[7/1, 4:48 PM] Aisha Galadima: *⚗⚗ MUSAYAR ZUCIYA...⚗⚗*                     ♥                  ♥♥          A true life story Na *K.A.S Precious Hajja ce*👈 *HASKE WRITER'S ASSOCIATION*💡 (Home of expert & perfect writer's) *DEDICATED TO* Sanah Isma'il matazu. Bismillahir Rahmanur Rahim.....   "Hakk'in mallakar Hajja ne, kar wanda yayi min sauyi a cikin sa please." Page *1* A makaranta.    "Uwani halilu?"      "Present sir.."    "Baraka lado?"      "Present sir.."   "Sahura Ayuba?"       "Present sir.."    "Indo malam Hamza?"   "Labbaika, present, sir, mah, nazo..." Saurin kallon ta malamin yayi jin yauma a yadda ta amsa mai kafin ya zare glass d'in dake manne akan saman idan fuskar shi, ya d'ora dara-daran idanun shi akan nata da nufin ko zata ji tsoron sa sai yaga ta kafeshi da idanuwan ta tamkar zata cinye shi, yayi saurin wurga mata uwar harara ranshi a matuk'ar had'e yace mata cikin tsawa. "Ke..! Baki da hankali ne...?!" Indo ta mik'e tsaye tana gyaran hijjab d'in ta wanda yayi dikil-dikil da daud'a wuyan ya yage tun daga wuya har zuwa k'irjinta sannan tace, "Da sauk'i dai malam..!" "Naga alama ai koma gurinki ki zauna wawuya kawai.." Ya fad'a ba tare da ya kalleta ba. Komawa tayi ta zauna sai faman soshe-soshe take yi akan ta wanda hakan da alama ba za'a rasa kwaron kwarkwata ba dan yadda take yi ya nuna hakan. sai da ya kammala kiran sunayen su tas! sannan ya mik'e ya fita yana jiran lokaci ya cika sai ya kuma dawowa yayi musu subject d'in turanci wanda aka sari basa fahimtar uban komai a ciki, idan kuwa yana son su fahimta toh sai ya had'a musu da yaren hausa sannan zaiji ruwan amsa da tambayoyi amma idan da turanci zai kwana yana yi sai dai su kafamai idanuwa tamkar zasu cinye shi. Yana fita wajan mintuna biyar sai gashi ya kuma dawowa hannun shi d'auke da wasu littattafai manya da kananu. yana shiga ya tarar duk sun kaure da surutu yayin da ya kai idanunshi can k'arshen ajin ya hango INdo da wani yaro taci uwar d'amara da hijjabin ta suna dambe. Dorinar hannun shi ya d'akko yayi gurin. sauran yara na ganin shi suka fara watsewa aka bar INdo da lurwanu a gurin. yana zuwa ya fara tsulawa INdo dorinar ganin ita ce me fifik'arewa kafin ya tsulawa lurwanu yana cewa. "Ke! Sakar mai riga wawuya kawai." Axabar bulalar ne yasa ta saki amma da ba tayi niyar sakin shi ba sai ta fasa mai baki kamar yadda ta furta tun farkon fad'an nasu. Malam Sadeeq na kallon su yace. "Me ya had'a Ku?!" Idanu kwal-kwal zasu kawo ruwan kuka lurwanu yace. "Malam itace..." Caraf be k'arasa fad'a ba INdo tace, "Malam wallahi k'arya yake shine ya fara..." Shima lurwanu dan kar tamai sharri ya kuma tare zan cen, "Wallahi malam k'arya take yi kawai na ajiye..." "Billahillaxi malam shine ya..." "Keep silent or something else's, sha-sha-shai kawai.." Babu abin da suka fahimta a cikin abin da yace dasu sai dai yana yin yadda yayi musu maganar da kuma kalaman shi na karshe ya tabbatar musu da cewar fad'a yake musu hakan yasa suka yi shiru suna bin kyakyawan bakin shi da kallo ba kamar INdo da take tunanin ko alawace ji take kamar ta lasa dan yadda ya burgeta. Komawa yayi wajan teburin shi ya zauna sannan yayi musu alamar suzo baki d'ayan, suka bishi INDO sai faman ture lurwanu take yi a haka suka k'arasa wajan da malam Sadeeq yake jiran su, "Kai me ya had'a ku da ita?!" "Malam itace kawai muna zaune sai tazo tana tab'ani da kafa nayi mata magana ta dena takani shine tak'i taci gaba har muka fara fad'a da ita." Tun kafin ya bata izinin magana INdo ta fara tana hararar lurwana bakin ta har kumfar yawu yake sabida masifa, "Kai..Kain uban can..! Na rantse da Allah malam shine ya d'alamin kaure a baya na shine na rama ya kuma yi min kawai muka fara fad'a dan shi masifaffe ne ya raina ni.." "Ya isah haka kowa yaje ya zauna bana son surutun ban za." Tashi suka yi suka tafi dama can karshen aji nan ne wajan zaman INdo dan haka ta tafi malam Sadeeq yayi saurin dawo da ita, tana zuwa yace da 'yan layin gaba suyi mata guri anan ta zauna cike da jin haushin malamin dan taga alamar baya son ta bare yabi bayan ta a duk cikin al'amarinta. A haka ya kammala musu yabar ajin duk sun gundure shi ga haushin basa ganewa da turanci har sai yayi da Hausa. Ana tashi ya hau mashin d'in sa kai tsaye ya wuce inda ya sauka. Wanka yayi sannan yayi sallar azahar ya koma gefe ya zauna bayan ya janyo wayar shi, laluban d'an uwan shi ya fara yi cikin sa'a ta fara k'ara yana d'agawa yace, "Hi twins ya gida ya gurin aikin naka?!" Daga can 6angaran ya amsa cikin sanyin murya kamar yana rad'a, "Lafiya lau all twins ya student's da fatan dai kana samun yadda kake so koh?!" Shafa k'eya yayi tamkar yana ganin shi sannan ya lashi lips d'in shi yace, "Nop! Twins ga baki d'aya makarantar bata yi ba wallahi, gashi nazo an wani bani formaster teaching kuwa sai dai nayi da hausa wata Kalmar ma ban san yadda zan fassara musu ba wallahi sai dai na barsu a haka." Dariya yayi mai sauti ya san dole a bawa d'an uwan shi haushi duba da yadda baya son wasa a harkar karatu gashi an kai shi inda zasu samai hawan jini, cikin basarwa yace. "Common Sadeeq ka sani ko anan ma girlfriend d'inka take, dan Allah kasaki ranka kasan 'yan kauye da son mutane za kaji dad'i kuma zasu soka kai dai kawai ka samo mana wifey d'in ka acan..!" Kit! Sadeeq ya kashe wayan sam beji dad'in wayar da suka yi da d'an uwan nashi ba yau, a maimakwan ya lallab'a shima a'a sai ma yi mai fatan tsiya da yake yi na samo mata dan wulakanci. shi kam Abubakar murmushi yayi jin ya katse ya san haushi yaji sabida yayi mai fatan tsiya. zai samu yaje garin har gurin shi ya bashi hakuri yaga kuma yadda suke yi. *** Bayan wasu awanni, Sauri yake yi ya k'arasa cikin masallacin dan gudun kar a tayar yana hanya, sai da yazo dai-dai wajan wata kwata zai tsallaka kawai yaji an kwararo ruwan kanzo gabaki d'aya aka b'ata mai wandon dake jikin shi. Bin katangar gidan yayi da kallo cikin wani mugun takaici kafin yayi wani yunk'urin tuni an fara zagaye shi abin takai cin ma harda d'aliban shi. sai sannu suke zabga mai tamkar wanda yaji ciwo. "Kai subhanallahi Malam Sadeeq ya a kai haka?" Kafin ya bashi amsa wanda yayi maganar ya kalli wani yaro tare da cewa, "Kai yi maza shiga nan gidan kace a temaka mana da ruwa a buta." Juyawa yaron yayi shi kuma headmaster ya kalli Sadeeq cikin jimami yace. "Garin Yaya hakan ta faru Malam Sadeeq?!" Da kyar ya samu ya tsaida takaicikin shi kafin ya kalli headmaster yana kallon inda aka b'ata mai yace, "Wucewa zan yi zuwa masallaci, su kuma ba tare da suna kulaba kawai suka watso k'azanta sai kace a cikin gidan su duk ba wannan ba sun b'atan lokaci na rasa jam'i." "Ashha-ashha malam yi hakuri kasan kauyan namu ne sai hakuri duk haka suke yi kayi hakuri dan Allah. Dai-dai lokacin yaron da aka aika suka fito shi da INDO hannunta rik'e da buta gefen butar ya fashe sai da ta d'an kar-kata ta taho tana cewa, "Waye yake neman ruwa a buta?!" Karaf suka had'a idanu da shi da sauri ta dashare baki tana matsawa wajan shi ruwan sai zuba yake ta kalleshi tare da cewa, "La'ilaha'illallahu Malam Sadeeq kaine a k'ofar gidan mu yau?!" Banza yayi mata yana kallon butar ganinta jage-jage gashi duk ta fashe ya sashi yin saurin juyawa tare da kallon headmaster yana cewa, "Rankashi dad'e bari  kawai na koma gida naga nan duk b'ata lokaci ne na gode..." Ba musu headmaster yayi mai sallama da sauri ya wuce sauran mutane na bashi hakuri ita kuma INDO tana fad'in, "Malam ruwanfa? ko na biyo ka dahi koka ka fasa na maidahi gida?!" K'in kulata yayi ganin haka yasa INdo ta murgud'a mai baki tamkar yana ganinta sannan ta koma gida tana mitar kawai yasa sunyi asarar ruwan su a k'asa bayan suma babu kala ne suke yi. ***   Yau kwana biyu kenan INdo bata zuwa makaranta, sai a kwana na uku taje tun daga bakin k'ofa zaka tabbatar da yau tazo sabida yadda ajin ya kaure da shegen surutu da hayani. yana shiga ya ganta zaune akan tabur d'in da malamai ke zama idanunta sanye cikin eye glass wanda idanun (glass) d'in suka ciccire ta rik'e pencil tare da d'ora kafa d'aya kan d'aya tana yin irin na Malam Sadeeq, "Mary alto." "Zuwaira jamilu." "Mansur bawa." Gabaki d'aya ajin aka d'auki ihu da shewa dan sam basu kula da zuwan shi ba. har INdo ta mik'e tsaye tana dariya tare da cewa, "Alkur'an haka malam Sadeeq yake yi.." Suka k'ara tuntsurewa da dariya ana cewa, "Ohhh ke INDO...!" Tsittt taji anyi hakan yasa ta waigawa bakin k'ofar dan ganin yadda kowa ke kallon wajan, karaf suka yi idanuwa hudu da malam Sadeeq wanda yayi kicin-kicin da fuska tamkar hadari tayi saurin komawa wajan zamanta wanda in dai shine a ajin toh anan take zama sai ya fita take komawa gurinta na ai na hi wato karshen aji. Yana shiga duk aka tashi ana gaida shi kowa ka gani cikin tsoro yake dan basu san matakin da zai d'auka akai ba, "Good morning sir..!" Sai da ya samu guri ya ajiye register da sauran littattafan hannun shi sannan ya kalle su yayi musu alamar su zauna da hannu, gyara glass d'in idanun shi yayi sannan ya kalli inda INdo take zaune ta kwalalo mai idanuwa yace mata, "You! come here.." Tashi tayi cikin d'ari-d'ari dan babu wanda be san kalmar come ba, tana zuwa ya matsa mata tare da nuna mata kujerar gurin yace, "Seat down..." (Zauna) Zama tayi dan taga ne abinda yace sabida yau da gobe idan sun gaida malamai ana ce musu seat down so kuwa ya san kalmar, ta zauna sai wulkita idanu take. register ya d'akko tare da bud'ewa ya mik'a mata jan biro da blue tare da cewa, "Oya started." Tayi saurin kallon shi tare da cewa, "Na'am malam.." Keya ya salle mata da hannunsa tare da cewa, "Ki fara kiran sunan idan ba haka ba zaki sha wahala dan naga alamar kin raina ni so ina son kiyi musu yadda nake yi nima na gani.." Kallon register d'in tayi sam kasa gane yadda take tayi bare aje ga karanto sunayen ciki ba zata iya ba kuma nan J.S one, kallon shi tayi tare da marairaicewa ta fara ba shi hakuri. "Malam dan Allah idan kana kaunar iyayanka kayi hakuri wallahi tallahi ba zan sake ba." "Au ba zaki fara ba sai na zane ki...?!" Ya fad'a yana gyara dorinar hannun shi, nan da nan INdo ta fara kuka dan tak'i jinin a doke ta da bulala. tayi saurin zamewa k'asa tare da sake bashi hakuri akan ya kyaleta ta tuba tabi Allah tabi shi. Ganin duk ta gigice yasa shi ce mata, "Tashi ki dawo nan kiyi naildown." "Malam baka hakura ba dan Allah?!" Ta fad'a tana matse idanuwa dan hawaye su fito amma ko d'igo, ganin yaje ya zauna ya fara kiran suna yasa INdo tashi taje tayi abinda ya sakata dan ta san ba hakura yayi ba. sai da ya kammala kiran sunan ya fara koyar dasu ya gama sannan ya kalleta yana nunata da yatsa yace, "Idan kika sake yin abinda nake yi in dai ba na karatu bane sai na 6allaki kina jina?!" "Eh malam ai baxan kuma bama." "Yafi miki.." Ya fad'a tare da kwashe kayan shi yabar ajin yana tunanin inda zai yi ya samu ayi mishi transfer ya tsani makarantar sam ba tayi mishi ba. Bayan sati biyu ranar wata Monday Sadeeq na shirin tafiya class d'in shi ya d'auki duk wani abu da yake buk'ata yana shirin fita kawai yaga Abubakar twins d'in shi tsaye cikin kananun kaya riga seegreen me dogwan hannu da wando baki sai farin eye glass wanda yayi mai matukar kyau, sosai suke matukar kama babu ta inda zaka iya bambance su sabida tsabar kamannin su. kallon shi Sadeeq yayi cikin tsananin mamaki tare da k'arasawa ya kalleshi cikin mamaki yace, "Yanzu muka gama waya da kai amma shine baka gaya min kana hanya ba why?!" Kafad'a Abubakar ya d'aga alamar ba komai sannan ya shiga ciki ya zauna tare da cewa, "Twin ko class zaka shiga ne?!" "Eh but tunda kazo sai mu wuce gida ka huta gobe na shigar musu." Yayi maganar yana k'okarin maida littattafan dake hannun shi, da sauri Abubakar ya mik'e tsaye yana tsayar dashi ta hanyar rik'e hannun shi yace, "No kazo muje sai na tsayaka ina nan tare da kai har zuwa gobe." Kafad'a Sadeeq ya d'aga sannan ya d'auka tare da juyawa yana fad'in. "Toh muje." Tafiya suke wanda ita kanta iri d'aya ce suke yi suna yi suna hira yara kuwa daga cikin tagogin ajin su sai lekowa suke suna mamaki da al'ajabi ganin malam Sadeeq guda biyu a haka suka k'arasa barandar ajin su INdo. Yauma kamar kullum cikin surutu suka gansu sam basu lura da zuwan su ba INdo suka hango a saman dest tana rik'e da kugunta sai gwada musu yadda malam Sadeeq yake tsayuwar shi take yi taji Uwani halilu ta janyota tare da nuna mata k'ofar ajin tana hango su ta shige k'ark'ashin benci cikinta sai kululululu yake sabida ta san yauma ta shiga uku. "Goody morning sirsss..!" 'Yan aji suka fad'a baki d'ayan su tare da mik'ewa tsaye. ciki suka shiga sosai Abubakar sai kallon su yake su kuma sun rasa gane waye malamin nasu a ciki. Sadeeq ya k'arasa wajan bencin da INdo ke k'ark'a shi yace. "Ke! Tashi ki fito ko na mareki.." Jikinta na rawa ta d'ago ai tana ganin still biyu take ganin shi sai ta koma tana ihu tare da cewa. "Wayyo Allah na higa uku malam nayi min fatalwa, wallahi tallahi ban yi niyar yi ba amma Maryam Aliyu tace nayi zata bani naira biyar dan Allah malam kadenayi min fatalwa wallahi ba zan sake yi ba idan na k'ara ka...." Bata k'arasa ba taji an janyo kafar ta sai ganinta tayi a gaban allo tana d'agowa still ta kuma ganin su biyu kawai a take ta sulale a wajan ta sume sabida tsabar kad'uwa da shiga cikin rud'ani. Ko gezau Abubakar beyi ba bare yayi yinkurin yin temako sai kallonta kawai da yayi yana mamakin ganin hauka irin nata, da sauri Sadeeq ya girgizata yana kiran sunanta cikin tashin hankali kar yaje ta mutu ya shiga uku 'yan aji kuma sai suka fara kuka cewar INdo ta mutu. "Aisha! Aisha!! Ke Aisha!!! Tashi mana me aka yi miki haka...?!" Sadeeq ya fara kiran sunanta ganin duk ya rud'e yasa Abubakar k'arasawa wajan ya dafa shi sannan ya kalle shi a hankali cikin rashin sonyin maganar shi yace, "Sorry my twins ba mutuwa tayi ba suma tayi da ansa mata ruwa zata farfad'o.." Shaf Sadeeq mantawa yayi da cewar d'an uwanshi likita ne sai da Abubakar ya samo ruwan wata yarinya a jarka ya shafawa INdo sannan ta farfad'o yana jin sanda d'an uwan nashi ya sauke ajiyar zuciya mai k'arfen gaske na farin ciki. Tana farfad'owa idanunta suka sauka a kansu da sauri tayi baya jikinta na rawa, ganin haka yasa Abubakar dama shine wanda baya d'aukar raini ya buga mata wata uwar tsawa tare da zare mata idanuwa tsit INdo tayi jikinta sai faman rawa yake. "Ke..! Karna sake jin bakin ki yayi mana ihu, wawuya baki san ana haifar 'yan biyu ba? Ko kinga munyi miki kama da mayu ko aljanu..?!" Cewar Abubakar wanda ke tsaye akan INdo, da sauri ta girgiza mai kai cikin tsananin tsoro sannan ya ce mata, "Tashi kije ki zauna na san yanzu garau kike ba kya buk'atar wani hutu." Da sauri ta mik'a ta wuce gurin zamanta, mik'ewa Sadeeq yayi ya koma kan kujera tare da janyo d'ayar ya nunawa Abubakar alamar ya zauna. kallon kujerar yayi sannan ya kallo inda yake hango INdo cikin yatsina fuska yace mata, "Ke..! Zo nan." Da sauri ta k'arasa tare da zubewa a gurin shi tace. "Gani malam." "Karki kuma kirana da malam kinji ko? Ni ba malamin Ku bane..!" Baki na rawa INdo tace. "Toh sir." Had'e rai yayi tare da tsuke baki cikin takaici yace, "Waye sir d'in?!" INdo tace, "Kai ne sir. ." Hard'e k'afa yayi yana kallonta cikin b'acin rai yace, "Stupid...! Ya sunan namijin saniya? ya ake kiran shi da hausa?!" Cikin sauri ba tare da takawo komai a cikin zuciyar ta ba tace, "Sunan shi sah." Abubakar yace, "Ahha kin ga nayi miki kama da shi?!" Da sauri ta girgiza Kai alamar a'a tana mamakin wannan abu, toh me zata ce mishi tace malam yace baya so tace mai sir yace ta kirashi da sunan dabba toh ko sunan shi yake son ta fad'a ko tace mai baba amma ai be haifeta ba bare tace mai hakan. Jan baya yayi kad'an tare da cewa, "Zoki gogemin kujerar da zan zauna." INdo ta mik'e tana mamakin toh yau malam sadeeq mugu ya zama kokuwa ba shi bane dan har lokacin bata  tantance waye malam Sadeeq ba cikin suba. kalle-kalle ta din ga yi ko zata samu wani kyallen da zata goge mai amma babu ganin haka yasa shi yin magana, "Ke..! wai ba zaki yi aikin da na saki ba kin barni a tsaye fa." "Mal.. Si.." Ta rasa me zata ce mai kawai ta kalleshi tana turo baki dan ya gundire ta tace, "Ai babu tsumma shi yasa." Cikin rashin damuwa ya kalleta daga sama har k'asa ya tab'e baki sannan yace, "Meye amfanin hijjabin jikinki ko d'ankwalin kanki su d'in ba tsumma bane?!" Da sauri INdo ta kalleshi ya d'aga mata gira guda d'aya tayi saurin kallon Sadeeq dake zaune ga mamakin ta register ma yake bud'ewa ta kalli hijjab d'inta wanda duk ruwan kashu ya dafar dashi gashi wuyan ya yage tace mai. "Ai hijjab d'ina ne bafa tsumma bane ba." "Idan baki cire kin goge min na zauna ba ranki zai 6aci yanzun nan kinji na gaya miki." Ya fad'a cikin tsawa wadda take a slow, ba yadda ta iya haka ta kama k'asan hijjab d'inta ta goge mai kujerar sannan ya zauna ita kuma ta koma wajan da malam Sadeeq d'in ya tanadar mata a gaba. Malam Sadeeq ya fara kiran sunaye sannan da ya gama yayi musu karatun da yake d'aukar su wato turanci, Abubakar dake zaune yaci dariyar zuci dan karma yayi a fili su raina shi ko idan yaji dariyar tayi mai yawa sai ya kara text book a fuskar shi yayi mai isar shi, lallai dole d'an uwan shi ya koka tab makarantun gwamnati sai addu'a yake ta fad'a a cikin ranshi har Sadeeq ya kammala musu sannan suka fita ana tashi suka wuce gidan da Sadeeq d'in yake haya a ciki..... *HAJJA CE*👈 [7/1, 4:48 PM] Aisha Galadima: *⚗⚗ MUSAYAR ZUCIYA...⚗⚗*                     ♥                  ♥♥          A true life story Na *K.A.S Precious Hajja ce*👈 *HASKE WRITER'S ASSOCIATION*💡 (Home of expert & perfect writer's) *DEDICATED TO* Sanah Isma'il matazu. Page *2*     Bayan an tashi daga makaranta, su Indo ta k'ofar gidan da su Sadeeq suke suka biyo. lek'en su suka din ga yi su dai suna jin hayaniya da guje-gujen yara amma basu kula ba sai can Indo da Maryam Ali suka kuma kutsa kai suka shiga suna lek'a tagar wani d'aki karaf suka hango Abubakar zaune a bakin katifa yana danna laptop wanda daga shi sai 3quarter da singlet sam beyi tunanin cewar ana lek'an su ba sai da yaji motsin yayi yawa sannan ya d'aga kai yana kallon gurin. Mamaki da al'ajabi yasa shi saurin mik'ewa tsaye su kuma suka zaro mai idanuwa kamar had'in baki su sam basu gane waye aciki ba kasan cewar kamannin iri d'aya ne. Suna k'ok'arin guduwa suka ga Sadeeq tsaye a bayan su ya rufe k'ofar gidan ya jin gina a jikin ta yana watsa musu wani mugun kallo. can Abubakar ma ya fito fuskar nan a murtuke. “Wayyo Allah dan girman Allah dan annabi Muhammad s.a.w idan kuna kaunar iyayanku kuyi mana hak’uri.” Cewar Indo tana faman tafa hannuwa alamun rok'o,itama Maryam tsugunnawa tayi tana magiya, “Dan Allah kuyi hakuri wallahi Indo ce tace muzo mugani ko aljanu ne ku, amma wallahi ni banyi niyar shigowa ba.” “Shhhhhhhhhhhhh..!” Abubakar yayi musu bayan ya d'ora yatsan shi d'aya akan Lip's d'in shi suka had'a idanuwa da Sadeeq suka fara matsowa gurin su yayin da jikin su Indo ya hau rawa kamar an saka musu shock ai kuwa suka fara kurma musu ihu. “Iiihuuu..! wayyo Allah a zo a temaka mana zasu kashe mu...!!” Kafin kace mene har unguwar ta cika da mutane sai bugan gidan ake amma sunk'i bud'ewa, yaran da suka taho tare da su Indo ne suka yiwa sauran mutanen gurin bayani kan cewar ai su Indo ne suka shiga wai sai sun kallesu. wani dattijo ya kuma buga gidan jin su indo na ihu yayi magana da d'an k'arfi yace, “Ku kuwa bayin Allah dan Allah kuyi hakuri ku bud'e su fito ba dan halin su ba.” Sai da Abubakar yasa su kamun kunne wajan mintina goma sannan Sadeeq yaje ya bud'e su indo suka kwasa da gudu suka bar gidan,hatta wad'an da suke mak'otaka dashi Sadeeq d'in sai da suka tambaya waye Sadeeq a cikin su yace... “Gani nan baba Al-hassan.” Wanda aka Kira da Baba alhassan yace, “Ikon Allah toh ai kud'in ne dole ku zama abin kallon jama'a sabida ba kasafai ake samun samarin matasa maza 'yan biyu masu matukar kama da juna ba. koni da Al-husain d'ina kafin ya rasu ana iya gane mu amma ko babu wata alama da zata sa a gane ku dole yara suzo kallan ku.” Murmushi Sadeeq yayi tare da shafa k'eya yayin da Abubakar ya kalle su sai kuma ya juya tare da komawa cikin d'aki yana tausayin d'an uwan shi akan wannan aikin nashi daya zoyi duk babu sa'a, ba'a makarantar ba ba kuma a garin ba duk babu sauk'i haukan garin yayi yawa. ** Abubakar da Sadeeq 'yan biyu ne wad'an da ba zaka ta6a iya banbance Hassan ko Husaini ba mudin suna tare sabida tsabar kamannin da suka yi. Hatta tafiyar su, dariyar su, yana yin maganar su sai d'abi'un su ne kawai idan ka zauna dasu zaka iya tabbatar da cewar sun ban-banta dana juna. Engineer Alhaji Salmanu Haruna shine mahaifin su, yana da arzik'in shi dai-dai misali Matan shi na aure guda biyu ne Mama A'i itace uwar gida kuma mahaifiyar su Abubakar da Sadeeq sune yaran Alhaji Salmanu na farko sai kannan su da suke uwa d'aya su biyar Hawwa, Halima, Hamza, Amina sai Khalifa sai ta biyun Umma Fatu tana da yara uku Khaleel, Mubasshir da Rukayya. Gabaki d'ayan zuriar sun taso cikin tarbiya da ilimin boko dana addini dan Alhaji Salmanu tsayayyan mai gida ne da yake tsaye akan matan shi da yaran shi. Wannan kenan.. ** Indo Aisha d'iya ce a wajan Hamza mai gyaran radio da Inna Mero sai kannanta guda uku Sagiru, Shehu sai Nafeesa. Malam Hamza ya dad'e yana gyaran radio dan da sana'ar yayi aure harya hayayyafa duk da suna matukar shan wahala dan wata rana ma basa samun na abinci sai dai su kwanta haka. Indo yarinya ce k’azama ainun domin wanka ma se juma’a jum’a take yi,shima se an tilastata agaba bayan haka kuma gagarumar fitinanniya ce ga d'an karan tonan fad'a da shiga fad'an da bana ta bane,tana da son wasa hakan yasa koda aka bud'e musu wata primary aka sanyata bata kwaso komai ba sai k'arin fitina da rashin kunya a haka harta zana jarabawar fita daga primary ta wuce secondary yanzu tana aji d'aya ko sunanta da kyar take iya rubutawa shima a karkace cikin rashin tsari, kuma kusan duk haka ajin yake monita ne kawai mai iya rubata sunan shi complete sannan ya rubuta na wasu suma ba duka ba. Gidan su na k'asa ne d'an k'arami wanda shi da kanshi Malam Hamza shi ya gina abunshi yayi d'akuna uku da makewayi katangar tasu gajeriya ce domin idan kai dogo ne to hak'ika idan kana tsaye sai an hangoka hakan yasa duk shirgin da suka kwaso suk'e iya cillashi ko su watsa shi ba tare da sanin koda mutum a wajan ba dan ansha fad'a dasu da mutanen unguwa amma sun kasa denawa har anyi shiru an zuba musu ido. ** Da gudun tsiya ta shiga gida tana sauke wani uban nishi Inna ta kalleta tare da cewa, “Ke kuma lafiya kuwa kika shigo gida bako sallama 'yar nan..?!” Inna ta fad'a kasan cewar bata iya fad'in sunan Indo sabida 'yar ta ce ta farko kuma sunan surikar ta ne wato mahaifiyar malam Hamza. cire daddauhar hijjab d'in Indo tayi me tashin hamamin wari tare da cillar dashi a tsakiyar gidan su tace, “Wato inna akwai abubuwan kallo idan mutanen cikin birni suka zo nan wai...!” Tah fad'a tana zaro idanuwa, kallonta inna tayi cike da takaici ta rasa gane kan Indo tunda aka kawo malam Sadeeq kullum taje makaranta ta dawo da saban labarin da zata bata akan shi dan haka tasan tatsuniyar gizo bata wuce ta kok'i inna tace, “Allah shi kyauta miki 'yar nan, tunda aka kaiki makarantar nan ban tab'a jin kinzo kina yin karatu ba yadda nima zanji dad'i ba sai dai tunda aka kawo sabon malamin ku toh babu ranar da zakije baki dawo da sabon labari akan shi ba sai kace shi aka ce kije ki koyo..” “Kai inna ana baki kina k'in k'ar6a.” “Eh ba zan k'ar6a ba bana so ki rik'e kayan ki.” Indo ta kuma gyara zama tare da bugun kanta da alama kwarkwata ce tayi motsi,cikin son bada labarin tace, “Aikuwa inna sai na baki labarin nan dan kuwa wallahi har suma nayi aka samin ruwa na farfad'o.” Jin abinda ta fad'a ne yasa inna zaro ido tana dafe k'irji tace, “Na shiga uku ni Maryama meya faru dake 'yar nan?!” A take Indo ta kwashe labari tun daga wanda ta sani har wanda d'alibai 'yan uwanta suka gaya mata ta k'arashe zan cen da fad'in lokacin da suka shiga gidan su shine fa ana bud'e musu ta shigo gida da gudu. “Ikon Allah kenan, toh ke dai babu ruwanki dasu..ah to karkije wata rana ki basu haushi suyi miki aika-aika su cuceki Allah ya tsare ba fata ba” “Toh inna ai na fisu iya gudu wallahi.” “Yi min shiru wawiya kawai an ce miki wannan muguntar ta gudu ce, ke dai babu ruwanki dasu na gaya miki.” Da haka suka dinga magana inna na son fahimtar da ita sai dai kunya da kawaici yasa ta kasa sai faman kwana-kwana take yi. Ita kuma wadda ake wa dama ba wani fahim ta ne da ita ba dan haka bata fuskanci inda maganar inna ta dosa ba. *** “Other half gaskiya ya kamata ka nemi transfer daga wannan gajarabal d'in makarantar, ah!wannan school da kauyan ai sai kaima su maida kai kamar su dan wallahi rayuwa a irin wannan gurin tsab zasu canza ka su 6ata maka hobby d'inka.” "”Kai twinnie God forbid wallahi sai dai ni na canza musu, ni sam basa yi min haka kawai zuwanka ne yasa dan sun ganmu mu biyu shashanci sai kace akan mu aka fara zuwa duniya mutum biyu iri d'aya...” Abubakar ya kuma kallon Sadeeq shi tausayin shima yake dan ya san kawai yana zaune a garin ne ba dan yana jin dad'i ba,ta6e baki yayi tare da d'aukar laptop d'in shi ya koma cikin bedroom ya k'agara gari ya waye ya bar garin dan jin shi yake yi tamkar akan k'aya. Mik'ewa Sadeeq yayi tare da d'aukar mukullin motar Abbakar d'in, fita yayi ba tare daya sanar mai ba yayi waje. Can cikin gari ya tafi wani restaurant ya shiga inda yake zuwa cin abinci yayi musu order mai rai da lafiya sannan ya siyo musu drink's masu sanyi ya dawo gidan lokacin ya tarar da Abbakar d'in ma bacci yake kasan cewar sun kunna inji akwai iskar fanka. kallon shi yayi sannan ya fito ya dawo parlor ya fara rubuta lesson plan har wajan la'asar sannan Abubakar ya farka yana fitowa yagan shi zaune gaban shi duk takardu ne da littattafai kawai ya kalleshi yace, "Wai twinnie har yaushe ne ka koma haka? duk ka takurawa kanka ya kamata ka sauya makaranta dan kafi karfin koyar da irin wad'an nan school d'in." Sadeeq ya numfasa tare da cewa, "Meye abin fin k'arfi twinnie ? a gani na tunda teaching nake sha'awa ai be kamata nayi korafi ba." Da sauri Abubakar yace, "Ba anan ya dace da kai ba twinnie kamata yayi yanzu ace kana wata university d'in kana bada lecture's dan kafi can-canta da dacewa acan, amma nan wallahi tsaf zasu nakasa maka ilimin da kakeji dashi ya kamata ka duba magana ta." Kallonsa yayi har ya shige cikin d'aki sannan ya sauke idanun shi, dama tun ba yau ba tun suna k'anana suke da ban-bancin ra'ayi wajan zab'ar samun gurin aiki sai dai shi Abubakar ya cika burin shi yayin da shi kuma Sadeeq be samu zama pilot ba sai aikin koyarwa a university of sokoto amma yak'i tafiya sai ya tafi ya samu a wani secondary school itama d'in a kauye, sai gashi sam baya jin dad'in ta. Abubakar ne ya dawo ya zauna tare da janyo take away d'aya ya fara cin abincin shi, Sadeeq ya kalle shi tare da ture takardun gaban shi yace, "Twinnie wai ya zancen Ummi kuwa ka kuma komawa kun dai-dai ta ko?!" Abubakar yayi murmushi tare da ajiye spoon d'in hannun shi yace, "Bari kawai twinnie ban koma ba sai aikowa gida da mahaifinta yayi wai ance angan mu a tsaye toh idan na shirya na fito. kaji fa? ni ai Ummi bata cika quality's d'in da nake da burin matata ta kasan ce ba dan haka nace a'a ban shirya ba ko ya ka gani?!" Dariya Sadeeq yayi sannan yace, "Kai ma ka tsaya ruwan ido meye ai bun Ummi tsakani da Allah, yarinyar nan fa yanzu s.s 1 zata shiga kuma gata kyakyawa to meye ya rage maka.?!" "Gayu, twinnie ka san ina son mace 'yar gayu mai aji wadda koni idan ina mata magana sai taga dama zata amsa amma fa Ummi kana magana kafin kakai k'arshe ta mayar maka, no gaskiya akwai wata dai a cikin hospital din mu da suka zo sanin makamar aiki na ga kuma kamar type d'ina ce sai dai ba zan iya mata magana ba karma ta rainani." "Rai ni kuma Abbakar? toh kenan idan kayi auran ma bashi da amfani tun da dole sai wani abun raini ya shiga tsakanin ka da matar ka.." "Kasan kuwa wani sa'in ina jin tsoron yin aure, sabida wani sa'in sai naga ba shi da amfani." "Ikon Allah." Cewar Sadeeq yana yi mai kallon mamaki yayin da Abubakar d'in ya mik'e yayi waje yana son ya samu almajirin da zai wanke musu toilet d'in su. Yana fita ya samu wasu yara zaune suna wasa ya kira wanda suka had'a ido da shi. yana zuwa yaron befi 10 years ba Abubakar ya kalleshi yace. "Kai whats your name?!" Yaron ya kura mai idanuwa kunnuwan shi sai bud'ewa suke dan beji abinda yace ba nan ya fara kwakular hanci har lokacin idanun shi na kan na Abubakar ganin kamar be gane ba yasa shi cewa, "Ya sunan ka?!" Ya dashare baki hak'oran nan yalaye kamar yasha d'orawa kafin yace, "Suna na Sagiru Hamza." Abubakar ya d'auke kai tare da kallon sauran yara, gaba d'aya kaf cikin su babu na za6a har garama Sagirun dan haka ya kalle shi yace. "Zaka iya wanke mana toilet?!" Da sauri Sagiru ya d'aga kai duk kuwa da cewar be gane abinda ake nufi da toilet din ba amma yaji ance wankewa yasan koma me ye zai iya wanke shi tatass. "Toh shiga muje." Abubakar ya fad'a yana komawa ciki, Sagiru ya juyo tare da yiwa sauran abokan nashi gwalo. "Yauwa Sagir kaga ga klin da hypo shi zaka d'auka ka kwanke shi sosai." Ganin inda ya nuna ne yasa Sagiru tabbatar da cewa ban d'aki ake son ya wanke, Abubakar na gama nuna mai ya koma cikin d'aki shi kuma Sagir ya shiga yana wankewa.sai da ya kammala tasss sannan Abubakar ya fito ya bashi naira d'ari biyu ai kuwa ya dinga murna sannan ya tafi gida da gudun sa yana murna tare da burin ramuwar abinda INDO tayi mai lokacin da tana da kud'in ta naira 50 ta dinga siyan awara tana hana su. "INDO..! INDO...!! INDO..!! nima yau zoki ga kud'ina wallahi na samo.." Sagir ya shiga gidan da gudu yana k'iran ta da k'arfi, da gudu ta fito daga ban d'aki hannunta rik'e da buta tana fitowa tayi wurgi da ita tana gyara kullin pant d'inta wanda yayi mata yawa sabida bud'ewar da yayi gashi kamar rai shi kad'ai gareta ta k'arasa kusa da Sagiru tana raba idanuwa. "Wai kai dalla meye kake ta kwad'a min kira ne?!" Be yi magana ba sai kud'in daya nuna mata yana tsalle, da sauri ta ware idanuwa cikin tsananin mamaki sannan tace, "Kai Sagiru a ina ka sato ko kuma waye ya baka kud'i har d'ari biyu haka...?!" "Yarinya wankin ban d'aki nayi shine aka bani ita lada." "Ikon Allah a wane massalaci ne haka?!" Sagir yace, "Ba'a matsallaci bane a gidan malamin ku wannan mesa glass d'in nan." "Tab d'i jam! toh Sagiru nawa zaka bani a ciki?!" Wani banzan kallo yayi mata tayi kallar tausayi tare da cewa. "Dan Allah kabani ko naira hamsin ce kaji kanina wallahi nima wata rana idan na samo zan baka." "Uhh-umm yarinya ba zan bayar ba." Cewar Sagir yana danna kud'in a cikin aljihun shi, ganin haka yasa ta cewa, "Toh kuwa yaro dama Inna tana ta neman kud'in da za'a siyo daddawa da kuka sai kazo ka bayar tun da ai kaima da kai za'a ci tuwan." "Ke wallahi ba zan bayar ba, ke rannan ba da naira goma a hannunki ba Inna tace ki kawo a siyo manja da ita ba amma kikak'i sai yanzu dan kud'in ba naki bane ba zaki ce na bayar a siyo kuka toh ba zan ba da ba." Ganin bashi da niyar bata ko sisi yasa ta fara kwad'awa Inna kira, yana jin haka shi kuma ya zura da gudu yayi waje nan ya barta sai faman masifa take tamkar kud'in nata ne... *HAJJA CE*👈 [7/1, 4:48 PM] Aisha Galadima: *⚗⚗ MUSAYAR ZUCIYA...⚗⚗*                     ♥                  ♥♥          A true life story Na *K.A.S Precious Hajja ce*👈 *HASKE WRITER'S ASSOCIATION*💡 (Home of expert & perfect writer's) *DEDICATED TO* Sanah Isma'il matazu. Page *3* Da sauri ta fito ta biyo bayan sa amma ko kyallin sa bata hango ba,ta ciza le6anta tare da ficewa daga gidan gaba d'aya.Gidan su Maryam k'awarta ta wuce tana wak'ar ta da d'an tsalle wasa hankalinta kwance.malam Sadeeq dake k'ofar gida ya bita da kallon takaici ganin yadda tayi fururu ba wanka,sam bata kula dashi ba sai faman wak'a take tana cewa. "Indo Aisha...ta zariya mai d'an kallabi..." Har tayi kwana sai tayo baya ganin shi da tayi, shi kuwa yana ganin zata dawo yayi sauri zai koma cikin gida be kai ga k'arasa juya wa ba yaji tace. "Wil dam malam. (Well done sir).." K'in kallon ta yayi yana dan na wayar sa domin service yake nema.Ya gane abinda take son cewa so take ta gaida shi, ko me ya kawo well done a tsayuwar da yayi.dan haka Murya k'asa k'asa ya amsa mata,Indo ta washe mai baki tare da matsawa kusa da shi yayi saurin daka mata tsawa ganin yadda take shige mai.kallon sa tayi cikin mamaki ido waje ta kuma bin sa kafin tace. "Malam Sadeeq baka gane ni bane?Indo ce fa ta makarantar gwamnati ta nan unguwar d'an Awaisu. Ka gane ni? Nan tsefawa fa gwamman sakandare sukul." (Tsefawa government secondary school). "Ke! Naji me zan miki ne..?!" Ya fad'a cikin k'ufula domin ta kai shi bango. Ita ma share shi tayi da masifar tashi da yake mata domin tana son yi mai tambaya wadda take son jin amsar su daga bakin sa dan haka masifar shi ba za ta d'aga mata hankali ba. kusa da k'afar sa ta k'ara sa haushin ta ya kuma zuwar mai wuya, tsoran sa d'aya kar 'yan kauyan suyi mai muguwar fahimta sai kauce mata yake amma ta kasa ganewa ya kuma had'e rai amma ko ajikin ta tace. "Malam tsakanin ka da Allah gaskiya da gaskiya zaka gaya min, shin ku 'yan biyu ne, ko kuwa dai ni kake bawa tsoro sabida ina kwaikwayon ka a aji...?!" Wata uwar harara ya narka mata dan yaga alamar kamar zata kawo mai rai ni shi kuma bezo garin dan su raina shi ba, wato ma k'arya yake mata shine zata zo ta k'ure sa dan tsabar ba ta da kunya. Fuskar sa a murtuke ya kalleta yace, "You're very stupid." Tana dariya cikin nishad'i tace, "Sanki u malam Sadeeq, (thank you) wallahi shi yasa kake birge ni sabida ka iya turanci mai kyau da dad'i. Amma dan Allah malam ka d'an fassaramin abinda ka fad'a da hausa he nima in rik'e gurin na iya sosai..." "Zaki bar gurin nan ko sai na 6allaki... mara kunya fitsararriya kawai.." Ya fad'a cikin d'aure fuska. tayi baya-baya tana kallansa tare da kama ha6ar ta tace, "Kai malam! masifa, daga tambaya sai cibi ya zama k'ari shi kuma k'ari ya zama k'ababa. na tafi kuma ba zan je makaranta ba a-he, sai ayi kuli-kulin tara sisi dani.." Ta yi maganar tana tafiya da baya da baya har ta shige lungun gidan su Maryam. tsaki yayi ya koma cikin gida yayi kudurin sai ya gyarawa 'yan makarantar zama. kowa tayi wa dan ba ta je makaranta ba oho mata. yara sai rashin kunya basu san komai ba dak'ik'ai zai nuna musu shima bashi da mutunci. Ranar haka ya wuni yana kunci jefi-jefi yakan yi tsaki har dare yayi be fita ba sabida takaicin Indo da sanya idon 'yan gari domin fita dubu shiga dubu sai sun kalle shi gashi ya tsani saka ido cikin lamuran sa. Washe gari da yaje makaranta Indo bata je ba yaga ashe da gaske take yi, still wata washe garin tayi nan ma babu labarin Indo sai ranar juma'a yana tsaye wajan black board yana koyarwa kawai yaji ana magana a taga, juyawa yayi sai yaga babu kowa domin da taga alamar zai ganta sai tayi saurin yin k'asa, dan haka ya cigaba da abinda yake yi. Can ya kuma jiyo kus-kus yayi a hankali ya kalli gurin caraf suka had'a ido da Indo tana cillowa Sa'ade wani abu a leda, dariya ta sakar masa ya k'arasa bakin tagar yana kallonta. Sanye take cikin house wear hannunta rik'e da faranti an jera kallik'ak'au da yajin masau da alama shi ta cillawa Sa'ade ya had'e girar sa tare da cewa. "Zo nan..!" Ita yake kallo amma sai ta juya wai ko zata ga wanda yake kira amma sai taga babu kowa sai ita, dashare mai baki tayi tare da d'an matsawa kad'an ba sosai ba tace. "Gani malam." "Jeki zaga yo ta k'ofa." Ya fad'a, Indo ta tsuke fuska tare da cewa. “Malam ai ba zuwa nayi ba yau d'in ma tallah nake yiwa mak'ociyar mu. Kasan idan na siyar mata mawa zata bani?” Yayi mata banza ganin ita yake kallo yasa ta juyawa ta dafe abubuwan cikin farantin ta ruga da gudu dan ba zata yadda taje ya hana ta fitowa. Kai ya girgiza tare da komawa ya ci gaba da yin aikinsa kuma a kwanaki biyun alhamdulillahi suna ganewa, tamkar dama Indom ce ke hana su rashin fahimta. Yana gamawa ya fita ya koma ofis haka ya dinga ci gaba da koyar musu har aka kusa fara jarabawa wadda daga ita zasu wuce j.s 2 amma Indo bata sake zuwa ba shima har ya manta da ita har ya Saba ma idan yana kiran suna ya samata absent. Ana gobe za'a fara jarabawa Indo ta dawo makaranta. washe gari aka fara musu sai da suka yi jarabawa hud'u sannan a ta biyar d'in zasu yi English language wato subject d'in malam sadeeq. Kasan cewar tun da aka fara beje ajin ba sai yau da za'a yi tashi jarabawar kuma dole sai yabi aji-aji ya kuma yi musu bayani sannan. Tare da Abubakar suka shiga domin lokacin yazo abinsu gwanin ban sha'awa, zasu gaida su Sadeeq ya hana dan karsu yi hayaniya, can k'arshen aji INdo take ta duk'ufa sai satar amsa take yi cikin littafin Ayuba mati sabida ita bata da ma littafin bare tayi karatu. Tsayawa Sadeeq yayi a gaban alo domin shi bema san ta samu damar zuwa ba ya fara musu bayani. Malamin dake tsare su yana zaune a kujera Abubakar yana tsaye ya hango wata ko d'agowa ba ta yi hakan yasa shi k'arasawa gurin da take ya lek'a yaga meke faru sai yaga ta bud'e littafi sai kwafa take yi har ta kusan cika shafin farko. "Ke.....!" Taji an fad'a dai-dai kunnan ta. tsoro da razana yasa ta sakin tusa burtt ba tare da ta shiryawa hakan ba 'yan aji suka kwashe da dariya ita kuma ta zaro ido ta fara rantse-rantsen kare kai. "Malam wallahi tallahi...." Da sauri ya kifawa bakin na ta mari tayi saurin toshewa da hannun ta. matsawa yayi tare da nuna mata hanya yace. "Fito waje kafin na yayy-yaga ki a gurin nan 6arauniyar amsa.." "Wallahi mal..." Zata tsaya yi mai gaddama ya yi saurin fin ciko ta tare da tura ta gaban ajin tayi taga-taga zata fad'a kan tebur Allah ya temake ta tayi saurin sanya hannu. Kwal-kwal idanunta suka kawo ruwa zata yi kuka Abubakar ya k'arasa gurin yace. "Shanye shi, idan kika bari hawaye suka fito sai na zane ki 6arauniyar amsa." Maida hawayen tayi tana nan tsaye har Sadeeq ya gama yi musu bayani sannan ya kalli Abubakar hace, "Twinnie bar yarinyar nan ko tayi ba dubawa zan yi ba sabida ta yaye kanta ba zuwa take yi ba tayi degree yanzu sai zuwa tallah." "Ohhh! No-wonder ashe dak'ik'iya ce, amma baki yi halin asalin me sunan ba shame on you.. Kawo wannan ta hannun taki da kika sato amsar, ki d'akko sabuwar pepper kizo nan ina jiranki." Tafiya tayi tana gunguni tare da murgud'a musu baki, sabuwar takarda ta d'akko tare da biro taje ya nuna mata gaban alo yace. "Zauna kiyi anan." Kallon gurin tayi sannan ta turo baki kai da kagani kasan zai yi fitsara tace. "Toh malam ai babu abin d'orawa kuma yagewa takardar zata yi" Ba tare da ya kalleta ba dama Sadeeq ya fita yace, "ki d'ora akan cinyar ki kiyi." "Amma malam ai..." Wata uwar harara daya yi mata ne yasa ta had'iye sauran maganar, zama tayi tana zumbura mai baki yace. "Idan kika sake kira na da malam sai na fasa miki baki." Bata sake kula shi ba ganin yafi malam Sadeeq zafi da saurin kai duka, har kowa ya gama ya fita INdo tana zaune a gurin sai raba ido take yi gashi bata rubuta komai ba sai jagwal-gwalo. Ganin bata da niyar kawowa ne yasa Abubakar k'arasawa wajan tayi saurin cukwaikuye takardar ya mik'a mata hannun alamar ta bashi amma taki, "baza ki kawo ba mara kunya?" Baki ta kuma murgud'awa mai aikuwa ya sanya k'afarsa ya doke shi da takalmin sa. INdo ta kurma wani uban ihu tare da fad'uwa k'asa tana ihu tana birgima. Sunkuya wa Abubakar yayi ya d'auki takardar ya sanya cikin sauran tare da bawa invigilator d'in, ko takanta be kuma bi ba sai ma tsallake ta da yayi yabar gurin. Ihu ta kuma saki tana shure-shure har daddaud'an pant dinta ake gani sabida wandon makarantar ya yage d'alibai suka zagaye ta ana bata hakuri da kuma masu yi mata dariya amma bata fasa shure-shuren ba shima malamin yayi tafiyar Sa dan yasan INdo sarai hakan yasa be kulata ba. "Allah ya isa ban yafe ba mugaye kawai anyi satar amsar, shi dama ba malamin muba yazo yana cin zalin mutane..." "Hahaha INdo me tusa burtt..." Uba Aminu ya fad'a yana nuna ta yana dariya, ai kamar jira take yi ta mik'e tare da cakumar sa suka fara fad’a. K'arfi ba d'aya ba shi namiji ya dinga gwarata da alo jikake k'um...k'um amma tak'i sakinsa sabida tsabar jaraba, can akaji Uba ya rushe da wani irin ihu mai had'e da kuka. "Kai..kai...kai! Lafiya meya faru haka.?!" Malam Zubairu daya zo wucewa yaji ihu ya tsaya yana tambaya. "Malam fad'a suke yi." "Waye da waye?!" "INdo da Uba." Ihu Uba yake yana hawaye gashi ya rik'e gaban sa, malam Zubairu ya kallesu ganin INdo na rik'e kugu yasa shi cewa "ku biyo ni ofis yanzun nan." Abokan Uba suka kamashi suka kaishi k'ofar staff room, ita kuwa tahowa tayi tana bugun cinya alamar bala'in be k'are ba taje ta tsaya malam Zubairu yakai takaddu ya ajiye sannan ya fito dan jin kanun zance, be fara bawa INdo damar magana ba yace Uba ya fara yi amma ya kasa sai shasshek'a yake yi da kuka. "Ke kuma gaya min gaskiyar abinda ya faru." Dai-dai lokacin Sadeeq da Abubakar suka fito daga cikin staff room, tsayawa suka yi Abubakar na waya ta fara baya ni. "Tonona yake yi shine muka fara fad'a." "Sai kuma aka yi yaya..?!" "Sai kazo kace mu biyo ka." "Kai Uba me yasa ka toneta gashi ta saka kuka..?!" "Malam cizo na tayi a anan." Ya fad'a yana nuna gurin, duk wad'anda ke gurin suka zaro ido Abubakar dake waya ya zare ta daga kunnansa yana kallon INdo cikin tsananin mamaki yace. "Ke mayya ce? Baki da hankali?ke wace irin yarinya ce ne da kika fitini kowa ne? Stupid,nonsense, what a fool wawuya kawai, mai wasa da maza karya.." Haushin maganar sa da kuma turancin da yake yi bata jinsa yasa ta fara murgud'a baki tana motsa lab6anta alamar magana take yi, da sauri Abubakar yayi kanta zai ham6are ta Sadeeq ya rik'osa yana kad'a masa kai alamar kar yayi yayin da zuciyar Abubakar d'in ke tafasa yanajin wani tururi cikin ransa dan yaki jinin rashin kunya da k'in gaskiya. A hankali Sadeeq ya dafa kirjinsa yana kalon INdo wadda ta makure jikin karfe tana jiran jin saukar duka yace... *HAJJA CE*👈 [7/1, 4:48 PM] Aisha Galadima: *⚗⚗ MUSAYAR ZUCIYA...⚗⚗*                     ♥                  ♥♥          A true life story Na *K.A.S Precious Hajja ce*👈 *HASKE WRITER'S ASSOCIATION*💡 (Home of expert & perfect writer's) *DEDICATED TO* Sanah Isma'il matazu. Page *4* "Aisha zo ki bawa yaron hakuri." Tamkar ba taji ba sai faman wasan ta take yi da k'asar gurin da d'an yatsan ta wanda alama ce ta baza ta bayar da hakurin ba ya kuma cewa. "Aisha ba magana nake miki ba kika min shiru ko..?!" "Malam fa shine ya fara tono na kuma sai na bashi hakuri ta6di jam.." "Duk da haka ki bashi hakuri tun da kin yi mai ba dai-dai ba.." "Hu’...uhm." Ta fad'a cikin k'asan mak'oshin ta, Abubakar yayi kamar zai wuce kawai yayi wuf ya dank'e ta, nan da nan ta fara ihu har wasu malaman suna sake fitowa ya damk'eta ta 6are baki tana ihu yaji wani sumumin wari ya fito daga bakin ta yayi saurin kawar da kai tare da hankad'a ta saitin Uba ta fad'i k'asa bata San lokacin da ta furta. "Allah ya baka hakuri Uba kayi hakuri kaji ka hakura..?!" "Eh." Uba ya fad'a yana share hawaye malamai aka yi ta yiwa Indo fad'a akan karta sake yin fad'a da Namiji sannan aka sallame su. Ana tashi daga makaranta babu wanda Indo ta kula tayi wuce warta, ba gida ta wuce ba kai tsaye ofishin 'yan agaji ta nufa tana zuwa ta sami ogan ya kalleta yace, "Yarinya ya aka yi aiko ki aka yi..?!" Tace "A'a shugaba k'ara na kawo dan ance shari'ar maita bata k'arewa toh wani malamin mu ya Ce min banza maiya jaka, toh ban yafe bane shi yasa na kawo k'ararsa abi min hakkina." "Au ke cema kika kawo k'arar?" "Eh sabida ance nan ake kawowa kafin akai kotu." Sosai ya kalli INdo wadda take faman turo baki tana taunar k'asan hijabin ta da hak'ori. "Toh naji yanzu shi malamin yana ina kuma a wacce makaranta yake koya muku duk da naga inifam (uniform) d'inki na makarantar tsefawa ne...?!" "Eh Shugaba acan nake kuma ma shi ba malamin mu bane d'ayan ne malamin mu amma kaga ya mareni, yayi min kutufo da k'afarsa sannan yace min Mayya, ance shira'ar maita baya k'arewa toh yazo ya fad'a a ina nayi maitar." Shugaban 'yan agaji na k'auyan ya sake kallonta sannan yace, "Ya sunan ki...?" Tace "INdo malam Hamza." "Toh INdo yanzu abinda nake so dake nasan yanzu an tasheku ki bari gobe idan Allahu ya tahemu lafiya he muzo ki nuna mana hi malamin kin ji ko.?!" "Kai! Shugaba, ai tafiya yake yi kuma idan an gama jarabawa ba dawowa zai yi ba a hanyar gidan mu suke kayiwa Allah kayi ma ma'aiki kazo muje ayi Mai jan kunne ya dena ce min mayya da dak'ik'iya." "A'a bada ni zakuje ba bari nasa wani yabiki suje yaji abinda ke faruwa." Ya d'aga murya yana k'iran, "Awaisu! Awaisu!!, zo dan Allah kabi yarinyar nan ta kawo k'arar wani malamin su." Awaisu na zuwa suka tafi suna tafiya suna hira tamkar dama sun saba har suka k'arasa k'ofar gidan su malam Sadeeq wanda shigowar su kenan dan sai da suka tsaya suka yi juyan bak'in mai. "Kika ce nan ne gidan ko?" INdo tace "Eh nan ne suna ciki." Kwan-kwan-kwan, Awaisu ya fara buga k'ofar gidan yana kwad'a sallama. Malam Sadeeq ne ya fito sanye cikin jallabiya ya kalli INdo sannan ya kalli Awaisu cikin rashin fahimta da kuma sanin dalilin zuwansu ya fara magana. "Lafiya dai ko bawan Allah." "Eh toh lafiya ba lafiya, wannan yarinyar ce ta kai k'ara cewar kana ce mata mayya. Toh bata yafe bane yasa takai mana k'orafinta shine shugaban mu yace nazo naji dalilin da yasa kake fad'a mata wannan kalmar." Mamaki da al'ajabi suka cika Sadeeq, sai yanzu ya k'ara tabbatar da hauka da rashin hankalin 'yan garin ya kuma kallon INdo wadda itama shi take kallo yayi shiru yasan Abubakar ne dan haka ya tsaya yana tunanin abin cewa yaji INdon tace. "Awaisu ka tambaye hi idan shine idan kuma ba hi bane toh d'ayan ne ya fito dan tagwaye ne.." Kallonta Sadeeq yayi ya sake tabbatar da lallai bata da kunya, shi kuma Awaisu sai d'aga kai yake yana kallon gidan ko zai ga wani ya fito amma ba kowa hakan da sadeeq ya gani ne yasa shi cewa. "Naga alamar baki da kunya Aisha, toh bazai fito ba ki shiga ki fito dashi fitsararriya kawai. Kai kuma SS ne ko d'an sanda ko soja ko menene da ta d'add'ago ka kuka zo nan..?!" "A'a mu mune 'yan kungiyar agaji na wannan kauyan kuma turo ni aka yi akan naxo naji abinda yake wakana dan tace bazata yadda ba." Cewar Awaisu Sadeeq yayi tsaki cike da takaici sannan yace, "Toh kaji abinda na fad'a idan ba maita ba waye zai ciji mutum a mafitsara? Kuma ma wai fad'a mace da namiji dan iskanci." "Haka ne kam malam kana da gaskiya ke INdo baki da gaskiya dan haka zanje na sanar cewa ga abinda ya had'a dan haka sai ki tafi gida ki dena wannan halin." Awaisu na gama fad'ar haka ya bawa Sadeeq hakuri sannan ya juya ya tafi INdo na kallonsa zuciyarta fal haushin sa. Da taga yayi nisa ta juya zata yi magana sai taga ashe shima Sadeeq din ya shiga ciki ta d'aga murya saitin k'ofar tace. "Kujini da kyau ni ba mayya bace sai dai kunemi mayya, kuma an dena zuwa bokon ai ba aikin Allah bane rawawul ni INdo na dena zuwa tsefawar yo dan banje ba ai ba mutuwa zanyi ba kuje ku cinye makarantar..." Suna jinta suka yi mata banza Abubakar ya shak'a iya shak'a Allah-Allah yake ya shirya yabar garin dan takaici. Ita kuwa tana gama fad'a tayi tafiyar ta gida tana zagin su tare da d'aura aniyar baza ta sake zuwa makarantar ba tunda ai sai taje zasu ganta har suyi mata maganar banza. K'arfe 3:34pm Abubakar ya idar da alwalar la'asar yana jiran Sadeeq su wuce masallaci dan da sunyi sallah yake son dawowa ya wuce gida. Jerawa suka yi suna tafiya suna hira abinsu gwanin ban sha'awa mutane sai kallansu ake yi. Sagiru dake tsaye a k'ofar gida ya hana INdo fita ya tsaya yana kallonsu, ita kuwa INdo ganin yace baza ta fita ba yasa ta komawa cikin gida. Dai-dai katangar gidan zasu wuce kawai Abubakar yaji an cillo wani abu ya rufe mai fuska suka tsaya ya cire yana dubawa yaga hijjab ne yayi dik'il-dik'il dashi ya yarda shi, kafin ya kuma yin taku d'aya yaji an kwad'o mai wani abu a gefen wuyan sa ya kalli k'asa takalmi ne d'an madina silifas yasha d'aurin leda a wajan sanya d'an yatsa suka kalli katangar da ake yo jifan kawai sai suka ga hannu hakan yasa ran Abubakar ya kuma 6aci sai ga k'afa can sai gata ta dirgo tim...! Da sauri suka matsa inda take tana d'agowa ta gansu a tsaye a gabanta bata san lokacin da ta kuma kurma ihu ba tare da juyawa zata kuma kama katangar ta koma gida Sadeeq yayi saurin janyo rigar ta mutane suka taru yayin da INdo ke faman basu hakuri. Gabaki d'ayan ta tsami take yi da zarni Abubakar ya tsinketa da mari tare da dungure mata goshi sannan Sadeeq ya sake ta Abubakar yace. "Baki da mutunci ko?Ke mara kunya kinga abubuwan tsimmar da kika watsa min? Toh ki saita kanki idan ba haka ba kafin nabar garin nan sai na ji miki ciwo idiot kawai sai zarni kike yi mai fitsarin kwance jibe ki dan Allah da wani billanki a goshi kamar zanan one..." Yana kaiwa nan yayi gaba yayin da Sadeeq ya harare ta shima yayi tafiyar sa suka shige masallaci. Mutane kuma suka k'arasa wajan INdo da tayi shiru tana kallon jikin ta. "Kedai INdo wallahi kowa sai yace baki da kunya, suma bak'i har kin fara yi musu.." Cewar Rabi bala wadda makarantar su d'aya amma ita a js 3 take, INdo ta harareta tare da cewa. "Anyi d'in kizo kiyi kuli-kulin tara sisi dani munafuka kowa yasa dake.." "Ke INdo dan ta gaya miki gaskiya shine zaki mata rashin kunya." Wani yaro Bala ya fad'a ta kuma juyawa kanshi cikin masifa tace, "ji banza kai tunda ga kan sunanka ansan kai d'in bala'i ne banza Bala bala'i mtwww." Nan da nan gurin ya kaure ita kad'ai su kuwa wajan mutum goma amma babu wanda ta ragawa, Sagiru k'aninta ya jata suka shiga gida sai da suka kai har tsakar gida sannan ta ture shi. "Dalla can ni kyale ni banza." Ruwa ta kindima a buta ta shiga band'aki shi kuma Sagiru ya kuma fita waje yana cewa, "Dama na barki sunyi miki shegen duka masifaffiya kawai." Fitowa tayi jikinta sharkaf da ruwa wanda da alama wanka tayo amma ba a saka sabulu ba. Cikin d'aki ta shiga Inna tana sallah ita kuma taje ta sake kaya sannan ta d'an d'ibi man shanu ta shafa dama tana sato chuck ta d'auki d'aya ta daddaka tayi hoda da shi ta shafa tayi kwalliya jagirar nan har wajan kunne ta sanya kantakile a lab6anta sannan ta d'aura d'an kwali tayi waje Inna na ta faman kiranta amma ko waigowa bata yi ba. K'ofar gidan taje ta zauna tana jiran su dawo, ana idar da sallah suka dawo gida tun daga nesa suka hangota kamar aljana dariya ta kusa kama Sadeeq ya daure yak'i yi a fili yayin da yace wa Abubakar. "Twinnie ga tanan fa kayi mata gorin wanka tayo tazo ta nuna maka." Dai-dai suka je k'ofa Abubakar ya kalleta wani takaici ya kuma kamashi INdo tace. "Gani yanzu kunsan abinda yasa bana kwalliya? Sabida mazan garin nan sun fiya kallona shi yasa amma ni bana zarni." Ta fad'a tana bubbuga kanta tare da sosawa, mtwww "ke wai kinga sa'anki anan gurin ne?" Kallon shi tayi tare da kura mai ido tamkar zata cinye sa ya d'aga hannu kamar zai bugeta tayi saurin matsawa tace. "Yoo ni ina ruwa na wannan ai ba wasa bane kuma idan anyi duniya da manzo na dena zuwa makaranta wata za'a sake min irin ta 'ya'yan gidan kansilan mu." Mtwwww Abubakar ya ja tsaki tare da shigewa gidan, itama ta doka cinyarta ta kalli Sadeeq tace "Duk haka kuke babu me imani." Sadeeq ya bita da kallo yana tunanin k'ila tana da aljanu yace. "Kije kiyi brush." Abubakar daya fito da car key dinsa yace. "Bakin ta kamar kashi. Kinga yadda ake son aga hakora ba irin naki ba kamar kina shan d'orawa." Ya fad'a yana nuna mata hak'orinsa fari kal. Wucewa yayi gurin motar sa Sadeeq yabi bayan sa dan suyi sallama, suna kallon sanda ta wuce tana sanya k'asan hijabin ta tana goge hak'orin. Sallama suka yi abubakhr na sake bawa Sadeeq shawarar ya k'arbi transfer ya k'ara da cewa. "Bazan sake zuwa garin nan ba sai dai na hakura har ka dinga zuwa can gida ma dinga had'uwa amma wannan garin beyi min ba." "Insha Allahu doctor karka damu kayi min addu'ar abinda yafi alkairi." "Toh amin ni na wuce." Suka yi sallama ya tafi shima ya Shiga gida. Tunda ga ranar kuwa har aka yi hutu Sadeeq be sake ganin INdo a makaranta ba sai dai a unguwar su ya ganta suna wasa ko da farantin tallah.. *HAJJA CE*👈 [7/1, 4:49 PM] Aisha Galadima: *⚗⚗ MUSAYAR ZUCIYA...⚗⚗*                     ♥                  ♥♥          A true life story Na *K.A.S Precious Hajja ce*👈 *HASKE WRITER'S ASSOCIATION*💡 (Home of expert & perfect writer's) *DEDICATED TO* Sanah Isma'il matazu. Note:- Assalamu alaikum masoya wannan labarin, dan Allah adalci d'aya zaku yi min idan kuna so toh ku ringa adanawa. Idan nayi nisa kuka ce na turo muku sai na rasa yadda zanyi gashi wayar ba lafiya gareta ba dan Allah kuyi min wannan agajin please.🤭 Page *5* Tafiya take tana dirzar hak’oran ta da k'asan hijjab ko zata samu suyi fari itama, ai kuwa da ta gogo zata duba jikin hijjabin taga gurin yayi yellow ta girgiza kai tare da cewa. "Kai...! Kuma fa da gaskiyar sa wallahi, dan gahi ina kankarowa yalo na fitowa, amma shi hak'oran sa har wuta-wuta suke yi sabida kyau." Wani shago ta tsaya a nan kusa da gidan su Sahura ta kalli me shagon tace. "Idirisu kana siyar da burushi da abin matsawa...?!" Yace "A'a bana siyo shi INdo sabida ba'a siyan shi, sai dai kije kasuwa ranar laraba ki siyo." Tsaki tayi tare da fad'awa gidan su Sahura, ita dai sam ba ta son zaman gidan su domin bata ta6a yin cikakkiyar awa d'aya sai ta fita, bata taya Inna da aikin komai sai dai da taji yinwa taje taci idan ba'a gama ba ta hau sababi. Sai kusan magariba sannan ta koma gida shima dan tana son tambayar baban su kud'i zata je mahad'a wato inda 'yan mata da samari ke had'uwa suyi hira. "Baba sannu da gida." Yana jin haka ya san akwai abinda zata tambaye sa dan haka yayi mata banza, ta kuma fad'a sai ya d'aga mata kai kurum ta ciza yatsan ta cikin ranta tace, "Wallahi sai ka bani abinda nake so, kaji shi daga gani na baba yayi wani shiru." Kusa dashi ta k'arasa ta zauna shi kuma da yake a kishin gid'e yayi saurin dan ne aljihun sa me kud'in a ciki dan ya san tun da ta fara wannan shisshige mai d'in toh rok'on sa zata yi shi kuma naira d'ari da sittin ne garesa kuma goma ba zai bata ba dan yau da kyar ya samu a gurin sana'ar sa. INdo ta cire hijjab d'in jikinta sannan ta kalli mahaifin nasu duk da ya had'e rai hakan besa taji zata fasa tambayar Sa ba, cikin rashin ladabin magana ta kallesa tace. "Baba nera (naira) hamsin zaka bani anjima zanje mahad'a, daga can idan naje kaga zan siyo burushi harda abin matsawa sai kuma ka bani nera ashirin wadda zan siya abubuwa naci.." "Bani da kud'i uwata yanzu, amma ki bari gobe idan na samu zan baki." Kallonsa tayi da alama bata yadda da abinda yace ba, ganin tana kallan sa yasa shi kuma kishin gid'a kan aljihun kud'in yana k'ara volume d'in rediyon sa duk kuwa da yana jin ana k'iran sallar magriba amma ba shi da alamar ta shi yayi alwala. "..'Yar nan zo kije kiyi alwala bana jin yauma ko sallar asubahi kinyi bare kiyi sauran." Inna ta fad'a tana kashe wutar kararen da ta gama tuwo. INdo naji ta turo baki sam bata kaunar taji ance tayi wani abun a harkar rayuwar ta abu in dai ba wasa bane ko kuma naci toh sam bata kaunarsa bare tayi. Bacci ma ban da 6arawo ne da baza ta dinga yi ba, ta mik'e tsaye ta shiga d'aki ganin baban nasu bashi da niyar bata ko sisi. Garam-garam inna ta jiyo ta tana tatta6a mata kwanukan jeranta na d'aki, saurin bin bayan ta tayi nan taga sai faman bud'e-bud'e take yi mata cikin fad'a inna ke magana tana kallon INdon tace. "Me kike nema anan? Ko kinyi ajiya a gurin ne zaki d'auka..?!" INdo ta ajiye kwanon hannunta kana ta kalli Innar ta tace, "Inna fisabilillahi baba ba zai bani kud'i naje mahad'a ba, salan naje naga su maryam su sahura Sa sauran k'awaye na suna siyan abubuwa su yi min gori...?" "Toh banda abinki baya ce miki babu ba idan ya samu zai baki, toh kiyi hak'uri mana nima kuma basu gare ni ba bare na baki." K'ad..! INdo tayi da harshe alamar jin haushi sannan tayi waje fuuuuu babu wanda ya kula ta shima baban nasu yana ji ana k'iran sallah amma ba shi da niyar tashi yayi yana kishingid'e abin sa. Tana fita ta shiga gidan Rukayya wadda amarya ce aka kawo ta unguwar take yin kayan siyarwa su alawar madara, gullisuwa, k'alli-k'a-k'au, yajin masau da dai sauran kayan siyarwa na yara, shine INdo take zuwa ta kar6a tana siyar mata sai ita kuma ta ringa bata ladan nera talatin ko asshirin da biyar. "Uhm su INdo sai yanzu aka ga damar zuwa ko..?!" Rukayya ta fad'a tana kallan ta, zama tayi a kan tabarma tana dariya Rukayya ta idar da alwala tazo ta zauna kusa da INdon tana kallonta tace "Toh me ya hanaki zuwa yau da wuri gashi ma har an siyar sabida yau na samu 'yan sari duk sun siye sauran albishir kawai na naira tamanin.." INdo ta zaro idanuwa tare da dafe k’irjinta yau kenan ba ta da kud'in siyan gyad'a, cikin karad'i tace, "kai Rukayya amma ko ki jira nazo ba komai tun da abin 'yar haka ce..!" Rukayya tace "A'a INdo ina zan ta jiranki bayan har gidan Ku na tura kizo aka ce min bakya nan, sai kawai na zauna jiranki bayan ga kustoma sun zo.." "Ai shikenan yanzu ki bani albishir d'in na tafi dahi.." Shiga cikin d'aki Rukayya tayi ta fito hannunta rik'e da leda ta mik'a mata. k'ar6a INdo tayi ta lek'a cikin ledar sannan tayi dariya cikin ranta tana addu'ar Allah yasa yau ta had'u da Shu'aibu saurayin ta ya ce ta shanye ya biya kud'in. Mik'ewa tayi tasa takalma tana cewa Rukayya. "Toh na tafi sai na dawo Rukayya kiyi mana adda'a (addu'ah).." Tayi dariya tana gyara hijabi tace, "Toh INdo Allah ya ba da sa'a a siyar baki d'aya." Tana fita ta d'auki guda d'aya tare da jefawa cikin bakin ta, zak'in ya gauraye mata bak'i ta lumshe ido tare da sosa cikin kunnanta. K'ofar wani shago taga malam Sadeeq hakan yasa ta k'arasa tamkar bata ganshi ba ta kalli me shagon tace. "Wale kana sai da burushi da abin matsawa..?!" Wale me shago yana k'ok'arin bawa malam Sadeeq klin da sabulon da ya siya yace. "Eh guda nawa za'a baki..?" INdo ta kuma kallon malam Sadeeq sai taga ko kallon tama baya yi sai kud'i da ya zaro yana k'irgawa zai bawa me shagwon ta ta6e baki. Yana sane ya zamar da naira d'ari k'asa as in be sani d'in nan ba sannan ya mik'awa wale kud'in sa ya mai da sauran aljihu. INdo na ganin kud'in tayi kamar zata d'auki dotse kawai ta d'auke d'arin ta maze sai mazurai take yi taji ko wani zai ce ya ga sanda ta d'auka, da taga babu wanda yace komai sai ta mik'awa wale kud'in tana cewa. "Toh bani guda d'aya-d'aya ka bani canji na." Sadeeq na gani ya wuce yana mamakin ta ashe har sace-sace da d'auke-d'auke take yi, lallai yarinyar bata da tarbiya sam sai dai be san dalilin da yasa yak'i yi mata magana ba bayan ya san hakan da tayi ba dai-dai bane ba a cikin addini dama rayuwar ta gaba d'aya. D'akko mata yayi sannan ya bata canjin naira talatin ta k'ar6a tayi gaba abinta. Cikin mararta ta tura brush da makilin d'in sannan tayi gaba tana d'aukar albishir tana sanyawa a cikin bakinta sai farin ciki take yi yau ta fito da sa'a zata yi brush ta basu mamaki gobe. Tana zuwa zata sha kwana taji ance mata "ke zo nan." Ta juya tana kallansa ganin malam Sadeeq yasan ya ta rik'e kugunta tana girgiza jijinta tana harararsa "yes.." Ganin yadda take mai ne yasa shi kuma d'aure fuska yace mata "fito min da naira d'ari ta da kika d'auke ko kin d'auka ban ganki ba." INdo najin haka ta gyara tsayuwar ta tare da sake danna brush d'in dan karya gani, cikin wayan basarwa tace "kai malam Sadeeq kud'in ka? yaushe na d'auka zaka ce in baka...?" Matsawa yayi kusa da ita tayi saurin yin baya ya mik'a mata dogon hannunsa tare da bud'e mata tattausan tafukan hannun da nufin ta sako mai kud'in sa ta kallesa tana muzurai tare da tsuke baki cikin yake tace. "Ni ban d'auki kud'in kaba, a inama muka had'u bare na gani na d'auka." Ya kuma had'e rai sai taga yayi mata kwarjini k'irjin ta ya hau harbawa ta fara jin tsoron Kodai ya ganta, toh me zai mata ko ba malam Sadeeq bane d'ayan ne masifaffan. Ganin yak'i d'auke hannunsa yasa ta tabbatar da cewar lallai ya ga sanda ta sace amma ya aka yi be nuna ya ganta ba a gurin? Cikin borin kunya tace. "Toh na d'auka abakacin kalamin herrin maita da kayi, ai dama nace ban yafe ba toh yanzu ka biya ni hike nan." "Ki mik'o min kud'ina nace bana son maganar banza kina jina..." Jin yana masifa yasa ta cewa "Toh na siyo burushi dasu ba kune kuka min wulak'anci ba, shi yasa nasiya nima na dinga yi wallahi a gobe zaku ga bakina sai yafi naku fari." Tana kaiwa nan tayi gaba haushi da takaici suka cika Sadeeq yama rasa gane meye matsalar yarinyar sai dai yafi dan gana hakan da cewar k'ila tana da aljanu. Gida ya wuce domin so yake daya gama had'a result ya tafi gida tunda anyi hutu sai kuma an dawo wanda yake son kafin sannan ya samu canjin gurin aiki. Cikin kwanaki uku ya kammala komai yabar garin sai farin ciki yake yi dan ba k'aramin takura yake yi ba da k'auyan. _Fatan alkairi ga masu bibiyar wannan labarin, ina ganin sakwannin ku Allah ya bar kauna. Muje ga page d'in gaba wanda daga shi ne zaku fara gano sirrin cikin labarin._🤭 *HAJJA CE*👈 [7/1, 4:49 PM] Aisha Galadima: *⚗⚗ MUSAYAR ZUCIYA...⚗⚗*                     ♥                  ♥♥          A true life story Na *K.A.S Precious Hajja ce*👈 *HASKE WRITER'S ASSOCIATION*💡 (Home of expert & perfect writer's) *DEDICATED TO* Sanah Isma'il matazu. Page *6* Zaune suke a cikin d'akin su, babban d'aki ne domin a da a matsayin sitting room yake lokacin da suka taso suka zama samari yasa abban su ya bar musu shi suka gyara shi aka sanya musu katifu guda biyu d'aya na gefen hagu d'aya na dama sai durowar kayan su ko wanne ya d'auki gefe d'aya domin kayan nasu ya bambanta. Abubakar shine yafi son sanya k'ananun kaya sa6anin Sadeeq daya fi son manya kamar su shadda boyal da sauran su. Shiru Sadeeq yayi idanunsa a sama kai da ka ganshi kasan ya fad'a cikin zurfaffan tunani, kallan sa Abubakar yayi cikin ta6e baki yace. "Twinnie ya aka yi ne kake wannan zurfaffan tunanin?" Sadeeq ya numfasa tare da tashi zaune ya janyo kofin zobon da Maman su ta aiko musu dashi ya d'iba yasha sannan ya zuba wani ya mik'awa Abubakar yana cewa. "Twinnie ina tuna nin maganar Mama ne ta jiya, kaga tace Abba zura mana ido kawai yake yaga dame zamu fara. Gaskiya ni yanzu na fara tunanin gara na fara yin gini na tunda ya riga ya bamu filayen kuma yace duk inda muka ga ya kakare mana toh muyi mai magana gara kawai nazo na fara dan ina son lokacin da zan fara neman aure toh ya zamto koda ban k'arasa ginin ba to ya zamana sauran k'arashe shi yasa kaji nayi shiru ina tunani." Kai kurum Abubakar ya jin-jina sannan ya mik'e tsaye, shirin tafiya asibiti yayi ganin be ce komai ba yasa Sadeeq cewa. "Toh kai naji baka ce komai ba ka kuma tashi zaka tafi meke nan hakan da kayi..?!" Shafa gashin kansa yayi tare da d'aukar turare ya fesa. "Karka damu twinnie da rashin maganata, kasan dole idan naga ka fara nima na fara har addu'a nake mana Allah yasa mu samu matan aure 'yan biyu kawai mu aure su, dan haka karka damu kai dai ka fara samo matar tukun na." Sadeeq yayi dariya tare da komawa ya kishin gid'a, yana murmushi yake cewa. "Lallai kuma a ce mun had'a gida kuma kamar su d'aya like me n you, ta6 ai sai mu kasa ganewa haka kurum wata rana in dirfafi matar ka ko kai ka shigar min gona toh a'a.." Abubakar ya kyal-kyale da dariya irin wadda be ta6a yi ba ya kalli Saddeq yana nuna shi da yatsa yace. "Amma dai my twinnie muguwar fassara gareka, babu abin da zai faru kai dai kayi mana fatan alkairi.." "Toh ai gaskiya na fad'a ko kuma matar ka ta fito ta ganni tayi tunanin kaine tazo ta mak'ale min ni bazan hanata ba tunda jiki da jini, ko kuma tawa matar ta ganka tayi tunanin nine gaskiya twinnie ka dena yi mana fatan auran twins dan ni gaskiya ka san bani da kauda kai, shi yasa ma da Abba yace baxai bamu gida kusa da juna ba banji haushi ba." "Hahaha twinnie ai ina tausa yawa duk wadda zata aure ka wallahi domin zata sha wahala, kana gani a yanzu ma baka da auran sai kayi dreaming sau uku hud'u bare kana ganin ta." Murmushi Sadeeq yayi tare da gyara kwanciyar sa yace "twinnie kayi tafiyar ka kana yin late ga marasa lafiya can na jiranka ni bacci ma zanyi dan ban gama va ka tashe ni bye." "Hmmm ka dai kore ni toh Allah ya baka mata a kauyan daka baro tun da baka son muyi iri d'aya." "Wallahi ba amin ba, duk basu da hankali musamman ma INdo kai! wannan yarinya ba hauka ne yake damunta ba harda jahilci kasan shi yafi hauka. Gasu k'azamai tunda naje garin banga wayayye ko wayyayi ya ba wallahi, ba amin ba dan kamar yadda kake son nutsattsiyar mata haka nima nake so kuma 'yar gayu mai ilimin zamani da na addini.." "Twinnie kad'auki zafi da yawa so sorry dan Allah, bari naje na dawo bye.." "Ok sai ka dawo." Da haka suka rabu sai da Abubakar ya shiga cikin gidan yayi sallama dasu Maman sa sannan ya fita, yayin da Sadeeq ya kwanta duk da cewar maganar da d'an uwan nasa ya fad'a tasa baccin ya gudu sabida takaici hakan yasa ya tuno da INdo yaja tsaki tare da mik'ewa ya koma cikin gida ko zaiji dad'in ranshi a gurin su Maman su. *IHSAN MEDICAL CENTER* Ahankali yake karasawa asibitin na ihsan medical center dake unguwar sultan road nassarawa gra agarin na kano,sanye yake cikin kananun kaya kirar suit blue tacikin kuma fara ce hannunsa rike da jakar laptop d’insa fuskarsa sakale da farin glass se bulbula kamshi yake haka yashiga harabar asibitin,yana shiga ya hango nurse hidaya k’ok’arin juyawa yake ta cinmashi da sauri, “Welkm Doctor,Ina kwana..?!” “Fine Alhamdulillah nurse hidaya..” Yana gama fada yai gaba ya barta wajen Office d’insa ya nufa inda sunansa ke rubuce boldly ajikin k’ofar office din ‘Dr Abubakhr’ kamar kullum Mani Cleaner ne aciki yana tsaftace office din se mopping terrazzo din yake dake ta shekin kyalli,da sauri Mani ya tsugunna yana kwasar gaisuwa “Sannu da xuwa yallabai Barka da safiya” “Barka dai Mani.” Kan kujera dr abubkhr ya xauna yana dudduba files din kan tebur din one by one,har Mani yakarasa ya feshe office din da freshener, “Yallabai na kammala” “Yawwa Mani godia nake xaka iya tafiya” Har Mani yakai kofa yadawo yana sosa keya, “Yallabai anbani sako wajenka amma wallahi na sha’afa da sunan,nurse dinnan ce de da tai transfer daga Cotonou” Sarai abubkhr ya gano wacece naccaciyar yarinyar data nace masa ce, “To Mani ba damuwa tunda kamanta sunan kaje kawai” Shiru Mani yai da alama ya zurfafa tunani be jima ba ya dago yana murmushi, “Yallabai natuno nurse natasha ce da sassafe xuwana kenan tabani sako nabaka nikuma hartamin alkhairin Naira dubu yallabai” “Toh madallah”cewar Abubkhr tareda shan kunu Kyakkyawar farar takarda datasha xanen heart Mani ya ajiye akan tebur se faman sosa keya yake don wannan bashine karo na farko ba da nurses suka sabayiwa ogan nasa haka,cikin dakakkiyar murya Abubkhr yace “Jeka Mani sena neme ka..” “To Yallabai Nagode ahuta lapia..” Mani nafita abubkhr yaja tsaki ko duban takardr beyiba ya mike don yin round na patients fitarsa kenan suka kusan yin gware da nurse Deexah uniform dinnan sun matse koina na jikinta ya bayyana se wani rausaya take tana karkada jiki, “Dr..Pls”tace hakan cikin wata irin siga “Please what ?!inada patients daxan duba pls..”yakarasa hade da kaucewa ta gefanta xe wuce tai hanxarin shan gabansa bayan tahada tafukan hannayenta biyu sama alamar roko, “Dan Allah dr ka saurareni minti d’aya pls” Allah data ambata yasanya shi tsayawa ba tare daya karasa tafiya ba amma bejiyo ba fuskarsa kan agogon dake daure a hannunsa yana jiran minti dayan ta cika, “Ki magana kafin minti dayan ki tacika pls” “Dr Meyasa kake mun haka? Kaso me sonka,ka agaxawa xuciyata kaceto ta daga fadawa kogin halaka,duk asibitin nan babu wanda na xaba amatsayin wanda zuciata take muradi sekai” Karasa maganar ta yayi dede da cikar minti dayan data ambata don haka yai gaba abinsa yashiga bin round na patients sedaya kammala tsaf sannan yashiga office din abokinsa wato dr luqman, Sundan taba hira sunayi suna tafawa sannan luqman yashigo da wata hirar, “Nikwa Abokina nagaji da kawo korarrafin da ake kawomun akanka wlhy,yanxunnan nurse deexah tafita hawaye kwance shabe shabe kan fuskarta dukde akan ka,dama yanxun nake maganar koba ka shigo ba xanxo na sameka don nikam nagaji” Murmushin takaici Abubkhr yayi cikin nutsuwa yace, “Toh Aboki bani shawara shin mexanyi akai?” “Ni Ina ganin kaxabi d’aya kawai ka aura kaga ai dole sauran su kyale ka ko?!” Ajiyar zuciya Abubakhr yai kafin yace, “Gaskia Aboki kabani mamaki wallahi domin bantaba saka a sahun mutanen daxasu bani shawarar naxabi d’aya daga cikin nurses dinnan na aura ba,karka manta duk wani namiji yana sone ya auro yarinya yar mutunci me dattako da sanin yakamata wadda ‘yayan daxata haifa ma xasuyi alfahari da kasancewarta uwa tagari, To axahirin gaskia de magana d’aya ce xanyi wallahi duk cikin nurses dinnan babu wadda xan iya xaba a matsayin wacce xan dauka nakai ta gidana wai amatsayin matata ta aure,Kowa Allah ya hadashi da rabonsa kawai ko ya kagani?!” Shiru dr luqman yai yana cin faratansa da alama yarasa tacewa,knocking akai a kofa har sau uku hakan yasanya abubkhr bada izinin shigowa bayan yace, “Yess” Shigowa tai sanye cikin abaya baka bakinta dauke da sallama hannuwanta rike da files cikin siririyar muryarta kamar anbusa sarewa tace, “Gashi Doctor,duk nagama komai har room 13 dakace nayi mata inducing ruwan..” “Okay nurse Mareeyah thank you..Xaki iya tafiya” Dama abinda Mareeya ke jira kenan tai hanxarin ficewa abinta,baki galala abubkhr yabude yanabin k'ofar data rufe da kallo kafin yadawo da kallonsa kan Doctor luqman cikin sauri yace, “Dr ai naxatan nurses d'innan sun gama aikinsu sun koma ya kuma Naga wannan?!” “Oh mareeyah riketa mukai wallahi yarinyar ta iya aikinta ga hankali da nutsuwa wallahi ba ruwanta da shiga harkar mutane kullum ita kad’ai xakaga tana aikinta” “Mareeyah..”Dr abubkhr ya maimata sunan “Kwarai sunanta mareeyah..A’a kode kafada’a da...”ai luqman ne k’arasa ba abubkhar yai hanxarin ficewa Cikin sa’a ya hangota tsaye a corridor tana shimfida sallaya xatai sallah, “Salam alykm..”cewar Abubkhr daga bayanta.. “Wa alykm Salam”tabashi amsa tana k’ok’arin gyara mayafin data yafa Ya salam,,abubkhr yafurta azuciyarsa Dakyar da lalubo salati yasamu ya saisaita kansa kamar bashi ba yace, “Dama uhm..Idan baxaki damu ba magana nakeso nayi dake” “Babu damuwa amma xanyi sallah de tukun..” “Tohm shikenan take ur time xanjira”cewar abubkhr Ya jima azaune sedata idar tai addu’ointa tukun sannan ta nannade praying mat dinta ta mayar cikin jaka, “Ina jinka dr..” “Okay.. Sunana Dr Abubkhr..” “Allah sarki..Ni sunana mareeyatul qibdiyya.” “Nice name qibdiyyah,” Nande abubkhr yashiga gaya mata meke tafe dashi da abunda ke cikin zuciyarsa,itade mareeyah kawai kallonsa take tana mamakin dama yana magana haka?!Abubkhr be bar maareryah ba har seda ya tabbatar ya dana mata tarkon son sa tukun sannan sukai exchanging numbers zuciyarsa fes yakoma gidah, Kullum de abinda ke faruwa kenan abubkhr har gidah yake xuwa xance wajen mareeyah ashema basuda nisa su su abubkhr suna unguwar Court Road ita kuma Mareeyah tana Hausawa,Sosai suke gwangwaje soyayya abun su shikuwa sadeeq har yanzu be samu wadda ta kwanta masa ba duk ya gwada amma babu sa’a ga cuku cukun transfer dayake nema amma yakasa samu haka ya hak’ura yafara shirin komawa makarantar tsefawa dake kauyen Sani a k’aramar hukumar sumaila.. **** Ranar asabar da safe sadeeq yatasamma titin sumaila bayan yasha adduoi daga mahaifansa da kuma dan uwansa abubkhr wanda sam be so komawar d'an uwan nasa kauyan kayayau d'inba, Yana shiga cikin unguwar kuka sunan unguwar tasu kenan ya fara jiyo hayaniya sama sama be tabbatar da muryar ba seda yaxo daf da dandaxon jama’ar da suka taru suna kallon fadan da ake ta muryarta yagane kowacece siririn tsaki yasaki jin muryar INdo ce dan turmutsawa taron yai ya hangota sanye cikin kodadd'un kayanta se jurwayen fitsari riga daban xani daban d"ankwali kuwa ba'a xancensa se tumurmusar fad'a suke da wasu yara maza kuma duk itace me karfin ciki,wani daga cikin taron ne yace “Ke y’ar nan kome sukai miki ki hak’ura ki kyalesu tunda ke macace dan allah” Cikin turo baki had'e da k'ank"ace idanuwa tana girgixa kugunta data d'aure da shamilallan hijabinta tace, “Ta kwarankwasa baxan hakura ba,Babban bala'in can,se in xauna gani sokuwa sumin lefin sannan na hakura wallahi babu xancen hak’uri a dishenari(dictionary)na ramuwa ta da ta taxama dole..” Tana gama fada tacigaba da kokawar da take yu cikin xafin nama sadeeq ya k'arasa cikin su ya wanke mata fuska da mari hade da hankadata gefe yatsan sa yasa yashiga nuna ta, “Ke wai wacce irin kidahuma ce ne eh?! Kina mace kike fad'a? fad'anma da maxa dandaxon mutane akanki ko kunya bakya ji? Tukun nama me akai miki da kika kamasu kina duka kaman wata tinkiya..” Rike baki Indo tai tana kada Kai “Kai ka Kai Kai Kai wacece tinkiyar?!” “Kece tinkiyar” “To wallahi ka bude kunnuwanka kaji niba tinkiya bace kuma kwarankwatsa ka kara cemin tinkiya seka gani. Haba nifa kana shiga rayuwata da yawa makaranta ce de nace ni INdo Malam hamxa nadena xuwa tsefawa inifam d'ina ma na yadashi amma saboda tsabar shisshigi da neman sani seka tsoma wannnan bakin naka a xancen da ba naka ba” Tana gama fada ta shuri bokitan su ubale da idi na talla da suke fad'a tai gaba dasu tana sharara uban gudu,ganin haka yasanya su ubale binta a d'ari suna rokonta da tabasu bokintan tallansu da ta kwashe, Karkad'a kai kawai sadeeq yai wani b'angare na zuciyarsa na tabbatar masa da lallai yarinyar nan ba aljanu bane kad’ai da ita Lallai babu shakku aciki kwakwalwarta ta tabu, da haka ya k'arasa gidansa yashiga bakinsa d'auke da sallama tamkar da mutane a ciki. *HAJJA CE*👈 [7/1, 4:53 PM] Aisha Galadima: *⚗⚗ MUSAYAR ZUCIYA...⚗⚗* ♥ ♥♥ A true life story Na *K.A.S Precious Hajja ce*👈 *HASKE WRITER'S ASSOCIATION*💡 (Home of expert & perfect writer's) *DEDICATED TO*:- Sanah Isma'il matazu. _Yau page d'in nakine k'anwara ta gidan mu, ki sani kina cikin ran Hajja domin Hajja takici my *MISS HAFCY BCH* dear kidena damuwa kina raina kun zama H³🤙mu shirya kinji..💋_ Page *8* INdo kuwa tunda ta koma gida take wanke hakorinta ko abinci k'in ci tayi sabida kar yayi daud'a malam Sadeeq ya hanata kyauta. kwanciya tayi male-male a tsakar gida kan tabarma tamkar me yin azumi, takaici da haushi suka cika inna ta kalleta tana daga tsaye Innan tace. "Ke! 'Yar nan ki rufawa kanki asiri kizo kici abinci kin ganin min sakarya, banda malamin naku mugune taya zai hanaku cin abinci sabida wani an goge baki, toh bari ki kashe kanki ai kinyi wa kanki..." INdo tayi shiru tana ci gaba da rik'e ciki tana birgima, baban su ne ya shigo ganin yadda INdo keyi ne yasa shi tambayar inna nan ta sanar mishi aikuwa ya fara fad'a tare da cewa ta tashi taci abincinta amma ko motsi INdo tayi shiru sai hawaye da take fitarwa a hankali. Juyawa baban nasu yayi direct ya wuce gidan da Sadeeq yake ciki, kwankwasawa yayi yazo ya bud'e sam be san shiba dan haka ya fara mai kallon rashin fahimta baban INdo yace. "Sunana malam Hamza uban INdo d'alibarku ta makarantar tsefawa, ga 'yata can zata mutu tak'ici tak'i sha sabilida kunsa musu dokar yin buruhi. Toh bazai yiwuba, tun wuri kaje kasa taci abinci dan idan ta mutu akan wata kyautar ku ba yafewa zanyi ba kur'anikuwa.." "Subahanallahi malam ai ni ba haka nake nufi ba itada ma ba..." Sadeeq be k'arasa magana ba malam Hamza ya cafe zancen ta hanyar d'aga masa hannu yace. "Karkayi min wani batukaji ko, tanacan tana malan geruwa dagani har uwarta munyi-munyi taci abunci tak'iya wai kar bakinta yayi daud'a. Ita Uwata ai batada jimirin yinwa ko azumi goma bata iyawa dan haka kokaje kasa taci abinci konaje har gidan protocol (principal) d'in nayi mai bayani zaka kashe mana 'ya'ya." Tsaki Sadeeq yaja a k'asan zuciyarsa sannan ya rufe gidan ya kalli baban INdo yace "Muje toh amma ni ba haka nake nufin suyi ba." Kwance suka tarar da ita tayi shame-shame tamkar wadda zata mutu gaban malam Sadeeq ya buga mamaki da tsoro suka dirar mai cikin sanyin jiki ya kalli INdo bakin sa yayi mai nauyi ya daure dai yayi mata magana cikin dakiya. "Aisha tashi zaune please." Da kyar INdo ta samu ta iya d'ago kwayar idonta tana kallon malam sadeeq d'in yayi mata alama da ka nan ta mik'e zaune da kyar jikinta duk yayi fututu da k'asar gurin da ta kwanta rigar jikinta daga wajan hammatar ta yage sikert d'in ma duk yasha faci tana son mik'ewa amma ta kasa, hankalinsa ya kuma tashi lokacin wayarsa na ta faman ringing amma ya kasa d'agawa bare yasan ko waye. Daurewa yayi ya kuma matsawa kusa da ita yana kallonta yace. "Aisha tashi kici abinci ai ni ba haka nake nufi ba, kinga idan kin gama cin abincin ma zaki iya yin brush d'in amma ba'a zama da yinwa idan ba haka ba mutuwa ake yi tashi kinji." Kasa mik'ewa tayi saida baban ta yace da innar ta mik'ar da ita sannan aka zaunar da ita ta jingina da jikin bango jikin duk babu kwari tayi zuru-zuru da ita kai daka ganta kasan tana cikin wani hali. Kallon Inna malam Sadeeq yayi gabaki d'aya tausaya musu yake sabida ganin halin da suke ciki na rashi, ya karyar da baki yace. "Mama a kawo mata abincin taci." Sai Inna taji wani banbarakwai daya kirata da Mama yayin da INdo ta ke numfashi da kyar dan da kyar take iya bud'e ido. Inna ta kawo dambun mazara ta turawa INdo gabanta Sadeeq ya kalli kwanon sam babu alamar akwai mai a ciki ya kuma kallon INdo wadda ta luma daddaud'an hannunta wanda duk k'asa ta 6atashi yaga ta fara watsa danbun cikin bakinta, mamaki yasa shi yin shiru ba tare da yayi magana ba har ta cinyee besani ba yana tsugunne yana tunani. Sai da ta gama cinyewa sannan Malam Sadeeq ya mik'e, ya yiwa Inna sallama sannan ya fita. A k'ofar gida ya tarar da baban INdo nan ya kuma bashi hak’uri da kuma k'ara yi mai bayanin abinda yake nufi akan su, mahaifin INdo naji ya dinga 6oye hakoransa wad'anda suke jawur sabida tsabar cin goro da rashin kula dasu. Yana shiga gida ya zaro wayarsa missed call ya tarar na Abubakar, sai da ya zauna a bakin katifarsa sannan ya kira layin har sai da ta kusan yankewa sannan yaji an d'aga. "Sadeeq ina ka shiga ne inata kira baka d'aga ba..?!" Cewar Abubakar cikin sanyin muryarsa da jan aji, Sadeeq ya shafa kai yana kuma sauke ajiyar zuciya yace. "Twinnie ina jin sai na d'auki shawararka, wannan kauyan yafi karfina wallahi haukan su yayi yawa sosai." Yayi shiru yana sauke numfashin takaici kafin Abubakar d'in yace. "Da kyau gara tun yanzu ka fara gane cewar kafi k'arfin secondary teaching ka dawo nan gara ko FCE kano ne kaje kayi lecturing." Shiru suka yi na d'an lokaci kafin Sadeeq yace. "Toh zan kuma yin shawara amma nima abun kauyan nan ya fara isata, abun nasu yayi yawa ga gidadanci." "Twinnie kullum haka kake cewa yanzu kawai aiwatarwa zaka yi mudai muna nan muna yi maka fatan alkairi." "Ok insha Allahu sai munyi waya anjima a gaida min da qibdiyyah." "Zataji dakyau gata nan ma muna tare." Beyadda sun gaisa da itaba ya kashe wayar dan yaji ta fiye shiru da yawa kuma shima ba surutu garesa ba. *** Tun ranar laraba Rukayya ta wanke mata kai bayan tasa mata fiya-fiya kwarkwatar sun mutu sannan tayi mata zanan Hausa shuku, kai idan kaga kan bazakayi tunani na jiya bane sabida ya kitsu sai dai jan gashi gareta ba bak'i ba. Uniform d'inta kuma ranar alhamis tasa zare da allura ta d'inke so gabaki d'aya inda ya yage ta kuma wanke su duk da sun riga sun kod'e kuma bata da wasu ba kud'in yin sabo ta goge fason k'afarta k'afar tayi kyau duk kuwa da be fitaba gaba d'aya. Gidan innatuwa me kunshi taje tasiyo lallen goma da talatin din da rukayya tabata,da kanta rukayyan ta yarfa mata jan lallen ta rufe mata fason kafarnan,a ranar da yamma indo tatafi kasuwar dakali wajen idi shoe shiner hannuwanta rike da wasu jemammun takalma kambos duksun fatattake, “Idi xaka iya gyara wannan takalman” “Mugansu”cewar idi “Gasu kambas(kambos) ne idi kaga insipehen(inspection)malamin mu xeyi ranar juma’ar nan kuma bakaga kyautar dayake be nikuma so nake naci shadda ma yasin” “Bari na gwada nagani xasu gyaru mana sede xaki biya kudi dayawa” “Kai idi nawa?!” “Nera hansin” Rantsuwa Indo ta dinga kwasowa tana kalallame idi da kalamai tana faman xabga masa roko ta karkare da, “Dan manzon salati idi kayi hak’uri ka temakamin nice fa indo..Indo Malam hamxa ta makarantar tsefawa nan nan kusa dakai.” Cikeda isar nacin da take masa idi ya wafci takalman yashiga gyara su,yadau lokaci yana dinkecan nane can da gum sannan yai polish d’insa se kyalli yake Kai kace bashi bane sannan ya mikawa Indo ,cikin murna ta karba harda lashe kasan takalmin “Ta kwarankwatsa ya fita kuma,lalle aiki seme hi,Sannu idi yasin kaci abaka hinkafa da miyar ja me nama” “Allah ko Indo?” “Yasin idi” Cikin sake gyara kananun kayan da sukai yawa ajikinsa Wai shi gaye yace, “Toh Indo nikuwa ina lami?(kawar Indo)” “Oh lami tana nan,oho de bansan mata bama kasan makarantar gangare take tunda mijin kanwar babar su ixama chayamen(chairman)” Kada Kai idi yai yana murmushi,cikin tsokana Indo tace, “Wai haryanxu kana ciki ne?!” “Eh mana Inason lami wallahi kawaide bata sona ne tafison shehulle” Cikin karkad'a kugu had'e da rausaya idanuwa INdo tace, “To ai kaine idi,dole lami tafison shehulle kullum fa tanada daurin tsire da leman roba na yangayu Kai kwa se mammakon bala'i” “Ba haka bane Indo amma xan gyara..” Da haka sukai sallama da ita tana tafe tana jujjuya takalmanta ranar kuwa barkakkiyar safar da tayi shekaru batako kallansu hasalima kama tukunya ake dasu ta dinga durxa tana wankesu ruwa uku tai musu ,Kai kowa mamakin Indo yake har inna tafara sanyata a sujjada idan tai sallah don gani take aljanun tsafta ne suka shafeta kwanan nan.. *** Rana bata Karya sedai uwar d'iya taji kunya yau take juma’a tashin Indo uku kafin asubah inna tana korata waita xata safiya tai,asubar fari kuwa ta mike tai bandaki ranar de atakaice baccin kirki Indo batai ba. Sega Indo tai wanka abinda yabawa kowa mamaki agidan nasu sede basu da man shafawa sai dai manshanu ko na girki shi kuma bashi garesu ba dan haka tana saka kayan makaranta ta fita zuwa gidan Rukayya lokacin mijinta na nan INdo ta kwankwasa musu k'ofar d'aki tare DA cewa, "Rukayya kina ciki kuwa? Zuwa nayi ki aramin kayan kwalliyarki inyi zani makaranta.." Ta k'arasa fad'a tana me shiga cikin d'akin sukayi kicib'is da ita, "Au ashe kinji ni." "Eh INdo bari na d'akko miki su nan tsakar gida." Cikin d'akin ta koma ta d'ebu mata su lokacin mijin ta shima yazo zai fita INdo ta ganshi ta dashare baki tace "Au kaima d'anlami ashe kana ciki yanzu ka tashi a bacci ne?" Ya tsaya kusa da ita yana kallonta yace "Eh INdo yau kuma za'a makarantar kenan." Tace "Eh gahima kuwa." Rukayya ce ta fito ta mik'awa INdo kayan kwalliyar shi kuma d'anlami yasa kai ya fita. Tana zaune tana yi Rukayya na kwarzanta ta wai tayi kyau ai yau sai dai in bak'in cikin ne zai hana malam sadeeq ya bata kyauta. Zuciyar INdo ta kuma shiga cikin wani irin yanayi najin dad'i, ita dakanta tanajin sauyi a cikin jikinta sabida iskar da take shigarta ta k'ofofin gashin jikinta. Da sauri ta kammala kwalliyar Tashi Rukayya tayi bayan ta kwashi kayan kwalliyar ta shiga cikin d'aki ta mayar dasu ta mik'awa INdo turare sai faman dariya take sabida yadda takejin ta wani daban yau. Tafeshe rigarta Rukayya tayi saurin cewa. "Haba INdo ya kike kuma 6ata kayan makaranta salan yaga jirwaye ya hanaki...? A jikin hammatarki zaki fesa.!" INdo tayi yadda ta gaya mata sannan tace. "Sai nazo kawo miki kayan da zan samo Rukayya..." Tayi dariya itama cikin jin dad'i da fatan alheri tace "Toh INdo Allah ya baki sa'a sai kun dawo." Gida ta shiga yau ko karin kumallo bata tsaya yi ba sabida kar bakin yayi daud'a tayiwa Inna sallama tabar gidan yau harda littattafanta da suka yayyage tazuba a leda ta tafi burinta yau ta samu atamfar ko ya bata wani abun da zata dinga alfahari dashi, yau sai da ta riga kowa a makarantar zuwa principal ne kawai da masu kula da makarantar bata riga ba taje ta zauna kusa da farkon aji da niyar ko masu gurin sunje bazata tashi ba tafi son a fara ta kanta yau. *** Lokacin 8:15am yana gaf da shiga ajin aka yo mai waya hakan yasa shi tsayawa dan ya amsa. Dubawa yayi sai yaga ansa my twinnie yayi murmushi sannan ya d'anyi baya da ajin sabida hayaniyar da suke yi ya d'aga tare da karawa a kunnansa. "Twinnie me ya how far..?!" Sadeeq ya fad'a yana d'an sosa k'eyarsa da k'asan biro, daga can 6angaran Abubakar yace. "Surprise..!" Sadeeq najin haka yayi murmushi tare da cewa. "Kana gate ko..?!" Abubakar yayi dariya yace "yah kana ina yanzu.?”Sadeeq ya kalli ajin sannan yace "twinnie me kashigo ciki ina aji uku jss 3c nima yanzu zan k'arasa shiga ciki." "Okay..." Suka kashe wayar Sadeeq ya shiga hannunsa d'auke da ledar viva yana shiga 'yan aji suka tashi ana gaida shi da k'arfin tsiya dan yanzu ba k'aramin so suke mishi ba, ya ajiye akan teburin sa ba tare daya kallesu ba yace su zauna nan ma suka ce "thank you Sir..." Shima da k'arfin su kamar kuma had'in baki. Waje ya lek'a ya gani ko ya k'araso yana hangosa ya d'aga mai hannu suka yiwa juna murmushi tundaga nesa har Abubakar ya k'araso suka yi musabuha sannan suka shiga cikin ajin, nan ma yaran suka sake tashi suka gaida d'ayan daya shigo amma kotakan su bebiba ya tsaya suna magana sai Sadeeq d'inne yayi musu alamar su zauna da hannu tunda shi ba yadda zaiyi d'alibansa ne dole ya kulasu. "Twinnie ga abin zama ka zauna." Avubakar ya kalli kujerar sannan ya juya yana kallon 'yan ajin sai ya gansu fes-fes dasu hakan ya bashi mamaki ya kuma rasa wadda zai kira ta goge mai kujerar dan bazai zauna a haka ba. Shi duk a tunaninsa ba wad'anda ya sani bane ya kalli Sadeeq yana shafa sajen fuskarsa yace. "Twinnie congrats an sake ma class." Sadeeq yayi murmushi tare da juyawa ya kalli 'yan ajin sannan ya kalli Abubakar yace, "twinnie sune dai wad'anda ka sani kawai canjin yanayi aka samu." "Woww good of you." "Thanks twinnie." Abubakar ya kalli 'yan matan ajin kawai ya nunu Maryam Ali ya yafitota, jikinta na rawa ta mik'e ta k'arasa inda yake tace. "Malam gani." Mtwww “wai ban hanaku ce min malam vane? Ko kunga nayi kama da teacher?" "Allah baka hakuri." Maryam ta fad'a bakinta na rawa, yayi banza da ita sannan yace "daga yau kar wanda ya kuma ce min malam ko sir suna na doctor Abubakar Salman Harun, karna kuma zuwa ajin nan wata tace min malam ko wani sir ku kirani da doctor Abbakar or doctor ASH." Ajin yayi tsit babu meyin motsi yaja tsaki tare da kallonta yace "Oya tashi ki goge min kujerar da zan zauna." Da sauri Maryam ta zaro ido jin abinda yace sabida ta tuno sanda yasa INdo ta goge mai da hijjab d'inta, ya zata yi gashi ba'a duba taba yau ta shiga uku zai ja mata. "Ko baza kiyi vane.?!" Ya tambayeta ganin bataje tayi abinda ya sanyata ba, hawaye suka zobu mata shi kuma Sadeeq yak'i yin magana jiki a sanyaye tana kuka taje tasa hijabinta ta goge mai tasss sannan ta koma gurin zamanta sai kuka takeyi shi kuma yaje ya zauna tare da d'ora k'afa d'aya kan d'aya yana d'an kad'asu. Sadeeq ya kalli Abubakar yace. "Bari sai na fara yi musu inspection." Abubakar ya kallesa yace "na ina kuma..?!" Sadeeq ya d'auki rular yana cewa "na jikinsu har kyauta nake basu that's why kazo ka gansu neat." Abubakar ya ta6e baki sannan Sadeeq ya tafi farawa wanda har lokacin bemasan INdo na ajin ba, Abubakar yace "okey twinnie duk wani wanda beyi maka wani abunba ka turosa nan gurin." Ya fad'a yana d'aukar wayarsa dan kiran Qibd'iyya yace mata ya sauka lafiya kuma yaji sassanyar muryarta mai sanyi. 'Yan aji najin abinda ya fad'a kowa ya fara duba abinda beyi ba dai-dai lokacin da Sadeeq ya k'arasa gurin bencin da yake farawa kuma INdo ce a farko dan haka kafin ta gama duba abinda bata yiba har ya k'arasa. "Ohh my God..! Wacece wannan kamar Aisha?" INdo ta dashare baki kamar gonar auduga yayin da 'yan aji suka bita da kallo shi kuma malam Sadeeq ya saki wani tattausan murmushi ganinta yau tsab-tsab da ita sai dai makeup d'in da tayi ne duk ya cuceta dan duk ta cika fuskar da d'ige-d'igen baki da janbaki sai dai yaji dad'i dayaga tayi wanki yace. "Toh muga bakin." Ta bud'e mai hak'oran nata ya gani ya d'aga kai sun d'an fi na baya ya kuma cewa "muga kanki." Nan ma ta bud'e da saurinta ya kalla gashin nan yayi d'as da kitso ya kuma kad'a kai domin tayi k'ok'ari sosai lallai hakan yana nuna masa cewar ba k'aramin son a bata kyauta takeyi ba yayi murmushi yana wani sak'e-sak'e cikin ransa kafin yace. "Toh kinyi komai Aisha muga farcanki." Sai a lokacin ta tuna sam bata yanke ba sai ta 6ata rai idanunta yayi rau-rau zata yi kuka dan tasan rashin yanke farcen ba k'aramin asara zai janyo mata ba Sadeeq ya kuma cewa "muga farcan ki Aisha." A hankali ta mik'a mai hakan yasa shi saurin kallanta domin beso ta fad'i tausayinta ya kamashi ba yadda zaiyi dole yace. "Aisha baki yanke farce ba, tashi kije wajan doctor Abbakar..." Tana hawaye tace “Amma malam hikadai nefa banyi ba kuma wabillahillaxi mancewa nayi dan Allah kayi hakuri kabani atamfar.." "Tashi ki fito Aisha." Tashi tayi tana kuka domin ba k'aramin haushi takeji ba ta k'arasa wajan Abubakar wanda waya take kare a kunnansa shi kuma Sadeeq ya cigaba dayi idan yaga wanda beyi wani abunba sai ya turasa wajan Abubakar, shi kuma ganin yara sun taru a gabansa yasa shi cewa Qibd'iyya. "M love bari na barki zan..." Ya kasa k'arasawa sabida ido hud'u da sukayi da INdo zuciyarsa tayi wani rass gashi idanta yayi jah sabida kuka sai kawai yaji zuciyar sa nayi mai wani irin zillo ya kashe wayar bema sani ba sannan ya mik'a hannunsa ya janyo na INdo ita kuma ta fara dak'irewa a tunaninta dukanta zaiyi ta fara ihu tana bashi hakuri shi kuma ya damk'e hannun nata sabida yadda yaji shi cikin wani irin mood akanta.... Love u m Fan's👍 *HAJJA CE*👈 [7/1, 4:53 PM] Aisha Galadima: *⚗⚗ MUSAYAR ZUCIYA...⚗⚗*                     ♥                  ♥♥          A true life story Na *K.A.S Precious Hajja ce*👈 *HASKE WRITER'S ASSOCIATION*💡 (Home of expert & perfect writer's) *DEDICATED TO* Sanah Isma'il matazu. _Shafin yau naki ne tawan daughter'n My Nana Hafsatu Xoxo da Nana Hafsatu Rano wato *BILLY S FARI* wannan mata Allah yayi miki abinda kikeso duniya da lahira, ya azurtaki da 'ya'ya na gari masu albarka. Hajja ce tana sonki kamar yadda take son H², Allah yabar k'auna da soyayya.😍_ Page *7* Da gudu suke bin ta suna cewa ta basu bokitan su na talla amma tamkar iska gudu kawai take har se da ta shige cikin gida sannan ta dire bokitan ta zauna tana maida numfashin wahala. Inna ta kalleta tana jimamin hali irin na 'yarta ta ganin babu ranar da zata fito ta fad'i INdo bata yi wani abun na zagi ba, wannan dalilin ne yasa tayi niyar zuwa gidan me salati ko zata samu wani temakon da za'ayi mata akan fitinar ta amma baban su ya hana yace shi 'yarsa lafiyar ta sumul. Kad'a kai kawai Inna tayi ta cigaba da mark'ad'an ta akan irin dutsen nan, INdo na gefe su kuma su Idi sai faman kumbura suke ta bud'i bokitan Ubale me d'auke da awara ta d'ibi guda biyu sannan ta tura mai bokitin nasa, ta janyo na idi shima ta d'ibi wainar rogo ta mik'a mai sauran tana cemusu. "Naci lada kuma wabillahillazi kuka sake ganina kuka fad'i wata kalmar sai na jamuku asara kuce ba suna na A’isha ba." Suka d'auki bukitan su sukayi waje kowanne da irin kalar wulak'ancin da zai mata a zuciyarsa, Nafeesa k'anwarta ta shigo gidan tana ganinta tayi saurin 6oye kwanon awarar dan karta d'aukar mata. "INdo rowar jaraba." Cewar Nafeesa tare da k'arasawa wajan INdon ta zauna harda su tankwasa k'afafuwa ta mik'a mata hannu alamar ta sammata. Mtww "idan ni marowa ciya ce dalla malama kekuma mecece? Ungoni ki matsa ki bani guri." Ta juya tana kallon Inna tace "Inna ga awara idan zaki ci." Inna ta k'araso gurin tana cewa "Ni wallahi 'yar nan bana son wannan fitinar taki, inda Allah ya temaka ma kun koma makaranta zaku shiga ajin gaba ni banaci na k'oshi da abin fitina." INdo ta fara sosa kai tana kanne ido d'aya sabida jin zafin yajin bakinta tace "Inna wallahi bazan koma makarantar nan ba wata zaku sakemin, wai d'azu harni malam Sadeeq zai cewa tinkiya! Wallahi toh bazan koma ba yaje yacinye makaranta." "Yanzu kin dena zuwa 'yar nan? Toh wacce kike son a mayar dake ke ba tsayayyan saurayi ba bare ayi miki aure yau na shigesu ni Maryama." "Inna wallahi bazan koma tsefawa ba na fasa zama likitar dama temako zan dinga yi toh yanzu kuma nafasa suje sunemi wata." Inna ta kad'a kai babu abinda zata iya cewa akai koda baban su ya shigo ma bata gaya maiba bare su d'auki wani mataki haka suka barta kullum bata nan unguwar bata waccen har aka d'iba sati biyu ko hanyar makarantar bata bibare asakaran zata shiga, tsab Sadeeq ya manta da ita domin ya toshe duk wata hanya daya san suna had'uwa. ** A 6angaran Abubakar kuwa yana matuk'ar son Mareeya har hakan ya fito fili ragowar nurses suka fuskanta, wasu suka hakura dashi yayinda wasu kuma suka d'auki tsana da takura suka d'orasa akan ita Mareeyan suna ganin itace tayi wani kulla-kullan har ya karkata wajanta ya barsu. Sosai suka shaku Abubakar har ya had'a su da Sadeeq awaya suna gaisawa hakan ya sake narkar da sonta a cikin zuciyar Abubakar d'in. ** Wata ranar juma'a ne Sadeeq dayaje makaranta dama duk juma'a yakewa 'yan ajinsa duban tsabta, yana duba farcensu, hak'oransu, mata ya duba kitso maza kuma aski da kuma uniform duk wanda yafi kowa tsafta zai bashi kyauta. Ashe INdo ta samu labari yau yana cikin dudduba su sai gata ta shigo askwane cikin ajin malam Sadeeq ya kalleta cikin tsananin mamaki kamar aljana uniform d'in nata sharkaf da ruwa a haka tasa su gashi tayi wata mahaukaciyar kwalliya kamar wata ifirituwa ta fara tafiya zuwa bencin su Uwani halilu suka matsa mata har ta kusa kai duwawunta k'asa yayi saurin dakatar da ita ta hanyar yi mata wata razananniyar tsawa ya had'a da cewa. "Ke meya kawoki wannan ajin? Wacece ke haka? Daga wane sahun aka zakuloki..?!" INdo ta kalli kan teburinsa taga kayan kyaututtukan da zai bayar sai ta dashare mai jawur d'in hak'oranta domin tunda ta siyi brush da makilin d'in nan bata ta6a yi ba zuwa tayi ta zubesu a gida toh dama ba'a sababa ta k'arasa zama tukunna tace masa. "Haba malam Sadeeq nicefa INdo malam Hamza." "Will you shut up...Nonsence, zoki fitar min daga aji wawuya waya kawoki jss 3? Keda har yanzu kina jss 1 shine yau zaki wani shigo min zoki fita kafin na lahira ya fikijin dad'i." Yayi maganar yana nuna mata k'ofar data shigo ransa a matuk'ar had'e, sai ta fara kallon 'yan ajin d'aya bayan d'aya tare da mutsittsike idanuwa taga dai still sune dai 'yan ajin nasu na da amma ya za'ayi yace wai nan ba ajinta bane dan shi munafukine, tokuwa babu inda zata dan nan gwamnati ta tsaga mata dan haka tayi kicin-kicin da fuska wai taga ko zai kuma cewa tafita. "Ke Aisha ba magana nake yi miki ba?" Ya fad'a yana k'arasowa bencin da take, INdo tayi saurin mik'ewa tana kallonsa tace "Yo toh malam duk fa k'awayena ne kuma 'yan ajinmu ne ya zakace na fita ina zanje ni." Yace "Tallah, koba ita kika fiso ba? And bakin ce bazaki sake suwa tsefawa fa yau kuma wane munafuncin ne ya shigo dake da wasu jik'akk'un kayanki kila ma fitsarin kwance kika yi, oya zoki out kina 6ata mana lokaci." Duk cikin maganarsa babu wacce take k'ona mata rai irin yace tazo ta fita, kuma kallon kayan kyautar tayi kawai sai ta rushe da kuka tana fad'in "Kai malam.. Kai malam, sai da kaga nazo na kusa cinye kyautar nan shine zaka ce natafi ba ajina bane. Toh malam wane ajin zan koma kuma?." Tsananin mamaki ya cika Sadeeq ganin tana kuka, tunda yake be ta6a ganin hawayenta ba sai yanzu haka kurum kuma sai yaji duk ya tsani kansa domin yasan ita d'in mahaukaciya ce ya kamata ya dinga bata kulawa ta wani 6angaran ko Allah zaisa ta gyara wani abun hakan yasa shi juyawa yanaci gaba da duba 'yan ajin har ya zabo mutum shidan da zai bawa kyautar . Yana zuwa kan INdo tundaga kan uniform ya fara rankwashin ta domin haka yake yiwa duk wanda yake da gyara, INdo tayi saurin dafe gurin tana furta. "Kai...kakai...kakai..! Malam da zafifa." Yace "ha..bakin muga teeth naki." INdo da taji yace ha bakin yasa ta bud'e mai tamkar zata cinyeshi yayi saurin matsawa sabida wani hamami dayake tasowa daga ciki yana toshe hanci yace. "Such a stupid hak'oranki zaki nuna min bawai cewa nayi ki hangame min ba." Hannu tasa ta toshe bakin tunawa da tayi lokacin da sukace bakinta yayi yalo ya kalleta yace. "Bazaki bud'e ba saina mareki..?!" Ta d'aga maikai bakinta a toshe da hannunta tace "Malam gara ka marenin da na bud'e ma ballahillazi." Mtwww yaja tsaki dan yasan babu abinda za'a za6a a gurinta, ya kuma matsawa ta baje hancinta tana shak'ar k'amshin turaren jikinsa yace "muga farcenki." Tana jin haka tayi saurin zame hannunta daga baki ta cukwaikuye hannuwan acikin hijjabi tana zaro mai ido ya kuma kuluwa yace "muga kanki..?!" A hankali ta bud'e shi ya kalla tare da ta6e baki ya bar gurin, akwai kitso saidai ya tsofa sosai dan ko tsagar ba'a gani gashi gashin nata jah ne kamar gashin akuya sai dai da ka ganshi kasan zaiyi laushi domin irin me yalai-yalai d'in nan ne, ta kalli Uwani halilu tana sosa hanci tace. "Uwani kin ta6a cin gasar kuwa?!" Uwani ta harareta tare da k'in bata amsa ganin haka yasa tayi mata kallon sama da k'asa tana fad'in "ji banza kina jima ina tambayarki." Malam Sadeeq ya d'akko wani yadi na maza ya mik'awa D'ahiru Miko ya durkusa har k'asa ya kar6a sannan yayi godiya malam Sadeeq yace. "Ku tafawa D'ahiru miko ya samu wannan kyautar ne saka makon d'inkin uniform d'insa sabo ne, yayi aski sannan baya barin farce zak'o-zak'o gashi yana k'amshi babu wari a jikinsa hak'oransa ma sun fara haske.." Aka fara tafawa raf-raf-raf INdo sai k'arayi take da k'arfi har aka gama yi sau biyar yadda ya koya musu INdo bata denayi ba sai da yace "ke inji..!, ya isa haka baki ji yadda suka had'u suka yi nasu ba ne a tare?" Sai a lokacin ta dena amma fa bakin nan a wangale tamkar ita aka bawa yadin. Mace kuma Murja Ashiru ce ta samu ya bata fallen atamfa biyu itama aka tafa mata still INdo sai da ta zarce har wani dak'irewa tayi sai da Atika bawa ta bige mata hannun sannan ta denayi yace musu "Yau Atika bawa tafi ko wace mace tayi kitso harda kunshi, kayan makarantar ta harda guga babu farce ta yanke itama tayi brush." Aka sake tafawa sam INdo bata iya ba da kowa zai denayi amma ita sai ta k'ara. har ya kammala bama ragowar suka koma suka zauna yayi musu nasiha akan tsabta sannan ya kwashi littattafansa zai fita INdo tayi saurin cewa. "Malam...!" Ya tsaya cak ba tare daya juya ba tace, "nima wata juma'ar zanyi duka amma ni hadda (shadda) nakeso ruwan bula kaji ko...?!" Juyawa yayi ya kalleta sannan yace "Toh kiyo amma bake zaki gaya min abinda kike so ba sai abinda nayi niyar bayarwa kinjiko..?!" Tayi shiru bata amsa mai ba yayi tafiyarsa ta zauna tana cewa "kajishi fa, salan kawai a baka abinda bakaso mtww." Babu wanda ya kulata ta mik'e ta koma wajan Atika ta k'arbi atamfar tana gani ji take inama ta tace har ta hango irin d'inkin da zatayi dan taga wani style a jikin Rukayya amarya. Duk wanda aka bawa kyauta sai da taje ta ansa ta gani har ta fara Allah-Allah wata juma'ar tazo itama taci za6e.... *HAJJA CE*👈 [7/1, 4:53 PM] Aisha Galadima: *⚗⚗ MUSAYAR ZUCIYA...⚗⚗*                     ♥                  ♥♥          A true life story Na *K.A.S Precious Hajja ce*👈 *HASKE WRITER'S ASSOCIATION*💡 (Home of expert & perfect writer's) *DEDICATED TO* Sanah Isma'il matazu. Page *9* Still hannunsa na rik'e da nata ya rik'e sai kallon fuskarta yake dan ba k'aramin kyau kwalliyarta tata tayi mai ba, INdo kuma sai k'ok'arin ture mai hannunsa take tana hawaye murya k'asa-k'asa kamar munafiki yake mata magana yace. “What's your name make up artist..?!” INdo tayi shiru sai tasa ka hijjab d'inta ta sharo hawayen fuskarta duk bak'in kwallin da tayi kwalliya ya wanke hijjabin daga gaba Abubakar ya kalleta sosai shi har lokacin begano taba domin be ta6a ganinta tsab-tsab kamar yau ba ya kuma cewa. "Baby ya sunanki ne.?!" Sai a lokacin INdo ta fahimta ya kalleta ya kuma cewa, "kinga kin goge kwalliyan naki da kuka ki dena kinji ko? Ya sunanki??" Ta share majina da bayan hannunta wanda be rik'e ba ai yana gani yayi saurin sakar mata d'ayan hannun ita kuma ta matsa baya tare da cewa cikin kuka. "INdo malam Hamza." Abubakar ya d'an zaro ido waje kad'an kafin yace. "Zonan gurin." Ya nuna mata inda yake son ta tsaya da k'afarsa, a hankali taje gurin ta tsaya sai dai idanunta nakan tebur din da malam Sadeeq ya ajiye kayan kyautar da zai bada. Tsaye tayi mai k'ik'am sam hankalinta baya kansa shi kuma ya kalleta yana murmushi yace. "Woww sunan Mama na gareki, toh amma ba zaki tsugunna ba kika min k'erere..?!" Da sauri ta tsuguna still fuskarta na wajan kayan, ganin bashi take kallo ba yasa shi maida kujerar sa saitin da idanta yake gurin tayi saurin kallansa ya tsuke fuska yace. "Menene baki yi ba aka fito dake?!" Ta cukwai-kuye hannunta tun kafin ta bashi ansa dan tasan mugune a hankali tana turo baki daya sha bakin kwalli a le6an tace. "Wallahi nayi komai, kawai farce na manta ban cire ba shine malam Sadeeq yace na fito kuma wallahi malam..." Ya zabga mata harara tayi saurin toshe bakinta da hijjab kafin taga ya dena tace. "Kayi hakuri dakta Habubakar mantawa na keyi kace ba sunanka malam ba, amma wallahi nayi niyyar yankewa niko dan naciyo atamfa amma duk saina manta hef (shaf).." "Ohh muga farcan naki.." Ta fito dashi yasha lalle a yatsun ta nuna mai, hannu yasa ya janyo nata yana kallah murya sanyaye INdo tace mai. "Dan Allah Dacta Habubakar kace ya bani ni yanzu ma zan iya cire farcen, dan iyayanka kace ya bani dan Allah kaji..?!" Sadeeq ne yazo gurin ya kalli d'an uwan nasa rik'e da hannun INdo hakan ya bashi matuk'ar mamaki da al’ajabi cikin sauri Sadeeq ya zare hannun INdon daga na Abubakar cikin harshen turanci Sadeeq yake mai magana cewa. "Twinnie why na?am i day dreaming or are you really the one holding a village girl hands,and if you have forgotten about it then I haven’t ,this villagers are cruel,I don’t want them to think something else in their mind ..This is so not you” Cikin ko’a jikinsa abubkhr ya daga kafada sannan yafara magana, "Habba twinnie sunan Momcy gareta fa shi yasa, gashi kuma tayi kwalliya irin wadda nake so that's y kaga ina iya rik'e hand's na ta." Mtwww "inajin baka ganeta bane shi yasa kake sakar mata fuska, toh bari na tuna maka kowa cece INdo malam Hamza, wannan me satar amsar ce me cizon maza nasan yanzu ka harbo ta." "Really my twinnie? Abubakar ya fad'a yana sake maida kallonsa fuskar INdo, kwakwalwarsa kuma tana sake hasaso mai lakacin daya kamata ta duk'ufa tana kwafar note dan sam koda ta kwafo ma bagurin da aka tambaya bane, ya kuma kallon Sadeeq cikin mamaki yace "Gaskiya m twinnie kayi k'ok'ari indai haka ne. Ashe k'azan tace duk ta maidasu mahaukata Gaskia I'm sure nan gaba za'a sha mamaki indai suka d'ore da haka za'aji dad'i sosai." K'afarsa yaji ana jijijigawa hakan yasa shi saurin kallon k'afar kawai yaga INdo ce take mai alamar magiya tana nuna mai ya samo mata kyauta kota meye Sadeeq dake fito da kayan zai bawa wad'anda suka ci ya kalli Abubakar dake kallon INdo kawai yaja tsaki sabida takaici. INdo kam sai nunawa Abubakar malam Sadeeq takeyi alamar be zabo mataba zasu k'are yayi dariya cikin zuciyar sa ya kalli sauran masu kuskuran yace. "Kuzo nan muyi photo daku." Suna jin haka suka ruga bayansa suka jeru amma sam INdo batayi gigin zuwa ba hankalin ta yana wajan malam Saseeq dayake ta rabo zuciyar ta tamkar ta fito tsabar fargaban karsu k'are. "Humaira zo mana ayi dake." Abubakar ya fad'a yana kallon Indo , ita kuwa bata masan da ita yake ba tana ji tana gani har malam Sadeeq ya kammala bada kyautukan taji wata muguwar tsanarsa tundaga k'asan zuciyar ta ya game da ilahirin jinin jikinta tayi ta zagba mai harara bemasan tanayi ba yana can yana sake yiwa wad'anda sukaci kyautar nasiha da kuma muhimmancin tsabta da Ilimi. “Kuje kuma ku zauna kowa yaje gida yayi karatu ranar Monday zanyi muku test duk wanda ya fad'i ni nasan irin hukuncin dazan d'auka akansa kunajina ko?!" Malam Sadeeq ya fad'a bayan yaga yau twinnie d'in nasa da mutunci ya shigo, duk 'yan ajin suka ce "OK uncle." Dayake yana k'ara d'an wayar dasu, amma INdo data tashi sai da ta d'auki ledar littafinta ta faki idonsu duk da cewar Abubakar nason yayi mata photo da kwalliyar ta yana can yana tambayar Sadeeq mezai iya bata koda ba babba bane ba sukaji tana cewa. "Baza'ayo karatun tess (test) d'in ba, kai idanma kun sake ganina a makarantar nan dan Allah ku soya ni. Wallahi malam Sadeeq yayi karya kuma ance babba me karya d'an wuta ne gobe k'iyama yana kusa da fir'auna, Allah ya sakamin sabida na kashe kud'ina garin yin kunhi da gyara kambas d'ina sai Allah ya saka min. Yo dan baka bani atamfar ba seme, nima Inna ta zata sai min ai sallah ta kusa." Tana gama fad'a ta murgud'a baki ta juya da gudu zata arce taji an rik'eta gam cikin tsananin tsoro da tashin hankali tayi k'ok'arin juyawa taga waye sai taga malama Murja ce ta cafketa tare da tura ta cikin ajin, tana zuwa ne da yake period d'inta ya shiga sai taji irin rashin kunyar da takewa malamin hakan yasa tayi shiru sai data kai k'arshe zata gudu tayi saurin kamata. Tsananin mamakinta suka kama Abubakar, sai yanzu ya kuma tabbatar da cewa itace ya tashi a fusace yayi kanta jin yadda take gayawa twinnie d'in nasa magana. Sadeeq ne yayi saurin taresa yana kad'a mai kai alamar karya doketa, yana wani irin numfashi ya ture hannun Sadeeq d'in daga kafad'arsa yana cewa. "Ka rabu dani Sadeeq bakaji yadda take had'aka zama da fir'auna ba, barni naci uban shegiyar yarinyar nan da har ina tausaya mata ashe batada mutunci har yanzu." "A'a twinnie barni da ita, kayi hakuri ka kwantar da ranka. Malama na gode da gudun mawarki, ke kuma zonan..." Sadeeq ya fad'a yana damk'o hannunta Abubakar kuwa jiyake tamkar ya ham6areta sabida 6acin rai. Fita yayi da ita sai ihu take musu har suka k'arasa cikin staff room ya kalleta yace. "Kama kunnanki." "Dan Allah malam kuyi hakuri." Babu wanda ya kulata sai dai duk malam cikin staff room d'in saida suka bada shedar rashin kunyar INdo, ganin babu mebada hakuri ne yasa ta sunkuya ta zura hannunta tana nishi tana cewa "malam wallahi hannuna baya kaiwa abakacin sa kace nayi nibdom (kneel down) kaji." Jiyosu ma tayi suna hira babu wanda ya kulata dan yau takaisu bango, tun tana magiya har tayi shiru. Ta dad'e tana kamun kunnen kawai suka ganta ta fad'i k'asa Abubakar dake kusa da gefenta besan lokacin daya kai hannu zai tarota ba amma saida tayi k'asan, ashe baccine ya kamata, kuma duk da fad'uwar da tayi hakan besa ta tashi ba saima zarcewa da tayi tafara sauke munshari. "Twinnie mu wuce tunda ka gama." Beh jira cewar sa baya k'arasa inda INdo take kwance sai uban munshari takeyi tamkar wata babbar mata a hankali ya dinga k'iran sunanta amma inah ko motsawa batayi ba, hannu yasa dai-dai kafad'arta yana jijjigata nan ma still bata motsaba. Ganin yadda yake bin ta a hankaline yasa Sadeeq mik'ewa ya d'auki dorina yana zuwa ya tsula mata a baya. A razane ta mik'e ta rarumi Abubakar dake tsaye kusa da ita tana cewa. "Wayo Allah atamfata ce." Sak'e tsula mata yayi tayi saurin sakin Abubakar tayi k'ark'ashin tebur d'in malam yahaya tana kuka tana sosa gurin cikin kuka take bashi hakuri yayin da shi kuma Abubakar ya fita daga cikin staff room d'in. Sai da wasu malam suka bawa malam Sadeeq hakuri sannan aka ce taje ta tsugunna ta bashi hakuri tayi sannan ya hakuri yace kuma duk sanda ta kuma yin fashin zuwa makaranta sai yasa ankamota yayi mata duka tace toh. Fitowa yayi amma bega Abubakar d'inba har ya fita gate babu bare alamun motarsa, sosai Sadeeq yayi mamaki sai ya nufi gidan shima amma abin mamaki bako motarsa a gurin hakan yasa shi kiran wayarsa aka sanar mai cewar a rufe take, mamaki ya kuma sark'e Sadeeq. Yana tsaye a gurin har su INdo suka wuce suna gulmarsa be kulasu ba. Shi kuwa Abubakar yana fita motarsa ya hau yakama hanyar gida, haka kawai yau yaji baya son jin kukan INdo zuciyarsa har zafi take mai duk kuwa da cewar yasan itace batada kunya amma ya rasa dalili, tunda ya taho tunaninta yakeyi yayi-yayi ya halasto qibd'iya ya kasa sai dai INdo da kamanninta ya buga sitiyarin motarsa yafi sau ashirin harya k'arasa gida. Yana shiga yaji Maman su na cewa. "Kajishi can najiyo tsayuwar motarsa da alama ya dawo. Toh shikenan 'biyu kyautar Allah kaima Allah yayi maka albarka." Sai da ya bari ta kashe dan yasan da Sadeeq takeyin wayar sannan ya shiga cikin gidan nasu bakinsa d'auke da sallama.... _Kuyi hakuri da wannan, kunsan bawa duk yadda yaso yayi abu idan Allah bebashi dama DA iko ba toh babu abinda zai iya yi a rayuwarsa. Nagode luv you all._ Gaisuwa da fatan alkairi zuwa ga aunty Sdy jegal, Ina miki fatan alkairi a duk inda kike, Allah ya raya mana baby boy d'inmu cikin addinin musulinci.😘 *HAJJA CE*👈 [7/1, 4:53 PM] Aisha Galadima: *⚗⚗ MUSAYAR ZUCIYA...⚗⚗*                     ♥                  ♥♥          A true life story Na *K.A.S Precious Hajja ce*👈 *HASKE WRITER'S ASSOCIATION*💡 (Home of expert & perfect writer's) *DEDICATED TO* Sanah Isma'il matazu. _Shafin yau na kune 'yan grp d'ina wato *HAJJA CE NOVELS GRP* da *ZAURAN BIEBIE ISAH* tare da *🅿HERTY NOVELS* da *MUSHA KARATU N YBK2* gara nayi muku jam'u domin idan na tsaya lissafoku sai kunji haushina kunce dama typing nayi muku da wannan lissafin. Hak'ik'i ina jin dad'in yadda kuke tare dani, comments d'inku nasani dariya da kuma nishad'i uwa uba kwarin gwaiwa. Nagode sosai #ana tare da INdo malama Hamza._🤝😍 Page *10* Amsawa Maman tayi tana had'a musu zo6o. k'arasawa yayi ya zauna akan kujera 'yar tsugunno sai faman shafa sajen fuskarsa yakeyi. Umma Dijeh ce ta fito daga parlor kasan cewar muhad'u a parlo ne ta kallesa tana murmushi cikin wasa tace mai. "Likita bokan turai, daga sallar juma'a kuma sai ina? Ko yauma za'a lek'a mak'ota ne..?!" Wayarsa ya zaro zai kunna domin tunda ya baro makarantar ya kasheta sabida yasan dole Sadeeq ya nemeshi, shikuwa beshirya abinda zai gaya masa ba. Kallan Umma Dije yayi sannan yayi murmushi yace. "Haba Umma jiya fa naje, kuma yauma bata nan." Dariya suka yi itada Maman sannan ya tashi ya fito yashiga d'akinsu, kayan jikinsa ya rage ya zauna daga shi sai vest da boxer shorts sannan ya kuma d'aukar wayarsa dai-dai lokacin kuma Sadeeq ya kuma kiransa. Babu yadda zaiyi dole ya d'aga kodan ya kare kansa daga wajan abokin haihuwar tasa, cikin basarwa ya kara a jikin kunnansa tare da fad'in, "My twinnie sai kaga na taho ko?!" Sadeeq dake zaune a k'ofar gida ya ta6e baki sannan yace. "Ba gani nayi ba nemanka nayi na rasa wanda kuma ni bansan dalilin yin hakan ba, twinnie kasan irin tashin hankalin daka sakani? Da police station zanje nakai report sai kuma muka yi waya da Mother take cemin gakanan ka k'arasa why did you do this to me ah?!" Duk sai Abubakar d'in yaji babu dad'i ganin yadda duk ya tayarwa da d'an uwan nasa hankali, da kyar ya samu mafitar da zai wanke kansa ya numfasa tare da cewa. "Kayi hakuri nima saida na taho naga rashin dacewar hakan tunda bamuyi sallama ba, abinda ya faru shine ina fitowa Dr Inuwa yake sanar dani ana nemana a cikin asibitin da gaggawa shi yasa duk na rud'e na kashe wayana dan karsu dunga damuna sorry twinnie kaji kayi min afuwa.." "Okk bakomai yanzu tunda naji kana gida sai anjima." Kamar ya tambayesa INdo sai kuma yayi shiru suka ajiye wayar shi kansa besan yadda zai fad'i abinda yakeji ba har mamaki yake yi ya ajiye wayar yashiga toilet. Wanka yayi lokacin har an kawo mai abincinsa an ajiye amma ko kallansa beyi ba sai wayar ya sake d'auka ya shiga gallery, hotunan dayayi mata ba tare da kowa ya sani ba. Yana gani yana duba na e so yake yagano meke damunsa amma inah..ya kasa tantancewa sai faman k'aryata zuciyarsa yake yi da abinda take shaida mai. INdo kuwa tana zuwa gida ta fara cire kayan jikinta tana killarwa ta sanya wata kod'add'iyar shadda doguwar riga wanda ta d'age mata sannan ta dawo tsakar gida ta zauna tana kallon kunshinta. Wani irin tsanar malam Sadeeq da Abubakar suka sake mamaye cikin zuciyarta ta cewa Inna. "Inna wanki zanyi gobe na tafi gidan yakumbo Tsahare, wallahi billahillazi bazan sake zuwa makaranta ba saye zan yi tafiya ta naga ta tsiyarsu mugaye." Cikin dafe k'irji Inna tace "ke 'yarnan saye kuma? Kiyiwa Allah da ma'aiki kiyi shiru da maganar tafiyar nan kinsan dai babanku baya son zuwanku garin nan tun abinda ya faru tsakaninsa da jummala." "Inna wallahi saina tafi, kina jinfa abinda mugun malamin nan yace, wai idan na dena zuwa makaranta saiya saka an d'akkoni toh wallahi barin garin zanyi hena dad'e sannan zan dawo a'he." Hankalin Inna ya tashi dan tasan idan baban su yaji toh lashakka sai anyi fitina duk da cewar tsaharan k'anwarsa ce amma tun a haihuwar shehu suka samu sa6ani akan naman suna shikenan sukayi baram baram kuwa yace bashi ba d'an wansa sannan yacewa Inna ya haramtawa 'ya'yansa zuwa garin idan sukaje kuma Allah ya isah. Tashi INdo tayi tabar gidan ta shiga gidan Rukayya, tana ganinta ta fara murna tare da cewa. "Kai INdo shine ko a kawo min kyautar ingani ko?!" Saida INdo tasamu guri ta zauna sannan tacewa Rukayyan "Yo ai basu bani ba, wai wani ban yanke farce ba ninasan dama malaman nan ba kaunata sukeyi ba kawai dan dai nafi karfin sune bayadda zasu yi dani shegun." "Kan uba! Yanzu kina nufin babu abinda malam Sadeeq yayi miki?!" "Sai duka nama dayayi kuma nace Allah ya isa." Nan suka cigaba da hira har INdo na bata labarin tafiyarta saye gobe Rukayya tace. "Kai INdo sai kuma yauhe zaki dawo?!" INdo na watsa shinkafa da wake tana cewa "babu lokaci idan na tafi henayi aure zan dawo yasin." "Kai INdo baxaki dawo ba kenan?!" Rukayya ta kuma tambaya cikin jimami, ita kuwa INdo ko'ajikinta tace "Eh bazan dawo ba he randa malam yadena zuwa garin nan." "Kai Allah ya wadaran wannan malamin da yaja zaki tafi, zamuyi rashinki INdo barema Inna." "Kyale Inna can na barota sai masifa take dan nace zani saye wai bazani ba toh alkur'an saina tafi." Haka suka dinga hira da Rukayya har bayan la'asar sannan ta koma gida inda ta tarar da Inna ta gayawa babansu yace toh babu inda zata ta kule d'aki bata sake fitowa ba. Tun asubar fari ta farka ta tsinci kayanta tasa a d'ankwali ta d'aure ta d'auk'e fitilar da aka haska d'akin da ita wato shekarau mekwayayen nan k'ananu a jikin katako tayi sad'ab-sad'ab gidan a kulle yake ta jefa kullin kayan ta katanga sannan itama ta kama ta dirga ta kwashe kayan nata ta an taya da gudu sai bakin titi ko tsoro bataji. Tayi tafiya sosai sannan gari ya fara haske daman babu buk'atar yin sallah dan bawani yi takeyi ba sai taga dama. Mota na zuwa ta tsayar dasu ta shiga dama da d'ari ukunta a hannu data ara wajan Rukayya. Can gida kuma tunda suka farka suke neman Inndo, duk gidan da akasan tana zuwa saida akaje bata nan. Kuka Inna tasanya domin tasan yau INdo tayi mata abinda zai iya 6allamata aure, lokacin da baban yaji cewa yayi k'arya Inna takeyi tasan ta tafi dan haka itama ta shirya tabi bayanta su dawo tare kasan cewar sunsan zata iya zuwa. Ko kud'in mota Inna batada su amma a haka malam Hamza ya takura mata kan cewa sai taje ta dawo da INdo haka ta fito tana hawaye. A bakin titi malam Sadeeq ya ganta harya wuce ya dawo duk da cewar ta rufe fuska da mayafin jikinta tana share hawaye yaje yace. "Baiwar Allah kiyi hakuri lafiya dai ko..?" Shiru batayi magana ba duk da besan kowace ba ya zaro d'ari biyar ya bata babu yadda zata yi ta k'ar6a tana ta zazzaga mai addu'a shidai ya wuce ita kuma mota na zuwa tashiga tana fatan Allah ya temaketa can din INdo ta tafi, ayau bazasu kwanaba zata dawo da ita. Wajan k'arfe biyu da rabi INdo ta shiga wata rugar fulani anan cikin sayen bakinta a washe hannunta d'auke da kullin kaya, suna zazzaune k'ark'ashin bishiya suka hangota nan da nan yakumbo tsahare ta had'e rai fuskar nan babu yabo babu fallasa tana dakan fura haka INdo ta k'arasa gurin tana dashare musu hak'ora. "Wacece wannan kamar mai sunan Gwaggo..?!" Cewar talatu yayar malam Hamza dake kwance, INdo ta k'arasa tare dayin cilli da d'ankwalin kayan nata tace. "Nice nan yakumbo talatu ahe duk kuna nan, yau dai gani a garin ku ina kwananku...?!" Duk suka amsa suna tambayar ta su Sagiru da Nafeesa da Shehu tace lafiya lau amma banda yakumbo tsahare daketa faman dakan fura, ko ajikin INdo ta mik'e tare da zuwa wajanta tana cewa. "Sannu yakumbo tsahare, ina su lawisa take..?!" "Ke karki yimin rahin kunya aradun Allah kuwa, idanma Ubanki ne yau ya turoki toh dagake harshi d'in zan iyayi muku rahin mutunci jacan ki bani guri ni." "Allah baki hakuri daga tambaya.." INdo ta fad'a tare da komawa wajan su yakumbo talatu aka kawo mata d'umamen tuwo da fura da nono tana ci suna hira har su lawisa suka dawo daga tallar nono, murna da farin ciki ba'a magana duk da cewar Lawisan cikima gareta har tayi aure tsiranta da INdo shekara biyu ne. Cikin gidan suka wuce suna zazzaga shirmen su. Inna kuwa la'asar sakaliya ta iso saye sabida da kyar ta samu motar da ta kawota a d'ari da talatin. Saida tayi sallah sannan taci kwad'on rama da fura bayan sun shaida mata cewar INdo tazo amma sun tafi tatsar nono, hankalin Inna ya tashi tace ta kalli malam iro mijin yakumbo talatu tace. "So nake a yau mu koma gida gahi bata kusa kuma ina neman yadda zanyi mu samu kud'in komawa." Malam iro ya kalleta da mamaki sannan yace. "Haba dai Maryamu, yanzu fisabilillahi har yaushe zaku koma gida, hasalima ita INdon bata kusa kuma da kyar idan zata yadda tabiki dan tasamu yara, kuma na tambayeta randa zata koma tace sai an kori wani malami a garin naku." Inna ta fashe da kuka malam iro ya kalleta yana jin tausayinta dan yasan tsoran d'an uwar matar tasa takeyi. Hakuri ya dinga bata ita dai hawaye kawai takeyi gashi tana matukar kaunar malam Hamza duk da cewar shima yana matukar santa amma hakan baya hanashi yimata wulak'anci. Har magariba su INdo basu dawo ba sai wajan k'arfe takwas na dare, koda taga Inna batayi wani murna ba kotaji tsoro ita kuma nauyin mutane ya hanata yi mata magana. Cikin dare Inna tasamu INdo ta gama lalla6ata akan ta yarda gobe su koma amma fir tace wallahi bazata koma ba nan zata zauna sai lawisa ta haihu koda zata koma. Da gari ya waye haka Inna ta kama hanya dama tunda taje yakumbo tsahare bata ko kalli inda Inna takeba har ta kama hanyar komawa sumaila. Koda Inna ta koma gida malam Hamza baya nan, kafin ya dawo harta sarrafa musu gero tayi musu burabusko yana dawowa yaci yayi hani'in data sanar masa cewar INdon tak'i dawowa sai yace. "Kyaleta Maryamu ni kaina na huta da fitinarta taje can karta dawo d'in." Bayan sati biyu. Tunani da damuwa da begen son ganin INdo suka addabi zuciyar Abubakar, duk iya yinsa na ganin ya kawar da hakan daga cikin zuciyarsa hakan ya gagara. Ya rasa meyagani a tattare da ita har yakejin irin abinda yakeji cikin ransa da gangar jikinsa, yasan duk lokacin da asirin zuciyarsa ya fito fili zaisha wulak'anci gurin Sadeeq dama sauran abokansa. Tashi yayi ya tafi Sumaila kauyen na sani direct babu wanda ya sanarwa. Yana zuwa zuwa ya tarar su Sadeeq sun tashi daga makaranta yarama sai fitowa sukeyi, samun kanshi yayi dayin gaba zuwa unguwar su INdo ko Allah zaisa ya ganta, amma har Sadeeq ya dawo ya tarar dashi besamu yaga ko kyallin kallabinta ba hakan kuma ya hargitsa ilahirin tunaninsa na Ina zai ganta? "M twinnie..! Ta6 lallai kaida kace min kaida garinnan saidai in wucewa zakayi shine yau na ganka at this time..?!" K'ak'alo murmushi Abubakar yayi yana kallon hanya dan befidda ran zai hangota ba. Ganin yadda Sadeeq d'in ke kallansa ne yasa shi saurin cewa. "Malam Sadeeq nasu INdo, wai kuwa har yanzu kana basu kyautar?!" "Meza'a fasa twinnie? Itace dai tun ranar bata sake zuwa ba, dana tambayi babanta rannan danaje gidan yace wai ta gudu kauyen su sai randa aka koreni zata dawo kaga kuwa ba rana kenan.." Daram..! K'irjin Abubakar ya buga besan lokacin da ya furta "what...?!" *HAJJA CE*👈 [7/1, 5:02 PM] Aisha Galadima: *⚗⚗ MUSAYAR ZUCIYA...⚗⚗*                     ♥                  ♥♥          A true life story Na *K.A.S Precious Hajja ce*👈 *HASKE WRITER'S ASSOCIATION*💡 (Home of expert & perfect writer's) *DEDICATED TO* Sanah Isma'il matazu. _Shafin yau naki ne tawan *HALEEMATU G KHALEEL* (Aneesa didi), Allah yayi miki albarka ya k'ara nisan kwana Allah ya tayaki rik'on Namcy na khadijatu (shareefat) Allah ya azurtaki da miki Nagari ina sonki fisabilillah like H³_💋 Page *11* Sadeeq ya bishi da kallon mamaki ganin yadda ya furta kalmar tamkar yace masa shine yabar garin ko Mama. Kallansa ya kumayi kafin ya juya yayi hanyar shiga gida yana cewa. "Kai twinnie bafa Qibd'iyya nace maka ba naga har kana ihu." Harya bud'e gidan ya shiga Abubakar betaso ba, hanyar gidan su INdo yabi da kallo ji yake tamkar zai ganta amma bako kurarta haka ya k'araci zamansa kafin ya tashi yabi Sadeeq cikin gidan. Lokacin daya shiga tararwa yayi Sadeeq harya shiga wanka hakan yasa shi zama tare da dafe goshinsa sabida tsananin saramai dayaji yana yi. Fitowa Sadeeq yayi zama yayi kusa dashi yana kallansa soyake ya gano wani abu a tattare da d'an uwannasa, Abubakar ya d'ago ya kalli Sadeeq ganin yana mai kallon tuhuma yasa shi wayan cewa ta hanyar cewa. "Twinnie wai yaushe zakuyi hutu ne?!" Sadeeq ya mik'e tare da janyo singlet zai sanya yace "kasan ba'a fiyeyin hutun maulud ba so kawai sai term ya k'are ni yanzu mafa na farajin dad'in makarantar sabida suna bani had'in kai yanzu shi yasa na dena neman transfer." "Oh idan na fahimta kana nufin kace dama Humaira ce ke baka matsala duk fad'in makarantar ko?!" Abubakar ya tambaya yana zaro ido, Sadeeq yafara shafa mai yana cewa, "eh toh idan nace maka a'a nayi kamar kuskure idan kuma nace maka eh toh shima banyi karya ba domin tun sanda ta dena zuwa nake ganin students d'in suna k'ara maida hankali, haka nima ban sake zagin wata ko wani ba, kai banma sake rik'e bulala ba kaga kuwa idanma nace itace matsalata banyi k'arya ba.." Abubakar ya dafe kai jin Sadeeq yace INdo ce matsalarsa yaji haushin Sadeeq sosai saidai ya danne dan yanzu so yake INdon ta dawo gida bayajin zai iya hakura har ranar da tayanke hukuncin zata dawo yayi yace. "Amma twinnie a ganina a matsayinka na malami kamata yayi ace kaine ka fara k'arfafawa yarinyar nan gwiwa wajan ganin tasamu wani kyakyawan abun dazai taimaka mata a rayuwarta kuma a matsayinta na mace." "Kai twinnie kasan kuwa yarinyar nan? Ka manta abinda tace min da addu'ar datayi min, wai ko'a lahira ina kusa da fir'auna. Wallahi a yadda naji zuciya ta a lokacin ko naso in targad'ata Allah yayi malamai suka saka baki na kyaleta." Ganin yadda Sadeeq yad'auki zafine yak'arawa Abubakar damuwa, babu ta yadda zai iya samun ganin INdo sai ta hanyarsa yau gashi ta kaishi bango yace bazai temaka mata ba. Cikin nuna halin damuwa Abubakar yace. "Okey naji ni nayadda zan tallafa mata koda dawani abunne nasan wata rana al'umma zasu amfana da ita. Yanzu inason kasanya kaya kaxo muje gidan su muji inda ta tafi." "Twinnie wai yaushe kadawo me sauk'in kaine? Kodai-kodai so kake ka kiwata ta tun yanzu kafara banruwa?!" Mtwww Abubakar yaja tsaki dan shi kansa jinsa yake a wani bai-bai, yau ko kiran Qibd'iyya beyi ba sabida zumud'in son ganin INdo. "Kai meye haka twinnie? Ni kamar ni zan tsaya jiran wannan kurkurar yarinyar, har yaushe ma zata waye tayi kamar yadda nakeson Qibd'iss? Kawai dai ina son mu sami ladane ta hanyar gina mata wata rayuwar sabuwa wannan shine kawai manufata..." "Ohh toh ai akwai irinta da suke buk'atar hakan m twinnie bawai dole sai itaba, ni wallahi na tsani yarinyar nan garama data bar garin wawuya kawai sai idanuwa kamar na mayu.." "Shhhhiii m twinnie duk meyayi zafi hakan? Kayi hakuri nitunda nayi niya zan temaka mata insha Allahu tunda kai kayi fushi..." "Hakan dai yafi.." Cewar Sadeeq. Sun dad'e suna hira har akayi la'asar zasu tafi masallaci Abubakar yake cewa "M twinnie idan mundawo ina son karakani muje gurin baban ta ko Maman ta dan Allah." "Ohh wai daman baka manta da zancen ba?" Sadeeq ya tambayesa yana dariya, Abubakar ya kalli katangar gidan ya tuno lokacin da ta watso mai hijjab da takallmi yayin da Sadeeq ya tuna sanda ta watso mai ruwan k'anzo suka wuce Abubakar na murmushi yayinda Sadeeq ke faman jan tsaki. Suna dawowa Sadeeq ya d'auka ko mutumin nasa ya manta dan haka yak'i kallon koda gidan su yarinyar, suna zuwa zasu yi kwana Abubkhr yayi saurin dakatar dashi ta hanyar rik'e masa hannunsa yana cewa. "Ya haka ne twinnie? Ina kuma zakaje?!" "Oh wai dama baka manta ba?" "Eh ai kasan ba'a manta yin alheri musamman idan mutum yayi niya." Sadeeq yace "naji toh karka gayan magana,ke shiga kice ana sallama da malam Hamza." Yayi maganar yana kallon Nafeesah dake zaune a k'ofar gida, ta kallesu ganin su iri d'aya sak bakinta bud'e haushi ya Kama Abubakar cikin takaicin kallon da take yi masa yasa shi cewa "Ke bazaki kibane kika saka mana na mujiya?!" Da sauri tayi firgit tana susa tace "Ai baya nan yana can wajan aikinsa a bakin hanya." Kallon Abubakar Sadeeq yayi dan yaga yazai yi amma sai yaga ya wani ta6e baki irin sunyiwa kansun nan amma cikin zuciyarsa kwata-kwata ba haka bane suka juya suna tafiya Sadeeq yace. "M twinnie muje na kaika inda zaka temaki masu neman temako domin bawai rayuwar INdo ce kad'ai take buk'atar hakan ba, indai kayi niyar temakawan to kazo muje wani gidan." Mtwwwww Abubakar yaja tsaki ganin yadda Saseeq d'in ke takura masa da zancen wani gidan, shi duk gaba d'aya mafa yafi buk'atar yaga INdon ko zaiji wani 6arin na gangari jikinsa da ruhinsa sun samu sassauci amma Sadeeq ya kasa ganewa ya kuma had'e rai cikin basarwa yace, "okey bari next week zan dawo sai musan abinyi yanzu bari na koma sabida aikin yamma gareni." Yafad'a yasan duk bala'i nan da ranar asabar INdo ta dawo, shi dai Sadeeq be damuba dan dama be d'aukarwa wani aiki ko takura ba bare yasa kansa cikin damuwa, yana yin alheri a duk lokacin da yake da kud'i. Sallama suka yi a bakin k'ofa Abubakar ya tafi yayin da Sadeeq ya shiga cikin gida cike da kewar abokin haihuwar tasa. Abubakar kuwa tsakanin sa da Qibd'iyya sai hange daga nesa, sam yanzu ya dena ganin kyawunta bare yaji kwarin guiwar zuwa wajanta. Ita kuma ta rigada ta kamu da kaunarsa domin ya riga yayi mata dashen zazzafar soyayyarsa gashi ta dena kula kowa sabida shi, yau kimanin sati uku kenan ta kasa ganokanshi ya rage nemanta ko kiranta a waya bare ya taka yaje gidansu tad'i sam ya dena har abun ya fara damunta. Kwanaki na tafiya Abubkhr na kuma shiga cikin damuwa da tunani. Ana ya gobe zai koma sumaila kauyen na sani k'aninsa Khaleefa ya shigo d'akin nasu, kwance ya tarar dashi yayi rub da ciki ko shirin tafiya asibiti beyi ba khaleefan ya k'arasa ciki tare da cewa. "Yaya Habu Abba na k'iranka yana d'aki." Beko juyo ba ya d'aga mai hannu sannan khaleefa ya fita shi kuma ya mik'e dakyar ya sanya zilaika sannan ya fita yana wani 6acin rai. Kwankwasa k'ofar yayi Abba yace ya shiga, yana shiga ya gaidashi sannan yasamu guri ya zauna abban yace. "Yauwa Abbakar dama zance Mariya ne, mahaifinta yayi min magana an tambayeta wanda ta tsayar tace kai shine nace toh ya bari nazo naji ta bakinka ya ake ciki." Gabaki d'aya ya daburce besan lokacin da yace. "Abba aure kenan fa..?" Yafad'a cike da tashin hankali dashiga cikin d'imuwa, Abba ya kallesa tare da cewa. "Eh Abbakar aure tunda ai kaine kaje gidan nasu." "Amman Abba da an d'an k'aramin lokaci kafin ayi maganar auran nawa zuwa nan da wani d'an lokaci." "Amman kai Abbakar kasan dai bazan zuba ido kaida d'an uwanka kuzauna har yanzu babu Aure ba? Kuma gashi kai har gidan su yarinyar sunsan da zamanka." "Eh Abba ai bayi ne baza muyi ba, lokaci kawai nakeso ka k'aramin dan inason tabbatar da wani abu dan Allah..." "Tom naji zan k'ara maka lokaci aman da sharad'in wanan maganar tamu ta karo karatunka zuwa k'asar Spain dan nariga na samu duk abinda ake buk'ata. Yanzu gobe nakeson kaje abuja zakayi wani signing na tabbatar da tafiyar taka, sai kuma na koma kan Saddiqu shima a sake mai wajan aiki." A rud'e yace "Abba har yanzu dama kananan da burinka na k'aro karatun mu? Innalillahi." Ya furta cikin sanyin murya, Abba yace "Eh Ina nan da wanan burin Abbakar Ina matukar kaunar naga kun cigaba a duniya, don Allah kucika min wanan burin nawa dan wata ran kune iyayen k'annanku, sannan nima naji dad'i a tattare daku." Nan da nan jikin Abbakar yayi sanyi, babu yadda zai yi dole yacikawa Abban su burinsa ya mik'e da kyar yana had'a bango harya koma cikin d'aki. Kwanciya yayi ruf da ciki ya fara tunanin taya zai iya samu yaga INdo har ya tallafi rayuwarta sannan ya bawa zuciyarta abinci dan yana son ganinta ra'ayul Ayn. Ina zaije yasake ganinta kafin ya tafi, yanzu ya yarda ba shida wani buri sai son ganishi tare da INdo... *HAJJA CE*👈 [7/1, 5:03 PM] Aisha Galadima: *⚗⚗ MUSAYAR ZUCIYA...⚗⚗*                     ♥                  ♥♥          A true life story Na *K.A.S Precious Hajja ce*👈 *HASKE WRITER'S ASSOCIATION*💡 (Home of expert & perfect writer's) *DEDICATED TO* Sanah Isma'il matazu. _*HASKE WRITER'S ASSO..* wannan shafin na kune yau na bakushi kyauta. Allah ya k'ara had'e kanmu ya kuma k'ara fasaha mai amfani #ana tare all_🤝😍 Page *12* Washe gari Abubakar ya tafi abuja danyin abinda Abba yasa shi. Tunda kuma ya dawo daga abuja kullum akwai inda zashi sam baya samun zama gashi yayi-yayi Sadeeq ya d'aukar masa amana da alk'awarin nemo INdo ya kula da ita amma Sadeeq yak'i shi adole idan zai tayashi toh saidai ya canza wata amma ba INdo ba, da haka sukayi bankwana baram-baram kowa najin haushin d'an uwansa. INdo kuwa wayyo Allah tazo saye kauyanci da k'arin abubuwa duk sun dad'a k'aruwa ta zama tamkar 'yar garin duk inda kaje sai kaji labarinta kaf kauyan sun-santa dan akwai shiga jama'a. Da mutum d'aya ne basa shiri wato yakumbo tsahare, sam basa jituwa da juna ko a layin band'aki. Ranar da lawisa ta haihu kuwa su INdo sune masu jigo, anyi ruwa anyi tsaki tazama tamkar itace me jegon dan ta kanainaye komai lawisa kuwa sai kawaici take bata magana. Ranar suna aka sanyawa yarinyar Raihanatu suna kiranta da Ladi kasan cewar ranar lahadi aka haifeta. Watan INdo biyar a garin saye ta kuma irin wayewar nan ta karkarar fulani. Jin dad'inta kawai takeyi samari kuwa su tara ne kowa sonta yakeyi suna yi mata kyaututtuka sosai dan da haka take tattara kaya sawa tana kuma siyan kayan kwalliya abin sai wanda ya gani duk bak'in cikin yakumbo tsahare sai dai ta kawar dakai. Ta manta dasu Inna tama manta dasuwaye malam Sadeeq sam yanzu rayuwarta takeyi babu takurawa... *BAYAN SHEKARU UKU* K'arfe hud'u da rabi da minti shida, Sadeeq Salman Haruna ne cikin mota 403 ash color yana bin bayan wata kyakyawar budurwa. Tafiya take cikin nutsuwa da iya bawa k'asar da take takawa hakk'inta, duk da cewar taga ana binbayanta hakan besanya ta waiga ko tayi alamum tsayawa ba har ta shiga kwanar gidansu. Shima beyi mata magana ba yana ganin gidan data shiga yayi murmushi sannan ya juya kan motarsa yabar layin yana sak'awa da kwancewa ta yadda zai fara tunkarata da kalma mafi tsada da daraja a gurin wata d’iya mace. Saida aka d'ibi kwanaki hud'u yana bibiyar rayuwar budurwar ba tare da tasani ba sannan. Ranar asabar da misalin k'arfe hud'u da rabi ya dira a k'ofar gidan, yaro yajira yazo yace yashiga ya k'ira masa Fatima Kabir ya'u. Ba jimawa sai ga yaron da wani matashin saurayi wanda zaiyi sa'an Sadeeq d'in sun fito tare, yana zuwa suka kalli juna cikin tsananin mamaki matashin yace. "Kardai ace twin's d'in dana sani ne? Abbakar ne ko kuma Sadeeq?!" Dariya Sadeeq yayi tare da bawa saurayin hannu suka tafa yana cewa "cinka da kanka Shamsu kabeer Ya'u dama kananan.?!" "Hahaha ina nan mana, dallah ka tabbatar min waye a ckinku kasan kud'inne sai a hankali." Sukayi dariya dukansu sannan yace. "Sadeeq ne Shamsu ya rayuwa." Shamsu yace "Alhamdulillahi, gaskiya na dad'e ban sake sanya ku cikin idona ba tun sanda mukayi candy a GSS kwankwaso, ya wai kaine kenan ka biyu sisi na gida." Shafa kai Sadeeq yayi bayan ya zame hular zannar shi sannan yayi murmushi yana cewa. "Wallahi kuwa ashe ma k'anwata ce. Anywaya nidai nagani kuma ina so ya za'ayi kenan?” "Toh ya zanyi tunda kazo kawai zaka jamin raini, k'anwata ce Fateema kuma kayi sa'a this year tayi graduation but gaskiya munan gidan ba'ayi wa mace aure sai tana da ilimin NCE ko Diploma, gashi ita kofarawa batayi ba yakenan?!" Murmushi Sadeeq yayi cikin jin dad'i domin hakan yayi dai-dai da lokacin dawowarsa daga k'wara state. Cikin rashin nuna damuwa yace. "Shamsu babu damuwa ni dai burina gidan ku susan dani, kuma a bani dama mufara fahimtar juna tun yanzu." "Karka damu tunda kana dani babban yaya, wai yanzu wane aiki kake yi..?!" Sadeeq yayi murmushi tare da cewa "Toh kasan rayuwa babu yadda bata zuwar mawa d'an Adam, da ina teaching ne a wata secondary school amma yanzu ina nan BUK shekarata d'aya da dawowa nan ina lecturing, sai dai akwai wani business danakeyi acan k'wara state hope babu wanda ya rigani Fateema..?!" Dariya Shamsu yayi tare da sake bawa Sadeeq hannu suka tafa yace. "Karka damu abokina insha Allahu zaku dai-daita bari ma naje nafito maka da ita." "Toh godiya nake dad'in aboki a gidan su budurwa🤪." suka kuma tafawa sannan Shamsu ya koma gida. Yana shiga falo ya kalli Fatima dake kwance tana karatun wani novel akan kujera, had'e rai yayi shi a dole babban yaya yace. "Ke Fatima tashi ki shirya kije waje abokina yana jiranki." Da mamaki ta d'ago tana kallasan yace "eh ko bazaki jeba ne?!" Fatima tace "Haba Yaya Shamsu amma kasan dai baba yace karna kula kowa ko..." Ya sake had'e rai sannan yace, "ke! Toh waye baban yanzu a gabanki? Zaki tashi kosai na bugeki, sakarai kawai." Tashi tayi tana zumburar baki ta kalli Umman su ganin harkar gabanta kawai takeyi yasa Fateema shiga d'aki tana gunguni. Hijabi ta zurma ta fito Shamsu ya kalleta tare da cewa. "Ke koma ki shafa hosa da janbaki, kinsan ko waye yazo gurinki kuwa.?" "Gaskiya ni Yaya..." Yayi saurin katseta ta hanyar daka mata tsawa yana cewa, "Baxaki je Kiyi abinda nasaki bane?!" Sake komawa tayi harda hawaye sannan ta shafa hoda tasa coffee d'in janbaki sannan ta kuma fitowa, Shamsu ya kalleta sannan yace "Good girl sauran kuma kije kiyi mai fitsara ko ki gayamai babu dad'i ranki saiya 6aci wallahi domin 6atamana suna zakiyi wuce." Fita tayi tana kunkuni, a zaure tagan shi suka had'a ido Sadeeq ya sakar mata Murmushi tayi saurin kawar dakai tare da tsayawa ta jingina jikin bango. Jitayi yayi mata sallama ta amsa yayi dariya kad'an ta kuma d'agowa ta kallesa karaf suka had'a ido. Samun kanta tayi dayin murmushi sannan ta gaidasa ya amsa tare da gabatar mata da kansa tana jidai amma batace komai ba sai daya ce mata. "Ina fatan zaki yarje min nashiga cikin rayuwarki har muyi aure, nayi miki alkawarin kare duk wani hakkinki da kare miki duk wani mutuncin ki burina kawai ki yarda dani." Samun kanta tayi da cewa "Shikenan na gode tunda har Yaya nane ya baka damar da banta6a tsayawa da wani ba kamar haka." "Toh godiya nake yiwa Yaya Shamsu, sai kuma yaushe zan kuma dawowa Zarah..?!" Ya tambaya yana kasheta da salon shi tayi murmushi cikin sanyi, ita kanta batasan lokacin da take maida reply ba. Ya had'u iya had'uwa dan k'irjinta banda bugawa babu abinda yakeyi. "Nima ban sani ba." Ta bashi amsa yace "Toh sai wani satin insha Allahu a gaida Umma." Da sauri ta shiga gida yayi dariya yana zuwa mota sai ga Shamsu ya fito yace. "Kai abokina irin wannan shaf-shaf d'infa wai har kagama siye tane?!" Sadeeq yayi dariya tare da cewa, "ban fad'a ba nidai, kawai dai dama zuwa nayi na gabatar mata da kaina." "Hakan ma yayi kyau mutumina, toh Ina Shi Abubakar d'in." "Yana Spain sun rik'esa amma nan da one month zai shigo k'asar insha Allahu." "Ahh lallai kaji manya toh Allah ya dawo dashi lafiya muna murna." "Toh Shamsu godiya yake bari na gudu nima ka kular min da mata." "hmmm harta zama makenan, Allah ya kiyaye hanya a gaida mutanan gidan." Suka yi sallama Sadeeq ya tafi, tun daga lokacin indai yana kano toh zaije gidan su Fateema idan baya nan suna mak'ale da waya ta hanyar shamsu domin babanta yaki yadda ta rik'e waya sai ta fara karatu. Sun shaku sosai fateema na sanshi shima yana sonta alkairi kuwa duk zuwa da abinda zai kaimata. Doctor Abubakar Salman Harun, matashin saurayi mai tak'ama da kyau da ilimi nagarta da wayewa ya zama babban likita wanda duniya ta sanshi take kuma tak'ama dashi. Tun bayan gama karatun sa da shekara biyu a, k'asar Spain suka rik'esa domin suma ya ceto al-ummar su ta hanyar kwarewarsa, yana gudanar da aikin cikin walwala da jin dad'i duk da cewa tunda yabar k'asar tunanin INdo be ta6a gushewa daga cikin al'amransa ba, ya sakawa ransa cewar Allah ne zai bashi INdo bawai wani abun nasaba hakan yasa ya kwantar da hankalinsa yacigaba da karatunsa cikin nutsuwa da sadaukarwa rayuwarsa akan Al-ummah. Ganin yak'i dawowa ne hakan yasa mahaifinsa ya umarce sa da yadawo gida domin taimakawa 'yan uwansa 'yan Nigeria, bai k'i tayin mahaifin nasa ba saboda shima bak'aramin missing d'in gidan yayi ba. Ga wasu mafarkai dayake yi game da INdo da yake kusan kullum yana son ya ganta yana kaunar sake had'uwa da ita. Hakan yasa yayi niyar komawa gida bayan yayi wa asibitin *CANTABRIA HOSPITAL* bankwana. ba suji dad'in barinsa aiki ba aman sun bashi damar duk lokacin da yake da buk'atar dawowa suna maraba a kowane lokaci.. Wednesday morning at 8:30am cikin airport d'in malam Aminu kano matashin saurayin mai shekaru 32 ya sakko daga cikin jirgin Nigerian airlines. Sanye yake cikin wasu dakakkun suit coffee color sai ta cikin white da cover shoe gashin kansa a saisaye bakikk'irn ya gyara kyakyawan sajansa sai wanda ya ganshi zai iya tantacce d'an wace k'asar ne. Sadeeq ne ya fara ganinsa dan haka shi yafara k'arasawa wajan cikin fara'a suka rungume junansu. Abba ma ya karasa Abubakar yayi saurin tsugunnawa yana mik'a gaisuwa mutanen gurin sai kallonsu ake, zuciyar Abba tayi fari ganin yadda 'ya'yan nasa suke bashi respect aduk inda suka had'u. "Welcome twinnie am glad to see you sai daifa yanzu bama kama kazama bature." Cewar Sadeeq suna tafiya ajere, Abubakar yayi dariya har suka k'arasa cikin mota suna tsokanar junansu. Kwanansa d'aya da dawowa batare da kowa ya sani ba yatafi Sumaila kauyen sani, ba laifi anyiwa kauyan sauye-sauye ya nufi gidan malam Hamza direct cikin ikon Allah kuma ya sameshi a k'ofar gida bayan ya tambaya annuna masa shi. Bayan sun gaisa ne shi duk a tunaninsa malam Sadeeq ne shi kuma Abubakar be nuna bashi bane ya kalli malam Hamza yace. "Malam INdo kuwa ta dawo?!" Malam Hamza ya kad'a kai cikin takaici yace "Ai malam Saddiqu uwata dai k'arfi da yaji ta gujemu, k'iri-k'iri tak'i dawowa, harma gidan su yaron dazata aura acan sayen sun aiko mun kuma bashi dan idan ba haka bama uwata ba dawowa zatayi ba. Wallahi har zuwa nayi da kaina nace mata kabar garin amma tak'i yadda mudawo." K'irjin Abubakar ya buga jin cewar an aiko, cikin d'imuwa yace. "Malam wane kauye ta tafi ne? Nidai wallahi inason ganin yarinyar nan tasamu Ilimi koyaya ne, idan babu damuwa kuma ka yadda dani kagaya min kauyan da INdo taje na dawo da ita zan samar mata da rayuwa mai inganci da ikon Allah nidai burina ka yadda dani." "Toh malam Saddiqu na yadda amma dasharad'in sai munje mun sanarwa dame unguwa, shima yasani da kuma aminina malam 'Dalha.." "Hakan ma dai-dai ne Malam na gode." Hannu yasa ya ciro kud'i duba ashirin ya mik'awa malam Hamza ya kar6a yana ta godiya tamkar zai mai ruku'u sannan yace suje gidan me unguwar. Suna zuwa aka yi komai sannan suka koma gida Abubakar suka gaida Inna bayan sun kwatanta mai kauyan sayen ya koma gida cike da murna. Da dare suna zaune a d'aki Abubakar ya kalli Sadeeq yace. "M twinnie zaka min rakiya gobe dan Allah." "Zuwa Ina kuma daga dawowarka?!" Cewar Sadeeq Abubakar yayi dariya tare da cewa. "Wani guri zamuje wajan k'arfe 12:00pm." "Allah ya kaimu tunda gurin bashi da nisa, kasan dai Qibd'iyya tayi aure ka yaudare ta." "A'ah twinnie Allah ne beyi ba." Suka cigaba da hirarsu gwanin ban sha'wa. Washe gari suka d'auki hanyar zuwa saye cikin suit d'insu iri d'aya da Abubakar ya taho musu dashi. Tafiya suke tun Sadeeq yana kawaici harya fara magana. "M twinnie wai ko katsina zamu je ne naga mun wuce dawanau..?!" Abubakar yayi murmushi sannan yace "A'a kaidai zuba ido kayi kallo." Cigaba sukayi da tafiya har suka d'auki hanyar saye Sadeeq dai yayi shiru idan ya gaji sai ya kira Fateema har yaga sun fara shiga daji da kewaye mugayen ramuka ya kuma yin magana. "M twinnine ko kafara sana'ar yankan kai shine zaka fara takaina?!" Abubakar ya kyalkyale da dariya tare da cewa. "A'a ban faraba zuciyata nazo d'auka a garin." "Tofa.. Waye zuciyar take twinnie??" Abubakar yace "Aishat Hamza,what I mean is INdo malam Hamza." "What.........???!" _Kuyi hakuri da wannan wallahi unguwa naje amma duk da haka saida nayi muku. Ina godiya a gareku masoya._ *HAJJA CE*👈 [7/1, 7:39 PM] Aisha Galadima: *⚗⚗ MUSAYAR ZUCIYA...⚗⚗*                     ♥                   ♥♥          A true life story Na *K.A.S Precious Hajja ce*👈 *HASKE WRITER'S ASSOCIATION*💡 (Home of expert & perfect writer's) *DEDICATED TO* Sanah Isma'il matazu. *VOTE me on wattpad @Hajjac* _page 13 na kune 'yan candidate d'in government girl secondary school Kwah, hope zakuji dad'in shi sannan kuma ina muku fatan alkairi a cikin rayuwarku kamar yadda kuke bin labarin nan_💍 Page *13* "Amman dai baka min adalci ba kasani ko m twinnie? A k'a'ida yau zanje gidan su fatma sabida gobe nakeson wucewa amma kayi min haka, wallahi danasan gurin wannan wayuwayar zamuzo bazan rakoka ba”mtww "Sanin idan na gaya maka bazaka yadda ba yasani k'in gaya maka sabida ina son muzo tare dakai." Sadeeq yayi mai banza har suka shiga cikin rugar fulanin, suna zuwa suka ga 'yan mata yara da manya sunzo zasu wuce. Ra6awa Abubakar yayi da motar gefe kasan cewar bazata wuce canciki ba sannan suka fito Sadeeq sai faman cin uban magani yake yi idonsa sanye cikin dark shade shi kuma Abubakar d'an siriri ne nashi fari kal kamar k'ank'ara. Suna fitowa INdo dake tsakiyar 'yan matan zasu tafi kasuwar badume tana ganinsu ta ganesu cikin karad'i tace. "Jakar uban nan,sun biyo ni masifaffun malamn nan." Kallon sauran abokan tafiyarta ta tayi tana gyara mayafinta tace. "Kowa ya samu sanda zamu k'arasa wajan wad'an can malaman, kawai danace muku kulle kukuma sai ku jibgesu." Suka ce toh kowa ya juya ya samu sanda harda ita sannan suka nufi gurin suma su Abubakar lokacin sun k'araso ciki sam basu ganeta ba sabida tayi girma ta zama 'yan mata, lokacin da ta baro sani tana 12years yanzu kuma tana 15years gashi tayi 'yar k'iba ta kuma canza. Abubakar shine ya taresu yana kallansu yace. "K'annena dan Allah muna neman gidan da INdo malam Hamza take, wadda tazo daga kauyen sani." Caraf ta cafe bayan ta rik'e kugu tace, "ga wata nan lafiya kuka zo inda nake..?!" Duk suka zuba mata ido Sadeeq dariya da takaici suka kusan kamashi ya kalleta kallo irinna raini sannan ya juya zai koma cikin mota yaji tace. "Wannene kaid'in dacta Habubakar ko kuma malam Sadeeq? Na ganeku rasai." Ko waigowa beyi ba sabida haushi ita kuma ta kalli Abubakar dake tsaye yana kallonta, sam bega wani aibu a tattare da ita ba yaji zuciyarsa ta sanyaya yanajin tamkar ya rungumeta amma bahali gashi ya gansu da sandina kuma su ba shanu a taredasu bareyayi tunanin cewar kiwo zasuje. Cikin sanyin murya yace. "Humaira inason muyi magana dake, naje munyi magana da mahaifinki sauran ke." "Allahu akubar kabiran, malam Sadeeq ni ba'a renamin hankali wallahi nan garin yanzu sai nasa su rakaku da duka wallahi." Ido ya zaro jin abinda take cewa ya fara bin hannayen yaran tare da tuna wata kalma ta bahaushe da yake cewa sarkin yawa yafi sarkin k'arfi, ya d'an kalleta cikin ransa yana tunano ko harsai yaushe ne zata yi hankali. Ya rasa ya zaiyi da su sai yayi murmushi tare da zura hannu cikin suit d'insa ya zaro wallet suka bishi da kallo ya ciro 2k ya mik'awa wata yarinya yace ga wannan kusha alawa. Kallon kud'in suka yi sai kuma sukayi baya-baya suna zaro idanuwa, ganin dalla-dallan kud'i yasa INdo tayi saurin k'arasawa zata fisge Abubakar yayi saurin janye hannunsa tare da kad'a mata kai yace. "A'a wannan ba naki bane, naki yana gurin Sadeeq sai kin yadda da abinda zan gaya miki sannan zamu baki su suna can dubu ashirin." INdo ta dafe k'irji tare da jan baya tace, "Dubu ahirin? Toh kaine dacta Habubakar kenan, meyasa kabari aka bawa malam Sadeeq kud'ina kuma alhalin mugune ba bani zai yi ba..?!" "Zai baki amma sai kin yadda da maganar da zamu gaya miki." Tana jin haka tace "kaltume ku kar6i kud'inku, kuyi gaba zan taho daga baya idan na kar6i kud'ina." Kar6a suka yi sannan suka tafi ita kuma ta yarda icen hannunta tare da goge hannun jikin zaninta, shi kuma sai kallanta yake yi, sam ya rasa abinda ya gani a jikinta yaji zuciyarsa na azabtar dashi, yace. "Toh kinga wani dutse can muje mu zauna in gaya miki abinda muka zo sanar miki." Ba musu suka tafi sai juyawa take tana kallon Sadeeq a cikin motar, suna zuwa Abubakar ya zauna ita kuma ta tsaya yace. "Humaira zauna mana." "Karkafa kuma cemin wani humaira hekace wata yarinya e'heee." "Sunan Mamana gareki shima humairan na fad'a ne sabida babu yadda zanyi, ki zauna kijini dakyau abinda zan sanar miki, idan baki yadda ba zamu d'auki wata yarinyar anan kauyan mu bata kud'in." Da sauri ta zauna ya kalleta yama rasa ta Ina zai fara mata bayani yadda zata faminta ta gane manufarsa karta yi mai hayaniya. Zare glass d'insa yayi sannan ya kalli fuskarta sai faman wasa take da k'ananun duwatsu yace. "Humairah kina son yin karatu?" Kai tsaye INdo tace mai, "A'a aradu nida zanyi aure." Abubakar ya kuma kallanta, ganin tayi maganar har cikin ranta yasa shi mik'ewa tsaye yace. "Eh ai zakiyi auran amma ki gaya min idan kinason yin karatu kema wata ran ki zama kamar matar gwamna ko shugaban k'asa kuma kema wata ran ki amfanar da bayin Allah da kuma 'ya'yanki wanda zaki haifa idan kinyi aure." Rufe ido tayi da tafin hannunta wai kunya sannan tace. "Eh toh bank'i ta bakinka ba amma ni bazan yi wani karatu ba haka kurum naje malamai su dinga jibgata ba a'hh jikina bana banza bane, kuma ma yazan yi da auran saleleh tunda shaura 'yan makwanni.." Mtwww Abubakar yaja tsaki jin ta kira salele cikin d'an 6acin rai yace. "Waye shi salelen? Me gareshi? Ana son fito dake daga cikin duhun kai kina wani sake dulmiya kanki? Kinga humaira ki yadda yanzu mu koma sumaila dake akwai kayan da na tanadar miki sababbi tindaga kan, atamfofi, shaddoji, materials, mayafai takalma, jakunkuna da kayan kwalliya, amma sai kin yadda zaki bimu mu koma can gidan ku..." Shiru INdo tayi ta fad'a cikin tunani, kallonta yayi ganin tayi shiru ya fara addu'ar karta ce mai bazata ba murya a raunane yace mata. "Please Humaira talk to me mana." Kallansa tayi jin yayi mata turanci tace "sake gaya min abinda ka fad'a yanzu da hausa ko da fulatanci sune yarena." "Oh cewa nayi kiyi magana mana, inason jin matsa yarki I told you zaki samu komai idan muka maida ke sani." "Kai dacta habubakar kun saba cewa zaku yi amma ni bakwa bani bare ma kuma malam Sadeeq”hmmmm. "Humaira wannan karan nine zan d'auki duk wani nauyin abunda kike so, fatana da burina ki yadda mu koma nayi miki alk'awarin yi miki duk abinda kike so indai befi k'arfina ba." "Harda kayan d'aki idan mun tashi yin aure da salele?!" Ta tambayesa duk da yaji haushi amma be nuna mata ba sai ma eh daya ce mata. "Toh kuwa zan biku amma hemunje mun gayawa baba iro dasu yakumbo talatu." Wani farin ciki ya ziyarci zuciyar Abubakar yace mata. "Toh muje." Jerawa suka yi INdo sai d'an tsince-tsince takeyi yana hanata da haka har suka k'arasa. Tun a bak'in k'ofa ta fara k'iran yakambo talatu tafito da d'aurin k'irji tana tambayar. "Lahiya mai sunan uwa.?" "Anzo tahiya dani gida, ina lawisa da kande suzo muyi bankwana” A gindin bishiya Abubakar ya tsaya yana kallon inda suke rayuwa ya kuma tuno cikin garin kano kafin ya tunano garin abuja zuciyarsa ta dira a k'asar Spain. Lallai Allah beyi ko ina dai-dai ba, wannan yafika kaima kafi wani sannan ya furta kalmar "Alhamdulillah." "Ina wanda yazo tahiya dake d'in, karki ce mini wannan ne?" "Aradu baba iro shine, d'an uwan malamin mune a sani." Tabarmar kaba aka shimfid'awa Abubakar ya zauna tare da baba iro k'arin bayani da kuma sanar dashi cewar da izinin malam Hamza yazo d'aukarta. Abinciccika aka kawo mai saidai beci ko d'aya ba sannan baba iro yace. "Toh gaskiya bazan baku yarinyar nan ku tafi da itaba, hedai muje tare har garin, idan kuma ka yankamu kaida Allah domin hine mesakayya." Babu gaddama Abubakar ya amince, aka sanar da mutanan gari INdo taje ta harhad'a kayanta akayi mata tsaraba da yawa sannan mutane mata da maza suka tafi raka ta gurin mota. "Yakumbo dan Allah idan salele ya dawo kice mihi na tafi amma ya dinga zuwa sumaila muna gaisawa kafin bikin mu kinji.?!" INdo ta fad'a Abubakar dake gaba ya dinga jan tsaki yana jin yadda take k'ara jajjada sak'on da za'a gayawa salele suka k'arasa wajan mota dama tundaga nesa Sadeeq ya hangosu ya dinga kwasar dariya ganin yadda sukayo gungo guda sai tada kura sukeyi, suna zuwa ya had'e rai sukuma mutanen suka dinga fad'in ahe 'yan biyu ne. INdo da baba iro suka shiga gidan baya sannan Abubakar ya zauna a driver seat Sadeeq na kusa dashi ya data motar suka dinga d'aga musu hannu anayiwa baba iro adawo lafiya. Har suka fito daga surkullen babu me magana sai INdo datake lissafo wad'anda zata yi kewa, suna hawa babban titi iska ta fara hurata ta A.C ta mirgina kai sai bacci har rawar sanyi take yi. ***** Sani...Suna zuwa har k'ofar gidan malam Hamza suka tsaya baba Iro ya tashi INdo duk ta cika su da munshari wanda hakan be damu Abubakar ba amma Sadeeq iya kuluwa ya kulu, ta bud'e k'ofar da sauri tana fitowa 'yan unguwa suka fara cewa. "Ga INdo... Ga INdo...!" Ta bud'e ido tare da kuma mistsike shi tana dariya, duk wanda ta gani saita fad'i sunansa kafin ta shige cikin gida da gudu tana k'iran Innar su. "Kai INdo yaushe kika dawo?!" Cewar k'aninta shehu yana wankin kayansa, bata kulasa ba Inna ta fito INdo ta d'areta cikin murna tana washe mata baki. "Oh 'yarnan kina nan da halinki ko??" "Ta6 Inna kenan Ina zeje, yana nan aradu wai ina Nafeesah da Sagiru duk bangansu ba..?!" "Suna waje k'ila dai suntai wani gurin ne, ahe yau zaya d'aukoki jiya malam ke gaya min yadda sukayi da malam Saddiqun." Cewar Inna INdo tayi dariya bata ma bata amsa ba tace, "Inna ina Rukayya kuwa, oh ni INdo tana nan kuwa?!" "Tana nan yanzu ma 'ya'yanta uku sai kuma wanda zata kuma haihuwa." "Kai Inna yanzu cikin wani gareta kama d'ahare ta saye? Bari naje gidan naganta nikam." "Haba 'yar nan daga dawowar ki?!" "Eh wallahi Inna ai Rukayya mutuniya tace kinga tunda na tahi ban mance da ita ba." Tashi tayi ta suri takalma tayi waje, a k'ofar gida taga su malam Sadeeq da baban ta amma ta wuce sai tsayawa take suna gaisawa da mutane. Lokacin da su Abubakar suka gama magana da malam Hamza abubakar kasa tafiya yayi domin yana son suyi sallama, k'ofar gidan Rukayyar ya k'arasa ya tura yaro ya kirata ya kalleta sai faman dashare baki takeyi tana rufe ido yace mata. "Humaira zan tafi gida, Zan dawo jibi insha Allahu karki dinga tafiya yawo idan ba haka ba bazan baki komai ba." "Ai bazan yiba dacta, ammafa karkak'i zuwa kaji?!" Yace "Toh Humaira Zan tafi amma fa kiyi wanka ranar dazan zo." Tace "Toh dacta Ina jiranka." Yana tafiya ta koma gidan Rukayya shi kuma ya shiga mota bayan sunyi sallama da malam Hamza da baba iro. Sadeeq yaja mota suka nufi gida. Da daddare suna zaune abin duk ya damu Sadeeq ya kalleshi yana danna laptop yace mai. "M twinnie can you tell me why cared Nd protect her? I know bawai dan wancen dalilin bane tunda gashi har kana cemin zuciyar kace please tell me." Ture laptop d'in yayi tare da kwanciya ya sanya hannuwansa ya tallafo kanshi yana kallon fankar sama yace. "Twinnie bazan 6oye maka ba hakan yasa naje tare dakai muka dawo da ita gida, twinnie I'm in love with her, I can not do anything with out her. Ina son ta zama matata, ina son na mallaka mata ragamar rayuwata koda kuwa bata zama wayayyar da nake da burin aura ba." Cikin tsananin mamaki da al'ajabi Sadeeq yake kallon Abubakar jin abinda ya fad'a. Ganin Sadeeq na niyar yin magana yasa shi saurin cewa. "M twinnie kayi min fatan alkairi, ka kuma taya ni yak'in neman yarda da soyayyar Humaira please n please twinnie." "Allah ya k'ara dankwan soyayya Allah yasa ayi komai muna nan." Cewar Sadeeq yana kallonsa, Abubakar yayi murmushi tare da cewa. "Amin m twinnie thank you." Kowa ya cigaba da abinda yakeyi zuciyar Sadeeq fal mamaki, shi kuma Abubakar tashi kaddarar kenan auran INdo Allah kadiran alaman yasha. Washe gari Sadeeq ya tafi k'wara state, a day after Abubakar ya shirya tafiya sumaila yayi sallama dasu Mama, sannan ya d'auki k'anwarsu Hawwah ya kaita wani shago yace ta had'a mai kayan kwalliya, tayi-tayi ya gaya mata na meye yak'i tana dariya ta had'a mai komai sannan ya bata kud'i yace tahau napep. Ya wuce a hanya ya tsaya ya shiga wani Boutique ya siyawa INdo wasu tsala-tsalan dogwayan riguna guda biyar da takalma guda uku ya had'asu da kayan kwalliyar sannan ya wuce sani... *HAJJA CE*👈 [7/2, 6:33 PM] Aisha Galadima: *⚗⚗ MUSAYAR ZUCIYA...⚗⚗*                     ♥                  ♥♥          A true life story Na *K.A.S Precious Hajja ce*👈 *HASKE WRITER'S ASSOCIATION*💡 (Home of expert & perfect writer's) *DEDICATED TO* Sanah Isma'il matazu. *VOTE me on wattpad @Hajjac* _Ina ganinku dearest comments d'inku na k'ayatar danifa_ *K'anwata Stylish, my Xoxo, Faxyfation, phartzarah, Nuceeyluv, khady, Mmn gausiya, UmmuMuhammad, Khady M/kano, Mmn nuceey, sumeey Q, Meela adeel, Mummy, Hafsat A Fulani buchi, Hafsat A shitu, aunty Ag,💞 Ummul Meenal, Habeeba M, aunty baraka, Mmn Nazir👜* gaskiya bazan iya duka ba kuyi hakuri naga nakusa yin rabin wani paragraphs d'in🤪. Page *14* Yana zuwa unguwar ya ganta a k'ofar gida a zaune tayi wanka tayi kwalliya irinta zamani lokacin ba'a gama sanin su concealer ba, amma tasa eyeshado red janbaki tayi kuma jagira.Tana ganin mota a k'ofar gidan su ta shek’a da gudu tana gayawa su Inna yazo kafin ta kuma fita kamar wata saban kamu lokacin harya fito yana rik'e da murfin ya kalleta itama ta kallesa. Sanye yake cikin wata dakakkiyar shadda getzner light blue anyi mata dinki na dark blue ya d'ora hula fuskarsa har wani kyali-kyali takeyi kawai INdo ta saki baki da hanci tana kallansa kallo na kurrullah tamkar tana son ganin wani abu ya mik'a hannunsa yana zagaya shi a saitin fuskarta tayi firgigita tare da yin dariya tace. "Dacta Habubakar wallahi kanada kyau ta6 heyau na ta6a ganin haka." Murmushi yayi tare da rufe k'ofar ga yara sun fara mai dandazo ya ciro 2k yabasu sannan ya shiga zauran gidan su ta bishi ya tsaya yana kallonta ganin tayi mai wankan dayace tayi harda kwalli sai ya ce. "Humaira babu gaisuwa? Bafa ki gaida niba." INdo tace "Au hakane fa ina yini ya gida ya iyaye..?!" "Lafiya lau baki tambaye ni malam Sadeeq ba why..?!" "Ta6 narasa wanda zan tambaya hewani malam Sadeeq Allah ya tsare ni wallahi." Kyaleta yayi ganin bilhakk'i bata son Sadeeq tun lokacin daya hanata atamfa, kallonta yayi yace. "Ina baba yake?” Tace "Baya nan." Abubakar yace "Toh Inna fa?" INdo tace "tana ciki." "Toh jekiki ce zanzo mu gaisa da ita." "Kai dacta Habubakar, kawai kashiga meye na tsayawa ai bazata hanaka ba." "A'a Humaira ba'ayin haka a musulinci dole sai kinje kin gaya mata." "Toh hikenan tunda baka yadda dani ba." Tana magana tana shiga gida, yana jiyo sanda take gayawa Inna sak'on duk maganar da sukeyi yana jiyo su. "Kai Inna toh meye na saka hijjabi dan nace miki dacta habubakar zai shigo. Lallai saban salo." Rintsa ido yayi jin yadda INdon keyin magana da mahaifiyarta, lallai yarinyar nan indai yana sonta yadda yake so toh akwai jan aiki a gabansa. Dawowarta kawai ya gani beji motsinta ba, tana dariya tare da wasa da gefen mayafinta tace. "Tace ka higo an hinfid'a maka tabarma a k'ofar d'aki." Tana gaba yana bayanta har suka k'arasa ya zauna, daga bakin k'ofar d'akin Inna ta tsuguna suka fara gaisawa. Shiru babu wanda ya sake magana sai gasu Nafeesa sun shigo itada k'awarta suka gaidashi, Abubakar yace ma Inna. "Inna dan Allah idan babu damuwa ina son ki bani aron su Humaira suyi min rakiya nan cikin gari." Shiru yaji Inna tayi kafin can kuma yaji tace. "Toh gata nan ai Nafeesah sai tazo kuje tare harda ita." "Toh Inna na gode." Tashi yayi yafita su kuma suka bi bayansa. A baya Nafeesa ta zauna yayin daya kwashe ledojin kayan yasa a k'asa wajan dazata saka k'afa tace ta shiga ta zauna sannan shima ya zagaya drive seat ya zauna tare da tayar da motar suka tafi 'yan kauyan sai gulmarsu akeyi. Cikin garin Sumaila suka shiga INdo badai surutu ba sai labari takeyi musu sanyin A.c yana ratsata ga k'amshi a cikin motar ta kalli Abubakar tace. "Dacta Habubakar wannan motar taka akwai sanyi karmuyi mura a bud'e gilahin." Dariya yayi sannan ya mik'a hannu ya rage A.c ya juya yana kallanta itama shi take kallo yace. "Humaira ya akayi ne?!" INdo tayi dariya tana tafa hannuwa tace. "Meye kuwa, wai Ina zaka kaimu ne hefanan tafiya muke..?" Parking yayi a bakin titi wajan wani shagon saloon ya kalleta yaga sai kallon window take ya juya bayansa Nafeesa sai bacci take a hankali ya mik'a hannu zai ta6a kafad'un INdo sai kuma yayi saurin janyewa tare da bud'e k'ofar yafita. Zagayawa yayi ya bud'e mata ta fito yace su shiga cikin shagon abar Nafeesah tunda tana bacci suka nufi shagon ya tsaya ta glass inyamurar ta hango su ta fito cikin azama. "Hey!good evening sir how are you.?!" "Fine madam how is your business." "Fine..fine oooh." INdo tabisu da kallo sai faman tabe baki takeyi ta samu sumintin gurin ta zauna tana kallon titi. Saidai Sadeeq ya gama gayawa madam Gloria abinda za'ayiwa INdo sannan ya kalleta yace. "Yauwa toh Humaira tashi ku shiga ciki." INdo ta kalli madam gloria cikin mamaki ta maida kallonta gurin Abubakar tace. "Mezai kaini wajan arniya dacta Habubakar? Arniya cefa kake cewa naje gurinta, me zata min...?!" Ganin yadda takeyi ne yasa hankalin Abubakar tashi har mutane sun fara taruwa da k’yar ya satayi shiru yace mata. "Kayanki zata baki amma tunda bakya so zomu tafi gida." Da sauri ta nufi madam guloriya tana cemai. "Yo toh ai kaine bakayi min bayani ba."Gloria na gaba tana bin bayanta Abubakar ya girgiza kai sannan ya koma wajan mota yana jiran fitowar Gloria . INdo kuwa suna shiga gurin taga abubuwa birjic ga manyan madubai ta kalli fuskarta sosai sannan ta fara gyara kwallin daya zazzago mata wajan kumatu Tese yarinyar Gloria ta cewa INdo. "Sister come and seat here." Sam INdo batasan da ita ake ba Tese ta kuma yi mata magana still INdo bata juyo ba Tese taja tsaki tare da zuwa ta janyo hannun INdo tare da zaunar da ita a wajan wankin kan sai masifa take da turanci ita kuma INdo tana Hausa. Cige d'ankwalin Tese tayi taja wani uban tsaki ganin ko tsefewa batayi ba, gashi Mommy d'inta tace tabita a hankali dan wanda ya kawota yace zata iya guduwa. Kibiya tad'auka ta tsefe mata gashi akwai laushi da tsayi saidai babu cika gashi kuma jah ne. Mayukan wanke gashi ta d'ebo sannan ta janyo kan INdo ta malala mata sai mita takeyi har aka gama Madam guloriya ta kuma shigowa hannunta d'auke da riga da takalmi wanda Abubakar ya bata yace abata tasa ayi mata kwalliya. Lokacin da aka saka kan INdo a dryer taji zafi sai ta saki wani uban ihu wai zafi, Madam Gloria tazo tana d'anyi mata wasa tare da takura mata har aka gama kannan yayi kyau gashi an tura mata shi yayi baki Tese ta nuna mata bathroom a shagwan ta nuna mata tace tayi wanka, INdo tayi da sabulai masu k'amshi gashi ruwan d'umi sannan ta fito sanya da kayan data cire babu wanda ya kulata Tese tayi mata kwalliya sannan aka bata doguwar rigar suka ce ta saka. Duk bayanin da sukeyi mata toh da hannun suke nuna mata tamkar wasu bebaye. Wata irin had'add'iyar abaya ce pink da belt black sai kwalliyan ma black ta jikin rigan, fitowa tayi daga d'akin bayan tasa saidai jikinta babu bra madam Gloria ta tambaye ta bayan ta nuna mata ta jikinta kasan cewar itama INdo akwa breast d'in ta turo baki tana k'unk'una da alamar dai batada ita. Babu kunya madam Gloria tafita wajan Abubakar yana zaune suna hira da Nafeesa tace k'anwarsa batada bra amma suna siyarwa ya bada kud'in. Abubakar kunya ta lullu6esa yace toh abata zai had'a a cikin kud'in gyara sannan ta koma aka cire dai-dai size d'inta ta saka suka d'aure mata belt d'in sai ta koma tamkar ba wadda ta shigo d'azu ba. Tese ta sa mata veil bayan ta jera mata ribbon INdo tayi d'as da ita tamkar ba INdo malam Hamza ba. "Wowww nawawoo see this girl ooooh, you look so beautiful my daughter." Ita kanta INdo data kalleta a cikin madubi saida ta sake ta6a fuskarta dan a tunaninta ba ita bace, Madam Gloria ta fesa mata turaruka sannan ta kamo hannunta suka fito Tese sai dariya takeyi. Abubakar na ganin sun fito ya mik'e yana kallon INdo k'irjinsa na mugun bugawa, ita kuma ta kasa kallonsa domin wata irin kunya ce da nauyinsa suka dirar mata a lokaci d'aya. Da kyar Abubakar ya iya kallon madam Gloria yayi mata godiya tare da zaro 15k ya mik'a mata ta k'ar6a sai k'ara kod'a INdo takeyi shi kuma ya juya tare da bud'e mata k'ofa ta shiga ta zauna ya rufe. Cikin tsananin mamaki Nafeesa ke zuro kai tana lek'en fuskarta kafin tace. "INdo..! Koba kebace ne? Nashiga uku, wallahi kece dan ga fashin gohi nan." Banza da Nafeesa INdo tayi domin ita kanta tunda aka haifeta bata ta6ajin ta a wani irin yanayi na cikar kamala ba irin yanzu. Abubakar ya kalleta yana lek'en fuskarta shima yayi murmushi tare da cewa. "Humairah kinyi kyau sosai." K'irjin INdo ya kuma bugawa kanta ya fara sarawa jitakeyi tamkar an sauyata gabaki d'aya, bakinta kuwa ji takeyi tamkar ansa zare da allura an d'inkeshi ta kasa cewa ko uffan ta kuma kasa kallonshi. Kunna motar yayi suka fara tafiya sai magana suke mata shida Nafeesa amma tayi shiru, farin ciki takeyi yau gata cikin rigar da ko a cikin mafarki bata ta6a zaton zata sanya taba ga takalmi d'an ubansu tayi shigar da duk kauyen Sani babu wanda ya ta6ayin irinta. Shin mezata cewa dacta habubakar akan wannan abun dayayi mata, shida ba yayanta ba, ba wani nata ba a'a d'an uwane a gurin wani malamin su..! Saida ya tsaya a wani shago ya siyo musu abubuwan kwalan da makulashe sannan ya nufi kauyen Sani. Daga shi sai Nafeesa kawai suke magana amma ita batayi rigar jikinta kawai take kallo tanajin ina ma salele zaizo yau ya ganta ta zama sabuwa. A k'ofar gida ya tsaya Nafeesa ta fito ya bata ledojin INdo ma tazo zata k'ar6a ya girgiza mata kai sai da Nafeesa ta dawo ya bata harda ragowar kayanta sannan ya kalleta yace. "Humaira kina son yin karatu..?!" Shiru tayi tana faman muzurai, a zahirin gaskiya batada wani sha'awar yin karatu domin tun farko dama batasa shi a cikin tsarin rayuwar taba. Gani takeyi ma yanzu wace makarantar zatayi dan tafi k'arfin tsefawa sabida duk mate d'inta sunyi candy dan haka ma ta kuma cire san makaranta a zuciyarta. Kallonta yayi yaga yanayinta ya canza ya ciro wayarsa yana yi mata photo wannan kuwa harda su style, ya d'an matsa kusa da kujerarta tare da cewa. "Matso toh muyi photon tare." INdo ta matsa suka kusan had'e fuska yayi musu selfie kusan sau biyar yana d'aukar su gaba d'aya sunyi kyau musamman Abubakar dayasan shika-shikan iya selfe. Agogon tsintsiyar hannunsa ya kalla biyar sauran minti uku yace mata. "Humairah zan tafi sai na dawo please take care." Murmushi kawai tayi mai sabida bata san abinda ya fad'a ba bayaga (zan tafi sai na dawo). Ya zaro 5k ya mik'a mata tana kallonsu ta wutsiyar ido tana son k'ar6a tana jin wani iri ya d'ora mata a kan cinyarta ta d'auka zata bud'e k'ofar yayi saurin rufewa tare da cewa. "Humairah baki min godiya bafa zaki tafi, haka akeyi daman." Tayi saurin rufe idanu tare da cewa. "Kayi hakuri inata son yima na manta, angode Allah ya k'ara bud'i." Yace "yauwa kokefa harnaji dad'i, duk wanda yayi miki kyauta ki dinga ce mai angode kinji ko?!" Tace "Toh zanyi sai anjima yaushe xaka dawo garin mu?!" Da sauri ya kuma kallonta jin tana neman ya dawo, cikin wata irin murya yace. "Humairah kina son na kuma dawowa?!" INdo ta d'aga kai alamar eh yayi murmushin jin dad'i sannan yace. "Toh shikenan wani satin zan dawo amma ki dinga kwalliya gashi can na siyo miki kayan kinji..?!" "Toh Nagode ka kaida gida." "Zasuji amma bakice nagaida malamin kuba." Tace tana yatsina fuska. "Ai bayida kirki da kaine bakada kirki amma yanzu shine bashida kirki." "Toh kiyi hakuri ya dena kinga 'dan biyu nane." "Naji na dena kace ina gaidahi." "Zaiji a gaiheda Inna da baba." Yafad'a cikin kwaikwayon maganarsu, ta fita daga motar lokacin su Uwani halilu sunzo gulma, shi kuma yaja motarsa yabar unguwar zuciyarsa na kudurta mai son auranta. *HAJJA CE*👈 [7/3, 10:06 PM] Aisha Galadima: *⚗⚗MUSAYAR ZUCIYA...⚗⚗* ♥♥ ♥ A true life story Na *K.A.S Precious Hajja ce*👈 *HASKE WRITER'S ASSOCIATION*💡 (Home of expert & perfect writer's) *VOTE me on wattpad @Hajjac* *DEDICTEED TO:* Sanah Isma'il Matazu _Shafin yau naki ne *Yayya Nabeelah* ina miki fatan alkairi aduk inda kike #much_😘 Page *15* Da sauri ta shiga gidan su Uwani da Maryam na biye da ita lokacin su duk da yaransu sunyi aure,tana zuwa taga Nafeesah tayi d'aya-d'aya da kayayyakin cikin ledar su Sagiru da shehu sai shan sweet da chocolate sukeyi INdo tayi kukan kura tare da fad'awa kan kayan tana yiwa Nafeesah masifa. "Dan uwarki wane d'an iskan ne yace idan kin higo ki bud'e min kaya na? Kodan kin rakani hine zaki dinga min hihigi cikin abubawa na, ai danni aka siyo. Bani kayana banza kawai sutofes (stupid)." "Ke INdon nan wallahi masiffiya ce, ba mubiyu ya siyowa kayancin ba, ai na san kayan sawar naki ne amma ai daya higa shigon nan ya dawo cewa yayi idan mun dawo muhya. Ke wallahi rintoh gareki." "Ah Kakan cewa yayi mu raba. ke waima wayake son ya dinga yiwa mutunci? Ni ko keh?" "Oho ba'a sani ba, kuma yasin komai rabahi za'ayi dai-dai." Sagiru daya hango wata alawa k'ark'ashin k'afar INdo yayi wuf ya d'auke tare da 6arewa yasa baki da sauri dan karta juyo yana cewa. "Wallahi kuwa Nafi karki sake ta cuceki a raba shi ki fara d'auka." Da sauri cikin bala'i wanda har rufe mata ido yake yi tace, "Toh munafiki algungumi zugata, wallahi hekaja ink'i rabawar banza kawai..." "Oho dai a raba mugani." Ya kuma fad'a cikin tsokana tayi mai banza tare da maida kayan da jakar kayan kwalliyar ta cikin leda sannan ta kalli Nafeesah tana hararart tace. "Ki za6a raban Allah za'ayi ko kuma raban gaskiya kike so..?!" Nafeesah ta murgud'a baki tare da cewa. "Rainin hankali, toh raban Allah da ma'aiki zaki yi mana babu wani rabon gaskiya 'yar latsi..!" Suna kallonta saida ta fara ware komai daban sannan ta kwashi me yawan ta turawa Nafeesah kad'an tace. "Gashi nan." Nafeesar ta kwaso wata uwar ashariya ta zubeta sannan tace. "Idan kin isa kice ba uwatace ta haifeni ba kanbala'i..." Inna na kallonsu tun shigowar INdo k'irjinta ya fara bugawa kanta yana juyawa ganin yadda 'yar tata tadawo sabuwa, Allah yasa dai ba wani abun yayi mata ba ko yake son yimata ya fara kowa mata shiga masu kyau. Duk fad'an da suke yi ta kasa cewa dasu uffan bakinta fal addu'a da fatan Allah ya cire mata wasi-wasin da take yi akan lamarin Abubakar. "Gaskiya kema INdo kinso kanki dayawa, taya ance kiyi rabo tsakani da Allah sai kiyi yadda kikaga dama dan mugunta..." Cewar Maryam Aliyu tana bawa d'anta nono. Can Sagiru ma yace rabo beyi ba Nafesah karta yadda ita kuma Uwani tana bayan INdo dankar sai an gama fad'an ta hanata komai. INdo ta matse nata tsakanin cinyoyinta tare da cewa. "Saida na tambaye ki rabon Allah ko rabon gaskiya kika ce na Allah toh ai Allah baya rabawa dai-dai sai dai yabawa wannan meyawa ya bawa wani kad'an, alal misali kinga ai Maryam ke mijinki yafi na uwani kayan gona kuma dacta Habubakar shima yafi baban mu kud'i ko ba haka ba..?!" "Oho miki banza muguwa kuma bari ya dawo saina gaya mihi." "Sai ki fad'a ko'a jikina wallahi." Ta fad'a tana jan tsaki. d'aya-d'aya ta bamawa su Uwani, babu wanda beji haushinta ba sabida ko 'ya'yansu bata bawaba suka tashi suka tafi. Kallon Inna INdo tayi ganin tayi tagumi yasa tacewa. "Inna kizo kiga kayan da ya kawo min, ya kaini aka sani a inji mezafi aka gasa min kai aka dinga hyafamin wasu abubuwa akaina Inna jibi yadda gahina ya zama.." Tana magana tana bud'e kanta, gabaki d'ayansu suka kalleta baki bud'e cikin mamaki Inna tace. "Nahiga uku ni Maryamu 'yarnan kanki nekuwa?" "Hehehe kaji Inna da wani batu, toh inba nawa bane jikin kuma nawaye kema dai." "Ta6 lallai INdo anyi klin kinga yadda aka nannad'a miki gahinki kamar na indiyawa." Cewar sagiru yana kwakulo chocolate d'in daya mak'ale jikin jajayan hak'oransa. Banza tayi mai taci gaba da nunawa Inna kayayyakin daya siyo mata, Inna tayi godiya cikin rashin nuna kyashi ga uwa a wani bigire da wasu 'ya'yan keyi INdo ta d'akko wani flat shoe tare da janyo k'afar Inna tana cewa. "Inna saka wannan mugani kozai yi miki." Tana saka mata kuwa yayi cif-cif a k'afar Inna INdo tayi dariya tare da fad'in. "Inna k'afarmu d'aya Ashe, toh nabar miki wannan innata kema kidinga sakawa idan zaki unguwa ko kauyen ku." Da sauri Inna ta zare takalmin daga k'afarta tare da rik'o hannun INdo tace. "A'a 'yarnan barshi na gode miki Allah yayi albarka amma bazan k'ar6a ba, sabida ke aka bawa tayaya zan k'ar6e miki ya gansu a jikina a'ah." "Toh danya gani kuma Inna heme? Zece kibahi ne? Kawai ki k'ar6a nina baki ai yariga ya siya min." Ganin ta dage yasa Inna ta k'ar6a tare dayin godiya sannan INdo ta shiga da kayanta cikin d'aki ta zuba a cikin Ghana must go d'inta. Tashi tayi tafita zuwa gidan Rukayya, duk inda tayi mutane sai sunyi mata magana, maza kuma su tsayar da iya amma sai hura anci take kanta a d'age tana 6are alawa tana sha hankalinta kwance duniya tayi mata sabunta jinta takeyi tamkar akan iska. **** Qarfe 2:35pm ya fito daga office d'inshi, sauri yake yaje gida yayi wanka dan yana son zuwa sani a yau. Da sauri yafita yana zuwa gida wanka yayi tare da shiryawa cikin k'ananun kaya white jeans da black shirt me dogwan hannu ya d'ora facing cap dama ya riga yayi sallah yaci abinci a office dan haka ledar d'in kunan daya bawa Hawwa ta d'inkawa INdo su ya d'auka yafita sai bulala k'amshi yake tamkar anyi 6arin turaren. Passenger seat ya ajiye kayan sannan ya tada motar ya wuce domin yau kwanansa goma sha hud'u rabansa da kauyan Sani, yayi missing d'in INdo ba kad'an ba domin babu waya a hannunta. Yana shiga unguwar yara suka yayyame shi yayinda suke ta mik'a mai gaisuwa, yau kam suna da yawa harda matasan samari ya ciro 3k ya basu yana mamakin abinda suka maidashi tamkar wani kansilan su ko chairman d'insu. Shehu ne ya k'arasa jikin motar yace. "Bari a k'irata tana gidan k'awarta." Abubakar yayi murmushi tare da d'aga kai sannan shehu ya ruga da gudu gidan Sahura kokafin yaje Ashe har an gaya mata suka had'u a hanya shehu na gaya mata irin kyawun da Abubakar yayi yau ita kuma ta k'agara tagani hakan yasa ta yin gudu. Ta glass ya hangesu ya zaro idanuwansa yana kallonta ganin tun rigar datasa ce a jikinta tayi jirwaye su manja bak'in tukunya ne gashi nan dai ya kifa kansa akan sea-tearing. Ashe babban aiki ne a gabansa na aniyar ganin INdo ta waye, toh meye amfanin wad'ancen kayan na gurinta gashi yau harda k'aro mata kala shida duk atamfofi, yasan ma aikin banza ne yanzu ya zaiyi. Kafin ya nemo amsa yaji tana mai magana a hargitse sai uban nishi takeyi ya d'ago da kansa a hankali tare da zuba mata fararan idanunshi akan nata yana lumshewa cikin wani irin salo. Bah k'aramin kyau da had'uwa taga yayi mata ba taji k'afarta na rawa zuciyarta na harbawa muryarsa a sark'e yace mata. "Humayrah ook at you, da alama yau ko wanka bakiyi ba a matsayinki na 'yanmata wadda ta kusa yin aure jibi tun rigar last week meye hakan..?!" Tana wasa da belt d'in rigar daya fara zarewa tace. "Wallahi dacta bansan zaka zoba yau danayi kwalliyar." Tsaki yaja d'an k'arami sannan ya fito daga cikin motar ya jingina yana kallonta. Tundaga sama har k'asa take binsa da kallo yace mata. "Dena kallo na." Toshe baki tayi tana dariya jin abinda ya fad'a ashe yana kallon yadda take mai ya kuma cewa. "Tunda naga alamar bakya son yin wanka toh zan canza ki na koma kan Nafeesah domin tafiki wayewa. Ko kuma na dena zuwa tunda abin naki haka ne." "Wayyo dacta dan Allah kayi hakuri wallahi ko hekaran jiya da salele yazo nayi kwalliya ka tambayi innan kaji, kaima fa dan bansan zaka zo bane." Tayi maganar tamkar zata rarume dan duk ta rud'e jin cewar zai dena zuwa. Komawa yayi ya zauna sannan ya kalleta yace. "Toh jeki ki wanka ki kuma saka sabuwar riga ina nan Ina jiranki." Da sauri ta shiga gida, kafin minti biyar sai gata cikin sabuwar riga yellow da kwalliyar gloden ajiki sai hoda data shafa da lipstick ta fito duk dan kada ya tafi. Kallonta yayi tare da yin murmushi yace. "Toh koke fa, shiga muje na siyo miki wasu abubuwan ina Nafeesah ta raka mu?!" Cikin sauri INdo tace "Bata nan taje kai nik'a muje kawai basai ta rakamu ba." "Toh shikenan." Ya fad'a tare da shiga motar ya bud'e mata ta shiga yaja suka tafi yana janta da hira cikin salo irinnashi. Cikin gari suka shiga yayi mata shopping abubuwa na buk'ata su brush, makilin, sabulun wanka na wanki, mayukan gashi turaruka, pad, cotton balls, panties dadai sauran su sannan suka juyo gida. Abubakar ya gargad'eta sosai akan yin kwalliya sannan ya bata d'inkunanta INdo ta dinga zuba mai godiya kamar bakinta zai tsinke sannan suka yi sallama zata fita kawai yaga k'asanta duk ya 6aci yayi saurin dakatar da ita ta hanyar cewa. "Humaira kinsan al'adarki tazo?!" Da sauri ta kalli bayanta domin wannan shine karona biyu data ta6a yi, na farko a saye yakumbo talatu tace mata kowace mace tanayi sunansa al'adah kuma inyaxo ba'a sallah ba'a ta6a kur'ani. Tace masa "Ban saniba yasin amma ba komai yakumbo ta gayan yadda zanyi." Hannunta ya janyo karo na farko da hakan ya ta6a faruwa, ledar hannunta ya kar6a tare da zaro pad yaciro guda d'aya yace. "Kinsan wannan." INdo ta girgiza kai yayi murmushi tare da zaro pant d'aya ya nuna mata yadda zata yi yace. "Yanzu idan kinje gida saiki saka a haka kinji? Duk sanda tajik'e saiki cire kiyar kisake wata bye-bye." Ya fad'a yana d'aga mata hannu, bud'e k'ofar tayi da ledoji a hannunta ta fita shi kuma ya janyo yare da d'ora kyalle agurin data 6ata mai ya bar unguwar. Bayan wata biyu. *HAJJA CE*👈 [7/4, 6:39 PM] Aisha Galadima: *⚗⚗MUSAYAR ZUCIYA...⚗⚗* ♥♥ ♥ A true life story Na *K.A.S Precious Hajja ce*👈 *HASKE WRITER'S ASSOCIATION*💡 (Home of expert & perfect writer's) *VOTE me on wattpad @Hajjac* *DEDICTEED TO:* Sanah Isma'il Matazu Page *16* Zaune suke a cikin ajin wanda yawancin su duk matan aure ne da alama makarantar manya ce ta yak'i da jahilci. Gefe guda kuma INdo ce ta duk'ufa tana kallon wani littafi na alifun ba'un sai faman mamul-mamul takeyi da bakinta da alama sotake tasan su ta kuma gane su a haka wata dattijuwar malama ta shigo hannunta rik'e da littattafai idanta sanye da glass fari ta samu guri ta zauna. Bayan ta kammala biya musu littafin ahkdari ta zauna tana kuma yi musu bayani har tazo tana yi musu sharhin isra'i da mu'iraji tana basu labarin ire-iren matan da annabi (s.a.w) ya gani a cikin wuta tace. "Manzon Allah sallallawa'alaihiwa sallam yana cewa aure sunnah tane duk wanda baya son aure baya tare dani, baya da alkairi mutum ya zauna yayi ta kace nace da mutum musamman idan bata fuskar addini ba. Lokacin da ma'aikin Allah (s.a.w) ya dawo daga isra'i Nana Fateema da megidanta sayyadina Aliyu suka je gurinshi suka tarar dashi yana kuka suka tambaye shi menene yasanya shi wannan kukan, sai ma'aiki yace, yaga mata dayawa daga cikin al'umarsa anayi musu nau'i-nau'in azabobi kala-kala. Yace yaga wata mata an d'aureta d'auri irinna azaba da gashin kanta, _itace mace baliga wadda take barin gashin kanta a waje dan wasu sugani_ ya kuma ganin wata an zaro harshenta an nannad'eta dashi, yace _itace wadda take d'aga murya idan tanayiwa mijinta magana duk yadda taga dama, duk abinda zai mata ta kushe, ta dinga ganin be'iya yi mata komai_ wata kuma an tsananta d'aurin nononta, _itace wadda bata kula da shimfid'ar mijinta, bata bashi hakk'insa, ko tayi ta garashi dan taga yana buk'ata, sannan tana bin wasu mazan a waje_ wata kuma aka maida fuskarta ta alade jikinta na jaki. _itace wacce ta kassance munafuka, annamimiya me d'aukar magana takaiwa wannan taje can ta kunsa wata maganar_, ita ake yiwa wannan azabar.." Akwai nau'ika kala-kala daya sanar dasu wanda ya gani, anan gurin kowacce tasan abinda takeyi na rashin dai-dai dan haka sai kowacce taje ta gyara wanda takeyi kafin tilon ganyenta ya bushe ya fad'o ma'ana kafin ta koma ga wanda yayita. Akwai masu iyaye a raye babanki neko Mamanki kiyi musu biyayya akan abinda besa6awa shari'ar musulinci ba domin sa6a musu babban laifine a wajan Allah dama cikin rayuwar mutum gabaki d'aya, Allah yayi mana kyakyawan k'arshe.." Duka ajin suka amsa da amin sannan malamar ta fita, kasan cewar ajin duk matan aure ne mutum uku ne 'yan mata yasa INdo bata irin wannan haukan gashi basa kulasu ita kuma karatun ba wani shigarta yake yi ba saidai tana matuk'ar san tarihi domin jinta takeyi tamkar agabanta akeyi wasu abubuwan. K'arfe shabiyu da rabi aka tashesu gaba d'aya makarantar hijjab suke sawa kuma kala d'aya shine ya zama kamar uniform d'insu. Yau kwanakinta talatin da biyar da kawota makaranta babu abinda za'ace sai hamdala domin ta fara iya yin sallah sai dai sam kwakwalwarta bata d'aukar hadda, a gurin za'a biya tanaji amma kuma ya zauna a cikin kwakwalwar ne wahala. Tana fitowa itada k'awayen da tayi sababbi Zainab da Hadiza suna maganar littafin k'awa'idi sai ga me mashin d'inta wanda Abubakar ya samar mata yazo d'aukarta, shine yake kawota ya kuma dawo ya d'auketa duk sati Abubakar yake bashi kud'insa sukayi sallama ta hau suka tafi. Zama tayi a cikin d'aki suna hira da Inna ita kuma tafito da littattafan tana kallonsu taja tsaki tare da fad'in. "Wallahi Inna karatun nan badai wahala ba, ni wallahi duk makarantar ta iheni dacta Habubakar ya takura min." Ta k'arasa maganar tana turo baki tare da yatsina fuska, Inna tayi dariya tace. "Haba 'yar nan ki dubafa kigani zuwanki makarantar nan yanzu sallah bata wuce ki, sannan kina zaune a gida kina k'ok'arin yin alifun ba'un d'inki aini kam naji dad'i wallahi." "Ta6 lallai Inna, nifa ma wallahi inajin film zan higa dan wallahi dana fara Inna zaki ganni da narkekiyar mota wadda tafima ta dacta." Tafad'a cikin nuna son yin abinda tace, Inna tace, "Ahir d'inki da wannan sana'ar, yanzu keko cewa akayi kihiga ai bakyaje ba sabida ma tsarinku ba d'aya bane su sunfiki kud'i da karatu." "Toh Inna bakiga 'yar autah ba me sa bakin janbaki, yanzu kina nufin kice min itama tafini kud'i ko iya film d'in...?!" "Oh ni maryama nace bana son kiyi amma kuna dagewa." "Toh kiyi hakuri Inna dan yau anyi mana magana akan yiwa iyaye abinda basa so,malam Hansa'u tace me sa6awa iyaye idan ya mutu Allah ze k'onashi na denayi miki na fasa higa film d'in." Daga nan suka cigaba da hira duk ranar asabar, lahadi da litinin INdo na makaranta kuma alhamdulillahi duk sanda taje ta dawo akwai abinda zata d'an tuna musamman idan anayi musu k'arin haske akan littattafan. Shi kuma Abubakar idan yazo zai kuma sanar da ita abinda shima ya sani da haka INdo ta fara gane fari da bak'i sannan gashi Abubakar yana iya k'okarinsa wajan ganin yayi mata abubuwan zamani wayace kawai yak'i siya mata sabida yasan ba k'aramin d'auke mata hankali zatayi ba shi kuma yana son yaga ta samu wani abun a Cikin addininta. *Bayan shekara d'aya DA rabi* Waya ce kare ajikin kunnansa yana ta faman cike-ciken files sai faman murmushi yake yi sannan yace. "M twinnie na riga na gaya maka bazan samu damar zuwa gidan su wata Fateema ba gobe sabida akwai inda zani, nifa Fateema ma ta rainani wallahi ko ta d'auka kaine babba dan cewa tayi min wai wasan k'anin miji ta farayi dani." Sadeeq yayi dariya tare da cewa. "My sweet heart kenan ai tayi min dai-dai kasan wayayyen mutum gashi dama ta shiga college abin ya kuma k'aruwar mata Ina son Zarah M twinnie." Abubakar ya ta6e baki tare da cewa "Yh I see. Yanzu dai sai goben idan ka dawo ma had'u nima idan naje wajan babyna zan baka ku gaisa da ita." "Okey no problem Allah ya kaimu." Daga haka sukayi sallama kowa ya ajiye wayar yana kewar d'an uwansa, har tsawon shekarar nan Sadeeq besan Abubakar yana tare da INdo ba domin duk iya hutun da zaiyi a gida baya ta6a gigin nuna mishi dan ko wayarshi gallery d'insa password d'in a jiki bazaka ta6a tunanin ma cewa yana ajiye hoton mace a cikin wayarsa ko laptop ko wani gurin ba sabida iya taku da d'auke kai irin nasa. Washe gari Sadeeq ya dawo ranar raba dare sukayi suna hira. Da gari ya waye su Mama da sauran yaran gidan anata shirye-shiryan zuwan budurwar Yaya Habu domin a ranar yake son kawo INdo gidan su ganta itama taga 'yan gidansu. Sam Sadeeq besan lokacin da Abubakar ya fita ba, sai shiga d'akin yayi ya tarar k'amshin turarensa, wanka yayi ya kwanta tare da janyo waya ya k'ara Fateema lokacin sun fito daga lecture around 2:45pm. Abubakar kuwa yana shiga kauyan Sani yayi parking a k'ofar gidan su INdo,malam Hamza ya fito suka gaisa sannan yace. "Ai uwar tawa tace idan kazo kajirasu su dawo taje gidan kwalliya, nace yanzu ita kwalliyar ce bazata yi ba sai anje har cikin garin sumaila. Wai ai waccan tafi kyau nace toh Allah ya kyauta." Murmushi Abubakar yayi yana shafa k'eya tare da rissinawa yace. "Ai babu komai baba zanjira." Fita malam Hamza yayi yana ta shiwa Abubakar albarka yana jin aransa zai iya bashi duk abinda yake so indai yana dashi burinsa ma a yanzu kawai yaji Abubakar d'in yace yana son INdo amma yayi likimo ko ita 6eta6a furtawa kalmar ba sai 'yan gidan su daya dama da zancen Aisha budurwarsa. A 6angaran INdo kuwa tunda ta fara gane kyautatawar Abubakar da karamcinsa a gareta da irin yadda yake nuna kulawarsa gareta yasa ta mallaka masa zuciyarta gabaki d'aya, ta sallami salele jira kawai takeyi taji Abubakar yace yana sonta amma hakan ya gagara, gashi zuciyarta ta riga ta mutu akan sa dan ji takeyi tamkar ta fad'a mishi sai dai yanzu tana da kunya dan a makaranta ana gaya musu cewar kunya adon macene duk macen da batada kunyar gayawa namiji abu toh k'imarta zubewa take yi kuma bazai sota ba hakan yasa ko abu take so yanzu bata iya gaya mai saidai ta hak'ura. Abubakar na zaune cikin mota ya ziro k'afarsa waje yana danna waya kamar ance ya kalli gabansa yaga su INdo da Nafeesah suna tahowa cike da nutsuwa tamkar basu ba. "Masha Allah." Yafurta a hankali yana yana me binsu da ido. Har k'asa suka tsuguna suna gaida ya kasa amsawa INdo sai kallonta da yakeyi. Sanye take cikin les Orange da ratsin green ajiki ta yafa mayafi green tamkar ranar da ake sanyata a alalle, wuyanta yasha sark'a tasa d'ankunne yatsanta da zo6e sai k'amshin turare sukeyi yace cikin fara'a. "Aishatul humairah da my sweet sis Nafeesatu kunyi kyau." Nafeesat tace, "Kai Yaya Abubakar ai kafimu nidai bari na shiga na sake takalmi." Tayi maganar tana mik'ewa daga tsugunnan INdo tayi saurin riko hannunta tare da mik'ewa suka shige gida ya bita da kallon mamaki ganin yanzu kunyar da take nuna Mai tayi yawa ya kad'a kai yanajin wani mugun dad’in yanayi yana ratsa shi. Suna shiga ba dad'ewa suka fito domin sunsan su yake zaman jira, Inna tayi musu fatan alkhairi da addu'ar Allah ya dawo dasu lafia. Yana jingine jikin mota suka fito a hankali ya juya yana kallon INdo suka yi four eye's ta sakar mishi murmushi da fararan hak'oranta daya kaita asibiti aka gyara mata su le6anta yashi red janbaki ta bud'e gidan gaba ta zauna tare da kawar dakai tana kallon k'ofar gidan su. Shima shiga yayi yana cewa Nafeesah, "Zamu tafi mubarki fa." Tayi saurin fisge hannunta daga rik'on da shehu yayi mata yana bata sallahun abinda zata siyo mai idan sun shiga cikin kano. A hankali ya dinga tafiya har suka fita daga sumaila sannan ya fara gudu dan ayau zai dawo dasu, suna ta hira wanda yawanci akan makaranta ne data ke zuwa lesson sai dai abin ayi addu'a kawai amma INdo kam bata fahimtar turancin da akeyi sai 'yan k'ananun words wad'anda basu da wahalar rik'ewa. A k'ofar gate d'in gidan su ya tsaya, ba wani gidane had'add'e ba sannan kuma ba wai gajari bane dai-dai magidanci me rufin asiri da kuma kwanciyar hankali. Suna tsayawa k'irjin INdo ya fara bugawa taji kamar bazata iya shiga ba Nafeesah ta fito INdo ta kalleshi kamar zata yi kuka ya sakar mata murmushi tare da cewa. "Ya aka yi naganki haka?" "Yaya Abbakar jinake inajin tsoro." "Oh toh ai bama cinye mutane kifito mu shiga." Dakyar INdo ta iya fitowa 'yan layin sai kallansu sukeyi suka shiga parking spaces sunzo wani d'an corridor ya janyo hannunta tayi saurin kallansa ya kai fuskarsa saitin tata kamar zai yi kissing d'inta yace. "Idan kina yin haka su Halima zasu rainaki, ki saki jikinki." Yafad'a tare da sakin hannunta, Nafeesah kuwa har takusa shiga ciki sannan ta tsaya suka k'arasa sannan Abubakar yayi gaba sukuma suna bin bayansa. INdo kuwa abinda yayi mata ba k'aramin sake tsuma jikinta yayi ba hakan kuma yasa ta fara mai wata fassara domin a makaranta ana gargad'in suka akan ta6a namijin da ba aure kukayi ba. Da gudu k'annansa suka fito suna musu oyo-yo suka rungume INdo suna cewa. "Yaya Habu itace ko?!" Ya dinga d'aga musu kai yana murmushi yadda INdo da Nafeesah bazasu gani ba. A k'atan falon gidan aka sauke su an baje musu kayan abinci dana sha kala-kala INdo kuwa kamar ta nutse cikin carpet d'in da aka malale falon dashi. Su Mama da Umma suka fito su INdo suka gaidasu har k'asa sannan suka huta k'annan su Abubakar sukayi ta janta da hira suna jefo mata turanci haushinsu ya fara cika ta domin baganewa takeyi ba su kuma a tunaninsu kunya ce take hanata yin magana basu san duk taci ubansu a surutu ba. Sun jima kafin su sauka zasu ci abinci domin tunda Abubakar ya shigar dasu ya koma d'akinsu ya tarar Sadeeq sai shak'ar bacci yake yi da alama ma ko sallan la'asar beyi ba Abubkhr yace. "M twinnie ka kashi kazo mu shiga ciki gashi na kawo maka wadda zan aura kugani." Da sauri Sadeeq ya mik'e cike da mamaki yace. "Are you serious?!" "Yap tana ma ciki gurin su Mama." Sadeeq yace "wai kana nufin kace min zuwa kayi ka d'akko ta, kuma babu wani labari?!" Abubakar yace "Ya daman Ina sonayi surprising d'inka." "Ya nagani toh bari naje nayi sallah sai na shiga, nasan ko wacece wannan toh ta had'u and degree nawa gareta M twinnie?!" "Idan zaka shiga ka gani toh idan kuma labari kake so toh kaci gaba da baccinka." "A'a zanso ganin matarka mana M twinnie." Ya fad'a yana shiga toilet dan shi a tunaninsa Abubakar ya manta dawani batun INdo. Saida ya watso ruwa yayi sallah yana idarwa Abubakar na shigowa Sadeeq d'in ya zura kaya sannan suka nufi cikin gidan, tun daga kan takalma Sadeeq yasan budurwar d'an uwan nasa ta had'u suka shiga tare dayin sallama Sadeeq ya zauna kan kujera ita kuma INdo ta d'an jiya ta kallesa suka had'a ido sam Sadeeq be ganeta har ta kaidashi sannan Abubakar ya kallesa cikin sign ya cewa Sadeeq. "Ya tayi...?!" Sadeeq ya jijiga kai yana kallon gefen fuskar INdo yayiwa d'an uwan nasa alamar 👌 yana kashe mai ido d'aya. Dariya Abubakar yayi ganin be ganeta ba yace. "Aisha ce fa student d'inka ta sumaila kauyan Sani Tsefawa secondary school, idan baka gane ba toh INdo malam Hamza ce..." Sadeeq dake zaune sai gashi a tsaye yana mata kallan mamaki. Sai yanzu ya gane domin ga fashin gushinta nan sannan ya fara tuna kamanninta cikin kwakwallawarsa zuwa idanunsa cikin tsananin mamaki yace..... [7/31, 5:13 PM] Aisha Galadima: *⚗⚗MUSAYAR ZUCIYA...⚗⚗* ♥♥ ♥ A true life story Na *K.A.S Precious Hajja ce*👈 *HASKE WRITER'S ASSOCIATION*💡 (Home of expert & perfect writer's) *VOTE me on wattpad @Hajjac* *DEDICTEED TO:* Sanah Isma'il Matazu. *Duk da cewar kinfi k'arfin page amma duk da haka zan bak'ishi ba a matsayin komai ba sai dan kawai naga nayi hakan, I am proud of you My Xoxo (miss Xoxo) Allah ya baki abinda kike so Duniya da lahira.*❤😍 Page *17* "Wallahi kuwa itace, INdo malam dama zaki iya zama haka? Ikon Allah da...." Cikiin sauri Abubakar yayi magana ranshi a bace ganin yana neman kwance mata zani a kasuwa yace, "M twinnie ya isah haka ko ka manta matsayinta a gurina ne ah..? Kake neman cin zarafina." Sadeeq ya k'arasa wajan Abubakar tare da dafa kafad'arsa ta hagu yace. "Oh sorry M twinnie ba nufina kenan ba abinne ya d'aure min kai." Jin-jina kai Abubakar yayi yana kallon yanayin INdo yaga ta cukume ta kasa boye fushinta sai faman cizon le6anta takeyi na k'asa tana murd'e k'asan mayafin jikinta ya kalleta yace. "Humaira zo muje kiga wani abu." Kamar jira takeyi yace taje ta mik'e suka fita lokacin Sadeeq na tsaye a parking space tsananin mamaki sun addabi zuciyarsa sai gasu, INdo na hangoshi ta k'arasa gurin Abubakar ya bi bayanta. Tsayawa tayi tana kallon Sadeeq cikin salon raini tace. "Oh malam Sadeeq kayi mamaki ko? Toh aishi dama Allah ba yadda bayayi da bawansa nasan baka ta6a kawowa ranka cewar zaka ganni a makamancin haka ba sai gashi ta silar d'an uwanka." "Hakane Aisha nayi mamaki kuma har yanzu ina kanyi, shin wace school kike yanzu.?” Ya tambayeta ta yatsina fuska tare da gyara mayafi tana gyara zaman d'ankwalinta tana son cewa, ba zamu iya magana anan ba da turanci dan ta bashi mamaki amma ta kasa tana dai d'anjin alamu-alamun zata iya amma batason ko gwadawa ne dan karyayi mata wani kallon (We can not talk here) tayi mata wahala kawai ta maze tace. "I dant talk." (I don't tell you) Suka kalli juna Sadeeq da Abubakar fuskar Abbakar a had'e ganin haka yasa Sadeeq girgiza kai yana kallonta yace. "Oh good Allah ya bada sa'a, Ina su Innar ku da malam..?!" INdo tace "K'alau suke duk suna gaihe ku." Tayi maganar tana matsawa kusa da Abubakar,murmushi ya sakar mata itama ta mayar mai sannan tace. "Kazo ka maida mu gida Yaya Abbakar dare nayi." INdo akwai dad'in murya saidai ta kasa dena sh da hi musamman idan tana magana cikin fushi. "Toh kuje ku shirya sai mun fara zuwa gidan su budurwar Sadeeq daga can sai mu wuce." Abubakar ya fad'a yana kallon fuskarta, wucewa tayi ta koma ciki shi kuma Abubakar ya gayawa su Mama cewar zaije ya maidasu. Nan fa kowa na gidan ya fara k'ok'arin fito da abinda zai yiwa INdo kyauta dashi baga k'annan ba baga su Mama ba, haka suka cika INdo da Nafeesah da tsaraba kala-kala. Fita suka yi duk 'yan gidan suka rako su mota anayi musu fatan sauka lafiya. Sadeeq ne yake tuk'in yayin da Abubakar ke kusa dashi suka su INdo suna baya har suka k'arasa gidan su Fateema, waya yayi mata dama dawowarta kenan daga gidan suna ta raka Ummanta, fitowa tayi lokacin anata k'iran magrib INdo ta kalli Fateema itama Fateeman ta kalli INdo kowa ya fara sak'e-sak'en abubawa a cikin ransa. "My Zarah ga girlfriend d'in M twinnie nan kusan juna bari muyi sallah tukunna." Cewar Sadeeq Fateema ta kamo hannun INdo tana cewa, "Okey My D sai kun dawo, shi yasa naga mutumin ankasa an tsare ashe-ashe." Tayi maganar tana kallon Abubakar ya galla mata harara tare da cewa. "Whatever dai please take care of her, if not.. Hmmm." Dariya Fateema tayi INdo kuma ta bita da kallo, oh itakam taji abinda yace tunda gashi tana dariya ita kuwa please d'in kawai taji amma raguwar duk bata ganeba shi kuma Sadeeq ya zauna saman motar kafin yace. "Ki kawo mana ruwan alwala karmu rasa jam'i." Jan hannun INdo tayi suka shiga Nafeesa na biye dasu, a falo suka zauna Fateema na zuba ruwa a buta tanayiwa Umma bayani kasan cewar itama alwala take a gurin. Bayan takai musu ta dawo suka gaisa da INdo ta kawo musu juice da cin-cin a cikin wanda tayiwa Sadeeq d'inta domin ba k'aramin so itama Fateema takewa Sadeeq ba kowa yasani tana mugun sonshi. Kad'an suka ci wai na 'yan birni karsuci da yawa duk da cewar yayi shegen dad'i amma haka suka hakura, suna Idarwa Sadeeq yayi mata waya cewar su fita zasu tafi. A bakin mota suka tarar dasu banda ban-bancin kayan jikinsu da babu wadda zata gane waye nata, suka k'arasa Fateema ta kalli Abubakar marainin wayon nata tace. "Toh gata na dawo da ita, kaga har 'yar k'ibama saida tayi a gode min." Murmushi yayi tare da zagawa drive seat ya zauna yana cewa. "Tayaya zan yadda bayan ni a yadda na baki haka na kuma kar6a, anyway thanks amma kad'an." Tayi dariya su INdo suka shiga mota bayan sunyi Sallama da Fateeman, a bakin titi suka sauke Sadeeq ya kalli INdo itama tad'ago ta kallesa tana faman had'e rai dan karma yayi mata turanci sai taji yace. "Aisha sai yaushe?!" Ta sauke numfashi tare da cewa, "Sai wata rana kuma." "Okey please send m regards to your parent." Mtwwww taja tsaki mai k'arfi cikin kufala tace. "Idan bazakai Hausa ba kayi gaba ai bada yaren annabi kayi min magana ba." "Lallai Aisha ni kike gayawa maganar nan?" Sai tayi mai da fulatanci itama shi kuma yayi shiru dan shima baji yake ba ta kallesa tace. "Ko bakaji abinda nima nace ba? Toh duk sanda zaka ganni kayi min wani turanci nima henayi maka wanda na iya ai kowa Allah ya tsaga ya bahi." Juyawa Sadeeq yayi yana taran napep yana mamakin INdo, wato yanzu ta koyi rainin hankali gashi yagano cewar tanada d'auke kai akan abinda beshafe taba amma idan ka shiga nata zata yimaka rashin kunya duk girmanka. "Humairah dawo gaba." Abubakar ya fad'a ba tare daya juyo ba, fitowa tayi ta koma kamar yadda ya umarce ta. Kallonta yayi ita kuma tana gyara rigarta yaja motar suka tafi. Tun suna hira dashi da Nafeesah hartayi bacci, sai da yayi nisa sosai sannan ya gyara murya yace. "Humairah meyasa kikewa Sadeeq rashin kunya..?!" Banza tayi Mai sai kunkuni takeyi ya kuma yin tambayar tayi mai banza sannan yace. "Baki ga d'an uwana bane? Kuma bakiga ta dalilinsa nasanki ba meyasa kikai mai haka." Tunda suka saba da juna bata ta6a jin haushinsa ba sai yau, Allah kuma ya k'imsa mata yin magana cikin taushi dan da wani ne k'ila su kwashi 'yar kallo tace. "Duk babu wanda yafiku sanin wacece INdo daga iyayena heku, meyasa hida yasan bajin turanci nakeyi ba amma heya dinga yi min, wannan ai izgilanci ne. Kuma malamar mu a islamiya tace mana, komai na Duniya jarabawa ce haka tace mana lafiya da Allah ya baka jarabawaci rashin Lafiya ma haka,idan Kud'i Allah ya baka hima jarabawa ce hakama talauci, Ilimi idan Allah ya baka jarabawa ne idan bebaka ba hima jarabawa ce, aure jarabawa ne rashinsa ma haka, amma himeyasa yake min haka kuma yasan ban iya ba? himeyasa baka yi mihi magana ba heni...?!" Shiru Abubakar yayi yana tuk'i, lallai wannan kad'ai yaci ace angodewa Allah tunda har INdo tasan shi. Murya a sanyaye yace mata. "Haka ne kiyi hakuri." Cigaba da tafiya sukayi har saida suka shiga garin Sumaila yayi parking akan kwanar dazata kaisu kauyen Sani ya kalleta ta kalleshi bayan ya kunna kwan cikin motar yace cikin wata irin murya. "Humairah kina sonah..?zaki iya aure na...?!" INdo tayi saurin rufe fuskarta da gyale tanajin wani farin ciki da annashiwa suna yawo aduk wani sashe na jikinta. Murmushi yayi shima yana jin tamkar an d'auke mai wani gungumeman abu aacikin k'irjinsa ya kuma tambayar ta INdo ta d'aga mai kai alamar Eh sannan ya furta kalmar Alhamdulillah. "Thank you Humairah Ina sonki so me tsanani, Zan kula dake iya gwargwadon iyawata, zan kare duk wani hakkinki daya rataya a wuyana zan baki kulawa a cikin rayuwar auran mu sannan zanyi iyayina wajan ganin kin cigaba da samun Ilimi ta kowacce hanya indai alkairinki na thanks again I love you." Tunda ta rufe Ido bata bud'e ba harya gama magana, ganin haka ne yasa shi rik'o hannunta ta fara k'ok'orin kwacewa murya a sark'e yace. "Idan kina son na sakar miki hannu sai kin bud'e fuskarki." Kad'a mai kai tayi sannan kuma tak'i bud'ewa, ganin dare nayi mai ne yasashi sakar mata hannun yana murmushi tare dajan motar suka shiga cikin kauyan har k'ofar gidan su lokacin malam Hamza na zaune zaman jiransu. Da sauri Abubakar ya fito yaje gurin Malam Hamza yana bashi hakuri, shidai malam Hamzah tunda yaga yaransa sai yaji hankalinsa ya kwanta yace ai ba komai. Sim-sim INdo ta shige gida Abubakar ya tambayi malam Hamza inda zaije ya nemi auranta Malam Hamza yace. "Ai malam Habu tunda ka tambayeni ai kagama tambayar duk wani wanda zai baka uwata, yanzu kawai kaje duk sanda ka kintsa saika kazo ayi." Godiya Abubakar ya dingayi tamkar cewa akayi an bashi kijerar president. Kayayyakin su ya ciro musu su Sagiru suka kwashe suka shiga dasu cikin gidan shi kuma yaja mota ya tafi yana mai jin farin ciki da nishad'i. Washe gari yayiwa abban su magana k'annan abban sukaje har kauyen Sani aka tambayowa Abubakar auran INdo malam Hamza ya tara abokansa suka shaida an bashi, a take a gurin k'anin abban su Abubakar ya bada kud'in nagani ina so dubu Hamsin sannan suka tafi suna mamakin gidan da Abubakar yazo neman aure sai dai sunsan ba yadda Allah baya tsara abinsa dan haka babu wanda yaja da al'amarin. Labari ya zaga gari an kawo kud'in INdo dubu Hamsin masu bak'in ciki nayi masu murna nayi dama haka lamarin mutane yake. A cikin satin ya siyo mata waya sabuwa tecno sabida anyi mai transfer zuwa abuja sabida haka zasu kuma yin nisa. INdo ta cigaba da zuwa makaranta duk da tana saka wasa a cikin lamari sai dai fa ta k'ara yin clean domin idan kaganta sai ka d'auka tana a matakin degree program ne nan kuwa ko secondary school bata kammala ba. Ta kuma rik'e alk'awari bata kula kowa duk kud'inka duk kyawunka duk ajinka duk meye d'inka bazata kulaka ba tace bazata yi *MUSAYAR ZUCIYA* da kowa ba Abubakar shine a cikin zuciyarta shi kuma take da burin aura... *HAJJA CE*👈 [7/31, 5:13 PM] Aisha Galadima: *⚗⚗MUSAYAR ZUCIYA...⚗⚗* ♥♥ ♥ A true life story Na *K.A.S Precious Hajja ce*👈 *HASKE WRITER'S ASSOCIATION*💡 (Home of expert & perfect writer's) *VOTE me on wattpad @Hajjac* *DEDICTEED TO:* Sanah Isma'il Matazu *Gaskiya ban san me zan cewa masoya maso bibiyar labarin nan ba sai dai nace muku love you all.* _Shafin naku ne My Shuwa Arab, Dota Fatima, Dota Marok'i, My Shama, My Olo, aunty Jidder_😍💋 Page *18* *Bayan wasu shekaru.* Gaba d'aya an kammala yin komai ansa rana da Fateemah ta kammala school za'ayi dan haka ginin su kawai suke yi. Gidane me kyawun gaske kowanne yake ginawa kowa kuma da yadda yake son abunsa. Gidan Abubakar yafi tsaruwa nesa ba kusa ba yafi na Sadeeq sosai kasan cewar shi yana son ya samu wani acan inda yake business dinsa idan sunje da matarsa babu wani fargaba dama yanada gidanshi dan haka biyu ya raba sa6anin Abubakar dashi a abujan ma yana da k'atan gida a quarters d'in asibitin da yake aiki. ***** Fateema na shekarar k'arshe domin sauran 'yan watanni ta kammala, yayin da a 6angaran INdo itama sai hamdala domin zata iya rubuta wasu kalmomin harma ta rubuta wasik'a da Hausa koda ajimi kuma iya yawancin surorin alkur'ani me girma an samu cigaba sosai. Kyawunta ya fito ta waye ta goge kai in baka cika ishasshe bama bata kulaka bare harkuyi hudd'a tare. Zaune malam Hamza da Inna suka suna tattaunawa akan yadda zasu yi da kayan d'akin INdo gashi INdo tace harda gararta zata tafi batason abin gori. "Toh malam ya zamu yi, iya abinda Allah ya bamu shi zamu yi mata ai suma sunsan damu dasu ba d'aya bane sun fimu ta ko'ina." "Hakane Maryamu yanzu dai dole naje na siyar da gonata dake can saye guda d'aya, sannan na siyar da shanuna guda biyu sai ayi mata amfani da kud'in nasan dai bazamu yi mata irin yadda take so ba saidai ai munyi k'ok'ari kuma mani wallahi dandai Dacta Habu zata aura hiyasa zanyi mata duk abinda nasan Zan iya sabida yaron nan d'an k'irki ne, duk sanda na kalli katangar nan naganta da suminti sai naji dad'i." "Hakane kam malam toh sai a siyar d'in Allah ya bada lada." Malam Hamza yace "Amin." Kwana hudu dayin zance ya d'auki abokinsa malam kallah suka tafi Saye bayan rabansa da zuwa kusan shekaru goma sha biyar kenan. Sun gaisa da kowa saidai tsakaninsa da yakumbo tsahare babu ko kallon banza, bayan an gayawa sarkin shanu aka yi cinikin shanun malam Hamza wanda shine ya baiwa yakumbo talatu su yace idan sun haihu ya barmata saidai duk lokacin da yake da bukata toh zai dawo ya karbi guda biyu. Dubu talatin-talatin aka siye su nan aka bawa malam Hamza kud'insa dubu sittin, aka koma kan gona wani mutum ya siya dubu cas'sa'in malam Hamza ya kar6o kudin suka dawo gida da dubu d'ari da Hamsin cas. Had'awa akayi da kud'in nagani inaso d'inta aka had'a suka zama d'ari biyu cif malam Hamza yace aje ayi cinikin gado madubi da wardrobe, nan aka nuna musu kud'ad'an ko wanne babu ma na k'asa da dubu d'ari a cikin irin wanda INdo ta nuna tana so. Na dubu d'ari da hamsin suka za6ar mata wata yayar Inna ce da take aure a dawakin tofa sukaje suka tayo. Sai kud'in gudun mawar da aka dinga kawo musu dan su kauye basai ranar biki suke bada gudunmawa ba. Haka dame d'ari d'aribiyu dubu biyu gashinan dai aka dinga vawa inna da malam Hamza suka had'e ya basu dubu hamsin da biyar da naira ashirin. Suka had'e da ragowar hamsin dinnan aka had'a d'ari na kujeru gaskiya INdo taci Kud'i wai...! Sai kuma masu kawo kayan amfani na kitchen me kofi , me tasa, me plate, gashi nan dai suma aka had'a Inna tasa aka siyar da gonarta itama sai aka sissiya abubuwan da babu a kitchen d'in. **** Gidan su Fateema kuwa ko shirin basu farayi ba sabida su ba wani case karatunta kawai takeyi hankali kwance. 'Bangaren mazan kuwa, kayan lefe ake had'awa komai iri d'aya Mama tace azuba colors ne kawai suke ban-bantawa da kuma size domin INdo tafi Fateemah jiki ita kuma Fateemah tafi INdo haske da tsawo. Akwatuna bakwai-bakwai akayi musu kowacce shak'are da kaya domin mazajen ba k'aramin k'ok'ari suka yi ba sun kashe Kud'i over. Ranar da su Fateema sukayi graduation a ranar aka kai kaya murna biyu ta had'ar mata. 'Bangaran INdo ma ankai kayan tana gidan Rukayya kwance tana waya da Abubakar, cikin salon mak'e muryar data koyo wajan su Zainab da Hadiza tace mai. "My key wai me kakeyi ne yanzu?!" "Ina office a zaune tare da frame d'inki inata kallonki." "Yeeee naji dad'i nima ka tambaye ni.." "Habibty mekike yi yanzu..?" Ya fad'a kamar yana cikin maye, dariya INdo tayi me sauti sannan tace. "Ni tunaninka nakeyi dan Allah yauhe zaka dawo.?!" Dariya yayi tare da cewa, "Sai ending d'in month d'innan, ya mekika tanadar min?!" Tace "kana nufin ending k'arhen Month watan nan ko?! "Eh haka nake nufi madam." "Toh kenan kana nufin ankusa biki." Yace "Eh amma ai Sadeeq yana nan ba kuma zai koma ba sai an gama biki kokina buk'atar wani abun nasa ya aiko miki dashi?!" INdo ta kuma gyara kwanciya domin yarinyar ta iya kar6ar sakwan love tace. "Eh akwai abinda nakeso." "Toh madam menene shi..?!" Tace cikin jan numfashi "Kai nake son gani." Abubakar saida tsigar jikinsa ya tashi yarrrr ya d'ora k'afarsa kan table tare da jin gina da jikin kujerar dayake kai, hannu yasa a k'irjinsa yana d'an bubbugawa tsawon wani lokaci sannan yace mata. "Sorry Habibty da ace da yadda zanyi danayi na taho, saidai na riga na k'ar6i aikin wani abokina inason idan na taho ya kar6i nawa sabida idan munyi aure bazan dawo da wuri ba sai na gama shan amarci na." INdo ta guntse baki jin abinda ya fad'a sannan taji yace. "Ko kina son da an d'aura aure na dawo." Da sauri tace "A'a bana son ka koma." "Toh ki tanadar min kanki a duk ranar da aka kawoki gidana." Kit..yaji ta yanke wayar ya sauke yana kallon screen d'in yana murmushi bata san wannan zantuttukan baya manta ranar daya fara gaya mata irin maganganun tace mai ita ba 'yar iska bace. Ranar yaci dariya kamar cikin sa zaiyi ciwo, bebi kiran ba yaci gaba da aikinsa yana ta murmushi INdo na bashi laugh yasan idan sukayi aure zai dinga shan dariya. INdo kuwa bata koma gida ba sai da tayi magariba sannan ta koma gida, wayyo Allah dataga irin akwatinan zamanin da Abubakar ya kawo mata bata san lokacin data fad'a jikin Inna ta rushe da kuka ba. Inna sai faman lallashi takeyi Sagiru da shehu suna kallon kayan kowa sai nuna abinda yake sukeyi da kyar tayi shiru aka cigaba da kallon kaya Inna ta nuna mata dubu hamsin tace, "Gashi 'yarnan sunce kud'in d'inki ne." K'ar6a INdo tayi tana godiya, tana gama kallon kayan suka rufe ta fita waje. Unguwar su kezy taje ta samesu zaune sai zuk'ar sugari sukeyi ta toshe hanci tana musu magana. "Kai kezy aji tsoran Allah dai za'a mutu." Tayi maganar tana sake toshe hanci, jazuli yace. "Kefa 'yar rainin hankalice dan kinzama babbar yarinya shine zaki dinga yi mana kallon equal.." "Kai masifaffe ni gurinku nazo, kunsan ankawo kayan aurena, toh sonake kuzo gida kuyi gadi Allah ma yace tashi intemake ka, idan ma kune 6arayin nidai kuzo gobe he'in baku dubu goma." "Kai hajiya INdo kin zama hajjaju fa Allah." Kezy ya fad'a tace "Eh koma dai meye nidai kuyi min." "Karki damu zamuci uwar hegen dazaiyi gigin zuwa." "Toh nagode." Tafad'a ta wuce ta shiga gidan su Sahura, ta dad'e kafin ta koma gida. Haka akayi suka yi gadin gidan Allah kuma ya temakesu babu wanda yaje. Washe gari ta basu 10k suka tafi, ta ciro atamfa d'aya ta bawa Nafeesa tayi ta murna sannan ta ciro tirmi biyar ta bawa Inna tace tasa da biki. Inna tace a'a itama INdo ta dage tace tabar mata. Cikin shaddojinta kuma ta za6o wata ash tace abawa babanta, gaskiya INdo batada kyashi wajan bawa iyaye abunta amma fur taki bawa Sagiru yayi mitar yayi magiyar tace bazata bayar ba yana da kud'i. Aikuwa yaji haushi duk abinda tasashi bayayi mata shima. *** Kowanne 6angare shiri akeyi ta kowanne side, 6angaran Fateema anje an fara jere haka itama INdo an fara, saidai tsarin gidan yasa bazasu iya cewa sai sun saka mata komai ba domin basu da halin yin hakan. Iya d'akinta kawai suka sawa kaya sai parlon farko dining area kuwa kokalansa basuyi ba gashi gida yayi masifar yin kyau domin yafi na Sadeeq had'uwa. Ana sauran sati d'aya biki Abubakar ya dawo kano, gidan su harya fara cika da bak'in nesa sai tsiya suke mai da masu nuna cewar ya auro 'yar talakawa ga gida har gida amma babu kaya. Sharesu yayi yana yin wanka Sadeeq yazo suka fita. Gidan Sadeeq suka fara zuwa sai sambarka domin kayane nagani na fad'a aka zubawa Fateema, royal ne furniture d'in sannan babu inda va'a k'awata ba sannan suka wuce gidan Abubakar babu abinda yaji aransa na 6acin rai suna shiga cikin bedroom d'in INdo ya fad'a kan gado katifar ta lotsa da alama sakance kuma ba vita form bace ya ware hannuwa yana cewa Sadeeq. "M twinnie remain 6days na kwana anan nida Humairah tah." Sadeeq yayi murmushi tare da girgiza kai gaba d'aya INdo ta rikita mai d'an uwa, shi har yau ya kasa manta INdon da ta baya can domin duk sanda zai tuno ta a k'azamarta yake haskilota har tausayin Abubakar yake idan yaka yana wani abun dominta. Cikin kwanaki uku Abubakar yasa aka sake zuba mai wasu k'awatattun furniture's a inda ba'a zuba ba aka sanya labulaye da site na dining area ba tare daya sanar da kowa ba sai Sadeeq domin cikin dare akaje akasa komai harda plasma TV. Koda dangin INdo suka dawo gidan ba k'aramin mamaki suka yiba. Ana gobe kamu/yini da d'aurin aure.... *HAJJA CE*👈 [7/31, 5:13 PM] Aisha Galadima: *⚗⚗MUSAYAR ZUCIYA...⚗⚗* ♥♥ ♥ A true life story Na *K.A.S Precious Hajja ce*👈 *HASKE WRITER'S ASSOCIATION*💡 (Home of expert & perfect writer's) *VOTE me on wattpad @Hajjac* *DEDICTEED TO:* Sanah Isma'il Matazu Page *19* Suna cikin d'akin su kowanne yana k'ok'arin k'arasa had'a ragowar kayanshi a cikin trolley domin da daddre idan zasu tafi gidajen su kowa ya tafi da abinsa, Abubakar sai murmushi yake yi Sadeeq na kallonsa amma be tambayesa ba domin yasan dole ya gaya mai tunda abin da alama na farin cikin sune. Jin yayi shiru yasa Sadeeq yin gyaran murya Abubakar ya sake yin dariya ya ganosa shima sarai hakan yasa shi k'in gaya masa saya wanashi tukunna, Sadeeq ya sake d'aukar towel yana yarfewa amma still Abubakar yayi shiru ganin haka yasa Sadeeq yin magana da cewa. "Kai twinnie kasani a gaba sai faman smiling face kakeyi, kagaya min muyi tare kak'i." "Oh sorry ai bansan kana son jiba, kawai tunani nakeyi naga tunda aka haifemu har muka girma bamu ta6a raba d'aki ba indai muna cikin garin nan, amma sai gashi m twinnie kana cikin garin kano Ina ciki amma mata sunsa zamu rabu muje mu kwana kusa dasu." Shima Sadeeq murmushin yayi yana k'ok'arin zuge zip d'in trolley d'in, shi kansa haskilo hakan yake yana hangosa da Zarahn shi abar kaunarsa. Duk jinsu sukeyi tamkar wasu sababbi a cikin duniyar suna jin wani nishad'i Abubakar yana hango yadda zasu kwashe a daran yau shida INdo ya kuma yin wani murmushin har yana fitar da sauti Sadeeq ya kuma kallonsa tare da mik'ewa yana cewa. "Amma dai ba abinda ka gaya min kad'ai kesaka wannan farin cikin ba dan abin naka yayi over..?!" "Ina tunanin yadda zamuyi rayuwa ne da Humairah, ina ganin kamar bazan iya barinta anan ba kafin a gama gyara min gidan danake acan, twinnie advice me please." Mamaki Sadeeq yake ganin wai INdo Abubakar yake yiwa wannan sambatun tun kafinma suyi rayuwar aure ya kuma fahimtarta. Jan trolley d'insa yayi yakaita saitin k'ofa sannan ya dawo yana k'ok'arin cire singlet d'in jiginsa zai shiga wanka dan sai anfara d'aura nasa auran sannan zasu wuce ayi nashi yace. "Toh mezai hana idan kagama 2weeeks d'innaka kutafi tare sai ta zauna a gidan haka tana ciki ana gyarawa ai tasaba da rayuwa a irin wannan yanayi bazata damu ba." Wani banzan kallo Abubakar yayi mai kamar yasan hakan zata faru yak'i kallonsa saima saurin shigewa toilet dayayi yana murmushi ciki-ciki. Kwafa Abubakar yayi tare da zuge tashi trolley d'in sannan ya kira INdo a waya ringing biyu ta d'auka yaji muryarta a dashe tana gaidashi yayi dariya yana cewa. "Kai babyna tun yanzu.?!" Tayi dariya murya a dashe tace "Tun jiya da yamma." Yace "Nikam banajinki amma tunda naji kad'an bari na kyaleki inyi wanka kafin gobe kizo kiyi min.." Kit.. Yaji ta kashe wayar dama yasan za'arina yayi dariya tare da ajiye wayar ya gama kimtsa komai nashi shima Sadeeq yana fitowa ya shiga kafin ya fito har abokansu sunfara zuwa. K'arfe 11:00am suka fito cikin shiga iri d'aya hatta aikin babbar rigar da agogonan su takalminsu da huluna duk iri d'aya ne sai faman k'amshi suke zubawa lokacin gidan yacika da mutane, waje suka koma inda maza suke suna gaggaisawa kafin a d'unguma a tafi gidan su Fateema bakunan su kaf yak'i rufuwa kai daka gansu kasan suna cikin farin ciki. Shad'aya da rabi dai-dai dubban mutane suka shaida auran Sadeeq Salman Harun da Fateema Idris yahaya. Sadeeq murna kamar zuciyarsa zata fito sai gaisawa suke da mutane wanda yawance basu gane waye angon yanzun sabida kowa akayiwa murna saiya amsa. Bayan sun shiga gidan su Amaryar sun gaisa da iyaye amarya ta fito cikin makeup tayi masifar yin kyau cikin farin les riga dazani tazo ita kanta kasa gane waye nata tayi saida aka ce za'ayi musu su biyu sannan aka musu su uku itace a tsakiya, ana gamawa suka fita. Bayan an koma gida mutane sunci abinci sukuma suka kumayin wanka suka sa wasu fararan kayan wanda suma babbar rigace kalar surfanine ba irin wanda suka cire ba nan ma sunyi masifar yin kyau Abubakar yayi ma INdo text message cewar gashi nan zasu taho. Motoci ne reras sunfi ashirin aka tafi Sumaila kauyen Sani unguwa kuwa unguwar su INdo akayi parking motocin, ana gayawa su INdo jikinta ya fara rawa hankalinta ya tashi tsoro ya fara shigarta suna zaune a gidan Rukayya ta kule cikin uwar d'akinta tayi shiru domin su Uwani su Rukayya duk suna bata labarin aure Abubakar nata kiran wayarta tana gani tak'i d'auka shi kuma befasa kiranta ba. Sai da su baffajo na saye suka shigo zauran gidan sukace a fito musu da ita sannan ta fita jikinta ya kuma yin sanyi. Hannayenta suka kama sanye take cikin shadda maroon color sai hijjab datasa fuskarta tashi kwalliya kaida kagani kasan amarya ce su Baffajo suka wuce da ita wajan masu d'aurin auran Abubakar na zaune aka zaunar da ita a kusa dashi ga uban maza waliyin amarya ya tambaye ta. "Aisha kina son Abubakar wanda za'a d'aura muku aure yanzu..?!" Kan INdo a k'asa jikinta sai uban rawa yakeyi Abubakar hankalinsa yayi mugun tashi ganin tayi shiru, ana k'ok'arin sake tambayarta ta d'aga Kai alamar Eh sai a sannan ya sauke wata uwar ajiyar Zuciya yana dafe k'irji shima wakilinsa ya tambayesa. "Abubakar kana son INdo zaka aureta da yardarka ba takurama akayi ba ko..?!" Yace "Eh uncle." Sannan akayi kabbara aka fara addu'ar d'aurin aure a gurin aka damk'awa INdo kud'in sadakinta naira dubu tamanin lakadan kowa ya shaida sannan su Baffajo suka shiga da ita cikin gida, fuskarta kunshe da murmushi ganin yadda Abubakar d'inta ya tsure taji ta k'ara sonsa cikin zuciyarta. Shigowa ango yayi da abokansa cikin gidan aka fara hotuna wasu sun tsaya sun shiga cikin matan yayin da wasu abokan da girman kai yayi musu kwaliya suka ja baya cewar mutanen basuyi musu ba wata ma mata tukin tuwo sukeyi suka saki dan ayi hutonan dasu, hatta Sadeeq buya ya dingayi a bayan Abubakar. Shikuwa babu ruwansa duk Matar data matso zai matsa suyi tare za'ayi musu shida INdo yayi k'ok'arin cafko hannunta ta cikin babbar rigarsa, da sauri ta kallesa cikin sa'a akayi musu hotuna sai hakan ya bada style zata yi magana yayi saurin sakin mata yana dariya Sadeeq yazo akayi musu su uku sannan suka tafi sam an hanashi amaryar su ke6e har suka kammala komai aka bar motocin da zasu tafi da amarya sukuma su Sadeeq suka wuce. Duk zaman dasu Abubakar sukayi a garin an hanasu ganin amarya sunyi magiyar sunyi duk iya yinsu amma mutanan bikin nan suka hana. Sai bayan la'asar an shirya amarya za'a tafi sannan Abubakar suka tafi yabar abokansa da zasu d'akko su duk da yasha wulak'anci wai yaja zasu d'akko 'yan kauye a motarsu. INdo na lullu6e su Inna nayi mata fad'a idanta har’wayau hawayen sunk'i zuwa sai Innace keyi dan tama kasa tsayawa sosai tayi mata fad'a sai faman cewa takeyi. "Tabi mijinta tayi zaman aure." Sune kawai kalaman Inna, haka ma malam Hamza shima abinda yace mata kenan sai kuma nuni dayayi mata da yadda Inna takeyi mai biyayya. 'Yan uwa duk sunyi mata fad'a ana k'ok'arin fita da ita saiga malamarsu ta islamiya malam Hansa'u tazo yi mata Allah yasanya alkhairi ta jata d'aki suka zauna ta Fara mata nasiha. "Toh Aisha yau dai gashi Allah ya kawo ranar da kika koma k'ark'ashin wani ba iyayanki ba, yanzu ya koma shine uwar shine kuma uba shine danginki. Aisha kiyi biyayya yin biyayya ga mijinki shine zaki samu aljanna, karki manta da karatun da ake koya muku duk abinda mijinki yace kiyi toh kiyi indai besa6awa addininki ba, ke ko cewa yayi Aisha ga wuta fad'a karkiji d'ar kifad'a din kawai, Aisha kibi aure karki yiwa mijinki rashin kunya ko gaddama ko kiyi musu dashi yin hakan Allah zaiyi fushi dake fushin Allah kuwa babban had'arine akan kowanne halitta. Allah ya bada zaman lafiya Aisha ya kad'e muku fitina a cikin auranku ya baku zuri'a masu albarka tashi muje akaiki gidanki mai tarin ni'ima da albarka.." Sai a lokacin INdo ta fara kuka tsoro ya kuma shigarta har aka shigar da ita jibgegiyar motar abokin Abubakar dayazo daga Abuja. Su uku suka shiga sai driver da friend d'inshi a kusa dashi, ana gama cika motocin suka d'auki hanya shikenan INdo tabar kauyen Sani saidai tazo da ziyara Allah ya d'agata. Gudu suka dingayi kafin wasu awanni sun k'arasa k'ofar gidan su ango lokacin duhu yafara yi. Bayan an kaita su Mama sunyi farin cikin shigowarta zuri'arsu sunyi mata nasiha aka sake d'inguma aka kai INdo gidan Abubakar masoyinta farin cikinta abin alfaharinta, fuskarta a lullu6e aka shigar da ita cikin d'akinta. Ita kuwa Fateema saida akayi sallar isha'i sannan aka kaita gidansu Sadeeq itama su Mama sukayi farin cikin shigowarta cikin su sannan aka wuce da ita gidan Sadeeq farin cikinta abin kaunarta, ta riga ta tsara musu yadda zasu gudanar da rayuwar auransu abinku da 'yar boko wayayya. Masu kawo INdon kauye sai da suka kwana Abubakar yace abarsu sabida dare yayi kuma duk masu motocin sun tafi wai bazasu koma wannan kauyan ba yadai sha iskancin abokai wanda hakan besa yaji kaunar INdo ta ragu koda da kwayar zarra ba. Sadeeq suka raka gidansa aka yi musu nasiha shida amaryar sannan Abubakar suna k'ok'arin fita yace ma Fateema dake lullu6e cikin mayafi. "Ke..! Sauran kibawa twinnie d'ina wahala ko kiyi mai rowa." Tana jinsa ta k'i cewa komai har suka fita Abubakar ya kalli Sadeeq tare da cewa. "Kai twinnie wallahi kabi yarinyar mutane a hankali, nasanka sarai a mafarki ma kana wuce k'a'ida bare kuma yau gaka ga mace mallakinka. Idan ka kirani da safe ba zuwa zanyi ba ah toh..." Hannu Sadeeq ya bashi suka tafa suna dariya kafin su rungumi juna Sadeeq yace. "M twinnie har gobefa kai saurayi ne sorry to you wallahi but zaka iya sato Aishan ku koma wani d'akin fa." "Nop karka damu zan hakura harsu tafi ai daga yau ne gobe zan samo musu mota ta maidasu." Kamar karsu rabu haka sukeji amma babu yadda zasu yi yana fita ya rufe gidan ya koma ciki. A hankali ya zauna kusa da ita tare da yaye mayafin kanta cikin kunnanta yasanya bakinsa yace. "Amarya muje kiyi alwala muyi sallah." A kunyace ta mik'e ya kama hannunta ya kaita har bedroom d'insa cikin toilet sannan ya fito ya shimfid'a musu sallaya ya ajiye mata sabon hijjab, tana fitowa shima ya shiga yayi alwalan sannan yazo yajasu sallah suka yi raka'a biya ya dafa kanta yayi mata addu'a sannan ya kalleta yace. "Nasan akwai yinwa a cikin nan tashi muje na baki kici bana son kwana dayinwa." Ya fad'a yana shafa mata ciki, Fateema cike dajin kunya ta mike yayi saurin rik'ota tare da janta jikinsa suka nufi parlor. Kajine gasassu sunsha kayan had'i da lemuka da fresh milk suka zauna yafara bata, a yangance suka gama ci sannan ya wanke hannunsa ya jata suka shiga d'akinsa. Kayan bacci yasa ya d'akko wata shegiyar rigar mata ta bacci ya mik'a mata yace tasa, ta d'aga rigar nan ta ganta 'yar firit Fateema aka dinga raba idanuwa ta kasa tashi tasa yayi murmushi tare da cewa. "Bari nazo na temaka miki." Ya mik'e daka bakin gadon tana ganin haka tayi wuf ta shige toilet yayi murmushi yana lasar leb6ansa. Fitowa tayi bayan tasawo sai kuma ta nad'e jikinta da mayafi kamar tasa lafaya ta kwanta a kunyace, shi kuma yayi musu light of (kafin naji kici-kicin su k'ila k'ok'arin kwance mata yake yi nidai Hajja nayi kwana dan d'akin badai duhu ba yau su Sadeeq za'a angon ce na fita zuwa gurin Abubakar.)..... *HAJJA CE*👈 [7/31, 5:13 PM] Aisha Galadima: *⚗⚗MUSAYAR ZUCIYA...⚗⚗* ♥♥ ♥ A true life story Na *K.A.S Precious Hajja ce*👈 *HASKE WRITER'S ASSOCIATION*💡 (Home of expert & perfect writer's) *VOTE me on wattpad @Hajjac* *DEDICTEED TO:* Sanah Isma'il Matazu Page *20* Around 1:45am Abubakar ya shiga cikin gidan nasa bayan ya gama kulle ko'ina yana son lek'awa yaga yasuke amma yana tsoran yadda zai shiga ya gansu dan yasan matan kauye basu fiye kwanciya da riguna ba dan haka ya koma yashiga d'akinsa ya kulle. Wayar INdo ya dinga k'ira amma ba'a d'aga ba ya ajiye tare da shiga wanka. Sukuwa su INdo bayan an kawota tafita suka zagaya gidan farin cikinta ya kasa 6oyuwa ganin irin gidan da take ciki gida irinna cikin films had'add'e wanda ko cikin mafarkinta bata ta6a zaton zata ta6a koda jikin gidan ba, tun shad'ayan dare suka barbaje bayan sinci sunyi hani'an ga iskar fanka na kad'a su ai babu wanda ya kuma motsawa munshari kawai kakeji yana fita hahhhussss ta kowace kusurwa. Tun sallar asuba yafita, su kuma suna tashi suka hau shirin tafiya, saida yaje gida yasa Mama ta bada abinci aka kaimusu sukaci wajan k'arfe goma na safe ya kawo musu buses biyu ya biya masu motar sannan suka tafi sunata yiwa INdo Allah sanya alheri. Saida yaga sun tafi sannan ya shiga gidan, a tsaye ya tarar da INdo tana wajan dining bakinta a bud'e sai shafar kujerun takeyi ya tsaya yana kallonta ba tare da tasan yana tsaye ba. Yana kallonta ta d'an d'osana d'uwawunta akan kujerar sai kuma tayi saurin mik'ewa tana dariya tana karkad'e gurin, ya shigo a hankali cikin rashin sa'a ta hangosa ta cikin glass d'in drawer flat's na dining dake wajan. Da sauri tayi hanyar shiga d'aki zata gudu yayi saurin cafko ta yana dariya yasanya ta a jikinsa. Fisgar jikinta takeyi zata gudu amma ya hana hakan faruwa, kanshi ya zura a wuyanta ya fara shin-shina wuyanta yana sanya siririn hancinsa cikin kunnanta iskah na shiga ciki, INdo taji wani irin abu hankalinta ya fara tashi kwakwalwarta ta fara aika mata da wasu bakwannin al'amra. Jin hannunsa a kan k'irjinta ne yasata kwallara mai wata uwar k'ara, Abubakar yak'i sakinta saima jikin bangon k'ofar da zata kaita bedroom d'inta ya jinginar da ita gaba d'aya ta tsure ya kamo fuskarta da duka hannunsa biyu, bakinsa yakai saitin nata zaiyi kissing d'inshi INdo ta kwalalo mai ido tana bin harshensa da kallo tamkar idonta zai fad'o sai girgiza kai take alamar bata so. Ganin kamar abinda yake shirin yi mata ne bata so yasa shi sonyi mata dan ta gane cewar ba wani abun aibu bane. Gate yajiyo ana bugawa nan INdo ta fara sauke numfashi dan tasan dole yanzu yaje ya bud'e, ba zato bare tsammani kawai taji ya zura mata tongue d'insa tayi-tayi ta datsa bakin amma ta kasa ya fara tsotsa tare da zame d'ankwalin kanta yana shafar gashinta. Nan da nan jikin INdo ya fara kyarma tamkar shocking yajata yayi k'ok'arin tattarota zuwa jikinsa still mouth nasa na cikin nata idanunta a tamke ta dunkule hannayanta jira kawai takeyi taji zubar fitsari. Sake bugun gate d'in ake da k'arfi amma yak'i kulawa hankalin INdo ya kuma tashi, sai da yayi mata ya tabbar da sakon salonsa na farko ya shigeta sannan ya cikata aikuwa ta zandama d'aki da gudu hartana bugewa da bango yayi dariya yana kallonta harta shige sannan ya gyara wuyan rigarsa ya fita yana bud'ewa yaga sisters d'in Mamansu ne da yaransu ya fara sosa k'eya aunty Shafa'atu ta kallesa dakyau sannan tace. "Doctor ko baku tashi bane ba tun d'azu sai faman bugu mukeyi..?!" "Ah mun tashi mana aunty yanzu ma na koma ciki da 'yan uwan Humairan suka tafi." "Oho toh." Suka fad'a tare da shiga ciki suna kiran sunan INdo. Shiru tanajin su tak'i fitowa sabida gani takeyi kamar idan ta fito zasu gane, yana zaune a gurinsu yaga tak'i fitowa yasan dalili hakan yasa shi ce musu yana zuwa. Kwance ya ganta kan gado ta yaye bedsheet d'in ta cukwikuye jikinta gabaki d'aya ta kudindine ya tura d'akin yana murmushi da mamaki ya hau kan gadon. Qarah curewa tayi Abubakar ya janyota gaba d'ayanta ya fara warware bedsheet d'in amma sai sake nad'ewa take cikin kasalalliyar murya domin wannan kokawar da sukayi wani shauk'i ne ya dinga saukar mai yace mata a hankali. "Please Humairah tashi kizo muje sisters d'in Mama ne suka zo, bana son naji sun fara yin k'orafi dake kinji...?!" Tana cikin zanin gadon tace mai. "Toh amma kafita sai na fito.." "Toh nafita kixo yanzo sai ki kawo musu lemo da ruwa." Yana fad'a ya fita daga d'akin sai dai yana la6e, tashi tayi ta sakko a hankali ta k'arasa gurin madubi tana shafa bakinta ta kuma bud'esa ta kallesa a cikin madubin a fili tace. "Kai likita da k'azanta kake wallahi irin na film yayi min, amma fa kamar da dad'i hi har wani lumshe ido yake yi." Dariya ce ta kusa tona mai asiri hakan yasa shi juyawa ya fita falon yana yi gashi ya kasa denawa mutanen dake falon suka bishi da kallo suma suna murmushin kowa da abinda yake kisamawa wanda yasa shi dariyan. "Abin na masoya ne me ta gaya maka haka kake 6a66aka dariya." Shafa k'eya yayi yana shirin yin magana sai ga INdo ta fitoh hannunta a saman bakinta sai faman rarraba idanuwa takeyi aunty Siyama tace. "Aunty amarya taho nan ki zauna." A d'ard'ar taje ta zauna kafin ta fara gaidasu k'ananun kuma suka gaida ita, had'a ido suka yi da Abubakar yayi mata alamar ta kawo ruwa cikin sa'a ta mik'e taje inda taga an ajiye lemukan da ruwan ta d'ako ta kawo da yawa sannan ta koma zata zauna Abubakar yace. "Hunairah baki d'akko musu kofina ba." "Au dan Allah kuyi hakuri kunji bari na d'akko." Ta fad'a tare da shiga tsalelen kitchen d'inta, kalle kalle ta farayi domin gabaki d'aya ta hargitse ta shagala da kallon dukiyar da aka kashe har ta manta da cewar aikota akayi. Itace ta6a nan shafa can shinshina nan haka ta dinga yi, shirun dayaji ne yasa shi mik'ewa yabiyo bayanta. Tsaye ya tarar da ita tana ta6a electric oven taga hotan kaza a jiki ya bita da kallo, sam baya ganin aibunta domin yasan dole tayi haka tunda ba ko ina akeda irin abubuwan ba dan ko gidansu Abubakar d'in babu wasu abubuwan da ya zubawa INdo. K'arasawa yayi ta kallesa tare da juya Mai baya yayi dariya yace. "Ohh su Humayrah daga zuwa d'akko cups sai mukaji shiru." "Lah wallahi mantawa nayi bari na kaimusu, amma wanne zan d'auka..?!" Ta fad'a ba tare da tajuyo ba, ya k'arasa tare da janyota jikinsa yace, "Kibar shi sun ma farasha da jarkar." "Toh sakarni na fita gurin su." "Nak'i d'in da wayace kik'i komawa..?!" Jin ya fara shafar jikinta ne yasa ta faraturesa ya juyo da ita ta kawar dakai sai ji tayi bakinsa a saman k'irjinta INdo ta zabura ya saketa ta ruga falo nan ma suka bisu da kallo ita dai INdo harta zauna jikinta be dena rawa ba a haka har suka gama zamansu sukayi musu fatan zama lafiya sannan suka fita suna tafiya wasu suka zo ranar ma dai haka suka wuni da baki. Misalin k'arfe goma na dare Abubakar ya shigo gidan, tsit ba kowa sai k'arar inji ya rufe ko'ina sannan ya shiga falon, zaune ya ganta tana kallo ta kurawa TV d'in ido sai dariya takeyi da alama film d'in yayi mata kyau. Duk sallamar da yakeyi bataji ba sai daya shigo har tsakiyar falon ya kare mata TV d'in sannan taganshi tana dariya tace. "Kai dacta dan Allah ka matsa kana kare min." Hannu ya bud'e mata alamar tazo suyi hugging amman tak'i sai ya kashe kallon gabaki d'aya tare da k'arasawa dining ya ajiye ledojin hannunsa. Tashi tayi tana turo baki ganin ya kashe mata gashi bata iya kunnawa ba dama su Hawwa ne suka kunna dasuka zo ya juyo ya kalleta tare da cewa. "Kin manta ko, da bakinki kika cemin malama ta baku labarin matar da bata bin umarnin miji da abinda akayi mata ko? Shine yanzu nace kizo kiyi min oyo-yo kikaki ba ruwana dake." INdo ta tuna tayi saurin zuwa gurinsa ta tsaya, ganin haka yasa shi kuma ware mata hannunsa a hankali ta shige bayan ta rintsa idanuwanta ya rungumeta shima. A saitin kunnanta ya tambayeta. "Kinyi sallah..?" Kad'a kai kurum tayi sannan nan yace. "Zo muje muyi wata mu yi addu'a alkairin dake cikin auran mu Allah ya tabbatar dashi." Tunawa INdo tayi da labarin dasu Uwani suka bata cewar indai taji miji yace ayi sallah akuma ci nama toh ranar aikwai aiki musamman ranar da aka kaika. Janta yayi suka nufi bedroom d'insa dama bata ta6a shiga ba, taga wani shegen gado me shegen kyau bakin ta yak'i rufuwa yace. "Zokije kiyi alwala." Tace "Dacta tsaya na gama ganin gadonka wallahi yayi kyau Allah sanya alheri." "Amin Humaira amma ai shima nakine, duk abinda kika gani na gidan nan nakine ko mutuwa nayi baza a raba gadona dasu ba." Cikin tsananin murna INdo tace tana kallonsa. "Dacta da gaske kake nawane.?!" Kai ya d'aga mata ta fara murna tana godiya sannan ta shiga bayin tayi alwala, tana fitowa shima yayi lokacin ta dawo daga d'akko hijjab, kar6a yayi ya bata sabo tasa sannan yajasu sukayi 2raka'at sannan ya dafa kanta yayi mata addu'a suka shafa. Hannunta ya kama suka koma falo ya kunna musu kallo suna dining suna kallo ya dinga feeding d'inta sai da taci ta koshi ta kora da madara sannan tace ta koshi. 12:49am suka shiga d'akinsa INdo sai hamma takeyi najin bacci, saida ya had'a mata ruwa tayi wanka sannan shima ya shiga ya fito sanye da boxer tayi saurin kawar dakai tana zaro ido gashi ya kulle d'akin itama daga ita sai towel ya kwashe mata kayan ta nema ta rasa. Turare ya shafa kawai sai na mouth sannan ya nufi gurinta dasu, zama yayi a kusa da ita tayi saurin matsawa shima ya matsa tare da rik'ota da sauri tace. "Na higa uku ni INdo dan Allah dacta kayi hakuri." "Shhhh." Yayi mata tare da matsa mata turaren ya ce ta bud'e bakin ya fesa mata da sauri ta tufar da yawu a k'asan bedside carpet yace. "Humaira ya haka.?!" INdo kamar tayi kuka tace "yo toh ai ba dad'i." Dariya yayi tare da girgiza kai sannan ya tashi ya mayar tare da d'akko handkerchief ya goge gurin. Light off yayi musu sannan ya kuma kunna bedside lamp bulb d'in green light ya haske d'akin yayi kyau INdo ta kalli d'akin ta kuma sakin murmushi ita dai yau tana ganin ikon Allah a gidannan. A hankali ya sargafota ta fara zillo towel ya fara kwancewa tace. "Wai kai bazan sa kaya bane.?" Cikin sanyin murya Abubakar yace "Eh a haka zaki kwana ko kina son nace bana so amma kuma kisa...?" Ya tambaya yana shafa gashinta, wani kakkawar yawu ta had'iya tana kad'a kai, ya janyota kan gadon towel d'in ya yaye daga k'asa INdo ta saki k'ara jikinta na rawa. A hankali ya kuma janta jikinsa sannan ya zare mata towel d'in gabaki d'aya ai INdo sai kuka tana cewa. "Yaya Abbakar karka kalleni in kanawa iyayenka, ni wallahi ka dena ta6ani banasan iskanci..." Sam bazai iya yi mata abinda take so ba, shi amatsayinsa na likita yasan idan ya barta besamu nutsuwa ba zai shiga tashin hankali ya kuma San akwai illah hakan. A hankali cikin wayewa da iya *TATTALIN MACE* Abubakar ya dinga hillatar da ita yana kuma nuna mata illar hanashin da takeyi a haka ya samu INdo ta yadda dashi ta bashi kanta duk da tasha kuka hardasu majina. Yana daga kwancen yace, "Ohh so sorry my wife, please zoki rama kema." Tana kukan ta k'asa-k'asa tace. "Meh...?!" Ai Abubakar besan lokacin daya kyalkyale da dariya ba haushi ya sake zuwar ma INdo ta juya ta fara dukansa yana karewa da hannu... *HAJJA CE*👈 [7/31, 5:13 PM] Aisha Galadima: *⚗⚗MUSAYAR ZUCIYA...⚗⚗* ♥♥ ♥ A true life story Na *K.A.S Precious Hajja ce*👈 *HASKE WRITER'S ASSOCIATION*💡 (Home of expert & perfect writer's) *VOTE me on wattpad @Hajjac* *DEDICTEED TO:* Sanah Isma'il Matazu Page *21* Ganin yak'i denayi mata dariya yasa ta lalubo towel d'inta ta d'aura ta kwanta tare da janyo bargo ta rufa sabida wani sanyi dataji yana shiga cikin jikinta. A hankali ya matsa kusa da ita tare da zura hannunsa ya rungumeta tana jinsa ta kasa yin koda kwakwaran motsi sabida jikinta duk ya lafe a haka bacci ya d'auketa shi kuwa kasa yi yayi se tashi mayayi yaje yayi wanka sannan yayi sallah ya d'auki sallayar ya maida ita inda zai dinga kallon fuskarta. Yana jan carbi yana shafar gashinta tare da shafar fashin goshinta wanda yake d'ansiriri. Har aka kira asuba INdo bata koyi juyi ba bare asaran zata tashi ya mik'e daga kan sallayar yashiga bathroom ya tarar mata ruwa sannan ya fito, a hankali cikin nutsuwa ya fara tashinta amma babu alamar zata motsa sai ya yaye mata bargon ya fara k'ok'arin kwance mata towel tayi saurin tashi tana rarumarsa tana furta "6arawo..!" ta d'auka 6arawo ne sabida a tunaninta wannan uban gidan baza'a rasa 6arayin dazasu shigo yi musu sata ba. A mamakin ce Abubakar ya kalleta ganin yadda ta cakumeshi tayi saurin sakinsa tare da saurin komawa ta kudindine a bargo yace mata. "Humairah a mimakwan yin auziya sai ki furta 6arawo? Toh ina 6arawon tashi ki gaya min ko mafarki kikayi..?!" Tana cikin bargon tace "Allah mafarki nayi kayi hakuri." "Toh tashi kiyi wankan tsarki sai kiyi sallah." "Wane iri kuma dacta?!" Ta tambaya da mamaki yace "na janaba ko bakisan anayi ba?" Sai yanzu ta gane kenan a makaranta da aketayi musu bayanin wanka haila, wankan janaba da wankan bik'i shi yanzu wanda zata yi shine na janaba ikon Allah dan ita a karatu idan ba practical ba toh theories dakyar suke shigarta. "Kin iya ko..?!" Ya tambayeta tayi shiru ya kwanta a bayanta tare da janyota ya matseta, ihu ta farayi sannan tace. "Toh sani nayi ne, ka gaya min mana." Yace "Okey kin iya wankan tsarki na haila?" 'Daga kai tayi yace "tashi ki nunin in gani ko dai-dai kikeyi?" Dakyar ta tashi zaune tana gwada mai ya gyagyara mata sannan yace taje tayi amma ta canzaxani.Ta shiga bathroom d'in da sauri wai dan yana kallonta, tana fitowa sukayi sallah sannan yace tazo su yi karatu, tundaga Nasi ya fara mata har akazo inda ta iya sannan yace toh zai dinga koya mata kullum da asuba indai yana gari. Gadon ya sake janta ita INdo bata sabayin baccin safe ba hakan yasa tace mai ita kallo zataje tayi ya hanata dole taje suka kwanta, romance d'inta kawai yayi mai tsayawa a wuya dan tana k'ar6ar sakon yadda ya kamata kafin kace mene tuni INdo tayi baci shima ya samu yayi har kusan 9:16am sannan ya farka yana zare jikinsa itama ta farka a kunyace dan ko kallonsa bata iya yi. "Muje kitchen yau dakan mu zamuyi breakfast." Kama hannunta yayi suka fita suna zuwa kitchen ya sargafe hannu a k'irji yana jiran yaga ta ina zata fara, itama tsayawar tayi tana kuma bin kayayyakin kitchen d'in da ido. "Jiya na shigo da slender bari na had'a sai ki soya kwai da tea." Tace "Toh akan slimba d'in Zan d'ora." "No Humairah slender itace abinda za'a zuba kalanzir toh ba shi za'a zuba ba gas za'a saka ajona na wannan sai da kin kunna zai kawo wuta idan ya k'are kuma zakiga yak'i kawowa." Jinjina kai tayi tamkar ta fahimta, shi kuma dayake yasan dawa yake tare sai ya kamo hannunta suka nufi bayan kitchen d'in, a kan idonta yasa dan watarana idan ba kowa ya zama na ta iya. Komawa cikin kitchen d'in sukayi sannan ya kunna cooker d'in sai ga wuta INdo ta dinga murmushi kusan duk shi yayi koma tana kallonsa suna yi yana nuna mata amfanin komai na kitchen d'in komai saida ya nuna mata sannan suka kwashi breakfast d'in suka kai dining. Yauma kamar jiya daddare shi yayi feeding d'inta taci sannan shina yaci suka koma wajan TV lokacin injinsu ya mutu suka kalli juna yace. "Muje d'aki ki gani." Yana rungume da ita yace suka shiga ya d'akko laptop d'insa ya kunna mata kallon yaga alamar tana masifar son yin kallo tana zaune a tsakiyar gado ya d'ora kansa a cinyarta tayi dariya tana kallonta. Hannunta ya kamo ya d'ora akansa tare da cewa. "Sweetie bazaki dinga shafani ba, please inason ki koyi soyayya fa ni Ina son love." Sosa mai ta fara yi ya dank'e hannun tare da cewa, "Bafa haka akeyi ba, haka...!" Ya fad'a yana rik'e da hannunta yana shasshafa kansa, haka Abubakar ya dinga tarairayar INdo yana nuna mata abubuwan da zata dinga mai cikin ko wane irin abu ko yanayi sai da ya nuna mata irin abinda zata yi mai tun tanajin nauyi da kunya harta fara sakin jiki tana yi mai ba tare da ya nema ko ya nuna buk'atar hakan ba. Cikin sati d'aya INdo ta kuma wayewa da wasu abubuwan tayi kyau abinta ranar da ta cika kwana takwas ya d'auketa sukaje gida su Mama suka dinga shi musu albarka INdo bajin kai k'annansa duk babu wanda bata wasa dashi sun dad'e Kafin su tafi gidan Sadeeq sai INdo tayi mamaki ganin gidanta yafi kyau sai akayi sa'a bata kwafsa tayi maganar ba. Sosai suka sha hira shima Sadeeq ya sakar mata fuska Fateema taja ta suka kule d'aki, nan ma sun dad'e kafin Abubakar yace tazo suka tafi. Washe gari ya d'auketa suka jajje gidan abokansa na nan sannan ya kaita har Munjibur park wayyo farin ciki a gurin INdo ba'a musallatawa duk abinda taga anhau sai tahau shi kuma ya biya duk bata san sai ya biya ba sha'aninta kawai takeyi suka yi hotuna wasu tare wasu kuma ita kad'ai. Sun dad'e kafin suka koma gida INdo cike da murna ya kalleta shima cikin shauk'inta da soyayyarta sannan yace. "Zo kimin tausa tunda yauma kin gajiyar dani." Zuwa tayi tana shan ice cream tana mai sannan shima ta bashi yasha wani shauk'i yana fisgarta bata san lokacin da ta kwanta a bayansa ba a hankali ta furta mai. "I love you mijina." "Oh my God what did you say? Allah yasa ba mafarki nakeyi ba sweetie d'an jijjiga ni." Cikin dariya INdo da bugeshi a baya ya juyo tare da janyo ta aikuma ice cream d'in ya zube a saman k'irjinshi yace. "Aikuwa sai kin lashe shi kuma ki gama ki wanke ni ah bazan yadda ba." "Ah my key nifa bani ce silaba kai kaiwa jikinka haka." Ta fad'a tana masa cukali tana d'iban na k'irjin nasa tana sha yanzu duk ta waye bata kyama ganin shima vaya nuna mata akan komai na jikinta. "Nifa inajin zafin na cukalin nan ki ajiyeshi." "Toh baki zansa?!" Ta tambaya kai tsaye shima kai tsaye yace mata "Eh shi nake so." Harshe tasa ta fara lasa har sai data sud'e tass sannan shima ya faki idonta ya d'akko ragowar na rubar ya 6arar mata a k'irji yace. "Ashhh sorry bari na ramamiki kema." Dariya suka saki tare cikin dariyar tace. "Kaifa kana sane." Ya rik'ota yasa baki tass shima ya lashe mata daga nan kuma al'amra suka canza. Ana gobe zai koma abuja suna kwance duk sun mak'ala juna suna sauk'e ajiyar Zuciya kad'an-kad'an Abubakar yana shafar kanta yace. "Humairah banson tafiya na barki anya bazan tafi dake ba?!" Shiru INdo tayi babu amsa ya kuma janta jikinsa yana d'an shafarta tana biye mai ya kuma cewa. "Kinyi shiru Humaira ko dama kin k'agara na tafi.?" Tace "A'a bansan abinda zance ba nima shi yasa nayi shiru fa." "Okey kema kina son ki bini ko?" Tace "Eh mana." Hannunta ya rik'o ya d'ora a k'irjinsa tare da cewa. "Ina sonki Humaih ina kaunarki ban ta6ajin Ina kaunar mutum ba kamar yadda nake sonki, please kema ki soni koda bekai yadda nake miki ba kinji..?!" "Toh ai Ina sanka nima." Ta fad'a cikin sanyin jiki suka rungumi juna da haka sukayi bacci, washe gari tunda asuba suka yi wanka INdo tayi kwalliya irinta kauye tasa zani daban riga ma haka da d'ankwali. Abubakar na shigowa d'akin daga shi sai boxer da singlet ya kalleta yana murmushi yaga kwalliyar tayi mata kyau ya k'arasa ciki yana cewa. "Woww sweetie gaskiya sai na biya wannan wanka I like it." "Toh nawa zaka biya domin da tsada...?" Ta tambayesa tana jan hancinsa, bakin gado ya zauna yana rik'e da kugunta yace. "Bari kigani." Kissing d'in bakinta yayi duk ya kwashe janbakin datasa ya matseta a jikinsa yace. "Allah ya miki albarka matata kafin in dawo Zan samar miki makaranta damun koma saiki shiga." "Kanason nayi karatu da yawa, nikuma kaga ban iya turanci ba." Ta fad'a tana shafar sajansa ya sanya kansa tsakiyar kirjinta yana goga fuskarsa a jiki yace. "Zaki iya kema sweetie ai da koyo akasan gwani, abaya ma dandai baki tsaya kin koya bane amma yanzu kisa aranki cewar kema zaki iya turanci kinji ko..?!" "Allah yasa toh.." Ta fad'a yace "Amin sai kuma abani bye-bye dan bazan tafi haka ba" Rufe fuska tayi ta zauna kan cinyarsa wannan karan itace ta fara sanya mai mouth nata cikin nashi ya k'ara tabbatar da lallai tana d'aukar naganar tana kuma jinta tare da aikata ta a aikace. Sai da ya samu nutsuwa sannan sukayi wanka kamar karsu rabu duk da yace mata kwana biyar zaiyi yaxo yayi weekend amma gani yake tamkar rasa ta zaiyi, itama haka ta dinga cewa ya barta su tafi abuja tare dama bata ta6a zuwa ba amma ya dinga kwantar mata da hankali yace kila ma jibi ya dawo idan yaje ya rage wasu abubuwa. 'Dakinsa saka koma ya shirya duk ta nanik'e mai ya kalleta yace. "Idan na tafi kiyi tafiyarki gidan Mama ko gidan M twinnie ki zauna kuyi hira zuwa yamma sai ki dawo dan nace dasu Haleema suzo su zauna a nan harna dawo kinji.?!" "Toh.." Tabashi amsa ta fesa mai turare sukaci abincin daya dafa musu suna gamawa sadeeq na yin knocking . Sai data fara sanyo hijjab sannan Abubakar yaje ya bud'e masa kasan cewar ya hanata zama a haka idan wasu suka zo. "Aishatu Hamza..." Cewar Sadeeq cike da zolaya tayi murmushi tare da cewa. "Malam Sadeeq ya gida..?!" "Kalau." Yabata amsa Abubakar yace. "Twinnie gidana a hannunka please ka kular min da babyna." "Au wai kana nufin sai an kula da ita? Ta6 Aisha ai ta iya haura katanga bakada case da ita ka kwantar da hankalin ka." INdo ta turo baki haushinsa ya cika ta Abubakar ya janyo ta tare da cewa. "Kabari twinnie ai dane kuma kaima ai kayi kana yaro." Ya kalli INdo tare da cewa "Sorry sweetie karki kulasa Zan dawo na d'aukeki." Suna dariya dukansu suka fita Abubakar ya shiga mota shida Sadeeq zai saukesa gidan Mama idan yaje, INdo ta zagaya 6angaran Abubakar idonta yayi ruwa murya na rawa tace. "Allah ya kiyaye hanya." "Amin." Ya fad'a yana zuro hannu sukayi musabuha yaja motar suka bar gidan, tana share hawaye ta rufe gate d'in tare da shiga cikin gidan. Suna hanyar zuwa gidan Mama Abubakar ya dinga ba Sadeeq hakkin lurar mai da gida musamman ma INdo abin ya dinga bawa Sadeeq mamaki wai yau INdo ce take da matsayi a zuciyar d'an uwansa, koda yake yafishi sanin INdo tun a kauyan Sani. Bayan sunyi sallama da mutanan gidan ya kama hanya ya tafi bayan ya bugawa INdo waya yace mata ya tafi tayi mai fatan sauka lafiya. **** K'arfe 11:36am tana zaune a falo tana kallo bama taje gidan Maman ba ganin an kawo wuta, shigowa yayi kai tsaye gidan tana ganinsa ta mik'e da gudu raje ta rungume shi kamar yadda ya sabar mata. Jin jikinsa yana rawa ne yasan ya INdo d'agowa tana kallon kafin k'irjinta ya fara bugawa sam bata gane bashi bane ta sha'afa da kayan dayasa tace. "My key menene? Inzo mutafi?!" Wani kallo dataga yayi mata ne yasa hankalinta dawowa jikinsa ta zaro ido tana kallon fuskarsa tace. "Malam Sadeeq kayi hakuri na d'auka Yaya Abubakar ne." Da kyar Sadeeq ya samu ya bud'e baki yace. "Aisha jeki d'akko hijjabinki zamu gidan Mama." INdo ta kallesa cikin sauke numfashi tana warware d'ankwalinta tayi mayafi dashi tana cewa. "Ah ai inajin sai anjima zani idan ma banjeba ai yace su Haleema zasu zo." "Ki d'akko hijjab nace miki kenake jiya bawai surutu ba." Juyawa tayi tana kunkuni ta d'akko ta fito shi kuma ya juya ya fita. Saida ta fito sanye cikin atamfa blue da zanen ganye fari ta sanya blue d'in mayafi suka fita ya rufe gate d'in suka shiga mota. Kasa tukawa yayi jikinsa sai rawa yake yi INdo ta bishi da kallo cikin mamaki k'arshe ya fito daga motar yace. "Fito muje." A k'afa suka taka har bakin titi ya tarar musu napep suka shiga aka kaisu gidan Mama lokacin har mutane an fara taruwa a k'ofar gida Sadeeq ya cewa INdo. "Shiga ciki gurinsu." Yana dad'a ya juya yabarta ita kuma ta nufi ciki tana bin mutanan da kallo. Tana shiga parking space taji abbansu yana waya yana cewa. "Eh wallahi Abubakar d’inne.... *HAJJA CE*👈 [7/31, 5:13 PM] Aisha Galadima: *⚗⚗MUSAYAR ZUCIYA...⚗⚗* ♥♥ ♥ A true life story Na *K.A.S Precious Hajja ce*👈 *HASKE WRITER'S ASSOCIATION*💡 (Home of expert & perfect writer's) *VOTE me on wattpad @Hajjac* *DEDICTEED TO:* Sanah Isma'il Matazu *MUSAYAR ZUCIYA:- Hak'ik'a banyi zato ko tsammanin makaranta labarin nan sunkai yawan haka ba sai da akazo page 21, a hak'ik'anin gaskiya naji matuk'ar tsoro na razana da ganin millions of people's da suk'e matuk'ar son Dr Abubakar da Aishatul humaira a ranar da waya nata tarwatsewa toh da tuni an wuce babin wayata, everywhere MUSAYAR ZUCIYA Hajja karki kashe Dr becan-canci haka ba, idan kikai hakan kin sakamu cikin tashin hankali INdo kuma baki kyauta mata ba. Karku manta Allah babu ruwansa da lokacin da zaka farajin dad'in rayuwa ya d'aukeka, anytime kowane irin yanayi kake ciki idan lokacinka yayi dole ka barshi katafi ba tare da kashiryawa hakan ba. A yanzu haka nasan wad'anda suka tanadi likaffani na mutuwarsu sabida suna ganin sun tsufa rayuwa ta k'are musu amma har yanzu basu mutuba sai 'ya'yansu da jikok'insu wad'anda ba'a saka musu ran mutuwa sune suke mutuwa. Dan Allah badan niba kuyi hakuri ku d'auka a cewar kuma akanku hakan zata iya faruwa sannan kuma kowacce zata yiwa Abubakar addu'ar Allah ya sadashi da rahamarsa. Labarin gaske ne domin da Ummi Aisha itace zata yishi so bansan Stylish Bch ta bata labarin ba sai jiya. Kuyi hakuri harda masu cewa sundena karantawa sabida sunsan karshe dai Sadeeq zata aura suzo suna kishi da fateema🤭toh duk kuyi hakuri kuma sannan ku yafewa 'yar uwarku, da ace tun farko bansa muku true life ba wallahi akwai yadda zanyi na sauya salon amma yanzu kona sauya toh araina zan dingajin abun tunda nasan ba haka yake ba, duk wanda na 6atawa tundaga kan fara novel din har zuwa wannan pagen kuyi hakuri ku yafewa Hajja ce👈 'yar Adam ce kamar ku sannan kuma meyin kuskure a duk inda ta samu kanta, wallahi dana dinga ganin comments d'inku dakyar nayi bacci zuciyata na rawa Ina ganin ban kyauta muku ba ciki rayuwarku. Nasan da yawanku zaku dena karantawa toh Ina fatan duk wanda ya tsaya iya nan ya d'auki wani darasi a ciki amma Zan samu na k'arasa shi a WATTPAD dan nima na samu nutsuwar Zuciya. Nagode gaduk wanda suka karanta farkon labarin Allah ya sadamu da rahamarsa a cikin kabarinmu Amin Love you all m fan's❤🤝❤* Page *22* Hark'asa INdo ta tsugunna tana gaida shi idanta akan fuskarsa tace, "Abba ina wuni?" Ya zura wayar cikin aljihunsa yana kallonta ya amsa. "Lafiya lau Aisha tashi kishiga daga ciki." "Toh adawo lafiya." Tafad'a tana mik'ewa ta nufi cikin gidan, tana shiga sallama tayi tana k'iran Haleema kamar yadda takeyi idan suka zo gurin da zasu had'u. Haleema dake zaune a falo tajiyo INdo na nemanta da sauri ta mik'e ta shige d'akin su dan bata son su had'u a cikin wannan yanayin. Mata tagani a zaune a falo wasu sunzo wasu kuma na shigowa Mama a gefe gurin kujera ta takure Umma kuma a bakin k'ofa INdo ta dinga binsu da kallo kafin ta k'arasa kusa da Fateeman Sadeeq ta zauna itama ta takure tana gaida su, suka amsa mata a sanyaye. Juyawa tayi tana lek'an fuskar Fateema wadda take faman hawaye a dai-dai fuskar tata tace. "Kai amaryar malam menene kike kuka? Ko malam Sadeeq ne,dan nasan shi sarai tun a makarantar mu meh yayi miki..?!" Zame jikinta tayi daga na INdo ta juya tana kallon Mama sai taga itama ta d'auke kai Fateema ta rasa yadda zatayi gashi INdon ta takura mata akan sanjin abinda takewa kuka,mutane dake shigowa ne ya k'ara sanya INdo cikin wasi-wasi kuma da sun shigo zasu samu guri su zauna a cigaba da zaman shiru sai kuma kallonta da ake yi. Mama ce tayi k'arfin halin yin magana tana kallon su fateema tace. "Fateema jata kushiga cikin d'aki mana." Hakan akayi kuwa suka shiga ciki nan INdo taga Haleema a mak'ure jikin gado sai shashekar kuka takeyi, cikin sauri ta k'arasa wajanta dayake Allah ya had'a jininsu da ita ta janyo ta da sauri cike da damuwa da nuna kulawa tace. "Haleema Hali dubu kyakyawa, me kikema kuka kema?!" Rungumeta Haleema tayi yayin da INdo tayi shiru tana rik'e da ita, ita INdo ba komai yake sanyata saurin kuka ba har sai abin yakai mak'ura sannan batada tsoro musamman a fagen magana kafin Haleema tayi magana Mama tashigo d'akin Fateema na zaune fuskarta cikin hijjab Mama ta rik'o INdo ita kuma jinta ajikin Mama yasa tayi murmushi sai taji tamkar Abubukar d'inne ya rik'ota. A bak'in gado ta zaunar da ita can suka jiyo muryar Wata tsohowa mak'ociyar su ta shigo tana fad'in. "Allahu akubar Garbati ankai sa'i, d'azu-d'azun nan yana fitowa daga gidannan ya lek'a zaurena muka gaisa yace min zai tafi birnin taraiya, Allah sarki kungani ya bani yaci inci goro Allah yajik'anka Garba.." Ta k'arasa maganar tana nuna musu naira d'ari biyar d'in daya bata, a cikin d'aki INdo ta kalli Mama tana zaro ido tace. "Mama waye Garba a gidannan da ya mutu?!" Cikin dakiya Mama ta k'arasa wajan wardrobe tana cewa. "Anan gidan yake Aisha zakiji ko waye." Farin hijjab ta zaro tare da mik'awa INdo shi tana cewa. "Ciro mayafin Aisha a ajiye shi." Kamar yadda Mama tace haka tayi tasanya hijjab d'in Mama zumbulele sannan Mama tace ta zauna karta fito. Suna zaune zugum sai ta d'akko wayarta number'n sa ta k'ira cikin sa'a aka d'auka cikin zumud'inta tace mai. "Salama alaikum my key kaje ko kakusa zuwa..?!" Taji ance "Sorry hajiya me wayar yanzu haka Allah yayi mai rasuwa." Da mamaki tace "Rasuwa kuma? Toma waikai waye ma tukunna?! Kashewa akayi INdo ta zaro ido tana kallon wayar tare da furta. "Rainin hankali toh ko fad'uwa wayar tayi wani ya sace shine zaice min haka. Aniyarka ta bika mugu 6arawo." Ta fad'a su kuma Haleema dasu Fateema da wasu da suka shigo d'akin suka bita da kallo. Hawwa ce ta shigo tana kuka sosai saida tazo falo ta kuma 6arkewa da wani kukan tana shashek'a tace. "Allah sarki Yaya Habu yanzu ya gama min waya Mama kinga kiran da yayi min yace gobe insa aje a d'akko min Humairansa... Tazo muyi hira da daddare a maida ita baya son ta zauna it...." Ta kasa k'arasawa sai kuka, INdo ce ta fito fululum cikin hijjab jin muryarta ta k'arasa kusa da Hawwa ai Hawwa na ganinta ta janyota jikinta kukan ya tsananta amma bakin be fasa magana ba. "Aunty Humairah kinyi rashi Allah yajik'an Yaya Habu yaso kuyi long life a tare sai gashi Allah ya d'aukesa ya barki...." Muryar Mama ce ta katsewa Hawwa kukan da takeyi cikin fad'a tace. "Amma dai ban ta6a sanin bakida hankali ba sai yau Hawwa, wannane wane irin hauka ne daga shigowarki sai kace ba gidan musulmai kika shigo ba. Toh kin gaya mata kinji dad'i tun zuwanta kowa ya kasa gaya mata saike wawuya kawai..." Da sauri Hawwa ta kalli INdo sai taga ta kura mata ido fuskarta a murtuk'e tun daga nan kuma sai bakin mutane ya fara bud'ewa aka fara zance mutuwar kunnuwan INdo suka dinga jiyo mata ai yana tafiya har ya wuce Kaduna Allah yayi masa rasuwa. Sosai hankalin Hawwa ya tashi ganin yadda INdo ta kafeta da ido hakan ya bata tsoro tayi saurin matsawa baya INdo ta bita cikin tashin hankali Hawwa tace. "Aunty Humairah Lafiya? Please wannan kallon fa..?!" A hankali INdo tasa hannu ta rungume Hawwa cikin rawar murya tace. "Yaya Hawwa kema sokike Yaya Abubakar ya mutu? Yanzu na buga mai waya wani ya d'auka yace min me wayar ya mutu ashe kema sokike ya mutu? 'Dazu ni narakasu mota suka shiga shida malam Sadeeq amma meyasa kike son yayanki ya mutu? Kinga yana sona dayawa d'azu fa har cemin yayi yana son duk wani mesona kuma zai sani a makarantar abuja..." "Kiyi hak'uri aunty Humairah nima inason Yaya Habu amma Allah yafimu sonshi shi yasa yayi hatsari..." Hawwa ta fad'a tana kuma sakin kuka, da sauri INdo ta hankad'a Hawwa baya iya k'arfinta jikake gam..! ta bugu da kujera cikin kukan bak'in cikin maganarta yasa INdo cewa. "Daga yin bikin mu shine zaki mana addu'ar ya mutu sabida bakya sonmu, toh insha Allahu sai Isyaku ya riga dacta mijina mutuwa fatanki ya biki, ance miki Garba ne ya mutu shine zaki zo kice Yaya Abubakar ne dan bak'in ciki..." Umma ce tayi saurin toshewa INdo baki cikin rufewar ido ta fara tureta domin ta baya ta rik'ota ta kuma toshe mata. Cikin kwantar da murya Umma kishiyar Maman su Sadeeq take mata magana a hankali. "Kinga Aisha kiyi shiru kinga mutane sun fara cika gidan yi hak'uri taho muje ki zauna kinji 'yar albarka." Tana nishi Umma taja ta still bata dena yiwa Hawwa kallon banza ba duk kuwa da cewar ta girmeta nesa ba kusa ba amma cewar Abubakar d'inta ya mutu shine ya d'arsa wata k'azamar kiyayya a zuciyar INdo. Fateema ce ta fito idanunta jawur ta kama hannunta suka koma cikin d'akin Mama, suna zama amma sai mita INdo takeyi Mama ta shigo ta kalleta tare da cewa. "Aisha kidinga hakuri kinji ko?" INdo tace "Toh Mama ki gaya mata bana son wasan mutuwa." "Toh zan gaya mata tashi muje ki wanke fuskarki da sabulu." Babu musu ta mik'e suka shiga bathroom saida ta gama wankewa sannan Mama ta kamo hannunta suka wuce, d'akin Abba suka shiga yana zaune yayi shiru yana bud'e likkafani gefe turare ne a kusa dashi suka shiga bayan Mama tayi sallama. Sake gaisawa suka yi da INdo sannan Abba ya kalleta tsawon lokaci ya kasa cewa komai, can dai ya nisa yace. "Aisha ke musulmace ko?!" 'Dan murmushi tayi alamar kunya tana sunkuyar dakai tace, "Eh Abba." "Alhamdulillahi ina son sanar dake Abubakar dai Allah ne ya bani shi, nina raineshi tundaga zanin goyo har girmansa da temakwon Allah, bayan ya girma ya mallaki hankalinsa shida d'an uwansa suka d'auke min duk wani nauyi nasu dana k'annansu, kafin ya aureki ya nemi auran wata yarinya Allah ya k'adarta beyi ba sai dake, toh Allahn daya baki Abubakar Aisha ya k'ar6i abinsa domin yanzu haka suna hanya za'a kawo gawarsa ina son ki daur...." Bek'arasa ba yaji ta fashe da kuka, kusa dashi ta rarrafo tare da rik'o Hannunsa tana jijigawa tana fad'in. "Abba... Abba wallahi ba dacta bane, ba shine ya mutu ba shi yatafi abuja k'ila dai malam Sadeeq ne, dan Allah Abba karku ce haka wallahi yace zai dawo ya tafi dani can garan..." Mama Abba ya kalla alamar tazo ta zanye ta, tana zuwa INdo ta juya kanta tare da rik'o hannunta itama tana cigaba da magana tana basu rabarin abinda yace zai yi mata nan gaba sai kawai itama Maman ta fashe da kuka Abba ya fara mata fad'a amma ina ta kasa yin shiru bare ta bawa INdon. "Kutashi kuje yanzu suna hanya zasu kawo shi, karku sake kubarta tafita ko'ina kinajina...?" Mama ta kad'a kai tare dajan hannun INdo suka shiga gidan sai ihu take mutane na kallonta cikin tsananin tausayawa. Tana shiga ciki ta zu6e ak'asa jikinta sai rawa yakeyi aka rufa a kanta kowa sai nemar mata d'auki yake ta zame jikinta daga na wata mata tana kallon Matan tace. "Sani zantafi." Umma ta rik'ota itada Fateema ta fara tirje musu dama INdo yaya lafiyar kura, dacta ne yasanta ya kuma san yadda zai biyo mata gashi babushi dan haka abin nata ya kuma yawa. Kullesu akayi a d'aki babu me fitowa suna jiyo kukanta har aka dawo daga d'akko gawar Abubakar, d'akinsu aka kaishi Sadeeq tamkar wani zararre fuskarsa fal hawaye idanunsa sunyi luhu-luhu tamkar kurji ya fito ya shiga cikin gida yana neman Mama. Da kyar ya iya tambayarta zani ta mik'e ta bud'e d'akin, suka shiga. Gaidashi mutanan d'akin suke suna mai gaisuwa, yana furta "Alhamdulillah." INdo tayi zumbar ta mik'e daga ruk'on da Zulaihat tayi mata, lokacin Mama ta mik'a mai zannin ya k'a6a kawai yaji INdo ta mak'aleshi katak'am tamkar ba rik'on mace ba tana kuka tana cewa. "Dacta ka dawoko? Nasan dama bazaka barni ba dan Allah da manzansa kace min Malam Sadeeq ne ya mutu ba kaiba, wallahi kaga zanyi kwalliyar da kace irinta d'azu, mu koma gidanmu nan kana da mak'iya ciki harda Abba duk fatan mutuwa suke ma..." "Aisha sakar ni please." Sadeeq ya fad'a yana 6an6areta daga jikinsa amma tamkar mutum biyu ne suka rik'esa, ya rasa dalilin dayasa takeja masa mugayan alkaba'i tun suna makaranta nan fa su Mama suka k'arasa suna nuna mata bashi bane amma tak'i sakinsa cewa take. "Duk inda zahi zan bihi wata k'ila akwai masu bibiyarsa basa sonshi toni ina sonsa." Janta yayi ganin ta mak'ale suka k'arasa bakin gado ya zaune tare da nunawa Fateema alamar tazo ta zauna kusa dashi. Tana zuwa INdo ta kare shi alamar karta ta6ashi Fateema ta toshe baki kuka na shirin kwace mata, haskilowa kawai takeyi tasan da shi ya rasu k'ila da tuni itace a cikin wannan yanayin da INdo take ciki. Kabeer ne ya shigo ya kar6i zanin domin sam INdo tak'i sakin Sadeeq, Mama kuwa so take ta 6an6areta domin tasan hankan ba dacewa bane kuma INdo tashiga cikin takaba hakan yasa ta fara sanya ta cikin dokokin da musulinci ya tanadarwa ga duk macen da mijinta ya rasu... *HAJJA CE*👈 [7/31, 5:13 PM] Aisha Galadima: *⚗⚗MUSAYAR ZUCIYA...⚗⚗* ♥♥ ♥ A true life story Na *K.A.S Precious Hajja ce*👈 *HASKE WRITER'S ASSOCIATION*💡 (Home of expert & perfect writer's) *VOTE me on wattpad @Hajjac* *DEDICTEED TO:* Sanah Isma'il Matazu *MUSAYAR ZUCIYA:- Hak'ik'a banyi zato ko tsammanin makaranta labarin nan sunkai yawan haka ba sai da akazo page 21, a hak'ik'anin gaskiya naji matuk'ar tsoro na razana da ganin millions of people's da suk'e matuk'ar son Dr Abubakar da Aishatul humaira a ranar da waya nata tarwatsewa toh da tuni an wuce babin wayata, everywhere MUSAYAR ZUCIYA Hajja karki kashe Dr becan-canci haka ba, idan kikai hakan kin sakamu cikin tashin hankali INdo kuma baki kyauta mata ba. Karku manta Allah babu ruwansa da lokacin da zaka farajin dad'in rayuwa ya d'aukeka, anytime kowane irin yanayi kake ciki idan lokacinka yayi dole ka barshi katafi ba tare da kashiryawa hakan ba. A yanzu haka nasan wad'anda suka tanadi likaffani na mutuwarsu sabida suna ganin sun tsufa rayuwa ta k'are musu amma har yanzu basu mutuba sai 'ya'yansu da jikok'insu wad'anda ba'a saka musu ran mutuwa sune suke mutuwa. Dan Allah badan niba kuyi hakuri ku d'auka a cewar kuma akanku hakan zata iya faruwa sannan kuma kowacce zata yiwa Abubakar addu'ar Allah ya sadashi da rahamarsa. Labarin gaske ne domin da Ummi Aisha itace zata yishi so bansan Stylish Bch ta bata labarin ba sai jiya. Kuyi hakuri harda masu cewa sundena karantawa sabida sunsan karshe dai Sadeeq zata aura suzo suna kishi da fateema🤭toh duk kuyi hakuri kuma sannan ku yafewa 'yar uwarku, da ace tun farko bansa muku true life ba wallahi akwai yadda zanyi na sauya salon amma yanzu kona sauya toh araina zan dingajin abun tunda nasan ba haka yake ba, duk wanda na 6atawa tundaga kan fara novel din har zuwa wannan pagen kuyi hakuri ku yafewa Hajja ce👈 'yar Adam ce kamar ku sannan kuma meyin kuskure a duk inda ta samu kanta, wallahi dana dinga ganin comments d'inku dakyar nayi bacci zuciyata na rawa Ina ganin ban kyauta muku ba ciki rayuwarku. Nasan da yawanku zaku dena karantawa toh Ina fatan duk wanda ya tsaya iya nan ya d'auki wani darasi a ciki amma Zan samu na k'arasa shi a WATTPAD dan nima na samu nutsuwar Zuciya. Nagode gaduk wanda suka karanta farkon labarin Allah ya sadamu da rahamarsa a cikin kabarinmu Amin Love you all m fan's❤🤝❤* Page *22* Hark'asa INdo ta tsugunna tana gaida shi idanta akan fuskarsa tace, "Abba ina wuni?" Ya zura wayar cikin aljihunsa yana kallonta ya amsa. "Lafiya lau Aisha tashi kishiga daga ciki." "Toh adawo lafiya." Tafad'a tana mik'ewa ta nufi cikin gidan, tana shiga sallama tayi tana k'iran Haleema kamar yadda takeyi idan suka zo gurin da zasu had'u. Haleema dake zaune a falo tajiyo INdo na nemanta da sauri ta mik'e ta shige d'akin su dan bata son su had'u a cikin wannan yanayin. Mata tagani a zaune a falo wasu sunzo wasu kuma na shigowa Mama a gefe gurin kujera ta takure Umma kuma a bakin k'ofa INdo ta dinga binsu da kallo kafin ta k'arasa kusa da Fateeman Sadeeq ta zauna itama ta takure tana gaida su, suka amsa mata a sanyaye. Juyawa tayi tana lek'an fuskar Fateema wadda take faman hawaye a dai-dai fuskar tata tace. "Kai amaryar malam menene kike kuka? Ko malam Sadeeq ne,dan nasan shi sarai tun a makarantar mu meh yayi miki..?!" Zame jikinta tayi daga na INdo ta juya tana kallon Mama sai taga itama ta d'auke kai Fateema ta rasa yadda zatayi gashi INdon ta takura mata akan sanjin abinda takewa kuka,mutane dake shigowa ne ya k'ara sanya INdo cikin wasi-wasi kuma da sun shigo zasu samu guri su zauna a cigaba da zaman shiru sai kuma kallonta da ake yi. Mama ce tayi k'arfin halin yin magana tana kallon su fateema tace. "Fateema jata kushiga cikin d'aki mana." Hakan akayi kuwa suka shiga ciki nan INdo taga Haleema a mak'ure jikin gado sai shashekar kuka takeyi, cikin sauri ta k'arasa wajanta dayake Allah ya had'a jininsu da ita ta janyo ta da sauri cike da damuwa da nuna kulawa tace. "Haleema Hali dubu kyakyawa, me kikema kuka kema?!" Rungumeta Haleema tayi yayin da INdo tayi shiru tana rik'e da ita, ita INdo ba komai yake sanyata saurin kuka ba har sai abin yakai mak'ura sannan batada tsoro musamman a fagen magana kafin Haleema tayi magana Mama tashigo d'akin Fateema na zaune fuskarta cikin hijjab Mama ta rik'o INdo ita kuma jinta ajikin Mama yasa tayi murmushi sai taji tamkar Abubukar d'inne ya rik'ota. A bak'in gado ta zaunar da ita can suka jiyo muryar Wata tsohowa mak'ociyar su ta shigo tana fad'in. "Allahu akubar Garbati ankai sa'i, d'azu-d'azun nan yana fitowa daga gidannan ya lek'a zaurena muka gaisa yace min zai tafi birnin taraiya, Allah sarki kungani ya bani yaci inci goro Allah yajik'anka Garba.." Ta k'arasa maganar tana nuna musu naira d'ari biyar d'in daya bata, a cikin d'aki INdo ta kalli Mama tana zaro ido tace. "Mama waye Garba a gidannan da ya mutu?!" Cikin dakiya Mama ta k'arasa wajan wardrobe tana cewa. "Anan gidan yake Aisha zakiji ko waye." Farin hijjab ta zaro tare da mik'awa INdo shi tana cewa. "Ciro mayafin Aisha a ajiye shi." Kamar yadda Mama tace haka tayi tasanya hijjab d'in Mama zumbulele sannan Mama tace ta zauna karta fito. Suna zaune zugum sai ta d'akko wayarta number'n sa ta k'ira cikin sa'a aka d'auka cikin zumud'inta tace mai. "Salama alaikum my key kaje ko kakusa zuwa..?!" Taji ance "Sorry hajiya me wayar yanzu haka Allah yayi mai rasuwa." Da mamaki tace "Rasuwa kuma? Toma waikai waye ma tukunna?! Kashewa akayi INdo ta zaro ido tana kallon wayar tare da furta. "Rainin hankali toh ko fad'uwa wayar tayi wani ya sace shine zaice min haka. Aniyarka ta bika mugu 6arawo." Ta fad'a su kuma Haleema dasu Fateema da wasu da suka shigo d'akin suka bita da kallo. Hawwa ce ta shigo tana kuka sosai saida tazo falo ta kuma 6arkewa da wani kukan tana shashek'a tace. "Allah sarki Yaya Habu yanzu ya gama min waya Mama kinga kiran da yayi min yace gobe insa aje a d'akko min Humairansa... Tazo muyi hira da daddare a maida ita baya son ta zauna it...." Ta kasa k'arasawa sai kuka, INdo ce ta fito fululum cikin hijjab jin muryarta ta k'arasa kusa da Hawwa ai Hawwa na ganinta ta janyota jikinta kukan ya tsananta amma bakin be fasa magana ba. "Aunty Humairah kinyi rashi Allah yajik'an Yaya Habu yaso kuyi long life a tare sai gashi Allah ya d'aukesa ya barki...." Muryar Mama ce ta katsewa Hawwa kukan da takeyi cikin fad'a tace. "Amma dai ban ta6a sanin bakida hankali ba sai yau Hawwa, wannane wane irin hauka ne daga shigowarki sai kace ba gidan musulmai kika shigo ba. Toh kin gaya mata kinji dad'i tun zuwanta kowa ya kasa gaya mata saike wawuya kawai..." Da sauri Hawwa ta kalli INdo sai taga ta kura mata ido fuskarta a murtuk'e tun daga nan kuma sai bakin mutane ya fara bud'ewa aka fara zance mutuwar kunnuwan INdo suka dinga jiyo mata ai yana tafiya har ya wuce Kaduna Allah yayi masa rasuwa. Sosai hankalin Hawwa ya tashi ganin yadda INdo ta kafeta da ido hakan ya bata tsoro tayi saurin matsawa baya INdo ta bita cikin tashin hankali Hawwa tace. "Aunty Humairah Lafiya? Please wannan kallon fa..?!" A hankali INdo tasa hannu ta rungume Hawwa cikin rawar murya tace. "Yaya Hawwa kema sokike Yaya Abubakar ya mutu? Yanzu na buga mai waya wani ya d'auka yace min me wayar ya mutu ashe kema sokike ya mutu? 'Dazu ni narakasu mota suka shiga shida malam Sadeeq amma meyasa kike son yayanki ya mutu? Kinga yana sona dayawa d'azu fa har cemin yayi yana son duk wani mesona kuma zai sani a makarantar abuja..." "Kiyi hak'uri aunty Humairah nima inason Yaya Habu amma Allah yafimu sonshi shi yasa yayi hatsari..." Hawwa ta fad'a tana kuma sakin kuka, da sauri INdo ta hankad'a Hawwa baya iya k'arfinta jikake gam..! ta bugu da kujera cikin kukan bak'in cikin maganarta yasa INdo cewa. "Daga yin bikin mu shine zaki mana addu'ar ya mutu sabida bakya sonmu, toh insha Allahu sai Isyaku ya riga dacta mijina mutuwa fatanki ya biki, ance miki Garba ne ya mutu shine zaki zo kice Yaya Abubakar ne dan bak'in ciki..." Umma ce tayi saurin toshewa INdo baki cikin rufewar ido ta fara tureta domin ta baya ta rik'ota ta kuma toshe mata. Cikin kwantar da murya Umma kishiyar Maman su Sadeeq take mata magana a hankali. "Kinga Aisha kiyi shiru kinga mutane sun fara cika gidan yi hak'uri taho muje ki zauna kinji 'yar albarka." Tana nishi Umma taja ta still bata dena yiwa Hawwa kallon banza ba duk kuwa da cewar ta girmeta nesa ba kusa ba amma cewar Abubakar d'inta ya mutu shine ya d'arsa wata k'azamar kiyayya a zuciyar INdo. Fateema ce ta fito idanunta jawur ta kama hannunta suka koma cikin d'akin Mama, suna zama amma sai mita INdo takeyi Mama ta shigo ta kalleta tare da cewa. "Aisha kidinga hakuri kinji ko?" INdo tace "Toh Mama ki gaya mata bana son wasan mutuwa." "Toh zan gaya mata tashi muje ki wanke fuskarki da sabulu." Babu musu ta mik'e suka shiga bathroom saida ta gama wankewa sannan Mama ta kamo hannunta suka wuce, d'akin Abba suka shiga yana zaune yayi shiru yana bud'e likkafani gefe turare ne a kusa dashi suka shiga bayan Mama tayi sallama. Sake gaisawa suka yi da INdo sannan Abba ya kalleta tsawon lokaci ya kasa cewa komai, can dai ya nisa yace. "Aisha ke musulmace ko?!" 'Dan murmushi tayi alamar kunya tana sunkuyar dakai tace, "Eh Abba." "Alhamdulillahi ina son sanar dake Abubakar dai Allah ne ya bani shi, nina raineshi tundaga zanin goyo har girmansa da temakwon Allah, bayan ya girma ya mallaki hankalinsa shida d'an uwansa suka d'auke min duk wani nauyi nasu dana k'annansu, kafin ya aureki ya nemi auran wata yarinya Allah ya k'adarta beyi ba sai dake, toh Allahn daya baki Abubakar Aisha ya k'ar6i abinsa domin yanzu haka suna hanya za'a kawo gawarsa ina son ki daur...." Bek'arasa ba yaji ta fashe da kuka, kusa dashi ta rarrafo tare da rik'o Hannunsa tana jijigawa tana fad'in. "Abba... Abba wallahi ba dacta bane, ba shine ya mutu ba shi yatafi abuja k'ila dai malam Sadeeq ne, dan Allah Abba karku ce haka wallahi yace zai dawo ya tafi dani can garan..." Mama Abba ya kalla alamar tazo ta zanye ta, tana zuwa INdo ta juya kanta tare da rik'o hannunta itama tana cigaba da magana tana basu rabarin abinda yace zai yi mata nan gaba sai kawai itama Maman ta fashe da kuka Abba ya fara mata fad'a amma ina ta kasa yin shiru bare ta bawa INdon. "Kutashi kuje yanzu suna hanya zasu kawo shi, karku sake kubarta tafita ko'ina kinajina...?" Mama ta kad'a kai tare dajan hannun INdo suka shiga gidan sai ihu take mutane na kallonta cikin tsananin tausayawa. Tana shiga ciki ta zu6e ak'asa jikinta sai rawa yakeyi aka rufa a kanta kowa sai nemar mata d'auki yake ta zame jikinta daga na wata mata tana kallon Matan tace. "Sani zantafi." Umma ta rik'ota itada Fateema ta fara tirje musu dama INdo yaya lafiyar kura, dacta ne yasanta ya kuma san yadda zai biyo mata gashi babushi dan haka abin nata ya kuma yawa. Kullesu akayi a d'aki babu me fitowa suna jiyo kukanta har aka dawo daga d'akko gawar Abubakar, d'akinsu aka kaishi Sadeeq tamkar wani zararre fuskarsa fal hawaye idanunsa sunyi luhu-luhu tamkar kurji ya fito ya shiga cikin gida yana neman Mama. Da kyar ya iya tambayarta zani ta mik'e ta bud'e d'akin, suka shiga. Gaidashi mutanan d'akin suke suna mai gaisuwa, yana furta "Alhamdulillah." INdo tayi zumbar ta mik'e daga ruk'on da Zulaihat tayi mata, lokacin Mama ta mik'a mai zannin ya k'a6a kawai yaji INdo ta mak'aleshi katak'am tamkar ba rik'on mace ba tana kuka tana cewa. "Dacta ka dawoko? Nasan dama bazaka barni ba dan Allah da manzansa kace min Malam Sadeeq ne ya mutu ba kaiba, wallahi kaga zanyi kwalliyar da kace irinta d'azu, mu koma gidanmu nan kana da mak'iya ciki harda Abba duk fatan mutuwa suke ma..." "Aisha sakar ni please." Sadeeq ya fad'a yana 6an6areta daga jikinsa amma tamkar mutum biyu ne suka rik'esa, ya rasa dalilin dayasa takeja masa mugayan alkaba'i tun suna makaranta nan fa su Mama suka k'arasa suna nuna mata bashi bane amma tak'i sakinsa cewa take. "Duk inda zahi zan bihi wata k'ila akwai masu bibiyarsa basa sonshi toni ina sonsa." Janta yayi ganin ta mak'ale suka k'arasa bakin gado ya zaune tare da nunawa Fateema alamar tazo ta zauna kusa dashi. Tana zuwa INdo ta kare shi alamar karta ta6ashi Fateema ta toshe baki kuka na shirin kwace mata, haskilowa kawai takeyi tasan da shi ya rasu k'ila da tuni itace a cikin wannan yanayin da INdo take ciki. Kabeer ne ya shigo ya kar6i zanin domin sam INdo tak'i sakin Sadeeq, Mama kuwa so take ta 6an6areta domin tasan hankan ba dacewa bane kuma INdo tashiga cikin takaba hakan yasa ta fara sanya ta cikin dokokin da musulinci ya tanadarwa ga duk macen da mijinta ya rasu... *HAJJA CE*👈 [7/31, 5:13 PM] Aisha Galadima: *⚗⚗MUSAYAR ZUCIYA...⚗⚗* ♥♥ ♥ A true life story Na *K.A.S Precious Hajja ce*👈 *HASKE WRITER'S ASSOCIATION*💡 (Home of expert & perfect writer's) *VOTE me on wattpad @Hajjac* *DEDICTEED TO:* Sanah Isma'il Matazu Page *24* Koda sukaje kauyan Sani bak'aramin mamaki Fateema tayi ba da ganin gidan su INdo da kuma kauyan da suke, lallai Allah ya d'aukakata daya aura mata Abubakar har kuma tashiga wannan uban gidan wanda yafi nata komai da komai. Basu jima ba Sadeeq yace zasu koma ya bada dubu ashirin Inna da malam Hamza suka dinga yi mai godiya amma INdo fateema kawai tayiwa sallama ta koma gida 'yan garin suka cigaba da zuwar musu gaisuwa. Rayuwa gaba d'aya ta sauyawa INdo komai yayi zafi tunda ta dawo kauyan Sani komai nata ya canza, tana takaba a gidan su kamar yadda malam Hamza ya buk'ata sai dai itace inzata bayan gida sai abata sanda da wuk'a wai ta tafi da ita ko idan zatayi bacci toh ruwanta a buta da wuka wai mijinta yana biye da ita duk da cewar ba'a gidansa takeba. Sannan ta dinga tafiya a hankali karya tad'iyeta. wayace haka ake zaman takaba?wannan ba musulinci ya koyar dashi ba kawai mutanene suka maidashi al'ada har hakan ya fara zama kamar ibada. Satin INdo biyu a gida lokacin sati uku kenan da rasuwar Abubakar su Mama sukaje garin domin ita sam hankalinta ya kasa kwanciya, a zaure suka tarar dasu INdo suna tsinkar zogale harta fara komawa kalarta ta dah gashi dai jikinta da kaya masu kyau amma babu tsafta tunda ta dawo sau biyu tayi wanka wai ai duk cikin takaba ne. su Hawwah suka dinga kallonta cikin tsananin mamaki ita kuwa ta kasa 6oye farin cikinta da ganinsu. Bayan sun gaggaisa ne Mama ta kasa yin shiru ta kalli INdo dake tsakiyarsu Haleema tace. "Aisha ya naganki haka?duk kinyi wani iri anya kina wanka da kula da lafiyar jikin ki?!" Cikin rashin damuwa tare INdo tace. "Ai Mama nida nake takaba ai ance ba'a wanka sai dai a sati sau d'aya shi yasa ma banayi..." "Subahanallahi inji waye ya gaya miki haka?" INdo tace "Su Inna ne." Inna nacan tana k'ok'arin had'a dambu ta samu tabasu suci Mama tace. "Zonan Aisha na shiga uku ba haka ake yi ba a musulunci, ba haka qur'ani ya gaya mana ba." Tashi INdo tayi zuwa kusa da Mama ta zauna Mama na kallonta cikin tsananin tausayawa ta janyo ta jikinta tace. "Mecece Takaba Aisha?!" INdo tayi shiru sai faman wulk'ita idanuwa takeyi Mama tace. "Aisha Takaba dai itace Zaman da mace zatayi bayan rasuwar megidanta na wad'ansu kwanaki sanannu a cikin gidanta batare da tayi ado da kwalliya ba, ba kuma data kuma yin wani auren ba, ko sanya dukkan abinda zai ja hankalin wani a jikinta ba na tufafi ko kayan k'arau. Aanan Takaba ta sha babban da Iddar saki, shi yasa naso a barki a can domin d'an zaman da kikayi a gidan mu na gano cewar kinada gyara a cikin rayuwarki. Banda iyayanki sun kafe kancewar gara kitafi babu me zuwa ya zauna dake a cikin gidanki sannan kowa yasan mijinki ya rasu gashi idan kikaga Sadeeq wani tashin hankalin ne da bazan bari ba wallahi yanzu gashi kinzo nan sun k'ara dilmiyar dake cikin wani duhun kan. Wallahi mahaifinki gaddama garesa Aisha ba yadda ba'ayi dashi ya barki ba yace dasun dawo bakwai za'a tafi dake sabida baya son abinda kikewa Sadeeq. Shin kinsan Gwargwadon kwanakin Takaba a musulunci Aisha?" INdo ta girgiza kai alamar a'a Mama ta d'ago ta daga jikinta tace. "Alokacin da mutun ya rasu, to zai bar iyalin shi ne a d'ayan hali guda biyu, kodai ta zama tanada Juna biyu ko kuma bata da shi. Idan bata da juna biyu to Takabarta itace tayi Wata hud'u da kwanaki goma Kamar yadda Allah yace cikin Suratul-Bak'ara _Kumma dukkanin mazan dake rasuwa daga cikin ku subar matayan su, to matan zasu zauna wata hud'u da kwana goma aya ta d'ari biyu da talatin da hud'u 234..._ To amma idan ya rasu ya barta da juna biyu a wannan lokacin k'arshen Takabarta shine ta sauk'e abinda take dauk'e da shi koda kuwa ranar da ya rasu ne ma'ana ta haihu ko tayi 6arin cikin. Misali ya rasu 10:00am na safe ita kuma ta haihu 10:05 na safiyar, shi k'enan ta kammala takabarta, idan wani ya gani yace yana so aka d'aura aure 2:30 na ranar aure ya d'auru _(ana k'ar6ar gaisuwa ana d'aurin aure)_ Dalili kuwa shi ne. fad'in Allah (s.w. a) a cikin Suratut-Talak aya ta 4 _Kuma dukkanin mata masu juna biyu to lokacinsu shine su sauk'e abinda suke d'auk'e dashi_ da kuma Hadisin Subai'a Al-aslamiyyah, Ita ta kasance tana auran Sa'ad Dan Khaulah, shi kuma ya fito ne daga gidan Amir d'an Lu'ayy, yana daga cikin wad'an da suka halarci yak'in Badar, sai ya rasu yabarta a halin bankwana tana da juna biyu, bata ko jima ba bayan rasuwar shi saita haihu, a lokacin data kamma biki sai tai kwalliya, sai Abu-Sanabil Dan Ba'akk yazo wurinta, shi kuma ya fitone daga gidan Abduddar, sai yace da ita Lafiya naga kin cancara ado haka, ko kina son ki aure ne? Na rantse da Allah lokacin auranki bai yi ba, harsai kin yi wata hud'u da kwana goma. Sai Subai'a tace Yayinda ya fad'a min haka maraice na yi sai na tattara kayana naje wurin Ma'aikin Allah tsira da amincin Allah su tabbata a gareshi, na tambaye shi hakan, sai ya ban amsa da cewa ai na kamala Takabata tun lokacin dana haihu, ya ban dama da inyi aure a duk lokacin da naga dama. Yanzu ke Aisha kina da ciki?!" INdo ta kalli Yayya Hawwah kafin ta maida idonta kan Mama tace "Wallahi ban sani ba nima." Mama ta sake kallonta sannan tace. "Kinyi al'ada sanda kika dawo?!" INdo ta sunkuyar da kai sannan tace, "Ai yanzu ma haka inayi yau kwanana biyu kenan." "Hazbunallahu wani'imal wak'il, yanzu duk da kina wannan jinin Aisha bakya wanka?!" INdo tayi shiru jin yadda Mama tayi magana da alama abin mamaki ya bata da haushi ita kuma ya zatayi tunda ance mata haka akeyi. Inna ce ta shigo tana tayi musu sanna tare da kawo musu ruwa a kwanan shin ruwan malam Hamza, tsabtar kyawun kwanon da yadda ruwan ciki yake garai-garai abin sha'awa shine ya sanya su Haleema shan ruwan gidan. Zama Inna tayi suka sake gaisawa Mama tayi gyaran murya bayan tace su Haleema su fita, suna fita tayi murmshi tare da cewa. "Dama munzo ne mu gaida ku sannan zamu tafi da Aisha za'ayi mata wani gwajin ciki sabida shi marigayi yace yasa mata wani abu wanda koda tana da ciki toh bazata dena jinin al'adaba toh yanzu shine zamuje a duba agani kar abar mata abu ba'a saniba ko yana amfani nan da kwana biyu za'a dawo da ita kinsan likitocin nan da k'ak'ale." Mama ta kifa Inna domin yanzu so take ta tafi da INdo can. cikin rashin damuwa Inna tace "Allah sarki ai babu komai an zama d'aya bari na aika a k'ira malam dama shine ai ke hanawa da yaji yadda takeyi idan taga shi d'an uwan marigayin." Fitowa tayi ta lek'a waje ta samu yaro yaje ya k'ira Malam Hamza a gurin sana'ar Sa. Tare da ila suka dawo tunda yaga mota yasan bak'i sukayi yana shiga kuwa Inna tace Maman marigayi ce tazo, d'akin ya shiga suka gaisa da Mama Inna kuma ta kawo mata dambu ta kaiwa su INdo ma. A nan Mama ta kuma tsara malam Hamza yayi jim sannan kamar bazai yadda ba sai kuma yayi murmushi yace. "Toh ai dama ni hajiya dalilin daya sa na kafe kan cewar saita dawo nan, gani nayi yadda shi Saddiqu suke tsananin kama dashi marigayin. Sannan tun a gurin gaisuwar naji ana zance ta fara rik'esa tana cewa be mutu ba harma sun fara samun sa6ani itada Saddiqun wannan dalilin yasa nace dole abani ita mu dawo nan zaman lafiya hajiya ai yafi zama d'an sarki. Amma yanzu tunda akwai wani dalili wanda kuma kune kuke da hakk'i akai toh saita shirya ku tafi idan an kammala yi mata sai a dawo da ita ai duk an zama guda.." Wani farin ciki ya lullu6e Mama sai ta share hawaye gani takeyi tamkar Abubakar d'in take yiwa a zahiri. Malam Hamza ya dinga bata hak'uri kafin ya tashi ya fita, gurin su INdo yaje yace ta shirya zasu tafi da ita. Wanka Mama tace tayi sannan tayi tasa kaya Mama ta girgiza kai domin duk kayan na kwalliya ne babu wanda aka ce na takaba ne dole idan sunje tasa a dinka mata wasu marasa style. Babu wanda yasani don Mama tace kar a fad'awa kowa kawai idan an tambaya tana Ina suce tana gidan su marigayi amma karsu sanar da kowa akwai abinda za'ayiwa INdo suka tafi cikin farin ciki da fatan alkairi. ***** Tunda suka maida ita Mama ta dakatar da Sadeeq zuwa gidan tace koda itace batada lafiya bata yadda ya shigo ba bare hakan nan. Haka kuka Mama ta cigaba da kula da INdo har aka yi arba'in d'in marigayi Abubakar sannu a hankali kuma Mama tana bibiyar al'amranta na addini tana gyara mata sannan tana k'ara nusar da ita abubuwa wad'anda mafi akasari suke k'ara tunawa INdo mijinta soyayyarsa kuwa bata ta6ajin ta kankare koda d'igo d'aya ne, bata komai sai dai taci tasha tayi bacci, idan kuma su Haleema na nan sai suyi hira d'an turancin da suke yi jefi-jefi itama ta d'an fara tsintar k'ananun tana had'awa da wanda Dr yake yi mata sai dai dakyar take iya rik'ewa dan sai tayi ta rik'e kalma d'aya a kwana biyu ko uku sannan take sake fahimtar wata word d'in. Kusan kullum sai Malam Hamza ya bugo musu waya tunda suka zo sadakar arba'in ya kar6i number abban su Sadeeq kusan kullum sai ya bugo musu yaji wai ko an cire mata abun sai suce a'a likitocin sun k'ara musu kwanaki da haka har INdo tayi watannin takabar ta wanda har lokacin Sadeeq baya shiga cikin gidan su dan ma Allah ya temake sa yana tafiya k'wara state dan wannan tafiyar tasa da Fateema sukayi sabida yana shan wahala. Ana sauran kwana biyu INdo ta kammala takaba su Sadeeq suka dawo, Fateema ce kawai taje gidan shi kuma su Mama suka fita parking space suka gaisa ya juya ya tafi. Ranar da INdo ta kammala takaba Abba ya k'ira Sadeeq yaje ya kaisa Sumaila suna zuwa ya samu malam Hamza bayan gaisuwa Sadeeq na mota a zaune ya bugawa Fateema waya suna hirar soyayyar su dan haka suke tamkar zasu cinye junansu Abba ya kalli malam Hamza yace. "Toh malam Abubakar dai Allah ya d'auki rayuwarsa a lokacin da yake tunanin ya fara rayuwa, ya tafi yabar matarsa yarinya d'anya yau gashi Allah yasa ta kammala takabarta kamar yadda addini ya tanadar. A zahirin gaskiya ba wani abu da marigayi ya sanyawa Aisha a jikinta, me d'akina ce taga bazata iya barin muku Aishan ba hakan yasa tayi muku dabara kuka bata ita mu kuma duk muka had'e muku kai muka nuna cewar eh lallai haka ne abinda ta fad'a." Malam Hamza yayi murmushi tare da cewa. "Ai munyi mamaki har muna tunanin k'ila abin k'in fita yayi ashe soyayya ce tasa kukayi hakan ai bakomi alhaji mune da godiya da baku nuna kyama a garemu ba, Habubakar shine sila hakan yasa bazan gajiya dayi masa addu'ar samun ni'ima a cikin makwancinsa ba, alhaji Allah yajik'ansa yayi masa rahama mun gode madallah." "Ba komai malam Aisha ma ai 'yata ce, sannan kuma babban abinda ke tafe dani shine. Kaf 'yan uwana da masu d'akina suna tausayawa Aisha, yarinya ce d'anya yau gashi Allah ya jarabce ta idan aka barta zata Shiga layin zawarci, sun had'u sun had'e kai wajan ganin bazasu iya bari matar d'ansu d'an uwansu abokinsu ta zauna a haka ba suna ganin yi mata hakan kamar basu rufawa Abubakar asiri ba hakan yasa ko wannen su yazo min da k'ok'an barar su na cewar mezai hana a mayeta da abokin haihuwar sa, ma'ana mu had'asu aure da Sadeeq domin rufin asirin mu gabaki d'aya sannan munsan Abubakar zai yi alfahari da wannan abun." Malam Hamza yayi shiru kafin yaje ya k'ira Inna ya kuma k'ira amininsa malam kallah suka zauna, Abba ya kuma maimaita musu zancen auran INdo da Sadeeq Inna dai bata ce komai ba tace sune maza masu d'aura aure dan haka ita addu'a ce kawai tata. Bayan Inna ta koma gida malam Hamza ya amince wasu mutanan suka zo a gurin aka d'aura auran INdo da Sadeeq Abba ya bada sadaki dubu ashirin Sadeeq yana mota a zaune duk wainar da aka toya besani ba har Abba yayi sallama da mutanan garin ya shiga mota Sadeeq d'in ya ajiye wayar suka tafi... #MZ #Fan's #luv-all *HAJJA CE*👈 [7/31, 5:13 PM] Aisha Galadima: *⚗⚗MUSAYAR ZUCIYA...⚗⚗* ♥♥ ♥ A true life story Na *K.A.S Precious Hajja ce*👈 *HASKE WRITER'S ASSOCIATION*💡 (Home of expert & perfect writer's) *VOTE me on wattpad @Hajjac* *DEDICTEED TO:* Sanah Isma'il Matazu Page *25* Har sukaje gida Abba be sanar da Sadeeq ba, suna zuwa Abba ya shiga gida shi kuma Sadeeq daya k'agu yaje gida ya juya kan motar ya tafi. Abba na zuwa fuskarsa cike da fara'a ya cewa su Umma. "Toh hajiya A'i an d'aura aure yau." "Alhamdulillah Allah ya sanya musu albarka ya kauda fitina ya basu zaman lafiya." Cewar Umma nan da nan fa gida ya cika da murna INdo kuwa bacci take a lokacin sai bayan da ta farka ne Mama tace. "Aisha jeki wanka kizo kuje gyaran kai." Da sauri INdo ta mik'e cike da murna domin tunda ta dawo gidan bata sake koda lek'awa k'ofar gida ba, sam sun hanata ko unguwa Mama zasu sai ta kafa mata doka akan idan ta kuskura ta lek'a waje, yau gashi zata fita kusan kwananta d'ari da takwas raban da ta kalli waje bare taga abinda yake wakana. Ta yi kyau tayi haske fatar jikinta tayi luf-luf sannan tayi k'iba da yake hankalinta a kwance yake suna kula da ita sosai dan ko 'ya'yan gidan basu kaita jin dad'i ba. Wanka tayi tana fitowa taga saban d'inki an d'akko mata a can gidan Abubakar da takalmi da jaka da mayafi su d'ankune sark'a da kayan kwalliyar su Haleema. Zama tayi tana kallon kayan tare da shafa jakar da takalmin sai hawaye a fili tace. "Allah sarki dacta kai ka saimin su.." Tashi tayi tasa kayan sai ga Mama ta shigo cikin wasa tamkar ba suruka ba tace. "Toh wa kika tambaya da kika d'auka kika sa? Idan kuma nawa nefa..?!" Dariya INdo tayi tana rufe baki tace, "Ai Mama ina ganin jakar na gane su, lokacin da zai kaimu gidan abokanansa da nad'akko zan rataya yace min basu yi match da kaya na ba na ajiye ta." "Allah sarki Abubakar Allah yayi masa rahama Allah yayi baxaku yi tsawon kwanaki tare ba." Cewar Mama tana d'akko mata humra ta ajiye mata a kusa da kayan tana cewa. "Daga yau zaki iya sanya komai Aisha sai dai zaki ci gaba dayin abubuwa irinna matan aure domin yanzu kema Matar aure ce." Sam INdo bata gano inda zancen Mama ya nufa ba, a tunaninta tunda ta ta6a aure toh zata ci gaba da suturce jikinta da kuma d'ora mayafi aka. Tana gama shiryawa Mama ta bata kud'in gyaran kai tasa suka tafi dasu Haleema. Lokacin da ta fara zura k'afarta a waje ji tayi tamkar yau aka haifeta. Wata ajiyar Zuciya ta sauk'e tare da kallon ko'ina na wajan taga mutane kowa yana harkar gabansa, wasu kuma da suka santa suna sake yi mata gaisuwa tana amsa musu har suka kai bakin titi Haleema ta tare musu napep suka shiga. Shagon saloon suka shiga sun d'an jima sannan suka fito suka dawo gida. Da dare bayan Abba ya dawo ya k'ira Sadeeq sannan ya k'ira INdo, Mama da Umma duk suna zaune a d'akin. Cikin muryar ta med'an k'arad'i tayi sallama tare da shiga ta zauna tana gaida Abba. A hankali Sadeeq ya d'ago ya kalleta sannan ya kawar da kai cikin ransa yana tambayar dama tana da ladabi ko kuwa har lokacin mutuwar mijinta na jikinta ta dai kusa tafiya shima ya samu 'yancin shiga gidan ubansa. Abba ne ya k'ira sunansa ya amsa tare da kallonsa abban yace. "Toh Sadeeq kamar yadda ka sani tagwai d'inka Allah yayi masa rasuwa ya bar matarsa, yau kuma Allah ya nuna mana cikar wa'adin takabar ta kamar yadda addini ya d'ora mata. Sadeeq kaine mutum na farko daya kamata ya rufawa matar d'an uwanka asiri ka dubi halin da zata shiga idan ta koma garin su ka kuma dubi k'ank'antar da tayi a matsayin bazawara bawai munaja da ikon Allah bane a'a duba da yadda rayuwarta zata fad'a yasa muka yanke wani hukunci akai." "Babu komai Abba ni dama tuni nayi alk'awarin zan dinga tura mata kud'i sannan zan dinga yi mata abinda take buk'ata idan har befi k'arfina ba dama jira nake ta kammala iddar sai na tambaye ta abinda yak'e matsalarta." Sadeeq ya fad'a ba tare da ya kawo komai ba dan sam beyi tunanin wani aure tsakaninsa da ita ba, Fateema yake so kuma ita ya aura baya tunanin zai yi *MUSAYAR ZUCIYA* da watanta nan gaba bare kuma nan kusa daga yin aure wata biyar. "Toh Sadeeq ai wannan abubuwan daka fad'a koni zan iya yi mata shi, mu yanzu fatan mu ka rufa mata asiri a matsayin ta na mace me rauni kuma matashiya domin a d'azu da ka kaini Sumaila k'auyan su naje ne mun d'aura muku aure dakai da ita ka maye gurbin d'an uwanka...!" A matuk'ar razana Sadeeq ya zaro idanuwa yana kallan Abban shi, zuciyar sace take rawa jikinsa na tsuma ya kalleshi yace. "Abba wani auran zan kuma yi? Abba ko wata biyar ban cikasa ba ace na kuma yin aure? Tayaya zan iya zama da mata biyu Abba bayan yanzu nayi d'ayan? Abba matar twin d'in zan aura? Ya akayi mutuwa tayi min haka..." "Kai ya isa haka karkayi min sakarci kaji ko? Idan baka aureta ba ya kakeso tayi bayan tana buk'atar temako da kuma mai lallashi da tausayawa a gareta...?!" "Amma Abba yau yau d'innan fa tayi takaba amma ace ayau za'a aura mana aure ko fuskanta juna bamuyi ba? Abba ya Fateema zataji wannan labarin." Ya fad'a tamkar wani maraya Abba ya wurga mai harara cikin 6acin rai yace, "Da kuma ace kaine ka rasu aka ce Abubakar ya auri Fateeman zakaji dad'i ko kafison ta tafi ta auri wani bare..?!" "Wallahi Abba gara ta auri bare haba-haba sai kace jira, dan Allah Abba kuyi tunani ni wallahi..." Bek'arasa ba Abba yayi saurin katse sa ta hanyar cewa. "Toh shikenan sakarta ni sai na aureta shikenan hakan yayi maka.?!" Cikin tashin Hankali Sadeeq ya kalli mahaifinsa sai zuba uban gumi yake baki na rawa yace. "Innalillahi wa'inna'ilaihir raji'un Abba ai babu aure tsakanin ku gara nid'in." "A'ah aini tausayinta nakeji Sadeeq kuma abinda zanyiwa Abubakar kenan yasan nayi mai kara ka sake ta sai na aureta ko kuma uncle d'inku Ahmad." "A'a Abba dan Allah ka rufa mana asiri na kar6i auran Allah yajik'an m twinnie yasa can tafiye masa nan." Duk suka amsa da amin banda INdo wadda tunda taji maganar da akeyi tayi kicin-kicin zuciyarta banda bugawa babu abinda takeyi wani rad'ad'i na shigarta. Abba ya maida hankali wajan ta ya kalleta cikin kulawa yace. "Aisha muna fatan bamuyi miki shishigi a cikin rayuwarki ba, muna fatan zaki yadda da auran Sadeeq gashi nan komai nashi iri d'aya ne dana marigayi..." Da sauri INdo tace "A'ah Abba wallahi ba halinsu d'aya ba koda can kafin mu saba." Abba ya kalli Mama itama shid'in take kallo sannan tace. "Aisha ai shima Sadeeq zai miki abinda marigayi yayi miki kiyi hakuri idan kuma bakya sonshi shikenan ai ke yanzu babu batun yi miki auran dole za6i gareki a wannan karan ma. Dama munyi haka ne dan karki shiga damuwa ko da idan kinga Sadeeq d'in." Shiru tayi batace komai ba sukayi-sukayi tayi magana amma tayi shiru Umma tace. "Toh da alama ta yadda Allah ya bada zaman lafiya." Tashi Sadeeq yayi ya fita Mama da INdo suma suka fita aka bar Umma kasan cewar itace da girki ranar. Dakyar ya iya kai kansa gida, lokacin daya shiga Fateema na kwalliya cikin bedroom taji shigowarsa amma bata ga ya shigo d'akin ba, shi kuwa guri ya samu a falo ya zauna kan kujera tare da dafe k'irji kanshi na barazanar fashewa ya tarwatse. Fateema ce ta fito cikin shirin bacci tayi kyau ta kuma fari kai da kaganta kasan tana cikin kwanciyar hankali, k'arasawa tayi kusa dashi ta d'are kan cinyarsa tana k'ok'arin d'ago mai kai. Janyo ta yayi jikinsa da k'arfi tare da sanya ta a k'irjinsa ya matseta da hannuwansa tamkar zai maida ita ciki ita kanta dakyar take numfashi zuciyar ta cike da mamakin yadda taganshi. "Wayyo Allah baby zaka karya ni." Ta fad'a tana k'ok'arin kwatar kanta sabida ba k'aramin azaba takesha a matsar ba. A hankali ya sassauta mata rik'on dayayi mata cikin sanyin murya Fateema ta kallesa tace. "Baby wai meyake damunka, haka kashigo fa ba sallama kuma naga duk jikinka a sanyaye meya faru..?!" "Bakomai kinci abinci dai ko?!" Ya tambaya yana shafar cikinta, kad'a kai tayi tana kallon shi ya lumshe idanuwa tare da kwantota jikinsa yace. "Toh why?!" "Baby kasan dai bana iya ci harsai kana nan, meyasa yanzu kake tambaya na...?!" "Kinsan ai bana son kina zama da yinwa, kinga gobe ina da lecture 9 to 11 kuma gashi banajin dad'in jikina ya zanyi ne.." Fuskar sa ta tallafo sukayi kallon cikin ido ta sakar masa murmushi tana shafar gashin dake ha6arsa tace. "Yanzu ai lokaci bek'ure ba goma da rabi saura minti uku kayiwa class captain waya kace musu bazaka samu damar zuwa ba suyi hakuri zaka samu wani time d'in sai kuyi musu amfani dashi..." "Ai kuma baby ban musu lectures bafa tunda aka koma gashi har an fara tambaya na exam questions, zanje ko abu d'aya ne nayi musu tashi muje kici abinci." "Inci abinci ko dai muci abinci?!" Ta tambayesa tana sake lafewa a jikinsa, suna zama yana cewa. "Kinsan Abba neya k'irani so munci abinci tare dashi." 'Dan hararasa tayi tare da cewa "Ai kasan dai nima nawa yana jiranka dan haka sai kaci babu wani batun kunci da Abba ko zakayi amai kuwa." Shi sam yarasa ma mezai yi yinwar ma bajinta yake yi ba shi yasa yace mata haka amma dan karta shiga damuwa sai yace. "Toh baby na ya zanyi amma nasan yau babu abinda zan iya tabuk'awa." Shi dai dakyar ya samu yaci duk tunanin yadda zai 6ullo mata yake yi a cikin zuciyarsa, sai da ya tabbatar taci ta koshi sannan ta rakashi yayi wanka ta bashi sleeping gown ta maza yasa sannan suka bi lafiyar gado. Kamar yadda ya sabar mata koda bazai yi komai ba toh sai sunyi wasa haka yauma har sai da yaga ya kwantar da kanta kan k'irjinsa zata yi bacci ya bud'e baki dakyar ya k'ira sunanta. "Zarah..." Tayi jimmm jin yadda ya k'ira tsohon sunan da yake kiranta dashi tun suna saurayi da budurwa, can dai ta amsa mai tana shafar k'irjinsa shi kuma yana shafar himilin gashin kanta domin akwai suma yace. "For example nine na rasu ba Abubakar ba idan aka ce ki auresa zaki iya..?!" Ya k'arasa maganar yana d'an d'ago mata kai. Shiru tayi na tsawon lokaci tana tunanin abinda yasa shi yi mata wannan tambayar marar dad'in ji bare sauraro, sai da ya sake tambayar ta sannan ta numfasa dakyar tace. "Haba baby ya zaka min wannan tambayar tunda dai bakai ne ka rasun ba?" Yace "Eh so nake naji zaki yadda idan aka ce ki auri twinnie d'ina ya zakiyi." "Gaskiya bazan auresa ba haba ai bashi na aura ba." "Toh idan aka tursasa kifa ko aka aura miki shi ba tare da kin sani ba ya zajiyi..?!" "Ta6 d'i wallahi baby sai ya sakeni uhm'um ni dan Allah ka dena yin irin wannan tunanin please." Jikinsa ya sake janyo ta yana shafar bayanta, so yake ya sanar da ita yau basai taji a bakin wani ba amma ya rasa hanyar fad'ar ya dai daure yace. "Toh idan hakan ta faru tunda ni bakya sona mutu aka ce na auri Humairah ya zakiyi?!" "Bama zata yiwu ba sabida INdo bata sanka har agabana ta fad'a." Shiru suka yi na tsawon lokaci gashi dare ya tsala ko'ina yayi shiru sai k'arar gen d'insu kawai akeji. Numfasawa Sadeeq yayi tare da janyota yace. "Kiyi hakuri baby na yanzu dawowar da kikaga nayi Abba ne ya sanar da ni cewar an d'aura min aure da ita ni kaina ba..." Jiyayi ta mik'e zaune a razane daga ita sai bra domin rigar ta zame Fateema ta bishi da kallo hannunta dafe da k'irji ya kalleta bayan shima ya tashi zaune. Wata shegiyar harara take wurga mai cikin zafin rai ta fara magana jikinta na rawa. "Yanzu kana nufin har an d'aura muku aure?" Sadeeq ya d'aga mata Kai alamar eh yasa hannunsa ya janyo ta a hankali ta fad'a jikinsa ta saki kuka me ban tausayi ya fara lallashinta shi kansa ji yake tamkar yaje ya bindige INdo. Babu yadda zatayi ita kuma haka tata k'addarar take daga yin aure sai kishiya suna cikin more rayuwarsu. *** A 6angaran INdo kuwa wani uban nishi ta dinga saukewa duk iya k'ok'arin Mama na ta gaya mata matsalar ta sam tayi shiru tak'i yin magana har gari ya waye bata yiwa kowa magana ba Mama ta rasa dalili dan ta saki ranta yasa Mama cewa. "Aisha gobe za'a kaiki gida kije kiyi kwana biyu kafin Sadeeq d'in ya ware yadda zai yi." Sai a sannan INdo tayi magana tana dariya tace. "Toh Mama amma dai ba shine zai maida niba...?!" "Toh ai Aisha yanzu dai komai yana hannunsa sai abinda yace kiyi mai biyayya kedai anan zaki samu aljanna." Ba zato cikin subutar baki tace. "Ta6 d'ijam.." Mama ta kalleta cikin mamaki amma sai taga INdon na mutsu-mutsu da baki alamar magana take a ranta lallai yaran nan da alama zasu basu mugun mamaki sam basuyi zaton INdo zatak'i Sadeeq ba ganin yadda suke kammani da mijinta ba.... #MZ #Fan's #luv-all *HAJJA CE*👈 [7/31, 5:13 PM] Aisha Galadima: *⚗⚗MUSAYAR ZUCIYA...⚗⚗* ♥♥ ♥ A true life story Na *K.A.S Precious Hajja ce*👈 *HASKE WRITER'S ASSOCIATION*💡 (Home of expert & perfect writer's) *VOTE me on wattpad @Hajjac* *DEDICTEED TO:* Sanah Isma'il Matazu *A gaskiya ina alfahari daku masoya, comments d'in ku yana sani jin dad'i both wattpad & WhatsApp. Bazan iya lissafo sunayanku ba sai dai ina yiwa duk wata mai bibiyar labarin nan fatan alkaira Allah kuma yabar kauna da soyayya love you all*❤ Page *26* A 6angaran su Sadeeq kuwa dakyar ya iya fita lecture, itama Fateema bata fasa yi mai breakfast ba sai dai duk babu wanda ya iya ci. Yana tafiya Fateema ta shiga cikin d'aki taci kuka sannan ta d'auki wayarta ta k'ira Ummanta, tana d'agawa ta fashe da kuka hankalin Umma yayi matuk'ar tashi tana tambayar lafiya. "Kiyi shiru kiyi min magana dan sai kin min bayani sannan zansan matsalarki." Cewar Umman ta cikin lalla6ata dan ta gaya mata. Cikin kukan Fateema tace. "Umma Sadeeq ne ya k'ara aure jiya..." Tayi maganar muryarta na hard'ewa hankalin Umman ta ya tashi tace. "Fateema a ina yayi auran bako labari?" "Umma yazan yi matar d'an uwansa aka aura mai jiya shima be sani ba, sai da Abban su ya k'irasa ya gaya mishi." Ji tayi Umma ta sauk'e ajiyar Zuciya hankalin Fateema ya tashi tana cikin bargo amma wani irin mugun sanyi takeji yana ratsata, jita yi Umma na cewa. "Oho Allah sarki, Fateema toh karki damu kinga kema wannan kaddarar batak'i ta sauka a kanki ba, kiyi hakuri ki zauna ki taya mijinki zama da ita ba'a san abinda Allah ya shirya ba akan al'amarin. Ina son ki kwantar da hankalinki karki sake ki nuna masa cewar kina bak'in cikin wannan auran idan kikayi haka nan gaba kezakiji kunya sabida shirin na Allah ne dan da be d'auki Abubakar ba da hakan baxata faru ba, ki kankaro mana mutuncin mu ta hanyar k'ar6ar wannan auran cikin nuna farin ciki koda ba hakan bane a ranki." Wani irin kuka Fateema ta kuma fashewa dashi wanda da kyar ta iya yin sallama da Umman tata. Kuma k'udindinewa tayi a cikin bargo tana cigaba dayin abinta har zazzafan zazza6i ya sake rufar mata. Sadeeq kuwa yana kammala lecture ya fito daga school d'in, kai tsaye ya wuce gidansu Fateema ya samu ba kowa sai Umma. Shiga yayi har cikin falonta ya zauna suka gaisa cikin fara'a ba tare da ta nuna mai komai ba. Cike da ladabi Sadeeq yayi ma Umma bayanin yadda lamarin ya wakana sannan ya dad'a da nunawa Umma ta yiwa Fateema nasiha tare da tayashi bata hak'uri, Umma tayi murmushi tare da cewa. "Karka damu Sadeeq Allah ne yasan abinda ya shirya har akan ta faru, insha Allahu kuma zanyi mata nasiha kaima sai kayi hakuri kasan irin wannan lamarin sai mutum yana kawar dakai dan zakaga ban-banci d'abi'a akan ta baya da kuka yi." Sadeeq yana sunkuyar dakai yace, "Insha Allahu Umma na gode Allah ya k'ara girma." "Amin a gaida mutanan gidan ace muna yi musu Allah ya sanya alkairi." Batare daya amsa mata ba yayi tafiyarsa baya tunanin ma zai sake zuwa gidan harsai ya samu labarin cewar INdo bata gidan. A kwance ya tarar da ita ko gidan bata bud'e ba sai da ya sanya mukulli ya bud'e. K'arasawa yayi tare da yaye bargon da ta rufa dashi ya ta6a jikinta mai d'auke da zazzafan zazza6i nan da nan hankalinsa ya tashi ya hau gadon gabaki d'aya ya d'aga zuwa jikinsa yana k'ok'arin san su had'a ido amma tak'i bari hakan ya faru. "Baby na kinji jikinki kuwa? Meya sameki?!" Wani kukan ne ya sake zuwar mata cikin rawar murya tace mai. "Banajin dad'in jikina kaina ciwo yake." "Oya tashi muje asibiti Allah yasa ma nayi ajiya." 'Dan janye jikinta tayi ba tare da ta kallesa ba ta koma ta kwanta tana cewa... "Karka damu basai munje asibiti ba dan yanzu ma haka ciwon mara nakeji." "Wayyo Allah baby na bana son wannan abun wallahi, nida da yadda za'ayi ma da nasa an tsayar miki ki denayin sa." Shiru tayi mai batayi magana ba shi kuwa duk so yake yi ta dawo dai-dai yadda suke amma ina sai tashi yayi ya koma falo dan bazai juri ganin yadda take sharesa ba, ba kuma yason ya dinga 6ata mata rai. Yana zaune a falo yana transfer d'in kud'i a account d'in mutanen daya k'ar6i kaya yaji wayarsa na ruri, d'auka yayi yaga Mama sai da k'irjinsa ya buga. Addu'a ya fara yi Allah yasa kar tayi mai zancen INdo domin sam baya k'aunar yaji sa. "Hello Mama antashi lafiya?!" "Eh Alhamdulillahi tunda bakaga damar zuwa ba, mekakeyi yanzu?!" "Kiyi hakuri Mama bak'in zuwa nayi ba yanzun nan na dawo daga lecture, ina gida nazo?!" "Eh dama cewa zanyi ka shirya kazo kakai Aisha garinsu ta d'anyi musu kwana biyu kafin ka samar mata gurin zama." Had'e rai yayi tamkar a gaban Maman ransa na suya baya son kuma komawa garin nan duk da cewar sunyi zaman amana dashi amma a yanzu ga Fateema ba lafiya sannan ance yazo yakai INdo garinsu sabida kawai shi aka sakawa ido komai sai ace shi dama shi ya mutu ba Abubakar ba da duk ba'ayi mai wad'annan abubuwan ba. "Kayi shiru Sadeeq kona shirya tunda nina d'akkota sai na mayar da ita." Yaji Mama na fad'a cikin fad'a-fad'a. Lumshe idanuwa yayi tare da shafar sajan sa yace. "A'a Mama kiyi hakuri bari nayi wanka zanzo." "Toh shikenan kazo kowane lokaci ne sai ka kaita duk ka gama walagigin naka muna nan muna jiranka." Tana kammala fad'a ta katse k'iran shi kuma yabi fuskar wayar da kallo, shikam ya shiga uku wannan wace irin kaddara ce ta hau kansa. Ya kasa gane abinda Abubakar ya gani a gurinta har yaji yana sonta, ita ba ilimi ba sannan ba Kud'i ba, ba wani shegen kyau ne da itaba sai shashanci ga6untaka kauyanci da rashin wayewa duk ita kad'ai shikam a takaitashi da auranta da aka bashi. Tashi yayi cikin sanyin jiki ya shiga d'aki, fuskar fateema ya kalla sannan yaje ya shafa fuskar yana kallonta. A hankali ta bud'e sukayi ido hud'u yace. "Tashi kisha magani kici abinci zansa su Haleema suzo su tayaki zama Mama ta kirani wai zankai Aisha gidan su yanzu kinji.?!" K'irjin Fateema ya fara harbawa ganin tun yau sun fara raba abubuwa tsakaninsu, da kyar ta daure tace. "Toh sai kun dawo amma kabar su Haleema basai sunzo ba babu abinda zasu yi min." Magani ya d'akko ya fita kitchen ya d'akko ruwa sannan ya zauna kusa da ita, dakyar tasha maganin sannan ta kwanta shi kuma ya shiga cikin bathroom yayi wanka gaba d'aya ma besan abinda zaiyi ba akan INdo. Fitowa yayi d'aure da towel a k'ugunsa ya k'arasa wajan mirror duk Fateema na kallonsa a sace ta cikin bargo. Sai daya gama goge ruwan jikinsa sannan ya zauna kan stool yana shafa mai. Yana gamawa ya nufi wardrobe ya zaro wata shadda blueblack ya sanya tare da d'akko bak'ar hula zannah ya kafa kan goshi, ya sanya agogon hannu ya zura takalmi bak'i tare da feshe jikinsa da turare ya d'auki comb brush ya kwantar da gashin daya zagaye kyakyawan bakinsa. Duk abinda yake yine yayi amma da Fateema tasan inda zashi sai taji k'irjinta na harbawa zuciyarta na zafi wani bak'in kishi ya mamaye ciki da wajan zuciyarta bata san lokacin da hawaye suka zubo mata ba tayi saurin maida fuskarta cikin bargon ganin zai juyo. Sadeeq ya k'arasa gurinta bayan ya durk'usa saitin fuskarta ya kura mata ido. "Babyna karki dinga sanya ranki cikin damuwa, kece mace ta farko dana faraso na kuma fara aura na fara baiyana mata sirrina na kuma yadda da ita, ina so ki dinga alfahari da hakan kina cikin zuciyata bazan ta6a yadda wani ya 6ata miki rai ba ko ya gaya miki ba dad'i in kyalesa. Ke ko Aisha da aka aura min idan batayi miki biyayya ba sai na sa6a mata wallahi ke nine nace ina sonki ita kuma mutuwar twinnie d'inane yasa aka bani auranta karki dinga damuwa kinji ko.?!" Sai a lokacin Fateemah taji sanyi ko ba komai ya kwantar mata da hankali da dad'ad'an kalamansa masu zak'in zuma. Kallonsa tayi idanuwanta duk sunyi jah tsabar kuka sannan ya zuro hannu ta shafi fuskarsa tace. "Nagode da wannan matsayin daka bani, ka tashi kaje kaga da nisa Allah ya dawo min dakai lafiya, a gaidasu Mama." Murmushi yayi mata tare dakai bakinsa kan nata yayi kissing d'inshi sannan ya mik'e tsaye yana ce mata. "Amin babyna sai na dawo." Fita yayi ya shiga mota yabar gidan. Kai tsaye gidan Mama yayi, a k'ofar gate yayi parking sannan ya fito ta shiga gida cike da tak'ama dan yau jinsa yake tamkar akan iska. Yana shiga k'annansa suka hau gaidashi ya amsa musu sannan ya lek'a d'akin Umma ya tarar tana sallar azahar ya koma ya shiga d'akin Mama. Cike d'akin yake da k'amshin turaran humra Sadeeq ya bud'e hanci yana shak'a, tsaye yaga INdo ta gama d'aurin d'ankwali ya kalleta tare da jinjina kai. Idan besan asalin INdo ba da ace yau shine karo na farko daya fara ganinta toh bazai mata hausa ba dan babu abinda zai hanashi d'auka cewar batayi degree ba a boko. Sai dai kashhh shine yasanta yasan ko wacece a fannin dak'ik'anci da rashin son karatu tun batakai haka ba dan haka yana shiga gurin Mama ya nufa yana mai cire hular kansa. "Mama na ina wuni?!" "Lafiya lau Sadeeq na d'auka ma bazaka zo yanzu ba, ya gidan ya Matar taka?" Sadeeq ya koma bakin gado ya zauna yana cewa. "Haba Mama na isa ink'i zuwa, lafiya lau take tana gida ma batajin dad'i." Yayi maganar yana kuma karya k'arin hularsa. INdo kuwa ci kanka batace masa ba Mama na ganin ikon Allah taga wazai fara yiwa wani magana sai taga kowa yana harkar gabansa. Kasa yin shiru Mama tayi sai da tace. "Aisha wai bakiga Sadeeq bane, naga ko gaidashi bakiyi ba!" Ba kunya INdo tace, "Mama ai yace idan na sake ganinsa na kusala tom d'ina, har wawuya yace min a ranar." Baki bud'e Sadeeq ya kalleta, rabon daya ganta tun rasuwar Abubakar sai jiya da Abba ya had'asu sai kuma yanzu amma ji sharrin da tayi mai cikin jin haushin ta yace. "Karki rainawa mutane hankali yaushe na fad'a.?" Nan ma ba tsoro bare kunya tace. "Lokacin rasuwar marigayi sanda nazata bashine ya mutuba Ina murna na rik'eka ka tureni kace karna sake kulaka, a lokacin ne na tabbatar da cewa Kaine malam Sadeeq, shi yasa bazan gaida kaiba tunda kace haka." Tsaki yaja tare da maida hularsa kansa, gaba d'aya ma besan ya fad'a ba yasan dai lokacin ta bashi haushine. Lallai yarinyar nan akwaita da rik'o toh kar Allah yasa ta gaidashi sai me (so what). Mama ce ta kalleta cikin nuna mata martabar miji tace. "Aisha ya kamata ki ajiye komai daya wuce tsakaninki da Sadeeq, yanzu mijinki ne dole zaki mai biyayya kamar yadda musulinci ya gindaya. Yanzu ki gaida shi bana son wani tashin zance." Babu yadda zata yi domin a haka tana ganin k'ima da darajar Mama, cikin turo baki tace mai. "Ina wuni?!" Dan kar shima Mama tayi mai magana yasa shi amsawa a takaice yace. "K'alau." Mama ta jijiga kai tare da rik'e ha6arta, Sadeeq kawai zata jawa kunne domin shine miji kuma shine sama da INdo duk abinda ya d'orata akai shi zatayi ta kuma k'ara akan wanda take dashi zama tazo yak'i dad'i suji kunya amma zata bari sai ya dawo daga kaita tukunna. Tashi yayi ya fita bayan yace su sameshi a waje. Sosai sukayi sallama da mutanen gidan suna mata fatan sauka lafiya INdo na amsa musu. Gaba Haleema ta bud'e mata babu gaddama ta shiga shi kuma Sadeeq yaja motarsa suka wuce INdo sai dariya take tana jin dad'in yadda duk suke sonta. Tunda suka fara tafiya yake amsa waya duk ya cika mata kunne, hannu ta zuwa ta kunna redion motar dan ta riga ta iya Abubakar ya nuna mata sannan ta kunna A.c ta zuge glass d'in kusa da ita. Sadeeq ya sanya hannu ya kashe redion yana wayar sa itama ta kuma kunnawa tare da cewa. "Haba Malam Sadeeq kana wayarka mana ni kuma ina jin redio na bashi kenan ba." Wata muguwar harara ya watsa mata ta ta6e baki tare da juyawa tana kallon hanya. Abinda yake k'ona mata rai da turanci yake maganar sai Hausa da yake d'an cillawa. Wayarta ta d'akko wadda tun Abubakar ne daya sai mata ta fara d'aukar photo tana selfie style kala-kala ko kulata beyi ba harya gama wayar ya ajiye ta. Gajiya yayi kunnuwansa sun cika da k'arar camera ya warce wayar daga hannuta tare da cilla mata ita kan cinya yace. "Ke bana san kauyan ci fa." Kallansa tayi hannunta rik'e da ha6arta tana cewa..... *HAJJA CE*👈 [7/31, 5:13 PM] Aisha Galadima: *⚗⚗ MUSAYAR ZUCIYA...⚗⚗* ♥♥ ♥ A true life story Na *K.A.S Precious Hajja ce*👈 *HASKE WRITER'S ASSOCIATION*💡 (Home of expert & perfect writer's) *VOTE me on wattpad @Hajjac* *DEDICTEED TO:* Sanah Isma'il Matazu Page *27* "Malam Sadeeq kenan, ai da kasani ba yanzu ba." Shareta yayi ya nuna tamkar ma bejita ba ta juya tana kallonsa ta kuma d'aukar wayarta daya cillo mata. Madubin saitin kujerarta ta bud'e tana gyara fuskarta ya girgiza kai dan shi dama yasan da wahala yarinyar tayi hankali sabida babu arabi ba boko yaja tsaki har kusan sau uku sannan INdo ta kallesa tace. "Babu kyau fa." Yace "Ni zaki cewa babu kyau? Ko kin fini sanine da zaki cemin babu kyau?!" "Allah ya baka hakuri, cewa akayi idan kaji wani ko wata sunyi abinda ba kyau ka tuna masa, toni tuna maka nayi." "Karki i sake tuna min domin tun kafin kisan hakan nasani, ke karki sake yin magana har muje inda zan kai kina jina.?!" Bata sake kula shiba har sukaje danja masu tallar abubuwa suka dinga d'ago musu taga me alawar madara da sauri ta zaro d'ari biyu ta mik'a masa ji Sadeeq kawai yayi tana cewa. "Bani ta dika." Aikuwa ransa ya kuma mugun 6aci Allah-Allah yake kafin a gama mik'o mata ya figi motar amma danja batazo kansu ba harsai da aka bata tasa a jaka sannan aka basu hannu. Leda d'aya ta mik'a masa tace. "Malam Sadeeq bisimillah." "Banasha." Maidawa tayi cikin jaka ta bud'e leda d'aya tana sha har wani kunkuni takeyi irin na zak'in nan idan ya gauraye kunne. Wayarsa ya d'auka yasa earpiece tare da kiran layin Fateema, sai da ta kusa yankewa sannan yaji ta d'aga cikin sanyin murya tayi mai sallama. "Ohh babyna har yanzu jikin ne?!" Ya fad'a cike da damuwa, can 6arin Fateema tace. "A'ah kawai dai bacci nake, kun tafi ne?" "Eh muna hanya ma yanzu zan dawo insha Allah, amma ki tashi ko tea ne kisha zaki kuma samun relief." "Toh Allah ya kiyaye hanya a gaida min ita." Tana kaiwa nan yaji ta katse, ba haka yaso ba yaso suyi hira ta d'ebe mai kewa amma tariga ta kashe ya cire earpiece d'in yana cigaba da tuk'insa ba tare daya sake kallon koda inda take ba. "Malam Sadeeq dan Allah ka kar6a kasha, wallahi tayi dad'i madara ce zallah." Yayi shiru ta kuma cewa. "Inkaji dan Allah sha d'aya kaji." A fusace ya juya yana kallonta shi har lokacin be manta yanayin ta na baya ba cikin 6acin rai yace. "Wai dole sai na Shane? Idan dole ne toh sani insha dan Allah." Ya fad'a tare da d'an kallon gabansa kafin ya juyo yana dank'ara mata harara, d'aya ta d'akko da sauri ta danna mai ita a baki ya yi saurin furzar da ita a k'asa amma duk da haka sai da zak'in ya shiga ko'ina na cikin bakinsa ya samu gefen titi ya tsaya tare da nuna ta da yatsa yace. "Wallahi tallahi Aisha ki kiyayeni karkija wata rana na 6allaki yasin. Kinga ina shiga sha'aninki ne? Toh ki kuka da kanki duk rashin kunyarki a tafin hannuna take...!" Jan bakinta tayi ta tsuke bata sake cewa komai ba har suka shiga garin Sumaila, tana ganin barkono dama sund'an tsaya sabida ana bada hannu batare da tayi mai magana ba kawai yaji ta bud'e k'ofar ta fita tana cewa. "Bari na siyawa Inna barkono da gyad'a ko kwano d'aya-d'aya ne." Kafin ya harzuka yayi magana ta k'arasa wajan, Sadeeq ya kifa kansa a steering shi kam ya shiga uku wannan wace irin yarinya ce tana ganinsu a tsakiyar titi amma ta 6alle murfin motar ta fita. Idan ta dawo sai ya mareta gobe bazata sake yi mai makamancin haka ba. K'arasowa tayi wani yaro na biye da ita a baya da kaya ta bud'e gidan baya ya zuba sannan ta bashi naira hamsin ta shiga motar ta zauna tare da kallonsa tana gyara mayafi tace. "Malam muje na dawo, wallahi kuma da arha shi yasa na siyo mata kwano biyu-biy....." Bata k'arasa ba taga ya d'ago hannu tayi saurin sunkuyar da kai tare da boyeshi tana sauke a jiyar zuciya cike da tsoro da mamaki. Fad'a ya fara yi mata kamar ya samu student d'inshi har ya gama bata d'ago ba ya figi motar taji sun fara tafiya sannan ta d'ago tana kallonsa. Kasa yin magana tayi ganin yadda yayi kicin-kicin da fuskarsa dan haka ta share Sa har sukaje k'ofar gidansu. Mutane kuwa aka fara murnar ga INdo ga INdo, wad'an da suka sanshi kuma suka dinga gaidashi yana amsawa da kyar tamkar 6eyi rayuwar garin ba. Kayanta ta kwasa tare da shiga cikin gidan su bata sake fitowa ba, shiru-shiru taji babu wanda ya lek'o shi kuma jira yake su gaida koda Inna koda Malam Hamza amma babu kowa daya fito daga gidan haushi da takaici suka sa shi ya tafi ba tare daya aika ankira wani ba. A cikin gidan kuwa INdo cewa tayi musu ai ya tafi hakan yasa Inna bataje sun gaisa ba su kuma murnar zuwan INdon yasa basu fita ba bare su ganshi harya tafi. Har Sadeeq yaje gida be denajin haushin abinda INdo tayi mai ba, lokacin da yaje gidan a cike yake da 'yan uwan Fateema hakan yasa shi juyawa yayi hanyar gidan su ba tare da ya shiga ba dan yasan akwai wad'anda zasu yi mai kallon banza. Mama na ganinsa hankalinta ya kwanta tace. "Yauwa Sadeeq har ka dawo?!" "Eh suna gaida ku." Ya fad'a yana k'ok'arin zama a kujera, Mama tayi murmushi cikin jin dad'i sannan ta shiga d'aki ta kawo mai abinci, beyi musu ba yaci dan yasan Fateema ba iya yi zatayi ba sabida ciwon marar daya barta tana yi. Yana gama ci ya fita yaje can gidan marigayi ya gano sannan ya wuce gurin abokinsa har sai da aka kira magariba sannan ya koma gidan. **** Bayan sati biyu Abba ya gaji da sanya mai ido da safe ya kirasa, yana zuwa sai daya shiga suka gaisa da Umma da Mama sannan ya shiga gurin abban. Gaisawa suka yi Abba ya kallesa tare da ajiye magazine d'in hannunsa yace. "Sadeeq yaushe zaka koma kwaran ne?" "Abba nan da kwana uku insha Allahu zamu koma." "Kai dawa?" Sadeeq yace, "Abba da Fateema mana." "A'ah Sadeeq ya kamata ka farayi musu adalci tun yanzu, ina son tunda zuwan nan na k'arshe da Fateema kukayi toh wannan karan sai ku tafi da Aisha bana son ta cigaba da zama da auranka acan gidan su ina fatan ka fahimce ni.?!" Wani irin 6acin raine ya ziyarci ran Sadeeq kansa a k'asa yana danna yatsansa cikin zuciyarsa kuwa abubuwane kala-kala a cikinta. Jin yayi shiru ne yasa Abba kuma yi mai magana Sadeeq yace. "Abba ai tafiya ta da Aisha garin nan bazai yiwu ba sabida kaga su ba Hausa sukeji ba itama kuma ba yarensu takeji ba dama tanajin turanci ne da sauk'i amma gaskiya tafiya da ita matsala zai jazamin wallahi, nasanta tun kafin Abubakar yasan ta." "Toh yanzu me kake nufi?!" "Abba kawai zan samu gida na ajiyeta anan idan yaso sai ta zauna a ciki har mu dawo." Abba ya kallesa sosai kafin yace. "Kana nufin ta dinga zama anan har lokacin da zaka dinga dawowa yayi." Sadeeq yace. "Eh Abba idan ba hakan ba wallahi bansan yadda zanyi da Aisha ba idan mukaje can, gashi ta raina ni sam bata ganin girmana tun sanda na koyar dasu a makaranta." "Shikenan kafin ka tafi kaje ka d'akkota sai ta tare anan gidan Najib tunda naga ya kammalasa kuma 'yan haya zai zuba gashi dai-dai itane gidan." Sadeeq yayi shiru tunani yake yana kuma jin takaici, kawai yana zaman-zamansa an d'akko mai wani aikin, yanzu duk shekara sai ya bada kud'in gidan hayar da INdo zata zauna dubu d'ari da talatin. Mtwww yaja tsaki ba tare da yasan ya fito fili ba sai da yaji Abba yace. "Sorry ko na shiga hak'inka ne??" Da sauri Sadeeq ya hau kad'a kai alamar a'a sannan yace. "Toh Abba kuma ni zanje na d'akkota? Na d'auka kawo ta zasu yi.?!" "Eh toh kuma hakan dai yafi, amma ina son ka k'ara d'aga tafiyar ka har ta tare sannan sai kutafi." Dakyar ya iya amsawa Abba sannan ya tafi. Yau ya kuma yin Nadamar zuwa tsefawa secondary school domin zuwansa ne yasa Abubakar ya ganta harya aure ta gashi ya mutu shi anbarsa da alak'ak'ai. Yana komawa gida ya bawa Fateema labari tace Allah ya sanya alkairi, kallonta kawai yayi ya shige d'aki. *** Cikin kwanaki biyu tal Abba yasa Sadeeq aka kwaso kayan INdo na gidan Abubakar harda wanda duk shine ya siya aka kaisu gidan da INdon zata zauna a matsayin ta na Matar sadeeq. Su Haleema Rukayya da Amina yasa sukaje suka kwaso kayan sawarta suka kai can gidan akajera mata sai dai babu dining area gashi INdo tana matuk'ar sansa dan idan tana kai ji take tamkar tana kusa da sharukhan. Sadeeq da Umma da Hawwa suka tafi d'akko INdo, hirarsu ce duk ta sashi mance wadda zasu je su d'akko har suka k'arasa k'ofar gidansu INdo wanda yake cike da mutane wai ashe su biki suke yi wannan abun ya k'onawa Sadeeq rai sai kace wani sabon aure mtww. Sun dad'e a ciki kafin a fito da ita su Uwani sai mata murna akeyi ta baro gidan dad'i zata koma gidan dad'i INdo taja tsaki ita kad'ai tasan gidan da zata shiga dan tasan sam basanta yake ba ta kuma riga ta shirya ma zama dashi a kowane irin yanayi indai vazai hanata abinci da fita yawo ba. A kusa da Umma ta zauna yayin da Hawwah ta zauna gefensa anata yi musu fatan sauka lafiya bayan Malam Hamza yazo sun gaisa dashi Sadeeq din ya kuma bashi amanar 'yarsa sukaja mota suka tafi. Tunda suka kama hanyar komawa yaja bakinsa ya tsuke jin INdo ta zage sai subirbid'a hira take tamkar ba amarya aka d'akko ba, yaja tsaki ganin sam babu jan aji a tattare da ita. Suna zuwa a k'ofar gidanta suka sauke ta su Umma suka shigar da ita ganin amarya yasa mak'otanta suka shiga suma dan su ganta. Har kusan k'arfe shad'aya na dare Sadeeq be shigo gidan ba, gidan yayi matuk'ar yin kyau domin yasha tile's bangon da k'asan ta ko'ina sai dai bekai girma da tsaruwar na marigayi Abubakar ba amma hakan be damu INdo ba domin na iyayanta sam be kama k'afar su ba. Kallon agogo Hawwah tayi tare dajan tsaki tace. "Wallahi Yaya Sadeeq d'an wulak'anci ne, yasan fa muna jiransa amma bazai zo ba ga mijina can sai waya yake yomin." "Kinga yayya Hawwah kiyi tafiyarki mu zamu jirashi." Haleema ta fad'a tana gyara kwanciya akan kujera hannunta rik'e da waya wanda hakan yake nuni da cewar chatting takeyi. "Ba haka mukayi da Abba ba, cewa yayi karna bar gidan nan sai na tabbatar mai da shigowar Yaya Sadeeq." "Toh saiki zauna gyara wani auran ke kuma ki 6allo naki ba." Waya ta zaro zata k'ira Abba sukajiyo sallamarsa a k'asan makoshinsa. Tashi kowanne yayi yana sanya mayafinsa ya zauna a kan kujera. "Toh Yaya Allah ya bada zaman lafiya." Yayi shiru yana canza channel Hawwah tace. "Yaya ina muku addu'a kayi shiru." "Ke malama ku wuce kutafi gida bana son sa ido." "Amin yayya Hawwah mun gode a gaida gida da abban siyama sai munzo." Suka jiyo muryar INdo tana fitowa daga bedroom, hatta shi kansa saida ya kalleta ta gyatsina mai hanci tabi bayansu danyi musu rakiya. "Amarya kamar karmu barki wallahi." "Allah sarki Aminatu idan Allah ya kaimu basai ku dawo ba." "Zamu zo amma da yamma kinga gobe monday akwai makaranta." Cewar Haleema INdo tace. "Toh koma dai yaushe ne sai kunzo a gaida Mama." "Zataji." Suka fad'a tare da juyawa su shiga mota da driver na jiransu itama ta juya ta shiga ba tare da ta kulle gidan ba. Zama tayi a falon tana wak'ar Nas ya shareta yana kallonsa itama bata kulasa ba domin ba so takeyi ba daman. "Ke jeki kwanta dare yayi." Yayi maganar yana gyara kwanciya akan kujera. Itama ta gyara zama tare da d'aukar remote tana murmushi tace. "Wallahi malam Sadeeq banajin bacci." Had'e rai yayi domin yana son yin waya da Fateema ya rage mata dare yayi mata alk'awari gashi wannan yarinyar zata samai ido. "Ke bakya jin magana ko? Kin tashi kosai ranki ya 6aci.?!" Tashi tayi cike dajin haushi ta shiga bedroom, kan gadon Abubakar datake so shi aka sanya mata a d'aki d'ayan kuma dayake matsayin nata aka sashi a d'ayan d'akin da ake nufin na sadeeq ne. Tana kwance kwai ya fad'o mata ta zura hannu k'ark'ashin filo wayam babu sweet d'insa da yake ajiyewa ta kalli agogo da yanzu suna tare kawai ta mik'e ta koma falon tana k'ik'ifta ido. "Idan Zan iya zama ni d'aya a d'akin Allah ya tsinen..!" Sadeeq dake manne da waya a kunnensa yaji da fad'a. A hankali yace. "Babyna wait zan sake kiranki." Kashewa yayi tare da juyawa ya kalleta sai kuma ya juya ganinta sanye cikin riga da wando pink and white na bacci sun kuma zauna a jikinta d'as duk da basu kamata ba yace. "Toh kina son nazo mu kwanta tare ne." "Malam Sadeeq ko bakazo badai toh kabarni anan." "No baki isaba ko kuma ki kwanta anan d'in ni saina shiga ciki." Zama tayi kan kujerar tare da cewa,. "Tunda waya kakeyi toh ka k'arasa anan idan ka gama sai ka tafi nasan sannan nayi bacci bazanji tsoro ba." Mtwww yaja tsaki ta kwanta suna kallo duk sunyi jigum har wajan 1:45am duk ya gaji ita kuma sai a lokacin tad'an fara lumshe ido ya zaro wayarsa ya lalibi Fateema amma abin mamaki switch off ya cillar da wayar gefensa yasan haushi taji be kiraba yanzu kila tana can tayi mai fassara kala-kala. A takaice duk anan falo suka kwana, haka har yayi kwanaki biyu a gidanta washe gari Sadeeq da Fateema suka wuce kwara state cike da farin cikin su ita kuma INdo aka turo mata Aminatu ta taya ta zama.. _M fan's kuyi hakuri gobe zakujini shiru zanyi 'yar tafiya insha Allahu dana dawo zamu d'ora I need ur prayers please._ *HAJJA CE*👈 [7/31, 5:13 PM] Aisha Galadima: *⚗⚗ MUSAYAR ZUCIYA...⚗⚗* ♥♥ ♥ A true life story Na *K.A.S Precious Hajja ce*👈 *HASKE WRITER'S ASSOCIATION*💡 (Home of expert & perfect writer's) *VOTE me on wattpad @Hajjac* *DEDICTEED TO:* Sanah Isma'il Matazu *Godiya mai yawa tare da d'inbin farin cikina zuwa ga fan's, na gode da addu'o'inku garemu munje Lafiya mun dawo lafi na gode sosai da sosai.😍 HAJARAH (MUM ILHAM) godiya mai tarin yawa a gareki domin kin nuna mana soyayya nida 'yar uwata STYLISH BCH da kuma 'yata IHSAN, Allah ya saka da alkairi ya bar kauna da soyayya Allah ya raya Ilham👏UMMUL MEENAL, BILLY S FARI & OLO addu'atw gareku bazata fad'u ba sai dai ince Allah ya baku abinda kuke nema duniya da lahira domin kuna nuna min sayayya ta hak'ik'a HAJJA CE na sonku fiye da yadda kuke nunan kauna.💋😍💋* Page *28* Tunda suka tafi koda wasa Sadeeq be ta6a gigin k'iran INdo a waya ba, bashi dama phone number d'inta bare yace zai nemeta. A 6angaranta itama bata ko tunaninsa tana gidanta hankalinta kwance babu abinda yake damunta. Ranar da su Sadeeq suka cika sati d'aya da tafiya a ranar INdo ta fara fita, kullum tana gidan mak'ota bata nan layin bata can sam bata zama cikin kwanaki takwas mutanan unguwar sun santa maza da mata yara da manya. Yayin da a 6angaran Sadeeq yana son ya kirata tunda yasan tana da hakki akan sa amma baya kaunar ya kirata tayi mai rashin kunya ko ta gaya mai maganar da zai kasa bacci dan ya lura akwaita da shuka magana ba kuma ta barinta indai harka gaya mai toh zata baka amsa hakan yasa ya shareta. Misalin k'arfe hud'u ta fito daga wanka tana shafa mai tajiyo me tallah a k'ofar gida, cikin sauri ta janyo doguwar riga a cikin wardrobe ta zura tare da d'aukar mayafi ta fita. A k'ofar gate d'in ta tsaya dan sake tabbatarwa da kunnuwanta abinda me tallar yake cewa still taji yana cewa. "A sai kajin gidan gona matasa..!" INdo tayi saurin fita tare da kwala mai k'ira ya dawo baya kasan cewar harya wuce gidan nata. Tsayawa tayi suka fara ciniki zata siya har yace zai siyar mata a yadda cinikin ya tsaya, guda bakwai ta siya ta shiga gida ta d'akko mai kud'in ta bashi ya tafi ita kuma ta shiga da 'yan kajinta sai kuka sukeyi iya-iya-iya tana ta murna taje ta zuba su jikin bathroom d'in tsakar gida dama ba'a shigar sa. A hankali ta ci gaba da kiwonsu tana bayarwa ana siyo mata abincin su hankalinta a kwance su Haleema idan suka zo suyi ta mata dariya ita kuma tace da tayi kud'i saudiya zata tafi idan ta dawo a dinga k'iranta Hajiya INdo kasan cewar sunan ya bazu cikin gidajen mak'ota k'annan su Sadeeq ne kawai ke kiranta da aunty Humairah kamar yadda marigayi ke fad'a mata. Rayuwar INdo ta cigaba da canzawa sana'o'i take yi kala-kala kajinta ma sunata girma har ta samu sun fara kwai tana tarawa taci takai gidan su Sadeeq sai da Mama tace ta fara siyarwa sannan ta fara. Da daddare tana kallon arewa 24 Sumayya tana gabatar da shirin tauraruwa taji yadda wata mata da ake hira da ita yadda rayuwarta ta faro tun daga tushe har yanzu da takai wannan matsayin nan da nan INdo tayi sha'awar yin karatu itama tana son ta iya turanci sai dai tayaya zata iya? Sam kwakwalwarta bata gane turanci ba kuma ta iya rubutawa sannan ba ta iya maida hankali wajan koya tayaya zata iya zama tauraruwa kamar yadda taga ana haskilo mata masu aji ana kuma alfahari dasu, tasa a ranta zata fara koyan turanci kamar yadda marigayi yaso tayi kafin mai rabawa ta rabasu. Sannu a hankali tana jin takaicin Sadeeq nak'in nemanta tun ranar da Aminatu ta guntsa mata cewar ai dan batajin turanci ne yasa Yaya Sadeeq cewa baxai tafi da ita can ba hakan yasa abin ya kuma ba ta haushi tsanarsa ta kuma hauhawa a cikin zuciyarta dama ya saba yi musu wulak'anci tun a tsefawa. M.M Haruna English academic taji anata tallar makarantar a gidan redion express, ta fara tunanin yadda zata yi ta samu shiga cikin ta. Tanason zuwa tana tsoron kar da taje ta tarrar da garzazzu wad'anda basa Hausa sai turancin, wai shin ma meyasa aka maida turanci tamkar saukar alkur'ani da komai za'a ce in zaka yi sai ka iyasa? Ga larabci yaran annabi amma ba a dagewa da zuwa islamiyoyi ba'a basu muhimmanci kamar yadda ake baya yaran jajayan farar fatar nan. idan aka kyaro baka iya bama sai ka zama wani hulugu ka zama abin raini da wulak'anci a wajan al'umma. Zata yi turanci itama za kuma taje ta koya badan wulak'ancin Sadeeq kad'ai ba sai dan wata rana itama ak'irata ayi hira da ita a kuma tambayeta tauraronta tace Abubakar ne,haka zakila kuma a Dama da ita ita duniya wannan burinta ne ba kuma zata canza shi ba koda Sadeeq zai saketa. "Hello mubassheer, kana Ina yanzu.?!" "Ina majalisa ya akayi ta samu ne..?!" "Kai d'an rainin wayo ne, kazo dan Allah zamuyi sirri." "Toh aunty Humaira gani nan zuwa amma fa zaki ban jarkar kunun aya guda biyu." "Dallah idan baxaka zo ba sai na kira khaleefa wallahi." "Sorry Matar broth ina zuwa." Kashewa yayi yana dariya sannan ya d'auki abokinsa guda d'aya suka tafi gidan a mashin. A falo suka zauna ta kawo musu kunun ayar da zobo da jallop d'in taliya suka ci sukayi dam sannan mubashsheer ya kalli INdo yana cewa. "Toh meye sirrin Matar broth, tunda kin bamu munci..!" Sai da ta hararesa sannan tace mai. "Dallah kaga ni ba surutu na tambaye ka ba, jujun labo store zaka dan Allah ka siyo min farm (form) d'in shiga makarantar M.M Haruna Englihi menene ma d'ayan na gaban ma oho na manta." "Ah Matar broth wai kina nufin shiga zaki yi..?!" INdo tace "Eh ya ranka? Zakaje kayi min duk abinda za'ayi na fara zuwa kokuwa wulak'anci zaka yi min Kai ma..?!" "Ah Matar broth na isa, kawo kud'in toh sai muje muji ya za'ayi, amma tukunna kin sanar da broth Sadeeq d'in zaki fara ne dan karya zo yayi min masifa." "Kai zaka siyo min ko kuwa na sake wani?!" "Ah na isa kawo kud'in muje muji ya za'ayi." "Toh nawa zan baka..?!" "Haba ki kawo ten thousand muje mu fara manage dasu." "Kana nufin nawa kenan?!" "Kai Matar broth dubu goma zaki kawo naga kina min wani kallo." "Ta6 goma fa kace? Wallahi ku tafi na fasa ai ba dole." Ta fad'a tana shiga cikin d'aki Mubasheer ya dinga yi mata magiyar ta fara bada ten thousand d'in tace ta yafe bazata ba sai da yace. "Toh kawo five thousand, dubu biyar wallahi Matar broth kin fiye san Kud'i da yawa, duk sati dubu biyar broth yake badawa a kawo miki ga kud'in zobo ga kunun aya ga gullisuwa da kwan kaji dan Allah mekikeyi da kud'i bayan duk akwai abinci a gidan..?!" Dubu biyar d'in ta bashi ya kar6a ya k'irga sannan suka tashi zasu tafi INdo tace. "Dan Allah k'anin miji a rage sa ido, duk lissafin ka yana kaina toh da ba kud'in zaka ci naman dakaci a cikin abinci ne? Ko zaka ci harda vegetables d'in ne d'an rainin wayo." "Magana ta wuce bari muje mu dawo." Yana fad'a suka fice ita kuma ta shiga d'aki. Ko Ina tas-tas a gidanta bata barin k'azanta sannan kullum cikin k'anshin turaran tsinke d'akin yake dan haka INdo tana samun customers a rana sai ta dura jarkokin zobo dana kunun aya guda d'ari biyu amma baya kaiwa dare Allah yasanya mata nasibi a ciki. A ranar bataga Mubasheer ba har kwana biyu sai gashi yazo, tsayawa yayi yace ya gama mata komai zuwa kawai zata farayi domin sai da ya sanar da abban su ya kuma bada goyan baya sosai. Juma'a na zuwa ta fara zuwa cikin tsoro da fargabar yadda zata tun kari malamai da d'alibai dan tasan duk sun fita k'ok'ari. "Matar broth ga class d'inku nan." Mubasheer ya fad'a yana nunawa INdo ajinsu. Ido ta dinga kwalowa waje hannun ta na dama dafe da k'irji ta kalli Mubasheer cikin tsoro tace. "Anya bazan koma gida ba, Mubasheer tsoro nakeji wallahi." "Kai Matar broth wallahi karkiji tsoro kowa fa da kika gani zuwa yayi a koya mai, idan kika nuna musu kina jin tsoro zasu raina ki kedai karki fasa yin abinda kike so ki shiga kawai." "Toh bari naje idan mun tashi zan yi maka waya kazo ka maidani gida." "Toh Matar broth Allah ya bada sa'a." A hankali INdo ta shiga tashin farko ganin yadda hall d'in yake yasa gabanta bugawa da k'arfi sannan ga d'alibai nan a zazzau ne duk sai ta daburce ta rasa inda zataje cikin sauri ta juya zata fita sai taga Mubasheer a tsaye yana dariya, cikin tsananin jin kunya tace. "Maidani gida bazan shiga ba." "Hahaha...! Wallahi babu inda zaki, muje na shigar dake haka kurum dan ayi asarar kud'i sai da aka gama komai zaki wani ce kin fasa." Yana gaba tana bayansa har ya k'arasar da ita tsakiyar kujerun sannan yayi wa wata budurwa magana cewar gata nan dan Allah ta fara helping d'inta ta wasu abubuwan. Karimatu tayi murmushi tare da mik'awa INdo hannu suka gaisa ta zauna a d'ari-d'ari kamar munafuka sai wulkita idanuwa take a haka Mubasheer ya barta yayi tafiyarsa. Malami na shiga ta fara sunkuyar da kai, nan aka fara gabatar da lesson kasan cewar ajin masu koyan turanci ne hakan yasa komai ake yi musu dalla-dalla cikin hikima da kuma kwarewar malaman ita dai INdo tayi tsit bata ko kwakwaran motsi dan karma malamin yayi mata tambaya koya saka mata ido. Alhamdulillahi kuma ta tsinto abubuwa kasan cewar sai anta maimaita musu abu anji kowa ya gane an kuma fahimta sannan za'a shiga wani abun haka aka dinga yi musu tana kuma zuwa duk juma'a asabar da lahadi da safe. **** Wata d'aya da sati biyu su Sadeeq sukayi a kwara state sannan suka juyo suka dawo kano. Lokacin satin INdo biyu da fara zuwa makaranta, sam bata yi wani murna da dawowarsa ba sema haushi da takaici dataji. Sai da yayi kwana biyu a gidan Fateema sannan ya waiwayo yau zaije gidan da INdo take. K'ofar gidan ta tsaya wajan k'arfe sha biyu na dare, key d'insa na gidan ya zura ya dan bud'e abu ya gagara sai yahau buga mata tana kwance a kan gado da littafi a hannunta tana Home work d'in da aka basu, tanaji saidai batasan kowaye ba dan haka batayi ma niyar tashi zuwa ta gano ba. Mtwwww yaja tsaki tare da ciro wayarsa ya nemo layin Haleema, mtwww ya kuma jan wani tsakin jin tana amfani da ita ya sake kiran khaleel cikin sa'a ya d'auka murya a shak'e Sadeeq tace. "Dan turo min da number'n Aisha." Khaleel yace "Yaya bani da ita sai dai ko yah Mubasheer." "Cene masa ya turo min." Ya fad'a a dak'ire sabida babu kowa unguwar sai shi kad’ai ga duhu. Yana tsaye yaji an turo ya kira number'n kamar bazata d'auka ba sai kuma tayi picking tare dayin shiru dan taji me maganar. "Ke zoki bud'e min gida kinaji Ina bugawa kik'ak'i zuwa ki bud'e min." Harzai katse yaji tace. "Waye kai d'in? Wa kuma kake nema..?!" "Au bakima san waye ba dan rainin hankali Aisha?!" Tace "Kai kaga k'ila wrong number ne go and check." Kafin yayi magana ta katse kiran ta cigaba da aikin ta, Sadeeq yabi fuskar wayar da kallon mamaki ya sake buga gate d'in da karfi cikin jin haushi amma tak'i bud'ewa cikin 6acin rai ya buga number'n Mama tana bacci Haleema ta d'auka tana dubawa taga Sadeeq dan haka ta d'an janye wayarta daga kunne da takeyi da saurayinta ta kara tare da cewa. "Yaya lafiya? Mama tayi bacci fa." "Yauwa Haleema kira number'n Aisha kice ta bud'e min gidan Ina waje." "Okey tom Yaya sai da safe." Tana kashewa ta kira layin INdo, tana kwance duk tama rasa yadda zatayi Home work d'inta taga kira ta duba a tunaninta number'n d'azu ce tayi niyar d'agawa tayi mai rashin mutunci sai kuma taga Mmn dacta da haka akayi mata saving sunan tayi murmushi tare da karawa a kunne tana shirin gaida ita taji Haleema na cewa. "Aunty Humairah Yaya fa yana k'ofar gida yace kije ki bud'e mai nidai sai da safe." "Dama shine? No wonder naji ya fad'a da gadara zoki bud'e min gida, d'an rainin hankali ai na d'auka harka koma bazaka zo ba." Hijabi tasa ta d'auki mukulli tayi waje, cire kwad'on (pad lock) d'in tayi ta bud'e mai ya shigo sannan ta juya ta koma, shi ya bud'e gate din yasa motar sannan ya rufe gidan ya shiga ciki. Bata falo ya bita bedroom fuskarsa a had'e yana shiga ya ganta kwance da littattafai a gabanta da biro da alama rubutu takeyi baki bud'e cikin tsananin mamaki yace... *HAJJA CE*👈 [7/31, 5:13 PM] Aisha Galadima: *⚗⚗ MUSAYAR ZUCIYA...⚗⚗* ♥♥ ♥ A true life story Na *K.A.S Precious Hajja ce*👈 *HASKE WRITER'S ASSOCIATION*💡 (Home of expert & perfect writer's) *VOTE me on wattpad @Hajjac* *DEDICTEED TO:* Sanah Isma'il Matazu. Page *29* "Aisha wannan kuma books d'in waye kike ta lalatawa haka.?!" Cikin rashin damuwa tace, "is my own." "Ooh your own?!" "Yes..!?" "Toh zane-zane kikeyi or what.?!" "Home work nake yi." Tayi maganar tana sake karkad'a biron hannunta, Sadeeq ya zaro idanuwa yana rik'e da ha6arsa kafin ya matsa kusa da ita yanan kallon littafin da take yin rubutun yana jijiga kai ganin note d'in tamkar tafiyar tsutsa wani yayi k'asa wani tsakiya wani sama ya zauna bakin gadon tare da kallon littattafan gurin ya gansu duk na turanci. Karo na farko daya fara zama kusa da ita duk da cewar ba kusa da jikinta ya zauna ba ya d'an bada gap. 'Daukar littafin kusa da ita yazo zai yi INdo tayi saurin janyewa ta 6oye k'ark'ashin cikinta tana faman harhad'e fuska dan bata son ya kushe mata rubutunta, ya ta6e baki tare da d'aga kafad’a yana cewa. "Toh furniture's d'in d'akin kike drawing d'insu ko me kike yi hakan?!" "A'a ba d'aya malam Sadeeq, makaranta nake zuwa kuma acan ake koya min wannan karatu." "Ooh which school ne suka iya d'aukarki a haka Aisha..?!" Cikin jin haushin sa INdo ta tashi zaune tana kuma 6oye book d'inta tana rurufe idanuwa tace. "Dan Allah malam Sadeeq ka kyale ni haka nayi abuna ka takura min, neman ilimi naje yi sai yanzu Allah yayi zanyi, lokacin da marigayi dacta yana da rai bashi da wani buri daya wuce yaga nayi karatu amma kai sai afkin yiwa mutane gori toh nima na shiga school yanzu zan zama tauraruwa wata rana so what.?!" Sadeeq ya tsaya kallonta, sosai tayi k'iba tayi bulbul da ita tayi fresh, duk da Cewar sleeping gown ce a jikinta kuma me d'an kauri hakan be hana bayyana yadda cikar halittar k'irjinta bayyana ba, Sadeeq ya d'auke kansa tare da ta6e bakinsa yace. "Kinyiwa kanki gata kuwa Aisha, sai dai nasan zaki sha wahala tunda ba iyawa kika yi ba tun farko sai yanzu ne kika fara, shin waye ya kaiki school d'in and waye yake biya miki kud'in?!" "I am, kasan ance sa kai yafi bauta." Ta fad'a tana jin tsoran kartaje ya gwasaleta yace ba haka zata ce I am ba, sai kuma taji yace. "Good hakan ma yayi kyau, but zan cigaba da biya miki ai ilimin yana da dad'i nan gaba zakiji dad'insa idan kika yi." "No kabar abunka zanyi abuna da kaina, ko ka manta sabida rashin Ilimi na yasa kace ba zaka tafi dani inda kukaje da Fateema ba? Hmm! Allah yaji k'an dacta na, cewa yayi wallahi babu inda baxai iya shiga da niba dan har gaban Obama zai iya zuwa dani kuma yace matarsa ce. Ka tashi ka tafi ka kwanta ni bacci nakeji." Tayi maganar tana share hawayen daya fad'o mata. Kallonta yayi tsab yaga ta tsuke fuska bayan ta goge kwallar sannan yace. "Aisha ki lalla6ani, wallahi Zan iya hanaki zuwa school d'in inga ta tsiya dan dama baki gaya min ba ai kika fara zuwa." Tace "lallai malam Sadeeq, ai wallahi tallahi sai dai ka sakeni in tafi gida dama baka sona nima bana Sanka kaga sai kaje kaji da matarka Fateema nima inje inyi karatuna so what." "Wato har yanzu baki da kunya ko Aisha? Wallahi zaki sha mamaki na." Ya fad'a tare da barin d'akin cikin sauri ya koma falo yana jin wani mugun 6acin rai, ko wane munafikin ne yazo ya gaya mata wannan maganar, wannan yarinyar idan ta kuma wayewa sai tafi k'arfinsa gara ma ya togeta daga makarantar ya sanyata islamiya ko zata dinga rissinawa. *** Washe gari yana farkawa ya fito yayi hanyar bathroom d'in tsakar gida, yana zuwa yaga kaji gaba d'aya gurin ya zama tamkar dama dansu yayi, cikin tsananin mamaki ya fara tunanin toh kajin waye ta kar6o haka dan wulak'anci ake 6ata mai gida. A fusace ya koma ciki ya nufi bedroom d'inta, tana kwance sai shak'ar bacci take tayi d'ai-d'ai da ita books d'in wasu sun fad'i k'asa wasu kuma ta dannesu ya k'arasa kusa da ita cike da masifa zai tashe ta yaga abunda yasa shi saurin shigewa toilet d'inta yana dafe k'irjinsa. Ya dad'e a tsaye kafin yayi alwala ya fito beko kalleta ba ya fita falo yayi sallah, yarinyar akwai d'aukar hankali komai nata a wannan stage d'in ya cika yaja tsaki tunowa da yayi sanda take zuwa da yagaggun kaya ya kwanta akan doguwar kujera yana sauke numfashi. Jiyo motsinta yayi sai da ya d'an dad'e har gari ya fara wayewa sannan ya mik'e ya shiga cikin bedroom d'in nata. Tararwa yayi tana k'ok'arin fitowa suka yi karo da goshinan su INdo ta dafe gurin tare da fad'in. "Kai-kai-kai..!" Shareta yayi domin shima sauran k'iris yayi wai-wai-wai sabida tsabar zugi amma ya maze. "Ke meye wancan a bayin waje.?!" "Ina kwana?" Itama ta fad'a kafin ta bashi amsar daya tambaye ta, a ciki ya amsa bata damu ba tace. "Kaji nane." "Wai Aisha haka kikeyin duk abinda kika ga dama ne? Yanzu me kikeyi da kaji.?" "Masu kwai nefa malam, idan suka yi kwai nikuma sai na siyar, ance macen da bata sana'a aurace toh ni Ina yi kuma da kud'ad'an na shiga makaranta nayi kud'in napep. Malam tunda ka dawo baka ce INdo sau nawa kikayi rashin lafiya ba amma sai tambaya ta kakeyi abubuwan k'aruwata." Shiru yayi domin tafishi gaskiya kuma sam beyi tunanin tambayar tata ba dan haka a wannan maganar yaji kunya, amma dan ya raina ta sai cewa yayi. "Toh dama ke kina rashin lafiya ne? Naga tunda ban ta6a jin ance kinyi cuta ba, kuma da kinyi toh Abba zai gaya min." Shiru tayi ta shiga kitchen, indomie ta jik'a sannan ta jajjaga kayan miya ta ajiye tare da komawa cikin d'aki yana zaune a falo yana waya da Fateema ta sharesa dan sam batajin haushi bare ya d'aga mata hankali. Sai da ta dubi lokaci tasan indomie d'in ta jik'u sannan ta shiga kitchen ta soya ta dafa tea ta kawo kan center table ta ajiye da kofu na guda biyu ta zauna tare da cewa. "Ga abinci malam Sadeeq." Lokacin sun gama waya yana chatting ya kalleta ya kalli agogon dake kafe a falon yaga k'arfe bakwai sauran minti uku, yanzu ne za'ayi breakfast sai kace ba yanzu aka tashi daga bacci ba yace. "Tun yanzu ake yin karin kumallo.?!" "Eh ai garin ya waye malam Sadeeq me zamu jira." "Aci lafiya toh." Ya fad'a ta kallesa cikin mamaki sannan ta fara had'a tea d'inta, ta iya cin abincin kuwa kad'an kad'an harta gama ci yana satar kallon ta. Tana gamawa taje ta fara dafa zo6on ta kasan cewar ranar Monday ce batada school ta wanke ayarta tana jiran lokacin da almajirinta zai zo ya kai mata markad'e. Shima Sadeeq bacci yayi yana jiran lokaci yayi ya tafi gidan Fatima yayi wanka dan zaije lecture. Bata tashesa ba sannan duk batasan zai fita ba domin be sanar mata ba har tara da kusan kwata sannan ya farka yana duba agogo yaga har lokaci yayi da sauri ya mik'e ya d'auki mukullin motarsa, beyi mata sallama ba kawai sai tashin motarsa tajiyo taja tsaki sam malam Sadeeq bashida mutunci a jerin da ta sanya shi kenan. *** Yana zuwa gidan Fateema yayi wanka ya shirya ya tafi, around 12:30pm ya dawo, cikin murna ta tare sa tare da rungumeshi ya d'agota yana cewa. "Akwai bayani baby na zauna ki gaya min." Sakinsa tayi ta k'arasa kan TV stand ta d'akko mai wata takadda, bud'ewa yayi ya karanta tare da zaro idanuwa yana kallonta cikin murna ya kuma rungumeta yana cewa. "Woww babyna am so much happy wallahi, kin zama malama sai yau Allah yayi." "Aikuwa baby kaji yadda naji kuwa, anjima zanje gidan Aisha idan zaka tafi please zanje kaga mun jima bamu had'u ba." "Toh kinsan itama ta koma school fa." "Kai baby shine koka gaya min sai yanzu danace zani gidan? Sadeeq yace "A'afa nima sai jiya naji kuma kinga ai ban zauna ba sai yanzu, kinga bani abinci naci." Tashi tayi ta shiga kitchen yayi farin cikin samun aikinta sosai domin yana son abinda take so, yana kuma son farin cikinta. Egg into egg ta kawo mai tare da kunun gyad'a ta zuba mai yasha madara ya zauna a hankali ta dinga bashi harya cinye yasha kunnun sannan suka ci gaba da soyayyar su tamkar babu gobe har mantawa suke yi da matsayin INdo. Bayan yaje gidan Mama ya dawo sai ya d'auke ta suka tafi, gidan cike da masu siyan zo6o da kunun aya wasu na fita wasu na shiga inji yana tayi mamaki ya cika ransu sai da suka shiga sannan suka tarar da ita a zaune gaban k'atuwar kula duk wanda ya bata kud'i saita bud'e tabashi ya tafi, Sadeeq ya shiga ciki ransa a mugun 6ace shin yarinyar nan meta maidashi ne, wato ma ashe harta zama big hajiya besani ba Allah ya kaisu dare sai ya 6ata mata rai. Sosai suka yi hira da fateema ta yadda har ta gano lallai itace star a gurin Sadeeq, anayin magariba ya maida ita gida wajan k'arfe goma yazo gidan INdo lokacin tana zaune a falo tana kallon film d'in Basaja na farko. "Ke Aisha daman haka kika mayar min da gida tamkar gidan kallo? Maza da mata su dinga min strolling a ciki?!" Tayi shiru ya kuma harzuk'a ta kuma yi mai shiru ganin yana masifa yasa ta cewa. "Wai malam me yasa ka tsaneni ne? Nifa kamar yadda bakai kace kana sona ba haka nima bance Ina sonka ba. Yanzu da yake ita Fateema matarka ce ta so ai d'azu tazo ta nuna min takardar fara teaching d'inta kai da kanka ka kawo ta sai ni da nake sana'a a cikin gida da kud'ina amma ka dinga min fad'a kana Sa min ido? Toh ka sake ni dan Allah ka gani idan bazan rayuwa ba." "Ni zaki cewa na sakeki Aisha? Toh bazan sakeki ba kuma karna sake ganin wani yaro ko yarinya sun shigo min gida." Yana kaiwa nan ya kuma barin gidan sai dai be fita da mota ba, anya ta d'aura a zuciyarta na cewar bazata denaba tunda taga alamar bakin cikin ganin tacigaba yakeyi. 11:49pm ta d'auki pad lock zata kulle gidan taji sa daga waje jikin gate din yace. "Malama karki rufemin gida." "Gidan hayan." Ta fad'a tana shiga falo yayi kwafa tare da shigowa ya rufe. Tuni ta shiga d'aki ya bita dan sake ja mata kunne kawai ya tarar ta cire riga tana niyar saka ta bacci hankalinsa yayi mugun tashi ya kasa controlling d'in kansa ita kuwa sam batasan yana tsaye ba saida ta gama saka rigar ta tashi tsaye domin da a zaune take ta ta6e baki tare da hayewa kan gadon. Jikinsa na rawa dama Yaya lafiyar kura domin yana da tsananin buk'ata tun yana saurayi bare yanzu domin fateema harta saba da halinsa. Cikin rawar jiki ya k'arasa kusa da ita kan gadon ya hau sam bata kulasa ba kawai taji ya janyo ta jikinsa suka fara fad'a Sadeeq yayi nasarar rungumota jinta a jikinsa yasa jikinsa ya kuma narkewa ya rasa abinda yake tunzura shi duk da irin naushin da yake sha a gurinta amma yak'i ya saketa. "Wai meye hakan ne kake yi min." "Shhhiiii..." Yace da ita a dai-dai kunnanta, duk k'arfin INdo amma ta gaza kwatar jikinta Sadeeq ya sake rungumeta jikinsa sai karkarwa yake yi, cikin k'arfi da yaji sai da Sadeeq ya samu abinda zuciyarsa take muradi a gurin INdo. Jikinta daya raina yau sun had'u danasa, bakinta da yake ganin koda million d'ari bazai iya ta6awa ba yau sai da suka had'u danata tana ta kuka ya rasa yadda zai yi a ganinsa tunda tayi aure ta riga tasan komai be ta6a tunanin zai jita a yadda yaji yanzu ba (k'ila ya manta suna cikin amarci Allah ya d'auke mata angon domin Abubakar ba kullum yake yi mata ba wani sa'in making romance kawai zaiyi da ita) INdo cikin kuka tace. "Tun farko haka zaka ce ga abinda kake so dani bawai ka hanani yin sana'a taba. Wallahi malam Sadeeq bana sanka duk da a makaranta ance bakyau a gayawa miji haka wallahi ni bana sonka Allah kuma saiya saka min." "Please Aisha b..." "Karka yi min magana tsakani na dakai babu magana daga yau wallahi bazan sake yi maka magana ba ko me zakayi min." Ya kasa rik'ota domin daya kai hannu zata yi mai wata uwar mahangur6a takai mishi naushi da k'afa da hannu tilas yabar d'akin ya koma falo. "Innalillahi wa'inna 'ilaihir raji'un why? Why? Sadeeq, Aisha ce fa INdo malam Hamza tsefawa secondary school ita kayiwa haka.." Da sauri ya mari fuskarsa ya gani wai ko mafarki yake amma sai yaji zafin marin sannan kunnuwansa na jiyo masa kukanta. Rintsa idanuwa yayi tare da toshe kunnansa yana faman girgiza kai dan yadda yaji wata bahaguwar kaunarta na tafasa cikin zuciyarsa yayi saurin tashi tsaye ya shiga d'akin da take kwance ya durkusa saitin kanta gwaiwarsa a k'asa ya...... *HAJJA CE*👈 [7/31, 5:13 PM] Aisha Galadima: *⚗⚗ MUSAYAR ZUCIYA...⚗⚗*                    ♥♥                       ♥              A true life story Na *K.A.S Precious Hajja ce*👈 *HASKE WRITER'S ASSOCIATION*💡 (Home of expert & perfect writer's) *VOTE me on wattpad @Hajjac* *DEDICTEED TO:* Sanah Isma'il Matazu. _Alhamdulillah³ naji sauk'i godiya me tarin yawa ga masoya, naji dad'in addu'@r ku gareni gashi Allah ya amsa nagode Allah yabar kauna da soyayya._🤲🤝 Dan Allah duk wanda yayi min magana jiya zai ga ban amsa ba wallahi wayar ce tayi wiping kuyi min afuwa dan Allah, na gode❤ *Today is my daughter’s birthday🎂🔥🎂, Fateema Omar Farooq Pz. Wishing you long life, Allah ya raya min ita ya shirya min ita ya tsare min ita da duk 'ya'yan musulmai baki d'aya love you so much my daughter*🎂🔥🎂 Page *30*    Hannu ya kai zai ta6a ta amma sai ya kasa, kallon bayan ta yake yi kawai zuciyarsa na tsananin harbawa.Tashi yayi ya koma gefen gadon ya d'an zauna a hankali ya kira sunanta cikin sanyin murya a kuma dai-dai kunnanta yace. "Aisha bari muyi magana kota minti d'aya ce please." Motsi INdo ba tayi ba bare yasa ran zata juyo ko ta tashi zaune, yana jin yadda take sauke ajiyar zuciyar ta amma ji yake tamkar tashi ake bubbugawa sabida tsananin yadda yake ji. Hannu ya kai ya rik'o kafad'unta ta baya amma ko motsi bata yi ba ta dak'ire mai daga kwancen sai ya samu kanshi da kwanciya a bayan ta ya rungumeta a jikinsa tsam amma still bata motsa ba, ya d'ora kansa a wuyanta yana shafar kitson kanta zanan hannu, nan ma ko gezau INdo bata yi ba. Duk wani hanyar lallashi da Sadeeq ya sani yabi INdo dasu amma taki motsi duk da cewar tana numfashi hasalima idanunta biyu amma ya gagara ko mirgino da fuskarta gurinshi sabida yadda tayi mai taurin kai ta kafe a guri d'aya tamkar mutum mutumi. "Aisha me yasa bakya jin maganata ne? Shin baki son matsayina a gurinki bane kike yi min haka? Nace ki tashi dan Allah zamu yi magana kinji ko..?!" Wayyo Allah..! ko pillow'n kanta be motsa ba bare ta mik'e, Sadeeq yayi ya kad'a ya raya, yayi magiyar yayi lallamin tare da lallashi amma tayi gardama. Ya manta INdo amma yanzu ya tuna ko wacece, ya tuna lokacin da tace ta dena zuwa makaranta kuma hakan aka yi ta dena zuwa sai da taji labarin ana bada kyauta sannan ta fara zuwa, ya tuna lokacin da tazo dan samun kyautar atamfa bata yanke farce ba ya hanata tace ta dena zuwa k'arshe ma ta yi hijira daga kauyan sani zuwa kauyen saye bata dawo ba sai da marigayi yaje ya dawo da ita. Wannan suna d'aya daga cikin taurin kanta daya sani dan haka yanzu ya zai yi mata gashi zuciyar sa na buk'atar kasancewa tare da ita, shin me zai yi mata ta huce gashi tace bazata sake mai magana ba, meya kai shi haike mata bayan duk basu shirya yin hakan ba daga shi har ita. "Ya ilahi...!" Ya fad'a cikin zuciyar sa. Har kusan k'arfe biyu na dare yana kusa da ita, haka ya gaji ya mik'e ya shiga toilet wanka yayi sannan yayi alwala yaje falo yana fita ta sakko daga kan gadon ta rufe d'akin tamkar dama jira take yi. Yana shimfid'a sallaya yaji ta rufe  ya kalli k'ofar cike da mamaki kafin ya tayar da sallah. A ranar Sadeeq be runtsa ba ya dinga sak'e-sak'e da neman hanyar dazai sassauto da zuciyar INdo, har yayi asuba a gurin sannan ya samu 6arawon ya sace sa bayan ya gama samun mafita. INdo kuwa tana kulle k'ofar ta hau kan gado sai kuka take yi, tasan yayi mata ne dan mugunta amma tayi alk'awarin ba zai sake ta6a ta ba bare har yayi gigin yi mata wani abun. wata sabuwar tsanarsa ta kuma shiga cikin zuciyarta. Sai da asuba sannan tayi wanka tayi sallah duk a nan cikin d'akin sannan ta koma ta hau gado dan ta san yana nan kuma idan ya ganta zai iya yi mata magana abinda ta tsana yanzu kenan ko kallen ta bata son yayi. Misalin k'arfe bakwai na safe ya nufi d'akin ya bubuga mata amma tak'i bud'ewa haka ya hakura yabar gidan kasan cewar yana da lecture da k'arfe takwas. Tana jiyo shi ya fita ya rufe gate tayi saurin hantsilowa daga kan gadon taje ta gark'ame gidan da padlock sannan ta koma falo ta zauna sai zabga tsaki take tana harara-harare tamkar ance mata yana gurin ranar bak'in ciki ya hanata yin zo6o da kunun aya sai gurin kaji da taje ta kwashe kwan da suka yi.    *** Shi kuwa Sadeeq yana zuwa gidan Fateema yasa key ya bud'e, shiga yayi a kwance ya tarar da ita tana ta bacci ya lalla6a ya kwanta a bayanta tare da shiga cikin bargonta ya rungume ta tsam a jikinsa yana cizon lip's d'in sa tare da goga goshinsa a bayan ta. Yadda taji ya nanik'eta ne yasa ta rik'o hannunsa da ya mak'alota dashi ta d'ora akan k'irjin ta shi kuma ya matse ta jikinsa sai rawa yake yi. Gabaki d'aya ransa INdo ce daya rufe ido zai tuno abinda ya faru tsakaninsa da ita, haka ma daya bud'e idon zai dinga ganinta gashi ya tabbatar da yana da mugun tabo a gurinta. Yanzu ya zai yi wajan ganin ya wanke kansa a gurinta? sam beyi tunanin cewar hakan zata ta6a faruwa a tsakaninsa da ita ba sabida tsananin yadda yake ganinta tun zamanin tana INdon ta ba yanzu ba da ta koma aunty Humarah ko aunty Aisha ba.   Da kyar ya iya shiryawa yaje yayi lecture ya dawo, directly ya wuce gidan INdo, cikin tsananin mamaki ya tsaya yana kallon gate d'in gidan ganinsa a gark'ame. Mota ya koma ya wuce gidan su yana tunanin can ta tafi amma abin mamaki sai yaji su Mama suna tamyarsa ita amma ya maze tare da cewa. "Tana nan Lafiya lau." Ya d'an jima a gidan ya mik'e ya fita, Haleema ya k'ira a waya tana d'agawa yace. "Haleema d'an k'ira Aisha a waya naji ina ta k'iran ta not reachable please yanzun nan amma." "Toh Yaya bari naji." Wayar INdo Haleema ta k'ira, tana d'agawa tace. "Aunty Humaira ina kika shiga ne keda wayar ki?" INdo ta yatsina fuska tamkar a gaban ta take cikin takaitawa tace. "Ina gida.." "Okey tom shikenan." Haleema ta k'ira Sadeeq yana d'agawa tace. "Yaya tana gida wai." "Okay thanks." Suka kashe wayar, Sadeeq ya dinga mamaki wato ma ashe tana jin motarsa amma tak'i bud'e mai lallai yarinyar nan ta mugun raina sa gashi ya kuma siyowa kansa wani sabon rainin. Juyawa yayi ya koma gidan Fateema yak'i kuma bari ta gano yanayin sa. Haka Sadeeq ya dinga sintiri a ranar daga gidan Fateema zuwa gidan INdo amma abin mamaki har kusan magariba bata bud'e gidan ba, sannan ya kirata a waya yafi sau ashirin amma bata d'aga ba ya san ba k'aramin 6ata mata rai yayi ba.   Har ya kammala kwanaki biyun sa a gidan Fateema INdo bata bud'e gidan ba haka kuma duk wanda yaje bata bud'ewa. Sadeeq kuma ya rasa yadda zai yi tsoransa d'aya karta mutu a gidan besan mezai ce ba. 10:35pm yana zaune a falon Fateema ya shiga cikin tunani yaji Fateema na shafar sajan sa ya kalleta yana murmushi tare da lumshe ido tamkar ya sha kwaya don sunyi wani iri tace. "Baby ya kamata ka tashi kaje gidan Aisha dare nayi maka fa." "Ai bata nan taje garin su." Ya samu kanshi da fad'ar haka yana kallonta, Fateema tana da kyau sosai domin tafi INdo haske da idanuwa ga gashi amma cikar hallitta gaba da baya INdo tafi Fateema. Ya lumshe idanuwa tare da janyo ta jikinsa yana shafar bayan ta, sai dai cikin ransa so yake yaga INdo kota halin k'a-k'ane amma ya rasa hanya. Friday morning INdo ta shirya tsab ta tattara littattafanta tasa mayafi ta fita, bud'e gidan tayi sannan ta rufeshi daga waje ta tari napep ta wuce makarantar M.M HARUNA. Submitting d'in books na Home work d'in da aka basu aka yi dan malamin ya duba yana zuwa kan na INdo yaga ba kanta hakan yasa ya kira sunanta da ya gani a jikin littafin yace idan an tashi taje ta samesa a office. Hakan kuwa aka yi ta sami M.m harunan a office d'insa ya nuna mata guri ta zauna yace. "Aisha Hamza daga wace school kika taho nan..?" INdo tace "Gaskiya malam ban gama makaranta bani, ni yanzu ne dai nake son yi sabida gaskiya kaga mijin da aka bani d'an rashin mutunci ne kuma a jami'a yake koyarwa, nidai malam dan Allah kuyi iya k'ok'arin ku wajan ganin na iya nima shida matarsa duk malamai ne shi yana min gori kar nan gaba itama tazo ta fara yi min.." M.M HARUNA yace "Toh karki damu Aisha tunda dai har kinsa a cikin ranki zaki koya toh nasan ba zaki sha wahala ba, yanzu zaki fara tun daga kan alphabets kije ki kwafe su cikin note book d'inki gobe ki kawo min ki kuma dinga k'ok'artawa wajan yin magana da turanci koda kuwa za'a yi miki dariya dan ni daga yauma ki dena min hausa da yawa understand.?!" "Toh malam yes." Ta fad'a tana rufe fuska yayi dariya shima tare da cewa "Good." Littafi ya d'akko sabo ya rubuta mata from A-Z yace taje tayi irinsu duka. Allah sarki da yake tana so ba taji wani girman kaiba ta kar6a tana komawa gida a kwance ta tarar da Sadeeq har ya shigo gidan da yake babu abinsa padlock daga waje, ta wuce cikin d'akin ta yayi saurin tashi ya bita a baya ya tsaya a wajan wardrobe ko kallansa ba tayi ba bare ta gaida shi yace. "Aisha fitsara.., wato ni kika hana shigowa gidan ko? I think nawa ne, koda yake kin ce gidan hayane amma wayake biyan kud'in gidan.?!" Ko kallansa ba tayi ba ta zare hijjab d'inta ta ninke tasa a wardrobe taje zata shiga toilet Sadeeq ya fizgota nan ma tak'i yin magana ganin haka yasa shi fita yabar gidan, yana tafiya ta kuma kullewa taje tayo fitsari ta shiga kitchen ta dafa abinda zata ci ta koma falo taci ta k'oshi sannan ta fara assignment d'in ta tana gamawa tayi bacci bata sake bud'e gidan ba sai washe gari da zataje makaranta. kullum haka take yi bata bari su had'u dashi kwata-kwata.       Ranar litinin Fateema ta fara zuwa gurin aiki, damuwa da shiga tashin hankali suka taru suka yiwa Sadeeq yawa ya rasa yadda zai yi da INdo, sam ta dena bari ya kwana a gidanta sabida da anyi magariba zata 6ame gidan har Fateema ta gano suna da Matsala a tsakaninsa da Aishan sai dai bata nuna mai san jin abinda ke faruwa kasan cewar bata son shiga cikin abinda duk be shafeta ba.      **** "Abba wannan karan ina son tafiya da Aisha sai dai tak'i yadda ma muyi maganar da ita." "Sadeeq kenan yanzu kai da iyalinka ka kasa shawo Kansu waye toh kake son yaje ya shawo maka kanta? Duk tsaya ai kaine kafi mu kusanci da ita ya kamata kasan yadda zaka yi ta yadda har Ku tafi tare." Shiru Sadeeq yayi ya rasa ya zai yi gashi ranar Thursday yake son komawa, ga Fateema tunda ta fara zuwa makarantar nan yasan itama ba yadda zata yi ta bishi ba kasan cewar ya mata alk'awarin idan har takardar aikinta yafito toh zai barta tayi, gashi bazai iya tafiya shi kad'ai ba tunda ya riga ya saba kasan cewa da mace. "Sadeeq ya kayi shiru? Idan ita Aishan tak'i binka ba saika tafi da wadda kuka saba tafiya tare ba." "Abba ai Fateema ta fara aiki dan tun yanzu ma ta fara nuna k'in bina wallahi." "Toh ya zaka yi da rashin iya yaren su da ita Aishan bata iya ba? Kar taje tana baka matsala fah tun da a baya haka kace." Kan Sadeeq a k'asa yana goga yatsansa a k'asan carpet d'in d'akin, shi kansa yasan ba zai iya tafiya kwara state ba sai da matarsa a kusa dashi gashi abban da zai temaka mai shima yace yaje su sasanta da d'aya a cikin su. "Shikenan Abba zanje na kuma tambayar su, sai da safe Allah ya k'ara girma." Abba ya kallesa tare da cewa "Amin Sadeeq a gaida min dasu baki d'aya. Fita yayi ya wuce gidan Fateema ranar ma anan ya kwana. Washe gari ta kasance Wednesday bayan Fateema ta tafi gurin aiki misalin k'arfe goma Sadeeq ya shirya cikin wani rantsatsan yadi mai matuk'ar taushi sky blue ya d'ora hula yasa turare sannan ya fita. Gidan INdo ya wuce yayi niyar yau kota halin k'ak'ane sai ya shiga gidan ya kuma nuna mata kuskuranta na rainin da tayi masa. Cikin sa'a ma yana zuwa ya tarar da gidan a bud'e nan da nan zuciyarsa ta sanyaya, a k'ofar gidan yayi parking sannan ya shiga gida bakinsa d'auke da sallama. Takalma ya gani a k'ofar d'akin hakan ya tabbatar masa da cewar bak'i tayi, ya shiga ciki da mamaki sai yaga su Nafeesa, Sagiru da Shehu sai wani wanda besan ko waye ba amma da alama tare suke. "Yaya Sadeeq ina kwana?!" Yaji Nafeesa ta fad'a bayan ta durkusa k'asa, murmushi yayi tare da k'arasawa ciki yana amsa mata su kuma Su Sagiru ya basu hannu suka yi musabuha. "Yasu Inna da malam Lafiya dai ko?" "Lafiya lau, sunce suna gaida kai." "Ina amsawa yaushe zaku koma..?!" Sagiru yana shafa k'eya kasan cewar yanzu duk sun girma yace. "Nan da anjima zamu wuce." "Okey tom Allah ya kaimu." Yana fad'a ya wuce d'akin INdo a tunaninsa zata biyo shi irin abin nan na tsakanin mata da miji da idan ya dawo zata bishi taji abinda yake da buk'ata ko kuma a sake yin wata special Oyo yon amma yaji shiru sai ma dariyar ta da yake jiyowa ya dafe goshi tare da rintsa idanuwa daga bisani ya mik'e yabar gidan. Tunda ya fita be sake dawowa ba sai da akayi magriba sannan ya shiga gidan lokacin bata rufe gidan ba suna zaune da 'yar mak'otansu Mansura suna kallo suna hira. Ganin ya dawo ne yasa Mansura tayiwa INdo sallama ta tafi shi kuma ya zauna a falo yana kallonta. Sanye take cikin atamfa me ratsin green, white, brown, da purple d'inkin riga da zani sun cika ta sunyi mata d'as tayi kyau sosai ya kalleta amma ita hankalinta na kan TV, sadeeq ya d'auki remote ya kashe TV d'in tare da kallonta sai yaga tana kokarin mik'ewa ta shiga d'aki yayi saurin rik'ota ta fara fisge-fizge zata kwace ya jingina ta jikin bango bayan ya rik'e mata hannuwa. Murya tamkar ta marayan daya kwana biyu be samu abin kaiwa baki ba Sadeeq yace. "Aisha what's wrong with you ne ah? Dani zaki yi gaba? Kin manta matsayi na a wajanki ne? Ko baki san wannan abin da kikeyi min ba kina cikin fushin ubangiji ba? Please Aisha ki bari mu fahimci juna I beg of you please..." Still shiru tayi Sadeeq yakai fuskarsa saitin k'irjinta yana goga fuskarsa yaji tayi magana. "Wai malam Sadeeq ya haka ne?!" "Aure ne haka if you don't know." INdo ta dinga mai-maita if you don't know cikin zuciyar amma ta kasa gane me if d'in take nufi dan tasan don't know da you dan haka tayi tunanin ko wata maganar ya gasa mata dan haka ranta ya kuma 6aci ta zabga mai harara yakai bakinsa ta kauda kai amma duk da haka sai daya laso idon rashin kunyar da harshensa yace. "Aisha you don't know me shi yasa kike min duk abinda kikaga dama ko.?!" INdo ta ta6e baki tare da yatsina fuska ta daddage tace. "Ta6 I know you're noun, ko banda malam sadeeq kana da wani sunan..?!" "I know you're noun." Ya maimaita a fili yana kallon gefen fuskarta still yana rik'e da ita a jikin bango ya rasa gane me take nufi hakan yasa shi lek'a fuskarta yace. "Mene kuma noun a cikin maganar da kika min Aisha.?" Ta murgud'a baki tare da cewa. "Sakar min hannu malam Sadeeq, kace ban sanka shine na nuna maka nikuwa na sanka, noun is a name of person, animal, place or tins (things) ko ka d'auka yanzu ma banajin abinda kake fad'a? Never past tense kenan wallahi (Da kenan)." Sadeeq ya cuno baki, so yake yayi dariya amma baya son yayi taji haushi dan so yake ya lalla6a yayi mata wayo ya samu ta bishi dan haka ya dinga gumtse dariyarsa ita kuma tana k'ok'arin kwatar jikinta yace. "Very Good Aisha you're trying, but kin san menene? Ki shirya kayanki gobe mu tafi kwara state a can wallahi zaki iya komai domin su basa Hausa sosai kafin kiga bahaushe sai kin dad'e, muje ki shirya kayan ki sai na taya kima." Ya fad'a tare da janyo ta jikinsa ya rungume ta. Cikin sauri INdo ta fisge tare da cewa.... *HAJJA CE*👈 [7/31, 5:13 PM] Aisha Galadima: *⚗⚗ MUSAYAR ZUCIYA...⚗⚗* ♥♥ ♥ A true life story Na *K.A.S Precious Hajja ce*👈 *HASKE WRITER'S ASSOCIATION*💡 (Home of expert & perfect writer's) *VOTE me on wattpad @Hajjac* *DEDICTEED TO:* Sanah Isma'il Matazu. *THANKS ALL FAN'S, baki, hannu bazasu iya rubuta yawanku ba domin kunada yawa wlh. Na gode all grps da sukayi ma ihsan wishes. Allah yabar so da kauna.* _My wattpad so sorry please wallahi nayi nayi yaki yin update kuyi hakuri wallahi tun safe yak'i yi nasara dalili😪_ Page *31* "Wallahi ni dai baza ni ba, haba-haba da bakin kafa kace wai ba zaka je dani ba sabida ni banajin turanci, toh wallahi yasin yanzu dakaji na faraji ba zan bika ba Allah kuwa." "Idan nace kuma sai kinje fa ya zaki yi?!" "Ai karka ma fad'a dan ba binka zanyi ba, kaje ku tafi da Fateema." "Aisha...!" Ya fad'a cikin gentle mood wanda yasa INdo saurin kallonsa cikin ido hudu, hannunta ya janyo yana kallon fuskarta a fili ya fara magana besan ma a filin yake yi ba. "Aisha My heart is filled with instant joy, you give me everlasting warmth. Aisha your eye's, your nose, your pretty cheeks your mouth, your chin, the whole of you all are sweet and so you are. Please Aisha ki bini wallahi babu abinda zan miki kinji na rantse." Kallonsa kawai INdo tayi sam duk ta kasa gane abinda yake cewa hasalima dabarbarta ta yayi kwakwalwarta ta fara hasashe kafin tace. "Dare nayi malam Sadeeq kaje ka kwanta nima kwanciya zanyi na gaji." "Toh zaki bini mu tafi d'in..?!" "A'ah wallahi bance ba." "Wai me yasa kike da taurin Kai ne Aisha.?!" "Malam Sadeeq wane kai ne me laushi?!" Mtwwww yaja tsaki tare da sakin mata hannu yaje ya d'auki mukulli ya tafi rufe gidan sannan ya dawo, yana dubawa ya tarar ta rufe d'akin ta ya san ko magana yayi ba bud'e mai zata yi ba kawai ya kwanta a falo. Washe gari yana yin sallah yabar gidan bayan ya ajiye mata 10k ya tafi gidan Fateema. Yana zuwa ya tarar harta gama had'a mai kayansa ita kuma tana k'ok'arin shirin zuwa gurin aiki. Sai da ta temaka masa ya samu relief sannan suka shirya tare suka fito ta samu napep shi kuma ya Shiga mota yayi gidan su dan yi musu sallama. Suna gamawa ya juya ya d'auki hanya bayan yasawa ransa cewar zai gwada musu shi d'in namijin duniya ne sai sun nemesa musamman INdo da bata ganinsa da gashi aka. **** **** Bayan watannin uku. 12:30pm tana tsaye a mak'ale jikin bishiyar darbejiya sai makaka ruwan sama ake yi, ta jik'e tayi sharkaf da ita, ganin tamkar ruwa da iskar yana k'ok'arin jijjige bishiyar yasa ta ci gaba da tafiya sai faman tangad'i take tamkar ana tura ta, sam ba tayi tunanin ruwan zai yi yawan haka ba kafin ta k'arasa gida data fito daga school. Hakan ne ya bata damar tahau napep tayi gidan Asma'u tsautsayi kuma yasa ta fito tace ita gida zata tafi. Horn d'in mota taji amma bata juya ba sabida ko ganin hanya bata yi sabida k'arfin ruwan. Kuma yi mata horn yayi da nufin idan tana son temako idan kuma yayi mata sau uku toh zai rabu da ita ya k'ara gaba k'ila ba bil'adam bace. Tana jin ya kuma yi ta fara lalu6en inda taji mutar har Allah ya temake ta ta6ota, a hankali taje wajan k'ofar ta bud'e a she ta saitinsa ce sai ji tayi ya ce. "Ke daga ina kike haka..? Ki zagaya ba ta nan zaki shigo min ba." "I am not ke sir..., I am Aishat Hamza by name so please don't call me ke again..!" Ta fad'a tare da d'an bud'e ido ta kalli motar, da sauri ta zagaya ta d'ayan gefen ta shiga ganin Sadeeq ne jikinta sharkaf ya kalleta baki bud'e ta zauna sai ya kauda kai tare da mik'a mata wani d'an kyalle ta kar6a tana goge fuska dashi kafin shi kuma yaja motarsa suka fara tafiya a hankali kasan cewar ruwa ake yi sosai tamkar da bakin kwarya. "Ke wai daga ina kike haka cikin wannan ruwa?" "Please sir I told you am not ke, kace min Aisha and daga school nake.." "K'arya ne ya aka yi banga students ko d'aya ba sai ke kad'ai zaki tsaya yi min wani turancin banza." "Hmmm oga Sadeeq you don't know justice is the best policy ko?!" "Kut..!" Ya fad'a ba tare da ya san ya fito fili ba sabida tsananin mamakin ta da d'aurewar kai jin abinda take ce mai. Juyawa yayi yana kallonta tana goge fuska ya cije lips d'insa na k'asa har suka k'arasa bakin gate d'in gidan ta, tayi niyar fita taji motar a kulle sai ta kallesa tace. "Malam Sadeeq we are here fa, please ka bud'e min zan fita thanks for the help." "Karki fito ki zauna a ciki na gaya miki." Yafad'a tare da zarar mukullinsa na gidan ya fita da kanshi. Kallo tabishi dashi sai tayi murmushi lokacin ta tuno da Abubakar sam baya d'aure mata fuska tun lokacin da ya d'akkota daga Saye, yakan yi mata duk abinda zai satayi dariya ko tayi farin ciki amman wannan gadai kaman nin sak amma zuciyar ta banbanta. Dawowa yayi cikin motar shima duk ya jiki, shigar dasu yayi har parking lot da yake k'arami ne dai-dai mota d'aya INdo ta bud'e ta shige d'aki kasan cewar babu nisa befi taku hudu ba. Shima yana gama parking ya shiga falo bata nan ya wuce bedroom d'inta, tsaye ya ganta d'aure da zani ta juya baya wanda da alama da taji motsinsa ne tayi saurin yi. A hankali ya taka yaje har kusa da ita ya tsaya, matsawa yaga tayi gaba shima ya matsa har takai k'arshe sannan yace. "Go on.." "Aisha you're beyond my control ko meye dalili ne?!" "Because we don't love each other." "You dai but me...." Yayi shiru yana kallon keyarta don har lokacin bata juyo ba sabida wani dalili nata da bata son ya gani. Ji tayi ya rungumeta ta tayi saurin rintse idanuwa jin yadda tsigar jikinta ta tashi yarrr yana k'ok'arin d'ora hannun a saman cikinta tayi saurin rik'e mai hannu. "Please don't touch me." "Akan wane dalili? Shin Aisha an hanaki yin yaren Hausa ne?" Tayi shiru tana kauce mai da sauri ya finciko ta suka fad'a kan gado har zanin da tayi d'aurin k'irji dashi yana zamewa tayi saurin tashi a firgice shi kuma yasa hannu ya dawo da ita duk da cewar kayan jikinsa a jik'e suke. "Innalillahi wa'inna ilaihir raji'un malam Sadeeq ka tak'aita ni k'il...!" Da sauri ya mik'e zaune jin abinda ta fad'a, itama ra mik'e cikin kid'ima ta sauke zanin k'asa ya zamana bra ce kawai tayi saura daga cibinta zuwa sama, hannunta a saman cikinta daya d'an fito wanda ba kowa yake gani ba idan ba kwance pzani tayi ba ko kuma tasa t.sheet yaga tana shafar cikin bakinta a cune tana shirin yin kuka yace. "Aisha what's going on.? Ciki gare..Ki..ne...!" Bata lokacin da ta d'aga mai kai ba sabida Asma'u tace mata kar tayi abinda zai sa cikin ya samu matsala yau gashi Sadeeq zai nakasa mata shi. A zabure ya dawo k'asa idanuwa waje INdo na hawaye ta narkamai harara mai tattare da tsananin bak'in ciki ya kalleta k'irjin nan fam ya kuma yin kyau cikin in'ina yace. "How come's daga yi d'aya...?!" "Ka kaini asibiti nidai, idan ba bakayi ba yau ai gashi ka dauje ni." Ya akai haka daga one day wanda yasha matuk'ar wahala ace mai tana da ciki ga Fateema da suka dad'e tare ko 6atan wata bata ta6a yiba amma INdo nada Ciki.., ya kuma kallonta sai hawaye take yi bayan ta gyara d'aurin zaninta gashi har lokacin ruwa ake tsugawa Sadeeq ya koma kan gadon tare da zama a bayanta a hankali ya rungume ta tare da rintsa idanuwansa yana jin wani feelings har cikin k'ahon zuciyarsa. "Aisha Allah ne ya baki Abubukar a lokacin da zaku fara sabuwar rayuwa sai ya d'auke sa ba tare da kowa yasan manufar yin hakan ba, an had'a mu aure ba tare da muna so ba sai dai ko wannen mu ya d'auki hakan a matsayin kaddara. Aishi kiyi hakuri ki gafarce ni wallahi ko wanne tafiyar dani nayi tane cikin damuwa da tashin hankali amma ke babu abinda ya dameki why." "Nidai ka kaini asibiti kawai dan Allah." "A cikin ruwan nan? Dama gashi kinje kin kaimin shi ruwa ya jibgeshi k'ilama kinja mata/masa mura." Sake rik'ota yayi sosai a jikinsa yana yawo da hands d'insa tayi d'if, ganin haka yasa Sadeeq matsawa ya kwantar da ita kan gadon ya kura mata kyawawan idanunsa yana shafar cikin ta a hankali saitin kunnanta yace. "How many months." INdo ta kawar da kai tace "Ai bakaso ka dawo ka tarar dani a raye ba malam Sadeeq, sabida tunda ka tafi ko please call me baka ta6a gigin yi min ba. A gabana kasha yiwa Fateema waya sabida ita *Son ranka ce* ni kuma *Za6in iyayanka* hakan yasa baka san komai daya danganceni ba. Duk surutuna wallahi danaga kana yin haka ka watsar dani yasa nak'i nunawa kowa ina da ciki sai Asma'u da Mama sune kawai suka sani, sai gashi Allah ya raya ni da abinda yake cikina cikin k'oshin lafiya. Baya sani wani laulayi yadda neke komai a baya haka nake yi har yanzu. Malam Sadeeq baka sona sabida kasan cewa ta 'yar kauye, matalauciya, marar Ilimi. Karka manta Allah dayayo ka cikin wadata bawai yafi sonka bane, Allah dayayo ka hazik'i fasihi mai d'in bin basira bawai dan yafi sonka bane ko kuma dabarar ka da iyawarka ba kawai hakan ma jarabawa ce sai gashi kana min gori akan hakan. Shin ka manta twinnie broth d'inka duk ya fika wannan felek'an amma da Allah ya tashi sai ya bashini, ya zamto a duniya ni yake so har ya koma ga mahaliccinsa. Shine mutum na farko daya fara tsamoni daga k'angin wahala da toshewar kwakwalwa Allah ya gafarta mai haka kuma har cikin zuciya ta yana nan I will never forget him..never..never...." "Kiyi hakuri Aisha." Yayi maganar jikinsa a sanyaye, INdo ta share hawayen fuskarta tana cizon lips, ruwan da akeyi ne ya haddasa wani sanyi me ratsa cikin tsokar mutum hakan yasa INdo takure guri d'aya, Sadeeq na ganin haka ya xura kansa cikin wuyanta idanunta a lumshe yace. "Aishi kinyi hakuri kin yafe min? Namiki alk'awarin maye miki wanda yafi Twinnie d'ina, bazaka sake yin kuka dani ba har nima lokacin da tawa zata kasance. Ina son ki bani dama na shiga cikin rayuwarki nima na d'an yi miki koda rabin abinda Marigayi yayi miki ne, ina rok'onki alfarma ko yaya ne ki bari muyi rayuwa tare." *HAJJA CE*👈 [7/31, 5:13 PM] Aisha Galadima: *⚗⚗ MUSAYAR ZUCIYA...⚗⚗* ♥♥ ♥ A true life story Na *K.A.S Precious Hajja ce*👈 *HASKE WRITER'S ASSOCIATION*💡 (Home of expert & perfect writer's) *VOTE me on wattpad @Hajjac* *DEDICTEED TO:* Sanah Isma'il Matazu. _Na baku page d'in nan kyauta danjin dad'in ku, *Home of novel, Tsakar Munay, Zauren Sadeeya, Khadija candy, Rano online, Feedohm novella, Dandalin Billy bilya, Basma elr Lele grp,* Tnxs n I really appreciate ur love's care's of d comment's_😍👍 Page *32* 'Dan zame jikin ta tayi daga nasa ta kallesa, "shin da gaske ni yake so ko kuma cikin dake jikina? Anya malam Sadeeq kana sona kuwa? Amma zamu gani idan gaske ne." "Kin yi shiru." Dariya ce ta su6uce mata ganin yadda yake kallonta tamkar wani mara lafiya, ganin tana dariya yasa shi jin wani farin ciki har cikin ransa ya kuma janyo ta cikin jikinsa yana shafarta, ba zai mata komai ba dan karma tayi tunanin dan hakan yake sonta yanzu gara ya daure ya hakura ana d'auke ruwa kawai ya gudu gurin Fateema tunda Allah ya kasa ya bashi biyu. "Kana ganin yanzu babu abinda ya samu cikina?!" "Insha Allahu karki damu, ko kina jin wani ciwon ne?" "A'ah bana jin komai ni sai yunwa." "Okay sorry bari ruwan naga ya fara d'an tsagaitawa sai na samo miki wani abun kici. Bafa ki bani amsa ta ba Aisha baki ce kin yadda zaki zauna dani ba." Dariya da kuma yi tunowa da maganar Asma'u da tace tayi hakuri wata rana sai labari, shi gani zai yi kamar an shiga rayuwarsa ne shida Fateema amma tunda had'in Allah ne wata rana sadeeq zai kulata sai so ta koda bekai na Fateema ba tunda har Allah ya kuma had'a su a bed gashi harda rabo. "Aisha me kikema dariya ne? Ko gemun dana tara kikewa dariya.?" "Kai a'ah wallahi ni ina ruwana da wani gemu." "Toh kina so kenan in barshi yamin kyau?!" "Lalalah bance ba yadda kagani kai dai, kuma tunda ka barshi ai kowa yasan so kake yi taya za ai nace beyi maka ba ni INdo." Tayi maganar tana rik'e ha6arta cikin nuna k'ask'anci dan ta san bata kai wannan matsayin ba da har zata bashi umarni yabi ba. Yatsansa yasa a goshin ta wajan billenta yana shafawa ta lumshe idanuwa tana tuno Abubakar sabida duk sanda zai ganshi sai ya ta6a mata shi, sai dai idan ta d'aura d'an kwali ta cukaro shi ya rufe shine kawai ba zai ta6a ba. "INdo malam Hamza...! Wai me yasa ake ce miki haka ne, a memakwan Aishat Hamza." Ya fad'a cikin wani irin style wanda yasa ta kalli cikin idanunsa shi kuma ya kanne mata nasa tayi murmushi tare da cewa. "Haka mutane suke kiran baban mu, toh lokacin da aka sani a makaranta dama kowa INdo yake cemin banda Inna ita sai dai tace min 'yar nan, shi kuma baba yace min uwata shine da aka kaini sai aka tambaye ni sunana baban mu yak'i fad'a ni kuma karna fad'i sunansa sai nace INdo Malam Hamza shine kawai sunan ya zama haka." "Ummm! Good, toh yanzu kuma fa a school? Ko har yanzu kina nan a INdo malam Hamzan?" "No..no..noooo, Aishat Hamza tun lokacin da Mubasheer yaje yamin registration ya saka min haka shikenan nima na cigaba da sawa." Kallonta yayi yaji wani mugun tausayinta sai dai shi kansa yasan ya makaro, tun a baya ya kamata yaji tausayinta amma beji ba ganin batada nutsuwa a memakon ya tallafa mata sai ya k'ita sam baya k'arfafa mata gwiwa akan sha'aninta amma ya zai yi da sharrin zuciya dana shed'an, yasan dai marigayi shine ya kwashe ladan gashi har yau da baya duniya ta kasa manta shi. Yana fatan shima wata rana tayi mai irin wannan abun ko yana da rai ko kuma lokacin yabi d'an uwansa. Uban ruwan daya jibgeta ne gashi kuma ya rungemata a jikinsa ta takure yasa wani daddad'an bacci ya sace ta ba tare da tasani ba. Shima sai da ya janyo ta yaji jikinta ya saki hakan yasa shi leken fuskarta kawai sai yaga ashe har tayi ya bacci, ya juya yadda zai dinga kallon fuskarta ya kura mata ido. Ya dad'e yana kallon kyawunta mai kwantar da zuciya kafin yayi murmushi tunowa da yayi sanda ta d'auke mai naira d'arinsa daya je siyayya. A hankalli yaka sanya hannunsa saman cikinta yana shafawa zuciyarsa na tsananin harba mai cikin wani masifaffan son kasancewa tare da ita ya kai lips d'insa kan nata ya sumbace shi sannan ya mik'a a hankali ya sanya mata pillow a inda ya tashi tare da rufa mata lallausan bargo ya mik'e da sauri kasan cewar an tsayar da ruwan har an fara k'iraye-kirayan sallar juma'a. Cikin sand'a ya fitar da motarsa sannan ya kulle mata gidan ya tafi gidan Fateema da zafi-zafinsa. A k'ofar gida yayi parking motar ya tura gate d'in a kulle, wayarsa ya janyo ya kirata ringing d'aya ta d'aya cikin murna da zumud'i tace. "Allah yasa dai baby haka zaka cemin ka iso cikin Kano..?!" Muryasa cikin murmushi yace. "Fito ki gani ina gate." Zaro idanuwa Fateema tayi tamkar tana gabansa cikin sanyayya murya tace. "Baby kadawo kana waje? Please I'm so sorry kaga yanzun nan muka tashi yara sabida ruwa, dan Allah baby kajira ni in k'araso." "Okey toh kiyi sauri kinga karna rasa sallahn juma'a." "Toh godiya nake baby na sai na k'araso." Sallama tayi da sauran malamai matan da suka fito tare, cikin sauri ta tari Napep kafin wani sakannin har ya kawo ta. Cikin mota ta tarar dashi ya ziro k'afarsa waje hannunsa rik'e da wayar marigayi yana kallon pic's d'insa dana INdo wanda yayi mata tun tana INdo malam Hamza ranar da taso cin atamfa Allah beyi ba, dana d'aurin aure harda wad'anda suka yi a Munjibur park da wad'anda yake mata a cikin gida sai dai duk babu hotan banza a ciki Fateema na k'arasawa wajan Motar yayi saurin zura wayan a cikin aljihunsa. "Oyo-yo baby nah, taho mushiga ciki." Ta fad'a tana kallonsa cikin murmushi tare dayin gaba ta bud'e k'ofar gate d'in shi kuma ya biyo bayan ta. A parking lot ta tsaya yana shigowa suka rungume junansu cikin nuna kewa kafin yace. "Bari nayi alwala naje nayi sallah kafin na dawo ki samar min wani abincin kiyi da d'an yawa za'a kaiwa Aisha na biya naga ashe batajin dad'i." Kallansa tayi tana dariya tace. "Wai wannan uban k'asumbar daka tara gashi hardasu gemu duk na meye." Shafar faskar yayi yana tafiya yana cewa. "Baby wannan gemun na komai ne wallahi, hmmm danma Allah ya temake ku a iya tara gemu na tsaya, bari dai naje na dawo please ki d'ora girkin." Dai-dai lokacin suka shiga cikin Falo ya shiga toilet ita kuma tayi bedroom d'insa dan k'ara masa k'amshi duk da cewar kullum tana k'amsasa shi. Yana yin alwalan ya tafi masallaci, ana idarwa ya wuce gidan su suka gaisa dasu Mama tana tayin murmushi a tunaninta be fara ganin cikin INdon ba tasan zai yi murna d'an k'aniya da ana bashi yana nuna baya sonta. **** Yana dawowa ya tarar ta gama dama already tana da miya wadda tayi jiya tasha kifi sai k'amshi takeyi. Rungume ta yayi cikin tsananin so da buk'atuwa domin da k’yar yayi sallah banda ta juma'a ce da bazai yi ba sai ya fara samun nutsuwa. Sannan baya son komawa gidan INdo da wannan matsalar dan kar tayi tunanin hakan ne yasa shi cewa su shirya yanzu yana sonta, ya fison ya fara nuna mata yanzu ita d'in yake so kafin ya fara nuna mata ainihin waye shi. Bedroom suka koma hakan ya tayarwa da Fateema hankali dan tasan a wannan yanayin ita yak'e muradi gashi ita kuma tana period ya zata yi mai? Ganin yadda yake mata zafi-zafi yasa ta rik'o hannunsa tare da kwato shi saman k'irjinta murya a karye tace masa "Sorry baby.." "For what.?!" Ya tambaye ta yana matsar ta da gashin kanta, nuna mai tayi hakan ya tayar mai da hankali duk iya k'ok'arinta na ganin ya samu nutsuwa abin ya faskar sai da kawai ya nuna mata yayi normal sabida baya son damuwarta yasan da zata iya d'auke blood d'in da yanzu tayi. "Baby Ina abincin Aishan, kawo naje nakai mata zan biya can gurin Anas akwai abinda zan k'ar6o a gurinsa." Kallonsa tayi tasan k'ila yaje gurin Aisha, amma a k'a'ida yau itace dashi sai dai baxata so ta ganshi cikin matsala ba, tayi murmushin yak'e tana shafar gashin da ya lullu6e k'ewayan bakinsa tace. "Yana falo na zuba." Tashi yayi ya mayar da kayansa ta rakosa ya d'auki basket d'in k'irjinta na bugawa dan tana zargin akwai abinda zai had'asa da INdo amma tasan basa shiri zai iya sharewa ya jira har lokacin da zata samu tsarki. "Bye-bye baby ina dawowa zanci abinci nayi bacci dan agajiye nake munyi kwanan mota." "Toh sai ka dawo ayi mata sannu, kona zo muje tare?!" Kallonta yayi na 'yan dak'ik'a kafin yayi murmushi yace. "Yanzu kika dawo daga gurin aiki, sannan kice zaki fita bayan mijinki ya dawo daga tafiya me nisa. No ki zauna ki tanadar min dadd'ar hirar da zaki min idan na dawo." Fateema tayi dariya tare da d'aga mai hannu ya fita tana kallonsa kishinsa fal cikin k'ahon ziciyarta. Yana fita ya shiga mota yayi gidan INdo, yana zuwa a bud'e yaga gidan yayi parking a gefen gidan ya d'auki kayan abinci ya Shiga. Babu kowa har ya shiga cikin bedroom d'inta bayan ya ajiya abincin a falo. Tararwa yayi ta idar da sallah, ya tsaya a bayanta yau INdo ce take sallah harda su addu'a, lallai Allah buwayi mai sauyin lamari kamar yadda ya sauya salon alak'arsu daga malamin ta zuwa mijin twinnie d'insa daga nan ya sauya zuwa mijinta. "Humairah." Taji ya fad'a k'irjinta yayi tsananin bugawa tayi saurin waigawa tana kallonsa ido waje. Murmushi ya sakar mata tayi saurin d'auke kai dacta ya fad'a mata jin muryar data fara kiranta da sunan. Anya ba munafuntar ta akayi ba Sadeeq ya mutu aka raina wayonta aka ce Abubakar ne, anya shima ba yaudararta yake yi ba aka had'a baki dashi zasu raina mata hankali. Bata gama dai-dai tuwa ba taji ya zauna a kusa da ita har suna gogar juna ya lek'a fuskarta tare da cewa. "Tunanin me kikeyi haka? Ni ko Abubakar." Ta zame hijjab d'inta ba tare da ta kallesa ba. Shin me yayi mata a cikin rayuwarta da zata wani dinga tunaninsa, wanda yayi matan ya koma ga Allah ko kuma dan yayi mata ciki shine zai sa ta dunga tuna sa kila haka yake nufi. "Okey yanzu bazaki kulani bama.?" "Welcome back malam Sadeeq." "Sai da na rok'a, ai ba haka kikewa M twinnie ba oya hug me." "Kitchen zani mafa ko indomie na dafa, nasan dai kai bazakaci ba." "I said kiyi min Oyo-yo, kamar yadda kika min ranar danaje d'akkoki kika yi tunanin marigayi ne, oya am waiting." Tura baki tayi tana mamakinsa ganin irin yadda dacta yake mata abubuwa tace. "Ni a'a, ka kyaleni naje wallahi inajin yunwa." "Na kawo miki abinci, amma sai kin min oyo-yo sannan zan baki." A hankali ta juya ganin ya takura mata ta rungumesa bayan ta rintsa idanuwa. Jin k'irjinta a nasa ya sashi jin wani shock ya sanya hannunsa ya mak'alota gabaki d'ayanta jikinsa ya hau rawa tana jin haka ta kwace kanta ya samu da kyar yajata suka fita falo. Da kanshi yaje ya d’akko plate a kitchen ya zuba mata, tunda taji k'amshin kifi take jin tamkar ta cinye abin miyar ya zuba musu tare sai kallonsa take yi ganin yanzu yana mata wasu abubuwan da marigayi yake mata hakan kuma ya sa ta d'an sakar masa tun yana bata a yangance taji ko abinda ke cikin nata besan ana bata abinci ba yasa ta cewa. "Kawo ni na dinga baka gaskiya." A tunaninsa ko ta fara sonsa yayi murmushi tare da sakar mata spoon da pork d'in, idan ta bashi sau d'aya sai tayi kusan spoon biyar sannan zata kuma bashi, ya dinga bin fuskarta da kallo yana jin wani abu tamkar magnet yana fisgarsa. Sai da suka k'oshi sannan ta kwashe kwanukan takai wajan wanke-wanke yana binta da kallo duk da cewar doguwar riga ce a jikinta sai dai komai na jikinta rawa yake yi Sadeeq ya jingina da kujera shi kam bazai iya kwana a haka ba, tunda yasawa ransa idan ya dawo zai samu nutsuwa koda a gurin Fateema ne toh gashi tana off yayi 3mothns a wahale bazai iya kwana haka ba. "Sir Sadeeq na gode sosai, a cewa Fateema itama na gode ga kwanukanta." INdo ta fad'a tana k'ok'arin ajiye kwandon akan center table. Shi kuwa tamkar me bacci haka yayi nan kuwa yana kallonta ta k'asan ido yaga tana kallonsa jin yayi shiru yasa ta shiga d'aki ta zauna a bakin gado tare da d'akko jakar makarantar ta ta fito da books d'in wanda duk iya kunshesun da tayi a jiki saida ruwa ya ta6a su ta bubbud'e su akan gado tana turo baki ganin duk sun sha ruwa. Ta bayanta taji ya rik'o ta, sharesa tayi ta cigaba da hura book d'in hannunta da baki ya sa hannu ya k'ar6a ya ajiye akan gadon ita kuma ya jata suka kwanta akan gado INdo tace. "Ana k'iran sallar la'asar." "Uhmm naji Humaira but I need your help please." "Tofa name.?!" "I need you, dan Allah humaira karki min wata fassarar karki hanani ina cikin matsala humaira wallahi I love you... I love you Aisha karkiyi tunanin kodan wannan abun ne." Jikin INdo yahau rawa ta fashe da kuka tana jin yadda yake mata amma ta kasa hanasa domin tana jin hirar matan ajinsu akan mazajen su. Shi kuma jin bata yi masa irin na farko ba yasa shi cikin karyar da kai da nuna tsantsar nadama yasa har ya cinma muradinsa akan ta sannan shima yahau yin nasa hawayen. _"Twinnie kasan nifa ni bazai yuwu nazo gidana naga matata ba sannan na kyaleta ba no Zuciya ta baza ta bari bama tunda nasan mallakina ce."_ Ya tuno irin hirarrakin su da Abubakar cikin shak'kk'iyar murya Sadeeq yace wa INdo. "Skukran-laki Aisha Humaira. Do you love me? Please humaira love me as I love koda na iya yau ne kawai." "Malam S.." Ya rufe mata baki da nasa cikin son katse ta da sunan da yaji zata kirasa sannan ya cire yace. "Don't call me malam again. please change my name in dai har kin yadda zaki soni kamar yadda kike son twinnie d'ina." Hannunsa zagaye da wuyan ta suna had'a numfashi INdo tace..... *HAJJA CE*👈 [7/31, 5:13 PM] Aisha Galadima: *⚗⚗ MUSAYAR ZUCIYA...⚗⚗* ♥♥ ♥ A true life story Na *K.A.S Precious Hajja ce*👈 *HASKE WRITER'S ASSOCIATION*💡 (Home of expert & perfect writer's) *DEDICTEED TO:* Sanah Isma'il Matazu. *VOTE me on wattpad @Hajjac* Page *33* "Toh mezan ce maka? Kaga kaima Fateema ka fara aura, kuma ita kake so kafin ni. Toh nima ina sonka amma nafison marigayi dacta nima kaga ma an raba kar wani yaji haushin wani." Fuskarta yakai dai-dai tata ya had'e hancinsu guri d'aya yana rik'e da hannunta yace. "No Humaira wannan ba magana bane har yanzu ke yarinya ce. Idan nace zan dinga nuna miki soyayyar Fateema a fili zaki sha wahala tunda kinga ina nuna mata itama zata fallasa nata. While ke kuma idan kika ce zaki fifita soyayyar m twinnie a gurina babu abinda zanji sabida yadda muke dashi kuma baya raye bare ya dinga rama miki kamar yadda zamu yi nida Fateema a gabanki. So kidena kawo wannan abun a ranki yanzu ni zaki saka a cikin zuciyarki ba wani ba." INdo ta juya baya tare da cewa. "I love him tayaya zank'i fad'a kawai dan ya mutu? Dama haka soyayya da amana take idan ka mutu a shafe babin rayuwarka? No gaskiya nayi mai alk'awarin bazan manta da shiba har k'arshen rayuwa ta." Rintsa idanuwa Sadeeq yayi, sam Baiyi tunanin zaiji kishi haka ba amma yaji ransa na sosuwa jin yadda take cewa tana son wani mamaci ba shiba. No wonder mutane suke tsoron auran matar mamaci sabida koyaya zaka yi mata abu sai ta fad'esa ta nuna maka yafika, shi kam ya shiga uku gashi wani sanyayyan sonta sai sake shigarsa yake. Ba shakka indai haka Abubakar yaji a baya dole ya rikice yace yana sonta a duk yadda take, dole ya kira ta zuciyarsa sabida yadda a yanzu ta kuma shiga cikin tunanin Sadeeq d'in. "Juyo toh kiji." Yayi maganar yana kallon bayanta, a hankali ta juyo sai dai idanunta a kulle suke gam yace. "Zaki bini idan zan koma kwara state? Karki ce min a'a kinga ina son hakan so nake na shirya yadda zanyi tun daga yanzu." "Kai karatuna fa?!" "Karki tashi hankalinki kina dani zan dinga yi miki wannan makarantar duk k'aryar banza ce. Ki bini kigani zaki sha mamaki in a few days." (Kunji wayo... Wai makaranta ce karyar banza dan kawai yana son yi mata wayo maxa..maza mutanan mu). "Amma kuma fa malam Sadeeq..." Yayi saurin katseta bayan ya janyo ta jikinsa yana zagaye hands d'inshi a k'irjinta yace. Shhhii “ba anan zaki dinga kirana malam ba sai munje teburin d'aukar darasi but wannan gurin kam ki dinga kirana da wani sunan special da zai zama kene kike k'irana dashi” “Kamar irin su honey, sweetie, heartbeat, July juice, mango, touch light, tomato, vest....." "Ke.. Ke..! Uhm..uhm duk wannan sunan fa, na waye ne.?!" "Toh ai lissafo maka nakeyi sai ka za6a a ciki." "Shine harda su July juice, vest, tomato? You ko.." Ya fad'a tare da ja mata hanci tayi dariya har hak'oranta suka fito murya k'asa-k'asa tace. "Ashe kaima wata ran kanada kirki..?!" "Eh dama kece bakya lura but yanzu ai kin fara gani, tashi muje muyi wanka gashi bamu yi sallah ba." "Toh amma ka fara yi." "A'a tare xamuyi tunda komai tare muke yi." "Innalillahi nidai gaskiya ka fara zuwa ka yi." "Yauwa kin tuna min ma, baki gaya min ba zaki bini muje? Kinga a lokacin nake son dana koma na sake bud'e wani gurin kema ya kasan ce idan muje kina da naki d'akin, bana son business a nan sabida sa ido da nan kawai zan dawo gabaki d'aya." Shiru INdo tayi dan a gaskiya bata son zuwa garin tunda yanzu ta fara iya turancinta, itada ba kwarewa ta gama yi ba kawai ya jata su tafi sai sun je shima ya sauya mata tana tsoron Allah tana tsoron butulcin d'an Adam. "Tunda ba gobe zan tafi ba zan kyaleki kiyi shawara kinji?!" "Toh." Ta fad'a ya mik'e ya shiga toilet ya tarar musu ruwa ya dawo, da kyar ta bari suka je wanka suka yi tare duk da dakyar ta tsaya. Sai da suka d'auro alwala sannan suka fito yana rik'e da ita duk asan samunsa na ganin ta aminta dashi ta saki jiki ta kuma yadda da shid'in me sonta ne da gaskiya. Riga tasa ta atamfa da skirt sannan ta shimfid'a musu sallaya ta bishi da kallo ganinsa a zaune bashi da niyar sa kaya tace. "Sallan fa, kona yi tawa?!" Ido ya lumshe tare da hura iskar bakinsa yace "wane kayan zansa.?!" "Lallai ni ina na sani, ai kasan fa ko hularka babu a cikin gidan nan. Nidai bari nayi tawa sai ka tafi gidan Fateema kayi acan." Tana fad'a ta fara k'ok'arin tayar da sallah ya mik'e tsaye tare da tsayawa a gabanta yace. "A'a bari nasa riga ta ai doguwa ce ta rufe min gwiwa." "Nashiga uku haka zaka yi babu wando ji kafafuwa a waje a haka zaka yi sallan? Oh ni INdo..." "Eh aini an hallarta min yin hakan kune dai aka haramta muku yin sallah idan baku lullu6e jikinku duka ba, Allahu akubar²." Taji kawai ya tayar. A ranta kawai ta barsa dan tasan sallar malam Sadeeq bata kar6u ba. Suna idarwa sai ga su Haleema tayi sauri zata mik'e ta fita Sadeeq ya rik'ota suka yiwa juna kallon ciki ido. "Ina zaki?" "Su Haleema nefa ba kaji muryar su ba." "Naji amma ai baki tsaya kinyi addu'a ba kamar d'azu, zo kiyi addu'a sai ki fita gurin nasu." Komawa tayi ta zauna su kuma sai rangad'a sallama suke yi jin shiru yasa Aminatu lek'awa d'akin. "Au ashe sallah suke yi Yaya ma nanan." Guri suka samu a falon suka zauna suna jiran fitowar su. Matsawa yayi kusa da ita tana addu'a saitin kunnanta yace. "Kiyi mana addu'a, amma dan Allah karki rok’ar min mutuwa da gaggawa." Bata juyo ba tayi murmushi jin abinda ya fad'a. Shi kuwa tsoran irin addu'o'in da takeyi mai a baya ne yasa shi fad'ar haka yanzu tunda sun fara shryawa . Kuma mik'ewa tayi ya janyota tare da waigawa yana kallon k'ofa sannan ya sumbaci saman lip d'inta ta fita. "Aunty Humaira ya gida??" Ta zauna tana kallon Haleema sabida itace me kallonta tunda ta fito, INdo tace. "Ke wai meye ne? Sai wani kallon tuhuma kike min." "Kai aunty Humaira, missing d'inki nayi fa kinsan kwana hud'un nan duk a cikin hostel nayi su, bama haduwa sai naji kamar shekara nayi ban ganki ba." "Oho ni kuwa banyi wani missing d'inki ba sabida kullum idan baki zoba bacci na nakeyi." "Aisha.." Sadeeq ya kira ta ta mik'e taje d'akin. Tsaye ta gansa yana gyaran hular kansa ta d'an tsaya nesa dashi ya janyo ta yace. "Zan fita anjima zan zo muyi sallama." Tace "Toh sai kazo." "Is this all abinda zaki ce min?!" INdo ta d'an kallesa kafin tace. "Toh kayi shaving wannan gemun yayi ma yawa." "Sunnah ce fa cutie amma tunda bakya so zan cire." "Toh sai ka dawo." "Kin gaji ne? Na tafi na baki guri ko?" "Ah kawai kaga dai su Haleematu na nan." "Okey bari naje na dawo, give me good bye hug." Ya fad'a yana bud'e mata hannuwa, ya zata yi dole taje ta rungumesa ya matseta a jikinsa kafin ya sake ta suka fito tare, 'yan k'annan nasa suka gaidashi sannan ya fita ita kuma ta zauna gurin su suka sha hira har Aminatu ta dafa musu Indomie suka ci. Sadeeq kuwa gidan Fateema ya koma, tare suka yi sallan isha sam be nuna mata cewar gidan INdo yaje ba nuna mata yayi yana kai abinci gurin Anas ya wuce. Suna idar da sallahn isha'i yace mata. "Baby na bari naje can gidan nayi mata saida safe, daga can zan tsaya nayi aski ki dafa min tea kafin na dawo." Fateema da shagwa6a tasan yana son shagwa6a tana jikinsa a tsaye tace. "Gaskiya Baby karka yi aski ni dai ka barshi ina son shi yayi ma kyau." Idanuwa Sadeeq ya zaro jin ita kuma abinda tace, INdo tace bata so ita kuma tace ya barshi tana so ya shiga uku. "Menene naga ka zaro idanuwa haka? Shikenan jeka aske tunda baka son ka barmin kuma ina so." "Ah baby na isa, tunda kina so ai dole na barshi uwar gida sarautar gida. Bari toh naje na dawo." Fateema tayi murmushin jin dad'i ganin yana yi mata duk abinda take so. Sai da ta raka shi har gate ya juyo yana kallonta bayan yayi kalar tausayi yace. "No bye bye kiss ko? Shikenan nayi fushi." Da gudu ta rik'osa ganin zai fice tana dariya ta kamo wuyansa ya sunkuyo da kansa tayi kissing d'inshi tare da cewa. "Sai ka dawo karka dad'e." "Okey as you wish baby." Sannan ya fita yana tunanin yadda zai yi musu. Su Haleema kuwa Sai wajan k'arfe takwas na dare sannan suka tafi gida ya rage sai INdo kawai tayi sallahn isha'i ta cigaba da gyaran littattafanta. Jam-luck tasa hakan yasa yana sanya mukulli k'ofar ta bud'e. Shiga yayi tana jin motsinsa tayi saurin kwanciya tayi baccin k'arya. Kallonta yayi ganin yadda ta kwanta akan books d'in gashi ta kudindine fuska cikin bargo, ya k'arasa kan gadon tare da sanya hannu ya cire mata shi daga fuskar ta. "Oh harma bacci kika yi bayan nace miki zan dawo ko?!" Yayi maganar cikin kunnanta, INdo tayi mik'a alamar wai ya tashe ta sannan ta fara mistsike idanuwa murya a shak'e tace. "Au ka dawo?!" "A'a ina can." Ya bata amsa yana kallon fuskarta ta wani maze tamkar daga baccin gaske ta tashi. "Shikenan sai da safe in tafi..?!" "Eh sai da safe amma 8:00am zan tafi makaranta fa." "Ba nace kin dena zuwa ba?!" "Kai malam Sadeeq weekend fa nake zuwa ita kuma Fateema yau da gobe bata da aiki kuma dama acan kake toh kaga ai ba abin hanani zuwa, ni dai gaskiya zani Ina son school d'in gashi malamin shima yana son yaga na iya wallahi yana da k'irk'i yana sona." "Yana sonki kuma?!" Cewar Sadeeq a mamakance, cikin rashin fahimtar fassarar dayayi ma maganar INdo tace. "Eh wallahi har extra lesson yake min." "What...!" "Kai malam Sadeeq dafa ace bankai kaina wannan makarantar ba da nasan wallahi har yanzu baxakai marmarin so naba. Toh meyasa yanzu na shiga kake kuma k'ok'arin rabani da ita bayan akan rashin iyawa t...." Be bare ta k'arasa magana ba taji bakinsa cikin nata. Irin deep nd passionate kissing d'in nan ya dinga tura mata har jikinta ya kasa d'aukarta ta shiga biye mai ba tare da tasan ta iya hakan ba. Cikin rashin sani suka sake kasan cewa da juna musamman Sadeeq da sai da ya jima sannan ya gano da tabbacin abinda ya sake faruwa. "Na barki... Na barki Humaira kiyi karatunki zan cigaba da baki nawa gudun mawar insha Allahu. I love you with all my heart and soul Aisha please say you love me dan Allah...." Shiru INdo tayi ta kasa fad'a ji take yi tamkar idan ta fad'a tayi k'arya dan bataji wani love dinsa ba dazai iya sawa ta gaya masa. "In tafi bakya sona ko?!" "A'ah ni bance ba, amma ka tafi dare nayi Fateema na jiranka." "Aisha bakya sona ko? Shikenan." "Toh ina sonka, aini bance bana sonka ba." Agogo ya duba yaga sha biyu saura minti goma, da kyar ya tashi ya sa kaya INdo na kwance idanunta a rufe yaje ya sumbaceta sannan ya tafi ya kullo mata gidan da mukulli. Yana zuwa ta dinga kallonsa wanda yasa shi tsarguwa yayi murmushi tare da d'aukar ta suka wuce bedroom. Romance d'inta ya dinga yi har sai da ya nuna mata shima fa yana buk'ata yasan hakan ne kawai zai wankesa da zargin da ya hango a cikin idanunta, ganin ya fita birkicewa ne kuma ya tayar mata da hankali ta koma bashi hakuri tana lallashinsa sannan yace. "Toh baby ya zanyi bari kawai naje nayi wanka amma kwanakin da kikeyi sunyi yawa har 7days." Tana nan kwance yaje yayi wanka ta had'a masa tea yasha sannan suka kwanta bacci bayan sun nanik'i juna kamar za'a sace d'aya. Sai da yayi kwana biyu a gidan Fateema sannan ranar lahadi da daddare ya koma gidan INdo wanda a lokacin sai da tayi rok'on zuwan period amma ina sabida cikin jikinta gashi a gurinta kawai yake hucewa tunda ya dawo har ta fara jin haushinsa amma baya damuwa bare ya nuna ya gane nufinta. Abu d'aya yake mata ya d'auke hankalinta shine zai ce tazo suyi lesson wannan abun kawai yake sawa yaga ta sakar mai jiki har itama takan faranta masa ta hanyar kwanciya a jikinsa. Sadeeq kuwa ta k'arfi da yaji ya zama mak'arya ci a gurin INdo sabida tace bata son gemun Fateema kuma tana so dole yace wa INdo inda ake mai askin ne suka yi gobara yanzu gyara gurin suke yi sai sun gama, gashi shi baya son zuwa ko'ina idan ba gurin ba. Ita kuma Fateema ya rasa yadda zai sanar mata da cikin INdo domin zata yi mamakin tayaya hakan ta faru shida baya nan har tsawon 3months. *** Ranar Sunday misalin k'arfe 4:30pm Sadeeq da Fateema suna toilet sai rigima suke yi ya rik'e mata hannuwa yana cewa. "Bake kika hanani yin shaving d'in ba dan haka yanzu babu abinda zai sa kice sai nayi tunda kina so." "Nidai to yanzu ka rage please, Allah yanzu ta sake yin yawa." Ganin ta kafe ne yasa shi k'ar6a yayi ya rage iya yadda yake barinsa sannan suka yi wanka suka fito. Shiryawa sukai ko wannce cikin shigar daya fiso sannan suka fito zuwa gidan INdo dan can gidan su Mama zai kaisu ana kawo kayan sa ranar Haleematu. "Wait anan inje insa ta fito karku shiga ku shantake." Tashi yayi yashiga gidan ita kuma ta zaro phone d'inta ta kunna data kafin su fito. Yana shiga zaune ya tarar da ita tayi shirinta tsab mayafinta a kan cinyarta yayi sallama ta amsa tare da kai idanunta kansa, har ya k'arasa bata dena kallonsa ba ya mik'a mata hannu ta bashi nata ya d'ago ta tayi murmushi tare da cewa. "Ko kaifa da kayi wani kamar tsoho.." "Okey ko shi yasa ma kallon tsufan da kike min yasa kikak'i kar6ar tayin soyayyata?!" "A'a nidai ban fad'a ba." Yana rik'e da hannunta ya durkusa yasa gwiwarsa d'aya a k'asa d'ayar kuma ya ajiye ta kamar dai yadda turawa sukeyi yana faman kashe mata narkakkon eye's d'insa yace. "Humaira kina sona?!" Ta kallesa ta tuna ajinsa da matsayinsa da kud'insa da martabarsa tun tana cikin duhun kai amma yazo yana rok'on ta so shi duk da har yanzu bata kai matarsa ilimi ba amma itama ta waye dan duk wanda ya kalleta sai yayi tunanin ko ta kammala degree ko tana kanyi. Murmushin jin dad'i tayi sannan tace. "Ina sonka amma sai kayi k'ok'arin wajan Musanya Zuciya ta daga kan doctor domin har yanzu yana cikin Zuciya ta bazan munafince kaba." "Aisha...! Are you in your right sence?I'm your husband but kullum sai kin min zancen marigayi why? Please we should help ourselves in one way or the other. Yanzu dai am asking you kina sona??" "Eh ina sonka.. I love you." Yana jin ta fad'a ya mik'e tsaye tare da yi mata alama da ta zo su wuce. Har ya d'an tafi yaji ta rik'osa ya kalleta fuskarta a narke ya tsaya yana zaro ido yace. "Menene kuma?!" INdo tace "kayi hakuri nafa ce ina sonka." Rik'ota yayi yana murmushi sannan ya kar6i mayafin ya yafa mata suka fito ya kulle falon still yaga tana kallonsa yaje ya rungume yana cewa. "Is okay cutie na yadda but sai kin fara nuna min from now on kinji ko?!" "Toh.." Ta fad'a tare da gyara swagger bag d'in hannunta. Itace ta fara fita shi kuma ya tsaya rufe gidan. Zaune taga Fateema tana danna waya a gaba ta yatsina fuska ganin sai dai fa ta shiga baya sannan taje ta zauna suna yiwa juna kallon yake har ya shiga shima ya zauna ya tayar da motar suka tafi. Suna zuwa tare suka shiga lokacin har an kawo kayan anata gani. 'Dakin Mama suka shiga nan suka ga su Hawwah aikuwa suka had'u suna ta hirar su. Har aka yi magrib suna tare sai da INdo ta cire mayafi ta shiga toilet tayo alwala tana fitowa taga suna kallonta alamar dai sunyi gulmarta Hawwa tayi dariya tare da cewa. "Su aunty Humaira kuma ashe-ashe...." INdo ta ta6a baki cikin rashin fahimta tace. "Ashe-ashe me?!" "Wallahi matar broth wannan ciki ne, haba shi yasa sai wani shining kike yi sannan kin kuma yin kubul-kubul ga shi kuma ya fita." "Toh ai ba haramun bane ko kin manta a gidan miji nake. Allah sister Hawwah keda Hali dubu (Haleema) kun saka min ido ya isheku haka." Tunda suka fara magana Fateema take kallon cikin INdo, tabbas wannan ciki ne ba te6a ba. K'irjinta ne ya dinga bugawa yana mata wani rad'ad'i har tana jin tamkar zai fasa mata zuciya. Lallai no wonder taji Sadeeq yanzu baya mata zance yana son yaga ta haihu ashe tuni yaje ya kunsawa INdo. Babu wanda beyi magana ba a cikin d'akin face Fateema domin idan tace zata tanka babu shakka hawaye zata yi har a samu wasu suce bak'in ciki takeyi mata, sai kawai tayi shiru dama a kwance take hakan yasa ta lumshe idanuwa har aka kira sallan isha'i sannan ta fita basu sake sanya ta a ido ba har Sadeeq yazo d'aukar su... *Page d'in naki ne aunty Mammn Mu'aleem. Ina fatan zai sanyaya miki rai kamar yadda naji dad'in kulawarki.*🤩 *HAJJA CE*👈 [7/31, 5:13 PM] Aisha Galadima: *⚗⚗ MUSAYAR ZUCIYA...⚗⚗* ♥♥ ♥ A true life story Na *K.A.S Precious Hajja ce*👈 *HASKE WRITER'S ASSOCIATION*💡 (Home of expert & perfect writer's) *DEDICTEED TO:* Sanah Isma'il Matazu. *VOTE me on wattpad @Hajjac* Page *35* Shirin zuwa Sumaila kauyen sani suke farin ciki ya cika zuciyar INdo har ta kasa 6oyewa, kallonta yayi bayan ta rufo d'akinta ta juyo gashi cikinta ya fito yace. "Cutie koma d'aki gaskiya mun fasa zuwa." K'irjin INdo ya shiga bugawa hankalinta duk yayi mugun tashi ta kallesa dan san tabbatar da maganarsa. Gani tayi yana dariya hakan yasa ta yin kansa zata dokesa yayi saurin guduwa cikin shagwa6ar da ta farayi wadda yanzu take neman zame mata jiki tace. "Ka tayar min da hankali Allah ya dawo damu lafiya sai na rama." Fitowa suka yi suka shiga mota Sadeeq ya d'auki hanya, wannan karan cikin hira suka ta kai da ka gansu kasan masoyane sa6anin lokacin da aka ce ya kaita garinsu ya dinga kumbura tamkar wanda aka sanyawa yeast. Cikin kwanciyar hankali suka shiga garin sumaila, suna zuwa kan kwanar da zasu shiga kauyen sani adeeq ya kalleta yana murmushi yace. "Cutie ga barkono da gyad'a bazaki siya bane?!" Juyawa tayi tana kallon gurin kafin tace. "Eh wallahi kuwa, dan Allah kaje ka siyo min kwano d'aya-d'aya." "Ke wasa nake miki ni." Ya fad'a yana tafiya, kallonsa tayi shima ya kalleta tare da d'aga mata girarsa. Hannunsa yasa ya janyo nata yana matsawa ta lumshe idanuwa tana shafar cikinta da d'ayan hannunta. A k'ofar gidan su yayi parking, gidan yana nan yadda yake tun lokacin da Abubakar ya gyara musu katangar su ya maida ita ta bulo sa6anin da datake na k'asa. INdo ta kallesa tare da Kama hannunsa tace. "Wait for me, naje na sanar ma Inna zaka shigo ku gaisa." "Hmm lalle wariyar launin fata, meyasa ni bazan shiga direct ba sai an wani yi min iso? Ban yadda ba tare zamu shiga kema ai idan mukaje gidan Mama wani sa'inma kina rigani shiga." "Hehehehe lallaima, toh ai ni macace zan iya shiga direct, kaifa sabida su Mubasheer na zuwa su shiga kai tsaye kasa duk muke kulle gidajen sai an buga munji ko waye sannan mu bud'e." "Toh ai ni har yanzu saurayi ne, su kuma su Inna sun tsufa toh meye a ciki." "Kai My super glue, wallahi Inna ta ba tsohowa bace rayuwa ce kawai ta maida su haka amma ka bari na kammala karatuna sannan cinikin zo6o ya kankama zaka sha mamakin Inna da baba wallahi. Kuma kasan dai ai abban ku dasu Mama sun girmi su Innata." "Kaiii cutie..?!" "Yanzu dai bazaka barni in shiga ba." Tayi maganar tana turo baki,janta yayi kasan cewar tinted glass ne yasa ba'a ganinsu. Sadeeq ya shafo cikinta tare da cewa. "Yau dai ina zata ga k'ok'arina, but dan Allah cutie karki bari ta ankara harsai nazo mun gaisa na fito, wallahi kuma sai naji inajin kunya." "Kunya kuma? Hahahah ta6 ai aikin gama ya riga ya gama, yanzu wannan abun taya yaya za'aiyi ya 6oyu? Dama hijabi ne ko duguwar riga shine zan iya d'anyin dabara amma ai yanzu kuwa ka makaro hakan nan zan shiga Inna ta gani kuma ka shiga ku gaisa da ita." Sadeeq ya turo bakinsa tare da dafe kuncinsa yana kallonta yace. "Toh ya zanyi? Dole na shigo tunda an banike." Tana dariya ta bud'e k'ofar yaran unguwar da suka zo gurin suka dinga kallon INdo wasu na cewa itace wasu kuma suna cewa ai k'anwar Inna ce dan ga kama nan. Gidan ta shige tana dariya jin abinda suke fad'a, tana zuwa tsab ta ajiye cewa itace 'yar fari ta d'ane Inna dake sharce gurin da tayi wanke-wanke. "Oh ni Maryamu waike yaushe ne zaki san kin girma 'yar nan.?!" Inna ta fad'a tana janye jikinta daga na INdo. Dariya kawai ita kuma takeyi tare da kallon Innar tana cewa. "Kai Inna Oyo-yo fa mukayi, nayi missing d'inku wallahi Inna dake da baba tunda aka kaini baku jeba sai su d'an rainin hankalinnan Sagiru..." "Ga INdo... Ga INdo, yeeeeee sannunku da zuwa." Nafeesah ta fad'a tana rungume INdo, murmushi tayi cikin nunawa wayewa da kuma zaman birni tare da nuna zaman teburin class ta kamo hannunta tace. "Su Feenah 'yan mata daga ina haka..?!" Ta fad'a tana jan hannunta suka nufi cikin d'akin Inna. "Kinga Feenah d'auki tabarmar baba ki shimd'a anan sabida Malam Sadeeq zai shigo su gaisa da Inna." Sabuwar tabarmar malam Hamza aka shimfid'a sannan INdo ta ciro d'ari biyar ta bawa Nafeesah cikin k'asa-k'asa da murya tace. "Mazaki siyo min lemon roba da ruwa zanba shi yasha." Kar6ar kud'in Nafeesah tayi sannan ta fita da saurinta, sai da ta kuma tsayawa wajan Sadeeq yana tsokanarta kafin ta wuce zuwa shagon da zata iya samowa mijin yayarta ta lemo da ruwan jarka. "Sannun ku da zuwa, ke d'aya kika zo ko hardashi me gidan naki?!" "Inna tare muke dashi zai shigo ku gaisa ma, wai ina baba?!" "Malam yana can gurin sana'arsa, bari wani ya shigo sai yaje ya kirasa ku gaisa." INdo dake bakin gadon Inna na k'arfe tace "toh.". 'Dan kuma gyara d'akin tayi sannan ta share shi ta ciro turare a handbag d'inta ta fesawa d'akin da kan tabarmar da Sadeeq zai sauna sannan tace. "Inna bari nace ya shigo ko? Karya ga an barshi a mota shi d'aya." "Toh kice ya shigo barina saka mayafi na nima." Fita tayi suka yi karo da k'awarta Uwani da Sahura da alama sunji labarin zuwanta. "Ahhhh kaga su hajiya INdo amaryar Malam Sadeeq oh harda su abinga." Sahura ta fad'a tana d'aga mayafin jikin INdo, kaf d'insu sunyi wani bululumu dasu Uwani ma harda tsohon ciki kai idan ka gansu bazaka ce k'awayanta bane sabida tsabar yadda kalar wayewar ta bambanta. "Kai sahura kina nan da gulmarki, ku shiga ciki ina zuwa." Ta fad'a tare da dukan bayan Uwani ganin yadda ta rik'e ha6arta tana kallonta. Cikin gidan suka shiga ita kuma ta shiga motar Sadeeq wanda ke jingine jikin kujera ya sanya hularsa a fuska yana kuma zagaye kwantaccen quarter million d'in fuskarsa. Jin an bud'e k'ofar motar ne yasa shi cire hularsa ya kalleta, zama tayi tana kallonsa da murmushi a fuskarta yace. "Uhmmm wato anzo gida harma kin manta tare muka zo ko?" Hannunsa ta kamo cikin nata cikin kalar jimami tace. "Ni na isa, tunda na shiga mafa koda Inna bamu gaisa ba kuma babu kowa duk basa nan amma ni banajin zan iya mantaka a yanzu domin ka zama ni na zama kai kadena sawa ranka cewar duk inda zan shiga wai Zan manta dakai no, idan nayi haka toh Zan iya mantawa da kaina nima." Sadeeq ya lumshe idanuwa tare da jan hannunta murya a shak'e cikin wani irin salo yace. "Kina nufin kenan munyi *MUSAYAR ZUCIYA* dani dake a yanzu? Ba kamar da ba yadda kike nuna min cewar zuciyarki ta M twinnie ce shi kad'ai yanzu zaki iya mallaka min ita...?!" "Sosai ma kuwa na baka ita ina fatan ka rik'eta amana. Anan aka d'aura mana aure dan haka anan na kuma baka amanar kaina da duk abinda ya shafeni." "Na kar6a cutie Allah kuma ya bani ikon rik'ewa gam-gam, a baya ma *Illar Zuciya* ce tasa nake ganin kamar anyi min ba dai-dai ba amma a yanzu..." Yakai bakinsa kan hannunta ya sumbace shi yana kashe mata idanuwa tayi saurin kawar da kai tana dariya. Nafeesa ta hango hakan yasa INdo fitowa da sauri. Amsar aikenta tayi ta shiga ciki Nafeesah kuma ta tsaya a gurinsa suka dinga hira har su Shehu suka dawo suma suka gaida shi. Cikin gida kuma INdo ta gama jerawa Sadeeq abin tarba dan inna ta gama dafa wake da shinkafa Allah sarki harda yanka mai lawashin albasa kuma duk INdo bata hana ba domin ta haka ne zata iya kuma tabbatar da kaunar da yake cewa yana mata dan marigayi baya kyan-kyamin duk abinda zata bashi bare yanzu tasan kanta tasan me takeyi ta kuma san waye mijinta. "Lallai INdo wai duk malam Sadeeq d'in kikewa wannan tanadin?!" Uwani ta tambaya tana ta6e baki, gani take kamar INdo ta zurma da yawa duk miji akewa wannan hidimar. "Toh Uwani bakin ciki kikeyi ko me? Ina zan samu kifi ma dan yana son wake da shinkafa da kifi ko dafaffen kwai." "Ta6 lallai INdo Hamza, toh k'ila dai yana baki kema ba irin muba da sai dai komai kayiwa kanka." "Kwaji dashi gulmammu, Inna bari naje nace ya shigo." Tana fad'a ta kuma fita tace ya shigo. Jerawa suka yi shida Nafeesah yana kallon INdo daga baya. Gaskiya ikon Allah baya k'arewa a duniya ko kana menene sai ya nuna ikonsa akanka yau shine da INdo harda kunshin cikinsa a jikinta "Allah astagfurullah." Ya fad'a cikin ransa tare da shiga gidan yana sallama, su Sahura da Uwani suka amsa bakinsu a washe yayin da Inna ke tsaye kanta a k'asa sam bata iya kallonsu tun zamanin Abubakar. Cikin d'aki Nafeesah ta shigar dashi ya zauna yana sosa keya yana shafa wuya. Daga bak'in k'ofa Inna ta tsugunna suka gaisa da Sadeeq sannan su Uwani ma suka sake gaidashi duk da cewar sun gaidashi a cikin mota INdo ta kallesu tare da makewa Sahura hannu ganin yadda take leken sadeeq tana wangale baki. "Kedallah can malama kina da miji kina kallon mijin wasu haba." "Kai INdo bana san herri." Tashi Inna tayi ta shiga rumfar malam Hamza bayan ta tura Nafeesah tace ta kirasa. Kallonsu tayi tace. "Zan shiga daga ciki, karku ce na barku anan." "Lallai ma INdo toh ba abinci zaici ba? Toh ki zauna muyi shira mana kafin ya gama." Uwani ta fad'a tana hararta cikin jin haushin yadda take wani nan-nan da malam Sadeeq sai kace su basuda mijin. "Toh kuje ku gama muna nan hajiya INdo." "Toh hajiya Sahura." Itama ta fad'a tare da shiga cikin d'akin. Kallonta yayi ta zauna kusa dashi tare da d'akko Coca-Cola ta bud'e mai cikin halin damuwa tace. "Kayi hakuri kasha a haka da bakin jarkar, nan gidan bamu da kofuna kaji my super glue ka daure." "INdo Aisha ta zaria med'an kallabi..!" Ya fad'a tare da matsawa kusa da ita. Lek'awa yayi k'ofa aikuwa karaf suka had'a ido dasu Sahura da Uwani suna lek'owa yayi dariya tare da Kai bakinsa saitin kunnen INdo yace. "Gaskiya d'aliban nan nawa gulmammu ne, sai lek'en mu suke kamar a gidan zoo." Itama dariya tayi cikin hillata da shagalta yaci wake da shinkafar nan dan sai da suka cinye ta cikin kwanon silbar da Inna ta kawo musu. Suma su Sahura da suka kasa suka tsare aka zuba musu sukaci lokacin malam Hamza ya shigo fuskarsa kunshe da fara'a Sadeeq yayi saurin tura kwanon gaban INdo da ragowar lemonsa da ledar yajin ya maze sai wani danne-dannen waya yake shi a dole beci da yawa ba. INdo kuwa banda dariya babu abinda takeyi mai amma still ya maze su Uwani na jiyo ta sai mamakin abinda yasa ta dariyar suke yi. "Sadeequ ashe kunzo? Sannunku da zuwa. Ah kaga uwata an zama manya." Sadeeq ya fara motsi yana gyarawa malam Hamza guri dan ya shigo. Gaida shi suka yi sannan yayi ta sanyawa Sadeeq da marigayi albarka ganin yadda INdo ta canza tamkar ba 'yarsu ba. Tare da malam Hamza Sadeeq suka fita ita kuma INdo ta koma tsakar gida gurin su sahura Inna ma taje ta zauna. Suna zaune Rukayya ta shigo murna ba'a magana sabida ganin INdo da ciki, nan fa suka shiga hira baji ba gani amma duk da haka zuciyar INdo bata manta da Sadeeq a mota ba. Nafeesah ya d'auka suka shiga cikin garin har sai bayan sallan la'asar sannan ya dawo dan su tafi. "Gaskiya Inna zan baki kud'i a hannunki a samu dan Allah a gyara band'akin nan, habba wallahi za'a iya d'aukar larura tunda aka haifeni a haka yake. Ga dubu sha biyar nan ita kad'aice a hannuna nasan k'ila malam Sadeeq zai bawa baba ma wasu amma idan be bayar bama dan Allah Inna a fara da wannan kud'in ko buhu d'aya ne na siminti a siyo a malale k'asan band'akin can kosu Sagiru ne da Shehu sai suyi ai sun iya." Kwallah Inna ta share tare da yin godiya sam bata ta6a tsammanin akwai ranar da 'ya'yanta zasu yi mata wani abunba ganin itama ba tayi wa nata komai sabida rashi gashi ance sai kanayi za'ayi maka. "Inna ya kike kuka? Karki bari na tafi haka dan bazan yafewa kaina ba bayan na barki cikin kuka." Murmushi Inna tayi tare da cewa. "Allah nakewa godiya 'yar nan domin ban ta6a zata zanga irin wannan ranar ba musamman akanki, sai gashi Allah ya shirya minke ya kuma azurtaki gashi har kina tallafa mana da abinda kike dashi, Allah yayi muku albarka dukanku." "Amin Inna ta, karki damu dana gama karatu na kware insha Allah zanyi kud'i duk gidan nan sai an gyarasa." "Toh Allah ya yassare miki." "Feenah dan Allah idan ya koma kwara state zan cewa Sagiru ya kawoki mu zauna tare ko bakya so?!" "Ke! Ina so mana ai wallahi kin more gidan miji INdo." Mtwww "Ban hanaki cemin INdo ba gatsal? Ki kirani yayya Aisha ko Yaya INdo karki sake cemin wani INdo mara kunya." Kallonta Nafeesa tayi tana ta6a baki kafin ta kad'a kai tabar d'akin. Har zaure Inna ta raka ta tana yi musu fatan alkhairi bayan Sadeeq yazo sunyi sallama. Dubu d'aya ta kar6a gurin Sadeeq ta bawa su Sahura su raba d'ari biyar-biyar suka dinga godiya suna k'ara jinjina arzikin da INdo ta samu sannan ta shiga mota suka tafi cike da farin ciki. *** Kwanaki biyar yayi bayan sunje kauyan Sani sannan suka d'aga suka tafi kwara state da Fateema bayan yayi yayi da INdo ta bishi tak'i sabida karatunta. Yana tafiya da kwana biyu tasa Sagiru ya kawo Nafeesa duk ranar school d'inta zasu je tare ta zauna a barandar ajinsu INdo idan sun tashi su koma gida ta koya mata abinda ta iya itama hakan ya k'ara bud'e brain d'inta ga cikinta yana ta girma cikin kwanciyar hankali. Duk wata Sadeeq suke dawowa kuma INdo bata nuna damuwarta duk da bata son tafiyarsa amma bata son nuna mai dan karya kansile mata karatunta, gashi dama ya sanyata a makarantar dare ta islamiya ta matan aure anan unguwarsu hakan yasa ta kuma zama busy tana kuma wayewa ta fannoni da yawa a cikin rayuwarta. Cikinta har ya shiga 10months bata haihu ba sai dai yayi girma har bata iya zuwa ko'ina. Ranar wata laraba cikin dare ta farka lokacin Sadeeq na mak'ale da ita duk da girman cikin jikinta hakan baya hanashi nanik'arta. Kallonsa tayi tana faman rintsa ido cikin wani irin mugun rik'o yaji ta rik'e mai hannu hakan yasa shi saurin farkawa. "Cutie what happen?" Shiru sai cizon lips d'inta takeyi tana matse idanuwa ya mik'e tsaye ya sakko yace. "Cutie kodai haihuwa ce? Bari nazo muje asibiti." A gigice ya sanya jallabiya ya zari mukulli yayi parking lot. Motar ya fitar da ita shiru garin babu kowa ya kuma komawa gidan da kyar ya kimtsata ya fito da ita mota lokacin mak'ocinsa ya leko sabida yaji k'arar mota. Ganin halin da ake ciki ne yasa shi taso matarsa ta bisu zuwa asibitin. Duk ya rud'e ya bugawa Fateema ya gaya mata itama hankalinta ya tashi gashi babu abin hawa bare tabisu gata mace. Ganin abun yayi yawa ne yasa suka kira Sadeeq d'in ciki INdo tana ta kuka ya rik'e hannunta zuciyarsa na bugawa da k'arfi da k'arfi tace. "Dama a makaranta malama tace idan mace zata haihu k'afarta d'aya a duniya d'aya kuma a k'abari. Malam Sadeeq kayi hakuri nasan nima yau dacta zan..." Sadeeq yayi saurin rufe mata baki yana kad'a kai, da k'arfi ta fizge kanta ta juyar da kai tana ci gaba da magana. "Sai na fad'a d'in ka bari in gaya maka mana, dacta zanbi nima yau amma dan Allah tunda ance namiji zan haifa dan Allah koda na tafi malam Sadeeq ka sawa d'an suna Abubakar Sadeeq kar kuma a 6oye mai suna dan Allah." Jikin sadeeq ya dinga rawa gumi gaba d'aya ya gama jik'asa, tana gama yin magana kawai nurse d'in dake gurin tasa hannun zureren jariri ya santalo kan hannun nurse d'in INdo na kwance tayi shiru yayin da Sadeeq ya bud'e baki yana kallon fuskarta gumi na d'iga akan hannunta na jikin fuskarsa.... *Fatan alkairi gareku masoya, a koda yaushe Ina alfahari daku cikin labarin MUSAYAR ZUCIYA. Hajja ce take muku fatan alkairi tare da d'in bin godiya marar adadi*💘 *HAJJA CE*👈 [7/31, 5:13 PM] Aisha Galadima: *⚗⚗ MUSAYAR ZUCIYA...⚗⚗* ♥♥ ♥ A true life story Na *K.A.S Precious Hajja ce*👈 *HASKE WRITER'S ASSOCIATION*💡 (Home of expert & perfect writer's) *DEDICTEED TO:* Sanah Isma'il Matazu. *VOTE me on wattpad @Hajjac* Happiest bday ASMY B ALIYU🎉you are truly one of the most amazing writers I knw..Forever and a lifetimes to come tawan...🎊 Page *34* Tana fita napep ta tare ya kaita gidan su. Tana shiga ta fashe da kuka tare da fad'awa kan kujerar d'aya daga cikin falon. "Ke lafiya kuwa kamar wadda aka yiwa mutuwa?" Cewar yayan ta Shamsu yana kallonta, Fateema bata yi shiru ba tana ta kuka Shamsu ya tashi ya dinga mata fad'a yace idan baza tayi magana ba ta tashi ta koma inda ta fito. Mama ma kallonta take yi tana jiran jin abinda zata fad'a ranta cike da addu'ar Allah yasa ba tsakaninta bane da mijin. "Ke wallahi karki bari na tashi tsaye dan sai na fasa miki baki, aikin banza kawai kiyi magana shine zaki tsaya yiwa mutane kuka." "Mama Sadeeq ya munafurce ni, Mama be ta6a gaya min matarsa Aisha nada ciki ba sai yau da muka gani gashi har ya fito. Wallahi bazan koma gidan saba yaje can su k'arata munafiki kawai, dama ance duk wacce ta d'auki namiji uba toh lallai zata mutu ma..." Mtwww "Shut-up Fateema, bakida hankali ne? Toh sakinki kike so yayi?!" "Nidai kam bazan koma ba yaje can su k'arata." "Toh idan ya sakeki sai kizo na aureki nine kawai idan na aureki za'a haramta min k'ara aure bare har matar ta rigaki haihuwa." "Yaya Shamsu ka aureni kuma?!" "Eh toh kince maza ba 'yan goyo bane, kinga ni uwa d'aya uba d'aya muke ki goyani na goyaki babu mejin haushin wani, amma ko barin Sadeeq kikayi toh wani mijin zaki aura kuma shima wata ran zai miki wani abun sannan ba lallai ki kuma samun saurayi ba sai da kema ki shiga gidan wata." "Umma...." "Karki min magana Fateema, dai-dai gwargwado kina da ilimin addini shin na zamani ne ya rinjayi da addininki ko kuwa wani saban iskancinne haka? Karki manta wannan auran nasu had'in Allah ne duk wanda yace zai ja da ikonsa akan lamarin toh bazai kwana cikin jin dad'i ba. Fateema karki manta nima da yanzu bani bace mahaifiyarku, amma kinga da yake Allah yayi ta hanyata zai samu haihuwa sai ya d'auke matarsa ta farko da kyar mahaifinku ya yadda ya aureni da yace ya gama aure amma a satin da na tare a satin na samu cikin yayan ku ki gaya min da mahaifinku yayi butulci ya kafe akan bazai sake aure ba ta wace hanya zai sameku tunda Allah yayi yana da rabonku a duniya?!" Fateema ta kuma fashewa da kuka tare da mik'ewa zaune tace. "Toh Umma kiyi hakuri wallahi sharrin shaid'anne, amma kuma me yasa koda wasa be gaya min ba ya yi min shiru sai yau naji na kuma gani?!" "Hmm Fateema kenan, toh ko tunda kuka yi auran Sadeeq be ta6a kusantarki bane har sai da aka yi musu aure da ita Aishan?!" "Kai Umma.." Fateema ta fad'a da alama nauyi tambayar tayi mata, kallon Yaya Shamsu tayi k'asa-k'asa kawai suka had'a idanuwa ya zabga mata harara tare da cewa. "Ke..! Kallon me kike yi min haka? Ko kin d'auka bansan meye auran ba sai ke kika sani.??" Da sauri ta zaro udanuwa hannunta a baki tana girgizawa tare da kallon Umma Fateema taga Umman ma ita take kallo, lallai Yaya bashi da kunya ma wallahi a gaban Ummansu. Koda yake itace ta kallesa dole yayi mata bayani. "Fateema karki yadda ki nunawa mijinki bak'in cikinki akan cikin matarsa, ina son ki nuna masa kinfishi son cikin ma. Sannan karki bari abban ku ya dawo ya ganki a cikin gidan nan wallahi kinsan ranki ne zai 6aci abanza, gara kije kiyi zaman aurenki har Allah ya baki kema wata rana idan kina da rabo." "Toh Umma, amma dan Allah ki tayani da addu'a dan wallahi ina jin zuciyata nayin zafi da nauyi." "Kidena sawa a ranki insha Allahu zaki ji bakya ji shaid'an ne kawai yake son shiga cikin lamarinki, ki yawaita azkar zakiji dad'in ranki." Wayarta ce dake cikin jaka taji tana ta ringing amma tak'i d'agawa dan tasan baxai wuce Sadeeq ba ita kuma bata shirya abinda zata ce masa ba. Tashi tayi suka yi sallama Yaya Shamsu yace bari ya kaita gidan da kansa, suna tafiya yana k'ara bata shawarwari wani maganar ma har mamakinsa takeyi lallai yayan nata aure kawai yake jira amma babu abinda be sani ba. *** Shi kuwa Sadeeq k'arfe tara yaje d'aukar su amma aka ce Fateema bata nan, duk an duba bata gidan ya kira ta yafi sau goma amma ba'a d'agawa hakan yasa yace INdo ta fito su tafi. Gidan Fateeman suka fara biyawa amma akulle hakan yasa Sadeeq tafiya yakai INdo gida tunda ranar a gidan Fateema yake. "Malam Sadeeq d'an tsaya a can gurin me balangun can na kan kwana ka siya min." Kallonta yayi sai yaga ita kalle-kalle takeyi abinta cikin mamakin daya mak'ale mai a wuya yace. "Cutie ballangu kuma." "Eh dan Allah kace su sa yaji daban." "Ikon Allah shi kike son ci kenan." "Eh, akwai fura da nono da ake damawa a gurin, ana sa kwakwa da ayaba da madara please dan Allah itama ka siyo min." Dai-dai lokacin suka tsaya a gurin ya kalleta tare da cewa. "Toh ke ya akayi kika son nan gurin harda abubuwan da ake siyarwa.?!" Juyawa tayi ta kallesa suka kalli junansu tayi murmushi tare da cewa. "Bafa zuwa nake yi ba da kai na, a'a ina dai bawa khaleefa yana siyo min nima rannan ne Abba ya aiko min dashi. Naci naji dad'i shine nake bayarwa yana siyo min." "Okey yanzu naji batu na d'auka kinyi tunanin nan ma kauyan Sani ne, kowa zai iya fita san ransa." Baki ta turo tana yatsina fuska ya fita, leda biyu yayo musu sannan ya dawo motar yana kallonta yaga still a shagwa6e fuskarta take ya shareta domin so yake su k'arasa gida zaifi jin dad'in lalla6a ta. A bakin gate ya tsaya ta fito suka shiga gidan, tun a parking space ya rik'ota tana turesa yayi niyar d'aukarta sai dai yana ganin bazai iya ba sabida cikinta gashi ba laifi INdo kamar (Ummi Aisha take ba ruwa na lol). "Goya ni toh." Sadeeq ya zaro idanuwa jin abinda ta fad'a, yana kamo hannunta suna tafiya yace. "Ina tunanin yadda zan iya d'aukarki ke kina cewa na goyaki kin manta abinda yake cikin ki ko." "Toh gaskiya tunda kayi niyya malam Sadeeq to ka goya ni." "A'ah cutie ni ba niyya nayi ba, cewa nayi Ina tunanin yadda zan d'aukeki kekuma ma goyo zaki ce." A bakin k'ofar d'akin ta tsaya ya ajiye leda d'aya kusa da k'ofar yaje ya tayar da gen ya d'auka ta shiga ciki amma sai ya ganta tayi kalar tausayi ta kuma turo baki yayi dariya. "Mata problem. Nan kiyi can tayi Allah ya sa in iya muku." 'Daukarta yayi suka shiga ya dinga k'ak'aro nishi tana dariya, yana ajiyeta ya zauna ya d'aura kansa akan cinyarta. "Masha Allah sati d'ayan da nayi a garin nan yasa kin kuma yin k'iba, nan gaba sai kin kasa tashi cutie Aisha." "Ni kadena cemin nayi k'iba." "Na dena ina balagun naki?ko bazan ci ba?!" INdo tace. "Kaje kuci kaida Fateema nima kaga mu biyu zamu ci wannan." "Nak'i wayon wannan zanci." Tashi yayi yaje ya shigo da ledar ya kuma zuwa ya d'akko plate da zo6o tare da kofina ya ajiye, anan falon ya rage kayan jikinta ta zauna daga under wear sai have vest kasan cewar yanzu bata sanya bra tana d'an takura mata ciwon k'irji. Kallonta yake tamkar zai shige cikin jikinta farat d'aya, remote ta d'auka tare da kunna TV ta juyo zata ci naman taga sai kallonta yake cikin mamaki tace. "Wai ya haka ne?!" Sadeeq ya shafa k'eya tare da komawa kusa da ita ya zauna ya sanya hannu ya rik'ota tare da kwanciya a bayanta murya sassanya yace. "Aisha banyi tunanin zaki dawo haka ba, lokacin da kuna j.s one ko k'irg..." Bata bari ya k'arasa ba tayi saurin rufe mai baki da hannunta. Dariya ya dinga yi ta d'auki naman tafara ci sannan ta sakar mai baki yace. "Zanci." 'Daukowa tayi ya rik'e mata hannu, fuskarta ya kama sannan ya sanya bakinsa a hankali cikin nata sai faman zaro ido takeyi. Gani tayi ya ciro na cikin bakin nata yana k'arasa taunawa ta bishi da kallon mamaki, yanzu kam ta tabbatar da cewa Sadeeq yana sonta, a shirye yake tsab da ya shiga cikin rayuwarta yayi mata duk abinda take so. Jiyayi kawai ta rungumesa tsam a jikinta a hankali kuma yaji tana zubar da hawaye ya d'agota yace. "Sorry na 6ata miki rai ko? Bazan sake ba, bana son ganin hawayenki musamman ace nine silar zubar su." Sabo ta d'akko tasa mai a bakin yayi murmushi ya fara taunawa idanunsa akanta, tana ganin ya fara taunawa itama ta rintsa ido tare da kai nata bakin cikin nasa kamar yadda taga yayi mata ya tura mata shi a bakinta da kanshi sa6anin shi da ya ciro nata da harshensa. "Ashe ba haushi kikaji ba d'azu?!" Ya fad'a yana lasar lips d'inshi. Juyawa tayi tana murmushi ta fara dangwala yaji tana sawa a baki. Mik'ewa yayi yana gyaran rigarsa yace. "Na tafi na tabbata duk inda taje yanzu ta dawo, idan na isa zan kiraki." "Toh a gaida ita." "Ba rakiya?" Dariya tayi ta mik'e suka fita tare, kamar karsu rabu haka sukeji amma babu yadda zasu yi dole ya fita ita kuma ta rufe gidan ta koma ciki zuciyarta fal Sadeeq domin ya tafine ya barta da abinda bazata ta6a manta shi bakoda da second d'aya ne. **** A falo ya zauna tare da d'aukar laptop d'insa daya bari jikin charge. Fateema na jinsa ta d'an Lek'o har lokacin tunanin abinda zata cemai takeyi, ganin tana k'arasa 6ata lokaci yasa tayi shahada kawai ta shiga falon tana sanye cikin kayan bacci me wando k'arami wanda ko cinyarta be gama rufewa ba. Kusa da k'afarsa taje ta zauna, shafar k'afar ta farayi wanda take cike da kwantaccen bak'in gashi. Sak'e mak'alo k'afar tayi sannan ya saki mai kuka a hankali hawayen na sauka a k'afarsa, har cikin zuciyarsa yake jin kukan amma ya shareta yana aikinsa, ganin haka yasa ta fara magana. "Baby kayi hakuri dan Allah, wallahi raina ne ya 6aci akan abinda ka 6oye min kaida Aisha." Jin abinda ta fad'a ne yasa shi cewa, "Me kuma muka yi? Duk abinda muka yi Fateema ya dace idan har na kiraki ki amsa min amma kikak'i toh ina kikaje ma tukunna..?" "Kayi hakuri baby, yanzu duk matsayin da nake a gurinka na matarka ace ka kasa gaya min cewar Aisha ciki gareta? Ko kana ganin kamar zan cutar da itane? Wallahi kaji dalilin da yasa kawai da na gani yau kawai sai na tafi gida, can kuma ina zuwa Yaya Shamsu ya dinga min fad'a, baby kayi hakuri da 6ata maka rai danayi dan Allah." Zuciyarsa ce tayi sanyi jin itace ma take basa hakuri, ture laptop d'in yayi tare da janyo ta jikin sa. Gashin kanta da bata mai kitso ya dinga shafawa sannan ya numfasa yace. "Kamata yayi tunda nine na kaiku duk abinda zai faru ki tsaya naxo na d'auke ku, amma ba komai nasan sharrin iblis ne. Sannan kuma ke ya kamata nayiwa wannan k'orafin cewar baki sanar min da cewar Aisha nada ciki ba sabida ku na bari tare har tsawon 3months amma baki gayan ba sai da na dawo na gani why baby?!" Fateema ta d'ago tare da kwantar da kai cikin maganar tace. "Wallahi ban ta6a lura ba kuma dai gaskiya bana wannan tunanin ganin nima har yanzu babu. Sai d'azu da na ji Hawwa na fad'a kuma na gani a zahiri." Sadeeq ya sake kamota tare da cewa. "Kinga kenan duk babu me laifi, Fateema bana son ki tashi hankalinki domin ina sonki a duk yadda kike. Kema Allah ba mantawa yayi dake ba domin da yawan aikin ne toh da yaci ace kema yanzu kin kusa ma saukewa amma fa Allah me meyi, yanzu three months da tafiya ta ita kuma cikinta wata hudu kinga kenan bayin kaina bane. Ina son dan Allah karki tayar da hankalinki rashin haihuwarki bazai rage soyayyarki ba a cikin Zuciya taba *I love you* Fateema Allah shine shedata." " *I love you too* baby nima ka taya ni da addu'a na samu kafin na mutu." Shhhiiii yayi mata bayan ya d'ora yatsansa akan lips d'inta. Shiru tayi sannan ya janyo ledar da ya shigo da ita taje ta d'akko cup's ta zuba musu furar suna manne da juna suna cin abin su idansa akan agoga yana son ya kira INdo kamar yadda yayi mata alk'awari. Daya rasa yadda zai yi kawai sai ya tura mata text message. "Affuwan cutie na ba credit da yawa a ciki gashi masu shops sun rufe, zamu had'u gobe I love nd miss you (#DeepKiss)." Yana ganin sak'on ya tafi ya gogesa tas daga cikin wayar (tamkar miss Xoxo da take da cutar clearing masseges). INdo na kwance ta gama duba littafin ta taji shigowar sako, a hankali d'aya bayan d'aya (word by word) ta karance sakon kafin ta tattarashi ciki kwakwalwarta ta sake nanata sakon gaba d'ayan sa sannan tayi murmushi ta kashe wayar ta kwanta, wani sabon yanayi na soyayyarsa yana shigarta haka ta dinga murmushi ita kad'ai a kan gado har bacci ya d'auketa. Yayin da shi kuma yake can suna soyewa da Fateema wadda itama fatan ta da burinta da addu'arta a daren be wuce itama Allah ya azurtata da ganin gudan jininta ba. *HAJJA CE*👈 [7/31, 5:13 PM] Aisha Galadima: *⚗⚗ MUSAYAR ZUCIYA...⚗⚗* ♥♥ ♥ A true life story Na *K.A.S Precious Hajja ce*👈 *HASKE WRITER'S ASSOCIATION*💡 (Home of expert & perfect writer's) *DEDICTEED TO:* Sanah Isma'il Matazu. *VOTE me on wattpad @Hajjac* Page *36* Gurin d'ayar nurse d'in ta k'arasa ta bawa baby boy d'in kafin ta dawo gurin ta kalli Sadeeq dake shafar kan INdo yana hura mata iskar bakinsa ganin bata bud'e ido ba. "Angon k'arni leave us please kafin a gama shirya ta." Da kyar Sadeeq ya iya yin magana ba tare da ya kalli nurse d'in ba yace. "Ki fara duba ta tukunna naga tayi haka bata k'ifta idanuwa sosai." "Ah karka damu wannan ba wani abu bane ba, kawai wahalar haihuwa ce kad'an bamu guri tunda kaima ka bamu gudun mawa." Tashi Sadeeq yayi yana kallon INdo wadda idanunta ke a rufe sannan ya fita. Maman Sayyid mak'ociyar su da suka zo tare ta kallesa tana zaune ta mik'e duk da cewar tajiyo kukan jariri tace. "Malam Sadeeq yayi ita d'in?!" "Sun ce zasu gyara sune but ni banga ita Aishan tana wani abu ba da zai nuna min cewar komai normal ba." "Insha Allah komai lafiya lau karka damu shi yasa banso ka shiga cikin ba naso ace kawai sai dai a kiraka ace kazo ka gansu." Numfashi yaja tare da yi mata godiya sannan ya wuce masallacin dake cikin asibitin kasan cewar anata kiran sallan asuba. Kafin ya dawo daga massalacin an gama kintsa su duk da basu zo da kayan haihuwa ba, nurse d'in da ta k'arbi haihuwar tana siyar da kayan babies ta sanyawa yaron ita kuma INdo ta bata sabon zani wanda shima itake siyarwa ta d'aura tare da bata maternity pad da pant. Resting room aka maida su Maman Sayyid na zaune kusa da ita tana mata barka INdo kuwa ji take wani girim-girim ganin cewar wai yau itace ta haihu ga d'ama har tana bashi yana shi. Sadeeq kuwa sai da ya gama sharara addu'a sannan ya fito daga massallacin har gari ya d'an fara yin haske. Yana shiga reception yaga Fateema tana kalle-kalle tana juyowa kuwa ta ganshi dai-dai lokacin nurse ta fito ta nuna mai d'akin da aka kaisu. "Baby ina kwana? Ya su Aishan?!" Ta fad'a tana kallonsa kai da ka ganta kasan itama tunda ya sanar mata suna asibiti bata samu wani ishasshen bacci ba. Hannunta ya kama ganin babu mutane suka shiga cikin d'akin da su INdo ke kwance Maman sayyid na ganin su ta mik'e daga bakin gadon tana musu murna. Rufe idanuwa INdo tayi dan wata irin kunya takeji azo aga ta haihu. Yaron Fateema ta k'ar6a tana kallonsa yana ta bacci yasa yatsansa babba a cikin bakinsa, ta k'arasa wajan Sadeeq dake zaune a wajan INdo ya rik'o hannunta yana murmushi ganin yadda tak'i bud'e ido. Jaririn ya kar6a yayi mai hud'u ba sannan ya ciro wayarsa, su Mama ya kira ya sanar dasu yayin da Fateema ta kuma kar6an yaron ta zauna kusa da Maman sayyid. Yaron jawur dashi me kyau k'irjinta ya dinga bugawa tana dannewa sabida jinsa take inama daga nata cikin ya fito sai dai baza ka gane hakan ba sabida tayi nasarar fin k'arfin zuciyarta. "Wai cutie wa kikejin kunya a gurin nan da kika k'i bud'e idanuwanki.?!" Kad'a kai tayi still idanta a kulle yayi murmushi tare da mik'ewa ya fita. Gurin doctor yaje dan yana son a basu sallama su tafi gida dan kar a cika asibitin. "Mu wuce gidan Mama Fateema." Ya fad'a bayan ya dawo d'akin. Da sauri INdo ta juyo tana yin kamar zata yi kuka tace. "Gidan Mama kuma? Ni dai wannan karan baza ni gidan Mama ba can gida za'a maida ni." "Aisha wane gidan za'a maidake bayan haihuwar fari ce.?!" Sadeeq ya tambayeta bayan ya mik'ar da ita zaune. "Sani, ni dai can zan tafi gaskiya." "Au lallai gidan namu ne bazaki zauna ba?!" Shiru tayi tana tutturo baki su Fateema suka yi dariya kafin tace. "Gaskiya ranka ya dad'e a al'adance haka ake yi, a kaita gida har tayi arba'in ko sittin sannan sunyi kwari ita da baby sai a dawo dasu." "Haka ne kam." Maman sayyid ta sake gasgata zancen, Sadeeq ya shafa kai lallai akwai kwarbai kenan duk da ba zama yake yi ba ai zai so ya zauna dasu ko na d'an wani lokaci ne tayaya zai bari su wani tafi kauyan Sani. Account number d'in nurse d'in ya k'ar6a dan zai tura mata kud'in kayanta sannan ya siya magungunan me jego suka wuce can gidan INdon kasan cewar tak'i yadda ya kaita gidan Mama wannan karan da hankalinta dan haka bazata yadda taje gidan sirikai wankan jego ba. Suna komawa kuwa 'yan uwa suka fara zuwa dole tasa Sadeeq kwasar yanashi-yanashi na gidan ya tafi dasu gidan Fateema. "Allah sarki, dama rabon wannan yaron ne Allah ya d'auke Habu. Gashi daga tafiyarsa har Allah ya bada arzik'in yaro zuk'e-k'e tubarkallah." Cewar k'anwar abban su Sadeeq da tazo ganin d'ah. Hakama duk mutane suka fad'a duk wanda yaji labarin haihuwar wanda hakan sai da yasa INdo yin kuka sabida surutun mutane da tada mata da baya. Haka aka dinga zarya zuwa gidan INdo da nufin idan anyi suna za'a maida ita sani bayan Mama ta nunawa Sadeeq amfanin komawar tata tunda tafi son can. Ba k'aramin k'ok'ari Sadeeq yayi ba wajan ganin ya fita kunyar mejego da baby harma da mutane, Fateema ma be barta haka ba sai da yayi mata na fitar suna sannan itama da su Ummanta sunyi rawar gani sunyi musu kayan barka tamkar ba kishiya ce ta haihu ba. "Cutie me jego, naga alamar haihuwar nan wata wawuyar kunya ta sanya miki why?" INdo ta tura mai baki ya sanya hannunsa yajasa tayi 'yar k'ara tare da d'an dukan hannunsa. Rungumeta yayi kafin yace. "Toh me ake buk'ata na gobe wanda ba'ayi ba.?!" "Ba komai hakan ma mun gode." "Toh gobe dai nasan ganinki zai min wahala sabida mata dan ba shigowa zanyi ba, idan ma kuna son wani abun ki kira Mubasheer ko khaleefa sai ki sanar musu." INdo ta kallesa, wani irin tausayinsa takeji sabida ganin hidimar da yayi tundaga kan abincin sunan da za'aci zuwa kayan rabo na sunan da ragunan da za'a yanka ga kayan barka dayayi musu yace. "Allah yasa ayi taro lafiya cutie, please karki fushi da kowa kinga duk wanda kika gani zuwa yayi dominki domina domin marigayi infact dai kowa yazo ne dan tayamu farin cikin samun k'aruwa. Na tafi sai gobe zuwa dare zan samu mu had'u." Kai ta d'aga sannan ya juya zai tafi, da sauri tasa hannu ta rik'osa sabida wani sassanyan sonsa daya kuma shigarta a d'an tsayuwar da suka yi. Rungumesa tayi shima yasa hannu ya rik'ota yana shafar bayanta murya na rawa yaji tace. " *I love you* Sadeeq forever, I'm also wishing you all the best in your life. You are always by me, to share simple joys and each Nd every need and now with out your loving presence I'm very lonely indeed I love with all my life my husband..." A yadda yaji tana fitar da words d'in ba k'aramin tsumashi suka yi ba, a hankali ta dinga jerosu dan ba k'aramin k'ok'ari tayi ba. K'ok'arinta da kuma son ganin tayi abu yake k'ara sonya shi cikin k'aunarta, ya d'ago da fuskarta cikin lumshe ido ya zura bakinsa cikin nata. Kissing juna sukeyi cikin wani irin shauk'i har Sadeeq yaji yana neman fita a hayyacinsa sannan ya kyaleta da kyar ya shafi fuskarta sannan ya bar d'akin da sauri sabida yasan mutane na nan sun sawa d'akin ido suga mintuna nawa zaiyi a ciki. 'Yan saye duk sunje da 'yan uwan Inna daga dawakin tofa su Uwani, Sahura, Rukayya, su Maryam haka 'yan kauyan sanin nan suka yo mota guda suka zo duk da ance su bari zata dawo amma wasu suka ce ai daman basu san gidanta taba dan haka sai sunje. Washe gari suna yaro yaci sunan Abubakar dan haka ko ajikin kalandu da key holders da sauran abubuwan da akayi aka sanya mai Abubakar A (Ayman) wanda Fateema ce ta za6i lak'anin yace wa INdo yana son ta bari a sanya mai tunda dama shima uban sunansa ne dan ayi mata kara. 'Yan kauyan nan an samu shinkafa dasu zo6o lemukan jarka da sauransu suka dinga lodawa cikin jakunkunan su, gidan ya cika mak'il da al'umma su Xoxo sai nan-nan ake da little Sadeeq (ayman) duk nacin yayya Nabee ta hanata d'aukarsa sai dai ta kallesa a hannunta. 'Yan grps da fad'ar yawansu bazai musaltuba suma sai salfie suke da mejego dan a samu na sawa a status da dp, su Sis Mom s/fulani, princess meenat, Olo, aunty jidda musa, mmn ansar, ummi k.d, mmn sadeeq³ aunty baraka, yayya Ummi s/fulani aunty Fatee, sis Ummi A shitu, Heedah, Muhmeelat, redbutterfly, B s fari, meela adeel, ummul m, mrs splined (ko? Sunan ne na 'yan gayu Allah yasa na iya rubutawa dai-dai lol) su Sum-Q, Kaumi shaddad, matar shehi, my Halymah, (yasin da yawa kuyi hakuri dan idan nace zan jeroku ta6...) Duka masoyan INdo da Fateema duk sunje kuma sunci sunsha alhamdulillahi taro yayi sweet mejego an yi fitar suna ta kece raini. Yamma nayi 'yan sumaila suka kama hanyar komawa bayan sun jajjada ma INdo cewar ta taho musu da naman sunan su. K'arfe tara na dare Sadeeq yazo k'ofar gidan yana fitowa daga mota mutane dake wajan suka dinga mai barka fuskarsa cike da farin ciki. "Yaya Sadeeq kenan kwana biyu." Yaji an fad'a cikin nok'e murya, kallonta yayi bayan ya zare glass d'in idansa. Sanye take cikin wani fitinannan material anyi mata d'inkin riga da skirt sun d'ameta sosai, gashi kwan lantarkin k'ofar gidan ya haske su ya zabga mata harara cikin tsuke fuska yace. "Chuchu wai banace ki dena yin irin wad'annan banzayen d'in kunan ba? Wallahi Zan je na samu uncle Ahmad d'in wata k'ila baya lura da yadda kuke rayuwarku." "Kai Yaya Sadeeq yanzu nan meye na rashin dai-dai a cikin rayuwata..?!" Tayi maganar tana d'aga mayafin jikinta, tsaki yaja tare da kara wayarsa a kunne taji yana cewa. "Cutie lalla6o kizo waje ina mota." Mayar da wayar yayi cikin aljihu tare da komawa cikin mota chuchu ta matsa jikin murfin ya kalleta tare da cewa. "Matsa ki bani guri." "Kai Yaya Sadeeq dan Allah, wai kana nufin kace har yau baka gane inda Zuciya ta take ba akan ka? Please Yaya Sadeeq tun kafin na mallaki hankalin kaina nake sonka amma sai wani shareni kake yi ko banyi maka ba Yaya Sadeeq?!" "Ke! Zaki matsa ki bani guri anan ko sai nayi ball dake." Turo baki tayi tana sake matsawa kusa dashi, cikin nuna izgilanci tace. "Hmmm Yaya Sadeeq duk matanka nasan tarihinsu kuma duk cikinsu babu wacce takaini komai ba kamar wannan aunty Aishan me jego, ita da ko wayewar ma anan gurinka tayi 'yar kauye da..." Kwaf... Taji ya kwad'e mata baki da phone d'in daya d'akko, dai-dai kuma lokacin INdo ta fito tayo gurin motar Sadeeq yace. "Chuchu bar gurin nan kafin raina ya kuma 6aci, k'atuwar banza sakarya kawai." Kuka tasa ganin harda jini ya fito INdo taga ta tafi tana kuka ta shiga motar shima ya kulle suka kalli juna tace. "Me kuma ya sanya chuchu kuka my super glue? Allah yasa dai ba wani abun kayi mata ba tana da kirki." "Cutie rabu da ita rashin kunya takemin. Kinga bama wannan ba ya taro hope kunyi komai cikin jin dad'i da wal-wala..?!" Hancinsa INdo taja tana murmushi jin dad'i sannan tace. "Kana sona mijina Allah ya shi albarka ya k'ara bud'a maka hanyoyin samu, mu kuma Allah ya bamu ikon yi maka biyayya kamar yadda kake iya k'ok'arin ka wajan ganin ka faranta mana." "Amin Ummi ayman ina jin dad'in yabon nan da yake fitowa daga bakinki. Ina d'ana baki taho min dashi ba, kinsan yaufa tun asuba rabona dashi." Dariya tayi sannan ta zuge jakar hannunta ta fito da kud'ad'an ciki wanda duk na barka ne. Mik'a mai tayi be kar6a ba ya kallesu tare da cewa. "Uhmm k'arin bayani tukunna cutie ai bakya mik'on Kud'i haka ba bayani ba." "Toh ka kar6a mana ai zan maka bayani, kud'in da mutane suka bani ne na barka. Ka kar6a kayi amfani dasu kaga akwai k'ananu nima sai nayi wani abun ko idan za'a nema." Dariyar shima yayi zuciyarsa fara kal, chuchu na can gefe a tsaye tana gunguni sauran 'yan uwa na mata sannu amma idanunta suna kan motar Sadeeq haushi kamar zata had'iye motar. "Cutie wannan ai naki ne, ni babu abinda zan kar6a Allah yayi miki albarka ya albarkaci yaron da kika Haifa min Ina alfahari dake Ina sonki har cikin k'ahon Zuciya ta." Kowa dad'i yake ji sun dad'e a cikin motar kafin ya duba agogo ya kalleta cikin yanayi nasan nuna rashin son abinda zai fad'a yace. "Zan tafi, gobe insha Allah ance za'ayi suyar nama acan gida kinga kar a 6atawa masu gidan idan an kammala za'a kawo jibi idan Allah ya kaimu za'a kaiku sumaila sai kuma kinyi arba'in." "Ko baka son na tafi ne..?!" Yayi murmushin yake domin harga Allah baya son suna rabuwa amma ya zai yi ko ta zauna fitina zai dinga jawa kansa gashi kuma zai koma kwara Fateema baza ta bishi ba wannan karan sabida zasuyi wani taro a makarantar da take aiki dole ya barta taje. Hannunta ya kamo tare da cewa. "Cutie karki damu kije ki dawo hmmmm zaki shaaaa." Da sauri ta bud'e motar suna dariya bata bari ya k'arasa, lek'ansa tayi sunata dariya yace. "Idan kin shiga kicewa Fateema ta fito mu tafi." Baki ta turo ya shafa kansa ganin harta mai fassara ya kashe mata ido d'aya sannan ta tafi, tasan komai shi kenan yanzu shida Fateema zasu cigaba da zama sai taji wani iri a cikin zuciyarta da kyar ta iya fad'an sakon sannan Fateema ta fita, chuchu na ganin haka ta kalli su Haleema tace. "Kuzo muje wajan Yaya Sadeeq ya rage mana hanya duk da munyi fad'a." Tashi suka yi da sauri suka k'arasa wajan motar yana kokarin tadawa suka rok'esa, sai da ya fara dank'arawa Chuchun harara kafin yace. "Ku shiga amma wallahi badan halinku ba ku dukan sakarkaru kawai." Shiga suka yi ya ya dinga jan Fateema da hira dan ya denajin muryoyinsu musamman ta Chuchun da take kamar ta gyare kyar-kyar-kyar. Yana zuwa suka fita chuchu ta kallesa shi kuma yak'i bari su had'a idanuwa sabida mugun haushinta yake ji sabida yadda yaji zata ta6a mai mutuncin matarsa uwar d'ansa. **** Washe gari bayan anyi suyar nama an kasa kowa an bashi. INdo ta kimtsa musu kaya itada ayman da Nafeesah da daddare Sadeeq yazo gidan ya kuma siyo mata wasu abubuwan da zata buk'ata na ayman sannan ya tafi. Washe gari da kanshi ya shirya zuwa kaisu sumaila tun a hanya suka fara jin kewar junan su sai dai yayi mata alk'awarin zuwa duk sanda ya dawo kano. Yana kaisu ya juyo dan INdo har kuka tamai wanda da kyar ya lalla6a ta sannan ya tafi bayan ya bata kud'i tak'i kar6a sabida akwai na barkar data samu a hannunta... *HAJJA CE*👈 [7/31, 5:13 PM] Aisha Galadima: *⚗⚗ MUSAYAR ZUCIYA...⚗⚗* ♥♥ ♥ A true life story Na *K.A.S Precious Hajja ce*👈 *HASKE WRITER'S ASSOCIATION*💡 (Home of expert & perfect writer's) *DEDICTEED TO:* Sanah Isma'il Matazu. *VOTE me on wattpad @Hajjac* *Shafin yau naki ne m sweet heart SOFIYYA GALADANCI, I love you Allah ya nuna mana ranar Auranki da rai da lafiya nasan ke ko...?🤨kawai dai Allah ya k'ara miki baseera dear Bari nayi tsit*❤💘 Page *38* Alama yayi mata da hannu ta saki labulen da aka nannad'e aka d'ora akan k'ofar d'akin. Murmushi tayi tare da zaro idanuwa tana girgiza kai alamar a'a, ganin haka yasa shi matsawa yana kallon k'ofar ganin babu me kallonsa yayi saurin sauke labulen INdo tace. "Kai.. Kai... Kai! ba ruwa na nidai Inna ce fa ta d'aga shi wai sabida akwai zafi." Hannu yasa ya janyo ta kusa dashi yana kallon fuskarta, ya kaleta ya kalli Ayman a hankali ya kai bakinsa saman goshinta ya sumbace ta INdo tasa hannu ta bayansa ta rungume shi itama sannan ta kallesa tace. "Ka zauna ka tsaya." Hannunsa cikin nata suka zauna yana kuma rik'e da Ayman. Kwantar da Ayman yayi a gefe kasan cewar yana cikin towel sannan ya juya yana kallon INdo wanda ke kallon k'irjinsa dan wani iri taji da yadda yake mata wani irin kallo. "Sannu da zuwa, ya gurin su Mama?" "Kin yi kyau cutie na, kinyi kamar ba me jego ba dan babu wani alamun da zai nuna hakan meye sirrin?" "Inna ce." Ta bashi amsa tana wasa da yatsun hannunsa yayi murmushi tare da matso da ita kusa dashi yana mak'alota jikinsa. "Ko kawai ma idan zan wuce mu tafi tare tunda kun gama wanka ai kin fara sallah ma ko cutie?" INdo ta zaro idanuwa tana kallansa yayi murmushi yana d'aga mata girarsa kafin yaji tace. "Ta6... In bikafa kace? So kakeyi insha zagi kenan a cikin garin nan, kasan mu bazan koma gidan ka ba dole sai an yi garar barka sannan za'a maida ni." Kallonta yayi cikin rashin fahimtar maganarta ta sannan ta d'an zame ta janyo kayan abincin ta tsiyaya mai lemo ya kar6a har yana cewa. "Cutie ban gane abinda kike nufi bane wace irin garar suna? Kuma wazai kai? Wa za'a bawa.?!" "Kayan abinci ne ake kawowa gidan su me jego,su anan sun maida hakan kamar ibada dan haka idan miji be yi ba sai abin ya zama gori har jikokin mutum." "Ikon Allah, Allah guda d'aya amma garuruwa daban-daban ni ban ta6a ji ba koda wasa wallahi. Toh idan kuma mijin bashida halin yi fa sai ayi ya ya cutie?" INdo tana gyara k'afar Ayman ba tare da ta kallesa ba tace. "Idan miji beyi miki ba shikenan sai a rabu dashi baza a mayar da ita ba. Idan aka ga ya takura da zaryar zuwa gidan su kuma sai ad'auke ta a kaita inda bazai sake ganinta ba har sai ya kawo kayan." Sosai mamaki ya cika masa zuciya, lallai akwai d'inbin gyara a cikin kauyan nan amma banda haka ya za'ayi a hana miji matarsa akan abinda ba alkurani bane ya wajabta shi ba. Lallai yadda ya k'agu ta koma su tafi kwara state tare dole yaje a harhad'o a kawo,yarinyar tayi tsada da yawa daga wannan sai ace maka wannan. "In zuba maka yanzu ko sai kayi sallan azahar naga an kusa kirawo wa." "Bari sai nayi sallah cutie, dawo nan in dinga jin duminki a jikina." Matsawa tayi ya rungumeta, yana yawo a jikinta da hannunsa ita kuma ta lumshe ido tana sauraransa. Sallamar su Uwani suka jiyo Sadeeq yayi saurin zame hannunsa daga jikinta yana yatsina fuska yace.. "Su waye?" "Inajin su Maryam ne naji muryar su da Uwani da Sahura." "Kai nashiga uku ni Sadeeq, wai hardasu nake aure ne da kullum na shigo garin nan sai sunzo sun samin ido? Ko 'yan uwanku ne cutie?" "A'ah k'awaye nane amma kuma su haka suke duk inda sukaji labarin wani abun tofa sai ka gansu sabida dama ba wani tambayar miji fita suke yi ba." "Ai munafukai ne wallahi." Ya fad'a a kufule kafin ya matsa sun shigo cikin d'akin bakunansu a washe. Zama suka yi daga bakin k'ofar amma hakan be hana warin ranar jikinsu da kaurin icen girki shiga cikin hancin Sadeeq ba ya tuna da tuni itama INdon haka take amma Allah ya d'aukaka ta. Da kyar ya amsa musu a ciki-ciki sabida yadda suke kallansu suna rik'e ha6a sabida sunga sun manne jikin juna. "Cutie zanyi alwala." "Okey toh bari akawo ruwa k'ofar gida, ko zaka yi anan ciki." "A'ah Inna na nan da dai bata nan sai nayi." Tashi yayi suka d'an ra6e ya wuce sannan INdo ta fito suma suka bita a baya, tunda tazo gida suke bibiyarta ganinta suke tamkar Matar wani shugaban me rik'e da wani muk'amin. Ruwa ta zuba tasa mayafi takai mai wajan mota sannan ta koma ciki. Hira suka farayi dasu har aka idar da sallah Sadeeq ya dawo daga massalaci dan har tsayawa yayi suka d'anyi hira da principal d'in tsefawa makarantar su INdo daya bari. Nafeesah ce ta kuma fita ta shigo dashi sannan INdo ta bishi su kuma su Uwani suka ci gaba da hira da Inna duk da bata cika sanya musu baki ba. "Cutie Ina baby na kika kaishi?" "Inna ta goyashi ko na kar6osa?!" "Ah no kyalesa kar ace nayi rashin kunya." Waina ta zuba masa da miya sannan ta matsa kusa dashi, had'e hannuwa yayi a k'ijinsa tare da bud'e baki alamar ta bashi da kanta. Murmushi tayi tana girgiza kai ta fara bashi kunnuwansa har motsawa suke yi sabida yadda miyar tayi mai dad'i idan ta bashi sau d'aya itama sai ya tura mata wanda ta kuma d’ebowa yasa mata a baki haka suka dinga yi har suka kusa cinyewa yace ya k'oshi. "Cutie gaskiya ranar Sunday zaki koma zanyi duk iya yadda zanyi na tabbatar da an kawo kayan nan, sannan direct za'a wuce dake can gidan marigayi acan zaki ci gaba da zama an raba gado Abba yace idan kin koma zaizo yayi miki bayani kinji.?!" Kifta idanuwa ta shiga yi alamar hawaye take son karsu fito ya janyo ta tare da kamo fuskarta yana san saka kwayar idanunsa cikin nata. "Karki zubar min da hawaye kinga nima ina tattala nawa, keda ma ba'ayi miki da yawa ba tunda an baki me kamadashi iri d'aya sak sannan kina cikin zuciya ta kamar rai. Ni kuwa tare muka taso mu kwana tare muyi fad'a mu shirya ba tare da kowa ya sani ba, shine ni nine shi amma yau babu shi." "Ka d'auka kaima a ranka nice shi tunda dama silarsa ce ta sa muka zama abu d'aya dakai, na zame maka shi kaima karka sake yin kuka mun riga munyi *MUSAYAR ZUCIYA* ni da kai fatana a yanzu shine na zama tauraruwa kamar yadda yake so yaga na zama kayi min addu'a malama Hannatu tace addu'ar miji akan matarsa tana saurin kar6owa." Bakinsa da yake ta motsi tun d'azu shi ya zura cikin nata cikin wani mugun tausayinta da wata azababbar kaunarta da soyayyarta da ta taso mai. Kissing d'in ta yake cikin wani irin salo wanda yasa INdo ta kasa gane kansa, ya shagala kawai suka ji muryar malam Hamza a tsakar gida amma Sadeeq ji yayi tamkar a tsakiyar d'akin yayi sabida tsabar tsoro. "Na tafi cutie kar nayi abun kunya a gidannan a d'akin baba dan naga kema ba hanani zaki ba." Dariya INdo take yi sosai wanda tasa Sadeeq kallonta yana hararata dan har rik'e ciki takeyi ya matsa can bakin k'ofa-k'ofa tare da maida hularsa yana jiran shigowar malam Hamza d'akin dan yaji Inna tana cewa suna ciki. "Matsoraci kawai Abu Ayman, uhm...uhm..uhm.." INdo ta fad'a cikin dariya ya juya yana mata gwalo shima. muryar malam Hamzan yaji a bakin k'ofar Sadeeq yayi saurin d'aga labulen ita kuma INdo ta fara matsar da kayan da suka ci abinci kamar masu gaskiya. "Baba sannu da shigowa, gashi duk mun tsare maka d'akin." Sadeeq ya fad'a yana gyara zama tare da turo hula gaba yana kuma mai da ita baya alamar kunya ya keji. Malam Hamza yayi dariya tare da k'arasawa cikin d'akin ya zauna a bakin gadon sa yana cewa ba komai Gaidashi Sadeeq yayi cike da girmamawa har suka d'an fara hira ita kuma INdo ta kwashe kayan ta fita dasu can su Uwani aka ci ragowar ana jinjinawa INdo ganin duk da kud'inta tayi wannan shagalin. Malam Hamza da Sadeeq sun jima suna hira kafin malam Hamza ya fita INdo ta shiga tare da d'ora mai ayman akan k'afarsa kasan cewar ta kar6o masa shi dan tasan yana son ganinsa. "Cutie ni kikawa dariyar mugunta ko? Hmmm zan rama ai zaki zo inda nake." "Toh ai kaine da abin dariya wallahi." "Za dai mu had'e you will see." Kallon ayman yayi tare da cewa. "Cutie wannan da wa yake kama sam na kasa ganewa?!" "Ban sani ba nima kasan ance ba'a gane kamanin jarirai harsai sun fara girma." "Ki dinga karanta mai ayatul kursiyu kina tofa mai a mad'igarsa ai kin iya ta ko?" Tana kallonsa yatsan hannunta k'arami a cikin bakinta tace. "Eh na iya mana." "Matso nan toh kiyi min inji ko dai-dai ne." Cikin jin wani iri dan kar ta kakare ta matsa jikinsa ya rik'ota, a hankali ta fara karanto mai inda yaji zata 6ata wani gurin sai ya gyara mata harta gama sannan yace. "Yauwa ki dinga yi mai Allah ya kare mana shi daga sharrin shaid'anu." "Amin abu Ayman." "Zan wuce sai kinzo cutie ki yo shiri sosai dan wannan karan hmmmm." Dariya ta kuma yi sannan ya zaro kud'i 10k ya bata ko zata yi wani abun idan zata dawo sannan ya mik'e itama ta tashi suka rungumi juna kamar basa son rabuwa cikin yanayi na ba haka aka so ba Sadeeq ya bata Ayman sannan ya fita suka yi sallama da Inna su Uwani sai subirbid'a mai addu'ar sauka lafiya suke yi dan har lokacin suna gidan. A zaure Sadeeq yaga malam Hamza kan wata guntuwar tabarma yana gyaran redio suka yi sallama bayan ya ajiye mai 5k yana ta godiya. Yana shiga mota INdo tazo nan ma suka yi sallama ji yake tamkar ya tafi da ita amma ba yadda zai yi dole ta fita yaja motar ya tafi cike da kewarta ji yake ma tamkar basu had'u ba kamar yanzu ne ma yake kan hanyar zuwa ya gansu.... *HAJJA CE*👈 [7/31, 5:13 PM] Aisha Galadima: *⚗⚗ MUSAYAR ZUCIYA...⚗⚗* ♥♥ ♥ A true life story Na *K.A.S Precious Hajja ce*👈 *HASKE WRITER'S ASSOCIATION*💡 (Home of expert & perfect writer's) *DEDICATED TO:* Sanah Isma'il Matazu. *VOTE me on wattpad @Hajjac* Page *39* Tunda Sadeeq ya koma gida be sanar da kowa zancen da suka yi da INdo ba kasan cewar baya son duk wani abinda zaija ayi mata gori akai ba. Gidan k'anwarsa Hawwa yaje suka yi magana hakan yasa duk abinda ya siyo ita yake kaiwa ga shirin gidan da ake yi mata wanda zata koma. Cikin kwana biyu ya gama had'awa washe gari ana sauran kwana biyu INdo ta dawo yasa aka kai hawwa gidan su INdon takai kayan. Sosai aka dinga murna ana yiwa INdo barkar cewar mijinta ya fitar da ita kunya da kayan da babu wacce aka ta6a yiwa kowacce mace irinsa a kauyan. Shiri tayi sosai ciki da waje Rukayya ta kawo mata kayan INdo ta sake yin wani sassanyan kyau sam bata bari a sauya mata ak'idar da take da ita dan yanzu a kauyan akwai 'yan matan da suke kwaikwayar shigarta da kwalliyarta har yafa mayafi ma. *** "Gaskiya Fateema kina da hakuri, ki duba ki gani a cikin shekara d'aya da auranku kishiyarki tayi zaman gidaje gashi yanzu mijinku d'aya amma zata koma wannan uban gidan na alfarma ke kina wannan duk da cewar shima yana da kyau amma nata yafi girma da kuma kyau ya kamata kema kiyi bori wallahi asan yadda za'ayi dake." Cewar wata malama da suke k'awance da Fateema tun zuwanta school d'in. Numfasawa Fateema tayi tana jin k'irjinta na bugawa zuciyarta na zafi dan ta tabbatar da zancen aunty Hafsat gaskiya ne, gashi uwa uba ita bata haihuwa duk da bata fitar da rai da rahamar ubangiji ba a kan samun ciki. "Amma ni ina ganin ba wani abun d'aga hankali bane Hafsat ganin dama tun farko a cikinsa ta fara zama, karki manta gidan mijinta ne na farko kafin tazo mu had'e. Kuma a k'ishin-k'ishin d'in da naji cewar an bashi gidan kinga dan ya mayar da ita baxan d'aga hankalina ba tunda itace ta fara zama a cikinsa." "Lallai Fateema toh ai nan gaba na san zaki gane abinda nakeso ki fahimta." Murmushi tayi kawai bata son nuna hassada akan lamarin tunda taga wanda ya narka kud'in yayi abunsa Allah be barsa yaji dad'in da ya tanadarwa rayuwarsa a cikin gidan ba. Idan ta tashi hankalinta akan abun itama Allah sai ya d'auke ta aga ta tsiya tunda kamar yadda Ummanta ta fad'a auran Sadeeq da Aisha Had'in Allah ne. Shiga yayi gidan ya tarar tayi tagumi sam ba taji shigowarsa ba sai tsayuwar sa taji Sadeeq ya zauna a gefenta yana kallonta. Murmushi tayi mai sai dai iyakarsa le6anta kasan cewar ita kanta taga yadda yake rawar k'afar dawowar matarsa dan yakan iya gaya mata zata dawo kusan sau biyar arana duk shigowa sai ya gaya mata hakan yake bata mamaki har take tunanin ko yanzu ya dena sonta ne, duk da cewar be sauya mata ba yana nuna mata soyayya fiye da tunanin me tunani. "Baby tunanin me kike yi haka?" "Babu komai baby kawai ina tunanin rayuwa ne." "Hmmm da alama dai zaman kad'aicin nan ne yasa ki shiga tunani, toh na dawo kuma bazan fita ba yau ina tare dake soyayya zamu yi." Yayi maganar yana rik'ota yana shak'ar k'amshinta, ita ma tayi k'ok'arin Kawar da abinda yake damun cikin ranta. "Kai baka gajiya da aiki ne baby?" "Ehmm kinsan ai ked'aya ce yanzu, kuma duka duka yaushe na dawo ai kinga nayi k'ok'ari baby." Dariya tayi tana shafa kanshi ya lumshe idanuwa. Wato mata biyu Lafiya ne daga nan kayi nan babu fargaba bare tashin hankali dole maza suyiwa Allah godiya daya basu wannan damar. Sai gaf da magriba ya samu ya fita bayan sallan isha'i suka yi waya da INdo sannan ya shiga gidan ba tare da Fateema ta gane sunyi ba. washe gari ya tafi Sumaila kauyan Sani yaje ya d'akko matarsa. Yana zuwa ya buga mata waya ba'a d'auka ba sai gani yayi Sagiru ya fito, gaisawa suka yi sannan ya sanar masa cewar tana wanka Sadeeq yace ba komai sannan Sagiru ya koma gidan. Tana fitowa ta buga mai ya katse ya kirata da kanshi dan shine yafi can-cantar yin hakan ba itaba. "Cutie meye nayin wanka, da kin bari idan mun koma gida sai muyi tare." "Hahaha..lallai a haka kake son na bar Sani zuwa cikin gari ko? Ban yadda ba gashi na fito kaya kurum zansa sai mutafi." "Shikenan ai tunda abun 'yar haka ne, ki turo a kawo min yaro na mu fara gaisawa nayi missing d'insa." "Okey shi zaka fara gani ba niba ma ko?shi kenan bari a kawo shi sai ku tafi ni saina zauna a gidan." "Wayyo cutie ki rufamin asiri I can die idan kika k'i bina Zuciya ta zata iya shiga rud'ani zan iya rasa nutsuwa ta. Cutie kin zamo wani jego a cikin rayuwata Ina sonki dan zan iya cewa nafi m twinnie kaunarki Ina jin zuciyata na bugawa a duk lokacin dana tuna cewar bani na fara nuna miki soyayya ba but ki yadda cewar ni d'in ina wahala a cikin raina da rayuwata idan bake a kusa dani, please kiyi sauri ki fito mu tafi dan Allah." "Gani nan fitowa barima a fara fito da kayan namu." Tana fad'a ta ajiye wayan sannan ta lek'a tsakar gida ta kira su shehu suka fitar da kayansu. Tsab INdo ta shirya Nafeesah ta shirya Ayman sannan ta fitar dashi, sai da suka gama shiryawa ta fita kallansa tayi ta glass d'in motar tare da cewa. "One minute." Mak'ota suka shisshiga suka dinga yi musu sallama har sai da suka zagaye unguwar sannan suka koma Sadeeq ya gaida Inna sannan INdo suka yi sallama da kowa na gidan suka shiga mota Sadeeq yaja zuciyarsa shar daya juya yagan su sai yaji wani farin ciki yana kuma ratsashi. "Cutie me d'ah, wai ke dan Allah bakya mamakin hakan?" "Bana yi, kai da ace fa marigayi be d'akko ni daga Saye ba da inajin yanzu 'ya'yana biyu ko uku da wani saurayi na salele." "Toh naji abar maganar waye wani salele ba ko dad'in ji. Cutie nayi missing d'inki amma ke da alama kamar bakiyi nawa ba." "Abu Ayman kenan, karka fad'i haka domin zaka zalince ni. Kawai ba yadda zanyi ne ko na nuna babu yadda zanyi tunda ko a gidan ka na zauna dole baka nan amma nayi missing dinka dan ma akwai Ayman ina kallonsa Zuciya ta na ganin kamar kaine shi yasa kaga banyi ramar rashinka ba." Dariya yayi hannunsa na ta6o k'afar Ayman, haka suka dinga hirar yadda suka yi rashin juna har suka k'arasa k'ofar gidan marigayi wanda zata ci gaba da rayuwa a cikinsa. K'irjinta ne ya dinga bugawa Sadeeq yaje ya bud'e gate ya shigar da motar duk yana ganin yadda ta sauya jikinta yayi sanyi hannunta dafe da k'irjinta idanunta a rufe. Hannunsa INdo taji a wuyanta hakan ya sake tayar mata da hankali kawai sai ta sakar masa kuka mai sauti. Ayman ya k'ar6a kafin yayi wani abun su Haleema sun fito suna musu oyo-yo kasan cewar suna ciki sune 'yan taryar su. "Cutie ya haka? Kuka? Ohh ya subahanallahi danasan zaki kuka da wallahi baxan yadda na kawoki gidannan ba, cutie bakya sona ko? Please dan Allah kiyi shiru bazan iya barin ki fita daga motar nan ba alharin kina kuka dan kinga mun shiga nan gidan ba. Ki dinga sawa a ranki nine Abubakar Sadeeq gaba d'aya ki tuna cewar kina da irinsa kamar yadda nima nake ganinki a matsayinsa please." Share mata fuska yayi sannan yasa hannu a baya ya d'akko jakarta ya zare powder da kanshi ya shafa mata ya gyara mata fuskar ya sakar mata murmushi tare da cewa. "Kinfi ma kyau yanzu da nayi miki kwalliyar kin ganki kuwa Son Sadeeq k'in wanda ya rasa zuk'i..." Dariya yaga tayi sannan yayi unlock d'in motar su Haleema suka bud'e tana kar6ar Ayman tana cewa. "Wai toh me kuke yi a motar kuka dad'e aunty Humaira." "Toh gulmammiya ina ruwanki bana son saka idofa." "Sorry broth sannun da hanya." Shareta yayi yana hararta INdo dasu Aminatu suka shiga ciki shima yabiyo bayansu. Kujerun d'ayan falon na ciki wanda ba'a shiga su aka dawo mata dashi falon farko kasan cewar da nata aka kai mata can gidan Sadeeq dining room d'inta yana nan tad'al-tad'al tayi fuskarta nason yin hawaye amma murmushi kwance a fuskarta lokacin da take tuno yadda suka yi rayuwa da marigayi,Sadeeq ya shiga tare da kama hannunta ya nufi bedroom su Haleematu suka zare idanuwa hannu rik'e da ha6a sannan suka ta6e baki. Suna shiga ya jata jikinsa suka tsaya wajan madubi yana kallonta. Hannu ya d'ora saman k'irjinta yana wasa dashi bakinsa saitin kunnanta yace. "What happen to my cutie angel ne? Aisha I love you but naga ke har yanzu akwai marigayi a cikin zuciyarki kin kasa sanyani a ranki why.?” Numfashinta na sama-sama sabida yadda taji yana mata murya a sark'e tana narke mai sabida yadda k'afarta take neman kasa d'aukarta tace. "Wa yace maka baka cikin raina? Shin duk yadda nake cewa kana cikin raina kazama ni nazama Kai duk a tatsuniya kake d'aukar su?" Juyo da ita yayi yana kallonta yace. "Na kasa ganewa but prove me now." A hankali ta sanya hannu a wuyansa ta sargafo shi tare da had'e hancinsu guri guda cikin salo ta zuro bakinta cikin nasa Sadeeq yayi saurin kar6ar sakon tare da rik'ota shima. Kukan Ayman ne ya sanya suka tsaya da abinda suke yi jin kamar hanyar d'akin aka yo dashi, sadeeq na matsawa sai ga Sajida da Ayman tana cewa. "Aunty Humaira wai kuka yakeyi inji yayya Haleema." Kar6arsa tayi sannan ta fita Sadeeq ya zauna a bakin gado yana cewa. "Wallahi munafincin Haleematu ne dama naga take-taken su nasan ganin gulma." INdo tayi dariya tana k'ok'arin ba Ayman.... Sadeeq ya mik'e yana cewa. "Bari naje na maida su gida bana son kinibibin yaran nan." "A'a dan Allah ka rabu dasu kana ganinfa ko gaisawa bamu yi ba." "Yanzu cutie kin fison su zauna akan ni na zauna?!" "A'ah ba haka nake nufi ba, amma kaga ba dad'i ka kyalesu basu yi niyar tafiya ba toh ka kyakesu dan Allah." "Shikenan toh bari naje d'ayan gidan ai Fateema na nan." Yana fad'a ya fita INdo ta bishi da kallo, ai dole yace haka tunda ta dawo gurin sa. Tashi tayi ta koma falo wajan su haleema suka fara murnar dawowa da hirar yaushe gamo. Sai da akayi magariba sannan su Haleematu suka tafi ita kuma ta cigaba da gyara kayanta. Har kusan tara na dare Sadeeq be shigo gidan ba hakan ya 6atawa INdo rai ganin ko dai ya dawo da itane dan ya fara wulak'anta ta. Shirin bacci suka yi itada Ayman gashi ko gen ba'a kunna musu ba kuma bata damu ba domin a can gidan su ko wearing na nefa basu dashi, tana gamawa tayi kwanciyar ta zuciyarta na k'una ta janyo pillow ta rungume tare da rufe idanuwa. Sai wajan 10:15pm ya shigo hannunsa rik'e da ledoji, kayan ya ajiye a falo sannan ya fita ya tayar da injin taja tsaki tamkar yana gurin ta kuma rufe idanuwa dan ba k'aramin haushinsa takeji ba na watsar da su d'in da yayi. "Cutie..! Cutie..!" Yaji shiru sai ya shiga cikin d'akin, kwance ya gansu da alama sunyi bacci ya lalla6a ya k'arasa kusa da ita yana son juyo da ita yaji tayi tauri hakan ya tabbatar masa da cewar idanunta biyu. "Haba cutie ba Oyo-yo shine zaki zo ki wani kwanta tashi muje falo." "Sorry bacci nake ji ka koma inda kafi so." "What..?!" Banza tayi mai ya kuma komawa wajan fuskarta yana matsa hannunta yace. "Amma ki bari sai munzo kwanciya sai muyi wannan wasan but yanzu dai taho muje falo." "Nace kayi tafiyar ka wajan matarka, nasan dama can itace za6in zuciyar ka bani ba da aka lik'a maka, toh kaje katafi gurin Fateema daka fi so na bar mata kai. Banda mutuwa ma me fallasa ai da hakan bata faruba bare kamin wulak'anci harda cewa toh kaima ka tafi wajan Fateema shine sai yanzu goma da wani abun zaka ce ka dawo in tashi." Ta k'arasa maganar cikin kuka tare da tura fuskarta k'ark'ashin pillon da kanta yake kai. Ba k'aramin tashin hankali Sadeeq ya shiga ba jin abinda take fad'a, ya janyo ta yana lallashi kan ta sanar mai da abinda yayi mata amma tak'i, har zai rabu da ita yaji bazai iya ba sabida zuciyar da take tsananin sonta tak'i jin haushinta sai ma k'ara k'ask'antar da kansa da yayi yana cewa. "Kinga ba wai da gangan kika ga nayi dare haka ba no, ana yin sallahn magrib muka tafi gidan wani malami nida Abba bamu dawo ba sai bayan sallahn isha'i naje nakaisa gida sannan nayo muku siyayya naje ko dad'ewa banyi ba a gidan Fateema nayo nan amma shine zaki min wulak'anci ko? Shikenan tunda har kin fara yi min mumunan zato." Yana fad'a ya fara k'ok'arin sauka a gadon sai kuma yaji ta rik'osa, itama bazata iya fushi dashi ba ya lek'a fuskarta ta kallesa sannan ya tashi tare da d'agata suka nufi falo. "Cutie ki dena min saurin fushi bana so yana sani cikin damuwa da tashin hankali kinji?!" "Toh amma nima ka dena barmin gidan ka dad'e baka dawo ba tunda kana garin." "Insha Allahu." Ya fad'a, kitchen taje ta d'akko plate da cups ta dawo. Gashasshiyr kaza ce da aka sanya mata kwai tasha kayan lambu ga yajin tafarnuwa suka zauna suka ciyar da juna ranar sunyi kwanan farin ciki marar bayyanawa bare rubutawa. Satin INdo uku da dawowa da kyar da nuna jajircewar shine mijin ba ita ba ta yadda zata bisa zuwa kwara state sabida ta kafe ita karatunta zata koma amma yak'i har kuka tayi suka yi fad'an kwana biyu amma yaki sakkowa dole ta hakura ta bisa suka tafi aka bar Fateema... Nd Page finale is loading🤨 #love you #my fan's *HAJJA CE*👈 [7/31, 5:13 PM] Aisha Galadima: *⚗⚗ MUSAYAR ZUCIYA...⚗⚗* ♥♥ ♥ A true life story Na *K.A.S Precious Hajja ce*👈 *HASKE WRITER'S ASSOCIATION*💡 (Home of expert & perfect writer's) *DEDICATED TO:* Sanah Isma'il Matazu. *TUKWAICI GA:-* Dota Fateema (Marok'i). *DAN JIN DAD'INKI:-* Billy S Fari. *VOTE me on wattpad @Hajjac* *End* Page *40* Tun a cikin mota suke yin fad'a k'asa-k'asa yadda ba kowa ne zai gane ba bare aji. INdo mita kawai take masa sabida tsabar ta gaji da zama bata ta6a yin tafiya irin me nisan haka ba gashi tun a cikin motar ta fara ganin ban-bancin kano da inda za suje domin duk cikin motar yare ne basufi su shida bane hausawa kuma suma ba wai zaune suke a guri d'aya ba kowa yana kan kujerarsa. Wani yare dake kusa dasu yana ta kallon Ayman ya zuro hannunsa yana shafar kanshi tare da tambayar INdo ya sunan d'an cikin yarbanci k'irjin INdo ya dinga bugawa jin bata gane abinda yake nufi ba, sai kallon mutumin take shi kuma yana faman kuma tambayarta. Kallon Sadeeq tayi kawai taga yayi tamkar baya jinsu yana karanta jarida tasa hannu ta zunguro shi ya kalleta sannan ta kawar da kai tare da cewa. "Ana maka magana fah." Kallonta yayi yana k'umshe dariyar sa kafin ya kalli bayeraben sai taji ya gaya masa sunan Ayman bayeraben ya jinjina kai bakinsa a washe ya cewa Sadeeq yaron yana da kyau Sadeeq yayi dariya duk babu abinda INdo taji a cikin maganar gashi sai dariya bayeranen yake hakan ya sake k'ona mata rai domin abinda take gudu ne yake shirin faruwa wato a dinga magana bata son me ake cewa ba. Sun tsaya anyi sallah anci abinci an rage mara sannan suka kuma d'aukar hanya ran INdo ba k'aramin 6aci yayi ba har suka k'arasa garin cikin tsakiyar dare. Duk da tayi bacci a mota amma ji take tamkar bata ta6a yin bacci a rayuwarta ba, ko wanka bata yi ba dakyar ya samu tayi sallan magrib da isha'i tabi lafiyar gado. Da kyar Sadeeq ya samu ta farka k'arfe takwas tayi sallah dan tunda ta kwanta ba tayi juyi ba, ko kukan Ayman bataji sai dai shi ya farka ya ciro.. sannan ya samai abincinsa a baki idan ya saki kuma sai ya mayar mata sam bata sani ba sai da tazo suna gaisawa yake bata labari suka dinga dariya. Fita Sadeeq yayi ita kuma ta shiga taga yadda gidan yake bayan ta goya Ayman. Be jima ba ya dawo hannunsa rik'e da leda yaje kitchen ya juye musu abincin daya siyo musu suka tafi falo. "Wannan kuma bak'in abun menene haka." "Amala ce da miyar ayayo da dad'i kuma cutie ci kiji." Zama tayi suka faraci tana sawa abaki ta dinga yatsina fuska daga k'arshe ta matsa ta had'iye ta cikin bakinta da kyar. Sadeeq ya kalleta cikin mamaki yace. "Cutie ya haka? Ba kya ci ne?" "Gaskiya bana ci wallahi wannan abu a samo min wani." Shima jiyayyi sam ba zai iya ci ba duk kuwa da son amala da yake yi. Kallonsa tayi tana goge hannu cikin shagwa6e fuska tace. "Kuma ni yunwa nakeji wallahi kamar inci babu, ko cinyeka nayi ji nake bazan k'oshi bama gashi da Ayman ya farka zaice zai sha kuma babu komai a ciki wallahi duk ya tsotse." "Kai cutie wai ba komai a ciki, toh duk meye wannan abun a ciki?!" Yayi magana yana kallonta da mamaki, ta kuma narkewa cikin nuna jin yunwa sosai tace. "Shikenan tunda baka yadda ba, ni dai ka samo min abinci." Tashi yayi da sauri tun yanzu yaga ban-banci tsakanin su da Fateema domin duk abinda ya siyo ko bata ta6a ciba toh zata ci amma ita common amala tace wai ba dad'i. Tunani ya dinga yi yana neman abinda zai siyo mata gasu da shegen tsadar abubuwa daya rasa yadda zai yi kawai sai yaje gurin wata k'awarsa cinyere da take dafamai abu idan bezo da Fateema ba yasa ta dafa mai indomie da ruwan tea ya kar6a ya kai ma INdo, harda su murmushi tayi mai sabida ganin abinda zata iya ci. Kad'an yaci kasan cewar bata damesa ba ita kuwa taci sosai kad'an ta bari tasha tea sannan walwalarta ta dawo taje kuma ta dinga narke mai tana takura mai. Satinsu d'aya da zuwa garin babu inda INdo take zuwa ko lek'e batayi ba, aranar kuma ya fara fita gurin aikinsa yana tafiya ita kuma tana gyaran gidan sai ga wasu 'yan mata kowacce da 'yar bingilar riga da mini skirt suka shigo. "Madam excuse us,can we come in please?" INdo ta bisu da kallo ita kuwa me ya had'a ta da arna da har suke neman shigo mata gida? Ganin tayi shiru ne yasa d'aya daga cikin su tace. "We are friends of your husband,can you let us in..Mrs sadeeq?!” "Me..? For what reason??" "Don't get wrong Mrs sadeeq,we are friends of sadeeq ,we just came by to see his newly born baby” Shi kuma ya rasa da suwa zai yi k'awance sai da mata dan rainin hankali, toh baxata bada d'an su ganshi ba bama su da kunya basu santa ba kawai zasu wani zo k'ilama k'arya suke salon su sace mata d'ah ne. "Madam please..." "Eyyah m sorry he is sleeping.." Ta fad'a tana d'ari-d'ari kar su gano cewar 'yar koyo ce a cikin yaren turancin. Suka ce zasu dawo anjima ko gobe, suna fita ta kulle gidan bata bud'e ba sai da ya dawo ya buga mata waya taje ta bud'e. "Ya aka yine cutie wallahi yanzu kin fiye rigima kamar ma k'aruwa take yi. Sam kamar baki haihuba yanzu kuma meye ya faru ko yaro nane ya ta6oki ne..?!" Yana rik'e da hannunta suka shiga falon ta kuma had'e rai ya juyo da ita suna kallon juna yace. "Gaya min menene ko kina nufin dad'ewa nayi ban dawo ba?!" Zaunar dashi tayi taje ta kawo ruwa yasha kad'an sabida baya tare da k'ishi dan kar tayi zargin wani abun ne yasa shi yasha. Zama tayi Ayman na kan kujera yana bacci ta kwantar da kanta a cinyarsa yana jan hancinta tace. "Bayan ka fitane wasu mata arnaye gunduma-gunduma suka shigo su hudu ko wacce da wani banzan skirt, wai dan son maidani wata sakarai suke ce min sunzo ganin Ayman ne wai ka gaya musu kanada d'ah." "Ohh su Juliet ne da blessing sauran ne dai ban gane ko suwaye ba. Toh kin basu sun ganshi ko?" "Kut in basu kuma..?! Wai kaima ka d'auka har yanzu bani da hankali ne? Kawai ban san su ba baka yi min bayanin su ba zan d'auki d'ana na basu, lallai da hankalina wallahi yanzu ba dah bane." Kallonta yake shi yanzu baya ganin wani aibunta komai tayi sai yaji zuciyarsa ta aminta da abun koda kuwa yana son yi mata gyara. Hannunta ya rik'o ya sumbata sannan ya fara shafar fuskarta yace. "Cutie su Juliet mak'otan mune wannan benan na jikin mu shine gidan su, please ki bari kuyi mutunci musulunci be hana ba suna da kirki basuda matsala suna ganin girmana sosai." "Lallai in rasa da wad'an da zanyi k'awance sai da arna wallahi ba ruwa na bazan yi ba sam." Shafa kanta yayi lallai ashe akwai gwarmai domin idan yazo da Fateema suna zuwa kuma bata kyarar su hakan yasa suka saba ita kuma ko me ta d'auki Christians oho mata. Share zancen yayi ya d'agata tare da janta suka shiga kitchen dan yaga alamar har lokacin haushin bak'in basu barta ba. "Cutien Sadeeq da Ayman a dafa min wannan abun." Yafad'a yana ciro wani magani a cikin aljihunsa, tana tsaye tasa shi ya d'akko tukunya tace ya tari ruwa a sink ta kunna gas ya zuba maganin yana dariya k'asa-k'asa dan dama yasan INdon sa tun a tsefawa 'yar rigima ce dan haka yanzu in tayi abin bazai damesa ba sosai kuma tafishi gaskiya tunda bata sansu ba tayi hankali da ta hanasu dan za'a iya zuwa a damfareta hakan kuma da tayi ta nuna mai ba da kowa zata dinga yadda ba kamar yadda wasu suke ganin hakan cinyewa ne sai kuma an cucesu suzo suna kuka. Har ya dahu suna kitchen d'in tana ta6ara. "Muje falo naga wasu littattafan turanci, tunda maganin ya dahu kafin ya huce na karanta maka kaji." Hannunsa ta fara jah yayi saurin rik'ota tare da girgiza mata kai ta had'e rai. Maganin ya d'auka ya kai bathroom ya juye cikin bahon wankan Ayman sannan ya mayar da tukunyar kitchen ya kalleta ta zauna kan kujera sai cuno baki take yi ya zauna kusa da ita yana rik'o hannunta murya a sark'e yana narke mata idanuwa yace. "Cutie rigima, zo muje ai naki ne shiga ciki zaki yi." INdo ta zaro idanuwa fuskarta a d'aure tana mai wani irin bahagwan kallo, ganin yadda take kallansa a hagunce yasa shi shafar fuskarta yace. "Whats wrong?" "Shin bakajin nutsuwa dani ne ko kuwa dai wani abun kakeji a tattare dani? Ko kuma me kake nufi malam Sadeeq da zaka kawon abu wai in shiga ciki...?!" Hannu yasa ya rik'e kansa tare da rintsa ido jin yadda ta mayar mai da abunsa. 'Dagowa yayi idanunsa jawur sabida yadda ransa ya sosu dajin abinda tace ba tare da yayi magana ba ya d'auki phone ya kira Fateema bayan ya had'iye 6acin ransa. "Hello baby na ya aiki? Yasu my sweet Ayman?!" "Lafiya lau baby ya skull kin dawo ko?" INdo ta mik'e zata bar gurin yayi saurin rik'ota ta fara k'ok'arin kwatar kanta dan wani haushinsa takeji. Ji tayi ya cigaba da yin wayarsa hankali kwance kafin taji yace. "Ammm baby ko kina son na taho miki da wannan ganyen maganin naga wannan zuwan ma na kawo shi kina so?!" "Woww babyna ina so mana dan Allah kaje ka siyo karya k'are please my awesome husband." "Okey tom zan kawo miki insha Allahu bye zan kiraki anjima." "Thank you baby a gaida min da Ayman my son." "Insha Allahu." Kashewa yayi yana kallon INdo wadda still fuskarta a had'e take. Janyo ta yayi ta fad'o jikinsa tana turesa ya matseta tare da zura kansa saitin wuyanta yace. "Banyi tunanin cewar akwai abinda zan saki kiyi amma ki tsaya tuhumata ba, Aisha ko wuta na rura nace kishiga hakan ya nuna min bazaki shiga ba sabida bakya sona da kina sona duk abinda zan ce kiyi bazaki tsaya wani tunani ko gaddama ba sai gashi kinyi na gani shi kenan na gode Allah yaso ina da wadda ta yadda dani 100%." INdo najin haka ta saka kuka shi kuma ya tureta ya juya kan kujerar yayi kwanciyar sa duk da yanajin kukan har cikin k'ahon zuciyarsa. Tashi tayi a hankali tana kukan ta shiga bathroom, shiga tayi cikin ruwan tana ciki tana jan majina yayi murmushi ya kuma k'i bin bayanta, bata fito ba har sai dashi kansa yaga dacewar lokacin tafito yayi amma tak'i fitowa. Zaune ya ganta a ciki ta saka fuskarta tsakankanin jinyoyinta sai gunjin kuka takeyi, k'arasawa yayi ya tsugunna a gabanta tare da saka hannu ya fara k'ok'arin d'ago fuskar ta amma tak'i ta kafe. Taurin kai na INdo sai addu'a ya mik'e tare ya d'agota cikin nuna k'arfi sannan ya fito da ita suka shiga bedroom yana rungume da ita suka zauna a bakin gado. A gabanta ya zauna tare da rik'o hannunta kanta a k'asa idanuwanta a rufe sai faman sauke ajiyar zuciya takeyi. Kallon fuskarta yakeyi cikin tsananin sonta da kaunarta yace. "Cutie nine fah ya kamata nayi kuka sabida kin kasa yadda dani, cutie i love you..ban san yadda zanyi na misalta miki ba duk abinda kikaga nayi dan ina sonki ne. Cutie koda kikaga na dage sai kin biyoni nan karkiyi tunanin cewar ko bana son kiyi karatune a'a ina son zuwa dake ne sabida ko bayan rai na kiyi alfaharin kema naje dake inda nake zuwa shi yasa kika ga na dage sai kin bini amma duk abinda nayi miki na rashin dad'i cikin sani ko rashinsa kiyi hakuri ki yafemin." Hawaye suka kuma zubo mata ya tashi ya zauna kusa da ita tare da janyo ta jikinsa yana buga bayanta cikin muryar kuka take magana. "Ni ka dena bani hakuri bayan baka min komai ba, nice zan baka hakuri sabida nice nake 6ata maka rai amma dan Allah abu Ayman kayi hakuri ka dinga yafemin koda a cikin zuciyar kane nasan ina 6ata maka rai dan All..." A hankali yasa hannunsa ya toshe mata baki yana kad'a mata kai alamar tayi shiru, da sauri ta rungumesa suka k'ank'ame junansu cikin shauk'i. Basu fito ba sai da kowa yasan ya farantawa d'an uwansa sannan suka yi wanka suka ci gaba da soyayyarsu yana kuma koya mata karatunta cike da kwarewa yadda kuma zata gane ta fahimta duk da cewar tana d'an dad'ewa kafin ya zauna a kwakwalwarta danma understanding takeyi ba wai hadda ba. Bayan sati uku Lokacin sun cika wata d'aya da zuwa cikin ikon Allah kuma ya samu INdo ta fara sakarwa su blessing fuska sai dai yawanci sunfi yin wasa da Ayman kasan cewar turancin INdo ba nisa yayi ba kamar su da yazama shine yarensu na biyu da suke ji bayan inyamuranci. Itama takan d'an lek'a gidan su amma ba sosai ba dan su kan yi yarensu wanda yafi bawa INdo haushi sabida ko "zo" bata iya ba su kuma sunfi yinsa. Sosai suka sake kulla babin soyayya dan zaman su anan su biyu ya kuma kulla sabuwar alak'a dan har basa son wani yayi nisa sukanji har zazza6i amma da an had'u sai a warke zuciyar su ta riga ta zama d'aya, duk abinda d'aya yakeji wala na dad'i ko rashinsa sai duk sunji yanayin a jikinsu, ciwon kai idan d'aya yayi sai d'ayan ma yayi koda kuwa fad'uwar gaba ce wannan yanayin yana basu mamaki da al'ajabi, sun kuma sake tabbatar da cewa sunyi *MUSAYAR ZUCIYA* ya kar6i tata itama ta k'ar6i tashi suna kula da junansu sannan ta rage yi masa taurin kai musamman da yake karanto mata tarihin annabawa duk dare idan sunje bacci. Ayman yana ta wayo suna kula dashi sosai sannan koda second d'aya Sadeeq be ta6a manta Fateema ba yakan buga mata waya a rana kusan sau biyar yayi missing d'inta sosai domin ko wacce mace tana da nata matsayin a zuciyar miji musamman da ya kasan ce ita ya fara furtawa kalmar So ya kuma fara auranta ya fara saninta a matsayin matarsa. Yana jin dad'in zama da matansa su duka musamman yanzu da soyayyarsa ta kuma zama a cikin zuciyar INdo, yafi ta sonta amma yakan daure domin karya d'ora mata girman kai karta dinga d'aukar kanta a wani abun tunda yanzu ne yake d'orata akan sabuwar rayuwa dan yanzu ne take kuma sanin komai na rayuwa duk abinda ya d'orata akai zai ga shi takeyi bata ta6a k'etare duk wani abu da ya karanto mata ya fassara mata. Watansu biyu suka shirya komawa lokacin INdo ta kuma wayewa tayi kyau tayi k'iba ta zama tamkar wata k'aramar hajiya tayi dam kwanciyar hankali ya fito a jikinta da yanayinta dama yadda take gudanar da abubuwanta dan takanji zata iya gogawa da ko wacce irin mace a fad'in duniyar nan duk da cewar iliminta bema kai na Fateema ba amma yadda zata gudanar da wani abun sai mutum ya rantse ko tana kanyin master's ne. ***** Kwance take a jikinsa tana kuka domin ba k'aramin rashinsa tayi ba wata biyu ba wasa bane a gurin miji da mata musamman idan basu tare. Gashinta yake shafawa yana kuma rik'e da hannunta yana matsawa Sadeeq yace. "Baby dan Allah kiyi shiru kinga dai ba zuwa nake garin can ina yawo in dawo ba, kinsan abinda nakeyi kinfi kowa sani tun kafin kowa ya sani hatta Abba kin fishi sanin me nake zuwa inyi dan haka bana son kukan nan please yana sani cikin shakku da kokwanto." "Toh baby amma dai ka dena dad'ewa dan Allah. Ko kuma ka tattaro ka dawo nan kano shikenan kana tare damu koda yaushe." "No... Fateema bana son zaman garin nan ga sa'ido sai dai ke idan kin yadda ki ajiye aikin ki idan zan tafi sai na tafi dake na ajiyeki a can kinga na huta kina can bani da fargaba ita kuma Aisha tana nan kun hutar dani ma." "Nayi shiru baby nigara ku dinga tafiya da ita can babu kowa d'an uwa dangi duk babu sai sababbin da zaka yi na hakura zan dinga jiranka har lokacin da zaka dawo." "Ummm kaji me wayo, wato ke k'ink'i bina sabida aikin ki. Amma ni kina son na dawo nan da zama shi kenan kullum a ce mijinku yana guri d'aya baya zuwa konan da can toh na gano ki kuma nak'i wayon." Ya fad'a yana mata cakulkuli a cikinta suna ta dariya dan baya son yaji ta sako mai zancen rashin haihuwarta sabida shi be ta6ajin haushin hakan ba ko yaji sonta ya ragu a'a kullum yana jin sonta musamman da take mai biyayya da nuna soyayya. Haka Sadeeq ya cigaba da rayuwa da matansa cikin kwanciyar hankali duk da wani sa'in yakan fuskanci matsala ta kowane 6angare amma yakan warware ta cikin hikima ta yadda ya san halin kowacce a cikin su. 'Daukar su yayi su duka sukaje aka yi musu hoto ya bud'a su ko wane gida yasa d'aya guda d'aya babu kuma wadda ta nuna mai bata so. **** "Hello, Rasheedat. Okey ai zan shigo nan da 11:00 tuna sai 11:30 ko.? Okay sai na shigo." Kwance yake akan kujera INdo na k'ok'arin zuba masa fruits salad duk tana jin abinda yake fad'a ranta yayi mugun 6aci zuciyar ta na zafi kishi ya turniketa sai faman had'e gira takeyi. Tashi tayi jikinta har rawa yake yi taje takai mai fruit salad d'in ya d'ago ya kalleta ganin yanayinta yasa shi riko hannunta ta fizge ya kuma rikowa ta kuma k'ok'arin fizgewa ya janyo ta kusa dashi ta zauna kirjinta sai dokawa yake yi Sadeeq yace. "Toh yau kuma me Sadeeq sarkin 'yan masu laifi yayiwa cutien sa cikin 'yan sakanni.?!" "Ba komai kyale ni zan shiga d'aki." "Toh ki fara bani na gama sha sai kije kiyi aikin ki." INdo ta kuma yin kicin-kicin a kufule tace. "Ka kira Rasheedat ta baka mana amma ba ni ba." "Rasheedat kuma cutie? Kin santa ne ko kuma dan kinji muna waya ne zuciyar ki ta fara halin nata." Turo baki tayi tana harare-hararen gefe ta kasa cewa komai, Sadeeq ya janyo ta jikinsa yasa hannu a tsakiyar k'irjinta yaji yadda yake bugawa cikin tashin hankali ya mik'e zauna dan da a kwance yake yana rik'e da ita. "Subahanallahi cutie kishi ne haka? Rasheedat ba budurwata bace d'alibata ce yau zanyi musu lecture shine take tambaya na shin zanje nace eh su shirya shikenan fa." Sadeeq yana jin sanda ta sauke wata muguwar ajiyar zuciya sannan ta kallesa ya sakar mata murmushi tace. "Toh banda basu da kunya meye na bugo maka, su ba students bane baxasu jira har kaje ba zasu wani bugo maka waya. Ina monitor da bazai bugo ba sai ita tana mace banzar kawai." "Ta6 cutie har ina cewa zan k'ara aure sai kema na barki anan ki cigaba da karatunki Fateema tayi aikinta ita kuma amaryar na barta acan kwara gidana na Ilorin kunga an huta da zirga-zirgar fitar ku." Share sa tayi ta d'ibi fruit d'in a cokali ta sanya mai a baki, yana dariya ya kar6a har ta gama bashi sannan ya janyo ta k'irjinsa yace. "Cutie I love you zan iya mutuwa a duk sanda kika juya min baya, ki kula damu dani da yaro na dama wad'anda zaki haifamin nan gaba please cutie." Sumbatarsa tayi a goshi sannan ta kwantar da kanta a saman k'irjinsa tana shafar kansa tace. "Nima ina sonka my super glue, your my Biggest comport..my breath... My heartbeat.. Kai my everything but ka dena min zancen zaka k'ara aure, a cikin shekara d'aya kayi mata biyu sannan kace kana shekara ta biyu zaka yi ta uku ai sai ka jamana surutu. Dan Allah ka barmu mu biyu ka dena tunanin wata idan ba haka ba zanyi kuka." "Yi muga irin kukan da zaki yi idan zan k'ara au..." Tayi saurin toshe mai baki da nata kafin ta cire ta kalli cikin idanunsa daya bud'e su a hankali duk sun zama na rigima tace. "Haka zanyi uhm..uhm..uhm..ahhh..wayyoooo...!" Suka kyalkyale da dariya Sadeeq ya rungumeta akan kujerar yanajin k'aunarta har cikin ransa. Sun dad'e suna faranta ran juna duk sun manta da rigimar su ta baya Sadeeq ya kawar da rayuwarta ta baya a cikin ransa yana ganin tamkar dama a hakanta ya santa. Watan Ayman takwas kenan har gidan Fateema ake kaisa ya d'an jima kafin a dawo dashi tana son yaron har cikin ranta domin tana masifar son mahaifinsa. ***** K'arfe takwas ya shiga gida, zaune ya ganta tana gyarawa Ayman kwanciya a falo, dariya yayi har yana rik'e ciki ganin yau kuma da salon da za'a siyeshi can ta tsuke cikin riga da wando nan kuma tayi mai shigarta daya santa a real INdon ta zamanin tana kauyan sani. "Kai malam Sadeeq he wani kallona kakeyi he kace baka sanni ba." Wayyo dariya Sadeeq ya tsugunna agurin ya dinga yi dan gani yake tazo mai da wani sabon salon soyayya. Ta dashare mai baki tare da k'arasawa wajan sa tasa hannu ta rik'osa da nufin ya tashi aikuwa ya janyo ta itama ta fad'a kansa suka dinga dariya cikin shauk'i. "Cutie I love you so much." "I love you too Abu Ayman." "Allah yajik'an M tiwwine yasa rahama ta baibayesa yasa yana cikin farin ciki kamar yadda muke a yanzu." "Amin ya Allah." Ta fad'a tana wasa da ma6ullayen rigarsa nan suka dinga hirar baya suna dariya. Shirye-shiryen bikin Haleematu suka farayi Sadeeq yayi k'ok'ari sosai dan da su biyu suke had'uwa suyi komai shi yayi kayan d'akin hawwa Abubakar kuma yayi na falo amma yanzu baya nan daga shi sai Abba suka dinga yin komai. Duk matan sa kuma sun zage anyi komai dasu cikin farin ciki dajin dad'i, suna nan kuma har yanzu a tare mijin su yana sansu iya gwargwado yana bawa kowacce hakkinta. ALHAMDULILLAH. Allah na gode maka daka nuna min farkon labarin nan da kuma k'arshensa, Allah kaine abin godiya kuma abin alfahari alhamdulillah. Allah kajik'an marigayi kasa aljanna ce makomarsa da aiyukan alkairinsa. Duk wad'anda suka rigamu gidan gaskiya a cikin musulmai Allah ka yafe musu mu kuma kasa mu cika da kyakkyawan aiki. Dole na godewa masoya masu kaunar Hajja ce da kuma rubutunta, hakika wannan novel d'in ya sadani da mutane masu d'in bin yawa wad'anda baki baxai iya fad'ar yawansu ba, haka kuma hannu bazai iya k'ididdige yawanku ba sai dai nace Allah yabar soyayya da kauna tsakaninmu yasa sakon ciki ya amfanar daku. Nasan na 6atawa wasu rai toh dan Allah kuyi hakuri, nasan na farantawa wasu rai toh kuma kun faranta min, nasan na nishad'antar da wasu nima kun sani nishad'i kusani reader's kune jigon saka duk wata writer cikin farin ciki haka kuma kune kuke saka writer cikin damuwa domin idan bakwa karantawa bazataji dad'in yin rubutun ba duk kuwa dason yin rubutunta nidai na gode muku masoya na fili dana 6oye na kusa dana nesa bazan iya lissafoku ba domin hakan ya janyo min fitina harma wasu daga cikin wad'anda nake alfahari dasu suka gujeni sabida ban yi musu dedication ba amma still suma idan sun karanta karshen page dinnan suyi hakuri ni 'yar Adam ce me laifuka kala-kala a doran k'asa suyi hakuri but bazan manta dasu ba a cikin zuciya ta ba. *K'ANWATA STYLISH.*:-Dake aka shirya za'ayi rubutun nan kika gudu kika barni, but ba komai nasan dama ke lazy writer ce (smile) nayi na gama kuma na gode miki da sake zakulo min muhimman abubuwan cikin labarin Allah ya barki da mijinki Lafiya keda k'anwarki Abler. *MISS XOXO:-* Bazan iya kammala rubutu na ba ban sakoki ba koda kuwa wasu zasuji haushina, kin taka muhimmiyar rawa a cikin rubutuna ta yadda nake hanaki bacci nake hanaki jin dad'i har sai kin bada taki gudun mawar hakan kuma yasa labarin ya tafi cikin tsari da jin dad'in karanta shi, Allah yayi miki albarka ya nuna min lokacin auranki autarees Ina alfahari dake ked'in masoyayyar Hajja ce wanda babu algus. Ina alfahari da duk me bin labarina grps d'in da nake ciki da wanda bana ciki Ina alfahari daku. 'Yan wattpad ina alfahari daku Ina sanku har cikin kalbina kud'in na daban ne. My co-writer's da suka bi labarin nan ku sani naji dad'i sosai duk da wasu na sansu wasu kuma ban sani ba amma sun karanta Ina fatan duk wacce taga gyara ko kuskure zata yi min domin Ina son hakan Allah ya k'ara baseera da kwarin ido. Olo my one &only Ina alfahari dake ked'in aminiya ce ta kwarai.Tare da aunty na Maijidda musa da yayata barrister Fateen Bch. *HAJJA CE NOVELS GRP*❤👍😍 *HASKE WRITER'S:-* kungiya ta Ina alfahari daku Allah ya k'ara baseera ya k'ara had'e kawunan mu amin. *HAJJA CE*👈 *HAJJA CE*👈