu yunwa nake ji sosai ganin wanan ya hana in nema tun da na shigo haka dai kuke so mutum kada ya huta ko yaushe sai aiki. Mikewa sukayu zuwa table din suna kara tattaunawa akan kasuwan cin Sulaiman din wanda ya fara yanzu a logos da Abuja wanda yake kuma son karawa a wasu jahohin kasan nan. Cewan da nayi wanan ya isa daddy ko a kara ne nace da daddy din sai suka maida kallon su ga abincin dana zuba masu daidai anty na kawowa wurin. Dakyau safiya inji anty ai gwauna da kika tula masu abinci yau muga iyakar son cin tuwon su suma dariya suka sake a lokaci daya. Daddy ne yace Safiya sannu da aiki kinji Allah dai ya saka maki da alheri anty tace ya nuna muna auren ta da oga koda yake ma na fasa bada kawar tawa ai don sai mu ja maka rai muma. Daddy ya jawo plate din shi gaban shi yana cewa a a haka kuma zaki muna kinyi niyar yin abin arziki kuma zaki zuga yarinya Safiya karki dauki maganan ta ina bayan ki kinji . Fuska na daure ba annuri na azuba masu ruwa na juya na wuce lokacin ya jawo plate ya fara cin abincin kamar bai son ci zuciyar shi ba dadi a lokacin. Sai mamakin su yake yi kawai sunyi nisa da cin abincin shiru yai yawa daddy ne ya kawar da shirun da cewa wanan maganan yai min dadi danaji. Don shawara ne may kyau madam ta kawo sai a lokacin yai magana yace tare da dakatar da cin abincin da yakeyi amma sai nake ganin wanan abin kun san bamai yuyuwa bane. Daddy ya tare shi da cewa kana ganin zamu hada abinda bai dace bane a kan ka ko zamu cuce ka ko yarinyar ?. Gaba daya ture plate din dake gaban shi yayi daddy yace kaci abincin kamana naga abincin yayi dadi ai . Baiki ba yasa hannu ya mayar ga abincin daddy yaci gaba da magana yace ka kwantar da hankalin ka ka saurare ni. ZAINAB IDRIS MAKAWA SEENABU 8/14/20, 7:12 PM - Ummi Tandama: BAHAGGO, , , , , , , 🧕🏿3️⃣9️⃣🧕🏿 INA MAKU FATAN ALHERI ACIKIN WANNAN TAKIN DA MUKA SHIGA UBANGIJI ALLAH YASA MU DACE DA RAHAMOMISA AMIN YA ALLAH YAR UWA, , , , , , , Har ya juya ya tafi motar shi ta fita get din gidan tana tsaye tana daga mashi hannu tana murmushi a fuskan ta ta sauke ajiyan zuciya ta juya zuwa cikin gida. Still su Faiza na falon ta shiga tana fadin aaah lafiya baku ga lokacin sallah yayi bane kuna zaune kuna kallo . Nan suka bata rai sai anty tace may nene haka wai ina kuma safiyan ta shiga kuma bata zuwa ta dauke kayan nan a nan tashiga da su . Faiza ce tai karfin halin fadin baza a bude muga abinda aka sayo ba shi muke jira mu watse dama wani kallon banza anty tai mata har ya sata natsuwa . Tace don Allah baku jin kunyan hakan da kuke yarinyar nan bata saka maku ido amma ku kokarin ganin kwakwaf dinta kike yi ko yaushe. Dan malama taya ni kwashe kayan nan mukai mata ciki kafin mu watse haka nan cikin bacin rai suka taya ta daukan kayan zuwa daki na sun shiga ga dakin tas sai kamshi ke tashi na gyara gado kamar wadda keda mijin aure a dakin. Ina bandaki koda suka shigo sai maganan anty naji tana cewa ga kayan ki nan mun shigo maki dashi kafin fito ta face daga dakin don haka na tsaya nayi alwala nai sallah. Sai da na idar da sallah duk suna falo sun fito na dauko kayan zuwa wurin anty da su buda tashiga yi tana yabawa da kyan abubuwan tace wanan irin kyauta haka Safiya ? Na dan marairaici nace wallahi anty ni har abin yaban tsoro don haka yau ta diban kayan duk abinda yai mashi dadi a rai. Wani irin dariya ta kwashe dashi tace ina ruwan sabon shiga dake dashi yanzu duk kun zama kamar yan koyo Faiza ce ta dakatar da duban wani ruba da ta dauka tana dubawa don bata san ko may ye a ciki ba. Tai saurin aje roban a hannun ta tana kallon anty gami da cewa ko dai da walaki ne wanan sayayyan haka nikan nayi mamaki haka kawai zikau mutum zai yi hidama haka. Ashe zamu sha buki kenan ta fada a cikin gatse wa mu biyun duka sai anty tace inda rai da lafiya mun kusa cassawa. Tsukin da Fati taje ne ya katse hiranda faiza da anty keyi kan kaya tamike but ta shige tana ambatan munafunci shi kadai na iya ji cikin maganan ta. Bayan shigewan tane anty tace wawiya kawai mara hankali don rashin wayyo wai ke ke gwada ma namiji kina son shi baza ki jira ya furta maki ba da bakin shi. Sai faiza tace wanan shi ne son maso wani anty ta karasa da koshin wahala ba tana daki tana hauka shi hankalin shi na inda yake so. Ashe bata karasa shiga ba tana jin duk abinda suke fadi sai dai bata ga bakin su sai ni da banyi magana ba taji haushi na. Wai dama mu yan kyauye mun iya shige da fice wurin kwantan maza an raba kayan bayan anty ta fitar min da masu amfani naci din ne kawai tace a raba. Bayan na koma daki wayana dake cikin jakkata yai kara da sauri najawo jakar ina daukan wayan wani irin firgita nayi don ganin kudi a jakar nawa. Har wayan ya katse ban samu dauka ba don kudin ya firgitani kara waya ya kara yi sai na dauka a firgice ina sauke ajiyan zuciya. Ummi na ce muka gaisa da ita na tambayi mutanen gida take cewa kowa lafiya sai dai mahaifin ki ne baiji dadi ba kwanan nan. A firgice nake tambayan abinda ya samay shi take cewa dai je asibiti an bashi magani amma bin sai gaba yake yi kuma. Na dauki salati nace ummi zan zo ko gobe ko zuwa jibi in Allah ya yarda mukai sallama hankali na bai kwanta ba ga zancen kudi ga maganan baba da ya tsaya min a rai. Don haka na kasa bari sai da safe na saka hijjab a firgice tare da daukan kudin da wasu kaya daga cikin na dazun na hari dakin anty din. Nayi sa a tana dakin bata nufi dakin daddy ba lokacin tana gani na ta mayar da hankalinta gare ni tare da fadin Safiya lafiya kuwa. Karasawa nayi bakin gadon ta na zube kasa sai ta mayar da hankalinta gare ni na fitar da kudin ina mika mata nace anty yanzu nagan su a cikin jakkata ba san da su ba kuma. Murmushi tayi ta karbi kudin a hannuna tana dan juya kudin tare da yi murmushi tace wa zai saka maki in ba Sulaiman ba don yasan in ya baki ba karba zakiyi ba don ya fada min kin ki ki saki jiki ku fahinci juna . Dukar da kai nayi kasa ina tunanen yaushe ya zuba min su ban sani ba to wai ma ni ina zan kai wanan kudin haka masu uban yawa. Ita ce ta katse ni da cewa indan kina tambaba ne bari yanzu in kirshi muji sai ta shi ga lalavan wayan ta dake bayan ta, alokacin nake fada mata cewa mun yi waya da ummi yanzu take fada min jikin baba ba dadi . Sun je asibiti wai amma abin bai ja baya ba na karasa fadin ina son inje gida anty don in ga halin da yake ciki. Ashe har ya dauki wayan ban sani ba yaji may nake fadi yake cewa tare kuke da mutumiyar ke nan tace eh wallahi gata nan tazo min a firgice wai taga kudi a cikin jakkanta. Murmushi yayi yace rabon ta ne ya shiga jakkan ta kila tace ai dama nasan aikin kane amma dai ka ruda min kauna ka sani. Dariya yayi yace ina son ta saba da halina ne tun yanzu idan zan ba mutum abu bana bashi ya sani sai baya na. Tace kabi mun kauna a sannu ko muce mun fasa kaje gaba ka samu daidai da kai yace tuba nake babban yaya kin san kaunar taki sai a hankali. Nan take fada mai zancen mahaifina da nazo mata dashi ya kama fadin subbahanallahi yazu yaya ke nan tace wallahi fa daddy nake son ya shigo musan yaya za a yi don tace zata tafi. Yace OK kuyi magana dashi muji yaya za a tsara mata tafiyan don ba abin da za a tsaya bane wasa saboda ba a san halin da yake ciki ba. Nan dai su kai sallama ta kashe wayan tare da mayar da kallon ta a kaina tana fadin dama yakanyi ciwo haka ne na girgiza kai tare da fadin gaskiya bai taba yin haka ba sai wanan karon. Turo kofan da akayi ne muka mayar da hankalin mu ga may shigowa daddy ne yace a a kuna meeting ne haka komay ? Tace dashi uhumm wallahi mahaifin ta ne aka bugo waya yanzu baida lafiya shi ka gan mu haka. Subbahanallahi shi ma ya ambata yana cewa tunda suka bugo jikin ya matsa mashi ke nan kwarai tace ai itama maganan da takeyi yanzu ke nan hankalin ta ya koma can. Yace dolle ne amm yazu dai abari zuwa safe sai inga yadda ya dace ayi ta tafi har ya juya zai fita daga dakin sai ya juyo yace shi sulaiman din yasan da zancen ? Koda yake ma baridai zan sam abin yi akai adai bari har Allah ya kaimu gobe din tukun na ya fice daga dakin ta dawo da hankalin ta gare ni. Tace yanzu dai ki kwantar da hankalin ki sai da safe din in Allah ya kai mu jeki ki kwanta har da safe. Haka na mike gwiwa na yayi sanyi nace sai da safe anty tace Allah ya tashe mu lafiya ki dai kwantar da hankalin ki kinji na fada maki. Nace tau anty na gode na fice tare da rufo mata kofan dakin ta bini da kallon tausayawa gare ni ta sauke ajiyan zuciya. Tun da na tun karo dakin na fahinci an shiga min dakin na karasa shiga aiko nan naga kayana a hargitse alaman an tone min kaya ana neman abu. Bandai san may aka dauka ba na gyara kayan tare da hayewa gado ina ci gaba da tunane a raina dole ne baba yai ciwo abu yai mashi yawa a zuciya yanzu. Ga nawa matsalan ga na Saadatu sanan kuma ga na gida mazan gidan mu duk ba wanda ya mayar da kan shi abin kwarai. Dole abu yai mai yawa a zuciya tausayin halin da gidan mu ke ciki ya kamani na kalli kayan da sulaiman ya kashe min kudi a kan su nace a raina ai wanan da kudin ya bani na sai wa yan gidan mu abinci dashi zai kai su har tsawon wani lokaci suna ci. A haka har barci ya dauke ni sai asuba na falka na yi sallah ina idarwa kuwa na kira ummi ina tambayan ta yaya suka kwana. Tace gaskiya kan jiya ba ai barci dashi da dadi ba yanzu ma yaya Sani yashigo yana shirin su koma dashi asibiti. Nace a bashi waya mu gaisa in ji may ake ciki yake fada min wallahi kan baba yana jin jiki yanzu asibitin zasu koma. Babu kudi da asibitin birni zasu tafi dashi aje can a duba shi a san may yake damun shi nace yaya ko yanzu can zaku tafi. A ari kudi ko nawa ne idan nazo zan biya yace ai an nema ba asamu aro ba sai nace yaba ummi wayan muyi magana da ita. Ya bata wayan nake ce wa tabada kudin da zasu sarin kaya tace jiya suka saro kaya dasu nace a je wurin gwagon ta duk inda zasu samo kudi a samu kafin in zo. A haka muka rabu sunje sun samu kudi kudin dan gidan mama ne kaunar ummi na sadakin shi aka ara nace ba matsala insha Allahu idan nazo zan biya. Ban fito ba yadda na saba sai ga anty dakin a lokacin nayi kuka idona yai ja ta zauna a kusa dani tana cewa kuka kikayi ne Safiya. Na dukar da kai ina zubar da hawaye nace anty jikin na baba ya matsa mai jiya wai basuyi barci ba dashi. Subbahanallahi suko sai su zauna da mutum gida haka yana jin jiki ba zasu kaishi asibiti sai su zura mai ido. A sanyayye nace da ita wai ba kudin da zasu kai shi asibitin ne suka ce ikon Allah toh Allah ya sauwaka. Yanzu dai ina gani sulaiman zaki bi yau ku bi jirgi idan kun isa Abuja sai ya saka ki mota da za a kai ki gida yau zasu tafi da shi da daddy can. Jin tace da daddy zamu tafi yasa hankalina kwanci don da zance mata ta bari in tafi a mota yafi don gudun zargi amma jin da daddy zamu tafi sai hankali na ya dan kwanta. Yanzu dai ki tashi ki shirya zan fita inga abinda ya dace ayi kafin ki wuce ta fita nikuma na tashi na shiga shirin tafiya. Su faiza basu san da zancen tafiyana ba sai da na fito don daddy yace ace na fito shine suke tambaya anty ke fada masu mahaifina ne baida lafiya. Fati tace shine kawai zata bi daddy da uncle don mahaifinta baida lafiya sai dai inda wata manufa zata tafi. Da sauri anty tace may kike nufi ko may kika mayar damu ne kina nufin mu din mutanen banza ne komay ? Shiru tayi don maganan itama haka yazo mata nan yar nata tai mata tas sai da ta raina kan ta Faiza cewa tayi zata rakani. Anty tace da ita kema kin san yayan ki ba zai yarda ba ki tafi kar ma ki dauko wa kan ki wani magana a na zaune kalau. Haka muka shirya muka fito motan daddy muka shiga zuwa airport din inda anty tai muna rakiya ita da Faiza . Acan muka samu sulaiman nan sukai shige da fice har aka kira mu tafiya ya tashi ban san lokacin da kuka yazo min ba. Anty tace dani a a kukan may kuma safiya kamar wacce ta tafi ke nan ashe akwai aiki randa zaki tafi gidan mijin ki. Daddy yana muna sheri haka na barsu don anty itama ta karaya da kukan da taga ina yi din har sai da jirgin mu ya daga suka koma gida. A jirgin kujeran su daya da daddy inda na samu wata mace tana da yawan surutu don har muka kawo hira take min a inda take ce min wai tazo ganin mahaifan ta ne a lagos. Abuja take zaune ita da mijin ta sai dai mijin nata bayerabe ne ita kuma uwarta bayeraba ubanta bauhaushe. Yaran ta biyu yanzu take tambayana ni a lagos nake zaune nake bata amsa da a wurin anty nake zaune zanje gida ne mahaifina baida lafiya. Ta tausaya min har ta karbi lambana tace inda mun sauka zata kirani taji lafiyan mahaifin nawa. Mun sauka duk a tsorace nake don ban taba ko ganin jirgi ba balle in shiga sai gani yau a cikin sa kuma mun sauka lafiya da kudirin ubangiji. Mota yazo ya dauke mu muka tafi gidan daddy bamu dade ba suka fice suka barni ina zaune tunane ya cika min zuciya zuwa . Zuwa sha biyu da rabi sai gasu sun dawo gidan sai dai sulaiman ne kawai bai ko son kallo na sosai ya zauna a kujeran yana fuskantana. Yace sorry ko yanzu dai ki fara isa ga mota nan za a kaiki har gida sai kudi da zan baki ki yi duk yadda ya dace ayi. Naso mutafi tare amma hakan ba zai yuyu ba don wasu yan matsalolin da nake dashi ki tabbatar anyi masa abinda ya dace dashi don Allah kudi ba matsala bane duk yadda ake ciki sai ki buggo min. Nace a hankali na gode sai dai akwai kudi a hannu na don wanda ka bani anty ta bani kuma ta kara min wasu. Yace bana son gardama kin san abunda zaki sama a can ne ya mike yana cewa ki kula da kanki kuma ai mashi duk abinda ya dace don Allah in akwai wani matsala a bugo min in sani . Ki fito mota na jiranki a waje ku tafi daddy yace in maki sallama aiki ya rike shi bazai samu zuwa kuyi sallama ba. Ban san lokacin da nakai har kasa ina mashi godiya irin wanan harcin da yai min ba dan haduwan mu dashi haka. Murmushi yayi yace haba haba ba komai ki dai kula da kanki sai yai gaba na tashi a sanyayye nabi bayan shi. A waje naga wata mota da driver naji yana cewa driver indan dare yai mashi goben in ban gama ba zai iya kwana ya bude min na shiga ina mashi godiya. Muka wuce yana daga muna hannu sai lokacin na sauke ajiyan zuciya ina mika godiyana ga Allah da wanan baiwan da yai min dan lokaci guda. Motar mu ta halba saman titi ina ta kallon yanayin garin zuciya fam da tunane kala kala muka nausa ga tafiya. ZAINAB IDRIS MAKAWA SEENABU 8/14/20, 7:12 PM - Ummi Tandama: BAHAGGON, , , , , , , 🧕🏿3️⃣8️⃣🧕🏿 UBANGIJI ALLAH YA BA MU IKON BAUTA MASHI, BAUTA TSARKAKKEKE, YA ALLAH KA KARBA MUNA IBADUN MU, , , , Tsura ma dan uwan nashi ido yayi yana sauraren bayanin shi daddy yaci gaba da cewa kamar dai yadda aure ya cika kan wanan cutar haka itama aure ne sanadin samun wanan cutan a gare ta a halin yanzu. Innalillahi yake iya fadi acikin ranshi da fili yace wai kuna nufin wannan yarinyar ta taba aure har an cuta mata irin haka. Yace cikin garin nan na Lagos tana zauna da miji ta sai dai auren anyi zaman ne a cikin ukuba sai kuma ga wannan cutar ya baiyyana mata. Ya ce Ya Allah kaza ma gatan mu yanzu wanan abin da mai yai kama mutum yasan cewa yana da cuta a tare dashi amma don ha inci sai yaki fadi har sai ya lika ma dan uwansa abu ya baci adawo ana dodofar tsiya. Sun dauki lokaci suna magana daya kafin ya mike yace zai tafi har a lokacin ranshi bai mashi dadi sam don abin yadawo mashi sabo a rayuwan shi. Yai masu sallama anty tana tabayan shi yaushe zai bullo kuma tasa aimai girki sai yace yana dan aiki idan ya rarage zai shigo. Daddy ya mike suka fice daga gidan tare dashi sun shiga gari tare don duban wasu aiyuka da ya bayar aimashi tun wancen lokacin. Washegari anty da zancen nama turkey ta dole shi aka dafa mata nai miyan shi nan aka taru a falo kowa na kwasan dafuwa. Sai da anty ta bari sunyi nisa da cin abincin ne take cewa damu aduniyan nan babu abinda nake kamar wanan namar . Nan kowa ya shiga fadan albarkacin bakin sa akan naman bandani dana ce ban taba cin shi ba a rayuwana dariya suke min sosai saka su daddy sun shigo gidan shi da Sulaima a bayan shi. Daddy ne ke muna kallon mamaki ganin irin dariyan da sukeyi din yake tambayan maiyai maku dadi haka irin wanan dariya. Fatine ta iya bashi amsa da cewa wai Safiya ne ke fadin ita bata taba cin naman turkey ba shine tabamu dariya sai daddyn ya mayar da kallon shi inda nake yana zama a kusa da matar shi yace. Kauna na kada ki damu da dariyan su watarana sai kin ci abinda duk kan su basu taba ci ba don haka kema zaki rama nan ba da dadewa ba insha Allahu. Yanzun dai tashi kin ji ki debo muna muma mu dandana muji santin da sukeyi akai don da gani yayi dadi tunda naga Fati yau haka baje baje. Na mike zuwa hada masu abinci daddy ya kalle matan shi da dariya ya cika yace kar kuyi mamaki zama kauye don nan da wani lokaci ta fiku bude ido . Dariya ya ci karfinta tace ai bamu haka da Safiya yadda take juya naman a kyamace ne yaban dariya. Sulaiman ya katse ta da cewa ai cin nama ra ayi ne idan bata so sai a saya mata wani mana taci kuma kuna kallo. Sai gani na dawo ina ce ma daddy na hada abincin dama na hada tun basu dawo ba anty tace dani to ke kin ji uncle yace tunda mun bata maki rai zai fita dake ki zabi naman da kike son ci a sayo maki muna kallo. Na da yi mata murmushi nace ni fa anty kin san nama bai damay ni bane kawai ba wai wanan ba. Kowa wurin yai mamakin jin abinda uncle ya fada do cewa yayi idan baki son nama sai a sayo maki wani abin don haka dana gama zamu fita. Da sauri na dan kalle shi sai naga ba wasa ga maganan shi sai Fati ne tace Safiya muje mu shirya dama nima ina son fita kin ga sai mu tafi tare. Anty tace waya kasa dake a ciki babu inda zaki sarkin son yawon tsiya kawai daga jin za ayi fita sai ki ara ki yafa har kina wani muje ki shirya kedin a shirye kike. Faiza ne tace don Allah anty ki bari mu fita muma mu lakaci arziki ta sake cewa na fada maku ba mai bin su ko ina nice nace amma da twins zamu anty? Ke kan ana kau da wasu kina jan wasu ai gara zuwa da wa yan nanbda zuwa da wa yancan yan sa maganan. Shine yace da ita dana ai sune gaba wa yan nan din dai da kika hana su sun hanu babu wacce zamu fita da ita sai dai suga mun dawo. Nai mamakin jin ashe yana magana mai tsayi irin haka don ban taba jin yayi magana mai tsawo ba duk sani na dashi. Amma yau tun shigowan su na fahinci akwai canji a tare dashi sosai kodan ganin daddy tare dashi ne oho ? Daki na shiga ba wani dogon shiga nayi ba dogon riga ne kawai sai dankwalin shi dana yane kaina dashi. Zama nayi ina tunane ni kadai a daki na yadda zamu fita dagani sai shi sai ga su yan biyu sun shigo da murnan su wai in fito in ji uncle mu tafi. Sai da na dan bata lokaci na fito anty bata falon sai su Fati ba wani magana mai dadi sai harara da suka raka ni dashi. Ina tambayan su anty sai Faiza ne ta bani amsa da cewa tashige ciki nace in ta fito ki gaya mata mun tafi tace a sayo dawisu idan anje sai musan ke yar gaban goshin tane. Nasan magana tasa min ban kulata ba na fice kawai abin yana sosa min zuciya fati ko tsaki naji taja tana bakar magana . A mota na samay su shida su yan biyu zaune a baya hakan ya nuna min ke nan a gaba nibzan zauna kenan. Kafin ma in karaso ya bude min gaban mota haka na daure na shiga duk a takure dani muka fice a gidan. Tafiya muke babu mai magana sai su yan biyu dake ta hiran su a bayan motan basu ko kula mu ba fuskan shi na kallon titi niko na mayar da fuskana gefen da nake zaune ina kallon yadda garin a kullun yake da da girma da bunkasa duk da an dauke headquater anan. Naji yace Safiya kin san abin da madam ke shirin shiryawa a tsakanin mu ko ? Na kalli yaran dake bayan motan naga hankalin su baya wurin mu nace a hankali nadai ji tana fadi amma bamu yi magana da ita ba tukun. Yayi ajiyan zuciya sanan ya nisa yace ya kamata in san raayin ki kiyi hakkuri muyi magana anan don bamu da wani lokaci na sake haduwa irin haka. Shiru na dan yi kafin in sauke ajiyan zuciya ince dashi to uncle , uncle ina anty ta fada maka matsalan da nake ciki, din haka ni naga kawai ayi hakkuri ba abu bane da zai yuyu a tsakanin mu. Saboda gaskiya sai na kasa magana karshe dai nace uncle mudai yi hakkuri kawai ya dakatar dani da fadin saboda may zamuyi hakkuri da maganan bayan abune wanda zai yuyu. Ko bata fada maki cewa nima a halin da nake ciki ke nan ba sai na dan kalle shi kadan yace yes nima victim ne amma sai wanda ya sani zai sanda hakan. Idana na kallon kasa look safiya ba wai abune da zamu tsaya muna yi wa juna kwana kwana ba da maganan. Ina son ki sani wanan abinda mutanen nan suke kokarin hadawa a tsakanin mu gani sukayi mun dace da junane. Ina son ki sani koda wanan matsalar ko babu shi akan mu wallahi ni son ki nakeyi tsakani da Allah ina mai tabbatar maki ba zan iya hakkura dake ba a yanzu. Ya nisa ya sake cewa wallahi ina son ki sani ban taba haduwa da macen da hankalina ya kwanta da dabiun ta ba irin ki. Gashi dan haduwan na dake da madam ta fara min maganan nan maganar sai bibiyata takeyi na rasa sukuni a tare dani. Sai kuma naga yayi murmushi yace sorry bazan iya ci gaba da fada maki ba amma na gaya maki gaskiyan zuciya na don ba wani lokaci nake son a dauka ba ga zancen. Nayi shiru ina sauraren shi sai da naji abunda ya fadi a karshe nai saurin dago fuskana sai wanan lokacin muka hada ido dashi. Take gabana ya fadi don kwarjinin sa da na ga ya fito fili a idona nace da wuri uncle yace dani yes I mean it, idan kina shakkun hakan gara ki daina ko kuma kina iya bani baki ki gani. Nayi shiru na rasa may zance dashi yadda naga ya zare min a lokaci guda to ni may zance dashi eh ko a a . Har ga Allah uncle ya samu karbuwa ga zuciyana don ina son shi har cikin zuciyana saboda me ne sulaiman dai namijine wanda duk wata mace ke burin mallakan shi a matsayin mijin aure mutunci addini kamala da natsuwa da gaskiya irin na nuna shi din daban ne da sauran mazan dana sani akwashi. Amma kuma nauyi da kunya ban taba ganin wanda nake jin nauyin shi da kunya ba irin shi don haka bazan iya nuna mashi kai tsaye na amince da bukatan shi ba. Bai kara yi min magana ba har muka isa wani shopping mall anan ya tsaya yace mu fita kowa ya dauki abinda yake so. Kunya bai bari na dauki komai ba sai wani turare dana dauka ganin kuya bai bari na dauki wani abu sai naga ya shiga daukan duk abinda yaga ya dace yana kadawa kwado sai da basket din ya cika sosai har yana zuba ya bari. Mukaje gurin biya ya biya akai muna packeg din su a ledojin shagon muka fito. Bai tsaya ba sai wurin wani shagon sai da nama kala kala nan ya shiga shi kadai sai gashi ya fito da ledoji shake a hannun shi yaja mota muka tafi. Ba magana haka muke tafiyan sai ya koma hira da yaran har muka kawo gida sun fita na bude mota har na saka kafa na daya a waje naji yace dani ina sauraren ki nan da two weeks. Ban ce dashi komai ba sai da na fito daga motan ne nace mun gode bai bari mun dauki komai ba ya kira security daya ya taya shi shiga da kayan ciki. Lokacin yamma yayi sosai suna falo zaune muka shigo duk idanuwan su a kan mu anty farin ciki ya kasa boyuwa a fuskanta. Suko nasan ba komai ya zaunar dasu ba sai gulma basuyi mamaki da irin kayan da muka shigo dashi ba don sanin waye sulaiman din da sukayi. Bai tsaya ba baya ya aje sai yace da anty zai koma sai dai da safe idan ya shigo karyawa mikewa tayi ta bishi baya suka fita gidan tare. Sai lokacin Faiza tace yau kan kun sha dadi wallahi naso ace anty ta bari mun bi ku muma mu lakato arziki don ba a barmu mu dawo haka ba. Wai safiya kodai wani abu na shirin faruwa ne keda uncle nace may ko ke shirin faruwa rabona ne kawai ya koka a wurin shi dariyan ku akaina yazama min sanadin samun alheri yau a gurin sa. Tace indai yai wari maji amma ai banza baya haka da sauri fati tace balle ma may zai yi wari a nan wanda ke gogayya da mata hamshakai ne zai tsaya a nan. Nace ako hakan in Allah ya nufa sai ki ga ya faru anan din inda ba komai tai saurin cewa ki iya lafazin bakin ki ramin kura ba wurin wasan yaro bane koda kuwa an rika masa. Dariya na wuce dakina ina yi ga leda a gaban su babu halin budawa su gani kada anty taci masu mutunci akai dole suka zauna zaman jiran ta ta dawo. A can waje kuma sun tsaya wuri motan shi ne yayin da ya dafa mota da hannun shi daya suna magana da anty din tace to yaya ina fatan dai kun dan fahinci juna wanan fitan da kukayi tare. Yai murmushi cikin jin kuya yace mata wanan kaunar taki kunya yai mata yawa taki sakin jiki mu fahinci juna kamar mai tsoron kar na sayar da ita. Tayi saurin fadin may Safiyan tayi maka kuma yace yace kiyi hakkuri zakiyi mamaki amma wallahi nidai yarinyar tayi min so sai ta tsaya min a rai. Amma naga kamar ba za iya shawo kanta ba don tana da kunya sosai ga kurciya a tare da ita kuma. Anty zatayi magana ya hanata yace don Allah madam ki taimaka min ki shawo kanta wallahi son safiya nake yi da zuciya daya ina son ga na taimaka wa rayuwanta . Auren ta nake soyi na bada dadewa ba sai dai ban san yaya zaku dauki maganan ba yanzu. Ga baki daya maganan shi ya gama kashe mata jiki da mamaki don bata taba tunanen zai afaka haka da sauri a sona ba shiru kawai tayi ma rasa may zatace dashi. Ganin tayi shiru yace madam kina mamakina ne ko tace ina jin ka dadi ne ya kashe ni wallahi wai yau kaine kake maganan aure haka a gabana babu kunya sanan wace kake so din gata yar gida ce. Sulaiman gaskiya ka gama kasheni da jin dadi don haka ka kwatar da hankali ka da yardan Allah kamar ka auri safiya ka gama. Bari ma ka gani yanzu da na shiga zan tun kare ta da maganan har sai ta bani baki ayi don yarinyar na jin magana na sosai. Don haka ka barni da ita kawai zan san yadda nayi da ita kar abin ya dauki lokaci mai tsawo iyayyen ta kuma zan san yadda na lurar dasu akan zancen. Yaji dadi har ya kasa boyewa ya rika fadin na gode madam thanks alot Allah ya bar min ke kin zama babban yayada gaske. Tace au dama ke nan ta karyace yace ai da madam kike yanzu ko zamu zama sarakai dake tace aban tukwaici na yace ai tukwaicin ki shine daga ke ba wata a gidan nan . Na biyun bazan fada maki ba sai abin ya yuyu zaki sani sai suka sa dariya a tare a haka ya tafi tana shamatar shi yana cewa yaji. ZAINAB IDRIS MAKAWA SEENABU 8/14/20, 7:12 PM - Ummi Tandama: BAHAGGON , , , , , , 🧕🏿4️⃣0️⃣🧕🏿 YA ALLAH MUNA ROKON KA KABA MU IKON BAUTA MAKA BAUTA TSARKAKKEKE KA KUMA KARBA MU NA IBADUN MU, , , , , Lumshe idona nayi tun da muka fara tafiya ashe da haka nayi barci sai da mukai nisa sosai ni kadai a baya zaune sannan na falkafirgigi daga barcin ina kallon gaban mota inda driver keta faman sharara gudu. Sai yamma lis muka iso makwabtan karkaranmu nan na dan fahinci ida muke don da gaba yana tafaduwa don ban fahinci komai ba. Garin muke shiga lokacin marance yayi sosai don haka mazaje da yawa suna kofan gidan su suna dakon kiran sallah. Kwantace hanyan gidan mu nake mai har Allah ya kawo mu lafiya na nuna mashi gidan mu ya nufi kofa yai packing a kofar gidan . Duk hankalin mutane ya dawo kan motar suna son su ga wanda zai fito a wanan mota mai kyau haka ganin ta tsaya a kofan gidan mu ya su yaya sani tasowa da abokan shi. Da sauri driver ya fito ya bude min mota na sagalo kafa daya dayan na a ciki na tsaya dauko hand bag dina zan fito. Yaya sani yace ah Safiya ne fa da sauri yazo yana kokarin rike marfin motan da nake fitowa ciki daga ciki suma sauran sannu da zuwa suke man na gaishe su cikin mutunci sai na nufi cikin gida. Nan suka fara biyo ni da kayan yar wurin mamace zata fito sai gani ta tsaya tana kallo na don bata sanni ba sai da nace da ita maimuna ina zaki sai ta dauki muryana tace Safiya ke ce nace nice maimuna. Nan ta fara ihu lah ga Safiya ga safiya daidai lokacin da nake kutso kaina cikin gidan kenan duk hankalin su ya koma wurina suna mun kallon kurrullah. Duk suka rufe ni suna min sannu da zuwa yayin da abokan yaya sani suke ta shigo min da kaya daga ciki ni kaina abin ya bani mamaki ko shiga daki ban yi ba bayan mun gaisa dasu mama sai na wuce dakin baba kai tsaye don in ga halin da yake ciki. An zaunar dashi wai yai sallah amma saida ummina ta tsaya daga bayan shi na shigo dakin ina cewa sannu baba yaya jikin ? Yadago kai zabban tausayi yace safiya kece tafe nace eh sannu baba yana fadin wai may yasa su ka fada min baida lafiya banji may yake fadi ba sai da na tambayi mama dake gefen shi take fada min. Na juya wurin mama ina tambaya anko tafi asibitin birnin yau sai tace man wai kudin da aka samu arro baya isa don tun a daukan mota da za a tafi rabin kudin ya kara nace haba haba mama nace a kaishi ko nawa ne , gani nan tafe ai zan biya. Na dan tsaya tsaye shiru ina kallon yadda baba yake wahala da bautar Allah sai na fita dafa daki na samu kanne na sun shiga min da kayana dakin mu . Sai dai suna waje suna gardaman wai kwali goma ne inji yar wurin inna sai dan wurin ummi kanina yace hummumm sha biyu ne na gardama ya kaura a tsakanin su. Inna ta kwala ma yar ta kira wai ina ruwanta ko kwali dari ne na shigo dashi tasan sanan da nake yi na samu kwalayen da na shigo dasu iyayyayena suna murna. Kai kawai na girgiza na ce a ban buta nayi alwala daga dakin ummina ban tsaya sauraren ta ba bayan munyi sallah ne na fito na samu yaya sani nake cemai yaka mata mu tafi asibiti da baba sai yace ai maganan kudi ne da mota nace motar da na zo da ita zamu tafi. Yace sai a bari sai da safe ina shiga dakin nace dashi yau dai zamu tafi yanzu ma zamu kama hanya dawa zamuyi tafiyan ? Nake tambaya yaya Sani din ina dafa baba ina kai sannu yaya jiki ya gyada min kai alaman da sauki jikina ya kara yin sanyi don dai ni a yi sani na dashi ban taba ganin yayi ciwo irin haka ba. Mama tace bari taje ta shirya don da ita za a tafi inna da ummi su zauna gida amma da inna ta samu labari sai ta tada fitina wai ita zata . Yaya sani yace ai ba kasuwa zamu ba da kowa zaice zai tafi da mama kawai zamu sai ni da Nura yace mata. Na fita naiwa driver magana kamar yadda Sulaiman yace in sanar dashi duk abinda nake so nasa ankai mai ruwa da maltina da abinci yana ci ne sai gani na fitinan nake fada mai tafiyan mu birni. Sha daya na dare muka isa asibitin basu so su karbe mu ba a lokacin sai da na nuna masu kudi sannan suka fara nan nan da mu, har likita suka tayar cikin daren nan yazo ya duba baba maganin da ya rubuta. A cikin daren nan su yaya Sani da driven nan suka fita neman magani anyi saa an samu a wani shago sai dai shi yaya sani yana ganin yawan kudin don dubu ashiri da wani abu suka kaso . Ya dawo yana fada min nace mun yi arziki ai tunda an samu tun cikin dare akaiwa baba aluran da bashi maganin sai gashi ya samu barci sosai ranan. Washegari nacewa driver ya wuce sai yake cewa ai sunyi waya da maigida yake cewa ya dan tsaya don zirga zirgan mu ya taimaka muna naji wani iri a raina sai dai a fili cewa driver nayi anya ayi haka bazamu takura maka ba ? Haba madam aini a kan aiki na nake daganan har ki gama banda damuwa ko kadan Allah dai yaba baba lafiya. Nai mashi godiya sosai yace babu damuwa hajiya ai mu aikin mu ne naga kuma oga ya damu sosai da ciwon na baba murmushi nayi kawai. Sai na tuna ban kirashi ba tun jiya kamar yadda yace in kirshi din don ya anshi wayana yasa min nombashi da zamu wuto. Gefe na koma saida na tattara natsuwa na wuri daya sanan nai dialing din nomban na shi ringi na uku ya daga wayan yana cewa. Safiya yaya ai na zaci bazaki kirani ba kin ga mutanen gida kin manta da kowa. Murmushi nayi nace wallahi ba hakana bane ya dan kwaikwayeni yace to yayane nace kawai dai jikin babane ya tsoratani jiya da na samay shi jikin ba dadi wallahi. Amma yanzu ya samu lafiya sosai don maganin da aka rubuta mai da allurai tunda ya sha su ya samu barci jiya sosai. Yace masha Allah haka akeso to yaya mutanen gida nace suna lafiya sai nai shiru kusan tare mukai magana ina cewa kuma har da wani dawai niya haka mai yawa. Yace bake nai wa ba iyayyena da kanne na naiwa tsaraba ki basu godiya na fara mai yace haba na fada maki bana son haka nifa iyayyena ne yanzu koba hakana bane ? Murmushi na danyi yake cewa yanzu dai hankalin ki ya dan kwanta ko baba ya samu lafiya sai na sauke ajiyan zuciya nace hakane amma da hankalina a tashe yake so sai. Don mu din tallakwa ne na karshe indan baba ya kwanta wa zai dube mu shi kaga hankali na ya tashi sosai. Yace karki manta da cewa Allah ne mai yi ba wani ba yanzu bagashi ya samu sauki cikin yardan ubangiji ba nace haka ne kuma. Yace idan ya tashi ki gaida min shi zan shiga meeting yanzu dama don baki kirani ba ne yasa ban kiraki ba yanzu kuma naji dadi alama ya nuna na dan samu karbuwa ke nan. Kai nace haba uncle kabar wanan magana tukun yace na bari as you wish ganin zai kashe wayan yasa nace sai kuma driver yace kace ya tsaya damu. Yace eh haka na umurce shi don idan ya wuce ina zaku samu abin yin zirga zirga shine nace ya dan dakata har muga yadda hali yayi. An gode na kara fadi zan shiga godiya naji ya kashe wayan shi kit na dubi wayan ina murmushu na shiga dakin da aka aje baba din har lokacin yana barci naja kujera na zauna tare da kafa mai ido. Mama tana zaune a kasa saman tabarma tana karyawa da abincin da na sa yaya Sani ya sayo muna don bamu da kowa a garin. Na dan dade a zaune sai ya motsa da sauri na dago ina cewa sannu baba yaya jikin ina dan gyara mashi kwaciya yace Safiya ke ce yaushe kika dawo ? Nace a sanyayye jiya na dawo baba yaya jikin yaya jikin baba ? Yace jiki da sauki Safiya na gyara mashi kwaciya yace baiyi sallah ba da tai makin mu nida mama muka kamashi ya kewa yayi alwala. Bayan ya idar da sallah ne yake cewa nan ina ne mama ne ke fada mashi ai asibitin birni aka zo dashi jiya da dare da safiya ta iso. Yace Allah sarki sannu Safiya nagode nagode ubangiji yai maki albarka yasa ki gama da duniya lafiya nace amin baba mama tace yau ga ranan diya mata mun gani a gidan. Don badon Allah ya taimaka ba da bamu san yadda wanan alamarin zai kaya muna ba kana zaune a gida ciwo zai halaka ka babu yadda muka iya . Gashi daga zuwan mu jiya jiya har mun ga haske gashi yau ubagiji ya nufa ka bude ido nace baba don Allah ka rage yawan tunane don likita yace tunane yai maka yawa har zuciyar ka ya kumbura. Murmushin karfin hali yayi yace yaro yaro ne tune ne ai dole mai rai yayi shi balle ni da gidana yake batun fin karfina inda rai na kuma don may bazanyi tunane ba safiya ? Nace baba hakkuri za a yi abar ma Allah komai ubangiji yana sane da komai da bawa ya gani yanzu dai may zaka iya ci a sawo ma ? Yace ban jin cin komai sai barcin da nake bukatan komawa don idon nan nawa kamar asa min abu mai nauyi nake jin shi. Nace baba ka daure kasha tea mai dan zafi ko hajin ka zai warware ka kara samun karfin jikin ka. Yace dadai kune ne kila zan dan iya sha da sauri nida mama muke cewa ga kunu nan an sawo bari a baka yaya sani ne suka shigo shida driven nan suka shiga gaida shi. Bai sha wani abin kirki ba ya koma barcin muka sauke ajiyan zuciya muna kallon yadda yake sauke numshi a wahale wai ma cikin yaji sauki ke nan. Sama sama muke hira da mama ina fada mata irin zaman arzikin da muke yi da anty da yan uwanta tace Safiya haklin ki ne ya ja maki . In dai baka dauki kan ka da fadi ba Allah yana taimakon bawan sa ta ida bai zata ba Allah ne ya kawo ta cikin rayuwan ki don ta taimaka maki. Gashi tun yanzu muga haske badon Allah ya kawo ki ba wanan alamarin yaya zamuyi kena da haka zamuyi ta kallon shi a gida babu mai taimaka muna. Shiyasa nake ganin haukan innar ku da bata da kalamin alheri sai na tsiya akan yayan mutane duk da wanan abin da ya cika dasu kuwa. Murmushi nayi nace banga ranan da inna zata daina halinta ba ita haka Allah ya halicce ta da hassada don bata bar kowa ba a gidan. Tace bata fa dainawa don dubi abinda tayi jiya Sani ne kawai mai taka mata burki don badon shi ba jiya ba karamin tashin hankali za a yi ba. Nace niko ban ga Saadatu ba ma tace tana nan daki bata jin dadin jikin ne don duk da malam ya hana a zubar da cikin jikin ta amma bai hana uwan bata abubuwa a boye ba. Nace na shiga uku mama karfa ta kashe ta tace in ma ta kashe ta ai ita ta sani waya ci baya ina mahaifiyar ki data rungumi kaddara ba ga abin yazo mata da sauki ba. Mu dai fatan mu ubangiji ya baki miji ki aure ki huta da zargin cewa zaman banza kike yi a can na ce ai Allah yagani mama. Ban yi ba da sai yanzu da lalura a jikina zanyi in cutawa mutane ko mai tace ai bata gane hakan ita don idon ta ya rufe ko. Motsawan da baba yayi yana fadin a bashi ruwa yasa mu tashi muka ce yayi hakkuri an daura mai ruwa nace barin fita in nemo likita a fada mai. Naje gun nurse din ward din mu na fada mashi sai yazo ya duba baban ya fita kiran likita sai gasu sun dawo tare da likitan yadan duba baba din tare da zare mai ruwan da suke kara mashi din. Yace a barshi ya dan huta zai daina jin kishin da yake ji nan dai suka kara taruwa a kasa suna mashi gwaje gwaje irin nasu na likitoci. Yaya Nura suka iso shi da su ummi da mama da rana nan suka samu yana barci bayan gaisawan da mukayi dasu ne mama take masu bayanin halin da baba din ke ciki yanzu. Nan dai muka wuni dasu sai zuwa yamma sukace zasu tafi drive nan dan arziki yace in bari ya mayar dasu sukace ya bari zasu shiga motar kasuwa inna sai baza ido takeyi wirin kalle kalle a asibitin. Ya kwashe ya wuce dasu hankalin gida zai kwanta yanzu da suka zo suka gan shi dan da basu zo ba duk wayan da muke yi dasu basu yarda a yadda muka fito dashi gida wai ya samu lafiya yanzu. Baba yana samun kulan da ya dace sosai dashi sannu a hankali yake samun sauki na shigan shi yana dan dada murmurewa . A kwana na uku ne driver da ya kawo ni yace zai koma gida na bashi kudi yaki karba amma sai naba yaya Sani ya bashi idan sun fita. Ban wasa da shan maganina don dama ina dashi anty tana kaini ansa a sace bada sanin kowa ba a can lagos din don haka ban da matsala wurin amsan maganin . A kwana na shida aka sallamay mu nan muka samu motar muka dauka ta dawo damu gida kowa na ta farin ciki yadda suka ga baba ya samu sauki. Sai dai an bashi dokoki na ya rage tunane da abincin da ya kamata yaci don ya samu lafiya muka sayo magani wadatacce muka dawo gida dashi. Dakin mu na shiga na cire kayan dake jikina don duk warin asibiti duke yi wanka naje nayi na shirya sai na fito zuwa dakin inna. Saadatu na kwance duk ta kumbure nace subbahanallahi Saadatu may ke faruwa haka kina zuwa asibiti kuwa maimakon tai magana sai kuka ne yazo mata. Zama nayi a kusa da ita nace bari kuka saadatu haka Allah ya nufa damu sai dai istigifar ga bawa nace kin je asibiti tace wa zai kaini Safiya dan jike jike dai inna ke bani ina sha. Nace zuwa zamuyi gidan mau ta dubaki mu gani tace uhumm Safiya ai da na dauka halin innan mu yasa kin fita batuna ne dan da kika zo baki nemay ba harda kuka nayi gashi ban iya fita ko ina. Nace haba saadatu may zai sa inyi fushi dake ke fa yar uwata ce ta jini halin inna kuma inda sabi ai na saba yanzu sai dai addua kawai. Da taimako na ta samu ta shirya don inna na dakin baba sai fitowan mu suka gani kawai take cewa ina kuma zaku haka ? Nace wiri mau ta duba lafiyan jikin ta don ba a barta haka ba tana wahala tace ai ita taja wa kanta ina ruwan wani saaden tace dani mutafi kin ji safiya. Nan muka fice muka barta mashin na tare ta hau nima na hau mukaje gidan an dubata take muna bayani bata samun kulawa ne sosai an mata allurai don tace akwai maleria masu ciki a jikin ta do haka tabar bari sauro na cizon ta ta bamu magani tare da fada mata abinda ya kamata taci kuma ta dinga zuwa ana dubata akaiakai. Bamu dawo gida ba sai da na sayo mata abin bukatun ta harda gidan sauro muka dawo gida yamma tayi a lokacin nan ina ta ke cewa . Yanzu dai anyi kudin da bamu san asalin shi ba anzo ana muna facali a gida indai tai wari ai maji komai daren dadewa . Ba wanda ya kulata sai dare muka samu kebewa da ummina nan muka shiga hiran yaushile rabo da ita nake fada mata duk yadda nake can. ZAINAB IDRIS MAKAWA SEENABU 8/14/20, 7:12 PM - Ummi Tandama: BAHAGGON, , , , , , , 🧕🏿4️⃣1️⃣🧕🏿 Ummi ta nisa bayan ta gama sauraren magana na tana cewa dani anya yar nan baki iya tsaga fadi ba wanan mutumin bai fi karfin mu ba. Na ce ummi nima abinda nake tunane kenan amma ita anty bata son ina fadin haka din tace yanzun dai ki dan kara nazari kafin ki kai ga gabatar dashi nan din. Fadan inna da mukaji shiya dakatar damu daga maganan da mukeyi din da muka saurara muka fahinci da saadatu ne take fadan akan daura gidan sauron da muka sayo. Fada sosai suke yi a tsakanin su nice na fito nayi wa saadatu magana sai take cewa wai inna tace bata yarda ta daura gidan sauron ba a dakin ta. Nace haba inna tana da wani daki yanzu a gidan nan bayan naki don Allah ki yi hakkuri kibarta ta daura daidai inda take kwanci. Nayi dana sanin fitowa raba fadan nan tsakanin inna da diyar ta don abin karshe a kaina ya dawo babu irin kazafin da inna bataimun ba ranan kowa najin ta a gari. Dole naja kafana na koma dakin mu bisa umurnin mama har lokacin bata daina fadan da take yi ba ta hade mu ta zage tas tana cewa sai dai yawon banza amma badai aure ba gare ni. Naje nayi fasikanci na nadawo ina wa mutane sallo sai inyi wa wa yanda basu san abinda nake yi ba . Ummi tace da na hanaki fita zakiga kamar ban son zaman lafiya ne ai gashi kin jawo wa kanki kwana da bakin ciki a ran ki. Nidai shirin kwanciya nake yi ina kara jimamay maganan Inna datake yawan fada min a koda yau she magana ya hada ta damu. Ya zama min dole in yarda da bukatar Sulaiman akaina kamar yadda yace bai son abin ya dauki lokaci don shi yanzu bai ga abinda zamu tsaya jira ba . Magana ummi keyi dani amma banji ba nayi nisa sai da ta kara daga murya na ji ta nai saurin cewa ummi kanin mijin anty na ne. Kuma su suka hada ni dashi don shima irin matsalar mu guda dashi aure yayi matar ta rufe mai tana da lalura sai da akayi abin ya bayana mata. Bacin rai yasa ya rabu da ita duka duka watan su shidda da aure suka rabu da ita tace amma ko bai kamata ya sake ta ba tunda ya dai riga da ya kamu da ciwon. Nace ai nima abinda nagani ke nan amma sai anty tace dani dama ba sonta yakeyi ba itace ta like mashi. Yanzu ke baki ganin akwai matsala idan kika bashi baki akan ya fito nifa ina tsoron masu kudin nan don da wuya suke rikon aure. Nace ummi duk wanan tunanen nayi shi kuma na fada ma anty amma sai cewa tayi nasan dai ba zata kaini inda za a cuce ni ba kin ga banda ta cewa don darajan ta a gare ni. Amma dai ni sanin da nai mai baida wani matsala rayuwa sai dai ba a san abinda ke boye ba kwai ne. Tace yanzu dai kafin ki koma sai ki shirya kije can gida ki ga baba da yaya Adamu ki fada masu in ma mallam ya yarda sai mu tafi tare dake mu gan su. Nace to ummi hakan ya kamata ayi nima dai hankali na bai gama kwatawa ba dashi amma babu yadda zanyi ne kawai sai ya zama kamar na watsa ma anty kasa a ido bisa kokarin da takeyi dani. Haka na muka kwanta kowa da tunanen da yake yi a zuciyar shi sai asuba muka tashi bayan nayi sallah na fito na share gidan na tara kwanonin da akai amfani dasu. Ina cikin wanke wanke ne na kusa gamawa sai ga inna ta fito sai cewa tayi dama ko acan abinda ke yi ke nan anzo nan za ai muna barkadon banza. Nace inna ina kwana bata amsa min ba ta shiga daki sai gata tafito da kwanoni masu yawa ta zube min su ashe mama na daga kofan ta tana kallon mu. Inna ta wuce tana maganganun ta sai mama tace kai wanan balain da may yai kama don Allah ba a barin mutane suji da abinda ya damay su sai bakin fitina tun da farin safiya haka. Wa na hana yadda yake so a gidan nan idan kuma kin saka kan ki ne sai a sayar maki ba abune mai wuya ba ehhy. Mama tace in ma zaki iya nan da shekara sai ki tayi bama sayar ba ko kwasa ne sai ki yi gaki ga wuri ai. Wanan abu damay yai kama kin kwana fitina kin tashi dashi duk yarinyar nan bata kula ki ba ba sai kiba kanki lafiya ba wanan ai zubar da mutunci ne gare ki. Nan dai sukai dan cacan baki tsakanin su ba wanda ya kula ta ni dai na gama na shige dakina na barsu nan. Wanka na fito nayi ina cikin gyara jikina sai ga Saadatu ta shigo dakin ummi din ta samay ni muka gaisa. Nake tambayan ta yaya jikin ta sai tai murmushi tace jiya na samu barci sosai wallahi Safiya na gode kwarai wallahi banda abinda zan fada maki sai dai kuma kiyi hakkuri da halin inna don Allah. Na yi murmushi nace ai inna uwane fadan su gare mu taki wata rana zai muna amfani a gare mu dariya ta dan yi tace kayya ke dai kiyi hakkuri kawai. Muna nan muna dan hira sai jin muryan inna mukayi tana kwala ma saadatu kira share uwar tayi kamar bata jita ba. Sai da ta kara kiranta tace tana zuwa ta ci gaba da maganan ta sai da nace taje taji kiran da inna ke mata ta dawo. Bayan fitan ta ne na ci gaba da shiri na nace ma ummi gidan gwagon ta zan tafi in gaida ita tace dani aiko kin kyauta. Nace a debi tsaraba abawa kowa har da makwabta tace kidai diba sai ki ba mutanen gidan abasu sai na makwabtan duk ki diban masu. Dole na tsaya nayi kamar yadda tace inyi din tace haka yayi bayan na raba na dauki na fanin su gwago aka fita min dashi waje inda zan samu mashin din da zai kai mu gidan gwago din. Mu kafito ni da kauna na da zata rakani gidajen uwayen mu muka hau mashin sai gidan gwago anan muka shiririce da ita har lokaci yayi mun fito. Mun tashi muna batun zuwa gida maman mu bayan muyi sallah azahar ta dafa muna taliyan hausa da manja munci mun fito sai ga kani na saman keke ya biyo mu. Nace lafiya ka biyo mu haka yace anty wai kizo wasu mutane suka zo wurin ki a wata irin katuwar mota. Anty baki gansu ba kamar bature dayan mutumin suna nan sun shiga gida gaida baba shine ummi tace in zo in kiraki. Na ce ni fa kace shafiu yace wallahi anty don Allah kiyi sauri don da ganin su masu kudi ne baki ga motan da suka zo da ita ba fa. Gwago tace yi maza ki je tunda an aiko kiranki Allah dai yasa muji alheri dariya nayi kawai sai nace bari mu aje maki sakon su mama anan mi tafi. Juyawa mukayi zuwa gida tun da muka karyo kwana na hango motan take naji gabana ya fadi nace to waye yazo har nan wuri na ? Haka dai muka shiga gidan da fargaba ko waye yazo a kofan ummi muka hango takalman su ga awakin ina sun zo suna hawan takalmin nasu mama tana korewa muka shigo. Wurin mama na nufa ina tambayan ta ko su waye tace haba Safiya ashe abin arziki muka samu baki sanar da kowa ba sai yanzu da bakin ki suka shigo gaida mahaifin ku suke sanar damu. Na danji kunya nace kai mama ho baga shi kun sani ba yanzu ai sai yace cikin shake muryanta ai baki sani ba tun shigowan su mutumiyar ta shige daki bata fito ba nace wake nan mama. Tace wa kika sani banda innar ku uwar yan hassada kuwa ake dai bari shiga dakin baban ku kiga abin arzikin da suka zo muna dashi. Yaya sani ne ya shigo da kwalaben abinsha gidan a cikin leda yana sauri ya nufi dakin ummi dashi nace Allah sarki dan uwa ko ina ya samu kudin da ya karma min bakin dashi oho ? Ya fito dakin ya ganni yace a, a ashema kin dawo ga baki mun samu daga abuja sin zo wurin ki kin kuma zo nan kin tsaya jin na dawo yasa ummi dake zaune a takure dakin fitowa ta bamu wuri. Nan na shiga da kunya dakin da sallama na suna zaune saman tabarman da aka shimfida masu hankali kwance ga dan wake a gaban su da akayi gidan suna dan cokala suna ci. Hamza ne ya amsa min sallama na yana dauko dan wake a kwano yace a a amaryan mu ina kika je bamu baki izzini ba haka. Dan dariya nayi nace gidan kakata naje don tun da nazo ban je na gaida ita ba sai yau sai kuma akace min nayi baki. Nan na dan dago kai na kalle shi bai ko dago kai ba sai cin dan wanken shi yakeyi kamar bai san ina wurin ba ma. Yace dama ai ba ita mukazo gani ba mun dai ga wanda muka zo dubawa gashi har ummin mu ta bamu wanan abincin da na dade ban ciba muna ci. Nace aiko abu yayi kyau amma sai dai kaci kadan kasan a gidan sarakkai kake yace ina nan ai yanzu nima na zama dan gida baki ganina a kuryan dakin uwana zaune. Kara shiga dakin nayi yayin da na dan rakube a gefen dan gadon katakon ummi sai hamza ke cewa dashi a gara ki fada mai don naga yana batun mubar kwanon kawai. Nace yaya hanya suka amsa da lafiya nace amma uncle shine da mukai waya dakai dazun baka fada min kuna haya ba a shirya ma zuwan ku. Sai yace akwai shirin da yafi wanan ne a gare mu munzo munga mai jiki kima mun gabatar da kan mu an kuma ce ambamu abinda muke so gaya min akwai abinda yafi wanan farin ciki . Sai ya samay hannushi daga kwanon tare da aje fork din da suke cin danwaken dashi yace naji dadin da ummi tace kin fada mata komai a kaina shi kuma baba ya amince dani albarkacin madam. So ni yanzu banda wani shaku na neman ki don naga inda kika fito dakuma yan uwanki na kuma yaba da abinda idona ya ganan min. Karya da rashin asalin shine ba a son a cikin zance naga komai kuma na gamsu da hakan yazu idan na koma munyi waya da madam da mijin ta za a zo a nema min auren ki kamar yadda sharia da alada ya tana da don na fada maki ban son wanan abin ya dauki lokaci mai tsawo . Ina bukatan azumin bana inyi shi da matata a dakin ta don ban son a sakani cikin gwauraye kuma. Kaina na kasa duk kunya da nauyi sun cika ni suka ce in kira masu ummi suyi sallama da ita don zasu kama hanya saboda nisa. Na daga tsam zuwa kiran ummi din na samu tana dakin mama can na samayta na fada mata zasu wuce ta taso sunyi sallama da ita bayan godiya suka aje mata kudi suka mike. Sai ta bukaci da su je su gaisa dasu mama sukace sun gode nan akai masu iso suka shiga wurin su kowacen su ya aje mata daurin yan dari biyar biyar a gaban ta. Yaran gidan mu sai binsu suke yi suna kallo wasu na fadin wai batare ne shi saboda farin shi suma uncle bai barsu hakana ba sai da yai masu nasu alherinl. Mun fito muka samu yaya Sani da driver a waje suna ganin mu suka taso nace yaya sani bakin ka zasu wuce don naga kaine mai ma saukin baki agidan. Yace ai dole safiya ance min bakin kauna na ai banda zama don murna murmushi nayi don jin abinda ya fada nace yayana nakaina ke nan Allah barmin yayan mu. Amin sukace muka karasa wurin mota sai shi hamza yace barin dan ga nan baya yaya garin yake ne sai ya wuce ya barmu mu kadai daga ni sai shi su yaya sani sin mara ma hamza baya. Jin gina mukayi a jikin motar su yace safiya bazan boye maki ba naji dadin yadda iyayyenki suka tare mu sosai kuma mahaifinki na samay shi yadda nake so don ba masu kwadayi bane sai anbasu suke karba. Yace shi wanan yayan naki yaya kuke dashi ne naga yana da kirki sosai sai dai alamu ya nuna min baiyi karatu mai zurfi ba ko ? Nace yayana ne kuma mai kula dani sai na dan bashi labarin shi sama sama muna cikin hira ne hamza ya dawo yace kai muje inba son kake mu kwana garin nan ba dare fa yayi yanzu. Yace ni ba bako bane kaine dai bako yanzu don ni in ta kama a kwana gida nazo hamza ya dan harare shi yace haka zakai min ko Safiya kin dai ji abinda ya fada murmushi nayi kawai. Zai bani kudi nace a, a wanda ka bani da zanzo ban kashe ba duka sunanan su nake da amfani dasu yace to kara kikuma kashe su din don ki kashe wa yan uwa na baki kagin in godiya. Ya juya wurin yaya sani sukayi magana da cewa ina fatan idan zata dawo zakai mata rakiya yaya sani ya washe bakin jin dadi yace ko yanzu ta tashi a shirye nake ni. Sai naji yace ki tabbatar tare zaku dawo dashi don Abuja nake son ya tsaya ba sai ya biki lagos ba. Nace angode indan kin shirya sai ku sanar dani driver zai zo ya daukeki nace mun gode baiyi magana ba suka shiga mota muna tsaye muna kallon su suka bace muna. Sai naji wani irin ba dadi a raina nace may nake yi haka ne badai har son sulaiman ya kamani haka bane maganan yaya sani ta katse zuciyana da samo ansa da take so. Don cewa yayi ikon Allah safiya ina kika samo wanan hadeden mutumin mai karamci diba fa kudin da ya bani bai ko kirga ba ya debo su ya jinka min. Yaya Nura ne ya iso da sauri yace ina can wurin gina labari ya samay ni wani yazo gidan mu yana rabon kudi har da yan unguwa sun samu. Yaya sani dake sa kudin shi a aljihu yace anshaka ai har sun tafi ko mukan muji dumus a aljhun mu naga yayi wani iri nace yaya Nura kar ka damu in kadawo sai muga juna. Muka jera zuwa cikin gida tare inda muka samu suna ta farin ciki da zuwan bako suna ganina mama tace kaga yar albarka yar tohun lada haihuwan ki tankar da dubu . Murmushi nayi tace Allah bai maka fada kayi hakkurin ki ya zama maki taki a rayuwa don yau mukan mun sheda kuma mun gani. Dakin mu na shiga inda na samu ummi tayi tagumi zaune tana gani na ta wani nisawa tace sun tafi ko nace eh tace. Kin ga irin alherin da yazo muna dashi kuwa yar nan ni abin ma na kasa gaskats shi a raina wai yau kece Allah yaiwa wanan budin haka a gidan nan. Ga inna ku can harda ita wurin yabo ba kunya kamar ba ita ke tujara ba jiya a gidan nan nace kyale ta ummi ni bata gaba na fito mata da tulin kudin da ya bani nace gasu ya bani. Zaro ido ummi tayi waje tace duka wanan kudin haka kodai sai tai shiru kuma sai ta kara cewa ni abin fa tsoro yake bani. Nace ummi addua zamuyi don aikin gama ya gama tunda yace baba ya basu baki ko kiran da ake min a waje ne ya katse mu na fito da sauri nabar ummi da kidin a gaban ta. Ina fitowa akace baba na kirana dakin shi na rude na koma daki na sako hijjab dina zuwa wurin amsa kiran baba din. Ina shiga dakin baba idona yai tozali da kayan abinci a gefe guda tare nai mamakin yadda suka dauko kaya haka a motar su. Na shiga da sallama na na samu baba ya dan dago daga kwaciyan dayayi nace baba ya karfin jikin naka ya amsa da lafiya lau safiya sai kuma ga baki mun gani da rana tsaka yau. ZAINAB IDRIS MAKAWA SEENABU 8/14/20, 7:12 PM - Ummi Tandama: BAHAGGON , , , , , , , 🧕🏿4️⃣2️⃣🧕🏿 YAN UWA MUSULUMAI INA MAKU BARKA DA SALLAH DA FATAN ALLAH YA KARBA MUNA IBADUN MU YASA MUNA CIKIN YANTATTUN SHI ALLAH YA MAI MAITA MUNA WANAN RANAN MAI TARIN ALBAKA A RAYUWAN MU ALLAHU MA AMIN👏 Kai na dukar kasa yake cewa ai da kin sanar damu zuwan su ba sai a san shirin da za ai masu ba yanzu gashi sun zo babu komai sai dan waken da uwar ki tayi aka basu. Nace baba ai sunci sosai sun gode yace kayya ai ina da yan kaji da su aka yanka masu amma dai na fada mashi wani zuwan ya sanar damu ida zai zo. Safiya ina kika hadu da wanan mutumin ne bafa karamin mutum bane da ganin sa ma ba sai an fadawa mutum ba. Na dukar da kai kasa a hankali nace baba kanin mijin maman biyu ne da nake wurin ta a can lagos. Sai yai dan shiru sai kuma yace yasan da matsalan da kike ciki kuwa don kar ai abu a duhu a cutawa dan mutane rayuwan shi irin da sukai maki. Kaina a duke kasa nace baba ya sani don shima matsalar mu daya dashi shiyasa anty ta hada ni dashi da sauri yace subbahanallahi. Yanzu shima yana dauke da wanan lalurar a jikin shi nace baba yana da shi yace subbahanallahi nace shima aure yayi ashe matar nadashi ba su sani ba saida ta shigo aka sani. Yace waiyazu billahi kai mutane basu da imani a rayuwan su mutum kamar wanan amma an cuce shi an hada shi da may ye sunan ciwon ma nace tsida don ya gane. Yace Allah ya baku lafiya nace amin baba yana ta jijiga kanshi alaman jimamay a ran shi yace yazo da bukata auren ki nayi duk wasu kwana kwana amma yace ayi hakkuri a bashi ke yasan matsalar ashe abinda yake nufi kenan dama. To nadai bashi baki yace zaizo da magabatan shi a tsayar da rana don bai son abin yayi nisa sosai don haka zamu iya ganin su kowani lokaci. Nace to baba yakara dacewa Allah yasa muce gwama da akayi a raina na amsa mai da amin a fili kuma shiru nayi mashi yace Ai na tambaya aka ce kunje gidan gwago ne nasan fitinar inna kuce yasa ki barin gida kada kije ko ina don ta nan gidan kune gidan ubanki. Sai dai ita ta fita ta har maki gidan amma bake ba nace a a baba ai inna uwatace don haka inda sabo na saba da fadan ta akaina bani daya kowa ma bata bari ba. Mun dade da baba muna magana akai sai yaya Nura ya kirani daga dakin baba na amsa baba ke cewa mai yake sone sai nayi dariya kawai nace baba barin ganshi yanzu in dawo yace jeki ma ki huta ai kina da gajiya a jikin ki Allah dai tai maki albarka yasa ku gama da duniya lafiya. Na amsa amin baba na tashi na fice daga dakin zuwa wurin yaya nura nan na samay shi a dan gaba da kofan baba yana jirana. Ina fitowa ya miko min hannu yace bani nawa duk gidan a jike suke sai ni da bana nan nace muje daki yaya biyo ni yayi zuwa dakin ummi ya tsaya daga kofa na shiga na dauko mai kudin. Ina bashi ya washe baki yana cewa sai kin zama matar gwauna da yardan Allah sai mun je shan jar miya gidan ki. Inna dake duke tana talgin abincin dare na semon da akazo muna dashi ta kasa kannewa da kirarin da yake min tace kuke nan da baku san ciwon kan ku ba kai da dan uwan ka. Ku baku ko kishin zucin kanku kuyi ma kanku fada ka tsaya kanayiwa mace kirarin da yakamata aima maza. Yace kai ina haba ai kema kin sa fadi kikayi ina mu ina kama kafan safiya ai ita tariga ta take ko sai dai bi yanzu ko mutum bai so. Sakarai kawai Allah waddai naka ya lalace mama ta katse da da cewa a a fa ai gaskiya ya fada ke da aka baki baki karba har fa dubu hamsin aka aje maki yau a gidan nan. Duk zaman ki a rayuwa kin taba rike dubu biyar na kanki na kan ki aiko kamar azuba mata fetur nan ta hau sai da baba ya fito duk da halin da yake ciki har yana sarkewa . Take nasa masu kuruwa ina cewa dan Allah inna ku bari kada ku kashe muna uba da fitinan ku Saadatu ma ta saka ihu take muka sa mata kuka muna kama baba dake ta tari aiko gida ya rude da kuka yara na cewa wayyo baban mu. Mutanen waje suka shigo gida ya cika ana tambayan may nene muke cewa babane nan maza suka kama shi zuwa daki . Inna jikin ta yai sanyi ta koma ta rakube sai ga yaya sani da yaya nura aka ce dasu ga abinda ya faru aiko ya fito yana cewa uwar in kin kashe shi sai ki huta na tabbatar ciwon baba na da halaka dake inna. Amma ke kulun baki saduda maimakon ki rage sai ma kara baiyana halin ki kike yi nan dai maza suka taru a kanta sukai mata tas suka fice daga gidan. Muka taru a dakin baba kowa yayi jugun jugun baba yace idan inna ta kara kulani a gidan nan sai ya saketa. Wanan fitinan shi yasa inna laushi sosai ta koma shiru shiru a gidan kowa ya fita batun ta bayan kwana biyu na samu saadatu a dakin su. Tana gani na ta zauna nace ya kamata ki rage wanan zaman haka kidan rika motsa jikin ki zai fi kullun kina daki kumshe murmushi kawai tai min. Na miko mata kudi ta karba tana cewa na may ye nace ki rike a wurin ki ki dan sai kayan baby da abin bukatan ki. Ta fara hawaye tace Safiya halin ki na alheri ne a gare mu ko yaushe abin ki bai taba rufe maki ido ba wanan kaddaran da ya samay ni nayi kuka a zuciya na nayi a fili. Da kina nan da haka bai samay ni ba don kudin mai man gyadan da nake daukowa a wurin shi in na sayar in kai mashi kudi sai kudin ya kare a kaina. Kin san kudi in ana tabasu ba a kari yadda suke sai kudin ya rushe a hannu na shi kuma ya matsa min shine daga baya daya ga banda kudin ya nemi da in bashi hadin kai sai ya yafe min kudin. Shine na diga zuwa yana amfani dani ya mayar dani kamar wata matar shi sai da cikin nan ya samu ne ya guje gare ni tare da fadin shi ba zai karbi cikin ba. Safiya nasan inda ki na nan haka ba zai samay ni ba don zaki san hanyan da muka biya shi kudin shi ita kuma inna uwace a baki bata damu da damuwar yar ta ba. Sai dai in kawo mata tayi bushasha shine da ya daina bani ki ka ga muna yawan samun matsalan nan da ita. Na share hawayen da ke fuskana nace kiyi hakkuri kin san duk mai rai nada nashi kaddara a rayuwan shi. Na fito ina hawaye dakin ranan na kasa barci ina tunanen matsalan saadatu ina neman mafita a kai. Karshe dai na samu hanya mafi sauki na da haka na kwanta washe gari muka tashi kamar kullun a gidan kowa na ta har kokin gaban shi. Na fita waje acan daban su yaya Sani na samay shi nan na kirashi shi da amin shi na kut da kut na kirasu gefe muka kebe dasu. Nan na fara jero masu bukata na suna saurare na karshe dai yaya Sani ya nuna baruwan shi ga maganan sai da abokin ya kwantar mashi da hankali ya yarda. Akan zasu je su samu mutumin nan da yai mata ciki aji hadin ta dashi sai dai zasu biya wirin kanin mahaifin mu don a samu wani babba ya tsaya muna ga maganan. Sun yarda da hakan na shiga gida suka wuce wurin dan uwan baba sun mai bayani sai yace wanan maganan fa maganan kudi ne. Abokin yaya sani yace adai tun kare shi aji don aiwa abinda zata haifa din gata baba baiki ta nasu ba ya tashi suka samay shi a shagon shi na kasuwa ya na tsaka da kasuwancin shi. Sun kira shigefe da suka fito mai da maganan sai cewa yayi shi sam bai san maganan ba suka ce to za a zauna gaban hukuma. Sai cewa yayi aje mana abu na kudi haka suka dawo da labari babu dadi daga gare su bayan sun gama magana nace haka yace suka ce eh. Nace a hadu din babu komai nasan dai dan kudin da suke hannuna suna isana kashe maganan kauye. Don haka washe gari muka maka shi kotu tare da ganin mai shari a saadatun tai mashi bayanin komai da zamu tafi na kawo hamsi na bashi nace ga goro. Haba abin nema ya samu aiko take ya aika yana neman shi washe gari za a zauna kotu bai ji wani tsoro ba don yasan dubu ashirin na raba su da alkali. Ya rigamu isa kotun don yaga alkali nan ya cin na mai dubu ashirin din ya karbe da farko sulhu ya kiramu yi don dani aka je amma nace ban san hakaba nan na dan turza har ina cewa idan sharian baiyi anan zamu tafi abuja. Kajini fa sai alkalin ya rude nace idan mun tafi can ai akwai awon da za a yi a tabbatar idan na shi ne koba nashi ba. Sai ga Isah mai mangyada na share gumi a fuskan shi yana cewa ai maganan bai kai can ba ciki dai nawane amma kuma ai ba wurina kadai take zuwa ba. Saadatu tai saurin rantsewa akan bata taba zuwa wurin wani ba in ba shi ba nace tun da bai yarda ba abari kawai aje birni a hadu a can . Daga alkali har mutumin suka fara cewa haba ki kwantar da hankali abi maganan sannu a hankali a fahinci juna. Kowan su na gudun zuwa gaba don ba zasu ji dadi ba sai suka ce mu fito waje suyi shara muka fito wajen muka basu wuri. Kiran abikin yaya Sani sukayi suna tambayan shi wai yanzu may na zama ne sun ga na waye da yawa idona ya bude sai yace masu kai yanzu fa ta wuce sanin ku. Don wani hamshaki daga Abuja ne yazo neman auren ta sukace gaskiya kan na ganta haka idon ta ya bude da yawa. Sun fito suka kiramu ankan ya yarda zai karbi cikin nace ita fa to sai ya fara shafan gumi alkali dai ya tillasta mai akan idan ta haihu za a daura masu aure. Muka samu madafa akan ta sai da naji ta sauke wani ajiyan zuciya don a kusa da ita muke da muka fito yana yi min magana ban tsaya ba. Muka dawo gida sai da dare na muka samu baba ni da yaya Sani mukai mashi bayani halin da ake ciki kan Saadatu din. Bai iya magana ba sai hawayen da yake yi kawai muna bashi hakkuri har ya daina mun fita ne ya kira su mama gaba dayan su yana masu bayani abinda muka zo mashi dashi. Nan inna ta tsaya tai tagumi ta rasa abinda zata ce sai kuka aka bata hakkuri haka dai suka watse ni har na kwanta sai ga inna dakin mu. Ina ganin ta na mike zaune don ban san da may tazo ba wuri ta samu takai zaune sannan ta soma maga Safiya wurin ki nazo nace to inna gabana yana faduwa. Ban san abinda zance maki ba ga kokarin da kikayi ga yar uwar ki indan bake ba da haka zama zauna da wanan bakin cikin a rayuwan mu. Don Allah kuyi ta hakkuri damu karkubi ta namu kishin mu ba karewa zaiyi ba sai ranan da muka kare nai murmushi nace inna kudai yi hakkuri da junan ku. Ummina tana zaune batace muna komai ba har inna ta fita tace munafuka kamar da gaske nayau ne kawai baikai ciki ba don bata san kuya ba har zatazo wai wani godiya. Nace kai ummi baku dai barin halin ku wanda kukeyi a kan shi ma yana fama da kan shi bai son fitina wallahi. Ummi tace tadai bari ita da ta dauki duniya da fadi yar bakin cikin mata kawai na kwanta ina mata dariya nace kishin ku dai bai karewa. Kwana goma na kara jikin baba yayi sauki sosai na fara shirin komawa don kullun su yan biyu waya suke suna tambaya na yaushe zan dawo sai ince masu gobe. Damuwan da sukeyi yasa nace zan koma nan muka fara shirin tsaraba abin da nasan suna so shi muka saya zan je masu dashi tsaraba. Sai da na shirya na sa ranan tafiya mu nan yaya sani ya zake dama yana damuna yaushe zamu tafi sai gashi nace mai ranan asabar mai zuwa zamu wuce. Ranan ina zaune na dawo sallaman uwayena ta famnin ummi na ina cire kayan jikina dana sa waya na yai kara ina dauka naga yaya Saadune. Da murna na na dauki wayan nan na zauna a bakin gadon ummi nace yaya ina kashiga nayi kiran wayan ka yafi a kirga baka dauka ba. Yace kedai bari wasa wasa nayi tafiya zuwa ghana sai gani har togo shiyasa ba a samu na ko an kirani. Nai mashi sannu da zuwa yake ce min yanzu ma yazo ne matar shi zata haihu shine yadawo gida yace kin san halin gwagon ki. Idan bani nan ba komai zasu yi ba shiyasa na dawo gida don ayi komai a gabana nace Yaya ashe zamu samu karuwa kwanan nan. Nace idan na dawo lagos zan zo inda kuke yace zakizo lagos ne nace ai yayanan nake yanzu. Yanzuma nazo gidanane baba baida lafiya shine nazo amma ya samu lafiya yace subbahanallahi may ya samu baban ? Nace ya samu sauki ai amma yaji jiki sosai wallahi amma yanzu yana samun lafiya yace a gaida mashi baba insha Allahu zai shigo kafin ya koma. Yace yaya labari safiya ina fatan komai na tafiya daidai ko nayi murmushi nace yaya komai lafiya sai dai mun hadu kawai yace akwai labari kenan ? Dariya nayi nace ya gaida matar shi yace zataji zan fada mata kin ce zaki zo nace insha Allahu zan zo. Mukai sallama na kashe wayan ina jin dadi a raina na yaushe rabo ina fada ma ummi ya na gaishe su wai matar shi nada ciki zata haihu. Addu a tai masu ta na Allah ya raba lafiya nace amin muka dan taba hira da ummi akan matsalolin duniya na gidan mu dana waje. Sai ranan jumma a inna tasan da tafiyan mu duk ta rude sai ta kira yayan a daki tana ce mashi yanzu kai don kasada binta zakayi baka san mutum ba baka san sanaar shi ba. Baka gudun aje a yanke ma kai ko a sayar dakai kaida ganin wanan mutumin kasan kudin shi ba na kai sake bane kuma gashi yaro ina zai samo kudi irin haka ? Da sauri ya katse uwar da cewa ke inna zaki fara ko zaki fara halin ki yanzu duk halarcin da yarinyan nan tai maki baki gani ba zaki nemi wani sheri ki lakaka mata. To ki iya bakin kin ki kada ki je ki zauna da wani kiyishi ya fita muji kunya yarinya na bin mu da arziki ke kina binta da sheri Saadatu dake zaune tace fada mata dai ko zata ji . Yace nidai zan bita ki min addua Allah yasa karshen zaman banza ne yazo in samu abin yi acan in dawo maki da arziki sai lokacin tace to Allah ya sa hakan ne kadai kula da kan ka don Allah. Ya fito nikan shiri nakeyi na zabi kaya cikin wanda nazo dashi naba Saadatu na raraba masu kayana wanda naje lagos dashi don yanzu ban iya sa su naba mutanen gidan mu. Da dare driver ya iso don sammako zamuyi tun da safe zamu bar garin ranan mun raba dare da ummi muna hira sai wani lokaci muka kwanta tun da safe muka kama haya nabar su da kewan mu muma muna kewan rabuwa dasu. ZAINAB IDRIS MAKAWA SEENABU 8/14/20, 7:12 PM - Ummi Tandama: BAHAGGON, , , , , , 🧕🏿4️⃣3️⃣🧕🏿 YAN UWA BARKAN MU DA SALLAH DA FATAN MUN WUNI LAFIYA YAYA AIKI YAYA SHAN KAMSHI ALLAH YA MAIMAITA MUNA AMIN. Mun yi nisa ga tafiya yaya Sani da driver nata hira ina naya ina karatu a wayana har muka kai wani gari driver yace zai tsaya yasai ma iyalin shi abu. Suka fita suka barni a cikin motan nan na dago kaina ina kalle kallen garin mutane nata hada hadan su. Nace a raina kowa yanzu wirin nan da abinda ke damun zuciyar shi atake na tuno a yadda na bar gidan mu don dai na tabbatar da inna kiran da taiwa yaya Sani jiya da dare magana ce a kaina. Hango su nayi sun riko ledoji ga abin saya inkai tsaraba babu hali don nasan jirgi zanbi in koma kamar yadda nazo. Suka dawo suka shiga mota muka fara hanya sai lokacin nace wa yaya Sani mutanen gida dai na tuna. Yace ai baba ya samu lafiya yanzu baki ga har kofan gida ya rakomu ba nasan tunda yace afito mai da tabarma anan zai zauna. Nace ni ban san lokacin da rikicin gidan mu zai kare ba kullun ace sai makwabbata sun shigo rabon fada a gidan mu. Yace ai ba laifin kowa bane sai inna kin ga ana shigowa raba mama da ummi fada inma har matsala ya afku a tsakani su ba mai tsawo bane kowa ya bari. Amma ita inna da kowa tana yi a gida har baba har yaran gida kin ma san abinda ta fada min ne jiya kan tafiyan nan namu ? Sai nace inna dai nidai Allah yasa su bari yace to amin amma da wuya su bari din don ko kowa ya bari na tabbatar inna ba zata bari ba. Sai dai yadda kuke hakkuri kuna take halinta kucigaba dayi har Allah ya kawo muna dauki ajiyan zuciya nayi nace Allah ya kyau ta. Karfe biyu saura muka shiga Abuja nan yaya ya dinga baza ido wurin kallo nima din ba a barni a baya ba don kallon abin mamaki da aljabi nakeyi don garin yadda yake komai a tsare. Direct gidan Sulaiman muka nufa don daddy ya koma lagos ko tun satin da mukazo dashi sulaiman din ne ya fito ciki bayan mun shiga mun zauna a wani irin yanayi. Da ganin sa baijin dadin jikin shi sai dai yana dauriya irin na maza cikin karfin hali yana muna sannu da hanya. Mun gaida shi a cikin ladabi da biyayya ya samu wuri shima ya zauna yana kara yiwa yaya sani yaya hanya yaya sani daketa washe baki ya amsa da lafiya. Ya tambayi jikin baba muka amsa mai da sauki sosai tun wanan maganan naja bakina nai shiru suke hira sama sama yayin da mai aikin shi ke ta faman jera abinci wanda nasan don zuwan mu aka girka shi. Driven da muka zo dashi ne yashigo falon yake gaishe shi ya amsa mai cikin dakiya irin na masu gida da yaran su yake tambayan shi yaya hanya ? Ya amsa mai Alhamdullahi ya mike zai fice sai sulaiman din yace kada kai nisa don four zaka kai madam airport zata tafi lagos yau. Sai lokacin na sauke ajiyan zuciya na dan dago na saci kallon shi ban san shima kallon nawa yake yi ba sai ya dan murmusa yace ga abinci can an shirya maku bissimillah ko. Dagani har yaya Sani ba wanda yake da alaman motsawa sai naji yace barin dan fita na baku wuri kunji dadin sakewa sai dai ba dadewa zanyi ba zan dawo. Ya mike ya fita ya barmu nan sai lokacin na dago na kalli yaya sani nace yaya kaci abinci gashi can saman table anjera. Ya juyo yace kefa nace a a yaya ban jin cin komai yace may kikaci tun fa karin safe da mukayi gida ne a cikin ki nace yaya ban iya ci ne gaskiya. Mikewa nayi shima ya tashi ya bini zama nayi ina nuna mai yadda zaici koma duk ya rude yaga abinci kamar a banza. Ya sake jiki yaci sosai ina kara fada mai ya rike amana da gaskiya don zai yuyu gwada ka zai yi ya ga halin ka yace . Safiya kada kiji komai akaina insha Allahu zaki samay ni kamar yadda kike son in kasance nace nagode yaya. Yace safiya aini keda godiya ina na taba tunanen zan zo irin wanan wirin a rayuwana gashi ta dalilin ki Allah ya kawo ni. Yace wanan mutumin waliyi ne Safiya akwai mutunci a gare sai dai muyi fatan Allah ya sanya Alheri ga alamarin. Kamar yadda yace ba zai dade ba haka din ne kuwa ya shigo muna da sallaman shi mukai mai sanu da dawowa yaji dadi har cikin ranshi. Ya nasa a zuciyar shi dama ace nazo kenan ba tafiya zan yi ba don yau da ya samu masu mashi sannu da zuwa agidan shi har yaji daban. Ya samu wuri ya zauna yana cewa i hope kunci abinci sai nace mun ci yake cewa good yaya ne yace a a Safiya nayi da ita taci bataci komai ba. Yace a wani irin cool voice why Safiya ko kina ganin zan cuta makine da bazaki ci abincin gida na ba ba fa anan aka girka ba odan shi nasa akai maku don gidana gidan gwauro ne. Nace ba hakana bane na koshine yaya Sani yace haka take bata son cin abinci ko a gida sai yace a a baki ko kyauta min ba. Why kike wasa da cin abinci bayan kin san halin da muke ciki don Allah ki bar wasa da cin abinci please ? A sanyaye nace mashi tau yace good sai yayi dan shiru can ya nisa yace zaki barmin yaya Sani anan idan mun gama abinda ya kawo shi zai koma gida. Nace an gode yada dan harare ni ya ce ban so na fada maki ko yanzu nima basu zama yan uwa na bane ? Nace ban ce ba. Yace barin dan shiga na fito sai ki shirya nan ya mike ya shige ya barmu a falon yaya sani ya bishi da kallo sai ya juyo ya dube ni. Yace Safiya kin dace kin samu miji dai dai da halinki murmushi nayi nace Allah yasa yaya don ni yanzu tsoron auren nake yi don ban san halin da zan tarar ba saboda auren Ahmed ya sani tsoron maza. Kibar wanan maganan don Allah auren Ahmed ai auren kaddarane ga kowan mu kibar tunawa don Allah. Kuka na fara yaya sani na bani hakkuri yana cewa ki bar kuka don Allah kada mutumin nan ya fito ya samu kina kuka bamu da abinda zamu fada mai. Jin haka yasa na dakatar da kukan nawa nace yaya dole in kuka don in ina tuna wanan auren sai inji dama mutuwa nayi. Yace subbahanallahi safiya kibar wanan magana don Allah hakkuri zakiyi mana gashi ubangiji na son ya musaya maki da alherin sa cikin hikima irin ta ubangiji. Kan shi ya cuta idan yayi maki ne don ki wulakanta suka ci amanar ki Allah ya tausaya maki yaba ki wanda ya fishi ta ko ina. Shiru kowan mu yayi zuciyar mu tana tunane kala daban daban sai ji mukayi ya fito daga dakin haka yasa mu natsuwa . Sallah yace muyi kanfin na wuce suka fita da yaya sani zuwa yin nasu sallahn suka barni nan zaune Da yake ba sallah zanyi ba nan na zauna naci gaba da damuwa a raina ina mai jin ba dadi a zuciya ta tare da bin gidan da kallo. Sai gashi ya dawo nan yake cewa na shirya nace eh yace na tashi mu tafi kai yadan dafe nace sannu sai ya sake yai murmushi. Nace kamar baka da lafiya ko kallona yayi yana girgiza kai yace yaya akayi kika sani ? Nima murmushin nai mashi nace tun shigowan mu naga hakan a tare da kai ban dai yi magana bane kawai. Yace don baki damu dani ba komay ? Nace bagashi na maka sannu ba yanzu? Yace yana kokarin tashi wallahi jikin nawa ne yadan motsa min kwana biyun nan kuma laifina ne nai tafiya ban dauki magani na ba. Nace haba dai may yasa kai ko ? Yace da rabon insha wahala haka ne. Yace tashi muje kada lokacin ya wuce muna nan yau na shiga uku da madam don na fada mata azo airport a dauke ki. Mikewa nayi yana gaba ina binshi baya zuwa wurin da mota ya ke kafin mu karasa inda su ke yace kayan na nan sutura naki ne sai tsaraban mutanen gida kuma sai na zo idan naji sauki. Nago, , , ban saki kimin godiya ba kaina nayiwa don yanzu hakkina ne na baki duk wani kula da kike so numfashi na sauke. Don ya hanani magana ina isowa driver ya bude min mota muka na shiga shima ya shiga yaya Sani da driver a gaba. Ko da muka isa ban dauki lokaci ba jirgin mu ya daga sai lagos shida da rabi muka sauka inda naga anty ce da kanta tazo dauka na sai faiza. Da murna suka tare ni bayan an dauko kaya na muka muka nufi gida yaran basu gida sun fita da daddy sai fati ce kadai a kida. Itama ba laifi ta tareni ba yabo ba fallasa don tun da tace in andawo bata sake fadin komai ba kamar bata san jiyan mahaifina naje ba. Ban shiga da kayana ba na ware wanda nazo masu dashi da wanda ya bayar a kawo masu murna ta shigayi tana cewa . Safiya keda kika je jiyan kika tsaya muna tsaraba haka mai yawa ta bude naman da aka soya na zabbi wanda kaunan mama ta soya muna shi yaji hadi ta fara ci. Tace kai Safiya mai wanan naman idan da agarin yake ai kullun ina shagon shi ke kinji nama zau da dadi ta bude kayan miya taita murna ganin na hado masu kayan miya na garkajiya ta shiga yabawa kamar nakawo masu wani daula. Tasa funke ta kwashe kayan zuwa kitchen don su faiza sun far ma naman da ci tace su bari hakana sai ta dibawa daddy na shi. A dakina muna like da su yan biyu da suka mane min sai hira suke so in masu na kauyen mu, suna son hiran kauye sosai sai faman tambaya na suke yi ina basu amsa sai da daddy ya dawo ya kirasu. Na fito cikin dogon riga sai hijjab dana saka a sama yar karama don bani zuwa gaida daddy hakana sai dai idan ya girshe ni a gidan ba hijjab a jikina kuma idan ya samay ni hakana bani iya sakewa dashi. Yana gani na ya na cin naman dana zo kasu dashi anty na gefen shi zaune itama naman take ci yace a a amarya andawo. Kunya ya kamani na soke kaina nace daddy mun samay ku lafiya yace lafiya Safiya yaya baban naki da jikin ? Nace yaji sauki yace a gaishe ku ai mashi godiya a wurin ku sai yace ai ba komai Allah dai yaba shi lafiya. Nace amin tare da mikewa daga tsugunnin da nayi har na juya zan wuce sai naji yace ashe sulaiman ya samu zuwa garin naku ? Na juyo tare da dan dukar da kaina kasa saboda kunya ya sake cewa yanzu sai batun aure don bana son a dauki wani dogon lokaci ba a yi ba . Bandai yi magana ba na juya na wuce zuwa dakina inda ma na rufo dakin don ina son in duba kayan da ya sawo min shake a troler. Sai da nagama komai na jawo akwatin na buda idona ya fara tozali da wasu irin dogoyen riguna masu kyau da daukan ido . Guda guda nake fitar wa saida na fitar da kala bakwai sai kuma wasu lace da aka dinka su kamar an gwadani guda ukku suma. Ya tashi kala goma ko wani da gyalen shi da takalman shi ido na runtse tare da sauke ajiyan zuciya nace a fili Allaj miskara ziratin . Yau ni safiya keda wanan kayan da sai a film ko a jikin wata data kai, nake ganin su yau ni safiya gani dasu a matsayin nawa ga wa yanda ya saya min kafin in tafi gida. Na hada suka tashi sha biyar kenan nace wanan wani irin mutum ne da baya jin kyashin kashe kudin shi haka sai naji ina son kiran shi a wanan lokacin in dada mashi godiya. Waya na mike na dauko bayan na mayar da kayan na kirashi ringing uku ya dauka yanayin shi kamar na mai barci. Yaya jikin na yimashi yace yaji sauki yace kin sauka lafiya kin samay su lafiya ko ? Nace suna lafiya sai dan shiru sai naji yayi murmushi nace dama dai na bugo inji yaya jikin naka yace ashe andamu dani ke nan da har za a kirani. Murmushi nayi kamar yana gabana sai nace yallabai kuma wani hidima akaimin haka yace yes kin san yanzu matar sulaiman kike dole ne nayi maki ko kina son a ganni cikin sutura ne ke kuma azo a ganki haka ? Nace to na gode kwarai sai naji ya kashe wayan murmushi nayi nace har kullun idan kai min alheri baki bazai gaji dama godiya ba don kacancanci hakan. Gidan Ahmed dana zauna har nabar gidan ko kyale bai hada ni dashi ba banda tsaraban kanjamau dana samu koma wani hali yake yanzu oho ? Muna gama wayan dashi ya tuna da cctv din da ke gidan ya jawo ya hada ya fara kallon barin mu gidan da yayi da yaya sani. Don yaga fuskana na sai ko ya fara ganin badakal da muka yi da yaya din tun fitar shi har shigowan shi da shiga dakin shi da yayi ya bar mu. Lumshe ido yayi yana jin wani iri a ranshi yanayin da yaji a lokacin da haka ya samay shi har yakwanta ciwo don bakin ciki gani yake a lokacin kamar zai mutu ne a take. Kamar ba zai yi wanan rayuwan da yake yi ba yanzu har da fadawa vikin soyayyan yarinya karama da yake jin shaukin ta akoda yaushe. Lumshe idon shi yayi yana jin wani irin yanayi a zuciyar shi a haka barci ya dauke shi da tunane barkatai a zuciyar shi. Washe gari da ya tashi sallah yayi bai kara kwantawa ba yayi abinda zai yi ya fito yaya Sani ma ya fito yana falo zaune shi kadai. Yana ganin ya fito yake ce mai ina kwana yaya ce yaya sani ashe ka tashi ya gaida yaya sani din nan suka zauna suna dan hira a kaina a wurin yaya sanin ne yaji labarina tsab ba ragi ko kari. Yace in sha Allahu karku ji komai a kaina zaku samay ni da yiwa yar wanka a dalci sai dai idan wani abu ya fito daga gare ta. Yaya Sani yaji dadi sosai har ya kasa boye farin cikin shi sun karya yace zai fita sai ya dawo akwai maganan da zasu yi da yaya sani din. Ya kara da cewa idan yana son fita ya zaga gari yayi magana sai a fita dashi driver yana nan waje Kwarai yaya sani yake jin dadin zama garin ko ba komai yaci mai kyau yasha mai kyau idan zai fita ga mota nan a fita dashi yana kallon gari Gashi har yau sulaiman bai samu zama ba balle suyi maganan da yace zasuyi dashi shi kuma yana cikin fargaba don bai san maganan da zai mashi ba. Ko yaushe muna waya da yaya sani din yana fada min daular da yake ciki a gidan na sulaiman din Nakan yi mashi dari idan yace Safiya kin ko ga yadda na koma wani dan birni dani sati gudan man danayi a gidan ku. Nakan ce kai yaya wai gidan gidan mu yana can kauye gidan sulaiman din dai sai yace gidan ku mana aini inna nake son tazo taga irin gidan da Allah ya nufa zaki zauna aciki. Muga yadda zata yi ranan nasan bata da bakin magana nasha gayawa inna tun kina yarinya akan ta daina irin abinda take gwada maki don bata san abin da Allah zai mayar dake ba wata rana. Amma sai inna tace min wai ni yaro ne bani sani komai ai yadda uwar ki take yar kauye basu da komai kuma diyan ta haka zaku taso baku da komai. Yanzu gashi Allah ya gada masu shike da komai yayi ikon shi a kan ki wanda nasan har duniya ya nade gidan mu babu mai cin maki a ratuwan duniya. Nace kai yaya banda sheri dai don kaga inna bata nan kai mata kaza fi yace safiya ke baki ganewa ne inna fa sam bata son kowa a gidan mu in ba mi diyan ta ba ni kuma wanan halin nata yana damu na sosai a raina. Nakan yi mashi nasiha akan ya tuna fa inna uwa ce a gare shi sai yace ya sani shi dai halinta ne baya so sai nace sai hakkuri da iyayye yaya. ZAINAB IDRIS MAKAWA SEENABU 8/14/20, 7:12 PM - Ummi Tandama: BAHAGGO, , , , , , 🧕🏿4️⃣4️⃣🧕🏿 DA FATAN ANYI SALLAH LAFIYA ALLAH YA MAIMAITA MUNA NA BADIN BADADADA YA BAMU CIKAWA DA IMANI A ZUCIYAR MU, , , , Sai bayan kwana takwas ya samu zama da yaya sani din bayan sun gaisa dashi ne yake cewa yaya sani dama maganan da zamuyi akan yadda za a gyara gidan nan naku ne kafin daurin auren mu. Yaya Sani ya dago ya kalleshi da sauri yace kana nufin gidan baban mu ko ina yace cikin gyada kai eh nan nake nufi a gyara . Ya ce dashi dakuna nawa ne a gidan ya fada mashi yadda tsarin ginan gidan mu yake sai yace ba a samun fili daga waje sai a kara yawan fadin filin gidan. Yaya Sani yace daga gaban mu har bayan mu filin babane wanda yake shuka masara da damana a cikin su don haka akwai fili sosai daga bayan. Yace abu yazo ka da sauki nan ya fitar da plan din yadda yake so a yi ginan gidan namu nan yace gobe in Allah ya kaimu nake son ka tafi amma kuma idan akwai fili a kusa daku kadan ina so don akwai abinda zanyi dashi. Yaya sani ya rasa abinda zai ce mai sai ya kama kuka kawai don bama zai iya bude baki shi ya yi mashi godiya ba. Ranan haka ya wuni suku suku yana tunanen wai gidan su ne za a mayar kamar na yan birni a garin mu gidan bulo da bulo wanda sai wani da wani suke ginan bulo da bulo zalla. Gaskiya Safiya ta kasance alheri a cikin mu dan ta zama muna hasken rayuwa shi ko ma a haka aka tsaya ai ta wadatar dashi don ya samu karuwa. Washe gari tunda safe ya gama shirya mai komai na tafiya yaya sani ya fara hanya shi wanda zai mayar dashi gida. Sai yamma suka isa don sun tsaya hanya sun sai doya da su majan da sauran tsaraban Abuja suka kama hanya. Mutane na zaune sunyi daba kamar yadda yanzu maza suka koyi yi a ko wani gari gungu gungu ya shigo garin sai budawa yake yi shi a dole ga dan birni ya dawo. An bi motar da kallo har ya tsaya a kofan gidan mu abokan shi na ganin ya fito suka dauki ihu shiko sai faman washe baki yana mika masu hannu . Da kyat ya samu ya shiga gida bayan an gama kwashe mashi kaya daga cikin mota zuwa cikin gida. Yara na shiga gidan da kayan sai suka nufi kofan ummina da shi kamar yadda ya fada masu sai inna tace maza su kawo kayan a kofan dakin ta. Yana shigowa ana mashi sannu da zuwa bai ko amsa ba ya hango an tara tulin doya kofan inna yace kai amma yaran jan nan suka zube kayan nan kuma bayan na fada masu inna zasu kaiwa. Inna tafito da sauri daga dakin ta tace kamar yaya akai kofan Rabi kuma ba kai kazo da kayan ba ? Yace kayan ummi ne don ita surikin ta yace a kawo wa don haka ku kwasa ku mayar don Allah yace ma yaran dake shirin fita daga gidan. Bayan an gama kawarwa sai da ya tabbatar sun kwashe komai ya kara yana cewa mama, mama ga mutan Abuja sun dawo fa. Mama tace ai naga kashigo kana ta sababi da yaran ta fada a fakaice yace wallahi fa ga inda akace sukai abu sun kwasa sun kai wurin da bashi ba. Inna tace muma Allah ya bamu ba sai anbamu ba ta diya har ana daga muna kai a cikin gida yaya sani ya kada kai yace inna ke nan. Kin ko san gidan da Allah yakai Safiya kuwa inna da kike fadin wanan magana haka gida ne fa gidan bene sai inna din ta katse shi tace rufa mana baki sakarai kadawo kenan da katobaran ka kamar , , , Tau tau baba ya fada may akai wa cirko cirko haka kuma ya fada daidai yana shigowa gidan da leda baka a hannun shi. Mama tace umm umm mutan Abuja ne suka iso muke shan labari yace to kai haka akeyi kazo da mutum sai ka barshi a waje kuma ? Sai lokacin ya tuna da yabar driver a waje baiko kai mashi ruwan sha ba sai inna tace ya kai kai ruwa yaya nan yana fadi ba a tambayeka ba. Mama tace ai abinda ya gani yake fadi magana ne yakawo magana har yake fada muna yaya Sani ya fita daga gidan yana aiken yaro ya sawo mai ruwan pure water. Bai shigo ba yana can yana nema wa bakon shi wurin kwana don haka bai samu zama su gaisa da mutanen gida ba ranan. Sai washe gari tun da safe inna ta samu baba a dakin shi wai yaya sani yazo da tsaraba inna takama tasa shiyan ta. Bata raba ba yace anya Rabi zatai haka kuwa a gidan nan amma barin kira ta inji dalilin ta nayin haka din ? Da bi ar bane in magana ya kama ya kirasu dukan su don haka har da mama aka kira suka zo bayan sun zauna yace da ummi na. Rabi yaya akayi kuma sani ya dawo da tsaraba kin kwashe kin tura dakin ki ko dan tsaraban ya fito daga gefen diyar ki ne kikai haka don yanzu Rakiya ta samay ni da maganan . Salati ummina ta saka tace ni malam da dare fa Sani yazo da kayan kuma tun fitan shi bai dawo gidan ga ba balle inji yaya kayan suke ya dai ce ma yaya akai kayan kofana . Sai mama ta tara tace kai ba haka zancen yake ba da yara suka shigo da kayan ita Rakiya tace su kawo kofan ta. Sani na shigowa yace su kwashe sukai kofan Rabi surukinta ne yace a kawo shine ma ka shigo ka samay mu muna maganan dashi jiya. Ko da dare Rabin ta samay ni da zancen kayan nace tabari har Sanin ya shigo muji yaya kayan suke sai kuma nace ta kwashe tasa daga cikin dakin ta don sata kuma da dabbobi. Ya juya ga inna yana ce mata kinji dama na fada maki tun farko Rabi bata yin haka ke gajin hakkuri gareki Rakiya. Ta mike zabban kuya tana cewa in ba a bayarwa ne a barshi mana doya ne mutum bai taba ci ko manja tana kokarin fita yaya Sani yana shigowa gida neman kulan da zai ba bokon shi abin karyawa a ciki. Ummi ya nufa yana kiranta yace ummi don Allah bani kula zan sai ma boko na abin karyawa ta mike a kasalance tana cewa dashi ai nasa an mashi abin karyawa ko. Yace da kyau ummi ashe barince mai abincin ta wuce din har na tsayar da ita baba da yaji muryan shi yace kai sani kai ka dawo baka zauna da mutane ba. Yace baba ina zuwa akwai labari mai dadi yau a gidan nan barin ba bako abin karyawa jin haka da inna yayi sai ta shiga daki ta aika yaro ya kira yaya sani. An samay bai ko tsaya sauraren yaron ba ya korashi ran inna yakara baci sosai dashi ta cika fam tana jiran shigowan shi gidan. Don taso ta jamai kunne akan in alheri ya samo da kada ya fada kowa yaji a gidan subar zancen a yi su dakin su ba sai kowa yaji ba sai ga yaya sani din yaki shigowa. Sai da ya gama da bakon ya samu shigo dakin baba ya nufa direct nan ya samu baba yana shirin fita kasuwa don yakan dan leka saboda sabo kasuwan. Yace baba mun samay ku lafiya yaya jikin naka baba ya amsa mai da Alhamdulillahi baba yace yaya kabar su can ya gyara zama yace lafiya . Ai ita Safiya tun ranan da muka rabu nan ta hau jirgi ta wuce lagos daka can bata kwana abujan ba don ba mace a gidan. Baba yaji dadi yace dakyau dama tunanen da ya tsaya min acikin raina ke nan yaya yace ai baba sai kaga gidan da aka gina ma Safiya. Wai ita zata zauna a ciki da mijin ta baba mutumin nan ba karamin mai kudi bane ko a abujan don gidan kawai zai nuna wa mutum haka a zahiri. Baba albishirin ka yace goro sani don naga a rude kake yace ai dole ne baba kaga zuwan nan da nayi baba ya amsa mai da eh sani. Yace baba nazo ne da shirin rushe gidan nan gaba daya a gina ma wani. Baba yace kai sani a cikin hankalin ka kake kuwa koko dai ? Yace wallahi baba abinda ya kawo ni ke nan yanzu yau din nan zamu je birni muzo da masu aikin da zasuyi ginan don yace bai so ya wuce wata daya ba a gama komai ba. Ido baba ya zaro yace Allahu Akbar wai sani da gaske kake yi ko kowa wasa yace wallahi baba da gaske nake yi abin da ya kawo ni ke nan yanzu haka. Su mama ya kwala ma kira yana fadin kuzo kuji ikon Allah da sani yazo muna dashi gidan nan. Da yara da manya suka nufo dakin baba nan yace yaya sani ya kara maimaita abin da ya fada mashi ya mayar masu. Gida ya dauki ihu mama tace haihuwa tai ranan ta safiya kin kai diya Rabi kin iya haihuwa tankar da dubu. Mama na guda ummi ko ko bakin magana bata samu ba inna tace a dai yi sannu kar aje a debo muna wahala muna zaune zaman mu. Don yan birni babu abinda basu iyawa sai ta tashi ta fita daga dakin tana maganganu tana fadin ba inda zan daga ni. Tana fita ummi na ta nisa tare da fadin anya malam ba a bin abinga sannu ayi binciken wani irin miji yarinyar ta kwaso muna kada idon mu ya rufe. Yace nima dai abinda nake tunane kenan yaya Sani yace zaka iya yin bincike mutumin da keda company na tayoyin mota da da gidajen mai zaku tsaya yin wani bincike. Su wayanda take wuri su amana basu san ya kamata bane da zasu hada ta dashi basu hana ba ya mike yana fadin ni zamu shiga birni yanzu sai na dawo. Kaunana baba yace ta lalabo ni a waya sai aka samu akasi ba layin neatwork wayan bai shiga ba lokacin. Zuwa rana su yaya sani suka zo da mutane masu aiki har cikin gida suka shiga aka shiga aune aunen gidan da baysn gida inda filin baba ya tsaya. Za a fara daga dakunan su inna don haka zasu fake a wani wurin sai ko inna tace bata san da hakan ba sai da baba yayi da gaske yace sai dai tabar mai gidan shi. Mutane suka shiga tsakanin su duk wanda ya tambaya sai a fada mai mijin Safiya ne da ta samu ya aiko a rushe gidan nasu. Karamin gari da daukan magana sai magana yabi gari washe gari suka tashi da masu aiki a gidan. Inda suka koma gida jen yan uwa da zama suda yaran su ummi na kan gidan gwagon ta koma ita da yaranta da kayan su. Mama ma haka inna kuma gidan yan uwanta ba wanda ya yarda ta koma can dole family house din su baba ta koma. Ko wani gida yaya sani yakai masu abinci kamar yadda aka umurce shi yayi aiki ake yi ba dare ba rana gari duk an dauki maganan kwaaaa. ********* ********* ********* Jinya yayi so sai duk ya ramay ya fita hayacin shi karshe ma sai da ya dawo gidan gwago akai jinyan shi. Yanzu kowa yasan abinda ya samay shi don tun a karuwan shi aka san suna dauke da cutan an kaita gida ta mutu can. Gwago kulun kuka takeyi tana fafin Ahmed baka kyauta min ba kasa na cuci diyar mutane gashi yanzu ni da garin mu amma ina kunya zuwa. Don ko naje ban san da wani ido zan kalle su ba kasa na rabu da dan uwana mutumin arziki da sanin ya kamata. Yarinyar nan tana da ma bidi amma don a raya zumunci ya rufe idon shi yace sai kai kuma akayi hakan. Ahmed dake kwace saman wani tsohon katifa yace mummy kada ki bleming dina ni kadai a cikin maganan nan ai gaban ki nake dauko mata tun ina yaro na amma baki hanani ba. Sai yanzu da abu ya baci muna ne zaki tsamay hannu ki ciki duk waja muna saboda fitinar ki baba ya bar garin nan . Kin hana ya zauna kusa damu ya ga halin da muke ciki ya kwabe mu tun yana zuwa har ya daina zuwa yanzu ya tare a gurin sabuwar matar shi. Tace abinda zaka fadamin ke nan ko bayan komai a kanka ne ya faru don yana ganin yarda nake sakar maka kudi yai magana nace ina ya fito. Nan dai sukai ta sa insa da dan nata sai da sadiya ta shiga tsakanin su taja gwago din waje kar abin yai masu yawa gashi kwance ba moriya. Zuwan yaya Saadune ya kaishi asibiti suka karbi magani har ya fara jin saukin jikin shi ya tatara ya koma gidan shi sai dai hakan bai sa yabar halin shi ba. Yaya saadu yazo gida kamar yadda yai alkawari ya samu ana aikin gidan mu gadan gadan ya samu baba yaji sauki sosai har yana dan fita kasuwa. Yai masu alheri ya dawo bai tsaya lagos ba don wurin matar shi dake shirin haihuwa ya wuce direct sai da ya isa ya kirani washe gari da karfe hudu. Ban daki na bar wayan na caji sai da na shigo ne na samu miscall din shi a nan nan nai mai kira biyu bai dauka ba ga na uku matar shi ta dauka tana cewa bai nan ne. Nace madam yaya kike yaya tsufa ta amsa min da murmushi da lafiya tace ke haka akeyi baki lekomu ba kuma kina lagos. Nace kada ki damu idan kin haihu zan shigo sai nayi maki one week zan koma tace kamar da gaske nace bari ki gani ko yanzu shiga daki ki haihubin banzo ba . Ta kwashe da dariya tace to Allah ya kaimu lafiya idan ya dawo zan fada mashi kin kira baki samay shi ba. Mukai sallama na kashe wayan na koma har kokina sai dai ban faye fita irin da ba don gidan in ba anty ke nan ba kamar suna shan kanshi. Shiya sa ban damu da shiga harkan kowa ba a cikin su sai dai ina tunanen Ita Faiza idan fati na fushi dani ne akan dalilinta na son sulaiman . To ita akan may take fushinta dani ni dai ban san nayi mata wani abu ba kafin in wuce gida. Abinda ban sani ba ashe baya na ashe sunyi meeting a kaina kan nazo na samay su a gida anty ta fifitani a kan su . Bata kallon kowa da gashi a gidan sai ni su tun yaushe suke ba a nema masu miji ba sai ni da zuwa don nazo da sihirin mu na yan kauye sai ace nice ake kokarin zuwa dani wuri. Sai suka yanke shawaran su hade mi kai ta yadda in na dawo zan rasa gane kan su sai na raina kaina a cikin su. Wanan dalilin yasa ban gane ma kan su sai waccan tabi can wanan tabi nan sai su watse su barni ni kuma dana ga hakan sai nima na fara share su kawai. Gashi yanzu na dawo sai shige da fita nake yi na doke sanin su sai suka shiga gulma wai kila ba gida naje ba mun hada baki ne da anty ta turani wurin maza na samo kudi. Tun sunayin zancen a boye har na tsura su sunayi nan nai masu tas sai suka shiga rokona wai inyi masu hakuri kada anty taji nasan korar su zatayi a gidan. Nace amma idan na karajin wani abu makamancin haka zan fada mata dan ta dauka min mataki akansu. ZAINAB IDRIS MAKAWA SEENABU 8/14/20, 7:12 PM - Ummi Tandama: BAHAGGON, , , , , , , , , 🧕🏿4️⃣5️⃣🧕🏿 YAR UWA KI TUNA NOVEL NA KUDI NE DON DARAJAN ANNABI KADA KI FITAR MIN DA NOVEL WAJE KE KUMA IDAN AN FITAR KIKA KARANTA BAKI BIYA HAKKINA A KAN KI, , , , , , , Bayan anty ta fita wurin aiki ita da yara na gama abinda zan iya taya funke na fannin aiki sai na koma daki na kwanta abina. Can barci ya soma dauka na sai naji anturo kofan dakin alaman mutum ya shigo haka yasa na bude idona don ganin ko waye ya shigo din. Faiza ce fuskanta dauke da murmushi tace ba dai kin kwanta ba ne nace na kwanta eh barci nake son in dan yi na wani lokaci. Zama naga tayi a bakin gadona abinda ta dade batai min ba sai gashi yau tazo tana yi don haka nasan da wani manufa tazo. Magana muke yi amma sai bin dakin nawa take yi da kallo kamar mai son ganin wani abu tace gida fa ya karbe ki safiya. Kin ga yadda kika sauya gaba daya kamar bake ba sai nayi murmushi nace kin san gida dadi gare shi ai. Tace sai kuma naji wani labari a bakin anty da nai mamakin jin shi wai Sulaiman zaki aura ba da dadewa ba ? Faiza ke nan idan haka ne ai gida guda muke dake da a bakina zaki ji labari sai tace gaskiya kan ai na dauka da gaskiya ne sai in ce halan baki san abinda ke damuwan shi ba. Da sauri nace may fa ? Sai tai shiru tace kardai aji a bakina fadi ba a tambayeka. Nace ai ya kamata na sani don kariya sai tace dama ji nayi ana fadin kila yana da cutane a jikin shi shiyasa bai son ai maganan aure dashi. Haka naji a gida suna fada shiyasa nace barin fada maki don ki sani kada matar gidan nan ta cuta maki don kudi. Baki ganin yadda take nan nan dashi ta kwace ma kowa shi idan ba itaba babu wanda yake shiri dashi a cikin yan uwan mu kaf. Ita kadai ya yarda da ita yake mu,amula da ita itama din nasan don kudin shi ne take hurda dashi fiye da kowa. Mamaki ya hana ince mata komai sai sauraren ta da nake yi rashin magana na baisa ta fasa magana ba. Taci gaba da fadin kin gashi nan haka yake kamar bakin bature komai nashi a ka,idance yake yin shi. Idan bai so ba sai ya nuna kamar bai sanka ba , babu dan uwan dake jin dadinsa sai wanda yaso. Haka shima bai kula kowa yana takama da kudi a cikin dangin idan kinga gidan da ya kera a bauchi sai kin kama baki. Babu kowa a ciki sai mahaifiyar shi da kaunar shi dake bangare guda amma duk girman gidan nan part din shi a rufe yake bai sa kowa a ciki ba. Ni ina ma mamakin yadda idan na gaidashi anan yake amsa min a sake don a gida baka ko ganin shi balle ma ku gaisa dashi. Nace aiko wanan halin bai kamance shi ba sai ka ganshi kamar babu ruwan sa ashe haka yake ? Ta mike ta na cewa barin koma dama shiya kawo ni in fada maki in baki sani ba kada ai maki rifa rufa saboda kudi. Nace amma ni sai banga wani kudin da zai rudi anty dashi ba don ko mijin ta ma yana dashi itama ba a zaune take ba. Sai tace Safiya kenan. Wa yaki kudi ko wa yaki kari a rayuwa balle ma ita ai ba abinda take so kamar kudi ta fadi tana kara nufar kofan fita daga daki sai ta juyo tace amma fa maganan nan ya tsaya dagani sai ke. Nan ta fita ta barni da tunane fan a raina duk kokarin da boyar Allah nan take muna amma suna fakewa a bayanta suna zagin ta. Nan dai nayi ta tunane kala kala har nagaji barci ya kwashe sai dai a cikin tunanen nawa ba abinda nake tunawa kamar abinda ta fada gamay da sulaiman din. Sai kuma abin ya tsaya mun a raina nace kardai zan kara tsundumawa ne ga auren ukuba a rayuwa nace ni kuma haka rayuwa tazo min a bahaggon rayuwa komai zan gani sai akasin sa. Karan wayan ummi na ne ya tayar dani daga barci na mika hannu na jawo wayan dake caji don na samata ringing din mamana mamana mai share hawayena. Na yi sallama ta karba nan muka shiga gaisawa ina tambayan mutanen gida tana bani amsa da suna lafiya. Tace yar nan shi kuma wanan bawan Allahn haka yasama kan shi lalura akan mu nace ummi wake nan fa ? Tace mai neman ki mana ya turo yayan ki sani da abin arziki doya sai da aka shake bayan mota da shi da manja muna murna. Ashe magana bai kare ba sai ga sani yace wai ya turo shi a rushe gidan mu a gyara a cikin wata daya anya yar nan kinyi bincike a kan sa kuwa. Kwance nake bansan lokacin dana mike zaune ba nace ummi a rushe gidan mu fa kikace ? Ta au ke baki ma sani ba ke nan ai yanzu duk bamu gidan kowa na gidan su sai inna ku ce a family house yan uwanta sunki yarda ta zauna masu a gida don sanin halinta. Assha baiyi kyau ba tace halinta ya ja mata koda akazo da zancen gyaran gidan ai sai da tai halin nata mama ku ne kawai tai ta samaku albarka kedashi. Taki kwashe kayan ta sai da mutane suka taru a kanta tonon asiri zallah abin ba dadin ji wallahi nace Allah ya kyauta. Amma ummi ni abin ya bani maki don ko yau da safe mun gaisa dashi amma bai sanar dani zancen ba. Watau yana son ya bani mamaki ko kuma baison godiya kamar yadda yace bai son yayi alheri a tsaya ana mashi godiya. Sai naji ummi tace ikon Allah shine kyauta sahihi wanda ake so Allah zai saka ma mutum da alheri. Nisawa nayi nace ummi nifa yanzu har tsoro nake ji bakiga kayan da ya saya min ba da zan dawo har akwati guda shake da kaya. Ummi tace ikon Allah shi bai gajiya ne ? Na amsa mata da kuma bai son godiya. Tace Allah ya kyauta kuma ya saka da alheri ni abinda na fahinta shine bai son azo daurin aure a raina ma inda ya dauko mata ne shiyasa yace ai gyara a cikin wata guda kacal. Nace ummi ai kowa yasan ni yar tallakane tun da ubana ba kowa bane da aka sani tace Allah ya sanmu ai nace shi kan. Mun dade muna magana da ummi a waya har ta bani gwago buka gaisa nayi masu godiya tace akan may ai nan gidane ga ummi. ********* ********* ********* Sai da nayi sallah na fito daga daki ban dade da fitowa ba anty ta shigo gidan mun tare ta da sannu da zuwa kamar kullun. Security din gidan yana biye da ita da kayan da ta dawo gidan dashi na mike na karbi kayan daga hannun shi zuwa ciki . Bata zauna ba ta wuce dakin ta nasan kaya take son sauyawa tayi sallah kafin ta fito cin abinci don haka take yi idan ta dawo a wanan lokacin. Ta sauko lokacin ta sauya kayan jikin ta tana zuwa ta zube tana fadin don Allah ku taimaka min da abinci. Ni na mike naje hado mata sai take cewa su Faiza wai ku baku da aiki sai kwanciya ko mutum na magana bakwa dagawa. Faiza ne tace kai madam kafin mutum ya daga safiya ta tafi hado maki sai fati dake ta faman dakalan wayan ta dago tace ba yar neman suna bane. Komai sai tai ta nuna ita ta kamar tafi kowa alhalin bata kai kowa acikin mu ba ita ma yar kauye da ita ba a raina ta ba zata raina mutane. Kallon ta anty keyi tace Fati ina wanan magana ya fito haka daga bakin ki har kike kokarin aibanta yar uwata a gabana. Bari kiji ba a raina mutu idan kaga mutum baka san abin da Allah zai mai dashi ba wata rana kafinta karasa sai fati tace. Ba dai wanan banza ba za ace wai tafini wata rana may zata iya gwada min ko ayanzu inba farin fata ba ni ma idan ina so sai in sayo a shago inyi. Amma ke baki da hankali sha sha mara hankali ke wai sai yau shene zakiyi hankali a rayuwan ki ? Ta mike ta shige tana guna guni na aje abincin a gaban ta don nasan bata tashi zuwa dining ci yadda take kiran yunwa take ji. Nan muka zauna da anty tana cin abinci tana bamu labarin iri kayan da suka kama a office din su na yan smogal. Nace anty yanzu may zakuyi da kayan tace idan sun dade basu iya kwata ba sai muyi option din shi gama su so. Nace wai amma anty sai kuma nayi shiru tace fadi mana tana kai spoon din abinci ga bakin ta nace babu komai. Sai tayi dariya tace haka aikin namu yake Safiya sai nayi murmushi kawai nace ai na fahinta har yamma muna wurin zaune sai sallah muka tashi zuwa yi. Ban fito ba ko da na idar sai anty ni ta aiko kira na don haka na tashi na tafi amsa kiran nata bata falo tana dakin ta don haka na haura sama. Tana zaune a kasa tana waya na shigo don haka na samu wuri gefe daya ina jiran ta ledan da ta shigo dashi ta nuna min da hannu alaman in dauko mata. Na dauko na ajeye taimin alama da in bude na durkusa a gaban ta ina bude ledan ina gama budewa ta fara ciro kayan dake ciki. Tana dubawa ina binta da kallo wanda kayane nasi yan biyun ta a ciki nace a raina ita dai bata gajiya da kwaso ma yaran ta kaya. Na nisa tare da cewa a raina haka sulaiman yake so na dashi ya cika ni da suturu ni kuma ban saba da hakan da yake son koya min ba. Muryan anty ne ya katse ni da cewa kayan suna da kyau Safiya na fara tanadin kayan da zasuyi bukin kune dashi don naga sulaiman bada wasa yake yi ba. Kin san shi idan ya tashi yin abin shi bai tsaya bata lokaci naso ace kun dan kara fahintar juna dashi. Amma kuma naga har daddy ya goya mashi baya wai ai ba bukin saurayi da budurwa zakuyi ba may za a tsaya jira kuma. Jiya ma mahaifiyar shi ta kirani akan maganan naku nake mata bayani abinda ake ciki a zancen. Nace anty ashe gida daya suke da mahaifiyar shi ta dago kai da sauri tace waya fada maki safiya ? Sai nayi shiru tace don Allah a ina kikaji nai murmushi tun da ta hadani da Allah nace Faiza. Sai naji tace munafuka yaya tayi ta sani duk wanan boyon da nake masu munafuka sai da ta gane. Kai faiza akwai gulma wallahi. To da suke gida guda da mshaifiyar shi ke ina ruwan ki tunda sai wani dalili yake zuwa ba tare zaku zauna. Koma tare ne fa anty nace mata ? Tace ai shi na gani. Wai ma yaya akayi tazo maki da zancen ne sai na dukar da kai tace lah bazaki fada min ba ? Ko dai ke kika fito mata da zancen ? Nai saurin cewa a a wallahi ita dai ta samay ni da maganan wai tazo fada min gaskiya taga kamar yana sona to shine take son ta fissheni . Don taji ana rade radin kamar baya da lafiya a jikin shi. Salati ta saka nai sairin cewa anty tace kada in fada ma kowa don Allah abar zancen a rufe don ba zata ji dadin fada min wani ba gaba tace hakane. Na dai kwashe yadda mukayi amma ban fada mata zaginta da tayi ba na boye wanan sai na sulaiman din na fada mata. Tace wa yan nan yaran gulman su yayi yawa wallahi ni duk nagaji da zaman su anan don ma zuwan ki ne da duk sun koma gida. Nace a raina don ma baki ji sauran ba aida kin rage su gaba daya sai naji tace dani gulmana fa suke yi sosai harda sakaran nan Fati da bata san ciwon kanta ba. Naiyi saurin kawar da zancen da cewa ayyawa anty kin san ko abinda uncle yayi tace may yayi safiya ban san komai ba. Nace dazun muke waya da ummi take fada min cewa wai ya tura a gyara gidan mu nan da wata daya a gama komai. Ummi tace aiki akeyi ba dare ba rana sai naga ta kwashe da dariya tace namijin duniya ai tun ranan da ya tafi mukai waya dashi. Tausaya maku yayi ya damu da yanayin da ya samu gidan ku a ciki ai ke ki godewa Allah don Allah ya kashe ya baki. Sulaiman ban sanshi da halin banza ba sai dai mutane ne da basu fahince shi ba kawai suke gani bai son mutane ne. Tace aiko zan kirashi in shamce shi don yasan mun sani nace anty da ki kyale shi maga gudun shi tace ai shine. Ke har kin ma fara fahintar halin shi tun yanzu zai ce wani dan gulma ya fada min kiko ga bazan iya ce mai ummi ce ba. Dariya na kwashe dashi nace ai sai ko ki fada tace wane ni wallahi safiya idan kin fahinci waye sulaiman shike nan kin huta. Sai dai kinyi hakkuri da shirun shi don shi mutum ne wanda bai son magana sosai haka yasa mutane suke mashi kallon miskili. San nan kuma dole ne in kaiki ki koya wasu abubuwa don ko shi din ba karamin dan gaye bane in dai zaki daure gaskiya kin huta safiya. Ta tambaye ni labarin inna da za a rushe gidan yaya tayi na fada mata nan tai ta kwasan dariya tana mamakin karfin hali irin na inna. Taci gaba da min bayani kan halin sulaiman din dana yan uwanshi da kuma halayen shi da damuwan da yake ciki. Kaina na dukar ban iya magana ba tana ta fada min halin shi ina kara fahinta komai sai goma nabar dakin ta koda na sauko ba kowa a falon har funke ta rufe gida ko don daddy yayi tafiya kwatonu. Har na kwanta ina tunanen maganganun da ta fada min a kanshi nace Allah ka bani ikon yin biyyyan aure Ina tunanen ko yaya zama zamu yi dashi har mada yan uwan shi don na fahinci sudin masu haline zurian su niko gashi iyauye na ba kowan kowa ba. Ai so ya na hana komai idan dai shi ya kamani da mutunci ai dole yan uwan nashi su soni ko don shi tun da dai dan uwan su ne na aura ZAINAB IDRI MAKAWA SEENABU 8/14/20, 7:12 PM - Ummi Tandama: BAHAGGON, , , , , , , , 🧕🏿4️⃣6️⃣🧕🏿 AMANA YAR UWA KADA KI FITAR MIN DA NOVEL IDAN KI BA WATA BAN YAFE MAKI BA, , , , , , Tun karfe shida na safe na samu wayan yaya Saadu cewa matar shi ta haihu nayi murna sosai tare da kwararo mata addua yana cewa amin cikin jin dadi da adduan da nakeyiwa yarinya. Na gama yace yaya alkawari nace yana nan daram nace so ace daya daga cikin su ummi zata zo mu tafi tare amma yanzu babu hali don gyaran gidan da ake masu yace ai ya sani. Nace ka sani yaya yace to baki fada min ba Safiya yays zanyi ido kawai na saka maki ai nace wallahi yaya nima sai last week na sani ummi ta kirani take fada min. Yace you are free don da har na kullace ki don yanzu bakiyi dani nace da sauri wanne ni yaya ai kaine nafarko a zuciyana. Yace to mu bar zancen sai kinzo muyi don baiyi a waya yace zai kira su gwago ya fadamasu do nice ta farko daya fara fada mawa. Mukai sallama ma kashe wayan ina mai farin ciki a zuciya na ranan duk wanda ya ganni yasan na tashi a cikin farin ciki. Anty tayo shirin zuwa office bayan mun gaisa nake fada mata zamcen haihuwan matar yaya Saadu itama ta tayani farin ciki. Nace zan tafi banda gobe don nayi mashi alkawarin zuwa sai naga antu batai farin ciki da hakan ba, bata bani amsa ba, ta dai fita tana muna sallama. Hakan bai min dadi ba amma zanyi hakkuri in ga tafiyan ta akan zancen don ba zan saba ma yaya Saadu alkawari ba gaskiya. Bayan na gama aiki na shiga daki na buga ma anty waya ina fada mata zancen haihuwan na matar yaya saadu. Itama tayi murna sosai tayi ma yarinyar adduan sosai nace mata ina son zuwa kamar yadda nayi masa alkawari don wanan kawai zan mashi in iya rama mai halarcin da ya gwada man. Tace dako kin kyauta yar nan nace sai dai ina ganin kamar anty bazata yarda da zuwa na ba tace sai ki lalashe ta kada kiyi gaban kan ki. Nikan shiri na fara yi sai dai ban fada ma kowa ba kamar yadda ya saba kirana a ko wani rana safe da yamma yauma ya kirani da dare bayan na kwanta nan nake fada mai cewa matar yaya na ta haihu ina son zuwa Carlaba wurin suna ya taya ni murna tare da tambaya na yaushe ne suna na fada mai tare da cewa ina son in tafi suna. Sai naji ya danyi jim sai yace yaushe ke nan kike son zuwa nace banda gobe don haka nayi ma yayana alkwari don yace yana son inzo da wuri. Don banda kamar shi a cikin yan uwa ya taimakeni a lokacin da nake neman taimako banda wanda zai taimaka min. Yace lallai kina ji da wanan yayan naki sai ki turo min da layin sa in mashi godiya nace angama yallabai. Da jirgi zaki tafiya ko da mota sai nayi saurin cewa jirgi kuma zan dai bi mota in tafi yace ban faye amincewa da batun motar nan ba. Ki dai bi jirgi ki tafi yafi tafiyan a mota sai ki kai da wuri yace zanyi magana da madam sai a san yadda za a shirya maki tafiyan dan ni bani kasan yanzu haka. Nayi saurin duba lanban wayan nashi naga daga kasar South African yake magana tirkashi nace a raina. Mukai sallama na kashewayan tare da kwantawa naja bargo na rufe ina mai ci gaba da tunane a zuciya na. Anty ta fita aiki da safe bai kirani ba sai nayi tsamani aikin da yaje yi ya dauke mashi hankali ne a can. Da ta dawo ne take ce min munyi waya da sulaiman nace a a sai tayi shiru can tace ashe kina ga zuwa Calabar din ne don naji sulaiman na fadin a sayo maki ticket din jirgi. Nace a dake eh anty gobe nake son zuwa don hakane kawai zan iya rama ma yaya Saadu halarcin da yai min a baya. Ta gyada kai tace shike nan da amma ni naga da kifita hanyan duk kansu baki daya har saadu din zai fi tunda sabon aure zakiyi yanzu. Da sauri nace anty kina ganin zan iya yanke zumuncin da ke garemu da yaya Saadu shine fa dan uwa na farko da yai min tsaye na samu lafiya. Kuma ana haihuwanan bai kira kowa ba nice ya fara kira ya fadawa idan nai haka na zama butulun a duniya har da wurin Allah. Sai tayi shiru bata kara yi min magana ba hiran ma sama sama muke yin shi da ita taje sallah azahar nima na tashi na idar na fito bata falo. Na samay ta a dakin ta sama nace anty ina son in dan fita in sayo wa baby tsara ba don kada naje hannu sake. Ok ai yanzu muka gama magana da sulaiman bance da ita komai ba nace zan wuce sai naji tace dan dakata min in zo. Na samu wuri na tsaya daga kofan daki ta mike zuwa safe din ta ta bude ta fito da kudi kashi biyu tace ga wanan sulaiman din ne yace a baki ki yi sayayya sai kuma wanan nawane asaya wa baby kaya. Nace Lah anty ai da ku barshi ina da dan kudi hannuna da na dawo gida dasu tace kin raina kenan ko da sauri na isa wurin ta ina karban kudin. Sai naji tace Safiya kamar maganan danayi akan saadu bai maki dadi ba ko nace ba haka bane anty ai gaskiya kika fada min. Sai dai shi yaya Saadun ne banga laifin shi aciki ba don bai min komai ba tsakani na dashi sai alheri har gobe don ko dawowanan da yayi sai da yaje gida duba jikin baba. Tace ai nayi tunane daga baya naga kina da gaskiya tace ki dai zabo abin kwarai don Allah kada ki kwaso shirmay. Nace to anty na gode na juya zan wuce tace dani zan kira driver sai ya kai ki godiya na kara yi mata na fita. Faiza tana ganina take tambayana inda zan tafi na fada mata sai tace zata rakani ta dan mike kafan ta. Na jirata ta shirya ta tafi ta fada ma anty muka fita tare nan muka samu driver yana jiran mu a waje muka fada mota ya fice daga gidan. Kaya na kwaso na baby da na uwa sai da na cika akwati dashi muka nufo gida Faiza take ce min tana son mu tafi tare nace sai mu fada ma anty idan zata yarda. Bayan ta gama ganin kayan ta sauke ajiyan zuciya tace wai Safiya kaya haka kamar mai shirin bude shago ai kin fanshi uban diya. Nake cewa anty dama ai fannin uba muke sai lokacin ne Faiza take gabatar mata da son zuwanta tayi saurin cewa da jirgi fa zatayi tafiyan. Ba zai yuyu kuje tare ba da dai a mota zakuyi tafiyan zan barki ki tafi Faiza bataji dadin haka ba kuma gashi taji ance a jirgi zan tafi wai. Sai yake ta mamaki wani irin asiri nayi ma anty ne haka da basu jin wuyan kashe min kudi har yaushe na dawo gida akaje airport dauko ni. Yanzu kuma ace a jirgi zan kara tafiya kodai maganan Fati gaskiya ne da take fadin tana turani karuwanci ne wurin maza. To amma kuma wanan uban kayan da muka sayo fa namay ye shi gashi kuma taji nace fannin uban jegon nake bukin dai zan tafi amma akwai dai daurin gindi wani wuri. Yadda tasan anty da kudi bazata iya biya min kudin jirgi ba har Calabar in je in dawo na kwashi kayan zuwa dakina ina shiga daki kiran shi ya shigo wayana. Ban dauka da wuri ba sai da nayi halin mata jan rai na dauka tare da sallama sai naji ya sauke ajiyan zuciya yana fadin. Ke idan ba a kiraki ba baki kiran mutum watau nace na dauka kana uzuri ne tunda banji ka ba yace ban uzurin komai fushi dai nake yi dake. Nace ni kuma may nayi yallabai ? Sai yace ashe bukin dangin mijin ki na da zaki tafi ban sani ba nace kwarai dangin shi ne nima kuma dangi na ne ba gaiyan sodi zan tafi ba sai na fara bashi labaron irin halarcin da yaya Saadu yai min a lokacin. Yace kin fini gaskiya daga baya madam ta fahintar dani ai daga baya yanzu na fahinta Allah yakai lafiya. Nace amin yace tace girgin karfe hudu zaki bi sai ki sanar dasu can azo a dauke ki nace nagode yace ban son tsaron lafiyar matata nakeyi. Ya kashe wayan nabi wayan da kallo tare da tunanen watau anty ta fada mashi abinda ta fada min ke nan da farko. Idan haka ne bata kyauta min ba kuwa zuciyana ta nasa min cewa kodai abinda su Faiza ke fadi gamay da ita gaskiya ne ? To inma gaskiya ne ni dai batai min komai ba don bazan manta da halarci ba kuma ban iya matawa da mafari. Da dare na kira yaya nake sheda mai karfe shidda azo dauka na a airport yace bazaki zo ba kenan amma safiya baki kyauta min ba. Gashi na sa rai kece zan gani cikin yan uwa da zaki zo ki zama min garkuwa don suna fadin ba a san yan uwana ba. Nace yaya karfe hudu nace azo airport a dauke ni ba wasa nakeyi ba in Allah ya yarda gobe zan shigo yaya yace masu gari don Allah da gaske nace Allah yaya. Koda gari ya waye na shirya tsab sai dai yan gyare gyaren daki da na tsaya yi don kada in dawo in samay shi ba gyara. Wayan shi ne ya shigo min muka gaisa yace an shirya ko nayi murmushi nace kamar ka sani komai na hada tafiya kawai ya rage min yanzu yace nasan dari biyu zai ishe ki yin komai su nace ma madam ta baki jiya. Nace ta bani na gode ubangiji ya kara rufa asiri amma dai kai baka gajiya da yi mani dawainiya haka ? Yace idan banyi wa matata dawainiya ba in yiwa ai ke da hajiya baaba kune dole na yanzu ba zan taba dana sanin yi maku ba a rayuwa na. Mun dan taba hira mukai sallama yake cewa idan na isa zai kirani yaji sauka na nace nagode. Mun kashe wayan ya barni da tunanen maganan anty watau kudin da ta bani dubu goma cikin kudin da ya bani ne don dubu sittin ta bani tace inji shi. Amma kada in zargeta zan bari in gani ko idan zan wuce zata ban sauran inma bata bani ba taci halas ai albarkacin ta nake ci da badon itaba ina zan samu wanan gatan. Karfe uku ta dawo gidan don tafiyan nawa take cewa nayi na shirya kafin hudu driver zai kaini airport. Nace mata tau. Uku da ashirin na fito tafiya tana dakin ta naje mata sallama fuskan ta da fara a take ce min tau safiya Allah ya kiyayye haya agaida su ina masu barka. Yaushe zaki dawo nayi murmushi nace sai dai idan na je can anty zamuyi waya sai in sanar dake tace to Allah ya kiyayye hanya na ce amin na fita da kayana Faiza tai min rakiya har waje sai da muka daga ta dawo ciki. Mun fara hanya na nisa tare da fadin mutum kasan shi baka san halin shi ba yanzu ba don Allah yasa ya fada min ba ba zan taba sanin komai ba akan anty. Bamu dade da isa airport din ba jirgi ya tashi dan wani lokaci naji ana sanarwa jirgi zai sauka mu shirya . Mun sauka na fito tare da kaya na ina faman rabon ido ko ta ina zan ga yaya Saadu sai gashi tare da abokin shi. Yayi murna kwarai da ganina yana ta faman washe baki yana fadin safiya ashe da gaske kike yi kin san Allah karfin hali nayi nazo airport kawai ba don na yarda ba na dauka kin fara wasan cousi ne dani. Nayi murmushi ina gyara gyalen kaina dake kokarin walwalewa a kaina nace haba yaya ai bamu yar haka dakai. Suka dauki kayana zuwa motar da suka zo da ita nan muka kama hanyan zuwa unguwar su sai faman zolaya na yakeyi yana fadin waiko Safiya kece nake gani a gabana ko mafarki nakeyi kin koma haka ? Ni dai murmushi nake mashi ina bin gari da kallon mamaki abubuwan zamani irin nasu na arna da kallo. A can wani ungwa mai kama dana hausawa muka shiga don akasarin mazau na ungwan hausawa ne amma na gari daban daban sai hausan su ya juye kamar yare. Mun tsaya a kofan wani gida nan yace min tau Safiya yau kin zo gidana muna maki maraba da zuwa murmushi nayi nace na gode. Mun fito suka bude bayan motar suna fito min da kayana daga ciki a tare muka shiga gidan dasu sai ga matar shi Samira ta fito da gudun ta tana min oyoyo . Muka run gumay juna da ita tace ashe gidan gidan yawa ne mai apartment da yawa ban luraba sai naji tana fadin ku fito ga kaunar miji na tazo. Nan naga mata na ta firfitowa daga sashen su suna zuwa yi min sannu da zuwa niko sai faman washe baki nakeyi ina karba masu. An shiga dani dakin su dan part ne mai kumshe da ciki da falo sai wani dan daki karami da kicin a cikin part din dakin su aka kai min kayana. Shiko yaya saadu ya rasa ina yaka saka dani don farin cikin shi baya boyuwa ranan bayan na zauna falo . Nan ta fara gabatar min da abinci da abinsha ban wani ciba sosai don banda yunwa a tare dani aka kawo min baby a daidai lokacin da yaya ya shigo yana cewa kin ga Safiya karama ko ? Na dago kai da sauri nace yaya sunan da aka samata kenan yace Sunan ki taci Safiya ko bai maki dadi ba na lumshe idona sai ga hawaye yazo min. Yace kuka kuma kike yi har yanzu baki daina halin nan naki da na sanki dashi ba na saurin kuka nace yaya bansan irin godiyan da zan maka bane. Bayan taimako gashi kuma har sunana kasa wa yarka ta fari a duniya matar shine ta fito ta samay mu zaune take cewa yaya naga kamar kina kuka. Gaki ga yayan ki ga takwaran ki kin dauka kuma sai yaya yace wai duk farin cikin yi mata takwara takewa kuka. Tace ai dole ina haihuwa na dauka sunan mummy zai sa kona mama na sai naji yace wai sunan yarinya safiya sai da nayi makin wanan irin shakuwa naku wallahi. Bari kedai Samira ni duniya yaya ya gama min komai Allah dai yabar zumunci ya raya min takwara na ta famnin addinin musulunci yasa mata albarka sukace amin. Nan muka zauna muna hira yake ce min sai yaje gida ya samu baba ya samu lafiya sosai sai dai su ummi ba kowa a gidan anata gyare gyaren gida. Na nisa nace bari yaya nan na fara bashi labarin yadda abin ya faru da irin taimakon da yake min shi da uwar dakina. Sai da ya gama saurare na yace Alhamdullahi Allah maji rokon bawan sa Allah ya amsa min addua na kullun ina rokon Allah akan kada rayuwan ki ya kare hakana baki more ma rayuwa ba safiya. Don ina ganin yadda rayuwan masu wanan matsalar yake karewa a lalace saboda rashin gata da samun kulawa da basuyi. Nacs haka abin Allah yake yaya sai dai muyi fatan dacewa da rahaman ubangijin mu yanzu. Amma yaya inda son samu ne asamu wanda zaiyi bincike kwakwara akan Sulaiman din don kada ai abu cikin duhu a dawo ana da an sani kuma irin na farko. Ya nisa yace insha Allahu kuwa zanyi kuma da yardan Allah sai Alheri don yadda yake kulakin nan akwai alaman nasara ga abin. Don da akwai matsala da tun yanzu zaki dan fahinci wani abu daga gare shi sai dai zaki iya tara matsololin da ake fadi nasa ki auna ki gani . Amma dai duk da haka zanyi kokari in bincike a kan shi don wani lokaci yin binciken yana da kyau. Na fara hamma yace naje na kwanta mu hadu da safe sai lokacin nace dashi yanzu wani sana a yakeyi ne ? Jeki ki huta da safe mayi magana naga kin fara hamma ni yanzu fita zanyi ya kwala ma matarshi kira tazo ta kaini daki. Naga ta nufi dakin su dani nace ai da kun barni in kwanta a falo ma nan ya yi min yace haba dai ai kinzo taya ta aiki ne don haka ni na bar ki da ita ke nan. Yai muna sallama cewa zai fita ya dawo na mike zuwa dakin inda na samu gadon dakin yasha gyara dakin sai kamshi yakeyi . Na yi shirin kwanciya dukkan mu a saman gado daya muka kwanta muka sa baby a tsakiyan mu asuba ta gari yan uwa. Idan zaki fitar min da novel na barki da raddin ubangijin mu je ki tayi tunda baki san hakkin amana ba zaki fada ranan da baki baya magana sai hali. ZAINAB IDRIS MAKAWA SEENABU 8/14/20, 7:12 PM - Ummi Tandama: BAHAGGON , , , , , 🧕🏿4️⃣7️⃣🧕🏿 Ni safiya ace mutum bai tsoron Allah shi dole ne karatun nan ance ba a yafe ba an hada ki/ka da Allah an hada ku da darajan annabi amma kuna wasa dashi ku sani fa hada mutum da Allah ba karamar kalma bace akwai ranan haduwa dashi ranan nadama ranan da baka da abin bayar sai ladan da ka tara ma kan ka. Mutuna ko yanzu ko anjima koyau ko gobe ko ko ko ko zamu koma ga Allah koda ciwo ko babu ciwo may zamu fada wa Allah. Dabara ya rage ga mai shiga rami shi kadai ni dai tun da asuba na mike batare da samira ta sani ba nayiwa gidan ta kwal ga ruwan zafi da na sa masu na wanka ya ya tafasa na sauke na fara hada mata abin karyawa. Sai da naje daukan baby dake barci a gefen tane ta bude idanun ta tana fadin subbahanallahi gari ya waye ne ? Murmushi nayi nace madam ki tashi ruwan zafin ki na jiran ki a bayi ban saurara mata ba na fara cirewa baby kayan jikin ta na nufi bayin da ita inda maga kayan wankan ta aje a gefe. Wanka nayi mata na gasa mata jiki dama na iya tun ina gida idan ummina ta haihu nakan taimaka mata da wankan yara. Na fito na fara shirya baby sai lokacin Samira ta samu ta mike zuwa wanka tana cewa yau wata rana zamuyi wanka da safe haka yadda ya dace. Nikan naji dadin ziwan nan naki Safiya wannan kokari haka ta mike take bin dakin da kallo tace wai ko kin yi barci safiya wanan irin aikin haka ? Kafin ta fito na saka wa yarinyar kaya cikin kayan da nazo mata dasu uwar ta fito wanka tana kallon mu da sha a wa tare da fadin aa lalai takwara tazo wanan kaya ai da ki bari sai ranan suna ki saka mata. Murmushi nayi kawai na goya yarinyar na na fita daga dakin sai gani na dawo da cup cike da shayi mai kauri dana hado mata. Na aje a gefen ta dago kai tayi ta kalle ni nace madam sai a sakai a shanye kafin ya huce nace za a daukan maki kaya ne ki saka ? Tace gaskiya Safiya zaki shagwaba ni da yawa ki wuce ki barni da kewan ki nace kada ki damu madam dama shi nazo yi yanzu aiki na ne nakeyi. Batai sanya ba ta kafa kai ta shanye shayin duka sai ga zufa ya karyo mata nan ta mike ta dauko kayanta tana sawa. Na fito falo naji ana bude karamin dakin nan dake rufe ashe yaya ne anan ya shige ya kwana na juyo don ganin ko waye mukayi tozali dashi. Nace yaya barka da kwana yace an tashi lafiya Safiya nace Alhamdu lillahi yaya yace yau takwaranki ne ta samu goyo haka ? Gaskiya banji kukanta ba yau da safe don kullun itace ke tayar damu da safe da kukan ta nace yau tasan gwagon ta na gari batayi kuka ba tun da nai mata wanka takoma barci. Yace kai har wanka ta samu yau da wuri haka nace gwago tazo fa yaya zanbar diyana takai wani lokaci bata gasa jikin ta ba. Nan ya fara bin gidan da kallo yaga gyaran da ya sha yace keko kinyi barci kuwa nace may ka gani yaya yace wanan irin aiki haka tun da farar safiya haka ? Nace shiya kawo ni may zan kwata wa inyi ga aikin madam a gaba na yanzu lokaci ne da take sin hutu a jikin ta don haka ta kwanta ta huta jikin ta ya watsake. Na shige kitchen na barshi yana mamaki ya raya a ranshi da haka uwar shi ta rike zumuncin da mahaifina yaso su kulla da abin yazo da sauki. Ya shiga daki nan ya samu samira tana ninke kayan da ta cire ta juyo tana kallon shi tace kaga aikin kanwaka ko sai yau na karkare yarda da abinda kake fadi nata. Na shiga dakin na samay su suna magana nace yauwa bari ma in baku sakon ku tunda gaka a dakin nan na jawo akwatin kayan da nazo dashi zuwa gaban shi na juya wirin hand bag dina na ciro kudin da na ware mashi tun a gida na bashi. Sai bina yake da kallo yana neman karin bayani nace yaya kana kallona mana yace ban fahinta bane safiya nace to kaya da na takwara nane da uwar ta gashinan akwati guda sai kudi kai kuma ka kara kai hidiman buki da su. Tsaye yake dama zai shiga bayi sai naga ya kai zaune a wurin yayi shiru can ya dago kai yace Safiya duka wanan dawainiyar ani kika yi shi bayan zuwan da kikayi kuma ga wanan wahalar. Ba wahala bane idan duk abinda nake dashi zanyi maka bazan taba yin da na sani ba yaya kai kaja in maka hakan da nayi. Samira kan kallo na take da mamaki da kyat ta samu bakin magana tace wai safiya kin wanke ni ga bakin jamma a kin gama muna komai a duniyan nan. Kin san yayan ki aikin company yake yi gashi wata uku ba a biya su jiya jiyan nan muka gama magana dashi na yaya zaiyi ko zamu daga sunan nan har zuwa gaba. Nayi saurin cewa a uzubillahi a daga suna kuma yaya Allah ya rufa muna asiri ashe gwama da na daure nazo don da anty ta so hanani zuwa na nace nace sai nazo. Tace Allah ne ya kawo ki yar uwa ta fara jawo kayan tana bude zip din jakkan don na karshen ne babban duka duka nazo kasu dashi. Shiko yayi mutuwar zaune ya kasa fadin komai har lokacin tana budewa ta sake karamin ihu da fadin wai Safiya ? Shago ke nan ta fara budan kayan tana azawa a saman gado karshe rufe akwatin tayi tai tagumi kawai sai can ta nisa tace dear ka ga ikon Allah. Sai lokacin ya nisa a sanyaye yace na gani samira ban san may zance bane kawai imani da tsoron Allah sun cika min zuciya samira. Kawar da zancen nayi da fadin ni kaga malam kai wanka ka shirya kazo ka karya in ka gama ka fita ka sayo muna abinci azo a aje a gidan na ciro kudi ina mika mai. Ido ya zaro yace na may ye kuma wannan kudin nace abinci zaka sayo mana dashi wanan ba na hidimar suna na baka kayi ba sai naji yace haba kai safiya haba dai. Tare shi nayi da fadin ka gode ma Allah adduan ku gareni ya karbu ga ubangiji shi ya wadatani da wanan niimar idan ban gode nima na na rama maku ba may zanyi da kudi. Kudine ina samu alhamdullahi don sulaiman yana wadatar dani dasu kuma yana fada min in yiwa yan uwana alheri daga niimar da Allah ya wadatar dani. Yace Allahu akbar haka abun Allah yake safiya shiya sa idan kaga ubangiji ya yi ikon shi akan mutum kai dai kabishi da addua don baka san hikimar ubangiji ba a kansa. Abinda nai maki a baya har ga Allah nayi maki ne a matsayin ki na yar uwata ta jini da kuma matar yayana da hadi na musulunci banyi don zaton wata rana zaki zama wani abu har ki rama min ba. Nace na sani yaya nima kuma ba zan taba iya rama maka abunda kai min ba har abada duk wanda yai maka abu a lokacin da kake bukatan taimako a kan shi ai baka da kamar mai shi a duniya ba don kai ba da yanzu na wullakanta. Yai saurin cewa Allah bai yoki wullakantata ba dama safiya ki godewa niimar da Allah yai maki tun farko tunda kin samu kiyi karatun boko. Nan dai mukai ta hira dasu har ya gaji ya mike zuwa wanka yafito ya karya ya fice daga gidan baby Safiya ta tashi na kaita wurin uwarta na dawo na ci gaba da aiki na. Tuwo na tuka mata na Semon da na gani a kitchen din da miyar yauki ina gamawa yaya ya dawo gidan da kaya niki niki tare da abokin shi. Wai ya kirashi yazo yaga abinda na kawo masu abinci na gabatar masu bayan sun gama gani yaya yace safiya sai kina sa ina ganin gidan yau kamar ba nawa bane. Muna tsaka ga magana Samira ta fito daki da wayana a hannu tana mika min ana kirana a lokacin. Na karba naga Sulaiman ne da sallama na koma gefe daya ina amsa wayan yace gida yai maki dadi kin manta da kowa ko ? Murmushi nayi nace yallabai an tashi lafiya yaya aiki yace lafiya kalau watau ke dai baki kiran mutum ko nace tsoro nakeji kada in kira ka kana cikin uzuri. Yace don gani agogo sarkin aiki sai ba zan tsaya na saurari kiran mata na ba ko ? Nace tuba nakeyi katse shi nayi da fadin ga yaya na ku gaisa yace af yana kusane nace yana nan yanzu ya shigo namika ma yaya Saadu wayan. Sun gaisa yake ma yaya barka da samun karu sai yaya yace Allah ya mayar gare ku kuma da kunyi aure a sama mana tagwaye. Murmushi yayi kawai yaya yake mashi godiya a bisa ga kokarin da yayi masu yace na komai ai anzama daya yanzu. Yake tambayan yaya din wani aiki yake yi sai yace mashi a wani company yake aiki yanzu kuma company tai sanyi sai dai dan buga buga da suke yi sunyi hira sosai kafin yaya ya bani wayan mu ci gaba da magana dashi har yake tambayana da yaushe ne zan dawo ? Nace jiya fa nazo har ake batun dawowa na yanzu sai nayi a kalla wata daya ko biyu kafin in dawo sai takwara na tayi kwari zan dawo. Yace kina hauka ne nifa in badon madam ta fada min yadda kuke dashi ba kuma yanzu a wayan da mukayi na fahinci mutumin kwarai ne don gashi har yana min fatan samun tagwaye da auren mu. Da hankalina bai kwata da zuwan ki garin nan ba sam nace sace ni za a yi komay ? Yace yana da wuya ne nace ni ko kofan daki ban taka ba tun zuwa ina ciki kumshe ina za a gani har a dauke ni ? Yace ki dai bi sannu don Allah ban son yawo please zan ma fada ma yaya don ya saka maki ido sai nace ai ka hutar da kan ka ni din kifin rijiya ce fita a guna sai ya kama dole nake fita. Yace daya fi maki ashe ba zamu samu matsala ba ban son mace mai yawo a rayuwa na ko gadan. Yace kin san may ? Na ce aa yallabai yace yau yayan ki ya fama min wani ciwo a zuciyata sai nayi sauri cewa subbahanallahi. Yace dakata mana kiji ai ba wani abu yace min ba illar cewar da yayi Allah ya bamu tagwaye da munyi aure. Sai nayi murmushi yace ban taba jin ina son haihuwa ba nima sai yau daya fada min haka naji nima ina son in ga zuria na a duniya koda kuwa bazan rayu tare da su ba. Nace balle zamu rayu tare dasu insha Allahu ai Allah shi ya fimu sanin daidai ga rayuwan mu ni dai mu bar wanan zancen ba yanzu ba tukun. Yace saboda may ? Ko ba kya son haihuwa ne ke nace wai kuwa kasan sunan yarinya Safiya ? Kin kawar da zancen ke nan ko? Safiya yaya yasa wa babyn namu nace wallahi ina zuwa yace ga takwara nan yayi min ya ce Allah ya raya muna ita a tafarkin addinin musulunci nace amin. Yanzu yaushe zaki dawo lagos ba wasa nake yi ba fa ina son in sani ne ? Nace kaida baka ko kasan kake tambayana yaushe zan dawo bafa a gari daya muke zaune ba balle kuma baka ma kasar baki daya. Murmushi yayi yace ina son in san lokacin da zaki dawo idan yayi daidai da dawowa na Nigeria don ta lagos zan sauka. Nace gaskiya ban sani ba tukun sai dai idan anyi suna naga yadda yanayin ya ke zan saka ranan dawowa na. Munyi sallama dashi naci gaba da aikina na fito inda na samu su yaya sun gama cin abinci sun cinye duka sai kwano. Na kwashe zuwa kitchen tare da kokarin dora girkin yamma don inyi in gama da wuri in huta ina aiki yan barka suna shigowa jefi jefi kamar yadda ake zaune a bariki. Na gama na gyara wurin na koma ciki nayi wanka sai lokacin na samu zama da samira muka fara hira wanda hiran namu akan yanayin garin nasu take min da kuma bani tarihin ta. Da yadda suka hadu da yaya saadu yan uwanta suka so su hana auren su wai ba a san asalin shi ba sai da kyat aka yarda ta aure shi don suna son junar su. Nace ai yanzu aure babu inda bai kai mace gashi ban taba zuwa bauchi ba amma aure yana shirin kaini can din. Tace wanda zaki aura dan bauchi ne shi nace mata dan bauchi ne tace a can yake zaune nace da ita a a . Sai nayi dariya nace shi wanan ai baida takamaimai zurin zama dan kasuwa ne baya zama sosai sai dai ina ganin abuja zai aje ni amma dai ban sani ba dai. Waya na jawo na kira anty don nasan yanzu ta dawo gida kira uku ta daga wayan tana fadin mutanen kalaba kun sauka lafiya yaya baby da maman ta. Nace lafiya lau anty baby safiya tana gaida ke tace a a safiya aka sama yarinyar nace eh anty . Tace ashe gaskiya kika matsa da zaki kin san abinda kuka kulla da yayan na ki nace wallahi anty ban san safiya ya samata ba sai da nazo naji. Tace sai yaushe zamu ganki nace anty sai anyi suna zamu zauna da yaya saadu don yanzu bai samun zama a gida. Tace yana da buki yaushe zai zauna gida kuma Allah yasa a watse lafiya ki gyayar min dashi don Allah ina mashi barka idan ya shigo . Mun gama ina cewa ta gyayar min dasu yan biyu tace kin sa sun zo sun damay ni da tambayan ina kika je nayi murmushi nace nasan dama zasu tambaya ai. wayan nake aje wa sai naji samira na fadin itace wacce kike a wurin ta lagos halan ? Nace eh wallahi mutumiyar arziki bata da matsalan komai wallahi ta rike ni tankar itace ta haife ni. Tace kinyi dace da uwargijiya yar albarka samun irin su yanzu da duniya ya dauki zafi ai sai dace. Yan barkan da suka shigo yasa ni tashi na basu wuri falon su na koma na kwanta ni kadai babu komai a raina sai tunanen rayuwa. Maganar haihuwan da mukayi da shi dazun nake tunane a irin wanan halin da mutum yake ciki har zaiyi tunanen haihuwa wa a hakan. Yaya taran zasu taso suji halin da iyayyen su ke ciki a duniya kuma ba wani dadewa zasu iya yi da iyayye su a raya sam wanan tunanen na sulaiman ban kwanta mi ba arai nikan. Mu dai samu mu raka da rayuwan mu a hakana batare da mun jefo wasu a cikin matsalar mu ba yara su taso a wahalce babu iyayyen su a duniya. Shigowan mahaifiyar samira da ba sai an fada ma mutum ita ta haife ta ba don kamar da sukayi da ita. Sannu da zuwa nake masu tace a a lalai kuwa ga gwagon baby na gani sukeyi min sannu da zuwa na amsa masu a sake tare da masu jagora zuwa daki. Bayan na gama wadatasu da abin sha saina koma falo ida nake zaune da farko na kwanta ina jiyo hiran su daga inda nake zaune samira na fada mata abin arzikin da na kawo masu. Tunanen ummi na ya fado min a raina din haka na ja waya ina laluban ta nayi saa wayan ya shiga muka gaisa nake fada mata ai ina kabala tun jiya na iso. Tayi ta samin albarka da na samu zuwa nake tambayan mutanen gida tace duk suna lafiya aiki dai yayi nisa jiya da yayan ki sani yazo. Yake fada min wai yanzu window za a sa sai kuma aci gaba da sauran aiki nace yaya sani ana nan dai ana ta fama tace bari kedai. Ai kina shan albarka a wurin shi kullun yazo maganan ke nan a bakin shi nayi dariya nace yaya sani ho yana nan dai da halin nasa Tace may zai fasa take bani labarin harkan sana a ta nace ummi ai yanzu ya zama naki sai dai ku kula kada kudin ya karye . Mun gama waya na sauke ajiyan zuciya ina mai ci gaba da tunanen duniya a raina har har mahaifiyar samira suka fito daga daki suka dawo wurina muka zauna muna dan fira jefi jefi basu dade ba sukai muna sallama. Ban shiga ba anan nake zaune don akwai kawarta a dakin bata fita ba don haka na basu wuri su dan tatauna a tsakanin su. ZAINAB IDRIS MAKAWA SEENABU 8/14/20, 7:12 PM - Ummi Tandama: BAHAGGON , , , , , , , , 🧕🏿4️⃣8️⃣🧕🏿 Daf da magariba yaya saadu ya shigo ya iskani zaune a falo nayi zugum cike da tunanen zucci muryan shi naji daga sama yana fadin. Safiya haba zaki bata min rai fa idan kina zama ke kadai kina saka damuwa a ranki da tunane tunanen banza marasa amfani gare ki. Nisawa nayi nace duk abu mace mai rai da lafiya in tana da hankali dole tayi tunane a rayuwan ta. Zama yayi a kujera da ke fuskantana na sake cewa dashi yaya ke nan ai dole mutum yayi tunanen rayuwa din ni yanzu kaina ya daure don ban san makoma na ba. Yace come on, wace irin magana kike fadi haka? Wace irin magana kike fada safiya may yasa kikace hakan ? Ta dukar dakai na kasa nai shiru da alaman tunane nakeyi abinda zan fada mashi. Yaya wai ba za a kara ma auren nan lokaci ba don ni kwata kwata ba wai na shirya mayin aure bane yanzu. Abu ne mai wuya yan uwanshi su yarda dani ko su soni far daya don dukkan su fa masu kudine family su cap yaya, yaya za a yi inyi daraja a wurin su. Ya kalle ni kafin yace shi zaki aura ko yan uwan shi na ce shine yaya. Sai naji ya kyalkyale da dariya yana mikewa yace kai amma ku mata wani lokaci sai mutum ya rasa ina tunanen ku ya tafi ne wai. A daidai lokacin Samira ta fito daga dakin ta tana ce min tare da miko yar ta naga yamma yayi a goya ta ko ? Karban yarinyar nayi nake mata kirari ina kokarin goya ta a bayana yaya yake cewa zai tafi masallaci yai sallah. Yana fita Samira ta kalle ni tana cewa kin ko ci abinci safiya don ni banga kin ci komai ba tunda safe ? Nace dazun da safe na karya ai ni dama haka nake abinci bai damay ni ba tace ko wani abin kike son ci baki magana ba. Bari yayan ki ya dawo sai ai mashi magana ya dan samo maki wani abin marmari ko zaki iya ci amma kan kya zauna da yunwa hakana. Nace ai banjin yunwa ne da zanci abincin baidawo ba sai taimai waya da zai dawo gida sai gashi da drinks mai sanyi da gasassan kaji biyu ya dawo dasu. Gaba ya sani dani dashi da samira sai da yaga na ci kaza guda daya aje min amma rabi banyi ba na dan kora da drinks din na ji nauyi a cikina. Sai dai cikan da cikina yayi ya hana ni barci da dadi da dare sai da na sha magani na samu shakkat a rayuwana. Ana gobe suna ban zauna ba don aiki yai yawa a gidan bani na samu kaina ba sai dare shima ba wani barci na samu nayi sosai ba. Asuban farko na tashi kafin gari ya waye na gama ayukan daya dace duk wacce tazo sai dai in debo mata abinci da abin sha in bata. Anyi suna lafiya aka watse kuma lafiya sai mu da wasu yan uwan Samira aka bari muna gyara gida anan muka kwana tare da su. Washe gari muka kara gyara gida sai suka fara tafiya dama su uku ne bayan tafiyan su ne na samu wuri na kwanta don duk na gaji sosai a lokacin. Barci nayi sosai a ranan sai karfe hudu na tashi ina duban lokaci samira tace ai taki tasheni ne don taga na gaji. Sallah nayi nazo na hada masu ruwan wanka sukai wanka muka zauna hira da ita yaya bai dawo gida ba sai da dare. Nan ya zauna muka sha hira dashi har yaci abinci ban dade ba na basu wuri zuwa ciki nan barci ya dauke ni koda Samira ta dawo dakin ta samu har munyi barci nida safiya karama. A kwana uku da suna muka zagaya gidanjen yan uwa da abokan arziki da suka zo mata suna da barka. Duk gidan da muka shiga zanga sun kira samira a gefe suna tambyan ta ni wacece a gare su ? Wasu su fadi alheri akaina wasu kuma suce tayi hankali dani tunda ba uwar mu daya uban mu daya ba zan iya aure mata miji. Ita dai dariya take masu kawai a gidan su muka dawo muka ya da zango anan don sai dare muka koma gida don uguwar su guda sai dai da dan nisa da gidan su. Ina cika sati daya da zuwa na fara zancen komawa don kullun na kira anty sai ta tambaye ni yaushe zan dawo ne. Shiyasa nake son komawa yaya yaso yai min sayayya amma na hana shi sai mun komai sai cake da akai masu wanda zanje dashi a matsayin kayan buki da sauran tarkace na kwalam din yara. Munyi waya da sulaiman na fada mashi ranan da zan taso sai yace inba yaya nombashi ya kira shi nabawa yaya ya kirashi ashe zai turo da kudi sai min ticket ne yakuma bawa yaya din wasu kudi. Ranan monday na dawo lagos da karfe goma na safe muka sauka lagos din bansan wazai zo daukana ba don da niya ta in shiga taxi a kaini har gida. Amma sai ganin Sulaiman nayi shida kanshi yazo dauka na ban ma san yadawo kasar ba sai dai yanzu da na ganshi. Bayan an gama saka kaya a motar shi ya dauki hanya dagani sai shi a motan sai da ya fara tuki ya dan kalle ni a daidai lokacin da nike mashi sannu da zuwa. Yace ai yanzu ke keda sannu da zuwa bani ba yace yaya ki ka barsu acan nace lafiya kalau suke sun ce ai masu godiya a gun ka. Yace namay fa nace daiwaniyan da kasha na bari na in zo masu buki har kwana goma sha hudu. Murmushi yayi yace wanan sakon yaya saadu ne ko don shine namiji dan uwana shiya san irin halin da na shiga don ba karamin hakkuri nayi ba da na barki kika tafi. Dan kallon shi nayi nace kai uncle kamar a gidan ka nake zaune zaka fadi haka. Ba tare da ya kalle ni ba yace in a gidana kike ai bazaki tafi ko ina ba saar ki guda yanzu baki zo gidana ba tukun. Ban iya magana ba nayi shiru yace zan so ace kin fara koyon nisa da mutane don na fada maki matata bata yau yana daya daga cikin abinda ya dani da mata ta tafarko. Bayan wanan magana babu wanda ya kara furta wani abu daga cikin mu har muka kawo gida ya shiga da mota ya tsaya bai barni na shiga ciki. Mun tsaya yana kara min korafi dadewan da nayi ban dawo ba na ce in sha Allahu zan kiyayye a gaba ya lumshe ido yana bude min motar na fito da sauri kamar wacce za a kama. Ina shiga Faiza ne kawao zaune a falo tana karyawa tana gani na ta tare ni da fara,a a fuskan ta tare da tambayana yaya gajiyan buki. Ban dade wurin ta ba na kwashi kayana da security din gidan ya shigo min dashi zuwa dakina ba bata lokaci na fada saman gado ina tunanen tsaurin ra,ayi irin na sulaiman daya fara nuna min tun ban shiga gidan shi ba. Barci ya dauke ni maitsawo ban falka ba sai biyu da rabi koshi don sallah na tashi bayan nayi sallah na dan gyara kayana sai na fito falin gida. Babu kowa a falin sai tv dake aiki shikadai a falon nan na samu wuri na zauna tare da kokarin bude wayana miscall din yaya Saadune a wayan har kira biyar yai min. Kiran shi nayi ya dauka da korafin ina na shiga tun dazun yake kiran wayana ban daga ba har hankalinshi ya tashi sai da ya kira Uncle yace mashi na iso lafiya. Nace wallahi yaya barci ne ya dauke ni sai yanzu na tashi naga miscall din ka yace har kin daga muna hankali kin isa lafiya ? Nace nace lafiya na isa yaya yaya safiya da mamanta yace gasu zaune suna gaida ke mun dan taba hira yace bari na barki ki huta sai mun sake waya nagode kwarai safiya da zumuncin da kika raya. Nace ba komai yaya ai yiwa kai ne kamar yadda shima yake yawan fada min idan yayi min wani abin alheri ina mai godiya. Bayan mun gama waya dashi ummina na kira ina sheda mata na dawo lagos yau take tambayana lafiyan su? Mun dade muna hira nayi mata sallama na kashe wayan tare kwantawa a daya daga kujerun falon. Sai uku da rabi anty ta dawo gidan tashigo falon ina jin muryanta na dago mukai arba tace a a mutanen kalaba ne aka dawo ? Namike zaune ina mata sannu da zuwa bata amsa min ba takai zaune tana cewa yaya kika barsu nace lafiya anty suna gaida ke kuma suna godiya. Tace ina sauran mutanen gidan suke bayan ta dan bi wurin da kallo, nace da ita suna dakin su bata kara magana ba sai ta mike zuwa dakin ta kawai. Bin ta nayi da kallo ta shige na sauke ajiyan zuciya tare da komawa saman kujera na kwanta lokacin sallah yayi na shige nima ciki. Tunda nayi sallah ban fito ba don banji kowa a falon ba don haka nima na zauna a dakina sai bayan sallah isha,i Faiza ce ta fara fitowa sai anty. Can na fito dauke da tsaraban da na dawo dashi a hannu na su yan biyu na gani na suka nufo ni da sauri suna murnan gani na. A gaban ta na aje kayan ina ce mata ga tsaraban suna nan anty tace cikin nuna jin dadi wanan duka namu kice dai mu muka haihu din. Ballan cake din tayi takai a bakin ta sai yaran suka nufuta suna fadin suma a basu suci nan suka far ma cake din da ci tana fadin yayi dadi sosai wallahi. Fira muke yi jefi jefi sai ta jefo min tambaya da cewa Sulaiman ko yazo ya ci abinci kai na kada mata tare da fadin ban sani ba anty . Ta juya wurin Faiza tana tambayan ta ko ya zo gidan nan itama take cewa barci tayi wayan ta ta dauko tana lalaban layin shi amma bai shiga ba. Taji tsuki tace wayan nashi ma a kashe yake tace Fati wai ba zata fito bane komay takeyi a dakin ne har yanzu ? Aika yara tayi su kira Fatin sai gasu sun dawo wai ta koro su daga dakin basu gama fada mata ba sai gata ta fito tana wani shan kamshi ta daure fuska. Nan take tambayan ta ko uncle ya shigo da rana tace tun dazu ina daki ban fito ba kawar da kai tayi daga gare ta. Fati mun samay ku lafiya nace da ita bata amsa min cikin dadin rai ba wuce wa tayi kitchen ta hado abinci ta shige dakin ta dashi. Ni dai ban dade ba na mike zan tafi daki sai take cewa da ni dan Allah kwashe min wanan kayan zuwa sama kafin in tashi. Na kwasa nakai mata daki na dawo na gyara wirin a lokacin tana waya sai ga daya daga cin security din gidan ya shigo yana fadin oga ya kirana a waje. Da sauri na dan juyo ina kallon anty da hankalinta yake ga wayan ta da take dakila sai ta dago take tambaya ko waye ? Yace da ita Uncle ne daga Fati har Faiza suka kallo ni lokaci daya ban kulasu sauraren umarnin anty nakeyi a lokacin sai ta dago tace dani ba kiran ki ake a waje ba yau ban san may ya hana shi shigowa gidan ba. Nidai na wuce daki don in shirya yayin da Fati taja dogon tsuki sai da suka kallo ta anty tace da ita wawiya kawai. Nafito da shiri na nayi dan simple makeup sai dogon riga dana saka mai shara shara ligt green da takalma plat nace sai nadawo ban tsamani sun amsa ni ba na fita daga gidan zuwa wurin shi. Yana cikin bai fito ba yana hango ni ya bude kofan motar ina karasowa wani kamshi ya daki hanci na a raina nace uncle ke nan badai kamshi ba kan. Sannu da zuwa nace dashi ya sauke ajiyan zuciya tare da karasa fitowa daga cikin motar yana amsa min. Ya gyara tsayi yana ce min yaya gajiyan hanya naga alaman baki gaji ba na katse shi da fadin yaya akayi yau baka shigo cin abinci ba ? Ka bar anty tana tambaya yace nayi tunanen hakan sai dai idan na shiga ne ba zan samu ganin ki ba shiyasa nayi shawaran na fara kiran ki tukun. Nace OK, Tambayana yayi wasu kaya nafi sakawa sai kuma yace koda yake naga kin fi son irin wanan kayan da kika sa. Murmushi kawai nayi batare da nayi magana ba yace ina son kafin nan da sati biyu a kammala komai daya kamata ayi sai a saka ranan buki. Nidai har lokacin ban yi magana ba sai yace ko zancen bai maki dadi bane ina magana kin kyale ni ba amsa. Uncle may zance ni yanzu duk abinda anty tayi daidai ne ni ba ruwana a zancen yace OK yanzu bari mu shiga sauran magana mukarasa a waya tunda baki iya magana a fili. Na sake cewa uncle ba magana na bane don Allah ka bari mana na fada a tsigar shagwaba ya nuna min hanya alaman in wuce mu shiga. Make kafada na nayi ya gane abinda nake nufi sai ya fara hanya na biyo shi a baya a tare muka shigo falon da sallama. Tana shirin shigewa daki sai gamu ta dago tana kallon mu ba ita kadai ba duk wanda ke falon kallon mu yake yi a lokacin da muke shigowa gidan. Ta bishi da dan hararan wasa tana cewa ai na dauka yau yajin shigowa gidan kake yi don ko da rana baka shigo ba akace. Yace yana zama wallahi ban gama abinda nakeyi bane a bakin ruwa shi ya dauke min lokaci tace yau kuma abin yar tsayuwa kofan gida ne kawani aiko wai a kirama safiya ? Yace No na kirata ne taimin iso in shigo kin san yanzu kin zama antyn mu ta harare shi tace waye antyn ? Ni dai ban zauna shigewa nayi na barsu a nan suna wasan shammatan juna su ina kokarin cire gyale naji anty ta kwala min kira. Da sauri na fito daga dakin tace ba mutumin abinci mana kin shige daki kuma kafin in juya yace No ta barshi kawai i am ok. Yau ban jin cin komai tace yanzu naji magana amma da na dauka ko kana yajin cin abincin gidan namu ne yanzu. Jin haka yasa najuya zan wuce tace kaga mutanen kalaba sai yau taga daman dawowa garin kallon ta kawai nayi na dan yi murmushi . Yace na ganta har tana wani wai bata so ta dawo yanzu don ke ta dawo garin yau. Tace ai da baki tafi kin barni ba kika je can kika zauna abinki hankali kwance. ZAINAB IDRIS MAKAWA SEENABU 8/14/20, 7:12 PM - Ummi Tandama: BAHAGGON, , , , , , , , , 🧕🏿4️⃣9️⃣🧕🏿 NOVEL DINA NA KUDINE IDAN KI FITAR MIN BAN YAFE BA IDAN AN FITAR KI KA KARANTA INA BINKI HAKKINA A KAN KI. Ina kwance saman gadona da waya a hannu na na mayar da hankalina sosai a kan wayan ina duban sako naji an shigo dakin. Na dago don ganin ko wacece sai Fati na ganj tsaye a kaina tana huci idanuwan ta sun kada sunyi jawur dasu aje wayan nayi a gefe na duk da ban karasa karanta sokon ba. Ta harde hannayen ta saman kirjinta ta wurga min kallo mai tattare da tsana zallah a cikin shi ta fara tafa hannu ta biyu tamai kara bina da wani irin kallo na tsana. Zama nayi da kyau ina fuskanta ta don inji abinda take shirin fadi lalai Safiya kin cika rikkan yar yaudara kin kai maciyiya amana. Ke yanzu bakiji kunya ba don Allah to ki sani in takaman ki iya asiri da kwatar maza yau kin kai karshe don baki da wayau yanzu ina ke ina uncle ko a kafa akadaura mashi ke ai ba zai iya ja ba. Sai lokacin nayi murmushi nace da ita balle a daurin da akewa ko wace mace da mijin ta za ai muna kuma na dauke shi kamar yadda ko wata mace take dauke mijin ta. Hannu ta daga wai ta kai min mari kafin hannun ta ya iso gare ni na kwashe ta da mari biyu masu kyau nace kin zo har dakina ki fada min abin da yai maki dadi ki wuce kice kinci bulus. To bari kiji uncle kamar na aure shi na gama da yardan Allah ke ce wahalala da faman dakon son wanda bai masan dake ba a duniya. Ashe Faiza na jin mu ita ta kira anty sukazo tare daidai Fati na fadin aure fa kikace kodai karuwanci waye baisan abinda ake turaki yi wurin shi ba banza kawai ana turaki gurin shi kina samo kudi don zubar da kai dama zubun ki baiyi kama da ta mutanen kwarai ba. Muryan anty ne ya karade dakin tana cewa wake turata karuwancin nike nan kike nufi kowa fati ? Da sauri muka juya kofan ta karasa shigowa ita da Faiza dakin tana cewa Fati nace uban wa ke turata karuwanci tambayan ki nake yi ki fada min ? Nace anty wanan maganan da take fada min kullun ya isheni don ba yau ne farko fada min haka da takeyi ba wai kina turani wurin maza ina samo maki kudi. Ko zuwa gida da nayi jiyar baba sai da ta fada min ha gashi kuma yau ta sake fadin wai kin turani kalaba na samo maki kudi wurin maza dama haka kike yi. Inna lillahi anty ke nanatawa a gigice tana kallon Fati din takeyi rai bace tace kazafin da zakiyi min ke nan Fati sakkaiyan da zaki mayar min ke nan ? Na dauko ki cikin wahala da lalace nazo dake nan don ki zama mutum ki dogara da kanki shine zaki saka min da wanan a gidana. Tace da kike fada a kan sulaiman ya ko san da zaman maki a duniyan nan halin ki na banza ya barki ki aikata alheri ne ne fati ? Karshe kasa karasa magana tayi nasan takaici ya rufe ta sai juyawa tayi ta fice daga dakin rai bace. Muka dawo da kallon mu ga juna sai gata ta juyo tace ki fice daga dakin nan tun raina bai karkare baci ba Fati. Ta kalle ni taiyi kwafa tana cewa kin ci bashin marin da kikai min don sai na rama abina ki sani nace daga baya ke nan na nuna maki ni yar kauyen gidi ne. Ta fice fuuu anty ta mara mata baya suka fice aka barni da gani sai Faiza tace don Allah Safiya ki boye ni kada ki fadawa anty anbin da nace hannu na daga mata nace Faiza ki fice please. Batayi musu ba ta juya ta fita daga dakin simi simi na sauke a jiyan zuciya tare da komawa saman gado na zauna ina tunane ni may ye laifina a cikin maganan da bazata samay shi da maganan ba shi da take so. Na dade wurin zaune na rasa amsan da zan ba kaina dole nake kwance ina ci gaba da tunane a raina sai da naji yunwa na iya fitowa don neman abinda zanci don ko karyawa banyi ba ta samayni da magana. A falo na ga Faiza zaune wuce ta nayi zuwa kitchen batare da nayi mata magana ba na hado abinda zanci na dawo zan shige sai naji tace Safiya fushi kike yi hardani ne wai ? Nace fushi akan may aini Allah yayi min fada akan may zan tsaya bata lokacina kuma aida ban gode masa ba. A gaban anty ta nanata da kunnen ta taji ai hali shike nuna kansa wanan ya nuna bata da alhakin ku kuke fakewa a bayan ta kuna mata sheri har na gama na wuce bata ce dani komai ba. Ban iya cin abincin ba don raina ya na bace har lokacin twin's na ta shigo tana ce dani maman su na kirana abinda ya sani fitowa kenan. A falo take zaune ga Fati da Faiza a zaune suma na samu wuri na zauna in ji abinda zata ce muna. Mun zauna shiru sai can ta nisa tace Faiza ta amsa naam Safiya nima na amsa mata da naam Fati ta amsa mata ciki ciki da naam. Tace na koraku nan ne don in yi magana da ku baki dayan ku akan abinda ya faru dazun tsakanin Fati da Safiya a gidan nan. Banyi mamakin jin abinda kika fada ba don nasha jin ire iren wa yan nan maganganu daga bakunan mutane dake fitowa daga bakin ku. Amma wanan yafi min munin saurare don da kunuwa na naji ba wani ya fada min ba sai fatin tace ni may na fada anty maganan mu mukeyi kawai. Kina rufe min bakin kin ki ko sai ranki ya baci yanzu in maki tsinanen duka anan sai ta ja bakin ta tayi shiru tare da dukar da kanta kasa tace idan da banji ba sai ince kaka tayi maki. Ba wani ya fada min ba ni naji da kunne na abinda kika fada kenan ni ke tura ta wirin maza tana samo min kudi kike nufi. Ta dago za tai magana ta tare ta da tsawata yana fidin tayi shiru dole ta sake kyalewa tai fada sosai a cikin bacin rai sai ta juya kan Faiza tana cewa. Aure Safiya zatayi nan da dan wani lokaci zan iyacewa nan da dan lokaci mai zuwa bazaku ce baku san da zancen ba. Don haka zan iya hakkurewa har lokacin da tayi aure wace taga zata iya zama dani ta zauna bazan kori kowa daga cikin ku ba don ku kuka kawo kan ku na. Sai dai idan na sake jin wani rikici a tsakanin ku kafin wanan lokacin dukkan ku rayukan ku zai baci dani amma ke fati tun yanzu nasan matakin da zan dauka a kanki. Gida zaki koma don ba zan yarda ki bata min suna a banza ba da abinda banji ban gani ba ki dora a kaina duk wanda yaji wanan zancen sai yace idan baki gani ba baki fadi. To komawar ki gida shi yafi zama alheri a gare ni don haka sai ki shirya next week zan sa a kai ki gida kafin in zo muyi maganan a can. Hakkuri ta shiga bayarwa sai ta bani tausayi ban san lokacin da nace don Allah anty kiyi hakkuri. Ta dago kai ta kalle sai na saukar da kaina a kasa na kara fadin don Allah anty kiyi hakkuri sherin shedan ne . Kina ji da bakin ki abinda ta fada akaina kuma kince ba yau ta fara fada maki haka ba sai fati tau sarin cewa wallahi bani na fada ba Faiza ce ta far fadi nima naji na fada. A take Faiza tace kada kimin sheri yaushe na fada ta juya gare tana cewa wai Safiya ranan wa kiji ya fada har muka baki hakkuri akan karki bari anty taji zancen. Murmushi nayi nace anty don Allah kiyi hakkuri da zancen in ma har suna hasashen haka ne a ransu ai Allah shiyasan gaskiya. Haba haba kuyi min adalci mana maye laifina na ajeku a gida na danayi tare dani ? Idan bani ba wacece zata ajeku haka a gidanta amma tunda ku kuka kawo kanku gareni na karbe ku hannu bibiyu na zauna daku may na rage ku dashi a gidan nan na jin dadin rayuwa. Duk mukai shiru muna sauraren ta tace ke Faiza ai akwai gidan anty Ai a abuja may yasa baki je can kin zauna ke kuma akwai gidan anty mami a kaduna ai uwarku daya may yasa baki tafi wurin ta ba. Sai nan bayan haka da halina ne hakan da ku da kuka riga Safiya zuwa nan aida daku zan fara ba Safiya da tazo daga baya ba. Ko don ita din ta fiku kyau kuke tsamanin haka zanyi da ita toni aure na hada don raya sunnan ma,iaki SAW ba yin zina ba yadda kuke tsanmani. Allah ne ya yanke mata wahala da zuwanta ta samu miji ku da kuka dade da zuwa aida aikinane hakan akwai maza da yawa may zai sa ban hada ku dasu ba ku samo min kudin ko ku ba mata bane yan uwanta. Faiza tace munyi kuskure amma kiyi hakkuri ba a karawa in Allah ya yarda ta ja tsaki tare da kawar da kanta gefe. Nan muka zauna zugun zugun damu ita dai bata sake magana ba sai duban tv da takeyi tana sauke ajiyan zuciya kawai. Nice na fara mikewa na bar falon zuwa daki ban san lokacin da sauran suka watse ba tun wanan ranan aka rage yawan gulma a gidan. Sai dai ban yarda na sake wa Faiza dake yawan shige min ba wai ita ala dole tana tsara yadda zamuyi buki in ya taso. Na fito daki da safe na samu anty a falo don yau ba ranan fitanta aiki bane don haka mukan wuni da ita a gida bata fita ko ina a wanan ranan ne takanyi gyaran jikin ta. Sai yanzi na gane hakan da nake zaune a gidan ta ina fitowa tare da gaida ita tace yauwa Safiya kin fito don Allah ki taimaka min da kan nan nawa. Yau kitso nake so da gyaran jiki tace yan biyu ta dauko mata kayan kitson su nan na zauna muka fara banyan kai muna hira sai ga Faiza ta fito zauna nan take fada mata ai kan yayi dauda nan dai mukai ta mahara karshe dai tace zataje wankin kan. Wayana dage gefena ne yayi kara alaman sako ya shigo min a lokacin ban dauka ba sai anty ta lura dani take cewa in diba mana ko soko ne mai muhinmanci. Ga abinda na gani rubuce ga sakon. Safiya badon na isa ba sai don girman Allah Safiya ki taimaka ki kashe min wutan kaunan ki dake famar kunar zuciyata har kullun, Safiya ina sonki ina kaunar ki wallahi wallahi ina son ki tsakani da Allah, Auren ki nake so don auren ki alheri ne a gareni. Ki taimaka ki kirani a wayan ki inji muryan ki don in samu natsuwar gudanar da ayyukan dake gaba anan idan kina raayina ki kirani inji muryan ki Sulaman Habbi Bauchi. A hankali na runtse idona bayan karanta sakon ina sauke ajiyan zuciya sai kuma gabana ya fara bugawa a hankali kamar zai tsage min. Ganin sakon na rinkayi kamar a mafarki na shiga tambayan kaina may ya kawo wanan sakon haka har uncle ya tsaya ya rubuto min shi. Na sake tambayan kaina may ke faruwa ne wai muryan anty naji tana cewa dani kin gama karanta sakon ki sance ma su yan biyu nasu muje a wanke muna. Cikin dauriya na amsa mata da eh sai dai saukina kitson kan su ba wani mai yawa bane ina gamawa na shige daki don ban da kwanciyar hankali a tare dani a lokacin. Acan kuma uncle one two ya duba wayan shi yana tsamani ko sakona zai shigo kai sai yaji shiru hakan yasa ya fara zargin ko maganan da yaji ya zama gaskiya a kaina. Zama nayi ina kara karanta sakon sai zuciyana ta bani cewa da Allah fa ya hadani mai zai hana na kirashi inji komay ke gudana. Yana zaune a office din shi na abuja tunane na kawai ya keyi akan don may zanyi mashi haka bayan tafiya ya nisa in nemi canza raayi a kan sa kuma. Sai yaji kira ya shigo mai a waya da sauri ya dauko wayan don ya matsu ya dauki wayan ya tabbatar da zargin shi. Yana dauko sunana ya baiyya na fuskan wayan sai da yaji gaban shi ya fadi don bai san may zan fada mai ba. Ya amsa wayan da hello, Murya kasa kasa nace mai salamu alaikum. Ya amsa min da wa, alaikumu salam Safiya, tare da karfin halin cewa yaya naji muryan ki a sanyayye ? Murmushi yaji nayi wanda ya fara kwantar mai da hankali nace haba uncle wanan irin sako ai sai ka tayar min da hankalina. Bancin kasan ka riga ka gama daure zuciyana da sarkan kaunan ka kasan yadda na dauke ka da muhinmanci . Uncle kafi kowa sanin kunya ke hanani kiran ka kan ina matukar jin nauyin ka da kunyar ka fiye da kowa yanzu. Shine kuma zaka rubuto min sakon da ya tayar min da hankali kasa zuciyata cikin kwankwanto tun dazu. Ajiyan zuciya naji ya sauke ya gyada kai tankar ina ganin shi yace safiya ina son ki sani yau da baki bugo min wayan nan ba sai ince abinda ake fada a kanki gaskiyane. Da sauri nace Uncle may ake fada a kaina kuma yace forget it, bar zancen kiyi hakkuri amma ina son ki sani akwai ta inda aka fara ma zancen mu zagon kasa . Amma ni kaina na yi tsamanin haka tun farko yanzun dai ina son ki sani ni kaina ba karamin kokari nayi ba da na iya turo maki sokon nan don in tabbatar da zargin da nakeyi maki. Luckyly sai gashi kin kirani din kamar yadda na bukace ki kiya kin ga hakan ya tabbatar min da cewa akwai matsala kenan. Shiru mukayi dukkan mu na dan wani lokaci kowa na tunane a ranshi kawai sai yaji na fara yi mashi kuka a wayan ina fadin ni may nayi wa wani da yake son rabani dakai ? Safiya come on ki tsaya ki saurare ni kada wani yazo ya samu kina wanan kuka haka kuma a san abinda ake ciki. Ki saurare ni kiji idan da ana iya rabamu da tun farko na dauki maganan da muhinmaci a zuciya na kwata kwata ni maganan bai tsaya min azuciya ta har da zan daukaba. Haka kuma idan baki daina kukan nan ba mai sakon zai fahinci mun samu matsala dake . Sanin mun rabu lafiya dake last week yasa kawai nayi tunanen in gwadaki in gani da kwata kwata ba zan taba barin ki san abinda ke zuciya ta ba to amma ba zan iya bane wallahi na kasa daurewa sai da na jerabaki yanzu share hawayen ki muyi magana na fahinta a tsakanin mu. Share fuska nayi kamar yadda ya bukata ina fadin don Allah uncle may aka fada ma a gamay dani ne wai ? Naga tun farko ba a boye maka komai nawa ba, nisawa yayi yace baki jin magana ko ta bari in kashe wayan tunda baki tsayawa ki saurare ni. Na nisa nace uncle kayi hakkuri amma gaskiya maganar ne koda banji ba akwai cin rai don sheri baida kyau sam wallahi. Kalmomin da nakeyi tuni suka jefa zuciyar shi a cikin tunane fiye da musali saboda bai taba tunanen haka ba da tun farko in yasan za a samu wanan matsalan ba zai tsaya har muyi nisa haka ba Amma a fili cewa yayi dani come on ba nace ki manta da komai ba kiyi kamar bakiji komai dake gudana ba, idan na zo zan maki bayani yadda zaki fahinci abin Ko kinfi son ki tadda min da hankali anan har in kasa yin aiki aiwatar da ayyukan dake gaba anan. Shiru nayi ina sauraren maganan shi karshe na kashe waya ina mai bin lafiyan gado na tunane kuma yazo ya lulube a wirin. ZAINAB IDRIS MAKAWA SEENABU 8/14/20, 7:12 PM - Ummi Tandama: BAHAGGON , , , , , , , , , 🧕🏿5️⃣0️⃣🧕🏿 NOVEL DINA NA KUDI NE NA FADA MAKI TUN FARKO INDAN KIN FITAR BAN YAFE MAKI BA IDAN KIN KARANTA BAKI BIYA BA ALLAH YA ISAR MIN. Yanzu ni yar uwa may zace dake tunda tun farko na fada maki kada ki fitar min ai kadan kika gani ga wanda bai tsoran Allah . Nace tun farko kada ki fitar min da novel kin dauka kalman Allah ya isa wasa ne sai da abu ya cika dake zaki dawo kina na yafe maki. Baki san ni ba baki kuma san inda na fito ba ina dai novel kina karantawa nace ga yadda nake son abina baji ba yanzu kizo min da wani magana ban damu ba tunda tun farko na fitar maku da hakkina na fada maku ban son a fitar min ke da sauran kadan kuka gani muje zuwa indai nice kullun ya diga bibiyar ki ke nan ai tunda kin zabi kalman Allah ya isa to ya isar min din sai may kuma ni na gama magana na ai tun shekaran jiya ku kaka rage da raddin ubangiji kuma. Tun safe ban tashi ba ina kwance kamar mara lafiya nake jin kaina ko abinci bam iya fita na nemo ba din ban majin cin komai a raina. Dawowan su anty da yara danaji hayaniyar su yasa ni mikewa na shiga ban daki wanka nayi na fito na shirya don ina fashin sallah a lokacin. Bayan na gama shiri ne na nufi part din anty don in mata sannu da zuwa a hankali nake hawa steps din na kawo daidai window din ta dake bude naji ta ambaci suna na har zan wuce sai na tsamaci ita da wani ne a dakin sai daga baya na gane waya takeyi ashe. Naji ta sake fadin anty uwa na fada maki na Safiya mai sauki ne nasan abinda zan fada mata gamay da sulaiman din ta fahince ni. Shidai sulaiman din ne yanzu shawo kanshi abune mawuyaci da sauki don ban taba zaton zai mutu ga son yarinyar ba haka. Shiru tayi tana sauraren maganan anty uwa din sai naji tace gaskiya anty ni safiya bata taba yi min komai ba harda zan mata korar kare a gidana. Don yarinya nada hali mai kyau wallahi don duk tafi min wayan nan kattan bazan dana tara Fati da Faiza. Ke dai ki bari mubi abin sannu dan Allah a samu a rabu lafiya da ita ba tare da ta fahinci komai ba. Anty uwan ke magana ta tsaya tana sauraren ta sai naji tace ba haka bane Anty uwa wallahi wallahi sam ban kawo Nafisa a raina in ba don kinyi magana ba yanzu ai mai sauki ne tunda ba aure aka daura masu ba dashi. Anty uwa din ke magana sai naji anty tace gaskiya ne zaman ta haka a gida kan baida amfana gaskiya zan san duk yadda zan yi ya koma ga Nafisan batare da an samu matsala ba. Shiru tayi anty uwana magana sai naji anty din tace Safiya bata da matsala zan san yadda na raba ta da son shi ai don ba wani wayewa tayi ba sosai. Naji tace to sai kin shigo din next week ina expecting din zuwan ku din ai kafin nan ma tun yanzu na fara aiwatar da shirina a kan su ko may tace mata naji tace ba hakana bane Allah anty yarinya ta bani tausayi ne don wahalan da tasha tun farko a gidan mijin ta. Anty uwa din ke magana ta tsaya sauraren ta alokacin na yo baya baya tare da dafe bakina dake shirin sake kuka asirina ya tuno gaida ita da banyi ba ke nan na dawo daki na. Sai ranan naga amfanin rashin zaman da su fati basuyi a falo don ko yau yai min rana sosai inba don haka ba da wani yana iya ganina a cikin su. Ina shiga daki na rufe tare da fadawa kan gado na sake kuka mai tsuma zuciyan mai saurare na ina kiran sunan Allah da karfi nace ni Safiya wanan irin bahagon rayuwa da nake gani damay yai kama haka duka duka shekarana 21 amma gashi ina ta haduwa da kaddarorin rayuwan duniya. Yanzu idan sulaiman ya kubbace min ina zan sa kaina ko sherin inna ya isheni a gidan mu ai da mutanen garin. Zuciyana taban amsa da fadin ki rike Allah don yana sane dake mai hakkuri baya tabewa a duniya. Haka yasa naji wani kwarin gwaiwa yazo min sai na dakatar da kukan da nake yi ina neman wa kaina mafita zancen tunane na ya tsaya akan in bar gida kawai shi mafita gare ni. Ban tsaya yin wani shawara ba na mike na fara hada kayana a cikin trolleys dina sai da na shake su da kayan da anty da sulaiman sukai min guda biyu na saka sauran komatse na a baccon da na dawo dashi daga kalaba. Komawa nayi na zauna a bakin gado ina tunanen abinda zan fadawa anty idan zan tafi don na fasa gudun da nayi niyar yi kada su dora min sata banji ban gani ba tunda mafita suke nema a kaina dama. Ina nan zaune har yamma yayi min sai na fito falo don dama ina jin motsin su a falon ta kalloni fuska sake tana cewa dani ina kika shiga tun dazun muka dawo. Nace wallahi barci ya kwashe ni daga dan kwantawa in huta sai na dauki lokaci ina barci Faiza dake gefen ta zaune tace ai da banji motsin ki ba nayi tunanen haka. Tambayan da anty ta jefomin ya hana ni magana tace kun ko yi waya da Sulaiman yau Safiya ? Sai na samu kaina da yi mata karya da cewa bai kirani ba anty tace nima haka kwanan nan akwai tsiyan da yake ji wata kila yaji wani magana ne yake son ya ja baya kuma. Murmushi nayi nace in haka yafi alheri a gare mu Allah ya kawo muna saukin rabuwa tace nima shina gani dama can ba son aure yake yi ba da ayi yazo ya kawo muna wani matsala gara tun wuri dai a watse. Nuna mata nayi maganan bai damay ni ba naci gaba da harkana tai shiru ta shiga dogon tunane sai can security din su ya shigo yace tana da baki a waje. Ganin ta tashi yasa muka watse wurin kowa ya shige dakin shi kofana na rufo don magariba yayi a lokacin gashi kuma ina fashin sallah don haka sai na jawo tasbahana ina ja kwai. Kiranshi ne ya shigo min na dauka a sanyaye da sallama na yayi saurin cewa dani yaya kuma naji muryan ki kamar baki da lafiya ne ? Kodai zancen jiya kika sa a ranki yake damun ki kuka ne ya zo min shiru yayi yana saurare na tun yana fadin subbahanallahi har ya kyale ni ina tayin kukan. Sai naji ya kashe wayan bai fi minti talatin ba ya kara kirana na dauka yace look ki tsaya ki saurare ni ban son wanan kukan da kike yi kamar ance za a kwace maki ni. Murmushin dole yasani yi nace uncle ba haka na bane yace to yaya ne kin bi duk kin tayar min da hankali har jirgi nace a bincika min da daren nan saboda rudani da kikayi ba a samu ba. Nace cikin dan kuka Uncle gida nake son wuce wa gobe in Allah ya kaimu da sauri naji yace saboda may zaki koma gida gobe shiru nayi kawai ina sauraren shi. Sai da ya gama cikin kuka na fara fada mai abinda naji anty da yar uwar mijinta suna tataunawa a kaina. Yace oho dama nufin su ke nan shiyasa tace min ba sona kikeyi ba don dan uwan tsohonijin ki dake kalaba ke kike so. Watau gani mutumin banza zasu gara ni yadda suke so ki saurare ni kiji ni zan tsara yadda zakiyi tafiyan gobe zan kiraki in sanar dake yadda mukayi da ita kafin goben kada ki kashe wayan ki kinji ko na amsa da eh. Naci gaba da tunanen zancen nace a raina watau anty uwa ita keson anty ta hada diyarta da Sulaiman shine suke son raba mu. Nasan anty uwa tun zuwan mu Abuja bude company sulaiman din da mukaje yi wata yar bariki ne don idon ta ya bude sosai don ko shigan da tayi a wurin sai da nayi tir da ita da diya ta wai ita wayewa ke nan. Yaran ta mata uku tazo dasu wajen biyu sun yi aure amma sun fito ita kuma babban ko auren batayi ba zata kai shekara talatin kila . Itace ke nan ake son a hada ta da sulaiman nace to ke nan itama din victims ce na HIV komay don naji sunce a huta da ita. Ban yi barci ba zuwa goma da rabi naji ya kirani yace gobe zaki kibi jirgin safe karfe bakwai za a kaiki airport na fada mata jikin baban ku ne ya tashi aka kirani kuma ina son ki koma gida har yadda hali yayi. Ta amice don naji tace abin ma yazo da sauki don haka idan ta tambaye ki ki fada mata yadda na fada maki din nayi mashi godiya mukai sallama na kashe wayan. Muna gama waya dashi na bi gado na lafe kamar ina barci sai gashi an turo kofan ddakin naji tana cewa kin yi barci ne Safiya ? Na dago da sauri ina fadin yanzu na falka tun tara barci ya dauke ni daga karatu a waya na yanzu fitsari ya taddani ta samu wuri ta zauna tana cewa mutumin ya kiraki ne nace bai kirani ba anty. Tace yanzu na samu wayan shi wai an bugo mai daga gidan ku mahaifin ki jikin shi ya tashi don haka gobe ki shirya kije gida. Rudewa nayi ina salati tace ki kwantar da hankalin ki nace shine basu kirani ba anty tace ai sun kiraki wai basu samay ki bane tace ai nima nayi mashi wanan tambayan. Ta mike tana cewa sai ki shirya goben karfe bakwai jirgi zai tashi yace a sayo maki ticket yau da daren nan za a kawo muna. Ta fara tafiya sai ta juyo tace dani ina ganin zaki dauki lokaci a can don haka ki debi kaya masu yawa da zasu isheki zama nace cikin rudewa tau anty. Tana fita na daga hannu sama inayiwa Allah godiya da ya bani mafita da saurin tun ban wulakanta ba a gare su. Karfe shida na gama komai ban bar komai na wa ba a gidan don nasan ko na bari ba a amfani dashi katshen ta yarwa zasuyi ko su kona. Security ya gama samin kaya a mota Faiza ce da tayo min rakiya take fadin wanan uban kaya da kika kwasa haka safiya kamar wacce bata dawo wa. Nace zan rage kayan ne shiyasa na kwasa don in bawa mutane can a gida tace haka na da kyau kuma. Anty dake bayan mu saye da hijjabi tace Allah dai ya kaddara saduwan mu da alheri ki gaishe sai munyi waya inji saukar ki da lafiyan baban tana magana da gani tana cikin bacin rai. Na tako gaban ta nace anty na gode Allah ya saka da alheri ki yafe min zaman da mukayi tare idan na saba maki ki gafarce ni anty nace wa Faiza ma haka tare da yi masu sallama na shiga mota ta rufe. Motar na fita na lumshe idona hawaye na zuba min ji nake kamar ba zamu sake haduwa ba daga nan. Ita ko anty tun barina gidan sai maganana ya tsaya mata a rai hartayi wanka tana tunanen zancen mu da nace duk abinda nayi mata ta yafe mun. Tana shirya wa dakina tayo bude ta shiga kallon gadon tayi dana gyara kafin in wuce tace badai tsabta ba safiya tawuce wurin wardrobe dina ta bude sai wayam babu komai a ciki sai zanin gado dana bari nasu. Da sauri gaban ta ya fadi tace kardai yarinyar nan ta fahince ni ne ko may nake plain a kanta da sauri ta dauki wayan ta tana kiran driver ya dauka tace bani Safiya yace ai jirgin su ya daga gani hanya dawowa gida. Zama tayi saman gadon tana magana ita kadai tace sam bata ji ba sai dai idan yadda tace ne zata rage kayan a gida. Da wanan tunanen ta mike ta bar dakin zuciyar ta fam da tunane a ranta tana fadin haka ma yafi sauki da sai anty uwa ta zo suyi mata korar kare a gidan gashi ba mutunci je da su ba. Tun da muka daga babu abin da nake tunane banda zama na da ita tun farkon haduwan mu da tazo tana tamnayan ko nan ake kitso wata yar wajen aikin su ce tai mata kwatance dani nakai kallo na ga ayan tagwayen ta nace nan ne anty gashi kuma yamma yayi tace ko yaran nayiwa don gobe monday nace to su zauna sai na sake kan wace nakewa kitso na shiga na dauko ma yaran abin sha na kawo masu. Matar dake zaune tace na nuna masu banbanci su da suka dade da zama ko ruwa ban basu ba sai wanan da tazo yanzu. Nace ai Sister dina ce ita dole in karrama su naga masu kitson harda ita kuma naki karban kudin lokacin ne Ahmed ya dawo tana jin fadan da yake min akan na tsaya kitso har dare . Da na fito take tambyana mijinane na bata amsa a sanyayye da eh tace shine yake maki fada akan neman kudi tun wanan rana mu ka saba da ita. Gashi yau wani matsala ya gitta a tsakanin mu har yana son raba mu da ita lumshe idanuwa na nayi ina mai ci gaba da fitar da hawaye. Bamu dade ba muka iso abuja da sanyin safiya sai ka dauka a nan muka kwana shida kan shi yazo dauka na yana saye cikin suit irin na maza farare kayan sunyi matukar karban jikin shi sosai. An gama sa min kaya a mota ya bude min na shiga sai lokacin yayi min magana naji yace ta gudu an iso lafiya ? A jiyan zuciya na sauke na amsa da lafiya lau yace kin sa mun yi wa baba karyan ciwo Allah ya kara mai lafiya nace amin na gode. Yace ina mamakin mutane yanzu son kai sai yasa mutum yayi abinda ba halin shi ba sam na rasa gane yaya akayi madam ta yarda wanan matar tayi convices din ta haka. Hauka nakeyi ko matsuwa nayi da yin aure ai ba zan taba auren Nafisa ba a rayuwa na bayan ta gama watsewar ta a titi ace za a dauko a kawo min gida na barin ga iya gudin su ai. Get din gidan aka bude ya shiga da mota ni dai ban yi magana ba har lokacin yace ki huta driver yana zuwa yanzu zaku tafi. Muka fito daga cikin motar shi yayi min jagora zuwa cikin gidan a falo nan muka zube dukkan mu yace yanzu dai hankalin ki ya kwata ko kin gudo wurin antyn ki. Murmushi nayi ina gyara gyalen kaina nace abin ne ba dadi ni tsoro na kada anty uwa su zo su samay ni a gidan don ban san abinda zasuyi min ba. May zasu yi maki kuwa banda suyi haukan su su wuce ai ita madam tana da hankali nace haka dai yafi mun an rabu lafiya gida zan koma gidan mu ya fiye min komai zan zauna har ranan da Allah zai kawo min dauki. Dariya yayi yana mikewa yace ko kin zo ke nan sai in bugawa baba a daura muna aure ke kin tare ko da sauri nace hai uncle abin kuma yar zolaya ne ? Yace Allah ba wani abu bane ai sai kawai a dauro aure ke kin riga kin tare nace ba aikaina za a fara ba ni dai driver bai iso bane mu kama hanya. Yace amma dai kya bari ki karya ko ga table can an hada muna tashi ki yi breakfast ki huta sai ku wuce. Nace ban jin cin abinci ne Uncle yace kina wasa ne maza tashi kici abinci ko in hanaki tafiya yau da sauri na mike ban ci wani abin kirki ba sai dai na dan taba kadan sai ga driver ya shigo yana gaida shi. Nima gaida ni yayi tare da min sannu da zuwa na karba mai fuska sake don mun saba dashi dan haduwar da mukeyi. Key ya karasa inda suke ajewa ya dauka yana cewa zai fita yayi services din motar yace mai sai ya dawo. Yana fita ya fuskance ni tare da cewa jinan sai na tattaro hankalina zuwa gare shi yace idan kin je gida yau ina ganin next week magaba tana zasu shigo. Don a daidaita maganan auren mu ban son abin ya dauki lokaci mai tsawo tunda kin ga an fara samun matsala a ta inda bamu zata ba. Don haka next Saturday in sha Allahu iyayyena zasu zo sai a saka muna rana dan naga amaryan nawa har yanzu hankalin ki bai kwanta ba. Murmushi nayi tare da fafin Allah ya kaimu lafiya amma ni ai ban tayar da hankali na ba don nasan komai Allah ke yi . In bashi ba ina ni ina ja da yar wurin anty uwa wa yan nan yan gaye wa yanda boko ya ratsa su ciki da bai din su ai sune suka dace dakai. Murmushi yayi yace a naki ganin ke nan ni sam bani rayin irin su nafi son wacce zan iya controling ba tayi controling dina ba ko may kika ce ? Nace Allah yasa mu dace yace amin mun ma dace din sai dai muyi adduan Allah ya hada hankali baki daya. Driver ya dawo bai dauki lokaci ba muka kama hanya bayan sun gama ganawa da maigidan nashi ni kuma ya cika min jakkana da kudi wai don bukata acan . Yace ba lalai bane mu hadu da sauri don zaiyi tafiya cikin wani sati don haka koda zasu zo yana ganin ma bai kasan. Da haka mukai sallama dashi muka dauki hanya sai garin mu zuciya na cike da damuwa don ban san zan zo gida ba a wanan lokaci. Mun shigo da dan sauran lokaci don sam bayi tsamanin cewa an gama ginan gidan mu ba har sun tare a ciki. Sai driver ne naga yaja ya tsaya a kofan gidan mu nan na fara raba ido ina kallon aikin da sulaiman yayi mu agidan muna tsayawa su yaya Sani dake daban su suka taso da saurin don ganin motan da tazo kofan gidan namu. Ina fitowa suke fadin a safiya ashe ke ne tafe yaya sani da ke kokarin kama marfin kofan ya ce safiya lafiya kuwa ? Na kalleshi da murmushi nace lafiya yaya mun samay ku lafiya ? Ya amsa da lafiya aka fitar min da kaya zuwa cikin gida ina biye dasu duk kan gidan ya juye min kamar ba dan kangon gidan mu ba. Dakin ummi suka nufa da kayan nawa ana cewa Safiya duk suka firfito waje din taro na da murnan su Sai mamakin tsarin gidan nakeyi ina mai kara bin ko ina da kallo muryan mama naji daga baya na tana fadin kina kallin ikon Allah ko. Kin ga yadda ubanigji ke nasa ikin haihuwar mace yayi muna rana a gidan nan don gashi ta mayar damu yan birni a lokaci guda har wutan Nepa mun samu bana. Nayi dariya nace mama mun samay ku lafiya tace aikece abin gayarwa keda kika sha hanya mai nisa. Takalmana na cire na shiga dakin ummi tana zaune saman kujeran da aka saka masu a falon na rungumo ta sai ta ture ni tana cewa rabani da abin kunya kiji. Nace kai ummi har yanzu kunyan ne haka takalman da na cire kanne na suka dauka suna kallo gardama ya kaure a tsakanin su wanan yace kwalba wanan yace roba ne da filawa cikin sa. Dukawa nayi ina gaida ummi ga hasken wutan lantarki da ya haska dakin ya baiyyanar da farin da lafiyan da na kara a lokaci guda. Daidai inna ta tunkaro dakin a take taji wani irin tsana na ya shiga zuciyar ta lokaci guda cikin yake tace Safiya ne yau gidan namu. Da sauri nace eh inna mun samay ku lafiya ina saadatu tace ai tana tafe na barta daki ne wai kan ta ke ciwo yau nace ayya ai gani tafe in duba ta. Kanne na suka kwashi kayana zuwa kuryan dakin ummi sai bin ko ina nakeyi da kallon mamaki acan ma da na shiga an gyara shi tsab ga gado har da sphare din kujera dogo. Na aje jakkana na fito zuwa duba saadatu a dakun su sai muka hade da ita ta taso da kyar muka koma dakin nasu nan naga watau kowa da kalar kayan da aka saka mai a dakin shi. Munyi yaushe rabo da saadatun inna tana kurya tana jin mu saadatun ke ce min komawa zanyi ne ko zan kwana biyu . A nace cikin dariya a a saade na dawo kenan sai yadda hali yayi kuma tace kice muna nan ke nan dake kwana biyu nace kwarai da gaske. Nan dai muka sha hira da ita na tashi ina cewa zan tafi in gaida mama dakin ta. ZAINAB IDRIS MAKAWA SEENABU 8/14/20, 7:12 PM - Ummi Tandama: BAHAGGN , , , , , , , , , , 🧕🏿5️⃣1️⃣🧕🏿 NOVEL DI NA NA KUDI NE NA FADA TUN FARKO KARKI FITAR KARKI KADA KUMA KI KARANTA IDAN BAKI BIYA BA, CIN AMANA BIBIYA TAKAI TA INDA BAKIYI TSAMANI BA, , , Tun farko na fada maki karki fitar min da novel don karatun ba dole bane ba kowa nake ba amma nasan Allah ya isana dama bai tafiya ga banza. Bakiji bake kaida bane don akwai wata mai fitar wa bayan ke ke ce kika fara gani saura dayan nata sai yafi naki don ko abin ba zai zo mata da dadi ba ita. Akan novel akan son kai tajawa kanta masifun duniya sai da na fada maku dan Allah kada ku fitar min don kada in dauki alhakin ku a kaina. Kullun ina nanata maku kin dauka wasa ne ba abinda zai faru dake har yau kaf makaranta novel dina ba wanda zaice maki yasan makawa ko ya san ida take da idon shi hmmm muje zuwa yanzu aka fara ai ya kama binki ke nan ta hanyar dabaki zata ba yar uwa. Ganin gidan namu nakeyi kamar bakon wuri a idona don komai ya canza min a idona sai nake jin wani irin dadi a zuciya ta. Ranan barci dai ne barawo da ya iya dauka na safiyan fari kiran sallah masalacin da Sulaiman ya gina wa mutanen unguwar mu ya karade min kunni na dole mutun ya tashi saboda karan lasifikan da yai yawa. Duk da bani sallah amma na tashi a lokacin na kewaya na dawo na kwanta ban iya kwaciya ba na mike zan fita don shara ummi na dake falo kwance ta dakatar dani da fadin. Dama kin koma kin kwanta don ko dan Albarkan nan ya rabawa kowa wurin ta don haka yanzu ma ba komai akeyi a gidan gaba daya ba. Na koma na kwanta kamar yadda ummi ta umurce sai dai ba barci nayi ba kwantawa kawai nayi zuciya ta fam da tunane. Misalin sha daya saura na safe na fito saye cikin kayan barci na da ban cire ba a falo na samu ummi da kanne na suna karyawan safe tayi masu faten doyan da nazo masu dashi jiya. Na fada saman kujeran da babu kowa saman shi don kasa suke zaune dukkan su tare da yin mika nace duk na gaji kamar nayi wani aiki mai yawa. Ummi ne tace min ai tafiyan mota mai nisa gajiya yake sawa mutum ajiki na gyara kwanciya ina fuskantar su dakya nace ai rabin tafiyan a jirgi nayi ummi daga nan dai zuwa abuja ne ya saukar min da gajiyan. Tace masu gari yau kece mai tafiya a jirgi yar nan lalai duniya abin da ya baka tausayi wata rana shi zai baka mamaki. Kwarai da gaske ummi wallahi ni kaina ganin abin nake kamar a mafalki don nakan yi tunanen hakan a raina. A jiuan zuciya naji ummi tayi tace mhmm ai tun dawowan mu gidan nan yau sati uku ke nan inna ku sai ta baka tausayi don zaman ta a babban gida ta raina kanta sosai a can don basu raga mata ba ko kadan. Tace yaya wajan anty naki suna dai lafiya ko bansan adduan da zawa wanan matar ba a rayuwana sai dai fatan gamawa da duniya lafiya. Shiru nayi ina mai ci gaba da tunane sai da naji ummi tace yanzu yaushe zaki koma naga kin kwaso uban kaya kamar baki da niyan komawa can. Nisawa nayi na dawo daga tunanen da nakeyi nace ummi ba zan koma gidan anty ba indan ba aure nayi ba in je in gaida ita. Da sauri ummi tace akwai matsala ke nan a tsakanin ku ganin kanne na dake zaune sun kallo ni lokaci guda yasa ni cewa babu komai haka dai na yanke a raina. Shiru naga ummi tayi sai can tace a zubo maki faten ne kishashi da zafin sa tun baiyi sanyi ba ki kasa sha barshi ummi ban iya cin abu mai nauyi da safen nan. Sai kaunana tace ai kin san anty Safiya bata son cin abinci ummi kina dai wahal da kankine sai zuwa rana zakiga tana neman abu mai ruwa ta sha shi ne karin kumallonta ita. Ummi na mikewa take fadin mukan na kauye ne sai da abu mai dan nauyi muke jin dadin karin Safe don badon doyan nan da kika zo muna dashi ba da shin kafa da wake zan masu da safen nan su karya ko wanan wanan yar sa idon ne nayi aune da ita tana ferewa wai fate zasu sha da safen nan. Muryan baba danaji ya nufo kofan mu yasani mikewa na isa kofa ina fadin baba har ka fito banje mun gaisa ba. Yace zan fita Safiya jinki shiru yasa na dauka ko barci kikeyi yaya hanya yaya wajen su hajiyar taki nace suna lafiya sun mace agaida kai. Yace ina karbawa yaya wajen gwagon naki kina lekasu kuwa na dukar da kai sai yace aiko baki kyauta ba Safiya ai ba a yanke zumunci tunda ita ta yanke da sai ke ki raya shi lada zaki samu a wurin Allah. Nace baba ai zan tafi amma gaskiya ba yanzu ba yanzu ba nafi son sai ina da aure inje da mijina yafi sauki. Yace kuma fa kinyi tunane maikyau kuma Allah yasa mu dace yaya shi Alhaji sulaiman din suna dai lafiya ko na amsa kasa kasa da lafiya yake shima yana gaida kai baba. Ya juya yana magana da ummi da take kofan daki hakan yasani mikewa na shige uwar dakin namu ban zauna ba wanka na shiga don makewayin da ke akwai a dakin kuma da ruwa a ciki. Na fito ina shafa mai ummi ta shigo kuryan dakin tana ce min may ke faruwa tsakanin ki da uwar dakin naki naga ganin kannen ki yasa baki fada min ba. Nace ummi ba wani matsala sai dai akwai matsala kadan nan dai na fara bata labarin abinda naji da kunne na anty din tana fadi. Ta nisa tare da fadin ikon Allah ai tayi kokari ko wanan da datayi Allah ya saka mata da Alheri ai an gode. Shi son kai sone ba wanda yaki nasa ya samu bata so ki ba taki dangin mijin ta don ko sune nata don da su take zama. Nace aini ummi banga laifin anty ba don sanin ko waye anty uwa danayi don ba karamar macen duniya bane sosai anty uwa. Tace Allah yai muna mafi alherin sa nace amin tace yanzu shi may yace a nasa bangaren nace yace wani sati magabatan shi zasu zo sai a saka ranan aure dayani. Tace to Allah ya kyauta muna magana kiran wayan shi ya shigo nan ta fice dakin ta barni ina karba wayan nayi sallama ya karba yace. Watau kin ga ummi kin manta da kowa ko nace ba hakana bane yanzu na tashi ina batun kiran ka sai gashi ka kirani yanzu. Yace yaya gajin hanya don nasan akwai gajiya nace Alhamdullahi yaya na barku can? Ya amsa da kalau sai nace yallabai naga ka mayar muna da gida kamar bila ubangiji Allah ya saka da alheri ya dada daukaka da yalwatan arziki murmushi naji yayi yace anty ki ta kiraki kuwa ? Ya kawar da maganan nan take nima murmushin nayi mashi nace baka son godiyan nawa ke na ko ? Yace tambayan ki nake yi antyn ki ta kiraki da kika zo arewa? Nace har yanzu bata kirani ba yace na san za a rina ai, kyale ta, jiya ta kirani yau ma da safen nan munyi magana da ita. Sai naji bakina yana tambayan shi may tace ma ? Sai yace min ina ruwan ki da maganar mu da ita. Haba uncle dina don Allah yaya kukayi da ita yace maganan dai ne na in rabu dake in auri diyar hajiya uwa don tafi asali. To kai may kace mata yace cewa nayi haka shine daidai don dama ke baki waye ba. Nace to Allah ya hada kowa da rabon sa yace amin ai ya hada tunda ya hadani dake kin sace min zuciya yanzu bani jin maganan madam dina kuma. Murmushi nayi wanda ya baiyanar mashi da jin dadi na a fili tare da sauke ajiyan zuciya tare dacewa nagode uncle dariya yayi yace aini zan gode maki da baki yarda sun hadani da ke ba. Murmushi nayi nace ai ba zasu iya ba don hadin Allah ne bana mutum ba da zasu iya da sun raba ko tunda duk wanda aka fadawa irin kazafin da sukai min dole ya dauka gaskiya ne. Ya katse ni da cewa ai baki san wani abu ba nace ina jinka. Yace ai tunda ta gabatar min dake da farko hankali na ya kwanta da zancen ki don haka ma daddy su twins shima ya yaba da hankalin ki. Banga abinda zaisa yanzu daga baya ba kuma ta kawo min zancen wata na dai ce da ita haka ne daidai sai idan lokaci yayi zata sani. Mun dauki lokaci muna waya dashi kamar ba kudi yake kashewa ba sai da ya gaji don kanshi yai min sallama na tashi na karasa shiri na dakin mama na fara shiga muka gaisa muka dan taba hira sai na wuce dakin inna inda na samu saadatu ita kadai a dakin wai inna tafita unguwa. Nan na sake jikina muka dauki lokaci muna hira da ita nake tabayan ta fanin Isah dayai mata ciki take fada min bata da labarin shi. Nace baya kawo maki komai ne tace tun wanan lokacin bai kara kulata ba kuma ba wanda yai masa magana akai ana batun ginan gidan mu. Da yaya sani ya shigo na tuntube shi da zancen sai cewa yayi min ai shi ba abinda ke gaban shi ke nan ba nace haba yaya sani idan baku tsaya muna tsaye ga alamarin mu ba wa zai tsaya muna akai yace zai duba yagani yadda za a yi. Anan muka bar zancen ban jima da fita dakin nasu ba inna ta dawo gidan tana shigowa sai ta fara budan hancin ta tana shakan kamshina dana bari dakin tace. Safiya ta shigo dakin nan halan sai Saade tace eh tace karuwan banza ina shigowa naji kamshin turaren ta. Haba inna Safiyar ce kuma karuwa Saa ta fada mata haka na tace idan ba karuwa bane may nena ita uban wa take nema a birni. Abinda kikeyi gaskiya inna baida kyau shiyasa kullun bamu ganin karuwa ga alamarin mu don bakin hassada irin naki. Aiko tayi cikin Saade din da fitina ita kuma kamar mai jiran uwa nan suka shiga yaba ma juna bakar magana har ya jawo hankalin mutanen gida aka tsaya sauraren ta yaya Nura da yaya Sani ne suka shigo gida suke tambayan ba asin maganan. Inna ta kama inda inda sai Saaden ne ta fada masu abinda ya hada fadan da sukeyi daidai ina fitowa daga daki kenan maganan ya daki kunne na. Cak na tsaya raina ya baci sai yaya nura ne yace in ma karuwanci Safiya ke yi a birni ai anci albarkacin karuwancin ta a gidan nan. Yaya Sani ya karbe da fadin wallahi fa ke yar taki mai take zaman suna takeyi maki a daki da tsohon ciki komay ba gara safiya ba kowa ya san alherin ta ne ya kaita ga haka. Wallahi inna idan kice bazaki bar halin nan ba watarana sai kinji kunya ba kadan ba zuwan Safiya dakin ki alheri ya kawo ta ba tsiya ba. Don zuwa tayi ai magana da Isah asan halin da Saadatu ke ciki don bai waiwaye ta ba har yau mama tace kai kedai Rakiya halin ki baiyi ba wallahi. Safiya tayi maki kama da wacce take karuwan ci koda ba a ganin zuciyar mutum ai abin duniya baya boyuwa da muji tun tuni. Daki na koma van iya tsayawa na saurari sauran maganan ba sai dai na sa a raina cewa ba zan sake shiga dakin inna ba komai ya faru kuwa. Har yamma naji anty bata kirani ba don haka na dauki waya na kirata amma har wayan ya katse bata dauka ba. Ban kara kiranta ba da dare muna zaune a dakin mu sai ga baba ya aiko a kira masa ummi ta dan dade wurin sa ta dawo muna hira da kanne na sai tambayan ta kauna tayi tace halan baba yaji zancen maganan dazu ne ummi ? Tace ina ruwan ki sai kin san abinda naje yi gunsa nace kai kedai baki da kunya Aisha may zai kara ki idan kin ji ni ban ma son baba yaji zancen tace sai dai kada a kara don Nura ya tare shi da zancen a waje. Ina ga ki je gun su kawun ki kafin bakin ki su iso kin dawo zaifi nace to ummi zan tafi amma ba don naso a raina ba don dai ta ce in je ne kawai ba yarda zanyi. Kwana biyu da zuwa na na shirya dani da kani na sai kyauyen su ummi na ida mahaifanta suke da zama. Tafiyan safe mukayi don haka muka isa da wuri mun samu karbuwa na mutunci a wurin su aka kai muna kayan mu dakin kakan mu mace . Bayan muci mun sha daga abincin su da suka fi karfi suka gabatar muna dashi muka zauna a na gaigaisawa da yan uwa. Sai yamma mazajen suka dawo daga gonakin su wanda dashi suka dogora suna ci suna sha daga gare shi sai kiwo da suke hadawa dashi. Kakan mu ne na karshen shigowa gida sai da ya huta mukaje gaida shi bayan mun gaisa ya tambaye mu mutanen gida. Yake tambayana zancen aure nace insha Allahu malam ba za a dauki lokaci ba zanyi yace ko dai anzo sallaman mu ne gaba daya nayi dariya ina ce mai a a na dai zone in duba ku. Shekaran jiya na zo shine ummi tace in iso nan in gaida ku yace ai ta kyauta tun bayan abinda ya faru dake bamu sake ganin ki ba sai nake ji wai kin samu mane mi a can birni har yai masu abin arziki a gida. Na soke kaina kasa din kuya yace yanzu dai ciwo ya wuce ko nace malam yadai lafa dai amma ai ciwon ba mai barin jiki bane kwata kwata. Yace ummh ummh kar ki yarda da wanan ki sa a ranki Allah zai baki lafiya ko yana nan baya tashi har a manta cewa kina dashi a jikin ki nace Allah yasa malam. Yace ai kin ga rakumi nace eh malam yace to komai na jikin shi magani ne bani na fada ba in ji fiyayyen halita SAW ya fadi. Yace da zaki samo fitsarin nan nasa koyaushe ya zama maki kamar ruwan shan ki to da kan ki zaki dawo nan ki bani labari bance zaki warke ba atake amma akwai faida a gare shi. Nace shi fitsarin rakumin yace kwarai kuwa sannan namar shi ya zama maki abin ci ko yaushe akalla a sati ki kici shi ko sau biyu. Sai kuma nonon shi ki dinga sha akai akai shima yana da faida sosai a jikin bawa ya dan kurkure baki da ruwan butan dake gefen shi yace sannab kin ga kashin rakumi nace eh malam yace ki samu kashin ki gone shi zai ya kono sosai sai ki daka ki dinga sha da albarkan annabi zaki neme ni indan muna raye. Ba fa wai matsalan ciwon da ke damun ki ba kawai a a koda jikin ka ne baka gane kansa ba ne mi daya daga cikin sassan jikin rakumi ka riki sahihi da yardan ubangiji zaka ga faidan shi. Nace ikin Allah yace shiko kashin nan nasa da kika gani nace eh malam mutane ne basu gane mai ba ai da zaki samay shi. Ki busar dashi ki samu kanufari ki hada dashi kina yin hayakin shi a jikin kin ki sai yayi murmushi yace aiko maza dake samun matsalar rashin karfin gaba gane wa ne ba sayi amma da mutum zai samay shi yayi yadda nace maki sai ya dinga hayaki a gaban shi dashi ai ba katamin taimako yake yi ba za ka iya kuma dafa gaban shi sai dai ba a faye samun shi ba don tun wurin soke shi ake sayewa. Namiji in dai yana amfani dashi ai masa romon shi da bakin iri ban san yaya kuke kiran bakin iri ba ku. Nace ko habbatussaudat yace sunan sa ke nan ko nace eh yace sai a hada da kanumfari da citta da masoro da tafarnuwa yace ai bashi ba gazawa ga iyalin shi don karfi ne zai taso mashi sosai yaji shi gyagyan kamar dan shekara a shirin a duniya. Yace kaiyya ai abar gado tun baya an dauki aladun wasu mun dora wa kan mu amma kin ga mu na kauye ai bamu bar gado ba, kin ga ko mun fiku karfi da lafiya don mu ciwon nan da ake fadi duk bamu sanshi ba. Nace hakane malam amma ai inda mutum zai samu rakumi ne aiki malam har ya tara fitsarin shi da yawa haka. Yace kuke nan dake birni amma munan ai shi yafi komai sauki ko yanzu kafin ki tashi zan iya sa a tara maki jarka kuma samo maki sauran sassan jikin ki jeraba ki gani. Godiya na fara yi masa yace may ye abin godiya a ciki lafiyar ki ai namu ne duka yanzu barin fita idan na dawo maci gaba don lokacin sallah yayi yanzu. A Zuciya na fara tunabe nayi yadda mutum zai sha waban abin da ya fada min amma dai ko yaya ne zan nema un jeraba in gani nma mikewa na yi zuwa rumfar kakata inda dakin ta yake na zauna rubuta duk abinda yace min nayi a wayana. Bayan munyi sallah aka gabatar muna da tuwon surfafen dawa da miyar danyen kuka an lema man shanu a saman shi. Kanina yace bazai ci ba shi zai fita yasamu bread da shayi ya sha azuciya ta nace ikon Allah ashe akwai abincin da dan gidan mu zai kyamaci ci a yanzu. Nikan naci shi sosai nayi kat tare da hamdala na wanke hannu na sai naji kawo habu ya shigo yana cewa ina bakuwar tamu ga dan tsaraban kauye nasan ba iya cin abincin namu zakiyi ba ya miko min leda na karba hannu bubiyu ina cewa ai ko naci kawu sai da na koshi. Ledan na aje a gefe na shima ya samu wuri ya zauna muna hira kakan mu tana sa muna baki jefi jefi. Nan dai har ya gan garo kan zancen aure na nake fada mai halinda ake ciki yanzu ga zancen nawa ban boye mai komai ba ya murmusa yace abinku ne na yan birni. Baku neman gida sai abu ya kure maku gani kuke yi kamar mu kauyawa ne komai bamu sani ba banda noma da kiwo amma ai aiki sai kauye. Nace kawu ba hakana bane nayi nisa ne daku ko gida sau biyu ke nan nazo tun tafiya na yace to kin ga tunda kinzo yanzu ai ba a barki haka ki koma ba ai wani dan abu ba. Kin ga ki samu kaucin gwandan daji da kan tunkiya ki daka ai maki miya dashi kaucin zaki iya dafawa kuci har da yara in Allah ya kawo su amma fa banda mai gida wanan mallakane sahihi. Sai na neman farin jini ga dukkan dangin miji da ma mijin kan shi zaki samu farar dawa da farin goro farin kudi kurma farar kaza sayen tunfafiya na gabas din shi ki hade ya bushe kiyi wanka dashi da hayaki bayan kin dake su wuri daya, sai naga yayi murmushi. Don watse makircin makiya kuma zaki karanta Lah illah hailala muhammadun rasulallah, hasbunal lahu wani imal wakil kafa dari duk safe zaki ga yadda zasu kwashe da yardan Allah. Domin tsarin jikin ki kuma zaki samu ganyen hankuwa da ganyen sabulun dawaki da ganyen geza wanda suka fadi kasa da kansu a dake ki sha. Wanan ma na tsari ne zaki samu gero wanda ya fidda kai ya baci yayi geza da suren fatake a dake asha da kunu . Kiran da matar shi ta aiko tana mashi ne yasa ya tashi badon ya gama bani ba sai da ya fita nace ma kakana ni ina zan samu wanan abin daya fada min tace Allah ya kaimu gobe sai in zagaya nan bayan gari in harhado maki su wanda babu in kin koma can gwagon ummin ki sai ta samo maki ban samu ganin kakana ba don ance yana waje da bamin fulani da suka zo wurin shi. Don haka nayi shirin barci na kwanta da wuri sai barci can cikin barci na naji Shafiu ya dawo kakan mu nace mashi ya dauki ga leda nan da kawun mu ya sayo muna nama ciki. Ban iya bude idona ba don barcin da yaci karfina a lokacin har ya gama ya fita ban tashi ba tagama abinda take yi ta rufe kofan daki ta sauke min gidan sauron da ta kafa min na gyara kwanciya na asuba ta gari yan uwa. ZAINAB IDRIS MAKAWA SEENABU 8/14/20, 7:12 PM - Ummi Tandama: BAHAGGON , , , , , , , , 🧕🏿5️⃣2️⃣🧕🏿 NOVEL DINA NA KUDI NE NA FADA MAKI KADA KI FITAR MIN DA NOVEL AMANA NE GARE KI IDAN KUMA BAKI BIYA BA KIKA KARANTA ALLAH YA BI MIN HAKKINA A KAN KI DON BAN YAFE MAKI BA Washe gari malam yayi sakon fita zuwa wani kauye da fulani da mano ma suke rikici akan gona don haka ban samu ganin shi ba ranan sai dare sosai mota ya dawo dasu har kofan gidan shi don haka ba halin in ganshi da daren nan. Gashi washe gari zan koma don shirin taron bakin da zasu zo min anan kauyen su ummi na sayi kwan zabbi mai yawa da kuma zabbin da ransu wanda zamu gyara masu idan sunzo . Nono har na rasa inda zan sakowa yana kawo min kyautar kwai da nono tsaraba. Naje sallama da malam yace Allah sarki Safiya sa ar safe gashi ban samu ganin ki ba har zaku wuce nace malam ai zan dawo kafin na tare yanzu ma zan koma ne na tari bakin da zasu zo yace to ga nawa gudun mawa rago nan sai a soya masu idan sun zo Allah ya tabbatar muna da alheri yasa muce gwanma da akayi. Nace amin a kunyace yace banyi fushi ba duk da an kasani amma in mun hadu da abokin nawa watarana zai bani kudin fansan ki a gareni. Nayi dariya kawai na mike ina mashi sallama muka fito don mota nasa aka dauko muna shata dagani sai Shafiu kawai sai kayan mu. Mun iso gida kafin sallah azahar aka fitar muna dakaya zuwa cikin gida na sallami driver tare da yi mashi godiya nace ya ban nombashi idan muna da sako yakai muna. Don tunda muka kama hanya yake muna hiran yanayin kasar da sauran su shafiu ne ke bashi amsa ni sai jefi jefi nake saka masu baki ga hiran nasu. Mun shiga gida sai bin mu akeyi da kallo Aisha ke fadin ga mutanen kauye sun dawo munko ga alama don ga tsaraban kauye nan hardasu zabbi da kwai. Ummi ce ta buge mata baki tace kai surutu muka shiga daki na huta mama tazo ta tare mu ta tambaye mu yaya muka barsu nace lafiya suna gaida ku. Zata juya nace mama ga nono nan da kwai da zabbi nazo dashi don bakin da zasu zo jibi sai a gyara masu. Taji dadi tace a a baki muke dasu tafe ashe sai ta karasa shigowa dakin tana cewa yanzu yaya za ayi masu dashi don mu fara saboda akwai aiki sosai. Nace mama yadda ya dace zakuyi dashi mana tace to yanzu bari in aika ma mamakin suzo asan abinyi kafin gobe a makara. Ta aika kiran su mama zuwa karfe biyu sai gasu sun iso nan ta gabatar masu da komai don haka suka fara tsara abinda zasu yi na kawo kudi na basu wanda za a sai kayan aiki. Da farko an yanka ragon da malam ya bani nan suka shiga gyara saadatu ne kawai ta fito inna cewa tayi wai ba a sata a maganan ba. Kowa ya share ta a gidan yaya Sani yayi fada har ya gaji baba yace a kyale ta ranan asabar mi salin karfe dayan rana sai ga su kawu abu sun shigo wai babane ya aika su zo nace kai baba ho tambayan aure shine harda taso su kawu su zo kuma. Zuwa karfe biyu saura suka iso mota biyu akai masu taron mutunci sunci sun sha sai suka gabatar da zancen neman aure da kuma suna son a yanke masu sadaki kafin su wuce. Baba yace sadaki dubu ashirin zasu bayan ba kuma zasu wuce ba sai an daura aure don ni ba budurwa bace. Duk yadda suka so baba yaki yarda dole suka amince za a daura kagin su wuce mu dai sai ji mukayi mai shela na sanarwa a na gaiyatan mutane kofan gidan babana. Nan dai aka sheda daurin auren na da sulaiman akan sadaki dubu ashirin kacal ina daki kwance shafiu yazo min da labari. Zubur na mike ina cewa yaya uncle zai min haka kuma ai ce min yayi tambaya zasu zo da kuma saka rana. Mutane sun rage yawa sai ga bakin daya daga cikin su ya shigo na fahinci kannin Sulaiman ne don naji yana cewa ina amaryan nawa take na ganta don ban santa ba. Nayi saurin boye sai da mama ta shigo tace in fito mu gaisa hijjab kawai na saka na fito yana zaune falin ummi yana gani na yace ba laifi shiya sa bross ya lake sai ke amma kamar na san fuskan nan taki wani wuri. Gaida shi nayi shiko sai sheri yake min yana fadin yau ban san yadda zai ji ba idan yaji har an daura aure gaba daya akwati biyu na gani anshigo dasu yace ga sakon baaban mu nan tace a kawo maki na mun gani muna so gashi kuma har kin zama namu gaba daya. Na dago kai da kyat nace aimin godiya wurin baaba kafin inzo yace zata ji ya mike yana fadin zamu tafi do garin naku akwai nisa sosai wallahi ai gara da aka daura gaba daya muka huta. Mukai sallama ya fita nan aka fara fita masu da kayan da aka hada masu na ganima suka ce harda wani dawai niya haka kuma. Nan sukai min sallama suka tafi cike da farin cikin irin karramawan da suka samu a wurin mu sun kuma yaba da halin baba da bai yi zari ba da kwadayi ya karbi kudi kadan a sadakina. Nan aka bude akwatin mama ta fara daga dankara dankaran zannuwan dake ciki da lece har goma sha biyar dayan akwatin sauran tarkace ne a ciki aka zuba. Baba ya shigo har dakin ummi da kudin sadakina a hannun shi yana cewa ina Safiyan ga sadakin ki nan hakkin kine ba namu ba sai dai nayi karanbanin yake masu mafi saukin sadaki don samun albarkan aure. Na mika hannu bibiyu na karbi kudin tare da nufan ummi na dake zaune gefe dasu tace a a rike abunki Allah yasa albarka duk wanda ke dakin yace amin. Ya fita na koma kuryan dakin na haye gado tare da lafewa kamar mai yin barci ina jin suna watsewa da guda guda. Ya saura sai ni kadai da yan gidan mu kowa ya kama gaban shi daga inda nake kwance na jawo waya na naji ina son kiran anty in fada mata ta ida aka hau tanan ake sauka. Amma har ya katse bata dauki wayan ba na kara kira yan biyu ta dauka tana fadin tana sallah na kira sunan ta take ta gane ni mukai ta hira dasu har tagama ta dauki wayan. Muryan ta ba yabo ba fallasa muka gaisa tace abubuwa sukai mata yawa shiyasa bata samu kirana ba amma tasha ganin miscall dina. Mukai sallama nai mamakin jin bata tambaye ni Sulaiman din ba nima kuma ban mata maganan shiba. Faiza na kira tace ke yar kasa ai na dauka ki manta danine ina son in kiraki ina jin tsoron kada ki fada ma mutumiyar tamu nace haba don kin kirani sai in fada mata kuma. Naji ta shake murya tace dama ina son kiranki in sheda maki anty uwa nan tazo ita da yaranta sai faman shuka muna tsiya suke a gida. Nace don Allah yaushe tazo tace yau kwananta biyu da zuwa wai may ya hadaki dasune Safiya? Nace ni kuwa ina na san su banda wurin liyafan da muka hadu a abuja. Tace aike gara da baki gidan don ko ita anty ta gaji da su wai kuma sati daya zasuyi a gidan nace tirkashi . Tace ke dai ai kin auna arziki da kika tafi basu samay ki ba gani nan kamar aiki zai kashe ni yan iskan yara kawai komai basa iya yiwa kansu sai dai ai masu. Amma kamar naji ana maganan Sulaiman da suka ganin sai sukayi shiru basu san naji abinda suke fadi ba sai dai banji ba sosai kamar suna cewa inba shi ba mai zaiyi da yar kauye ga mata birjit a birni. Nace nice yar kauyen ke nan ko tace wa yasanar masu yan bakin ciki kawai. Mun dauki lokaci da ita muna hira ta kashe tana cewa wai ana kiranta don haka mukai sallama tace idan taji wani abu zata kirani. Ta barni da tunane nace a raina ashe sunzo din Allah ya taimakeni dani ce zan zama masu jakar aiki harda gaiya zasu hada min ga korar karen da sukayi niyar yi min a gidan. Da dare na yi shirin kwanciya sai ga wayan sulaiman ya shigo min ina dauka naji ya kwashe da dariya yana fadin Allah dai ya sakawa baba da alheri. Wanan irin halarcin haka aiba kowane zai iya ba zankadedeyar kyauta haka abin yazo min da sauki da na dawo yanzu sai kawai nazo na dauki matata mu tafi. Nace sai kace amaryan dako yace ai itace don ko baba ya hutar dani ga komai yayi yadda sunna yace ayi saura may kuma ba in daukeki ki tare a gidana ba. Nace kana fara yi min haka aiko dan walima ka bari muyi don Allah yace kai Safiya bansan baki da tausayi ba . Allah ya kawo min sauki kina son kuma ki kirkiro wani abu na daban kisa ai walima ko a dakin ki kaso sai ai maki. Kara marairaicewa nayi nace don Allah uncle kada muyi haka dakai yace kedai zancewa kada muyi haka dake shekarana nawa ina zama gwauro yanzu kuma da aure na zaki mayar dani gwauro da karfi da yaji. Kunyan zancen nake ji don haka nayi kokarin kawar da zancen da tambayan shi ka fada ma anty kuwa ? Yace bari nayi sai taji ta kirani zamuyi maganan da ita don yanzu ban shirya abinda zan fada mata ba. Ajiyan zuciya na sauke nace ashe su anty uwa sun tafi lagos din yau Faiza ke fada min yace itace info dinki a gidan ke nan nace a a magana ne ya kawo ta fada min. Bayan muyi waya dashi ya sheda min a sati biyu yake son in tare gidan shi don haka na fara shirina da wuri zai dawo next week in Allah ya kaimu. Bayan na kashe wayan ne na sauke ajiyan zuciya sai yaya Saadu ya fado min a rai don haka na kirashi don in sheda mashi. Kira biyu ya dauka yana cewa yar halas yanzu muke maganan ki don ga takwaran kinan ta hanamu shakat sai kuka take muna nace subbahanallahi. Kun bata magani kila cikin ta ke ciwo ina jin yana tambayan Samira ko an bata magani tace bata bata ba. Ya juyo gareni yace yaya garin kina lafiya yaya logos nace ni ina gida yaya yace kina gida tun yaushe ? Nace sati daya ke nan lafiya kika je gida yanzun Safiya kodai auren ya tashi ne ban sani ba ? Nace aure sai dai ayi fatan dacewa da zaman lafiya yanzu yace may kike nufi tukun nace abinda na fada yanzu yaya. Wai tsaya don Allah da gaske kikeyi ko wasa nace wallahi ko yau baba ya daura min aure daga zuwa tambaya sai daurin aure daya ni. Yace don Allah ki bari ni ina nan ina cewa ni zan bada ke don asan ba zumuncin wasa ke tsakanin mu ba ashe baba ya rigani. Nace wallahi yaya ni yanzu duk abin ma ya daure min kai wallahi duk na shiga rudu wallahi ban shirya komai ba yaya. Yace Allah yasa haka yafi zama muna alheri nace amin yace yaushe ne tarewan naki yanzu nace ban sani ba yaya amma dai naji yace in two weeks yake son in tare. Yace haka yayi yanzu ki bari zamuyi waya zan kiraki ansan abin yi kafin in zo nace yaya kada kace zaka wahal da kan ka don yace baison inje da ko tsintsiya gidan shi mata ya nema mata za a kai mashi. Yace ayi haka bari dai mu gani zan kiraki da safe in nayi shawara mukayi sallama ya kashe wayan. Na sauke ajiyan zuciya tare da kifa wayan nawa ina mai sauke numfashi tare da lumshe idona sai na mike zubur na fada ban daki tare da dauro alwala na fito. Na dade zaune ina kai kukana ga ubangiji da ya tabbatar min da alheri ga wanan auren ya kawar da duk wani abin ki a gare mu. Na dauki lokaci mai tsawo a zaune itama ummina tana nata a falo sai kanne na ne ke ta kwasan barcin su hankali kwance na shafa tare da mikewa na nade abin sallah. Sai naji Ummi tace min kin idar na amsa mata tare da fitowa falon na samay ta na zauna anan. Take cewa dani gashi dai yau Allah yayi ikon shi kina da aure a kan ki a gidan nan abinda kowa bai zata ba akan ki. Don haka sai dai muyi fatan Allah yasa ma auren albarka Allah dai yanufa shine mijin ki kece matar shi kada kisa kowa a ranki ita ma wace tayi maki wanan dalilin aure kada ki yarda ki yashe ta komai ritse don ita din ba abin yaddawa bane a gare ki. Ki manta da komai ku zauna lafiya don alaka ya sake hadaku dama duk wa yan da zaki samu a zurian shi ki zauna lafiya da kowa. Kin daiga shi abin duniya bai rufe mai idon shi ba to kema ki zama haka na ga yan uwanshi da nasa sai a zauna lafiya. Yanzu sai mu jira dawowan shi muji yaushe yake son ki tare dakin ki nayi saurin cewa ummi waifa a cikin sati biyu yake son in tare. Sai naji ummi tace to shike nan mana Allah yakai mu lokacin nace ummi may aka shirya da za a biye mashi don yace cikin sati biyu yake son in tare ? Tace akwai Allah shi zai hore muna abinda zamu kai masu a matsayin gara bashi kenan ba sai ki tare shike nan sai kuma a jira suna idan muna da sauran kwana. Cike da jin kunya na sauke kaina kasa ina cewa kai ummi sai tayi dariya tace to may za a jira kuma yanzu bayan wanan sai maman ku ta shiga zuwa reno. Kunya naji nace kai ummi tin yanzu har an fara wani maganar haihuwa can a dai samu a tare din don dazun Faiza ke fada min wai anty uwa tana lagos gidan anty kan maganan. Sai naji ummi tace ai basuyi kamar Allah ba don aure ya riga ya dauro a tsakanin ku ko ba kuma zasu iya rabawa ba insha Allahu. Mun dauki lokaci muna magana kafin mu kwanta barci da safe ma da muka ta shi da maganan muka tashi kuma a dakin mu. Kiran shi ne ya shigo min na dauka da ladabi ina gaida shi bayan mun gama gaisawa yace Safiya a gidan ku wa kike ganin ta samu kebewa da Nafiu kanina da suka zo. Gaba na ne ya fadi dam nace a gidan mu kuwa gaskiya ban sani ba don ni ina daki har suka wuce yace ki dai bincika din akwai wace ta fada masu wai. Rufa rufa za ai min kina da cuta a jikin ki abincika kafin ki tare don kar a cuce ni da sauri nace ba kowa zai min haka ba sai inna . Yace wacece inna nace dashi maman su yaya Sani don itace kadai zata iya yimin haka don tasha fadawa mutane hakan. Yace subbahanallahi nan na fara bashi labarin zaman ukuban da nakeyi da ita tun tasowa na a gidan har zuwa yanzu. Yace ok ita din ce na fada ma hajiya baaba da ta tuntube ni da zance nace ba gaskiya bane sai da mukayi gwaji dake kafin mukai ga matsaya nasan kuma ta gamsu da magana na. Zan kuma kara yi mata bayani yadda zata fahince ni amma dai wanan matar ko bata da hali mai kyau yace zan gaya wa baba da kaina don ya dauki mataki akan ta kada yan uwa na suzo ta bata auren. Nan dai ya kwantar min da hankalina muna gama waya na kira ummi na ina fada mata ita kuma bata tsaya ba ta kira mama tana sheda mata abinda ke faruwa. Mama tace a bari baba ya dawo gidan ai ba kyale ta za a yi ba dole ai mata magana wanan karon. Basu gama magana ba sai ga baba ya shigo a fusace tun daga kofan gida yake kwadawa inna kira mama tace gayacan ma shigo ko yaji ne ma ? Inna tafito tana cewa malam wanan kira haka kamar makaho ni har gabana ya fadi ai. Yace gaban ki ya dade bai tarwatse ba munafukan banza muna fukar wofi kawai ta Allah ba taki ba. Munafincin ki bai ciba sai ki canza wani kafin ma ki canza badai a gida na bakan don safiya bata tarewa kina gidan. Fadin haka yasa yaya sani dake bayan shi yana sauraren maganan baba din yace saboda may baba ? Yace sani wanan uwar taku wani irin hali ke gareta yanzu ace duk halarcin da yarinyar nan take muna agidan nan kaf bata debe kowa ba wai amma Rakiya bata gani. Sai tabi baya ta yi munafinci akan auren Safiya don ta kumsa muna bakinciki kawai duk a taru a lalace uwa zaune diya zaune a gida kamar yadda take da yar ta a daki. Yaya sani ya sake fadin may ya faru ne baba may kuma innan ta sake yi ne wai ? Yace sani wai ka diba ashe zuwan mutanen nan garin nan Rakiya ta sillace jiki ta ja daya daga cikin bakin nan ta fada masu wai ba lafiya ke ga Safiya ba ayi bincike kafin ta tare. Sai gida ya dauki salati dama kowa ja waje cirko cirko a tsaye ana sauraren baba yaya Nura yace an ko yi haka wallahi dama nayi tunanen in ba wani abin zata fada mai ba don naga lokacin da ta fito suna alwala ta kirashi gefe ni kuma muna shagon musa mai tereda zaune wallahi na ganta. Kai munafuki da ka ganni sai akace abinda na fada mai kenan ko may yace nidai na gan ku tsaye wallahi ba wani ya fada min ba da idona na ganki inna. Baba yace yanzu yaron nan ya kirani yana fada min sakon da aka kaima uwarshi gida don haka ban zama da macen da bata son diyana da karuwa a gidan ki tafi gidan ku har, , , Yaya Sani ne yace don Allah baba kada ka karasa don Allah sai ya fashe da kuka sauran yaran suka dauki kuka gaba daya. Ummi tace malam kayi hakkuri ko don yaran nan idan ka sallamay ta yanzu ga Saadatu da ciki ina zata yace inko ban sake ta ba yanzu bata zaka min gida sai safiya ta tare. Nan dai gida ya dauki kuka kowa da abinda yake fada yafice yabar gidan nace gidan mu gidan danger. ZAINAB IDRIS MAKAWA SEENABU 8/14/20, 7:12 PM - Ummi Tandama: BAHAGGON 🧕🏿5️⃣3️⃣🧕🏿 NOVEL DINA NA KUDI IDAN KIN FITAR MIN ALLAH YABI MIN HAKKINA A KAN KI IDAN KI KARATA BAKI BIYA BA BAN YAFE BA NA FADA NA SAKE FADA A KIYAYYE DON ALLAH DON CIN AMANA BALA,I NE, , , , , Shigana daki yayi daidai da shigowan wayan Faiza nayi saurin dauka don nasa magana ya samu ke nan ina dauka tace wai safiya may ya faru ne daga jiya zuwa safe dai surfa maki zaki ake a gidan nan babu kakautawa. Tace bari dai zan kiraki ina zuwa sai ta kashe wayan nata na bi wayan da kallo kamar shine faiza na bashi amsa da cewa sunji zancen auren ke nan. Shigowan gwagom Ummi na gidan ne ya dawo da kowa a cikin sai tin shi don ta shigo gidan ne da gudan ta tana fadin ayyurriri amarya Allah ya kawo mu lokaci ya kawo mu yan bakin ciki kunji kunya masu hassada kubi bango ku narke don Saifiya da Sulaiman zama daram. Su yaya Nura ne ke fadin gwagon ummi gudan bai isa ba sai ta kara fadin ayyurriri Amarya. Yar shagali yar biyan bukata yar galari , makulin mota ke akaba na kofan daki ke akaba sai yaya Sani ya manna mata kudi a goshi nan ta kasa karasa kirarin nata ta saike guda tana fadin Amarya bakya laifi, ina amaryan take ne. Sai mama tace a a gwago karkizo ki sa min yarinya kuka fa munyi arziki tunda aka daura aure bata wani bata rai ba. Gwagon ummi ta juya ta kalli mama tace kuka kuka fa kikace Yo kukan may ina so kina so sukayi fa kinji ki da wani zancen badai yaran yanzu kuka kan. Aiko na munafunci basa yi koda kuwa budurwace sun daina kuka tace yo Allah na tuba wanan din ma ai tayi kawaici da watace da yanzu ta kafa muna DJ a gida ta ruda unguwa da gaiyatan shedanu masu hana auren zaman lafiya. Ummi ce ta fito fuska a daure tana yiwa gwagon sannu da zuwa ta bi yar dan uwan nata da kallo tana amsa gaisuwa nan tabar mama da sauran yara tsaye ta nufi dakin umin nawa. Kara gaisawa sukayi ta kasa daurewa tana tambayanta make faruwa ne naga ranan farin ciki a gare ki gashi kuma kin bi fuskan ki duk kin daure ? Ummi bata iya yin magana ba sai hawayen dake zubo mata sai nice nayi karfin halin fito ina cewa gwago an shigo tace a a kina ciki dama ? Nace na kwanta ne dama tace may ya samu uwar taki ne haka kuma ranan farin ciki a gare ta gata tana kuka kuma ? Nace ba wani ubu bane zancen Inna ne dai shine takema bacin rai , Innan taku tayi wani abune mara kyau ne kuma nace gwago takan rasa ne ai mai hali baya barin halin shi. Zuwa tayi ta fadama ma dagin mijin antyn mu wai suyi bincike anty mu na da cuta a jikin ta amai rufarufa ne don acuce shi. Salati gwagon ta saka tun kafin taji karshen maganan tana fadin amma dai anyi yar banza mata anan . Da ita nufinta haka za a hada auren bai san halin da take ciki ba to mu bamu da gadon sheri a tare damu. Yanzu may ake ciki tana sake tambayan Aisha kauna na don ta san ni da ummi ba zata gane komai a wurin mu. Aishan tayi mata bayanin komai yadda zata fahinta tace hakan da malam din yayi yana da kyau tunda dai Rakiya bata da niyar gyaran halinta. Nace ni gwago na rasa mai nayi wa inna a duniya tun ina karama bata kauna na haka. Tace bazata ko kaunace ki ba don indan kika ga mutum da yafaye wanan halin yaje bakar bincike binciken ta an fada mata abinda ya tayar mata da hankali shi ne abin yake wahal da ita haka. Kin san wasu basu da dogaro gun Allah da zaran kishiyar su ta samu ciki zasu je a bincika masu mai zata haifa da sauri nace kai haba gwago tace Allah sarki ai wanan abin abu ne da ya kewaye birni da kauye don ko ina akwai marasa imani. To duk yadda akayi irin haka ne ke damun Rakiya taje an mata buncike an fada kata cewa abinda zaki haifa na da arziki sai ta ce a jefo mao kaddara da karshe kuma ba mai iya hana ikon Allah sai kaddaran ya juye Alheri ga bawa. Shiru mukayi muna sauraren gwago da al,ajabin abinda take fada muna tace don yanzu an daina wasu abu saboda wayewan kai da mutane suka samu. Amma har gobe a kwai masuyin zagon kasa don su basu bar gida ba don haka yake da kyau mutum ya nema wa kansa rigakafi tun kan rana ya baci. Don haka kema yanzu ki saurare ni don zaki tafi cikin bakin fuska da baki san su ba baki san halin su ba . Don haka zan baki makarin kwarce ko wani zai maki ba zai kamaki ba murshi nayi a raina nace kai gwago ho. Zaki samu kwai na zabo guda ukku sai ki samu kayan aduwa 99 a hada su da kwanzaben nan a dafa sai ki hada bawan kwan da kayan aduwa a dakesu adinga zubawa a kunu anasha. Maganin walwale turbuda shine turbuda kuma idan kina zargin wani na maki asiri shine, Zaki samu ruwan tsami ko ruwan tsami da ganyen zogala wanda aka shuka iyankan gona sai ki jika da kai kayi koma kan mashekiya ki hada da ruwan tsamin da zogalan na iyakar gona kiyi wanka ki sha. Da yardan Allah komai mutum ya dauko a kanki sai dai ya koma mai badai ya kamaki ba. Wayana yai kara sai na mike na koma daki na bar gwagon nan falo zaune da ummi da su Aisha. Na dauko wayan da sauri gabana ya fadi don ganin lambar anty na kira na a lokacin wada dama ina tsamanin hakan ko yaushe. Na dauka da sallama ta, sai naji ta katseni da cewa amarya ke nan ke nan kai duniya ina zaki damu ashe tsintaciyar mage dai bata taba zama mage. Lalai mutane sunyi gaskiya da suke fada min cewa ke din tsintaciyar mage ce a gare tabbas ko ya tabbata hakane. Kafin in magana sai naji ta kashe wayan ta dip ajiyan zuciya na sauke tare da sake murmushin bakin ciki lokaci guda. Na a sanyaye na fito falo inda suke na zauna ban iya cewa na fahinci hiran su alokacin sai da naji tace ai kinga idan yaro ya na dauke dauke zaki samu kaucin malge a samu kashin mai satan a hada da malgen a shaya in ya bushe a daka in ya zama gari sai a dinga sa ma mai shi a kunu ko shayi yana sha har kwana bakwai da yar da Allah zai bar satan don da yaje daukan abu warin kashin shi dayaci zai hana shi daukan abu yaji satan ya fice mashi a rai. Sai kuma mallaka da sai abinda kika ce a gidan zaki samu kaucen gwanda na daji ki dake shi ya zama gari a samun kan tunkiya da ta kosa adafa su tare in ya dahu sosai ki zauna kici duka amma bada kashin ba. Allah sa mu dace naji tace sai lokacin na kallo ta ina cewa ummi yanzu anty ta kirani fa. Da sauri tace yaya kukayi da ita ta sake fadin taji ke nan dai ko ? Na gyada mata kai da alaman eh gwago ne tace may taji auren sai ummi tace eh gwago tace dama bata sani bane Aisha dake zaune ummi ta kalla sai tayi shiru. Na ce ummi ai yanzu ba maganan boyo bane tunda abin na ta kamari tace wai may ke faruwa ne kumbar mu a duhu haka ? Ummi tace ummi kin san sun samu matsala da uwar rikon nata tace subbahanallahi shine baku fada muna ba asan abin yi. Ummi tace abin ne wallahi da daure kai zaman su ba wani matsala sai daga baya ne kuma wani hali ya shigo masu. Don ita bayan ta hada su da kanin mijin ta sai kuma daga baya bata son hadin wai tana son hada shi da wata yar yar uwar mai gidan ta. Shine ita ta risketa tana waya suna fadin wai zasu zo suyi kata korar kare a gidan da take zaune shine shi wanda ta aura din ya bata shawaran ta dawo gida. To shine da nake fada ma malam halin da suke ciki sai malam din ya yanke shawaran cewa da sun zo tambaya sai a daura aure da yani. To yanzu nasan taji ne shine wai ta kirata yanzu din sai gwago tace may tace dake to ? Nakwashe abinda ta fada min na fada mata sai tace aikin banza ai Allah ya riga yayi ikon shi ko a kan su yanzu sai dai hakkuri. Nace ni yanzu ce min da tayi wai tsintarciyar mage bata zama mage shine abin ke damu na wallahi tana ganin nice na yaudare ta ko may gwago ? Tace kun ga yanzu duk ba wanan ne a gaban mu ba koma may ye idan kin tare daga baya sai ki nemi shiri da ita da sannu zata fahinci ke ba tsintaciyar mage ba sai ta soki fiye da magen da aka haifar mata a gida. Ummi tace shine kan mafita gwago don yanzu duk yadda za a fahintar da ita ta riga ta hau ba ta yarda damu ko kadan. Gwago tace may ake ciki ne don shi ya kawo ni yau din don nasan baku shirya komai ba ga auren nan gashi kuma ba kananan mutane bane su. Ummi tace wallahi gwago abinda muke shawara ke nan akai tun jiya da malam ya daura wanan aure don nasan ba komai zamu samu a bangaren shi ba. Gwago tace karki yanke hukunci da sauri don baki san ajiyan shi ba nace humm gwago ai abar zancen baba kawai don yanzu baida yaushe ne ya fara fita kasuwa. Nace akwai wasu kudi a hannu na barin dauko sai a kaima su mama asan shawaran da za a yi dasu na mike sai gwago tace dawo ki zauna zasu yanzu don na fada masu mu hadu nan ban san abin da ya tsayar dasu ba. Sallaman su mukaji a tare suka shigo suka tsaya suna gaisawa da mama dake zaune a kofan ta tana raba abinci. Suna shigowa suka fara gaisawa nima gaida dsu nayi da zuwa sukace amarya ke ce haka ba wani shiri da zai nuna farin ciki a gare ki? Murmushi nayi nace kai haba mama tace ai gaskiya ne Safiya tun yanzu fa za a fara shirya ki don wanan auren ba irin wancan bane. Tace to ai kune uwayen nata kuka tsaya nawa na fada maku mu hadu nan tun da safe amma sai yanzu kuka zo. Yanzu dai ba wanan ba yanzu shafiu ke fada muna abin da bakar daga can tayi jiya kuma asirin ta ya tonu. Gwago tace don Allah ku fita batun ta kuyi abinda ya kawo yanzu don ba isasshe lokaci ake dashi don tace yace a sati biyi yake son ta tare gidan shi. Suna hada bakin wurin fadin sati biyu fa ? Yo mai za a tsaya jira kuma aure ya dauro ba sai ta tare gidan ta ba yanzu duk wani abinda za ayi ai aladane kawai don wajibi ya auku ko tunda an daura aure may ya rage kuma ? To yanzu gwago maye abin yi tace yanzu take fada muna akwai kudi a wirin ta sai a san abin yi nace ta bari har ku iso ne muga kudin sai a san yadda za a kasafa su. Mikewa nayi na shiga daki tare da kirgo kudi dubu dari uku na kawo masu na mika ma mama Jummai don itace babba a cikin su. Tana kallon kudin tace ai ina ga a dai tallakance wanan din zai isa ko sun kai dari biyu ai nake gani nace dari uku ne nan tace tirkasa. Ta juya gun su ummi tana cewa may ye abin yi yanzu ga dai kudi sun samu gwago ta katse su da fadin akwai raguna na sai a kama biyu ku hada a laurar taku. Nace gwago baki barin abinki tace ai don haka dama nake kiyon su yanzu ba sai ai lalura dasu ba sai dai zanso ku soya masu shi ku jefa a gara kun dai ga gidan masu shi zaku kai kayan. Zan so ace kun tsaya kunyi abinda zai cika ido yadda ba za a raina maku ba. Mama Suwaiba tace mu dai yi iya karfin mu amma ina zamu ita dasu nace mama may zai hana ku kira mama na nan gidan kada a kebe ta zaifi ace anyi komai da ita. Gwago tace yanzu abin da nake shirin fadi ke nan kika riga ni fada sai ummi tace gaskiya kan kiranta aka tura Aisha da ta make dakin tana sauraren mu akayi . Bata dauki lokaci ba sai gata nan dai akai mata bayanin ta nisa tace da son samu ne kada muyi kayan abinci mu dai tsaya ga wanda za a rabawa yan uwa da abikan arziki don shine abi magana. Alabashi gaba in ta haihu sai ai mata wanan ko yaya kuka gani ta dago kai tana kallon su ko wayace sharan ta yayi. Na suka fara kitasta abinda zasu inda za a kai yin cicin din a birni can wajen kaunan miji mama jummai dake zaune a birni su kuma zasu yi sauran abubuwan a nan . Kowa ya dauki part din abinda zai yi a cikin su inda aka bar wa mama da ummi yin suyan kaji da ake so cika roba guda dashi. Tun wanan ranan basu zauna ba kowa da abin da yakeyi don kar a girshe shi muna waya dashi ko wani rana yana kara kwantar min da hankali. Faiza ne ke fada min cewa su anty uwa sun koma abuja a fusace wai Nafisa tana ta kuka tana fadin ba zata yarda ba. Ita sai ta auri uncle ko ta halin kaka wai da kyat ta yarda ta bisu ta kare da cewa wai yanzu ashe an daura auren ku da uncle baki fada mu na ba sai a bakin mutane mukaji. Nace wallahi Faiza nima ban san za a daura min aure ba a wanan lokacin kawai daga zuwa tambaya sai gashi ance daurin aure za ayi. Tace ai dake da madam din mu ne yanzu don naji tana ta zage zage tana ta fada daga ke har uncle din wai kun munafunce ta. Nayi murmushi kawai nace ba haka bane wallahi kowa baba bai fada wa zancen daurin auren nan ba sai da akazo yi aka sani wallahi ki yarda dani Faiza tace wallahi na yarda. Tace yanzu yaushe ne tarewa kuma ? Nace da ita babu rana Faiza don bamu tsaraba sai ya dawo zai saka rana tace aini abin yayi min dadi wallahi sai dai nasan yadda madam ta hau ba zata barmu mu zo wurin bukin ba. Kin san may nace a a Faiza tace naji suna magana wai ai gidan ku ba abinda zasu kai tin anan zaiji kunya ita ko mutumiyar kullun tana daki tana kuka wai bata da lafiya. Allah ya kyauta nace da ita ban yarda na furta wani kalma da zata kaini gaba ba don sanin halinta da nayi. Mun gama wayan ta barni cike da tunane halin da muke ciki da anty don da ka gan ni na ramay babu walwala a tare da ni kamar wacce za ayiwa auren dole na koma. Nasan dawowan shi Nigeria sai da ya kwana biyu ya wuce bauchi wurin mahaifiyar shi don kiran gagawa da tayi mashi akan maganan mu. Ya iso sai dai mutane basu bari ya samu kebewa da ita ba sai da dare suka samu ganawa da mahaifiyar tashi. Yana zaune kasa tana saman kujera ta kafa mudubin ido a fuskan ta da ke taimaka mata vurin gani. Shiru dakin yayi kafin tace babana wata irin mace ka dauko muna don ban ji dadin labarin da ya kawo min ba. Ko da yake mutanen duk da bamasu karfi bane amma sun san mutuncin kan su a yadda mahaifin yarinyar bai karbi sadaki mai yawa ba kuma da irin taron da sukai ma wayanda na tura daga nan. Sun yaba kwarai da mutuncin da aka nuna masu a gidan sai da abin damuwa wanan labarin da Nafiu yazo min dashi shine banji dadin shi ba. Nafi son kayi bincike mai karfi kafin yarinyar nan ta tare don ni ban kita ba don kaine mai zama da ita amma tunda kananan magana ya fara fitowa daga gare su sai a tsaya a bincika a hankali kada azo ai abu a cikin duhu. Ban son ka kara auren dana sani kamar yadda kayi a baya auren da baida amfani a gare mu sai barnan suna. Shiru yayi kafin ya dago kai yace hajiya akwai abin da nake boye maki da dadewa wanda baki sani ba har yau. Gyara zaman tabarau ta tati dakyau ta dago kai tana sauraren shi tare da fadin baba na maye kake boye min wanda ban sani akan ka. Ashe akwai abinda zaka iya boye min wanda ya shafi rayuwanka yace hajiya kiyi hakkuri don Allah fada maki wanan zancen tashin hankali ne a gare ki. Nan dai ya fara bata labari tun auren shi da Samira matar shi ta farkko sai innalillahi kawai take furtawa har yakai yadda anty ta hada ni dashi dakuma yanzu da take shirin ruguza auren namu. Innalillahi take ambata tace yanzu shi Nuhu da matar shi sun san maganan ga suka iya boye maka sirin ka ta yadda ko ni da na haife ka ban sani ba. To amma ita maimuna may zai sa tayi haka bayan ta hada alheri kuma ta bata rawanta da tsalle a karshe. Yanzu na gamsu da kai sannan ita wanan yarinyar itane rufin asirin ka ga kowa ta yadda ba kowa zai san abinda kake ciki ba. Allah ya albarkaci aure ya baku zuria mai albarka ya amsa da amin tare da mata godiya ta kara kwantar mashi da hankaki tayi tare da cewa tasan yadda zata kashe maganan daga bakin kowa. ZAINAB IDRIS MAKAWA SEENABU 8/14/20, 7:12 PM - Ummi Tandama: BAHAGGON , , , , , , , , 🧕🏿5️⃣4️⃣🧕🏿 NOVEL DINA NA KUDI NE WANDA YA SAN BAI IYA RIKON AMANA TA FADA MIN IN BATA KUDIN TA , , , Shirye shiryen buki aketayi amma ni hankalina baya gare su cike yake da damuwa don ban san yadda zai kwashe da mahaifiyar shi ba. Na kwanta zuwa dare naji kiran wayan shi ya shigo min a sanyayye na daga wayan gami da sallama a bakina. Yace kin fara barci ne nace ina naga barci ban san hukuncin da baaba zata yanke a kaina ba kuma ma ai yanzu barci bai ga idona ba tunda nace aure nake so. Dariya yayi sosai har yana lyalkyatawa yace fada min may zai hana ki barci don Allah ? Na abubuwa da yawa mana Uncle yace kamar su mai nace wayan san iyaka sai dai ranan da na tare a gidan ka. Don kullun cikin kawo kudi ayi kaza nake yace look nafa fada maki bana son tarkace daga ke sai boxes din ki za a kawo min na fada maki . Nace naji uncle amma dai ai za ayi abinda zan ba yan yinin buki ko ? Yace kai mata ho wanan kuma kina son ki sawa kan ki nauyi ne nace ki bari inzo in dauke ki daga ni sai ke sai gida na amma kin ki. Nace wani gidan uncle yace gidana na Abuja mana ba anan zaki zauna ba ? Nace haba uncle kai ka ga haka ya dace ga hajiya baaba da ranta da lafiyan ta a dauke akaini gidan ka na Abuja ? Ai ka bata damarta na mahaifiya ta sa muna albarkan aure dariya yayi yace Safiya wanan halin ya kara sa ina son ki wallahi yanzun dai sai an kaiki bauchi ke nan wurin hajiya baaba ko ? Nace a wani irin murya mai sanyi shiya yafi mutunci uncle yace to shike nan hakan yayi kyau zan fada mata su shirya nan za a kawo ki direct idan an dauko ki. Muka dan taba hira yana fada min yadda suka kwashe da mahaifiyar tashi nace uncle dama bata san halin da kake ciki ba duk wanan dadewan yace bata sani ba. Kuma ko yanzu na fada mata ne don kada daga baya tazo ta zargeki ga abinda ba laifin ki ba ya kawar da zancen da fadin zan turo maki da sako gobe sai ki kara kiyi hidimar bukin dashi yan uwa na zasu zo ranan alhamis da kayan lefen ki wanda naso ace madam ne zata zo dashi. Amma wanan matsalar yasa baaba tace daga wurin ta za a kawo komai yadda ya kamata nace Allah ya kaimu lafiya amma ni da an bar lefen don baaba ta riga ta aiko min da akwati biyu yace ta fada min wanan ai mun gani muna so ta hada maki wanan kuma ni na hado maki shiya kaini Dubai dama. Mukayi sallama ina mai kara yi mashi godiya ya kashe wayan na sauke ajiyan zuciya. Ina mai ci gaba da tinanen wanan baiwa da ubangiji yai min amma ma kuma baiwan sai yazo min a bahaggon rayuwa. Washe gari ya shiga gaida mahaifiyar tashi nan yake fada mata yadda mukayi akan nafi son in tare anan bauchi don ta sa muna albarka. Murmushin nuna jin dadi tayi tace mashi shiya har kullun bani dana sani da zaben ka don nasan bakayin abinda za a yi da an sani cikin sa. Ko wanan auren kaddaran na Samira da kayi don yan uwanka ne da sukai hadin ba bincike yanzu gashi an bar mu ciki. Daren jiya banyi barci mai dadi ba a rayuwa na amma da nai tunane sai naga bawa bai wuce kaddaran sa mutuwa kuma tana iya riskuwan bawa a ko wani lokaci. Don haka yanzu kafin ka tafi sai a fara shiye shirye tunda buki ya dawo wurin mu don da ina dauka acan za a yi komai. Bai baro bauchi ba sai da suka gama shirin komai da za ayi a nan ya san nan ya baro garin ina kwance naji waya alaman sako ya shigo min ina dubawa kudine wanda sai da ya sani kaduwa. Na duba na kara dubawa naga milayan guda chur ya turo min tare da sakon da ya biyo baya na . Nasan wanan zasu ishe ki komai da kuke son yi har da gyaran dakin ummi yadda ya dace asha buki lafiya. Ummi na kira kurayan daki nake fada mata abinda ya turo min tsaye take sai da takai zaune tana fadin. Yarinya wanan mutumin kuwa yasan ciwon kudi ashe nifa abin nasa yana ban tsoro wallahi. Nace ummi samu kudin yake a lokacin su kuma nema akeyi ko yaushe wanan ai ba koma a wurin shi sai kin ga company da ya bude nasa na kan shi. Tayi shiru tace duk dai da haka abi abin sannu dai yaya Sani na kira da ummi ta fita yazo nake neman shawara a wurin shi yace yanzu abinda za a yi shiryawa zakiyi mu samu Amina aminiyar ki can birni ita zata taimaka maki da sharan da ya dace tunda sune yan birni su suka san abinda ya dace ayi. Banki ta nashi ba don shawara ne mai kyau ya bani ko banza ya kamata tun farko in neme ta amma na manta da ita. Don haka shiryawa na yi muka nufi gidan su ni dashi da Rukaiya da tace zata bimu mun isa mun samu taro na arziki a wurin mummy din . Bayan ta gabatar muna da abinsha cikin wanda takeyi na sana an ta sai na fito mata da maganan abinda ya kawo mu. Taji dadi sosai tace bari ta kira Amin nan taji yaya za ayi nan ta buga mata waya ta dauka sun gaisa sai take fada mata gani a gidan ta ga kuma bukatan da ya kawo mu zamu zo wurin ta. Ina jin yadda take murna tace ai ba sai na zo ba gobe ita zata shigo sai a san abin yi mun ji dadi sosai don haka muka koma gida. Daga yaya sani har yaya Nura basu zauna ba don duk abinda ake so suke zuwa birni su sawo su dawo shafiu kani na ma ba abarshi baya ba. Amina ta iso da kaunan mijin ta dake zawarci a wurin ta nan suka shiga shiri do ba lokaci issashe gare mu. Komai an kamala don haka aka kai gidan gwago ana tarawa a can nima na bar gidan mu can gidan gwago din na koma. Ranan da yan uwanshi zasu iso ana gobe zamuyi walima sai abin ya taru yai masu yawa nidai nawa ido sai dai ina kewan anty na don da yanzu itace zata shirya min komai. Maimakon bakin da muke jira su iso yaya Saadu ne da iyalin shi suka iso da mahaifiyar Samira da yayanta mace da na miji sai Sadiyan shi da tace zata biyo su. Nan aka shiga murnan ganin su sai dare bakin shi suka iso garin don haka aka kaisu gidan su Amina a can aka sauke su. Su yaya Saadu kuma suka sauka wurin mama amma ita Samira da yarta dakin ummi na suka sauka don tace can ne dakin su. Sai da safe suka gabatar da kayan lefen da suka zo dashi bisa jagorancin mahaifiyar Amina da ta zamay masu uwar daki anan don har sun saba da itako sabon mata baida wuya. Ga ganin lefe ga shirin walima da za ayi wanda duk kusan matan karkaran mu mama ta aika masu da mintin gayyata wurin. Inda Amina ta gyato malama khadija daga birni tazo ta wayyar ma mata da kai akan hakkin aure da na yayan su. Tako zo din don ta wayar dakan mata a wurin da sanyaya masu zuciya da nasihohin ta daga niimar da Allah yaba mace ta gari da jin tsoron Allah a cikin rayuwan airen ta bawa yaya hakkin da ya dace na fanin kula da hakkin su daya rataya akan uwaye mata. Alamarin ya kayatar sosai don bazaka fahinci haka ba sai kaga yadda mata suka natsu a wurin har da mazaje a can baya da suka zo don saurare. Ko wace mace a wurin ta natsu ta kama kan ta alokacin kalaman malama na shiga jikin ta nan aka kai karshe su Amina dasu samira suna ta faman raba masu abinda aka tana don waliman buta da dabino sai abinci a cikin take away. Taro ya watse lafiya kowa sai sam barka akewa juna inda mafi yawan mata basu koma gidajen su ba suka shigo yinin bukin da ake yi a gidan mu. Sai da dare ne mahaifiyar Samira da su mama suka kaini wurin baba don muyi sallama saboda da safe sammako zamuyi a tafi. Ina sungun ne a gaban baba yayi gyaran murya ya fara da fadin ikon Allah Safiya kin ga yadda rayuwa ya koma muna a dalilin ki. Ni banda abin cewa dake sai fatan alheri da gamawa da duniya lafiya Allah ya baku zuria masu albarka. Ki rike hakkin aure ki rike mijin ki amana don ko shi din ba makyataci bane irin wancan na farko da mukayi maki jeki ubangiji ya kara sa maki albarka. Kuka ne yaci karfi na lokacin da naji baba yace don Allah ki gafarce ni Safiya dani da duk wani wanda ke gidan nan. Shima baba kuka ne ya kumbce mashi don haka da sauri mahaifiyar samira ta jani mukabar dakin nashi zuwa dakin mama sai dakin inna. Tana uwar dakan ta muka shigo Saadatu ne ta shiga kiranta tace tazo ga Safiya nan an kawo ta wurin ta neman gafara. Muna jin ta tana cewa ni may zan mata su tafi dai Allah ya sa mu sheda sai mama Jummai da dake tare da mu ta bata amsa da cewa ai mun riga mun sheda sai dai muce gwamma da akayi ba wani abu muka kawota yi ba wurin ki don zama tare a sahirce ma junane. Ta fito don bata dauka anji maganan ta ba sai cewa take naga dai yanzu Safiya ai ba yarinya bace don duk abinda zamu fada mata ta sanshi Allah ya bada zaman lafiya. Suka mike dajin abinda ta fada suna fadin amin tare da ja hannu na da uwar Samira tayi muka bar dakin ina sa takalma na naji Saadatu na fadin kai Inna sai yaushe zaki ja muna farin jini gun yan uwan mu ne ? Ni dai mun tafi banji amsan da zata ba yar nata ba don jasan ba mai dadi zataji ba ga bakin inna. Mun koma wurin ummi na can suka tasa ta gaba wai tayi min fada nasan ba abinda ummi zata iya fadi a gaban su dama sai cewa tati Allah ya albarkaci aure ku yarinya. Bayan shi bata ce komai ba sai sharan hawayen da takeyi nima kukan nakeyi a lokacin wanda dagani har ummi bamu san ko kukan may mukeyi ba. Sai mahifiyar Samira ce ta iya cewa haba ai bai kamata ace kuna kuka ba don abin farin ciki ne ya samay mu bana kuka ba mama jummai tace kuka dole ne gare su ai. Haka dai aka watse ina jin suna hiran lefen da aka kawo wanda mama tasa akai dakin baba wai akwati har set biyu babu ne kawai babu a cikin sa. Nan suka shiryasu tun cikin daren da za a tafi na kira mama nace a rabawa yan uwa da abokan arziki da sukayi tsaye a wurin sha anin nan suka zaba daga cikin wanda baaba ta turo dashi akabawa wa yanda suka dace aba. Mutocin tafiya sun iso da dare nan suka kwana inda yaya Saadu da yaya Sani suka zabi masu zuwa kai ni. Don dogon luxuries aka zo da ita sai karama don daukan amarya ni dai ban san masu zuwa ba na dai san Amina da Samira da yar uwar ta ne. Daya daga cikin kayan da hajiya baaba ta aiko dashi nasa wanda Amina ta bayar aka dinka min a birni. Sai da akazo shiga mota na ke jin yadda suke ta hayaniya nadan bude fuska na ina kallon su nace a raina wai ni Safiya yau akema gardaman rakiya gidan miji haka abinda irun su inna basu so gani ba gare nu gashi yau Allah ya nufa anayi akaina. Yaya saadu ne a gaban motar da na shiga sai gwagon ummi da mahaifiyar Samira matar shi su samira karamar mota suka shiga da su Amina. inda yaya Sani da yaya Nura suka jegoranci doguwar motar da mutanen dake cikin ta don shiya bugo yace a cika motar azo da mutane. Mun sha hanya don duk da sammakon da mukayi sai bakwai na yamma muka isa garin bauchi nan naji abinda uwar Samira take cewa shi yasa ni dan bude fuskana nima in gani. Acan lagos kuma sai faman zage zage anty ke durawa da taji ance mahaifiyar shi ta tura akai kaya ta wurin ta don har kiranshi tayi din ta fada mai bakar magana sai bai daga kiran nata ba. Da daren nan maigidan ta ya dawo garin nan ya samay ta tana cika tana batsewa sai da ya huta yake tambayan ta abinda da ke faruwa. Nan ta shiga labarta mashi karya da gaskiya yana sauraren ta sai da ta gama yace amma ban taba sanin baki da wayo haka ba maimuna. Jin ya kira sunan ta kai tsaye yasata natsuwa yaci gaba da fadin yan zu ke uwa ce zaki bari har ta saki a gaba ki yarda da bukatan ta bayan kin fi kowa sanin halin ta dana yaranta. Waima tsaya don Allah idan uwa ta juyaki zata iya juya Sulaiman ne kai tsaye ke kin fi kowa sanin ko waye sulaiman don shi dan kaifi guda na kuma ya nuna maki koshi waye. Ya nuna maki in dake ayi in ma babu ke zai iya gashi sunyi bukin su hankali kwance yace amma ko da labari za a bani cewa zaki iya yin haka bazan taba yarda ba. Sai gashi keda bakin ki ba kunya ba tsoron Allah kike labarta min shirin ku na shirmay kin dauka kowa baida hankali ne irin ki. Jikin ta yai sanyi don ganin daddy bai goyi bayan ta ba dama dashi ta dogara ya dawo suyi ma sulaiman din sheri sai gashi ya dawo bakin su daya da sulaiman din. Bata san cewa da daddy ake kulla komai ba akan bukin nan yayi mata tas yace yanzu dabara ya rage gareta ta gyara tsakanin ta da sulaiman din da ni. Nan ya shige ya barta tana tunane tare da yin na daman abinda ta aikata gashi anty uwa taja mata hasara da tasan ita zai ba hadin lefen da yaje da yar uwan shi suka yi. Don ba karya ba ne anty tana da son abin duniya dama maishi akace abu bai isan shi su ko yan uwan Sulaiman sai murna sukeyi yana yi dasu yanzu. Don dama hurda da ita ya hana shi ya kula da yan uwanshi amma yanzu gashi su yaba su aiwatar mai da komai yadda ya kamata su yi. Gida ne mai kyau na zamani wadda ya tsaru iya tsaruwa wurin haduwa wata da gani tobashiyan shi ne ita tazo tana muna jagora zuwa ciki sai zolaya take yi. Maman Samira ta sani karanta wasu ayoyi daga cikin kurani tare da wasu adduoi na neman tsarin ubangiji. Part din din mu aka fara kaini ko zama banyi su gwago suka ce akaimu wurin uwar mijina. Mutane suna biye damu inda har zuwa dakin sai dai yan uwana sun tsaya a part dina basu biyo mu ba sai gwago da mahaifiyar Samira da mama da su samira da amina su bakwai dai suka rufa min baya. Ta idar da sallah ke nan aka ce mata ga amarya an kawo mata tace sun koyi sallah mahaifiyar Samira ne tace yanzu dai muke so a bamu wurin muyi mun kawo amarya masauki ta ne. Dariya tadan yi tana mikewa daga inda take tare dafadin aiko na gode da wanan zumuntan da kuka nuna min iso inda nake rufe da fuskana ta rugumay ni tana kokarin zaunar dani saman kujera. Sai na zamay na zube kasa tace a a taso ki hau kujera mana kai na girgiza mata tace Allah yai maki albarka tasa hannu tana bude rufin fuskana. Naji tace tubarkallah masha Allahu tare da zubamin idanunta akaina ina duke da fuskana kasa ban yarda na dago kaina ba munyi ido biyu da ita. Gaba sai faduwa yakeyi ta juya wurin sauran yan uwanta dake shake a dakin tace tubar kallah kunga baba na ya iya zaben mata Allah yasa yadda fuskan ki yake dakyau har da halin ki mai kyau ne inji wata daga cikin matan dake dakin tace. Mahaifiyar Samira ta amshe dace insha Allah yadda take dakyau haka ma zuciyar ta yake farar belbelace wanan mai farin nama. Sai suka sa guda dakin ya amsa da shewan su nan dai su gwago suka mike suna fadin a basu wuri suyi sallah. Nima daga inda nake zaune a kasa rufe da fiska nace sallah sai wata daga cikin kan nen shi tazo tace may kike fada amaryan mu kasa kasa nace sallah zanyi. Baaba wai amaryan mu zatayi sallah tace kaita daki don Allah suyi sai sukace wani abu sai amaryan Abbati baaba dako jikoki bata yarda su shiga mata bayi yau gashi tace amarya ta shiga nan na fahinci yawan tsabtan da tijuwar ashe a gunta ya gado tsabtan shi. Ni da samira Amina da yaya Samira muka shiga dakin sai lokacin na bude rufin kaina ina jin Samira na fadin ikon Allah wai dakin tsohowa ke nan garin dadi na nisa. Bayan munyi sallah an wadda tamu da abinci da sha zuwa takwasa akace in fito a kaini part dina mun fito tare da rakiyan matan da hajiya baaba tace su rakani wurina. Nan muka shiga suka bude dakin dake rufe wanda nasan shike zamana a gidan muka shiga . Nan suka fice suka barmu sai nida yan uwana a dakin wanda sai lokacin na bude rufin fuskana don in sha iska tare da bin dakin da kallo. Nan kowa ya sake yana diban abin da yake so da aka wadata mu dashi a part din nawa sai hira ake kwasa sai jefi nake saka baki don zulmin da ya ke damuna a raina. Yaya Saadune suka shigo wurin mu dasu yaya Sani nan akai ta bakwanci dasu suna biyewa gwago da take jan su. Wurina ya nufa yana fadin amarya yaya dai na duk kinyi wani laushi dake ajiyan zuciya na sauke tare da kakaro murmushi a fuskana. Nan muka zauna dashi yana kara yimun nasiha a kan sabon wurin da na shigo yake fafin in kwantar da hankali na in fahinci yanayin su. In zauna lafiya da kowa a yadda ya fahinci family kamar Sulaiman bai shaku da su ba sosai don duk wanda yazi sai yaji suna mai korafin bai zuwa gida. Yace kin ga yanzu sai kiyi amfani da wanan daman ki sakashi a hanya ta yadda zai mami yan uwanshi kan sashi kuna zuwa gida lokaci lokaci. Ki kuma sa ya danga masu alheri yadda ya kamata ke ma dai kin san sauran ba sai na gaya maki ba. Dagowa nayi idona yana zubar da hawaye nace na gode yaya insha Allahu zanyi kokari inyi yadda ka koya min din. Nan su yaya Sani suka shigo suma mun dauki lokaci dasu muna hira a wurin sanan sukai muna sallama suka fice. Amina ta dawo wuri na tana kara haska min rayuwa abinda ya dace in daga yi da yadda zanyi in sa sabo a tsakanimu daidai sauran su. Naji dadin shawaran ta duk da dama nasan wasu a dan zamana da anty danayi sai dai karin da tayi min na wasu da nake ganin kamar ba masu amfani bane a lokaci. Sai dare sosai muka samu muka kwanta inda suka ce da safe zasu fita zuwa cikin gari don su bada labarin garin bauchi idan sun koma gida. Washe gari akai haddaden walima a gidan aka watse lafiya nan mutanen mu suka shiga zaga gari ya rage saura ni da gwago da mama a dakin. Sulaiman ne ya shigo don ganin fitan su da yayi yana saye da babban riga da yar ciki na farin voile sai dan dinkin da akaimai ba mai yawa ba can. Ganin su gwago yasa shi jin kunya zai koma gwago tace mukan bari mu fice wurin hajiya mu barku ku gaisa yana fadin su zauna amma sai suka fice. Acan suka samu su hajiya na al,ajabin kayan garan da muks kawo masu sukace kuko wanan dawai niya haka babu iyaka don roban guguru har bakwai da ruban nama biyu na ragon da aka soya sai zabin da ya sha gyara da hadi biyu alkaki roba biyu kwan zabbi an cika roba biyu sai jarkan man shanu da na nono da sauran tarkace masu muhinmanci. Bai iya tsayawa ba a dakin don kunya yace barin in fita na dauka ai ke kadai ne a dakin na shigo yana magana yana min wani irin shuumin kallo har sai da gabana ya fadi. Bai iya tsaya ba juya zuwa wurin baaba nan ya samu suna kallon kayan da aka baza a kofan dakin hajiya baaba ana kallo. Lumshe ido yayi dayaji baaba da yan uwanshi na ta yabon karanmacin da muka nuna masu da kawo wanan kayan haka a matsayin gara. Nima kuma a nawa bangare sai yabo sulaiman din da yan uwanshi ke sha wurin yan kawo ni don irin karamcin da aka gwada masu a gidan. Washe gari suka kama hanya sai dai an bar gwago da mahaifiyar Samira su zasuyi min rakiya Abuja sauran aka tafi dasu mun dade da Amina muna tataunawa. Gidan ya rage daga ni sai su mummy kamar yadda naji samira na kiran mahaifiyar nata. Babu kowa a dakin nawa ya shigo ina tsaye gaban mirrow dakin ina kokarin tubke kaina da ya sha kitso ya zubo min a fuska. Kamshi turaren shi ne ya fara sanar min da shigowan shi dakin nawa sai kuma na gashi ta cikin mirrow tsaye ya soka hannayen shi a cikin aljihun wandon shi tare da kare min kallo don bai taba ganina haka ba hijjabi ajikina ko gyale duk sai na daburce na rasa natsuwana a lokaci guda. Daidai baya na yazo ya tsaya daidai inda nake a hankali ya ciro hannun shi daga aljihun da suke ya sauke su saman kun kuruna ban san lokacin da na lumshe idanuwa na ba. A hankali ya dora kanshi saman bayana ban daina abinda nakeyi ba amma na kasa yi masa magana a lokacin saboda kunyan shi da nake ji. Wai nice yau gani ga uncle a karkashin inuwa daya a matsayin ma aurata nauyi da kunya sun hanani juyowa gare shi in fuskance shi. ZAINAB IDRIS MAKAWA SEENABU 8/14/20, 7:12 PM - Ummi Tandama: BAHAGGON, , , , , , , 🧕🏿5️⃣5️⃣🧕🏿 NOVEL DIN NAN ONLINE NOVEL NE NA KUDI IDAN KIN SAN DARAJAN ALLAH DA MAZON SA KADA KI FITAR MIN DA NOVEL DINA YAR UWA. Fuska biyu ga mulsumi abune mai muni ga alumma a hada dashi da Allah bai san darajan shi don zuciyar ta tayi tsauri shedan ya rinjaye shi amma kuma yana musulmi babu Allah a zuciyar shi. Kafiri ma yana tsoron Allah balle ke mai sallah biyar a rana ina zaki da hakkin wani a kan ki naki ma ya ishe ki kaya gobe kiyama. Bai damuwa don nasan da kayana zaki dauka ranan dauka akai babu mai taya ka sai halin ka muje zuwa yar makawa yanzu ta fara novel yar matashiya ce a cikin ku. Ana cewa novel ba dadi ba ma ana kuma gashi ya zama kamar dole a karanta harda sato maku akeyi don kawai son duniya. A hankali ya sa hannuwanshi ya juyo ni ta yadda zamu iua fuskantan juna dashi irin tsabar soyayyan da nagani a cikin kwayan idon sulaiman din ban taba ganin shi a cikin kwayan idon wani na miji ba. Haka yasa ni sunkuyar da kaina kasa da sauri gabana ya na bugawa uku uku don firgice sai ji nayi idanuwa sun ciko min da hawaye ban san sun zobo ba. Sai gani nayi yasa hannun shi yana sharewa a hankali jikin shi babu idan inda bai rawa a lokacin don wani irin sha,awa dake fisgan shi a lokacin. Sannu a hankali yake goge min hawayen sai naji sun zubu gaba daya kuka ne yaci karfe na ji nayi ya rugumoni zuwa jikin shi. Cikin sautin kuka nayi karfin halin bude baki na ina cewa dashi Uncle, , , Uncle sulaiman don Allah , , , don Allah ka rike ni amana karka ci amanata don Allah ka soni tsakani da Allah ka so ni saboda Allah badon wani abu ba. Sassauta rikon dayai min yayi don yaji maganan ya doki kwakwalwan shi a lokaci guda. Sai kuma naji ya riko ni fiye da na farko kamar zai hadiye ni, shima magana ya soma cikin sanyin murya kamar haka. Safiya ki kwantar da hankalin ki mu fahinci juna mu zauna lafiya wallahi Safiya bazan taba hada son ki da wani ko wata ba. Ina son kine tsakani da Allah, ina son ki sani ni ban soki dan wani abu ba ko wata manufa nawa, ina mai tabbatar maki ba zan ci amanar ki ba a rayuwana don banga ribar da zan samu ba ga yin haka. So dan Allah ki saki jikin ki dani mu zauna lafiya cikin amincin Allah, ina tare da ke komai wuya komai dadi. Don ba zan taba hada darajan girman ki ba da wata mace a fadin duniysn nan mahaifiya ta ce kadai zan iya hada son ta da naki don ita kadai ne mafi daraja a gare ni a duniyan nan yanzu bayan ke. Don haka ku biyu ne kada yanzu zaku iya juya ni yadda kuke so a rayuwan ku. Ni nace ina son ki duk yadda kike ba zan taba kowa dake ba mudin na samay ki yadda nake so muyi zaman mu lafiya mu karasa rayuwan mu a tare cikin salama. Ya kare da fadin okey ? Ajiyan zuciya na sauke amma ban iya dago kai in kalle shi ba har wanan lokacin sai kawai naji yayi amfani da hannun shi na dama ya dago min habana. Kafin ince zan mayar naji ya hada fuskan shi da nawa yana kokarin neman baki na da na sa idanuwan shi a lumshe suke lokacin. A tsorace nake an ma na kasa hanashi abin da yake min din sai ji nake yi tsikar jikina yana tashi sai kuma naji hannun shi na hagu na kaiwa da komawa a godan baya na. Tankar yana lalashi na harshe shi naji ya zura a tsakiyar bakina tare da maida hankalin shi wurin shafar wasu sassan jikina musanman godon baya na zuwa mazauna na. A lokaci guda kuma naji yana yana sumbatar tsakankanin wuyana da kaina haka yasani dole na shiga magana cikin inda inda ina fadin. Uncle, , , , , uncle yi hakkuri don Allah shiko wani irin zaki yaji muryan nawa yai masa kawai sai naji ya sunkuceni har wanan lokacin bai zare bakin shi a nawa ba bai sauke ni ba sai a tsakiyar makeken gado dake dakin. Ya kwantar dani haka ya bani daman tokara hannuna saman kirjin shi da hanayena guda biyu don gudun kar jikin mu ya hade wuri guda. Amma sai ji nayi ya kama hannuwa nawa ya ware su sosai sai ya dafe su da nasa saman godon dole jikin mu ya hade sosai son ran shi. Kirjin sa na saman nawa ya shiga lasar kunne na yana rada min wasu kalma na soyayya masu dauke da sunayen mu. Rintse idanuwa nayi suratan da yake yi na sunayen mu wanda suke daidai da sambatu sam ba zan iya amsa ko daya ba. Hakan kuma na kasa aiwatar da komai a bangare ns duk yadda yaso haka yake yi dani don tuni ya gama tafiya da hankalina da irin siddabarun sa wanda ya gama sanin sirin mallakar mace dashi don ya lura idan ba hakan yabi dani ba, ba zai sameni cikin sauki ba. Sai da ya gaji don kan sa ya sarara min tare da sauke ajiyan zuciya tare da mirginawa gefe daya yana sauke numfashi a hankali. Da sauri na jawo zanin dake gefena na saya jikina dashi ji nayi yayi murmushi kawai ya juya min baya. Da haka muka kwanta sai can naji ya mike ya shiga ban daki da alamar wanka yake yi don dadewan da yayi a ciki. Haka ya bani daman mikewa da sauri na gyara kaina kafin ya fito naji ya turo kofan ya fito da sauri nima na mike na fada ban dakin don tsarkake jikina. Ko da nafito baya dakin zama nayi a bakin gadona ina sauke murmushin da ban san na maye ba wata kila na yau muradina ya cika ne ko kuma na na samu mai sona tsakani da Allah ne. Haka na kwanta ban sake bi takan shi ba sai can cikin dare sosai na jishi a baya bai hanani barci na ba amma dai nauyin shi a kusa dani shiya hanani sakat. Washe gari ya rigani tashi bai dakin sai dana gama komai na fito don in gaida su mummy sai na samu dakin nasu ba kowa har kayan su. Na juya zan koma sai gashi ya fito daga dakin da nake tunanen nasa ne ban yarda mun hada ido dashi ba na dan sunkuya ina mashi ina kwana. Murmushi naji yayi yace an tashi lafiya yaya bakunta nima murmushin na dan kakaro a fuska na kadan. Au su gwago kike nema naji yace abinda yasa na dago kai na kalle shi kenan da sauri alaman eh yace sun kama kan su ai tun jiya da yamma don sun ga mai masukin nasu bata su take yi ba. Suna part din hajiya acan suka kwana don haka muje mu karya sai muje gaishesu daga nan sai ki masu bayanin abinda yasa kika watsar dasu a garin mutane bayan ke kika kawo su garin. Nace kai uncle na watsar dasu kuma fa kace ya fara tafiya yana cewa kin kula da kina da baki ne a gidan tunda kika dafe kan angon ki. Binshi nayi a baya zuwa dinning inda naga ya nufa tare da zama yana kokarin jawo plate a gaban shi. Da sauri na karasa wurin ina karban plate din tare da jawo wormer din abincin ina budewa nace amma dai a bari in fara aiki na kar kuma ace min na shagala dayin haka don naga ango na zaune. Murmushi shima naji yayi bai hanani zuba abincin da nake zuba mai har na cika plate din da shi na juya na zauna ina jawo plate zan zuba ma kaina naji yace wanan da kika zuba dani da waye ? Dole na dauki spoon din na saka a plate din da kyat na diba sau daya nakai a bakina don kunya ganiin bazan ci ba yasa shi diba ya miko min yana fadin bude bakin ki dole na bude badon na so ba. A haka muka koshi muka mike zuwa part din hajiya baaba bayan na kawar da kayan zuwa kitchen muka nufin wurin su baaba din. Shike gaba ina bayan shi muka shiga da sallaman mu don tun bamu shiga ba muke jin hayaniyar mutane a part din nata. Sallaman shi yasa duk suka juyo gare mu zama yayi saman daya daga cikin kujerun falon ni kuma sai na zube kasa daidai inda ya aje kafan shi. Sai naji wata daga cikin wa yanda ke falon tace da alaman amaryan tamu tana da kunya don naga ko ranan da aka kawo ta bata zauna akan kujeran ba. Murmushi naji yayi tare da fadin kun tashi lafiya sai kuma naga ya dan zamo saman kujerar yana hajiya barka da Safiya yaya gajiyan jama a ? A lokacin nima na samu daman gaida ita da kwana ta amsa min fuska sake tana cewa yaya bakunta ? Komawa yayi saman kujerar ya zauna da kyau tare da tambayan ta ina bakin ta suke tace suna ciki sai wacce tai maganan farko taci gaba da magana tana fadin kada kiji kunyan mu munan duk yan gida ne. Yace Well, Safiya meet my sisters wanan itace Aisha wanan kuma khadija, and that is my cousin sister jamila and nuriya duk anan wurin hajiya mu suka tashi. Na dago kai ina bin su da kallo araina ina cewa ashe yana da yan uwa mata haka ya lakewa anty kawai kamar wanda baida kowa. Mikewa yayi yana cewa bari mu gaida bakin mu kafin in fita don ina son zuwa gidan su kawu kafin mu wuce. Hajiya ne tace dani bishi mana ku shiga suna ciki a dakin muka samay su kwance suna jin sallaman mu suka mike zaune. Ni na fara shiga shi ya biyo ni a baya sai da na zauna na fara gaida mummy sannan na juya wurin gwago dake gyara daurin dan kwalin ta nace gwago yaya bukun ta. Tace bari kedai ai har tunanen komawa gida nakeyi wallahi wanan uban nisan da muka kwaso nayi dariya nace gashi kuma gobe zaki kara kwansan nisan . Tace yar nan kin faye zari da har idon ki ya kyala har wata kasan dauko miji. Dariya yayi mata yace gwago ai tafiya yanzu kika fara don yanzu aka fara yi wata rana har waje zamu fita dake garin masu jan kune. Zaro ido tayi waje tana cewa rufa min asiri dan nan nan ma ya isa haka ai an gode ta kalle mu tace to yanzu dai Allah ya hada wanan aure don Allah a yaki zuciya yi nayi bari na bari sai a zauna lafiya Allah ya kawar da idon makiya a tsakanin ku. Mummy ne ta amsa da karfi da amin ya Allah tana mai daga hannuwa sama alaman addua ya karbu. Nan dai aka dan taba hira ya mike yana fadin zai fita ya juya gare ni yana fadin zaki iya komawa part din mu yanzu don babu kowa a cikin sa. Sai mummy tace bari ta taso zata samay ni a can tare muka fito ya tsaya magana da yan uwan shi nikuma na wuce part din mu. Bayan na dan gyara wuri sai ga mummy ta shigo da gwago nan na dawo falo na zauna wurin su tare da kuna tv dake falon. Kwantawa nayi saman doguwar kujeran dake falon tare da lumshe idanuwa na a han kali ina mai ci gaba da tunanen makomar rayuwa na. Ban san lokacin da barci ya dauke ni ba sune zaune suna hiran su jefi jefi wanda hiran akan inna ne da halinta. Shigowan sisters din shi ne yasa na farka naji suna cewa ayya barci takeyi ne sai na bude idona tare da tashi zaune ina masu sannu da zuwa. Wuri suka samu suka zauna suna fadin mun zo muyi maki sallama ne don yau zamu koma gidajen mu sai dai Aisha ce don ita a abuja suke zama da mijin ta. Murmushi nayi ina mikewa nace har zaku koma ke nan suka may kuma zamu yi nace ai kunyi kokari an gode nace ina zuwa daki na shiga na bude akwati na hado masu kayan shafa da kayan buki na fito masu da leda hudu a hannu na. Mika masu nayi mamaki sukayi suka kayan naki kika kwaso muna kuma nace ai don amfani aka sayo su godiya suka yi man, nayi tare da sallama na raka su har kofa. Bayan tafiyan su na dawo na zauna inda su gwago suke muna hira jefi jefi dasu Uncle ya dawo gidan da sallaman shi ya shigo falon. Su gwago suna mai sannu da zuwa suna kokarin mikewa su bar falon yake ce dasu don Allah ku zauna abinku yaya kuma zaku tashi amma sai basu tsaya ba sukace dama mun shigo ne don tana ita kadai zamu wurin hajiya mu taya ta hira. Suka fice ni kuma da nake zaune ina kallon draman su sai lokacin nayi mai sannu da dawowa. Zama yayi kusa dani batare da ya amsa ba sai dai ni kuma ban yarda mun hada ido dashi ba ji nayi ya kamo yan yatsun hannu dake saman jikina ya rike. Ya dago hannun nawa yakai masu sumbata tare da kura min idanuwan shi a kaina, ji nayi kamar in nutse a lokacin don kunyan shi da nake ji. Jawo ni naji yayi zuwa jikin shi yana kokarin runguma a jikin shi nayi karfin halin ce mashi uncle baka gudun wani yashigo ya samay mu a haka ? Cikin karfin hali ya iya fadin wazai shigo nan ko mm a sun shigo ba matana suka sama ina runguma ba da banda aure sun ga na rungumi watane. Nace amma, , , katse ni yayi da fadin amma may ke kuwa zamu shirya dake don naga kina neman hanani abinda Allah ya halasta min. Murmushi nayi nace ban dai son wani ya samay mune a hakan yace and so what inda an samay mu su gwago da suka san kan su baki ga sun fita ba. Dole haka na kyaleshi yaci gaba da murzana yadda yake so ina runtse idanuwa na don kanshi ya kyale dama jan magana yakeso. ya sumbaci kuncina tare dan dagowa daidai kunena yana magana kamar maiyin rada kina kunyan azo a same mu ne ina taba mata na. Nace kai da baka jin kuyan ai sai kayi tayi amma ni ina gaban sarakuwa ina zan biye maka ace min jarababban amarya. Ya fidda karamar dariya yana matsa min hannaye na yace af nine banda kunya barin nuna maki banda kuyan yanzu. Na dan shagwabe mashi murya ina cewa Uncle kabari Allah kuwa zamuyi rigima dakai yanzu. Dariya na kara bashi ya sake jawo ni jikin shi gaba daya yana fadin bari mu fara rigimar tun yanzu. Zillewa nayi ya sake ni yana dariya dakin shi ya shiga ban ji fitowan shi ba har na mike nima zan shiga daki sai gashi ya fito. Yana fadin ki fa shirya jirgin bakwai zamu bi zuwa Abuja gobe don haka ki fada ma su gwago su zauna da shiri don kar a girshesu. Ina mamakin shi gashi dai yana son yan uwa don shi da kanshi ya kawo shawaran abar mutum biyu da zasu rakani Abuja yace kuma da gwago cikin wanda za a bari da da mama zasu tsaya sai kuma aka tsaida shawaran mummy ta tsaya su yaya Saadu zasu biyo tanan sai su dauke ta. Amma kuma na fahinci yan uwanshi kamar basu jin dadin shi kamar yadda Faiza ta taba gaya min amma dai koma may ne yanzu tun da Allah ya jefani cikin su da sannu zan fahinci komai. Washe gari dukan mu muna zaune gaban hajiya baaba tana muna nasiha sai lokacin take ce ga yar kanin ta nan zahar ta karbo muna zamu zauna da ita . Koshi ashe baisan da maganan ba sai naga yayi saurin dagowa yana duban mahaifiyar tashi don kawar da komai da sauri nace mun gode baaba Allah ya taya mu riko. Tace keda kika fishi hankali baki ki alherin da nai maku ba amma shi har yanzu ban san abinda yasa baka mantuwa ba a ranka ana son musulmi da yawan yafiya ko yaushe. Murmushi yayi yana mike wa tare da sosa kan shi yace hajiya mu zamu tafi ai muna fatan alheri. Addua ta shiga kwararowa tana bin mu da fatan alheri har muka fice part din su gwago kan har an shiga motar da zata kaimu airport. Sai da muka sauka ne naga ashe da Aishan shi zamu tafi zata koma itama gidan mijin ta tare muka shiga jirge gwago kan sai kama mummy take yi. Mun bar yarinyar zata biyo driver da zai zo da motar da sauran kayan mu don suma sammako zasu yi don su isa da wuri. Mun isa lafiya motaci biyu suka zo daukan mu zuwa gidan shi harda Aisha duka muka tafi gidan nasa. Mun samu an kara gyara gidan anyi abinda ban san gidan dashi ba ya kara wani kyau da daukan ido na juyo na kalleshi da mamaki ya gyada min kai kawai yana lumshe idanuwan shi. Gwago da mummy sun kasa boye farin cikin su na ganin gida sai yaba kyawon gidan suke yi har muka zauna nan mai aikin shi ya fara gabatar muna da abinci. Mun ci mun sha a tare dasu mummy da Aisha don shi ana sauke mu ya shiga ya canza kaya ya fito bayan ya nuna muna dakuna ya fita. Tare da Aisha da mummy muka gyara dakin da ke zaman nawa tana da sakewa sosai don tana jana da hira sai dai nine ban sake jiki da ita ba. Take fada min yaran ta uku yanzu duka mata ta barsu nan Abuja ne a wurin kishiyar ta nace Anty Aisha kina da kishiya ne? Tayi murmushi tace mu uku ne ai dayar tana can bauchi don a can take aiki ita kuma dayar da suke nan dama anan ya aure ta. Sauke ajiyan zuciya nayi batare da na kara magana ba sai naji tayi dariya tace kwantar da hankalin ki yaya na mai son yawan tara iyali bane. Idan kika dubi yanayin shi rayuwan shi kaf na turawa ne don dan kaida ne shi sai kinyi da gaske kafin ki fahince shi amma idan kin fahince shi zaku zauna lafiya. Ina son ki jajirce wurin hakkuri da kawar da idon ki a alamuran shi bai faye son mamuwar mutane ba don Allah Safiya ki taimaka muna ya ja mu a jiki dan yazo kice kadai hope din mu. Murmushi nayi kawai nace a fili Allah yasa tace yayana yana da saurin fushi amma kuma yana hucewa a dan lokaci musasnman idan kai mashi laifi ka bashi hakkuri. Tace ina fada maki halin shi ne don ki kiyayye don naga kamar ba wani sanin juna kukayi sosai ba. A raina nace ashe akwai aiki kuwa ashe ganin kitse saman ruwa nake mashi ke nan sai naji tace idan kin ga ya tashi bai son magana kada ki damu kanki kidan nisance shi sai ya nemo ki don kada ku samu matsala tace bani wayan ki in saka maki layi na don mu ringa waya dake. Na mika mata tasa layin ta ta kira ya shiga tayi adding dina a contact din ta isowan driver da kayan mune yasa mu fitowa daga dakin muna taron su. Nan dai Aishan ta taimaka min muka kawar da kayan komai mukai mai mazauni munyi sallah la,asar mijinta yazo ya dauke ta tana mai ce min baya sati zata shigo ta duba mu. Bayan tafiyan ta na sauke ajiyan zuciya naga yanzu may abin yi nan na fara shawaran ko girki zan dora muna amma sai na samu har mai aiki ya gama ko yana shirin wuce wa gida. Wuein su mummy na koma na zauna nan muka fara hira dasu mummy ke cewa dani taji abinda kaunar mijina le fada min dazu don haka take son fada min . Inyi amfani da baiwar da Allah yai min na mace wurin canza mashi halayen da suka ce yana da musali idan yai fushin ba kaucewa zan yi ba kokari zanyi in jawo shi a jiki ta hanyan yin kwalliya da girki mai dadi da nasan yana so. In kuma tabbatar da na hada da addua da yaiwata sadaka din ganin haske ga alamarina in kuma yi kokari in koya mashi bin yan uwan shi ya saba dasu amma indinga boye sirina dana mijina tsakani na dasu . Do ba komai nai ya kamata su sani ba tace kinga wanan yarinya da aka hadoki da ita to itace ido da kunnuwar uwar mijin ku. Don haka koda zaki sake mata ba irin sosai din nan ba kada ki dingayin abu a gabanta do shine zai sa ta dinga kwasa tana fadi a gida. Ga kayan kwalliya ga sutura Allah ya wadataki dasu don ha ki daure da yaiwata kwalliya ajikin kina lamshi da saurar su zurfin karatu ba shiba ba indan akwai kudi babu abinda mutum ba zai iya ba sai ki dan more ma wanda kika samu a baya. Sai dai mijin nan naki naga mai wayayyen kai ne mai yuwa ya barki ki koma makaranta ki kara ilimi. Nan dai muke sai biyar da wani abu ya dawo gidan lokacin naci kwalliya da wani English wear a jikina ina tsaye ina magana da zarah a falo yashigo gidan. Sannu da zuwa mukai mashi nida Zarah bai amsa ba sai kallon zarah da yayi bat ta bar wurin kai tsaye yanufo inda nake tsaye. Kai tsaye ya hada bakin sa da nawa ya manna min ragowar lemon plus din dake cikin bakin shi na rufe bakina da sweet din ina ce mai thanks. Yace kin ga irin gaisuwar da nake so daga gare ki daga yau sai ki saba dashi murshi na sauke mai laushi. Ya koma saman kujera ya zauna na wuce na dauko mai ruwa mai sanyi na kawo mai tare da kokarin zubawa a kofi ya dagakatar dani da amsan goran ya kwankwade ruwan roban gaba daya. Yana sauke numfashi nace bakaci komai ba tun karyan safe ko? Ido ya lumshe min na koma kitchen na hado mai kayan bukin da muka zo dashi na da alkaki da goran juice ya karba yana min godiya. ZAINAB IDRIS MAKAWA SEENABU 8/15/20, 7:51 AM - Ummi Tandama: BAHAGGON, , , , , , , , , 🧕🏿5️⃣6️⃣🧕🏿 NOVEL DINA NA KUDINE KADA KI KARANTA IDAN BAKI BIYA NA SAUKE HAKKINA A KAN KU MAI FITARWA KUMA UBANGIJI YA BI MIN HAKKINA AKANTA KO WACECE. Bazan gaji da jan Allah ya isa ba a kanki mara tsoron Allah don ki gyara masu kike daukan nauyi a kan ki don baki san nauyin Allah ya isa ba zaki fadi ranan da nadama zata riske ki ko zata riskeka yadda baka/ki fasa fitar min ba nima ban gajiya da bin hakkina a kan ku dabara ta saura gyaraka/ki mara zuciya da gudun goben ta Duk da gajiyan dayake tare da shi bai hanashi mike wa yana ce min sorry na barki ba bayanin komai a gidan. Kamoni yayi ya mikar yana fadin muje kiga tsarin gidan naki ko ban musa ba na bishi yana rike dani yake nuna min ko ina na gidan. Sai naga ashe kallon tsoro nakewa gidan dama duk ban san komao ba a tsorace nake kallon gidan ashe yace da fatan komai yayi maki yadda kike so. Murmushin da yake so nayi masa daidai lokacin da muke komawa falon don zama yace yanzu may kike son a karo maki a gidan koda na nauin kayan kitchen ne nace komai yayi a yanzu daga baya idan ina so zanma magana. Hannu na ya kamo ya danka min mamullaiyan da alama na gidan ne sai wani wanda ban fahinci ko na maye ba. Kallon mamaki nake mai sai naji yace makulin motar ki ce tana waje aje sai ki shirya koyon mota yanzu sauran kuma na sauran dakunan gidan ne don ni ba zaunin gida ba ne koda bukatan shiga ya taso maki. Ban iya magana sai mikewa da nayi na durkusa a gaban shi gwiwoyi na biyu na saman carpet din falon hannaye na biyu na dora a kan cinyan shi na fara zanbga mashi godiya. Yace No no stop it safiya do you know how much i care for you? Na gyada mashi kai hawaye na zuba min a idona bayana naji ya fara shafawa a hankali tare da share min hawayen dake zuba min a fuska da hannunshi na dama. Cikin raunin murya na craking nace uncle dole in yi kuka ka nuna min kaunar da ban taba zaton samu ba a rayuwa na. Sai naji ya sunkuya ya rungumoni zuwa jikin shi ya na zaunar danu saman kujera yake fadin you deserve morethan this a wurina kin dawo min da farin cikin da na cire tsanmanin zan sake samu a rayuwa na. Yan zuma haka in bakiyi hankali ba ina dap da in baki kaina gaba daya ji nayi kamar dariya zai kubce min a hankali na zare jikina daga nasa na zauna kusa dashi. Gaba daya rikewa bayi wai yau nice a cikin wanan rayuwan da na dade ina mafalkin samu wanda sai dai inga anayi a tv ko wani gida gani yau na tsinci kaina ciki tsundon. Sai nake ganin abin kamar yar koyau na koma don ban saba da irin wanan rayuwan ba tun daga farko ji nayi yana tsiyaya lemon dake gaban mu a cup ya dan kurba sai ya miko min sauran gaba daya na zuke. Naji muryan shi yana fadin baki ce min komai ba batun kara karatun ki ko da yake idan son samuna ne ki zauna gida as a house wife zai fi min dadi naki jinin mace mai yawan fita a rayuwa na sha fada maki hakan a baya. Zan maki kokarin da duk wani abin da zaki bukata na rayuwa idan kin yi laakari da irin halin da muke ciki na rayuwa rayuwan ma har nawa take a gare mu yanzu ? Na dago idanu na dan kalle shi kadan sai naga ya zuba min idanun shi yana yana sauraren amsan da zan bashi. Haka yasa nayi saurin sauke idanuna kasa ina wasa da yan yatsun mu dake hade a hankali na iya furta mashi uncle na hakkura da karatu. Kin hakkura fa kika ce da karatun na kada mashi kai alaman eh yanisa yace saboda may ke fa kika ce min kina sha, awan karatu a baya . Na nisa nace yanzu na fasa a hankali. But why , ? Ko dan abinda na fada yanzu ne kika fasa cika burin ki ? Nace a hankali eh to duk mai hankali yayi tunane haka din ne don may kuma nake bukata ga karatu yanzu banda in zauna dakina in nemi ladan aure. Don maganan ka gaskiya ne har wani rayuwa zai ba ni shawa yanzu kuma bayan wanan da nake ciki indan nayi duba da dafin mutuwan da ke a jiki na karatun ma karshen inyi ban mora ba gara kawai in zauna in rugumi kaddarata da hannu biyu yafi. Yace hakan yayi maki don ban son daga baya ki koka dani ko kadan duk da zanyi iya kokari na wajen kare maki hakkin ki dana bukatun ki. Na na insha Allah yayi min zan zauna in kula da gida da bukatun ka na lura kaima hakan yafi maka don dai kaga ina sha, awan karatun ne ka mara min baya akai. Guntun Murmushi naji yayi mai alaman da magana na dago kai na kalle shi sai yace hakan na dakyau don kin fara cinye jerabawan da nake gwadawa akan ki. Saboda haka nayi maki alkawarin zaki rika amsan albashi kamar yadda nake ba sauran maikatana duk wata. Katse shi nayi da fadin a a Uncle gaskiya ni hakan ya, , , , ji nayi yarufe min bakina da hannun shi tare da fadin Shhhh, , , , . A hankali yace min shine magana na don may ake aiki ba saboda neman kudi da tallafa ma kaiba don haka shawaran da na yanke ke nan a kan rashin karatun ki. Duk kuma lokacin da naga kin samo sallon batani da irin takon ku na mata sai in canza raayina zuwa wani nauin don kin san mace bata da wuyan bata namiji da halin ta don gashi kwana nawa da auren mu har kin koya min rasgin zama gurin aiki gashi yanzu sai da na dawo gida don ki. Mikewa nayi tsaye ina kokarin gudu cike da jin kunyan shi amma sai ya kamoni zuwa jikin shi yana fadin. Where do you think you are going ? Yana sakin dariya yana kokarin janyoni jikin shi ina fadi kada mummy tafito fa ta samay mu haka yace may zai kawo mummy nan part dina. Da kyat na samu ya sake ni koshi don an fara kiran sallah ne a lokacin don haka muka watse zuwa sallah. Da dare har dakin da su gwago ke ciki ya samay su akan yana son su fito muci abinci tare dasu basu so ba amma haka suka fito yana jan su da fira har suka sake jiki da shi suna cin abincin. Bayan mun gama na kwashe kayan ya zauna dasu suna mashi hira anan yake fahintar yaya Saadu company da yake aiki dasu yanzu sun durkushe. Ni dai daki na koma na fada wanka don naga sabon angon nawa ba na wasa bane wurin son tsabta da lalubar mace bayan na shirya waya na dauko muna magana da Amina don wani ruwa da ta bani ina son tai min bayani akan shi. Nan muka tsaya tana min hira bayan komawan su gida yadda suka kwasa wirin rabon kudin da aka basu tukwaici acan. Kofa naji an turo ko ban duba ba nasan cewa shine ya turo kofan dakin ya shigo yana tsaye da jallabiya baka mara hannu. Ya rike cup yana shan abu a ciki sai dai bani iya cewa ga abinda yake sha a cup din kai tsaye ya nufo ni sai da ya zuke abinda yake shan ya tambaye ni da kin sha maganin ki kuwa ? Kai na girgiza mashi alamar a a zama yayi yana fadin dauko tare da fadin kina wasa da shan magani ko safiya baki san in kin kiyi kwana daya baki sha ba zai iya tambayan ki ba. Mikewa nayi na bude wardrobe dina na dauko kwalin maganin ina barewa sai yace miko min in gani ya karba ya dan duba sai ya miko min tare da fadin akwai wanda na anso a italy zan baki ki gwada sai dai yana da matukar karfi sosai idan kin sha zai sa ki cin abinci sosai amma yana aiki sosai a jiki. Kofa na nufa don in dauko ruwan da zan hade maganin dashi sai naji yace dani no barshi in munje daki kya hade. Kallon shi nayi da sauri yace yes dakina zamu yau ko kin fison kullun dan kwali ya jawo hula har a saka muna ido a gidan. Don ni gaskiya ba yanzu nake son gwago ta koma ba so nake ta dan zauna damu na dan wani lokacin kafin a maida ta in son samu ne har da mummy din don matar na da dadin zama. Murmushi nayi nace uncle ai sai kasa a zage mu daga kawo amarya sai su samu wuri su zauna. Ina fadi kamar zanyi kuka yace common wa zai san ma suna gidan nan balle a fadi haka ko baki son zaman su ne sun takura maki keda angon ki. Wani kallo nayi mai na ba haka bane sai naji ya sukkuce ni bai tsaya dani ko ina ba sai tsakiyar gadon dakin shi. Da kyat ya barni na sha maganin nawa duk rokon da nake mai baijini ba sai da yayi abinda yake son yi ya samu natsuwa. Washe gari su yaya Saadu suka iso Abujan don daukan mummy su tafi amma sai Uncle ya dinga masu delay da tafiyan sai da suka share kwana hudu tare da mu. Ranan da zasu tafine yaya ke gaya min Uncle ya dauke shi aiki a company shi tare da bashi wuri zama da iyalin shi kuma yaya sani zai zo don shima an sama mashi aiki anan. Nayi murna kwarai ko banza nima na samu dan uwa a kusa dani yanzu abokin shawara ga matar shi Samira akwai shiri sosai a tsakanin mu da ita. A ranan na biyar suka kama hanya nan suka barni cike da kewan su don dan zaman da mukayi ba karamin jin dadin hakan nayi ba. Gidan ya rage daga ni sai gwago wace da kyat a rana ta fito falo sau biyu ko yaushe ta daki daga sallah sai lazimi tana kallo. Sai in dare yayi ya dawo gida zai dan je gunta su dan taba hira wani lokaci har da ni sai Zarah da har yanzu bata gama sake jiki dani ba sai dai akwaita da son kallo ko yau a cikin kallo take ita. Na tambaye ta karatu fa take ce min ta gama secondry bana jiran jerabawa take yi yanzu ina kula dashi da duk yazo ya samay mu da ita zaune sai in ga ya daure fuskan shi har yarinyar ta dan shiga tsarguwa da taga lokacin dawowan shi gida yayi zata shige daki bata kara fitowa kuma. Ranan ina tambayan shi may sa yake mata haka sai cewa yayi dani cikin tsawa gada ki kara yi min maganan wanan yarinyar don ba zamana takeyi ba a gidan nan . Da sauri nace Uncle in ba zaman ka takeyi ba zamanwa take a gidan ina kai hajiya taba ita muzo da ita don debe kewa bai yi magana ba sai mikewan da yayi ya fice dakin ya koma dakin karatun shi ya zauna. Nikan abin ya daure min kai sai na ja baki na nayi shiru har naje gun gwago na zauna muna hira hankali na yana gurin shi don haka nace ma gwago ina zuwa. Kitchen na shiga na hado mai snack da drinks na nufi dakin da yake da sallama na tura kofa ban tsanmani ya amsa min ba sai dai dan juyowa da yayi ya mayar da kanshi ga abinda yake yi cikin laptop din shi. Sannu da aiki uncle sai da ya sauke ajiyan ziciya ya iya amsa min da yauwa sannu madam nace ga abin motsa baki nan na kawo maka kadan jika makoshin ka. Na aje na juya zan fice daga dakin sai naji ya riko min hannu yana cewa ba tare da ya bar abinda yake yi ba bazaki karasa ladan ki ba kin kawo min abin sha baki zuba min ba zaki wuce. Dawowa nayi na tsaya ba tare danayi magana na fara zuba mashi acin cup din dake saman tire din, mika mashi nayi tare da dan rusunawa. Sai lokacin naga ya dauke kan shi saman sytem din yana fadin thanks nace aiki nane hakan ya zuke yana lumshe idanuwan shi. Ya mayar da cup din cikin tire din yana maida kan shi saman laptop din jiki a sanyaye na fita daga dakin yana aiki yana cin dabun naman daya ji curry da kayan kamshi ya lumshe idanuwan shi. Ban koma ta kan shiba na tsaya kitchen da falo na gyara ina gap da karasawa naga fitowan shi daga dakin har yanzu fuskan shi babu walwala a cikin sa. Da gefen ido ya kallo ni ya shige part din shi tare da rufo kofan da karfi araina nace ga maganan Aisha ya fito take maganan mummy ya fado min a rai. Idan yayi fushi ke ki kwantar da fushin ki ki bishi sai zama yayi dadi amma kin hau namiji ya hau wazai kwantar ma wani da fishin shi wata kila ma fushin da dalili yake yin sa. Dakin gwago na leka na gaishe ta nake gaya mata lokacin sallah ya gabato tace ai har na dauro alwala wanan gida naku ba ajin kiran sallah. Dariya nayi mata nace baga agogo nan ya sayo maki ba don ya dinga kira maki sallah kina ji tace kaiya ban faye amincewa da wanan abin nasaran ba ai. Nace yanzu dai da kinji ya kira sallah sai ki mike lokaci ne yayi baya karya sai idan batir din da yake aiki dashi ne ya kare tace bakaji ba. Ina dariya nace gwago kafin ya kare fa sai nan da kusan wata biyu tace wata biyu ni ina, ina yar nan ai kisa a dauke mu mutanen banza nifa har na fara yiwa maigidan ki tunin gida don naga so kuke sai kinyi ciki ina gidan nan kulle kamar kurkuku. Fita nayi na barta ina dariya kada in makara da dauro alwala a lokacin naga gittawan shi zai fita zuwa sallah don ko yaushe sallah jam,i bai wuce shi. Bayan isha,i na gama komai har abincin shi yana saman table na koma daki na shirya tsaba a cikin wani dogon riga baki mai hanuwa shara shara yaji kwalliya har kasa da kananan duwatsu an dan buda kasan shi kadan. Ban fito ba sai da na ji motsin shi a falo ya na sauraren News hakan ya sani fitowa daga daki ture kusan kala uku na shafe jikina dasu yan saudiya. Kamshi ya hade da sanyin da AC falon yake saukarwa ya bada wani inrin yanayi a falon tun fitowa ya dago ya kalleni ya kauda kai yaci gaba da kallon TV dake gaban shi. Har na karaso gaban shi cikin daurewa na karaso gaban shi na dan duka daga bayan shi tare da sagala hannu na daga bayan shi nace sannu da hutawa Uncle. Dan murmushi ya sake da bai sauka ciki ba yace barka da gida madam din Uncle zagayo dani yayi zuwa gaban shi ya zaunar dani saman kujerar daga gefen shi yana mai ci gaba dakallon shi sai dai har wanan lokacin bai sake min yatsun hannu na da yake wasa dasu ba. Cikin daurewa nace Uncle abinci fa yace dauko min nan zan ci na mike cikin wani tako da ban san na iya irin sa ba na nufi dining din kwaso kayan da na jera akai. Sai lokacin ya sauke wani iri ajiyan zuciya har ina jin shi don na kusa kawowa wurin shi a raina nace su zuciya manya. Ashe akwai aiki a gabana dan wanan magana yake ta jawa rai haka anya kuwa zan iya sai da na gama jerawa nace bissimillah na samu wuri a kasa na zauna tare da jan plate zan fara zuba mai. Ganin kayan tare a gaban shi kashi kashi yasa yace min may ye haka yau John ya girka muna? Banyi magana ba sai ci gaba da bude warmer din nayi inda na fara ziba mai tuwon shikafa da miyar shawaka da yaji agusi da manja sai nama manyan yanka da nayi amfani dashi wurin hadawa da dan man gyada kadan. Kamshi me ya kaure falon alokacin da na bude ferfesun kifin dana hada wanda nayi amfani da kayan yajin mu na gargajiya sai ruwa dana zuba da maggi. Gani nayi ya sauko kasa abin wanke hannu na jawo tare da dauko ruwanda na tanada don wanke hannun nashi. A hankali ya miko hannuwa fuskanshi akan tv ina zuba mai ruwan ya na wankewa a hankali na jaye ruwan gefe guda sai ya kallo ni yace ke ba zaki ci ba nace munci da gwago da Zarah tun dazun dana gama. Naga ya kara hade rai yayi bissimilla ya fara ci har ya kare bai yi magana ba ni dai ina zaune na saka ma tv ido nima kamar mai saurare abinda ake fadi nan ko zuciya ta tambaya kanta take yi mai ya kawo wanan matsalar haka wai ? Naji yace amma ba John yayi abincin nan ba eh kawai na bashi amsa dashi na fara hada kayan ina kwashewa na barshi dana ferfesun yana sha a hankali yana kallon tv. Bayan ya gama na kwashe na dauko kamshi na bude falon dashi yadda ba za a ji karnin kifin ba idan an shigo falon. Zama yayi a kasan tare da jingina bayan shi da kujerar daya sauka a kai tare da mike kafafuwan shi a kasa yana kadasu a hankali zaman naji shiru yayi yawa don haka na mike zan leka gwago a dakin ta. Yace jimana sai na dawo na zauna cikin basarwa yace gwago tayi min maganan zuwa gida yau da safe don haka nake son ku fita ai mata tsaraba zuwa gobe. Allah ya kaimu nace sai na juya na wuce bina yayi da kallo komay ya tuna a ranshi sai yaga bai kyauta min ba sauke ajiyan zuciya yayi may ye laifina a cikin wanan magana daga tambaya kawai ya dora min laifin dabashi ba. Nasan nayi laifi na kuma dauka ina binshi don yayi hakkuri ya kasa cire laifin da bani nayi shi ba akaina. ZAINAB IDRIS MAKAWA SEENABU 8/15/20, 10:51 PM - Ummi Tandama: BAHAGGON, , , , , , , , , , , 🧕🏿5️⃣7️⃣🧕🏿 NOVEL DINA NA KUDI NE IDAN KIN FITAR UBANGIJI YABI MIN HAKKINA A KAN KI/KA. YAR UWA MAINE RIBAN KARANTA KAYAN ALLAH YA ISA KARATU FA IYAKAR SHI DUNIYA. Karfe goma saura har lokacin ina zaune dakina na kasa zuwa dakin uncle don ban san da wani fuska zai karbe ni har nayi kamar in share shi saidai na mike na fara shirin zuwa wurin shi. Komai na falon an an kashe alaman dai ya shige tuni dakin shi sai wutan da zai sadani da nashi part din ne kawai a kunne. Ahankali na kwankwasa kofar tare da turawa sai najita a bude nasa kai na shiga dakin can na hango shi tsaye bakin window dake kallon wajen gidan yana tsaye ya rike labule da alama iskan dake busawa a lokacin yake shaka don yana mai dadi. Shigowana baisa ya juyo gareni ba har na karasa inda yake tsaye batare da jin kunya ba na rungumay shi ta baya tare da zagaye hannaye na saman ruwan cikin shi. Ajiyan zuciya naji ya sauke a sanyayye nace uncle may kake yi anan tsaye kai kadai batare da ya juyo ya kallene ba ya bani amsa da yanayin yana min dadi ne madam. Sake shi nayi nima nakoma gefen shi na tsaya ina kallon waje sai naga motoci suna wulgaiya jefi jefi ga iska mai dadi na hurowa ta tagan dakin. Gwaron numfashi na sauke amma a fili na kasa fadin komai sai tsayawa danayi ina kallon wajen kamar yadda shima yake kallo. Shi ya kawar da shirun da cewa na dauka kinyi barci ne dana jiki shiru ai ajiyan zuciya na sauke nace uncle ina zan iya barci bayan miji yana fushi dani karo na farko a rayuwan mu tare. Murmushi yayi tare da sanya hannuwanshi saman kirjin shi yace bada ke nake fushi ba sai dai maganan ki ce ta jawo min fushi na. A marairai ce nace kayi hakkuri uncle ban san maganan zai bata maka rai ba haka da banyi ba ni gani nayi yarinyar tana zaman kane a gidan kuma bata samu sakin fuska a wurin ka ba. Naji na gode amma ke bakuwa kike a cikin mu shiyasa zan daga maki kafa ga maganan yanzu amma indai akan zancen wanan zurian ne bani son daga yau ki kara yi min shi a gidan nan. Ki barni da yan uwana ki zauna matsayin ki na matana a cikin su bani son ki zure masu har su samu kafar shige min haka. Murmushi nayi na kwantar da kaina saman kafadan shi nace uncle yadda kake so haka za a yi har kullun a shirye nake da in maka biyayya a rayuwana. Amma Uncle ina son ka zama mai yafiya ga duk wanda ya zulunce ka saboda kayi koyi da sunnan mai,akin Allah sallalahu Alaihim wassalam. Yau uncle in har akwai abinda sukai ma rayuwan ka sai ince ya zama maka taki ayanzu don hassada ga mai rabo taki ne. Uncle har kullun sai dai inci gaba da yima addua da fatan alheri a garemu uncle ba zan boye maka ba bantaba ganin mutum adali irin ka ba uncle. Sai dai kuma cikar kamalan mutum baya kammals sai ya cika sharudun Allah a kan shi yanke zumuta dasu don sun taba yi ma rayuwanka illar killa can baya ba shine mafita ba a gare ka. Kamata yayi uncle kai ka saka masu da alherin ka barsu da halin su Allah shine mai hisabi arayuwan biyan sa. Amma uncle akan may zaka rike gawarshin wuta a hannuwan ka su kona ma aikin na alheri har ka gamu da fushin ubangiji ka ta sanadin su. Uncle kafan Allah yana fushi da may yanke zumunci sannan na fahinci baaba tayi hakane don kawar da wani abu a gare ka. Sannan Uncle ba, , , , ji nayi ya dora dan yatsanshi saman bakina yace ya isa haka naji na gode zanyi iya kokarina inga na fitar da abin a zuciyata. Ina alfahiri da kasancewar ki matana a yanzu don samu mace ta gari yana haifar da alheri acikin zuri,a dawamamiya. Ya rugumay ni zuwa bakin gadon shi sai lokacin da ya sauke ajiyan zuciya yace may kika tanadarwa tafiyan gwago ne ? Ban bata lokaci ba nace gwago mai za a tanadar mata dayafi jarin kuli da takeyi ba dare ba rana duk shi ya hanata zama hankalin ta na can wurin masu zuwa sarin mangyadan ta. Kai naji yace yanzu kina nufin gwago har yanzu tana irin aikin wahalan nan na kuli nace da hannunta ko take komai wallahi. Nisawa naji yayi yana kaiwa kwance nace Uncle kuna waya da anty kuwa ? Yayi dan guntun murmushi tare da fadin ina jiran sai ta huce da kanta zata nemomu don yanzun ta hau sosai . Nisawa nayi nace a kullun idan na tuna irin alherin dake tsakanina da ita ban jin dadi a raina da haka ta kasance a tsakanin mu. Baiyi magana ba sai kamomi dayayi zuwa jikin shi muka kwanta anan labarin ya canza sallon shi. Washe gari bayan ya gama karyawa ne alokacin gwago na da mako biyar a wurin mu kamar yadda yace kudi ya dora min saman cinya na yana fadin ku shiga kasuwa da gwago asaya mata duk abinda take so don Allah kada kibi son ranta a sai mata duk abinda ya dace da ita. Dago fuska nayi ina kallon shi ganin yadda ya daure fuska yasa na kasa fadin abinda nayi niyar fada mai din. Sai dai da ganin fuskana kasan so nake ince mai hidamar da yakeyi a kaina sunyi yawa haka gani nayi ya gyada min kai tare da fadin karki ce min komai indai ba so kike ki bata min rai ba. Ajiyan zuciya na sauke tare da fadin Uncle ni may zance sai dai inci gaba da maka fatan alheri Allah ya saka da alherin sa. Sai dai ba zan iya boye maka ba ban taba ganin mutum irin ka ba a rayuwa na har tsoro nake ji kada yan uwanka su fara zargina akan haka. Murmushi nan nashi ya sakar min inda ya fara tafiya yana fadin yau ba zan samu rakiyan bane ? Na mike da sauri ina fadin ban isa ba ai a tare muka fito ina rike da yar briefcase din shi har zuwa bakin motar shi inda iya nan nake tsaya dama. Sai da yayi kissing din goshina ya fara tuki yana cewa ku fita da wuri don idan yamma yayi tafiyan ba dadin fita garin. Na dawo ciki cike da murna a nan falo na samu Zarah ta fito ban tsaya ta kanta ba na nufi dakin gwago tabi bayana da kallo. Zaune na samu gwago ta kura ma tv ido ga tasbaha a hannun ta tana ja tayi kyau ta kara kiba da haske sosai nace kai gwago wanan irin kyau haka karfa ki koma inji zawarori sun fara zuwa wurin ki. Dakuwa ta nuno min tana fadin wani shegen bazawari zai zo wurina yanzu ai sunyi nacin su sun barni nan so sukeyi su dan cinye abinda muka dan gada su barmu muna leke a gidan wasu. Don gaskiya gwago batayi tsufan da za a ce bata da aure don kunsan yadda aure yake a kauye irin auren nan na wuri atara zuria da wuri. Sai da na zauna kusa da ita sannan na fito mata da kudin na aje a gabanta tabini da kallo sai kuma ta juya ta kalli kudin dake gaban ta tare da zaro ido. Dariya nayi nace gwago kidin ki ne yace zamu shiga dake gari a sayo maki duk abinda kike so kuma ya ce don Allah a saya maki abinda naga zaki bukata indan kin koma gida. Zaro ido ta karayi tare da fadin yar nan duk wanan uban kudin duka nawa ne haka gaskiya sunyiwa ki raba uku ki maida mashi da kashi biyu kice na gode. Sauran na samu na kara jari ai sun isheni sayen buhun gyada goma nan gaba kin ga jari ya tasa ke nan nan gaba. Da sauri nace a a gwago Allah ne ya kawo muna hutu a karkashin shi Allah ya duba wahalan mu na can baya lokacin da sai kin dauko abinci a gidan ki kin kawo muna muci da sauran abin amfani. Don haka ma kin madaiji abinda ya fada wai na kaso maki su duka idan mun fita da sauri naji tace waneni wanan kudi yai yawa da kashewa yar nan. Haka dai na lalabata ta shirya driver ya fita damu mu uku da zara muka fita gwago batayi niyar a sai mata abin kwarai ba so tayi ta dunkule kudinta ta koma gida dasu. Amma naki yarda sai da na sai mata abinda naga zasuyi mata amfani idan ta koma da tsaraban da zata kai ma mutanen gida. A gajiye muka dawo gidan sai dan abin motsa baki da muka sawo muka zauna nan mukaci muka kora da drinks zarah ta mike ta shiga dakin ta tare da abinda na sayo mata a fitar namu. Bayan mun huta na dora girki na dawo wurin gwago na dubata tare da dan taba hira na koma ban sake dawowa wurin ta ba saida dare bayan na gama komai kafin ya dawo don ranan yayi dare bai dawo da wuri ba na fara hada mata kayan ina mata bayanin komai da wanda na sayo masu mama Jummai zata kai masu tsara da yaran su. Sulaiman ya dawo gidan da alamun a gajiya ya dawo don tun bai shigo gidan ba ya rage sassauta tie di wuyan shi tare da balle rabin anineyan gaban rigan shi. Sannu da zuwa muke mai daga ni har gwago yana amsawa da kyat yana kaiwa zaune yace gwago ana nan anashiri ko tace kaidai dan Albarka sannu da kokari wanan irin abin arziki haka mai yawa baka gajiya da dawainiya damu ? Yace kai gwago ai albarka ku muke nema ko yaushe don abinda muke nema yayi albarka tace haka nane ubangiji ya kara rufa asiri Allah ya kara daukaka da nisan kwana . Ya amsa cikin jin dadi da amin gwago abinda muke nema ke nan gare ku addua da fatan alheri ya juya inda nake tsaye ina saurare su bayan na gama hada mata kayan. Yace madam yaya gida yana mikewa tsaye yake fadin haka nace Alhamdullahi yaya gajiya aiki yace not bad nabi bayan shi muka fita tare har zuwa dakin shi dauke da briefcase din sa dana karba. Muna shiga dakin ya zube saman gado gaba dayan shi na aje na juyo ina kallon shi bayan na aje jakkan a ma ajiyar shi takowa nayi zuwa wurin na duka a hankali na fara cire mai takalman dake kafan shi tare da safa sai naji ya sauke ajiyan zuci bandaki na shiga na hada mai ruwan wanka. Na fito still yana kwance a yadda na barshi ga ruwa can ya hadu uncle na fada mashi ina kokarin fita dakin don na dora ruwa a kattle. A lalace naji muryan shi yace madam na juyo da ina kallon shi yace da wanan yarinyar kuka fita sayayya dazun ? Nace eh zarah ko ? Sai naji yayi gajeriyar murmushi yace I know it dama mikewa yayi zaune bai bi ta kaina ba ya fara kokarin cire kayan shi. Ya barni tsaye ina jimamay tambayan shi gare ganin baita kaina yasa na fita dakin naje yin tsabgan gabana. Bayan ya fito yaci abinci bai dade ba ya koma dakin shi tun bayan gama kallon news da yayi tare da cin abinci. Nima sai banyi nawa ba na gama na samay shi a dakin amma yana waya a lokacin ga yadda na fahinta kafin in shigo fada yakeyi a waya amma ina shigowa sai ya rage sautin fadan shi tare da fadin na fada maku bazan dauki wanan halin ba. Wuce shi nayi na dauki flask din na tafi daga dakin har na dawo waya yake na aje na samu wuri na zauna a bakin gado wayan ya kashe yana mai sauke numfashi tare da wurga wayan saman gado ya shiga ban daki nikan kwaciya nayi kafin ya fito. Banji fitowan shi ba sai muryan shi da naji yana fadi daga bayana don may kika dauki yarinyar na kuka je sayayya da ita? Na juyo da sauri yana goge jikin shi da towel nace uncle naga zamu barta gida ita kadai ne yace a harzuke ku barta mana sai may? Ai dama bari nayi kisan halin su da kanki basai nayi warning dinki ba yanzu kin ji abinda tayi ta buga waya tana cewa wai kudi nake sakar maki kamar may don ko gwago da zata tafi wai ba karamin kudi na bayar ba akatafi kasuwa mata sayayya. Ban san lokacin da na mike zaune ba yace yes dama na sani kadan daga cikin aikin su ne wanan. A mairaraice nace uncle wani abu yafaru ne ? Ya faru mana daidai lokacin da yake hawa saman gadon yace waya tayi gida wai take fada masu a hankali nace Zarah din yace dama may ya kawo ta ? Shiru nayi a raina nace wai rufin kofa da barawo ke nan ashe idon su hajiya ce Zarah ban sani ba ashe da munafuka muke zaune a gida aiko nawa ya ya samay ni. Tunanen may kike yi dama baki san ma,anan zuwa da ita da uwarta ta matsa ma hajiya sai munyi da ita ba. Aisha ta fada min komai tun can hannatu ta fada min komai amma tunda naga ke kina da raayin zama da ita yasa na kyale sai tayi maki. Da wanan bakin cikin na kwana a raina na Zarah da safe da na tashi bayan nayi sallah naje muka gaisa da gwago ban tsaya ba kitchen na shiga don dora breakfast. Sai na samu har Jonh ya shigo yana yayanka kifin da zaiyi ferfesu dashi don shine mai muna abinci ni kuma kazantar cin abincin shi nakeyi shiko uncle bai damu ba cin abinsa yake yi. Na gaisawa mukayi da shi tare da fada mai ya barshi zanyi baiso ba amma ban bashi fuskan tsayawa ba ya fita daga kitchen din. Bai dade da fita ba sai ga zarah tashigo muryan ta naji daga bayana tana fadin anty ina kwana ? Dan juyowa nayi ina amsa mata tace dani may zan kama maki anty ? Nayi mamakin jin tambayan don bata fitowa haka da safe sai idan mun gama tace barci ne ya dauke ta bata san gari ya wayewa ba. Yau kuma ko tafito ganin wani abin ne ta sake fada ban sani ba sai nace da ita ki barshi kawai ba wani aiki mai yawa zanyi ba ai. Tayi dan jimmm sai naga ta nufi wurin dankali nace ki barshi yau ba zan soya dankali ba ai nan naci gaba da aiki na share ta. Ta dan jima atsaye sai ta juya ta fita daga kitchen din na gaba na ba kowa nasa wanka nayi kafin ya fito na shirya cikin wasu atamfan Super mai launin makuba na fito zuwa wurin shi. A tare muka fito dashi daya gama shiri tana falo wanan lokacin ganin mu yasa ta zamo daga saman kujera duk ta daburce da ganin ta bata da gaskiya ko kadan ta na gaishe shi a daure ya amsa mata. Bayan kwana biyu gwago ta koma gida tare da abin arziki mai yawa da ta samu wurin maigida don har injin din tatsar mai ashe ya saya mata duk bamu sani ba sai da ta koma nakejin labari. Naso bayan tafiyan gwago in daure ma zarah amma sai nayi shawara na fasa nuna mata nayi ban san komai ba gaba na da yawa ai. Sai dai na bar yin komai a gaban ta yanzu na kuma rage bata fuskan da nakeyi sosai so nake ita da kanta tabar gidan batare da wani abu ya fito daga gare mu ba. Wata na biyu cur a gidan uncle na canza acikin dan kankanin lokaci saboda abin more rayuwan da nake samu a gidan shi. Don babu abinda ya rage ni dashi na fannin rayuwa duk wanda ya ganni sai yayi maganan canzawa na ni kaina nasan ina daga cikin matan da suka dace da gidan miji. Banda tunanen komai a raina in ma ina da bai wuce na ciwon dake jikin mu ba kuma Alhamdullahi muna samun kula yadda ya dace sosai dama abinda ciwon ke bukata kenan. Haka zai sawo abubuwan kara jini ya sakani a gaba sai munci tare magani kuma idan yana gari a tare muke sha kullum kafin mu kwanta don ka,idar shan shi ke nan. Yaya Saadu yazo sau biyu a lokacin don ba a gama gyaran gidan da zai zauna ba sai yake zuwa yana komawa. Ranan ina daki kwance dakina da yamma daidai lokacin dawowan uncle gida ta kusa sai ga zarah ta shigo da sallaman ta dakin tayi sallama na amsa mata ta shigo ba kasafai take shigo min daki ba sai idan da wani dalili. Anty kin yi baki tace min na dago daga kwancen da nake ina fadin baki tace eh suna falo zaune suna jiran ki. Dama bani zama babu kwaliya a gida tsab nake banda wani kushe a jikina kara dan gyarawa nayi dakyau na fito don ganin ko su waye suka zo. Mata na hango zaune su hudu a falo sai dai ban sheda ko su waye ba daga nesa sai da na karso wurin ina fadin sannu ku da zuwa gaba daya suka juyo sai da gabana ya fadi. Fon ganin bakin nawa don ba kowa bane anty Uwa ce da yaranta uku gaba daya a gidan namu, , , ZAINAB IDRIS MAKAWA SEENABU 8/17/20, 10:17 PM - Ummi Tandama: BAHAGGON, , , , , , , , , , , 🧕🏿5️⃣8️⃣🧕🏿 NOVEL DIN NAN NA KUDI NE IDAN KIN FITAR UBANGIJI YABI MIN HAKKINA A KAN KI/KA DON WALLAHI BAN YAFE BA, , , , Ganin bakin nawa take naji gaba na yayi wani irin bugawa don tsoro da fargaban ganin su haka a gida na may ya kawa su kuma nake tambayan kai na. Muryan anty uwa ne ya dawo dani daga duniyan tunanen da na lula da farko naji tana fadin a, a tau, amaryan ce wanan masu gari tana bin zanin jikina da kallon tun daga sama har kasa na binshi da kallo sukeyi. Allah ya rufa min asiri yau da safe bai fita gidan da wuri ba don haka na sha kwalliya tun da safe da atamfan brocade a jikina. Dinkin shi mai kyau tun daga Dubai ya sayo min shi hakana din kakken shi murmushi na kakaro a fuska na ina cewa dasu sannuku da zuwa tare da sakin fuska sai da na zauna nake cewa ina wuni Anty Uwa kamar yadda naji anty na na lagos na kiranta dashi. Waya na dauka ina latsawa mai aikin mu na kira ina fadin make something special for our visitor's. Na gama na dago tareda cewa sannun ku da zuwa duk naga sun kura min ido sai bin gidan suke yi da kallo sauran yaran nata itako sai faman tabe baki take yi. Mun gaisa sai dan shiru ya biyo fallon anty uwa din ne ta kawar da shirun da falon yayi a lokacin. Ji nayi tace dani maigidan ya fitane ko yana ciki nace ya fita yana gun aiki sai zuwa yamma zai dawo gidan. Dakatar, ni , wata daga cikin diyan nata, tayi da fadin ai dama bashi muka zo gani ba gun ki dai ke snacher muka zo, Murmushi nayi don jin sunan da suka kirani da shi wanda su ya dace a kira da sunan tun farko amma sai gashi suna lakakamin sunan don basu da kunya. Uwar ne ta dakatar da ita da fadin dakata lawisa sai ta juyo gare ni tana fadin ke wama kike da suna what ever dai ba mun zo bane nan don dogon surutu sai don mu zo mu ga idon yar kauye kamar ki da har ta iya kwacen maza haka son ranta. Tun wuri ki san da sanin Nafisa zata shigo gidan don haka ki zauna da shirin taron ta ke wanan gidan ma ai sam bai dace da irin ki ba yar kauye ga gida har gida amma wai yar kauye gaja ce irin ki a gidan ba ilimi ba komai. John ya shigo da tire shake da drinks da sauran abin taba baki ya girke a gaban su don basu da kunya sai suka zari guda guda suna balla bakin su tare da kafa kai. Duk da uwar taji kunyan abinda sukayi sai dai banda ita Nafisa din fada ta fara yi musu akan su natsu mana suyi abinda ya kawo su. Ina zaune na kafa masu ina kallon abinda ke wakana nasa yatsan hannu na guda na tallaba haba na dashi tare da kura masu ido. Bayan sun dan natsu ne uwar taci gaba da fadin yanzu ke har kin san ki yaudari matar da ta tsamo ki a cikin talauci da wahala ki tsallakata bayan ta gama maki komai kin gudu kin barta don halin dan adam butulu saboda kina hangen nesa. Yanzu ke baki ji kunyan asirce ta da kikayi tun farko ba bai maki ba kuma kika asirce mata kanin miji da bakar asirin ki don kawai kin samu labarin yar waje na yake nema yanzu. To ai baki sani ba idan asiri kike takama dashi nafiki idan kuma barikanci da iya duniyan ci kika ce kin iya duk na dama ki na shanye. Gidan nan sai Nafisa ta shigo shi ko yau ko gobe ki zauna a cikin shiri don da ta shigo waje kika yi ke. Don gidan nan ba gidan zaman ki ba bai dace da mace yar kauye kazama irin ki ba don haka ki sani, , , , , , , Madam yaya gida ya fada ba tare da ya kallo mu ba driver shi na binsa baya da jakkan shi na ai har ya nufi hanyan dakin shi sai kuma ya juyo yana cewa sorry baki kikayi ne ? Murmushi nayi tare da fadin anty Uwa ne fa da yaranta da, , , ji nayi ya katse ni karasa magana na da tambayan da ya daure min kai. Uwa waye uwa ya fada yana maimaita sunan cikin daure fuska dan gyara zama tayi tana fadin Sulaiman baka gane ni bane ? Uwa sister din yaya Lawal soja dake Lagos minjin maimuna wai kana nufin ka manta dani uwa na gidan malam garba teacher. Katse ta yayi da fadin kenan ke sister din lawal ne ko kece ke zaune a nan garin da sauri tace eh nice ai , yace anzo diba madam ne ? Wani kunyan ne ya kamata ba ita ba har diyan nata sai da sukaji nauyi don yanzu suka gama cika baki akan shi gashi kuma ya shigo ya nuna baida halaka da su asalima bai san su ba. Yana batun wucewa na bude baki da sauri ina fadin Uncle bakin ka ne fa , don wurin ka suka zo da mamaki yake kallon fuska na kuma ya dan kallon su sai ya dawo ya zauna. Na mike zan nasu wuri ya ce No zauna idan sunzo wurina ai kamar wurin ki suka zo so ki zauna ba wani abu bane ya juya wurinta yana cewa lafiya ko hajiya ? Duk sun natsu ta kasa magana sai mai bi ma Nafisan ce ta fara mikewa tana fadin sai da na fada maku kada muzo gashi munzo an wullakanta mu a banza. Karamar tace wai kana nufin ba ka masan Anty Nafisa ba ko may ta juta wirin uwar tace mummy duk wanan abin da akeyi dama bai san ku ba ne ? Mikewa yayi yana fadin tunda baku ma san abinda ya kawo ku ba zaku iya fice min daga gida don Allah bana son a shigo ana damuwar mu. Waima yaba su daman shigo min gidane ya fadi tare da mikewa yana fita hanyan waje suma da sauri suka mike zasu tafi nace to Anty uwa na gode da ziyaran da kuka kawo min sai gani na biyu kuma. Ban san ko ina gidan ko kun fitar dani don yarki yar birni zata shigo niko yar kauye ne bankai matsayi zama da su ba. Sai dai zaku ya tafiya da drinks din nace ma yaran tare da nuna masu tire din da suke ciki nace don naku ne ku aka kawo ma kushi daga haka na juya na fara tafiya komawa ciki nan na barsu tsaye da takaici. Suna jin yadda yake ma maigadi fada duk wanda yazo kada ya sake barin shi ya shigo mai gida kai tsaye batare da an bashi umurnin ya bude mai ya shiga ba. Ko ba komai naji dadin yadda uncle yayi masu a raina don da bai dawo ba Allah kadai ya san irin cin fuskan da zasu yi min su tafi sunci bulus. Da ya shigo nan falo ya zauna yana huce har yana fadin zai kori maigadi da sun shigo sunyi wani abu fa may zaice shi. Na dai samu ya sausauta ta hanyar kawo mai ruwa da bashi baki yayi hakkuri ya kurbi ruwan ya dago kai yana fadin kin san ida Allah bai dawo dani yanzu ba iya abinda zasu yi maki. Zan kira in fada ma mijin ta kada ta kara zo min gida may ye hadina da ita da dan uwanta nake da zumunta ba itaba. Ya dafe kai da hannu guda tare da lumshe idanuwan shi don takaicin da ke damun shi lokacin ranan haka ya karasa shi babu wani walwala a tare da shi. Washe gari da muka tashi yana kule dasu a ranshi ya baci da su sosai sai zuwa sha daya saura ya fito falo ya zauna. Na fito da kayan yake farce a hannuna ina son gyarawa sai naji yace da zaki iya dakin fara gyara min nace Uncle ke nan may zai hana in iya aikin lada. A hankali na sauko kasa inda na fara da yanke mai na kafafuwan shi gyara nake mai yana waya sai ajiyan zuciya yake sauke wai. Har na gama gyara mai kafafun shi yana a kan wayan naji yayi sallama da wanda yake wayan daidai zan tashi in koma saman kujera in fara yanke mai na hannuwan shi. Ya kare wayan daidai na dago hannunwan shi zan fara gyarawa yake ce abokina na Canada yana gaida ke ina sa ran zamu tafi nan da wani dan lokaci. Da sauri na kallo shi nace uncle dani fa kace ya dan subbanci kuncina yace ke fa madam nace Allah ya nuna muna lokaci lafiya Amin yace. Ya soma magana kamar mai rada bakinshi a daidai kunne na naga alaman kina farin ciki da tafiyan nan ko ? Nace ai dole uncle don ban taba fita daga cikin kasan nan zuwa wata kasa ba sai wanan karon. Ya fiddo da karamar dariya yana matsa hannun dake cikin hannun shi yace tafiya ai yanzu kika fara shi don tare zamu dinga fita duk inda zan tafi sai dai idan kinyi ciki ya tsufa zan dan baki hutu a lokacin. Da shagwaban murya nace uncle ka bari don Allah ni fa ban shirya haihuwa yanzu ba da sauri ya kalle yace baki da tausayi ne ? Yanzu duk su Aisha suna da yara wanda ada hakan baya damu sai yazo da nayi aure naji nima ina son na shigo gida in samu mai min daddy oyoyo . Shiru nayi ina tunane don nima yanzu haihuwa ne tashin hankalina don wanan ne karo na biyu da yake nuna min yana son haihuwa sosai. Don haka ba abinda zan iya farauta mashi rai da shi a wanan lokaci sai daukan ciki da ya kwallafa rai gare shi. Na nisa ta yadda yake iya jina yace da sauri naga kamar ke abin bai damay ki ba ko nace ba hakana bane Uncle. Haihuwar dai naga baizo inda ake neman shi ba sai wurin da ba a maraba dashi ina tuna haihuwa na na baya ne kawai. Da sauri yace kin taba haihuwa ne a hankali na gyada mashi kai alaman eh naji mamaki da baka san na taba haihuwa ba uncle. Yace ban samu wanda ya fada min ba cikin masu bani labarin ki a hankali na fara bashi labarin haihuwa nawa fuskan shi kawai zaka kalla kaga alaman tausayawa a cikin ta. Shafo fuskana naji yayi gami da lumshe idanuwan shi yana sauke ajiyan zuciya yace haka abin yake ya samu yai sakaci da samun shi. Abin da nake gani ya taba yarinyar don baku amsan treatment a lokacin har yakai abin ya shafi yarinyar a ciki nace uncle sai bayan haihuwar ta nasan cewa ina da cutar a jikina. Koshi sai da yaya Saadu yaga zan halaka ne yasa a kaini asibiti a dubani shine aka san ina dauke da cutan a lokacin don kowa bai kawo haka ba a ranshi. Yace ni kin ga tun da na samira ya baiyana na tafi akaimin awo sai aka samu nima na dauka sai dai nata yafi karfi akan nawa ne. Sun dai cuce mu nace dashi yace sun cuci kan su dan zunubi akan su yake Allah ya gani bata zina muka samay shi ba shine saukin mu ga Allah. Ciwo kuma kaffara ne ga bayin sa kin ga mun samu riba biyu ga abin koma ukku zance idan ba ta sanadin hakan ba ai wata kila ba zamu hadu ba. So ki fitar da zancen cewa sun cuta muna don ni tu lokacin na bar ma Allah sanin sa akai kin ga ta ida ya saka min dashi kuma. Na gama yanke mai akaifar na tatara na zuba a inda muke zubawa kafin mu binne wani akaifa da suma da nake tarawa idan sun cika sai na fita baya can in tona rami in rufe su. Koda na dawo saman kujera two setter na koma na kwanta nayi rigingine ina lallon fankan dake kadawa a hankali falon. Shima dai shiru yayi nasan akwai abinda yake tunane a zuciyar shi wanda kila bai wuce zancen haihuwan da yaji na taba yi ne koma may ye ai bai nuna min komai ba a fili. Sai naji ya jefo min tambaya a bazata dacewa na dauka idan mace ta taba haihuwa ai ana ganewa ne ? Murmushi nayi na dago tare da cewa uncle may kake son ka gane uncle a kai sai ya murmusa kawai yace forget. Nace tau ni dai tun haihuwana yarinyar bata ma sha nono ba don haka har ta koma banda ruwa bata sha wani abuba a duniyan nan. Yace kai labarin akwai ban tausayi wallahi abinda mutane da yawa ke fuskanta ke nan yanzu har bakin ciki ya kashe mutum yanzo idan da za a fadi halin da mutane da yawa ke ciki akan lalurar nan sai ka tausaya masu. Nisawa nayi daga inda nake kwance nace Allah ya sauwa yace amin wayan da aka bugo ne ya dakatar muna da hiran namu nan dai na mike na shiga kitchen ban fito ba don yau yana gida na tsaya hada mashi abinci da zamuci. A kitchen din ya samay ya byo bayana lokacin ina motsa miya sai jin hannayen shi na ji saman jikina ya rugumay ni ta baya yana fadin. Na ga dai baki aminta da aikin John a gidan nan ba yanzu na nisa tare da fadin Uncle da raina da lafiya na zan kwanta kato na yi min girki ina ci. Juyo dani yayi daidai na gama motsa miyan ya juyo dani muna fuskantar juna yace idan aikin namiji ne baki so sai a canza muna da mace dama dauko shi nayi a maaikatar su . Don banda mace a gida ne nace a bani na miji yafi yanzu kuma tunda kin zo da magana sai a bamu mace don gaskiya bazan lamunci kina shiga kitchen wanan jikin naki da nake huta gajiya na a cikin sa ba yana daukan zafi. Kunya maganar ta bani na yi saurin dukar da kaina daga kallon shi yace ai gaskiyana fada nafison ki huta ko yaushe sai idan yara sun zo kuma ki ji da namu lalurar duka. A hankali na dago nace uncle kana ganin hakan ban cutawa shi john din ba dakai naga sabo ya shiga tsakanin ku kama a gaskiya yana jin dadin aiki dakai din. Kada nazo na shiga rayuwan shi in nayi mai haka kamar na toshe mai wurin samun shi ne ai murmushi yayi tare da dan buga mi baya na yace . John zai zauna sai ki sama mai abinyi a gidan kada yayi ta karban kudin banza ko macen kuma za a kawo maki ita goben nan in Allah ya kaimu hakan yayi maki ko. Nace yayi uncle na gode sai dai macen ta kasance musulma uncle don Allah yace kuma dai za a duba ba matsala da haka har na kare na kwashe na koma nayi wanka na shirya na fito muka zauna cin abinci . Ban yi fushi da zarah ba ina dan kula ta muna zama muyi hira sai dai bata gane komai a gidan yadda take so. Ranan yaya Saadu ya shigo da marance bayan na cika mai ciki da abinci nan suka zauna da shi suna fira ganin sun dauko hiran aiki yasa na dan basu wuri na samu zarah a dakin ta kwance. Tana ganina ta mike zaune nace ai na dauka barci kike yi ne tace a a kwantawa dai nayi naga yau yaya yana gida bai fita bane shiyasa ban fito ba. Wuri na samu na zauna kusa da ita ina cewa don yana gida shine baki fita ta dan murmusa tace ban san abinda nayi wa yaya ba baya kallona a yar uwanshi kamar kice yar uwar tawa yanzu don kice kawai may kula ni a gidan. Nace a a zarah kin fi ni sanin waye uncle fa dan a tare kuka taso wuri daya dashi yakamata ace kin san ko waye uncle yanzu. Murmushi tayi kawai mai kama da yake tace nima ina ganin dai gida zan koma nace tun yanzu Zarah mai mukayi maki kuma ? Tace babu komai anty gani dai nayi kamar zaman nawa yana takura maku ne nace ko daya wallahi kece dai kika kasa sakin jikin ki damu. Nan dai na zauna mukai ta hira da ita sai da uncle ya kirani nabar dakin nata yaya Saadu ne zai tafi shine kiran da yake min din. Nan yaya din ke fada min zai koma gobe dawowan da zai yi tare da iyalin shi zai dawo garin naji dadi sosai yake ce min yaya waya gida dazun da yana hanya. Naji dadin haka yace baba ya fada min abin arzikin da maigidan ki yayi masu da sauri na juya na kalli uncle din . Yace tau bai fada maki bane bana baba da ummi zasu sauke farali a kasa mai tsarki har da Sani don ya kula dasu. Bansan lokacin da na juya wurin uncle din ba ina murna yaya yace ai na rigaki yin godiya ko ya fice yana yi min dariya. Ranan ban san ma irin godiyan da zan ma uncle din ba mun dai kwana muna farantawa juna rai kawai don banda abin bashi bayan wanan din. Kwana biyu dayin haka na samu uncle a daki yana shirin fita nake cewa ina son zuwa gidan Anty Aisha. Kamar ba zai yi magana ba sai can yace nafa fada maki ban son yawo a rayuwana nafin inganki a gida kullun. Nace don Allah uncle kayi hakkuri ba dadewa zamuyi ba koshi don munyi waya da itane tace yaran ta biyu ba lafiya. Yace sai ki shirya in sauke ku in zan fita nima in duba yaran daga can naji dadin hakan don dama tana min korafin bai taba zuwa gidan ta ba. Mun isa gidan akai muna iso mun samu maigidan ta dakishiryata zasu fita a lokacin nan dai muka gaisa dasu. Mijin nata yana ta faman kamay kamay da gani baida gaskiya nan suka fice suka barmu da ita munga yaran basu da lafiya har lokacin. Yake tambaya ko an kaisu asibiti tace baban nasu ya sawo masu magani dai tace baida kudin kaisu asibiti sai naga ya tabe baki kawai. Yana bin gidan da kallo bai dade ba yace shi zai tafi zai dawo karfe hudu ya dauke mu naji dadi sosai da zai fita ya kira Aishan suka fita tare. Ta dawo tana murna tana fadin yau maganan hajiya ya tabbata yau yaya ne a gidana Safiya ? Murmushi nayi nace albarkacin yaran ki ne ya kawo shi tace a a albarkavin ki dai gashi har da zama gidana yau safiya abinda kullun gidan nan ake min gori dashi. Nan dai ta shiga bani labari don ta tura zarah tai muna girki haka yasa ta samun daman sakewa tana bani labarin halin da take ciki a gidan. Na fahinci abubuwa da dama a gare ta sai da bance komai ba banda hakkuri da na bata ta fitar da kudi masu yawa tana nuna min wai uncle ne ya bata su takai yara asibiti. Nace kin ga ko sai ki kai su don asan halin da suke ciki tace ai gobe in sha Allahu zan kai su anan dai muka wuni tana cikin farin ciki damu. Ya dawo ya kwashe muka tafi tana ta mashi godiya mun dauki hanya ne naji ya nisa tare da fadin mai kika fahinta a zaman Aisha a gidan nan ? Nace bari mu sauka uncle akwai magana ai sai ya dan kalli zarah dake baya zaune yayi tsaki har muka kai gida ba wanda yayi magana a cikin mu. Sai da mukai sallah ishai muka dawo falo nan na dauko mai maganan Aisha din yace tun farko sai da na fada masu ba mutumin kirki bane suka ji. Alokacin yana sakar masu kudi sun dauka mutumin kwarai ne niko tun tasowan mu dashi nasan dan karya ne sosai. Nace uncle yanzu tunda har akwai haihuwa har uku a tsakanin su baza a bi ta wanan ba taimaka mata ko masu su duka ya kamata kayi. Ta hanyar sama masu sanaa da zasu dogara dashi da yaran su don na fahinci tana cikin wani hali a gida don baka ga part din kishiyar taba tsan wallahi amma ita ga nata kamar na wata tsohuwa can. Tsaki yayi yace ko an bata wanan mugun mijin ai ba zai bar mata ba nace uncle adai tamaka mata din yafi don gorin da suke mata a kan ka. Yace gori fa ? Shi har yana da bakin da zai min gori akai wanda kulun yana office dina da bukatar shi nace kagani shike morar ka itako bata kosan anyi ba. Yace zai kira Aishan idan yaranta suji sauki ansan abinda za ayi mata din nace uncle mun gode wallahi. Kallo na yayi yace wai ke a ina kika koyo wanan godiyar taki ce haka tun bakiga may zanyi ba kina zabga min godiya haka. Nace koma may zakayi indai ka gyara mata wurin zamanta ka bata abinda kudi zai dinga shigo mata ai ka gama mata komai. Yace ai ido nasaka masu daga su har hajiyan don naga gidun su nace uncle kayi kuskure wallahi idan basu dadi a wurin ka ba duniya wurin wa zasu ji. Nan dai nayi ta kawo mashi musalai iri iri yana saurare na bai yi magana nasan dai ya gamsu da bayani na ne da nakeyi. Yace wai ke indan da kin yi karatu mai zurfi zan iya dake kuwa Safiya ? Nace uncle don may ba zaka iya dani ba ai fahinta daban fannin aure daban don haka karkaji komai a kaina . ZAINAB IDRIS MAKAWA SEENABU 8/18/20, 10:16 PM - Ummi Tandama: BAHAGGON, , , , , , , , , 🧕🏿5️⃣9️⃣🧕🏿 NOVEL DIN NAN NA KUDI NE IDAN KIN FITAR UBANGIJI YABI MIN HAKKINA A KAN KI/KA DON BAN YAFE BA, , , , Kamar yadda yaya Saadu ya fada haka ne ya faru don yayo kaura daga kalaba zuwa abuja da iyalin shi inda suka zo da yar uwan Samira da mijinta ya rasu zata dan kwana biyu a wurin su. Sai bayan kwana biyu suka zo gidan mu don bamu da wani nisa sosai dasu dasu ban san da zuwan su ranan ba sai ganin su nayi kawai a gidan. Sun shigo ina daki Zarah ce tazo tana fada min zuwan su cewa tayi nayi baki suna falo azatona ko anty uwace suka sake dawowa gidan. Amma kuma sai nayi tunanen mai zai kawo su kuma in ba rashin zuciya ba yadda aka kwasa dasu din nan ya nuna shi sam bai san su ba. Wanda kuma nasan yayi hakane don ya kakabe su daga gidan namu gaba daya da zuwa don zuwan nasu babu alheri a cikin sa. Fitowa nayi sai mukayi arba da sister kamar yadda suke kiran safiya karama dashi. Nace Lah bakin kalaba ne a gidan namu baku tsaya munzo taron ku ba har kun tula min nauyi na aka ? Samira tace a, a mun huttar dake aikin san ke amarya ce ba a matsamaki yanzu na samu wuri na zauna ina mikawa sister hannu tazo wuri na sai yarinyar ta make hannun ta bata zuwa. Gaisawa mukayi ina tambayan su mutanen gida da sauran yan uwanta tare da fadin ai na dauka zaku zo min da mummy ne wallahi. Tace mun so mu zo da ita kodan azumi dake tafe takine sai da gabaya zata biyo mu in dan ta shirya. Nace kai mummy ho har wanu shiri zata yi kuma makin ta biyo ku kawai kuzo tare samira ne tace wai Safiya kin ko ga yadda kika canza gaba daya. Nace kai samira dashi kuma zaki tare ni tace wallahi safiya kin canza gaba daya komai naki ya canza kamar ba Safiyan yaya saadu ba. Dariya muka ka kwashe dashi gaba dayan mu falon nace aikin Uncle tace aina gani wallahi gaskiya aure ya karbe ki sosai wallahi. Nayi murmushi dadi har cikin rai na nace bakomai bane Samira sai kwanciyan hankalin da na samu yanzu. Nura na kira sabuwar mai aikina yar kabilar yarbawa ce ita ta shigo nake cewa ta kawo ma bakina abin sha ta kuma hada abinci dasu don da mu zasu wuni. Samira ne ta dakatar da ita da cewa wallahi a koshe muke don bamu dade da karyawa ba muka fito gidan. Gaba daya Samira sai yabawa da yadda aure ya sake ni take yi nan take fada min ai jiya yayan ki yayi waya gida ashe ita yar uwar ki ta haihu ne kuma mijin yaki aurar ta ? Nace wallahi ai yanzu takai wata biyu da haihuwa kyale dan iska so yake sai anbiyu mai ta bayan gida akan zancen zaimai da hankali ayi. Tace ai naji yayan ki na fadin karshen mako zai tafi abinda ya hana Sani zuwa kenan cikin satin nan yace ya jirashi sai ya zo. Nace kai mutane sai sannu baison ta yayi mata ciki dan iska kawai tace ai haka yayan ku ya fada shima yace dole ya aure ta don bai baro garin nan sai an daura auren su. Nace haka yagi wallahi don idan anyi mai sakwa sakwa tsarewa zai yi ya barta da yaron tana wallaha ita kadai. Tace ga uwar su wata kala ita kuma naji sani ya bugo ma yayan ku waya yana fada mashi rashin mutuncin da tayi ma mama ranan. Nace kai inna ai sai a hankali ta tare da fadin akan makkan da su baba zasu tafi ne wai mama na maula gashi an biya wa mahaifiyar ki anbarta nan. Wanan matar ai halin ta sai ita Samira ni ban taba ganin mace irin ta ba wallahi diyan ta tun suna bayan ta har sun gaji sun gane ta yanzu. Tace wai itama ko yadda minjin nan naki ya rike Sani bata ko jin kunya ta rage wani abin amma sam bata san wanan nace wa inna aima yanzu ta rage wani abu don baba ya fita bayan ta yanzu. Nan dai muke ta hira har muka shiga hiran gidan su yaya Saadu take fada min kwanaki sun tafi gaida gwago sun samu jikin yaya Ahmed yayi mai tsanani yana kwance yana jiya a gida. Allah ya bashi lafiya nace da ita don dan uwana ne ko banja Allah ya isa ba Allah zai isar min da cin amanan zumuci da suka. Murmushi nayi ina tambayan wai su habiba fa ko sun yi aure ne yanzu tace ke dai bari sadiya ce kadai a gida wai ita habiban ta tare gidan wani saurayin ta. Sadiyan ce ta bugo waya kwanaki tana fada ma yayan yace zai zo har muka taho kuma bai je ba ko ta dawo gida ban sani ba. Sadiya din ai da tace wai zata biyo mu ta dawo nan shine yaki yarda yace ta zauna ta kula da uwa don yanzu ba wani karfi ne gare ta ba. Nifa Safiya ba wani shiri nake yi da mutanen nan ba tun zuwan da nayi na farko uwar da habiba ke cewa wai ya auro masu kwatakwalin ghana. Na lah kece wai kwatakwalin ghana tace wallahi ko ai nace masu ni uwana da ubana yan katsina ne aiki dai ya kaimu kalaba baba kuma yayi ritaya bai koma gida damu ba amma har yanzu muna zuwa garin mu. Dariya nayi kawai ina tunanen rayuwan da ya wuce baya irin cin fuskan da gwago da habiba suke min sai sadiya ce mai kula ni a garin da ban san kowa ba. Su kuma sauran mazan biyu yanzu duk sun kama gaban su kowa ya watse dama haihuwan bariki ke nan. Mun dade muna hira sai da muka mike zuwa sallah muka dawo muka zauna cin abinci tare muka gyara gidan dasu kafin su wuce sai yamma yaya Saadu yazo ya kwashe su. Kafin su tafi mun dan tsaya da yaya saadu munyi magana akan matsalar saadatu dashi in da nace kafin ya wuce gida ya biyo ta wurin tukun. Mukai sallama suka tafi lokacin shima mai gidan ya dawo wurin aiki ya samay su a gidan mintsila naji yakai min gefe na na dafe wurin da sauri ina kallon shi. Yace yau don kin ga yan uwanki shine ko hugging ban dan samu ba nace afuwan yallabai kasan dan uwa aikwai dadi wallahi. Ya riko min hannu muka shiga ciki yana fadin tafiyan mu fa yana matsowa don haka nake son muje ai maki pasphot din ki. Naji dadi nace uncle ashe da gaske kakeyi batun tafiyan dani zaka tafi kai ya gyada min tare da fadin kin dauka wasa nake yi baza mu dawo ba sai mun tsaya umura daga don watan azumi da zai kama. Don ni ban azumi a kasan nan a can saudiya nake azumina don haka nake son mu samu lokaci muyi list din mutanen da za a taimakawa. Nisawa nayi alokacin da muka iso wurin kujerun falon tare da zaunawa sama har lokacin bai sake min hannu ba. Nace uncle, , in uncle dama akan maganan su Aisha ne har yanzu naji shiru akan zancen shine nake maka tuni na fada tare da dukar da kaina kasa. Tallabo habana yayi yana fadin ban manta ba ai akwai abinda nake shiryawa a kan su su ukun duka har ma da sauran yan nasu. Sai dai da farko tunda kin matsa sai ku shiga da ita Niima house decoretion ku zabi abinda ya dace da ita sai a gyara mata part din nata ni inda mijin zai yarda sai in bata gidan da zata zauna da ga ita sai yaranta kawai. Dadin maganan shi naji kamar yan uwa na za aiwa hakan sai nakai mashi runguma tare da bashi kiss gefen fuskan shi. Murmushi ya sauke yace ashe kin iya nokewa kawai kikeyi yanzu da nayi maganan masoyiyar ki aikin bani ba tare da na nema ba. Nan dai muka zauna har lokacin sallah yayi muka mike zuwa sallah ina maijin dadi sosai a raina bayan na idar da sallah ne na jawo wayana dake jone a caji ina kiran Aisha din. Ta dauka tana fadin matar yaya dazun fa nake maganan ki a raina nace na zama yar halas ke na kin ki ambato tayi dariya kawai. Nace kin samay tace a a matar yaya sai kin fada nan dai na kora mata albishir din dayayi mata akan gyaran wurin ta da kuma zancen mijin ta ko zai yarda a bata wurin zama ta zauna daga ita sai yaran ta kawai. Tace cikin sauke ajiyan zuciya wallahi da yaya yaimin haka da ya kyauta min wallahi ni ko bai yarda ba komawa zan yi idan ya bani wurin zama. Nace ki dai lalabashi ko zai yarda da hakan tace wallahi ba wanda yasan halin da nake ciki a gidan nan ne da yaya ba zai fadi haka. Daga maigidan har abokiyar zaman nawa hakkuri kawai nakeyi a zaman mu don dai kada in koma gida ne aimun dariya da kuma yara da suke samun karatu a nan. Nan dai mukayi ta hira tana fada min irin kuntatawan da suke fuskanta ita da yaran ta a gidan wurin kishiyar ta da mijin ta. Shigowan shi dakin nawa ne ya katse muna hiran mu sai da ya zauna bayan mun gama wayan naji yana tambayana ke da wakuke wayane haka tun dazun. Nace anty Aishan kace yace ok nan dai nake fada mai halin da take fuskanta a gidan har na gama baiyi magana ba dama kuma ni ban tsanmaci yayi din ba yana dai iya bani lokaci wurin saurare na. Da safe Aisha tayi sakkon samun shi gida kafin ya fita nan dai na basu wuri suka kebe da dan uwan nata karshe dai da ya fita na shigo na samu tana share hawaye. Ruwa na koma na dauko mata na kawo mata ina fadin tasha ko zataji sanyi take ce ai bata ko karya ba ta fito Nura na kira nace ta hada masu breakfast a daning. Sai da taci ta koshi har yaran nace Anty Aisha kiyi hakkuri don Allah komai na duniya mai wucewa ne ga bawa. Tace matan yaya ban san abinda yasa yaya ya kasa fahinta na ba har yanzu maganan shi guda koda yaushe akan miji nima inda nasan haka tun farko aida ban aure shi ba. Hakkuri nake ta ba ta tare da fadin ki shirya driver zai dawo ya kaimu mu duba kayan yanzu na juya wurin yaranta ina tambayar su ko sun koshi. Kada kai sukayi alaman sun koshi din nace to ku tashi kutafi wurin anty Zarah tana dakin ta kuyi mata fira sai lokacin take cewa zarah na gidan nan ne ? Nace tana nan dakin ta bata fito bane sai bayan fitan yaran ne na samu magana da ita inda mukayi magana na fahinta nake kara bata hakkuri tabar bari yaran suna jin damuwan ta da mijin nata ko yaushe. A karshe dai driver yazo na muka fita gidan bayan na rufe ko ina na gidan Nura kawai muka bari a gidan tana aikinta. Mun tafi wurin mun kuma duba suna da kaya sosai a wurin mun zabi mai kyau cikin mafi tsada da daraja har labulen da za a saka mun zaba bayan mun gama muka kirashi mukai mai bayani. Yace mu bashi shugaban wurin suyi magana dashi nan na bashi matar sukai magana ta fada mai kudin kayan sun tasan ma milayan daya da dari biyar yace ta bashi account din su. Mun dawo gida a gajiye don dan zakayawan da mukayi a wurin akarshe falo muka zube duk mun kwaso gaji a tare damu sai Nura ce ta kawo muna ruwa da abinsha muka dan sha ga abinci ta gama mukaci muka tafi sallah. Aisha ganin abin takeyi kamar a mafalki sai maganan takeyi duk zaman da mukayi daki na bude mata don ta shiga da yaranta su huta a ciki inda nima na wuce nawa dakin don yin sallah. Bayan na idar da sallah na zauna ina tunanen ratuwan Uncle da yan uwanshi na rasa gane may ye matsalan shi da su haka. Gashi ni yana iya yiwa yan uwa na dama wasu lalura ba tare da jin kyashin komai ba a ranshi amma nasa kafin yayi sai ya ja masu rai zaiyi. Koma may watarana tunda ina cikin su zan ji ko may ye matsala da inda abin nasu ya samo asalin faruwa. Ita ko Aisha tana shiga dakin dana bude masu wanda yake gyare komai akwai a cikin sa gashi kuma kullun a gyare yake duk da ba kowa a dakunan. Wayan ta tadauko a cikin jakkan ta ida ta kira mahaifiyar ta bayan sun gaisa take cewa hajiya maganan ki ya fara tabbata gaskiya. Yau yaya yasa mun fita da matar shi muje in zabi kayan dakin da nake so a wani shago nan dai take fada mata duk yadda akayi a wurin da kuma fadan da yayi mata kafin ya fita. Murmushi mahaifiyar tayi tace kamar yadda nake fada maku wanan yarinyar zata zamay muna alheri a cikin mu sannu a hankali zamu samu ta canza muna shi amma fa sai kin bita a sannu komai zai daidaita. A hankali tace kwarai hajiya aina ga alaman hakan tun yanzu gashi yaya har da zuwa gida na yayi ta dalilin ta nan dai take fada mata son canza mata wurin zaman da yake son yi ma,ana ya raba masu gida da kishiyar ta. Wanan maganan mahaifiyar taji dadin din shi sosai inda tace Allah yasa Aisha su kuma Allah ya saka masu da alherin sa. Ki barshi da mijin naki ai kar tasan kar shi da shi, shi yasan ta inda zai fito mashi da maganan a tsakanin su har ya yarda da maganan a saukake. Bayan la,asar muka fito nan falo muka zauna muna hira sai gashi ya dawo gidan yaranta dake waje suna wasa ya shigo dasu rike a hannun shi. Sannu da zuwa mukeyi mashi amma hankalinshi na ga hiran da yaran suke yi mashi sai dai da kai yake iya amsa muna gaisuwan da muke yi mashi. Ina zaune rakube ina kallon yadda yakewa yaran tausayi ya bani don nasan yadda yake tsananin son haihuwa a wanan lokacin. Ido na zuba masu sosai daga inda nake zaune tashin hankali na da uncle yanzu shine haihu wata shidda kenan cur a gidan shi ba bu wani labari ciki a gare ni shiko yanzu ba abinda zai farauta mashi rai kamar ya ganni da ciki. Nace oh safiya wai haihuwa bai zuwa a inda ake neman sa ne ga gidan Ahmed da bai son haihuwan a can Allah ya bani gashi a gidan uncle wanda yasan daraja da kimar haihuwa shiru kake ji. Jin yana magana dani yasani dawowa cikin hayaci inda yake fadin may yasa baku sayo wa boy abinda yake so kuka sayawa amira ? Murmushi nayi tare da sauke ajiyan zuciya nace uncle rabuda boy din nan rikici yake ji dai shifa yace a saya masu wanan din da yake ma fushi tun dazu bayan an sayo kuma wai shi bai so a canza mai. Ya rugumo yaron zuwa jikin shi yana fadin kyalesu zamu fita in sayo maka wanda kake so yanzu barin in ci abinci sai mu fita dakai bada su Amira ba. Abinci na gabatar mashi da kaina ya zauna tare da yaran sukaci suna ta zuba mai surutu har suka gama suka fice gidan shida yaran. Aisha ta kalle ni tace ashe yaya yana so yara haka wallahi ban taba sanin yana kula yara ba ke kuma gaki shiru har yanzu babu labari kodai kina planning ne safiya. Ajiyan zuciya na sauke nace nawa na aje da zanyi planning anty wallahi nima nasan haihuwa yake so Allah dai ne bai kawo ba har yanzu. Take cewa ki dinga shan miyan kuka tun da safe haka ma idan zaki kwanta barci in Allah ya nufa zaki iya samu da wuri ki haihu. Nace aiki na gode kice in samo kuka ke nan in dinga sha don nasan idan hakkurin uncle ya kure zai kai ga yi min magana nima kuma ina son in ga na haihu wallahi na kare ina lumshe idanuwa na. Sai dare ya dawo da yaran idan kafin ya dawo ya kira wayana in fada mata ta shirya gashi nan zuwa zai maida ta gida na fada mata tare da hada mata tsaraba ya iso bai ko shigo ba muka fita . Inda muka samay shi da yaran a mota nan mukayi sallama suka wuce gidan Aishan dashi koda ya je gidan bai shiga sai cewa yayi ta sallamo mashi maigidan nata. Tana shiga shiko ya hau ya zugo a wurin kishiyar ta tana sa kafa tana fadin gidan uban wa kuka tafi har dare haka uban wa zai dafa maki abincin dare a gidan. Sai dai ku kwana da yunwa ke da yaranki don ba zan bata kudina wurin sayen wani abu don ku ci. Shi mai kudin gidan naku da baida moriya kije ya baki abinda zakuci da diyan naki kishiryarta na zaune gefe da diyan ta suna shan cornflake tace ta aje jaka a gida mana to ban dafa ba in an dawo acine. Wani kallo tayi masu tace kaje yana waje yana sallama da kai yace wa cikin zaro idanuwan shi tace yaya Sulaiman da sauri ya zura sillifas din shi a kafa ya fice a hanya ya hadu da yaron gidan yana shigo da manyan kwalayen da ya sayo masu tsaraba wanda dagani har Aishan bamu san ya saye ba. Kishiyar kuma baki ya mutu ganin kwalayen da ake shigowa dasu gidan ana dire su kofan Aisha din wani irin kishi ne ya kamata a lokacin. Ya fita sun gana dashi ban san yadda sukayi ba dai da mijin Aishan can ya dawo ciki bayan sun dauki lokaci da uncle a waje yana cewa boy yau uncle ya kaiku shopping ne haka ? Yana ta faman washe baki namiji dama baida kunya nan yabar kishiryar zaune tana kallon mamaki shine har da yiwa yara wasa a lokacin. Uncle bai dawo ba sai tara da rabi ya shigo da ledan kajin da ya sayo wanka ya shiga sai bayan ya fito wankan ya fito falo yana fadin in bude mai kajin su zai iyaci kawai yau. ZAINAB IDRIS MAKAWA SEENABU 8/21/20, 6:24 AM - Ummi Tandama: BAHAGGON, , , , , , , , , 🧕🏿6️⃣0️⃣🧕🏿 NOVEL DINA NA KUDI NE IDAN KIN FITAR MIN KO KA FITAR MIN BAN YAFE MAKU BA UBANGIJI YABIN HAKKINA AKAN KU DA DUK WANDA YA KARANTA BAI BIYA BA. Satii biyu ya rage mu daga zuwa kasar Canada wanda yai dai dai da kwanan kin azumi baifi kwana goma ba tsaka ni. Zaune yake a saman gadon ya mai da hankali ga laptop din shi daya tasa a gaban shi ya mai da hankalin shi gaba daya akan abinda yake yi din. Dakin na shigo dauke da abinda ya sa in dafa mashi na nauin samun lafiyan maza na shigo dakin dakin da sallama na. Har na isa saman dan katamin table din dake dakin na aje tire din da ke dauke a hannu na da kayan shaye shaye irin na maza mai kara masu lafiya karfi. Bayan ma aje na samu wuri na zauna a kusa dashi ina fadin uncle ga yanan na gama hada maka idon shi na akan laptop din shi nima dai ba wai shi nake kallo ba ko da na zauna hankalina yana ga wani takarda da na gani saman gadon shi a lokacin. Amma wanan kamar wurin da muka sayo ma Anty Aisha kaya mana, nake cewa dashi cikin dan, kallon fuskan shi dake duke saman laptop din. Bai ce komai ba sai ci gaba da abinda yake yi yana murmushi nagama kallon takardan na aje inda na ganshi tunfarko tare da mikewa zan bar dakin . Da sauri ya dan riko min hannaye na yana fadin ki dan dakata min in gama please komawa nayi na zauna tare da dan kai kafaduna saman gadon nayi rigingine. Bai dade ba naji ya sauke ajiyan zuciya ya juyo yana dubana tare da kokarin rufe laptop din da yake aiki a cikin sa . May zaki yi yanzu idan kin fita, yace dani, sai tambayan nashi ya bani mamaki sai dai ban kai karshen tunane ba naji yace dani zuba min ruwan maganin na. Na dago a hankali zuwa gaban dan table din na fara tsiyaya mai ruwan ganyen maganin da ya sa na dafa mai. Muryan shi naji tana cewa yanzu yaya zamuyi da mutane ga tafiya a gaban mu kafin azumi wanda ba zamu dawo ba sai bayan sallah insha Allah kin ga ban gida za ai azumi da sallah ke nan. Juyowa nayi gare shi dauke da cup ina mika mai nace hakane Uncle a yadda kace za ai tafiyan ya amshi ruwan maganin dake tiriri a cup ya dan kurba yaji da saura zafi. Ya dago ya kalle ni nace da sauran zafi ko kai ya gyada min amsa nayi nadan kada spoon a ciki ina dan motsawa a hankali yana zaune ya mayar da hannuwan sa baya ya tokare a saman gado. Ya kura min ida baya ko kiftawa na dago kai ina cewa dashi sai dan ban san abinda kake shirin yi wa mutane ba kan azumin da sallah. Yace in banda abinki yanzu ai wanan a cikin aikin ki yake ni dai kawai idan kin tsara sai ki sanar dani komai ake ciki da can madam maimuna ce take tsara min komai indan lokaci yayi. Na ce a raina akwai aiki gaba na ashe don ban san komai a yadda take shirin ta amma dai ba matsala zan yi iya kokarina yadda ya dace. Mika mashi cup din ruwan maganin nayi ya karba ya kafa kai bai cire ba sai da ya kurbe duk ruwan maganin a lokaci guda. Ya kare yana ya mutsa fuska da alama bai da dadin sha ya dauki ruwa kadan mara sanyi ya dan kora a cikin shi. Gauron numfashi na sauke ina fadin wai wanan maganin may ye haka kake sha kwanan nan yace ba matsalan ki ba ne yanzu. Mikewa yayi tsaye yana fadin ke nake saurare yanzu don bani son a makara zan baki list din last year don ki san mutanen da ake aikawa . Wurin wani dan drower dake dakin ya nufa yana tono list din ya juyo yana fadin sai dai ta wajen baba can gida ban san wa yanda kike so aiwa sadakan acan. At list mutane hamsi maza nake son a raba ma abinci da mata hamsin suma a basu abin azumi dana sallah haka nakeyi duk shekara daga riban da nake samu na wurin masana,antan taya na. Duk bayanin da yake min bai dago kai ya kalle ni ba sai da yake miko min takardan ne ya kare da fadin ki duba idan an samu kari sai a kara dasu. Ni zan fita dama maganin nan ya tsayar dani yau akwai aiki a gaba ina son in kammala komai a yanda nake so shi a cikin satin nan. Namike tare da daukar mai jakkan aikin shi yana gaba ina binshi baya har muka isa haraban aje motocin gidan bai dauki driver ba shida kan sa ya tuka motar ya fita. Nayi ajiyan zuciya na juya zuwa cikin gidan zuciyana fam da tunanen nauyin da ya dora min akai yau a gidan. Dakina na wuce sai da na kara yin wanka na gyara jikina na dawo na zauna na fara tunane gashi yana jaddada min kada nayi mashi delay a tsarin ni yanzu ta ina zan fara ne. Anty Aisha ne ta fado min a rai da sauri na jawo wayana ina kiranta har kiran ya katse na sake danna kiran sai nayi sa a ta dauka. Mungaisa tare da tambayanta yara da gida ta amsa da suna lafiya kafin ta fadi wani abu nace Anty Aisha ki taimake ni don Allah banda wani mafita yanzu sai gare ki. Tana dariya tace niko matar yaya mai zan taimaka maki dashine haka a rayuwana nace bari kedai yayan kine ya dora min nauyin rabon kayan azumi da na sallah bana. Dariya naji ta kwashe dashi tare da fadin Allah mun gode da ka nuna muna wanan ranan don wanan magana kika tayar min da hankalina da farko. Ai wanan abin farin ciki a gare ki don dama matar yaya na can lagos ne take yo mashi sayayyan sai abinda muka gani zata bamu. Nace to yanzu yaya zamuyi don kawai mu kawar da zancen anty da take son daukowa nan dai tayi min bayanin abinda suka samu last time sai na kwatanta na gani idan nabi list din zasu samu abinda yafi haka. Godiya nayi mata ba tare da na tsaya sauraranta ba tace wai ko kin san kokarin da yayana yayi min na maganan canza gida nan take kora min bayanin abinda ya kasance tsakanin shi da maigidan ta. Tace yanzu tunda aka fara zancen ba zaman lafiya tsakanin shi da kishiryar ta kullun fitina suke kwasa a tsakanin su ita yanzu ta matsu ta tashi ta bar mata gidan ta koma gidan ta. Nace kin ga haka yafi aiyafi ance kazantar daba kagani ba sunanta tsabata shi takewa bakin ciki yanzu true colour din ta zai fita a tsakanin su. Kin ga sai yasan halin ta na gaskiya shi take ma gudu dama tace gata ragguwa ko jikin ta bata iya gyarawa balle na diyanta. Mun dai dauki lokaci muna magana akan gidan mijin nata a karshe mukayi sallama nan ta barni ina tunane ai ita tasan tana da kishiya ke nan ni yanzu ban san idan na dosa don wanan nauyin da ya dora min zai iya saka wani sabon tsana tsakanina da anty kuma. Kamar yadda yace duk cikin kwana kin nan abinda muke fita ke nan yi daga sayan kayan masrufi zuwa tufafi da kayan tea da sauran su . Ga kuma shirin komawan Aisha sabon gidan ta a wani sati da muke yi a makon nan muka shiga bauchi inda na samu taro na mutunci a wurin yan uwan Uncle da mahaifiyar shi don yanzu Aisha ta gama shigar dani a gare su ko. Saida mukayi sallah muka shiga wurin hsjiya baaba don mu gaida ita tana zaune cikin kamala duk muka zube kasa a gaban ta . Da fara,ata take muna sannu da zuwa da yaya hanya daga nan kuma suka fara dan hira da danta a cikin hiran ne yake mata bayanin tafiyan da zamuyi. Wanda yasa muka zo kawo masu abin sallah dana azumi kafin mu wuce din tayi farin ciki da jin haka tace babana kokai fa abinda nake fada ma ke nan da dadewa cewa samun mace ta gari zai iya canza maka rayuwanka. Yanzu gashi tun ba a je ko ina ba abubuwa suna canzawa sannu a hankali a wajen ka wanda wanan kokari ba kowane ya kawo shi ba sai ke mai sunan gwago na. Na dago kai na dan kalle ta cikin mutunci da nuna alkunya gare ta tace eh a dalilin ki na samu farin ciki da hadin kan diya na da yan uwan uban su suka watsa min kawunan su a baya saboda son zuciya. Yau gashi babana dake zaman yaya kuma uba a gare su ya dawo ya rugumi yan uwan shi da hannu bibiyu abinda na dade ina fatsn gani a gare su. Yau ko wacen su tana farin ciki a dakin auren ta ta sanadin ki kin saka ya sauya masu rayuwan su na kunci don dan abinda suka gada a wurin mahaifisu dama yan uwa sun ciyen shi kaf gare su basu barsu da komai a hannun su ba. Fatana gare ku yanzu shine Allah ya baku zuria masu albarka nima in ga jikokina ta wurin babana in runguma in goya kamar yadda ko wace uwa ke burin gani a rayuwan ta. Kaina na dukar kasa don kunyan abinda ta fada a karshe sun dauko maganan da ya shafi gida don haka na zamay jiki zuwa inda kaunar shi take wacce baaba ke riko a gidan a wurinta nake jin ashe ya gyara ma sauran sisters din shi dakunan su a nan garin kamar yadda ya gyarawa Aisha nata. Naji dadin jin wanan labarin da ta bani nan muka zauna ina fahintar wani abu a cikin hiran ta sai da zai fita ne hajiyan ta kirani na fito muka tafi. Muna shiga part din mu na kai mashi runguma ya juyo yana kallona da mamaki nace Uncle naji abin alherin da kayiwa su anty suwaiba unangiji ya saka da alheri ya kara budi. Murmushi yayi ya kamoni zuwa jikin shi tare da subbatan goshina sai ya soma magana kamar mai rada bakin shi a daidai kunne na yace ba wanan godiyan nake so ba kin dai ji abinda baaba tai muna addua a kai. Kunya ne ya kamani na kara shigewa cikin jikin shi sosai ina dariya don kunya ina fadin insha Allah soon. Ya jawo ni ya kara matseni sosai yana fadin da kyau bari ma yanzu mu fara gwada sa,ar mu mu gani ko zamu dace dariya ya bani da haka muka kwanta barci don muna da gajiya dama. Washe gari muka tashi da aikin rabon kaya wa yan uwa da abokan arziki don motar kaya ta isa da daddare sosai ne. Saboda hakan ne muka bari sai da safe banga zarah ba tun jiyan da muka iso tana gidan iyayyen ta tunda muka zo. Saida muka share kwana uku muna abu guda ana hudu ne muka dawo abuja sai dai uncle ya hanani zuwa gida in kai wa mutanen gida abinda ya saya masu da kaina a cewar shi sai mun dawo zamu tafi gaida su. Yaya Sani aka kira nayi mashi bayanin komai da wayan da zai ba na hada dashi da kayan suka tafi nan muka fara shirin tafiya wanda ni ta fanni na ba wani shirin da nayi don a shirye din nake dama. Ina murnan tafiya sai ga shi yana fada min gidan anty zamu sauka indan mun tashi daga nan abinda ya sani cikin damuwa ke nan kuma. Shiko naga ko a jikin shi bai damu ba kamar ba wani abinda ya faru tsakanin mu tun farko da ita sai ni ya bari da tarin damuwa a zuciyana. Ana gobe zamu tafi ne dadare muna zaune falo yake cewa dani wai may ke damun ki ne kwanan nan naga kin shiga damuwa ? Gwauro numfashi na sauke tare da kakaro murmushin dole a fuska na nace babu komai may kaga ? Ya tsuramin ido kafin yace dani tun fa ranan da mukayi magana dake na sheda maki lagos zamu fara tsaya muyi kwana biyu naga kin ta da hankalin ki a gidan nan. Ajiyan zuciya nayi wanda ya baiyana a fili nace uncle bawai nadamu bane kawai dai ina tunanen yadda zan hada fuskana da ita ne bayan abinda ya faru a tsakanin mu din. Murmushi yayi ya kamo ni zuwa jikin shi yace kin san ko muna waya da ita a yan kwanakin nan kuma ni bata nuna min komai akan abinda ya faru din. A raina nace kaika ai ba zata gwada ma komai ba nice dai matsala dama a tsakanin ku ji nayi yace dani kin dai san ba zan taba barin ta muzanta baki ba kina a maysayin mata ko ? Nace amma uncle abinne da nauyi wallahi yadda anty ta rike ni ace haka ya kasance a tsakanin mu aikasan da nauyi wallahi. Yace koma dai may ne yanzu sai ki bari idan mun je ayita ta kare yafi wanan boye boye da kike yi mata kamar mara gaskiya a tsakanin ku. In ke kina da laifi ai itama tafiki laifi a wanan magana don ko dani dake itace ta hada mu don may daga baya zata kawo wani zance kuma. Haka dai yayi ta karfafa min gwaiwa har na danji raina ya dan sake koma may nene gara dai ayita ta kare ma nace a zuciyata. Washe gari yan uwa da abokan arziki sukayi ta zuwa sallaman mu yaya don sai da yamma ne zamu tashi. Yaya saadu da anty Aisha kusan anan suka wuni damu shiga na alfarma nay duk da ba wasu kaya na kwasa ba ga tafiyan. Mun sauka lagos da karfe shida da wani abu hotel muka wuce bamu tafi gidan ba a ranan anan hotel din muka tsaya. Washe gari ma da yafita bai dawo banan ya barni ina ta barci abina hankali kwance sai bayan karfe biyu ya dawo yai wanka ya ci abinci yake fada min in shirya muje mugaida anty din da mijin ta. Kayan da Anty Aisha ta zabar min don in sa idan zamu gidan na saka wani lace ne da suka sayo dubai lokacin da suka tafi sayayyan auren mu da ita shine na saka. Sai sarkan gwalal da zaikai kimanin kudin nigeria milayan daya da dan kai wanda shi yafi tsada a cikin kayan da suka sayo da wasu takalma masu dan hill da duwatsu masu kyan sin shiga da lace din sune a kafana da jakkan su. Na gama tsab ban san yana zaune yana kallona ba sai da na gama shiri na na dago zan yi mashi magana na samu ya kafa min idanuwan shi a kaina. Murmushi nayi ina isowa wurin shi da sauri yace ashe matar tawa ta iya shiga ne haka ban sani ba. Yace ai wanan shiga zaki sa yau madam ta rude tace koba safiyan ta bane da ta ke dauka yar kauye bata dace dani ba. Ya miko min hannu a haka muka fito zuwa lifter muka sauka kasa inda muka shiga mota muka kama hanya. Ko a hanyama sai faman zolayata yake yi wai zan hana shi tuki da kamshin turaren da na sa a jikina yace turaren yana da dadi shi nake son ki dinga amfani dashi ko yaushe. Mun isa gidan musalin karfe hudu na marance lokacin na tabbatar da daddy yana gida don motar shi da nagani a waje abinda ya sani sauke ajiyan zuciya ke nan don nasan ko maue zai zo muna da sauki tunda yana gida. A tare muka fito zuwa cikin gidan inda ya danna bell din shiga cikin gidan ba ajima ba na jiyo tafiyan mutum xuwa bude muna kofan nace ko yaushe suka fara rufe kofa haka kuma. Zuciyana sai duka yake uku uku fargaba da tsoro suka mamaye min zuciya a lokaci daya sai dai hakan bai hanani yin addua a bakina ba. ZAINAB IDRIS MAKAWA SEENABU 8/22/20, 5:53 AM - Ummi Tandama: BAHAGGON, , , , , , , , , , 🧕🏿6️⃣1️⃣🧕🏿 NOVEL DIN NAN NA KUDI NE DON ALLAH KADA KI KARANTA IDAN BAKI BIYA BA YAR UWA DON ALLAH ZAI SAKA MIN A KAN KI, , , , A hankali kofan ya bude shike gaba ina daga bayan shi cikin fargaban ko wa zai bude kofan a lokacin gabana sai danka yake uku uku. Muryan Faiza ce naji tana fadin a yaya sannu da zuwa ya amsa mata kamar yadda yake amsa muna a can baya idan muna gaida shi a gidan idan ya shigo. Fara takawa yayi don shiga gidan na bishi a baya wanda sai lokacin Faiza ta ganni taa sake dan ihu da karfi sai kuma taja bakin ta har da rikewa tace ashe tare kuke cikin washe baki tana nuna farin ciki da gani na a lokacin. Gaba dayan su har daddy suna falo zaune a lokacin da twins din ta Fati ce kawai bata cikin su jin muryan shi da twins sukayi yasa suka mike gaba dayan su suka nufashi da murnan su. Suna gani na kuma sai suka barshi suka nufoni tare da fadin anty safiya oyo,yo duk suka fada min a jikina nima rungumo yaran nayi zuwa jikina cikin shaukin junan mu da andade ba a hadu ba. Daddy ke fadin kar ku karya mummy naku mana wurin murna lokacin shi har ya kai inda suke zaune yana kokarin zama. Dayar tace anty safiya shine kika gudu kika barmu muna ta kewan ki kin dawo ke nan inji dayar take tambayana cikin kallon fuska na. Nace na dawo yan biyu ba gani kin ganni ba ba na fadi ina kara rungumay su a jikina cikin jin dadin ganin su da nayi yau. Mummy ga anty Safiya ta zo suke cewa uwar tasu data mayar da hankalinta ga uncle suna gaisa wa dashi bayan ya zauna. Tace da yaran naga safiya kuda kuke kewanta sai ku tare ta nidai ba wurina tazo ba sai in wurin ku tazo hakan yasa na karasa gurin ina fadin haba anty kiyi hakkuri mana. Dariya daddy yayi yace kin ji tun ba a kai ko ina ba ma ta baki hakkuri na karaso ina durkusawa a gaban su tare da gaishe su. Daddy ya amsa min cikin daddin rai da sakin fuska yace yau yar gidan antyn ta ne gidan namu nayi dariya ina noke kaina a tsakiyan kafafuwa na don kunya. Na dago kaina cikin kunya ina gaida ita ta amsa min ba wani walwala a fuskan ta da cewa lafiya lau yaya gida. Uncle ya maiyar da bayan shi a makariyan kujeran da yake zaune yana fadin yau dai ga kaunar ki nan na kawo maki don damuna da take yawan yi akan ki. Murmushi tayi tace aikuwa ga Safiya na gani a gabana yau ga kuma uncle nidai kaina na duke sai da daddy yace tashi mana ki zauna saman kujera Safiya nace a kunyace daddy nan ma yayi mun ai. Na kara dukar da kaina kasa nace daddy nan ma yayi min a lokacin ne faiza ta iso wurin dauke da tire da abin sha a sama. Ta dire a gaban mu tana cewa yau ga amarya a gidan mu anty ta ce ga fa amarya da akai muna rowan buki a gidan tazo Daddy yace aure yayi kyau dukkan su sai wani sheki suke yi da annuri tace sulaiman ba amma itakan ai auren ma rama ya sakata yi. Murmushi uncle yayi don yasan gatse tayi min kawai da wata manufa ta fadi maganan ta ya mika hannu ya dauki goran ruwan yana ballewa tare da kafa bakin shi akai bayan ya goge bakin goran da hannun shi. Ga ruwan nan tace dani cikin rashin fuska a gare ta na dan dago kaina nace da ita na koshi sai dai anjima tace yayi sai ta juya ga uncle din sukaci gaba da magana dash. Nan su yan biyu suka shiga hira dani ina dan basu amsa a hankali tana kallona ta gefen ido tana mamaki a ranta yadda na juye kamar bani bace a lokaci guda. Kayan dake jikina kawai ma abin kallo da yadda na tsara kwalliya kamar wata balarabiya dani babu inda nake da mukusa a jikina. Ya gyara zama tare da fuskantar anty din bayan ya kai duban shi gare ni yaga yadda nake zaune a takure gashi kuma matar gidan sai basar dani takeyi a wurin. Dan uwan nashi ya fuskanta tare da fadin mu zamu koma yaya dama na kawota ne ta gaishe ku kafin mu tafi da sauri daddy din yace tun yanzu zaku tafi ba a ko gaisa ba. Ido da ido ya kalli anty din yace matar gidan ce naga bata maraba da zuwan mata na gida so ba zan juri ganin wanan a tsakanin su ba. Saboda may daddy yace idan bata mara ba daku ai mu da twins muna maraba daku don wurin mu kuka zo. Yace na dauka abin da ya faru a tsakanin su ya wuce don da nasan har yanzu madam tana rike da ita a zuciyar ta ba zan kawo ta gidan nan ba. A yadda yayi maganan ya nuna ranshi ys baci ga abinda tayi muna ya juya inda nake zaune yana fadin tare da mikewa tsaya yace tashi mu tafi. Dago kai nayi ina kallon shi tare da dan marairaicewa nace Uncle kayi hakkuri ka bari a bata hakkuri ta yafe min. Tare suke hada baki wurin fadin ta yafe maki da kikai mata may zaki ce ta yafe maki inji daddy ya fadi yana mai kura mata ido. Yadda sukai mata yasa taji nauyi da kunya ta fara kamay kamay tana fadin yanzu may nace ina wanan maganan an wuce shi ko. Uncle yace cikin girgiza kai madan bayi expecting din haka daga wajen ki ba don kece ki ka nuna mun Safiya a gidan nan duk abinda mukayi mun yi biyayya ne bisa umurnin ki. Banji dadin yadda haka ya kasance a tsakanin ku ba a sanadiya na na dauka kin fahinci ni kowaye zuwa yanzu ni mutum ne da ban magana biyu a rayuwana. Don , , , , daddy ne ya katse uncle da fadin ya isa haka please sulaiman dauki matar ka katafi Allah ya tsare Allah ya baku zaman lafiya. Sulaiman don Allah kuyi hakkuri da kai da Safiya in Allah ya yarda haka ba zai sake faruwa ba ta fadi tana duban sulaiman din. Daddy ya rausaya kai yana nuna ma uncle kujera ya zauna lokacin ne su twins ke cewa in tashi in zo inga gadon da daddy ya sake masu a dakin su. Dole na tashi na bisu dakin nasu nan suka samu daman sakewa inda daddy yai mutaukar nuna mata bacin rai ga yadda ta tare ni. Har yake cewa bata san Allah ne ya rufa mata asiri da anty uwa da Uncle ya yarda da auren diyar anty Uwa da kashinta ya bushe. Karshe tace amma anan zaka barta sai dare ka dawo daukanta don karkace ban kula maka mata don naga tun yanzu ka nuna min matarka kake so dani. Dariya suka kwashe yace ba dole ba ai safiya ta yi don yarinyar ce data san kanta wurin komai na rayuwa ya fadi hakane don ta san bada wasa yakeyi mata ba. Ta mike tana fadin barin rafi wurin Safiyan in barku kar kuma nayi wani laifi ga mai gidan again nan ta mike ta barsu da dan uwan nashi. Muna daki da yaranta sai gata ta shigo dakin kallon da take min yasa na dukar da kai cikin fargaban abinda zata fada min din. Sai da ta samu wuri tavzauna take ce min Safiya kin san baki kyauta min ba don kin yaudare da sauri na dago ina kallon ta don jin kalman yaudarar da ta kiramin din. Tace kin san kun shirya komai da Sulaiman kika boye min hakan sai jin zance buki kawai nayi gun mutane amma ke baki sanar min ba. Nace anty bansan da auren nan ba ba fada maki tun farko daga zuwa tambaya aka daura muna aure dashi. Nakiraki kuma in maki bayani baki saurare ni ba a lokacin kin dauki zafi dani, duk yadda na so ki fahince ni kin ki saurararona a lokacin. Tace ai dole a daura maki aure daga zuwa tambaya tunda kuna matse ku samay shi kada ya kubce maku a hannu. Naji wani zafi a raina nace haka ne anty don masu son su samay shi a lokacin muna da yawa da yake Allah yayi nice matar ai an daura dani ba shiri. Kallo na tayi kamar zata yi magana sai kuma tayi shiru kawai ta murmusa a ranta tace eh lalai kin zama matan manya a yanzu safiya . Amma a fili sai tace dani yaya zaman ku da yan uwan sulaiman din yake yanzu na gyara zama nace da ita lafiya kalau muke satin da ya wuce ma muna bauchi din mun tafi sallaman su kuma ya kai masu kayan azumi da na sallah. Da sauri ta kallo ni tace what har sulaiman yayi rabon kayan azumi da sallah banda labari wa ya saka ya dauko mashi kayan da ya raba bana. Nace yan uwanshi yaba nauyin yin hakan don sune sukayi rabon da muka je acan shiru tayi na dan lokaci sai tace zan ganshi inji yadda akayi hakan ya faru. Nan dai muka zauna wanda duk hiran namu bugun cikina take yi amma sai in nuna mata ban san komai ba a kai har ya turo yan biyu kirana wai zamu tafi. Tare muka fito da ita daga dakin take cewa dani kin dai san namiji ba ai mashi farar daya don haka duk abinda kike samu sai ki turo ai maki tanadin shi yafi. Nace to anty insha Allah zan dinga turowa sai dai na fahinci uncle ba irin mazan dake ba mace kudi bane haka na amma yana kashe min kudi ga duk abinda nake so. Tace may ye baki dashi yanzu dole ne kisan yadda zaki juyashi ya dinga sakar maki kudi kina turowa nan ana maki tanadin su. Ina gyara gyale nace insha Allahu anty duk abinda nake samu zan dinga turowa gare ki da zaran na samu tace koke fa haka yasa muka fito muna dariya sau mazan suka dauka mun shirya a tsakanin mu ne. Daddy ne ya nuna ma uncle din mu yace gani ba dama nace ma ai sun fi kusa kaga kamar ba yanzu muka shirya su ba. Nan dai muka samay su tana kara jaddada min karfa ki manta da sakona nace in sha Allahu anty. Gaban daddy nazo na durkusa gaban daddy tare da sunkuyar da kaina ina fadin daddy zamu tafi yace ubangiji ya kaiku lafiya ku dawo lafiya safiya ayi ta hakkuri shi zaman aure dan hakkuri ne. Har waje suka rakomu muka wuce suna daga muna hannu sai da muka bar area din na sauke ajiyan zuciya a fili. Uncle yace dani yanzu dai hankalin ki ya kwanta kun shirya da anty ki ko nace ai hakan yafi don da ba haka ba bazan taba samun kwanciyar hankali ba a raina. Amma cikin zuciyana kuma tunanen anty din nake yi ashe dai duk rayuwan mutun sai mutane sun gane halin shi na banza mutum dai dan tara yake bai cika goma ba wallahi. Nan dai muka isa masaukin mu kowa da abinda yake sakawa a zuciyar shi a lokacin bayan munyi sallah mukaci abinci bamu dade ba muka shiga barci. Tashin asuba zamuyi don hakane muka kwanta da wuri shiya tadamu mukayi wanka karfe biyar a airport yayi muna mun gama komai kafin shidda muna cikin jirgin da zai daga. Na dauka zuwa Canada wasa ne ashe ba karamin tafiya bane nan na jinjina ma uncle da bai jin wutan tafiye tafiyen da yake yawan yi ko yaushe sai da muka kwana washe gari muka sauka canada din. Inda abokin shi yazo ta tare mu wani dan gida madaidaici ya kaimu nikan ban boye kauyancina sai kallon abin mamaki nakeyi a garin. . Wanka mukayi da sallah sai abincin da mukaci nan muka kwanta ranan duk kwakwan uncle sai da ya barni shima barci yake yi sosai. Sai wani lokaci muka tashi ko shi zuwan wanan abokin nashi da iyalinshi yasa mu tashi barci don sun kawo muna abinci irin namu na bakaken fata. Matar shi tana gani na tashiga yaba tana fadin lalai Uncle bakayi ruwan idon banza ba wirin zaben mace haka maikyau ga tsari ga hankali. Mijin yace na gaya maki ai mutumin nawa ruwan idon shi da dalili ya tsaya yin shi nan dai sukayi muna fatan alheri basu wani dade ba sukayi muna sallama suka tafi. Kwana biyu uncle baya fita ko ina muna gida acewan shi yanzu ne yake more amatcin shi dariya nayi nace wani amarci ya saura amarya wata shidda a dakin ta kuma. Yace ai wuyan aiki ba a fara ba don ni so nake kafin mu bar nan din sai kin samo ma hajiya baaba dan jikan da tace tana son dauka nawa. Daya fara fita ko saida na raina kaina naji dama ya barni a gida ne yafi don ko yaya muna dan hira da zara ko Nuratu mai aikin mu. Amma nan haka zan wuni sai kallo sai ko kwanciya ban tsinana komai a rayuwa tunda safe in yafita sai dare sosai yake dawowa gidan. Haka kuma idan gari ya waye zai sa kafa ya fice gidan sai kuma dare kwana zai dawo duk suna wurin harkan kasuwancin su. A kasan muka fara azumi duk da ba musulmi a kasan sai jefi jefi wani lokaci zai dawo gida da wuri tunda azumi ya fara. Mukan dan fita idan ya dawo da wuri yadan nuna min garin mu dan yi sayayya mu dawo gida bai kara fita sai kuma gobe. Ranan ya dawo gida da wuri ya shigo da sallaman shi da gani a gajiye ya shigo gidan don yanayin shi kawai zai nuna hakan. Kwance nake saman carpet ban ko iya daga kai in mashi sannu da dawo ba a lokacin don tun cikin dare nake jin jiki kuma ga azumi a bakina. Ya cire takalmanshi akofa kamar yadda mukeyi acan tare da rataye rigar sanyin da ya dora saman kayan jikin shi. Ya tako har inda nake tare da sunkuyowa gaba yana fadin madam yau lafiya kike kuwa da kyat na iya dago kai na dan dube shi da idanuwa na da sukayi min ja saboda wahala. Na mayar dakai na kasa ina wani irin numfashin wahala nace da kyat uncle sannu da dawowa. Kasa yakai zaune a inda nake don ya tabbatar da ba lafiya nake ba a lokacin zama yayi saman carpet din tare da dan tallabo kaina yana fadin may ke damun ki ne haka ? Na runtse idanuwa tare da cije baki na nace uncle banda lafiya ne tun da dare nake jin zazzabi yana damuna sai kuma amai ya biyo baya bayan fitar ka gidan. Dan taba jikina ya shiga yi yazo daidai wuyana yaji yadda jikina yayi zafi ya gashe sosai a lokacin yace shine baki kirani ba ana wasa da ciwo ne komai karantar shi akace maki. Ya ce ki tashi muje asibiti yanzu a duba ki ansan abinda za a baki na cije baki nace uncle bari in ansha ruwa mu tafi don yanzu ina dauke da azumi. Ya katse ni da cewa wani azumi kina haraswa haka sai ya mike tea mai zafi ya shiga ya hado min ya dawo inda nake yana min sannu ya mikar dani ya matsa min sai da na sha ina runtse idanuwa don ba dadin tea din nakeji ba. Ina sha yana min sannu da fadin dan kara dai ko kadan ne na cije baki na kara amsar cup din ina kurbawa da gudu na mike zuwa bandaki sai da na amaye shi kaf na samu saida a raina. Yana tsaye a bayana yana min sannu na dago cikin cije baki ina maida numfashina dakyat ya rungumoni muka dawo falo daki ya shiga ya dauko min hajjab dina na sa. Sai faman cije baki nake yi haka ya kamani zuwa waje inda muka shiga motar da yake amfani dashi a kasar wani asibiti mukaje. Nan ya yaki kati inda babu dadewa suka shiga yimin gwaje gwajen su na likitoci tare da yan tambayoyi. A karshe da result ya fito likitan yayi mashi albishir ina dauke da juna biyu na wata biyu a jikina hakan ya nuna tun a gida nageria nike dauke da cikin a jikina bamu sani ba. Tun fitowan mu yake faman washe baki shi yana jin wani irin dadi a ranshi yana yi yana dan kamoni tare da fadin Allah ya karba adduan mu dana hajiya baaba. Ni dai ban iya ce mashi komai ba har muka shigo gida har na haye kujera na kara lafewa kafin ya shigo yakkule ko ina na gidan haka yasa na fahinci bai kara fita ko ina ke nan ranan. ZAINAB IDRIS MAKAWA SEENABU 8/23/20, 5:39 AM - Ummi Tandama: BAHAGGON, , , , , , , 🧕🏿6️⃣2️⃣🧕🏿 NOVEL DIN NAN NA KUDI NE DON ALLAH KADA KI KARANTA IDAN BAKI BIYA BA YAR UWA IDAN KUMA KIN FITAR MIN DASHI UBANGIJI ZAI SAKA MIN A KANKI KAN NOVEL. Ina kwance na saman kujera na dunkule a ciki naji ya sauke min kiss a goshina yana fadin Alhamdullahi kinga Allah ya amsa muna adduan mu yanzu ni na gama aikina saura naki. Da sauri na bude idanuwa na dake lumshe na sauke su gareshi acikin sanyayyar murya nace dashi. Uncle kada ka zamo mara tausayi mana kana nufin yanzu aikin nawa ne ni kadai kai ka gama naka ke nan ? Ya mike ya samu wuri ya zauna yana fadin eh to ai gaskiya na fada don nayi yadda duk wani kosashen namiji ya kamata yayi dasa ciki a jikin mace. Kin ga yanzu ke kuma sai kiji da amai da daukan nauyin ciki amma kada ki damu zandan rika taya daukan shi ta hanyan rage maki jin nauyin shi a jikin ki. Sai idan haihuwan yazo kuma ai tare zamuyi labour dake ba inda zan fita ranan hararan shi nayi sai muka kwashe da dariya kuma. Nace ashe kai har wahala kayi wurin dasa vikin a jikina yace ba kadan ba ai nayi kokari sosai wallahi yanzu jina nake wasai don na fara sauke nauyi na. Murmushi nayi mai ina gyara kwanciya ban san lokacin da barci mai nauyi ya dauke ni ina dan tunane daga inda nake kwance. Ban falka daga barcin ba shikuma bai tadani ba sai karfe takwas na dare lokavin yana zaune yana buda baki a falon kusa dani. Jin motsin da nayi yasa shi dago idanuwan shi ya dube ni ganin shi nayi zaune yana yana buda baki da sauri na mike ina fadin anyi sallah ne Uncle ? Yayi murmushi yana fadin kin falka yays jikin nace da sauki tare da sauko da kafafuwana kasan kujera da nake sama. Yun kurawa nayi don in tashi zuwa sallah sai na gaza tashi wani irin jiri ya dauke ni da sauri ya mike ya taso zuwa inda nake yana fadin yi a hankali fa. Kin san ba ke saya kike ba yanzu dole kibi sannu don Allah zama yayi saman kujeran tare da riko min hanaye na ya mayar dani ya kwantar yana fadin sannu bari ya dan sake ki sai ki tashi. Na dan dade kwance a wurin sai da naji jirin ya sake ni na mike na shiga dakin kwanan mu wanka nayi don nauyin da jikina yayi a lokacin ko zai sake. Na fito na tada sallah bayan na idar na dade a wurin zaune ina mika godiyana ga Allah tare da fatan Allah ya bani mai albarka. Ina nike abin sallah nawa sai gashi ya shigo dakin dauke da abinci a hannun shi wanda noddle ne ya dafa a lokacin yake shan ruwa dashi kallo daya nayiwa abincin naji wani amai yazo min a bakina. Da sauri na juya tare da boye fuskana ga ganin abincin dake gaba na tashi na shiga ban daki banyi komai ba na fito. Yana zaune bakin gado yake fadin abincin bai maki bane kuma na cewa ban dai jin cin shi ne a raina kawai. To may zaki ci ya tambaye ni nace zan dai ci fruits in na samu falo ya koma ya debo min fruits mai yawa zai juya sai gani na fito falon na karbi plate din a hannun shi da sauri na koma saman kujera na zauna. A hankali nake taunan apple dana fara dauka naji yayi min dadi a baki na muna hira ina cin abina sai gashi na cin fruits din sosai. Naji yace a lissafi na cikin nan tun kan mu tafi bauchi gaida hajiya kika samay shi idanuwa na na lumshe kawai tare da daukan dan annibi in jefa a bakina. Tun wanan lokacin na ke samun wani kula na mussanman daga wurin uncle din nawa ciki kuma na bunkasa acikin koshin lafiya da samun kulawa a jikina. Don ban damu da cin abinci ba saidai bani wasa da cin diyan itatuwa dama gashi akwaishi kasan da muke kamar banza. Tun Uncle na fadan rashin cin abinci ya gaji ya kyale ni tunda yaga diyan iccen kawai zanci ya zauna lafiya a cikina abincin da raina ke so babu shi a kasan. Alhdullahi uncle ya gama abinda ya kawo shi kasan kai ya kammala sunyi nasaran shiga da kayan su daga nageria sun kuma juya su sun zama kudi sun saro abinda suke so a can sun tura nigeria din. Saura sati daya mu bar kasan zuwa kasa mai tsarki ya dauke ni mukaje shopping din kayan baby acewar shi yana da wuya ya samu dawowa kasan kafin in haihu. Mun dawo a gajiye gida ba abinda nake so kamar indan watsa ruwa lokacin sai in dan kwanta kuma don in huta saboda naci gaba da azumi da na samu sauki. Bayan na fito daga wanka falo na dawo inda yake zaune yana wani lissafi a cikin laptop din shi a lokacin. Kujera na samu na zauna ina kokarin kwanta a lokacin sai ga kiran Faiza ya shigo min na dauka da sauri muka shiga gaisawa da ita din. Yana zaune yana jin hiran mu take fada min wai ashe haka mukayi ma anty bana na hana uncle ya bata rabon kaya wa yan uwa sai ni na raba. Nan dai take fada min irin zagin da nake sha gun anty yana jin mu sai murmushi yake yi kawai yana ci gaba da aikin shi mukayi sallama na dago ina sauke ajiyan zuciya. Tare da fadin nikan na shigesu ga anty wai sai yaushe ne wanan abin zai kare a tsakanin mu ne wai ? Bata tare da ya kalli inda nake yana aikin shi yace sai ranan da zaki bar mata mijin ki ta aura ma wacce take son ta aura min din. Nace zan dai bita a hankali in gani ko zamu kawo karshen matsalan amma zancen in bar mata mijina ai ko a mafalki bata raya haka gare ni yanzu. Ina wurin kwance har lokacin shan ruwa yayi na mike jiki a sabule na har hada muna komai anan mukayi buda baki shine yake bamu sallah kullun dani da shi. Mun idar muka zauna cin abinci kowa yayi shiru sai cin diyan icce na nakeyi hankali kwance naji yace dani zanso kafin mu bar kasan nan mu koma asibiti su baki don kin san asibitin irin ta masu lalurar mune zallah a wurin. Da sauri na dago kai na dan kalle shi nace uncle kana nufin duk mutanen da na gani a wurin suna da cutar dake karya garkuwan jiki a tare dasu. Yace ai kin san kasan nan mafiyawan su kasan baki ne don haka kowa ke abinda ya ga dama a kasan shiyasa har suka kai ga bude asibiti irin haka. A hankali na shiga tunane a raina don zama da uncle yasa yanzu har sai in manta cewa muna dauke da matsala a jikin. Tuno abinda zan haifa nayi ko in haifi mai lafiya ko kuma kasin hakan Allah kadai ya sani banyi aune ba naji idona yana fitar da hawaye tausayin kan mu da abinda zamu haifa din ya kamani a lokaci guda. Dago kai yayi ya dan kalle ko ban fada ba yasan abinda nakewa kuka a lokacin don yasan tunane na idan ya nufa. Ji nayi yace dani kiyi hakkuri madam ni kaina wanan tunanen kanzo min a rai har a baya nikan raya ba zan yi aure ba balle har in haihu in mutu in bar yara a cikin maraicin iyayyen su. Amma da na natsu sai naga ai Allah mai kashewa kima shine mai rayawa ga masu lafiya suna mutuwa subar marasa lafiyan abin daga hannun Allah yake don haka sai na barwa ubangiji sanin sa. Haduwa ta dake kuma sai kika kara mantar dani daga damuwan da nake ciki a baya don haka yanzu na ragumi kaddaran da ubangiji ya jarabi rayuwan mu dashi a duniya. Ga komai na rayuwa ubangiji ya hore ma rayuwan mu dashi amma sai dai muna rayuwan ne cikin BAHAGON RAYUWA. Domin bamu san yadda abin zai kasance damu ba a karshe sai dai muyi fatan gamawa da duniya lafiya don wanan rayuwan yishi kawai ake a bahagon yanayi. Nado kai a hankali muka kalli juna sai naji so da kaunar shi da tausayin mu ya dira min a zuciyana. Nace Uncle mu namu kaddaran ke nan yazo muna a haka sai muyi fatan samun mai lafiya mutaima mu bashi tarbiya mai inganci koda bayan mu bazai samu matsalan rayuwa ba. Naji ya riko min hannuwana da na sake fruit din da nake sha a hankali yana dan murzawa yace Safiya har kullun addua na shine mu samu zurian da zamu bari a duniya ko bayan mu zamu samu masu muna addua da tunamu a matsayin iyayye a gare su. Addua na yanzu shine Allah ya sauke ki lafiya ina mai tabbatar maki bayan haihuwan ki zaku samu kullan yadda ya dace a gare ni. Don a lokacin zan tabbatar maku dani din zsn zamay muna jigon rayuwa da ko bayan raina zakuyi alfari da samu na a tare daku. Nayi murmushi tare da fadin insha Allahu a tare zamu raka da junan mu har diyan da zamu haifa din yace tau Allah ya bamu rai da lafiya din nace amin da sauri don yadda ya karasa maganan shi akwai tarin damuwa a zuciyar shi sosai. Nayi ajiyan zuciya tare da kokarin hada kayan da mukaci abinci ina gyara wurin ina gamawa na shiga wanka don a gajiye nake lokacin. Bayan shima ya fito wankan ne ina zaune bakin gado na mayar da hankalina sosoi a wayana ina duban sakon nin dana samu ranan. Yafito daga wankan yake cewa dani ya kamata dai tunda anji sauki kuma sai in samu tukwaici haka horon yayi yawa mana madam ya iso gare ni yana kokarin taba min , , , . Da sauri na manna mashi cizo daidai kunnen shi cikin rashin damuwa sai dai kokuwan da muka fara yana sai ya rama a lokacin na shiga rokon shi sai kirjina yake hari wai anan zai rama cizon shi na fara tsala mai ihu bai sa ya sake ni ba. Sai dariya da yake kwasa yana fadin sai ya rama cizon shi anan din saman kirji dole na kyaleshi yayi abinda yake so din. Washe gari muka tafi asibitin kamar yadda yace munga likita yakuma dora mu a maganin da zanyi amfani dashi da kuma yadda zan kare lafiyana dana jariri har reno da komai sai da yayi muna bayani yadda ya dace. Yaje ya sayo maganin masu inganci da amfani wanda bazamu samu a gida nigeria ba sai a nan din ko wata kasa da taci gaba sosai a duniya. Mun hada komai na ranan thursday muka tashi da dare zuwa saudiya inda zamu yadda zango a wata kasa kafin mu isa can din. Sai dai duk wani sayaya da mukayi a canada ya tura gida Nigeria za a tafi muna dashi a cikin sabin kayan da zasu tura can. Mun sauka a birnin madina direct inda already an sama muna masauki inda zamu zauna wanka kawai mukayi muka isa masallacin fiyayyen halita muka mika gaisuwan mu gare shi bamu dawo masaukin mu ba sai da mukayi sallah ishai acan muna ta rokon Allah saukin alamura. Kwanan mu takwas a madina muka wuce birnin makka mukayi umurah sai mu muka shiga zama ko yaushe a massalaci barci ne kawai ke kaimu masaukin mu. Ban taba sanin haka uncle keda yawan ibada ba sai wanan tafiyan namu don duk da yasan ina cikin lalura hakan bai sa mun dan huta ba sai dai ko yaushe yana kara min karfin gwiwa da fadin in dai jajirce in matsa mu samu wanan falalan. Cikin ikon Allah Allah ya bani lafiya sosai dana samu kwarin yin abinda ya kaimu kasan mai tsarki ranan da aka sha ruwa washegari muka fara shirin komawa gida . Ban samu zuwa sayayya ba shida wani abokin shi da matar shi suka tafi sun ko sayo muna kaya masu kyau koni naje da kaina iyakar abinda zan sayowa kaina ke nan. Jirgin mu ya sauka lafiya a Abuja inda su yaya saadu suka zo taron mu da dawo kallo daya mutum zai min ya fahinci na samu sauyin rayuwana. Na murje na zama wata katuwa na kara girma da cika ta ko wani sassan jikina haskena na asali ya fito sosai a jikina. Rigar dake jikina ya biye cikin jikina sai may kaifin tunane ne zai gane hakan gare ni da sauri amma wanda bai san ciki ba sai yace na samu lafiya ne kawai. Na dan jirkita don zaman jirgin da nayi don haka hutu kawai nake bukata a lokacin don tafiyan dare mukayi muka iso da safe. Don haka muna shiga gida sallah na gabatar sai na samu wuri na kwanta sai barci da zazzabi mai karfi ya rufe ni ga samira da su Aisha duk gidan amma ban samu zama dasu ba a ranan. Sunzo sun fahinci banda lafiya haka yasa jikin su yayi sanyi sai kuma aka shiga yi min sannu ina dunkule a cikin bargo shi yashi ya bani magani na sai barci ya dauke ni. Ni dai har suka watse gidan ban sani sai mummy maman samira da yarta aka barmin so zauna dani a gidan sai da nayi kwana biyu sannan na samu zazzabin ya sauka min. Na fito falo da yamma na zauna don jikin nawa ya dan kara sake min sosai ya shigo gidan anan ya samay mu zaune muna dan hira jefi jefi dasu. Zama yayi a kusa dani yana gaida mummy da gida sai ya juya inda nake yana fadin jiki ya jikin madam ? A hankali irin mutum ya tashi ciwo yadda yake ji nace mai naji sauki tare da lumshe idanuwana a hankali. Mummy dake gefena zaune ta nisa tare da fadin amma sai ina ganin kamar wanan madam din ta samu karuwa ne don tun ranan da kuka dawo nake ganin haka a gareta. Uncle yayi saurin dago kai ya kalleni na dukar da kaina kasa yace mummy na magana dake fa. Nace aiba dani take magana ba dariya yayi ya gyara zaman shi yana fuskantar mummy din sai dai ina ga in jikin bai bari ba zuwa gobe sai mu koma asibiti. Da sauri nace mashi ai naji sauki ba gashi na fito ba yace kin ci abinci nace kai nake jira ka aika a sayo min fruit in sha. Mummy tayi saurin cewa bana fada maka ba wanan ciwon nata da walaki a cikin sa mutum yace baicin komai sai diyan icce kawai yake dura ma cikin shi. Ya dan kalle ni yayi murmushi yace mummy ko acan shine kawai abincin ta duk abinda taci sai ta amaye shi shi kadai take ci a zauna lafiya. Mummy ta sake cewa ai duk wanda yasan ciki ya kalli Safiya yasan tana da ciki ubangiji ya raba ku lafiya yaba rayayye mai albarka ya amsa da amin da sauri. Mikewa yayi yana fadin barin in sa a sayo maki yanzu ki samu kisha ko jikin zai kara sakewa yace mummy dai ta gano abinda kike boye masu. Murmushi nayi kawai idan yaso wasa sai ya juye kamar ba shi ba a gidan amma indan yan kai na saman kan shi zaifi sati daya yana dunkulan baki rai bai magana da kowa bayan gaisuwa. Ni yanzu na saba da halin shi don haka duk irin yadda ya juya nasan yadda zan bi dashi a zauna lafiya masan mun dawo gida yanzu halin zai tashi mai. Don a can ko yayi fushin bai jimawa yana yi zai sake mu koma daidai amma da zaran naga ya fara daure fuska nima sai in kama kaina dashi. Washe gari ne mukayi baki daga bauchi inda yan uwanshi ne mata zallah hajiya baaba taba mota wai su zo su dubani su kuma ga sauksn mu. Basu fada muna suna tafe ba sai ganin su mukayi Allah ya taimake ni mummy na gidan kafin wani lokaci tayi masu abinci mafi sauki don har Nura ta tafiko yamma yayi. Dole na mike haka na ba dadi jikin nawa muka shiga hidimar baki a gidan ya dawo ya samay su don sun fita da yaya Saadu a lokacin . Yayi murnan ganin su sai dai tunda suka gaisa ya shige dakin shi bai sake fitowa ba sai da naji shi shiru ne na leka shi dakin nashi. Na samu ya fito wanka yana saye da jallabiya a jikin shi haka yasa na gane zai fita sallah ne a lokacin yana gani na yace ashe baki gare ki haka gidan ? Murmushi nayi don jin abinda ya fadi nace wallahi aisun yi kokari da suka zo dubamu don basu taba zuwa ba sai wanan karon. Gashi kuma naji suna fadin wai gobe zasu koma baaba tace dasu lalai su dawo a gobe din yace kai haba ai ta bari su dan kwana biyu dai. Nace to sai kayi masu magana ai suma zasu so hakan wallahi don akwai gajiya a jikim su. Tare muka fito ya wuce massalaci nikuma na koma daki na don inyi shirin alwala sai da na bi ta wurin su naga basu bukatan komai na wuce bayan sun dan jani da wasa irin ta kannen miji da akeyi. Naji dadin kansan cewar mummy a gidan don tana da matukar kokari sosai bata jin nauyin jikin ta ko kadan kamar ba ita ta haifi Samira ba, don samira bata kaita kiza kiza ba. Bayan na idar da sallah nan dai na dan kai kwance don yanayin jikin nawa da bai gama sake ni a lokacin wanda nasan gajiyan aikin da mukayi ya dan tambaye ni da zaman jirgi. Yar uwa riban da kike samu wurin fitar da novel dina sai ki shirya dake da masu karatun novel din sata don taki ta samay ki a rayuwa muje zuwa in dai kin ce wasa da kallaman Allah kike yi . ZAINAB IDRIS MAKAWA SEENABU 8/25/20, 10:38 PM - Ummi Tandama: BAHAGGON, , , , , , , , , , , , 🧕🏿6️⃣4️⃣🧕🏿 NOVEL DINA NA KUDI NE IDAN KIN FITAR ALLAH ZAI FITAR MIN DA HAKKINA AKAN KI IDAN KUMA KIN KARANTA KI SAN HAKKINA NA KAN KI. Yar uwa na fadi zan sake fada ban yafe ba idan kin fitar min da novel waje Allah yabi min hakkina akan ki don bayan yafe ba. Idan kin karanta min novel baki biya ba ubangiji ya kwato min hakkina a gunki cikin gagawa. Bakin mu sun tafi cikin dadin rai muka rabu dasu lafiya suna ta farin alherin da dan uwan su yai masu da zasu tafi koni nayi mamaki don a yanda uncle yake bakacewa yana da tarin arziki irin haka a rayuwan shi. Kyaunta yamun dadi har cikin raina don yadda ya dauko yiwa yan uwa alheri ba karamin alheri bane agare ni don na fita zargi daga bakuna su. Yadda nake jin suna zagin anty kan ta kakace komai da karshe akaina zagin zai dawo sai gashi ya sauya gaba daya wanda suke ganin wai nice na sauya shi hakan. Ko yan uwana bai bari ba don kullun aiken shi na hanya zuwa wirin yan uwana da iyayyena sai dai inji sun bugo waya suna min godiya abinda ya aika masu din. Gashi dana fara mai godiya zai daga min hannu alaman ya isa haka na sai da yayi dana gode mai bani fasawa. Ba abinda ke mun dadi kamar yadda mahaifan mu ke sa mashi albarka har nima abin ya shafe ni don da hajiya baaba da babana ida sun fara mai addua idan ina kusa sai na lumshe idona don jin dadi. Sai dai halin shi na fushi yanzu ya rage don baya wuce kwana daya yana fushi dani ko don cikin dake jikina ne yake raga min ban sani ba. Don Uncle akwaishi da saurin fushi abinda baka dauka abin fada ba yanzu zakaji ya juye ya koma fada gare shi. Sanin halin shi da nayi yanzu na gane bai son kana magana yana yi sai in ja bakina inyi shiru sai ya gaji ya kyale don kan shi. Abin da kan yawan hada mu shine fita a dade duk da ba fita nake yi ba don bai bari na mami kowa a garin ba sai yan uwa tsiraru da muke dasu ko nafita sayen wani abu da zaran ya kira nace ban koma gida ba ya ishe shi jidali har wani lokaci. Ya hana mummy komawa gidan yaya Saadu wai ta zauna dani har in kara jin karfin jikina don acewar shi ban gama warwarewa ba har yanzu. Ina jin dadin zaman mummy don mace mai dadin zama ga sa mutum hanyan daya dace yabi na alheri ga kuma bata jin kiuya ko kadan aiki ba sha mata kai ga tsabata gidan nan ko yaushe kwal yake don tsabtan ta. Hakan yasa ya yanke sharan bata albashi duk wata da farko taki karba wai ai an zama daya don yaya saadu yana kokari dasu. Sai uncle yake cewa ta karba ai duk wanda ke karkashin shi haka yake masu shine dalilin karban kudin ta duk wata. Yaya Saadu da matar shi samira sunzo kan hakan da yake yi sai cewa yayi shi in son samune ma mummy ta zauna damu tunda ba komai take yi ba acan. Idan tana son zuwa ganin yaranta ba zai hana ba taje tayi kwanakin da zatayi ta dawo don shi hankalin shi ya kwanta da ita don ko na haihu dole ne ya nemo wanda zai kula da baby din. Yaya Saadu yai mata magana kuma ta amince mashi din da hakan tunda dama zaman hakkuri takeyi can yara kowa ya kama gaban shi. Muna waya da anty don dawowan nan namu na tura mata kudi wanda yake bani duk wata na hada dari biyar na tura mata don dai a zuna lafiya ni da ita don kawai na fitar da komai a ranta mu zauna lafiya. Ranan nasha yabo a gunta take cewa in dan hada da dabara ina rika amsan kudi idan sun taro sai ta san abinda zatayi min dasu nace anty na gode. Wanan yasa ko yaushe yanzu muna waya akai akai da ita ba kamar baya ba can da ta share ni din haka yasa han kalina ya kwanta yanzu don da ina cikin damuwa idan na tuna halin da muke ciki da ita na rashin shi. Yau tun safe uncle bai fito ba yana dakin shi bayan na gama karyawa na nufi dakin shi don in duba shi sai na samu yana rufe yana barci haka yasa nayi zaton hutu yake yi kawai. A hankali na jawo mai kofa na rufe sai naji muryan shi yana kirana don haka na tura kofan na koma ciki karasawa nayi bakin gadon da yake. Murya ta alaman rashin lafiya yake magana da cewa don Allah hado min tea ki kawo min nan zan sha magani da sauri na duka ina fadin Uncle baka da lafiya ne? Kai ya gyada min alaman eh sai nakai hannuna saman laulausar kan shi dako yaushe bai rabuwa da gashi irin na fulani yayi kwance lup a saman kan shi. Zafi naji jikin nashi yayi nace subbahanallahi Uncle kuma kake kwance jiki ba dadi haka a gida gyara kwanciya yayi yace jeki hado min tea din don Allah. Fita nayi da sauri nan dai na hada mai komai na dauka zuwa dakin har lokacin da na dawo dakin yana kwance a yadda na barshi na fita. Bayan na aje ne na dan taba shi ina fadin ga tea din na hado maka Uncle ya dan yi mika tare da bude idanuwan shi ya sauke a kaina. Ina tsaye akan shi cikin damuwa na kura mashi ido sai da ya dan jima ya mike zaune tare don son yunkurawa ya tafi ban daki nasan kewaya yake son yi amma ya kasa. Tsoro naji sosai a lokacin nace in taimaka maka ne ka tashi ya dago kai yadan kallene sai ya girgiza kan shi yace hada min ruwa dai a ban dakin . Na shiga na hada mai na dawo wurin shi har lokacin yana zaune a yadda na barshi hannunwan shi na rike sai ya dafa ni ya tashi tsaye da taimoko na ya je ban dakin ganin ya shiga ya fara tubewa na barshi na fito. Wayana na dauko na kira yaya Saadu nake fada mai yau Uncle ba lafiya da sauri yace gashi nan zuwa yanzu ya dan jima ciki ya fito bai ko tsaya share jikin shi ya dawo saman gadon dana gyara bayan tashin shi. Kurban tea din yayi bai sha wani abu ya koma ya kwanta tare da dan yin nishi nace maganin fa yace barin dan huta zan sha ai. Ina tsaye a kan shi ina kura mai ido idanuwan shi a lumshe ina tunanen lokacin da yaya Ahmed yayi jinya ina gidan shi yadda yayi tayi mun a lokacin da yadda hankalina ya tashi gani ni kadai a gida dagani sai shi haka nayi ta jiyar shi har ya samu lafiya. Nace kilama lokacin duk yana dauke da cutan yake jiya hakana ni ban sani ba saboda kurciya da nake dashi. Wayana yai kara ne yasa nasan yaya Saadu ya iso ke nan da sauri na juya na fita zuwa wurin shi yana tsaye falo ko zama baiyi ba. Ina fitowa ya tare ni yana fadin yana ina nace yana dakin shi bai tsaya ta kaina ba ya nufi dakin nashi da sauri ina biye dashi a baya nima da sauri nake mara mai baya hankali na yayi kololuwar tashi da yadda yake kwance sharaf. Muna isa kofan ya shiga da sallaman shi uncle yana kwance a yadda na barshi ciki jin muryan yaya daji yasa shi dan dagowa kadan yana amsa sallaman da kyat. Yaya ya karasa gun shi yana fadin yallabai yau jikin ba dadi ne haka yadan dago yana dan yake yace Saadu ta taso da kaine kuma ? Yace wallahi fa na kirata mu gaisa sai take fada min jikin naka yau bakajin dadin sa sosai ya dan kara gyarawa yace wallahi ai duk kwanan nan karfin hali nake bana jin dadi. Nabishi da ido da mamaki cike a fuskana sai naji yaya Saadu na tambayan shi ko zasu tafi asibiti ne sai yace kasan matsalan ciwon mu da zaran mutum yayi dan ganganci yanzu ciwon zai bugar dashi ne. Akwai wani yaro dake zuwa nan gida ya kara min ruwa shima yana da irin matsalan tare dashi yana kokarin jawo wayan shi dake karshin filon da yake kwance akai. Yace amma kafin yaron yazo barin in hade magani da zai saukar min da zazzabin don baa shan maganin sai aci abinci sosai. Cikin marairai ce murya nace dashi a kawo ma wani abu kaci ne yanzu kai girgiza min ya bude baki da kyat yana cewa tea dana sha is ok for me. Drower ya nuna min da hannu yace jawo wancan zaki ga wani dogon roba fari ki dauko min na isa wurin da sauri na tare da jawo drower din na dauko mai maganin. Yaya ya karba naje dauko mai goran ruwa mara sanyi ko da na shigo na samu yana kiran mai kara mai ruwa din a wayan shi. Jefi jefi yake jefo ma yaya magana wanda nasan don ya kwantar muna da hankali yake yin haka amma ta yanayin maganan zaka gane yana jin jiki karfin hali ne kawai irin na maza. Doctor ya iso idan ya kira wayan shi yaya saadune ya fita don ya shigo da likitan dakin shi bayan fitan yaya ne ya kalle ni sai yaga ina hawaye a lokacin. May kike ma kuka madam baki son in mutu in barki ne kai na gyada mai tare da fadin don Allah uncle kabar wanan magana haka insha Allah bazaka mutu yanzu ba sai ka tsufa damu . Murmushin karfin hali yayi yace kaiyya ko daina wanan tunanen daga ni har ke ko yaushe mutuwa ai zata riskan mu koda ciwo ko babu ciwo don haka addua kawai ya kamata ki muna shine mafita. Shigowan su yaya Saadu ne dakin da likita wanda yanayin shi ya nuna kamar kabila ne shi yake cewa yaya ga kaunar ka nan kuka takeyi wai bata son in mutu in barta. Murmushi yaya yayi wanda nasan na karfin hali ne shima yace ki kwantar da hankalin ki Safiya in sha Allahu zai ji sauki. Jikin dai ne nashi ya dan motsa mai kin san sha anin yau da kullun dole haka ya kasance ga bawa ko yaya ne don haka ki koma dakin ki kiba likita wuri yayi aikin shi. Dagawa nayi jiki a sabule zan fita a dakin Uncle ya kirani yake cewa don Allah kada ki bugawa kowa waya banda lafiya har Aisha . Kai na gyada mai na fice daga dakin raina ba dadi don duk na tsarace da ciwon nashi wanda dan lokacin kadan duk ya ramay kamar ya dade yana jinya akwance. Ina fito sai ga mummy ganin yanayi yasa take tambayana ko lafiya taga Saadu yazo gidan ya shiga dakin maigida kuma. Nace yau baya jin dadin jikin shi ne shine yaya saadu ya dauko mai likita da sauri tace subbahanallahi da sauki dai ko ? Ta tambaya cikin son karin bayani nace jikin da sauki mummy nan muka zauna tana kwantar min da hankali har likitan ya fito dashi da yaya. Yaya yace in je yana kirana sai dai kafin in isa dakin ya samu barci a lokacin nan dai na zauna wurin shi ina kallon yadda ruwan da ake kara mai yake shiga jikin shi. Yaya Saadu bai dawo wurin shi ba haka yasa na dauka ko ya wuce office din sune ashe yaje ya sawo wani magani ne da fruit da dai wasu abubuwa. Da ido yaya saadu yayi min magana na biyo shi muka fito daga dakin a falo muka tsaya ya juyo yana fuskanta na tare da cewa ki kwantar da hankalin ki. Insha Allahu zai samu lafiya zazzabi ne mai karfi yadan bugeshi kin san mijikin baya hutu sai irin haka ya kasance dashi. Kamata yayi ace ya ware wasu ranaku da zai rika zama gida ya huta don jikin nashi bai maison wahala bane ko kadan don Allah ki san yadda zaki kawo mai wanan shawara nima zanyi nawa kokari inga na fahintar dashi. Nace na gode yaya yace shi zai tafi don suna da aiki akwai kayan da zasu shigo masu daga waje zai je yaga komai ya kammala a wurin. Na sake mai godiya yace ba komai wanan ai duk ya shafe mu har zai tafi sai ya juyo yana fadin don Allah kada a tasheshi idan ba shi ya falka da kansa ba. Mummy tafito jin muryan yaya tana fadin zaka tafi ke nan yace eh zai koma wurin aiki sai dai an jima zai dawo ya duba jikin nashi. Bayan mun dayi magana da mummy na koma dakin wanda har lokacin ya sharar barci sai dai dan hannushi da ya dan karkace mai na gyara mashi a hankali hakan bai sa ya falka ba daga barcin da ya samu din. Zaune nake na kura mai ido daga saman kujeran da nake zaune zuciya sai faman sake sake take min a kan shi ban sani ba har barci ya dauke ni a wurin mai nauyi nima. Ban san tsawon lokacin da na dauka ina barcin ba shi ya fara falkawa ya hangoni zaune nake barci tausayi na bashi. Don yasan wai gadin shi nake a haka barci ya dauke ni a gurin ya dade kwance yana kallon yadda nake barci a wahalce daga zaune. Ga ruwan dake makale a hannun shi saura kiris ya kare a ledan jin kamar motsi yasa na zabura shi na gani a zaune yana cire roban ruwan a hannun shi. Da sauri na mike na isa wurin shi ina fadin ka tashi yaya jikin na ka ina kokarin taimaka mai da ledan ta hanyar rataye ledan da allura sama. Sai da ya dan dade zaune ba tare da yayi magana ba sai ya mike zuwa ban daki ya dan jima ya fito tare da dauro alwala zai yi sallah. Nace dashi lokacin sallah yayi ne yace kina barci ina zaki san lokaci yayi anya haka ake jinya mai jinya barci mai ciwo barci ni dake wazai dubi wani a haka. Murmushi nayi ina shimfida mai abin sallah tare da cewa wallahi ban san lokacin da barci ya daukd ni ba a haka zaune bai magana ba sai murmushi ganin ya tada sallah na nufi dakina don nima in gabatar da nawa sallah. Na dade zaune bayan na idar ina kai kuka na ga Allah yabamu lafiya ni da mijina a wuri san nan na mike na fito abinci na fara hada mai nakai mashi. Har lokacin yana zaune yadan kara jikin shi da bangon dakin kamar yana tunane na shigo dauke da abincin na zauna bayan na aje mai a gaban shi. Ya dago kai yana kallona tare da da fadin zan ko iya cin abincin nan da dai fruit kika hado min watakila zan iya dan sha. Nace uncle kayi ko two spoon ko three zaifi ka zauna bakaci komai duk yinin yau hakan zai iya jawo ma wani matsala kuma don Allah kadan daure kaci ko kadan ne. Baiki ba na zuba mai ganin baya son ci yasa na karbi cibin a hannun shi ne debo nakai mai a bakin shi. Murmushi yayi ya bude bakin ya karbi abincin yaci nima na debo nakai bakina don dai ya danci Alhamdullahi na samu yaci yakai cibi hudu yace ya koshi. Mike nayi na kwashe kayan sai ya riko ni yana fadin ke ba zakici ba kin san fa kin finu lalura sosai kada kije ki haifa muna baby ba kosasshe ba. Murmushi nayi nace nima fruit din zan sha idan na gyara hakan yasa shi ya kyale ni na fita da kayan nakai kitchen nan na tsaya na hada muna fruits salad. Nan mummy tazo ta samay ni ina gap da gamawa take tambaya na yaya mai jikin nace da sauki mummy har ya danci abinci yanzu. Tace a da sauki ke nan in dai ana cin abinci ai zai zo da sauki ciwon da ba a ci ba a sha ai yafi wahala ga mai jinya. Nace muje ki duba shi mana mummy tace a bana shiga dakin mijin ki ba nace haba muje dai ai ba a kwance yake ba. Ina gama mummy na bayana na shigo dauke da bowl din dana hada salad din daga kofa mummy ta tsaya take gaida shi ya amsa da mummy ne shigo mana. Bata dai shigo har cikin dakin ba ta tsaya daga kofa tana mashi yaya jiki ya amsa da mummy naji sauki sosai tace Alaji ka dan dinga hutawa mana haba ga kunan kullun cikin aiki ba hutu. Murmushi yayi yace mummy ai aikin nawa mai sauki ne da wanda ke yini a cikin rana ko yaushe jikin dai ne dama ba lafiya gare shi ba. Tayi mashi sannu ta fita daga dakin ya mata godiya tana fita na zauna a kusa dashi tare da fara zuba mai yana zaune ya kura min ido kawai har nagama na miko mai. Yakarba tare da fadin thanks gefe na koma na zauna tare da tsura mai ido da ido yayi min alaman in diba mana sai na kada mai kai tare da fadin ban jin sha. Yau din baki shan fruits din nace na koshi ne sai naga ya debo ya mika min ba yadda na iya dole na bude baki ya zuba min amma sai naji yau abincin nawa ya koma min kamar madaci. Da kyat na iya hade wanda ya rage min abaki na sai na samu kaina da tura kaina cikin kafafuna na dunkule a waje daya ina kuka. Ji na ya kamoni zuwa jikin shi tare da dan bubuga min baya a hankali ba hana ni kukan ba sai da nayi may isa ta ya mika min ruwa in sha. Ban ki na karba na dan kurba na aje kofin shidai yana zaune ya kukara min ido muryan shi naji ya katse min tunanen dana fara yi a lokacin wai may kike ma kuka ne haka. Na bude baki nace Uncle bani son in rasaka cikin wanan halin da nake ciki kaine uwa da uba a gare mu idan na rasaka yaya rayuwa zata koma ? Sai na fashe da wani irin kuka mai tsuma zuciyan mai sauraron ta kamoni yayi zuwa jikin shi ya lalashi na wayan shine yayi kara a lokacin hakan ya dakatar damu da maganan da mukeyi. Ji nayi bayan ya amsa wayan yana fada min ga yaya Saadu nan yadawo duba jikina yana falo. ZAINAB IDRIS MAKAWA SEENABU 8/28/20, 11:45 PM - Ummi Tandama: BAHAGGON, , , , , , , , , , , , 🧕🏿6️⃣6️⃣🧕🏿 Barci mai dadi ne ya dauke ni bayan sallah azahar inda na sallamay sallah a wurin na kwanta saman ties sai barci. Muryan mummy nake ji sama sama a cikin barcin nawa take fada min ga dan uwan ki nan yazo da kyat na bude idanawa na ganta tsaye akaina. A cikin idon barci nake magana da ita nace mummy kina magana ne tace eh dan uwanki ne yazo daga gida. Da sauri na mike zaune don nasan da zuwan yaya sani din a lokacin na dan jama zaune bayan mummy ta fita daga dakin . Na fito yana zaune yana cin abincin da mummy ta gabatar a gare shi cikin jin dadi da ganin shi ina murmushi nace yaya sani kaine a garin yau? Shima murmushi yake da gani na yace wallahi nine Safiya ai tun jiya naso zuwa to nakai su babane da ummi wurin alluran mahajta shiyasa na bari yau na taso. Nace Allah sarki kuna kuna shirin tafiya zaku taka kasa mai tsarki abinku yace wallahi kin ga ikon Allah ke nan Safiya. Ai maganan baba kullun yanzu akan mijin ki yake yana yawan cewa bai san itin adduan da zaiwa bawan Allah nan a rayuwan shi ga gida kuma ga makka kusan lokaci guda. Nace haka abin Allah yake sai yazo ma ta inda baka zata ba a rayuwan ka na fadi ina zama kusa dashi. Yace wai naso ummi taga yadda Safiyan ta ta koma kamar wata irin hajiyan birnin nan wallahi safiya haka kika koma yanzu. Dariya nayi mai nace kai yaya sani ho yau kuma yar kaunar taka kake zolaya haka ? Yace wallahi ba zolaya bane kin koma din ne yace ashe maigidan ya fita waje sai yanzu nake ji a wurin mummy da nazo gashi kuma shiyace in shigo a cikin satin nan. Nace ai ina ganin yaya Saadu ne zaka hani don yabar sakon ka a gunshi koda yake ba,ayi dani ba amma kamar sakon na babane. Yace kuma dai baba bai sani ba da bai bari nazo ba don sai da yaja min kunne tace kada in yarda yace zai yimin wani dawainiya gidan zumu ba kasuwa bane. Murmushi nayi Allah ne kadai zai saka mashi da alherin sa ai amma Uncle yana dauwainiya dayawa wallahi bamu kadi harda yan uwanshi haka yake fama dasu suma. Yace haka aike so indan ka samu yan uwanka ma su su san ka samu ba kazo masu inuwar giginya ba hange daga nesa. Fitowar Mummy daga daki ne ya katse muna magana inda take tambayan shi Rukkaiya yace tana can gidan mijin ta ai yanzu. Nace banko tambaye ka labarin mutanen gida ba mun zauna muna zuba hira yace cikin dariya kowa lafiya lau yake wallai. Nan itama ta zauna mukai ta hiran gida dashi yana bamu labarin kasawar shanun baba da yadda abin yazo mai amma baba ya rabe wa mutane naman duka yace shima ai a alheri ya samu ya saya. Sai da akai kiran sallah laasar yafita sallah muma muka kama gaban mu daga can ya fice gidan ya nufi gurin yaya Saadu. Na idar da sallah ke nan waya na yayi kara na dauka hajiya baaba ce ke kirana da ladabi na amsa wayan kamar tana gaba na a lokacin. Mun gaisa da ita take tambaya muna dai lafiya nace mata lafiya muke tace ashe shi yayi tafiya ne kuma nace hajiya bai fada maku bane ? Tace ina zai fada muna don yasan in ya fada bazan barshi ya tafi cikin yadda tsufa din nan nace ai lafiya nake hajiya tace to aidaiyi ta hakkuri kin dai san yanayin mijin naki yanzu ba wani don haka zama tare sai da hakkuri nace nagode hajiya. Tace yaya wurin su Aisha nace ta kwana biyu bata shigo ba amma dai lafiya take dai tunda naji shiru munyi sallama har zata kashe wayan naji ta tambaye ni. Yanzu ke kadai ne a wanan katon gidan naku dariya nayi nace hajiya ai akwai mutane agidan yan aiki suna tare dani ban yarda na fada mata mummy na gurina don ban san yadda zata fasara abinba. Tace hakan yayi ni dai ba zaku ganin ba sai idan Allah ya sauke ki lafiya zan zo inga jika na tunda nasan ba a nan zaki haihu muna ba. Nace haka dai ummina tace bazata zo gida na ba sai na haihu tace ai shine mutunci ina dadi kullun kana yawo gidan dan ka. Tasan mutuncin kanta ne tunda ta fadi hakan nace indai ummi ne hajiya nasan ba zuwan zata yi cewa zatayi ga iyayye na da yawa su zasu zo tace wanan shine daidai. Kada kiga laifin ta dariya nayi nace amma ai hajiya mu bamuki ko yaushe mu ganku ba in zamu samu. Ina jin dariyan ta tace bakuma zaku samu ba mudai fatan mu ku zauna lafiya shine adduan mu kullun akan ku. Mun gama wayan naji dadin yadda hajiya ke jana a jiki tana nuna min kauna kamar yar cikin ta ko yaushe. Wayan na jona charji zan fita daga dakin sai ya koma yin kuka na juya na dauka anty ce ke kirana saida gaba na ya fadi dam. Na dauka da sallama muka gaisa tace kwana biyu najiki shiru nace barin in kiraki nace wallahi anty banjin dadi ne shiyasa ban kiraki ba kwana biyu. Tayi min yaya na kara ji nace naji sauki ta dora da fadin kodai abin arziki ya samu ne kin ga ai magana na nafita yanzu sai mu tara kudi da tushe. Zuwa haihuwan ki mun san abin da muka tanada ba sai dai kawai aga muna bushashan mu ba da kudi amma kin tsaya kina noke noke. Ke barin fada maki duk wata mace da kike ganin tana heleke da haka ta tara ga gumin mijin ta amma ke naga tsoro yayi maki yawa baki karban kudi yadda ya dace ki tatse shi. Murmushi nayi nace anty matsalan shi baya bada kudi ne sai dai yayiwa mutum hidima tace aike zaki koya mashi bayarwan . Yanzu dai kin ga kin samu ciki kila don haka sai ki mayar da hankali kafin haihuwar ki musan abinda muka samu a wurin shi. Ni dai murmushi nake mata kawai nace anty zanyi yadda kikace din idan ya dawo tace ina ya tafi nace yaje Spain ne. Allah dawo dashi lafiya tace tana kara jaddada min in yi kokari ina yagan wani abu a wushin nace mata to anty tana fadin nan da yan watanin ai mun tara maiyawa yanzu haka daddy su twins ba karamin karba nake a wurin shi ba kin gani na. Kokari nake yanzu in fara sanaa in bar wanan aikin nagaji dashi wallahi kullun mutum baida hutu a rayuwan shi yana hanya aiki. Nayi mata godiya muka kashe wayan fitan da banyi ba ke nan na zauna ina tunanen maganan mu da ita yadda zan mu kwashe a karshe. Don dai ni ban fada mata ina da ciki har ya tsufa a jikina ita da ke maganan nan da wasu watanen masu zuwa can. Nidai buri na shine in samu mu rabu lafiya da ita don haka na yanke shawaran tura mata wasu kudi da ya bar min a gida don kawar da maganan. Bayan sallah magariba su yaya saadu da yaya sani suka shigo gidan na fito falo wurin su nan muka zauna muna gaisuwa dasu. Yaya Saadu sai sheri yake min wai na tsufa sosai na wani kara girma kamar bani ba kodai biyu na kwaso masu ne ? Dariya na kece dashi nace aida sai Samira ta dawo gidan nan don ba zamu iya mu kadai da mummy ba. Yace kina wasa mummy sarai ta iya rike so akwaita da kokari fa nace ai na gani wallahi itace ra fito daga daki tana masu sannu da zuwa. Ta tambaye shi mutanen gidan shi yace suna lafiya yaji suna fadin gobe anan zasu wuni ai nace nikan ai saidai kuyi hakkuri dani yaya . Don Allah ya hada ni da miji mai kule yace ai shi yafi Safiya mace mai yawan yawo ai bata da dadi sai da aiyi hakkuri kawai. Mummy tace banda samira don ko dazun ta kirani wai suna kasuwa yayi saurin kare ta da fadin sun je sayayya ne fa mummy . Don ni banda lokaci shiyasa nake bata kudi ita taje tace kudai zama yan bariki ai kaida matar taka dariya yayi yana kare matar shi wai ai bata da yawo. Yaya sani ya kawar da hiran yace Safiya ki ji mijin ki wai ashe shanaye yake son sai wa baba . Ido na zaro waje yaya Saadu yace yasan shanun baba ya kasa ne ko nace eh da yaya sani ya bugo waya muna tare anan yaji amma bai mun magana ba tun lokacin. Yaya yace ai ya fadi don yace wai kada a fada maki nima next week nake son mushi wirin su muyi sallama don zuwa wani satin sama zasu fara tashi. Mummy tace nasan dai kafin su daya suna samun kin haihu nace mummy tun yanzu tace laila da wuya in ba hakana zai faru ba kan. Nace wai idan na haihu ummi bata kasan sai yaya sani ya tare ni da cewa ba aikwai mutane a gida ba sai wayanda ke nan suyi buki mana. Shiru nayi dan tuna katobar dana so yi a gaban shi nace ai fa akwai mutane kan dayawa a gida zan dai ga yan gida kan. Munyi hira dasu inda yaya Sani yace zai bi yaya saadu gidan shi ya kwana washegari samako yake son yi kada a nemay su baya nan. Nace wai Alhaji sani ke nan yace bari ke dai Safiya har fa mutane sun fara kirana da Alhaji wasu ma gani suke da farko kamar karya ne ba zan tafi ba. Nace wai ina yaya Nura yace yana nan wallahi ai yaso ya bata rai sai da mama ta fita bayan shi ya shiga hankalin shi. Nace ya sani ko idan zamu tafi badi in Allah yakai ran mu muje tare yaya saadune yace dayake shi baida aiki sai kai yan uwan ki makka ba. Dariya mm ayi tare da fadin yaya Allah ne ya kawo mu lokacin hutu mummy tace don haka sai a huta kuwa ai lokacin abu ayishi. Mun dan jima muna hira mukayi sallama suka tafi mummy ta hada min abinci wai inci ban son ci amma dole tasani gaba dole na ci shi. Daki daya muke kwana da mummy a dakina don haka muke kawa wani lokaci mu dan hira da ita sai mun gaji mu kwanta. Washe gari su samira suka zo gidan nan muka wuni da ita da yar uwar ta anan nake jin wai yar uwar nata ta samu miji aure a inda suke. A cikin hiran mu ne nake fada ma Samira abinda ke faruwa tsakanina da anty zancen in tura mata kudi tace. Amma dai wanan matar ta fadi kasa wallahi ita duk kudin ta sai tayi zari haka mummy tasa muna baki a maganan mu tace hakan da Safiya keyi yayi kyau su dai rabu lafiya da ita ba shike nan ba. Kudin may mutuncin da tayi mata yafi kudi ai tunda halin ta ke nan ba sai ai mata yadda take so ba a rabu lafiya rashin yin zai haifar da wani rikici a tsakanin su ne kuma. Tunda yanzu mutane ba tsoron Allah ne da su ba kun sani ko har yanzu suna ga bakan su na son mijin ta ya auri yar wanan dayar matan. Nace mummy in dai ma auren zasu yi su barni da lafiya suje suyi tayi kowa ya tsaya a matsayin shi mummy tayi saurin cewa dani. Umm umm yar nan kada ki soma fadin haka kishiya idan ba dace ba babu wanda ke son ayi mashi sai dai in ya kama dole shine ba mafita. Ai da zaran ya kara aure yanzu duk wanan mutuncin da kikaga yana maki sai ya ragu namiji ai ki barshi kawai. Idanuwa na na lumshe ina tunanen maganan ta idan uncle yayi min kishi ni ai na shiga uku ko a gidan mu ba balle gun bakin jama,a. Samira ne ke fadin jifa kishirya Aishan ku sai da mijin ya bata saki kwanan don ta ishe shi akan zancen gida da motar da aka sai wa Aisha din ji da muka je take fada muna. Nace ai kaji matsalar duk da ba mijin nasu ya saya masu ba amma bata bari an zauna kalau ba kuma ? Tace wai har nan gidan Aisha ta biyo shi da masifa anan ya dankara ma yar iska saki sai gata kuma ta zube tana kuka a gidan. Mummy tace shine ai matsalar matan yanzu dan abu ba abu ba su mayar dashi fitina su hana kan su shaka da abokan zaman su. Nace ai wanan zaman namu mummy sai mu, mace ta samu gidan aure amma kishi sai ya rufe muna ido mukasa koyi da halin iyayyen mu na baya. Kuma mafi yawan mata haka muke yanzu da bakin kishi bamu natsuwa muyi kishin hankali sai na hauka wanda idan mutum yaji sai ya rena masu hankali. Mun wuni cikin dadin rai dasu Samira a gidan sai yamma lis yaya yazo ya dauke suka tafi daga gidan. A gaskiya ina jin dadin zama da mummy don ba karamin debe min kewa take a gidan ba bata bari taga na shiga damuwa ko kadan. Mahajjata sun tashi lafiya har sun sauka kasa mai tsarki inda suka bugo min waya na samu layin da zan dinga kiran su a can . Yaya sani ne ke rike da wayan a hannun shi don haka idan zan kira ummina ko baba sai nakirashi yake mika masu waya muyi maganan da zanyi dasu wanda duk wayan namu gaisuwa ne. Har yanzu uncle yana gurin tafiya bai dawo ba a wani dare ya bugo muna hira yake fada min ba zai samu dawowa ba daga can zai wuce saudiya ya sauke fari a can. Nace Uncle kayi min wayo ke nan ka tafi saudiya au na manta fa ki shirya gobe kema zaki biyo jirgin safe ki samay ni anan. Kai daddy kana son a koroni tun filin jirgin Nageria ke nan a yadda nake nan na tun kare su ai sai suce ban da hankali yace. Ki fada masu ke fa matar uncle ne ai zasu bari ki wuce kawai nace uncle abin ya koma yar haka ne kuma tsakanin kai dai kawai ka yarda kayi min wayo yace to na yarda madam ai min afuwan ko nace ayi ma Uncle. Munyi hiran sosai dashi kwana biyu aka hau arfat nan mahajata na jirgin yawo suka fara shirin dawowa gida acikin su harda uncle. Sallah da kwana biyar na tashi da matsanacin ciwon mara cikin dare mummy ta rude duk da tasan cewa haihuwa ne yaya saadu ta kira baizo gidan ba sai tare da likitan uncle da wata nurse. Don haka agida Allah ya saukeni lafiya da taimakon Allah da tasu na likitoci na samu na haihu karfe biyar na asuba. Nurse din ce ta taimaka min har wankan yaro da komai da itace tayi nan a gaban mummy bayan yan aune aunen da sukayi min sukace kada aba yaron nono wai ina da matsalan kaikayi a jikina wanda ni san suyi hakane don kawai batar da sawu. Likitan ya kara dacewa mummy ba kowa za a bari yasan yaron bai shan nono ba don yawan surutun mutane amma zan dan iya bashi lokaci lokaci kafin yayi wayo. Don sun diba zan iya shayarwa na dan wani lokaci yaya yace tunda akwai abinda zai sha kawai kada ma na bashi nonon ita mummy tace hakan ma yafi. Tace ta fahinta yaya Saadu ma ya gara gargadin ta kada ta bari kowa yasan zancen mummy tace ai ko samira baza taji ba don bama zata bari aga yaron ba. Nan ya kwashe su ya mayar gida don lokacin har gari ya haska ko an fara fitowa shaanin yau da kullun. Mummy ne ta miko min yaron bayan sun wuce na kalli yadda ya kwaso uban shi da kama wai jinin uban shi yafi kadfin nawa a cewar ta. Murmushi nace mummy ke nan daga inda nake zaune ba tare da na karbe shi ba nake kwararo mai addua. Barcin gajiya ne ya dauke mu a gidan dagani har mummy din sai tara na safe su yaya saadu suka shigo da su samira gidan. Shigowan su ne yasa muka tashi basu jima ba sai ga Aisha ta iso kowa sai yaba kyau yaron yake yi don ya gado kyau ta ko ina daga iyayyen shi. Aisha sai cewa tayi dasu yaron yafi kama dan ya dauko fuskan yan gidan su ne ni dai sai murmushi nake masu karshe ma barci nayi na barsu nan. Ganin na sake komawa barci mummy tace su dawo falo su bar ni in huta yaya Saadune ya shigo dauke da madaran da za a ba yaron da ruwan zamzam . Nan dai yadan bata lokaci yana buga ma mutanen su matar oga ta haihu yau na tashi mummy tace na danje na gasa kaina a bayi. Naje na taba ruwa na dawo dai dai lokacin da Uncle ya sake buga waya akace dashi na falka daga barcin. Wayan yaya saadu ya miko min yace madam barkan mu da arziki ashe an sauka bayana dariya nayi nace Allah ya sauke ni uncle Allah ya rufa min asiri baka garin na haihu baki alaikum. Yace kudai kunyi min wayau naso ace nine zanyi karban haihuwan ai naga kalar rakin ki har video zan yi maki a lokacin. Murmushi nayi nace wanan dai ya wuce ka yayi saurin cewa saura wani uncle rufa min asiri nace dashi da sauri tare da kashe wayan ZAINAB IDRIS MAKAWA SEENABU 8/29/20, 11:42 PM - Ummi Tandama: BAHAGGON, , , , , , , , , , 🧕🏿6️⃣7️⃣🧕🏿 Ranan duk da gajiya ban samu hutawa da amsan wayan daga yan uwa da abokan arziki ba masu bugowa su na min barka da arziki. Sai da dare samira suka bar gidan amma yar uwarta ta zauna a wurina zata taya mummy aikin jego nima naji dadin zaman nata. Nafito bayi don yin tsarki dare saboda zan kwata a lokacin ina tsaye ina shiryawa wayana yayi kara mummy ke fadin wa kuma yakiraki yanzu kina shirin kwanciya ? Daukan wayan nayi amma sai gabana ya fadi mummy tana ganin yadda na firgita da ganin mai kira na din a lokacin. Waye mummy ta tambaya cikin son ji nace mata anty lagos ne bata san ina da ciki ba nassan taji zancen haihuwan ne take kirana anty tace dauka mana sai ki fada mata kin dauka ta sani ne ai. Kiran ya katse sai ni na kirata kira biyu gana uku ta dauka nace mata anty ina bayi ne da kika kira tace yanzu nake jin wai kin haihu sulaiman yakira yana fada min. Nace eh anty kin kyauta tace min lalai Safiya yanzu nasan yadda kika dauke ni har kiyi ciki ban sani ba sai dai inji haihuwa kawai daga sama. Ko shekaran jiya fa kin kira ni mun gaisa dake amma baki fada min cikin ki ya tsufa ba haka sai dai inji haihuwa kawai. Nace anty kiyi hakkuri na bansan yadda zan fada maki bane da baki na na dauka ai ya fada makine da dadewa. Ya fada min may shine zai fada min ko ke to bari kiji kada kiyi tsamanin kiyi min kan ki kikayiwa sai ta kashe wayan kit. Wayan nabi da kallon mamaki a hannuwan kamar ita ke gabana sai kuma na sake wani murmushi kawai. Don nasan inda maganan ta ya dosa alokacin bai wuce zancen kudi ba ne don ko gabanin sallah na tura mata da kudi ta account din da ta turo min. Mummy takatse da tambayan cewa may take nufi da kinyi wa kanki ko da ban san ta ba nadai san a yanzu babu abinda zata gwada maki na rayuwan duniya. Tana miko min tea mai kauri take fadin haka nace mummy anty tayi abinda bazan iya mantawa da ita ba rayuwana . Ta katseni da fadin don kaiwa mutun alheri ba saboda Allah kayi sai kuma mutum ya zama bawan ka saboda Allah haka Allah yace ayi taimako duniya? Tea din na karba na shaye sai ga zufa na karyowa a jikina na aje cup din ina shirin kwanciya yaron mummy ta miko min tana fadin taba yaron ga tunda yazo duniya baiji dumin uwar shi ba. Karban yaron nayi na rugumay shi a jikina kamar wani babba da yasan may ake nufi da haka sai naji ya sauke ajiyan zuciya a hankali a jikina. A hankali hawaye ke zubuwa daga idanuwa na wanda ban san ina yin su ba alokacin tausayin kan mu dana yaron ne ya kamani a lokaci guda. Mummy tace a a yaya haka kuma daga karban yaro ki kama hawaye haka don Allah kibar irin wanan dabiar mana ta mika hannu ta karbi yaron daga hannu na. Har lokacin ban daina kuka ba wiwi badai ce min komai ba da kukan ya isheta sai kuma ta koma lalashi na tana fadin. Haba Safiya ke da zakiwa Allah godiya sai kuma ki gode mai da kuka kamar baki gode mai da kyautar da yayi maki ba. Tadai samu nayi shiru tare da nadewa saman godo ni kadai nasan abinda ke damun zuciyana a lokacin wanda ita mummy ba ta sani ba. A haka barci mai nauyi ya dauke ni sai da asuba naji motsin mummy ta tashi zuwa ban dakin ta wanda acan take kewayawa bata shiga nawa har wankan yaron acan take yi mashi. Yau da yake ikilima yar ta na gidan sai ta dan jima bata dawo ba haka yasa na samu daman komawa batcin dake idona. Sai wani lokaci naji tana ta dani wai in tashi inyi wanka tun rana bai yiba sosai haka na tashi na shiga na gasa jikina a ban dakin. Na fito na shirya cikin wasu super masu launi ja da fari dinkin shi mai daukan ido don an tsara shi dakyau da fasahan teloli na zamani. Wayan Uncle ne ya shigo a lokacin da na gama saka sutura a jikina mun gaisa yake tambayana babu matsakan komai a tare dani ko ? Nace lafiya kalau muke Uncle sai dai kewan ka daya cika muna zuciya baka gidan gidan babu dadi yace muyi hakkuri zamu ganshi nan da sati uku mai zuwa. Nace haba uncle har sati uku baka zo kaga kyautan da ubagiji yayi maka ba yace karki damu ina nan ina gode ma Allah ki san a gaban shi nake ma yanzu don ina dawfin bankwana ne yanzu haka ina fitowa daga cikin kaaba ne. Allah ya tsare nayi mashi yake tambayana mummy nace tana dakin ta da baby suna karyawa ya sake tambaya idan muna da matsala in fadawa yaya saadu nace uncle bamu da matsakan komai a tare damu. Mukayi sallama naci gaba da shirina zuciyata cike da kewar miji na da bai kusa damu a lokaxin da muke bukatan shi a tare damu din. Goma da rabi ma,iakatan wurin su yaya saadu suka shigo min barka bisa jagorancin yaya saadu din sun kai su goma duk kan su sun sha corth a jikin su bakake. Wanda nake gani haka yanayin shigar wurin aikin nasu yake a falo suka girshe ni zaune dasu mummy ba hijjab a jikina kafin a dauko min hajjib duk sun kare min kallon da yaba hallitana a zukatan su. Yaron mummy ta dauko masu nan suka shiga yaba kyawon yaron wasu na fadin wai ni ya biyo wasu kuma suna fadin ogan su yaron ya biyo. Basu dade ba suka aje muna kyatutukan da suka zo muna dashi sukayi muna sallama suka tafi yaya saadu ne yadan tsaya fada muna samira na tafe ta tsaya gyaran gida ne yanzu zai koma ya dauko ta. Basu zo tare ba sai gata wai wani driver yasa ya dauko ta shi ya shiga kasuwa muna zaune sai hira ake faman zubawa irin na mata idan an hadu. Sai ga matan maikatan su Uncle sun shi su da yawa muka zauna ana gaisawa wanda duk basu sanni ba sai a wanan lokacin. Wata daga cikin su ce ke tambayan waye mai haihuwan sai samira ta nuna na turancin yan Nigeari suka fara yi suna cewa ayyah. Very young Lady nan hira ya kaure a tsakanin su suma dai yaba kyawon jaririn suke ta faman yi zasu tafi suka aje muna kyautan da suka zo muna dashi. Sun fice muna masu godiya naji Samira tace shegu muna fukai kawai ina ruwansu da kurciyan ki dama sun zata ke tsohuwace ko may ? Na da sauri nace kai Samira daga abin arziki sai zagi haka kuma tace ke baki san komai ba ina wanan maidan jan gyale wai ita mijin ki take mutuwar so kamar ta mutu. Nace wa uncle tace shifa wallahi kyale wahalaliya wai kuma a wurin dan uwan ki take kamun kafa wai ya shawo mata kan shi. Dariya nayi nace ashe aiki ja yagan ta kuwa sai kuma ita bakar nan mai kama da zubin arnan daji itace ta lakewa yayan ki sai da na kirata ranan naci mata mutunci sosai. Dariya ta bamu dukan mu mummy tace ashe kina da aiki wanan zamanin idan kince zaki dinga kiran yan mata a wayan miji kina zagin su. Don haka zasu samu damar shige mai su nuna ai su na kwarai ne sai tafiya yayi nisa su fitar da halin su na boye. Nace ni yanzu mata sun baci mummy tace bari ke dai mace fa yanzu ba abin kunya bane ta tunkari na miji da kalman son shi takeyi . Nace ni mummy ba abinda keci mun rai da matan yanzu sai kiga mace na tafi taga mota tafe ta kasa kawar da idon ta ga mai motar. Har ba da matan aure dabi an su ne yanzu bin namiji da kallo cikin mota ba birnin ba ba kauye ba. Samira tace ai sai kiyi ai wanan yanzu ya zama ruwan dare a ko ina mata da sunji rurin mota basu da kwanciyan hankali sai mai motar ya wuce su. Yaya Saadu ne ya shigo gidan yana neman Nura akace tana kitchen kiranta ikilima tayi sai gata da saurin ta ta fito yake ce mata tazo ta duba kayan kitchen abinda babu ta fadi a sawo zata koma kitchen din yace mata a a tafito suje waje suka fice tare dashi samira ta tashi ta bisu wajen. Dariya muka kwashe mata dashi tace kuka ga abin dariya tsaron kaya yafi cigiyan shi ai nace ke dai baayi niyya ba mai zaki iya hanawa samira. Mummy tace rabu da mahaukaciya sun dade a waje sai gasu suna shigowa da kayan abinci cikin gidan katon katon komai an sawo. Zai fita nace haba dan uwa zauna na mana kaci abinci nasan wanan zirga zirgan da kakeyi baka tsaya kaci wani abu ba. Mummy tace ga matar shi sai kishin hauka takeyi bata san ta tambayi lafiyan mijin ta ba. Tace ai nasan ko nayi mai tayi bai zama yaci yana wanan zirga zigan haka mummy tace haka ake son aminin kwarai yayi maka tsaye da gidan ka idan bukatan haka ya taso bai kusa. Abincin yaci yana ci muna hira yake fada min sunyi waya da baba yaya sani ya fada mashi kila jirgi na biyu zasu biyu don da shi suka tashi. Mummy tace kafin su dawo ai mu mun sha bukin mu sai dai suji labari a bakin mu . Wai yaushe shi maigidan zai dawo take tambayan yaya saadun yace basu yi waya ba don ko yabar saudiya Dubai zai tafi daga can sai dai ranan da muka gane shi. Banji dadi ba a raina har hakan ya baiyana a fuskana yaya saadu ne yake mun sheri dan murmushi nayi kawai ban iya bashi amsa ba. Jego ya karbe ni sai dai ina makin yadda nono na basuyi min ambaliyan ruwa ba sai na fahinci kila maganin da likita ya bani ne ya kawo hakan. Suna saura kwana ukku muna daki da dare mu uku muna shirin kwanciya ikilima tana muna hira a dakin mu mukaji bell din gidan na kuka alaman ana sallama ke nan. Mummy ce ta fita zuwa duba ko waye goye da yaron a bayan ta don takan goyashi kafin mu kwata don tace idan yaro yasha baya kafin ya kwanta yafi dadewa yana barci da dare. Shiru bata dawo dakin ba yasa ikilima fita ta dubo ta sai gata ta dawo tana fadin Safiya maigidan ki ne fa ya dawo. Gadunan dasu yaya saadu a falo ana shigo da kaya cikin gida wani iri naji gaba na ya amsa min mummy ta dawo ta sauke yaron dake bayan ta tare da kiran ikilima suka fita. Ya shigo dakin a daidai lokacin da nake aje kofin tea saman dan drower dake gefe na dago kai nayi ina kallon shi. Yaja yayi tsaye daga kofan dakin yana kare muna kallon cikin shaawa daga nesa tasowa nayi zuwa gare shi . Take ya ware min hannuwan shi na shige ciki ya mayar da hanayen shi ya rungumay ni tare da matse ni cikin jikin shi. Ajiyan zuciya kowan mu ke saukewa a lokacin babu abin da nake tunawa sai haihuwan wahalan danayi na farko babu muji babu aike shi. Allah mai yin yadda yaso ga bayin shi na furta a raina yanzu gani gidan akwai gidan mutunci inda akasan daraja na da kimana ana tarairariyana kamar kwai. Sake juna mukayi tare da jana zuwa wurin gadon da yaron yake kwance yana barci acikin net din jarirai . Hannu na ya sake ya duka ya dauko yaron dake ta barcin shi hankali kwance ya rugumay shi a jikin shi. A hankali bayan yagama mai adduan da yake mai a duka bangarorin jikin shi ya dago yana kallona inda nake zaune a bakin gado na zuba masu ido. Sannu madam yace tare da sake min murmushi mai ma,anoni da yawa a zuciyar shi nima murmushi nayi mai kamar yadda yake min. Yace wanan katon baby haka yaya kika iya haihuwan shi a gida nace da taimakon Allah da na nurse Lidia na haife shi uncle. Zama yayi da yaron a hannun shi yana mai kura mai ido babu ko kiftawa nace uncle shine baka fada muna zaka dawo yau ba mu sani a shirya ma abinci. Yace aini akoshe nake ganin ku ya kosar dani da komai yanzu ya sake dago kai yace sannu safiya ubangiji ya raya muna wanan yaron yasa mashi albarka a rayuwan shi kin min komai tunda kin haifar min baba na a yau. Nace sunan Abba ke nan zaici yace ba dole ba Safiya ina matukar son mahaifina shima yana sona amma mutuwa ta raba mu alokacin da muke jin dadin junan mu. Allah ya gafarta masu na furta yace amin yau ki dawo min da tsohona dana rasa wanda har yau cikin yan uwana babu wanda ya taba min kara yace zai saka sunan shi. Nace ai gashi Allah ya baka yanzu ka huce haushin hakan yace wallahi na dade ina jiran wanan ranan a raina har da na cire tsaman sumun shi a rayuwa na. Sai gashi a lokacin da ban taba zato ba ubangiji ya dawo min dashi a rayuwa safiya zan so yaron nan kamar yadda nima mahaifina yaso ni a rayuwan shi ki taimake ni ki tayani sin shi don Allah. Nace har ma zan fika ni da yake babana kuma sukina ina kewar rashin shi a lokacin da muke bukatan shi a tare damu a lokacin da ya kamata ya kasance dakai yaji dadin haihuwan ka. Mummy ne ta leko dakin tana fadin Alhaji ga abinci can an hada maka yace mummy sannu da kokari ina jin labarin kokarin da kikewa babana sosai a wurin safiya. Murmushi mummy tayi tace masha Allah tsohon gida ne ya dawo ashe? Ya na aje yaron yake cewa baba na ya dawo mummy ku tayani farin cikin samun wanan daman da ubangij yayi min . Ya aje yaron yana kallona yace zan je in watsa ruwa sai da safe idan Allah ya kai mu don naga kuna shirin barci ne yanzu. Nace barin taso in hada ma ruwan wanka don ban hada heater ba yace na hutar dake yi zaman ki sai da safe ma hadu ai mummy sun kawar da komai yadda ya dace. Yana fita mummy ta shigo dakin tana cewa kin ga kyautar ubangiji watau sunan tsoho yaro ci ubangiji ya raya muna shi nace amin mummy. Nace da alama akwai shakuwa mai tsanani tsakanin shi da mahaifin shi tace ai da ganin yadda yake yi akan yaron kin sani kema. Yanzu aiki ya samay ki yadda yake ji da yaron nan sai ki taimaka ku bashi kulawa yadda ya dace in kina cire wanan filancin da kike yi yanzu sai ki cire don haka zai iya kawo matsaka a tsakanin ku. Murmushi nayi ina gyara kwanciya na nace mummy ai naga alama nasan akwai aiki a gabana sosai haka ta kashe wutan dakin muka kwanta asuba ta gari yan uwa. ZAINAB IDRIS MAKAWA SEENABU 8/31/20, 11:07 PM - Ummi Tandama: BAHAGGON, , , , , , , 🧕🏿6️⃣8️⃣🧕🏿 Washegari tunda ya shigo ya duba mu da safe ban sake ganin shi ba sai dare ya dawo gidan a lokacin na samu kebewa dashi da yaron dauke a hannu na na shiga wurin shi. Na samu ya fito wanka yana shirin fitowa falo don cin abinci sai gani na shigo dakin nashi yana goge jiki amma idon shi yana a kan mu har na karaso bakin gado. Inda na aje yaron saman gado na nufe shi tare da kokarin karban da dan towel dake hannun shi na fara goge mashi kan shi a hankali. Murmushi naji ya dan sake tare da rike min hannu ya fara fadin duk da gajiyan da kike ciki zaki koma wahal da kanki ga waban kuma ? Nace gajiya ai yabi jiki yace haba in shirya baki wani baban nawa ko hajiya baaba ke nan da sauri nace kai Uncle sai ana zaune kalau ka dauko maganan da zai firgita mutum. To be frank ba wasa a magana na sai ki fara shiryawa nan da kwanaki funda naga baki gaji ba kin ga sai mu tara zurian mu hankali kwance ko yaya kikace hararan wasa nayi mai tare da kawar da zancen da ki sa gabana faduwa idan naji. Nace daddy nazo ne in fada ma ma,aikatan ku sun zo sun kawo muna abin arziki da baka nan yace yana dan duba yaron Saadu ya fada min sun zo sai dai nayi mashi fada may yasa ya bari suka shigo min gida. Nace uncle ai danka ne ya jawo su da ba a haife shi ba aibasu zo gidan ka ba yace ai sun dade suna son zuwa basu ga fuskan haka bane. Kila ma sun gama kalle min ke ban sani ba nace ko sun kalle ni nan zasu barni tunda ba kayan su baca ni ina da kishi sosai fa yace min . Nace ai naga alama amma ai har da budurwan ka akazo ko itace baka son ta gani don yar kauye ce ni da sauri ya kallo ni don jin abinda na fada mai. Bayi magana ya juya zuwan wurin kayan shi ya dauko wani light brown din jallabiya yana sawa a jikin shi sai da ya gama dakan shi ya dauko yaron dake kwance saman godon shi ya gyara shi da kyau a kafadan shi yana fadin in kin gama fadin maganan ki muje inci abinci. Tashi nayi nabi bayan su har lokacin bai kara yin magana ba sai da zai zauna cin abincin ya miko min yaro wuce wa nayi wurin su mummy nakai mata yaron. Ban dawo wurin shi ba sai da ya neme ni na dawo na samu har ya gama cin abincin nace mai na kewa yane bayi, Tambayana yayi may kuka shirya na maganan suna ne don nasan gobe gidan nan zai cika da baki masu zuwa suna duk da nace su huta aiyi buki acan bauchin . Amma hajiya tace min dole sai wasu sun zo nan idan sun koma zasuyi bukin su nisawa nayi tare da fadin ni ba wasu mutane nake dasu nan din ba karfin mutanan duk baki ne da zasu zo daga bangaren mu. Yace ok na dai sa a gyara masu gidajen da zasu sauka a ciki don nan din ba zai ishe mu ba sai abinci naso inji shirin da kukayi akai don zan bada aiki a hotel ne ai muna nace da Aisha da mummy ya kamata kayi maganan don Aishan nan bata wuce ba. Yace may take yi har yanzu anan nace dashi aiki sukeyi a kitchen shiru yayi sai can yace yimin magana da mummy din da ita Aishan. Zuwa nayi na kisu sai gasu sun fito daga dakin zuwa gare shi bayan su zaune yayi ma mummy yaya gida ta amsa da Alhamdullahi . Yake tambayan ta abinda ake shiri akan suna tare da mata bayanin yadda ya tsara abin gaba dayan su sukace hakan yayi dama har Aisha na tunanen yadda zasuyi dahuwa a nan gida . Yace da sauri a ina zakuyi wanan aiki tace wai da anan mana yaya murmushi yayi kawai tare da kada kafan shi sunci gaba da tsara yadda abin zai kasance da yar uwanshi sai mummy da take a bangare ne. Nikan mikewa nayi na shige na barsu a wurin don na fara jin barci na damuna sai da na falko ne naga har mummy tashigo ta kashe muna wutan dakin ko na gyara kwanciya na da kyau. Washe gari zuwa karfe ukun rana baki sun fara isowa duk na matsu inga masu zuwa daga bangare na alokacin sai hudu na yamma suka shigo garin inda yaya Saadu yaje ya taro su a hanya. Shigowan su yayi daidai da fitowa na daga bayi don tsarkake kaina da nake yawan yi lokaci lokaci saboda in samu walwala a jikina. Samira naji tana masu oyoyo yasa nasan sun iso ke nan don haka na fito taron su falo da shafiu kanina na fara arba da sauri yayo wuri rungumay shi nayi cikin murna da jin dadin ganin shi. Don Allah ya hada jina da yaron sosai duk da bashi ke bin mun amma shine abokin shawara na a dakin mu mama na gani na sake shi na rungumay ta. Abin mamaki shi har da Inna yau a gidan aure na da kannen ummi na da suka zo mutum hudu da gwago nan dai gida ya cika alokaci guda. Zama sukayi aka fara gaisuwa tare da gabatar masu da abinci da na sha wanda har uncle ya fara odan su a gidan don bakin mu da suka zo. Yan bauchima sun iso mota biyu suka zo dashi bus cike da mutane gidan sai ya koma min kamar ba gidan mu ba duk girman gidan inda ka duba jama, a ne tako ina. Inna ta koma can hanya coridor din shiga part din uncle tayi zaune tana raba ido tana kallon ikon Allah tana anyanawa a ranta. Wai yau gidan Safiya ne haka safiyan da taso agida ita da uwarta ko na sabulu wuya yake masu gaskiya nake ganin kowa na rawan kafa da ita yanzu ashe sun san abinda suka gani ne. Tasa hannu ta shafo ties din kasan da ta zauna tana kallo wanda aka malalashi kamar ruwa da kifaye suna yawo acikin sa. Mummy ne ta katse ta da cewa aa Rakiya nan kika zo kika zauna hanyan dakin surukin ki kuma tashi mana ki shiga dakin diyar taki tana can ciki ai. Tace ummm, ummm aiko nan ma yayi min tace a a taso dai ki shiga wurin ta sauran jamma, an da kuka zo ai suna can tare da ita. Janta tayi har zuwa daki inda nake tsakiyan su mamana suna min bayani kan abinda suka shirya akazo min dashi wanda ummi tabar kudi da zata tafi sai su kuma su kara tasu a wurin dawai niyar. Nayi mamakin abunda suka zo min dashi don ba karamin kashe kudi akayi ba kamar lokacin aure wanan karon ma haka suka hado mi gara mai yawa akazo dashi. Sai hango inna nayi can daga kofa ta rakube wuri guda tana bin dakin da kallo har tana dagen kai wurin kallon dakin nawa. Nace a a inna karaso mana shigo daga ciki ki zauna na mike ina fadin kinci abinci kuwa na juya wurin khadija kauna ta ina cewa khadiza debo ma inna abinci don Allah tana fadin anbata abinci ai taci. Nace jeki debo mata nama ki kawo masu ta karaso ciki ta samu wuri ta zauna nace a mika mata jaririn dake goye a bayan gwago dake zaune a kasa. Aka kawo mata nama cike a plate ta karba tana washe baki ina kallon ta ta fakaici idon mutane ta juye a wani tsohon jakka dake rataye a kafadan ta. Murmushi nayi don bata ganni ba mama ma tashigo nan suka zauna nace su shiga bayi suyi alwala a dakina suka fito na mike da kaina na dauko masu abin sallah. Karshe wasu waje suka koma suka zauna saman fararen kujeron roban da aka baza a wurin sai ci ake da sha ga ma aikata wuri su Nura sai raba abinci sukewa mutane. Fitowa nayi zuwa wurin yan bauchi muna gaisawa dasu gungu gungu tare da masu ban gajiyan tafiya. Dare yayi yaya Saadu yashigo gidan yana fadin yan bauchi su fito akaisu masaukin da zasu sauka suka fara fito fogayen mota wurin aikin su Uncle suna waje ciki suka shiga aka tafi dasu. Suka dawo aka kwashi yan garin mu aka tafi dasu zuwa wirin da suma akai masu masaukin su gidan ya rage daga mummy sai gwago da yayan samira da muke zaune sai Rukaiya da na hana wucewa da Khadija na. Hira mukai tayi da rukaiya a daki tana bani labarin auren ta da Ado mai mai da yadda zaman ta da kishiyoyin ta yake yanzu a gida. Rukaiya tace dani na shigo dakin dada sai kika ga Inna ta biyo mu nace wallahi ai nayi mamakin zuwan su duka su biyu tace. Ita fa akace ta zauna gida da yara taki wai sai tazo yaya Sani kuma dama yaja mata kunne sosai kafin ya tafi. Nace kai Inna ho har yanzu dai tana nan da halin tace ai dole ta rage yanzu da kika ganta nan bata dako lafiya tafiyan karfin hali ne kawai tayi inji khadija na dake gyara ma yaro jiki a hannun ta ya gama shan madara zata kai ma gwago ta goya shi. Washe gari kafin wani lokaci aka fara shaanin buki baki da yan gari sun fara cika gida don haka kowa ya koma busy cikin mu maigidan tunda ya shigo da safe yace zai tafi unguwa bai dawo gidan ba. Kowa yasan sunan yaro Abdulrahaman nan yan bauchi suka fara kiran Abbamu ya dawo yaro yaci sunan tsoho ke nan. Anci ansha an raba kyaututuka masu ma,ana dake dauke da photo jariri da sunan shi a jikin kyauntan sai ga wasu mata sun shigo wai mata yan kasuwa ne suka zu taya mu murna har da yan wurin aikin su uncle wasu sun turo matan su wasu kuma ma,aikatan su mata ne masu aure suka zo. Alhamdullahi har dare babu wanin hayaniyar da akayi sai faman ci da sha mata keyi koma anyi ba mai yawa bane abinda ba a rasawa ne kawai na taron mata. Na shiga na fita walima mukayi inda wata malama da tazo daga bauchi tayi mu nasiha akan "ya"ya da hankin uwa akan dan ta. Nashiga na fita daga suturun da Uncle ya waddatani dasu don fitan buki wanda daga Dubai wanda duk wanda nasa sai an kalle ni daga ni har yaron. Ban da abin cewa sai hamdala ga ubangiji subbahanahu wata,ala da ya wadatani daga cikin ni,imomin shi nake rayuwa kamar banda wani tabo na tashin hankali a jikina. Har kishiyar Aisha da abokan aikin ta sunzo mata karan suna da makwabtan Samira da suke zamar arziki dasu suma sunzo mata kara. Sadiya kaunan su yaya saadu yasa tazo daga lagos don halartan sunan kawai naji mamakin ganin ta kwarai da gaske don yaya bai fada min cewa zata zo ba sai ganin ta nayi kawai da safe da suka shigo. Mun rage daga mu sai bakin mu suma da dare aka maidasu masauki don a gajiye kowa yake yana son hutu. Khadija ne dakin da samira suna nade min kayan da nayi amfani dashi da rana ni kuma ina zaune bakin gado rike da wayana a hannu. Ina kokarin neman layin anty mu gaisa Uncle ne ya shigo dakin suka shiga gaida shi da gajiya dago kai nayi ina kallon shi yana wasa da khadija na. Yace ke budurwan kauye kin boye kawai abinki a kauye baki ko tuna mutane ta turo baki gaba tana cewa ai mu yanzu garin mu ba a kiran shi kauye don mun waye. Yace amma dai zaki dan zauna kwana biyu nan ko don ki kara wayewa dakyau dariya tayi nayi saurin cewa a a kan tace nima bance zan zauna ba ai. Nace dama shafiu ne da ko wata nawa zaiyi ban damuwa amma wanan wataran zaka dawo ka samu tamin dan karen duka a gidan nan. Tace kai anty Safiya ai dane muna kanana ko tun da muka girma ai muka bar fada dariya su samira suka kwashe dashi. Yace au ashe da gaske da kina dukan min mata tace wallahi yaya sherin anty Safiya ne itace dai mai dukan mu din. Nace ke khadija ni yaushe nake dukan ku ina kafa kafa kada inna ta cuta maku a lokacin tace ai kin yi kokari wallahi. Nan Samira ke fadin munafuka sai gata tazo tana simi simi da ita Uncle yace tazo ne ita ma khadija tayi saurin fadin tazo gulma bata da ko lafiya. Shirin fita dakin sukayi su sai ya dakatar dasu da fadi No ku zauna abinku ni fita zanyi nazo duba madam dina ne. Samira tace gako madam nan ta sauke gajiya yaron ya tambaya khadija tayi saurin fadi yana gurin gwago ai kun samu maigadi yau gwago bata bari kowa ya dauke shi ba yau ita da mummy. Yace amma sun kyauta min ina can ina tunanen wanan taron dana gani za ai ta jagulamin yaro da kuma na tuna mummy na nan sai ban damu sosai ba. Khadija tace oho ita anty nawa fa dariya kawai yayi ya fita dakin har ya kai kofa ya juyo yace khadija ba fa dake za a koma ba kinji na fada maki. Samira ce tace bayan ya fita daga dakin ashe uncle yana magana haka mai tsawo nace yan maganan dai ke kusa yau. Washegari baki basu shigo da wuri ba don gajiyan da suka tara sun fita zuwa kasuwa masu shiga gari ma sun shiga ziyaran yan uwa sai iyayyena da suka ce gidan yaya Saadu zasu tafi suga gida. Dare anan sukaci abincin dare aka kwashe su zuwa masauki sai washe gari zasuyi asubancin komawa gida. Zaune muke daki suna ta faman saka kaya a leda wanda yaya Saadu ya shigo dashi gidan da za a bawa baki sallama matsayin kyautar bukin su. Na kalli Rukaiya nace yanzu haka kike zaune a gidan baki sanaan komai Rukaiya ga yaro ta dago kai tace to yaya zanyi Safiya. Ni dai zaman yafi min zama gida wurin inna don yanzu sai ta ganin zatai fitinan ta ranan da ya samu ya kawa muci randa bai samu ba muyi hakkuri hakana. Nace yanzun dai zan baki wasu dan kudi sai ki dinga juyawa shima zan baki kikai mai amma don Allah ki bashi don zaman magidanci ba sana,a ba dadi wallahi. Don ina tuna lokacin da muke kanana baba baida wani sana,a irin wahalan da iyayyen mu mata suka dinga yi a gida. Tace bari kedai lokacin ai ba a magana amma yanzu ga baba nan kamar ba ayi ba ya gyagije ya zama kamar yaro dashi. Nace wanan leda ta saka mai turmi uku takai wa kishiyoyin ta komai ta saka ma nan na shiga lissafa masu duk muka cire ma wa yanda suka zo sai mahaifiyar Amina don Amina nada tsohon ciki bata samu zuwa ba. Kudi na mike na dauko na bata nace ta cire dubu hamsim taba mijin nata dubu hamsim Khadija ne ta katse ni da fadin itafa ba a cire mata leda ba. Nace ba kinji uncle yace ba tare dake zasu koma ba nasan kuma da gaske yake yi tunda kikaji ya fada. Tace ita dai a cire mata nace zabi wanda kike so ba shike nan ba Rukaiya na ta min godiya nace tadai samu sana,a da zatayi dasu nasan zasu isheki ai. Washe gari ko wani mota ya basu na shan ruwa hanya kusanna lokaci daya suka tashi sai gidan ya koma saura mu kadai a ciki. Sai yan wirin aikin su Nura dake ta faman gyaran gida don tsabatace wuri uncle badai tsabta ba kan don bai son kazanta ko kada shi. ZAINAB IDRIS MAKAWA SEENABU 9/2/20, 11:42 AM - Ummi Tandama: BAHAGGON, , , , , , , , , 🧕🏿6️⃣9️⃣🧕🏿 Ban fasa ja maki Allah ya isa ke ko kai mai fitar min da novel waje ubangiji yayi min bakar isa akan ko waye don gangancin yayi yawa baki da tsoron Allah ko baka da tsoron Allah na roki Allah yabi min hakkina akan wanda ya fitar da wanda ya karanta bai biya ba cikin gagawa. Allah nasan kana amsa min rokona don akan hakkina na nake magana bana wani ba ubangiji na kara kai kuka na gare ka kahana ma mai shi farin cikin da yake nema don shiga hakkina da yake yi. Ranan da bakin mu suka tafi munyi barcin gajiya sosai a gidan sai yamma kowan mu ya ya tashi naji dadin barin khadija da akayi min don zata debe min kewa sosai a gidan. Yaya Saadu na samu ya tsaya min akan ta tsaya din don su mama sun kafe sai da ita zasu koma don baba zaiyi fada idan ya dawo. Sai yaya yace ace shiya ce ta tsaya din haka yasa sukai shiru suka kyale ta badon sun so ba tun dai inna da tasan zaman na ta na iya zama wani alheri a gare mu. Samira bata shigo ba sai bayan kwana biyu da suna tazo gidan nan muka baje muna duba kyaututukan da muka samu ga bukin. Itace da dago tana fadin yanzu ai zaki fara shiga mutane musanman matan yan wurin aikin mijin ki da sukazo maki kara kin san dole suma idan ya samay su kije masu. Nace nasan zamu kwasa da uncle ta wanan fanin don ba ko wani zai bari naje ba tace ana dai son mutum da zumunci ba ko yaushe ki zauna sai dai azo maki ba. Muna cikin hiran ta jefo min tambaya tace anty ki dai bata zo ba bata turo maki sako ba ko nace antyn nan nawa fushi take yi dani har yanzu samira. Ai dole tayi fushi dake tunda baki bar masu miji sun aura ba nace ba haka na bane akwai dai kila abinda nayi mata wanda ni ban sani ba. Samira tayi saurin cewa ga abinda kikai mata nan kuwa Allah ya kyauta nace da ita tare da fadin ni ban son komai ya fito daga wuri na don irin halarcin da tayi min a rayuwa na ba zan iya matawa da ita ba. Ikon Allah yanzu kayan da khadija na take sakawa sai naga sun zama min na yan kyau wanda a da ni bani ko saka irin su don ban ma samay su ba. Haka yasa na bude wardrove dina na fitar mata da duk kayan da nasan ban amfani dasu yanzu don samun ci gaban rayuwa da na samu a tare dani . Wanda Allah yayi min gatan da ban taba zaton zan samay shi a rayuwa na sai gashi cikin hukucin Allah ya wadatani da abinda ko a mafalki ban taba mafalkin haka ba agare ni. Yau da nayi wanka na tunkari dakin Uncle dauke da Abbati a hannu na wanda yasha kayan sanyin da mummy ta saka mai cikin kayan da muka da uncle a kasan Spain. Kayan sun matukar karban jikin yaron don ko wa yaga kayan zai yaba da kyawon su a jikin yaron ya hade da kyau halittan da Allah yayiwa yaron. Sallama nayi tun daga kofan dakin uana ciki kwance ya amsa min na shigo tare da kura mai ido ina mamakin ganin shi kwance har wanan lokacin. Sai da na samu wuri na zauna na fara gaida shi da kwana ya karba min cikin dan dagowa yana kokarin mikewa zaune nace Uncle yau ba aiki ne , ? Murmushi yayi yana kai hannun shi ga yaron haka yasa na mika mai yaron dake hannu din gaba daya ya karbe shi ya rungumay a jikin shi tare da fadin. Bawan Allah ka yafe muna Abbana ba laifin mu bane hana maka abincin ka da mukayi son lafiyan ka ne ya kawo haka gare ka. Wani irin abu ne naji ya ziyarci zuciyana lokaci guda tausayi da damuwa nace tamu kaddaran ratuwan ke ne ubangiji ya bamu ikon ciye jerabawan mu. Amin ya fada cikin lumshe idanuwan shi yana sauke ziciya yace duk abinda nake yi tunanen yaron nan yana cikin raina wallahi. Uncle sai hakkuri ai tunda ma yana shan madara da sauki sosai wallahi yace yana sha sosai ko nace yana sha cikin sanyin murya. Yace ai mu godewa Allah da ya nufe mu da rike zurian mu da hannun mu sai muyi fatan Allah ya raya munashi nace amin Uncle. Dakata yace dani nayi saurin dago kai ina kallon shi yace ni wanan Uncle da ake kiramin ya isheni fa yanzu Allah ya bani da kamar kowa don haka akirani da sunan baban dana. Dariya ya bani nace ai su yan biyu suka sakani kiran ka uncle da sauri yace dama ina son in tambaye ki wai ko madam ta kiraki tunda kika haihu ? Nace eh ranan da na haihu ta kirani da yamma tana fada dani wai ban fada mata cewa ina da ciki ba sai haihuwa kawai taji a wurin daddy. Bata ji ba fatace maki nace abinda ta fada min ke nam yace tun muna Spain na kira su na she da mata zancen cikin ki. Wai may matar nan take nufi ne haka shiru nayi mashi ya sake cewa ko bayan maganan mu akwai abinda ya farune a tsakanin ku na kada kai tare da fadin wallahi ni matsalan komai bai taba shiga tsakani na da ita ba. Doka tasa min in dinga tura mata kudi zata san abinda zatayi min dashi nan gaba kuma ina tura mata da kudin duk karshen wata idan kaba salary dina. May ne ? Ya tambaya cikin dan zaburowa daga inda yake kishingide da yaron saman kirjin shi yana dan shafan bayan yaron a hankali. Nace a hankali ina tura mata kudin kamar yadda ta bukata yace Safiya ashe baki da wayo haka ban sani ba ? Yanzu ko shafiu ku ko khadija suna iya yin wanan wautan da kikayi to bari kiji ni ina baki kudin nan ne don ki tare lalurar ki wanda ba sai kin fada min ba. Na dauka gida kike tura masu suna amfani dashi ashe ke baki san ciwon kan ki ba ban sani ba to bari kiji. Inda maimuna ko ba da ita tunda Allah ya kadara aure a tsakanin mu har da rabo ita bata isa ta hana ba ko ta sa ayi wanan abu ne nufin Allah. Allah dai ya nufa ta dalilin ta zamu hadu idan kuma yaso zai iya hada mu ta wani dalilin bata gurin ta ba. Daga yau na yanke duk wani hurdan dake tsakanin ki da ita har ma da kowa nata idan kina yi don ban son rainin hankali. May ta mayar dani ne wai taga ta biyo ta hanyana bataci galaba na ba shine yanzu ta dawo gare ki . Zan kira mijin ta yayi mata iyaka dake tun wuri ta shiga hankalin ta dani kafin rayuka su baci kada tace ko ban san abinda takeyi bane a baya na sani sarai albarkacin mijin ta da yaranta take ci gare ni. Mun kwasa da ita akanki sosai amma ke baki sani ba don ba dole bane sai kin san yadda mukayi a kanki da ita shine ta biyo ta baya wurin ki tana min yankan baya ko ? Ta nuna min cewa ke ba komai bane na nuna mata cewa ke wani abune mai muhinmanci a gare ni yadda take daukan ki kin wuce nan a gare ne. Don so tayi shawaran komai dole sai da ita zanyi ban isa in ma dan uwana wani abuba ko ke ba ta hanyan ta ba. Ranan ta jini sosai don rufe ido nayi naci mata mutunci ta yadda bata zata zan iya masu ba. Na nuna mata kina da mahinmanci a gare ni fiye da kowa nawa a yanzu da taga hakan ta bai cin ma ruwa ba sai ta juyo tanan din dake. To zanyi maganin ta tasan nafi karfin ta da mijin ta taci albarkacin shi wallahi da yau nasa ta dawo maki da kudin da duk ta karba daga gare ki. Zan kara maki kashedi a kanta kada naji kada na gani na yanke duk wani alaka da ke tsakanin ki da ita daga yau din nan kinji na fada maki ko ? A sanyaye na amsa mashi da eh ya koma ya kwanta tare da lumshe idanuwan shi ya fita batuna ranshi na bace da maganan da mukayi akan anty din. Na dade zaune na kasa ko motsawa daga inda nake shi kuma ya fita batuna sai can na yunkura na mike na fita dakin na barshi da yaron . Daki na koma na samu khadija kwance tana kallon tv dake aiki tana kallon wani series na yan Chaina kin dawo tace min na amsa mata rai babu dadi da eh kawai na bata amsa dashi. Samun wuri nayi na kwanta ba tare da nakara magana ba nasan itama ta fahinci akwai matsala ne sai ta kyale ni taci gaba da kallon ta. A idan nake har barci ya dauke ni ban sani ba ina cikin barci ne naji yana kokarin ta dani daga barcin yana dan jijigan yaron dake dan kuka a hannun shi. Mikewa nayi zaune ina kokarin amsan yaron a hannun shi yace abashi abinci ina ganin yunwa yake ji ya fada. Madara khadija ce ta mike da sauri ta hada ma yaron madara ta karbe shi a hannu na ta fara bashi ya karba da sauri yake jan feeder. Uban ya dan dade tsaye yana kallin yadda yaron ke jan feeder da sauri murmushi yayi ya nufi kofan dakin yana cewa Khadija ashe kin iya reno ne haka ? Dariya tayi kawai bata samu bashi amsa ba hankalinta na ga yaron da take ba abinci saida ya fita dakin na samun bakin magana. Nace dama bai sha ba da akai mai wanka yayi barci shine na kai shi wurin baban shi su gaisa nasan ya tashi ya damay shi da kuka ne ya kawo shi. Hira muka dan fara yi da ita kadan kadan har na dan sake na fitar da damuwa da nake ciki tana mi labarin yadda zaman gidan mu yake yanzu. Nace yanzu da baki koma ba wazai dubi su wasila dake gida tace ai gwago ta fada ma su mama Jummai su koma wuri su da zama kafin ummi ta dawo. Amma kuma nasan ko basu koma can din ba ai mama zata kula dasu a gidan don mama na kokari sosai wallahi duk da gorin da inna take mata akan abinda take yi din. Yunwan da na fara ji yasa muka fito falo in ci abinci khadija na goye da yaron a bayan ta lokacin su gwago suka fito daga dakin da suke suka samay mu a falon. Mummy ne ke fadin ai na dauka kuna barci ne danaji shiru nace barcin baiyi nisa ba muka tashi sallaman akayi kofan shigowa muka amsa. Aisha ne tare da wata makwabciyar ta suka shigo gidan nan aka shiga gaisuwa ta kalle ni tace wai madam wanan irin kiba da kike narkawa fa ? Dariya ne nace ina kiba anan duk na zube yanzu ma haka wallahi banjin dadin jiki na karfin halin kawai nake yi wallahi. Mummy ne tace akasarin mata idan sun haihu dama sai sunyi zazzabi wanda ake kira dahuwan kassa don wahalan haihuwa da sukayi . Kin san mace a wurin haihuwa duk sassanta jiki ta sai ya motsa to wanan motsawan shike haifarwa mata da irin wanan zazzabi daga baya. Kayan da na ware zan bata cikin wanda muka samu daga yan uwa da abikan arxiki nabawa samira nata na Aishan ne dama ya rage shi nace khadija ta dauko mata a daki. Basu dade suka tafi tun tafiyan su na kwanta zazzabi wasa wasa sai da ya kwantar dani dole washegari sai da muka tafi asibiti wuri likitan shi. Magani ya rubuta min da allura akai min yayi muna bayani cewa dole dama sai nayi ciwo saboda jinin da na zubar a wurin haihuwa saukin abin ma don ina samun kulawa yadda ya dace ne. Sai dai in matsa da cin abubuwan da zasu kara min jini a jiki don kada na jirkita da yawa kamar yadda masu irin lalurar ke shan wahala yayin da suka haihu don jinin da ya rage a jikin su. Duk da allurai da maganin da aka bamu sai da na wahala sosai don ba karamin jin jiki nayi ba har na ramay sosai. Wanan raman da nayi shiya daga hankalin Uncle sosai har ya koma wurin likita yace mai babu komai zan samu lafiya haka abin yake wani lokaci. Ai nawa matsalan yana da dama don kafin ciwon ya bugeni sosai an daukar mai matakin daya dace gashi kuma ina kula da shan magani. Na dan fara jin saukin jikina wanda ya koma nake jin shi kamar ba jikina ba ya shigo dakin yana min sannu cikin nuna kulawan shi a gare . Zaune nake lokacin da ya shigo dakin yake tambaya na ko ina jin wani abu yanzu a jikin nawa ? Nadan lumshe idona a hankali na nace mashi banjin komai uncle sai dai jikin nawa ne ban jin karfin shi ko kadan. Kina ko shan maganin kin akai akai nace ina sha na yaune ban sha ba don ban karya ba tukun yace may kike jira baki ci abinci ba har tara da rabi na safe yanzu. Nace bakomai a hankali bakin nawa ne dai banjin dadin shi dan sunkuyowa yayi gare ni yana fadin may kike son kici sai a dafa maki. Kunu da kosai nace mai sai naga ya daga yana murmushi yace khadija taje ta fada ma mummy asa Nura tayi min . Tana fita yace bari ya dauko min fruits in sha kafin a gama kada yunwa yai min yawa a ciki nace uncle banjin cin komai wallahi bakin nawa ba dadi nake jin shi. Ido ya dan tsura min sai yake kai zaune bakin gadon cikin kwantar da murya yace dani ki daure ki ci diyan icce zasu taimaka maki wurin gyaran dandanon bakin ki kai na gyada mai alaman to. Ya mike ya fita yasa aka wanke fruits shida kanshi ya shigo min dasu dakin ina zaune a yadda ya barni lemo mai bawa ya fara bani don zai wanke min bakin nawa yace. A haka dai har na dan ji sauki saboda kulan da nake samu ta ko wani bangare har naji sauki na murmure kamar bani ba. Ranan ina zaune kwatsan sai ga Faiza gidana tazo nayi mamakin ganin ta kwari da gaske tace wai anan abuja ta kwana ta fito lagos zata gida bauchi ne. Nan da nan nasa a cika mata gaban ta da abinci da abin sha muna hira tana cin abincin dake gaban ta labari take bani na anty yadda take zagina wai yanzu na guje ta don ina ganin na samu gidan miji. Ai tasan asiri nayiwa Uncle ya aure iyayyena makwadaita ne sun ga kudi idon su ya rufe wai idan ummi na ta kira ta tana ganin kiran sai taki dauka. Dariya nayi nace anty ke nan yanzu kuma nice na koma abin zagi a wurin ta tace tun yaushe ai na fada maki halinta tun farko shiya kike ganin ina fada maki . Yanzu haka Fati tabar wirin ta uwarta ta dauke ta ta mayar da ita can yobe garin su don yawan matsalan da suke samu akan fati din. Ranan dai a nan ta kwana sai dai ban yarda na fadi komai ba akan anty din don yanzu mutum abin tsoro ne washe gari ta wuce bayan na cika ta da abin arziki . Kwana biyu sai ga yaya saadu yazo yana ce min zai tafi lagos an bugo mai waya jikin gwago da na Ahmed wai ya tsanan ta don haka zai tafi ya dubo ta. Kudi na dauko nace ya kaiwa gwago ya gayar min da ita idan yaje yaso yaki karba amma na matsa mai sai da ya karba don sako ne na bashi. ZAINAB IDRIS MAKAWA SEENABU 9/3/20, 8:54 AM - Ummi Tandama: BAHAGGON , , , , , , , , 🧕🏿7️⃣0️⃣🧕 Tu wuce wanan yaya saadu ban tuna da zancen gwago ba sai da yake da kwana biyu da tafiya ya bugo min waya ya hada mu da gwago wai mu gaisa da ita. Ba yadda na iya shiru ya dan biyu bayan wayan can na ce salamu alaikum ta amsa da fadin Safiya nace naam gwago kuna lafiya yaya jikin naki. Ta cikin wani murya mai rauni ta amsa da jiki da sauki safiya yaya wajen ku kuna lafiya ko nace lafiya muke gwago tace naga sakon ki wurin dan uwan ki na gode Safiya. Nace babu komai gwago Allah dai ya baki lafiya tace amin sai ta kama kuka tana son yin magana amma kuka ya rinjayi maganan da take son yi din. Nikan sai na kashe waya don kada ta kashe min jijiya bayan na kashe ne yaya Saadu ya kirani ya ce kinji gwagon ki ko ga Ahmed yana gaida ke jikin nashi ne ba dadi sosai nace ka gaida shi Allah ya bashi lafiya. Ya san ban amsan wayan shi ke nan yasa ya kyale ni bai hada ni dashi din ba ya tambaye ni yaya Abbati nace yana wurin gwago ta goya shi. Bayan mun gama wayan khadija dake zaune gefe na da mummy suka ce wai amma kina da karfin hali wallahi. Mummy tace ai gara da tayi masu haka na ta barsu da aniyar su ko yanzu Allah ya gwada masu abin su ai. Ni dai murmushi nayi kawai ban ce komai ba sai dogon tunanen da nashiga tun lokacin kuma na watsar da zancen su a zuciya na gaba daya. Haka rayuwa ke ci gaba ga duk mai rai da lafiya cikin hukuncin ubangiji har gashi nayi arbain da haihuwa yaro kuma yana cikin koshin lafiyan shi. Yayi mulmul dashi bazaka ce bai shan nono ba idan ka ganshi don iri kulawan da yake samu na abinci da magunguna da zai bashi lafiya da kuzari. Tun da nayi arbain nake ta shirin zuwa gida kunsan maza da jan fitina amma sai uncle yace ba zan tafi ba sai munje bauchi mun kai ma baaba yaron ta gan shi. Naso tayar da hankali mummy da gwago suka sani gaba sukace ko murai kada na nuna mashi komai yadda yake so in bishi da hakana muje mukai ma mahaifiyar shi jikanta ta gani. Haka yasa na daure ban nuna mashi komai ba da yake tsanmanin zan ce ban yarda ba da hakan daya tsara muna don yasan yadda nake dokin zuwa gida . Wanda tun aure na dashi banje garin mu ba ina binshi a yadda yake sona dashi din don kawai a zauna lafiya. Dole akalan tafiyan yacan za ta zuwa bauchi din mummy da gwago zamu barsu gida sai mun dawo da khadija kawai zamu tafi. Mun shirya tsaba inda ranan jumma, a zamu bi jirgin safe mu tafi kamar yadda ya tsara don har da buki zamuyi na diyan wani kawon shi haka yasa na dauki kaya na alfarma don tafiya dasu. Inda motacin shi na shiga biyu sun kama hanya da tsaraban mu da kayan mu zasu samay mu acan kamar yadda ya tsara din. Mun sauka lafiya inda su Nafiu suka zo daukan mu zuwa gida da motaci biyu mun isa mun samu yan uwan shi mata suna gidan kaf din su sun zo tariyan mu har da Aisha da ta tafi sati daya daya wuce bukin kannen mijin ta. Mun sauka inda suka fito waje taron mu yaron yana hannun khadija har muka isa gidan nan suka karbe shi kowa na nuna kulawan shi akan yaron sai fadi suke Abban mu Abban mu. Suka nufi cikin gida da yaron su kuma suka tsaya muna gaisawa tun a waje part din hajiya baaba muka nufa gaba dayan mu don mika gaisuwa a gare ta. Koda muka shiga mun samu ta karbin yaron tana fadin Allahu akbar yau jinin babana a hannu na haka ina kallo da raina da lafiya na. Muka shigo da sallaman mu muna gaida ita ta juyo gare mu cikin farin ciki tana muna sannu da zuwa tare da fadin ai yanzu kin zama uwar mijina kuma wanan irin mijin da kika haifo min haka? Murmushi nayi ina kai gwiwana kasa dukka guda biyu tare da fara gaida ita cikin girmamawa . Amsawa take yi yayin da hankalin ta ke yaron tana fadin wanan duk gida ya kwaso wallahi ana fada ban yarda ba sai yanzu dana gani da ido na. Uncle ya ce hajiya mun samay ku lafiya tace sannu kai dai dan Albarka ai duk na rude da ganin wanan mijin nawa da Allah ya nuna min zuwan shi da raina da lafiya na. Sai da ta jagula yaron anty Suwaiba ta karbe shi sannan ta dawo da hankalinta gare mu sai lokacin taga khadija da muke tare tace a a da bakuwa kuke ashe ? Da ganin wanan yar uwar Safiya ce don kama ya nuna kanshi basai antambaya ba wanan kamar uncle ne ce kaunar ta dake wurin ta ne ai tunda ta haihu suka zo suna take nan tare da mu. Gaisawa sukayi da khadijan tare da tambayanta yaya hanya ta amsa cikin ladabi da lafiya lau hajiya. Juyawa tayi tana fadin ku kawo masu abinci mana kun tsaya kuna shiriri ta haka suka ce hajiya baki ce a dauko masu bane ai. Yau ga tsiya tace dasu abincin ma sai nace ku kawo masu zaku dauko masu uncle ne yace hajiya bar abincin nan yanzu a dai kai muna can part din mu zamu fi jin dadin ci acan. Nan aka shiga kwasan abincin zuwa part din mu dashi shi kuma suka ci gaba da gaisawa da mahaifiyar tashi. Nan na juya wurin Aisha nace mutanen bauchi ke nan ina yaran suke tace suna can gida na barsu banzo dasu ba yau. Hiran mu muke yayin da hajiya da dan ta suna can zaune a inda muka barsu suna magana a tsakanin su. Karshe ma sai su Aishan suka jamu zuwa cikin uwar daka nan muka shige daki guda daga cikin dakunan part din nan dai muka fara hira tana cewa ai ta godewa Allah da muka iso yau gobe ne bukin gidan su sai muje mata karan buki da sauran yan uwa. Kiran da hajiya tayi ma suwaiba sai gata ta dawo tana fadin wai mu fito zuwa part din mu uncle yana son ya huta haka muka fito muka nufi can har lokacin yaron na wurin hajiya tana bashi madaran da khadija ta hada mashi. Mun shiga part din komai neat kamar muna cikin shi ko yaushe yasha gyara sai kyali yake yi nan na aje handa ban dina Aisha ta biyo mu da dan troley din da muka riko. Abincin da aka aje muna muka fara zama ci inda masa ne wanda yasha mai sai kyali yake fari tas a cikin kula sai miyar kassan rago da akayi da ganye alaihu sai kamshi ke tashi ga ferfesun kaji dayaji kayan kamshi yana tashi shima a kulan shi. Nan dai muka taru muka fara cin abincin sai santi kowan mu keyi kan dadin masan dake gaban mu uncle ne kawai bai magana sai murmushi yake muna kawai. Mun ci munyi kat ko dinban ferfesuf din bamuyi ba ni da uncle sai khadija ne ta dan sha kadan ta ture don ta koshi da masan da taci . Yaron ne aka shigo dashi yana kyallara ihu kamar wanda wani abu ya sama karban shi nayi ina fadin yanzu haka fitsari yayi yake damun shi haka yake yi idan ya bata pemppers din jikin shi. Tube shi nayi gaba daya na cire mai tufafin dake jikin shi don in sauya mashi wani na shan iska nagama shirya shi na kara mai madaran tare da bashi grive water yasha sai gyatsa na bawa khadija shi ta goya. Kwantawa nayi don in huta don tafiyan safe da mukayi barci ne taf a idona lokacin shima uncle ya kwanta bai fita hanin kowa ba a lokacin don yace yana son dan hutawa ne . Koda na farka khadija na kwance sunyi barci da Abba a jikin ta haka yasa na dan mike a hankali kada na tayar dasu daga barcin dakin . Na samay shi yana barci ga sanyin AC ya karade dakin zuwa nayi wurin shi na dan taba mai huska a hankali sai ya bude ido nace lokacin zuwa masallaci yayi kada ka makara. Salati yadan yi tare da juyawa yana fadin badon kin shigo ba da na makara don naji dadin barcin nan sosai wuce wa nayi bathroom na hada mai ruwan wanka na dawo ina fada mashi ruwa ya hadu. Ok kawai yace na juya zan fita daga dakin yace ai na dauka za a bani goron jumma a ne kuma sai zaki fita . Na juyo da dariya na nace kai uncle har a garin mutane ba a bakun ta na fice ina dariya don nasan in nayi sake bai da wasa wirin wanan harkan. Wanka nayi nima na sauya kaya a lokacin sai gashi ya shigo cikin wani farin yadi mai laushi da taushi yana daukan ido da hular shi a hannu yana gyara karata da kyau. Wayan shi ne tayi kara ya dauka su musa driver ne suka iso suke sanar dashi zuwan su tare da tambayan ina za a nufa da kayan. Yace su shigo dashi part din shi nan ya juya zuwa wurin su yana fadin daga can zai wuce masallaci ne nayi mai a dawo lafiya. Lokacin khadija ta falka bayan fitan shi ne tace sai yanzu masu motar suka iso garin kai amma akwai nisa ashe haka ? Kodon da jirgin mukazo mu sai naga kamar ba nisa wallahi nace kema kin san ai da nisa mana zaki hada tafiyan mota da jirgine. Shigo da kayan yasa na fito falon ina gwadaasu inda zasu zube muna kayan don ba karamin tsara muka lafto masu ba wanda zamu raba har uncle na fada wai kayan sunyi yawa haka. Sallah na dawo na tayar don lokaci ya gabato ina son inyi nafila kafin jumma a din sai da na idar na juya wurin khadija dake kwance har lokacin nace hajiya sallah fa. Ta nuna min yaron dake saman hannun ta kwance wai kada ta tashi yaron ya motsa na watsa mata harara nace yanzu don kada ya tashi ne bazaki je kiyi sallah ba. Tana mikewa yaton na wani irin zabura ya fara dan shure shuren kafa yana dan kuka sama sama nace ashe aiki ya ganku kuda kuka koya mashi hakan ? Nikan ba wanda zai hanani barci yanzu kuka yake sosai dole nabar adduan da nakeyi na kamashi ina lalashin shi. Dan shiru yayi dole na goya shi a karo na farko tunda na haife kasan cewa su mummy da gwago ke faman dawainiya dashi a gida. Ni iyaka na dashi in dan dauke shi inyayi koka kuma in mikawa mummy shi su karata can amma kasancewa yau basu kusa dole reno ya dawo kaina. Khadija na fitowa bayi wanda nake ganin wanka ta tsaya yi ta kalle mu ta tuntsure da dariya tace ai na fada maki bai yarda wallahi ya saba da dumin mutum a jikin shi. Idan bayaji mutum a tare dashi ba bai yarda yayi barci nace ai duk ku kuka shagwabashi dake dasu mummy yanzu gashi yazo nan yana wahalda mutane. Sallah ta tayar muryan Aisha naji tana fadin ina matar gidan nan take ni zan tafi nawa masauki yanzi yaya gobe din in sa rain zuwan ku ne cika muna taron buki. Allah ya kaimu nace da ita har zaki tafi ke nan gashi ko da ina son zaki tayani fitar da tsaraba wa mutane. Sai naga ta kalle ni ta tuntsire da dariya tace yau Allah ya kamaki mummy bata kusa ai dole baban mu ya samu baya ya hau. Dan tsaki naja nace ai uwar shi ta idar da sallah ta karbe shi su da suka saba mashi da jiki nace muje falo ki ga kayan da muka zo dashi din don yanzu su musa suka iso dasu suna can sun tafi masallaci da uncle. Falon muka fito ta kalli kayan tare da fadin dan kari duk wanan uban tsaraba haka safiya nace to kin san mun dade bamu zo ba ai. Nan muka fara aikin in duka yaron yace baison dukawa sai ga khadija ta fito daga daki tana zuwa ta karbe shi saman cheast din ta ta dora shi tana lalashin shi. Nan naji dadin aikin da muke inda muka kwashe sauran zuwa wani daki tace ko da daga baya zaki tuna wani ba a bashi ba kin ga sai a diba anan. Sai bayan mun gama ne ta wuce har waje muka fito rakiyan ta da motar ta tazo don haka a ciki muka saka mata nata tsaraban nan muka tsaya take fada min kishiyar ta lami tazo tana nan sun hada kai da uwar gidan ta suna kulla mata muna funchi. Nace rabu dasu Allah ya fiso duk abinda zasuyi basuyi kamar Allah ba ai tace wallahi da da yaya baya kulamu an samu abin fada yanzu kuma da yake muna ance ina muka fito Mun dauki lokaci muna magana tsaye a waje nace taje ta kama yaranta dake gida tace wallahi nasan suna can yamzu wuri wuri suna nema na mukayi sallama badon mun gama gulman mu ba ta wuce tana jaddamin batun zuwa na gidan su gobe. Ciki muka koma muka kwaso ma hajiya tsaraban ta zuwa part din ta su kuma su anty suwaiba duk wanda zai tafi na bashi nashi tsaraban. Sai dare su uncle suka dawo gidan lokacin muna falon hajiya baaba muna hira don gidan an watse sai mu da tsirarun mutane wa yanda ke gidan wurin ta muka rage a gidan. Yashi alokacin ya cire babban rigar dake jikin shi ya rage daga shi sai yar ciki a jikin shi tafiyan shi kawai ya isa ka gane a gajiye yake a lokacin. Sannu da zuwa mukayi mashi ya isa gaban mahaifiyar shi yana gaida ita inda ya juyo gare ni yana fadin . Madam yaya bakunta nayi dan murmushi nace ai mun sauke shi yanzu mun zama yan gari ko dariya yayi yace yana zama na gaji wallahi. Hajiya ta tambaye shi ina ya shiga haka shiru shiru yace yarima ya jani muka dinga zuwa ziyara tsufin abokan mu har yamma yayi muna haka. Tace ai hakan na dakyau ba karamin lada kuka samu ba wallahi ai ziyara nada kyau mutane ne basu gane ba. Ban iya magana ba don hajiya na wurin ina jin kunyanta don haka ma sai na kawar da kaina gare su muna hira da su khadija mikewa nayi. Abinci na mike na dauko mai tare da aje mai komi da zai bukata a wurin shegewa mukayi can wurin yaran hajiya don mu basu wuri su tatauna da mahaifiyar shi. Muna shiga tace mashi babana harda wani uban tsaraba haka mai yawa kuka zo wa mutane dashi bayan kullun dawainiyar ka bai karewa gare mu. Yace hajiya ban ko san ta hada tsaraban nan ba sai gani nayi ana sakawa a mota tace yanzu duk itace da wanan dawainiyar haka , ? Shiyasa ake son samun mace tagari wacce zata dinga kare wa mutum mutuncin shi dana yan uwan shi wanan yarinyar gata dai karama amma kuma tana da wayau wallahi tasan darajan mutane sosai. Sai bayan goma na dare muka fito zuwa shiyan mu bayan mun yi shirin kwanciya ne nake fada mai zancen zuwa gidan su Aisha buki da muke son yi gobe. Yace mantawa nayi Aisha na garin nan dana dage tafiyan mu sai wani lokaci don nasan yawo zata jaki ku dinga yi a nan niko kin san ban bukatan hakan ko. Shiru nayi don idan na tanka zai samu hanyan da zai hana fitan gobe wanda ba zaimin dadi ba har Aishan bayan nayi mata alkawari. Jin nayi shiru ne ya kyale baici gaba da maganan ba sai ji nayi ya jawo ni zuwa jikin shi nace a raina nan kafi auki dama. Yana fafin kima ganin khadija zata iya kwana da yaron nan kuwa nace ita tace ai a barshi tunda ba nono yake sha ba. Yace tana da kokari wallahi shine hikimar da nayi ai wirin cewa a barta don nasan zata temaka maki ta hanyoyi da dama. Washe gari tun tashin mu gyaran part din mu mukayi muka fita zuwa gaida hajiya din mun dan jima wurin ta har da karyawa mukayi kafin mu dawo mu fara shirin zuwa gidan Aisha wurin buki inda yan uwa zasu taro sai mu dunguma mu tafi gaba dayan mu gidan bukin da abinda za a kai mata don da autar dakin su maigida cikin bukin. ZAINAB IDRIS MAKAWA SEENABU 9/5/20, 11:23 AM - Ummi Tandama: BAHAGGON RAYUWA, , , , 🧕🏿7️⃣1️⃣🧕 Uncle ya shigo dakin da muke wanda shine kamar mallakina a gidan shi na bauchi sai faman shiri baby khadija keyi acikin wani riga da wandon maza duk da kayan yara maza ba a faye samun wani sauyi a cikin su ba iya ka dai wando da rigace kawai kayan adon su. Amma shi wanan din da uncle ya sawo yazo muna dashi yana da matukar kyau sosai don gaskiya ya hadu sosai. Ina zaune gafenta ina waya da ummin mu da suka dawo bamu samu ganin su ba tana bani labarin taba inna tsaraba ta dawo mata dashi wai bata so saboda anyi rikici da ita anka yara tsakanin su. Nace yanzu ummi ya kamata ace kin fahinci waye inna ita kullun gari ya waye tana neman wanda zata sauke masifan ta ne akan shi. Ban karasa maganan ba iya abinda yajike nan shigowan shi sai na kara da fadin ta kyale ta kawai ta aje kayan indan ta sako daga fushin ai zata dawo ta karba ne. Maganan da yakewa khadija dakewa yaro shiri tana fashi wasa yace zaki koya mai kiuya yazo bai san kowa ba sai ku ko? Katse wayan nayi da ummin nace uncle fita zakayi ne yace eh daga can yana son ya samu halartan daurin auren gidan su miji Aisha din da zaayi. Nake cewa zamu tafi dasu anty suwaiba idan sun zo yace yaji kawai nasan fitar ya zama mai dole ne kawai ya barni kudi ya fida yana miko min wraper din yan diri biyar biyar har biyu tare da fadin a watse lafiya. Godiya nayi mai ya miko ma khadija dake zaune itama sai dai ban diba a lokacin balle in san ko nawa ne ya bata. Yadan dauki Abba yana mai wasa tare da fadin kayan nan sun matukar karban ka babana nace anbinda khadija take fadi ke nan. Ya aje yaron ya fara tafiya ya juyo yana ce min sai kuyi amfani da dayan motar don ni zan fita da dayan ne. Makuli ya miko min tare da tambaya ko ya bar muna driver ne nace ai zan iya ja kada ya zauna a takure a cikin mata. Murmushi yayi yasa kai ya fita mukai mashi adawo lafiya yace amin fitan shi khadija tahau murnan kudin da ta samu awurin shi ta shiga kirgawa cikin murna. Nice na kawar mata da murnan da jefo mata maganan su ummi dake ci min rai tace ba dai ummi ta karbi kayan ba nace eh ra karba tunda har daki ta kai mata. Tace ai shike nan mana inna fa sune basu san halinta ba har yanzu gurin ta shine kada ta ga wani yafi ko ta wullakanta mutum kan abinda bai kai ya kawo ba. Muna cikin maganan su anty suwaiba ta shigo nan muka shiga gaida ita take fadi bamu shirya ba don mu samu waliman da za a yi . Aisha tace ta bugo min waya ban dauka ba sai na tuna wayan na guda yana dakin uncle na barshi acan tunda safe ban dauko ba . Nace ai wayan yana dakin uncle na barshi yana caji a can tace tana tambaya ko anbarki zuwa gidan nasu nace mata mun rabudake jiya akan zaku zo din ai. Nace tasan halin dan uwanta shiyasa take ganin kamar ba zamu zo din ba tace ita fa so take muje mu cika mata daki lami tasan tana da yan uwa da yawa. Aiko zata ga gaiyya yau don kowa zai tafi yar dariya nayi kawai nace ana dai zuba kishi a gidan su Aisha kan. Tace ai yanzu haka ne ako ina kedai sai idan baka da kishiyace ka huta da wanan kwamacalan rayuwan. Ba birni ba ba kauye ba duk abin daya ne wallahi nace lokacin muke da kishin fili akeyi bana boye ba irin na iyayyen mu da ya wuce. Fita tayi da Abba a hannun ta tana jadda muna muyi mu shirya don Allah idan sauran sun iso sai su samay mu a can. Nace yanzu anty gamunan fitowa wani buje da riga na saka dan dubai wanda tsayawa fadin shi bata lokaci ne sai gyalen su mai kyau ga taushi da sanshi yana lefewa ajikin mutum. Takalma da jakka da suka dace da kayan jikina takalman mai tsones da hill sai daukan ido yake yi don kyau da har handbag din shi sai sarka da awarwaro dana zuba a jikina masu tsadan gaske. Turare na shafe jikina da gyale na dashi itama khadija shigan ta na yan matan zamani ta yi don shigan yayi mata kyau sosai a jikinta. Mun rufe part din na kai wa baaba makulin koda uncle zai shigo bamu nan khadija na rataye da dan jakkan da muka zuba kayan Abba a cikin sa maikyau dashi. Muna shigowa kallo ya koma kan mu a falon na baaba inda yan uwa duk sun hadu bamu jima ba muka fito don tafiya don mutum uku ne basu iso ba a lokacin. Hajiya baaba tace mutafi zasu samay mu acan haka yasa muka mike tafiya gidan su Aisha din gaba dayan mu dake falon. Mun fito alokacin sauran sun iso aka tsaya don motacin su anty suwaiba dake wurin zamu tafi dasu a zaton su da tasu zamuyi amfani dukkan mu. Nan nace da suwa zamu tafi a motar mu motar suka kalla gaba dayan su suna fadin au da taku motar zaku tafi ashe nace eh kawai. Yan matan suka ce a tamu zasu tafi don haka na bude na shiga suma suka biyo mu a jera mota hudu muka nufi unguwar su Aisha din inda a tsohon uguwar su gidan yake. Suke gaba muna bin su a baya har muka kai gidan dake can unguwan su tsoho wurin a cike yake da jamma, a maza da mata saman kujeru roba kungiya kungiya. Duk sai kallo ya dawo gare mu a wurin wuri muka samu muka tsaya inda ba mutane da yawa mun fito muka kulle motocin mu. A lokaci daya muke shiga gidan wanda da alama gidan yawa ne mai part aciki lungu lungu har muka isa wani wanda yafi yawa anan dakunan su Aisha din yake. Kafin mu iso labari ya iso mata na mun iso duk mutanen sai kokarin kallon mu suke suna aiki Aishan ne ta ratso mutane tana muna sannu da zuwa inda bata bari mun shiga daki ba sai da takai mu wurin uwar mijin su a gidan. Nan muka shiga dakin dattijuwar ta tare mu ba yabo ba fallasa a fuskan ta tare da tambayan hajiya baaba muke tana gaida su. Har mun juya zamu tafi take cewa ance har da matar Sulaimana a ciki ko itace wanan yar farar ko tana nuna ni cikin su. Aisha ne ta bata amsa da eh tace ai naga alama mukan muka fita zuwa dakin ta anan muka ga lami a kofar su suna hada zobo na buki. Tunda ta dago ta kalle mu tayi muna sannu da zuwa ta dukar da kai kasa tare da ci gaba da abinda takeyi bata sake dogo kai ba har muka shishiga dakin Aisha din. Wanda a falo muka zube mutanen dake cikin dakin kafin mu shigo suka firfito daga dakin a kujaran dake fuskantar waje na zauna don haka ina iya hango wanda ke waje suna gittaiya a inda nake zaune din. Aisha tazo muna gaisawa da ita tama rasa da wanda zata gaisa a cikin mu a lokacin don mu goma sha biyar muka zo gida cika taron buki. Nan ta juyo kaina tare da dafani tace madam kin kuru da kika zo da wanan mijin naki mai rowan matar shi wa mutane sai nayi masa yajin wata uku gidan shi ban leka ba. Dariya nayi ina kamota nace aida kin ga nazo bikon ki har wata uku bakizo inda muke ba da zama bai ganin ba. Tashi tayi tana dariya ta fita daga dakin mu kuma akaci gaba da hira irin na mata idan an hadu wanda gulman Lami aka dauko da uwargidan Aisha din. Ido na zuba masu ina sauraren kalamin kowacen su a lokacin don har yanzu ba sabawa nayi dasu sosai ba shigowan Aishan daki anty suwaiba ke ce mata ashe lami tazo ne ? Tace gashi ko jiya ina fadi cewa ta shigo tun shekaran jiya da kawayen ta suna nan sai feleke suke muna a gidan. Ido na kurawa Lami din a inda nake zaune don ina iya hango su daga zaunen da nake din kafin wani lokaci ancika muna gaban mu da abinci kala kala na nau,in bukin da sukayi. Nan aka baje ana ta faman ci ana raha kamar yadda mata suka saba idan aje buki sai anty suwaiba ne ta farga bani cin komai a wurin take tambayana. Murmushi nayi ina fadin a koshe nake sai dai idan anjima din kila zanci maryam ta ce kin san fa su ba abinci suke ci mai yawa ba yan kaidan cin abinci ne kada suyi kiba. Dariya nayi kawai tare da cewa kai anty maryam zolaya ne kuma haka Lami ne ta shigo dakin tana gaida mu sai raba ido take a kan mu tana raba ido da alama wani gulma sukayi a wajen tazo gani don hankalina na gare su da suke maganan a waje. Nan dai ta juya tafita tabar dakin don ta gama ganin abinda tazo gani din a cikin mu naga ta koma tana magana da sauran abokan hiran nata. Munkai awa daya da rabi aka fito don yin walima bamu fito da wuri ba don har an fara waliman munka fito wuri ta tanadar muna daga can baya inda matan da muka samu a wurin idanuwan su ya dawo a kan mu kamar ba walima akeyi ba. Mun zauna muna sauraren walima hankali na wurin matar dake muna waazi akan aure inda wasu matan ke gulma suna dan leken mu lokaci lokaci. Zuwan mu wurin ya hana Lami da kawayen ta shakat a lokacin don ji take kamar ta bada umurni a kore mu a gidan bukin don duk wani ahurin da ta shirya ma bukin don taso ta gwada ma kishiyoyin nata ta zarta su ne. Amma sai taga cewa Aisha yanzu ta mata zara a ko wani fage duk da bata aiki itace mai aiki da uwar gidan su . Bata san cewa uncle yanzu yanawa yan uwanshi ihisani ba duk wata da dan abinda ya ware ake basu suna samun na kashewa. An tashi walima lafiya an raba snack's da drinks a wurin da aka mika min da sauri yaran da mukazo tare dasu suka karba daga hannun mai rabawan. Ciki muka koma inda wanan karon ban zauna a falo ba kuryan Aisha na shige nida maryam muka baje saman godon ta daya sha gyara nan wasu suka shigo sai firan yadawo kuryan dakin. Muna ciki ne mijin ya shigo gaida mu har kurya inda nake yana fadin hajiya safiya ashe kun samu shigowa yana ta min godiya don ya dauka bukin ya kawo mu muma. Yana fita yake tambayan abba nace yana nan falo wurin yan mata nan ya fice maryam tace dan iska mai ladanin shegu ai dole yazo gaida ke ya samu gurin tatsa yanzu yadda yake so. Dariya nayi mata nace kaji min mata tatsar may yake yi kuma tace da ba gori suke hadewa suyiwa Aishan ba yanzu daya ga akwai ci shine babu kunya yake wani ashe kunzo ne ? Aisha da ta shigo taji tana zagan mata miji tace wa ake zagi tace mijin ki mana da baida kunya nake zagi. Tace wanan shigowan dayayi gaida ku yanzu sau yaja fitina a gidan nan gun matan shi da mahaifiyar shi in ba ai hankali ba. Nace gaisawan kawai kuma muna gidan akai sallah mun yi sallah a dakin ta sai bayan mun idar aka shigo muna da abinci . Jeloup yaji hadi sai tuwo da miyar taushe nace aban tuwon shi zan ci sai gashi an zubo min da yawa a plate nace wai anty kubara ina zan kai wanan abincin haka maryam tace abarshi muci tare. Mun zaune akace mu fito wurin wanke amare nan kowa ta gyara muka fita dakin Abba ke ta kuka wanda nasan zafi ne ke damun shi. Muna dakin sai da mukayi mashi wanka khadija ta saka mai wasu kaya muka fito inda ake wasan a fitar da amare a tsakiyan fili ana ta zuba masu kudi suna rawa a hankali. Anty suwaiba tace muje muyi wa amaren liki take muna kwantancen kaunan su Ado din mijin Aisha din muka saka Aisha gaba muna binta a baya haka muka ratso tsakiyar filin nan kallo ya dawo gare mu . Mun zuba mata kudi sosai inda yan matan bukin ta ke kwashewa suna zubawa a wani jakka. Nan wuri ya dauki sowa da fitowan mu sai gulma mata keyi ni dai na fito na zauna a ida muka tashi don a tsawale nake gurin. Abba khadija ta miko min tana fadin tana zuwa na karbi yaron da duk wahala ya jirkitar dashi a lokacin maryam ta dawo tana zama nake ce mata mu koma ciki in kwantar da yaron ta suri jakkan ta muka shiga ciki. Mun dan jima zaune sai fa su anty suwaiba sun shigo na dan make murya nace anty gida tace yanzu nima maganan da nakeyi ke nan nasan baaba tana can tana fadan rashin dawowan mu akan lokaci. Haka yasa muka mike don haramar komawa gida inda sai da aka nemo muna yan mata muna doso gida naga motan uncle a waje alaman yana gida ke nan. A falon gidan da ban daka ana amfani dashi ba naga takalman maza wurin zube ba iyaka haka yasa nasan da mutane yake lokacin. Muna shiga ina gaida baaba tambayan mukulin mu nayi ta miko min tana fadin mijin ki yazo yana fada wai may kuka tsaya yi tun da safe gidan mutane nace dama nasan sai yayi fada don mun dade. Nan na fita zuwa part din mu na barsu nan muna shiga na shiga cire tufafin dake jikina don wanka nake son yi sai dai ban shiga ba na tsaya tube Abba da har yanzu fita yake yi fanka na dan sake mai da ac sai yayi shiru ina fitowa na kashe fanka na bar mai ac din. Zaune nake kafin magariba yayi nasa wani dogon riga na shan iska a jikina sai gashi ya turo kofan khadija na kwance da Abba saman kirjin ta tana dan buga bayan shi a hankali. Kallo daya nayi mai na hango fitina a kwayan idon shi gaishe shi muke da kyat ya amsa ma khadija yace sai yanzu kuka dawo ? Zan yi magana ya tare nan ya haufada har yagaji ya fita sai bayan ya fitane khadija ke fadin ashe haka yake da fada ? Nace kadan ma kika gani don ya ganki ne baiyi fada sosai ba kuma bai son abashi hakkuri shiyasa kikaji na kyale shi ai. Mun idar da sallah muna zaune muna hiran bukin ne maryam ta shigo muna da ledojin bukin a hannun ta na juya gun khadija ina tambayan zataci ne tace a koshe take gaskiya nace maryam kije dashi ku kara ko kin barshi nan ba ci za muyi ba. Tana fita sai gashi an shigo muna da abinci na karba na aje saman dining table din dake part din nace mun gode kafin ya shigo na gyara wurin ya shigo har yanzu fadan nan a fuskan shi. Don haka ban wani zure mashi ba don sanin hali da nayi raban dai haka muka kwanta yana hasale dani a ranshi washe gari na fahinci Abba baijin dadin jikin shi ne don da dare koka yayi tayi sai da khadija ta tadani na bashi magani ya sha nakoma dashi dakin uncle muka kwata dashi can. Ranan kan nasha fada sai da nakai ga yin magana nace uncle a cikin taro mukaje fa kana ganin zan dawo na barsu can ne ni kadai na dawo gida ? Ya dauki yaron yafita dashi sun dauki lokaci basu dawo ba sai can gashi da magani a leda yace a bashi yasha idan ya falka daga barci. Tunda naje gaida baaba da safe ban koma part din ba ina cikin barci naji muryan ta a wurin mu tazo duba jikin Abban tace uban shi yana ta fada wai kun kwaso mai zazzabi a gidan buki. Murmushi nayi nace haka yace min har yana fadin wai zamu koma abuja idan banyi hankali ba. Murmushi tayi tace kyale shi kinji haka dai ya fada nace mai ya taba ganin yaron da aka haifa bayi ciwo ba ai da shima baijin dadi hakan don ranan da zai yi ba za ayi mai kyau ba. ZAINAB IDRIS MAKAWA SEENABU 9/6/20, 10:18 AM - Ummi Tandama: BAHAGGON RAYUWA, , , , 🧕🏿7️⃣2️⃣🧕 ZAINAB IDRIS MAKAWA SEENABU KU, , , Duk da bakunta muka zo amma bai hana uncle sheri ni ba a gaban kowa akan bukin gidan yar uwar shi da muka tafi har khadija ta fahinci bamu cikin dadin rai dashi. Sai dai yazo ya duba dan shi yadan yiwa khadija magana ya fice dakin batare da ya kalli inda nake ba a rana ta uku yashigo duba Abba da ke kwance saman gado yana ta wasa irin na yara. Nikuma ina wa khadija kalaba a kan ta ya shigo ina kwana khadija tayi mai ya tambaye kin tashi lafiya ta amsa mai da lafiya kalau. Yadan yiwa yaron wasa ya juya ya fita ajiyan zuciya na sauke bayan fitan shi daga dakin har tana iya jiyo ni lokacin. Muryanta ne ya katse ni ga dan tunanen da na fara a lokacin tana cewa wai anty mijin ki fushi yake dashi haka ne ? Tun dan maganan fitan nan yakewa fushi haka naga ko abincin da ake aje mai baya ci haka yake fita ya bar shi anan nace a gun hajiya yake zuwa yaci ai. Ashe haka yake da fushi anty ? Na sake sauke numfashi nace matsalar shi ke nan wallahi khadija ni abin na damu na ko an bashi hakkuri kamar zugashi mutum ke yi. Tap ai irin su ko wuyar zama gare su may acikin wanan dan maganan don Allah da zai rike haka kuma fa bukin yar uwar shi ai muka je. Nace wallahi haka yake khadija sai kiga magana bai kai abin fushi ba amma sai ya saka a ranshi har ka gaji da fushin. To kema ba sai ki koya ba idan ya hau ki hau sai ai tayi nace ban taba gwada hakan ba ina dai iya kokarina naga ya sauko daga fushin nasa ne. Aiko ki na da aiki to wallahi bari kiji abinci ma yanzu idan an kawo mayarwa zance ayi mun koshi kuma ba zamu sake fita ko falon hajiya ba indan yayi magana in baki iya bashi amsa ni zan nashi ne. Yaya zai kawo mu garin mutane kuma yasan din shi muka zo zai kama wullakanta ki haka a gaban kowa. Itama mahaifiyar tashi bazatayi mai magana ba wanan abu yaki ci yaki cinyewa kamar cin kwan mahaukaciya. Barshi haka muka saba da kan shi zai sauko ai tace wallahi sai mun gwada maza fa sai da harbi yanzu idan yana takama dashi ne aikema kina takama da kimar ki ta mata don Allah ki kwantar wa kanki yanci . Idan ya hau kifishi hawa aga wa zai wahala ko dakin shi kada ko koma zuwa idan nashi ya nemoki ba. Ni wai auren Ahmed ya mai dake haka ko may ko dama haka kike han sani ba don wayau na baikai in gane bane. Nifa yanzu ko a kidan mu na koyi abubuwan zaman aure da dama wallahi zan iya zama cikin mata uku in tashi tsaf dasu. Dariya ta bani har nakai mata dan gwara a kai tare da fadin na raba ki mata uku wasane kin kuwa san kishin yanzu khadija. Tace tsab kuwa wallahi na miji idan baka wana shi sai ka koma shata, lalaganshi a gaban kowa yana iya muzanta ka ji fa jiya gaban su anty suwaiba ya disga ki. Nace ai shi bahagon mutum ne ga dadin zama ga wuyan zama dadin shi kawai idan yana cikin dadin rai da kai idan kuma ya hau abin ba dadi duk nakan tsawala ne wallahi. Kowa ya mashi darasi aike ma mutunce kamar kowa kina da inda kike da ranan ki bawai kudine zai ba mutum abinda yake so ba ko yaushe. Ni ba don kudin shi na aure shi ba don rifin asirin kaina da samun inda zan fake ne tace sai kuma akace bazaka san darahan na tare da kai ba nace kai khadija ummi ke nan . Tace ban son abin haushi ne wallahi shi daga ma kin rufa mai asiri ya tsufa ko kwai baka aje ba ka samu mata yarinya ke idan lafiyan ki kalau yadda kike nan ba sai kin darje kin samu miji ba na zaba. Ji yadda kika koma kamar wata matar gwauna can dake kin yi wani kiba kinyi jajir duk inda kika shiga abin kallo ne ga mutane baki da inda za a raina ki in ba wurin ilimi ba. Dangwara na kara kai mata nace badai ina da na zuwa lahira ba ashe ko ina da ilimi don may yafi kana da karatun ka na Allah dadi. Nifa abin da yasa kika ga ban wani damuwa da karatun ba khadija na ga dai har guda nawa duniyan take a yanzu dai ban rasa komai ba nasan kuma idan karatun zan yi shi zaita hada mu fada kishin shi. Don haka ne kawai na rungumi aure na na zauna dakina tunda ban rasa ci da sha ba da sutura tace ai shine na gani tunda a lokacin kowa gani yake mutuwa zaki yi amma yanzu gashi har ana mantawa ma da akwai wani matsala a tare daku. Shi wanan ma bai ishe shi ba har sai yayi wani fushi kana cikin irin hali haka na ubangiji. Sai naji maganan ta na shiga dama mun je gaida baaba da safe tun lokacin bamu kar fita daga part din ba akwai drink's da su kayan tea a wurin mu da dabun nama shi muka yini ci don ko da aka kawo abincin rana sai nace a mayar abawa mutane mun gode a koshe muke mu. Ga na dare ma haka nace a maida kar ya baci mun koshi ina gama sallah ishai muka rufe dakin mu anan dakina wirin khadija na kwanta. Ya dawo sai mahaifiyar tashi ke fadin yau ko matar ka lafiya suke daga ita har kaunar ta dake zuwa wurin yaran nan hira ba wanda ya leko mu tun safe. Abinci ma ankai masu suka ce a dawo dashi sun koshi ban san may sukaci ba ka bincika min su don Allah. Koda ya shigo part din mukan har munyi nisa da barci a lokacin a zaton shi ina dakin shi kwace don wutan ko ina a kunne yake. Ya kashe wutan ya ya shige yana waigen kofan dakin mu don yasan yanzu khadija tayi barci ko ba daman ganin yaron shi. Yana shiga dakin duhu ya ziyarci idon shi da kyat ya nemi makunnin wuta ya kuna haske ya gauraye dakin lokaci guda yakai duban shi saman gado don a cike ya shigo ya sauke min fada rashin kashe wutan falo da ban yi ba na kwanta abin namu kuma ya karu. Har ya na shirin shi yana yi yana kallon kofan daki har ya gama ya kwanta ban shigo dakin ba har ya kwanta yana faman juye juye saman gado don bai saba kwana shi kadai ba sai tare dani. Yau kuma ya rasa dalilin kaurace mai gaba daya danayi ga hajiya tace tun safe bamu ci abincin gidan da masu aikinta ke girkawa ba a gidan gaba daya. Nikan ina dakina mun baje a gado sai sharar barcin mu mukeyi duk da hankalina kafin inyi barci yana gun shi. Da safe ma da muka tashi ban shiga wurin shi ba har ya shirya zai fita komay ya gani sai gashi dakin namu. Kwace nake kishingide sai Abba dake wasa kusa da cheast dina saman gado yana gwalanniya iri ta yara yana faman har ba kafafuwan shi sama dayan yatsan shi na rike a hannun na . Khadija na gefe saman gadon tana kallo a wayan ta jin sallaman shi yasa ta dan dago tana kallon shi tare da fadin yaya ina kwana ta mayar da kanta ga kallo kafin ma ya amsa. Ina kwana nima nace mai daga inda nake kwance rigingine ban tashi ba kamar ba zai amsa min ba sai naji ya amsa a wani irin yanayi. Ban kawar da idona gare shi ba yadan yiwa Abba din wasa sai ya juya kamar zai wuce sai kuma ya juyo yana cewa dani jimana. Sai ya fara tafiya zuwa falo anan na samay shi tsaye kamar mai nazari nace gani fuska a daure babu fara a gare ni. Ba a kawo abin karyawa bane daga wurin hajiya nace an kawo yace ina yake nace an koma dashi don babu maici idan an aje a nan din. Kamar yaya ba maici ku baku ci ne nace akoshe muke mu wani kallo ya watso min naji tsoron kallin amma na dake na bar tsoron a raina. Kina nufin baku iyacin abincin gidan nan ne komay ? Akan may bamu iya ci agidan mu akwai irin sane kawai de banjin cin komai ne ai idan zaci ba bakuwar hajiya nake ba sai naje can in diba kai kuma naga ba a nan kake ci ba shiyasa. Hannu ya daga min alaman dakatar dani yana fadin ya isa haka ban tambaye ki dogon shirhi ba na fahince ki yanzu. Akan may fa ? Na tambaya cikin dakewa kamar zaiyi magana sai kuma ya sakai ya fita daga dakin na juya na koma daki na nima. Ya isa wirin hajiya ta ga yana cika yana batsewa kamar zai fashe tace dashi ina son ka da hakkuri kada ka dauko yar mutane uwar duniya kazo nan kana cuta mata akan dan abu kadan. Hajiya kyale wanan yarinyar rainin wayo take son kawo min idan ma ta kawo ma raini ba mijin ta kake ba ? Ka tsaya ku fahinci juna da ita yanzu haka ba wani matsala bane amma kai ka dauke shi babba haka kada fa ka koya ma wanan yariyar halin da ba nata ba. Don ba zai maka dadi gaba ba gashi kun fara tara zuria da ita kowa na murnan haka ni banga wani matsalan da take dashi ba. Bai iya magana ba sai faman tura abincin da yake yi a bakin shi murya ta daga ta kira yarinya guda tazo tace jeki part din su kikira min matar shi yanzu. Yarinyar ta fita zuwa part din taci gaba da mashi nasiha a kusan tare muka shigo falon na hajiya da yar aiken. Ina saye da hijjabin sallah na ajikina na shigo da sallama na sai da na kara gaida ita na samu wuri na zauna a kasa gefen kujera. Dan shiru ya biyo a falon sai faman shan ferfesu take ba tare da ya daga idon shi ba balle ma yasan na shigo falon a lokacin. Safiya ta kira sunana da sauri nadan dago kaina dake kasa na kalle ta tare da fadin naam hajiya. Tace may ke faruwa ne tsakanin ku da mijin ki kunzo min lafiya yanzu kuma sai na fahinci akwai abinda ke wakana a tsakanin ku dukkan ku ku biyu don ba haka kuka zo min ba nan. Shiru nayi ban dago kaina ba sai da ta kara maimaita maganan ta tace kada ki boye min idan wani abu ke faruwa ni uwa ce ga dukkan ku. Kai na kara saddawa kasa nayi shiru sai tayi murmushi tace bai fada min kinyi mai wani abuba sai dai na fahinci kwana biyun nan da yana zuwa nan cin abinci. Kuma ke idan an aika maku sai kice a dawo min dashi ko an barshi acan babu mai ci yaya zaku zo min bakunta gidana kuma ku tsiru min wani hali na daban ? Haba safiya ki fada min idan wani abu ke faruwa na sani tun baku koma haka a dunkule ba kin ga sai in zama uwar banza gare ku. Sai lokacin na dan dago kaina nace ba haka na bane hajiya ba komai wallahi ta katse ni da fadin akwai komay idan babu may kuke ci keda yar uwar ki data rako ki kuma ? Hajiya nima ban san may nayi mai ba tun ranan da muka je gun bukin gidan su Aisha yake wanan fushin dani kuma ya daina zama yaci abincin a can ko nayi mai magana baya amsa min sai dai yayi ta fushi. Wanda ni ban san dalilin yin hakan da yake min ba na bashi hakuri da fada mai tare da yan uwa muka tafi ba zan dawo na barsu can ba tunda tare muka tafi dasu. Tana cewa kwarai kuwa shi kuma yana fadin karya kike yi ai kin san bana son yawo amma kika tafi kika zauna sai da kika kwaso ma yaron nan zazzabi da ya wahala. Sokike ki, , , , , , Ya isa haka baba ya isa nace maka ko yace hajiya could you belief wai har tana iya fushi akan na dauki mataki akan abinda tayi min. Kai baba karage wanan zuciyar naka ina ce ka daina jin ku shiru danayi ashe kai har yanzu halin naka nan maka ? Bukin yar uwakar fa taje tare da yan uwan ka kuma ashe kai wanan ba abin farin ciki bane gare ka yau ga iyalin ka cikin yan uwan ka anayi dasu. Ciwo koma da yaro yayi ai canjin ruwa ne yara dawa haka na faruwa dasu idan anje sabon wuri da basu saba da yanayin shi ba. Kaiwa yarinyar nan adalci mana haba yanzu cikin wanan magana may ye na zafi haka a cikin shi don Allah kai ka hau ita ta hau kaga abin bai yi kyau gani ba wallahi. Shi fa mutum mai hakkuri ba a son a kure shi idan yake an kure shi abin bai kyau yanzu gashi kace wai tana fushi da kai ? Ta gaji ne da baka hakkuri ta kyale ka hakana tunda kai ba a iyaka ina da labarin zaman ku sarai a kunne na yarinyar tsoron ka take ji kada ka kaita makura ta koma ma kamar sauran mataku na bariki. Ke kuma ba a gajiya da hakkuri tun dai ga miji zaman takewan aure da hakkuri ake cin riban shi ba zaki biye mai ba har ku kai ga sabon Allah don haka na kashe wanan magana. Tashi ki koma dakin ki wanan magana kuma ya mutu a nan kada in kara jin irin shi don Allah na dago tare da fadin baaba na gode. Na mike na fita tace ku samu abinda kukaci ke da yar uwar ki kada ku zauna da yun wa haka ba a bakun ta da yunwa ko ai fushi da abinci. Ina sa takalmina a kofa naji tana fashi fada sosai irin na da mahaifi ni dai na wuce part din don ko fada ta yi mai kan shi da yanzu sai yiwa wasu fadan haka kuma ahi din yake yin haka a gidan shi. Ko da na koma Khadija tana nan tana kallon ta a waya shigowa na yasa ta dago kan ta tana fadin may akayi anty ? Nace kila kara na yakai gun baaba ban sani ba ta dai yi muna magana ne akan abinda ke faruwa tace ai yanzu kiga ya gyara nace kila ba. Wai kina ma da hakkuri nace in ban yi hakkuri ba khadija may kike son inyi a nan ai hakkuri ya zama min dole tunda haka halin sa yake cikin ma wai ya rage ke nan fa. Falo muka dawo muna kallo har anty suwaiba tazo a gurguje ta leko mu tana fadin sauri takeyi ta kawo ma hajiyan su sako ne. Na dan rakata zuwa part din baaba din na dawo ban dade da zama ba sai gashi ya dawo gidan sannu da zuwa muka mai cikin rashin sakewa tare da mu. Kallon khadija yayi yace khadija har dake ake fushin da ni ko ? Tace a a yaya wane ni shiga tsakanin miji da mata ai kun fi kusa ni ba ruwana da maganan ku yana zama yace ban yarda dake ba. Idan ita bataci abinci ba ke may ke hana ki cin abinci tace kasan ni ba damuwa nayi da cin abinci ba dama. Yace ban sani ba don ban je gidan ki ba koda yake naga alaman kamar yan bauchi zasu sake samun karuwa don naji ance kin yi saurayi a nan ko. Maganan da yake yi ne yasa nasan ya sauko daga fushin da ba dalili da yake yi din na mike na barsu nan suna ba,a da ita dining naje na hada mai abincin ranan da aka kawo muna part din mu. Ga abinci can uncle na fada yace cikin sakin fuska kamar ba shi ba barin dan shiga in fito kafin in zauna ci. Ya juya ya shige tana jin karan rufe kofan shi ta juyo tana kallo na tace aina fada maki irin su sai da saiti wallahi nace ai naga alama. Ya dan jima ya fito daga dakin ya sauya kayan jikin shi don zafin da ake a gare direct dining ya nufa don haka na tashi naje don zuba mai abincin har lokacin ba wani walwala a fuska. Har na zuba mai na juya zan wuce yace yaya haka ku kunci abuncin ne halan ? Nace mun ci tun dazu yace ta ki zauna na gama kin san ban son a bani abinci a wuce dole na dawo na zauna ina dakilan wayana can naji yace ki shirya da dare zamu tafi gidan su babffa mu gaida su. Allah ya kai mu na bashi amsa har ya gama ina kokari kawar da kayan ne naji yace naso zuwa Abuja gobe in dawo jibi amma sai abin da hali yayi goben. Allah ya kaimu na bashi amsa tare da cewa wani abune zaka je naga saura yan kwanaki mu koma can din ai. Zan tafi duba wasu kayane da suka iso Saadu ya bugo min waya wai kayan basu cika ba kuma ba irin wanda mukayi oda aka kawo muna ba. Goben dai zaka tafi ke nan na sake tambayashi ya mike saman kujera daga zaune ya balance da kafafuwan shi yace ai dole in je in gani da ido na kada su cuce mu kafin a bude don ban son abinda zai kashe muna kasuwan mu. Allah ya kaimu nace dashi tare da ci gaba da abinda nake a wayana wanda hankalina yana a kai. ZAINAB IDRIS MAKAWA SEENABU 9/7/20, 8:07 AM - Ummi Tandama: BAHAGGON RAYUWA , , , 🧕🏿7️⃣3️⃣🧕 ZAINAB IDRIS MAKAWA SEENABU Kamar yadda ya fada haka tafiya ta kamashi don an sake bugo mai waya da dare akan kayan da aka shigo masu dashi dole ya shirya da safe ya bar garin. Sai mu ya bari a bauchin koshi don zai dawo buki ne yasa ya tafi ya barmu sai gidan ya koma muna ba dadi muna part din mu ni da khadija sai yan mata da suke dan shigowa wurin khadija jefi jefi. Tashi nayi nacewa khadija ta zo mu shi wuri hajiya mu gaida ta na lura bata so zuwa ba don tana kallon wani india film ne. Amma bata iya mussa min dole ta tashi muka shiga don Abba yana can gurin yan matan sun dauke shi da suka shigo dazun. Tana zaune a falon ta kamar kullun tare da wasu mata da suka shigo wurin ta amma matan na shirin wuce wa don naji suna sallama da ita har daya ta mike tsaye daga cikin su. Shigowan mu matan suka mayar da hankali sun su a gare mu, gaida hajiyan mukayi bamu tsaya wurin su ba sai muka nufi hanya shiga dakunan hajiya din. Muryan hajiya naji tana fadin maman Abba zo ku gaisa da sarakunan ki matan baffanin ku ne suka shigo dubani. Sai dayan ke fadin ko matar baba ne don kin san ai bamu santa ba tace dasu eh itace kin san sun zo don kawo muna yaro mu gani. Haka mukaji ta haihu kwanaki da su suwaiba suka tafi suna can abujan, dawowa nayi na duka ina gaida su don cewa da baaba tayi sarakunnena su yasa na duka masu. Masha Allahu suke fada yarinya ce ashe ikon Allah matar mutum ance kabarin sa har can akace ya auro ta ko baaba dai dariya tayi na mike ina jin suna magana a kaina ban tsaya sauraren su ba. Dakin yan matan suna barbaje a dakin nasu na zauna a gefen gadon su suka shiga cewa ashe tare kuke da anty khadija tace eh. Hira suke yi in dan jefa baki a hiran nasu amma hankali yana ga waya na da muke charting da samira tana zolayana wai naji dadin bauchi naki dawowa gashi ance uncle ya shigo abuja yau. Nace da ita bauchi zama daram ai tace kina fara shi ai da mun biyo ki nan muma dariya ta bani har ina darawa ni kadai da wayan . Yar wurin anty suwaiba da tafita duba girkin da sukeyi ta dawo tana fadin mummy hajiya tana magana dake. Haka yasa na mike ina rubutawa samira yanzu idan kin gani ai baki gane ni saboda dadin da sarakuwa na ke bani kullun. Na tura mata daidai ina isa falin hajiya nayi saurin kashe wayan na karasa ina fadin hajiya gani tace kunyi waya ko yace ya isa ? Eh baaba ya sauka tunda safe ina ji aiki ne yasha mai kai be kara kira ba tun bayan isar nasu ta sake fadin yace yau yake so ya dawo in da hali nace haka ya fada baaba. Nakai zaune a saman dan Center Capet din falon tace su dai maza basu mayar da tafiya a bakin komai ba ni gashi kullun ina waken zuwa duba masaukin ku acan amma ban tsayar da lokaci ba har kuka kai ga zuwa. Nace ai shi uncle tafiya ko acan muke haka yake yawan yin shi idan ya kama mashi tace ai hakan na dakyau don bidan na kai ne. Ni dai abinda zan fada maki shi ne ki kara hakkuri hakan danaji yasa na mayar da hankalina gare ta taci gaba da fadin ko can da maza sai a hankali balle mazan wanan zamanin da muke ciki. Ko wani gida kika gani ta kalar tasu matsalan daban don haka idan ya na fushin shi ki bar biye mai kuna zama daya shi wanan fushi da zan iya raba babana dashi da na rabashi dashi tun yana yaro . Don haka ya tashi shi yanzun ma ai ya rage sosai wallahi sai ma ince shigowan ki yasa ya daina abubuwa da dama ni ban san halin wanda ya dauko haka ba wallahi. Murmushi nayi nace baaba ai yanzu na saba da halin shi ni abinshi bai kan damay tun farko Anty Aisha ta sanar dani halin shi shiyasa abin yazo min da sauki. Abinci da suka gama suka kawo suna fada mata ga abinci nan an gama hajiya shiya dakatar da mu ga hiran tamu nan take fadin. Ai ku zubo mutaru muci anan don zumunci wanan halin na hajiya yana matukar burge ni sosai don sam bata da matsala irin na wasu uwayen miji da nake gani. Birbiscon gero sukayi da miyar taushe sai man shanu da za a zuba ga mai so da dan miyan dage dage ga wanda baison ci da miyar taushen. Fitowa sukayi daga dakunan su nan aka shiga zuzuba abincin kowa yaja nashi plate din khadija ce ke tambaya na wai wanan wani irin abinci ne haka ? Dariya muka soma yi mata nan hajiya ke mata bayanin akan abinci sai faman juya cibi take a cikin sa nan hajiya tace taci taji yana da dadi sosai. Muna ci hajiyan hankalin ta yana wurin mu a ranta take cewa Allah ka shirya tsakanin yaran nan su zauna lafiya ban son fitina sam a tsakanin su. Don yarinyar na da tarbiya sosai gashi sanadin ta abubuwa sun sauya ga rayuwan baba na sosai wallahi ba zan so ace yana yawan samun matsala ga auren shi ba. Mun kare lokacin sallah yayi nace zamu tafi muyi sallah tace mu shiga daki muyi hijjabai na nan saman kujeran dakin nata don haka sallah ma anan mukayi . Bamu koma shiyan mu don na tsaya na taya yan matan aikin abincin dare duk da hajiyan ta hana nace ko a gida hajiya ai nakan yi girki sosai . Tace kin ko kyauta ma kanki wallahi yo may nene auren dama ai girki yana cikin ginshikin aure sosai amma matan yanzu basu gane hakan. Sai su dauka wai wayewa ne daukan yar aikin da suke yi basu san wani daman su bane suke ragewa har ga Allah. Kwanan uncle biyu ya dawo ranan da ake ta shiri zuwa kamun amare da za a yi don bai nan nima kuma fitan yanzu bai a raina don na saba da rashin fita tunda shike jawo muna matsala tsakani na dashi. Sai ban mai da kai da mutafi ba misakin sha biyun rana ya shigo bauchi da gajiya don haka tunda yayi wanka ya kwanta wai yana son ya huta ne. Khadija sun fita tare da yan matan gidan zuwa gidan bukin haka yasa na dauki Abba muka samay shi a dakin shi. Barcin nima nayi a lokacin sallah azahar ya tayar damu sai kuma cin abinci misalin karfe hudu sai ga anty suwaiba ta shigo lokacin muna falon mu zaune da shi. Sun gaisa tayi mai yaya hanya ya amsa mata da lafiya sai da suka gama gaisuwa ne tajuyo tana cewa dani Safiya yaya haka kuma naga baki shirya ba kun san kuma karfe hudu ne akasa program din. Nace anty ku tafi kawai ba zan samu zuwa ba yace mata ina zaku kuma tace gidan su kawu wurin kamun amare zamu tafi yace oky, . Bai sake magana ba sai ita ke fadin amma ko banji dadin rashin zuwan ki ba wallahi gaku cikin gari kin san fa mune zamu wakilci baaba fa. Anty kiyi hakkuri ba zan samu fita ba don kin ga ma yau ya dawo tace oky yayi ta juya tana fadin to mukan sai in mun dawo zamu fita don sauran sunce mu hadu a can. Dama don ke nazo don mu tafi tare daku din ashe ma baki samun zuwa din a dawo lafiya nayi mata ko kallon mu bai sake yi ba tunda ya kawar da kai. Sai bayan fitar ta yake fadin saka lalle din ne har sai anje yin wani program can don sun bidia kawai irin na mata shiru nayi ban yi magana ba ya mike yana fadin bari in leka hajiya tunda na shigo ban fita ba. Itako anty suwaiba tana shiga tana fada sai hajiya tace kada kiga laifin yar mutane kin san fitan ku na satin da ya wuce sai da suka samu fitina a tsakanin su. Bar mashi matar shi a inda yake son ganin ta don Allah kin dai san halin shi ko tace amma baaba ai suma suna son idan nasu ya tashi a tafi ko ? Bata san yana shigowa ba saiji tayi yana fadi daga bayan ta nace baza ta fita ba ku baku iya zama gidajen mazan ku kullun kuke nan hanyar gidan buki ? Banzo nan da ita don yawon buki ba don haka kada na kara jin wanan magana ya fadi yana hararanta yana zama tace amma dai yaya zaka bari ranan buki ko ? Ta tambaya tana kallon fuskan shi don son jin amsa kafin yayi magana hajiya ta amsa mata da cewa a a ranan buki kan zata tafi mana tunda suna gari. Kallin mahaifiyar tasu yayi sai bai ce komai ba tunda ta yanke hukunci yake cewa shike nan ai amma ku rage wanan yawan zuwa bukin naku. Ku wai mazajen ku basu kishin ku ne wai? Dariya tayi tace kai yaya kowa fa ba irin ka bane mai kishi wai ko don matar ka tana da kyaune haka yasa baka son a ganta ? See you yace don na hana ta fita shine wani abu baaba tace shifa raayin shine haka kin manta lokacin da kuke yan mata yadda kuke kwasa dashi ne ? Safiyan ma tana da hakkuri wallahi tace tunda sukai aure fa bata je gida ba har yanzu ido hajiya ta fitar waje tace kai baba na kada ka raba yarinya da iyayyen ta don Allah. Yace haba baaba may zata je tayi kullun ba suna waya ba tana jin lafiyan su kadai samu mai hakkuri ne tace amma wanan samiran taka ta farko ai shashani ce sarkin yawo. Tsaki yaja yace don Allah ku bar dauko min maganan wanan macuciyar ban ma son in tunata a rayuwa na wallahi. Mikewa suwaiba tayi tana fadin ni zan tafi kada a fara badani ba hararan ta yayi kawai ya kawar da kai ta fice tana mashi dariya hajiya na mata sai sun dawo. Babana zumunci yana da dadi ba yawo bane haka don mutum ya ziyarci bukin yan uwan shi ka rage wanan tsananin da ke wa yarinyar nan don Allah ka bata freedon din kanta itama ta shiga yan uwanta matsin yayi yawa wallahi. Murmushi yayi ya kawar da zancen yana fadin ai hajiya gara dana daure nayi tafiyan nan don mutane yanzu basu da gaskiya ashe laifin wanda muka tura odo kayan ne yayi muna wanan sheri. Nan ya fara mata bayani komai da ya faru tace yanzu yaya zakuyi da kayan da kuka ce basu da kyau ? Yace dole zamu karyar dasu a farashi mai sauki shi kuma mun sallamay shi don ba zan zauna da mahainci ba. Nikan ina can part din mu damuwa da kadaici ya ishe ni a lokaci ga khadija dake debe min kewa ta fita yau don haka dagani sai Abbati ke part din namu. Haka yasa na dauko waya muna hira da ummi na haka ya dan rage min zaman kadaicin da nake yi ni kadai babu abokin hira. Idan banda wanan matsala na uncle da sai in ce banda matsala ko da muwa a wanan auren nawa don zai bani ci da sha da sutura mai kyau amma ba fita ko ina sai dai idan mutum yaji marmarin ganina yazo gidan. Don na fahinci har da yan uwa na idan banyi da gaske ba uncle zai rabani da su ne don basu zaman zuwa wurina kullun ni ban zuwa gurin su. Saukin abin ma yanzu da yaya Saadu ke kusa dani yana debe min kewan yan gidan mu sai ko yaya sani da kan shigo jefi jefi idan yazo yin wani abin. Tun da ya fita gun hajiya bai dawo ba don yayi baki daga cab suka fice da mutanen bai dawo ba sai bayan sallah ishai ya shigo lokacin khadija bata dade da shigowa gidan ba. Muna zaune tana min hiran event din da akayi sai gashi ya turo kofan dakin da sallaman shi sannu da zuwa mukai mashi. Ya dan je nakin mirrow ya tsaya tare da jingina jikin shi akan mirrow din yana fadin naga alama khadija garin nan ya amshe ki fa ? Dariya tayi tace kai wane ni yaya nida na matsu mu koma mu tafi gida inga ummi na da sauran yan uwa . Yace ba yanzu ko mun koma sai na tafi Egypt na dawo zaku tafi gida da sauri na dago kai na dube shi ban kuma kawar da idanuwa na akan shi ba Ya gane may nake nufi don ba haka mukayi da shi da gida zan tafi sai yace mu dakatar da zuwa gida sai idan mun koma daga bauchi zamu tafi. Yes yace haka na tsara tsara yanzu don nima ina son in tafi in duba su idan ban samu zuwa tare da kuba tafiyan zai min nauyi ne daga baya. Haushi bai bari nayi magana ba alokacin don khadija kuma dake wurin sai kawar da kaina da nayi daga duban shi kawai. Sun dan taba hira da khadija sama sama ya fita ban bishi ba yana fita nace mutumin nan ban san abinda yake nufi ba a kaina khadija ? Kiyi hakkuri kibishi yadda yake nidai da mun koma zan tafi don bazan tsaya jiran ku ba don babu ranan tafiyan ku gwago ma nasan ba zata tsaya yadda ta matsu din nan. Ta yunkura tana tashi daga inda take zaune tace nasan ko ya dawo cewa zaiyi zai tafi Etopiar kuma dariya ta bani nace a a Niger zai tafi tace a ba ya zama sarkin yawo ba shi. Nace ni kuma wanan bahagon rayuwan na sake fadawa idan ka fita wanan ka fada wancan idan bakai hakkuri ba sai ace kai mace sai aga laifin ka amma saboda Allah don kana aure sai ka watsar da iyayyen ka ai ba komai kudi ke sayawa mutum ba a duniya. Sai da na gama abinda nakeyi na fito don duba shi waya yake yi don haka na juya na koma don shi wayan shi ba mai karewa bane da wuri. Fita nayi zuwa wurin hajiya nayi mata sai da safe a lokacin take cewa ga abin bukina da suwaiba ta bayar a bani don ba ta tsaya ba sauri take yi da ta shigo. Na karba cikin ladabi na juya na koma part din namu, daki na shiga na shirya tare da gyara Abba don yau khadija na san a gajiye take sosai a ranan don haka na dauki yaron na tafi dashi. Koda na tura kofan ya fito daga wanka yana tsaye yana goge jikin shi jin shigowan mu yasa ya maida hankalin shi gare mu. Yaron na shimfede saman godo na juya na fita naje dauko abincin shi duk da bai faye falkwa da dare ba sosai amma ban kwanciya sai da abincin shi a kusa dani. Na dawo dakin da sallamata na shigo na samu wuri na aje a gefen da zamu kwanta fita nayi na rufo kofunan part din namu tare da kashe wutan ko ina na dawo dakin. Zama nayi a bakin godan dakin tare da zuba tagumi a lokaci daya tare da dukar da kaina kasa may ke faruwa ne koma naji ya jefo min tambaya. Na dago nace yanzu uncle don Allah bazaka bari naje gida naga iyayye na ba sai ka tsiru da wani zancen tafiya kuma bayan ba haka muka yi da kai ba kuma ? Ke dakata may kike so dani ne wai so kike ki na aje abinda ke gaba na don na dadada maki ranki komay , ? Da mamaki nake kallon shi don kaina ya daure sosai ga maganan shi yace nace bazaki ba sai na dawo Egypt period. Ya juya ya dauki laptop din shi ya haye gado batare da ya kara bi ta kaina ba har ya fara latse latse sai kuma ya juya gare ni yana fadin . Kuma bari kiji idan har zaki tayar min da hankali akan maganan nan gaba daya sai in ce bazaki tafi ba inga yadda zakiyi ? Da mamaki na sake dago kaina kamar zanyi magana sai kuma na fasa naja bakina na rufe a raina nace ashe maza duka haka suke. Nadan saci kallon shi aikin shi yakeyi bai kulani ba na gyara na haye gadon tare da rungumay dana muka kwanta tare da bashi baya. Ban jima ba da kwanciya barci ya dauke ni don ban yarda na saka zancen shi a raina ba tunda naji ya fada ya tabbata ke nan ba zan tafi din ba sai ya dawo. Sai dai na san cewa gwago da khadija bazasu iya kara lokaci haka ba suna jira na don kullun maganan su ta zuwa gida ne tun da nayi arbain. Juya yayi yakalle mu ina kwance ina yadda na kwanta na kankamay yaron ga jikina kamar za a sace min shi a jikina shima yaron sai kwasar barcin shi yake yi hankali a kwance. Rufe laptop din yayi tare da kashe wutan dakin ya hawo gadon ya kwanta rigingine tare da harde hanaye shi wuri daya yana tunane. Don shi gani yake na canza mai yanzu bani bin umurnin shi ina son in tsiro da wasu halaiyan da bai sanni da shi ba a baya. Ya rasa ko may ya canza ni haka lokaci guda ya zama mai dole yayi wa wanan halin da na tsiro mai waige tun da wuri. ZAINAB IDRIS MAKAWA SEENABU 9/9/20, 9:20 AM - Ummi Tandama: BAHAGGON RAYUWA, , , , , , , 🧕🏿7️⃣4️⃣🧕 ZAINAB IDRIS MAKAWA SEENABUN KU Gari ya waye mun tashi lafiya ban yi mamakin rashin taya ni da baiyi ba rana don in da sabo na saba idan yana fushi bai kallon inda nake nima kuma a yadda nake ji haka yafi mim sauki ai. Kafin ya fito bayi na koma dakina tunda nayi sallah ina wurin zaune ina azzakar din safiya da neman cikawa da imani tare da rokon Allah abubuwan bukata ga bawa. Na gama na tashi ina nade abin sallah lokacin khadija ta motsa inda take kwance don tana fashi sallah haka yasa bata tashi ba daga barci . Fita nayi falo na gyara ko ina saura da kuna wanka na shiga don in gyara jikina na fito na zauna na shirya kaina ina gab da zan gama shiri naji kukan Abba daga falo nasan uncle ne ya dauko shi ya tashi daga barci yana jin yunwan safe. Ya shigo dakin dashi na karbe shi don ihun da yake tsalawa sosai a lokacin ya fadin fuska a dake ki bashi abinci yaci ya falka yana kuka haka. Karban yaron nayi daga hannun shi tare da fadin ina kwana uncle ya amsa min a dake ya fita na bishi da kallo ina fadin ikon Allah a raina. Wanka na fara yiwa yaron sai da na shirya shi khadija lokacin ta mike tana hada mashi abinci tace amma anty dole ki samu yarinya da zata zauna dake ko , ? Nace ba gaki nan ba na bata amsa a takaice. Dariya tayi tace in na zauna ummin mu fa dawa zata zauna nace ke din zaki tabbata a dakin ummi ba zakiyi aure ba khadija ? Dariya tayi tace ko zanyi ba yanzu ba ni sai nayi karatu ina zama saman gado da yaron tana miko min feeder shi nace kin yi sa a yanzu baba ya sauko sosai idan kin ce zakiyi karatu na san a yanzu zai iya barin ki. Don darasin da ya samu a kaina amma in bashi ba ai da kema nasan abinda ya faru damu zai faru dake asamu wani dan uwa a laka maki. Tab wallahi ni ba zan yarda da wanan abinda sukai maki ba ai fuskana yana ga yaron nake cewa baidai kama ba khadija. Tace ai yanzu ba shi ba ma yarinya auren dole kullun yana fadi bai son ma ku hadu idan ya tuna da abinda yayi maki shi da su inna sai yaji ranshi na baci. Murmushi nayi nace baba ke nan ai ubangiji yakawo muna saukin abinda da yanzu kila an manta dani ko ina nan ina wulakanta wurin yan uwa. Shiyasa kika ga duk abinda mutumin nan yayi min khadija nake shanyewa don tuna inda rayuwana ya fito cikin kaskanci . Matsalan shi dai shi ne wanan saurin fushi da rikon magana amma don don fitan da yake min na cewa kada na fita ni dama can ba ma,abociyar son fita bane ke kin sani yanzu ne ma ai har nake shiga mutane da ummin mu da yan uwan ta kawai muka bude ido kin ga abin ya zo min da sauki ai. Sallaman yan matan hajiya da suka shigo muna da abin karya ne a falon muka amsa kusan a lokaci daya da khadija bayan ta aje ta leko muna ina kwana. Nace ki cewa baaba mijin tane ya tashi da fitina ban samu shigowa da wuri ba yarinyar ta dauke shi tana fadin yau mijin hajiya ka dagawa mutane hankali ko ? Nace wallahi idan ya tashi shi ba abinda yake nema sai abinci kamar an fada mai shi kawai ake zaman ci daukan shi tayi ta dan mai wasa nace ta ajeshi yayi kashi zan canza mai permpas din jikin shi ta fita tana mashi sheri. Khadija ce ta shiga dashi bayi ta wanke mai jiki ta fito dashi tana saka mai wani fita nayi na barsu na je hada muna abinci ida naga sinasir sukayi da ferfesu sai tea da dankali nace a raina wanan uban abinci haka duk na karin safe. Nasan sinasir din don uncle sukayi shi don yana son cin sa sosai ni kuma ban iya ba don haka ne ban mashi a gida amma zan koya a wurin su da birabisco din da naga sunyi ranan na gero. Da sallama a bakina na shiga dakin shi yana saka tufafin shi a lokacin ya dan juyo ya kalle ni yana amsa sallamana. Nace an kawo abin karyawa ne nazo fada ma oky naji yace dani yaci gaba da abinda yake yi zanin gadon na juya na yaye don canza wani don wanan yayi dauda. Ya gama ya fice ya barni a dakin sai da na gama na fito yana zaune a gurin cin abincin yana waya cikin fada fada gurin na nufa na fara zuba mai. Yana kallon yadda nake zuba mai yana wayan sai da yakai munzalin yadda yake so yace dani barshi haka na. Na rufe na juya na tafi ya bini da kallo bai daiyi magana ba ina shiga na samu ta fito wanka tana zaune tana shafa mai a jikin ta. Nace yau halin mutumun nawa ya tashi bari ya gama ci sai muje muci namu abincin tace ikon Allah haka kike fama anty ? Murmushi nayi ina kaiwa zaune nace to yaya zanyi khadija haka kuma Allah ya jerabi ni da gani ni yanzu ma kamar kada in haihun ga sai naga fushin ya karu mai sosai wallahi. Dariya tayi tace ko da abba yake kishi kin mayar da hankalin ki ga yaro kin daina bashi kulawan da kike bashi a baya ? Hali ne dai kawai dama haka akace yake wai ma ya rage ne yanzu da fa da kowa bai hurda cikin yan uwan shi kowa mai laifine a gare shi. Dariya tayi tace barin je in samay shi ai mu gaisa tun bai fita ba karasa shiri tayi a gurguje ta fita wurin shi falo inda yake kwantawa nayi kafin ta dawo. Tare da lumshe idanuwa ina tunane duk maza halin su daya sai dai halin zamantakewar ne ya banbanta wani ya dara wani. Mu mata a biye muke dasu komai kyautatawan mace sai namiji ya kaita iyaka da zata sauya halin ta a gare shi ko yaya ne khadija naga ta dan dade sai can gata ta shigo. Tana fadin ya fita har na kwashe kayan kai uncle oho ya fasan abinda yake maki sarai anty haka dai halin shi yake in ba shi yace abuba ba zai yarda ayi ba. Yanzun yake ce min wai kina fushi dashi don yace ba zaki gida idan mun koma ba to haka yace hakan kuma ya tsara abinsa tace ni dai hakkuri na bashi nace aiko baki yi fushi ba don banji kin sake maganan ba. Can wurin baaba da ya shiga gaida ita take mai yaya gajiyan tafiya ya amsa mata ba a sake ba ta fahinci yana cikin yanayin nasa ke nan. Take tambayan shi anyi wani abune ya zauna yana hura iska tare da fadin yarinyar nan tana son ta fito da wasu hali da ban santa da shi ba yanzu. Ba dama ince mata ga abinda nake so sai ta kawo nata korafin akai wallahi zanyi maganin ta ne a gidan nan. Babana may kuma ya faru a tsakanin ku ne wai haka dama kake zama da yar mutane da wanan halin nan dai ya koro mata yadda mukayi. Murmushi tayi mai tace yanzu may ye laifin yarinyar nan a cikin zancen nan daka fada kace bata zuwa ta kara cema wani abune kuma ? Ko taki kula kane akan maganan kai dai ne ke tsiru da wasu abu yanzu ko kana cikin mazan da dazaran mace ta haihu sai su fara kyamkyamin ta ne. Ya dago da sauri ya kalle ta tace in ba haka bane may ya kawo wanan yawan fitina haka ko acan ma haka kake mata ne ? Yace ina na zauna gida balle ta ganni ina wurin bidan na kaina babana ka gyara halin ka wallahi yarinyar nan tana da dadin zama ga ladabi da biyayya gare ta to may kuma ake so ga mace. Tun ina ji har gashi na gani da idona bata da wani matsala wallahi yace ai ban ce tana da matsala ba nima ban dai son abinda take min ne kawai ina fadi tana musayawa ita wacece da ba zata abinda nake so ba wai ? Nan dai ta kara mai magana tare da nuna mashi bacin ran ta sosai akan halin da yake yi wanda ta nusar dashi da fada mai kada fa ya manta halin rayuwan da muke ciki dani dashi. Idan bai bi a sannu bai a sannu na har na gaji da hakkuri na gudu fa yasan dai ba kimai kudi ke samuwa zai iya samun wata mace amma ba mai irin hakkuri na ba. Wanan maganganun na baaba sun tsaya mashi a rai sosai don da zancen ta ya wuni yana mai yawo a zuciyar shi. Ni dai naga ya dawo gida bayan la,asar ya shigo da dan sakin fuska alikacin muna falon mu zaune muna hira har da yan mata hajiya dake shirin fita gidan buki da khadija. Mun gaida shi ya shiga dakin shi bai zauna falon ba don ganin su a part din da yayi muryan shi ya daga ya kirani na amsa na tashi zuwa gare shi. Tsaye yake yana rage kayan jikin shi na shigo dakin daga inda yake tsaye yake magana yana fadin hada min ruwa in dan watsa ma jikina. Ban yi magana ba na kama hanyan ban dakin kamo hannu na naji yayi na juyo ina kallon shi batare da sakin fuska ba sai naga yayi murmushi yana fadin. Wai fushin zuwa gidan ne haka har yanzu akeyi nace fushi akan may zanyi fushi uncle idan ma kace ban zuwa gaba daya ai ba zanyi fushi ba. Tunda nasan kana da dalilin fadin haka kawai dai idan mun koma sai gwago da khadija su wuce don ba zasu zauna har zuwa lokacin da kake son mu tafi. Haba dai yace nace a matse suke da gida don dai kawai ba yarda zasu yi ne ina kokarin kwance hannu na daga rikon da yai mun din. Bina yayi da kallo sai kuma na bashi tausayi sosai yaji bai kyauta min haka kawai ya hana zukatan mu samun sanyi a wani dan lokaci da ya kamata ace mun samu shakuwa sosai a tsakanin mu na zaman da mukeyi a nan din. Har na fito daga bayin yana tsaye a idan na barshi jingine da wardrove din dakin uncle na hada ruwan, nace mai ya nisa tare da fadin nagode. Na juyo ina kallon shi ya wani lumshe idanuwan shi ni dai na fita na barshi a wurin yana kallo na har nakai kofa yace zo nan safiya. Na juyo gare shi ina dan kallon shi ya bude hanayen shi yana jiran in iso gare shi din nace daga inda nake ba wanka zaka shiga ba uncle ? Idan wanka zan shiga bazaki zo ba don ina da kazanta a jikina komay ? Dariya maganan shi ta bani har na dan murmusa kadan yace to ko ke fa duk na rasa gane kan ki kwanan har kin sa na fara zargin yan uwana ko su ke zuga ki ga abinda kike min din. Da sauri na karaso inda yake ina fadin wallahi haram kada ka zarge su da komai idan basuce in soka ba in ma biyaya kasan dai ba zasu taba cewa in guji dan uwan su suba. Zama lafiya kawai ke tsakanina dasu har kakai ga fahintar haka a gare mu ya rugumoni zuwa jikin shi yana fadin to ke din ce yanzu naga kina son yi min gardama ga abinda na fada. Uncle may na fada ga maganan tunda kace ga yadda kake so ayi murmushi yayi ya rungumini kawai ban son kina min gardaman ga abinda nace. Insha Allahu nace tare da kokarin jaye jikina daga nashi na juya kawai ban kara cewa komai ba tsayawa yayi yana bina da kallo har na fice daga dakin. Falo na dawo na samu har sun gama shiryawa suna jira inzo in karbi Abba su fita nace ku dai kula da kan ku don Allah idan kun fita. Insha Allahu suke cewa kusan a lokaci daya nayi masu a dawo lafiya tare da daukan yaro na nasa saman jikina. Sai da ya gama shirin shi ya fito ina kwance saman dogon kujera da yaron da yayi barci a jikina nima barcin ne keson daukana a lokacin. Badai barcin marace zakiyi ba kin san baida kyau nace shidai nake ji tare da dan dagowa kadan daga yadda nake kwancen. Wurin cin abinci ya nufa yana bude kayan abincin sai wayan shi yayi kara daga cikin aljihun shi ya ciro ya duba ya dan ja tsuki tare da daukan wayan ya kara a kunnen shi. Naji ya amsa tare da fadin ba ida zan tafi yanzu na gaji sosai yau ina son in dan huta gidana da iyalina a raina nace kamar wanda yasan damuwan iyalin nasa. Muna zaune a falon daga ni sai shi sai dan mu dake barci a gefe na sai karan na,uran sanyi dake ta aiki a falon ya gama waya yaci abinci ya dawo saman kujerun falon ya zauna. Khadija fa yake tambaya na nace ta fita da yan matan hajiya zuwa gidan buki rai naga ya bata baidai yi magana ba nima ban yi ba na share shi kawai. Kwance yake yana fadin mummy tace wai kada ki manta da sakon ta ko may ye sakon nace ai nayiwa anty suwaiba magana masan bauchi take so azo masu dashi idan zamu koma. Yace masa kuma ba ko kirdamo ba nayiwa mutanen gidan gona na magana su sama muna kindarmo da zai wadace mu idan mun koma. Nace amma ko naji dadi tundai da nazo nan na koyi shan shi da shinkafa yana min dadi sosai wallahi yace au ashe kina so ke nan ? Ai kullun sai na tsiyayo a falon hajiya don akwaishi koda yaushe mutum ke so dama ita hajiya tana son shi sosai awurin ta ma muka koyi shan sa. Sallama akayi muryan namiji ne daga kofan shigowa falon ya amsa mai da fadin mustapha shigo mana na fara dan kamay kamay jikina don nasan ba abu mai wuya bane hakan ya hada mu. Yace ki zauna abin ki baki san mustapha ba ko kanin yayana ne mijin anty ki ai bakon ke fadin bamu taba haduwa ba da ita ko kin sanni ya juyo yana tambaya na. Kai na girgiza mai alaman ban san shi ba mike wa nayi ina fadin bari na leka baaba na dawo nan na fice na barsu sai yaron dake barci. Ita kadai a wurin ta sai tv dake ta faman aiki tana zaune tana waya na shigo ganin tana waya yasa na mayar da hankalina ga tv dake aiki a falon. Hankalina naga tv naji ta ce dani maryam tace a fada maki wai gobe zata zo damai gyaran jiki a gyara maki kan ki da kumshi dariya nayi nace wai data barshi ai don na kaina bai dade ba ma tace sunyi magana don itama ina gani za ai matane. Allah ya kaimu nace tace ai ku yara gyara jiki gareku baya baci balle wanan miji nake dake da saka ido dole ki mayar da hankali ga gyara don shi dan korafi ne. Nasan shi sarai da son gyara ga mace don yaran nan shike basu kudi suje kitso suna kanana kin ga ko yanzu a kan ki zai koma ke matar shi. Dariya nayi tace nasan halin shi sarai wurin tsabta indai babana nace wallahi ko baaba haka ma yake ko acan ina da matar dake zuwa har gida tayi min kitso ko wanke kai tace bakaji ba baida wasa wirin tsabata shi. Alhamdullahi duk abin da nake jiye mashi ya samu a wurin ki tunda ba wanda ya taba jin kan ku ai kin ga an zauna kalau ba korafi. Sai dai abinda nake so dake shine ki kara hakkuri nasan kina da da baki da shi da yanzu anji kan ku da wanan fushin nashi nayi mai magana kan zuwa gida da kike son yi shikuma yana son hanawa. Da sauri na dago kai na dan kalle ta ina mamaki a raina ina taji wanan zancen don dai ni ban fadawa wani ba ko kuma wurin khadija yan matan hajiya sukaji suka kwarmata mata. Kai khadija bata fadi na sani to a ina taji nake tambayan kai kamar tasan abinda nake tunane naji tace nan yazo da safe yake fada min na nuna mashi kuskuren shi. Nan dai ta shiga yimi fada nima tana kara lurar dani zaman takewan zama tare da yadda hakkuri ke jawa mutum riban aure a rayuwa. Shi ya shigo yana fadin Abba ya tashi yana dauke da yaron a kafadan shi ya miko min shi tashi nayi na fita don abincin shi nacan part din mu don haka na koma can. ZAINAB IDRIS MAKAWA SEENABU 9/9/20, 9:21 AM - Ummi Tandama: BAHAGGON RAYUWA, , , , , , 🧕🏿7️⃣5️⃣🧕 ZAINAB IDRIS MAKAWA SEENABU KU NOVEL DINA NA KUDI NE IDAN KI FITAR MIN HAKKIN AMANA YA BI IDAN KIN KARANTA BAKI BIYA INA BINKI BASHI HAR BAYAN RANKI, , , , Nabiku bashi masu karantawa ta sace har bayan ran ku don online novel ne na kudi kun sani kuke take sani saboda son zuciya idan baki biya ba don girman Allah kada ki karanta min novel don Allah Allah kuma ba wasa bane. Kamar yadda maryam tace sai ga mai gyaran jiki da yaranta tun da safe a gidan namu suka sallama tare da fadin itace tace suzo suyiwa anty safiya gyaran jiki. Allah ya taimake ni nagama dan abinda nake yi na koma daki na fada ma uncle Allah ba da saa yace min ya koma ya kwanta. Da yake su hudu ne nan wasu suka fara sance min kaina dake da kitson da nazo dashi wasu kuma suka kama kafana suka shiga wanke min shi mai min dilka tanayi. Kafin wani lokaci sai gashi ya fito da shirin shi yace zai shiga wurin baaba acan zai karya haka yake kamar mai gudun baki har nakan yi maki yadda yan uwana ke zuwa ya sake dasu. Kafin wani lokaci sun gama sance kan ka shaga wake wa ni kaina yau nasan na hadu da gamo na wurin gyaran jiki haki ne turare na duk anbini an shafe jikina da komai nidai iyakata ido suce yi kaza in yi shine nawa. Kafin wani lokaci munyi nisa ga komai sun gyara ni tas mun kusa gamawa sai ga maryam din ta iso tana min dariya nace ke baki fada min in shirya da wuri tace nasan ba zaki jure wanan abin ba idan na fada maki. Gaisawa sukayi nan suka juya a kan ta wanda suka gama aikin su suka shiga gyarata ita ma ko ban duba madubi ba yau na san an hadani iya haduwa nan take fada min cewa ai yan sundan ne su aikin su ke nan gyara. Nace wanan ai in da Abuja suke dana samu wirin gyara matar tace min ai akwai yar uwarta dake yi acan zata ban nombanta idan mun gama. Kafin wani lokaci sun gama maryam zata sallamay su nace ta bari in sallamay su na shiga na dauko kudi duba ashirin na basu a mu biyu suna ta godiya suka wuce tare da bani wasu turaruka wai idan zanyi wanka in dinga digawa a ruwa. Maryam ta koma part din hajiyan su ta barni na shiga wanka in gyara jikina washe gari ina cikin wasu material yellow nayi mai dinkin bubu tare da daura dan kwalin shi akaina. Sai ga diyan baaba sun shigo gidan alokacin ina wurin ta muna hiran masu gyaran jikin da suka zo jiya mun gaisa dasu suke fadin yawwa safiya da anty suwaiba ta iso sai mu tafi tunda kun shirya nace ina da sauri ? Maryam tace gidan buki mana nace sai kun dawo may kike nufi baki zuwa ko may nan suka hau bakin su sai ga Aisha ta shigo itama ta hau bakin ta tace wallahi ni na dauka shirin ke nan kikayi ai. Nace ba zan samu zuwa ba kun ga ma ranan da naje sai da Abba yayi zazzabi zasuyi magana hajiya ce ta katse su tace kun fa san halin mijin ta wacan ma zuwan gidan ku da tayi ba karamin tashin hankali sukayi da shi ba. Sai ga anty suwaiba tashigo ta samu ana maganan tace gaskiya hajiya don ko ni ranan dana biyo daukan ta muje wurin kamu a gaban shi amma wallahi kemay may yaya ya hanata zuwa. Nace bama zan tafi ba ban iya jidalin shi ke Aisha aikin san halin shi ba sai na fada maki ba don kin san komai na karasa fadi ina kauda kai gefe. A sanyaye tace nafa sani gaskiya yaya baida dadi halin shi sai ke Safiya hajiya tace bani waya na ku kira min shi ai mantawa nayi har ya fita ban fada mai ba. Nace hajiya da kin barshi don Allah ni ba zan tafi ba amma bata bi ta kaina ba sai da ta kirashi tace matar ka zasu gidan buki da yan uwan ka nakuma ce ta tafi amma tace bata zuwa don sanin halin ka datayi. Yace tunda kince ta tafi ta tafi mana tace gata kai mata magana tamiko wayan na karba tare da karawa a kunne na inajin shi yace wai bazaki tafi ba kikace nace eh banjin fitanan ne. Yace to ki shirya ku tafi yanzu zan turo maki da mota don ina nan gidan gonane zanyi magana yace nace ku tafi ko ? Ya kashe wayan shi wallahi hajiya dakun barshi Uncle bahagon mutum ne yanzu sai na dawo zai samu wani laifin yace nayi mai ni na gaji da halin shi wallahi. Nan dai suke ta magana ba yadda na iya dole na mike zuwa part din mu don in shirya tare da maryam muka tafi bayan tafiyana hajiya tace. Abinda nake fada mai ke nan kada yakai yarinyar nan makura ta daina jin tsoron shi Aisha tace ai in dai yayane yafi danan tana dai iya halin shi ne kawai. A daki kuma shiri nake yi muna maganan da Aisha take cewa kin gani ba idan mutum bai sani ba sai yace kece ke juyashi ke amma fadi ai don da akaga yana muna abu yanzu cewa ake kece ke sakashi yi. Wai duk yan uwanki sun mamaye shi sai abinda kikace yake yi Aisha ce ke fada ma hajiya karya ne kema ba dadin sa kike ji ai. Di dai hajiyan bata da daukan irin maganan ne kin ga shegiyar yarinyar nan da aka tura maku kwanaki yar isakan yarinya ce sosai wallahi duk ita tazo da wanan zancen. Nace zarah ko tace ita mana nayi bakin cikin da hajiya ta yarda tabi ku a lokacin wai mako tazo gaida ke da kuka zo ? Nace ban ganta ba wallahi nima na dauka ko bata garin ne ai tace tana nan yar iska in kinji abinda take fada ai abin bakyau wallahi akan ku. Har na gama shiri muna hira akan zarah da iyayyen ta wasu kaya ta gani ta yaba nace idan kina so ki dauka ban taba saka su ba ma. Tace cikin murna ashe abinda ake fada kan ki gaskiya ne nan ta barni ina shirya Abba ta fita don khadija sun fita da yan matan gida da wuri yau. Tsaba na shirya na dauko yaron da jakkana dana abincin shi na rufo kofan part din mu zuwa part din hajiya ko da nazo maryam har ta shirya cikin kayan dana bata ta kwabe wanda tasa. Ina shiga suka dauki ihu suna fadin dole ma yau mu fasa taro don dole kallo ya dawo wurin mu murmushi nayi ina aje kayan dake hannu na na mika wa hajiya key din idan uncle ya dawo. Bamu jima ba muka kwasa sai gidan bukin kofan a cike yake da jamma a yan buki har ta cikin haraban gidan inda muke kokarin shiga. Matane ko ina zazaune saman kujerun roba ana nuna hali tun da muka tun karo wurin kallon su ya dawo kan mu wata tobashiyan su ce ta tare mu tana fadin matar sulaiman di ne nan ? Gaskiya yake daga hanci ashe yasan zarin da yayi mun gaisa da ita tana mi ba ina dariya dago kan da zanyi in kalli wurin sai a idon anty dake min wani kallo tun daga nisa. Gabana yaba da wani irin kara a lokaci daya nace innalillahi Aisha ga anty can tace wata anty suna kokarin kallo suga wacece nake magana. Anty suwaiba tace ko maimuna kike magana wai nace ita jikina sai rawa yakeyi da ganin ta Aisha ne tace kin ga tsaya safiya maimuna may can ai itama yanzu tasan kin fi karfin ta tako ina wallahi ki dake kamar ba abinda yafaru ku gaisa kawai idan ta jaki da mutunci ayi . In kuma ta nuna maki wani abu akasin haka gamu wurin ai sai na dake sai da muka dan gaisa da mutane muka karasa wurin da suke zaune da wasu mata ashe su anty uwace. Mun karaso aka fara gaisawa yan biyun ta suna gani na sukayo kaina da murna suka rungumay ni nima na rungumay su muna murnan ganin juna. Sai can na dan juyo ina fadin anty sannun ku da zuwa tace ai dukan mu ke da sannu da zuwan don duk baki muke anan . Anty uwa sai kallon na takeyi tana batsarwa kasa da sama tana tabe baki nace da ita anty ina wunin ku tace lafiya kawai ta juya kai ga kallo na. Sai yanzu na fahinci inda muka zo watau family house din su daddy ne mijin anty gidan su hajiya baaba kenan famnin mahaifan ta gidan kawunan su uncle ke nan. Mun gaisa dasu muka wuce zuwa cikin gidan don gaisawa da mutanen gida mun bar maryam a wurin tana magana da wata basu ankara ba gulma ya ci su a wurin basu kula da ita ba. Suna hada baki wurin fadin duniya maimuna yar aikin kine ta koma haka inji anty uwa ke magana sai anty din tace bari ke dai ai ni na suma zaune wallahi . Uwa din ta sake cewa kin ga kayan jikin ta da sarkan ta kuwa tace ai shi nayi wa mutuwar zaune ana inji anty ta basu amsa . Anty uwa tace da bamu san asalin ta ba sai mu dauka ai yar wani da wata ce nan ko ba diyar kowa ba wallahi. Maryam ta kasa hakkuri tace shi fini da uba ai in fiki da miji yanzu haka abin yake ba yar kowa ba gata Allah ya kaita gaba ta basu amsa sai duk suka yake don basu san tana kusa ba. Suka mayar da abin wasa don dama tobasai suke tace yayan mu ya iya kiwo ke nan ashe ta fadi tana wucewa suka bita da harara. Nan sukaci gaba da zagina har uncle din sai da yasha zagi ranan wurin su anty dai kasa magana tayi tace ni abin ma mamaki yake bani wallahi. Mun shiga ciki mu dakin tsohuwar gidan ana gaisawa sai ina akasaka take faman yi damu nan aka kawo muna abinci da sha su yan biyu su manne da mu. Sai faman daukan Abba suke suna tambaya na wai yana tafiya nace ko zama bai fara ba ai maryam ta shigo nan dai take fada muna abinda suke fadi a gamay dani. Murmushj nayi kawai nace dama nasan abinda zasu fada ke nan bayan mu bayan mun gama cin abincin ne ni dai ban taba komai ba a wurin muka fito waje don mu sha iska. Kujeru aka kawo muna muka zauna dukkan mu ahankali nake fahintar komai a wurin ina kallon su yan biyu suka kai mata abba ta dauke shi tana mai wasa. Kamar babu wani abu a tsakanin mu take nunawa a lokacin sai wani washe baki suke yi karshe dai muka hade wuri daya dasu don rana da yacin ma inda suke zaune. Nan suka kare min kallo tsab ba yawan magana nake dashi ba ko banza balle yanzu da nake jina kamar a bakin kura na zauna. Naga Faiza nake tambayan ta fati tace tanan garin amma bata shigo wurin bukin ba sai da anty uwa ta tashi don an kirata na samu tayi min kallon mutunci. Kamar mai jin tsoron ta dai nan muka zauna muna hira kamar ba abinda ya faru a tsakanin mun dan taba hira har zuwa karfe uku da wani abu nace zan tafi gida tace ba zaki zauna har a wanke amare ba. Nace zan kai Abba ya huta ne gida anty don bai da jimirin dauka da yawa murmshi tayi kawai nace yaushe zaku koma anty tace daddy bai yi magana ba amma tana ganin basu kai ranan tuesday. Nace zan shigo in gaida ke su yan biyu suka lake min wai sai sun bimu zata hana wata yar uwar daddy tace ta barsu mana su bine ai za a dawo dasu. Ko da nace zan wuce su Aisha basu hana ba don duk sun san kwanan wasan tare da maryam da Aisha muka dawo gida muka bar sauran a can. Tunda muka shigo yaran suka ga uncle suka koma wurin shi mu kuma aka zube falon baaba sai hiran abinda ya faru ake yi a wurin. Baaba sai murmushin manya take yi kawai tana sauraren mu sai can tace kuma maganan kuke so ai kusan dole tayi bakin ciki tunda ba haka taso ba . Har ga Allah banjin dadin aibanta anty da suke tayi don dai ni kan batayi min komai ba sai alheri a tsakanin mu. Duk abinda tayi min ban dauke shi komai ba a raina uncle dai ne da yayi min iyaka a tsakanin mu nan dai na mike zuwa part din mu don in sauya kayan jikina. Sai da dare ya mayar da su yan biyu gida wurin mahaifan su, su sundage wai anan zasu kwana wuri nace suje gobe zan zo in dauke su. Sai da ya dawo ne muna shirin kwanciya yace danu ashe yau kin hadu da anty ki nace wallahi uncle baka fada min sun zo ba ai. Na manta ne ya bani amsa a takaice sai na kyale shi don nasan baison maganan ne yasa nayi shiru sai can naji yace yaya akayi ta bari twins suka biyo ki ? Nace wata mata tayi mata magana don bata so su biyu ni ba ai yace naga alama ni yanzu sama sama muke da ita. Mijin ta dai ne bata da yadda zata rabamu dole ta saka ido itama uwar da take mara wa baya naji ance kwanaki sunyi rikici a tsakanin su ai. Nace tare muka gansu zaune yace zaman dai ne amma sunyi ba dadi har mijin ya tashi sakin ta wai su uwa sun sama mashi wata bazawara a abuja shine taji dama ko akwai kudi ne a tsakanin su ban dai saurari maganan ba sosai. Nace kuma suna fada haka a tsakanin su ba aminan juna bane na gani yace ke ma ba uwar dakin ki bace kuka samu sabani da ita. Washe gari da yamma sai ga daddy ya kwaso su sun zo gaida hajiya baaba lokacin duk muna falon ta zaune mun masu taro na arziki sosai daddy ke fadi a a Safiya jiya su yan biyu ke fada min sun ganki har da baby ki wai. Dariya nayi na durkusa har kasa na gaidashi a lokacin yake min barka ya karbi yaron hannun khadija anty dai sai kamay kamay take yi kawai a wajen. Tana fadin gashi nan safiya ya biyu sak sai daddy da hajiya ke fadin ai wanan yaron duk gida ya kwaso wallahi ba inda ya raga sulaiman ko kadan. Yace ni ban ga inda ya biyu safiya ba ai da anganshi anga wanda ya dauko gidan su sak tace don dai kai baka kallon safiya ne killa shi yasa. Hajiya ta dan yi dariya tace ba abinda ya debo na uwar shi kowa ya gane shi yana fadin gida ya biyo sai dai ke ce ke ganin kamar shi da uwar. Fita nayi daga falon dasu yan biyu sai zuwa part din mu sai da na fice ne hajiya ta dauko maganan abinda ke faruwa a tsakanin mu din . Nasiha tayi wa anty din sosai sai da jikin ta yayi sanyi ta kara da fadin ku sasanta dake da yar uwar ki wanan duniya har nawa yake gamay tunane ? Nan dai anty tace da hajiyan babu komai komai ya wuce ita dama bata dauki abinda zafi ba safiyan dai na ta dauki magana da zafi har waya ta daina bugo min yanzu hajiya bata ji nauyin fada mata cewa uncle ne ya hana in buga mata waya don bai iya jure wulakancin da take min din. Tayi wani iri tare da dukar dakai tace hajiya wallahi yarinyar nan makira ce ban san may ta fadawa sulaiman ya dauka haka dazafi ba. Daddy ne ya katse ta da fadin a a maman twins safiya bata tatanci wannan shedan da a gare ki ke dai sai dai in akwai wani abin a lokacin uncle ya shigo falon don daddy ya buga mai waya gasu gidan shi. Tace kin gan shi nan hajiya yanzun ko wayana ya daina dauka sai ya ga dama safiya ta shiga ysakani na dashi ban san may ta fada mai nayi ba. Safiya bata shiga tsakanina dake ba don ba ita ta hadani daku ba kawai dai ba zan yarda bane da wulkanta min mata da kike yi koda kuwa ciki daya kuka fito da ita. A iya sani na har zagina mutane ke yi akan ki yau ko ashe duk abinda na ji na gani ina so ashe in akwai amana takamata kiso abin nan. So nikuma shiyasa nace duk ranan da na sake ganin ta buga maki waya sai na bata mata rai sosai don ba zan juri gani irin yadda kike mata gaskiya. Tunda ya fara magana kallon shi suke yi dama daddy ba gwanin surutu bane sosai don haka kai kawai yake kadawa yana saurare. Sai da uncle ya gama magana yace dashi duk sherin uwace na fada mata tun farko ta fita hanya uwa ba son zaman lafiya suke yi ba su taki yarda yanzun da yafita a tsakanin su ai tayi hankali. Sun kai wani lokaci a falon hajiya tana sulhunta su sai daga karshe anty ta mike zuwa part din mu inda ta samay mu da su yan biyu muna ta zuba game abin mu hankali kwance. Mun dan zauna kowa bai sake da dan uwa ba sai da zasu tafine take cewa ashe mijin ki ya hana ki hurda dani ne ban sani ba ? Nayi dan murmshi nace akan may anty tace nasan abinda kika fada mashi ne tunda ya iya cewa hakan sai dai ina son ki tuna koda shi ko ba dashi ba zan iya rayuwa a duniya. Nace na sani anty amma kiyi hakkuri tace wa yaran ta su tashi su tafi yaran basu so wucewa ba dole suka mike suka wuce nayi masu rakiya tare da basu tsaraban da na saka masu a leda suka wuce na sallami daddy ya amsa min cikin dadin rai. Tare da dan yi min nasiha akan duniya bayan wucewan sune khadija tace wai anty may wanan matar ke nufi dake ne haka ? ZAINAB IDRIS MAKAWA SEENABU 9/11/20, 7:20 AM - Ummi Tandama: BAHAGGON RAYUWA, , , , , , , 🧕🏿7️⃣6️⃣🧕 ZAINAB IDRIS MAKAWA SEENABU KU Washegari da rana uncle ke fadin gobe zamu koma Abuja maganan tafiyan yazo min a bazata don ban shirya komai ba namu. Dole haka yasa mu shiri da tanadar duk wani abinda muke bukata a bauchi wanda muke so sai dai ba a cikin dadin rai muke shirin ba don rashin sanar damu da wuri da bai yi ba. Sai dare na samu shigo gun hajiya baaba tana gani na tace ashe gobe zaku koma nace haka yace muna hajiya nima banda masaniya akan tafiyan. Babana bai kyauta ba aika fadawa mutane su shirya ko amma haka da rana tsaka kace tafiya zakuyi nace baaba yadda yake so haka yake muna tace sai dai hakkuri shi kuma nasa halin ke nan gadara ga wanda yafi. Abinda da ta tanadar muna ta nuna min inda nayi godiya tare da nuna mata farin ciki na akan hakan. Tafiyan safe zamuyi don haka sauran kayan mu hajiyace zata turo min dasu ban samu koyin sallama da yan uwanshi badon ba lokaci. Washe gari gare goma muna cikin garin Abuja a gajiya don akwai barci a idanun mu mun samu su mummy da gwago lafiya inda suke ta cewa bauchi ya karbe mu sosai. Ni dai sai murmushi nake masu Uncle bai dade a gidan ba ya fita zuwa wurin aiki muma barcin mukayi don mu huta ranan Samira ta zo ganin mu da yi muna sannu da dawowa. Motar kayan mu sai washe gari zasu taso don a hada muna kayan mu da kyau koshi sai da hajiya baaba ta roka muna saboda masan da nace mummy tace muzo mata dashi. Mun dade da Samira a dakina muna hira sai dare yaya yazo ya dauke su suka tafi washe gari motar suka iso wajajen uku na rana da kayan mu ciki. Sai da na kawar da komai yadda ya dace na dawo falo bayan nayi sallah laasar na zauna tare da mummy da gwago da suka fito falon. Mummy ke fadin gwago sai kuma shirin gida yanzu ko kafin in magana khadija ta cabe zancen da cewa cabdi gida kan ai ba yanzu ba. Don dai mai tafiyan yace wai sai yadawo kasan waje zamu tafi gwogo tace wane ni nan ashe ko zan barku anan don yanzu haka munyi suna fada min wai ragona ya kasa shekaran jiya. Nidai ban yi magana ba tana ta fadin ita gida tayi bata kara lokaci sai mummy ce tace da gwogo din kada kuyi haka don Allah don baku san tsarin shi ba. Ni dai abinda nake so ku saka mashi ido akan zance musanman ke gwago da kin yi magana zai iya sa ya zaci wani abu don Allah ku sa mai ido kubi sannu. Tace shine kuma amma gaskiya badon nauyi ba da nayi gaba ni daga baya basai su su iso ba idan ya shirya masu tafiyan. Nidai jinsu kawai nake yi da khadija ta matsa nace a zafafe aiko yanzu zaki iya tafiya khadija ba sai kin jira zuwa wani lokaci ba. Sanin baka nayi mata yasa taja bakin ta tayi shiru bata kara magana ba a gaba sai kumbure kumburen da take faman yi ita kadai. Gwago ma da yake kakace sai cewa tayi kun dai rike mu ke nan ke da mijin ki ai na gane nufin ku damu sai dan ku ya iya tafiya kila zaku bari muje gida. Dariyan dole tasani nace wai gwago may zaki je gida kiyi ne don Allah baya kina nan hankalin ki kwance. Da sauri tace ina ne hankali na akwance garin naku da haka ganin kowa kullun gaka gida a kumshe kamar kayan wanki. Acan din yawo kike zuwa ne ba ko yaushe kina cikin soyan gyada da fitar da mai ba nasan duk wanan aikin ke a ranki. Mummy tace ashe ki gane gwago dai ta juya wurin khadija da ta cika fam tace ta wuri kyale su kinji dole sai yadda sukayi damu yanzu mmutum ko hanyar fita unguwar nan bai sani ba balle ya guda. Dariya duk muka kwashe dashi nan dai akai ta hira har lokacin sallah magariba yayi muka watse kowa ya nufi wurin sallah. Yau kwanan mu biyu da dawowa bauchi kowa ya sake a gidan ba zancen zuwa gidan da suke min matsi a kan shi kuma. Suna zaune falo na fito cikin wani dogo riga green color har kasa sai shape din da aka fitar ma rigan aka dan buda kasan shi sosai cup ne a hannu na na ciko da kindarmo dana dan zuba shikafa a cikin sa kadan ina sha. Mummy dake zaune tana ba Abba abincin shi tana magana da khadija da ta mimike kafa saman kujera kafin in kai zaune nace ta kwashe kayan da ke saman sauran kujerran don Allah ta kawar dasu. Tace yanzu nake magana ai don nasan gidan yan tsabta nazo ko tsinke ba a gani a gidan ku zama nayi ina ce mata yanzu wake son kazanta khadija. Ai ba dadi ne aganka a waje fes azo gidan ka asamay ka ciki kazanta kin ga hakan ai ba dadi a riskeka ta yadda baka so ba. Ta kawar da komai ta dawo zata zauna sai ga driver shi ya shigo da wasu kwalaye gidan yana gaishe mu da gida mummy ne ke tambayan shi tare kuke da ya bata amsa da eh sai naga sun shiga mikewa suna shigewa dakunan su. Sai ni da khadija aka bari a wurin muna masu dariya ya shigo yana waya muna mashi sannu da dawowa yana amsa muna da kai kawai. Dakin shi ya nufa ta kalle ni tace kamar kin san yana zuwa yanzu kika ce in kwashe kayan saman kujerun nan anty khadija nasan zai iya dawowa ko wani lokaci shiyasa ban yarda ya riske mu a hakan ai. Fitowa yayi daga dakin bayan ya rage kayan jikin shi ya sauya wasu nan yazo falo inda muke zaune ya zauna khadija zata tashi yace No zauna abinki ba komai zanyi ba ai. Ba ta dai zauna ba ta mike ta shige wurin su gwago tana dariya ya juyo gare ni tare da dan furzar da iska daga bakin shi yace ina son kiyi min list din abinda kike bukata na tafiyan ku. Da wanda za a saiwa gwago da khadija ko kuma dai ki kira samira ku fita tare kiyo masu sayyaya don banda lokaci gobe ina son zuwa lagos in dawo gobe din kuma. Don jibi nake son muyi tafiyan nan nakaiku gida kafin in dawo kin dan sha gida kadan, wani irin dadi naji ya ziyarci zuciyana a lokacin wanda ban san lokacin da nayi mai godiya ba. Daga gwago har khadija duba dari dari ya basu su sayi abinda suke bukata na kasan su da zasu tafi dashi gida. Sai kuma yace ke kuma ban san irin tsaraban da kike son ki tafi dashi ga dai wanan sai ki shiga kasuwa ki gani zan sa a kawo maki shadda da a tamfofi so ba sai kin saye su ba su. Har kasa nakai ina mashi godiya tare da nuna farin cikina a gare shi waya aka bugo mai ya mike ya fita waje haka yaba ni daman mikewa zuwa masu bayani a dakin su. A dakin su na shiga da sallama na nan na samay su suna hira ana dariya na zauna tare da fito da kudin ina mika wa kowa nasa sai kallo na suke yi da mamaki a fuskan su. Nace Uncle yace na baku wai gobe a shiga kasuwa a sayo wa kowan ku abinda take so na tafiya shiru dakin yayi na dan wani lokaci. Sai mummy ne tace Allah ya umfana ya saka da alheri yayiwa dukiya yawalta nace amin mummy gwago ta bude baki da kyat tace ni na rasa abinda zance wallahi. Shi baya gajiya da dawainiya ne kullun kazo da alherin da za a bika dashi haka ba kadan ba kuma ? Haihuwa ne tayi ranan ta inji mummy hakurin yar ku ne yaja maku haka da Safiya bata da hakkuri a rayuwa da ba acin ma hakan ba. Biyayyan aure ba abinda baisa miji yayi ma mace da yan uwan ta sai aga kaman wani asiri take wa mijin yake sakar mata hannu haka. Nan ko mutane basu san iya hakkuri da diya mace ke hadewa a dakin auren ta ba sai idan dadi yazo ne zakaji ana fadin ta mallakeshi ne musanman dangin miji. Sun fi jin zafin macen da mijin ta ke yawan kyautata mata da yan uwanta koda yana ma nashi yan uwan sai suga ai yafi kyautatawa matarshi da yan uwanta. Gwago tace haka abin yake a ko wani gida wallahi mu dai bamu da abin da zamu ce wa wanan yaron sai dai muyi mashi fatan alheri da gamawa da duniya lafiya. Duk muka ce amin dakin nan khadija ta shiga rawan kai tana lissafo abubuwan da take bukata na rayuwan ta. Gwago tace ke arr wawiyar banza baki lissafin kayan daki ba sai shirmay kike faman lissafa muna kawai ko kwabo bazaki taba ba cikin kudin nan. Uwarki za a kaiwa su gida idan mun koma lafiya take ta turo baki gaba tana magaba kasa kasa. Rankwashe gwago takai mata akai nace gwago rabu da ita don Allah kudin tane fa yaba ta ne don bukatunta mana. Tace kaiyya yaro mankaza yanzu har dake kike bata shawara ta kashe kudin nan ga banza ba zata kai ma uwar ta tasai mata abin kwarai ba. Nace haba gwago ayi fatan a samu wadata mana kafin auren anci gaba ai gaba gaba muke fata a rayuwan mu shiru tayi nace khadija barin buga ma Samira waya ta shigo gobe sai mu fita kasuwan. Khadija ta fara murna ji zan barta tasai abinda ranta ke so gwago tace miko min kudin nan baza ki kashe su duka ba mara hankali kawai. Tace anty wai may yasa kika bani nawane a gaban gwago yanzu zata sakani gaba da tsegumi wallahi bayan itama an bata nata ta kulle a lalitan ta. Gwago zata taso tabar dakin da gudu tana dariya ta juya gare ni tana fadin Allah dai ya shirya ku mummy tace ai idan zaki kara mata da naki indai yaran yanzu ne tas zata kashe su wallahi. Ban zauna ba nabi yar uwana muka zuwa daki nan muka zauna muna hiran da ita har na kira samira tace zata shigo goben mu fita. Washe gari Uncle yayi asubancin barin gida kamar yadda yace bayan yaja min kune akan kada mu dade idan mun fita ya kama hanyan airport. Sai misalin sha biyun rana samira ta shigo gidan bamu jima ba muka tafi bayan mungama zolayan gwago ta kawo kudin ta a kaso mata. Tace Allah ya tsari kakanta kande da tashi fatalwa ai idan mun anshi kudin nan a hannun ta kashe ta mukayi. Bamu dawo gida ba sai da muka cika bayan hilux din da muka shiga kasuwa dashi fan na hado tsaraba mai himilin yawa muka dawo gida karfe biyar da wani abu na yamma. Mun shigo a gajiye mummy tana muna sannu da zuwa gwago dake daki tafito tana daura dankwali a kanta tana fadin . Yau kan akuyan daure ta samu saki naso ace mijin nan naki yana gari inga karshen yawon ku sai da aka fara shigo muna da kayan ne ta kama fadin dan kari. Ban tsaya ba na shige daki wanka nayi na rage kayan jikina n tare da jero sallah da ake bina na fito falon. Sannu a hankali muke bude kayan da ba ayi packeding din su ba muna gyawa dani da samira da mummy muka hade komai gwago na kallon mu. Sai dare uncle ya iso gida don tafiyan yini yayi ranan tunda ya shige bai fito ba sai washe gari nan yake fadawa gwago washe gari zamu tafi in Allah ya kaimu. Murna wurin gwago ba a cewa komai do haka ban samu kaina ba ranan sai faman shirin tafiya nake yi sai yamma na samu kaina na huta. Kayan da uncle yaga na dauka yasa shi yin magana wai yaushe ne zaki dawo wanan uban kayan da kika dauka haka ? Nace ko kwana nawa ka bani ai shi zanyi bakari cikin sa murmushi ya gyara zama yana fadin kwana hudu yayi maki ko da kallon fuska na don son jin amsan da zan bashi a lokacin. Nace na gode Uncle ya ce ki kwanta don sammako nike son muyi don inje in dawo gobe din don jibi zamu daga zuwa Egypt. Mun raya daren mu cikin dadin rai inda nayi asubancin tashi tare da tayar da su gwago muka shiga shirin tafiya kafin shida duk mun shirya ko . Ban san da yaya Saadu za ai tafiyan ba sai da yazo da safe yake fada muna ai dashi zamu tafi inda mummy zata je fatakwal kafin mu dawo ta duba yaran ta nacan amma ba ranan zata tafi ba gidan yaya Saadu zata dan zauna tukun. An gama saka kaya a motocin da zamuyi tafiya dashi mu uku baya su biyu da yaya Saadu a gaba sai dayan motan driver da wani mutum ke ciki da kayan mu wanda ban san mutumin ba ko gaisuwan kirki bamuyi dashi uncle ya tsare ni da ido. Ban son yawan gaisawa da mazan da ban sani ba duk da wurin shi suke zuwa amma da naga bai so sai nima nake share su kawai. Don ko zuwa da ma aikatan su sukayi da na haihu ba karamin fada yayi ba daya dawo wai na zauna wasu kattan baza suna kallo na dama suma abinda ya kawo su ke na don su ganni saboda sun ga bai gari. Wanan abin tun yana bata min rai har nagaji na bari don halin shi kishin maza irin na haukan nan har ba a san abin fadi ba. Shida yaya saadu ke fira sai jefi jefi nake saka masu baki daga inda muke zaune a bayan motan don gudun zurewa ya kuma samu abinda yace nayi mai abinda ba dadi don ba freedom yadda ya dace. Tunda zamu taso na buga ma ummi na waya cewa zamu taso don haka ayiwa su uncle abinci kafin mu iso don yau zasu juyo su. Mun sauka mi salin kare biyu saura na rana don ba karamin gudu yaya yake yi ba shiyasa muka sauka da wuri wani iri nake ji a raina yau zanga yan uwana da iyayyena dana dade ban gani da sauran abokan arzikin mu. Tunda aka ce gamu mun iso yan uwana sukayo waje da gudu don taron mu abin gwanin ban shaawa kaina sukayo ni da khadija. Da murna muka rungumay juna kowa yazo kokari yake ya rungumay ni kamar bani bace safiyan da suke gudu da karna shafa masu cutan dake jikina a baya. Sai gashi yau sanadin auren mai kudi da samun gata an manta da komai da ya faru a baya an koma kamar ba a yi ba muryan shi naji a bayan mu yana fadin. Watau yar uwarku kawai kuka sani baku san kowa ba ko nan suka shiga mashi sannu da zuwa wasu suna fadin ashe da mijin ki kuka zo yaya saadu yace ai kauyawa ne wa yan nan. Nan muka shiga gida suka dinga kwaso kayan da yaya saadu ke dora masu yana masu sheri irin na tobasai uncle sai murmushi yake yi kawai . ZAINAB IDRIS MAKAWA SEENABU 9/11/20, 8:20 AM - Ummi Tandama: BAHAGGON RAYUWA, , , , , , , , 🧕🏿7️⃣7️⃣🧕 ZAINAB IDRIS MAKAWA SEENABU NOVEL DINA NA KUDI UBANGIJI YABI MIN HAKKINA AKAN WACCE KE FITARWA DAGA GROUP DINA ALLAH NA KAI KUKA NA GARE KA KA BI MIN HAKKIN CIN AMANA AKAN KO WACECE, , , Ya ubangiji Allah kayi gagawan daukan min fasa akan muna fuka ko munafukin dake fitar min da hakkina waje. Ya Allah kayi gagawan amsan min hakkina akan wanda duk yafitar da novel din nan waje ko wacece annaminiya mai fuska biyu ko a lahira Allah ya baiyana ta gaban jama, a wacce bata da amana kawai. Sai dai dadin abin na fada tun farko na kudi ne kuma online novel ne kika yar da kika shigo group din Alhamdullahi ina jin dadi idan na tuna hakan. Mun shiga cikin gida su mama da ummi sai taron mu suke yi da fadin maraba da mutanen Abuja suna kokarin amsan Abba dake hannun yara. Idon kowa na a kaina har muka karaso cikin inda kofan dakin ummi yake muka nufa ciki muka shiga da farin ciki a zukatan mu. Daga mu har mahaifiyar tamu da akewa lakani da uwar mata don mata mun fi yawa a cikin yaranta. Kayan da nazo dashi ake ta faman shigowa da su gidan ana jibge su dakin ummi na kofa kuma suna ajewa a kofan dakin. Mun tasa ummin mu a gaba da kallon yaushe tabo aga juna sai muryan yaya saadu mukaji yana fadin a kawo wa baki ruwa mana. Da sauri ummi ta tashi ta hado ruwa sanyi a cikin plate taba yaro ya kaiwa mazan dake waje da sauri nace ku rage kayan nan da kuka tara nan ashiga dasu ciki da sauri yaran suka fara kwasan kayan suna shigewa dasu. Uncle ne da yaya Saadu suka shigo gidan da sallaman su nan su mama da ummi suka shiga kankantawa don suruki ya shigo a lokacin. Sai lokacin na lura tun shigowan mu ban ga inna ba a gidan ina tambaya kafin mama ta bani amsa yaran dake wurin su ke fadin tana daki bata da lafiya. Subbahanallah nace tare da kara tambayan su bata da lafiya may yasamay ta ? Ina fita daga dakin dake cike da yan uwana da abokan arziki da suka shigo taro na da zuwa jin murya na inna tayi dan tambayan yanta sai gata ta fito waje tana yamusan fuskan ta alaman akwai yani guri dake matsa . Gaishe ta nayi tare da tambayan yaya gida tana tambayan uncle nace tare muka shigo dashi gaya can dakin ummi. Yaran dake cikin dakin khadija ta koro zuwa waje nan dai suka samu gaisawa da su ummi da mama sai gwago dake ciki zaune dasu. Sun yi wa ummi yaya hanya Allah yasa makasudiya ce ummi ta amsa da amin tana dada godiya yana fadin bako mai ai mama. Muryan baba ne ya shigo gidan da farin ciki dakin dan ganin su sannu da zuwa yake ta faman yi masu suna amsawa cikin alkunyan daga inda yake yake tambayan ina yaron yake jin muryan baban mu da nayi yadawo gida yasa na juyo na bar wurin inna din da nake tsaye. Yana tambayana na amsa mashi daga inda nake tafe a bayan shi da fadin baba mun samay ku lafiya na durkusa har kasa ina gaida shi. Yace tashi tashi yar albarka ashe yau kuna yafe garin namu ne sai da safe Rabi ke fadin kin ce yau zaku zo. Murmushi nayi kai na kasa nake fadin baba an dawo lafiya Allah ya karba ibadun da akayi yace amin amin yana karban yaron da shafiu ya fito dashi wurin abokan su yaya sani a waje. Yace ikon Allah yaron ke nan yayi wayau haka tubarkallah masha Allahu abu ko yayi kyau wallahi sosai yake fadi ni dai murmushi nayi daga inda nake tsugunne ina gaida baba ya juya zuwa sashen shi dauke da yaron a hannun shi. Dakin na koma inda na samu ummi tasa khadija ta baza masu uncle da yaya kayan abinci suna ci a falon nata sai kuma wanda ta bayar akaiwa driver da muka zo dasu waje. Dakin na shigo yaya saadu ke fadin Safiya ki debi abincin ki ci mana ga gwago nan tana cika cikin ta itama nace ai zanci ba yanzu ba yaya . Sun gama sun tashi zuwa dakin baba don su gaisa nan yaya Saadu ya barshi dakin tare damu inda yace ummi ina ganin na fita ke nan don zamu kama hanya da wuri muke son barin garin nan. Daga inda nake zaune a gefen shi ya juyo yana kallo na tare da fadin ina ganin sati biyu ko uku zanyi acan so zaki yi kwana goma zan turo Saadu ya zo ya dauke ku kafin in dawo daga Egypt din . Wani dadi naji har cikin raina kamar na sani kwana hudun da yace zanyi kawai na dai dauko kaya daya fi na kwana hudu kamar mai shirin yin wata daya. Ya kirgo kudi ya ba ummi masu yawa ya kara kirgowa ya ba gwago tare da khadija sai kuma su shafiu dake dakin suma ya basu already ya bani tun kafin mu zo. Nan ya fita sun dan jima da baba ya fito bayan yayi mashi alheri yaba su mama nasu tare da sauran yaran gida bamu samu yaya sani a gida ba ko da muka zo. Mun fita rakasu ne na hango shi can ya tsallaka wurin datawan unguwan mu da matasa yana masu alheri abinda ya sauka a gare shi. Sai dai na lura bada motar zasu tafi ba saboda ganin sun shiga hilux din da takawo muna kaya da zamu zo haka yasa na gane bada ita zamu koma ba sai wanan mutumin kamar security yake a gare mu ashe ma a nan zuwa dashi ke nan da mukayi Ya dawo na dan dade gaban mota muna magana dashi mutane sun kura muna ido a zaton su wani hiran dadi mukeyi a lokaci. Amma a zahiri warning dina yake yi da baison yawo ya barni gida ne in dan jima don ganin yadda yan gidan namu suke kewan gani na. Wanan abin yake fada min wanda bai sani ba sai yayi zaton wani hira mai dadi mukeyi a lokacin kasancewar duk fuskokin mu yana dauke da murmushi ne a lokacin. Nan mukayi sallama suka ja mota suka tafi yau gida yayi bakin abuja cike dakin ummi yake da yaran gidan mu suna min hira shafiu ko yana makale da Abba bai bari kowa ya dauke shi cikin yaran. Sai da suka rage a dakin ya rage sai mu da yan dakin kade a lokacin nake cewa ummi wai may ke damuwan inna ne haka ta zube a lokaci daya ? Shafiu yayi saurin cewa injin bakije dakin ta ba anty da sauri na kalle shi nace may ye a dakin nata da ba a shiga ? Yace ance ciwon tari ke damun ta don haka baba yayi muna kashe a kanta da kuma taba kayan da tayi amfani dashi don gudun daukar cutar gare mu. Wani irin ras gaba na yaba da a lokaci daya nace ummi da gaskiya abinda ke damun inna ke nan shine ba afada min ba ko a waya. Hankali na ne bai kai da in fada maki ba ai hakan bai hanata rashin mutuncin da ta saba yi ba a gidan shiyasa malam ya kafa doka akanta har yaranta. Nan dai suke muna hira yadda abin yake mata da dalilin daya baba har ya kafa mata doka mai tsanani a gidan kamar yadda likita yace a kiyayye don gudun daukan cutar. Gwago ce da zata gida muka fito sai lokacin na ke magana da baba don aba driver da wanan mutumin da ya bar min zamu zauna dasu don kaini wurare inda zasu zauna. Baba yace a gyara masu dakin yaya Sani don dama shi driver ya saba zuwa tun kafin muyi aure da uncle ya zama dan gida yanzu. Nasa shafiu ya gyara dakin tare da kai masu abubuwan bukata a dakin don bukatun yau da kullun. Da yamma yaya Sani ya dawo garin nan ya samu mun zo da murnan shi ya shigo dakin ummi yana taron mu ya samay ni zaune Abba na kuka ina lalashin shi . Yace ummi ashe yau baki ne haka a gidan namu khadija ce ta leko daga kuryan daki tace yaya sani oyoyo yace ho yar birni an dawo tana fitowa yace kai kai kai. Ummi ki ko ga yadda yarki ta koma wata big girl haka wai ma tsaya naga alaman fa kin cinye masu kayan abincin gidan su fa khadija. Nace wane ita tadai ci iya cin ta ta dawo ta bar muna saura yaya ka dawo lafiya mun zo bamu samay ka gashi har da mutumin ka muka zo yau din. Yace haka naji tun a waje nazo na iske su Adam nata washe baki yau a jike suke dumus suke labarta min sai kuma naga musa drivern ku a waje. Nace nan ya barsu wai zasu kula damu a nan kasan mutumin naka bashi da yarda don wai kada in ta yawo mutane suna gani na. Dariya sukayi har ummi tace ai shine maganin matan yanzu da basu mai da fita a bakin komai ba sai kiga mace ko bada sanin mijin taba ta saba gyale akai ta fita. Yaya Sani ne yace ummi ai har mata kauye yanzu sun koyi wanan dabian kwana ki nan rikice ya barke tsakanin isah da matar shi wai taje buki bata fada mai ba sai dawowa tayi gida ya samu ta Ummi tace kaga abinda ke sauri halaka mace a yanzu don ace da mijin ka ya dawo gida daga tafiya ya samu mace bata gida. Gara ya dawo ya samu gawan ta a gidan yafi sauki amma kin ga matan yanzu basu damu da wanan abubuwan ba sam. Khadija dake shiri fita waje tace cabdi yanzu kan ai sai Allah ya gyara kawai dama akwai irin su anty masu tsoron miji kin ga yadda take tsoron mijin ta kuwa ummi . Ummi tayi saurin katse ta da cewa masha Allahu ai gara da naji wanan shedan da kikayi wa yar uwar ki din don yanzu na gamsu da irin tarbiyan da na dora ku a kai. Kallon ummi tayi kawai ta girgiza kai irin watau ummi din bata san komai ba ke nan yaro yayi sallama yashigo da abinci yana fadin inji Saadatu tace ya kawo wa baki. Karban abincin nayi ina ma yaron godiya na ce shafiu ya bashi dari biyu a cikin jakkana dake kusa dashi. Yaron yana godiya ya fita nace ya gaida ita ummi tace Allah sarki wace ke fama da kanta kuma har da kokarin kawo abinci haka. Yaya Sani yace ummi ai shine zumuncin ko yayane kaima dan uwanka shima yasan ka damu shi ba kullun sai dai aita baka ba kana karbewa. Hakane inji ummi tace naga tana cikin yanayi ne kawai mijin nan nasu yana ta kan shi yanzu ba wani sana a mai karfi yake yi ba. Bude abincin nayi inda naga tuwon masara da miyar busassan kubewa da kifi bussashe ba wasu manya ba miyan yana kamshin dadawa da kayan yaji. Zama nayi muna hira da yaya naci abincin sosai don na dade banci irin shi ba sai mamaki suke yadda nake kai loman tuwon a bakina ina yaba dadin da tuwon yayi. Yaya sani ya fita ina shan miyar ummi tace da alama miyan yayi maki dadi sosai ko ? Nace wallahi ummi naji dadin miyar sosai don na dade ban ci miyar kubewa busassa ba tun bari na gida fa ummi. Sai bayan da na wanke hannu na dawo na zauna nake tambayan ummi may ye matsalan mijin saadatu ne wai ? Tace masu bashi kayan ne da farko suka daina yanzu wai don ya auri Saadatu din ashe dama wani dan uwan matar shi ne yake bashi kayan yana sayarwa. Kai na girgiza kawai ba tare da na furta komai ba sai dai cikin zuciyana ina tunanen may ya kamata nayi akan maganan ne ? Ranan mun kai wani lokaci muna hira da ummi na inda take goye da Abba a bayanta acewar ta wai zai dade yana barci idan ya kwanta ga ruwan zafi daya sha a jikin shi ya gasu sosai a wurin mama da tayi mashi wanka. Khadija kan tun da ta shigo ta kwanta tana sauke gajiya a gida wanda ta dade tana kewan gida a ranta don zamanta na abuja a matse take ba fita ko ina. Washe gari ban tashi da wuri ba don dadewan da mukayi da ummina muna hiran yaushe rabo tare da ita daren jiya din. Shogowan dan gidan da Ainau ke aure yar wurin anty da kwanon kosai da koko na daka wanda yasha kayan kamshi yana tashi a cikin shi yace wai ance ya kawo wa bakuwa da tazo daga Abuja. Fitowa nayi don in ba yaron wani abu don naji ummi na sallaman shi tana fadin kace mata an gode kaji na fito ciki ina fadin ga wanan a bashi kace ina gaida ita na gode kwarai. Wanan abin da yan uwana suka yi min naji dadin shi sosai a raina hakan na nuna yaran gidan mu akwai hadin kai sosai wurin son junan mu. Ban fito ba sai da nayi wanka na shirya cikin wani dogon riga mai taushi na fita zuwa gaida mutanen gidan mu. Dakin mama na fara zuwa tana ciki sun baje da yaranta suna karyawa na shigo dakin da sallamana a dakin na samu Abba a bayan mama tana goye dashi yana barci. Na dan dade dakin muna hira dasu sai na tashi zuwa dakin inna inda na samay ta zaune a falon dakin ta tana zaune ita kadai yaran dakin ta duka suna kofan ummi na suna karyawa a lokacin. Na shigo da sallama na nace inna ashe baki ji dadi bane haka ta gyara rufin zanin da ta rufa a jikin ta tace wallahi ke dai safiya. Ciwo wasa wasa gashi sai gaba yake min nace inna kuna na asibiti kuwa tace tau safiya waye zaiyi jimirin kaini asibiti ko wani lokaci. Tausayi tabani sosai nace to inna sai a zauna da ciwo haka a gida ai gara dai a tafi asibiti a gani zaifi hawayen da yazo matane ta shere a fuskanta Tace safiya yan uwan ki kowa gudu na yake yi a gidan nan har malam din kanshi guduna yakeyi yanzu wakike gani zai kulani a hakan bayan duk suna tsoron zuwa kusa dani don cutar da nake dauke dashi. Koma asibitin nace zan tafi ba wasu kudi issasu a hannuna da zasu kaini ance maganin tsada gare shi wai. Ba komai inna bari yaya sani ya shigo sai muji yadda za a yi amma ai ba a zauna haka da ciwo a gida ba kullun yana kara maki illa a jiki haka ? Abin mamaki sai ga inna tana cewa da bakin ta ubangiji Allah yai maki albarka safiya na gode kwarai wallahi Allah ya kara arziki , . Mikewa nayi nace bakomai ina har na kai kofa nace ki ko karya tayi murmushi kawai tare da fadin abinda akace inci ne ba samun shi nakeyi ba akai akai. Fita nayi daga dakin inda ban koma dakin mu ba baba bai gida ya tafi zanen suna tun da safe ya fita gidan don haka na leka waje na kira yaya sani yana zuwa nace mashi. Haba yaya sani kasa halin da inna take ciki shine kuma ka kyale ta haka a daki ko karyawa batayi har yanzu ace mara lafiya bai karya ba har wanan lokacin. Humm yace safiya jiya da mijin ki yazo ai ya basu kudi ina takai nata nace babu ruwan ka yaya ladan haihuwa zaka nema a wurin ta ai. Ba zakayi fatan kaga ka rama mata abinda tayi maka ba kana yaro yanzu har zaka tsaya yaya duban wai tana da kudi tayi amfani dasu . Ka sani ko tana da abinda zatayi da kudin data samu jiya don Allah yaya ku daina wanan hali kune fa manya a gidan nan da zamuyi koyi da halin ku na gari. Yace wani yanzu ai mun baki girman safiya kece antyn mu kaf a gidan nan mun biki mun bi Allah don shi ya baki girman dariya ya bani har yasa na kasa karasa maganan da nake mashi don banbadancin da yake zuba min a lokacin. Nace ni dai yanzu muje in baka kudi ka sayo mata abinda ya dace zan maka list din komai ta fara karyawa kafin mu je asibiti da ita. Yace amfa je asibitin ita ce taki yarda ai mata alluran wata uku da sukace zasu yi mata wai karya da kazafi ake mata akan ciwon. Nace inma da tace karya ne yanzu batace ba don munyi maganan da ita daga dakin ta nake yanzu ma yace tunda ke ce ai yanzu ta yarda. Mun je dakin na kirga kudi na bashi anan muka aje magana zai dauko wanda zai mata alluran da aka rubuta mata tayi din da magani sai yazo zamuji ko nawa za a kashe sai a fara mata alluran ranan. Kunun da Ainau ta kawo min na zauna nasha ina wurin zaune na dauko waya na kira uncle yace ya kirani bai samay ni ba gashi zasu tafi airport yanzu Allah ya tsare nayi mashi muka kashe wayan bayan ya tambayi Abba dasu khadija nace suna lafiya. Tsaraban kayan abincin da nazo dashi na fara raba sai kuma na shiga rabawa yan gidan mu tsaraban da nazo ma kowa a gidan mata sun samu turamay zannuwa da sabulai da man shafa ida maza shadda na raba masu da turare da takalmomi matan sun fi maza samun tsaraba sosai dana kawo masu. Yaya sani ne ya shigo da malamin asibiti muka shiga dakin inna dashi inda yayi bayanin a gaban ta da abubuwan da zata daina ci da wanda zataci har tsawon wata uku . A gabanta na biya kudin komai da za a yi mata kukan da ta fara ne yasa na bar daki na koma dakin ummi jiki a sanyayye ida yan gidan mu kaf suke dakin na ummi khadija tana masu hiran abuja da bauchi. ZAINAB IDRIS MAKAWA SEENABU 9/12/20, 7:42 AM - Ummi Tandama: BAHAGGON RAYUWA, , , , , , , , , 🧕🏿7️⃣8️⃣🧕 ZAINAB IDRIS MAKAWA SEENABU Muna tsaye kofan inna muna kallon yadda likitan yake mata allura zabban tausayi har ya gaba ya fito yana cire safan hannu da takunkumin da ya rufe hancin shi dashi inda ya jefa a wani leda zai fita dashi. Nan yake fadi a gaban kowa yace a kikyayi zama kusa da ita a daina amfani da duk wani abin amfanin ta don ciwo ne mai saukin dauka ga mutum idan da hali a raba makwanci da ita. Kuka inna ta saka mai ban tausayi tana fadin ni rakiya yau naga ta kaina na zama abin gudu har ga diyan da na haifa a duniya. Daga kofa inda nake nake fadin cikin murya mai rauni inna kiyi hakkuri ciwo ba mutuwa bane zaki samu lafiya in Allah ya yarda adai kiyaye abin daya fada kawai. Yaya sani yace yau bagaki ba safiya may ye ba ayiba a lokacin ciwo ki a gidan nan wanda ba kowa ya sa ai maki ba sai ke inna ina fada maki ki bari amma kamar zugaki nakeyi a gidan nan. Har kika fara gaba dani ummi gata da ranta ita tayi min fada akan in bi maganan ki in bar fushi dake komai Safiya ta taba a gidan nan damun bi ta naki inna kona shi zamuyi a lokacin. Likita yace ai wanan ciwon yafi kanjamau saurin kisa yanzu baga safiya ta gyagije ba kamar ba a yi ba da ta fake magani . Ai ba a gudun mai kanjamau kamar may irin cutar nan don saurin dauke gare shi sosai ga wa yanda ke kusantan ka sai kawai mukaji inna ta saka wani irin kuka mai kama da ihu a lokaci guda duk muka rudu ga kowa na tsoron shiga dakin wurin ta don kada ya kamu da ciwon. Nayi kundunbala na fada dakin ina bata hakkuri sai fadin take safiya dole inyi kuka cutar nan kila kasheni zaiyi safiya. Ina naje dana dauko wanan mumunan cutar a jikina yaya sani shima ya shigo daka ciki muna bata hakkuri likitan yace idan zamu shiga wurinta mu dinga saka takukumi a hancin mu dau saukin shakan nufashin ta. Mun fito muka sallami likitan na bashi duk wani abin bukata har zuwa lokacin da alluran zai kare. Shigowan Saadatu ke nan gidan da goyon ta wanda yayi wayo sosai yaron ganin mu a kofan dakin inna yasa hankalin ta ya tashi bamu ko gaisa ba take tambayan mi may ke faruwa ne ta gamu cirkocirko haka tsaye ? Bakomai na fada ina karban dan dake goye a bayan ta amma sai yaron yaki zuwa wurina don kiuya irin na yara da yake dashi. Dakin ta shiga ta ga uwar a zaune a tsakiyan falon ta tace inna yaya jikin naki tace da sauki nan dai ta dan tsaye, tsaye jim sai ta fito waje. Lokacin na koma bangare ummi na ina batun aika yaro yakai ma mahaifiyar Amina sokon a gidan su sai da nagama bada sokon na juyo gareta ina Saadutu an shigo ashe ? Gaisawa mukayi tare da tambayan lafiyan su sai godiyan abincin da ta aiko min dashi daren jiya din da tayi shima nayi mata godiya akan shi. Tace kai don Allah nasan ai bazakici ba na dai aiko ne kawai kada dan uwanka yazo gari baka aika mai da komai na sannu da zuwa ba. Kika ce wai ba zanci ba toga ummi nan tambaya kiji sai da naci fiye da rabi nakuma shanye miyar tas wallahi taji sadi don fuskanta yanuna hakan. Tace ikon Allah har abokiyar zama na fadin wai zan dai kawo ne amma ku yan birni ai ko kallon wanan abincin bakuyi ai haka dai na daure na kawo maki shi. Nace aini banki ba kullun kina kawo min irin wanan din don ina son shi sosai wallahi samu dai ne ban yi a can. Ikon Allah na katse ta da fadin yaya Adamu maigidan ki yake dariya tayi tace mutumin ki yana nan lafiya wallahi sai dai yanayin garin da muke ciki yanzu kawai amma ya daina halin nan yanzu lafiya lau muke dashi sai abinda ba a rasa ba. Tace ai yaji dadin kudin da kika aiko mai kwanaki har ya fara sana a sai wa yanda suke sana,an tare ashe suna bishi kudi nan sukayi karan shi karshe har da na wurina muka hada aka bashi yanzu yana zaune bai komai kuma. Na tausaya mashi nace mutum magidanci ya zauna ba sana,a haka ai abin baiyi ba wallahi tace ai yace yana nan zuwa ya gaida ke da zuwa. Nan Ainau ta shigo gidan itama da goyon ta muka hade mu uku duk sun girmay ni amma samun wuri da kuma maganin da nake sha wanda ya hurani na danyi kiba ba sosai ba. Anan muka wuni tare da su inda na dauko masu tsaraban su na basu sai farin ciki sukeyi da murna ga abinda na basu din. Sai yamma suka tafi gida inda nace masu idan na huta zan shigo gidajen nasu mu gaisa na dan raka su na dawo na dibi ruwa zan watsa ma jiki sai ga shafiu ya shigo da Abba a hannun shi yana fadin wai ga Adamu nan mijin Saadatu yazo gaida ni ya shiga ya gaida inna da sauri na mayar da rigan dana cire a jikina kafin ya shigo dakin ummi din mu gaisa dashi. Da sallama ya shigo ina saman kujera na mike ina ce mashi ga wurin zama nan ya zauna yace a a zai zauna kasa na hana shi dole ya hau kujeran ya zauna. Ni kuma na koma daga kofan kuryan dakin ummi na fara gaida shi yace kunzo lafiya nace Alhamdullahi yace to barka da arziki ashe an sauka murmushi nayi yace bamu ba da komai ba sai kuma ga sako na gani nagode nagode kwarai Allah ya kara rufa asiri. Nace kai haba bakomai wallahi kasuwa dai yana tafiya yanzu ko na tambaya kamar banji komai ba a kan shi yace tau Alhamdullahi zamu ce hajiya don ba a cewa komai sai hamdala. Amma gaskiya yanzu komai ya tsaya ne cak wallahi kudin da kika turo min kwanaki na fara dauko mai jerka biyar dashi tunda wa yanda muka fara sana, a dasu sukaga na dan samu suna bina kudi sai sukayi karana dole na hada kan kudi na biyasu abinsu shine yanzu nake zaune ina zaman ba sana a . Kin san ance wanda ya amshi kudi hannu mace yana tare da gori komai daren dadewa to abinda ya cini ke nan dama yan uwan matane suke bani yanzu kuma wanan abin daya gitta har na auri saadatu sai suka karbe dukiyan su a hannu na suga yadda zanyi watau. Dariya nayi nace baduk mata suke haka ba ai wasu dai ne haka suke shiyasa nima banyi maganan komai da Saadatu ba har tazo ta wuce ta dai fada min kamar yadda ka fada min yanzu din yanzu a misali idan na baka dubu dari biyu zasu isheka ka fara sana,a mai dan kauri dasu. Hajiya dari biyu ai ba karamin kudi bane yanzu nace to zan baka sai ka fara mu gani ya katseni da cewa har zuwa yaushe zan maida maki kudin ina mikewa nace a a baka nayi halal malak kaja jari dasu ba rance na baka ba ni kyautan su na baka. Zamowa yayi saman kujeran da yake zaune da farko ya hada hannayen shi biyu a wuri daya ya fara zabga addua da fatan alheri a gare ni. Nace ba sai ka fadawa kowa ba Adamu nidai bukatana a gareka shine ka rike min yar uwata amana don Allah ka kula dasu dukan su ukun matan kane. Godiya ya kara min yana kokarin tura kudin da ya karba a hannu na cikin aljihun rigan shi tare da yi min sallama har yake kofa ya juyo yana fadin gobe gobe in Allah ya kaimu zanyi asubancin zuwa birni wurin saro man in sayo. Nan dai ya fice cike da farin ciki nikan yana fita daga dakin na mike don duk zafi nake ji a jikina ina son in dan watsa ruwa inji sayi. Kafin wani lokaci gari kowa yasan na zo wasu idan sunga mota a wajen gidan mu ne suke tambayawa a fada masu. Wasu kuma idan na aika masu da tsaraba suke sanin na zo garin ban fara fita ba sai da na kwana uku yan uwa da abokan arziki suna zuwa gaida ni suna kuma aiko min da abinci da dan abin marmari don kulawa. Har da makwata dana ba tsara ba sun shigo taro na da gani dan da na haifa wasu dai gulma ne ke kawo su ganina kawai suga yadda ake fadin na koma yanzu. Gidan mummy mahaifiyar Amina kawana na fara zuwa inda musa driver ne ya kaini gidan shi da security din mu na dade gidan muna hira da mummy inda nace ai zan shiga wurin Amina kafin in koma in Allah ya yarda. Ina fitowa na wuce gidan su mama jummai na gaida su suma duk inda naje sai na jima a gidan daga wurin su na dawo gida. Duk abinda nasan inna naso wanda akace tace na sa yaya sani ya sayo mata inda nayiwa yaranta nasiha su kula da uwar su don Allah. Wanda ba kowa ta jawo hakan ba ga yaran gidan mu sai inna din don batayi zoton abin zai shafe ta ba haka. Washe gari gidan Ainau na fara zuwa tun da safe muka fita sai karfe daya na bargidan na wuce gidan saadatu . Gidane may irin dakunan nan ajere suke guda hudu sai baranda ba wani siri da mutum zai iya yi ba a ido yan uwa ba. Yaran gidan sun kai bakwai saadatu ne ke da daya a cikin su na samu wata mata da daure gaba tana tuka tuwo a tsakar gidan inda suke girki. Yin sallamana yasa sauran fitowa daga dakunan su mai tuka tuwon tunda tayi muna sannu da zuwa ta mayar da kai ga aikin ta bata kara juyowa gare mu ba. Tare da su khadija muke muka shiga dakin saadatu din daki daya ne single da gado da mirrow sai drower gadon dake gefe an dagwara mai roses guda guda da ledan kasa malale a dakin . Kujara mai zaman mutum uku damai zaman mutum daya sune a dakin zama mukayi aka fara gaisuwa a tsakanin mu saiga wanan matar da tafita tare mu dauke da kwanon sha cike da ruwa ta kawo muna. Tana fadin safiya ko ai yanzu bata gane ni tunda an dade ruwan na karba na sha nace wallahi kan ban gane ki ba yar uwa tayi dariya tace mune senior ku don muna gaban ku da shekara uku sai dai ni ban gama ba nayi aure lokacin mai yawo dasu Aisha sani na kusa da gidan ku. Nan dai suka shiga min bayani ita da Saadatu saida na gane ta nace ankoyi haka tace gamu mun hade da yar uwarki muna auren miji daya yanzu. Allah sarki nace kuna lafiya yaya yara yaron ta karba a hannun kauna na yar wurin mama da muka zo da ita tace tubarkallah yaro yayi wayo sosai. Mun dayi hira ta fita dakin mukaci gaba da hiran mu na abinda ya shafemu na gida maigirkin taba dan tuwo kasan kwano a kawo muna mukace a maida mata a koshe muke mu. Sai lokacin ta shigo tana fadin bazakuci abincin mu ba nace gidan Ainau muke sunci taliya acan ni kuma na koshi yanzu ganye kawai nake son in samu inci. Ta juya ta wuce saade tace ganye kike so nace eh tace barin nemo yaro ya sayo maki sai khadija tace baga maimu na ba abata taje ta sayo bakin kasuwa mana. Dubu daya na zaro a jakkana na bata tace na nawa nace ta sayo na duka ido suka zaro mun a lokaci daya suna fadin har ganyen dubu daya haba dai. Na dari biyu dai ko daya nace kuba zaku ci ba ne sukace zamu ci yar uwar zaman saade ne ta shigo dakin tana fadin ko zaki sha fura ne a sayo maki nace ganye dai nake son ci ga kudi na bada a sayo min tace wa zai sayo sai khadija tace maimu zata sayo. Ta sake tambayan da kuli zance ko soya min za ayi nace da kuli dai za a gyara min tace to ki sayo na dari biyu di sai kayan hadi sai saade tace kuje kiyi mata bayanin abinda zata sayo. Suka fice dakin nan dai mukaci gaba da hiran mu sai ga maimu ta dawo ba, a jima ba aka gyaro ganyen sallah muka farayi muka zauna gaba dayan mu muna hada hannu muke ci a katon tire dukkan mu. Khadija ce take fadin amma anty saade kunfi zaman lafiya da wanan matar data gyara muna ganyen nan tace ba ruwanta ai bata da fitina amma ita dayan haka take kamar innar mu wurin fitina. Kullun sai tayi fada da wani cikin mu kan diya ko kan girki sanan tana muna kurin yan uwanta na da kudi a cikin mu har gori tayi min da muka taba fada. Wai yar uwar tawa da nake kuri tana birni bata ko san dani ba a duniya sai ta kashe take bamu dariya nayi nace badai kina da mai kashewa ta baki din ba ai yafi babu. Tace ina ma kika sani dana dawo wurin sunan yaron nan da naje cewa tayi kuma wai naje nayo maula ne gurin ki ai ba shiri a tsakanin mu da ya dakin ku. Nace fita batun ta don Allah irin matan nan ne da sai su zuga ka har ka aikata abinda baka tashi yi ba tace ai na gane ta yanzu ban biye mata. Khadija na bawa makulin mota don bamu fito da su malam musa ba mu kadai muka fito yau, nace ta je ta dauko min kayan dake bayan seat a farar leda. Ta fita sai gata ta shigo da ledan nan nanuwa saade turamay zani da sabulu nace tabawa kishiyoyin nata. Tace duka safiya nace kada ki damu girman ki nake ja maki a hakan ai fita tayi sai nabi dakin da kallo don in san abinda zan mata a dakin nata don ace inna batai mata komai ga auren nata wai bata son auren. Ta dawo sai gasu tare sun shigo dasu sukayi godiya suka fita khadija ke fadin dama Atikan kawai kiba wallahi nace ai ba ayin hakana kuko. Nace saade yanzu kina ganin dakin nan yana daukan fridge da kayan kallo kuwa tace aiko bai yi zan sa afita da kuje daya sai in samu wuri nace to yayi sai ki gwada mu gani mikewa nayi nace barin shiga dakin senior dina mu gaisa na suri jakkana na fita daga dakin. Ina jin khadija na fadi zataje tayi mata dumus ke nan tunda kinga ta dauki jakkan hannunt ban tsaya bana fice daga dakin. Tana gani ta kama washe baki tana sannu da zuwa dakin nata gwanin ban tausayi wallahi kai mata muna cikin wani hali a rayuwan auren mu har na tuna da dakunan su ummi na da. Sai a kai mace da kayan mutunci gidan su amma sai a kashe kayan da miji ba zai damu da ya sayawa matar wasu ba tunda a tare ake amfani dasu sai dai ita mace ne zata kama kulla kulla har ta samu ta dan saye nima nasan da ina gidan Ahmed da har yanzu da dan gadon katakon dake daki na zan ta rayuwa. Mun dan zauna ina tambayan ta wa yanda mukai karatu a tare tana bani labarin su hannu na tura a jakka na na kirga dubu ashirin na aza mata a gadon ta nace ayi hakkuri akwai abubuwa da yawa amma wata rana zakiji sakona da yardan Allah. Na fice tun bata fara yi min godiya ba na shiga dakin dayar mai kurin arzikin gidan itama babu komai a dakin sai wani tsohon gadon na katako da wasu rubabun kujeru manya a dakin dubu biyar na bata na fito bayan mun gaisa da ita. Ina shiga nace ku taso mu tafi saade sai na sake dawowa maimu da hindutu ne ke rige rigen karban jakkar hannu na khadija tace naga alama mai kamar dai dake za a koma Abuja nan ko ? Nace maimu da hindatu kan ai tashina tashin su tunda ke kin gudo ban yarda in rasa abokin hira a gida ni kadai sai mummy. Nan suka shiga masu sheri suko yaran sai murna sukeyi zasu tafi abuja khadija na fadin kuje kuyi zaman kurkuku ai ba shiga ba fita sai zaman gida. Na bude mota muka shiga na tayar ina masu horn duk suka daga muna hannu muka tafi sai gida tun dawowan mu na dan leka inna wacce yanzu maganin ya fara bata reaction tana yawan galabaicewa sosai na samay ta zaune yaya Sani ya sawo mata lemo mai bawa tana sha. Na gaida ita na fito na shiga wuri mama itama na gaida ita na koma dakin ummina ina fadin wai kamar nayi wani abu yau duk na gaji ummi na sai dariya take yi cikin jin dadi da kulawa. Mun dan taba hira wanda kusan hiran na kishiyoyin Saadatu ne sai nace maimu dake lake dani ta kira min yaya sani a waje idan yana nan tashi maimu ummi tace ashe kin samu yan rakiya Abuja ne yanzu maimu ke fada min da su za a tafi wai ? Nace haka nake so ummi shima yayi mi maganan hakan don yaso khadija ta zauna damu amma taki kanta na rawa. Ummi tace bar ta kawai mara hankali ba komai ya hata zama ba sai wanan sauryin nata mara mutunci da take son dauko muna wahala taki zama. Nace nima dai ummi yaron bai kwanta min a raiba wallahi don ba yan mutunci bane ta rasa wanda zatayi soyayya dashi duk garin nan sai zurian su inna. Gaskiya nima hadin bai min dadi ba gaskiya ummi ai ta samu wasu a bauchi da muka tafi ban dai sani ba ko har yanzu a kan shi take. Ummi tace kinga ko bata fada ba don karnaji nayi mata fada tana tsaye daga kofan kuryan ummi tana sauraren mu ta turo baki gaba. Ummi tace tsayin may zaki zo ki muna a kai in kina tsayawa kima kan ki fada tun wuri gara ki tsaya ga masu son ki na kwarai don dai ni ba yarda zanyi da wanan zaben naki ba. Juyawa tayi ciki da fushi tana magana kasa kasa nace ji wawiya don Allah ana fada maki gaskiya har kina ganin laifin mutane akai. ZAINAB IDRIS MAKAWA SEENABU 9/13/20, 7:47 AM - Ummi Tandama: BAHAGGON RAYUWA, , , , , , , 🧕🏿7️⃣9️⃣🧕 ZAINAB IDRIS MAKAWA SEENABU Shigowan yaya sani ya katse muna maganan da muke akan khadija din don ko ba komai baza mu so yaji muna sukan dan uwan mahaifiyar shi ba a fili. Ya shigo yana fadin yanzu maimu da hindu suka tare ni a hanya suna fadin wai dasu zaki tafi idan zaki koma ? Nace a sanyaye haka nake so indan zan samu baba ya yarde min don gidan yana min girma ba kowa a kusa dani. Yace ai ba wani matsala bane idan mijin ki zai yarda da hakan sai dai kin san wasu baza basu son haka sam a rayuwan su. Nace shi ya bani shawaran hakan ma sai dai bai san da zancen maimu ba hindu dai mukayi magana a kanta da zan zo saboda ita khadija taki zama can. Yace khadija kan ai tafi son nan tana gudun kada a kwace mata guy din ta sanusi sai dai kuma ni naga sanusi baida alkibila don da batan yar gidan hakimi ya koma nema. But khadija ta fito daga daki tace yaya sani may kace yace au ashe kina ciki takara tambayan shi yace mata bai sani ba tace uhumm ummm ai naji abinda ka fada dama shafiu ya fara fada min yace kinji shine kike kara tambayana kuma. Nace yaya sani kaga muyi maganan abinda yasa na kira ka don Allah bar wanan zancen nata na shirmay ko a gidan shi kike da ke kadai zaki zauna balle bakuyi aure ba yana saurayi zai zauna dake ke kadai. Yaya sani ni kaga shawara na kiraka muyi don Allah yace to anty ina jin ki da sauri nace kai yaya sani nine kuma antyn naka kuma ? Bakiji abinda na fada maki ranan ba ne Safiya yanzu ai kin zama antyn mu gidan nan don ko maishi a yanzu shine babba don shawaran komai shike kawowa kin ga ko dole ne mu girmamaki ai. Ummi tace kai kaidai sani baka rabuwa da barkwanci wallahi yace ummi wallahi gaskiyan ke na ai anty ina jin ki. Dariya ya bamu sosai gaba dayan mu dakin sai da muka dara mai nace dama shawara nakiraka muyi akan Saade da Ainau. Yace bakaji magana na yafito ba ummi yanzu ni da ke nan ai ban taba shawara akan su ba ko yanzu ita gata tazo da shawara kuma nasan wanda zai amfane su ne. Murmushi nayi wanan karon ban dara ba don abin na yaya sani ya wuce sani na yanzu ya juyo yana fadin ina jinki anty safiya ? Nace yau naje dakunan su ziyara naga halin da kowacen su take ciki to ina dan son inyi wani abu akai ne a halin da suke ciki din na farko dai shin gyara masu daki zamuyi ko abin sana,a zamu ba ko wacen su ta kama sana,a kanta. Yana fadin a a ummi ma tana fadin ummu ummm kudai yi shawara don ko kun basu kudi mazajen su zasu karbe kudin nan ne. Yaya sani yace abinda zan fadi ke nan ummi kika rigani fadi yanzu wallahi nace to yanzu idan na saiya wa kowacen su freezer yayi da kayan kallo a daki don debe masu kewa da kira masu kasuwan sana, an su hakan zaiyi yaya ? Kwarai kuwa ummi ta fada da sauri shiko yaya sani kai ya fara girgiza yana fadin Allahu akbar lalai safiya samun mai irin zuciyar ki yanzu sai antona wallahi. Yanzu har kin manta da irin wullakancin da suka dinga maki a baya a gidan nan da sauri ummi ta tare shi da fadin ummm umm sani idan ana tuna baya ba, a zumunci yanzu. Don Allah ku bar tuna wanan magana ya wuce sai dai zumunci tsakanin ta da yan uwanta irin haka ai Allah bai maja fada ka tsaya kuma ranawa. Sai ga hawaye a idon yaya sani din ya fito har yana sharewa da bayan hannun shi nace haba yaya sani may ye haka kuma ashe ba godiya yakamata kayi wa Allah ba da ta buda muna ta hanyar dabu zata ba yanzu. Wa ya dauka zan rayu har na kai wanan lokacin da Allah ya kawo mu har ya bani daman taimakawa yan uwana da iyayyena. Yace wallahi ummi jiya ni kadai a daki sai da nayi ta kuka in na tuna irin abinda inna tayiwa safiya a gidan nan sai in kama jin kunyan kaina duk da bani nayi abin ba amma uwatace fa tayi dole inji kuyan kaina. Yanzu badon zuwan safiya da ta bata kulawa ba ai mu nan duk ido muka sa mata a gidan don bamu da hankalin fahintar haka gare ta. Ummi tace sani abar tuna baya don Allah don tuna bayan baida amfani sai yasa mutum ya sare yaji bai iya aikata wa dan uwanshi alheri. Nan dai muka tsayar da magana nace gobe sai ku shiga birni kaida su malam musa ku sayo masu abinda ya dace a saya masu ko wace zan bada duba dari dari a kashe mata sauran canji a basu abinsu idan ya rage dama kudin da yake bani ne duk wata. Ban yin komai dasu ba don idan nazo gida inyi amfani dasu yadda ya dace kaga su sunci nasu rabon ke nan yanzu. Wani irin dadi ummi taji har cikin ranta nan ta shiga samin albarka yata sani na fadin amin ummi ya mike zuwa dakin inna wai zai dubata nasan kuma zancen zai kyankyasa mata taji. Don har zuciyar shi yake magana don bazance ga wani rana da yaya sani ya taba kuntata min ko ummi na a gidan mu tun tasowa na ahaka yake damu kamar dan ummi da ta haifa. Shiya mahaifiyar shi ke fadin wai ummi ce uwar dakin shi tabi boka tabi malam ta mallake mata da ta hana shi hurda da ita da yan uwanshi sai mu. A can dakin inna nan yaya sani yasa ta gaba yana fadin inna kin gani kin ga kunyan da kika ja muna agidan kirikiri kin san kina cin zalun din wanan boyar Allah a lokacin. Amma kika rufe ido kuka dinga cusguna mata a gidan nan ita da diyar ta da mama ta gane hakan ba daidai bane sai ta zamay jiki ta barki ke kadai kina masu cin fuska yadda kike so. Yanzu gashi dama irin haka ne akarshe irin mutanen da akaci zalum din shi suna hadiyewa suna hakkuri suna shayewa Allah bai bari su tabe banza. Yau gashi ina ciwon safiya baika yadda ke ake gudun ki ba a gidan wanda har diyan cikin ki suna gudun su shigo dakin nan wurin ki. Wanda ita alokacin ba a gujeta ba haka kamar naki ni nasan duk wanan abin ishara ne kawai Allah ke nuna maki abinki da zaki roki yarinyar nan safiya tun wuri ta yafe maki da zaifi sauki wallahi inna ga wanan halin da kike ciki. Da kyat inna ta iya dago kai ta kalleshi tana share hawayen dake fuskanta tace sani na dade yin wanan tunanen a raina nasan na zulunci yarinyar nan sosai a rayuwana. Ba kowane sillar auren ta da yaron wurin gwagon kuba sai ni jin dani yaran basu da tarbiya, ni na je nabata gwogon ku shawara mai zai hana ta nemawa danta safiya tunda gashi ta kusa gama boko. Nayi hakane don inga rayuwan safiya ya tarwatse ban tuna da cewa ba ayiwa Allah wayo ba sai yanzu na fahinci hakan. Da farko har ina murna naga bayan su ita da uwar ta a gidan nan sai kuma gashi ubangiji ya kawo mata miji ta sanadin ciwon da ta dauko wurin dan uwar ku. Sai yan, , , , , katse ta yayi inna mai sukai maki haka mai zafi har kika bisu da wanan mugun nufi haka a rayuwan su. Kishi ne kawai sani kishi tun ranan da malam ya auro uwar safiya a gidan nan na dauki karar tsana na dora a kan Rabi ba don komai ba sai don ganin tafini kurciya da kyau . Wanda zai sa malam ya dauke hankalin shi a gare mu da diyan mu gashi kuma ta dage ta saka diyan ta a makarantan boko wanda ku diyan mu talla yafi muhinmaci a wurin mu duk bakuyi karatu ba sai nata diya. Kuka ne yaci karfin yaya sani yake fadi wallahi inna kin cuci kan ki kin cuce ba komai ki bibiyar mu ba sai alhakin wa yan nan bayin Allah dake kan ki. Mikewa yayi yabar dakin cikin bacin rai ya fita daga gidan can ya koma waje ya samu wuri yana kuka har yagaji sai da abokin shi shamsu yazo ya bashi hakkuri ya samu yayi shiru. Washe gari kamar yadda mukayi magana da yaya sani hakan ne ya kasance don yaya sani sun kama hanyar birni shida su malam musa da shamsu abokin shi suka tafi sayayya. Sai laasar suka dawo gidan mun fito mun ga kayan ba a sauke su ba mukace a wuce masu dashi gidan su . Sai tambaya su mutane ke yi kayan waye haka yaya sani din ke fadin nasu Ainau ne da Saadatu safiya ta bada kudi a sawo masu a birni. Murna ya cika yan gidan mu sai shewa suke da murna nan yaya sani suka wuce da kayan zuwa gidajen su saadatu din. Ranan ba a kwana ba saida su suka zo gidan Ainau da sarakuwar ta ita kuma saadatu da kishiryata da suke shiri suka zo godiya. Kullun ina waye da uncle sai dare yake kirana ko da safe haka yasa na samu daman fita wurin yan uwa duk inda nake so yau zan shiga birni wurin Amina ida can zan kwana wurin ta. Da khadija zamu tafi don tana son zuwa sayen abu acan sai sha biyu muka bar gida inda muka kama hanya da su malam musa driver da yaya sani zamu tafi. Mun isa lafiya sun sauke mu suka shiga gari wai zasu diba masauki inda zasu sauka mun shiga wanda yake orin ginan quaters din nan ne mai daki biyu da falo sai ban daki da kitchen. Muna zaue a falon ta ida take ina aka saka damu a gidan tasan da zuwan mu don mummy ta bugo mata tun ranan dana je wurinta nace ranan monday zan tafi wurin Amina din. Zzaune muke ta cika muna gaba da abinci sai hira mukeyi da ita ga jaririn da ta haifa nan bayan haihuwana har ya dan yi wayo shima. Bayan mun yi sallah mun huta khadija ta fita zuwa kasuwa sayo abinda ta shigo saye ni kuma Amina ta jani zuwa gidan kawayen ta tana nuna masu ni. Yaya sani ne yakirani a waya wai gasu sun dawo yasa muka bar gidan kawarta na uku da muka shiga muka dawo gida. Nan ta basu abinci sukaci muka dan taba hira dashi mijin ta ya dawo nan suka fita waje suka hade dasu malam musa sai hira. Sai yamma khadija ta dawo da kaya niki niki data sayo tana cewa ai na fada maki anty garin ku yafi nan tsada wallahi. Amina ce ta tare da fadin ke ko khadija ina zaki hada tsadan birni da na nan ai ba daya suke ba, zama tayi tana cewa garin nan akwai zafi Anty Amina mun fiku sanyi a gida. Nace ba yanzu kika shigo ba ai dole kiji zafi Amina tace tadai saba zama a cikin AC can abuja amma ai kusan sanyin mu dayane da gida . Magariba akayi muka tafi zuwa sallah tunda nayi sallah nake zaune a daki ban fito ba don naga mijin ta na gida a loikaci khadija na kwance saman gado tana sauraren waka a waya ta ni kuma ina kasa zaune saman sallaya da casbi a hannu na ina ja. Amina ta shigo dakin ta zauna tana cewa Abba yayi barci ne ashe kallon inda yaron yake kwance tare da khadija nayi naga yana barci. Tace ku fito muci abinci mana kun zauna a daki nace gani nayi kada mu takura ma maigidan ne yasa muka zauna a daki tace ai ya fita sai goma ko sha daya yake dawowa gida. Kasa boye mamaki na nayi nace Amina sai sha daya yake dawowa fa kika ce tace watarana har yakan wuce sha daya wurin hira. Addua na nayi tare daa aje tasbahan cikin handbag dina nace Amina ke kuma kika kyale shi a hakan kinaa kallon shi. Kin san fa irin abinda ya ci ni ke nan a baya da yaya Ahmed ke irin wanan rayuwa bani da wayon da yancin da zan hana shi fitan dare har yazo ya zama min ja iba daga baya. Don Allah kiyi kokari kisan yadda zaki hana mijin ki fitan dare duk wani hiran da zaiyi yayi shi agida tare dake da yaran ki. Yawon namiji kada ya wuce takwas na dare zuwa tara indan yakai goma abin yakan baci ne sai dai idan da uzuri ki daga mai kafa akan haka. Tace niko ban dauke shi komai ba wallahi nace Amina shine komai kuwa don nasan illan yin haka a baya kokari zakiyi cikin hikima da basiran ki irin tamu na mata zaki hanashi wanan yawon daren ba a cikin haukan kishi ba. Amma ai duk wani magidanci na gari marancen farko ya kasance yana a cikin gidan sa sai dai idan wani uzuri ya fitar dashi waje. Tace kin ga yanzu kaina ya kawo wuta wallahi don idan za a fita din sai anyi kwaliya an fesa tura da sauran su ake fitan. Nace ba zugaki nake yi Amina amma ke da sauran mata yan uwa na yakama mu gyara ko da neman matan mijin ki keyi to ya zama may tsaba yake yi. Da yawa mu mata muke bada gudunmawar haka ga mazajen mu don bamu tsayawa muyi masu abindaya dace mu jawo hankalin su gare mu. Sai kiga mace da kayan da wuni dashi a jikin ta dashi kuma zata tari miji dashi daa dare ba wani kamshi a gidan kamar mai taron wanda yayi tafiya ya dawo. Ko wani canza na,uin girki zuwa kalar da yake so a koyaushe ki canza nauin abincin ki ki gyara kanki da yaran ki gidan ki ya kasance a gyara har shimfidan ki zuwa bandaki da tsakar gida da sauran su. Ajiyan zuciya ta sauke tace wallahi ni wanan duk bai damay ni ba, a dade da nake wanan shirin na gyara gida inyi komai da kika fadi yanzu. Amma yanzu tunda na fara aje yara na tatara nabar komai wahalaan aiki dana yara sun isheni a gida safiya ga zuwa wurin aiki kuma. Amina nace cikin wani irin murya yasa ta natsu ta daina maganan da takeyi tace safiya . Nace don Allah ki mai da hankali ga mijin ki yanzu ba ai ma maza hakan ke da kan ki kike shirin rusa gidan ki tayaya bazaki ja mijin ki a jiki ba. Har zaki ba wasu matan waje kafan ashe maki miji daga hannun ki wallahi ki mayar da hankalin ki kishiga karatun na natsu ga maza. Mazan yanzu ma kayi masu ba tsira kake yi ba balle kaba su lasisin fita bariki suyi don Allah mu mayar da hankali mata shike sa matan waje suke shigo su raina ta gida don yin sakaci tundaga farko musanman mace da take ita kadai bata da kishi idan kinayi sai kikara akan wanda kike yi din. Kamar yadda tace hakan ne kuwa sai sha daya da rabi naji dawowan mijin nata lokacin munyi sallama da ita ina kwance barci bai dauke ni ba. Godiya nayiwa Allah da ya fitar dani cikin wanan rayuwa ina tuna lokacin da nake gidan Ahmed da yake dawowa cikin dare a buge ko da karuwa . Sai dai dayake nan arewa ne fitsaran su baikai na mazau na kudu ba da basu da nauyin kowa a ransu abinda suka ga dama sukeyi sai wanda ke da tsoron Allah a zuciyar shine Allah ke tsarewa. Amma nan arewa a cikin tako suke alamarin na yadda kafin a gane halin na miji sai ta dade yana cutar da mutane wani kuma ba yadda za a gane halin sa sai Allah. Da ire iren wanan tunanen barci ya dauke ni bamu falka ba sai asuba don abba tunda ya tashi kafin mu kwanta na bashi madara yasha ya koma barci bai kara falkawa da dare sai dana tashi zan yi alwala don yanzu ya fara wayau ya tashi yana ta kuka. Saida khadija ta kamashi ta goya ta hada mai madara yasha ya koma barci ina zaune take cewa yanzu fa ya fara gane ki anty. Don daga tadhin ki yasa kuka wai don may kika tashi nace bari zaiyi ai idan mun koma don dan tafiyan da mukayi bauchine gashi kuma bamu zauna ba mun taho nan. Hmmm aini idan na tuna badakal ku da uncle a bauchi abin dariya yake bani nace in dai uncle ne ai kadan ma kika gani don ban biye mashi ne kawai. Yanzu baki ga dana nuna mashi ban damu ba dayace ban zuwa gida ban san abinda ya gani ba kuma yazo ya barni inzo da yaso ne fa da na zo mu koma tare dashi. Tace hakan yana yuyuwa kuwa anty dz fa duk wanan ziyarar bakiyi shi kai koma a garin ba inda zaki ai. Uncle ai halin shi sai shi wallahi wanda bai san halin shi ba sai yayi ta wahala da daki nakan shiga inta kuka daban gane haka yake ba. Amma anty maganan da kika fada ma anty Amina daren jiya naga jikin ta yayi sanyi nace tayi sake ne tun farko ta saba mashi da hakan da tun farko ta koya mashi zama gida ba zai yi hajan ba koda zaiyi ba hakan da yawa ba dai. Mazan mu na hausawa na da saukin kai idan mace ta san yadda zata bi dasu sai dai abinda basu so mace ta nuna masu kamar tana commading din su sai suce ka raina su. Tun da mukayi sallah muke hira duniya dani da khadija anan na samu daman yi mata magana akan ta rabu da Sanusi dan uwar inna. Na nuna mata illar abinda take shirin yi din dayin hakan nasan dai magana na batai wani tasiri a zuciyar ta ba sai dai a sanu zata gane abinda muke nufi gare ta. Nayi mamakin ganin sai da rana ta take Amina ta tashi ida na fahinci ba wani dogon addini suke yi ba da ita da mijin nata don ta fito tana fadin wai sun makara ne. Nace Amina ya kamata fa yanzu ki daina wasu abubuwa domin ke din uwace a yanzu kina kwaciya barci har asuba ta wuce bakuyi sallah ba ta yaya kike ganin zaki koya ma diyan ki ibada da hakan. Shifa yaro anbinda kake yi yake koyi dashi mai kyau ko mara kyau don shi gani yake komai daidai kake yi. Tace wai ni Safiya wanan mijin naki halan ustzune naga duk halaiyar ki sun kara canzawa yanzu ba a yanda na sanki ba duk da dama can babu ruwan ki baki kaimu rawan kai ba. Dariya nayi kawai mun karya ban wani jin dadin zama a gidan ba don haka kamar yadda muka bar gida sha biyu haka muka baro gidan Amina zuwa gida bayan na masu alheri muka dawo gida. Saboda gaba daya naga Aminan ta canza tabar halaiyan ta dana san ta dashi a baya sai wani nuna waye taki wanda bai dace da diyan musulmai ba da matan hausawa. Abinda nake son mata su gane shine bawai sai mun nuna wayewa a fili za a san mun waye ba dabiun ki na diyar bahaushe musulma a ko ina ya rinjayi zuciyar ki. Ako ina kika samu kan ki kada kiga kina zaman bariki ki watsar da tarbiyan da kika samu ki manta da rayuwan ki a yanzu yafi muhinmanci ga Allah. Ki dinga fita yadda kika ga dama batare da kin rufe jikin ki ba wai ke zaman bariki kina daukan hakan a wayewa gare ki. Kamata yayi yar musulma bahausa ta nuna a ko ina ta mai cikaken tarbiyane a duk inda ta riski rayuwan ta wanan rayuwan duniyan ba komai bane a gare mu. Wataran kana gani anayi ba dakai ba lokacin ka makara ga gyaran dabi,un ka don yara sun taso sun dauki rayuwan da suka samu kanayi suna kanana. Badon kan mu zamu daina wasu abubuwan ba sai don tunanen makomar yayan mu na yanzu da wanan tunanen na canzawan Amina a raina har muka iso gida a lokacin. KUYI HAKKURI DA MAGANA NA YAN UWA MUNA CIKIN WANI HALI NA SAKACI DA ADDININ MU YANZU DON MUNA GANIN KAMAR WAYEWA NE. MUN MANTA YAYAN MU NA TASOWA SUNA KOYI DA DABIUN MU MU CUSA ADDINI GA ZUKATAN YAYAN MU YAN UWA. ZAINAB IDRIS MAKAWA SEENABU 9/14/20, 10:25 AM - Ummi Tandama: BAHAGGON RAYUWA, , , , , , , 🧕🏿8️⃣0️⃣🧕 ZAINAB IDRIS MAKAWA SEENABU Mun dawo gida mun samu jikin inna ba dadi ranan basu kwana da ita da dadi ba don maganin da ake mata allura a fara aiki a jikin ta sai ya jikin ta sakewa. Dakin inna muka wuce don har baba yana gida ranan bai fita wurin sana,a shi ba don yanayin jikin inna din mun samu ta samu barci mun dade a wurin ta muka fito daga dakin. Yan uwanta ma da suka zo a waje suka zauna suna tsoron shiga dakin inda take don gudun daukan ciwon da akace masu anayi. Sai da na fito muka gaisa da su ban tsaya ba na wuce daki bamu dade da dawowa ba naji shigowan Saadatu gidan ashe dama tana nan ta fitane zuwa sayo masu abu. Ina daki zaune da ummi na muna hira naji muryan ta tana cewa ashe bakin birni sun dawo nace eh anty Saa kin shigo ashe tace dama ina nan na dan fitane dazun . Mun gaisa na jajanta mata akan jikin na inna ta samu wuri ta zauna a dakin ummi din tace ashe kin je wurin Amina ne birni nace eh munje ziyara wurin Amina. Mun dade a dakin muna hira da ita tana bani labari har ta fara sana,a da fridge din ta kayan kallo kuma tun ranan aka hada mata su yanzu bata da wani damuwa ko zaman kadaici Kiranta akayi waje ta fita na mike ina son in yi wanka dama sai ga mama ta shigo gaida mu da dawo nan na tsaya muka gaisa tana fadin ai babaku bai san zaku kwana ba ya dawo yana fada jiya. Nace Amina tana da muhinmanci a wurina shiya naje na kwana mata daya yanzu saura kuma in tafi kauyen su ummi inyo ziyara in dawo in fara shirin tafiya don mun kusa cika kwanakin da aka bamu. Tace au har can zaki tafi ashe nace ba dole inje in duba ma ummi yan tsofinta ba kada ta hake ni daga inda ummi take zaune tace ai ba a saki zuwa dole ba. Dariya mukayi mata mama ne ke fadin ba a sata zuwa dole ba amma idan ta koma bata je ya isa ai mata gori ai tazo taki zuwa duba su. Ummi dai dariya tayi da jin dadin zai tafi in duba yan uwan ta kuma nace kwana biyu zanyi a can fitan mama dakin yasa na mike na shiga bayi na watsa ruwa a jikina. Na fito na samu shafiu ya dawo yana cika yana batsewa a falon ummi nake tambayan shi may ke faruwa shafiu yace bakomai cikin fushi. Nace kuma ga yanayin ka ya nuna fushi kakeyi mana shafiu may akayi maka waya taba min kai nazo kusa dashi na zauna. Ya wani turo baki a shagwabe yana fadin wai da su maimu zaki tafi indan kin tashi bayan na fada maki zan biki. Murmushi nayi tare da dafa shi nace shafiu aikai namiji ne kuma in na tafi dakai wazai taimakawa ummi ga sana,an ta ? Yace namiji bai zuwa gidan yayan shine akace nace kana zuwa shafiu idan anyi hutu sai yaya sani yakawo min kai hakan yayi maka ? Dan shiru yayi kafin yace indai zaki sa ya kaini yayi mun don wallahi ina son zuwa wurin ki hutu anty nace zakazo shafiu. Yanzun dai ka shirya zamu wurin su kawu dole gobe mukai masu ziyara kafin in koma yace ni sai kauye za a dani kun tafi birni bakuje dani ba ? Wai shafiu yaushe ka zama haka ban sani ba bann saka da yawan hayayya ba fa ada ? Ya mike yana fadin komai sai ace waini namijine namiji akace ba a yi dashi wallahi nima zan bar gidan nan ne. Barci nayi ranan ban ko fito tsakar gida ba din ina son in dan huta ina jin ummi suna faman rikici da Abba a falon ta amma na kasa tasowa inzo inji may ya samay shi. Har yaron yayi shiru ban sani ba don barcin dana koma a lokacin shigowan yaya Nura wuri na yasani tashi zaune. Falo naa fito wurin shi mmun gaisa nace yaya Nura yaya akayi ne yace wallahi Safiya garin ne yayi zafi yanzu sam babu aiki tunda dama ya kama mutane sun mayar da kudin su gona. Nace yanzu may ye shawara yaya ya shafa kan shi yana dan murmushi yace zuwa nayi wurin ki ki dan taimaka min da wani abu in dinga juyawa. Shiru nayi ina nazari a raina sai nace yanzu dai ba wasu kudi nake dasu anan ba yaya gashi zan shi kauye wurin kawun ne na sai dai indan mun koma idan zaka iya shigowa Abuja sai musan abinda za ayi a can din . Zaiyi magana na rigashi fadin barin in baka dubu ashirin duk da nasan zasuyi ma kadan amma kayi hakkuri dasu jibi zan koma ba dadewa zamuyi ba dama sai kazo mu san abinda za a yi don yaya Saadu na can. Bva zai rasa wurin da zasu saka ba yafi wanan aikin da kakeyi a nan zaifi ma sauki nake gani idan zaka iya idan kuma kafi son zaman nan zan sama maka abin juyawa yace sai nayi shawara da mama ummi dake kofa tace shine daidai. Na shiga daki na fito mai da dubu ashirin din na kawo mashi ya mike yana godiya ya fita daga dakin sai lokacin ummi tayi magana. Kin san dai Nura ba kamar Sani yake ba karki saka shi a cikin harkan mijin ki ya yaudare shi bake kadai abin zai shafar mu nan zai iya shafan mu. Nace har yanzu yaya Nura bai daina halinsa bane ummi tace ina zai daina tunda bajin maganan iyayye yake yi ba. Shi haka rayuwan shi take a tsatsaye yake har yanzu baya ganin kowa da mutun ci a idon shi ko gidan nan ya shigo bai iya gaida mutane yanzu ma mamakin ganin shi a wurin ki ai. Murmushi nayi nace amma duk abinda yake ummi ai bai kawo gare ki damu ko iya wanda ya shiga harkan shi yake tsayawa. Ina dai ja maki kunne kisan abinyi tun wuri nace ummi ki bari a gwada shi ko sau daya ne kin ga ai mama bata jin dadin ganin da yaya sani kawai muke mu,amula a gidan nan ranta baya dadi nunawa kawai ne batayi. Ba fa gwadawa a fili amma nima nasan abin yana damun ta nace ba a dukiyar uncle zan sakashi ba ai ummi nima nasan abinda nakeyi. Washe gari muka isa garin kakan nina mun samu taro na mutantawa a wurin su irin taron da mutanen kauye kiwa wanda suke mutuntawa aikai muna a gidan. Su yaya sani basu kwana ba suka dawo bayan sunci abi mukai sallama dasu suka tafi naji dadin kasan cewa a cikin yan uwan ummi danayi saboda yadda suke nuna muna don dukkan mu yaran ummi mukaje garin. Mun so zuwa da ummi amma baba yahana ta zuwa don haka muka zo bada ita ba sai yamma mazan suka dawo daga gona wurin aiyukan su don da aiki noma da kiwo suke dogara su. Sai da suka huta muka bisu daya baya daya muna gaida su a part din su najin dadin ganin mu a yadda sukaga munzo mu duka. Mun fi dadewa a wurin kakan mu wanda tsofa ya kama yanzu har dan rankafa abu ga dogon mutum wanda ya manyanta don ko diyan shi ba yara bane balle shi tsawo rai daine daya samu yakai hakan. Washe gari da muka tashi jumma a ne don haka kowa na gida basu zuwa gona duk ranan jumma, a ranan suke samu su dan huta a gida don yin sallah jumma a din. Tsaraban da muka kawo masu ake ta rabawa a kofan kakan mu mace duk da ita ta haifi ummi mu ba wanda ta haife ta ta rasu tun ummi bata girma ba. Amma ta rike su kamar ita ta haifesu yadda ta rike su a gidan nan suka fara shigowa godiya a gare mu duk mazan shaddan da ya bani na kawo masu dama na aje masu nasu. Mun je wurin kakan mu gaida shi sai jan mu da hira yake yi yana bamu labarin rayuwa shi na baya yana kuma fada muna dan tarihin ummin da tasowan wata har auren ta a kauyen da tayi ta koma wurin gwago a garin mu. Abba ke rikici a gaban shi yayi murmushi yace miko min shi nan khadija ta mika mashi yaron ya dauke shi tare da kara shi saman kafadan shi daidai saitin kunnen yaron ya dora bakin shi a hankali yana karato adduan daba mu san may yake fadi ba a lokacin. Kara juya shi yayi bangaren hago ya kara maimaita abinda yayi mashi a bangaren dama ya gaba sai ya dan hura mai fuska take yaron ya zauke numfashi a hankali yake rage sautin kukan da yake yana ajiyan zuciya shikuma yana dan jijigashi a hankali saman kafadan shi har yai shiru ya lafe sai ajiyan zuciya yake sakewa a hankali. Mudai mana kallon abinda yakewa yaron yace idan kunga yana kuka haka daukan yaro akeyi aimai kallaman shada sau uku a ko wani kunne da bissimilah zaku fara kowani sai kuga yaro ya yi shuru koda kuwa shedanune suka shafi yaro yana yawan kuka akai akai. Nace aiko mun karu tsoho ya nisa tare da tambayana jiki na nace da sauki sosai yanzu gaskiya don ina shan magani kuma ina cin abinda zai gina min jikina ko yaushe. Yace kin dai daina amfani da fitsarin rakumin ko don banga kin kara aikowa in sama maki ba nace gaskiya malam tunda na shanye wanda ka bani da farko ban kara amfani da shi ba kuma naji dadin shi sosai wallahi. Yace tsiyan ku ke nan yaran yanzu baku tsaya ma magani har kuga aikin shi da kyau sai ku camza wani . Nace tsoho ba inda zan samu ne a can kaga muna da nisa sosai yace kinzo a saa ai yau jumma a za a soke rakumi ayi tom tom din shi zan sama maki wasu abubuwan amfani da dama a ciki sai kije kiyi amfani dasu can idan kinji dasin su keda kan ki zaki aiko a kara maki wani. Godiya nayi mashi tare da dan bashi kudin da na riko mashi duk da ina ganin basu da yawa amma shi sai washe baki yake yana saka min albarka. Tashi mukayi daga wurin shi wanka mukayi muka shirya muka zagaya gaida dangin da suke a cikin gari Bamu dawo ba sai yamma lis agajiye kowan mu yake abincin da suka aje muna na rana muka samu ba wani ci mukayi ba dama na bada sakon a saya min ganye da kwai da man shanu mai yawa da zan koma dashi Abuja. Ganye nace khadija ta dan gyara min naci har dare dashi na kwanta a cikina don banji wani yunwa ba kuma. Washe gari sai shirya muna tsaraba suke yi kin san kauye da kara wanan ya kawo wanan ya kawo sai gashi mun tashi da tsaraba mai yawa a gidan. Sha buyu rana driver dasu yaya sani sun iso daukan mu bamu jima ba mukayi sallama dasu muka kama hanyan gida biyu da wani abu muna a cikin gidan iyayyena. Kwana biyu yarage muna a garin sai shirya muna ummi da mama keyi nan ma dai tsaraban ake ta kawo min don duk wanda na ba tsaraba dana zo sai da ya dan samu abin da ya bani da zan koma sai dana ragewa su ummi wani abin. Ana gobe zan koma ne da safe sai ga maimu da kuka ta samay ni wai baba yace ba zan tafi da kowa cikin su ba. Hakkuri na bata nace zanyiwa baba magana da yamma da yadawa gida naje gaida shi yana zaune yana cin abinci mama na gefe shi na shiga wurin shi. Gaisawa mukayi nayi mai yaya kasuwa ya amsa min cikin fara a na samu wuri na tsugun na yace kuna ta shirin komawa gobe ko nace eh baba. Shine ma nazo fadama zan tafi da maimu da hindatu suyi min hutu idan hutu ya kare sai a dawo dasu. Dan jimm yayi sai yace Safiya maigidan ki bazai ga rashin hankali mu ba kuwa nace ko daya baba babu ruwan shi ai shi bamai zama gida bane ko yaushe. Sai yayi kwana nawa ma bai gansu a gidan ba idan ba ya kama ba yace nasan halin yaran nan basu jin magana kada kina zaman ki da mijin ki lafiya su je su tayar maki da hankali can. Nace baba babu komai wallahi ai khadija ma baiso ta dawo ba itace ma ta matsa zata dawo din yace dayake tasawa kanta shiriritan son wanan yaron ba. Niko da raina da lafiya na wanan abin ba zai yuyu ba muddin ina raye shirmay ta dai takeyi kawai. Mun dan taba hira dashi yana ta min nasiha akan zaman aure da zaman takewa a cikin mutanen da ban saba dasu ba har magariba ya gabato muna wurin. Haka ya mike yaje yayi alwala ni kuma na koma cikin gida ina shiga mama ta biyo ni dakin tana fadin kai Safiya ke kika iya da halin mahaifin ku. Nace mama nasan halin baba don haka ban fito mai kai tsaye da daukan su zanyi ba sai na laba ga hutu ba sai ya gansu ba kuma ko yayi magana nasan abinda zan fada mashi gaba. Yaran da sukaji za a tafi dasu suka fara murna mace kada su dauki wani kaya mai yawa kada baba ya gane tafiya zasu yi kayan sallah ku kawai zaku dauka. Tun da safe ana ta fita muna da kaya waje duk sai naji raina ba dadi a lokacin ina kuryan dakin ummi ina shiri ta shigo dakin nace ummi amna dai ya kamata kizo kiga gida na idan na koma gaskiya. Tace ba iyayyen ki sunje sun gani ba zuwan may zanyi kuma ni nace haba ummi kamar wace bata da gata ai dai dake da baba ku dan leka watarana ko ? Tace ba dai yanzu ba sai maigidana zaiyi aure ko nace haba ummi khadija dake zaune gefe na tace kyale ta ninan zan rakota har Abuja idan kin koma. Gwago dasu mama jimmai sun shigo sallama na dasu Saadatu har da mijin ta da kishiryar tan nan na fito tsab dani na shiga wurin baba na rusun na tare dasu maimu nace baba zamu tafi asa muna albarka. Yace kullun cikin sa maku muke safiya nan yayi wa su maimu fada sosai na su natsu har su dawo lafiya na shiga wirin inna mukayi sallama nayi mata Allah ya sauwaka. Na fito kofan gidan namu ya cika da jamma a ina tayiwa mutane ban kwana na shiga mota Adamu ya zo mukayi magana dashi ba wanda yaji may nake fada mashi. Sai dariyan da yayi yana daga muna hannu nan muka barsu tsatsaye suna bin motar da kallo idona na lumshi ina jin wani iri a zuciya na gida a kwai dadi wallahi indai kazo da zuwan bakunta nace a raina. Suka yaran sai farin ciki sukeyi yau zasu birni duk sun sallami abokai da yan uwa sai washe baki sukeyi cikin murna. Sai karfe biyu da rabi muka shigo garin Abuja inda muka wuce gidan mu direct daga shigowan mu kanne na da suke ta surutu sai suka koma kallon gari. Mun iso gidan duk zuciya ba dadi har lokacin a hankali na furta Alhamdullahi a fili tare da yunkurawa ina shirin fita daga motan ji nayi sunce anty mun iso ne eh kawai na iya ce masu. Security din ne ya fito ya bude muna mota tare da fadin sannu madam sannu ismail na iya fada mai nace nagode. Fita nayi daga motan tare da amsan Abba dake jikin maimu yana barci saida na karbeshi suka fito daga motan tare da daukar min jakkan hannu na muka nufi kofan shiga gidan. A rufe gidan yake na dan danna bell ajima kadan sai aka bude Nura ce ta fito tana ganin mu tace ah wellcome madam. Thanks nace mata ta matsa muka shiga tare da kanne na dake bina a baya tsakiyan falon na nufa na shimfede yaron saman kujerun falon da suka sha gyara. Na juya naje kuna Ac da fanka a lokaci guda take falin ya fara canza yanayin shi daga zafi zuwa sanyi. Har yanzu su maimu basu zauna ba nace dasu ku zauna mana gaku kamar masu tsoro da sauri suka zauna a takure saman kujeran duk sun matse juna. Zama nayi ina kokarin dauko key din daki na a cikin jakka na can kasa naji key din na fito dashi daidai lokacin da Nura ta kawo muna ruwa da juices din kwali gaban mu da kofuna ta aje. Goran ruwan na dauka na fara tsiyaya a cup tare da masu nuni da su dauki ruwa su sha mana suma da sauri kowa ta dauki cup din zasu zuba ruwa nace bazaku sha lemon bane muna sha maimu tace min da sauri. Bayan na shanye ruwan na aje cup din na mayar da jikina ga makarin kujeran tare da lumshe idanuwa a hankali na danyi tunane sai kuma nayi ajiyan zuciya. Wayana yayi kara daga cikin jakka na na jawo jakkan ina duba wayan yaya Saadune yake kira na alokacin na dauka tare da fadin hello yaya . Yace Safiya yaya hanyan na amsa da Alhamdullahi yaya. Yace kuna ina yanzu ? Gamu gida yaya na bashi amsa a takaice. Yace ashe kun iso ke nan , ? Eh yaya Yace OK sannun ku da zuwa gani nan tafe yanzu mu gaisa Sai kazo yaya kawai nace na kashe wayan ina kara mayar da kaina yadda yake da farko. Mikewa nayi na bude dakina yayin da su malam musa ke ta shigo muna da kaya cikin gida shi da wanan security din Nura ta tarawa daidai kofan kitchen din mu. Dakin na shiga sai duhu na kunna wutan dakin tare da jefa jakkana saman gado kaya na fara cirewa a jikina na shiga wanka na dan dade ban fito ba. Sai can na fito na sauya kayan jikina na samu Abba ya tashi daga barcin da yake yi tv na kunna kafin in zauna na kalli dining naga Nura ta jera muna abinci a wurin. Makulin da nafito dashi daga daki na bude wani daki a kusa da na mummy nace da su maimu ku taso kuga dakin ku ko. Da sauri suka taso zuwa inda na kira su wanda sai kayi dan tafiya zuwa wurin nace nan yayi maku ko yanzu dai gaku a cikin gidana. Fushi ya kare maimu da baba dakin muka shiga dukan mu sai baza ido sukeyi kamar matsorata a raina nace rayuwan kauye baiyi ba gaskiya. Ji yadda yara ke wani iri kamar wa yanda basu yarda dani ba ko wani saman gadon dakin na zauna nace suma su zauna Abba nake kokarin cire ma kayan jikin shi a lokacin. Nace kunga ga bayi nan don Allah banda kazanta don shi zai hadani ku ba komai ba a kullun a wake bayin nan sau uku ko sau hudu a rana. Taso muje in gwada maku yadda zakuyi amfani dashi nan dai na nuna masu komai nace su kwaso kayan su sushigo dashi dakin a tare muka fito ina ce masu suyi wanka muci abinci. Sun gama sun fito shima Abba wanka nayi mai muka fito muka ci abinci muna kan ci yaya saadu suka iso gidan shi da samira. Ina ganin su nace chewgun ke nan kina lake ko yaushe masu miji ke nan ina kuma kuka baro min diyata ? Tana wurin uwarta tace ganin yaran yaya ce ina kuma kika kwaso wayan nan yan kauyen haka hararan shi nayi nace ina kaga yan kauye kuma anan ? Tace ke ko kin so dawowa ji yadda kika koma kin je kin cinye ma tsofi abinci kin ki dawowa. Na lumshe idona nace bari samira wallahi gida akwai dadi kamar karna dawo nake ke ji sai naga gidan nan yayi mi wani irin girma wallahi ba hayaniya ba motsin kowa. Kajiki da wani zance har yaushe kika bar nan din da zakice wai wani gida dadi ai da ki zauna gida in baki dawo kin samu munyiwa uncle din ki aure ba. Samira ke da kanki ke fada min haka lallai wata shigowan kishirya ki ya tsaya don wanan watan zamu kawo maki wanan karfen kafan da ta leke wa yayana. Don Allah Safiya ki daina zancen wanan gajan matar da ta tashi aiki don wulkanci ta rasa wanda zata lekewa sai mijina yar iska. Yace ai shike nan tunda kin san takon ta kuma da tayi maki tsiya bani go ahead kawai safiya na shigo da hafsat kai tsaye ZAINAB IDRIS MAKAWA SEENABU 9/15/20, 7:06 AM - Ummi Tandama: BAHAGGON RAYUWA, , , , , , , , 🧕🏿8️⃣1️⃣🧕 ZAINAB IDRIS MAKAWA SEENABU Bayan tafiyan su samira da basu dade ba na shige daki nayi laasar na fito muka fara gyara kaya da Nura su maimu suna taya mu. Kafin wani lokaci muyi ma komai muhalin shi mu aje a inda ya dace kuma na nuna masu wanda zasu ci inda suna bukatan ci din. Falo na dawo inda kanne na suke suna kallon na zauna sai dai ni ba kallon nake yiba waya nake amsawa daga mutanen gidan mu suna tambaya na mun sauka lafiya . Abincin dare suka ci ina zaune a kasa idan na sallamay sallah ishai wayana yayi kara uncle ne ya kirana a lokacin na dauka da sallama tare da karawa a kunne na. Uncle ina wuni na fara fadi ya sauke a jiyan zuciya kadan yace madam kun dawo ko kuna can har yanzu nace uncle gani daki na muna ta kewan ka, gidan ya koma ba dadi da baka nan. Murmushi yayi tare da fadin I miss you to my wife ina Abba dasu mummy nace ga Abban nan hannun maimu mummy kuma bata dawo ba. Maimu ya maimaita sunan da na fada nace eh tare da su nazo ita da hindatu sin zo muna hutun kwana biyu ne . Yace bana ce ki samu yarinya kizo da ita ba idan zaki dawo don ki samu abokiyar hira a gida nace ko yanzu ga su suna debe min kewa a gidan. Bai kara yin magana sai cewan da yayi kara ma Abba waya inji muryan shi sai na manna ma yaron waya a kunnen shi nan ya fara yin gwalanci kamar ya san abinda ake nufi mika ma maimu wayan nayi tace ina wuni yaya yace a a ke yar kauye ashe kun shigo gari sai yarinyar tace eh. Amshe wayan nayi ina fadin kin yarda ke nan ke yar kauye ce ko na kara ma hindatu tace cikin muryan ta mai sanyi ina wuni yaya ya amsa mata tare da tambayan da wa nake magana tace hindu ce. Sun jima yana masu tambayoyi wani su bashi amsa daidai wani kuma su fada mashi ba daidai ba Mukai sallama dashi yana fada min kada in rufe gida yanzu zaa kawo min sako in kar ba godiya nayi mai tare da tambayan shi yaushe zai dawo ? Yace kin damu in dawo ne ko wani abin kike so madam nace babu komai sai dai kewan ka da mukeyi na rashinka a kusa damu. Kararawa kofa yayi kara ni da kaina na tashi na bude gidan malam musa driver ne da ledoji da kwalaye ya shigo dasu ya koma ya dauko sauran sai leda daya miko min hannu da hannu na karba . Bayan na karba na fahinci maye a cikin ledan don jin zafi danayi daga cikin ledan yana tashi da kamshi. Yayi muna sallama nace ya tsaya ina zuwa yace a a hajiya nima maigida ya saya min nawa na gode wallahi sai da safen ku yana dan dukar da kai kasa alaman girmamawa gare ni . Yana fita na koma wurin kayan daya shigo dasu ina duba inda naga kayan tea ne mayan gwangoni madara biyu sai na milo da nescafe da ovoltin sai katon din sugar na kwali. Dayan kuma fruit ne a ciki iri iri masu kyau fresh one murmushi nayi don akwai wanan abin daduk aka sayo muna a gidan. Ledan da kamshi ke tashi a cikin sa wanda tun ban bude ba na fahinci may ye a cikin wanan ledan kaji ne gassasu guda uku kosassu sun gasu dakyau irin gasuwan resturant din nan da albasa da kabeji da sauran tarkace wanda yakan sawo muci a gidan. Yaran dake satan kallo nace hindatu ta dauko plate a kitchen guda uku kowa ya dauki kazan daya yaci maimu tace anty duka nace eh duka maimu. Ban koma ta kansu ba ina faman dakilan wayana suna ci suna dan magana kasa kasa danaji maganan yayi yawa na dago ina cewa dasu wai may kuke fadi ne kasa kasa. Wai cewa tayi kada mu cinye duka mu rage gobe muci saura nace akan may zaku rage idan kuna iya ci duka kuci mana. Basu iya cinyewa dukka ba duk zalaman su anan suka barshi nace suje su saka a fridge ban ci nawa sai fruit din naci kawai bamu dade ba nace suje su kwanta su huta. Sai da na tabbatar sunyi barci na dauki Abba zuws dakina na kashe wutan falon komai daya kamata in kashe na kashe na shiga na kwanta asuba ta gari. Da safe muna tashi bayan munyi sallah nace suje suyi wanka kuma kullun da sunyi sallah haka zasu dinga yi suka shige daki don yin wankan dana ce suyi. Abba nayiwa wanka na shirya shi na dauke shi nakai masu dakin shi na dawo nayi nawa wankan na shirya. Nura ta iso ta fara aikin hada muna breakfast din safe a lokacin na shiga kitchen din nace kada tayi wani mai yawa don ba a ci sosai. Bayan mun karya ne muka zauna su kallo ya dauke masu hankali waya na na dauko na kira samira muka dan taba hira da ita nace idan ta samu lokaci ta shigo don Allah ina son tayiwa su maimu sayayya kayan sawa don ni ba dama in fita uncle bai gari. Tace zata shigo zuwa rana asan abinyi din akai nan muka kashe wayan nima kallon na kama yi don shine aikina kawai tunda ba fita nakeyi ko wani abuba. Sai idan uncle yana gari ne watarana nakan shiga in muna abincin garagajiya don yana so ita kuma Nura bata iya ba sosai. Hajiya baaba na kira don mu gaisa tace na dawo ko ina gida har yanzu nace hajiya mun dawo jiya muna Abuja yanzu. Tace yaya muka baro su nace suna lafiya suna gaida ku baaba tace to yanzun dai kinje gida hankali ya kwanta ko ? Don Allah safiya ki bi mijiki a yadda yake so ku zauna lafiya don Allah yanzu tunda kin san halin shi kibishi a yadda yake ban son yawan fitin da kuke wayan yi ko yaushe din nan. Insha Allahu baaba zanyi yadda kikace din tace nasan komai safiya nasan kina hakuri sosai dashi shima din halin shine kawai haka bawai yana yi cikin son ranshi bane. Godiya nayi mata na kashe wayan ina tunanen maganan da mukayi da hajiya din shigowan samira gidan ya kawar min da tunanen da nakeyi. Samira ta shigo na bata kudi nace taje dasu don kada a samu akasi tace bata zuwa da kauyawa ko ina nace watarana kina ganin su nan sai sun fiki wayewa. Tana masu sheri suka fita taja motan yaya tabar gidan tare dasu haka yasa na samu kwaciya nayi barci sosai dani da Abba kadai a gidan. Zuwa rana suka dawo da kayan da ta sawo masu din kayan sunyi kyau sosai na bata atamfofi a cikin kayana da zata kai masu dinki. Nace ina son yaran nan suyi clean ne samira su din rabin jikina ne da komai nawa watarana sune wa yanda zasu tallafa min a lokacin da nawa kadfin ya kare. Tace gaskiya ne Safiya da har ina ganin wautar ki na dauko su sai yanzu na gane hikimar yin hakan da kikayi akan su. Zasu taimaka maki kwarai a rayuwa ki don naka sai naka haka abin yake wallahi Allah ya taya ki rokon su nace amin samira. Sannu a hankali nake koya masu komai kuma suna ganewa sosai don sun sauya kamar basu ba don da gani sun saurari fadan da akai masu da zasu zo. Sai da uncle ya kara sati biyu ranan alhamis ya dawo da dare ni dai ina barci naji wayana yana ruri na dauka muryan shi naji yana fadin bude min gida don Allah. Da sauri na mike tare da daukan key na fita daga dakin na bude gida da sauri yana tsaye yadan jigina jikin shi a bango suith din shi na sagale a kafadan shi. Mirmushi na sake a fuskana tare da fadin sannu da zuwa uncle hannuwan shi ya bude da sauri na shige ciki . Yana rike dani muka shiga gidan bai nufi dakin shi ba sai da ya tafi yaga Abba dake barci na wuce na bude mai daki tare da kunna naurorin dakin na hada mai ruwan wanka. Kayan shi ake shigowa dasu gidan daya dawo dasu sun gama na rufe gida tare da yi masu sai da safe. Ya dauko yaron ya nufi dakin shi dashi a kafadan shi nan na gama komai nabi bayan su nima tari naji yana yi sai muryan shi daya dan shake bai fita sosai. Uncle baka jin dadi ne dan murmushi yayi yana kara gyara ma yaron shi kwanciya da kyau ya juyo gareni yana fadin . Mura ne ya kamani kin san yanayin sanyi da ake yi yanzu acan ya fara kokarin cire kayan jikin shi na juya na fita zuwa kitchen inda na hada mashi shayi da cita da kanunfari na kowo mai dakin har lokacin bai fito daga wanka ba. Bakin gado na zauna ina jiran shi koda ya fito yana goge ruwan dake jikin shi tari ya kama yi a lokacin tashi nayi na fara tsiyaya mashi ruwan tea din dana hada mashi a kofi. Ya gama yasa kaya a jikin shi ya nufo inda nake jiran shi da cup din tea din da nake dan motsawa a hankali cup din na miko mai bayan naga ya zauna a saman gadon. Karba yayi yana tari sosai hankali na ya daga sosai ya dan kurba kusan sau biyu yace na kwana biyu ina tarin nan tun acan. Sannu nayi mai nace yi kokari ka shanye tea din zai taimaka maka ka samu barci da sauki don wanan tarin dake damun ka. Ido ya dan lumshe kadan yace yaya kibaro mutanen gida nace duk suna lafiya suna gaida ku sun ce kuma ai masu godiya sosai. Da akai may yana miko min kofin daya shanye tea din na aje a saman dan drower dake gefe na hawayayi saman godon ya dan dukule a wuri daya kamar mai jin sanyi. Hankali ya tashi ga yanayi da naga yake ciki sai dai yana kokarin kwantar min da hakali da fadin ai murna ne kawai ke damun shi a lokacin. Ki kwanta yace dani haka na kwanta a sanyayye tare da tausayin kan mu ga halin da muke ciki na rashin lafiya a jikin mu . Ni yanzu in uncle ya mutu ya barni yaya zanyi da rayuwana jamma, a da sauri na kawar da wanan tunanen a raina tare da kai hannu na na dan shafa Abba dake barci a gefe na. Ina sauke ajiyan zuciya hannu na guda nakai a saman goshin uncle wanda idon shi ke a lumshe a lokacin. A haka barci ya dauke mu dama karfe uku na dare yayi ko haka yasa mu makara da safe ba laifi ya samu barci kamar yadda nace mashi din zai samu. Washe gari ban fito daga dakin uncle da wuri ba don makaran da mukayi yan matana har sun fito sun zauna falo kin san dan kauye bai barcin safe shi. Sai raba ido suke suga inda zan fito a gidan har Nura ta shigo ta fara aikin ta sacen na fito ganin inda na fito ina sabale da Abba daya tashi daga barci nayi mai wanka acan. Da sauri suka taso suna gaida ni da kwana na amsa masu cikin dadin rai ina fada masu baban Abba ya dawo jiya da dare . Sun nuna farin cikin su a hakan daki na shiga tare da kiran su muje dakin nawa a lokacin a saman gado na aje Abba na juya dauko mashi kaya in saka mashi. Hindatu ta dauke shi tana mashi wasa maimu tace anty na zata kin fita ne da ban ganki ba nace aini maimu ban faye fita unguwa ba sai idan ya kama. Mun gama muka fito falo bayan na shirya suna zaune suna jirana a dakin sai da nagama tsab muka fito lokacin had Nura ta hada abinci a table na dan duba nake fada mata dawowan uncle tea din jiya na kara hada mai tare da bude fridge na dauko hadin tsoho na zuba a cup na nufi dakin shi. Na samu ya tashi yana zaune yana duban wasu takardu a hannun shi nace uncle ina kwana yaya jiki da gajiyan hanya. Na aje kayan kafin ya amsa na juyo na dan kai mai kiss a saman goshin shi yace da sauki madam yaya gida yaya bakin ki kuma ? Suna lafiya na bashi amsa ina zama kusa dashi nace yaya jikin naka don yanzu na kulla a raina duk fushin shi ko shirun shi zanyi kokari inaga na kara kawo kusanci a tsakanin mu. Ko zan samu in rage mai yawan saurin fushi a rayuwan shi wanda ni kadai ne a yanzu zan iya kawar mashi da hakan. Na fada masu ka dawo suna can suna murna na barsu suna karyawa a falo yanzun haka. Yace akwai kaya cikin kayan da na dawo dashi ki duba ban samu wani lokacin tsaya yi maku tsaraba sosai ba don yanayin jiki na. Uncle aimu kullun cikin tsara ba muke ina kai hannu na saman cup din maganin tsoho daya bamu musha. Dauka nayi na kurba na kara kurbawa sosai sai na mika mashi don kawar da zargin wani abu a ranshi duban cup din yayi yace wanan kuma may nene haka ? Magani ne kasha uncle yana da kyau sosai wallahi tsoho ne danaje ya sama muna don yanayin jkkin mu sai dai ban fada mai ko may ye ba don kada yaji kazantar sha. Amsa yayi ya kurbe duk ya aje cup din tea din na mika mai yasha nace irin na jiya ne na hada ma naga ka samu saukin tarin jiya da dare. Kwana kikayi ke nan gadina ashe naji ya fada nace ba dole ba baban mu ya dawo gida ba lafiya ina naga kwanciyan hakalina. Murshi yayi ya karba ya fara dan spping din tea din a hankali yana lumshe ido har ya shanye ya dan yi gyaran murya nasan cittan ne ke aikin shi a lokacin. Tashi muje in gaisa da bakin nawa yace min bayan tea din ya dan fada mai wurin na dan gyara kafin mu fito na kwaso kayan da na kai mashi tea din zuwa kitchen. Suna zaune sai wasa suke ma abba yana dariya suka ji muryan shi a bayan su yana cewa wasu kauyawa ne haka a gidan namu ? Juyowa sukayi suna gaishe shi ban fito kitchen din ba sai dana dauraye kayan dana shiga dasu din don rage ma Nura aiki. Na fito na samu yana hira dasu cikin natsuwa yana tambayan su aji nawa kuke yanzu aji uku maimu ta fadi yace kaji ba kauya ba haka zaki ce ba . Sai hindatu tace primary three yace a a ashe hundatun dai ta waye tafi maimuna jin turan ci ke nan nace ko go and come back ba wanda ya sani cikin su. Anty munaji fa ana koya muna maimu tace nace makarantan da sai an kora ku kuke zuwa yaushe kuka tafi har ku iya wani abu. Shigowan yaya saadu ne ya katse muna hiran ya shigo yanayi mai sannu da zuwa sun dan gaisa yace da cashiar suke haka yasa uncle fita. Don bai yarda a shigo mashi gida kamar yadda sauran maza suke amincewa da kowa ya shiga masu gida kai tsaye. Haka a kidojin shi suke kamar mutumin da shi yawan tsare iyali da sa ido akan mace ga komai da takeyi fitan su falon mukaci gaba da hiran makaranta da yan kanne na . Yaya Saadune ya dawo yana fadin ashe maigida baijin dadin jikin shi ne ko da ya dawo yanzun naji yace likitan shi yazo ya duba shi. Nace yace sanyi ke damun shi mura ya kamashi yace yadai boye maki amma ai ke ma kinga ya ramay sosai ciwo yayi sosai acan fa. Wani iri naji a raina sosai a lokacin nace nima nayi zargin haka yaya yadda naga ya ramay sosai wallahi. Yace kafin in gama tunane yace ki bani takardu a saman gado daya aje tashi nayi zuwa kwaso mashi takardun a dakin shi. Bayan na dauko na kai mashi na koma dakin don hada sauran takarcen daya dawo dasu daga tafiyan nan naga takardan asibiti a ciki na dauka na duba abinda na dan fahinta ciwon nashi ne ya tashi mai acan har ya kwanta asibiti. Shine kuma uncle zai boye min hakan idan wani abu ya faru dashi fa fiye da funanen shi sai banji dadin yin hakan da yayi min ba ai ba a boye ciwo ga masoyi nace wa kaina. ZAINAB IDRIS MAKAWA SEENABU 9/21/20, 9:58 AM - Ummi Tandama: BAHAGGON RAYUWA, , , , , , , , , 🧕🏿8️⃣2️⃣🧕 ZAINAB IDRIS MAKAWA SEENABU NOVEL DINA NA KUDI NE IDAN KIN KARANTA BAKI BIYA BA NA BARKI DA ALLAH KE/KAI MAI FITAR WA HAKIN AMANA YA HAUKAN KU DON BAN YAFE BA. Wasa wasa sai da uncle ya share sati daya a gida yana jinyan jikin shi wanda yawan jigilan da yake yi ya jawo mashi hakan. Dani da yan kanne na dana dauko daga gida muke jiyan shi ida ya hana mu fadawa ko wani dan uwa nawa da shi. Muna cikin sulilin rashin lafiyan uncle duk da yaji sauki zuwa yanzu ya dan samu sauki sosai sai dai bai fita har yanzu. Labarin sakin anty ya zo muna inda ake fada mashi faruwa abin yau kwana biyu ke nan waya yakeyi ina sauraren shi hankalina yayi matukar tashi dajin abinda ya furta din a waya. Take na fara maimaita innalillahi wa inna alaihim rajjiun a fili har ya gama wayan ya dago kai nace da sauri uncle anty na daddy ya saka. A hankali ya sauke ajiyan zuciya yana fadin innalillahi shi ma cikin tashin hankali yake maganan nace may yayi zafi haka uncle ? Tace wai kudine ya hadasu fada ya shigo da kudin aikin su gidan washe gari zai fita dasu sai ta taba yayi yayi ta fito mai dasu taki shine ya kawo masu sabani. Nakai zaune don tsaye nake dama akan shi na dauko mai waya a daki sai na tsaya bayan kujera daga bayan shi. Nace haba anty wai may takeyi da kudine haka don Allah kudi dai tana samun su mijin ta kuma tana samu a gare shi. May zai sa ta daukan ma daddy kudin shi kuma har abin yakai ga jawo masu sabani haka ina magana ina girgiza kaina a hankali cikin damuwa. Nisawa uncle yayi tare da fadin nima tunanen da nakeyi yanzu kenan a raina don son kudin maimuna yayi yawa wallahi. Wanan labarin mutuwar auren anty ne ya kashe min jiki yinin ranan haka na wuni a lalace ina son kiranta ban san amsan da zan samu a gare ra ba. Washe gari mummy ta dawo daga wurin yaran ta da taje gani mun yi murnan dawowan ta sosai a ranan gidan ya koma muna happy house don kowa na nan. Nan su maimu suka koma hira da mummy dawuya su fito falo wurin mu suna wurin ta koda yaushe. Har uncle ya fara fita aiki bai kara magana kan su anty ba kuma gashi ina son in tamabaye shi halin da ake ciki da zancen na su. Ranan na kira hajiya baaba ina gaida ita bayan mun gaisa mun dan taba hira da ita take cewa dani sai kuka ji labari ba dadi rabuwan maimuna da mijin ta. Nace wallahi hajiya tace manya sun zauna akan zancen ya nuna masu sam ba zai sake zama da ita ba kuma yanzun haka aure zai yi. Don su uwa sun hada shi da wata nan abujan har anje tsayar da magana akai mutumiyar adamawa ce wacce ya samu din. Inna lillahi nake iya maimaitawa a bakina nace hajiya yanzu shike nan su rabu da anty din tana ina yanzu hajiya ki bashi hakkuri mana da kan ki tunda daddy yana jin maganan ki sosai. Murmushi naji tayi tace kaiyya safiya ai labarin ba dadin jine wallahi tun da abin har da zargi a ciki sosai. Munyi sallama ina tunanen maganan hajiya din da mukayi data ce har da zargi ni dai iya sanina shine anty tana da yawan ibada kuma banga wani alama na wanan halin a gare ta ba tunda muna fita tare wani lokaci. Da dare da uncle ya dawo nake fada mai munyi waya da baaba har nake fada mai yadda mukayi akan maganan anty din da ita. Yace koma may ye ai zalaman ta zai iya sawa suyi mata hakan tunda ita ta yarda dasu a marairaice nace uncle kasa baki ga maganan nan don Allah. Yaran nan nake tausayi wallahi yace yanzu ke duk abinda sukayi maki baki tsane ta ba saboda su fa ta gujeki har abada take fushi dake. Nace uncle ba a duban wanan domin tayi min a rayuna yadda ba zan taba mantawa da ita ba a rayuwana. Yace yanzu yaya kike son in yi ke nan nace uncle baki ya kamata kasa a zancen anty uwa yar sherin matace sosai wallahi komai suna iya yi din su kuntatawa mutum don ba tsoraan Allah garesu ba. Shiru yayi na dan wani lokaci tare da ci gaba da cin abincin dake gaban shi har ya gama idona yana kan shi don son jin may zaice akan maganan. Bayan kwana uku da mukai waya da hajiya ne sai ga anty taje gidan nata duk cikin son a shawo kan daddy din take fada mata ai munyi waya nima abinda na fada mata ke nan. Tace zatayi wani abu akan zance zata kira daddy din su zauna dashi koda tafita tunane takeyi ashe safiya har yanzu bata fita zance na ba har zata iya bada hakkuri akan magana na. Haka yasa ta shirya washe gari sai gata ta iso abuja a lokacin mu kadai ke gida uncle yana wurin aikin shi. Ina daki hindatu ta shigo tana ce min anty wai kinyi bakuwa tana falo nace wacece tazo tace nima ban santa ba anty na dan gyara na fito taba da baya don haka ban gane ta ba. Nace daga bayanta sannu da zuwa ta nata bin gidan da kallo ko ina a lokacin ta juyo da sauri tana amsa wa ganin itace da sauri na karasa wurin ta ina fadin lah anty sannu da zuwa. Yanzu kike tafe ashe duk na rude da ganin ta nayi kamar zan zauna sai kuma na nufi kitchen na hado mata abin sha. Bayan na aje na zauna ina gaishe ta ta amsa min cikin sanyin rai ba kamar yadda take amsawa mutum da izza ba. Nan dai nace anty kisha ruwan mana tace bari Safiya ashe kin ji abinda ya faru tsakani na da baban su yan biyu da yan uwan shi. A sanyaye nace da ita naji anty abin baiyi dadi ba wallahi hankalina a tashe yake akan maganan tun ranan dana samu labarin. Amma anty uwa basu kyauta maki ba anty duk irin yadda kike dasu kike kyautata masu haka zasuyi maki sakaiya dashi kuma. Safiya bari wanan zance yanzun ai duniya ta koya min darasi sosai wallahi wai har uwa ke cewa daddy maza nake bi idan bai jan shi kuma ya yarda. Could you believe that safiya wai uwa ke fadan haka kuma aka yarda ita ba a ce mata haka ba sai itace zata fadi haka a kaina a yarda. Nace anty kiyi hakkuri don Allah tace ina sulaiman yana gari ko na kirashi bai dauki waya ba har sau biyu da abin ya faru. Wayana na dauka na kirashi ina fada mashi zuwan ta yace tana ina nace gata zaune a gida wuri na yace yana zuwa ta kura min ido tana kallon yadda nake wayan cikin ladabi kamar yana gabana a lokacin. Na sauke ajiyan zuciya nace anty wai yana zuwa ki sha wani abu don Allah ki rage wanan tunanen haka bakyau komai zai zo da sauki da yardan Allah tace safiya kina ganin hakan zai yuyu yadda daddy ya hau din nan ? Nace anty babu abin da ya gagari ubagiji ai idan ke ce da gaskiya Allah bai basu ikon samun galaba akan ki dayardan ubangiji. Tayi ajiyan zuciya ta dan tsiyaya ruwan ta kurba tasha mukaci gaba da maganan ya dan dauki lokaci sai gashi ya shigo gidan . Yace madam ashe kina tafe tace ba dole ba na yanke shawars inzo wirin ku ne ku taimaka min ga abinda daddy ke shirin yi min. Yace saki nawa ke tsakanin ku ina jin haka sai na mike uncle yace ina zaki kuma ana magana kin kuma tashi. A marairaice nace dashi zan baku wuri ne da yace ai wanan maganan ta shafe ki tunda ta shefi anty ki ki dawo ki zauna ya fadi cikin daure fuskan shi. Da sauri na dawo na zauna tace saki biyu ne don da cen da dadewa ya taba sakina sai kuma yanzun da ya kara daya. Nan dai yake mata tambayoyi tana bashi amsa duk muna sauraron su yace ke ma kina da laifi wallahi. May yasa dayace ki bashi kudi shi baki mayar mashi ba tun abin baiyi maku nisa haka ba tace sjerin shedan ne kawai ya kawo haka. Yace ga tanan tun lokacin da muka ji zancen take bina akan in sa baki tace ban son shiga tsakanin miji da mata ne ban kula mata ba da tun tuni nayi magana akai. Juyawa tayi ta dan kalle ni sai ta sadda kanta kasa tace nasan nayi kuskure babba a kanki safiya sherin shedan ne dana hajiya uwa da take zugani a kan ki. To yanzu bari in kirashi inji ta bakin ki uncle yace yana lalubo wayan shi a cikin aljihu yake fadin wani yasan kin zo nan ne da zaki zo tace ba wanda na fadawa zanzo nan din. Neman layin shi yayi kira biyu a na uku ya dauka yana fadin kadawo kenan tunda naga nomban Nigeria yace two weeks kenan da dawowa na ai na yi rashin lafiya ne dashi na dawo shiyasa baka jini ba. Yayi mai jajen jikin yace ai bansan cewa kana kasan ba wallahi yace yana na sai dai wani magana nakeji mara dadi yana faru ? Dariya yayi kamar a fili yake kusa damu yace may kaji kuma yace maganan ku da madam gaskiya brother banji dadin hakan ba sosai . Daddy yace to yaya za a daurowa ne abin maimuna ta ishe ni dan uwa uncle yace dakata yaya aure ba a cewa haka abune da akeyi da fatan har mutuwa amma ba daga dan magana kadan ace rabuwa ba. Yace na sani Sulaiman amma yanzu banjin zan iya mayar da ita gida na doni aure zanyi very soon taje ita ma ta samu wani a a dan uwa hakkuri dai zaka yi zan cen maganan auren nan don Allah kabar shi. Sai daddy yayi murmushi wanda har muke iya jin shi yace ai magana har yai nisa yace to ni nace ka fasa tace har yanzu baka san wace zaka auro wa kan ka ba ne da bakayi ba. Don nayi bincike a kanta bada da record mai kyau sam wallahi yace uwa fa ta sama min ita kuma ta yarda da natsuwan ta anty ta daga hannu alaman kinji ko nima da baki nayi magana irin ta kuramay nace ah tare da rike habana da mamaki. Uncle yace kasan ba zan cuce ka ba don Allah ka janye maganan nan kayi hakuri madam ta koma dakin ta kuyi hakkuri da juna please ? Yace to shike nan don kasa baki ne amma ka ganta ka ja mata kunne idan zata ji maganan ka don yanzu ban daukan iri halayen nan nata. Yace insha Allahu nan dai ya gaya mashi irin halaiyan su hajiya uwa da abinda suke aikatawa a gari yace shine take son rabaka da matar ka ta hada ka da balai ko ? Sun dan jima suna magana uncle ya kashe wayan bayan sunyi sallama da junan su ya juya wurinta yana fadin uwa yar iskan matace na sani ba yau ba shiya kika ga sam ban dauki maganan ta ko kadan da muhin manci ba don nasan kowaye uwa. Tana share hawaye tace ni kaina nakan yi mamakin yadda tazo daga baya ta shige min jiki duk da yana fada akan in rabu da ita amma banji ba. Ya mike yana fsdin shi zai koma sai gobe ne zaki tafi ko tace wai da yau nace zan koma yace yau kan ai dare yayi yaushe zaki isa bauchi a wanan lokacin ki bari gobe sai ki koma. Ya fita nace ta taso ta shiga daki wani dakin na bude yana a gyara dama don baki irin haka muka gyara shi nan na sauke ta na fita na kawo mata abin bukata a dakin . Sallah tayi na kawo mata wani dogon riga da nake ganin zai mata nace ta canza kayan jikin ta na juya zan fita daga dakin tace safiya sai na juyo da sauri. Ganin taba da magana yasani dawo wa inda take na samu bakin gado na zauna ina sauraren abinda zata fadi a lokacin. Tace nasan nayi maki ba daidai ba a cikin zaman mu amma duk da haka ke kina bina da alheri har yanzu banta dana sanin rabuwa dake a rayuwana ba sai yanzu da na shiga wanan halin. Uwa ta cuce ni safiya ta cuci rayuwana wanda nasan ba banza ta barni ba a yanzu da nake tuna irin yaudara na da taitayi ita da diya ta da sunan zasu taimaka min. Ashe ha,inta na sukeyi ban sani ba ni na dauka so ne ance ka samu dangin miji ka rike mutum guda a ciki shine na riketa ashe ita bada zuciya daya take zaune dani ba. Ni dai hakkuri nake bata kawai don ban ma san may zance da ita ba a wanan lokacin sai bata hakkuri nake kawai dakin su mummy na shiga don in duba su. Yaran suna kallo nace mummy kuna ciki ne tace eh ai dazun zan fito naga kuna da bakuwa bakuwa kukayi ne a gidan nace eh mummy anty ce tazo. Wata anty ta tambaya cikin son sani ko wanake nufi nace anty na da nayi zama a wurinta lagos itace tazo dazun . Allah sarki ashe da rabin zan santa bata taba zuwa ba nake gani ai nace ko yanzu ma ba zuwan lafiya tayi ba na zauna ina bata labarin abinda ke faruwa. Sai dana gama fada mata tace ikon Allah haka abin Allah yake fa gashi tun ba a je ko ina ba Allah ya fitar maki da hakkin ki baki da Alhakin ta ke nan. Ai wanan zamanin ana abu wallahi da karfi da yaji akeson tubbuke ka a gidan auren ka don kawai wani ta shiga ko idan shi yashiga alhaki zai barshi ya zauna ne shi ? Mata kyashi da hassada yayi muna yawa yanzu sai kiga ko da yan uwa na jini da nine yanzu suna kyashin junan tun dai idan an ga daya ya dara daya sai hassada yazo ya shiga tsakani. Ke dai fita batun yan duniya ki rungumi mijin ki tunda bai raga ki da komai ba na bukata kuyi zaman ku lafiya ba fita kike yi balle ki ga wani abun a kan shi. Shine amfanin zama guri daya yau idan baka kula mutane ka huta ma rayuwan ka sai zuciyar ka ta zauna lafiya da kowa ba abinda ya damay ka. Amma kinga yawan kwashe kwashen na babu abinda bai haifarwa shi nake guje wa mutumiyar ki ai kullun ina kan bakina da ita samira bata san ciwo kan ta ba wallahi. Nace mummy may tayi kuma tace waya san iyaka yar nan gashi yanzu yar uwanta ke fadin dawowan nan danayi tace wai sabbin abaikai tayi ko yaushe idan su basu zo ba ta taje wirin su. Kinga ai irin haka mutum ke gudu wa rayuwanshi don ba a gane mugu a goshi tunda ba zuciyar mutane ake gani ba wanan abin na yarinyar nan yana damu na wallahi. Nace ni mummy sai yanzu nake ganun fa,idar barina in fita da uncle bai yawan yi koma wani wuri zan tafi in ba wurin Aisha ko samira zan tafi sai dai mu fita tare sai kuma idan wani abu zan fita in sawo mai muhinmanci a gare ni. Mun dauki lokaci muna hira da ita nafito daga dakin don magariba ya kawo jiki a lokacin don haka na fito don zuwa sallah. Ko da uncle ya dawo da dare tafito sun dan taba hira dashi ta koma daki ni dai sai haba haba nakeyi da ita a gidan in samu mu rabu lafiya ina mai kara bata hakkuri. Washe gari ta wuce da safe tana matukar bani tausayi tace don Allah in kara yiwa uncle magana akan zancen nace insha Allahu anty zanyi bayan tafiyan ta muka zauna nan da mummy a falo muna hira. Duk jikina yayi sanyi wai yau anty ne take kumsan bakin cikin da na miji a kanta matar da suke gwanin ban sha,awa agidan su ita da mijin ta da yayan ta a gida har damu da mu kaje cin arziki a gidan. Yau sai gashi wai sun samu sabanin mai muni a tsakanin su dole mata mu rika taka tsamtsam da maje komai dadewan mu a gidan miji. Haka rayuwa ke guda yau dadi gobe madaci ga bawa watarana kuma a dara uncle yayi kokari ya mayar da anty dakin ta tare da basu hakkuri daga ita har daddy din. Haka yasa anty uwa da kawar ta suga shiga tashin hankali don komai sunyi na shirin buki a lokaci da bincike da komai suka gano uncle ne yayi sanadin komawan anty gidan daddy din. Haka yasa suka niko gari zuwa gidan namu uncle ya shawo kan daddy ya yarda a tsayar da zancen auren su da sahura. Muna zaune a falo duk da safiya ne amma hakan baisa sun shigo sun samay muda shirin mu a gidan bamu da wani makusa sai kanshi ke tashi yana kwance saman dogon kujera don ranan babu aiki. Abba yana saman jikin shi yana mai wasa sai ni dasu maimu dake zaune muna mashi hiran shirmay su don yace zai saka su islamiya shine suke biya inda suke. Sallaman su mukaji daga sama shigowa falon gidan kai tsaye da mamaki nake kallon su don shi yana kwance a lokacin. Baiga fuskokin su ba sai dai yana kokarin mikewa zaune a lokacin gane su da yayi yasa ya daure fuskan shi yana cewa uwa kune tafe ? Tace eh gamu mun shigo yau ziyara sannu ku dazuwa kawai nace dasu ban kara bita kan su ba kuma ban bar wurin ba sai cewa dani dasu hindu su shige ciki. Ban kuma mike zuwa dauko masu abinsha ba na zauna tare da harde hannuwana wuri guda jikina yana gugan na shi a yanayin zaman da muka dashi. Bayan su gaisa dashi anty uwa ta dan dube ni tace don Allah bamu wuri magana mukazo yi dashi kallon ta nayi na cewa ni tare da nuna kai na ? Tace eh magana ya kawo mu wirin shi mukazo kafin ince wani abu don yau nayi niyar mata rashin mutunci sosai sai naji uncle yace da ita. A, a bakizo ganina bakan duk abinda zaki fada min idan baki iya fada a gaban matana ai ba alheri ya kawo ki ba ke nan. So idan kinyi niyar gani na ba idan zata tafi don gidan ta kika shigo kinga ko baki da right din cewa ta baki wuri ki fadi maganan ki kai tsaye kawai naji. Don ni mata itace abokiyar rayuwa abokiyar shawarana gaba daya don ko kin fada a bayan ta ma fada mata zanyi tsab. Nisawa tayi tace dama bawani abu ya kawo mu ba sai zancen yayana da kawana sahura gata har an saka lokacin aure yanzu kuma yace wai ya fasa komawar wanan macuciyar matar tashi da ta shiga ta fi, , , , Dakata uwa don Allah ban son sha shanci kin sani ke har zaki iya dauko kafa kizo min gida da wanan zancen naku na banza . Yanzu don baku da kunya kuke kokari shiga tsakanin mijin da matan da suka shafe sheru goma sha wani abu da aure kina kokarin cusa mashi wata bare can. To bari kiji ban cikin wanan magana naki na hauka kuma aure yaya ba zai taba kara aure ba muddin maimuna na gidan nan. Tashi tayi da fushi tana fadin don munzo wurin ka neman taimakon bawai yana nufin munzo roko ko maula ba balle kayi kokarin fada min magana haka ? Dole yasa ka ga mun zo wurin ka don kawai ka dafa muna ba wai wani abu ba yace oho gani mahaukacin daure kun kwaso kafan ku kunzo a hada kai ayi cuta to ban iya ba ku bace min da ga tun raina bai baci ba na kira maki yan sanda yanzu. Sai da ta watsa min hara nima na mayar mata daga inda nake zaune ta fita fuuuuu sauran suna biye da ita a baya. Yaci gaba da fada a falon yana fadin wanan matar tana da hankali kuwa ko abin nata ya zama hauka ne wai ? Naji dadi sosai har cikin raina yadda uncle bai raga masu ba ya kore su ya kira wayan daddy yana fada mashi abinda ke faruwa a gidan. ZAINAB IDRIS MAKAWA SEENABU 9/21/20, 9:58 AM - Ummi Tandama: BAHAGGON RAYUWA, , , , , , , , , 🧕🏿8️⃣3️⃣🧕 ZAINAB IDRIS MAKAWA SEENABU Haka rayuwan mu yaci gaba da tafiya a gidan muna samun kula yadda ya dace daga wurin uncle har yasa yan kanne na wani school mai tsada a nan cikin Abuja. Sa su makaranta yasa yanzu ina fita in kai su in kuma je hudu in dauko su in sun shirya nakaisu islamiya ranan da ban iya fita kuma sai driver ya dauko su daga school din. Yau haka na kwana ba lafiya a jikina sai karfin halin da nakeyi ban son asan halin da nake ciki a gidan sai dai jikin ya matsa min har ban iya boyewa mutane halin da nake ciki. Wanda ya saukar min da zazzabi zuwa rana mai karfi har yakaini da rufuwa da bargo da kyat barci ya dauke ni cikin zafin jiki nake barcin a wahale a lokacin. Jina shiru ban fito ba tun safe da na sauke yara makaranta yasa mummy lekowa dakina ta duba ni ganina kwance na rufe da bargo har kaina yasa ta shigo tana fadin . Safiya yau lafiya kike kuwa abinda ya falko dani daga barcin dana dan samu ke nan na bude idona dakyat nace. Mummy ban jin dadin jikina ne yau tun dare zazzabi ya rufeni sai da nasha magani ya lafa yanzun kuma ya kara dawowa. Ina gyara kwanci nace karfe nawa yanzu mummy tace uku da rabi ya wuce dan yunkurawa nayi ina son in dauko waya amma na kasa. Sai mummy ta gane abinda nake son yi tazo da sauri ta dauko min wayan ta mika min neman layin uncle nayi don in fada mai a dauko min su maimu daga school . Jin murya na yasa shi fadin may ya samay ki safiya ? Banda lafiya na iya fadi kawai sai naji ya kashe wayan da sauri na gyara kwanciya nayi don ko sallah ban iya yiba a lokacin. Ba afi wasu mintina ba sai gashi gidan yacewa malam musa yaje ya dauko yaran daga school ya dawo yanzu ya juya ya fita daga gidan kamar yadda ya umurce shi dayi din. Ciki ya shigo bayan ya sallami malam musa din dakina ya nufo don yafi tsamanin ina can din a lokaci ya turo kofan da sauri. A kwance ya hangoni kwance na dunkule a wuri daya ina makarkyatan dari duk jikina rawa yake a lokacin . Bargon dana rufe jikina ya kwarai tare da dan taba jikina a hankali zafi yaji radau a jikin nawa jin hannun shi a jikin nawa yasa na bude ido na hanshi zaune a kusa dani yace . Safiya baki da lafiya ne har haka baki fada min ba kuma baki kirani ba take ya daga waya ya kira likitan shi yace yana wani wuri amma gashi nan zuwa yanzu. Yana dakin har likitan ya shigo gida fita yayi sai gasu sun shigo tare da likita dakina ya ce madam sannu yaya jikin ? Nace da sauki ina takurewa a wuri daya yace yaya nake ji ne ? Nan na fada mai yau kwana hudu da amai amai ya fara min sai kuma daren jiya ya saukar min da zazzabi . Yayi min yan tambayo na bashi amsa uncle na zaune ya kafeni da idanuwan shi sai yace bari ya fara saukar min da zazzabin gobe zai dawo akwai awon da zai min. Wani irin ras ras naji gabana ya bada don ambatan awon da yace na dauka akan maysalan ciwon mu zai mun awo din na yaba allura har biyu tare da magani. Suka fita da uncle daidai lokacin yan makaranta suka dawo dakina suka shigo don tun a hanya malam musa ya fada masu banda lafiya shiyasa banzo daukan su ba. Don su fison in tafi dauko su don duk abinda suka gani na marmari a hanya sukan ce min insaya masu ko kuma in tambaye su asai maku abu kaza ne ? Gaishe ni sukeyi kowa tana kokarin ganin fuskana kamar an fada masu a fuska na ciwo dake damu na yake min. Dan samun saukin da nayi na rarafa naje ban daki na dauro alwala nazo na tayar da sallah don har da azahar banyi ba ina kwance. Ina sallah naji shigowan uncle dakin bai fita ba don ina sallah zama yayi har lokacin da na idar da sallah din ya miko min maganin da likita ya rubuta mai ashe shine ya fita sawowa. Nan ya tsaya sai da na shaye maganin na koma na kwanta fita yayi ya samu Nura mai aiki yace ta hado min tea takai min dakina. Ina kwance sai ga Nura ta shigo dakin dauke da dan karamin tire a hannun ta da kayan tea ta kawo min tana min sannu. Ban tashi ba sai ga uncle ya shigo dakin na lura sallah yayi yana fadin kinsha tea din kuwa yana kai idon shi inda kayan suke aje kai kawai na girgiza mai alaman ban sha ba. Zama yayi ya hada min tea din yana tashi kisha cikin commad yayi maganan shi bawai alaman lalashi ba dole na tashi na sha tea din rabin kofi na koma na kwanta ya mike yana fadin zai dan fita ba dadewa zaiyi ba zai dawo. Har yakai kofa wani irin amai ya taso min da sauri na yunkura zuwa ban daki kafin in isa na sake amai mai karfi a tsakiyan daki na. Wani irin kallo ya bini dashi tare da yi min sannu cikin tausayawa a gare ni na karasa zuwa ban daki amai nayi sosai duk da ba komai a cikina. Fita yayi ya fadawa mummy nayi amai na bata dakina dashi da sauri ta taso da Abba goye a bayan ta ta nufi dakin nawa. Mummy ta gashe ni ta sauke yaron ta fara gyaran wurin dana bata din da amai sai sannu nake mata ina fadin ai da ta barshi zan gyara wurin ko ta turo su maimu su gyara don suna gida yau ba islamiya. Tace haba wanan ai ba komai bane aikina ne barin yi ta gama gyara wurin ta dawo tadan zauna sai ga maimu tashi tana saye da wandon tie baki iya gwiwa da yellow din dan riga sannu take min cikin tausayawa. Nace jeki kitchen ki dauko min lemo guda biyu ki wade min su ki kawo min da sauri ta fita ta dan dauki lokaci ta kawo min na yunkura na tashi dakyat na iya shaye guda na koma na kwanta don sam banjin dadin jiki na. Ban dade da kwanciya sai barci yau ni dake hana wasu barcin bayan laasar sai gashi ni ina yi fita mummy tayi da yara don kada su ta dani tare da jawo min kofan dakin. Uncle ya dawo gida kafin magariba ya wuce dakina kai tsaye ya tura kofan ya samu ina barci ga lemon da aka wade min a gefe na aje yadan dade tsaye kaina ban san ya shigo ba. Ya dan taba ni kadan sai na bude idona yace tashi magariba ya gabato da kyat na samu na tashi zaune yayi min sannu da kara tambaya ko na sake yin aman bayan fitar shi nace banyi Allah ya sauwa yayi min. Bayan fitan shi daga dakin na daure na tashi na shiga bayi wanka nayi da ruwa masu dumi sosai na dan gasa jikina tare da dauro alwala na fito. Sai da na zauna na dan huta na mike na gabatar da sallah a inda na idar na sake dunkulewa a cikin hijabi na banyi barci ba ina jiran inyi ishai a wurin mummy ne tashigo duba na. Ta samu nayi sallah ta yi min yaya jikin nace da sauki mummy murya can kasa kasa na amsa mata tace har yanzu bai fada maki ba ? Nace na rage jin sanyi yanzu kaina ke ciwo kamar ya tsage nake jin shi sannu tayi min ta dan jima zaune a wuri duk da ba hira muke yi ba a lokacin sallah ya tayar da ita tana idar wa suka dawo tare dasu hindatu suka zauna a dakin. Uncle ya dawo dauke da ledoji a hannun shi dakin ya nufa dasu su Mommy na ganin shi suka shiga gayar dashi hindatu da maimu suna rige rigen amsan ledojin dake hannun shi din. Mika masu yayi tare da fadin su aje karamin su tafi da babban suci ya juya wurin mommy data mike tsaye ko tana shirin fita dakin . Yana tambayan ta bata kara amai ba ko mummy tace bata sakeyi ba sai dai kanta tace yana mata ciwo sosai kamar zai tsage. Yace kuma again ban san may yasa zata boye min bata da lafiya haka ba har saida abin yayi nisa sosai yanzu ai ba a wasa da ciwo. Tace kila bata dauka sosai bane haka ko irin dan zazzabin da kan zo ya wuce ma mutum ne shaaa . Fitan mummy ya dan kwanto yana tambayana yadda nake ji nace da sauki yace kan fa ya lafa yanzu nace eh kawai badon ya lafa min ba din. Ya ce in tashi inci wani abu ga nama na da fresh milk in sha kai na girgiza alaman a a yace to a hado maki tea ki sake sha nacs uncle ko nasha ba zai zauna min ba ne . Ya mike yana bakuma zaki kwanta da yunwa ba kin sani dole ne kici wani abu sai cewa nayi koko zan sha ka fada wa mommy. Koko kuma a ina za a samay shu yanzu da daren nan nace muna da abindama shi a fridge mommy ta san inda yake na bashi amsa. Uhmmm yace kawai ya mike tsaye ya nufi wurin mommy din ya fada mata abinda nace ta tashi da sauri ta shiga kitchen din don Nura ta tafi gida ko dare yayi. Ta damo min kunun ta kawo min shi na dan samu na sha ya zauna min a cikina har na samu barci ya dauke ni sosai ban farko ba sai cikin dare fitsari ya tayar dani. Nan dakina naga uncle kwace a kusa dani yana barci jin motsina bayan na fito banda yasa shi falkawa yace yaya ne kuma ? Nace ban daki na fito da sauri yace haras wan ne kuma nacs fitsari nayi yaya jikin yanzu nace da sauki cikin gundura da magana na haye gadon na kwanta a bayan shi. Haka barci ya kara daukan mu sallah asuba ya fita yi don jin jikina yadda ya gashe kuma ina rawan sanyi yasa shi fita bai tayar dani ba. Har yaje massalaci ya dawo ina kwance sai kaduwa jikina keyi ina wani irin sam bato hakorana suna kadawa da yan uwan su na kasa. Hawowa yayi saman gadon tare da dan tallabo ni yana fadin tashi muje asibiti hakana . Kasa tashi nayi dakyat ya samu na tashi nace kuma zanyi sallah kina iyawa yace dani kai kawai na gyada mai na shiga ban dakin ya biyoni ciki har nayi alwala na gama na fito ya miko min hijjab dina. Da kyat na sallamay bai saya jiran komai ba ya dagani muka fita daga dakin da kanshi ya toka motar muka fice a gidan bayan ya buga ma mommy zamu tafi asibiti tace jikin ne har yanzu ? Eh kawai yace ya fice bamu dawo gida ba sai da suka bani gado suka kwantar dani likitan shi ne a kaina sai wasu dakan dan shigo sun debi fitsarina da jini zasu auna su gani. Alluran da akai min yasa ni barci sosai fita yayi ya kira yaya Saadu ya fada mai anbani gado ya kashe ya kira Aisha tace gata nan zuwa da ta sauke yara makaranta. Gida ya kira mommy ya fada mata don hankalin ta ya kwanta shigowan yaya Saadune da samira na dan falka ban dade ba na koma barcin don karfin alluran da akai min din. Zuwan su samira yasa shi komawa gida don anan suka barsu a tare dani sai barci nakeyi hankali kwance ga ruwa daure a hannu na . Aisha ta zo nan suka hade wurin suna dan hira mummy da zai dawo bayan yara sun tafi makarantane yazo da ita don ance sai sha biyu result zai fito na test din da akayi. Bai shigo dakin ba amso result din yayi suka hade da likita bayan ya karba yafita sai ya dawo dakin da nake kwance din sun gaisa dashi ya nufi wurin gadon yana tambaya ban falka ba har yanzu ? Samira tace na dan falka dazu ban dade ba kuma na koma barci ya dade tsaye a kaina ya juya ya fita sai suka hade da likitan. Hannu likitan ya mika mai yana fadin congratulation sir madam.cikine gare ta har five week shine ya jawo mata ciwo haka kuma kasan yanayin jikin nata gashi kuma bata dade da haihuwa ba strees yayi mata yawa ne. Wani irin lumshe ido uncle yayi tare da dan rike hannun likitan yana fadin ya gode kamar shi ya bani cikin. Takardan magani ya mika mai yace asamo wanan maganin idan ta tashi zata samu sauki sai tasha don jikin nata ya samu dan karfi don yanayin ta. Bai dawo dakin ba don mata sunyi yawa a ciki yake gani wurin sayen magani ya tafi daga can ya wuce office ya duba wasu bakin da yayi sai bayan la,asar sosai ya shigo asibitin. Lokacin ina zaune ina tauna Apple din da nace yaya Saadu yazo min dashi idan zai zo gaishe sukayi ya amsa a duduke ba tare da ya kalle su ba. Bakin gadon ya karaso yana tambayana yaya jiki da sauki kawai na iya bashi amsa ya kalle ni duk na ramay na fada a lokaci guda kamar na dade ina ciwo . Fita suka fariyi a dakin kamar wa yan da ya kora bansan may sa suke shakkan shi idan yana wuri har samira bata sakewa takan ce dani mijin nan naki kamar ustazu yake baya kallon mutane ko kana gaida shi sai ya dinga yi kamar yana tsoron mata. Muryan shi naji yana ce min cin fruits din ya tashi ko da sauri na kalle shi sai kuma na sadda kaina nayi kasa . Sai kuma na dago nace dashi ciwo yasani ci idan bashi na dan ci ba banjin dadin baki na yace aifa yanzu banda sauran wasa da saye fruits . Haba uncle daga ciwo kuma sai in buge da shan fruits ko yaushe murmishi yayi yana gyara zama da kyau yace yanzu yaya kike ji naji sauki na fadi a hankali kamar banson magana. Ga magani likita ya rubuta yace a sayo dazun sai kin ci wani abu zaki sha don haka barin fita in kira Aisha ta zuba maki kici sai ki sha ido na lumshe a hankali tare da fadin bazan ci abinci ba zan dai sha koko da mummy ta damo min. Yace ok kisha din sai ki sha maganin ya mike ya fita ya kira Aisha tazo ta zuba min ya dawo ya zauna inda ya tashi yana zaune har na gama sha ya bare maganin ya bani na hadiye na koma na kwanta. Kwana daya nayi aka sallamay muka koma gida ba laifi don na samu lafiya sosai sai dai jikin nawa ba karfi har lokacin su Maimu da hindatu keyi wa Abba wasa ina zaune na kura masu ido kawai banjin dadin hayaniyar nasu amma kuma ban iya tsawata masu su bari. Mummy ne ta fito tana masu fada daga dakin ta lokacin uncle ya shigo gidan zama yayi nan falo inda muke mommy ta gaida da dawowa. Bayan ya tambayeni jikin yana yi ma abba dan wasa ya leke mai wai ya dauke shi yace tafi wurin uwar ka maimu zan dan watsa ruwane a jikina. Ya mike ya shiga dakin shi ya jima a ciki na tashi na bishi dakin nashi don ban iya jure hayaniyan da yaran ke yi haka kawai nake jin haushi komai ba gaira ba dalili. Shiga nayi na kwanta saman gado har ya fito ya samay ni a nan nan kika dawo kuma nace haniyan yaran nake jin shi har cikin raina wallahi. Sai da ya gama shirin shi yasa jallabiya ya fesa turare a jikin shi haka yasa nasan bazai fita ba ke nan yau kuma don baya fita hakana. Takowa yayi inda nake din yazo ya zauna safiya naji ya kira sunana a hankali na dan bude idona da suke lumshe na sauke akan shi tare da dan kakaro murmushi a fuskana kadan. Kin san kina dauke da ciki a jikin ki na wata daya da kwanaki da sauri na daga daga kwanciyan da nake ina fadin na shiga uku. Kin sha uku akan may safiya ban taba zaton jin wanan furucin daga bakin ki ba domin ko abin farin cikine ya samay mu bana shiga uku ba. Uncle abi fari ciki fa kace yaro na yana da wata bakwai uncle zakace wai abin farin ciki ya samay mu ? Kallon da yake min ne yasani natsuwa na farga da katobaran da nake shirin yi a gaban shi a yadda na san shi da son haihuwa yanzu. Yana yawan fada min shi haihuwa yake so yayi yanzu yana son ganin yara sun cika mai gida kamar sauran gidajen yan uwan shi da abokai. Sai gashi ina shirin yin baranbarama da albishir din da yake min na dan cikin da ke jikina wanda ashe shiyani zazzabin nan da nake yi duk dare. A hankali na koma na kwanta tare da lumshe idona ina mai jin zafi a raina da samun wanan cikin na jikina a wanan lokacin da ban tsamace shi ba. ZAINAB IDRIS MAKAWA SEENABU 9/21/20, 9:58 AM - Ummi Tandama: BAHAGGON RAYUWA, , , , , , , , , 🧕🏿8️⃣4️⃣🧕 ZAINAB IDRIS MAKAWA SEENABU Fita yayi daga dakin batare da ya kara magana komai ba nima komawa nayi na kwanta ina jin zuciya na yana min zafi maikon in ji farin ciki a raina. Ba don komai ba sai irin surutun da mutane zasu dinga yi ga haihuwa na a kai akai da nake yi kowa zai fassara min shi da wata manufa ta daban. Na dade a wurin kwance ban motsa ba shi kuma bai shigo dakin ba har wanan lokacin barci ne ya dauke ni wanda na dade ina yi sai a zahar na tashi don sallah. Ko da na fito nasamu bai gidan sun fita da yaran zuwa shan ice cream dakina na nufa ban iya yin wani abuba a dakin sai kwanciya da nayi. Ina nan kwance sai ga hindatu ta shigo da Abba dauke a hannun ta maimu na bayan ta dauke da ledan tsara da ya sayo masu. Suna zuwa suka fada min a jiki gaba dayan su na dan lumshe idanuwa a hankali ina jin su a jikina kun dawo nace dasu anty kin ga abubuwan da baba Abba ya sayo muna yakai mu mun ga biri da zaki abubuwa da yawa muka gani inji hindu. Murmushi nayi nace su bude kayan in gani ba komai bane sai tarkacen kayan lashe lashe na yara dasu yought din robobi nace sai kuje wurin mummy kuyi ta sha ai. Na samu na iza su suna fita na sauke ajiyan zuciya har wani lokaci banji motsin uncle da banyi ba yasa banji dadin haka ba a raina nasan idan na biye mashi fushin nan nashi ne zai wakana a tsakanin mu kwana biyu. Haka yasa na dan mike jiki ba kwari na nufi dakin shi don bai falo a lokacin dakin shi na nufa na tura da sallama yana ciki zaune ya tasa laptop din shi a gaba yana aiki dashi. Jin sallama na da yayi ya dago kai ya dan dube ni kadan ya mayar da kan shi ga abinda yake yi a hankali na karaso inda yake zaune nace. Uncle sannu da aiki kun dawo yau kasha kiriniya da rawan kai wurin su maimu ya ce na kaisu shan iskane da Abba don kin san farin cikin yara shine nawa a yanzu. Nasan magana ya fada min a fakaice cikin dakewa nace Allah ya raya muna su ta farkin addinin musulunci yace amin kawai ba tare da ya dube ni ba. Gyara zama nayi da dakyau a kusa dashi na dan dora kaina saman jikin shi ajiyan zuciya naji ya sauke a raina nace su zuciya manya. An fara sauka ke nan don naji ya sauke ajiyan zuciya karo na farko shiru ba wanda yayi magana a cikin mu har na wani lokaci sai aiki yake yi wanda nake gani sako yake turawa a lokacin. Gajiya nayi da kwanci haka na na sai na dan juya ina kokarin jawo filo in kwanta sama muryan shi naji yana fadin kin ci abinci kuwa nasha koko nace mashi. Koko ba abinci bane kin dai ji likita yace ki dinga cin abinda zai gina maki jiki ko yaushe uncle zan ci nace a takaice. Rufe laptop din yayi ya mike ya fita sai gashi dauke da abinci yazo ya aje a gabana yana fadin oya tashi ga abinci ki ci na kai duban ga abincin . Sakwara ne da miyan gaye yaji agushi sai manja da tayi amfani dashi da nama manyan yanka da ta saka sai kamshi ke tashi a gabana. Take naji warin abincin ya nashe ni har amai na son taso min a lokacin amma don dai kawai in farauta mashi rai haka na daure nayi loma biyar da kyat har nayi kusan rabin plate din dake gaba sai dai ban kai ko ina na ba koda ya dawo mayar da kayan abincin ya samay a bayi ina haraswa sosai. Na galabaita abinda yasani barcin yamma ke nan ranan sai magariba na falka jina na shiru da mommy tayi ta tambaya lafiya nake kuwa ? Murmushi yayi yace mummy jikin nata yanzu sai a hankali ai don lalurar juna biyu sai a hankali. Murmushin jin dadi mommy tayi tana fadin masha Allah nikan nayi tunanen haka yadda naga ta koma kwanan amma naji dadi jin haka wallahi . Maganan mummy wanda yasa shi jin dadi har cikin ranshi yace mummy na gode kwarai don Allah a tayani kulla da ita a gidan idan ban nan. Kada kaji komai suriki wanan ai farin cikin mu ne mu duka Allah dai ya raba lafiya ya bamu masu albarka rayulayyu masu tarbiya yace amin mummy. Dana tashi don sallah magariba da yayi na dawo dakina na yi ban fito ba har ishai sai da mayi wanka na fito falon bai shigo gida ba har lokacin. Mommy tazo ta samay ni a falon zaune wuri ta samu tana fadin ayya safiya ashe abin arziki muka samu da sauri na kalleta tace mun zamu samu karuwa . Murmushi nayi na sadda kaina kasa don kunya tace wanan abin yayi dadi wallahi da sauri nace haba mummy. Dudu fa Abba yanzu wata na bakwai yake shiga ko fafiya bai fara ba kuma ace na samu wani ciki a jikina. To may ye naji ta katsani yo mai shege ma ta goya balle ke naki da ubansu zaki wani ce bai yi ba ai indan ma wata uku uku zakiyi kina haihuwa ba wani matsa bane a hankan yanzu. Don ko uban su na da halin kula abin shi yanzu ai gara mutum yayi ya gama da wuri wanan haihu mai wahala na yanzu. Shiru nayi ina nazarin maganan ta sai kuma na tuna a garin mu matar da tai ciki da goyo har waka ake mata da shagube bata da sauran shakat a rayuwan ta kuma. Ummi tayi haka lokacin goyon hindatu ta samu cikin autar mu har girkin ta inna tace basu ci a gidan wai tayi kazanta tayi abin kunya don bakar jaraba. Ta shiga wani hali a lokacin sosai a gidan mu duk da banda wayo amma na fahinci halin da mahaifiya na take ciki a lokacin. Dole kula da hindatu ya dawo kaina sai inda na fita zuwa makaran ta hindatu ke raban ummi a lokacin inna na bin ta da gori tsakar gida. Muryan mummy ya katse ni tana fadin ai yanzu mata sun waye da ne can ake daukan shi wani abu amma yanzu ai ya zama isa ga mace goyo da ciki ikon Allah. Ni dai murmushi yake nayi kawai taci gaba da fadin balle ke da ba nono ma diyan ki ke sha ba ai gara kiyi abinki da wuri ki gama ki gyagiji ko taso tare da su. Dariya ta bani don jin wai in taso tare dasu da tace sai dai banyi magana ba hira take min uncle ya dawo daga wurin sallah. Muka gaida shi da dawowa daki ya wuce nasan ruwa zai watsa mu kuma mukaci gaba da sha anin mu a falon har lokacin da ya fito mommy ta shige ta bar mu da su maimu dake kallon katun da Abba dake kiriniya ya koyon mikewa tsaye suna ihu su kuma idan ya mike din. Zama yayi har lokacin fuskan shi babu annuri a ciki sai dai bai daure sosai ba zama yayi yana kallon yaran yana murmushi. Juyowa yayi gare ni yana fadin maimuna na gaida ke takira wayan ki a kashe sai ta kirani nace ayyah suna lafiya tun da na dawo asibiti ban koma ta wayan nan ba ai zankira mu gaisa idan na tashi. Abinci ya mike yaje yaci anan ya barni kwance sai da ya gama ya dawo dauke da fruits a plate ya aje a gaba hindatu na bayan shi dauke da cup din koko mai zafi yana tururi. Kallon shi nayi na yamotsa fuska yace kina nufin haka zaki kwanta da yunwa a cikin ki dauki cup din nan kisha kokon tunda shi kike so in kin gama ga fruits nan ki sha. Ya koma ya zauna yana facing dina dole na dauka na dan kurba ina yamotsa fuskana ba halin magana ya tsureni da idanuwan shi da kyat na shaye dan cup din kunun ina sauke numfashi. Gyatsan haraswa nake yi har na samu ya fada min ban fito ba na koma nakai kance alokacin komai ban so don jikina gaba daya ba dadin shi nake jiba. Ashe barci ya dauke ni har yayi kallon news yaran suka shige sai lokacin daya gama naji yana tayar dani inje in kwanta yace ya rufo min dakina don haka muka wuce dakin shi gaba dayan mu. Ba laifi na samu na dan warware don kulawan da nake samu gurin uncle da mummy sosai suke bani kulawa yan kaina ma ba a barsu a baya ba suna nasu kokarin dani sosai a gidan har gyaran wuri suke taya mummy da yan sauran aiyukan daba su fi karfin su ba. Anty tazo daga lagos gani na da yaran ta har da funke mai aikin ta don ita kadai ke gidan yanzu su fati da faiza kowa ya koma gidan su da zama. Naji dadin wanan zuwan na anty da dare muna dakina da ita tace ashe cikine yake wahalal dake haka amma wanan cikin yazo maki da wahala don kamar bakiyi haka ba cikin Abba ko ? Idona ya kawo hawaye nace anty sam banyi tsamanin samun ciki yanzu ba duka duka fa Abba wata bakwai yake da haihuwa na takwas yanzu yake bidan shiga. To shine may safiya ga mijin ki shi yana ta farin ciki da samun cikin shi ke fada min kin samu ciki mai wahala wanan karon cikin yana wahal dake sosai. Ni gaskiya anty ban son daukan ciki yanzu gaskiya da sauri tace saboda da may nace kinga wata da muke zuwa amsan magani da ita tayi irin haka. Sai jinta yayi week kamar zata mutu wallahi da kyat ta sha har an debi tsamani a gare ta sai likita ya fada mata masu irin lalurar mu bai dace suna saurin haihuwa ba da wuri haka saboda jinin su dake ragewa suna iya shiga wani hali kan haka. Shi kuma uncle ya kasa fahinta na gaba daya yama ki bari muyi maganan dashi na fahinta tace toke yanzu yaya kikeso bayan cikin ya riga da ya samu dole zaki kula da kanki sosai yanzu. Shiru nayi ban fada mata nufina na son in zubar ba don naga tana goyon bayan uncle tace kada ki hada kan ki da waccan don kila ita bata samun kulan da kike samu. Mun dade muna hira ta tafi ta kwanta nima na shige kwana daya sukayi muna suka juya lagos don dama ganina kawai suka zo yi. Yau na tashi da son gyara jikina don yanzu shagon matar nan yar uwar wacce tayi min gyara a bauchi na karbi lambata can nake zuwa tayi min gyaran da nake so. Tare da kanne na na tafi har da mummy amma tace kitso kawai take so nan samira tazo ta samay mu tunda nace mata gamu wurin gyaran jiki tace gata nan zuwa itama ayi da ita. Angama ma mummy kitso ganin yaran zasu damay yasa sakina ta kaisu gidan ta su zauna ta dawo mukaci gaba da hira. Nan nake fada mata ina son zubar da cikin jiki na ido ta zaro min tace saboda may madam niko a gani na da kibar abinki kwana nawa kin haife abinki safiya. Wata mata da ta girmay muna tana jin mu tace mai zai sa ki zubar yar uwa idona yayi kwalkwal ya kawo ruwa nace yanzu fa dana watan shi bakwai da haihuwa hajiya. Shine suke son in bar cikin kuma inyi yaya da su su biyun don Allah tace ashe ba a yaye shi ba ma lalai wata bakwai kan akwai wahala wallahi. Yakai wata nawa cikin jikin naki nace yanzu wata biyu da kwanaki bai cika uku ba cif tace ai mai sauki ne barin rubuta maki su kwaya sai ki saya ki sha mu gani idan bai fita ba sai ki hada da alluran shi. In haka yaki fitar dashi sai kin je an cire maki ke nan ta bude jakkata ta ciro takarda da biro ta rubuta min nayi mata godiya na karba har mukayi musayan lamba da ita a wurin. Ban je gida ba sai dana biya na sayi maganin a wani babban chemist dake hanyan mu na kwaso mummy da yaran gidan su samira muka dawo gida. Kai aka wanke min sukayi min kitso sai dai ba kanana ba sai gyaran jiki da sukayi min don jina nake na koma wata irin gaja dani rashin gyaran da ban samu kwana biyu inyi. Jin jikina nake yau kamar ba nawa ba sai dare Uncle ya dawo don suje site din su dake sulaje yau a can store din su yake babba inda suke tara kaya indan an kawo masu. Idan yaje can ya dawo yakan gaji sosai don aikin wahala akeyi a wurin har shi yakan taba aikin aje a dawo basu da hutu ranan. Ko da yadawo ya gaji sosai wanka yayi yaci abinci ya kwanta nima ban dade ba na samay shi a dakin har ya kwanta ko sai dai bayi barci ba. Na shigo na rufe kofa ido ya tsura min daga inda yake kwance har na iso gare shi yace yau wanan gyara haka sai ya mayar min dake wata irin yar yarinya under age. Murmushi nayi na karasa hawa godan na kwanta nace under age haka kamar kumama dani yace to be serious yau kin koma yarinya sosai murmushi nayi kawai ina gyara kwanciya na. Ranan bai barni ba sai da ya dan lalube ni muka gama muka sake wanka na kwanta zuwa asuba sai zazzabi ya rufe ni kuma da kyat na tashi nayi sallah na kara kwantawa. Har ya gama shirin shi ban sani ba sai da zai fitane yake tayar dani zai fita indan jikin ya matsa ki kirani mu koma asibiti tau kawai na iya ce mai na koma na kwanta. Yafita ya sauke yara makaranta ban fito ba sai kusan shabiyu koshi na fito in samu dan ruwan liptop ne in sha. Anan falo na zube na umarci Nura ta hado min ruwan liptop jin muryana yasa mummy fitowa tana min yaya jikin , ? Fuska a yamutse nace mummy da sauki take cewa ko jigilar gyaran jikin da nayi jiya ne ya saukar min da zazzabi ciwon ne kawai ya dawo mummy. Litop din ya taimaka min naji bakina ya koma min dan daidai har na sha lemu anebi wanka na naje nayi dakina koda na fito wayana yana ruri a lokacin. Na dauka da dan sauri kada ya katse uncle ne yake kirana a lokacin ina dauka nace uncle yaya aiki shiku bai tsaya bani amsa ba sai tambayana yayi da yaya jikin naki ? Nace da sauki uncle kin ci abinci ya tambaya nace mai naci alhalin banci din ba bani mummy yacd nace mommy tana dakin ta nima dakina nake kwance. Ok sai ki sha magani kafin in dawo Allah ya sauka nace dashi amin ya kashe wayan na wurga wayan saman godo naci gaba da shirina. Bayan yadawo gida da yaran ya samu naji sauki sosai zaune ma nake da Aisha data kwaso yara tabiyo tanan dubani da jiki mun da ita kafin ta wuce gidan ta. A gida yayi magariba duk banda wani matsala komai zuwa tara kaina ta fara ciwo kamar zai tsage min haka yasa dole ya fita ya samu min magani nasha. Zazzabi sosai nayi da dare dole da safe muka nufi asibiti ban so zuwa ba amma ba yanda zanyi dole naje aka dubani muka dawo gida. A hanya ya matsa min may nake so ya saya min nace ban son komai sai masa mai zafi idan zan samu dariya yayi yace aiki ko ya samay ni ni madam wani irin ciki kika dauko wanan karon kuma ? Haka mukayi ta yawo gidajen abincin hausawa ana muna kwantace sai da kyat muka samu masa yayo min take away leda biyu muka juyu gida ina ji a mota yana ma hajitan shi waya ta sa a turo muna da masa bana ya samu dan gargajiya a gidan shi. Dariya tayi tace insha Allahu goben zata sa ai min za a samu wanda zai kawo min in Allah ya yarda tace ya bani waya idan ina kusa muka gaisa tayi min yaya jiki har muka iso ina magana dasu. Ban tsaya falo ba dakina na nufa na aje jaka da maganin da aka bamu asibitin irin ta masu lalurar mun ta masu ciki sai na saka a jakkana. Ruwa na watsa ma jikina don in ji dadi nafito nayi sallah sai na dawo falo na zauna masan naci shi sosai kusan na kusa cinye take away din. Na sha ruwa nan muka zauna hira da mummy shiya dawo gida da yaran yau ma ya zauna kusa dani yana wasa da Abba kamshin turare shi ya haddasa min wani irin ciwon kai. Gudu nayi na shige daki na kwanta sai kuma amai yazo min nan na amaye dan masan danaci koda zai saura a cikina sai kadan. Shine ya shigo yana tambayana a harasawan ya dawo ne kuma yanzu kai yace har ya juya yace kin sha maganin ki kuwa nace ban kai gasha da na bari idan zan kwantane tunda sunce yana da karfi. Ina kika a je maganin yace min tare da kafe ni da idanuwan shi bako kiftawa nace gayan nan cikin hand bag dina ina fadi ina mikewa zaune don nasan shan maganin zanyi. Sai damay yana cikin tona jakkan ya jawo wanan maganin da na sawo a chemist wanda matar nan ta banj na zubar da ciki. Jin shi shiru danayi yasani juyowa inga may yake yi a lokacin maganin na ganshi rike dashi a hannun shi yana karanta wa. Take naji gabana ya fadi a wurin juyowa yayi yana tambaya na wanan maganin may Safiya ? Magani na ne nace mashi yace ai nasan maganin ki ne na may ye na tambaya ? Kaina na dukar kasa ban ce dashi uffan ba Safiya naji yace na dago kaina yace cutana zaki yi komay ? Shiru nayi na kasa magana sai naga ya fita da maganin a hannun shi take fuskan shi ya juye ya koma wani irin zaki a gabana. ZAINAB IDRIS MAKAWA SEENABU 9/21/20, 9:58 AM - Ummi Tandama: BAHAGGON RAYUWA, , , , , , , , , 🧕🏿8️⃣5️⃣🧕 ZAINAB IDRIS MAKAWA SEENABU NOVEL DINA NA KUDI NE DON ALLAH DON ALLAH IDAN BAKI BIYA BA KADA KI KARANTA DON DON SHIGA HAKKIN WANKI DON GIRMAN ALLAH Ke kuma mai fitar min da da novel nasan basai anje lahira ba ubangiji yazai daukan min fasan akan ki don kin nuna baki da imani da tsoron Allah a fili. Mai imani bai wanan halin ko yaya yana nuna tsoron Allah ba zance dake komai ba amma zaki ga ni a rabon ki shi amana bibiya yake ta inda baki zata ba. Jin dakin shiru bakajin komai sau karan nauran wutan dake aiki a dakin sai ko ni da nake sauke numfashin wallah har wani zufa nake yi don tsoro da fargaba alokaci daya. Da kyat na yunkura na mike na sauke kafafuwa na daga saman gadona cikin karfin hali na nufi dakin shi don babu kowa a falo gidan yayi wani tsit a lokacin. Ganin kofan shi a bude ya tabbatar min yana gidan har wanan lokacin bai fita ba ke nan da far gaba na tura kofan a hankali na shiga dakin. Ya tsaye bakin window dakin dake kallon haraban gidan ya harde hannaye shi duka biyu a saman kirjin shi kamar bai san na shigo dakin ba ya nuna min. A hankali jikina a sanyaye na karasa inda yake tsaye har na iso gab dashi na sa hannu na da nufin in rungumay shi ta baya ya juyo a zafafe cikin zafin rai ya kwashe da wasu irin lafiyayun maru guda biyu masu kyau. Sai da na kai kasa ban sani ba ya nuna ni da dan yatsan hannun shi yana fadin ashe baki da mutunci baki da tausayi ban sani ba Safiya. Ashe ke mutumiyar banzace nake zaune da ke ban sani ashe baki da tsoron Allah a rayuwan ki ban taba zaton haka ba a gare ki ban taba ba Safiya. Ashe daukan da nake maki ba hakana kika dauke ni ba ke may nayi maki da kike son ki cuce ni haka da zafi may na rage ki dashi wanda na kasa baki kike son saka min da wanan abin da kike shirin yi min. Ni dai ina duke na rike kumci na sai hawayen da ba kuka nake fitar wa wani nabin wani iri rike da kumatuna da yasha mahaukatan maru gare shi. Kuma cikin maganan da yake fadi wani ma ban fahintar shi a lokacin wanda nake ji kuma ta yaya zan fara bashi amsan su don suyi min yawa a lokacin. Naji yace uban wa ya baki wanan magani a ina kika samo shi yau naji na tsane ki nayi dana sanin auren ki dana nayi safiya tunda baki so na da karuwa banga dalilin zama dake ba a rayuwa na. Dago kai nayi na kalle shi karo na farko bayan marin da yayi min da hawaye na shabe shabe a fuskana. Mikewa nayi daga inda nake tsam ina shirin fita dakin wani tsawa ya daka min yace dakata baki bani amsa na ba tukun . Uban wa ya baki wanan maganin nace tare da nuno min maganin a hannu shi dan kuturun yazo min nima a lokacin ban bashi amsa ba kawai na fice a dakin ba tare dana kara juyowa gare shi ba. Daki na koma na haye gado na dunkule a wuri daya take wani irin kuka yazo min a lokaci daya mummy ne ta shigo dakin don taga fitowana daga dakin shi ita da Nura suna magana a falo. Hajiya lafiya may ke faruwa ko jikin naki ne ya matsa maki haka take tambayana a jere lokaci daya sai kuka nake ban iya magana ba. Banko kofar dakin da yayi da karfi shiya dakatar da mommy dake tsaye a kaina tana jera min tambayoyin ta a lokacin. Ganin mommy bai hanashi fadin abin da yazo fada min ba yace ni zaki mayar mutumin banza ina magana ki wani fitowa ki barni yau sai kin fada min wanda ya baki maganin nan ko ki fice ki bar min gida na don ba zan zauna da macen da zata haince ni ba. Da sauri mommy tace subbahanallahi Alhaji mai yayi zafi haka tsakanin ku har kake fadin wanan maganan haka ? Kallon mommy yayi cikin bacin rai kamar zai mata magana kuma ya fasa nasan zuciya ce ta kawo mashi maiyi a banza balle yau ga dalili. Ya juya gareni yace ke har kin isa baki san halina bane wallahi da bakiyi min hakan ba ban cutan na tare da ni shi kuma Allah bai yarda ya cuce ni. Don Allah Alhaji kayi hakkuri ku bi abin sannu niko ina saman gado na dunkule sai kuka nake yi ya juya wirin mommy yana fadin mummy ashe duk ciwon da yarinyar nan keyi ita taja wa kan ta. Da sauri mommy ta mayar da han kalin ta gare shi tace ita taja wankanta garin yaya haka ya faru kuma hajiya ?. Gata nan shi nake tambayan ta tana son raina min wayau yanzu bayan Allah ya tona mata asiri wai mummy kin san zubar da ciki take kokarin yi yanzu na kamata. Innalillahi safiya baki da hankali ne may yayi zafi haka cikin da kowa ke farin ciki da samun shi zaki ce kuma zaki fitar haba haka baiyi kyau ba wallahi. Ni dai kukana nake ban saurare su ba don Allah Alhaji kayi hakkuri tunda ta gane kuren ta ai mata afuwan kurciyane ya kai ta ga hakan da batayi ba idan ta sani. Kurciya ina kurciyan yake anan tunda har tasan ta zubar da ciki ta cuce ni ga abinda nake so don tana munafuka wawiya. Zagin yayi min yawa uncle na iya furtawa da karfi a cikin kuka ya watsa min harara yana fadin ok har ma kina da bakin magana zagi yayi maki yawa ko ? Alhaji kayi hakkuri don Allah ka bar zancen nan haka na tunda ta gane kuren ta yace sai fa ta fada min a inda ta samo wanan maganin zan barta mommy yace. Zuwan yaya Saadu da ya kira ne ya katse shi ya fita falo wirin shi ya samay shi nan yake fada mashi abinda ke faruwa a tsakanin cikin bacin rai. Mommy ce ta fito dakina a lokacin goye da Abba bayan ta da yake barci ta karaso inda suke tana gaisawa da yaya Saadu daya shigo. Yaya saadu yace mummy abinda safiya take shirin yi ke nan ashe shiya tare da fadin ina mommy zata san mugun nufita tunda batason kowa ya sani nima Allah ne ya nuna min tun batayi min sawalwalin cikin ba. Ka fada mata idan bata fada min wanda ya bata wanan maganin ba sai ta barmin gida na yau don ban zama da mace da bata sona da karuwa . Yi hakkuri yallabai ina Safiyan take yana tambayan mommy tace tana nan dakin ta yace mommy ai min magana da ita don Allah. Nan mommy ta juya ta shiga wurin ta fada min ga yaya Saadu yana magana dani azuciyar ta kuma sai addua take Allah dai yasa ba samira bace don rawan kan samira na da yawa. Sai can na fito saye da hijjabin sallah na har kasa ina yiwa yaya saadu sannu da zuwa cikin miryan na da ya dishe saboda kuka da ciwo da fargaba. Ina zama Uncle yana bina da harara yaya saadu ne yace safiya yaya haka kuma ya faru cikin lalama yake min magana wanda shi uncle din bai so haka ba a gare shi so yayi ya balbala ni da bala,i a lokacin. Sai kuma yaji yana min magana may kama da lalashi yace may ya kawo haka safiya haihuwan ne baki so ko tsoro kike ji ne ? Haushine ya kama uncle yace kaga malam ba lalashinta na kiraka kayi ba ta fada muna inda ta samo maganin nan in ba haka ba bata zama min gida. Na dago cikin zafin rai nace samay idan na bar maka gidan ina dai da gidan ubana ko sai kuma idan ginan da kai muna zaka sa a rushe ka mayar muna da namu. Tashi yayi kamar kububuwa yayo kaina yaya saadu ya tare shi yana fadin bari mubi a hankali yallabai abin bai kai haka ai zata fadi nasan halin safiya. Yace amma kana jin har ta samu bakin fada min bakar magana ko da mamaki yake kallona ni kuma cikin zafin rai da hasala nace. Dole in fada maka kana ta magana in bar maka gida, gida kan tunda ba anan aka haife ni ba ai nasan ba gidan ubana bane sai in bari din sai may. Safiya ashe haka kike inji yaya saadu nace yaya abin yayi min yawa ne wallahi daga magana sai ya wanke ni da mari kawai. Mari kinyi laife mai muni ne safiya dole ya mare ki ko nine abinda zanyi sai yafi wanan da yayi maki ai don may ba zaki tsaya kuyi magana ta fahinta ba kin tsaya garda yace ki fada mashi inda kika samo magani kin tsaya kina ja. Wai may ma zai sa ki zubar da cikin ne safiya may cikin ya tare maki da kike son zubarwa ne da baki iya hakkuri ki haife shi. Yaya maganin nan ya dade a cikin jakkata wallahi ba yanzu na saye shi ba da yake nufi ni kuma ba wanda ya bani dama na san shi tuntuni sai na sayo da nake ganin kamar ciki ke gare ni a baya. Ba yanzun na saye shi ba yaya karya take wallahi yanzu ta sayo shi take sha don cikin ya bare to bari kiji ni ba dan rayuwa kawai na kawo ki gidana ba. Don raya sunnan ma,aiki na kawo ki mu hayayafa mu cika sunna mai karfi ba a haihuwa ke aka haife ki yana fadi kamar zai buge yaya saadu ya rufe da duka. Ranan iyakan bacin ranshi na gani a gidan ni kuma naki fadin inda na samu maganin na tsaya kai da fata maganin ya dade min a cikin jakkana kuma ba wanda ya bani maganin saye kawai nayi don na san shi. Naki fadi ne don kada naja wa matar mutane jiddali daga taimako nasan kuma idan na fadi gaskiya abin zai iya shafan samira duk da bata da laifi aciki amma muna tare aka bani. Har magariba ya gwauta muna wurin zaune yaya Saadu da mommy sai bashi hakuri suke yi suna fadin nayi kuskure sosai na bashi hakkuri. Nace ni ban sha ba koda yake fadin nasha ban sha maganin ba aida cikin ya fita inda nasha din yace cikin dai yafi karfin ki ne yaki fita. Nace ban dai so zubar dashi ba da babu abinda zai hana na zubar din yace yaya Saadu kana dai jin abinda take fadi. Tayi laifi ban isa ta bani hakkuri akan abinda tayi min din nace ni ban san nayi laifi ba tunda ban sha komai ba. Yaya Saadu ya tursasa akan in bashi hakkuri a gaban nace nayi kuskure ka yafe min daki ya wuce zuciyar shi nayi mai kuna sai tuna maganan hajiya baaba yake yi da tace mai ya rage matsamin don zan iya bijere mai daga baya. Yanzu ko gashi ya ga na fara din wai safiya ce yake fadi take fadi har tana ikirarin na rushe gidan da nayiwa mahaifanta na mayar masu da kangon su. Kwafa yayi yace dani kike wasa yarinya zan nuna maki kuren ki a gidan nan zaki san kin taba ni don sai kin gane kuren ki. Yana alwala yana maganan zuci a falo kuma yaya saadune yayi min fada sosai akan yadda nayi ban kyauta ba nayi laifi kawai in bashi hakkuri. Nace yaya kanaji fa yana fadin ban kwana mashi gida yau akan maganan ga zai ta fadin haka in ba dama ya gaji dani bane yana son mafita akaina. A daidai lokaxin ya fito daga dakin shi ya kallemu kamar harara yana fadin Saadu muje muyi sallah rabu da ita mommy jekiyi sallah lokaci ya kure ko. Yaya Saadu ya kalleni yana mikewa yace safiya yaushe kika kuma haka ne wai duk kin bi kin tada hankalin mutane a lokaci daya haka. Don Allah ki kara bashi hakkuri idan na wuce don ba lalai ne in dawo tanan ba yayiwa mommy saida safe ya fice daga gidan, itama mommy tashi tayi zuwa sallah inda na dan dade zaune ina tuna irin karfin halin dana rufe idona nayi masu. Mikewa nayi zuwa sallah nima ban fito don ishai yayi nan na zauna abina sai su hindatu ne suka shigo dakin suna min hira wanda ba fahintar su ma nakeyi ba. Fitar maimu sai gata ta dawo tana fada min anty baban Abba ya dawo yana falo zaune nace ku tafi ku gaida shi yau banjin dadin jikinane. Yaran suka fita zuwa wurin su suna gaida shi da dawowa ya amsa masu fuska a sake kamar yadda ya saba yi dasu kullun. Nan suka dan zauna suna mashi hira suke fada mai antyn mu tace yau jikin ta yana damun ta bata iya fitowa Allah ya sauwaka yace ai na bata magani dazun. Mommy ce ta kirasu suka shige ciki wurin ta ya gama abinda yake yi ya shige dakin shi batare da ko waigowa kofana ba. Nima nasan da hakan shiyasa nayi zama na a daki ban fita don yasan nima ina jan zancen na gama har na kwanta a lokacin naja bargo na rufe kaina a ciki. Da safe Samira ne tazo gidan dubani da kuma tambayana yadda akayi haka ya faru har na bari uncle yaga inda na aje maganin. Nace kedai bari Samira baban Abba yakai dan halas wai mutumin da bai taba, taba min jakka ba shine wai da yake Allah yayi asirina zai tono sai gashi yaje daukan maganin da muka karbo asibiti a cikin jakka ta. Na manta shaf wallahi da wanan maganin ai da na yunkura na tashi komai ciwon da nake ji na rufawa kaina asiri. Tace ke dai bari aini da yayan ki ya fara min maganan baki ga yadda na tsure ba ina gudun suna na yafito a maganan tawa ta samay ni, in shiga uku gashi muna alkunya da mutum da ina zan saka kaina. Dariya nayi mata nace ni zan fara ne in fadi gaskiya da fa har gidan matan nan yana iya zuwa yai mata cin mutum ci shiyasa na kafe dacewa dama nasan maganin na dade da sayan shi. Zai kuma iya hani zuwa gyaran jiki shiyasa nayi mai borin kunya na labe ga zancen gida don yabar maganan. Kuma nasan abinda yasa yayi sanyi ke nan a yadda ya dauki niyar ci mun mutunci ido rufe tace kai safiya sai kika lauye bawan Allah da jijiyoyin shi. Nace ke kuwa kin san yadda uncle ya hau har fa maru biyu ya bani masu kyau rabona da duka tun gidan yaya Ahmed fa samira. Tace ni banga dalilin ki sin zubar da cikin nan ba safiya baki rasa ci ba baki rasa shaba a gidan nan wanda zai gina maki jiki. Don may zaki nace sai kin halaka dan cikin ki kika sani ko gwauna ko shugaban kasa kika samo muna zakiyi muna sawalwalin tsiya haka. Nace samira ai yanzu na yi nadama sosai yadda naga uncle ya kwalafa rai ga haihuwan nan haka yasa jikina yayi sanyi wallahi. Tace yanzu dubara ya saura gare ki ai sai ki san yadda zaki bashi hakkuri ya sauko maki don nasan yanzu ya hau sosai dake a gidan nan. Nace ya hau kan zan jira sai ya sauka don yanzu yi mashi magana wani jidalin zan kara jawowa kaina barshi mu tafi haka har ya sauko da kan shi dai. Tace kina ganin haka zaifi safiya nace ni na san halin uncle Samira barshi dai muje a hakan tace to shike nan ai mai daki shiyasan inda ruwa ke yoyo. Tace sai da na fada maki tun farko safiya kada ki yunkurin zubar da cikin nan don dan halas sai an haife shi tunda an samu. Wasa wasa mun share wurin sati biyu yanzun ba mai kula wani sai dai zan mai ina kwana ya amsa min a dake ba sakin fuska ko kadan. Tun ina dari dari har abin yazo ya daina damuna tunda ban rasa ci da sha ba ba kuma korana yayi a gidan shi ba. Sai dai wani lokaci abin yakan damay ni amma yaya zanyi tunda yaki tsayawa mu fahinci juna har in bashi hakuri ga kuskure na. Allah ya gani tsoro nake ji don abin da ya samu kawata shine ya tsaya min a raina sosai saboda irin haka tayi tasha da kyat. YAR UWA BA SAI KIN RUBUTA BATSA BA NOVEL DIN KI ZAI SAMU KARBUWA, KE MAI GYARA TARBIYAR AL, UMMA CE BA MAI BATA WA BA. KIN SAN YARA NAWA NOVEL DIN KI YA HALAKA DA WA YAN DA KIKA SAKA ZINA TA SANADIN NOVEL DIN KI NA BATSA. KI WA KANKI FADA TUN LOKACI BAI DAINA YI DAKE BA ABIN KWARAI AKE YAYI BA NA BANZA BA, , , , , , , ZAINAB IDRIS MAKAWA SEENABU 9/21/20, 10:00 AM - Ummi Tandama: BAHAGGON RARYUWA, , , , , , , , , , 🧕🏿8️⃣6️⃣🧕 ZAINAB IDRIS MAKAWA SEENABU Yau ya kama jumma, a tunda safe ina shirya yan kanne da zasu makaranta don dole duk safe koni ko mummy daya ya tsaya wurin su don su shirya. Idan ba haka sai su tsaya shiririta da gardaman banza har su makara don yanzu sun rage zagwadi son makarantar da sukeyi . Tunda sukaji baba ya yarda da zaman su a guri don da farko kin yarda yayi lokacin da hutun su ya kare yaji shiru sai gashi ya bugo min waya wai baiga yaran shi ba. Nace baba yaran ka suna nan lafiya makaranta ne ya boye su yace wani irin makaranta kuma nace ai mun saka su school a nan din dana boko dana muhamdiya. Yace bam yarda da wanan tsari ba don ba haka mukayi dake ba nace baba na sani amma kayi hakkuri da hakan da nayi. Fada yayi sosai a wayan ina sauraren shi saida ya gama nace baba nasan munyi kuskuren yin haka da mukayi. Amma ba nayi bane don mu raina maka nayi ne don taimaka wa rayuwan mu baki daya saboda indan suna nan zasu samu karatu mai inganci da ci gaban rayuwa. Kayi hakkuri baba don Allah kabar min su anan don zama su a nan din yana da matukar muhinman sosai yace. Safiya ai wanan rashin hankalin ne ki dauki yara har biyu ki kai wa mutum gida wanan ya zama rashin hankali ai. Baba shi ya yarda da zaman su don shi da kan sa ya kaisu makaranta mai tsada ta kudo anan din munyi kuskure ba zamu kara ba in Allah ya yarda. Bayan ya gama saurare na ya kasha wayan ya nufi wurin su ummi da fada mama ya fara kira sai ummi suka fito yake fadin. Ashe kun hada kai da yarinyar nan safiya ne ta yaudareni ta kwashe yaran nan, ta tafi dasu su zauna a wurin ta ne ? Haba malam ai wanan abin kamar taimokan ne tayi inji mama ta katse shi ga maganan shi yace ke dakata min. Taimakon may nace na gaza da "ya"ya ne ita a ina ta taso in ba nan din ba ummi tace amma ni wanan abin sai naga kamar taimakon kane yarinyar nan tayi banga abin fada ba don safiya ta dauki kannen ta ta kaisu gare ta. Mijin ta baiyi fadan haka na sai kaine zakiyi haka dakan shi ya bata baki kan hakan yace ke nan da sanin ku aka yaudare ni ? Yaudara kuma malam babu yau dara acikin hakan wata rana hakan zai maka dadi yaya Nura ne yashigo gida a lokacin yake tambayan may ke faruwa. Ummi ke fada mai yace baba koni safiya zata dauka yanzu ai zuwa zanyi da gudu balle maimu da hindatu yara nacen cikin daulan duniya za ai masu bakin ciki kuma. Kaifa mahaukacine sakaran banza kawai waye zai masu bakin ciki din niko uwar ka ya wuce yana a bakin ciki za ai masu mana mai kaya ya daure sai mai cira ke wassh Allah. Uwarka nace ya nufe shi gadan gadan shiko ya fice gidan yana dariya wanan abin yasa su ummi saurin watse wa gaban shi yaci fadan shi yana fadin ai zai gamu dani ne. Murmushi nayi da tuna wanan magana da ummi ta fada min ya faru a gidan mu sauri muke mu tafi sai Abba ya kama kuka ina jin mommy tana lalashin shi yaki shiru. Uncle ne ya leko daga dakin shi yana fadin wai may yaron nan yake ma kuka haka ne ke kuma baki dubashi ba ? Bai mai magana ba sai wucewa da nayi dakin kawai na samu mommy tana lalashin shi yaki shiru daukan shi nayi ina lalashi bai yi shiru ba. Mummy ta tara hannun yaki zuwa wurin ta dole sai na goya shi don yayi shiru saboda mommy ta saba mai da goyo yau kuma bata jin dadin jikin ta ne. Ya fito daukan ruwa ya samu su maimu zaune falo suna jirana yake fadin baku tafi bane har bakwai da minti goma yanzu suka ce anty muke jira ta fito Abba ne ke kuka yaki yin shiru. Sai gani na fito dakin mommy da goyon shi da goran ruwa a hannun shi ya dago yana kallona goye da yaron a bayana. May ya samay shine yau ya fadi yana kallo na cikin dakewa nace fitane kawai yake ji mommy bata jin dadi tun jiya miko min shi nan yace dani ina kokarin sance yaron a baya ma in mika mashi sai yaton yaki ya kara lafewa. Ke mi ko min shi yace goyon nan zai iya maki illar koda dama ba son cikin kikeyi ba nace yake zaune a jikina idan ban so ka barshi kawai mutafi in kaisu in dawo. Barshi in kaisu naji yace tare da fadin ku tashi kada ku makara sosai yaran suka mike sai maimu ke fadin anty kudin exam din fa uncle zai bada ? Nace ku bari monday zanje in biya maku idan na kaiku yake cewa nawane kudin suka ce five hundred kowan mu fita yayi baiyi magana ba ya wuce suna biye dashi a baya. Nan suka fice na sauke ajiyan zuciya yaushe rabon da yayi min magana haka sai yau sanadin Abba dake kuka a gidan ya jawo yayi min magana. Da motana ya fita dasu bai jima ba ya dawo ina zaune goye da Abba a bayana ya shigo wurin mu yayo direct yana fadin . Babana may ya hadaka da mommy yau kake fushi haka ban san ka da fushi na fa ya dan duka yana yiwa yaron wasa sai kuma yace. Kin bashi abinci yaci ko yunwa yake ji kai na girgiza mai yace ki bashi a gani ko yunwa yake ji don yanzu dai madara ba isan shi zaiyi ba. Mikewa nayi zuwa inda Nura tafara jera abincin na dibo mashi dankali kadan na dawo ina sance yaron sai ya karbe shi a bayana shi da kan shi yake bashi abincin yaron yana karba. Yace don Allah ku bar barin shi da yunwa haka yaya madara kawai zai ishi yaro dan wata tara yanzu nace ya dai so cin abincin ne yanzu amma in an bashi sai yaga dama yake ci. To na dai ce a dinga bashi in baici a barshi daga yau naji nace dashi ya gama sai kuma yace sai in kara goya shi yasa muna fitina a wurin yana jawo zanin da na sance goyon shi a bayana. Wuf uncle ya dauki yaron yayi ciki dashi murmushi nayi bayan sun shige daki da yaron wanda nasan ya fara saukowa ne da kanshi da ina binshi ina bashi hakkuri da yanzu bai isa saukowa ba haka. Ya fito cikin shirin fita yake cewa Abba na nace daki yana barci ki lakashi don kada ya tashi yana kuka ya fado ya fada ba wani sakin fuska gare shi. Fita yayi daga gidan mukai mai a dawo lafiya bayan awa daya ne naje dakin leka yadon yana kwance yana barci abinshi hankali kwance har lokacin nan nabi dakin da kallo yayi kaca kaca sai na fara gyara bathroom na fito na gyara ko ina na goge na sa mai room fresh yaron ya tashi kafin in gama. Na sauke shi na canza mai zanin gadon na jawo mai kofa sha biyu daidai na fito zuwa dauko su maimu ni da Abba ne muka fita na dauko su tare motan mu ya kunno kai kwanan gidan. Bayan mun shiga ciki na rufe mota bai fito ba har na shiga gida sai can gashi ya shigo muna falo zaune muna cin marasa gasas da muka sayo a hanya hajiya tana hanya zata shigo yace dani. Ras naji gabana ya fadi ban san lokacin da nace mai hajiya baaba ba yace ita yana wuce wa dakin shi bai tsaya falon ba nasan shirin jumma,a yadawo yayi lokacin. Yana shiga idon shine ya sauka a dakin dana gyara mai shi tson ya sauke ajiyan zuciya ya aje waya ya nufi ban daki nan ma a gyare yake komai sai walkiya yakeyi a wurin yasha gyara. Murmushi ya sauke a fuskan shi shi kadai a dakin yace mata halin su sai su watau tunda yau nayi mata magana shiyasa ta shigo tayi min gyara itama ta iya ke nan yanzu. Daren jiya kamar ummi ta sani tasa ni gaba a waya tayi min tas sai da nayi kuka sosai tace lalai lalai in bashi hakuri don nice ban da gaskiya ko ina akaje kuwa da maganan mu. Kuma akan may zance wai ya rushe gida ya mayar muna da namu yaushe na koyi rashin kuya haka ko nice nasa ya gina muna gidan. Idan banyi hankali ba zata hadani da mahaifin mu kuma zata kira uncle ta bashi hakkuri da sauri nace ni ummi ba sai kin kirashi ba ni zan bashi hakkuri da kaina. Sai washe gari kuma na tashi naga ya rigani ma saukowa ko shima mahaifiyar shine tayi mai magana oho ? Yanzun kuma da yace zata shigo sai tunane na ya kai ga ko tasan da matsalan ne zata zo inko har uncle ya fada ma hajiya yabar ni cikin tsunbul. Fitowa yayi cikin farin voil na maza wanda har zaka iya hango farar singlet din shi na shiki yana haskawa a inda ya bar mu ya samay zaune har lokacin muna wurin. Ke maimu ku shiya kafin in gama mu je masallaci ku shirya Abba yace dasu ya nufi hanya waje dama yakan je da yaran idan ya bushi iska amma ya dade bai tafi dasu ba sai yau. Namike na nufi dakin mommy nace ta ban kayan shi zasu je masallaci ne da baban shi nan na zauna dakin ta na shirya yaro tsab anan kuma nake fada mata yau sarakuwa na zata zo. Tayi murna da jin haka sai dai tace dani zato za ta samay ki cikin wanan zaman doya da manja da kukeyi a tsakanin ku haka ? Ni mommy yaya zanyi tunda in ya hau bai sauka sai yaga dama don kan shi tace ke ko keda yadda zakiyi don ke ce mace safiya nasha fada maki kada ki fushi haka dashi tunda ke ce baki da gaskiya. Babu namijin da zai kama mace da wanan laifin ya iya kyale ta ni naga hakkurin shi kwarai da gaske wallahi. Mommy har yanzu fa fushi yake yi dani kan maganan kuma sai kice kinga hakurin shi mommy ? Tace kin san girman laifin da kika aikata kuwa yar nan ai sai baka son namijine kake gudun haihuwa dashi nace shima yasan ai bada wata manufa nayi ba mommy kawai dai lafiya na nake jawa . Amma ni ba wai don ban son haihuwa dashi bane kawai dai haka Allah ya nufa sai ya faru a tsakanin mu yaki yarda ya saurari manufata kuma. Maza fa a sannu ake binsu diyar nan don Allah ya riga ya basu girma a kan mu ki lalaba mijin ki ku zauna lafiya yadda kuke yafi. Hindatune ta shigo daukan Abba a lokacin ban koma daki ba na nufi kitchen don shirya ma hajiya abinci sai dai ban san ko su nawa zasu zo ba kuma. Kafin su dawo nayi nisa ga aiki sosai don da Nura muke aikin abinci nagama abinda zanyi na fito kara gyara gidan su maimu na taya ni. Mun hada komai zuwa hudu hudu da rabi suka iso gidan yafita a lokacin dakin da aka gyara masu na kaisu ita da anty suwaiba sai yan matan ta biyu da tazo dasu. Mun gaisa na tambaye su sauran yan uwa suka ce duk suna lafiya abinci na gabatar masu sai da sukai sallah suka zauna ci . Ban koma wurin su ba na barsu su dan huta don sun kwaso hanya mai nisa dakina na koma na dan kwanta kadan don na gaji a lokacin. Cikin yan matan da suka zo da su ne daya tazo ta kirani. Na samu har sunci abinci ko na shigo dakin dayar yarinyar naa kwashe kayan abincin daga dakin tana kaiwa kitchen baaba yaya gajiyan hanya nace bayan na kai zaune kasa gefen gadon. Garin nan naku akwai nisa yar nan shiyasa ban sa kaina zuwa ba tun farko ko yanzu don naji ance kinyi fama da jikine har kin kwanta asibiti koda yake ke da ke da mijin nake ba fadar ciwo kukeyi ba. Ko sannu akace maku ai an rage maku ciwo a daidai lokacin uncle ya shigo dakin yana fadin sannu ku da zuwa naje dan nesa shiyasa ban shigo da wuri ba. Bata fasa maganan da takeyi tace idan shi bai fada min ba aike kya gaya min tunda muna waya kusan ko yaushe dake. Zaune yakai kasa shima don mika gaisuwa ga mahaifiyar ta shi cikin girmamawa ta amsa mashi tana ci gaba dayi muna fadan rashin fada mata matsalar mu da baya yi. Yace aiyi hakkuri baaba ai ta dade da samun sauki dama ba wani matsala bane sosai ke damun ta a raina nace ka fadi hakan mana tunda cikin ba ajikin ka yake ba ai. Allah ya sauwaka tace muka amsa da amin tace Safiya kije ku bude tsaraban nan kada su lalace a saka a fridge nace baaba har da dawainiya aka zo muna kuma ? Kin jiki da magana ina dawainiyar yake anan ni mai gida na nayowa tsaraba dama ba ku ba yar uwar ku dai ta kawo maku tsaraba. Ina mikewa nake fadin baaba ba a zo da maryam na dai tace maryam din nan tana fama da laulauyin ciki bata iya zuwa ai taso ta biyo mu hakana hanata nayi. Nace Allah sarki ashe zamu sha suna idan rai ya kai mu lafiya tace a toh zaku sha kan don wanan cikin ma ya zo mata da matsala sosai wallahi ba kamar wanda take a baya ba. Yace dama ai haka ciki yake ko wani da kalar tashi zuwan fita nayi daga dakin na nufi inda kayansu yake yan matan na zaune falo da su maimu suna hira. Da dare na shirya bayan na idar da sallah na shiga dakin nasu suna ciki dukan su muka gaisa na samu wuri na zauna muna fita da anty suwaiba hajiya na lazimi saman carpet din sallah har lokacin. Ya shigo cikin jallabiya baka sai kamshin turare yake yi yace ke kije ki kama yaron nan haka na yau mommy bata jin dadin jikin ta. Mikewa nayi na bar dakin ba tare da nayi mashi magana ba zuwa kama Abba din dake ta kuka a dakin mummy baaba ne ta shafa ta juyo gare shi tana fadin kullun ina fada maka kabi yarinyar nan a sannu. Ji yadda kake faman daure mata fuska babu walwala a tare da ita duk tabi ta fige ta koma wata iri jikina yayi da bayan shi a bango yana fadin ni bani na fige ta ba baba halinta ne ya fige ta. Dan kallon shi tayi kamar harara tana fadin wani hali ke ga wanan yarinyar banda kai dake son takura mata a kullun hakan da kake wallahi tun tana tsoron ka na fada ma zata zo ta daina ne. Wani matsi ai bai da kyau wallahi idan yayi yawa ya danbala mutum ko ya hinjira shi murmushi yayi yace yanzu kuma wani matsi nake mata. Yarinyar da take gani ban isa da ita ina fadi tana fadi tace ba zan taba yarda da wanan magana duk da karya ba haki ka bane a baya. Hajiya yanzun haka ciki ke gare ta na kamata tana yunkurin zubar wa nayi magana tason tayi min rashin kunya kuma. Kira min ita suwaiba tace anty suwaiba ta tashi zuwa kira na muna kitchen muna hira a can ta samay ni . A daki kuma ce mata yake hajiya ban san may take nufi da yunkuri zubar min ciki da take yi ba ka zauna kunyi magana ta fahinta da ita ka saurare korafin da yayin hakan da tayi niya ? Lokacin na shigo dakin nuna min wuri tayi alaman in zauna nakai zaune jiki a sanyaye sai da taja dan lokaci tace min. Safiya yanzu mijinki ke fada min wani magana da banji dadin jin shi ba sam na dukar da kaina kasa sai haaaye tace Safiya may zai sa kiyi yunkurin zubar da cikin jikin ki kuma ? Har kin sa zargi ya shiga tsakanin ki da mijin ki yana zaton kin yi haka ne don baki son shi ko baki son haihuwa dashi ? Da kyat na dago kaina ga nauyi ga kunya dake cina nace ba hakana bane baba yaki ya fahinci manufata ne a hankali na kora mata bayani na da dalilin daya sa nake yinkurin cire cikin da farko. Tace banda abinki ai komai na Allah ne Allah daya baki shine kuma zai raba ki dashi lafiya ai kowa da irin tashi kaddaran rayuwa. Sai kiga ke kin haife komai ba zai samu ba cikin hukuncin Allah wani kuma sai yasha bakar wahala haka abin yake ga Allah. Kinyi kuskure babba don kisan kai kika so kiyi ba don Allah ya gyara kin fahinta daga baya ba kiba mijin ki hakkuri ban son irin yadda na samay ku din nan sam. Ana maku kallon sha,awa daga waje a ciki kuma baku da jittuwa tsakanin ku abin bai yi kyau ba wallahi kuna zaton wani bai san halin da kuke ciki ba to kirana akayi aka fada min abinda kuke ciki a gidan. Da sauri kowan mu ya kalle ta da mamaki tace eh ba dole bane in fada maku wanda ya kira amma dole tasani tasowa in zo don in tsawa ta maku. Dan shiru ne ya biyo dakin cikin sanyi murya nace uncle nayi kuskure ka yafe min don Allah babu komai yace a takaice. ZAINAB IDRIS MAKAWA SEENABU 9/22/20, 8:13 AM - Ummi Tandama: BAHAGGON RAYUWA, , , , , , , , 🧕🏿8️⃣7️⃣🧕 ZAINAB IDRIS MAKAWA SEENABU Bayan baaba ta shirya mu ne abin ya danyi sauki sosai tsakanin mu kwanan baaba biyu tare da mu a gidan bata tafi ko ina ba suka shirya komawa bauchi. Ko gidan Aisha da kyat na samu ta tafi bamu dade ba muka dawo sai sahad store da muka shiga ta dan duba abinda take bukata ita da anty suwaiba da yan matan ta. Kudin da uncle ya basu shi suka sawo yan kayayankin fashion dashi a cikin saukin farashi washe gari zasu tafi don haka bamuyi barci da wuri ba a gidan. Da safe kuma na tashi nayi sakkon dora masu abin karayawa kafin su wuce saida suka karya suka dauki hanya anan suka barmu cike da kewan su a gidan. Sai gidan ya koma muna tsit bayan wucewan su zuwa azahar na shiga kitchen na hado masan da nayi warming da miyar kassa na dawo falo na zauna kasa saman carpet ina ci. Mommy ta shigo falon masan takai ma kallo daga inda nake zauna ina ci a hankali ina kallon tv take fadin wai ni na rasa yaya mutanen nan ke masan su yafi na ko ina dadi ? Nace da ita suna tsaya su gyara ne ko ke a gidan ki mommy idan zaki tsaya ki gyara kamar yadda sukeyi zai koma ki. Mommy ko na zubu maki ne na dago kai ina tambayan ta don nasan gwanace wurin cin masa nawa mai dalili ne cin da nakeyi don saboda ciki nake cin masa yanzu. Zama tayi tana jawo Abba zuwa jikin ta na fadin Abba bazakaci masan nan mai miya ba don ruda ma ciki zaiyi nace bazan bashi bani idan kuna so ku debo naku ku dumama kuci. Zan jira yan matana suzo ne sai mu dumama muci don suma suna son masan nan sosai nagani tace dama magana nazo muyi dake yanzu gaki kuma kina cin abinci. Mommy may nene nace cikin dago kaina ina fuskantar ta ta ce ba wani magana bane dama gani nayi tunda an kai karshen matsalar ku da maigidan ki . May zai sa har yanzu baki zuwa gare shi kike baya baya dashi bayan kisan kece mai laifi kuma an shirya maganan nan a tsakanin ku kuma kon kasa bashi hakkin shi har yanzu. Jikina ne yayi sanyi sosai da maganan mommy saboda ban dauka ta fahinci ban shiga turakar incle ba dama don tana rigamu shigewa dakin ta. Maganan ta yasani dagowa na sake kallon ta da tace indan kina haka kina cutar da mijin ki ne da kan ki zamana a cikin ku kima baida wani amfani ke nan. Nasiha sosai tayi min akan abinda nakeyi akarshe nace na gode mommy in Allah yaso zan gyara mommy tace ki kulla don Allah diya ta. Nace mommy ba wai ina share shi bane dama ban san may zai mun bane idan na kusanci ida yake kin san shi bai iya fishi ya sauka maza ba. Komai zai maki dole ki shanye don shine gaba dake kece a kasa don haka ki maza ki shirya tsakanin ku komai ya wuce a tsakanin ku. Mommy in sha Allahu komai ya wuce zan shanye duk wani abinda zai min kan hakan koda bai hakkura da hakkurin da mahafiyar shi ta bamu ba zan shaye duk wullakancin da zai min. Allah yayi maki albarka da kika fahinci haka komai zai wuce da zaran yaga kin bishi kin kara bashi hakkuri. Banki ta mommy ba da na gama na gyara mai daki tsab na feshe da room fresh na wanke ban dakin na rufo mai na dawo part dina. Sai yama ya dawo gida lokacin muna falo zaune dukkan mu har mommy muna hira su kuma suna cin abinci. Ya shigo da alaman a gajiye yake na mike nabi bayan shi zuwa dakin bayan na kara gaida shi na wuce ban daki hada mai ruwan wanka na fito ina fada mai na hada mai ruwa ok kawai yace min yana duban wasu takarda a hannun shi. Ban tsaya ba na fice a dakin na koma falo na zauna ya gama ya fito cikin kayan da yake zama dasu a gida da alaman ya rufe fita ke nan yau din. Gurin cin abinci ya nufa ya ja kujera ya zauna isowa nayi gurin ina kokarin bude kukolin abincin da aka aje don shi a wurin. Sai da ja zuba mai tuwon semo da miyar yauki Nura tayi muna na abincin dare ya wanke hannun domin fara ci . Daya daga cikin kujerun na jawo na zauna nima a wurin abincin shi yake ci hankali kwance kamar bai san ina wurin zaune ba a lokacin . Sai zuwa Abba ne wurin namu ya fara magana yana fadin babana kaci abincin kuwa banga cikin ka ya cika ba shiko yaron kokarin daukan goran ruwan dake gaban shi yake yi. Yace zuba mai ruwa kila kishin ruwa yake ji baida bakin fada na zuba zan ba yaron ya karba daga hannuna yana kokarin bashi yaron na kawar da kai sai goran yake son dauka kawai. Daukan yaron yayi zuwa jikin shi ya dibi abincin ya fara kai mashi a baki tare da balle goran ruwan dake gefen shi ya kafa mai a baki sosai ya zuki ruwan daga cikin goran ya cire bakin shi yana mai da numfashi sama sama . Ina zaune gefe na harde hanayena ina kallon su hankali kance yadda suke yi ba karamin son yara uncle keyi ba dole ya yi min masifa kan barar da cikin da nake shirin yi din don ko banza ya kamata ace yana da yaran da suka kai biyar yanzu a shekarun shi. Ban ankara ba ashe ya dago yana fadin kin kuwa fara bashi maganin da hajiya ta kawo mai nace cikin kada kai tun tana nan aka fara bashi sai dai bai son sha idan an bashi sai da dare idan zai kwanta ake bashi. Ke maimu dauko mai biscuit din shi ko zai ci nace biscuit kuma uncle da daren nan zai iya saka shi kashi don ruda ciki yake yi. Ba tare da ya kalle ni ba yace ke ke wankewa idan yayi ko ba za a bashi idan yana so shiru nayi kawai ina kallon su mommy har ta mike ta shige tun fitowanshi nasan kallo take a dakin ta. Ganin ya gama na hada kayan zuwa kitchen sai hindatu ta taso tana tayani kwashe kayan a wurin anan yake mata ba a tana murmshi. Yau bai dade a falon ba ya shige sai dana dauki lokaci na gama hada mai blact tea din shi na ganyen na,ana na samay shi a dakin. Kamshi ke tashi a jikina sosai a lokacin yana zaune yana aiki a laptop din shi tsab na gyara komai kafin in kwanta a bayan shi. Bai daina abinda yakeyi din ba har wani lokaci ya rufe tare da mikewa ya nufi bayi can ya fito ya zauna yana shan tea da na aje mai a bakin gado. Sannu a hankali na dago daga inda nake nakai zaune ina fadin Uncle don Allah kayi hakkuri ga abinda ya faru a baya ba munafata ke nan ba ga abinda kake tuhuma na dashi. Har tsawon wani lokaci bai mun magana ba nima ban sake magana ba ina zaune shiru a inda nake a bayan shi cikin fargaba. Sai can naji yace yanzu may kike son in ce tunda ke baki son haihuwa dani ni kuma ina son haihuwa a rayuwana baki min adalci ba Safiya ban cancanci haka a gare ki. Baka yarda dani ba ke nan uncle nace akan may zan yarda dake yanzu bayan ba wani ya fada min ba ni nagani da ido na a lokacin da baki zata ba. Murmushi nayi nace to shi ke nan na dauki laifina tunda haka kake son ji a bakina ko nayi kuskure a yafe min daidai yana kaiwa kwance yace min . Magana daya ne yanzu inga kin haife cikin nan lafiya shine kawai zai sa hankali ya kwanta dake nace har yanzu kana zargina kenan bai yi magana ba sai kashe muna wuta da yayi yana gyara kwanciyan shi da kyau. Nima komawa nayi na kwanta tare da lumshe idanuwa ina tunanen wanan hali na uncle duk abinda ya kamata nayi dai nayi mai a yanzu. Ban tsamanin jin hannun daya kai jikina ba a lokacin amma sai tunane na ya kwance a lokacin may yasa maza suke hakane a wurin wanan fannin basu jin kunyan yin haka ko wani lokaci suke da bukata. Washe gari ban koma barci ba don yace yana da tafiya zuwa Niger state sayen wasu kaya don haka na wuce kitchen don hada mai abinci da wuri kafin Nura tazo aiki. Ina tsaka ga aiki sai gashi ya biyo ni da wayana a hannun shi da na baro dakin yace yaya Saadu ne ke kirana a lokacin . Nayi mamakin kiran yaya Saadu haka da safen nan na karba daidai lokacin daya kara kirana din na dana wayan ina fadin ina kwana yaya . Yace lafiya Safiya kin ga na kiraki da safe haka ko wallahi waya aka bugo min daga gida da dare Allah ya karbi ran Ahmed jiya da daren. Innalillahi wa inna alaihim rajiun ya rasu yaya yace wallahi safiya da dare jiya suka bugo min waya yana tsaye daga kofa yana saurare na. Na dago kaina na kalle shi ya tsure ni da idanuwan shi cikin son jin abinda ke faru a lokaci a sanyayye nace wai yaya Ahmed ne ya rasu jiya da dare. Waye haka na yace dani a sanyaye nace yayan yaya Saadu dana taba aura a lagas Allah yai mai rahama yace yana wucewa zuwa dakin shi. Jikina yayi sanyi na bishi da kallo dakin mommy na nufa a lokacin don fada mata abinda ke faruwa damu duk ta rude dataji maganan. Na dan dade muna maganan na koma kitchen na karasa aikina hakana a dadafe sai tunanen zaman da mukayi dashi a gidan shi nakeyi. Nashiga dakin bayan na gama komai na samu yana tsaye yana shiri har yayi wanka a lokacin ga abin karyawavcan nace mashi sai kuma naja na zauna bakin gado har ya gama shiri ban yi magana. Tare muka fito a dakin nashi a lokacin zama yayi yake cewa mommy bata fito bane har yanzu nace ina ga shiryawa take zata gidan su yaya Saadu tace . Baiyi magana sai jawo plate dayayi a gaban shi ganin duk a sabule nake a lokacin sai lokacin na natsu na mike na fara zuba mai arish din a plate. Sai da ya fara cin abincin yace zasu tafi can lagas din ke nan yau da sauri nace ban sani ba don bamuyi maganan haka dashi ba. Wayan shi ne yayi kara yaya saadu dine yakirashi a lokacin yake fada mai rasuwan dan uwan nashi yace eh ai daka bugo mata muna tare Allah ya jikan shi yasa ya huta. Zaka tafi lagas din ke nan yace eh da yau nake son mu shirya mutafi da iyalina mota zaku bi ko jirgi yace ina ganin mota zamu bi don mu uku ne. Bari kubi jirgi zaifi ku isa da wuri zan fito yanzu zan biyo ta gurin ku kafin in wuce ni dai sauraren maganan su nake yi banyi magana ba. Sai dai zuciya ta ba dadi a lokacin don mutuwa ko na wanda baka sani ba yana shiga ranka balle ga wanda ka sani din. Har ya gama yana min sai ya dawo ban iya cewa dashi zan tafi gidan yaya Saadu in mai gaisuwa ba don kada ya fassara min magana da wata manufa kuma. A dawo lafiya nake yi mashi har yakai kofa yace idan mommy ta shirya sai ku tafi tare ki sauke ta ki masu gaisuwa. Na gode nace mashi ya fice gidan na sauke ajiyan zuciya mikewa nayi zuwa dakina ko kayan ban ita kwashe wa na soma shiri nima. Sai da na sauke kannena a makaranta muka wuce gidan mun samay su har sun shirya da ganin yaya Saadu kasan yayi rashin dan uwa a lokacin . Don ya fita hayacin shi sosai kan mutuwan da akai mashi din samira ke fada muna ai Uncle yazo yanzu ya wuce shine ma ya biya muna kudin jirgi zuwa lagos din. Nayi ma yaya Saadu gaisu nace idan sun je ya mika min gaisuwa ga sauran yan uwa yace zasu ji safiya . Yace Ahmed dai ya rasu bai samu rokon ki gafaran abinda yayi maki ba har ya mutu nace babu komai yaya na gafarta mai. Allah dai yayi mai rahama yasa mutuwa hutu ne gare shi yace amin safiya muna gidan har suka shirya muka raka su zuwa airport muka sauke su a can muka dawo gida. Ranan dai haka na wuni jiki ba dadi zuwa rana samira ta kirani tana fada min sun isa lafiya yanzu haka suna gidan ma ana batun kauda shi ne. Wani iri naji a raina na kara mata gaisuwa tace ga sadiya mu gaisa sai da na gyara na fara amsa mata gaisuwan tana kuka sosai a lokacin ni dai hakkuri na basu nace ta gaida min da gwago ina mata gaisuwan rashin da akayi din. Sai yamma ya dawo a daki na samay shi muka gaisa na hada mai ruwan wanka na fita bayan ya fito falo ne yana cin abincin dare nake mai godiyan abin da yayiwa su yaya Saadu din. Yace halin shine yasa nai mashi hakan din don yana da rikon gaskiya da amana a tare dashi banda abinda zan saka mai dashi in ba haka din ba. Shiru nayi shima bai kara magana ba ya gama ya mike yana tambaya na mommy nace suna daki basu fito ba yau. Bamu dade ba muka shige ciki nikan kwanciya nayi don har lokacin jiki na ba karfe don mutuwan ya shige ni sosai ranan. Sai dai ina kokarin ganin bai fahinci hakan ba don gudun zargina zai sa yace na damu aiko ban tsira ba sai jin muryan shi nayi yana fadin yau dai kamar kina cikin damuwa ko ? Da sauri nace damuwa kuma uncle akan may kuma zan damu an maki mutuwa yau mana uban diyar ki ya rasu. Naji zafin maganan nashi amma a fili cewa nayi mutuwa ko na wanda baka sani ba kana tausayawa mamaci ai balle wanda ka zauna dashi a baya . Ko ba komai kuma ai dan uwana ne shi kaga dole inji mutuwar a raina wanda nima ba komai nake tunane ba sai tawa makomar a yanzu. Naga alama yace yana gyara kwanci ba tare da ya kara magana ba muka kwanta hakana ba wani abu daya shiga a tsakanin mu ranan. Da safe ne yaya Saadu ya kirani wai zamu gaisa da gwago na dan jim nayi na karbi wayan muryan ta na rawa cikin gurbatacen hausan ta da ya gauraye yanzu tace Safiya ke ce yaya gida yaya maigidan naki. Nace muna lafiya gwago yaya akaji da hakkuri tace hakkuri ya zama dole Safiya Ahmed ya rasu yana fadin a rokar mashike ki yafe mashi don Allah. Nace gwago ni na yafe mashi tun tuni ai dan uwana ne sai naji ta kama kuka dole na kashe wayan don ban iya jimirin sauraren kukan nata a lokacin. Nima kukan na kama a wirin sai dai nayi saurin share hawaye na kafin kuka yayi min yawa don ta bani tausayi sosai sai dai shedan na rudina ina tuna irin cutar da sukai min a lokacin. ZAINAB IDRIS MAKAWA SEENABU 9/24/20, 5:48 AM - Ummi Tandama: BAHAGGON RAYUWA , , , , , , , , , , 🧕🏿8️⃣8️⃣🧕 ZAINAB IDRIS MAKAWA SEENABU Haka rayuwa ke ci gaba da gudana a gidan uncle watarana mu tashi a farinciki har dare wata rana kuma haka kawai zai daure fuska gare ni ba gaira ba dalili yayi ta fushi dani ga laifin da ban san nayi ba. Ga dai ci da sha da sutura wadatace a gidan amma banda kwanciya zuciya a gurin uncle ga fargaban ciwon dake jikin mu yau kaji ance babu wani a cikin masu irin lalaurar mu gobe kaji ance wata ta rasu akan laluran nan. Ga ciki yayin wani irin girma a jiki saikace cikin tagwaye na dauka wanda bai san halin da nake ciki ba sai ya dauka ai ina cikin daular duniya ne ina cin ta da tsunki ba abinda ke damu na. Sai dai da zan zauna dake in fada maki ciki na zaki fahinci rayuwan da nake yi a yanzu wanda zan iya kira maki shi da BAHAGGON RAYUWA . Daga bakin ciki na fito na fada rashin kwanciyan hankali a gidan uncle don kullu a fargaba nake dashi kada yace ga laifin da nayi mai a gidan. Amma idan yana cikin dadin rai idan ka ganmu saika dauka ba wanda ya kaimu soyewa a duniya a yanda muke daga bakin rayuwa zuwa haske da mai kumshe da magana a zuciya🧕🏿🧕. Cikin wai a hakan ina jin yan uwan shi na fadin wai ya rage a cikin halin shi na baya sai nakan tuna da maganan da Faiza ta fada lokacin muna gidan anty a lagos. Dadi na guda shine akwai waddata kuma yana taimakawa yan uwa da nashi da duk wanda yake rabe damu kodan wanan abin dole in yi hakkuri tunda na saba da irin rayuwan shi yanzu. Su baba da mama sun tafi lagos gaisuwa sun kara tula ma gwangon mu nayi a ka wanda ranan da ta gansu taji kunya sosai ba kadan ba. Baba yace ai zumunci bai yake ba don Saadu bai yarda zumunci ya lalace ba a tsakanin mu idan ma ke da Amadu bakuje ba ai shi yatafi gurin mu kin ga ko dan shi mazo wanan gaisuwan tunda bai yar damu ba ya dauke mu da muhinmaci sosai a rayuwa. Mama kuma ta saka gwago a gaba tace yanzu n saboda son kai kika zabi wanan rayuwan a tsakanin kina ganin kin kyautawa kanki ne a hakan da kukayi. Kun cuci yar mutane badon Allah ya kawo mata mafita ba a rayuwa da anmanta da rayuwan wanan yarinyar a duniya. Da yake Allah bai barin bawan shi haka ya tabe sai ubagiji yayi mata dubaiya ya saka mata da miji yau itace ke rike damu da yan uwan ta baki daya duk ko da bakin cikin da ta fuskanta da farko a cikin mu bai sa yanzu da ta samu ta watsar damu ba ta jawo mu ta rungumay mu a jikin ta. Kuka gwago keyi sosai na nadama mama ta gagaya mata magana masu zafi tace kiyi kokarin ganin ta ki roketa gafara zai fi. Cikin ikon Allah na haifi dana lafiya asibiti don uncle yana gari a lokacin don haka a asibiti na haihu lafiya. Bai samu gani na ba sai da aka fito dani dakin hutu suka shigo dakin ina kwance shida yaya saadu da mommy dasu samira . Tunda mommy ta mika mai yaron ya rungumay shi a jikin shi bai yarda ya mikawa wani ba ya dade yanawa yaron addua. Ya dago kai yace yaya Saadu kaga baiwan da Allah ya karamin kaunaka taso ta min bakin ciki ga hakan da Allah ya azurtani a dan lokaci kankanni ? Murmushi yaya Saadu yayi yace yallabai ai mata hakkuri ta tuba murmushi yayi kawai ya mikawa yaya Saadu yaron. Sun dade a dakin ana muhawaran wa yaron yabiyo cikin ni da uncle mommy tace wanan duk fuska gidan su suke daukowa Abba zai koma watarana don da ubansu suke da kama sosai. An sallamay mu mun koma gida bayan dan wani lokaci sai dai ciwon kai da jiri da ke damu na akai akai wanda ya hanani walawa mun koma asibiti washe gari ba abinda likitan mu ya bani sai cewa yayi hutu jikina yake bukata kawai. Kaina yana rike da hannuna na dafe goshina da hannu daya yana tuka mota muka nufo gida magana yake min amma ban iya bashi amsa a lokacin. Har muka shigo gida ban tsaya ba na shige daki na kwanta maganin da aka rubuta min ya sayo na sha na samu barci mutane na shigowa amma ban sani ba. Sai bayan karfe hudu na falka daga barcin da nakeyi kewayawa nayi sai dai daga ban dakin sai da mommy ta kamoni na dawo daki. Uncle ta kira take fada mai abinda ke faruwa dani yace gashinan zuwa gidan dole ya baro aikin ya nufo gidan da sauri a ranshi yana fadin kardai yar mutane ta mutum dama abinda take gudu ke nan gashi kuma yana shirin faruwa da ita. Gudun da yakeyi ne yasa shi isowa gida da wuri dakina yayo derict ina mai da numfashi guda guda ina fadin mommy kaina kamar zai fashe min nake jin shi. Turo kofa yayi da sauri ya shigo dakin yana fadin Safiya har yanzu kan bai bari ba na dago idona da suka kade sukai min ja sosai gaban shi ne ya fadi yadda dan lokavin gadan na sauya nayi wani irin baki sosai. Gashi na ramay lokaci daya kamar bani ba rike min kan yayi yana addua yana yarfarwa gefe ya dago yana tambayan mommy ko naci abinci tace ban ci komai tashina ke nan na shiga bandaki acan na tashi faduwa sai da ta kamoni muka fito. Mommy hada mata tea mai kauri sosai ki kawo madarar ruwa da tomotor da gwagwanin maltina in fara bata da sauri mommy ta juya ta dauko abindaya lissafa mata ta shigo dasu take a wurin ya hada ya bani na sha. Ta kawo tea din nace mata na koshi ba zan iya sha ba suka matsa min nasha rabin cup din nayi getsa sai ga zufa na karyo min lokaci daya na koma na kwanta tare da lumshe idona. Ya dade a wurin tsaye ganin na samu barci yasa su fita su barni dakin ni daya mommy na goye da jiririn abayanta kallon mommy yayi yace ina ganin jinin da ta dan rasa ne a jikin ta yake haifar mata da ciwon kan haka. Mommy tace dama shine fargaban ta a kullun wallahi ko haihuwan Abba tayi ciwon kai sai dai bai kai haka din ba gaskiya. Yaron dake goye a bayan mommy ne yayi kuka ta sauke shi tana dan jijiga shi ajiyan zuciya ya sauke yace ina ganin kamar a kira gida gwago tazo ko khadija su taimaka maki don abin yayi maki yawa ke kadai haka. Tace don dai abin yazo da akasi ne amma ai bai da matsala don ga yan matan tana suna taimaka min da kula da Abba idan suna gida. Naji dadin kamun kan da yayi min don shi ya lafa min da ciwon kan da nake ji a baya sosai dana falka cikin dare ni da kai na nemi a bani abinci inci. Na dauka dare yayi a lokacin sosai ashe wajajen karfe tara na dare muke a lokacin don ganin su maimu da nayi basuyi barci ba na tambaya mummy ke fada min time. Ganin na tashi ne sukazo kusa dani suka zauna hindu na goye da jariri maimu kuma ta goya Abba. Ido na lumshe a hankali tare da tunanen yanzu duk yaran nan nawane gasu kamar tagwaye don ba wani tserayan kirki a tsakanin su tunda Abba ma bai wuce goyo ba. Uncle ne ya shigo dagin ya ganmu shiru sun tasani a gaba ba mai magana cikin mu duk da yawan rakafi su yau sun natsu sanadin rashin lafiyan da suka ganni ciki. Wuri ya samu ya zauna a kusa dani yana ce masu kune yan jiya naga kunyi cirko cirko a dakin mommy dake zuba min ruwa ina wanke hannu tace dashi ba dole ba. Sunga yar uwarsu a wani hali da basu saba ganin ta ba yace mommy ina ganin ba zan tsaya ayi suna ba zan fita da ita waje taje can ta samu hutu na dan wani lokaci. Tace Alhaji kadai yi hakkuri yaron ya karbi sunan shi a nan don kasan mutane akwai tsegumi in anyi suna sai ku tafi. Mommy ban damu da abinda mutane zasu fada ba kan haka lafiyan ta nake jawa kawai shine muradina, ina gudun kar abinda take gudu ya faru da ita don ta riga da ta nasa hakan gashi yana shirin faruwa da ita kuma. Haba dai Alhaji bai kamata kayi saurin saka wanan a zuciyar ka ba don Allah ne mai yin komai ga bawan shi dama dai tasan irin kalubalin da hakan ke haifarwa ne tun wuri. Kaida ayi fatan ta samu lafiya kanfin suna zaifi abar wanan maganan yanzu mu koma na neman lafiyanta kawai. Ajiyan zuciya ya sauke mai nuna gansuwa da maganar mommy shine amfanin zama kusa da maya din da akeso a hankali nace ya kara min adduan da yayi min dazun don naji dasin shi sosai daya min. Yaran mommy ta kada kan su zuwa waje dakin ya rage dagani sai shi a lokacin rugumay ni yayi zuwa jikin shi tare da dan shafa min baya yana fadin Allah ya baki lafiya matana ina jin da da halin in karbe ciwon nan a jikin ki. Murmushi nayi nace Uncle ai ciwo kaffara ne ga bawan shi da yardan Allah zan samu lafiya in koma daidai dama sun fada muna haihuwa akai akai yana haifar da irin matsalan a gare mu rashin daukan matakin da bayi bane bayan haihuwar Abba yasani saurin daukan ciki da wuri. Yace da rabon wanan yaron kuma yazo a wanan lokacin yasa muka manta da yin plaining a ziciyar mu sai dai yanzu dole a dauki mataki tunda na hango illar yin hakan yanzu. Kaina ya kama ya fara min adduan da yayi min da rana sai da ya gama yace ki kwanta ki huta kinji abinda likita ya fada muna hutu kike bukata da cin abinda zai gina maki jiki da sauri jinin da kika rasa ya dawo. Allah ya baki lafiya yace yana kokarin kwantar dani kamar karamar yarinya bakin ba don zaman dama ya isheni na koma na kwanta . Da safe da ya shigo yake fada ma mommy ya dage sunan sai sarin mai zuwa har na kara jin sauki zai dai yankawa yaro rago idan sunan yazo buki sai wani sati. Shi ida hali ma bukin ba sai anyi ba don in samu in huta a dakina baison azo a damay ni da hayaniya da yawa don taron suna hayaniyane kawai ba komai ba. Yadda ya fada hakane ya faru don samira da Aisha sun ta kiran mutane suna fada masu suna sai wani sati idan Allah ya kaimu za ayi. Sannu a hankali nake jin sauki har na dan bar jin ciwon kan sai dai yawan jiwa dake damuna idan na mike shima yana ragewa a hankali. Haka dai suna yazo lokacin na samu lafiya sai dai a tsatsaye nake har lokacin akai suna yaro ci sunan uncle din sulaiman. Na dauka zai min kara ya sa sunan nawa mahaifin sai naji yace wa mommy sunan yaro sulaiman nayiwa kaina takwara don kada a manta baya. Yan uwana da nashi sunzo akai buki suka koma gida don ba wani hayaniya tunda ba lafiya gare ni ba haka yasa ummi na zuwa ita da su mama da babanmu da mommy mahaifiyar Amina kawata da motan gidan su suka zo. Suna da kwana uku suka shigo garin da yamma da taimakon yaya Sani wanda yayo masu jagora. Ba mu san da zuwan su don haka suka shiri da yamma sai ganin su mukayi suna shigowa da sallaman su muna zaune falo a lokacin sisters dina suna min hira mummy kuma na bawa Abba abinci kafin yayi barci. Matan suka shigo baba sai baba ya tsaya a kofan gida bai shigoba a lokacin munyi mamakin ganin su sosai da tafiya haka babu sanarwa. Yaran najin ance da baba akazo yana waje nan suka fice da ihun su suna murnan ganin shi yace ho yan nema mutan abuja ke nan. Watau kuna nan kun shige birni kun manta da kowa ko dariya sukayi gaba daya sun sauya a idon shi sosai yaga sun kara mai girma sosai ba kamar yadda suka bar gida ba. Da murna muka tare su sai fadin lalai Safiya ba lafiya jiki duk ya zube haka a lokaci daya murmushi nayi ina fadin ai naji sauki mama yanzun gashi ina iya mikewa kai tsaye ban taba komai ba. Waya na dauka bayan mun gama gabatar masu da abinsha na kira uncle da bai dade da fita ba a lokacin ganin kirana yasa gaban shi faduwa sosai ya dauka cikin murya na yanayin mai ciwo nace su ummi na sun zo uncle har da baba. Nan Abuja suka zo ko ina nace nan suka zo uncle yanzu suka iso garin da sauri yace gani nan tafe na kashe wayan na dago kai na kalli mummyn su Amina nace. Mommy yaya hanya yaya wajen su Amina da yaranta tace suna lafiya naji tana fadin ai zats zo idan an kwana biyu tace yaya jikin naki yanzu ? Naji sauki sosai mommy yanzu tace amma dai kan kinji jiki wallahi duk kin zube haka kamar kin dade kina jinya. Mama tace yanzun kin ji sauki ke nan a haka gaskiya hankalin yan uwan ki ya kasa kwance sun koma suna fada muna ba dadi wallahi. Sai da uncle ya iso ya matsa ma baba su shigo da dan uwan mommy daya jawo mota da yaya sani matan suka mike suka bi mommy zuwa ciki. Har kasa muka zube muna gaida baba sai yaya jikin yake mun tare da jajantawa sun dade suna magana da uncle bai yarda yasha ko ruwa a gidan ba munyi munyi dashi yaki shan komai . Gab da magariba yaya Saadu ya iso suka fice tare baba na fadin gidan dan shi zai tafi sai gobe idan sun shigo. Mukai mai sallama ya tafi Allah ya taimake ni nura bata tafi ba a lokacin ta dora girki da sauri saboda bakin da tagani a gidan sun zo. Gaskiya ina jin dadin zama da ita don tasan ya kamata sosai koda nace mummy taje asan abinda za a ayi masu sai ta samu har ta kusa gamawa a lokacin . Ranan ban san irin farin cikin da nake ciki ba yau ummi ce da kanta a gidan aure na wani abu sai ciwo wallahi da ban san ranan zuwa mommy gidana ba. Muna dakina dasu tunda akayi sallah suka shigo dakin lokacin ina ciki na dan kwanta anan suka samay ni mommy ce tayo masu jagora zuwa dakin. A nan aka kawo masu abinci mama sai bin su maimu sukeyi da kallo wai yaran sun girma sosai yanzu.. Ranan dai kwanan farin ciki mukayi ga iyayye na a gidan uncle ya rasa ina zai saka su ya kwaso wanan ya sayo wanan yace a ba baki su ci. Da safe suka tashi da shirin haraman komawa don wai kwana daya zasuyi muna anan uncle ya dago da maki da na samay shi a daki ina fada mai shirin tafiya sukeyi. Take ya kira yaya Saadu yace mai yayi magana da baba ba zancen tafiya yau gare su sai gobe ko jibi idan an duba masu motar su. Dole badon baba ya so ba ya hakkuri suka kara kwana yaya Saadu yazo ya dauke su suka tafi gidan shi ya kaisu kuma gidan Aisha. Uncle ya shigo ya samay ni da rana yana fada min cewa ummi fa ba zata koma ba dasu don zata kwana muna biyu ina son muyi tafiyan nan da ita. Yaya Saadu nace yayi wa magana don nasan ko baba ya yarda ita tana iya kin yarda tace bata zama gidan suruki komawa zatayi gida. Hakan ko akayi shima baba bai so yarda ba da farko sai da yaya saadu yayi mai magana akan yara yake son a tafi da ita ya yarda. Ita ko da aikai mata magana kafewa tayi bazata zauna ba su mommy suka ke be da ita a idon mama suka ce kada tayi haka. Ko wace uwa tana fatan haka a wanan zamani Allah yayi mata baiwa don may zata guje ma haka dole bataso ba ta yarda ta zauna tana kallon washe gari suka kama hanya zuwa gida. Kwana biyar muka kara wani yammaci sai gashi ya shigo har dakina yace an gama komai a shirin tafiyan mu don haka ranan monday zamu tashi har da yara zamu tafi don zamu kwana biyu a can. Ban dauka har mommy su samira zamu tafi ba don ganin dawainiyar yayi yawa sai gashi da yaba pasphot na ga har da ita a tafiyan. ZAINAB IDRIS MAKAWA SEENABU 9/25/20, 5:46 AM - Ummi Tandama: BAHAGGON RAYUWA, , , , , 🧕🏿8️⃣9️⃣🧕 ZAINAB IDRIS MAKAWA SEENABU Mun sauka lafiya gidane da mai kyau irin ginan kasashen waje akwai da kuna sama da kasa da katon falo a cikin gidan. Komai akwai na rayuwa a gidan kwana daya mukayi a kaini asibiti kusan bayanin su daya da likitan da ya dubani a Nigeria sai dai su, sun bada maganin da zai yi saurin shawo min matsala ta. Sannu a hankali jikina ya fara dawowa normal har na fara dan kumatu a fuskana komai mai gina jiki da yananyin garin suka taimakamin wurin saurin cike wa da samun lafiya. Ga mama da mommy dake kula da yaran da ni kaina a can ma bai bar kanne na hakana ba sai da ya somo masu makaranta suna zuwa. Bai faye zama a guri daya ba ko yaushe yana wurin neman halak din shi zama wuri daya ya ishi ummi sai dai babu yadda zatayi ne kawai yasa tayi shiru. Daga ita har mommy sun canza jikin su yayi kyau sosai dan samun hutu da sukayi a can ga kula da muke samu daga wurin uncle . Baifi yayi kwana hudu ba ko biyar ya kama idan yazo har Nigeria yake zuwa ya dawo ya samay mu a nan dadi da daula mun samay shi a wurin uncle sosai watan mu takwas cur muka dunkulo maka dawo gida cike da abin arziki a tare damu. Tun baba na fada a dawo mai da matar shi har yasa ido ya daina tambaya yaushe zamu dawo ne wai. Niko banki muyi ta zama dasu haka ba har abada don ummi na kula min da yara sosai tana kuma basu tarbiyan daya dace a basu. Wani irin kiba nayi ga haske dana kara da wayewa a lokaci daya mun zo mun samu komai na gidan an sauya muna anyi gyare gyare an canza ma gidan fasali sosai. Saukan dare mukayi duk da haka su yaya Saadu sun zo taron mu da wasu ma, aikatan su gaba daya sai naga gidan ya sauya min gaba daya kamar ba gidan da muka bari ba a baya. Mun shiga gidan kowa na mamakin sauyawan gida don uncle bai taba fada min cewa ana gyaran gidan sai da muka dawo kawai na gani yayi surprise din mu ga hakan. Gaba daya komai ya sake dole muka tsaya a falo kafin yazo ya fada muna inda part din kowa yake mu shiga bayan ya gama sallaman mutane yace muyi hakkuri ya barmu a falo dakin su mommy ya fara nuna masu sai na su maimu kowa ya tashi da zumudi zuwa dakin sai lokacin ya nuna min part dina dake wani bangare nashi ma a dayan bangaren yake. Duniya tayi min dadi yanzu sosai har nakan manta cewa ina da cuta a jikina a baya saboda yadda nake jin jikina a lafiye. Ummi sati daya ta kara a tare damu muka kaita gida kwana biyu kawai nayi wanan karon na juyo ban samu tsayawa ba don zamu bauchi muga baaba da yan uwa. Yarana sun girma don ko karamin da mommy tasa mashi suna azahabi yana tafiya yanzu da kafan shi ko ina yayi saurin girma sosai don ba jikin Abba da mahaifin shi ya debo ba shima Abba din ya girma sosai dan har ya fara karatu a can . Ranan da muka dawo gida da yamma yaya Saadu yazo gidan yake fada min an bugo mai waya jikin gwago ya tsanan ta sosai don haka gobe zai tafi. Na jajanta mashi tare da fatan Allah ya bata lafiya yadan dade wurin uncle suna fira ya tafi don dare yayi a lokacin . Yaran ke rikice a gaban mu akan remote din tv nace wa Abba ya bar ma Azahabi kallo na uncle yayi cikin tsawa yace ma yaron ya kawo mashi remote din ya kora su zuwa dakin mommy wai suje ai masu shirin barci su kwanta dare yayi. Bayan sun wuce ne don suna matukar tsoron shi ta juyo gare ni dama nasan ba zai barni ba sai na samu rabona a gurin kan hukuncin da na yanke din ga yaran. Yace yanzu kinga kinyi wa Abba adalci ke nan a hakan shine babba fa ama kika ce karami ya rike remote din yanzu ne kike son sulaiman din fiye da Abba. Uncle ba hakana bane nace gani nayi shine ya fara dauka shiyasa nace ya bar mai kai ya girgiza min yace ina lura dake kin fison shi akan Abba din don kirikiri yanzu a gabana kuka zalunce shi. Nace cikin dago kaina ina kallon shi Zalunci uncle akan may zamu zalunce shi kuma wai ke baki san hakan da kike yi ba zalunci ne maimakon ki karbe duk a hannun su sai kice yabarwa kanin shi. Shiru nayi kada zancen yayi nisa a tsakanin mu ya mike yana fadin irin haka sai ya kawo raini a tsakanin su balle yana ganin ya cin mashi da girma yanzu uncle har wanan yasan wanj abu raini a yanzu. Yace a haka ake tasowa dashi ki taimake ni ki hada kan yayan nan don Allah kada ko bayan mu su samu matsala idan kan su yana hade babu wanda zai iya shiga tsakanin ko gaba. Nasan inda maganan shi ya nufa yadda ya taso da yan uwan shi ne baison hakan ya faru da diyan shi daki ya wuce ni kuma na mike na shiga dakin nasu don in ga kwanciyan su. Na samu mommy har ta shirya su ana rikici wurin kwanciya nace su kwanta su rike junan su sai suyi barcin a tare ba tare da sun rungumi mommy ba da suke ma fada. Kwana biyu muka shirya muka tafi bauchi ganin hajiya taji dadin wannan ziyaran don mun dade bamu zo gida ba irin haka. Banzo da kanne na badon makaranta da suke zuwa nan na barsu da mommy Abuja da yaran kawai nazo garin. Mun dan zaga wurin dagi da sauran yan uwa mun gai dasu muna bauchi kwana hudu da zuwa bauchi sai ga sakon daddy sun yi nutsu a cikin ruwa inda suke aiki. A ranan uncle da wasu yan uwa suka wuce lagas sun barmu hankali a tashe a gida sai zuwa safe muka samu labarin rashin dadddy din da akayi. Hankali ya tashi sosai dole uncle yace mu biyo jirgi mu dawo Abuja in gari ya waye mu nufi lagos din don har wasu sun tafi ko. Yadda yace haka mukayi hankali a tashe muka iso gida nike fadawa mommy abinda ke faruwa hankalinta ya tashi matuka da jin labari mara dadi daya dawo damu ba shiri. Mun isa Abuja washe gari har lokacin ba a kawo gawan shi gida ba suna abinsu na yan kaki da gawan . Mun shigo anty suna falo zaune gani na yasa ta sake wani kuka mai tsuma rai nima rungumay ta nayi ina kukan rashin da mukayi na daddy mutumin arziki. Sai yamma suka bada gawan su nan aka shirya masu bi harda mu don zamu dafa ma anty baya. Mun kwasa mun koma bauchi da gawan a jirgi guda da yan uwa isar mu da gawan ya tayar da hankalin yan uwa da abokan arziki. Zuwa safe aka kaishi gidan shi na gaskiya har rana ban samu ganin uncle ba mu zaune a dakin anty cikin tashin hankali don ni na zamay mata kamar yar uwarta na jini a wurin duk da ga yan uwan nata a kusa da ita. Shigowan yan uwan daddy maza a cikin su har da uncle sukayi gaisiwa tare da addua ga mamacin nan sukai dan bayani akan gobe zasu koma lagos dan ana son ganin su acan akan komai na daddy din. Suna fita nabi bayan shi dole ya dan tsaya min na iso kallo daya nayi mai naga a lokaci daya duk ya sauya min a idona uncle kako ci wani abu na iya fadi. Kai ya girgiza min yace yanzun dai nake son in karya magani fa nace dashi da sauri yace ban sha ba safiya ji nayi ina son in kebe dashi don ya samu ya karya yasha maganin shi kada ai biyu babu. Su hajiya baaba ma suna gidan don haka na karbi makulli a hannun ta na fito muka wuce gida a sai da na zuba mai abinci na dauko mai maganin mu na bashi. Yana zaune ya dafe kan shi a hankali na iso gare shi na zauna a gefen shi kuka yake yi nace uncle kayi hakkuri kowa yayi rashi amma ansan kai da anty akafi yi ma wanan rashin . Yace safiya daddy mutumin kirki ne ya tafi ya barni a lokacin da nafi bukatan shi a tare dani rugumay shi nayi don maganan kara mashi bakin ciki yakeyi. Sai da naga ya natsu sosai naji yace kinyi waya da mommy yaran na lafiya nace lafiya suke sai dai Abba ne tace yau ya tashi da mura ta bashi maganin shi. Gobe zamu tafi lagos kuma da madam zamu tafi ina ga gida zaki koma don yaran sai ke tsaya Abuja ya kamata ki huta yanzu jigilan yayi maki yawa hakana. Nace uncle ai kai keda jigila ga rashi ga ba hutu a tare da kai yace yaya za a yi dole nine zan bi komai nashi yanzu har komai ya daidaita. Hari aka kawo masu na bazata shine ya zama ajalinsu haka su goma sha bakwai suka rasu a lokacin . Allah dai ya jikan daddy nace yace amin yanzu ban san plain din madam ba nasan dai a can lagos din zata zauna saboda aikin ta ko kuma ta dawo arewa da aikin ina ganin zaifi mata sauki kusa da gida. Haka dai sukai ta jigilan akan alamuran daddy har komai ya kammala ya dawo gida bayan wasu watanni aka nenawa anty trasfer ta dawo Abuja da aiki tare da yaranta. Jikin gwago ya kiya baba yace a dawo da ita gida ayi na gargajiya a gani gashi basu jittuwa da Samira duk kokarin da take mata gwago bata gani sai zagi kawai ke shiga tsakanin su. Haka yasa hankalin yaya Saadu yafi kwantawa da akaita gida don yawan fitinan da ake samu da samira duk da kokarin samira din. An kaita gida ba afi wata biyu ba Allah ya amshi ranta muka je gida gaisuwa nan na samu zance aure yaya Sani ya tashi sai gina yake tayi inda zai saka matan shi. Don yace bai son zama ko kusa da gida don gudun samun matsala da inna duk da inna yanzun tayi laushi sosai da fitina har in nazo takan dauki su Abba tayi masu wanka da sauran su. Uncle yazo da ma, aikatasu sai dai basu kwana ba suka juya ranan mu sai da mukai kwana biyu muka dawo gwago ba karamin dukiya ta bari ba wa yayan ta. Yaya Saadu yace yabarwa kannen shi mata idan sun samu mazan aure ai masu aure dashi sadiya ta dawo da zama wurin yaya Saadu. Tare da mama da inna muka sauke farali inna ta saka hakora uku a bakin ta inda mama ta saka biyu sunyi dani in saka nace uncle yace baya so sai suka kyale ni. A wurin jefa inna ta tashi mutuwa da kyat muka cetota wanan abin ya kara tsorata inna duk inda na jefa kafana tana biye dani. Mu dawo lafiya saida suka kwana biyu a wurin mu suka wuce gida don ta Abuja suka tafi sai da muka dawo muka je gida bukin yaya Sani da yar wurin mai unguwar mu. Abubuwa da yawa suna faruwa inda girma kuma ke kara shiga uncle da nauyi na yan uwa da abokan arziki idan aka kwana biyu kuma ya debe mo zuwa waje mu huta. Bayan shekara hudu na sake haihuwa yar budurwa taci sunan hajiya baaba muna kiranta da baaba din sai na dakatar da haihuwan jikin kan dan motsa muna wani lokaci wani lokaci kuma sai ka gan mu kamar ba mu ba. Yanzu nasan cuta baya kashi sai kwana ya kare do ga daddy mai lafiya ya tafi ya barmu gwago na ta tafi ta barmu muna rayuwan mu a cikin salama. Yarana suna nan duk lafiyayun su basu da wata matsala a tare da su sun girma sun zama kyawawa dasu gwanin ban sha awa. Ina kula da yan uwana da yan uwan miji nice na zama jigo a gidan mu inda ake girmama ni kamar wata babba a cikin zurian mu komai za ayi sai da shawarana. Yanzu inna taba kai bori ya hau sai bi da lalami a tsakanin har in wani yaron ta yayi wani abin tana kawo min kara in yi mashi fada. Rayuwan mu sosai yaci gaba don uncle ya bunkasa sosai ni da anty mun dinke sosai dawowan ta Abuja mun zama kamar uwa daya da ita. Uncle ya dawo daga dubai bamu san da zuwan shi ba sai ganin shi mukayi ya sagalo jaket din shi a kafada Azahabi ya fara ganin shi . Lokacin ina zaune dasu a dining suna cin abincin safe daddy daya ce yasamu duban kofa da gudu yaran suka nufe shi ya rugumay su duka ukun a jikin shi sai da ya gama sun batan su ya dago yana kallo na ina tsaye na taso taron shi na harde hannaye na wuri guda. Yace madam Family yaya kuke nadan lumshe idona tare da yowa inda suke nima na rugumay su kit naji maimu ta dauke mu hoto daga inda take tsaye. Alhamdullahi nan na kawo karshen labari na bahaggon rayuwa wata rana baki wataran fari haka rayuwan bawa yake tafiya har lokacin da naba da labarina gare ku muna nan raye da yaran mu lafiya lau cutar jikin mu bai nakasa mu ba. Muna rayuwan mu normal kamar kowa ana bin mu kuma don baiwan arzikin mijina da muke ci tankar babu wani cuta a tare damu babu mai kyaman mu a cikin alumma komai daidai mukeyi da yan uwa. Nima mai rubuta labarin na kare da cewa cuta ba mutuwa bane sai kwanan bawa ya kare uban giji yasa mu cika da imani a tare da mu. Wanda na batawa ya yafe min don Allah. ZAINAB IDRIS MAKAWA SEENABU