*NAGA TAKAINA* *NA SADNAF*🌸🌸🌸🌸🌸 ®️ *_PURE MOMENT OF LIFE WRITERS_* _{We Don't just entertain nd educate we also touch the heat of readers P.M.L}💪🏻_ *Free Novel* *Tun kafin nayi nisa a rubutu nake da burin rubuta wanan labari Allah bai nufa ba sai yanzu labarin Nan ya faru a gaske tun 19's wahalar rubuta shi nake gani Sabida yanda xan na had'a present da past Amma a yanzu Allah ya nufa zanyi insha Allah zai na zuwar muku sau uku a sati idan na samu sarari ma zaku iya samun pages fiye da haka labarin Nan ya bambanta da sauran novels Dina na baya za'a ga abubuwa da za'a ga Anya dagaske zai faru kuwa ya faru dagaske zaka iya aikata Abu da baka d'aukeshi a bakin komai ba sai bayan shekara da shekaru sai abun ya dawo maka Allah ya tsare mu da tsarewarsa ya tsaremu da imanninsa Ameen* *Page 1* *1992* Da Sauri na shige d'akina na rufo k'ofa a lokacin da Umma ta hangoni ta biyoni a guje ko nauyin cikin dake jikina banji ba sabida tsabar tsoronta da nakeji. Jingina nayi da k'ofar d'akin Ina sauke numfashi Umma kuwa sai tura k'ofar take Tana auna min zagi iyayena da kasa ta Dade da rufe musu Ido da take ta Kiran sunansu Tana zaga yasa naji wani irin hawaye na zubomin Sanin na riga da na kulle k'ofar yasa naja k'afana na nufi Kan gadona Sabida kaina danaji Yana neman fad'owa sabida tsananin ciwo rabona da abinci har na manta lemon kwalba da bredi su kawai suka zama abincina a matsayina na Mai tsohon ciki nida gidana ban Isa na fita ba sai uwar mijina ta nada min duka bredin ma da lemo sai na fakaici Bata palon nake fita na siya kamar yanda yanzu na faki idonta na fita Ina dawowa ta gani ta biyoni a guje sabida kawai na fita siyan abinda zan sawa cikina. Dan cikina dake ta mutsu mutsu yasa na tuna da yunwar da nakeji na tashi na mik'e dak'yar na jawo ledar bredi da lemo Dana siyo na fara tusa bredin Ina hawaye Dan ko kad'an ba dadinsa nakeji ba ci kawai nake. Abban Zahira daya fad'omin a Raina yasa naji na k'asa ma had'iyar bredin bansan lokacin da kuka ya k'wacemin ba na fara magana a fili cikin tsananin kuka "Nasiru Mai nayi maka haka Dana cancanci haka daga wajen Kai da mahaifiyarka?laifine Dan na zab'eka a cikin dumbin masoyana na aureka ka raboni da dangina da kowa nawa ka kawoni wani garin kana wulakantani Mai nayi Dana cancanci haka daga wajenka"? Kukan dayaci k'arfina yasa na kasa cigaba da maganar da nake a fili na koma na kwanta sabida rawar da jikina keyi na cigaba da kukan da ya zame min jiki ko da ba'a min komai ba fuskata Bata rabo da hawaye sosai nake k'ewan yarana Amma uwar mijina ta hanani ganinsu Mahaifinsu kansa sai dai na jiyo muryarsa rabon Dana saka shi a idona wata hud'u kenan da sunan muna gida daya. Mahaifiyarsa ta zama tamkar itace matarsa Dan komai ita ke masa kwana ne kawai Bata yi a d'akinsa. "Mommy Mommy" Naji siririn muryar Zahira Tana tab'a k'ofata Zumbur na mik'e nayi hanyar k'ofa har Ina cin tuntub'e rabon dana ga ita da Nadiya har na manta Dan k'arfi da yaji Umma ta hanani ganinsu a d'akinta suke kwana ko d'akinsa da ta ga sun nufo d'akina zata daka musu tsawa tasa kanwar Nasiru Safiyya ta d'aukesu ta maidasu daki ta kulle tun yaran Ina jin suna kukan hanasu da akayi su zo wajena har suka zo suka Saba Idona ya rufe sosai da San ganin yarana hakane yasa ko kad'an ban tuna da wata Umma na palon ba Dan inajin tashin muryar ita da Safiyya da kanwar Safiyya Lami a palon suna Hira. Da Sauri na bud'e k'ofar banyi wata wata ba na d'aga ta Sama na rungume ta a jikina inajin wani irin Sanyi a zuciyata Wai ace Kai da danka karfi da yaji a nemi rabaku itama zahiran lamo tayi a jikina Tana sauke ajiyar zuciya ko damuwa banyi da yanda naji cikina ya dunkulle ba sabida yanda na Dora Zahira a jikina wuwurga Ido na fara yi ko zan hango Nadiya Amma Banga alamarta ba da Sauri na sauke Zahira na ruk'o hannayenta nace Mata "Ina Nadiya"? Cikin maganar Yara tace min "dazu Yaya ya rik'e hannunta suka fita Ni Kuma inasan ganinki Dana ga Umma Bata kallona shine na taho wajenki mommy Dan Allah zan kwana a dakinki Aunty Safiyya Tana yawan dukana ta mitsini na har da tsintsiyar kwakwa take Zane Ni" Zahira ta karasa fada tana Kara fad'awa jikina Rungumeta nayi kukan da nake d'annewa ya k'wacemin Wanda hakan ne ya jawo hankalin su Umma da kallo ya d'aukewa hankali kaina Wani irin Ashar Umma ta lailayo tayo wajenmu har zaninta na neman fad'uwa Kara rungume Zahira nayi a jikina ko kad'an banji tsoron yanda ta taho wajena gadan gadan ba Dan gani nake kamar Zahira na iya taremin dukan da zata kawo jikina Tana isowa ta fusge Zahira da k'arfi daga jikina ta wancakalar da ita daga Ni har Zahira ihu muka saka lokaci guda Dan Zahira ta Bugu Ina k'ok'arin mik'ewa Umma ta jawo hannuna ta murd'a Tana "Bana hanaki tab'a yaran Nan ba kin Raina Ni ko toh wlh Kika Kara tab'a yaran Nan sai na saka waya na zaneki babu ruwana da cikin jikinki shegiya Yar mayyu jikar mayyu gidan uban wa ma Kikaje dazu"? Duk maganar da take sheshek'a kawai nake Ina kallon hannun Zahira daya kumbura sabida bugawar da tayi ko kadan banji zafin yanda take murd'amin hannu ba Kamar numfashina zai d'auke na fara magana Ina "Umma idan Wani Abu nayi Miki Dan Allah Dan annabi kiyi hakuri ki yafemin Dan Allah ki daina azabtar Dani banida kowa sai Allah sai ku Dan Allah kiyi hakuri kibarni Naga yarana" "Kinci ubanki Naeema ba dai kin dage sai kin zauna da Nasiru ba azaba yanzu na fara gana miki nace miki bana sanki bana kaunarki tunda Kika Haifi wanan faratun Yar Taki nace ki tafi Kika k'i sabida maita kafin ma tayi shekara Kika Kara k'unsar wani cikin ke gaki kin Samu gidan arzkiki Zaki baje ki cike Mana gidan da Yaya itama Nadiyar ko shekara biyu batayi ba Kika Kara d'aukar wani cikin Zakici ubanki Dani kike magana wlh azabar da zan gana Miki a gidanan sai kin roki mutuwa da kanki Nasiru kuwa sai dai ki hangoshi daga nesa ya Miki nisa wanan tsinanan cikin jikin naki Kuma ki haifeshi nagani" Ta karasa Tana wancakalar da hannuna tare da juyawa ta fusgi hannun Zahira dake ta tsunduma ihu har lokacin tayi hanyar dakinsu da ita ta wurgata Kan katifa ta jawo k'ofar ta rufe. Ni kuwa kukan ma kasawa nayi na koma na zuci Ina kallonta ta dawo zauna ta cigaba da kallo ita da yaranta da duka suka girme min Dan banfi Sha takwas ba lokacin Dan inada shekara Sha hud'u Mukayi aure da Nasir shekara hud'u kenan da auren mu. "Ke Naeema zo ki wuce kiyi wanke wanke zan Dora Mana girkin dare kafin Yaya ya dawo" Safiyya tace Tana jefomin harara. Ban tashi ba sai da Umma ta juyo ta Kara zabga min wani mugun harara na mik'e jikina na rawa cikin dafa bango na Isa kitchen din na fara tattara lodin kayan wanke wanke Wanda wasu Dan keta ba amfani akayi dasu ba aka jibgashi wajen wanke wanke Dan kawai a bani wahala. A hankali na fara wanke wanken hawaye nata zubarmin har da majina ban damu duk na hanasu zubowar ba Dan gani nake zan samu sa'ida idan suka zubo zuciyata datamin nauyi zata ragemin nauyi Guntattakin abincin da suka rage na hada naci Dan banida abinda xan sawa cikina anjima bredin Kuma na gaji da ci Yanzu wajen sati kenan bana iya ba haya sabida Basir daya sakoni gaba. Bani na fito daga kitchen din ba sai da na musu jajjagen kayan Miya na Dora musu farar Shinkafa sanan Umma ta umarceni da na fito na koma d'akina Dan danta ya kusa dawowa Bata San yayi arba Dani zuciyarsa ta tashi. Ahaka na koma d'akina inajin duk gabobin jikina na min ciwo sallah ma kasawa nayi sai kwanciya kawai da nayi Ina tunanin shekara biyu da.suka wuce da nake rayuwa da mijina Naseer dake balain Sona kamar ya goyani da irin soyayyar daya shayar Dani daga Kan haihuwar Nadiya zuwa Kan cikin jikina Naga ya fara sauyamin tunda mahaifiyarsa ta dawo gidan da kannensa Akan tunda babansu Tijjani ya saketa Bata da gidan zama sai gidansa tunda shine babban danta d'akin daya Kamata ya zama mallakin su Zahira ta gaje d'akin da yayanta. Da tunanin da iyayena suna raye da kila duk Banga irin wanan rayuwar ba mahaifina da kowa ke shakka da Yana Raye da kila ya kwatomin yancina da kila ban Sha wanan wahalar ba sai dai Kash Allah baya barin wani Dan wani yaji dadi bansan lokacin da baccin wahala yayi awon gaba dani ba *Mafarki* Karar bud'e k'ofar d'akina ne yasa na bud'e idona da Sauri na mik'e na zauna Ina tunanin kila Umma ce na mata ba daidai ba tazo jibgata Ganin babu wanda ya shigo d'akin yasa na mik'e daga kwancen da nake Ina mamakin wanda ya turo k'ofar Ina k'ok'arin nufar kofar na rufe kawai Naga mahaifiyata ta shigo da farin lullubi har saman kanta fuskarta kawai ne a waje. Gwallo Ido nayi nace "Ummaaaa" Kallona kawai take batayi magana ba Ni kuwa na durk'ushe akan gwiwata na fashe da kuka Ina "Haba Umma meyesa Kika tafi Kika barni a lokacin da nake tsaka da bukatarki? Umma kinsan wahalar Dana ke Sha kuwa a gidanan Dan Allah karki Kara tafiya ki barni ki tafi Dani Dan Allah" Nace Ina Kara fashewa da kuka Har lokacin Bata ce da Ni komai ba in Banda kallona da takeyi Ni kuwa Ina ganin haka na mik'e da sauri Dan na d'auko mayafina Dan bazan Kara yarda ta tafi ta barni ba nagaji da zaman gidan Naseer da bashida bambanci da kurkuku gwara nabi mahaifiyata zanina dake Kan gado kawai na rarumo na juyo da Sauri Dan ko batamin magana ba wlh sai na bita sai dai Ina nufar kofar Naga Ina ta tafiya na kasa isa wajen da take a tsaye sai kallona take idonta itama kamar da hawaye har da Dan guduna Ina mik'a Mata hannu Amma sai Naga kamar nisa takemim Ina hangota daga nesa kuka na fashe dashi Ina "Umma Dan Allah karkimin haka ki tafi Dani wlh azaba nake Sha a gidanan Dan Allah Umma ki tafi Dani ko ki Kaine wajen yan uwanki ko na Abba Ihu nake sosai ina Kiran Sunan Umma da take tamin nisa Ina ta k'ok'arin tadota a haka naga ta zauna a dakalin dake tsakar gidan ta jawo buta naga ta fara alwala cak na tsayar da kukan da nake da naji muryarta Tana "Naeema bazan iya taimaka Miki ba Shawarar da zan baki shine ki daina Wasa da Sallah ki Kara kusanta kanki ga Allah ki Kai masa kukanki Yana sane dake Yana Kuma ganin duk abinda ke faruwa dake addu'a na iya canza komai ki dage da addu'a Naeema daga ni har mahaifinki ba zamu iya taimaka Miki da komai ba ki dage da addu'a Naeema ki tashi daga baccin nan kije kiyi sallah Naeema ki gayawa Allah komai Yana jinki Kuma zai kawo miki mafita ki tashi Naeema Umma ta fad'a da k'arfi tana cigaba da alwalar da take" A firgice na tashi daga baccin da nake duk nabi na had'a Gumi k'ofar na kalla Ina Umma tare da wuwurga idona a tsakiyar d'akin Dan gani nake kamar ba mafarki nayi ba kamar dagaske Naga Umma maganarta sai dawomin yake ni ba wani ilimi ba ballantana inyi addua iya fatiha kawai na iya shim wajen Naseer na koya dan Naseer nada ilimi sosai yayi sauka har sau biyu sai da mukayi aure yasan banida ilimin Arabi na bokon ma iya Aji biyu nayi aka cireni daga makaranta Ana ta zuga mahaifina idan nayi karatu zan zama 'yar iska hakane yasa daga na bokon har na islamiyyar banyi ba Sallar ma ba sosai nake maida Hankali nayi ba Kuma hakan bai wani dameni ba sabida bani kadai bace duk yan garinmu da saoi na kusan haka muke rayuwarmu. Mafarkin danayi da Umma ba karamin tsayamin yayi a Rai ba hakane yasa na mik'e da sauri na shiga bandaki nayi alwala na fito na fara Rama Salolin da banyi ba Dan sallar asuba kawai nayi a rashin ilimina gani nake shi ne ya zama Dole ayi sai Dana auri Naseer yake Dan nusar Dani nasan duk salolli biyar din wajibine sai Naseer na nan ma nakeyi cikakkiyar sallah Idan baya Nan kuwa ba kasafai nakeyin biyar d'in ba Naseer Yana Dab da kawo haske rayuwata mahaifiyarsa ta shigo rayuwarmu ya juyamin baya inasan ganin Mijina inasan muyi magana naji idan Wani Abu nayi masa na nemi yafiyarsa Amma mahaifiyarsa ta kafa ta tsare ta hanani ganinsa Ina daga Kan sallaya na cigaba da zubar da hawaye mafarkin da nayi da Umma ya tsayamin a Rai sosai Allah datace na kaiwa kukana na tuna na d'aga hannayena na fara gayawa Allah matsalolina Ina rokonsa ya kawomin agaji ta window labule d'akina nagane dare yayi duk da bansan ko karfe nawa ba a lokacin Haka kawai naji inasan ganin Naseer a yau d'inan ko ta halin k'ak'a abinda Umma kemin bai min ciwo kamar yanda Naseer ya shareni ya watsar Dani a kwandon shara ko da ba auren soyayya mukayi ba bai Kamata ya watsar Dani haka ba ballantana auren soyayya mukayi Yana Sona Ina Sansa mukayi aure hasali ma duk Wanda yasan mu yasan yafi Sona Amma bansan Mai ya canzamin shi haka ba har yasan akwai cikinsa a jikina ya manta Dani haka bayan duk alkawarin dayamin na zame min uwa da uba tunda iyayena suka mutu yayi alkawarin rik'eni da Amana sanin banida kowa sai Allah Yaya na daya tal danake bi ya tafi makaranta Sojoji har yau bamu Kara Jin labarinsa ba ballantana na saka Rai Yana Raye tun Kan iyayenmu su rasu ake nemansa banida kowa sai Allah sai Naseer Dan haka na taso iya iyayena kawai nasani ba wani wajen muke zuwa ba ballantana nasan danginmu haka ma ba Mai zuwar Mana lokacin banida wayo balle nayi tambayi mahaifina ko mahaifiyata danginsu. A hankali na mik'e daga Kan sallayar na nufi k'ofa na tsugunna Ina lek'a palon ta Ramin mukullin k'ofata ganin ba kowa a palon fitilun gidan ma a kashe yake yasa nasan dare yayi sosai Dan su Umma basa kwanciya da wuri sai wajen Sha biyu ko dayan dare suna kallo. Bud'e k'ofar nayi a hankali gabana na fad'uwa addua kawai nake Allah yasa Kar Umma ta kamani cikin sand'a na nufi d'akin Naseer dake can karshen palon gabana Banda fad'uwa babu abinda yake yi Ina zuwa Tsakiyar palon haske ya gauraye palon gabana yayi wani irin tsinkewa na tsaya cak jikina na rawa ko kad'an bansamu k'arfin gwiwar juyawa ba. "Shegiya tsinananiya Mayya wato ke Mai wayo ko? kina tunanin nayi bacci shine Zaki tafi d'akin Naseer sabida tsabar kwartuwa ce ke Ana dole ne Naeema wlh bazan Kara yarda ki rab'i Naseer ba asirin da iyayenki suka miki kike neman juyar min da Kan d'a na karya asirin lokaci nake jira kawai nayi maganinki Umma tace Tana juyo Dani a fusace. Da Sauri na runtse idona a lokacin da muka had'a ido da ita sabida yanda na tsorata da ganin ta Jan doguwar Riga ta saka har kasa ta rambada kwalli gata da manyan idanu hakan yasa na balain tsorata da ita kunnena data Kama da k'arfin tsiya yasa nayi saurin Kai hannuna na dafe hannayenta Dan kamar zata ciremin kunnen ko damuwa batayi da cikin jikina ba ta fara jana da karfi tayi hanyar d'akina sai da muka shiga d'akin ta sakarmin kunnen tare da rankwashina Tana "Wlh duk ranar da Kika Kara gingin zuwa d'akin Naseer sai na kusa kasheki a gidanan kinyi kad'an ki b'atamin aikina D'ana Yana da arzkiki bana San ya zauna da macen da zata Haifa masa ya ko d'a Sama da daya tunda Kika Haifi Zahira nace ki tafi Kika k'i tafiya ke alailai sai an zauna dake toh wlh tunda Kika min taurin Kai zakigane shayi ruwana idan ma tunaninki idan Kika Haifa masa Yaya Zaki samu lasisin zama dashine toh karyarki taci karya Dan ko na jikin Nan naki wlh baki Isa ki haifeshi ba sai kin tafi D'ana ya auro wata tsalelliyar itama taci rabonta ta tafi banasan in Kara ganin kafarki a waje kiyi zamanki a d'akin Nan duk ranar danaga kafarki a waje wlh sai na b'allaki banza shashasha" Umma tace Tana Kara dunguremin Kai tayi waje a fusace Tare da bugomin k'ofa Kuka na fashe dashi Ina Kiran ummana akan tazo ta taimakeni ta tafi Dani nagaji a daren ranar ko kadan bacci bai ga idona ba tunanin rayuwata kawai nake da ace nasan hanyar garinmu wlh da na gudu na koma garinmu gashi ba 'yan uwa ne Dani ba banida kawaye ba Wanda na sani ballantana na Gaya masa halin da nake ciki ya kawomin agaji. Naseer kuwa a lokacin daya dawo daga wajen aiki a Palo ya tarar da Umma dasu Safiyya sai Mai bi masa Tijjani da shima yayi rashe rashe a palo Yana Kai lomar abinci bakinsa sannu da zuwa suka masa ya amsa Ya tsugunna gaban mahaifiyarsa ya gaisheta tare da jawo hannun Zahira dayake Jin Santa daban a zuciyarsa wanda hakan nada Nasaba da balain kamar da take da mahaifiyarta rungumeta yayi a jikinsa Yana "Mamana kinci abinci"? "To da zamu barta da yunwa ne kake wani tambayarta taci abinci nifa bana San irin haka" Umma tace Tana banka masa harara sauke Zahira yayi ya sunkuyar da Kai Yana "Allah ya baki hakuri" Ya mik'e Yana satar kallon d'akin Naeema Yana Jin wani iri a zuciyarsa bai San Mai yasa idan zai tuna ta sai yaji kansa kamar ya rab'e gida biyu ba Yana balain kewarta a zuciyarsa Yana balain San ganinta Amma ya rasa Mai ke sa shi Jin wani irin nauyi da d'ad'aurewar jiki "Ka tafi d'aki kaje ka watsa ruwa kazo kaci abinci" Umma tace Tana Kara hararsa sabida yanda taga yana satar kallon d'akin Naeema. Su Safiyya da suka zubawa tv ido yabi da kallo Yana Jin wani irin Mugun Haushin rashin tarbiyya da basu dashi A tsawace yace musu "Kunyi Sallah kuka zauna Kuna kallo"? Da Sauri suka mik'e mahaifiyarsu kuaa tace "Ku koma ku zauna ku cigaba da kallonku sabida na tab'a yar gold yake neman hucewa akanku Banda iskanci irin na Naseer har yazo Yana tambayar 'yarsa taci abinci a gabana" "Umma wlh ba haka bane gani nayi Ana sallar isha suna zaune suna kallo shiyasa nayi musu magana" "Dalla rufemin baki bazasu tashin ba sai ka bugesu yanda ka Saba bugunsu akan wancan mayyar matar taka" "Allah ya baki hakuri" Naseer yace Yana Kara kallon su Safiyya da suka koma suka zauna har da Kara volume din tv shi kuwa ya wuce d'akinsa Yana Jin wani irin d'aci a makogaransa shi Kuma nashi jarrabtar kenan Mahaifiya bai San Mai yasa take masa haka ba har gida ya Kama Mata tak'i yarda ta dage sai ta zauna dashi da kannensa wajen su uku. Alwala ya daura ya fito ya tafi massallaci bashi ya dawo gidan ba sai wajen takwas da rabi har a lokacin suna zaune suna kallo. Ko sallamar da yayi ba Wanda ya amsa masa Inda sabo ya Saba hakane yasa ya kinkimi Zahira da ke bacci a kasan carpet ya Kai ta d'aki ya dawo ya d'auki Nadiya itama ya kwantar da ita a gefenta ya dawo palon ya zauna duk da ba yunwa yake ji ba bai isa yace ya koshi ba dan Umma fad'a zata rufeshi dashi kamar zata Kai masa duka. Yana zama umman ta mik'e ta nufi kitchen da kanta ta d'auko farantin data jera abincinsa a Kai ta ajiye masa yace mata ya gode. Yana bud'e abincin yaga baki bakin gari a kwance akan farar Shinkafa a hankali ya saka cokali ya fara jujjuyawa Yana mamakin abubuwan da yake yawan gani a abincin da umman ke bashi Amma bai isa ya tambaya Bismillah yayi ya fara cin abincin. Umma kuwa tayi Tsaki Tana zabga Mai harara taurin Kan Naseer din na balain Bata mamaki. Yana gama ci ya koma d'aki ya kwanta ya zubawa Zahira Ido Yana kallon ta tamkar itace Naeema sosai yake so ya tuno ta wani Abu na danne shi har karfe goma sha biyu na dare bacci yak'i zuwar masa hakane yasa ya d'aura alwala ya hau Kan sallaya ya tadda sallah Dan tun Yana shekara goma sha biyu ya sauke al qurani Mai girma Naseer nada ilimin addini sosai Wanda duk mahaifinsa Mallam Ibrahim ya gado Dan shahararren mallami ne Sosai har almajirai ne dashi da yawa har sai daya rasu. Har karfe biyu Yana Kan Sallaya a zaune Yana Jan carbi maganar da yake juyowa kasa kasa yasa ya mik'e a Hankali ya bud'e k'ofar d'akinsa ya fito a tsakiyar palon ya hango mahaifiyarsa sanye da jar doguwar Riga har kasa hannunta rik'e da kunnen Naeema. Sallati ya fara yi dayaji kansa ya balain Sara masa ya koma d'akinsa da Sauri ya zauna akan sallayar ya dafe kansa da hannu biyu Sabida nauyin da kansa ya masa. "Naseer ka dage da Addu'a mahaifiyarka Tana cikin kungiyoyi da yawa bansan wacece ita ba sai Dana aureta" Kalaman da mahaifinsa ke yawan Gaya masa kenan a lokacin da yake rayye. "Watarana zaka ganewa idonka watarana zaka San wacece ita Naseer mahaifiyarka Bata bacci daddare" Kansa ya Kara rik'ewa Gam a lokacin da yaji kansa ya Kara Sara masa daya tuno maganar mahaifinsa..... Share[6/26, 6:15 PM] Buhari Yusuf IBr: *NAGA TA KAINA* *NA SADNAF*🌸🌸 ®️ *_PURE MOMENT OF LIFE WRITERS_* _{We Don't just entertain nd educate we also touch the heat of readers P.M.L}💪🏻_ *Free Novel* *Page 2* *Naseer* Mahaifinsa Mallam Ibrahim Dan Asalin Kauyen Modobi ne dake jihar Kano fitattacen Mallami ne a kauyensu har daga wasu garuruwan Ana zuwa d'aukar karatu wajensa manomi ne Yana Kuma had'awa da kiwo tun Yana da shekara ashirin yayi aurensa na fari da wata hindatu a cikin shekara hud'u ya auri Mata hud'u bayan hindatu akwai Aisha akwai Fatsima sai Zinnira Zaman lafiya ake sosai a gidansa Dan matansa sun had'e kansu Mallam Ibrahim a tsaye yake sosai Akansu hindatu nada Yara biyar Aisha nada hudu Fatsima nada hudu itama sai Zinnira dake da biyu Duk yayan Mallam ibrahim suna da shekara goma sha Suke sauke Al Qurani Mai girma da littattafan addini ya tsaya musu sosai wajen inganta tarbiyyarsu ko kadan bai wani damu suyi Boko ba sai dai idan yaran sun girma akaran kansu wasu suka shiga na Boko wasu Kuma suka rungumi sanaar da mahaifinsu ya dorasu akai wato noma da kiwo a lokacin Mallam ibrahim Yana cikin masu kudin garin Dan Yana da shanaye da yawa gonakinsa ma bazasu kirgu ba Hakane yasa yaransa maza dukansu suke da sana'ar da sukeyi har da masu Dan fita zuwa birni Yaya matansa kuwa duk ya aurar dasu Dan suna shekara goma sha yake aurar dasu. A haka rayuwa take tafiya girma na zuwar wa Mallam Ibrahim da matansa Watarana hindatu uwargidansa ta kamu da rashin lafiya kwana biyu da fara rashin lafiyrta ta amsa Kiran mahallacinta Sosai Mallam Ibrahim yaji mutuwarta Inda aka ringa zuwar Mai gaisuwa ko ta ina dalibansa da duk sukayi karatu awajensa haka sukayi ta zuwa daga garuruwa daban daban suna Masa gaisuwa da suka ji labarin mutuwar a cikinsu Akwai wani Kabir da ya kasance dalibinsa Dan garin borno kasuwanci ne ya maidashi garin Calabar anan ya had'u da matarsa Sakeena ya Aureta yayansu Hud'u Sulaiman shine na fari sai Mai bi masa Hajara sai Hassan da Husaini duk a cikin yayansa. Hajara ta fita daban a cikinsu taurin Kai ne da ita da ruk'o gashi ko Yaya kayi Mata Abu ko bisa kuskure ne sai ta nemi hanyar da zata Rama ko mahaifiyarta da mahaifinta Bata barsu a baya ba indai suka yi Mata sai ta San hanyar da ta bi ta rama batare da sun sani ba wani irin bakin haline da ita Kabir da matarsa Sakeena har mamakinta suke a irin haka watarana aka aiketa ta Kai Nikan Massara a hanyar ta tafiya wani yaro ya tsokaneta ta zubar da nikan tabi shi a guje Dan baa Mata ta kyalle Sai data tayiwa yaron lilis ta dawo ta d'auko buhun ta koma gida tace wa Sakeena massarar ya zub'e ta ajiye Mata buhun a gabanta ta nufi d'akinta kamar batayi komai ba Sakeena kasa magana tayi Tabita da kallo Sulaiman kuwa dake palon a zaune ya mik'e a zuciye ya bita a baya ya hau ball da ita sai daya Mata lilis ya fito daga d'akin Dan yana Jin Haushin taurin Kan hajara. Yana fitowa daga d'akin itama ta fito a guje tayi waje Tana ranstuwa da sai ta rama. Abu kamar Wasa har Sha biyun dare Hajara Bata dawo gidan ba anan hankalinsu ya tashi suka hau nemanta Hajara kuwa Tana fita daga gida ta nausa cikin daji ta samu wani katon bishiya tayi zamanta a wajen Tana ta kuka alwashi kawai take akan sai ta Rama dukan da yayanta sulaiman yayi Mata har dare ya farayi Bata motsa daga wajen ba mugayen abubuwa kawai take ayyanawa a ranta tsabar rufewar da idonta yayi da San d'aukar fansa akan yayanta Bata San dare ya Yi ba wajen karfe Sha biyun dare ta fara Jin wani irin busa da tafiyar mutane sun kunna acibalbal sun Dodora Akansu sunyi layi suna ta tafiya sunyi daurin kirji da jajjayen yadi da tukunyar kasa a hannunsu dukansu Mata ne sunfi su Ashirin. Hajara kuwa Ido ta zuba musu ko kadan Bata tsorata da ganinsu ba Su kuwa mamakin ganin yarinya a gindin bishiya yasa shugabarsu tayi musu magana da idan sunje wajen bishiyar su tsaya haka kuwa akayi suna Isa wajen da Hajara take zaune suka zagayeta suna kallonta. Zubinsu bai saka ta tsoro ta ba illa mik'ewa ma da tayi ta kakk'ab'e rigarta ta fara k'ok'arin matsar da d'aya daga cikinsu tayi wucewarta. Shugabarsu kuwa dariya ta kyalkyale dashi ta jawo Hajara Tsakiyar su da karfinta ta wancakalar da ita Tana tambayarta wacece ita. Tsaki Hajara tayi ta Kara mik'ewa ta zabgawa shugabarsu harara Tana "Ina ruwanki Dani"? Mudubi shugabarsu ta ciro daga tukunyar kasar ta zuba masa Ido bayan yan sakanni ta dago ta kalli Hajara Tana "Kinaso ki dau fansa akan yayanki daya dakeki Sabida kin zubar da Massara"? Da Sauri Hajara ta gyada kanta ta matsa kusa da ita Tana "Inaso na dau fansa inaso nima na zaneshi kamar yanda ya zaneni" Dariya shugabarsu ta kwashe dashi tana "matso Nan kigani wanan shine"? Jiki na rawa Hajara ta matsa kusa da ita ta lek'a mudubin Tana lek'awa taga yayanta a tsaye da mahaifinsu a k'ofar gida suna ta dube dube almar dai ita suke nema. Da Sauri tace mata "eee shine yayan nawa" "Ungo Nan Rama dukan da yayi Miki" Hajara da Sauri ta karbi bulalan da shugabarsu ta mik'o Mata ta daddage da iya karfinta ta fara laftawa mudubin Sulaiman dake tsaye da Mallam Kabir kuwa ya hau zunduma ihu Yana burgima a kasa. Sai da bulalan duk ya karye Hajara ta jefar da bulalan Tana Jin wani irin farinciki na ratsata rungume matar tayi tana "Nagode Ina sanki" Wani irin dariya shugabarsu ta kwashe dashi tana "Nima Ina sanki shiyasa nake so ki zama daya daga cikinmu sabida ki ringa taka duk Wanda ya taka ki karbi ki shanye" Hajara da Sauri ta karbi kwaryar da ta mik'a Mata da Bata San ko menene a ciki ba ta kafa Kai ta shanye tas ta mik'a Mata tana "Yanzu kina nufin duk Wanda ya tab'ani zan iya dukansa ta irin mudubin nan"? "Sosai ma kuwa cire kayanki ki tsaya a tsakiyar mu " Da Sauri Hajara ta hau cire Kayanta cikin murna suka hau zagayeta suna Mata wani irin hayaki bayan sun saka Mata Jan yadi a jikinta A takaice a ranar Hajara sai karfe biyu ta koma gida fuskar ta a had'e Gidansu kuwa Sakeena da Mallam Kabir hankalinsu a balain tashe yake da suka ga Sulaiman na birgima jikinsa ya tatashi lokaci guda tuni Mallam Kabir ya hau totofa Masa adduoi Yana tunanin ko Aljannu ne suka shige shi. A lokacin da Hajara ta dawo kasa Mata magana sukayi gabadaya suka ringa binta da Ido Sabida yanda suka ga ta canza kamar ba ita ba Sakeena kuwa tsigar jikinta har wani tashi ya ringayi idan suka had'a ido. A takaice tundaga lokacin Hajara ta fara wasu irin Abubuwa daya dasawa Iyayenta tsoranta Sulaiman kuwa tunda ta zaneshi bai Kara samun cikakken lafiya ba . Duk dare mahaifiyarta idan ta shiga d'akin Hajara haka zata ga tayi d'aura kirji da Jan yadi Wanda hakan ke haddasa Mata tsoron Hajara sai ta fito daga d'akin da Sauri. Ahaka ta tari Mallam kabiru da zancen Hajara Akan kila ba ita kadai bace Hajara nada Aljannu. Tuni Mallam Kabir ya gasgata zarginsa akanta Inda ya bazama Nemo Mata magani a wajen mallaman addini Idan ya kawo Mata a gabansa zata zubar dashi bai Isa yyi magana ba hakane yasa ya shiga matsanacin damuwa ya fara tunanin hanyar da zai bi Dan ya raba Hajara da Aljannun dake jikinta a cikin irin wanan yanayin yaji labarin rasuwar Matar Mallam Ibrahim da yake ta San zuwa wajensa akan Maganar Hajara. Da Wanan damar daya samu yazo bayan anyi Sadakar Bakwai ya samu Mallam Ibrahim da zancen Hajara da Abubuwan da takeyi dake nuni tana da Aljannu Inda ya roki ya taimaka masa ya rabata dasu. Mallam Ibrahim kuwa ce Masa yayi yaje ya taho da ita zai rabata dasu insha Allahu. Hakan kuwa akayi bayan sati daya da komawarsa Calaba ya zo da Hajara wajen Mallam. Mallam Ibrahim da karfinsa ya dagewa Hajara da addu'a da manyan ayoyi Al Qurani Wai Nan duk so yake ya raba Hajara da Aljannun jikinta Nan kuwa bai San Shugabarsu d'auketa takeyi idan an fara rukiyyar ahaka yayi mata rubutun kwana bakwai Washegarin da suka cika sati yacewa Mallam Ibrahim zasu iya tafiya Yana kyautata zaton insha Allahu Hajara ta rabu da Aljannun. Mallam Ibrahim kuwa gefe yaja Mallam Ibrahim cikin sunkuyar da Kai ya nemi alfarmar da ya auri Hajara Dan a ganinsa in Yana tare da ita sai tafi samun lafiya. Mallam Ibrahim kuwa bai k'i tayin da Mallam Kabir yayi Masa ba a cikin Sati d'aya aka daura auren Hajara da Mallam Ibrahim washegarin da aka daura auren Mallam Kabir ya dauki hanyar Calaba cikin tsananin farinciki Yana tunanin auren mallam Ibrahim da Hajara shine zai saka Hajara ta samu lafiya. Hajara ko kadan Bata damu ba a lokacin da mahaifinta ya Gaya Mata ya aura Mata Mallam Ibrahim da zai iya jika da ita Dan tasan akwai abinda ta taka. Shi kuwa Mallam ibrahim ganin yarinya sabuwar jini yasa ya Dan fara rawar kafar zai angonce da yarinya lafiya Lau yayi mata kwana bakwai dinta cikin doki a ranar da zai bar d'akinta a ranar ya fara dasa zargi Akan hajaran tunda tazo gidan bai tab'a ganin ta kalli gabas ba gashi indai zasu kwanta sai ta daura Jan yadi. Kuma idan dai zaiyi adduar Daren daya Saba tashi take ta bar d'akin ta koma waje har sai ya Gama Hakane yasa washegari ya shirya zama a d'akin Dan ya gasgata zargin da yake Mata na ko da sauran Jinnu a jikinta. A ranar bai fita Waje karatu ba wajen karfe Takwas na safe ya kalli Hajaran da ke ta sharar bacci Sabida bata baccin dare. Ido ya zuba mata Yana ganin yanda ta rambada kwalli a goshinta da idonta. Matsalar Karfe Hud'u yake fita massallaci da asuba sai karfe shidda na safe yake dawowa gida hakane yasa baya sani ko tayi sallar Asuba ko batayi ba Azahar da sauran salllolin kuwa Yana k'ofar gida da dalibai da suke d'aukar karatu hakane yasa baya sanin tana sallah ko batayi. Hannu ya Kai ya fara bubbuga pillon data Dora kanta akai. Hajara ta bud'e idonta da suka kad'a sukayi ja Dan meeting suke a cikin baccin da take Mallam Ibrahim ya tasheta. Mallam Ibrahim da Sauri ya k'au da kansa a lokacin da suka had'a ido da ita. Hajara kuwa tace Masa "Mallam lafiya baka fita karatu ba yau"? "Kinyi Sallah Asuba kuwa? Cikin mamaki Hajara ta Masa wani irin kallo tana "Nayi Mana Mai yasa kake tambayata"? Mallam Ibrahim baice komai ba ya tashi daga Kan gadon a zuciyarsa Yana zargin har yanzu Hajara Tana da Jinnu a jikinta Alwala ya dauro ya dawo d'akin ya shimfida Sallaya ya d'auko Al Qurani ya bud'e Yana gyaran murya Hajara ta duro daga Kan gado da Sauri tana "Mallam yau Kuma karatun a daki zakayi"? Wani irin kallo ya Mata ita kuwa tayi waje da Sauri. Mallam kuwa ya girgiza Kai Yana gasgata zarginsa ya fara karanta Suratul Baqarah. Hajara k'in dawowa tayi d'akin ta fita zaure tayi Zamanta Sallamar da ake tayi da Mallam Ibrahim ne yasa akan Dole ya fita bayan ya shiga d'akin Fatsima da suka koma zaman d'aki tunda aka d'aura auren Hajara da Mallam Ibrahim Dan sosai suke ganin wani Abu a tattare da ita indai suka had'a ido sai gabansu ya fad'i sosai sukejin tsoranta hakane yasa duk suke zama a daki abinda ke fito dasu kawai girki ne da alwala Mallam Ibrahim kuwa bai tab'a lura ba Dan shi ba zama yake ba. Fatsima tsugunnawa tayi ta gaishe shi daya shigo shi kuwa yace Mata "aiki nake so kimin naso nayi aikin da kaina Amma Ana ta zuwa nemana Ido nakeso ki sawa yarinya Nan Hajara akwai zargin da nake akanta inaso kiga idan Tana sallah kinsan Ni ba zama nake ba ballantana nasan ko tanayi ko batayi har yanzu akwai wayanda ilimin addini bai je musu ba a zub'e kawai suke suna rayuwa" Fatsima kamar zatayi magana Kuma ta fasa Dan a cikinsu ba Wanda ya tab'a sa Abu tak'i yi Ko kallon Hajaran dake zaune a zauren baiyi ba ya fice Dan a yau zai rabata da bakaken Jinnun dake jikinta. Hajara kuwa Yana fita ta nufi d'akin Fatsima kanta tsaye ta bankad'a labulen d'akin Fatsima dake kwance akan Gado ta tashi zaune gabanta na balain fad'uwa da ganin Hajara a d'akinta Dan Bata tab'a shigo Mata ba. A haife dai ta haifi Hajara Dan zata iya cewa ma zata iya jika da ita. Wani irin kallo Hajara ta Mata tana "Wato kece munafikar gidanan kece Zaki sakamin Ido kenan toh sai Naga da bakin da Zaki Gaya masa nayi Sallah ko banyi ba. Daga nan Hajara ta juya ta bar d'akin. Fatsima kuwa ta hau sallati Tana adduar duk daya da yazo bakinta. Mallam Ibrahim bai shigo gidan ba sai karfe Tara na dare. Yana shiga gidan d'akin Fatsima ya shiga da Sallama. [6/26, 6:15 PM] Buhari Yusuf IBr: *NAGA TA KAINA* *NA SADNAF*🌸🌸 ®️ *_PURE MOMENT OF LIFE WRITERS_* _{We Don't just entertain nd educate we also touch the heat of readers P.M.L}💪🏻_ *Free Novel* *Page 3* Fatsima da kanta ke balain ciwo tunda Hajara ta shigo Mata daki ta tashi zaune dak'yar. Bata tab'a Jin tsoron mutum kamar yanda take Jin na Hajara ba ta tsorata da maganganun da Hajara tazo tayi mata dazun hakane yasa ko kad'an Bata samu nutsuwar saka Mata Ido ba "Ina aikin Dana saka ki" Fatsima murza hannu ta fara yi ta rasa ta Inda zata fara Masa bayani kamar ance ta dago ta kalli bakin kofa aikuwa ido biyu tayi da Hajara ta zubo Mata Ido" Inda Fatsima kuwa ta daka tsalle ta tsaya tana Shirin magana bakinta ya karkace. Sallati Mallam Ibrahim yayi ya ajiye jarkokin rubutun da ya shigo dasu yayi Kan Fatsima dake ta zabure zabure. Sosai hankalin Mallam Ibrahim ya tashi a ranar yayi ta totofawa Fatsima adduoi Dan gani yake kamar itama gamo tayi abinda ya d'aukewa Mallam Ibrahim hankali daga Kan Hajara kenan. A takaice tundaga ranar Hajara ta ringa hargitsa gidan cikin sirri batare da an ganota ba Dan dai kawai Kar Mallam Ibrahim ya samu nutsuwar tunkararta da Sunan rukiyya. Nan kuwa Mallam ibrahim tuni ya gane Hajara ba Jinnu ke damunta ba ba dai San a wane matsayi zai ajiyeta ba Mayya ce ko matsafiya addua kawai yakewa kansa da sauran iyalinsa da duk sai da Hajara ta tab'asu. Duk abinda yayi na addua Dan ya kawo karshen abinda Hajara yak'i tasiri akanta Dan yanzu Bata ma Abunta a boye a Sha biyu nayi zata zura jajjayen Kaya tayi ta abubuwanta Zuwa lokacin an fara gane wacce Mallam Ibrahim ya aurowa kansa. Waazi da nasiha ba Wanda Mallam baiyi wa Hajara ba Amma duk a banza. Ana saura sati biyu tayi shekara a gidan ta haifo santalelen danta Mai Kama da Mallam Ibrahim sak. Mallam Ibrahim na d'aga bakin kofa ta haihu Ana yanke masa cibi Yasa aka mik'o Masa shi ya kafa bakinsa a kunnen jariri ya masa huduba ya lullubeshi ya bar gidan da jaririn Dan ya Sha alwashin Hajara bazata ga kalar jaririn ba ballantana ta shayar dashi. Tunda yaganta da ciki ya Samu wani amininsa Mallam Hassan dake Jos da sukayi makaranta tare ya zayyana Masa komai Dan har yafi Mallam Ibrahim din ilimi hakane yasa Mallam Hassan yace Masa tana haihuwa ya kawo masa jaririn. Ruwan zam zam yayi ta bawa jaririn har suka Isa garin Jos Da isarsa Matar Mallam Hassan ta karbi jaririn tayi Masa wanka a cikin matan Mallam Hassan d'in akwai Mai shayarwa aka bata Jaririn ta shayar dashi. A takaice Kwanan Mallam Ibrahim uku a Jos ya dawo bayan ya bar amanar Jaririn daya sawa suna Naseer a hannun amininsa da yake hazikin mallami ya Kuma ce Masa duk tsafin Hajara Bata isa ta gano Inda Naseer yake ba hankalinsa kwance a dawo gida. Inda dawowar da yayi yazo ya tada tashin hankali Dan Hajara haukace musu tayi a gida Akan sai an fito Mata da jaririnta Inda tayi ta azabtar da matan gidan akan su fito Mata da jairirnta ko ta kashe su. Ahaka ta rik'ewa Zinnira da kafa Fatsima kuwa har lokacin bakinta a karkace yake Aisha kuwa ta Mata turen Aljannu Mallam na dawowa gidan taci kwalar rigarsa akan ya bata danta shi kuwa yace Mata ita da ganin danta sai dai a lahira domin dansa Jinin musulunci ke yawo a jikinsa. A takaice sosai Hajara ta hargitsa gidan yan kungiyar ta suka ringa tayata Sai da Mallam Ibrahim ya dage da Addu'a sosai a ranar da yaga abin yaci tura ya yanke igiyar auren dake tsakaninsu. A takaice silar rabuwar Mallam da Hajara kenan. Inda rabuwar ma da yayi da ita ya Kara haddasa wani tashin hankalin duka iyalinsa sai data sako su a gaba har Fatsima ta Kai ga rasa ranta. Hajara sosai ta dage Masa akan idan Yana San ta bar rayuwarsa gabadaya ya bata danta Dan har yan kungiyar su sun kasa gano Inda Mallam ya boye Naseer. Mallam Ibrahim kuwa tuni ya daina bacci ya dage da Addu'a da Saukar Qurani kafin ya d'an Samu Hajara ta rabu dashi duk da hakan Bata fasa zuwa tambayarsa danta ba. Koda lokacin da suka rabu da Mallam ibrahim data koma Calaba ta tarar da Sulaiman ya rasu Mahaifiyarta ma haka Dan lokacin ba waya ballantana taji labari Bata wani damu ba Mahaifinta da Hassan da Husaini ne kawai sukayi bakin cikin mutuwar Aurenta tunda Mahaifiyarta ta rasu Mahaifinta bai cika lafiya sosai ba. Ita kuwa Hajara baje kolinta kawai take cikin shekara Biyu manema sukayi Mata caaa dayake tana da kyanta ba laifi a wanan lokacin. A cikin manemanta ta zabi wani Tijjani Cikin wata uku sukayi aure lokacin da matansa guda biyu. Ko wata uku batayi a gidan ba tasa duk ya saki matansa ta ringa ganawa yayansa azaba Tijjani nagani babu yanda zaiyi Dan bashida bambanci da danta Sabida ta riga da ta Mallakeshi sai yanda tayi dashi. A cikin shekara Shidda ta Haifa masa Yara Uku Danta na fari yaci Sunan Mahaifinsa Tijjani sai Mai bi masa Safiyya Sai Lami har a lokacin ita da yan kungiyarta suna iya kokarinsu wajen ganin sun gano Inda Mallam Ibrahim ya Kai Mata danta Amma Ina abin yaci tura sun kasa gano Inda Mallam din ya kaishi wanan kenan. B'angaren Naseer kuwa sosai ya karantu ya ilimantu ya tarbiyyantu a hannun Mallam Hassan ya samu ilimin Arabic da Boko daidai gwargwado Mallam Ibrahim na zuwa ganinsa akai akai Dan duk cikin yayansa yafi Jin Naseer a Ransa ya Kuma fi tausaya Masa sabida halin mahaifiyarsa har Misra Mallam Ibrahim ya tura shi ya Karo karatu Sabida Yana so Naseer yayi ilimi Mai zurfi da zai iya na Kare kansa daga sharrin masu sharri duk cikin yayansa babu Mai balain hakurin Naseer ga k'ok'ari Yana da shekara Ashirin ya fara kasuwanci Dan ba laifi Naseer nada zafin nema cikin kankanin lokaci at Age of 23 ya zama successful bussines man duk abinda ya juya sai Allah ya saka Masa albarka. Har a lokacin Yana wajen Mallam Hassan jefi jefi yake zuwa Modobi wajen mahaifinsa ya Sha tambayarsa game da mahaifiyarsa sai Mallam Ibrahim yace yayi hakuri ya bashi lokaci zai bashi labari wanan kenan. Naeema Mahaifinta Lawan yaren Ribina ne dake Kauyen Toro dake jihar Bauchi Shida matarsa Aminat Auren Zumunci akayi musu Mahaifin Naeema maharbi ne Kuma Yana had'awa da noma kyakyawa ne kamar Fulani gasu da gashi har gadon Baya Lawan karfaffan mutum ne Mai balain Zuciya ya tsani raini da wulakanci shiyasa bai fiye huld'a da kowa ba iyalinsa kawai ya sani sai mak'otansa matarsa Aminat Mahaifinta da mahaifinsa uwar su daya ubansu daya wuta ce ta Kama bukkarsu daddare sukayi gobara Inda iyayensu duk suka rasa ransu Lawan da Aminat ne kawai Allah ya tseratar hakane yasa awancan lokacin rukon Amina ya koma hannun Mai gari har ta Isa Aure ya aura Mata Lawan da tun mutuwar iyayensu yake Fadi tashi. Tunda sukayi aure Amina inta samu ciki sai ya zub'e idan kuwa ta haifeshi sai yazo babu Rai ahaka sukayi shekara Goma da aure kafin Allah ya tsayar musu ta haifi Namiji da suka sawa suna Aliyu bayan shekara hud'u ta Kara haifar 'ya mace Inda aka saka Mata Naeema. Naeema kyakyawa ce sosai Dan tun tana jaririya take da balain farin jini Sabida kyanta rububin zuwa daukarta sai zata sha no-no ake dawo da ita da kuwa aka yaye ta idan makota suka d'auketa sai dare suke dawo da ita. Daga Lawan Har Aminat din ba wani ilimi sukayi ba a wancan lokacin balle su saka yaransu masu karatu ma a wanan lokacin sai yan wajen gari haka. Aliyu ba inda ya baro mahaifinsa a wajen k'arfi da Zuciya hakane yasa Mai unguwa ya shawarci Lawan ya saka Aliyu a makarantar Sojoji da Lawan k'i yayi dak'yar aka samu aka shawo kansa ya amince. Few mutane lokacin suna Dan zuwa karatun allo a lokacin hakane yasa Aminat ta yiwa Lawan Magana ko zaa saka Naeema da take da shekara goma a lokacin bai k'i ba Naeema ta fara zuwa sai dai tana fara zuwa Samari sukayi ca akanta Dan Naeema nada tsayi sosai hakane yasa wasu suke ganin girmanta sosai ga kyaunta daya fita Dan tana da Dan girman jiki she so innocent and Calm Dan haka ma Mahaifiyarta take. Ko wata uku batayi da fara zuwa makarantar ba Lawan ya cireta dayaga yanda maza ke bi masa ya har gida Inda tuni ya koma Yi Mata kulle. Tana da shekara Sha uku Lawan ya fara barinta kula Samari a wancan lokacin Dan 13 ko 14 anyiwa yarinya aure a wancan lokacin idan Kika Kai 15 16 haka zaayi ta kanannun maganganu kin tsufa bakiyi aure ba. One faithful day Naseer ya Kai kayan daya Saro garin Bauchi cikin kwana uku ya Gama abinda ya Kai shi a ranar da zai tafi wani abokinsa mustapha ya nemi ya raka shi kauyen dasu Naeema suke zai Kai Sako ahaka kaddarar Had'uwar Naeema da Naseer ya kasance. Naseer dake Shirin barin garin Bauchi sai gashi ya fasa komawa a ranar Dan ba karamin kamuwa yayi da San Naeema da itama ruwa taje dib'a suka had'u dashi a hanya Bata wani kula shi ba Amma fuskarsa na Nan daram a kwakwalwarta. Dayake ba wani fita take ba hakane yasa Naseer bai Kara samun ganinta ba da aka kwana biyu. Lawan kuwa sosai ya damu da rashin ganin Aliyu da aka ce Masa Zai na zuwa ganin gida duk karshen wata hakane yasa yaje wajen Mai unguwa Akan yaji ko lafiya Dan shi ya had'asu da mutumin daya tafi da Aliyu a lokacin Mai Unguwa ya d'auko letter da aka kawo masa daga birni dayake ba dukansu ne sukayi Boko ba basu San Mai wasikar ya k'unsa ba sai da aka Nemo Wanda ya d'an iya karatun a wasikar ake bayanin baa ga Aliyu ba sun b'ata shi da wasu dalibai da sukaje. Hankalin Lawan Dana Amina ba karamin tashi yayi ba sosai aka hau neman Aliyu cikin samu ganinsa ba addua kawai suke akan Allah ya bayyana musu shi rashin Aliyu yasa Amina ta Dan fara rashin lafiya a cikin irin wanan Halin Naseer yaje neman Auren Naeema da kansa a wajen Lawan Inda farkon ganin da Lawan yayiwa Naseer yaji Naseer din bai kwanta Masa kamar yanda wani abdullahi yafi kwanta Masa a maneman Naeema ba Dan har a zuciyarsa yafi San Abdullahi ahaka iya shi ya yarjewa Naeema take kulawa sabida yabawa da yayi da hankalinsa Dan Naeema nada manema da yawa daga Samari zuwa manyan masu kudin sai dai ya lura kamar Naeema tafi San Naseer Kuma baya San yayi Mata dole. A takaice ahaka Mallam Hassan yazo ya nemawa Naseer auren Naeema bisa jagorancin Mallam Ibrahim daya sakarwa Mallam Hassan ragamar komai. Cikin mutunci akayi komai bayan Lawan ya danyi bincike akan Naseer da a garin Jos yayi binciken nasa bai San suwaye asalin iyayen Naseer ba. Naeema kuwa kawayenta sai tayata murna suke da samun miji kamar Naseer Dan Naseer San da yake yiwa Naeema baya b'uya. Wata uku aka saka bikinsu. Inda matan Mallam Hassan su suka Dan had'a Masa lefe aka Kai lokaci kawai ake jira. Naseer kuwa tuni ya Gina katafaren gidansa a garin Jos. B'angaren Hajara kuwa haikan ita da yan kungiyarta suke neman Inda Mallam Ibrahim yaje ya b'oye Naseer Dan har lokacin Hajara na zuwar wa Mallam Ibrahim akai akai akan a nuna Mata Inda danta yake. A cikin irin wanan lokacin Ana saura wata daya auren Naseer da Naeema . Naseer da Mallam Hassan suka tafi Modobi wajen Mallam ibrahim. Dan shima Mallam Hassan akwai wani kanin mahaifinsa dake garin Modobin dayake San duba jikinsa. Suna zuwa aka musu tarb'a Mai kyau Mallam Ibrahim sai murmushi yake Yana bin Naseer da kallo a Ransa Yana tunanin a yau zai Dan bashi labarin Mahaifiyarsa Amma bazai Gaya Mata wacece ita ba. Zai dai bashi wasu adduoi ya ringayi na kariya daga sharri duk da Yana tunanin duk hatsabi bancin uwa bazata tab'a danta ba. Wajen karfe hud'u suna zaune gabadayansu a k'ofar gida har da yayyen Naseer da ke zuwa wajen mahaifinsu haka da yamma duk da ba uwa d'aya ce ta haifesu ba suna da balain had'in kai. Cikinsu kuwa har da Mallam Hassan Kamar wacce aka jefota haka suka ga Hajara a gabansu. Dan shugabarsu ce tagano Naseer ta mudubi shi da Mallam Hassan hakane yasa tayi saurin gayawa Hajara shine ta bayyana gabansu afujajan. Mallam Ibrahim Sallati ya saki a lokacin da ya ganta ya hau addua a Ransa. Mallam Hassan shima Yana ganinta yasan itace duk da bai taba ganinta ba. Hajara kuwa Naseer kawai ta zubawa Ido tana kallonsa tamkar yanda yake kallonta yanajin wani iri a jikinsa Hajara kuwa da Sauri ta dauke idonta daga kansa data ga katon tabon Sallah Goshin Naseer nata shigar Mata Ido haka kawai taga kamar kallonsa na neman haddasa Mata ciwon Kai. Ranar wanka ba a boye cibi inji Mallam ibrahim "wanan itace mahaifiyarka Naseeer" Naseer mik'ewa yayi da Sauri ya Isa gabanta ya tsugunna har kasa ya fara gaisheta Hajara kuwa kamar ta Kama da wuta sabida tsananin bakincikin ilimin addinin data ga ya ratsa Mata d'a Dan har ga Allah hakan na iya zame Mata barazana. A takaice a ranar Hajara ta kebbe da Naseer tana Masa masifa bai tab'a nemanta ba hakuri kawai yake Bata Yana shima bai San dalilin daya sa Mahaifinsa yak'i Basa labari game da ita share maganar tayi ya hau Masa fadan da yanzu basu had'u ba sai dai yayi aure batare da sanin ta ba. Anan mmaki ya rufe Naseer Dan yasan bai mata zance aurensa ba Kuma tunda tazo bai ga ta kebb'e da wani ba ballantana yace anan taji labari. Hakuri kawai ya bata Ita kuwa tayi murmushi tana "Ai matar da zaka aura kyakyawa ce ba laifinsa" Kara dagowa yayi cikin mamaki Yana "Kinsanta ne"? "Sosai ma nasanta dazu duk naji labarinta da zuwanka gurin mahaifinka Kai yanzu dai kafisan mahaifinka akaina ko shiyasa baka tab'a nemana ba Dan haka yanzu gobe zanzo na d'aukeka muje gidana ka Kuma ga 'yan uwanka" "Murmushi Naseer yayi Bai ce komai ba Yana Dan Jin wani iri a jikinsa kasancewarsu waje daya data zo tafiya kuwa sai data bi Mallam Hassan da wani irin kallo tayi kwafa tayi tafiyarta. Bayan sallar isha Mallam Ibrahim ya d'an fara yiwa Naseer hannunka Mai sand'a da Naseer ya bashi labarin Hajara zata zo gobe su tafi yaga gidan da take zaune. "Naseer ka dage da Addu'a mahaifiyarka Tana cikin kungiyoyi da yawa nima bansan wacece ita ba sai Dana aureta zama Bai Kama ka ba Dan kaima baka wuce ta sako ka a gaba ba Dan su ba basu San Allah bama balle suji tsoron sa a zuciyarsu basu San Mai tausayi ba ballantana suyi Imani" Watarana zaka ganewa idonka watarana zaka San wacece mahaifiyarka tun sanin Dana Mata Bata baccin dare bansan a wane matsayi zan sakata ba Mayya ce ko matsafiya Allah kadai ya barwa kansa sani Allah kadai ke kareni sanin wacece ita yasa na dauke ka tun kana jariri na kaiwa aminina Sabida ya kularmin da Kai Ina tausayinka Naseer a cikin yarana kafi kowa hakuri Kaine Kuma bakayi dacen uwa ba tun a yanzu ka dage da Addu'a Naseer. A takaice ire iren kalmomin Nan ya koma Yiwa Naseer da Naseer ya haddace Gam a kansa Amma a akaran kansa ji yayi ya kasa gasgasta zancen mahaifiinsa a wajensa mayyu apperance dinsu daban yake Dana mutane Amma zai dage da Addu'a kamar yanda mahaifiyansa ya bashi shawara.... Share dis page is fiction gaskiya Dan wacce ta bada labari Bata San ya mahaifiyarsa ta zama matsafiyya ko Mayya ba but tunda novel ne hakane yasa zamu Nemo yanda ta zama mayyar Next page zamu tsunduma cikin labarin gdan gadan insha Allah ur comments give me strength d more u comment d more na samu kwarin gwiwa tnk u [6/26, 6:15 PM] Buhari Yusuf IBr: *NAGA TA KAINA* *NA SADNAF*🌸🌸 ®️ *_PURE MOMENT OF LIFE WRITERS_* _{We Don't just entertain nd educate we also touch the heat of readers P.M.L}💪🏻_ *Free Novel* *Page 4* Washegari Naseer suka d'au hanyar Calabar shi da Hajara da a fad'arta tazo ne Dama Wajen wani kawunta a modobi taji labarin zuwansa. Kwana biyu Naeeer yayi a Calabar a cikin kwana biyun da yayi ya ga abubuwan mamaki da Al ajabi daya d'aure Masa Kai ya Kuma kasa tunkarar Hajara da tambayar daya dank'are Masa a zuciya. Farko suna Isa gidan ya tarar da kannensa Tijjani Wanda yake da shekara Ashirin a lokacin Sai Safiyya da take da Sha bakwai sai Lami da take da Sha uku a palon gidan a zaune Hajara batayi Sallama ba da suka gidan hakane yasa shi Kuma yayi Sallama ga mamakinsa babu Wanda ya amsa mishi sallamar da zaiyi magana sai ya fasa Hajara kuwa cikin washe baki tace musu ga yayansu Nan da take basu labarinsa kadaran kadahan suka gaishe shi shi ma ya amsa musu Yana Dan karewa palon da aka rataya wasu irin Abubuwa a kowane kusurwar palon har da su Kaho haka. Muryar Hajara dake kwallawa Tijjani Kira yasa ya maida hankalinsa kanta har Yana mamakin ya za'ayi ga Tijjani a gabanta Kuma ta ringa kwalla Masa Kira haka. Da Sauri yaga wani datijjo ya fito daga wani daki dake Gefen palon kallo daya zaka mishi kasan Yana balain Shan wuya har wani irin furfura ne suka yayame fuskarsa. Yana isowa gaban Hajara ya zub'e Yana Mata sannu da zuwa. Naseer kuwa tsananin mamaki yasa ya saki baki Yana kallon ikon Allah. Hajara kuwa Bata amsa gaisuwar da yake Mata ba tace "Naseer ga Babansu Tijjani Nan ku gaisa" Da Sauri babansu Tijjani ya isa wajen Naseer yana neman durk'usa Masa. Naseer kuwa ya mik'e cikin tashin hankali da Alajabi ya taro shi ya kalli Hajaran Yana "kina nufin Wanan shine Mahaifinsu Safiyya ma'ana mijin da Kika Aura da kuka rabu da Abbana"? Hajara d'auke idonta tayi daga kansa ta watsawa Tijjanin wani irin kallo. Shi kuwa jiki na rawa yayi waje da Sauri har Yana tuntub'e Yana zuwa Dab da kofa tace Masa ya shiga kitchen ya tuka musu tuwon Massara da miya. Da Sauri ya gyada Mata Kai ya fice yana sharar hawaye. Tunda ya Auri Hajara yasan ya aurowa kansa balai bashida ilimin addini da zai Kare kansa daga Sharrinta baya iya ketara umarnin ta Yana ji Yana gani ya rabu da matansa biyu Yana ji Yana gani ta watse Masa Yaya suka shiga duniya Banda biyu da suka rasu da yake zargin itace ajalinsu ya Riga da yasan wacce ya aura ya Sha yunk'urin guduwa tana kamoshi sosai suka d'aure shi da tsark'a har addua yake mutuwa ta d'aukeshi da irin rayuwar da yakeyi da ita. Naseer kuwa bayansa yabi da kallo har ya fice ya dawo da kallonsa Kan Hajara data balain had'e Rai hakane yasa ya kasa Maganar dayake da niyyar Yi ya koma ya zauna tunani barkatai na zuwar Mishi "Abba bazai min karya ba duk da ban tashi nasan wacece mahaifiyata ba ni akaran kaina nasan itace mahaifiyata Amma wane irin Abubuwa nake gani haka ta yaya Mahaifina da yake Shahararren mallami zai auri wacce ake zargin matsafiyya ce ko Mayya Astagafurullah Mahaifiyata ba Mayya bace ba matsafiyya bace insha Allahu Ina dai tunanin tana da fad'a. Naseer duk ke maganar a zuciyarsa. "Karka manta Naseer Allah Kan fitar da matacce a cikin Rayyaye ya fitar da Rayayye a cikin matacce Ka yarda da zancen Mahaifinka ka dage da Addu'a. Maganar Hajara ne ya dawo dashi tunaninsa "A Ina zaku Zauna Kai da matar taka"? "Zamu zauna a garin Jos ne Umma anan na siyi fili har na Gama gini" "Toh ban yarda ka zauna a Jos ba kaji ko ban yarda ka zauna da Dan iskan abokin babanka da ya d'aukemin Kai ko fuskarka ba'a Bari nagani ba ka Kara ma mu'ammalla dashi Naseer sai na tsine maka daga Yau ba Kai babu shi Dan babu yanda zanyi ne Dana ce har mahaifinka ban yarda ka cigaba da mu'ammalla dashi ba Ban yarda ka ringa b'oyemin komai ba da yanzu a gabana ka girma da duk bazaka zama wani susu su haka ba" Naseer rusunawa yayi a gabanta cikin tashin hankali Yana "Umma Abba fa shi ya Raine ni ya rik'eni tamkar Dan daya Haifa a cikinsa Dan Allah Mai yasa kike so ki rabamu Dan Allah kiyi hakuri nasan anyi Miki laifi Bai Dace a rabamu ba tun Ina jariri Dole zakiji ba dadi Amma Dan Allah kiyi hakuri Umma wannan matakin da kike San d'auka a kaina yayi tsauri Umma" "Toh sai dai ka zab'a ko Ni ko shi Naseer idan Kuma ka zabe shi Banga abinda zai Hana nayita tsine maka ba daga yau babu Kai babu shi ko Jos d'in ma bana so ka Kara zuwa zamanka a wajensa ba alheri bane a gareni sai Sharri" Sosai Hajara ta ringa bambamin fad'a har tana neman yiwa Naseer baki. Shi kuwa Naseer sosai hankalinsa ya tashi Sosai da rabashi da Hajaran ke neman Yi da Mallam Hassan Wanda ya Masa abinda ko Mahaifinsa Bai Masa ba tun daya taso ya fara wayo ya fuskanci irin Kaunar da Mallam Hassan ke Masa ba k'aramin jajircewa Mallam Hassan yayi a kansa ba ko Sana'ar da ya farayi da kudin Mallam Hassan ya fara kafin Mallam Ibrahim ya turo Masa kudi ya Kara Jari Taya Sama ta Ka shekara da shekaru da suke tare ace lokaci guda mahaifiyarsa tace su rabu har tana barazanar tsine Masa. Tunda ya taso Abu bai tab'a d'aga Masa hankali kamar yanda rabuwa da Mallam Hassan ya d'aga Masa hankali ba hakane yasa ya dage ya cigaba da rokar Hajara ita kuwa ta cigaba da Shan alwashin tsine Masa matsawar Bai bi umarninta ba. Kiran Sallah ne yasa Shi mik'ewa ya fita waje ya d'aura alwala ya nufi Massallaci yayi Sallah azahar. Yanda zuciyarsa ta cunkushe da tashin hankali yasa ya d'auki Qurani daya gani a Massallacin ya fara karatu ahankali yaji ya fara samun nutsuwa a Massallacin yayi zamansa har akayi Sallar ishai Dan Bai San Mai yasa yaji yafi samun nutsuwa da iska Mai dadi a Massallacin akan gidan Hajara ba. Hajara kuwa sosai hankalin ta ya tashi da yanda taga Naseer nada ruk'o da addini Dan taga alamar bazata iya mallake shi yanda take so ba duk da wani Abun zai iya tasiri akansa Amma zai na sakin shi nan da Nan sosai tayi ta tsinewa Mallam Hassan da Ibrahim Dan har yan kungiyar sun so tab'a Mallam Hassan Wacce taje Masa a Siffar Mujiya ya watso Mata ruwan rubutu Wanda ya k'ona Mata Rabin Fuskarta Sosai shugubarsu ta fusata suka Kara d'aura damaran ganin Bayan Mallam Hassan da suka lura idan basuyi da gaske ba zai iya cin Galaba Akansu Dan a tsaye yake sosai duk jifan da suka masa baya kama shi da alamar shima Naseer din kusan hakan ne Hakane yasa Shugabarsu Hajaran ta cewa Hajara lailai ta raba Naseer da Mallam Hassan. Wani Abu suka bawa Hajaran akan ta dafawa Naseer abinci dashi indai yaci zasu Dan ci Galaba akansa wajen Mallakeshi. Sai dai har ta Gama girkin Bai shigo ba har dare yayi. Naseer kuwa har Sha biyun dare Yana Massallacin har zai bar Massallacin Kuma ya koma ya zauna daya ga wasu su biyu sun shigo da alamar kwana zasuyi suna karatu aikuwa tuni ya koma ya zauna ya shiga cikinsu suka kwana suna Karatu Sabida biyan bukatar gabansa yasa ya tashi da azumi. Sai washegari ya koma gidan Hajaran data cika tayi Fam Dan duk yanda taso ganin Inda yake ta cikin mudubi,Bata samu ganinsa ba illa haske kawai data ke gani anan ta Kara sanin Naseer ya karantu akwai Kuma dafai a jikinsa. Dak'yar ta amsa gaisuwar sa ta hau surfa Masa Balai shi kuwa yayi ta Bata hakuri sai data Gama Dan kanta tace ga abincinsa Nan ya tashi ci. Wani irin kallo ta watsa masa lokacin da yace Mata azumi yake. A takaice duk yanda Naseer yaso shawo Kan Hajara abin yaci tura ahaka ya Mata Sallama ya taho Modobi zuciyarsa a cunkushe Dan ta rantse Masa idan Bai rabu da Mallam Hassan ba sai ta tsine Masa ta Kuma ranste bazai zauna a Jos ba yaje ya siyar da gidan ya dawo Calabar yayi gini su zauna. Allah yayi wa Mallam Hassan baiwa sosai na gane Abubuwa Wanda har idan wani mummunan Abu na neman far'uwa dashi Allah Kan nuna Masa a mafarki shi Kuma sai ya dage da Addu'a idan ma abin zai faru zai zo Masa cikin sauki ya Dade da sanin irin harin da Hajara take kawo masa hakane yasa yaci damarar Kare kansa ko tafiyar da Naseer yayi da mahaifiyarsa sai daya dage da Addu'a cikin Mafarki Allah ya nuna Masa komai ya Kuma Godewa Allah. Hakan yasa yak'i komawa Jos ya zauna zaman Jiran dawowar Naseer Dan ya Kara Masa wasu adduoi. Naseer kuwa a lokacin daya iso kasa magana yayi da Mallam Hassan Yana Jin kamar lokacin Hajara ke rantsuwar Yi Masa baki indai ya Kara kulashi sosai kirjinsa ya Masa wani irin Nauyi ya hau zubar da hawaye Bai San maanar tashin hankali ba sai daya ga Hajara na neman rabashi da Wani b'ari na jikinsa. Murmushi Mallam Hassan yayi a lokacin da yaga idon Naseer ya kad'a yayi Ja ya sunkuyar da kansa ya kasa Bari su had'a ido. Mallam Ibrahim kuwa wani irin ajiyar zuciya ya sauke da yaga Naseer ya dawo ba abinda ya same shi. "Karka damu na Riga da nasan Komai D'ana Ni nasan zatayi haka Dan Bata da makiyin daya wuceni Uwa ba Wasa bace kabi Umarninta Dan Allah sai dayace kabi Uwa sau uku kafin a ambaci Uba Abu daya zan Gaya maka karka sake da Addu'a ka dage da Addu'a dan Mahaifiyarka shu'uma ce ta gaske ta wuce tunaninka Sabida Kai yasa nak'i bud'e Mata wuta Amma da yanzu an shafe labarinta ita a tunanin ta idan ta rabamu shine zata iya cin Galaba a kanka tun kana jariri ban barka haka ba Naseer sai Dana Dage maka da Addu'a Kuma Alhamdulillah gashi ka girma cikin kariyar Allah a yanzu ne zaka fara fuskantar kalubale a rayuwarka domin Mahaifiyarka itace kaddararka duk lalacewa dai mahaifiyace Amma addu'a na iya canza komai idan rabbi ya sota da Shiriya zata shiryu kafin lokaci ya Kure kayi Mata biyayya ba zan fasa maka adduar dake daga mata hankali ba Kai yanzu ba yaro bane tunda baifi saura makwani ka Rayya Sunnar Ma'aiki ba Naseer ba kanka kawai zaka dagewa da Addu'a ba ka fara saka matar da zaka Aura a addua domin rayuwata itama Tana cikin hatsari karka tab'a kwanciya babu alwala Naseer daga Kai har iyalinka a yau da ba Hajara ce ta haifeka ba ace wani daban ta Haifa wlh Tallahi sai na kawo karshen tsafinsu Allah ya Kan Arawa bawa Dama yayi ta shagalinsa Wala Ala a gaba ko zai gane abinda yake Yi ba daidai bane ya gyara kafin lokaci ya Kure maka Amma Hajara ta Riga da tayi nisa ba Kuma ta Jin Kira Allah ya shiryeta ya ganar da ita gaskiya Bata isa tayimin komai ba sai dai idan Allah ya kaddara ta silarta zan tafi dawowar ka kawai nake jira Dama da tuni na tafi Amma duk da haka a yanzu zan d'au hanya Allah ya kareka da karewarsa ya baka ikon cinye wanan jarrabawa." Daga haka Mallam Hassan ya mik'e ya jawo jakar kayansa Naseer kuwa duk dauriyarsa a matsayinsa na d'a namiji sai da ya fara zubar da hawaye kamar mace Yana kallon Mallam Hassan ya fice daga d'akin Mallam Ibrahim na rokarsa ya kwana gobe ya dau hanya ya dage sai ya tafi. Motarsu Bata tashi ba sai wajen karfe biyar na yamma Yan kungiyarsu Hajara kuwa Suna kallon komai ta cikin Mudubi hakane yasa Motarsu na d'aukar hanya duk suka rikid'e suka koma siffar Mujiya suka tashi lokaci guda kusan su dari. Mallam Hassan kuwa tunda ya hau motar ya rufe Ido Yana tayiwa Annabi Sallati Bai ankara ba yaji an driver yataka wani irin birki Sakamakon Mujiyoyin da suka cike gaban glass din motar Wanda hakan yasa driver ya daina ganin gabansa har ya Kai shi da buga wani katon dutse dake Gefen hanya Motar ta kife. A takaice mutane biyu ne suka Rayu a Hatsarin Motar ahaka Mallam Hassan ya amsa Kiran Allah Inda sai da Mallam Ibrahim da Naseer suka yi kwana uku a asibiti Sabida yanda mutuwar Mallam Hassan ya gigitasu. (Allah ya jikanka Baba Ibrahim Allah yasa Aljanna ce makomarka a gaske akayi hatsari ya Kuma rasun Inda da yawa ake zargin yan kungiya ne suka haddasa Hatsarin Sabida biyu daga wayanda basu mutu ba suka bada labarin yanda Mujiyoyi suka rufe gaban motarsu Allah ya tsare Mana imaninmu Ameen) Har Mallam Hassan ya samu sati biyu da rasuwa Naseer bai dawo daidai ba haka Mallam Ibrahim Dan tunda akayi rasuwar yake kwance ya Kuma daina magana. Dak'yar Yan uwa da abokanan arzkiki suka samu rarrashi Naseer ya fara dawowa daidai Yana yiwa Mallam Hassan addua da yake ganin kamar zaa tashe shi ace mafarki yake ba mutuwa yayi ba Ashe duk maganar da yake Masa a ranar na bankwana ne daya sani ya rakashi daya Sani ya tashi ya rungumeshi kafin ya tafi. Hajara kuwa sosai sukayi kwana bakwai a daji suna abubuwa na murnar Mutuwar Hassan Dan Dama shine ya zame musu karfen k'afa. A takaice bayan Sati uku da rasuwar Mallam Hassan aka daura Auren Naeema da Naseer ba'ayi komai ba bayan daurin Auren Dan har a lokacin Naseer ba wani dawowa daidai yayi ba San ma dayake yiwa Naeema da San mallakarta ne yasa ma yake Dan samun relief. Kamar yanda Hajara ta tsara ya nemi gida a Calabar haka ya samu karamin gida ya siya gidansa na Jos kuma ya zuba 'yan haya. Hajara duk da gidan karami ne daki biyu da Palo sai kitchen da toilet gani take gidan yayi wa Naeema girma ita kadai Sosai idanta ke Kan komai da Naseer zaiyi naira Hamsin ma da Naseer ya biya Sadaki a wancan lokacin sai data nemi ya rage Dan Naira Ashirin shine highest din kudi a time din dak'yar ya samu ta barshi ya bada naira Hamsin din. Naseer Sanin darajar uwa da masifar dake tare da Bijirewa uwa yasa yake balain yi Mata biyayya ba Kuma yasan tayi fushi dashi zuwa Lokacin ya fuskanci Rashin ilimn da basudashi gabadaya a Kuma iya saninsa baiga Hajara ta tab'a sallah ba balle Kannensa. Wani zubin yakan so ya gasgata Abinda ake zarginta dashi Amma kyakyawar zuciyarsa sai ya ringa zata Mata zato Mai kyau. Sai da akayi Sati da Daurin auren Naeema da Naseer ta tare bayan Mahaifinta Lawan ya damka amanar Naeema a hannunsa ya kuma rok'esa daya riketa Amana Bata da kowa sai shi tunda sunyi nisa da juna zasu ringa aikawa Juna wasika ta Fax suna sanin halin da suke ciki. Mahaifiyarta da tun b'atan Aliyu Bata Kara samun cikakken lafiya ba itama sai datayi kukan rabuwa da Naeema Dan har ga Allah bataso Naeema tayi Mata Nisa haka ba taso Aurenta tayi a garin ko a kusa da garin Kar abin ya.mata yawa duka yaranta biyu babu Wanda take gani addua kawai tayi musu itama ta roki Naseer daya rike Mata amanar Naeema kamar bazasu rabu ba aka fito da Naeema dake Jin kamar ta hakura da auren Naseer tana fitowa ta fara k'ewan Iyayenta. Makotan arzikine suka Rakata har Calabar Lawan Kuma yace idan an kwana biyu zai saka shima a rakashi ya gano Inda suke zaune. Wayanda suka raka Naeema washegari da suka kaita suka juyo bayan ya Naseer ya musu goma sha Tara ta arzki shima a b'oye Sabida Kar Hajara ta gani tayi Magana. Sosai yake dokin kasancewa da Naeema Sabida tsananin San da yake. Gida uku ne tsakanin gidan Hajara da gidan Naseer din Hakane yasa Dan Abubuwan daya siyo ya siya guda biyu ya fara shiga wajen Hajara Dan ya Mata sai da safe. A palon ya tarar da ita a zaune ta Sha dogon Jar Riga har kasa ta rambada kwalli Tana ta karkada kafa Fuskarta a had'e gefenta Kuma Mijinta ne.tijnani ya sada Kai kasa kamar Mai neman yafiya. Wani irin tausayinsa ne ya rufe Naseer wanda hakan yasa Naseer danne nauyin Hajaran da yake ji bayan sun gaisa da Hajaran dake Masa wani irin kallo tana mamakin shakkarta da ta ga Naseer ba yayi idan tayi shigar dake saka hantar mutane kad'awa ko had'a ido baa iya Yi da ita intayi Shigar meeting d'insu. "Umma Miji shugaba ne a wajen matarsa sai mace tabi mijinta take samun Aljanna Umma bana jin dadin yanda nake ganin Baba bana Jin dadin yanda yake neman maidaki shugabarsa Umma Dan Allah banyi magana Dan na b'ata Miki Rai ba bana San ki shiga fushin ubangiji" "Kaiiiiiii dakata wa'azi zakamin har ka Isa kazo ka tsaya a gabana kana gayamin abinda ya dace da Wanda Bai Dace ba Ni Hajara baayi Wanda zan bishi ba daga yau karka Kara tarata da magana irin wanan wlh ranka zaiyi mumunan b'aci duk abinda zanyi idone naka kawai Kuma daga yau karka Kara tilastawa yayana suyi Sallah ai kowa na da raayinsa ko karka zo ka cusa musu abinda basuyi niyya ba ka dai ji na Gaya maka wanan ledojin daka shigo dasu na menene"? Naseer dak'yar ya hadiye yawu sabida b'acin Rai dayaga yanda baba Tijjani jikinsa ke balain rawa da Hajara ke magana "Kayan marmarine da kaza na siyo shine nace Bari na fara kawo miki kafin na wuce gida" Karbe ledojin tayi gabadaya ta d'auko iya ledar Ayaba da lemon ta mik'a Masa tana "Zaka iya tafiya Kazar Kuma zan bawa kannenka suci ai Suma suna bukata" Naseer baice komai ba ya karbi ledar ya mik'e ya Mata sai da safe. Yana fita ta dakawa Baba Tijjani tsawa Akan ya tashi ya Bata wuri. Waje yayi a rude Inda ya tarar da Naseer ya zubawa waje daya ido da ledar lemonsa a hannu. Baba Tijjani baice Masa komai ba ya wuce shi Naseer ya fara binsa a baya. Sai da suka jere ya fara magana Yana "Ka dage da Addu'a Allah ya kawo maka mafita kayi hakuri da tambayar da zan maka kana Sallah kuwa" "Ada inayi kafin na aurota sai Dana aurota ta ce Kar na sake Mata sallah a gida. Wani irin nauyi yaji a kirjinsa ya zubawa baba Tijjani Ido da duk ya firgice "Ka ringa sallah a boye kana gayawa Allah Yana jinka Yana Kuma sane dakai zai kawo maka mafita" Sosai.Naseer ya bashi shawarwarin da take baba Tijjani ya fara aiki dashi yayi alwala ya shiga wani Massallacin daya gani a bud'e. Naseer kuwa Yana Isa gida yajasu sallah shi kadai ya Sha lemonsa da Ayaba Dan mutanen da akwai azabar kunya Tama k'i bari su had'a ido balle ta saki jiki ta Sha lemon. Shi kuwa ko a jikinsa Dan yasan kunya ke dawainiya da ita. Daren farko yakan zama Daren tarihi ga maurata karfe goma.sha daya Naseer yayi Shirin kwanciya Yana cikin yiwa Naeema magana yaji an fara buga k'ofar gidan a haukace. Mamakine ya rufeshi ya zura jallabiyarsa ya fito Yana "waye"? Tara da bud'e k'ofar sakin baki yayi a lokacin dayaga Safiyya da Lami da uban Kaya "Lafiya kuwa"? "Eee Umma ce tace muzo mu Taya Naeema kwana idan an kwana biyu sai mu koma. Daga haka suka shige gidan suka bar Naseer da sakaken baki a bud'e. A takaice amarcin da Naseer baiyi cikin dadin Rai ba kenan dan Safiyya da Lami sosai suka sa musu Ido duk abinda akayi idonsu na Kai sai Kuma sun kaiwa Hajara rahota. Naeema kuwa ko kad'an Bata tab'a damuwa ba Dan tana da balain hakuri idan kuwa Naseer ya fita ya d'an siyowa Naeema Abu tofa an shiga uku Dan sai sun gayawa Hajara ita Kuma sai ta Masa tas kamar ta dakeshi....... [6/26, 6:15 PM] Buhari Yusuf IBr: *NAGA TA KAINA* *NA SADNAF*🌸🌸 ®️ *_PURE MOMENT OF LIFE WRITERS_* _{We Don't just entertain nd educate we also touch the heat of readers P.M.L}💪🏻_ *Free Novel* *Page 5* Naeema sosai take tsoron Safiyya da Lami Dan sun girme Mata indai Naseer baya Nan sai dai tayi ta zaman d'aki. Ahaka ma bata tsira ba haka zasuyi daidai a Palo suna zuba mulki tunda suka lura Bata da wayyo ga Kuma yarinta ga balain tsoro da take dashi. Da tsoron da take dashi suke tak'ata yanda sukeso Bata tab'a d'aga Kai ta kallesu ba ballantana ta Kai kararsu wajen Naseer da zamansu Safiyya a gidansa yafi k'ona Masa Rai irin rayuwar daya so Shimfid'awa da Naeema idan ya Aureta ba irinshi yakeyi ba Dan Su Saffiya ma ba wani shak'arsa suke ba idan yaso tsawatar musu ma yasan Ransa sai ya b'aci. Hajara kuwa ko tari Naeema tayi a gidan sai su Saffiya sun bata labari Naseer ma in zaiyi kwanciyar Aure da Naeema a b'oye shima hankali ba a kwance ba Sabida fargabar su Saffiya na iya fad'o musu d'aki sosai Naseer ya takura da irin zaman da su Safiyya ke Masa a gida hakane yasa wani dabara ya fad'o Masa ranar da Naeema tayi wata biyu a gidansa daddare ya shirya ya nufi gidan Hajara. Da isarsa kuwa ya sameta a zaune a Palo da wata doguwar mata sun saka ja doguwar Riga iri daya har yanayin Saka kwallin ga wani bak'in tukunyar kasa a gabansu an sosoka allurai haka a saman tukunyar. Ko d'ar Hajara batayi ba ta matsar da tukunyar gefe ta kalli Naseer tana yamutsa fuska Dan ko kad'an Bata so zuwansa a yanzu ba taso sun Gama abinda sukeyi da wata kawarta Yar kungiya da hatsabibancinsu ya zo daya da rashin Imani da Suke ganin gidan Duniya gidan zamane dazasu ringa tsulla tsiyarsu San ransu. Naseer kuwa wani Yam yaji a jikinsa ya d'auke idonsa daga Kan tukunyar ya Kara Sallama Ya durk'usa a kasa ya hau gaishe su. "Lafiya naganka.yanzu"? Naseer kasa magana yayi Sakamakon yanda kawar Hajara ta zubo Masa na Mujiya Kamar idonta ya fad'o kasa sau biyu suka had'a ido yaji kansa ya Sara masa take ya karanta addua a hankali. Hajara kuwa ta kalli Kawarta ta tana "Kibi a hankali wanan D'ana ne nasan kinfi kowa sani Naseer ne Kar naji Kar nagani ki d'auke idonki a kansa" Wani irin murmushi kawar tata tayi tana "Ai Sanin danki ne shiyasa kawai na tsaya iya kallo" "Auzibikallimatillahi tammat Naseer ya hau Dan karantawa a fili. Hajara kuwa ta daka Masa tsawa tana "Dalla gayamin abinda ke tafe da Kai ka tashi ka bani guri inada abin Yi" "Umma Dama wani islamiyya Na samowa Safiyya da Lami shine nace Bari Nazo na fara fad'a Miki Dan Naga alamar basuda ilimi a cikin duhu suke rayuwa har yanzu Banga alamar suna maida hankali wajen Sallah ba" Kamar wacce aka cakawa wuka haka Hajara ta mik'e Tana "Ban yarda ka samin Yara a makaranta ba nice Banga Daman saka su yanzu ba idan lokacin saka sun yayi zan saka su da kaina idan ma ka tsiro da hakane Dan su bar maka gida zasu bar maka gida a yau d'inan ba sai gobe. A takaice da Wannan damar Naseer ya samu suka bar Masa gidansa kafin ya samu Sa'eeda sai dai kasan zuciyarsa Yana balain bakin ciki da halin mahaifiyarsa gashi yak'i yarda maganar da ake fada akanta Amma hakan Bai saka yayi Sake da Addu'a ba Dan bazai yaudari kansa ba Dole mahaifiyarsa tana cikin wani kungiyar daga irin shigar da takeyi duk dare. Sai da Su Saffiya suka bar gidan Naeema ta samu Sa'ida take Kuma Jin a yanzu ne zatayi amarcin ta sosai Naseer ke tattalinta kamar kwai duk wani Abu na Jin dadi yagani sai ya siyo mata. Ba abinda Naeema ta nema ta rasa tunda su Safiyya suka bar gidan babu Wanda ya Kara zuwa Sosai Naseer Yaji dadin yanda suka d'auke kafa daga gidan Hajara ma tunda Naseer ya mata zancen Saka su Safiyya a islamiyya ta d'auke Masa wuta Gaisuwa kawai ke had'asu Dan ko yaje.haka zai karaci zamansa idan ya gaji sai ya tashi ya tafi bayan ya Ajiye Mata kayayaki da kudi. Nan kuwa Hajara kallon Naseer kawai take Tana tarashi Dan sun gano a kungiyarsu Naseer na taimakon Baba Tijjani da Addu'a har Baba Tijjani na iya adduoi da kansa yanzu ya Kai ya kawo Baba Tijjani baya kwanan gidan a Massallacin yake kwana sai yayi kwanaki ma Bai zo gidan ba aikin Kuma da tayi akansa taga idan Bata dage ba warwarewa zaiyi Kuma ba kowa ne ya ja Mata hakan ba sai Naseer hakane yasa take fushi dashi sosai shi Kuma Bai sani ba. A d'an Zaman da Naeeer yayi da Naeema ya fahimci Bata da ilimin Addini babu Kuma abinda ta sani Dan ko wankan tsarki ma shi ya koya Mata. Hakane yasa ya Dan fara koya Mata gajerun surori da Addu'oi da kwakwalwarta zai iya d'auka sai dai Naeema tana cikin irin mutane Nan da ake cewa Slow learner hakane yasa ta kasa d'auka da wuri fatihar ma sai da suka kusa Sati. Sabida Naseer na yawan tafiye tafiye hakane yasa Bai wani Samu lokaci ba ballantana karatun ya zauna a kanta. Ko kad'an Naseer baiyi Sake da Addu'a ba Dan Dama shi akwai jajircewa Dan Bai fiye kwana bacci ba Rabin Daren yakan raya shi tun lokacin ma dayake yaro hakane yasa ya Riga da ya saba. Indai ya kwana bacci to bashida cikakken lafiya. Tunda ya kyalla ido.yaga Naeema ta samu ciki yaji kamar ya taka rawa hakane yasa ya Kara zagewa wajen kyautata Mata duk da ba abinda Naeema ta nema ta rasa kudi kuwa har ta rasa Inda zata ajiyesu Dan kullum in zai fita sai Ya Ajiye Mata naira Ashirin Wanda yake kamar Dubu daya na yanzu. A cikin akwatinta ta ringa Tara kudin Inda ta ringa cin burin yiwa Iyayenta siyayya idan ta tashi zuwa gida Dan Naseer yace Mata sai ta haihu zata je gida. Cikinta na da wata bakwai Naseer ya Gama Siyayyar kayan Jarirai cikin akwati haka ma Naeema sosai yake ji da cikin Naeema ya Kuma matsu lokacin haihuwar ta yayi Dan Yana so tana haihuwa ma ya sakata a islamiyya ba iya shi ba har Dana bokon. Har a lokacin Hajara Bata sake Masa maganar komai ba Inda ya ringa mamakin Canzawarta sai watarana dayaje.ya Mata Sallama zai tafi yazo fita tace Masa "Kai Yanzu ya dace ace tunda ka auro matarka Bata tak'a k'afarta tazo gidanan gaisheni ba Ni kake so naje na gaisheta kenan ko"? Hajara tace Tana watsa Masa wani mugun kallo. Naseer kuwa cikin kunyar rashin kyautawar da baiyi ba ya tsugunna Yana "Dan Allah kiyi hakuri Umma nayi kuskure laifina ne da ban Bata izinin zuwa ba Amma gobe insha Allahu zan kawota" "Au Bata da k'afa kenan sai ka goyata ka taso ta a gaba zata zo ta gaisheni sai ma na roki gaisuwar ta ko Naseer"? Naseer hakuri ya Kara Bata Hajara ta girgiza Kai batare da ta ce komai ba sai da Naseer ya gaji Dan kansa ya mik'e ya Mata sai da safe. Washegari kuwa kamar yanda ya alkawarta da sassafe yasa Naeema ta shirya har da sata ta soya Kajin da zata Kai mata. Naeema cikin kunya cikinta daya turo sosai ta nufi gidan a lokacin Naseer Vespa ne dash. Sai daya Dan rage Mata hanya duk da gidan ba nisa ya Nuno Mata gidan akan ta shiga Dan yasan idan ya rakata cikin gidan Nan ma case ne har Naeema ta doshi gidan ya kirata ta dawo. "Ki kula da kanki Naeema" Murmushi ta Masa ta gyada Kai har zata juya Naseer ya tsinci kansa da ce Mata "Ki kula da abincin da Zakici kinji idan an baki abinci kice bismillahi rahamanir Raheem ai kin iya ko"? Da Sauri Naeema ta gyada Kai tana har Alhamdulillahi rabbil Ala meen na karanta zuwa karshe kafin naci abincin ko"? Murmushi Naseer yayi Sabida yanda tayi maganar cikin yarinta ya gyada Mata Kai tana "eee a hankali Zaki karanta kar ki Bari kowa yajiki daga Nan sai ki faracin abincin" Gyada Masa Kai tayi ta nufi gidan shi Kuma ya wuce Tasha karbar wani Sako. Naeema da Sallama ta shiga gidan. Ganin babu Wanda ta gani yasa ta cigaba da kwada Sallama Ta kusa minti goma a tsaye tana Sallama kafin taga an d'aga labulen palon an zubo Mata Ido Ana kallonta. Da k'arfi Dan cikin Naeema ya motsa gabanta yayi balain fad'uwa cikin tsoro Sabida Bata tab'a ganin Hajara ba sai Yau. Hajara kuwa sosai ta gwallo idonta dake d'auke da kwallin tsafi tana kallon cikin Naeema da take ji kamar ta fusgo cikin ta bawa shugabarsu. Naeema kuwa cikin rawar jiki ta zub'e a kasa da Kular hannunta ta hau gaisheta. Kallonta Hajara ta cigaba yi dayi Tana Jin kamar ta shak'e Naeema ta rabata da numfashin jikinta. Bata ji tsanar Naeema ba sai Jiya da Shugabarsu ke Gaya mata irin San da Naseer ke yiwa Naeema har tana ce mata Naseer zai iya sadaukar da rayuwarsa sabida ita a yanzu ma haka dukiyar Naseer duk akan Naeema yake tafiya Dan haka ta tashi tsaye ya kwato danta idan Naeema ta Haihu ta saka Naseer ya saketa idan ma Dan Dan dazata Haifa xaa fake sai a rabata da jaririn. Naeema Bata Kara dagowa ba sabida yanda jikinta ke rawa a Dan karamin shekarunta tana ganin Abubuwan ban tsoro Amma mahaifiyar Naseer ta balain kad'a Mata ciki har lokacin cikin jikinta mutsu mutsu yake. Hajara sai data gama ayyana mugayen Abubuwa ta saki labulen ta koma ciki babu alheri ko kad'an a zuciyarta Bata da burin daya wuce duk Wanda take muamalla dashi ya zama a kasanta tana mulkarsa haka ma taso Naseer ta ringa mulkarsa sai dai duk abinda takeyi a kansa ta kasa cin Galaba a kansa Amma ta silar matarsa zata ci Galaba akansa. Sai da Naeema ta kusa awaya daya a tsakar gida kafin ta ce Mata "Jira kike na shigo dake ko kuwa"? Da Sauri Naeema da baganta ya kage ta shiga palon har lokacin ta kasa daga Ido ta Kara kallon Hajara. Hajara sai data Gama kare Mata kallo taga tsadadden zanin data daura a jikinta ga fatarta datayi fresh ta girgiza Kai tana "Ke dago ki kalleni" Naeema da Sauri ta daga kanta ta kalleta Sabida Allah ya zuba Mata tsoro Tana Shirin maida kanta kasa da Sauri sabida yanda idon Hajaran ke tsorata ta Hajara ta daka mata tsawa tana "Karki Sake ki sunkuyar da kanki ki kalli idona kiji Mai zan ce miki Naseer Dana ne Ni nake da alhakin na zab'a Masa matar da nakeso ya aura na barshi ya aureki ne sabida wani dalili nawa Izuwa yanzu ai kinci rabonki yanda ya Kamata ko to kina haifar abinda ke cikinki ki gaggauta had'a kayanki kice ya sakeki Dan banida burin daya wuce Naga idan ya auri mace Tana haihu ya saketa Dana Yana da arzkiki bazan Bari mace daya ta nanike Masa tayi ta morarsa ba kinci rabonki haka Nan ki Bari wata itama ta zo taci nata Rabon dafatan kinji Mai nace" Da Sauri Naeema ta gyada mata Kai tana hawaye Dan Abu kad'an ke sakata kuka. Hajara Bata Kara ce Mata komai ba ta tashi ta shige daki bayan Yan mintina ta dawo da langa hannunta dake d'auke da tuwo da miya da yaji barbaden maganin da zai kashe abin cikinta Dan bama taso abin cikinta yazo da Rai. Naeema duk da Bata Jin yunwa da Sauri ta karbi abincin cikin ikon Allah Bata manta da yin Bismillah ba har da fatiha har karshe ta fara cin tuwon. Hajara kuwa kul ta Kure ta da Ido har ta Gama ci. Daga Nan ta hau saka Naeema aiki sai data Gama gyare gidan tas sanan ta bar Naeema ta tafi bayan ta Bata manja Mai d'auke da maganin da zata samu Galaba akan Naseer tace ta ringa musu girki dashi. Inaso mu tsunduma cikin labarin Dan Yana da Dan tsawo sai na danyi briefing. A takaice lafiya Lau Naeema ta Haihu da taimakon Allah da na Naseer daya dage da Addu'a ba dare ba Rana duk da irin harin da Hajara tayi ta kawo musu Dan ganin jaririya Bata so da Rai ba hakane ya Kara dasa tsanar Naeema a zuciyar Hajara. Sosai ta bud'ewa Naseer wuta akan ya saketa Amma yak'i ya saketan har ya gwammace yayi tafiya Mai nisa kafin ya dawo duk sabida ya kaucewa maganar Hajaran arzikinsa sai bunkasa yake har da San Naeema. Yarta da aka sawa Zahira nada wata uku Allah yayi wa Aminat Rasuwa Inda sai da akayi Sadakan bakwai kafin Naeema taji labari sosai Hankalin Naeema ya tashi tayi ta kuka Haka Naseer ya d'auketa da kansa ya kaita garinsu. Sosai Naeema tayi kukan rashin mahaifiyarta data ci burin Kara haduwa da ita. Mahaifinta da shima yake dauriya Sabida ya Dade a kwance ba lafiya har ma yafi Aminat Jin jiki amma abin Allah ita tazo ta Riga shi tafiya. Sosai ya roki Naseer rike Naeema da Amana ya had'asu ya musu naseeha. Naseer anan ya tafi ya bar Naeema akan shima zaije Jos wani aiki idan ya dawo ya biyo ya d'auke ta. Kwana ashirin da rasuwar Aminat Lawan shima ya amsa Kiran Mahallacinsa. A shekarar Nan anyiwa Naeema mutuwar da sai da Naseer yayi da gaske ta dawo daidai Dan har kwanciya tayi itama a asibitin. Bayan wata hud'u da rasuwarsu Hajara ta cigaba da matsawa Naseer akan ya saki Naeema da Allah ke ta kareta daga sharrinsu Wanda hakane ya ruru Mata wutar tsanar Naeema har tana tunanin itama Naeema ilimi ne da ita har take adduoi da take Kare kanta. A irin wanan yanayin Naeema ta sake samun ciki Zahira nada wata takwas. A daidai lokacin da Naseer ya Gina gidan dayafi gidan da suke ciki kyau suka koma. Hajara kuwa ganin idan batayi dagaske ba bazata iya raba Naeema da Naseer ba yasa ta biyo ta bayan gida ta fara Jan Naeema jikinta sai data tabbatar ta saki jikinta da ita taje gidan tayi musu girki da kanta daya Sha barbaden maganin lokacin Cikin Naeema nada wata shidda. Tsautsayi baya wuce ranarsa a ranar Naseer ya dawo a gajiye da yunwa Naeema na bashi abincin ya cinye tundaga lokacin ya fara Dan canjawa Naeema ahaka ma Wai dan Yana addua Dan so akayi ya mata saki uku har da duka Amma Allah baiyi ba. Ahaka ta Kara haihuwa cikin ikon Allah ta Kara samun mace aka saka Mata Nadeeya zuwa Lokacin an Kai Hajara bango hakane yasa ta fusata suka dage ita da kungiya har sai da suka Yi wani irin aiki akan Naseer a lokacin suka ci Galaba akansa Sabida babu tsarki a jikinsa tun daga lokacin Naseer ya Dan fara wulakanta Naeema har Allah ya Kara kawo rabon wani cikin Inda Hajara kuwa tasha alwashin bazata haife cikin ba indai tana rayye take ta tattara ta dawo gidan ita dasu Safiyya da Tijjani gabadaya Dan Baba Tijjani ya Dade da guduwa daga Nan suka hau matsawa Naeema suka juyarwa da Naseer hankali ya fara manta Naeema a kansa ahaka Naeema ta kasance a mawuyacin Hali har dukanta Hajara keyi ta gaje gidan ta ringa laftawa Naseer abinci Mai barbade barbaden magani a yanzu haka cikin Naeema ya shiga watan haihuwa. Cigaban Labarin Nayi mantuwa sabida Ina Sauri mu cigaba da labarin A shekarar da aka haifi nadeeya 1991 a shekarar Allah yayiwa Mahaifin Naseer rasuwa Wanan kenan*NAGA TA KAINA* *NA SADNAF*🌸🌸 ®️ *_PURE MOMENT OF LIFE WRITERS_* _{We Don't just entertain nd educate we also touch the heat of readers P.M.L}💪🏻_ *Free Novel* *Page 6* Cigaban Labarin "Tunda Umma tazo min cikin Mafarki ban Kara Wasa da sallah ba Sosai Nake kaiwa Allah kukana cikin Sujjada Dan Nagaji da irin Rayuwar da nake a gidan Aurena k'arfi da yaji zaman d'aka ya aureni nida gidana horar yunwa kawai Umma kemin Bata da burin daya wuce taga yunwa ya zama ajalina tunda nayi yunk'urin zuwa wajen Naseer daddare ta Kara matsa min lamba wajen gana min azaba Dan bredi da lemon da nake samu na siya a b'oye yanzu duk ta hanani Dan kullum Tana zaune a Palo Dana bud'e kofa zata min kallon da zai kusa sakani fitsari a wando hakane yasa nake komawa d'akina aguje. Dan wanke wanken da suke Sakani ma na samu naci ko da kanzo ne sun daina Sakani ruwan bandakina kawai nake Sha na rasa Mai taimakamin a rayuwata na Gaji da zaman takunkumin da nake a gidan Nan na Riga da na gwammace Dana gudu na shiga duniya da irin wahalaliyar rayuwar. Da nake a gidan Naseer kila a duniya na samu Mai taimakamin. Kwana biyu kenan dana ji cikina ya daina motsamin nasan Kuma ya daina motsine Sabida abincin da bana ci duk da banyi karatu ba na iya lissafi nasan cikina ya shiga watan haihuwa har ya kusa shiga wata na goma Amma shiru har yanzu ban haihu ba wanan shine haihuwar da zanyi batare da na tanadi komai ba na samu ma Mai zanci a cikina tukunna kafin nayi tunanin tanadar wani Abu Dan Ma Allah ya rufa asiri ina da alkinta Abu akwai kayayakin Zahira da Nadeeya da suke ajiye Kamar ban tab'a amfani dasu ba. Sosai na fara Jin tsanar Naseer a Raina gani nake da gangan ya shareni da gangan ya watsar Dani Mai nayi Masa haka Dana cancanci haka daga wajensa Mai nayi Masa da muna gida daya baifi taku biyar zaiyi zuwa dakina ba yak'asa lekoni. Kuka nake sosai jikina na rawa sabida yunwar danakeji. Mutuwa kawai nake fata ya daukeni da irin Rayuwar da nakeyi a gidanan. Har gobe nakan yi mamaki wane irin zuciya ne a kirjin Umma da Bata tausayamin take burin na tagayyara da farko bana damuwa idan tace na haifi cikin jikina tagani yanzu kuwa Dana wuce watan haihuwa na fara tsorata da kalaman Koda mutuwar zanyi Ina fatan na ga abinda zan Haifa Ina addua ya zamto Namiji Mai Kama da Naseer. Cikina daya harb'amin da k'arfi yasa na cije lebb'ena Ina Dan Jin dadi a raina hakan na nunawa Yana Nan lafiya yunwa yasa ya bar motsi Kamar wacce aka mitsina haka na mik'e duk da babu kwari jikina Haka na nufi kofar dakina Ina gayawa kaina na rage tsoro haka na Nemo abinda zan sakawa cikina karshenta dai Umma ta jibgeni kamar yanda ta Saba Amma ya zama Dole na nemi abinda zan sawa cikina ko Dan jaririn cikina har zan murd'e kofar na fita na dawo Baya na dauki Hijabina na saka na bud'e akwatina na Ciro Naira Ashirin a cikin iirn kudin da Naseer ke bani a lokacin da yake kaunata Ashe dai kudin zasu min amfani. Duk da gabana dake balain fad'uwa ahaka na bud'e k'ofar na fita na tsinci kaina da karanta Fatiha Dana balain haddacewa Dan shi kadai na iya sai suratul iklas da shima sai Dana Dage na iya. Wani irin ajiyar zuciya na saki a lokacin danaga ba kowa a palon. Sai kamshin abinci danake jiyowa daga kitchen daya saka cikina fara motsawa sosai naji wani irin bakar yunwa Ni danayi niyyar yin waje sai gani nayi na nufi kitchen. Ba Wanda nagani a kitchen illa Dan madaidacin tukunya da aka Dan bude Mai dauke da farar Shinkafa daya saka yawuna tsinkewa gefe Kuma Miya ne dayaji namomi. Bansan ya akayi na dauki tukunyar Shinkafar na Dora na miyan akai nayi hanyar dakina dashi ba zubawa nayi niyyar Yi a plate Amma sai na tsinci kaina da daukewa gabadaya na kai d'aki lokacin idona ya rufe da yunwa ballantana nayi tunanin idan aka kamani fa Ruwan da suka dura a Robobi dake cikin fridge na koma na dauki guda biyu Dan karfinn hali irin nawa har da d'aukar bredi guda biyu dake ajiye a kitchen din. Ina shiga dakina na kulle d'akin tun kafin na zauna na fara dibar Shinkafar Ina kaiwa bakina ko zafin abincin banaji tsabar yunwar danakeji. Ina cikin ci naji an fara buga min kofa Muryar Lami Dana Safiyya naji suna ta auna min zagi suna cemin Barauniya wlh idan na Bari suka shigo d'akin sai na lahira yafini Jin dadi ya zaayi su Gama Shan wahalar girki na sace abincin. Ko kulasu banyi ba na cigaba da cin abincina nasan ban Isa na guje musu ba Dole sai sun dakeni ko naci ko banci ba gwara ma naci abincin. Koda sun dakeni zasu dakeni da kwarina. Da hannu bibiyu nake tusa abincin duk uban yajin dake cikin miyar dayasa nayita kwarewa yanda suke jijjiga k'ofar.kamar zasu b'alla ne yasa na dage na cigaba da auna abincin bakina da iya karfina ko taunawar kirki banayi. Cak na tsayar da cin abincin danaji kukan Zahira muryar Saffiya na tashi cikin balai "Wlh idan baki bud'e k'ofar Nan ba yau kwana zanyi Ina dukan Zahira da Nadiya sai sunyi kwana uku basu ci abinci ba. Wani irin mik'ewa nayi cikin tashin hankali Jin Safiyya zata dakarmin yaran da nake tunanin su suka ragemin a rayuwata. Aguje na nufi kofar na bud'e. Ban karasa bud'ewa suka banko d'akin suka shiga Safiyya da Lami kuwa suka rufeni da mugun duka suna kaimin naushi ko ta ina nidai durkushewa kawai nayi inata Kare cikin jikina Sabida Kar su kawo min duka sai hakuri nake basu. Lami da nake tunanin sai ma tafi Umma mugunta idan ta samu waje naji ta harba min kafarta cikina. Take na saki wani irin ihun azaba na wargaje a kasa. Nadeeya da Zahira kuwa ihu kawai suke suna kuka suna rike Lami da Safiyya Nadeeya da k'ok'ari har da kankame Lami ta Kai Mata cizo a kafa. Take Lami ta bar kaimin dukan ta dau Nadeeya tayi cili da ita. Ihun da Nadeeya ta saki yasani mik'ewa tare da manta azabar danake ciki. Safiyya dake ta kaimin duka na wawuro na damfara ta da kasa a zuciye Ko a mafarki akace min xan iya karfin dagata sama karyatawa zanyi Lami ma dake neman Kara kamoni na wawuro tukunyar Shinkafar da har lokacin da Saura na hau kwada mata akanta Ina ihun kuka. Sosai idona ya rufe sabida tab'a min 'ya da sukayi. Sai da Safiyya ta fusge tukunyar nayi wajen Nadeeya aguje da jini ke ta zubar Mata Sabida kanta daya fashe. Bansan tashin hankali Hawa Hawa bane sai ranar duk dukan da sukamin nemansa nayi na rasa sabida tashin hankali ganin jinin dake zuba a Kan Nadeeya. Ihu kawai nake Ina sun kashemin 'ya da hannu bibiyu na d'aga Nadeeya nayi waje Ina ihun a taimakamin. Ina fita Naga wani Dan taxi nace ya taimakamin ya kaini asibiti 'yata zata mutu. Tun Bai gama tsayawa ba na bud'e k'ofar na afka ciki Nadeeya rungume Dani Ina ta kuka jinin dake zuba Akan ta ba karamin girgiza ni yayi ba. Asibitin da muke zuwa na Kai Nadeeya Mai taxi kuwa ganin halin da nake ciki yasa Bai tsaya amsar kudinsa ba yayi tafiyarsa. Da yake nurses da likitocin sun sani sosai Sabida haihuwar Nadeeya Dana Zahira duk a asibitin nayi Kuma Naseer na musu alheri sosai Sabida bashida rowa har gida suna zuwa dubamu idan Wani bashida lafiya. Da Sauri suka karbi Nadeeya suna tambayata Mai ya sameta. Ko magana ban iya Yi ba in Banda ku taimaka.min danake ta cewa. Wani daki aka Kai Nadeeya suka hanani shiga. Minti talatin din danayi Ina jiran fitowarsu sai Dana ga kamar awa talatin ne duk na matsu su fito Naga lafiyar 'yata. Fitowar Likitan yasa nufeshi da Sauri Ina tambayarsa jikin 'yata Sai Dana ga yana ta k'ok'arin fusge hannunsa daga ruk'on danayi Masa nasan Ashe ma hannunsa na ruk'o sabida tashin hankali. K'ofar d'akin ya bud'e min ya Nuno min Nadeeya da sukayi wa dinki akai da ke ta sharar bacci ya bani hakuri akan Kar nashiga sabida Kar na tasheta. Sai sannu yakemin sabida cikina dayayi turtsetse a gaba yace na samu waje na huta. Ban iya zama ba Haka nake ta Kai kawo ko nauyin cikina banaji har sai Dana tuna Ashe banyi Sallah Laasar ba kafin na nemi buta na daura alwala Allah daya taimakeni da hijabi a jikina Dama ban cire ba. Kebabben waje na samu nayi Sallah duk ba nutse ba sai Dana iddar da sallahn na fashe da wani irin kuka danake taso nayi tun dazu yak'i zuwa Sosai na jika gaban hijab Dina da hawaye Ina tunanin halin Danake ciki Sabida kawai abinci kannen mijina suka rufeni da duka Haka har abin ya shafi 'yata su fasa mata Kai. Sosai nake kudirtawa Raina guduwa daga asibitin Amma Zahira Dana tuno yasa na Kara fashewa da Kukan Dan bazan iya guduwa na barta ba da da ita na fito da wlh babu abinda zai maidani gidan. Gani nake babu Wanda ya Kai Su Umma rashin Imani gani nake babu Wanda ya Kai Su mugunta da rashin tausayi. Bansan Magriba tayi ba sai da naji wata nurse ta tsugunna a gabana Tana bani hakuri akan na bar kukan Haka komai yayi tsanani maganinsa Allah. Bansan ya akayi na kwanta a Jikinta na riketa Gam Ina cigaba da kuka ba so nake na fada Mata halin da nake ciki ko Yaya ne Amma tsabar kukan danayi maganar tawa taki fitowa sai sheshek'a nake. Dak'yar ta kwace jikinta daga nawa idonta itama da hawaye tacemin nayi hakuri ga mijinta can yazo daukarta ta Gama duty dinta. Ji nake kamar na bita aguje Dana hango tausayina a idonta kamar na riketa Gam na hanata tafiya sabida kawai ta taimaka min. Nadeeya data fad'omin yasa na mik'e da Sauri nayi wajen d'akin da aka kwantar da ita. Ina bud'e k'ofar tana bud'e idonta. Da Sauri na ka rasa gadon na jawota jikina na rungume Ina fashewa da wani sabon kukan Sosai nake tausayin kaina Dana yayana. Ummata kawai nake kira da Abbana. Wata nurse ce ta shigo ta bani hakuri tace zamu iya tafiya Dan Naseer ke biyan kudin asibitin ta bani ledar magani. Kalmar xamu iya tafiya data ce ne yasa na Kara fashewa da kuka na tsani gidan Nan inama da Zahira na fito wlh Tallahi babu abinda zai maidani gidanan na gwammace na gudu da yayana. Nurse din kuwa Tsaki tayimin tayi tafiyar ta Tana Jin Haushin yanda nake ta kuka akan 'yata taji ciwo ita Kam batasan kukan da nake ba. Duk da nauyin cikina ahaka na kunce dankwalina na goya Nadeeya muka d'au hanya a lokacin dare yayi. Ba fita nake ba ballantana nasan ko ina a yanzu ma bansan hanyar komawa gida ba. Tafiya kawai nakeyi Ina tunanin inama mota tazo ta bi ta Kaina da Nadeeya mu mutu itama Zahiran ta mutu mu huta. Sai danayi ta zagaye kafin na gane hanyar gidan da sai Dana balain gajiya. Ina zuwa kofar gidan na kunto Nadeeya dake bacci na kwantar da ita a kasa Ina fargabar kwankwasa k'ofar Gidan Ciki kuwa Umma ta cika tayi fam tana jiran dawowata Dan Bata Nan mukayi fada da su Saffiya tana dawowa suka Gaya Mata Kan lami data gani a kumbure ne kawai ke tafasa zuciyarta sosai takeji lokaci yayi da zata saka Yaya matanta a kungiya ko Dan irin abinda ya faru Allah Allah kawai take taga ta Inda zan shigo Dama idan ranta ya b'ace yake shigar bak'akken Kaya takeyi. Naseer kansa daya dawo gidan sai daya San yau Mahaifiyarsa ba daidai take ba hakane yasa daya shiga dakinsa ya kulle Dan Haka kawai yau bayajin dadin Jikinsa Yana so ya tambayi Zahira da Nadeeya Yana Jin tsoron tambaya Kar yayi laifi. K'ofar kawai Hajara ta zubawa Ido tana kallon Naeema datayi zaman dirshen a k'ofar Gidan tana tsoron kwankwasa wa. Hajara kallonta kawai take Tana tunanin matakin daya Dace ta d'auka akanta Wata biyu ya rage wa Naeema Dan sun Gama tsara abinsu kamar idan tazo haihuwane ta mutu Amma mutuwar tata sune sila a da batayi niyyar kashe Naeema ba taso su rabu Salin Alin data haifi Zahira Amma sabida taurin Kan Naeema shine tayi mata gardama, taki tafiye tana ta Mata haife haife ita Nan Mai wayo baa ja da ita Amma Naeema ta ja da ita gani take Dole Naeema akwai abinda ta dogara dashi shiyasa take tsallake duk abinda tayi Mata. A yau Naeema ta Mata abinda takejin kamar tun a daren yau ta rabata da ranta. Ahaka ta zubawa kofar ido Bata motsa ba. Naeema itama Bata kwankwansa ba sabida tsoro har karfe dayan dare Naeema na waje ta kasa kwankwasawa Sabida masifar tsoro. Haushin karnuka ne yasa na jawo Nadeeya jikina na fara kwankwasa k'ofar a hankali tun inayi a hankali da Sauri na fara bubugawa Sabida tsananin tsoro ga wani irin Kara da nakeji. Da iya karfina na fara buga gidan Ina waige waige ai kuwa waigawar da zanyi Naga wani irin bakin mage ya zuromin ido. Wani irin razanann Kara na saki na fara kwalawa Umma Kira Dasu Safiyya tsabar tsoro har da Naseer na hau Kira. Ina jijjiga k'ofar. Karar buga k'ofar ne yasa Naseer da bacci ya fara dauka akan Sallaya mikewa da Sauri tare da yin waje. Wani irin fad'uwa gabansa yayi a lokacin dayaji muryar da yaso tuna na waye Amma ya kasa tuna Mai muryar sai kiransa take Tana yazo ya taimaka Mata. Gadan gadan ya nufi kofa. Hajara ta Dago manyan idonta ta watsa Masa shi kuwa Naseer ya tsaya cak Yana Dan addua a Ransa a idonsa sai yaga kamar ba Hajaran ba wata hallita ce zaune Mai ban tsoro. Da hannu ta nuna Masa d'akin shi kuwa ya juya da Sauri ya koma d'akinsa. Hajara kuwa ta mik'e ta nufi kofar tana bud'ewa Naeema ta fado jikinta sabida tsananin tsoron Magen daya nufota Yana Dab da Isa wajenta taji an bud'e k'ofar. Wani irin kallo Hajara ta hau Mata Naeema kuwa ta sunkuyar dakai ta na bata hakuri idonta a rufe Gam Sabida tsoron Hajaran Ji nayi kawai ta finciki hannuna tayi dakina Dani. Muna shiga ta watsar Dani tana hucci ni kuwa na rungume Nadiya gam jikina na rawa addua kawai nake a raina. Umma ta Dade tana kallona kafin naji ta juya ta fita tare da bankomin k'ofar. Dan yanda ranta ya b'aci ba a iya duka zata tsaya ba sai ta raba Naeema da ranta sai dai lokacin yin hakan baiyi ba. Ni kuwa Tana fita na shige bandakina da Sauri na daura alwala Nazo na tada sallah Dan nasan bazan iya bacci ba har yanzu Ina hango katon bakin magen Nan a idona. Ina Kan Sallaya bacci ya daukeni bansani ba. Naseer kuwa Yana shiga d'akin ya rik'e kansa Gam Sabida mugun ciwon da yake masa muryar Naeema kawai yake ji a kansa tana kwalla Masa Kira sosai yake so ya tuno Mai muryar matsawa.kansa da yayi da San tunawa ya haddasa Masa mugun ciwon kai. Shi kansa yasan ba daidai yake ba ya rasa Mai ke damunsa ya Dade a Haka kafin bacci ya d'auke shi batare da.yasani ba *Mafarki* Naseer akwai aiki a gabanka idan baka dage da Addu'a ba bacci Bai ganka ba Naseer ka tashi ka gana da mahallicinka ka ware murya ka fara karatun Qurani a gidanan matarka na bukatar taimakon ka. Murya kawai Naseer Yaji Bai San Wanda ke Masa magana ba da sallati ya tashi mafarkin na sake dawo Masa kamar a gaske. Da Sauri ya mik'e ya shiga bandaki ya d'aura alwala yazo yayi kyakyawan Sallah raka'a biyu Yana iddarwa ya jawo Qurani ya Ware muryarsa ya fara karanta Ali Imran dayake dare ne take muryar sa ta karade ko'ina. Hajara dake zaune a d'akinta tana ayyana mugayen abubuwa kuwa ta mik'e zumbur tayi waje da saurin ta jikinta na d'aukar zafi..........[6/26, 3:25 PM] +234 803 635 0240: *NAGA TA KAINA* *NA SADNAF*🌸🌸 ®️ *_PURE MOMENT OF LIFE WRITERS_* _{We Don't just entertain nd educate we also touch the heat of readers P.M.L}💪🏻_ *Free Novel* *Page 7* Salon da Naseer ya b'ullo dashi na karatun dare ba karamin dagawa Hajara hankali yayi ba Dan Naseer tunda yayi wanan mafarkin ya zage damtse wajen kusantar Allah. Sosai ya fara Dan jin canji a jikinsa duk da har lokacin ya kasa tuna Naeema Sabida ba karamin aiki sukayi a kansa ba. Koda aikin da sukayi Masa ya dauko hanyar warwarewa daya ci abincin da Hajara ke tilasta Masa yaci daya Sha barbaden magani sai aikin ya cigaba da tasiri akansa Hajara da Yan kungiyanta sosai hankalinsu ya tashi da yanda Naseer ke neman zame musu barazana Dan Ta Kai Hajara Bata iya kwanan gidan Sabida kwana da yake Yana karatu Wanda idan tsautsayi yasa ta kwana a gidan komai na iya faruwa babann tashin hankalinta Bai wuce Kar aikin data Masa na manta Naeema ya wargaje ba. Bata da burin daya wuce har ta Gama da Naeema Kar Naseer ya dawo hankalinsa. Sanin idan Hajara ta b'ata Rai Naseer Kan shiga tashin hankali Dan sosai yake Mata biyayya Kuma bai San b'acin ranta. Magani Shugabarsu ta Bata Wanda zata na zubawa Naseer abinci a ciki da indai ya Kai abincin bakinsa toh duk jikinsa zai mutu bazai iya aiwatar da komai ba Daga Nan ma bacci Mai nauyine zaiyi awon gaba dashi. Da Wanan salon suka samu Naseer ya daina karatun daren Dan Da farko da Hajara ta bashi abincin dage mata yayi da ya koshi duk da yana tunanin Hajara bazata iya cutar dashi ba Amma abincin da take bashi zuciyarsa Bai kwanta da abincin ba shi ba yaro bane Dan abinda yake gani a abincin da taste din abincin na nunawa Abu aka saka a abincin. Har a lokacin ya kasa tuna Naeema Amma idan zai kalli Zahira da ba Inda ta baro Mahaifiyarta sai yaji Yana San tuno Naeema Inda Yana matsawa kansa da tunanin kansa zai hau ciwo. Naeema Tun da mukayi rigama dasu Safiyya babu Wanda ya Kara kallon Inda nake da Umma Wanda hakan ya balain bani mamaki Dan na d'auka washegari Umma zata sakosu a gaba su nada min duka ga mamakina babu Wanda ya kalli ma d'akin da nake da farko a tsorace nake Ina tunanin bazasu shareni a banza ba kila akwai wani mugun abinda suke San kulla min. Hakane yasa na dage da Addu'a Ina gayawa Allah Dan zuwa yanzu da cikina yake neman shiga wata goma Sha daya na balain fara tsorata da haihuwar da banyi ba har yanzu gashi cikin nawa ya Kara tsini ya koma kasan marrata. Abinda ya Kara bani mamaki Bai wuce yanda Aka bar Zahira da Nadeeya suke zuwa wajena har suke kwana ba. Kwana biyar da rigimata dasu na fito daga d'akina Sabida yunwar daya koroni dama bredin Dana d'auko daga kitchen nake ta cancanawa Ina ci da ruwa dazu na cinye ragowar yanzu kuma naji Ina Jin yunwa da biyu na fito sabida na ga ko su Umma zasumin masifa kamar yanda suka Saba Dan Ni tun sanina dasu tsawa da hantara ne a tsakaninmu sai rankwashi da duka. Hannuna rike Dana Nadeeya data mak'alemin tunda Lami ta fasa.mata Kai muka fito Ina Dan Jin fad'uwar gaba. Duk suna zaune a Palo suna kallon Indian film Nagi Fitowa ta yasa Umma ta juyo ta zubamin Ido Ni kuwa jikina ya hau rawa Dan tun lokacin Dana dawo ta saka wanan bakar doguwar rigar bamu kara haduwa ba sai yanzu. Tsintar kaina nayi da nufar wajenta. Ina zuwa na zub'e a gabanta Akan gwiwata na hau hawaye. Bata cemin kalla ba in Banda wani irin kallo da take Bina dashi tana jifana da wani irin murmushi daya saukarmin da wani irin tsoro da fad'uwar gaba Hajara kuwa kallon gawa kawai take wa Naeema Dan a yanda suka tsara Naeema saura Mata sattika biyu ko.uku ta bar duniya abinda basu sani ba shine ran Naeema ba ahannunsu yake ba a hannun Allah yake. Cikin kukan da bansan d'annewa nake ba na rik'e kafar Umma na fara magana Ina "Umma Dan girman Allah ki Yi hakuri ki yafemin idan laifi na miki Umma banida kowa sai ku ke nake wa kallon iyayena da suka ragemin Umma Mahaifina da Mahaifiyata sun tafi sun barni yayana shima ya tafi ya barni banida kowa sai ke sai Naseer da yarana Umma idan Wani Abu nake yi da bakiso Dan Allah ki gayamin wlh xan daina wlh bazan sake ba Umma duk abinda Kika Sakani zan Miki Umma Dan Allah ki rik'eni tamkar su aunty Safiyya insha Allahu zan bauta Miki na miki biyaya kamar yanda nake yiwa iyayena Umma ki taimakamin Dan girman Allah wlh banida kowa sai Allah sai ku" Kasa cigaba nayi da Magana sabida kukan dayaci karfina na rik'e kafar Umma Gam Ina cigaba da kuka abinda bansani ba Umma ita Bata San wani Abu tausayi ba ballantana tasan yanda yake tsugunnawan da nayi agabanta Ina rokonta ita hararo gawata take a kwance Sabida tsananin Tsanar da tamin. Irin ruk'on dana yiwa kafarta Yasa ta janye kafarta ta Dago hab'ata ta zuramin Ido cikin wani irin murmushi da idan tamin gabana ke tsinkewa banga alamar alheri a Fuskarta ba sai Sharri. "Bakimin komai ba Naeema bana sanki ne kawai Sabida San danaga d'ana na miki da har ya kasa b'oyuwa Naeema tun Kafin ki haifo wanan er Taki Mai zubin Aljannu na baki shawara da idan kin haihu ki saka Naseer ya sakeki wata itama tazo taci rabonta Kika k'i Naeema Kika min taurin Kai Kika ja Dani ba abinda ban miki ba Dan ki rabu dashi Kika k'i Kika sake haihuwa alamar akwai abinda kika tak'a Dan Haka nayi abinda zanyi ke gaki D'ana tare aka haifoku duniya bazaki iya rayuwa idan babu shi ba nayi abinda zanyi to nayi abinda zanyi Naeema ki haihu nagani ki tashi ki bani guri yanzu Zaki iya duk abinda ranki keso bazan hanaki ba Dan na d'an lokaci ne" Umma tace tana Kara min wani irin murmushin daya sa na Dora hannu a aka na fara kuka. Tuni na nemi yunwar da nakeji na rasa yau kalaman Umma sun tsoratani sun saka min balain fargaba da na hau nadamar Mai ya hanani tafiya lokacin da na haifi Zahira a Palo duk suka watse suka barni. Ni kuwa Jin zazzabi na neman rufeni sabida tashin hankali yasa na rarrafa na shiga d'akina. Ina kwanciya wani irin Mugun zazzabi ya rufeni. Nadeeya da Zahira kuwa na gefena suna ta min Sannu. Bansan ya akayi bacci ya d'aukeni ba A cikin baccin da nake Naga kamar mahaifiyata ta shigo d'akina ta tsaya daga bakin kofa tana kallona tana ta hawaye Ni kuwa sai mik'a Mata hannu nake Akan ta tafi Dani ita kuwa ta ringa girgiza min Kai sosai nake ta kokarin mik'ewa Dan naje gurinta naji jikina yayi balain nauyi na kasa tashi a Haka na zuba Mata Ido Ina kuka tana kuka sai gani nayi ta nufi dakalin dake tsakar gida ta d'au buta ta hau alwala tana gamawa na ga ta shimfida Abu ta tada Sallah tana iddarwa ta daga hannunta sama tana ta maganar da ba jinta nake ba tana ta hawaye sai jijjga hannunta take alamar rok'on Allah take. Idona na bud'e a hankali sai Dana kwashi Sakani nasan Ashe mafarki nake ba da gaske bane mafarkin Nan da nayi kamar ba mafarki ba. Yanda naji jikina yamin nauyi a mafarki yasa na fara k'ok'arin mik'ewa sai dai me Ina duba jikina Naga duk na kumbura kamar wacce aka hura k'afafuna ma sunyi wani irin nauyi da kumburi jikina yayi wani irin Haske Kamar wacce Bata da jini. Take maganganun da Umma tamin dazu suka fad'omin mafarkin danayi da Mahaifiyata tana hawaye tana rokon Allah a mafarki shima ya fad'omin. Girgiza Kai kawai nake hawaye na zubomin Ni nasan tawa ta zo karshe mutuwa zanyi haihuwa da Umma take ta cemin nayi tagani Ashe mutuwa zanyi bazan haihun ba mutuwar da zanyi Ashe shiyasa Naga Mahaifiyata a mafarki tana kuka tana rokon Allah. Kuka na fara sosai Ina tausayawa kaina ganin ban shirya ba mutuwa tazo min tausayin yarana da zan tafi na barsu a hannun Umma kawai ya balain Sakani kuka banso a yanzu zan mutu ba naso Na haihu Naga abinda ke cikina inkare yarana daga sharrin Umma da yayanta naso nasake ganin Naseer muyi magana kafin na mutu naso Na samu ilimi da zan San Mahallicina Sabida na bauta Masa na samu guzurin da zan tafi kabarina. Kuka nake sosai Ina Kara kallon jikina dake ta kumbura kamar Ana hura min iska. Hannuna kawai nauyi yayi min Kamar dutse ballantana na iya daga jikina na tashi nayi alwala nayi Sallah idan akwai abinda nake San Yi yanzu bai wuce nayi Sallah ba inama inada ilimin addini inama yanda Naseer ya iya Karatun Qurani dake balain Sakani nutsuwa idan Yana karntawa da yanzu na karanta naji nutsuwar da zanyi addua na roki Mahallicina ya kularmin da yayana dan shi kadai gareni yanzu. Ni nasan mutuwa kawai zanyi daga yanda nake ta kumburan Nan Ashe Umma tasan kasheni zatayi shiyasa kwana biyu ta shareni ko Mai nayi Mata haka da take ganin kasheni shine mafita a gareta. Bansan tsawon lokacin Dana d'auka a kwance a Haka ba ko kaina bana iya dagawa ballantana na kalli window naga ko dare yayi. Sallatin da iya shi na iya da fatiha da iklas kawai nake yi a zuciyata Dan nasan kowane lokaci zan iya tafiya yayana dake ta bacci a gefena nake wa kallon tausayi Ina hawaye. Yanayin danaji garin ya dau shiru sosai sai Haushin karnuka sama sama yasa nasan dare yayi sosai ko karfe dayan dare ko biyu. K'ofata da aka bud'o yasa na kalli bakin kofar. Umma ce ta shigo cikin jajjayen Kayanta hannunta d'auke da wani bak'in tunkunya an rufeshi da farin kyalle Fuskarta kuwa d'auke da murmushi. Kallonta kawai nake hawaye na gudu a fuskata na rasa Mai nayi Mata rayuwa ta tsaneni Haka. Ajiye tunkuyar tayi bakin kofa ta karaso kan gadon cikin murmushin daya bayyana hakoranta. Tace "Kai da wuri Haka aiki ya fara ci lailai Shugaba aikinta yayi kyau Nan da wani satin Ana Nan ana zaman makoki Naeema Kinga illlar taurin kai ko toh Allah ya jikanki. Daga Haka ta koma wajen data ajiye tukunyar ta tsugunna a bakin kofar Naga ta Ciro wani Abu kamar Sand'a ta fara taune kasar bakin kofar. Nidai Ido kawai na zuba Mata Ina kallonta Tana Gama hak'a kasar ta d'auko wani Abu Mai siffar mutum mace da ciki ta zura hannu ta d'auko farin kyalle ta nanade abin dashi ta zura a Ramin ta saka kasa ta rufe tana gamawa ta juyo ta kalleni ta sakarmin murmushi ta d'auki tukunyarta tayi waje tare da rufemin kofa Tana fita Naga na cigaba da kumburi jikina na wani irin rawa Rufe idona nayi na tuno iyayena na tuno fuskar Naseer da rabon Dana saka shi a idona da ganin danayi Masa na karshe ta gefen idona hawaye ya ringa zubomin inajin idona namin nauyi shima sabida kumburin danayi Sallati kawai nake Ina jiran mutuwa tazo ta d'aukeni. Naseer A ranar shima wuni yayi da zazzabi a jikinsa gabansa na balain fad'uwa hakan da ya gani ne yasa ya nufi wajen wani Sheik Musbahu daya zama babban mallamin da Mallamai ma suna zuwa wajensa daukar karatu. Da Magriba Naseer ya Isa Massallacin sa da mutane ke cike suna sauraran tafseer daga wajen Mallam Musbahun Waje Naseer shima ya samu ya zauna ahaka har sukayi Sallar Ishai Wajen takwas da rabbi aka Dan watse daga Massallacin ya rage daga Mallam Musbahu sai wasu guda biyu da Naseer. Naseer shi dai shiru kawai yayi kamar mara lafiya aka kawo abinci daga gidan Mallam Musbahu suka had'u suka ci. Anan Musbahu ke fad'a musu zasu iya tafiya shi a Massallaci zai kwana sabida akwai wani addua da yake so yayi. Naseer da bayajin zuwa gidan shima da Sauri yace shima bazai je gida ba zai kwana a Massallacin haka ma sauran biyun Ahaka suka fara adduoi da karatun Qurani Naseer kuwa ya balain dagewa ko kad'an bacci Bai zo Masa ba. Wajen karfe biyu bacci ya dauki Mallam Musbahu da ke rike da Qurani. A hannunsa. Ko minti goma baiyi da fara baccin ba ya farka da sallati ya Ajiye Qurani a gefensa ya kwanta a hannun Dama bacci ya Kara daukarsa. Kwanciyarsa da minti goma ya sake farkawa Ya Kara juya kwanciyarsa ya sake farkawa da sallati a bakinsa. A hankali ya Kai kallonsa Kan Naseer dake ta karatun Qurani ya zuba masa Ido Yana kallonsa tare da tuno mafarkin da yayi . Bai ce komai ba ya mik'e ya fita waje ya daura alwala ya dawo ya tada sallah sai daya jima Yana sallahn yaja manyan adduoi. Tare da yin istihara. Wajen karfe ukun ya Gama ya kalli Naseer da ya Ajiye Quraninsa a gefe ya mik'e Yana Shirin tada sallah. Gyaran murya yayi ya kirashi Naseer kuwa ya nufi wajensa ya zauna ya tankwashe kafarsa Yana kallon Mallam Musbahu. "Ina iyalinka take Mallam Naseer"? Wani dum Naseer Yaji a kansa kalmar iyali na Masa wani iri a kunne. "Iyali"? Naseer yace shima cikin tambaya. "Ee Ina nufin Ina matarka take"? Wani irin dum yaji kansa ya Kara Masa ya rik'e kansa da hannu biyu kalmar matarsa na amsa kuwwa a kunnensa. "Baka San Inda matar taka take bane"? Naseer shiru yayi yana so yayi tunani take fuskar Naeema ta hau gilma Masa a Ido. "Matarka na da ciki ne"? Kalmar da Musbahu ya sake jefawa Naseer kenan. Inda kalmar ta tarwatsa duk wani shiri da akayiwa Naseer. Naseer ya mik'e zumbur Yana kwala Kiran sunan Naeema tare da tuna karshen ganin da yayi Mata a dakinsa tana Masa zancen cikin dake jikinta da take fatan ya kasance namiji Mai Kama dashi. Murmushi kawai yayi Mata ya rungumeta yayi waje da Sauri sabida Latin da yayi karshen ganinsa da ita kenan sai yanzu daya dawo hayyacinsa. Naseer hankali a tashe ya fara k'ok'arin yin waje still Yana Kiran sunan Naeema. Mallam Musbahu kuwa ya jawo hannunsa ya zaunar dashi. Yana "Alhamdulillah daka dawo hayyacinka dazu Allah ya nuna min a mafarki a ciki dalibai na matar wani a cikinsu ta rasu da ciki munje mun binneta da zamu dawo sai na juya na hangoka a Kan kabarin kana ta kuka sau Uku nayi mafarkin a jejjere hakane yasa nace Bari dai nayi istahara sai Allah ya nuna min matarka tana d'auke da tsohon ciki shaidanun mutane zasu kasheta Amma mutane zasu dauka da tazo haihuwa ta mutu yanzu Haka kwana bakwai ya rage su cimma burinsu Dan Haka zan baka adduar da zakayi na kwana bakwai a ranar da zaka cika kwana bakwai kana adduar a ranar ka siyi tunkiya Mai tsohon ciki da ta Isa haihuwa itama sai ka yanka ta ka binne insha Allahu a ranar matarka zata haihu lafiya batare da ko ciwon Kai ba Amma fa daga yau karka sake sake irin wanan Dan kana dab da rasa matarka kaje idan matarka ta haihu ka dawo zan baka wasu adduoi Allah ya Dora ka akan makiyanka Dana matarka. Naseer dak'yar ya tsaya Mallam Musbahu ya nuna Masa adduoin cikin Quraninsa tsabar matsuwa da yayi yaga Naeema. A cikin Daren kafa ba takalmi hankali a balain tashe da gudun balai Naseer ya dauki hanyar gida kuka kawai yake Yana tuno maganganun Mallam Musbahu. Ki yafemin Naeema wlh bana cikin hankalina shine kalmar da yayi ta fada har ya Isa k'ofar gidansa. Bai tsaya ma kwankwasa k'ofar ba yayi wa k'ofar wani irin Bugu ya fada palon hajara dake zaune a Palo da tukunyar kasarta tana ta murmushin cikar burinta ta mik'e da Sauri tana kallon Naseer daya fad'o palon kamar an jefoshi. Naseer ko kallonta baiyi ba ya nufi d'akin Naeema aguje Yana kwalla mata Kira. Ihu Hajara ta saka ta Sha gabansa hankalin ta a balain tashe adaidai lokacin da tukunyar kasr ta fado kasa ta tarwatse shi kuwa Naseer da idonsa ya rufe ya ture Hajara data Sha gabansa ya banka k'ofar d'akin Naeema ya tsaya a bakin kofa yana kallon Naeema data kumbure kamar ba ita ba zubewa yayi akan gwiwarsa jikinsa na kwasar wani irin rawa. Kamar a mafarki Naga Naseer ya banko k'ofata ya tsaya a bakin kofa yana kallona............. Duka page dinan wlh babu fiction [6/26, 3:25 PM] +234 803 635 0240: *NAGA TA KAINA* *NA SADNAF*🌸🌸 ®️ *_PURE MOMENT OF LIFE WRITERS_* _{We Don't just entertain nd educate we also touch the heat of readers P.M.L}💪🏻_ *Free Novel* *Page 8* Da kumburarren Fuskata nayi murmushin tare da Kara rufe idona ganin Fuskar Naseer da nake tunanin a mafarki yazo min Dan Ni nasan babu yanda za'ayi Naseer ya zo Inda nake naso ace na ganshi na bashi amanar 'ya'yana. Zuwa yanzu farinciki barin wanan azababen rayuwa dana tsinci kaina nake Ina Kuma bakin cikin rabuwa da Nadeeya da Zahira ko ya rayuwarsu zata kasance bayan Raina. Gunjin kukan Naseer ne ya saka na Kara bud'e idona na kalli Naseer dake durk'ushe a bakin kofa jikinsa na rawa ko ta Ina hawaye na zubo masa. Umma kuwa Tana daga bayansa hankalinta a balain tashe sai rawa jikinta yake tana Kiran sunan Naseer da k'arfi Dan Had'uwar Naeema da Naseer na nufin duk aikin da tayi akansa ya wargaje ita kanta Naeema duk Shirin da tayi akanta wargajewa zaiyi Dan tasan Naseer sai yayi tsayuwar daka akanta. Gashi tukunyar da ta tsaface mutane da Dama ya fashe Wanda hakan ke nuni duk a yau zasu dawo hayyacinsu waye ya Mata wanan danyen aikin Naseer ya dawo hayyacinsa Bata da burin daya wuce janye Naseer Kar ya Kai ga isa wajen Naeema dan ita tasan wahalar da ta Sha kafin ta iya shiga tsakaninsu da iya karfinta ta cigaba da Kiran sunan Naseer. Ni kuwa ganin Naseer na ta kuka Yana kallona tare da Kiran sunana yasa na d'an runtse hannuna sabida Naga kodai ba mafarkin nake ba. Ganin tabbas ba mafarkin nake ba yasa naji wani irin hawayen farinciki ya zubomin da Allah ya amsamin addua ta da zan Kara ganin Naseer na bashi amanar yayana kafin na mutu. Ganin Naseer bashida niyyar tasowa sai sharbar kuka yake Yana Kiran sunana yasa na gwada magana "Naseer karaso gareni Dan Allah na baka amanar Zahira da Nadeeya kafin na mutu" Naseer mik'ewa yayi Yana Jin kafafunsa kamar bazasu d'aukeshi ba halin da yaga Naeema a ciki ya balain daga Masa Hankali yanzu Naeemarsa ce ta dawo haka. Duk tsawon lokacin Nan tayaya take rayuwa a Haka ita kadai anya ya rik'e amanar da Iyayenta suka bashi kuwa Ina hankalinsa yake duk lokacin Nan ya iya manta matarsa uwar yayansa. Kuka yake sosai jikinsa na rawa yanda ta kumbura yasa hankalinsa ya balain tashi a Haka ya Isa wajenta. Tun kafin Naseer ya karaso wajena wani irin kuka ya k'wacemin sai da mutuwa tazo min Naseer zai zo wajena Mai nayi Masa Haka ya watsar Dani. Hannuna daya ruk'o cikin nasa hawaye na ta zubar Masa yasa na fara magana Ina "Haba Naseer Mai nayi maka Haka Dana cancanci Haka daga wajenka? Mai nayi maka da zafi Haka Naseer da zaka watsar Dani bayan kasan banida kowa sai Allah sai Kai idan wani Abu ma nayi maka Naseer Mai yasa bazaka gaya min na nemi yafiyarka ba Naseer kasan rayuwar da na ringa Yi kuwa a cikin gidanan sai daka ga mutuwa tazomin zaka zo Naseer" "Bazaki mutu ba Naeema insha Allahu bazaki mutu ba yanzu na dawo gareki Naeema wlh duk abinda ya faru ba a cikin hayyacina nake ba Naeema ke Mai bawa wani labarine wlh ko dabba bazan iya cutar dashi ba ballantana ke da Kika kasance rabin rayuwata wlh Naeema sai a yau na dawo hayaccina wlh duk tsawon lokacin nan kaina a juye yake Dan Allah ki yafemin Naeema" Mai ya kumburaki Haka Naeema Mai ya Sameki Haka? Innalillahi wa Inna ilaihi rajiun Innalillahi wa Inna ilaihi rajiun"? Kawai Naseer ke iya maimaitawa Yana tattab'a jikin Naeema dake kumbure. Cikinta ma yayi wani irin tsini da kumburi kamar zai fashe "Naseer ga amanar Zahira da Nadeeya Nan Dan Allah ka Kular min dasu karka Bari a cutarmin dasu Naseer mutuwa zanyi" "Insha Allahu bazaki mutu ba Naeema Zaki samu lafiya insha Allahu yanzu ba abinda zai Kara samunki Ina Nan tare dake Zaki haihu lafiya kinji Naeemata" Girgiza Kai kawai nayi Dan ni nasan Mai nakeji a jikina. Naseer da Sauri ya shiga band'aki ya d'aura alwala ya fito ya shimfida Sallaya dama da akwai Qurani a d'akin ya bud'e ya tadda sallah ya fara adduar da Mallam Musbahu yace yayi sai da ya kusa awa a tsaye baiyi rukuu ko Sujadda ba Haka ake yin adduar sai da ya fara Jin Kiran Sallahr asuba yayi ruku'u da Sujjada yayi ta kaiwa Allah kukansa Yana nemawa mahaifiyarsa Shiriya da yafiyar Allah. Ni kuwa kasancewar Naseer a d'akin da Karatun Qurani da ya fara Yi ya Sanya min wani irin nutsuwa bansan lokacin da bacci ya d'aukeni ba. Naseer kuwa kasa ma fita massallacin yayi a d'akin yayi Sallahr Asuba daya iddar kuwa ya cigaba da Addu'a da Mallam Musbahu ya bashi. Sai daya Gama wajen karfe bakwai ya bar Kan Dadumar ya kalli b'arin da Naeema take Yana Jin wani irin tausayinta Zahira da Nadeeya daya ga sun tashi yasa ya karasa Kan gadon ya sauko dasu. Ya zauna a Gefen Naeema da har a lokacin a kumbure take ya fara totofa Mata adduoi Yana shafe Mata jikinta shi kansa yasan wanan kumburin ba na lafiya bane. Ya dade Yana tofa mata adduoi kafin ya rik'e hanunsu Zahira yayi waje sai a lokacin Hajara ta fado Masa ko Ina tayi oho. Bai kalli ma Inda d'akinta yake ba ya shiga dakinsa yyi wanka a gurguje yayiwa su Zahira brush ya fito ya shiga kitchen ya had'a musu breakfast dayake ba abinda Naseer bai iya ba Har a lokacin baiji motsin kowa ba Yana gamawa ya fito daga kitchen din tare da breakfast din daya had'a ya nufi d'akin Naeema ya Ajiye ya had'awa Su Zahira tea har a lokacin Naeema bacci take hakan kuwa ya Dan kwantar Masa da hankali ya Ajiye abin karyawar ta a Gefen gadon ya fito waje. Duk abinda Hajara zatayi Masa bazai tab'a iya canzata ba itace dai Mahaifiyarsa Bai Isa yayi fushi da ita ba. D'akinta ya nufa ya tura k'ofar yaga ba kowa har su Safiyya ma Bai gansu ba hakane yasa ya fara mamakin Inda suka kwana ba Inda Bai duba ba Bai gansu ba. D'akinsa ya koma ya dauko radionsa da cassette din dake d'auke da Karatun Qurani izzu Sittin ya jona radion ya saka cassette din aciki tare da kunnawa. Take Suratul yunus ya fara tashi ya karasa wajen Naeema ya fara tashinta. Kamar a mafarki naji Ana tashina daga d'add'an baccin daya d'aukeni wanda rabona danayi irin shi zan iya cewa tun farkon Aurena. A hankali na bud'e idona Naga Naseer a tsaye akaina. Na rufe idona na sake bud'ewa Ashe dai a gaske Naseer yazo dakina ba mafarki bane yanda gari yayi haske yasa nasan gari ya waye kuma ban mutu ba kamar yanda nake tunanin a jiya zan koma ga Mahallicina. A fili na fara Hamdala Ina nanatawa jikina dayamin nauyi da nakejinsa a d'ad'aure yanzu duk babu sai kumburin dai da nayi da ban sace ba har a lokacin Shima Naseer Tayani Godewa Allah yake Na mik'e zaune Ina "Naseer ban mutu ba Alhamdulillah" "Karki damu Naeema bazaki mutu yanzu ba insha Allahu. Mik'ewa nayi da Sauri Naseer yayi saurin taroni Yana cemin nayi hankali nace Masa Kar ya damu Sallah kawai nakeso nayi. Sai Dana yi wanka na wanke Bakina na daura alwala na fito na saka doguwar Riga na tadda sallah duk Sallar da banyi ba jiya na Rama na zo nayi Sallah Asuba Ni nasan ikon Allah yasa har yanzu nake rayye. Naseer yana Gefen gado a zaune Yana kallona Yana ganin na iddar ya kawo flask din kayan karyawar gabana ya had'a.min shayi Mai balain kauri ga kwai shima da kaurinsa daya soya. Tankwashe kafarsa yayi ya fara k'ok'arin bani. Ni kuwa hawaye suka hau zubomin Ina ganin Kamar dai mafarkin nakeyi yaushe rabona Dana Sha shayi Haka yaushe rabona Dana ga mijina a d'akina ko Ina Umma take data min adduar Allah ya jikaina Kofin shayin ya Kara dosar bakina dashi. Ni kuwa na kau da Kai Ina "Ina Umma ka shigo d'akina har ka kawomin abincin karyawa"? Wani irin kallo Naseer yayi min Yana "da ba'a baki abincin karyawar ne, "? Ganin yanda idonsa ya kad'a yayi Ja da alamar Kuma dagaske Bai San Ana min horar yunwa ba yasa na karbi kofin shayin daga hannunsa na fara kurba batare da na sake cewa komai ba cikin kankanin lokaci na Gama shanyewa ya Kara hadamin wani na Kara shanyewa. Dauriya kawai yake agabana Amma so yake ya kebb'e yayi ta kukan tausayina. Bakin kofar da Umma ta binne Abu jiya na zurawa Ido inaso nayiwa Naseer maganar binne Abu da Umma tayi Ina tunanin yanda zan Gaya masa da yanda zaiji. Naseer kuwa ganin ta ci abinci ya mik'e Yana Bari yaje ya dawo akwai abinda zaije yayi baxai Dade ba. A tsorace na gwallo Ido Ina mik'ewa tare da waige waige Ina "Dan Allah Naseer karka Kara tafiya ka barni ka tafi Dani duk Inda zakaje ko ka kaini wani wajen. Ido ya zubamin Yana kallona dayaga yanda jikina ke rawa cikin tsoro. Hannuna ya rik'e ya ruk'o hanun Nadeeya da daya hannun yayi hanyar fita daga d'akin damu. Kafin mu Isa bakin k'ofar nayi saurin tsayawa Dana tuna abinda Umma ta binne Ina tsoron na tsallaka Dan abinda ta binnen kamar Mai ciki. Lafiya "? Naseer yace ya juyo Yana kallona. Inda ta binne abin na nuna Masa Ina "akwai Abunda Umma ta binne anan Ina tsoron tsallakawa"? Wajen ya zubawa Ido batare da yace komai ba ya saki hannuna ya dauko wani abin labule ya tsugunna tare da Addu'a a bakinsa ya fara tone ramin. Da addua a bakinsa ya zaro farin abin Yana Jin wani irin nauyi a kirjinsa Wai duk wannan tsafin mahaifiyarsa ce takeyi Bai San lokacin da hawaye ya hau zubo masa ba. Shi kunyar ma Naeema yakeji data San wacece mahaifiyarsa waje yayi da abun ya k'ona ya dawo. Ya rik'e hannuna mukayi waje dasu Nadeeya ya kaimu d'akinsa ya koma ya d'auko radionsa da har lokaci yake karatun Qurani ya Kure volume din radio ya kwantar Dani akan gadon Yana "yanzu Nan zan dawo insha Allah akwai adduoin danakeso na karbo nayi Miki Dan wanan kumburin naki bana lafiya bane kiyi kwanciyarki anan Babu Wanda zai shigo zan kulle ku ta waje idan na dawo zan bud'e ku. Sosai naji na rage tsoron danake Ina kallonsa ya fice daga d'akin tare da kullemu. Yana fita Bai zame koina ba sai wajen Mallam Musbahu Inda ya bashi labarin yanda na kumbura. Shi kuwa ya d'auko Masa ganyen magarya da ruwan zamzam da adduoin da zaiyi a cikin ruwan zam zam din da zai shafe jikin Naeema dashi. Naseer Bai dawo gidan ba sai daya biya ta wajen da ake siyar da tumakai ya siyi wani katon tunkiya Mai dauke da ciki haihuwa yau ko gobe Kamar yanda Mallam Musbahu yace. A hanyar komawarsa gida ya siya musu abincin da zasu ci. Naseer na fita wani baccin ya Kara awon gaba dani Mai dadin gaske. Sai danaji karar bud'e k'ofar na bud'e idona. Tunda Naseer ya dawo Bai Kara fita Waje ba. Adduoi kawai yake Yi da Karatun Qurani Sosai na shiga tausayin mijina Sabida tsayuwar dayake Sha tun dayan dare Haka yake tsayawa da Qurani a hannunsa Yana karantawa duk kafafunsa sun kumbura Kuma nasan duk sabida Ni yake wanan adduar abincin da zamu ci kawai ke fita dashi idan ya kawo Mana sai ya Dora daga inda ya tsaya Nima baa barni a baya ba sosai Nima na dage da Addu'a Akan Allah ya saukeni lafiya duk da na rage kumburin sosai tunda Naseer ya shafamin ruwan zamzam da ganyen magarya. Sosai nake mamakin Inda su Umma suka shiga Dan Ni nasan basa cikin gidan sau biyu Ina tambayar Naseer sai yacemin shima bai San Inda suka tafi ba. Hajara da 'yan kungiyarta sosai ransu ya b'aci da wargaewar da aikinsu yayi tunda suke a kungiyar baa Taba samun wacce ta basu ciwon Kai kamar Naeema ba Hajara kuwa har da kukanta wiwi tana cewa shugabarta tayi mata mumumman aikin da zata kawo karshen Naeema data zame Mata karfen kafa har take neman rabata da Naseer akan ta Naseer ya rufe ido ya tureta. Dayake mugaye ne tuni suka hada k'arfi Dan su kawo karshen Naeema ko ta k'ak'a su kasheta Amma Ina duk aikin da sukayi wargajewa yake sabida karfin adduar da Naseer yake yi. Babu wacce Bata zama miciji da mage dan su kashe Naeema ba Amma suna zuwa gidan suke bacewa Sabida Karatun daya karade gidan. Sosai suka cigaba da gwada saarsu akan Naeema amma duk a banza hakane yasa Hajara fara kukan bakin ciki Dan gani take Yar karamar yarinya Naeema Wai har ta gagareta Sam Bata yarda Allah ne ya shiga lamarin Naeema ba gani take akwai abinda Naeema ta taka shiyasa ta kasa cimma burinta akanta. Sosai tsanar Naeema ya ninku a ranta ta ringa Shan manyan alwashin Halaka Naeema. Naseer kuwa ita kadai tasan Mai zata Masa daya fifita Naeema akanta. K'arfi da yaji suka kasa komawa gidan Sabida adduoi da karatun da Naseer ya dage da Yi daidai da su Safiyya suma ta saka su kungiya Wai duk Dan su ringa taka duk Wanda ransu ke so karsuyi tausayi Kar suyi yafiya. Ranar da ya rage kwana biyu Naseer ya Gama adduar da yake yi da Rana Hajara tazo gidan da su Safiyya data daidai ci Naseer na girki Dan tana ganin komai ta mudubi ta shiga gidan. Fuskarta a balain had'e Naseer na ganinta ya tsugunna ya gaisheta Bata amsa ba ta samu waje ta zauna dasu Safiyya ta kalli Naseer tana "daga yau ban yarda ka Kara kunna wanan radion ba idan ka Kara wlh xan maka baki. Naseer Bai ce komai ba Dan duk yagane matsalar mahaifiyarsa abinda Bata sani ba ko Bai kunna radio ba zai iya karatunsa da kansa. Hajara zaginsa kawai take Tana neman Yi Masa baki Bata da burin daya wuce Naseer yaje Massallaci ta fada d'akin da Naeema take ta caka Mata wukar Tsafi sai dai Kash ba Inda Naseer yaje a ranar Yana d'akin tare da Naeema da yayansa. Sosai Hajara ta ringa neman hanyar da zata cimma burinta akan Naeema amma Naseer bai Bata wanan damar ba. A ranar daya Gama adduar ya faki idon Hajaran ya fita Dan yaje ya yanka Tinkiyar ya binne. Daji ya Kai Tinkiyar ya yanka ya binne. Inda take Naeema ta fara Nakuda gadan gadan ta fara Sallati tana Kiran sunan Allah Dana Naseer da yayanta. Hajara kuwa shigowarta kenan gidan taji muryarta . Dan Bata kwana a gidan indai Naseer zai ware murya yayi karatun Qurani. D'akin Naseer ta lek'a taga Naeema ita kadai. Wani irin farinciki ya lullubeta ta fito da Sauri ta shiga d'akinta Dan ta dauko wukar tsafin ta. Ni kuwa ganin Umma yasa naji duk azbaar danakeji ya d'auke diff daga yanda ta fita nasan zata dawo Kuma nasan zata iya kasheni. Da hanzarin da bansan inadashi ba na bud'e window d'akin da babu bugla a wanan lokacin duk da window yamin kad'an kuma ya danyi sama ahaka na hau danne window na dura kamar ba Mai Nakuda ba Ina dura na gurje a kafata ban tsaya ba na fara gudu. A daidai lokacin da Umma ta shigo d'akin ganin Bata gani ba ta lek'a ta window ta hangoni Ina gudu cikin tsananin bakinciiki tace da k'arfi "Allah ya tsine Miki albarka Naeema....[6/26, 3:25 PM] +234 803 635 0240: *NAGA TA KAINA* *NA SADNAF*🌸🌸 ®️ *_PURE MOMENT OF LIFE WRITERS_* _{We Don't just entertain nd educate we also touch the heat of readers P.M.L}💪🏻_ *Free Novel* *Da farko idan baku manta ba sau uku nace zan ringa posting a sati sabida tight schedules Dina but yanda kuka karbi labarin da Kuma comment dinku akan labarin yasa nakeso na ringa faranta muku yau muka fara page nine Amma I received alot of call akan Anya Haka na faruwa kuwa Anya ba Nigeria film na kwafa ba Kai anya zaa samu mace mara Imani Haka kuwa sai duk dariya ya kamani ai Mai Imani da tsoron Allah zai na ganin kamar mutum bazai yiwu ya aikata Haka ba kamar abin yayi yawa sabida wata data kirani daddare jiya zanyi bayanin nan acikin lavarin Nan na rage halin Hajara kashi hamsin Dan wasu bazasu yarda ba nasani a ranar da Nima Naeema ta fara bani labari wlh Tallahi tana kuka inayi na kusa sati ban dawo daidai ba sunan Hajara ban sakaya ba Amma sunansu Naeema na Dan Sakaya yanda na fara labarin Nan Allah ya bani ikon gamawa shine fatana ku pacigaba da bibiyar labarin kawai*😃😃😃 *Page 9* Ba gabana nake kallo ba Sabida waigen Umma da nake hakane yasa naji nayi Karo da mutum a daidai lokacin da marata tayi wani irin murd'amin k'afata ta rik'e Take na fara zubar da jini guda guda. Na durk'ushe awajen Ina neman taimako. Nasan dai mutane sun kewaye ni Ina Kuma kallonsu dishi dishi Kafin idona ya Kai ga rufewa naji muryar Naseer akaina Yana kwalla min kira cikin tashin hankali. Naseer kuwa Yana binne Tinkiyar yayo hanyar gida da saurinsa Dan Haka kawai yaji zuciyarsa Bata kwanta da barin Naeema ita kadai da Hajara ba. Sauri yake ta zubawa sosai Dan Bai fita da mota da kafa ya fita. Tunda ga bakin kofa gidan ya farajin fad'uwar gaba. Inda ya fada gidan da Sauri tare da nufar d'akinsa daya hango a bud'e. A daidai lokacin da ya shiga d'akin yaji Hajara na tsinewa Naeema albarka da wani irin kaifafen wuk'a a hannunta tana hucci. Cikin wani irin tashin hankali ya je jikin window tare da matsar da Hajara adaidai lokacin da yaga ta bangaji wani ta Fadi kasa. Kwalla Mata Kira yayi ya bar bakin window da sauri Hajara kuwa ta Sha gabansa tana neman hanashi wucewa k'arfi da yaji takesan Naeema ta mutu jinin data hango a kafar Naeema ya balain faranta Mata Rai Bata San wani ya taimaketa. Naseer cikin rufewar Ido ya kwace hannunsa tare da hankada Hajara yayi waje da balain Sauri ya zagaya ta bayan gidan Da gudun balai ya Isa wajen Naeema har wani Mai mota ya tsaya wasu na neman d'aukarta. Da saurinsu ya turesu yana Kiran sunan Naeema cikin tashin hankali ya rungume Naeema Yana "Dan Allah karki tafi ki barni Naeema na shiga uku Umma Mai nayi Miki Haka kike san kashe min farinciki na" Dak'yar mutane suka bambare Naseer daga jikinta suka hau Masa fadar ba mutuwa tayi ba Suma tayi asibiti ya Kamata a kaita Sabida irin jinin da ke ta zuba a jikinta. Naseer Bai iya d'aukar Naeema ba sabida rawar da jkinsa keyi cikin tashin hankali Sam bai yarda Naeema zata rayu ba ganin irin jinin da take zubarwa gani yake kamar Hajara ma ta Samu nassarar caka Mata wuk'ar. Bai ma San lokacin da suka iso asibitin ba sai dayaji mota ta tsaya ya fita da Sauri kafa ba takalmi Allah daya taimaka ma asibitin da suke zuwa ne. Da Sauri aka zo da gadon marasa lafiya aka Dora Naeema akai sukayi ciki da ita. Naseer kuwa kamar ya bisu ciki sai da Wanda ya Kai Su yace ya kwantar da hankalinsa babu abinda zai faru insha Allahu. Kafin Naseer ya hau Masa godiya Dan mutumin ya Masa mutunci ba kadan ba duk motarsa ta b'aci da jini. Tuni Nurses suka rufu akan Naeema tana farfadowa ta cigaba da Nakuda tana Kiran Sunan Allah cikin minti goma ta haifo katuwar 'yarta da kana ganinta zaka San ta kusa shekara a ciki Sabida girmanta. Naeema na Jin kukan jaririyar hawaye ya fara zubo Mata ta daga hannunta sama tana Godewa Allah Bata tab'a tunanin tana rayye zata haihu ba. Tun basu goge jaririyar ba ta mik'a musu hannu ta karbeta. Ta Kura Mata Ido tana Jin kaunar jaririyar na ratsa ta ko ta Ina har hawayen da take na diga a jikin jaririyar Sabida tuna wahalar da ta Sha da cikinta da itama jaririyar ta Sha duk ukubar Nan da aka gana musu Bai sa Yar ta mutu ba Allah yayi sai ta Rayu. Bakinta ta kafa a kunnen jaririyar ta karanta Mata fatiha a kunnenta Dan gani take duk da ba zurfi tayi a ilimi ba fatiha data karanta Mata zai Kare Mata ita daga duk wani sharri ita kanta tasan ba ikonta ko dabararta bane yake kareta daga sharrin Hajara Allahu Arhaman Arahim Al malikul qudusu Sallam shi yake kareta. Mik'a musu Jaririyar tayi ta kwanta tana cigaba da hawaye. Tana Jin nurses din na Kara Mata jini sabida jinin data zubar Suna ta hirar girman jaririyar da kyaunta. Shigowar Naseer Kamar Wanda aka hankado d'akin yasa Naeema bud'e Ido tana kallonsa hawaye na cigaba da zuba a idon ta. Naseer kuwa ajiyar zuciya ya sauke daya ga Naeema ta Haihu lafiya ga jaririyar an kwantar da ita a gefenta. Hamdala kawai yake a zuciyarsa ya karasa Kan gadon a madadin ya d'auki jaririyar ya ruk'o hannun Naeema cikin nasa ya Dora hannunta a saman fuskarsa Dan bayaso taga hawayen dake neman zubo Masa daya kasa rik'ewa. Ya kasa yarda mahaifiyarsa ke San kashe Masa mata har rashin Imani da kiyayyar da Mahaifiyarsa ke yiwa Naeema ya Kai ta nemi d'aukar ranta da tsohon ciki batare da tausayi ba shi kam iya saninsa mata da tausayi aka Sansu tayaya Mahaifiyarsa zata kashe mace Yar uwata da ciki har rashin Imaninta ya Kai Haka har yanzu yana cikin shock din ganinta da wuka Wai to Dama hake take ta yunk'urin kashe Naeema kafin ya dawo hayyacinsa. Wai laifin Mai Naeema tayi Mata haka da zafi da har ya Kai data nemi d'aukar ranta. Naeema kuwa Tana Jin danshin hawayensa a hannunta ta fashe da kuka daga ita har shi babu Wanda yayi magana sai da Naeema ga Gama Dan kanta Ta Kira sunansa tana " "Naseer na rasa Mai nayiwa Umma ta tsaneni bansan Mai nayi Mata ba take San kasheni Cikin Ikon Allah na Rayu har na haihu da kaina Wanda ba Haka Umma taso ba bansan Mai yasa take San rabuwar mu ba Amma Naseer tunda har Umma ta iya d'auko wuka Dan kawai ta kasheni zamana da ita wlh Tallahi hatsarine Naseer inasan na Rayu sabida yayana bazan Rufe idona sabida Kaunar San zama dakai na saka rayuwata a Halaka ba har yaushe zamu cigaba da irin wanan rayuwar Dan Haka Naseer Dan Allah Dan annabi ka sauwake min zan je na nemi Inda zan ringa Koda wanke wanke ne na rik'e kaina tunda banida kowa sai Allah Ni nasan Allah Yana sane Dani na gwammace nayi rayuwa da kowa akan nayi da Umma Naseer Dan Allah ka sauwakemin na samu kwanciyar hankali tunda Umma ta sakoni gaba da Ido daya nake bacci Ina tsoron Mai zatamin yanzu idan tayi nassarar kasheni rayuwarka zaka cigaba dashi Naseer Dan duk San da kake min bazaka bini ba ka hakura ka mata biyayya Sabida na tsira da Raina" Rufe idonta tayi a lokacin da Naseer ya dago jajjayen idonsa Yana kallonta Wanda Hakan ya balain karya Mata zuciya itama duk maganar da take ba kaiwa zuci yake ba itama tasan bazata iya rabuwa da shi ba ta dai gaji ne kawai tana ganin kamar rabuwar tasu shine mafita a garesu. Cikin karyayar murya daya Kara saka Naeema zubar da hawaye Naseer ya fara magana Yana Kara damke hannunsa cikin nata "Naeema Ina kaunarki Ina Kuma San na rayyu dake har karshen rayuwata ba'a San Raina Mahaifiyata ta kasance a Haka ba wanan Ni Kuma shine jarrabawata Kamar yanda Abba Hassan yace daidai gwargwado Ina iya kokarina Dan Naga na Mata biyayya Ina nema mata shiriya a wajen Allah ban tsorata da Umma ba sai Yau Dana ganta da wuka a hannu bansan Umma tayi nisa a tsanarki ba sai Yau Naeema na Kuma rasa Mai Kika mata. Naeema na tsinci kaina a tsaka Mai wuya gefe gaki da kika kasance Rabin rayuwata gefe ga Mahaifiyata da ta kawo Ni duniya Naeema ba rabuwar mu ne alheri ko mafita ba kamata yayi mu hada hannu ki Tayani na samu na cinye wanan jarrabawar karki gujeni a daidai lokacin danake bukatar kafadarki Sabida ki rarrasheni insha Allahu zamu Yi magana ta fahimtar juna da Umma zan Bata duk abinda takeso idan ya Kama ne na mallaka Mata duk dukiyata sabida ta barni na Rayu dake" Tsakanin Mata da miji sai Allah cikin kankanin lokaci Naseer ya shawo Kan Naeema duk da Naeema tasan indai Hajaran data sani ne da Kamar wuya iya magana yasa ta rissina har ta ajiye makamanta. A ranar a asibitin Suka kwana sabida Jinin da aka karawa Naeema da sauran treatment din da akewa Mai jego Ba karamin bacci Mai dadi Naeema tayi cikin kwanciyar hankali Wanda taji inama su dawwama a asibitin Kar su koma gida. Wajen karfe goma Sha daya na safe aka sallamesu bayan ya biya duka bills din Dan daidai da paint dasu always da zani a asibitin suka siya sabida basuje da komai na haihuwa ba. A hanyar komawarsu gida Naseer ya sisiiyi kayan jaririrai da komai da suke bukata. Suna Isa gidan Gaban Naseer da Naeema ya fara balain fad'uwa har Mai taxi ya sauke musu kayansu ya tafi sun kasa shiga gidan Naseer sai da suka iso gidan ya tuna ma da ya ture Hajara data Sha gabansa Wanda hakan ko kad'an Bai Masa dadi ba dak'yar ya tattara courage ya kwashi kayan Ya bud'e gidan ya shiga Naeema na biye dashi a baya rungume da jaririyar a balain tsorace. A hankali Naseer yayi Sallama a palon Yana kallon Hajara dake zaune ita kadai a palon sanye da doguwar rigar atamfa idonta a rufe tana karkad'a k'afa. Kamar Mai neman gafara Haka Naseer ya zauna agaban Hajara Naeema itama ta durk'usa daga bayansa. Naseer cikin muryar da yake tunanin idan yayi magana Hajaran zata iya yafe Masa. "Umma Dan Allah Dan Annabi kiyi hakuri da duk abinda nayi Miki Umma ke Mahaifiyata ce inasan na Miki biyayya da har zai zama silar shigata Aljanna Umma uwa da tausayi aka santa Umma ki tausayamin na samu kwanciyar hankali da iyalina idan wani Abu Naeema tayi Miki Dan Allah Dan annabi ki yafe mata marainiyya ce Bata da kowa sai mu Umma duk abinda kikeso wlh zan Miki Dan Allah ki taimakamin na rik'e amanar Dana d'auka Umma ya zakiji yau idan su Saffiya sukayi aure uwar mijinsu na musu Haka ya zakiji Umma"? "Kul Naseer ka gyara lafazinka ba'ayi matar da zata tab'a min yayana ba babu Wanda ya Isa ya tak'a Safiyya ko Lami idan dai Ina rayye ko da bana rayye zasu tsaya su tsaya da kafafunsu ka daina ma had'asu da Wanan mayyar Naseer bana Santa so nake ka Saketa tun kafin ka rufeni da duka akanta Naseer jiya bangajeni kayi har sai Dana Bugu da bango duk sabida ita" Hmmm Hajara tace tana cigaba da girgiza kafarta Naseer hakuri yayi ta Bata Yana janyo mata ayoyi Yana mata naseeha cikin siga Naeema itama cikin kukan ta ringa Bata hakuri Suka hadu sukayi tayi. Hajara tuna yanda duk yan kungiya suka tsara Mata a jiya yasa ta daure ta saki Fuskarta ta boye fushinta Ta bud'e idonta tana "Naji na hakura Washe baki Naseer yayi cikin farinciki ya fara Mata godiya kamar zai Mata Sujadda. Naeema kuwa fargaba ne ya cikata ko kad'an Bata yarda da hakura da Umma tace tayi ba indai Umma ta Ari irin wanan fuskar ta ba komai to tafi hatsari hakane yasa hankalinta ya kasa kwanciya Naseer kuwa sai washe baki yake Yana murna ya karbi jaririyar daga hannun Naeema ya mikawa Hajara. Shi kansa Naseer sai daya karbe Jaririyar daga hannuna da dan k'arfi Sabida yanda na kamkameta a hannuna kamar na zunduma ihu Haka naji Kamar nace Masa wlh akwai wani mugunta da Umma take had'awa Dan Allah Kar ya Bata yata Amma ba damar nayi hakan. Addua kawai nake a zuciyata akan Allah ya Kare min yata daga sharrin Umma Naseer Bai San waccece Umma ba shiyasa yayi saurin yarda da ita. Karba jaririyar tayi ta zura Mata Ido tana ayyana abubuwa da Dama a ranta kamar ta saka hannu ta shake jaririyar take ji kamar ta zaro wuk'arta daga kugunta ta cakawa Naeema har lahira ahaka ta rik'e jaririyar badan ranta naso ba. Nidai kwanakin da suka biyo Baya duk a tsorace nake da Umma Dan ban ganewa shirun Nan nata ba kwana hudu kenan da haihuwar Ameena da Naseer ya Mata huduba da Sunan Mahaifiyata Wanda hakan ya faranta min sosai sosai nake Jin Ameena a Raina da Naseer yace zamu na kiranta Minal. Naseer tun Yana dari dari da Umma ganin babu abinda ya faru ya saka ya saki jikinsa Yana Godewa Allah da kila Allah ya amsa masa adduarsa Hajara ta hakura. Sosai ya saki bakin Aljihu aka fara shirye shiryen suna har dasu Safiyya da Lami a cikin masu tsare tsaren Sunan. Naeema dai har lokacin hankalinta Sam bai kwanta ba Dan tana ji a jikinta akwai abinda suke San Yi Mata gashi Naseer ya Mata wahalar gani daya doso d'akin Hajara zata ce Mai yakeso Dan jarraba bazai iya kyalleta ba duk da ta haihu. Naseer Bai tab'a kawo komai ba Dan ko kad'an baiyi sake da addua ba. Ana gobe suna da yamma Safiyya ta shigo d'akina da kofi a hannunta Cikin murmushi ta mik'o min tana "ga kunnu Nan Umma tace ki Sha sabida ki Kara samun ruwan no-no". Da Sauri na karba Ina mata godiya a madadin ta fita sai ta samu waje ta zauna. Ni Kuma ko.kadan banji zuciyata ta kwanta da Shan kunnun ba Ni nasan dole akwai wani abu a cikin kunnun Nan babu yanda makiyanka zai tashi dare daya ya dawo masoyinka. "Ki Sha Mana" Safiyya tace Tana Kara murmushi Nima na mata murmushin Ina cigaba da juya kofin a hannuna bazan soma gangancin Nan ba ni nasan Umma Bata Sona ba ynda zatayi ta bani Abu na Sha. "Ko baki yarda da umman bane shiyasa bazaki Sha ba"? Safiyya ta Dan ce a tsawace . Wayyo Allah na Naseer ka kawomin agaji nayita cewa a Raina. Ganin Safiyya ta mik'e na saki kofin kunnun da gangan ya zub'e a kasa. Ga mamakina Yana zubewa ya canja kala. Safiyya kuwa tace Umma ta zubar wlh. Hajara da lami dake bakin kofar da tundazu suke lekansu suka fad'o d'akin Hajara kuwa tsananin bacin rai da bakinciiki yasa ta kasa cigaba da pretending din ta shiga d'akin ta nufi wajen Naeema dake d'auke da Minal ta hau jibgarta su Saffiya na tayata Rik'e Minal kawai nayi Ina ihu Umma kuwa tayi ta zagina tana tsinemin Akan babu abinda bata min ba Amma Dan taurin Kai irin nawa Ina ta ja da ita. Kare Minal kawai nake sabida Kar dukan ya sameta. Umma kuwa ta zage da iya karfinta tana dukana Dan gani take shine kawai hanyar da zai rage Mata abinda takeji a zuciyarta. Basu San Naseer ya shigo d'akin ba sai ji nayi ya Kira Umma cikin wani irin murya Amma Ina Umma idonta ya rufe sai dukana take. Ido rufe ya karasa wajen da muke ya jawo Umma da k'arfi ya wancakalar da ita ya zare belt din jeans dinsa ya hade Saffiya da Lami ya fara dukansu.... [6/26, 3:26 PM] +234 803 635 0240: *NAGA TA KAINA* *NA SADNAF*🌸🌸 ®️ *_PURE MOMENT OF LIFE WRITERS_* _{We Don't just entertain nd educate we also touch the heat of readers P.M.L}💪🏻_ *Free Novel* *Page 10* Ihu Umma kawai takeyi tana Kai wa Naseer duka akan ya cika Mata yayanta Dan duka Naseer ya zage iya karfinsa yake musu ba na Wasa ba. Ni kuwa jikina babu Inda bayamin Zugi kamar fatata zata zagwanye Dan Umma tana da fartuna hakane yasa ta ringa Jan fatata tana mitsini na Minal kuwa sai kuka take Dan ta matsu a jikina Sabida gudun Kar dukan ya sameta. Hajara kuwa ganin idan batayi da gaske ba sai ya lahanta su Safiyya yasa tayi waje da gudu ta d'auko wuk'ar Tsafinta ta fada d'akin tare da nufar wajen Naeema da balain saurinta Dan kashe Naeema ne kawai zai saka Taji sanyi a ran ta tunda sabida ita ake dukan Mata Yaya da ta San baa Tab'a musu irin dukan da Naseer ke musu ba. Ni kuwa Ina ganin Umma ta yo kaina da gudu nayi wani irin tambul na haye tsakiyar gadon tare da kwalawa Naseer kira. Naseer kuwa da Sauri ya Yar da bulalan cikin zafin Nama ya ruk'o kafar Hajara da k'arfi Dan har ta hau kan gadon ita a Dole sai ta cakawa Naeema wuka. Ni kuwa Ina ganin Naseer ya rik'e kafarta na rungume Minal a kirjina nayi waje da Sauri Dan gwara na bar gidanan na shiga duniya dana cigaba da zama da Umma dake farautar Raina jikina sai rawa yake sabida tashin hankali. Naseer kuwa tsananin bacin rai da bangon da Hajara ta Kai shi Yana jawo kafar Hajaran ya Yar ya ya daga hannunsa Sama kamar zai Mareta. Hajara kuwa cikin tsananin mamaki tace "Ni Mahaifiyarka Zaka mara Naseer akan matarka Ni zaka daga hannu kamar zaka Mareni bayan dukan da kayiwa yarana a gaban idona duk akan matarka" Cikin wani irin B'acin Rai da rufewar Ido Naseer ya damko Kafadun Hajara ya fara girgizata Yana "Ki kasheni ki Huta Umma Nagaji da abinda kike min na gaji Mai nayi miki a rayuwata da Kika sakoni agaba Kika hanani sukuni da zaman lafiya da Iyalina Ni kadai ne danki kije ki samu Tijjani ki Masa Haka Mana Mai Naeema ta tare Miki Mai kikeso da ita da kike neman d'aukar ranta Mai marainiyya yarinya Nan ta Miki bakya Jin tsoron Allah ne Umma ki had'u ke da yaranki kuyita dukanta kamar Kun samu jaka karki manta fa itama Yar wani ce Inda Iyayenta sukaje Umma sai kinje kinsan hakkin mutum kuwa Umma? Umma uwa da tausayi aka santa Umma uwa Bata cutar da danta a cikin yayanki Ni kadai kike ware kike takawa yanda ranki keso Ina iya kokarina Dan Naga na Miki biyayya Ina gudun b'acin ranki Umma Mai kikeso Dani so kike sai na mutu yau bakya tunanin Makomar Wadanan Yan iskan yaran naki marasa tarbiyya Kika San hannu wa zasu fada ayi musu irin abinda kikayiwa Naeema Umma mutuwa fa Bata Sallama idan mutuwa tazo Miki akan wanan turb'ar fa"?duk abinda kikeyi fa Allah na kallonki Umma kinyi tsafin kinyi asirin babu abinda bakiyi ba Dan ki kashe Naeema Umma Allah Bai baki Nassara ba duk wanan abin bai Isa yasa ki gane Allah ne ya tsaya mata ba Umma bayan wuyan da kika Bata da cikin jikinta ta haihu da d'anyen jego a jikinta ya kwana shidda da haihuwa Umma sai ku had'u da tsinannu yaran Nan kuyi ta dukanta da jariri a hannunta Umma wane irin Zuciya ne a kirjinki Umma nagaji Umma Nagaji ki kyalleni nayi rayuwa da iyalina cikin kwanciyar hankali Umma Ina daga Miki kafa ne sabida ke Mahaifiyata ce ban Isa na canja ki ba Amma Ina nema miki Shiriya a wajen Allah" Daga Haka Naseer ya juya a fusace ya bar Hajara Da ta daskare a tsaye sabida tsananin mamaki Yana fita Safiyya ta mik'e cikin kuka tana "wallahi sai na Rama dukan da yamin wlh sai na Rama" Tayi d'akinsu da gudu ta d'auko mudubin da aka basu da zasu na d'aukar fansar abinda aka musu wuk'ar Tsafin da itama take dashi ta d'auko ta nuna mudubin dashi take Naseer dake wani irin hucci hannunsa janye da Zahira da Nadeeya ya bayyana. Ta daga Wuk'ar Sama Dan ta caka a kirjin Naseer Hajara ta shigo a guje tare da hangad'ata. Tana "Kina da hankali kuwa yayan naki Zaki kashe" "Ki bani wukana wlh sai na Rama dukan da yamin" Take Hajara ta tuno Sulaiman yayanta data dage akan sai ta Rama Wanda ramawar da tayi sai data Kai shi ga rasa Ransa. Hajara waje ta samu ta zauna tana Shirin magana taga Lami itama ta d'auko nata mudubin ta daga wuka zata caka. Da saurin balai ta wafce mudubin Tana "ku Wai bakuda hankali ne Dan kawai ya dakeku zaku kashe shi bama zanewa ba kamar yanda ya zaneku ga abin kashewa can Baku kasheta ba sai Yayanku. An gaya muku karamin Abu ake d'auko mudubin tsafi ko kun manta dokar ne daga yau Kar wacce ta sake irin wanan gangancin Naseer Kuma ku barni dashi Ni nasan matakin da zan dauka a kansa har Ni ya rik'ewa kafadu yake jijigani kamar 'yarsa har Ni ya d'aga hannu kamar zai Mareni har Ni zai saka agaba ya ringa fadawa maganganu matsayina na mahaifiyarsa duk sabida wanan tsinananiyar yarinya hmmm Naseer Bai San ya tsokanowa kansa tsulliyar Dodo ba Naseer Bai San ya taka wuta ba har Agaban idona ya Fifita matarsa akaina da kanensa har Naseer ya jijigani Ina mahaifiyarsa. Taya ma zan bari ku kashe Naseer yanzu da yake ma cikin Jin dadi Taya ma zan Bari ku kashe Naseer alhalin Bai ga gawan Naeema a kwance a gabansa ba? Tayaya zan Bari ku kashe Naseer alhalin Bai fara dandanar gudansa Yana min irin biyyayar dana keso?tayaya zan Bari ku kashe Naseer alhalin Bai Auri Yar Shugaba ta haifo Mana Sarauniya ba wani irin dariya Hajara tayi ta mik'e da mudubin Lami a hannunta ta karasa gaban Safiyya da Fuskarta ya kumbure sabida duka ta sunkuya ta dauki mudubinta itama ta juya musu baya tana "Naseer zai dawo da kafarsa ya sameni zan girgiza shi tamkar yanda ya girgizani yanzu zan watsa masa farinciki kamar yanda ya watsa Nawa tun lokacin Dana saka ya saki Naeema yak'i Zan kashe Naeema da hannuna ya Kuma ga gawanta a gabansa Naga yanda zaiyi bana San kuyimin hauka shiyasa na karbe mudubin ku Zan dawo muku dashi Amma ba yanzu ba ku tashi ku Dora ruwa ku gasa jikinku Anjima zamu Rama dukan a jikin Naeema Yar gwal da bayaso a tab'a" Daga Haka ta fice daga d'akin. Naseer kuwa Yana barin d'akin Hannun Zahira Dana Nadeeya ya rik'e ya bud'e motarsa ya saka su a ciki ya San Naeema guduwa tayi Amma sanin halin tsoron ta yasan bazata tayi nisa ba. Ransa a balain b'ace yake Yana sake sake a Ransa da irin mahaifiyar da Allah ya bashi ya zama Dole yayi wa tufkar hanci ya gaji Haka nan. Dayake hanya daya ce daga layinsu har titi hakane yasa ya ringa tuk'a motar a Hankali Yana Dan adduoi ko zai Samu nutsuwa har ya bar layin Bai ga Naeema ba a Haka ya cigaba da tafiya Yana ta waige waigen ko zai ganta Amma ga mamakinsa Bai ganta ba anan hankalinsa ya tashi ya fara k'ok'arin juyawa ya koma kafin ya hango ta ta yanki wani lungu tana ta zabga Sauri Minal sab'e a kafadarta. Ko kadan mota bazai iya shiga lungun ba hakane yasa ya sauka daga motar ya rufe yabi bayanta da sauri. Tun Kan ya ci Mata ya ringa kwalla Mata Kira amma taki juyowa sai zabga Sauri take Tana kuka. Gudu ya saka ya Sha gabanta Yana "Wai Ina Zaki ne kike zabga Sauri"? "Naseer wlh Tallahi bazan koma gidanan ba Dana koma gidanan gwara na samu bola na Mana shimfida nida Minal Naseer bazan koma Umma ta kasheni ba nagaji Naseer wlh Nagaji har tsawon wane lokaci Zan ringa tsallaka rijiya da baya wlh watarana zata samu nassarar kasheni kayi hakuri bazan koma ba kaje ka Kular min da Zahira da Nadeeya wlh bazan koma ba" Kuka take sosai Kamar zata shidde ga rigarta data b'aci sabida Mararta dake murd'a Mata. Naseer hannu ya Kai zai kamo hannunta idonsa jawur sabida b'acin Rai shi kadai yasan Mai yake ji da bashida dauriya wlh ba abinda zai saka ya yanke jiki ya Fadi Naeema baya taja da Sauri data ga zai rik'e Mata hannu cikin ihun kuka tace ya kyalleta ita bazata koma ba. Naseer zuwa Lokacin Ransa ya Kara b'aci. Da Karfin tsiya ya rik'e hannunta ita kuwa ta saki ihu tana "Wlh bazan koma ba Naseer wlh bazan koma ba ka cikamin hannu na shiga duniya wlh bazan koma ba Ina koma Umma sai ta kasheni kaga fuskata kaga yanda ta yayakusheni a jikina Dan Allah ka kyalleni karka kaini gidanan ta kasheni"? Sosai hankalin Naeema ya tashi tana kuka tana tirjewa Naseer kuwa ya daka Mata wani irin tsawa daya saka ta nutsu lokaci guda taji tsoronsa ya shigeta lokaci guda Dan tunda take Bata tab'a ganin b'acin Ransa Haka ba "Da wane zanji Naeema da zafin da Umma ta hadamin ko da Wanda kike shirin hadamin yanzu ranki a hannun Allah yake Bata isa ta kasheki ba sai dai idan lokacinki yayi ki wuce mu tafi na bar su Zahira a mota. Da Sauri nayi gaba jikina na rawa dan sosai naji tsoron irin tsawan da Naseer ya daka min. Ahaka nayi gaba muka fita daga lungun har muka Isa mota ya budemin na shiga. Tsoron sa yasa ban Kara iya magana ba sai kuka danake kasa kasa Zahira da Nadeeya ganin Ina kuka yasa suma Suka hau kukan. Naseer Bai ce komai ba ya tada motar muka fara tafiya idonsa ya kad'a yayi ja jijjiyoyin kansa duk yayi rudu rudu ji nake kamar na bud'e murfin motar na fita daga cikin motar na gudu. Nidai nasan yau sunana gawa matsawar na taka k'afata a gidanan. Ban dago kaina ba sai danaji ya tsayar da motar cikin fad'uwar gaba na Dago. Bansan rik'e numfashina nayi ba sai dana ga ba gida muka koma ba a Wani katon gida muka tsaya gaban gidan na dauke da katon Massallaci. Naseer baice min komai ba ya bud'e motar ya fita sai daya Dan kwashi mintina ya dawo ya bud'emin kofa na fito Ina kalle kallen wajen. Ya bud'e bayan motar ya sauko dasu Zahira. Yana rufe motar yayi gaba dasu Zahira na ringa binsa a baya Ina tunanin Ina ne Nan ya kawo mu. A harabar Massallacin Naga ya tsaya a wajen wani daya Sha fararen Kaya gemunsa yayi kasa sosai hannunsa d'auke da carbi fuskarsa nata fitar da annuri. Agabansa Naga ya tsugunna Nima nayi saurin tsuggunawa da Minal a jikina na fara gaishe shi. Cikin fara'a Mallam Musbahu ya amsa Mata gaisuwar tausayin Naeema ya balain rufeshi ganin kankantar shekarunta Amma su Hajara Suka sakota a gaba. Daga zuwan Naseer ya karanta Masa komai in brief Inda yace Masa kansa ne ya kulle shiyasa.yayi.nan dasu. Hakane yasa Mallam Musbahu yace yayi tunani Mai kyau da basu koma gidan ba Nidai sunkuyar da kaina nayi ban Kara dagowa ba Sabida yanda na ga kwarjinin mutumin ya cika wajen. Sunana daya Kira yasa na Dago ya mikomin hannu na mik'a Masa Minal banma San hawaye nake ba sai dayace "Ki goge fuskarki kinji insha Allahu watarana sai Labari babu abinda baya wucewa Allah ya Kara kareki da Karewarsa Allah yana sane dake ki cigaba da Gaya masa rayuwa sai da jarrabawa ke Kuma Taki jarrabtar kenan idan kikayi hakuri insha Allahu watarana sai Labari kinji ko Allah ya Miki albarka ya rayya Miki zuriarki" "Ameen nace hawaye nata zubomin inajin kalmar Allah ya Miki albarka dayace min daya Sanyaya min zuciya Dan rabon danaji kalmar tun iyayena na rayye sosai naji dadin adduoi dayamin. Sallamar wata danaji a kaina yasa na Dago da kaina. Babbar macece zatayi Sa'ar Umma ko ta girmeta sanye da Hijabi har kasa ta rusuna tana "Gani Mallam" Shi kuwa ya nuna mu Yana ta shiga damu ciki Ya Mik'a Mata Minal ta amsheta tana Bismillahi na mik'e na rik'e hannun su Zahira na Dan saci kallon Naseer da ya sunkuyar da kansa ya kurawa waje daya Ido wani irin tausayinsa ne ya rufeni ahaka nayita kallonsa ko zan samu ya Dago Amma har muka bar harabar Massallacin Bai Dago ba. A wani katon daki ta kaimu Ni kuwa nafara k'ok'arin tsugunnawa na gaisheta tayi saurin taroni ta zaunar Dani akan gadon d'akin. Ta kwantar da Minal a gefena ta zaunar dasu Zahira a tsakiyar carpet Naga ta jawo Kular abincin ta zuba musu. Ni kuwa sai godiya nake Mata Ina Jin wani irin niima dake ratsani iskar ma danake shak'a daban yake Dana gidana. Take na fara Jin wani bacci bacci. Fita tayi daga d'akin bayan 'yan mintina ta dawo da ruwan zafi a bokiti ta shige bandaki ta dawo ta d'auko min zani tace na daura na shiga wanka. Kamar kuwa ta San Ina bukatar wankan Dan ban samu nayi ba sabida tsoron barin Minal ita kadai a daki. Da Sauri na mik'e Ina Mata godiya na karbi zanin na shiga band'akin Dan Ina Jin kunyar cire Kaya a gabanta ko Ina Naseer ya samo mutane masu karamci Haka oho yasan duk tsawon lokacin Nan akwai.mutane irin Haka shine Bai kawoni ba ko wanke wanke na ringa musu indai zasu rik'eni a wajensu. Sosai na gasa kaina da ruwan zafi inajin dadin jikina yaushe rabon dana jini a sake haka har na manta inama Naseer ya barni a gidanan da yayana inama mutanen Nan su zama iyayena su rik'eni a wajensu da naji dadi. Duk Inda Umma ta yakusheni na gaggasa Dan kamar ba yakushi ba sabida zafin danake ji gashi jikina yayi rudu rudu abinka da fara ahaka na fito da Daurin kirji. Ina fitowa tana Gama yiwa Minal wanka Su Zahira ma har an musu wanka an canza musu kayan jikinsu an kwantar dasu sosai naji dadin yanda matar tayi Mana da alama itace matar Mallamin. A Gefen gadon ma an ajiyemin kayan da Zan saka da auduga. Godiya na ringa Mata sosai har sai data nuna b'acin ranta. Ina Gama saka Kaya ta turomin flask din tuwon Massara da miyar yauki yaji namomi yaushe rabon Dana samu irin wanan abincin gefe Kuma ga shayi Mai zafi Tana Gama shirya Minal ta ajiyeta a gefena ta fita sabida na sake naci abinci. Banyi falako ba naci na koshi Maganin data bani na ciwon jiki na Sha Ina kwanciya bacci Mai nauyin gaske yayi awon gaba dani Naseer kuwa Yana ganin Su Naeema sun shige gida ya fara kukan bakin ciki Dan sosai yaji kirjinsa ya cushe idan ba kukan yayi ba bazai ji saukin abinda yake ji ba. Mallam Musbahu kuwa Bai Hana shi ba sai daya Gama Dan kansa ya fara bashi baki Yana Masa nasiha da yarda da kaddara da hakuri. Naseer dagowa yayi Yana "Mallam Nagaji inaso na gudu da iyalina ko zan samu kwanciyar hankali hakane yasa Nazo wajenka ka bani shawara wani gari Zan koma" Mallam Musbahu murmushi yayi Yana "ko da baka zo da maganar ba shawarar da nake taso na baka kenan ka koma Garin Kano da zama batare Mahaifiyarka ta sani ba Kar wani Abu ya Kara maidaka gidanan Sabida kaima kasan bazasu barka Haka ba Haka ma matarka. Akwai kanina a garin Kano Yana zaune a goron dutse Zan baka address dinsa kaje ka same shi ya nema maka gidan haya ka fara Kama muku kafin komai ya lafa" "Mallam idan ma na samu gidan siyarwa Zan siya sabida Ina da kudin siyan akwai gidana a Jos Dana siyar wanan Kuma Zan barwa mahaifiyata ta zauna da yayanta Zan Kuma aika Mata sakon kudi idan ta hucce an kwana biyu Zan dawo" Haka kuwa akayi Washegari da sassafe Naseer ya d'au hanyar Kano cikin Sati d'aya ya samu kato gida ya siya ya zuba komai dazasu bukata a gidan a unguwarsu Kanin Mallam Musbahu ya samu gidan shima kanin Mallam Musbahu mallami ne Mai mutunci da dattako Mallam Haruna. Sai da Naseer ya Gama komai ya koma Calaba Dan ya d'auko su Naeema. Naeema A bakin Matar Mallam da nake cewa mama naji Ashe Naseer tafiya yayi Haka kawai naji babu dadi da Naseer bai nemeni ballantana ya gayamin bansani ba ko fushi yake Dani sabida Dan tirjewar dana Masa Akan bazan koma gidan Umma ba. Sosai naji dadin sati dayan danayi a gidan Mama tunanin halin da Naseer yake ciki ne kawai ya ragemin Jin dadi. Har wani Dan kib'ar kwanciyar hankali nayi yayana Suma sun samu gida sai watayarsu suke suna Wasa sosai nake adduar Allah yasa mu dawwama a wanan gidan Dan babu yanda Zan sake komawa gidan Umma na Sha yunk'urin Sanar da Mama halin da nake ciki Koda shawara ne ta bani sai naji na k'asa Mata maganar sai Naga kamar ban kyautawa Naseer ba idan na fadawa wani halin mahaifiyarsa. Da magriba Ina zaune a daki Ina shayar da Minal naji sallamar Naseer a bakin kofa da Sauri na dago na zuba Masa Ido. Su Zahira kuwa suka tafi da gudu Suka rungumeshi. Sosai Naga ya rame yayi baki sai tausayinsa ya rufeni. Sai daya Gama dad'agasu Ya nufo wajen da muke ya sunkuya ya d'auki Minal ya Dan saci kallona sai naji duk ba dadi kamar kunyata yake ji yabi ya canza kamar bashi ba. Gaishe shi nayi ya amsa ya zauna Akan side drawer jikin gadon Ni kuwa na mik'e na fita Waje Dan na d'auko Masa ruwa Ina fita naci Karo da Mama da farantin ruwa har da lemon kwalba da kofi. Godiya na mata na koma ciki na zuba Masa ruwan ya karba ya Sha Ni kuwa nace Masa ya hanya yace Alhamdulillah. Daga Nan yacemin "Gobe ku shirya da wuri zamu dauki hanyar kano. Kamar na tashi na dakka tsalle Haka naji sabida tsananin murna Amma tuna ko da Umma zamu koma Kano yasa nace "Kano zamu koma da zama su Umma fa"? Ambatar su Umma da nayi yasa ya mik'e da Sauri Yana "anan zasu zauna iya mu zamu tafi gwara mu nisanceta kafin Allah ya warware Mana komai" "Allah yasa Hakan shi yafi alheri" Ameen kawai yace ya Ajiye Minal Yana "Bari naje wajen Mallam bamu gaisa bama nashigo. Sosai naji kamar anmin albishir da gidan Aljanna barin garin Calaba da zamuyi mu nisanci Umma Wanda hakan na nufin Zan samu kwanciyar hankali babu Mai kawo min farmaki. Wajen karfe Tara na dare Mallam ya aika a kirani Ina zuwa Naga Naseer a gefensa hadamu yayi ya Mana nasiha tare da bawa Musbahu Adduoi Mai yawa Inda Nima ya bani gajeru da yasan Zan iya haddacewa idan na nace ya bamu shawara da duk da zamu bar garin Nan Kar muyi sake da addua mu zage damtse mu cigaba Dan ko shi daya taimakemu sai da suka so kawo mishi Hari Inda basu San shi ya Riga da yafi karfinsu ba daya shiga bayi aka zo Masa a siffar mage shi kuwa sai daya tabbatar da ya makawa Magen Abu a gadon Baya ga mamakinsa Yana ihu yaji muryar mace. Shi ma yasan da zamanmu a gidan za a Kai ga Haka shiyasa d'akin da aka saukeni ya zagaye shi da Addu'oi da tuni an tab'ani ko an tab'a yayana. Sosai naji Kuma hankalina ya tashi da maganar Mallam Musbahu Inda na fara kuka shi kuwa ya hau kwantar min da hankali. A ranar a tsorace na kwana Washegari da asuba muka d'au hanya...... [6/26, 3:26 PM] +234 803 635 0240: *NAGA TA KAINA* *NA SADNAF*🌸🌸 ®️ *_PURE MOMENT OF LIFE WRITERS_* _{We Don't just entertain nd educate we also touch the heat of readers P.M.L}💪🏻_ *Free Novel* *Page 11* A gajiye muka iso garin Kano da tunda muka iso naji wani sakayau Dani iskar ma garin ya bambanta Dana garin da muka baro. Sosai nayi mamaki ganin katon gidan da Naseer ya siya mana Dan gidan bene ne kasan Kuma shaguna ne da alama sabone fil duk da jikina ba kwari Haka na zage muka gyara gidan washegari nida Naseer. Gidan sosai yayi kyau Dan d'akinsu Zahira ma yafi k'awatuwa duk da ba abinda muka d'auko a wancan gidan Nan ma komai akwai Dan har yafi na gidanmu dake Calabar da yamma mak'ota sukayi ta shigo mana naji dadin shigowarsu sosai Dan da alama suna da mutunci Dan har Dan Tayani sauran aikace aikacen gidan sukayi. Naseer Sam bai wani zauna ba tunda muka dawo ya Kuma canjamin bansan dalili ba Haka kawai naji ba dadin canzamin daya yi hakane yasa na shirya Masa magana idan ya dawo. Wajen karfe Takwas ya dawo Yana dawowa na bashi abincinsa yaci. Yana gama ci naga ya koma tsakiyar palon da wani dogon takarda Yana ta rubutu. Su Zahira sun Dade da bacci Minal kuwa Tana goye a bayana. Nima tsakiyar palon naje na zauna Ina kallon rubutun da yakeyi da nakeso ya Gama muyi magana D'agowa yayi yace min "Lafiya kuwa ko akwai wani matsala ne"? "Aaa Babu wani matsala nadai ga ka canjamin ne tun ranar da abinan ya faru shine nace ko Dan na d'an tirje ranan ne shiyasa kake fushi Dani idan ma shi din ne Dan Allah kayi hakuri. Ajiye biron yayi akan takarda ya murza yatsun hannunsa sai daya d'auki tsawon lokaci ya fara magana "Ba daga ke bane Naeema abinda ke damuna daban tun ranar da muka Samu sab'ani da Umma nakejin ba dadi Umma Mahaifiyata ce ban Isa na canza ta ba nasan daraja mahaifiya shiyasa nake ganin Kamar ban kyauta Mata ba a matsayinta na wacce ta raini cikina har ta haifeni na fada Mata maganganun da basu Kamata ba duk da na baro garin sai nake jin ba dadi sai nake jina kamar a d'ad'aure Kamar Idan na Bata hakuri ta hakura sai nafi samun sukuni bansan mai kika Mata ta tsaneki ba bansan Mai yasa Umma ta Dora Miki Karan tsana ba abinda ke damuna kenan ba wani Abu ba. Da Zan samu Umma ta kaunaceki ta rungume ki tamkar 'yarta Naeema da na fi kowa Jin dadi duk Inda na Kai ga na nusar da Umma ta kasa ganewa yau da ace nasan wani dangin Umma Wanda nasan suna gaba da ita da na Kai kararta wajensu sun mata naseeha k'ila taji maganarsu. Sosai nake ganin ciwon da Naseer yake ji a zuciyarsa da koma waye Dole ya shiga cikin damuwa. Cikin kwantar da murya na fara kwantar Masa da hankali Ina "Addua zamu cigaba da yi Naseer insha Allahu Umma zata Soni za kuma ta kaunaceni duk da munyi nisa ka cigaba da kyautata Mata kana Mata aike idan an kwana biyu sai kaje da kanka" "Hmm abin da Kamar wuya Naeema Amma tunda Kika ce Allah ba abinda baya yuwa ga form nan na karbo Miki na islamiyya Dana Boko kina yin arbain Zaki fara zuwa insha Allah" Kamar na tashi nayita rawa Haka naji da Naseer yace min Zan fara zuwa makarantar godiya nayita Masa shi kuwa ya jawo takarda ya cigaba da rubutu a ciki. Bansan Haka zaman aure yake da dadi ba sai da muka dawo kano da zama bansan Haka ma'auratan da basu had'u da jarrabawa irin tawa suke cikin kwanciyar hankali ba sai da muka dawo kano bansan Haka mu'ammalla da mak'otan arziki yake da dadi ba sai da muka dawo kano Wai nice yanzu Zan kwanta batare da fargabar komai ba Wai nice yanzu Zan shiga kitchen na dafa Mana abinda ranmu keso muci mu koshi batare da fargabar komai ba. Babu abinda Naseer Bai wadata mu dashi ba dan Zan iya cewa a wanan lokacin za'a iya saka Naseer a sahun masu kudin unguwar. Tsabar matsuwar da nayi da na fara zuwa makaranta ko arbain din banyi ba na fara zuwa Dan ba zanyi gangancin Wasa da Wanan damar da Allah ya bani ba inaso na nemi ilimi da Zan kusanci mahallacina sosai na cigaba da Kai Masa kukana. Cikin ikon Allah kuwa da fara zuwana makaranta na ringa ganewa da wuri sabida na saka San koya Raina. Su Zahira ma tuni Naseer ya nema musu makaranta suka fara zuwa zan iya cewa banida matsalar komai sai karatuna Dana saka a gaba da rainon Minal danake. Tsakanina da Naseer kuwa soyayya ce Mai tsafta da girmama juna duk da munyi nesa da Umma Hakan Bai saka mun saki jiki ba addua muka cigaba dayi Dan nima na koyi tashin dare kamar yanda Naseer Naga ya zame Masa jiki. Sosai dawowar mu Kano ya zame Mana alheri Dan bayan sanin kaina Dana farayi ta hanyar cud'anya da mutane na fara Dan samun wayewa da bud'ewar ido ta hanyar muamalla da mutane Dan daga zuwa na makaranta na had'u da wata Aisha da ake cewa mmn Mannir yanda banida ilimin komai hakane ya kasance gareta hakane yasa tamu tazo d'aya da ita abin mamaki har na Kan Dan nuna Mata abinda bata gane ba nacewar da nayi da San koyon ilimin addini yasa nake ganewa Nan da Nan daga kasa aka fara Mana wato fatiha aka ringa had'a Mana da huruf Wanda ya taimakamin sosai wajen gane bak'i. Mmn Mannir gida hud'u ne a tsakaninmu tana da mutunci sosai duk da ta girme min nesa ba kusa ba Amma Haka muke Dan kawancenmu da ita takan Dan fadamin abinda ya shafi rayuwar Aurenta Ni kuwa sai dai naji ta kawai bana iya fadan abinda ya shafeni Dan Ni Dama can Ina da zurfin ciki balle rayuwar gidan Aurena a ganina ba abinda Zan fito na ringa labari akansa bane. Naseer kuwa shagunan dake kasan gidanmu duk sai daya cika su da kayan siyarwa Wanda ya samu wasu suka rik'e Masa shagon a cikin shagunan akwai Inda Nama da kifi kawai ake siyarwa layin namu dayake ba masu siyar da nama da kifi sosai Ake cinikin Nama da kifi inda cikin kankanin lokaci Nan da Nan zai Kare tun Naseer na yanka raguna biyu ya koma Yana yanka Dan Sa Daya shagon nasa Kuma lemuna yake siyarwa akan sari masu kananan shaguna gurinsa suke zuwa siya. Daya shagon Kuma kayan awo ne Kama daga su shinkafa gero dawa wake shima buhu buhu yake siyarwa dawowarmu Kano da wata shidda Naseer yayi wani irin kudi Dan Motocin hawansa sai da suka Kai uku. Har ya Kara siyan wani katon fili a layinmu . Sosai ya daina samun lokacin kansa tafiye tafiyen da yake Yi Bai fasa ba yakan yi kwana uku Haka ko biyar kafin ya dawo. Ni kuwa ba wani damuwa nayi ba sabida karatuna Dana saka a gaba. Har Lokacin ban saki jikina ba Ina Kan addua Naseer da Bai fiye zama ne bansani ba ko ya rik'e addua kamar yanda Mallam Musbahu ya bashi shawara. Sosai nake addua Allah yasa na samu hutu kafin na Kara samun wani cikin Dan a lokacin ba wani sanin tsarin iyali nayi ba. Hutu da Jin dadi sosai ya nuna a jikin Ni da yayana Dan har mota Naseer ya Ajiye da sunana akan duk Inda zani wani yaro matuki dake kasan layinmu ya ringa Kai mu Yana dawo damu duk wata zai na biyansa kudaden cinikin shagon sa kuwa Ni ake kawowa duk ranar Jumma'a wani yaronsa ke had'a lissafin kudin ya Kai banki. Naseer kuwa bud'in dayake samu sosai yasa yake wa Hajara Aiken kudi masu kauri har wasika yake rubuta mata duk da yasan ba ilimi ne da ita ba yasan zata samu Mai karanta Mata wasika ne na neman yafiya da ban hakuri gareta akan tafiyar da yayi batare da saninta ba zai dawo idan ta huce Yana rokonta ta cigaba da saka Masa albarka a rayuwarsa. B'angaren su Hajara kuwa a ranar da Naseer da Naeema Suka bar gidan ta nufi Kungiya dasu Safiyya da sai data zauna ta gasa musu jikinsu da ruwan zafi sosai zuciyarta ke tafasa da irin dukan da Naseer ya musu Inda take Jin da yau wani ne yayiwa su Safiyya Haka ko duk karfinta zai Kare sai ta aika shi barzahu. Da isarsu kuwa ta korawa shugabarsu komai. Take duk suka hau ce Mata Kar ta yarda ta d'au mummunan mataki akan Naseer da Naeema taya zaayi Naseer yayiwa su Safiyya Haka kawai Sabida sun daki Naeema ya zama Dole ko Yaya ne a koyawa Naseer hankali a Kuma dau mummunan mataki akan Naeema tunda a lokacin Bata da tsarki duk abinda aikin da zasuyi akanta zai Kamata Nan da Nan. Take shugabarsu ta d'auko kwaryar tsafinta dake d'auke da wani irin ruwa tayi surutai tana shafawa Naseer da Naeema Suka bayyana lokacin Naseer na gaban Mallam Musbahu Naeema Kuma tana d'akin matar Mallam Musbahu. Cikin wani irin murya Shugabarsu tace ta zama Dole su hukunta Naseer tunda ya tab'a musu Yan kungiya har ya fitar musu da jini wato Safiyya da lami Hajara na Shirin magana Dan tace da a hukunta Naseer gwara a hukunta Naeema Wani irin kallo Shugabarsu ta Mata ta ja bakinta tayi shiru ita kuwa shugabarsu ta daga wani irin bulala dake d'auke da allurai tana Shirin makawa Kwaryar da hoton Naseer ke bayyane har lokacin. Taga Naseer ya bace daga ruwan mamaki ne ya Kamata ta Kara surutan tsafi Amma me hoton Naseer ko na Naeema Bai Kara bayyana ba Dan a lokacin Naseer ya shiga Massallaci Naeema kuwa Tana d'akin Mama dake d'auke da manyan adduoi na tsari a kowane kasurwar d'akin. Duk yanda sukayi Dan su Kara bayyana abin gagara yayi a karshe akan Dole Suka bawa Hajara wani irin tsafi Akan idan taje gida ta zuba a bakin kofa Naeema zata haukace Naseer Kuma sai yanda tayi dashi. Suna komawa gida ta saka bakaken Kayanta Ta zauna jiran dawowar Naseer da Naeema sai dai shiru basu dawo ba Wasa Wasa har akayi kwana uku babu su babu labarinsu ahaka suka Kara komawa kungiya Inda sai da suka buga sosai suka gano Inda Naeema take Da Naseer har tafiyar da Naseer yayi ta mudubi Suka gani. Anan Suka yi Shirin zuwa gidan Mallam Musbahu Dan su Dan tab'a shi sanin Kuma babu Inda zasu same shi batare da su sun fuskanci wani matsala ba sai a bandaki hakane yasa Suka aiki Lami akan taje gidan idan ta samu Nassara akan Mallam Musbahu ta tab'a shi idan Kuma Naeema ce ta kasheta da wuk'ar Tsafi. Lami kuwa jiki na rawa ta zama katon bakin mage ta shiga ta rufin gidan Mallam Musbahu ta tsaya daga wajen window bandaki. Wajen Karfe dayan dare Mallam Musbahu yaga komai a mafarki Dan Allah ya Masa wanan baiwar idan Abu zai same shi zai gani a mafarki. Wajen daya da rabi ya farka Sakamakon fitsarin daya matse shi har zai shiga band'akin ya tuna mafarkin da yayi hakane yasa ya dawo Baya ya d'auki wani katon Sandan daya gani Yana shiga band'akin da Addu'a shiga bandaki yayi Ido biyu da Bakin Mage Yi yayi kamar Bai ga Magen ba ya juya bayansa aikuwa take mage ta fara shirin dirar Masa ta baya ya juya cikin zafin Nama ya maka Masa sand'a kafin magen ya dira ta waje ya Kara mak'a Masa a gadon Baya take yaji ihun mace. Ya fito daga band'akin da Sauri bakinsa d'auke da Addu'a ya zagaya ta bayan gidan Amma Bai ga komai ba baccin da bai koma ba kenan. Ya turare gidan da hayakin daya San basu Isa su Kara dawowa ba Ko kusa da Gidan bazasu iya zuwa ba. Lami kuwa sosai Mallam Musbahu ya sameta a baya a lokacin da ta koma siffar ta ta koma kungiya Inda Sam Bata iya mik'ewa tsaye. Sosai hankalinsu ya tashi Yan kungiya duk dabarun da sukayi Dan suga Lami ta warke Amma abin yaci tura abinda ya d'auke hankalin Hajara kenan daga Kan Naseer da Naeema har tsawon wata hud'u tana jinyar gadon bayan lami da take Shan alwashin in ta warke babu abinda zai Hana ta kashe Mallam Musbahu. Wata biyar da barinsu Naeema Calabar taje kungiya aka bincika Mata Inda su Naseer suke da irin kudin da yayi da irin hutun da Naeema ta samu. Anan ma sukayi ta k'ok'arin wajen kashe Naeema ta hanyar tsafi Amma abin ya gaggara Dan yanzu Naeema ta Dan samu ilimi Kuma tana adduoi Dan saken da Naseer yayi da adduoi sabida neman kudin da yake ba dare ba Rana yasa Suka Dan karkato da zuciyar Naseer wajen Hajaran ya hau Mata aike Yana Mata wasika. Anan shugabarsu ta Bata shawarwarin hanyoyin da zata bi wajen mallake danta ta Kuma kau da Naeema ta bar duniya na har abada sosai take ganin sabon salon da suka d'auko zai bille dasu su kau da Naeema cikin sauki wanan kenan. A cikin kwanakin Nan Haka kawai na tsiri mafarki da Umma a mumunan yanayi tana ta Bina zata kasheni. Ganin inata mafarkin a jejjere yasa na sake dagewa da Addu'a dayake Ina da kudi kuma muna cikin wadata sai na tsiri Sadakan dafaffen abinci duk ranar jumaa tunda Sadaka maganin masifa ce. Kamar zanyiwa Naseer zancen mafarkin da nake yawan yi da Umma sai Kuma na fasa Sabida nasan zaiji ba dadi zai ga ma kamar zargin mahaifiyarsa nake. Zuwa yanzu Naga ya danyi sake da Addu'oi ba kamar da ba Dan yanzu Inya dawo ya Dan Yi nafilfili takardarsa yake daukowa ya hau lissafi da rubuce rubuce. Ahaka wani zubin bacci ke daukarsa ni Kuma sai na dauke takarda da biron na ajiye idan na Gama adduoi na sai na tofa Masa adduar kwanciyar bacci da yarana. Dan wata shidda danayi Ina zuwa makaranta na San adduoi sosai na Kuma San daga fatiha zuwa izu uku. Watan Minal Tara na samu wani cikin a ranar Dana San ciki ne Dani a ranar sukuku na wuni Dan banji dadin samun cikin yanzu ba naso ko shekara biyu tayi kafin na samu wani cikin. Zuwa lokacin nasan nayi nisa a makaranta. Sai dai ya zanyi kana naka Allah na nashi. A Daren ranar na shirya gayawa Naseer cikin danake d'auke dashi A dakinsa na same shi ya janyo akwati Yana ta had'a Kaya. Na dauka wani tafiyar ne ya Kara taso Masa kamar yanda ya Saba shiyasa ban Masa magana na na je kusa dashi Ina Taya shi had'a kayan. Shi kuwa ya dago yacemin. "Gobe idan Allah ya kaimu zanje Calabar dazu an turomin wasika Umma Bata Jin dadi an kwantar da ita a asibiti Dan Haka gobe asubanci zanyi na tafi. Bansan rigarsa ta sub'uce daga hannuna ba gabana ya yanke ya Fadi take jikina ya hau rawa. Hakane yasa yace min Lafiya. Ni kuwa cikin dauriya nace Masa ba komai Allah ya sauwake ya Bata lafiya. Bai Kara cemin komai ba ya gama karasa hada kayan ya shige bandaki Ni kuwa na fice daga d'akin da Sauri na koma dakina hankalina a balain tashe Allah yasa ba wani Abun ke Shirin samuna ba sabida yawan mafarkin danake da Umma bansan Mai yasa hankalina ya tashi da Naseer yace zaije Calabar ba Ina tsoron Umma Ina tsoron abinda zuwan Naseer zai haifar. A ranar ko runtsawa banyi ba Sabida yanda na dage da Addu'a. Washegari da assusuba Naseer ya d'au hanyar Calabar ni kuwa ya barni cikin Zullumi da tashin hankali ya zanyi toh mahaifiyarsa ce ban Isa na rabasu ba Allah ya dubeni da idon rahama ya kareni da karewarsa nidai da da yanzu ba daya bane bazan Kara yarda Umma ta bani wahala kamar yanda ta bani a baya ba. A ranar da Naseer ya cika kwana uku da tafiyarsa Calabar da yamma na dawo daga islamiyya Ina girki a kitchen su Zahira Kuma suna Palo naji Ana kwankwasa kofa. Da Sauri na fito daga kitchen ganin yanda ake kwankwasawa da k'arfi hannunsu Zahira Bai Kai handle din ba ballantana su bud'e. Ina bud'ewa nayi tozali da Umma da Safiyya ga manyan jakankuna a gaba bayansu Kuma Naseer ne ya d'auko musu sauran kayansu daga cikin taxi. Murmushi Nan da Umma kemin dake tsinkemin zuciya shi ta sakar min Ni kuwa jikina ya hau b'ari na Kuma kasa basu hanya su shiga sabida mutuwar tsayen da nayi Ni nasan da zaa auna jinina ba karamin Hawa yayi ba bugun zuciyata kuwa tun daga nesa zaka iya jiyowa. Maganar Naseer ne ya dawo Dani hankalina. "Ki bawa su Umma hanya su wuce Mana bakida hankali ne Zaki tare musu hanya" Naseer yacemin a tsawace Ni kuwa na matsa da Sauri na zub'e a kasa Ina musu Sannu da zuwa Naseer kuwa hannunsu Jaye da akwati ya shige Safiyya ta bi bayansa tana kalle kalle Umma kuwa muka tsaya kallon kallo har lokacin Fuskarta d'auke da Wanan murmushin sai data zo dab Dani tace "kin Kara d'aukar wani cikin kenan".......... [6/26, 3:26 PM] +234 803 635 0240: *NAGA TA KAINA* *NA SADNAF*🌸🌸 ®️ *_PURE MOMENT OF LIFE WRITERS_* _{We Don't just entertain nd educate we also touch the heat of readers P.M.L}💪🏻_ *Free Novel* *Page 12* Cikin tsoro da mamaki na kalli cikina da baifi wata biyu ba cikina a kwance babu alamar ma cikina ya taso ballantana ince tsinin cikina ta gani. Da Sauri na Kara d'agowa na kalleta ta sakarmin murmushi tana "ke Kuma aikinki kenan ko Naeema kin samu Naseer Zaki cika Masa gida da 'ya'ya toh yayi kyau" Daga Haka ta wuceni tana karewa palon kallo. Jikina Banda rawa bbu abinda yakeyi ahaka na rufe k'ofar na juya na nufi palon Ina zufa. A daidai lokacin da Umma ta zauna a kujera ta kalli su Zahira da shigowarsu yasa Suka mik'e tsaye suna zazzare Ido. Hannu ta mik'a musu tana "Kuna ganina bazaku zo wajena ba ko har Kun manta Dani ne? Tace tana kallon Naseer Zahira da Nadeeya da Sauri suka yo wajena suka fara k'ok'arin b'uya a bayana. Naseer kuwa ya daka musu tsawa Yana "bazaku je ku gaida Umma ba"? Da Sauri suka nufi tsakiyar palon Suka tsaya nesa da ita Suka hau gaisheta Ita kuwa ta amsa tana murmushi nima na karasa tsakiyar palon na zub'e a kasa Ina gaisheta cikin rawar murya. Wani irin kallo tamin ta amsa da murmushi nan nata da babu alheri. Kafin na mik'e Naseer har ya kawo musu ruwan Sanyi da lemo jikinsa sai rawa yake Yana ajiyewa ya koma ya juyo kazar da nake soyawa gabadaya a faranti yazo ya Ajiye musu. Nima mik'ewa nayi nabi bayansa Dan na zubo musu abincin tunda na Riga da na Gama dama kwashewa nakeso nayi. Kafin ma na isa kitchen din har ya Kara fitowa da wani farantin Mai dauke da soyayayyen kifi da nama dan Dama Haka nake soyawa da yawa na zuba a fridge kawai idan zanyi girki sai na dib'a da yawa ake kawo Mana daga shagonsa. Mamakine ya Dan kamani ganin bama d'ebowa yayi ba juyowa yayi gabad'aya. Bance masa komai ba na shiga kitchen. Na jawo kula na zuba musu shinkafa da miyar. Na koma palon na ajiye a tsakiyar palon. Naseer kuwa na zaune daga gefensu a kasa ya tankwashe kafa sai murmushi yake Yana su fara cin abincin Mana. Umma kuwa farantin da ya jere Mata a gabanta kawai take kallo tana gyada Kai Safiyya kuwa tuni ta sauko ta fara yagar kaza. Ina Shirin juyawa na zubowa su Zahira abinci naji Umma ta fara Jan majina kamar Mai kuka tana "Naseer yanzu Haka kuke Jin dadi kuka gudu kuka barmu a can abinda zamu sakawa cikinmu ma na neman gaggararmu kasan kuwa mun Sha kwana da yunwa akan karamin kuskure Naseer ka d'auki matarka ka gudu ka barni bayan kasan Kaine babban Dana babu Mai iya d'aukar dawainiyarmu idan ba Kai ba. A garin nemawa Lami kudin magani na gurd'e a k'afata Haba Naseer abinda Kayi baka kyauta ba karka manta Ni Mahaifiyarka ce Bai Kamata ka fifita matarka a kaina ba a baya nasan bana San Naeema Sabida shaidan daya sakoni a gaba Amma yanzu na gane Dan Haka kuyi hakuri da Kai da Naeema bazan sake ba" "Haba Umma Mai yasa kike bamu hakuri ke ya Kamata mu bawa hakuri mun Miki ba daidai ba Dan Allah kiyi hakuri da matakin da muka dauka bazamu sake ba insha Allahu fatana kawai ki cigaba da saka Mana albarka Naeema Kuma zata kasance Mai biyayya a gareki insha Allahu" Naseer yace Ni Kuma na koma na zauna hankalina a balain tashe shekara biyar ba Wasa bane zuwa yanzu na gama sanin wacece Umma ciki da Bai gwara Umma ta fito ta nuna min kiyayyarta data fito min da Wanan fuskar tata daya fi kowane hatsari Ni nasan Umma ba karamin shiri tayi ba kafin tazo Ni nasan idan ban dage ba wanan Karin sai taci Nassara akaina bansan Mai yasa Naseer ya kasa Gane wacece mahaifiyarsa ba gani nake duk abinda zaayi babu abinda zai saka tayi laushi Haka a Karan kanta sai dai idan Allah yaso ta da rahama ya ganar da ita gaskiya. Daga yanda Naga Naseer na rawar jiki nasan shima ba'a barshi Haka ba. Sosai nayi k'ok'arin b'oye tashin hankalina na Dan saki fuskata cikin yak'e Ina Kara bawa Umma hakuri wanda naga Naseer ya ji dadin hakan sosai Mik'ewa nayi Sabida cikina danaji Yana juyamin Dan idan na tsorata Haka ko na shiga tashin hankali sai na shiga bandaki. Kafin na Kai ga shiga dakin naji muryar Naseer Yana in gyarawa su Umma d'aki suzo su huta. Sai Dana fito daga band'akin na fito na nufi d'akin dayace na gyara musu Dan dakuna biyune bama amfani dashi shima babu abinda babu a ciki. Kafin na shiga d'akin inajin tana Masa tambayoyin Inda ya samu kudi Haka shi kuwa cikin rawar jiki ya hau Bata labarin yanda ya samu da kudaden dake shigo Masa. Sai Dana gyara na fito na nufi dakina Dan nayi Sallahr Magriba. Ban Kara fitowa ba sai da nayi sallar isha shima sai Dana d'auki Qurani na Mai izu goma na karanta surorin Dana iya kafin na fito wajen Taran dare. Ban ga kowa a palon ba sai su Zahira da bacci ya d'auke su a tsakiyar palon. Daukarsu nayi na kai su dakina Dan Dama a d'akina suke kwana idan Naseer na gari Kuma sai na kwana a d'akinsa. Sai Dana kwanatar dasu na tofe su da Addu'oi na kunna wani karamin radio mai daukar cassette daya Dan biyu ne damu ko uku ma akwai Mai d'aukar cassete biyu akwai Mai d'aukar daya (Kila ku gane radio danake magana ba plate ba cassete Mai zare a ciki) Taro shi nayi sai daya faro daga Suratul Baqarah na ajiye musu A gefen gadon. Na fito daga d'akin na nufi kitchen Dan na d'ebo abinci Ina Jin muryar Naseer a d'akin Dana gyarawa Umma suna ta Hira. Abincina na zubo inata mamakin yaushe Kuma Naseer ya fara sakewa da Umma suyi Hira Haka ko duk cikin Salon da Umma tazo dashi ne Haka na zubo abincin ba nama Dan duk Naman Naseer ya kaiwa su Umma Kuma a palon ma Banga farantin ba Nan kuwa su Umma Ashe da farantan Suka shiga d'aki. Dayake Haka ma ake jibge Mana lemo a store Kuma bama rabuwa dasu a fridge lokacin lemon kwalba ne coke Haka Pepsi na d'auko daya Mai sanyi Na koma d'akina sai Danaci na koshi na Kara fitowa wajen goma na dare har lokacin Naseer na d'akin Umma ta rik'e shi da labarai babu yanda zaiyi Nan kuwa ya gaji Kuma Yana Jin yunwa Amma bayaso ya tashi Umma taji ba dadi. Ni kuwa kwanciyata nayi Ina jiran daya da rabi yyi na dare na tashi Dan yanzu Banga ta bacci ba sai na dage da Addu'a Ina Kuma fatan Naseer ya lek'o dakina na Dan Masa maganar dagewa da Addu'a. Gani nake irin azabar da Umma ta gana min lokacin cikin Minal Haka zata ganamin da Wanan cikin tunanin Haka kawai da nayi sai daya Saukar min da fargaba Wanda tuni bacci yayi nashi gurin na tashi na daura alwala na hau kan Sallaya. Naseer kuwa Bai samu barin d'akin Umma ba sai Sha biyu Dan ahaka sai daya ce Mata Sallah zaiyi . Ita dai ba Haka taso ba sosai take so ta jawo Naseer jiki yanda zai na shagala sosai da ibada Ba karamin kokari tayi wajen Kai zuciyarta nesa ba Dan ta lura sai ta biyo wa Naseer da Naeema ta bayan gida zata ci Galaba a kansu Kamar ta Kama da wuta data ga Naeema tayi wani irin kib'a ta samu kwanciyar hankali Karin bakin cikinta tana zuwa ta Gane Naeema na dauke da ciki Mai Naeema take nufi da ita ne wato bazata rabu da Naseer ba sai dai tayi ta haife haife ta haifi cikin jikinta tagani. Sosai taji bakin cikin daular data ga Naeema a ciki hakane yasa ta ringa Dan bugar cikin Naseer game da dukiyarsa aikuwa ta samu yanda takeso Dan Naseer ya Gaya Mata komaii game da dukiyarsa a duk hirar da sukayi Bata ji ya mallakawa Naeeema wani ba Amma duk dahaka kaji da namomin da take ci ma ai Jin dadi ne Ina zaune akan Sallaya Naseer ya shigo d'akina hannunsa d'auke da abinci da lemo. A kasa ya zauna ya fara cin abincin Yana "Ai na dauka kinyi bacci" Girgiza Masa Kai nayi Ina "Baka shigo ba tayaya zanyi bacci" "Ai Umma ce take ta Jana da Hira tundazu dak'yar na fito" "Kayi Sallah kuwa"? Zaro Ido yayi Yana "Subhanallahi wlh Banyi Sallah ba Naeema banyi Magriba da Isha ba innalillahi yau Mai ya sameni Haka"? Yace ya mik'e da Sauri ya shiga band'akin d'akina ya d'aura alwala ya shimfida Daduma ya tadda Sallah. Lailai Umma ba k'aramin Kama Naseer tayi ba sosai naji jikina ya Kara sanyi Dan Naseer mutum ne shi jajirtace Mai ibada Zan iya cewa Yana bacci Yana mafarkin Sallah Amma sai gashi Wai shine ya shagala Haka Bai Yi Magriba da Isha ba. A haka na cigaba da Jan Hasbunallahu wa neemal wakil Yana iddarwa Naga ya fara Hamma idonsa ya kankance Sabida bacci daya cika Masa ido. Ganin Yana k'ok'arin mik'ewa yasa na saka hannu na dafe cinyarsa ya koma ya zauna Ni kuwa cikin murmushi nace "Wai har kayi me"? "Nayi Sallah Mana wlh yau bacci ne a idona Naeema bazan iya adduoi Mai tsayi ba" Rik'e Masa hannu nayi cikin Dan fargaba yanda zai dau maganata nace "A gaskiya Naseer Bai Kamata ka shagala da.hira har Sallah Magriba da Isha ya kwace Maka ba Haba Naseer yaushe Kuma Abu ya fara Sha maka Kai da zaka na mantawa bakayi Sallah ba ka manta Shawarwarin Da Mallam Musbahu ya bamu ka manta da addu'ar da yace mu dage dashi Sabida mu samu kariya daga wajen Allah ko ba Dan kariya ba ko iya Niimar da Allah ya maka kake Samun bud'i ko ta ina ya Kamata ka Kara kusantarsa ka cigaba da gode Masa Kar bud'in daya maka yasa Kuma ka manta dashi. Daga yanda Naga ya nutsu Ya bani hankalinsa sosai yasa nasan maganata ta shige shi A Haka na cigaba da shigar Masa maganata cikin siga wajen dage Mana da Addu'a na Kara da "kasan kafini zurfin Ilimi Dan Allah ka dage Mana da Addu'a Kar mu koma gidan Jiya Naseer ka mantani da sai Dana kusa mutuwa ka dawo hayyacinka yanzu Haka Ina d'auke da k'aramin ciki na wata uku bansani ba sai a satin Nan ranar da nake Shirin Sanar maka a ranar kayi tafiya kaga kuwa Ina bukatar addua Akan Allah ya saukeni lafiya" Hannuna ya ruk'o da k'arfi cikin farinciki Yana "Dan Allah dagaske kike cikine dake"? Gyad'a Masa Kai nayi ya daga hannu Yana "Alhamdulillah naji dadi Alhamdulillah Naeema banida burin daya wuce yanzu ki Samu ciki ki haifomin namiji Ina yawan mafarki naje Massallaci da Dana Yana kiran Sallah Allah yasa Rabon da namiji ne a jikinki Na gode da tunatar Dani da kikayi da Shagalar da nayi insha Allahu Zan gyara Dan Allah kiyi hakuri ki Kai zuciyarki nesa akan Umma kinsan wani zubin Tana iya rikicewa duk da Ina kyautata zaton insha Allahu ta Gane gaskiya kamar yanda ta fada Dan da naje bakiga kukan da ta ringayi tana neman yafiyar mu ba Akan tayi nadamar Abubuwan da ta miki" Murmushi kawai nayi ban Kara ce komai ba Dan Naseer bazai Gane ba kila sai Umma ta Kara gwada halinta da zai balain bashi mamaki zai San wacece ita. Sosai Naga Naseer na farincikin da cikin Dana samu Inda ya balain kwallafa Rai da insha Allahu namiji ne ahaka ya Kara mik'ewa ya kawo nafiloli ya karanta Qurani Inda lokacin Ni Kuma naji bacci na neman daukata hakane yasa na mik'e da hijabin jikina na d'auki plate din da Naseer ya shigo dashi Dan in mayar kitchen Ina bud'e kofa Naga na buge Umma dake bakin kofa ta sunkuya Haka ta Kara kunnenta a jikin k'ofar da alama dai lebb'e take Mana Cikin borin kunya ta ja da baya tana "dama k'afata ce ta matsamin nace bari nazo ko zan samu magani a wajenku" "Wlh babu maganin ciwon kafa sai dai paracetamol" Nace Mata jikina na Dan rawa Dan indai Zan tsaya kusa da Umma sai naji Kamar zata zaro wanan kaifafen wuk'ar ta cakamin Wani irin kallo tamin ta juya tana toh shikenan Dawowa nayi d'akin Dan Haka kawai naji tsoron ma zuwa kitchen din na ajiye plate din na kwanta Ina mamakin Halin Umma yanzu har ta Kai Umma lab'e take Mana da Naseer da yanzu kwanciyar Aure mukayi da Haka zata na Mana lab'e ko Kuma ta lek'o mu kenan. Zan iya cewa tunda muka dawo kano sai da Umma tazo gidan na kasa bacci cikin nutsuwa sai wasu irin mafarkai nake. Akan Sallaya bacci ya d'auki Naseer Ni kuwa sai Kiran Sallah ne ya tasheni. Inda na tashi Naseer ni Kuma na nufi band'aki na dauro alwala Ina fitowa Naseer shima ya fada band'akin. Ya d'aura alwala ya nufi Massallaci Nima na tada nawa sallar a gida [6/26, 3:27 PM] +234 803 635 0240: *NAGA TA KAINA* *NA SADNAF*🌸🌸 ®️ *_PURE MOMENT OF LIFE WRITERS_* _{We Don't just entertain nd educate we also touch the heat of readers P.M.L}💪🏻_ *Free Novel* *Page 13* Ina iddarwa na nufi kitchen na Dora Mana abin karyawa Ina cikin soya Dankalin Inata Sauri sabida na Gama na shirya su Zahira Nima na shirya na tafi. Kamar ance na waiga Naga Umma ta hard'e hannayenta a kirjinta ta Sha jajjayen Kaya har kasa da wani irin Hula idon nan nata ya Sha kwalli. Kau da kaina nayi da Sauri cikin Dan fad'uwar gaba Naja A'uziya na nace Mata Umma Ina kwana Bata amsa min ba sai gani nayi tana shigowa kitchen din matar data so kasheni kota halin Kaka tuni jikina ya dau mugun rawa na kashe gas din na juyo Ina kallonta. Wani irin kallo ta Gama min tunda ga sama har kasa a karshe ta zubawa cikina Ido kamar ta cinye Ni Ni kuwa nayita adduoi neman tsari a Raina Da kyar ta dauke idonta daga cikina ta fara wuwurga idonta cikin kitchen din tana dage dage store din dake jibge da kayan abinci ta zubawa Ido Ni kuwa har lokacin rasa nutsuwa ta nayi Ina ta addua a Raina. A bakin store din ta tsaya ta juyo ta kalleni tana "Lailai Dole ki k'i Tafiya Naeema Dole ki k'i rabuwa da Naseer wanan daula da Jin dadi haka ko nice ke bazan rabu dashi ba Amma fa inaso ki saka a ranki Bana kaunarki ba wacce na tsana sama dake yak'i ne tsakanina dake Dole zaa samu Wanda zai ci mu zuba mugani Naeema" Tuni hawaye ya hau wanke min fuska Sabida irin kalmomin dake fitowa daga bakinta banma ankara ba sai ganinta nayi a gefena tayi saurin d'aukar cokali tana juya Dankalin Ashe Naseer ta hango ya dawo daga Massallaci ya nufo kitchen din. Ni Kuma tsalle na daka na koma gefe Dan na d'auka ko man zata watsamin Shigowar Naseer yasa nagane wayon da tayi. Naseer kuwa ganin Umma a kitchen tana Taya Naeema girki ba karamin faranta masa yayi ba hakane yasa yana shiga ya tsugunna har kasa ya hau gaisheta. Ita kuwa Hajara ta washe baki tana amsawa tare da cigaba da juya Dankalin da Naeema ta Dade da kashe wuta Wanda duk Naseer Bai lura ba "Umma ai da kin Yi zamanki ba sai kin fito tayata ba zata iya ita kadai ai" Murmushi Hajara tayi tana Ai Naga ta fito sassafe ne shiyasa nace Bari Nazo na tayata. "Aaa ki barshi Dan Allah Umma ki barta tayi ita kadai idan ma tayin ne.ai gwara Safiyya ta fito ta tayata. Naseer yace yana washe baki shi a lailai Umma Tayani take idonsa ya rufe da Bai hango hawayen danake zubarwa ba. Toh shikenan Umma tace ta ajiye cokalin ta fita waje tana jifana da mugun murmushi. Naseer kuwa sai murna yake Umma ta canza Tsabar haushi ban kula shi ba na juya na kunna gas na cigaba da soya Dankalin Ina gamawa na hada na Umma da Safiyya na Kai musu d'aki. Ko kallona basuyi ba na had'awa su Zahira nasu muka karya gabadaya Nima na shirya cikin uniform Dina Dan sai an sauke su Zahira ake wucewa Dani a yanzu da Naseer yake Nan nasan shi zai kaimu. Sai Dana kulle d'akina na fito hannuna cikin nasu Zahira muka shiga d'akin su Umma a zaune suke suna ta auna Dankali bakinsu suna had'awa da naman jiya da Naseer ya juye musu sakin baki sukayi suna kallon nida su Zahira Ina shirin ce Mata Zanje makarnata Naseer ya shigo d'akin shima cikin Shirin.kaimu da mukullin mota a hannunsa Naseer ne ya fanshe Ni da "Umma Bari na mik'a su Makaranta na dawo" "Makaranta Kuma har da Naeema"? "Eee Umma har da ita muna dawowa na samo mata islamiyya da Boko take Dan zuwa sabida Karatun Yana da amfani a gareta ko Dan yaran Nan idan an basu gwaji ko karatu zata iya duba musu har ta koya musu" Sosai Naga b'acin Rai a fuskar Umma Amma sabida makirci ta hadiye tana "Naseer Anya Naeema Bata girma da karatu ba Ya Kuma zatayi da kula da yaran har Kai Ni sai nake ganin kamar karatun zai saka ta kasa samun lokacinka har dana su zahiran" "Ai Kuma tana dawowa da wuri Umma Kuma su Zahira ma sai wajen Shidda ake tashinsu. A lokacin kuwa har ta dawo ta Dora Mana abinci "Toh naji idan yaranka suna dawowa shidda mu Kuma fa Mai zamuci kafin ta dawo" Murmushi Naseer yayi Yana "Haba Umma ga Safiyya Nan ai zata iya sama muku abinda zakuci kafin Naeema ta dawo ai gidan ba bakonta bane akwai komai da ake bukata yanzu ma zaa kawo kaji da nama sai ta silala ta soya Mana" Hajara yak'e kawai take ba Kuma tasan Naseer ya gano ta da wuri badan ranta naso ba ta barmu muka tafi. Naseer kuwa yaje ya saukemu a makaranta. Sosai nake takatsantsan da su Umma da nake musu kallon dodo zuwa yanzu na balain iya takuna Dan idan na fita makaranta sai na ci abinci a gidan mmn Mannir nida yayana muke dawowa gidan Sam ban yarda dasu ba Dan tunda Naseer yace Safiyya ta ringa musu girki ta tsiri dafa na duk gidan gabadaya a haukanta ita da Umma da Naseer kawai take dafawa sai ta bar Mana kanzo nida Yara Ni kuwa idan na dawo sai na juye kanzo na shiga d'aki dashi na juye Leda nasa a karkashin gado. Abincin Naseer ma fakar Ido nake na juye na zuba irin abinda suka girka a ciki Dan Ina tsoron a Kara juyar Masa da hankali. Ko shi Naseer Bai San na dauki kayan abinci a shagonsa ba na Kai gidan mmn Mannir duk wani Abu da nake bukata dauka nake a shagon har nama da kifin. Mmn Mannir kuwa ba tambayar da batamin ba Akan meyesa nake zuwa dafa abinci a gidanta nace Mata ba komai idan lokacin tasan dalilin dafa abinci a gidanta idan yayi Zan Gaya Mata Kuma cikin ikon Allah Mmn Mannir da mijinta basuda matsala ba Kuma su nuna min komai ba Dan ban Dora musu nauyin komai ba har risho da kalanzir jarka guda na ajiye a gidan sabon tukunya da komai nawa ba abinda nake tab'a musu. Karfe uku ake tasomu daga makaranta idan mun dawo a gidan mmn Mannir nake Gama komai nawa idan naci na koshi yayana ma aka d'auko minsu sai na basu suci na zuba sauran a Leda na jefa a jakata idan na faki idonsu sai na juye a Kular Naseer. D'akina kuwa kullum kullewa nake Kuma Haka nake kunna karatu a d'akin har na dawo sai dai idan an d'auke wuta. Har su Umma sukayi wata uku a gidan Ina mamaki da Banga ta aiwatar da komai ba Kuma ganin hakan Bai saka na saki jiki ba addua nake haikan idan Naga Naseer na neman yayi bacci cikin siga Zan Masa magana akan ya Kara min karatu ahaka muke rayya daren shima Naseer ba laifi tunda na Masa magana ban Kara ganin yayi sakaci da Addu'a ba Kuma ikon Allah tunda su Umma suka zo garin bai Kara tafiya zuwa wani wajen ba. Sosai nake mamakin idon da Umma ta zubamin duk da wani zubin takan manta ta zageni ta tsinemin ta Sha mugayen alwashin akan sai ta Kau Dani nidai rabbi samawati na dogara dashi Kuma shi nake neman kariya wajensa. Ban taba kwanciya banyi tunanin Umma na iya kawo min Hari ba a Haka har cikina ya shiga wata na shidda. Ba zama nake a gida ba ballantana nasan ko akwai wani mugun Abu da su Umma suke hada Mana ahaka watarana Mun shirya zamuje makaranta Naseer ya cewa Umma zaiyi tafiya sai an kwana biyu zai dawo. Sosai Naga wani irin farinciki ya bayyana fuskar Umma ita da Safiyya har a idona Naga sun Yi magana da juna ta Ido. Sosai ta Masa addua dawowa lafiya. Shi kuwa yayi waje muka bishi a baya hankalina balain tashe Dan Ni nasan akwai wani Abu da Umma ke kullamin Amma bansan menene ba Anya kuwa Zan kwana gidanan idan Naseer baya Nan? Ahaka Naseer ya saukeni yamin Sallama Yana ta Sauri kamar na Hana shi tafiya Amma Haka na barshi ya tafi. Ahaka aka tashi bangane komai ba mmn Mannir sai tambaya ta take Mai yake damuna na kasa Gaya Mata cike nake da fargaba. Muna isowa gidan mmn Mannir na hango wasu irin Kati biyu suna ta kallon gidan mu ban dai kawo komai ba muka shiga gidan a ranar ma ko yunwa banji ba inata so na yiwa mmn Mannir magana Ina ganin Kamar Bai dace na fallasa sirrina ba Abun mamaki a ranar Nan da Nan naga lokaci yaja har su Zahira sun taso. Sai da suka dawo da. Wajen awa daya kafin na iya mik'ewa na yiwa mmn Mannir Sallama Dan Naga mijinta na Nan Kamar Kuma Yana so su kebb'e da ba Haka ba da mun kwana. Cikin fargaba da Addu'oi na karasa gidan yanda nake Jin jikina nasan akwai Abunda zai faru Dani Amma me na dogara da Allah shi zai kareni insha Allahu ( duk Wanda ya dogara ga Allah Allah zai isar Masa insha Allahu) Muna Sallama Naga Umma ta taremu da faraa ita da Safiyya sunci kwalliya suna ta murmushi anan nasan Ina cikin danger irin wanan tarbar Umma tamin na hau kumbura da na kusa mutuwa. Tashin hankali ne ya saukarmun da zazzabi tamkar wancan lokacin A madadin na kwanta alwala na daura na hau kan darduma nayi sallah Ina iddarwa na hau yiwa Allah kirari Ina hawaye Ina rokonsa kariyarsa a gareni. Ban iya motsawa daga Kan sallaya ba ballantana in kwantar dasu Zahira da sukayi bacci Ina ta juyo hirar Umma da Safiyya suna ta shewa a Palo sai yaga kaza suke. Wajen karfe goma Sha biyu naji Ana kwankwasa kofar gida gabana ya yanke yayi wani irin fad'uwa na mike da Sauri na lek'a ta k'ofar dakina Naga Naseer ne ya shigo da suka bud'e kofa. Wani irin Sanyi ne ya tsirgamin zuciyata bansan lokacin Dana koma Kan sallaya nayi Sujadda Ina Godewa Allah daya dawomin da Naseer ba. Umma kuwa da Safiyya sosai hankalinsu ya tashi da dawowar Naseer suka hau tambayarsa Mai ya dawo dashi yace musu Dama Kaya zai Kai Yobe toh kayan ma basu samu ba shiyasa ya fasa tafiyar. Matsuwar da yayi daya ganmu yasa ya kasa Gane tashin hankali da suke ciki. Ahaka ya wuce su ya nufo d'akina. Yana shigowa na mike da Sauri naje na rungume shi Dan sosai naji duk wani fargaba da tsoron danake ciki ya tafi. Murmushi yayi min ya janye Ni gefe Yana na bar Masa Yaya a kasa ya d'auke su Zahira ya kwantar dasu ya nufi bandaki ya watsa ruwa ya dawo Yana ya gaji nazo na Masa tausa. Da hijabina na hau gadon na hau daddana Masa kafarsa bansan lokacin da bacci ya d'auke shi ba. Nima Haka kawai naji baccin nake San Yi sai na kwanta a gefensa cikin kwanciyar hankali Yana gefena. Karfe biyun dare Naga an banko k'ofar dakinmu da k'arfi daga Ni har Naseer muka Mike a firgice da sallati. Kattin Maza ne akalla zasuyi su bakwai uku d'auke da bindiga kanananu sauran hudun Kuma d'auke da wukake dogaye masu kaifi. Daga Ni har Naseer sallati muka hau Yi Ni kuwa naji cikina ya wani irin murd'amin take naji wani irin gudawa kamar Zan saki sallati kawai nake Ina kankame da Naseer. Fusgoni sukayi daga jikin Naseer Suka ja hannuna suka wurgani palo Naseer na San magana suka buga Masa gindin bindiga. A tsakiyar palon aka jeramu har da Umma da Safiyya da suka kwanta a kasa suna ta magiya suna bada hakuri tunda nake bantaba ganin bindiga da idona ba sai ranar. Daga Ni har Naseer sallati kawai muke Ina Jin kamar Dan cikina zai fito. A hankali na daga kaina su bakwai ne Fuskarsu duk a rufe Naseer kuwa sai ce musu yake akwai kudi a daki suyi hakuri ya dauko musu. Ni kawai suke kallo suna magana kasa kasa . Inda naji daya daga cikinsu Yana cewa "Ai ba sai munyi amfani da ita ba cikine fa a jikinta muyi abinda ya kawo mu kawai mu ware. Ana fadar Haka Naga uku sun zo kaina sun dagani wani Kuma daga cikinsu ya saitoni da bindiga. Aguje Naseer yaje ya zub'e Agaban Wanda ya nuna Ni da bindiga yana ya Masa Rai Kar ya kasheni zai basu duk abinda suke so idan ma shine su kashe shi Dan Allah. Wani irin Ball sukayi da Naseer ni kuwa tuni na fara juyo kamshin lahira na kalli ringa karanta la illaha illa anta subhanaka inni kuntum Minal zalimin innalillahi wa Inna ilaihi rajiun abinda nayita fada.kenan.kafin nace Naseer Dan Allah ka kularmin da Zahira da Nadeeya Umma na yafe Miki duk abinda Kika min dafatan zakimin addua idan na mutu. Ina Gama fadar kalmar nan Naga Wanda ya saitoni da bindiga bindigar ta silmiye daga hannunsa ya cire abinda ya rufe fuskarsa ya kalleni Yana kikace kin yafe Mata abinda ta Miki" Ban kulashi ba na cigaba da sallati shi kuwa ya maida kallonsa Kan Umma data sunkuyar da Kai tana Jin asiirinta na neman tonuwa "Ke tsohuwa Mai yarinya Nan ta tare Miki da.kike San kasheta. Wanda ya saitani da bindiga yace Yana zuwa Kan Umma ya tsaya. Umma mik'ewa tayi tana fiki Fiki da Ido tace kamar ya bangane ba wa zan kashe. Wani irin Mari ya d'auke Umma dashi da har sai da Gefen bakin umma ya fashe Yace "Ni zakiyiwa bariki Zaki gayamin ko sai na b'allaki Mai matar danki ta Miki da kikesan kasheta sabida rashin Imani Kika biyamu mu Mata fyade mu kasheta Mai ta Miki Haka Yar yarinya Nan dake d'auke da ciki. Umma da Naseer. Ke jifanta da wani irin kallon mamaki cikin borin kunya da rashin kunya tace Kai yaro ka shiga hankalinka idan ma shaye shaye kayi ka dawo hankalinka a Ina na Sanka da zakamin sharri Dan ubanka wlh Zan saka Dana ya kamaku bakada hankaline Bata Gama magana ba ya Kara d'auke ta da Mari Yasa yaransa suka rik'e masa Umma ya hau naushin Umma Yana ball da ita......[6/26, 3:26 PM] +234 803 635 0240: *NAGA TA KAINA* *NA SADNAF*🌸🌸 ®️ *_PURE MOMENT OF LIFE WRITERS_* _{We Don't just entertain nd educate we also touch the heat of readers P.M.L}💪🏻_ *Free Novel* *Page 14* Bugun Umma yake sosai kamar ya samu kato Dan uwanshi Dan Raina masa hankali da tayi duk yafi Bata Masa Rai kisan Kai aikinsa ne rashin Imanin aikinsa ne kawai Maganar da Naeema tayi akan ta yafe Mata ta Mata addua ne ya tab'a shi Bai kawo Yana Ido biyu da Naeema bazai d'auke ta da bindiga ba Dan Dubu goma su Umma suka biyashi da a lokacin kudine Mai balain yawa tunda Suka ga Naeema Bata Zama Safiyya ta bazama Nemo Inda zasu samu Yan d'abba da zasu zo gidan su kashe musu Naeema cikin sauki Dan sunga alamar duk Inda suka kai da suyi asiri su saka Mata gubar duk yak'i tasiri akanta Amma idan suka samu Dan dabba lokaci guda zai d'auke kanta da bindiga. Ahaka Safiyya ta Samo Garba da ake wa lakabi da No mercy ta kawo shi har gidan da su Naeema basa Nan suka Gama magana ta Masa bayanin ayiwa Naeema fyad'e a Kuma kasheta. Safiyya ce har dacewa idan suka tashi Mata fyad'e su Mata yanda bazata moru ba Naseer zai tsaneta ya saketa Anan No mercy ya cajesu kudi take Umma ta d'auko kudin ta bashi Dan sosai Naseer ke Bata kudi tunda Suka zo gidan Yana karbar kudin ya tambayesu yaushe zai aiwatar da aikin Suka ce Masa ya Bari sai Naseer yayi tafiya yanda ma babu Wanda zai ceci Naeemar. Shine da Naseer yace musu zai yi tafiya Suka hau murna suna fita Safiyya taje ta samu No mercy Akan yazo yau Naseer baya Nan Ihu Umma take sosai tana Kiran sunan Naseer daya zo ya ceceta Dan daga tukunyar Tsafin nata har komai na karfinta sun baro shi a Calabar daga ita har Saffiya dan Shugabarsu ce ta kwace Sabida tana ganin kashe Naeema sai da dabara ba Tsafi ba Kuma ita Hajara akwai bakin zuciya kurkusa bazata iya ba sai tace sai tayi amfani da k'arfi Inda take Naseer da Naeema zasu harbo jirginsu Susan ba tuban tayi ba shiyasa shugabarsu ta kwace Akan su kashe Naeema ta wata hanyar tinda tsafin yak'i ci sai gashi sun biyo ta wanan hanyar da ba'aje koina ba asirinsu ya tonu. "Naseer bazaka zo ka ceceni ba sai sun kasheni" Umma tace bakinta cike da jini idonta yayi luhum luhum Naseer kuwa hankalinsa gabadaya Yana Kan Naeema da Mazan suka cikata Wanda suna cikata yayi kanta sabida yanda numfashinta ke barazanar d'auke wa sabida firgita da tayi kwantar da ita kawai yayi a jikinsa Yana jijigata tare da tofa mata adduoi Shi kuwa no mercy cewa.umma yake "Ke Kika aiko mu kasheta ko ba ke bace wlh sai kin amsa da bakinki Zan cika ki shegiya tsohuwar Banza" Umma kuwa dataji azaba da Sauri tace "wlh ni na biyaku nace ku kasheta Amma kuyi hakuri sharrin shaidan ne" Naseer kuwa cikin wani irin shock da mamaki ya zubawa Umma Ido hawaye na zubo Masa. Ni kuwa har lokacin a firgice nake Amma duk abinda sukeyi Ina jinsu Kuka kawai nake na Kara kamkame Naseer Dan gani nake har lokacin zasu iya harbina Hambarar da Umma yayi Yana "Duk zalunci na kinfini wlh Ina daraja mace Mai ciki a rayuwata duk aikin da aka bani idan Naga mace nada ciki Ina daga Mata kafa Amma ke dayake azzalluma ce ahaka kikace mu kasheta bayan mun Mata fyade badan kin min tsufa ba da wlh ke zanyi wa fyaden kiji ya akeji Amma duk da Haka lokaci Bai Kure ba. Barin gaban Hajaran yayi ya kaiwa Safiiyya data k'ifar da kanta kasa duka a duwawu da kafarsa Yana "kece kike cewa ayi Mata fyade yanda bazata moru ba ko to ke zaa muyiwa fyaden ku shigar min da ita daki. Wani irin ihu Umma ta saki Safiyya itama ta hau ihu. Kafin kace me tuni yaransa uku suka kinkimi Saffiya dake wantsal wantsal da kafa suka shige daki da ita sai ihu take Tana Kiran sunan Umma Akan tazo ta taimaketa Shugaba ta cucesu data rabasu da mudubin tsafinsu Naseer kuwa har lokacin Bai dawo daga shock din daya tafi ba Bazai iya fasalta halin daya tsinci kansa a ciki ba har Mahaifiyarsa tayi nisa Haka har yanzu ya kasa gasgata abinda yake ganin na faruwa a gabansa. Umma kuwa bayan no mercy ta bi aguje daya nufi d'akin da aka shiga da Saffiya dake ta kurma ihu tana rantsuwar indai suka Mata wani Abu sai ta kashe su daya bayan daya. Bayan No Mercy Umma ke k'ok'arin jawowa tana Jin inama da tukunyar tsafinta a wajenta da yau gunduwa gunduwa zatayi dashi. Wani irin wurgi yayi da Ita ya rufo k'ofar. Safiyya kuwa ta hau zunduma ihu Umma kuwa aguje tayi wajen Naseer dake rungume da Naeema jikinsa na wani irin rawa sosai yake Jin kirjinsa na Masa suya sabida abinda Umma tayi. Jijjiga shi ta hau yi tana Naseer ka tashi kaje ka Hana su tab'a min Safiyya kaje ka hanasu Naseer karka Bari wani Abu ya Sameta yau na shiga uku Ni Hajara Dan uwarki daga shi yaje kika kwanta a jikinsa wlh wani Abu ya Sameta kin shiga uku a hannuna Naeema kin zame min masifa a rayuwa ki daga shi nace" Umma tace a fusace tana k'ok'arin janye Ni daga jikin Naseer da ya kankameni jikinsa na wani irin rawa ganin k'arfi da yaji take Jana yasa ya d'ago cikin rinannun idonsa Yana "Ki cikata Umma babu Inda zani domin ban San su ba ke da kanki Kika kirasu gidanan abinda Kika so ayiwa Naeema Allah ya mayar Kan Safiyya Dan Haka babu abinda ya shafeni Umma ko kasheta zasuyi babu ruwana Dan ke Kika jawo Umma yanzu tsanar da Kika yiwa Naeema ya Kai har Haka ki hayi Yan d'abba kisa su zo su kashemin Mata su Mata fyad'e innalillahi wa Inna ilaihi rajiun Umma Mai na Miki Haka a rayuwa Mai baiwar Allah Nan ta Miki kike San kasheta k'arfi da yaji" "Naseer kanwarka ce fa Saffiya kake cewa babu abinda ya shafeka yanzu kafi San Abu ya Samu Safiyya akan matarka Naseer Anya yarinya Nan ta barka Haka kuwa Naseer kana Jin ihun Safiyya fa" ihun Safiyya data juyo da k'arfi tana kwalla Mata Kira yasa ta nufi bakin kofa ta ringa bugawa tana jijjigawa tana rokon a cika Mata 'ya sai da suka Dade a d'akin suka ringa fitowa daya bayan daya suna gyara Riga No mercy ne karshen fitowa. Yana fitowa Umma ta fada d'akin tana ihun an kashe Mata 'ya Shi kuwa no mercy a gabanmu ya tsaya sai daya Gama gyara rigarsa Cikin tsawa yace ke "tashi tsaye" Da Sauri na mik'e tsaye kamar ba mai.ciki ba jikina sai rawa yake sabida tsoro "Mai Kika Mata take san kasheki"? Wlh ban Mata komai ba" "Kai Wai dagaske Bata mata komai ba? No mercy yace Yana kallon Naseer dake tsaye a gefena ya Dan dafani sabida Kar na Fadi Cije lebb'e Naseer yayi Yana "dagaske ne babu abinda ta Mata Haka kawai ta tsaneta" "Toh ke Dan ubanki Dole ne zama dashi ki rabu dashi mana ki tsira da rayuwarki tunda ta nuna Bata sanki har tana neman d'aukar ranki wanan tsohuwar muguwa ce azzalluma inkika dage sai kin zauna da danta wlh watarana sai tayi nassarar kasheki yau idan Allah ya taimake ki ni ban kasheki ba idan ta hayo wani bai zama lailai yaji tausayinki ba kasheki zaiyi wlh" Kai Kuma tunda kasan uwarka azzalluma ce ka Bata takardarta tunda ba ita kadai ce mace ba ka Saketa ta samu wani ta aura Kai Kuma ka zauna da uwar taka tunda inaga Haka take so ko? kaji ko baka ji ba"? Da Sauri Naseer ya gyada kansa sabida yanda yake ta nuna mu da bindiga shi kuwa no mercy yace yauwa tana haihuwa ka saketa idan ba Haka ba Zan ringa biyowa ta Nan inama zuwa" Yace ya juya Yana nufar d'akin da Umma take Yana shiga ya fito da Umma gabanmu Yana "yarki dai ai ta Gaya miki yanda aka sani ko toh wlh Bari kiji na Gaya miki Zan ringa zagayowa Ina tambayar mutane yanda zamanku yake da yarinya Nan duk ranar da Kika Kara tab'ata ko kikayi yunk'urin kasheta wlh sai na fasa miki Kai da bindiga ko ban zagayo ba nasan na bar miki abinda Zaki ringa tuna Ni Dan kila nan da wata Tara Zaki samu jika Killer" Wani irin dariya ya kyalkyale dashi ya Kara kallo nida Naseer Yana kundai ji abinda nace ko idona yana kanku" Daga Haka yayi waje tare da yin pito sauran Suka bi bayansa da Sauri suka fice daga gidan Suna fita na zub'e a kasa na Dora hannu aka na fara zunduma ihun kuka Umma kuwa tamin wani irin kallo ta tashi da Sauri ta nufi d'akin da Safiyya ke Sume. Naseer kuwa ganin irin ihun kukan da nake yasa ya fara k'ok'arin janyoni jikinsa Dan ya rarrasheni Ni kuwa na saka musu ihu Tare da janye jikina Ina "Naseer na gaji Dan Allah Dan annabi ka sakeni indai kana kaunata zaka so ka gani a rayye ko dansu Zahira su girma su San Ni Umma Bata Sona Umma Bata da burin daya wuce ta kasheni har guba Umma ta zubamin a kunnu ta biyoni da wuka ta binne Abu duk Dan na mutu ban mutu ba yanzu ta hayo Yan d'abba Dan su kasheni Naseer iya wandanan Abubuwan Dana lissafa maka ya Isa yasa kagane Umma Bata kaunata Kuma babu abinda baza tayi Dan ta kasheni ba Dan Haka Naseer na gaji wlh duk San da muke wa juna Dole mu hakura da juna duk da banida kowa ka Sakeni bazan rasa Wanda zai taimaka min ba Naseer duk da cikina Haka Umma ta biya azo a kasheni ayi min fyad'e haba Naseer abin yayi yawa Dan Allah ka sakeni. Kuka nake sosai Naseer da idonsa ya kad'a yayi jawur ya sunkuyar da kansa Yana Jin duk ihun kukan danake ahaka mukayi kwanan zaune dagani har Naseer Ni Ina kukan fili shi Yana na zuci har aka Kira sallah asuba dagani har shi babu Wanda ya mik'e daga irin ajiyar zuciyar da Naseer ke yi nasan shima ba karamin kukan zucci yayi ba Ni jikina dake rawa har lokacin yasa na kasa mik'ewa nayi Sallah shi Kuma Naseer zurfi da yayi a tunani yasa Bai ma ji Kiran Sallahr ba. Shidda saura Yan mintina na safe muka ga an bud'e k'ofar d'akin dasu Umma suke. Umma ce ta fito daga d'akin hannunta d'auke da jakar kayansu har akai ta Dora wani kayan kamar Mai talla. Ko kallon Inda muke batayi ba idonta yayi luhun luhum abinka da farar mace ta bud'e kofa tayi waje Daga Ni har Naseer kallonta muke har ta fita ta sake dawowa babu Kayan a hannunta ta shiga d'akin shigarta da 'yan mintina sai Gata ta fito hannunta rik'e Dana Safiyya data tattale kafa tana tafiya dak'yar. Basu kalli Inda muke ba suka fita Waje Ganin Naseer babu alamar zai tashi yabi bayansu yaji dalilin tafiyarsu yasa na Kira sunansa cikin dashashen murya Ina "Naseer bazan so ku ringa samun Sab'ani da Umma ba bazan so na zama silar da zatayi fushi dakai ba zaka iya sake Mata sau Dubu baka Isa ka sake Umma ba ka tashi kabi bayanta ka ce mata zaka sakeni ta Bari na haihu tunda na kusa haihuwa daga Nan sai mu dage da Addu'a idan da rabon mu cigaba da zama dakai zaka ga ta sauko idan babu rabo sai mu rabu Naseer ka tashi kabi bayanta Naseer daga abinda ya faru Dani a yau Allah ya kareni na yarda duk Wanda ya dogara da Allah Allah zai isar Masa Yana sane Dani Kuma zai cigaba da kareni insha Allahu Amma dai mafita shine mu rabu muga ko Umma zata sauko ka tashi kaje Naseer" Mik'ewa yayi batare da yacemin komai ba ya fita wajen Yana fita yaga suna ta tafiya a kafa Sabida masu Abun Hawa duk basu fito ba Safiyya tana tafiya tana hutawa. Binsu ya ringa yi a baya har sai da ya ci musu Yana ta yiwa Hajara magana ta share shi hakane yasa ya rik'e jakar hannunta sabida ta juyo aikuwa tana juyowa ta d'auke shi da wani irin Mari tana hucci Naseer kuwa ya dafe kuncinsa cikin mamakin Marin data Masa alhalin shi tayiwa laifi Amma takeso tayi borin kunya "A gaban idona ka fifita matarka a kaina Agaban idonka aka ringa dukana Ana kwallo Dani Naseer kana kallo amadadin ka kawomin d'auki sai ka jawo matarka ka rungumeta. Agaban idonka aka shige da kanwarka daki maza sukayi layi akanta Suka Mata fyad'e baka Kai Mata d'auki ba ka rungume matarka Naseer karka manta fa Ni na raini cikinka har tsawon wata Tara nayi Nakuda na Haifeka kamar bazanyi Rai ba shayar dakai ne kawai banyi ba amma Naseer Agaban idona kake fifita matarka a kaina daka kawo min d'auki nida kanwarka gwara.ka rungume matarka Naseer Anya kana San kayi albarka kuwa Naseer Anya yarinya Nan Haka ta barka kuwa? Naseer ta ya bazan tsaneta ba ? tayaya Zan sota ?Ba dai ka zabi Naeema a kaina ba toh kaje na yafe maka ita karka Kara nuna wa ka sani karka Kara kirana da Sunan Mahaifiyarka Naeema ta zama uwarka" Naseer ji yayi kalmomin sun Masa tsauri ya tsugunna akan gwiwarsa Bai damu da awaje suke ba ya rungume.kafafun Hajara Yana "Umma ya kikeso nayi a rayuwata Umma mutanen nan ke Kika biyasu da kudinki akan suzo su kashe Naeema su mata fyad'e bansan Mai yasa Suka maida abin kanki da Safiyya ba Umma tayaya Zan kawo Miki dauki alhalin ke Kika Sansu tayaya Zan kawo Miki dauki alhalin da bindiga a hannunsu Umma Kinga keyata yanda suka fasamin da gindin bindiga Umma so kike kiga na mutu da Raina Umma Naeema Amana ce agareni nayiwa Iyayenta alkawarin riketa da Amana Bata da kowa sai Ni Bata San danginta ba ta Haifa min Yaya uku ga na hudu a cikinta Umma idan na rabu da ita Ina zata je umma idan na rabu da ita wa zai Kular min da yayan data haifamin Umma Mai yasa bakya tausayin Naeema"? "Sabida bana santa Naseer sabida ka nuna itace rayuwarka sabida ka nuna tafiye maka kowa rayuwarka Naseer bana San Naeema Kuma bazan tab'a santa ba wlh idan kana San albarka ta ka saketa bansan a baya ba tsanar ta nayi ba sai yanzu danaga ta silarta an min duka kana kallo ta silarta maza bakwai sunyi wa yata Fyad'e kaje Naseer ka tafi kawai na yafeka" Daga Haka Umma ta hankada Naseer ta d'auki Jakarta tare da Jan hannun Safiyya suka cigaba da tafiya Naseer kasa motsi yayi ya zuba musu Ido har Suka tare taxi Suka shige suka tafi. Naseer dak'yar ya dawo gida sabida jirin dake dib'arsa Ahaka ya dawo gida ya sameni Akan sallaya Bai cemin komai ba ya shiga bandaki ya sakarwa kansa ruwa da kayan jikinsa sai daya gaji ya d'aura alwala ya fito ya tada sallahr asuba Yana iddarwa ya kwanta akan Sallaya ya rike kansa da hannu biyu sabida Sara masa da kansa keyi. A ranar Sabida tashin hankali ko makaranta su Zahira basu je ba Abu kamar Wasa sai gashi zazzabi ya kwantar da Naseer har tsawon sati daya tuni na hau jinyarsa Naseer yayi wani irin Rama sosai na hau tausayinsa inaso ya samu lafiya muyi magana Dan bana so ya cutu ta silata. Ranar da aka samu kwana takwas da tafiyarsu Umma ya Dan ji kwarin jikinsa Ina tararsa da maganr ya sukayi da Umma yacemin na ajiye maganar Nan a gefe sai na haihu kamar yanda nace din Dan Allah Kar na sake tayar Masa da maganar. Haka kuwa akayi ban Kara yiwa Naseer maganar ba duk da Ina cikin Zullumi da tashin hankali nafi tsoron Umma yanzu akan da fatana Kar ta min wani Abu har na samu na haihu lafiya. Naseer kuwa sosai Naga ya dage da Addu'a kamar yanda ya Saba Zan iya cewa baccin awa biyu kawai yakeyi. Nima ban saki jiki ba duk da tsohon cikina Haka na dage da Addu'a Nima. Haka Naseer ya cigaba da kula Dani Yana min rubutu Ina Sha ahaka har Allah ya saukeni lafiya na Kara haihuwar mace. Naseer kuwa a fuskarsa sai Dana ga baiyi wani doki ba addua kawai ya mata ya saka Mata Aisha zaa na kiranta Humaira. Bamuyi taron suna ba raguna biyu kawai ya siyamin ya siya Mana komai na bukata. Naseer Bai fito ya fadamin ba Amma Ni nasan Yana cikin damuwa Dan tunda Umma ta tafi yayi wani irin Rama Kuma Ni nasan tunani ne ya haddasa masa ramar tunda Naga Umma Bata biyoshi ta dawo ba nasan kila fushi tayi sosai. Kwanana talatin da haihuwa yacemin zaije Calaba wajen Mallam Musbahu daga Nan zaije wajen Umma suyi magana" Haka kawai naji jikina yayi sanyi adduar dawowa lafiya nayi Masa ya shirya ya tafi bayan ya cikani da kudi...... [6/26, 3:27 PM] +234 803 635 0240: *NAGA TA KAINA* *NA SADNAF*🌸🌸 ®️ *_PURE MOMENT OF LIFE WRITERS_* _{We Don't just entertain nd educate we also touch the heat of readers P.M.L}💪🏻_ *Free Novel* *Naeema ta bani sako na Baku tana karanta labarin haka ma yaranta comment din ma mutane duk tana Gani tace ace muku ta gode da Kaunar da kuke nuna Mata har da masu San ganinta duk ta gode ahaka ma da baa tsunduma cikin labarin ba inaga an fara labarin ta roki arzikin a daina yawan tsinewa Hajara ko Dan Naseer uban yayanta duk da shi baima San Ana rubuta labarin ba ita dai fatanta a nema Mata adduar Shiriya tagane Kar abin ya Mata yawa akwai dalilin daya sa take so asan labarinta ta na mik'a sakon gaisuwa ga duk masu bibiyar labarin ita Kuma Mai rubutawan Allah ya bata ikon rubuta duk labarin. Naga dayawa wasu na tambayar Inda Mahaifin Naseer yake ya baa sake Sako shi a labarin ba duk Wanda ya karanta daga page one zuwa 5 a karshen page 5 nace muku mahaifinsa ya mutu wayanda basu karanta wajrn ba su duba page 5 *Page 15* Yana Isa Calabar Bai zarce ko'ina ba sai wajen Mallam Musbahu dan ko wancan zuwan da yayi Bai samu zuwa wajensa ba Sai dayaci abinci ya huta mutane Suka ragu daga wajen Mallam Musbahu kafin Naseer ya Isa wajensa. Gaisawa sukayi kafin Naseer ya fara fada Masa duk halin da yake ciki da yanda suka rabu da Hajara da Kuma shawarar da Naeeema ta bashi shi kam Yana cikin tsaka Mai wuya Dan Allah Mallam Musbahu ya taimaka masa da shawara shi kam Bai San ya zaiyi ba Murmushi Mallam Musbahu yayi Yana "Naseer a gaskiya na Dade Banga Mai irin Halin mahaifiyarka ba nidai a ganina kayi istahara Nima Zan maka insha Allahu idan har rabuwarku da Naeema shi yafi alheri gwara ku rabu Dan a gaskiya Mahaifiyarka Bata San Naeema Kuma zata iya komai Dan ta ta cima burinta tunda Naga halin da suka fara jefa ta a ciki nake balain tausayinta shiyasa tunda kuka tafi tana cikin Addu'oi na dani nasan Mahaifiyarka bazata tab'a barinta ba Amma tunda abin ya Kai ga ta hayo mutane Dan kawai a kasheta toh a ganina gwara ku hakura da juna kawai" "Mallam Inasan Naeema banasan rabuwa da ita yanzu idan na rabu da ita waye zai kularmin da yarana sanan ita Naeema wajen wa zataje ita da Bata da kowa wlh Mallam Ina balain Tausayinta Bata da kowa sai Allah sai Ni" Toh ya zakayi Naseer ai bance lailai ku rabu ba ce maka nayi kayi istahara Nima Zan tayaka zuwa gobe insha Allah idan zama Bai Kare a tsakaninku ba sai mu San yanda zamu b'ullowa mahaifiyar taka" Sosai Naseer Yaji ya rasa Mai ke Masa dadi tunda ya auri Naeema Bai tab'a hararo wa kansa rabuwa da ita ba zancen ma rabuwa da ita Bai taso ba zai dai dage da Addu'a Akan Allah ya kawo masa d'auki ya sa mahaifiyarsa ta sauko. Naseer tsabar fargaba kasa ma istaharan yayi sai Mallam Musbahu ne yayi istaharan na kwana uku Inda washegari ya Kira musbahun Yana "Mallam Naseer nayi istahara sosai Akan Kai da Naeema Zama Bai Kare a tsakaninku ba akwai ma sauran rabo a tsakaninku insha Allahu Amma matsalar bansan ta yanda zaka b'ullowa mahaifiyar ka ba Amma Ina ganin zaka rakani wajenta Zan rok'eta na kuma Mata nasiha akan ta barka da matarka karta rabaku Amma idan Taki Naseer Kayi Mata biyayya ka hakura da Naeema inyaso sai ka dage da Addu'a idan da akwai rabon ku cigaba da zama sai kaga ta dawo maka" Naseer Sam baiji zai iya rabuwa da Naeema ba ya dai yarda Zai Kai Mallam Musbahu ya roki Mahaifiyar tasa kila ya samu ta ji maganarsa. Da Yamma Mallam Musbahu ya shirya shi da Naseer suka nufi gidan Naseer da ya zama na Hajara. Suna Isa k'ofar Gidan Gaban Naseer ya hau fad'uwa haka kawai yaji Yana tsoron had'uwa da ita Kwankwasa wa sukayi sai da suka Dade kafin suji takun tahowa Ana bud'e k'ofar suka ga Hajara ce da kanta tana sanye da bak'ar doguwar Riga. Tana had'a Ido da Mallam Musbahu ta juya da Sauri tana k'ok'arin rufe k'ofar Mallam Musbahu kuwa tura k'ofar da karfinsa Dan yasan za'ayi Haka yasan Dole idan ta ganshi ta tsorata Ja baya tayi da Sauri ta kalli Naseer dake bayansa tana "Mai yasa ka kawomin wanan gidana"? Murmushi Mallam Musbahu yayi Yana "Ni na saka ya kawoni Kuma ba abinda kike tunani bane ya kawoni Ni banida wani had'i dake Dan Haka ki kwantar da hankalinki muyi magana" Hajara kwarjinin da yayi Mata yasa ta kasa musa Masa ta samu waje daga tsakar gidan ta zauna tana jifan Naseer da harara. Mallam Musbahu babbar rigarsa ya nade ya zauna Akan dakalin daya gani. Naseer kuwa ya shiga ciki ya d'auko tabarma ya shimfida ya zauna Mallam Musbahu kuwa yace ya barshi daga Inda yake zaune Naseer kuwa sai gaishe da Hajara yake ta had'e Rai taki kallonsa Mallam Musbahu gyaran murya yayi Yana "Mmn Naseer wajenki Nazo Dan muyi wata magana da Kuma rokon arziki da Kuma wata Yar Nasiha da Zan miki Mmn Naseer Duk halin da kike ciki keda Naseer nasani duk wani Hali da kike ciki nasani Abu daya nakeso kisani Allah ya hallicemu ne Dan mu bauta Masa Bai hallicemu Dan muzo mu ringa zalintar juna ba nadai San kin fahimci maganata Naseer da kike gani yarone Mai hankali da ladabi kema kinsani Naseer zai iya amfani da ilimin da Allah ya bashi ya kawo karshen zaluncin da kikeyi Amma Sabida darajar ke mahaifiyarsa ce ya kyalleki bansan dadin da kikeji a halin da Kika jefa kanki ba bansan dadn da kikeji a sab'awa Allah da kikeyi ba Abu daya kawai Zan Gaya miki wlh kiji tsoron Allah kiji tsoron ranar da Zaki mutu ki tsaya a gaban Allah da littafinki a hannunki duniya ba gidan Zama bane gwara tun lokaci Bai Kure Miki ba ki tuba ki koma ga Allah ki nemi wayanda Kika zalunta ki nemi yafiyarsu idan ba Haka ba wlh ki rubuta ki ajiye zakiyi nadama a lokacin da bashida amfani Kar biyan bukata ta duniya ta saka ki ki yanki ticket din da Zaki dawwama a wutar jahanama karki dauka mutuwa da kwanciyar kabari da hisabi duk tastuniya ce wlh ba tatsuniya bace gaskiya ce nasan dai kinsan wayanda suka mutu toh basu bambanta damu ba ba kuma.wasu hallittar bane su mutane ne irinmu gwara ki shiga hankalinki ki nutsu tun kafin lokaci ya kure Miki na sauke nauyin dake kaina na Gaya miki gaskiya ruwanki ne ki dauka ko akasan Haka Sanan magana ta biyu inaso na Dan Allah ki bar Naseer ya zauna lafiya da matarsa idan yaso duk wani Abu da kikeso sai ya Miki uwa fa an Santa da Kaunar Dan data Haifa da Kuma San farincikin danta sabida me kike San ki raba Naseer da Naeema,Mai yarinya ta Miki Kika tsaneta Haka"? Hajara sosai take Jin shakar iska na neman Yi Mata wahala sabida waje daya da suka zauna da Mallam Musbahu har wani zafi zafi takeji a jikinta gashi ji take kamar ya daudaureta yau badan shi bane bata Jin akwai Wanda ya Isa ta tareta da wandanan maganganun "Ni kawai bana santa ne sabida Naseer ya Fifita ta akaina bana santa bana kaunarta sanadinta ba irin masifar da ban gani ba Dan Haka Ina Kan bakana ko Naseer ya rabu da ita ko ya canja wata uwar"? Tace tana jijiga kafa Naseer durk'usawa yayi akan gwiwarsa ya hau Bata hakuri akan ta barshi da Naeema Wanda Naseer Bai San hakan balain kona Mata Rai yake "Ki dai Yi hakuri mmn Naseer ki barshi ya zauna da matarsa idan yaso ki gindaya Masa duk sharadin da kikeso"? Shiru Hajara tayi Tana tunanin duk shawarwarin da Yan kungiyarsu Suka Bata da hanyar da zasu bi cikin sauki su raba Naseer da Naeema "Naji Zan yarda ya cigaba da zama da ita Amma da sharadin wlh bazai bar garin Nan ba sai ya auri yar kawata Hindatu idan kuwa ya dage bazai Aureta ba wlh nima sai ya rabu da Naeema" Naseer jin bazata raba shi da Naeema ba yasa yayi saurin cewa ya amince duk da har a Ransa baya San Karin auren A takaice Mallam Musbahu sai daya Kara yiwa Hajara wa'azi Wanda Hajaran kuwa take Allah Allah ya tafi ganin yak'i tafiya yasa ta tashi tayi shigewarta ciki. Mallam Musbahu kuwa fitowa yayi Naseer ya biyoshi a baya Mallam Musbahu ya kalleshi Yana "Naseer badan nasan addua na iya canja komai ba da nace maka ka hakura da Naeema ka samu sukuni a rayuwarka itama ta samu kwanciyar hankali akwai wani babban Al amari danake hangowa a gaba daga Kai har Naeema bazai muku dadi ba wani Kuma babin ne zai bud'e muku Amma fa bansan ko menene ba Amma ka dage da Addu'a Dan babu Abinda addua baya canzawa Zama Kuma Bai ganka ba addua ka dage akai fiye da na d'a mahaifiyarka tayi nisa da Bata Jin Kira iya kalmomi nasan bazai saka tayi laushi ba tunda har tace ta yarda ka cigaba da zama da Naeeema Amma ka sake aure akwai wani Abu a ranta Allah shi ya barwa kansa sani. Naseer Naeema Amana ce a gareka idan kaga zata cutu zamanka da ita akwai cutarwa bi maana mahaifiyarka zata cutar da ita gwara ka Sawwake Mata Dan duk Inda ka Kai ga Santa watarana mutuwa sai ta rabaku ko ka rigata tafiya ko ta Riga ka Kuna cikin addua ta insha Allahu Allah ya shiryi mahaifiyarka yasa ta Gane daidai ka daina damuwa da Naeema Bata dangi idan dai kaga Abubuwa sun ci tura ka Sawwake Mata Ni Zan zame mata uba insha Allahu" "Yaushe zaka koma"? D'agowa Naseer yayi jikinsa a sanyaye da maganar da Mallam Musbahu ya masa yace "Nima bansan ranar da xan koma ba kafin na koma Zan zo Dan naji tana sai na auri wacce zata hadani da ita Zan bar garin Nan" Yauwa kazo akwai sakon da Zan baka ka kaiwa Naeema insha Allahu ba Tsafi ba koma me zasu Mata insha Allahu bazai yi tasiri akanta ba Godiya Naseer ya hau mishi. Sai daya rakashi har bakin titi ya juyo ya dawo gida. Inda yana dawowa Hajara ta hau Masa masifa akan me zai d'auko mata Mallam Musbahu ta Inda take shiga Bata Nan take fita ba Bai ce Mata komai ba Dan shi dai lallab'ata yake. D'akinsa na da ya shiga Inda ya tarar da komai nasa na Nan Kamar ma baa shiga d'akin sabida lodin littattafan addini dake cikin d'akin. Da kansa ya samo tsintsiya ya share d'akin ya gyara yayi wanka ya fito Dan ya tafi massallaci da zai Samu da ya juya gobe Amma yasan Bai Isa ba yanzu Hajara zata Masa fassara. Bai dawo cikin gidan ba sai da akayi Sallar ishai ya take cikinsa a waje ya shigo gidan wajen karfe Tara na dare. A Palo ya tarar da Hajara da Safiyya da Lami da bayanta yayi kamar Mai Kusumbi Sai wata da kallo daya ya Mata ya dauke idonsa Dan Haka kawai yaji jininsa Bai d'auketa ba Sanye take da Bakin Riga Mai ratsin fari. Su Safiyya kawai ya amsa gaisuwar su yayi wa Hajara barka da hutawa ya sa.kansa xai shiga d'akinsa Hajara kuwa ta dawo dashi tana ya zo ya zauna A kujerar da babu kowa ya zauna ya had'e Rai sabida yanda bakuwar ta zuro Masa Ido kamar Mayya "Wannan itace matar ka Hindatu sai ka fara Zama da ita anan kafin ka koma can garin wurin wancan mayyar matar taka Dan Dole sai naga Kun fahimci juna kafin ku bar garin Nan kasan Kai yanzu idonka a rufe yake babu wacce kake gani da gashi idan ba wanan Aljanar ba" Wani fari Hindatu ta hau Yi Masa da Ido Naseer kuwa ya d'auke kansa yana "Umma bana San na haura jibi Dan inada ayyuka Dana baro da yawa acan da zan samu da gobe an daura auren jibi sai mu wuce da ita "Wanan ne Kuma baka Isa ba Nasiru wlh a baka Dade ba sai kayi sati a daura dai auren goben Dan baka Isa ka maida Hindatu bora ba gwara na fara ganin yanayin Zaman naku agabana. Naseer Bai iya Kara ce komai ba ya mik'e Yana Allah ya kaimu Ya shige dakinsa ya zauna a Gefen gadon tare da dafe kansa ba abinda yake tunani Sama da ya Naeema zata karbi zancen Karin aurensa gashi hindatun ma ko kad'an Bata Masa ba. Bai San da shigowar mutum ba sai ji yayi an zauna a gefensa Da Sauri ya dago da kansa Suka had'a Ido da ita ya mik'e zumbur Yana ke Mai Haka kika shigo min daki? Murmushi ta Masa da shi a idonsa yake tona asirin muninta tace "Umma ce ta turo Ni tace muyi Hira" "Toh sai ki Bari sai an daura ko Kafin ki fara shigo min daki Dan Allah tashi ki fita Wani irin kallo ta Masa kafin ta mik'e ta fita a fusace. Naseer kuwa yaja dogon Tsaki ya d'auko Quraninsa ya hau Kan sallaya Ita kuwa Hindatu tana fitowa ta kalli Hajara data zuba mata Ido tana "wlh wanan Dan naki yaci sa'a ina Sansa da wlh yau na hukuntashi Bai San wacece ni ba ko" "Karki damu zamu yi maganinsa Dani yake magana anjima ki zuba maganin Nan a bakin kofarsa indai ya tsallaka angama sai yanda kikayi dashi" Murmushi hindatun tayi ta samu waje ta zauna Sha biyun dare Hajara sukayi shigar jajayen kayansu suka fita Hindatu Kuma ta Ciro garin maganinta daga rigar no-no taje k'ofar d'akin Naseer ta Barbada daga bakin kofa Tana murmushi Naseer kuwa duk abinda tayi akan idonsa ne.hakane yasa tana barbadawa ya girgiza Kai ya cigaba da Addu'oinsa sai daya Gama tas Ya d'auko tsintsiyar bandaki ya share garin maganin da Addu'a a bakinsa. A takaice washegari Hajara ta Sako Naseer a gaba aka daura auren Naseer da Hindatu ta Kuma tilastawa Hindatu tarewa a d'akin Naseer a ranar. Naseer kuwa ko kallonta baiyi ba ya d'auko Quraninsa ya hau kan dadumarsa ya ware muryarsa ya hau karatun Qurani. Hindatu kuwa aguje ta baro d'akin Ta fito ta zauna a Palo Dan gidan ba kowa suna can suna shagali Yar shugabarsu ta auri Naseer. Naseer kuwa anan ya Gane itama Yar kungiyar mahaifiyarsa ce shi kuwa ya dage ya cigaba da karatu. Wasa Wasa Haka sukayi sati Inda Naseer ya fara had'a kayansa akan zai tafi Hajara kuwa kamar ta fashe Dan bakin cikin Dan babu irin aikin da basuyi akansa ba Amma fir tak'i kamashi abin har mamaki yake bata har a abinci sun saka Kuma yaci duk a banza. Akan dole suka shirya raka Hindatu Kano da sunan zasu kaita wanan Karin Hajara ce da wata Yar kungiyarsu sai Hindatu. Naseer kuwa babu abinda baiyi ba akan su zauna Hajara kuwa ta dage su zasu Kai Hindatun. Bai Kuma manta da zuwa wajen Mallam Musbahu ba Inda ya karbo mata Sakon da zai Kai Mata ya Kuma gayya Mata yanda za'a amfani dashi. Sosai yayi kewar Naeema da yayansa. Ahaka suka dau hanyar Kano Yana ji Kamar ya shake Hindatun dake ta Karo jikinta a jikinsa Yasan hanyar da zai rabu da ita cikin sauki wuyanta Hajara su dawo su barota da ayar Allah zai Gama da ita a Dan zaman da yayi ya Gane su Saffiya ma sun xama Yan kungiya Har tambayar lami yayi Mai ya sameta a bayanta tace Masa fad'uwa tayi. Naeema Tunda Naseer ya tafi nake cikin Zullumi da tashin hankali bansan Mai yasa hankalina ya kasa kwanciya da tafiyar ba ga wani irin hargitsatsen mafarkin da nake fama dashi hakane yasa na zage da Addu'a ko makaranta bana zuwa sabida rashin kwanciyar hankali a Dan tafiyar da yayi mmn Mannir ta ringa shigomin anan take wuni ta debb'emin kewa ahaka ta sakoni gaba da tambayar Mai ke damuna badan Raina naso Na na bud'e Mata cikina na Gaya Mata halin da muke ciki da uwar mijina mik'ewa tayi sabida girgiza da tayi da labarina Ni kuwa nayi murmushi ta koma ta zauna ta hau bani shawarar indai Umma ta Kara matsamin na saka Naseer ya sakeni kawai Kar na zauna idan ba Haka ba wlh watarana Umma zata ci Nassarar kasheni dayake ta girmeni sosai ta bani shawarwari na Kuma ji dadin gayawa wani damuwar danake ciki. Na Kuma zauna Akan shawararta na idan Abu yak'i ci yak'i cinyewa nasa Naseer ya sakeni. Amma kasan zuciyata bana Jin Zan iya rabuwa da Naseer din Kuma bawai sonsa ne yasa nakejin Haka ba illa rabuwa da yayana Dan Ni nasan Naseer bazai Taba bari na tafi dasu ba uwa uba Umma ko Dan ta kuntatamin ta hanani daukarsu tunda ta lura farinciki na shine Naga yayana a kusa Dani. Gashi cikin ikon Allah yaran nawa duk da karancin shekarunsu Allah ya musu baiwa ta hankali da k'ok'ari gashi kansu a had'e yake duk kuncin da nake jina aciki da na kalli baiwar Yaya matan da Allah yamin sai naji wani irin Sansu Ina Addua Akan Allah ya raya min su yasa Naga girman su humaira. Kullum aka kwankwasa kofar gidana sai na saka Rai da ganin ko Naseer ne ya dawo. Yau ma Ina zaune a palon na Gama duka aikin gidana na kwantar da Humaira a tsakiyar palon su Zahira sun tafi makaranta Minal kuwa Tana wajen mmn Mannir. Tv na kunna Ina kallo Amma hankalina baya Kan kallon Yana can Calabar. Kwankwasa kofar danaji anayi ne yasa na mik'e a Raina Ina tunanin kila mmn Mannir ce ta Gama ayyukanta ta dawo banma tsaya tambayar waye ba na bud'e k'ofar Inda kuwa nayi tozali da Umma da wata da bansanta ba bayansu Kuma wata ce zatayi Sa'ar Umma Idona Sam bai hangomin Naseer dake sauko da Kaya daga bayan mota ba. Cikin wani irin fad'uwar gaba naja da baya banma.san na zub'e a kasa ba na hau gaishe su. Wani mugun harara.umma da yarinyar suka zabgamin sai Saar Umma ce ta amsa da wani shu'umin murmushi. Umma kuwa shigowa sukayi suka barni a durk'ushe tana " babu yanda kika iya Dani Dan gidan Dana ne sai dai ki hadiyi zuciya ki mutu Aurene dai Naseer yayi Dan badan ke kadai na haifo.shi ba tunda kin k'i Tafiya na saka shi yayi aure idan kin Isa kisa ya saketa anan Zan nuna Miki karfin ikona" Tunda naji kalmar aure naji jina na neman daukewa ko maganganun da Umma keyi sama sama nake jinta. Banma San lokacin da Naseer ya shigo ba sai ji nayi ya dagoni daga tsugunnen danake Yana "Naeema lafiya Kika zauna anan"? "Ya bazaka ganta a zaune ba tana bakin ciikin ganina tana bakin cikin ganin kayi aure dalla Ni ku taso ku nuna Mana d'akin da zaa Kai kayan Hindatu" Da Sauri na mik'e cikin San danne abinda nakeji duk da jirin dake neman kayar Dani na nufi palon Ina Kara musu sannu da zuwa tare da nufar kitchen Dan na dauko musu ruwa. Ina Jin muryar Umma tana cewa asirce Naseer nayi ita tasan duk abinda Naseer keyi ba a hayyacinsa yake ba. Inaji ta Kira sunan Hindatu tana ta lek'a dakunan ta zabi Wanda takeso su shigar Mata da kayanta Ni kuwa kasa fitowa nayi sabida rawar da jikina yake sai lek'a Hindatu nake da ta kusa biyuna a tsayi Gata da girman jiki idonta kawai ya Isa ya tsorata Ni ba auren ne ya d'aga min hankali ba yanda zan zauna gida daya da ita shi yafi dagamin hankali. Hannuna na rawa na dauko musu ruwa Mai sanyi Ina zuwa na ajiye musu agabansu Adaidai lokacin da Hindatu ta fito daga d'akina tana cewa Umma d'akina ne ya Mata a fitomin da kayana....... [6/26, 3:27 PM] +234 803 635 0240: *NAGA TA KAINA* *NA SADNAF*🌸🌸 ®️ *_PURE MOMENT OF LIFE WRITERS_* _{We Don't just entertain nd educate we also touch the heat of readers P.M.L}💪🏻_ *Free Novel* *Page 16* Ta zauna Gefen Umma tana kad'a kafa. Naseer wani irin Mugun kallo ya Mata Yana "ga dakuna can guda biyu ki duba Wanda ya Miki ki saka kayanki a ciki idan Kuma Bai Miki ba sai kisan nayi babu yanda za'ayi sama taka ki zo ki wani ce a tasar Miki daga d'aki. Daga Haka Naseer ya mik'e fuskarsa a balain had'e ya ko kallon B'arin da Hajara take Bai kalla ba ya shige dakin Naeema ya banko k'ofar Ni kuwa Yana shigewa na mik'e da Sauri cikin fad'uwar gaba da rawar jiki na fara k'ok'arin juyawa na koma kitchen Umma kuwa ta daka min tsawa tana na koma na zauna. Da Sauri na zauna a gabansu Kamar Mai neman gafara kafin kace me har hawaye ya fara wanke min fuska Umma na k'ok'arin Magana naji muryar Hindatun tana "Hajara zamu daidaita da Wanan Dan naki kuwa Kinga yanda yake min fa ita Kuma nasan badan komai yasa yake Haka ba sai Dan wanan kod'add'iyar Koda uban me ta fini oho" Da Sauri Hajara ta karbe tana "ki kwantar da hankalinki Ni zanyi maganinta idan Bata bar gidanan ba zata bar gidanan idan wuya ya kusa kasheta ko Kuma a fita da gawarta bantaba ganin nataciya irin yarinya Nan ba ni farkon ganina da ita naji batamin ba Dan Ni idan mace ta fiye kyau Tsanar ta nake Ni nasan Bata bar Dana Haka ba wlh akwai abinda tayi Masa ta juyar Masa da Kai Amma da sannu Zan dawo da hankalin Dana kanki Hindatu ke dago ki kalli cikin idona. Da Sauri na Dago har a lokacin hawaye kawai ke zuba a fuskata "Ga Auntynki Nan Hindatu matar Naseer Kuma zabina duk abinda take so shi za'ayi a gidanan duk aikin data sakaki ki tabbata kinyi Mata idan ba Haka ba wlh ranki ne zai b'aci kindai San halina sai dai ki bawa wani labari Dan Haka Maza tashi kije ki zab'a a cikin Dakunan can Wanda yafi girma ki gyara ki zo ki kwashe Kayanta ki Kai Mata ki saka Mata kuma.ruwan wanka idan kin fito ki daka Mana Sakwara muci kinji ko bakiji ba"? Da sauri na gyad'a mata Kai na mike na nufi d'akin karshe Dan yafi na tsakiyar girma da Umma ta zauna ita da Saffiya. Ina gyara d'akin Ina kuka wai ni Haka rayuwata zata Kare daga wanan sai wanan Mai Nayiwa Umma Haka ta tsaneni. Ina Gama gyara d'akin na wanke band'akin dayake da ruwa a band'akin na tari ruwa a bokiti Yana cika na fito. Na koma palon na fara kwaso kayan Hindatun Ina kaiwa daki Umma sai zagina take Tana zagin iyayena ita kuwa kawarta kur tamin Ido kamar zata cinyeni Ni kuwa na hau addua a Zuciyata Dan kallon da takemin yayi yawa ita kuwa Hindatu sai wani girgije girgije take Tana yatsina fuska. Ina fitowa daga d'akin na shiga kitchen na fito da doya manya guda biyu na fara feraye wa Ina cikin ferayan naji Sallamar su Zahira. Babu Wanda ya amsa musu bansan ya akayi ba sai ji nayi Zahira ta kwalla wani uban ihu sai dum dum nakeji kamar irin an samu babba Ana duka. Jikina ne ya hau rawa na runtse Ido hawaye na zubomin ko ban lek'a ba nasan Umma ce ke dukan Zahira na Dade da sanin Umma ta balain tsanar zahira Ni nasan tsanar data min ne ya shafi Zahira shiyasa ma a cikin Yarana Zahira ko muryar Umma taji sai ta nutsu kaga alamar tsoro ya bayyana fuskar ta sosai dukan da takewa zahira na ringa jinsa a jikina ta Sha dukan Zahira ba tare da ta Mata komai ba na Kuma rasa Mai Yar yarinya da Bata fi shekara bakwai ba ta Mata. Zagin Zahira kawai take Tana durma Mata duka tana "shegiyar yarinya tun kina karamarki an koya Miki bakin Hali baki iya Gaisuwa ba wane irin tarbiya Naeema ta muku wato ita ta kitsa muku idan Kun gani karku gaisheni ayi yara basuda tarbiyya balle wanan Yar iskar yarinya Ni nasan yarinya Nan idan ta girma Yar iska zata Zama shegiya Mai halin uwarta" Naseer dake Sallah a a guje ya fito daya Sallame Sallar sabida yanda Zahira ke ihu Dan ba karamin Jibga take mata ba. Nadeeya kuwa Tana gefe tana kuka Fusge Zahira yayi cikin wani irin B'acin Rai ya kalli Hajara Yana "Haba umma Mai karamar yarinya Nan ta miki kike dukanta Haka kamar kin samu babba haba Umma " "Zaka iya Rama Mata tunda na daki Yar gwal Naseeru Kai baka ganin irin tarbiyya da shegiyar matarka ta musu kwanaki Dana zo suna kallona Suka k'i gaisheni yanzu Kuma sun shigo wanan Yar iskar yarinya ta zo zata wuce ta gabana har da taka min kafa duk idonka Bai bud'e kaga irin tarbiyyar da Naeema ta musu ba sanan Dan na daketa kazo ka tsaya kana min tambayoyi Na daketa Naseer zaka iya Rama Mata nidai sukayi ba daidai ba Dole na hukunta su daga Kai har Naeema San Yaya ya rufe muku Ido Kun kasa musu tarbiyya ko baki akayi ai Dole aji kunya ai tunda yarinya Nan ta kwaso uwarta nasan inta girma ba lailai tayi albarka ba" "Allah ya Miki albarka Zahira zakiyi Albarka insha Allahu nace Ina kankame wuk'ar hannuna da har ya yankeni jini na zuba bansani ba sosai kalmomin da Umma ke jifan Zahira dashi ya ringa min ciwo har tsanar ba iya Ni ya tsaya ba har Kan zahira da bani kadai na haifeta ba Jinin Naseer daya kasance danta na yawo a jikinta har Umma tace Zahira Yar iska zata zama baza tayi albarka ba wanan wane irin kiyayya ne kuka nake kasa kasa Ina jiyo muryar Naseer na "Umma wane irin kalamai kike Yi Haka karki manta fa yarinya Nan jikar ki ce akan me Zaki na cewa baza tayi albarka ba insha Allahu yayana zasuyi albarka Umma Dan Allah Umma kiringa kiyaye kalmomin da zasu fito bakinki Zahira fa yarinya ce ballantana kice ta mallaki hankalinta Umma Kinga yanda Kika kumbura Mata jiki fisabillilahi idan Haushin Mahaifiyarta kike ji ai Bai Kamata laifinta ya shafeta ba nawa Zahira take tsakani da Allah Naeema na iya kokari Akan yaran nan ba Kuma Ina fada Dan na kareta ba" "Ai duka nake jira kamin Naseer ya ka tsaya iya surutai" Naseer da idonsa ya kad'a yayi ja Bai ce komai ba ya daga Zahira da numfashin kirki ma Bata iyayi ya Kai ta d'aki dawo ya rik'e hannun Nadeeya ya d'auki Humaira da ihun zahira ya tasheta take ta kuka itama" Nima kukan Humaira ne yasa naso fitowa daga kitchen din na d'auketa na goya ta sai Naga Naseer ya d'auketa Hakane yasa na koma kitchen na daure hannuna da jini ke ta zuba na cigaba da aikina Ina kuka Ina tunanin abin Yi Taya ya ma Zan iya barin yayana tayaya Zan iya tafiya na bar yarana a hannun Umma da Raina Agaban idona tana azabtar min da Yaya inaga bana Nan. Ina cikin had'a Miya naji Sallamar Mmn Mannir nasan Minal ta kawomin tunda Magriba ta kawo Kai Gaida su Umma take naji Umma na tambayarta daga Ina take Mmn Mannir kuwa Tana Mata wanan tambayar tasan wacece ita kuwa ta had'e Rai tana Ina matar gidan take"? Take Hindatu ta watsa Mata harara tana "Gani Nan nice matar gidan ya akayi"? Wani kallon Tara saura kwata Mmn Mannir ta mata ta ja Tsaki tayo hanyar kitchen da take Jin motsina ciki. Ni kuwa Ina kitchen Ina Jin maganr da suke jikina ya hau rawa. Har kitchen mmn Mannir ta shigo ta ajiye abincin hannunta ta kunto Minal da Saura wata biyu tayi shekara biyu da bacci ya d'auketa tana "Gata Nan tayi bacci Naga alamar yau gidan naki a cike yake toh nidai shawarar da Zan baki shine wlh ki kwatarwa kanki 'yanci ki rage tsoron Nan idan babba Bai ji kunyar hawa jaki ba toh jaki bazai ji kunyar kayar dashi ba. Ihu kawai mukaji Umma nayi ta hau kururuwa Sosai hankalina ya tashi na rude da ganinta a bakin kitchen abinda ya ban tsoro yanda take zunduma ihu "Yanzu Ni kike cewa jaka Yar nan Mai na Miki"? Naseer a guje ya fad'o kitchen din mmn Mannir kuwa ta saki baki cikin mamakin sharrin da Umma ke neman Yi Mata Kuka umma ta saka ta kalli Naseer dake ta tambayar Mai ya faru Ta hau cewa "wanan yarinya Nan ce tayi Sallama muka amsa tana ganinmu taja Tsaki ta wuce mu ta shiga kitchen dinan shine Ni Kuma nayi mamakin tsakin da ta Mana shine na biyota naji dalilin dayasa ta Mana Tsaki Ina zuwa naji tana cewa Naeema wacce jakar ce wancan Yanzu Naseer har maganata Naeema keyi da wasu har a shigo Inda nake ace min jaka toh wlh daga yau Kar na Kara ganin kafar matar Nan a gidanan wlh daga yau Kar na Kara ganinta da Naeema idan ba Haka ba daga Kai har Naeema sai na dau mummunan mataki akanku da ganin matar Nan ba matuniyar arzki bace" "Innalillahi wa Inna ilaihi rajiun yanzu mama da girmanki kike karya da girmanki Zaki min sharri Ni nace Miki jaka kiji tsoron Allah" Naseer kana kallo tana cemin Ina karya bazaka dau mataki ba" Mmn Mannir Bata Bari ma Naseer yayi magana ba ta mik'a min Minal tana "ba sai kin biyo ta Haka Zaki rabani da Naeema ba ki kwantar da hankalinki bazan Kara zuwa ba kamar yanda kikeso sabida na lura bakyaso kowa ya rab'i Naeema Sabida ki yi ta azabtar da ita Kar tayi hulda da kowa ballantana a kawo mata d'auki toh Bari kiji na fada miki kiji tsoron Allah domin shi sharri Dan aikene watarana zai dawo Miki tun a gidan Duniya Allah ke hisabi kuma Zaki ga karshenki Naeema Zan tafi xan Kuma baki shawara idan Kinga akwai cutarwa a zamanku ki hakura da Naseer tunda Zama da danta ba Dole bane daga Haka ta bangaje Hajara tayi wucewarta. Umma kuwa hannu ta hau tafawa ta kalli Naseer tana "Ashe gulmana Naeema keyi Ashe Haka Naeema take bin mutane tana musu gulma ta abin har ya Kai har da ta tamin sharri Dama Haka kike Naeema toh wlh daga yau makarantar ma kin daina zuwa tunda acan kike haduwa da mutane kiyi gulmana har ki zageni Naeema Ina uwar mijinki toh wlh duk zagin datamin ba Ni ta zaga ba uwarki ta zaga Kai Naseeru wlh Tallahi na soke zuwa makarantar ta ko k'ofar gida bana so Naga kafarta a da sati daya zanyi Amma na ma fasa tafiya sai na kwana biyu shegiya Mayya" Daga Haka ta juya ta barni a durk'ushe Ina ta kuka ko kad'an ban kawo sirrin Dana gayawa mmn Mannir zata zo ta tona a gaban Umma ba Dama gudun Haka yasa tun farko naki Gaya Mata ko Naseer ma ai bazai ji dadi na fadawa wani maganar ba duk ba wanan yafi bak'anta min Rai ba sai makaranta data ce bazan koma ba Allah yasan idan akwai abinda ke faranta min a rayuwa yanzu Bai wuce makarantar da nake zuwa nake samun ilimi ba sosai nake Kara sanin rayuwa sai gashi lokaci guda Umma ta katsemin Mai yasa mmn Mannir zata min haka" Dafani da akayi yasa na Dago Naga Naseer ne da idonsa ya kad'a yyi ja idan ba karya idona yamin ba har hawaye ne ya Dan kwanta a idonsa "Kiyi hakuri Naeema ki cigaba da hakuri watarana sai Labari nafiki Jin ciwon abinda ke Miki Amma ba komai Zan sadaukar da farincikina na faranta Miki idan Naga Umma ta cigaba da matsa Miki Zan sawwaake miki sabida ki samu yancin Mahaifiyata ce bansan ya zanyi da ita ba Dan Allah kiyi hakuri mu cigaba da gayawa Allah Yana sane damu ko auren Nan data k'ak'a bamin ba so nake ba tilasta min tayi idan kin Gama kizo akwai sakon da Mallam Musbahu ya bani na baki" Daga Haka Naga ya mik'e da Sauri ya nufi dakina da Minal a hannunsa. Ahaka na daka Sakwaran Ina kuka Sosai naji komai ya ficemin a Rai na ringa Jin inama inada damar da Zan gudu da yayana ko bara ne ma na ringa Yi a titi Ina ciyar dasu Amma aka cigaba da Haka zaa Kai ga na gudun Dan na gaji Kuma Ina gudun ba'a garin Nan Zan tsaya ba Tasha zanje na hau motar da zata kaini garinmu. Har daki na Kai musu abincin Dan sun bar palon Hindatu da Kawar Umma ne kawai a zaune Umma da alamar ta shiga bandaki. Nazo fitowa Hindatu ta tsayar Dani tana na kawo Mata wani lemon Bata San wanan tace tana hararata Haka na fita na dauko Mata wani na fito daga d'akin na shiga d'akina Dan nayi Sallah Magriba Dan Ina shiga d'akina Naga Zahira a kwance tayi rub da ciki bayanta yayi jawur dayake farina ta d'auko sai sauke ajiyar zuciya take. Naseer Kuma na d'aga gefenta Yana Dan mulka Mata jikinta da Robb bandaki na shiga da Sauri sabida kukan dake neman k'wacemin. Ahaka naci kukana na Godewa Allah nazo na tadda sallah Ina iddarwa na maida kaina nayi Sujjada na fara kuka Ina rokon Allah ya kawomin d'auki. Naseer shima Yana daga daya barin nawa bansan.mai ya hanashi zuwa Massallaci ba ahaka mukayi sallar Isha muna iddarwa.naje kitchen na dauko Mana abinci dayake indai Naseer na Nan a faranti daya muke ci da yaran Minal ce kawai nake Dan Bata a baki Sabida Naseer da su Zahira na zubo abincin Dan bazan iya cin abincin ba sabida b'acin Rai. Zahira har lokacin sauke ajiyar zuciya take Ni Kuma bana San ma na jawota jikina Dan yanda nakejin Raina kuka zanyi sosai bazan iya rarrashinta ba. Naseer shima gani nayi ya kasa cin abincin ya hau bawa Nadeeya abinci a baki ganin Zahira Taki cin abincin yasa yace Mata taci Mana bud'ar bakinta sai cewa tayi "wlh Tallahi Abba ban yiwa Umma komai ba Nadeeya ce ta fara gaisheta shine na tsugunna Dan na gaisheta Dan Haka Umma ta koya.mana mu ringa tsugunna wa idan zamu gaida babba shine Ina tsugunnawa ta hau dukuna wlh ban Mata komai ba ta karashe tana fashewa da kuka. Kau da kaina nayi Sabida hawayen dake tsere a fuskata Naseer kuwa sai daya hadiyi yawu Mai daci kafin ya jawo Zahira jikinsa ya hau Bata hakuri Yana Bata abincin a baki wanda dak'yar ta fara karbar abincin tana ta sauke ajiyar zuciya. Yana cikin Bata muka ji a banko k'ofar Umma ta fado d'akin tana "badai kana nufin a d'akin ta zaka kwana ba ka dai San sai kayiwa Hindatu kwana bakwai ko"? Dan Haka maza kazo ka wuce matarka na jiranka kafin Nan da wani wata Taran wanan Mai gindin haihuwar ta Kara haifo Mana Yarinya Mara tarbiyya" Daga haka ta zabgamin harara ta Kara banko Mana k'ofar. Daga Ni har Naseer babu Wanda yayi magana a cikinmu Ni zuwa yanzu ma na kasa kukan filin sai na zuci Naseer shima sai daya Dade Bai motsa ba Bai Kuma min magana ba kafin Naga ya mik'e ya janyo jakar kayansa yan Ciro wani bak'in Leda ya bud'e. Yana "Ga sakon da Mallam Musbahu ya bani na kawo Miki" Da Sauri na saka hannuna na karba na duba Yar wasikar da yamin Inda yake cemin na rataya wani rubutu daya nanade da takarda a bakin k'ofata. Sai wani shima da akayi rubutun a ciki aka nannade shi da laya yace na makala a kaina Amma na ringa kiyayewa idan Zan shiga bandaki na ringa cirewa ya Kuma ce Kar manta na ringa kwanciya da alwala a jikina. Sosai naji dadin Aiken da Mallam Musbahu yamin Naseer ne ya ratayamin a saman bangon kofata na samu pin na makala abin akaina. Zage zagen da muka jiyo Umma nayi na Naseer ya rainata yasa ya mik'e da Quraninsa a hannu da Sallaya da carbi ya kalleni yacemin sai da safe. Bance masa komai ba ya fita a Daren ranar xan iya cewa sai bacci barawone ya sace Ni akan sallaya. Naseer kuwa Yana shiga d'akin yaga Hindatu taci kwalliya ta Dane gado tana ta Masa fari Umma kuwa Dama a Palo ya barota da jar doguwar Riga ita da kawarta. Bai kalli Inda Hindatun take ba ya hau Kan darduma ya bud'e Quraninsa yayi gyaran murya Hindatu kuwa ta duro da.sauri ta tsaya gabansa tana "Wai an Gaya maka Ni hoto ce ko wancan kanjalalliyar matar taka Haka kake Mata idan ka shiga d'akinta. Karatun da Naseer ya fara Yi da k'arfi cikin zazzakar murya yasa ta fice da sauri. Yanaji Umma tana kiransa daga nesa Dan Bata iya isowa bakin kofar ba ya shareta ya cigaba da karatunsa Dan ko umman ma da Karatun zai koreta daga gidan Sosai ran Hindatu ya b'aci ta hau surfawa Umma masifa Umma na Bata hakuri. Washegari sai Dana shirya su Zahira Dan su tafi makaranta wani irin bakin ciki ya Kara turnike Ni da yanzu nima na shirya na tafi. Tamkar baiwa haka na zama.a gidan Dan sosai nake bautawa Umma da Hindatu dake balain.jin haushina Dan gani take duk sabida Ni Naseer yak'i kwanciyar Aure da ita Dan karatun Qurani dayaga basa so kawai yake yi daddare da safe Kuma sai ya fito ya shiga d'akina ya Sha baccinsa zuwa Sha biyu ya fice daga gidan. Yana fita kuwa Haka zasuyi ta zagina har Hindatu ta ringa gwada kawo hannu jikina Abinda na lura dashi basa iya biyoni dakina su mun Dan Umma ta Sha gwada shigowa d'akina sai Naga ta koma da gudu ta ringa cemin Mayya. Banma San a rahama nake a baya ba sai da Hindatu tazo gidan ko hanyar waje Umma Bata barina nayi. Naseer kuwa ya Sha fadan ya Sha zagi a wajenta Akan yak'i kula Hindatu shi kuwa sai dai ya Bata hakuri yace akwai adduar da yake yi yana gamawa zai kulata. Ranar da su Umma suka cika sati da zuwa da sassafe na farka kamar yanda na Saba na Dora abincin Safe na fito na tashi su Zahira Dan na shirya su su tafi makaranta. Zahira na fara yiwa wanka ta zauna a d'akin Dan indai Umma na Palo Bata fita Haka take zama adaki a yarana Zahira tana da balain San kallo duk Santa da kallo idan Umma na palon hakura take Haka ma take tsoron Hindatu sabida rankwashin da take Kai Mata a Kai. Nadeeya ita Kuma rawar Kai ne da ita da Wasa hakane yasa Ina Mata wanka ta fito waje na hau yiwa Minal duk na dauka suna d'akin sai dana Gama yiwa Humaira na fito daga band'akin na ajiye Humaira Akan gado na fita zuwa kitchen Dan na juye ruwan tea d'in. Ina gama juyewa na fito Naga Umma ta Sha bakakken Kaya har kasa gefenta Kuma Hindatu ce tayi irin shigarta Haka kawai naji gabana ya Fadi da muka hada Ido ta min wanan murmushi nata Mai tsinka min zuciya da Sauri na shige d'akina Ina jan Allahuma ajirni fi musibati wa aklifnin khairin minha. Ina shiga d'akin naji duk ba a nutse nake ba ahaka na dauko Vaseline na hau shafawa su Zahira Sam ban lura Nadeeya Bata d'akin ba sai Dana Gama shafawa Humaira na lura Nadeeya Bata dakin. Da Sauri na kalli Zahira cikin fad'uwar gaba Ina tambayarta ina Nadeeya take"? Sai tacemin ai Ina mata wanka ta fita waje aguje ko wandon ma Dana d'auko musu Bata saka ba. Hankalina a balain tashe nayi waje na tsaya a Palo Ina dube dube banganta ba na shiga kitchen da Sauri Ina kwalla Mata Kira Nan ma shiru. Kara dawowa nayi na shiga band'akin palon shima Bata Nan bana shiga d'akin Umma Dana Hindatu Amma sabida tashin hankali Haka na shiga Ina kwallawa Nadeeya Kira amma banganta a d'akin ba. Haka kawai naji jikina ya fara balain rawa cikin tashin hankali Nazo tsakiyarsu Umma Ina "Dan Allah Umma kungane min Nadeeya"? Umma ko.kallona batayi ba sai Hindatu ce tacemin ajiyarta Kika bamu" Da Sauri nayi waje na sauka ringa hada stair uku biyu Kamar Zan hantsulo sabida tashin hankali. Lukman babban yaron Naseer da fitowarsa kenan Yana bud'e shagunan Naseer na nufa da Sauri.ina tambayarsa ko ya ganemin Nadeeya ko amsa gaisuwar da yakemin banyi ba. Girgiza min Kai yayi Yana Bai ganta ba. Ban tsaya ma Jin Mai yake cewa ba na Kara Hawa Sama Dan sai yanzu na tuna Nadeeya Bata iya saukowa sai dai a sauko da ita Dan balain tsoro ne da ita Dan Zahira ce ma take iya Hawa bene amma Nadeeya ko lekowa tayi ta kasa aguje take ja da baya Dan gani take zata iya fadowa Dan mmn Mannir har tsokaneta take ta ringa daukarta kamar zata jefota idan tazo. Ina hawa sama na ware murya Ina cigaba da Kiran Nadeeya ya Ina duba kowane lungu da Sako nice har da duba karkashin kujera da gado. Umma da Hindatu suna zaune a Inda na barsu ko gezau basuyi ba kamar ma basu San da hallita ta a wajen ba. Zubewa na yi a gabansu Ina "Dan Allah Umma Baku ga Nadeeya ba wlh Ina Mata wanka Nan ta fito Palo Kuma Bata iya sauka kasa sai dai a d'auketa Dan Allah Baku ga Inda tayi ba"? Ba Wanda ya kulani a cikinsu kamar ma bad'asu nake magana ba hannu na Dora a kaina na fara zabga Sallati na Kara d'aukar hanyar waje a guje ko Humaira danake juyo kukanta daga d'aki ban bi ta kanta ba A bakin kofa na ci Karo da Naseer da tunda ya fita massallaci Bai dawo gidan ba Dan yaje kasan layinmu adduar mutuwar wani bawan Allah daya rasu. Ina ganinsa nasan shima lukman ya Gaya masa Banga Nadeeya ba Kara tambayata yayi "Wai baa ga Nadeeya ba"? Ban iya bashi amsa ba na cigaba da kuka Ina na shiga uku da Sauri Naga ya hau saman Benen batare da yabi ta kaina ba nabi bayansa da Sauri.......... [6/26, 3:27 PM] +234 803 635 0240: *NAGA TA KAINA* *NA SADNAF*🌸🌸 ®️ *_PURE MOMENT OF LIFE WRITERS_* _{We Don't just entertain nd educate we also touch the heat of readers P.M.L}💪🏻_ *Free Novel* *Page 17* D'akina ya shiga kansa tsaye Yana kwallawa Nadeeya Kira ya fito ya duba koina yana "Wai kamarya Ba'a ga Nadeeya ba sai kace almara Taya ya daga yiwa yarinya wanka ta fito kice baki ganta ba"? Wajensu Umma da har lokacin basu nuna sun San Mai ke faruwa ba ya nufa Yana "Umma Dan Allah bakiga Nadeeya ta fito daga d'akin Naeema ba? "Toh ko Ni na saceta da zaka zo kana min tambaya"? B'acin Rai ne yasa Naseer yace a Dan tsawace "Umma daga tambaya sai kice ko saceta kikayi wanan wane irin magana ne" Tsaki da Bai shiryawa fitowarsa ba yayi ya wuce waje fuu Hajara kuwa ta girgiza Kai tana har dasu Tsaki yayi kyau" Zuwa lokacin Ni nasan jinina ya hau sabida tashin hankali. Daga farkon layinmu zuwa karshen layin mu Haka muka zaga muna kwallawa Nadeeya Kira Amma shiru. Mmn Mannir da itama ta fito ita da yaranta tuni ta fasa fita suka hau tayamu Neman Nadeeya makotana suna da balain kirki Dan ba iya matansu ba har da mazajensu Haka suka hau tayamu neman Nadeeya Inda sukayi ta mamaki idan nace musu daga wanka ta fito na nemeta na rasa Kuma duk Wanda yasan Nadeeya yasan Bata iya saukowa daga Sama. Kukan ma kasa wa nayi sai sallati nake har komawa nake gidan na shiga d'akina Naga ko zan ganta har zazzaga kayan wardrobe Dina nayi ko shigewa tayi Amma ba Nadeeya babu labarinta Humaira kuwa har ta gaji da kuka tayi shiru a bayan Zahira da itama ta hau kuka. Sosai nake mamakin Umma da ta kasance kakar Nadeeya da Bata nuna ta damu da neman da muke wa Nadeeya ba hasali ma tea Dana dafa Suka zubo ita da Hindatu da kwai suka dauko gwangwnin Madara Dana Milo suna Shirin hada shayi su sha Waje nake so na sake yi Amma na tsinci kaina da nufar wajensu Sabida daga murmushi danaga.umma na min yasa nasan tana da masaniyar Inda yata take. Agaban Umma naje na zub'e Ina "Umma Dan Allah na hadaki da Wanda ya halliceki ki gayamin Inda Nadeeya take Umma daga d'akina ta fito Kuma Kuna zaune anan ta fito daga d'akina Dan Allah Umma kimin komai idan ta Kama yau na hada kayana na bar gidanan wlh Zan hada Dan Allah ki dawomin da Nadeeya na tuba Umma Nadeeya bata Miki komai ba Ni na Miki Aunty Dan Allah Kuyimin Rai karku yiwa Yata komai" Nace Ina k'ok'arin kamo hannun Hindatu Adaidai lokacin da Naseer ya shigo da Sauri kana ganinsa kasan hankalinsa a tashe yake Turus yayi Agaban mu Yana yiwa Umma da Hindatu wani irin kallo da yaga kayan shayi a gabansu Cikin wani irin murya ya fara magana Yana "Umma Anya ke Kika haifeni kuwa Umma Anya Gaskiya Abba da Baba Suka gayamin da sukace ke Kika haifeni Umma 'yata ce fa ta b'ata ake nemanta Umma jinina fa yata da ta kasance jika a gareki ita ake nema Umma Kika zauna ke da Wanan tsinaniyar zaku hada shayi ku Sha alamar ba Abunda ya shafeku Umma wlh ba Naeema Kika tsana ba Ni Kika tsana Umma Dan da kina kaunata bazaki ringa min abinda kike min ba Zaki so farinciki na Umma mak'ota da masu wucewa ma suna tsyawa sabida su Tayani neman Yata amma ke kin zauna Zaki sha shayi wane irin kallo kike so a Miki Umma ga wayanda suka san ke Mahaifiyata ce Umma Koda baki hada jini Dani ba Bai Kamata ace mutum Mai Rai sukutum guda ya b'ata batare da kin nuna damuwarki ba Umma,Umma lamarinki ya daina bani mamaki ya koma bani tsoro Umma insha Allahu Zan ga yata Kuma zan kawo karshen komai Dan Nagaji Umma" Daga haka yayi ball da flask din gabansu ya shige daki ya canzo kayan jikinsa ya fito da Sauri hannunsa d'auke da mukullin motarsa da k'aramin passport din hoton Nadeeya da aka Mata lokacin da zaa Saka su a makaranta ya fice da sauri. Ni kuwa na durk'ushe a wajen na cigaba da kuka na kasa yarda Wai Nadeeya ta b'ata yarinya da nayiwa wanka da hannuna ko wando babu. Maganar da Umma keyi cikin huci yasa na tsayar da kukana Ina kallonta "Yau ni Naseer ya ke d'agawa murya yake min ihu sabida yarsa ta Bata lailai Naseer yayi Nisa ba karamin asiriceshi wanan tsinananiyar tayi ba ba dai Dan Nadeeya kike wanan kukan ba ba Dan Nadeeya Naseer yamin ihu Ina mahaifiyarsa ba toh sai ku ganta nagani" "Duk wannan Abun fa laifinki ne Hajara ke Kika bar yarinya nan ta zauna dashi har yanzu har ta juyar Masa da kwakwalwa ace yau sati biyu da auren mu ya kasa kallon Inda nake tsabar wanan kanjalalliyar ta asirice shi ki barwa Umma komai ta Miki maganin shegiya" Ta ce tana jefomin harara Umma kuwa tayi wani irin murmushi ta mik'e tana k'ok'arin shiga daki. Da Sauri na rik'e kafarta na saki ihu Ina ta taimaka ta fitomin da yata wlh idan Naseer ne Zan rabu dashi a yau Tureni tayi ta shige daki. Zahira dake lab'e a bayan kofar dakina ta fito ganin Ina ta rusa kuka Ina Kiran sunan Allah Dana Nadeeya ba irin tunanin da ba darsu a Raina ba Kar dai su Umma kashemin Nadeeya sukayi. Zahira Humaira ta mik'o min dake ta tsalla kuka daga ita har Minal ba Mai Kaya a jikinsu sai Zahira karbar Humaira nayi na sa Mata no-no a baki take ta karba na umarci Zahira ta d'auko wa Minal Kaya ita da Humaira. Tana tashi Mmn Mannir ta shigo ita da wasu makotana wasu ma ban San su ba duk sun zo min jaje sai Kara tambayata suke Taya Nadeeya ta b'ata ban ma iya musu magana ba sai bani baki suke suna kwantar min da hankali akan za'a ganta an Kai cigiya gidajen radio har da tv dayake Naseer nada Abun hannu duk an raba musu passport din Nadeeya. Ni dai har lokacin sai Naga kamar zanga Nadeeya ta fito daga d'aki. Mmn Mannir kuwa Humaira ta karba daga hannuna ta goyata Ni kuwa na mike na Shiga bandaki na daura alwala na fito na hau Kan Sallaya na tadda Sallah karatun Sallah ma da k'arfi na ringayi Ina kuka a Sujadda kuwa Haka na ringa rokon Allah ya Kare min yata a duk Inda take ta dawo gareni cikin koshin lafiya Ni nasan su Umma ne suka daukemin 'ya har tsawon wane lokacin Zan ringa irin wanan rayuwa a yau na gaji wlh na gaji ya zama Dole na dau mataki. Ina iddarwa na fito nayi k'ofar gida Inda duk makotana suke tsaye duk Yan layin ban gansu ba sun tafi neman Nadeeya daidai da masu shaguna duk basu bud'e ba sabida mutuncinsu Amma ace uwar mijina ita Tana daka ko a jikinta. Waje daya na samu na zauna Ina ta tunanin ganin ta Inda zanga Nadeeya ta b'ullo addua kuwa na fili Dana zuci Haka na ringa Yi. Lukman da danladi Mai Kai su makaranta sun dawo gidan yafi a kirga Akan suji ko an ga Nadeeya Amma shiru ba a ganta ba ahaka har Yamma tayi babu Naseer babu dalilinsa. Kuka nake sosai Ina rokon Allah ya karemin Nadeeya har yanzu na kasa yarda Wai daga fitowa Nadeeya wanka an nemeta an rasa. Naseer kuwa kudi ya saki sosai ya bada cigiyar Nadeeya gidajen radio da unguwa unguwa har Inda baa yi tunanin zuwa ba Haka aka ringa neman Nadeeya da passport din hotonta Sallah ma Naseer ba a nutse yake Yi ba har kunyar ya cewa mutane daga wanka Nadeeya ta fito aka nemeta aka rasa sai kace wata Kaya. Ahaka suka danganta neman Nadeeya kusufa kusufa lungu da sako kwaryar Kano baa ganta ba wajen Magriba Naseer da wasu Yan unguwarsu suka tsayar da motarsu Dan suyi sallah a wani unguwa kawo dayake unguwar Bata fiye cika ba a wanan lokacin Kamar daji ne sai a lokacin ake yankar fili ake ginawa. Daya daga cikinsu ne ya nausa wajen daji dajin da yayi fitsari ya fito yayi alwala daga nesa dashi ya hango wani katon Rafi ruwa nata Dan gudu gashi wawakeke wata Yar karamar yarinya ta bada baya tana Dan jefa abu a ciki ba Kaya a jikinta. Murza idonsa yayi ya sake murzawa idonsa duk da Bai ga fuskar yarinya ba sai yake ganin kamar Nadeeya Amma Dan ya gasgata zargin da yake ahaka ya ringa matsawa kusa da yarinya kafin a hankali yace "Nadeeya" A hankali Nadeeya ta juyo idonta yayi jawur hancinta duk Majina kana gani kasan taci kuka ta gode Allah wajen a ruwan yake ma da alama baa fiye wucewa ta wajen ba Ihu ya saka ganin Nadeeya na ganinsa ta fara k'ok'arin mik'ewa tana mik'a Masa hannu Dan Dama Mai kawo Mata d'auki take nema shi kuwa cikin zafin nama ya Isa wajenta ya tarota da Sauri Dan kiris ya rage ta fada ciki. Wani irin ajiyar zuciya Nadeeya ta ringa saukewa tayi lamo a jikinsa jikinta yayi zafi zau. Shima Salisun kamkameta yayi yayi wajen da suka Parker motarsu da har Naseer ya iddar da sallah ya gaji da jiransa. Kamar a mafarki ya hango ya fito da Nadeeya rungume a kirjinsa Bai San lokacin da ya nufesu da Sauri Yana "Mai ya sameta? A Ina ka ganta"? Yace Yana karbe Nadeeya daga hannunsa ya hau tattab'a jikinta Inda Nadeeya tana ganin Abbanta ta fashe da kuka tana Kara kamkame shi. Naseer kamar ya maida ta cikinsa ya rungumeta Yana shafa jikinta Salisu kuwa ya hau bashi labarin yanda ya ganta ya Kuma ringa Al ajabin yanda Nadeeya ta iya zuwa tunda Goron dutse zuwa Kawo idan ba mutum ne ya kawo ta Nan ba Taya zaayi tazo Nan Naseer Bai iya Jan motar ba sai salisu ne yaja motar shi kuwa ya zauna daga bayan motar da dayan makocinsa suna ta mamakin Inda suka tsinto Nadeeya Naseer kuwa rufe idonsa kawai yayi Yana Jin kukan Nadeeya a kirjinsa Yana Jin wani irin suya a kirjinsa shi ba yaro bane yasan d'auke Nadeeya akayi Kuma ba wasu ne.suka d'auke.ta ba sai Mahaifiyarsa tunda yasan wacece ita. Baiyi magana ba har suka iso gidan da mutane ke cike Suna jajanta b'atan Nadeeya. Naeema kuwa taci kuka ta gode Allah tayi zaman dirshan a kasa Ana ta Bata baki Tsayuwar motarsu yasa ta mik'e da sauri Inda Naseer shi.kuma ya bud'e motar ya fito rungume da Nadeeya Mutane na ganin ta suka hau hamdala suna "Alhamdulillah Anga Nadeeya a Ina aka ganta"? Sosai mutane Suka nuna farincikinsu da ganinta suka hau tambaya inda aka ganta. Naeema kuwa da Sauri ta ture mutane ta karbi Nadeeya daga hannun Naseer tana sauke wani irin ajiyar zuciya. Ta rungume Nadeeya Gam tana hamdala Hajara da Hindatu ihun Murnar anga Nadeeya ne yasa Suka fito daga d'akin da Sauri suka lek'o ta saman bene cikin tsananin mamaki Dan bakin ruwa Suka kaita Kuma suna da tabbacin fad'awa zatayi ta mutu Amma ga mamakinsu Wai an ganta Kuma su sun San Inda suka kaita sai anyi dagaske xaa San wajen. Wani irin ihu Hajara ta saka ta sauko daga Kan benen ta zub'e a kasa ta hau buburwa ta cire zaninta ta Yar ya rage daga ita sai Dan skirt sai kuka take Tana zubawa kanta kasa. Mamaki ne ya rufe mutane suna kallonta tare da mamakin Mai ya kawo ihun nata ita da zatayi farinciki anga Nadeeya (wlh page dinan babu fiction ko daya a gaske Haka matar Nan tayi Dan bakin ciki an ga Nadeeya) Ni kuwa ko kallonta banyi ba na rungume yata na haye sama Naseer kuwa kamar kasa ta bud'e ya shige Dan kunyar yanda take ihu tana watsawa kanta kasa Wai Nan da Sunan Mahaifiyarsa ce wato gawan Nadeeya taso gani Mutane kuwa da basu San Mai ke faruwa ba hakuri Suka hau bata suna ba kuka zatayi ba ta Godewa Allah da aka ga Nadeeya ba Kuma abinda ya sameta. Naseer shima da Sauri ya hau saman bene Yana Jin kamar kirjinsa ya fad'o Sai Hindatu ce ta sauko ta dauko mata zaninta ta mikar da ita suka koma ciki. Da yawa ta basu mamakin abinda tayi sabida tunda aka fara neman Nadeeya Bata lek'o ba Amma abin mamaki ana ganinta ta fito tana ihun kuka Mai hakan ke nufi. Wasu Kuma basu kawo komai ba sun dauka kukan farinciki take da ganin Nadeeya. Ni kuwa Ina shiga ciki d'akina na wuce da Nadeeya na kullo k'ofar na kwantar da ita na fara duba jikinta Naga babu abinda ya sameta sai kafafunta dai da suka balain suntume sukayi budu bud' da kasa Sai jikinta da yayi zafi sosai. Bana rabo da ruwan zafi hakane yasa na hada ruwa Mai balain zafi na wanke Nadeeya tas na Kara zuba wani na hau dadanna Mata kafa sai danaga ya fara Sab'ewa sanan na dauko robbb na shafe Mata jikinta dadin wankar yasa take bacci ya d'auke ta tana ta sauke ajiyar zuciya Ni kuwa na zuba Mata Ido hawaye na sauko min ko a Ina su Naseer suka ganta. Naseer kuwa a Palo ya zauna ya rik'e kansa sabida azabar ciwo da tunanin halin mahaifiyarsa ahaka su Hajara suka hawo sama tana ta kuka Suna dab da wuce Naseer Naseer ya dago Yana "Umma ba Haka Kika so ba ko?kin so ace gawar Nadeeya na shigo dashi gidanan Umma Mai na Miki Haka Dan Allah Dan annabi Umma Mai na Miki Dan Allah Dan annabi ki gayamin na nemi yafiyarki Umma" Naseer yace Yana durk'usawa Akan gwiwar sa kukan dayake d'annewa ya kwace Masa. Hajaran Bata ce komai ba ta Shige d'akinta tana Jin kanta na ciwo sabida a rayuwarta Bata da burin daya wuce taga Naeema ckin bakin ciki a Rayuwa tunda ta kasa rabata da Naseer gwara ta Taba abinda tasan sune ranta Dan taso Zahira ta d'auke Dan ta lura itace Mafi soyuwa a wajen Naeema sai Zahira bata futo ba Nadeeya ta fito sai gashi cikin sauki wai har anga Nadeeya bama ta mutu ba da ranta lailai Naeema tabbas akwai abinda ta taka da Bata iya cin Galaba Akan ta. Har wani zazzabin bakin ciki tayi Naseer shima halin mahaifiyarsa da matsanacin tunani sai daya saka Masa zazzabi Ni kuwa Ina daga d'akina Ina Jin duk abinda Naseer ke cewa Umma kukan da Naseer keyi ya tab'ani sosai hakane yasa na Sha alwashin kawo karshen wanan matsalar da muke ciki. A Daren ranar duk mu ukun babu wand yayi baccin kirki Dan Naseer zazzabi halin mahaifiyarsa ya hau Yi ko shigowa d'akin baiyi ba a palon yayi kwanciyarsa ko sallah daya Saba yi daddare ma a ranar baiyi ba Ni Kuma hanyar da zata bille Dani ya hanani bacci ita Kuma Umma bakin ciki. Duk Abubuwan da takemin Ina tsallakewa gashi shugabarsu tayi fushi tace zata kwace komai daga hannunta tunda Naeema tana neman fin karfinta. Washegari Nadeeya ta tashi fes ba wanan kumburin ahaka na had'asu na musu wanka na rufo kofata na nufi kitchen Dan na Dora Mana abinci banyi tunanin shiryasu su tafi makaranta ba Naseer ma ban ganshi a palon ba Dan tunda ya fice da asuba bana Jin ya sake dawowa sosai naji Ina tausayinsa. Daga Umma har Hindatu banji motsinsu ba har na Gama Abunda nake na ajiye musu nasu a Palo na Kai Mana namu daki Dana Naseer. Dan nayi alkawarin har na cimma burina bazan Kara Shiga dakinsu ba. A faranti daya muka ci Abinci da yayana Sansu na ratsani Ina kwarara musu addua a Zuciyata. A hankali Kuma Ina tambayar Nadeeya yanda ta ba ce bamu ganta ba Bata iya min magana ba Dan tana da Dan nauyin baki. Har Minal ta Dan fita baki. Wajen karfe goma na safe na fito daga d'akina bayan na kulle k'ofar dakina har lokacin Naseer Bai dawo ba Kuma banji motsinsu Umma ba Naseer nafi damuwa nasan halin da yake ciki ba Umma ba hakane yasa nayi waje. Ina su lukman suka hau gaisheni suna tambayar Nadeeya Ni kuwa nace Tana Nan lafiya Lau daga Haka na wuce gidan mmn Mannir Dan zuwa yanzu banida dai Sama da ita bayan Naseer dan naji Dadin yanda ta nunamin damuwarta jiya tamkar yar uwa ta Haka nake ganinta. Banyi tunanin Zan sameta a gida ba Dan na d'auka taje makaranta amma Ina zuwa na sameta taji dadin ganina anan muka gaisa taso ta tada maganar abinda ya faru tsakaninta da Umma har ta Dan sakomin zancen tana zargin ita ta d'au Nadeeya Ni kuwa na Kau da zancen na hau Gaya Mata abinda ke tafe dani da taimakon danake so tamin Dan Nagaji da irin wanan rayuwar da muke nida yayana Kuma idan na biyewa Naseer Haka zamuyi ta zama muna cutuwa. Sai data Yi Dan Jim kafin tace zata taimaka min ta hau tsaramin yanda zamuyi take naji dadin shawararta Inda ta tsaramin duk yanda zamuyi Amma fa tana tausayin Naseer. Murmushi kawai na nata Dan Mai daki shi yasan Inda yake Masa yoyo. Sallama na Mata akan Zan dawo anjima Ina koma wa gida Naga Naseer ya dawo idonsa ya fada sosai yayi wani sanyi kalau kamar mara lafiya Bai cemin daga Ina nake ba na Shiga d'aki na dauko masa abincinsa Ina k'ok'arin ajiyew yace min azumi yake bance komai ba na dauke abincin na mayar kitchen na fara k'ok'arin Dora Mana abinci Rana Ina cikin girkin Hindatu ta shigo ta ajiye kwanuka tare da dalla min harara sai anan nasan Ashe ma suna Nan Ina gamawa na Kara shigewa daki a Inda Naga Naseer har yayi wanka zai fita. Yacemin bazai dawo da wuri ba fatan dawowa lafiya kawai na masa Yana fita na dauko katon akwatina na hada Mana kayanmu nida Yara sai danaga ba kowa a palon Naja akwatin na Kai gidan mmn Mannir Kuma cikin ikon Allah babu Wanda ya ganmu. Kamar Naseer yasan Mai nake shiryawa tunda ga ranar Bai Kara fita ba. Nima sai neman hanya nake kwana biyar da faruwar.haka Umma ta fito palon Wanda tunda aka ga Nadeeya ta shige daki ban Kara ganinta ba sai ranar Dan Hindatu kawai nake ganin tana Shigar musu da abinci. Wani irin kallo take min Ni kuwa na dauke kaina Zan iya cewa wnan shine Karo na farko a rayuwata da naki gaisheta. Girgiza Kai tayi ta had'e Rai ta zauna a Palo Naseer kuwa Yana ganin ta fito ya mik'e ya fita. A ranar wani kallo Umma take jefamin na tsana Kamar zata kamoni ta yankani Ni kuwa Ina Gama ayyukana na shige daki. Washegari jikina duk ba kwari na shirya su Zahira suka tafi makaranta Wajen Sha daya Naseer na fita na goya Humaira na karewa d'akina kallo hawaye na zubomin Na ajiye wa Naseer wasika a karkashin gado na fito da ga d'akin Banga kowa a palon ba Ina fita na amshi kudi wajen lukman a cikin kudin Naseer wajen Dubu goma wanan lokacin. Na dau hanyar makarantarsu Zahira Ina zuwa nacewa mallamarsu inasan zamuyi tafiya ne an Mana rasuwa take ta Kira su Zahira suna zuwa na rik'e hannunsu muka hau tafiya sai da muka je karshen layin na had'u da mmn Mannir dake ta jirana da akwatin kayanmu..... [6/26, 3:27 PM] +234 803 635 0240: *NAGA TA KAINA* *NA SADNAF*🌸🌸 ®️ *_PURE MOMENT OF LIFE WRITERS_* _{We Don't just entertain nd educate we also touch the heat of readers P.M.L}💪🏻_ *Free Novel* *Page 18* Bansan hawaye nake ba sai da mmn Mannir da itama Naga jikinta duk yabi yayi sanyi tace "Anya Naeema kina ganin wanan matakin shi ya dace ki d'auka?Anya kina ganin kinyiw Naseer adalci kuwa? Ban iya ce Mata komai ba Dan matsawar nayi magana kukan danake dannewa zai iya k'wacemin Agaban yayana Zahira tana da wayo tunda muka fito daga makaranta take min tambayoyi Ina zamuje yanzu ma sai kallona take. Mmn Mannir itama sosai Naga idonta ya kad'a yayi ja Ina biye Mata Haka zamuyi ta tsayuwar hakane yasa na Ciri hannu na fara k'ok'arin tsayar Mana da taxi Dan lokacin ba adaidaita sahu. Dak'yar muka samu Wanda ba kowa a ciki na sunkuyar da kaina nace ya kaimu tasha. Sai daya fito ya saka Mana kayanmu na bud'e bayan na saka su Minal Ina k'ok'arin kamo hannun Zahira ta Kara cemin "Umma Ina zamuje Dan Allah idan tafiya zamuyi mu tafi da Abba Kar shima Mama ta ringa dukansa dayake mama suke ce Mata"? Hada Ido mukayi da mmn Mannir da har hawaye ya fara zubo Mata tana daukewa sabida Kar a gani. Ni kuwa na saka Zahira a cikin motar da k'arfi Dan banasan magana kukan danake dannewa ya fito. Ina zaunar da ita na shige na rufo k'ofar Ina k'ok'arin yiwa Mmn Mannir godiya Naga ta bud'e gaban motar ta hau. Ba Wanda yayi magana a cikin mu har muka Isa Tasha muka sauka na biya Mai taxi bayan ya sauke Mana kayanmu Mmn Mannir ce ta shigemin gaba wajen Nemo motar garinmu aka cajemu na biya sai da su Zahira suka hau sanan na juyo na rik'e hannun mmn Mannir Ina "Nagode da alkhairinki a gareni bazan manta dake ba" Hawaye ne ya hau zubo Mata ta damke hannuna tana "Naeema Dan kin dage ne Zaki tafi da kin hakura kin zauna wuya Bata kissa watarana sai Labari da Zaki bani hadin Kai wlh zamuyi maganinta ya Naseer zaiji idan ya dawo yaga bakya Nan kin Kuma tafi da duka yaran wlh Naeema bazaiji dadi ba" "Bazaki gane ba Mmn Mannir bazaki gane Hatsarin Zama na da Naseer ba Mmn Mannir da iya Ni kadai ummaa zata tab'a kila na iya jurewa da iya Ni kadai zata ganawa azaba kila na iya daurewa ko Dan sabida yarana Amma me Umma yanzu ta bar kaina ta koma Kan yayana Wanda duk abinan sabida su naki tafiya tuntuni Akan me Zan cigaba da zama yau idan Allah ya karemin Nadeeya gobe nasan salon da zata zomin dashi wlh Nagaji mmn Mannir ko baccin kirki bana iya yi na rasa Mai na Mata laifine Dan na auri danta yau kina ganin da iyayena suna rayye zata min abinda takemin banida kowa sai Allah sai Naseer toh shima Naseer din tace sai mun rabu toh na rabu dashi rabuwar mu bazai saka na kasa cigaba da rayuwa ba na barwa Naseer wasika Akan ya sakeni bazan iya ba Zan koma garinmu ko wanke wanke na ringa Yi Ina ciyar da yarana Dan bazan tab'a barin yarana da Naseer mahaifiyarsa ta kasheminsu ba Wlh mmn Mannir banji Ina nadamar matakin Dana dauka ba wlh nesa ma danayi daga gidan bakiji iskar danake shak'a Mai kyau ba nidai kawai ki Tayani da Addu'a watarana insha Allahu zamu sake had'uwa" Mmn Mannir kasa magana tayi sabida kukan da take dak'yar na kwace hannuna na Shiga motar Ina shiga muka samu Karin passenger daya Yana shiga motar mu ta d'au hanya Haka kawai naji wani Abu ya tsayamin a mak'oshi tambayar da Zahira ta Kara jefomin Akan tafiya zamuyi mu bar abbansu yasa na kifa kaina akan hannuna na fara kukan danake ta dannewa tun lokacin Dana shirya rabuwa da Naseer. Allah yasan ba Haka naso ba Dan mijina Yana Sona Yana Kuma iya kokarinsa Dan yaga ya kyautata Min nida yayana Amma mahaifiyarsa ta daka tsalle tace sai mun rabu bansan Umma tsanar da takemin har ya tashi daga kaina zata iya tab'a min Yaya ba gaba gaba kila wuka zata d'auko ta caka musu ni har mamakin halinta nake Dan wlh ko dabba bazan iya cutar dashi ba ko ragon layya a da idan zaa yanka tausayi yake bani sai da akacemin babu kyau na daure na daina Dan bana ma tsayawa Inda ake yanka d'abba Amma Wai Umma ita ce take zuba wanann zalincin har Yara kanana Bata Bari ba idan dai har zata iya yiwa Nadeeya Haka na tabbata ma Naseer Bai tsira a wajenta ba. Addua kawai nake Allah yasa na Gane hanyar garinmu Dan shekaru dayawa rabona da can toh waye ma nawa acan ne inama Ina zuwa Naga Yaya Aliyu yazo shima Yana nemana inama na samu wasu suzo suce sune dangina inama na tambaya Mahafina ko Mahaifiyata.wani nasu da yanzu na samu wajen zuwa Amma ba komai Haka zanje ko makotammu na da idan na samu na tambayesu game da gidan da mahaifina ya Bari dan nasan kila yana hannun Mai unguwa idan Allah yasa basu siyar Mana ba sun ajiye Mana kayanmu sai na zauna nida yarana na nemi sana'a. Biscuit da ruwa na siyawa su Nadeeya da sai Dana tashe su daga bacci. Zahira ce kawai batayi bacci ba ta Yi jigum da biscuit dinta a hannu ta kasa ci Dan sai data karamin tambaya na daka Mata tsawa akan ta kyalleni naji da iya damuwar da nake ciki. Sai da mukayi nisa da Kano Naji wani irin tausayin Naseer ya rufeni ko ya zaiji waya sani ma ko har yaje gidan yaga wasikar abinda nakejin Kuma nadamarsa Bai wuce ce Masa danayi na tafi garin kaduna ba Dan nasan kila ya tafi can neman mu alhalin ba can mukayi ba. Ahaka nayi lamo Ina kallon Motocin dake ta tsere a titi Ni nasan Umma sai ta kusa taka rawa sabida murnar tafiya ta. Naseer kuwa tunda ya bar gida yake Jinsa kamar Mai zazzabi ahaka ya daure yayi ta zama a katon shagonsa daya bud'e dake sabon gari dake d'auke da kayan electronic Dan Naseer Kam fanin arzki sai daya ce alhamdulillah dan shagunansa zasuyi uku a sabon gari shidda kenan har Dana kofar gidansa. Yanzu Haka ma Yana Gina wani katon gida a kasan layinsu ko Naeema Bai gayawa da ace mahaifiyarsa Bata Sako shi a gaba ba da ace mahaifiyarsa ta rungumi Naeema a matsayin matar danta da ya ce shi kam ya samu rabon duniya sai dai Kuma na lahira. Sam yaji zaman shagon ya gundureshi ba Kuma yajin dadin jkinsa hakane yasa duk da yawan mutane dake zuwa siyayya ya Sallame su akan bayajin dadin ya rufe shago ya nufi gida. Ganin lokacn tashinsu Zahira ya kusa yasa ya tsaya a makarantar su Dan saura Yan mintina su tashi Kansa tsaye ya shiga cikin makarantar ya nufi office din headmistress din tana ganinsa ta hau gaishe shi tana Masa gaisuwar rasuwan da aka musu Cikin mamaki Naseer yace Bai Gane ba Itama headmistress din cikin mamaki ta Kora Masa zuwan Naeema makaranta da Sunan an musu Rasuwa ta tafi da su Zahira. "Kin tabbata Mahaifiyarsu ce tazo ta d'auke su"? "Itace Mana Alhaji Naseer yanzu ma wajen awa biyu kenan" Naseer Bai tsaya jiran sauran bayananta ba ya fita da Sauri gabansa na fad'uwa Mai ke faruwa Naeema tazo ta dauki su Zahira lokacin tashi baiyi ba ko Ummansa ce ta Kara musu wani Abu Da ikon Allah ya Kara sa gida ko parking Mai kyau baiyi ba ya hau sama g da balain sauri. Naeema ya hau kwallawa Kira Yana kiran sunansu Zahira Haka kawai gabansa ya tsinke ya Fadi daya shiga d'akin naeema.ya duba koina Bai ganta ba fitowa yayi da Sauri.ya fada Kitchen nan ma Bata nan. Da sauri ya fito ya Kara sauka kasa. Yana sauka ya hau tambayarsu lukman ko sunga Naeema da Zahira. Dukansu girgiza Masa Kai sukayi sai Mai Zama a dayan shagon ne yace yaga ta sauko ita da Minal da Humaira a goye a baya tayi hanyar titi. Naseer Bai tsaya ya Gama Jinsa ba ya da dan gudu ya nufi gidan mmn Mannir daya San Nan kawai take zuwa Sosai yaji Yana tsoron darsa tunani a Ransa akan ko wani abun ne ya faru addua kawai yake.Allah yasa tana gidan mmn Mannir. Tsabar tashin hankali Bai tsaya Sallama daga waje ba ya fada cikin gidan da Sallama a bakinsa Mmn Mannir dake zaune ta buga tagumi tunda ta dawo ta mik'e da Sauri tana sallati ganin Naseer a rude yasa jikinta ya hau rawa cikin jarumta tace.masa.lafiya Naseer da Sauri ya hau tambayarta inda take ita da Yara. Ita kuwa tace masa Bata ganta ba sosai taji wani irinn tausayinsa daya zaro Ido Yana sallati. Ya juya da Sauri ya bar gidan Sosai hankalinsa ya tashi ya koma gidan a hargitse Yana Kara kwallawa Naeema Kira Dan gani yake.kamar Tana gidan.. Sai a lokacin tunanin shiga d'akinsu Umma ya Fado Masa. Da Sauri ya fada d'akin suka dago suna kallonsa "Umma Mai Kika yiwa Naeema Dan Allah Banga Naeema ba Banga yarana ba Umma Mai Kika musu Dan Allah ki gayamin kimin komai Umma Banda rabani dasu" Wani irin kallo umma.ta hau yi.masa Hindatu kuwa ta fara zuba Mai harara cikin kishi a ranta tana ayyana Allah yasa ma Naeema ta mutu Umma kuwa taja Tsaki ta Kau da kanta. Fitowa ya Kara Yi daga d'akin Yana sallati Ya Kara Shiga d'akin Naeema tsabar rudewar da yayi ya hau daddaga Kaya ahaka ya d'ago pillow har zai mayar ya Ajiye yaga farar takarda Baisan lokacin daya dauka ba Yana bud'ewa numfashinsa ya fara barazanar d'aukewa "Kafin kaga wasikar Nan munyi nisa Naseer Kayi hakuri da matakin da na dauka Naseer nagaji da ace Umma iya Ni takewa Zan iya jurewa Amma yanzu ta fara tab'a min. Yaya daga ni har Kai munsan ita ta d'auke Nadeeya duk sabida kiyayyar da takemin na rasa Mai na Mata idan bamu rabu ba Naseer watarana zaka rasani ko ka rasa yayanka Wanda nasan hakan sai yafi maka ciwo akan dai rabuwar mu banida kowa sai Allah sai Kai Amma Umma ta dage sai mun rabu na dauka auren data saka kayi zai saka na samu sassauci daga wajenta Amma bansamu sassauci ba sai Karin azaba hakane yasa na yanke guduwa da yayana muje garin kaduna ko Allah zai kawo Mai taimaka Mana rabuwar mu sai yafiyemin alheri Naseer kayiwa Umma biyaya ngd da alherinka a gareni dafatn bazaka..... Wani irin sallati Naseer ya doka cikin fitar hayyaci Bai ma iya karasa.karantawa ba ya fita aguje ya nufi d'akin Hajara takarda rik'e a hannunsa Yana "Umma shikenan kin kasheni Umma Naeema ta gudu ta barni ta tafi da yarana sabida azabar da kikee gana Mata Umma kalli takardar Nan kiga mai tace Umma Naeema ta shiga duniya da yayana innalillahi wa Inna ilaihi rajiun" Hajara duk da batayi karatu ba karbar takarda tayi ta mik'e zaune Dan Dama a kwance take "Mai kace Kara maimaita min naji kace Naeema ta gudu da Yara"? Umma Naeema ta gudu da Zahira da Nadeeya da Minal da Humaira Umma tace ta gaji da azabar da kike gana Mata Umma Mai na Miki kika tarwatsa.min rayuwa? Mai na Miki kika rabani da farincikina"?Umma Naeema fa Bata da kowa sai Ni Umma Mai yasa kikemin Haka idan wani Abu mahaifina ya Miki kike San ki dau fansar hakan akaina ki gayamin na nemi yafiyarki Umma uwa da tausayi aka santa umma uwa Bata cutar da dan data Haifa Umma ban miki komai ba kina ta cutar Dani Ina Miki biyayya daidai gwargwado Naeema tana Miki bansan Mai yasa Kika dage sai kin rabamu ba gashi dai ta tafi min da yara har su hud'u" "Rufemin baki shasha lusari Kai yanzu akan mace kake kuka ka dagawa kanka hankali Haka?Kai yanzu Sabida Naeema ta rabu da Kai kake wanan surutan?anya Naseeru Haka yarinya Nan ta barka?Naeema kadai ce mace a Duniya ko sai akace ma Dan ta rabu da Kai rayuwarka tsayawa zatayi? Karka manta fa kana da kudi kana da damar da zaka auri duk kalar macen da kakeso ta kuma Haifa maka maza" "Ni kuma Mai matsayina a wajensa kenan da kike cewa zai auri wacce Ransa keso"? Hindatu tace tana jifan Hajara da harara "Ga Hindatu Nan dame Naeema ta fita Naseeru"? "Ya kake Abu kamar ba Ni na Haifeka ba"? Naseer kallon Hajara kawai yake hawaye na zubo Masa shi kadai yasan halin da yake ciki shi kadai yasan Mai yakeji a zuciyarsa. Juyawa yayi a hankali ya fice daga d'akin Yana dafa bango Dan sosai yake Jin jiri na neman kayar dashi Yana fita Hajara ta hau rawar murna rabonta dataji ta a farinciki Haka har ta manta gaskiya tafiyar Naeema da yaran ya balain faranta mata take ta fara addua Allah yasa Naeema ta lula duniya Tama hadu da ajalinta ita da yaran Dan batasan Nasser ma ya kalli wani Abu da zai tuna Masa Naeema. Palon ta fito tana washe baki ganin Bata ga Naseer a palon ba yasa ta zauna a kujera palon tana zai Gama koke kokensa ya gama ne. Zamanta da Yan mintina Naseer ya fito daga d'akin Idonsa ya kad'a yayi jawur.hannunsa rik'e da mukullin mota yayi hanyar waje. "Ina zakaje"? Ko kallonta baiyi ba ya fice waje. Gidan mmn Mannir ya Kara komawa da takardar a hannunsa Dan gani yake kila tana da masaniyar Inda Naeeema taje Yana k'ok'arin Sallama mmn Mannir ta fito cikin tashin hankali ya Mik'a Mata takarda Yana "Dan Allah Mmn Mannir idan kinsan wajen Wanda Naeema taje a kaduna ki gaya min nasan bazata ki Gaya miki ba sai dai kawia ki boyemin Dan darajar Allah ki gayamin idan kinsan Inda zata a kaduna ki taimakamin sabida kananan yaran data tafi dasu Naeema kanta Bata gama mallakar hankalinta ba ba kuma ta da kowa babu Kuma Wanda ta sani karki boyemin Dan Allah idan kin sani ki gayamin"? Sosai ya kashewa mmn Mannir jiki bare data ga Yana ta hawaye Tayi wa Naeema alkawarin bazata gayawa kowa ba Amma a yanzu Anya zata iya cika alkawarin data daukar Mata bayan taga halin da Naseer yake ciki "Dan Allah kigayamin mmn Mannir Kar ta fada hannun mugayen mutane"? "Naseer a gaskiya Mahaifiyarka ta takurawa Naeema Mahaifiyarka tana cin zalinta sabida tana ganin Bata da kowa mai Naeema ta Mata Haka data tsaneta nidai bansan Inda Naeema taje ba ta dai cemin zata gudu Amma bansan dgaske ta gudun ba sai yanzu da kazo kana tambayata Amma a gaskiya bansan Inda taje ba da nasani Zan Gaya maka" Mmn Mannir tace tare da kau da kanta data tuna girman Alkawarin data daukarwa Naeema Naseer cije lebb'ensa yayi batare da sake cewa komai ba ya tafi. Motarsa ya bud'e ya Shiga ya zauna ya rufe Ido yana tunanin ta Inda zai fara neman Naeema wa ta sani a kaduna da zata tafi wajen wa zataje ?Mai yasa Naeema zata Masa haka ta gudar Masa da Yaya shi akaran kansa akwai abinda yake tsara musu Gaya Mata ne kawai baiyi ba Dan ya Kara shirya su gudu zuwa wani garin na Dan lokaci kafin suga ko Umma zata hakura ta kyallesu. Amma sai gashi Naeema.ta gudu da yayansa tashin hankalinsa Bai wuce Ina zata je ba wajen wa Kuma zata sauka Bai San har Naeema tayi wayo yin wanan tunanin ba Naeema daya sani tana da tsoro Mai yasa zata Masa Haka yanzu idan sun Isa kaduna Ina xasu kwana ita da yaran tunani iri iri Haka ya ringa yi kirjinsa na Masa nauyi. Take zazzabi Mai zafi ya rufeshi Sai su lukman ne Suka Gane bashida lafiya Suka Kira likita a kasan layinsu yazo ya duba Naseer ya mishi allura ya Sha magani. Dak'yar ya koma cikin gida Inda Yana Hawa sama.yaga Umma taci kwalliya ita da Hindatu fuskarsu kamar gonar auduga sai cin kaza suke Bai kallesu ba ya Shiga d'aki a ranar ko runtsawa baiyi ba washegari da sassafe ya dau hanyar kaduna. A takaice sai daya kwana uku a kaduna Yana bulayi duk da Bai San takaimaimai Inda zai ga su Naeema ba a cikin kwana uku ya zama kamar mahaukaci Dan ko wanka baya yi balle ya samu cikakken bacci. A ranar daya kwana biyar a kaduna Yana yawon nemansu Naeema Tasha tasha.unguwa unguwa ya yanke zuwa garin su Naeema Dan Haka kawai yaji kuma zuciyarsa ta karkata can. Naeema Duk da sauye sauyen da aka samu a garin na cigaba hakan Bai Hana ni Gane unguwarmu ba rabona da garin tun rasuwar mahaifina da Mahaifiyata kaina tsaye gidan Mai unguwa na nufa da su Zahira da har kuka suka ringa min da Sunan sun gaji. Sosai na ringa adduoi a Raina Akan Allah yasa Kar Mai unguwa ya canjamin sabida Yana ganin iyayena sun rasu. Ga mamakina muna Isa ya.gane Ni Suka Kuma Mana tarb'a Mai kyau Inda naji wani irin kwanciyar hankali da nutsuwa Wanda rabona ma danaji Haka Zan iya cewa tun kafin na auri Naseer. Sai da muka huta daddare ya aika a kirani Inda ya hau tambayata mahaifinsu Zahira dafatan lafiya yagani da Yara. Kuka na fashe dashi na tsinci kaina da karyar Naseer s'akina yayi Sosai ya nunamin baiji dadin abinda ya faru ba ya min nasiha akan na rungumi kaddara zasu rik'eni tunda banida kowa sun Kuma Yi zaman mutunci da mahaifina Amma fa sai.na mayar dasu Zahira Dan bazai iya rikesu ba baima Kamata na taho da yaran gabadaya ba. Anan hankalina ya tashi danaji abinda yace kuka na fara yi.masa inaso na Gaya masa gaskiya abinda ke faruwa bakina yamin nauyi Kamar an dinke inaji Ina gani yace na tashi na tafi idan an kwana biyu zai saka a cikin yaransa wani ya rakani na mayarwa Naseer yayansa. Sosai hankalina ya tashi na hau nazarin abin yi Inda a karshe na yanke kafin ya karamin magana gwara na Gaya masa gaskiya ko da zai iya taimakamin tunda Naga gidanmu na Nan a kulle Dan har maganar gidan yamin akan mallakina ne gwara na gyara na zauna a ciki nida yarana Dan canjin hannuna na ringa juyawa. Ranar da muka cika kwana biyar a garin washegari.na karbi mukulin gidan nace Zan je na Dan gyara. Na tafi da yarana gabadaya shigata gidan ya hau fad'omin da irin Rayuwar danayi da.iyayena cikin so da Kauna da kwanciyar hankali. Haka kawai na samu waje na zauna na hau bawa yayana labarin iyayena da yayana da ya tafi soja har yau banji labarinsa ba da irin San da sukemin.ina basu labari Ina kuka Inda mahaifina yake yawan Zama nake nuna musu Ina murmushi kamar ance na juya na kalli bakin kofa Naga Naseer a tsaye ya zubomin Ido Yana kallona badan nasan Naseer ba danace mahaukaci ne a tsaye a bakin kofa....... Iabarin na da Dan tsayi shiyasa nake typing kullum na matsu Nazo. Ta tsakiyar labarin Dan haka inaga Zan Dan daddatse sabida mu fara Dan bana shiri da novel Mai tsayi Nan da Nan nake gajiya😃😃😃 [6/26, 3:28 PM] +234 803 635 0240: *NAGA TA KAINA* *NA SADNAF*🌸🌸 ®️ *_PURE MOMENT OF LIFE WRITERS_* _{We Don't just entertain nd educate we also touch the heat of readers P.M.L}💪🏻_ *Free Novel* *Page 19* Cikin fad'uwar gaba na d'auke kaina banji dadin yanda mmn Mannir ta karya alkawarin data daukar min ba ba yanzu naso Naseer ya ganmu ba naso sai mun Dade na samu hutu kafin ya ganmu kasan Raina Kuma tausayinsa ne ya cike min zuciya amma kuwa saman fuskata hade Rai nayi Dan bazan tab'a binsa ba nafi jina cikin kwanciyar hankali tunda na baro Garin Kano Jiki ba kwari ya daga Minal Ya Dan matsar da Zahira da Nadeeya da suka kankameshi suna ihun murnar ganinsa. Ina Jinsa suka karaso gefena ya sauke Minal ya saka hannu ya dauki Humaira Dana kwantar da ita a gefena Ya sauke wani irin ajiyar zuciya. Har lokacin ban yarda na kalleshi ba duk da Yana ta lallubar kwayar idona Dan mu had'a Ido daga ni har shi ba Wanda yayi magana Ni kuwa sosai na Kai zuciyata nesa wajen ganin na danne hawayen tausayinsa dake neman fitowa ta k'arfi da yaji ko ince tausayinmu gabad'aya. Shi kuwa ganin naki kallonsa yace "Taimakamin da ruwa in Sha Naeema" "Mik'ewa nayi nayi hanyar waje Dan babu komai a gidan. Cikin gidan Mai unguwa na Shiga na d'ebo Masa ruwa a kwanun Sha na rufe na kawo masa na ajiye a gabansa. D'auka yayi ya kafa baki sai daya shanye tas ya Ajiye anan na saci kallonsa Naga yanda yayi wurjan wurjan lebb'ensa duk ya bushe. "Naeema Mai yasa Kika min Haka a ganina bai Kamata ki dau matakin guduwa da yaran ba da kin fadamin da na San Abunda ya Kamata nayi Sabida ki wahalar Dani Kika cemin Kaduna Kika tafi sai danayi kwana hudu a can kafin tunanin zuwa Nan yazomn haba Naeema Mai na Miki Dana cancanci ki zabi rabuwa dani"? Cikin hade Rai Dan yasan dagaske nake bana San komawa gidansa marairaicewar da.yake bashi zai Saka na bishi da yarana ba "Idan na Gaya maka Naseer hakuri zaka bani kace mu cigaba da Addu'a kullum kalmar kenan alhalin sababin abubuwa Umma ke kara bijiromin dashi kana kallon irin dukan da take wa Zahira duk sabida tsabar tsanar da tamin ta ringa jifanta da mugayen kalamai Wai baza tayi albarka ba Yar iska zata Zama kuka na fashe dashi Dan kalmomin Nan data jefi Zahira dashi ya balain yimin ciwo na cigaba da Magana Ina iya wanan Bai isheta ba ta d'auke min Nadeeya tsabar bakin cikin an ganta Naseer ta fito tana kururuwa Tana watsawa kanta kasa Naseer da kiyayyar ta zata tsaya iya kaina wlh Zan jure amma yanzu ta fara tab'a min Yara bazan jure ba Naseer ba tare aka halliceni dakai ba zaka iya rabuwa Dani ka cigaba da rayuwarka kana da Daman da zaka auri Mata hud'u ka Shimfid'a irin rayuwar da kake so dasu a ganina idan kana kaunata zaka so samun kwanciyar hankalina na Kuma Rayu cikin farinciki Ina kaunarka har a Raina Amma idan akwai cutarwa gwara mu hakura ka sauwake min ikon Allah yasa kagani a zaune a yanzu har nake maka magana a cikin Minal ba irin azabar da Umma Bata gana min ba ta window na duro danake nakudarta sabida Kar ta kasheni banajin addua Zai iya sauko da Umma ta kaunaceni Allah na tuba Umma sosai nake ganin tsanata a idonta Dan Haka Naseer na hadaka da girman Allah ka sauwakemin albarkacin yaran Nan ka gyara min gidanan da iyayena Suka barmin na Rayu da yayana cikin kwanciyar hankali idan ma bazaka iya bani jari ba Ni zan nemi aikin da Zan ciyar dasu Naseer Dan Allah ka sauwakemin na gaji wlh Nagaji" Na karashe Ina fashewa da kukan da nakejin yinshi ne kawai zai saka naji zuciyata ta rage nauyi da zafi idan har Zan tuna wani zalunci da umma tamin sai kirjina yyi nauyi Haka Zan ta kuka har sai naji sanyi a Zuciyata Naseer kuwa Bai iyamin magana ba in Banda idonsa daya kad'a.yayi ja jijjiyoyin kansa sukayi rud'u rud'u ni nasan sabida gaban yayansa yake shiyasa yake ta mayar da hawayen daya cike Masa ido. Zahira kuwa da Nadeeya duk da karancin shekarunsu Haka suka hau kuka suma. Naseer kuwa kamar maganuna bulala Suka Masa a jiki a Haka ya zauna jiki duk ba kwari nasan Dan muna gaban yarane da ya janyoni ya rungumeni ya rarrasheni. Sai Dana ci kukana na koshi na mik'e tare da d'aukar Humaira. Ban kalleshi ba nacewa su Zahira suzo mu koma gidan Mai unguwa Dan ko tabarma babu a gidan namu bansan wayanda suka kwashe ba Naseer Bai mana magana ba har muka fice Muna zuwa na bawa Zahira tabarma da ruwa a buta Akan ta Kai Masa yayi sallar Magriba. A hanyar Kai masa ruwa da tabarmar Mai unguwa ya ganta ya hau tambayarta inda zata je ita kuwa tace Masa Abbanta zata kaiwa. Take Mai unguwa ya hau washe baki cikin farinciki zuwan Naseer Yana iddar da sallah ya shigo har d'akin da aka bamu muka zauna da yayana ya daga labulen Yana "Ashe babansu yaran Nan yabi yo sahu Kai Masha Allah naji dadin zuwan da yayi Allah ya daidaita ku Dama kullum sai nayi addua akan Allah ya sa ya mayar dake dakinki Dan shine rufin asirnki an Riga an haifi Yara har hudu ai sai Kuma ayita zaman hakuri Allah ya Kara kau da fitina Zan Masa magana shima Bari na saka a kiramin shi Nauyin Mai unguwa da yanda ya nuna farincikin zuwan Naseer yasa na kasa Koda magana har ya fice daga gidan. Sosai naji da gasken bazan koma gidan Naseer ba shiyasa na bi dashi ta ruwan Sanyi Dan ya bani takarda ta Amma idan yak'i kuwa ya zama Dole na fito na gayawa Mai unguwa halin da nake ciki da mahaifiyarsa nasan shima idan yaji bazai so na koma ba tunda neman rayuwata Dana yayana mahaifiyarsa take. Ana iddar da sallah ishai Mai unguwa ya aiko a kirani Ina zuwa yace na Kira Masa Naseer ba yanda zanyi Haka na juya na nufi gidanmu Dan na Gaya masa rufin asirinsa shine ya sauwake min cikin ruwan Sanyi sabida bana San na ringa fallasa Sirrin mahaifiyarsa. Ga mamakina Ina Isa Naseer na zaune a Inda muka barshi ga tabarma da ruwan da Zahira ta Kai Mai a gefe ya tsurawa waje daya Ido kirjinsa sai sama da kasa yake Bansan lokacin Dana taka da Sauri na Isa wajensa tare da durk'usawa a gabansa ba Yana dagowa ya wawuroni ya kankameni cikin wani irin murya daya karyar min da ba iya zuciyata ba komai na jikina "Naeema taya Zan soma rayuwa batare da ke ba Taya Zan soma rayuwa da wata matar idan ba ke ba Naeema nafiki Jin ciwon halin da kike ciki sanadin halin Mahaifiyata na kamu da mumunan hawan jini ban taba fada Miki bane Naeema Tayaya Zaki ce na sawake Miki ya kikeso nayi da Raina ke da yarana nake gani nayi farinciki da Ana canja uwa da na Dade da canja Umma badan Mahaifina da Abba sun tabbatarmin da ita ta haifeni ba Naeema da sai nace Umma ba Mahaifiyata bace Dan Uwa da tausayi aka santa uwa bata cutar da dan data Haifa na rasa yanda zanyi da Umma nayi nasihar nayiwa waazin duk tak'i ji bakece Bata kauna ba Naeema Ni data Haifa nine Bata so Dan tasan farinciki da kwanciyar hankalina kune Naeema wlh da Umma zata ce na mallaka Mata duk abinda nake dashi zata barni mu Rayu cikin kwanciya hankali ko daki dayane na Kama Mana na ringa dako muna ci muna Sha da.naji dadi na.rasa yanda Zan mata Dan Allah Naeema rabuwa Dani bashine mafita ba na yarda Zan Kara nema miki wani gidan batare da saninta ba Ni Kuma zance Mata har yanzu banganki ba" "Naseer bazan koma Garin kano ba sai dai ka gyarmin Wanan gidan ka ringa zuwa kana ganinmu " "Ya zamuyi da Karatun yaran namu kasuwanci na fa danake yi a garin Kano wlh Zan iya takuna bazan Bari Umma ta.san naganki ba Zan ringa zuwa ko sau ukune sati Dama akwai wani karamin gida Dana siya a sharada inaso na zuba Yan haya tallansa akamin Mai gidan na bukatar kudi shine na siya kawai Zan gyara miki ki koma can wlh Umma bazata Sani ba" A takaice duk ta Inda na b'ullowa Naseer sai ya zame ya kalamanceni abinka da tsakanin mata da miji sai Allah tuni Naseer ya shawo kaina duk alwashin Dana Sha yabi iska muna zuwa gaban Mai gari yayi wa Naseer fada da naseeha washegari muka fara shirye shiryen komawa Naseer sai lallab'ani yake Yana riritani (Nafeesa Naseer na balain Sona rabuwa daya k'iyi Dani ya jawo Mana masifu da ko makiyina bana fatan yyi kwatan rayuwar da mukayi) Matar Mai unguwa ita ta yarfamin kitso da Jan lalle na garjajiya yayana ma.aka musu kitso Naseer kuwa ya cika Mai unguwa da abun arzki da matansa da yayansa tun kafin mu taho aka fara gyara gidanmu Inda Naseer ya bawa Mai unguwa kwangilar Ana Gama gyarawa a nemi Yan haya a saka a ciki kudin Kuma ya ajiyemin. Hotel ya Kama Mana da muka iso sosai Naseer jikinsa ke rawa kamar Wanda yayi sabon aure duk wani Abu daya gani sai ya siyo Mana Dan sati daya ya kama Mana abinda ke fita dashi kawai gyaran gidan sharada ne da Abubuwan bukata da zamu yi amfani dashi. Inama Umma ta saka Mana albarka a aurenmu ta daina daga Mana hankali da sai nafi kowace mace dacewa da gidan miji Dan ranar da muka kwana biyar Naseer ya siyomin set din sarka da dankunne har da zobe na daham Dubu talatin a lokacin ba karamin kudi bane sababin Kaya kuwa Haka ya cike Mana shi a akwati biyu atamfofi na ma kuwa Mai karamin kudi a ciki shine dari bakwai Wanda a kudin yanzu Zan iya yin Dubu biyar. A Dan tsakanin kuwa sosai na dage da Addu'a Naseer kuwa shima Bai zauna ba. A ranar da muka cika sati daya muka tare a karamin gidan Naseer dake sharada. Cikin kwana biyu ya samowa su Zahira makaranta har da Minal suka fara zuwa Har wani Dan sheki yake Yi na kwanciyar hankali. Ni kuwa Inda ya kasance d'akina sai Dana rataya abinda Mallam Musbahu ya bani Dan dazan tafi sai Dana cire na kaina kuwa bana Wasa dashi sai idan Zan shiga bandaki nake cirewa Ina fitowa kuwa na maida kayana. Dak'yar na samu na Shawo Kan Naseer akan ya koma gidan Sabida Kar Umma ta zargi wani Abu Yama nuna Mata ya hakura Dani zai zauna da Hindatu anan ya harareni nayi dariya nace yayi maganinta cikin sauki da kafarta zata gudu sai a lokacin yace na kawo shawara Mai kyau shi Kuma zai na karyar tafiya Yana zuwar mana. A ranar da zai koma goron dutse da yamma Inna zuwaira da zata iya haifata tazo gidan Ashe Naseer Mai Tayani Zama ya Nemo min wacce Kuma zata ringa Tayani aikace aikace idan ya dawo Kuma sai ta tafi idan zai tafi sai ta dawo. Sosai naji dadin zuwanta Dan Zan samu Mai debb'e min kewa kila ma har Abu Idan ya shigemin duhu Zan iya neman shawarar ta. Naseer sai daya ajiye Mana komai har da kudin da bansan Mai zai yi.dasu ba Wanda har dagewa.nayi bazan karba ba Dan cemin yayi kullum sai yazo har abinci ma anan Zai ringa ci kwanciyar bacci ne zai ringa Mai dashi gidan. Wajen karfe Tara ya Isa gidan fuskarsa kalar tausayi kamar gaske irin neman Naeema yake. Tun Kan ya karasa Hawa sama yake jiyo Shewa. Da Sallama ya tura k'ofar Ba Wanda ya amsa sai juyowa da sukayi gabad'aya suna kallonsa Hajara har da mik'ewa tayi dage tana kallon bayansa Wai ko ya dawo da Naeema sai data ga shi ka dai ne ta washe baki tana "ko Kai fa ka hakura kazo ka zauna da Yar albarka tace.tana nuna Masa Hindatu. Naseer Bai ce komai ba ya hau kallon mutanen palon Hindatu ce da Saffiya da Lami har dasu Tijjani sun zauna a tsakiyar Palon sai barjen Naman kaza suke ga kwalaban lemo a bubude. Wato ma budurinsu kawai suke da Naeema ta tafi shi Kuma daga tafiyarsa shine su Saffiya suka dawo gidan. Ba wacce yayiwa magana a cikinsu har Tijjani dake gaishe shi Ya d'auke kansa tare da nufar d'akinsa Kai tsaye yana Jin muryar Umma tana duk hade Ransa Naeema bazata dawo ba idan ma.zai ware ya ware. Sai daya Dan gyara d'akin ya watsa ruwa ya kwanta ya hau tunani su Naeema Dan lokacin ba wayar hannu da ya Kira yaji lafiyarsu Naeema Dan kwanakin da yayi dasu ba karamin nutsuwa da kwanciya hankali ya samu ba babu abinda ya Kai Zama da iyali dadi. Bai San da shigowar Hindatu ba sai ji yayi ta fado kansa shi kuwa ya mik'e da Sauri ya wancakalar da ita ya fara binta da wani mugun kallo Yana "duk ranar da Kika Kara shigomin daki wlh sai na balla Miki kafa juya ki fita" Hindatu da Sauri ta fita ko minti biyu baayi ba Suka dawo d'akin da Hajara cikin masifa ta fara magana tana "Wai Mai kake nufi dani.ne. Naseer akan me zaka auri Yarinya Kuma ka ringa wulakanta ta toh wlh ka kaini bango Kar sake ka Kara korarta daga d'akin Nan Dan nan da wata tara inaso a haifomin jika Ni naga masifa duk da shegiyar matarka ta Shiga duniya ka ki nutsuwa ka dawo hankalinka toh wlh ka nutsu Dan nasan Tama Dade da mutuwa an rage mugun iri" Wani irin kallo Naseer yabi Hajaran dashi ya d'auke kansa Bai ce Mata komai ba sai data gaji Dan kanta ta fita waje tare da Kara rufo musu kofa har da su mukullin. Hindatu kuwa har da wani murmushnta ta Kara haye.gado tana murmushi. Naseer shima mik'ewa yayi ya kullo k'ofar da mukulli ya zare ya saka key din a aljihunsa ya Shiga bandaki ya dauro alwala yazo ya hau Kan Sallaya. Tuni ya ware murya ya fara karatun Qurani Hindatu kuwa ta mik'e hankali a balain tashe ta nufi wajen kofa ta fara jijigawa sabida Karatun sosai yake kona fatar jikinta. Naseer kuwa Yana ganin Haka ya mik'e ya Ajiye Quraninsa ya nufi wajen Hindatun ya rik'e hannayenta biyu da k'arfi ya cigaba da karatunsa da k'arfi Yana tofa Mata yawun bakinsa. Hindatu kuwa da iya karfinta take ihu tana Kiran sunan Hajara Dana Mahaifiyata take Hajara ta Gane Mai ke faruwa hankalinsu ya tashi. Hajara kuwa ta bud'e k'ofar d'akin sai dai Naseer ya kulle k'ofar ta ciki itama da Sauri ta dawo Baya Abinda basu fiye Yi ba b'acewa Dan sai Abu yaci tura sosai suke amfani da Wanan karfin. Akan Dole Hindatu ta b'ace daga hannun Naseer Duk da Naseer ya tsorata sai Haka ya cigaba da karatunsa da k'arfi tsoro na Kara shigarsa [6/26, 3:28 PM] +234 803 635 0240: *NAGA TA KAINA* *NA SADNAF*🌸🌸 ®️ *_PURE MOMENT OF LIFE WRITERS_* _{We Don't just entertain nd educate we also touch the heat of readers P.M.L}💪🏻_ *Free Novel* *Page 20* Duk da yasan Hindatu da mahaifiyarsa suna cikin kungiya Bai San haka Abun yake ba yanzu macen da take tsafi wacce take Mayya mahaifiyarsa ta aura Masa Maganar Allah ne basa so suji kenan ma Mahaifiyarsa ba musulma bace toh a wane sahu zai sakata kenan kafura ko me innalillahi wa Inna ilaihi rajiun Amma Abun mamaki mahaifinsa ya bashi labarin Mahaifin Hajaran Dalibansa ne Kuma musulmi toh Ina Hajara ta Samo wanan halin nata ko a cikin danginta akwai kafuran arna da basa sallah ne shiyasa ta Kauce hanya Haka bacewar da Hindatu tayi a hannunsa ya Kara gasgata Masa zargin su suka d'auke Nadeeya Yana ta imagining yanda hakan zai yiwu Wai mutum.ya b'ace sai da yaga zahiri. Sosai.ya Kara k'arfin muryarsa Yana Shan alwashin ma Kiran mutane zaiyi suzo su Masa Saukar Qurani a gida. Yana Jin Hajara na kwalla Masa Kira daga nesa da d'akin ya shareta Shugubarsu kuwa ranta ba karamin b'aci yayi ba dan karatun ba iya Hindatu ya tab'a ba har da ita hakane yasa cikin bacin rai ta bayyana gabansu Hajara da lami Hajara kuwa suka zub'e a kasa suna k'ok'arin Magana ta daga musu hannu ta Shiga d'akinsu ta d'auke tukunyar Tsafin su da mudubinsu da duk shine karfinsu. Tace wa Hajara sai ta hukunta su zata dawo musu dashi Kuma Hindatu bazata sake dawo wa Naseer ba Kafin ma suyi magana har ta b'ace. Hajara zaman dirshan tayi a kasa ta hau kuka Dan ko kad'an Bata San abinda zai rabata da Karfin tsafinta gashi Naseer yaja Mata daga ita har yayan nata an kwace musu k'arfin. Naseer kuwa tsoro yasa ko bacci baiyi ba sai da aka Kira sallah asuba ya fito da alwala baiga kowa a palon ba sai Tijjani dake ta sharar bacci. Shau da Masa carbin hannunsa yayi ya mik'e a firgice Naseer kuwa yace Masa ya tashi su tafi.massallaci ya Fadi hakane sabida yaga ko shima baya sallar ga mamakinsa sai yaga ya mik'e yayi band'akin palon ya d'aura alwala ya fito. Tare.suka.tafi Massallaci Naseer kuwa Bai dawo gidan ba sai da gari ya waye sosai wajen Shidda da rabi ya shigo gidan. A Palo ya tarar da Hajara da idonta ya kumbure sabida kuka ta zauna tana ta jijiga kafa. Wani irin kallo take Masa kamar zai wuceta kuma ya fasa ya tsugunna ya hau gaisheta. "Burinka ya cika ka batamin komai Naseer na Haifeka Amma bakada burin da ya wuce ka bak'antamin toh burinka ya cika Hindatu ta bar rayuwarka Amma fa kasani wlh Tallahi sai na Kara Nemo wata na aura maka ita Idan Dan Naeema.kake ta haukar Nan toh wlh gwara ka Shiga hankalinka" "Umma Maganar Allah ne bakwaso ko me karatun Qurani ne bakwaso nayi a gidana umma kinsan kuwa Allah ya hallicemu ne Dan mu San shi.mu Kuma bauta Masa Umma jiya karatun Qurani nake Hindatu ta b'ace a hannuna Umma kinsan kuwa hanyar da kike Kai b'ataciya ce ba mai billewa bace Umma Dan Allah Dan annabi ki tuba ki komawa Allah Umma wanan tsaface tsafacen ba Inda zai bille dake Umma tun sanin Dana Miki ban taba ganin kinyi Sallah ba Umma balle azo Kan sauran ibadan Umma lokaci Bai kure Miki ba ki tubarwa Allah ki dawo kan hanya Umma na saka ki a islamiyya ko Ni na koya Miki sabida kisan Allah " "Naseer Ni ka saka a gaba kana zagi yanzu so kake kace bansan Allah ba kafura ce Ni ko me a takaice dai kana so kace Ni jahila ce ko Naseer Dan Hindatu ta b'ace a hannunka sai aka ce maka nima Ina bacewar Naseer Banga laifinka ba Naseer Kai da ka daga hannu ma zaka Mareni yanzu ai kanka ba daidai bane tunda wancan mayyar yar ta Shiga duniya ka haukace tunani ma ba daidai kake ba maganar da nake ma daban Wanda kake min daban idan ma.duk.kana wanan surutan ne Dan Kar Kayi aure wlh sai kayi Kaji ma na Gaya maka.sanan wadanan munafikan daka saka a shago ban yarda dasu ba ka koresu Tijjani ya rike maka shagon. "Umma Tijjani bazai iya rikemin shaguna uku ba ba yanda Zan Kori mutanen da suke samu a karkashina Zan dai bawa Tijjani jari ya rik'e kansa namiji ne shima ai ya kawo girman da zai Yi aure. Safiya da Lami Kuma ya dace ace sun fito da mazajen aure Haka Dan wanan ba rayuwa Mai kyau suka zabawa kansu ba" "Naseer a takaice dai kora da Hali kakeso kayi Mana toh bari kaji na fada maka babu Inda zamuje Kuma jari ba iya Tijjani zaka bawa ba har dasu lamin ka Gama duk abinda ka Dama Aurene sai kayi Dan ban Haifowa Naeema Kai ba yarinya duk tabi ta saka ka fice daga hayyacinka" Naseer tashi yayi ya Shiga d'aki ita kuwa ta cigaba da bambamin fad'a kamar zata Ari baki. Ahaka ya shirya ya zo ya fice daga gidan Bai tsaya a koina ba sai a sharada lokacin Naeema tana daki tana bacci Inna zuwaira Kuma tana Dan Kara gyagyara gidan su Zahira kuwa Suna makaranta Sai a gidan ya Rama baccin dake kansa yaci abinci ya huta sukayi ta Hira kamar basu da wani matsala yaso kwana sai da Naeema ta dage Masa Akan Kar ya kwana Dan Hajara na iya ganewa Yana dawowa kuwa gidan ya d'auko Quraninsa a Palo ya hau karatun Qurani Dan sosai yake so su Umma su ma su bashi space ya sarara Amma ga mamakinsa ba Wanda ya tashi a cikinsu ya gudu kamar yanda suka Saba. Sosai kansa ya daure da mamaki Hajara kuwa sai jefa Masa harara take sai daya Kai Aya ya mik'e zai Shiga d'aki tace "wato k'arfi da yaji kake so mu bar gidanan babu Inda zamuje Naseeru muna Nan tare da.kai zanyi maganin taurin kanka A Haka rayuwa ta kasancewa Naseer da Naeema. Acan yake yin komai kwana ne kawai baya yi a gidan shima da an kwana biyu zai cewa Hajara tafiya ta taso Masa ahaka zaije yayi sati ko sati biyu a gidan Naeema sosai suke taka tsantsan Dan Kar Hajara ta gano suna tare. Duk da lokacin sosai ta matsa Masa da zancen aure har mamaki take yanda Naseer din yake rayuwarsa batare da ya damu ba gashi ba komai na tsafi da zasu iya gano komai a game dashi Koda akwai yanzu idan Suka so ganin Naeema ta mudubi basa iya ganinta har mamaki suke Nan kuwa basu San layyar data saka a kanta bane.ya hanasu ganinta shugabarsu ma sai cewa.tayi kila ma Naeema mutuwa tayi shiyasa basa ganinta Naeema sosai Jin dadi da kwanciyar hankali ya zauna Mata har ta ringa tunanin duk wanan lokacin Mai yasa dabaran hakan Bai fad'o musu ba. Naseer shima sosai ya samu kwanciyar hankali sai zai je gidansa da mahaifiyarsa take ciki yake d'auko wata fuskar ya aza idan yaso ma tsokano Hajara idan tana Masa zancen aure shi kuwa sai yace Mata Shi bazai yi aure ba sai Naeeema ta dawo anan fa Hajara xata hayayyako kamar zata masa.baki tayi ta cewa Naeema ai ta mutu ko ba mutuwa tayi ba Bata isa ta dawo gidansa ba. Ahaka har sai da suka kwashi watani shidda cas watarana ya dawo daga gidan Naeema. A Palo ya tarar da Hajara ta balain had'e Rai Safiyya Kuma tana zaune a gefenta. Gaishe ta yayi ya mik'e zai wuce d'akinsa Hajara ta dawo dashi ya zauna. Ta fara magana cikin b'acin rai "Naseer kana so kaga b'acin Rai na ko kana so sai na balain Bata maka kafin mu shirya dakai ko ka Nemo matar aure ko na nemo maka da kaina na gaji da ganin ka Haka ko na nemo maka matar auren Sai ka wulakanta ta kamar yanda ka wulakanta Hindatu na baka Nan da sati biyu ka nemo matar aure idan ba Haka ba wlh da kaina Zan Nemo maka Kuma baka Isa ka wulakanta ta ba" "Tom Umma Zan nema Ina ta ganinsu babu wacce tamin ne Amma insha Allahu zanyi kokari na nema din" Daga Haka ya mik'e ya shige dakinsa Fada Hajara ta ringa yi bayan ya Shiga d'akin Saffiya kuwa ta tab'a ta tana "Umma Anya Yaya baya tare da Naeema kuwa "? Wani irin hantsulowa Hajara tayi daga Kan kujeran ta dafe kirjin ta tana "Mai kikace Suna tare fa kikace Mai kika gani kikace Haka"? "Umma kema kinsan yanda ya Naseer yake San Naeema yake Kuma San yaransa banajin da basa tare zai samu kwanciyar hankali Haka ke bakiga yanda.yaya ya danyi kib'a Yana sheki ba wlh kila Raina Mana hankali yake"? "Zan Miki baki wlh Safiyya karki soma min wanan fatan idan suna tare a Ina ya ajiyeta Naga dai gida yake zuwa ya kwana sai idan tafiya ta Kama shi yake kin kwana a gida kin manta bama.ganinta a mudubi shugaba.kuma data duba da kanta tace kila hatsari sukayi suka mutu" "Hmmm toh shikenan tunda Kikace Haka Amma nidai gani nake da Yaya baya tare da Naeema bzaki kansa fes Haka ba" Mik'ewa Hajara tayi da Sauri tana "idan kuwa hakane Safiya na gano rainamin hankali sukayi wlh sai nayi wa Naseer baki wlh sai na kashe Naeema da hannuna Kinga Banga ma ta zama ba ya zama Dole mu koma Calabar muje mu bawa Shugaba hakuri ko Dan na ringa sanin abubuwa da ke wakana wlh tunda ta kwace komai namu banajin dadi Banga ta zama ba ya zama Dole mu d'auki hanya gobe" Sosai hankalin Hajara ya tashi da maganar da Safiyya ta Mata washegari kuwa da sassafe Bata ma jira Naseer ya dawo daga Massallaci ba Suka dau hanya su uku Dan Tijjani tunda Naseer ya bashi jari ya Kama wani shago a gwammaja ya zuba kayan provision yake siyarwa Bai ma fiye dawowa gida ba. Naseer sosai yaji dadin tafiya da Hajara tayi dasu Safiyya cikin kwanciyar hankali ya koma sharada da zama dama sabida gidan ya masu kad'an ya Kara siyan fili a jikin gidan aka hade da yake da kudi a hannunsa tuni gidan yayi kyau da tsari. Arziki Kam har yaci uban na da Dan Naseer yanzu Yana da gidaje sun Kai shidda filaye kuwa zasuyi hudu Kuma duk manya shagunansa kuwa shidda.banda wasu kasuwanci da yake danyi kudi na shigo Masa. A cikin wanan shekarar yake burin idan Allah ya amince zasu je aikin Umara shi da Naeema. A kuma cikin wanan yanayin Naeema ta Kara samun ciki Wanda Naseer ya balain kwallafa Rai akansa yake Kuma sawa a addua Allah ya azurtashi da samun da namiji. Naeema kuwa tunda Naseer ya dawo gidan yace Masa Hajara sunyi tafiya hankalinta ya kasa kwanciya Haka kawai takejin kamar babu alheri a tafiyar tasu hakane yasa ta dage da Addu'a duk da Bata tab'a Zama ba adduar ba Naseer ma har ya zama Masa jiki adduar. Hajara kuwa dak'yar shugabarsu ta hakura ta maida musu karfinsu Inda ta gargadesu da nisantar duk Inda ake Karatun Qurani anan Hajara tasa a duba Mata Naeema ta mudubinsu ko tana rayye anan suka duba Amma duk Inda suka kai ga tsafinsu basu iya ganin Naeema ba Naseer kawai suka gani a zaune a kasuwa Yana ta zabga lissafi. Satinsu uku a Calabar suka dawo. Naseer bai.ma San sun dawo ba sai daya zagayo wajensu Lukman Dan ya karbi takardar lissafi da sukeyi yasan sun dawo. Sosai yaji Bai ji dadin dawowarsu ba. Ahaka ya b'oye abinda ke Ransa ya musu Sannu da zuwa. Sai a lokacin Hajara ta ga kibar da Naseer yayi na kwanciyar hankali. Yana tashi ta kalli Safiyya tana "Akwai wani Abu a kasa wlh ban yarda da Naseer ba gobe idan ya fita inaso kiyi ta bimin bayansa har kiga Mai yake ciki" Naseer kuwa ba a San Ransa ya kwana a gidan ba Washegari da sassafe Naseer ya fice daga gidan ya nufi gidansa dake sharada. A Haka Safiyya tayi ta binsa a baya batare da yasani ba har ya Shiga gidan. Sabida tsabar balai Haka Safiyya ta labe a kangon jamaa sai da Naseer yaci ya koshi yayi wanka ya shirya tafiya kasuwa. Haka kawai Naeema ta ringa Jin fad'uwar gaba jikinta ba dadi addua kawai take a ranta har Naseer ya tafi. Safiyya kuwa cikin mamaki ta ga Naseer ya fito daga gidan daga wajen gate Naeema ta rakoshi da Hijabinta tayi wani irin fari Kamar ba ita ba Bata tsaya ma ganin tafiyar Naseer ba ta fita titi da balain gudu ta hau taxi Suka nufi goron dutse sai vibrating take Kamar itace Hajaran. Ko parking din kirki Mai taxi Bai Gama yi ba ta fito daga motar ko kudin Bata bashi ba ta hau sama da balain sauri Tana kwallawa Hajara Kira Zumbur ta mik'e tsaye Tace "Wlh Naga Naeema Yaya Yana tare da naeema" Yaraf Hajara ta zub'e a kasa kamar an doka Mata guduma ta Kara mik'ewa cikjn tashin hankali tana Kika ce me"? Safiyya hannun Hajara kawai ta jawo Suka sauka da gudu Suka fada taxi din tana ce Masa ya maidata Inda ya d'auko ta zata hada Masa kudinsa. Hajara wani irin jijjiga kawai take Tana vibration har suka Isa sharada. Jikinta sai rawa yake yanda zata.shake Naeema. Suna sauka Safiyya ta hau buga gidan da hannu biyu. Ina zaune naji Ana buga gate da balain k'arfi mik'ewa nayi cikin fad'uwar gaba na dafe kirjina haka kawai Umma ta fado min a Raina. Inna zuwaira ce ta bud'e gidan tana bud'e gidan Safiyya ta bangajeta suka shige suka hau kwallawa Naeema Kira ahaka har Suka shiga palon dana daskare a tsaye tunda naji muryar Safiyya. Kallon kallo muka fara da Umma tana tsaye daga bakin kofa Ni kuwa in Banda sallati babu abinda nakeyi....... [6/26, 3:37 PM] +234 803 635 0240: *NAGA TA KAINA* *NA SADNAF*🌸🌸 ®️ *_PURE MOMENT OF LIFE WRITERS_* _{We Don't just entertain nd educate we also touch the heat of readers P.M.L}💪🏻_ *Free Novel* *Page 21* Kirjina bugawa yake bakina d'auke da sallati ganin Umma tamkar ganin malaikan da zai zaremin Raine bamu tab'a had'a inuwa da Umma Bata nemi cutar Dani ba har ya Kai indai zanyi Ido biyu da ita tsigar jikina sai ya tashi. Abinda ya bani mamaki irin tsoron danake ji idan naganta banji irin Wanan tsoron ba duk da dai a tsoracn nake. Kallona kawai take daga bakin kofa jikinta na wani irin rawa Zan iya cewa ban taba ganin ta a cikin wanan yanayin ba wani irin Mugun tsanata nake hangowa a idonta da ace zanje hannunta Ni nasan sai ta rabani da numfashina. Hakane yasa na tsaya akan kafafuna sosai Ina adduoi a Zuciyata Saffiya ce ta shigo palon tana ta duramin zagi tana tsinemin sai zagin iyayena take Inna zuwaira kuwa sai cewa take daga Ina kuke wa kuke nema"? "Shegiya Mayya nataciya tsinaniya Banda maita ana dolene? munce bama sanki Umma tace Bata sanki ki rabar Mata da D'a Mana shegiya akuya Mai gindin haihuwa kinsamu waje sai haihuwa kike kamar akuya ko akuya ma na Dan bada tazara Banda ke duduu yaushe Kika haifi wancan bak'ar yar taki" "Kema ki zuciya ki haifi naki Safiyya" Na tsinci kaina da fad'a Nima cikin mamakin kaina "Nace ki zuciya kema ki zama akuya ki haifi naki ba ki sakoni agaba ba Saffiya Ni ba Mayya bace Yayanki ne Mayya ya Kuma nace min kije ki nemi miji kiyi aure ki samu ki haihu Safiyya bibiyata da sharri ba naki bane Dan Allah shi ya halliceni rayuwa da Kika ga inayi shi ya tsaramin yayan da kike magana shi ya bani Kuma iya yayan da ya hukunta Zan samu shi Zan Haifa Safiyya babu yanda zakiyi Dani" Daga Saffiya har Umma wani irin kallon mamaki suke min Safiyya kuwa tuni idonta ya kad'a yayi Ja ta nuna kanta tana "Ni kike fadawa maganganun nan Naeema"? Maganar mmn Mannir na tuna "duk ranar da Kika kwatar wa kanki yanci zakiyi mamaki wlh sai sun fara shakarki suna tunanin kila akwai abinda Kika tak'a "Eee ke nake fadawa maganganun nan ko Haka zai saka ki zuciya ki kyalleni Kun takura min Kun sakoni agaba ku kyalleni Dan Allah" Cikin wani irin zafin Nama Safiyya ta daga hannunta zata kawomin Mari. Nima cikin zafin nama na tare Marin tare da yarfar da hannunta duk wani Abu da suka Dade suna min na dawomin cikin zuciyata da zata lura da kyau zata ga yanda jikina ke rawa sabida tsoro Amma abinda sukemin ya isheni rayuwata a hannun Allah take iya rayuwar da Allah ya yarjemin shi zanyi na tafi na Kai matakin da na gaji da d'aukar abinda sukemin. "Karki sake ki Kara yunk'urin kawo hannunki jikina wlh bazan dauka ba abaya na biku na rokeku na shanye duk abinda kuka min Amma yanzu Kun kaini bango Nagaji ku sakarmin Mara nayi fitsari Safiyya kuje ku nemi miji kuyi aure ya zakiji idan kikayi aure kanwar mijinki da mahaifiyarsa na musguna Miki Haka ya Zaki ji Dan Allah ku kyalleni Allah yayi Naseer mijina ne duk Inda kuka Kai da kuga Kun rabamu idan Allah Bai nufa ba wlh babu yanda zakuyi" Hannu ta Kara kawowa jikina na kauce da Sauri Kafin na ankara ta kawomin shak'a wuyana "Har Ni kike gayawa maganganu har wuyanki ya Isa yanka Naeema Mai kike takama dashi? Inna zuwaira ce ta bambare hannunta daga wuyana dayake tana da tsayi ta wancakalar da hannun Safiyya tare da kwasheta da Mari "Sai na tsine Miki Safiyya idan har baki Gama da yarinya Nan ba Kika bari na karaso da kaina" Umma tace tana wani irin hucci Inna zuwaira ce ta tare wawuran da Safiyya taso kawomin ta Kara kwasheta da Mari tana "ke Wai wacce irin Mara tarbiyya yarinya ce ke ya zaku shigowa mutane gida kice Zaki Kama matar gida da k'ok'awa" "Kina Wasa da wuta idan baki cire kanki a maganarmu ba Marin da kikamin Kuma wlh sai kinji a jikinki ki matsa min tsohuwa babu ruwanki a maganarmu" "Ta Allah ba Taki ba yarinya Nafu karfin sharrinki ba abinda zanji a jikina Naga alamar baki da tarbiyya ku juya ki koma daga inda kuka fito Dan bazan Bari hannunki ya tab'a jikin hajiya ba Dan Haka" Safiyya Bata Bari ta karasa ba ta d'auke Inna zuwaira da Mari kafin kace me sun fara wani irin k'ok'awa mamakin karfin halin Safiyya data iya kaiwa Inna zuwaira duka yasa jikina ya fara rawa kafin kace me ta hau ruwan cikin Inna zuwaira ta hau Kai Mata duka ko ta Ina Hankalina a tashe nayi kansu na fara k'ok'arin daga Safiyya daga jikin inna zuwaira Ina sallati Dan duka take kai Mata kamar wata saarta Sai a lokacin Umma ta shigo palon tana idan Kika barta da ranta Safiyya bani na Haifeki ba gwara tasan rijiya ba wajen wasan makaho bane. Jinin Dana ga Yana fita daga hancin Inna zuwaira yasa na saki sallati na fara ture Safiyya da iya karfina Ina ihu Dan nasan iya karfin Safiyya bazai saka ta iya dukan inna zuwaira ba sai dai idan da tsafi take dukanta Nima duka na fara kaiwa Safiiyya Dana ga alamar so take ta kashe Inna zuwaira dake ta sallati. Da Hannu daya ta tureni sai gashi na Fadi kasa nayi zaman dirshan Kara mik'ewa nayi cikin tashin hankali ba dai kashe inna zuwaira zatayi ba kamar yanda Umma tace. Kansu na Kara yi kafin na isa wajensu Naga ta mik'e daga Kan Inna zuwaira tayo kaina taku uku nayi na shige d'akina na kullo k'ofar Ina ihu Dan sosai na ji tsoron Safiyya ya rufeni idan har zata iya dukan inna zuwaira Ina tsaya Kam kasheni zatayi. Ina Jin Safiyya ta ringa jijjiga kofata da k'arfi tana na fito Kar na Bari ta balla k'ofar ta shigo ai ta d'auka wani Abu na taka nake zaginta Ashe karyar iskanci nake. Ina ji Inna zuwaira nata sallati Umma na gobe ma ki Kara Shiga abinda Bai shafeki ba Har k'ofar dakina naji Umma tazo suna ta tura k'ofar Dan ta karfi suke so su shigo Kuma yanda sukeji wlh sai sun rabani da Raina sai dai duk abinda zai faru ya faru. Sosai na ringa Kiran sunan Allah Ina neman ya kawomin d'auki Umma kuwa cewa take wlh a yau zata nuna Mana bamuda wayo har nida Naseer mun Isa mu Raina Mata hankali wlh a yau ko Naseer ya sakeni ko ya zab'a ko ita ko Ni sosai Naga alamar ranta ya b'aci take kirjina yayi ta bugawa wani irin balain tsoro na rufeni A haka sukayi ta zagina suna tsinemin suna ta k'ok'arin shigowa d'akina Bansan tsawon lokacin Dana d'auka daki ba gabana ne ya tsinke a lokacin Dana ji sallamarsu Zahira da maganar daya fito daga bakin Safiyya. Ai Zaki bud'e ki fito idan Kika ji Ana dukan yaranki ko Kafin kace me sai ji nayi Ana dukan Zahira da Nadeeya har da karamar Minal ihunsu kawai nakeji Ana dirmarsu. Cikin tashin hankali na bud'e kofa Umma Zahira kawai take dagawa tana nunawa Allah Tana makata da kasa.dan a yayana tafi tsanarta sabida kawai tana Kama Dani Safiyya kuwa had'e Nadeeya da Minal tayi tana ta duka tana ganin na fito ta cikasu tayo kaina Ni kuwa bansan wane irin Zuciya ne yazomun ba tana a haukace na daga ta na nuna wa Allah na makata da kasa Nayi Kan Umma da take ta buga zahira da kasa. Wani irin wawuro nayiwa Umma na Kai hannunta bakina na kafa Mata hakorina Ina ihu sai a lokacin ta cika Zahira. Tana "wlh yau sai na kasheki Haka wuyanki ya Isa yanka Wani irin shak'a ta kawomin da.hannu biyu Safiyya ta hau kaimin kafa ko ta Ina suna yi suna zagina. Umma kuwa da iya karfinta ta shakemun wuya Bata da burin daya wuce ta rabani da Numfashina Safiyya kuwa hambara ta kawai take da kafa yarana suna ihu. Ni kuwa ihun ma kasawa nayi sabida shakar da tamin "Badai kince ke Mayya bace bazaki rabu da Naseer ba wlh yau sai na kasheki. Tuni numfashina ya fara daukewa Ina juyo kamshin lahira muryar yayana kawai nakeji suna ihun kuka. Sallati kawai nake a raina muryar Naseer naji da k'arfi ya gwada sallati. Take naji Safiyya ta daina kawomin kafa Sosai jikinsa ke rawa da yaga yanda Umma ta shakemun wuya tana San kasheni Kuma shigowar sa Bai sa ta cikani ba illa ma Kara shakeni da tayi Wani irin finciika yayi wa Umma Kafin na dawo daidai sai karar Mari naji Tau Duk da ba a hayyacina nake ba sai da na saka ihu danaga Naseer ne ya Mari Umma Shi kuwa Naseer yabi hannunsa da ya Mari Umma da kallo jikinsa na wani irin rawa da alama bai San sanda yayi Marin ba. Da alama bada niyya yaso marin Umma ba Amma sabida rufewar da idonsa yayi ya Mareta Safiyya kuwa da hannu biyu ta rufe bakinta cikin mamakin abinda Naseer yayi. Umma kuwa ta dafe kumatunta tana kallon Naseer cikin wani irin rawar jiki Ni kuwa kuka na fashe dashi Ina sallati Bazan tab'a manta ranar Nan ba Naga tashin hankali da ko makiyana bana fata ya gani ranar da wani sabon Shafin kaddarar tashin hankali ya bud'e mana Wanda da nasani da ko kukan jini Naseer keyi da ban dawo gidansa ba Cikin wani irin murya Umma ta nuna kanta tana "Naseeru Ni ka mara? Ni Mahaifiyarka ka Mara akan matarka Naseer Ni na Haifeka fa Naseer bayan karyar da kamin akan Naeema ta gudu bayan munafurtata da kayi Akan Naeema ta gudu baka ganta ba shine wanan duk Bai isheka ba sai ka daga hannu ka Mareni Ni Mahaifiyarka Dana dau cikinka tsawon wata Tara ka Mara akan wacce zaka iya canjata sau Dubu Ni baka Isa ka canjani ba" ? Naseer durk'usawa yayi Akan gwiwarsa jikinsa na wani irin rawa har ga Allah Bai San ya akayi ya Mari Umma ba bada niyya ya Mareta ba tayaya ma zai mari mahaifiyarsa "Umma ba da niyya na mareki ba Umma idona ne ya rufe danaga Zaki kashe Naeema Umma ya zanyi kin hargitsamin rayuwa kin hanani zaman sakat Umma na Miki biyayyar na buyan na rasa ya Zan Miki Umma tayaya Zaki zo gidana ki nemi kashe Naeema Umma kisan Kai fa kikeso kiyi baki ga cikin dake jikin Naeema ba Mai Naeema ta Miki Haka a rayuwa Mai na Miki Haka a rayuwa umma kodan rabon dake tsakaninmu ai ya Kamata ki kyallemu Umma Kinga fa Naeema wani cikin ne a jikinta da ba matata bace wlh bazata haifi wanan yaran ba Umma ya kikeso nayi kiyi hakuri Umma inasan matata bazan iya rabuwa da ita ba ki yafemin Marin Dana Miki umma.ki taimakamin" "Naseer Zan yafe maka Marin da kamin idan dai ka saki Naeema wlh a yau sai ka zaba ko Ni ko Naeema idan dai Ni na tsugunna na Haifeka sai ka saketa idan dai ni na raini cikinka har tsawon wata Tara wlh sai ka saki Naeema bana San Naeema bana kaunarta akanta ka Mareni Naseer sabida ita zaka iya kasheni Naseer bazan tab'a san Naeema Ina umartarka daka saketa yanzu Nan Naseer." "Umma bazan iya sakin Naeema ba kiyi hakuri idan na saketa wa zai rikemin yarana" Ka bani su Zan rikesu nidai kawai ka saketa "Umma Naeema Bata Da kowa gurin wa kikeso ta tafi idan na saketa" "Ta Shiga Duniya Naseer babu abinda ya shafeni ka Saketa nace Naseer. Umma kiyi hakuri bazan iya sakin Naeema ba "Dan ubanka tare kukazo duniya da bazaka iya sakinta Naseer wlh Tallahi na baka zabi na karshe ka saki Naeema ko na Sallama maka ita Kuma sallamawar na har abada Dan na rantse da Allah sai na tsine maka Naseer idan dai har Akan Naeema ka Mareni ka ki bin umarni na to bakada amfani wlh tsine ma zanyi ka saketa nace" Naseer kuka kawai yake jikinsa na wani irin rawa. Ni kuwa mik'ewa nayi naje gaban Naseer Ina Dan Allah ka sakeni Naseer kabi Umarninta Dan Allah Naseer karka Bari ta tsine maka Dan Allah ka sakeni Nima nace Ina jijjiga Naseer Ina kuka "Ina umartarka Naseer ka saketa yanzu nan idan ba Haka ba wlh Zan Sallama ka ta zama uwarka Kuma Zan baka mamaki wlh tsine maka zanyi tsinuwar da bazaka yarda Zan iya maka shi ba Idan dai har zaka iya marina Akan Naeema Nima babu abinda zai Hana na tsine maka ka saketa nace Naseer" Umma tace a tsawace cikin mugun b'acin Rai da ban taba ganinta a ciki ba Nikuwa jijjiga Naseer kawai nake Akan ya sakeni shi kuwa ya dafe Kai da hannu biyu Yana "Kiyi hakuri Umma bazan iya sakinta ba ki yafemin Dan Allah Umma Zan Miki duk abinda kike so auren da kikeso nayi wlh Zan Yi Dan Allah karki tilasta min na saki Naeema" "Haka kace ko bazaka iya sakin Naeema ba ko Akan Naeema ka daga hannu ka Mareni Naseer akan Naeema kak'i bin umarnina toh yanda kaki bin umarnina Nima sai na tsine maka" Da Sauri umma tayi wurgi da zanin jikinta har da skirt kafin kace me har paint dinta ta cire cikin Sauri gaban Naseer tsaya a Haka nikuwa tashin hankali yasa jikina ya hau rawa Ina sallati. Naseer kuwa har lokacin kansa na kasa. Cikin Wai irin murya Umma ta fara magana tana kaiwa gabanta duka. "Naseer idan dai Ni na tsugguna na Haifeka sai ka tagayyara Naseer sai ka ga tashin hankali da ifitilai rayuwa Bansan ya akayi na tsinci kaina Agaban Umma na rufe Mata baki da k'arfi cikin ihu Ina "Dan Allah Umma karki tsine Masa wlh Zan tafi Umma wlh Tallahi Zan bar rayuwarsa har abada Dan Allah karki Masa baki Naseer bakada hankaline kanajin kalmomin dake fitowa daga bakin umma fa kasan bakin uwa kuwa Dan Allah ka sakeni Naseer" Nace da k'arfi Umma kuwa ta tureni. ta fara dukan gaban ta tana cigaba da Magana "Naseer idan dai Ni na Haifeka sai kayi bara abinda zaka saka a cikinka sai ya gaggareka Indai ta Nan ka fito Ta Kara kaiwa gabanta duka "Naseer kudi sai sun.maka wahalar samu sai dai ka gani a hannun mutane" Sallati kawai Naseer keyi Ni kuwa na ringa ihu Ina rokon Umma ta daina tsine Masa wlh Zan kwashe kayana wani irin finciko kafadata.tayi ta dagani sama Dan rike Mata kafa nayi cikin wani irinn murya tace "rokon me kikemin Badai abinda kikeso kenan ba Badai burinki ki zauna dashi ba toh gaki gashi tunda ya zabeki akaina zai Gane tasirin bakin uwa kizauna ki cigaba da cin arziki Naeema ki cika Masa gida da Yaya ki maye Masa gurbina na barku har abada" Daga Haka Umma ta wancakalar Dani ta dauko zaninta ta daura ko kallonmu Bata Kara Yi ba ta fice. Safiyya tabi bayanta Jikinta asanyaye. *True life haka Hajara ta tsinewa Dan cikinta wajen Nan ya girgiza ni a lokacin data bani labari* *AL-BISHIRIN KU MATA !!!* INA KUKE MATA INA AMARE INA MANYAN MATA CHEF DEEJARH BERVER SISIN MAMA MAMAN FAREEDA(MAI TSUMIN 'YANGAYU) ANEESA_DIDI SALWISE'S KITCHEN SUNZO MUKU DA YADDA ZAKU KARA ILIMI AKAN GIRKUNA DA GYARAN JIKINKI DA SIRRIN SACE ZUCIYAR MIJI DA YADDA ZAKUSAN MAGUNGUNAN DA YADDA ZAKI HADA CIKIN SAUKI.... GYARA SHINE MACE... YADDA ZAKI GYARA JIKINKI YADDA ZAKI HADA MAGUNGUNAN DA KANKI..TSAFTA KWALLIYA DA GYARAN JIKI.. GIRKI MAKAMIN DIYA MACE INA MACCEN DAKE DA MATSALA DA GIRKI INA MACCEN DAKESON KARA ILIMI AGIRKI DA LEMOKU INA MASU SON KOYAN BIRTHDAY CAKE ?? KINA FAMA DA MATSALAR MATA KO INFECTION KINASO KISAN YADDA ZAKI SAMU MAGANIN GYARAN JIKINKI??? KISSA DA KISISINA IYA KWALLIYA JAN HANKALIN MAIGIDA NUNAWA KAUNA GA MEGIDA SOYAYYA KAUNA HAKURI DA IYA ZAMA.... ZAMU GABATAR DA KOYARWAR NAN DUK AKAN NAIRA DARI BIYAR (500)NAIRA ONLY ZAMU KOYAR NE A WHATSAPP GROUP.. ZAMU FARA RANAR 20 JUNE 2021 KOWACCE MACE ISHASHIYACE... KOWACCE MACE TANADA KYAU .... KOWACCE MACE SARAUNIYA CE .... KOWACCE MACE TAGABAN GOSHIN MAI GIDA CE..... KOWACCE MACE TANADA BAIWA BABU BALLAGAZAR MACE SAI WACCE TASO TA MAIDA KANTA HAKAN...💃🏼💃🏼 KINA SON SANIN SIRRIKAN HAKA??? TO KI GARZAYO CIKIN GROUP DIN MU KIKARA ILIMI DUK ALAN 500 NAIR ONLY *SA'ANNAN AKWAI BONUS NA BIRTHDAY CAKE GUDA2 DA CHEF DEEJAH BABA ZATA KOYAR* GA ACCOUNT NUMBER NAN GA MASU BIYA 0003434251 Sadiya Garba khalil Jaiz bank DOMIN NEMAN KARIN BAYANI TUNTUBI WADANNAN LAMBOBI KAMAR HAKA:- CHEF DEEJAR BERVER 08108696754 SISIN MAMA 08107499249 MAMAN FAREEDA 07033742833 SALWISES KITCHEN 08066914136 ANEESA_DIDI 08036660796 *KIYI SECREEN SHOT KITURA SHAIDAR BIYANKI TA WANNAN NUMBER 08107499249* [6/26, 3:37 PM] +234 803 635 0240: *NAGA TA KAINA* *NA SADNAF*🌸🌸 ®️ *_PURE MOMENT OF LIFE WRITERS_* _{We Don't just entertain nd educate we also touch the heat of readers P.M.L}💪🏻_ *Free Novel* *Kuyi hakuri na rubuta labarin Nan yanda aka bani some comment are really annoying ba wacce na tilastawa karantawa Wai an tab'a Zama a rayuwa ba jarrabawa Ni na fahimci wasu readers din suna San rayuwar soyayya Jin dadi daga farko har karshen labari Amma in reality Kuma kunsan ba Haka bane wlh Ana fuskantar kalubale da jarrabawa na wani yafi wani ne kawai and shi wanan labarin badan aji dadi ko ayi nishadi nake rubutawa ba darasin ciki nake so duk mu karu dashi idan a da kafin ka karanta kana ganin wuyan rayuwa kake Sha idan ka Karanta wanan zaka ga Ashe Kai a rahamar Allah make Ashe Kai baka ga komai bama Wanan kawai zai saka ka kusanci Allah ka Kara gode Masa da naka kaddarar yazo da matuk'ar sauki ahaka ma Naeema idan taga na wani zata ga Ashe itama a rahamar Allah take karku manta fa wani na iya Gama Shan wuyan Nan ya mutu Kuma Amma ita taga rayuwa ko nace sugani Amma Allah ya basu tsawon rayuwa dagani har ku bamu San tanadin da Allah ya musu ba namu yin Dana Allah ba daya bane na Allah shine daidai Abu daya fa danake so ku Gane Hajara a duhu take rayuwa ma a duhu take yin shi duk wani Abu da takeyi a jahilce take yinsa babu Wanda yasan Dan wuta da Dan Aljanna zaka Dade kana aikin Lada saura kiris ka Shiga Aljanna sai kayi aikin Yan wuta Haka zalika zaka iya Kare rayuwarka kana yin abun Yan wuta idan Allah yaso ka da rahama wlh sai kayi Abun Yan Aljanna sai ka tafi straight karku manta karuwa fa sabida ta saka dankwalinta ta d'ebowa Kare ruwa a rijiya aka yafe Mata zunubanta our thinking is different from that of Allah Kai dai da kake Raye kayi addua Allah ya rabaka da mumunan kaddara alot da suke kashe mazajen su Kila basu tab'a sanin Yana cikin kaddararsu ba a case din Nan mu kiyaye kalmomin da zai na fitowa daga bakinmu Kar Allah ya jarrabcemu Allah ya tsare mana imaninmu Ameen* *Page 22* Mik'ewa na Kara yi da Sauri nabi bayan Umma a guje Sauri take ta zubawa tana surutai Safiyya kuwa har da Dan gudunta Dan ta tadota. Banji nauyin cikin jikina ba Haka na saka gudu na tadota na zub'e a kasa tare da rike Mata kafa Ina "Umma Dan girman Allah ki janye bakin da kika yiwa Naseer Kar tsanar da kikamin ya rufe Miki Ido kiyi Masa baki Umma nice bakya so tare dashi wlh zan debbo kayana yanzu a gabanki na tafi Tasha kiyiwa girman Allah ji janye kalamanki ki saka Masa albarka Umma ki yafe Masa Dan girman Allah wlh Zan bar rayuwar sa" Kuka nake sosai Ina Kara kankame kafar Umma dake min wani irin kallo da nasan da ace da Hali kwaf daya zata min ta rabani da Numfashina sabida tsabar kiyayya har lokacin jikinta wani irin rawa yake tunda nake a rayuwata ban tab'a ganinta a cikin wanan halin ba Damkar kafada ta akayi da k'arfi na daga kaina Safiyya ce da itama idonta ya kad'a yayi wani irin ja ta fara magana cikin b'acin rai "Magiyar uban me kikeyi Naeema ai murna ya Kamata kiyi kinyi Nassara wajen raba uwa da danta ba abinda bayi dake ku rabu ba Kika makale Kika nace sabida tsabar maita toh gashi dai kin janyowa Yaya Naseer tsinuwa agurin Umma Akanki Yaya Naseer ya wankawa Umma Mari na tsaneki Naeema na balain tsanarki shegiya tsinaniya" Daga Haka ta wancakalar da ni ta kalli Umma tana "Umma kalamanki sunyi tsauri Akan yaya Naseer ki janye Sabida muma sai ya shafemu karki manta Yaya Naseer shine cinmu shine shanmu komai namu shine yaya Tijjani ma arzikinsa yake ci tayaya sabida wata jakar Naeema zaki zuciya ki Masa baki Haka Umma"? Wani irin kallo Umma ta yiwa Safiyya cikin wani irin murya tace "na gwammace nayi yawo tsirara nayi bara naci na Sha da na janye kalamai na Badai kudi Naseer ke takama dashi ba Badai Dan kudi Naeema ta makale Masa Taki rabuwa dashi ba har Ni yau Dan Dana Haifa ya daga hannunsa ya mareni ya Kuma k'i bin umarnina Wlh Naseer Bai ga komai ba ke kuma" Umma tace tana Nuno da hannu "Badai ke Naseer ya zaba akaina ba zaki gani Badai kina da Yaya ba Zaki gani" Daga Haka ta wuceni fuuu Safiyya tabi bayanta Ni kuwa na fashe da wani irin kuka Ina sallati. Ina kallo Suka tari abin Hawa Suka tafi kukan danake a zaune dirshan a kasa yasa aka fara Dan taruwa Ana kallona hakane yasa na mik'e dak'yar na nufi gida Ina Jin jiri. A yanda na fito Na bar Naseer ahaka na taddashi Kuka yake kawai Yana "Umma ki.yafeni wlh bada niyya na mareki ba bansan ya akayi na d'aga hannu na Mari Mahaifiyata ba Wanan wane irin kaddara da mumunnan Rana ne Umma Mai na Miki da zafi da Zaki min irin wanan kalaman Umma nifa danki ne Dan Allah ki yafemin. Yarana kuwa curewa kawai sukayi waje daya suna kuka. Tashin hankalin danake ciki Bai saka nabi ta kansu ba ba abinda ke yawo a kunnena sama da kalmomin Umma masu nauyin gaske ga Naseer. Haushin Naseer ne ya danne tausayinsa a Zuciyata Cikin kuka na fara magana Ina "Haba Naseer idan rai ya bace ai hankali ke Nemo shi Naseer kasan girman uwa kuwa tayaya zaka Mari Umma?tayaya zata baka umarni ka k'i bi kana Jin irin kalmomin da take jifanka dasu fa haba Naseer Ina iliminka da tunaninka suka tafi Taya zaka dage sai ka zauna Dani yanzu idan na mutu zaka iya Bina ne?kana da damar da zaka sake aure bakada damar da zaka sake uwa Naseer ka mike yanzu tun lokaci Bai Kure ba kabi bayan Umma kaje ka nemi yafiyarta ka rubuta takarda sakina agabanta sabida taji dadi kamin saki daya ko biyu sai mu cigaba da Addu'a kila a gaba sai mu maida aurenmu. "Naeema Umma tayi fushi Dani sosai bazata saurareni ba zuwana yanzu na iya sawa ta hau ta cigaba da min kalamai marasa dadi naso bin Umarninta Amma bakina yak'i bani hadin Kai jinayi bakina yamin nauyi na kasa bud'e na furta Miki kalmar saki Wlh da hankalina da tunanina Naeema bazan daga hannu na Mari Umma ba bansan.mai ya hau kaina ba burina kawai lokacin na Hana Umma ta kasheki burina kawai lokacin na tseratar da ita daga Halaka kar ta d'au nauyin kissan Kai a yanda na taho so kawai nake na ceceki ba wai na Mareta ba bansan Mai ya sameni ba da ilimina na aikata irin wanan danyen aikin ya Allah ka yafemin ka sauko da zuciyar Mahaifiyata innalillahi wa Inna ilaihi rajiun" Yanzu ma Bai b'aci ba Naseer kaje ka Bata hakuri burinta kawai ka sakeni ka Kai mata takarda sakina ni nasan zata yafe maka" "Bazan iya hada Ido da Umma ba tunda na Mata ba daidai ba na kasa hada Ido da ita Naeema ki kyalleni naji da ciwon dana keji a kirjina da asuba zanje zuwa lokacin nasan kila ta sauko Kuma Zan bi umarninta tunda Haka take so" A Ranar daga Ni har Naseer bamu runtsa ba sosai Naga tashin hankali a tare da Naseer Duk jarumtarsa ranar haka ya zama kamar mace Haka nayita bashi baki. Haka nayita bashi magani sabida zazzabin dake ta rufeshi. Washegari da asuba Naseer ya nufi goron dutse duk a hargitse Dan sallar ma ba a nutse yayi ba. Turus yayi a lokacin da yaga gidan a kulle da kwado sosai yaji hankalinsa ya tashi yayi zaman dirshan a k'ofar Gidan lailai ba karamin fushi Umma tayi dashi ba yanzu ya zaiyi" Yana zaune a wajen su Lukman suka fito suka hau gaishe shi suna tambayarsa dafatan lafiya Dan kana ganinsa kasan baa hayyacinsa yake ba "Bai iya musu magana ba Dan ji yayi idan zaiyi magana zai iya fashewa da kuka hannu Lukman din ya saka a Aljihu ya dauko mukullin gidan ya mik'awa Naseer Yana gashi Hajiya ce ta bani jiya Akan na baka idan ka dawo sun koma garinsu jiya daddare inata ma hanasu tafiyar Taki saurarata. A zuciya Naseer ke nanata innalillahi wa Inna ilaihi rajiun. Bai ma ji Mai Lukman ke cewa ba ahaka ya mik'e ya hau taxi ya dawo gida. Ni kuwa tunda Naseer ya fita massallaci Ina iddar da sallah na dawo Palo na zauna na buga tagumi Ina ta tunanin abinyi hankalina gabadaya na wajen Naseer ko ya zasu Kare da Umma tunanin hada kayana Dana yarana ne ya fad'omin Dan Naseer na dawowa Zan tafi garinmu bazan Kara Sakan daya ba su Zahira ma a ranar da suka gani a zaune basu min zancen na shiryasu su tafi makaranta ba suma duk jikinsu ba kwari Haka suka tashi daidai da Humaira karamar yarinya ma kamar tasan Mai ke faruwa Haka tayi lamo da ita. Wajen bakwai da rabbi Naseer ya dawo duk a firgice mik'ewa nayi da Sauri na tare shi Amma sai ya matsar Dani gefe ya shige daki. Ahaka na bi bayansa Inda Yana shiga daki kwanciya yayi ya fara hawaye nayita tambayarsa Mai ya faru yak'i kulani. Hasali ma da yaga na dameshi da tambaya sai ya daka min tsawa akan na fita na bashi waje yaji da Abunda ke damunsa Haka na fito daga d'akin Nima Ina hawayen Inna zuwaira Bata Nan balle nace ta dafawa su Zahira abinci jiya bansan ya akayi ma ta bar gidan ba ahaka na daure na Shiga kitchen na Dora musu ruwan tea Yana tafasa na juye a flask na hada musu tea na ajiye musu bredi na koma Kan kujera na zauna sosai naji Haushin abinda Naseer yamin Naga dai duk shi ya jawo Mana wannan tashin hankalin da yabi umarnin Umma da duk Haka Bai kasance ba ina Jin ciwon tsanar da umma tamin na ba gaira ba dalili na rasa Mai nayiwa Umma a rayuwata k'arfi da yaji take so ta tasheni daga Kan yayana. Haka nayita zubar hawaye sama da awa biyu sai dana gaji Dan kaina kafin na mik'e na Kara komawa d'akin Dan so nake Naseer ya gayamin yanda sukayi da Umma ya bani takarda ta na tafi Dan indai ya sakeni bazan zauna ba tafiya zanyi tsinuwar da Umma tayiwa Naseer sosai ya tsayamin a zuciya tsinuwar kawai idan na tuna sai gabana ya tsinke ya fadi sosai duk kalmomin suka tsayamin a Rai suke razanani" Rawar Darin da Naseer keyi yasa nashiga d'akin da gudu Ina tab'a shi naji jikinsa zafi zau. Ahaka na kwasa nayi waje na Nemo Mai taxi ya shigo ya Tayani kinkiman Naseer mukayi asibiti bayan na Kai su Zahira gidan mak'ota a takaice sai da Naseer yayi sati a asibiti Inda aka ce jininsa ne yayi balain Hawa sabida damuwar daya saka a ransa. Sai da aka sallamo mu da kwana biyu yake bani labari su Umma sun koma Calabar Wanda hakan na nuni da Umma ba karamin fushi yayi ba shi Marin daya matane inya tuna yake daga Masa Hankali. Shawara na bashi akan yabi bayanta zuwa Calabar ya nemi Mallam Musbahu ya raka shi su bawa Umma baki ya Kuma tabbata da ya sakeni sabida Taji dadi idan na furta kalmar saki Ina ganin wani irin tashin hankali a idon Naseer Amma ahaka yake daurewa. Sai da jikinsa ya Kara kwari kafin ya shirya tafiya Calabar tunda abinan ya faru bana iya cikakken bacci idan bacci ya d'aukeni haka nake mafarkai marasa Kan gado masu firgitarwa nayita ganin Naseer a mumunan yanayi idan na farka sai na danganta Haka da tsinuwar da Umma tayiwa Naseer na saka a Raina dayawa hakane yasa nake mafarki da Naseer. Sosai na sake zage damtse wajen kaiwa Allah kukana Ina Addua Allah yasa Kar bakin umma yayi tasiri akan sa Dan nasan duk a dalilin yak'i sakina tayi Masa wanan bakin uwa Kan sadaukar da farincikinta sabida yaranta Akan Umma na fara ganin uwa Mai San danta ya wulakanta ya tozarta har da su kudi sai ya Masa wahalar samu sai dai ya gani a hannun wasu Mai yayi zafi haka. A ranar da Naseer ya tafi a Haka nayi jigum Kamar Mara lafiya ba lokacin da ake da yawaitar waya bane ballantana na kirashi naji ya sukayi. Naseer kuwa addua d'auke a bakinsa Akan Allah ya sauko da zuciyarta ta yafe masa ya Isa gidan Hajara a lokacin da ya sauka a Calabar Sai dai me Yana zuwa gidan yagan shi a kulle Wanda hakan ya haddasa Masa fad'uwar gaba sai daya tambayi mak'ota akace Masa ai sunce sunyi tafiya sai an kwana biyu zasu dawo. Sosai hankalin Naseer ya tashi Dan yaga alamar Umma ta d'au zafi gashi Bai San ta Ina zai soma nemota ba har tsohon gidanta yaje shima a kulle jiki ba kwari a Haka ya nufi gidan Mallam Musbahu shima sai ce Masa akayi sun bar Calabar sun koma garinsu Dan Dama kasuwanci ne ya kawo Mallam Musbahu sosai Naseer Yaji baiji dadin abinda ya faru ba duk Inda yake tunanin zai ga mahaifiyarsa ya nemi yafiyarta ya samu nutsuwar zuciya ya nema Bai sameta ba yasan Umma tasan zai zo neman yafiyarta shine ta nisanceshi ahaka yayi kwana biyu a Calabar kafin ya juyo ya dawo. A takaice zuwan Calabar biyar Yana dawowa Bai samu ganin Umma ba Akan dole ya hakura da nemanta muka dage da Addu'a Akan Allah ya sauko da zuciyarta daga fushin data hau. Addua Naseer keyi sosai ba dare ba Rana Akan Allah yasa Kar bakin data Masa ya bishi. Duk Wanda yasan Naseer a baya idan ya ganshi tunani zaiyi shekara yayi Yana jinya sabida damuwar daya saka a ransa sai nice ma nake Dan kwantar Masa da hankali sosai yake nadamar k'in bin umarni Umma Dan tunda ta tafi ya rasa nutsuwar zuciya. Ni kuwa kullum cikin addua nake da sadaka Dan sadaka maganin masifa ce idan wani abune ma zai Same mu Allah ya kawo Mana da sauki. Mafarkan danake na d'aga min hankali Amma bantaba gayawa Naseer ba. Naseer kuwa har tausayinsa nakeji nayita kuka a boye. A cikin wanan yanayin Allah ya saukeni lafiya na Kara haifar mace sosai naso ace namiji na Haifa amma Ina ganinta naji kaunarta ya rufeni. Addua na Mata Naseer shima kadaran kadahan Bai nuna komai ba ya saka Mata Raheema yamin komai kamar yanda ya saba na kyautata wa. A Haka rayuwa ta cigaba da tafiyar Mana tun muna dari dari daga Ni har Naseer har muka zo muka saki jiki. Naseer kuwa sai Kara samun budi yake duk da Yana Dan samun sarari Yana zuwa Calabar Amma har lokacin baya ganin Hajara. Ahaka akayi shekara biyu babu abinda ya faru sai a lokacin Hankalina ya fara kwanciya sai na danganta yawan mafarkin danake da kila dan na Saka abinda ya faru tsakanin Naseer da umman ne a Raina. Shima Naseer zuwa Lokacin ya Dan saki jikinsa duk da abin na Fado Masa a Rai Kuma Yana addua sosai Sai watarana ran Monday bazan tab'a mantawa ba Na shirya su Minal Dan lokacin Zahira na iya yiwa kanta komai ita da Nadeeya tana da shekara goma lokacin Nadeeya nada takwas da watani Zahira na primary 3 a lokacin Nadeeya na primary one Minal da Humaira Kuma suma nursery section Raheema ce kawai Bata fara makaranta ba Naseer ne ya shirya Kai su makarantar Dan Dama shi ne yake kaisu Har k'ofar gida na rakasu sai danaga tafiyarsu na dawo Ina kwanciya bacci yayi awon gaba dani na hau mafarki Wai gidan danake ciki ya Kama da wuta. Da sallati na tashi a firgice ai kuwa na jiyo kauri da Sauri na mik'e na nufi kitchen Ashe Wai heater na kunna ruwan ya kone shine heater tayi jawur shap na manta cikin zafin nama na zare socket din na koma Palo na zauna Ina Dan Jin fad'uwar gaba ahaka nayi jigum na zauna na rasa Mai kemin dadi. Naseer kuwa yana sauke su Zahira ya bisu har cikin makarantar sai daya ga shigarsu Aji ya juyo ya hau motarsa ya fara k'ok'arin tayarwa Kamar ance ya juya yaga wata Mata ta tsaya a bakin gate din makaranta ta yafito shi Akan yazo. Fasa tada motar yayi yana mamakin Kiran da matar ke masa anan ya fara tunanin kila a cikin mallaman makarantar ne shine take so ta fada Masa wani Abu game dasu Zahira hakane yasa ya fasa tada motar ya fito. Yana barin jikin motar da taku biyu. Motar ta Kama da wuta. ....... *Wlh Haka Naseer ya tsallaka rijiya da baya da ya Bata lokaci wajen fitowa daga motar da yanzu sai dai wani bashi ba* [6/26, 3:37 PM] +234 803 635 0240: *NAGA TA KAINA* *NA SADNAF*🌸🌸 ®️ *_PURE MOMENT OF LIFE WRITERS_* _{We Don't just entertain nd educate we also touch the heat of readers P.M.L}💪🏻_ *Free Novel* *Page 23* Cikin fad'uwar gaba Naseer ya juya da Sauri Yana sallati daya ga yanda Motar ke ci da wuta mutane masu wucewa kuwa sai Sallati suke Dan wasu sun ma dauka da mutane a ciki. Naseer kamar Wanda aka dasa shi Haka ya daskare a wajen sabida shock jikinsa sai rawa yake. Da yanzu fa Yana cikin motar dake ci da wuta Kamar an watsa fetur. Sai a lokacin ya tuna wata ce ta yafito shi daga bakin makaranta tana sanye da fararen Kaya Da Sauri ya juya ya kalli bakin makaranta yaga ba ga matar data kirashi ba sai Mallamai maza biyu dake nufo Inda suke cikin turanci suna ihun konewar da motarsa keyi Tuni mutane suka zagayeshi suka fara Masa barka da arziki wasu kuwa cewa suke Mai ya haddasa hakan motar ita kadai ta Kama da wuta. Naseer Da har a lokacin jikinsa Bai daina rawa ba most especially dayaga yanda Motar ke taci da wuta. Makaranta ya nufa Dan yaga matar data taimaka masa ta kirashi Wanda ba Dan ta kirashi ba da yanzu Yana cikin motar. Sai dai ga mamakinsa har office din headmistress din yaje Yana tambayar ko akwai mallamar data Yi Shigar fararen Kaya tazo yau Take aka Kira duka Mallamai matan babu wacce ta saka fararen Kaya hakan kuwa ya Kara d'aurewa Naseer Kai Dan fa yaga.mace da fararen Kaya ta yafito shi Akan yazo hakane yasa ya fito daga motar. Sallati kawai yake a zuciyarsa har lokacin jikinsa na balain rawa sai shigowa ake makaranta ana kallonsa Ana Masa barka da arziki idan aka ga yanda Motar tasa ke ci. Sai daya Dan samu nutsuwa tsoron dayake ji ya Dan ragu kafin ya mik'e ya fito waje ya tari taxi ya nufi gida har lokacin jikinsa rawa yake akwai kudaden dake cikin motar da zasu Kai Dubu dari da hamsin da a lokacin kudine Mai yawa Yana so Yana sauke su Zahira ya wuce kasuwa ya Saro Kaya shi konewar motar da kudi duk Bai dameshi ba Kuma yasan ba mafarki yake ba ballantana yace idonsa Bai Gane Masa matar data Kira shi ba da fitowarsa daga motar da taku biyu motarsa ta Kama da wuta iya saninsa motarsa lafiya Lau take balle yyi tunanin Ko wani abune yasamu motar shiyasa ta Kama da wuta. Wacece matar da ta kirashi daga mota idonsa ba karya yayi Masa ba a bakin gate ya ganta ko wani Abu tagani a cikin motar shiyasa take kiransa abinan ya daure Masa kai. Ina Nan zaune jikina duk a mace na rasa Mai kemin dadi bansan ma tunanin daya Kamata nayi ba Ahaka naga Naseer ya fad'o palon a hargitse da Sauri na mik'e Ina sallati tare da tambayarsa lafiya Ina su Zahira duk na dauka ko wani abun ne ya same su. Bai cemin komai ba in Banda Zama da yayi Ya kurawa waje daya Ido ni kuwa tuni hawaye ya cikemin ido a rude na cigaba da tambayarsa lafiya na gansa Haka. A hankali ya fara bani labarin abinda ya faru dashi ya Kara da "har yanzu abinda ya daurmin Kai Bai wuce matar data kirani na fito daga motar da banganta ba da Bata kirani ba Naeema da wlh yanzu sai dai kiji labarin mutuwa ta bansan wacce Mata ce wanan ba bansani ba ko alama tagani motar zata Kama da.wuta ta kirani" Tunda Naseer ya fara bani labari jikina ke balain rawa Ina zabga Sallati hararowa kawai nake da ace Yarana hudu suna ciki da mahaifinsu fa da yanzu haka zaa kawomin labarin mutuwarsu Allah ya kiyaye. Sosai na ringa tsoron darsa wani tunanin a Raina ba Kuma nasan na danganta konewar motarsa da wani Abu duk da idan Ina tuna irin mafarkan danake yi hankalina Kan tashi wani zubin har sai ya kaini ga yin sadaka. Boye tashin hankalina nayi na fara kwantarwa da Naseer hankali akan kila dai ba wacce ya gani idonsa ne anan Kuma yayi ta min musu Akan shi mace Mai sanye da fararen Kaya ce ta kirashi ya fito daga motarsa shi damuwarsa Bai wuce yasan wacece matar ba shi konewar motar ba damuwarsa bace tunda Alhamdulillah lokacin Motocin hawansa sun Kai hudu duk da asara ko Yaya take Bata da dadi. Nidai dak'yar na samu ya Dan nutsu take kuma Naga ya ware sai da ya sake wanka abincin Dana samu na girka.na Rana da duk ba a nutse ba sabida tashin hankali da nake ciki da fargaba tsinuwar da Umma tayiwa Naseer ne ya hau dawomin ya tsayamin a rai bandai Bari Naseer yasan halin danake ciki ba har yaci abinci ya sake ficewa akan zai d'auko su Zahira tunda lokacin sun tashi yacemin Yana saukesu a k'ofar gida zai wuce Kasuwa kwana biyu Bai ma lek'a su Lukman ba har yake cemin gwara ma ya saka gidan Haya tunda ba kowa a gidan ko da Allah yasa Umma ta yafe Masa ta dawo sai ya Bata gidansa na kasan layin mu daya Gama ginawa karshen kad'an ne. Addua na Masa ya fice Ni kuwa na zauna cikin damuwa da fargaba Anya shirun Nan da Umma tayi na lafiya ne tun sanin Dana yiwa Umma daga aurena da Naseer zuwa yanzu bata taba share mu Haka har tsawon shekara biyu ba duk da nasan fushi tayi naso ta dawo ko ta Bari Naseer ya ganta ayi wacce zaayi na samu nutsuwa zuciya amma shariyar nan data Mana na damuna Ina fargabar abinda zaije ya dawo ya kawai motar Naseer zata Kama da wuta batare da wani dalili ba wacce Mata ce ta Kira Naseer sabida Kar ya kone Allah ubangiji ya tsaremu daga duk wani masifar da zata tunkaromu idan Yana cikin kaddararmu Allah ya bamu ikon cinyewa. Sallah ma kasa tashi nayi nayi sai da naji sallamarsu Zahira naji hankalina ya Dan kwanta a Raina kuwa na Kara yiwa Naseer addua kariya daga sharrin karfe da komai ma Dan a wani motar ya Kara fita. Naseer kuwa tuni ya ware ya danganta konewar motar da kila wani abune ya samu engine din yayi zafi shi yasa ya Kama da wuta abinda kawai ya tsaya.masa a Rai Bai wuce matar data kirashi da yake tunanin Anya kuwa ma mutum ce. Isarsa kasuwa da yawan mutanen dake San siyayya yasa ya manta da abinda ya same shi a ranar yayi cinikin da zai iya cewa ya Dade baiyi ba Dan Haka akayita tururuwa a shagonsa ahaka ma akwai yaransa biyu. Dake Taya shi Sallama sauran shaguna biyun ma akwai wayanda ke rik'e dasu. Irin cinikin da yayi da ribar daya samu yasa yayi ta Godewa Allah Dan a ribar ma ya kusa hada kudin motar daya yi a asararsa. Duk yanda yaso zuwa gadon kayar Bai samu zuwa ba sabida yanda kansa ya dau zafi sai karfe Tara ya koma gida agajiye. Yana komawa gida abinci kawai ci yayi wanka ya shige daki. Ya bar Naeema dasu Zahira a Palo tana duba home work dinsu. Sai da Naseer ya dawo gidan hankalina ya kwanta duk da kasan zuciyata cike take da fargabar Mai zai Kara faruwa. Sosai naji inaso na Kara yiwa Naseer maganar zuwa Calabar wajen Umma ko Allah zai saka ya ganta ya nemi yafiyarta. Sai da su Zahira suka gama home work na raka su daki suka kwanta na tofesu da Addu'a na kashe duk wani electric fanka kawai na bar musu a kunne na ja musu k'ofar na koma d'akina. A kan Sallaya na tadda Naseer a zaune da Qurani a hannunsa Yana Dan gyangyadi shigowata yasa ya bud'e ido tare da Hamma ya rufe Quranin ya mik'e Yana cemin bacci ne a idonsa kwanciya zaiyi wajen karfe daya ko biyu na tashe shi akwai Addu'a dayake so yayi. Toh kawai nace Masa ya Kwanta na shige bandaki na daura alwala nayi shafai na dau carbina nayita istigifari Ina yiwa Annabi Sallati bansan adadin danayi ba sai da naji idona ya fara yaji na ajiye carbin na maida kaina nayi Sujadda nayita rokon Allah Ina adduar Kariyarsa a garemu bansan Mai yasa nake Jin tsoro ba bansan Mai yasa kalmomin Umma Mai nauyi ga Naseer ke dawomin ba tamkar a lokacin take fada Masa Haka nakejinsa a kaina. Wajen Sha daya da rabbi na shafa na hau Kan gado Dan Nima tuni naji idona ya cika da bacci. Daga kwanciya ta na hau mafarkai marasa Kan gado Ina ta mafarki da Naseer sai Dana farka ya Kai sau uku Ina komawa Wajen biyu da rabbi na fara mafarkin d'akinsu Zahira naci da wuta yarana nata ihun Kiran sunana. A firgice na tashi Ina sallati aikuwa sai na jiyo kauri bansan lokacin Dana duro daga Kan gado.ina kwalawa Naseer kira da ya.tashi a firgice Sabida Kiran Dana Masa ba. Ihu na saka a.lokacin Dana fita Naga hayaki ya cike palon wuta nacin labulen palon Wanda da ace ya Kai ceiling gidan gabadaya xai Kama da wuta. Tashin hankali yasa nayita zunduma ihu tare da daskarewa waje daya nama Shiga d'akin yarana na duba na kasa. Ina kallon Naseer da shima jikinsa ke rawa Yana sintiri daga kitchen zuwa palo Yana d'ebo ruwa Yana watsawa labulen bakinsa d'auke da sallati cikin Ikon Allah kuwa wutar ta mutu. Ya saki wani irin ajiyar zuciya ya juyo Yana kallona Ni kuwa tuni nayi zurfi a tunanin Mai ke faruwa damune Mai wutan Nan danake ta gani a.mafarki ke nufi Innalillahi wa Inna ilaihi rajiun. "Naeema Mai kuka Bari a kunne ne da baki kashe ba"? Maganar Naseer ya dawo Dani hankalina bance masa komai ba na nufi d'akin yarana Dan na duba lafiyarsu. Dukansu baccinsu suke cikin kwanciyar hankali Ni kuwa na Shiga d'akin na zauna a kasa tare da zabga tagumi Ina tunanin dazu yanda muka so yin gobara Allah ya Kare gashi yanzu ma labule naci da.wuta bansan daga Ina wutan yazo ba Dan Ni na tabbata ban bar komai a kunne ba ga motar Naseer shima da Haka kawai ya Kama ci da.wuta Anya kuwa. Naseer naso yiwa magana Amma bansan na daga Masa Hankali inaso ya Gane da kansa Akwai matsala Dan Ni nasan akwai matsala. Naseer kuwa ganin naki kulashi nayi zurfi a tunani yasa hau min fadan nayi sakaci na bar fitilu a kunne an kawo wuta Mai k'arfi hakane yasa bulb fashewa Dan gashi can bulb wajen biyune suka fashe. Bance masa komai ba ya gama fadansa ya fita Ni kuwa Yana fita na fara kuka a boye bansan.mai yasa nakejin tsoro ba bansan Mai yasa nakeji kamar gidan Nan na iya kamawa da wuta ba tunda har nayi mafarkin wutan har sau biyu. Ban iya komawa bacci ba sai danaji Ana Kiran Sallah asuba na fito daga d'akin na koma.dakina na daura alwala Naseer ya tafi massallaci. Duk jikina ba kwari Haka nayi ayyukana yanda na Saba gabana na balain fad'uwa. Ina ta addua a Zuciyata. Su Zahira sun Gama Shirin makaranta na Shiga d'aki Dan na gayawa Naseer sun Gama a bakin kofa muka hadu ya shirya shima Suna shirin fita waje Naseer ya juyo Yana min fadan na ringa kiyaye kunna su heater tunda kamar wutar Mai k'arfi suke kawowa. Bance Masa komai ba Dan bazai Gane tunanin da nake ba. Sallama mukaji ana kwadawa da k'arfi Kafin ma Naseer ya amsa an fado palon a hargitse Lukman ne da danladi jkinsu na ta rawa Tuni.naji gabana ya tsinke kfin ma suyi.magana na fara Jan innalillahi wa Inna ilaihi Lukman kuwa cikin tashin hankali ya hau magana Yana "Yallabai gidanka da shagonka duk sun Kama da wuta an Shiga sallar asuba kafin a fito daga Massallaci gidan ya Kama da wuta har shagunan babu yanda mak'ota basuyi ba Dan a kashe wlh Yallabai an kasa kashewa har yanzu gidan ci yake abinda ya daga Mana hankali wlh bai wuce yanda aka rasa sanin Mai ya haddasa gobaran"? Dagani har Naseer sallati muke cikin tashin hankali Naseer kuwa cewa yake "gida da shaguna na uku duk sun kone kake nufi Innalillahi wa Inna ilaihi rajiun". Ni kuwa zubewa kawai nayi a kasa Ina Dora hannu a ka tare da fashewa da kuka. Naseer kuwa sallatin kawai yake Yama kasa motsi. Sai Lukman ne yace ya Kamata suje ya gani. Haka kuwa akayi Naseer ya bi bayansu duk a hargitse cikin tashin hankali suna Isa unguwar aka yo kansa Ana Masa jaje kowa na labarin yanda wuta ta Kama gidan da yanda aka so kashewa Taki mutuwa the more ma aka so kashewa da the more ya Kama da wuta kamar Ana zuba petur. Maganar Umma ne ya Fado Masa a Rai " Naseer idan dai Ni na tsugunna na Haifeka Sai ka tagayyara Naseer sai ga tashin hankali da ifitilai rayuwa" Hawaye ne suka zubo Masa Bai ma kalli wayanda ke ta Masa magana ba ya shige motarsa ya koma gida wanda ikon Allah ne kawai ya maidashi gida sabida bama ganin gabansa yake sosai ba. Tunda nake a rayuwata bantaba ganin Naseer a cikin irin tashin hankali Dana ganshi a ciki ba tunda suka fita nake kuka Shigowarsa yasani mik'ewa Bai kalleni ba ya Shiga d'aki nabisa a guje A tsakiyar d'akin ya tsaya hawaye na cigaba da zubo Masa Ni kuwa na hau tambayarsa komai na gidan da shagon ya kone dagaske. Idonsa a rufe yace "Naeema na fara ganin tashin hankali da ifitilai rayuwa Naeema maganar Umma na neman tabbata a kaina Naeema kinsan yawan dukiyar dake shaguna ukun nan kuwa Naeema kinsan dukiyar Dana rasa kuwa ?Naeema jiya motata ta Kama da wuta yau Kuma gidana da shaguna uku shima ya Kama da wuta jiya gidanan ma Allah ne ya rufa Mana asiri sai da labulen palo ya Kama Naeema na Shiga uku Naeema a Ina zanga Umma Naeema wayasan Mai zai faru a gaba idan ban ga Umma ba nashiga uku Naeema Allahuma ajirni fi musibati wa aklifnin khairin minha" Kuka Naseer keyi sosai Nima Ina kukan gabadaya ma Ni tsoron gidan nake Ina ganin kamar gidan na iya kamawa da wuta Sallamar da ake tayi ne yasa na lek'a palon Naga Tijjani ne kanin Naseer da Sauri na dawo d'akin na fadawa Naseer. Ya kuwa fito da Sauri Tijjani kuwa jajen abinda ya faru ya hau mishi Inda yake ce Masa baya Nan ne yau ma ya dawo daga Lagos Saro Kaya yace Bari ya lek'o sa shine yaga abinda ya faru Dayake shima tijjanin tunda Naseer ya bashi jari Allah ya dafa Masa daga shagon provision ya sake bud'e wani Yana siyar da atamfofi da shadodi yanzu Haka ma har ya samu matar da zai aura saura sati biyu bikinsa. Naseer hannayensa ya ruk'o Yana "Tijjani ka taimaka min ka gayamin a Ina Zan ga Umma nemanta nake Tijjani inata zuwa bana ganinta"? Cikin mamaki Tijjani yace Masa "Umma Kuma ai Umma Naga tana garin Nan Mai ke faruwa ne kana nufin baka San Inda ta koma ba" Damke Masa hannu Naseer yayi Yana kaini wajenta Tijjani ka taimaka min na Mata laifi na nemi yafiyarta. Tijjani tambayoyi kawai yake Masa akan Mai ke faruwa ne Naseer kuwa hannunsa kawai yake.ja Suka Shiga cikin motar sai Tijjani ne ya karbi tukun motar suka dau hanyar gwammaja. A wani karamin gida Tijjani yayi parking Suka fito suka Shiga ciki Naseer burinsa kawai yaga Umma. A karamin Palo da Tijjani ya Shiga suka ga Umma a zaune tana jijiga kafa Ido kawai ta zubawa Nas eer daya zub'e tun daga bakin kofa ya fara kuka........ "*NAGA TA KAINA* *NA SADNAF*🌸🌸 ®️ *_PURE MOMENT OF LIFE WRITERS_* _{We Don't just entertain nd educate we also touch the heat of readers P.M.L}💪🏻_ *Free Novel* *Page 24* Wani irin murmushi kawai Umma keyi tana cigaba da jijjiga kafarta Naseer kuwa ya Shiga palon da rarrafe Yana "Umma kiyiwa girman Allah ki yafemin Umma nabi Allah nabiki ki taimaka min ki sakamin albarka a rayuwata Umma nayi nadamr k'in bin umarninki Umma Dan Allah ki yafemin" ",Waccece ummanka? Ina ka baro Naeema Ni asuwa dazan saka maka albarka Naseer Ni ai ba komai bace a wajenka ai Naeema Uwarka ce Kuma matarka Kuma rayuwarka da idan kuka rabu mutuwa zakayi Naseer ai ba abinda kayimin Banga dalilin da zai saka kazo kana neman yafiyata ba kaga Dana nan" Tace tana nuna Tijjani Shi na sani sai su Safiyya Kai na Dade da Sallama ka na dade da barwa Naeema Kai banida wani had'i da Kai Naseer ka daina batawa kanka lokaci ka tashi ka tafi" "Wai me ke faruwane Umma"? Tijjani yace cikin rashin fahimtar abinda ke faruwa Sam bai San abinda ke faruwa ba ya dai San Umma Bata San Naeema haka ma kannensa shi dai ba ruwansa da tsanar da suka Mata shi irin mutanen Nan ne da Bai fiye Shiga abinda Bai shafeshi ba" "Mai ka Mata ne Yaya Naseer"? "Ba abinda ya Shafeka Babu Kuma ruwanka idan ba kana San b'acin Raina ba uban waye yace ma ka kawo min shi gida"? "Umma Mai yayi zafi Haka Yaya Naseer ne fa'? Tsaki Hajara tayi ta d'auke kanta tana cigaba da jijjiga kafarta. Naseer kuwa ya cigaba da magiya Yana "wlh Umma yanzu Zan bi umarninki a gabanki Zan rubuta takarda ki aiki Tijjani ya Kai Mata Amma Dan Allah ki yafemin ki janye kalamanki Umma na fara ganin masifa tun ba'aje koina ba Umma ki tausayamin" Wani irin kallo Hajara tayiwa Naseer ta mik'e cikin wani irin B'acin Rai ta Isa wajen da Naseer ke zub'e akan gwiwarsa "Sai a yanzu Dana rufe babinka na sallamaka zaka cemin zaka bi umarnina sai da ka fara ganin masifa zaka bi umarnina toh ka makara Naseer ko ka rubuta ko baka rubuta ba babu abinda ya shafeni kudin da kake dashi yasa kake Jin Kai wani ne bazaka iya bin umarnina ba ka fifita mace Naseer a kaina Sabida matarka ka daga hannu ka Mareni" Wani irin jijjiga Kai Umma tayi cikin fushi ta cigaba da Magana tana "kaci Sa'a Kai Dana ne Ni na Haifeka Naseer da ace wani ne ya mareni da yanzu sai dai ayi labarinsa Bazan janye kalmata ba Naseer da sai da kaga alamar masifa na tunkaroka ka taho wajena wlh baka ga komai ba Naseer" "Haba umma wane irin magana ne wanan haba Umma Naseer Bai cancanci Haka daga wajenki ba karki manta fa duk abinda kike takama dashi daga ke har mu shine fa ko gidanan da Kika siya Umma da kudinsa ne yau idan kina jifansa da irin kalaman Nan ya Shiga cikin masifa ai muma sai ya shafemu" "Kayimin Shiru Tijjani wlh Kai ma Zan maka baki Dan ubanka kayimin Shiru idan Kai ma Marin nawa zakayi kamar yanda ya mareni zaka iya matsowa ka Mareni da kake cewa shine rufin asirinmu Dan ubanka yanzu a gidansa nake zaune ko shi yake bamu abinda muke ci yaje can ya rik'e arzikinsa ya zauna da matarsa ban rokesa ya Kara min komai ba bana bukatar komai nasa yaje can ya karata" "Umma Dan Allah Dan Annabi kiyi hakuri ki yafemin Tijjani Dan Allah Tayani Bata hakuri wlh Zan saki Naeema yanzu indai haka zai saka ta yafemin ta janye kalamnta akaina" Wani irin kallo Umma ta jefashi dashi taja Tsaki ta shige d'akinta. Naseer kuwa ya cigaba da kuka Yana Tijjani ya taimakeshi Tijjani kuwa cikin b'acin Rai yace "Mai kayi Mata da Zan Bata hakuri sabida me Zan Bata hakuri Dan Allah Yaya ka tashi kayi tafiyarka Umma Haka halinta yake duk da bansan Mai asalin abinda ya faru ba Ni nasan laifinta ne Kai Kuma kuskuren da kayi da ka Mareta Amma ka tashi kayi tafiyarka insha Allahu babu abinda zai sameka karka sake ka danganta abinda ya sameka da ko bakinta ne arzikin Nan waye ya baka"? "Allah" Naseer yace Yana Jan majina Toh kasa a ranka zai iya karba Dan ya jarrabceka yaga ya zakayi Dan shagonka da gidanka.ya kone bashi yake nufin Wai Dan Umma na fushi dakai Dan ko dan ta maka kalamai ne marasa dadi ko mu Nan Bata barmu ba idan muka Bata Mata Rai kamar ta Mana baki har tanayi din ma ka daina wahalar da kanka ka tashi kaje kawai" Tijjani "naji duk Mai kace burina kawai tace ta yafemin ko Zan samu nutsuwa a Raina" Haka Naseer yaje bakin kofa d'akin Hajara Yana ta kuka da magiya Inda b'acin Rai ma yasa Tijjani ya ficewarsa ya bar sa a wajen Ahaka Safiyya da ta fita yawon gantali ta dawo ta tarar dashi Tana ganin Naseer ta Shiga da Sauri Dan har ga Allah Naseer na ranta daga canjin rayuwar ma kawai da suka samu da basa komai waja waja tunda Umma ta dawo gwammaja ta siyi karamin gida yasa takeso taga Naseer ko ta San halin da yake ciki. Ummansu Bata tab'a kudurta mugayen Abubuwa data Sha alwashin samun cikar burinta ba sai Akan Naseer har rokonta tayi akan ta yafewa Naseer ta kashe Naeema tak'i sosai ta fusata da ko maganar Naseer din Bata so ayi Mata Ita dai tasan sun Cutu Kuma suna Kan cutuwa dan badan Tijjani shima Yana musu abubuwa ba da abinda xasu saka a bakinsu sai ya gaggaresu Lami kuwa Tana Calabar abinta tak'i ma zuwa kanon a satin Nan ma take cewa ta samu wani zai Aureta zasu zo wajen Umma ta Kai su wajen dangin babansu Dan ba saninsu sukayi ba Da Sauri ta Shiga palon tana Yaya lafiya naganka Haka"? "Dan Allah ki Tayani bawa Umma hakuri nayi nadamar abinda nayi Mata Kuma wlh yanzu a shirye nake Dana bi umarninta Safiyya jiya motana ya konne yau Kuma gidana na goron dutse da shaguna ukun.ya kone kurmus kinsan kuwa yawan dukiyar danayi asararsa kuwa Safiyya ki taimaka ki bawa Umma hakuri Ina tsoron bakin umma ya kamani" Tunda yace gidansa na goron dutse ya kone Safiyya ta zaro Ido waje tana Kara tuno girman gidan da shagunan Naseer uku dake cike da.kaya. Sosai hankalinta ya tashi itama ta hau bubuga kofar d'akin tunda ta nunawa Umma tana tausayin Naseer Bata San wani Abu ya sameshi Umma ta fara Mata boye boye ba komai ta sani ba yanzu game da.umma Umma yanzu ta kara canjawa tundaga lokacin da suka baro gidan Naseer Amma daga abinda Naseer yace yanzu yasa ta fara zargin tabbas da saka hannun Umma a konewar gidan Naseer da motarsa "Umma Dan Allah ki bud'e k'ofar nan haba Umma ke yanzu Sabida Wata Naeema Zaki juyawa Yaya Naseer baya yanzu bakisan Haka Naeema keso ba Dan Allah kifito ki saurari Yaya" "Safiyya" Naam Saffiya Naam "Wlh ranki zaiyi mumunnan b'aci inkika Kara Shiga maganar Nan babu ruwanki ku kyalleni Naseer ya fice ya barmin gida Dan wlh idan Bai fita ba Zan Kara Masa wani bakin na barwa Naeema shi ya dauka karya nake ko? ya d'auka duk rantsuwar da nayi akansa zai tashi a banza ne ko? Ya tun Bai fara ma.ganin komai ba zai zo neman yafiyata ai Bai ga komai ba ba dai Naeema ya zaba a kaina ba" "Umma kiyiwa Allah ki yafemin Umma Allah ma muna Masa laifi mu nemi yafiyarsa ya yafe mana Umma nasan nayi kuskure Dan Allah ki yafemin" "Tashi ka fitar min daga gida Naseer idan na fito daga d'akin Nan kalmar da Zan maka sai yafi wancan Muni" Naseer da Sauri ya mik'e yayi waje Safiyya cikin Sanyi jiki tabi bayansa tana bashi hakuri. Har wani jiri Naseer keji Tijjani kuwa a halin daya ganshi yasa ya taso ya karbi mukullin motar yaja suka nufi sharada. Tijjani sai bashi baki yake Yana rantsuwar Bazai dau abinda umma ke Masa ba shi idan ma Umma zata takura masa.wlh bar Mata garin zaiyi ya siyar da komai nasa ya koma wani garin ya daina wani damun kansa ya shareta. Naseer Bai iya magana ba har Suka iso gidan Tijjani ya sauka ya Masa Sallama akan zai Kara lekoshi idan ya samu lokaci Dan ya kwantarwa da Naseer hankali yace Masa idan Umma ta sauko zai Bata baki. Godiya Naseer ya Masa bayan tafiyar tijjani sai daya Dade a mota tunanin Asarar dayayi ya balain tsaya Masa a Rai. Yama rasa tunanin da zaiyi. Jiki ba kwari ya fito daga motar ya nufi cikin gidan. A bakin kofar palon ya tsaya Yana kallon Naeema data zauna a 3 seater da uban akwatuna taci hijab ga su Zahira suma a Gefen ta Suma ta shiryasu Kallonta kawai yake Yana Jin wani iri a zuciyarsa da alama Naeema bama ta San da shigowar shi ba sabida zurfin da tayi a tunani lokaci lokaci takan share hawayen da ya zubo Mata da hijabin jikinta. Tunda Naseer Suka fita da Tijjani nake Jin fad'uwar gaba zuciyata a balain cunkushe fargabar yanda Umma zata yiwa Naseer ya cike min zuciya ni dai nasan idan Naseer Yana San yafiyar Umma sai ya sakeni Dan nasan indai ya sakeni taga shaida zata iya yafe Masa Hakane yasa ban tsaya yaudarar kaina ko sai Naseer ya dawo naji yanda sukayi ba Dan nasan Idan dai Yana da hankali dole yabi umarnin Umma ya sakeni. Kayanmu na hada Mana tsaf nida Yarana Dan bazan tab'a iya barin yarana da Naseer ba Dan nasan Umma ko Dan ta galazamin zata so na bar yaran sabida taci zalinsu. Zan tsugunna na roki Naseer ya barni na tafi dasu garinmu na tashi Yan hayan da nake tunanin kila.mai unguwa ya zuba a gidanmu nayi zamana acan na fara neman kudin da Zan kula da yarana duk da nasan Naseer bazai barmu Haka ba zai bamu wani Abu Abu dayane yake San karyamin komai tausayin Naseer ko ya zaiyi idan ya waiga yaga bana Nan yaransa ma.haka Naseer.mutum.ne shi Mai balain San Yara Dan wani zubin idan abin ya motsa Masa d'akinsa yake tafiya da su su kwanta a gadonsa dayafi nawa girma Shi Kuma ya kwanta a doguwar kujera Ni kuwa idan Naga Haka Akan Dole Zan bisu haka na shimfida bargo na kwanta a kasa yayi ta tsokanata Yana cemin matsoraciya idan na Isa na kwana Ni kadai Mana ba sai na biyo su ba Idan Kuma Yan tsokanar na kansa idan yaran basuyi bacci ba zaice duk su tashi zaune dashi Dani wane Suka fiso Hade Rai nakeyi Dan nasan Zahira kadai ce take cewa ni tafiso su kuwa sauran duk shi suke cewa sabida yakan yaudaresu da alewa ko yayi ta musu signa da ido akan zai siyo musu kayan Wasa sabida yarinta da gudu suke cewa shi suke so Zahira kuwa komai zai Bata sai tace ita tafi San Umma hararta zaiyi tayi idan tace.haka Wanda a karshe sai ya koreta daga Kan gadon akan tazo wajena tunda tafiso na Ni kuwa sai nayita Masa gwalo Ina harararsu Nadeeya zaman mu gwanin shaawa da bamuda matsala da Umma Naseer mutum ne shi da nake fatan ya zama miji a gareni har a Aljanna sai dai k'arfi da yaji Umma kesan rabamu. Tunanin Nan danayi na irin Rayuwar Dana shimfida da mijina da yayana cikin so da Kaunar juna yasa kukan danake dannewa ya k'wacemin na Shigar da fuskata cikin hijabi na naci kukana na gode Allah kukan Zahira Dana fara ji kasa kasa yasa na Dago Na share hawayena anan idona ya fada Kan Naseer daya zubamin Ido cikin jajjayen idonsa Yana min wani irin kallo da na kasa ganewa. Mik'ewa nayi na dauki Raheema dake gefena na sab'ata a kafadata daga yanda Naga idon Naseer ya kad'a yayi ja Ni nasan ya sakeni ya kasa shigowa ne sabida Ni. Umarni na bawa su Zahira akan su tashi mu tafi Dan so nake idan naje waje na samo Mai mota yazo har k'ofar Gida na kwashi akwatunan kayanmu Kukan dake San k'wacemin nake ta dannewa Na nufi wajen da Naseer da har lokacin yakemin wani irin kallo. Cikin muryar kuka na mik'a Masa hannu Ina ya bani takarda Zan tafi banasan nayi Rana Murmushiin dayafi kuka ciwo yamin ya matsa daga bakin kofa cikin wani irin murya ya hau magana Yana "Zaki iya tafiya ke kadai ba sai kin tafarmin da yarana ba Naeema baki zabi ki gujeni ba sai da masifa ta tunkaroni Naeema baki nemi rabuwa Dani ba sai a yanzu danake cikin tsaka Mai wuya ?baki nemi na baki takarda ba sai a yanzu da nake neman Wanda Zan Dora kaina a kafadarsa ya rarrasheni shine a yau da Kika ga nayi asarar dukiyata a yau Zaki hada kayanki ki tafi Naeema" Bansan lokacin da na fashe da wani irin kukan bakin cikin fassarar da Naseer yamin ba na hau magana numfashina Kamar ya d'auke "Haba Naseer Mai yasa zaka min wanann mummunan Fassarar wlh badan Haka na had'a kayana ba Umma tace indai kana so ta yafe maka sai ka sakeni Kuma fitar da kayi Dan kaje ka nemi yafiyarta ne hakane yasa na hada kayana Naseer wlh ba dan komai haba Naseer bazan tab'a guje maka Dan ka tsinci kanka a cikin wani Hali ba" Bai cemin komai ba da ga kallon dayake min ya nuna ko kad'an maganata Bata shigeshi ba girgiza kansa kawai yayi ya nufi d'akinsa ya shige Ni kuwa na zub'e a kasa na fashe da kuka Mai ciwo. Sai danaga yarana suma suna ta kukan na daure na share hawayena na koma Kan kujera na zauna. Abincin Rana ma banyi ba Sabida tashin hankali Cabin biscuit kawai na rabawa yaran Haka nayita Zama a palon Ina tunanin Naseer zai fito ya tafi massallaci yyi sallah Magriba Amma shiru Bai fito ba. Nadeeya da Bata da juriyar yunwa ita ta fara min kukan yunwa hakane yasa na tashi na Shiga kitchen na dafa musu shinkafa tunda Ina da Miya na sati nakeyi. Gabadaya na rasa Mai kemin dadi ga wani irin tsoron gidan da nakeyi sai Naga kamar gidan zai iya kamawa da wuta na rasa Mai ke sakamin wanan tunanin Har karfe goma na dare Naseer Bai fito ba na buga Masa ko gezau baiyi ba har kuka na Masa Ina Masa rantsuwar ba Dan ya Shiga wani Hali zan tafi ba Amma duk da Haka Bai bud'e k'ofar ba. Da farko na dauka ko wani abune ya same shi sai danaji muryarsa Yana karatun Qurani hankalina ya kwanta nayiwa yarana shimfida a d'akina naje na kwantar dasu. Na buga tagumi Ina tunanin halin da muka tsinci kanmu a ciki dayake fashin sallah nake hakane yasa banyi sallah ba surorin Dana haddace a kaina kawai na ringa karantawa ko zanji sanyi a Raina. Bansan lokacin da bacci ya d'aukeni ba. A cikin baccina na fara mafarkin Wai shagunan Naseer na Sabon gari Wai Yana ta konewa Ana rik'e Naseer Wai zai Shiga ciki shagon daya ragewa Naseer kenan Umma Wai ita Kuma tana daga nesa tana ta Mana dariya tana kad'an muka gani bamu ga komai ba" A firgice na tashi da sallati jikina na balain rawa duk na hada zufa sai waige waige nake ganin ba wuta dake ci a d'akin yasa na fita da Sauri na duba Palo da kitchen Naga ba komai har store da d'akinsu Zahira. Muryar Naseer dake ta karatun Qurani dayake dare yayi muryarsa sosai yake fita daga muryarsa kawai zaka San Yana cikin damuwa. Bakin kofar naje.na tsaya nayita Kiran sunansa Amma babu alamar zai saurareni a Haka na hakura na koma d'akina Ina tunanin mafarkin da.nayi hankalina na Kara tashi bansan lokacin Dana daga hannu na fara rokon Allah Ina "Ya Allah ka Mana maganin masifar daya tunkaromu ya Allah ka dubemu da idon rahama ka tsayar Mana da Wanan masifa ya Allah Kaine masanin Sirrin sake bayyane da b'oye bamu San komai ba ya Allah mun yarda Kaine Mai bayarwa Mai Kuma karba a duk lokacin daya so ya rabbi ka bamu ikon cinye wanann jarrabawa ka bawa mijina ikon cinye wanan jarrabawa ka Kare Mana shagunan da suke rage mana ya hayyu ya qayyum" Bansan Mai yake sani tsoro da fargaba ba Ina tsoron wani Abu ya Samu shaguna ukun daya ragewa Naseer. Ina Nan zaune bacci ya Kara kwasheni cike da.mafarkai marasa.dadi. Bani na farka na sai da gari ya waye. Kukan Raheema ne ma ya tasheni. Zumbur na mike nayi waje Dan na makara k'ofar Naseer danagani a bud'e ne yasa na shiga ciki Amma baya ciki alamar ya fita banji dadin yanda Naseer yamin ba ya kamata ace yafi kowa sanin abinda zanyi da Wanda bazanyi ba. Ahaka na Shiga kitchen na samawa yarana abinda zasu ci da abinda zasu tafi dashi. Zahira kuwa har ta Tayani shirya Minal da Humaira Nadeeya itama ta iya shirya kanta. Ganin babu Mai Kai su makarantar yasa na saka hijabina na dauki naira Ashirin na rufe gidan na tare Mana taxi ya Kai mu har makarantar sai Dana ga shigarsu makarantar na Kara hawa taxi na dawo. Na sauke Raheema Dana goyata na fara aikina gyara gidan zuciyata kuwa na wajen Naseer. Naseer kuwa daga Massallaci sabon gari ya nufa jikinsa duk a mace jiya kwana yayi Yana addua Akan Allah ya Kare Masa shaguna ukun da suka rage Masa zuciyarsa kuwa sosai tayi nauyi sabida halin daya ke ciki Haka kawai yake Jin Naeema so take ta rabu dashi Sabida ifitilai data fada Masa alhalin duk ma halin da ya tsinci kansa a ciki Sabida kin sakinta da yayi ne badan Allah ya bashi dangana ba da zuciyarsa na iya bugawa ya rasa yanda zaiyi Umma ta sauko ta yafe mishi. Sabida Kar ma wani tsautsayi ya gifta duk sauke layin NEPA yayi daga shagunansa ya Kuma gayawa yaran shagonsa su ringa kula da shagon nasa sosai. Yau ma Bai hau motar tasa ba taxi ya hau Haka.kawai.ma.yake tsoron Hawa motar tasa. Wajen karfe daya na Shiga kitchen Dan na Dora Mana abincin Rana Dan karfe biyu yarana ke dawowa daga makaranta . Da yake na gama komai Zama nayi a palon Raheema na d'aga gefena tana bacci Nima sai na Dan kishigida bansan lokacin da bacci Mai nauyi ya d'aukeni ba. A cikin baccin nawa na fara mafarkin kitchen Dina ya Kama da wuta har ya fara cin ceiling din Palo. Sai ihu nake inaso na tashi na dau Raheema mu gudu Amma na kasa. A Haka Wai Naga Mahaifiyata ta shigo palon ta tsaya a bakin kofa Tana "Tashi Naeema so ake wuta ta Kama gidan kina ciki ki tashi nace ki tashi Naeema" A firgice na tashi idona cike da bacci wutan dake ci a kitchen Dina ne yasa na wartsake na rarumi raheema Ina ihu tare da yin waje da gudu Ina ihun neman taimako. Cikin Ikon Allah akwai Samarin dake gini a Gefen gidanmu da Sauri suka Shiga gidana da bokitan ruwa suka Yi ta watsawa ni kuwa sai ihu nake jikina na rawa. Suna watsa ruwan dayake suna da yawa cikin Ikon Allah wutar ta mutu duk da sun kashe wutan kasa Shiga nayi gidan nayita tsoro sai a gidan mak'ota na zauna har yarana Suka taso suka sameni a gaskiya ya zama Dole mu bar gidanan sau.uku kenan gidanan na neman yin gobara. Ahaka muka zauna har sai da Naseer ya dawo. Tun Kan ma ya Shiga cikin gidan aka hau Masa jaje Mai gidan mak'otan da muka shiga ne yacemin Naseer ya dawo. Da saurina muka fito daga gidan muka Shiga gidan mu Inda na tada Naseer a tsaye a tsakiyar palon Yana kallon yanda kitchen din yayi bakikirin har k'ofar kitchen din sabida konewar da yayi Ni kuwa cikin kuka na fara magana Ina "Naseer ya zama Dole mu bar gidanan wlh tsoro nakeji sau uku kenan muna neman yn gobara Ina yawan mafarki Ina tsoron muna ciki da tsakar dare wuta ta tashi Dan Allah Naseer mu bar gidanan ko haya ka Kama Mana" "Naeema ki daina Mana baki insha Allahu babu abinda zai Samu gidana idan bazaki Fadi alheri ba kiyi shiru Kuma Ni nasan duk sakacinki ne kila Abu Kika dora Kika manta dashi har gobara ya tashi ta Inda Naseer ke shiga ba ta Nan yake shiga ba Nidai shiru na Masa har ya Gama fadansa Tunda nake da Naseer bamu tab'a samun Sab'ani Mai tsayin wannan ba ahaka mukayi ta zama cike da fargaba yanzu kuwa ba karamin taka tsantsan nakeyi ba idan na Dora Abu akan wuta Zan iya cewa da Ido daya nake bacci Sabida fargaba Dak'yar na samu Naseer ya sauko daga fushin da ya hau.ahaka har muka samu wata biyu da gobarar da mukayi na shagonsa da gidansa. Hajaraa ke zaune a palonta Safiyya da Tijjani suna ta Bata baki akan ta yafewa Naseer Bata kulasu ba ta bawa banza ajiyarsu Tijjani kuwa ganin Haka ya mik'e Yana zai tafi sai da safe Umma.kuwa ta mik'a Masa hannu tana ya Bata Dubu ukun da ta tambayeshi.bata San iskanci ahaka tun baiyi aure ba yake neman ya ringa hanata kudi. Tijjani kuwa hannu ya zura a Aljihu ya kirga Dubu daya Yana "Sai dai kiyi hakuri da wanan wlh hidima ce a gabana badan kin dage kinyi fushi da Naseer ba da ko Dubu goma Kika tambayeshi zai baki" Tsaki tayi.ta fusge kudin daga hannunsa tana ya fice Mata daga gida Shi kuwa yayi waje Yana dariya ya rasa Gane wane irin haline da Mahaifiyarsu. Suna Nan a zaune har Sha biyun dare Safiyya ta sako Jan doguwar rigarta Hajara ma ta saka nata. Safiyya na k'ok'arin yiwa Hajara magana kawai suka ga kitchen din gidan na ci da wuta kafin su ankara har wuta ta fara cin Ceiling din kitchen din . Ihu Safiyya ga saka tayi waje. Umma.kuwa da taso tsayawa yanda wutan ya Kama ko'ina gadan gadan yasa itama tayi waje tana mamakin Mai ya haddasa Mata gobarar Nan toh Mai hakan ke nufi. Tana ji tana gani wutan ta cinye duka.gidan har da mudubinta a ciki sosai hankalinta ya tashi da konewar gidan nasu. Tsirarun mutane ne suka ringa fitowa suna Mata jaje. Safiyya kuwa cewa take "Umma Kinga abinda nake Gaya miki ko idonki ya rufe kina San ganin bayan Yaya Naseer kina so kiga ya Shiga ifitilai alhalinn kin manta da kudinsa Kika siyi gidan toh idan ma.arzkinsa konasu kikayi toh gashi Nan har gidan da Kika siya da kudinsa ya kone Umma Bata iya cewa komai ba ahaka har gari ya Dan fara wayewa makotansu sai ce musu suke su shigo daga ciki gidansu Amma fir Umma Taki kallon gidan kawai take daya ruguje katakwaye naci. Wajen karfe shidda na safe Tijjani ya taho wajensu a guje kafa ba takalmi duk ya hargitse hajara kuwa ta d'auka labarin konewar gidanta ne.ya je.masa sai dai kalmar daya fito daga bakinsa ne ya kusa sata suman wucen gadi Agabnta Tijjani ya zub'e Yana "Umma shaguna na duk sun kone haka kawai wuta ta tashi da tsakar dare na Shiga uku Umma komai nawa Yana cikin shagon. Ko biyar ban tsira dashi ba Innalillahi wa Inna ilaihi rajiun Tijjani yace Yana hawaye. Safiyya kuwa ta daka tsalle cikin tashin hankali tana asirinmu ya tonu Umma kin jawo Mana.........[6/26, 3:37 PM] +234 803 635 0240: *NAGA TA KAINA* *NA SADNAF*🌸🌸 ®️ *_PURE MOMENT OF LIFE WRITERS_* _{We Don't just entertain nd educate we also touch the heat of readers P.M.L}💪🏻_ *Free Novel* *Page 25* Wani irin fusga Hajara tayiwa Tijjani cikin tashin hankali tana "Kana da hankali kuwa ko mafarki kake tayaya shagonka zasu Kama da wuta abinda ya rage mana kenan fa da Kai na dogara fa na Shiga uku Ni Hajara Mai ke Shirin faruwa Dani Banda Tijjani fa nace" "Kikace me Umma zargina ya tabbata Umma wlh kina da hannu a konewar shagon Yaya Naseer da gidansa da motarsa Umma ,Umma sai danace Miki karkiyi Haka Naeema ce ta Miki laifi ba Yaya Naseer ba Umma karki ce min duk dukiyar Yaya Kika k'ona Ni nasan tunda Kika fara min boye boye nasan akwai abinda kike kulawa toh ga irinta Nan idan ma.da Yaya Tijjani kika dogara toh shima shagunansa ya kone tunda Yaya Naseer ne ya basa kudin" Hannu Hajara ta D'ora akanta tayi zaman dirshan akasa. Tijjani kuwa cikin rashin fahimta ya kalli Safiyya Yana "Bangane ba Wai Mai kike nufi ne Umma ce tayi wani Abu Dan arzkiin Yaya Naseer ya k'one ko me"? Hajara ido ta hau kiftawa Safiyya. Safiyya dake cike da balain haushin Hajara kau da.kanta tayi ta hau bawa Tijjani labarin duk abinda ya faru ta Kara da "tun Akan hanya nake Bata hakuri tana rantsemin sai Naseer ya talauce ya tsiyace yyi bara Naga dai idan ya talauce ya tsiyace muma sai ya shafemu data ga alamar bana goyon bayanta shine ta daina min maganar Ni dai daga abinda ya faru wlh nasan Umma ce silar komai.ta Kona arzkin Yaya Naseer a kungiya" "Wane kungiya.kuma Mai nake ji Haka Innalillahi wa Inna ilaihi rajiun Ashe dai maganganun da ake Yi akanku gaske ne kenan Safiyya? Safiyya sai a lokacin ta tuna Tijjani baisan duk suna cikin kungiya ba "Umma Ashe dagaske ne labarin da nake ji a Calabar kina cikin kungiya Umma yanzu Sabida rufewar ido da Baki samu yanda kikeso ba Kika k'ona dukiyar Yaya Naseer?Umma.ina tunaninki ya tafi Umma karki manta fa duk abinda kike takama dashi daga ke har mu wlh shine toh shikenan ai kin huta kin zama silar da na rasa komai nawa yanzu kowa sai yayi ta kansa dan wlh banida shi bazaki Sakani sata ba ko me Naseer yayi miki Bai Kamata kiyi Masa Haka ba Dan kawai yak'i rabuwa da matarsa" "Marina fa yayi Tijjani Marina yayi Akan Matarsa har Ni Ina mahaifiyarsa ya daga hannu ya mareni"? "Haka kawai ya mareki ba shake Masa Mata kikayi ba kina neman kasheta Kuma Naga Yana ta baki hakuri akan Bai San ya mareki ba Amma duk da Haka shine Kika k'ona dukiyarsa toh sai ku nemi gidan Zama ai tunda kunsan nima a shago nake zaune Allah Kuma ya shiryeku ya sa ku Gane gaskiya " Daga Haka ya fara k'ok'arin juyawa Safiyya ta tsayar dashi da Sauri tana "Yaya ka taimaka.mana da kudin mota komai namu ya kone fa" Wani irin kallo ya wurga Mata yaja Tsaki ya tafi Safiyya ta juyo a fusace ta kalli Hajara tana "Sai kisan yanda Zaki damu ai" Safiyya Shugaba bata min adalci ba wlh ba Haka mukayi da ita ba" "Ahap kenan kece Kika k'ona dukiyar Yaya Naseer Umma" "Aaa na dai fada Mata inaso ya Sha wahala rayuwa idan kudi ne ma yasa Naeema taki rabuwa dashi ya rasa kudin Tijjani shi Kuma yayi kudin tace na bar Mata komai a hannunta bansan Haka abubuwa zai kasance ba" "Duk wannan balai ke Kika sakamu a ciki Umma Naeema ya Kamata ta Sha wahala ba Naseer ba Naeema ce take ja dake Kuma duk tsawon lokacin Nan kin kasa komai a kanta Haka kawai muna zaune kin janyo Mana balai rufin asirinmu daya shine gidanmu na Calabar da asirinmu ya tonu. Mik'ewa Hajara tayi tana yanzu Bari na nemo Mana kudin mota a mak'ota mu samu mu tafi daga baya ma san abinyi" Daga haka Hajara ta nufi gidan mak'ota sai data shiga gida.hudu Bata samu ba sai a gida na biyar ta samu kudin. Ahaka suka.nufi tasha daga su sai rigar.jikinsu Safiyya kuwa sai Masifa take Hajara kuwa Bata ce komai ba Dan tayi nisa a tunani. Da yamma Likis Suka Isa Calabar sai dai da isarsu Suka sake tarar da wani sabon tashin hankali gidan da Naseer ya bar musu katoto naci da wuta mutane sun zagaye gidan suna ta watsa ruwa. Hajara jiki na rawa suka fito daga motar aikuwa ganin yanda wuta keci yasa ta cire zaninta ta fara kurma ihu tana a taimaka Mata Dan karamin gidan Naseer ma ta siyar dashi tuntuni. Ihu take sosai Safiyya kuwa ta Dora hannu aka itama tana zunduma ihun Mutane sai basu baki suke suna Haka kawai suka ga gidan ya Kama da wuta Hajara Kamar tayi karamin hauka.har wani rukota ake tana fusgewa Bata tab'a tunanin Abubuwa zasu juye Mata Haka ba Bata kawo Abinda tayiwa Naseer zai shafeta Haka ba ta d'auka shi da Naeema ne kawai zai shafa Tijjani shi Kuma ya cigaba da kula dasu sai gashi tun ba'aje koina ba komai ya juye. Allah Allah kawai take dare yayi ta nausa daji wajen shugabarsu. Safiyya kuwa ce wa take ta cucesu. Dayake An Dan San Hajaran acan hakane yasa ta samu wayanda suka dan taimaka Mata da wajen zama na Dan lokaci kafin su san abin Yi. Sosai Hajara taci kukan yanda abubuwa Suka juye tsanar Naeema na Kara sab'untuwa a ranta Dan gani take duk ita taja Mata wanan masifar Karfe Sha biyun dare ta fito daga gidan mutane Safiyya kuwa Taki binta sabida takaici. Tana Shiga daji ta fara yarensu na tsafi. Sai data Dade tanayi kafin shugabarsu ta bayyana a gabanta da fitilar kwai ranta balain b'ace Bata Bari ma Hajara tayi Magana ba ta hau magana tana "mun cireki daga kungiya mun karbe karfinmu sabida kinyi sakacin da mudubinmu ya kone Dan Haka Abu daya kawai zan iya Miki shine idan wani Abu ya taso miki.ki zo ki fada min Zan Yi iya k'ok'arina ki samu cikar burinki ita Kuma matar danki yak'i ne tsakanina da ita Ina dab da samun cikar burina akanta ki juya ki tafi Hajara abinda kikeso na Miki ba Abunda Kuma Zan iya Yi akai" Daga Haka ta b'ace Bata Bari ma Hajara tayi Magana ba. Haka Hajara ta Kara dawowa tana rizgar kuka. Sosai zuciyarta ta Kara taurara da mugayen alwashi duk akan Naeema da Bata ji ba Bata gani ba Safiyya Kamar ta rufe Hajara da duka Dan gani take duk ita taja musu wanan masifar. Hajara kuwa Bata ita take ba abinyi kawai take tunani "Nidai Umma Ina Samu kudin mota wlh gidan Yaya Naseer Zan koma can Kano Dan shine dai gatanmu a yaushe zamu cigaba da zama a gidan mutane nasan ai Yana da Dan sauran Canji "Bashida wani sauran Canji Safiyya lokaci kalilan ne shima zai dawo Kamar mu gwara mu Kara sanin abinyi Umma wlh kin cucemu yanzu har yaushe zamu cigaba da zama a gidan mutane wlh komawa Kano ya Kama mu Dole Yaya Naseer da yaya Tijjani su San yanda zasuyi damu" Naeema Daga Ni har Naseer sosai muka dage da Addu'a Dan har lokacin ban fasa mafarkai ba Haka Kuma karamin Abu sai Naga kamar gidanmu zaiyi gobara yawan damun Naseer da nake da maganar yasa muke samun Sab'ani hakane yasa na daina Gaya masa.mfarkin da nake idan nayi kawai na tashi washegari Zan danyi sadaka. A haka watarana da bazan tab'a mantawa ba bayan an iddar da sallah asuba Naseer ya dawo da wuri yacemin bacci yake ji ya kwanta Nan da Nan bacci yayi awon gaba dashi Nima Haka kawai naji bacci na cin idona Akan Sallaya baccin ya kwasheni. Kamar a mafarki naji mutane a waje suna ihun wuta wuta wuta. Amma abin mamaki na kasa bud'e idona sabida nauyi. Sallatin Naseer kawai naji da k'arfi Yana Innalillahi wa Inna ilaihi rajiun. Dak'yar na bud'e idona Naga hayaki ya cika Mana daki na mike da balain sauri Ina sallati jikina na rawa Dan dakinmu ma ya fara ci da.wuta. Naseer kuwa window ya bud'e ya fita aguje ya Shiga d'akin yarana da Suma bacci Mai nauyi ya daukesu. Duk su ukun Haka ya rungumosu a kirjinsa Zahira na kamkame da hannunsa sai sallati take Zahira na ihu Ni kuwa numfashina ne ya ringa k'ok'arin daukewa sabida tashin hankali Kamar an Dasani na kasa motsi Ahaka Naseer ya zura yarana ta window Yana ta min magana Dan ba Inda Bai Kama ba har k'ofar dakin Inda nake tsaye kawai da gadon ne Bai Kama da wuta ba. Yana zura Raheema ceiling ya fado Kan katifar d'akin Cikin zafin nama ya duro daga Kan gadon ya kama.hannuna Dan bbu ta Inda xamu fita sai ta window ahaka ya kamani ya zurani ta window Dan lokacin window ba Mai burgular bane wani ne Mai guda biyu haka Ana bud'ewa mutanen d'a zasu iya gane window. Har lokacin ban dawo cikin hankalina ba Yana durowa shima.kwanu da ceiling din suka ruguzo mutane kuwa da suka kewaye gidan Suka zo suka ja hannun Naseer da ya ji ciwo a hannu. Suna barin wajen Gidan ya fara wani irin rugujewa wuta na tashi kamar an watsa fetur. Motocin Naseer guda uku da komai.namu.muna ji muna gani Suka kone har lokacin bansan Inda hankalina yake ba Naseer kuwa sai Sallati yake hawaye na zubo Masa zuwa yanzu yasan mahaifiyarsa ce silar komai dake faruwa dashi. A gidan makotanmu aka Kai mu dasu Zahira. Inda aka ringa tausaya Mana da Wanan mumunan gobara daya tashi a gidanmu da aka rasa Mai ya haddasa shi. Haka matan mak'otana suka zagayeni suka hau yayyafa min ruwa wasu na min tofi Ina dawowa cikin hankalina na mike zumbur na fara Kiran sunan yayana ganin suna kewaye Dani yasa na saki ajiyar zuciya na mik'e da Sauri nayi waje kafa ba takalmi nesa da gidan na hango Naseer ya tsugunna mutane na kewaye dashi ya zubawa konannan gidanmu ido da babu ma abin mora a ciki. Wani irin tausayinsa ne ya rufeni Mai ya rage mana yanzu Babu sai shaguna uku da gidansa na goron dutse da Bai karasa ba. Ban damu da yawan mazan dake wajensa ba Haka na nufi wajensu Ina zuwa na fashe da kuka suka kuwa baje suna bamu hakuri akan mu yarda da kaddara. Naseer Bai Dago ya kalleni ba na tsugguna agabansa Ina "Naseer Kayi hakuri Dan Allah ka yarda da kaddara Allah Yana sane damu Dan Allah karka saka damuwa a ranka" Wani irin murmushi Mai ciwo yayi ya dago da jajjayen idonsa ya kalleni "Naeema komai Kika ga ya samu bawa daga Allah ne duk abinda ya faru Dani Allah ne ya hukunta zai sameni bansan Zan samu dukiyar Nan ba Allah ya bani Dan Kuma ya jarrabceni bazan yi fushi ba Zan Kara gode Masa da har mukayi irin wanan gobarar daga Ni har iyalina babu abinda ya samesu Alhamdulillah iya Rai da lafiya da ya bamu Naeema arzkine shika shikan musulunci akwai yarda da kaddara Mai kyau ko mara kyau Allah ya Mana zabin dayafi alheri nidai roko na a gareki shine kiyi hakuri da yanda rayuwa yake juyawa Dani mu rungume abinda kaddararmu yazo Mana dashi insha Allahu watarana sai Labari ku kwana a gidan Mallam hafizu ni.kuma Zan kwana a shagon k'ofar gidan gobe da safe zanje na na saka a Dan gyara Mana gidan mu na goron dutse danaso Umma ta koma ko iya katifa ce sai na saka Mana muna daga ciki sai mu karasa wasu Abubuwan tashi ki koma ciki" Tausayin Naseer yasa na kasa mik'ewa idonsa kawai ya nuna dauriya yake kawai amma.yana cikin tashin hankali ahaka na mike na koma gidan a ranar naci kuka kamar Raina zai fita nayi nadamar dawowa rayuwar Naseer da zuwana yazo ya zame Masa masifa Taya Zan manta Naseer a rayuwata. Naseer kuwa kamar yanda ya alkawarta washegari ya nufi goron dutse tsohuwar unguwar mu da mukayi gobara gidan dayake ginawa a kasan layin da rufi kawai akayi yaje shagonsa na Sabon gari ya d'auko kudi Nan da Nan aka fara saka Mana cieling aka Yi plaster ko penti baayi ba muka tare a Haka. Tijjani kuwa Dan kudin da yake tarawa a banki ya Ciro ganin da Dan yawa yasa ya Kama karamin gida Sabida bikinsa da akeyi Ya Dan Yi hidimar biki da canjin hannunsa sauran Kuma ya kafa kanta anan k'ofar gidansa ya zuba Dan abinda bazaa rasa ba. Yan unguwar da yake zaman mutunci dasu ne Suka Masa komai da dangi ya Kamata su Masa Sati biyu da aurensa yana Kan benci zaune ya ga an sauke Hajara da Safiyya a taxi sun nufo wajensa Hajara kuwa na washe Masa baki...... Ayi maneji kaina yau Dan ciwo yake wlh kamar bazanyi bama na daure nayi [6/26, 3:38 PM] +234 803 635 0240: *NAGA TA KAINA* *NA SADNAF*🌸🌸 ®️ *_PURE MOMENT OF LIFE WRITERS_* _{We Don't just entertain nd educate we also touch the heat of readers P.M.L}💪🏻_ *Free Novel* *Page 26* *JIYA NAYI MISTAKE WAJEN DA NASEER YAKE CEWA YANA CIKIN SHARUDAN MUSULUNCI YARDA DA KADDARA MAI KYAU KO MARA KYAU INSTEAD CIKAR IMANIN.MUTUM SHINE YA YARDA DA KADDARA MAI KYAU KO MARA KYAU THOUGH NASAN ZAKU SAN MISTAKE NAYI DAN BAN BI BA JIYA LABARIN NAEEMA AKWAI TAUSAYI ALAJABI MAMAKI KU DAINA KOKWANTO AHAKA WLH NA CIRE WASU ABUBUWAN BAN SAKA BA KUNJI NACE WLH ALLAH YA BAMU IKON CINYE NAMU JARRABAWAR AMEEN* Tijjani sakin baki yayi Yana kallonsu har Suka karaso cikin mamakin Mai ya kawo su wajensa Yama akayi suka San gidan daya koma Nan kuwa bai san tsohuwar unguwar daya baro Nan suka je aka kwatanta musu ba. Daga yanayin fuskar Tijjani yasa itama Hajara ta had'e Rai tana San amfanin da karfinta na uwa sabida Tijjani ya Shiga hankalinsa "Baka ganemu bane ka saki baki kana kallonmu"? "Ba Dole na saki baki na kalleku ba umma ai Naga bansan da zuwanku ba Kuma kema kinsan halin da.muke ciki Kuka kwaso Kuka taho. Umma Kinga kayan Dana kasafta nake siyarwa duk a dalilin tsanar da kikayi wa Naeema Kika jawo mana "Dan ubanka zaka wuce muje ciki ko tareni zakayi da surutu mu Sha wanan uban tafiya ka tsaya kana min zancen banza" Hajara tace tana harararsa Mik'ewa yayi Yana cigaba da Magana ciki ciki. Yayi gaba suka bishi a baya. A madaidacin palon suka yada zango Tijjani ya hau kwallawa matarsa kira Murja Hajara kuwa cikin mamaki ta kalleshi tana "wacce Haka naji kana Kira"? "Matata Mana Umma"? "Matarka Tijjani yaushe kayi auren yanzu Ina mahaifiyarka Tijjani kayi aure batare da nasani ba" "Ai fa Umma nayi aure sati biyu kenan ki saka albarka kawai" Hajara na k'ok'arin Magana Murja ta fito daga d'akin tana Hamma ganin Hajara da Safiyya yasa ta katse Hamma Cikin dan murmushi tace "Ashe bak'i mukayi sannunku da zuwa" Ta karaso tsakiyar palon Hajara kuwa ta tab'e baki tana binta da kallo tundaga sama har kasa. Safiyya itama.kallon Sama da kasa take Mata ganin yanda take ta tsatsare su da Ido tana kad'a k'afa. "Ba bak'i bane Mahaifiyata ce da kanwata suka zo bansan da zuwansu ba kwatsam na gansu" "Aaa lalle sannunku da zuwa Umma dafatan.kun iso lafiya" Murja.tace tana Dan rusunawa "Yauwa" Kawai Hajara.tace Murja ta mik'e tayi.waje Dan ta kawo.musu ruwa Ko Gama fita batayi ba Hajara ta rufe Tijjani da fad'a "Bacemin Kai bakada kudi ba ina ka samu kudin da kayi aure?ka Kuma rasa wacce zaka aura sai wanan mummunan da gani ma Bata da tarbiyya Ji yanda take tsatsarmu da ido "Aaa umma Dan Allah kiyi hakuri bana San tashin hankali daga aurena bazaki zo ki dagamin hankali ba gaskiya ki barni naji ma da talaucin danake ciki" "Tijjani Ni kake gayawa magana Haka gatse gatse daga aurenka Tijjani"? "Umm Bari na tashi na Baku guri a huta lafiya" Daga Haka Tijjani ya mik'e ya fito Hajara ta bishi da kallon mamaki. A daidai lokacin da Murja ta dawo palon hannunta d'auke da ruwa. Ganin Tijjani baya Nan ta dungurar da ruwan a gabansu ta koma Kan kujera ta zauna tana kad'a k'afa Dan duk abinda Hajara tace tana jinta "Mai wanan ya zamu kwaso yunwa da gajiya ki wani kawo Mana ruwa"? Safiyya tace tana hararar Murjan "Toh ba abinci a gidan Sata zanyi na kawo Miki"? Itama tace tana hararar Safiyyar. Hajara kuwa mik'ewa tayi tana "Nida gidan Dana ai baki dai Isa ki Mana iyaka ba ko Naga alamar bakida kunya idonki Kuma Bai ga kunya ba daga take takenki nasan ke ba matuniyar arziki bace" Wani irin Dariya Murja ta kwashe dashi tana "Hakane Umma gidan danki ne fa Amma kayan ciki nawa ne ki tab'a iya gidan karki tab'a min Kaya ehe" "Tab Umman kike gayawa magana Haka dan ubanki" "Kul Kika zageni gwaggo dan har gidan mijina Kika zo Kika sameni kema ki zuciya kije naki gidan mijin kiyi mulkinki a can Idan Kuma kina da aure Zaki iya komawa naki gidan mijin. Tsabar mamaki Hajara kasa magana tayi Tana kallon Murja tare da jinjina K'arfin Hali irin nata. Zage zage Suka hau Yi da Safiyya Hajara kuwa tacewa Safiyya ta rabu da ita ta Kira Mata Tijjani a waje. Waje tayi fuuu kamar zata tashi Sama bayan Yan mintuna sai gasu sun dawo tare. "Tijjani Ina ka samo yarinya Mara tarbiyya Haka zagina tayi fa daga Safiyya ta tambayeta ya zata bamu ruwa ba abinci"? "Haba Umma yaushe na zageki ce min kukayi ya zan kawo muku ruwa ba abinci alhalin Kun d'ebo yunwa shine nace Miki wlh ba komai a gidan sai ka kawo Zan girka Amma yaushe na zageki haba Umma ya da girmanki kike karya"? "Umma nifa bana San hayaniya da tashin hankali maganar Allah wlh banida komai a gidanan Rabonmu da abinci tun Karin safe yanzu ma so nake nayi ciniki na samu kudin cefanen dare idan zaku ci bredi ko biscuit Safiyya tazo ta karba muku kuci kafin ayi girki idan kuma Kuna ganin bazaku iya ba wajen Naseer dai da bakiso kije Nan zakije ki samu yanda kikeso Kinga bazai yiwu nayi sata ba" "Ke Zaki karbo muku bredi" Tijjani yacewa Safiyya Yana ficewa daga palon Safiyya kuwa da take ji Kamar taci babu tabi bayansa ta karbo bredin Yana ta masifa Yana gwara ma su koma gidan Naseer shi bazai iya ba Hajara kasa ma cin bredin tayi Sai Safiyya ce take ta tusa bredin Kamar tayi kuka sai zabgawa bredin harara take Suna Jin Murja nata kananan wakoki a daki Makircin Murja ya bawa Hajara mamaki tsananin bakin ciki da takaicin Tijjani duk ya tsaya Mata a rai. Matarsa kuwa da yau akwai karfin tsafinta a tare da ita da yau sai dai wani ba ita ba amma a hakan ma zata san abinyi . Safiyya kuwa Tana cin bredin ta fara magana tana "Gaskiya Umma gobe mu tafi gidan Yaya Naseer Zaman mu anan bazai yiwu ba Dan wlh zuciya na iya sawa na kashe wanan matar da duka. Gashi Yaya Tijjani shima sai wani wulakantamu yake yi.abinda yaya Naseer bazai Tab'a Mana kenan ba bama Zan iya jure yunwa ba gwara.mu koma can banza banza zamu ci abinda ranmu yakeso ko bashida kudi wlh zai Nemo ya kawo Mana duk wanan masifar Umma wlh ke Kika jawo Mana Kika cucemu yanzu rabon Dana ci nama har na manta" "Hmmm bazanje gidan Naseer ba Safiyya Amma idan kina San zuwa Zaki iya zuwa ke kadai" Extra d'akin da babu katifa sai Leda anan su Hajara suka.kwana Inda ta ringa cin alwashin cin uban Murja ta tsani mutane biyun Nan Naeema da murja. Naseer. Wani irin rama yayi Sabida tunanin halin daya fara tsintar kansa a ciki. Tunda wanan ifitilai ya Fad'o Masa shagonsa ma ya fara ramewa kamar.ana yashe kayan ciki ya rasa ma Ina kudin shagon yake zuwa balle azo Kan riba. Tsabar ma San ya Dan tattala kudin nasa kasa sakin kudi yayi ya gyara gidan da suka koma dakuna hudu ne a gidan manya sai paluka biyu ba Wanda yayi wa fenti dakuna biyu kawai ya gyara sai kitchen da band'aki biyu. Dak'yar ya sakewa su zahira makaranta Mai Dan saukin kudi. A Haka rayuwa ta ringa tafiyar musu Naseer Duk kudin daya juya baya Masa albarka yaran shagonsa kuwa Suna ganin ba wani Samu suke ba Suka ware. Halinn da Naseer ya tsinci kansa a ciki na iya sawa Mai raunin imani zuciyarsa ta buga Naseer da ya saba kama kudi sai gashi kudin suna neman Yi Masa wahala tunda ya Shiga halin Nan Bai tab'a hawaye ba sai daya wayi gari yaga duka yaran shagonsa dayake taimakawa duk sun gudu tun shagonsa na da kyaun gani har yazo ya zamana babu Kayan ma sai daidaiku. Ahaka ya Kara siyar da filayensa da gidajensa suka kone na Sharada da gadon kayan har Dana Gefen gidansa na gadon kayan ya Kara zuba Kaya a shagon nasa. Sai dai me Dan kananan hidindimun da yake yi na gida kawai sai yaga kudin ya Kare Bai cire ma kudin Kaya ba ballantana ya samu riba. Sosai yake boyewa Naeema halin da yake ciki Dan yasan Abu kad'an ke iya daga Mata hankali Naseer Duk yanda.yaso Kar kudi ya sub'uce masa ya Dan samu abinda yake juyawa.sai gashi an wayi gari kayan.shagonsa.sunyi kwaraf Babu komai sai rufe shagon yayi ya hau buga buga Nan ma yana dan samu Nan da nan kudin zai Kare. Allah kawai yake kaiwa kukansa A cikin irin wanan lokacin aka koro su zahira gida sabida school fees kayan abinci suka kare. Sai Dan abinda.bazaa.rasa. ba Wai ahaka.ma Naeema tana iya k'ok'arinta dan taga asirinsu ya rufu. Tsanani yayi tsananin da Naseer wani zubin idan ya fita yanda.ya fita haka yake dawowa gidan ba ko sisi. Hakane yasa Bai shawarci Naeema na ya tafi Modobi wajen yayyensa Dan su Dan taimaka masa a cikinsu mutane uku ne Suka iya hada Masa kudi sauran kuwa daga Mai cewa babu sai Mai cewa shima hidima ta.masa yawa. Dan dukansu sun wacece mahaifiyarsa sun kuma San Abubuwan da ta aikata hakane yasa suke Tsoron jawo shi jikinsu wasu Kuma suna kyamatarsa.da mahaifiyarsa Mayya ce ko Yar kungiya kamar ma shine Hajaran sabida yanda Suke Masa. Ahaka ya dawo zuciya ba dadi. Dan kudin ma daya samo yake tunanin yin jari sai a abinci da zasu saka a bakinsu ya tafi. Naeema Bamu tab'a Shiga matsi da tsanani rayuwa ba irin wanan lokacin nayi kukan filin nayi na boyen tausayin Naseer da nakan kamashi Yana kuka daddare Amma bana San na nuna Masa nagani sabida nasan b'oye min halin dayake ciki yake (Ya Allah kayi Mana suttura ka bamu arziki mara Yankewa wlh duk Wanda yake da arziki Allah ya jarrabe shi da karayar arziki Yana cikin tashin hankali da sai Mai Imani ke iya jurewa wlh wani.ma na iya haukacewa idan ya juya yaga abinda yafi karfinsa ya wayi gari.ya gaggareshi Zan takaita wahalar da suka Sha Dan bana so na fadi komai wasu zuciyarsu bazata iya dauka ba Amma Zan Fadi kad'an daga ciki Allah ya doramu akan makiyanmu ameen) Har ya Kai abincin da zamu saka a bakinmu na neman gagararmu wani zubin ma sai na danyi Yan dabaru muke samun naci Idan Naseer ya fita Bai samo komai baya iya shigowa gidan Haka zai zauna a waje sai dai idan yarana sun Dan fita waje sun ganshi zasu rugo su gayamin anan Zan Gane Bai samo komai ba Ni Kuma Zan zura hijabina na fita na tsugunna a gabansa na bashi baki akan Kar ya damu Allah na sane damu baya iya dagowa ya kalleni balle yayana da suke kallonsa sabida yunwar da.suke ji gani suke idan suka ganshi ya kawo musu abinda zasu ci ne. A Haka Zan rik'e hannun Zahira na zaga unguwar neman taimako Ina kuka wayanda suka sanmu a baya sukan tausaya Mana su Dan taimaka Mana idan Kuma ban samu ba Haka zanje tsohuwar unguwar mu da ke da Dan nisa a kafa. Naje gidan mmn Mannir da bazan taba manta ta ba a rayuwata sabida taimakon da tamin dayake tasan halin da muke ciki Nan da Nan zata hada min kayan abinci mijinta shima ya bamu wani Abun. Yanda na fita na bar Naseer ahaka Zan dawo na tarar dashi sai ya ganmu da Leda yake samun kwanciyar hankali.ni kuwa Nan da Nan Zan sarrafa abinda.ma samo na bawa Yara na zubawa Naseer naje har waje nayita rokonsa kafin ya yarda.ya.shigo.abinci kuwa sai nayi dgaske yake ci Dan cemin yake kunyar mu yake ji muyi hakuri ya kasa.kalmar Nan na sakani zubar hawaye. Yarana Kuma sabida yarinta da basu San halin da muke ciki ba ahaka zasu zo suyi ta suna so su koma makaranta basu da wancan basuda wanan ko ma na basu abincin suce min basu koshi.ba. Ahaka muke ringa rayuwa cikin kunci Naseer kuwa yabi ya saka damuwa a Ransa abubuwa sai Kara matse Mana suke duk inda.naseer yaje neman aiki ko kudi baya samu idan kuwa yayi aikin k'arfi Dan abinda yake samowa Bai taka Kara ya karya ba Yana kawowa xamu siyi abinci muci. Nasha farkawa daddare nga baya dakin idan na fita Haka Zan tada.shi a k'ofar gida Yana kuka ahaka zamuci kukanmu mu biyu na Masa naseeha ya bani hakuri sai mu koma cikin gida. Idan bacci Bai zo Mana ba sai mu rayya daren muna kaiwa Allah kukanmu Ahaka muka samu shekara biyu cikin matsin rayuwa zuwa yanzu ma wayanda nake zuwa neman taimako a wajensu sun gaji Dani Mmn Mannir kuwa sabida Kar ta gaji Dani yasa na daina zuwa wajenta. Sai dai na Dan shiga gidan masu Hali na musu wanke wanke ko wanki ko shara su bani na abinci Nazo na bawa yarana. Ahaka Watarana naje gidan wata baiwar Allah da itama bazan mantata ba a rayuwata na nemi ta bani wanki na Mata ta biyani mu samu na abinci. Ta Debbo min wankin na fara Ina cikin Yi ta Leko Wai na Shiga wancan d'akin akwai kayan yaranta na d'ebo na wanke Ina Shiga d'akin. Naji ta fara min ihun barauniya kafin kace me Mata sun cika gidan an zagayeni mai dunguremin Kai nayi Mai. Rankwashina nayi ahaka suka rakoni har k'ofar gidana suna min ihun barauniya nayi kukan nayi rantsuwa Amma sun k'i yarda Dani bansan Mai nayi matar ta nemi ta wulakantani ta tozarta tani ba. Naseer dake gida da Yara da ciwon baya ya Hana shi fita sabida d'aukar Kaya masu nauyin ya fito jikinsa na rawa duk dauriyarsa Haka ya hau hawaye suka.gama.ci Mana mutunci suka tafi. Naseer kuwa ya ruk'o hannuna ya kaini har daki. Ya tsugunna ya hau bani hakuri. Ban iya magana ba sabida halin da nake ciki. Ahaka Naga ya saka doguwar Riga ya fita. Bai dawo gidan ba sai wajen goma yarana sun Sakani a gaba suna ta kukan yunwa. Zahira ce kawai take Gane halin da muke ciki. Niki Niki Naga ya shigo da kayan abinci. Cikin murna na mike Ina tambayarsa Ina ya samo yace Kar na damu na dorawa yaran abincin. Nan da nan na dafa musu abincin Suka hau ci Kamar basu tab'a cin abincin ba Ni kuwa tambayar Naseer kawai nake Ina ya samo kayan abinci Sai anan yake cemin a Lukman ne ya taimaka masa yaron shagonsa ya hada Masa da Dubu biyu lokacin da kudi ne Mai Dan yawa. Sosai na hau shiwa Lukman albarka Naseer kuwa ya ruk'o hannuna Yana bani hakuri halin daya jefamu na gazawar da yayi Ni kuwa na rufe Masa baki Ina ya Bari jarrabta ce ta Allah. A ranar sai da muka Kai Sha biyu muna Hira cikin siga Naseer na bani amanar yayansa da Sam ban kawo komai ba a Kuma ranar muka samu nutsuwa da juna Wanda rabonmu da samun nutsuwar har mun manta sabida matsin da muke ciki. A Haka bacci yayi awon gaba dani. Naseer ya tashi ya tsarkake jikinsa ya d'auko wani Leda ya zuba kayansa kala biyu ya ajiyewa Naeema wasika a karkashin pillonsa. Ya duka ya sumbaci Goshin ta Yana kuka yabi yayansa ma ya sumbace su daya bayan daya kafin ya Kare musu kallo Yana hawaye cikin sand'a ya bar gidan.............. *Comment* [6/18, 7:59 PM] Zee Smy: Naga sabon book dinki amma ban fara daga farko ba,yayi kama da lbrn wata amma ita uwar mijin dayar ba yar secret society bace,ruwan asiri Kawai take mata hadda na ta haukace,amma har yau auren na nan,almost 31yrs of marriage...suma sun shiga tashin hankali mara fasaltuwa,itama har danta take ma asiri kada ya cigaba arayuwa sbd kada matar taji dadi,as am reading some pages they’re reflecting the story of someone I know, [6/18, 8:13 PM] Sadnaf💥🔥: Am happy [6/18, 8:13 PM] Sadnaf💥🔥: Akwai Mai irin labarin Amma wasu na karyayawa [6/18, 8:13 PM] Sadnaf💥🔥: Karyatawa [6/18, 8:24 PM] Zee Smy: Wllhi my dear am a living witness of such [6/18, 8:31 PM] Zee Smy: The mother in law did everything possible tarabasu but Allah beyiba,kuma harta koma ga Allah bata kaunar matar Dan nata...Wllhi Idan taga kina son matar Danta kema ta tsaneki knn,Idan na baki lbr itama sekin mata kuka...har danta take ma asiri kada ya Cigaba arayuwa,aikuwa ya rasa aikinsa taita farin ciki shima kmr Naseer shine ke riqe da mmn shi dakuma siblings...Allah ya shiryi masu irin wannan halin amma akwai su koba suda yawa [6/26, 3:38 PM] +234 803 635 0240: *NAGA TA KAINA* *NA SADNAF*🌸🌸 ®️ *_PURE MOMENT OF LIFE WRITERS_* _{We Don't just entertain nd educate we also touch the heat of readers P.M.L}💪🏻_ *Free Novel* *Page 27* Naseer Bai Yi minti biyar da fita ba na Kai hannuna wajen da yake kwance a gefena. Na shafa naji ban jishi ba mik'ewa nayi zaune da Sauri Haka kawai naji fad'uwar gaba duk da na Saba farkawa ban ganshi ba amma duk da Haka yau sai nake Jin wani irin tsoro. Durowa nayi daga Kan gadon na fara Kiran sunansa nayi hanyar k'ofa bayan na lek'a band'akin ban ganshi ba. Haka kawai na tsinci jikina da rawar tashin hankali ban damu da tsakar dare bane na ware murya na fara kwalla Masa Kira na bud'e kofa da Sauri na fita Waje duk tsorona Haka na cigaba da kwallawa Naseer Kira na Kara komawa.dakinmu Wai na duba ko dai Yana dakin nice ban gansa ba. Ina Naseer yaje da tsohon Daren Nan tuna amanar yayansa da ya ringa bani dazu Kamar Yana min hannunka Mai Sanda yasa na Kara Jin fad'uwar gaba da tsoro na hau kwallawa Masa Kira Ina Kara Shiga band'aki. Tsabar gushewar hankali har karkashin gado na lek'a ban ganshi ba. Rawar da jikina ya d'auka yasa na samu waje na zauna a gefen gadon Ina Kara kallon agogo karfe uku da minti ashirin. Ba yau na Saba farkawa na duba Naseer Naga baya Nan ba Amma baya wuce k'ofar gida Ina Naseer yaje Daddaren Nan"? Na rik'e zuciyata dake bugawa tunani iri iri na zuwar min Zuciya. Kara mik'ewa nayi Dan nayi waje a wajen mik'ewa hannuna ya Kai Kan pillonsa hannuna ya tab'a farar takarda daya sakamin wani irin fad'uwar gaba tare da rawar jiki Cikin kakarwa kamar wacce tayi arba da mugun Abun tsoro na dauki wasikar tunanin Lokacin da na taba ajiyewa Naseer wasika na fad'omin. Warware wasikar nayi numfashina na sama sama Ina Jan innalillahi wa Inna ilaihi rajiun *Assalamu alaikum matata uwar yayana Naeema a lokacin da zakiga wasikar Nan kila na Dade da nisa Naeema Allah ya Miki albarka Ina rubuta wasikar Nan ne cikin raunin zuciya da hawaye da rashin mafita Naeema dauriya nake yi a gabanki Amma Ni kadai nasan ciwon da nakeji a Zuciyata game da rayuwar da muka tsinci kanmu a ciki ba'a San Raina kike fita neman abinda zamu ci ba har ya Kai Naeema yau a garin nema an kala Miki Sharrin Sata bazan iya jurewa Ina ganin kina Shan wahala ba na kasa Baku kulawar daya dace na kasa sauke muku hakkin ku dake kaina shekara biyu kenan rabon yarana da makaranta da yanzu Zahira da Nadeeya sun Isa Shiga makarantar gaba da primary ganinku a cikin irin wanan halin na iya sawa na yanke jiki na Fadi ko zuciyata ta buga a yau da aka tozartaki Naeema zuciyata tayimin ciwo Ina ganin kamar duk laifina ne da ace na Nemo da Baki fita ba har a.miki wanan tozarcin hakane yasa Ina fita dazu nayita bin mutane irin wayanda na taimaka wa a baya ko zasu taimaka min sai Lukman ne ya taimaka min na samu wanan Kayan abincin da kudin da Kika gani dashi Naeema na gaji da ganinku haka a wahalce hakane yasa na yanke tafiya zuwa wani garin na nemi kudi ko Allah zai saka na samu kudi Dan Allah kisakani a cikin adduarki ga amanar yarana kiyi hakuri da tafiyar danayi nasan zakiji ba dadi Amma gani.nake kamar hakan shine mafi alheri a garemu tunda banida amfani idan na kasa ciyar daku na shayar daku Dan Allah ki kularmin da yarana kiyi hakuri na barku a hannun Allah insha Allahu zai kularmin daku* Ban iya karasa karantawa ba na fita aguje Ina ihun Kiran Naseer daga Ni sai rigar bacci kafa ba takalmi Duk da karnuka dake ta haushi Haka na fita aguje nabi layin dazai fita Dani titi kamar mahaukaciya ina " Naseer ka dawo karkamin Haka karka tafi ka barni wlh nasan Allah ne ya jarrabcemu ba kasawa kayi ba ya zaka gudu ka barni da Yara biyar Naseer karka manta fa Kai kadai gareni" Kuka nake sosai Ina gudu Ina dube dube ko xan ganshi ahaka naje har titi Banga kowa ba Akan titi na durk'ushe Ina ihun kuka Ina surutai. Ban ankara ba sai Kiran Sallah naji. Gwiwa a sage.kamar wacce akayi wa mugun duka na tashi na koma gida ji nake inama mafarki nake Taya Naseer zai gudu ya barni muna cikin wanan halin taya Naseer zai gudu ya barni da Yara Ina ilimin Naseer da ya kasa tawakali ya jure jarrabtar da Allah ya mana. Dak'yar nayi wankan tsarki Ina kuka sallah ma ba a nutse nayi ba Ina iddarwa wani irin Mugun zazzabi ya rufeni. Takarda daya rubutamin na rukunkume a hannuna. Ina kallo su Zahira suka shigo d'akina da Sallama Dan suma sun Saba da asuba suke sallah. Suna iddarwa d'akina suke zuwa su gaisheni. A Haka zamu zauna Gabadaya Dan karatun da Suka iya mu hau Yi gabadaya A Haka Naseer ke dawowa daga Massallaci ya same mu shima sai su gaishe shi. Zahira nada Sha hud'u lokacin tana da wayo da hankali a guje ta karaso wajen da nake kwance ta ruk'o hannayena tana "Umma bakida lafiya ne? Dukansu zagayeni sukayi Ni kuwa ganinsu yasa na Kara fashewa da sabon kuka Zahira itama kukan ta fara yi Dan Haka take ko Yaya ta gani a cikin damuwa itama Nan da Nan take Shiga cikin damuwa. Dak'yar na tsagaita kukan da nake na ce ta dafa musu abinci suci Dan ba laifi ta dan iya. A ranar dauriya kawai na ringa yi sabida yarana danaga sun fara Shiga cikin damuwa. Tafiyar Naseer sosai ya karyani ya Sakani cikin tsananin damuwa. Bana rabo da hawaye. A Haka muka ci wata daya kullum Haka nake zuba Ido Naga ko Naseer zai dawo har ta kai.ma bana rufe k'ofar Gidan. Ban fara Shiga tashin hankali ba sai da kayan abincinmu ya kare anan na fara tunanin hanyar da Zan Nemo wa yarana abinci sai nake Jin kamar nauyi ya kararmin kamar bazan iya kula da yaran nikadai ba. Ahaka na fita Shiga wanan gidan Shiga can ahka na tattara abinda na samu na dawo gida na Dan Mana abinda yarana zasu ci. Haka nake Hana cikina sabida yarana su koshi idan ka gani zaka dauka na shekara Ina jinya sabida ramar da nayi Duk dare sai nayi kuka idan na gaji sai na daura alwala na kaiwa Allah kukana Rabin addua ta akan Naseer ne Allah ya karemin shi ya dawomin dashi lafiya. Rayuwa babu Naseer sosai ya Karamin zafi Kan zafi Dan ya Kai yanzu idan na fita wani zubin bana samo Mana abinda zamu ci. Ahaka Zan zauna da yarana muci kukan mu tare na basu ruwa. A ranar Daga Kan Nadeeya zuwa Raheema basu iya runtsawa ba sabida yunwa na Kuma rasa ya zanyi Dan duk Inda naje bansamu komai ba. Gabanin asuba bacci yyi awon gaba dasu. Ina iddar da sallah na saka hijabina na fita. Bansan Mai yasa bana San nayi bara ba Gidan mmn Mannir na tsinci kaina da nufa. Bama su tashi ba lokacin Dana je Kwankwasar da nayi yasa suka bud'e. Mijin mmn Mannir ne ya bud'e k'ofar Yana ganina yayi saurin cewa na shigo dafatan lafiya. Ban iya ce Masa komai ba Ina ganin mmn Mannir na zub'e a kasa na hau kuka ita kuwa ta saki sallati Tana tambayata Mai ya faru. Dak'yar na tsagaita kukan da nake na Bata labarin tafiyar da Naseer yayi ya barni da Yara. Da irin wahalar da nake Sha har jiya ma bamu samu munci komai ba. Nan da Nan itama mmn Mannir ta hau zubar da hawayen tausayina ta hau cewa Naseer Bai kyauta daya gudu ya barni ba. Mijin ta kuwa ya hau fadan Mai yasa banzo sun bani wani Abun ba su kansu sun San halin da muke ciki bazasu gaji damu ba Dan Shima Naseer ya Masa alherin da bazai manta ba. Cewa mmn Mannir yayi ta tashi ta Dan harhado Mana kayan abinci. Jiki na rawa ta mik'e ta Shiga store dinsu. Shi Kuma ya koma cikin daki. Jim.kadan da shigarsa ya fito hannunsa rik'e da hamsin hamsin sababi Mai yawa Ya mik'o min jiki na rawa na amsa na fashe da kuka Ina zabga Masa godiya shi kuwa yace "Dubu biyar ne Dan Allah ki ja jari ko Yaya ne ki ringa wani sana'ar a gida da zai na shigo Miki da kudi Allah Yana sane daku watarana sai Labari Allah ya dawo da Naseer lafiya ya Riga rufa asiri" Bazan taba manta mutanen a rayuwata ba duk kankantar alheri idan kamin bana mantawa shiyasa har na mutu Ina yiwa mutanen Nan addua dacewa duniya da lahira. Sai daya fice daga gidan dayaga Ina ta Masa godiya. Mmn Mannir kuwa ta kusa cikomin bakin buhu da kayan abinci har da suturun yaranta da zasuyi wa wasu daga cikin yarana. Nima ta bani a nata wajen kala hudu Dan Ina fama da rashin sutura har yayana. Har bakin titi ta rakoni na ringa zabga Mata godiya. Tana tafiya na fara zabga Sauri. Kyashin ma taba kudin da suka bani na hau mota nake sabida Kar ya Kare. Ina Isa gida na tarar da duk sunyi rub da ciki suna hawaye har da Zahira da take da juriyar yunwa suna ganina da buhu suka taso da Sauri. Tausayinsu yasa na fara zubar da hawaye nima.cikin rawar jikin na bud'e buhun. Naga har da bredi manya guda biyu mmn Mannir ta hadoni dasu. Basu tsaya ma jiran na basu ba suka daka wa bredin Wawa har da Raheema suka ringa tusawa a baki Kamar basu tab'a cin abincin ba. Gefe na koma naci kukana na koshi na share hawaye na na hada katakwaye na Dora Mana shinkafa Mai Dan yawa da zamuci har dare. Dayake da tumatirin gwangwani na Mana Miya Dan har Mai da maggi mmn Mannir ta bani. Sai Dana Gama na kara zuba musu Nan da Nan sukaci. Sai da suka.koshi Zahira da Nadeeya suka gyaran gidan Ni Kuma na zuba nawa na Shiga d'aki Dan naci Nazo nayi tunanin Sana'ar da zanyi. Sai dai Ina yin.loma biyu.naji zuciyata na tashi kafin kace me na kece da amai. Sai Dana Gama amai na hau kuka Dan na Gane cikine Dani Dan bana Aman banza sai a dalili. Banji dadin samun cikina a irin wanan lokacin ba shaf na shaafa Dan Ina yawan zazzabin dare. Kuka naci na Godewa Allah sai Dana Sha magani na fito wajen yayana hannuna rik'e da kudin da mijin mmn Mannir ya bani na zauna a tsakiyarsu Nan da Nan suka zagayeni suna washe baki budar bakin Nadeeya sai cewa tayi "Yauwa Umma tunda kin samu kudi Dan Allah ki samu a makaranta wlh.inasan komawa makaranta". Minal kuwa cewa tayi "Umma ki siya Mana kayan abinci Mai yawa sabida mu daina Jin yunwa" Humaira kuwa cewa tayi Umma ki siyamin sabon takalmi takalmana duk ya tsinke Raheema dake karamarsu itace Bata ce komai ba sai a lokacin na kalli Zahira nace Mata "bakice komai ba" Murmushi tayi tana "Umma nidai ki dafa min Abu na ringa fita Ina siyar miki sabida karki ringa rasa kudi a hannunki Umma Wai yaushe Abban mu zai dawo"? D'auke hawayen dake neman zubomin nayi na kalli Zahira Ina "Abbanku Yana Nan ya kusa dawowa Zahira yanzu wane Abu kike ganin ya kamata mu siyar unguwar Nan sabida na samu kudin da Zan saka ku a makaranta na siyawa Minal takalmi na siya Mana kayan abinci da yawa"? "Umma ki ringa siyar da kankankara Ana siya sosai"cewar Minal "Umma ki ringa siyar da abinci Amma fi siyan shi" Cewar Nadeeya mayyar abinci "Umma kiringa siyar da kayan Yara da Yar tsana" Cewar Humaira Sanin Raheema bazata ce komai ba yasa na kalli Zahira ita kuwa tace "Umma kiringa siyar da kosai a k'ofar gida tunda Babu masu siyar da kosai a layinmu" Murmushi na saki Dan shine a Raina Ina mamakin kaifin tunanin Zahira Ina ganin siyar da kosai shine mafita kawai. Hannun yarana na ruk'o gabadayan su Ina "Allah ya muku albarka ya rayamin ku ku kadai kuka ragemin a rayuwata nake Kuma ganinku Ina Jin dadi. Zan saka ku a makaranta insha Allahu Zan siya muku Kaya da duk abinda kukeso lokaci yayi da Zan taka rawar da mahaifi yake takawa akan yayansa" Hira da nakeyi da yarana kowaccensu inajin abinda take buri a rayuwa.naji na Dan rage damuwa. Da yamma Zahira ta siyomin komai na bukata da zamuyi kosai. Tabi mak'ota duk ta Gaya musu. Washegari tun karfe hudu na tashi duk da inajin zazzabi sabida laulayin da na fara haka na wanke wake Ana iddar da sallah asuba na Kai markade Ina dawowa na hada wuta. Ina zazzabi a Haka na fara saka kosai Zahira na d'aga gefena cikin Ikon Allah kuwa masu wucewa suka fara tsayawa suna siya..... Yau bak'i nayi wlh wata fans din Naga ta kaina tazo ganina Kamar nice Naeema ngd ER uwa Allah ya bar zumunci Habeenart Naga sako Allah ya bar zumunci ngd *Comment* Allah sarki Naseer da Naeema😭kuntunamun halin dana taba tsintar kaina nima aciki,wallahi Sadnaf ina karantawa ina ganin kamar labarina kike rubutawa,yanda Naseer zai fita neman na abinci yadawo bai samu komiba yazauna waje yakasa shigowa,wallahi haka muka taba tsintar kanmu,Naira biyar dazamu samu musai gari da suger haka zai wuni yana yawo bai samuba😭ya dawo yakasa shigowa,banbanci kawai su gidan kansu ne mukuma family house ne,wallahi kuma duk sharrin makiya ne,gashi saidai inbada labari,wanima inna fada sai yaga kamar karya yakalleni yace yanzu kece kikayi irin wannan rayuwar? Nakanyi😊kawai ince kina mamaki ko?. Allah kashiga tsakaninmu da makiyi ka karemu sharrunsu dun inda muke.[6/26, 6:13 PM] +234 706 571 7620: *NAGA TA KAINA* *NA SADNAF*🌸🌸 ®️ *_PURE MOMENT OF LIFE WRITERS_* _{We Don't just entertain nd educate we also touch the heat of readers P.M.L}💪🏻_ *Free Novel* *Wanan Shafin naki ne Ateekah Nagode da soyayyarki a gareni Allah ya bar zumunci*🌹🌹🌹 *Page 29* Ba karamin duka Safiyya taci a hannun Murja ba ta watsar da ita a tsakar gidan ta shige daki da bredin ta. Daga Hajara har Safiyya babu Mai rarrash wani duk kamaninsu ya canja. Allah ya Isa kawai Hajara Da Safiyya Suka ringa jawa Murja Hajara kuwa tayi ta rantsuwa da idan Tijjani ya dawo wlh sai ya saketa ko ta Masa baki. Haka suka shige daki ga duka ga yunwa dake nukurkusar Hajara Bata tab'a tunanin akwai ranar da Yar cikinta zata iya daga Ido ta kalleta har Wai ta iya kawo hannu jikinta ta haye ruwan cikinta ta Mata duka a gidan danta sabida ta dauki bredi. Ita da idan aka hada Ido da ita sai gaban mutum ya Fadi Take ta hau tuna yanda idan Suka had'a Ido da Naeema jikinta ke kwasar Bari sabida tsoro. Muryarta ma idan Naeema taji tana ganin yanda tsoro ke bayyana a Fuskarta Amma Wai yau itace Murja da take kyautata zaton Lami ta girmeta itace ta Mata Haka Kai Ina da sake zama a Haka Bai Kamata ba Dole ta koma kauyensu ta nemi shugabarsu tayi ta Bata hakuri ta dawo Mata da Karfin tsafinta a ranar da ta Bata a ranar zata kashe Murja Naeema Kuma da take daurawa alhakin duk halin da suka tsinci kansu a ciki ta sakata a uku ta Sha bak'ar wuya Kafin ta rabasu da Naseer Dan har gobe tana Nan Akan bak'anta na yak'ine tsakaninta da Naeema ko taci ko Naeema taci. Muryar Safiyya ne ya dawo da ita hankalinta "Wlh ya zama Dole mu bar gidanan Umma Dan wlh Tallahi na gaji da zama da tsinaniyar matar Nan da Bata da mutunci gwara mu koma gidan yaya Naseer koda kuwa a daki daya yake. Akan abinci tsinaniyar Nan ta Mana irin wanan dukan Ni nasan ba ita ta iya Mana wannan dukan ba wlh Aljannu ne da ita. Dan Haka Umma a yau ba sai gobe ba mu tattara kayanmu mu koma gidan Yaya Naseer kema kinsan Naeema ma ko numfashin kirki Bata iya yi idan muna waje daya ballantana ta kawo Mana iskanci shi kuwa Yaya Naseer sai yanda kikayi dashi Kuma wlh ko Dan wanan matar Umma ya Kamata muje mu roki Shugaba muna bukatar mudubin mu ko Dan gudun Kara faruwar Haka yau da ace da Karfin mu a tare damu ai sai dai wata a yau ba ita ba" Wani irin girgiza Kai Hajara tayi zuciyarta fal cike da mugunta da San d'aukar fansar abinda Murja ta musu "Sabida abinda yarinya Nan tamin Zan nemi kudin mota naje wajen shugaba ko da Bata maidamin karfina ba inaso a hukunta min ita inaso a makantar min da ita na dawo na zaneta na saka Tijjani ya saketa bayan nayi aiki a kansa Dan Ni nasan bata barshi Haka ba asiri tayi Masa. Idan zaman Nan din bai yiwu ba sanan muyi tunanin zuwa gidan Naseer. "Toh Ina zamu samu kudin motar tafiya"? "Idan Tijjani yazo sai ya Nemo min kudin motar duk Inda ya shiga kuwa wlh idan yak'i bani sai na tsine Masa Dan bashida amfani a wajena tunda har ya iya fifita matarsa akaina ya ringa toshe kunnensa idan na masa maganar matarsa tashi ki lek'a min kiga ko ya dawo Dan bazan Kara kwana a gidan Nan ba" Safiyya fitowa tayi daga d'akin da kumburarren baki A Palo ta tarar da Murja tayi hadin kauri ga kwai ta shimfida tana ci tana gyad'a kai sai murmushi take. Safiyya da kumburarren idonta ta hau hararar Murja. Murja kuwa ta saki murmushi tana "Wanda ya ja Dani wlh zai Sha wuya dama idan kun samu kudin motar kun taimaka wa kanku Kun siyi abinci Dan duk Inda zakuje ma wahalar da kanku zakuyi ba Abunda zaku iyamin" Tsaki Safiyya tayi Dan ta d'auka lab'ewa tayi taji abinda suke cewa A k'ofar gida ta tarar da Tijjani ashe ya dawo Yana zaune Akan benci kusa da kantarsa. Safiyya tana Isa wajensa ta fashe da kuka Tijjani ya d'ago ya kalleta ganin jikinta duk a kumbure yasa ya mik'e Yana "Ke lafiya Mai ya Sameki Haka"? Cikin kuka Safiyya ta bashi labarin abinda Murja ta musu. Ta Kara da cewa "Yanzu Yaya tsakani da Allah Haka zamu cigaba da rayuwa a gidanka matarka na Mana horar yunwa tana dukanmu da anyi magana sai kace Umma ce ta jawo komai Kai baka San tashin hankali har matarka ta saka hannu ta daki Umma toh kaje tana kiranka Dan ta rantse bazata kwana a gidanan ba tafiya zatayi" "Murjan ce ta daki Umma Akan abinci"? Tijjani yace cikin mamaki Bai tsaya ma jiran Mai Safiyya zata ce ba ya shiga gidan Sai dai me suna Shiga palon Suka ga Murja a kwance a kasa tana ta numfarfashi kayan jikinta duk a yayyage jikinta ya wani kumbure Yana ta kyalli Kamar wacce akayiwa shegen duka Shigowar Tijjani yasa ta fashe da kuka ta hau mik'a Masa hannu tana "Zo ka taimakeni zasu kasheni"? Dak'yar.tayi.maganar tana numfarfashi. Tijjani kuwa ya saki sallati ya karasa wajenta a guje ya d'ago ta cikin tashin hankali Yana duba yanda jikinta ya kumbure. Safiyya kuwa mamakine ya kasheta a tsaye ta saki baki tana kallon Safiyya Hajara ma fitowa tayi daga d'akin dataji muryar Murja kamar wacce aka daka.kafin ma ta fito ta hau addua Allah yasa ruwan zafi ne ya kwarowa Murjan. Amma abinda ta gani ne ya sa ta kasa motsi daga ita har Safiyya kallon Murjan kawai suke suna Jin Mai ke fitowa a bakinta "Na shiga uku Tijjani mahaifiyarka da kanwarka zasu kasheni kaga yanda suka dakeni suka had'u akaina sukayita jibgata akan sunce na kara musu abin karyawar bazai isa ba Shine nace musu bredin guda daya ka kawo babu wani shine Ina ajiye musu kayan shayin suka yi ball da shayi da bredin suka tashi Suka rufeni da duka" Ta karashe tana matsar kwalla" Tsabar mamakin makircin Murja Safiyya zub'ewa tayi a kasa. Tana "Yaushe muka dakeki? A yaushe Kika bamu shayi da bredin" kiji tsoron Allah ke Kika dakemu ko mu muka dakeki"? Tijjani kuwa tuni idonsa ya kad'a yayi ja halin dayaga Murjan ya balain b'ata Masa rai. Mik'ewa yayi a fusace Yana "A gaskiya na gaji wlh Nagaji Umma Akan me zaa ringa dukan matata akan abinci kuka had'u kuka Mata irin wanan dukan Umma wlh bazan d'auka ba Dan Ni ba Naseer bane ku barni Mana inji da masifar da nake ciki akan me zaa zo a Kara min wani a ringa dagawa iyalina hankali ahaka kuka sako matar Naseer agaba yanzu Kun bar kanta Kun dawo Kan matata toh a gaskiya bazan yarda ba na gaji Umma ki koma gidan Naseer kawai kasheta kuke so kuyi akan abinci?kunsan da yanda nake Samun ma abinci"? "Ke Kuma Dan uwarki har wuyanki yayi kaurin da Zaki kawo hannu jikin matata Sa'oinki suna can daga Mai yaya bakwai sai takwas ke kinzo Nan Zaki daga min hankali maza ki shiga daki ki kwaso kayanki Kar na sake ganin kafarki a gidan Nan" Kuka Safiyya ta fashe dashi tana "Wlh Tallahi yaya karya take Mana Ita ta dakemu fa daga Umma ta Shiga kitchen dinta ta d'auko bredi zata ci shine ta hau Umma da duka na fito Zan ceceta ta had'a Dani haba Yaya Kar San matarka ya rufe maka Ido ka kasa Gane sharri take Mana ka kalli fuskata ka kalli fuskar Umma mu zamu daketa mu Kuma daki kanmu" "Wayyo Allah kaina wayyo Allah bayana" Kawai Murja ke cewa tana matsa kwalla Tijjani kuwa hakan ba karamin Kara Masa Haushin Hajara da Safiyya take ba. Bakin cikin sharrin da ta musu yasa Safiyya ta fara kuka Hajara da wani irin Abu ya tokare Mata wuya Tama kasa magana sabida sharri da.makircin da Murja ta had'a musu Tijjani ko bincike Bai tsaya Yi ba ya hau Kai ya zauna Yana fadar duk maganar data fito daga bakinsa. "bani kudin mota na bar maka gidanka a yau Tijjani yau Akan mace ka rufe Ido kake gayamin bakaken maganganu matarka ta daki nida kanwarka ta Kara hada Mana sharri ka goyi bayanta ka k'i bincike kaji daga bakinmu. Tun aurenku da ita ban saka albarka ba nace maka Bata min ba sabida ba matuniyar arziki bace kak'i ji a karshe ta ringa Mana horon yunwa sabida na Shiga kitchen na dau bredi ta rufeni da duka kazo ta Mana sharri ka yarda da maganarta. Tijjani a yau Ina umartarka da ka saketa saki uku ko na maka baki" Tijjani kallon Hajara kawai yake cikin mamaki Yana "Da tamin me Zan saketa Umma kawai Dan matata ba ta kwanta Miki ba sai ki dage na saketa yanzu idan na saketa ke Zaki Nemo min wacce Zan aura wai.mai yasa bakida burin daya wuce ku watsa rayuwarmu ne ki hanamu sukuni da zaman lafiya Umma karki manta fa akwai hakkinmu akanki Haka zalika hakkinki akanmu Umma bakida burin daya wuce ki cutar damu muna yayanki Haka kika Sako Naseer a gaba sai da Kika Hana shi sukuni Umma yanzu Nima din baki kyalleni ba sai kin rabani da matata toh a gaskiya bazan iya rabuwa da ita ba Dan babu abinda tamin matsayinki daban matsayinta daban" "Au Haka kace ko toh shikenan gata Nan na sallama Mata Kai Tijjani daga Yau Murja ta zame.maka uwa karka Kara doso.inda nake tunda ka k'i bin umarnina sai ka tagayyara ka wulakanta Sai wanan tsinaniyar matar ta zama ajalinka" "Innalillahi wa Inna ilaihi rajiun Allahuma ajirni fi musibati wa aklifnin khairin minha Umma yanzu akan naki rabuwa da matata kikemin baki Haka"? Hajara Bata kulashi ba ta koma daki ta d'auko buhun Kayanta Ta fito tayi waje. Safiyya itama ta mik'e ta shiga d'akin ta d'auko Kayanta tabi bayanta. Tijjani kuwa tsananin mamakin kalmomin Umma ya hanata motsawa. Murja kuwa cikin makirci tabi bayansu tana "Umma Dan Allah kiyi hakuri ki dawo ya sakeni. Tana Isa Dab dasu ta Sha gabansu ta saki murmushi tana "Kar na sake na Kara ganin kafarku a gidana duk Wanda ya ja Dani wuya zai Sha Dan Baku San wacece ni ba Kuma danki auren zobe mukayi mutuwa ce zata rabamu karki wahalar da kanku wajen yimin wani Abu Dan Babu abinda zai sameni. Daga Haka ta matsa daga gabansu ta sakar musu murmushi fitowar Tijjani yasa ta zub'e a kasa da Sauri ta rik'e kafar Hajaran tana "Umma Dan Allah kiyi hakuri ki koma Zan saka ya sakeni." Tsabar bakin ciki Hajara kasa magana tayi har Tijjani ya karaso wajensu. Ya mik'awa Safiyya kudi Safiyya ta d'auke kanta ya daka Mata tsawa kamar zai Kai Mata duka tayi saurin juyowa ta karbi kudin Shi kuwa Tijjani yace "Allah ya kiyaye hanya Umma idan kin huce zamuzo" Daga Haka ya juya ya koma ciki. Murja kuwa ta musu gwallo ta bi bayansa. Daga Hajara har Safiyya ba Wanda ya iya magana har Suka Isa Tasha suka hau mota. Sai da motarsu ta d'au hanya Hajara ta rufe fuskarta ta fara kukan bakin cikin abinda Murja ta musu yanda take Jin zuciyarta da zata samu wuka daga Murja har Tijjani zata iya kashe su. Sai a yanzu ta Gane Naseer Dan halak ne Yana kuma Mata biyayya Naeema ce dai data tsana yak'asa bin Umarninta Karo na farko da tayi Nadamar abinda tayiwa Naseer. Naeema ta tsana ba Naseer ba da ta sani tun farko Naeema tasan yanda akayi ta kau da ita duk da Naeema duk abinda take tayi dan ta cimma burinta ta kasa samun Galaba a kanta Bata San Mai yasa yaran nata maza suke k'in Mata biyayya Akan matansu ba. Tuna Naseer da Naeema ya Kara taso Mata da tsanar Naeema da take ganin ita ce silar dayasa idonta ya rufe tayiwa Naseer abinda tayi Masa. A yanzu Kuma ba wacce take San ganin ta aikata barzahu sama da Murja da take Jin kowacce fitar numfashinta da tsanarta take fita. Bata da burin daya wuce ta Isa Calabar. Tsabar b'acin Rai ma neman yunwar tayi ta Rasa. A lokacin da suka Isa Calabar sanin babu Inda zasu sauka yasa Suka nufi gidan Lami. Lami Bata ma iya musu magana ba sabida yanda suka had'e rai. Bata San da zuwansu ba Amma abincin data girka Haka ta juye ta kawo musu Daga Safiyya har Hajaran Loma kawai suke kaiwa bakinsu har suna neman fada akan abincin. Sai da suka nutsu Lami ta hau tambayarsu abinda ya faru tagansu Haka. Cikin bakincki Hajara ta hau Bata labari tana cin alwashin irin Abubuwan da zatayi wa Murja Naeema da Tijjani. Safiyya kuwa cewa take Banda dai Tijjani tunda nasu ne Kuma ita tasan bayin kansa bane. Lami girgiza kanta tayi tana "Umma a gaskiya shawarar da Zan baki shine ki hakura ki koma ga Allah Ni yanzu nasan asiri da tsafi duk karyace Umma a sanadin tsafi Umma bayana ya koma haka Umma shekara nawa muna had'awa Naeema abubuwa tana tsallakewa kin taba tunanin da wa Naeema ta dogara take neman fin karfinmu nidai Umma Dan Allah ki hakura ki dawo hanya" "Kimin shiru Lami zan sauke fushina akanki idan bazaki tayani ba karki soma hanani" Ta Inda Hajara take Shiga Bata nan take fita ba. Lami kuwa d'akin ta baro musu tana musu adduar Shiriya Karfe Sha biyu Hajara da Safiyya suka nausa daji. Duk yaren tsafin da suka ringayi Shugaba bata bayyana gabansu ba . Sai da suka Sha bak'ar tafiya ko tsoro basaji suka iso wani wawaken waje Mai dauke da wani gini a tsakiya shi kadai wanda na shugabarsun ce. Suna Isa wajen suka ganta a zaune ta daura Jan zani Ido ta zuba musu har suka zube a gabanta. Hajara kuwa cikin kuka ta hau rokonta ta yafe Mata ta maido Mata mudubinta ta tuba bazata Kara ba tana San daukar fansar abinda Murja ta Mata. Sai data Gama tsaf Shugabarsu ta jawo wani katon mudubi Mai dauke da wani irin zanne ja Tayi surutai ta ajiye a gaban Hajaran da Safiyya. Sai ga wata Mata ta Bayyana sanye da bakakken Kaya Fuskarta gwanin ban tsoro. "Wannan itace mahaifiyar Murja ko ni ban Isa Naja da ita ba Dan Haka ki bar zancenta Dan idan ta gano daga ke har Ni sai ta kashemu idan kina da wani Abun ki fada kawai Banda wanan" "Yanzu Bazan iya d'aukar fansar abinda Murja tamin ba kenan mahaifiyarta sabida babba ce itama a kungiya Mai zaman kanta"? "Abinda nake nufi kenan" Hajara tsabar bakin ciki kuka ta fashe dashi sai data gaji dan kanta tace "Dan Allah ku maidamin karfina Shugaba Ina bukatarsa" "Bazai yiwu ba Abu daya Zan Miki karbi Nan. Duk Inda kike idan Kika turara Zan bayyana ki fadamin abinda kikeso" Sai a lokacin Hajara ta Dan ji sanyi a ranta "Dan Allah inaso a dubamin Inda Naseer yake yanzu shida matarsa Naeema" Wani Abu ta watsa Akan mudubin sai ga Naseer ya bayyana a cikin mudubin Yana zaune a benci a k'ofar wani katon gida ya zurawa waje daya Ido ya rame sosai Kamar bashi ba rigar jikinsa har ta Masa yawa" "Ga danki nan ya zama driver a garin Abuja Yana neman kudin da zai dawo wajen iyalinsa. Matarsa ita Kuma tana Nan a gidansa na gadon Kaya tana d'auke da ciki har ya tsufa" Shugabarsu ta hau kwararawa Hajara bayanin komai "Wanan yarinya anyi shegiya tana so ta kashemin d'a da Ransa in Banda balai suna cikin wanan matsin zata Kara k'unsar wani cikin ba Dole ya gudu ba Amma ba komai nasan abinda zanyi ngd Shugaba idan Ina bukatar taimakon Zan turara" Suna k'ok'arin mik'ewa Safiyya tayi caraf tace "Shugaba inasan nayi aure sai dai babu mijin aure ba Wanda ya tab'a cewa Yana Sona ga Lami har tayi aure cikine da ita" "Karbi kwallin Nan duk wanda Kika gani kikaji ya kwanta Miki a Rai ki saka kwallin wuyanta ku hada Ido. Da tsananin farinciki suka dawo Duk da kasan ran Hajara ba Haka taso ba taso ko Yaya ne taci Galaba Akan Murja. A takaice kwanansu Uku suka shirya tsaf suka karbi kudi a wajen Lami suka dau hanyar kano. Naeema Sosai Nake samun bud'i ta sanadin siyar da Zobo da ruwa. Zuwa yanzu Zan iya cewa idan akwai abinda yake damuna Bai wuce rashin Naseer ba har adashe na Shiga Ina tara kudi sabida cikin da nake d'auke dashi sosai nake adduar Allah yasa Kafin na haihu Naseer ya dawo inaso na ya dawo kafin ya haihu. Cincin din danake Yi da Dankali da yamma shima ba karamin cinikinsa nake ba ahaka na Kara Tara kudi na siyi engine markade danaga layin namu babu masu engine markaden sai an fita titi. Ba karamin ciniki nake ba da Wanan engine Dan Nadeeya da Zahira indai suna Nan ba islamiya haka zasuyi ta markaden ganin Ina samun kudi ko ta Ina yasa na fara gyara gidan namu Dan dakuna biyu ne kawai gyararru siminti nada araha a lokacin hakane yasa na siya wajen goma aka fara Mana plaster banida burin daya wuce na gyara gidan idan Naseer ya dawo yaji dadi a Ransa. Kamar Wasa sai gashi nice har da pentin gidan gabadaya daga engine markade daya sai gashi na Kara ya zama guda biyu Kayan abinci kuwa sai dai Nima na bawa wani Mai bukatar. Yanzu da muka samu kwanciyar hankali banida burin daya wuce ganin mijina ko nasan halin da yake ciki har makarantar islamiyya su Zahira nake zuwa da waina na roki mallamin ya rabawa almajirai ya Tayani da Addu'a Akan Allah ya dawo min da mijina lafiya. A Haka watarana daddare wajen karfe Takwas na iddar da sallah ishai Zahira tana tsakar gida tana markade. Su Nadeeya Kuma suna tsakiyar palon Dana sakawa Leda suna home work dinsu Ni Kuma Ina daga d'akina. Haka kawai naji gabana ya yanke ya Fadi na ba gaira ba dalili hakane yasa carbina rik'e a hannuna na turo cikina na fito na tsaya a bakin kofa Ina kallon su Nadeeya jefi jefi Kuma Ina kallo tsakar gidan Sabida k'ofar Palon a bud'e yake Zahira na tsaye tana ta markaden Banko k'ofar Gidan da akayi da k'arfi ne yasa na kalli k'ofar da Sauri gabana yayi wani irin fad'uwa dana hango Umma ta shigo Safiyya na biye da ita abaya. Zahira kuwa Tana ganin ta ta saki robar hannunta ta kwaso aguje ta shigo palon ta buya abayana jikinta na rawa. Umma da Safiyya kuwa a tsakiyar gidan Suka tsaya suna karewa koina kallo. Ni kuwa sallati kawai nake jikina na rawa......... *Nagode da kauna Allah ya saka da alheri ya bar zumunci Ina mutukar Kaunar Mai kaunata Fatima salis da Umma misbah Allah ya biya muku bukatanku na alheri Allah ya bar zumunci ga masu neman lambata ido rufe ga lambata Nan Mata kawai pls 08033719070* [6/26, 6:13 PM] +234 706 571 7620: *NAGA TA KAINA* *NA SADNAF*🌸🌸 ®️ *_PURE MOMENT OF LIFE WRITERS_* _{We Don't just entertain nd educate we also touch the heat of readers P.M.L}💪🏻_ *Free Novel* *Page 28* Ban kawo Zan siyar da duka kosan ba sai gashi kafin Tara na siyar gabadaya har Ana Kara tsayawa a tambaya ko da akwai. Zahira sai washe baki take tana murna cinikin da mukayi. zazzabin daya rufeni da k'arfi yasa na dauki gwangwnanin kudin na bawa Zahira umarnin ta kashe itacen ta shigo da komai. Daki na shige na kwanta na rufe kaina. Dan Sosai Nake Jin wani irin Sanyi Bansan Mai yasa wanan cikin yazomin a Haka ba Dan ban fiye laulayi ba iyakacina zazzabin dare Ina tashi Kuma shikenan Amma wanan kuwa amai da zazzabi nake wuni har dan yawu nake yi Wanda duk cikin da nayi ban taba yinsu ba. Zahira kosan Dana zuba musu a flask ta juye musu a faranti ta had'a musu da ruwan Lipton suka Sha sai da suka Gama gyara gidan ta shigo d'akina tana min Sannu. Dan ta San banida lafiya Kosan da ta rage ta zubomin har da tea tana "Umma ki daure kici abinci sai ki Sha magani" Ganin duk ta damu yasa na mik'e da kyar na Kai kosai bakina sai dai ko uku banci ba na fara kwara amai. Sai Dana Gama nasa ta d'auko min pcm na Sha da ruwan shayin na koma na kwanta Nan da Nan bacci ya d'aukeni Zahira kuwa Bata tsaya jirana ba dayake ta Dan iya girkin ta kirba musu jollof din shinkafa a kula jifa jifa Kuma tana lek'o Ni taga ko na tashi. Bani na tashi ba sai wajen karfe daya na Shiga bandaki nayi wanka Dan na d'an ji kwarin jikina nayi Sallah na fito na tarar da Zahira da kannenta da tsofaffin littafinsu Wai Nan gwaji take basu itace mallamarsu Sai tausayinsu ya rufeni nasan suna San komawa makaranta Babu yanda zasuyi ne. Suna ganina Suka hau min Sannu na musu murmushi na zauna Ina ganin rubutun da suke. Wa zai ce yarana sunyi makaranta.mafi tsada a gadon Kaya da sharada Amma ji yanda duniya ta juya damu ko makaranta gwamnatin ma sun kasa zuwa sabida babu ko wane Gari Naseer yaje ko ya yake rayuwa yanzu dan nasan ko a Ina yake Yana can ne zuciyarsa na Nan. Gwangwanin kudin nasa zahira ta d'auko min na fito da kudin ciki na kirga kudin abinda na kashe na ware na kirga ribar da shima ba laifi mun samu. Kudin na Kara Bata ta siyomin komai na kosan gobe na saka ribar a gwangwani Dan inaso ko yayane na nema musu makaranta yaran nawa girma suke Kara yi Sai dai Mai washegari kasa tashi nayi Sabida azabar zazzabi jikina kamar garwashin wuta amai kawai nake Ina Jin jiri Kosan da ban iya fita na soya ba kenan har cikin gidan aka ringa kwada Sallama Ana nema. Kafin ma Rana tayi jikina yayi wani irin laushi ko kaina bana iya dagawa na bud'e baki ma na yiwa Zahira magana na kasa. Ina dai kallonta ta Dan gyara gidan tayi musu abinci suka ci. Ta dawo gefena tana min Sannu hannun data kawo jikina taji da zafi yasa ta mik'e ta fita. Bata fi minti ashirin da fita ba ta dawo tana "Umma ki tashi muje asibiti jikinki yyi zafi da yawa na Kira Mai taxi" Gwallo Ido nayi Ina kallonta Taya zanje asibiti banida kudi canjin wajena da ribar Bai fi Dubu da dari biyu ba Kuma shima banaso na tab'a. Bansan ya akayi tasan yawu ne a bakina ba ta nemi gwangwanin Madara ta kawomin tare da dago kaina na zuba yawun a ciki Ina "Zahira sabida mai yasa Zaki Kira Mai mota banida kudin zuwa asibtii fa ki barni na Sha magani Zan warke" "Aaa Umma gwara muje asibitin bakida lafiya sosai gwara likita ya dubaki Dan Allah ki tashi muje" Ba yanda zanyi Haka na mike tana rik'e Dani na zura hijabi muka fito ta d'auko kudi a cikin gwangwanin muka fito waje ta cewa Nadeeya ta rufe gidan Kar ta bud'ewa kowa har sai mun dawo Muna zuwa asibitin daga su dubani suka bani gado sabida jikina ba kwari Ina Kuma bukatar Karin ruwa. Abu kamar Wasa sai gashi kamar zuwa na asibitine yasa jikina ya Kara rikicewa. Duk kudin da ke ajiye a gida sai gashi duk ya kare. Zahira ke Tayani kwana ta roki makotana akan su Nadeeya zasu ringa kwana a wajensu. Kwana na hudu a asibiti na Dan ji sauki. Ahaka aka sallameni muka dawo gida. Kayan hadin kosan kuwa tuni Zahira ta girke Dan abincin da mmn Mannir ta bamu ba wani yawa ne dashi can can ba tsitsinta Mana tayi. Ganin babu kudi Kuma bbu kayan abinci yasa na fara neman yin wani rashin lafiya abinda muke dashi Bai wuce Kofi hudu na shinkafa ba sai dari da ashirin ni nasan badan rashin lafiyar Nan da nayi ba da Kila na Dan samu kudin ta silar siyar da kosai Inaji Ina gani duk burin Dana ci na juya kudin Nan ya Kare a hannuna. A ranar na kasa bacci Ina tunanin Kuma abin yi dan da kunya na Kara komawa gidan mmn Mannir to daga Ina Zan fara. Washegari sauran abincin Zahira ta dafe musu. Ni kuwa na rik'e dari da ashirin a hannuna Ina juyawa. Har d'akin Zahira ta shigo ta zauna a gefena tana "Umma ya baki Fito ba ko jikin naki ne"? "Zahira ba jikina bane Ina tunanin Inda Zan samu kudi na Kara siyo kayan yin kosai Zahira bamuda komai a gidanan abincin daya yi saura Kika dafa muku yanzu anjima daddare Mai Zakuci babu abinda ya rage mana sai dari da ashirin din hannuna shiyasa ranan nace Miki bazanje asibiti ba Yanzu Ina zanje na samo Mana abinci daga Ina Zan fara mutane sun gaji ma da taimaka min" Kamar wata babba na hau yiwa Zahira maganganu Ina kuka Itama kuwa ta hau kukan ta kawo hannunta ta karbi kudin hannuna tana "Umma wannan ma zai isa muyi wani Abun ki kawo kigani" Bata Bari nayi magana ba ta fita da hamsin tare da ajiyemin sabain. Ina zaune a daki Naga ta shigo da farin Leda irin na kulla kankara. Ta Shiga kitchen ta d'auko Kular ruwan Sanyi mu ta wanke sosai. Sai a lokacin nace "Wai Mai zakiyi ne Zahira"? Murmushi tamin ta dauki bokiti Mai kyau ta taro ruwa Dan muna da pampo a gidanmu Mai dadi kuma. Ina kallonta Naga ta dauki farin ledar ta fara diban ruwan Tana zubawa a Leda tare da kulawa. Nidai kallonta kawai nake Ina mamaki Dan Ni nasan bamuda freezer ballantana nace so take mu fara siyar da kankara. Tana gamawa ta rufe ta Kara fita Bata Jima da fita ba sai gashi ta dawo da kankara manya guda biyu ta faffasa ta zuba tana "Umma naira biyar biyar ake siyar da ruwan Sanyi a bakin titi Ana ciniki sosai anjima zanje na siyar zamu samu kudin da zamu ci abinci" "Aaa Zahira bazan Bari kiyi talla ba Ni da kaina zanje indai kinsan Ana siya" "Umma bakida lafiya fa ki Bari naje Zan iya wlh" Kare Mata kallo nayi Zahira duk doguwa ce sosai fara gashi ta ma Dan fara kirgan dangi bazan iya Bari ta tafi talla ba mutane basu da Amana Kar su yaudare min ita. "Na warke Zahira Bari ayi sallah naje ganin tana San sake Musa min yasa na hade Rai baa San ranta ba ta fice daga d'akin Cikin Dana samu na yawan Sakani Jin bacci ko Yaya naji iska ya kadani bansan sanda bacci ya d'aukeni ba. Sai wajen biyar na mike a firgice tare da yin palo da Sauri. Nadeeya da kanenta ke wasan Yar baby Da Sauri nacewa Nadeeya Ina Zahira Sai tacemin ai tundazu ta fita da kula a kanta. Banji dadi ba Dan har ga Allah Ni naso zuwa. Daki na fad'a da Sauri Na daura alwala nayi Sallah La'asar duk da jikina ba kwari Haka na fito na dau hanyar titi kafin na isa titin na hangota tana ta zabga Sauri daga yanda yake cila Kular nasan ta siyar. Tana hangoni ta nufoni da Sauri Ni Kuma na tsaya jiranta. Tana karasowa ta mikomin ledar hannunta d'auke da biyar biyar Lodi guda har da goma goma "Umma Kinga na siyar da duka har yanzu nema ake" Damke ledar nayi cikin murna Ina "Shikenan Zahira mun samu Sanaa Amma daga yau bazaki Kara fita da kanki ba da kaina Zan ringa fita" Muna karasawa gida.na zazzage kudin na kirga Naira dari uku har da Sha biyar. Kamar waccce akayiwa kyautar dubunai Haka naji. Naira dari na Bata ta siyo Mana gari da suga har da gyada Wanda zamu Sha daddare . Tana dawowa tacemin na Bata dari ta siyo min kayan hadin zobo mutane suna so Dan har tambayarta ake tayi. Kamar Wasa na Bata ta siyo komai har da suga da yake komai lokacin da sauki ba kamar yanzu ba suga ashirin ma zaiyi Kofi uku a lokacin. A ranar ban kwanta da fargaba ba Dan Ina kyautata zaton mun samu hanyar da kudi zai ringa shigo Mana Dan har kudi na bawa Zahira ta kaiwa Mai kankara akan gobe zamu karba har farin Leda na Karo. Washegari na bada kudi Suka siyo Mana koko da kosai. Da Rana ma garin muka Kara Sha. Biyu da rabi na Gama hada Zobon dayaji kayan kamshi da suga na kukula na zuba a babban kula dayafi Wanda Zahira ta fita dashi jiya Wanda Zahira ta tafi dashi kuma.na kukula ruwa muka zuba kankara Ana iddar da sallah La'asar na dau babban Zahira ta d'au karamin muka Mika bakin titi. Muna isa Kamar irin mu ake jira ko mu kadai ne masu siyar da ruwan Sanyi da zobon. Nan da Nan aka hau siya ko awa daya bamuyi ba ya Kare. Hamdala kawai nake a raina. Dan na rubanya kudin Dana kashe sosai. Daga Ni har Zahira sai murna muke. Kayan abinci na Dan tsitinta na siya Mana mukaje gida. Zahira ta Dora Mana abinci. Farinciki danake ciki kamar Naseer ne ya dawo. A takaice tundaga lokacin nida Zahira muke fita siyar da ruwa da zobo. Allah kuma.ya saka Mana albarka Dan har sawu biyu Mukeyi. Cikin wata guda sai gashi na Tara kudin da banyi tunani ba. Dama rashin kudi yasa ban saka yarana a makaranta ba. Wani karamin private school dake kusa damu.na Kai yarana gabadaya Sai dai kudin dake hannuna iya mutane uku zai Isa a saka babu kudin biyu Raheema da Humaira kuma.ya Zama Dole na saka su Tsugunna wa nayi nacewa Mai makaranta ta karbi dukansu Zan ringa mata.aikin nanny har na Gama biyanta. Cikina daya fara fitowa.ta kalla tace zan iya kuwa Nace Mata Zan iya kamar Wasa kuwa washegari yarana suka tashi tun asuba suna ta murna zasu fara zuwa makaranta Nima sai murna nake. Abincin Dana dafa musu Basu wani ci sosai ba Haka na kulle gidan muka tafi. Naci saa Mai makarantar nada mutunci duk da arniya ce Sannan Zan na musu aiki yasa ta bawa yarana uniform har da littattafai duk akan bashi. Ni kuwa na wanke band'akin makarantar na share koina sai Dana Gama naji bayana namin ciwo. Karfe daya ake tashi gabadaya yarana sai su kirani idan na Kara gyara makaranta sai mu dawo gabadaya Ina dawowa Nadeeya zata Tayani Dora musu abinci Ni Kuma a lokacin Zan huta na awa daya Ina Kara tashi sai na dau Kular zobo da ruwa Dan na sama musu makarantar Allo da biyar kawai suke kaiwa duk sati sai Dana Yi dagaske Zahira ta yarda ta fara zuwa Dan dagewa tayi sai ta ringa Tayani neman kudi. Tuni na Saba da wahalar aikin duk da cikin jikina Mai tausayi daya Saba ganina yasan Ina cikin wahalar rayuwa cikina daya fito sosai da a lokacin zaiyi wata shidda yasa wani bawan Allah ya bani shawarar danaje siyar da ruwa da zobo Akan na nemi almajiri Mai Amana na ringa Dora Masa tallan Ina bashi Lada ko abinci Dan Yana tausayamin idan yaga yanda nake Dora Abu Mai nauyi a kaina. Godiya na Masa dan tunanin hakan Bai tab'a zuwarmin ba. Ya d'auko hamsin hamsin guda goma ya bani. Kamar hadin baki Haka aka taramin kudi wanda sai Dana hau zubar da kwallar farinciki. Na koma gida cikin murna akan hanya na tsaya na Mana cefanen da zai Mana kwana biyu har da Naman Miya Yarana kuwa sai murna suke da suka ga abincin Dana dafa da.nama sai da suka koshi na fara gayawa Zahira shawarar da wani bawan Allah ya bani. Cikin farinciki tace min akwai wani isuhu a makarantarsu zata Gaya masa gobe. Ita kadai ce take da wayon sanin mutum ne a cikina Amma kannenta duk sun dauka ciwon ciki nake idan suga ga cikin Haka zasuyi tamin sannu Sosai na Dan fara samun kwanciyar hankali daga ranar da isihu ya fara d'aukar min ruwa da zobon Yana kaimin dayake yaron nada kwazo har sahu biyun yake Yi Kuma Yana da amana. Haka Zan bashi kyautar kudi na bashi abincin dare. Abinda ke fita Dani kawai shine aikin makarantarsu Zahira itama matar a Karan kanta tace na daina zuwa na bari sai na haihu. Sosai naji dadin mutuncin data min Kamar a mafarki Naga Ina wayar gari Ina cin karfin bukatun gidana ta silar siyar da ruwa da zobo na hada da siyar da kananan abubuwa a gida Yarana kuma suna zuwa makaranta islamiyya Dana boko ba abinda Zan cewa Allah sai dai godiya abinda ya ragemin a rayuwata shine ganin Naseer Yana Raina kullum dak'yar nake samun bacci Mai nutsuwa sabida tunaninsa idan kewarsa tamin yawa Haka Zan hau shafa cikina Ina tuna ranar karshen da muka rabu da shine yasa na samu wanan rabon Kaunar abinda ke cikina nake sosai inajin yana ragemin kewar Naseer idan na kalli cikina. Murja Hatsabibiya ce ta karshe kuma makira Mai fuska biyu. Wani irin wahaltacen zama Hajara da Safiyya sukeyi a gidan Dan duk Inda suke tunanin sun Kai da mugunta ko makirci ta zarce su Dan sosai take musu biyayya Agaban Tijjani Amma idan ya bada baya Haka take musu rashin mutunci San ranta. Hajara kuwa Bata tab'a tunanin bazata iya cin uban Murjan cikin sauki ba Har wani horan yunwa Murja ke musu Dan ko Tijjani ya samo abinci ya kawo ta dafa Haka zata juye a kula ta Kai d'akinta ta kankaro kanzo ta basu . Hajara kanyi zuciya Taki ci Safiyya kuwa Haka zata ci Tana zagin Murja Hajara kuwa Tana Kiran Tijjani Dan ta Gaya masa Zai daga hannu ya hau cewa baya San tashin hankali Kar tazo ta daga Masa Hankali shi bazai jure ba idan taga bazata iya zaman gidansa ba Dan Allah ta tafi sosai yake Jin Haushin Hajara sabida yasan duk masifar da suka tsinci kansu a ciki itace sila . Hajara har da kukanta Dan Tijjani ko kad'an yak'i binta sau da kafa balle yabi umarninta ya saki Murja da ta balain tsana Kamar ta jefata a wuta. Idan taso yiwa Tijjani hargagi akan zata tsine Masa idan Bai bi umarninta ya saki Murja da ba Yar arzki bace murmushi takaici yake Yana "Tsinuwa Kuma na nawa Umma Kinga fa halin da Kika jefamu akwai masifar da yafi wanan Umma ba abinda matata ta Miki bazan saketa ba. Daga Haka zai kad'a kansa ya fice Safiyya kuwa data ga alamar yunwa zai kasheta kudin mota ta nema ta tafi Calabar. Inda ta nemi Lami da itama taje wajen dangin babanta suka daura Mata aure da wani gurgu tuni ta dawo daga rakiyr Hajara ta tuba. Kwana uku kawia tayi a gidan lami Suka fara samun Sab'ani Dan Safiyya Bata rik'e girmanta na Yaya ba tuni ta Kara ficewa daga gidan. Ta koma gidan kanin mahaifinta Dan mahaifinta tuni ya bar garin tunda ya dawo hayyacinsa shi kuwa kanin mahaifinsu ya Riga yaci Dubu sai ceto ba abinda Hajara zata iya Masa hakane yasa bai k'i karbar su ba Dan shima tamkar mahaifinsu ne. Sai dai itama zuwa gidan datayi sai da sukayita fada da matar kanin babansu a karshe shima yaga bazai iya ba ya Bata kudi akan ta koma Inda ta fito ko ta zuciya ta Nemo mijin aure. Ahaka ta Kara dawowa gidan Tijjani tare da cin alwashin neman mijin aure. Sai dai dawowarta yasa Murja ta daura damarar cin ubansu Dan ta balain tsanar Safiyya sabida Bata da mutunci itama. Kwana biyu da dawowar Safiyya da safe Tijjani ya fita da wuri. Daren jiya Hajara kwana tayi da yunwa Dan Dan kanzon da Murja ta basu Nan da Nan Safiyya ta cinye hakane yasa yau ta fito da wuri ganin murja bata palon yasa ta nufi kitchen da Sauri jikinta na rawar yunwa. Ido biyu tayi da katon bredi ta Kai hannu ta d'auka cikin murna ta rufo kitchen tana juyawa suka yi Ido biyu da Murja dake mata wani irin kallo . Hajara gabanta sai daya Fadi Amma ta maze ta matse bredin a hammatar ta tana hararar Murjan tana "Na dauka nida gidan Dana k'arfi da yaji ki ringa Mana Horan yunwa Dan uwarki wlh kyalleki nakeyi bakisan wacce ce Ni bane Ni nasan baki bar Dana Haka ba asirce shi kikayi Amma wlh zanyi maganinki Bari na samu kudi nayi tafiya na dawo" Wani irin Dariya Murja ta kece dashi tana "Naji barauniyar bredi kafin kiyi magani na ki bani bredina" Ta Kai hannu ta fusgo bredin Hajara ta kwace cikin zafin nama kafin kace me sun kaure da kokawa. Murja Bata duba Wai uwar mijinta bace ta haye ruwan cikinta ta hau Kai Mata naushi ihun Hajara ne ya tashi Safiyya ta fito a guje ta hau kaiwa Murja duka. Murja kuwa ta tashi daga Kan Hajaran ta jawo safiya ta matse a hammatar ta ta hau dirkarta......... [6/26, 6:13 PM] +234 706 571 7620: *NAGA TA KAINA* *NA SADNAF*🌸🌸 ®️ *_PURE MOMENT OF LIFE WRITERS_* _{We Don't just entertain nd educate we also touch the heat of readers P.M.L}💪🏻_ *Free Novel* *Page 30* "Lailai Ashe su Naeema haka aka samu duniya mu kuwa muna can muna garari Umma Kinga katon gidan da suke fa har tsinaniyar matar Yaya Tijjani ta ringa gasamu a wancan tsinannen gidan nata" Cewar Safiyya tana zagaye tsakar gidan tare da lek'a ko'ina Umma kuwa itama karewa koina kallo take Ni kuwa ganin engine nata yi cikin Dan fad'uwar gaba na fito bansan Inda na aro jarumtaka ba na saki murmushi Ina "Umma Kune Ashe sannunku da zuwa" Na karasa wajen da aka jona engine na kashe. Daga Umma har Safiyya ba Wanda ya amsa gaisuwar da na musu illa ma cikina da suka bi da kallo wanan kallon tsanar kamar su jefani a wuta suka ringa Bina dashi nikuwa a Zuciyata na hau adduar tsari daga duk wani sharri. Bana San na wuce ciki suga Kamar rashin kunya na musu hakan ne yasa nace "Umma ku Shiga daga ciki Mana kuka tsaya a tsakar gida" "Ai ko baki fada ba zamu Shiga ciki tunda ba gidanki bane gidan Dana ne Koda kudinki Kika Gina"? "Aaa" "Ke Dan uwarki bakida wani aiki ne sai haihuwa yau Naga masifar jarrraba a gurin yarinya Nan ke kenan Ana tab'a ki sai ciki ko ya aka Dan kwana biyu ba a ganki ba indai aka tashi ganinki sai dai a ganki da ciki" "Umma Ni bakin cikina ma duk Mata take ta Tarawa Yaya Naseer Bata tausaya Masa da talaucin da yake ciki ba gashi ta Kara k'unsar wani cikin" Cewar Safiyya tana harara ta. "Haka kawai da lodin yaran Nan zaiji da Kika tarasu duk Mata zaiji ko da me kikeso yaji na ce bana San ki ki rabu da Naseer Kika k'i ke a lailai sai kin zauna shine yanzu ma halin da Naseer yake ciki Baki duba ba Kika Kara kwasar wani cikin ko to shikenan ki haifeta nagani shegiya tsinaniya Mayya" Fuuu Suka wuceni ni kuwa naji wani Abu ya tsayamin a mak'oshi sosai Raina ya b'aci da abinda Suka min Naga Yara matan Nan Allah ne ya bani Kuma cikin Nan ma shi ya bani insha Allahu lafiya Lau Zan haifi cikina sosai na ringa mamakin abinda yasa banji azabar tsoro da rawar jiki Dana Saba ji ba Dana tsaya dasu waje daya gabana ba tsinke ba Dana had'a Ido da Umma duk da na Riga da na Saba da Jin tsoronta ko Yaya ma naji muryarta Zan Dan ji fad'uwar gaba. Cikin palon na Shiga ga mamakina basa cikin palon sai muryarsu naji Yana tashi a d'akina yarana Kuma suna rak'ube a waje daya Zahira kuwa jikinta sai rawa yake Nadeeya ma kina ganinta kinsan a tsorace take daidai da Raheema da take karamarsu sai data nutsu. Idan a da ne ban Isa na Shiga d'akin ba Amma sai na tsinci kaina da shiga d'akin a tsakiyar d'akin umma ke tsaye Safiyya ita Kuma ta zauna akan gadon tana "dakuna biyu ne fa kawai Mai katifa da fanka mu dau wanan din kawai ita Kuma taje ta karata da yaran" "Aaa Aunty Safiyya Wanan d'akina ne sai dai ku zabi na d'aya b'angaren tunda a na gyara" Wani irin kallo Umma ta juyo ta min tana "iyyeee lailai wuyanki ya Isa yanka wato wanan dakinki ne sai dai mu zab'a a daya bangaren gidanki ne ko gidan Dana ke har kina da iko da gidanan har kina da Bakin zab'a Mana inda zamu Zauna iyye"? "Kiyi hakuri Umma ba Wai zab'a Muku nake ba Naga can din ma yafi Nan girma lokacin da muka dawo gidanan iya dakuna biyun Nan Naseer ya iya gyara Mana da Palo sai Dana samu kudi na gyara can din" "Ahap Umma kinji ko sai data samu kudi Ni Dama nasan Yaya Naseer da baya nan bin maza take Haba umma.kiga ga yanda gidanan aka gyara ko Ina na kyalli wlh Ni nasan a Rina karki yi mamaki ma cikin jikinta bana Naseer bane" "Innalillahi wa Inna ilaihi rajiun Innalillahi wa Inna ilaihi rajiun Aunty Safiyya wane irin magana ne wanan ya Zaki min kazafi da Kuka shigo injina nawa Kika gani ban bi maza ba Ina gidanmu bana Jin yanzu da yarana da Aurena Zan bi maza Koda Naseer zaiyi shekara hamsin Bai dawo ba Zan rik'e amanar aurensa har sai ya dawo gareni" Na karashe da Bakin ciki sharrin da Safiyya ke neman Yi min "Allah ya Miki Albarka Safiyya badan kin ganota ba da Haka zata linkemu ta cuci Dana da baiji Bai gani ba ta lika Masa cikin da ba nasa ba maza tashi kije ki shigo Mana da kayan mu" "Umma kiyi hakuri ku koma can d'akin wanan d'akina ne" Mamaki ne ya rufe Safiyya da Umma Ni kuwa bansan Mai yasa naji ko kad'an banji tsoronsu ba Taya ma sama ta ka zasu zo su rasa Inda zasu zabi su zauna sai dakina Inama laifin wani d'akin inyaso sai na Kai musu katifar su Zahira yarana su dawo d'akina mu ringa kwana gabadaya duk da tun ranar da Naseer ya bar gidanan waje daya muke kwana dasu katifarsu suke daukowa su kawo d'akin su saka a kasa su uku su kwanta akai Ni kuma da Raheema da Humaira mu kwana a Kan gadon "Kikace Nan dakinki ne Naeema da kudin ubanki aka Gina da har kike zab'a Mana inda zamu Zauna"? Safiyya tace a fusace tana doso Inda nake a tsaye "Mahaifina Allah ya Masa rasuwa aunty Safiyya Dan Allah ki daina zaginsa bada kudina aka Gina ba Amma Nima akwai kudina a cikin gyaran gidan" "Uwarki Kike jira Safiyya da Bazaki zubar Mata da hakora ba ki naushe min tsinane Nan cikin Nan Naga da wane baki zatayi magana" Kamar Mai jiran umarni tayo kaina nayi Baya da Sauri ina San juyawa Amma na rasa Mai yasa na tsaya akan kafafuna Tana isowa ta daga hannunta kafin ta sauke shi a jikina na rik'e hannunta jikina na Dan rawa "Ina Wai Mai na muku a rayuwata ne Mai na muku kuke San kuka ga bayana kiji tsoron Allah aunty Safiyya karki manta kema mace ce bakisan ya rayuwa zata kasance Miki a gaba. Ba abinda na muku Kuna ta cutar Dani Yayanki ya gudu ya barni da yayansa cikin azabar talauci ban karaya ba na zame wa yayana uwa da uba nake neman kudin da Zan kula dasu wlh gidanan dakuna biyu ne kawai gyare sai Palo da kudina na gyara gidan Rana da ruwa Haka nake neman kudi duk Dan na gyara Masa abinda ya rage Masa iya wanan Bai Isa sarara min ba sai an biyoni Nan ma an takani karku manta fa Nima haifa ta akayi" "Baki haifu ba Safiyya idan Kika Bari na karaso Baki bajeta a kasa ba" Kara kwace hannunta ta fara k'ok'arin yi kafin kace me k'ok'awa ya kaure Mana tana ta k'ok'arin harbina a cikina a ranar Zan iya cewa yin Allah ne ba yina ba kuka nake a zuciye muna k'ok'awa da Safiyya bansan ya akai na kayar da ita ba duk da sai da bayana ya amsa na hau Kai Mata duka. Umma a guje tazo kanmu da balain k'arfi ta damke kafadata ta Jani daga Kan Safiyya ta wurgar Dani ta cillo kafarta da zumar harbina a ciki sai gashi zaninta ya tad'e ta tayi zaman yan bori a kasa tana washhh bayana Dan ba karamin buguwa tayi a da kasa ba Washh wash kawai take Tana "Itama ta Shiga kungiya Safiyya yanda Murja ta zanemu itama take San zanemu" Safiyya Kara mik'ewa tayi tayo kaina Nima na mike da Sauri muka cigaba da k'ok'awan na Kara bajeta a kasa Ina kuka Ina "Kasheni zakuyi Mai na muku haka" Umma sosai ta ringa k'ok'arin mik'ewa ta kasa yarana kuwa suka shigo d'akina aguje suka hau kuka suna Jana daga Kan Safiyya da ta samu Saar kaimin naushi a cikina sau biyu a karshe dataji azabar nauyina abinka da Mai ciki Nishi ma dak'yar takeyi Hannuna ta Kama ta hau ciza hakane yasa na fusge tare da dagata Ina cigaba da kuka. Ita kuwa ta mik'e ta zauna idonta ya kad'a yayi ja sai numfarfashi take. "Zoki dagani ni nasan ba ita take da Karfin yi Miki dukan Nan ba kungiya ta Shiga Dani take maganar wlh ta janyowa kanta sai na gana Mata azaba da sai ta nemi mutuwa da kanta tashi ki dagani" Umma tace tana cije lebb'e Safiyya mik'ewa tayi tana "ba dai ni Kika daka ba wlh Zaki ci ubanki mu zuba nidake Kuma wlh d'akin nan zamu Zauna Zo ki fita damu nagani" Ta karasa tana nufar wajen Umma tare da dagata tana wash wash suka nufi bakin gado ta zauna. Ni kuwa tunda naji suna Zan ci ubana jikina ya hau rawa tsoro ya rufeni ban manta cikin Minal wuyan Dana Sha ba ban.manta kumburin da nayi a cikinta ba Ina tono wahalar Dana Sha gabana har fad'uwa yake zama nayi a d'akin Nima a kasa. Yarana suka zagayeni Umma da Safiyya kuwa sukayita zagina suna tsinemin yarana kam ta musu baki yafi cikin kwando duk Kuma a cikinsu sunfi zagin Zahira da ta d'auko komai nawa har da tsoro sosai.nake hango kiyayyar da suke Mata na daban ne ita kuwa jikinta sai rawa yake kamar ta tsaga jikina ta shige Nadeeya ita ma sai kuka take kasa kasa. "Ki tashi ki dauko Mana abinci Dan uwarki ko sai mun roka"? Umma tace tana jifana da harara Ni kuwa ko gezau banyi ba Dan gani nake idan na bar d'akin Yar tsana Mai ciki zasu binne a bakin k'ofata na hau kumbura kamar lokacin cikin Minal zuwa yanzu da zasu lura zasu ga azabar rawar da jikina yake sabida tsoro. Haka suka yi tamin magana na sharesu Suka cigaba da zagina a karshe sai Umma cewa Safiyya tayi ta fita ta samo musu abincin Banyi magana ba Safiyya ta fice ta zubo tuwon Massara Dana tuka da miyar kubewa da har dumame nayi Dan yarana suna so Kuma basu ci abinci ba. Haka suka zauna Akan gadona suna cin abinci Mu kuwa muna rab'e a gefe Raheema ce ta hau zungurina Tana Jin yunwa sai kallonsu take. Safiyya ta hau zaginsu tana basuda tarbiyya karuwai. Sai anan nayi.magana Ina "yarana ba zasu tab'a karuwanci ba insha Allahu" Kamar wacce aka tsikara na mike na nufi wajen da akwatin kayanmu yake dayake ba wardrobe a d'akin. Na hau Kai akwatuna na waje sai Dana kwashe komai tsaf ya rage daga su sai.gadon da suke.kai. Na fito da yarana cikin.kuka na cewa yarana su hau kai Mana kayanmu daya b'angaren. Dake d'auke.da karamin Palo da dakuna manya guda biyu Dan ginin gidan Kamar na mai Mata biyu Naseer yayi sai da shi lokacin wanan da muka koma shine b'angarensa Wanda na barowa Umma shine b'angarena Dana yarana. Dan gyaran danayi ma so nake na zuba Yan haya na fitar musu da kofa ta tsakar gidan ganin gidan ya Mana girma idan Ina Jin motsin mutane ma zanfi Jin dadi inyaso idan Naseer ya dawo sai na sallamesu sai gasu Umma sun duro. Har tarkacen d'akin su Zahira sai da muka kwaso daga b'angaren Na dawo dashi b'angaren Naseer na saka katifar d'akinsu a daki daya Zahira ta.musu shimfida. Ni kuwa na Shiga kitchen na juyo musu tuwon a faranti da Miya har da ruwa na kullo kitchen din Abinka da Yara Basu ma.wani San Mai ke faruwa ba sai zahira Nan da Nan suka hau ci. Zahira.kuwa sai Daka Mata tsawa ta yarda ta fara ci Dan sosai ta Shiga damuwa da hawayen dake zubomin Ina daukewa haka na zauna Ina tunanin masifar dake neman kunno min tashin hankalina Bai wuce karsu cutar Dani ba Kar bacci ya d'aukeni su biyo dare su caka min wuka gashi Naseer baya Nan. A Haka nayi zurfi a tunani har bacci yayi awon gaba da yarana Zahira ta gyara musu kwanciyarsu. Tare da.kunna musu maganin sauro. Sai data tab'ani na dawo daga duniyar tunanin Dana tafi. Abincin da suka ci Suka rage ta kawo gabana cikin karyayar murya da tayi kasa.dashi sosai ta hau magana tana "Umma kiyi hakuri kici abinci insha Allahu ba Abunda zasu Miki" Maganarta kuwa kamar tunzurani yayi na hau rera kuka Ina Mata surutai Kamar wata babba na hau Bata labarin irin abinda su Umma suke min Dana rasa Mai na musu suke San kasheni" Bansani ba ko kwakwalwarta zata d'auki maganganuna kuka kawai take itama Ni kuwa na mike na fito karamin Palo Naga ko sun fito daga d'akina sai dai Ina lek'awan Naga har sun turo k'ofar sun rufe Kamar d'akinsu. Ina mamakin Halin Umma da Safiyya k'arfi da yaji sun kwace min d'akina. Haka na koma dakina Ina Jin inama inada halin da Zan samu kudi Mai yawa a daren Nan na kwashe yarana na bar musu gidan. Tunda na samu ciki Ina da Jin bacci ina Kuma bacci Mai nauyi ban fiye tashin dare ba idan bacci ya d'aukeni Amma zuwansu Umma yasa na nemi baccin na rasa Zahira itama haka ta zauna wajen karfe daya na dauro alwala Ina kallon Zahira ta biyoni itama tayi alawalar tazo gefena ta tsaya muka hau nafilfili. Ban iya yin raka'oi Mai yawa ba na zauna na dau carbi nayita sallati da istigifari har lokacin hawaye Bai d'auke daga idona ba sosai na saka a Raina a wanan lokacin da wasu ke bacci Ni Kuma na zo gaban Mahallicina ina kuka zai magance min damuwata A da Inada Allah Ina da Naseer Amma yanzu banida kowa sai sarkin sarakai da baya zalunci da idan ka Kai kukanka wajensa zai magance maka damuwar ka Ni nasan badan baya sona nake rayuwar azaba a gidan Naseer ba yanda ya halliceni Haka ya hallici Umma dake neman rayuwata shi Zan kaiwa kararta yamin maganinta yau ko Umma tayi nassarar kasheni nasan a rubuce yake a ita zata zama silar mutuwata Dan kowa da hanyar tafiyar sa. Tsabar Jan carbi da adduar zuci sai da yatsuna Suka hau ciwo. Inajin Zahira na adduar "Allah kasa Kar suyi wa Umma komai Allah ka dawo da Abban mu lafiya Allah kasa Kar su cutar damu su cutar da Ummana" Ahaka ta Gama hada Addu'ointa bacci ya d'auketa Nima bansan lokacin da bacci yayi awon gaba dani kaina jingine da bango ba *2am* Hajara ce zaune da Safiyya a tsakar d'akin da wani bak'in tukunya suka dibi abinda shugaba ta basu Suka watsa take hayaki ya fara gauraye d'akin Shugaba ta bayyana da fitila a hannunta Safiyya da Umma Suka zub'e a kasa Umma ta hau magana "Naeema yau dukan Safiyya tayi Nima ta zubar Dani a kasa a sanadinta nayiwa Dan cikina mugunta ya rasa komai nasa na tsani yarinya Nan Shugaba banida burin daya wuce na Gama da ita na huta inaso kimin aikin da jini zai balle Mata tayi ta zubar jini har ta mutu yau yarinya Nan har gadara take ta gyara gidan Dana so take ma ta nunamin gidan nata ne" Hannu kawai ta mik'a mudubi ya bayyana ta ajiye agabansu tayi surutai sai ga Naeema ta bayyana ita da Zahira akan Sallaya suna sallah tana k'ok'arin magana Hoton Naeema da Zahira ya d'auke mudubin ya fara tsagewa . Shugaba kuwa ta duka ta d'auke mudubin tana "Ina zaune zaki janyomin balai wannan yarinya fa aiki akanta zaiyi wahala matsawar zatayi sallah dak'yar duk abinda zaa Mata ya sameta ki duba kiga daka ganin ta mudubi ya tsage Amma karbi wanan ki jarraba zuba Mata a abinci indai ta Kai bakinta sai dai ku hadu a lahira" Ta jefawa Hajara wani Leda Mai dauke da garin magani. Daga Haka ta b'ace Hajara taja Tsaki Tana "Ni matar Nan ma.bana Gane Mata wlh yanzu kamar itama Bata da wani k'arfi kame kame kawai take" "Mu jarraba zuba Mata mugani dai" Haka Suka zauna suna kulla sharri da yanda zasu kawo karshen Naeema "Ni kuwa mafarkai nayita Yi a hargitse Wai Umma sun shigo d'akina da wuka zasu kasheni Cikin Ikon Allah na samu na kwace wuk'ar suka fita a guje na bisu. Bayan nayi wanan nayi mafarki da mahaifiyata yanda na Saba ganinta ta daura alwala ta hau kan Sallaya ta daga hannu tana ta rokon Allah na Dade ban ganta a mafarki na ba bansan fassarar mafarki ba Amma zuwa yanzu nagane indai Ina cikin matsala ko Zan Shiga matsala sai nayi mafarki da Ummata tayi alwala tana adduar Wanda Ni na fassara Haka da tana nuna min na dage da Addu'a in ta gayawa Allah. Wajen hudu na farka baccin da ban koma ba kenan. Har sai da akayi sallah asuba yarana ma har sun Saba tare duk mu kayi Sallah zuciyata fes ba tsoron komai muka fita kitchen nida Nadeeya. Zahira Kuma ta hau yiwa su Naeema wanka. Cikin awa daya na Gama soya musu Dankali da tea har da jollof din shinkafa na juye a babban coleer na samu cooler madaidaiciya na zuba wa su Umma duk abinda na dafa. Na bar musu a kitchen din na dauki namu na Kai d'akina. Haka kawai na tsinci kaina da kwashe kayan abincinmu har Mai na Kai d'akinsu Zahira da kayansu yake ba katifa iya ashana kawai na Bari da kwandan kwanuka. Kafin takwas tayi har Zahira ta Tayani tace zobo ta had'a sun hada hannu ita da Nadeeya sun kulla zobon cikin kular biyu Dan Haka suke Tayani kafin su tafi makaranta. Ni Kuma idan na tashi sai na kula ruwan Isihu idan yazo sai ya amso kankara na watsa sai na bashi abinci safe karfe Sha biyu yake zuwa ya d'auka wajen biyu ya sake dawowa na basa abinci na bashi na biyu wajen hudu ya dawo.ya kawomin kudin sai Kuma gobe. Karfe bakwai da minti hamsin na raka yarana makaranta bayan na kulle k'ofar daya Shiga babban palon da zai sadaka da b'angaren Dana koma. Masu markade kuwa sun fi goma suna jirana sai Dana ga sun Shiga makaranta na dawo. Na cire hijabina na kunna engine markaden daya kasance na wuta lokacin Wanda ake sawa fetur Bai fito ba inaga. Ina markaden Ana Kara tururuwa zuwa a irin wanna lokacin idan Isihu yazo daya engine yake kunnawa ya hau Tayani ahaka har mu Gama idan nagaji Haka zai cigaba sosai nake Jin Isihu a Raina kamar Ni na haifeshi Ina Kara Jin shaawar inama na haifo namiji Mai irin kokarinsa har gobe Isihu tamkar Dan cikina nake Jinsa. Ahaka na zauna a gefe Ina satar kallon su Umma da suka fito babban Palo suka.zubomin Ido suna ta kallona. Har layi ya fara raguwa robar custard din da nake saka kudin markade har ya cika. Sai da isihu ya Gama markaden ya kashe engine ya kawo robar custard din gabana Ni kuwa na bud'e na dauki ashirin na bashi nace ya siyo koko da.kosai ya Sha Dan tea da Dankalin ya Kare. Da sauri yayi waje Ni kuwa na bud'e robar na hau hada kudina Ina jerawa sai Dana gama tsaf na hau kirgawa Kudin a wajena yake Amma Umma da Safiyya dasu na kirga kudin suna gwallo Ido Kamar basu tab'a ganin kudi ba sosai suka ringa mamakin yawan kudin hannuna. Ni kuwa Ina gamawa na mike da kudina a hannu Na shiga babban palon na dauke kaina kamar ban gansu ba "Ke Na fa ga alamar kin Raina Ni Dan uwarki wucewa zakiyi batare da kin gaisheni ba Wai dame kike takama ne Naeema karki ga kinyi amfani da tsafi kin daki Safiyya jiya wlh kikamin da kaina Zan dakeki" "Ina kwana Umma" Nace Ina cigaba da tafiya "Zaki bamu abinci ko sai mun roka"? Ta Kara cewa tana jifana da harara "Abincinku na Kitchen Umma" "Kinfi karfin ki dauko Mana kenan" Ban tsaya ma Kara Bata amsa ba na zura hannu a zanina na dauko mukulli na bud'e k'ofar karamin palon na shige. Inaji suna ta Auna min zagi. Ina Shirin Zama naji masu kawo markade suna ta Sallama kudin hannuna na ajiye a cikin akwatina Na fara k'ok'arin fitowa naji Safiyya na "Wlh umma kin cucemu ji lodin kudin hannun Yar iskar matar Nan Ni na tabbata kudin Yaya Naseer ne ya koma wajenta yanzu ita ta zama.mai kudin" Dalla tashi kije ki faki Ido ki zuba Mata maganin kafin ta fito. Girgiza Kai nayi na bud'e kofa Safiyya tayi sauri ta koma ta zauna tana boye maganin a bayanta Ban kalli.inda suke ba na fita na Kara kunna engine na fara markade Ahaka har Isihu ya dawo ya cigaba da Tayani Ni kuwa nace Masa idan ya gama ya kawomin kudin d'akina. Ban kalli Inda suke ba na Kara komawa d'akin Ina mamakin halinsu wato har yanzu nemana suke da sharri Allah ya taimakeni na kwashe komai daga kitchen din Ina Shiga d'akin Safiyya ta mik'e da Sauri ta Shiga kitchen kulolin data gani Bata tsaya dubawa ba ta bud'e shinkafa ta watsa maganin Haka ma Dankalin ta fito ta dawo ta zauna. Suna kallon yanda ake ta kawo markade Isihu kuwa sabida kwarewa injina biyun ya kunna Yana tayi hakane yasa Nan da Nan ya Gama kudi ya Kara cika rubber custard har da gwangwani Sai daya wanke wajen ya dauki rubber custard din da gwangwani ya nufo b'angarena ganin bakin fuska yasa ya hau gaishe su ya hau raba Ido yaga ko Zan fito daga d'akina Safiyya kuwa mik'ewa tayi ta nufi wajensa tana "kawo a Kai Mata" Isihu da wayonsa ya kamkame rubber custard da gwangwani yana "hajiya nake nema" Ita kuwa a hasale ta kai hannu ta kwace gwangwani a daidai lokacin Dana fito danaji muryar isihun Ina fitowa Umma ta mik'e tayi daki Safiyya har da gudunta Dan su shige daki. Cikin zafin nama na saka gudu tana dab da Shiga d'akin na damke kafadarta na juyo da ita tare da kwace gwangwani da k'arfi "Ina akan me Zaki daukemin kudi"? "Wlh idan baki danne ta kin kwace kudin Nan ba sai na tsine Miki"........ *Huuuh Ashe Haka nake da masoya har gajiya nayi da amsa waya toh ngd da soyyaya da Kauna Ameenat abdlouye ngd Allah ya biya miki bukatunki na alheri* *Wnan Shafin sadaukarwa ne ga duk masoyan Naga ta kaina da masu Kaunar Naeema da ita kanta Sadnaf din mungode sosai* *DAGA PAGE ONE ZUWA 30 WANE DARASI KUKA DAUKA A LABARIN NAEEMA MAI YAFI BAKU MAMAKI DA ALAJABI MAI YAFI BAKU TAUSAYI TSAKANIN NASEER DA NAEEM WAYAFI SHAN WAHALA DISCUSS KO BAMA GRP DAYA IDAN KAYI ZAAYI FORWARDING YA ISA WAJENA DA NAEEMA NGD* [6/26, 6:13 PM] +234 706 571 7620: *NAGA TA KAINA* *NA SADNAF*🌸🌸 ®️ *_PURE MOMENT OF LIFE WRITERS_* _{We Don't just entertain nd educate we also touch the heat of readers P.M.L}💪🏻_ *Free Novel* *Page 31* "Kiji ki da wani magana ke ki matso ki danneta ki kwace kudin kina kallon yanda muka kwashe da ita jiya ta Taki wani Abu ba tsoronmu takeji ba yanzu tsinaniyar ban shirya ta danne Ni ba da sasafen Nan "Ke dai anyi matsoraciya asarariya bani guri" Ni kuwa juyawa nayi na nufi wajen Isihu na karbi robar custard din hannun Isihu Ina juyowa Naga Umma a gabana ta balain had'e Rai cikin mugun kallo ta mik'o min hanun tana "Tafi da kudin robar ki bani na gwangwanin Nan dan Ni nasan da kudin Naseer kika siyi engine dinan" Ja da Baya nayi na kamkame kudina Ina "Umma bada kudin Naseer na siyi engine Dina ba na Sha wahala kafin na iya siyan engine Nan da shi asirina yake rufe Dana yarana da Naseer ya gudu ya barni Dan Haka bazan iya Baki kudin Nan ba Naseer watansa bakwai da sati biyu kenan da tafiya Bai barni da ko sisi ba Umma a Haka na ringa bin gida gida Ina neman abincin da xamu ci kafin Allah ya dubeni ya kawomin hanyar Dana samu kudi har na siyi engine dinan Umma kudina ne bana Naseer ba" Nace na juya da Sauri Ina k'ok'arin nufar karamin palon ta jawoni da Karfin tsiya ta kawomin duka cikina na kauce cikin zafin nama "Dan uwarki rashin kunya zakimin yaushe Kika zama Haka?mai Kika taka da har Zaki iya tsayawa agabana ki ringa fadar duk abinda ya fito daga bakinki indai ba karuwanci kikayi da Naseer baya Nan ba babu yanda Zaki iya siyan injina har biyu nama ji dadi da kikace ba kudin Naseer bane duk lokacin da ya dawo wlh sai.ya sakeki shegiya fitsarariya wlh zanyi maganinki a gidanan ba dai Dani kike ja" To karashe tana Kara kawo hannunta jikina na kauce tare da nufar karamin Palo ina cewa Isihu ya zo ya sameni Ina Shiga d'akina kuka na fashe dashi Dan har ga Allah Umma da Safiyya sun isheni na gaji da halinsu shekara goma Sha biyar Ana Abu guda sun ki rage kiyayyar da sukemin a yanzu ma da Naseer ya gudu ya barni bazasu sarara min ba Karo na farko da naji Haushin guduwar da Naseer yayi ya barni sosai na ringa Shan alwashin matsawar zasu cigaba da takuramin wlh siyar da gidan zanyi batare da saninsu ba na gudu da yarana Dan bazan tafi na bar musu gidan ba gwara na koma.garinmu na zauna da yarana a gidan mahaifina tunda Shi kansa Wanda nake zaman aurensa talauci yasa.ya gudu ya barni Hawayena na share na fito na samu Isihu dake ta rafka Sallama na dauko wani Dan jaka da nake Tara kudina tare da rubber custard da gwangwanin cinikin da mukayi yanzu na zauna Akan tabarmar dake shimfide a kasan palon na hade kudin na kirga Naga ba laifi kudin da yawa. D'agowa nayi nacewa Isihu "Kasan Inda ake siyar da katifa babba irin wannan da muke kwana akai"? Nace Masa ina Nuno Masa d'akin da muka kwana Gyad'a min Kai yayi. Ni kuwa nace yaje ya tambayomin ya dawo cemin yayi Bari ya fara min wanke wanke kafin ya tambayomin Sai a lokacin na tuna baiyi wanke wanke ba Dan har wanke wanke Isihu kemin Sanin kwanukan da muka Bata na dakina yasa na tashi na dauko kwanuka da kofuna da su Zahira suka ci abinci na kawo Masa shi kuwa ya kwashe ya fita wajen kitchen din ya hada wanke wanke ya fara Yi. Su Umma kuwa sai harararsa suke jira kawai suke Naeema ta fito ta dauki abincin da suka zubawa magani suci tsabar mugunta ma yunwar suke ji amma sunfi San ta fara d'aukar abinci taci kafin su d'auko abincinsu. Suna kallon Isihu ya Gama wanke wanke ya Kai kwanukan kitchen ya had'a kulolina masu kyau da yawanci ba a kitchen nake barinsu ba daki nake kaiwa har Wanda na zubawa su Umma abinci a ciki shi kuwa ganin akwai abinci a flask din Dana zubawa su Umma yasa ya bar abinci ya taho min da Wanda ya wanke Bangarena Yana shigewa su Umma suka hau murna ya kawomin abincin da suka zuba magani. Ina karbar kulolin na Kai d'akina shi Kuma ya wuce wajen Dana aikesa. Yana fita Safiyya ta nufi kitchen cikin farinciki har.da.wake wakenta ta dauko flask din Dankali da tea d'in Wanda ba Dan rufewar ido ba da yaci ta Gane shine Wanda ta zubawa maganin Dan iya abincinsu ne a kitchen shayi ta zuba musu tana "Umma ai yau sai dai wata Naeemar Kuma su Naeema sai dai Kuma a lahira nidai tana tafiya kudaden Nan Zan debo shegiya Mayya a karshe dai zamu huta da naci" Ta Kai Dankalin bakinta Umma kuwa tsabar murnar cikar burinta a koshe ma take jinta kunnuwa kawai ta baza tana jiran ta fara jiyo ihun Naeema. Safiyya kuwa sai Loma Dankali take tana Shan Shayin dan murna ma tayi da Hajaran Tak'i cin abincin Dan ita Tana da balain ci hakane yasa ta cigaba da Jan Umma da Hira mutuwar Naeema Cikin kankanin lokaci ta Gama cinye duk yawan Dankalin Umma kuwa sai data Kai hannu Dan ta dauko taga wayam ta hau surfawa Safiyya Zagin cinye Dankalin da tayi Safiyya na k'ok'arin Magana taji wani irin azababen ciwon Mara daya kusa d'auke Mata numfashi Hannu biyu ta Kai ta dafe cikinta tare da kurma ihu Jkinta ya hau wani irin rawa da jijjiga Hajara kuwa hankali a balain tashe tayi kanta tana ke me Haka"? Birgima kawai Safiyya ta ringa yi kafar ta na jijjiga kafin kace me wani irin mahaukacin jini ya balle Mata Wani mugun ihu Hajara ta kwalla. Ni kuwa da bacci ya fara fusgata ihun Umma yasa ni mik'ewa hankali a tashe nayi waje da Sauri. Umma kuwa ihu take Tana "Abincin Naeema Kika dauko Kika ci Safiyya na Shiga uku na lalace" Ni kuwa jikina ne ya hau rawa Dana ga irin jinin dake zuba a jikin Safiyya da cikin ta ke wani irin zillo shi kadai. Cak na daskare waje da naji maganganun da Umma keyi cikin fitar hayyaci Ashe Ni suka so naci abincin Nan bansan sanda na durk'ushe wajen kuka na kwace min ba Wai Mai nayiwa mutanen Nan suke Neman rayuwata. Da yanzu Ni Zan ringa zubar da irin wanan jinin da Safiyya ke zubarwa toh garin ya ma.suka dauko abincin da da kansu suka zuba maganin Ina kallo Umma ta shige daki aguje tana Shiga d'akin cikin rawar hannu ta d'auko Abunda suke turarawa ta zuba a bakin tukunya jikinta sai rawa yake tana Shugaba ta rufa Mata asiri yarta zata mutu Sai da hayaki ya gauraye d'akin ta bayyana cikin ihun kuka Tana ta taimaka Mata Safiyya ce taci abincin da suka barbadawa magani Jini sai zuba yake a jikinta. Shugaba b'acewa tayi Hajara ta Kara kwashe da ihu da kuka bayan Yan mintina sai ta Kara bayyana ta mik'a Mata wani ruwa a kwarya tana "Kiyi Sauri ki zuba Mata a jikinta" Wani irin fusga tayiwa Kwaryar Bata tsaya jiran sauran zancen ba tayi palon tana zuwa ta watsawa Safiya da jikinta ya Dan fara saki jini kuwa Kamar an yanka Dan Saa sabida yawa. Take kuwa jinin ya tsaya. Safiyya tayi wani irin fari fat Kamar matacciya idan ba Kura ido kayi ba zaka dauka mutuwa tayi. Wani irin Ajiyar zuciya Umma ta sauke ta dago da rinannun idonta ta kalleni da Nima ita nake kallo Idan a da ne kallon Nan da takemin na iya sawa na fara nakudar da ban shirya ba Tana k'ok'arin Magana na Riga ta fara magana kasan zuciyata Ina Jin dadin tsorona daya ragu "Umma Raina a hannun Allah yake ba a hannunku ba duk yanda Ku so ku kasheni idan lokacin tafiyata baiyi ba babu yanda zakuyi Koda kuwa zaku Haka ramine ku binne ne duk tsawon lokacin nan Umma da kukemin abubuwa Allah na tsallakar Dani yaci ku hakura ku kyalleni Umma kin min horar yunwa ban mutu ba Umma kin kumburani ban mutu ba kin zuba min guba a abinci ban Sha ba kuka rufeni da duka Umma kin hayo yan d'abba har gida Dan su kasheni Allah ya tsallakar Dani kinyi abubuwa da yawa sabida kiga bayana Allah Bai nufa ba Mai na Miki da zafi Haka ?Mai laifina laifine Dan Ina Auren Naseer Umma tun lokacin Dana haifi zaheera Kika so rabamu Allah baiyi ba Taya Zaki raba auren da Allah ya raya bayan Zahira.na haifi Nadeeya Minal Humaira da Raheema ga cikin na shidda a jikina duk wanan Bai Isa ki Gane auren nida Naseer Bai Kare ba Sabida rabon dake tsakaninmu ya zakiji yau idan aunty Safiyya tayi aure mahaifiyar mijinta na gana ma ta azaba Tana neman rayuwarta yanda kike San Aunty safiyya har Kika rude da Kika ganta a cikin wannan halin Haka iyayena suke Sona Umma mutuwa ta rabamu Inda iyayena suka je kowa ma sai yaje Koda banida kowa Umma ai inada Allah daya halliceni Umma tunda na auri Naseer ba dadi nakeji ba ba wani dukiya na Tara ba shekara goma Sha biyar Ina cikin wahalar rayuwa Ina cikin tashin hankali da fargaba Mai zai sameni idan Allah ya tsallakar Dani daga wani mugun abin da Kika so ya sameni Umma iya sanina ban miki komai ba laifina daya Dana auri Naseer na Haifa masa Yaya Ni ba bakin haline Dani Ni ba wani abu nake ba da zakice shine dalilin daya sa bakya Sona Kika tsaneni Umma Akan tsanar da kikamin Kika yiwa Naseer Baki komai nashi ya Kare har sai data Kai shi da guduwa ya barni Umma yau idan kikayi nassarar kasheni menene ribarki Umma. A yau abinda ya faru yasa na Kara gasgata irin tsanar da kikamin a Kuma yau zan miki alkawarin rabuwa da Naseer har abada Umma kimin hakuri na haihu tukunna a yau Ina haihuwa naji kwarin jikina zan d'auki yarana na bar miki gidanan na bar rayuwar Naseer har abada" Na karashe kuka nacin karfina. Na dauka kalamai na zasu saka Umma jkinta yayi sanyi ko taji tausayina sai dai maganar daya fito daga bakinta yasa na tsayar da kukana Ina kallonta "Ai ko kin tafi yanzu ban samu cikar burina akanki ba a sanadinki ba wahalar Da ban Sha akanki ba Dana ya daga hannu ya mareni ya nunamin ya gwammace ya rabu Dani mahaifiyarsa daya rabu dake fitarkin shine ki kwashe yaran naki ki bar gidanan kqmar yanda Kika fada idan ba Haka ba sai na samu cikar burina akanki Zan samu kwanciyar hankali bana kaunarki bana jin akwai ranar da Zan kaunaceki na gwammace ya auro koma wacece da dai ya cigaba da zama dake Ban taba ganin yarinya mai taurin Kai irinki ba gashi sai cika gidan Naseer kike da mata marasa tarbiyya masu irin halinki kiyi addua Kar wani Abu ya Samu Safiyya idan ba Haka ba zakiyi mamakin abinda Zan Miki "Wane dare ne jemage Bai gani ba Umma mai zakimin da zai zame min sabo magani kuka zuba abinci Dan naci Allah ya tsareni ya Dubi zuciyata Ita data zuba garin magani da kanta Kuma ta d'auko abincin taci iya wanan ya Isa kigane Umma Allah ba azzallmin sarki bane Koda wani Abu ya Samu Safiyya ita ta jawowa kanta Dan ta Haka Ramin da Zan fada da zurfi sai ya zama itace ta fada" Fuuu ta taso tayo wajena abinka da Mai ciki kafin na mik'e har ta iso ta rufeni da duka tana zagin uwata da ubana wai.maganar da nake Mata rashin kunya ce Nidai fuskata da cikina kawai nake ta karewa Ina cigaba da Magana cikin kuka da a ce Safiyya ce zanyi k'ok'arin Rama dukan da tamin Amma wanan mahaifiyar Naseer ce bazan iya ramawa ba ko maganar da nake ta fada Mata baa San Raina nake fada ba Dan gani nake dgske rashin kunya nake Mata Amma Naga sai nayi maganar Zan jin sanyi a Zuciyata sai data gaji Dan kanta ta kyalleni na mik'e dak'yar na Shiga d'akina jikina namin ciwon dukan da Umma tamin. Kuka nayita yi Ina tunanin Abunda ya dace nayi Sosai nake ji Kamar na hada kayanmu a goben Nan mu bar musu gidan. Sai dai karatun yarana da suke tsaka da yinsa suna Kuma Jin dadinsa na hau tunani yanzu suna zango na karshe da zaayi canjen aji Zahira ta tafi primary 4 badan rayuwa data juya ba yaci ace tana jss 2 Nadeeya Kuma tana primary 3. Shigowar Umma a fusace yasa na mik'e zaune Dan a kwance nake dube dube da hau yi bance Mata komai ba ta hau daddaga kayana tana watsi dasu. Nidai Ido na zuba Ina kallon ikon Allah sai data hargitsa d'akin ta juyo a fusace ta mik'amin hannu tana "Bani Kudi Zan Kai Safiyya asibiti Dan ta zubar da jini da yawa Ina binki cikin Salama Naeema kulleki a d'akin Nan na banka Miki wuta ba wahala zaimin ba Maza bani kudi karki batamin lokaci. Sauka nayi daga Kan katifar na d'aga na Ciro kudin da na kakkasa a.karkashin katifar na zaro dayake ware biyar biyar goma goma.har zuwa hamsin nayi cikin Ikon Allah kuwa biyar biyar din na zaro.ina k'ok'arin duba kudin ta fusge daga hannuna tayi waje. Inajin motsin fitarsu a daidai lokacin da Isihu ya dawo Ni kuwa na mike na fita jinin palon Naga Yana bi da kallo Ni kuwa na bashi umarnin ya wanke palon gabadaya Ina tsaye a bakin kofar karamin palon ya wanke palon sai karni ke tashi hakane yasa na saka ya amso min garwashi muka saka turare wuta Nasa ya Shiga karamin Palo na zubo Masa abincin da lokacin tafiya da ruwa.da.zobon yayi. Sai daya fara ci ya ke gayamin kudin katifar dana saka ya tambayomin. Ban ce Masa komai ba Dan yanzu Bata katifa nake ba wani abune Kuma a Raina. Sai daya gama cin abinci ya fita da ruwa da zobon da sukayi sanyi sosai akwai wani shima dake tayashi dauka Suka tafi Ina nan a zaune su Zahira suka dawo. Sukaci abinci suka Kara gyara gidan har lokacin su Umma Basu dawo ba. Har Isihu ya dawo ya Kara fita da wani ruwa da zobon. Zahira da Nadeeya kafin su tafi islamiyya.suna ta Tayani markade sai da lokaci yayi suka.shirya.suka tafi. Na cigaba da markaden wajen hudu da rabbi Isihu ya dawo lokacin na Gama markaden na hade Kan kudadena na zuba su a Leda Dana kasan gadon na canza musu wajen ajiya. Na saka hijabina na kulle gidan na nufi makarantarsu su Zahira. Mallam ala ramma shine babba a makaranta Yana da balain mutunci Isihu na saka ya kiramin shi Yana zuwa na tsugunna na gaishe.shi shima sabida sanin darajar mutum Haka shima ya zub'e yasan komai a Kan gidana yasan babbnsu Zahira baya Nan Ni na fada Masa sabida shima sananne ne a unguwar Kar Yan unguwar suga ba namiji a gidan su Raina min hankali. Koda yanzu shawara na yanke Na Masa magana Ina bukatar ayimin sauka a gidana ko na kwana bakwai ne sabida Allah ya Kara tsareni daga sharrinsu Umma da lokacin da Naseer ke Nan ne da sauki yanzu daga Ni sai yarana Ina bukatar tsari daga sharrin masu sharri. Banma Gama iddawa ba yace min Kar nadamu zai turo yaransa su ringa zuwa karfe Tara suna karatun Qurani a gidan karfe goma sai su dawo zasuyi Haka har tsawon kwana bakwai zai Kuma ringa min addua daga nan Akan Allah ya saukeni lafiya ya dawo da mijina lafiya. Godiya na ringa Masa na dauko kudin sadaka na bashi ya dage bazai karba ba ahaka na dawo gida Ina Dan Jin nutsuwa insha Allahu albarkacin Quranin da zaa sauke a gidan ba abinda su umma zasu min. Tundaga nesa na hango masu markade da Umma da.safiyya a zaune a k'ofar Gidan.umma Nata magana tana yarfa hannu alamar masifa take sun dawo na fita na kulle gidan Safiyya kuwa ta Yi wani sanyi kalau Dan kwance ma.take jikin Umma Ina karasawa Umma.ta hau zagina wai.na tafi.karuwanci na kulle gidan bazata laminta ba daga Yau idan Zan tafi gantalina Kar na Kara kulle mata gida Agaban wayanda Suka kawo markade tayi ta zagina har na bude na Shiga suka shigo ni kuwa na kunna engine na fara markaden Ahaka na bawa banza ajiyarsu Safiyya Bata iya magana sai Umma Sai wajen Shidda na Gama markaden a daidai lokacin dasu Zahira suka dawo Muka Shiga babban palon gabadaya Zahira na hada Ido da Umma ta zub'e ta hau gaisheta. Kannenta take suma Suka zub'e suna gaida Umma.Minal ce ta tsaya cak Bata zub'e ba hasali ma cunno bakinta tayi ta kau da Kai. "Shegu Yan iska marasa tarbiyya uwarku duk ta koya muku munafinci da gulma ke Dan uban uwarki wa.kike cunnowa Baki"? Umma tace tare da mik'ewa su Zahira kuwa kafin ta karaso suka baje Suka shige Palona a guje. Amma Minal ko gezau batayi ba Ina tsaye Nima a bakin kofar mamakin abinda Minal din tayi nake. Umma kuwa Tana Isa wajenta ta rufeta da duka Ni kuwa na runtse idona inaji kamar Ni take bugu sai cewa Minal take tsinaniya Minal ko tari batayi ba ballantana tayi kuka kafa ta daga zatayi ball da Minal sai gashi kamar Jiya zaninta ya tadeta ta tafi gabadaya akan fusktarta ta Fadi. Minal dariya ta kyalkyale dashi ta nufo palona a guje tare da tureni danake bakin kofa Umma.kuwa ta dago tana rik'e da bakinta data Bugu sosai ta hau zagin Minal "Tana tsinaniya yarinya Mara albarka Zan kamaki idan uwarki ce ma ta zugaki kikamin Haka akanta Zan Rama ke Kuma zaki.bamu abinci muci ko sai mun roka" Bance komai ba na juya na Shiga palona Ina zuwa na rik'e hannun Minal Tare da Jan kunnenta na hau Mata fadan rashin.kunyar da tayi wa Umma a yarana Ni nasan Minal nada zuciya bansan ta had'a har da rashin kunya ba Hakuri tayi ta bani akan bazata sake ba Ni kuwa na zuba abinci a flask. Da Zan aiki Zahira ta Kai na tuna halin Umma na Kai abinci na ajiye musu a Palo Dan sun shige daki sai Masifa take ita kadai. Daki na dawo nayi Sallah na juye Mana abincinmu a faranti muka ci gabadaya. Ahaka mukayi sallar Isha ban Kara Jin motsin su Umma ba Ido na rufe Ina Jin gajiya da ciwon jiki Naseer na fad'omin a Rai inasan naji haushinsa a Zuciyata na kasa inaji kamar Inda yake wuya yake Sha. Ahaka nayi zurfi a tunanin halin da Naseer yake da Kuma dalilinsa nak'i waiwayarmu motsin da naji cikina yayi ya Sakani sakin murmushi tare da bud'e idona Dan wani ikon Allah indai Zan Yi tunanin Naseer sai cikina ya motsa Ni nasan macece a cikina Dan na riga da na cire Rai da haihuwar maza inama cikin jikina namiji ne na haifo Mai Kama da Naseer. Su Zahira Ina kallonsu Suka Gama home work dinsu Humaira da Raheema da Minal tuni bacci yayi awon gaba dasu. Akan katifa ta kwantar dasu ta shimfida bargo ita da Minal suka kwanta a kasa. Sallama Isihu danaji a Palo yasa na fita Inda yake sanarmin masu karatun sun zo Iso nace ya musu na Kara shimfida musu tabarma a babban Palo Suna shigowa Umma ta fito da Daurin kirji tana binsu da kallo ban kalleta ba nace su zauna su fara karatun Kafin ma tayi Magana na koma ciki abuna Ina Jin muryar ta tana Ashe maza nake kawowa gidan karuwanci ma Agaban idonta zanyi na shigo da Tika tikan maza hudu su kuwa Suna ganin alamar rigimamiya ce Basu saurareta ba Suka hau bud'e Quraninsu suka hau karatunsu. Sai goma Suka gama suka tafi. Na fito na kulle gidan Hankalina a kwance a ranar ma ban wani Yi bacci ba sai Dana rayya daren. Kafin bacci yayi awon gaba dani da asuba Ina iddar da sallah na Dora Mana abinci kamar dai jiya na Mana tazarce na Kai komai d'akina na ajiyewa su Umma nasu a kitchen. Sosai nake taka tsantsan da duk abinda zanci. Indai zanyi girki bana barin kitchen sai na Gama ko cokali na daina Bari a kitchen din sai risho Tsakanina da Umma kuwa zagi ne da tsinuwa idan tsautsayi yasa yarana suka Dan tsaya wajen da take sai ta Kai hannu jikinsu Safiyya kuwa Bata samu kwarin jikinta ba sai da aka yi sati biyu itama ta cigaba da Taya Umma wajen musgunamin Amma ban taba tanka musu ba indai Safiyya tamin sai na rama. Alaramma har cassete ya aikomin Mai dauke da izzu sittin na siyo karamin radio na ringa kunnawa duk dare. Ni kuwa ganin na samu kudi dayawa yasa na siyi katifar na saka a daya dakin har da sip Mai saukin kudi na sakawa su Zahira. Cikina na da wata takwas da sati biyu na siyo kayan jaririrai na mata mai saukin kudi shima. Sosai nake adduar Allah ya saukeni lafiya Dan insha Allahu indai na haihu na samu kaina sai na bar gidan Amma bazan tafi ba sai na siyar da gidan tunda takardun gidan. Na wajena. Hakane yasa na cigaba da Tara kudina Banda dashin da nake. Yanzu wani Abu da su Umma suka tsiromin idan nayi girki sai suce bashi zasu ci ba sai su zabi wani abincin suce shi zasu ci Idan nace babu bazasu cemin komai ba sai sun ga Isihu ya dawo daga tallan Yana shigowa sai su kwace kudin Sau uku suna min Haka Ni kuwa nace ya daina kawomin kudin ya ringa kaiwa matar Ala ramma Dan muna mutunci da ita Nan ma ban tsira ba idan nayi markade na Gama hada kudin sai Umma tazo da k'arfi ta rabani da wani abun. Sosai zamana dasu waje daya ya gundureni na matsu na haihu na bar gidan. Wanan ma Bai musu ba da suka ga Ina d'auke Kai sai Suka koma Kan zahira Tana dawowa daga makaranta Umma da Safiyya zasu tsiri sakata aiki tayi.musu wanki ta wanke.musu bandaki sunayi suna zaginta wani zubin har duka suke Kai.mata tun Ina kawaici Naga abin ya fara yawa Dan ta Kai ma sai ta shirya zasu tafi islamiyya Haka Safiyya zata kirata ta hau sakata aiki karshenta makaranta da bazata je ba kenan tana Shan aiki. Ni kuwa ganin abin yayi yawa yasa na fara takawa Safiyya birki idan ga saka ta aiki zance ta Bari sai ta dawo Anan Umma zata hau zagina bana ce musu komai Amma Zan rik'e hannun Zahira tabi Yan uwanta. Idan Kuma ba ranakun makaranta bane a daki nake cewa tayi Zamanta karshenta sai Umma ta biyoni har d'akin ta min tas daga Ni har Zahira Tana Shan mugayen alwashi akanmu . Ahaka Watarana lokacin daya kasance alhamis ba makaranta Ina kitchen Ina girki Zahira namin markade Nadeeya Kuma na wanke uniform din bokonsu. Minal Kuma tana Taya su Humaira home work Umma da Safiyya suka fito daga d'aki hannayensu d'auke da lodin wanki Kansu tsaye suka.nufi wajen da Zahira take suke zuba kayan wankin a kasa Safiyya ta Kai hannu ta kashe engine tana "ke maza hada Mana kayan Nan ki wanke Mana yanzu yanzu" Na gaji sun kaini bango Ludayin hannuna na ajiye na nufi wajensu Ina "Nagaji aunty Safiyya Kun takura wa yata Kun hanata sukuni koni kuka bawa wankin Nan bazan iya ba sabida yawansu ku Bari na nemi almajiri yazo ya muku Zahira bazata iya wankin Nan ba" "Wlh ita zata Mana wankin Dan uwarki ke Nan kin dauka tarbiyya kike musu yaranki ma baa Isa a saka su aiki ba" Umma tace tana k'ok'arin jawo Zahira da har ta fara kuka jikinta na rawa. Ni kuwa na shiga tsakiyarsu Ina "Wlh bazata yi wankin Nan ba" A zuciye umma.ta saka hannu biyu ta hankadani Yarana Suka saki ihu gabadaya nima na Gama sadakarwa fad'uwar Nan da zanyi na iya haddasa min komai amma a madadin najini a kasa sai ji nayi na an tareni ban Kai kasa ba. Bud'e idona nayi na kalli Wanda ya tareni numfashina naji Yana neman daukewa da mukayi Ido biyu....... 🙆🏻‍♀️NAGA TA KAINA🙆🏻‍♀️ Page 1 to 30 Assalamu alaikum barka da warhaka🙋🏻‍♀️ Ta bangarena abinda na samu acikin wannan buk din shine 1-duk wani dabara da wayo naka da wani inda-inda bazai taba sawa ka gujewa kaddarar da Allah ya rubuto makabah ako'ina kake sai dai addu'ah tana ragemata kaifi sosai fiye da tinani mai tonani dan idan ba karfin addu'ah ba babu wanda zai taba tinanin naema zata rayu kafin ta haifi nadeeya kinga kuwa addu'ah ce taragewa wannan kaddar tata kaifi ta dawo mata da hankalin mijinta a ranar da aka yanke mutuwa zatayi 2- akwai riko da addini, sallah akan lokaci da yawaita addu'o'i da kuma rage yawan bacci da daddare, sallah shine jogsran cewa kai cikakken musulmi ne sannan sallah akan lokaci yana tunkude masibu kala-kala. Addu'o'i suna rage kaifin kaddara wani lokacin ma yakan chanja maka ita daga mummuna zuwa kyakykyawa sannan takan shiga tsakanin nagari da mugu misali a page 30 din nan karfin addu'ah ne ya ceci naeema akan hajara da ta fadi kunkuru ya rike mudage da addu'a koda lokacin bamuda tsarki a jikinmu. 3- Hakuri wanda yaxama jagora akan rayuwar zaman duniya wanda shine yake zaune da naeema agidan naseer har wannan lokacin Allah yakara mana hakuri da imani 4- Biyayya koda kuwa wanda kake yiwa baya gani indai akwai hakkin biyayyarshi akanka to kayi iya bakin kokarin ka matukar batakaika ga shirka ba biyayya ma wani babban jagora ne arayuwa misali, koda babu auren naseer akan naemah a yanxu tinda har 'ya'ya suka shiga tsakani to akwai hakkin biyayya atsakanin umma da naeema Allah yasa mudace👏🏻 5- neman nakai rashin zaman banza da ace naema ta cigaba da zaman banza babu sana'a da ayanxu sun tagayyara arayuwa Amma dayake ita sana'a maganin takaici kuma idan ka dace da Allah ya sa maka albarka akai to wllh zaka samu rufin asiri acikinta. Ina bama 'yan'uwanmu mata akan mutashi munemi sana'a dan zaman banza na abune mai amfani bah. Allah yakara rufamana asiri duniya da lahira yasa muyi kyakykyawan karshe yamana katangar karfe da makiyanmu aduk inda suke Ina mika jinjinata ga sadnaf daya tamkar dubu Allah ya kara baseera ya biyaki albarkacin wannan fadakarwar da kike Ina mika gaisuwata ga naeema jarumar mata Allah yayi ma rayuwar 'ya'yanki albarka ya karamana hakurin zaman duniya Mrs naseer ceh👉🏻 *NAGA TA KAINA* *NA SADNAF*🌸🌸 ®️ *_PURE MOMENT OF LIFE WRITERS_* _{We Don't just entertain nd educate we also touch the heat of readers P.M.L}💪🏻_ *Free Novel* *Page 32* *ZAFIN NEMA* *baya kawo samu* Lokacin da Naseer ya bar gida Bai zame ko'ina ba sai Tasha baiji tsoron duhun dare ko karnuka ba Haka ya rungume kayansa kala biyu ya rungume a kirjinsa ya samu waje ya zauna dan lokacin ba wani motoci Haka ya zabga tagumi Yana tunanin Naeema daya bari da Yara Yana tunanin Anya shawarar daya yanke Na guduwa ya nemi kudi shi ya dace yayi ko kuwa ya koma su cigaba da zama a haka. Ko shi daya fito daga gida Bai San garin daya nufa ba. Ahaka ya zauna zuciya fal da tunani har akayi Kiran a sallah asuba Ya nufi Massallaci dake kusa da tashar yayi Sallah Asuba sosai yayi ta addua Akan iyalinsa Ji yake kamar Bai kyautawa Naeema ba kamar tafiyar tashi ba mafita bace a garesu Amma tunanin barin garin ya danne tunanin Haka a Ransa. Karfe Bakwai yaga wani karamin mota na loda fasinja Abuja Haka ya shige motar Yana tunanin zuwansa Abuja zai saka ya samu kudi. Duk tafiyar da suka Sha zaune kawai yake a cikin motar Yana tunanin Naeema zuwa yanzu yasan ta tashi taga wasikar da ya bar Mata ko ya zataji a ranta. Sai da wani a gefensa ya taba shi ya dawo daga duniyar tunanin Daya tafi Nan fa Kuma daya Bai San Ina zai nufa ba Bai Kuma San ta Inda zai fara ba Hakane yasa ya sauka daga motar ya samu wani benci ya zauna. Yana kalle kallen mutane pure water kawai yayi ta durawa cikinsa. A takaice Haka yayi ta zama a cikin tashar har tsawon sati guda Dan ya lura Abuja ba kamar Kano ba kowa shaanin gabansa yake. Wani Abdullahi Mai lodin mota daga Kano zuwa Abuja ne ya fara Gane halin da Naseer yake ciki. Dan ya Dan Saba da Naseer a Haka Naseer ya Dan bashi labarin halin da yake ciki shi kuwa ya Masa alkawarin taimaka masa ta hanyar nemo Masa motar haya ya ringa ja. Cikin Sati daya da maganar Abdullahi ya had'ashi da wani Alhaji Idris wani Mai kudi dake da motoci da taxi na haya. Take ya bawa Naseer mota da zai na Lodi daga garin kogi zuwa Abuja ya Kuma yanke masa kudin da zai ringa biyan shi. Sosai Naseer ya hau murna kwana biyu da bashi motar ya fara aikin sai dai duk yanda Naseer yayi tunanin aikin tukin nada sauki sai yaga ba karamin wahala ne da tukin ba gashi bashida cikakken nutsuwar zuciya Dan zuciyarsa na kano gangan jikinsa ne kawai a Abuja. Ko abinci baya iya ci Dan idan yazo ci ya tuna iyalinsa sai yaji cikinsa ya cushe ya kasa cin abinci Daddare kuwa tunani baya iya Bari ya samu cikakken bacci idan ma ya rayya daren Yana sallah ba nutse yake yin sallah ba sabida tsabar tunanin su Naeema. Halin tunanin dayake ciki sai daya kusa saka shi hatsari sau da Dama Inda tuni fasinjoji suka fara Gane shi indai motarsa ce bazasu hau ba sai su ce Yana tafe yana tunani. Ahaka Watarana garin tunanin ya bugi motar wani Mai kudi Wanda ya Masa asarar glass din gaba sai gashi case din sai daya kaisu ga tafiya police station Alhaji Idris na zuwa motarsa kawai ya karba ya Kara gaba. Karshe dai sai Dan kudin da Naseer ke tarawa ya biya mutumin kudin glass din motarsa. Wata biyar da yayi a Abuja a wahalce yyi shi cikin tsananin wuya duk inda ya Kai ga fara wani Abun sai wani sanadin yazo kudin ya tafi. Yayi garuwa,ya siyar da bonse ya siyar da ruwan Sanyi ba irin Sana'ar da baiyi ba Amma abinda yazo nema a Abujan Bai samu ba ahaka a garin siyar da bonse ya hadu da wani shima dake yawan wucewa ta danger da yake tsayawa ya siyar da bonse yayi parking ya fara tambayarsa ya iya tuk'i Gyad'a Masa Kai yayi da Sauri. Kamar Wasa ya zama driver mutumin ya Kuma barshi yake kwana a boy's quaters din gidan Sai dai rashin nutsuwar zuciya da tunani iyalinsa yasa ya kasa maida hankali a Haka ya Kara cin wata uku da sati biyu a gidan. Mai gidan kuwa tuni ya Gane Naseer Yana cikin matsanacin damuwa Dan duk Wanda ya San Naseer idan.ya ganshi bazai Gane shi ba sabida yanda ya rame ya lalace ga kasumba ya rufe masa.fuska har wani Dan tsufa yayi. Cikin tausayawa ya kira Naseer ya hau tambayarsa Mai ke damunsa Haka cikin karayar zuciya Naseer ya fara bashi labarin yanda ya baro iyalinsa sabida talauci. Yana bashi labari Yana kuka Shima sosai ya tausaya Masa Inda ya Shiga d'aki ya d'auko kudi Yan dari bibiyu na Dubu dari biyu da a lokacin kudi ne Mai yawa da zai Isa Naseer yaja jari ya cika shagonsa. Ya Ajiye a gaban Naseer Yana ya d'auka ya koma ga iyalinsa. Naseer zubewa yayi Yana ta Masa Addu'a Yana ji kamar an tsoma shi a Aljanna. Sosai ya ringa zumudi Yana murna komawa da zaiyi ga iyalinsa Yana kyautata zaton kudin da ya samu zai Isa yaja jari. Yaso tafiya a washegarin daya samu kudi sai dai Alhaji Ismail ya dakatar dashi akan ya Bari sai wani satin sabida akwai kudin da yake sa Rai idan ya samu zai Kara Masa baa San Ransa ba ya hakura ya Kara cin sati daya duk a takure Wanda yayi daidai da cikarsa wata takwas da sati uku Gabadaya hankalinsa yayi gida Ido biyu Ido rufe Naeema yake gani da yayansa a cikin mawuyacin Hali hakane yasa Bai tsaya jiran Alhaji ismail ba ballantana ya Masa Sallama ya kwashi kayansa da kudi ya nufi Tasha da asusuba. Karfe Takwas suka dau hanyar kano sai dai gani yake kamar ba Sauri driver yake ba. Suna dab da shigowa Kaduna yaji motarsu taci wani irin birki kafin su ankara mutane masu sanye da bakakken Kaya sun zagaye su Da manyan bindigogi. Tuni suka bud'e motarsu suka hau fito dasu Naseer kuwa sallati kawai yake. Duk kansu a sunkuye Barayin Nan suka caje kayansu suka kwashe komai nasu. Basu iya dagowa ba sabida bindigar da aka Dora musu akai ahaka suna ji suna gani suka rabasu da komai suka haye motarsu suka tafi Sallati da ihu kawai Naseer ke yi kamar ya haukace. A takaice a Haka suka hau motar suka nufo garin Kano wajen uku da rabi ya iso. Sam hankalinsa ba ajikinsa ba a tashar ma.wani ne ya taimakawa.Naseer da kudin motar da ya iso gida kafarsa ma ba takalmi. Sai dai Yana isowa unguwarsu tundaga nesa yaga yanda gidan nasa ya canja ya Sha gyara tuni gabansa ya yanke ya Fadi Yana tunanin kila Ma talauci yasa Naeema ta siyar da gidan. Ba dai ta gudu itama da yaran ba hakane yasa ya taka da sauri ya Isa k'ofar Gidan ya tura da k'arfi a daidai lokacin da Hajara ta hankado Naeema ta fado jikinsa.ya cafeta "ABBAAAA" Su Zahira sukace da ihu a lokacin da idonsu ya sauka Akan Naseer da ya zuba min Ido kamar yanda na zuba Masa Ido Ina ganin kamar a mafarki nake ganin Naseer ba gaske ba Fusge jikina nayi daga nasa nayi hanyar cikin gidan da Sauri na shige adaidai lokacin dasu Zahira suka rungumeshi suna ihun murna Raheema ce kawai Bata karasa wajenshi ba. Hajara itama daskarewa tayi a tsaye a lokacin da Naseer ya shigo suna had'a Ido ta juya da Sauri ta nufi daki Dan Haka kawai taji Kuma tana Jin nauyin ganin da Naseer yayi Mata a gidansa bayan cika bakin da tayi akan bazata Kara tak'a kafarta gidansa ba. Itama Safiyya bayanta tabi da Sauri. Naseer kuwa wani irin Sanyi da nutsuwa ya ji Yana shigarsa a lokacin. Da ya rungume yayansa a jikinsa. Kasan zuciyarsa kuwa Allah Allah yake yaga Naeema da idonsa ya Gane masa ta na dauke da tsohon ciki Ashe Dama da ciki ya tafi ya bar Naeema. Da Sauri ya cire su Zahira daga jikinsa ya nufi d'akin da yake kyautata zaton na Naeema ne da su Umma suka gaje. Yasan yaga Umma Amma San ganin Naeema yasa yak'i Bari ma tunaninsa ya rabu gida biyu. "Wai me Kika shigo daki a guje ne tsoron Yaya Naseer din kikeji ne ko me? "Aaa Safiyya kunyar ganin dayamin a gidansa nake bayan na Gama Shan alwashin ba abinda zai saka na Kara tak'a k'afata a gidansa Kar ganina da yayi a gidansa ya d'auka banida wajen da Zan zauna ne kinsan na cicika Masa baki" "Tab kiji ki Umma ai borin kunya zakiyi ki hade ranki idan ya gaisheki ma ki amsa da kyar yanzu Yana ganin kina Jin nauyi wlh Raina ki zaiyi kamar yanda Yaya Tijjani ya rainaki" Tana rufe Baki Naseer ya turo kofa tayi Sauri ta Samu waje ta zauna tare da had'e Rai. Sai Safiyya ce ta amsa sallamar tana kallon yanda Naseer ke mamakin ganinsu d'akin Naeema Amma ya hadiye mamakin da yake ya zub'e a kasa ya hau gaida Hajara data k'i kallon Inda ma yake sama sama ta amsa gaisuwar sa. Safiyya tayi caraf ta fara magana tana "sati daya kenan da muka zo dak'yar na samu Umma ta biyoni da mukaji labarin Naeema Bata da lafiya sai da nayita rokon Umma Allah da annabi kafin ta yarda ta biyoni. "Dama Naeema Bata da lafiya"? Naseer yace hankali a tashe tare da mik'ewa da Sauri yayi waje batare da ya tsaya sauraron sauran maganar da Safiyya take ba. Inda yakejin muryarsu Zahira yayi da Sauri sosai yaji dadin yanda aka gyara gidan b'angaren ma da Bai gyara ba ya gansa fes. Amma Bata gyaran gidan yake ba ta Naeema yake. Dakuna biyu dake jere ya shiga na farkon daya kasance nasu Zahira Yana daga labulen ya ga Naeema a zaune Akan katifa tana ta share hawaye daga labulen da yayi yasa ta dago ta zuba Masa Ido. Shima idon ya zuba Mata Yana Jin wani irin tausayinta na nukurkusar koina na jikinsa. Dak'yar ya iya daga kafa ya Shiga d'akin Naeema kuwa kukan da takeyi kasa kasa ta kasa dannewa ta fara yinsa a fili. Da rarrafe ya karasa kusa da katifar ya ruk'o hannun Naeema cikin rawar murya ya fara Bata hakuri daya hannun nasa Kuma ya Kai cikin ta Yana shafawa. A durk'ushen ya hau Bata labarin duk wahalar daya Sha daya tafi da yanda barayi suka tare su a hanya suka kwace Dan kudin daya samo musu. Sosai Tausayin Naseer ya rufeni Dan ko Bai bani labari ba daga yanayinsa kawai nasan ya Sha bak'ar wahala Dan ba karamin Rama yayi ba. Nidai ban iya bashi labari ba ya hau min tambayoyi game da rayuwar da mukayi ya akayi yaga na baro wancan d'akin na dawo Nan waye ya gyara gidan Ina muka samu kudi. Ce Masa nayi ya Bari Anjima Zan bashi labari daga Haka na mike na nufi kitchen Dan na karasa girkina Inda Naga har Zahira ta karasa ta juye a kula har nasu Umma ta zuba musu. Nadeeya Kuma nata markade. Namu abincin na dauko na ajiye a karamin Palo Inda na tarar da Naseer a tsaye Yana ta kalle kallen gidan kamar bakonsa. Su Minal kuwa sai danne shi suke suna Masa surutai. Kiran Sallah Magriba ne yasa ya d'aura alwala ya nufi Massallaci cikin farincikin dawowarsa cikin iyalinsa dayaga alamar suna cikin rufin asiri sosai ya matsu yaji a Ina suka samu kudi Haka har da engine markade guda biyu. Naseer na fita kuwa Umma ta mik'e da Sauri ta kalli Safiyya cikin b'acin Rai tana "Kinga Bai ma damu da ya bani hakuri ba ya nufi wajen Naeema Sabida yaji ance Bata da lafiya k'arfi da yaji yake nuna Kaunar yarinya Nan a fili Kinga fa yanda ya rud'e dayaji munce ba ta da lafiya. "Hmm Umma Naeema fa ba Haka ta barshi ba tun lokacin da ya gwammace ki Masa baki Akan ya rabu da ita nasan ta asirce shi Dan Haka ki daina ganin laifinsa ba a hayyacinsa yake ba asiri aka masa" Sosai ran Hajara ya b'aci da abinda Naseer yayi na nuna damuwarsa Akan Naeema sai alwashi take ci Akan Naeema Safiyya na zugata. A faranti daya mukaci abinci da Naseer da ke ta washe baki kamar gonar auduga idan muka hada Ido sai ya sakarmin murmushi. Nasan ba yanda zaiyi ne Agaban Yara da ya rik'eni a jikinsa. Duk cika bakin da na ringayi na zanyi fushi dashi sai gashi Nima Ina cikin tsananin farinciki zuwan Naseer at least I felt Safe da dawowarsa (bansan yanda zan saka da hausa ba shiyasa na saka da turanci ayi hakuri) Karfe Tara su Zahira sukayi bacci. Sai Dana tofesu da Addu'a na fito daga d'akin tun tafiyar Naseer sai a yau zasu kwana su kadai. A Gefen katifa na samu Naseer a zaune Ina shigowa ya mik'e ya ruk'o hannuna ya zaunar Dani a gefensa sai wani rawar kafa yake kamar Wanda yayi amarya Ni kuwa dariya yake bani ma Dan ni cikin jikina ma ya isheni. Tambayoyin da yayi ta jera min Akan Inda na samu kudi. Yasa na fara bashi labarin duk abinda ya faru bayan tafiyarsa irin wuyan Dana Sha da yanda na Sha laulayi Zahira ta kawo Mana shawarar siyar da ruwa da har gobe shi ya zame silar rufuwar asirinmu da yanda na Tara kudi na siyi engine daya har na Kara samun kudi na Kara siyan wani da yanda na gyara gidan. Da zuwansu Umma da irin abinda suka ringa mun ba abinda na boye Masa. Da har zuwan da yayi rigimar da mukeyi da su har ya kai Umma ga tureni ya cafeni. Naseer sosai ya matse hannunsa cikin nawa idonsa ya kad'a yayi jawur sai sallati yake Yana jijjiga Kai Bai tab'a tunanin har yanzu su Umma Basu daddara ba. Ni kuwa halin Dana ganshi ciki na b'acin Rai yasa na hau basa Baki duk da kasan Raina Ni nasan na Gama yanke hukunci rabuwar mu idan na haihu Amma bazan Gaya masa ba. Daga rarrashi Kuma muka farantawa juna Rai duk da cikin jikina. Sai da muka yi wanka bacci yayi awon gaba damu Mai nauyi. Karfe Hud'u ciwon Mara da baya ya tasheni haihuwa na shidda take nasan Nakuda ne gashi kasana naji kamar Ana danno ni. Saukowa nayi daga Kan katifar tare da tashin Naseer. Ai Yana bud'e Ido naji kamar ya tasomin da Nakuda gadan gadan sallati kawai nake shi kuwa ya zura doguar Riga yayi waje kafa ba takalmi. A mak'ota ya samo Aron mota Yana zuwa ya taimaka min na mik'e cikin tashin hankali ya hau cemin bashida kudi. Kasan katifata nasa ya daga ya d'auko jakar kudina. Jiki na rawa ya d'auki kudin ya dau jakar Dana hada kayan haihuwa Dan Ina shiga watan haihuwa na hada komai na bukata. Asibitin dake kusa mukaje. Zuwa lokacin sosai naji kamar Ana dannoni da k'arfi. Ko tafiyar ma ban iya yi ba sai da gadon marasa lafiya aka zo aka daukeni aka Shiga Dani dakin. Muna Shiga d'akin kafin nurse ta saka Safar hannu naji faya ta fashe nayi Nishi da k'arfi. Sai kuka baby mukaji. Take naji kamar an d'aukemin duk ciwon da nakeji. Na hau numfarfashi Ban damu da kallon abinda na Haifa ba Dan nasan macece. Inaji suka yanke cibi tare da zaro mahaifa daya nurse din ta hau goge BBY dayar Kuma na kaina. "Juyo kiga Mai Kika Haifa naji nurse din tace" Ban juyo ba nace "Macece Rabbi ya Albarkaci rayuwarta" "Sai dai ya albarkaci rayuwarsa Dan namiji ne" Wani irin juyowa nayi da balain sauri a daidai lokacin data doramin jaririn a kirjin........ *NAGA TA KAINA* *NA SADNAF*🌸🌸 ®️ *_PURE MOMENT OF LIFE WRITERS_* _{We Don't just entertain nd educate we also touch the heat of readers P.M.L}💪🏻_ *Free Novel* Hannuna har karkarwa yake wajen d'ago da jaririn Dan na tabbatar da Namijin ne. Take na hau hawayen farinciki na Kara kwantar dashi a kirjina inata Godewa Allah da Wanan kyautar da yamin a cikin jaririn Nan ne kawai ban saka Rai da samun namiji ba Amma sauran duk saka Rai nake da maza ne sai gashi a lokacin da ban kawo ba na cire Rai da haihuwa Namiji Allah ya bani. Kasa d'auke idona nayi daga kansa har Nurse din ta saka Mai Kaya bayan ta goge Mai jiki da man zaitun Yanda taga Ina binsa da Ido Ina murmushi yasa tace halan ban taba haihuwa d'a namiji ba gyada Mata Kai nayi a lokacin da take sake mikomin shi na karbe shi da Sauri na tashi zaune na zuba Masa Ido ba Inda ya baro Naseer kamar an tsaga Kara Haskena kawai ya d'auko. Sosai na ringa Jin kaunar jaririn a Raina inajin nurse din na Bari tayiwa Naseer albishir tayi waje da Sauri Dan tasan indai ta Gaya masa kila ya mata kyauta A bakin kofa ta tada Naseer din kamar zai fado d'akin Ana bud'e kofa yyi Kan nurse din da Sauri. Ita kuwa ta mik'a Masa hannu tana ya Bata goron albishir Washe baki yayi daya ga alamar Naeema ta sauka lafiya addua ya hau yi Yana "Na Riga da nasan Mai ta Haifa Allah yayiwa rayuwarta albarka" Murmushi nurse din tayi tana mamakin yanda daga Naeema har Naseer din suka cire Rai da haihuwar da namiji "Sai dai Allah ya Masa albarka Dan namiji ta Haifa katoto" Naseer Ido ya gwallo Yana me kikace. Kafin ma ta bashi amsa ya fada d'akin da Sauri har Yana tuntub'e. Daga yanda yaga Naeema na murmushi yasa ya Isa wajenta da Sauri tare da saka hannu ya karbi jaririn Bakinsa har kunne sai hamdala yake Yana kamkame jaririn a kirjinsa. Sai albarka yake shiwa Naeema ji yake kamar baa Tab'a Masa haihuwa bama inama lokacin da yake da kudi Naeema ta haifi namiji da yaron ya Sha Gata. Bakinsa ya kafa a kunnen jaririn ya Masa huduba ya d'ago ya kalli Naeema Yana "Allah ya raya Naseer sunana na saka mishi" Murmushi na saki Ina Jin dadin sunan daya saka mishi nace "Allah yasa ya gaji halin Mai sunan ya bashi ilimin addini irin na Mai sunan insha Allahu addua kawai ce tsakanina da yarana Allah Kar ya jarrabceni da fushi dasu" Na tsinci kaina da fad'a duk da kallon da Naseer kemin yasa na hadiye sauran maganar. Karfe takwas na safe aka Sallame mu daga asibitin bayan Naseer ya biya kudin komai. Hamdala kawai yake a Ransa da Allah yasa Naeema nada kudi da yau asirinsa ya tonu ta Ina zai samu wanan kudin da suka kashe a asibitin. Naeema sai data saka ya siyi kayan shayi da sauran Abubuwan a zata bukata kamar yanda yake siya idan ta haihu shi kuwa sai dari dari yake baya San kashe kudin Wai Dan Kar ya kare. Lokacin da muka Isa gida Naseer ne ya rungume jaririn a kirjinsa daya hannunsa d'auke da kayayakin mu Ni Kuma Ina biye dashi a baya Ina takawa a hankali kamar iska zai d'aukeni nakeji sabida rashin kwarin jiki banida burin daya wuce na kwanta sabida ciwon baya danake yi Bakin Naseer a washe ya Shiga palon Da Sallama Umma da Safiyya kawai muka samu a palon Umma ta hade Rai tana ta jijjiga k'afa Ina ganin Haka nasan wani rashin mutunci Umma zatayi. Naseer kuwa tuni Naga ya nutsu duk da gabansa sai daya Fadi da ganin Umma Amma Haka ya nufi wajenta ya tsugunna Ya hau gaisheta. Wani irin kallo ta Masa ta d'auke kanta batare da ta amsa ba Shi kuwa ya Kara gyara Jaririn a hannunsa Yana "Umma Naeema fa ta haihu Kinga" "Sai me dan ta haihu yau ta fara haihuwan?Mai abin murna a haihuwa Naeema da take cike.maka gida da tarin Mata" "Umma wanan Namiji ne wanan Karin Allah ya azurtamu da Samun namiji" Ina dab da Isa k'ofar karamin Palo Amma sabida Naga ya Umma zatayi idan taji Namiji na Haifa yasa na tsaya. Mik'ewa tayi da Sauri ta lek'a fuskar jaririn da Naseer ya juyo dashi Sabida Umma ta ganshi sosai ta gaskata maganar da yake. Ja da baya tayi tana "Kuma sai ka yarda wanan danka ne. Sai ka yarda wanan Jininka ne? Watanmu kusan hudu a gidanan tunda muka zo Maza suke sintiri a gidanan wayanda zasu Zo da safe daban wayanda zasu Zo da Rana daban Sabida Kai dakiki ne an asirceka idonka ya rufe shine zaka ringa murnar ta haifo maka namiji. Kar idonka ya rufe ka kasa gane gaskiya har Ina Naeema zata samu kudin da zata gyara gidanan Bata tsaya iya Nan ba ta siyi engine biyu Kai Kaga irin kudin datake rik'ewa kuwa Amma dayake zuciyarka ta mace idonka ya rufe duk baka gani ba ka hau rawar kafar ta haifo ma namiji indai Jininka ne ai mace zata haifo iya wanann ma ya Isa yasa ka Gane Dan Nan ba naka bane" Yanda nakejin zuciyata da jirin dake d'ibana sabida tsananin bakinciiki sheganta min da da Umma keyi da kazafin da take neman yimin yasa.na shige palon Dan Ina cigaba da tsayuwa zuciyata zata iya bugawa Ni Kam wane irin nauyin kiyaya Umma zata gwadamin Wanda Bata gwadamin ba ya isa Haka ai batare aka halliceni da Naseer ba tafiyar Naseer ban fasa numfashi da rayuwa ba Dan Haka barin rayuwar Naseer na huta bazai Hana shi rayuwa ba Haka Nima idan akwai abinda ke damuna Bai wuce yarana ba Dan Ni nasan matsawar na tafi dasu kamar inasan Naseer ya dawo rayuwata ne. D'akina na Shiga na kwanta ganin Banga kayan makarantarsu Zahira da jakunnan makarantarsu ba yasa nasan sun tafi makaranta. Hawaye kawai nake Ina tunanin hanyar da Zan bi wajen barin rayuwar Naseer na har abada. Allah yasan Ina kaunarsa Amma ya zama Dole mu rabu idan kuwa ya zargeni sabida bashida kudi na rabu dashi baimin adalci ba Dan ko kanwarsa ake matsawa Haka ya Bata shawarar ta hakura da auren. Ina jiyo Naseer na Mata kana Nan rantsuwa Akan yasan Halina ko shekara goma zaiyi Zan rik'e Masa amanar aurensa wlh Dan Nan NASA ne Dan Allah ta karbi jaririn taga yanda Suke kama. Ita kuwa Umma dagewa kawai take Tana rantsuwar ba dansa bane Wai Ni Mata nake Haifowa inaji tana balai Yana Bata hakuri. Inaga Safiyya ce ta saka Baki naji ya daka Mata wani uban tsawa daya saka jaririna razana ya saka kuka. Naseer kuwa kukansa Bai sa ya bar wanke Safiyya.kamar zai ajiye jaririn ya rufeta da duka ba yayi ta cewa ta Kai shi bango wlh xai koreta daga gidansa Dan bazata Zo tana hura Masa wuta a gida ba shiyasan wani zubin ita ke zuga Umma. Ita kuwa Umma cewa take "Kar ka wani wayance Ni zaka yiwa fada ba ita ba tunda Ni nake Maka magana" Kukan Jaririn yasa Naseer bai ce wa Umma komai ba ya nufo d'akina Ransa a balain b'ace Yana shigowa d'akin. Ya mikomin shi na karbe shi take kuwa yayi shiru na Ciro abincinsa na saka Masa a baki tare da bismillahi ya kuwa cafe da Sauri a fili nace "Allah ya rayaka Walid ya shiryaka bisa tafarkin musulunci" Ameen Naseer yace can kasar murya idonsa ya kad'a yayi jawur ban nuna Masa naji Haushin abinda umma tamin a fuska ba Amma ya juyo ya hau bani hakuri Yana na taimaka masa mahaifiyarsa ce babu yanda zaiyi da ita Yana Nan Yana gayawa Allah. Murmushi kawai nayi Dan daya bani hakuri da Kar ya bani hakuri na Riga da na yanke hukunci a raina. Ce Masa nayi ba komai kar ya damu. Sai a lokacin ya saki ajiyar zuciya masu markade da suka zo yasa ya mik'e Yana Bari ya markada musu. Amma kafin Nan Bari ya saka Safiyya ta dafamin ruwan tea da Sauri na ce ba sai ya sakata ba ya Bari na Gama bashi Zan fito na Dora ruwan da kaina tunda Dama Ina bukatar ruwa Mai yawa sabida ma nayi wanka na wanke Walid. Har zai Musa min Kuma ya fasa Yana bari ya fara doramin ruwan inyaso sai ya fara markaden. Nima.fada kawai nayi bazan iya tashi ba sabida jirin danake ji. A kitchen ya tarar da Safiyya itama ta juye musu ruwan zafi a jug ga kwai ta soya a faranti duk a kudin Naeema da suke Mata fin k'arfi su kwace. Yanda Naseer ya hade Rai yasa ta fice daga kitchen din da Sauri. Tana fita ya Dora ruwa a babban tukunya ya fito ya kunna engine ya fara markaden. Yana cikin yi ma Isihu ya shigo ya fara markaden. Shi kuwa Naseer ya koma.dakin ya d'auko ledar zanin da Naeema ta Bata ya zuba a katon baho dayake akwai Omo da dettol a bandaki ya zuba ya koma kitchen Ganin ruwan yayi zafi sosai yasa ya cika flask ya Kai daki ya juya sauran a katon Bokiti. Duk abinda yake Umma da Safiyya binsa kawai suke da kallo. Umma kuwa kamar ta fashe Dan bakin cikin yanda Naseer yake neman Zama bawan Naeema Shayi Mai kauri ya hadamin ni kuwa na fara sha Ganin Yana k'ok'arin fita yasa nace Masa Dan Allah ya bawa Isihu kudi idan ya gama markaden ya siyo.min nama bakina ba dadi. Zama yayi a gefena Yana "Naeema ba asan Raina Kika haihu banida ko sisi ba wlh bana Jin dadi Amma ba yanda zanyi Haka Allah ya hukunta Naeema na baki labarin ban zo gidanan da ko biyar ba Kar muzo muyita kashe kudin ya Kare kiyi maneji da Abunda Kika samu gaba idan Allah ya hore duk Zan Miki Abunda ban miki ba a haihuwar Nan" Murmushi nayi na ajiye kofin hannuna Dana Gama shanye shayin na kalli Naseer Ina "Naseer karka damu Ni Mai fadawa wani ne halinka idan kana dashi ma baya b'uya amma karka damu Ina da kudi ba iya na hannunka ne damu ba a d'akin Nan ma akwai kudi Banda dashin danake har ajiya nake badawa ka Bari idan na samu Kaina sosai zamuyi shawara ko zaka fitar da shago ka Dan zuba provision ka ringa siyarwa da zaman hakan. Tun kafin na karasa Naga Naseer ya washe baki ya hau murna Yana shimin albarka. Yana "Kice idan su Zahira sun dawo na fita kasuwa da kaina na siyo Dana Kaya Dan Naga kayan mata Kika siyo Masa yanzu na kashe duk kudin wajena"? "Gyad'a Masa Kai nayi Ina murmushi" Ya fice waje da Sauri Yana murmushi Ni kuwa Jin na Dan ji kwarin jikina yasa na mik'e na hada ruwan zafi a na wanke Walid na shirya shi na rufo kofata Nima na Shiga wankan. Naseer kuwa Yana fitowa daga d'akina kayan Naeema daya jika ya sunkuya Dan ya wanke. Hajara ta mik'e a fusace Tare da daka Masa wani uban tsawa "Kai yanzu Dan asara da mutuwar zuciya Mai aiki Naeema ta maidaka kenan sabida baka da kudi shine ta hadoka da wankinta kayi Mata kana matsayin mijinta? Da lokacin da kake da kudi Kai kake mata wankin dayake Bata da mutunci sabida taga bakada ko sisi shine zata ce ka wanke mata kayan jini toh wlh bazaka wanke ba indai nice na Haifeka bazaka yi wankin Nan ba" "Umma wlh Ni nake Mata wanki idan ta haihu bawai ita ta Sakani ba Dan gani nake Bata da Mai matan idan bani ba" "Toh wlh bazaka wanke ba idan Kuma ban Isa dakai ba zaka iya wanke Mata" Umma tace tana jijjiga k'afa. Duk Inda Naseer yaso shawo Kan Umma tub'urewa tayi. Ni kuwa Ina Jin duk abinda ke faruwa hakane yasa Ina saka Kaya na fito Ban ko kalli Inda Umma da Naseer suke tsaye cirko cirko ba na jawo bahon na hau wanke kayana. Umma kuwa ta hau zagina tana ita tasan asirce mata da nayi ban Isa na bautar Mata da D'a ba. Bance Mata komai ba Naseer kuwa kamar yayi kuka sai neman kwayar idona yake Dan ya bani hakuri nak'i kallonsa. Sai Dana Gama wankina na shanya na Shiga kitchen Dan Ni Dama tunda na auri Naseer bansan Zama Wai na huta idan na haihu ba Ni nake komai nawa. Girki na Dora naje na dauki robar custard da gwangwanin da ya cika da kudin markade Na zuba a ledar dana gani na ajiye gwangwanin custard din na koma d'akina. Ina cikin had'a kudin Naseer ya shigo yana k'ok'arin Magana nayi sauri na dakatar dashi. Ina Kar yace komai indai Umma ce na Riga da na Saba da kome zatamin ba wani Abu sabo. Bai iya cemin komai ba yayi shiru Ina Gama hada Kan kudin na cusa a akwatina ganin waleed na bacci yasa na Kara barin d'akin na koma kitchen na zauna Dan girkina yayi na sauke. Ina cikin juye abincin su Zahira suka dawo. Ina ganin ta dawo na bar kitchen din dan nasan zata karasa min girkin. Su Minal kuwa d'akina sukayi aguje suna murna sunyi Kani irin murnar da suke ne Yasa na manta da damuwar da nake ciki. A takaice da kudina na wajen Naseer Naseer ya siyowa Waleed Kaya har dasu Zahira ya taho da Naman danace Masa. Duk abinda Muke ciki Umma idonta na Kai. Kudin dashina kwana uku da haihuwa nasa aka karbomin na bawa Isihu Dubu goma akan ya kaiwa Matar Ala.ramma Dan a gidansu na siyi katon ragon da zaa yanka duk da ba haihuwar fari nayi ba Amma kasancewar namiji ne hakane yasa na saki bakin Aljihu nayi dinkuna nayi komai na taron Sunan Waleed Naseer sosai.nake ganin farinciki kwance a fuskarsa Dan shima burinsa yayi taron Amma bashida kudi Shima dinki na Masa kala biyu. Umma kuwa ta Kira shi ta hau balai tana masifar sai ya tambayeni Ina na samu kudi Haka sanan ya zaayi nayiwa kowa dinki har da shege Isihu ita da Safiyya ban.musu ba. Naseer kuwa ce Mata yake ba shi yayi dinki ba Ni na musu komai.na gidan Ni nayi. Ita kuwa Umma dagewa tayi sai Nima na musu dinki. Ni kuwa Naseer da Yar murya ya zo wajena Yana na bashi Rance Ni kuwa na murzawa idona toka nace Masa bazan bayar ba Dan kudin karuwanci ne Ashe Umma na labe tana jinmu ita kuwa ta hau tsinemin tana gwara Kar na Bata mantawa.ma tayi kudin karuwanci ne. Sosai sunan Waleed ya cika da mutane har k'ofar gida. Abinci kuwa sai da aka rabawa mak'ota mmn Mannir ma sai data zomin itama da abun arzkiki har da.makotana da mukayi zaman mutunci dasu. Na yarda idan kana da abin hannun ka mutane har rububin muamalla suke Yi dakai. Bazan iya lissafa Abubuwan Dana samu a sunan Walid ba Dan har na kusa maida kudin Dana kashe masu kawomin markade da customers Dina masu siyan zobo da ruwa duk baa barsu a baya ba Haka suka ringa zuwarmin barka da abin arziki. Daga Ni har yarana da Naseer Shar mukayi bazaka yarda muna cikin wani matsala ba. Umma kuwa da Safiyya tsabar bakin ciki barin gidan sukayi Basu dawo ba sai da aka Gama taron Makotan arziki suka Tayani wanke komai da gidan. Ai fa Bayan suna Umma kamar ta jefani a wuta matsamin tayi ta sakoni a gaba a gaban Naseer zata Zo har d'akina tayi ya zagina tana tsinemin Wai nayi asiri na kwace dukiyar Naseer. Naseer ya zama kamar Dan aiki a gidan Dan Haka na fada Mata Inda naje nayiwa Naseer asiri. Idan Ina San nayi magana sai ta saki ihu ta hau cewa na Mata rashin kunya Naseer na kallo. Naseer masifar.umma yasa Dan kwanciya hankalin daya samu ya fara Rama. Ni kuwa a hankali na fara kwashe.kayana Ina bawa Isihu Yana kaimin gidan matar Ala ramma Dan Bayan mmn Mannir itace mace ta biyu Dana bud'ewa cikina duk da shawarar data bani na sakani zubar da hawaye naji kamar bazan iya ba Amma babu yanda zanyi Haka Allah ya kaddaramin. Kwana hudu kenan Ina rashin lafiya da kuka a b'oye da Naga lokacin Dana saka wa.kaina barin gidan Naseer nata matsowa. A cikin yarana ba wacce nake balain tausayi kamar Zahira da Raheema ba Naseer ne a gabana ba yanzu yarana kawai nake tunani. Idan Naseer yaga Ina kuka hakuri yake bani Dan ya d'auka takurar da Umma takemin ne Nan kuwa bai San tunanin da nake daban ba. Ahaka dai ranar Dana sakawa kaina Bayan da Naseer ya tafi massallaci nayi sauri na goya Waleed a bayana. Na Shiga d'akin yarana a zaune na tada Zahira kamar ma batayi bacci ba Haka kawai naji hawaye na neman zubomin nayi sauri na mayar Ina ta tashi kanennta suyi sallah. Yanda na hade Rai yasa ta Shiga band'akin tana waiwayena kamar tasan tafiya zanyi. Dak'yar ta Shiga band'akin. Ni kuwa na toshe bakina sabida kukan dake neman k'wacemin na karewa yarana kallo na fito daga d'akin na ajiye zungureren wasikar Dana rubutawa Naseer a bakin kofar dakina na na fice daga gidan nabi ta Bayan gidanmu ta hanyar da ba fiye bi ta hanyar ba inayin Nisa da gidan Waleed ya fara tsalla kuka....... *NAGA TA KAINA* *NA SADNAF*🌸🌸 ®️ *_PURE MOMENT OF LIFE WRITERS_* _{We Don't just entertain nd educate we also touch the heat of readers P.M.L}💪🏻_ *Free Novel* *Page din jiya duk haushin Naeema akeji akan ta gudu inaso ku ringa saka kanku a matsayinta she is a human being itama mutum ce Kamar kowa ita tasan azabar da take Sha a hannun uwar mijinta karku manta mutuwa ma na raba uwa da Yaya har uba ma Yara su tashi ba uwa ba uba Kuma yaran bazasu fasa rayuwar da Allah ya tsara musu ba yanda Allah ya tsallakar da ita da ga duk wani sharrinsu take rayye har yanzu Allah Nan zai Kare Mata yaranta Wanann shine guduwa da tayi na biyu na farko da yaran Naseer yabi bayansu ta dawo abubuwa suka Kara cakudewa har ya Kai su ga Zama a cikin wanan halin ta bar Yara Dan Naseer Kar ya biyota kila ta gaji yau da gobe a Kuma Yi hakuri dai a cigaba da bibiyar labarin Ana Kai zuciya Nesa Kar a daki Naseer ko Naeema*🤣🤣🤣🤣🤣🤣 *This page is yours Surayyams Marubuciyar Ajalin so Ina San yanda kike bin novel din kike Kuma fito da lessons din ciki kina fahimtar da mutane* *Page 34* Kuka nake kawai Ina jijjiga Waleed da naji kukansa ya karade ko'ina kamar ya saka lasifaka Sauri nake ta zabgawa Ina ganin Kamar Kukan waleed na iya sawa Naseer ya biyomu tunanina rabuwa gida biyu yayi Ina tuno yanda Zahira ta Shiga band'aki tana waiwayena. Irin dukan da Safiyya da Umma ke Mata Agaban idona sabida kawai a yarana tafi Kama dani komai nawa ta d'auko kiyayyar da sukemin ya shafeta Anya matakin Dana dauka shi ya dace kuwa na bar Wa Umma yarana Ni nasan sai ta kashe su. "Idan Kika biyewa Makomar yaranki Uwar mijinki watarana zata ci Galaba akanki wajen rabaki da Numfashinki ganganci ne cigaba da zama da ita tunda kiyayyar da take Miki a bayyane yake Naeema rayuwa da kike gani kowa da yanda Allah ya tsara Masa yau da mutuwa kikayi fa Kika bar yaran?ko kinsan akwai yaran da tun suna kananu Suka taso ba uwa ba uba kin taba zuwa gidan marayu Kinga yaran da basu da kowa suke rayuwa su kadai Zahira shekararta Sha hud'u ta tafi na Sha biyar Nadeeya tana da Sha uku har ta iya girki ta kula da kanenta Kinga kuwa da wayonta. Kina ganin Naseer zai Bari Mahaifiyarsa ta cutar da yaransa idan ke ya bar mahaifiyarsa ta gana Miki azaba bana Jin zai Bari a tab'a Masa yaransa Dan Haka tafiyarki shi yafi alheri Neeema inyaso kiringa zuwa kina duba yaranki a Kai akai" Maganar matar Ala ramma da nake cewa Aunty ya fad'omin yanzu Haka ma gidan kanwar ta zanje na jirata idan gari ya waye zata kawomin kayana daga Nan su rakani Tasha Dan isihu ya dage sai yaje ya ga garinmu yaga Inda nake zaune kafin ya dawo Duk da hankalina ya rabu gida biyu ahaka nayita zabga Sauri har na iso bakin titi na tsallaka na cigaba da tafiya har lokacin kuka Waleed yake Ina jijjiga shi Nima kaina kukan nake a Haka na iso gidan kanwar Aunty na bubbuga ba dadewa kuwa ta bud'e dayake mun tab'a haduwa a gidan Ala ramma ta sani ta kuma San da zuwana Ciki na shiga ta rufe k'ofar Haka kawai na fashe da kuka da yake mijinta baya gari Palonta muka Shiga na kunto Waleed na rungume shi a kirjina Waleed Kamar yasan Mai ke faruwa bashida kuka amma sai gashi yana ta kuka. Hakuri kawai take bani tana rarrashina. Nidai gani nake kamar bazan iya tafiya na bar yarana ba ada na dauka zan iya Amma yanzu Kuma da na fito daga gidan Ina tuno yanda Suke wa yarana sai naji bazan iya ba. Dayake itama kanwar matar Ala ramma yayarta ta Bata labarin komai a kaina cikin tausayawa ta fara min magana tana "Ni sai nake ganin kamar guduwa ki bar yaranki bashine mafita ba Naeema kikayi hakuri duk tsawon lokacin Nan ballantana yanzu Agaban idonki ma Ana cin zalin yaranki Ina ga bakya Nan nidai Dan aunty ta dage ki tafi ne wlh da kinyi zamanki ai wuya Bata kissa Kuma komai Mai wucewa ne idan kayi hakuri idan. Allah ya raya Miki yaranki wlh da kansu zasu iya kwato Miki yanci a wajensu tunda ance Minal karama ma na musu rashin kunya Amma har ga Allah Nima ban goyi bayan tafiyarki ba" Cikin tsananin kuka na fara magana Ina "Ya zanyi Nagaji ne mmn Abdul nayi hakurin nayi biyayyar nayi rokon duk a banza shekara Sha biyar Ina k'unsar bakin ciki mmn Abdul ba Dan Ina da tsawon rayuwa ba da sun Dade da kasheni wlh gajiya nayi da abinda sukemin tacemin Ni Mayya ce naki rabuwa da danta Ina neman na kaina tace karuwanci nake yaron Nan sai data sheganta shi Naseer baya iya komai sai dai ya bani hakuri nace Miki da cikin yaron Nan guba suka zubamin a abinci Dan kawai naci na mutu yau da gobe watarana zata iya cin Nassara akaina shiyasa na yanke tafiya na bar Mata gidan indai na tafi da yarana wlh Naseer sai ya biyoni Ni Kuma shiyasa na bar yaran Dan tasan dgsk nake zan iya rayuwa babu Naseer Amma yanzu Dana bar gidan wlh sai naji kamar bazan iya tafiya ba Ina tausayin yarana da basu ji ba Basu gani ba bana San a cutarmin dasu gwara Ni na cigaba da Shan wahalar da su Sha wahalar. Kuka itama mmn Abdul ta hau yi tana "Allah ya tsinewa matar Nan Albarka k'arfi da yaji ta hanaki zaman lafiya da miji ta Kuma rabaki da yaranki Allah ubangiji ya saka miki" Kuka nake sosai har ta mik'e ta fita bud'e kofa da ake kwankwasawa sai Gata ta shigo ita da aunty da Niki Niki kayana Isihu shima da wasu kayan jikinsa a sanyaye shima Kamar zaiyi kukan Aunty palon ta shigo ta zauna tana "Ya Naga kuma kina kuka kinsan Allah Kika biyewa tausayin yaran bazaki iya tafiya ba gwara ki tafi tsinaniyar ta Gane ke kike rik'e da gidan ko ba ke bace kina da amfani a gidan ko bakida shi. Yanzu Nan na biya na karbi kudin engine nacewa wacce ta siya anjima ta je ta dauki injina Naga ta tsiya ba dai kin bar Wa Naseer kudi ba" Gyad'a Mata Kai kawai na iya Yi Ita kuwa ta cigaba da bambami "Maza share hawayenki ki tashi muje Tasha Dan inaso na dawo a yau d'inan karbi kudin injin" Tace tana mik'o min kudin hannunta Kasa karbar kudin nayi inajin kamar bazan iya tafiya ba nadamar ma siyar da engine din markade na nake yanzu dame su Naseer zasu ringa samun na abinci Ni sai na ringa nadamar ma daukar shawarar ta duk da nasan duk tayi hakane Wai Dan Umma ta Sha wahala Amma Ni Naseer da yarana nake tausayi. Tana k'ok'arin Magana mmn Abdul ta fara magana tana "Aunty sai nake ganin kamar tafiya ta bar yaran Nan bashine mafita ba ki dai sake tunani duk tsawon lokacin Nan wuyan data Sha sabida yaran Nan ne Bata gudu tun lokacin ba sai yanzu Kuma Naseer ya Mata hallaci da Bai cancanci Haka daga wajenta ba taurin Kai daya gwada.yaki bin umarnin Mahaifiyarsa ya jefa shi a halin da yake ciki Amma kwatsam yanzu yaga ta gudu ta barshi da Yara wlh zaiji ba dadi a ransa Ni nasan Mai yasa Baya iya yin komai mahaifiyarsa ce Bai San ya zai Mata ba Yana k'ok'arin biyayya ma tace Yana fifita Naeema akanta inaga Kuma ya fito ya nuna bayaso abinda ake yiwa Naeema kinsan abinda zatayi sai yafi Haka a gaskiya aunty ki duba maganar nan" "kimin shiru larai kinsan Mai matar Nan take yiwa Naeema kuwa?kinsan Abubuwan da duk take mata kuwa kasheta takeso tayi fa akan me zata cigaba da zama a gidan? Ke idan kece Zaki iya jure duk abubuwa da ake wa Naeema.?Naseer da kike magana akansa Naga guduwa yayi ya barta da yaran Naeema ita ta tsaya tsayin.daka ta nemi kudi duk da cikin jikinta ta tsayawa yaranta itace cinsu da shansu makarantar su abinda Naseer ya guje wa itace ta ringayi kwatsam wanan tsinaniyar matar Nan ta danno ita da kanwarsa suka hau gallaza Mata duk abinda zatayi idonsu.na Kai Naseer din ma ya dawo ba abinda ya canja sai ma gaba da yayi Dan me zata cigaba da zama wlh cigaba da zama a gidan kamar tana Wasa da rayuwarta ne Yara nawa ne suke rayuwwa ba iyaye ballantana yaran Nan da ubansu Dan nasan tafiyar.Naeema bashi zai saka shima ya tafi ba Dan Haka ya zama Dole ya kula dasu Kuma Nima duk abinda zasuyi idona na kansu tunda Isihu zai cigaba da zuwa gidan Kuma yaran na zuwa islamiyya Mallam idan dai ta musu wani Abu wlh Tallahi sai na Kai kararta na tsani matar Nan wlh Tallahi yau da nice Naeema da tuni nayi maganin matar nan" "Duk da haka Aunty Tafiyar Naeema bashine mafita ba dann kamar ka kashe miciji baka sari kansa ba Naeema zata tafi ne Amma tunanin ta na Nan Dan Haka Aunty Mai zai Hana tayi Zamanta a garin Nan Amma a wani unguwar hankalinta sai ya Dan fi kwanciya inyaso duk lokacin data so ganin yaranta zata iya zuwa gidanki a boye idan sun zo islamiyya sai ta gansu batare da Shi Naseer yasan Inda take a garin Nan ba ta Kama haya ta had'a Kan kudinta ta ringa sana'a Bansan lokacin Dana mik'e na rungume Mmn Abdul ba na kalli Aunty Ina "Aunty Dan Allah muyi hakan nima sai nafi samun kwanciya hankali a Haka ma wataran na kwashe yarana gabadaya batare da sun sani ba ki taimaka min Dan Allah banida kowa sai Allah sai ku danake ji Kamar Yan uwana" Aunty ajiyar zuciya ta sauke tana toh shikenan. Ni kuwa take naji sanyi a Raina Aunty ta koma ta zauna Suka fara shawarar Inda ya dace a samo min karamin gida na haya na zauna ahaka suka yanke nemo min gida a dorayi Dan suna da Yan uwa acan Amma kafin a samo gidan na dai tafi Bauchin na duba gidanmu na siyar sabida na samu ishahsen kudi a hannuna da zan ja jari. Haka kuwa akayi wajen karfe goma na nufi Tasha bayan Aunty tace min ita Kuma zata wuce dorayi ta cigitamin gidan Haya idan an samu kafin na dawo zata biya kudin hayan. NASEER Haka kawai yaji ya kasa nutsuwa yayi sallah hankalinsa yayo gida gabadaya hakane yasa Ana iddarwa ya fito da saurinsa a bakin kofa yayi kicibis da zahira dake k'ok'arin yin waje cikin tashin hankali Gabansa yanke wa yayi ya fadi Yana "Ke lafiya Ina Zaki"? "Abba Umma nake nema yanzu tace na Shiga bandaki nayi alwala na tashi su Nadeeya shine Dana fito banganta ba na duba koina banganta ba" Ta karashe da rawar murya idonta na cika da hawaye Naseer jikinsa ne ya hau rawa cikin tashin hankali ya Shiga gidan ya duba koina ya fito Yana sallati Tare da yin waje kafa ba takalmi duk nisan titi Haka ya je kafa ba takalmi Zahira na biye dashi tana kuka. Ba ta Inda Bai duba ba Bai ga Mai Kama da Naeema ba. Kamar Wanda ake sassarewa kafa Haka ya dawo gidan Yana Jan kafa Zahira nata kuka Dan tasan Naeema ta tafi ta barsu tunda kwana biyu kenan tana cewa ta kula da kanenta idan tace Umma tafiya zakiyi sai tace aa Naseer d'akin Naeema kawai ya nufa Yana Jin jiri na dib'arsa. Bayan ya d'au takardar da Naeema ta ajiye Mishi a bakin kofa. Ya kwanta rigingine hawayen da yake San maidawa ta karfi Suka hau zubo masa. Zahira kuwa Kamar wacce akayiwa duka tabi bayansa tana cigaba da kuka Ahaka Hajara da Safiyya suka fito sabida yanda kukan zahiran ke tashi Har d'akin Naeema Suka Shiga suna dube dube har Hajara na fatan Allah yasa Naeema ce ta mutu Zahira na ganin sun shigo ta hadiye kukanta da Sauri jikinta ya hau rawa Naseer kuwa ya bud'e idonsa yana kallon Hajara dake kalle kalle a d'akin ta dawo da kallonta Kan zahira tana "Ke Dan uwarki kukan me kike Mana da asubar nan"? Zahira bata iya magana ba ta matsa kusa da Naseer daya tashi zaune ya jingina da bango Yana kallon Mahaifiyarsa har lokacin hawaye na gudu a fuskar sa hawayen da ke Kara saka Zahira damke bakinta Dan Kar kuka ya kwace Mata a gabansu Hajara da take ganin tamkar malaikan da zai zare Mata Rai. "Dan uwarki bazaki gayamin ba kukan me kikeyi ke da ubanki ko uwarki ce ta mutu"? Wani irin murmushi daya fi kuka ciwo Naseer yayi ya d'auke hawayen fuskarsa ya kalli Hajara Yana " Ba mutuwa tayi ba ta dai tafi ta bar miki gidan Kamar yanda kikeso ta tafi da Waleed ta bar sauran yaran" Hajara Kara dudduba d'akin tayi Wai Dan ta gaskata maganar da kunnenta ke jiyo mata Naseer kuwa yanda Safiyya ta washe baki murnarta na fitowa fili yasa ya fara jifanta da wani irin kallo tayi waje da Sauri Hajara kuwa ta fito ta lek'a koina taga dagaske dai Naeema Bata Nan ta koma d'akin taja Tsaki Tana "Ni zaku rainawa Hankali yau ta Saba guduwan ta Kuma dawowa Naga Haka kuka rainamin hankali na gano kuna taren yanzu ta Inda kuka Kara b'ullo wa kenan ta tafi idan an kwana biyu sai ka bita Kai da yaran ko"? "Umma Naeema ta tafi idan da hada Baki mukayi da ita wlh bazaki gani a d'akin Nan Ina kuka ba da ace hada Baki mukayi bazata bar min yaran Nan ba barin yaran Nan da tayi ya Isa yasa kigane gajiya tayi da abinda kike Mata Umma sanin kanki ne banida komai Naeema ita ke rike da gidanan daidai da abincin da zamu ci ita take bamu yanzu data tafi daga Ina Zan fara Umma Ni Kam bansan Mai na Miki a rayuwata ba bansan Mai yasa kike San ganina a kuncin rayuwa ba" "Ba abinda kamin Dan albarka Naeema ce kawai na tsana karka wani damu da tafiyar da tayi dama so take kawai ta gudu Dan taga ka talauce iya tafiyar da tayi yaci Yasa kagane ba Dan Allah take zaune da Kai ba karka wani damu da ita take komai a gidanan Nima Zan cigaba daga Inda ta tsaya markade ne na iya zobo da ruwa nima na iya k'ulawa ai Dan Haka Kar ka wani damu Dan albarka idan Allah ya yarda da kaina Zan Nemo maka matar da zata zauna da Kai Dan Allah Mai ake da Naeema" Ta karashe tana yin waje cikin tsananin farinciki kamar wacce akayiwa bushara da gidan Aljanna. Naseer Bai iya ce Mata komai ba har ta fice Zahira kuwa ta matsa daga kusa dashi ta fita d'akinsu ta cigaba da kukanta Su Nadeeya na k'ok'arin fitowa daga d'akin Dan su shiga d'akin Naeema Suka hadu da Naseer a bakin kofa hakane yasa Suka koma ciki Naseer ya shiga d'akin ya zauna a tsakiyarsu Yana Jin zuciyarsa na Masa wani irin Nauyi Raheema da ke da shekara hudu ya kala ya d'auketa ya dorata a cinya Yana maida hawayen dake neman zubo Masa ya hau magana a fili Yana "Baki kyauta min ba Naeema baki min adalci ba da Kika gudu Kika barni da yaran Nan Mai yasa Kika gudu a lokacin da muka fi bukatarki?Mai na Miki da zafi Haka zakimin Haka"? Kinsan banida kowa sai Allah sai ke sai yarana ku nake gani naji dadi Amma Naeema Kika Shure Kika tafi sabida Mahaifiyata Tana Miki ba daidai ba duk hakurin Dana ringa Baki akan kiyi hakuri da halinta Nima addua nake Akan Allah ya shiryeta Naeema baki zabi guduwa ba sai a irin wanan lokacin ? akanki Mahaifiyata tamin Baki har yau bana ganin daidai duk kudin Dana rik'e basa albarka na zabi Zama dake a kowane Hali na zabi nayi rayuwar talauci Dan kawai na zauna dake Bayan irin kudaden Dana Kama a baya duk ban damu da rasa sun danayi ba sabida ke Amma yau sabida tsangwamar da Mahaifiyata ta Miki Kika gudu Kika barni da Yara Mai yasa Naeema Mai kikeso nacewa yaranmu"? Naseer ya karashe muryarsa na rawa magana yake shi kadai kamar da Naeema yake magana Nadeeya da Minal kuwa cewa suke Ina ummansu taje.haka Suka lek'a d'akin Suka dawo Suma Suka hau kukan. Hakane yasa Naseer ya share hawayensa Yana Zahira ta tashi ta Dora musu abinci su tafi makaranta. Zahira hka tayi waje tana share hawayenta. Naseer kuwa ya warware takardar da Naeema ta ajiye Mishi ya fara karantawa *NASEER KAYI HAKURI DA MATAKIN DANA D'AUKA NA RABUWA DA KAI NAGAJI DA ABINDA UMMA DA AUNTY SAFIYYA KEMIN NAGAJI NASEER UMMA TACE NI MAYYA CE TACE NI KARUWA CE BA IRIN ABINDA UMMA BATAMIN INA SHANYEWA AMMA YANZU NAGAJI DAN NAGA KIYAYAR DA TAKEMIN KARUWA YAKE BA RAGUWA BA KIYAYYAR DA TAKEMIN YA SHAFI YARANA GABADAYA DAN HAKA KAFIN NA HAIHU NA MATA ALKAWARIN RABUWA DA KAI INDAI ALLAH YA SAUKENI LAFIYA HAKANE YASA NA CIKA MATA WANAN ALKWARIN DANA D'AUKA NA TAFIYA NA BAR RAYUWARKU NA HAR ABADA ZAN RINGA ZUWA GANIN YARANA INSHA ALLAHU KASA KANKA A MATSAYINA KO KAINE MATAKIN DA ZAKA DAUKA KENAN A KARSHE NASEER NA HADAKA DA GIRMAN ALLAH KA KULARMIN DA YARANA KARKA BARI A CUTARMIN DASU NASEER BAZAN YAFE MAKA BA IDAN WANI ABU YA SAMESU NASERR UMMA TA TSANI ZAHIRA ITA DA AUNTY SAFIYYA NA BAKA LABARIN YANDA SUKE CIN ZALINTA A GABAN IDONA NASAN ZASU IYA KOMAI YANZU A BAYAN IDONA NASEER YARAN NAN AMANA NE A WAJEN MU KARKA BARI MAHAIFIYARKA TA CUTARMIN DASU NASEER KASAN YANDA NAKE KAUNAR YARANA BA ASAN RAINA NA TAFI NA BARSU BA DAN ALLAH KA KULARMIN DA SU NA BAKA AMANARSU AN FI TSANAR ZAHIRA KA SA IDO AKAN SU NA AJIYE MAKA KUDI A KARKASHIN KATIFA MAI YAWA ZAI ISA KAJA JARI KA KULARMIN DA YARANA NA SIYAR DA INJINA NA GUDA BIYU SABIDA NA HADA DA KUDIN WAJENA NA JA JARI NIMA KAYI HAKURI HAKA ALLAH YA KADDARA MANA RABUWAR MU SHI YAFMIN ALHERI DAN UMMA KARFI DA YAJI TAKE SAN KASHENI KAYI HAKURI BA A SAN RAINA NA GUDU BA NGD DA KAUNARKA A GARENI DUK.LOKACIN DANA TASHI ZUWA GANIN YARANA ZAN TAHO DA WALEED KA GANSHI* cukwikuye takarda Naseer yayi batare da ya karasa karanta Takadar ba sabida yanda jikinsa ke rawa zuciyarsa tayi balain nauyi a fili yace "Ni kuma tawa kaddarar kenan Allah ka bani ikon cinye wanan jarrabawa ka bani ikon sauke nauyin daka doramin na yarana. Waje ya fita yaga Safiyya na shara tana wake wake su Nadeeya sunyi cirko.kamar marayu Zahira kuwa Tana Kitchen ta kurawa waje daya Ido Kitchen din ya Shiga ya cigaba da girkin yacewa zahira ta shirya kannenta kafin ya Gama Yana gamawa a faranti ya juye musu ya Kai abincin har Palo ya zaunar da Raheema a cinyarsa ya hau Bata a baki Nadeeya da Zahira kuwa kasa cin abincin sukayi duk yanda yayi dasu kuwa Akan suci abincin. Ahaka suka fito Bayan ya d'auki naira Hamsin ya rakasu har bakin makaranta sai daya ga shigarsu ya koma gida. Sai dai tundaga nesa ya hango Hajara taci uwar damara ta Hana a fita da engine da wasu maza Suka zo dauka sai balai take tana tsalle tana hango shi ta nufo wajensa da Sauri tana "Kajimin shegu tsinannu Haka kawai suka zo d'aukar engine Wai wacce ta siya ce tace su zo su dauka Naga engine Naeema ne wacce matar Kuma suke magana kaji barayi" "Naeema ta siyar da engine yanzu ba nata bane masu shine suka zo d'aukar kayansu" Naseer yace tare da cewa.mazan su dauka su tafi Ya shige gidan ya bar Hajara na balai bazata yarda a fita da engine ba Samarin kuwa ganin er tijara ce da k'arfi Suka fita da engine Hajara data tare hanya suka hankadata gefe ta zub'e a kasa Safiyya itama ta hau rantsuwar bazaa fita da engine ba Dan sosai suka.gama lissafa yanda zasu samu kudi da engine Umma har da lissafin zata siyi fili Dan sunga yanda Naeema ke samun kudi da engine markaden sosai suka tiki rawa a dakin Dan murnar tafiyar naeema.sai gashi Ashe ma ta siyar da engine Suna ji suna gani aka tafi da engine Hajara Kamar tababbiya ta nufi d'akin da Naseer ke kwance......... *Comment* Nikuwa aganina batayi kuskure ba Ayadda Dan Adam,musamman ma mace take da rauni ai baza'ace ma naeema komi ba Dan kuwa tayi balain kokari... Awajena bunda ya dace tayi kenan adaidai wannan gabar. Ki duba fa Da can sunce arxikin shi yasa ta makale masa Amma yanzu itace mai rufin asirin Amma kuma sunce kudin karuwanci ne Kuma dan naseer na taimakonta da aikin gida sunce tayi kudi ta mai dashi boyi boyi. Haba jamaa abun Sam babu dadi gaskiya ko mai tsananin Imani ne saiya raunana.. Tunda har ba ita da bakinta ta nemi saki kotayi fitar fushi wallhy harga Allah batada wani lpya Her decision was based on nazarin data rinka yi ba acikin son zuciya da gaggawa ta yanke shi.. Inhar da ace nice naseer wallhy zan kyaleta hakanan itama taje ta huta Amma bazann taba in saketa ba,ai zataje din Kuma itama zataji abunda yaji aransa lokacin dayayi tunanin guduwa ya barsu acikin ukubu shine mafita. Hanklinta na kwanciya zakiga ta dawo ,but ni banga lefinta ba kokadan Every body derserve a break and refilled. In dauriya yayi yawa sheidan yakan saurin batar da mutum ta hanyar rusa masa aikinsa da mugayen tunani har akaiga kayi asarar tulin hakuri da jajircewan da kayi,Is best dat she leave queitly gaskiya.👍🏻 *NAGA TA KAINA* *NA SADNAF*🌸🌸 ®️ *_PURE MOMENT OF LIFE WRITERS_* _{We Don't just entertain nd educate we also touch the heat of readers P.M.L}💪🏻_ *Free Novel* *Page 35* "Kana kallo Suka fita da engine baka hanasu ba yanzu ta Ina zamu ringa samun kudin da zamu kashe"? "Toh Mai engine ta siyar da kayanta Mai shi yazo ya d'auka ta Ina Zan Hana Umma abinda ba nawa ba" "Kai Amma yarinya nan Allah sai ya tsine Mata muguwa idan ba mugunta ba ai ko Dan yaranta ta bar engine dinan sabida a samu na kula dasu Amma dayake bata da mutunci shine ta siyar da engine duka biyu idan ma tayi hakane Dan mugunta ai har da yayanta ta cuta wlh dadin abin ba iya markade akeyi a gidan ba Ana kulla zobo da ruwa Kuma a siyar Nima dai ba kuturwa bace inada hannun da Zan kula ruwa da zobon na samu na kaina wlh ko kallon yaranta bazan yi ba Kai Kuma zaman gida ai Bai kamaka ba tashi zaka Yi ka fita ka nemo kudi ba kazo ka shige daka ka kwanta Kai ga uwarka ta rabu da Kai ai Zama Bai kamaka ba ya zama dole kaje ka Nemo duk inda kudi yake ka nuna Mata Kai Dan halak ne insha Allahu sai kafi da arziki tashi Maza idan wanan shegen isihun yazo Zan aikeshi yamin cafenen zobon na hada ya kaimun" "Ko na fita Umma bazan samu ko sisi ba ko na samu ma bazai Yi albarka ba Dan kin riga da kin tsinewa samuna Umma ko mantawa kikayi kin Kona duk dukiyata ta bakin naki kudi sai yamin wahalar samu yanzu gashi ai kingani kudi Yana min wahalar samu Umma kusan wata Takwas nayi a Abuja Ina neman kudi cikin tsananin wahala Umma Wanda ma na Dan samo sai da Yan fashi suka kwace a hanya ba abinda na taba yanzu dayake albarka" "Duk ba Kai ka jawo ba sabida tsinanen taurin.kanka zuciya ya debeni nayi abinda nayi da Nima yazo ya shafeni Dan Haka batun ma Ni na jawo duk laifinka ne na saka albarka yanzu idan Allah ya yarda zaka samu kudi ka shirya kaje ka nemi kudi" Daga Haka ta fito tana tsinewa Naeema akan ta siyar musu da engine. Rai a bace Haka Suka zauna a tsakar gidan suna ta kwashewa Naeema albarka Dan canjin daya musu saura tasa Safiyya ta d'auko Suka lissafa abinda zasu kashe na hadin zobon suka zauna zaman jiran Isihu sai dai har karfe Sha biyu Basu ganshi ba ahaka Hajara ta lek'a da kanta Wai ko zata hango shi Nan ma Bata gan shi ba haka ta dawo ta Kara komawa d'akin Naeema ta tarar da Naseer a zaune a Kan Sallaya Dan tunda ya iddar da walha Bai bar Kan sallaya ba carbi kawai yake ja. "Kaga shegen almajirin Nan Bai zo ba inata jiransa tundazu ko dashi ta tafi ne"? Alama ya Mata da hannu alamar Bai Sani ba Hajara kuwa ranta ya b'aci tana "Kai bana San iskanci Naga duk abinda ma shegiyar matar Nan tayi ba abinda ya dameka sai Abu kake Kamar wani maraya toh tunda Bai zo ba Kai Kuma ka k'i fita ka Nemo Mana kudi sai ka tashi kaje kayo min cafenan zobo idan zuciyarka ta mutu Ni tawa ba ta mutu ba idan tafiyar Naeema ne ma yasa kake wani nonok'ewa zaka ware me dalla tashi ka siyomin zobo da suga da farin Leda" Ta karashe tana jefa mishi kudin hannunta. Naseer ya d'ago da rinannun idonsa Yana "Ina Safiyya Umma da Ni zanje na siyo Umma Dan banida kudi Bai Kamata na zama kamar yaro da sai yanda akayi dashi wanan ma na iya janyo min raini a wajen Safiyya Ina gaba da ita ki wuceta kizo ki aikeni haba Umma" "Kace kawai ban Isa dakai ba Naseer ai kafita sanin unguwar Nan sai ka fita sanin Inda ake siyar da kayan zobon shiyasa na kawo maka" "Ki Bata idan ta fita tayi tambaya zaa nuna Mata" "Nifa bazaka zauna a gida ni Kuma na ringa fafutukar neman kudi ba Dan Haka ko bazaka siyo ba ka zura rigarka ko dakone kaje kayi Dan Idan ma takamarka Kayan abinci da ake dashi a gidanan ne kwanan Nan zai Kare wlh Nima yanzu sama na da kasana iya kudin Nan ne Dani Dan Haka nemo kudi ya kamaka" Daga Haka ta fice daga d'akin ta bawa Safiyya kudin ta lissafa mata abinda zata siyo Mata ta karbi kudin tayi waje tana zagin isihun da Bai zo ba Naseer kuwa Yana fitowa Kitchen ya Shiga ya fara k'ok'arin dorawa su Zahira abincin Rana Hajara kuwa tace ya fita idan Safiyya ta dawo zata Dora musu abincin. Naseer Bai. Ce Mata komai ba ya cigaba da abinda yake Dan wasikar da Naeema ta bashi na ya rik'e amanar yayansa ya rik'e gam akansa bazai soma barin Safiyya ko mahaifiyarsa su dafawa yaransa abinci ba. Haka Hajara tayi ta bambamin fad'a har Safiyya ta dawo. Dayake taliya Naseer ya Dora musu Nan da Nan ya Gama Dan akwai Miya Mai yawa a freezer din dake d'akin Naeema Dan har freezer ta siya da ta samu kudi ta daina siyan kankara. Haka take Miya Mai yawa sai dai su dafa shinkafa ko taliya Miya tuwo ma Haka take yinshi da yawa. Yana gamawa ya zuba wa su Hajara a kularsu ya d'auki sauran ya Kai daki Kamar yanda yaga Naeema nayi Ya daura alwala ya fice daga gidan Hajara da Safiyya dake kula zobo da ruwa suka bishi da kallo har ya fice. A Kular da Naeema take zuba zobo da ruwan Suka zuba Hajara ta nufi d'akin Naeema Dan ta dauko kankara sai dai tana zuwa taga k'ofar a kulle. Masifa ta ringa surfawa akan me Naseer zai kulle k'ofar d'akin Mai ya mayar dasune. Haka ta koma ganin Bata San lokacin da Naseer zai dawo ba yasa ta bawa Safiyya sauran kudin hannunta ta siyo musu kankara Suka zuba Suka zauna zaman jiran Isihu da sai daya Sha tsinuwa yafi cikin kwando Hajara har da Shan alwashin wanka Masa Mari idan yazo. Naseer kuwa Yana fita a Massallacin dake kallon gidansa yayi zamansa bayan ya iddar da sallah Yana tunanin yanda zai fara fuskantar rayuwa batare da Naeema ba Bai San Mai yasa Bai tab'a koyawa kansa rayuwa batare da ita ba a yanzu da ta tafi a lokacin da Bai tab'a tunani ba sai yaji Kamar rayuwarsa ce ta tsaya Amma ba yanda zaiyi Haka zai rungume sabon Shafin kaddarar daya bud'e Masa. Ganin biyu tayi yasa ya fito daga Massallacin a daidai lokacin daya hango su Zahira suna Shiga gidan. Hakane yasa yabi bayansu. Suka Shiga gidan kusan a tare. Daga Safiyya har Hajaran ba Wanda ya amsa Sallamar da sukayi. "Ka ajiye Mana abinci ba Miya ka Kama kanya ka fice tare da kullo k'ofar d'akin da bansani ba ko Gwal aka saka da zaa ringa rufewa sanan name idan an gama girki zaa wani shige dashi d'aki to daga Yau wlh idan anyi abinci Kar akara Shiga dashi d'aki idan uwarsu na Shiga dashi d'aki sabida Bata yarda Dani ba Kai ma yarda ne bakayi Dani ba shiyasa kake kaiwa daki kenan toh wlh Kar a sake idan ba Haka ba sai ranka ya b'aci" "Ke maza ajiye jakar hannunki ki je Makarantar islamiyyarku ki kiramin wanan shegen almajirin tundazu na zauna Ina jiranshi yazo.ya kaimin zobo da ruwa har yanzu Bai zo ba narasa Mai ya Hana shi zuwa ko Uwarku ce ma ta zuga shi tace.kar yazo Dan ta tafi" Hajara tace tana hararar Zahira data yi saurin ajiye Jakarta cikin rawar jiki zata yi waje Naseer yayi saurin rike Mata hannu Yana "Bari ta fara cire uniform din jikinta taci abinci tayi Sallah kafin ta tafi yanzu Nan ta shigo gidan fa Bari ta Dan huta" "Iyyeee Naseer Ni nake Aiken Yarka kake hanata akan sai ta huta kafin taje kana cikin hayyacinka kuwa ko Tafiyar Naeema yasa ka fara shaye shaye toh wlh sai taje Naga idan ma aka siyar da ruwa da zobon Kai ma zaka ci a kudin Dan Haka maza wuce ki kiramin shi kafin naci ubanki" Da mugun gudu Zahira tayi waje. Naseer kuwa idonsa ya kad'a yayi ja shi kam zuciyarsa na Dab da bugawa sabida tashin hankali da rashin nutsuwa sosai yake Jin gidan na Masa zafi kamar ya hada kayansa ya rik'e hannun yayansa ya gudu barwa Hajara gidan Ahaka ya rik'e hanunsu Nadeeya suka Shiga karamin Palo ya cirewa Raheema uniform ita da Humaira ya saka musu wani kayan ya zubo musu abinci suka fara ci Nadeeya kuwa cewa take Umma Bata dawo ba? Bai kulata ba sabida gani yake magana ma wahala yake masa. Muryar Zahira dayaji yasa ya mik'e ya fita "Ance Baya Nan yayi tafiya" Zahira tace da rawar.murya "Maganata ta fito Ni nasan dashi ta tafi Dan da safe yake zuwa gidanan nan wanan abun da tayi ya tabbatar min da ita muguwa ce ta karshe wato shima isihun bazamu more shi ba toh ai shikenan kanta ta cuta wlh Dan ke Zaki kai min ruwa da zobon bazan dau asara ba wlh maza jeki cire Kaya kici abinci kizo ki dauka yanzu yanzu ki siyarmin" "Aaaa Umma Zahira bazata taba talla ba ba iya ita ba insha Allahu yarana baza suyi talla ba Haba Umma ko wani Kika ji Yana cewa zai Dora wa Zahira tala ai ke Mai hanawa ne Umma karki.manta yaran Nan ba iya Naeema ce ta haifesu ba yayana ne Kuma jikokinki Dan Haka Bai Kamata kiyayar da kikewa mahaifiyarsu ya shafesu ba da Raina bazan iya Bari yarana suyi Tallah ba Umma kiyi hakuri" Sakin Baki Hajara kawai tayi tana kallon Naseer dake ta kwara bayani "Yau Ina ganin ikon Allah toh iskanci nace taje tayi kake zabga min wanan Bayanin Naseer daga Kai har Naeema idonku ya rufe da San Yara bakwa so moresu ko ayi musu tarbiyya Naseer Naga idan ta siyar da ruwa da zobon kananun Abubuwan da babu Zan iya d'auke maka a gidanan tunda Kai zuciyarka ta mutu ka kasa fita ka nemo tundazu nake binka akan kaje ka Nemi kudi ka kasa sanann Dan nace Zahira ta Kai Mana tallan ruwa da zobo kace bazata je ba toh wlh sai taje idan dai har ka dage bazata je ba toh wlh sai dai Kai ka dauka ka kaimin da kanka tunda Ni na Haifeka na Kuma Isa dakai" "Da Zahira ta je tallan Nan Umma gwara na je da kaina Sanan Mai amfamin ita Safiyya da bazata je ba sai Yar karamar yarinya Nan zaa ce taje" Hajara na k'ok'arin Magana Naseer ya dakawa Safiyya tsawar daya gigita Safiyya ta mik'e batare da ta shirya ba "Dan uwarki d'auki zobo da ruwan kije ki siyar tunda kin k'i fito da miji kiyi aure Maza mik'e dan yarana ba bayi bane da Zaki Mike kafa a nemo.a kawo.miki ki dauka nace kafin na hada.kanki da bango Naseer yace Yana nufar Inda Safiyya take. "Wlh bazata je ba Naseeru tunda ka Hana Zahira zuwa Kai da kanka zaka je" "Wlh Nima bazanje ba Umma Dan Babu yanda kanwata tana zaune kina kallonta kice Zahira taje talla ko Ni wlh ko ta Kai tallan Nan ko ta barmin gidana umma Dan Nagaji da Zamanta a gidana ki dauka nace" "Wlh bazanje ba Haka kawai Zan d'auki kula akaina na fita talla da girmana da komai" Safiyya tace tana k'ok'arin Shiga d'akinsu. Naseer kuwa ya fusgota cikin zafin nama zuciyarsa na tafasa kwallo kawai yake da Safiyya tana zunduma ihu duka yake Kai.mata ko ta Ina Hajara kuwa ta hau rike Naseer tana ihun wlh ya cikata zata tsine Masa kashe Safiyya zaiyi Naseer da Ransa ya Kai kololuwa wajen b'aci idonsa ya rufe sosai baya ma Jin abinda Hajara ke cewa dan ji yake kamar dukan da yake wa Safiyya ne kawai zai rage Masa radadin zafin dayake ji a zuciyarsa . Hajara kuwa ganin idan batayi da gaske ba zai kashe Safiyya tana ji tana gani Muciya ta dauko aguje tayi Kan Naseer......... Ayi.maneji yau naje Dubiya *NAGA TA KAINA* *NA SADNAF*🌸🌸 ®️ *_PURE MOMENT OF LIFE WRITERS_* _{We Don't just entertain nd educate we also touch the heat of readers P.M.L}💪🏻_ *Free Novel* *Page 36* Kafin ta Kai wajen Naseer din ta wurga tabaryar Naseer ya kauce da Sauri Safiyya kuwa a garin mik'ewa ta gudu muciya ya sauka akanta ta saki ihu tana dafe keyarta. Hajara Kuwa tsantsin Inda Suka kulla zobo da ruwa ya deb'eta ta Fadi kafarta ta lankwashe baya ta saki ihu. Naseer kuwa yayi kanta da Sauri ya dawo Mata da kafarta daidai Ita kuwa sai girgiza Kai take tana wayo kafata "Kaga abinda ka jawo ko Sabida Naeema ta tafi shine ka haukace kake neman kashe Safiyya Dan kawai nace Zahira ta Kai min talla shine ka dage bazata Kai ba sai dai Safiyya ta Kai tayaya Zan dorawa Safiya talla tana budurwa Banda bakada hankali Zahira kuwa yarinya ce Amma dayake bakada mutunci kana so ka nunamin ban Isa da Kai ba shine zaka ce bazata je ba gwara Safiyya ta tafi iya Nan Bai isheka ba sai ka hada Mata da duka" "Kiyi hakuri Safiyya Bata fi Zahira ba yanda kike ganin Bai Dace Safiyya ta je talla ba nima.haka nake ganin Bai Dace na bar Zahira ta tafi talla ba bawai Dan Baki Isa da ita bane kema kinsan duk abinda kike cewa ta Miki ban taba hanata ba Amma talla ne bazan yarda Zahira tayi da Raina ba Umma matsawar kudin kikeso sai dai ta Kai Miki tallan gaskiya amma matsawar bazata Kai ba wlh sai dai mu zauna Haka Umma Banga amfanin da Safiyya take min a gidanan ba Dan Ni nasan wasu Abubuwan wlh ita ke sawa kiyi shegiya Shaidaniya Wlh Nagaji da Zamanta a gidana Ki fada Mata ta fito da mijin Aure ko kunya Bata ji tana ta tsufa agabanki a madadin ta nemi Wanda zai Aureta shine ta zaune min a gida tana hadamin balai Umma keda yarana ne kawai kuka zame min Dole Safiyya ba Dole na bace Dan Haka wlh ko kudin na samo iya ke da yarana Zan ciyar bazan ciyar da ita ba" "Ai Ni nasan ka samu tabin hankali Naseer K'arfi da yaji ka haukace sabida Naeema ta tafi Safiyya ba akanka take zaune ba yata ce Kuma dolene ce tunda Kai Kace ba Dolenka bace Ni nasan zafin talauci dayake damunka ne yasa kake Neman hucewa akanmu talla Kuma danace Yarka tayi ai sabida Kai din ne Amma tunda kace Haka naji Amma wlh wanan dai bazanyi asararsa ba sai ka Nemo Mai zuwa ya siyr min dan yanda ka rantse ba Inda zahira zataje nima.na rantse ba Inda Safiyya zataje miji Kuma da kake magana idan Ana siyarwa a kasuwa ka siyo ka kawo Mata Naseeru da kake zancen ta fito da miji kana da kudin da zaka Mata kayan d'akine bakada ko sisi kazo kana zancen tayi aure idan Auren yazo yanzu da uban me zaa kaita bamu ajiye ko sisi ba kafita ka Nemo kudi ka k'i ka zauna zuciyarka ta mutu mace na ciyar da Kai Dan ta tafi ka haukace kana neman kashe min 'ya Naseer hannun Zahira ya rik'e da jkinta ke rawa sabida tsoro Rai a bace Suka Shiga karamin palo yabar Hajara na cigaba da masifar yazo ya biyata kudinta idan ba Haka ba ta huce akan yaransa Bazai iya cigaba da sauraren maganganunta dake barazanar buga Masa zuciya ba Naseer daki ya shige ya kwanta ringingine sabida ciwon da kansa keyi Sosai yake jinsa a takure kamar a prison a yau da Naeema ta tafi bazai iya misalta caza Masa Kai da Mahaifiyarsa tayi ba Wanda yakeji Kamar ya kwashi yayansa su bar Mata gidan inaga Naeema da ta kwashi shekaru tana fama da ita sosai yaji tausayin Naeema ya danne haushinta da yakeji wacce zata iya hakurin Zama da Mahaifiyarsa idan ba Naeema ba. Ya dauka Naeema Mahaifiyarsa ta tsana kila data tafi zai Samu sasauci daga masifarta sai gashi daga shi har yaransa Basu tsira ba ya rasa gane irin halin ta. Dak'yar ya taushi zuciyarsa ya fito wajensu Zahira da har ta ci abinci itama sun saka kayan islamiyya. Hannun Raheema da Humaira ya rike sukayi waje Minal da Nadeeya da Zahira suka bishi a baya Basu samu kowa a tsakar gidan ba sai Dan ihun Safiyya da ke tashi a d'akin Sabida daddane Mata jiki da Hajara keyi da ruwan zafi Dan ba karamin dakuwa tayi a wajen Naseer ba keyarta da muciya ya sameta ba karamin kumburewa yayi ba sai Allah ya Isa take zabgawa Naseer tana rantsuwar sai ta Rama Akan Zahira. A Haka Naseer ya rakasu har makaranta sai da suka Shiga ya juyo ya dawo gida. Yana Shiga gidan yayi kicibis da Kular ruwa da zobon Hajara na zaune ita kadai sai jijjiga k'afa take tana ganinsa ta mik'e tana "wlh ka dauka ka kaimin tunda ka dage Yarka bazata Kai ba dan bazan dau asara ba wlh kaji na rantse maka Safiyya Kuma da kake magana gata can a kwance bama gani take sosai ba sabida yanda ka kumbure Mata jiki. Nima ga k'afata Nan a kumbure inajin ma sai naje Naga likita sabida zugin da yake min banida Kuma ko sisi sai ka siyar Zan samu kudin ganin Likitan maza d'auki da ruwa da zobon na dari biyar da talatin ne" Naseer matsar da kulolin yyi gefe ya wuce ciki Hajara kuwa ta biyo shi tana cigaba da masifa a tsakiyar d'akin ta tsaya ya Shiga bandaki ya d'aura alwala Dan lokacin sallah La'asar ya wuce. Yana tada sallah tayi waje tana ya iddar tana jiransa Sai daya iddar da sallah ya daga katifa ya d'auko kudin da Naeema ta ajiye mishi. Wajen Dubu hamsin ne maida kudin yayi Bayan ya Ciro dari biyu guda uku ya saka a Al jihunsa ya yi waje. Har Hajara zata taso taga ya d'auki kula yayi waje ya dawo ya d'auki daya ya fita k'ofar gida Ya rabar wa da Yara ruwa da zobon yayi zamansa a k'ofar gida Yana tunanin Sana'ar da ya Kamata yayi da kudin da Naeema ta bashi batare da yayi nisa da gida ba Dan ko Naeema Bata ce Masa ya sakawa yaran Nan Ido ba halin mahaifiyarsa bazai Bari yayi nisa dasu ba. Sai da su Zahira suka dawo suka Shiga ciki gabadaya da kulolin Hajara da Safiyya na zaune Akan tabarma. Minal ya bawa kudin Akan ta kaiwa Hajaran Dan bama yaso ya karasa wajenta ta Kara tare shi da wani masifar . Minal na mik'a Mata kudin ta karbe da sauri ta hau kirgawa sai data tabbatar ya cika har da doriya ta washe baki tana k'ok'arin cusa kudin a zaninta Safiyya ta wafci dari biyu tana "bazaki janyo min wanan dukan kici kudin ke kadai ba anjima balangu Zan siyo naci" Hajara hannu ta Kai Dan ta kwace cikin masifa Safiyya ta rik'e kudin gam. Abincin dare ma Naseer ne ya dafa musu. Sai daya tabbatar da sunci sun koshi yasa suka fito da home work dinsu sukayi. Kafin bacci ya d'auki Zahira haka ta ringa Masa maganar Naeema Akan Dan Allah yabi bayanta ko ya Kai su wajenta sai daya daka Mata tsawa ta rufe bakinta da sauri. A ranar Naseer Bai iya runtsawa ba sabida tunani a karshe ya yanke Kara siyan engine markade guda biyu sauran canjin ya siya musu kayan abinci Yana kyautata zaton markaden ne zai saka su Dan samu kudin da asirinsu xai rufu batare da Kuma yayi nisa da yaransa ba duk da yasan sai n an samu matsala ta b'angaren mahaifiyarsa Amma da dai ta dorawa yarsa talla gwara ya siyi engine tunda abinda yasa takesan Zahira tayi tallan sabida rashin engine ne. Haka kuwa akayi Washegari da safe Bayan su Zahira sun tafi makaranta. Ya dauki kudin ya tafi kasuwa ya siyo injina biyu sauran canjin ya siya musu kayan abinci har dasu kayan sawa ya siyowa su Zahira da takalma. Kasancewar ranar Jumaa ne hakane yasa Bai iya komawa gida da wuri ba. Bai karasa gida ba sai wajen karfe uku na rana. Mai taxi na ckin sauke Masa injina yaji ihun zahira hakane yasa ya Shiga gidan aguje. Safiyya ce akan Zahira tana ta dukanta kamar ta Samu babba Hajara kuwa na zaune Akan kujera Dan tsugunno ta saka tsinken a bakinta tana ta sakace hakori Kamar Bata wajen. Minal da Nadeeya sai duka suke kaiwa Safiyya suna kuka. Tsabar rufewar da idon Safiyya yayi Sam Bata San da shigowar Naseer da jikinsa ya kwashi wani irin rawa ba Hajara kanta sai data tsorata da yanda ya shigo da balain sauri ta mik'e tana k'ok'arin yiwa Safiyya magana Naseer ya isa wajensu ya kaiwa Safiyya wani irin wawura ya hadata da bango ya shaketa Ta fara kakarin mutuwa. Hajara kuwa ihu ta saka Dan dagaske Naseer so yake ya kashe Safiyya fata kawai yake ta mutu a hannunsa a Kai shi gidan yari ya huta da bakin cikin Safiyya da Mahaifiyarsa. Duk dukan da Hajara take kaiwa Naseer Sam baiji ba har muciya sai daya karye a jikinsa Bai cikata ba Safiyya kuwa tuni ta sume a hannunsa. Hajara sai waje tayi da gudu ta Kira aka zo aka bambara Safiyya daga hannun Naseer. Hajara tayi Kan Safiyya tana ihun Naseer ya kashe Mata ya. Naseer kuwa d'akin ha Shiga ya hau watso da kayan Safiyya waje Yana ta bar Masa gidansa bazata Kara kwanar Masa a gida ba. A ranar ba karamin rikici akayi tsakanin Hajara da Naseer ba Dan da Safiyya ta farfado sai da Naseer ya fitar da ita waje Akan bazata Kara kwanan Masa a gida ba Hajara kuwa ta dage akan sai dai ya koresu su biyun K'arfi da Yaji Hajara ta Masa fin karfin ita mahaifiyarsa ce ta kulle Safiyya a daki Akan ba Inda zata je ai ba Haka kawai Safiyya ta daki zahiran ba rashin kunya tayi Mata. A ranar Naseer kwana yyi Yana kuka daga tafiya Naeema da zaa auna jininsa zaa iya ganin ya mugun Hawa sabida tashin hankali shi kam yasan rayuwar Zahira na cikin hatsari Bai tab'a ganin uwar da Bata San danta bata San jikokinta ba sai Mahaifiyarsa ya yarda uwa na iya tsanar matar danta Bai San uwa na tsanar danta ta tsani zaman lafiyarsa ba. Ya Zama Dole ya d'auki mataki inama Naeema ta tafi da Zahira da Nadeeya ta bar mishi sauran yaran bazai dauwama Yana zaman gida ba Dole wani uzurin ya taso yyi nesa da gida Amma in ya fita yasan yana ckin fargaba da rashin kwanciyar hankali. A takaice tundaga ranar Safiyya ta fara balain tsoron Naseer indai Yana Nan ko fitowa Bata iya Yi gashi baya fita sai dai idan Massallaci zaije. Akan engine markaden ma sai da sukayi rikici da Hajara ta dage sai dai ya bar Mata guda daya ya dau daya idan aka kawo.markade ita ta d'au daya shi ya dau daya sai dai me tunda aka siyo engine sau biyu aka kawo markade baa Kara kawowa ba Sabida masifar Hajara har suna Suka saka Mata a unguwar suna kiranta da masifafiyar tsohuwa. Naseer yanda ya d'auka zai samu kudi idan ya siyi engine markaden lura da yanda Naeema ke samun kudi Bai samu ba Dan bama zuwa ake ba wani zubin yana ma zaune a k'ofar gida zaa wuce gidansa a Kai wajen bakin titi da dai a Zo gidansa tuni damuwa tayi.masa yawa kasa da wata daya komai na gidan ya Kare Wanda sai da ta Kai shi da siyar da engine guda daya Dan Bai shigo Masa da kudin ba. A cikin kudin ya biya kudin makarantar su Zahira sauran canjin shima Nan da Nan ya Kare. Kafin kace me dayan ma sai daya siyar. Hajara kuwa masifa ta hau yi akan ita tasan Naeema ce tayi asiri aka ki kawo musu markade k'arfi da yaji tana ji tana gani Naseer ya siyar da engine data ci burin samun kudi dashi ta siyi filaye. Kamar ta fashe dan bakin ciki wata uku da tafiyar Naeema sai gashi abinda zasu saka a cikinsu Yana neman gaggararsu. Safiyya kuwa data ga bazata iya ba aikatau taje ta nema a wani gidan masu kudi zata ringa zuwa tana dawowa daddare. Idan taje abincin da ake Bata shi take kawowa gida taci Hajara na kallo idan tayi Magana kuwa Sai tace Mata kowa tasa ta fishe shi Naseer kuwa Dan abinda ya fita ya Dan samo sabida tuni ya nemi aikin lebura na gini ya farayi Dan kudin daya samu yake siyowa su Zahira abinda zasuci ahaka ma sai dai shi ya hakura Dan bazai iya barin Hajara da yunwa ba. Ahaka Safiyya tayi albashi Hajara tayi ta rokon ta Allah da annabi kafin ta yarda ta Bata wani Abun. Tana Bata kuwa ta siyo shinkafa da kayan Miya ta girka ta kakasafta a kwanu. Zahira na dawowa daga makaranta tasa ta cire uniform ta Dora Mata farantin Ta bawa Nadeeya Yar robar miyan tace musu su dau hanya su tafi su siyar Mata taja musu kunne akan kar su sake su dawo gida batare da sun siyar Mata ba idan Naseer ya Isa idan ya dawo ya mata magana yaga yanda zata Yi dashi Suna fita ta dakawa Minal tsawa Akan su saka kayan islamiyya su tafi. Minal sai data Dan gwada Mata taurin Kai ta dan bubuge ta kafin suka bar gidan. Naseer dake ta Dora bullo a wani gida da ake ginawa kamar ance ya daga kansa ya hango Zahira da Nadeeya na tafe a Gefen titi suna rarrabewa a gefe ga uban faranti akan Zahira ga Nadeeya itama da nata robar miyar. Naseer Bai San sanda ya duro Yana mirtsika Ido ba Dan ya tabbata da su Zahira yake gani. Jiki na rawa ya Isa wajensu. Ya sauke farantin dayake ganin yayi wa Zahira nauyi yace musu waye ya Dora musu talla. Ce Masa sukayi Hajara ce. Yayi shiru Ransa na balain baci. Dak'yar ya hadiye b'acin Ransa yace su zauna a wani dakali su jira shi Yana zuwa. Ba a cikin hankalinsa Suka karasa aikin ba Dan har sai da bulo ya Fado Masa a kafa Sabida tunani. Ana biyansa kudinsa ya wanke jikinsa ya cire kayan aikinsa ya maida Mai kyau jikinsa. Ya tsallaka wajen su Zahira ya d'auki farantin abincin. Ya rarrabawa almajirai Ya Kama hannunsu ya tare musu bus Suka hau suka nufi gwammaja. Bashida tabbacin Gane gidan Tijjani Amma ahaka yaje sai da kyar ya Gane gidan da kwantance. Suna zuwa k'ofar Gidan Tijjani na isowa a vespa. Ko parking baiyi sosai ba ya duro daga vespan Dan murna ya rungume Naseer cikin murna Naeema Kwana biyu kawai nayi a garinmu danaje da Ashe sun Dade suna nemana sosai naji mutuwar Mai unguwa da nake Jinsa tamkar mahaifina ashe shekara daya kenan da rasuwarsa Kafin rasuwarsa ya siyar da gidanmu ya boyemin kudin Dan lokacin sosai ake San siyan gidan hayan daya saka kuwa sai yaga ma.kamar mutanen ciki Bata gidan suke hakane yasa ya siyar da gidan Akan duk lokacin da Nazo zai bani ya kuma San bazanji Haushin siyarmin da gidan mu da yayi ba Dubu dari uku da sabain ya siyar da gidan namu. Kafin rasuwarsa Haka yayi ta rokan yayansa da matansa akan Dan Allah Kar su tabamin kudina duk lokacin Dana Zo a damka min kudina. Sosai naci kuka na Godewa Allah da rashin Mai unguwa a Haka na kwana biyu cikin zuciyata ba dadi uwa uba ga tunanin yarana daya dameni ko baccin kirki bana iya yi sabida Ina tunanin kamar suna can suna Shan duka a wajen Safiyya abinda zai taimakeni kawai shine Kila Naseer bazai yarda a tab'a min su ba da Wanan tunanin hankalina ke Dan kwanciya. Sosai iyalin Mai unguwa suka nunamin soyaya Dana tashi dawowa Dan Kaya Suka bani sosai na amfani Dan ban Gaya musu abinda ke faruwa Dani ba. Karfe uku na rana na iso gidan kanwar Aunty Ina zuwa kuwa na tada Aunty a gidan. Bazan manta Aunty a rayuwata ba tamin abunda har na mutu bazan manta alherinta a gareni ba. Ina sallahr La'asar muka nufi dorayi da ita. Ta kaini gidan data kama min ta hau min bayanin da kyar Mai gidan ya yarda ya bada haya Dan yace siyarwa zaiyi Amma ko yanzu ya samu Mai siya zai maidamin kudina ne na siyar. Gidan Mai kyau ne dakuna biyu da bandaki biyu da Palo sai dan karamin shago a k'ofar gida Gwada tambayarta nayi nawa ne gidan. Tacemin Dubu dari uku da ashirin Take nace Mata Zan siyi gidan Kamar Wasa ta rakani wajen Mai gidan na nemi ya siyarmin Dubu dari biyu da hamsin dak'yar ya siyar min a Dubu dari biyu da casain Washegari muka Kai Masa kudin gidan ya d'auko takarda gidan ya bani Aunty sai murna takemin ni kuwa sai tambayarta nake tana ganin yarana cemin tayi tana ganinsu kar na damu Naseer na kula dasu Dan ta saka Ido a kansu Take naji hankalina ya Dan kwanta. A. Cikin kwana uku naja wutan.nepa gidan Aunty ta Nemo min Katifa second hand na biya da Dan ledar tsakar daki da Dan kayan amfanin gida da bazaa rasa ba. Wata Hassana da take bazawara da ta kasance Yar uwarsu ta kawomin Akan mu ringa kwana tare Dan Ina tsoron kwana Ni kadai. Hassana kuwa zata iya girme min Amma tana da kirki Makotana na zaga na Dan duba abinda baa samu unguwar Naga har da dai markaden sai sunyi tafiya Mai nisa suke samu. Ana Kuma neman ruwan Sanyi kayan provision ma sai sun Yi tafiya Mai nisa. Take kuwa na nemi engine second hand na siya Dan gaskiya Ina San sanaar markaden dan ya shigomin da kudi Cikin Ikon Allah kuwa sati daya da siya aka faramin layi. Dan har Hassana Tayani takeyi idan na gaji. Kamar Wasa sauran kudin hannuna na Nemo kafinta ya bubbuga min canter na Dan zuba provision din kad'an su Maggi biscuit bredi da alewa da littattafai makaranta Dan Naga Ana yawan nema Shima sati da fara siyar da provision din Rabbi ya Sanya min albarka a hankali sai gashi shagon k'ofar gida ya cika da kaya. Sai gashi a cikin wata biyu har freezer na siya shima na saka a shagon Ina siyar da ruwa. Nikam a wanan gabar sai dai nace Alhamdulillah Dan kudi ko ta Ina shigomin suke abinda yake damuna Bai wuce kewan yarana danake kwana Ina mafarkinsu ba wani zubin a mumunan yanayi wanan Abu shi yake hanani sukuni ko abinci bana iya ci.gashi dai komai na samu cikin rufin asiri Amma tunanin yarana ya Sakani balain Rama Nafi tunanin Zahira Dan jikina na gayamin tana Shan wahala a hannun Umma da Safiyya Koda kuwa Naseer na nan. Sau uku Ina zuwa unguwar da likkaf na tsaya a k'ofar gida Naga ko Zan ga wani ya fito daga gidan a cikinsu sai dai bana ganinsu sai dai Naga Naseer daya balain Rama ya fita hayyacinsa sosai yake karyamin zuciya idan na ganshi ahaka zan karaci tsayuwata idan na gaji na karasa gidan Aunty tacemin Kar na damu dazu ma tagansu lafiya Lau suke ba Abunda ya samesu har tambayar Zahira tana yi dake da balain zurfin ciki tace mata ba komai. Ahaka Zan dawo da tunaninsu a Raina Nima rashinsu kusa Dani ne ya saka Ni mugun Rama Dan Sana'ar tawa Dan hassana na rik'ewa ne da bazan iya tab'uka komai ba a yanzu da aka tafi wata uku rabona da yayana naji bazan iya jurewa ba Ina bukatar ganinsu ko ta halin Kaka hakane Yasa na yanke zuwa gidan aunty idan sun zo islamiyya nagansu Koda daga nesa ne. Naseer.......... *NAGA TA KAINA* *NA SADNAF*🌸🌸 ®️ *_PURE MOMENT OF LIFE WRITERS_* _{We Don't just entertain nd educate we also touch the heat of readers P.M.L}💪🏻_ *Free Novel* *Page 37* *Naseer* Tijjani cikin tsananin murna ya rik'e Hannun Zahira da Nadeeya yace su Shiga daga ciki Naseer ya girgiza Masa Kai Akan bazai shiga ba ya dai Shiga da yaran ciki su gaida Murjan Tijjani girgiza Kai yayi Yana wlh sai ya shiga ciki Taya ma zai Zo gidansa Bai Shiga ba Akan dole Naseer ya yarda suka shiga ciki Tijjani sai washe baki yake cikin murna. A tsakar gida Naseer ya coge. Tijjani kuwa sanin halinsa yasa ya dau babbar tabarma ya shimfida Naseer ya zauna shi ma ya zauna ya hau kwalawa Murja Kira Su Zahira kuwa sai kalle kalle suke suna daga gefensa hannunsa cikin Na Nadeeya. Yana tambayarsu Makaranta Murja fitowa tayi tana Hamma da cikinta da baifi na wata biyar ba ta tsani tana bacci a tasheta ko kad'an batasan da zuwan su Naseer ba hakane yasa ta fito da Daurin kirji Ganin Kuma Naseer Bai saka ta koma ba illa yatsina fuska da ta farayi tana karewa Su Zahira kallo da Tijjani keta washe baki yana cigaba da Jan su Zahira da Hira Naseer kuwa kansa a sunkuye yake so yake idan matar gidan ta fito su ka gaisa sai su fita da Tijjani waje suyi magana dake tafe dashi. Tijjani kuwa sai daya d'ago yaga Murjan ta daga labule daga bakin kofa ta toge Daga yanayin ta yasan Yan rashin mutunci ne Suka motsa hakane yasa ya mik'e ya Shiga ciki tare da Jan Murja su koma ciki yayi kasa da murya Yana "Ya Ina kiranki kizo ki gaisa da yayana zaki kame daga bakin kofa shine fa yayana Naseer danake baki labari wadanan yayansa ne Dan Allah ki Sako hijabi kizo ku gaisa Bata ce komai ba ta koma daki ta sako hijabin a rayuwarta ko kad'an Bata so wani ya rabesu har Tijjani ma bataso.taga Yana muamalla da mutane Dan ko abokaina ma cikin makirci take rabasu. Idan kaga wani a gidan toh danginta ko kawayenta ne Amma Tijjani kam bataso wani nasa yazo wajensa hakane yasa ta Sha mugayen alwashi idan tsautsayi ya sa su Hajara suka Kara dawowa gidanta sai ta musu abinda har su koma ga Allah bazasu manta da ita ba. Tijjani kuwa Yana fitowa Bai tsaya jiran fitowar Murja ba Dan ya Riga da yasan halinta ruwa da abincinsa ya d'auko yazo ya Ajiye a gabansu Naseer Yana yayi hakuri yanzu murjan zata fito yasan halin masu ciki. Daga Nan ya dau plate ya bud'e flask din ya hau zuba shinkafa da wake da akayi jollof dinsa da bushashen kifi Murja kuwa har wani turus tayi dan bakin ciki Dan tana da balain rowa ko wani ne ma yazo daga gidansu Haka zai karaci zamansa ya tafi batare da ta Masa tayin abinci ba ko da kuwa Tana cikin girkin kazo zata iya gwammacewa ta zauna da yunwa har sai ka tafi. Dak'yar ta saki Fuskarta Ta tsugunna daga bakin kofa ta hau gaida Naseer cikin faraa Naseer kuwa ya d'ago ya amsa cikin sakin fuska Yana Dan karantar yanayin Murja a fuska dai Kamar babu ruwanta zatayi saukin Kai hakane yasa ya Dan ji sanyi a Ransa Bayan sun Gama gaisawa ta koma ciki ta lab'e a jikin labule tana kallon Zahira da Nadeeya dake ta zabga Loma Sabida yunwar da suke ji Dan uniform kawai suka cire Hajara ta Dora musu talla Bata Bari sun ci abinci da Naseer ya boye musu a daki ba dan waje na musamman Naseer yake boye musu abinci a d'akin da iya su zahiran ne kawai zasu San abinci ne a wajen sabida Kar ma Hajara ko Safiyya suzo d'akin su dauke Kamar ta fashe Dan bakin ciki shi kuwa Naseer ture abincin da Tijjani ya ajiye daga gabansa yayi ya gyara murya ya Dan fara bawa Tijjani labarin duk halin da yake ciki da tafiyar Da Naeema tayi Sabida masifar Mahaifiyarsu da yanda itama Safiyya take cin zalin yaransa har zuwa Kan tallan da Mahaifiyarsa take dorawa yaransa da yasa ya zarto gidansa dasu. Tijjani shima labarin irin zaman da sukayi da ita ya bashi a karashe da "Wlh Naga bazan iya ba nace su tafi Dan wlh bazan iya jure abinda kake iya jurewar ba Umma a madadin ta ringa rike girmanta tana kwantar Mana da hankali sabida halin da muka tsinci kanmu na babu wanda duk ita ta jawo Mana fa hakan Bai isheta ba sai ta daga Mana hankali ba irin surutan da bata yimin Akan na rabu da Murja ba daga Aurenmu fa Ni ban taba ganin Mai irin Halin Umma ba wlh ita Kuma shegiya Safiyya a madadin ta ringa Gaya Mata gaskiya shine take tunzurata kamin daidai da ka Hana ta dorawa su Zahira talla Dan nikam bama Zan iya da ita ba Dan da nine ma wlh siyar da gidan zanyi na gudu da yarana k'arfi da yaji kana zaune kalau da matar rufin asiri ta rabaku toh Yaya yanzu wane aiki kake yi Taya zaka ringa aikin lebura dake da wahala nawa ma kudin yake da zai isheka ka kula da yaran nan.mai zai Hana ka nemi aiki wani wajen ko Allah zai saka ka Dace Kamar yanda Nima Allah ya taimakeni na samu aiki a wani company robobbi a sharada duk sati suna bamu Dubu biyu karshen wata Kuma su biyani Dubu goma da zaka samu irin wanan aikin Yaya nakega da yafi nima wani ne ya nemo min aikin Zan Masa magana idan Allah yasa. An Dace sai Kai ma ka ringa zuwa da Wanan aikin wahalar da kakeyi. "Tijjani Ina neman aikin samun ne dai banyi ba bazan iya kirga guraren Dana Kai takarduna ba Amma har yanzu baa Dace ba ya zanyi dole na ringa leburancin mu samu na abinci. Yanzu dai abinda yasa nazo wajenka so nake ka taimaka min Dan Allah Yaran Nan su zauna a wajenka zuwa Dan wani lokaci kafin na Shawo Kan Umma Dan wlh bana San tallan Nan duba kaga Zahira ta girma dan ma Bata da girman jiki Amma kana gani kasan ta fara Zama budurwa Taya Zan yarda a ringa Dora Mata talla Zahira da Nadeeya Umma tafi takura wa hakane yasa nace Bari na kawo su wajenka su zauna Ni Kuma yanzu idan na koma Zan nuna kamar bansan Inda suke ba kaga idan an kwana biyu sai nazo na daukesu Kamar angansu ne inaga hakane kawai zai saka Umma ta hakura da tallan da takeso suyi na k'arfi da yaji. Naso Naeema data tashi guduwa ta tafi da ko iya zahiran ne Ni Kuma bana San bin Bayan ta sabida Naeema tayi.hakurin da Umma koni bazan soma bin bayanta nace ta dawo ba gwara ta huta idan an kwana biyu sai na Kai Mata yaran intaga zata rikesu shikenan idan taga bazata iya ba sai mu dawo "Yaya ba sai ka hadani da Allah ba yaran Nan nima yayana ne Nan ma gidansu ne sauran ma idan kana ganin Umma zata takura musu ka kawo su wlh Zan rik'e su yanzu Ina cikin rufin asiri abinda zasu ci bazai gagareni ba insha Allahu Umma Kuma Allah ya shiryeta sai dai makarantarsu ne bansan ya zaayi ba tunda kace Zahira na primary 4 Kuma 3rd term "Hakura zasuyi na Dan lokaci kafin komai ya warware zanje makarantar da kaina Tijjani Nagode sosai da taimakonka a gareni Zahira da Nadeeya kawai nakeso su zauna anan Dan su tafi matsawa gobe zan dauko musu kayansu a boye na kawo musu insha Allahu sai dai ka taimaka min Kar su zauna haka su ringa zuwa islamiyya Dan Naga kamar akwai makarantun islamiyya a layin naku "Haba Yaya wlh bazan iya biyanka alherinka a gareni insha Allahu baka da matsala Kaya ka barshi Zan siya musu Koda gwanjo ne basai ka wahalar da kanka ba Zan Kuma saka su a islamiyya Ina samu kudi har bokon Zan iya saka su insha Allahu" Dafatan matarka bazata damu ba Dan bana San na takura ta "Haba Yaya wlh bazata damu ba ai Tama samu Yan tayin hira tana da san mutane sosai" "Tabdijam" Murja tace bayan ta Gama Jin duk abinda sukace Ta nufi d'akinta a fusace Naseer kuwa yayi ta yiwa Tijjani godiya Ya mike akan zai tafi ya Kira Murja ya Mata sallama. A daki ya tadda Murjan tana kad'a kafa ko lura da Fuskarta baiyi ba yace ta fito suyi Sallama yayansa zai tafi Daga hakanya saki labulen yayi waje Murjan ta bishi a baya tana kakalo faraa tana fitowa tayi kasa da Kai tana "Har zaku Tafi" "A uwargida Ni Kadai Zan tafi dai Su Zahira zasu Dan zauna su kwana biyu sabida wani Dan dalili dafatan Dan Allah ban takuraki ba" ? "Haba Yaya wane irin takura Nan ma ai gidane karka wani damu" Godiya Naseer yayi ta yiwa Murja. Murja kuwa har da rike hannun Nadeeya suyi rakiya har waje. Sai da suka daina hango su Tijjanin da suka hau Vespa Dan ya fita dashi titi Murja naganin sun wuce ta yarfar da Hannun Nadeeya ta ja baya tare da musu wani irin Mugun kallo tana "Yan bura uba daga zuwanku sabida kwadayi zaku hau cinye min abincin Dana girka shegu dangin kwadayi zaku ci.ubanku ne Dani kuke maganar Haka kawai Ina zaman zamana a kwaso.min gayya Yaya har guda biyu Uwarku ma ta kasa rikeku ta gudu shine Ni aka rainawa wayo.zaa wani kawoku wajena shi Kuma Tijjanin zai Zo ya sameni Kuma wlh kun Gama cin rabonku" Daga Haka ta wuce daki fuuu tana bakin cikin abincin ta da suka ci sosai ta ringa shirya ukubar da zatayi wa Yara da basuji ba Basu gani ba Wanda idan sukaji azaba da kafarsu zasu gudu. Zahira kuwa kuka ta fara yi Nadeeya kuwa na kikifta Ido Zahira duk da kankantar shekarunta gani take Bayan mahaifiyarsu da mahaifinsu Babu Mai kaunarsu har suna murna zasu zauna a gidan baba Tijjani da suke ganin kamar sai sunfi jinn dadin zaman Nan Akan gidansu sai dai daga yanda Murja ta musu yasa Zahira taji dama sun bi Bayan mahaifinsu. Tijjani kuwa Yana fita da Naseer bakin titi ya d'auko duk kudin jikinsa ya bashi ya kara Masa alkawarin idan ya samu sarari zai Zo idan sukayi albashi. Godiya Naseer ya Masa sosai ya tari bus da zai je gadon Kaya ya hau Tijjani Kuma ya juya ya koma gida Murja tana Jin karar vespa ta duro daga Kan gado tayi waje tayi wajen da su Zahira ke rab'e ta ruk'o hannun su biyun a daidai lokacin da Tijjani ya shigo da vespa ya Parker Murja kuwa ta hau cewa "kaga tunda kuka tafi nake fama dasu akan su shigo Suka k'i wanan kamar wata karamar Yarinya har da kukanta Wai sai tabi bayan Abbanta" Fa karashe tana nuna Zahira "Kukan me kike Yi Zahira bakya San ki zauna damu"? Tijjani yace a daidai lokacin da ya karasa wajensu Yana ruk'o hannun Zahira Girgiza Masa Kai Zahira tayi Murja kuwa ya harareta a fakaice sosai take ganin kamar Zahira munafinci ne yasa take kukan sabida ta hadata fada da Tijjanin. Dan duk da kame Mata Tijjani da mahaifiyarta tayi wani zubin inya tashi sai ya botse Mata. Cikin palon suka Shiga Tijjani ya zauna akan kujera Ya zaunar da Nadeeya a gefensa ya kalli Murja Yana "Dan Allah Kara Dora Mana wani abincin yunwa nakeji wlh" "Wlh na dazu ma dakyar na dafa ko dandanawa banyi ba ka bawa yaran Nan da babansu" "Toh sai nak'i Basu Murja wane irin magana kike Haka yayana na bawa abincin fa ke Mai yasa kike haka ne Mai da anzo wajenka ka bada abinci anci gaskiya ki gyara halinki Bari nayi Sallah na Shiga da kaina na dafa abincin Daga Haka ya mik'e ya shige dakin Murja ta bishi da wani irin kallo ta maido kallonta kansu Zahira datake ji kamar ta jawosu ta rufesu da duka Ahaka ta daure tayi waje ta Dora musu jollof din taliya tana zagin Naseer da yayansa da take ganin sun zo sun takura Mata. Taliyar kad'an ta dafa duk da basu da matsalar kayan abinci sabida su kadai ne Murja kuwa rowa bazai Bari ma ta dafa abincin da yawa ba ballantana har ya ragu su bawa almajiri. A plate ta juyo musu abincin Dan tare suke ci A Palo ta tarar da Tijjani dasu Zahira Yana ta jansu da Hira sabida su saki jikinsu sai dariya yake kyalkyalewa Dan Nadeeya sosai ta zage take Masa surutu ita kuwa Zahira da Bata da surutun murmushi kawai take. Murja kamar ta fashe Dan bakin ciki tsabar jahilci ma kishi ne ya rufeta data ga yanda Tijjani ke kyalkyala dariya a Haka ta ajiye taliya ta zauna a gefensa zahira tayi saurin barin kujeran. Nadeeya kuwa ko a jikinta "Ina abincin su Nadeeya Naga kin zubo Mana mu kadai"? "Ai Naga sunci abinci shiyasa ban dafa dasu ba ga saura can ma na Kai kitchen" "Zahira kin koshi Wai"? Da Sauri ta gyada tare da sunkuyar kai kasa sabida mugun kallon da Murja ke jifanta dashi "Nadeeya ke Kuma fa kin koshi"? Girgiza masa Kai Nadeeya tayi Shi kuwa yace toh shikenan Bari muci gabad'aya jeki wanke hannunki Waje Nadeeya tayi da Sauri Ta wanko hannunta Suka fara cin abincin Murja kuwa tusa abinci kawai take Dan bakinciki ji take kamar ta shake Nadeeya A takaice Tijjani da kansa yayiwa Su Zahira shimfida har da Kai musu bargonsa ya musu adduar kwanciya bacci tare da ja musu k'ofar Murja kuwa tsabar bakin Hali Kamar ta fashe da kuka Dan gani take Tijjani Dan tattalata da yake yi daga zuwansu Nadeeya ya shareta. Rai ba dadi Haka ta kwana tana Shan mugayen alwashi aranta Naseer kuwa sai daya yi sallah ishai ya karasa gida A k'ofar gida ya tarar da Hajara ita da Safiyya sunyi jugum jugum sai kalle kalle suke Safiyya kuwa Tana hango Naseer ta diba da gudu tayi ciki Hajara kuwa duk da jikinta rawa yake sabida tsoro Mai zata cewa Naseer game dasu Zahira da Basu dawo ba ahaka ta maze Yana isowa gabanta ya gaisheta Yana k'ok'arin Shiga gidan kamar Bai San komai ba Hajara kuwa kamar ta Dora hannu a ka Shigar Naseer da Yan mintuna ya fito waje Ya kalli Hajara datayi tsuru tsuru Amma tsabar karfin hali ta daura fuska "Umma inasu Zahira ne ko kin aikesu" "Aaaa eee kana ji wlh talaucin Nan da muke fama dashine ya isheni shine na Nemo kudi na d'afa abinci da suka dawo na dorawa Zahira da Nadeeya akan su kaimin bakin titi su dawo sabida ma mu samu abincin da zamu ci daddare. Wlh tun uku Suka fita har yanzu basu dawo ba naje titi nida Safiyya yafi sau biyar ko Mai kama dasu bangani ba ba Inda ban dubasu ba a unguwar Nan wlh ban gansu ba yanzu ma Haka daka ganmu a k'ofar gida wlh daga nemansu muke "Innalillahi wa Inna ilaihi rajiun Innalillahi wa Inna ilaihi rajiun Umma talla Kika dorawa Zahira da Nadeeya kinsan kuwa akwai Yan yankan Kai a garin Nan Umma Kar fa masu satar mutane ne ne fa suka sacemun Yaya Umma Akan me Zaki Dora musu talla haba Umma kema kinsan idan na dawo ko ba yawa Zan taho Mana da abinda zamuci irin Haka nake gudu tun farko shiyasa naki Bari a Dora musu talla yanzu daga Ina Zan fara ta Ina Zan soma neman su Umma"? "Insha Allahu baa sacesu akayi ba abincin dari takwas fa na Dora musu da hamsin" "Umma ta abinci kike ko yarana Umma ta kudinki kike ko yarana Ina Miki zancen yarana kila sun b'ata kina min zancen abincin dari takwas Kika dora musu" A takaice sosai Naseer ya tashi hankalinsa kamar gaske baiyi bacci ba Bai Bari Hajara tayi ba Dan itama sosai hankalinta ya tashi da rashin dawowarsu zahiran. Tana ta bakin cikin asarar da tayi kasan zuciyata Kuma tana addua Allah yasa ba sacesu akayi ba. Abinda suke turarawa shugaba ta bayyana kuwa sun nemeshi sama ko kasa sun rasa ballantana tasa shugabarsu ta gano Mata Inda suke. Ahaka washegari Naseer ya bar gidan da wuri Akan ya tafi neman su Nadeeya Bai damu da tsayawa ya bawa su Minal abinci ba Dan ya karanci a yaran nasa tafi San Minal Humaira da Raheema har abinci tana ragewa ta basu idan taci duk da Minal na musu rashin kunya wani zubin hakan Bai saka ta wani tsaneta ba. Zahira ma ta tsaneta ne sabida balain Kama dataga tanayi da Naeema Hankali ba a kwance ba Haka Hajara ta shirya su Minal suka tafi makaranta bayan sunci abinci. Tijjani kuwa karfe shidda yake barin gida hakane yasa Yana dawowa daga Massallaci yayi wanka ya shirya ya kalli Murja dake Kan sallaya Yana "Zan fita Zahira da Nadeeya Basu tashi daga bacci ba Dan Allah Dan annabi ki Basu abinci suci su koshi Dan Allah nace Miki karki damu da Wai Dan kin bayar zai Kare wlh Zan Kara siyo wasu yaran Nan Kinga amanarsu yayana ya bani Dan Allah ki Tayani kula dasu kinji" "Wai toh Mai ya kawo maganganun Nan baka yarda Dani bane Akan me Zan k'i Basu abinci bana San Haka wlh" "Allah ya baki hakuri ba Haka nake nufi ba Bari na tafi sai na dawo Mai Zan taho miki dashi"? "Ayaba kawai nake shaawa" "Toh shikenan sai na dawo" Daga Haka ya fito daga d'akin ya lek'a d'akinsu Zahira da har lokacin suke sharar bacci. Har waje Murja ta rakashi sai data daina hango shi ta rufe gidan. Direct ta Shiga kitchen ta bud'e karamin fridge ta d'auko karamin bokitin fenti dake cike da ruwan da ya fara Dan kankara. Tayi d'akin dasu Zahira suke kwance Sai data janye bargon da suka lulluba sabida Dan sanyin da suke ji ta daga robar sama ta watsa musu. Wani irin ihu Suka saa Suka mik'e a gigice sabida yanda ruwn sanyin ya ratsa su "Shegu Yan bura uba dole kuyi ta sharar bacci ku ga gidan ubanku maza ki fita waje kuje ku dau tsintsiyarku ku sharemin ko'ina kumin wanke wanke yanzu Nan ku Shiga d'akina kuzo ku gyara min" Daga Haka tayi waje tana cigaba da danna musu Ashar. Zahira da Nadeeya kuwa Suka kankame jikinsu suna rawar sanyi kayansu sai digar ruwa yake ahaka suka fito Suka daura alwala da jikakken kayan sukayi sallah suna ta rawar sanyi Zahira kuwa har da kukanta Dan Abu kad'an ke sakata kuka Cikin awa daya Suka Gama aikin da Murja ta saka su dan gyara gida Kam sun Riga da sun Saba Koda Bata saka su ba zasuyi. Murja kuwa ba karamin mamaki tayi ba a lokacin data fito taga koina fes ko ita kanta bata taba gyara gidan kamar yanda Suka gyara ba. D'akinta tace su shiga su gyara Mata Nan da Nan suka gyara d'akin suka wanke band'akin tas. Duk aikin data saka su Nan da Nan taga sunyi har a karshe ma ta rasa aikin da zata saka su Wajen karfe goma ta Shiga kitchen ta dafa ruwan tea Kofi daya ta soya kwai guda hudu tayi hadin kauri ta zauna a Palo ta fara ci Tana kallonsu Zahira dake rab'e a gefe Nadeeya kuwa sai had'iyar yawu take Dan ita Bata Wasa da cikinta Zahira kuwa tsoro ma yasa ta kasa d'ago Kai ta kalleta. Suna kallon Murja ta Gama Shan shayinta tsaf ta rufe sauran bredin ta mik'awa Zahira Kofin Akan ta wanke ta mayar kitchen. Zahira jiki na rawa ta mik'a hannunta Dan ta karba Murja ta Kara daka Mata tsawa akan ta karba mana aikuwa tana karbar kofin nan ya sulmiye daga hannunta ya fashe........ *Wlh babu fiction a rayuwar da su Zahira sukayi a gidan Tijjani akwai Abubuwan da bazan rubuta ba sabida wasu zuciya bazata dauka ba sabida tausayi Kuma kamar Yanda na fada labarin nada tsayi masu Dan mahimmancin Zan rubuta sabida Allah na fara gajiya Ya Allah kar ka kawo sanadin da zamu rabu da yaranmu kasa mutuwa ce zata rabamu ameen* *NAGA TA KAINA* *NA SADNAF*🌸🌸 ®️ *_PURE MOMENT OF LIFE WRITERS_* _{We Don't just entertain nd educate we also touch the heat of readers P.M.L}💪🏻_ *Free Novel* *Page 38* "Kutumar uba kofin danake ji dashi Kika fasamin" Zahira kasa ta zub'e akan gwiwarta jiki na rawa ta hau Bata hakuri. Murja kuwa kofin kawai take kallo Wani irin mik'ewa tayi ta fusgo Zahira ta hau dirmarta Kamar ta Samu babba sai wuli take da ita sabida Zahira siriiriya ce Bata da jiki Nadeeya sai kuka take Tana rik'e Murja da idonta ya rufe ko tausayin Zahira da ta kasa kuka bata ji ba sai data gaji Dan kanta ta kyalleta tana sosoka mata Ashar. Tsawa ta daka Mata akan ta tashi ta kwashe Mata fasassun kofin kafin ta Mata bille a fuska Zahira ta rarrafa wajen da kofin ya fashe jikinta yayi jawur sai rawa Yake. Fasassun kofin na yayanke Mata hannu Haka ta kwashe ta Kai dustbin Ta tsaya a tsakar gida. Murja kuwa ta hankada Nadeeya tsakar gida ta rufo k'ofar Palon tana kiransu shegu. A Haka Suka zauna a tsakar gidan cikin rana. Daga Zahira har Nadeeyan kuka suka ci su ka Godewa Allah har gwara gidansu sau Dubu da gidan da mahaifinsu ya kawosu Dan Safiyya ce ma take takura musu Hajara kuwa ita zagine tsakaninsu sai rankwashi Bata Kuma tab'a Hana su cin abinci ba Ga zafin Rana gana dukan da zahira ta Sha Haka Suka zauna a ranar Dan tsakar gidan a wawuke yake iya dakuna ne masu rufi ballantana su samu inuwa su rab'e Murja Bata fito ba sai karfe Biyu da rabi na Rana ta musu wani irin kallo ta nufi kitchen. Ta dafa taliya daidai cikinta ta zubo a plate ta shige palon ta hau ci Zahira da Nadeeya kuwa zuwa lokacn yunwa taci ta cinye su Zahira ta Dan fi Nadeeya dauriya dan Bata da ci sosai tafi auki a wajen kayan kwadayi su biscuit da alewa Haka. Nadeeya kuwa Sam Bata da juriyar yunwa tana da balai ci Dan bama tasan koshi ba in zaka Bata abinci sau goma sai ta karba taci Cikinta ta rik'e tana kuka wiwi ganin Murja da plate din taliya yasa ta Kara Jin wani azbar yunwa. Bata iya jurewa ba tana ganin ta shige ciki ta mik'e ta nufi kitchen Zahira kuwa ta hau kwala Mata Kira cikin karamin murya akan ta dawo Nadeeya kuwa ko kallonta batayi ba Ta shiga kitchen din Tsakin garin masara data gani ta zuba a kwanu ta zuba suga akai da ruwa Ta saka cokali biyu cikin sand'a ta karasa wajen Zahira dake a tsorace tana suci. Zahira girgiza mata Kai tayi tana "ki Mayar Nadeeya Kar ki janyo Mana wani dukan Dan Allah " "Wlh bazan iya mayarwa ba Aunty Zahira yunwa nakeji kici Dan Allah" Zahira Bata kulata ba tayi ta kallon k'ofar palon tana tsoron Murja ta fito Nadeeya kuwa ta hau Danna tsakin massarar da ruwa ya shanye da suga a bakinta Sosai take zabga Loma kamar wacce ta samu garin kwaki Fitowar Murja da plate din data Gama cin abinci yasa Zahira ta mik'e a tsorace jikinta na d'aukar rawa. Nadeeya kuwa dayake Baya ta Bata Sam Bata San da fitowar Murjan ba Murja kuwa ganin Nadeeya da plate dinta yasa ta nufi wajenta da gudu tana "Barauniya uban me Kika dauko kikeci iyye wato har kitchen Dina Kika Shiga waye ya Baki izinin shiga" Kafin kace me ta fusge plate daga hannun Nadeeya itama ta hau kilarta "Gobe ko Tijjani ne yace ki Shiga kitchen Dina Zaki ji tsoron shiga shegu Mayyu Haka kawai Ina zaman zamana an kawomin jarraba maza kuje ku dau bokiti ku debomin ruwa" Ta karashe tare da daka musu tsawa Zahira kuwa a guje ta kinkimi bokiti Nadeeya itama tabi bayanta Ta dau Wanda Bai Kai na zahiran girma ba har waje Murja ta rakasu ta ce suje can kasan layin wajen makabarta akwai rijiya su debo Mata ruwa maza tana jiransu. Siyan ruwa take Kuma tana da ruwan tsabar mugunta yasa ta aikesu diban ruwa. Nadeeya Dan tsakin data ci ya Dan rage Mata yunwar da take ji Zahira kuwa kasa tafiya tayi sabida rawar da jikinta keyi kafin su karasa karshen layin ta samu inuwa ta zauna ta rik'e cikinta Tana kuka. Nadeeya kuwa cewa take "Aunty Zahira mu ajiye bokitin mu gudu" "Ai bamu San hanya ba Nadeeya Kar mu Bata nidai idan baba Tijjani ya dawo Zan rokeshi ya maidamu gida yunwa nakeji cikina ciwo yake da Umma tana Nan da Abba Bai kawo mu Nan ba" Zahira tace tana fashewa da kuka "Wai toh Ina Umman ta tafi ne ta barmu"? "Bansani ba Nadeeya Abba Bai fada min ba" "Idan Baba Tijjani ya dawo sai na Gaya masa dukan data Mana ta Hana mu abinci" Nadeeya tace itama hawayen na zubo Mata. Ta mike ta nufi shagon data gani a bud'e tana zuwa ta zub'e a kasa tana "Dan Allah ka bani bredi na bawa yayata yunwa takeji tace cikinta ciwo yake" Mai shagon kallo Inda ta nuna Masa yayi yaga Zahira a zaune sosai yaji wani irin tausayin su ya rufeshi ya hau yiwa Nadeeya tambayoyi Ina iyayensu suke Mai ya Hana suci abinci Nadeeya dake tana da surutu take ta hau bashi labarin abbansu ne ya kawosu gidan kaninsa shine matarsa taki Basu abinci. Tambayar Nadeeya yayi gidan da suka zo ta kuwa nuna Masa gidan Ya girgiza Kai gidan Dan ya San Murja zata Kuma aikata basa shiri da ita sabida Tijjani na zuwa wajensa hiran Dare. Hakane yasa ta zo har shagonsa ta Masa tas akan shi munafiki ne ya Rabar Mata da miji k'arfi da yaji ta kuwa rabasun yanzu Haka ko siyan Abu batayi a shagonsa ta gwammace taje wani wurin . Bredi ya d'auko Mai Dan girma ya bawa Nadeeya da kananan lemo guda biyu Nadeeya kuwa jiki na rawa ta hau mishi godiya tana tambayarsa Dan Allah ya sunanshi Murmushi ya Mata dayaga yanda take da wayo yace sunansa Jamilu bud'ar bakinta sai cewa tayi "Allah ya saka ka a Aljannna Yaya jamilu daga Haka ta diba a guje ta koma wajen Zahira dake rik'e da cikinta Zahira kuwa na ganinta da bredi da lemo ta fusge bredin daga hannunta ta yaga ledan ta hau dannawa a bakinta ko ta Kan lemon Bata bi ba. Nadeeya itama sosai ta ringa cusa bredin a bakinta sai da suka ji Dama Dama suka Kora da lemon hannunsu. Zahira kuwa tuni taji ta Dan koshi sanin Nadeeya Bata San koshi ba yasa ta fusge bredin tana "Karki cinye duka ki kawo na boye Mana anjima daddare muci Dan nasan bazata bamu abinci ba" Daga Haka Zahira ta danne bredin ya kankance ta cusa a skirt dinta. Suka dau bokitansu Suka dau hanyar karshen layin sai da suka tambayi Inda rijiya yake aka nuna musu Yana gaba da makabarta kad'an abinka da yarinta ko tsoro Basu ba ahaka suka Shiga ta cikin makabartar kafin su Isa wani ya taresu tare da tambayarsu Ina zasuje Gaya Masa sukayi ruwa zasu d'ebo Mutumin kuwa yace "Wane mahaukacin ne zai aiko ku Nan diban ruwa duk rijiyar unguwar Nan maza ku juya ku koma baa bi ta nan" Juyawa sukayi da Sauri. Suka koma suka Kara d'aukar hanyar da suka biyo Zahira kuwa ta hau cewa "idan muka koma bamu Kai Mata ruwan ba zata dakemu mu nemi wani wajen mu dibi ruwan "Toh ai ba Inda muka sani" "Kije ki tambaya mutumin Nan daya bamu bredi haka.kuwa akayi Nadeeya na tambayarsa ya nuna musu wani gida a kusa da shagon suka shiga gidan suka dibi ruwan suka tafi gida. Sai da suka dade da ruwan Akansu Kafin murja ta fito tana zaginsu Akan Ina suka tsaya suka Dade haka a amadadin ta sauke musu ruwan Bata sauke musu ba ta Shiga kitchen. Zahira kuwa bokitin sai rawa yake akanta Nadeeya kuwa data ga bazata iya ba sakin bokitin tayi ya Fadi kasa ya fashe Murja kuwa ta lailayo Ashar ta fito ta daya kitchen ta wawankawa Nadeeya Mari da rankwashi tace Mata ta d'au tsintsiya ta share Mata Inda ta jikam Zahira kuwa tsabar tsoro Kara rike bokitin tayi akanta sabida Kar ya Fadi Sai da Murja ta Dora girkin dare. Ta fito.ta sauke mata bokitin data ga yanda jkin Zahira ke rawa tana kuka. Sai data Gama girkin da take tsaf ta daka musu tsawa akan suje suyi wanka ta Kara da "Mitsiyacin ubanku ma daya tashi kawoku ko hadoku da Kaya baiyi ba ai kuwa shi zaku Kara maimaitawa maza kuyi wanka ku maida kayan jiknku kuzo ku sameni a Palo" A band'akin Tsakar gidan sukayi wanka. Jikin Zahira yayi jawur sabida dukan data sha Nadeeya ma. Yatsun Murja sai daya fito a kumatunta A Haka suka Shiga palon suna rab'e rab'e sai data Kara daka musu tsawa Suka zub'e a gaban ta jikinsu na rawa. Wukan data ajiye a gaban ta ta Dago musu tana "Mai wanan"? Hade jikinsu sukayi waje daya jkinssu na balain rawar tsoro Zahira har wani fitsari ne ya matseta "Dan ubanku nace me wanan" "Wukane Aunty Dan Allah kiyi hakuri karki yanka mu" Zahira tace tana fashewa da kuka. "Toh wlh idan Tijjani ya dawo kuka ce na muku wani Abu kukace na Hana ku abinci na rantse da Allah sai na cire muku Ido kunji na rantse muku idan ya dawo kuce Masa kunci abinci Kun koshi ke Kuma da ganinki kin iya munafirci Abu kad'an sai ki hau hawaye wlh ya dawo kikamin wanan kalar tausayin gobe Yana fita sai na yanka ki kunji Mai nace ko bakuji ba"? Gyada.mata Kai sukayi a tare Dan har ga Allah sun yarda zata yankasun sabida yaran da akwai tsoro ba Kamar na yanzu ba sai a lokacin ta barsu suka zauna a Palo. Duk a tsorace Suka Kamar su zura da gudu Ana Kiran Sallah magriba Tijjani ya dawo Murja tayi sauri ta jawo Nadeeya ta kwantar da kanta a cinyarta Ta hau shafawa tana "in cigaba da muku tsatsuniyar"? A daidai lokacin da Tijjani ya shigo Niki Niki da ledoji A hannunsa Nadeeya kuwa sai mutsu mutsu take sabida danneta da Murjan tayi a cinyarta tana shafa Mata Kai Tijjani kuwa washe baki yayi Yana "Uwar biyu keda yaran naki ne kuke Hira"? Murmushi Murja tayi tana "wlh fa Wai tsatsuniya nake musu ai ba karamin dadi naji ba da zuwansu Dan wlh suna ta deb'emin kewa da sai dai nayi zuru Ni kadai kamar Mayya Nadeeya dai tafi yayarta wayewa Dan ita ta saki jikinta ita kuwa yayarta sai noke noke take Taki sakin jikinta" Murja ta karashe a daidai lokacin da Tijjani ke amsa gaisuwar da Zahira take Masa kanta a sunkuye Nadeeya itama gaishe shin tayi a lokacin da Murja ta daina shafa kanta ta mik'e zaune. Shi kuwa Tijjani cikin Jin dadi ya amsa gaisuwarsu Yana "Ai Zahira Haka take tana da wuyan sabo ko gidansu Kikaje Bai zama lailai kiji maganarta ba har ki dawo Nadeeya ce dai ba ruwanta. Kuzo maza kuga kayan Dana siyo muku Tijjani yace Yana janyo katuwar ledar daya shigo dashi. Murja kuwa kamar ya caka Mata wuka Haka taji a lokacin da ya jawo ledar ya bud'e Nadeeya kuwa tuni ta Isa wajensa Zahira kuwa ko dagowa batayi ba ballantana taje Inda yake zaune Ki taso Mana Kika zauna. Murja tacewa Zahira cikin murmushi yak'e dayafi kuka ciwo Zahira kuwa jikinta na rawa ta Isa wajen Tijjani ta zauna a wajen kafarsa Nadeeya kuwa a gefensa ta zauna Tana murna da ganin kayan data ke kyautata zaton nasu.ne Kaya ne masu Dan saukin kudi guda shida shidda iri daya Sai takalma guda biyu brush biyu har da Mai da Dan turarensu. Bai tsaya iya Nan ba har da yatsana ya siya musu. Kamar an cinnawa Murja wuta haka ta ringa ji sai juye juye take ita kadai ita da take d'auke da ciki Tijjani ko pant Bai siya na jariri ba Amma ya laftowa su Zahira uban Kaya Nadeeya kuwa tsalle tsalle kawai take akan kujeran tana murna yartsana da aka siyo musu shap tama manta da wata Murja a palon balle ta tuna dukan dataci. Zahira ce ma ta kasa sakin jiki ta ringa satar kallon Murja dake musu wani Irin kallo Manyan biscuit ya d'auko ya bud'e musu ya bawa kowace guda guda Yana maza suci Nadeeya da Zahira kuwa sukayi ta mishi godiya Har wani Dan hawayen bakin ciki ne ya Dan taru a idon Murja Tana hada Ido da Tijjani ta kakalo murmushi tana "gaskiya ka kyauta Allah ya Kara budi dama dazu nake ta ce wa Basu zo da Kaya ba ko Mai zasu saka" "Aikuwa gashi na samo musu Wanda zasu ringa Dan sawa Kafin na Karo musu idan na samu kudi. Ga ayabar da kikace na siyo Miki ga Kuma balangu Nan Leda biyu ki dau babbar ki bani dayan Murja Haka ta mik'a Masa ledar kamar ta kurma ihu Tijjani kuwa ya bud'e ledar balangu ya Ajiye Agaban Zahira Nadeeya ta sauko ta hau CI Zahira kuwa sai juye juye take tana satar kallon Murja a tsorace sai da Murja ta tafi dauko abincin ta iya Kai Naman bakinta. Nadeeya kuwa ko kallon murjan batayi ba tayi ta Loma balangun "Murja kuwa abincin ta d'auko ta zuba Masa faten wake da doya Dan Tijjani Yana balain san faten wake da doya "Aaa Yau Mai dadin Kika Mana kenan" Zahira maza ku tashi ku wanko hannun ku muci abinci" Caraf Nadeeya tace "Ai bamu iya cin wake ba" "Mun koshi Abba dazun Nan mukaci abinci" Zahira tace cikin rawar murya "Shaf na manta fa Baku iya cin Wake ba laifina ne da ban gayawa Auntynku ba" "Ai sun gayamin Dama danake girkin hakane yasa na dafa musu taliya sukaci Kallon da tayiwa Zahira ne yasa Tijjani na tambayarsu sukayi saurin cewa sunci.taliyar. Nadeeya kuwa ta maida hankali ta cinye biscuit din da balangu Zahira kuwa tsatsakura tayi sabida tsoro. Ahaka lokacin kwanciyarsu yayi sukayi shiga daki suka kwanta Murja kuwa dak'yar tayi bacci sabida bakin ciki. Washegari Tijjani na fita Tayi wa Nadeeya mugun duka ta Kara saka su aiki kamar Jiya har dasu wanki Wanda a tunaninta wahala take basu Bata San sun Saba da aikin ba . Kayan ma kwacewa tayi ta karya ita kadai batare da ta Basu komai ba Zahira kuwa bredin da suka boye na jiya Suka ci a boye Dan guntun biscuit din ma ta kwace. Sai data Kara turasu debo ruwa Dan duk a tunaninta a makabartar suka je jiya Nan kuwa Inda suka je jiya Nan suka debo ruwan Jamilu kuwa Mai shago daya gansu Basu tambayeshi ba ya Basu kyautar biscuit da lemo suka boye a jikinsu Suna zuwa suka ga ta d'ebo wake ko tsincewa batayi ba ta Dora waken Mai uban yawa ta daka attaruhu ta zabga a ciki Sai daya dahu ta d'auko Sabulun Canoe data jika tun safe ya narke "(nasan mutanen da zasu Gane koren sabulu Canoe Zahira da wayonta lokacin ita ke bani wanan Labarin Nadeeya ma Bata manta komai ba) Juye canoe din tayi a cikin waken ta gwamutsa ta d'auko wani farin roba Mai Dan Fadi ta juye a ciki ta saka a fridge ta kalli Zahira da Nadeeya tana "Daga yau wannan shine abinci ku Badai bakwa cin wake ba shegu tsinanu Zakuci ubanku ke Kuma na rantse da Allah idan kina wanan rawar Kan Agaban mijina kina surutu da wanna shegn bakin naki sai na yankaki ta karashe tana rankwashin Nadeeya A takaice karfe shidda ta zubo musu waken Akan suci Zahira kuwa ta ki ci tace ta koshi Nadeeya kuwa duk da Zahira nata Mata Ido Akan Kar taci Nadeeya a Haka ta zauna taci waken Nan Yana d'ade Mata harshe tare da soya Mata zuciya (Wani ikon Allah ba abinda ya samu Nadeeya tana Nan da ranta har yanzu har da yaranta ma ) A takaice sosai Murja ta bud'e babi babi na mugunta tana ganawa su Zahira Tijjani Bai taba Sani ba Dan idan ya kusa dawowa sawa take suyi wanka ta dauko musu kayan da ya siya musu da Yar tsana akan su ringa Wasa dashi shi kuwa Tijjani idan ya dawo Baya ganewa sam Sosai take musu horar yunwa Zahira ta ringa wani irin Rama. Indai ta saka wani abu a bakinta jamilu Mai shago ne ya Bata Nadeeya kuwa haka take dirkawa kanta faten wake Mai Sabulun Canoe tayi ta Kashi Ga uban duka da take musu da sun danyi wani kuskure. Kullum mak'ota sai sunji ihunsu Zahira. Tana dirkarsu A Haka har jamilu Mai shago da abin ya ishe shi sabida tausayinsu Zahiran.yaje har gidan ya kwada Sallama Murja na fitowa ya hau Mata masifa Yana "Kiji tsoron Allah ki daina zalintar yaran Nan idan babu idon iyayensu Allah daya hallicesu Yana kallonki Banda mugunta Mai yaran Nan suka tare Miki da kike musu irin Haka " "Ina ruwanka Shugaban munafikai ko kashe su nayi Ina ruwanka ka Shiga uku da munafirci wlh ka ficemin daga k'ofar gida kafin na debbo ruwan zafi na watsa maka" Murja tace cikin masifa Jamilu zaginta ya cigaba da yi Yana rantsuwar akan sai.ya hadata da hukuma ya kaucewa ruwan data watso Masa ta rufe kofarta Tana Shiga ciki tayi.kan Zahira da Nadiya ta hau duka Akan sun Kai kararta wajen Jamilu. A ranar Kuma jamilu yayi ta jiran dawowar Tijjani Dan ya Gaya masa sai Tijjani Bai dawo da wuri ba har ya tashi Washegari Kuma daya fito Tijjani ya fice. Karfe takwas yaga Zahira ta fito ita da Nadeeya da bokitan ruwa Akansu Shi kuwa ya kirasu Suna zuwa yace "idan na Baku kudin mota zaku iya komawa gidanku" Da Sauri Zahira ta gyada Masa Kai tana "a gadon Kaya gidanmu yake indai aka saukemu a junction xamu iya xuwa gidanmu a kafa Dan Allah ka taimaka Mana da kudin motar" Naira Hamsin Jamilu ya d'auko ya bawa Zahira Yana ta ajiye bokitin ma yanzu ta rik'e hannun Nadeeya su gudu. Ai Zahira da sauri suka dire bokitin ta rik'e hannun Nadeeya suka fara tikar gudu suna wuce gidan Murja ta bud'e kofa Dan ta siyo Madara aikuwa ta hango su Zahira na tikar gudu. Itama binsu ta fara Yi agujen Taji kafarta ya rik'e. A daidai lokacin da wani mai vespa yazo wucewa tayi saurin tsayar dashi Akan ya taimaka Mata subi bayan wadancan yaran guduwa zasuyi Da Sauri ta haye vespan Zahira kuwa Tana ganin Haka ta Kara rike hannun Nadeeya suka cigaba da tikar mugun gudu suna zuwa titi wani bus na k'ok'arin tafiya Zahira.kuwa ta daga hannu biyu ta hau tsyaar da kwandastan Yana tsayawa suka Shiga motar da Sauri a daidai lokacin da Murja ta sauka itama daga Kan vespan ta hau tsyaar da kwandastan Zahira kuwa ta hau rokansa Kar ya tsaya kashe su zatayi basu kuwa tsaya ba driver ya ja bus din Suka tafi Murja kuwa ta tari wani bus din tabi bayansu....... Wlh biki muke wata danake Jin kunya sisi mama ta roki nayi typing ko ba yawa to gashi Nan nayi da yawa *NAGA TA KAINA* *NA SADNAF*🌸🌸 ®️ *_PURE MOMENT OF LIFE WRITERS_* _{We Don't just entertain nd educate we also touch the heat of readers P.M.L}💪🏻_ *Free Novel* *Page 39* *Naeema* Wani irin rashin lafiya Waleed ya ringayi daya dagamin min hankali duk yanda naso zuwa gadon Kaya gidan Aunty Dan Naga yarana sai ban samu zuwa ba sabida zaryar asibitin da nake fama dashi wani irin kuraje ne suka feso Masa kananu ga Kashi da yake yawan yi. Ko no-no sai nayi dagaske yake Sha shima Yana Sha wani zubin Haka zai ta kwara amai daddare kuwa Haka nake zaman dirshan Ina jijjiga shi Dan kuka yake kwana yi duk magangunan da nake bashi Banga alamar Yana Jin sauki ba sosai hankalina ya rabu gida biyu ga na rashin lafiya Waleed ga na yarana danakeji Kamar na mutu sabida kewansu. Idan bacci ya saci daukana kuwa Haka Zan hau mafarki dasu Zahira suna kuka suna mikomin hannu wani zubin Kuma Wai sai Naga suna gudu wata Mata na binsu da wuka. Sosai nakejin Kamar yarana suna cikin mawuyacin Hali ya zama Dole naje Koda kuwa Waleed din bashida lafiya. Sai dai abinda ya hanani zuwa gidan aunty shine wani Mai maganin gargajiya da aka hadani dashi da ke hanyar Zaria da akace na Kai waleed wajensa zai Samu lafiya idan dai na Kai shi Dan Kamar cutar tasa Bata asibiti ba. Banso zuwa ba sai da hassana ta dagemin akan naje suna da dangi acan na sauka a gidan Har mai maganin ya Gama duba waleed Dan idan dai kaje baya Bari ka taho sai yaga alamar maganinsa ya maka aiki. Baa San Raina ba Haka muka je kauyen da Waleed da kwatancen da Hassana tamin na Isa gidan yan uwansu Da wata a gidan ta rakani wajen Mai maganin yana duba waleed kuwa ya hau hadamin magangunan gargajiya Yana a cikin kwana uku insha Allahu zanga canji na ringa kawo shi safe da yamma. Cikin Ikon Allah kuwa da fara amfani da maganin Naga Waleed ya fara samun sauki A madadin kwana uku Dana so yi sai gashi sai danayi satin Sati dayan Nan danayi Allah yasan baa nutse nake ba ba kuma a hankalina nake ba sabida tunanin yarana Dan ban fasa mafarki dasu ba. Ni nasan mafarkina wani zubin yana Zama gaske duk da Ina Taya yarana da Addu'a ya zama Dole Ina komawa naje na gansu. Haka kuwa akayi Ina dawowa washegari da sassafe na goya Waleed na saka nikab na nufi gadon Kaya Gidan aunty na Isa kaina tsaye. Lokacin zuwansu makaranta baiyi ba hakane yasa muka ringa dan tab'a Hira da ita hankalina gabadaya Yana Kan agogo uku na yi kuwa Yara suka fara cika k'ofar gidan Ni kuwa tsabar matsuwa San naga yarana haka na saka nikaf naje na tsaya a bakin kofa Ina kallon duk Yan makarantar da suka ringa zuwa . Duk yanda aunty tayi dani Akan na zauna na ci abinci Kar na damu har cikin gida zata kirasu k'in saurarenta nayi ahaka nayi tsayuwar awa daya kafin na hango Minal Humaira da Raheema sun nufo makaranta hannunsu rik'e Dana juna. Uniform dinsu yayi wani irin dati ko wankewa baayi ba bana Jin ma ko wanka sunyi Raheema ma sai tsince tsince take a kasa tana kaiwa bakinta Minal na hanata. Hawaye.ne Suka hau zubomin kirjina na bugawa da Sauri wai da Raina yarana Suka Zama Haka toh Ina Zahira da Nadeeya Na Kara dage wuyana ko Zan gansu daga bayansu sai dai Banga Mai Kama dasu ba har su Minal din Suka karaso suka zauna Akan tabarma sosai naji hankalina ya tashi na fara k'ok'arin fita wajensu. Aunty dake gefena a tsaye ta rikemin hannu tana na koma ciki Bari ta fita ta kirasu. Da sauri na Shiga palon aunty na zauna sosai na matsu da su shigo gashi aunty ta Hana ni cire nikaf din fuskata Tunani kawai nake mai ya Hana su Zahira zuwa makaranta ko Aiki Safiyya da Umma suka saka su shiyasa Suka Hana su zuwa.ko dai Kuma dukansu ma Safiyya ko Umma keyi amma idan Naseer ya Bari aka ci zallin yarana bazan yafe masa ba sosai hawaye ya jika nikaf Dina Waleed kuwa na Kan kujera Yana ta baccinsa Shigowar Aunty dasu Minal ne yasa na Kara Jin bugun zuciyata ya Karu ahaka na ringa rarraba idona Akansu tausayin yarana na rufeni sunyi wani cirko cirko dasu Kamar basu ba Kamar na Isa wajensu Naga Aunty ta girgiza min Kai Na daure na zauna na cigaba da kallonsu Ina adduar Aunty ta musu tambayar dake Raina Abinci Aunty ta d'auko musu a faranti Tana direwa suka hau ci Kamar wayanda Basu tab'a cin abinci ba aunty a gefena ta zauna ta Dan matsa hannuna sabida sheshekar kukana dake fitowa Ana ji Dan sosai naji zuciyata ta karye da ganin yarana a yanayin Nan Dubi yanda Raheema ta zama bak'a yarinyar da duk yayana ba Mai farinta Dayake cire hijabinsu sukayi kitson kansu ma ya balain tsufa ko tsagan baa gani "Minal Dama Baku ci abinci bane"? Aunty tace tana Kara Dan tattab'a hannuna alamar Kar nayi magana "Munci bamu koshi bane" "Waye ya Baku abincin" "Mama ce ta bamu"( Haka suke cewa Umma ) "Ina Abbanku"? "Baya Nan ya fita da sassafe " "Bakuje makarantar boko bane"? "Eee bamuje ba an koremu kudin makaranta" "Ina Zahira da Nadeeya ya Banga sun zo makaranta ba sai ku kadai"? Kirjina wani irin bugu yake a lokacin Dana ga Minal ta kalli Aunty tare da cire hannunta daga cikin abincin tana "Abba da Mama sunce sun b'ata mun daina ganinsu Aunty Ummanmu ta tafi ta barmu Aunty zahira.ma da Nadeeya sun tafi sun barmu ba Mai Mana wanki da wanka kullum sai abbanmu yayi kuka daddare"? "Innalillahi wa Inna ilaihi rajiun Aunty nashiga uku na lalace yarana sun b'ata Zahira da Nadeeya sun Bata fa" Nace cikin azabar tashin hankali Ina mik'ewa tsaye Muryata dasu Minal sukaji yasa suka Mik'e a tare cikin ihu sukace "Ummaaaaa" Bansan lokacin Dana fashe da wani irin kuka ba na fusge nikaf din fuskata na durk'ushe na fara kuka Yarana suka debo aguje suna ihun Umma Suka zo suka rungumeni gabadaya. Minal kawai na iya rik'ewa Ina "Minal Mai kikace Kika ce Zahira da Nadeeya sun b'ata kamar ya sun b'ata Minal kinsan.mai kike cewa kuwa tun yaushe suka B'ata"? "Umma sun Dade da b'ata mama ce ta Dora musu talla abinci shine Basu Kara dawowa ba Naji Abba yace an sace su" Wani irin mik'ewa nayi na fara k'ok'arin nayi waje da gudu Aunty kuwa ta rik'eni Gam Ina "Ki cikani Aunty wlh yau sai dai su kasheni kina ji Zahira da Nadeeya sun B'ata aunty ta yaya yarana zasu B'ata wlh bazan yarda ba sun Dade suna min Abu Ina kyalesu Amma wlh bazan yarda su b'atarmin da yarana ba Mai na musu Haka suka tsaneni wlh gidan zanje aunty ki cikani" Nace Ina ihun kuka Aunty kuwa ganin dagaske nake Yasa ta Kira alaramma mijinta Ina balain Jin nauyi da kunyarsa Yana shigowa na nutsu Amma ban fasa kukana ba sai Kiran nashiga uku na lalace nake ko Waleed dake kuka ban kalla ba sai aunty ce take jijjiga shi su Minal kuwa manne min sukayi suna tsoron Kar na Kara tafiya na barsu Aunty ce ta Kora Masa jawabin abinda ke faruwa Shi kuwa cikin mamaki yace "Sun b'ata fa sukace Amma ai muna gaisawa da Naseer din Bai taba cemin sun b'ata ba Dan ko shekaranjiya Dana Kara tambayarsa yasu Zahira suka daina zuwa makaranta cemin yayi hutu ya Kai su Banga Kuma alamar tashin hankali a fuskarsa ba Cikin kuka nace "wlh b'oyewa yake bayaso aji labarin sun b'ata Dan yasan zan iya jin labari Mallam nasan wacece uwar mijina wlh zata iya b'atarmin da yarana Dan Allah ku barni naje gidan da kaina su fitomin da yarana Haka ma Suka tab'a batar da Nadeeya dak'yar aka ganta Dama sun tsanesu Dan Allah Mallam kubarni naje da kaina" Na karashe cikin ihun kuka Ina dafe kirjina Dana ji Yana min suya Wai yarana sun b'ata da Raina aka dorawa yarana talla Innalillahi wa Inna ilaihi rajiun "Ki kwantar da hankalinki Naeema Bari na tura mmn Sadiya ta je gidan da kanta mubi komai a hankali insha Allahu Ina kyautata zaton hutun ya Kai su basu b'ata ba Bari taje ta dawo Muji ya sukayi da Yan gidan Nidai Dan yamin Dole ne da tuni na kusa Isa gidan. Aunty kuwa Hijabinta ta zura tayi waje. Yarana kuwa Suka hau bani labari irin rayuwar da sukeyi da su Umma Umma dai Bata dukansu Amma Safiyya kam tana Kai musu duka a labarin ma da Minal ke bani dayake tana da surutu cewa tayi wani kullum.yana zuwa wajen Safiyya zance Sam bana wani Gane maganar da Minal kemin zuciyata tana can wajen Aunty fatana ta dawo tacemin ta gansu Minal ce Bata San Mai take cewa ba Raheema kuwa sai wani narke min take tana min kananan shagwaba Humaira kuwa hannuna ta rike Gam a cikin nata tana "Umma Dan Allah karki Kara tafiya ki barmu kinji"? Aunty kuwa a lokacin data Isa gidan. Da Sallama ta Shiga gidan Hajara na zaune tana Shan garin kwaki da Yan canjin da Naseer ya Bata Safiyya Kuma tana can gefe tana cin abinci a farin roba da kana gani kasan na siyarwa ne shinkafa ne da Miya har da lemo taci uban kwalliya. Ba Wanda ya amsa Sallamar da tayi Safiyya kuwa har wani yatsina fuska tayi tana wa aunty kallon up and down tare da cewa "lafiya daga Ina"? Wani irin harara aunty ta watsa Mata ta kalli Hajara da ta karasa kwankwade garin da take Sha tana "shigo Mana daga Ina"? " Ciki Aunty ta karasa tana kallon yanda gidan yayi gaja gaja ba kintsi Ta zauna a gefen tabarmar da Hajaran ke Kai ta hau gaida Hajaran Hajara ta amsa cikin Dan sakin fuska tana jiran Karin bayani " Sunana Hafsa Matar mallamin su Zahira ce ni kwana biyu bamu ga Zahira da Nadeeya sunje makaranta ba shine Mallam yace Nazo gida naji lafiya suka daina zuwa" "Dolene sai sunzo makarantar lafiya Lau kawai bamu ga Daman suzo bane" Safiyya tace tana Harare Harare "Baiwar Allah ba wajenki Nazo ba ba kuma dake nake magana ba da mahaifiyarki nake magana Dan ita nakewa kallon Mai hankali sanin bakida hankalin yasa ko kallon naki banyi ba Wani irin Ashar Saffiya ta lailayo Aunty kuwa ta ja Tsaki ta kalli. Hajara da ke ta juye juye kafin ta saukr ajiyar zuciya ta ce "wlh sati biyu da kwana shidda kenan da b'atan Zahira da.nadeeya tsautsayi daga Dora musu tallan shinkafa da miya su Kai titi su dawo har yau dawowar da basuyi ba kenan ba neman da bamu musu ba "Innalillahi wa Inna ilaihi rajiun kawai aunty ke maimaitawa hankalinta a balain tashe ya tabbata dai su zahiran sun b'ata yau Mai zata cewa Naeema "Kullum sai babansu ya fita da sassafe nemansu sai daddare yake dawowa sai dai ku tayamu kawai da Addu'a Abu Bai dadi ba" Aunty Bata iya Kara ce komai ba ta mik'e ta fita Tana hada hanya sosai taji hankalinta ya tashi Dan tasan Yau Naeema sai ta kusa karamin hauka ita ma da nata sakacin da Bata duba yaran akai akai Kamar yanda ta alkawartawa Naeema. Lokacin data Isa kasa Shiga gidan tayi sai da Mallam ya hangota ya iso wajenta ta ja shi gefe ta Gaya masa yanda sukayi da mahaifiyar Naseer sosai.hankalinsa ya tashi yana mamakin ya Yara zasu B'ata har guda biyu Amma Naseer ya boye musu Anya akwai gaskiya a lamarin Nan kuwa A tare Suka Shiga gidan Ina ganinsu na mike da Sauri naje wajen aunty a rude Ina "Kinga su zahiran ko? karya Minal take basu b'ata ba ko"? Na jerowa Aunty tambayoyi Ina rik'e hannunta Gam "Zauna muyi magana" Mallam yace Ni kuwa.na zub'e a kasa Ina sallati ta tabbata dai yarana sun b'ata sallati kawai nake Ina ihun kiran.zahira.da Nadeeya Ina nayi nadama Dana tashi tafiya ban tafi dasu ba Ashe kallon.karshe nayiwa zahira shiyasa take ta waiwayena da Zan tafi Mai nayiwa su Umma Haka suka nemi su b'atarmin da yarana mai Zahira da Nadeeya suka musu da zafi haka" Dak'yar na tsagaita kukan da nake Mallam.yace "ki kwantar da hankalinki a gaskiya bana Jin yaranki sun b'ata dan da sun Bata gaskiya zamu ji labari.ina dai zargin Naseer dai hutun.ya Kai su Dan Ina ganinsa a bakin titi wajen ginin shaguna Nan na bakin titi da yaranki sun b'ata bana jin zai iy wanan ginin Dan Haka yanzu ki Bari daddare zanje wajen.Naseer da.kaina nace Masa nji a gari ance yaransa sun B'ata dagaske ne ko.karya ne" Karki damu insha Allahu yaranki Basu B'ata ba "Sun B'ata Mallam boyewa kawai Naseer keyi Dan Ni bansan Inda zai Kai yaran Nan hutu ba Dan Allah kubarni naje gidan Dak'yar suka shawo kaina akan na Bari gobe naje gidan Dan dagewa nayi sai naje su Umma sun fito min da yarana. Su Minal din ma rikesu nayi na dage akan wlh bazasu Kara komawa gidan ba Suma kuka suka ringa Yi wiwi akan bazasu tafi su barni ba dak'yar Mallam ya Basu Baki akan suje gida gobe Zanzo na daukesu da kaina Kuma karsu gayawa kowa sun gani ya hada musu da alewa dak'yar suka yarda suka tafi bayan na musu alkawarin zuwa gobe na tafi dasu Duk da har ga Allah daga aunty har mijinta Dan sunmin fin karfine da wlh ba abinda zai Kara rabani dasu. Ko gida ban iya komawa ba sabida har ga Allah gobe da sassafe Zan dira gidan Daga Umma har Naseer wlh sai sun Fito min dasu Nadeeya har wani zazzabi naji Yana neman rufeni. Alaramma kuwa masu d'aukar karatu Wajen sa ne yasa a ranar Bai samu zuwa gidan ba nikam Dama yanda Naga Rana Haka Naga dare ko ya na Dan rufe idona sai Naga kamar Zahira da Nadeeya na kuka suna cikin wani Hali idan dai wani Abu ya samesu Nima kaina bazan yafewa kaina ba. Da asuba naso dira gidan Sabida inasan na samu Naseer a gida Sai dai Mallam.dake waje Zaune da almajirai yasa na koma ciki. Aunty ma Ni haushinta nakeji da rarrashin da takemin ita kuwa ganin na matsu na fita yasa ta saka Hijabinta ta fita wajen Mallam ba jimawa kuwa sai ga ta dawo tana na tashi mu tafi. Da Sauri na sab'a Waleed a bayana muka dau hanya bani burin daya wuce na Isa gidan Muna kuwa Isa gidan ban tsaya wani buga k'ofa ba na hankada k'ofar na Shiga. Naseer ne a tsakar gidan da tsintsiya Yana shara Umma Kuma tana daga bakin kofarta a zaune Su Minal Kuma ma Kan tabarma suna Shan Koko da kosai Naseer tsintsiyar hannunsa ne ya kubce daga hannunsa a lokacin da muka hada Ido dashi Umma kuwa har tana tuntub'e wajen mik'ewa Yarana kuwa Suka taso aguje suka rungumeni suna ihun Umma Ni kuwa Raina a had'e nace "Naseer Ina Zahira da Nadeeya Naseer Ina ka kaimin su"? Ko kallon.umma banyi ba da ke masifar uban me Nazo nema banma San ta zo kusa Dani ba Naseer kuwa kamar.mai tsoron magana Naga Yana ta min magana da Ido. Ni kuwa cikin Jin haushi.nace "Naseer Ina Zahira da Nadeeya nace Wlh Tallahi bazan yarda ba a yau sai an fitomin da yarana Naseer idan ba Haka ba wlh hukuma ce zata rabamu na rantse da Allah" "Yaranki sun b'ata kiyi.abinda zakiyi Yar iska kaji Mara mutunci ke kadai Kika haifesu Naga shi Naseerun.yafiki iko Akansu shima ya fara d'aukar dangana ballantana ke din banza da baki ma San ciwon su ba kizo Nan kina Mana hauka kin Dade Baki hadamu da hukuma ba idan ma salon da Kika zo dashi kenan Dan ki dawo gidanan wlh bazaki dawo ba muguwa azzalluma daga fitarki Kika je kikayi wa yarona asiri duk ya tsiyace" "Umma ba abinda zai Kara dawo Dani gidanan kince bakya Sona na rabu da danki na Kuma tafi Dan Haka a bani yarana na tafi dasu Kar a sake a yarda wani Abu ya Samu Nadeeya da Zahira Dan ba Abunda suka muku" "Muje waje muyi magana Naeema " Naseer yace a hankali kamar Mai ciwon makogaro Tirjewa nayi Umma tayi ta auna min zagi Aunty kuwa Taja hannuna mukayi waje Dan ta lura kamar akwai maganar da Naseer yake so yamin Amma baya so yayi maganar a gaban Umma. Su Zahira kuwa kwandastan tambayarsu yayi Ina zasuje Suka ce Masa gadon Kaya sukayi shi kuwa yace ba Nan sukayi ba su dorayi sukayi Amma zasu dorasu a motar gadon kayan. Zahira da Nadeeya kuwa sai juyawa suke suna kallon motar da Murja ta hau dake bin bus dinsu bumper to bumper Sai da.suka iso junction bus dinsu ya tsyaa sabida su Dora su Zahira a motar gadon kaya Wanda Murja Kuma ta hau ya wuce Sai da sukayi nisa ta lura da motarsu Zahira ya tsaya tayi saurin cewa akwai na Nan ta sauka da Sauri Ta dawo Baya sai dai kafin ta Isa wajensu zahiran har sun samu motar gadon Kaya sun hau driver ma ko karbar kudin baiyi ba yace su barshi Ahaka Murja ta Kara tare wani bus din tabi bayansu fatanta kawai ta Isa wajen su kafin suje gidan su su tona Mata asiri. Sai dai duk Inda suka so tadda bus din su Zahira sai days Dan musu nisa. Suna Isa junction din gadon kayan su Zahira Suka sauka da Sauri suka hau gudu Murja dake ankare dasu tana ganin kwanar da suka Shiga ta cewa kwandastan akwai na Nan ta sauka da Bakin Sauri Tana bawa.kwandastan kudi Ta tari machine akan ya Shiga kwanar Nan ga wasu Yara can suna gudu Dan Allah ya ta dosu. Su Zahira kuwa gudu.suke.suna fad'uwa.dan sunga hawanta machine Ta kusa ci musu Nadeeya ce ma Bata iya gudun sosai sai Zahira ta Dan jirata ahaka machine din Murjan ya taddasu ta Kai.hannu ta daki bayan Nadeeya tana Daga Bayan machine din duk da Yana tafiya.ce wa take su tsaya Amma Ina Zahira da Nadeeya Kara gudun suka sa Dan sun fara hango k'ofar gidansu. Murja kuwa sai kaiwa.mai machine duka take Akan yayi Sauri. Ni kuwa Ina fita waje Naseer ya.jani gefe Yana k'ok'arin min magana Umma kuwa ta fito daga gida tana zagina tana surfamin zagi akan na bar Mata k'ofar Gidan da Ni kuwa na dage bazan bar k'ofar gidan ba wlh sai an fitomin da Nadeeya da Zahira. Dukanmu ba Wanda ya lura Dasu Nadeeya dake nufomu suna tikar gudu Tun kafin su iso naji suna kwalla Mana Kira Abba Umma Muna juyowa suka iso a daidai lokacin da Naga wata Mata itama ta sauka daga Kan machine din ta damko Kafadun zahiran data cala wani uban ihu........... ?*NAGA TA KAINA* *NA SADNAF*🌸🌸 ®️ *_PURE MOMENT OF LIFE WRITERS_* _{We Don't just entertain nd educate we also touch the heat of readers P.M.L}💪🏻_ *Free Novel* *Page 40* Idon Murja sosai ya rufe da San ta damke Zahira ta faffala mata Mari ko kad'an Bata lura da su Naseer dake tsaye ba ta daga hannunta da zumar wanka Mata Mari Ni kuwa tundaga yanda nagansu a firgice hankalina ya tashi yanda ta damke kafadar Zahira yasa nayi wani super na Isa gabansu tana daga hannunta na tare Marin tare da rike hannunta na wancakalar da Karfin tsiya Zahira kuwa ta taso aguje ta buya a bayana tare da kankameni jikinta na balain rawa. Sai a lokacin Murja ta lura dasu Naseer da jikinsa ke rawa shima cikin tashin hankali ganin su Nadeeya da Zahira dake tikar gudu Murja na binsu a Baya Jikinta ne ya dau rawa cikin tsoro ta zub'e a kasa tare da fashewa da kuka Ni kuwa nace "Ke jahilar inace da Zaki biyo yara har gidan ubansu a gaban iyayensu Kuma ki nemi dukansu Mai suka Miki"? Nace wa wacce ta biyo su zahiran da bansan dalilin dayasa ta biyosu ba banma San daga Ina suke ba "Murja lafiya kuwa"? Shine abinda naji Naseer yace Mata ita kuwa sai rizgar kuka take" Tana k'ok'arin magana naji muryar Nadeeya data rungume kafafun Naseer ta Baya ta lek'o da fuskata tana "Allah ya isa tsakaninmu dake muguwa Azzalluma sai Allah ya saka Mana bazamu tab'a yafe Miki ba Abba muguwa ce kullum sai ta dake mu ta d'auko wuka Wai sai ta kashemu Bata bamu abinci sai dai Wake da sabulu" "Innalillahi wa Inna ilaihi rajiun Nadeeya Mai na Miki da zakimin wanan Sharrin Yaya Naseer wlh karya take min tunda ka Kai su kullum sai sunyi kuka Akan suna San su dawo kullum sai na rarrashe su shine yau daga Shiga wanka na fito mak'ota sukace min gasu can sun gudu shine fa na biyosu har Nan Dan bana San wani Abu ya samesu Amma wlh ban musu komai ba" "Wlh Abba karya take yi kaga shattin tsintsiyar kwakwan data dakemu dashi kaga Gefen fuskar aunty Zahira wlh muguwa ce yanzu ma sai data dakemu Wani Mai shago ya bamu kudi Akan mu gudu kafin ta kashemu" Murja na k'ok'arin Magana Hajara da tunda ta ga Murja ta daskare a tsaye Ganin irin sharrin data kula musu Kafin su har gidan Tijjani irinsa take kulawan yanzu yasa ta daka wani uban tsalle ta tsaya Agaban Murja tana "Karya kike wlh shegiya munafika kafira makira Yar wuta duk abinda yarinya Nan tace wlh Zaki aikata tsaf Yau kinzo har inda nake kin sameni kin rabani da Dana kin sa ya koreni hakan Bai isheki ba sai kin taba jikokina toh wlh yau sai na Rama abinda kikamin" Hajara tace tana cakumo rigar Murjan tare da ware murya ta hau kwallawa Safiyya dake daki tana bacci batare da tasan duk abinda ke faruwa ba yanda ta ware murya ne yasa Safiyya ta jiyota ta kuwa fito a guje. Murja kuwa irin cakume mata Riga da tayi yasa ta mik'e tana "Umma Mai na Miki Dan Allah Mai na Miki kika tsaneni" "Allah ya tsinewa bakinki albarka da kike KIRANA Umma dashi Ni da kika zaneni wanan Bai isheki ba Kika hada da makirci sai da muka bar gidan nida gidan Dana k'arfi da yaji Kika hanani abinci dayake bakida ta Ido ni Zaki kalla kicewa Umma Allah ya tsine Miki Murja Nan ma makircin zakimin kenan duk da babu idon Tijjani? "Murja sosai.ta ringa Kai zuciyarta nesa Dan ji take kamar ta daga Hajaran ta maka da kasa Amma Bata San ta kwafsa sabida Naseer da ya saki baki Yana kallonsu Hawaye ta hau yi cikin shesheka tana "Haba Umma kiyayar da kikemin har ya Kai Haka da Zaki min sharri" Ke Amma bakida kunya Yanzu anan ma makircin Zaki mana" Safiyya tace tana nada hannun rigarta "Haba Umma" Wani irin Mari Hajara ta d'auke Murja dashi sabida bakin cikin yanda Murja ke neman nunawa ita ta Allah ce Murja kuwa ta dafe kumatunta tana Jin zuciyarta na zuwa wuya tana k'ok'arin Kara magana ta Kara kwashe Murja da.mari Murja kuwa zafin Marin Yasa ta manta da wani Naseer da ke tsaye ta daga Hajara sama duk da uban cikin jikinta ta makata da kasa Safiyya tayi Kan Murja ta hau Kai Mata duka Naseer kuwa dake sallati Ya nufi.kansu aguje Yana ihun Kar a tab'a Murja ciki ne da ita adaidai lokacin da Hajara ta samu ta mayar da.murja kasa ta d'ebo kasa.ta cusa a bakin Murja Naseer kuwa ya wancakalar da safeeya ya ruk'o Hajara da k'arfi da itama kamar karfin aka Kara Mata sai ma k'ok'arin tak'e cikin Murja dake kawo Mata duka itama take. "Cikani munafiki Ashe Dama gidan Tijjani ka Kai yaran Nan shine kacemin sun b'ata ka dagamin hankali Naseer Ni zaka yaudara Naseer Akan na Mori yaranka mu samu na rufin asiri gabadaya ka gwammace ka Kai su gidan azzalluma Nan makira har kazo kamin karyar sun B'ata Naseer Dan kawai Kar na Dora musu talla? Tallan Dana Dora musu Dan wa na Dora musu Naseer ba Dan mu samu abinda yaran naka Zasu ringa ci bane tunda ka kasa Nemo Mana kudin kirki tunda shegiya matar Nan taka itama.ta bar gidanan ta asirceka komai naka ya tsaya cak daga Kai har Tijjani kun auro shegu tsinannu" "Wlh Ni ba shegiya bace Umma kuma danki da kike magana ai na bar.miki shi tunda bana gidansa yanzu Yara Kuma da kike magana wlh a yau Zan kwashe su na tafi dasu Dan bazan Kara barinsu a gidanan ba Ni Zan iya kula dasu ke D'an naki ya kula dake kedai Umma ki nemo masa wacce ta kwanta Miki ki aura Masa" Nace Ina rik'e da hannun Zahira Dana Nadeeya daga abinda ya faru.nagane Murja ce matar Tijjani tunda Naseer ya rik'e Umma.ta kwashi takalmanta tare da furzar da kasar da Umma ta cika Mata bakinta dashi. Da sauri.ta hau tafiya tana rufe fuskarta da mayafi Safiyya kuwa har da diban dutse ta jefa Mata "Karki sake Kimin rashin kunya in Banda kaddara Mai Naseer zaiyi dake Yara Kuma da kike magana ba Inda Zaki tafi dasu ko kwaki ya samo ya Basu suci so kike ki tafi da yaran sabida ya biyoki ko toh na Gane wayonki ba Inda zakije da yaran"? "Wlh sai na tafi dasu Umma Banga uban da zai Hana ni tafiya dasu ba" Nace Rai a bace tare da rike hannayen yarana nayi gefe dasu Nadeeya kuwa Naga ta Dan tirje Naseer da idonsa ya kad'a yayi wani irin ja dak'yar ya bud'e bakinsa yana "ki tafi dasu Naeema Allah ya musu albarka" Ameen nayi saurin cewa na fara k'ok'arin juyawa hannuna rik'e Dana yarana Zahira kuwa har tayi gaba. Aunty ita Kuma tana rik'e da hannunsu Raheema. Umma kuwa tace "Kace ta tafi dasu kana da hankali kuwa"? Naseer Bai ce Mata komai ba Illa ma hannunsa da ya mikomin Yana "Dan Allah Dan bani Waleed Naganshi Naeema" Ban ma saurareshi ba duk da tausayinsa na nukurkusar zuciya ta Aunty kuwa ganin na ma share shi na dau hanya zan tafi yasa ta saki hannunsu Raheema ta karaso wajena ta kunto Waleed Ni kuwa nace Mata "Kar fa ya hanani Dana" Bata saurareni ba ta mik'awa Naseer Waleed Waleed kuwa ya karbe shi da hannu biyu ya rungumeshi a kirjinsa adaidai lokacin da hawaye suka zubo Masa yayi saurin d'auke hawayen ya sumbaci Waleed a goshi Yana "Allah ya maka albarka Naseer" Daga Haka ya mik'awa Aunty shi Ya kalli Zahira da har sunyi gaba Yana "Ba Sallama Zahira Raheema.humaira bazaku zo kumin Sallama ba" Da Sauri duk.suka nufi wajensa ya sunkuya ya rungumesu ya shafa kansu gabadaya har da Nadeeya dake gefensa yace "Maza kubi ummanku ku tafi kunji Allah ya muku albarka kuringa yiwa Abbanku addua Allah ya bashi kudi kunji"? "Abba bada Kai zamu tafi ba"? Nadeeya tace hawaye na cika Mata Ido adaidai lokacin da su Zahira suka.dan Kara yin gaba Dan suna tsoron Naeema ta tafi ta barsu Murmushin karfin hali Naseer yayi Yana "badani zaku Tafi ba Nadeeya Amma zanzo kinji maza Kibi Yan uwanki ki tafi" Hawaye ta hau Yi Tak'i motsawa Ni kuwa na daka Mata tsawa Ina "Dan ubanki kizo ki wuce mu tafi" Umma kuwa sai zagin Naseer take tana zagina Akan na asirice Naseer yace na tafi da yaran Ga mamakina Nadeeya girgiza min Kai tayi tana "Umma idan bazamu tafi da Abba ba a wajen Abba Zan zauna bazan biku ba" Ta karashe cikin kuka.tana kankame Naseer Ni kuwa na Kara daka Mata tsawa Ina "kizo ki wuce mu tafi Nadeeya wlh Zan zaneki Dan idan Kika zauna a Nan duka Zaki ringa sha a Dora Miki talla ko makaranta ma bazaki je ba" "Nidai ba Inda zani wajen Abba Zan zauna umma" Naseer kuwa banbare ta yayi daga jikinsa cikin murmushi da kana gani kasan na yak'e ne ya sunkuya ya rik'e hannun Nadeeya Yana "Karki damu Nadeeya ta zanzo na sameku Kibi ummanki ki tafi kinji idan Kika zauna anan ba Wanda zakiyi Wasa dashi" "Nidai ba Inda zani Abba indai bazaka bimu ba a wajenka Zan zauna" A zuciye na nufi wajen Naseer da niyyar na fincikota ita kuwa ta dib'a aguje ta Shiga gidan tana hankada Umma dake bakin kofa........ Toh ga readmore biyu Nan tunda kun matsamin😝😝😝😝😝😝😝😝 *NAGA TA KAINA* *NA SADNAF*🌸🌸 ®️ *_PURE MOMENT OF LIFE WRITERS_* _{We Don't just entertain nd educate we also touch the heat of readers P.M.L}💪🏻_ *Free Novel* *Page 41* Har ciki na bita Nima Ina dan bangaje Umma datayi bake bake a bakin kofa ita kuwa tayi ta auna min zagi Wai na fito Mata daga gidan d'a Kar na Musu Sata. Ban saurareta ba na bi Nadeeya har d'akina na da Dan Nan ta shige Tana ganina ta kankame jikinta tana ihun kukan "Ba Inda zani Umma bazan biki ba a wajen Abba Zan zauna Umma idan Kika tafi damu waye zai zauna da Abba ba Inda zanje Umma" Haushin taurin Kan Nadeeya yasa na Kai Mata duka na rik'e hannunta da Karfi da nufin janta a kasa sosai Kuma nake mamakin Inda Nadeeya ta samo taurin Kai bazata Gane Gata nake Mata da rabata da gidanan ba daga Ni har sauran yaran nawa ai ba a San ranmu muka bar Abban nata ba Dan muma ba finmu San shi tayi ba Kara fincike hannunta tayi da k'arfi ta hau burgiman ba Inda zataje Ni kuwa na cire takalmina da niyyar zaneta. Naseer ya shigo da Sauri ya rik'e hannuna Yana "kiyi hakuri karki bugeta Bari na rarrasheta" Ya saki hannuna ya durk'usa gaban Nadeeya tare da dagota ya hau rarrashinta Akan ta bini ita kuwa sai tirjewa take Akan bazata bini ba ita a wajensa zata zauna a karshe ma sai ta fita aguje Ni kuwa na fara k'ok'arin bin bayanta aguje naji Naseer ya ruk'o hannuna ya Kuma jawoni jikinsa ya kamkameni ta baya tare da Dora kansa a kafadata naji dumin hawayensa a kafadar tawa daya haddasa min wani irin raunin zuciya da San na juya na rungumeshi na rarrashe shi Cikin rawar murya ya fara magana Yana "kiyi hakuri Naeema nsan kinyi hakuri Zama da Mahaifiyata tsawon shekaru Wanda sai da Kika tafi nagane irin hakurin da kikayi da ita Naeema na kasa sauke nauyin da Allah ya doramin na gaza ciyar dasu na gaza tufatar dasu ba irin kudin da ban nema ba ban samu ba Naeema Dan Allah idan Kika tafi da yaran Nan ki Kular min dasu Allah ya Baki Lada ita kuma Nadeeya tunda ta dage bazata biki ba ki barmin ita Zan kula da ita insha Allahu na Kai su gidan Tijjani ne sabida Ina tunanin acan babu Mai musguna musu bansan matarsa itama ba matuniyar arziki bace na Miki alkwari bazan Bari Umma ta Taba Nadeeya ba indai ta Taba ta insha Allahu da kaina Zan kawo Miki ita" Duk maganar Nan da Naseer kemin Yana kamkame Dani kansa Akan kafadata Yana zubar da hawaye nima hawayen nake sosai Dan. Har ga Allah a yanzu ne Naseer ke bukata ta a kusa dashi yau da Umma Bata sako mu agaba ba Dan abinda nake samu iya zaman duniya dai zai ishemu dagani har yarana da Naseer Amma Umma ta dage sai mun rabu. "Daga Bauchin Kika zo"? Naseer yace Girgiza Masa Kai nayi Ina k'ok'arin Magana naji muryar Umma cikin ihu tana "Yau Naga karuwa har cikin gida yau Naga ikon Allah yanzu har daki Kika shigo Dan ki yaudari Naseer ya Kara miki wani cikin kenan kamar yanda Kika Saba Kai jamaa wannan yarinya anyi jarababbiya kwartuwa" Fusge jikina nayi daga na Naseer da har lokacin yake rik'e Dani tsayuwar Umma a bakin kofar d'akin Bai saka ya cikani ba Ni kuwa na ja Tsaki na bangaje Umma dake bakin kofa ta kawo hannu zata kawomin duka Dan sai data Kusa fad'uwa dana bangajeta na kauce "Shegiya karuwa Dole ki hankadani tunda na kamaki kina k'ok'arin yiwa Dana fyad'e" Bance Mata komai ba na fice waje ta biyoni har waje tana min ihun kwartuwa Naseer kuwa magana yake Mata Yana k'ok'arin hanata Amma sai ihu take cigaba da yi. Hannun Raheema kawai na rik'e Dan Waleed na hannun Aunty su Zahira Kuma suna can gaba dasu Minal. Muka hau tafiya Ina danne kukan dake neman fitomin ta karfi Dan har waje Umma ta fito tana min ihun kwartuwa karuwa. Wai nice karuwa ban waiga ba duk da naji Naseer ya daka Mata wani uban tsawa akan tayi shiru Amma a madadin tayi shirun sai cewa tayi "Saukar Mari nake jira naji Dan ka Riga da ka Saba marina Maza Mareni sabida wancan karuwar data biyoka har gida zata maka fyad'e. Naseer bakin ciki ne yasa ya koma ciki ya lek'a dakin Umma ya ruk'o hannun Nadeeya suka fice daga gidan. "Gaskiya ban taba ganin uwar miji irin Taki ba Naeema duk yanda Zaki bawa mutum labari bazai Gane ba sai ya ganta da idonsa wlh rabuwarki Da Naseer yafi alheri Kai wanan Mata anyi tsinaniya yanzu Nadeeya dagewa tayi bazata bikin ba"? Mai yasa Baki tilasta Mata ba Naeema kinsan yarinta ke damunta ita gani take ba Wanda zai zauna da abbanta shiyasa ta dage bazata biki ba" "Hmmm" Kawai na iya cewa Aunty Dan Sam bana Jin yin magana sabida abinda ya tsayamin a mak'oshi yak'i tsirgamin Muna fita titi na tare Mana taxi su Zahira suka Shiga na karbi Waleed daga hannun Aunty A k'ok'arina na inyi magana na fashe da kukan dake cina tundazu "Sai hakuri Naeema Allah dai ya shiryi matar Nan idan tana da rabon Shiriya Ban ce Mata komai ba na Shiga taxi Ina cigaba da kukana. Sunkuyowa Aunty tayi daidai window motar tana "zanzo jibi kafin na Zo dai Zan lek'a gidan Naga ko Zan iya shawo Kan Nadeeya dan inaga sai kinfi samun kwanciyar hankali idan Kika gansu a gunki gabadaya. Kai na gyad'a Mata muka wuce. Muna Isa Muka sauka gabadaya na karbi kudi a wajen Hassana dake ta markade na bawa Mai taxi. Na dawo muka zauna a palo gabadayan mu. Yarana sai kalle kalle suke. Sosai nake Jin ba dadi da Nadeeya Bata biyoni ba da nasani na Mata tsinannen duka na taho da ita Dan ai ba fin karfina tayi ba Naseer ne ma yake wani lallaba ta. Kitchen na fita na Dora Mana ruwan tea Dan Nima ban karya ba na fita shagon k'ofar gida da Isihu shima tafiya da nayi karbowa Waleed magani Nazo na same shi ya dawo daga garinsu rashin nutsuwa yasa ban ma bi ta kansa ba Hassana dai tacemin shi yake jire min shagon Kayan shayi na d'aukar Mana da manyan bredi har da kwai wajen goma Na koma ciki na soya Mana na fito da kofuna na kwallawa Zahira Kira tazo ta d'aukar Mana flask din shayin. Sosai jikin yarana ya ringa rawa farinciki shimfide a fuskarsu ahaka na zubawa kowace Madara da bournvita Dan gwangwanin su na dauko. Kwan Kuma na ajiye a tsakiyarsu. Sosai jikinsu ya ringa rawa wajen Shan shayi Kamar basu tab'a cin abinci ba. Bare Zahira da duk zafin shayin Haka take kurba sosai tausayinta yasa kwalla zubomin Dan ga shattin tsintsiyar Nan a kwance a wajen idanta ga jikinta Nan ma yayi rudu rudu sabida duka. Hannunta kuwa ya Kara sirrancewa kasancewarta Mara jiki. Ganin ta a irin halin Nan yasa nama.kasa cin abincin nace "Zahira Mai ya samu jikinki haka"? Hadiye kwan data saka a baki tayi tana "Aunty ce take zanemu kullum" "Da kuka Mata me take zaneku kullum"? Shanye shayin daya Mata saura tayi ta hau bani labari irin rayuwar da sukayi a gidan Tijjani da yanda Take dafa wake Mai uban attaruhu da sabulu Tana bani labarin tana kuka Dan Abu kad'an ke saka Zahira kuka ko tsawa ka daka wa Zahira yanzu Nan zaka ga idonta ya ciko da hawaye Sosai na ringa kuka Ina duba jikin Zahira daya Sha tabon bulala da dorina "Allah ya Isa tsakani na da ita bazan tab'a yafe Mata cutarmin daku da tayi ba Mai kuka Mata da zata azabtar daku Haka har ta muku horon yunwa ta ringa bawa Nadeeya Sabulu da wake sabida mugunta Allah ya Isa bazan yafe Mata ba Allah sai ya muku sakayya tun a gidan Duniya idan Allah ya yarda Allah sarki Nadeeya yanzu Haka ta ringa cin wake da sabulun babu abinda ya sameta"? "Eee umma sai dai tayi ta kashi Mai kumfa tacemin duwawunta na yaji idan na hanata cin wake sai tacemin yunwa takeji sai taci" Kaina har ciwo yamin sabida kukan zalincin da matar Tijjani tamin Sai da Hassana ta Gama markaden tazo ta zauna na Dan Bata labarin duk wuyan dayarana suka Sha taci kuka itama tana Dama Nadeeya ta biyoni . Nima iirn wuyan da Zahira ta bani Akan nadeeya ta Sha naji inasan na dawo da Nadeeya gabana na kula da ita Ita da Minal suna da balain ci Anan Zan Basu duk abinda suke so ta dawo Nan tabar Naseer Yaji da kansa Hassana ce ta Tayani tsefewa su Raheema Kai har Minal ta musu wanka ta wanke musu Kai. Zannuwana na raba musu Suka daura na janyo gwangwanin na danake Tara kudi . Na duba Naga kudin ciki da Dan yawa na dibi yanda zai isheni karfe uku na nufi Sabon gari Dan acan na Dan Tsintowa Waleed Kaya masu kyau kamar sababi Kuma a kudi kalilan. Sosai na jiddo wa yarana Kaya har da panties Zahira danaga ta fara kirgen dangi har ves ves na siya Mata dasu under wear duk abinda na daukarwa Zahira sai Dana d'aukar wa Nadeeya Dan nasu zahiran yadan fi yawa. Kala.uku na daukarwa Isihu shima Dan ya zama tamkar Dana Tinda barina gadon Kaya yasa shima ya hakura da makaranta ya dawo wajena duk da ba a gidana yake kwana ba a wani makaranta Allo dake unguwar yake kwana a Kuma Nan yake karatu. Sai wajen Magriba na isa gida. Yarana sai tsalle tsalle suke suna Wasa Zahira itama sai washe baki take abinda ya ragemin Jin dadin kasancewata dasu shine Nadeeya da Bata Nan Dan da tana Nan da kila hankalina Bai rabu gida biyu ba. A Daren nida hassana har da zahiran muka wanke kayan gabadaya. Suka saka vest din Dana sisiyo.musu. Zahira akwai San.kallo Dan tv black and white Dana siya karami da lokacin tashar Nta ne kawai da ctv suke Dan drama Dan sai kana da video kake iya siyan cassette kayi kallo. A gaban tv tayi zaman dirshan tana ta kallo har kannenta sukayi bacci suka barta. Sai da zamu kwanta na umarceta data kashe. A daki daya muka kwana gabadaya Banda hassana. Ni kuwa Sam baccin ma Bai min wani dadi ba sabida zuciyata dake wajen Nadeeya. Naseer kuwa Yana barin gidan Bai zame ko Ina ba sai wajen da aka basu kwangilar gini. Ya samo benci ya zaunar da Nadeeya ya siyo Mata shayi da bredi har da kwai ita kuwa ta hau ci tana Masa hiran sabulu da waken da Murja ke basu sunaci. Ta dage rigar jkinta tana nuna Masa shattin bulala dake kwance a jikinta tana "Abba kaga yanda ta zanemu kullum sai ta dakemu ta zageka ta zagi Umma Wai an kawo Mata jarraba" Naseer kasa magana yayi Sabida tsananin b'acin Rai dayake Nadeeya tana da surutu a take ta bashi labarin duk rayuwar da sukayi a gidan. Naseer sosai ya daure baiyi kuka Agaban Nadeeya ba sabida yanda yake ji a Ransa wai da Ransa aka zalunci yaransa Haka Bai taba tunanin Murja Haka take ba Taya yaransa zasu Sha wanan bak'ar wahalar Tijjani yace ko sau daya Bai taba Sani ba baya ganin jikin yaran nasa ne Zahira dake ruwa ruwa wajen kuka ai ko kallon minti uku ya Mata yaci ya Gane Ana gana musu azaba. Sosai ya rik'e tijjjani a Ransa. Dan Bai ga wani laifin Murja ba Tijjanin da Bai saka Ido a gidansa ba yaga laifinsa. A Haka ya saka kayan aikinsa suka hau aikin ginin. Nadeeya nadaga inuwa tana surutai har ta Saba da Yan aikin wajen wani ya siya Mata shinkafa da miya har da nama surutunta da manyance ta yasa tayi farinjini akayi ta Mata siye siye tana Jin dadi Dan inda tafi kwarewa kenan Ahaka wani Abba magini da gidansa ke kusa da wajen da suke aiki ya Dan hau tambayar Naseer dalilin dayasa yazo da Nadeeya wajen. Shi kuwa yace Masa ba kowa a gidan ne iyalinsa sunyi tafiya shiyasa ya taho da ita Dan mak'otan nasa Basu fiye shiri ba. Take shi kuwa Abban yace Mai zai Hana idan sunzo ta ringa Shiga gidansa idan sun tashi Kuma sai su koma gida tare. Sosai Naseer Yaji dadin maganar Abba Dan Dama Yana ta tunanin Inda zai na Kai Nadeeya Dan Sam Baya San barinta a gida makaranta ne dai sai ya samu kudi zai saka ta islamiyya Kuma zai nema anan din har uniform ya Dinka Mata ta ringa zuwa Wanda yaran Abban ke zuwa. Sai da suka Gama aikin Suka koma gida Naseer ya Dan siya musu kayan shayi ya tafar musu dashi. A tsakar gida ya samu Safiyya taci uban kwalliya tana zance da wani. Shi kam ya gaji da kwashe kwashen da Safiyya ke Masa a gida hakane yasa ya Isa wajensu Ransa a had'e ko amsa gaisuwar da suke Masa baiyi ba Naseer yace Masa "idan dagaske kake kana San ka Aureta ka turo magabatanka" "Dama yau tacemin na maka magana Dan inaso na turo magabatan nawa sai Kuma fad'uwa tazo daidai da Zama acan garin da dangin mahaifinta yake anan nake aiki. Inada Mata daya da Yara shidda "Zanje jibi insha Allahu mu tsayar da Magana Dan Nan da wata biyu nakeso ayi bikin namu" "Allah ya yarda" Kawai Naseer yace Dan har ga Allah gani yake Safiyya ta na cikin wayanda suke Masa Karen tsaye a rayuwarsa shiyasan ita ke saka Umma yin wani Abun. A ranar Nadeeya ce ta ringa deb'e Masa kewa da surutanta ya hada da Bata tarihi annabi Yusuf Dan surutan nata ma ba wani Kan gadone dashi ba hakane yasa ya hau Bata tarihin Annabi Yusuf ta kuwa nustu tana ji ahaka har bacci ya d'auketa shima ya d'aura alwala Yana iddar da shafai da wutr ya d'auko Quraninsa Dan ya karanta. Hajara ta fado d'akin kamar an hankadota. A Gefen katifa ta zauna tana "Kai Naseeru dazu naji kana cewa saurayin Safiyya ya turo da fatan ka tanadi kudin da zaka Mata kayan daki Dan kasan banida ko sisi ban Kuma bawa wani ajiya ba". "Banida ko sisi Umma Nima ban bawa kowa ajiya ba idan sun turo taje wajen dangin mahaifinta su harhada kudi su Mata kayan daki kamar yanda sukayi wa Lami Umma Nima ta kaina nake bazan iya zuwa nayi sata ba" "Ai nasan da dangin mahaifin nata nace ka Mata kayan d'akin Dan ko Lami da iya katifa aka kaita har gobe Gori ake Mata ita kuwa Safiyya tana da kishiya Dole ayi Mata kayan daki " Naseer Bai ce Mata komai ba ta Gama surutanta ta tafi. Murja kuwa tana komawa gida ta fara tunanin hanyar da zata bi batare da Tijjani ya zarge ta ba Dan tasan Ransa sai ya b'aci idan yaji Mai tayi Su Hajara kuwa bashi suka dauka sai ta Rama abinda suka Mata idan ta samu ta Shawo Kan matasalar daya kunno mata Kai Sosai ta ringa tsinewa Nadeeya da Zahira tana Jin inama taga Nadeeya a gabanta da ba abinda zai Hana ta shaketa har lahira. Bata San Mai yasa duk kamun da take wa Tijjani baya kamuwa ba tsinanen taurin Kai ne dashi ta Rasa dalili ballantana ta Mallakeshi Wai a Haka ma Mahaifiyarta tayi aiki babba akansa. Daba haka ba da tuni ya saketa Dan bashida mutunci ko kad'an daga aurensu zuwa yanzu ya Mareta ya Kai sau uku gashi ita Kuma balain San shi take. Ahaka ta zauna a gidan cike da fargaba dawowar Tijjani duk da ta gama.hada makircin da zatayi idan ya dawo. Karfe shidda taji karar vespa dinsa. Tayi sauri.ta zauna a tsakar gidan kafarta a kumbure Yana kyalli Dan ta kware a kumbura jikinta da wani hoda da Mahaifiyata ta Bata sai numfarfashi take idonta ya kad'a yayi.jawur Abinda ya Bata mamaki Bai wuce yanda taji har lokacin Bai shigo ba hakane yasa ta lek'a cikin sand'a Inda kuwa ta hango Tijjani a tsaye ya Kama kugu Jamilu Mai shago nata kwara Masa bayani. Gabanta ne ya yanke ya Fadi a lokacin data ga Tijjani idonsa ya kad'a yayi jajir sunyi musabiha da jamilun ya nufo gidan Ita kuwa Murja cikin tashin hankali ta Shiga palo da sauri ta zauna jikinta na Dan rawar tsoro tana tunanin hanyar da zata Kare kanta Daga yanda ya bugo k'ofar hantar cikinta ya kad'a Ta daure ta mik'a kafarta tana ta adduar Allah ya dorata akansa. Wani irin kallo ya hau jifanta dashi daya shigo cikin wani irin murya yace "Ina zahira da Nadeeya"? Kuka ta fashe dashi ta Kara Mika kafarta daya suntume Yana kyalli ta hau cewa "Kaga k'afata wlh a garin na bisu nayi tarkade Nazo Zan Shiga wanka naji mmn Hafsa ta shigo aguje tacemin gasu can zasu gudu kwana uku kenan suna cewa zasu gudu wlh a garin nabi bayansu na Fadi har bugewa nayi a cikina" Ta karashe tana fashewa da kuka Tijjani kuwa ya karasa wajenta Yana "Muga kafar ya sunkuya ita kuwa cikin makirci ta Kara mika kafarta tana cigaba da kuka Tijjani kuwa Yi yayi kamar zai duba kafarta aikuwa ya zaro belt ya hau tafkarta tana daga zaune....... *NAGA TA KAINA* *NA SADNAF*🌸🌸 ®️ *_PURE MOMENT OF LIFE WRITERS_* _{We Don't just entertain nd educate we also touch the heat of readers P.M.L}💪🏻_ *Free Novel* *Page 42* Sosai.ya ringa tafka Mata belt din Yana soka Mata Ashar sai daya Mata lilis ya koma gefe Yana "Maza tashi ki tafi gidanku shegiya makira na tsaneki wlh Allah na tsani mutum munafiki Ashe tunda na kawo yaran Nan Haka kike azabtar dasu ba iya jamilu ne ya tareni ya gayamin ba har Mallam Ashiru wajen aikina yaje ya sameni ya gayamin Ina dawowa shima jamilu ya tareni da zancen ke wacce irin muguwa ce kina d'auke da ciki a madadin ki ringa addua Allah ya saukeki lafiya aa sai Kika saka mugunta agaba kina zalintar yaran da basuji Basu gani ba shegiya munafika Mai fuska biyu Maza tashi ki barmin gida. Tijjani yace a fusace ya ruk'o hannunta ya fara janta da kasa ita kuwa sai numfarfashi take tana Magiyar yayi hakuri sharrin shaidan ne Bai saurareta ba sai daya kaita har waje. Ya watsar da ita ya koma ciki ya cillo Mata takalminta da mayafinta. Ya kulle gidan ya danne vesparsa tare da bada Mata k'asa. Sai data daina hango vesparsa ta mik'e dak'yar tana cije lebb'e sabida yanda jikinta ke balain rad'adi ko ta ina sabida ba karamin Jibga ya Mata ba. Gidan dake jikin gidansu ta shiga ko Sallama babu A tsakar gida ta tarar da matar gidan na zaune a Kan tabarma tana yiwa yarta kitso Mallam Ashiru Kuma na zaune akan kujera Yar tsugunno da buta agabansa da alama jira yake a Kira sallah yayi alwala. "Lafiya Kika shigo Mana ba Sallama " Dalla rufe min Baki Dan ba wajenki Nazo ba wajen wanan Dan iskan Mai dogon wuyan Nazo wato sabida munafinci shine kaje ka samu mijina kace Ina zalintar yaran da aka kawomin Ina ruwanka da rayuwata da ina ruwanka da abinda nakeyi shege munafiki tsinane kaji da matsalolin da ke gabanka Mana na me sai ka Shiga abinda Bai shafeka ba toh burinka ya cika ya ce na tafi gida wlh Allah kayi addua Kar munafirci da kayi ya zama sanadin mutuwar aurena Dan wlh idan Aurena ya mutu zakayi mamakin abinda Zan maka sai ka gwammace ma da baka sani ba" Daga Mallam Ashiru har matar tasa ba Wanda ya iya magana har ta juya ta tafi. "Sai Dana Gaya maka ba ruwanka Dan matar Nan wlh ba mutunci ne da ita ba kaf unguwar Nan ba Wanda take muamalla arziki dashi ba Mai Shiga harkarta sabida mugun halinta Amma gashi" "Dalla kirufemun Baki Taya zakice Kar na Gaya masa tana zalintar yaran daya kawo gidanan ke kanki anan kin Sha kukan tausayin yaran idan kika jiyo tana jibgarsu aikin kenan Haka zatayi ta zaginsu tana duka Akan me bazan Gaya masa ba sabida yayi wa tufkar hanci kafin ta Kai ga tayi kissan Kai yanzu Dana fada Masa bashine ya sani ya dau mataki ba" "Allah ya kyauta" Kawai matarsa ta iya cewa Shi kuwa yaja Tsaki Yana Dan Jin sanyi a Ransa Dan sosai yake tausayin Su Zahira idan Yana jiyo irin bugun da take musu Badai tab'a yiwa su Zahira magana bane. Murja kuwa tana fitowa daga gidan Shagon Jamilu ta tsaya sukayi ta zagin Juna tana rantsuwar sai taga bayansa tunda ya hadata da mijinta shima rantsuwa yake akan ba Abunda zata iya Masa Dan Kar yake kallonta idan takamarta uwarta matsafiya ce zata Masa wani Abu ta gwada ta gani wlh sai ya kawo karshenu shima ai ba Haka yake zaune ba" Murja kasa magana tayi sabida mamaki yanda Jamilun yasan Mahaifiyarta matsafiya ce ba ta iya Kara magana ba ta fice daga shagon tana cigaba da Shan alwashin sai ta ga karshen Jamilun. Tana Isa gida ta zub'e a tsakiyar palon nasu ta hau kuka. Mahaifiyarta Rabi ido ta zuba Mata Bata ce Mata komai ba. Sai da Murja ta gaji Dan kanta ta bud'e baki da zumar Mata magana Rabi ta daga Mata hannu fuskarta hade tana "Ba sai kin gayamin komai ba Naga duk abinda ya faru dazu kawai na dauko tukunya ta Dan na duba halin da kike ciki Naga Yana ta jibgarki ai sabida Dan iska ne shi bashida mutunci Bai ga cikinsa da kike d'auke dashi ba yayi ta dukanki ai ba jaka na aura masa ba Amma ba komai yyi na farko yayi na karshe shi da ganin Haske sai dai a lahira" Rabi tace Tana k'ok'arin mik'ewa Murja kuwa cikin tashin hankali ta dira gabanta tana "Mama Dan Allah karki Masa komai wlh inasan mijina Dan Allah karki Masa komai wlh ba laifinsa bane Mama karki makantarmin da miji Dan Allah Fusge kafarta Rabin tayi tana "wlh sai nayi Abunda nayi niyya Dan ya kaini bango na tsani mijin Nan naki wlh tunda Naga Yana da taurin Kai duk aikin Dana Yi akansa Baya ci na tsane shi na rasa Mai yasa Kika nace kina San zama dashi" "Nidai Ina San shi mama Dan Allah karki Masa komai nidai burina kimin aiki akansa Mai zafi yazo da kansa ya maidani gidansa a Kuma mallake min shi ya daina min taurin Kai duk abinda nace yayi shi zaiyi. Mutane biyu nakeso kimin maganinsu wani jamilu da wani Ashiru makocina su nake so ki Gama min dasu Dan su suka hada min munafirci Nan sai Kuma uwar mijina da kanwar mijina Umma inaso Suma ki kawomin karshensu duka sukamin yau har kasa suka bani naci" Tsaki Rabi tayi ta janyo bakin tukunyar tsafinta gabanta dake cike da wani irin ruwa tana "Daga Kan shegen mijinki zan fara Dan wlh Bai daki banza ba Take ta hau surkulle Tijjani ya bayyana saman ruwan Yana Kan vespansa Yana ta tuk'i Murja cikin tashin hankali ta hau ihu tana Mama Dan Allah karki Masa komai ki taimaka min wlh inasan mijina" Wani dogon Abu Rabin ta d'auko kamar kibiya zata caka a ruwan. Murja ta fizge kibiyar da k'arfi. Rabi kuwa ta girgiza tukunyar da Tijjani har lokacin yake bayyane Yana tuki. Take kuwa vespan nashi ya hau tangal tangal dashi har sai daya bige wani Mota dake gabanshi ya hantsulo daga Kan vespan. Ta daki ruwan Tijjani ya b'ace Murja ta hau zunduma ihu Ita kuwa ta daka Mata tsawa tana ban masa.komai ba na dai Masa gargadi ne kawai Dan wlh wanan shine na farko na Kuma karshe idan ya Kara tabaki wlh sai na raba shi da numfashinsa Sai wa kikace "Nidai nunamin shi nagani na tabbatar ba Abunda ya sameshi" "Ba Abinda ya sameshi dalla karki dameni wlh Kika batamin Rai Zan Masa Mai gabad'aya Tace a tsawace Tana Kara surkulle Sai ga Mallam Ashiru ya bayyana a cikin Massallaci a zaune tana daga kibiyar tsafin ta ya b'ace Duk abinda take Murja na kallo "Wanan sai anyi da gaske Dan Baya Wasa da Addu'a" Surkulle ta Kara Yi amadadin Jamilu ya bayyana sai Murja ce ta bayyana Hankali a tashe Rabi ta girgiza tukunyar tana "wanan Dan iskan ne Ina tab'a shi kanki zai dawo shima sai na shirya sosai Dan bahaka yake zaune ba Ita Kuma uwar mijinki da kanwar mijinki kibarni dasu sai kin koma.zaki dau fansar abinda suka Miki Wanan mijin sai nayi dgsk Zaki mallakeshi taurin Kai ne dashi" Sosai Murja ta ringa Jin dadin mallake Mata Tijjani da mahaifiyarta tace zatayi Tijjani kuwa Yana hanya zaije gadon Kaya wajen Naseer yana dab da Isa wajensa yaji Kan machine din na rawa Yana neman kwace Masa duk yanda yaso rik'e Kan machine din kasawa yayi har sai daya buge wani Mota dake gabansa ya hantsula. Sallati mutane Suka saki sabida duk an dauka Tijjani bazai Kai labari ba sabida ya daki motar gabansa sosai Ga mamakin.mutane Kuwa suka ga ya mike tsaye Yana karkad'a jikinsa Mai motar kansa da aka buge sai daya fito ganin Tijjani Bai ji ciwo ba yasa ya koma ciki yaja motarsa batare da ya tsaya sauraran hakurin da Tijjani ke bashi ba Dan ya fasa Masa glass din motarsa. Vespa din ya hau ya koma gida dan kayansa sun b'aci washegari da sassafe ya dau hanyar gidan Naseer sai daya fara tsayawa a tsohon gidan Naseer ya tambayi Inda suka koma da kwatance yaje har k'ofar gidan. Da Sallama ya Shiga gidan Nadeeya dake shara a tsakar gidan ce ta amsa ganin Tijjani ne yasa tayi wurgi da tsintsiya hannunta taje ta rungumeshi tana Masa oyoyo. Naseer dake kitchen fitowa yayi da kofin shayi a hannunsa. Duk da Yana Jin Haushin tijjanin Haka ya saki fuskarsa Ya Yi wa Tijjani iso har palon Hajara dake zaune da Safiyya a daki suna Shan shayi kamar a mafarki taji muryar Tijjani ta kuwa Mike da Sauri tayo waje Dan ta gaskata zarginta Wani irin hade Rai tayi ta fito daga d'akin a daidai lokacin. Da Tijjani ya zauna Akan tabarma dake shimfide a palon hannunsa cikin Na Nadeeya "Uban me kazo nema a gidanan Tijjani"? "Aaaa hajajju makatu Ashe kina ciki Rai kanga rai hajiya Umma" Tijjani yace Yana dariya dayaga yanda Hajara ta had'e Rai Hajara kuwa tace "ubanka kake rainawa Hankali Tijjani bani ba maza kafin na kirga uku tashi ka bar gidanan Dan na Gaya maka na yafeka banasan ganinka" Dariya Tijjani ya sakeyi Yana "Sai hakuri fa Umma nazama Dolenki ba ynda zakiyi inkika koreni Ina kikeso naje" "Kaci ubanka Tijjani ka dauka Wasa nake ma ko Ni da ka kora daga gidanka har da biyomu da kudin mota ka zabi Zama da matarka Tijjani akan dai kabi Umarnina baka darajani ba a matsayina na mahaifiyarka ka zabi tsinaniya da Bata tsoron Allah k'arfi da yaji ta zaneni Akan shegen bredi kana shigowa ta had'a makirci ka k'i yarda da maganata har sai daka koreni daga gidanka ka dauka Wasa nake Akan na yafe ka a cikin yarana Murja tazama uwarka tunda ita ka zaba akaina Tijjani idan baka San na Kara maka wani bakin ka tashi ka bar gidanan Dan wlh ganinka b'acin Rai yak'e Kara sani" "Umma Nima fa bansan makira na aura ba wlh sai Jiya nama koreta tana gidansu yanzu Haka Dan wlh bansan Haka take ba kinji na rantse Miki ban taba sanin munafika bace Mai fuska biyu ba sai Jiya da makocina da Mai shagon unguwarmu ya gayamin yanda take yiwa su Zahira bantaba sani ba sai Jiya shiyasa ma Nazo Dan na bawa Yaya Naseer hakuri kema na baki hakurin" Sai a lokacin Hajara ta Dan saki fuskarta tana "Kana nufin yanzu Haka tana gidansu"? "Eee tana can" "Saki nawa kayi Mata"? "Ban dai sakenta ban nace taje gida" "Zancen banza baka saketa ba zaka dawo da ita kenan"? "Aaa bazan dawo da ita ba hajiya Umma ai kina da kudin da Zaki aura min wata matar tunda gashi Nan kin raba Yaya Naseer da Aunty Naeema ya zama gwauro na k'arfi da yaji Nima ba sai na dawo gabanki kiyita kallonmu ba" "Gwara nayita kallonku a gabana da dai ku zauna da wadanan shegun matan naku" "Murja dai nasan shegiya ce tunda ta iya makirci ita aunty naeema fa mai ta Miki bakya santa"? "Bansani ba ubana zaka iya matse bakina in gaya maka Naga alamar ka ma Raina min hankali toh gwara da kazo ma auren Safiyya Nan da wata biyu masu zuwa jibi xaaje neman Aurenta can wajen baffaninku kasan yanzu Naseeru bashida ko sisi Haka Muke zaune Dan Haka ka kawo kudi mu fara rage wani Abun " Duk maganar da Tijjani da Hajara sukeyi Naseer Bai tofa musu Baki ba kansa a sunkuye yama tafi wata duniyar tunanin "Umma kema da abin dariya kike Ina Naga kudin da Zan siyawa Safiyya wani Abu ai ko sisi bana magani nima.murja ke ci damu a gidanan tunda Kika Mana abinda kikayi arzikinmu ya tafi muke fama wanan Dan canter da Kika Sani dashi har yanzu shine Dani maneji kawai nake Dan Haka ki San yanda zakiyi da ita" Dagowa da Naseer yayi ya kalleshi yasa ya kifta Masa Ido Hajara kua ta dage wlh su biyu su nemo kudin da zasu yiwa Safiyya kayan daki ko satane suyi ita ba ruwanta Tijjani dariya yayi Dan shi Sam Baya d'aukar ma maganar Hajaran da wani mahimmanci inzata matsa Masa ma saka takalminsa zaiyi yayi tafiyarsa Hakuri ya bawa Naseer game da abinda ya faru Naseer kuwa yace masa ba komai Suka hau Hira da Nadeeya da ta hau bashi labarin irin dukan da Murjan ke musu ba abinda ta rage a azabar da ta gana musu Inda ran Tijjani ya Kara b'aci sosai dayaga tab'a b'unan jikin Nadeeya wake da sabulun ma datace Ana Basu suci yafi balain kona Masa Rai Bai taba sanin muguntar Murja ya Kai har. Nan ba Bai taba sanin ma Haka halinta yake ba. Ita kuwa Hajara cewa take zatayi abinda yafi wanan Dan Haka ya saketa. Tijjani cewa yyu in ya koma gida zai aika Mata da saki daya Naseer kuwa yayi saurin girgiza Masa Kai Akan Kar ya saketa ya dai Mata fada sabida ita kanta Bata San ya rayuwa zata kasance Mata a gaba ba ko shi kansa Bai taba tunanin akwai ranar da wani Abu zai saka ya Kai yaransa wani wajen ba sai gashi kaddara ta sa ya Kai su Zahira gidan nasa. Tijjani sosai yaji tausayin Naseer Dan har ga Allah yasan dauriya kawai yake Yana cikin damuwa. Bai bar gidan ba sai wajen Sha daya na Rana tare suka fito da Naseer da Nadeeya. Hajara duk rokon data masa.akan ya Bata kudi dagewa yyi bashida ko sisi Naseer har mamakin Tijjanin ya ringa Yi Dan abinda Sam bazai iya ba kenan. Har wajen da Naseer ke aikin ginin Tijjani ya raka shi Suka samu inuwa suka zauna Naseer ya Dan Kara bashi labarin yanda Naeema tazo ta Debi yaran Da yanda Nadeeya ta dage bazata bisu ba da shi zata zauna Ajiyar zuciya Tijjani ya sauke Yana "can garin nasu ta Kai yaran"? "Wlh bansni ba Ina cikin tambayarta Umma ta shigo ta hau ce Mata karuwa k'arfi da yaji Umma ta hanani zaman lafiya ta hanani na samu nutsuwa inasan na kasance da iyalina ta hanani" "Kaine ka barta fa Yaya Naseer wlh Kai kabari take maka abinda ranta keso Ni bazan iya d'aukar abinda take ma ba Kai ma kagani ai Umma wani zubin zuma ce ita sai da wuta idan inasan Abu wlh sai dai tayi hakuri ta kyalleni ai ba Dole bane sai ka zauna da ita ka Kama Mata haya ka dawo da iyalinka gabanka idan tak'i ka siyar da gidan ka gudu ka barta Dole dai ta koma Calabar" "Mahaifiyarmu ce fa Tijjani idan na siyar da gidan na gudu a Ina zata zauna Naga basa shiri da matarka balle nace gidanka zata dawo bama Zan Sam kwanciyar hankali ba idan Naga tana garari" "Toh naji yanzu dai abinda zaayi kayi k'ok'ari ka nemi Inda Naeema take ka ringa zuwa kana dubasu Koda baka Kai musu komai ba yaranka su ringa ganinka Suma suna Jin dadin kaima sanin halin da suke ciki zai saka ka Dan samu kwanciyar hankali Sanan Nadeeya gaskiya gwara ka maidata wajen Naeema Sabida daga Kai har Naeema sai kunfi samun kwanciyar hankali bazai yiwu ka ringa fita kullum da ita sai kace namiji ba ke Nadeeya ki Bari Abbanki ya maidaki wajen ummanku shima Nan zai dawo idan an kwana biyu" Nok'ewa tayi Tijjani ya hau rarrashinta da Mata alkawarin siya Mata kaza da nama take ta hau washe baki tace ta yarda. Tijjani kuwa yacewa Naseer yayi kokari yasan Inda su Naeema suka koma Bauchin ne ko Kano ya maida Nadeeya ya Kuma ringa lek'a su akai akai. Naseer godiya ya Masa sosai Yana Jin dadin shawarar Tijjani Dan kwana biyun Nan sosai ya ji Yana k'ewan Naeema. Har kyautar kudi Tijjani ya bashi kafin ya tafin Naeema Washegari da safe na bazama nemowa yarana makaranta Mai Dan saukin kudi. Dan Zahira Naga ta tsayi Tama Zama budurwa tunda a yau na wayi gari Naga period ya zo mata boye boye ta ringa min duk da ciwon marra da take fama dashi Amma kasancewar waje daya muka kwana yasa nasan halin da take ciki. Zaunar da ita nayi na Bata ilimin Shi kansa haila banji kunyar ta ba na fada Mata komai da yanda zatayi wanka idan jinin ya d'auke har yanda zata tsaftace jikinta da Kuma Kara kame Kanta daga wasa da maza Daidai da kuzungu ma Ni na koya Mata yanda zata saka Dana saka tayi wanka ta wanke zanin data b'ata sai wani sunne Kai take Wai kunya ta takeji. Ni kuwa a Raina ma mamakine nake yaushe har nayi auren wai Yar cikina ta fara period kila kwanan Nan ma naga ana Sallama da ita Akan Ana Santa. Hakane yasa Dana karya na bazama nemo makaranta Dan so nake ma ta fara secondary daga jss 1 Wani karamin makaranta na samu Mai Dan saukin kudi. Sai dai ba secondary sch Wai sai dai ta zanna common entrance tunda baifi saura sati biyu a zanna ba samun secondary bazaiyi wahala ba indai ta zanna common entrance din. Sai Dana koma gida na tafi dasu Zahiran gabadayansu sabida tace zata musu gwaji sabida tasan ajin dazata saka su. Ba laifi yaran nawa na da Dan kokari duk da akwai slow learner's a cikinsu kasancewa na biya duk kudin da aka bukata har na uniform text books kawai Zan siya musu littattafai Kuma inadashi a shago Nadeeya ce kawai nace mata Zan kawota Bata Nan ne ta bani uniform dinta na tafi dashi yarana kuwa kamar Wasa Naga sun shige aji. Zahira Kuma ta wuce primary 5 Cikin farinciki na dawo gida Na dau littattafai dozen uku da fensura na bawa Isihu ya Kai musu da biscuit ya zama Dole na dauko Nadeeya Dan nasan Bai Zama lailai Naseer ya samu kudin sakata a makaranta ba. Safiyya Kwana biyu da maganar da Naseer yayi wa Saurayinta Umar akan ya tura neman aurenta. Yaje har garin calabar ya nemi kanin mahaifinsu ya gabatar da kansa dayake a shirye yake har Sadaki ya bayar Dan sosai kwallin da Safiyya ke sawa ya rikita shi yaji idan Bai Aureta ba bazai samu nutsuwa ba. Anan garin calabar yake zaune da matarsa Hafsa da yayansa. Matarsa macece Mai balain kishi masifafiya a unguwarsu kowa yasanta shegen bin Mallamai ne da ita dan wanann bashine Karo na farko da yake neman aure tana wargazawa.ba Har mallake Umar din tayi sai yanda tayi dashi. Karfin kwallin tsafine yyi tasiri a wajen Umar din ya kamu da San safiyya dayazo.kano.wajen abokinsa da Safiyya ke aiki a gidansa. Ita kuwa Tana ganin Yana da Dan canji yasa tana dawowa gida ta hargitsa d'akinsu har sai data samo kwallin daya shiga rububi ta rambada kwallin a idonta ta koma.da.sauri tana adduar Allah yasa Bai tafi ba Tana kuwa zuwa taci Karo dashi a bakin kofa yazo fitowa daga wanan hada.idon Umar ya kamu da San Safiyya. Kwana uku yayi a Calabar ya dawo ya sanar da Safiyya duk yanda sukayi da kanin mahaifinta Nan da wata Mai zuwa zaa daura aurensu. Safiyya sosai hankalinta ya tashi dataji wata guda kanin mahaifinta yasa Dan tasan Basu tanadi komai ba Hakane yasa Yana tafiya ta sako Hajara da maganar kayan dakin da za Mata harda kukanta. Akan Hajara tasan yanda zatayi da ita Dan Bata San kishiyar ta ta rainata tunda Umar yace a gida daya zasu zauna. Hakane yasa Hajara itama ta Sako Naseer agaba da maganar kayan dakin Har fargabar dawowa gida yake Dan shi Dan kudin da yake tarawa so yake idan ya tashi zuwa gidan Naeema ya Dan yiwa yaransa siyayya Kar ya tafi haka hannu na dukan cinya Dan ya je har gidan Alaramma ya tambayi matarsa ta Masa kwatance Gidan da Naeema sosai yaji dadi da Naeema ta zauna a kano bataje garinsu ba da yasan ma Tana garin Kano Nan kusa dashi da tuni ya nemeta. Hakane yasa ya Tara kudadensa da zumar yiwa su Zahira siyayya har Naeema ma sai ya siya Mata wani Abun. Rabin kudin kuwa Dama Waleed zai kashewa Dan yayi kewarsa sosai shima Gobe ya ke Shirin siyayyan daga wajen aiki ya shirya shi da Nadeeya su wuce Yana shigowa gida ko palon Bai Kai ga shiga ba Hajara ta tare shi da maganar kayan dakin Safiyya. Baya San wani Abu ya dameshi sabida farinciki da yake ciki Cewa Hajara kawai yayi toh zai nema suka shige shi da Nadeeya Ta kaiwa Nadeeya rankwashi akan Bata gaisheta ba ta hau bambamin Kar ya Kara fita da Nadeeya Bata San iskanci idan Nadeeya ta zauna ta tayata aikace aikacen gida laifine.? Naseer Bai dai tanka mata ba ya d'aura alwala ya tafi massallaci sallah Magriba Bai dawo cikin gidan ba sai da akayi sallah Isha ya tsaya a shago ya Dan Yi aski. Daga nan ya Kara sa Bakin titi yayi siyayar da duk zaiyi a wani shago Dan da safe yake San suje wajen Naeema. A shagon ya bar kayan akan gobe idan zai wuce zai dauka. Ya dawo gida ya tarar da Safiyya tasa Nadeeya ta wanke Mata Kaya tana ganin ya shigo ta hau zunduma kuka Sabida har Dan zaneta sai da Safiyya tayi. Naseer kuwa a fusace ya Shiga har d'akin Safiyya ta buya a bayan Hajara Naseer kuwa hakan Bai hana ya cire belt ya tsula Mata ba Hajara sai Masifa take akan me zai daketa Dan ta daki Nadeeya ai Nadeeya Bata da kunya ne. Haka ya fito daga d'akin Ransa a bace Ya rik'e hannun Nadeeya sukayi d'akinsa. Nadeeya kuwa ta hau ce Masa ya Kai ta wajen Umma Aunty dukanta takeyi. Murmushin Naseer yayi yana ",Kin fasa Zama a wajena"? Gyada Masa Kai tayi ya saki dariya Yana "daga aunty ta dakeki shine Zaki gudu ki barni" Kara gyada masa Kai tayi tana ita dai ya kaita wajen Umma. Naeema Sosai naji dadin makarantar da yarana ke zuwa da alamu Kuma suna Gane abinda ake koya musun Har islamiyya na Nemo musu idan suka dawo daga Boko sai su wuce sai karfe shidda suke dawowa. A yau ma bayan na rakasu har makaranta gida na dawo na gyara ko'ina Hassana Bata Nan ta tafi bikin Yan uwansu Nima sai anjima Zan je idan yarana sun dawo daga makaranta Dan yau ba islamiyya. Isihune keta markaden. Ni Kuma duk abinda aka zo siya Zan fita da kaina na bayar dayake na fitar da kofa ta cikin gida. Gidan na gyara na Dora ruwan tea Dan nida Isihu bamu karya ba Zobon Dana hada na kukula na zuba a kula na Kai bakin shago Dan Sana'ar zobon shima ya karbeni alhamdulillah duk da Ina siyar da lemon kwalba Duk Sana'ar Dana Dan gwada Allah Yana Sanyamin albarka Zuwa yanzu engine markaden nawa ma biyune Har kujeru masu Dan saukin kudi na saka Mana a gidan Isihu na mikawa shayinsa ya fita shago Ni Kuma na koma ciki na Shiga wanka Dan nasan kafin na fito shayin ya Dan hucce. A band'akin d'akina na Shiga wankan Ina fitowa Naga Naseer a zaune a Gefen gadona Waleed rik'e a hannunsa. Wani irin ihu na kwalla na koma band'akin aguje Dan gani nake gamo nayi idona yake ganemin Kamar Naseer na gani.............. *AYIMIN HAKURI BANJI DADI BANE JIYA SHIYASA AKA JINI SHIRU SHEKARANJIYA KUMA AIKI NAYI NAGAJI SHIYASA BANYI POSTING BA INA MASOYAN SADNAF TRUE LOVERS NGD DA KAUNARKU A GARENI KU DIN MASOYANA NE NA HAKIKA BAZAN MANTA ALHERIN KU A GARENI BA ALLAH YASAKA DA ALJANNATUL FIRDAUSI YA BAR ZUMUNCI* *WANAN SHAFIN NAKINE UMMA YAHAYA MUSA NGD DA KAUNARKI A GARENI MAI KAUNARKA SHI ZAIYI TUNANIN KYAUTATA MAKA ALLAH YA FARANTA MIKI NGD* *NAGA TA KAINA GRP 1 KUN NUNA MIN KAUNA KUMA NGD SOSAI ALLAH YA BAR ZUMUNCI* *SAKON GAISUWA GA DUK MASOYANA* *NAGA TA KAINA* *NA SADNAF*🌸🌸 ®️ *_PURE MOMENT OF LIFE WRITERS_* _{We Don't just entertain nd educate we also touch the heat of readers P.M.L}💪🏻_ *Free Novel* *Page 43* Muryar Nadeeya dake dariya tana Umma mune fa Yasa kirjina ya bar buguwa na sauke ajiyar zuciya na bud'e k'ofar Ina mamakin yanda suka Gane gidan. Nadeeya ma Sam ban lura da ita ba Ko kadan ban sa Rai da zuwan Naseer gidana kurkusa ba Ban kalli B'arin dayake ba na fito Nadeeya dake zaune dirshan a kasan d'akina na nufa kofin shayin Dana ajiye da zumar na Sha shine a hannunta, Gaisheni Nadeeya ta hau Yi Ni kuwa nace "Yar babanta Mai kikazo nema wajena acici daga zuwanki kin dau min shayi" Duk maganar da nake wayancewa nake Dan bana San hada ido da Naseer dake ta kallona kamar ya hadiyeni. Nadeeya uwar surutu take ta hau zuba tana surutu har da dukan da Safiyya ta Mata jiya ta sakata wanki Naseer kuwa yace mata "uwar surutu fita waje kiyi Wasa daga zuwanki kin hau surutu". Kofin shayin ta d'auka tayi waje. Ni kuwa nasan dalilin dayasa ya koreta Sai data fita na juyo Muka hada Ido Na saki murmushi na gaishe shi bai amsa ba ya Ajiye Waleed dake hannunsa ya nufo wajena Wai sai na tsinci kaina Kuma da Jin kunya Yara shidda Yana Abu kamar wani saurayi ko sababin Aure Ajiyar zuciya ya sauke a lokacin daya rungumeni Nima rungume shin nayi Dan nayi kewarsa har ga Allah muna San junanmu Umma ce ta dage sai mun rabu Mun dau tsawon lokaci a Haka sai danaga Yana neman wuce gona da iri na janye na koma gefe baa San Ransa ba ya koma bakin gadon ya zauna ya Kara d'aukar Waleed Yana "Ashe a garin Nan kike shine baki gayamin ba ai da tuni Nazo" "Ai bazan so kazo ba sabida Kar Umma tagane Ina Nan din Dan nasan Idan tasan Ina kano Kai kanka bazaka samu kwanciyar hankali ba Murmushi kawai yayi ya koma ya zauna ya hau karewa ko'ina kallo Yana "Naeema kinyi kokari duk da Baki tafi da komai ba shine har Kika siyi kayan gida Haka Ina yaran nawa suke ganinki ma yasa na manta ban tambayesu ba"? "Suna makaranta" Washe baki yayi cikin murna Yana "Allah ya saka da alheri ya Kara bud'i naeema hakika ke matar rufin asiri ce Umma bansan Mai yasa ta kasa ganin haka ba. Yanzu ma Naga engine dinki ma biyu anan har da shago a k'ofar gida Gyada Masa Kai nayi na hau bashi labarin komai har gidan da muke ciki yanda na siya da kudin gadona. Sosai ya ringa murna yanda Allah ya bud'amin yace "Ni kuwa ba irin wahalar da ban Sha ba Naeema Amma kudi yak'i samuwa aikin ginin ma da nakeyi wlh bai taka Kara ya karya ba Nima kudin da Kika ajiyemin naso Na juya Amma abin bai yu ba" Murmushi nayi Ina "Karka damu Allah na sane dake watarana sai Labari insha Allahu ka cigaba da gayawa Allah" Gyada min Kai yayi ya nuna min manyan ledojin daya zo dasu Akan na duba. Bud'ewa nayi na hau fito da kayan ciki Kayan sawa ya jiddowa Waleed su zahira ma Bai barsu a baya ba sai turmin zani da undies da ya siyomin nima. Dagowa nayi da zumar nayi magana ya girgiza min Kai akan Kar nace komai. Idan nace banyi murnar ganin mijina ba nayi karya Ido nake ta daukewa da naga Yana ta nunamin Yana bukatata Dan ban shirya tarben nasa ba haihuwa na Allah ne bana San nayi ciki yanzu kullum adduata ma Allah yasa haihuwa ta tsayamin kenan Duk yanda naso Bijirewa sai da na barshi ya samu nutsuwan Nayi sauri na fada bandaki nayi wanka na fito shi Kuma bacci ne yayi awon gaba dashi Hakane yasa na dau Waleed muka bar d'akin na rufo Masa Kofa Waje na fita na tarar da Nadeeya nata zuba ita da Isihu ga layin markade Nan suna jirana Dan shagon ma a cike yake da mutane masu siyan Abu Isihu na fama da mutane ahaka yake biyewa Nadeeya dake ta bud'e alewa tana Sha Tsawa na daka Mata Akan ta fito Dan Nadeeya dai ba yarinya bace sosai Engine na kunna nace ta hau markaden Dan wani zubin Tana Yi tsayine dai Bata dashi sosai Amma inta taka Abu shikenan Sai danaga ta markada biyu Naga Kuma ta markada yayi laushi. Na koma kitchen na fara had'a hadan girkin Rana Yanda dai na Saba Miya Mai yawa anan ma Haka nakeyi Dan nafi ganin aukin kayan miyan idan na siya da yawa ganin inada miyan yasa na Dora Mana shinkafa. Na fito wajen Isihu na bashi dari biyu ya siyomin naman Miya Wanda a lokacin Naman dari biyu Mai balain yawa ne Sosai na tsinci kaina cikin farincikin ganin Mijina da kuma iyalina guri daya yanda nakejin kadaici tunda na dawo gidanan Zuwan.naseer yau yasa naji na daina Jin kadaicin Inama mu dawwama Haka Astagafurullah a wanan lokacin har sai danace inama Umma ta mutu mu samu kwanciyar hankali Dan itace babbar matsalar mu. Naseer kuwa baccinsa yake Sha Mai dankaren dadi daya Dade baiyi irinsa ba. Dawowarsu Zahira daga makaranta da ihun murnar ganin Nadeeya yasa ya farka daga baccin daya daukeshi. Mik'ewa yayi zaune Yana murmushin Jin dadi Dan har ya fidda rai Kara kasancewa da iyalinsa waje daya rigarsa ya saka ya fara k'ok'arin fitowa. Su Zahira suka Fado dakin gabadaya suna ihun murna Nadeeya tace da abbansu Suka zo Naeema kuwa duk yanda taso hanasu Shiga d'akin ko sauraranta basuyi ba Suka fada d'akin Cikin murna duka Suka rungumeshi. Shima Naseer cikin tsananin farinciki ya rungumesu sai dayaga suna neman kayar dashi ya janye jikinsa ya zauna a gefen gadon hannunsa cikin Na Raheema dayaga har wani kib'a tayi sabida kwanciyar hankali Binsu ya ringayi da kallo cikin tsananin farinciki ganin yanda Suka canja gabadaya sunyi fes dasu ba Kamar lokacin da suke can wajensa ba Zahira har canjawa tayi a idonsa ta zama budurwa Dan ita Bata Yi haukan da taga kanenta nayi ba inama ya dauwaama Haka daga shi sai iyalinsa da ba Wanda zai Kai shi Jin dadi duk Wanda ya tsinci kansa da karayar arziki irin nasa mutum.kan dauwaama bashida wani buri daya wuce kudin su dawo wajensa kota halin k'ak'a ne Amma shi karayar arzikinsa Bai dameshi Kamar yanda rabuwa da iyalinsa ya dameshi ba. Da tarin kudi gwara ya dauwama da iyalinsa cikin rufin asiri. Sai da Naeema ta shigo d'akin ta koresu kafin Naseer ya samu ya Shiga wankan ya dauro alwala A palon gidan yajasu Sallahr azahar. Suna iddarwa Zahira taje kitchen ta d'auko musu abinci har da zobon da Naeema ta had'a. A faranti daya sukaci abincin gabadaya duka fuskarsu dauke da farinciki Naseer da Naeema ji suke.inama su dauwaama Haka ba abinda zai sake rabasu. Su kansu kasancewarsu waje daya yasa yaran cikin tsananin farinciki sai cewa suka Abba Dan Allah ka zauna anan Kar.ka Kara komawa. Yinin bikin da Naeema Bata je ba kenan Bayan tafiyar yaran islamiyya har da Nadeeya Hira Naseer da Naeema suka.hau yi Inda Naseer Duk yake Bata labarin halin da yake ciki da Hajara da yanda ta matsa Masa yayi wa Safiyya kayan daki. Sosai nayi murnar da auren da Safiyya zatayi Dan gani nake Rabin matsalar mu ya k'au sai dai Yar muryar da Naseer kemin akan idan inada kudi na bashi ya Basu zai bani idan ya samu yasa na hade girar sama da kasa nace Masa banidashi Naga duk halin da muke ciki su suka jawo Mana ko Naman jikina nake yanka musu ba burgesu nake ba Dan Haka ko sisina bazan iya bayarwa ba Naseer Bai ja zancen ba dayaga yanda na hade Rai muka cigaba da Hira da aka fara kawo markaden yamma kuwa shi yaringayi Ni kuwa na Dora Mana girkin dare Dan inaso ya cika cikinsa kafin ya tafin nasan yanzu tunda yasan gida zai na zuwa ganinmu akai akai hankalina yanzu a kwance yake. Sai dai me a lokacin da muka ci abincin daren da nayi tunanin Naseer zai tafi k'in tafiya yayi yacemin kwana zaiyi na Bari ya Dan samu kwanciyar hankali na kwana biyu Dan idan ya koma gidan ma yasan bashida kwanciya hankali Umma Sako shi zatayi a gaba. Ni kuwa.dage Masa nayi ya tafi Dan idan Bai tafi ba Umma zata xargi Yana wajenmu kafin kaceme zata gano Inda muke. Ba yanda banyi ya tafi ba yak'i dayaga ma na dameshi sai ya shige daki ya barni dayake a tsakar gida muke Zaune. Ba yanda na iya ahaka na hakura yarana Suka kwana a d'akin da hassana ke kwana nikuma da Naseer da Waleed muka kwana a nawa d'akin Namiji a gida ma wani abune Dan a ranar ko juyi banyi ba har gari ya waye Ina rungume a kirjin mijina. Har makara nayi Dan sai wajen bakwai da rabi na farka. Agurguje nayi Sallah na fito sabida Na Dora musu abinci su karya su tafi makaranta. Sai dai Ina fitowa ma na tarar suna cin abincin sun ma saka uniform sosai naji dadi Dan yanzu Zahira duk ita kemin komai tama Riga da tasan duk abinda nakeyi da safe Inda yarinya ta Kara kwanta Min arai fiye da sauran kanennta kenan. Nadeeya ce kawai Bata saka uniform ba hakane yasa na Shiga na koma d'akina na dauko uniform dinta na Bata Dan Dama an bani uniform dinta littattafai ne ban siya Mata ba Sai da suka shirya tafiya na koma daki Naga har lokacin bacci Naseer keyi Bai tashi ba Tashinsa nayi na fito na raka su har makaranta na karbawa Nadeeya text books Dan na Bata littattafai da pencil Primary 4 aka Kai Nadeeya da aka Mata gwaji. Sai da duk suka Shiga aji na dawo. A takaice tun Ina damun Naseer akan ya koma sabida Kar Umma ta gano muna tare k'i yayi akan Dole na hakura ya Mana sati daya sati dayan da naji inama mu dawwama Haka batare da ya Kara Mana nisa ba inama Umma ta Sanya Mana albarka Naseer ya ringa Zama a shagon k'ofar gida. Ni Kuma na ringa markade Ina kananun Sanaa a gida da nakeyi yanzu kudi na shigomin da nasan sai munfi kowa farinciki tunda munfi karfin ci da Sha alhamdulillah Shima Kamar bazai tafi ba sai Dana karfafa Masa gwiwa akan ya tafi idan yaje yace Abuja yaje neman kudi na Kuma bashi Yan kudaden dai da Bai taka Kara ya karya ba. Dan sati dayan dayayi har Dan murmurewa yayi. Sai daya hau taxi na dawo gida duk jikina ba dadi Dan nasan yau sai dai na rayya Daren dadin ma.danaji yace zai na zuwa ganinmu kullum idan Bai zo bama kullum xai na zuwa akai akai Safiyya Sosai ta Sako Hajara a gaba da kananan koke koke Akan Aurenta na matsowa Anki a Mata kayan daki Hajara kuwa sosai itama ta damu da kukann da Safiyya keyi hakane yasa ta Sha alwashin tarar Naseer a Daren da Bai kwana a gida ba Akan idan ya dawo yasan duk Inda zai nemi kudi ayiwa Safiyya kayan daki. Sai dai Haka Suka karaci zaman jiran dawowarsa Bai dawo ba daga shi har Nadeeya. Washegari ma Haka hakane yasa hankalin Hajara ya fara tashi tana tunanin Inda Naseer yaje shi da Nadeeya Safiyya kuwa kuka ta saka Akan Naseer guduwa yayi ita.kam ta Shiga uku ta lalace asirinta zai tonu. Fadar hakan da Saffiya tayi tana kuka wiwi yasa hankalin Hajara Kara tashi tana "Yanzu sai Naseer ya gudu sabida nace ya Miki kayan daki Safiyya ko dai wajen Naeema yaje ba guduwa yayi ba" "Guduwa yayi Umma Dan idan Kika tuna Bai tashi guduwa ba sai daya ga kin Kara Masa maganar kayan dakin nidai Umma wlh kisan duk yanda zakiyi Dani Aurena nata matsowa ace ko cokali Baki siyamin ba karki manta fa kishiya ce Dani tayaya ma zanyi aure batare da kayan daki ba da kunya na tareshi nace Masa an kasa.min.kayan d'aki" Safiyya tace tana Kara fashewa da kuka "Ki bar kuka Safiyya nace ko wajen kanin mahaifinku zamuje muga ko zamu samu wani Abu" Wani irin harara Safiyya ta d'auke Hajara dashi tana"kin manta katifa kawai ya siyawa Lami Taya zanje na same shi wlh bazan je wajensa ba" "Toh yanzu ya zamuyi Safiyya kinsan dai banida ko sisi gashi Da Naseer na dogara shi Kuma kince guduwa yayi Tijjani kuwa Dama ba mutunci ne dashi ba kinsani Dan Dana Masa magana anan dariya ya ringamin ya maidani mahaukaciya Haka ma.ya tafi ko sisi Bai bani ba Naseer ne dai zai iya kukutawa ya Miki kayan gashi yanzu wajen kwana biyu kenan bai dawo gida ba" "Yanzu ya zamuyi toh Safiyya " "Nidai a siyar da gidanan Umma a fitar Dani kunya idan ba Haka ba kinsan ba Inda zamu samu kudin da zaa siya min kayan daki" Gwallo Ido Hajara tayi tana "A siyar da gidan Naseer Kuma Safiyya Taya Zaa siyar da gidan Naseer kawai Dan a Miki kayan daki karki manta fa wanan gidan kadai ya rage mishi muma ba Dan gidan Nan ba da yanzu muna titi muna gararamba" "Toh idan ba a siyar ba Umma da uwar me za'a min kayan dakin tambayar ki nake idan baa siyar ba da uwar me zaamin kayan d'akin"? Safiyya tace a tsawace "Naga duk masifar Nan ke Kika janyo mana muna zaman zaman mu Kika k'ona dukiyar Yaya Naseer ya talauce muka Shiga uku yanzu da baki Kona dukiyar sa ba ai da Yanzu Bai gudu akan kin Masa maganar yamin kayan daki ba Dan Haka wlh gidanan zaa siyar kawai ayimin kayan d'aki" Kamar Mai tsoron Safiyya Hajara tace "toh idan mun siyar da gidan Nan Safiyya a Ina zamu koma da.zama nida Naseer din tunda nasan sabida zakije gidan miji kike cewa mu siyar da gidan nidai nasan wanan gidan yanzu shine rufin asirina Dana Naseer tunda Naeema ta Kara gaba da yaranta" Sai a lokacin ta sasauta Fuskarta tana "Umma ai wani karamin gidan zamu siya idan muka siyar da Wanan Kinga gidanan babba ne zaa siyi gidan da daraja a ciki zamu siyi karamin gida ki siyamin kayan daki sauran kudin Kuma kija jari kafin ki ankara kema kin zama hajiya har macca ma sai kije ki Naseer dawowa yayi idan yaganki da kudi bazai yi magana ba kinsan shi ba Kamar Yaya Tijjani ba" Washe baki Hajara tayi Dan maganganun Safiyya sun shigeta ta Kuma Yi naam da shawarar ta "Toh wa kike ganin xai siyi gidan" "Ki bar komai a hannuna" Safiyya tace cikin murna a ranar ta shiga d'akin Naseer ta birkita Kaya har sai data samo takardun gidan Ta fito sai murna take da zaa samu kudin da zata siyi kayan daki ya zama Dole ma ta koyawa kishiyarta hankali Dan Kaya zatayi na fitar hankali da kishiyar ta zata shak'a sosai take Jin dadi da had'asu waje dayan da zaayi tasan kishiyarta sai ta kwashi kashinta a hannu Dan sai ta bar Mata gidan ta mallake shi ita kadai. Washegari da sassafe ta bazama ta Nemo dilalai a cikin kwana biyu aka samu mutane masu San gidan har su uku. Dan gidan Naseer din babba ne kuma a fuska Mai kyau Safiyya Bata yarda anyi cinikn gidan Agaban Hajara ba ita ta saka hannu akayi komai da ita Akan Dole ta Nemo wasu Suka Mata shaidan ta siyar yanzu ba mallakinsu bane ta Basu kudi Suma masu siyan gidan suka bada kudi da shaidunsu suka karbi takardun gida. Sai da Safiyya ta zabtare kudin wajen rabi ta b'oye. Ta Kai sauran kudin gaban Hajara. Hajara dai tana San magana kudin gidan yayi araha da yawa Amma babu yanda zatayi da Safiyya datayi Kane Kane. Safiyya ita ta raba kudin gida biyu ta dauki iya kudin da zai isheta ta siyi kayan daki da komai Ta bawa Hajara sauran Hajara kuwa sai a lokacin tace "Safiyya kudin Nan bazai Isa mu siyi wani gidan ba ballantana har na samu na jari" Karki damu Ni Zan Nemo miki gidan da kaina zaa samu Jiki a sanyaye Hajara tace "toh yaushe masu gidan suka ce mu tashi nidai Safiyya ba Haka naso ba wlh gidanan babba ne wayanda Suka siyi gidanan sun cucemu" "Notice din wata daya suka bamu karki damu kafin lokacin na samo Mana wani gidan Ahaka ta lallab'a Hajara tayi shiru. Kafin sati daya da tafiyar Naseer har ta Gama siyan kayan daki na gani na fad'a Iya Nan Bai isheta ba sai data tab'a kudin da ta bawa Hajara data Masa kyakyawan b'uya shirye shiryen bikinta kawai daya rage sati biyu take tana facaka da kudi har wani karamin lefe tayiwa kanta Hajara idan tana San tayi Magana sai ta hayayyako akan Dole take shiru. A ranar da Naseer ya koma kuwa sosai Hajara ta tsorata Dan Bata kawo zai dawo kurkusa ba ta d'auka dagaske guduwa yayi. Safiyya kuwa kwantar Mata da hankali tayi akan Kar ta sake ta gayawa Naseer sun siyar da gidan. Sai idan sunzo tashi shima idan yasani ta haharde Rai ta Masa fin k'arfi tuni zai mata biyaya. Naseer kuwa sosai yayi mamaki da Hajara Bata tambayeshi Inda yaje ba sai wani susune Kai take. Shi kuwa dadi yaji yace Mata Abuja yaje neman kudin da zaiyiwa Safiyya kayan daki toh shima yaje Bai samu ba sai Yan canji ya samo tayi hakuri zai cigaba da nema Kai a sunkuye Hajara tace Kar ya damu ta siyawa Safiyya komai. Wani irin dadi Naseer Yaji yace Mata Ina ta samu kudin Tace Kar ya damu zai sani a hankali Naseer kuwa har a Ransa yaji dadin ganin Hajara ta Dan sauya Masa Ashe har ta samu kudin kayan d'akin. A ranar zuciyarsa fes batare da wani fargaba ba ya kwana da tunanin iyalinsa Washegari da safe yaje gidan Naeema yake Gaya Mata duk yanda sukayi da Hajara Nidai sosai nayi mamakin Inda Umma ta samu kudin. Haka kawai jikina ke gayamin akwai dai ta hanyar da aka samu kudin bandai cewa Naseer komai ba danaga yanda yake murna Yana cemin ko fada Umma Bata Masa ba kila Allah ya fara karbar adduarsa. Bandai ce komai ba a ranar ya wunar Mana daddare na raka shi ya tafi Yawan zuwa da Naseer keyi gidan Naeema yasa Sam bai San halin da ake ciki ba dan Yan canjin daya samu ma shinkafar da Hajara zatayi taron biki ya siyo Mata har da yiwa Hajara dinki kala biyu wai duk Dan ya faranta Mata. Hajara kuwa damun Safiyya ta ringa Yi da zancen gidan data ce zata siya musu Dan lokacin barin gidansu nata karatowa Amma Safiyya haka ta ringa tsara Hajara tana d'auke mata hankali daga zancen Dan tabi ta Kan kudin tuni burinta kawai a daura auren Ta bar gidan Hajara da Naseer su San nayi tunda ita dai ta samu cikar burinta. A Haka aka fara bikin Safiyya Tijjani ma yazo bikin da Murja Dan tuni sukayi katon aiki Akan Tijjani har sai daya je har gidansu Murjan ya dawo da ita. Duk da kamun da suka Masa ba sosai ya Kama shi ba Hajara kuwa irin gayyar da Safiyya tayi yasa hankalinta ya d'auke daga zancen gidan Bata Kuma bi takan Murja da suke Yar kallon kallo ba Sai da aka zo tafiya da Safiyya washegarin daurin Aure. Hankalin Hajara ya dawo jikinta daki ta ja Safiyya ta hau Mata maganar gidan ita kuwa Safiyya ta Mata karyar ta siyi gidan anjima wani zai zo.ya kaita taga gidan Hajara badan ta yarda ba tana ji tana gani aka tafi da Safiyya mutane Suka watse ya rage saura ita daya da Naseer. A lokacin saura sati daya notice din da aka basu ya Kare. Kamar tayi kuka ta Shiga d'akin Naseer Kuma ya Shiga har d'akin ta daya hada musu abin karyawa ya Kai Mata Yana "Umma lafiya kuwa Yana ga kamar bakida lafiya"? Hajara na k'ok'arin Magana Wani yaro ya doka Sallama Wai Mai gidan Yana Sallama da Safiyya Gaban Hajara ne ya yanke ya Fadi. Naseer Kuma cikin mamaki yace "Mai gidan kuma waye Haka" Yayi waje Dan yaga Mai sallamar...... *NAGA TA KAINA* *NA SADNAF*🌸🌸 ®️ *_PURE MOMENT OF LIFE WRITERS_* _{We Don't just entertain nd educate we also touch the heat of readers P.M.L}💪🏻_ *Free Novel* *Page 43* Muryar Nadeeya dake dariya tana Umma mune fa Yasa kirjina ya bar buguwa na sauke ajiyar zuciya na bud'e k'ofar Ina mamakin yanda suka Gane gidan. Nadeeya ma Sam ban lura da ita ba Ko kadan ban sa Rai da zuwan Naseer gidana kurkusa ba Ban kalli B'arin dayake ba na fito Nadeeya dake zaune dirshan a kasan d'akina na nufa kofin shayin Dana ajiye da zumar na Sha shine a hannunta, Gaisheni Nadeeya ta hau Yi Ni kuwa nace "Yar babanta Mai kikazo nema wajena acici daga zuwanki kin dau min shayi" Duk maganar da nake wayancewa nake Dan bana San hada ido da Naseer dake ta kallona kamar ya hadiyeni. Nadeeya uwar surutu take ta hau zuba tana surutu har da dukan da Safiyya ta Mata jiya ta sakata wanki Naseer kuwa yace mata "uwar surutu fita waje kiyi Wasa daga zuwanki kin hau surutu". Kofin shayin ta d'auka tayi waje. Ni kuwa nasan dalilin dayasa ya koreta Sai data fita na juyo Muka hada Ido Na saki murmushi na gaishe shi bai amsa ba ya Ajiye Waleed dake hannunsa ya nufo wajena Wai sai na tsinci kaina Kuma da Jin kunya Yara shidda Yana Abu kamar wani saurayi ko sababin Aure Ajiyar zuciya ya sauke a lokacin daya rungumeni Nima rungume shin nayi Dan nayi kewarsa har ga Allah muna San junanmu Umma ce ta dage sai mun rabu Mun dau tsawon lokaci a Haka sai danaga Yana neman wuce gona da iri na janye na koma gefe baa San Ransa ba ya koma bakin gadon ya zauna ya Kara d'aukar Waleed Yana "Ashe a garin Nan kike shine baki gayamin ba ai da tuni Nazo" "Ai bazan so kazo ba sabida Kar Umma tagane Ina Nan din Dan nasan Idan tasan Ina kano Kai kanka bazaka samu kwanciyar hankali ba Murmushi kawai yayi ya koma ya zauna ya hau karewa ko'ina kallo Yana "Naeema kinyi kokari duk da Baki tafi da komai ba shine har Kika siyi kayan gida Haka Ina yaran nawa suke ganinki ma yasa na manta ban tambayesu ba"? "Suna makaranta" Washe baki yayi cikin murna Yana "Allah ya saka da alheri ya Kara bud'i naeema hakika ke matar rufin asiri ce Umma bansan Mai yasa ta kasa ganin haka ba. Yanzu ma Naga engine dinki ma biyu anan har da shago a k'ofar gida Gyada Masa Kai nayi na hau bashi labarin komai har gidan da muke ciki yanda na siya da kudin gadona. Sosai ya ringa murna yanda Allah ya bud'amin yace "Ni kuwa ba irin wahalar da ban Sha ba Naeema Amma kudi yak'i samuwa aikin ginin ma da nakeyi wlh bai taka Kara ya karya ba Nima kudin da Kika ajiyemin naso Na juya Amma abin bai yu ba" Murmushi nayi Ina "Karka damu Allah na sane dake watarana sai Labari insha Allahu ka cigaba da gayawa Allah" Gyada min Kai yayi ya nuna min manyan ledojin daya zo dasu Akan na duba. Bud'ewa nayi na hau fito da kayan ciki Kayan sawa ya jiddowa Waleed su zahira ma Bai barsu a baya ba sai turmin zani da undies da ya siyomin nima. Dagowa nayi da zumar nayi magana ya girgiza min Kai akan Kar nace komai. Idan nace banyi murnar ganin mijina ba nayi karya Ido nake ta daukewa da naga Yana ta nunamin Yana bukatata Dan ban shirya tarben nasa ba haihuwa na Allah ne bana San nayi ciki yanzu kullum adduata ma Allah yasa haihuwa ta tsayamin kenan Duk yanda naso Bijirewa sai da na barshi ya samu nutsuwan Nayi sauri na fada bandaki nayi wanka na fito shi Kuma bacci ne yayi awon gaba dashi Hakane yasa na dau Waleed muka bar d'akin na rufo Masa Kofa Waje na fita na tarar da Nadeeya nata zuba ita da Isihu ga layin markade Nan suna jirana Dan shagon ma a cike yake da mutane masu siyan Abu Isihu na fama da mutane ahaka yake biyewa Nadeeya dake ta bud'e alewa tana Sha Tsawa na daka Mata Akan ta fito Dan Nadeeya dai ba yarinya bace sosai Engine na kunna nace ta hau markaden Dan wani zubin Tana Yi tsayine dai Bata dashi sosai Amma inta taka Abu shikenan Sai danaga ta markada biyu Naga Kuma ta markada yayi laushi. Na koma kitchen na fara had'a hadan girkin Rana Yanda dai na Saba Miya Mai yawa anan ma Haka nakeyi Dan nafi ganin aukin kayan miyan idan na siya da yawa ganin inada miyan yasa na Dora Mana shinkafa. Na fito wajen Isihu na bashi dari biyu ya siyomin naman Miya Wanda a lokacin Naman dari biyu Mai balain yawa ne Sosai na tsinci kaina cikin farincikin ganin Mijina da kuma iyalina guri daya yanda nakejin kadaici tunda na dawo gidanan Zuwan.naseer yau yasa naji na daina Jin kadaicin Inama mu dawwama Haka Astagafurullah a wanan lokacin har sai danace inama Umma ta mutu mu samu kwanciyar hankali Dan itace babbar matsalar mu. Naseer kuwa baccinsa yake Sha Mai dankaren dadi daya Dade baiyi irinsa ba. Dawowarsu Zahira daga makaranta da ihun murnar ganin Nadeeya yasa ya farka daga baccin daya daukeshi. Mik'ewa yayi zaune Yana murmushin Jin dadi Dan har ya fidda rai Kara kasancewa da iyalinsa waje daya rigarsa ya saka ya fara k'ok'arin fitowa. Su Zahira suka Fado dakin gabadaya suna ihun murna Nadeeya tace da abbansu Suka zo Naeema kuwa duk yanda taso hanasu Shiga d'akin ko sauraranta basuyi ba Suka fada d'akin Cikin murna duka Suka rungumeshi. Shima Naseer cikin tsananin farinciki ya rungumesu sai dayaga suna neman kayar dashi ya janye jikinsa ya zauna a gefen gadon hannunsa cikin Na Raheema dayaga har wani kib'a tayi sabida kwanciyar hankali Binsu ya ringayi da kallo cikin tsananin farinciki ganin yanda Suka canja gabadaya sunyi fes dasu ba Kamar lokacin da suke can wajensa ba Zahira har canjawa tayi a idonsa ta zama budurwa Dan ita Bata Yi haukan da taga kanenta nayi ba inama ya dauwaama Haka daga shi sai iyalinsa da ba Wanda zai Kai shi Jin dadi duk Wanda ya tsinci kansa da karayar arziki irin nasa mutum.kan dauwaama bashida wani buri daya wuce kudin su dawo wajensa kota halin k'ak'a ne Amma shi karayar arzikinsa Bai dameshi Kamar yanda rabuwa da iyalinsa ya dameshi ba. Da tarin kudi gwara ya dauwama da iyalinsa cikin rufin asiri. Sai da Naeema ta shigo d'akin ta koresu kafin Naseer ya samu ya Shiga wankan ya dauro alwala A palon gidan yajasu Sallahr azahar. Suna iddarwa Zahira taje kitchen ta d'auko musu abinci har da zobon da Naeema ta had'a. A faranti daya sukaci abincin gabadaya duka fuskarsu dauke da farinciki Naseer da Naeema ji suke.inama su dauwaama Haka ba abinda zai sake rabasu. Su kansu kasancewarsu waje daya yasa yaran cikin tsananin farinciki sai cewa suka Abba Dan Allah ka zauna anan Kar.ka Kara komawa. Yinin bikin da Naeema Bata je ba kenan Bayan tafiyar yaran islamiyya har da Nadeeya Hira Naseer da Naeema suka.hau yi Inda Naseer Duk yake Bata labarin halin da yake ciki da Hajara da yanda ta matsa Masa yayi wa Safiyya kayan daki. Sosai nayi murnar da auren da Safiyya zatayi Dan gani nake Rabin matsalar mu ya k'au sai dai Yar muryar da Naseer kemin akan idan inada kudi na bashi ya Basu zai bani idan ya samu yasa na hade girar sama da kasa nace Masa banidashi Naga duk halin da muke ciki su suka jawo Mana ko Naman jikina nake yanka musu ba burgesu nake ba Dan Haka ko sisina bazan iya bayarwa ba Naseer Bai ja zancen ba dayaga yanda na hade Rai muka cigaba da Hira da aka fara kawo markaden yamma kuwa shi yaringayi Ni kuwa na Dora Mana girkin dare Dan inaso ya cika cikinsa kafin ya tafin nasan yanzu tunda yasan gida zai na zuwa ganinmu akai akai hankalina yanzu a kwance yake. Sai dai me a lokacin da muka ci abincin daren da nayi tunanin Naseer zai tafi k'in tafiya yayi yacemin kwana zaiyi na Bari ya Dan samu kwanciyar hankali na kwana biyu Dan idan ya koma gidan ma yasan bashida kwanciya hankali Umma Sako shi zatayi a gaba. Ni kuwa.dage Masa nayi ya tafi Dan idan Bai tafi ba Umma zata xargi Yana wajenmu kafin kaceme zata gano Inda muke. Ba yanda banyi ya tafi ba yak'i dayaga ma na dameshi sai ya shige daki ya barni dayake a tsakar gida muke Zaune. Ba yanda na iya ahaka na hakura yarana Suka kwana a d'akin da hassana ke kwana nikuma da Naseer da Waleed muka kwana a nawa d'akin Namiji a gida ma wani abune Dan a ranar ko juyi banyi ba har gari ya waye Ina rungume a kirjin mijina. Har makara nayi Dan sai wajen bakwai da rabi na farka. Agurguje nayi Sallah na fito sabida Na Dora musu abinci su karya su tafi makaranta. Sai dai Ina fitowa ma na tarar suna cin abincin sun ma saka uniform sosai naji dadi Dan yanzu Zahira duk ita kemin komai tama Riga da tasan duk abinda nakeyi da safe Inda yarinya ta Kara kwanta Min arai fiye da sauran kanennta kenan. Nadeeya ce kawai Bata saka uniform ba hakane yasa na Shiga na koma d'akina na dauko uniform dinta na Bata Dan Dama an bani uniform dinta littattafai ne ban siya Mata ba Sai da suka shirya tafiya na koma daki Naga har lokacin bacci Naseer keyi Bai tashi ba Tashinsa nayi na fito na raka su har makaranta na karbawa Nadeeya text books Dan na Bata littattafai da pencil Primary 4 aka Kai Nadeeya da aka Mata gwaji. Sai da duk suka Shiga aji na dawo. A takaice tun Ina damun Naseer akan ya koma sabida Kar Umma ta gano muna tare k'i yayi akan Dole na hakura ya Mana sati daya sati dayan da naji inama mu dawwama Haka batare da ya Kara Mana nisa ba inama Umma ta Sanya Mana albarka Naseer ya ringa Zama a shagon k'ofar gida. Ni Kuma na ringa markade Ina kananun Sanaa a gida da nakeyi yanzu kudi na shigomin da nasan sai munfi kowa farinciki tunda munfi karfin ci da Sha alhamdulillah Shima Kamar bazai tafi ba sai Dana karfafa Masa gwiwa akan ya tafi idan yaje yace Abuja yaje neman kudi na Kuma bashi Yan kudaden dai da Bai taka Kara ya karya ba. Dan sati dayan dayayi har Dan murmurewa yayi. Sai daya hau taxi na dawo gida duk jikina ba dadi Dan nasan yau sai dai na rayya Daren dadin ma.danaji yace zai na zuwa ganinmu kullum idan Bai zo bama kullum xai na zuwa akai akai Safiyya Sosai ta Sako Hajara a gaba da kananan koke koke Akan Aurenta na matsowa Anki a Mata kayan daki Hajara kuwa sosai itama ta damu da kukann da Safiyya keyi hakane yasa ta Sha alwashin tarar Naseer a Daren da Bai kwana a gida ba Akan idan ya dawo yasan duk Inda zai nemi kudi ayiwa Safiyya kayan daki. Sai dai Haka Suka karaci zaman jiran dawowarsa Bai dawo ba daga shi har Nadeeya. Washegari ma Haka hakane yasa hankalin Hajara ya fara tashi tana tunanin Inda Naseer yaje shi da Nadeeya Safiyya kuwa kuka ta saka Akan Naseer guduwa yayi ita.kam ta Shiga uku ta lalace asirinta zai tonu. Fadar hakan da Saffiya tayi tana kuka wiwi yasa hankalin Hajara Kara tashi tana "Yanzu sai Naseer ya gudu sabida nace ya Miki kayan daki Safiyya ko dai wajen Naeema yaje ba guduwa yayi ba" "Guduwa yayi Umma Dan idan Kika tuna Bai tashi guduwa ba sai daya ga kin Kara Masa maganar kayan dakin nidai Umma wlh kisan duk yanda zakiyi Dani Aurena nata matsowa ace ko cokali Baki siyamin ba karki manta fa kishiya ce Dani tayaya ma zanyi aure batare da kayan daki ba da kunya na tareshi nace Masa an kasa.min.kayan d'aki" Safiyya tace tana Kara fashewa da kuka "Ki bar kuka Safiyya nace ko wajen kanin mahaifinku zamuje muga ko zamu samu wani Abu" Wani irin harara Safiyya ta d'auke Hajara dashi tana"kin manta katifa kawai ya siyawa Lami Taya zanje na same shi wlh bazan je wajensa ba" "Toh yanzu ya zamuyi Safiyya kinsan dai banida ko sisi gashi Da Naseer na dogara shi Kuma kince guduwa yayi Tijjani kuwa Dama ba mutunci ne dashi ba kinsani Dan Dana Masa magana anan dariya ya ringamin ya maidani mahaukaciya Haka ma.ya tafi ko sisi Bai bani ba Naseer ne dai zai iya kukutawa ya Miki kayan gashi yanzu wajen kwana biyu kenan bai dawo gida ba" "Yanzu ya zamuyi toh Safiyya " "Nidai a siyar da gidanan Umma a fitar Dani kunya idan ba Haka ba kinsan ba Inda zamu samu kudin da zaa siya min kayan daki" Gwallo Ido Hajara tayi tana "A siyar da gidan Naseer Kuma Safiyya Taya Zaa siyar da gidan Naseer kawai Dan a Miki kayan daki karki manta fa wanan gidan kadai ya rage mishi muma ba Dan gidan Nan ba da yanzu muna titi muna gararamba" "Toh idan ba a siyar ba Umma da uwar me za'a min kayan dakin tambayar ki nake idan baa siyar ba da uwar me zaamin kayan d'akin"? Safiyya tace a tsawace "Naga duk masifar Nan ke Kika janyo mana muna zaman zaman mu Kika k'ona dukiyar Yaya Naseer ya talauce muka Shiga uku yanzu da baki Kona dukiyar sa ba ai da Yanzu Bai gudu akan kin Masa maganar yamin kayan daki ba Dan Haka wlh gidanan zaa siyar kawai ayimin kayan d'aki" Kamar Mai tsoron Safiyya Hajara tace "toh idan mun siyar da gidan Nan Safiyya a Ina zamu koma da.zama nida Naseer din tunda nasan sabida zakije gidan miji kike cewa mu siyar da gidan nidai nasan wanan gidan yanzu shine rufin asirina Dana Naseer tunda Naeema ta Kara gaba da yaranta" Sai a lokacin ta sasauta Fuskarta tana "Umma ai wani karamin gidan zamu siya idan muka siyar da Wanan Kinga gidanan babba ne zaa siyi gidan da daraja a ciki zamu siyi karamin gida ki siyamin kayan daki sauran kudin Kuma kija jari kafin ki ankara kema kin zama hajiya har macca ma sai kije ki Naseer dawowa yayi idan yaganki da kudi bazai yi magana ba kinsan shi ba Kamar Yaya Tijjani ba" Washe baki Hajara tayi Dan maganganun Safiyya sun shigeta ta Kuma Yi naam da shawarar ta "Toh wa kike ganin xai siyi gidan" "Ki bar komai a hannuna" Safiyya tace cikin murna a ranar ta shiga d'akin Naseer ta birkita Kaya har sai data samo takardun gidan Ta fito sai murna take da zaa samu kudin da zata siyi kayan daki ya zama Dole ma ta koyawa kishiyarta hankali Dan Kaya zatayi na fitar hankali da kishiyar ta zata shak'a sosai take Jin dadi da had'asu waje dayan da zaayi tasan kishiyarta sai ta kwashi kashinta a hannu Dan sai ta bar Mata gidan ta mallake shi ita kadai. Washegari da sassafe ta bazama ta Nemo dilalai a cikin kwana biyu aka samu mutane masu San gidan har su uku. Dan gidan Naseer din babba ne kuma a fuska Mai kyau Safiyya Bata yarda anyi cinikn gidan Agaban Hajara ba ita ta saka hannu akayi komai da ita Akan Dole ta Nemo wasu Suka Mata shaidan ta siyar yanzu ba mallakinsu bane ta Basu kudi Suma masu siyan gidan suka bada kudi da shaidunsu suka karbi takardun gida. Sai da Safiyya ta zabtare kudin wajen rabi ta b'oye. Ta Kai sauran kudin gaban Hajara. Hajara dai tana San magana kudin gidan yayi araha da yawa Amma babu yanda zatayi da Safiyya datayi Kane Kane. Safiyya ita ta raba kudin gida biyu ta dauki iya kudin da zai isheta ta siyi kayan daki da komai Ta bawa Hajara sauran Hajara kuwa sai a lokacin tace "Safiyya kudin Nan bazai Isa mu siyi wani gidan ba ballantana har na samu na jari" Karki damu Ni Zan Nemo miki gidan da kaina zaa samu Jiki a sanyaye Hajara tace "toh yaushe masu gidan suka ce mu tashi nidai Safiyya ba Haka naso ba wlh gidanan babba ne wayanda Suka siyi gidanan sun cucemu" "Notice din wata daya suka bamu karki damu kafin lokacin na samo Mana wani gidan Ahaka ta lallab'a Hajara tayi shiru. Kafin sati daya da tafiyar Naseer har ta Gama siyan kayan daki na gani na fad'a Iya Nan Bai isheta ba sai data tab'a kudin da ta bawa Hajara data Masa kyakyawan b'uya shirye shiryen bikinta kawai daya rage sati biyu take tana facaka da kudi har wani karamin lefe tayiwa kanta Hajara idan tana San tayi Magana sai ta hayayyako akan Dole take shiru. A ranar da Naseer ya koma kuwa sosai Hajara ta tsorata Dan Bata kawo zai dawo kurkusa ba ta d'auka dagaske guduwa yayi. Safiyya kuwa kwantar Mata da hankali tayi akan Kar ta sake ta gayawa Naseer sun siyar da gidan. Sai idan sunzo tashi shima idan yasani ta haharde Rai ta Masa fin k'arfi tuni zai mata biyaya. Naseer kuwa sosai yayi mamaki da Hajara Bata tambayeshi Inda yaje ba sai wani susune Kai take. Shi kuwa dadi yaji yace Mata Abuja yaje neman kudin da zaiyiwa Safiyya kayan daki toh shima yaje Bai samu ba sai Yan canji ya samo tayi hakuri zai cigaba da nema Kai a sunkuye Hajara tace Kar ya damu ta siyawa Safiyya komai. Wani irin dadi Naseer Yaji yace Mata Ina ta samu kudin Tace Kar ya damu zai sani a hankali Naseer kuwa har a Ransa yaji dadin ganin Hajara ta Dan sauya Masa Ashe har ta samu kudin kayan d'akin. A ranar zuciyarsa fes batare da wani fargaba ba ya kwana da tunanin iyalinsa Washegari da safe yaje gidan Naeema yake Gaya Mata duk yanda sukayi da Hajara Nidai sosai nayi mamakin Inda Umma ta samu kudin. Haka kawai jikina ke gayamin akwai dai ta hanyar da aka samu kudin bandai cewa Naseer komai ba danaga yanda yake murna Yana cemin ko fada Umma Bata Masa ba kila Allah ya fara karbar adduarsa. Bandai ce komai ba a ranar ya wunar Mana daddare na raka shi ya tafi Yawan zuwa da Naseer keyi gidan Naeema yasa Sam bai San halin da ake ciki ba dan Yan canjin daya samu ma shinkafar da Hajara zatayi taron biki ya siyo Mata har da yiwa Hajara dinki kala biyu wai duk Dan ya faranta Mata. Hajara kuwa damun Safiyya ta ringa Yi da zancen gidan data ce zata siya musu Dan lokacin barin gidansu nata karatowa Amma Safiyya haka ta ringa tsara Hajara tana d'auke mata hankali daga zancen Dan tabi ta Kan kudin tuni burinta kawai a daura auren Ta bar gidan Hajara da Naseer su San nayi tunda ita dai ta samu cikar burinta. A Haka aka fara bikin Safiyya Tijjani ma yazo bikin da Murja Dan tuni sukayi katon aiki Akan Tijjani har sai daya je har gidansu Murjan ya dawo da ita. Duk da kamun da suka Masa ba sosai ya Kama shi ba Hajara kuwa irin gayyar da Safiyya tayi yasa hankalinta ya d'auke daga zancen gidan Bata Kuma bi takan Murja da suke Yar kallon kallo ba Sai da aka zo tafiya da Safiyya washegarin daurin Aure. Hankalin Hajara ya dawo jikinta daki ta ja Safiyya ta hau Mata maganar gidan ita kuwa Safiyya ta Mata karyar ta siyi gidan anjima wani zai zo.ya kaita taga gidan Hajara badan ta yarda ba tana ji tana gani aka tafi da Safiyya mutane Suka watse ya rage saura ita daya da Naseer. A lokacin saura sati daya notice din da aka basu ya Kare. Kamar tayi kuka ta Shiga d'akin Naseer Kuma ya Shiga har d'akin ta daya hada musu abin karyawa ya Kai Mata Yana "Umma lafiya kuwa Yana ga kamar bakida lafiya"? Hajara na k'ok'arin Magana Wani yaro ya doka Sallama Wai Mai gidan Yana Sallama da Safiyya Gaban Hajara ne ya yanke ya Fadi. Naseer Kuma cikin mamaki yace "Mai gidan kuma waye Haka" Yayi waje Dan yaga Mai sallamar...... *NAGA TA KAINA* *NA SADNAF*🌸🌸 ®️ *_PURE MOMENT OF LIFE WRITERS_* _{We Don't just entertain nd educate we also touch the heat of readers P.M.L}💪🏻_ *Free Novel* *Page 44* Naseer na fita Waje ya hango wani Alhaji a zaune a cikin motarsa ya zuro.kafafunsa waje Yana kad'a mukulli. Naseer ganin yanda yake kallon gidan yasa ya nufi wajensa yayi Sallama tare da mik'a masa hannu Sukayi musabiha "Kaine kake neman Safiyya"? "Eee Nine" Murmushi Naseer yayi Yana "Allah sarki ai tayi Aure Dazun Nan ma aka tafi kaita gidan mijinta". Murmushi shima mutumin yayi Yana "eyya Allah ya Sanya alheri dama Akan maganar tashinsu daga gidan Nan nazo Dan bana so su wuce lokacin da mukayi dasu Dan inaso na danyi gyare gyare a gidan. Kafin daurin Auren Dan nawa Dan shi zai zauna a gidan Naseer murmushi yayi ya kalli gidajen dake jere da gidansa Yana "Ai inaga Alhaji ba Nan Dan kazo ba ko kila a mak'otan namu akwai Mai sunan Safiyya Dan wanan gidan da kake magana gidana ne Kuma ban siyarwa kowa ba" Duk maganar Nan da ake mutumin na cikin Mota abinda Naseer yace ne yasa ya fito daga cikin motar Yana "Bangane gidanka bane baka siyar ba kaga na maka Kama da Dan shaye shaye ballantana kace bansan Mai nake cewa ba wanan dai gidan da ka fito daga ciki shine gidana da nake magana akai wajen sati uku kenan da biyan kudin gidan na Basu notice din sati hud'u" Murmushin karfin hali Naseer ya Kara zuciyarsa na balain bugawa har ya wuce misali Cikin rawar Baki yace "Waye ya siyar maka da gidan"? "Safiyya ce dai ta siyarmin da gidan ita da Mahaifiyata Dan Nima ban yarda da Safiyya ba sai da muka Shiga har cikin gidan na duba koina na tabbatar da gidan yamin na Kuma tambayi mahaifiyarta Anya gidan nata ne tacemin Kar na damu gidanta ne na siya gudun ma.irin Haka yasa nak'i Bata kudin sai data Nemo shaidu da nima nasansu suka shaida ta siyarmin Nima na bada kudin na karbi takardun shaidun gida ya zama mallakina Dan Haka" Naseer Bai tsaya saurarensa ba Kamar Wanda ake turawa Haka ya nufi cikin gidan Yana Jin duniyar na juyawa dashi Direct d'akin Hajara ya Shiga data kasa zaune ta kasa tsaye Yana Shiga d'akin ta mik'e da Sauri tare da juyawa Naseer baya. "Umma dagaske ne Kun siyar min da gidan da ya ragemin a rayuwata Gidan da shi kadai ne rufin asirina Umma dagaske ne Kun siyar"? Naseer yace Yana dafe kirjinsa dayaji Ya Masa nauyi Yana ta sukarsa. "Kayi hakuri Naseeru akan Dole muka siyar da gidanan Dan na d'auka guduwa kayi banida Mai bani kudi idan ba Kai din ba nayiwa Safiyya kayan daki hakane yasa na siyar Dan na fita kunya Amma sauran kudin na Nan zai isheni mu" Fad'uwar Naseer da tunda tace sun siyar yaji Kamar an harbe Masa kirjin da har yau daya tsuffa idan Ransa ya b'aci Haka yake fama da ciwon kirjin. Sam Bata San halin dayake ciki ba dayake juya Masa baya tayi sai dataji karar fad'uwarsa ta juyo hankali a tashe tayi kansa. Naseer sallati kawai yake Yana juya Kai hannunsa dafe da kirjinsa dayake ji kamar zai fashe. Kuka kawai yake yana "Umma Mai na Miki Haka a rayuwa kin rabani da komai Dana mallaka Umma iya sanina ban taba Miki komai ba Dana cancanci Haka daga wajenki sau daya nayi kuskuren da har gobe nake nadamarsa na marinki danayi shima wlh Umma bansan lokacin danayi ba Umma iya biyayya Ina Miki kin rabani da matata kin rabani da yarana bance komai ba iya Haka Bai Isa ba Umma sai da kika rabani da gidan daya ragemin a rayuwata da nidake muke ciki Umma Akan kayan daki Kika siyar da gidana Umma yanzu Ina kikeso mu koma innalillahi wa Inna ilaihi rajiun Umma kin kasheni" Naseer ke fada Yana dafe da kirjinsa "Ka kwantar da hankalinka Naseer ba duk kudin aka siyawa Safiyya kayan daki dashi ba akwai sauran da zai Isa ka siyi karamin gida har aure ma sai kayi Bari kiga" Hajara race da Sauri ta daga katifar sama da ta b'oye kudin da Safiyya ta Bata. Ras gabanta ya Fadi a lokacin data ga ba kudin sai Yan dari bibiyu guda goma. Cikin tashin hankali tayi wurgi da katifar ta hau duba koina tana ta Shiga uku ta lalace ba Inda Bata duba ba Amma Bata ga kudi ba "Na Shiga uku Yarinya Nan ta cuceni shegiya tsinanniya Allah dai ya tsine Miki albarka Naseer ta bani kudin Kuma ta kwashe na Shiga uku na lalace Hajara tace Tana fashewa da kukan bakinciki tare da zaman dirshan tana tsinewa Safiyya albarka. Naseer kuwa ko kallonta baiyi ba ya mik'e hannunsa dafe da kirjinss dayake ganin Yana saki zai iya fadowa jiri na dib'arsa Haka yaje ya kwanta a d'akinsa ya hau kuka Kamar karamin yaro Dan gani yake kukan kawai shi zai saka yaji kirjinsa ya rage nauyi. Hajara itama kukan taci ta koshi bakinta sai tsinewa Safiyya yake tana Shan alwashin samun kudin mota taje har calabar taci uban Safiyya. Taya ma akayi ta biyewa Safiyya ta siyar da gidan da itama kanta shine rufin asirinta yanzu idan Mai gidan ya koresu Ina zata koma data ita har Naseer Bata tab'a sanin Haka Safiyya take da San Kai ba sai Yau. Ya Zama Dole su San nayi kafin a koresu bakin cikinta ma shegen Dubu biyu da Safiyya ta ajiye Mata da ba abinda zai iya Mata. Wajen karfe hudu na yamma ta fito daga d'akin tashin hankali da take ciki Bai Bari taji yunwa ba. D'akin Naseer ta nufa tana zuwa ta iske jikinsa na wani irin rawa sabida zazzabin da ya rufeshi lokaci guda. Ihu ta saka ta fada d'akin tana tab'a jikinsa ta d'auke da Sauri tana "Haba Naseeru Mai yayi zafi haka kayi hakuri bansan Safiyya Haka take ba da ban Soma biye Mata ba sam banyi tunanin yaudarata take ba kayi hakuri ka tashi kaji" Ganin Naseer Kamar Bai ma San Inda kansa yake ba yasa tayi waje tana dora mayafinta aka. Wani chemist taje dake kasan layinsu. Dayake su biyu ne a chemist din ahaka ta roki dayan ya biyota har gida ya hau duba Naseer. A takaice sai da Naseer yayi kwana uku a kwance ba lafiya a kwana na hudu yaji sauki saukin jikinsa kirjinsa ne dai har lokacin ya Masa nauyi. Hajara ce ta ringa dawainiyya dashi Dan Dubu biyun dashi ta siya Masa magangunan Har da girki ita ta ringa Masa wai duk Dan Naseer ya ji dadi. Naseer kuwa ko San ganinta baya so yayi Dan shi kadai yasan Mai yakeji a kirjinsa idan ya tuna Wai wanan kantamemen Gidan nasa Mai part biyu da zai iya zama a bangaren da su Hajaran suke wanan Kuma ya zuba Yan haya ya samu kudi. Ahaka ma filin tsakar gidan da girmansa da zai iya tasar daki biyu a ciki Amma ahaka mahaifiyarsa ta siyar masa da gida sabida kawai tayiwa kanwarsa kayan daki. Hawayene suka zubo Masa ya runtse idonsa Yana Jin yanda kirjinsa ke Bugu a duk abinda mahaifiyarsa ta ringa Masa wanan yafi Masa ciwo Dan yanzu bashida komai a rayuwarsa. Hajara dake zaune agabansa tana hada Masa shayi ganin hawaye na zubo masa ta hau magana tana "Haba Naseer Kayi hakuri Mana wlh Nima bansan yarinya Nan iskancin data min ba kenan da ban Soma biye Mata ba Dan Allah ka daure ka Zama namiji insha Allahu zaka samu fin wanan ita Kuma Safiyya wlh Bari na samu kudin mota har can zanje na kwashe Kayanta na siyar na kawo maka kudin shegiya tsinaniya uwar San zuciya kayi hakuri kaji Naseeru na maka ba daidai ba ka daure ka Sha shayin Nan tunda ka kwanta baka sa komai a bakinka ba ka taimaka ka Sha musan nayi Dan Naga Mai gidan Nan har ya fara kawo kayan gyaran gidan Jiya ma sai daya zo da alama bashida mutunci" Naseer Bai ce Mata komai ya tashi ya shige bandaki. Ya daura alwala yazo ya tadda sallah Yana ji kamar iska zata d'auke shi sabida rashin kwari. A sallah ma sai dayaci kuka ya gayawa Allah halin dayake ciki yayi adduar ya shafa Hajara na zaune ta buga tagumi tana kallonsa. Shi kuwa mik'ewa yayi ya fita batare da yace Mata komai ba duk da tana Masa maganar Ina zaije. Daya fita ma opposite din gidansa ya zauna Yana karewa gidansa kallo ji yake inama mafarki yake ba dagske ya rasa wanan tangamemen gidan nasa ba daga Ina zai fara yanzu. Abinda Umma ta Masa ba shi kadai ta cuta ba har kanta ta cuta sani ne batayi ba. Mik'ewa yayi ya fita har bakin titi wajen wani dilali Mai siyan Kaya fairly use ya Masa bayanin Yana da kayan siyarwa na gida ya lissafa Masa Abubuwan gidansa Kama daga gadon da Hajara ke kwana har cokali Dan so yake yayi gwanjon komai ya siyar na gidan Dan Bai San Ina zai Kai kayan gidan ba tunda bashida gida yanzu. Har gida suka zo yaga duk kayan ya musu kudi Wanda duk kayan ma tayin wulakanci ya Masa Amma ba yanda zaiyi ahaka ya siyar da kayan gabadaya ya kirga kudinsa ya bashi ya tafi tafiyarsa da minti ashirin sai gashi ya dawo da mai kurkura suka hau fita da kayan Naseer kuwa ya hade kayanshi Dana su Zahira a bako biyu jiri ke dib'arsa Amma ahaka ya hade kayansu ya fito dashi Bayan ya kwashi duk wani Abu nashi Mai mahimmanci Hajara kuwa hankali a tashe ta hau tambayarsa ya taga Ana fita da Kaya Ina zasuje. Tunda ya kwanta sai a lokacin yayi magana Yana "Umma duniya Zan Shiga na nemi kudi Dan kin rabani da komai banida gida banida komai Dan Haka Nima zanje na nemi shagon da Zan ringa kwana tunda banida gida yanzu" "Naseer Mai kake cewa haka ni Kuma fa wajen wa zani Haba Naseeru yanzu Ni Kuma a wajen wa Zan zauna nidai na Shiga uku na lalace Dan Allah kayi amfani da kudin nan na hannunka ka Kama Mana haya Naseer kasan banida Inda zan zauna ko na koma calaba Naseer" "Ki koma gidan Safiyya Umma Dan da duk kinyi wanan tunanin da Baki siyar da gidnan ba kin siyar Dan ki farantawa Safiyya Rai da ba ko sisinta a ginin gidanan Bata San da yanda na samu kudi na Gina gidana ba Umma toh gashi kin rufa Mata asiri tana gidan mijinta namu ya tonu Dan Haka Umma babu yanda zanyi dake Dan Nima shagon abokina zanje na ringa kwana Kinga bazai yiwu na tafi dake shagon abokina ba" "Naseer nayi nadamar biyewa Safiyya kayi hakuri Ni nasan Kai Dan albarka ne bazaka Bari na tagayyara ba ka taimaka ka sama Mana wajen da zamu zauna" Naseer da yazo har wuya a tsawace yace "Umma ki kasheni Dan Allah Dan annabi ki Huta Umma bayan abinda kikamin har Zaki iya cewa na nema Mana wajen da zamu zauna umma Nagaji Nima.yanzu ta kaina zanyi tunda kinyi nassarar rabani da komai Abu daya Zan Miki shine na baki kudin mota kije calaba wajen Safiyyan data Baki shawarar ki siyar da gidana ta San yanda zatayi dake bani kadai ne danki ba Umma idan bakya San zuwa calaba kije gidan Tijjani yanda Kika haifeshi Haka Kika haifeni Umma bazan kashe kaina akanki ba Umma na rasa Mai na Miki a rayuwata Umma kin kassaramin rayuwa yanzu banida komai a rayuwata sai wanan Kayan sawan nawa Umma Dan Haka nima Zan Shiga duniya naje na nemi kudi tunda yarana ma da matata duk kin rabani dasu" Kuka Hajara ta fashe dashi ta zub'e a kasa tana ta Shiga uku taya zataje gidan Tijjani da matarsa ke dukanta take Mata horar yunwa Taya zataje gidan Safiyya da ko sati biyu batayi da aure ba" Naseer kuwa kudin hannunsa ya raba gida biyu ya Ajiye Mata agabanta ya kinkimi bakonsa ya tafi ya barta tana ihun Kiran ya dawo Kar ya tona Mata asiri. Yana kuwa fita yasamu taxi daya zo ya sauke Kaya a wani shagon provision Ya tsayar dashi ya saka bakkonsa biyu a ciki ya Gaya masa Inda zai kaishi. Yana kallon Hajara ta fito daga gidan hankalinta a tashe har Dan biyo taxin tayi shi kuwa ya d'auke kansa Dan ya gaji da halin mahaifiyarsa zata Dade Bata Kara ganinsa ba Baa sauke shi a koina ba sai a gidan Naeema. Ina zaune da Yara na a tsakar gida suna home work dinsu Ni kuma gabadaya hankalina na wajen tunanin Inda Naseer yayi daya kwana biyu Bai zo ba sosai na damu da rashin zuwansa Dan tunda yasan Inda nake Bai taba fashin zuwa ba hakane yasa na damu da Jinsa shiru Dan Ni nasan da lafiya yake ba yanda zaayi ya k'i lek'omu yanzu Haka ina tunanin idan gobe Bai zo ba Zan tura Isihu unguwar ya gano min ko zai ganshi Naga ya shigo gidan da bakko manya guda biyu a hannunsa ya ajiye. Daga yanda Naganshi sai da gabana ya tsinke sabida yanda ya rame ya fice daga hayyacinsa kamar bashi ba. Hankalina a tashe na mik'e Ina kallonsa ko kallon su Zahira dake Masa sannu da zuwa baiyi ba ya cire Raheema data je Masa oyoyo daga jikinsa ya shige dakina. Ni kuwa na bishi da Sauri Dan ban taba ganinsa ahaka ba. A Gefen gado na sameshi ya zauna ya sunkuyar da kansa Ni kuwa na zauna a gefensa tare da ruk'o hannayensa Ina tambayarsa lafiya Mai ke damunsa. Bai d'ago ba sai sheshek'an kukansa naji daya tayarmun da hankali yasani jawo shi jikina Shi kuwa ya Dora kansa akan kafadata ya cigaba da kuka kasa kasa. Ba karamin Abu ke saka Naseer kuka ba hakane yasa hankalina a tashe nima na hau kukan Ina tambayarsa abinda ya saka shi kukan. Sai daya yi kukan Mai isarsa da har sai dayaji nauyin da kirjinsa ya Masa dake barazanar dauke Masa numfashi ya ragu kafin ya hau bani labarin duk abinda ya Faru. Bansan lokacin Dana Zamo daga Kan gadon na zauna a kasa na hau sallati ba Dan ban tab'a tunanin Rashin Imanin su Umma har ya Kai Haka ba tayaya zasu siyar da gidan Naseer Dan kawai ayiwa Safiyya kayan daki Ni kaina na kashe kudi a gidanan sosai kafin yayi kyau Tambayarsa nayi nawa Suka siyar da gidan yacemin shi Bai tsaya tambaya bama Dan da alama safiyya kadai ce taci kudin Bansan lokacin Dana hau musu Allah ya Isa ba Dan ba iya Naseer Suka cuta ba har nida yarana sun cucemu. Daga Ni har Naseer bamu iya wani bacci ba Dan sosai siyar da gidan ya min ciwo har hango gidan nake a idona. Ganin damuwar da nayi na Kara saka Naseer cikin wani damuwar Dan ko abincin Dana zuba Masa Bai iya ci ba yasa na daure na hau bashi baki dak'yar ya ci abinci ya Sha magani bacci yayi awon gaba dashi. Ni kuwa sanin bacci bazai d'aukeni ba yasa na rayya Daren Ina rokon Allah ya kawowa Naseer mafita ya musanya Masa da abinda yafi alheri. Hajara kuwa ita kadai ta kwana ko bacci Bai ga idonta ba sosai hankalinta ya rabu gida biyu tana tunanin Inda ya Kamata ta dosa. Sosai Naseer ya Bata mamaki da har ya iya tafiya ya barta Amma duk abinan Safiyya ce ta jaza Mata Bata Isa ta soma dosan gidan Tijjani ba Dan Murja Yar iska ce shi kansa Tijjani bashida mutunci da Yana Mata biyayya kamar yanda Naseer ke Mata biyayya da zata samu saukin wani abun babu ma yanda zatayi ta soma dosan gidan Murja da take ganin tafi kowa mugunta ga makirci ga horo da yunwa idan ta gayawa Tijjani ma ba yace ta dameshi. Tsinaniyar Safiyya data saka ta siyar da Naseer gidan Safiyya zata je a goben tasan yanda zatayi da ita. Washegari kuwa da sassafe Mai gidan ya duro ko kallon hajara dake kwance a kasa ta shimfida zaninta baiyi ba aka hau buge buge a d'akin Tana ji tana gani Yan aikin Suka Mata watsi da.kayanta waje ita kuwa ta fita waje tana matsa kwalla ta had'a Kayanta ta nufi Tasha Bata Sha wahalar samun motar calaba ba suka dau hanya tana cin alwashin irin bugun da zatayiwa Safiyya idan ta Isa gidanta. Safiyya Sosai taji dadin ganin bangarenta fes da kayan data siya da suka kasance tsadaddu. Agajiye suka Isa calaba da Kuma bak'ar yunwa hakane yasa wayanda Suka rakata da suka kasance Yan calaba suna kaita Suka tafi. Sai data Gama Shiga koina a gidan sanan ta fito palo ta zauna tana Allah Allah Umar ya shigo tace Masa tana Jin yunwa sai dai har akayi sallah Isha Bata ga keyarsa ba. Sai muryar Yara ke tashi a tsakar gidan tana ta daga wuya taga ko zata ga uwargidanta data matsu taganta itama sai dai Bata ga alamarta ba. Ahaka yunwa keta nukurkusarta Ta rik'e cikinta wajen karfe Tara taji muryar Umar take Taji wani irin Sanyi a zuciyarta ta mik'e da sauri tayi waje. Sai dai me tana fita taga Umar din a tsaye da manyan ledoji ya mik'awa wata datake kyautata zaton itace kishiyarta taci kwalliya cikin doguwar riga. Ta yiwa umar din magana taga Umar din ya shige b'angaren ta batare da ya ma kalli bangarenta ba Mamakine ya kasheta data ga uwargidanta ta nufo b'angarenta da ledojin a hannunta Ita kuwa Safiyya ta gyara tsayuwarta tana jiran isowarta Dan daidai take da ita Tana kuwa zuwa ta hau bin Safiyya da wani irin Mugun kallo tana "Ke a lailai Baki yarda ke amaryar bace koh duk mazan duniya Nan ki rasa wa Zaki aura sai mijina ko hmmm lailai yaro bai San wuta ba sai ya taka wlh Tallahi da kafafunki Zaki bar gidanan Dan Miji a tafin hannuna yake tsakaninki dashi sai gani sai hange. Na Bari ya auroki ne Dan na samu Yar tayin aiki Dan Haka a goben Nan ba sai na Gaya miki ba karfe shidda kifito ki Dora Mana abincin karyawa kaza Kuma nida mijina da yarana ne zasuci Zaki ci ubanki ba dai mijina Kika Aura ba hmmm" Tace tana k'ok'arin juyawa ta tafi Safiyya kuwa ta damko kafadarta da zumar dawo da ita. Ita kuwa tana juyowa ta kwashe Safiyya fa lafiyayyun Mari biyu ta hankadata har sai data Bugu da kujera dake palon Ta Kara Mata wani mugun kallon ta tafi. Safiyya kuwa kamar mahaukaciya ta bita aguje ta cakumeta ita kuwa ta daga Safiyya sama ta hau ruwan cikinta ta hau dukanta kamar yar cikinta. Ihun Safiyya ne yasa Umar fitowa daga b'angaren kishiyar Safiyya ya nufi wajensu........ *NAGA TA KAINA* *NA SADNAF*🌸🌸 ®️ *_PURE MOMENT OF LIFE WRITERS_* _{We Don't just entertain nd educate we also touch the heat of readers P.M.L}💪🏻_ *Free Novel* *Page 45* Da saurinsa ya Isa wajensu ya rik'e hannayen hafsa dake ta buga Kan Safiyya da kasa Dan karfafa ce ita Bata Wasa ba wani zubin shi kansa Umar din idan Abu ya hadosu tana Masa mugun duka idan fada ya kaure musu. Safiyya dafe keyarta da takejin lema tayi da alamar.jinine ta mik'e da kyar tana jiran Umar ya d'auke Hafsa da Mari sai dai a madadin Marin sai ya hau Bata hakuri Yana rarrashinta. A wahalce Safiyya tace "Umar kanka daya kuwa Taya zaayi matarka daga kawoni yau ta hau dukana amadadin ka tsawatar Mata sai ka hau Bata hakuri"? Ko kallonta baiyi ba ya cigaba da bawa hafsa hakuri dake cika tana batsewa. Mamaki yasa Safiyya wartsakewa daga azabar da takeji a keyarta Dan Umar din ma hannun Hafsa yaja suka Shiga bangarenta suka rufo k'ofar batare da ma ya Mata ko kallo daya ba Safiyya kasa ma motsi tayi sabida tsananin mamakin abinda Umar din ya Mata gani take Kamar ba Umar din data aura bane. Sai da Sauro Suka fara kaiwa fatarta cizo ta koma bangarenta da mugun ciwon Kai ga mugun yunwa da takeji ga ba abinda zata saka a bakinta a tsakiyar palon ta zub'e tana tunanin abinda zai saka Umar ya Mata Haka a Daren ranar da ta tare a gidansa da yake ta dokinta kamar ya cinyeta. Gwallo Ido tayi data tuna kwallinta data manta dazaa daukota hannu ta Dora aka Dan kwallin Nan shine yake balain tasiri a wajen Umar yau kuwa ko kwallin Bata saka ba. Ya Zama Dole ta nemi shugabarsu tunda tana garin calabar zata nausa daji nemanta ta Kara Bata kwalli tare da damke Mata Umar ta kuma cin uban kishiyar Nan tata Mai Kama da maza sosai ta zargi kila sabida bata saka kwali ba shiyasa Umar ya wulakanta ta batasan shi kansa Umar din sai yanda uwar gidan sa tayi dashi ba. A ranar Bata iya bacci ba sabida mugun yunwar da takeji ga azabar ciwon Kai Dan keyarta ya kumbura yayi suntum. ruwa kawai ta ringa dirkaka wa kanta cikinta na Kara kullewa. Wajen karfe shidda na asuba baccin wahala yaso ya d'auketa. Har ta fara baccin sama sama taji an banko k'ofar dakinta da balain k'arfi. Mik'ewa tayi a firgice Dan ta balain tsorata. Hafsa ce ta shigo cikin kayan bacci har kasa kanta a bud'e Yana ta digar ruwa. Cikin wani irin murmushi hafsa tace "Amarya dafatan kin tashi lafiya baccin ya Isa Haka a fito a Dora Mana abincin karyawa Dan Yara zasu tafi makaranta Dan nasan kinsan Yana da Yara masu zuwa makaranta dole zasuci abinci kafin su tafi makaranta". Wani irin Mugun kallon tsana Safiiya ta kwashe Hafsa da shi tana "Juya ki barmin daki kafin na tureki da kaina uwar abincin Zan dafawa Yara ba abinci ba ke da kwana da miji Ni da dafawa Yara abinci kin dauka Yar aiki aka kawo Miki wlh bashi kikaci duk abinda Kika min sai na Rama bakisan waccece ni bane kina Wasa da wuta Bari na kamaki" Wani irin Dariya Hafsa ta kwashe dashi tana "Zaki sha wahala idan kikace zaki ja Dani a yau Zan tabbatar.miki da ke Yar aikin ce tunda har.kika auri mijina idan Kika min gardama Kuma wlh na Miki shegen duka da kafarki Zaki bar gidanan" Ta juya ta fita daga d'akin Safiyya kuwa ta buga uban Tsaki Tana Shan alwashin gari na wayewa zata tafi wajen shugubarsu Kuma indai taje sai ta saka an kashe Mata hafsa. Fitar Hafsa da Yan mintina sai Gata ta dawo da Umar daya balain had'e Rai ya saka doguwar rigar maza Safiyya kuwa Ido ta zuba Masa tana mamakin yanda yake mata wulakanci Agaban kishiyar ta duk da tasan idan ta saka kwalli Yana rikicewa akanta Amma wani zubin Bata saka kwalin idan yazo Kuma Baya canja Mata haka. Fuska a had'e yace "Ki tashi ki Dora wa Yara abin karyawa Dan zasu tafi makaranta sai kinyi kwana bakwai Zaki ajiye girki kafin hafsa ta karba" "Idan ni kuke jira na Dora muku muku abinda zakuci wlh sai dai ku mutu da yunwa yaushe kuka tab'a Jin daga auro amarya ta fita ta Dora girki.naga ma ba a d'akina ka kwana ba akan me.zan Dora girki wlh Umar ka bani mamaki ban taba sanin Haka. Kake ba wlh Allah ban taba sanin wulakanta ni kakeso kayi ba shiyasa ka auroni agabanka wanan shegiyar matar taka Mai zubin maza ta Dokeni" Jinta ne ya d'auke na wucin gadi Sakamakon Marin da Umar din ya d'auke ta dashi Yana "daga yau karki sake ki Kara zagarmin Mata idan kina San zaman lafiya a gidanan ki tashi ki dorawa yarana abinci karyawa karsu makara zuwa makaranta" Umar yace a fusace Yana barin d'akin Hafsa kuwa cikin wani irin murmushi ta karasa gaban Safiyya dake dafe da kumatunta har lokacin sabida tsananin mamaki Marin da Umar ya Mata tace "Baki ga komai ba wlh da kafarki Zaki bar gidanan Dan mijina yafi karfinki na Gaya miki ba yanda zaayi sama ta kizo ki aure min miji alhalin bakisan wuyan Dana Sha dashi ba" Daga haka ta fice daga d'akin Safiyya ta zub'e kasa ta fashe da kukan bakinciki. A takaice a cikin kwana bakwai da Kai Safiyya tayi wani irin Rama tayi wurjan wurjan Dan duk Inda take tunanin Hafsa ta wuce Nan Dan muguwa ce ta karshe horar yunwa da take Mata yasa ta yarda ta fara girkin duk Yan gidan Sabida ta samu na abinci Nan ma idan ta girka Hafsa ke zuwa ta juye a babban kula ta bar Mata kanzo ta kankara Dan kudin Hajara data kwaso ma yaranta sun bita har d'akinta sun kwashe ballantana ta siyawa kanta abinci Duk yanda taso fita Umar ya hanata Dan mugunta ma Safiyya kulle gidan take idan ta saka ta aiki tak'i sai ta jibgeta. Yaranta ma a palonta sukacin abinci su Mata kaca kaca da Palo da daki Bata Isa tayi Magana ba da mugunta ma yaran Suka fafarka kujerunta da Reza da Zuciya ya d'ebbeta hade Yaran tayi ta zanesu dayake sabida bakin cikin ganin tsadaddun kujerunta da suka yaga Sai dai yaran na fita sai ga Hafsa Nan daga k'ok'awa ta Mata shegen duka ta kumbura Mata fuska tundaga ranar Bata Kara gigin tab'a yaran ba Tana ji tana gani yaran Hafsa ke wulakanta Mata Kaya Bata isa tayi magana ba kuka take ci sosai tana nadamar ma auren Umar din dan gwara Zamanta ba auren da irin wanan kuntacecen rayuwar da take sati daya da kwanakin da ta tafi ji take kamar tayi shekaru a kurkuku ta Sha yunk'urin guduwa daddare Hafsa datake cewa Mayya na dawo da ita Dan Hafsa so take sai ta azababtar da ita kafin tasa Umar ya saketa. Dan ba karamin kamu tayiwa Umar ba,Bai Isa ya ketare umarninta ba A yau ma Kamar yanda Hafsa take tilasta Mata aikin gidan. Ta fito Ana iddar da sallah asuba ta fara aikin gidan. Da gayya ma yaran da suka jiku da makirci ke B'ata katon gidan ta share ta goge ta zo ta Dora babban tukunya ta Dora musu abinci Ita kuwa hafsa Haka zata fito da jikakken Kai tana Mata murmushin mugunta Dan Umar sau uku kenan Yana kwasheta da Mari idan ta Bijirewa umarnin Hafsa zuwa yanzu ba abinda ta tsana sama da zaman gidan auren dan tayi auren ne Dan taji dadi sai gashi tana Shan wuyan da ko a mafarki Bata tab'a hasasowa.kanta ba muryar Hafsa kawai fadar.mata da gaba yake Ahaka ta Gama abincin Hafsa ta juye ta bar Mata kanzo ta kankara taci ta Kara wanke wanken Yaran Suka fita gabadaya har da Hafsa. Sosai Safiyya taji dadin fitarta ta Shiga d'aki da Sauri ta d'auko mayafinta ta fita itama. Duk da nisan dajin da suke zuwa wajen shugabarsu ahaka ta Nadi tafiya Mai nisa tana Isa bukkar ta hau yaren tsafin su sai dai har ta Gama babu shugubarsu babu dalilinta. Kamar tayi kuka ahaka ta fito daga dajin ta koma gida tana Shan alwashin kwashe Kayanta ta tafi Dan bazata iya cigaba da zaman bauta ba. Sai dai tana dawowa ta tarar Da Umar a d'akinta. Ya wani marairace ya hau Bata hakurin Bai San Mai ya hau kansa ba a takaice a ranar ya kwanta da Safiyya Yana samun nutsuwa ya sauka daga kanta ya rufeta da dukan ita ba budurwa bace Yar iska ce ita a ranar Umar ne ya karbi ragamar mugunta yayi ta azabtar da ita da aiki.yana zaginta akan ita Yar iska ce . A irin wanna yanayin da Safiyya ke fuskantar.azabar wahala daga wajen Umar da Hafsa da yamma Safiyya na jidar wankin da Hafsa ta loda Mata bayan ta gama wawanka Mata Mari Hajara kuwa suna isa Calaba ta d'au hanyar gidan Umar da yake sananne da lodin Kayanta data Dora aka. Ko Sallama batayi ba ta Shiga katon gidan da tun a waje ta fara dan Jin sanyi samun wajen da zata zauna Mai kyau Dan ko Mai zaayi sai dai a ayi wlh Zamanta zatayi a gidan tunda Safiyya ce silar siyar da gidan da take zaune cikin rufin asiri. Kamar a mafarki Safiyya taji muryar Hajara tana dagowa kuwa taga itace Aguje tayi wurgi da bokitin hannunta taje da zumar kankame hajara Dan gani take kamar zuwanta ne zai saka ta bar gidan Hajara.kuwa sakin kayanta tayi a kasa ta matsa tana isowa wajenta ta kwashe Safiyya da wani mahaukacin Mari tana "har ni Zaki yaudara Ina uwarki Safiyya har Ni Dana Haifeki Zaki cuta ki hainceni kisa na siyar da gidan Naseer Dan na Miki kayan daki iya nan Bai isheki ba sai da Kika kwashe kudin da Kika bani dan na siyi karamin gida Toh wlh Tallahi sai kin fito mun da kudin gidan ko Kuma na zauna a gidanan tunda banida gidan da Zan zauna" "Safiyya hannunta ta fara k'ok'arin ja Dan ta kaita daki sabida Hafsa dake zaune a Kan tabarma data zubo musu Ido sam.bata san tasan abinda ke faruwa. Hajara cigaba da bambamin masifa tayi tana kwashewa Saffiya albarka dake ta Jan hannunta Hafsa kuwa ta mik'e tana dakawa Hafsa tsawa tana "Wacce wanan Zaki shigo.mana da.ita gida"? Hajara wani mugun kallo ta Mata ta kalli Safiyya tana "Halan wanan Mai zubin mazan ce kishiyarki"? "Nice Mai zubin mazan? Hafsa tace cikin mamakin Hajara . Hajara kuwa ta ja Tsaki ta fara k'ok'arin Shiga b'angaren Safiyya. Hafsa kuwa ta jawota ta kifa mata Marin da sai da Hajara taga walkiya a takaice har waje Hafsa ta fitar da Hajaran ta Kuma rantse bazata kwana a gidan ba. Hajara haka ta kwashi Kayanta ta nufi gidan Lami tana Shan mugayen alwashi akan kishiyar Safiyya Dan ta Gane Safiyya Bora ce a gidan. Sai dai shima gidan lamin data Isa kwana uku ta iya yi Sabida abinci sau daya ake dorawa a gidan Sabida talaucin da suke fama dashi. Gashi shi kansa mijin Lami wani gani gani yake wa Hajaran hakane yasa ta Kara tattara Kayanta da kudin mota ta nufi Tasha ta hau motar Kano Inda ta yanke Zama a gidan Tijjani tunda Bata da Inda zata zauna har.daji ta nausa Dan shugabarsu ta gano Mata Inda Naseer. Yake ta kuma.kara rokarta mudubin tsafi Dana karfinsu har ta karaci yaren tsafin dake sa ta bayyana a gabansu Bata bayyana ba. A mugun gajiye ta isa gidan Tijjanin Inda taci Karo dashi a bakin kofa zai fita massallaci turus yayi daya ganta da Niki Nikin Kaya Hajara kuwa ta sauke kayan daga Kanta tana "Bani hanya na wuce ka tsaya kana kallona kamar baka sani ba ka shigo min da kayan Nan maza" Tace tana matsar da Tijjanin tare da shigewa cikin gidan tana Kara hade Rai Dan so take ta gwada karfin uwa akan Tijjani ya mata biyayya kamar yanda Naseer ke Mata duk da kasan zuciyata tana Dan Jin shakkar Murjan A.palo ta tarar da Murja da jaririyar ta a hannu da Bata fi kwana biyu da haifarta ba. Kallon kallo suka yiwa Juna a daidai lokacin da Tijjani ya shigo da bacconta Yana "Umma Wai daga ina kike naganki da Niki Nikin kaya"? Daga calaba nake na Kuma dawo Nan da Zama Dan Safiyya ta siyar da gidan Naseer tayiwa kanta kayan daki banida wajen Zama shiyasa nayo Nan Dan Ni na Haifeka Ina Kuma da iko dakai matarka Bata Isa ta hanani na zauna a gidanan horar yunwar datamin a baya wlh bazan dauka ba indai ta gwadamin kuwa wlh sai ka saketa" "Mamakine ya rufe Tijjani a lokacin da Hajara tace Safiyya ta siyar da gidan Naseer anyiwa Safiyya kayan d'aki cikin mamaki yace "Umma Safiyya ta siyar da gidan Naseer fa kikace bangane ta siyar da gidan Naseer ba Umma yanzu gidan Naseer kuka siyar Dan ayiwa Safiyya kayan daki innalillahi wa Inna ilaihi rajiun" Hajara Tsaki tayi ta mik'e tana "Duk ba laifin Kai da naseerun bane kuyiwa Safiyya kayan daki kunce bakuda kudi karka sake ka dameni da tambayoyi kaji ko" "Umma kinsan Allah bazan d'auki abinda kuke yiwa yaya Naseer ba bazan hanaki Zama a gidana ba Amma wlh bana San hayaniya da takura Dan gaskiya bazan dauka ba. Daga Haka ya fice waje.yana Jin bakinciki siyar da gidan Naseer din datace sunyi har mamaki Naseer ke bashi daya bar Hajara take garashi yanda ranta keso. Hajara kuwa Inda suka zauna da Safiyya Nan d'akin ta shige abinta da kayanta. Ta fito daga d'akin ta shiga kitchen Kai tsaye ta zubo abincin da ta gani ta dawo palo ta zauna tana hararar Murjan dake Mata wani irin shu'umin murmushi tana girgiza kai Dan ta daga Mata kafa ne kawai Dan Tijjanin na Nan. A takaice duk inda Hajara taso itama ta nuna iko da isarta kasawa tayi Dan Murja shu'uma ce ta gaske Dan haihuwa da tayi yasa danginta suka cika gidan Tijjani Kuma ba wani Zama yake ba yana fita zasuyi tayiwa Hajara rashin mutunci Bata Isa ta tanka musu ba idan kuwa ta saka Abu a bakinta sai dai idan Tijjani ne ya dawo ta rokeshi ya Bata makirci kuwa sai abinda ya dadu da Murja ta Karo Dan kawai ta bar gidan Hajara kuwa duk yanda taso yiwa Tijjani bayani sai yace Mata shi Baya San tashin hankali Shifa ba naseeru bane. Idan ta masa hargagin ita fa uwarsa ce Bai Kamata ya Fifita Murja akanta ba sai yace wane shi ya Fifita Murja akanta ahaka zai maidata mahaukaciya Yana Mata dariya. Sosai ta gwammaci zama a koina da zaman gidan Tijjanin Dan sau uku kenan Murja na Mata duka. Ba yanda batayi da Tijjani ya saketa ko ta tsine masa ba yak'i sakinta yace Mata Yana San matarsa. Ahaka zata rufe ido. Ta Masa mugayen kalamai idan Murja ta Mata wani Abun shi kuwa Tijjani sai ya fice ya bar gidan A ranar data cika wata uku a gidan Tijjani A ranar Safiyya itama ta duro gidan da cikinta da takardar sakin da Umar ya Mata wiwi tana kuka da lodin Kayanta. Tijjani kuwa rantsuwa yayi bazata zauna Masa a gida ba sai dai ta nemi wajen Zama sai da.hajara ta hau Masa kuka ya bar Murjan ta zauna Dan ko ba komai taji dadin ganin Safiyya da sakin da aka Mata Dan zuwanta zai saka ta Dan samu saukin wani abun daga wajen Murja su Kuma nemi hanyar da zasu ci uban Murjan su dau fansar duk abinda ta musu. Sai dai zuwan Murja gidan yasa.tijjani ya bud'e kwandunan. Rashin mutunci Baya dagawa Safiyya kafa ko kad'an duk da kanwarsa ce ya balain tsanarta Ga Murja itama a gefe tana Gana musu azaba Dan kudin da Safiyya tazo dashi na kayan d'akinta data siyar a can calaba da baiyi albarka ba dashi Suke siyan abinci idan Murja ta hanasu Sosai suke rufe Ido suna neman bokon da zai.musu aiki akan.murja,Hafsa da Umar da suke ganin sune makiyansu a Duniya Bayan Naeema. Ganin kudin su ya tasama karewa yasa Suka yanke shawarar fara siyar da kosai a waje. Safiyya ce ta tafi siyan kayan da zasu bukata na kosai A wani shago dake can kasa dasu Kamar ance ta waiga ta hango Naseer da Tijjani a tsaye nesa dasu suna magana hakane yasa ta gwallo Ido tana kallonsu Ganin Tijjanin ya hau vespensa ya tafi shi Kuma Naseer ya fara k'ok'arin tarar taxi yasa tayi saurin fitowa daga shagon itama ta nufi titin da Sauri tana rufe fuskarta. Tana Isa titin Naseer.ya samu taxi ya shige Itama.ta tari wani da Sauri ta shige ta ringa bin bayan Naseer. A takaice ahaka ta rufe fuskarta tabi Bayan Naseer har k'ofar gidan Naeema Ta gwallo Ido a lokacin da ga su Minal sun fito suna Masa oyoyo. Ya rik'e hannunsu Suka Shiga gidan Sai da Safiyya ta Fadi ya Kai sau uku sabida azabar saurin ta koma gida ta Sanar da hajara Kamar ta tashi sama. Ido rufe ta Kara Hawa taxi ya maidata unguwar su Tijjani tace ya jirata gata Nan fitowa. Hajara kuwa Safiyya na Bata labari ta hau had'a Kayanta tana Godewa Allah. Cikin kankanin lokaci suka jiddi kayansu suka zuba a taxi Suka dau hanyar dorayi Kamar su karbi tukun Dan gani suke Kamar ba tafiya taxin keyi ba..... *Inaso na Dan Yi shi a gurguje mu shiga ainihin chapter 3 na labarin Naeema Dan na Gaya muku Yana da tsayi ahaka ma masu Dan mahimmancin nake rubutawa* *NAGA TA KAINA* *NA SADNAF*🌸🌸 ®️ *_PURE MOMENT OF LIFE WRITERS_* _{We Don't just entertain nd educate we also touch the heat of readers P.M.L}💪🏻_ *Free Novel* *Page 46* Suna isowa k'ofar Gidan jiki na rawa suka mik'awa Mai taxin duk kudin hannunsu kowacce ta fito da kayanta da kanta bakinsu a washe Kamar gonar auduga sosai sukeji Kamar sun samu yancin kansu. A k'ofar shagon da Isihu ke sallamar mutane suka tsaya suna karewa gidan kallo. Hajara ta Shiga shagon ta daga Kai sama tana kallon yanda shagon yake cike da Kaya har da buhunan danyen abinci ake siyarwa a shagon Da farko Bata Gane Isihu ba sai daga baya tace"Shege Ashe kaima Nan din ka gudo shiyasa baa ganinka Kai Kai kai Safiyya Kinga katon shagon da Naseer ya bud'e amma muke zauna a gidan Tijjani muna Shan bak'ar wahala kawai sabida an siyar Mai da gida sai yamin karyar zai Shiga duniya Ashe Yana. Nan Yana Jin dadin rayuwarsa da Naeema da yayansa. "Wanan ba shagon Yaya Naseer bane shagon aunty Naeema ne" Isihu yace Yana had'e Rai tare da fusge bredin da Safiyya ta d'auka Dan bak'ar yunwa takeji cikin jikinta balain sakata cin abinci yake. "Iyye a gidan uwarka ya Zama shagon Naeema wato abinda aka kitsa maka kenan ka.ringa fada zaka ci ubanka Bari nashiga gidan wlh sai na saka Naseer ya koreka daga shagon Nan" Daga haka ta fito daga shagon Safiyya na dannawa Isihu zagi tare da dumbuzar garin kwakin dake cikin buhu ta tura a bakinta Dan kamar taci babu Haka takeji. Ba Wanda yayi Sallama a cikinsu suka Shiga gidan. Ina zaune a tsakar gidan Ina yiwa Zahira kitso su Nadeeya su Kuma suna cin shinkafa da miya da kifi Naseer kuma ya Shiga d'akina yayi wanka Dan ya canja Kaya ya Kara fita Dan Tijjani ya Nemo Masa irin aikin da yakeyi a wani company duk da albashinsu ba yawa Haka Naseer ke fita da sassafe idan sun samu break sai ya dawo gida yaci abinci ya Kara watsa ruwa ya fita bazai dawo gidan ba sai wajen Goman Dare. Dawowar Naseer da siyar Masa da gidan da su Umma sukayi sai Dana Yi dgsk Naseer ya iya fawwalawa Allah komai Dan sosai yayi rashin lafiya gidansa. A ranar da Umma taje gidan Tijjani take Sanar.masa da sun siyar da gidan A ranar Tijjani ya nemi gidanmu yazo ya kuwa tarar da Naseer a gida. Sosai ya nuna Jin haushinsa da Naseer ya Bari Suka cutar dashi Bai dau mataki ba har korar Hajara yayi niyyar yi ya Bata kudin mota ta koma calaba wajen Lami ko Safiiyya Naseer yayi ta rokonsa akan yayi hakuri Kar ya koreta tausayin Naseer yasa ya Nemo Masa aikin dak'yar da albashin ba wani taka Kara yayi ba Amma ya gwammace ya ringa fita din daya zauna Haka Naeema na d'aukar Nauyin shi da yaransa. Naeema kuwa budi take samu ko ta ina Dan har katon fili ta siya da Sunan Waleed. Tunda Naseer yayi ramar siyar da gidansa da su Umma sukayi Bai Kara maida jikinsa ba. Ni kuwa daga Ni har yarana munyi sharr damu ban taba tunanin Zan danyi kib'a a rayuwata ba sai yanzu Zan iya rantsewa ban taba jina a cikin kwanciyar hankali batare da fargabar komai ba sai a yanzu da babu umma da Safiyya dake dagamin hankali Ashe Zan tab'a tsintar kaina a cikin kwanciyar hankali Haka kudin da nake samu Bai taba sawa na Raina Naseer ko na nuna Masa iko da dukiyata ba duk da Naga alamar Yana da gudun zuciya Dan karfin Hali irin nasa yasan muna da komai Amma idan aka bashi allowance din sati ko albashi sai ya Dan tsinto Mana wani Abu ya kawo na amfanin gidan. Sai danayi dagske ya daina siyowa nace ya ringa Tara kudin ya samu na siyan fili Dan Naga rashin gidansa har yau yasa bashida walwala Kuma Yana fama da ciwon kirji har yanzu. Yarana kuwa duk suna ingantaciyar makaranta Dan Zahira yanzu tana jss 2 San Sai da aka Mata tsallaken jss1 sabida tsayinta. Sosai nake mamakin girman Zahira da kyaun da Allah ya Bata da ko Ni Dana haifeta wani zubin bana iya d'auke idona akanta. Ga balain farin jini da Allah ya Mata na kawaye tun ma ba'aje koina ba Wai wasu ke zuwa Sallama da Zahira. Nadeeya ce take primary 5 yanzu Minal a primary 4 Humaira 3 Raheema a primary 2 Waleed Kuma na nursery Dan makaranta ma Dana saka shi na daban ne. Shigowar Umma da Safiyya yasa na saki baki Ina kallon ikon Allah. Yarana dake cin abinci kuwa duk suka Mik'e tsaye Suma Kamar sun ga dodon Ni Safiyya kuwa idonta kur Akan abinci da yarana keci Umma Kuma ta tsaya a tsakiyar gidan tana karewa ko'ina kallo tana "Lailai Naseeru Ashe Haka yake.jin dadin rayuwarsa shine muke cin ubanmu a gidan tsinannen yaron can Banda abin Naseeru Dan zai zauna da Naeema har sai yamin karyar zai Shiga duniya" Muryar Hajara ne yasa Naseer dake sallah yin saurin Sallame sallahrsa ya fito Dan ya gasgata muryar wacce yake ji. Daskarewa yayi a bakin kofa a lokacin daya daga labule ya hango Hajara da uban Kaya agabanta tana karewa gidan kallo Allahuma ajirni fi musibati wa aklifnin khairin minha ya hau fada a fili Sam bai lura da Safiyya ba sai daya ji tashin muryarta tana "Mai kuka wani tsatsaremu da Ido kamar Baku sanmu ba shegu Wanan uban abinci da kuke ci Haka har da kifi lailai kun samu duniya Umma Bari na fara cin wanan tukunna na samu nutsuwa kafin a zubo Mana Dan Naga matar gidan kanta a sama yake Bata so ganinmu ba" Ta nufi wajen su Nadeeya gadan gadan Naseer kuwa ganin Safiyya ya tayar Masa da ciwon kirjinsa Yana jin ciwon siyar Masa da gidan da tayi na dawo Masa tamkar a lokacin ta siyar. Bai San lokacin da ya isa gaban Safiyya dake k'ok'arin Zama Dan taci abinci ba Ido rufe ya cakumeta ya tsayar da ita ya hada kanta da bango tare da shake Mata wuya Yana k'ok'arin rabata da numfashinta da yakeji a Ransa tabbas kashe Safiyya ne kawai zai saka ya daina Jin ciwon dayake ji a kirjinsa. Hajara. Hankali a tashe ta nufi wajen Naseer ta fara ihun ya cikata kar ya kasheta Bai ga cikine a jikinta ba Amma Naseer ko gezau baiyi ba sosai ya Kara shake Safiyya Yana ta biyashi kudin gidansa. Ni kuwa ko kallonsu banyi ba na ja hannun yarana na turasu dakina na rufe k'ofar dakina na nufi daya d'akin shima na rufe na saka kwado. Kitchen Dina ma Haka na koma na zauna akan kujera danake Kai na dau Reza na fara gyara farcena. Dan Basu isheni kallo ba wajen Naseer Suka zo ba wajena ba so nake su Gama abinda suke su juya su bar min gida. Dan Naseer a yau zai San da da yanzu ba daya bane ko kusa ko alama bazan dau abinda sukamin a baya ba a da Dan Ina zaune a gidansa ne suka min abunda ransu keso Amma yanzu kuwa gidana ne Bari Naga iya gudun ruwansu. Azaba ne yasa Safiyya sumewa Dan ba iya shak'a Naseer ya Mata ba sai daya hada.mata da duka. Duk dukan da Hajara ke Kai Masa tana ihun kuka har da su cizo Naseer Duk baiji ba sabida yanda idonsa ya rufe. Sai dayaga Bata motsi ya cikata Hajara ta zub'e gaban Safiyya tana zagin Naseer akan gida zai kashe Mata 'ya Naseer kuwa a tsawace yace"Umma Mai kuka Zo Nema Kuma a gidanan"? Hajara butar data gani da ruwa ta watsawa Safiyya. Safiyya kuwa taja dogon numfashi Hajara ta saki ajiyar zuciya tana "Naseer bakada hankali ko kasheta kake so kayi sabida kawai ta siyar maka da gida ba na baka hakuri ba a gidan uban wa kakeso ta samo kudin da zata biyaka. Naseer karka manta nifa Mahaifiyarka ce kaina Kuma babbn D'ana yanzu Dan an siyar ma da gida shine zaka min karyar ka Shiga duniya Ashe kana Nan kana Jin dadinka da Naeema Ni danake mahaifiyarka Ina can Ina Shan wahala abinci ma na neman gagararmu Tijjani dayake tsinanne daga shi har matarsa azabtar damu suke idan baka rik'eni ba wa kake so ya rik'eni Safiyya ma da ciki tsinannen mijinta ya korota bamuda kowa sai Kai d'in Dan Haka hakuri zakayi mu zauna a nan gashi Allah nata Buda maka ga katon shagonka cike da Kaya ga Dan karamin gida karka wani damu tunda ka dage zaka zauna da Naeema ba yanda zanyi Haka zamu zauna" Sai a lokacin na Dago kaina daga yanken farcen da nake na mike Ina "A Ina zaku zauna Umma ba dai a gidana ba ko? Dan wanan karamin gidan da kike gani halal Dina ne da kudina na siya babu ko sisin Naseer a ciki. Gashi Nan agabanki ki tambayeshi kiji shima Dan yaransa na barshi yake zaune a gidanan Dan Haka ki nemi wani gidan ki zauna ba dai gidana ba idan ma Dan Naseer na gidan ne shima wlh Tallahi Zan hado masa kayansa ku tafi Dan bazan yarda ku zauna a gidana ba kamar yanda Baku yarda na zauna a gidan Naseer ba" Hajara tsananin.mamakin Naeema yasa ta kasa magana Naseer kuwa b'acin Rai ma Bai Bari ya iya magana ba sabida karfin halin mahaifiyarsa da kanwarsa shi kam badan Kar yayi sabo ba dayace Allah ya dau Ransa da Wanan abinda mahaifiyarsa ke Masa "Karya kike Yi Naeema wanan ba gidanki bane gidan Naseer ne Kun hada Baki da Naseer ne Dan kuce min ba gidansa bane Dan Kar mu zauna toh karyarki ta Sha karya wlh sai mun zauna dan bake Kika haifamin shi ba da zai tare a gindin keda yaranki gida Wasa ne da Zaki iya siya ki bude katon shago ga injinan markade har biyu yanzu Naseer Dan Kar mu zauna a gidanka shine zaku hada Baki kucemin gidan Naeema ne toh ko uwar gidan Naeema ne wlh sai mun zauna Dan itama ai da kudinka tayi arzkin. Hajara tace tana k'ok'arin komawa ta zauna a gefen Safiyya da ta Dade da farfadowa tsoron Naseer yasa ta kasa bud'e idonta Tana Jin duk abinda suke cewa Ni kuwa Ina ganin ta zauna na kalli Naseer nace "Kasan wlh Tallahi bazan yarda su zauna min a gida ba Naseer kasan yanda zakayi dasu. Idan dai har Dan kaima na barka ka zauna ne suka biyoka suna takamar kana gidana ne a zaune wlh sai dai kayi hakuri ka bisu Abunda na dauka a Baya wlh Tallahi bazan dauka yanzu ba" "Umma wlh Nan ba gidana bane Nima albarkacin yarana nake ci shiyasa ta barni na zauna Kun siyarmin da gida hakan Bai Isa ba sai Kun biyoni Inda zaa taimakamin "Nima albarkacin jikokina zanci ta hakura ta barni na zauna Dan na Gaya maka ba Inda zanje kaji na rantse maka" Umma tace tana Kara gyara Zamanta Ni kuwa mik'ewa nayi da zumar shiga daki Naga Naseer ya rigani Shiga d'akin Rai a b'ace ya fara tusa kayansa a cikin bakkonsa ban ce Masa komai ba ya gama had'awa ya fito daga d'akin ya kalli Hajara Yana "idan ma Ni kuka biyo toh na barwa Naeema gidanta sai kusan Inda dare ya muku bazaku kasheni da Raina ba" Daga Haka ya fice daga gidan Ransa a b'ace yarana na San suyi magana na daka musu uban tsawa Suka koma ciki da Sauri. Na Kara rufo kofata na kalli Umma da ta bi k'ofar gidan da kallo tana mamakin tafiyar da Naseer yayi ya barta Ni kuwa Isihu na kwallawa Kira ya shigo da Sauri Na nuna Masa bacconsu Umma Ina "Fitarmin da kayan Nan can waje Zan Shiga daki idan sun tafi ka rufemin k'ofata Dan wlh bazasu zauna min a gida ba" Safiyya da Umma mik'ewa sukayi da ganinsu da zasu samu wuta zasu iya jefani a ciki Umma cikin wani irin murya tace "Naeema sai kinyi danasanin korarmu da kikayi wlh ko zanyi yawo tsirara sai na ga bayanki ba dai mu Kika Kora ba wlh Zaki gani" Umma tace tana yin waje Ni kuwa nace "Insha Allahu ba Abunda Zaki iyamin alheri Zan gani idan Allah ya yarda" Hannuna Zahira ta ringa ja Dan har fara hawaye Safiyya kuwa idonta ya sauka Akan Zahira da ta Dade Bata ganta ba wani irin murmushi naga ta sakarwa Zahiran daya sa naji gabana ya tsinke kamar wancan lokacin da idan zasumin mugun Abu kirjina ke tsinkewa. Tura Zahira daki nayi da Sauri na fito daga d'akin ina "Dalla fitarmin daga gida" Na karasa wajenta Ina turata waje Ita kuwa ta Kara sakar min murmushi tana "ki shirya tarbar balain da zan jefo Miki" Daga Haka ta fice waje. Ni kuwa na rufo kofata Ina adduar insha Allahu ba balain da Zan gani Hajara kuwa Tana fita ta hango Naseer daya kusa Isa bakin titi ta dib'a aguje ta bishi abaya. Tana kwalla Masa Kira. Naseer Bai tsaya ba har sai data cimmasa ta zub'e a gabansa ta fashe da kuka tana Kar ya tafi ya barta ya rufa Mata asiri Bata da kowa sai shi. Kafarsa ta rik'e tana rusa uban kuka. Naseer kuwa hankali a tashe ya Ajiye bakonsa Yana "Umma Mai Haka Zaki taramin jamaa Dan Allah ki mike tsaye wlh Umma Nima bansan Inda zanje ba Ina Zan tafi dake banida gidan da Zaki zauna umma wlh wancan gidan na Naeema ne Dan Haka ki koma gidan Tijjani ki zauna kafin na samu wajen Zama" "Aaa wlh Dana zauna a gidan Tijjani gwara na kwanta a bakin titi kasan wuyan da muke Sha kuwa agidnsa Tijjani Bai d'aukeni da daraja ba a gaban idonsa matarsa ke azabtar damu Baya ce Mata komai idan na Masa magana sai yace Baya San takura ai Allah ya Isa no-no na da Tijjani ta Sha" "Innalillahi wa Inna ilaihi rajiun Umma Wai Mai yasa burinki ki yiwa yaranki mugayen kalamai Umma a cikin mu hudu waye Baki yiwa Baki ba Umma kinsan bakin uwa kuwa daidai da shedaniyar yarinya can Haka Kika Yi ta Mata Baki gashi baa je koina ba Aurenta ya mutu ta dawo gabanki da ciki Umma bahaka uwa take wa yaranta ba Umma Yara koda kuskure suke Yi addua ya kamata ki bisu dashi gashi duk kin Mana baki Umma kema abin na shafarki" A takaice Haka Hajara ta marairacewa Naseer da kuka har sai daya kaisu gidan wani da suke mutunci dasu Akan su kwana daya kafin ya samo musu Inda zasu zauna ya rasa yanda zaiyi da Hajara. Gidan da suka sauka.kuwa tarb'a Mai kyau aka musu sai da suka ci abinci nutsu suka hau hirar Naeema da irin Abun da zasu Mata idan sun samu wajen Zama. Shawarar da Safiyya ta kawo akan Naeema ne yasa Hajara mik'ewa ta taka rawa Dan idan suna San su cimma burinsu wajen tarwatsa rayuwar Naeema sai sun hada da makirci tamkar yanda Murja keyi. Washegari Naseer ya samo musu gidan Haya Mai had'aka da.mutane da yawa a ciki daki dayane sai tabarma da ya saka musu Dan bashida kudin katifa Cikin murna su Hajara suka koma gidan Dan gwara.munsu kwana a Kan tabarmar da dai zaman gidan Tijjani Naseer kuwa ce Mata yayi shi a company da yake aiki zai ringa kwana tunda ta koreshi daga gidan Naeema Budar bakin Hajara sai cewa tayi Kar ya wani damu ya koma gidan Naeeema su zauna ita dai fatanta ya ringa lekosu Yana kawo musu na abinci ya Kuma Bata jari tana siyar da kosai tunda ta lura gidan kowacce na Sana'a Har hakuri ta bawa Naseer Akan wnan karin da gaske take yayi zaman aurensa da Naeema. Naseer kuwa ya zub'e a kasa ya hau Mata godiya *Chapter 3* *Dama ku barni na huta sai bayan sallah na dawo muku da karfina Dan chapter 3 yafi na daya Dana biyu Kuma wlh na gaji**😟😟😟😟😟😟😟😟😟 *NAGA TA KAINA* *NA SADNAF*🌸🌸 ®️ *_PURE MOMENT OF LIFE WRITERS_* _{We Don't just entertain nd educate we also touch the heat of readers P.M.L}💪🏻_ *Free Novel* *Page 47* Nidai tunda Suka tafi naji hankalina ya tashi da irin kallon da Safiyya tayiwa Zahira da alwashin da suka Sha na ganin bayana dauriya kawai nake Amma bansan Mai yasa nake cike da fargaba da Kar su yiwa Zahira wani Abu ba Dan nasan halinsu nasan abinda zasu iya Yi na rasa wane irin masifa da balai ne wanan na rabu da Naseer ma na dawo gidan kaina Amma duk a banza hakan Bai saka sun sararamin ba nikam inaga sai na saka Naseer ya rubutamin takardar Saki na Kai musu sun ga shaida sanan zasu shafamin lafiya. Ban damu da Rashin dawowar Naseer da sai daya kwashi kwana uku Bai lek'o mu ba Ni kuwa tunda Suka tafi na sake zage damtse wajen yin addua Ina rokon Allah Kariyarsa gareni da yayana addua ma ya Riga da ya zama jikina bana sake idan lokacin da nake tashi idan yayi sai na tashi daga bacci naje gaban Mahallicina A Rana na hudu Naseer yazo.min da yamma bakinsa a washe ya hau bani labarin Umma ta bashi hakuri ta Kuma sawa aurenmu albarka Wai yanzu ba ta da matsala dani tunda ya Kama Mata gida ya Kuma Bata jari. Wani irin murmushi takaici nayi ina "Umma ce ta baka hakuri akan ta Kuma yarda mu zauna ba matsala Naseer.kai Kuma sai ka yarda" Dan rage faraa daya shigo dashi yayi ya cigaba da kallona "Naseer halan ka manta wacece.umma Taya Umma zata ce maka Bata da matsala da zamanmu tare.har ka yarda Bayan gidana ta zo naki yarda su zauna Kuma Haka kawai sai tace ma ta sawa aurenmu albarka ka yarda Naseer inaga har yanzu baka San wacece Umma ba idan ka manta Ni ban manta ba idan kaga Umma ta biyo ta wanan fuskar toh wlh wani mugun abun zata Mana sai dai na roki Allah ya kareni da yarana haihuwar Minal Haka tace Mana tayi nadama Mai ya biyo baya guba ta zuba a kunnu ta bawa Safiyya ta kawomin.na Sha Akan zan samu ruwan no-no akan naki Sha Suka rufeni da duka Naseer har sai da ka shigo ka k'waceni a hannunta Naseer har ga Allah na gaji da abinda umma kemin wlh Nagaji na rasa wanan masifar da.mai yayi kama tunda na aureka ban taba samun kwanciyar hankali ba daga wanan sai wanan da Ido daya nake bacci sai a yanzu Dana fara samun nutsuwa Umma da Safiyya suka Kara durowa ranar da.suka.zo sun Sha alwashin ganin bayana Safiyya ta kalli Zahira ta girgiza min Kai Naseer idan wani Abu ya Samu yarana ko Ni wlh Tallahi bazan yafe wa Umma da Safiyya ba sai na Kai kararsu gaban Allah nidai ka koma wajenta kar.ma tayi tunanin kana gidan Nan ma ringa lek'omu idan ka samu sarari" Na karashe Ina fashewa da kuka Dan har ga Allah su Umma sun isheni Naseer.ya bani takarda ta kawai na huta Zan jure komai banda su tab'a min yarana ba dole bane sai nayi rayuwa da Naseer auren Naseer ya isheni ya gundureni bazan karashe rayuwata Su Umma na wahalar Dani ba. Naseer rarrashina ya hau yi Yana "Yana Naeema wlh da ikon Allah kawai nake rayuwa har.yanzu rabona Nima da kwanciyar hankali tun ranar Dana budi Ido nasan Umma a matsayin Mahaifiyata na Sha Zama nayi tunanin Anya Umma ce ta haifeni kuwa Dan har yau danake yawo.ban tab'a ganin Mai irin Halin mahaifiyata ba ko a tarihi Umma gaba take da kwanciyar hankalina nayi kukan nayi naseehan duk a banza Nima data ce min naje ba komai a zuciyarta nasan ta fada ne kawai Bai Kai zuci ba Amma koma menene Zan cigaba da Addu'a Allah ya shiryeta ta Gane gaskiya wlh Naeema nasan tsinaniyar yarinya Nan ce ke zuga umma.na balain tsanarta duk wani mugun Abu ita kesa Umma amma karki damu insha Allahu ba Abunda zasu iya Miki ko yarana kema shaida ce akan yanda nake Addu'a" "Duk da Haka ka koma wajenta Naseer zamanka a gidana hatsarine" Nace na mik'e tsaye Dan har ga Allah banasan zaman Naseeru a gidana Ni nasan zamansa a gidana sai saka Umma ta cigaba da nufata da mugunta "Taya Zan koma gidanta alhalin haya na Kama Mata daki daya" "Naseer kayi hakuri ka koma wani wajen da Zama ka ringa zuwa kana ganinsu Waleed wlh zamanka anan zai saka Umma ta ringa kuntata min Amma idan taga baka gidana Zan samu saukin wani Abun Dan idan ma Dan Kai zata min wani Abu idan.taga bama.tare zata kyalleni. Rai a Dan bace Naseer ya mik'e Yana "Mai yasa kike sawa a ranki Umma zata iya Miki wani Abu duk wani Abu da kika ga ya samu bawa daga Allah ne Umma Bata Isa ta Miki Abunda Allah ya Bai hukunta zai sameki ba wuyanta ki dogara ga Allah" "Naseer inaga ka manta Abubuwan da Umma tamin ne inaga ka manta Kuma wacece ita shiyasa kake fadar Haka ganganci ne ma na saki jiki nace Umma bazata min komai ba duk wadancan data min a baya ai ita ta ringa min Allah na kareni din" Katseni yayi a tsawace Yana "kice na fita na bar miki gidanki kawia Naeema ba sai kin biyo min ta wanan hanyar kina fakewa da Umma ba Karki.manta Nima ba a San Raina nake zaune a gidanki ba Naeema a matsayinki ta matata Naeema kaddara ce ta hau kaina na rasa komai nawa amma.kinsan badan kaddara ba Ni Mai bawa wani kyautar gidane Amma ba komai Naeema Zan tafi bazan zauna a gidan naki ba Allah ya bani arzikin da Nima zanyi gidan kaina idan na samu sararin Zan ringa zuwa Ina duba yaran nawa kamar yanda kikace" Daga Haka ya juya ya fice daga gidan Kamar zai tashi sama Kan kujerar na koma na zauna Ina fashewa da kuka mumunan fassarar da Naseer yamin Dan har ga Allah bazai Gane Mai nake fada ba da abinda nake gudun Amma Ni nasan watarana zai Gane Idan nace fushin da Naseer yayi Bai dameni ba karya nayi Dan Naseer nada hawan jini na Kuma San duk a dalilina yak'i rabuwa Dani yake ta fuskantar wadanan tashe tashen hankulan Amma Allah yasan na gaji bazan iya cigaba da jure abinda mahaifiyarsa kemin ba abinda na jura a baya bazan dauka yanzu ba sabida Kar ma ya fassarani yasa ban nemi ya sakeni a halin yanzu ba har sai idan ya Dan farfado daga karayar arzikinsa. Ban Bari na saka wani damuwa a Raina ba na maida hankalina Kan sanaoina da yarana da na balain sawa ido.nake.kuma addua kariyar Allah a garesu Safiyya da Hajara a hankali Suka fara karantar mutane da suke zaune dasu wayanda.zasu iya yin talatin sabida gidan katon gaske ne. Wasu matan Aurene wasu zawarawa har da Yan bariki ma ahaka suke.gwamutse a gida daya. Sati d'aya kawai da sukayi a gidan suka fahimci mutanen gidan basuda mutunci ko kad'an kowa ta kansa yakeyi Ga balain Sa Ido da munafirci da suke dashi. Amma ahaka Safiyya ke fito da tabarma bakin kofar d'akinsu tayi ta kallon mutane dake gidan tana musu shishigi tana Shiga abinda Bai shafeta ba a cikin kwana goma ta Gama Gane matan da suke da aure da zawarawa da Kuma Yan barikin Akwai wata Iyyatu da hankalinta yafi karkata wajenta matar aurece Mai Yara biyu hatsabibiya ce lamba daya data maida mijinta tamkar yaron cikinta Dan mijinta shi yake Mata wanki ya Mata girki komai dai daya Kamata ace ita takeyi mijinta keyi ita kuwa Iyyatu tana zaune tana karkad'a kafa tana zuba mulki hakane yasa Safiyya fara shishige Mata Amma Iyyatu na shareta Sai data Sha kwandunan wulakanci a wajen Iyyatun kafin ta fara sakar Mata fuska suna Hira sama sama ahaka har suka Saba Safiyya fa fara bugar cikinta Tana gaya Mata yanda ta mallaki mijinta ta hanyar wani kungurmin boka dan kafin ta aureshi Yana da Mata daya da Yara biyar daga shigowar ta gidansa ta asiriceshi ya saki matarsa ya Zama Kamar bawanta Safiyya kuwa kamar ta Kama rawa take ta hau rokon Iyyatu ta sadasu da bokan. Cikin kwana uku Hajara ta bawa Safiyya kudin mota itama zuciyarta cike da farinciki Dan kosai ma da ba wani ciniki take ba a kudin ta bawa Safiyya kudin mota akan taje. Yanayin zaman munafirci da ake Yi a gidan yasa suka Gane Safiyya da Hajara basa sallah wanda take suka.hau kirnsu da basa sallah aka hau ma kyamatarsu Akan Dole Hajara da Safiyya suka hau sallah Dan su samu mutanen gidan su so su. Safiyya kuwa Basu dawo Gidan ba sai wajen Goman Dare. Jiki a sanyaye Hajara ko Zama bata bari Safiyya tayi ba ta hau tambayarta ya sukayi. Safiyya jiki a sanyaye tace mata "Hmm Umma mutumin ya iya aiki Dan ko shegiyar Shugaba Bata kamo kafarsa a iya aiki ba sai dai matsalarsa sai ka ajiye Masa mugun kudi Mai balain yawa Dan yau ma sai danaga Naeema da su Zahiraa Kwaryar ruwansa bance Masa komai ba ya hau bani labarin komai game damu da abinda muke San muyiwa Naeeman Sai dai a dubawar da yayi Yaya Naseer baya gidan aunty naeema Yana wajen aikinsa anan yake.kwana kamar dai sunyi fada da Naeema ne" "Hmmm daya kwana a gidanta da Kar ya kwana a gidanta wlh sai Naga bayanta tunda har ta koremu daga gidanta Badai yanzu tayi kib'a ta samu kwanciyar hankali tana ganin yaranta Agaban ta zuciyarta na sanyi ba zata Gane kurenta Dan ko cewa nayi a Kona arzikin ta bazata wani damu ba idan tana ganin yaranta agabanta Amma idan na hargitsa Mata lissafi fa zata Gane shayi ruwane yanzu dai a Ina zamu samu kudi a Mana aikin Nan Kinga yau ma ko cinikin kosai bamuyi ba yanda na soya Haka na shigo dashi shi zai xama abincin darenmu" Umma kiyi karyar rashin lafiya kawai kamar Zaki mutu Yaya Naseer da Tijjani su Shiga su fita su nemi kudi Dan na matsu Naeema ta fara hawaye da idonta wlh wlh Umma banida burin daya wuce na samu cikar burina akanta dukan da Yaya Naseer yamin duk sai na dau fansar sa Akan Naeema"........ *NAGA TA KAINA* *NA SADNAF*🌸🌸 ®️ *_PURE MOMENT OF LIFE WRITERS_* _{We Don't just entertain nd educate we also touch the heat of readers P.M.L}💪🏻_ *Free Novel* *Page 48* Tuni Hajara kuwa ta hau rashin lafiyar karya Safiyya ta tasa cikinta gaba ta nufi gidan Tijjani duk a firgice Kamar gaske. Wajen karfe biyar na yamma ta Isa gidan Sai dai tana zuwa gabanta ya yanke ya Fadi. Dan Naseer da Tijjani ta samu a k'ofar Gidan suna zaune a Kan tabarma Tuni jkinta ya dau rawa kamar ta juya Dan idan akwai Wanda take balain tsoro Bai wuce Naseer ba sosai take.ganin kiyayar da yake Mata a idonsa. Sam Bata kawo zata sameshi anan ba Dan so tayi ta gayawa Tijjani shi Kuma ya gayawa wa Naseer. Har ta juya zata koma ta tuna yanda take San ta samu cikar burinta akan Naeema. Wajensu ta nufa tana matsar hawaye kamar irin ta Dade tana kukan Nan Tana Isa gabansu ta zub'e ta hau sheshek'ar kuka tana "Yaya Tijjani Yaya Naseer umma na kwance tun jiya ba lafiya sai suma.take.ku taimaka Mana Kar ta mutu" Naseer Bai kalli Inda take ba Dan sabida tsanar da yayiwa Safiyya yasa ma Baya Shiga gidan ko kadan Baya San ganinta. Sai dai ya tura a kaiwa Hajara Dan kudin kashewa Wani irin kallo Tijjani ya watsawa Safiyya dake.ta sheshek'a.yana "toh Dan Bata da lafiya shiyasa Zaki dira gabanmu Haka a firgice ba Sallama yanzu da Kika zo Nan mu zamu Bata lafiya uban me ya Hana ki kaita asibiti da yanzu bama Nan ya zakiyi kenan"? "Yaya banida ko sisi shiyasa ban kaita asibiti ba" Tsaki Tijjani yayi ya k'au da.kai Yana Allah ya sauwake Naseer kuwa ya saka hannunsa a Aljihu ya Ciro duk kudin dake jikinsa ya mik'awa Tijjani Yana Bata ta Kai ta asibiti gobe na dubota Dan yau aikin kwana nake" "Kai kake wahalar da kanka Yaya Naseer Ni ban yarda da shegiyar yarinya Nan ba tashi muje Naga jikin nata Ya maidawa Naseer kudinsa. Safiyya mik'ewa tayi da Sauri tana ji kamar ta rufe Tijjani da duka a ranta kuma sai zagin Naseer da shima take Jin kiyayarsa a ranta take bakin cikinta ma ko kallonta baiyi ba ballantana yayi tunanin binta suje gidan Hajara ta tilasta Masa Nemo kudi ya kawo Mata Dan.tasan Tijjani shegen kansa ne Bai Zama lailai ya bada ko.sisi.ba. Tana ji tana gani suka hayye vespan Suka tafi Naseer Kuma ya mik'e ya nufi titi dan.ya koma wajen aiki Tijjani.ke tilasta Masa zuwa.gidansa cin.abincin Rana Dan ba Abunda ya b'oye Masa game da abinda ya had'ashi da Naeema da hutun da yake so ya Bata tasamu kwanciyar hankali kafin ya koma gidan. Safiyya ce tayi ta Masa kwatance har suka iso gidan Yanda Tijjani ya had'e.rai Yasa tayi gaba ya bita a baya tana Addu'a Allah yasa Hajaran a kwance take Kar ta tona musu asiri. Sai dai suna zuwa suka ga Hajara tayi dare dare a tsakiya d'akin tana ta zabga Loma abincin da ta siya Dan taci kafin Safiyya ta dawo Dan idan ba cika cikinta tayi ba Safiyya na iya rabata da kudin hannunta ta siyi abinci ita Kuma ta barta da Shan garin kwaki ko sandararen kosai. Shigowar su Tijjani yasa ta ture abincin da Sauri ta hau yamutsa.fuska Tijjani kuwa Safiyya ya kalla Yana "Inaga daga fitarki umma ta samu lafiya ko tunda gashi har abinci Naga take ci Umma ya jikin naki Tijjani yace Yana guntsa dariyar Dan sosai ta dage take yamutsa fuska.tana kakarwa ga hannunta duk.miya da Gefen bakinta Safiyya kuwa kamar ta fashe Dan bakin ciki sai hararar Hajaran take. Tijjani kuwa ya Kara cewa " toh nidai Bari na tafi Umma Bari na siyo Miki pcm na kawo Miki inaga zazzabi ne" Bakin ciki ne yasa Hajara mik'ewa ta hau zagin Tijjani Tijjani kuwa ya karasa Kan tabarmar ya zauna Yana dariya "Ka dauka.wasa nake maka ko ka tashi ka fitarmin daga gida. Wlh yanda nakejin zuciyata Tijjani Zan iya fasa.maka Kai Tijjani hannun Hajara.ya ruk'o.da k'arfi Yana cigaba da dariya har.sai daya zaunar da ita Yana "Allah ya bar.mana ke hajiarmu kiyi hakuri muyi magana" "Umma Dan Allah Dan annabi na hadaki da girman Allah ki daina duk abinda kike wa Yaya Naseer da matarsa Umma na rasa Mai Yaya Naseer ya Miki Kika saka shi a gaba kika.hana shi zaman lafiya da matarsa, Umma yanda kike da hakki Akan Yaya Naseer shima Yana da hakki akanki Umma karki biyewa tsinaniya yarinya Nan ta Kai ki ta baro tun muna Yara nasan yarinya Nan Shaidaniya ce babu alheri sam.a ranta Umma komai Naeema ta Miki ya Kamata ace kin hakura ko Dan zuria dake tsakanin ita da Yaya Naseer a iya sanina ba abinda ta Miki shima.yaya Naseer ba Abunda ya Miki da ya cancanci Abubuwan da kike Masa Umma har gidansa daya rage Masa kuka.siyar da.ke da shegiyar.yarinya Nan Umma idan ba Yaya Naseer ba wa zakuyi.wa.haka ya barku"? "Umma duniya ga ba gidan Zama.bane wlh watarana dole.mu mutu mu koma ga Allah Allah ya hallicemu ne Dan mu bauta Masa Umma.Allah baya san.zalinci ki daina amfani da.ikon da Allah ya Baki akan yaran ki.ki ringa cutar.dasu Umma Ni.ba yaro bane.duk.abinda.kikeyi ba akan daidai.kikeyi.ba ya Kamata ki gyara.kafin lokaci ya kure Miki Umma yau ba Dan kin Kona dukiyar Yaya Naseer ba da kema.kanki Baki tsinci kanki a irin wanan gidan Sabida wani.biyan bukatarki kiyi.karyar.ciwo ba umma nidai shawara ce nake Baki kibi Allah da manzonsa.ki tsarkake zuciyarki ki zauna da.kowa.lafiya ki koma.ga Allah kalau Umma mutum.da kansa yake Gina lahirarsa idan ya gina da kyau kiga da kyau idan ma.baki Gina da.kyau ba Umma ke Kadai Zaki zauna a kabarinki ki guji.hawayen.wanda Kika zalunta Dan idan.ya barki da Allah wlh Sai Allah ya saka Masa ko bajima ko ba Dade Umma wlh akwai rayuwa Bayan mutuwa wayanda suke kwance a kabarinsu karki gansu a kwance ki dauka bacci sukeyi wlh rayuwa ce sukeyi Mai tsayi cike da irin Rayuwar da.sukayi a duniya Wala khairan ko sharran "Umma.kiringa sallah kiringa azumi ko Zaki samu haske a rayuwarki ke Kuma Safiyya Ina tausaya Miki wlh Dan ke macece bakisan ya gaba Zata kasance Miki ba nasan halinki gabaki daya daga auren da kikayi Kika fito.ya isheki ishara.kigane ba akan daidai kike ba duniya gidan aro ce duk sharrin da kikayi ko Wanda Zaki saka ayi wlh zai dawo kanki ko bajima.ko ba Dade. Umma Dan Allah kiyi hakuri ki yarda makamanki Allah yayi aure Bai Kare tsakanin Yaya Naseer da Naeema ba ki Sanya musu albarka sukoma su zauna idan Baki sani ba ki sani Yaya Naseer Yana d'auke da hawan jini tunda kuka siyar Mai da gidansa yake fama da ciwon kirji umma.naseer dinan ke Kika haife shi ya Kamata ki tausaya.masa iya abinda Kika Masa ma.ya Isa Ni Zan tafi umma.ga wanan ba yawa Zan ringa lek'o ku akai akai" Daga haka Tijjjani.ya mike ya fice daga gidan.batare da ya ko kalli Safiyya data sada Kai tana tsine Masa ba. Hajara kuwa kamar wacce aka sawa Gam aka like Mata Baki Haka ta bi Tijjani da kallo Yana fita Safiyya taja uban Tsaki Tana "kawai Dan ance su kawo kudi ya hau waazi sabida tsinannen rowa ke Kuma Umma sai kikayi shiru Kamar bakida Baki" "Taya duk abinda Naeema ta.mana ma.mu kyalleta korarmu fa tayi.daga gidanta Yaya Naseer ya zabeta akanki daya rabu da ita har.ya gwammace ki Masa baki keda danki wata ta kwace Miki shi nidai karki sake ki saurari wanan Yaya Tijjanin bakinsa daya da Yaya Naseer Naeema ma.tana ganin Haka zatace taci Galaba akanki" Hajara sosai maganganun tijjani.suka shigeta hakane yasa jikinta Yi sanyi idan akwai abinda taji ba dadi Bai wuce Naseer data zalinta ba ta hanyar siyar Masa da gidansa Amma Naeema Kam ba abinda zaayi taji tana Santa Dan abune kamar ya tsaya Mata a kahon zuciya har sai ta fito dashi zata ji dadi fitowar kuwa shine ta samu cikar burinta akan ganin Bayan Naeema da take ganin ma duk halin da take ciki yanzu itace sila maganganun Safiyya Kuma ya Kara.tunzurata tana ganin tabbas idan ta bar Naeema ma taci Galaba a kanta abu daya ne tasan zatayi shine ta daina takurawa Naseer akan Naeema Amma fa Naeema sai ta kwashi kashinta a hannu Sannan sallah da azumi da Tijjani ya Bata shawarar ta ringayi zata ringayi Dan babanta cikakken musulmine Mai addini ko Kafin ta hadu da Yan kungiya tana sallah shigarta kungiya yasa ta daina sallah Amma yanzu zata cigaba da sallah da duk wani Abu da musulmi zaiyi na ibada tunda Bata cikin kungiya yanzu. A takaice Safiyya sai data Kara taso da maganar kudurinsu Akan Naeema data ga Hajara tayi wani sanyi Tsabar bakin Hali da mugunta ita ta cigaba da neman kudin da zata kaiwa bokan da zai Mata aiki akan Naeema A cikin irin wanan halin ta haihu Inda ta samu da namiji ta saka Masa suna Bashir Tunda Safiyya ta haihu duk rayuwarta ba abinda take so sama da Bashir danta sosai take cin burin inganta rayuwar Bashir Amma tana burin tarwatsa rayuwar yaran naeema. Ko arbain bata yi ba ta samo wani gida ta fara aikatau duk Wai Dan ta samu kudin da zata kaiwa boka ya Mata aiki Akan Naeema Dan duk wani motsin Naeema ta sani duk da tazarar dake tsakaninsu. Hajara kuwa itama.tana.kan.bakanta akan Naeema da yarta Zahira Amma Bata matsa can Kamar yanda Safiyya ta matsa ba Dan abinci ma wahalar samu yake.mata Dan aiken da Naseer da Tijjani ke mata ma idan Safiyya ta kyalla Ido taga kudin to Bashir zata kashewa kudin tana ji tana gani Bata Isa tayi Magana ba. Naeema Ban fasa adduoina akan yarana ba ban Kuma takura kaina da tsawon lokacin da Naseer ya d'auka Bai lekomu ba duk da Naseer Yana Raina inaso.naji ko lafiya yake. Ga yaransa.dake.balain takuramin da tambayarsa balle Nadeeya da har sai na hada Mata da Bugu wani zubin take kyalleni sadaka kuwa bana Wasa dashi. Dan Indai Zan tuna kallon da Safiyya tayiwa Zahira sai kirjina ya buga Gashi zahira girma take tana Kara Zama kyakyawar budurwa. Kullum sai an aiko ana Sallama da ita bakina har gajiya yake wajen cewa bana barinta zance Kuma.masu neman zahiran manyan mutane ne masu kudi daga Mai Mata sai samari. Yau daya kasance alhamis Ina zaune a tsakar gida Ina Yankewa Waleed farce shi da Raheema Zahira Kuma tana kitchen tana girki Nadeeya kuma tana wanke musu uniform dinsu tana ta zabga surutu a cikin surutun nata naji tana "Dazu fa Naga Aunty Safiyya a Gefen makarantar mu tana lek'omu tana ganin na ganta ta b'uya da Sauri" Cikin fad'uwar gaba na ajiye rezar hannuna Ina "kin tabbata Anty Safiyya Kika gani Nadeeya ba Mai Kama da ita Kika gani ba"? "Tab Umma ita na gani Mana sau uku kenan. Ina ganin ta idan taga na ganta sai ta b'uya mantawa nake ban Gaya miki ba sai Yau na tuna" Haka kawai naji hankalina ya tashi Dan Ni nasan ba alheri ne yake Kai Safiyya makarantar yarana ba har na Dan saki jiki danaga an tafi shekara ba abinda ya biyo baya Kuma abinda ya bani mamaki Bai wuce yanda take zuwa makarantar ba lura da ba unguwar mu daya ba Dan Isihu ya bani labarin suna zaune ne acan tsohuwar unguwarmu Dan Yana yawan zuwa gidansu aunty duk inada labarin zaman da sukeyi a can da haihuwar da Safiyya tayi da aikatau din da takeyi ita Kuma Umma na siyar da kosai a bakin titi Labarin Naseer ne kawai bani dashi Zurfin Dana Yi a tunani yasa Sam bansan Naseeru ya shigo ba sai ihun yarana naji suna ihun murna Abba Gabadaya zuwa sukayi Suka rungumeshi sun ma ki Bari ya Ajiye manyan ledojin daya shigo dasu. Ni kuwa Ido kawai.na zuba Masa Ina kallonsa ba laifi ya Dan ciko ba Kamar kwanaki ba Kuma har ga Allah naji dadin ganinsa Ido muka had'a ya Dan saki murmushi Yana "Hajajju Mai gida.zan.iya shigowa ko na koma"? Bance Masa komai ba Dan nasan magana ce yake gayamin a fakaice da Sunan gidana ne Bai Isa da gidan.ba Har Kan tabarma danake Kai ya karaso ya zauna yaransa suka ja manyan ledoji gabansa Ashe har da kayan abinci ya taho.mana dashi manja da doya dasu Dankali Ledojin Kuma Kaya ya siyowa su Zahira Ledar Waleed kuwa daban yake dan Waleed.ma Dora shi yayi a Kan cinyarshi Ni nasan a yaran mu gabadaya Waleed na daban ne a zuciyar Naseer yanda nakejin Kamar Zahira itama ta dabance a yarana ba Kuma komai ya jawo haka ba sai hankalin zahira da yanda take nuna tana Tausayina banida babbar kawa ma daya wuce Zahira yanzu tunda idan Abu ya dameni Ina Gaya mata ko Bata iya bani shawara ba Ina Jin sanyi a Zuciyata. Koni sai da Naseer ya cikomin Leda da Kaya na Kuma ji dadi Sai danayi dagske na nuna Masa b'acin Raina ya daina cemin Mai gidan Bamu samu kebb'e wa ba sai da Yara sukayi bacci Muka hau hira na dawo da maganar dalilin daya sa naki Bari ya zauna a gidana sabida yaranmu ne.ba komai ba Shima.yace min "Badan kin bijire bama da bansamu wanan aikin da nake yi ba dake Dan shigomin da kudi ba Dan a gaskiya a ranar Dana bar Nan naji Haushin abinda kikamin ban Kuma boyewa Tijjani komai ba na Gaya masa yacemin Kar na damu na Miki uzuri ba laifinki bane dole tasa kikamin Haka nayi hakuri har sai kin hucce sai na dawo ya Kuma nunamin kila yanzu idonsu Umma na kaina na daga kafar Kar Nazo Da shawararsa nayi amfani nake kwana a company mu kamar wasa. Mai gidanmu yamin tayin aiki a company su dake can Abuja ya Kuma bani Dan matsayi sabida rukon amanar daya ce Ina dashi Da wanan na koma Abujan na fara aiki ya bani daki daya nake kwana acan Ke.kadai ce bana yiwa aike Dan nasan kina da kudin da Zaki kula da yaranmu Amma Ina yiwa Umma aike na Kuma ringa Tara kudina har sai Dana ga sun isheni nazo.gida na duba ku na muku kwana biyu na koma Kinga dalilin dayasa ma Kika ga na kwana biyu ban lek'o ku ba banida burin daya wuce na samu kudi na siyi fili nayi gini Naeema inasan Naga Nima inada gidan kaina" Sosai nayi murna da aikin da Naseer ya samu da ke nuni Ana Dan biyansa albashi Na Kuma ji dadi daya kasance ba a garin nan ya samu aiki ba dan nasan ko bibiyarmu Umma keyi zata ji baa gidana yake zama ba. Zuwan Naseer ya mantar Dani batun ganin da Nadeeya tace tayiwa Safiyya. Sai da Naseer yayi sati kafin ya shirya yacemin zaije ya dubo Umma Dan gobe yake San wucewa Sosai naji dadin cigaban da Naseer ya samu Kamar nace Masa ya dib'arwa Umma Mai dasu doyan daya kawo Mana na Kuma fasa Dan bana San Masa shishigi yanda bayamin maganar Umma Nima bana San na Masa maganarta. Naseer kuwa a lokacin daya Isa gidan jikinsa ne yabi yayi sanyi dayaga yanda Hajara ta hade girar sama da kasa Tama k'i amsa gaisuwar daya Mata Dan a ranar daya dira garin Kano sai da Kawar Safiyya dake unguwarsu naeema ta Bata labari Saude da itama ta kasance bazawara tana aiki.a wani gida dake kusa da gidan da Safiyya ke Aiki Da biyu Safiyya ta kula kawance da Saude Dan ta ringa gaya Mata komai Akan su Naeema da yaran nata cikin Ikon Allah kuwa sai halinsu yazo daya ta mugunta da balain San bin Mallamai da bokaye saude ta tsani Naeema ne sabida ta daina Bata bashi idan taje Dan sako Naeema tayi da karbar bashi ba dare ba Rana Naeema tun tana.kawaici har sai data daina Bata bashin Dan idan saude.nada.kudi wani shagon take tafiya idan Kuma Bata da kudi sai ta taho shagon ta bashin data daina Bata sai ya tsayawa saude a wuya ba iya Wannan ba yarta dake Saar Zahira maimuna da ajinsu yake daya sai zahira tafi maimuna kyau da k'ok'ari sai hakan ya Kara asasa tsanar da take wa Naeema Safiyya na Mata maganar Naeema ta karbi maganar da hannu bibiyu hassada da kyashi yasa itama take San ganin Bayan Naeema data Mata fintinkau. Idan sun tashi daga wajen aikatau gidan su Safiyya take zuwa ta hau Basu labarin ai taga Naeema yau taga kaza taga kaza ahaka Hajara da Safiyya ke samun labarin duk motsin da Naeema tayi da yayanta Washegarin da Naseer ya dira garin da sassafe ta je gidansu Safiyya ta hau Basu labarin zuwan Naseer da lodin kayan daya kawowa su Naeema cikin akori Kura ta karkace ta Kara Gishiri da maggi. Sosai Hajara taji ranta ya b'aci ta hau jiran zuwan Naseer Amma ko gezau Naseer Bai zo ba ahaka take kwana da bakincikin zuwan Naseer gidan Naeema batare da ya waiwayeta ba ba abinda ya Kona Mata Rai kamar uban kayan da akace ya kaiwa Naeema wato ita Tana Nan tana soya kosai a Rana Naseer Kuma ya tare a gindin Naeema Safiyya kuwa a gefe zuga Hajara kawai take akan taci mutuncin Naseer. Sai gashi Naseer Bai tashi zuwa ba sai daya kwashi kwana bakwai a Rana na takwas kuma.haka.yazo musu babu ko.leda a hannunsa Naseer kuwa jiki a sanyaye yace "Umma ko akwai lefin da na Miki ne"? Girgiza masa Kai tayi tana "ba wani laifin dakamin Naseeeru ya wajen aikin ya wajensu Naeema yaushe kazone? Da Zuciya daya Naseer yace "kwana bakwai kenan da zuwana Umma na Dan yi.ziyarce ziyarce gobe Zan koma nace Bari Nazo na Miki Sallama dafatan.sakona Yana Isa wajenki" "Eee Yana isa wajena Kam Ashe kwana bakwai.kayi a garin Nan Amma sai yau kazo ganina Kuma daka tashi zuwan sai.ka.taho Haka" "Yi hakuri Umma nayi laifi Abunda yasa banzo da komai ba Dama kudi nayi niyyar Baki shiyasa ban taho da komai ba" "Toh yayi.kyau Naseeru" Daga Haka Bata Kara cewa komai.ba ta ringa kudurta Abubuwa a ranta. Naseer kuwa banza ta bawa ajiyarsa sai daya gaji Dan kansa ya ciro kudi Mai Dan yawa ya Ajiye Mata a gefenta Yana "Umma bari na koma inaso naje gidan Tijjani akwai maganar da zamuyi gobe Zan koma insha Allahu" "Allah ya bada saa" Daga Haka Bata Kara cewa komai ba ya tashi ya tafi Safiyya dake labbe a d'akin kusa dasu ta fada d'akin tana "Mai na Gaya miki Umma wlh Naeema ta kwace Naseer yanzu ya fara samun kudi a madadin ya kawo Miki sai ya ringa kaiwa shegiyar Naeema da take da uban kudi Kinsan kuwa saude tacemin layi akeyi a gidan ta masu San wanan shegiyar Yar tata mai.kama da Aljanna Haka suke cicika ledoji suna kaiwa Gidan Mu kam muna Nan a wahalce kina siyar da kosai Cikin bakin ciki Hajara ta dau kudin da Naseer ya Bata tana "Hada da kudin Nan da kike tarawa kiga idan ya Kai kije gurin mutumin nan ya Mana aikin Nan nida Dana ta rabamu ta karfi da yaji zata Gane shayi ruwane Maza jeki duba min kudi Nan idan sun Kai gobe da sassafe ki tafi wajensa Cikin murna Safiyya ta jawo gwangwanin kudin da suke Tarawa ta fito da kudin ciki ta had'a taga kudin ya Isa ta hau murna Dak'yar tayi bacci sabida tsananin mugunta da asuba suka dau hanya.ita da Saude. Sai da aka Dade layi yazo kansu cikin mugunta Safiyya ta karkace ta hau gayawa boka bukatar ta akan Zahira 'Yar Naeema data tsone Mata Ido sau uku tana zuwa makarantar Dan kawai taga wayanda ke muammalla da zahiran Sai Kuma abin yazo a daidai makarantarsu Zahira daya da Yar Sauden. A gajiye Suka dawo gida suna dawowa Suka.samu hajara suka.hau Kora Mata jawabi Kamar Haka "Umma Kinga abinda ya bamu Kamar yanda na fada Miki ayi Mana Aiki Akan zahiran ta ringa sata Kamar b'era toh gashi ya bamu wanan yace mu samu zahiran ta Sha alewa ne Kato kamar suga yace ko kad'an ta diga a bakinta wlh b'era ma.bazai Kai ta sata ba kuma ko a Ina ta zauna sai tayi satar" Wani.irin dariya Suka kwashe dashi gabadaya Hajara tace "Haka nakeso Saude gashi nan ki bawa yarki Maimuna ta jawo zahira jiki ta Bata tunda kince ajinsu daya idan.ta kama.ne.ma ta siyi alewa da Sunan sadaka ta rabawa.yan ajin gabadaya yanda zahiran zata saki.jiki ta Sha" Jiki na rawa Saude.ta karba tana doki Dan ta tsani Zahira sabida yanda ta yagawa yarta ko ta Ina Haka.kuwa akayi tana zuwa gida ta siyo alawa Mai irin gidan alewar da zaa bawa Zahira ta bawa maimuna akan gobe ta rabawa Yan ajin wanan Kuma ta tabbata ta bawa Zahira ta Sha. Washegari kuwa Haka maimuna tabi Yan ajinsu da alewar.ta dau na maganin ta mik'awa Zahira Sai dai me duk yanda taso Zahira ta karbi alewar kin karba tayi tace ita Bata Shan alewa kashe Mata hakori yake Rai ba dadi ta taho gida da alewa a hanya ta Dan bude alewa taki yawunta ya tsinke ta gutsuri kad'an ta Sha Ta maida cikin ledar ta kaiwa Saude ta Gaya Mata yanda sukayi da zahiran Saude.kuwa cikin Jin Haushin ta karbi alewar taje gidansu Hajara ta Gaya musu Safiyya kuwa ta karba tana Kar ta damu wlh gobe sai ta danne Zahira ta Sha alewar Nan Hajara kuwa cewa take ta tabbata ta danne ta Dan bazata yi asarar kudinta a banza ba. Da mugun nufi Safiyya ta ajiye alewar tana Shan alwashin har aji zata je.ta danne Zahira ta saka mata alewar a Baki. Daddare ta fita Dan ta siyowa Bashir danta kamu ta Dama Masa tana dawowa taga ledar alewar a hannunsa Yana mumul mumul da Baki. . Cikin tashin hankali ta saki ihu ta nufi wajen Bashir din.......... *A DAINA BIYONI ANA MIN TAMBAYOYI AKAN LABARIN NAGA TA KAINA A DAINA KIRANA ANA MIN TAMBAYOYI AKAN LABARIN NA GA TA KAINA DUK MAI SO YA CIGABA DA BIBIYAN LABARIN A DAINA CEMIN DAGASKE NE KO BADA GASKE BANE SANAN DAN ALLAH DAN ANNABI A DAINA CEWA NACE ZAHIRA ZATAYI KARUWANCI NI NAFEESA BANCE HAKA BA BA KUMA A JI A BAKINA BA DUK WANDA YAKE GANIN BAZAI IYA CIGABA DA BI BA DAN ALLAH BAN MASA DOLE BA YA HAKURA NGD* *NAGA TA KAINA* *NA SADNAF*🌸🌸 ®️ *_PURE MOMENT OF LIFE WRITERS_* _{We Don't just entertain nd educate we also touch the heat of readers P.M.L}💪🏻_ *Free Novel* *Page 49* Hajara kuwa data fara Dan gyangyadi ihun Safiyya ne yasa ta mik'e a firgice a daidai lokacin da Safiyya ta Isa wajen Bashir din ta kwace ledar hannunsa ganin babu alewar a ciki ta saki ihu Tana "Nashiga uku na lalace Bashir ya Sha alewar" Ta Danna hannunta a bakin Bashir din Dan ta ciro alewar da Sauri sai dai tana Danna hannunta sauran alewar ya wuce Bashir ya hadiye alewar hankali a tashi ta hau zurmaka hannunta gabadaya a bakinsa tana dukan bayansa Wai duk Dan yayi amai amma a banza Dan kakarin amai yayi kawai baiyi Aman ba hannu Safiyya ta Dora a ka tana "Umma kin cuceni Bashir ya Shanye alewar Sata Umma kina zaune anan fa Bashir ya d'auki. Alewar ya sha Baki Hana shi ba" "Ta Ina na ganshi nida bacci ya fara daukana ki kwantar da hankalinki ba abinda zai faru gobe da sassafe sai muje wajensa mu Gaya masa A ranar Safiyya ko kad'an batayi bacci ba hankalinta a balain tashe tana tsoron ta budi Ido taga dan data ci buri akansa ya Zama likita ko Dan siyasa ya zama barawo idan ta tuna yanda bokan yace Zahira zata ringa sata sai cikinta ya murd'a ta tafi bandaki Sosai taji Haushin Hajara tana ganin har da sakincinta yasa Bashir ya sha alewar Dan tana d'akin Bashir ya d'auki alewar. Gari Bai Gama wayewa ba ta Sabi Bashir a baya Hajara sanin halin Safiyya da azabar masifa yasa ta bita Dan ita Kuma Haka kawai take shak'ar Safiyya tana Kuma tsoronta. Sai da suka Dade kafin su samu ganin bokan Suna Shiga Safiyya ta kunto Bashir daga bayanta tana "ka taimaka min an samu matsala d'anna ne.ya Shanye alewar a taimakamin a rufamin asiri" "Garin ya ya Shanye alewar"? Cikin kuka Safiyya ta bashi labari shi kuwa bokan ya girgiza Kai Yana "Ba abinda zan iya Yi akai Dan ke kikace muyi aikin da duk abinda maman yarinya zatayi bazata iya karya shi ba hakane yasa Dana hada maganin na baki Akan ki zuba a cikin ruwa indai ya baje toh Mai karya asirin sai ya iya hado maganin daga cikin ruwan zai karye" Ihu Safiyya ta ringa zunduma wa.tana ya rufa Mata asiri zata bashi ko nawane Hajara itama ta hau rokonsa shi kuwa yace musu ba abinda zai iya Yi akai Amma suje zai nema idan ya samu zai Basu. A Haka suka dawo Safiyya na zunduma.kuka Bata tab'a kawowa Bashir ne zai Sha alewar ba Hajara kuwa sai rarrashinta take Safiyya na daka Mata tsawan Akan laifinta ne sakacinta ne yasa Bashir ya Sha alewar sai rashin kunya takewa Hajara tana neman zaginta Amma Hajara Bata ce Mata komai ba Ko baccin kirki Bata iya yi Sabida tashin hankali kasan zuciyarta kuwa wani balain tsanar Naeema da zahiran ne ya Kara rufeta tana Jin duk a sanadinsu danta ya Sha alewar Sata ya Zama Dole ta d'au fansa sai ta wahalar da Naeema ta wahalar da Zahira da Bata ji ba Bata gani ba matsawar danta ya tashi da sata abinda zata yiwa Zahira Allah kadai ne ya sani Hankali dai ba akwance ba kullum cikin Zullumi ta cigaba da fita aikatau da zumar samun wasu kudin ta Kara komawa wajen bokan Dan yanzu zuciyarta Kara taurara yayi wajen San ganin bayan Naeema data Mata Karen tsaye a idonta ma gani take Kamar Hajaran ta fara sanyi da batun Naeeman Sosai tayi mamaki da ganin Saude Bata Zo musu ba kwana biyu ganin an tafi Wajen wata Bata ganta ba yasa ta shirya bayan ta dawo daga aikatau ta nufi unguwarsu Naeema Wajen karfe Biyar na yamma ta nufi unguwar tana zuwa tun kafin ta Isa gidan Saude ta hango wani dalellen mota a k'ofar Gidan Naeema. Mai gidan da take wa aikatau Yana jingine a bakin mota Yana kad'a mukullin motarsa Wajen shagon Naeema kuwa cike da.mutane masu siyayya Wani irin bakin ciki ne ya cika kirjinta Ta jingina da bango tana tunanin Mai Alhajin Saad yake Yi a k'ofar Gidan Naeema ko shima siyayyan yazo shagon Naeema. Tana tsaye taga yaron daya aika cikin gidan ya fito wajen sa ko Mai ya Gaya masa oho ya Kara aika shi gidan. Sai gashi yaron ya dawo wajensa da Minal biye dashi Ji tayi inama.tana Jin Mai suke cewa Tana kallo Alhaji Saad din ya bud'e bayan motarsa ya fito da manyan ledoji ya mik'awa Minal ta ja da Baya tare da girgiza Masa Kai Ganin Taki karba yasa ya mik'awa almajirin ya bashi kyautar kudi tare da Shiga motarsa ya tafi Tsabar bakin ciki har wani dafe kirji Safiyya tayi tana tsaye Naeema ta fito.tana sanye da hijabi ta taso.almajirin da ledar daya Shiga gidan sai Masifa take Sam Safiyya ba jiyo abinda take fada take ba har ta gama ta Kira Isihu dake shagonta ta bashi ledar ta koma ciki. Safiyya zuciyrta cike da tunani ta Shiga gidan Saude Inda ta tarar da ba kowa a gidan. Ta fito daga gidan kenan taci Karo da Saude data shigo gidan itama a firgice hannunta rik'e Dana Maimuna data ci kuka ta gode Allah rigarta duk a yayyage Saude tana ganin Safiyya ta fashe da kuka tare da rike hannunta suka koma ciki Suka zauna akan tabarma. Safiyya kuwa ta bi maimuna da.kallo da.kayanta ya yayyage tana "Wai Saude lafiya kuwa yana ganku Haka Mai ya samu maimuna Haka"? "Safiyya Ashe alewar Nan da muka bawa Maimuna ta bawa Zahira sai data gutsara ta Sha a ciki bamu sani ba tunda ta Sha take jawomin magana sata ko ta Ina rabona da cikakken bacci wlh na manta Safiyya shiyasa ma bakya gani na koni Maimuna Bata kyalle ba duk abinda ta gani a gidnan dauka take idan kuwa ta fita waje sai dai azo a kirani ace gata can an Kamata tayi sata. Yanzu ma Haka wani babban shago taje ta yi sata kafin azo a gayamin shine aka Tara Mata jamaa aka fara dukanta aka yayyaga Mata Kaya har wajen Yan sanda suka Yi niyyar kaita sai danayi ta hadasu da Allah da annabi Safiyya Ina zaman zamana na Kai kaina Halaka na cuci kaina garin tsinannen.kwadayi irin na yarinya Nan taje ta gutsuri alewar Nan ta sha. Ihun da Safiyya ta saki tana Dora hannunta aka yasa Saude ta tsayar da maganar da take Safiyya ta hau birgima a kasa tana "Na Shiga uku Saude Bashir Nima ya Shanye duk alewar idan har maimuna gutsura kawai tayi take wanan Satan Ina ga Bashir daya shanye duka Na Shiga uku Saude na Shiga uku yanzu Haka Bashir zai ringa sata naje gurin bokan akan ya karya Mana asirin yace bazai iya ba sai dai ya duba" Kuka take sosai Ita kuwa Saude ajiyar zuciya ta sauke tana Jin Sanyi a zuciyarta da ba iya maimuna ce zata yi Satan ba har da Bashir Amma a fili kuwa kuka ta hau Yi tana sun Shiga uku yanzu ya zasuyi ahaka suka Gama jajjantawa juna suna tunanin neman kudi su nemi wani ya karya asirin Safiyya kuwa ta hau yiwa Saude tambayoyi akan Naeema Saudee kuwa ta hau Bata labarin yanda manyan masu kudi suke Neman Zahira masu nemanta har da Yan siyasa ta had'a da Gaya Mata taga Alhaji Saad ma Yana zuwa gidan shima Wai San Zahira yake Wani irin abune ya tokare zuciyar Safiyya Dan so tayi Zahira ta ringa sata tayi bakin jini a wajen Samari Amma tunda abin ya koma kansu ya zama Dole su sake wani shirin Akan Zahira Dan sai ta samu cikar burinta zata samu kwanciyar hankali ahaka suka Kara kudurta mugayen Abubuwa akan Zahira Saude ta raka Safiyya ta tafi Naeema Maneman Zahira tuni suka isheni da sintirin da suke min a k'ofar gida Zahira yanzu tana da shekara Sha shidda tana Kuma jss 3 Sam ban shirya ta kula wani saurayi ba Dan inada burin tayi karatu Mai zurfi ba ita kadai ba har sauran yarana Ina burin suyi karatu Mai zurfi tunda Ni bansamu wanan damar ba Amma ga mamakina ko secondary Zahira Bata Gama ba masu nemanta da Aure sun Sako mu a gaba suna Santa da aure akwai wani Alhaji Saad danaga yafi matsawa da zuwa har aikowa yake akan Yana Sallama da Naseer a ranar Dana fita. Dan na bashi hakuri Akan ba yanzu Zahira zatayi Aure ba Yana ganina ya tsugunna ya hau gaisheni Ni kuwa na bashi hakuri akan ba yanzu zaayi yiwa Zahira Aure ba yayi hakuri. Daga Haka na koma ciki sai dai ga mamakina Bai fasa cigaba da zuwa ba A ranar daya zo na karshe ya Bata min Rai Dan Yana aikowa nace ace Bata zance ya Kara aikowa na tura Minal Akan ta bashi hakuri sai dai suna dawowa Naga Almajirin daya fara aikowa da Niki Nikin Kaya Wai a bawa Zahira Ban Bari ma ya karasa shigowa ba na wafci hijabina na fita dan na Masa kashedi sai dai Ina fitowa Naga har ya tafi. Hakane Yasa na bawa Isihu Ledojin akan ya Ajiye duk ranar da Alhajin Nan ya dawo a bashi kayansa. Na koma ciki Ina Shan alwashin idan Naseer ya dawo ya zama Dole muyi shawara dashi Dan abinan ya isheni. Bayan tafiyar Naseer da wata biyu sai gashi ya sake dawowa da Niki Nikin Kaya na Kuma ji dadin yanda Naga ya fara samun kwanciya hankali Dan ba laifi ya samu alheri daga labarin daya bani Kamar dai wancan lokacin sai daya kwana biyu kafin yaje wajen Umma da Saude har ta isar mata da labarin zuwansa har da Karin gisihirin da sai da Hajara ta ji tazo wuya tsanar Naeema na cike Mata wuya. Duk da Naseer ya tafar Mata da abubuwa har da kudin. Sam hakan Bai faranta Mata ba burinta kawai taga bayan Naeema Saffiya kuwa abinda take so kenan ta hau zuga Hajaran har sai data rabata da kudin da Naseer ya Bata ta had'a Dana wajenta ta kwashi Saude Suka koma wajen boka suka hau Gaya musu abinda suke so ya musu cikin tsananin mugunta. Shi kuwa ya d'auko kwai guda biyu ya bawa Safiyya ya fada mata yanda zasuyi da Kwan a bayan Kwan kuwa sunayen Zahira ya rubuta kaca kaca Jiki na rawa suka koma gida Safiyya ta Adana Kwan ta hau neman Wanda zai Mata aikin batare da an samu wani matsala ba. Naseer kuwa Dana Masa maganar takuran da akewa Zahira cemin yayi kar na damu na Bari idan ta Yi placement sai a Mata transfer ta tafi boarding inyaso sai ta cigaba da ss dinta a wajen Dan shima.yana so yaga yaransa sunyi ilimi har ga Allah banasan yarana sumin nisa ballantana Wai su tafi boarding Amma ganin Naseer ya dage yasa na hakura Yaje makarantarsu ya musu bayanin idan sun Gama placement Yana so ayi Mata transfer zuwa makarantar boarding. A ganinsa a boarding ma anfi karatu. Tafiyarsa da kwana goma Ina cikin bacci nayi mumumann mafarki daya Sakani farkawa Bakina d'auke da sallati na kunna fitilar d'akin tare da haska yarana Naga duk bacci sukeyi cikin kwanciyar hankali Ajiyar zuciya na sauke na fito da zumar nayi alwala Dan Dama lokacin tashina yayi biyun dare har na Saba Dayake dare ne sosai buta na dauko daga bandakina Dan na Debi ruwa Dan na bandakina ya Kare. Sai dai maganganun danake ji kasa kasa yasa a bakin k'ofata yasa na tsaya cak gabana na fad'uwa. Muryar namiji da mace nake ji Hakan ya sa na nufi bakin kofar jikina na rawa Kasa kunnena nayi naji macen na "ka buga k'ofar tana bud'ewa ka jefa Kwan cikin gidan Shi Kuma Yana shi tsoro yake ji Idan aka kamashi fa Bansan lokacin Dana bud'e k'ofar ba matar ta dib'a a guje. Ni kuwa na rik'e Namijin Gam dake k'ok'arin guduwa saan Isihu ne ya ringa k'ok'arin kwacewa hannunsa d'auke da wani kwarya Cikin rawar jiki na kwace Kwaryar Ina rik'e da yaron da hannu daya....... *TOH SAI KUMA BAYAN SALLAH IDAN ALLAH YA KAIMU RAI DA LAFIYA* *NAGA TA KAINA* *NA SADNAF*🌸🌸 ®️ *_PURE MOMENT OF LIFE WRITERS_* _{We Don't just entertain nd educate we also touch the heat of readers P.M.L}💪🏻_ *Free Novel* *Dafatan munyi sallah lafiya Allah ya maimaita mana Ina muku fatan alheri Nagode da so da.kauna* *Page 50* Sosai ya ringa k'ok'arin kwacewa na rikeshi Gam Dan burina na ajiye Kwaryar da Naga kwayaye biyu a ciki na tambayeshi wacce matar data saka shi wanan aikin har lokacin jikina rawa yake.ina Jan innalillahi wa Inna ilaihi rajiun Cizon daya kaiwa hannuna da balain k'arfi yasa na cika shi ba Kuma zafin cizon yasa na cikashin ba bana San Kwaryar hannuna ya Fadi Kwan ya fashe tunda daga maganar Dana ji matar nayi so take Ana bud'e gidan a jefo Kwan tsakar gidan ya fashe Da mugun gudu ya dib'a Dana sake shi Ni kuwa na tsaya kamar mutum mutumi nabishi da kallo har sai Dana Diana hangosa. Dak'yar naja k'afata na koma ciki adduoi da nake tayi ya Dan sama min nutswa Ajiye Kwaryar nayi na kulle gidan.na Kara d'aukar Kwaryar na nufi dakina jikina na rawa A Gefen gadona na zauna na Dora Kwaryar a cinyata bakina d'auke da Addu'a na dauko.kwan guda daya na hau jujuyawa Ina kallon jan rubutun da akayi a jikin Kwan da Sunan Zahira ko ta Ina Sallatin da nakeyi ne yasa Zahira ta bud'e Idonta Dan Bata da nauyin bacci Sam Hawaye kawai nake Ina cigaba da jujuya Kwan a hannuna bansa lokacin data ma taso ta iso gabana ba sai muryarta naji tana "Umma lafiya kike kuka Mai ya faru"? Dagowa nayi na kalli Zahira da nake ganin kamar Jiya jiya nan na haifeta duk da ta girma ta zama budurwa.hakan Bai saka na daina Mata kallan yarinya ba Amma Wai Zahiran makiyana ke San ganin bayanta Sai a lokacin na tuna kallon da Safiyya tayiwa Zahira daya saka gabana tsinke wa ta Kara da na jira Naga balain da zata jefomin sai a lokacin na fashe da kuka.mai karfi Dan na d'auka ba abinda zai biyo baya tunda an kwana biyu Ashe suna kan bakansu Kuka nake sosai Ina kallon Zahira da Abu kad'an ke sakata kuka itama tuni ta hau kukan tana cigaba da tambayta abinda ya faru nake kuka. Nikam na rasa Mai nayiwa Umma da Safiyya a rayuwata mai na musu da zafi Haka da zasu bar kaina su dawo Kan yata da Bata musu komai ba. Wane irin kiyayya ne wanan suke min da Bai tsaya iya kaina ba har da diyata da muka Haifa da Naseer daya kasance jinin Umma ban taba kwokwanto a Raina na Umma ce ta haifi Naseer ba Amma zuwa yanzu na fara kwokwanto Dan ba iya Ni Umma ta tsana ba har da Naseer tunda ba Ni kadai na haifi Zahira ba Allah ne kadai yasan Mai Suka so yiwa Zahira Allah ya karemu na fito har na samu kwace Kwaryar daga hannun yaron da suka turo. Sosai hankalina ya tashi a Daren. Sallah ma ba a nutse nayi ba zuciyata na cike fal da tunani da tsoro tunanina ya rarrabu gida biyu jefi jefi nake dagowa na kalli Zahira dake gefena itama sanye da hijabi tausayin yata na Kara Sakani zubar hawaye duk cikin yarana babu Mai sanyin halinta da tausayin iyaye idan na tuna abinda Zahira tamin a lokacin da nake d'auke da cikin waleeed da muke cikin tsananin talauci har kuka nake nayita Mata adduar samun nagartacen miji lokaci bamuda komai a gidan dak'yar na samo musu garin kwaki Suka Sha suka kwanta itama sai Dana tilasta Mata Tasha Dan dagewa tayi sai dai Nima na Sha Wanda Ni nasan ko Ni na Sha garin Nan ba Inda zai kaimin ni xan iya hakura tunda yarane duk da balain yunwar da nakeji da ke Sakani Jin jiri Da wuri suka kwanta Ni kuwa bacci yak'i zuwarmin sai.juye juye nake Ina Dan hawaye Dan yunwa nake ji ba kadan ba ga jikina dake balain rawa. Ashe duk halin da nake ciki Zahira na kallona magana ne.kawai batamin ba. Mik'ewa nayi Ina bin bango sabida rawar da jikina keyi na fita kitchen Dana San babu abinda Zan samu na sawa cikina bansan lokacin da Zahira ta fita ba sai motsin bud'e kofa naji daya sakani.fitowa daga Kitchen da Sauri nayi wajen. Ban hango.kowa ba hakane yasa na dawo d'akina da Sauri anan nagane Zahira ce ta fita waje Ciikin tashin hankali nayi waje. Ina dube dube Ina mamakin Ina Zahira ta fita daddare Nan Sunanta na hau Kira da k'arfi Zahira kuwa Ashe data fita gida gida ta ringa bi tana rokonsu abinci wasu kuwa har zaginta suke Akan me zata buga musu gida suna bacci Wasu Kuma Haka zasu zageta ahaka ta cigaba da bin gida gida har ta iso wani gidan data ganshi a bud'e Tana Shiga ta zub'e a kasa cikin kuka ta hau ce musu "Dan Allah ku taimaka Mana da abinci ummana yunwa takeji ta kasa bacci" Daga Mai gidan har matar gidan tausayin Zahira ne ya rufesu duk da basu Santa ba. Abincin da matar ta kawowa Mai gidan da shima Bai Dade da dawowa ba suna Dan tab'a hirane hakane yasa Bai ci abinci ba Magana ya yiwa matar Akan ta Nemo Leda ta juye mata abinci shi Kuma zai Sha shayi da bredi Matar mik'ewa tayi ta d'auko Leda ta juya tuwon dake da Dan yawa a bak'ar Leda ta juye miyar yauki shima a wani Leda ta hadasu a wani Leda ta mik'awa Zahira data mike da Sauri ta wafci ledar tana ta gode. Ta fita a guje cikin murna duk da tsoronta da karnuka Haka ta ringa tikar gudu tana murna samo min abinci Ni kuwa hankali a tashe na koma ciki na Sako hijabi na Dan na nemota sai dai jiri kawai ke d'ibana jikina na rawa kasa mik'ewa nayi Dana zub'e a tsakiyar dakina. Kamar Wasa naji shigowrta tare da rufe k'ofar Gidan. Kitchen naji ta shiga Ni kuwa na hau sauke ajiyar zuciya dawowa da tayi Shigowa tayi da kwanu a hannunta daya hannun nata Kuma ledar tuwon ne. Kamshin abinci yasa naji jikina ya Kara kwasar wani rawan Ina kallonta ta juye tuwon ta zuba Miya a wani kwanun shima ta kawo shi gabana tana "Umma gashi na samo Miki abinci kici Bari na d'ebo Miki ruwa ta Kara yin waje. Ni kuwa banyi wata wata ba na hau Danna tuwon a bakina Ina hawaye. Dan inaganin tsaf Zan sume da ban samu tuwon nan ba fada nayi niyyar Mata Amma Ashe abinci taje Nemo min Kafin ta kawo ruwan ma har na kusa cinye Rabin tuwon Sai da tuwon ya kusa karewa naji hankalina ya dawo jikina jikina ya bar rawa. Ruwan data ajiye a gabana na kafa kaina na Sha Koshin da nayi yasa nayi hamdala a madadin nayiwa Zahira fada sai na hau shi Mata albarka Ashe dai yunwa masifa ce Dan sai yanzu na dawo daidai Abinan da Zahira.tamin a matsayin ta na diyata Yana cikin Abubuwan da bana mantasu ahaka tana yarinya tasan tausayin iyaye inaga ta girma. Amma Wai Zahiran Kuma su Umma ke San ganin Bayan ta Mai ta musu da zafi Haka A dadafe na yi sallah asuba Na tashi yarana sukayi Zahira kuwa ce Mata nayi kaina ke ciwo badan ta yarda ba ta hakura ta daina min tambayoyi. Yanzu su suke min komai hakan yasa ban bar d'akina ba Suka had'a hannu Suka Gama aikin komai na gidan suka fara shigomin d'akin Akan sun shirya zasu tafi Kansu na dafa daya Bayan daya Kamar yanda na Saba na musu addua suka ringa yin waje sai Dana Zo kan Zahira nace "Zahira kiringa addua kinji Allah ya kareki daga sharrin mutum Dana Aljann kiringa karanta ayatul kursiyyu Kafa bakwai idan Zaki bar gidan Nan idan kin dawo ma ki karanta ki kasance a cikin addua kullum Allah ya kareki da karewarsa karkiyi Wasa da Addu'a kinji Zahira Allah ya Miki albarka ban taba nufar Dan kowa da sharri ba insha Allahu ba Abunda zai sameki ki tsaya kiyi alwala sai ki tafi" Kallona kawai take har na idda maganata amadadin tayi wajen sai ta tsugunna daidai k'afata tana "Umma ko dai wani abune zai sameni dazu da nake shara Naga kwai a cikin kwarya da sunayena" Girgiza Mata Kai nayi da Sauri tare da mik'ewa. Ina "ba Abunda zai sameki Zahira Kar ki Kara kallon Inda Kwaryar Nan yake Abbanku nake jira ya dawo maza jekiyi alwala ki tafi karku makara" Na nufi wajen Dana ajiye Kwaryar da shima yake d'auke da Jan rubutu da sunan Zahira na d'aga katakon gadona na saka a karkashin gadon Dan so nake idan Naseer ya dawo na nuna Masa Yaga shaida wlh bazan d'auki a tabamin Yara ba" Yanda nake Jin jikina ma kamar na Hana Zahira. Tafiya makaranta Dan sosai nake a tsorace gani nake zasu iya binta har makaranta su Mata wani Abu Amma ba yanda Zan hanata tunda Bai fi sati biyu su zanna jarrabawa Gama jnr secondary ba" Har waje na rakasu Bayan tayi alwala yanda take Abu jiki ba kwari yasa na kwantar Mata da hankali har na daina hangosu gabadaya zuciyata ba dadi Haka na dawo gida Ina kukan tashin hankali da nake ji a jikina Yana tunkaroni a da na dauka na samu kwanciyar hankali Ashe akwai wani masifar dake tunkaroni bansani ba Masifar da nakeji zuciyata bazata iya dauka ba idan har su Umma suka ci Galaba Akan Zahira ga irin abinda nake gayawa Naseer Nan da har yake Jin haushina. . A ranar kasa komai nayi zuciyata na wajen su Zahira abincin rana ma ban iya Yi ba karshe dai waje na fita Dan sosai naji na kasa samun kwanciyar hankali sai Dana hangosu hankalina ya kwanta na koma ciki na daura alwala azahar. Ina iddar da sallah na fito na Dora musu farar taliya Dan inada Miya Sai a lokacin na daure na saka Abu a bakina shima Dan Kar Zahira ta zargi wani Abun Dan nasan halin ta A takaice ahaka na ringa dari dari indai su Zahira suka tafi makaranta sai sun dawo hankalina ke kwanciya Bacci Kam bana Iya yin shi cikin nutsuwa Rabin Daren rayya shi nake Ina kaiwa Allah kukana haka ma nake tashin Zahira tayi duk da Bata iya jurewan tana Yi sai dai na juya naga tayi bacci Ban iya larabci ba da hausa nake adduoina Dan nasan ba yaren da Allah baya ji Yana jina Yana Kuma ganin duk abinda ke faruwa Dani Allah yasan zuciyata tayi rauni bana Jin Zan iya jure ganin wani Abu ya Samu yarana da nake ganin su kadai ne farinciki na a gidan Duniya a lahira kuma Allah ya bani Aljanna. Har wani irin Rama nayi Sabida tashin hankali Dan idan dare yyi Haka Zan ta sintiri daga d'akina zuwa kofar gida Wai ko zasu Kara aiko wani. Duk da ban Kara ganin kowa ba sabida dadewar da akayi hakan bai saka na saki jikina ba A ranar laraba da bazan manta ba na Kara sanin suwaye Umma Ina zaune a tsakar gida Ina tsince wanke da Zan Mana abinci dashi ba kowa a gidan Dan dukansu sun tafi makaranta Isihu ma ya tafi wajen Aunty matar Mallam zai Kai Mata sako Sai dai idan anzo siyan Abu na Shiga ta tsakar gida na bada abinda aka zo siyan. Sallama da naji da yazo daidai da bugun zuciyata yasa na Dago bakina d'auke da Addu'a na amsa Sallamar a daidai lokacin da Wata Saude da take makociyarmu ta shigo makociyata ce data takuramin da karbar kayana Bata bani kudi hakane yasa Dana gaji na daina Bata shima su Nadeeya ne suka cemin tana zuwa wani shagon siyan Abu da kudi shagona ne take aikowa karbar bashi ko a yanzu ma data shigo bazan iya tuna adadin kudina dake wajenta ba. Cikin sakin fuska na Mata iso dana ga fuskarta a sake tana sanye da dogon hijabi hannayenta a ciki. Tabarmar danake Kai na Kara bajewa Ina "Zauna Mana mmn maimuna" Cire takalminta tayi ta hau Kan tabarma ta zauna tana "mmn Zahira Ina wuni" "Lafiya Lau ya su maimuna"? "Suna Nan kalau" Tace tana cigaba da jujuya hannu a cikin hijabi Ni Kuma Haka kawai naji zuciyata na bugawa bansan dalili ba. Adduoi kawai nake a Zuciyata ita kuwa tayi shiru Bata ce komai ba Ni kuwa nace Mata lafiya Dan bata Saba shigomin ba balle nace shigowa tayi Dan mu gaisa Murmushi tayi tana lafiya Lau shigowa kawai nayi mu gaisa Ni kuwa da zuciyata ke cigaba da bugawa nace mata ta kyauta na mike na Shiga kitchen na debo Mata ruwa a Raina Kuma inata addua fad'uwar gaban da nakeji tunda ta shigo Ina Kuma mamakin dalilin zuwan nata da Sam ban ji na yarda da ita ba Agabanta na ajiye ruwan Ina "Bismillah ga ruwa" Girgiza min Kai tayi da Sauri tana ta koshi har lokacin hannunta na cikin hijabi tana Dan kalle kalle "Ke kadai ce kenan a gidan banji Motsin su Zahira ba"? Tace cikin murmushi Nima cikin murmushi nace Mata eee wlh Ni kadai ce. Sallama ake ta rafkawa ana San siyan Abu Amma fir naki tashi Dan Sam ban yarda da Matar Nan da ta shigo min ba ita kuwa cewa take na tashi Mana na sallami customers Dina Ni kuwa na girgixa mata Kai Ina "ba wani abin arzkik zasu siya ba abinda ma suke nema babu" Na karasa Ina karantar yanda tayi Jim Bata ji dadin magana ta ba Hakan kuwa yasa na Kara gasgata zargin ba alheri ne ya kawota gidana ba. Zama na gyara sosai Ita kuwa ta cigaba da kame kame tana surutun ta ita kadai Ni kuwa jinta kawai nake Ina mamakin abinda yasa ta saka hannayenta a hijabi Sanin Dana Mata ma ba ma'abociyar saka hijabi bace ban dai ce komai ba na cigaba da wayancewa kamar gyara waken nake Amma idona na kanta Muryata daya doki kunnena da "Mmn Zahira wlh fitsari ne ya matseni Ina bandaki nayi Dan Allah" Sosai naji kirjina ya tsananta Bugu jikina na kwasar rawa Sai Dana dau mintina kafin na iya nuna mata band'akin Tsakar gidan Mik'ewa tayi da Sauri har lokacin hannunta na cikin hijabi ni kuwa nace Mata "Ga buta Nan da ruwa a ciki babu ruwa a band'akin Wajen band'akin ta nufa da Sauri tana ta mutsu mutsu da hannu Kafin ta Ciro hannu daya ta sunkuya ta dauki butar a garin ta mik'e Naga wani irin dunkullellen laya ya Fad'o Yanda layyan ya Fado Haka naji Kamar kirjina xai Fado. Da Sauri ta tsugunna ta rufe layyar da hijabinta ta d'auka tana k'ok'arin Shiga band'akin Cikin zafin nama na taso kafin ta karasa band'akin na jawo doguwar hijabinta da karfi da har sai daya shake Mata wuya na Kara jawo hijabin har sai data zub'e a kasa Banyi wata wata ba na Kara shaketa da hijabin Dana cukwikuye burinta kawai ta cire hijabin Dana shaketa dashi Sabida matsar Dana Mata Azaba yasa ta saki layyar Bansan inada karfi ba sai a ranar saman kanta na hayye har lokacin Ina shake da ita na dau daya hannun nawa dake balain rawa bakina d'auke da Addu'a na Dago layyar da aka caccaka allurai a ciki ga sunayen Zahira Nan a zagaye da layyar. Ihun sallati na saka na saki layyar Cikin tashin hankali na Kara shaketa da hannu biyu cikin kuka na hau ce Mata "Mai na Miki mmn maimuna da kike San ganin bayana Ashe kece kike San ganin Bayan Zahira Basu Umma ba Mai na Miki da zafi Haka Mmn maimuna da kike San ganin Bayan Yata a iya sanina ban miki komai ba hasali alheri na Miki kika zalunce Ni Mai na Miki Haka Mmn maimuna Mai Zahira ta Miki"? Nace cikin kuka Ina Kara shaketa da k'arfi sai kakari take Ni kuwa na hau jibgarta Ina buga kanta da kasa rantsuwar da nake akan wlh sai ta gayamin Mai Zahira ta Mata yasa take San ganin bayanta da irin shakar Dana Mata yasa cikin azaba tace na saketa zata fadamin Ban cikata ba nace ta gayamin a Haka Ina jinta ko kuma wlh na dauko wuka yanzu nan na kasheta Dan sosai na ringa Jin Zan iya kasheta yanda nake Jin zuciyata daga makotaka Mai hadina da ita da zata nemi cutarmin da ya Ganin magana na Mata wuya yasa na sausauta rikon Dana Mata a wahalce tace "wlh bani bace Mmn Safiyya da Safiyya ne Suka Sakani wlh Allah ranan ma da muka zo k'ofar gidan nan har da Safiyya muka zo. Tiryan tiryan ta hau bani labarin komai batare da ta rage komai a ciki ba har alewar da suka so bawa Zahira na sata da Abu ya juye ya koma Kan Dan safiyya da Maimunan Sosai jikina ya dauki rawa na hau sallati........ *NAGA TA KAINA* *NA SADNAF*🌸🌸 ®️ *_PURE MOMENT OF LIFE WRITERS_* _{We Don't just entertain nd educate we also touch the heat of readers P.M.L}💪🏻_ *Free Novel* *Page 51* Rawar da jikina keyi yasa na cikata na zub'e a kasa Ina juya Kai na danake ji kamar zai fado kirjina kuwa sama da kasa.kawai yake ita kuwa numfashin wahala kawai ta ringa saukewa tana "kiyi hakuri mmn Zahira Safiyya ce ta ringa zugani wlh a yau din ma kamar bazan zo ba taje har gida ta sakoni agaba Akan Nazo da kaina" "Da kin shiga da layyar band'akin Nan Ina Zaki saka layyar Kuma Mai zai biyo baya ki gayamin mmn maimuna"? Nace Ina tsareta da idona Dan Naga alamar tsorona take ji sosai har yanzu hannunta na rik'e da wuyanta Mutsu mutsu ta hau yi Ni kuwa Ina ganin Haka na mike na je na kulle k'ofar Gidan na dauko wani sharbaben wuka a d'akina na fito dashi daga gidansa tana ganin Haka ta gwallo Ido ni kuwa nace "Na rantse da Allah idan Baki gayamin ba sai na yanka ki mmn maimuna karki dauka bazan iya ba Dan tunda har a matsayinki na wacce itama take da Yara ta Haifa ta san zafin haihuwa xaa iya had'a Baki dake Dan kawai a cutar mun da 'ya toh Dan na kasheki wlh banyi asara ba Zan iya komai Akan yarana ki bude baki ki gayamin Mai zakiyi da layyar Nan da ace kin Shiga band'akin Nan asirinki Bai tonu ba" Na nufi wajenta na Kara jawo hijabin jikinta da k'arfi cikin azabar tsoro yanda na Dora wuk'ar a wuyanta ta hau min bayani. "Dama a ranar da muka zo gidanan da Kika bud'e kofar muka gudu nida Safiyya sabida karki Kama mu sosai muka ji takaicin da bamu idda nufinmu Akan ki ba Kika bud'e kofa a nesa da gidanki muka labe muna hango yanda kika rik'e almajirin da muka so Yana kwankwasa gidan kina bud'ewa ya jefa Kwan a tsakar gidan indai ya fashe toh yanda rubabben Kwan xai ringa wari Haka za a ringa toshe hanci Zahira na wari har ta Rasa Mai Aurenta Dan Safiyya tace Bata so Zahira ta samu miji Mai kudi ta aura har ki Huta Gudun da almajirin yayi da fad'a Mana da yayi kin kwace Kwan yasa Safiyya taji kamar ta haukace zaginki tayi tayi tana tsine Miki Akan Bata yarda.dake.ba kema akwai wajen bokan da kike xuwa yake Gaya miki duk abinda zai faru dake. Haka ta kwana a gidana ko bacci batayi ba muna Kara Shan alwashin komawa wajen bokan namu washegari kuwa da sassafe mukaje Muka Gaya masa duk abinda ya faru ya Kara cajar mu wani kudin. Dan dai ta Sakani a gaba ne banyi niyyar zuwa ba sabida banida kwanciyar hankali tunda maimuna ta Sha alewar Nan kullum cikin jawomin magana take. Ahaka taje.tayi buga buga bansan Inda ta samo kudi ba tazo ta sameni shekaranjiya na Rakata wajen bokan muka Kai Masa kudin shine ya d'auko layyar Nan ya bani yace ayi kokari a jefa a masan gidanan yanda Kashi keda wari Haka zata ringa Yi a wajen Samari Haka zatayi bakin jini Wanan Abu yasa hankalin Safiyya ya tashi Dan bamu San Mai zuwa gidanki har ya Shiga band'akin ki ba ahaka muka dawo gidana muna naziri a karshe tacemin Ni Zan Mata aikin Nan Zata bani Dubu daya Dayake Ina cikin bukata a Haka na karba ta bani kudin shine yau ta zo akan tana zaune a gidana tana jirana nazo na saka layyar a masai ai bakida wayo indai nace Miki inajin fitsari bazaki hanani shiga bandaki ba Nidai Dan Allah kiyi hakuri mmn Zahira sharrin shaidan ne nayi nadamar biyewa Safiyya" Ta karashe tana fashewa da kuka. Duk maganar da take min sama sama nakejinta sabida tashin hankali Dana shiga Ashe duk Inda nake tunanin su Umma sun Kai wajen mugunta ashe sun wuce nan" Wuk'ar hannuna na ajiye na cika mmn maimuna cikin rawar murya nace " Mmn maimuna akwai wani Abu Dana Miki da kike ganin na cancanci kiga bayana haka?idan nayiwa maimuna yarki Haka Zaki ji dadi ?mmn maimuna iya alewar da yarki ta Sha take sata Bai Isa yasa kigane Allah ke kareni da yarana daga sharrin su Safiyya ba iya sanina ba abinda na Miki Dana cancanci Haka daga wajenki mmn maimuna kudadena dake wajenki bazasu lissafu ba kema kinsani ban taba Miki Aiken ki bani kudina ba ban taba daga Miki hankali Akan ki bani kudina. Ba ban taba canza Miki fuska ba na daina Baki bashine sabida na lura bakyaso na karu dake ta gaban shagona yaranki zasu wuce wani shagon su siyi Abu da kudi Amma idan bashine sai ki taho wajena Dan Kuma na daina Baki bashin mmn maimuna sai kiga laifina ko kece inaga matakin Dana dauka Zaki dauka tunda kayan Nan ba kyauta nake samowa na zuba a shagona ba da kudi nake siyan kayan Nan mmn maimuna bayan hanaki bashi danake mmn maimuna akwai abinda na Miki Wanda bansani ba"? Girgiza min Kai tayi Tana "Kiyi hakuri mmn Zahira sharrin shaidan ne wlh ki yafe min" "Kiji tsoron Allah Mmn maimuna karki biyewa San zuciyarki kizo ki aikata abinda Zaki zo kina nadama daga baya ki fita daga abinda Bai shafeki ba Umma da Safiyya Allah yasan ba abinda na musu Suka tsaneni na rabu da Naseer ma basu kyalleni ba kiyayyar har ya tashi daga kaina ya koma Kan zahira da Bata ji ba Bata gani ba a iya sanina ba abinda Zahira ta musu kema Haka Amma tunda abinda kuka zab'a kenan. Mmn maimuna wlh station zamuje ayimin katangar karfe daku gabad'aya duk abinda ya sameni da yarana wlh kune" Ina fadar Haka na dauki layar da Addu'a a bakina na Shiga d'akina na daga gadona na dauko wanan Kwaryar na jefa layar a ciki na zura hijabina na dauki mukullin gidan nayi waje. Mmn maimuna a guje tayo wajena tana na rufa Mata asiri Kar na Kai su station ni kuwa hankadata nayi ta Fadi na fita tare da kulle gidan ta waje. Na dauki hanyar station Ina kuka Kamar karamar Yarinya Dan Nagaji da abinda su umma sukemin bansani ba ko matakin Nan da Zan d'auka shi zai saka na samu kwanciyar hankali gwara ayimin tsakani dasu tun kafin su shirya abinda yafi wanan tunda Ashe sau uku kenan suna gwada cutar min da 'ya Allah na Kare mu. Wanan shine karshen abinda zanyi da zai saka kila na samu Salama sai dai Naseer Yaji Haushin na Kai karar mahaifiyarsa da kanwarsa wajen yan sanda Da kafa na karasa station din da kyar na tsagaita kukan da nake na musu bayanin abinda ke tafe Dani Take kuwa wani daga cikin Yan sanda ya tambayeni Ina ita mmn maimuna take yanzu nace Masa tana gidana na kulleta Gyada min Kai yayi ya Kira wata Yar sanda da kallo daya zaka Mata gabanka ya Fadi sabida girmanta ga kib'a ga tsayi iya hannunta idan ta damke mutum dashi sai yaji a jikinsa ce Mata yayi su dau mota ita da wasu Yan Sandan guda biyu su bini gidana a d'auko mmn maimuna ta Kai su gidan su Safiyya a d'auko Safiyya da Umma daga Nan su taho station. Ni kuwa Ina Jin Haka nace Masa Ni ba wani Abu nace a musu ba katangar karfe kawai zaa Mana tsakaninmu a Kuma ja musu kunne na karashe da su taimakamin. Cemin yayi kar na damu na je Amma inza a d'auko uwar mijin nawa Kar na bisu na hau wani motar Nazo da Kwaryar da kuma Zahira yata da suke ta San ganin bayanta. A haka na hau motar Yan sanda nida mace Yar Sanda ta Bayan motar su Kuma mazan Suka hau gaban daya najar motar dayan nada ga gefe Ni na ringa nuna musu hanya har muka iso k'ofar gidana Inda na tarar da yarana a k'ofar gida duk sunyi Cirko cirko ciki kuwa mmn maimuna bubbuga k'ofar Gidan kawai take Tana su bud'e Mata ta tafi. Ina saukowa daga cikin motar yarana suka yo kaina a guje Ni kuwa Ban tsaya saurarsu ba na bud'e gidan Mace Yar Sandan na biye Dani a bayana Ina bud'e k'ofar mmn maimuna ta fara kokarin fitowa daga gidana Yar Sandar data gani a bayana yasa ta zub'e a kasa ta hau magiya Yar Sandar Nan kamar namiji Haka ta damko kafadar mmn maimuna ta jata cikin motar Tana ihun nayi hakuri Kar na Bari a tafi da ita. Dan Sandan dake zaune a daya B'arin ne ya daka Mata mumunan tsawa akan ta musu shiru ta Kai su gidan su Safiyya. Dayake tana da balain tsoro da hannu biyu ta rik'e bakinta ta shige baya ita da matar Dan sanda ya tadda motar ta hau kwatanta musu gidan dasu Umma ke zaune Ni kuwa Suna tafiya na Shiga ciki na d'auko Kwaryar Kwan da layar na saka a bakin Leda daga yanda na hade Rai yasa yarana Basu samu zarafin min tambayoyi ba Nadeeya na bawa umarnin kullemin gida kafin na dawo na rike hannun Zahira Dake sanye da uniform mukayi titi na tare Mana abin Hawa muka nufi station d'in Haka kawai Kuma naji jikina yayi sanyi sai nakejin kamar bai Dace na kawo Umma Kara ba Amma ya zanyi inaga hakan kawai shine mafita a gareni duk da a kasan zuciyata ma na yanke wani shawarar da nake tunanin insha Allahu shine zai kawo min karshen komai. Mun rigasu Isa station din haka yasa Muka zauna a benci nida Zahira Wanda ya dau statement Dina na dazu ya hau min tambayoyi Na cigaba da bashi amsa Yana mamakin Wai Zahira Dake karamar Yarinya ake San ganin Bayan ta haka Kwaryar Kwan da layyar kuwa daya karba a gefe ya Ajiye Yana jiran isowarsu ni kuwa na cigaba da rokonsa Kar ya musu komai kawai so nake ya Shiga tsakanina dasu na Kara jaddada Masa banasan ayi musu wani Abu sabida Umma uwar mijina ce Safiyya Kuma kanwar mijina. Baicemin komai ba ya cigaba da rubuce rubucensa Safiyya kuwa Jin Saude ta Dade Bata dawo ba yasa ta gudu daga gidan Saude Dan gani take kamar Naeema ta Kama Saude ne idan kuwa hakane gwara ta gudu A hanya kuwa kukan kudinta take Tana Kara tsinewa Naeema tana ce Mata Mayya sosai takejin itama akwai asirin da Naeema keyi shiyasa duk abinda suka Mata asirinsu ke tonuwa a kasan zuciyata kuwa tana adduar Allah yasa Saude ta jefa layar a masan ta matsu taga bayan Naeema ta matsu taga Naeema a cikin tashin hankali. Koda ta Isa gida ta bawa Hajara labari itama sosai taji Haushin yanda Naeema ke tsallake duk abinda suke Mata Hajara ta hau cewa ita tasan Naeema Dole akwai abinda ta taka da take tsallaka duk wani Abnda suka Mata yanzu iya kudaden da suka kashe ya Isa su siyi karamin fili tasan ma Asirin tayiwa Naseer take juya shi San ranta Safiyya na k'ok'arin Magana wata Mmn ayuba ta watso Bashir da baifi shekara biyu da watani waje tare da murd'e Masa kunne tana "Naga masifa da jarraba a gurin karamin yaron Nan kamar Danan yasan ya Shiga karkashin gado ya bud'emin tukunyar Miya ya hau tsamar.min nama Ke Safiyya wlh ki ringa rike danki duk Inda zakije Dan ya galabemu da kananan d'auke d'auke Yana mitsitsin shi dashi anya ma yaron Nan naki shi kadai ne kuwa ba wani Abu a jikin sa"? Ta karashe tana cika kunnen Bashir dake tsalla ihu. Safiyya kuwa wani abune ya tokare Mata wuya tama kasa mik'ewa sosai itama hankalinta ke tashe da yanda Bashir ke Shiga Dakunan Yan gidan yake musu d'auke dauke tun Bai girma bama abinda dai zai iya ci yake dauka Bai fara satar kudi ba tukunna har wajen wasu bokaye taje sabida su karya Mata asirin satar sai dai Kamar a banza sosai abubuwa ke cakude Mata a madadin tayiwa kanta fada aaa Sai take ganin kamar ma Naeema ce ta jefata a halin da take ciki a madadin tayi nadama cigaba da neman hanyar da zata ga Bayan Naeema take yanzu ma Allah ne yasan uban kudin da ta kashe wajen karbo layyar nan sai gashi babu Saude babu dalilinta tana zaune ne kawai a Nan Amma hankalinta na can burinta kawai taji Sallamar Saude Akan ta aiwatar Mata da aikin da ta Sakata. Mik'ewa tayi Dan ta dauko bashir dake ta kuka a bakin kofar mmn ayuba sauran mutanen gidan kuwa na ta kananan surutu Akan Bashir din ko kallonsu batayi ba Dan yanzu hankalinta baa jikin ta yake ba Shigowar mace Yar Sanda da excuse me ne yasa ta Dago tana kallonta kanta tsaye Yar Sandan cikin gurguraren hausa tace wacece Safiyya mmn Bashir da Hajara mmn Safiyya Da Sauri mutanen gidan da suka nutsu suka hau nuna Safiyya da ta daskare a tsaye tana kallon Yar Sandar data Kira sunanta kirjinta kuwa sai bugun Tara Tara yake Dan idan akwai abinda take tsoro a rayuwarta Bai wuce masu bakin kayan Nan da bindiga ba Kamar numfashinta zai d'auke a lokacin da Yar Sandar ta karaso gabanta ta damke hannunta tana Ina mamanki" Kinkina Safiyya ta hau Yi ta daka Mata mugun tsawan dayasa ta Nuno Hajara da tashi tsaye tana gyara daurin zanin jikinta sabida tashin hankali shigowar Yar Sanda. Da hannu daya ta rik'e Safiyya har suka karasa gaban Hajara Yar Sandar tace Musu su tafi station Ana nemansu Safiyya fusge hannunta tayi tana "Mai mukayi da zamuje station Anya mu kike nema kuwa ko dai b'atan Kai kikayi" Marin da Yar Sandar ta d'auke ta dashi daya d'auke jinta gabadaya ta barin kunnenta na hagu yasa tayi tsit Hajara kuwa Marin da Safiyya ta Sha yasa Bata tsaya gardama ba tayi gaba matar Kuma ta hau Jan Safiyya sukayi waje Basu Kara gingin magana ba suka hau motar Yan Sandan sai a lokacin Suka ga Saude data ci kuka idonta ya kad'a yayi jajjur Gaban Safiyya Dana Hajara sai daya balain fad'uwa tsoron Yar Sandar yasa ba Wanda ya iya magana a cikinsu duk da Safiyya nata yiwa Saude magana da Ido. Saude na dauke kanta Hajara da Safiyya sosai Suka rude hankalinsu ya tashi suna tunanin Mai ya faru Haka Saude ta d'auko musu Yan sanda ko dai Kamata Naeema tayi shine ta d'auko musu Yan sanda cikin wasu wasi Suka iso station din jiki na rawa suka sauko daga cikin motar Yan Sandan na daka musu tsawa suka Shiga ciki Suna shigowa muka had'a Ido da Umma da Safiyya da mamaki sosai ya bayyana a fuskarsu da ganina a zaune Akan benci nida Naeema. Take jikin Safiyya ya hau rawa Umma kuwa ta kasa hakuri ta nuna kanta tana "Naeema Ni Kika kawo wajen Yan sanda"? Wani mugun tsawa Wanda ya dau statement dina ya daka Mata tayi saurin rufe bakinta fuskarsa a balain had'e ya kalli wani daga cikinsu yace a saka su Umma a cell bama zai sauraresu ba sai Naseer mijina ya dawo" Ni kuwa Jin abinda yace yasa hankalina ya tashi Dan har ga Allah ba Dan a ci zarafinsu na kawo su ba kawai tsakani nakeso ayi Min dasu. Sai dai Dan Sandan ko kallona baiyi ba duk da uban magiyan da nakeyi Ina kallo aka tasa keyar Umma da Saude sukayi Bayan canter ita kuwa Safiyya sai da Yar Sandar Nan ta Kara Bata Mari biyu dayasa kanta juyawa. Ni kuwa na hau kuka Ina rokon Dan Sandan Dan har ga Allah ba abinda nasa yamin kenan ba nayi nadamar Kai kararsu Umma wajen Yan sanda Dan sai Dana gwammace na kwashi yarana na gudu na bar musu garin da abinda ya biyo baya. Dan Sandar kuwa cemin yayi bazai sakesu ba sai mijina yazo shi yayi mamakin Jin uwar mijina da kanwarsa ke yiwa Yar yarinya da Bata ji ba Bata gani ba irin wanan mugayen asiirn ganin inata magiya yasa yace na tafi gida gobe karfe Sha daya Na dawo zai min abinda nakeso din Amma sai fa sun kwana a yau. Inaji Ina gani badan Raina naso ba muka dawo da Zahira Gida a ranar ko baccin kirki banyi ba Dan sai nake ganin kamar kwanan da su Umma sukayi na bud'e musu wani k'ofar da zasu Kara nufana da mugunta ne nasan halinsu yanzu bakina zasu gani har ga Allah banji dadin abinda San Sandan Nan yamin ba idan Yana ganin ma taimakona yayi wlh bai taimakeni ba Dan nasan halinsu Umma Rashin nutsuwa zuciya yasa ranar ko sallah Daren banyi ba da asuba na tashi na hau aikin gidan Dan so nake naje station da wuri Dan hankalina gabadaya Yana can Su Nadeeya na Gama shiryawa suka tafi makaranta Zahira kuwa nace Mata ta shirya mu tafi station duk da lokacin dayace muzo baiyi ba Amma banida nutsuwa Sam gwara dai a fito dasu umman hankalina ya kwanta Ko abinci na kasa sakawa cikina. Yanda nake a hargitse yasa Zahira ta hadiye tambayoyinta mun fito kenan Ina k'ok'arin kulle gidan. Taxi ta Parker a k'ofar gidana Naseer ya fito daga taxin fuskarsa d'auke da faraaa yayi kyau har da kib'ar kwanciyar hankali Mai taxin kuwa booth ya bud'e ya hau firfito Masa da kayayyakinsa . Shi kuwa Naseer yanda yaga nayi zuru zuru yasa ya iso wajena da Sauri Yana "Lafiya kuwa Naeema ya naganki Haka Ina zaku Naga kuna kulle gida" Kuka na fashe dashi ban iya ce Masa komai ba Dan har ga Allah wandanan Abubuwan sun isheni na gaji da Naseer da Mahaifiyarsa Nagaji ma da komai Ni Hankali a tashe ya bud'e gidan Ya ja hannuna muka Shiga ciki ya umarnci Zahira data kwaso kayan ta kawo ciki Ya Jani har d'akina ya zaunar Dani akan gado shi Kuma ya duka wajen k'afata Yana cigaba da tambayata abinda ya faru Ban ce Masa komai ba nace Masa muje dai yagani da idonsa bazan iya Masa bayani da Baki ba Duk yanda yaso na Masa bayanin abinda ke faruwa k'i nayi. Hankali a tashe ya kulle gidan ya biyoni a baya shi da Zahira. Abin Hawa na tare Mana muka hau Bai Kara min tamabyaa ba har muka iso station din ganin ciki zamu Shiga yasa ya rik'e hannayena Yana "Naeema Dan Allah ki gayamin me ke faruwa mai mukeyi a police station na Shiga uku Ni Naseer" Ban kula shi ba na fusge hannuna na Shiga station din ya bi bayana shi da Zahira hankalinsa a tashe. A Kan benci Muka zauna Dan Wanda case Dina ke hannunsa Bai zo ba ance sai karfe goma zai iso. Naseer har tsawa ya ringa min akan Gaya masa abinda ke faruwa ban Gaya masa ba har sai da Dan sandan yazo Yana shigowa ya kallemu Yana "wanan ne mijin naki"? Gyada masa.kai nayi Ya karewa Naseer kallo ya shige wani office shigarsa ba jimawa wani Dan sanda yace mu Shiga ciki Naseer Haka ya bini office din Dan sanda. Muna Shiga Dan Sandan ya umarcemu mu zauna gaban teburinsa Kuma Kwaryar da kwai da layyar ke ciki ne a gabansa. Muna Zama aka shigo da Umma dasu Safiyya da sukayi zuru zuru Safiyya kuwa jikinta duk ya kumbure Dan ta Sha bak'ar duka a wajen wanan mace Yar Sandar . Saude kuwa tayi wani irin laushi Kamar Mara lafiya Umma ce dai naganta fes muna hada Ido da ita ta min wani mugun kallon daya tsinkemin zuciya Zahira kuwa ta Kara matsawa kusa Dani Kamar zata shiga jikina Naseer kuwa hankali a balain tashe ya mik'e tsaye Yana "Umma" Umma ko kallonsa batayi ba ta zauna a kasa kamar yanda su Safiyya Suka zub'e a kasa sai wani irin vibrating take Naseer kuwa hankali a tashe ya fara k'ok'arin nufar wajensu Umma Dan sanda yace ya koma ya zauna ba Dan Ransa naso ba ya zauna hankalinsa a balain tashe. Dan sanda Kwaryar ya nunawa Naseer Yana ya iso ya gani da idonsa Naseer kuwa ya nufi wajensa ya dau Kwaryar ya sunkuya ya hau ganin rubutun da akayi da Sunan Zahira Sam bai gane Mai hakan ke nufi ba Hakane yasa ya daga kansa ya kalli Dan Sandan ya dawo da kallon sa kaina Ni kuwa na dauke kaina Dan duk na bawa Dan Sandan labarin komai Dan Sandan kuwa cewa yayi Saude duk ta bashi labarin abinda sukayi da bakinsu kafin yasa a canja Mata kamani Dan taurin Kai ma Safiyya ta gwada musu Taki magana hakane yasa ta Sha mugun duka Yak'i Bari a daki umman ne sabida yanda Naeema ta daga hankalinta Kuma Yana ganin umman babba ce duk da akwai masu laifiin da Suka fita shekaru suke Kuma musu hukunci Jiki na rawa Saude ta hau bada labarin duk abinda Suka so yiwa Zahira Bata rage komai ba ta tonawa Umma da Safiyya asiri har asirin satar da suka so yiwa Zahira Allah ya mayar musu Kan kayansu Tana bada labarin Ina kuka Naseer dake tsaye sai gashi jikinsa na balain rawa har kafafunsa Suka gaza daukarsa ya zub'e a kasan Yana kallon Umma da Safiyya da suka sunkuyar da Kai Saude kuwa sai bada hakuri take tana a yafe Mata sharrin shaidan ne Zahira kuwa kukanta ne ya cika office din dan duk ta fahimci Abunda ke faruwa. Dan Sandan kuwa ya kalli Umma Yana "Mai jikarki ta Miki Haka har kike San ganin bayanta" "Babu komai" "Ke Kika haifi babnta kuwa ko tsintarsa kikayi ki gayamin gaskiya"? "Ni na haifesa ba tsintarsa nayi ba" "Amma ke kika haifeshi kike San ganin bayan yarsa data kasance jikarki Mai yayi zafi Haka ko wani Abu mahaifiyarta ta Miki shiyasa kike San ganin bayan yarta" "Ba abinda tamin yallabai sharrin shaidan ne ayi hakuri" "Ke Kuma uban me ta Miki kike kulla irin wanan makircin"? Murya a dashe Safiyya tace itama ba Komai ta hau bada hakuri Kamar yanda Umma ta bada hakuri. Naseer kuwa shima tunda ya sunkuya da kansa Bai Kara dagowa ba A takaice Dan Sandan kuwa ya jawa su Umma kunne sosai ya ce musu ko tari nayi Dani da Zahira ba Kuma iya Zahira ba har yarana gabadaya wlh sai sun Kama su Kuma an kullesu na har abada Duk da Basu iya rubutu ba sai da aka d'auko takarda Suka saka hannu Akan sun yarda ba abinda zasu Kara min na sharri indai kuwa anyi sune Ahaka aka Sallame mu gabadaya muna fitowa Saude ta dib'a a guje Umma kuwa da Safiyya wani azababen kallo Mai dauke da mugun tsana sukamin nida Zahira Suka dau hanya Naseer kuwa a ba yanda zaiyi yabi bayansu Amma ko kallon Inda yake basuyi ba Ni kuwa hannun Zahira Naja muka hau taxi muka koma gida. Duk da anmin tsakani dasu banji hankalina ya kwanta ba hakane yasa muna isa gida na bazama neman dilallai Dan wlh siyar da gidana zanyi da komai nawa na bar unguwar in ta kama ma na koma garinmu dan bazan iya ba. Naseeer kuwa har gidan yabi su Hajara Suna Shiga gidan. Safiyya ta d'auko danta daga wajen mmn ayuba data taimaka ta rikeshi Hajara kuwa a tsakiyar d'akinsu ta tsaya ta kalli Naseer cikin tsananin bacin rai tana "har ni Naeema zata Kai wajen Yan sanda ta kulle mu wani irin girgiza Kai Tayi" Naseer kuwa dake Jin yazo har wuya ya hau zabga masifa Yana ......... Karku manta nace Zan na tsallaken kwana daya *Comment* Haka aka taba yimun 😭niy yarana duka akasa sunansu su 7 aka hada da likafani da sanduna guda bakwai da duwatsu da turare irin na aikin junnu,akaje aka saka wani wuri ,wai yanda akayi dinnan haka yarana zasu zama kamar gawa bazasu taba tsinana ma Kansu komiba a rayuwa,shikuma duwatsun zai zama yadanne zukatansu bazasu taba tunanin nema ma Kansu maganiba,kuma ko annema anbasu bazasu iya amfani dashi ba ,ke mugun abudai😭kawai Allah yanuna mun a barci da kuma yarona guda daya shima Allah yanuna masa da asuba kuwa yazo yake fadamun,nayi mamakin yanda mukaga Abu daya duka lokaci daya,wallahi danayi magana kuwa saiga Abu ya bayyana shine akaje aka dauko abun shinefa akaga wadannan abubuwan Dana lissafa da sunayen yaran nawa duka aciki,aka fada mana kuma abunda akayi asirin yasamesun,Allah yakare ya nuna mana😭 *Advertisement* Yan uwana yan kasar Niger,chad,camaroon,ghana dama ko ina afadin duniya masu son siyan kaya a nigeria harda ma yan cikin nigeriar amma suna tunanin ta yadda zasu rika siyan kaya cikin aminci to ga dama ta samu cikin sauki da rangwame zaku samu kaya kamarsu kayan kitchen,atamfofi,shaddoji,laces,jakunkuna da takalma toga dama ta samu kawai ku tuntubi Oum_Aabid Herbals and more 08178586888 Whatsapp group https://chat.whatsapp.com/CRsFCyoGq3i628AujmbxvV domin samun kaya cikin sauki da rangwame. Masu fama da ciwon sanyi kunyi magani harkun gaji to kuma ga dama ta samu ku tuntubeta zaku samu magani sadidan insha Allah 08178586888 *NAGA TA KAINA* *NA SADNAF*🌸🌸 ®️ *_PURE MOMENT OF LIFE WRITERS_* _{We Don't just entertain nd educate we also touch the heat of readers P.M.L}💪🏻_ *Free Novel* *Page 52* "Mai na Miki Umma Mai na Miki a rayuwata kike San ganin bayana Umma wlh ba Naeema Kika tsana ba Ni Kika tsana Umma na rasa Kuma laifin Mai na Miki yanzu Umma Zahira yata kikesan ki watsawa rayuwa? Yanzu Zahira kike yiwa asirin Sata kike mata asirin wari Dan kawai Kar ta samu Wanda zai Aureta Umma Zahira yata ce fa innalillahi wa Inna ilaihi rajiun Umma tsanar da kikamin har ya Kai Haka Umma bayan kin watsa min rayuwa umma iya Haka Bai isheki ba sai kin taba min yata da bata Miki komai ba? Umma Anya kina tsoron Allah kuwa?Anya da Zuciya a kirjinki kuwa Umma tunda nake bantaba Jin uwar data ke azabtar da danta ba irinki ban taba ganin uwar da Bata da burin daya wuce taga bayan danta ba irinki duk burina na faranta Miki na miki biyayya har gidana Dana mallaka Kika siyar har gobe kece silar jefani a halin da nake ciki har yanzu ko bulo yanzu banidashi balle gida Amma iya Haka Bai isheki ba Umma har sai kin tab'a diyata toh insha Allahu idan Ina rayye ba abinda zai Samu yayana Naeema Kuma tamin daidai data Kai kararku wajen hukuma daga Rana irin ta yau duk abinda ya samu yarana wlh Umma kece Kuma ko ta kai kararku wlh Ni Zan Mata shaida" "Baka burgeni ba da tundazu banji ka d'aukeni da Mari ba Naseeru Ni nasan ba a hayyacinka kake ba Naeema ta Dade da asiriceka Dan da a hayyacinka kake mataki zaka dauka akan tsinananiyar yarinya Nan Naeema Ina mahaifiyarka tasa a kullemu har mu kwana" Naseer bakinciki ne yasa Bai iya ce Mata komai ba ya fito daga d'akin a fusace Safiyya dake labe San Bata San fitowa zaiyi ba kafin tayi k'ok'arin b'uya har ya Kai Mata wani irin cafka ya hau kwallo da ita. Dak'yar aka kwace ta a ahnnunsa bayan Hajara ta fito aguje tana zaginsa bakinta daya Saba da tsinuwa na tsine Masa Haka ta ringa Shan alwashin ganin bayan Naeema ko da zata mutu Naseer kuwa Haka ya fito Ransa a tsananin b'ace ya tari abin Hawa ya nufi gidan Naeema. A lokacin daya Isa Bai samu Naeema ba sai su Zahira. Shima Bai tambayesu ina taje. Ba ya Shiga d'akinta Agaban mudubi Yaga an ajiye Kwaryar Hakane yasa ya Shiga bandaki ya d'aura alwala ya fito ya dauki Kwaryar Yayi waje sai dayaje nesa da gidan ya fasa Kwan ya Kuma binne layar ya dawo gidan A daidai lokacin da Naeema itama ta dawo. Daga shi har Naeema ba Wanda yayiwa wani magana Dan Naeema ma wani irin hade Rai tayi hakane yasa Bai samu zarafin Yi Mata magana ba. Sai daddare da Yara sukayi bacci ya hau Bata hakuri Bata ce Masa komai ba Dan tasan ba abinda hakurinsa zai Mata ita dai yanzu mataki kawai zata dauka bazata tsaya mahaifiyarsa ta salwantar Mata da rayuwa ya ba Kwana biyu a tsakani akayi ta zuwa ganin gidan Wanda Sam Naseer Bai Gane zuwan da ake ba har sai da ciniki ya kankama Naeema ke Gaya masa matakin data dauka na siyar da gidan Dan ta bar unguwar. Naseer sosai yaji zuciyarsa ta sosu da hukunci da ta yanke batare da ta shawarce shi ba sosai yaga Dan tana takamar gidanta ne hakane yasa tayi Masa Haka Amma kasan zuciyarsa Kuma sai yake ganin Dan tsira da lafiyar yayansu yasa kila takeso su bar unguwar shima kansa hakan yaso yayi dan so yake ko haya ne ya Kama musu acan Abuja su koma can da Zama inyaso ko aike ne ya ringa yiwa Hajara Amma tunda ma Naeema ta Riga da ta yanke siyar da gidan shikenan Dashi akayi cinikin gidan da ba laifi an siye shi da daraja da saka hannun Naeema aka siyar da gidan Masu siyen Kuma suka bada kudi tare da notice din wata guda. Kayan shagon Kuma tayi niyyar siyarwa wani Mai shago dake can bakin titi da har Naeema ta Masa magana. Da injin markadenta kawai zata tafi Sai da Naseer ya tambayeta Inda take so su koma ta ce Masa garinsu zasu koma gabadyaa yanda su Hajara ma bazasu San Inda suke ba sosai Naeema ta shirya Yana Mata gardama tace ya Bata takarda sakinta Dan har ga Allah ta gaji sosai Naseer kuwa take takenta ya gani ya hau lallaminta akan ba sai ta Kai ga barin Kano ba ta nemi wani unguwar ko Dan makaranta yaran nasu Dak'yar da sidin goshi ya shawo Kan Naeema Dan tuburewa tayi bazata zauna a kano ba duk Abubuwan dake ciciyar ta a zuciya ta hau amayar dashi har da cewa ita dai ta gaji da aurensa indai wani Abu ya Samu yaranta bazata yafe ba Naseer Haka ya Shanye duk maganganun data ringa kwaba Masa har ya samu kanta Abinka da tsakanin Mata da miji tuni dai ya shawo kanta ya kwantar Mata da hankali Inda ya Kuma Bata shawarar Inda ya kamata ta samo.karamin gidan unguwa ne nesa sosai da Inda su Hajara suke. Hakane yasa Naeema ta sakar wa Naseer ragamar komai Inda ya nemo.mata karamin gidan Kamar dai wancan data siyar sai dai wanan Din ya Dan fi girma kawai matsalar ba shago a gaban gidan Sai da Naeema taje taga gidan taga komai yayi suka biya kudin gidann Cikin sati biyu suka dawo kawo dake unguwar hotoro Bayan anyiwa su Nadeeya transfer zuwa wani makarantar Zahira kuwa boarding Naseer ya dage zata tafi a fadarsa. Hakane kawai zai saka masu sintirin zuwa nemanta su daga kafa Zahira Kuma zata maida hankali tayi karatu sosai tunda yanzu zata tafi ss1 Nadeeya Kuma ta tafi jss.2 Dayake da Yan canji a hannun Naseer shi yayi cuku cukun sabon makarantar dasu Nadeeya suka koma dake unguwar da suka koma. Zahira kuma.aka hau Mata siyayyan boarding Dan itama an Mata komai.ta fanin registration. Har ga Allah ba a San Raina Zahira zata tafi boarding ba Dan dai Naseer yamin fin k'arfi ne kawai a matsayinsa na Mahaifin zahiran a rayuwata banasan abinda zai nesanta Ni da yarana nafiso ko yaya ne na ringa ganinsu a gabana har ya fara shirye shiryen Kai ta jikina a sanyaye yake ita kuwa zahira murna take sosai tana doki data ga yanda babanta ke mata siyyaya Nidai addua kawai nake akan Allah ya karemin ita Dan har yanzu gani nake su Umma zasu iya jefo min wani masifar amma.ina gayawa sarkin sarakuna duk gudun da zanyi nasan sai dai idan Umma basu so cutar damu ba kasan zuciyata Kuma sai nake ganin zuwan Zahira boarding zai.nisanta ta daga sharrinsu umman. Hakane yasa na kwantar da hankalina nayiwa zahira komai na jawota jikina na Bata shawarwari yanda zata kame.kanta da dagiya da addua A Haka nida Naseer muka Kai Zahira makaranta yata ta rungumeni muna kukan rabuwa dak'yar Naseer yaja hannuna Muka tafi Kamar Mara lafiya dai na dawo sai Dana fi sati kafin na fara Dan sabawa da rashin zahiran A Haka na maida hankali na fara tunanin Sana'ar da Zan Kama Kuma bayan.markaden Dan da alama unguwar akwai.masu markade.da.yawa ba shago a k'ofar Gidan ballantana nace Zan zuba provision kamar wancan unguwar da muka baro A Haka dai na yanke siyar da Zobo kafin na samu babba Sana'ar da zan ringa yi tunda kudin Sana'ar tawa suna ajiye Ba laifi kuma Ina Dan cinikin zobon Naseer wata biyu ya min ya koma Abujan. Ni kuwa na cigaba da kula da yarana sau biyu Ina zuwa ganin Zahira ba laifi hankalina ya kwanta da yanda naganta kawarta ma da kusan dabiarsu daya sunanta jameela sosai na yaba da hankalinta hakane yasa na Kara samun kwanciyar hankali. A Haka rayuwar ta ringa tafar Mana ban taba sakin jikina ba kullum cikin addua nake Dan nasan duk da anyiwa su Umma gargadi nasan halin su kila idan sun ga an kwana biyu zasu iya waiwayomu da sharri kullum cikin sadaka nake Dan nasan sadaka maganin masifa ce A Haka su Zahira sukayi first term dinsu a ss1 sukayi hutu suka dawo Fes Zahira ta Kara Yi kyaunta ya Kara fitowa tabarkallah Masha Allah Dan acan ma Mallamai santa sukeyi. Hakane yasa na yanke a Raina indai ta Gama din mu aurar da ita kawai inyaso ta cigaba a gidan mijinta Naseer shima a daidai lokacin da sukayi hutu ya dawo Cikin farincikin kudin daya samo inda yake cemin fili xai siya da kudin sosai na Taya shi murna Dan Kamar Wanda Bai taba gidan kansa ba yake murna da filin da yake San siya Gaba da gidana wajen bakin titi ya siyi katon filin a ranar ko baccin kirki baiyi ba sabida murna. Ahaka ya Mana sati biyu ya koma.batare da waiwaiyar umma ba A Haka aka Gama hutu Zahira na rakata makaranta Sati.uku da komawarta na fara mugayen mafarkai akan Zahira Daya dagamin hankali na hau sadaka Ina Addua Haka kawai naji Kamar wani Abu ne zai sameta daga yanayin danake.ganinta a mafarkina hakane yasa naji Sam na kasa samun kwanciya hankali na fara shirin zuwa dubo ta a ranar Dana shirya da sassafe Dan na dubota a ranar da bazan taba mantawa ba a rayuwata Mallamai biyu ne maza da mallama Mace daya sai kawar Zahira jameela da wata da suka ruk'o zahira Kamar matacciya suka shigomin da ita Suka shimfida min ita a tsakiyar gidana. Juyawar da kaina keyi da kirjina da nakeji kamar zuciyata ce zata fito yasa na kasa motsi na daskare a tsaye Kwantar da Zahira da akayi yasa na rik'e zuciyata tare da kallon zahiran. Abinda na gani ne yasa jiri d'ibana na zub'e a gefen zahiran....... Kuyimin.hakuri abubuwa ne Suka Sha kaina sai Sunday Zan dawo daidai ayi maneji pls. A next episode insha Allahu Zan k'ok'arin Yi dayawa Dan muyi mu Gama ngd *NAGA TA KAINA* *NA SADNAF*🌸🌸 ®️ *_PURE MOMENT OF LIFE WRITERS_* _{We Don't just entertain nd educate we also touch the heat of readers P.M.L}💪🏻_ *Free Novel* *Page 53* Na saki ihu tare da dagota Ina "Mai ya samu 'yata Haka Mai ya sameta waye ya kwakulo Mata idonta waje Haka Innalillahi wa Inna ilaihi rajiun" (Nafeesa sai dai na takaita Miki wuyan da Zahira ta Sha a cikin irin kaddarar data budemin daga auren Naseer wahalar da Zahira ta Sha yafi komai bani wuya tunda Nima sai Dana Zama tamkar tab'abb'iya wuyan data Sha shima labarine Mai zaman kansa sai dai na takaita Amma kyakyawan zuciya irin nata cewa take ta yafe musu abinda Suka Mata ko yanzu da Zan baki labarin wuyan da yata ta Sha ni kadai nasan Mai nakeji a Zuciyata ko nida Zahira mun yafe Sai Allah ya Mana sakayya" Ta fashe da kuka labarin da baa bani ba kenan a ranar sai washegari) Badan nasan Zahira 'yata bace bazan yarda ita Suka kawomin ba Dan gabadaya hallitar Zahira ta canja cikin sati uku kawai da Zahira tayi da komawa makaranta ta dawo kamar kwarangwal idonta ya firfito waje gabadaya wuyanta kuwa ya wani irin kumburo waje kallo daya zaka Mata ka d'auke idonka daga kanta sabida Dole ka tsorata da yanda ta dawo Ihun dana cigaba da yi Ina tattab'a zahiran da ba magana takemin ba illa manyan idon da kamar Kara Mata su akayi kawai take kallona hawaye na zararo mata Wuyanta daya kumburo kuwa sai motsi yake kamar ta hadiyi wani Abu kanta da jikinta kuwa har wani hucci yake sabida tsananin zafi Cikin azabar kuka yata rungume dani a kirjina na kalli mallaman da suka kawomin ita Ina "Ku min bayani Mai ya samu 'yata ta dawo Haka Innalillahi wa Inna ilaihi rajiun na Shiga uku na lalace jameela Mai ya samu kawarki Haka ki gayamin jameela"? Nace Ina Kara tab'a wuyan Zahira daya ke numfashi shi kadai Zahira kuwa har lokacin Bata cemin A ba sai kallona take da idonta tana zubar hawaye Daya mallamin ne yayi karfin halin magana Dan dukansu kuka sukeyi jikinsu a sanyaye suna kallon Zahira da Bata da bambanci da mataciya sai numfashi kawai da takeyi "Washegarin da suka koma hutu daddare wajen karfe Tara Zahira ta tafi bandaki ita da jameela Wai zasuyi fitsari Jameela ce ta fara Shiga ta fito kafin Zahira ta Shiga Zahira na Shiga ba dadewa sai ihunta jameela taji da ba iya jameelan ce taji ihun zahiran ba har b'angaren Mallamai munji wanan ihun hakane yasa duk muka bazama mukayi b'angaren daliban sai dai muna zuwa muka ganta shame shame a kwance tana wani irin jijjiga hakane yasa mukayi tunanin ko Aljannu ne suka shafeta a band'akin. Da addua muka fito da ita daga band'akin hankalinmu a balain tashe mun Saba ganin cases na dalibai masu Aljannu sai dai na zahiran sai ya bamu tsoro Dan bayan mun fito da ita daga band'akin wani irin zafi jikinta ya d'auka Kamar garwashin wuta idonta ya Zama kamar jini jikinta kuwa Banda rawa ba abinda keyi Mallamin Dake karantar dasu ta fanin islamiyya muka Kira Dan indai case ya taso irin Haka shi yake yiwa dalibai rukiyya sai dai duk Inda ya Kai da rukiyya ba alamar sauki kwana mukayi a kanta sai gabanin asuba Muka ga ta daina girgiza ta rufe idonta. Duk dauka mukayi bacci ne ya d'auketa hakane yasa muka Yi hayaki a office din da muka kwantar da ita Yan aji uku wajen su shidda.muka saka su karatun Qurani a fili tunda duk sun sauke Dan duk mun yarda gamo tayi a band'akin Wajen karfe Tara na safe ta kwalla wani irin ihun daya saka mu toshe kunnuwan mu Dan Kamar ba Dan Adam ne ya saki wanan karar ba fusge fusge ta hau Yi zata fita a guje muka riketa Gam sai dai abinda ya tsorata mu Bai wuce hallitar ta da muka ga Yana canjawa ba idonta kuwa kamar sunyo waje wuyanta ma ya kumbure duk da Bata da jiki sai Muka ga Kamar Naman jikinta ramewa yake kasusuwanta na fitowa na hallitar jikinta har d'auke hannunmu mukeyi sabida azabar zafin da jikinta ya d'auka kanta kuwa kamar baa Jikinta ba sabida zafi Hankalinmu tuni ya tashi.mukayi asibiti da ita sai da tayi sati biyu a asibiti Ana Bata taimakon gaggawa Amma a amadadin taji sauki.ma sai azaba take Sha hallitarta na Kara canjawa likita da kansa yace mu nemi na gida larurarta bana asibiti bane muna tsoron dawo Miki da ita Haka hakane yasa muka nemi mallami a can shima yayi iya kokarinsa Muka ganin Abun kamar Kara girmama yake Kar tazo ta mutu a hannunmu batare da kunsan halin da take ciki ba yasa muka yanke dawo da ita Dan tabbas abinda ke damunta bana asibiti bane kamar dai jinnu ne. Girgiza kaina kawai nake Ina rungume da Zahira da zafin jikinta ke Kona min jiki cikin ihun kuka na Dago da yata da ta tashi daga siffar mutane ta zama wani hallita daban Ina "Mai na muku Haka Umma Mai Zahira ta muku Umma Dan Allah kuyi hakuri da laifin Dana muku ku kyallemin yata Bata muku komai ba Umma Ni na muku laifi na tuba Umma ku cikamin yata da Bata ji ba Bata gani ba Umma Innalillahi wa Inna ilaihi rajiun Naseeru Zo kaga yanda Zahira ta dawo Naseeru kana Ina kazo ka kawomin agaji.kar Yata ta mutu" Kuka nake sosai Ina surutai mallaman kuwa sai Baki suke bani jameela kawarta da mallamar su mace da daya yarinya sai kuka suke suma Horn din da ake musu a waje sabida da motar makaranta aka kawo su. Yasa Suka hau min Sallama suna ajiyemin kudi Jameela kawar Zahira kuwa data ci uban kuka ta rik'e hannun Zahira daya Zama tamkar Kara tana "Allah ya Baki lafiya zahira idan mukayi hutu Zan Zo na duba ki ya Allah ka kawowa zahira Agaji ka Bata lafiya" ( Wlh Allah indai Zan tuna labarin wuyan da baiwar Allah nan ta Sha sai nayi kuka 😭😭😭😭😭😭😭😭😭 Allah ya Miki sakayya duk da ya wuce wlh Ina rubutu Ina kuka) Haka suka fita Suka barni da Zahira da har lokacin idonta Dake warwage take kallona dashi hawaye na zubo Mata Haka na d'auketa kamar ba mutum ba sabida rashin nauyi na kaita d'akina Ina kuka na shimfidar da ita Akan gado na cire Mata rigar jikinta ko no-nonta ma.shafewa yayi a kirjinta sai kasusuwa kawai kankara na dauko na zuba a katon roba da ruwa na dauko zani na na hau Danna Mata jikinta da ruwan Dan jikinta yyai zafi da yawa da kanta gani nake zata ji dadin Jikinta idan Ina matsa Mata ruwan sanyi a jikinta sai surutu nake kamar mahaukaciya kamar ma har sabo nayi Ina "Allah Mai na maka ka jarrabceni Haka Allah duk addua Nan da nakeyi nake Hana idona bacci sabida Kar wani Abu ya Samu yarana Kar wani Abu ya Samu Zahira Allah sai da Umma suka ci Galaba akanta Allah kaga yanda Zahira ta dawo Allah kaga yanda idonta ya firfito waje" Maganar da Zahira tayi yasa kukana tsayawa cak muryarta ya dawo na Yara sosai. Da sirirrin hannunta ta rik'e hannuna tana "Umma Dan Allah kimin addua mutuwa Umma indai kina kaunata kimin addua mutuwa Dan Allah Umma jikina kamar an hura mun wuta Umma" (Gaskiya bazan iya cigaba da rubuta wajen Nan ba Allah yasani kuka nakeyi ku Bari na tsallake kawai nayi shi a takaice) Jawota nayi na rungumeta cikin ihun kuka Ina "Bazan iya Miki adduar mutuwa ba Zahira sai dai na Miki adduar Samun lafiya yata da ki mutu gwara Ni na mutu Zahira Zahira ke yarinya ce Mai biyayya Mai tausayin iyaye albarkar annabi Muhammad Saw Zaki samu lafiya zahira Ni na musu laifi bake bace Baki musu komai ba Bai Kamata su tabamin ke ba wayyo Allah ka dubi halin da yata take ciki ka kawo Mata agaji ya Allah ban hada bautarka da kowa ba Kai kadai nake Kira nake kaiwa kukana bansan boka ba bansan Mallam ba Kaine mallamina Kaine Mai sharemin kukana Allah ga zahira Nan ka sasauta mata wuyan da take Sha ya Allah ka dawo da ciwonta jikina" Kuka nake sosai Kamar Zan shidde ahaka su Nadeeya suka dawo daga makaranta Suka shigo har cikin d'akina suna shigowa Naga duk sun ja da baya a tsorace cikin tashin hankali da ganin yanda Zahiran ta dawo Zahira kuwa hawaye na zubo Mata ta ringa binsu da Ido a karshe ta tsayar da idonta Akan Nadeeya tana mik'o Mata siririn hannunta cikin muryar yaran tana "Nadeeya Zo gareni" Nadeeya kallonta kawai take jikinta na rawa tana "Aunty Zahira Mai ya samu idonki Haka Mai ya Sameki Haka "? Hannu kawai Zahira ke mik'a Mata hakane yasa ta Isa wajen Zahiran. Tare da Kama hannun da take Mika Mata ta zauna a gefen gadon tana fashewa da mugun kuka Zahira kuwa tace "Nadeeya kimin addua mutuwa kinji Umma tace bazata min addua mutuwa ba Nadeeya jikina konamin akeyi wuyana ma kamar garwashin wuta aka sakamin Nadeeya kimin addua mutuwa kinji" Ihu Nadeeya ta saka duk da zafin jikin Zahira Haka ta rungumeta tana "bazaki mutu ba aunty Zahira bazaki tafi ki barmu ba aunty Zahira waye ya Miki Haka Mai ya Sameki Haka" Tuni.kannenta suka zagayeta suna kuka Ni kuwa na mike na Shiga bandaki na Dora alwala na dauko sabon doguwar rigar da ban taba sawa ba na zura a jikina na dauko sabon hijabina fari Kal shima na saka na na shimfida Sallaya a madadin na tada sallah kamar yanda nayi niyya sai na fashe da kuka na d'aga hannuna na hau rokon Allah akan ya kawowa zahira Agaji kuka nake akan Sallaya sosai goshina a kasa Ina rokon Allah ya kawomin d'auki halin Dana tsinci kaina a ciki. Sallah danayi ma bazan iya cewa a nutse nayi ba ahaka na shafa na nade Sallaya na nufi wajen Yata da buta a hannuna na Mata alwala na zura Mata hijabi na jinginarta a jikin gado Ina "kiyi sallah Zahira a zaune ki roki Allah Yana jinki Yana Kuma ganinki" Bata cemin komai ba Naga ta rufe idonta da Kamar Kara waje sukeyi Bansani ba tayi Sallah ko batayi ba dak'yar na Kora kannenta waje na saka Nadeeya Dora musu abinci Dan kuka take sosai Kamar ma zahiran ta mutu Yarana ba Wanda ya cin abinci har Waleed dake karaminsu danaga Yana buya a bayana idan Zahira ta kalleshi sabida idonta Dake bashi tsoro Duk yanda naso taci abinci ko bud'e Baki batayi yi Banga ta zama ba hakane yasa na bazama nemo Mai taimaka min Gashi lokacin farkon shigowar wayane ba mu Kai ga mallakar waya da har Zan samu hanyar da Zan sanarwa Naseer halin da muke ciki A takaice wajen Mallam naje mijin aunty Ina kuka na sanar dashi halin da muke ciki mutanen arziki daga shi har aunty da wasu daga cikin Dalibansa Haka Suka biyoni gida Duk wanda yaga Zahira sai ya girgiza da yanda ta dawo. Mallam kansa hankalinsa ya balain tashi shima dayake Yana da ilimi tuni yasa na fito da Zahira na shimfidar da ita a tsakar gida Suka daura alwala shi da Dalibansa sun Kai goma suka hau karatun Qurani Sai dai ba alamar Wai akwai abinda zai fito daga jikin Zahira Hakane yasa ya d'auko kwanun Sha Naga Yana ta tofa adduoi daya shafe awa guda Yana Yi sai daya Gama ya bani Akan na shafa Mata a jiknta ko zamu samu jikinta ya rage zafi Cikin Ikon Allah kuwa Ina fara shafa Mata jikinta ya hau rage zafi kanta ya shima Haka take Naga yata ta sauke ajiyar zuciya bacci yayi awon gaba da ita Ashe tunda ta hadu da Wanan masifar Bata bacci Ko a fuskarta zaka ga alamar taji dadin Jikinta kamar wacce har ta samu sauki na hau Godewa Allah Ina Godewa Mallam Basu suka bar gidan ba sai wajen Sha daya har lokacin zahira na bacci Cassette din Qurani na kunna Mata a gefen kanta daga Ni har Nadeeya bamu iya bacci ba Haka muka sakata a tsakiya muna kallo wajen daya naje na daura alwala na Zo na hau Kan Sallaya na tadda sallah Nadeeya kuwa bacci ne ya d'auketa a Gefen Zahira Wajen biyun dare Ina Jan carbi Ina kuka Naga ta bud'e Ido ni kuwa na zuba Mata Ido Ina kallon yanda ta zama kwarangwal Dan ba yanda ma zaka yarda itace tashi tayi zaune tana wurga manyan idonta daya Sakani runtse Ido Dan sosai idonta yayo waje Kamar fitilar kwai Ta zuro siraran kafarta kamar Kara Naga tayi waje Kamar iska zai d'auketa tsaf zaka kirga.kasusuwan jikinta Ni kuwa na mike da Sauri Dan nabi bayanta sai dai Ina fita banganta ba hakane yasa na hau nemanta hankalina a tashe Ina kwalla Mata Kira Nishinta danaji a Bayan fridge Dina dake Palo yasa na nufi wajenta da Sauri a tsugunne take a Gefen fridge din tana Kashi Bance Mata komai ba na Bari ta Gama na Kamata ma kaita bandaki na wanke Mata Ina "ya Kika baro bandaki a tsakar gida Kika zo Palo kina Kashi Zahira Bata cemin komai ba har na kwantar da ita na koma palon na kwashe kashin na goge wajen Sai dai kafin gari ya wayewa na Gane Kamar kwakwalwar Zahira ta tab'u Dan sau biyu Tana kashin amadadin taje bandaki na biyun a kitchen tamin na ukun Kuma a daya dakin da yarana suke kwana tana ta Abu Haka kamar mage tana kalle kalle abinan ya dagamin hankali daya saka ni kuka har garin Allah ya waye da asussuba na bazama neman Mai taimakamin Dan Kamar Mallam bazai iya da.larurar Zahira ba Bansan k'afata ba takalmi ba Ina tafe hannuna Dora akaina Ina kuka Ko ni bansan Ina na nufa ba sai danayi Karo da wata makociyarmu dake can kasan layinmu na dawo hankalina Rikeni tayi da hannu biyu tana "Lafiya kuwa mmn Nadeeya"? A sabon unguwar.mu da Sunan Nadeeya ake kirana sabida yanda take da farin jinin mutane sosai Zubewa nayi a kasa na rik'e kafar matar da ta kasance bafulatana ana ce Mata yaddiko tunda Muka zo unguwa na lura tana da balain kirki ba laifi Dan tasan hakkin makotaka "Ki taimakamin yaddiko yata zata mutu yata ta samu tab'in hankali" "Subhanallahi Mai kike cewa Haka Mmn Nadeeya Ta dagoni Ni kuwa na ja hannunta na cigaba da sheshek'ar kuka Ina bukatar Mai taimakamin Ina bukatar agaji Ina bukatar taimakon jamaa Dan ji nake kamar nayita kwalla ihu yarana ma zagaye suke da Zahira na fito neman taimako bansan Mai yasa nake Jan hannun.yaddiko.dan.tazo taga halin da 'yata take ciki ba kawai Ina bukatar taimakone Har d'akina na Shiga da ita a madadin Naga Zahira akan gado Kamar yanda na barta acan Gefen sip Dina naganta Tana kashin kannenta sun zagayeta suna kallonta Waleed ne kawai a waje sabida tsoronta da suke ji Sai wuwurga Ido Zahira keyi Kamar dai mage Zubewa nayi a kasa na Nuno zahiran da hannu Ina "Yadiko Kinga yanda yata ta dawo Kinga yanda aka dawomin da ita yadikko Kan yata ya tab'u kinga Inda take Kashi ki taimakamin yadikko idan akwai Wanda Kika sani na Kai Zahira wajensa ya Mata addua yaddiko ki taimakamin bansan kowa ba babansu Baya Nan Yana Abuja ba ta hanyar da Zan same shi na sanar Masa halin da muke ciki" Kuka nake sosai Yadiko ma Ina gani ta zub'e a kasa sabida tashin hankalin ganin yanda Zahira ta dawo Dan ta San Zahira sosai sosai take Santa sabida kyaunta har tana yiwa Dan autansu shaawarta Dan ya Aureta idan ta Gama makaranta Cikin tashin hankali tacemin "Innalillahi wa Inna ilaihi rajiun mmn Nadeeya akwai Wanda nasani zai iya taimaka Miki Bari na Kira mota mu tafi Amma fa wani kauye ne can gaba da jigawa Nima akwai kanwata datayi fama da Aljannu sai shi ya iya cire Mata su ko baa fada ba Zahira Aljannu ne a jikinta Kinga yanda ta dawo fa Ina zuwa yanzu nan kina da jan miski"? Girgiza mata Kai nayi da Sauri Tayi waje Ni Kuma na nufi wajen Zahiran na dagata nayi bandaki da ita na wanke Mata jikinta Nadeeya ta kwashe kashin ta goge Duk Kayanta sun Mata yawa yawo take a ciki daidai da kayan Raheema da take karamarsu ya Mata yawa sai a Haka na saka Mata pant kuwa Bai zai saku ba Dan ba kugun duk Inda Zan kwatanta muku yanda 'yata ta dawo wlh bazaku gane ba sai wayanda Suka Santa lokacin da abun ya sameta. Yadiko Bata fi minti talatin da fita ba sai Gata ta dawo da Mai mota datayi shatarsa. Ni kuwa karkashin gadona na d'aga a cikin kudin sana'ata na dauko kudin da Dan yawa na rik'e a hannuna Muka fito na roki Nadeeya data kularmin da gidan har ta rame itama. Idonta yayi jawur dan kuka.. Muna fitowa muka dau hanya Bamu Isa kauyen ba sai wajen karfe uku shima sai da muka hau machine Nadeeya na zaune a cinyata muka Isa gidan Mallam Mai sallati Haka ma Naga an saka daga wajen gidan Ga almajirai Nan birjik suna ta karatu Bamu Sha wahalar samun sa ba Bayan mutane biyu da suka Shiga ciki suna fitowa muka Shiga Muna Sallama ya d'ago Suka had'a Ido da Zahira Zahira ta kwalla wani mugun. Ihu daya saka kunnena Yinn wani iri Riketa nayi Kamar jaririya sai gashi ta duro da ga jikina ta hankadani tana k'ok'arin Yin waje. Da mugun k'arfi na riketa Amma ga mamakina wani irin tureni tayi yadiiko itama tayi saurin riketa Dan Kar dai ta fita a gujen Shafa Mata Jan miskin Nan a goshi Yi sauri Mallamin yace Yana k'ok'arin mik'ewa sai dai kafin yaddiko ta bud'e kwalbar miskin Zahira ta Kara sakin wani mugun Karan ta zub'e a kasa ta hau wani jijjjiga hankali a tashe na fara k'ok'arin yin kanta Mallam Mai sallati ya hanani akan Kar na sake na tab'ata Wani irin iska ne ya kaure a d'akin lokaci guda Kuma komai ya baje Naga Zahira ta bar jijjigan. Mallam Mai sallati ya tsuuggna a gaban zahiran ya shafa Mata Jan miski tare da daure kanta da farin kyalle yace na ja ta gefe. Da Sauri na dauki yata na Dora a cinya Dan tsayin kafafune kawai zai saka kasan babba ce amma ya dawo kamar dai yarinya siffar.dai Gata ga kamarta Kukan da nake Bai saka na iya ce Masa komai ba sai yaddiko ce ta Dan Masa bayani Shima Bai ce komai ba illa kasko Dana ga ya d'auko ya zuba wani hayaki a ciki ya hau bayani Yana "Kuna shigowa nasan turen bakakken Aljannu arna akayi Mata da har zai rabata da numfashinta zakuji jikinta na d'aukar zafi Bata iya bacci zatayi ta Abu kamar Mai tab'in hankali yanzu Kuna shigowa ma sun San ko yayane sai mun faffata dasu hakane yasa Kuna shigowa suka bar jikinta duk abinda zaayi yanzu basa jikinta Kuna tafiya zasu dawo jikinta Aljannu sun fi su ashirin kowane da aikin da yakeyi a jiknta. Zaki kashe kudi baiwar Allah Dan yanka zamuyi muyi ta Basu hakuri har mu samu nassarar Mai dasu wajen wayanda Suka Mata turen bakakken Aljannun Jiki na rawa na Ciro kudadeen Dana saka a Leda na mik'a.masa. Bai karba ba ya Kira baban Almajiransa akan ya karba ya siyo.masa katon bijimin saa.a daure Masa daddare akwai aikin da zaiyi A takaice Anan yadikko ta barni da Zahira tare da alkwarin duba min yarana A ranar a gidan Mallam Mai sallati na kwana matansa sai tausayina suke karfe daya daidai Naga an yiwa Zahira alwala Dan har lokacin Bata bud'e idonta ba Almajirai sama da goma suna zagaye da ita Mai sallati Ma na d'aga gabanta suna ta karatu Yana Yi Yana yarfa mata ruwan addua Yana goge mata jikinta da wani ganye Zahira dai Bata motsa ba Ina kallonsu har sai da Mai sallati yasa aka kawo Masa kasko ya watsa wani irin magani Mai kamar borkono ko mu damuke nesa sai da mukaji zafinsa ya hau shigar mana hanci Ahaka.yasa.mazan Nan suka d'ago.zahira da tana fara shak'ar hayakin ta bud'e Ido ta fara k'ok'arin fusgewa.ya da Danna kanta akan kaskon Yana saka kaskon a daidai hancinta ta kwalla wani irin Kara ta hau mimikewa idonta duk.ya yo waje Bulala Naga mallamin ya d'auko ya hau zabga Mata Wai zasu yi.magana ko bazasu Yi ba Tuni naji muryar yata ya dawo daidai ta hau ihun "Umma Dan Allah kizo ki.kwaceni daga hannunsa wlh Tallahi nice Umma Ni yake.duka" Aguje na Isa wajensu shi kuwa Mai sallati ya daka min tsawa.akan Kar.na matso.kusa dashi ba Zahira bace Aljannu ne "(Ashe dgsk zahiran ce yake duka ya d'auka.aljannu.ne Dan Wasa sukayi ta Masa da hankali Yana Dan da rukiyya suke.fita idan suka.ga zaiyi wani Abu sai su.shiga jikinta su Yi abinda zaa dauka sune. Ahaka yata ta Sha bulalai da hayakin Dake juyar.mata da.kai idan akayi har muka samu kwana uku ahaka a Rana na hudu da yace na Kara kawo kudi. A ranar Naseer ya duro gidan Mai sallati hankalinsa a balain tashe Yadiko ta rakasho Wanda zuwansa kenan su Nadeeya suka Gaya masa yaje har gidan yaddiko.ya rok'eta ta rakashi. Ina ganinsa na fashe da kuka Bai kalli inda.nake ba ya nufi wajen Zahira dake shimfide a kasa kamar gawa idonta kawai manya.datake wurgawa tana kalle kalle yasa zaka San tana rayye Tunda nake ban taba ganin Naseer a cikin tashin hankali Dana ganshi ba a lokacin Daya xube a gaban zahiran jikinsa na wani irin karkarwa cikin wani irin murya yace "Zahira" Zahira siririn hannunta ta mik'a Masa cikin muryar Yara tana "Abba kayimin addua mutuwa Dan Allah Abba jikina konewa Yake kamar an hura garwashin wuta a wuyana" Da hannu daya ya wawuro Zahira ya hadata da kirjinsa Yana "Innalillahi wa Inna ilaihi rajiun Innalillahi wa Inna ilaihi rajiun Innalillahi wa Inna ilaihi rajiun Allahuma ajirni fi musibati wa aklifnin khairin minha Allâhumma lâ sahla illâ mâ ja'altahu sahlan, wa anta taj'alu-l-hazana idhâ shi'ta sahlan. Addua kawai yake Yana kamkame da Zahira a kirjinsa dayake Jin fatarta na kona Masa jiki Cikin kuka nace "Naseer Dan Allah Dan annabi dan darajar Muhammad sallahu alaihi wa kaje wajen Umma da Safiyya ka Basu hakuri su kyallemin yata Bata musu komai ba ba abinda Zahira tayi data cancanci Haka daga wajensu kazo muje Naseer bana San na rasa yata ni suka tsana sumin hukunci Dan Allah Naseer kaga yanda suka dawomin da Zahira Zahira yanzu Kamar Mai tab'in hankali Naseer ka taimakamin muje na Basu hakuri kaga Zahira yanda ta dawo su sake min ita Dan Allah" Na karashe Ina kuka Mik'ewa yayi da zahiran a jikinsa Yana muje banyi gardama ba nabi bayansa Ko sauraren Mai sallati bamuyi ba Dan nidai a idona Banda dukarmin ya da yayi ba abinda ya iya min sai kudadena daya cinyemin gabadaya Dan sai da na tattaro sauran kudin nasa Nadeeya ta bawa. Yaddiko ta kawomin ta hanyar Mata wasika Shatar mota mukayi Naseer na rik'e da Zahira jikinsa Yana ta hawaye nidai burina nagani a wajensu Umma na kwanta nayita Basu hakuri Sai dai muna isowa Kano Naga Naseer na cewa driver ya Kai mu station Inda na Kai kararsu Umma Ni kuwa cikin tashin hankali nace Mai zakayi "Na gaji Naeema wlh zahira xan nuna musu suga abinda suka Mata wlh sai sun dawomin da yata daidai wlh Mahafina Bai gayamin gaskiya ba Umma ba ita ta haifeni ba Kinga yanda 'yata ta dawo Naeema Hankalina a tashe nace "Dan Allah karka Kai kararsu kararsu muka Kai Suka dawomin da ya Haka muje mu lallaba su Ko kulani Naseer baiyi ba yasa driver ya Kai mu station ban iya sauka a motar ba sai shi ya Shiga da Zahira Yana kuka wiwi Bayan shigarsa da. Mintina goma Sha biyar sai gashi ya fito da Zahira a sabe a kafadarsa Wanan Dan Sandan daya dau statement dinmu shi da Yan sanda wajen shidda da mace Yar Sanda Nan sun duru a motar Yan sanda driverr dayake janmu.ya dau hanyar gidansu Umma Naseer na Masa kwatance motar Yan sanda na biye damu a baya Nidai kuka nake ina cewa Naseer matakin da zai d'auka bashine mafita ba ya Bari mu lallaba su idan aka kullesu wlh ya Kara jazamin zaiyi ko kulani baiyi ba. Har Muka Isa gidan gabana ya hau fad'uwa Yan Sandan a fusace Suka duro daga motocinsu mace Yar Sandan na musu jagora Dan Ashe wanan Dan Sandan daya dau statement dinmu ya fusata muna Ransa Haka kawai yake tausayin nida Zahira. Naseer jikinsa na rawa ya fito daga motar Yana. "officer a taimaka min a matse su har sai sun dawomin da yata daidai Dan sai da suka rantse sai sun kasheta. Ina cikin motar ban bisu ciki ba sai kuka nake ina addua Allah yasa Kar wani balain ne zai kara tunkaroni nidai burina su dawomin da yata daidai............. Comment Labarin nan yayimin kala da halin da muka shiga a baya, amma alhamdulillh addua be bar komi ba, wlhi kakarmu da zata sami dama itama setayi abinda yafi na hajara amma inda Allah ya rage ma aya zaki ita din yar dangice sosai dan yanzu hakama su suke Sarautar garinsu amma fa maganar tsafi da asiri ba kalan wanda batayi, ba kalan Wanda batayi mana ba har na gobara😰 ta tura ma qanwata aljani me kunna wuta haka muna zaune waje ze kama da wuta akashe wani wuri yaqara kamawa daga karshe seda gidanmu yayi kurmus Babanmu ba kalan asirin talaucin da batayi mishi ba amma dayake Allah ba azzalumin sarki bane kuma shi yake ba ma wanda yaso ya hana ma wanda yaso haka tanaji tanagani Ze samu kudin amma sedAi kaman wuta yacinyesu zasu qare abanza baayi komi dasu ba, amma yanzu kumi yazama labari sedai abin da baza’a rasa ba tunda hausawa sunce me hali baya fasa halinshi amma yanzu ko ita kanta tasan munfi karfinta da ita da yayanta goma duka sun tsanemu ba wanda acikinsu baya mana asiri musamman takwaran safiya Tafi kowa mugunta cikin Yayan Kullum burin kakanmu bewuce baban ya mutuba taga yarda zamuyi, gwara ma hajara hankalinta na tashi in taga be lafia itakam babban burinta ace mutuwa ta riskeshi ace be barmana komi na gado ba mu wulaqanta Advertisement *Mg's herbal whitening black soap* Duk wacce batayi anfani da sabulunnan ba anbarta abaya acan karshen bayama kuwa duk Mai tantama akan sabulai nagyaranjiki cewa basa Aiki toh yacire mg's domin kankat ne insha Allah babu Wanda yayi anfani dasabulunmu yace baiyi ba koyaushe mg's sai sanbarka amare da uwargidaye hardama yanmata kuhanzarta kusamu naku ba karya domin bama cika Baki kugwada kubada labari da bakunanku sabulu daya tamkar dubu wadandama basasan using cream sabulun mg's herbal whitening black soap yawadacemuku jikinku zaiyi kyau koyaushe kukasance clean cikin kamshi Kuna glowing koda bakusa turare ba🤗 Kayanmu bana bleaching bn organic ne sunagyarajiki fiye da tsammaninku zaifiddomuku da ainihin natural beauty dinkine Wanda yagwada shi zaitabbar amare kuyi kokari kumallaki mg's domin baruwanku da zuwa adirjemuku jiki zakuga yanda fatarku zata dinga walwali Ina masu pimples Tabo(spot) Sunburn dama dukwani matsalar fata kuyi kokari kunemi soap dinnan before 2weeks zaisharemuku hawaye kuzama abun kwatance Sister's masu nankarwa kuma kunemi soap dinnan Yana rage nankarwa sosai🧖🏻‍♀️duk me shakku tayi kokari tagwada mg's insha Allah bazakiso rabuwa dashi ba Akwai maisa haske Amma kayanmu nafada bana bleaching bn zaifiddomiki d ainihin halittarkine yagoge dukkan dattin jiki Akwai Kuma Wanda zaimiki maintaining skin dinki yasaki fresh fatanki tazama kalar hutu Pls bamacika Baki you HV to try it and see for yourself 100%tested nd trusted Soap price:3k Location:kaduna buh munaturawa ko Ina Amma delivery is not free Maiso kindly message 08062991549 Call 08064532391 Note:Babu inda zakusami mg's herbal whitening black soap sai a number dinnan bairiga yakai market b inyakai we will let you know buh as for now wnn numbern ne kawai🙏 Maiso yahanzarta before yaji sold out akwaisu available now insunkare you HV to wait akawo so maiso yahanzarta🙏adade anayi sai gsky🤭🤝 Mg's skincare *NAGA TA KAINA* *NA SADNAF*🌸🌸 ®️ *_PURE MOMENT OF LIFE WRITERS_* _{We Don't just entertain nd educate we also touch the heat of readers P.M.L}💪🏻_ *Free Novel* *Nakine Mrs Sulaiman ta grp din Surayyams Marubuciyar Ajalin so son so* *Aishatu ladan da Yar mutan Bauchi Naga sakonku ngd son so fisabillahi* *Kuringa karanta comment din danake sawa akwai masu similar case irin na Naeema da suke baran adduoinku ngd* *Page 54* "Dan Allah ku taimaka min su dawomin da yata daidai" Abinda Naseer ke Fadi kenan har suka Shiga gidan a lokacin da suka Isa har k'ofar d'akinsu Hajaran Police din ma sabida tsananin fushi Bai Bari ma sun tsaya neman izinin Shiga ba Dan jikinsa har rawa yake da ya ga yanda Zahira ta dawo jaririyar wata hallita daban. Sai dai suna Shiga a madadin suga su Hajara wata mata suka gani da tsagu a fuska Kamar na Yan igala tana ta ninke Kaya shigowar Yan sanda yasa ta daka tsalle tayi gefe a daidai lokacin da Naseer shima ya Shiga ciki Yana wlh bake Kika haifeni ba ke ba uwata bace Ina Umman take yace Yana karewa d'akin kallo Dan Sam ba a hayyacinsa yake ba Abunda ke Kara daga Masa Hankali yanda jikin Zahira ke d'aukar zafi na tashin hankali sosai yake Jin ciwon kirjinsa na k'ok'arin taso Masa numfashi na Masa wahala Idan ya kalli Zahira da idanta ke warwaje sai yaji kirjinsa ya Kara nauyi da azabar zafi. Maganar matar da suka tarar a d'akin akan su Hajara sunfi wata uku da barin gidan yasa Naseer zub'ewa a kasa numfashinsa ya fara k'ok'arin daukewa Yan sanda sukayi kansa da Sauri Dan Yama saki zahiran kasa ta Dan bugu ta hau kuka kamar Yar yarinya Abinda ya saka Dan sanda kuka ganin yanda budurwar yarinya kyakyawa ta dawo. Yar Sanda ce ta dauki Zahira itama idonta na cikowa da kwalla Wasu Kuma Suka taimaka wa Naseer wajen daukarsa Dan sosai yake k'ok'awa da numfashinsa Dan sanda da sunansa ya kasance Aliyu cikin tsawa ya tambayi matar da suka Samu a d'akin Akan Ina su Hajaran suka koma jiki na rawa tace Bata sani ba A Haka ya fito duk ya tambayi Yan gidan Suka ce Basu San Inda suka koma ba Dan Basu gayawa kowa zasu bar gidan ba wayar gari kawai sukayi Suka ga basa Nan washegarin da aka sakosu suka dawo gida Ni kuwa shirun danaji yayi yawa yasa na fito daga Motar Na fara k'ok'arin Shiga gidan a bakin kofa mukayi kicibis dasu sun riko Naseer Zahira Kuma na hannun mace Yar Sandan Yanda Naga Idon Naseer ya koma sama numfashinsa na sama.sama yasa nayi kansu cikin tashin hankali na cakumo Naseer Ina na Shiga uku na lalace Mai ya same shi. Yan Sandan Basu saurareni ba suka saka shi a motarsu mace Yar Sanda tacemin na hau taxi mu biyo su asibiti zasu je Baa samu mamansu Naseer din ba hakane yasa Naseer yanke jiki Hannu na Dora akaina Ina kuka wiwi Nima inajin kamar na yanke jiki na Fadin A Haka muka bisu a baya har Muka iso asibitin d'akin emergency aka Kai Naseer Ni Kuma na karbi Zahira daga hannun mace Yar Sandan Likitocin tuni suka hau bawa Naseer kulawa da suka ga Yan sanda ne Suka kawo shi. Ni kuwa Dan sanda Aliyun yayo wajena Ransa a balain b'ace ya hau min tambayoyi akan Umma da Safiyya Yan asalin inane su wane Gari nake tunanin sun koma?Mai ya Kara hadani dasu na dai bashi labarin komai akansu? Cikin kuka na hau bashi labarin komai ban rage komai ba da yanda aka dawomin da yata daga makaranta? Sosai Naga idonsa ya kad'a yayi ja ya zubawa Zahira Ido da ta Kara kanjalewa idonta yayo waje daga Inda yake zaune ma Yana jiyo huccin jikinta sabida zafi Har yanzu ya kasa yarda kyakyawar budurwa Nan da ta ringa Masa gizo a idonsa ce ta dawo haka tabbas da ace zai Samu ganin Hajara da Safiyya da hannunsa zai harbesu take Kuma ba sai ya Kai ga kullesu ba daga bayanan da Naeema ta Masa ya fuskanci ba karamin mugaye bane yayi mugun nadamar sakinsu. Sosai yaji Yana tausayin Naeema da Naseer din uwa uba Zahira da bata musu komai ba Zafin jikin Zahira yasa ya Kira likitoci duk da yasan cutar Bata asibiti bace Amma gani yake kila akwai abinda zasu iya yi akai zafin jikinta ya ragu Idan har zaka Kai hannunka jikinta kaji tsananin zafi inaga ita kanta zahiran Ban ce Masa komai ba a lokacin daya karbi Zahira da ga hannuna kamar dai fa yarinya Zahira ta dawo siririya sosai wlh ka d'auke ta bazata yarda mutum ka dauka ba. Har d'akin da aka nuna Masa ya Kai Zahira da kansa ya roki Likitan akan ya bawa Zahira taimakon gaggawa ta samu relief a jikinta ko alluran bacci. Ne ma a Yi Mata tunda Bata iya baccin. Shi zai dau nauyin treatment din ko nawane. Kin barin d'akin yayi ya tsaya Yana kallon yanda Suka dukufa akan Zahira dake binsu da Ido daya Bayan daya wata nurse ma.gefe ta koma kila tsoron Zahira takeji ko tausayi Duk yanda suka so saka Mata ruwa kasawa sukayi Dan jikinta yayi laushi bama su hango jijjiya ba Allura suka iya Mata na bacci da sanyi jiki Sai dai kamar Kara Mata ciwo sukayi Dan ihu ta ringa Yi tana fusge fusge Jikinta ta Kara kwasar wani mugun zafin Ni kuwa ihunta yasa na Shiga d'akin Aguje Dan Sandan ne ya iya riketa Gam Ni kuwa na durk'ushe a Gefen gadon na hau kuka Ina kallonsa yana totofa Mata adduoi Likitan kuwa cikin tausayawa yace mu Kai Zahira wajen Mallamai cutarta bana asibitin bane jikinta yanda yake d'aukar zafi ba Normal bane. Likitan kuwa dak'yar ya samu ta bar fusge fusge ya Kira Yar Sandan Nan ta rik'e min Zahira ya fito na bisu a baya muka nufi d'akin da aka maida Naseer da aka Masa Karin ruwa da oxygen a hanci sabida Baya iya numfashi Ganin Naseer a wanan halin da Zahira dake hannun Yar Sandan Kamar jaririya sai idanduna yasa naji jiri na d'ibana na zub'e a kasa kaina Kamar ya Fado Sallati kawai nake zuciyata na bugawa yanda nake Jin kirjina kamar zai Faso Kamar na zauce Haka nakeji idan na kalli Naseer na kalli Zahira Sai da muka shafe kusan sati daya da kwana uku kafin Naseer yasan ma Inda kansa yake duk yabi ya rame ya fice a hayyacinsa Bazan manta Dan Sandan Nan ba a rayuwata Dan ya taimaka min sosai har matarsa yasa ta ringa zuwa duba mu inta tashi zuwa Haka zata Zo Mana da abinci da kayan marmari Sosai Dan Sandan ya ringa k'ok'arin nemo Safiyya da Umma da sai da suka koma can gidan da suke haya Suka Kara bincike Amma duk Basu San Inda su Umma suka koma ba Matarsa da nasan na girme Mata sosai Ita ta ringa Dan kwantar min da hankali da Wanan yadiiko makociyata Zahira kuwa amadadin sauki ma abin nata Kara jagulewa yake karfe dayan dare nayi zata hau kururuwa Tana zunduma ihu tana fusge fusge wani zubin ta kankameni tana na boyeta gasu Nan zasu caka Mata wuka wani zubin Kuma tana kuka tana na roka Mata Allah ya d'auki ranta ko zata huta da wutan da ake hura Mata a jikinta Naseer daya dawo hayyacinsa aka Sallame mu Haka ya zauna kamar mace Yana kuka wiwi Haka na tsaya akansa ya Dan samu lafiya Muka bazama nida shi Muka hau Nemo Mai taimaka Mana da magani Dan Zahira ta samu sauki Mutanen da suka San larurar Zahira Haka suka ringa zuwa kowane da kalar Wanda zasu ce muje wajensa ya kware a rukkiya mune Nan mune can fiye da wata hudu komai na mu ya Kare wajen. Bin Mallamai a karshe Naseer ya gaji yace mu hakura Haka mu Zo muyita gayawa Allah Yana kuka ya bud'e Baki Yana "Allah Kai ka halliceni ban nufi matar Nan da komai ba sai alheri ban taba bijire mata ba hasali sau daya nasan nayi kuskure hannu na ya Isa ga kumatunta da har gobe nake neman yafiyarka ba abinda Bata min ba karshe ta had'a da yiwa yata turen bakakken Aljannun ya Allah kayimin sakayya tsakanina da ita Allah ya Isa" Da Sauri na rufe Masa baki na girgiza Masa Kai Ina "Ba sai ka Mata Allah ya Isa ba ka Gama magana tunda kace Allah ya saka Mana kuka ba naka bane Naseer neman kudi zamuyi mu nemowa Zahira magani kaga yanda Yara suke cika k'ofar gidanan suna ce wa da dodo a gidanan Wai yata ce dodo Naseer Zahirata ce dodo" Kuka ne yaci karfina sabida yanda abin ke min ciwo. Idon Zahira daya fito warwaje da kasusuwanta da suka fito na jikinta da Abu da takeyi kamar Mai tab'in hankali yasa yaran unguwar wani zubin cika k'ofar gidana suna lekan Zahira Nadeeya da Minal ne ma wani zubin suke fita su Kori yaran wani zubin har da duka Wasu Kuma yaran haka zasu wayance da zasu Sha ruwa ko suna neman wani Abu Wai duk Dan suga Zahira K'arfi da yaji na koma kulle ta a daki Dan Sandan Nan ma Haka ya ringa kawo min mallamai masana addini suna iya kokarinsu akan zahiran Sai dai duk a banza abinda kawai Zahira ta samu saukinsa shine zafin Nan da jikinta ke dauka ya ragu Wani zubin Kuma tana iya bacci da Rana Amma fa idan dare yayi Haka zata tayi ta ihu tana fusge fusge har garin Allah ya waye Haka Naseer zai tsaya akanta dagani har Naseer ba Mai bacci a cikinmu Haka Nadeeya da kannenta sai dai idan bacci ne ya d'auketa Nakanji ma ance mak'ota nayi damu Wai Zahira na damunsu da ihu da Kara wasu Kuma tausayi take basu. Komai nawa ya kare a nemawa Zahira magani daidai da suturuna duk na siyar da rabi Naseer ma har filinsa ya siyar Bai gayamin ba yaje can har garin calabar neman su Umma Wai duk Dan ya rokesu su dawo Mana da Zahira daidai Amma ya karaci nemansu Bai gansu ba har Mallam Musbahu sai daya nema bai samu ma Mai labarinsa ba sai Haka ya dawo. Muka cigaba da neman Mai yiwa Zahira magani Har muka shekara a cikin wanan masifa da balain Sai maneman Nadeeya ke Dan taimaka Mana wani zubin har da na Minal din Dan duk sun kawo girma. Kuma ba laifi manyan mutane ke zuwa neman Nadeeya dayake baa nutse muke ba bama bi takanta ba laifi ba iya Zahira keda farinjini ba ga dukan alamu yaran nawa Rabbi ya musu farinjini Zan iya cewa albarkacin masu neman Nadeeya da auren yanzu asirinmu ke rufe Dan sukan mata kyautar ban girma ko su siyo kayayakin abinci Dana gida da Sunan kayan Dubiya kila sun San Daga Ni har Naseer din muna bukatar taimakone Ganin Nadeeya tana neman amfani da Wanan damar wajen wankar Samari yasa na taka Mata birki Akan ta tsayar da hankalinta waje daya ta ringa kula guda a cikinsu A Haka ta tsayar da Wanda yafi kudi a cikinsu da bansani ba Dan tana sanshi take kulashi ko Dan Yana kashe Mana kudin ne Dan ta taimaka Mana. Halin da muke ciki Bai saka na Bari sun dakata da zuwa makaranta ba da ace larurar Nan Bai samu Zahira da yanzu tayi candy Kila ma har ta samu Wanda hankalinta ya kwanta dashi ya fito na aurar da ita Amma Ina ga diyar tawa Nan rabi mutum rabi wani hallita Naseer kuwa ganin Abu yak'i ci yak'i cinyewa yacemin mu barwa Allah komai mu dage da Addu'a muyita Gaya masa yana sane damu. Take kuwa nayi naam da shawararsa Dan ko Ni Nagaji da yawon bin Mallamai da Kamar kudinmu kawai suke cinye Mana Daga Ni har shi Haka Muka dukufa da Addu'a. Kullum bakina d'auke da azumi Yata kuwa bazan iya bada labarin yanda ta dawo ba dan ba sauki wajenta sai a wajen Allah. ( Na Dan gajarta labarin sabida da yawa) A haka Watarana da Zahira ta samu shekara guda da wata hudu da Wanan lalurar ranar alhamis wajen biyar na yamma Naseer na zaune a tsakar gida a zaune hannunsa dauke da Qurani Yana Dan karantawa kasa kasa dayake dagani har shi azumi muke Nadeeya tana kitchen tana Mana abinci su Minal Kuma suna Palo suna duba littattafansu Ni Kuma Ina zaune akan tabarma na Dora Kan zahira a cinyata Ina Dan Mata fifita bama gashi yanzu a kanta kanta ma ya dawo kararrami. Ba bacci take ba idonta biyu tana kalle kalle tsullum Naga ta mik'e Ina ganin Haka nasan Kashi takeji Har na Saba da halin nata Bata Shiga bandaki ba Kamar iska zai d'auketa taje lungun band'akin ta tsugunna Dan ita abinda zai Zama daidai batayin shi sai dai akasin Haka. Tana gamawa na fara k'ok'arin mik'ewa Dan na wanke Mata Naga Minal ta fito daga d'aki taje ta wanke Mata tare da gyara gurin Ina Jin dadi da yarana basa kyankyaminta ko waleed da ya girma shima yanzu ya daina tsoronta wani zubin ma yakan wanke Mata kayayyakinta Dan ba laifi Waleed Dina akwai hankali ga hazaka da k'ok'ari tamkar mahaifinsa Haka kawai ma zai je kusa da Zahira ya hau Mata addua Allah ya Bata lafiya wani zubin sai yacemin ya fadawa mallaminsu yayiwa yayarsa addua samun lafiya Dawowa tayi wajena ta kwanta na gyara Mata rigarta daya Mata yawa da siyowa ma mukayi sabida duk kayan kannen ta ma sun mata yawa .iskar danaji Yana kadani ga Ina Dan Jin azumin yasa na kwallawa humaira Kira akan ta d'auko min pillow tana kawomin na kwanta Nan da Nan bacci yayi awon gaba da Ni. *Mafarki* A wani katon fili na tsinci kaina amadadin gida Ina kwance dai Akan tabarmar Zahira na gefena a zaune hakane ya na mik'e da balain sauri dana ga ta dawo daidai yanda take. Ada Ina k'ok'arin Magana na hango Yara sun kewaye wata Mata tana ta raba musu alewa suna ta murna suna tsalle. Haka kawai sai naji inasan ganin fuskar.matar tana juyowa Naga mahaifiya tace Fuskarta d'auke da murmushi tana ta rabawa yara alewa suna Kara titilowa suna tsallen murna wani irin mik'ewa nayi na fara k'ok'arin Isa wajenta cikin tsananin murna Ina Umma Sai dai tafiya kawai nake na kasa Isa wajenta har har ta Gama raba alewar Nan Naga ta nufi wajen wata dake kwance a kasa kamar matacciya Tana zuwa wajenta Naga ta ajiye kwanun abinci a gabanta matar kuwa ta mik'e da sauri ta hau ci tana yiwa Mahaifiyata godiya Tana Gama ci ta mik'e. Tana Mahaifiyata ta ceto ta tagode Ta fara tafiya Kamar ba itace a kwance kamar.mataciya ba Ni kuwa sai kwalla Mata Kira nake Amma Bata kalleni ba sai k'ok'ari nake na Isa wajenta Bubbuga pillon da nake Kai da sunana da Naseer ya Kira yasa na bud'e idona "Tashi kinsan babu kyau bacci uwar Haka Amma kusa Shan ruwa" Ban ma iya motsawa na dawo cikin hankalina ba sai Dana Gama karewa gidana kallo na tabbatar da mafarki nake Ashe Rabon da Naga mahaifyata a mafarki har.na manta Mai ma'anar mafarkin da nayi da Mahaifiyata"? Sosai mafarkin ya tsayamin a wuya Ina tuno yanda mahaifiya ta keta sadaka Yara na murna da abinci data bawa wata dake kwance kamar matacciya daga ci ta mik'e. Dak'yar na iya Shan kunu Dana Sha ruwa sabida tunani A karshe Dana kasa hakuri na gayawa Naseer mafarkin danayi Nace ko ya San fassarar mafarkin? Murmushi kawai yamin yace mafarki ne kawai Kar na damu kaina Ban dai iya cire mafarkin a Raina ba a ranar Wajen Sha daya bacci ya Kara kwasata na Kara irin mafarkin sak Kai Wasa Wasa sai gani nayi mafarki ajere cikin kwana uku Ana kwana ukun naji mahaifiya ta na cewa yaran "Sadaka maganin masifa" Kalmar Nan Haka na haddace shi a kaina har na tashi. Abinda ban Gane ba ko mahaifiyata Kara tuna min take Dana dage da sadaka toh Naga Ina yin Sadakan Nan. Haka mafarkiin ya tsayamin a raina na hau yiwa yara sadakan alewa ina rabawa Ina cewa kuyiwa Yata addua Allah ya bata lafiya take kuwa zasu hau tsalle tsalle suna yiwa Zahira addua cikin murnar alewar Dana Basu. Ban kawo komai ba kwatsam Ina zaune yaddiko ta shigo duba Zahira Dan takan Dan duba ta akai akai.makociyar arzki ce itama bana manta ta a rayuwata Muna cikin hirar sama sama kwatsam na tsinci kaina da Mata tambaya. "Ni Kam akwai tsohowa a unguwar Nan Haka da kike tunanin tana bukatar taimako haka"? "Kai akwai sosai ma ai suna da yawa. Amma akwai wata matar Mallam Amina Nima zuwa nayi na tarar da ita a unguwar Nan a can kasa layi take mijinta shekara goma kenan da rasuwa Bata tab'a haihuwa ba har ta tsufa mace ce Mai addini da tsoron Allah Kamar yanda na samu labari Rasuwar.mijinta yasa ta Dan siyar da gidan take juya kudin ta Kama haya toh shine wasu azzalluman Yan fashi suka dirar Mata suka.kwace komai a hannunta shine fa ta hau bara tana samun na abinci Shekara biyu da suka wuce mota ta bige ta shine ta daina fita baran sabida ciwon kafa da take fama dashi Ahaka Mai gidan hayan dayake Yana da Dan tausayi ya bar Mata daki daya a gidan Wayanda Suka San halin da take ciki sukan Dan taimaka Mata ko Ni Ina samu sarari Ina Mata Aiken abinci" Sosai naji hankalina yayi wajen matar da naji sunan Mahaifiyata gareta bandai nunawa yaddiko komai ba nace tamin kwatance Gidan tana min kuwa nagane. A Haka muka Dan Kara tab'a Hira ta tafi Washegari kuwa da sassafe na shirya abinci a kula. Na dibi danyen abincinmu na dauko xannuwa na guda biyu duk da Nima banida suturra na hada da sabulu na nufi gidan matar kamar yanda aka kwantan tamin Dana Isa gidan inata Sallama baa amsa ba hakane yasa na Shiga d'akin Dana gani a bud'e A kwance na tarar da ita tayi Kashi ma a jikinta ga kafarta a kumbure kamar rashin kudi yasa Bata iya Kai kanta asibiti Sosai naji tsigar jikina ya tashi Na ajiye kayayakin hannuna na Isa wajenta Ina "Sannu mama" Da Ido ta ringa Bina ban ce Mata komai ba na dagata na fita Waje tausayinta na balain rufeni dak'yar na samo ruwa na wanke Mata Jiknta batare da naji kyankyaminta ba na duba tsumokaran Kayanta Naga duk ta batasu da Kashi da fitsari Hakane yasa na dauko zanina Dana Zo dasu na daura Mata daya sosai naji kamar itace matar da nake ganin Mahaifiyata na taimakawa akwai dalilin dayasa nake mafarki da mahaifiyata kila matar Nan ke bukatar taimako. Yanda take kallona hawaye na zuraro Mata yasa na dauko Kular abincin Dana Zo dashi Sai dai Ina Isa wajenta jiki na rawa ta fusge abinci rashin k'arfi yasa ta kasa bud'ewa Ni kuwa hawayen tausayinta ya zubomin na bud'e Mata jiki na rawa kuwa ta hau ci da Sauri da Sauri tuna Nima halin Dana tsinci kaina a ciki kwanakin baya na azabar yunwa yasa na hau kuka Sai data ci na Bata ruwa. Ta sha ta fashe da kuka tana "Baiwar Allah daga Ina ya akayi kikasan Ina bukatar taimako yanda Kika ciyar Dani Kika shayar dani rabbi ya faranta Miki ya biya miki bukatunki na alheri nafi sati rabona da abinci Bana iya tashi idan Kashi ya matseni ko fitsari sai dai nayi daga kwance sabida ciwon kafa banida kowa sai Allah banida d'a banida jika bansan dadin haihuwa ba ballantana na samu Mai taimakamin Ngd yarinya Allah ya faranta Miki" Ameen mama Nima banida uwa banida uba dafatan Zaki zama mahaifyata Kalmar Nan ne yasakata kuka ta hau shimin albarka Nima dadin kalmar albarkar da take sakamin ya sakani kuka Tuni na tattaro zannuwanta data Bata na wanke Mata su na gyara daki dayan Ina kallo ta daga hannunta tana Godewa Allah daga adduoin da take nasan macece Mai ILimi da baiwa sai dai jarrabata da Allah ya mata hakane kuwa yasa na Sha alwashin faranta Mata har tsawon rayuwtaa Sai uku na koma gida Naseer Bai tambayeni Ina naje ba Nadeeya na Gama girkin dare na Kara zubawa a kula na saka hijabina na cewa Minal tazo mujr taga gidan A takaice tunda ga ranar na dauke Mata cin safe Rana dare Nakanje wajenta muyi hira sosai nake jinta Kamar mahaifyata Ko ban samu zuwa ba nakan sa yarana suje gidanta su Dan Mata gyare gyare su dawo.kuma.wani ikon Allah ban Kara mafarki da mahaifiyata ba Sabon da nayi da Inna Amina yasa na fara sakin jiki da ita Ina Bata labarin kaina har na Zahira da halin da take ciki Sosai hankalinta ya tashi tace na kawo Mata Zahira ta gani Washegari da yamma na goya zahira mukaje Sosai ta kad'u da ganin zahiran Tacemin zata taimakamin insha Allahu akan Zahira Allah ya Bata wnan ilimin ita da margayi mijinta Ko.kadan maganarta Bata shigeni ba lura da macece ita Kuma.manyan mallamai sun Yi iya k'ok'arinsu Basu iya warkar da Zahira ba Abubuwa ta lissafamun akan na siyo Mata har da su ruwan zam zam Jan miski ganyen magarya Wasu Abubuwan dai na manta su na dai siyo Mata ne kawai ba Dan na yarda ba A Haka tace na ringa kawo Mata zahiran tana Mata Addu'oi. Banki tata ba Dan bansan baiwar da Allah ya Mata ba na Kuma ga tabbas tana da ilimin Dakaina nayiwa zahira alwala itama da alwala a jikinta sai ta sa na samo kasko ta zuba wani turare data hada A.farkon ranar da tayiwa Zahira turaren A ranar Naga tashin hankali Dan sosai Zahira ta ringa ihu tana murya kala.kala tana rantsuwar kashe Inna Amina yarika sai datayi yafi kala ashirin yanda take k'ok'awa da Inna Amina sabida tana watsa Mata ruwan zam zam data kwana tana addua akai yasa.na baxama na Nemo maza Suka ririketa Amma a banza Haka ta watsar dasu Sosai muryarta ya dawo na maza na tsorota danaga yanda Inna Amina ta bada himma wajen turaren. A takaice sai gashi Aljannun da aka turawa Zahira suna magana wajen su bakwai a jikinta maza da mace daya Kuma arnaye yanda Inna Amina ke konasu da ayoyin Allah ta daure manyan yatsunta guda biyu yasa Suka hau cewa zasu fita Kar ta konasu aikosu akayi Take Inna Amina tace waye ya aikosu sukace Shugabansu ne ya aikosu tace waye suka Kira sunansa Inna Amina kuwa ta cigaba da gana musu azaba suna zuba yarika Haka muka kwashi kwana bakwai Inna Amina na fama da Zahira ko bacci bama Yi Dan gidanta muka koma gabadaya tunda muke zuwa wajen masu rukkiya ban taba ganin wanda ya haukata Zahira Haka ba sai Inna Amina A kwana na takwas zahira ta hau amaye amaye har da gashi Haka ta ringa amayo shi Inna Amina kuwa ta cigaba da zabga turare data hada sai gashi zahira na muryoyi kala kala Akan zata fita a yau su koma wajen wayanda Suka turo su Inna Amina dak'yar ta tsagaita tace sunyi alkawarin fita suka ce ee tace ta Ina zasu fita suka ce ta Baki a take kuwa Naga Zahira ta hau atishawa ba kakautawa. Can ta saki Kara Naga idonta nata fitowa waje daya saka hankalinmu tashi gabadaya Inna Amina kuwa tayi saurin cewa karka fita ta idonta Zan Kona ka sai dai ina aikin Gama ya Gama sai da daya ya fita ta idon Zahiran da har yau idan ka Kura Mata Ido zaka ga idonta daya ya Dan fi daya girma Kamar a mafarki Zahira ta zube a kasa. Hallitar jikinta ya hau canjawa idonta na komawa ciki Jikinta na cikowa *Alhamdulillah sadaka maganin Masifa wlh Tallahi akwai sirri a sadaka da ba kowa ne zai Gane ba ba sai kin Zama Mai kudi zaki iya sadaka ba akwai mabukata kana cikin matsala tsanananta da Addu'a da sadaka duk biye biyen da sukayi a sanadin farantawa baiwar Allah Nan Rai sun samu maganin matsalarmu Allah yasa mudace* *Comment* Wlh exactly irin abinda ya faru dani nikuma kishiyar mamanah ce tafara ne akan mamanah Allah bai bata sa,a ba sai tadawo kaina saboda mamanah tafiji dani duk cikin diyanta shine tayi amfani dani don ta kuntatawa mamanah wlh yadda idon zahira suke da bantsoro haka nau suke inka kalleni so daya baka marmarin kasake kallona wlh har kuka akeyimin ina sati kwance babu babusha kuma da anje dani asibi duk bincikenda za,ayi sai ace lpy ta lau banida matsalar komai duk inda mukaje bidar magani aikin banza munyi na asibiti ba,a gane komai ba aka komo na hausa shima shiru haka za,a kiro malamai suyita yimin rukiya amma basu magana wlh wani wuri da aka kaini hadda turaren barkono akayimin amma suka ki magana na wahala na wahala nasha azaba sosai wlh haka mamana zata sakani gaba tayita yimin kuka wlh gurin da muka fara zuwa da aka gayamana kishiyar mamanah ce bamu yarda ba sai da mukaje wuri yafi uku anagayama itace kafin muyarda itace tayimin ije da bakin aljanu guda uku wai su haukatani kuma su hanani aure da kyet da taimakon Allah akasamu naji dama nadaina rashin lpy amma duk da haka wlh basu rabu dani gaba dayaba don sunki barina inyi aure inaji Ina gani aure ya gagareni munyi magani munkashi kudi har karfinmu yakare amma wlh haryanxu shiru yanxu shekarata goma kenan cikin wannan matsala wlh matsalar sihiri babbar matsala ce. Slm.don Allah hide my ID wallahi wannan labarin yatuno min danawa rayuwan haka ya faru dani nima haka uwar mijina da kanwar mijina uwa daya uba daya sukayimin ni haihuwar fari danayi wallahi yaron tun bayan suna muka dena barci dashi haka xaiyi ta kara duk wanda yake kusa dani sai ya tausayimin dagaa karshe ma hannu da kafanshi aka canzama halitta😭😭😭haka na dunga wahalan neman magani baban kuma da farko yaki yarda sai daya ya ganinma idon shi sannan ya yarda muka fara neman magani maganan danake miki har yanxu ban huta ba kuma yaron ya xama saurayi har kanwanshi datake bimishi itama haka nayi wannan faman babancina da neema shine ni uwar mijina bata kungiyar matsafa sai dai tana bin matasfa da kuma bokaye iya wahala na wahala😭😭wani shari'an sai a lahira don nikam har yanxu abin yana damuna😭😭😭wallahi na manta rabon danayi barcin 2hrs da daddare dani dayarana haka xamuyi alwala mukaima sarkin sarakuna kukanmu ngd *Advertisement* Hlo sister's if you dnt use this soap before try and buy one use it you will never use any other soap again except mg's herbal whitening black soap🧖🏻‍♀️ it treat all skin prblms like Sunburn Acne it fade away black spot Clears pimples Reduces stretch mark it treat all skin prblm even if you don't HV any skin issue you can still use the soap it nourish nd keep ur skin fresh nd smooth,it will make ur skin to glow like never before nd gives ur body a pleasant smell🤭 This soap you jst HV to try it and see for yourself is one in a million this soap is organic soap 100% natural it does not bleach it will just bring out the beauty in you just give it a try your skin will thank you Just chat or call 08062991549 to plc ur orders Note you will not get this soap in the market it hvnt reach market for now you will only get it via this number Soap price:3k Location:kaduna buh we deliver Nationwide Delivery is not free Hurry nd grab urs dnt left behind😊 Mg's makeover Chat 08062991549 to buk for ur casual or bridal makeup @affordable price Location:kd You can still order ur slice cake, cupcakes,meatpie,samosa nd spring rolls,shawarma@mg's bakery for ur events at affordable prices kindly chat 07067210195 08062991549 Are you guys looking for where to buy ur kitchen stuffs,abayas,shoes nd bags,laces,Ankara,fabrics mg's collections is there for you,you can chat 07068707979 08062991549 Call 07046881166 08064532391 to plc ur orders May Allah bless you all🙏mg's lv you all fisabilillah🤭 *NAGA TA KAINA* *NA SADNAF*🌸🌸 ®️ *_PURE MOMENT OF LIFE WRITERS_* _{We Don't just entertain nd educate we also touch the heat of readers P.M.L}💪🏻_ *Free Novel* *Page 55* Haka na kurawa 'yata Ido Ina ganin yanda jikinta ke b'ari tana cikowa a hankali idonta Dake warwaje na komawa ciki Na kasa gasgata abinda nake gani har matse hannuna nayi Wai Dan na tabbatar da irin mafarkan Dana Saba yi bane nakeyi Akan Zahira ta warke ta dawo yanda take Amma da alama Kam ba mafarki nake ba. Kabbarar da Naseer ke tayi durk'ushe a gaban zahiran da jikinta ya bar B'ari sosai 'yata ta dawo yanda take sai dai Rama da idonta da naga ba Haka yake ba ya dai koma ciki sosai sai dai tuwon idonta dake warwaje ko iya Haka ta tsaya alhamdulillah bansan ma hawaye nake ba sai da naga Naseer ya d'ago Zahira da idonta ke rufe jikinta a mace kirjin ta sai sama da kasa yake Tana maida numfashi wahalar data Sha. "Naeema Kinga Zahira ta dawo daidai Zahira ta samu Lafiya Naeema ki tab'ani na tabbata ba mafarki nake ba? Naseer yace Yana d'ago Zahira da jikinta bashida k'arfi sosai har lokacin idonta a rufe yake Na kasa yarda da duk wuyan Nan da na Sha Ashe Mai Mana magani na kusa damu duk uban kudin da muka kashe Ashe Inna Amina ce zata Zama silar warkewar Zahira Ban tab'a tunanin ko turen da aka mata sun bar jikinta zata maida jikinta yanda take har ta koma siffar mutane kamar yanda take da kirijinta ya ciko.gashinta ya dawo komai nata ya dawo Inka d'auke ramar da tayi da baya rasa Nasaba da abinci da Bata iya ci amma ta dawo zahirarta Alhamdulillah. wajensu na karasa na durk'usa tare da ruk'o hannayen Zahira Na dag'ata tare da fashewa da Kuka Ina Godewa Allah. Dan na fidda rai samun saukinta gani nake kamar mafarki nake Bayan shekara daya da watani Zahira a karshe ta warke ba tare da mun kashe ko sisi ba. A hankali ta bud'e idonta tana "Zan Sha ruwa Umma kaina ciwo yake" Da Sauri na mik'e na fara k'ok'arin nufar randar ruwan Inna Amina Dan na d'ebo mata ruwa Inna Amina ta dakatar Dani tare da mik'a min wani Kofi da ta cika da ruwan zam zam Mai dauke da Addu'oi tace na bata Tasha Da sauri na karb'a na bawa zahiran ta kuwa shanye gabad'aya. Naseer kuwa yaje ya zub'e a gaban Inna Amina ya hau Mata godiya kamar zai kwanta rabon da naga Naseer cikin farinciki Haka har na manta Nima wajen Inna Amina na karasa na hau Mata godiya Ina "Bazan manta ki ba a rayuwata kin share Mana hawayenmu bayan mun fida ran samun sauki Allah ya saka miki da Aljannatul firdausi insha Allahu Zan iya k'ok'arina Dan na faranta Miki kin Zama uwa a gareni" "Nima Kin Zama Mahaifiyata daga Yau ki d'aukeni tamkar Dan cikin ki da Kika Haifa Mama mun sha wuya nemawa Zahira magani Ashe kece Zaki zama silar warkewar ta Mama ki d'aukemu tamkar 'yayanki Zahira kuma jikarki Naseer yace Inna Amina kuwa ta fashe da.mugun kukan daya daga Mana Hankali Hankalinmu a tashe muka hau tambayar ta abinda ya sakata kukan Dak'yar ta tsagaita kukan da take tana "Dadi nakeji da kuka kirani da kalmar mama Ashe Haka ake Jin dadi idan an Kira da mutum wanan kalmar ba'a tab'a kirana da kalmar mama ba Dan ban tab'a haihuwa ba ballantana na San dadinta ko iya wanan matsayin kawai Kuka bani kuka kirani da Sunan mahaifiyarku Kun Gama min komai 'Ya'yana ban Rasa komai ba a lokacin kuruciyata ba sai rashin haihuwa Da Allah ya jarrabceni dashi nakan ji inama ko Mara lafiya Allah ya bani amatsayin d'a a gareni Amma nasan kila haihuwar ba alheri bane agareni Amma a yau matsayin da Kuka bani yasa naji tamkar Allah ne ya amsa min addua ta ya bani ku a daidai lokacin da nake bukatar Mai kula Dani Mai tsayawa a kaina idan na koma ga Allah Alhamdulillah ya Allah Sosai na fashe da kukan tausayin Inna Amina wato a rayuwa kowa da irin jarrabawarsa wani gudun haihuwar yake wani kuma nema yake Ido rufe haihuwa ma arziki ce Ashe Alhamdulillah da Allah ya bani shidda da Umma take min surutun na fiye haihuwa banida bambanci da akuya ( *Ya Allah duk mai neman haihuwa ya Allah ka Bata Dan tsarkin mulkinka ya Allah ka dubi bayinka da idon rahama da ka jarrabta da rashin haihuwa ka musu wanan arzkin Dan su kadai suka San Mai sukeji a zuciyarsu da rashin haihuwa Nan idan Kuma Basu da rabon haihuwa Allah ka Basu hakuri da dangana ka sa hakurinsu ya Zama silar shigarsu Aljanna alfarmar annabi Saw*) "Banida uwa Nima mama ki rik'eni tamkar danki ki ringa saka min albarka bansan Mahaifiyata ba sai wata Dana d'auka Mahaifiyata ce mama tunda na Santa a matsayinta na uwata take azabatar Dani Sakin Baki nayi Ina kallon Naseer da ke magana cikin Jin zafin maganar dake cinsa a Rai ya hau bawa Inna Amina labarin daya girgiza ta tana sallati gani take Taya ma yanda take Jin da ta samu haihuwa zata iya Sadaukar da rayuwarta wajen farantawa abin da ta Haifa har tsawon rayuwar ta sabida so Amma har Allah ya Bawa mahaifiyar Naseer ta ringa azabtar dashi har dasu Zahira data kasance jikarta gaskkya badan tasan ba yanda zaayi Naseer ya kirkiri karya ba da ta karya tashi. Naseeha ta hau yiwa Naseer akan ya nemawa Hajara Shiriya a wajen Allah Kar yayi fushi Maganganu Inna Amina ta Mana cikin ilimi da muka Karu gabad'aya na ringa Jin tabbas na samu wacce zan ringa yiwa kallon mahaifiya Kuma sosai nake jinta a Raina tamkar Mahaifiyata. Adduar da ta ringa Mana da Naseer na dacewa da rabon duniya da lahira yafi komai faranta mana. A takaice sai ga Naseer ya rok'eta ta yarda ta bimu gidanmu ta koma can da Zama Sosai naji dadin shawarar da ya yanke. Inna Amina na zazamewa Dan gani take zata D'ora Mana nauyi mu kuwa muka dage A takaice silar komawar Inna Amina gidanmu kenan da muke jinta tamkar mahaifiyar mu. *Waiwaye* Har ni Naseeru zai yiwa wanan dukan har ya Kai ga ya ciremin hakori daya Umma Kinga fa yanda ya kumburamin jikina Umma Kinga idona? Duk akan Naeema iya station da Matarsa ta kaimu muka kwana Wanan tsinaniyar Yar Sanda tayi ta dukana kamar ta Samu jaka duk Wanan Bai Isa ba sai Naseer ya had'a da dukana toh na rantse da girman Allah sai Naga karshen Naseeru wlh sai Naga bayansa Koda kuwa zai mutu sai na zamewa Naseer da Naeema balai da Masifa bazan iya lissafa sau nawa ya dakeni duk Akan Naeema ba Ita Kuma Naeema Ni kadai nasan Mai Zan Mata wlh" Safiyya tace da kumburarren idonta da Baki Tana duba jikinta da yayi jajur "Naseeru fa ba'a hayyacinsa yake ba Asirce shi Naeema tayi kema kinsani ko Ni sai na dau fansar abinda ta Mana wlh sai tayi nadamar kullemu da tayi hakuri zakiyi Naseer Bai Mana komai ba Naeema dai zamu ga bayanta tunda har wuyanta yayi kaurin da zata kai kararmu ta kullemu" "da ya Zama a hayyacinsa da Kar ya Zama a hayyacinsa ba Abunda ya shafeni wlh sai na dau fansar dukan da ya dade Yana min idan na tashi ki hanani ko ki tsinemin" Hajara Bata ce Mata komai ba Dan tasan tana Kara magana tsaf zata zageta Safiyya mik'ewa tayi da kumburarren idonta ta yi waje Bata zame ko'ina ba sai gidan Alhaji Saad da isarta ta zub'e a gaban matar Alhaji Saad din ta hau cewa ta taimaka Mata da kudi zata tafi asibiti Yan fashi ne suka duro.musu jiya Suka musu shegen duka har hakorinta Suka cire Mata. Sosai matar Alhaji Saad ta tausayawa Safiyya ta shige d'akinta ta daukowa Safiyya kudin aikinta har da kari Tana mik'a Mata Alhaji Saad ya dawo shima ya d'auko kudi Mai yawa ya Bata sosai taji dadin alherin da suka Mata ta ringa musu godiya. tana zuwa gida cikin had'e Rai tacewa Hajara ta shirya Kayanta asubar fari zasu bar garin Kano Dan sun Gama zaman kano ba yanda za'ayi sai ta samu cikar burinta 'yan sanda suzo su Kara Kama su Hajara sosai taji dadin barinsu garin kano daza suyi Dan ta tsorata da kashedin da 'yan Sanda suka musu akan Naeema da Asubar fari kuwa suka dau hanyar calabar suka sauka a gidan Lami. tunda suka Isa Safiyya ta ba zama nemo musu gidan Haya Dan kudin da su Alhaji Saad suka Bata zai Isa su Kama haya sati daya sukayi a gidan Lami kafin Safiyya ta samo musu gidan Haya nesa da cikin gari Dan a wajen gari ta samo musu gidan Haya Dan Bata San kowa yasan Inda suke Kar ma ta Samu cikar burinta Naseer ko Naeema su zo nemansu. rufewar da idonta yayi da San ta ga bayan Naeema yasa suna koma gidan Haya ta hau neman bokan da zai Mata mugun aiki Akan Naseer da Naeema Dan sai ta samu cikar burinta zata samu kwanciyar hankali abinda ke Kara tunzurata da San ganin Bayan Naeema Bai wuce yanda Bashir danta ke jawo Mata magana da mugun satan da ko ita da Hajara Basu tsira daga wajensa ba Wanda dudu du Bai wani shekaru ne dashi ba ga mugun taurin Kai da rashin ji. ganin Dole sai ta samu kudi zata samu cikar burinta yasa ta nemi aikatau a wani gidan abinci da matafiya ke tsyawa su siyi abinci sai data samu wata uku kafin ta samu irin kudin da take so tuni ta cigaba da neman Mai Mata aikin Inda ta Dace da had'uwa da wani kungurmin boka arnen kan dutse da ya kasance bayarabe da ake Kira Oban ya azabar kwarewa akan mugunta Dan tsabar bakin mugunta idan yaso.yana iya maka aiki idan ka samu cikar burinka kafin ka biyashi kudin aikinsa Safiyya kamar ta taka rawa a lokacin da ya hasko Mata Naseer a Abuja wajen da yake aiki Naeema Kuma a gida tana girki Zahira data kwallafa yiwa mugunta a Aji suna rubutu Oban kuwa ya Kara da Gaya Mata abubuwa akan su Naeema cikin zallar mugunta da farin ciki Safiyya ta hau Gaya masa abinda take so ya Mata "Ina so Naseeru ya Zama kungurmin barawo inaso yayiwa wanan uban gidan nasa satar fitar hankali da zai saka Mai gidansa ya Kama shi ya kulleshi ya Kare rayuwarsa a gidan yari. ita Kuma Naeema Yarta Zahira Nan nakeso ayiwa turen bakakken Aljannun masu k'ona jiki da zasu ringa azabtar da ita suna zautar da ita su canja mata hallita daga na mutum zuwa wani siffa Mai ban tsoro Naeema ta Sha mugun wahala akanta duk Inda ta Kai da neman magani Kar ta Dace marasa Imani nakeso a tura jikin yarnya da har zai Kai ta ga Rasa ranta naso Naeema nayiwa Amma nasan nayiwa yarta na rabata da kwanciyar hankali kenan" wani mugun dariya Oban ya kwashe dashi yace aikin yafi komai sauki wani mudubi ya d'auko ya Bawa safiyya Yana "idan Kika je gida karfe dayan dare kiyi tsirara ki fito waje ki kalli mudubin ki Kira sunan Naseeru Sau uku.kina Gama Kiran sunan Naseeru Sau uku sai ki fasa mudubin karki yarda mudubin ya fashe sai daya Daren kinyi yanda na saka ki idan ya fashe Kan danki Bashir aikin zai koma" cikin murnar cikar burinta ta ce Masa zata kiyaye tana so ma ya taimaka ya Mata aiki akan Bashir din ya warke take ya d'auko ruwa ya Bata akan ta dafawa Bashir shayi dashi indai ya Sha zai daina satar kamar ta Masa Sujjada Dan murna ya Kara da "ita Kuma Zahira da kaina Zan tura Mata amintattun Aljannuna da sukemin aiki karfe dayan dare kafin Nan ki tashi ki Shiga d'akin duhun can ki tub'e gabadaya Aljannu zasu Miki aiki" Safiyya da fari taji tsoro Amma rufewar idon San ganin Bayan Naeema yasa ta nufi bakin kofar daya nuna Mata ta tub'e ta shige Oban kuwa yabi bayanta Dan Dama ba Kaya yake sawa ba da ganye ya rufe tsiraicinsa sosai yaci uban Safiyya dataji Kamar wuka ake.zurmuka Mata ahaka ta daure ya Gama ya fito ta fito kafarta a warware. ta zub'e Masa kudin daya cajeta ta dauki ruwa da mudubin ta nufi gida a k'ofar gida ta samu Hajara na soya kosai Dan kudin da ta samo a wajen Lami ta yanke siyar da kosai tunda Yana Dan shigo Mata da canji Dan indai ta dogara da Safiyya sai ta mutu da yunwa ahaka a kamfai dinta take boye kudin cinikinta Amma a banza indai Bashir yaso ya sata sai ya sace kudin karshenta idan ta gayawa Safiyya sai dai suyita fada. Bata cewa Hajara komai ba ta Shige gidan ta Dora ruwan zafi ta ringa gasa jikinta ba wani sauki taji ba murnar samun cikar burinta yasa taji bama tajin zafin a cikin farin ciki take sosai hakane yasa ko abinci Bata iya ci ba Hajara na shigowa bayan ta gama siyar da kosai ta tareta da labarin duk yanda sukayi da bokan cikin farinciki tare da nuna Mata mudubin cikin tashin hankali Hajara ta mik'e tana "Kina da hankali kuwa Safiyya kanki daya kuwa Mai Naseeru ya Miki da kike San ya Kare rayuwarsa a kulle karki manta fa Yayanki ne Kuma Dana Naeema da yarta muke San ganin bayansu ba Naseeru ba idan dai da Raina bazan yarda kiyiwa Naseeru komai ba duka kawai ya Miki na Kuma Baki hakuri kefa karki manta gidansa Kika siyar Masa da Raina wlh bazan Bari ki cutar min da D'a ba Amma indai Naeema ce Kam Nima sai Inda karfina ya Kare. murmushi Safiyya tayi ta fara k'ok'arin boye mudubin tana idan na tashi ki hanani cikin zafin nama Hajara ta kwace mudubin batayi wata wata ba tayi wurgi dashi Safiyya ta saki wani mugun karan tashin hankali tayi Kan Hajara Kamar ba uwarta ba suka hau dambe suna k'ok'awa. Hajara sai tsine Mata take Safiyya tafi.krfinta Haka ne yasa taci karfin Hajara ta Mata shegen duka ko a jikinta ta wurgo Hajaran waje da kayanta tana "wlh sai kin barmin gida sabida tsinannen danki Kika watsawa Dana rayuwa kin cuceni yanzu Bashir ne xaiyi satar da xaa kulleshi" "sai kin wulakanta Safiyya sai kin tozarta har na koma ga Allah adduar masifa da balai xan ringa Miki " Hajara tace tare da d'aukar Kayanta tayi gaba Safiyya kuwa cikin tashin hankali kafa ba takalmi ta yanka daji wajen Oban da zuwanta ta zub'e ya hau girgiza Mata Kai Akan ba abinda zai iya Yi akai sai wani shekarar zai duba kuka wiwi wiwi Haka Safiyya ta ringa Yi tana yiwa Hajara Allah ya Isa Hajara kuwa gidan Lami ta nufa sai data kwana biyu ta nufi tsohon unguwar su gidan da ta taso wato gidan iyayenta da suka rasu mugun halinta yasa ta watsar da kowa nata tasan yayanta ya rasu. Amma Bata San Inda Hassan da usaini kannenta suke ba su take so taji labari a kansu ko zasu iya taimaka Mata Haka ta karaci yawonta Bata samu labarinsu ba sai data shafe wata a gidan Lami kafin ta samu labarin zuwan Usaini da yayi aure Yana Kuma cikin rufin asiri shagonsa yazo dubawa dake calabar Hajara ta nufi wajensa afujajun Hassan da usaini suna sane da ita Sarai sun kuma San halinta hakane yasa Suka bar ma garin calaba gabadaya Dan sun San ko su Basu tsira daga wajenta ba sai dai Hajara ta shammaci usaini da zuwanta ta hau Masa koke koke akan sun watsar da ita a takaice dak'yar usaini ya iya Bata kudin da Bai taka Kara ya karya ba ya gudu Dan dayasan zai ganta ma bazai saka kafarsa a garin calaba ba shi a yanzu ma siyar da shagonsa zaiyi Bai zai Kara waiwaiyar garin ba sabida Hajara. da Dan kudin data samu a wajen usaini ta Kama wani mitsitsin daki ta cigaba da Sana'ar kosai tana Shan alwashin ganin bayan Safiyya har da Naeema Bata da makiya Kuma yanzu data wuce Safiyya da Naeema. kwana uku kenan Safiyya Bata saka bashir a idonta ba hakane yasa ta tashi hankalinta ta hau nemansa a yau ma Haka ta dawo daga nemansa Sam ko bacci Bata iya yi Dan tana tsoron Bashir yayi satar da xaa kulleshi. .duk da k'aramin yarone sai dai tana cikin tunanin taga an shigo da Bashir da ankwa a hannu da kafa an farfasa Masa jiki fuskarsa a kumbure..... comment : Uhmm wlh kuwa koni sis ni kam kwata kwata na kasa kata6u's a ciki 6allai nayi sharhi wlh Allah seriously nake gqya miki jiki,na har rawa yake hannu,na kuwa har karkarwa yakeyi wajen karanta,sa na rantse miki jiya har kuka nayi sssi jin sheheka,na yasa Ammy,na sukayi saurin xuwa gun tambaya'ta lfy anan nake 6asu lbr abun d yasani kuka sai ga Ammy,na ita ma d yinsa wlh d yayyu,na maxa har dasu a kuka muma lbrn ya tuno muna d ni d yayyu,na d Ammy,na lbrn 6akar wuyar d muma mu kasha 6abu kalar axa6ar d 6a'a gwada muna 6a har na talauci a ka ixo muna d 6akin jini sai daii Allah yanda y tsara rayuwa da6an domin kuw sa6anin 6akin jini sae farin jini d Allah y sako munq gami d saurin shiga rae Allah ba ya6on kaii ba d ni d yayyu na akaga hakn 6aiyu yu 6a wlh Allah kunji na rantse muku kunajin ana fadar duk wandq yaga aljanu asifarsu 6a'a koma kwana a duniy tom ni wlh nagqnsu ko ince mungansu dani d yayyu,na d Ammy mu ko Abbun mu yana ganinsu sai daii shi 6a kasafae ba sa6od shi matafiyi,ne aiki gwamnati yakeyi 6ai wancan gari bai wannan garin a cikin garuruwq afin ixaca Abuj toh idan yana a Abj 6a'a basa tsoro shi kum d xaran a kaga yayi tafiya tom'f a ranar, babu kalar tsoron d 6a'a bamu xamuga sun fito a mummunar halitarsu a6un xar tsoron ganin d uwayen jajjayen idonsu d hakoransu xat tsoron gani hakn xasu fito d sharbebiyar wukarsu wae ran mu daii d akace su dauka musmmm na Ammy mu shi suka xo su dauka ko ta halin kakaa wlh idan 6asu ci nasarar kaii muna wukar b sa6od maman mu 6ata wasa d addu'@ tom'f hakn xasuna ta dukan mu cike d mugunta d axa6a hakn camuna addu'a ga axaba bakin Ammy,mu ko bai ra6o d addu'o'e d karatun qur'ani a bakinta sannan'f idan sunji wuyaar addu'o'e su daii,na duk d a lokacin ina little girl sssi a cikin yan'uwa,na nite karama a cikinsu domn wani axa6ar nake iya tunowa wani ko 6ana iya tunosa sa6od qankanta ta sai daii su din anty's ko sun fada nake tunowa ke mu'f har takai ta kawo ko bayi ma wlh gagarar mu shiga yakeyi sa6od muna shiga wasu 6akaken halittta xamuna gani ko kum kaga mussoshi waton mage 6akake kiriin dasu d jajjayen idonsu kum sanye d kacha a kafafu nan su suna muna dry d gwalo ido su ko wani sa'in 6akin su na fidda wutaa jawur kum duk a 6ayi kum idan kin jiyo ki fita ba hali sa6od ga wasu nan sun tare kofar 6ayi diin uhmm addu'a,ce kawae ke fidda ke 😭😭😭😭 kum sis ko a6unci ba mu d ikon ci a waje ko a daki hakn xakiga magen nan suna ta watso muna kasa a ciki suna muna rawa d kachar su abun d bamu ta6a gani 6a wae mage d kacha humm kum wlh irin aljanunan d a ka turowa xahira hkn ne a ka turowa anty,nasu itama daga shigarta 6an daki shikenan sai kararta a kaji miyagun nan dakyar suka fice ta itama sai kinganta a6un tausayi Ammy,mu tasha wuyaa akan hakn ita ma duk ta rami dakyar dae suka fice ta sa6od ita ma Ashe tana d iska 6asu dai bayana 6a saii d wayan nan miyagun arna nq shige'ta su suka kwazga dacu d rokon Allah dakyar suka fice'ta 6ayan dukiyq tasha kashi ke muma'f har d sunannakin mi aka saka a laya dn mu tagayara damu har maman mu Allah 6ai nufa ba y tona asiri maman mu tagani d kanta miyagun aljannun d a ka ixomuna ne a gid sun gwada muna bane kaii har takaii ta kawo wlh kinsan tsarin nan d akeyi a gida a ke sawa na tsari har dashi a kasa Abbun mu yayi Ammn wlh miyagun nan marassa imani ke ciro,sa su aje masa abun sa a kofar daki ke fa ko daki xaki shiga idan basu so 6a cewa suke karki shiga dakin nan in kuw kishiga sai sunci u6anki ko su,ce karki rufe daki tom'f kikayi wlh sai kin ya bawa aya xakin'ta hmm duk yanda xan baku lbr nan xaka,na daukar kamr ba gaske,bane mu kadae mu kasan me muka gani ko mukaji wlh sis har dakansu d suke kina iya jiyowa gashi xamanin 6a'a san wani tayi'ss ba simuntin,ne akeyi iriin me sulmin,nan tom har dashi xakaji yana Amsa kuw sa6od dakansu a lokacin Abbun mu bayi 2 yayi d rixabuya maman,mu daii tasan lfy qlau ta kwanta can cikin 6accin ta taji an tsokale cikinta y dinga murda mata gashi 6ata son tadda mu 'ya'yan ta sa6od murnar ta mun samu yau an barmu munyi bacci d kum qarfin addu'a kingamu kamr wayand nasamu yan ci fitowa dagq wani kurkutu sin samu yan,ci hakn ne gun mu domn musamu munyi bacci sssi Ashe ace bakuwa xakuyi sa ba domn hakn suka sakowa mamn mu ciyon ciki gadan gadan a hankali ta dore bakinta sa6od kukan d yaxo mata na axa6a karta tadamu hakn cikin sanda tafito daki ta nufi bayi nan'f taga gari na juya mata hakn take kada kafarta tana axa kafa a 6ayin ana yanke 6ayin yana rusgawa ita dae 6ata d xato taji anfisgo'ta sae gata a gefen daki shikenan har rixa6uwar mu sae da ta rusga mukuwa tsawar ta taddamu gashi nice qarama a cikin su sssi sae er qanwa'ta dake bimun tagoyi jin wannan tsawar d aka 6uga,ne ta firgita mu muka kurma ihuu Allah sarki uwa mance ciyon d ke damunta tayi a guje tayo daki kanmu da addu'a lokacn Abban mu baya garI sannan kiji tsitss har d anty,na akaso kashewa 😭😭😭 hmmm kaii 6ari gsky komu munga rayuwa domn wani hakki sae inda Allah mu kam wacce taso ta Aure babqn mute tayi wannqn aiki ita d sauran makiya yan'uwanca masu 6akin cikin samun sa suka hada hannu d ita wurin ganin 6ayan mu dn ta Aure baban m dn acewarta baban mu yana sakarwa iyalinsa d ita yafi dacewq ba wamu ba d Ammy,mi 😭😭 [8/2, 3:53 PM] +234 810 713 7956: wlh ko wane dan adm d iriin tasa kalar rayuwar d rabbu y ru6uto masa wlh sai daii maganinta d warakar'ta addu'a CE domn kuw wayan nan d nayi muna hakn sunga karshen su tun anan duniyr kafi axo lahir wlh pg innan y tuno mina d namu qaddarr rayuwr d mu kayi mumq ta miyagu Allah ka isar miki ke ma xahira dake d umm naema wlh Allah sai y saka muku tun anan duniyr sakaya ke kqmasu insh Allah ni nace miki sae sun girbi shairin su d hannu musmmnb hegiyar nan safy ita d 6akar uwa hajr u6angiji y dibar muku hakkin ku tun a duniyr kafi aje lahir yayi muku hisabi d sakaya dae dai abun d suka gir6a Allah ni'ematar d rayuwarku advertisementUwargida da amarya harma da yanmata kuyi kokari kuma kumallaki sabulunnan daya tamkar dubu wato mg's herbal whitening black soap kunemi naku kujaraba kugani domin sabulun yayine bakarya Yana Repairing damage skin Ina Mai fama d pimples Black spot Sunburn Stretch mark Wrinkles Black head Dama dukwani matsala daya danganci fata wani abunma koda bakida komai you can still use the soap zai maida Miki fatanki luwai luwai kalar hutu😎 kunemi mg's kusha mamaki bazance komai b gani da ido ance yakoriji bama cika Baki jst gv it a try nd see for urself🥰 wise pupil nasan kunfahimci zncn👏 Amare Kuna Ina wnn🥰mg's yatanadarmuku soap nadaban duk wacce tayi using soap din Baku bukatar wani dilke kije aita dirjemiki jiki zakuga ynd skin dinki zaidinga haskawa Yana walwali😘 maiso yy mgn ta 08062991549 Call 08064532391 Muna maraba damasu siyan daya kosari maisokita glowing wani zncn dai sai kungani da idonku zaku sheda Har ilayau munada humra da turaren al'ajab na tsugunno maiban mamaki yahanzarta before yj sold out🥰be part of the glow gang say no to skn prblms🤭DNT be left behind Soap price:3k Pls kayanmu bn bleaching bn organic ne zaifiddomuku d ainihin natural beauty dinkune bn bleaching bn ko bakida komai you can use the soap zaikara gogemiki jikine fatanki tayi fresh Turare:3k Humra:2500 Maiso should chat 08062991549 Team glow skin🧖🏻‍♀️💋 *NAGA TA KAINA*      *NA SADNAF*🌸🌸 ®️ *_PURE MOMENT OF LIFE WRITERS_*          _{We Don't just entertain nd educate we also touch the heat of readers P.M.L}💪🏻_ *Free Novel* *Page 56*        Safiyya daskarewa tayi a tsaye jikinta ya kwashi mugun rawa data ga manyan bindigogi da 'yan Sanda ke rik'e dasu. Sunfi su goma kafin su karasa ma wajen Safiyya, Safiyya ta zub'e a kasa da kumburarren fuska Bashir ya nuna Safiyya Yana "ita na bawa Ajiya" Cikin inina Safiyya ta zaro idonta cikin  fad'uwar gaba tana "Ajiyar me ka bani Bashir'? Tsawan da aka daka Mata da mugun k'arfi daya kad'a mata yayan hanji ya sa ta kame bakinta da hannu Daya daga cikin Yan sanda ya Bawa sauran umarni Yana "ku Shiga ku hargitsa d'akin da kyau indai aka samu gwal da kudin to tabbas ita aka bawa ajiya tafiya zamuyi da ita" Safiyya ba damar magana sabida bindigar da aka Dora mata akai har fitsari ta saki a wando Dan kayayyakinta aka watso su waje Ana ta neman gwal din da Bashir ya sato daga shagon wani Mai siyar da gwalagwalai da akwatin kudi. Sai dai har aka Gama birkita d'akin ba'a  ga komai ba Dan abokanan Bashir masu irin halinsa ne Suka gudu da  kudi da gwalagwalan Bashir shi Kuma aka kamashi San a sake shi yasa yayi niyyar kulawa Safiyya sharrin ita ta saci kudin inyaso a cika shi ita a kamata. Bai tab'a Jin kaunar mahaifiyarsa a ransa ba hasali wani zubin zuciya Kan raya Masa abubuwa a kanta na ya Mata mugun abu ko ya ma kawo karshenta (Wanan Yana daya daga cikin asirin da Safiyya tayi daya jefa Dan cikinta a cikin wanan halin sanan nayi mistake sosai a wajen tsara rubutun labarin Dan sai da muka sake waya ta Kara fahimtar Dani labarin wajen auren Safiyya na Dan jinkirta shi a rubutun Dan Bashir din sa'a Minal ne  'Yar Naeema ta uku gudowar da Naseer da Naeema sukayi Kano a lokacin da ta haifi Minal a lokacin Safiyya tayi aure har ta haifi bashir Wanda ta ta sake samu ta  aura a shine suka siyar da gidan Naseer. Zawarcin da  Safiyya tayi  ne tare dasu ta tsula tsiyarta haka amma dai a karbi labarin Haka sabida ya tafi daidai tunda ban dai cire komai a game da rayuwarsu ba sai na Naeema dana dan rage sabida tsayin novel din zan dan Kara bada labarin Safiyya a takaice sabida labarin ya tafarmin dai dai Kar dai ku rikice sai da Naeema ta bibiyi labarin taci gyarana) Dan Sandan umarni ya bada a tafi da Safiyya a hada a kullesu tunda har Bashir din yace  Yana Bata ajiya ya zama dole itama a bincike ta da kyau dan bashir ce musu yayi idan yayi satar ita yake bawa ajiya. Wani irin ihu Safiyya ta saka a lokacin da taga ana k'ok'arin saka mata ankwa ko sauraranta basuyi ba. Suka buga Mata gindin bindiga da suka ga tana tirjewa suka sa.mata ankwan Suka zuba su a mota ita da Bashir Sai kuka Safiyya take tana rantse rantse Bashiri bai bata ajjyar komai ba. A takaice sai da Safiyya ta Sha bak'ar wahala a hannun 'yan sanda ta Sha bak'ar duka daya canja Mata kamani Dan Bashir dagewa yayi akan ita ya Bawa ajiya kudin. Sai data samu wata guda  a kulle kafin wani dan sanda dayaji Safiyya ta kwanta Masa ya taimaka wajen bincikar Bashir din ta hanyar rarrashinsa ya fada Masa gaskiyar wayanda Suka gudu da gwalagwalan da kudi. Sai da aka kamosu aka saki Safiyya da kyar. Safiyya kuwa masifar da Bashir ya jefa ta a ciki yasa ta Kara kullatar Hajara a ranta ta ke Kuma Kara Shan alwashin ganin bayan Naseer da su Naeema tunda Dan Naseer Hajara ta fasa mudubin daya jaza wa danta wanan masifa da ita kanta a rayuwata Bata had'a San Bashir da komai ba. Hakane yasa da fitowar ta ta koma wajen Oban ko zai iya taimaka mata a saki Bashir sai dai duk yanda Suka Kai da suyi aikin ba'a sake shi ba. Akan dole ta hakura ta saka aka mata aiki akan Ado dan sandan dake santa. Nan da nan kuwa ya fito ya aureta a madadin ya sata a gidansa sai shine yake zaune a gidanta da Sunan zai cigaba da biya Mata haya. (Karku rude a takaitacen labarin Safiyya nake Baku Aurenta na fari ta haifi bashir na biyu data tayi ta siyar da gidan Naseer ta haifi Asmau da   Safiyya wacce aka sawa sunanta. Mijinta na fari Saki uku ya Mata daya gano asirice shi tayi ya Aureta Na biyun Kuma data haifi Yan biyun barinsu tayi a can wanan sai da suka  yi wayo ta sa aka Mata aiki akan Umar ta karbo su daga wajensa  ta rik'e su  amma tabbas Bashir asirin Satan da suka so Zahira tayi shine ya Sha alewar daya saka shi satan bandai canza komai ba dafatan Kun Gane mu cigaba da tafiyar da labarin ahaka karku rikice laifina ne Dan yanzu idan na cigaba a haka kuka ga na Sako Asmau da Safiyya yaran Safiyya a labarin zaku rude bazaku gane ba shiyasa na baku labarin Safiyya a takaice) Sosai Safiyya take Jin dadin irin wahalar da Zahira take Sha ita da Naeema da Naseer karewar komai da naeema ke dashi yafi komai faranta Mata da zata samu ma abinci ma so take ya gaggaresu ci Ko sau daya batayi nadamar abinda tayiwa Hajara ba hasali duk lokacin data tuno halin da Bashir.ke ciki a kulle takan ji kamar ta nemo Hajaran tayi ta dukanta sosai ta saka Hajara a jerin makiyanta tsabar masifa ma tana sane da duk halin da Hajara ke ciki. Haka ma tana da labarin halin dasu Naeema ke ciki dan takanje wajen Oban yayi surkulle ya nuna Mata su Taji dadi sosai da Aljannu ke fita daga jikin Zahira idan za'a Mata rukiyya sai an Gama azabtar da  Zahira angama rukiyya Aljannun ke komawa jikinta. Taso ta Kara yiwa Naseer asirin Dan ta mugun tsanarsa sabida Hajara data ga bata  so wani Abu ya same shi,sosai ta Sha alwashin ganin bayansa dan har yanzu da tab'ab'unan dukan Naseer a jikinta. ta dan dakata  ne kawai Dan wahalar da suke Yi da Zahira har filinsa da ya siyar akan nemawa Zahira magani ya faranta mata sosai  burinta ma gidan Naeema shima su siyar a garin nemawa Zahira magani dan tasan kome za su yi bazasu Dace  da samun  magani da zai yiwa Zahira aiki ba. Auren ado da tayi ma ba Wanda yasani balle Hajara ta sani Ahaka har ta haifi yarta hauwa da itama taji tana balain Santa takan tuna yaranta asmau da Safiyya dake gidan Umar har jibi tana Kan bak'anta nasan ganin Bayan Hafsa da ta azabtar da ita a gidan umar. Sati sati take zuwa wajen Oban dan taga halin da su Naeema ke ciki A lokacin da asirin da tayiwa Zahira ya Kai  shekara da wata  uku Oban ya daina iya ganin komai akan su Naeema sosai hankalinsu ya tashi daga shi har Safiyya Oban yayi ta tsubbuce tsubbuce dan yaga halin da suke ciki sai dai har ya gama tsubbunsa bai iya ganin komai ba A lokacin kuwa Naeema ta had'u da Inna Amina har rabbi ya amsa adduarsu Amina tayi nassarar fitar da Aljannun daga jikin zahira. Safiyya tunda  Oban ya daina ganin halin da su Naeema ke ciki  hankalinta ke tashe ta tuna lokutan baya da idan suka yiwa Naeema wani mugun abu toh mudin suka daina ganinsu ta mudubin tsafi toh Naeema ta samu mafita ne tana tsoron aikin da tayi akan Zahira ya dawo mata. A haka ta kasance cikin Zullumi yau da safe Ado ya fita aiki da sassafe ta gama dan aikace aikacen gida tayi wa hauwa wanka da  bata fi wata biyu ba lokacin. Tamkar gwal take Jin hauwa a ranta Tun bata girma  ba take cin burin girman ta idan tana hararo girmanta har farin jinin Zahira take hango Mata da irin masu kudin da zasu ringa layi akanta idan kuwa Asmau da Safiyya suka dawo gabanta har maganin farin jini zata karbo musu dan sosai taci buri Akansu suma duk da basa gabanta tana balain Kaunar yaranta da bata San wani abu ya tab'a Mata su babban burinta yanzu ma ta Samu Bashir ya fito daga gidan yarin. Tana kitchen  tana k'ok'arin juye tuwon data dumama dan taci taji  hauwa ta fara tsalla kuka aguje ta fita daga kitchen din. Abinda ta gani ne yasa jikinta d'aukar rawa hallitar hauwa ne ya canja gabadaya ta koma wani irin hallita wuyanta ya kumbure exactly yanda Zahira ta koma Kamar wata kadangare haka hauwa ta dawo hankali a balain tashe Safiyya ta saki ihu tunaninta na bata Aljannun zahira ne suka dawo.mata jikin 'ya. Bata iya daukarta ba sabida zafin da jikinta ya d'auka ta hau kuka ta nananada Hauwa  zaninta  kafa ba takalmi tayi wajen oban. Tana zuwa ta zub'e a kasa ta ajiye Masa hauwa da siffarta ya Kara Zama na kadangare sosai Ihu take akan Oban ya taimaka Mata. Oban kuwa take ya hau surkulle Yana yare da shi da Aljannun jikin  hauwa kawai keji. Sai dai duk yanda Oban yaso su bar jikin hauwa k'i sukayi akan ba haka akayi dasu ba har sai sun kwashi shekarun da akace suyi tun farko. Oban kuwa baya so nunawa Safiyya ya kasa fitar Mata dasu hakane Yasa ya yanke Mata kudi Mai yawa akan ta kawo akwai Abubuwan da zai siya  ya roki Aljannun su fita dan zuciya sukayi sabida matar data fitar dasu ta kokona su. Safiyya hannu ta dora aka ta hau zunduma ihu tana ya taimaka Mata bata da ko sisi ado tana aurensa ne kawai Amma ba kudine dashi ba dan matarsa ke karbe albashinsa. Matarsa Kuma ta fita hatsabibanci tunda har Oban ya kasa aiki akanta kasancewarta itama bayarabiya. Ba Inda Safiyya bata je neman kudi ba amma Bata samu ba tayi kukan ta tsinewa Naeema da Zahira yafi cikin kwando Ado kansa guduwa yayi daya ga yanda hauwa ta dawo dan sosai ya tsorata da yanda hauwa ta dawo dadin daya ji Safiyya dama bata San  gidansa ba dadin dadawa ma Dama Yana neman hanyar da zai gudu sabida kudin hayan da Safiyya ke damunsa da ya biya. Sosai Safiyya ta rame ta kanjale a madadin taji tsoron Allah ta yarda Allah ke Kare Naeema tunda duk abinda ta nufeta dashi kanta yake komawa bata ga haka ba zuciyarta k'ek'ashewa tayi tana dora alhakin duk abinda ya sameta Akan Naeema da Naseer har da Hajara  sai Kara kula wani sharrin take Ta Kara komawa wajen Oban cikin tsananin san dai ta ga bayan Naeema da Naseer Ta karkace ta hau gaya masa abinda take so dan gani take ta haka kawai zata dau fansar yanda yarta ta dawo da ita kanta take fita aguje sabida tsoratatan da take yi "Kayimin aiki Mai k'arfi Oban inaso na ga bayan Mutanen nan duk Inda kudi suke Zan nemo na kawo maka "tunda Aljannun da aka tura jikin Zahira sun bar jikinta inaso a tab'ata inaso ta sakawa Naeema hawan jini Kar tayi albarka Sam tayi bakin jini Kamar ungulu ta tsufa a gaban Naeema. Shi Kuma Waleed dinan dana ga Kamar shine zuciyar Naseer inaso ya lalace a saka kiyayya tsakanin shi da Naseer a karshe Naseer ya zama ajalinsa Yan sanda su kulleshi. Oban kayi min wannan k'ok'arin ni Kuma duk abinda kakeso Zan maka tunda har 'yata hauwa haka Zan ringa ganinta zuciyata na ciwo inaso zuciyar Naseer da Naeema yayi bindiga bana San aikin Kuma ya karye duk Inda zasu Kai ga neman taimako" Mugun dariya Oban ya kwashe dashi ya d'auko wasu allurai da kwarya ya Bawa Safiyya yana ta jejjera alluran a ciki ya d'auko wani Abu kamar bby na namiji da mace yace ta binne akwai Wanda zaiyi daga Nan indai ta binne aikin gama ya gama Amma fa idan har akayi nassarar karya asirin duk wani Abu da zai biyo baya tayi kuka da kanta. Batare da tunanin komai ba tace ta amince sabida mugunta tace sauran yaran naeema ma a tab'a su. Sai da ta kwana da Oban ya ci ubanta yanda ya kamata ta dawo gida tayi zazzabin sati guda kafin ta samu karfin neman abinyi tunda ado ya gudu Ta dai saka Oban ya Mata aiki Dan ya dawo. A Haka ta samu ado ya dawo ya Kuma biya Mata haya. Halin da take ciki da hauwa da ita Gata kamar dabba Kamar mutum yasa ta nemi kudi taje unguwarsu Umar tsohon mijinta a lokacin data Isa Bata sameshi ba sai Hafsa. Yaranta duk sun tafi makaranta,Asmau da Safiyya nata zuba aiki kamar jakai yaran nata sun girma Masha Allah Kuma kyawawa kamar yanda taso ganinsu. Sai dai kana ganinsu kasan a wahalce suke dan Hafsa ba k'aramin azaba take gana musu ba. A takaice Hafsa k'in bari tayi ta kwashe yaran sai da suka ci uwar dambe Safiyya ta Sha kasa dak'yar da kyar Umar daya dawo ya samu Hafsa ta Bari Safiyya ta tafi dasu dan shima kasan tausayin yaran yake ji uwarsu ya tsana Amma Yana san yaransa tausayin yanda hafsa ke gana musu azaba yasa yaji dadin zuwan da Safiyya ta yi dan ta tafi dasu at least zasu samu yanci a wajen Mahaifiyarsu. Safiyya sai da umar ya Bata kudi Kafin ta yarda ta tafi  da yaranta da takejin zuciyarta fari Kal da dawowarsu gabanta. Hajara Sosai take Shan wahala da kosai da take siyarwa Bata da burin daya wuce ta samu kudi ta fara tab'a Safiyya da take Shan alwashin ganin bayanta ba ranar da zata wuce Bata tsinewa Safiyya ba takan Yi kuka idan ta tuna  irin korar Karen da Safiyya ta Mata Wai ace Yar cikinta data fi so duk a cikin yaranta itace ta daketa har ta koreta daga gidanta yau badan usaini kaninta ba da Bata da wajen da zata zauna lami ma Mai taimaka Mata kad'an kad'an itama ta bar garin calabar. Mai taimaka Mata a cikin yaranta Kuma Naseer ne shima Naeema ta kwace shi ya Fifita Naeema akanta Shiyasa a rayuwata ta tsani Naeema takejin itace duk ummul abaisin daya saka ta tsinci kanta a cikin wanan halin dan da ta rabu da Naseer cikin sauki da bata kai ga aikatawa Naseer Abunda ta aikata Masa da har yazo ya shafeta tafi Shan wahalarsa ba tunda da ace Naseer nada kudinsa da yanzu Yana da gidaje ya Kai uku tunda ada din ma ya mallaka Mata gida biyu. Ba abinda Naseer baya Mata Amma Naeema ta Mallakeshi ta rabata da danta Tijjani kuwa dama kullum cikin yi masa baki take tunda har ya Fifita Murja a kanta a wajenta Kam yaranta biyun Nan Tijjani da Safiyya idan tana da dama sai taga bayansu ba ma kamar Safiyya da take Jin da tana da dama kasheta zatayi tsaf abinda ke take Mata birki kawai shine kudin da bata dashi. Da zata iya samun damar da zata Shiga  wani  kungiya da ta  Shiga  dan ta samu cikar burinta da ta  saka an maidawa   Naseer arzikinsa. Ta rabashi da Naeema ta azabtar da ita da Zahira ta wahalar da Safiyya Murja da Tijjani a rayuwa sai dai ko kudin arziki Bata dashi kudinta ma yanzu na cinikin kosai a magani yake tafiya Dan fama take da wani irin ciwon kafa dake hanata bacci ta Rasa Mai ya haddasa Mata ciwon kafa. Tijjani Talauci da tsananin rayuwa yasa baya iya neman Naseer yanzu Dan wayar gari yayi aka koreshi daga aiki duk Kuma buga bugan da zaiyi baya iya samo ko sisi. Sai Murja ce ke dan iya rike gidan shima cikin wulakanci Sam Baya lallaba murjan tana Masa iskanci ko gori zai nada Mata na jaki ya Kuma bar Mata gidan Yanzu haka yaransu hudu duka Mata bayan yarsu ta fari ta Kara haihuwa uku da kusan kansu daya gwanin shaawa yaran Murja ko kuda Bata so ya tab'a Mata Yara Allah ya jarrabceta da balain San yaranta shiyasa duk Inda kudi suka shiga tana k'ok'arin nemowa dan ta farantawa yaranta Rai. Mahaifiyarta Rabi a haihuwa yarta ta uku Allah ya Mata rasuwa ta hanyar Hatsarin mota sosai Murja tayi kukan rashin ta. Yaranta kawai da take gani ke faranta Mata rai ko  a makaranta aka tab'a Mata su sai taje tayi masifa tayi balai ko yaran makota ne Suka tab'a Mata Yara sai ta Rama musu. Yarta Murja data ci sunanta  nada shekara goma  Mai bi Mata Ramlat nada shekara takwas  Fareeda na shidda sai ummi nada hud'u. Tashin hankalin da Murja ta fara fuskanta a rayuwarta Bai wuce rashin lafiyar da yaran nata suka fara lokaci guda ba Kamar ta zauce sabida tashin hankali Banda Murja takwararta Ramlat ce ta fara amsa Kiran Mahallicinta Inda Murja sai da aka dangana da kaita asibiti sabida sumewa tayi tayi Sati biyu kafin ta Gama dawowa hayyacinta  fareeda itama tabi Bayan Yar uwarta hauka tuburan Murja ta kusa yi sai da Karfin adduoi ta dawo daidai Fareeda itama satinta uku ummi tabi bayanta. Rasuwar yaran Murja uku yasa Murja ta dan samu tab'in hankali kad'an Amma ba sosai take tab'a haukan ba takan Yi Abun marasa hankali (Inaso na Dan bada labarinsu Suma gajerce Dan wlh na gaji Bai xama lailai na Kara tabo bagarensu ba Dan yanzu Haka ma daga Naseer har Naeema ba labarinsu sukeji ba tunda suka je suka nemi yafiyar Naeema dasu Zahira.) Bayan yaranta uku sai data Kara haihuwar biyu sai sun girma ta shaku dasu sai su koma ga Allah a irin haka yasa daga Tijjani har Murja Suka bazama neman taimakon Mallamai anan wani ke cewa Murja taje ta nemi yafiyar yaran data zalinta a baya sai ta nemi yafiyarsu zata ga daidai (Ba fiction a labarin zalincin da Murja tayiwa su Zahira da Kuma jarrabtar da Allah ya Mata a rayuwa na rasa.yaranta idan ta haifesu bamu sani ba ko ta Kuma haihuwa Dan tunda sukaje suka nemi yafiyar Naeema baa Kara Jin labarinsu ba) Naeema Samun saukin da Zahira tayi Yana cikin Abubuwan farin ciki da suka sameni da bana mantasu Haduwa da Inna Amina danake Mata Kallon Mahaifiyata dagani har Naseer shima Yana cikin Abubuwan da har gobe bana mantasu. Inna Amina tsohuwa ce Mai tarin ilimi dan Zan iya cewa har tafi Naseer ilimi shigowarta rayuwarmu yin Allah ne dan ta silarta na Kara samun warwarewa wasu matsalolinmu  ba iya ni kadai ba har Naseer. Satinta uku a gidanmu bayan tafiyar su Nadeeya makaranta muka Shiga wajenta dan mu gaisheta Zamanta a gidanmu yasa nake Jin kamar ita din wata garkuwa ce a garemu gabadaya Dan tace Mana zama Bai Kama mu ba makiyanmu zasu cigaba da bibiyarmu da sharri Addu'oi ta bani da Naseer take akan mu ringa yi daga mu har yaranmu. Zahira kuwa sabida ramar da tayi da kuma shiru shirun da takeyi yasa Inna Amina tace mu bari ta dawo daidai sosai ta samu wata uku tana Shan magungunan data had'a Mata kafin muyi tunanin Mai data makaranta. Hakane yasa muke kula da Zahira dagani har Naseer muke ririta ta. Nidai gani nake duk da sun fita kamar yata Bata dawomin yanda take ba Kamar  da da   nayiwa Inna Amina magana cemin tayi kar na damu zata dawo daidai mu dai cigaba da Bata maganunanta Koko da kosai da take Sha a lokacin da muka Shiga d'akin nida Naseer tana ganinmu ta saki murmushi muka zauna akan tabarma ita Kuma tana daga Kan katifa Sai data karasa kokon  ta ajiye kofin muka hau gaisheta Cikin faraa ta hau amsawa tana saka Mana albarka Kamar yanda ta Saba wanan albarka da take sa Mana da gamawa da duniya lafiya da take mana adduarsa ba karamin faranta mana Rai yake ba Sai da ta Gama saka Mana albarkan cikin murmushi ta kalli Naseer tana "Babana yaushe zaka koma wajen aikin naka ne kasan zaman Haka bazai yiwu ba" Murmushi Naseer yayi cikin Jin dadin kulawarta inama baiwar Allah nan ce mahaifiyarsa "Mama Abunda yasa bazan koma ba nasan Indan na koma ma korata zaayi dan na kusa shekara Kinga banje ba Batare da na Kuma Gaya musu dalili ba hakane yasa nake neman aikin anan ko Allah zai saka na Dace na samu idan ma ban samu ba Zan ringa aikin ginin da nake yi abaya" "Karka damu ka koma insha Allahu ba Abunda zai faru kana tare da Addu'a ta daukaka ma zaka samu" "Zan koma.insha Allahu mama ngd" "Mamana ke kuma wane sana'a zakiyi kinsan zaman haka ba dadi"? "Nasani mama kudi nake nema wuyanta na samu kudin bazan rasa sanaar da zanyi ba" "Allah ya dafa muku ya muku albarka ya yiwa yaranku albarka yanda Kuka taimaka min Allah ya taimake ku" Cikin farinciki muka hau amsawa da ameen sosai adduar da take Mana ke Mana balain dadi a zuciya. Washegari kuwa Naseer ya nemo kudi ya hada kayansa da zumar washegari zai tafi Muna zaune gabad'aya mu da yamma muna Hira da yaranmu a can gefe Kuma Inna Amina na zaune. Waleed nadaga Gefen Abbansa Yana Masa Magiyar ya tafi dashi Abujan gobe. Hannayen Waleed ya ruk'o cikin so da kaunarsa sosai yake Jin kaunar Waleed a Ransa sabida hankali da tarbiyya da Naeema ta bashi ga tausayi kamar me a islamiyya da Boko shi yake zuwa na daya Yan unguwar kuwa duk sun San Shi sabida sharan Massallaci Haka suke saka Masa albarka. "Idan ka bini Waleed ya zakayi da makaranta kayi hakuri idan ka Gama primary sai na nema maka secondary acan sai muyi zamanmu ko" Gyada Masa kansa yayi Ya kalli Nadeeya dake ta fama da.booklet tana karatun pass question papers Dan shirye shiryen exams din waec suke. Mita kawai take akan Bata iya Zane ba Naseer na Mata dariya a hankali ya ringa tambayarsu game da karatunsu Hankalina na wajen Zahira dake gefe tayi shiru ta kurawa waje daya Ido sosai tausayin yata ke dawainiyya dani dan badan wanan larurar bama da yanzu kila ta samu ma admission ko tayi aure Allah yasan su Umma sun cutar Dani said dai Allah ya saka Mana. Yata duk ta Zama shiru shiru Dan dai Inna Amina na Dan kwantar min da hankali akan Kar na damu zata dawo daidai Wuyanta ta gama Shan magungunan ta sosai na matsu ta dawo daidai na nemi kudi na biya Mata waec itama dan bana San kannenta su Mata nisa. Sallamar Tijjani da matarsa da yarsu ne yasa muka d'ago Naseer cikin farin ciki yaje ya tari Tijjani Dana ga yabi yafice a cikin hayyacinsa ya rame sosai bashi kadai ba har matarsa. Nadeeya mik'ewa tayi da Sauri ta shige daki Bayan ta gallawa murja harara Ni kuwa na hade Rai sosai Dan ban manta abinda tayiwa yarana ba har gobe da tabon dukan da tayiwa Zahira a jikinta,Nadeeya lokaci lokaci tana fama da ciwon ciki Mai tsanani sabida sabulun data ringa Bata a wake a gaskiya bana Jin Zan yafe Mata zalintar data yiwa yarana. Ban amsa gaisuwar datamin tana rau rau da Ido ba illa Tijjani kawai Dana gaisar Su Minal duk gaisheta sukayi Zahira itama ta gaishesu cikin sanyin murya. Kuka Murjan ta fashe dashi tana nuffar wajen Zahiran ta kamo hannayenta tana "Bayan duk abinda na Miki har inada mutunci a idonki da Zaki gaisheni bayan duk zalintarki da nayi bayan horar yunwa Dana Miki Zahira har ki iya gaisheni Dan Allah dan annabi ku yafemin keda Nadeeya wlh hakkinku ke dawainiya dani Yarana biyar Dana Haifa na shakku dasu mutuwa Suka yi sabida zalintar Dana muku na biyewa San zuciya ta Ina ganin ku ba yarana bane Dan Allah Zahira ki yafemin mmn Zahira ki yafemin Abban Zahira kaima ka yafemin wlh sharrin shaidan ne" Kuka take sosai cikin sheshek'ar tana bamu labarin yanda yaranta suka koma ga Allah take Kuma naji zuciyata tayi laushi tausayinta ya rufeni Zahira yata Yar albarka take tace Mata ta yafe Tijjani godiya suka hau mata Nima nace na yafe Dan Alhamdulillah tun a gidan Duniya Allah ke hisabi Murja a gidan Duniya Allah ya hukuntata Duk yanda mukayi da Nadeeya ta fito kin fitowa tayi Murja kuwa ta bita har d'akin Ta.kuwa shige bandaki ta rufo k'ofar tana "wlh bazan tab'a yafe Miki ba kin cutar damu batare da mun.miki komai ba kin bani sabulu a cikin wake kin Mana horar yunwa har yau Ina fama da ciwon ciki sabida sabulun da Kika bani naci wlh bazan yafe ba" Ta karashe tana kuka." A Haka Suka Mana Sallama Suka tafi batare da Nadeeya ta fito balle tace ta yafe ba sai Naseer ne ya kwantar musu da hankali akan Kar su damu zata yafe a hankali A waje Naseer da Tijjani Suka kebb'e Suka bawa juna labari halin da duk suka tsinci kansu a ciki Sosai Tijjani ya tsorata da hajara har Safiyya yacewa Naseer ya zama Dole ya Kara nisantar su Dan shi yanzu kaduna zasu koma zai nemi aiki a can ko zasu Dace Sai da suka tafi Naseer ya dawo yayi ta yiwa Nadeeya fadan Abunda tayi sai Inna Amina ce ta saka Baki bayan tayiwa Nadeeya naseeha kafin ta iya cewa ta yafe. Washegari da sassafe Naseer ya tafi cikin Ikon Allah kuwa Basu koreshi ba suka Karbeshi. Bayan tafiyarsa da wata biyu na fara lura da canji a wajen Yata Zahira na farko Bata San tayi sallah sanan abu kad'an sai ta hau yiwa kannenta masifa tana neman dukansu idan kuwa nayi magana sai ta dakamin tsawa Ba iya Zahira ba har Waleed na fara lura da canji a halayensa....... *Wlh Nagaji alhamdulillah duk sakon danake ya isa a gane an dauka a novel dinan yanzu maganar da nake labarin Naga ta kaina bashida karshe gaskiya Dan Haka a iya Inda aka bani labari anan Zan tsaya baifi saura 3 to 4 pages ba page 60 Zan tsaya idan Allah ya bani iko* *Comment* Dn Allah ki boyeni shiyasa n biyoki PC Namiki Nawa bayani koni antabamun wani Abu d yasa arayuwa nakara gasgata kada ka tsananta soyayya HK km kada ka tsananta kiyayya nima antabamin wani asiri saukarmin d jini saedae shekara cif Ina zubar d mini tsawon shekara dinnan baitaba tsaya dai dai d second daya ba cinyoyina hr sillewa sukayi sukayi baki km indai zan tsaya d namiji Wanda b muharramina ba zuban jinin zai karu ainun aka km aka hanani nutsuwa dmin kuwa zuciya ta kmar ana huramun Wuta kullum saena dingajin kawae na gudu n bar Gidan km al'amarin ubangiji hk aka dauke hankalin mahaifiyata akaina kwata a filli bata damuwa d halin d nk cikin saedae itama tayi ta rama alamun wani Abu n damunta arai gashi idn dare Yy bazantaba iya bacci ba hk zanyi taji motsi km nidin n kasance irin Yara masu kiba dinnan ne ainun amma duk saedae n kare n rame tas ta ynd idn akacemiki n nayi wannan kibar zaki karyata saeda na shekara cur Allah y budi Bakin mahaifiyata t fadama mahaifi na washegari d nj agaisheshi hankalinsa y tashi ainun toh akwae abokin babana a office babana Yy masa zancen t sanadinsa akasamamun magani mai maganin yace duk me wankekken ido toh zaifadamusu hayaki ne yake FIta ajikina dmin ansone n haukace sbd mahaifiyata tana sona acikin yaranta toh idn an watsar d rayuwata baxata taba samun nutsuwa ba saukin abun shine ni bana wasa d addu'a km lkcn ma ba Waya amma idn zan kanta xansa cassette a radio inajin karatu hr nayi bacci toh wannan abun shiya takaita guduwa ne n bar Gida amma agari mutane hr sunfara kirana mahaukaciya SBD ni daya HK zakiganni INA t Fada kokm INA tafiya INA surutu some some hauka😭😭😭 kai jama'a duniya INA zaki samu aranda n fara magani wani ikon Allah aranar n fara bacci koma saenakejin wani Abu me nauyi yn sauka kaina dafarko km Neman magani hr wani mutumin Ghana saeda y ban amma dif masu magani yn uwan mamana hr suka gaji d nema mun magani tunda lkcn mamana hnklin ta Baya kaina Masha wahala ainun. *NAGA TA KAINA* *NA SADNAF*🌸🌸 ®️ *_PURE MOMENT OF LIFE WRITERS_* _{We Don't just entertain nd educate we also touch the heat of readers P.M.L}💪🏻_ *Free Novel* *Page 57* Ina yiwa Zahira uzurin kila Aljannu da suka Shiga jikinnta suka fita ke haddasa Mata saurin fushi da kunci da take yi kwana biyu Hakane yasa na cigaba da lallab'a ta Yau da safe Bayan yarana sun gama shirin makaranta sai na ga Waleed a madadin ya saka uniform d'insa bayan ya ga ma cin abincinsa sai Naga ya koma d'aki ya kwanta. Nadeeya da Minal Basu iya jiransu Humaira ba suka tafi dan ba makarantar su daya ba. Humaira da Raheema da Waleed ke makaranta daya yanzu haka Waleed da Raheema ne kawai a matakin primary. D'akin na Shiga cikin mamaki uniform din da bai saka ba ya shige daki ya kwanta gasu humaira sun shirya alamar shi suke jira "Kai Waleed ya baka saka uniform dinka ba kazo ka kwanta"? "Ba zanje makarantar ba yau" "Dalili baka da lafiya me"? Nace cikin mamaki ma yanda yamin magana Yana wani fusgewa "Lafiyata Lau banyi niyyar zuwa bane kawai" "Kana da hankali kuwa makarantar dama sai anyi niyya ake zuwa yau Mai ya Shiga kanka ne ka tashi maza ka saka uniform dinka kafin ranka ya b'aci" Na karashe cikiin b'acin rai Ina mamakin abinda ya canza Waleed ya dawo haka yarone Mai ladabi da biyayya hasali ma yana riga yayyensa shirya wa idan zasu tafi makaranta duk ranar da kuwa ya min laifi raina ya b'aci haka zai ta bani hakuri yana bazai sake ba har sai yaga na saki fuskata yake kyalleni Ga mamakina Waleed din ke min magana Kamar da sa'arsa yake magana a madadin ya tashi yabi umarni na ya hada da bani hakuri ma kamar yanda ya Saba sai Kara gyara kwanciyarsa yayi. Inda naji raina ya balain b'aci banida saurin duka Amma abinda yamin yasa na isa wajensa tare da janyo wayar heater na tsulla Masa ya mik'e da sauri Rai a had'e ya rik'e wayar Yana wani hucci Kamar zai kawo min duka "Nifa bazan je makaranta ba gaskiya Kar a takura min" Kamar ya buga min guduma.haka naji rawar da jikina keyi yasa ya sakar min wayar yayi waje batare da na iya Kara tab'uka komai ba. "Umma mu fa Waleed na Bata mana lokaci yau bazai je bane mu tafi"? Munga ya fita batare da ya saka uniform ba Dak'yar na iya magana Ina "Kuje kawai Ina ga yau bashida lafiya" Da sauri suka fita ni kuwa na koma na zauna Ina mamakin canjawar da Dana yayi tunda na haifeshi bai taba min haka ba na kasa yarda ma a hayyacinsa yake. Ko dai shima Aljannu ne suka shiga jikinsa bansani ba Mik'ewa nayi Rai ba dadi na nufi wajen Inna Amina da ban samu Shiga ba tun safe dan dama sai na gama sallamar Yara sun tafi makaranta nake Shiga wajenta da abinci karyawarta Su Nadeeya na iya k'ok'arinsu wajen kulawa da ita dan ko band'aki zata Shiga su suke taimaka Mata ta Shiga tayi uzurinta tunda kafarta na ciwo. Har wanka ma wani zubin su suke mata sai dai idan basa nan.nayi Mata Ban ma yi Sallama ba sabida tashin hankali da nake ciki tana zaune ta jingina da bango tana jan carbi da har a bacci ma bakinta motsi yake tana sallati da istigifari A gabanta na zauna na sunkuyar da kai. Ina Jin ta idda sallatin da take na dago na hau gaisheta Bata amsa ba damuwa bayyane a fuskarta tace "Mamana lafiya kuwa ya naganki haka Mai ke damunki"? ina jinta a raina sabida yanda take damuwa da damuwata ko Yaya nake cikin damuwa tana ganewa Sai dana share hawayen daya zubo min nace "Mama Waleed a yan kwanakin nan naga ya canja min Kamar ba Waleed Mai sanyi hali da ladabi da biyayya ba Mama kema shaida ce a dan zaman da kikayi nasan zaki fuskanci halinsa yarone Mai gudun fushina Mama wai yau ni yaron nan yake yiwa rashin kunya har Yana Kar in takura masa bazai je makaranta ba iya wanan bai Isa ba sai daya galla min harara Mama Kamar ba Waleed Dina ba ya canza gabad'aya" Na karashe Ina fashewa da kuka Mama cikin damuwa ta hau kwantar min da hankali tana "karki damu mama na kila ya fara haduwa da mugayen abokanai ne ko Kuma wani abu ke damunsa bamu sani ba ki share hawayenki ki bar damuwa idan ya shigo Zan Masa magana ai bai tab'a Miki haka ba ki bari mu bincike shi a hankali muji mai ke damunsa" "Mama ko shima Aljannun ne Suka shige shi wlh ba haka Waleed yake ba Zahira ma mama Kinga tunda Suka bar jikinta bata koma yanda take ba itama yanzu wani irin hali ta koya kina cemin mu bita a hankali,mama Ina tsoron wani abu aka yiwa yarana ba abinda umma da Safiyya baza su iya aikata min ba bare idan sunga alamar anyi nassarar cire Aljannun daga jikin Zahira" "Karki damu Mamana ita Zahira dama sai a hankali zata dawo daidai indai na samu tana Shan ruwan adduoi da nake baki da turaren wuta zata dawo daidai Shi dai babana nake so ki bari mu bincika abinda ke damunsa wlh duk abinda Kika ga ya samu bawa rubutacce ne daga Allah wayanda kike tunani basu Isa su Miki komai ba sai idan Allah ya hukunta dama hakan sai ya faru tunda mumuni dole ya yarda da kaddara Mai kyau ko akasin haka alhamdulillah daga labarinki Allah na kaunarki mamana tunda duk Kika iya tsallake duk wani sharri da aka nufeki dashi Allah daya jarrabceki yana ta kareki ba hanyar da basu bi ba dan su ga bayan ki Amma da ikon Allah gaki nan a rayye ba abinda ya Sameki insha Allahu yaranki ma Allah zai karesu burina kawai ki dogara da Allah kiyi ta yiwa yaranki addua gabadaya. Da nasihar Inna Amina naji sausauci a zuciyata na fito na Kai Mana abin karyawa Muka karya a tare duk da zuciyata cike take fal da damuwa. Ko Ina Waleed din yayi yanzu Zahira dama tun safe bata tashi daga bacci ba Ina mamakin sababin halayyen da nake gani a tare da ita bansan na saka damuwa a raina hakane yasa muna gama karyawa da Inna Amina na d'auko qurani na dan ta karamin sosai nake Kara amfani da damar da na samu wajen Kara neman ilimi Kuma alhamdulillah Ina fahimta. Karatun da mu kayi tare ya sanyaya min zuciya sosai wajen Sha daya na fito daga d'akinta ita Kuma tace min zata dan kwanta tayi bacci tunda bata fiye baccin ba ta Kan rayya daren itama. Ina fitowa naci Karo da Zahira ta fito da Kofin kunu da alala ko kallona ba tayi ba ta fara k'ok'arin wuceni Haka kawai na kasa yarda wai Zahira ta ce ta dawo haka Koda lokacin da Aljannun Suka fice a jikinta magana ne kawai naga Bata yi ta zama shiru shiru,amma tana nan da sanyi halinta da ladabi da biyyaya na kasa gane Mai yasa kwanankin nan ta kara bijiro da sababin halayye da na kasa ganewa "Zahira baki iya gaisuwa bane wai Mai yake damunki ne"? Ciki ciki ta gaisheni ta shige daki ba Kuma tsayawa tayi ta gaisheni ba Sam ban yarda abinda suke shigeta suka fita ke saka ta haka ba dan da suka fita ma ta dawo min yanda take magana ne kawai bai dameta ba Kaina dana ji ya fara min ciwo yasa ban tsaya takura kaina da tunani ba na hau aikace aikacen gida da kafin ta Kara canjawa tana Tayani Hankalina Sam baya jikina Yana wajen Waleed daya fice bai dawo ba dan baya yawo daga gida sai makaranta abokinsa guda ne dan yadikko Abubakar a iya sanina ma dashi sai dai abubakar din ya zo wajensa bai fiye zuwa ba har tsokanar sa su Nadeeya keyi akan ko dan ball dinan da aka San maza nayi shi baya yi Yana nanike dasu Yana koyan jajjage da yanka albasa. A haka na gama girkin Rana. Ina zuba idon dawowar yarana har da Waleed da hankalina yafi karkata wajensa. Sai dai har Suka dawo suka ci abinci Waleed bai dawo ba. Sai tambaya ta suke Ina yaje nace musu bansani ba su dai dubo min gidan yaddiko ko Yana can wajen Abubakar. Dawowar Humaira aguje tana hakki tare da cewa "Umma Kinga Waleed can a tsakiyarsu shagari Yana ta Wasa da Kare nace kina kiransa ko kulani baiyi ba Umma shagari fa dan gidan dan kwaya" Tunda ta ambaci shagari yaron daya addabi Yan unguwar da fitina naji gabana ya yanke ya fadi sallati na hau yi Nadeeya ta mik'e da sauri tana "Humaira kina da hankali kuwa Waleed din Kika gani da shagari"? " wlh Aunty Nadeeya Waleed na gani har na Masa magana ya shareni" "Nadeeya bata iya magana ba daga ita sai doguwar rigarta tayi waje da Sauri" Nima tsintar kaina nayi da binta a bayan Ina sallati Shagari sa'an Waleed ne karamin yaro da bazan iya kirga sau nawa aka Kai shi a ka kulle ba sabida rigimamme ne na tashin hankali har d'auke d'auke Yana yi ga dukan Yara fitinanne ne na karshe shaye shaye ne kawai bamu sani ba Yana Yi ko baya Yi A zaune yake a tsakiyar su shagarin Yana ta Wasa da karnukan Nadeeya a tsawace ta Kira sunansa tana yazo nan Waleed yarone Mai girmama na gaba dashi dan daidai da Raheema da yake bi aunty Sama aunty kasa yake ce mata ga mamakina ko dagowa baiyi ba ya kalli Nadeeya Data ishe shi ma sai cewa yayi "mallama karki takura min idan Kuma Zaki iya daukana zo ki d'aukeni" Nadeeya sakin baki tayi tana kallonsa ta juyo ta kalleni...... *A yi maneji wlh abubuwa sun Sha kaina a ringa hakuri dai Kar ayi rushing Dina Ana rushing Dina zanyi a gurguje wlh alhalin labarin Bai Kai a Gama ba yanzu nan nayi typing dan karku jini Shiru Ina samu sarari gobe xaku jini idan ban samu ba ayi hakuri jibi na bada Mai yawa* *NAGA TA KAINA* *NA SADNAF*🌸🌸 ®️ *_PURE MOMENT OF LIFE WRITERS_* _{We Don't just entertain nd educate we also touch the heat of readers P.M.L}💪🏻_ *Free Novel* *Thanks all for d bday wishes and prayers I appreciate wanan Shafin na kine Ayshatfareeda tnks for d gift am greatful* Page 58 Sosai na rik'e kaina na tsaya akan kafafuna sabida rawar da jikina keyi jiri na d'ibana Ban saurari Nadeeya da itama ta daskare a tsaye ta juyo tana kallona ba sabida mamakin abinda Waleed yayi. Duk da inada tsoron Kare haka na daure na isa wajensu Waleed bai ji dar din ganina ba sai ma shagari da sauran abokanan sa ne Suka dan sunkuyar da Kai suna gaisheni dan ni nasan Ina dan musu kwarjini. "Waleed zo ka wuce mu tafi gida" Jim yayi kamar bazai tashi ba har sai da shagari ya Masa magana ya mike Yana wani fufusgewa yayi hanyar gida Na rik'e hannun Nadeeya data kasa katabus sabida mamakin abinda waleed yayi. Ni kadai nasan mai nake ji a Zuciyata "Umma Mai ya samu Waleed haka? Mai ya canza shi lokaci guda"? Ban samu zarafin yiwa Nadeeya magana ba muka cigaba da bin Waleed a baya har muka Isa gida. Butan dake tsakar gidan ya fara ball dashi kafin ya karasa dakin Minal kuwa ta kasa hakuri ta bi bayansa tana "Kai Waleed kana da hankali kuwa?Mai ya had'aka da shagari dan iskan yaron nan"? "Karki Kara cemin banida hankali mallama" Waleed yace Yana wani hucci kamar sa'arsa Da yake bai Saba da musu rashin kunya ba Sam haka ne yasa abin ya musu wani banbarakwai. Nadeeya ta fada d'akin a zuciye kafin na hanata ta wanke shi da Mari Minal kuwa ta hau zaginsa ita da humaira. "Wlh duk wacce ta Kara zagina sai na rama duk wacce hannunta ya Kara tab'a jikina wlh sai na rama" Waleed yace yana zuba musu harara. Daga yanda yake nasan zai aikata zuwa lokacin na yarda Waleed ba'a hayyacinsa yake ba D'ana an tab'a min shi dan ba haka yake ba tunda na haife shi bai tab'a gwada rashin kunya da naga Yana yi ba yau. Ina tsoron Umma da Safiyya suna cikin hannu a canzawar Waleed D'ana guda tilo da nake alfahari da hankali da tarbiyya dana bashi,idan har zasu iya yiwa Zahira turen bakakken Aljannun Mai zai hana su tab'a min Waleed tunda sun San namiji ne zuwa yanzu nasan sun gane an raba Zahira da Aljannun hakane zai saka su ce bari su dawo Kan Waleed na fahimci sun San rauni na akan yara na ne bana iya jure abinda zai tab'a su kila shiyasa Suka kara tab'a min Waleed. Tuni na tsayar da tunani na akan Waleed ba'a hayyacin sa yake ba duk Abunda yake yi yanzu kila ba a hankalinsa bane Da wannan tunanin na fara k'ok'arin tsawatarwa su Nadeeya da fad'a ke neman kaure musu suna neman dukan Waleed dake ta zuba musu rashin kunya da yake Yana da jikin girma Zahira da Nadeeya ne kawai zasu gaya masa tsayi Amma duk yafi su Humaira tsayi Zagin sa da humaira ta yi ya rama a take yasa suka rufeshi da duka Kafin na Isa wajensa ya watsar dasu ya cakumo humaira ya hau zuba Mata naushi daya daga min hankali Nayi wajensu a guje duk yanda muka so raba Waleed da Humaira kasa wa muka yi karku manta sai da aka haifi Raheema kafin Waleed akwai tazaran shekaru a tsakaninsu. Daga yanda yake dukanta na Kara gasgata dana ba'a hayyacinsa yake ba haka ne ya sa ni ma na hau Kai ma sa dukan Ina ya cika ta dan wani irin karfine da Waleed din daya sa muka kasa raba shi da humaira. Sai dana fashe da kuka Ina ihun a kawomin agaji kafin ya saki humaira daya Mata jina jina ya bangaje sauran yayyensa ya Kara yin waje A gefen gado na zube na fashe da kuka Ina sallati "Umma yau mu Waleed yake zagi har dasu duka Umma Waleed ko ya fara shaye shayene"? Cewar Nadeeya "Kema ai ko ba'a fada Miki ba kinsan ya fara shaye shaye Waleed Nan ko Raheema yayi wa ba daidai ba yayi ta binta Yana bata hakuri kenan bai tab'a maida Mana magana ba Amma kiga yau shine har da kokawa da humaira" Cewar Minal tana bubbuga bayan humaira dake numfarfashi Ban iya tanka musu ba dan ni kadai nasan Mai nakeji a Zuciyata muryar Inna Amina dake kwalla min Kira yasa nayi d'akinta Ina cigaba da kuka. A gabanta na zub'e Ina cigaba da kukan da nake Sanin kukana na d'aga Mata hankali yasa na tsayar da kukan Ina "Mama wlh an tab'a waleed dana ba haka yake ba mama kema shaida ce yanda yake girmama yayyensa Mama yau Waleed shine da zaginsu har da dukan Humaira wani yaro Mara kunya a unguwar Nan dasu naga Waleed fa Mama wlh an tab'a waleed mama kila shima an Masa turen Aljannu da zasu ringa saka shi Rashin ji Innalillahi wa Inna ilaihi rajiun na karashe Ina Kara fashewa da kukan. "Mama na rasa mai nayi wa bayin Allah nan suke san ganin bayana ko wata uku Zahira batayi da dawowa daidai ba yanzu Kuma sun dawo Kan Waleed laifine dan na auri Naseer mai na musu da zafi haka suke San tarwatsa min rayuwa"? Inna Amina bata hana ni ba sai data bari na ci kukana na koshi Ta fara rarrashina "ki kwantar da hankalinki mamana ki daina zubar da hawayenki,indai turen Aljannu aka yiwa Waleed insha Allahu zanyi iya k'ok'arina na Raba shi da su nima duk abinda kuke yi Ina jiyo ku daga yanda yake daga murya nasan yaron nan an tab'a shi banso kawai na Miki maganar ne na d'aga Miki hankali insha Allahu zai dawo daidai da iziinin Allah kiyi k'ok'ari ki turo min shi akwai Addu'a da Zan Masa indai da jinnu a jikinsa sai sun fita Kuma wanan Abunda ya faru da Waleed ya Zama dole mu dage da Addu'a har sauran yaran naki Allah ya karesu daga sharrinsu Ina mamakin halin bayin Allah nan da basa tsoron Allah nakan ji labarin mugaye Amma na bayin Allah nan na daban ne ace uwa ce ke san ganin bayan danta haka dana tunanina wlh bake suka tsana ba babana Suka tsana tunda har zasu iya tab'a yaransa Allahu ya shiryesu su gane tin lokaci bai kure musu ba" Inna Amina sai dai Allah ya Mata sakayya da Aljannatul firdausi tayi k'ok'ari a kaina sosai da yarana. Dak'yar na samu na bawa su Nadeeya baki akan su bi Waleed a hankali dan gani suke shaye shaye Waleed ya fara,nawa ma waleed din yake da zai yi wani shaye shaye. Haka na zauna zaman jiran dawowar Waleed har aka yi sallah Isha Sam hankalina ba'a kwance yake ba. Sallah ma ba'a nutse nayi ba sabida tashin hankali Ina tsoron Kafin Waleed ya dawo hayyacinsa ya jawo min wani maganar Yayyensa duk basu bi ta kansa ba suka duba littattafansu Suka je suka kwanta dan Haushin Waleed suke ji sosai suna ganin Kamar ban dau.matakin daya dace na dauka a kansa ba. Inna Amina ke dan Jana da Hira Wanda rabi waazi ne akan yarda da kaddara Mai kyau ko akasin haka a fadarta duk abinda zasu min yanzu ba zai kai na baya ba idan har Allah dana dogara dashi ya kareni da tsawon lokacin nan nayi Imani akan shi zai karemin yarana ruwan addua da ta saka a Kofi ta Kara nuna min akan Yana dawowa zata bashi insha Allahu zaa dace Hankalina ya dan kwanta sanin wacece Inna Amina macece Mai baiwa burina Waleed din ya dawo kawai na samu na bashi ruwan Addu'a. Agogo na duba Naga goma har ta dan.wuce ba Waleed ba dalilinsa Waleed da daga Massallaci sai makaranta sai.kuma gida sai gashi Waleed din ne yau bansan Inda yaje ba har karfe goma. Waje na fita da hijab a jikina na hau duduba hanya ko zan ga Waleed Wasa Wasa sai gashi nice har gidansu shagari ban same shi ba. Duk dandalin dana san suna zama na duba ban gansu ba. A haka na koma gida nayi zaman dirshan a k'ofar gida da za'a auna jinina ni nasan ya balain hawa daga safe zuwa yanzu Ashe haka uwa ke Shiga tashin hankali idan danta ko yarta ya d'auko hanyar lalacewa ko ya iyayen Yan d'abba sukeji da karuwai da kullum.a cikin d'auko magana suke kila ma bakin ciki ke Zama ajalin iyayensu Hawaye kawai ke zubomin Ina tuna irin tarbiyya da Allah ya bani iko na baiwa yara na da har ake Jin dadin zaman mu a unguwa anya da akwai ranar da zan tab'a farinciki a rayuwata?nidai badan Kar nayi sabo ba da nace nayi nadamar auren Naseer dan daga aurensa zuwa yanzu banga kalar bakin cikin Da ban kunsa ba,Ina fita daga wanan balain zan fada wani yanzu Kuma an bar kaina an koma Kan yarana Har yanzu ni nasan zafin da nakeji idan na kalli Zahira yarinya Mai balain tausayi da hankali yanda suka maida min ita a kwanan Nan ma sababin halayye nake gani a tare da ita yarinya Mai sanyi hali ta zama masifafiya Abu kad'an zata hau kananenta da masifa har dasu Bugu idan taso Ni da nake mahaifiyarta ma bata damu ta ringa gaisheni ba kullum tana d'aki a kwance. Zurfin da nayi a tunani bai saka nasan karfe dayan dare ta kusa ba sauro sai kai wa fatata cizo suke. Muryar Inna Amina data daddafa bango cikin dingishi ta fito waje Jin ban dawo ba ya saka na dago "Haba mamana zaman mai kikeyi a waje ke kadai duk rashin Waleed din ne"? Kukan da nakeyi a zuci na fashe dashi Ina "Mama bansan Inda Waleed yake ba Waleed bai dawo gida ba taya Zan samu kwanciyar hankali da nutsuwa" Inna Amina na k'ok'arin Magana na hango Waleed ya taho yana pito Wai Waleed dina ke fito Yana abun marasa tarbiyya. Ido na zuba Masa har ya karaso ganina a zaune a dakalin k'ofar gida bai saka ya tsaya ba illa ma wuceni da yayi ya fara k'ok'arin Shiga ciki Inna Amina dake tsaye a bakin kofa ganin Yana neman ratsawa ta gefenta ya wuce ciki yasa tayi karfin halin cewa "Babana ina kaje ne.kayo dare haka muke ta neman ka"? "Kallon ball muka je da abokaina" Yace ciki ciki Yana wucewa ciki Inna Amina tamkar Mahaifiyata na d'auke ta zuciyata ta sosu da yanda ya Mata hakane yasa na mik'e a zuciye zan bi bayansa Inna Amina Ta ruko hannuna tana girgiza min kai "Ki bishi a hankali Mamana ki Kai zuciyarki nesa bayin kansa bane ki taya shi da Addu'a ki Kara janyo shi jikinki kar duk abinda zaiyi ya b'ata Miki rai tunda kinsan ba yin kansa bane kila an Masa hakane ma dan a rabaku yayi ta Abu kina Jin haushinsa ko kina jibgarsa a karshe ma zuciya ya deb'eki ki furta kalmar da bata dace ba mu bishi a hankali kinji" Gyada Mata Kai nayi maganganunta na shigata sosai dan wanan sam ba dabiun Waleed bane taba min shi akayi. Ciki muka shiga na kulle k'ofar Gidan A tsakar gida Muka sameshi ya zauna akan tabarma Yana cin abincinsa dan abincin ranarsa Dana darensa duk Bai samu yaci ba Dak'yar na yakice shi ya daina cin abinci dasu Zahira dan a da tare suke cin abinci gabadaya ko fita yayi sai ya dawo suke yarda Suma suci akwai soyayya Mai k'arfi a tsakaninsu. Dan zaman da Naseer yayi damu Mai tsawo a jinyar Zahira yasa suka.koma suna cin abinci tare. Ko ya Naseer zaiji idan ya dawo yaga Waleed daya ke ji a Ransa Kamar me ya dawo yaro Mara ji Daki nabi Inna Amina na karbo ruwan Addu'a nazo na ajiye Masa agabansa Bai cemin komai ba ya gama ci ya Sha ruwan ya shige Palo yayi kwanciyarsa. Bacci bai ga idona ba ranar sabida dukufa nayi gaban Mahallicina Ina kaiwa Allah kukana akan ya karemin yarana ya dawo min da Waleed da Zahira yanda Suke a da Allah Kar ya Bawa makiyana dama suga bayana. Sai da aka fara kiraye Kirayen sallah asuba kuma naji bacci ya fara k'ok'arin daukana. Fitowar su Nadeeya daya bayan daya daga d'aki dan su yi alwala yasa na wartsake dan duka yarana sun Saba da tashin sallah asuba. Waleed shine ma kan gaba dan wani zubin yana riga Naseer tashi Yana alwala zai tafi massallaci Naseer ya bishi a baya Amma yanzu iya su Nadeeya ne suka fito Banda Waleed da Zahira. Ina kallonsu suka ringa alwala daya Bayan daya suna komawa ciki. Hakane yasa na mike na Shiga d'akinsu dan na tashi Zahira itama tayi sallah dan na lura kwana biyun Nan da ta tsiro da sababin hali sallah ma Kamar bata so tayi. Baccinta take ta shara ni kuwa na sunkuya na Dan bubbugeta dan ta tashi Yamutsa fuska tayi data bude idon tana kallona Cikin had'e rai nace ta tashi tayi sallah "Idan na tashi zanyi" Tace tana k'ok'arin gyara kwanciyarta Take raina ya b'aci na daka Mata mugun tsawa dan zan jure komai banda Wasa da sallah "Maza tashi sallah Bata jiran mutum sai dai mutum ya jira sallah tashi kije kiyi alwala kiyi sallah kafin raina ya b'aci" A madadin ta bi umarnina sai ta turo baki tana kunkuni. Take naji na zo wuya na kasa danne zuciyata na rufe ta da mugun duka dan ni nasan rashin kunya Zahira kemin ban zargi akwai wani Abu dake damunta ba tunda an riga da an rabata dasu kila dan Inna Amina tana cewa a bita a hankali shiyasa ta tsiromin da halayen nan. Dak'yar su Nadeeya suka kwaceta a hannuna dan kananan surutai ma ta ringayi tana wai an dameta tace baza tayi sallah bane" Ina cikata tayi waje fuuu tayi k'ofar dana kulle da mukuli tayi Zamanta a bakin kofar alamar dai baza tayi sallah ba Inna Amina ce ta Kara bani baki akan na bita itama a sannu Dak'yar dak'yar tayi sallah Waleed kuwa Ina tashinsa akan yayi sallah juyamin baya yayi Sai da shima nayi Kamar Zan buge shi ya mik'e Yana fufusgewa Kamar zai kawomin duka Wai Mai ya samu yarana ne suka dawo haka. Cikin kuka na koma Kan sallaya nayi Sujadda na Kara kaiwa Allah kukana Ina fada Masa duk abinda ke zuciyata da yanda yaran nawa suka dawo kafin na iya mik'ewa nayi Sallah Asuba duk ba'a nutse ba. Karfe shdda su Nadeeya suka fara aikace aikacen gida Haka yasa na fito tsakar gidan da suka share na zauna Akan tabarma Ina zaune ne kawai ba dan zuciyata na wajen abinda suke ba. Pito muka fara ji da Haushin karnuka a waje Kafin tunanina ya bani wani Abu Naga Waleed ya fito daga palon ya fara k'ok'arin yin waje. Da balain Sauri na mik'e na dakatar dashi Ina "Kai Waleed Ina zakaje da sassafe Nan"? Bai cemin komai ba yayi dage ya dauko mukullin ya bud'e yayi waje Kamar Zan Fadi nabi bayansa. Sai dai Ina fita Naga har sunyi nisa shi dasu shagari. Hawayene ya hau zubomin na kasa yarda Waleed Dina ne ya dawo haka ni dai nasan idan Naga kangararrun Yara nakan bisu da adduar shiriya ban tab'a kyamatarsu ko nayi Allah wadai dasu ba ballantana nace hakane yasa Allah ya jarrabceni. ( Hattara iyaye ku guji aibata ko kyamatar yaran da suka tsinci kansu a irin wanan hali dan ba iyayen da zasu so yayansu su lalace Kai dai ka kallesu kawai ka bisu da Addu'a dan baka San kaddarar data afka musu suka tsinci kansu a cikin wanan halin ba Kai ma da kake kyamtar su baka San ya naka kaddarar zai Zo ma ba dan bawa baa daina jarrabtarsa har sai ya koma ga Allah ya rabbi ya shirya Mana zuria wayanda Kuma suka d'auko hanya lalacewa rabbi ka Shiryesu ka hada yaranmu da abokanan arziki alfarmar annabi Muhammad Saw). Ni nasan Wanda yayi nisa baya Jin Kira ko na bi Bayan Waleed bai Zama lailai ya dawo ba hakane yasa na koma ciki Ina Jin zuciyata na radadi ga nauyi daya min Yarana cikin.fushi Sukace na rabu da Waleed yaje yayi ta abinda zaiyi Nan kuwa basu San duk abinda akeyi ba'a hayyacinsa yake ba. Da zazzabi jikina sama sama suka tafi makaranta ya rage dagani sai Zahira da Inna Amina Kaina kuwa Kamar ya Fado sabida ciwo na Kuma San dan banyi bacci bane. Abinci Inna Amina na Kai Mata Ina ajiyewa ta hau min waazi tana Kar na damu duk tana kallon abinda ke faruwa Na cigaba da Addu'a na Kuma dage da Sadaka kamar yanda nayi a baya. Toh kawai na ce Mata dan kirjina kamar zai fito daga kirjina hoton Waleed kawai nake hangowa dasu shagari suna tafiya da karnuka Yanda nake jina bazan iya sauran aikace aikacen da suka rage ba hakane yasa na nufi d'akinsu Zahira dan na tasheta tayi aikin Sai dai Ina tashinta ta hau min kunkuni kamar yanda ta min da asuba. Baki a ture ta fito daga d'akin wanke wanke danace tayi ta hau gara kwanukan Tana watsi dasu Kamar bazata yi ba. Wanke wanken ta hau yi Tana cigaba da kunkuni bama fita suke ba a Haka ta fasa plate din tangaran anan nazo wuya zuciyata na rayamin iskanci kawai yasa Zahira kemin haka. Wayar wuta na dauko na hau dukanta Ta dib'a a guje tayi waje itama A takaice daga ita har Waleed a ranar sai wajen Sha biyu suka dawo. Rashin dawowarsu da hade min Kai da sukayi suna neman lalacewa a gaban idona yasa zazzabi rufeni da har sai da Nadeeya ta kai ga Kiran likita yazo ya sakamin ruwa Tunda ga ranar Zahira ana Mata fada zata Yi zuciya ta bar gidan Bansanta da kawaye ba sai gata ta tsiri kawaye kawayen da kana ganinsu kasan basuda tarbiyya halin da ba na yata ba sai gashi Tana yinsu. Waleed kuwa kararsa da ake kawo min kawai ya Isa ya saka zuciyata tayi bindiga Dan shine daki wancan shine daki wanan kullum cikin zuwa gidajen Yara nake bada hakuri Zuwa lokacin Yan unguwa sun fara Gane halin da nake ciki game da yarana Allah na tuba har gwamma duk halin Dana Shiga a baya da irin kissan da su Umma suke min Akan yarana. Inna Amina tana iya k'ok'arinta wajen Tayani da Addu'a dan yarana su dawo daidai amma duk a banza Yata ta fari da autana sun d'auko hanyar lalacewa a gaban idona. Banda ma Inna Amina na rarrashina da nasiha da tuni na yanke jiki na Fadi rabona da baccin kirki na manta nayi kukan nayi rashin lafiya Watan Naseer uku da tafiya ya dawo da sabuwar motarsa dal da uban tsaraba Daga yanda ya gani a rame a lalace yasa hankalinsa ya tashi. Ni kuwa ganinsa yasa na hau kuka Karshe sai Inna Amina ke bashi labarin duk abinda ke faruwa Dani Dan ko a yanzu ma daya dawo. Daga Zahira har waleed basa Nan Naseer hankali a tashe ya hau sallati daya ji shagari yanzu Waleed ke bi Zahira Kuma tana bin kawaye. Da kansa ya saka Nadeeya a gaba ta raka shi gidan da Zahira ke zuwa idan ta bar gidan Faiza sunan yarinya Saar Zahira ce baa gun Iyayenta take ba a wajen kanin mahaifinta take ban dai San silar rashin jinta ba. Naseer sai daya nemi kanin Mahafin yarinya yace Baya San kawancensu da yarsa kafin ya ruk'o hannun Zahira Yana janta suka nufo gida sai tura Baki take badan shi yaje ba idan Zan kwana Ina Aiken ta dawo gida bazata dawo ba. Kulle ta yayi a daki dan duk Nadeeya ta bashi labarin kalar rashin Jin da take da fita da take batare da mun sani ba Nadeeya ya Kara cewa ta raka shi suje gidansu shagarin ko zai ga Waleed Kamar ciwon kirjinsa zai tashi sabida tashin hankali kafin su Kai gidan su shagari suka ga mutane da yawa an taru. Har zasu wuce ya nufi wajen Waleed ne ya fasawa wani yaro Kai da kwalba Mahaifin yaron ya rantse bazai yarda ba sai ya Kai Waleed station dan har ya tura babban dansa ya d'auko.masa Yan sanda. Naseer dak'yar ya samu hanya daya Isa wajensu sai dai Yana hada Ido da Waleed yaji kansa ya mugun Sara Masa kirjinsa na Masa wani irin zafi Adaidai lokacin da Yan Sandan suka iso Mutane Kuma suka gane shine Mahaifin Waleed sabida kamanin da suke sosai Take kowa ya hau fadar albarkacin bakinsa Naseer na tsaye yayi kikam Yana jinsu Yan Sandan na zuwa a madadin Naseer yayi k'ok'arin yin wani Abu ko ya bisu station din sai cewa yayi idan suka tafi dashi Kar su sake shi...... Advertisement Hlo Assalamu alaikum sisters,hp everyone is fn🙏 Nazo muku da labarin wani sabulune maiban mamaki🥺wato *mg's herbal whitening black soap*🧖🏻‍♀️ yan'uwa inamasu bukatar sugyara jikinsu fatarsu tayi kyau tazama Babu kuraje,tabo dama dukwani matsalan fata toh Yan uwa kuyi kokari kujaraba mg's Babu tantama zaisharemuku hawaye insha Allah duk wnd tayi using mg's koda roba dayane sai fatarta tagoge tabanbanta Dana saura,Ina maisan yaga fatarshi tayi smooth tana kyalli toh kujaraba mg's domin fatarku zata dinga haskawa tana walkiya da daukar Ido kmn kunsha supplement domin anyishine da ingantattun natural abubuwa masu gyarajiki cikin sauki batare da sunyima fatar mutum lahani ba😘 sister's duk ynd zanbaku lbrn soap dinnan yawuce nan domin zaku iya anfani da zallar sabulun batare da kunma bukaci cream ba🥰Amare gareku akwai hadinku na musamman wnd duk wacce tayi anfani dashi dawuya ango ya iyaganeta😁wani abunma saikungani da idanku👏gamasu nankarwa kuyi kokari kujaraba mg's domin Yana rageta sosai inkuncigaba da anfani da soap dinma saidai kuduba kuga Babushi😊duk wani prblm na skin kugwada soap dinnan Insha Allah zakuyi😂 Kayanmu bana bleaching bn organic ne nagyaranjiki zaifiddomuku da ainihin natural beauty dinkune anyisune d natural abubuwa Soap price:3k Maiso should chat:08062991548 Call 08064532391 Muna maraba damasu siyan daya kosari🙏 Be part of the glow team🤭say nooo to pimples, black spot,acne,sunburn,nd all skin prblms🙏 Mg's lv you guys fisabilillah🤭 *NAGA TA KAINA* *NA SADNAF*🌸🌸 ®️ *_PURE MOMENT OF LIFE WRITERS_* _{We Don't just entertain nd educate we also touch the heat of readers P.M.L}💪🏻_ *Free Novel* Page 59 Nadeeya Ido ta zaro ta kalli Naseer da ya fara kokarin barin wajen fuskarsa a had'e. Waleed shima wani irin Mugun kallo yabi Naseer dashi kamar ba mahaifinsa ba. Yan sanda tuni Suka tasa keyar Waleed suka saka shi cikin motarsu Nadeeya kuwa da hankalinta ya balain tashi da tafiyar da za'ayi da Waleed ta Sha gaban Naseer da Sauri dan duk da rashin Jin da Waleed yake gwada.musu yake Kuma musu rashin kunya hakan bai sa sunji kaunarsa ta ragu a zuciyarsu ba hasali yanzu tausayinsa suke ji tunda Naeema ta gaya musu duk abunda yake yi ba'a hayyacinsa yake yi ba. "Abba cewa kayi fa idan an tafi dashi Kar a sake shi Abba kaga zasu tafi dashi"? Naseer bai kalleta ba ya cigaba da tafiyarsa Yana zabga Sauri Dan sosai yaji zuciyarsa na kunna da ganin Waleed din dan ganin daya Masa ma ji yayi kamar ya shake shi yayi ta duka har sai ya daina numfashi. Wani abu yaji Yana danne zuciyarsa akan San Waleed da tausayinsa Nadeeya kuwa ganin Naseer ba alamar zai tsaya yasa tayi gida aguje tana kuka. Idona na Kan kofa tunda su Naseer suka fita da Nadeeya nemo Waleed bani da burin daya wuce irin naga sun dawo tare dashi dan yau ma ban saka shi a idona ba. Ina Jin Zahira a d'aki da Naseer ya kulleta tana kananan surutai Ni nasan da ikon Allah kawai nake numfashi har yanzu zuciyata bata buga ba idan na dubi Zahira 'yata da nake jinta duk a yarana sabida hankali da tarbiyya ta na ga yanda ta dawo yanzu yarinya fitsarariya sai naji kamar na cire zuciyata na Yar sabida ciwon da yake min a haka ma Wai dan Inna Amina na iya k'ok'arinta a kaina da yarana da babu ita bana Jin Zan kawo yanzu Waleed dana daya tilo da yayi hannu Riga da duk wani Abu Mai kyau ya koma Mara kyau ganinsa a Wanan halin kawai na iya sawa zuciya ta ta buga lokaci guda Na gwammaci ni su Umma suka hukunta suka ma kasheni da barina da sukayi a rayye da banida bambanci da mataciya sabida halin da yarana ke ciki. Sun watsa min rayuwar yarana da Karfin addua Yata Zahira ta tsaya a iya bin kawaye bata hada da bin Maza ba da Karfin addua Waleed ke rashin ji da bai had'a da sata da shaye shaye ba. Nakan hararo da yarana Basu hadu da wanan jarrabtar ba da kila Zahira ta Dade a gidan aure ko tana mataki na biyu a babban makaranta sai dai Kash gata a gabana ko secondary bata gama ba an susutar min da ita. Shigowar Nadeeya aguje tana ihun kuka yasa ni mik'ewa tare da dafe kirjina da na ji kamar an soka min kibiya. "Umma 'yan sanda sun tafi da Waleed station saboda ya fasawa wani yaro kai da kwalba Abba yace idan Suka tafi dashi Kar a sake shi" Tunda ta fara magana naji gidan na juyamin har Naseeru shima ya shigo a daidai lokacin dana tafi Zan zub'e a kasa ya taroni da sauri. Sai da na jima Ina sallati kafin naji kaina ya daina juyamin Maganar Nadeeya na Kara maimaituwa a kaina Ido na sauke akan Naseer Ina "Wai an tafi da Waleed station Kuma kace Kar a sake shi"? Kamar wanda na kwarawa ruwan zafi ya mike da Sauri yana "Duk ranar da Waleed ya taka kafarsa gidanan sai na raba shi da numfashinsa tunda ya zabi ya Zama dan iska gwara ya je ya cigaba da iskancinsa Kuma ban yarda wani yaje station dan yayi belinsa ba gwara suyita rikeshi acan" Yana gama fadar haka yayi daki a fusace Ni kuwa Zan iya cewa tunda ya fara magana nayi suman wucin gadi na kasa yarda Naseer ke furta kalmomin nan daga bakinsa. Na dauka zai fi kowa Shiga tashin hankali da halin da Waleed ya tsinci kansa lura da irin Kaunar da yake Masa ga mamakina Dan namu yake cewa Dan iska Bansan yanda akayi na mik'e na isa d'akin da ya Shiga ba yana Gefen gado a zaune Ban karasa ciki ba daga bakin kofa na Kira sunansa da Naseer dan Abban Waleed nake ce Masa tunda na haifi Waleed na bar ce Masa Abban Zahira. Indai na Kira sunansa toh ba karamin magana zamuyi dashi ba dagowa yayi da jajjayen idonsa Yana kallona "A hayyacin ka kake kuwa Naseer Waleed aka tafi dashi station a gaban idonka baka yi komai ba kace Kuma a idan an tafi dashi Kar a sake shi"? "Eee Ni nace Kar su sake shi Naeema Kuma ban yarda wani yaje belinsa ba dan bazai yiwu ya ringa jawo mana magana ba yaje can ya karaci iskancinsa" "Waleed kake jifa da munanan kalamai Naseer waye silar zaman Waleed haka?Mahaifiyarka da kanwarka su suka Zama silar gurbacewar tarbiyyar da na yiwa yarana Naseer Waleed da haka yake?Zahira da haka take a yanzu daka dawo daya Kamata mu had'a hannu wajen ceto yarana daga halaka Amma Kaine na farko wajen cewa yarona Dan iska? Tunda na aureka nake cikin tashin hankali ban taba samun nutsuwa ba daga wanan sai wanan yanzu Kuma an bar kaina an dawo Kan yarana Naseer na gaji wlh Tallahi na gaji idan har yarana basu dawo hayyacinsu ba bazan tab'a yafewa Mahaifiyarka da kanwarka ba" "Ke ya isa haka akan Waleed Kike jifana da maganganun banza ke yanzu ko tuntub'e kikayi sai kice mahaifiya ta ce,kin ma bar yarda da duk abinda ya Sameki yin Allah ne komai komai mahaifiyata ce da kanwata ki Shiga hankalinki Naeema Kar San Yara ya susutaki bin abokanan banza ya jefa danki a halin da yake ciki da kinsa Ido akansa da duk baa Kai ga haka ba lokacin da nake gari Mai yasa duk hakan bai faru ba sai da bana nan "? Zuwa yanzu shi kansa Naseer din na fara ganewa ba'a hayyacinsa yake ba yanda ya hayyayako min yasa naji na zo wuya na hau jifansa da maganganu masu zafi dan a lokacin zuciyata gayamin take kamar da biyu ma Naseer yake haka dan Yana ganin ya ruko canjina a hannu. Musayan kalmomin da muke ne ya dagawa yarana hankali suka hau k'ok'arin janye ni daga wajensa Amma fir naki na cigaba da jifan Naseer da magangunan da suka shake min wuya har sakina nace yayi idan yasan shi dan.halak ne dan aurensa bai kareni da komai ba sai wahala da nake sha tunda mukayi aure dashi bamu tab'a irin fadan da mukayi dashi ba ban Kuma tab'a ganin ya rufe Ido Yana cimin mutunci ba sai a wanan lokacin Kukan da inna Amina ta saka yasa na ja bakina nayi shiru zuciyata na wani irin k'unna Wa'azi ta hau yiwa Naseer Ni kuwa na saka hijabina nayi waje da Nadeeya dan ta rakani gidansu yaron da Waleed ya fasawa Kai tunda tacemin ta san yaron. Ga mamakina Ina zuwa ma nagane nasan mahaifiyar yaron. Cikin kuka na hau bata hakurin abinda ya faru na rik'e hannun dansu da waleed ya fasawa kai da ya Sha bandeji a kansa na hau Masa sannu. Bamu samu mahaifin yaron a gida ba da shi ya d'auki case din da zafi har aka Kai Waleed station hakane yasa muka zauna zaman jiran dawowarsa dan sai ya yafe Zan samu a sallami Waleed. Ana kiraye Kirayen sallah Magriba ya shigo gidan da sallama babban dansa na biye dashi a baya. Gaisuwar da muka Masa kawai ya amsa ya fara k'ok'arin Shiga falon matarsa ta dakatar dashi ta nuna mu tana wajensa muka zo ta Kara da bashi hakuri akan tunda Mai afkuwa ya riga da ya afku yayi hakuri kawai ya saki waleed. Yanda ya hade rai yasa na fashe da kuka Ina cigaba da bashi hakuri Ina "Kayi hakuri d'a na kowane wlh Tallahi da ba haka yaron nan yake ba daga baya ya zama haka kila Kuma bazaku rasa sanin sa ba yaron nan dake yawan sharar Massallaci a kasan layi wlh shine ya dawo haka lokaci guda muna ta iya kokarinmu dan muga ya dawo hanya ayi hakuri a yafe Masa duk abinda aka kashe wajen maganin yaron Nan Zan bayar ka taimaka" "Jikinsu sanyi yayi da suka ga yanda nake kuka a karshe mutumin yace ba komai Amma ya zama dole na dage Akan Waleed da yanzu abin yazo da tsautsayi dansa ya rasa ransa fa nasan yanda zanyi na raba Waleed dasu shagari. Kar Waleed ya jawo min abinda ba shi kadai zaa kulle ba har damu. Sai da yayi sallah Magriba ya huta duk.muna zaune kafin ya fito yace Mana muje. Dubu daya na ajiye a Gefen yaron na Kara Masa Addu'a samun sauki Na Kara yiwa mahaifiyarsa godiya na fito muka tafi station din. Sai da nayi da gaske da kuka da magiya kafin su yarda zasu bada belin Waleed dan rashin kunya Waleed ya ringa musu. Kudin da na basu da dan yawa yasa suka sakeshi. A yanda na fahimci waleed idan ana Masa fada ko aka hukunta shi zuciyarsa Kara taurara yake dan da aka sakeshi wani irin hucci ya ringayi Kamar wani Zaki yabi wani dan sanda da mugun kallon daya sa dan Sandar rantsewa akan duk ranar da tsautsayi yasa aka Kara kawo shi station dinsu wlh bazasu sake shi ba Waleed wani mugun Tsaki ya Masa ya wuce mu. Ni kuwa nabi bayansa da Sauri Ina kwalla Masa Kira. Da kyar ya tsaya ya zubomin Ido daya sa nake ganin kamar bani na Haife shin ba kamar ba dana Waleed dan Umma Dan lelen Abbansa yanda yayyensa kan tsokaneshi. "Waleed so kake ka kasheni da raina ko"? "Wai da nayi me har ni Abba zai ce a wuce dani station Kar a sakeni"? Wani irin girgiza kai yayi ya barni a tsaya ya hau zuba Sauri A haka muka ringa binsa a baya Ina kuka ni kadai nasan Mai nakeji a Zuciyata. Muna isa gida yayi fatali da butan daya samu a tsakar gidan ya wuce d'akinsu zahira dan palo yayi niyyar Shiga Naseer dake zaune a palon yasa yayi tsaki kasa kasa ya nufi d'akin. Butar da yayi kwalo dashi na dauko na zuba ruwa nayi alwala. Na Shiga d'akin Inna Amina dan nayi Sallah Magriba Nadeeya Kuma ta Shiga d'akinsu. Ina cikin rakaa na karshe na ringa jiyo hayaniya daga d'akinsu zahira take hankalina ya rabu gida biyu. Allah Allah kawai nake na iddar na tafi dakinsu Naga Mai ke faruwa Sujjada nayi naji ihun raheema da k'arfi. Da Sauri na Sallame sallahr na fito a lokaci guda muka isa d'akinsu zahira da Naseeru. Waleed ne yake ta kwallo da raheema yayyensa na k'ok'arin rik'e shi. Zahira na gefe kamar bata San Mai ke faruwa a d'akin ba. Naseer cikin zafin nama ya isa garesu. Ya damko Waleed da k'arfi. Kafin kace me ya rufeshi da duka Yana naushi Zagin Waleed kawai yake Yana jifansa da mugayen kalamai Waleed sai k'ok'ari Kare kansa yake ba ko tsoro a fuskarsa yanda ya tsaya ma Kamar zai iya rama dukan da babansa yake Kai Masa. Taurin Kan Waleed ma yak'i bari yaji irin dukan da Naseer ke masa shi ake duka Amma ni.nakeji a jikina. Tsakiyarsu na Shiga cikin ihun kuka Ina Naseer ya isa haka.kashe shi kake so kayi"? "Idan ban.kashe shi ba ai shi ya kashemin yarinya Raheema Saar sa ce da zai hau dukanta"? (Karku manta an Shiga tsakanin Naseer da Waleed shi kansa Naseer baa hayyacinsa yake ba) "Idan ba yaron nan ya zama dan iska ba"""" "Ka daina cewa dana dan.iska Naseeru kana mahaifinsa kana ce masa dan iska dana ba Dan iska bane" Nace a tsawace a daidai lokacin da Waleed ya fice daga d'akin a zuciye. Kafin na ankara har ya fice waje. A d'akinsu zahira ma ba karamin fada mukayi da Naseer ba kamar zai kawo min duka Dak'yar su Nadeeya suka janyeni daga d'akin Sai a lokacin na tambayi su Nadeeya mai ya hada Waleed da Raheema suka ce min Waleed ne yayi fatali da.kayan Raheema da take gogewa akan tayi magana shine ya zageta ta rama daga haka ya hau kwallo da ita. Dakin Inna Amina na koma Ina kuka itama kukan take tana adduar Allah ya kawo Mana karshen wanan fitintinun Allah ya gaggauta kawo karshen abinda aka yiwa waleed da Zahira. Naseeha ta hau min akan ta karanci kamar Naseer shima baa hayyacinsa yake ba shima kamar an Shiga tsakanin shi da Waleed. Na tuna fa ba haka.naseer yake ba a dan zaman da tayi damu ta karanci Naseer na mugun Kaunar Waleed tashi daya daga dawowarsa ya canja na daina biyewa Naseer muna fada akan Waleed Mu dage da Addu'a banji maganar ta ya shigeni ba dan.gani nake da gangan Naseeru yake haka tunda har Yana neman Kare mahaifiyarsa da kanwarsa daga cutar da suka min. Sosai nake ji a Raina lokaci yayi da zan ba zama nemawa yarana magani Allah na tuba Inna Amina na iya k'ok'arinta wajen Mana adduoi haka nima inayi Amma inaga sai na had'a da Kara neman taimakon. Zurfin da Inna Amina taga nayi a tunani yasa ta tambayeni tunanin mai nake. Ban boye Mata komai ba na gaya.mata abinda ke Raina. Murmushi tayi tana "Mallamai kawai da Kika bi wajen nemawa Zahira magani da baki samu kin dace da Wanda yayi nassarar cire mata bakkaken aljannu da aka Mata turensu kawai ya Isa yasa ki dau darasi.ki cire tunanin zuwa neman taimako wajen wani mallami. Ke ma zaki iya zama mallamar kanki ki roki Allah dan wayanda zaki je wajensu suma wajen Allah zasu nema Allahu samiu dua ne zai amsa Miki duk halin da kike ciki Yana sane dake daga lokacin da Kika fara zuwa wajen mallami neman taimako sai Allah ya barki da mallamin shi ya Miki maganin Abunda kike ganin bazai iya ba ko iya fatiha Kika sani ki karanta ki roki Allah dashi ta hanyar bin ladduban Addu'a Ki Kira Allah da sunayensa tsarkaka kyawawa kiyi wa annabinsa sallati ki Kara masa sallati a sujadarki ki yabe shi kiringa addua tamkar kina gabansa idan kin gama ki rufe da sallatin annabi saw insha Allahu zai amsa Miki. Na Karu sosai dan.a guntun ilimi na ma bansan ladduban Addu'a ba. A ranar Waleed bai kwana a gida ba Abunda bai tab'a yi ba kwana a waje. A ranar banyi bacci ba haka na ringa zarya tsakanin gida da waje ko Zan ga dana ya dawo. Sai dai bai dawo ba sai washegari Sha daya na safe Zahira kuwa ta saci fita duk da kulle ta da Naseer yayi. Akan Waleed wani irin Mugun fad'a mukeyi da Naseer dan idonsa idon Waleed sai ya dakeshi ko.ya koreshi daga gidan Wanda hakan yasa muke mugun fada har zuciya ta debbeni nace Masa ya barmin gidana ai ba nasa bane. A ranar yayi zuciya ya barmin gidan kamar yanda na nema. Inna Amina tayi ta min fadan ban kyauta Abunda nayi wa Naseer ba Bayan duk naseeha data min akan na yiwa Naseer uzuri baa hayyacinsa yake ba Har da kukanta na hau bata hakuri dan bazata gane ba Naseer ya ficemin a rai burina ma kawai ya sakeni. Insha Allahu ma.bazai dawo ya sake samun mu a gidanan ba dan mak'otan arziki sun shawaraceni da na bar unguwar hakan kawai zai saka Waleed ya nisanci su shagari Tuni na saka gidana a kasuwa sai dai duk Wanda yazo baya Taya gidan da daraja ballantana har kudin ya Kai na Kara siyan wani gidan. Sabida na nisanci Waleed da abokaina na siyar da gidana haka na Kama haya a wani unguwar. Sauran kudina na hau sana'a gefe guda kuma addua da sadaka daga ni har Inna Amina yi muke. Komawar mu wani unguwa yasa Waleed ya Kara haduwa da wayanda suka fi shagari hatsabibanci rashin jinsa ya Karu. Gefe guda Kuma ga maneman Nadeeya da Minal Ga babbar yayarsu itama da rashin jinta ya karu ta Kara haduwa da kawaye marasa Jin magana. Abu kad'an zaa Mata ta bar gidan sai nayi dgske zata dawo ta kwana Banida bambanci da zararriya dan Ina tafe Ina surutu sadakan nan Ina yi addua Nan ina yi Amma duk da haka Banga alamar yarana zasu dawo hayyacinsu. Ban gayawa Inna Amina ba na fara shirin tafiya Calabar neman su Umma suyi yanda zasuyi Dani su karya asirin da sukayi yiwa yarana...... Wlh banida lafiya Amma haka na daure nayi *NAGA TA KAINA* *NA SADNAF*🌸🌸 ®️ *_PURE MOMENT OF LIFE WRITERS_* _{We Don't just entertain nd educate we also touch the heat of readers P.M.L}💪🏻_ *Free Novel* Page 60 Tashin hankali da damuwa yamin yawa bana iya bacci sabida halin da yarana Suka tsinci kansu a ciki burina kawai yarana suyi hutun makaranta na tafi calabar Zan zub'e a gabansu ko kasheni ne suyi su karya abinda suka yiwa yarana Zan jadada musu na rabu da Naseer har takarda Zan nemi wani ya rubuta min su dai ga shaida ko hakan zai kwantar musu da hankali Ko ya na rufe Ido sai na ringa ganin Kamar zaa shigo da Waleed hannunsa d'auke da ankwa ya aikata wani Abun. Zahira kila ta janyo min magana da zai saka Mana tambarin da ba ita kadai ba har mu sai ta shafa Mana bakin fenti gashi duka yarana Mata ne yanzu ma iya kawaye kawai da take bi ana jifanta da kalmar Yar iska har da masu karyar ta zubar da ciki. Idan Abun jaje ko na alkhairi ya Kama daya Zama dole na Shiga mak'ota haka zanji Ana zaurence ana labari da ni nasan dani suke yara dai a iya sanina duk Inda ka kai ga ka basu tarbiyya sai Allah ya dafa maka a tarbiyyarsu Amma wasu basu gane haka ba masu yin haka ma sai iyaye uwa data Kira kanta da uwa ita zata zauna ta ringa gulmar Yar wacce Yar iska ce bana Jin akwai Uwar da ko karuwa ce zata so yarta ta zama Yar iska sai dai idan haka Allah ya kaddarta Mata babu yanda zatayi ni nasan nawa yaran na musu tarbiyya da taimakon Allah makiya kawai ke san ganin bayana. Har ta kai yanzu Zahira idan tsautsayi ya gifta ta samu matsala da kannenta zuciya take ta bar gidan ba Kuma zata kwana ba bansan a Ina take kwanan ba sai dai washegari ta dawo haka ma Waleed. Ko kullesu nayi sai sun San hanyar da suka fita daga gidan dan tamkar zaman gidan mitsininsu yake Yana musu zafi. Inna Amina musamman ta tsiri azumi sabida wanan matsalar da na tsinci kaina a ciki. Ba karamin damuwa take da rashin Naseer ba Duk gaisawar da zamuyi sai tace ban kyauta korarsa da nayi ba. Ni kuwa ban tab'a nadamar Abunda na aikata ba San yarana ya rufemin idon da nake ganin duk abinda ya faru shine sila ni da ban aure shi ba ma da kila ban tsinci kaina a ciki halin dana ke ciki ba yanzu. Damuwa baya bari ma na tsaya zurfin tunani har na gane halin Naseer ne ko ba halin Naseer ba burina dai kawai Allah ya kawo wa yarana sauki. Saura sati daya Nadeeya ta yi candy duk makaranta ayi hutu na Kara zage damtse wajen Tara kudin da zanyi tafiya dashi dan ba abinda zai dawo dani har sai sun warware abinda suka yiwa yarana. Nadeeya kawai da Minal na gayawa inaso na yi tafiya Inda na rokesu Kar su sake su bari Inna Amina ta sani dan bazan iya bijire mata ba idan ta hanani. Yanda take hanani neman taimako a wajen Mallamai ya sa wani zubin shaidan Kan rayya min kila dan bata San zafin haihuwa bane shiyasa take hanani sai idan naga alherinta Kuma a gareni sai nayi istigifari Tana iya k'ok'arinta wajen nuna min na rungume kaddarar da Allah yamin dan Allah Kan jarrabci bawansa dan.ya gwada imaninsa. Bansan Mai yasa akan yarana imanina yake neman yin rauni ba Ana saura kwana biyar na tafi Na hau mafarkin Ina hauka tuburan a mafarki kafafuna ba takalmi Ina tsince tsince a bola kaina na zura Leda Yarana nesa Dani Kuma suna ta kallona suna kuka. Naseer shima Yana daga gefe yana kuka Yana San zuwa wajena ana ririke shi. Waleed da Zahira su Kuma haka zan gansu a daddaure an jinginasu da bishiya suma suna kukan Ina ganin haka zan nufi wajensu a guje kafin na Isa wajensu zanga Mahaifiyata na shara tana "karkiyi tafiyan Nan indai Kika taka kafarki Kikaje garin nan sai kin haukace abinda suke so kenan karki je Naeema ki cigaba da ga yawa Allah Yana sane dake Naeema Daga haka Zan farka. A jajjere nayi mafarkin har sau uku kuma mafarkin iri daya. Sosai jikina yayi sanyi da irin mafarkin da nake yi dan ni nasan bana mafarki da mahaifiyata ya zama ba gaske ba Iya kan had'uwa ta da Inna Amina ya kara tabbatar min da haka. Amma kwadayin San yarana su warke yasa wani barin zuciyata cemin nayi ta sadaka insha Allahu mafarkine kawai. Ba nida kudi kamar da akan abinda ya samu yarana da San su samu lafiya na siyar da gidana ban taba zaman haya ba Amma gani Ina zaune a haya Sana'ar ma da nakeyi Yan bashi sunfi yawa. Da taimakon Allah da arzikin Yaya Mata da Allah yamin asirina ke rufe dan Nadeeya da Minal ba laifi ma nemansu suna iya k'ok'arinsu wajen kyautata musu Wanda a hasashena da biyu sukeyi tunda sunga halin da muke ciki. Duk da mafarkin Ina rufe Ido zanyi hakan bai saka na girgiza da san fasa tafiyar ba. Addu'a kawai nake da sadaka Ana saura kwana biyu na tafi da yamma Ina zaune a tsakar gida. Waleed ya shigo gidan ba Sallama bai Kuma gaisheni ba ya shige daki ya Tara uban gashi kamar mace yaron da bai wuce shekara Sha hud'u zuwa biyar ba Nan da Nan ya Ajiye saje da gemu. A duk abinan abinda ke kwantar min da hankali bai wuce shaye shaye da ba yayi ba Da Ido na bishi har ya shige daki. A hankali na cigaba da sauke numfashin da naji Yana min wahala kirjina yamin nauyi Daga ni sai Inna Amina ke gidan Dan duk sun tafi islamiyya. Mik'ewa nayi na Shiga d'akin da ya Shiga. A Gefen gado nagan shi a zaune yana gyara wani Abu irin da ake Jin kida dashi da matasa ke yayi (Bluetooth) Shigowana bai saka ya d'ago ya kalleni ba illa Yan kananan wukakensa daya ajiye a gefensa daya d'auke a mayarsu cikin gidansu ya saka a Aljihun wandonsa Girgiza Kai na nayi na zauna a gefensa kirjina kamar ya Fado danaga yanda ya Tara farce cikin sanyin murya nace "Waleeed" Sai dana Kira shi ya Kai sau uku kafin ya d'ago Hada idon da nayi dashi yasa hawaye hau zubomin. Waleed ya rame sosai yayi duhu duk da ba fari bane. Cikin idonsa kawai in ka kalla zaka san Sam dabiun daya ke yi aransa yayi ba halinsa bane. Yana Nan a yaro Mai hankali Mai tarbiyya canza shi kawai akayi. Shima rashin Jin Rama yake saka shi. "Allah ya shiryeka Waleed Allah ya dubeni da idon rahama yasa Kai da Zahira ku dawo yanda kuke a da Waleed nasan duk abinan da kakeyi ba yin kanka bane Waleed ka rage rashin ji kaji ka tausaya min Kar na mutu lokacina baiyi ba. Dan Allah bani wuk'akk'en nan da ka sa a Aljihunka"? Tunda na fara magana cikin hawaye naga Waleed jikinsa yayi sanyi Kamar ba shi ba Cikin bin umarnina daya saka naji kamar na taka rawa ya mikomin wuk'ar Ni kuwa na cigaba da Masa naseeha Rabon da na zauna waje daya dashi haka har na manta. Damar Dana samu yasa nace bari na dauko abin aski na aske Masa uban gashin daya tara da nake ganin kamar zai iya saka shi ciwon Kai. Ganin bai wani motsa ba yasa cikin farinciki jin Kamar Dana ya fara warkewa nayi d'akina da Sauri dan na dauko.abin askin Dana siya musamman dan shi dan ni ke masa aski. Sai dai Ina dawowa naga baya Nan sai wani farin takarda da ya Ajiye D'aukar takarda nayi Naga yasa "Ina yawan munanan mafarki akanki Umma ki dage da Addu'a" A ranar nayi kukan da ban taba irinsa ba wato Dana duk da an juyar masa.da.kai yasan yamin magana Mai dadi Kamar Wanda ya karamin karfin gwiwa nayi tafiya dan na samo musu lafiya. Na kudunduna takarda na fito daga d'akin A daidai lokacin da Inna Amina ta hau kwalla min Kira. Da Sauri na Shiga d'akin Bayan na share hawayena Ga mamakina ita ma sai cemin tayi "kwana biyu Ina munanan mafarki akanki mamana Ina yawan ganinki a mumunan hali dan Allah ki dage da Addu'a" Kamar ta sassareni da guduma haka naji ya akayi Inna Amina da Waleed sukayi mafarki iri daya Tuni na fara Jin tafiyar na ficemin a rai Amma kasan zuciyata kamar ingizani ake akan tafiyar da zanyi shine zai saka yarana su warke. Ina fitowa itama Zahira ta fado gidan Kamar wacce aka jefo tana sanye da matsassun Kaya Muna hada Ido ta sauke ajiyar zuciya ta kad'a kanta tayi daki. Itama bin bayanta nayi kamar yanda nabi bayan Waleed itama na hau Mata naseeha kamar yanda nayiwa Waleed ta nutsu kamar gaske duk da bata cemin komai ba Itama kusanci Dana samu da ita da karantar ta da nayi ya kwantar min da hankali ba kadan ba. Dan duk abinan tsorona ta wulakanta kanta a rabata da martabarta. Dawowar su Nadeeya gidan yasa suka haura da Minal ta zuciya ta bar gidan. Abinda ke ingizani nayi tafiyar tuni ya motsamin naji na matsu jibi tayi na tafi. A ranar bacci yayi ta daukata Ina mafarkin Ina hauka tub'uran Wajejan asuba nayi mafarki da mahaifiyata ranta a b'ace tana tamin gargadi Kar k'afata ta bar garin Kano Ina barin garin Kano an samu abinda akeso. Ba iya Mahaifiyata ba har da mahaifina da ba kasafai nake mafarki dashi ba. Kamar a gaske nayi mafarkin Tashina da Nadeeya keyi akan na makara sallah asuba yasa na mike a firgice Ina gumi. Kirjina na balain bugawa mafarkin da nake bai tab'a dagamin hankali Kamar wanan ba. Karo na farko da naji bana san yi tafiyar Amma abinda ke tunzurani nayi tafiyar na Kara ingizani. Nayi Sallah ne kawai amma ba'a nutse ba dan mafarkin da nayi ya tsayamin a rai sosai kwakwalwata ta kasa bani hadin Kai nayi tunani. A haka yarana suka bar gidan Jiki ba kwari na shiga d'akin Inna Amina. Ido ta zuba min har na ajiye flask din kunun dasu Nadeeya suka Dama mata Na gaisheta a madadin ta amsa min sai cewa tayi "Da kin d'aukeni tamkar Mahaifiyarki Kamar yanda kike fada da baki ringa min boye boye ba Naeema ni nasan akwai abinda kike boyemin da nake ji a jikina ba alheri bane a gareki Naeema sanin da na Miki ba haka kike ba kin kasance yarinya Mai balain hakuri da tunani duk abinda ya Sameki kina Imani cewar Allah ne ya rubuta a takardarki akan zai sameki ba mutum ba sai dai mutum ya zama sila tunda ga farkon haihuwarki har zuwa lokacin da zaki koma ga Allah Allah ya riga da ya tsara Miki rayuwarki babu dan Adam daya Isa ya canja shi Idan Kika duba baya da Abubuwan da Suka faru dake da Imani da kikayi da Allah kin samu maganin matsalolinki batare da kin wahala ba Amma akan abinda ya samu yaranki imaninki yayi rauni har kina tunanin sai kin je wajen wayanda muke hasashen sune silar shigar yaranki wanan halin kina nufin Allah baifi karfinsu ba sai har kinje kin rokesu su warware abinda sukayi. Abaya su ne suke Miki maganin matsalarki?su Kika je Kika samu akan larurar Zahira? Mai yasa bazaki dogara ga Allah ya isar Miki kamar yanda ya isar Miki a baya ba Naeema"? Tamkar yata na d'aukeki idan Abu ya Samu bawa Allah yake gayawa ya magance Masa matsalarsa domin Allah Mai jine Mai Kuma gani duk halin da bawansa zai Shiga yana sane sai dai mu muyi gajeran hakuri kamar yanda kike yi yanzu Karki ga muna ta ga yawa Allah har yanzu shiru wlh Yana sane zai amsa Mana a lokacin da bamu zata ba wuyanta muyi hakuri dan haka kiyi hakuri ki koma ga Allah ki cigaba da gaya Masa Yana sane dake zai amsa Miki insha Allahu. Domin matsalarsu nayi azumin kwana bakwai da niyyar Allah ya warware duk abinda aka yiwa yaran nan ga ruwan zamzam nan kiyi kokari su biyun su Sha ki Kuma shafe musu jikinsu dashi zamu dace watarana insha Allahu" Kuka na fashe dashi sosai dan tabbas duk abinda ta fada gaskiya ne imanina yayi rauni akan San yarana su warke. Ni kaina nasan yanda nake dukufa da Addu'a a baya ba haka nakeyi ba yanzu. Ina sallah Ina tunani karshe idan naga zuciyata baa nutse take ba sai na hakura da sallah. Godiya na ringa mata a raina Ina Jin na hakura da tafiyar ba Inda zani Zan cigaba da gayawa Allah sai a lokacin tunanin Naseer ya fad'omin arai. Har nayi tunanin ko ina yake yanzu na Kuma ringa Jin kamar ban kyauta korarsa da nayi daga gidana da bai kareni da komai bama sai asara dana tafka ta hanyar siyar da gidana "(Duk.mafarkin hauka dinan da komai ba fiction haka tayi mafarki Allah ya tsallakar da ita) Calabar Safiyya Tunda ta samu cikar burinta akan Zahira da Waleed take cikin tsananin farin ciki zuciyarta v bata tab'a k'issa mata alheri ba sai sharri A duk lokacin data bude ido taga hauwa yarta da ta siffantu da d'abba takan ji tsanar Naeema da duk ahalinta. A idonta gani take ko ta samu nassarar kashe Naeema da yaranta har da Naseer da ya Zama babban makiyinta zuciyata bazata taba sanyi ba tunda duk a silarsu take Kan Shan wuya da hauwa da take Mata fatan mutuwa sabida wahala da take Sha akanta Dakyar ta samu tayi abubuwan da tayi Bashir ya fito daga prison Wanda ta gwammaci har zamansa a can da sakinsa da akayi. Mugun barawo ne dan d'abba mashayi. Da cikin da ta Kara samu da baban Hauwa Bashir ke nada Mata mugun duka idan yayi shaye shayensa Sata kuwa baa Kama hannun yaro Halayen Bashir yasa mahafin hauwa sakinta saki uku bayan ya kwashe duka kayansa ya bar gidan Dan kananan sanaoi da take shi ke sawa ta samu na abinci har yaranta su samu Suma da sun kawo girman da take fatan su fara samun Samarin da zasu na kashe musu kudi. Kamar yanda taci buri akansu take fatan Yan biyun nata suyi farin jini irin na Zahira sai dai shiru. Da tsohon cikinta Bashir ya Sha jawo mata a kulle ta dan amfana da Oban keyi da ita yasa yake siddabarun da ake sakinta. A cikin wahala ta haihu da ita kanta batasan cikin na baban Hauwa bane ko Oban da baya iya Bata ko sisi amma duk wani Abu na mugunta Idan Tana so zai Mata akan bashi. Rabi ta sawa yarta data haifa Dan kudaden data samo dan ta dan siyi abinci da zasu ci ita dasu Yan biyu Haka Bashir yazo da wuka yace ta bashi. Tana gardama ya rufeta da duka Kamar ba uwarsa ba ya dau wukarsa Mai kaifi ya tsage Mata fuska dashi.. Sai da ta Sha Jinya ta dawo daidai baki.kam ba irin Wanda ba tayiwa bashir da tayi mugun nadamar aikin da tayi har aka sake shi ba Tana tsoron Bashir ya Zama ajalinta watarana Ta Kan je wajen Oban ya duba Mata halin dasu Zahira ke ciki halin da suke ciki kawai ke faranta Mata rai yanda Naeema take neman haukacewa Akan yaranta. Yanda Naseer ya tsani bud'e ido ya ga Waleed Yana balain saka zuciyarta sanyi uwa uba fadan da Naseer da Naeema ke yawan Yi komai yana Mata yanda takeso. Ko damuwa ba tayi da matsalar da take ciki ba tunda ta samu cikar burinta a haka a garin duba halin da su Naeema ke ciki Oban ya gano Mata Naeema na shirye shiryen zuwa calaba nemansu dan ta rokesu su karya abinda aka musu. Cikin tsananin mugunta Safiyya tace.masa tana san ya Mata aikin da Naeema tana shakar iskar garin calabar a ranar ta haukace hauka da zata na cire kayanta tana bin mutane da gudu. Oban take ya bata layoyyi masu yawa yace taje tashar da motar Kano ke sauka ta binne layyar a wajen. A duk ranar da Naeema ta taka kafarta garin calabar a ranar zata haukace Amma idan aka samu akasi Naeema bata zo ba abin zai koma Kan wani nata. Take ta amince Oban ya dirjeta ya bata layoyyi da kwallin farin jinin da zata kai wa Yan biyunta Suyi farinjini da zasu yi Samari. A daren taje Tasha ta binne layyar tana murna Naeema na dab da haukacewa wuyanta ta tako garin. Washegari ta nema kayan gumama ta baza yaranta neman saurayi bayan sunji uban kwalli. A ranar kamar ta kwana rawa da ta ga Safiyya da asmau sunyi Samarin Har an hidimanta musu ta samu abun duniya da bashir yazo ya musu fin k'arfi ya kwace. Gefe daya.tana murna kasuwar da yaranta sukayi gefe daya Kuma tana hanya zuwa wajen Oban dan taga halin da Naeema ke ciki ta taho ko bata taho ba. A yau ma a k'ofar gida ta bar Asmau da itace hassana sosai take ji da ita sabida tafi Safiyya farin jinin samarin yanzu ma wani dan acaba ne yazo wajenta zance A ranta ba haka takeso ba manyan masu kudi takeso su ringa zuwa Amma tafi tafi dai tasan zasu Zo. Wajen Oban taje ya duba Mata su Naeema inda yake gaya mata ai gobe Naeema na tafe. Dan Yana ta ingiza ta akan tazo A ranar sabida farin ciki a wajen Oban ta kwana da yarta rabi ya dirjeta San Ransa Washegari wajen Tara tayi gida zuciyarta fes a idonta hango Naeema kawai take ta haukace. Har Tasha zata je ta zauna taga yanda Naeema zata haukace Sai dai tunda ga nesa ta hango k'ofar gidanta dankar da jamaa kafin ta gane Mai ke faruwa Asmau da aka riririke tsirara ta kwace daga hannun mutane ta Kara fita a guje............. Kila gobe ajini Ngd en uwa da soyyaya da Kauna Allah ya biya muku bukatunku na alheri masu San cigabana ngd. Yar uwa na barar adduarku 👇 Hi sadnaf ykk ya karfin jikin Allah yasa kaffara ne Wlh Ina cikin rudani nikam yayata ce uwa daya uba daya takeda yaro marar jin magana Allah yamasa baiwar karatu takowane bangare dan shekararsa 10- yayi saukar kur'ani saidai a kyale Shima saboda rashin son zuwa makarantarshi gashi Yana Yan dauke dauke Amma a gidansu takai har ya dauki Abu a gidansu yaje ya siyar yau ma abunda yasa take bani lbr tace babansa ya siye bakin Mai na mota dubu 7 da wani Abu shine ya saceshi yaje ya siyar 5k 😭😭 wlh Allah Dan yayatane na farko shidaya ke gâresu lta da mijin Saïda yayi 10 yrs sannan Allah yabata wani yanzu yanacikin 2 yrs Dazun Nan take gayamini sunkaisa wurin wani malami akace ture akai Masa na bakaken Aljannu masu hanashi karatu Kuma suna sakashi Satan ,Kuma acikin satin da sukaje wurin malam Kuma malamin islamiyarsu ya Kira babban shi yake gayamasa an fara Masa Aiki Kuma tace rubutune ake wankemasa takebashi yanasha wlh tallahi tacemini sai Ranar karshe ta kuskure Shi malamin ma na farko dasukaje yabasu magani yace idan ya Kare sudawo cemin tayi a Ranar dasukaje wurinsa data dawo batayi kwana ba a ka dinga Bata tsoro tacemin in ma bayanzu datakemini firar ba tsakaninta da babbanshi basu taba dauko firar malamin ba Amir yanada tsananin ilimi n'a nan mamaki wlh KO islamiya sau 1 akemasa Kari ya hardace DUK da rashin zuwanshi kullum sbd ana kaishi zai tsere wani time in Amma a haka ya sauke malaminsu cewa yayi dayana tsayawa yayi karatun da tun ba'a Kai haka ba zayyi sauka zai kebeshi ba cikin ajiba Yana Masa Kari Amma Ina bayaji Iyayensu dukansa suke kamar jaki saboda karatu saboda sata Amma baya Bari Ranar akan Keke yaje maradi daga anbashi Dani 37 kilometers daga Nan zuwa maradi Amma yaje Tacemin yanzu sunbar dukansa ma Tunga aka gayamusu haka akace Kuma mace ce tamasa turen mamansa dai tacemini ita batada wani makiyi Kuma irin ma tace wane ko wance take zargi itadai Babu batadai San ko babanshi ba Kuma mezai hada babbanshi da mata har a turoma dansa wani abun Tacemini bazata manta ba lokacin suna tsohon dakinsu Amir Kuma Yana falo Yana bacci itakuma Tana tsakar gida acikin baccin yatashi ya rike kansa Yana ihu yanata kuka tun Yana primary 2 tace tayi tunanin ko cinnaka yacijesa a kunne amma yace aaa bayan gayama kukan ta tanbaya meyasa meshi yace wani suka harbamasa ball a Kai Tacemini wlh koma minene a lokacin yasamesa Kinsan Allah saboda hakinshi na daukar abun mutane yafita Raina ko inada Abu ban iya basa Yana batamini Rai kullum cikin warar sa nake Dan babbu jimawa an taba daukemini kudi bayan jaka 4500 Kuma Yana wurin Koda Naga bangansu ba nace shine Daman ma aikesu nabi bayansu su 3 shida autan Mu da dan yayata guda dana hangosu niyata idan n'a ISO na daukeshi da Mari Amma sai na fasa nacemusu Kai an daukemini kudi kutsa in lalubeku ke in karemiki karshen zance shidaya na lalube nace bakowa bane Kaine sai cemini yayi ya hade hannayensa haka🤌🏽ya daura a kirji yace yanzu tanti mina Ni kadai kike zargi na daukarmini kudi bakomi sai yabani tsananin tausayi jikina yayi sanyi Nasan fa Yana dauka Amma wadannnan bashi ya daukaba amma wlh har yau Abun Yana Raina dayacemini yau da mamansa ke gayamini saina Goda Allah da alokacin ban marésa Yanzu aji daya yake a secondary Amma exam na karshe bayyishiba Ashe koyafita gidan bazuwa yakeba Sai bayan angama iyayye suka sani Kinga sai Kora ko indai ba gyara akamasa ba Ya fa Yi sauka Amma har gobe saï akaishi islamiya muddin ba'a kaishi ba bayazuwa Saidai dayafita gidan ya tsere Wlh data ke gayamini lbrn zahira ya fadomini a rai Muma muna barar addu'a idan Kuma dawasu addu'o'i ataimakamana Allah ya taimakemu😭😭 Wlh hankalina yabtashi *NAGA TA KAINA* *NA SADNAF*🌸🌸 ®️ *_PURE MOMENT OF LIFE WRITERS_* _{We Don't just entertain nd educate we also touch the heat of readers P.M.L}💪🏻_ *Free Novel* *Ngd masoyana da suka nuna min kauna Kaunar da kuka nuna min yafi faranta min fiye da komai ngd* *Page 61* Hankali a balain tashe Safiyya ta bi Asmau a guje tana zunduma ihun a taimaka mata a ruk'o ta Amma duk yanda aka so riketa kasawa akayi dan ko an riketa sai ta kwace ta Kara fita a gujen Safiyya zub'ewa tayi a kasa ta hau birgima tana ta Shiga uku ganin Asmau a cikin wanan halin ya kusa sawa zuciyarta ta buga. Wajen Oban ta koma da isarta ta zub'e a kasa kafin ta Masa bayani yace mata "Naeema ce ta fasa zuwa shiyasa haka ta faru ga yarki duk iya k'ok'arina dan na ga na ingiza ta tazo taurin kanta yasa ta fasa zuwa matar Nan tana da wahalar shaani bansan ya akeyi take tsallake duk abinda mu ka mata ba yanzu abinda za'ayi kiyi Sauri kije tasha Inda Kika binne layyan nan ki hak'o ki kawo min nayi aikin da Asmau zata dawo daidai. Da balain sauri ta mik'e ta nufi Tasha dan ta d'auko layyar da ta binne sai dai tana Isa ta kasa gane Inda ta binne layyar. Kamar zautaciya ha ka ta ringa bin waje waje tana tonowa mutane sai kallonta suke. Mutanen da yawa sun d'auka itama hauka cewa tayi hakane yasa aka fitar da ita daga tashar ta karfi haka ta Kara komawa wajen Oban tana kuka akan bata gane wajen da ta binne layyar ba ya taimaka Mata yayi aikin da yarta zata dawo daidai. Oban haka ya hau tsubbuce tsubbuce ganin ba abinda zai iya yi akai yasa ya d'ago ya hau cewa ta nemo Abubuwan daya San ba yanda zaayi ta samo su Koda kudinta. Safiyya haukacewa ne.kawai bata yi ba. Haka ta koma gida tana rusar kuka. Tsanar Naeema da San ma rabata da ranta na darsuwa a ranta har yau Bata ga ribar data ci akan Naeema ba duk abinda take Mata kanta yake dawowa tunaninta bai tab'a bata Allah ne ya tsayawa Naeema Sharrinta ke komawa kanta ba hasali gani take duk abinda ya sameta laifin Naeema ne Bashir babban danta babban barawone, Asmau yanzu ta haukace Hauwa ga ta Nan kamar ba mutum ba Safiyya da Rabia jaririyar ta kawai ne wani Abu bai same su ba duk wanan tashin hankalin ta dalilin Naeema ne dan haka ta Sha alwashin sai dai idan mutuwa tayi sai ta samu cikar burinta akan Naeema zata samu kwanciyar hankali Dak'yar ta samu wasu matasa Suka kamo Mata Asmau da sai da tayi sati uku a waje tana bin bola tana bin mutane a guje tsirara ba kaya a jikinta Abinka da budurwa a haukace haka aka rabata da budurcinta kafin Safiyya ta gano Inda take ta saka a kamo Mata ita ta saka ta a d'akin da ta kulle hauwa ta datse da mukulli. A gaban idon Safiyya takwararta Safiyya ta fara bin mazan. Yar iskar da take San Zahira ta zama sai gashi Safiyya ce ta Zama a gaban idonta zaa Zo a d'auketa a dawo da ita washegari ko sisinta ba Kuma zata bata ba daga ita har Bashir Basu d'auketa a matsayin uwa ba ubanta kawai suke ci. Abu goma da ashirin haka suka hade mata duk lokacin data duba yaranta ta ga halin da suke ciki zuciyarta kamar ta buga sabida bakin ciki ga mugu mugun tsanar da ta yiwa Naeema da iyalanta gabadaya rashin nutsuwa yasa ta kasa komawa wajen Oban da ayi Mata mugun aikin da zai Saka Naeema ta mutu Tama bar Mata duniyar duk da tana ganin ko Naeema ta mutun hakan bazai sa taji sanyi a zuciyarta ba sabida tsabar tsanar da ta mata. Tana sane da Hajara bata taba tunanin waiwaiyar ta ba Dan gani take itama tana cikin wayanda Suka jawo mata Kara lalacewar Bashir. Haka Safiyya ta kasance cikin tashin Haukacewar Asmau da ta lura har ciki ne da ita. Wajen Oban ta koma ta cigaba da rokonsa ya Mata aiki Asmau ta dawo daidai shi kuwa Oban ya ringa kwasar rabonsa a jikinta Yana saka ta Nemo kudi ta kawo masa akan Kar ta damu Yana aiki akan Asmau zata samu lafiya. Haka tayi ta saka Rai da samun lafiya Asmau da ke haukanta tuburan da ciki har ta haifi yarta mace a cikin halin hauka. Safiyya tana ji tana gani tayi jika shegiya da Bata San ubanta ba haka ta hau rainon jaririyar cikin bakin cikin duk halin da ta tsinci Kan ta a ciki da take ganin duk Naeema ce ta jaza Mata. Wanan kenan Hajara Rayuwa ba karamin wahala ya Mata ba dan ciwon kafar da take yasa dan kosai da take soyawa ta daina iya fita soyawa dan canji Kan da take dashi haka duk ya kare a hannunta haka ma kudin hayan gidan da ta Kama Tana ji tana gani aka koreta daga gidan. A ranar da aka koreta da Jan kafa ta nufi gidan Safiyya dan bata da Inda zata je daya wuce wajen Sai dai da isarta Safiyya ta rufe idonta ta koreta akan bazata zauna Mata a gida ba itama ta kanta take abinci itama sai tayi da gaske take sa mu taci taje wajen Naseeru da ta zabeshi da sabida Kar ta Masa komai ta gwammace ta fasa mudubi danta Bashir ya Kara zama katon barawo. Hajara kuwa bakin cikin abinda Safiyya ta Mata yasa ta ringa tsinewa Safiyya tana jawo Mata iftilai rayuwa Zagi in zaga Haka sukayi kamar ba uwa da 'ya ba Hajara na kuka ta baro gidan Safiyya ta hau laluman Inda zata zauna dan Bata Isa ta soma tafiya Kano wajen Naseer ko Tijjani ba Safiyya ta Riga da ta cutar da ita intaje Kano ma kila Yan sanda su Kamata Yau da ba dan Naeema ba da rayuwata duk bata juya haka har wajen Zama ya gagareta ba. Haka ta ga ma kewaye unguwar Bata samu waje ba kamar tsinuwa duk Inda taje sai an koreta Sai a wani rumfa da Rabinsu mahaukata ne anan ta samu wajen kwana Anan Kuma ta mayar dashi gidanta K'arfin hali irin nata yasa ta hau bara tana neman kudin da zata ga bayan Safiyya da Naeema. Dan tsana take Mata da take Jin wani Abu ya tokare Mata kirji har sai ta samu cikar burinta zata samu sausauci a zuciyarta Wanan kenan. Naeema Tunda Inna Amina ta min fada na watsar da komai na maida lamurana wajen Allah nayi k'ok'arin rungumar duk jarrabtar da Allah ya min da hannu biyu addua Shiriya kawai nake yiwa Waleed da Zahira. Inna Amina na Tayani Dauriya kawai nake da muka tafi shekara biyu Naseer bai neme mu ba Ina tsoron ko wani abune ya same shi sai dana dawo hankalina na fara tunanin duk halayyen da ya ringa nuna min ba halinsa bane kila shima tab'a shin akayi. Addu'a nake akan Allah ya kareshi ya sa ya dawo hankalinsa ya dawo ko dan Nadeeya da yanzu ta fara jamia maneman Aurenta na ta zuwa ko ta Ina neman aurenta. Burina yanzu ko Humaira ce ta samu miji aurar da ita zanyi. Zahira da waleed Kam addua kawai Zan cigaba da tayasu dashi akan Allah ya shirya min su duk da bana San yaudarar kaina sai nake ganin kamar sun fara dan canjawa tunda Waleed na dan zama a gida yanzu inya ga dama har ya kwana. Zahira ma ta fi bani mamaki dan tana zama yanzu a gida sai idan an b'ata Mata Rai take fita. A yau da yamma muna zaune gabad'ayan mu atsakar gida har da Inna Amina dasu Nadeeya suka tilasta mata fitowa tsakar gida. Suna ta tsokanar ta itama tana tsokanarsu. A rayuwata ba abinda ke Sakani farinciki sama Dana ga yarana gabadaya a waje daya suna hira ko ban sa musu baki ba Ina Jin dadi a Raina. A hankali na ringa binsu da kallo dukaninsu sun girma sun Zama Yan Mata Masha Allah har Raheema dake da shekara goma Sha shidda. Abinda ya ragemin Jin dadi Bai wuce halin da yarana biyu suka tsinci kansu a ciki ba. Ko yanzu ma Zahira bata nan haka ma Waleed Ina zaune ne kawai amma zuciyata na wajensu. Shigowar Waleed da Sallama kasa kasa yasa na amsa da Sauri Ina lalubar kwayar idonsa Ina ganin canji sosai a tare dashi tunda aka juya Masa Kai bai tab'a shigowa gidan da sallama ba sai gashi kwana biyu na lura Yana shigowa da sallamar duk da kasa kasa yake sallamar. Girman jikin da yake dashi da kwarjini yasa k'arfi da yaji yayayensa suka koma shakkarsa idan ka ganshi zaka iya tunanin ya girmesu Sabida naseeha Dana wa yayyensa yasa suke hakuri da duk wani rashin kunyar da yake musu. Kitchen ya Shiga ya d'auko abincinsa har zai Shiga d'aki Inna Amina ta Kira shi akan yazo gefenta ya zauna. Gefenta ya zauna ya fara cin abincin kallona da Inna Amina tayi yasa na mik'e na Shiga d'akinta na dauko ruwan Addu'ar Waleed da Zahira na tsiyaya a Kofi na Kai Mata ta mik'awa Waleed ya karba. Jansa Inna Amina ta fara yi da hira Sai gashi Waleed ya saki jiki Yana hirar shima alhamdulillah Ina ganin canji sosai a wajen yarana. Kamar Dani yake hiran haka na zuba Masa Ido Inna Amina na Masa naseeha cikin siga har tana idan ya gama cin abinci yaje yayi sallah Yana kuwa gama ci yaje yayi alwala. Ya Shiga d'aki da zumar yin sallah Dan tsakar gidan namu karami ne sosai. Sallamar da akayi tare da shigowa yasa dukan mu muka kalli bakin kofa. Yarana Suka saki ihun murna sukayi wajen Naseer dana kasa d'auke idona akansa. Shima hadesu yayi ya rungumesu. Kwalla ya cikamin Ido Dana ga yanda ya rame har furfura ne suka firfito Masa Inna Amina kuwa tsabar murna tafi ta ringayi daga zaune tana Masa oyoyo. Dak'yar ya bambare su Nadeeya daga jikinsa Ya nufo wajen da muke Zaune yana zuwa ya zub'e a gaban Inna Amina ya hau gaisheta. Cikin murna ta ruko hannunsa ta hau amsawa tana had'awa da Masa tambayar Mai yasa ya Dade haka Bai waiwayo mu ba a matsayinsa na da namiji ai hakuri ya Kamata yayi bai Kamata yayi fushi ba. Fada da naseeha Inna Amina ta Masa ta had'a da bashi hakurin Abunda na Masa akan yamin uzuri idona ne ya rufe akan su Zahira shiyasa na Masa haka Murmushi yayi yana "Ba komai Mama wlh ban riketa a raina ba korar da tamin daga gidanta yasa Nima na samu Allah ya dafamin na nemi kudin da Nima na siyi filin nayi gini naje wancan tsohon gidan nata anan nake Jin labarin Kun tashi dak'yar na gane Kuna nan nima nasan Ina da laifi da Abubuwan da na ringayi a baya da Nima sai daga baya nagane ban kyauta ba sai dai na baku hakuri Allah ya kiyaye gaba" Sai a lokacin muka hada Ido dashi ya dan sakarmin murmushi Nima na sakar masa. Nadeeya ya kala Yana "Inna Zahira"? Nadeeya na k'ok'arin Magana Waleed ya fito daga d'akin. Na zubawa Naseer Ido naga ya zaiyi idan ya ga Waleed zai Masa wanan kallon tsanar daya Saba Masa Kallon kallo sukewa juna da yasa na kasa karantar kallon da Naseer ke yiwa Waleed har Waleed ya d'auke kansa yayi waje ba tare da ya gaishe shi ba Inna Amina da Sauri ta hau Masa bayanin halin da Waleed da Zahira ke ciki har yanzu da muke ta addua Allah ya shirya su. Girgiza Kai yayi Yana insha Allahu shima Yana addua Akan Allah ya warware abinda aka musu Daga haka ya cewa Nadeeya ta fita ta nemo masa Zahira A Dan karantar da na Masa sai Naga kamar har lokacin ba soyayar Waleed a Ransa (Duk da asirin da aka musu na karyewa har gobe Da nake rubuta wanan labarin wani zubin idan abin ya motsa Naseer da Waleed basa Zama inuwa daya bi maana Babu wanan soyayya d'a da uba Mai k'arfi a tsakaninsu) Nadeeya ya tasa a gaba suka je neman Zahira gidan kawayenta da wasu mun San gidansu wasu bamu sani ba da suka Taki saa gidan kawarta da muka sani anan suka same ta. Naseer ya taso ta gaba suka dawo gida. A Palo ya zaunar da ita ya hau Mata naseeha Inda ni Kuma jikina yayi balain sanyi da na ga kamar da Zahira kawai ya damu Banda Waleed. A ranar nayi kukan da na dade ban yi ba dan duk da a gidan ya kwana ya Kuma bani labarin Dana koresa daga gidan bai koma Abuja ba motarsa ya siyar ya hada da kudaden daya samo ya siyi fili Rabin filoti a gyadi gyadi ya hau gini ta hanyar neman kudi Yana buga buga har Sana'ar hannu sai daya koya dan kawai ya samu kudin da zai gina gidansa. Ko abinci baya iya sawa cikinsa sosai sabida kawai ya samu kudin gini Addu'ar da ya dage dashi yasa ya dawo hayyacinsa. Yana Kuma Kai karar mahaifiyarsa wajen Allah Dan ta cutar dashi. Cikin siga na hau shigar Masa da maganar Waleed da naga rabi yafi damuwa da halin da Zahira ke ciki har Yana cemin yanzu so yake idan mun koma gidansa ya dukufa da Addu'a Zahira ta samu Lafiya idan na Shigar Masa maganar Waleed sai ya Sako min wani zancen. Washegari da sassafe aka hau jiddar kayanmu Ana kaiwa sabon gida Ina ganin ya fita naje na samu Inna Amina cikin damuwa na hau gaya mata karantar da nayiwa Naseer akan Waleed. Hakuri ta bani tace na bi komai a hankali Kar na damu kila Abunda akayi a tsakaninsu bai gama warware bane mu cigaba da Addu'a. Yarana murna kawai suke zasu koma sabon gida Nima a kasan Raina na ji dadi sosai da Naseer ya samu ya Gina gidan kansa tamkar ni nayi gidan haka na ringa ji shima fuskarsa kawai zaka kalla kasan Yana dokin sabon gidan da yayi kamar bai tab'a gidan kansa ba. Ranar tashin namu daga Zahira har Waleed ba Inda suka je a ranar duk da Ina lura da Waleed da Naseer suna Yar kallon kallo Wanda hakan ya dameni sosai. Da yamma na shishiga mak'ota muka musu Sallama Inna Amina ita ta ringa lallaba Waleed dan kar ya botsare Mana yace bazai bi mu ba. Su Nadeeya dama sun dade a can dan tun safe Naseer ya Kai su dan su shirya Mana kayayyakin mu. Iya ni da Inna Amina sai Waleed da Zahira ne bamu tafi ba sai daddare Naseer ya kawo taxi muka hau Muka tafi gabadaya. Gidan yayi kyau ba laifi duk da gidan bai Kai girman gidajensa na baya ba dakuna hudu ne a gidan da falo kitchen da band'aki a kowane daki. Dan karfin hali har da dan kujeru sababi masu saukin kudi. Daga ni har yarana Sai murna muke Dakunan duk a cikin falo suke d'akin da bai Kai sauran girma ba aka sawa Inna Amina karamin katifarta da kayanta. Su Nadeeya Kuma suka dau d'akin tsakiya suka saka katifarsu guda biyu. Daya d'akin Kuma shine nawa dayan na Naseer. A Raina naso Waleed nada d'akinsa ba d'akin daya dace ya d'auka Sama da Wanda Inna Amina ke ciki Amma insha Allahu zanyi k'ok'arin sama Masa d'akin. Ban dawo daga tunanin dana tafi ba naji Waleed cikin dan daga murya Yana "Ni a wane daki Zan ringa kwana"? Naseer d'auke kansa yayi ya shige dakinsa Tuni naga Waleed na k'ok'arin Hawa wanan dokin zuciyar tasa dake sa yayi zuciya ya bar gidan Allah cikin ikonsa Inna Amina tayi saurin cewa a d'akinta zai ringa kwana ita a dakinsu Zahira zata ringa kwana dan Sam Bata San kwana ita kadai Inna Amina ce ta taimaka min aranar waleed bai zuciya ya bar gidan ba. Tunda Muka dawo gidan na lura Naseer bai fiye baccin dare ba yakan raba daren wajen sallah da Addu'oi tamkar dai yanda ya ke yi ada. Hakane yasa nima na Kara akan Wanda nakeyi da. Dawowar mu sabon gida tamkar k'ofar samun warakar yarana ne dan a hankali naga Zahira da Waleed sun fara nutsuwa suna Jin maganata har sallah da suke Wasa dashi yanzu suna maida hankali suyi duk yawace yawacen nan da sukeyi yanzu basa yi duk da Basu dawomin dai yanda Suke gabadaya ba Amma ko hakan suka zauna alhamdulillah. Allah kawai nake Godewa daya amsa Mana adduar mu akan yaranmu. Abu daya ke damuna Naseer da Waleed Dana ga Kamar basa ga miciji dan yanzu Waleed na gaishe shi wani zubin ya amsa wani zubin yyi kamar bai ji ba Inna Amina ke ta kwantar min da hankali tana hanani yiwa Naseer magana akan Kar na damu komai zai warware tunda har Allah yasa sun fara dawowa hayyacinsu ko Kuma muce sun ma dawo tunda yanzu duk sun daina Abunda sukeyi Waleed abinda kawai bai bari ba shine saurin zuciya da fushi. Itama Zahira hakane Amma ta dawomin zahirata yanda take a da. Burina Zahira da waleed su koma makaranta Dan an barsu a baya sosai hakane yasa nayiwa Naseer magana take ya Nemo makaranta ya biyawa Zahira waec shi Kuma Waleed da k'arfi nasa ya nema Masa makaranta ya fara daga jjs 2 duk da ya girma da jss 2 din Amma haka ya fara zuwa dan a haka ma mun masa tsallake. Sai a yanzu na samu kwanciyar hankali nake Kuma Godewa Allah da Kara neman kariyarsa a garemu gabaki daya Naseer yanzu kanannan sana'oin daya koya dashi yake rik'e damu duk da Nima Ina taimaka masa sosai dan ban saki sanaar da nake ba na siyar da kananan Abubuwa a gida. Zahira na dab da gama zana waec dinta tamkar yanda take da farin jinin samari awancan lokacin haka samari Suka hau layi a k'ofar gidanmu Wanda hakan ya sakani farinciki sosai dan inata addua Allah yasa Kar Nadeeya ta rigata aure tunda itace babba data samu Mai kaunarta Zan cewa Naseer mu aurar da ita. A Rana sama da mutane biyar na sallama suna neman Zahira Hakane yasa na zaunar da ita na gaya Mata a cikin masu kaunarta ta zabi wanda hankalinta ya kwanta dashi dan muna so tana gama jarrabawa idan Allah ya nufa tayi auren Ta cigaba da karatu a gidan mijinta sai dai budar bakinta sai cemin take ita so take ta cigaba da karatu tamkar yanda Nadeeya ta cigaba da karatun dan ita burinta tayi karatu Mai zurfi ta Zama lawyer dak'yar na shawo kanta ta amince zata tsayar da mutum daya Take kuwa ta tsayar da wani kabiru da Saurayine Mai Kuma kudi dan wlh duk Samarin Zahira ba karamin mutum. Tana gama jarrabawa ya turo magabatansa da kudin neman aurenta. Manyansa suka Kara da basa San a saka dogon lokaci kabiru yace zai dau nauyin komai ba sai mun wahalar da kanmu ba. Naseer kafewa yayi akan su bashi Nan da wata shidda zai Mata komai shi Baya so ayiwa Zahira gori. Sai dai dangin kabirun da roko da magiya da kyar suka shawo kansa ya amince aka saka wata daya da sati daya. Fadar halin farinciki Dana tsinci kaina a ciki bata Baki ne kudi na hau tarawa Inna Amina Tama fi kowa farinciki na kasa yarda zahirata da aka so watsawa rayuwa ce ta samu nagartacen miji har baifi sauran sati uku Aurenta ba. Dukanmu shiri muke har Naseer saura sati daya auren Zahira da kabiru aka kawo lefenta akwati shidda cike da kaya masu tsada a wancan lokacin. Nadeeya da Minal iyayen doki ba Wanda Basu Kira ganin lefen Zahira ba. Gefe daya Kuma dagani har Naseer da Inna Amina addua muka dukufa dashi ba dare ba Rana. Ana saura kwana uku daurin Auren Zahira kabiru ya aiko yan uwansa akan a bamu hakuri ya fasa auren Zahira hmmmmmm.... Advertisement Treat/repair your skin with mg's skincare today,are you battling with pimples, Black spot cream reaction eczema,acne, sunburn,spot, stretch mark, discoloration/skin damage, stretch mark ❌then mg's skincare is the plug for you,mg's skincare gat solution to all ur skin prblms😍everyone deserves a blended skin🌿 when it comes to skin issue😢gv it to mg's skincare 💯🔥 now is the time to take care of ur skin,this product is the real deal 🙌clears white patches✅dark patches✅dark feet's/knuckles ✅reduces the appearance of greenveins,it clears pimples,spot and make ur skin fresh nd glow like never before just gv it a try nd ur skin will definitely thank you💋✅evn if you don't HV anything mg's skincare gat you a soap that will maintain ur skin nd make the skin to glow🥰 Soap price:3k Chat 08062991549 to plc ur orders Call:08064532391 We deliver Nationwide buh delivery is not free🙏 we can't wait to be a part of your beauty story🤭 *NAGA TA KAINA* *NA SADNAF*🌸🌸 ®️ *_PURE MOMENT OF LIFE WRITERS_* _{We Don't just entertain nd educate we also touch the heat of readers P.M.L}💪🏻_ *Free Novel* Page 62 Suman zaune nayi bakina yamin nauyi ballantana na tambayesu dalilin daya sa kabiru yace ya fasa auren tunda Suka Fadi abinda ya kawosu naji kamar an sokeni da kibiya a kirji har yau da nake labarin nan Ina fama da Wanan ciwon kirjin idan abu ya girgiza ni. Muryar Zahira naji da bansan lokacin da ta fito da ga daki ba sai ganinta nayi a tsakiyarmu Kwalla cike da idonta ta zub'e a gaban wacce take yayar kabirun da itace Kan gaba wajen Shirin bikin kanin nata ba ma a garin Kano take aure ba daga Abuja tazo. "Aunty Mai nayi Masa yace ya fasa aurena"? Aunty yau saura kwana uku aurenmu ba Wanda Bai San zamuyi aure ba Mai nayi Masa da sai a yanzu zai janye"? "Wlh bansani ba Zahira jiya ya sako mu a gaba akan muzo mu baki hakuri akan ya fasa auren ba yanda ba muyi dashi ba ya gaya Mana dalili yak'i da yaga mun dage Masa ma sai ce Mana yayi idan muka matsa Masa Zai kashe kansa Akan Dole yasa muma muka zo yanda Kika ga Kuna ta Shiri wlh muma haka muke shiri ba Wanda bai zo ba duk gidan mu baki ga yanda muke kaunarki ba amma kabiru lokaci daya yace mu zo mu baki hakuri ga wasika nan ya bani na Baki" Yayar kabirun ta karashe kamar zatayi kuka tare da mik'awa Zahira da hawaye ya jika gaban bak'ar doguwar rigar da ke jikinta hannunta ya Sha Jan kunshi da baki gashinta har baya ya sauko dan Kamar yanda naji su Nadeeya na shiri a yau zasu yi kamu a gidan wani Alhaji dake kallon gidanmu yanzu haka ma su Nadeeya na can suna ta shirya wajen. Zahira ba ta iya karbar wasikar ba illa mik'ewa da tayi ko taku biyu ba tayi ba ta zub'e a kasa. Nayi kanta aguje a daidai lokacin da Waleed ya shigo hannunsa d'auke da kayan rabon da zasuyi a kamu. Zubar da kayan hannunsa yayi yayo wajenmu agujen ya Tayani tallafar zahira dan Nima jikina rawa yake d'aukar ta yayi cak yayi daki da ita. Ni Kuma na cewa yayar kabiru "Ba komai Allah yasa Hakan shiya fi alheri kila da ma Zahira ba matarsa bace shiyasa ya janye" Hakuri Suka cigaba da bani nace musu ba komai suyi min hakuri Nasir ya dawo na Masa maganar kudin auren da kabiru ya kawo a mayar musu da lefen da suka kawo dan dama Allah cikin ikonsa ban Bari ta tab'a komai ba ganin kabiru ya rage Mana nauyi sosai yasa nida Naseer muka Mata dinkuna daidai karfinmu. Mik'ewa suka yi da Sauri suna "wlh yace ya yafe mata komai ba sai mun karbo komai ba kuyi hakuri dan Allah" Nima da Sauri na girgiza musu Kai Ina "ba za'ayi haka ba idan har zai fasa Aurenta banga dalilin da zai saka ya bar mata lefensa har da kudi ba. Nayi dakina da Sauri Ina kwallawa Raheema da Humaira Kira da nake Jin shewarsu a d'akin Inna Amina da alama Basu San me ke faruwa ba kunshi ma ake musu a d'akin. Da Sauri suka fito daga d'akin hannun humaira d'auke da kunshi Dangin kabirun suka gaisar suka yo d'akin nawa. Danne zuciyata nake Ina mayar da kukan da ke neman cin karfina ya fito da k'arfi. Indai na nuna rauni na a gaban yarana su ya zasuyi kenan ya zama Dole nayi k'ok'arin danne zuciyata. Umarni na bawa su Humaira da su kai min akwatunan waje yanzu nan kar su b'ata min lokaci. Dan jikina rawa kawai yake ballantana na iya d'aukar wani akwati. Had'a Baki sukayi wajen cemin "Umma lafiya kuwa Mai yake faruwa ne"? Tsawa na daka musu a daidai lokacin da kuka ya kwace min Ina "Ku fitarmin da akwatin nan nace ku daina min tambayoyi sunce sun fasa aurenta"? Kamar wayanda na watsawa ruwan zafi haka suka ja da baya suna dafe kirjinsu Ni Kuma na zauna a gefen gadon na rufe fuskata Ina cigaba da kukan da na kasa dannewa. Ni kadai nasan mai nake ji a kirjina Waje sukayi gabad'aya Basu dau akwatin kamar yanda na umarce su ba sai ji nayi cikin muryar kuka suna tambayar danginsu kabiru mai Aunty Zahira ta yiwa kabiru da zai fasa Aurenta Raheema har da cewa "Ku rufa Mana asiri karku Mana haka yau fa zaayi kamu ba Wanda bamu gayyata ba Mai aunty Zahira ta Masa da zafi haka da saura kwana uku aurensu zai ce ya fasa idan laifi tayi muku dan Allah kuyi hakuri" Ta karashe tana fashewa da kuka dayake akwatin irin Mai taya dinan ne a zuciye na mike na hau Jan babban nayi waje. Ina zuwa na Kara daka musu tsawa Ina su je su debbo min sauran akwatin Ana dole ne. Humaira aguje tayi d'akin nawa Raheema kuwa ta cigaba da magiya bakin ciiki yasa nayi kanta a fusace wata dattijuwa a cikinsu ta tareni da Sauri tana "Kiyi hakuri mmn Zahira wlh baa San ranmu haka ya kasance ba yarone ka haifeshi baka Haifi halinsa ba wlh nasan da ciwo Abunda yaron Nan yayi Amma ba yanda zamuyi dashi" Da sauri na katse ta Ina "kabiru da ma ba mijinta bane shiyasa Allah baiyi zasuyi auren ba halin da yarinya kawai zata Shiga ganin Aurenta saura kwana uku an fasa ni shine damuwa na Allah yasa hakan shi yafi alheri Allah ya musanya Mata da Wanda yafi kabirun ga akwatunan ku nan kudin auren na wajen baban Zahira idan ya dawo ya turo a karba Masa" Kuka Humaira da Raheema kawai suke Waleed da ke tsaye a bakin kofar d'akinsu zahira da duk Abunda muke Yana kallonmu sai hucci yake. Suna kokarin Kara magana ya daka musu uban tsawan daya sa suka gigice dattijuwan tayi hanyar waje da Sauri "Dan ya fasa Aurenta sai me ku gaggauta kwasar kayanku.ku bar Mana gidanan kafin na muku watsi da kayan waje Banda kaddara Mai aunty Zahira zata yi da wannan Mai zubin tsofaffin" Tsawa na ringa dakawa Waleed akan yamin shiru Amma ko kallona baiyi ba Abinda har gobe ke hadani dashi kenan tunda aka tab'a shi zuciya da taurin Kai ne dashi wani zubin baka isa ka Hana shi ya hanu ba ko wani Abun yayi idan babansa zai dakeshi baya guduwa haka zai tsaya a ga ma jibgarsa har sai dai idan Naseer din ne ya gaji dan kansa. Inna Amina ce ma tace ya bar Masa irin wanan dukan sabida Kamar hakan na Kara taurara Masa zuciya mu cigaba da binsa da Addu'a A karshe Waleed da kansa ya rakasu waje da akwatunan su Suka hau ja da sauri dan ba karamin tsorata su Waleed yayi ba. Suna fita na zub'e a Palo na cigaba da rusa kuka takarda da ya bayar a bawa Zahira na hannuna Tunani iri iri haka suka cikemin zuciya Ina tunanin Mai dalilin fasa auren Zahira da kabiru yayi Raheema da Humaira d'akin Inna Amina suka Shiga suka gaya mata Ina jinta tana ta zuba sallati. Waleed Kuma ya zauna Akan kujera Yana hucci Yana girgiza kafa. Mik'ewa nayi na nufi d'akinsu zahiran dan Naga halin da take ciki Akwance na tarar da ita ta juya bayanta tana kallon bango daga gani kasan kuka take kasa kasa Daga gefen ta na zauna banyi Mata magana ba na warware takarda da aka saka a envelope dan na ga mai kabiru ya rubuto a cikin takardar *KIYI HAKURI BAZAN IYA AURENKI BA ZAHIRA DAN BURINA NAGA NA AURI MACE TA GARI NAJI LABARAI AKANKI KALA KALA A CIKI HAR DA WAI KIN ZUBAR DA CIKIN SHEGE BAN YARDA BA SAI DANA JE GIDAN KAWAR TAKI TA TABBATAR MIN DA HAKA ASHE BA KARAMIN RASHIN JI KIKAYI BA INA SANKI AMMA A HAKA ZAN HAKURA DAKE NA BAR MIKI KOMAI ALLAH YA KAWO MIKI WANI MIJIN AUREN* ban Iya karasa karantawa ba na runtse idona kirjina na min nauyi Abunda nake ta tsoro kenan sai gashi kabiru yaji labarin rashin jin da zahira tayi da ba halinta bane juyar min da Kan ya akayi ko da tayi rashin jinta Alhamdulillah Allah ya karemin ita da Karfin Addu'a baa rabata da budurcinta ba sai dai wayanda tayi muamallan dasu ne idan za'a kwana Ana rantsuwa ba halin Zahira bane ba lailai a yarda ba dan kawayenta duk ba mutanen arziki ni nasan zasu iya komai suma dan su rama abinda Zahira ta musu dan da ta dawo hayyacinta da kanta ta musu rashin mutunci tace su daina zuwa nemanta tana kuka tazo ta sameni tana wlh bata San ya akayi tayi kawance dasu ba ita da take da kunya Mai ya had'ata dasu. Murmushi kawai nayi dan ni nasan da ma ba halin Zahira bane sai gashi duk da mun bar unguwar suna nufarta da sharrin ta zubar da cikin shege Ina mamakin halin wasu mutanen da Basu da burin daya wuce su bika da sharri dak'yar na taushi zuciyata na rik'e hannun Zahira na hau rarrashinta Ina Mata nasiha. Nasan itama kawaici kawai take min tana nuna min ba komai. Shigowar Nadeeya da Minal ya Kara hargitsa gidan suna koke kamar gidan rasuwa sai dana musu da gaske suka Shiga hankalinsu Nadeeya ta hau jawa kabiru Allah ya Isa har da cewa zata je gidansu. Inna Amina ta taimaka sosai wajen kwantarwa da Zahira hankali ta hade har da kannenta ta musu naseeha. Wajen karfe Takwas Naseer ya dawo niki niki da kayan abincin biki har da dinkin Daurin auren da zai saka inaga farinciki da yake ciki bai bari ya karanci yanda mukayi cirko cirko ba dan duk mun kasa walwalar har gwara ni Ina dan dauriya sabida yarana Amma kannen Zahira da suka ci buri Kamar an musu rasuwa haka su kayi cirko cirko. Daga yanda suka gaishe shi yasa ya fara lura da halin da muke ciki. Sai a lokacin ya kalleni ya tambayeni Mai ke faruwa ya Kara da Ina Zahira take Dan har Waleed Yana zaune a palon Zahira ce kawai a daki Ban bashi amsar tambayarsa ba dan bansan ya zan Masa bayani ba illa takardar hannuna kawai Dana Mika Masa. Kafin ya bud'e Naga ya kallemu duka Yana "Wai Mai hakane ba zaku gaya min mai ke faruwa ba" Ya bud'e takarda hannunsa ya hau karantawa Sallati kawai yake ni kuwa na kalli su Nadeeya take Suka mik'e suka hau barin palon sukayi dakinsu Waleed ya mike yayi d'akin Inna Amina. Yanda muryarsa ke rawa yasa hawaye ya hau zubomin Ina "Dalilin da yasa wai ya fasa aurenta kenan abinda nake ta gudu kenan Naseer duk da dukanmu munsan Zahira baa hayyacinta duk tayi wanan rashin Jin ba Amma ba Mai yarda ba halinta bane kila wanan ya zame mana bakin fenti kenan tsorona Kar ba iya ita kadai ba abin yazo ya shafi su Nadeeya An cutarmin da Yara Naseer wlh an cutarmin dasu bazan tab'a yafewa ba yanzu idan har masu neman auren Zahira zasu ringa Jin irin wadanan maganganun dak'yar Zahira ta samu Mai Aurenta" Na karashe Ina fashewa da kuka Naseer bai iya magana ba har lokacin illa sallati da yake yi idonsa ya kad'a yayi jajjur Bai hanani kukan ba illa mik'ewa da yayi Naga ya nufi d'akinsu Zahira da shigarsa su Nadeeya suka Kara fitowa Suka barshi da zahiran da zazzabi ya rufeta Nasiha ya Mata ya rarrasheta da kabiru ba mijinta bane shiyasa bai Aureta ba Insha Allahu zata samu Wanda yafi kabirun. Sai daya bata magani da kansa ya fito daga d'akin ya shige dakinsa tare da rufo kofarsa nima ban bi takansa ba na Kara duba jikin Zahira na koma dakina dan nima zazzabin naji Yana neman rufeni. A haka cikin kunya muka hada karyar an daga bikin Zahira sabida Wanda zai Aureta bashida lafiya Nadeeya ma karyar mutuwa ta ringa lankayawa kabirun. Ba Abunda baya wucewa a haka fasa auren Zahira ya wuce kamar baayi ba. Ana samun kamar wata biyu Zahira ta sameni a daki tana min zancen San cigaba da makaranta dan Nadeeya har ta kusa diplomarta dan itama Wanda ke santa so yake tana gamawa ya turo mune muke dan ki da tuni ya turo,na karanci saurayin Nadeeya yana balain santa abu daya ke sanyaya min jiki wani zubin sai naga kamar laifin Zahira zai shafesu Amma Ina adduar Allah yasa Kar a Kai ga haka a Kuma burina Zahira nakeso ta fara aure kafin Nadeeya sabida zanji wani iri ace Zahira na zaune Nadeeya ta rigata aure sosai na dage da Addu'a akan Zahira har da yarana gabadaya ban saki jiki akan kila su Umma sun kyallemu ba hakane yasa daga ni har Naseer muke addua duk abinda ma zasu yi Allah ya maida kansu ko ya kawo Mana da sauki. Hankali na maida wajen neman kudi dan idan result din Zahira ya fito mu nema Mata admission itama ta cigaba da makarantar Nadeeya Saurayinta ne ya tsaya Mata wajen cigaba da makaranta ba dan Haka ba dak'yar in zamu iya sanin Nadeeya ta tsayar mana dashi akan shi zata aura hakane yasa bamu hana shi hidimanta Mata ba dan koda Naseer ya hana shi dagewa yayi. Lokacin da result din din Zahira ya fito bai yi kyau ba daga ni har Zahira bamuji dadi ba ganin damuwar da Zahira tayi yasa na boye nawa damuwar na kwantar Mata a hankali na Dade da karantar kamar taba Zahira da akayi yasa ta rage k'ok'ari bata Kai sauran kanenn nata kokari ba ko ni nakan ci gyaranta wani zubin. Rashin cin jarrabawar ta ne yasa bata samu admission ba Naseer yaje ya biya Mata wajen da ake koyan dinki da zaman da zatayi haka zuwa wani shekarar mu Kara biya Mata waec din Daga fara fita koyan dinki Samari Suka Kara yiwa Zahira caa abin har tsoro ya ringa bani da farko zahira rashin mutunci ta ringa musu dan na lura tun abinda kabiru ya mata take ganin kamar duk mazan haka suke dak'yar nida Naseer muka shawo kanta ta fara tsayawa tana kulasu A cikin ma nemanta akwai wani Khalid da ke balain santa mahaifinsa Mai kudine sosai dan sananne ne a lokacin Kuma dan siyasa. Nacin da yake yiwa Zahira ba dare ba Rana har wajen koyon dinki yake binta yasa ta fara sauraransa duk da ba wani San shi take ba. Kyautatawa kuwa sai da na sa Zahira da dakatar dashi dan ba karamin kudi yake kashe Mata ba Ba Kuma iya Zahira ba har kanennta da waleed. Kayan abinci haka zai jiddo a kurkuka a kawo mana. Gashi da hankali koni yafi kwantamin akan kabiru zahira ke hana shi turowa dan tana ganin kamar shima zai iya cewa ya fasa aurenta idan aurensu ya kusa har lokacin bata San dalilin daya sa kabiru ya fasa aurenta ba dan data ce mu bata wasikar da kabiru ya rubuto Mata k'in bata mukayi sabida Kar hankalinta ya tashi. Khalid yana ganin Zahira tak'i bashi dama ya turo ya nemi Naseer da kansa akan Yana san auren zahira. Maganin kada ayi kar a soma Naseer bai b'oye wa Khalid duk abunda ya faru da Zahira ba na juyar Mata da Kai da akayi tayi rashin ji a shekarun baya ya nuna Masa bai San suwaye sukayi yiwa Zahira haka ba da Karfin Addu'a ta dawo daidai wanan dalili yasa har Wanda yaso Aurenta ya janye dan haka baya so sai tafiya yayi nisa shima ya janye. Ga mamakin Naseer khalid sai ce Masa yayi ai ko da halin Zahira ne ba juyar Mata da kai aka yi ba Zai iya Aurenta ko haihuwa tayi shi bai had'a San Zahira da komai ba indai aka ga bai Aureta ba toh mutuwa yayi. Ba ni ba har Naseer a ranar ba muyi bacci ba sabida tsananin murna Zahira ta dace da Mai kaunarta duk fargabar daya cikemin zuciya duk ya kau. Sati d'aya a tsakani dangin kabirun manyan masu kudi Suka kawo kudin neman aure a shiryensu suke har da akwatunan lefe dozen. Ni kaina na tsorata da irin dukiyar da suka kawo. Kanenn Zahira kukan farinciki kawai suke suna wani hanin ga Allah baiwa ne. Mahaifin Khalid daya kasance dan siyasa a lokacin chairman ne da kansa ya taka yazo gidan Sabida San da yake yiwa Khalid. Bayan babban sallah da sati biyu aka saka bikin Zahira da Khalid. Iyayen Khalid sunce basa bukatar a kawo Zahira da komai. Su zasu mata dan ba Khalid kadai ke san Zahira ba duk dangin Khalid da iyayensa balain San Zahira suke so daga Allah. Tabbacin ba abinda zai hana auren nan idan dai ba mutuwa ba yasa hankali kwance muke ta shirye shiryen mu Allah kadai yasan farinciki da nake ciki dani da Naseer da inna Amina Addua kam ba dare ba Rana haka muke yi har da azumin mu sadaka duk alhamis da jumma da kaina nake girka abinci Mai yawa na ciyar da almajirai. Ana saura sati uku auren Zahira da Khalid mahaifin Khalid ya turo wasu mutane biyu da mukullin sabon gida da takardu akan an bar Mana gidan mu tashi daga wanan gida sabida ya Mana kadan a hidimar biki. Da alama ta silar Zahira arzikinmu zai farfado. Kukan farinciki dagani har yarana da shi kansa mahaifinsu haka muka ringayi ga Karin alkawarin bayan biki za'a nema wa Naseer aikin yi tunda iyayen Khalid su keda gwammnati a lokacin Cikin farin ciki muka koma sabon gidan da muke ganin kamar duk mafarki muke dan gidane irin na masu kudi Mai gate komai akwai Dukan mu sai da mu kaje gidansu Khalid muka yi godiya har da Inna Amina. Da a wajena saninta a rayuwarmu alherine. Khalid shi ya dau nauyin komai duk da muna ta hana shi ni kaina nasan bazan iya fassalta San da Khalid yake yiwa Zahira ba ga kyau ga kudi dan Zahira ma bazata gaya masa kyau ba duk da tana mace Ya ma fita fari. Saura kwana goma bikin Zahira da Khalid da yamma ya kawowa zahira dinkunanta da ya kai Mata dinki da kansa ba iya nata ba har da nasu Nadeeya. Suna hira a waje bayan ta shigo da ledojin ta koma wajensa. Yana saman motarsa a zaune suna cikin hirar Zahira tace Masa "Wai ni ya Naga kamar baka da lafiya ne sai ramewa kake yi" Murmushi yayi yana "Nima bansan Mai ke damuna ba Zahira kwana biyun nan bana Jin dadin jikina ne ga mugayen mafarki da nake fama dashi ayita tsorata ni daddare ban gayawa kowa ba idan bake yanzu da nake gayawa ba kema dan bana iya b'oye Miki komai shiyasa na gaya miki da Alhaji da hajiya sun San maganar Nan da sai sun daga hankalinsu amma ni nasan ba komai kila haka akeji idan an kusa aure" Ya karashe da murmushi Zahira kuwa hankalinta ya balain tashi Amma ta daure bata nuna Masa halin da take ciki ba yanzu tayi girman da tasan muna da makiya masu San ganin bayanmu tasan komai akan dangin babanta. Haka sukayi hirar sama sama ta shigo gida. Ta sameni a d'akina ta zub'e akasan carpet cikin kuka ta hau bani labarin abinda khalid yace Mata ta Kara da "Umma Ina tsoron umman Abba ko Aunty Safiyya suyi wani Abu ya wajen Hana auren Nan Umma kiji fa wai ana tsorata shi daddare. Tunda ta fara min magana nake sallati. Bansan ma na mike ba sai tsintar kaina nayi a d'akin Inna Amina Zahira na biye dani. Yanda ta ganmu a firgice ya sa ta mik'e zaune dan a kwance take Kuka na fashe dashi na hau bata labarin da Zahira ta bani ina "Mama Ina tsoron sharrin bayin Allah nan Ina tsoron suyi abinda zai saka a fasa auren nan ba abinda bazasu iya yi ba dan suga bayana dana Zahira kin San irin tsanar da suka yiwa Zahira sabida kawai tana Kama dani kinsan irin wahalar da suka bata Kar yanzu da suka ga ta dace da Mai kaunarta su cutar dashi" Na karashe Ina fashewa da kuka "Haba Naeema ki kwantar da hankalinki wlh basu Isa su hana abinda Allah ya kaddara ba ki mik'awa Allah lamuranki zai isar miki insha Allahu mu dai mu dage da Addu'a shima Khalid din idan yazo ta turomin shi Zan basa adduoi ya ringa yi ba abinda zai faru insha Allahu dan Allah ku kwantar da hankalinku idan dai kuga baayi auren Nan ba toh wlh dama Khalid ba mijinta bane haba Naeema kiringa amfani da hankalinki Mana yawan tsoron Nan naki ma na iya sawa Allah ya jarrbaceki Abu kad'an sai kice zasu Miki wani Abu kenan duk abinda zai sameki sune bazaa jarrabceki ba" Naseeha ta min nida Zahira Nayi k'ok'arin boye damuwa na ne kawai Amma hankalina a tashe yake. A haka lokacin biki yayi ta matsowa daga ni har Zahira jikinmu a sanyaye yake Naseer Dana gaya masa ma cemin yayi ba abinda zai faru insha Allahu dan baya bacci tunda bikin ya matso Ana saura kwana hudu daurin Auren Khalid da Zahira khalid yazo gidanmu a firgice bai tsaya neman iso ba ya fado palon ya zub'e a gabanmu ya hau bamu hakuri duka Muna zaune a Palo "Dan Allah kuyi hakuri na fasa auren Zahira wlh sunce idan na dage zan Aureta sai sun kasheni Ido bud'e Ido rufe haka suke biyoni da wuka. zasu kasheni har da micizai yanzu haka gasu Ina kallonsu da manyan micizai wlh tunda na had'u da Zahira suke tsoratani suke min kashedi nak'i ji yanzu naga da gaske neman rayuwata suke dan har hatsari suka saka nayi yanzu bansan Zan tsira da rayuwata ba dan Allah kuyi hakuri inasan Zahira wlh Amma bana so na mutu na fasa aurenta ne dan na tsira da rayuwata" Tunda ya fara magana muke kallonsa Muna zuba sallati Zahira kuwa Ashe ta Dade da sumewa Naseer ne yayi karfin halin cewa ba komai Allah yasa hakan shi yafi alheri Khalid daya jike da gumi idonsa duk hawaye Ya kalli wajen da Zahira ke kwance kamar zai karasa wajenta kuma.ya fasa ya fita waje da Sauri yabi ya rame Kamar bashi ba Wani mugun ihu na fasa na zub'e a kasa Kamar wayanda aka Mana rasuwa Muka hau kuka Naseer ya mik'e ya shige dakinsa ya rufo kofarsa da mukulli Zahira na farfadowa ta hau ihun kuka tana "Mai nayi haka a rayuwata nake ganin irin wanan jarrabawa sai ana dab da bikina sai a fasa Umma Mai nayi musu Abba Mai nayi laifine nazo a yarku?Mai yasa laifin wasu zai shafeni ?Umma a garin yaya Kika auri Abba kinsan basa sanki gashi yanzu ni da ban musu komai ba suna ta watsa min rayuwa kenan ni bazan yi Aure ba?daga wanan sai wanan Umma ban musu komai ba suka min turen Aljannu suka saka ban karasa makaranta ba iya haka bai Isa ba suka fitar dani a hayyacina nayita abubuwa yanzu Kuma na dawo daidai sunce bazan yi aure ba"? Kuka Zahira keyi kamar zuciyarta zai fita A fasa auren Khalid da Zahira nayi jinyar fiye da wata biyu a asibiti Allah ne yayi bazan yi ciwon B'arin jiki ba. A takaice a haka shima Khalid ya tafi. Yata aka cigaba da zuwa neman aurenta ana dab dayi sai a fasa bayan Khalid mutane biyu Suma. Daga haka.zahira tace ta cire rai da aure Ta rokeni.mu bar mai San Nadeeya ya turo neman aurenta Kar mu Hana shi sabida ita. Tunda kamar ya matsu haka kuwa akayi saurayin Nadeeya Umar ya turo manyansa neman auren Nadeeya aka saka Rana wata uku Calabar.... *NAGA TA KAINA* *NA SADNAF*🌸🌸 ®️ *_PURE MOMENT OF LIFE WRITERS_* _{We Don't just entertain nd educate we also touch the heat of readers P.M.L}💪🏻_ *Free Novel* Page 63 Safiyya Fadar tashin hankali da damuwar da take ciki b'ata bakine dan ko baccin kirki bata iya yi Sabida masifar da yaranta ke ciki. Asmau yanzu duk daurin da zata Mata sai ta kunce ta fito daga d'akin ta fita waje. A haukacen ma haka maza ke nemanta idan ta daureta ta karfi da yaji haka maza ke biyota gidan ba kunya ba tsoron Allah ga tsokanarta da sukeyi da uwar mahaukaciya. Abinda ya Kara daga Mata hankali bai wuce Bashir daya dawo gidan da Zama gabadaya ba ya Kori Asmau daga daki dayan data kulleta yayi zamansa a d'akin da macen da itama kana ganinta kasan Yar bariki ce ta ma girmi Bashir nesa ba kusa ba amma haka ta biyo bashir cikin gidan take zuba mulki San ranta Safiyya bata isa tayi magana ba. Har wajen Oban taje akan a Mata maganin budurwar Bashir din da aka cewa hajiyayye Ashe itama hajiyayyen tana zuwa wajen Oban ya Kuma Santa karya yayi wa Safiyya akan idan yayi aiki akan hajiyayye zata iya hauakcewa akan dole ta hakura. dan aikatau din da take zuwa yi ta samo abincin da zata saka wa cikinta da hauwa da tana Nan Kamar d'abba Kamar mutum tana samowa Bashir zai nada Mata duka ko shi ko budurwarsa hajiyayye. Safiyya takwararta itama data gama barikin tsarabar ciki tayo Mata ta dawo gidan ta zauna. Ga Yar Asmau Nana da Rabia yarta. Taurin zuciya yasa Zuciyata bata buga ba. Bashir haka zaiyi sata a biyoshi har gida Ana nemansa hajiyayye budurwarsa kayan mayye take siyarwa wani zubin aka ma su biyun wani zubin su tsere a kamata Duk jikinta tabon dukan ne na Bashir takan tsine Masa ta Kara tsine Masa har ta ringa ayyanawa da irin rayuwar Nan da take da yaran da basu Mata albarka ba gwara duk mutuwa sukayi. Bakin ciki daya Mata yawa ta nufi wajen Oban dan ya binciko mata halin da su Naeema suke ciki da take jinsu a kahon zuciyarta ba yanda zatayi tana Shan gararin rayuwa su Kuma su Sha iska Mai dadi. Gani take duk Wanan masifar Naeema da Naseer su Suka jawo Mata ta Kuma yarda da zancen Oban da ta fara ganin kamar bai iya aiki ba daya ce Naeema itama ba zaune take ba tana zuwa wajen Mallamai suna Mata aiki shiyasa duk abinda suka Mata yake dawowa kanta. Amfanin da Oban yake dan Mata yasa bata bar zuwa wajensa ba amma duk lokacin data samu kudi dole ta nemi wani bokan da zai mata mugun aiki ko ba Akan Naeema ba yarta Asmau ta samu Lafiya da hauwa da shi kansa Bashir din. Bata da burin daya wuce su samu lafiya. Jikewa tayi da gumi a lokacin da Oban ya nuna Mata wani yazo auren Zahira rashin Jin da tayi ne yasa aka fasa auren Yanzu haka ga wani Dan shahararen Mai kudin ya fito neman aurenta har an kusa ma auren an mallakawa Naseer gida. Oban ya Kara da "Yayanki zai dawo da arzikinsa har yafi na da ta silar Wanda zai auri yarinya Nan Dan aiki Mai kyau suke so su bashi. Matarsa Kuma zatayi kudi itama har ta fita waje Ba iya Kuma Zahira ba duka yaranta ba Mai auren karamin mutum" Kasa magana tayi tsabar kad'uwar da tayi da tashin hankali Taya tana nan na abinci na neman gagararta Naeema da Naseer su Kuma suna neman zama masu kudi? Taya yaranta daga mahaukaciya sai Mai bin maza da kungurmin barawo yaranta data ci mugun buri akansu ba Wanda ya mata albarka Amma yaran Naeema gasu Mai kudi ke nemansu ta silar Zahira ma har ana neman mallakawa Naseer gida Ita tana nan a wulakance ta Zama kamar zararriya Auren Zahira na nufin samun kwanciyar hankali Naeema da farincikinta Ita Tana Nan tana Shan duka awajen bashir yaranta mata ba ma na kwarai ballantana ta sa Rai suma zasuyi aure inaaaa Tace da k'arfi ta matsa kusa da Oban tana ruk'o hannayennsa tana "Yarinya Nan bana so tayi aure yanda yarana Suka wulakanta a gabana haka nake so yarinya Nan ta wulakanta a gaban Naeema bana San Naeema ta samu kwanciyar hankali daidai da second daya inaso yarta Zahira ta dauwwama a gabanta ba aure yanda naga alamar yarana haka zasu dawwama a gabana. Inaso kayimin aikin da zaa ringa tsorata shi a nemi ma ransa har sai ya janye daga neman aurenta Duk Wanda zai nemi Aurenta a ringa tsorata shi ko sai yaje wajen Zahira dab da aurensu ya ga Zahira na bashi tsoro har sai ya janye Ba iya Zahira ba duka yaran naeema haka nakeso su dawwama a gabanta taji abinda nakeji a Zuciyata Naseer a Kara saka Masa tsanar Waleed idan Zan samu ne Naseer nakeso ya Zama ajalin Waleed. Duk wani Abu da zasu samu ta silar yaransu ya lalace ko gidan ma da kace Ana shirin basu idan an basu Kar yayi albarka har sai sun koma wanan karamin gidan. Inaso Naeema ta Shiga ukunta ta lalace wanan shegiyar tsohuwar dake taimaka mata inaso!!! "Kullll Oban yace da Sauri Yana Karki soma kiramin tsohuwar nan dan na gwada aiki akanta komai.nawa lalacewa zaiyi nadai San Tana gidan ban Isa na Mata komai ba. Duk abinda kikace ayi yafi komai sauki zaayi Amma fa sai kin kawo kudin aiki dan iya jikinki bazai iya biyana ba" "Duk Inda kudi suka Shiga Zan Nemo Oban kwanciyar hankalinta ne dai banaso" Safiyya sai data had'a da satarwa hajiyayye kudinta data Shiga bandaki dan.tayi wanka ta kaiwa Oban ya Mata aikin. Kullum tana hanyar zuwa dan taga halin da suke ciki ahaka har Khalid ya fasa auren Zahira da ranar zuciyarta ya kasance fess tana Jin inama Safiyya batayi cikin shege ba da tayi aiki akan khalid yazo ya aureta. Duk halin da su Naeema ke ciki tana sane tana kuma da labari ta wajen Oban hakane yasa ta Kara dagewa wajen ganin Zahira batayi aure ba har dasu Nadeeya. Hajara Bata tab'a sanin haka ake samun kudi idan ana bara ba sai data fara daga fara baranta zuwa yanzu har ta Tara kudade masu yawa da Bata tab'a mafarkin samunsa ba. Ko kad'an bata yi tunanin kama haya ba ta cigaba da zama a rumfar mahaukatan da ta Riga da ta saje dasu Ciwon kafar da take fama dashi daya dan kumbura yasa mutane ke Kara tausayinta tana fita bara zasu hau Tara Mata kudi har da masu bata kayan sawa. Sai data tabbatar da ta Tara kudin da yawa daddare ta hau shiga mutane tana neman Wanda zai mata aiki akan Naeeema da Safiyya da take ganin sune manyan makiyanta a duniya. Tsohuwar unguwar da suka zauna ta nufa ta Kara da nausawa daji ko zata samu ganin shugabarsu ta matsafa da takejin da tana Nan da duk matsalarta ta Kau Sai dai ta karaci bullayinta a dajin bata sameta ba a wajen fitowa ta hadu da dattijuwa da zasuyi saani da ita ta kada baki ta tambayeta ko tasan Wanda zai iya taimaka Mata Wala mallami ko boka Dattijuwa kuwa cikin murmushi tace itama Nan tayi su tafi Silar haduwar Hajara da kawarta kenan Mai irin halinta da ita Kuma kishiya take San taga bayanta. Bokan shima bayarabe ne da suka Samu dan sunfi yawa acan garin Duk kudaden baranta ta zub'ewa bokan. Ta fara da "Inaso naga bayan matar Dana ta wahalar dani shekara da shekaru Muna Abu daya da ita ban taba cin Galaba a kanta ba sai da tayi ta tsallake duk abinda na mata iya haka bai isheta ba sai data rabani da d'ana har a cell yarinya Nan ta kullemu muka kwana inaso a tura Mata cutar da zaiyi ajalinta tayi mumunan rashin lafiya da zaa rasa maganinsa har sai ta mutu. Dana Kuma ayi.min aiki da arzikinsa zai dawo ya sake aure na Mori arzikinsa. Safiyya yata Kuma Ina so a watsa rayuwarta idan har ni Dana tsugunna na haifeta zata kora har tayi dambe dani inaso yaranta su Zama ajalinta ta rasa kwanciya hankalinta ta ringa Neman mutuwa ma mutuwa tak'i daukarta. Wani mugun dariya ya kece dashi yace mata "An gama amma duk abinda ya biyo baya kiyi kuka da kanki" Hajara kada Kai kawai take cikin farinciki a duk abinda tace ayi Mata idan har ta samu cikar burinta akan Naeema gani take burinta ya gama cika. Bata damu da yanda bokan ke ta nanata Mata duk abinda ya biyo baya tayi kuka da kanta ba. Cikin farinciki ta baro wajen bokan tazo ta cigaba da baranta dan bayan kwana biyu bokan yace ta koma Wanan kenan (A labarin naeema wlh Tallahi na rage abubuwa da yawa ba sai dai na ringa rantse muku ba amma dai na kusa zuwa Inda muka tsaya a labarin) Naeema Tausayin yata nake sosai dan ta cire rai daga auren duk Wanda yazo ma ta daina bashi fuska ballantana ta saurareshi Aikin koyan dinkinta kawai ta saka agaba da Kuma shirye shiryen bikin Nadeeya da duk ba wani dokinsa muke muna wani shiri ba dan gani nake ba iya Zahira aka yiwa mugunta ba kila har dasu Nadeeya. Banida k'arfi banida kowa Amma inada Allah duk abinda sukeyi min Allah Yana kallonsu nasan zai kawo karshen komai wuyanta nayi hakuri. Tashe tashen hankulan dana gani a rayuwata yasa yanzu na Riga da na fara sabo da duk wani jarrabta da Zan gani a ruyuwata ba abinda ya Kai lafiya dadi a wajena. Idan dai har bazasu cutarmin da Yara ta hanyar tab'a min lafiyarsu ba zasu barmu a haka inaga alhamdulillah banga abinda zai daga min hankali ba tunda na Riga da nasan Aure da mutuwa lokaci ne idan har lokacin auren Zahira yayi ni nasan ko mai zasuyi basu Isa su hana ba duk masu zuwa neman aurenta ba mijinta a cikinsu. Ban saka damuwar komai a Raina ba na Kara fawallawa Allah komai na cigaba da kai kukana gareshi. Naseer Zan iya cewa shi ya saka damuwa a Ransa sosai yanda hawan jininsa ke motsa Masa akai akai sabida damuwa yasa nida inna Amina muka Masa nasiha Dak'yar shima ya cire damuwa ya cigaba da gayawa Allah Alhamdulillah yarana sanin muna da masu San ganin bayanmu yasa Suma Basu Zauna haka ba Suka dukufa yiwa kansu addua kariya duk a cikin yarana Nadeeya da Humaira Zan iya cewa suna da Wanan k'ok'arin sosai wajen raba dare suna kaiwa Allah kukansu balle Nadeeya data ga Aurenta na matsowa sosai take adduar Allah yasa Kar wani Abu ya Hana auren dan Naga itama jikinta a sanyaye yake. Yanda muka amshi kaddarar mu da hannu biyu yasa komai ya zo Mana cikin sauki cikin rufin asiri muka cigaba da shirye shiryen auren Nadeeya Dan Abubuwan da muka siyawa Zahira muka yanke Kara Mata akai dan Umar Mai neman Nadeeya na Dan sakar mata kudi dashi muke samu mu rage wasu Abubuwan Bana Jin dadin yanda Zahira ke kin saurararen manemnta da duk da fasa Aurenta da ake tururuwar zuwa nemanta suke Kuma so suke mata ba na Wasa ba sai dai da mun Mata maganar ta kulasu sai tace mana ko ta kulasu ma a karshe guduwa zasuyi bata ga amfanin kula sun ba ita fa kila bata da rabon auren ne a duniya dan haka ta hakura. Sai dai a mane manta akwai wani Abubakar da babansa ya kasance babban mallami shima yayi gadon mallinta a wajensa ga ilimi ga kudi. Ba karamin naci yake yiwa Zahira dake wulakanta shi ba dan ko kad'an bata saurarenshi ballantana har ya Shiga zuciyarta ta sa rai da aurensa a karshe Kuma yazo ya fasa auren Har tausayi yake bamu yanda yake.sintirin zuwa wajenta tana kin bashi fuska Duk Kuma maganar da zamu Mata akan ta kulashi bazata kulashi ba idan an matsa mata kuwa sai ta saka kuka. A karshe sai Inna Amina ce ta samu dak'yar dak'yar ta fara kula Abubakar duk da ta Masa gargadin duk ranar da ya mata zancen aure sai sun rabu. A haka ya cigaba da zuwa sanin da aure yake Santa yasa daya tabbatar ta tafi wajen koyan dinki yazo ya tarar da Naseer a gida ya Gaya masa bukatarsa na san auren Zahira. Naseer bai b'oye Masa komai ba ya bashi labarin duk Abubuwan dake faruwa game da zahiran da yanda aka zo neman aurenta sai ana dab da yi a fasa. Abubakar murmushi yayi Yana Kar Naseer ya damu daga bashi labarin da yayi yasan da akwai aikin makiya a fasa auren zahiran Amma indai sihiri ne ko wani Abu da yardar Allah bazai yi tasiri akansa ba sai dai idan Allah ya rubuta Dama zahiran ba matarsa bace Shi dai a bashi dama ya turo manyansa dan aka biyewa Zahira cire rai zata yi daga auren sabida duk abinda ya faru da ita a baya Badan duk mun yarda wani Abu bazai biyo baya ba aka bawa Abubakar dama ya turo manyansa. Da.kudin aure Inda ya nemi a hada dana Nadeeya Amma ayi a sirrince Kar a nuna Dana Zahira zaayi sabida kar ma makiyan mu suji labari. Addua mukayi akan Allah ya tabbatar muka cigaba da Addu'a muna Shirin auren Zahira da Nadeeya Dan Ni har cewa Naseer nayi dama kawai a daura auren zahiran da Abubakar Kar a wani ja lokaci dan gani nake lokacin da ake ja ma yasa suna samun Galaba akanmu Amma Naseer yace Kar na damu mubi komai a hankali. Allah yasan da Auren Zahira da Abubakar zai tabbata da nafi kowa Jin dadi da gani zanyi na gama samun cikar burina. Ana saura sati uku bikinsu aka kawo leffen Nadeeya. Abubakar kuwa mu muka hana ya kawo na zahira sabida yanzu hankalin ta a kwance yake gani take Umar wahalar da kansa kawai yake aure tsakaninsu bazai yiwu ba duk da a ranta tana San sa Amma haka zata hakura dashi yanzu tana sanin da ita zaa hada auren zata tashi hankalinta. Sosai ta zage suke shirye shiryen auren Nadeeya ta d'au ragamar komai Kamar wata kawarta Ni Kuma yanda ta daukaki auren Nadeeya tausayi take bani. Har azumi.na tsiri yi akan Allah ya cikamin burina Naga auren Zahira. Ana saura kwana goma Sha biyu bikin Nadeeya da Zahira Daddare karfe daya da rabi Kamar yanda na Saba tashi na rayya Daren na mike na Shiga band'aki na daura alwala Naseer Ina jiyo karatunsu daga d'akinsa dan Yanzu bamu fiye kwana waje daya dashi ba sai dai idan ta kama ko Dan idon yaranmu da muke ganin sun kawo girma da Kuma wayonsu. Na fito kenan daga bandaki jiri ya d'ebbeni duhu ya mamaye min Ido ban Kara sanin Inda kaina yake ba. Sai dana yi.kwana uku bansan Inda nake ba kafin na iya bud'e idona nagani a gadon asibiti na Sha Karin ruwa. Azabar da nakeji a jikina da kaina danaji Kamar guduma ake bugamin yasa na runtse idona na hau girgiza Kai Ina sallati Wlh duk yanda Zan kwatanta abinda nakeji a jikina makaranci da ke da kike rubutawan bazaku gane ba Azabar Dana Sha a cikin Minal da kumburin da nayi duk nafila ne akan abinda nake ji Ina Jin yarana da suka zagayeni har da Naseer suna min sannu Inna Amina itama Ina Jin tana min tofi Ban iya bud'e idona ba sabida dai azabar da nake Sha Kirjina kamar an doramin Abu Mai balain nauyi. Tunda ga lokacin ban Kara iya bud'e idona ba Amma duk abinda ake Ina ji. Azabar da nakeji kawai a jikina yasa na fara kuka Ina rokon Allah ya dau raina dan a ganina gwara mutuwa da Wanan azabar da nake Sha Ina Jin yanda yarana da Naseer ke jigilar yawo dani a asibiti daga wanan asibitin zuwa wancan sai kashe kudi suke. Amma duk a banza likitocin sun kasa gano Mai ke damuna. Karshe sai wani private aka kaini da suka rubuta ayimin scan din duk jikina agano Mai ke damuna Daruruwa kudin da suka caza yasa dolen Naseer ya siyar da gidan da iyayen Khalid suka mallaka Mana ya tashi Yan hayan daya zuba a gidanmu Suka koma. Duk kudin gidan a asibiti ya Kare a sanadin rashin lafiyar da nake aka daga bikin Nadeeya da Zahira Naseer shima gadone kawai ba a bashi ba sabida tashin hankali Duk ba Wanda ya kawo ciwon nawa bana asibiti bane duk Inda aka ji kwararrun likitoci sai a tura mu can A haka nayi wata biyu a wahalce kafin saurayin Zahira ya bawa Naseer shawara akan a mayar dani gida cutar tawa bata asibiti bace. Sai a lokacin Inna Amina da Naseer da Kamar aka mantar dasu muna da makiya suka dawo hankalinsu aka mayar dani gida. Aka dukafa da min addua Naseer Inna Amina har da sirikina Abubakar da shima bazan tab'a manta shi da mahaifinsa ba Mahaifinsa Mallam isah ba karamin ilimi ne dashi ba. Abubakar na samunsa da zancen rashin lafiya ta yace a kawoni. Haka aka daukeni akayi gidansu Abubakar dani. Cikin Ikon Allah kwana bakwai da kaini na fara dawowa hayyacina har na bude idona nasan Inda nake. Kwana mahaifin Abubakar keyi Yana min addua A gidan Naseer da Waleed suke kwana Da asusuba yarana zasu dura gidan gabadaya. Cikin sati biyu na warke sumul kamar bani ba dan nakan iya tashi na zauna duk azabar nan danake ji a jikina na daina ji sai dai rashin kwarin jiki. A haka mahaifin Abubakar ya bamu ruwan adduoi a ranar da zamu bar gidan Ya zaunar da Naseer Dani yayi gyaran murya yana "Rashin lafiyar Nan turensa aka mata a gaskiya Kuna da makiya da suka shirya ganin bayanku Mata biyune suke ta k'ok'arin ganin sun tarwatsa rayuwarku adduar da nayi Naga kamar matan nada kusanci da kai duk auren yarku da ake sawa Ana fasawa duk sune yanzu Haka ma Allah ya nuna min duk wani shiri da suka Kara yi akanku nayi addua ya warware da ikon Allah Ina Baku shawara ku Kara dagewa da Addu'a yarku zahira sun balain tsanarta zasu iya komai dan suga bayanta dan haka insha Allahu Zan taimaka Mata. Mallam Naseer idan bazaka damu ba inaso a daura auren Zahira Yarka da Dana Abubakar a yau. Dagani har Naseer kasa magana muka yi duk maganar sa ba abinda ya bamu mamaki mun Riga da mun San su Umma ke San ganin bayanmu Maganar auren Zahira daya ce a daura a yau shi ya daskarar damu har naji na fara Jin kwarin jikina. Ban.yarda ba mafarki nake ba sai dana.ga Naseer ya shigo d'akin da aka ajiyeni da goro da alewar daurin Auren Zahira da sadakinta a hannu Dubu hamsin Hawayen farinciki ne.ya hau zubomin. Ashe dai yata tana da rabon aure daurin Auren Zahira tamkar Kara samun lafiya yayi Godiya sosai muka ringa yiwa mahaifin Abubakar bakin Abubakar a washe dan murna. A haka muka nufi gida cikin farinciki tun a hanya na fara sadaka a Raina Ina Godewa Allah. Umarnin mahaifin Abubakar nabi Dana Isa gida na fito da duka kayana daya ce Kar na sake sawa Kar Kuma na bawa wani dan zai iya cutar dashi. Dan kayan nawa ma an yi asiiri a ciki. Naseer da kansa ya Kona kayana. Yarana sai.murna suke na warke. Bamu fadawa Zahira an daura Aurenta ba. Sati biyu da samun sauki na aka cigaba da shirye shiryen auren Nadeeya Abubakar har akwatin kayan sawa ya kawo min Ranar 15 ga watan biyar shekara ta 2010 aka daurawa Nadeeya aure Aka hada da bikin Zahira da itama bata sani ba sai a satin auren Nadeeya kukan farinciki kawai ta ringayi tana a Ashe tana da rabon aure. Cikin rufin asiri akayi shagalin bikin yarana suka tare a gidajen mazajensu alhamdulillah Calabar A ranar da mahaifin Abubakar ya karya asirin da Hajara tayi daddare Hajara na kwance tana bacci. Taji kamar Abu ya ruguzo Mata a jiki Azabar data ji.yasa ta bud'e idonta. Kasusuwan jikinta Suka ringa kaskas Kamar Ana karyawa A firgice ta mik'e zaune data ga kashin jikinta na murdawa shi kadai kafin ta ankara sai gashi ta karkace gabad'ayanta gabanta ya koma gefe idan kana kallonta a madadin a tsaye straight sai ta karkace Fuskarta ta koma gefe Ihu ta saka da iya karfinta mahaukatan dake zagaye da ita Suka sakata gaba suna kallonta Masu wucewa Kuma idan Suka ganta sai su tsorata dan Basu tab'a ganin mutumin daya karkace haka ba. Wanan shine farin Shigar Hajara wahala Mai tsanani Dan mutane tsoron ta Suka koma yi ko tayi baran bata samu. (Har yanzu wlh Tallahi baiwar Allah Nan a karkace take a fadar Naeema ko accident mutum yayi Bata Jin zaiyi karkacewar da tayi Allah ya tsare Mana imaninmu na dai kusa gamawa Dan Safiyya da Hajara na rayye Basu mutu ba ba kuma su tuba ba yanda Naeema ta bani labari haka Zan Baku sai dai Kuma idan wani Abu ya biyo baya nayi alkwarin rubutawa insha Allahu) *TALLA* _Mai talla shike da riba_ *Mg's herbal whitening black soap* Idan akaji gangami to tabbas akwai labari. Ina Amare, Uwargida kai har ma da 'Yan mata masu tasowa, hakika mata da kwalliya aka sanmu, shin kuna so ku kara kyau fatarku tayi luwai luwai ki zama 'yan caras kamar madubi? To ga dama ta samu, mun zo muku da Sabulun Mg's a kan farashi mai sauki, duk wacce ba tayi anfani da sabulun nan ba an barta a baya, domin duk masu korafin cewar sabulan gyaran jiki basa Aiki to ina so ku cire Mg's a ciki domin shi kankat ne wajen mai da tsohuwa yarinya. Ko yaushe Mg's sai sambarka dan haka ku hanzarta ku samu naku, siyan na gari maida kudi gida, Mg's sabulu ne daya tamkar da dubu. Masu bukatar fatarku tayi haske to Sabulun Mg's herbal whitening black soap ya waratar daku, jikin ku zai yi kyau da sheki da kamshi. Kayanmu baya bleaching organic ne, zai fiddo muku da ainahin natural beauty dinki ne, dan haka duk wanda ya gwada shi ne zai bada labari. Amare da sauran Mata kuyi kokari ku mallaki Mg's domin ba ruwanku da zuwa a dirje muku jiki zaku ga yanda fatarku zata dinga walwali. Ina masu. Pimples Tabo(spot) Sunburn Nankanwa Dama duk wani matsalar fata kuyi kokari ku nemi soap din Mg's, insha Allah before 2weeks zai share muku hawaye, ku zama abun kwatance. You have to try it and see for yourself 100% tested and trusted. Soap price: 3k Location: Kaduna Muna turawa ko ina, amma delivery is not free Mai so kindly WhatsApp message to 08062991549 or Call 08064532391 _Note: Yan sauran state Babu in da zaku sami mg's herbal whitening black soap sai a number din nan, now Akwaisu available_yan kd akwai shops da zakusami sabulu ynx kuyi mgn 08062991549 abaku address Masusan suzama distributors a other state uw kindly drop a message via 08062991549🤭 we can't wait to be a part of your beauty story😍 *NAGA TA KAINA* *NA SADNAF*🌸🌸 ®️ *_PURE MOMENT OF LIFE WRITERS_* _{We Don't just entertain nd educate we also touch the heat of readers P.M.L}💪🏻_ *Free Novel* Page 64 Duk masifar da ta Shiga da b'acin rai bata taba tsintar kanta a farinciki kamar lokacin da Oban ya haska Mata rashin lafiya da Naeema ke fama dashi ba A karyar Oban ce mata yayi shi yayi aiki akan Naeeema tayi ta rashin lafiyar har ta mutu. Kamar wacce aka yiwa kyautar hajji da umara haka Safiyya ta ringa ji. Da kuwa Naseer ya siyar da gidansa akan rashin lafiya Kamar ta taka rawa Bata da burin daya wuce har daya gidan su siyar su koma ba suda gidan kansu kamar yanda itama bata da gidan. Idonta na Kan komai dake wakana dasu Naeema har irin wahalar da ake sha akanta. Abubakar data ga Yana San Zahira Yana Kuma taimaka.musu yasa ta roki Oban akan ayi ta tsorata shi idan har yak'i janyewa Oban ya kashe shi Haka kuwa akayi Oban ya hau tura Aljannu dan su tsorata Abubakar sai dai duk tsorata shi da suke ko gezau Abubakar baya yi daya tashi ma Kona Aljannun ya ringa yi yayi wa Oban barna sosai ta hanyar lalata Masa wasu kayan aikin nasa da Karfin Addu'a. Duk yanda Suka so yin aiki akansa hakan baiyi tasiri ba har aka daura auren Zahira da Abubakar da yasa Safiyya tayi karamin hauka tana sumbatun tsinewa Naeema da ita rayuwar yaranta gashi a watse Amma Zahira tayi aure. Dan Safiyya itama ta santalo Mata jika shegiya ga budurwar Bashir itama d'auke da ciki. Duk an cike mata gida da shegun yaya Gabadaya rayuwarta ta wulakance ta lalace ita da yaranta Amma gashi zahira ta samu tayi aure kenan ma Naeema taci riba akanta A hauakacen ta sa Oban ya Mata aiki akan Umar saurayin Nadeeya akan ya fasa auren Nadeeya sai dai tana ji tana gani aka daura aurensu. Bakin ciki yasa ta roki Oban akan a kashe mata Umar dan da alamu Abubakar yafi karfinsu dan duk abinda suka ringa tura Masa baya tasiri akansa Nan kuwa basu San mahaifinsa ba karamin aiki yayi akansa ba ba iya shi ba har su Naeema. Ba yanda ba suyi dan suga sun tab'a Zahira ko Nadeeya Amma Allah bai basu iko ba Hakane yasa Safiyya ta so maida Nadeeya bazawara a washegarin da Nadeeya ta tare a gidan ta. Wani Abu Oban ya bata Akan taje ta binne a tsakiyar titi kafin ta binne ta Kira sunan Umar sau uku Indai Umar a ranar ya hau mota ya hau kan kwalta sai yayi mumunan hatsari. Cikin mugunta ta binne kamar yanda ya umarceta Ta koma gida tana murna bakin cikin da Naeema zatayi har Naseer idan suka ga kwana daya da tariyar Nadeeya mijinta ya rasu Tana komawa gida ta iske Bashir a tsakar gida a zaune ya balain nutsuwa kamar bashi ba. Sannu da zuwan da ya mata yasa ta daskare waje daya tana murza idonta dan ta gaskata Bashir danta dai take gani ba wani ba Murmushi ya Mata Yana ta daina mamaki shine sati biyu da yayi baya nan Allah ya shiryeshi ya Kuma Gane duk abinda yakeyi ba daidai bane daga Yau ya daina. Safiyya tsabar farinciki kuka ta saka tana shiwa Bashir albarka Fadar farinciki da take ciki ma Bata bakine Ashe Bashir dinta zai tab'a nutsuwa haka har ya dawo hayyacinsa A takaice hirane ya barke tsakanin Safiyya da bashir Safiyya ta ringa ji kamar ta goyashi dan farinciki tuni ta hau tsare tsare a Zuciyarta. Murna da take ciki yasa tace Masa Bari ta Shiga daki ta yo musu cafene Bashir kafewa yayi ta bar kudin shi zai yo Mata cefanen. Safiyya da kallo ta bishi har ya bar gidan Kaunar Bashir na balain mamaye Mata zuciya kaf yaranta ba Wanda takeji a ranta kamar Bashir. Fitarsa da minti goma taji hayaniya a waje. Kafin ta gane Mai ke faruwa har mutane sun duru cikin gidanta suna zabga sallati Hankalinta a balain tashe ta fara tambayar me ke faruwa Sai dai baa iya bata amsa ba in Banda wani daya hau Jan hannunta. Kamar sokuwa haka tabi bayansa gabanta na fad'uwa. Mutanen da suka cika titin da ta binne abinda Oban ya bata yasa gabanta tsananta fad'uwa dak'yar ta suka bata hanya Bashir ne kwance cikin jini male male Idonsa a bud'e Yana kallon sama kana ganinsa kasan rai yayi halinsa. Wani razanannnen ihu ta kwalla ta zub'e a kasa. Bata Kara sanin Inda kanta yake ba har aka yiwa bashir sutura aka binne shi Ranar sadakar uku ta farfado Ta na ihun Kiran sunan Bashir ta fara k'ok'arin yin waje Sai sumbatu take tana ba Bashir tace ya mutu ba mijin Nadeeya tace Oban ya kashe Mata. Tab'in hankali da ta dan samu yasa ta hau tona wa kanta asiri tana Naeema ta cuceta Oban ya cuceta. Dak'yar aka Mata alluran bacci dan fusgewa take zata fita waje. A takaice sanadin dan samun tab'in hankali Safiyya kenan Dan har gobe bata cika hankali ba ita kadai haka za tayi ta zuba surutu tana fadar Abubuwan da tayi idan haukan ya motsa mata . Oban da take shuka tsiyar dashi data koma wajensa a kwance ta sameshi ya kumbura yayi himmm Yana zabga wani irin doyi Ita kanta Safiyya baka Isa tsayawa kusa da ita ba sabida warin da takeyi Wata daya da rasuwar Bashir Tana zaune ta zubawa waje daya Ido Hankalinta ya dan dawo jikinta yaranta duk take bi da kallo da jikokinta. Ita bata ga ma ribar da taci a rayuwarta ba Bashir danta namiji tilo Daya fi soyuwa a gareta ya tafi ya barta a lokacin da hankali ya fara zuwar Masa ya Shiryu Yaranta biyu daga mahaukaciya sai Mai bin maza Ba Wanda ya amfaneta da wani Abu. Sai Rabia da take wahalar da ita da bata da bambanci da wata dabbar tana girma tana Kara zama abin tsoro Tunani da abubuwa dake rayya Mata munanan abubuwa yasa ta d'auko wuka Ta nufi d'akin da Rabia ke kwance tana Isa wajenta ta daga wuk'ar da zumar soka mata dan ji tayi gwara.kawai.ta kashe Rabia ta huta Tana daga wuk'ar taji kamar anyi cilli da ita. Wani iirn gugguwa Mai k'arfi ya zagayeta Ta hau wani irin jijjiga tana Kara duk Aljannu dake azabtar da Rabia Suka bar jikin Rabia suka Shiga jikin Safiyya Wani irin canza Mata hallitar fuskata sukayi fuskarta ta dawo bakikirrin wuyanta yayi wani irin kumburewa idonta yayo waje gabad'aya Ihu kawai take Tana birgima. Har gobe haka Safiyya take fama da kumburarren wuya da Ido a warwaje takan dan tab'a hauka wani zubin. Daga ita har Hajara Basu nemi yafiyar.naeema ba suna Nan Kuma da tsanar Naeema dama ne kawai Basu samu ba Safiyya k'arfi da yaji ta koma yin Abun mahaukatan aka koreta daga gidan hayan Hajiyayye budurwar Bashir kuwa Yana rasuwa ta kama gabanta Asmau kuwa tana nan a haukacenta Safiyya data haihu guduwa tayi.ta bar gidan Rabia kuwa aljnnun suna barin jikinta ta dawo daidai. Ita kadai ce a yaran Safiyya bayan Aljannun sun bar jikinta wani Abu Bai sameta ba sai ita ke kula da yaran Safiyya da Asmau. Naeema Godiya kawai nake yiwa Allah daya bamu ikon ganin auren Zahira da Nadeeya da nake Jin tunda na auri Naseer ba Abunda ya tab'a faranta min rai sama da Aurensu. Yarana suna cikin rufin asiri a gidajen mazajensu. Yara na Kuma dake gabana suna cigaba da zuwa makaranta ina kula da tarbiyyarsu Naseer na cigaba da sana'oin hannunsa Wanda dashi asirinmu ke rufe. Ranar da bazan taba mantawa ba watansu Zahira hudu da aure daga amai da gudawa na kwana uku Inna Amina ta amsa Kiran Mahallici Ko lokacin Dana rasa iyayena banyi kukan da nayi da rasuwa Inna Amina ba Ba iya ni ba har Naseer da sauran yarana Allah ya jikanta ya Kai haske kabarinta sosai na ringa ji Kamar wani barin jikina ce ta tafi ta barni. Sanin watarana dole ko muna so ko ba ma so mu ma zamu amsa Kiran Mahallici dan mutuwa ta zama Dole akan kowa Haka muka bi Inna Amina da Addu'a dacewa da rahamar Allah Mu ka cigaba da fuskantar rayuwa yau da Dadi gobe akasin haka har Allah ya sauki Zahira lafiya ta haifi yarta mace Mai Kama da ita Inda Abubakar yamin Kara ya saka Mata sunana ake kiranta da iman Iman nada wata uku a duniya Abubakar da mahaifinsa da su kaje gaisuwa garinsu rano sukayi mummunan hatsari suka mutu A shekara 2012/10/10 wanan Rana Yana cikin ranakun da bazamu taba mantawa ba anyi Mana rasuwar da ya dakemu da har yata Zahira sai da muka dage Mata da Addu'a kafin ta iya dawowa daidai Bazan manta Abubakar da mahaifinsa ba har gobe Muna adduar Allah ya sadasu da rahamar Allah yasa Aljanna ce makomarsu Zahira na fita daga takaba naso ta cigaba da zuwa makaranta ta nuna min bata son komawa makaranta tafi so ta cigaba da sanaarta ta dinki har yanzu Zahira tana nan tana dinkinta Yarana dukansu rayuwar da Allah ya tsara musu shi suke dan Nadeeya yanzu haka yaranta uku Minal itama tayi Aurenta da yaranta biyu. Sai Humaira yanzu da aka sawa Rana Waleed toh sai dai nace Alhamdulillah Yana Nan da taurin Kai Bai koma min kamar Waleed din Dana sani ba abinda aka masa Kan motsa Masa wani zubin ba Kuma sa shiri sosai da mahaifinsa. Naseer ko tuna Umma da Safiyya baya so yayi. Shekara 2016 wani makocinmu Sagiru da muka zauna a garin calabar yazo garin Kano neman Naseer da kyar da.kwatance ya gane gidanmu. Sai da ya huta yake fadawa Naseer dalilin zuwansa akan Umma yazo shima bai fiye zama ba sabida tafiye tafiyen da yake Yi Sai kwanaki ya dawo ya Shiga kasuwa yaji an rik'e Masa Riga da kyar dak'yar ya Gane Umma Inda Umma ta fashe Masa da kuka dan ta Gane shi tace ya taimaka Mata ta Kira mishi Naseer yunwa zai kasheta mutane gudunta suke dak'yar take samun na abinci A labarin yake fadawa Naseer kila umma hatsari tayi sabida yanda kamaninta Suka canja dayake a can kowa yasan waccece Umma daidaiku ne basu san halinta ba naseeha sagiru ya hau yiwa Naseer Akan Bai Dace ya wulakanta Umma ba ko Mai tayi Masa kuwa yayi hakuri yanzu tana bukatar taimakonsa Naseer amsa shi kawai yayi akan zaije kwanan sa biyu ya koma A zuciya irin tawa da tausayi halin dana ji Umma na ciki ya sanyaya min jiki ya Kuma Sakani Jin tausayinta hakane yasa na hau yiwa Naseer maganar yaje ya ganta dan uwa tabbas ba Wasa bace Sai dai ga mamakina Naseer b'acin Ransa ya nuna min yamin gargadi Akan Kar na Kara Masa maganarta duk halin ma da take ciki ita ta jawowa kanta. Naso na share kamar yanda ya share din sai naji zuciyata ta ki nutsuwa yanda sagiru ya bada labarin wuyan da Umma ke Sha ya tsayamin a wuya Ni nasan hakkinmu kawai bazai bar Umma da Safiyya su zauna lafiya ba sai dai idan har mun yafe musu. Damuwarta Dana saka a Raina yasa har mukayi zancen da Zahira Zahira ta shawarci naje idan har abbansu bazai je ba mu Rama sharrin da suka Mana da alkhairi yanzu tunda tana samun kudi nayi amfani da kudinta na yiwa Umma siyayya nace Mata tana rayye tayi aure Allah kuma ya azurta ta da iman Ni nasan da biyu Zahira take san naje Ni nasan so take ta nuna musu ranta baa hannunsu yake ba yanda suka so kasheta Allah baiyi ba gata Nan a rayye Nima sai naji inasan na gansu Naga ya suka dawo din Dana tari Naseer da zancen zuwa calaba nida Zahira bai Hana mu ba Ya Mana fatan dawowa lafiya ya Kara da duk abinda ya biyo baya Kar muyi kuka dashi. Insha Allahu ba Abunda zai biyo baya Nima inaso suci arzkin yarana da suka so watsa rayuwarsu Zahira cemin tayi zata bini muje can calabar da biyu Kuma naji inasan zuwa sabida na cigita Mallam Musbahu dan har na mutu bazan manta alherinsa a gareni ba. Nadeeya har da turmin zaninta da kudi Wai mu bawa Umma muce Mata itama tana cikin rufin asiri a gidan mijinta. Dak'yar na gane unguwar da.muka zauna dan garin ya sauya sosai anyi gine.gine unguwar ta Kara cika ba kamar da ba Da taimakon Sagiru Muka gano Inda Umma ke zaune a rumfar mahaukata. Ganin Umma kawai da nayi yasa na fara yiwa annabi sallati mun kad'u mun razana da yanda ta dawo dan Zahira har buya tayi abayana sabida tsoratan da tayi Mun dauka ganinmu zai saka ta hau hawaye tana neman yafiyarmu. Sai dai fuskar ta a karkace. Take jifanmu da mugun kallo Da da yanzu ba daya bane Ina daga tsayen na gaisheta Ina karewa wajen da take kwana kallo. Akan tsomokara take zaune rumfar sai doyi yake. Bata ce Mana komai ba ta cigaba da shafa wani Abu a kumburarren kafarta. Ni kuwa ledojin da muka ciko Mata da kayan abinci na ajiye mata ina gashi inji zahira akwai sakon Nadeeya a ciki da kudi. Yarana dukansu sun hada kudi Akan mu bata. Na dauka zata watsar da ledar ga mamakina da hannu biyu ta fusge Leda fuska a karkace take hararana Tana "Wlh ko duk duniya Zaki bani Naeema bazan tab'a sanki ba har gobe Ina Kan bakata bana sanki bana kaunarki Dana Kuma da Kika rabani dashi Allah ya Isa tsakanina dake Kaya Kuma na karba Dan nasan bada kudinki Kika siya ba" Mai Umma zatayi da zai bani mamaki ban ganshi ba hakane yasa kalamnta ma Basu bani mamaki ba illa tausayi ma da tabani dan nasan Umma har yanzu Bata da rabo kila shiyasa ta kasa Gane gaskiya da tana da rabo iya karkacewar Nan da tayi ya isa.yasa taji tsoron Allah" Amma gashi a wulakance da take tana Nan da kiyayya ta a ranta Koda Muka bar wajenta Sai Dana siyi katifa na aika Mata dashi. Yanda akayi nasan halin da suke ciki kenan Safiyya ban samu na sakata a idona ba Amma naji labarin irin wuyan da take Sha da haukar da take dan tab'a wa Allah ya tsare Mana imaninmu Bazan iya cewa matsalarmu ya kau gabadaya ba ba a rasa dan jarrabta na rayuwa da bawa ke fuskanta yau fari gobe baki sai dai muyi fatan Allah ya bamu ikon cinye jarrabawarmu wanan shine labarina nakan ji labarin wahalar rayuwa da Umma da Safiyya suke sha ta wajen iyalan Sagiru duk wanan bai.isa su gane gaskiya su nemi yafiyar wayanda suka zalunta ba rayuwa tun a gidan Duniya Allah yake yin hisabi Allah yasa mu cika da kyau da Imani ameen Naeema. Ina godiya ga duk masoyan da suka kaunaceni daga fara rubuta labarina duk sakon masoya na isa gareni idan tana bani labari ko ta turamin sakon makaranta na kanyi murmushi yanda mutane suke so su gani har wasu na San kulla kawance dani toh daga labarina kunsan Na tsufa tunda nayi hamsin har da doriya tsakanina daku fatan alkhairi ne da shawara da Zan bada akan duk runtsi duk wuya duk wahalar da zaka Sha a rayuwa ka dogara ga Allah zai isar maka ba Abu dawwwama me da baya wucewa Kamar baayi ba wani zubin Ni kaina Ina mamakin yanda Allah ya tsallakar dani duk Abubuwa da nagani gani Nan a rayye har da jikokina ma Koda Naseer arzikinsa bai dawo ba Amma muna cikin rufin asiri Allah Alhamdulillah ayita hakuri da rayuwa dan duniya kurkukun mumuni ce Aljanna kafiri Ina muku fatan alheri gabadaya masu San su gani ko abasu lambata kuyi hakuri akwai abinda nake jira idan na samu Zan Kara yiwa Marubuciyar magana ta dan rubuta gajeran labarin da lambar tawa shima banyi alkawari ba dan Ina San Kare martabar ta data yayana Dan akwai abinda aka tab'a yiwa yarana Kuna dai kallo bamu San komai ba Amma laifin mahaifiyar Naseer da kanwarsa na iya shafar yarana har a musu kallon Ashe fa kakarsu Bata da hali ta Taba tsafi da sauransu Da yawa badan tausayi kila suke San saninmu ba ko dan aga ya muke zaa so ganinmu ayi hakuri an gajarta labarin ne Amma halin mahaifiyar mijina yaso ya dan shafi.yarana agujesu har wasu.ma na ganin hada zuria dasu matsalar ne tunda kowa yasan labari irin wanan ba lailai ya buya ba idan an tashi bincike wasu sai sun Kara abinda ba haka ba dafatan duk zaku fahimceni Ina muku fatan alheri Marubuciyar Kuma Allah ya saka Mata da alkhairinsa idan wani Abu na karuwa ko darasi ga rayuwarmu ya Kara afkuwa da ya Kamata mutane su karu dashi Zan Kara Bata ta rubuta Dani da iyalaina muna godiya da Addu'oi da soyayarku mungode. *HUDAH HUDAH HUDAH* *LABARIN TA LABARI NE DA KOWA ZAI SO YA KARANTA SABIDA YANDA YA SHAFI RABIN ABUBUWAN DAKE FARUWA A ZAHIRI RABI GASKE YA FARU RABI FICTION NE AMMA SAKON DA NOVEL DIN KE DAUKE DASHI ZAI ISA GAREKU* *Ban san iya adadin lokutan da zan dauka ina gayawa duniya da wasu ginshikokin rayuwata cewa Shi din zab'ina ne*. *Ban san yadda aka yi har na fada siradin rayuwa haka ba, na zata dan karamin motsi da nayi zai sanya a kalle ni da sanyin idaniya*.... *A'a sai gashi tun banyi nisa ba, na fara gane da naga ta kaina! Ba tare da na gama kimtsa tafiyar da take gabana ba, na fada rana zafi inuwa kuna* *Duniya tana bamu abubuwa da yawa masu kyau da marasa kyau, sannan duk wani majibanci yakan tsaya ka'in dana'in domin samawa wasu bigiri nashi kyakyawan makoma da tushe mai nasaba ta Alkhairi! Haba Hudah! Me aka yi jiya balle yau, mu iyayen ki ne kuma Muna fatan Alkhairi a gare ki karki juyawa kyakyawan niyyar mu fuska" inji Mahaifiyar Hudah ta faɗa cikin rarrashi da kulawa*. *Cike da bakin ciki yake kallon ta, shekaru sha yake rike da yarinyar nan a cikin tsuma. Koda yake ba wani abu bane idan yayi dubi da juyin juya halin da aka samu ta rayuwa inda har takai wasu abubuwan suka iya sauyawa ba tare da sanin ka ba* *Ba zan fusata ba, kuma ba zan d'aga amo na domin duniya ta Fahimci abinda nake nufi ba, amma nayi imani da Allah, na kuma yi alkawarin ba zan juya daga kudirina ba, matukar ina raye Tabbas al'amarin tabbataccen al'amari ne kuma zai faru da Yardan Allah" inji Baban Huda* *Cikin wani irin murmushi me had'e da kuka na kalle shi na wasu lokuta, kafin na dukar da kaina ina me harde hannuna*. *Wannan alƙawari nayi da makagina, kowacce taki da zira'i, ta rayuwata kai ne shugaba kuma kai ne jagorana, zan ajiye kalmar ka da yakinin ka, domin ya zame maka abun dubawa ga madubin gobe na, zan tattara duk wani mataki da nau'i irinta yanayi na ajiye a matsayin wannan shine kaddarata, amma kai na tsayar da kai ne a matsayin babban harsashin da zan a za duniya ta! Ka yarda Ni din daban ce kuma mai fada da idarwa wancan sauran baya gabana domin kai ne yankin rayuwata ka saka a ranka babu wanda ya isa nisan kiwo a da'irar ka" inji Hudah* *Dandano* *Hudah* Tun Ina yarinya karama na taso da maitar kallon Fina finan indiya bansan Mai yasa indiyawa suke burgeni ba a yarinta irin tawa har hasaso kaina nake a cikinsu tun bana gane mai film din ke d'auke dashi har na fara mallakar hankalina Ina gane Inda film din dana kalla ya dosa na fi karkata da San na kalli film din soyayya soyayar cikin film din indiyawa na balain burgeni nakanji inama nice wani zubin idan Ina kallon soyayan. Hakane yasa na taso da burin na gwada soyayya irin wacce nake kallo a fina finai Dana Zo na hada da karanta littattafai soyayay zalla sai Kuma na fara burin yanda Zan Gina rayuwata da Wanda nake Jin a Raina Zan kaunace shi ya kaunaceni kamar dai yanda na taso da kallon Ana Yi a indiya film da littattafai soyayyan da nake karantawa. Ina balain San soyayya a rayuwata a ganina indai na samu Wanda ya kwanta min a raina zai ga soyayya a wajena Zan iya Sadaukar Masa da komai nawa indai Ina sanshi. Na taso da burin San auren kyakyawa saurayi Dan a ganina shine Zan samu duk burikana su cika muyi irin soyayya da nake mafarki. Soyayya shine kan gaba da komai a wajena a raayina indai na hadu da Wanda nake kauna nake so a zuciya ta ko rumfa ne zan iya rayuwa dashi. "Na kasa yarda yanda lamura suka juye lokaci guda duk mafarkina da ke dab da tabbata a idona Naga Yana watsewa yana tarwatsewa shekara biyar Ina Gina soyayya ta Mai zafi tashi daya kaddara ta hadani da mutumin da duk fitar numfashina da tsanarsa yake fita. Ban ma hasaso yanda Zan fara rayuwa da Wanda ya girmewa mahaifina ba. Ina dai kallon fin karfin da ake San gwadamin na tilastamin Alhaji idris da ko ganinsa bana San yi. Yayyen mahaifiya ta da suka dage da mun kwalliya kawai nake bi da kallo idan na runtsa idona sai na hango Habib da San sa ke nukurkusar zuciyata Ina hango yanda aka min adon nan wajen sa naje ya ware hannayennsa ya rungumeni a kirjinsa Ina shak'ar daddan kamshin turarensa. A irin burina ya dagoni daga kirjinsa ya hade fuskarsa da tawa ya sumbaceni ya kaini wani duniyar da nake mafarkin idan ya kaini bazan dawo ba. Indai Zan tuna Habib a rayuwata sai nayi murmushi Ina Kaunar bawan Allah nan. Muryar yayar mahaifyata ne ya dawo dani tunanin Dana tafi. "Maza Yar albarka tashi kije waje Yana jiranki wlh bazaki yi nadamar Yi Mana biyayyya ba ko dan hajji da zaa kaimu ki nuna Mana kin haifu ke Yar albarka ce a gidan Nan waye yayi goshin da kikayi iyye zamani ya canja baa auren wani soyayya yanzu wlh ke matar manya ce ba kalar wanan sirrin yaron Mai fama da takardu ba" Mik'ewa nayi da Sauri dan a rayuwata na tsani inga an tab'a Habib data zagarmin shi gwara na fita wajen tsohon Dana tsana Mai zuciyar yara. Wajen nayi da sauri Ina Jin zuciyata namin nauyi da balain tsanar ganin wanda ya min Karen tsaye a rayuwata yake San rabani da farinciki rayuwata. Ina fita waje na coge a bakin kofa Ina kallon katuwar bak'ar Jeep din dake ta zuba kyalli. Da sauri drivernsa ya fito ya bud'e Masa k'ofar motar ya zuro k'afafun sa ya fito waje Ya nufoni Yana washemin jajjjayen hakoransa Ya kusa sabain Amma sabida budurwa zuciya kananan Kaya ya saka Kai da gani kasan dak'yar rigar ta shigeshi sabida yanda tumbinsa ya baje acikin rigar. Jikinsa har wani rawa yake daya Iso Inda nake tsaye. Ni kuwa isowarsa yasa na fara tunanin Taya ma Zan iya auren tsohon nan lebbensa na kalla Mai kauri tunanin har munyi auren ya kusantoni da shegen bakinsa yasa naji wani irin amai ya tahomin da balain k'arfi Kafin na juya na shige gida har na fara kwara Aman........ Novel din Hudah Zan fara sakinsa second week of September insha Allahu akan farashin 300 ga Mai bukata zai iya fara saka kudinsa ta acct dinan 2029764071 first bank nafisa Nuhu ko Katin waya ta layin Nan 08033719070 a turo da shaidan biya ta layin Nan 08033719070 Vip kuma zasu biya dari biyar zaa su na samun post sau biyu a Rana. Kar dai na cika baki Hudah zai iya fin Naga ta kaina dadi ko dadinsu yazo daya 😃😃