An dauko wannan littafi daga shafin https://novels.com.ng ku ziyarci shafin na https://novels.com.ng domin samun kayatattun littatafan hausa kama daga kan na yake yake dana soyayya Marubuci ko marubuciya zasu iya turo mana da littatafansu mu dora masu a shafinmu kyauta don masoyansu su rika Downloading a online, Sannan marubuta zasu iya turo mana da tarihin rahuwarsu da tarihin rubutunsu, dama sharhin littatafansu don masoyansu su gani kuma su karu da hakan Domin turo mana da littafi ko tarihin rayuwar marubuci ko marubuciya sai ayi mana magana ta whatssap da wannan nambar +2348062902098 A lura dakyau - kyauta muke saka littafi a shafinmu bama amsan ko sisin marubuci, duk wanda ya amshi kudinku da sunanmu babu ruwanmu, Alura dakyau - manazarta bama tura littafi ta private ku dena binmu private kuna neman mu tura maku littafi, duk mai bukatar littafi yaje website namu Alura da kyau - Littatfanmu suna fitowa cikin manhajoji uku ne PDF,TXT da DOC amman munfi amfani da PDF da TXT masu amfani da wayar android ko tablet ko computer zai fi kyau ku riga dauko PDF da DOC Masu amfani da kananan wayoyi java ko mara java TXT zakuna zaba don shine daidai wayarku This hausa novel was uploaded and downloaded from https://novels.com.ng You can download more hausa novels there Also you can send us your novel to upload it in our website for your fans to download it online It is free we do not charge for uploading novel Also if you are an Author be it online or Non online you can send us your biography including your book summary,commentary and others via this number +2348062902098 its free we do not charge for our services Note that - we do not charge for our services we uploaded novels and posted biography free, any person that collect your money in our name is your fault do not blame us Note that - pls readers stop calling us and be asking us to send you a novels we are not sending novels through whatssap or private our novels is public at any day, any time you can visits our site and download it Note that - our ebooks came as PDF,TXT or DOC format but the popular format are PDF or TXT, those with android or tablet or pc we suggest you to download PDF or DOC those with java phone or non-java phone we recommend you to download TXT ✨✨```ANEESERH```✨✨ *💥Aneeserh Just The Beginning.*💥 *Story $ Writing By:*✍️📚 *N $ N.* *🔥💫Nanameera $ Nainarh KD.🔥💫* *بسم الله الرحمن الرحيم* *Ep. One.* Shigowa suka yi ganin yadda aka taru yasa ta ce. "Dan Allah menene yake faruwa ne?." Kallonta guard ɗin ya yi yayi gaba abin sa, suna shiga compound ɗin gidan ƙara waro idanu tayi ganin jama'ar har sunfi na waje yawa har suka ƙaraso gabansa wani mutumine wanda aƙalla zaikai 65yrs ɗin ta kalleshi bakinta narawa ta ce. "Your Excellency ko bakai bane ba president of Nijeriya ba." Kamo hannunta ya yi ya ce, "Ni ne Aneeserh." Da mamaki ta ce "A'ina kasan sunana please and Menene waɗannan mutanen suke yi a gidan mu?." Kallon ta ya yi cike da tausayawa ya ce. "Aneeserh kinsan duk abin da ya faru da mutum Allah ya riga da ya rubutashi a cikin littafinsa, kuma ba'a gujewa ƙaddara saboda haka inason kizama mai ɗaukan ƙaddarar data zomiki mai kyau ko akasin haka." Shiru tayi dan ita batasan ma'anar waɗannan maganganun dayake ba kamar antsikareta ta ce. "Yawwa bari naje nagasu Abba suncemin yau zasu dawo." Gaba tayi dan shiga gidan tana zuwa entrance ɗin parlour'n su taga anjere mutane har uku akwance kowanne ansaka masa likkafani anrufe kamar gawa. Jikinta ne yahau rawa saboda Allah ya zuba mata tsoro tayi cikin gidan da gudu tana cewa. "Abba!! Ummi!! Yaya!!." Kowa na gidan kuka yake domin duk rashin imaninka sai kaji tausayinta. Haka ta gama bincike gidan amma bataga familynta ba hakan yasa ta fito lokacin His Excellency yazo ƙofar entrance ɗin tana fitowa ya riƙeta cikin rawar baki ta ce. "Ka sakeni waje zanje naduba naga su Yaya Farooq basu dawoba kuma sunce idan nadawo daga makaranta zanga sun dawo." Hawayen fuskarsa ya goge sannan ya ce "Kinga Abbanki da umminki can akwance an rufesu." Buɗe dara daran idanunta ta yi, sai kuma ta tafi kan gawwakin ta tsuguna a hankali kuma ta buɗe likkafanin ɗaya daga cikin su, wata ƙara ta saki cikin tashin hankali take faɗin. "Abba! Abba!! ka tashi, menene ya sameka Abba ka daina wannan wasan kaji bana so." Kowa na wurin kuka yake, ta ƙara buɗe ɗayar gawar inda tayi arba da Umminta sosai jikin ta yayi weak dan ganin abun take kamar mafarki cikin mutuwar zuciya dakuma rauni ta sake buɗe ɗayar, jikinta banda rawa babu abin da yake yi take faɗin. "Yaya Farooq! Ummi!! Abba ku tashi please ku daina irin wannan wasan please banaso zan mutu, kutashi kunji..." His Excellency ne ya ƙari so wajen ta, ya ɗago ta yana faɗin. "Ki nutsu Aneeserh kinji." Riƙe shi tayi gam bakinta na rawa ta ce. "Your Excellency please kacewa Abba na ya tashi kaji kacewa Yaya Farooq su daina wannan wasan Ummi ta tashi wayyo Allah." Ganin yadda ta rikice yasa ya rungumeta jikin sa yana shafa kanta yake faɗin. "Aneeserh kiyi haƙuri kinji amma Abbanki, Umminki, your brother Farooq sun rigamu gidan gaskiya kiyi haƙuri kiyi musu Addu'a kawai kinji..." Jin kusan two minutes amma babu respons yasa ya ɗagota kafin yayi magana ya ganta aƙasa jikake timm, cikin tashin hankali ya tsuguna kanta ya ɗa go ta, da aka kira guards dan kaita Asibitin. **** Har ranar bakwai batasan waye akan taba, suna uku kawai take kira wato "Abbanta, Umminta, sai kuma Yaya Farooq ɗinta." Yau ma kamar kullum Your Excellency ya shigo bakinsa ɗauke da sallama, zaune ya sameta ta rufe idanunta amma ba barci take yi ba, zama ya yi gefenta ya taɓa ta yana kiran Sunan ta. "Aneeserh!!" A firgice ta buɗe idanunta ta ce da shi. "Ummina." Kallon ta ya yi sai kuma ya girgiza kai ya ce. "Ba ita bace." Shiru tayi masa kusan five minutes sannan ya kuma cewa. "Ya kamata ki daina wannan tunane tunanen Aneeserh kisani duk wanda ya mutu baya dawowa kiyi haƙuri, ki koma cikin mutane ki dawo rayuwarki kamar da, ki dinga yi musu Addu'a a duk lokacin da kikayi sallah kinji?." Kallon sa take amma kana ganinta kasan ba fahimtar abin da yake faɗa take yi ba, girgiza kai ya yi yana tuna sanda sukai sallama da iyayenta bayan sun taho ne aka kira aka ce sunyi hatsari kuma babu wanda ya yi rai a cikin su... *FOUR MONTHS AGO* Fitowarta kenan daga ɗakinta ya kalleta ya ce. "Ke Aneeserh kiyi sauri idan ba haka ba wallahi zanyi tafiya ta na barki." Turo baki tayi tana ƙunƙuni ya kalleta ya ce. "Kee!! Ni kike yiwa tsaki ?." Shiru tayi masa ya ƙara cewa, "Ba magana nake miki ba?." Daidai nan wani Babban mutum ya fito wanda aƙalla zai kai irin 60yrs ɗin nan sai kuma wata mata a bayansa wacce kamarsu ɗaya da Aneeserh fara ce tass kana ganinta kaga asalin bafulatana. Ƙara sawa suka yi, ai kuwa ta fashe da kuka ta tafi wajensa ta ce. "Abba kaga Yaya Farooq ko?." Rungume ta ya yi ya ce "Farooq menene kayi ma ta?" Murmushi Farooq ya yi ya ce, "Ai Abba kasan halinta kawai dan nace tayi sauri taje nayi dropping nata tunda driver'n ta bayanan, shi ne take wannan kukan." Shafa kanta Abba ya yi ya ce. "Shikenan ya isa rabu dashi kinji ƴar albarka kiyi tafiyarki school kinji?." Goge hawayenta ta yi ta ce ''Abba zaka kaini shopping idan na dawo?." Dariya ya yi ya ce "In sha Allah amma kiyi karatu da kyau." Murmushi tayi ta ce "In sha Allah, Ummi ina abincina?." "Yana kitchen.' Ummin ta bata amsa. Kitchen ta tafi ta ɗauko sannan ta dawo kallonta Ummi tayi ta ce. "Aneeserh zo nan." Zuwan tayi ta ce "gani Ummi." Hijab ɗin ta ta gyara ma ta sannan ta ce "Naga randa zakiyi hankali Aneeserh.." Kwaɓe fuska ta yi Abba ya ce "Maza ki tafi makaranta banda wasa kinji baby na." Murmushi tayi ya miƙa ma ta tafin hannunsa ita ma ta sanya nata akai ya ce. ''Promise " gyaɗa kai tayi ta ce "sure'' sannan tayi waje da gudu. Kallon Farooq ya yi ya ce "Please Farooq kayi tuƙi a nutse banda gudu katafi a hankali sannan ka tabbata ta shiga makaranta sannan ka dawo. Girgiza kai yayi ya ce "In sha Allah Abba zan kula da rigimamiyyarka." Dariya suka yi duka sannan ya yi waje yana cewa "sai mundawo" "Allah ya kiyaye." suka amsa masa sannan yayi waje. Zashiga motar bayan sunbar layinsu ta kalleshi ta ce. "Yayaaa" Murmushi ya yi idanunsa akan titi ya ce "Na'am ƙanwaaa" Kyalkyalewa tayi da dariya shima yana tayata saida suka yi mai isarsu sannan ta ce. "Daman Yaya ka iya irin abuna?." Yana shan kwana ya ce " har ma nafiki iyawa, ni lokacin danayi tawa shagwaɓar ai tafi taki " ganin mai yalo ta yi ta taɓoshi ta ce da ƙarfi " yayaaaa " birki ya ja ya tsaya yana kallonta dan ya ɗauka wani abun ne ya sameta ta kalleshi ta ce. "Yaya kasi yamin yalo please." Wani mugun kallo ya yi mata ya ce. "Lallai ma Aneeserh bakida hankali to wallahi duk randa kika sake yimin wannan rashin hankalin saina miki dukan tsiya." Yana gama faɗin hakan ya ja motar suka cigaba da tafiya, ganin bai siyamata ba yasa ta fashe da kuka yana jinta har suka isa makarantar tasu sannan ya kalleta ya ce. "Sauka kona mareki." Goge idanunta ta yi ta ce. "To kabani kuɗin makaranta mana." Da mamaki ya ce. "Dama ni nake baki kuɗin makaranta?." Turo baki ta yi ta ce. "Ni sai ka ƙaramin." Girgiza kai ya yi sannan ya ɗauko ɗari biyar ya miƙa mata ya ce. "Ƙarɓi ki sauka malama." Kallon kuɗin tayi sai kuma ta ɗauke kai ta ce. "Ni ɗari biyu zaka bani wannan yayi min yawa." Maidawa ya yi ya ɗakko mata ɗari biyun sannan ta ɗauki jakarta da lunchbox ɗinta ta sauka tashiga makaranta, saida yaga tashiga sannan ya girgiza kai ya ce. "Aneeserh rigima Allah ya shiryeki." Tana shiga class ɗin nasu kasancewar private school ce yasa su goma ne ƴan ajin nasu biyar maza biyar mata zama tayi kusada seatmate ɗinta mai suna Asma'u amma suna cemata Ma'u murmushi Ma'u tayi ta ce. "Yau kuma waya taɓaki naganki rai ahaɗe?" harararta ta yi ta ce "ina ruwanki dani naga yayana nane yaƙi saimin yalo" murmushi Ma'u ta yi ta ce. "Yau shi ne ya kawo ki ke nan?, ina driver'n naki?." Shiru tayi ma ta ta ɗauko littafinta saboda malami daya shigo musu.. Wajejen ƙarfe biyar da rabi aka tashi daga makarantar kasancewar anan suke islamiyya, kusan mintuna goma da tashi amma ba'azo ɗaukanta ba tayi tagumi tana tunanin abinda ya hana azo a ɗauketa ta ji ya ce " ƙanwata " tajisa sarai amma sai tayi kamar bata jiba tayi shuru ko motsi batayi ba murmushi ya yi dan yasan tanajinsa batayi auneba taji ya ɗauketa gabaɗayanta ai kuwa suka hau kokawa sai ta kwace ƙarfin namiji da mace ba ɗayaba yasa ta haƙura, bayan ya sayanta a motar sun bar harabar makarantar ya kalleta ya ce " Sorry kinji Aneeserh wallahi nayi busy ne shiyasa banzo na ɗaukeki ba amma karki faɗawa Abba kinji " ɗaga kai tayi ta ce " chaɓ wallahi saina faɗawa Abba kuma sai faɗa masa bakazo ka ɗaukeni da wuri ba kuma...... Shuru tayi saboda chocolate ɗin love da kuma biscuit ɗin febs daya miƙo mata, murmushi ta yi ta karɓa ya ce " yanzufa zaki faɗa masa?" girgiza kai tayi tana buɗe chocolate ɗin tasaka abaki har wani lumshe ido take saboda daɗi. Ganin yanda ta yi busy tana shan chocolate yasa ya fashe da dariya ya ce " kwaɗayyiya " ko kallonsa batayiba ta cigaba da abinda take har suka ƙaraso gida... Yana parking ya buɗe lock ɗin motar ta sauka tana cewa "yaya ka tawomin da kayana " tayi gaba abinta, tsaki ya yi sannan ya ɗebo kayan nata ya rufe motar ya shiga gidan...... Zaune ya sameta tana cin cake ya kalleta ya ce " acici mala'ikun tauna " turo baki tayi ta ce " Ummi kin ganshi ko" murmushi Ummi ta yi ta ce " babu ruwana nayi masa magana anjima kaɗan kicemin ai yayanki ne " dariya ya yi ya ce " taje chan ta nemi yayanta badaini Umar ba " taɓe baki ta yi ta ce " ohhoo ay kowa yasan kai yayana ne saboda haka ina ruwana " ajiye mata kayanta ya yi ya ce " ga shirginki nan, bari naje nayi wanka nagaji sosai" ok ta ce sannan ya shiga ɗakinsa..... Ƙarar shigowar mota da taji yasa ta fito da gudu Ummi na kiranta amma ta yi mata banza ta fita, tana zuwa ta rungumeshi ta ce " Abbana oyoyo " shafa kanta ya yi yana murmushi ya ce " nagode babyn Abba ya school ɗin ?" murmushi ta yi tana karɓar jakar hannunsa ta ce " Alhamdulillah ni na matsu nagama wannan SS 3 wallahi nima nashiga jami'a " riƙe hannunta ya yi suna tafiya ya ce " Allah ya nuna mana lokacin" Ameen ta amsa dashi...... Suna shiga ganin Ummi a parlour'n ta ɓuya abayan Abba kalllonta Ummi ta yi ta ce "zan kamaki ne wallahi tunda ke bakyajin magana " Abba ne ya ce " me tayi miki?" zama sukayi ta ce " wai yarinyar nan kullum bazatayi hankali ba nahanata dan ka dawo tafita da gudu amman taƙi ta daina yanzu zata fita ina kiranta amma ta yimin kunnen uwar shegu " tashi Abba ya yi ya ce " to idan bata yiwa Abbanta sannu da zuwa ba wa zata yi wa?" da mamaki Ummi ta ce " au yanzu haka ma zakace?, ay shikenan ta cigaba idan mune yau dai ba mune gobe ba kuma watarana gidan wani zata idan ina raye nayi kallo " turo baki tayi ta ce " ni babu inda zani wallahi " kallonta Abba ya yi ya ce " kiyi shuru Aneeserh bari nayi taking shower kiyi zamanki kinji" ɗaga masa kai ta yi sannan ya yi gaba.... Tashi tayi zata gudu Ummi ta ce ".zo kiyi zamanki ina ruwana tunda ubanki ya tsaya miki " dawowa ta yi ta zauna kamar munafuka ita kuma Ummi ta shiga kitchen dan haɗa abin yin dinner..... Zaune take kusada Abbanta tana ta game da system ɗinta shikuma Abba yana danna wayarsa ta kalleshi ta ce " Abbana " bai kalleta ba ya ce " na'am Mamana" katse game ɗin ta yi ta ce " dan Allah Abba ranar Friday muje shoprite kaji " murmushi ya yi ya ce " ok Allah ya kaimu" cikin jindaɗi ta ce " yawwa thank you so much Abba " dariya ya yi ya ce " never mind "........ Ƙarfe bakwai da rabi tafito tana jiran yaya Farooq amma shuru bai fitoba hakan yasa ta tashi taje ƙofar parlour'n sa ta ƙwankwasa tana cewa "yaya kada na makara please ka fito kaji " tun tana faɗa ahankali har saida tafara wage murya tana faɗa sannan ya buɗe ƙofar ya fito ya galla mata harara, tura baki tayi sannan tayi gaba saida suka fito Parlour sannan Ummi ta ce " Aneeserh kinyi azkhar ?" ɗaga mata kai ta yi ta ce " to Allah ya tsare " har tayi gaba sai kuma ta dawo ta ce " Ummi dan Allah nataso Abba?" wani kallo da tai mata yasa ta juya ta fita tana harhaɗe rai.......... Har yakaita makaranta ba tace masa komai ba shi kaɗai ya yi murmushi ya ce " wai saboda bakiga Abba ba shine kike wannan haɗe ran?" bata kulashi ba ta sauka daga motar tayi cikin makarantarsu shi kuma ya juya dan tafiya wajen aiki.......... Yau kam da wuri yazo ɗaukanta bayan tashiga motar ganin wanda yake gaba yasa ta ce " ina wuni " murmushi ya mata ya ce " lafiya lao Aneeserh ya makarantar?" tana wasada ƴan yatsunta ta ce " wallahi lafiya lao Alhamdulillah yasu Nabila?" wallahi Nabila na gida ya bata amsa ta ce " Ayyah kace ina gaisheta please " ok ya ce sannan ta cewa yayanta " yaya Farooq please kabani irin chocolate ɗin jiya kaji " harararta ya yi ta madubi ya ce " toh uwata sannunki bazan bayarba" turo baki ta yi ta ce " wallahi kuma saina faɗawa Abba abunda kayimin jiya" sakar baki ya yi yana kallonta saida ta idar sannan ya ce " In kin fasa baki ƙaunar Allah kinji " langwaɓar da kai ta yi ta ce " ayyah yaya wallahi da wasa nake maka kabani kaji yayana ɗan albarkana " Jameel ne ya miƙo mata ya ce " ungo Aneeserh daman ya siya miki kawai so yake sai kinyi kuka " dariya ta yi ta ce " yawwa nagode sosai " ta farke ta hau ci, ganin yanda take ci saika rantse bata taɓa ciba yasa sukayi murmushi dukansu........ A bakin street ɗinsu ya tsaya ya ce " Aneeserh, zanje unguwa ki sauka ki ƙarasa da kanki " buɗe baki ta yi ta ce " ni wallahi Abba cewa ya yi ka kaini har gida kuma ni wallahi saika kaini gida sannan zan sauka " juyowa ya yi ya kalleta ya ce " bazaki sauka ba saina zaneki ko motar Abba ce naga motata ce " zunɓura baki ta yi ta ce " nidai Allah sai ka kaini ƙofar gida zan sauka Allah kuma idan baka kaini ba saina faɗawa Abba nace abakin street kake ajiyeni " tsaki ya yi Jameel ya ce " please ka rigada kasan halinta dan Allah ƙarasa da ita" kwafa ya yi sannan ya ja motar ya yi gaba yana ganinta ta madubi tana masa gwalo ya girgiza kai ya rabu da ita......... Comments, like and share. ✨✨```ANEESERH```✨ *💥Aneeserh Just The Beginning.*💥 *Story $ Writing By:*✍️📚 *N $ N.* *🔥💫Nanameera $ Nainarh KD.🔥💫* *Ep. Two* __________Yana sauketa bayan ta fito ya kalleta ya ce " ohya ki shiga gida karki tsaya wasa " tura baki tayi ta yi gaba saida ya ga tashiga gidan sannan ya yi reverse yabar street ɗin. Tana shiga bataga kowa a parlour ba hakan yasa ta yi hanyar kitchen dan tasan Ummi nacan.... A hankali ta buɗe ƙofar without making any sound Ummi na yanka allaiyahu ta tsaya a bayanta sai kuma ta fasa ƙara ta ce " waaaaaaaa " a firgice Ummi ta juyo ai kuwa tahau kyalkyala dariya harda kwanciya a ƙasa tsaki ta yi ta ce " naga ranar da zakiyi hankali Aneeserh" tashi ta yi ta ce " Ummi lemme help you " kallonta ta yi tana zuba Allayahun a colender ta ce " ki fara zuwa ki cire kayanki ƙazama " turo baki ta yi ta ce " to ay naga inada wasu kayan kibari mugama sai naje na cire please " daga haka ta karɓi colender ta tafi wankewa, rabu ta yi da ita dan tasan halin gaddamarta idan ta ce bazatayiba to ko za'a kasheta baza tayi ba ɗin Abba ne kawai ke iya controlling nata.... Bayan sungama girkin ta tafi ɗakinta ta yi wanka tasaka wata atamfa ɗinkin doguwar rigi amma A-shape tayi matuƙar amsar jikinta kasancewar bata damu da kwalliya ba yasa tasaka lip gloose a bakinta sai kwalli amma yadda tayi kyau sai ka ɗauka wata kwalliyar ta yi ta fesa turare ta fito. Tana zuwa parlour ta zauna akan kujera ta ɗauke remote ta kai tashar mbc bollywood inda suke haska dramar house Maya, sosai ta shagalta da kallon saboda tana matuƙar son , har batasan lokacin da Abba ya shigoba, har yazo kanta ya tsaya batasani ba jitayi ya rankwasheta aka, taɗauka wani ne ta fasa ƙara tana ɗago kai taga Abbanta. Ganin irin kallon dayake mata yasa tayi ƙasa da kanta zama ya yi sannan ya ce "mena faɗa miki?" tsugunawa tayi ta ce " i'm sorry Abba " tsawar daya daka mata yasa ta fashe da kuka cikin faɗa ya ce " sau nawa nake miki warning akan kunna Tv kina kallo har ya ɗauke miki hankali a shigo baki sani ba?, saboda kallo aka halicce ki?" tana toshe baki ta ce " A'a Abba dan Allah kayi haƙuri wallahi bazan sakeba " cikin ɗaga murya ya ce " daga yau nasake ganin ankunna Tv agidan nan idan ba weekend ba shashasha kawai get out of my side !!" da gudu ta tashi tayi ɗakinta saboda a rayuwarta ta tsani ayi mata faɗa ko kaɗan, Ummi ce ta fito ya kalleta ya ce " kina gani ta kunna Tv amma bazaki iya stoping nata ba " zama tayi ta ce " yanzu daka dawo bagashi kayiba naga idan nayi mata faɗa cewa kake yarinya ce shiyasa babu ruwana tayi duk abinda taga dama " tashi ya yi ya shige part ɗinsa dan a duniya ya tsani yaga yaro yana shagala da abinda bai daceba... Har akayi sallar isha bata fitoba sanda Farooq ya dawo daga masallaci ya cewa Ummi " wai ina Aneeserh ne Ummi?" murmushi ta yi tace " tun ɗazu da babanku ya yi mata faɗa bata sake fitowa ba kasan halin zuciyarta " murmushi ya yi ya ce " yau ta taɓo Abba kenan?" ɗaga masa kai ta yi ya ce " lemme check her " ok ta ce sannan ya yi hanyar ɗakinta..... Zaune ya sameta ta yi tagumi da filo ya zauna gefen gadon ya ce " Aneeserh keda wa?" shuru ta yi masa ta na kallonsa ya yi murmushi ya ce " faɗamin wanene ya taɓaki kinji ƙanwata " fashewa ta yi da kuka ya yi mata alama da tazo ta taso tana zuwa ya rungumeta ya ce " shikenan ya isa kiyi shuru kinji ƴar albarka " kukanta ta cigaba ya ce " ok tashi muje na siya miki chocolate kinji " tashi ta yi taɗau veil ɗinta ya riƙe hannunta suka fito...... Kallonsu Ummi ta yi ta ce " ina kuma zaka kaita ?" yana ɗaukan car keys ɗinshi ya ce " chocolate zamuje tasiya, sai mun dawo" Allah ya tsare ta amsa masa.... Bayan ya siya mata chocolate ɗin suna mota ta ce " yaya muje ka siyamin ice-cream kaji " kallonta ya yi ya ce " kinsan dai Abba faɗa zai miki ko?" shagwaɓe fuska ta yi ta ce " sai na shanye a mota please yaya " girgiza kai ya yi ya ce " idan kikazo kina mura ko athsmar ki ta tashi babu ruwana " ɗaga masa kai ta yi ta ce " Eh na yarda " ok ya ce sannan suka ɗauki hanya..... Sai kusan ƙarfe goma sannan suka dawo gida, suna shigowa Abba yana zaune yana karanta news ya ce " Farooq tun ɗazu shine sai yanzu zaku dawo?" zama ya yi ta zauna gefensa ya ce " sorry Abba banɗauka dare ya fara yiba "ok ya ce sannan ya kalleta ya ce" zo nan" tasowa ta yi kanta a ƙasa tazo gabansa zata tsuguna ya kamo hannunta ya zaunar da ita gefensa sannan ya ce " karki sake kunna Tv idan ba weekend ba ok" to tace masa sannan ya ce " kije ɗakina akan gado akwai wata leda ki ɗakko " tashi ta yi ta tafi ta ɗakko ta dawo ya ce " buɗe " buɗewa ta yi taga wasu chocolates da biscuit da yawa irin masu tsadar nan ya ce " Uncle ɗinki ya ce nakawo miki" murmushi ta yi ta ce " thank you so much " tashi ta yi zata tafi ɗaki Farooq ya ce " Aneeserh zo mana mu raba" ƙara riƙe ledar ta yi ta ce " kabari saida safe " tana gaba faɗin haka ta shiga ɗakinta murmushi sukayi ya ce " zan kamaki ne wallahi " dariya Abba ya yi ya ce " ya wajen aikin naka?"...... Yau kam bayan ta dawo daga makaranta bata kunna kallo ba ta ɗauki littafinta tana karatu har akayi sallar magrib sannan ta tashi dan yin sallah....... Ranar Juma'a kasancewar da wuri ake tashin su daga makaranta bayan sun fito suna tsaye da Ma'u yaya Farooq yazo, murmushi ta yi ta ce " sai Monday yayana ya zo " Ma'u ta ce " muje na gaisa dashi" ok tace sannan suka nufi inda ya yi parking... Ganin su biyu yasa ya sauke glass ɗin motar, suna zuwa Aneeserh ta ce " yaya ga seatmate ɗina nan Asma'u ku gaisa " Ma'u ta ce " ina wuni " murmushi ɗauke a fuskarsa ya ce " lafiya lao ya karatun?" ta ce "alhamdulillah" ya ce " masha Allah, Allah ya taimaka " Ameen ta ce sannan sukai sallama da Aneeserh ta koma su kuma suka tafi..... Bayan sunyi nisa ta ce " yaya kasan me wannan ƙawartawa ta ce mini?" girgiza kai ya yi ya ce " A'a sai kin faɗa " murmushi ta yi tana wasada fingers ɗinta ta ce " wai cewa tayi tana sonka inama ta aureka " haɗe rai ya yi ya ce " keee ina wasa dake?" girgiza kai ta yi ya ce" idan kika sake yimin irin wannan maganar sena fasa bakinki" turo baki ta yi ta ce " toni ba saƙo aka baniba zaka dinga yimin faɗa " a fusace ya tsaida motar ya juyo ya na kallonta ya ce " Ya ce" wlh saina kwaɗa miki mari idan kika sakemim irin wannan maganar " fashewa ta yi da kuka amma bata sake cemasa komai har suka je gida, suna shiga ko gama parking bata tsaya yayi ba taɓude motar tayi waje girgiza kai ya yi sannan ya gyara parking ɗin ya sakko shima. Zaune ya tadda ita gaban Abba sai rusa kuka take kamar wacce akawa wani mugun abu, zama ya yi aikuwa Abba ya rufeshi da faɗa shikam saboda mamaki ma kasa rufe bakinsa yayi jin abubuwan data faɗawa Abban, sukuyar da kansa ya yi bai ce komaiba har Abba ya gama faɗan sannan ya ce"sorry Abba" shuru Abba ya yi yana kallonta ya ce" tashi kije ki cire kayanki" toh ta ce sannan ta tashi ta shiga ɗakinta shima tashi ya yi ya wuce nasa ɗakin ransa a ɓace. Bayan sun shiga Ummi ta kalleshi ta ce" amma kasan halinta sarai ba baka saniba kasan babu yanda za'ayi Farooq ya daketa haka kawai ko wani abun tayi masa bazai daketa ba bare kuma haka kawai" Ajiyar zuciya ya sauke yana shan ruwan gabansa sannan ya ce" nasani itama ai kinsan halinta idan wani abun ya sameta fa?, kinsan lalurarta shiyasa ai nasan babu abunda ya yi mata" sakar baki Ummi ta yi ta ce" saboda kada wani abun yasameta yasa ka zauna kana yimasa faɗa irin haka kuma faɗanma a gabanta?, to Allah ya kyauta" ta tashi ta koma kitchen dan duba abunda take. Tundaga ranar bai sake kaita makaranta ba dan ko ganinsa cikin gidan batayi kuma ta damu sosai dan Allah ya gani tana son yayanta, yaukam saturday suna kitchen itada Ummi suna girki ta ce"Ummina wai ina yaya Farooq?" harararta Ummi ta yi ta ce. "Yaya Farooq ɗin da kikasa babanku yay taima faɗa?." Kwaɓe fuska ta yi ta ce"please Ummi yana ina wallahi so nake na ganshi" kallonta Ummi ta yi ganin yanda ta shagwaɓe fuska ta ce"yaje Abuja" ta ce" amma shine ba'a faɗaminba kuma nima inaso naje fa" banza Ummi ta mata ta cigaba da abunda take aikuwa ta kumbura kamar ta fashe ta juya ta fita a kitchen ɗin, Zaune ta tadda shi yana danna wayarsa da gudu ta tafi ta rungumeshi tana cewa"yayaaaa" dariya ya yi kawai ta ɗago ta kalleshi ta ce. "Yaya shi ne kayi tafiyar ka, ka barni ko?." Kumatunta yaja ya ce, "I'm sorry kinji" Kitso ta fara masa da gemu kamar yadda ta saba indai suna zaune, kwaɓe fuska ya yi yana riƙe hannun nata ya ce. "Ki yiwa Allah ki daina yimin wallahi da zafi."🥲 Turo baki ta yi tana faɗin"Dan ma zan maka kitso.." Langwaɓar da kai ya yi ya ce"to na yafe basai an yimin ba" tashi ta yi a jikinsa ta ce"shikenan babu ruwa na dakai" jawota ya yi ya ce" Allah ya baki haƙuri kinji, jeki ɗaki na tawo miki da abun daɗi" tashi tayi da gudu tashiga ɗakinsa, ta ɗauko sannan ta fito. Zama tayi ƙasan kujera zata buɗe ya ce" no ni zaki bawa ai" babu musu ta miƙa masa ya kalleta yana murmushi ya ce"closed your eyes" waro ido ta yi sai kuma a hankali ta rufe idanun nata ya ce"karki kuskura ki buɗe sai na ce miki" gyaɗa masa kai kawai tayi, a hankali ya kalleta ya ce. "Now opened it." A hankali ta buɗe idanun nata tana kallonsa, ya yi murmushi, ta kalla gabansa, ai batasan lokacin da ta fasa wata uwar ƙara ba, ta rungumesa tana wujijjigashi tana dariya ta ce. "Yayana i Love you wallahi har na manta yau birthday ɗina, thank you so much Yayana." Dariya shima ya yi yana cewa. "Happy birthday to you.." Ummi ce ta fito dan ta ɗauka wani abun ne ya faru, sai kuma taga suna ta dariya girgiza kai kawai ta yi ta koma, ya miƙo ma ta wuƙar ta karɓa ya riƙe hannunta yana ma ta waƙa har ta yanka cake ɗin ta saka masa a baki shima ya bata, sannan ta gutsura ta yi kitchen da saurinta, duk yadda Ummi tayi akan ta kyaleta ki tayi har sai da ta bata cake ɗin, sannan ta fito suka zauna ya dinga yi musu hotona suna dariya abin su. Yau tashi suka yi zasuyi tafiya lokacin kuma ya yi daidai da lokacin da su Aneeserh suke jarrabawa a school. Zama tayi gefen Abba tana kallonsa ta ce. "Abba Dan Allah ku tafi dani wallahi idan muka dawo za'amun make-up ɗin jarrabawar." Murmushi Abba ya yi ya ce. "No Aneeserh kiyi zaman ki kinji, nayi miki alƙawarin idan kun gama exams da kaina zan kaiki wajen Uncle naki His excellency kinji, amma yanzu kiyi tafiyar ki makaranta." Hawaye ne ya kawo idanunta ta ce "Amma Abba ni dawa zan zauna a gidan?." Ya ce "bafa daɗewa zamuyi ba gobe zamu dawo kinji na sanki jaruma ce zaki iya zama." Goge hawayen fuskarta ta yi ta ce. "Toh Abba harda Yaya Farooq?." Murmushi Abba ya yi ya ce. "Eh mana kema na ce miki zan kai ki" Shiru tayi bata kuma cewa komai ba, ya kamo hannunta ya riƙe ya ce. "Sorry baby kiyi karatu da kyau zan siyo maki chocolates da sweet da yawa." Rungumeshi ta yi batace komai ba. Ƙarfe biyu suka gama shiri dan tafiya ta rakosu har parking lot, Abba na kallonta ya ce. "Banda wasa kinji?." Ɗa ga masa kai kawai tayi Ummi ta rungumeta, ta ce "Bafa zama zamuyi ba karkiji tsoro." "Toh." Kawai ta ce sannan ta kalli Yaya Farooq kafin ta ce komai ya yi ma ta murmushi ya ce. "Sai mun dawo lil sis." Ya shige mota dan idan har tashi za'a bi baza'a tafi abar Yarinyar da bata wuce 15yrs ita kaɗai ba, kawai dan babu yadda zaiyi ne yasa. Kallonsu ta dunga yi har suka shiga mota tana ɗaga musu hannu suma suna ɗago ma ta a haka har suka fice daga gidan, ita kuma ta koma ciki. Washe gari da safe ta tashi ta dafa abinci ta zuba a flask sannan ta ɗau jakarta zata fito akayi kiran wayarta, ɗauka tayi ganin sunan Abba ta yi murmushi sannan ta ɗaga wayar, bayan ta gaisheshi ta ce. "Abba yaushe zaku dawo?." Ya ce "Idan kin dawo daga school zaki tarar da mu a gida kinji baby?." Murmushi tayi ta ce. "Tom Abba Allah ya dawo daku lafiya." Ya amsa ma ta da, "Ameen Aneeserh ki tafi karki makara." "Okay." Ta ce sannan ya katse wayar ta ajiye ta fito driver ya tafi kaita school. *Wannan shi ne abin da ya faru kuma sanadin mutuwar iyayenta da kuma Yayanta wanda kuma shi ne mafarin ƙaddarar ANEESERH kudai ku biyo dan jin yanda labarin ANEESERH zai kasance da kuma ƙalubalen da yake cikin rayuwarta.* *PRESENT*.... *CI GABAN LABARI*... ✨✨```ANEESERH```✨✨ *Queen Of Squad With Nkd's 🤙* *Ep. Three* *PRESENT*.... *CI GABAN LABARI*.. Dogon numfashi His Excellency yaja idanun sa akan Aneeserh cike da yake da tausayin ta, Yarinya ƙarama cikin shekarun ta da bata haura 14 to 15 yrs ba, tayi rashin iyayen ta da Yayan farouq, gaskiya dole mutum ya tausaya ma ta komai dakiyarsa kuwa. "Aneeserh ki daure kinji ɗiyata insha Allah zuwa anjima Jirgin mu zai ɗa ga zuwa Abuja acan zaki ci gaba da gudanar da Rayuwar ki, ina fatan ki fara sabuwar Rayuwa mai cike da farin ciki." Shiru tayi masa kamar bazata ce da shi komai ba, sannan ta sauke ajiyar zuciya tana faɗin. "Uncle wai yanzu fa shikenan bazan ƙara ganin Yaya Farouq na ba, balle har nayi masa tsokanar dana saba muyi nishaɗi, shikenan Abba na yafi bazai dawo gareni ba, bazai dinga yimin faɗa da nasiha ba, idan ina wani abu da bai dace ba, Allah Sarki ni na cika marainiya a yau babu Ummi da zan tayata girki, wayyo Uncle Zuciyata zafi take yimin sosai Uncle ji nake kamar nima na bisu kawai na huta." Cikin sauri His Excellency ya rungumota a ƙirjin sa ganin yadda tayi maganar idanunta suna lumshewa, tayi baya zata faɗi daga zaune da take saman gadon jinyar. Lumshe ido tayi yayin da take tuna siffofin iyayenta Abban ta mai ƙaunar ta Ummi Yaya Farouq ɗin ta duk sun tafi sun barta ita ɗaya a Duniya. ____________ A hankali ta buɗe fararen idanunta ta sauke su a window na private jet. da suke zaune ciki ita da Uncle nata da Matar sa Hajiya Aisha. Aneeserh mai yawan surutu barkwanci neman tsiwa yau gata so silent Kuma a cikin jirgi ba tare da Abba da Yaya Farouq ɗin ta a gefe ba, hawaye ne taji ya zubo ma ta, da dabara ta goge dan bataso Uncle nata da matar sa su gani. Jin gine kanta tayi gefen kafaɗun Her Excellency tana lumshe ido. Murmushi Hajiya Aisha tayi sannan ta gyara ma ta ta kwantar da ita saman lap's nata. A haka dai shiru har Jirgin su ya yi landing a babban filin saukar jirgi na Garin Abuja. Securities na musamman suka tar be su a Airport, sannan suka shishshiga tsalatsalan motocin guda biyar jeras suka bar Airport suna jiniya, yayin da Aneeserh take maƙale jikin Her Excellency duk wata iri take jin kanta. *** Koda isarsu Government House of President na Nijeriya gaba ɗaya, tsararren gida na gani na faɗa na nunawa a television, suka sama tarba mai kyau daga ma'aikatan gidan maza da mata cikin uniform white and sky purple color, masu aikin girke-girke sun ɗaura Apron saman kayan jikin, dukkanin su jere zagaye da motocin fuskokinsu ɗauke da walwala na dawowar His Excellency da matar sa Hajiya Aisha mutanen kirki cikin ƙoshin Lafiya. Nan ba tare da wani ɓata lokaci ba, suka fiffito Aneeserh tana rungume da Hajiya Aisha idanunta a lumshe sam taƙi bari tayi nesa da ita. A haka har suka shiga katafaren main palo na gidan ƙamshi kawai ke tashi ta ko'ina na palon gyare yake tsaf tsaf. "No, Bacci zan yi, ki kaini Bedroom ne Auntie." Aneeserh tayi maganar idanunta a lumshe lokacin da Her Excellency take ƙoƙarin a je ta saman Royal sofa dake zagaye da Palon. Ajiyar zuciya ta sauke zuciyarta cike fal da tausayin ta, sannan ta nufa upstairs da Aneeserh rungume da kafaɗar ta. Shimfiɗe ta tayi saman Bed Like a Little girl sannan ta ja ma ta Blanket ta lulluɓe ta, tana shafa sumar kanta dake baje saman goshin ta. "Ohya Sleep, kina buƙatar hutu kiyi bacci kinji?, And please ba Auntie zaki ke kira na ba, da Mommy nake so daga yau ki rinƙa kirana, okay!?." Buɗe lumtsatsun idanunta dake cike da gajiya da kuma Bacci tayi ta sauke su saman kyakkyawar fuskar matar bafulatana da ita. "Okay, Mommy Insha Allah, amma zan iya tambayar ki kuwa?." "Ina sauraren ki Shalele." Murmushi Aneeserh tayi a karon farko har sai da fararen haƙoran ta suka bayyana Yaya Farouq ne yake kiran ta da wannan sunan. Faɗar haka da Hajiya Aisha tayi saita tuno ma ta da Yayan ta, sai dai tun kafin Murmushin nata yaje ko'ina tayi saurin gimtse fuska idanunta tana tara kwalla tunawa da tayi yanzu ita kaɗai ce a Duniyar ta ba tare da Yaya Farouq abin ƙaunar ta ba, da Ummi da Abba ba. Cikin taɓe fuska na shagwaɓa alamar kuka ta kalle Her Excellency da rawar jiki da murya take faɗin. "Mommy! Menene zan dinga yi wanda ba zai saka na manta da Iyaye na ba?." Kwallar tausayin ta cike da idanunta Allah Sarki har ta ɗauki dan gana ta sakawa ranta. "Aneeserh saboda Mene kika yimin wannan tambayar?." "Saboda Ina Son Ummi na sosai ina son Abba da Yaya Farouq nawa Komai nayi masa baya duka na koda ya yi fushi dani baya taɓa dena siyomin chocolate Ina ƙaunar su sosai bana son na manta da su har abada a Rayuwata." Ƙaunar Yarinyar ne ya daɗa shiga ran Hajiya Aisha. Ta kamo ta ta zaunar da ita saman mattress ɗin sannan ta a je mayafin kanta gefen gadon, ta kwantar da kan Aneeserh saman lap's nata tana shafa ma ta sumar kanta mai yawan gaske take faɗin. "Ki dinga musu Addu'a duk lokacin da kikayi sallah kinji, wannan ɗaya ne daga cikin abubuwan da zan faɗa miki ki dinga yi saboda ki dinga tunawa da su forever." "Sallah!! Wayyo banyi sallah ba Abba zai dakeni wayyo ni Yaya Farouq." Aneeserh tayi maganar da sauri tana sauka daga saman Bed ɗin da sauri ta nufa hanyar bathroom take faɗin hakan. Sai dai chak taja ta tsaya ƙafafuwan ta suka ma ta nauyi sosai tuna cewa ashe Abba da yake ma ta faɗa idan batayi Sallah akan lokaci ba, bashi a Duniyar." Slowly Hawaye ya wanke ma ta fuska, cikin sanyin jiki ta juya ta kalla Hajiya Aisha da tayi ma ta Tsuru da ido tana kallon ta cike da tausayin ta, Tabbas ta ɗauki aniyar riƙe Aneeserh tsakani da Allah ta bata lokacin ta, wurin bata tarbiyya mai kyau Kamar yadda iyayenta zasu bata. Ba tare da Aneeserh ta ce da ita komai ba, ta juya ta shige cikin Bathroom ɗin cikin sanyi jiki. Alwala ta ɗauro duk wani motsi da zatayi sai ta tuna Rayuwarta da Ahalin ta Rayuwa mai daɗi mai cike da farin ciki mara adadi mai tsayawa a rai. Fitowa tayi daga bathroom ɗin bayan ta kammala alwalar sannan ita ma Hajiya Aisha ta shiga tayi Alwala ta fito suka yi Sallahr la'asar da aka kira basu samu sun yi ba sai yanzu. Duk wani motsin Aneeserh akan idon Hajiya Aisha yake gudana tana lura da yadda ta zubawa Bedroom ɗin idanu tana kalla bayan sun idar da Sallahr. "Bedroom ɗin da kayan cikin sa sun yi miki ko kuwa a canza bakyason kalar su?." Da sauri kuma a firgice Aneeserh ta kalla Hajiya Aisha da tayi ma ta tambayar tana kallon ta Murmushi ɗauke a fuskarta. Ƙasa tayi da idon ta tana wasa da Diamond ring dake hannunta wanda Yayan ta Farouq ya bata Ranar Birthday nata ta ce. "Kalar ruwan ɗakin kala ne mai kyau wanda matasan Ƴan Mata masu kamar shekaruna suke so wato sky purple color, sannan ɗakin ya haɗu sosai, domin ko ɗiyar president albarka." "HHhH to ai kece ɗiyar President ɗin, ko kin manta wanene Uncle ɗin naki President of Nijeriya ne guda, kinga ke nan kece ɗiyar President ɗin, dama kuma ɗa ɗaya garemu, shi kaɗai Ubangiji ya nufa da zamu haifa, sai dai yanzu kun zama biyu, dan ina fatan ki ɗauke mu Ni da Uncle ɗin ki, Iyaye a gareki Shalele, nayi Alƙawarin kula dake daga yau kuma yanzu har Ranar da zanga Auren ki."😅 Murmushi Aneeserh tayi tana rufe fuska domin Hajiya Aisha ta bata kunya sosai. Ita ma Hajiya Aisha Murmushin tayi dama Burin ta ke nan Aneeserh ta saki jikinta ta saba da su sannan ta ɗauke su Iyaye a gare ta.. Hajiya Aisha bata bar Aneeserh ba har sai da ta tabbatar da ta rage ma ta kaɗan daga cikin damuwa da take ciki sannan ta fito daga Bedroom ɗin ta bar Aneeserh tayi Bacci ta huta. A palo ta tarar da mijin nata zaune da alama ita yake jira dama. "Sorry Habibi kasan sabuwar ɗiyar tamu sai da lallashi da kuma bata lokaci yadda ya kamata, don tana cikin kewa sosai wanda bana tunanin zata fita daga wannan hali a wannan lokacin." "Masha Allah. Babu Komai Jannat karki damu, na gode miki sosai da nuna kulawa ga ɗiyar ɗan uwana, ina fatan kulawar ki a gare ta ya ɗaure har abada ki mayar da ita Tamkar ɗiyarki ta cikin ki." Zama tayi gefen sa saman 3sieter da yake kai ta kamo hannun sa ta haɗa da nata. "Insha Allah Habibi nayi alƙawarin kula da Aneeserh duk rintsi duk wuya a duk yadda take zan kula da ita na bata tarbiyya kamar ɗiya ta ta cikina wacce ban samu ba, sai yanzu wato Aneeserh." "Kai Amma naji daɗi sosai Jannat very proud of you." Murmushi tayi na jindaɗin alfahari da ita da mijinta abin ƙaunar ta yake yi ta kwanta jikinsa sanin su kaɗai ne cikin Palon babu mai shigowa. "Yauwa kaga yanzu sai mu zuba ido sosai akan abin da take so da kuma wanda bata so, yadda zamu fi janta jiki, ta manta duk wani abu mummuna a Rayuwar ta, farin ciki ya gauraye Insha Allah gobe ko jibi Ni da kaina zan aje duk wani aiki da yake a office na bawa ɗiya ta kulawa mu tafi yawo da ita mu zagaye Abuja gaba ɗaya nasan hakan zai taimaka sosai wurin rage ma ta kewa." "Kai Masha Allah amma fa naji daɗi sosai kuma insha Allah dani za'ayi wannan yawon Ubangiji ya kaimu." Amsa wa tayi da Ameen, sannan cikin nutsuwa irin na manya da kuma fahimtar juna dake tsakanin su suka ci gaba da tattaunawa akan yadda zasu ɓullo wa al'amarin Aneeserh... *Wannan ke nan kaɗan ko nace mafari daga cikin wannan Zazzafar labari mai suna ANEESERH Insha Allah idan mabiya kukayi juriya na biyo wannan labari gaba ɗaya zamuji yadda rayuwar Aneeserh zai kasance yanzu dai ga Aneeserh a Abuja gidan Uncle nata Mister President ko ya ya zamanta zata kasance???...* *💥Aneeserh Just The Beginning.*💥 ~Paid 500₦~ *WACCA TA SHIRYA BIYA SAI KI BIYA TA WANNAN DETAILS👇* *Account Name: Hauwa lawan.* *Account Number: 9086030007.* *Bank Name: Opay digital service.* *Sannan sai ki turo evidence of payment ta waɗan nan Countacts_08081129487 or 09086030007.* *MU TARA A NEXT PAGE DOMIN SANIN YADDA ZATA KASANCE.*😇🤸 *ANEESERH.* *Story $ Writing By:*✍️📚 *N $ N.* Ep- Four. Wajejen la'asar ta farka daga bacci, a hankali take buɗe lumsassun idanunta tana sake ƙarema ɗakin nata kallo wai yau ita Aneeserh ce zaune cikin garin Abuja ba tareda Abba, Ummi Yaya Farooq ba anya kuwa ba mafarki take ba?, ganin batada mai bata amsa yasa ta tashi tana tafiya kamar wacce kwai ya fashewa a jiki ta shige banɗakin.... Zaune ta tadda Mommy tana danna wayarta tana ganinta ta sakar mata murmushi tana ajiye wayar hannunta ta ce "Kintashi daga baccin?" Gyaɗa mata kai Aneeserh tayi dan har sannan bata wani saki jiki da'itaba, ganin ta tsaya yasa Mommy ta ce "ba sallah zakiyi ba?" tana wasada fingers nata ta ce "Eh sallah zanyi " girgiza kai Mommy ta yi ta ce "ok idan kin idar ina jiranki a parlona" tom kawai ta ce sannan Mommy ta fita ita kuma ta bita da kallo..... Ahankali ta tura ƙofar parlon kamar wata mara gaskiya, babu kowa cikinsa sai wani daddaɗan ƙamshi dake tashi a parlon iyaka haɗuwa parlon ya haɗu, zama tayi kan ɗaya daga cikin royal sofa ɗin dake parlon ta lumshe idanunta. Fitowa Mommy tayi ta kalleta ganin yanda ta rufe ido sosai takejin yarinyar a cikin ranta, ta zauna gefenta tana sake ƙare mata kallo, Aneeserh asalin kyakkyawa ce tun daga kan idanunta yanda suke a rufe gata da long eyelashers masha Allah, hancinta dogone sosai kuma ɗan ƙarami abin sha'awa, sai ɗan ƙaramin bakinta wanda yake jajur dashi koda yaushe saboda yawan tsotseshi da takeyi. Murmushi Mommy ta yi ta ce "Masha Allah" Buɗe idanunta ta yi tana kallonta sai kuma ta kwaɓe fuska ta ce "Why are u looking at me like that?" Murmushi Mommy ta yi ta ce" ina sake kallon kine saboda kada watarana na kasa gane ki sweetheart" murmushi Aneeserh tayi wanda iyakarsa lips ɗinta ta ce" ina Daddy?" sosai Mommy taji daɗi aranta jin sunan da takira his excel..ta ce "Yana office dear, kici abinci sai muyi hira sosai" daga haka ta dana wata ƙararrawa not too long wata maid tashigo ta sunkuya cikin girmamawa ta ce " gani maa" "Ki je ki haɗowa dear abinci, but abu mara nauyi haka" sunkuyarda kanta ta yi ta ce "okay maa" sannan ta juya ta fita..... Ajiye spoon ɗin tayi Mommy ta kalleta ta ce" mene?" Kwaɓe fuska ta yi ta ce "i'm full " haɗe rai Mommy ta yi ta ɗauki spoon ɗin ta ɗebi pepper ɗin offals ɗin takai bakinta, shagwaɓe fuska ta yi ta ce kamar zatayi kuka "Wlh Mommy na ƙoshi anjima zanci" "Promise?" Mommy ta faɗa. Gyaɗa mata kai ta yi alamar Eh sannan Mommy ta ajiye ta ce "Allah ya kaimu anjiman"...... Banda ƙarar spoons babu abinda kakeji a parlon, juya abincin kawai take amma ta kasa kaishi bakinta lura da haka ya yi ya ce "Aneeserh meyasa baki cin abincin?" Sunkuyar da kanta kawai tayi batace komai ba ya yi mata alama da tazo da hannunsa. Tashi tayi ta kowa kujerar kusada shi ta zauna yana kallonta ya ɗebi abinci ya ce "haaaa" kasa yimasa musu tayi a hankali ta buɗe bakin ya zuba mata abinci, haka ya dunga feeding nata har ta ƙoshi sannan ya rabu da'ita, yana kallon Mommy ya ce " Jannat ya kamata zuwa gobe akaita ta zaɓi kayan sakawa, nd gobe Bashir zai zo " ta ce "okay, in sha Allah " ya ce "good"........ Da sassafe ta farka kasancewar ta saba da tashin wuri a gida amma babu abin yi agidan nan dan komai anriga anyi, gani abun take kamar ba gaske ba yau itace irin wannan lokacin bata kitchen kuma badan lokacin makaranta yayi ba, wasu zafafan hawaye taji sun zubo mata ta ce "Allah ya jiƙanku da rahma, Allah ya gafarta muku"..Kwanciya ta kuma yi kan royal bed ɗin nata tana cigaba da tunanin rayuwarta ta baya da kuma wacce ta sameta yanzu....... Ƙarfe biyar saura Mommy ta shigo ɗakin tana kallonta ta ce "yawwa Aneeserh please duk abinda kika san zaki buƙata ki ɗauko dan Allah" murmushi ta yi ta ce "amma Mommy zan siyo chocolates da biscuit!" dariya Mommy ta yi ta ce" duk abinda kikeso ki siya dear ke ko duka shopping mall ɗin kikeso zaki samu" rufe fuskarta ta yi tana dariya dan sai asannan take jin kunyar abunda ta faɗa, girgiza kai Mommy ta yi sannan takama hannunta suka fita...... Har takusa kaiwa ƙofa ta ce "Au!, na manta kije kiyiwa Daddy sallama yana parlonsa uncle ɗinki ma yazo" toh kawai ta ce sannan ta kama hanyar parlon...... Da sallama tashiga parlon kanta a ƙasa, murmushi Daddy ya yi ta tsuguna gefensa tana kallon baƙin dake zaune a parlon ta ce "Ina yini" Cikin sakin fuska suka amsa mata sannan ta kalli Daddy ta ce "Daddy daman zanje shopping ne shine Mommy ta ce nazo na faɗa maka" shafa kanta yayi ya ce "ok tom adawo lpia dear" tashi tayi ta juya ta fita tana tafiya a nutse kamar ba itaba....... Ya ce" nikam yaya sai nake ganin kamar a aurawa Aliyu yarinyar nan ko Allah zaisa a dace" Shuru his excellency ya yi sai kuma ya ce "Amma meyasa ?" "saboda yarinyar tana da hankali kuma yarinya ce duk yanda yakeson ta kasance haka zata masa" Uncle Nasir ne ya ce "Bashir kazo da magana nima kuma wlh tunda na ganta naji sha'awar ya aureta" murmushi kawai Daddy ya yi yana kallon ƙannen nasa. Shuru suka yi dan sun rigada sunsan halin ɗan uwan nasu akwai kafiya masha Allah....... "Shikenan na amince" Da sauri suka kalleshi domin ba su yi tunanin haka daga gareshi ba Uncle Bashir ne ya ce" Masha Allah kawai abinda za'ayi a ɗaura auren yanzu tunda duk zamu iya wakiltarsu" Waro ido Daddy ya yi sai ya ce" kamar ana yaƙi?" murmushi sukai atare Uncle Nasir ya ce "Ai wannan ɗinma yaƙin ne kawai a ɗaura yanzu" Babu yanda ya iya da ƴan uwan nasa aka ɗaura auren Aneeserh da kuma ɗan gidan president Aliyu wanda bamusan ko wane ba ko waye Aliyun??????. Ɗaukan duk abinda taga ya yi mata cikin shopping mall ɗin kawai take hankali kwance dan securites ne zagaye da ita suna gadinta har ta gama sannan suka kama hanya suka nufo gida......... Tunda ya fara maganar take kallonsa with mouth agape tarasa ma me zata ce masa, ta rasa farin ciki take ko akasin haka. Ganin yanda ta yi shuru yasa ya ce "Ko akwai matsala ne?" Girgiza kai ta yi ta ce" kawai dai ina tausayin yarinyar ne kwata-kwata shekarunta sha biyar kaga kuwa akwai ƙalubale zamanta cikin kishiyoyi har uku kuma dukkansu babu wacce batayi degree ba kaga kuwa dole naji tausayin Aneeserh" Kamo hannunta ya yi ya ce "ki tayata da addu'a kawai" ta ce" in sha Allah, amma shi Aliyun yaushe zai dawo?" "Maybe gobe" ya furta yana kallon dramar da ake haskawa a Arewa24..... Ana kiran sallar magrib a masallacin gidan suka shigo, kai tsaye ɗakinta ta nufa dan bataga Mommy parlon ba, bayan ta idar da sallar ta ɗauki al-qur'ani ta fara karantawa har akayi kiran sallar isha'i.... Kallonta Mommy take har ta idar da sallar sannan ta ce" shine bakizo kin faɗamin kun dawo ba ko?" sunkuyar da kanta ta yi sai kuma ta ce "Daman naga kina sallane shiyasa " harararta Mommy ta yi ta ce "Babu wani kawai dai bakison sakin jikinki har yanzu" turo baki ta yi amma ba tace komai ba, miƙewa Mommy ta yi ta ce "Maid zatazo ta jera miki kayan naki" gyaɗa mata kai ta yi har takai bakin ƙofa sai kuma ta ce " nd ki fito yanzu" sannan tayi waje...... Kwanciya tayi kan gadon tana tunaninta as usual har kuma bacci ɓarawo ya saceta..... *ANEESERH* ~Paid 500₦~ *WACCA TA SHIRYA BIYA SAI KI BIYA TA WANNAN DETAILS👇* *Account Name: Hauwa lawan.* *Account Number: 9086030007.* *Bank Name: Opay digital service.* *Sannan sai ki turo evidence of payment ta waɗan nan Countacts_08081129487 or 09086030007.* *ANEESERH.* BY: *N $ N.* *Ep. FIVE* *DREAM!!!* Da gudu ta fito daga Bedroom ɗin jikin ta sanye cikin Expensive princely gown fuskarta wadace da make-up, hannunta dake riƙe da tsadadiyar wayarta, yatsun suna bada sauti mai daɗi sakamakon awarwaraye da take sanye da su. Dariya kawai take yi tana kuma ƙara gudu faɗi take. "Yehhhh!! Nayi ma Yaya Farouq wayo na rigasa ƙari sawa tarbar Abba!." Tayi maganar tana daka tsalle cike da farin ciki ta ɗafale saman jikin mahaifin nasu da Dawowar sa daga Austaraliya ke nan Jerin gwanin motocin sa suka shigo Gidan da fitowarsa ta basa kyakkyawar runguma. Daidai lokacin kuma shima Farouq da ya biyo bayan ta ya fito daga palon, tsayawa ya yi yana haki daidai entrance, Hannu yakai yana goge Cake da ta shafe masa fuska da shi har tayi masa wayo ta rigasa tarbar Abba. "Allah Abba wannan Yarinyar ta ka sai ana haɗawa da Addu'a fa, wannan shegen wayo haka ga gudu kamar wacce taci ƙafan kare." Dariya Abba da Ummi suka yi lokacin da suka zazzauna saman Royal sofa dake palon haɗaɗɗen gaske bayan sun shiga.. "HHhH ai Yarinta ne zata dena. But amma fa kayi kyau da wannan cake na fuskar ka kamata ya yi muyi pictures a hakan..." Abba ya yi maganar cike da zolaya yana dariya. "Yehh kuma wallahi Abba Gaskiya ka faɗa kamata ya yi muyi pictures a hakan kodan Tarihi gaba bamusan wanene gawan fari ba, koda dai bana fatan ku rigani tafiya ku barni." "Lalle Yarinya kince wani abu amma ki rubuta ki a je sai na rama nima." "Oho dai yanzu dai ku tashi muyi pictures ba sai an jira photographer ba." "Au wai da gaske kukeyi ne?." Farouq ya tambaya da mamaki Ganin yadda suka mimmiƙe ɗin. Hanyar Dining ya yi domin ya samu ya wanke cake ɗin a Tap. Lura da hakan yasa Aneeserh cikin sauri ta sha gaban sa, ya yi yunƙurin canza hanya ta kuma shan gaban sa ita da Abba da Ummi nan suka shiga ƴar tsere cikin palon Kamar wasu Yara sun biyewa Aneeserh sai faman zagaye Palon sukeyi wai a dole ba zasu bari ya wanke fuskar ba sai sun yi pictures da shi a Hakan....... *NOW* Wuntsilowar da tayi tun daga saman mattress ɗin ne, har ƙasan tiles, yasa ta farka a firgice tabi ta haɗa uban gumi Tamkar wacce aka watsama Ruwa a duka jikinta. Waige waige ta fara yi tana ya ye Blanket da take ƙudundune ciki, tunanin ina ne nan kuma take, sannan kuma ina su Abba da Yaya Farouq ɗin ta da Ummi suke, waye ya kawo ta nan, kodai har sun dawo ne bata sani ba???... Kuka ne taji ya suɓuce ma ta sosai lokacin da ta tuna Komai ya dawo kwakwalwarta, kewar iyayenta da Yayan cike fal da zuciyarta ta miƙe tsaye tana tangaɗi Kamar wacce ta sha giya, take zagaye Bedroom ɗin cikin rashin abin yi da tashin hankali hawaye na ma ta zirara a idanunta, takai hannu ta toshe bakinta, lokacin da ta ƙari sa gaban Akwatin ta da aka zo dasu, ta ciro wani frame na pictures nasu ita da Ahalin ta Abba, Ummi, Yaya Farouq, sun yi kyau sosai Ranar da ta cika fifteen years a Duniya suka yi shi. Kuka take sosai tun daga ƙasan ran ta, haƙoranta har ƙara suke badawa suna haɗewa wuri guda saboda tsananin kuka da take yi, a hankali bakinta take furta. "Wayyo Allah na Abba na Ummi, Yaya Farouq, Please ku dawo gareni, bazan iya jure rashin ku ba, wayyo ni Rayuwa ta Aneeserh wannan wacce kalar ƙaddara ce???." Zubewa tayi a ƙasa ita ba suma tayi ba kuma bata dena hawaye ba, gunin ban tausayi, ta daɗe sosai a hakan sannan can knocking ƙofar da taji ne yasa tayi saurin sha re hawayen ta, a tunanin ta Hajiya Aisha ce, da sauri ta mayar da Frame ɗin cikin Akwatin, sannan da hanzari ta shige Bathroom ta wanke gaba ɗaya fuskarta. Ta fito ta ƙari sa sannan ta buɗe ƙofar tana yunkurin ƙaƙalo Murmushi na yake saman kyakkyawar fuskar ta. Sai dai Ganin wacce take a ƙofar ne yasa, ta matsa gefe ba tare da ta ce da ita komai ba, ta koma ciki ta zauna gefen Bed tana wasa da finger's nata. "Am Maa!! Her Excellency ce dama ta ce...." Tun kafin ta ƙari sa faɗar abin da ke bakinta tayi saurin dakatar da ita, ta hanyar yi ma ta nuni da gefe wurin da tulin abubuwan da ta kwaso a shopping Mall da ta fita suke, kaya ne kala kala tun Daga kan na sakawa a jiki tufafi, biscuits chocolate cake babu abin da babu. Shiru maid ɗin tayi sannan ta ƙari sa wurin ta fara abin da ya kamata. "And she's call you.." "Okay, where is her?." "She's in main Palo in Downstairs.." "Okay, Thanks." Ta furta sannan ta miƙe tsaye ta kuma Gyara fuskar ta, kar a gane tayi kuka sannan ta fice, koda ta sauka Down babu kowa Palo, tunani tayi akan ƙilama tana kitchen, hakan ne yasa ta nufa kitchen ɗin kai tsaye. "Oh, My Son, I don't like this playing with my heart da kakeyi fa, Now Tell me, Yaushe ne zaka dawo?, and tell me the truth..." Shiru tayi tana sauraren abin da yake faɗa. Yayin da Aneeserh da ta shiga kitchen ta tarar da Hajiya Aisha tana wayar, kuma da alamu da yaron ta ne, yasa taja gefe tana jira ta kammala. *IN BRIEFLY* Haka Rayuwar Aneeserh ta ci gaba da tafiya cikin gidan Gwamnati Na President of Nijeriya, Kuma uncle nata da ya kasance Yayan Mahaifin ta mai rahusawa. Ba'ace tana jin daɗi na zama gidan ba, sannan baza'ace bata jin daɗi ba, saboda bata nema Komai ta rasa ba, komai ta tambaya, kai tun kafin tayi tambayar ma ake ma ta, sosai Her Excellency take jan Aneeserh a jiki tana bata kulawa da ya dace, shima His Excellency ba'a barsa a baya ba, duk da cewa ayyuka suna masa yawa, amma sosai shima yake bawa Aneeserh lokacin sa. Aneeserh zaman ta a gidan Uncle nata tana gudanar da rayuwa Normal babu wani walwala mai yawa a ciki. Lokuta da dama idan ta zauna da Hajiya Aisha da take kira da Mommy, yawancin fira da Hajiya Aisha take ma ta akan ɗan ta Hydar ne, sosai Aneeserh ta kula da ba ƙaramin ƙauna Mommy takewa Hydar ba, da ita Aneeserh ɗin bata san shi ba, kuma bata taɓa Ganin sa ba. Tun Aneeserh bata damu da zancen sa ba, har ta fara saka ayar tambayar ta akan sa, Ganin Kullum Hajiya Aisha idan tana waya da shi lokacin da suke tare babu tambayar da take masa, sai Yaushe zai dawo Nijeriya, aikin sa ke nan ja ma ta rai. Tambayar Aneeserh anan ita ce, wai shin to yana ina ne, kuma wanene shi ma gaba ɗaya sannan yana wata ƙasa ce questions dai Like this sune cike zuciyarta. Wasu lokutan har ta wurin Maids na gidan tana samun labari akan sa, anan ne ma take ji, wai shiɗin soja ne, kuma matsayin Likita yake cikin su, babban muƙami. Sosai ta shiga tsoro jin cewa Soja ne shiɗin, a Rayuwar ta babu irin mutane da ta ke tsoro a Duniya sama da Soja........ ```GA DAI ANEESERH NAN TANA GUDANAR DA RAYUWARTA BA TARE DATA SAN CEWA AN ƊAURA MA TA AURE DA MUTUMIN DA BATA SANI BA, BATA KUMA TAƁA GANINSA BA, SANNAN KUMA WANDA TAKE MATUƘAR TSORON AIKIN SA WATO SOLDIER, KO TA ZATA KAYA?????``` ```TOHM A TARA NEXT PAGE 😸``` 💞💞*ANEESERH*💞💞 💥*The Beginning*💥 *🔥💫Nanameera $ Nainarh KD.🔥💫* ~Paid 500₦~ *WACCA TA SHIRYA BIYA SAI KI BIYA TA WANNAN DETAILS👇* *Account Name: Hauwa lawan.* *Account Number: 9086030007.* *Bank Name: Opay digital service.* *Sannan sai ki turo evidence of payment ta waɗan nan Countacts_08081129487 or 0810 660 8363.* *ANEESERH* *💥Aneeserh Just The Beginning.*💥 ~Paid Book~ *😻🔥Wai shin baku da labarin cewa free page's Aneeserh suna daf da ƙarewa 🙀 kuyi gaggautawar yin payment domin wannan tafiyar Zazzafa karya kasance ba tare da ku ba. Don't Miss It Dearest Sister's.🔥😻* *Story $ Writing By:*✍️📚 *N $ N.* *💫Nanameera $ Nainarh KD.💫* *EP. Six-Seven.* Yau Saturday dan haka da wuri ta tashi tayi wanka sannan ta shirya cikin wata abaya peach colour wacce tayi matuƙar amsar jikinta, saida tagama shiryawa tsaf sannan ta sauko ƙasa......... Babu kowa a parlon hakan yasa tayi zamanta ta kunna tv tana aikin kallo, nikam nace daman su Aneeserh ansami waje. "Ai ya cemin zuwa tuesday zai dawo" Mommy ta faɗa lokacin da suke fitowa itada his excel., zama sukayi kan royal cusuion ɗin parlon da murmushi a fuskarsu, sunkuyawa ta yi ta ce" Daddy good morning, Mommy good morning" "morning dear" suka faɗa atare Daddy ne ya ce" kallo ki keyi?" murmushi ta yi sannan ta ɗaga masa kai, kallonta Mommy ta yi ta ce" ai kin kusa komawa makaranta in sha Allah" dariya tayi dan daman burinta kenan tana kallon Mommy ta ce" Mommy yaushe?" "Sai Aliyu ya dawo" shuru ta yi dan har ta fara gajiya da maganarsa a gidan, maids ne suka fara shigowa suna jere kayan breakfast ɗin har suka gama sannan suka fita su kuma suka nufi dinning area ɗin dan fara cin abincin.............. Wajejen la'asar tana zaune duk gidan ya gundureta, Mommy ta shigo hannunta ɗauke da plate wanda akayi sliccing pineapple da apple aciki. Zama tayi gefenta kasancewar akan kujera 3seater take ta dafata, kallonta ta yi ita kuma ta yi murmushi ta ce "Kin gaji ko daugher?" murmushi kawai tayi amma ba tace komai ba, ta ce" ga fruit nan kisha kinji zanje gidan wata friend ɗita" kallonta tayi har zatayi magana sai kuma tayi shuru ganin haka yasa Mommy ta ce" ko zaki bini?" gyaɗa mata kai tayi dan daman abinda zata tambayata kenan. Ta ce" ok tom jeki shirya sai muje" tashi tayi ta wuce ɗakinta dan sanza kayan kamar yarda Mommy ta ce mata................ Wani irin babban gidane sosai kuma ya haɗu iya haɗuwa, sai kallonsa take dan tunda ta shigo abuja banda gidan president bataga wanda ya kaishi kyau ba.......... Da murmushi ta ce"oyoyo yau kece agidan?" dariya ta yi tana zama ta ce" tunda ke kin kasa zuwa ni gani nazo ai" girgiza kai Hajiya Zainab ta yi ta ce"wlh ba haka bane your excel kinsan Ayrah batajin daɗi shine abinda ya hanani fita wlh" "Allah sarki kece jikin ne?" ta ce" wlh kam abunnata ne kamar tasamu sauƙi kamar kuma bazata warkeba, ɗazu mijinnata ya bar gidan nan wai cewa ya yi azubar da cikin kawai" da mamaki Mommy ta ce" amma dai baku yarda ba ciki ai lokaci ne da Allah yabasu daman duk wata mace ai dole zatayi laulayi saidai wata tayi mai zafi wata kuma da sauƙi" ajiyar zuciya ta sauke ta ce" wlh nima abinda nace masa kenan duk yabi ya damu", murmushi Mommy ta yi ta ce" kawai rabuwa zaki yi dashi Allah ya bata lafiya" Ameen ta amsa dashi sannan ta kalli Aneeserh ta ce" Hajiya ina kika samo budurwar ƴa?" kallon Aneeserh Mommy ta yi tana murmushi ta ce".wlh ƴa nayi daga kano, Aneeserh tafi ɗaki kiyi kwanciyarki" da sauri ta tashi dan daman ta gaji da zaman parlon..... Bayan tashiga ta kalli Hajiya Zainab sannan ta ce" matar Aliyu ce" da mamaki ta ce" wata matar kuma?, anya kuwa abun baiyi yawa ba?" girgiza kai Mommy ta yi ta ce" ƴar ɗan'uwansa ce toh iyayenta ne suka yi hatsari sunzo wajensa bayan sun koma a hanya sukayi hatsari duka suka mutu, toh shine ya ɗauko yarinyar ya tawo da'ita, shine fa aka aurawa Aliyu ita wai ko za'a dace" jinjina kai Hajiya Zainab tayi alamar gamsuwa sannan ta ce" toh Allah yasa hakane mafi alkhairi Allah kuma ya kawo zuri'a tagari" Ameen suka amsa dukansu............ Sai bayan magrib sannan suka dawo gida duk tagaji kodan daɗewa da tayi bata fitaba?. Tana shiga ɗakinta ta waɗa banɗakin dan yin wanka ............ Suna gama cin abincin Daddy ya kalleta ya ce" Aneeserh!" "na'am" ta amsa masa da hannu ya yi mata alama da tazo ta taso ta zauna gefensa dan haka ya koyar da'ita. Kamo hannunta ya yi ya ce" Aneeserh zan faɗa miki wata magana inaso ki kula da'ita sannan ki riƙeta kinji" gyaɗa masa kai ta yi ya ɗora da faɗin "Nasan kinaji ana cewa Aliyu ko?, to ba kowa bane Aliyu face ɗana kuma shine kaɗai ɗan da Allah yabani, yana da mata guda uku duka kuma suna zaune lafiya dashi, Aƙalla Aliyu zai kai shekaru 35yrs a duniya kuma ya yi auren fari tun yana ɗan shekara 28 amma har zuwa wannan lokacin Allah bai bashi haihuwa ba wanda kuma duk ya damemu duka, inaso idan ya dawo ki ɗaukesa matsayin Abbanki kamar yanda kika ɗaukeni domin wajensa zaki cigaba da zama saboda ki samu ki ƙarasa secondary school ɗinki idan yaso daga baya zaki iya dawowa wajenmu kinji" shiru ta yi sai kuma ta ta ce" in sha Allah Daddy zanyi kamar yanda kace Allah ya dawo dashi lafiya" sosai yaji daɗin furucinta bashi kaɗai ba harda Mommy dan basu ɗauka zata amince da sauƙi ba, ita kuma tayi hakane kodan ta samu damar komawa kano cikin ƙawayenta............. Ganin dare nayi yasa Daddy ya ce" tashi kije ki kwanta dare ya fara" kwaɓe fuska ta yi ta ce" Daddy zan kalli film ɗin happy New year ƙarfe goma a mbc bollywood" murmushi ya yi ya ce" bazaki ji bacci ba dear?" gyaɗa masa kai tayi ya ce" tom shikenan Allah ya kaimu" ta ce "Ameen" sannan suka cigaba da ɗan taɓa hira........... Yaukam makara tayi dan jiya sai wajen ƙarfe 12pm sannan ta kwanta bayan ta ɗan taɓa chat da ƙawayenta, tana gama shiryawa ta sake naɗewa a gado saboda wani bacci da keji. Da sallama ta shigo bedroom ɗin ganin har kusan ƙarfe 11am amma bata fitaba, hangarta tayi tana kwance sai baccinta take hankali kwance, murmushi Mommy ta yi sannan ta kashe mata a.c ɗin ɗakin saboda ana sanyi ba laifi sannan ta juya ta fita.......... Da sauri ta miƙe tana kallon agogon gefenta ta ce" nashiga uku ya akayi nayi bacci mai nauyi haka" sannan ta tashi da gudu yashiga banɗaki dan sake yin wanka........... Fitowa tayi cikin wata doguwar riga ta atampa maroon colour anmata ɗinkin A-shaped ta zauna das a jikinta, lip gloose kawai ta shafa abakinta sai eye pencil data saka a idanunta amma tayi wani sihirtaccen kyau mara hayaniya........... Zama tayi gefen Mommy da take ta murmushi tun fitowarta ta ce" masha Allah shalele kinyi kyau sosai abinki" dariya Aneeserh ta yi ta ce" Mommy good morning" kwaikwayar maganarta Mommy tayi ta ce" Mommy goood morning" ai kuwa ta fashe da dariya tana kallonta ta ce "Daman kin iya irin magana ta?" dariya itama ta yi ta ce" baki gani nayiba dear na iya sosai" shuru tayi dan babu abinda ta tuna sai sanda yaya Farooq zai kaita makaranta ahanya ta kira sunansa shima ya kira irin yanda Mommy tayi yanzu, nan da nan hawaye ya kawo fuskarta. Lura da hakan yasa Mommy ta ce" lafiya dai shalele?" tana goge hawayenta ta ce" Mommy yaya Farooq na tuna shine yake yimin irin abinda kika yimin yanzu"rungumeta Mommy ta yi ta ce" kiyi haƙuri Aneeserh Allah ubangiji ya jiƙansu da rahama" ta ce "Ameen"............. Ana idarda Sallar la'asar ta shigo ɗakin Mommy time ɗin tana zaune tana danna wayarta ganinta yasa ta ajiye ta ce" naga kinyi kwalliya dear?" sunkuyar da kanta ta yi sai kuma ta ce" Mommy daman chocolates ɗina ne suka ƙare" murmushi Mommy ta yi ta ce" ok yanzu zaki fita siyowa ne?" ta gyaɗa mata kai, tashi Mommy tayi ta ɗauko mata ATM card ɗinta sannan ta ce" gashi nan duk abinda kike so ki siya kinji, amma karki daɗe". Murmushi ta yi ta ce"tom Mommy nagode sosai saina dawo" ta ce" tom Allah ya dawo dake lpia" na ce" Ameen".......... *Nikam burina naga wannan Aliyun da aketa faɗarsa ko ya yake ohhho?* *Kudai ku biyo mu cikin book ɗin Aneeserh* ~Paid 500₦~ *WACCA TA SHIRYA BIYA SAI KI BIYA TA WANNAN DETAILS👇* *Account Name: Hauwa lawan.* *Account Number: 9086030007.* *Bank Name: Opay digital service.* *Sannan sai ki turo evidence of payment ta waɗan nan Countacts_08081129487 or 0810 660 8363.* EP_8_9. ~Paid Book 500₦~ *ANEESERH.* *Free Page na kusa da na ƙarshe 😹.* *💥Aneeserh Just The Beginning.*💥 *Story $ Writing By:*✍️📚 *N $ N.* *🔥💫Nanameera $ Nainarh KD.🔥💫* EP. Eight-Nine. Tunani Hajiya Aisha tayi lokaci guda ta canza shawara, kallon Aneeserh da ta kusa ƙofa tayi. "Babyna tsaya kawai na rakaki mu tafi tare dama ba kince kina so ki zagaye Birnin Abuja ki buɗe ido ba?". Juyowa Aneeserh tayi fuskarta ɗauke da ƙayataccen Murmushi ta amsa ma ta da faɗin. "Yeah Mommy please muje?." "Okay karki tohm Karki damu yau zamu yawata ko'ina da ina." Hajiya Aisha tayi maganar tana Murmushi tana son Yarinyar Sosai wasu lokutan abin har mamaki yake bata. Cikin ƙankanin lokaci ta shirya tsaf cikin rantsatsiyar lace milk color sama sama ta saka make-up artist nata Saima tayi mata Make-up ita ma Aneeserh aka kuma tsantsare ta da make-up tamkar wata bride. "Oh Mommy sai kace zamu tafi wurin Birthday Party wannan make-up haka...* Aneeserh tayi maganar cike da shagwaɓa tana juyo da fuskarta tana fuskantar Hajiya Aisha bayan Saima ta kammala ma ta make-up. "Wow Masha Allah, kai kai Baby Aneeserh dama haka kike da wannan uban kyau haka sai kace Queen Of Beauty Gaskiya bazan yarda ba har sai mun yi Pictures fa, lallai Hydar ya yi dace da wannan zuƙe ƙe kiya haka..." Hajiya Aisha ta ƙari sa maganar ƙasa ƙasa ba tare da ta bari Aneeserh taji ba. Sai dai kaf Aneeserh taji abin da ta faɗa, but confusing kawai ta shiga bata gane Komai ba. "Common Saima ƙari so ta nan ki kafta mana pictures ko kala uku da wannan Glam Babyn tawa mana." Hajiya Aisha tayi maganar cike da nishaɗi fuskarta cike da wadataccen walwala. Murmushi Saima tayi ita kanta ta yaba da Irin kyau da Aneeserh tayi. Sosai suka sha pictures kala kala mai kyau da mara kyau cike da farin ciki suke. "Yauwa barima na nuna Miki Pictures na Yayan ki Hydar da yake ta jamin rai zai dawo zai dawo amma shiru tun ina saka rai har na fara karaya." Hajiya Aisha tayi maganar ne bayan sun fito daga Bedroom sun nufo Down suna taka Stairs. "Eyya, wata ƙila wani abun ne ya riƙe sa Mommy kinsan fa yanayin aikin nasu." Aneeserh tayi maganar Kamar wacce tasan wani abu dangane da Aikin soja. "To ya zanyi yana yimin iya yi ne, saboda a tunanin sa shi kaɗai ne Baisan cewa na sama 'Ya ba da daɗewa ko kewar sa ma na dena." Dariya Aneeserh tayi ba Tare da ta kuma cewa Komai ba. "Oh Dam it, oh Allah Ni Aisha naga Ikon Allah...." Her Excellency tayi maganar tana riƙe baki. Ganin yadda Wayarta da ta juya bayan ta lalubo picture na Hydar zata nunawa Aneeserh kamar an tankaɗe wayar daga hannunta haka wayar ta goje ta faɗa ƙasa Glass ta yi tatsa tatsa. "Oh am so sorry Mommy saboda Ni Gashi Wayar ta farfashe." Aneeserh tayi maganar idanunta rau rai kwalla cike Tabb tana shirin fashewa da kuka. "No ba laifin ki bane dama haka Ubangiji ya ƙaddara, karki damu yanzu muje daga nan sai na nema wata Kafin a sake kawomin kalar samfurin ta." "Tohm." Aneeserh ta faɗa a gajarce, ba tare da ta saki fuskarta ba. Wasu lokutan dole sai ana ma ta uzuri kodan halin da take ciki. **** Sosai suka sha yawo cikin Garin Abuja suka yawata lungu da saƙo Aneeserh ta sha kallo Sosai duk da cewa ba karon ta na farko da zuwa Abuja ba ke nan. Sosai Aneeserh ta jido Chocolate cake biscuits shawarma kamar hauka a cewar Hajiya Aisha ta ɗauka duka abin da take so. Bata da wata matsala. Aneeserh tanajin daɗin Zama a gidan Uncle nata President of Nijeriya Sosai. Domin kulawa ta musamman His Excellency da Hajiya Aisha suke bata Fiye da wasu Iyayen ke bawa Yaran su. Koda gama yawace yawace da suka sha sun kwaso gajiya sosai domin har wurin Salon na manyan yara masu ji da Dukiya Hajiya Aisha takai Aneeserh aka ma ta mai kyau. "Jay Kuma anan Nijeriya gida na, to Yaushe ke nan ya dawo ƙasar?." Kallon Hajiya Aisha da idanunta ke kan tsalatsalan motoci da suke pake gefe kuma take wannan maganar, Aneeserh tayi tana nazari akan abin da taji ta ce da kuma tunanin wanene kuma Jay?..... Sai dai bata ce Komai ba, kamar yadda ita ma Hajiya Aisha ba ta kuma magana ba, har suka shiga tsararren palon kai tsaye Bedroom Aneeserh ta wuce bayan ta gaisar da mutum da suka shigo suka tarar a Dining hakimce yana Kai Loma. A gajiye take sosai shiyasa bata tsaya ba, kuma sannan a wannan lokacin bata cika son Hayaniya ba. "Jay! Yaushe ka dawo Nijeriya ne ban sani ba, sannan ina ne ka tafi babu ko waya, wato ka girma ka manta da Irin walahar da muka sha akan ko???." Juyowa Matashin Mutumin da ba zai haura 40 years ba a Duniya ba, Ya yi yana kallon Yayar ta sa sannan ya ce ma ta. "Gajiya nayi da ƙorafin ku akan Rashin Aure da Banyi ba, shi ne kawai na shiga Yankin Turawa domin lalubo muku ita....." Cike da mamaki ta katse sa cikin hangame baki Galala tana kallon sa, da kyar maganar ma ta fito daga bakinta. "Ita wa ke nan????." "Ah ah ita Matar Auren mana..." Ya bata amsa tsakani da Allah, yana bawa Saima da ya tsareta dole a Dining ɗin tana masa hidima a dole, umarni da ta zuba masa juice dake jug a cup. "Jay!!!." "Na'am!! Yes it's my name. Kune fa kukace kuna Buƙatar suruka daga gareni, shi ne na tafi samota, sai dai ba'a samu ba." Ɓoyayyiyar Ajiyar zuciya ta sauke jin abin da ya faɗa, sai dai tun kafin ta gama sauke numfashin ta kuma zaro ido waje, jin abin da ya ci gaba da faɗa. "Sai dai yanzu na samu waccan kyakkyawar Sweet 18 daga ina kuma kuka samota, kawai ki Aura min ita, kinga shikenan." "Subhanallah ya Ubangiji waccan da ka gani tare dani matar Hydar ce a yanzu kuma 'Yar ƙanin His Excel... Da suka yi Hatsari da matar sa suka rasu..." Hajiya Aisha tayi maganar cikin suɓutar baki, duk saboda jin abin da ya faɗa da tayi. Umarni ta bawa Saima da ta bar wurin. "Okay!! No problem na bar masa ita, kawai saboda ya kasance jinin ki ne, sannan ki Aura min wannan Yarinyar kawai don naga alamar zatayi biyayya." "Ya Salam Jay!! Kana wahalar dani fa, ita Saima da kake gani ba House maid bace, make-up artist ce Kuma kwararriya domin ta fannin tayi karatu." "Okay!! Ki ce idan na Aureta na huta raka ta wurin Make-up ke nan, ina sauraren ki faɗa min wasu abubuwa akan ta domin na kiyaye." Ya yi maganar bil-haƙƙi yana juyo da Kallon sa gareta, tare da bata gaba ɗaya hankalinsa. Shiru tayi dan bata da abin faɗa domin wannan ƙaramin ƙanin nasu da ya kasance Namiji ɗaya tilo gidan su, sauran duka mata ne su uku sai kuma shi, sosai suka sha fama da shi, tun Yana Yaro domin bayaji ko kaɗan kuma har girman sa gashi yaƙi ya yi Aure babu kalar naci da basuyi masa ba amma yaƙi, daga ƙarshe ma ya bar musu ƙasar, gashi kuma yanzu ya yi musu Dawowar ba za ta kuma ya fara da gidan ta, dama kuma Rayuwarsa yafi yi a gidan wurin ta muddun yana ƙasar. *Aneeserh p.o.v.* Da shigarta Bedroom nata da ya gaji da haɗuwa wanka tayi sannan ta buɗe leda ta ɗauki cake guda, ta zauna gefan Bed tana ci, sosai ta ci har sai da taji cikin ta ya cika da kayan zaƙi sannan ta Bari, kwanciya tayi saman Bed Kamar da wasa har Bacci Ya yi gaba da ita...... *Tofah ga fa Jay ya bayyana a bazata, 😸😸 sannan Hydar yaƙi ya bayyana kansa mu san shi, 🌝🌚 to ai hi ke nan.*🤸🤸 ~Paid 500₦~ *WACCA TA SHIRYA BIYA SAI KI BIYA TA WANNAN DETAILS👇* *Account Name: Hauwa lawan.* *Account Number: 9086030007.* *Bank Name: Opay digital service.* *Sannan sai ki turo evidence of payment ta waɗan nan Countacts_08081129487 or 0810 660 8363.* https://chat.whatsapp.com/GGPVCQ6ozk64RL5o2dARsT *ANEESERH* *💥Aneeserh Just The Beginning.*💥 *Story $ Writing By:*✍️📚 *N $ N.* *🔥Nanameera $ Nainarh KD.🔥* ______________ *This page is last of free page's.🧏* _________ *Idan kin shirya biya 500₦ only ki biya ta nan Details ɗin 👇.* _______________ 9086030007 Hauwa lawan Opay or 8106608363 Hauwa lawan Palmpay _______________ Evidence 09121033575 Or 07085212808 Via WhatsApp Only. *Ep-10.* Wajejen ƙarfe sha ɗaya jirgin ya yi landing a filin jirgi na garin abuja, fitowa ya yi cikin tafiyarsa ta cikakkun maza dan adire yake sosai, da sauri wasu guards suka zo suka buɗe masa ƙofa ya shige suka kama hanya. Fitowarta kenan cikin wata riga doguwa fara ƙal da'ita sosai rigar ta kama jikinta dan irin silky riga ce, baya tayi jin ta buge wani abu kamar dutse, waro idanunta ta yi ganin wani babban mutum dan yafi yaya Farooq ɗinta nesa ba kusa ba, gashi wani irin murɗaɗen jikine dashi kana ganinsa kaga zam soja, fari ne sosai kuma asalin kyakkyawa dan yafi kamada half-caste ɗin nan yana da manyan idanuwa kamar zasu fito su zageka, kana ganinsa kasan ajebo ne iya ajebo dan yanda fatarsa ke glowing kaɗai zai tabbatar maka da haka. Da gudu ta koma cikin gidan tana kiran "Mommy!! Mommy!! Mommy!!" Da sauri Mommy ta fito daga kitchen tana kallonta da tsoro ta ce "Aneeserh lpy?" Kasa magana ta yi sai nishi take tana nuna mata waje, daidai nan Aliyu ya shigo bakinsa ɗauke da sallama, murmushi Mommy ta yi tana kallonsa ta ce "oyoyo Aliy sai yau?" cikin sassarfa yazo ya shige jikinta yana sakin ajiyar zuciya ya ce "i miss you so much Mommy" shafa kansa tayi ta ce" nima haka son" zame jikinsa ya yi sai asannan ya kalli Aneeserh da take ta kallonsa kamar ta samu tv, zama ya yi kan royal sofa ɗin parlon yana sakin ajiyar zuciya akaro na babu adadi "Safeena ki zauna mana" Mommy ta faɗa tana kallon matashiyar budurwar wacce bazata shige shekaru 22 ba, zama ta yi tana kallon Mommy ta ce" Mommy ina kwana?" murmushi ɗauke a fuskar Mommy ta ce "lpy lao Safeena ya gida?" "Alhamdulillah ina Daddy?" kallon Aneeserh ta keyi ta ce" ya fita ɗazu wai naji ya ce za suje kano maybe zuwa la'asar ya dawo" tashi Aneeserh ta yi tana kalle-kalle Mommy ta ce "Aneeserh ga yayanki fa" da sauri ta sake kallonsa jin ance wai yayanta, kasancewar da baƙin glasses a idanunsa yasa bata gane ba ko shima kallonta ya ke "Ina kwana?" Ta faɗa a ɗan rikice, ba tareda ya kalleta ba ya ce "lpy y kk?" "Alhamdulillah" ta furta sannan ta bi bayan Mommy kitchen. Murmushi Mommy ta yi ta ce "meyasa ɗazu kika tsorata ne dear?" waro idanunta ta yi ta ce "Mommy ganinsa nayi kamar dodo wlh irin wadannan mutanen waɗanda suke wristling a Mbc max ne" dariya Mommy ta yi tana kallonta ta ce" Allah ya shiryamin ke Aneeserh toh yayanki ne sunan sa Aliyu waccen kuma matarsa ce" "Mommy batajin tsoronsa?" Girgiza kai Mommy ta yi tana jinjina yarintar Aneeserh ta ce" daman mata najin tsoron mijinta Aneeserh?" da sauri ta ce" wannan ai sai ya zaneta baki ganshi ba jibgege" murmushi ta yi ta ce "yanzu idan akace shine mijinki sai kiji tsoransa?" dafe ƙirji ta yi ta ce "Wlh Mommy sai na mutu saboda tsoro yanzu mafa banason ganinsa gani nake kamar zai dakeni" fitowa Mommy tayi daga kitchen ɗin bayan ta gama bawa maids din instructions da sauri Aneeserh ta haye sama kamar zata waɗi saboda kada su sake haɗa ido da Aliyu. Aliyu ne zaune gefen gadon ɗakin yayi shuru, zama ta yi kusada shi tana kallonsa ta ce" G.A lafiya?" kallonta ya yi sai kuma ya miƙe kamar zai shiga toilet sannan ya ce "Nothing" Ajiyar zuciya ta sauke dan daman ta san halinsa kenan, Aliyu bashida ɗaukan raini kuma bashida rashin mutunci amma mutum ne irin kaifi ɗayan nan idan ya ce zai yi abu tofa babu wanda ya isa ya hanashi haka idan ya ce bazai yiba babu wanda ya isa ya saka shi, sannan kuma akwai shi da izza kodan ya kasance jinin sarauta ne ga kuma mulki da mahaifinsa keyi???? bashida shiga harkar mutane da yawa amma idan ya sanka zai mutuntaka, kowa na wajen aikinsa sonsa yake kasancewar mai kyawawan ɗabi'u uwa uba kuma addini dan bashida flaws a wannan ɓangaren babban abinda ya fiso a rayuwarsa shine mahaifinsa yana matuƙar jinsa a ransa kamar yanda shima Daddy yake matuƙar sonsa ba kowane lokaci yake kula mutane ba kuma ba kowane irin mutane yake mu'amala da suba, wannan kenan daga cikin halayen General Aliyu Muhd Baira A.K.A G.A. Da sauri ta buɗe idanunta tana kallon agogon gefenta dafe ƙirji ta yi ta ce" wayyo Allah na ya akayi nayi bacci haka it's almost magrib banyi sallah ba, tashi ta yi ta shige toilet dan ɗauro alwala. A gurguje ta shirya tayi sallah sannan ta fito cikin wata abaya ash colour ta ɗaura veil ɗinta akanta ta shafa lip gloose a bakinta, sosai ta yi kyau masha Allah dan sai ta ƙara zama wata budurwa da'ita. Zaune ta samesu suna ɗan taɓa hira sai wani shagwaɓe fuska yake kamar Baby tsayawa ta yi tana kallon ikon Allah lokaci ɗaya kuma Abbanta ya faɗo mata "Shalele lafiya kike kuka?" Sai a sannan ta taɓa fuskarta taji danshin hawaye dan batasan ma ta fara kuka ba, da hannu ya yi mata alama da tazo ai kuwa ta ƙaraso zata tsuguna ya zaunar da ita kan cinyarsa yana share mata hawayen fuskarta da hannunsa ya ce "Ke dawa shalele?" Girgiza kai tayi sai kuma ta fashe da kuka, kuka take mai tsuma zuciyar duk wani mai sauraro dan kukan daga ƙasan zuciyarta yake fitowa, bai hanata ba sai shafa mata bayanta da ya dunga yi har kusan 10mins sannan ta fara sauke ajiuar zuciya tana shashsheƙa a hankali "Yanzu faɗamin mene ne ya saka ki kuka?" "Daddy Abbana, Ummin, yaya Farooq ɗina yaushe zan sake ganinsu Daddy?" Rasa abunda zai faɗa mata ya yi ya tsurawa kyakkyawar fuskarta irinta fulani ido ba zaice ga abinda yake tunani ba amma tabbas yana matuƙar tausayin Aneeserh yau da ace Farooq ko ɗaya daga cikinsu bai mutu ba to da tabbas zataji sauƙi amma ace duka family ɗinka ka rasa su abun isn't easy. Shikam Aliyu kallonsu kawai yake dan baisan inda wannan yarinya t samu ba, kallonta Daddy ya yi ya ce "Shalele!" ɗago kanta ta yi ta ce"na'am Daddy" numfasawa ya yi sannan ya riƙo haɓarta yana kallonta ya ce "Daga yau ki ɗauka ni ne Daddynki, shikuma wannan ki ɗauka shine Abbanki kinji, duk abinda uba yakewa ƴarsa to Aliyu zai miki shi Shalele understood?" ya ƙare maganar yana nuna mata Aliyu. Da ɗan firgice a tareda ita ta ce "Abbana wannan?" Murmushi Daddy ya yi sannan ya gyaɗa mata kai, a hankali ta sauka daga jikin Daddy ta ce "zani wajen Mommy" okey ya ce mata sannan ta shige. Kallon Daddy ya yi ya ce "Dad wannan ƴar daga ina?" ajiyar zuciya ya sauke sannan ya ce " zan baka labarin komai son ka bari sai gobe" "Why not today Daddy?" Tashi Daddy ya yi ya ce" gobe Uncles ɗinka zasu zo tom za'a faɗa maka yanda zaka fahimta" daga haka ya fara taka stairs ɗin. Ɗaga kafaɗa Aliyu ya yi irin abun bai damesa ba sannan ya miƙe a nutse ya fara tafiya torward direction ɗin fita daga parlon. Zaune yake kusada wani ƙaramin swimming fool yana kallon ruwan da yake gwanin ban sha'awa, ajikinsa yaji ana kallonsa ai kuwa ya juya karaf idanunsa ya shiga cikin nata, cikin hanzari ta zuwa amma kafin tayi taku ɗaya yazo gabanta, hannunsa yasa ya kamota aikuwa ta fashe da kuka tana haɗe hannayenta guri guda ta ce "Dan Allah dan Annabi kayi haƙuri wlh bazan ƙaraba na rantse" shuru ya mata kuma har sannan tana riƙe a hannunsa, sake fashewa ta yi da kuka tana kare idanunta ganin yana kallonta ta ce" wlh banaso kana kallona kamar dodo" waro idanunsa ya yi yana kallonta wato shine ma dodon?? Kwafa ya yi kawai sannan ya koma ya zauna kan kujerar har sannan tana hannunsa. Iyaka rikicewa Aneeserh ta rikice dan Alah ya gani idan da abunda tafi tsoro a rayuwarta bai shige soldier ba shiyasama ɗazu ta tashi tabar wajensa da ƙaryar wajen Mommy zata je, tun tana koke-kokenta har ta gaji tayi shuru tana kallon inda yake kallo "what's your name?" Kallonsa ta yi sai kuma.ta ce " Aneeserh" Yana kallonta shima ya ce" daga ina kike kuma me ya kawo ki gidan nan?" turo baki ta yi ta ce "irin wannan tambaya haka nima bansani ba" da sauri ya kalleta yaga ta ɗauke kanta tana ƙunƙuni wanda kuma daman ɗabi'arta ce, girgiza kansa ya yi sannan ya sake ta "Tashi ki tafi" Ya furta ba tareda ya kalleta ba, da sauri kuwa ta miƙe har tana tuntuɓe wajen shigewa ta ƙofar sa ta fito. *ANEESERH*. *ANEESERH* *💥Aneeserh Just The Beginning.*💥 *Story $ Writing By:*✍️📚 *N $ N.* *💫Nanameera $ Nainarh KD.💫* *EP. ELEVEN* ```WASHE GARI``` Cike da magagi ta kuma kai hannu tana laluba saman mattress ɗin tare da saka ran taɓosa, sai dai jin alamar babu kowa ne yasa ta buɗe idanunta masu cike da Bacci ta ware su saman Bed ɗin, da sauri ta tashi zaune, saukowa tayi daga saman Bed ɗin tuna a'ina suke yasa ba tare da damuwar rashin ganin sa ba, ta shiga bathroom domin ɗauro alwalar Sallahr Asuba da bata samu tayi ba tun lokacin da G.A ya tashe ta sai yanzu. "Barka da safiya Mommy na ina fatan na sameku lafiya jiya bamu samu mun gaisa sosai dake ba." Ƙayataccen Murmushi Hajiya Aisha tayi tana shafa kansa mai cike da tarin suma take faɗin. "Lafiya Qlau muke Hydar da fatan kun kwana lafiya?." "Lafiya Qlau Alhamdulillah." "Masha Allah, ina ita Safeena ɗin take kodai ta koma Bacci ne?." Shiru ya yi na 'yan sakanni sannan ya bata amsa da faɗin. "Tana part ɗin mu ina ga ta koma ɗin ne." "Okay Tohm amma me yasa banga kazo tare da sauran Matan naka ba, Humaira da Yasmeen fatan dai kuna zaune lafiya gaba ɗaya." Tambayar tayi masa cike da kulawa idanunta akan tilon ɗan nata tausayin sa fal zuciyarta. A hankali ya miƙe tsaye zura hannayen sa ya yi cikin trouser pocket nasa, sannan ya ƙari sa kusa da window na Bedroom ɗin idanunsa ya lumshe tsawon sakanni sannan ya bata amsa da cewa. "Duka suna lafiya sai dai basu damu dani ko magana ta ba, ita Humaira bata dawo Nijeriya ba, ta wuce Asturaliya wurin iyayen ta, ita kuma Yasmeen tana Kano a halin yanzu. Safeena ita ce ta biyo ni, kuma muke tare da ita" Ajiyar zuciya ta sauke ɓoyayyiya tana kuma tausayawa halin da yake ciki mata har uku cikin su kuma babu wata da tasan menene ma Auren yake nufi gaba ɗaya. Ko wacce sha'anin gabanta kawai take yi babu ruwanta da wani Aure dake kanta. Sanin da tayi ci gaba da maganar ma ɓacin rai zai haddasa masa kuma abin da bataso ke nan, yasa ta canza maganar tare da faɗin. "Nace kuwa kaje kira da His Excellency ya yi maka jiya naji kamar ya ce ka same sa?." Huro iskar dake cike da bakinsa waje ya yi, idanun suna sauyawa daga rinewa da suka fara lokaci guda. "Ban tafi ba." "Me yasa." "Haka Kawai naji kamar babu Alkhairi a nema na da yake yi kuma ya ce Uncle Bashir suna nan tafe Kinga kuwa akwai ayar tambaya a lamarin." "Amma ina ga da kaje ɗin kaji koma Menene Kamar zai fi ko?." "Okay." Ya faɗa a taƙaice. Hajiya Aisha tana shirin ƙara Magana ke nan, aka turo ƙofar aka shigo. Juyawa suka yi gaba ɗaya domin ganin ko wani mahaluki ne. Shigowa Bedroom ɗin tayi tamkar wacce aka jefo ta babu ko sallama Kallabi a hannunta take faɗin. "Wato Mommy shi ne ma kika manta dani ko tashi na bakizo ba, to ma nayi fushi." Tayi maganar cike da shagwaɓa ba tare da ta lura da shi dake tsaye bakin window ba, shi kuwa zuba ma ta idanu ya yi yana kallon ta da nazarin ta ba tare da ya ce Komai ba. "Oh am sorry Dear ɗokin Dawowar Hydar ne yasa na sha'afa gaba ɗaya." Turo baki tayi tare da kifa kanta saman lap's na Hajiya Aisha Bayan ta ƙari sa wurin ta tare tana faɗin. "Chabb wannan mai ƙirar dodan nin Allah jiya dana fara ganinsa na zata wannan Lion ne da ake haskawa a Tv ne fa, bakiga yadda yake tafiya bane a wani hakimce gashi jikin sa a murɗe ta ko'ina kamar kamar....." Wani irin zaro ido tayi waje cike da tashin hankali da yasa babu shiri ta miƙe daga jikin Hajiya Aisha sakamakon Four eyes da suka haɗa da shi, yunƙurin ficewa daga Bedroom ɗin tayi gaba ɗaya, sai dai ko kafin ta kai ga ƙofa taku ɗaya ya yi ya damƙo ta, ta dawo faɗa saman faffaɗan ƙirjin sa. Cike da mugunta ya saɓata a kafaɗar sa ba tare da ya ce Komai ba. Ihu ta fara tana roƙon sa da ya sauke ta, sai dai da alama bashi da niyyar hakan, cizo da yaƙu shi ta fara masa amma ko'a jikin sa, sadaƙarwa tayi ta fara basa haƙuri harda hawayen ta. "Hydar sauke ta mana ƙanwar ka ce fa, Yarinta ke damun ta ba Komai ba." Sauke ta ya yi ƙasa Aikuwa bata jira Komai ba ta ruga da gudu har da haɗa hanya ta bar Bedroom ɗin. "Huh kaga ka tsoratar da ita ko, ya yi maka kyau." "Mommy hakan ne ya kamata da ita ai." Ya yi maganar yana sakin Murmushin mugunta. Ya lura Yarinyar Akwai tsokanar tsiya sai shegen tsoro. Shiru Mommy tayi ba ta kuma cewa Komai ba. Tunanin ta gaba ɗaya ya koma ne kan yadda za'ai Aneeserh ta iya Rayuwa da Hydar ne As Matar sa kuma cikin kishiyoyi har uku gaskiya lamarin kamar da wuya. *Kano, Nigeria.* *G.R.A* Gidan ya haɗu sosai kuma katafaren gida ne wanda ba'a ko'ina ake samun gida mai kyau da tsaruwa kalar sa ba, daga ko'ina na gidan securities ne birjik suna gudanar da aikin tsaron Gidan kamar ko yaushe dama kuma Gidan baya rabuwa da masu tsaron sa ko da yaushe. Jin da tayi knocking ɗin da ake ta faman bugawa daga palon ya yi yawa ne, yasa cike da kasala da gajiya ta kawar da laptop dake Gaban ta gefe sannan ta miƙe tsaye a kasalan ce ta fito daga Bedroom ɗin ta ƙari sa ƙofar palon ta buɗe. "Oh Sabeera kune ashe. Ku shigo ciki please." Tayi maganar tana kallon su fuskarta cike da Murmushin farin ciki na Ganin su, tafawa suka yi cike da farin cikin sake Ganin juna bayan sun zazzauna a haɗaɗɗen palon saman lumtsa lumtsan kujerun alfarma dake zagaye da Palon. "Wai amma Suhaila ta ya ya securities suka bari kuka shigo ciki?." Tayi musu tambayar lokacin da ta dure musu faffaɗan Tray dake cike da kayan qwalam gaban su saman Center table. Su biyu ne 'Yan matan da bazasu haure shekaru Ashirin da bakwai ba, suka tafa cike da salon bariki da jin kalar tambayar da tayi musu ɗaya cikin su da alama ita ce Suhaila ɗin ta ce. "HHhH Yasmeen ke nan Kamar kin manta su waye mu ko, waɗannan ƙananan balagaggun salo ɗaya ya rikita su suka bamu hanya cikin fita hayyaci ba tare da sun sani ba." Kuma tuntsire wa da dariya suka yi suna tafawa ɗayar ita ma ta ce. "Yasmeen ya kamata Ku canza securities na gidan gaba ɗaya domin za'a iya haɗa baki da su wata Rana a ga bayan ku wallahi shawara ce wannan." Dariya Matar Gidan wacca suka kira da Yasmeen tayi tana zama saman Sofa ta ce. Babu Ruwana su wallahi Aliyu da ya kawo su shi keda ikon sallamar su duk lokacin da ya so bawai Ni ba. "Ke kika sani dai da bakya jin shawara ko kaɗan, wai amma nace ina shi General ɗin yake ina ce jiya kuka dawo ƙasar kodai shi bai dawo ba ne?." Sabeera ce tayi ma ta tambayar cike da son Sanin Komai. Taɓe baki tayi cike da rashin wayo ta Gyara zama tana zayyano musu yadda suka kwashe da shi akan ya yi, ya yi da ita ta bisa Abuja su gaishe da Iyayen sa sannan su dawo Kano ɗin amma taƙi ta taho Kano kai tsaye. Sai da ta gaba faɗa musu Komai har ƙin ɗaukar Wayarta da ya yi yau da ta kira sa, sannan suka tafa suna faɗin gwara da tayi hakan wallahi domin da hakan ne kawai zata ɗa ga darajar ta wurin surukan ta. Fira suka ci gaba da kwasa suna bugun ruwan cikin ta tana basu Labarin Komai dake tsakanin ta da mijinta Aliyu har kalar Rayuwar aure da suke gudanar wa. Yasmeen ke nan 'Ya wurin Alhaji Isah Sambo Ministan harkokin waje na Nijeriya, ita ce 'Yar sa ɗaya tilo a duniya, shekarun ta Ashirin da bakwai zata shiga da takwas ta taso cikin gata da sangarta ta Iyaye domin babu abin da nema ta rasa, lokacin da ta kammala University nata ne ƙasar America bayan ta dawo aka ɗaura Aurenta da General Aliyu, sam Yasmeen bata da wayo kwata kwata a Rayuwarta, Sabeera da Suhaila sune kaɗai ƙawayen ta domin batada tara ƙawaye barka tai dukkan su anan Kano suke Kuma tare suka yi Karatu acan America acan ne ma suka haɗu har Kammala karatunsu kuma suke tare yanzu sai dai bada zuciya ɗaya suke zaune da Yasmeen amma sam ta kasa fahimtar Hakan. * Sydney. Australia.* Kallon ta ta kuma yi a karo na babu adadi sannan cike da ɓacin rai ta kira Sunanta bata jira ta amsa ta ci gaba da faɗin. "Humaira!! Kina da hankali kuwa yaushe Ilimin ki da tunanin ki gaba ɗaya suka bar ƙwaƙwalwar ki da har zaki zo nan ɗugui-ɗugui har Austaraliya ki bar mijin ki a can Nijeriya kuma ma ba tare da san Ransa kika zo ba, yanzu yanzu ki shirya ki koma Nijeriya kafin na sassaɓa miki kamanni a Gidan nan, don na lura kwata baki da hankali a rayuwa." Turo baki tayi cike da shagwaɓa tana shirin magana, takai hannu zata bige bakin, da sauri ta matsa gefe cike da tashin hankali ta ce. "Hajiya mana!! nifa babu inda zan koma don na gaji da wannan Auren da ya ƙi ci yaƙi cinye wa wallahi." Jin abin da 'Yar nata ta faɗa ne yasa Hajiya Khareema sassauta Murya ta ce. "Haba mana Humaira ta 'Yar Albarka wai kin manta burin mune kiyi haƙuri ki koma mana lokacin kaɗan ya rage da zaki rabu da wannan Auren domin nima ba ƙaunar sa nake ba." "Ni dai gaskiya na gaji kawai ki faɗa min menene shiri da kika shirya muji." Humaira tayi maganar a sangar ce cike da rashin ta ido tana kuma turo baki. Ƙara ƙasa da murya tayi ta ce. "Matso da kunnen ki kiji Abin domin sirri ne." Cikin sauri ta matsa kusa domin jin koma menene. Sun daɗe sosai suna ƙus-ƙus da tattaunawa akan lamarin. Sannan daga bisani Humaira ta fara shirin komawa Nijeriya ko zuwa marece ta gama shiri Mahaifiyar ta ta da ƙaninta suka rakata Airport domin dawowa Nijeriya..... *WANNAN KE NAN.* *ANEESERH* *💥Aneeserh Just The Beginning.*💥 *Story $ Writing By:*✍️📚 *N $ N.* *🔥💫Nanameera $ Nainarh KD.🔥💫* *EP-Twelve* Kallonsa Mommy ta yi ta ce" wai Aliyu me kake jira baka je kiranba?" Murmushi ɗauke a fuskarsa yake cewa" calm down Mommy yanzu fa zan tafi" harararsa ta yi ta ce" karma ka tafi kaida shi" bai ce komai ba ya juya zai fita, da sauri ta koma baya tana kalle kalle hankalinta tashe ta ce " dan Allah kayi haƙuri wlh ban kula ba" hannunsa yasa ya ture ta sannan ya shige batareda ya ce komai ba, ajiyar zuciya ta sauke tana hamdala aranta dan ita babu wanda take tsoro agidan nan sama dashi. "Aneeserh kinje kiran Daddyn?" Gyaɗa mata kai tayi tana lumshe ido bayan ta kwanta kan royal bed ɗin Mommyn ta ce" cewa yayi naje anjima zai kirani" okay Mommy ta ce sannan ta miƙe ta fita. Zaune ya tadda ƙannen mahaifinnasa su biyu sai Daddy na uku suna ɗan taɓaa hira, cikin ladabi ya gaishe su sannan ya zauna ƙasa kan carpet ya ce" Daddy gani" gyara zama Daddy ya yi sannan ya ce "Daman akwai wata magana da nakeso zamuyi dakai kuma tanada muhimmanci sosai maganar saboda haka ka nutsu kaji abunda zamu faɗa" kansa ƙasa ya ce "in sha Allah" Uncle Bashir ne y ce"Aliyu kasan kasan ɗan uwanmu Ahmad wanda ya rasu shida matarsa few months ago?" girgiza kai ya yi ya ce" A'a bansani ba" "Tom shiɗin ɗan uwanmu ne na kusa bana nesa ba kawai yanayin rayuwane yasa bamu mu'amala dashi sosai har ku baku sanshi ba, wannan yarinya da kake gani Aneeserh ƴarsa ce ɗan uwanta ya yi hatsari tare da iyayen sai ita kaɗai ta rage, saboda haka ku kaga ya dace mu sake ƙulla wani zumuncin a tsakaninmu shiyasa muka aura maka ita lokacin da ta dawo gidan nan da zama" Da wani irin expression yake kallon Uncle B with mouth agape wane irin aure aka masa da wa kuma????? Ganin yanda ya yi ne yasa Uncle Nasir ya ce" munyi hakane saboda ka kula da rayuwarta Aliyu ka ɗauketa matsayin ƙanwarka kayi mata abinda iyayenta zasu yi mata ka kula da rayuwarta fiyeda kowa Aliyu dan Allah" Tsabar takaici ya kasa magana sai binsu yake da kallo Daddy ya ce "Kayi shuru ana yi maka magana" "Daddy meyasa zaku yimin haka please?, ya zanyi da waccen ƴar ƙaramar yarinyar wacce da Allah ya bani haihuwa da wuri ya ci ace na haifi kamarta haba Daddy?, sau huɗu fa kenan ban taɓa auran mace sabida ina sonta ba kawai kuna aura min matane saboda ban samu haihuwa ba kuna nuna kamar baku yarda da ƙaddara ba, amma ni mezanyi da yarinya kamarta matsayin mata?? Asake duba lamarin nan please" Murmushi Daddy ya yi yana kallon ƴan uwan nasa ya ce" bana faɗa muku ba Aliyu bazai karɓeta matsayin mata ba? Yanzu gashi nan kowa ya gani da idanunsa ni kuma bazan maka dole ba har ka dinga gani kamar ba'ason yarinyar ne yasa aka aura maka saboda haka kana iya sakinta yanzu" Uncle Bashir ne ya ce" bafa za'ayi haka ba dole zai zauna da ita yake zama da ƴaƴan wasu ma bare kuma ƴar uwarsa kodan maraicinta ai ya ci ace kaji tausayinta ka ɗauketa matsayin ƴarka" Shuru Aliyu yayi bai ce komai ba amma tabbas this time around bazai yarda da irin abunda ake masa akan aure ba,kallon Uncle Nasir ya yi wanda shine kaɗai yasan zai goyi da bayansa ya ce "Please Father kace abar wannan maganar wlh banida intention ɗin yin aure anan kusa please Father" Murmushi Uncle N ya yi ya ce "Karka damu Aliyu na tabbata zakayi farin ciki da abinda muka aikata kayi haƙuri ka ɗauka hakanne mafi Alkhairinka" Shuru Aliyu ya yi ransa duk a dagule murmushin ƙarfin hali Daddy ya yi ya ce" banason aja maganar nan da tsayi Aliyu zaka zauna da Aneeserh matsayin mata ko A'a?" Da sauri ya kalleshi sai kuma ya sunkuyar da kansa ya ce"sorry Daddy gaskiya bazan iyaba saboda tamin ƙanƙanta" "maganar nan ta shige yanzu kawai ka furta ka saketa shikenan daman ba idda zata yi ba" Zai yi magana Uncle N ya ce "Ba haka za'ayi ba yaya, tunda yarinyar nan tana karatu a kano kuma Aliyu a kano yake zama kawai abar masa ita ya tafi da ita idan yaso tana ƙarasa karatunta sai ya dawo daita ko gurina ko gurinka please" Shuru Daddy ya yi dukda ba haka yaso ba yaso ace ya raba auren dake tsakaninsu ta cigaba da karatunta a Abuja, amma shi kuma Uncle N ya yi hakane saboda zama yau da gobe yafi ƙarfin wasa dole a hankali yarinyar taza fara shigar masa rai har yaji yana son zama da ita. "Ka amince ko baka amince ba?" Daddy ya tambaya yana kallon Aliyu "Babu komai in sha Allah zan riƙeta zuwa tayi graduation ɗin" Okay Daddy ya ce sannan ya danna wayarsa not too long Mommy suka shigo itada Aneeserh, zama suka yi ta gaishesu sannan Daddy ya ce "Daughter kinason zuwa kano ko?" Da sauri ta gyaɗa masa kai dan ta ƙagu ta koma kano kodan ƙawayenta "Tom zaki koma yanzu in sha Allah" Murmushi ɗauke a fuskarta ta ce" thank you Daddy" Yana nuna mata Aliyu ya ce "Kinga wannan?" Kallonsa ta yi sai kuma ta sunkuyar da kanta tana ɗaga masa kai alamar E "Tom zaki koma gidansa da zama a kano ki ɗaukeshi matsayin Abbanki Aneeserh ki ɗauka duk abunda kike buƙata Abbanki zai yi miki sannan kuma mijin kine" Da wani irin sauri ta ɗago kanta tana kallon Daddy jin furucin da ya yi, fashewa ta yi da kuka tana kallonta ta ce "Daddy tsoronsa nakeji please ka barni anan" Murmushi Mommy tayi tana riƙeta ita kuma tana cigaba da kukanta "Kiyi haƙuri Aneeserh babu abinda zai sameki ki ɗauka shiɗin Abbanki ko kina tsoron Abbanki?" girgiza masa kai ta yi ya ce "Toh shima karki ji tsoronsa in sha Allah kuma zan dinga kawo miki ziyara" Gyaɗa kanta ta yi tana sake rushewa da kuka jikin Mommy, kallonta kawai Aliyu yake dan gani yake shine wanda yafi dacewa ya zubar da hawaye ba ita ba "Aliyu kaji tsoron Allah cikin riƙon da zaka yiwa marainiyar Allah ka ɗauki Aneeserh matsayin ƴar cikinka ka kula da rayuwarta please banson mu samu saɓani akan rainon Aneeserh dan ni bama haka naso ba" Okay Aliyu ya ce sannan ya miƙe jiki a sanyaye ya yi waje. Sosai suka yi mata faɗa da kuma kwantar mata da hankali har tayi shuru sannan Mommy ta ɗauketa suka koma ɗakinta. Tunda ya koma ɗakinsa bai kula kowa ba ya yi kwanciyarsa itama Safeena sanin halinsa yasa bata wani damuba tayi kwanciyarta. Wajejen ƙarfe 11am suka gama shiri da jirgin su ya kusa tashi, zaune take ɗakin Mommy gaban mudubinta bayan ta gama ƴar kwalliyarta dukda ba wani abun ta shafa ba daga powder sai lip gloose sai ta saka kwalli shikenan amma tayi wani sihiritaccen kyau dan Aneeserh nada jikin girma bazaka taɓa cewa batakai irin 18yrs ɗin nan ba komai nata irinna manya ne. Dafata Mommy ta yi tayi saurin kallonta sai kuma ta sunkuyar da kanta haka kawai taji tana jin kunyar Mommy, murmushi Mommy ta yi ta ce "Aneeserh lokaci na shigewa zaku wuce" Hawaye taji ya kawo idonta amma tayi sauri shanyewa dan tayi alƙawarin bazata sake zubarda hawayenta ha kamar yanda Mommy ta roƙa, kama hannunta ta yi sannan suka jero tare suka sakko. Bai tsaya kallonta ba ya yi gaba suka bi bayansa itada Safeena dukda ita batasan mene ne yake faruwa ba, guards ɗinsa na tsaye suna jiransa ya shiga mota sannan suma suka shiga Mommy na ɗaga musu hannu suka bar gidan dan daman Daddy bayanan. *Nassarawa G.R.A Kano state.* *ANEESARH* *💥Aneeserh Just The Beginning.*💥 *Story $ Writing By:*✍️📚 *N $ N.* *🔥💫Nanameera $ Nainarh KD.🔥💫* *Ep. Thirteen* *Nassarawa G.R.A Kano state* Sosai Yasmeen da ƙawayen ta Sabeera da Suhaila suka sha fira kafin daga bisani suka shiga haɗaɗɗen kitchen na Gidan suka shirya lafiyayyun girke girke kala kala domin Yasmeen kam ba baya ba wurin iya girki iri iri na zamani dana gargajiya yadda bata wasa da cikinta haka batayi sake wurin ƙin koyan girka lafiyayyun gaske ba, shiyasa kuwa ta kafa dafa a zuciyar mijin su Hydar ta wannan fannin. Sai wuraren ƙarfe 2:30pm sannan Sabeera da Suhaila suka ma ta sallama suka tafi. Yayin da ita kuma ta koma cikin Gidan, fara tattare plate's da suka yi amfani da su tayi ta kai kitchen ta wanke ta zuba kowanne a ma'ajinsa sannan ta dawo ta gyara palon da su Sabeera suka yi kaca kaca da shi kuma suka tsallake suka bar ma ta shi a Hakan, sai da ta gyara palon tsaf komai ya yi tsaf tsaf yadda ya kamata sannan kai tsaye Bedroom nata ta wuce, tayi wanka da Sallahr Azhur da bata samu tayi ba daga nan Bacci ɓarawo ne ya yi gaba da ita. Sai wuraren ƙarfe 5:20pm ta farka tana salati sannan ta shiga Bathroom ta kuma yo wanka cikin ƙanƙanin lokaci ta shirya sauri sauri take yin komai domin shaf ta manta G.A ya ce da ita yau zasu dawo Kano, Sallahr La'asar tayi a gurguje sannan ta fito Palon Gidan. Hango mutum tayi zaune saman Sofa 1sieter ta bata baya tana kallon gaban ta da alama system take sarrafawa. "Hello." Ta faɗa tana yin gaba ba tare da ta jira ta amsa ba domin ta gane Safeena ce. "Hii." Ita ma Safeena ta faɗa a taƙaice idanunta cikin system nata, dama haka suka saba babu Magana daga hello sai hi. Kai tsaye part ɗin G.A ta nufa sallama ɗauke saman laɓɓanta ta ƙari sa shiga cikin Main Bedroom ɗin. Hangosa tayi zaune In bedside saman Sallaya da alama ya idar, Addu'o'i yake yi. Murmushi ta saki sosai takeson mijin mana General Aliyu sama da komai domin ya tara dukkan abin da mace zata so samu wurin mijin Aure. Na farko dai ya kasance kyakkyawa ne shi ajin farko kuma fari ne fal sol, ya kasance murɗaɗɗen jiki garesa gunin burgewa gashi ya kasance adire yake ga kwarjini izza dama kuma yana da alaƙa da sarauta, ba koda yaushe General Aliyu ya cika son magana ba, sai dai sam baya da wulaƙanci amma baya ɗaukar raini sam ko kaɗan, yana son mai son sa ko'a wurin Aikin sa na Soja yabawa akeyi da nagartattun halayensa, gashi ma'abocin ibada sam Sallah bata wucesa kuma, Aliyu yana daga cikin Mazen kirki da suke wahalar samu cikin wannan Rayuwar a yanzu shiyasa Yasmeen take mugu mugun ƙaunar sa kamar ranta kuma yana bata kulawa daidai yadda ya kamata haka ma sauran matan sa babu wacce zata ce bata jindaɗin zama tare da General Aliyu duk da cewa duka ga irin Auren da suka yi, dukkan su Aura masa shi aka yi.... "Her Heart ka Kammala idar da Sallahr?." Ta tambaya Ganin alamun da tayi. Ba tare da ya yi magana ba, ya ɗa ga ma ta kai idanunsa akan nata. "Sorry Please, ka dawo ina ta Bacci gajiya ne yasa, ina Fatan ka dawo Lafiya?." Still ba tare da ya ce komai ba ya kuma jinjina ma ta kansa. "Oh Her Heart!! menene yake damun ka haka ne ya naga idanun ka sun yi firi firi haka kamar wanda tunani yayima yawa menene ya faru a Abujan Allah ya sa dai Komai lafiya?." Ta jero ma sa tambayoyin tana miƙe wa tsaye cikin sauri ta ƙari sa garesa ta zauna suna fuskantar juna ta kamo fuskar sa saman tafin hannunta. *Aneeserh P.o.v.* Kam tun bayan faɗa ma ta komai da Daddy ya yi wai wannan mutumin mai kama da Dodo a wurin ta shiɗin mijinta ne kuma zata kasance tare da shi a nan Kano bayan sun zo. Komai ya dawo ma ta sabo cikin zuciyarta taji ta kuma kewar Ahalinta Abbanta, Ummin ta, Yaya Farouq nata da'ace duka suna nan tasan ba za'a taɓa bari ayi ma ta wannan rashin adalci ba. Karo na farko da taji Daddy bai kyauta ma ta ba, akan me ma za'ayi tunanin haɗata da wannan mutumin wanda ta lura ma sam ba ƙaunar ganinta yake ba. Kuma gashi wai har ma ta uku garesa, ita kuwa Aneeserh ina zata kai wannan ƙaddara haka na Auren sa. Duk abin da take yi daurewa kawai take yi tana pretending domin kar Hajiya Aisha ta gane komai. Tun barin Abuja da suka yi suka shiga jirgi har izuwa ƙari sowa nan Kano da suka yi ba ta kuma furta komai ba, kuma bata kuma cin komai a bakinta ba. Domin koda suka ƙari so katafaren gidan na General Aliyu tsaban ruɗewan da tayi na ganin securities da uniform na soldiers yasa ko tsayawa kallon kyau da tsari da kuma haɗuwar Gidan ba tayi ba. Da shigarsu palon gidan da ya gaji da haɗuwa sai ƙamshi ke tashi ta ko'ina ya juyo a bazata gareta yana kallon ta da rikitattun idanunsa, a lokacin tsaban tsoro kusan fitsari ne ya kusa Zubo ma ta, amma ta daure, tana sauraren umarnin da yake bawa Safeena da zuwa lokacin ranta yake a mugun ɓace domin kuwa a cikin jirgi Hydar ya sanar da ita komai, umarni ya bata akan ta kai Aneeserh zuwa Bedroom nata sannan ta bata duk Wani abu da take buƙata sannan ya yi gaba izuwa Up part nasa. Yayin da Safeena badan taso ba, ta kai Aneeserh wani Bedroom dake cikin Palon ba tare da tayi ma ta bayanin komai ɗin ba da Hydar ya umurce ta, ta fito a fusace. Aneeserh kuwa zubewa tayi saman gwawowin ta a tsakiyar ɗakin tana kuka mai tsuma zuciya kukan da babu mai rarrashin ta, ji take yau ne ta kuma tabbata marainiya a duniya, batasan haka rashin iyaye yake da zafi ba, tayi kuka sosai taba uku lada, har sai da ta gaji dan kan ta sannan ta haƙura. Yanzu haka ma da kyar ta samu ta daddafa ta shiga bathroom tayo Alwala sannan ta fito da kyar ta yi Sallahr La'asar kana ta kuma zubewa saman carpet tsakiyar Bedroom ɗin tana kukan zuci domin zuwa lokacin hawayen ya dena ma fito ma ta sam, daga haka ne kuma Bacci da ya kasance ɓarawo ya yi gaba da ita.... *ABUJA* "Humaira wai daga ina kike haka tun jiya Hydar ya zo sun kwana anan shi da Safeena, ɗazuma suka wuce Kano tare Aneeserh ke duk kina ina?." Hajiya Aisha ce take jerowa Humaira waɗan nan tambayoyin, tun bayan barin su Aneeserh daga gidan babu daɗewa ita ma motar ta shigo gidan acewarta wurin Mijinta Aliyu tazo dama ya ce da ita Abuja zai fara zuwa before yaje Kano, shi ne fa yanzu Hajiya Aisha da Mijinta His Excel. Suka zaunar da ita a Palo Hajiya Aisha tana tambayar ta. Ajiyar zuciya ta sauke tana Gyara zama saman carpet na Palon ta ce. "Sorry Mommy and Daddy dama abin da yasa ban biyo Hayatie ba Oumun mu ce batajin daɗi acan Austaraliya, shi ne na wuce na duba jikin nata sai dai ma ta sama lafiya, eyya ban san har Hayatie ya bar nan ba.." Maganar tayi garesu cike da tsantsan ladabi tana ƙasa da kanta. Cike da mamaki His Excel... A karo na farko da ya yi magana a wurin ya ce. "Ai dama ita Oumun taku bata da lafiya shi ne bata faɗa ba, an tura Doctor?." "To Mun gode Allah tunda kince jikin nata ya yi sauƙi ina fatan kowa yana lafiya acan ɗin?." Cike da ladabi ta kuma amsawa Hajiya Aisha da tayi maganar daga ƙarshe da faɗin. "Eh duka suna lafiya, sun ce ma a gaishe ku." "Yauwa Toh muna amsawa kam." "Toh Mommy and Daddy zan wuce zuwa Kano ɗin banason dare ya yi min ban ƙari sa ba." "Toh Humaira Dan Allah a kula kinji kuma ko mai zaki tarar a gidan ki daure koda bai miki daɗi ba kinji Ɗiyata?." Kallon Hajiya Aisha Humaira take yi da mamaki na jin abin da ta faɗa sai dai ta daure ta amsa da cewa. "Tohm shikenan Insha Allah." Sallama suka yi sannan ba tare da bata lokaci ba. Driver ya wuce da Humaira zuwa Airport da zata hau Jirgin komawa Kano. Yayin da Hajiya Aisha da mijin nata suka ci gaba da tattaunawa akan wannan lamarin. Dama Humaira da Mahaifiyar ta sun kasance Ahalin Abokin His Excel... Ne wanda ya kasance ya rasu da daɗewa sakamakon 'yan damfara da ya samu suka masa Babbar cuta cikin kasuwanci da suka haɗa hannu gaba ɗaya Dukiyar sa ya rasa, sanadin haka ciwon zuciya da hawan jini yasa ba tare da jan lokaci ba ya rasu. Sosai matar sa ta shiga cikin wani mummunar hali na rashin sa, saboda ita ɗin marainiya ce ba ta da kowa, hasalima a gidan marayu mijin nata ya ɗaukota suka yi Aure. Ganin irin tashin hankalin da Ahalin abokin nasa suka shiga ne kuma ba shi da Burin sake Aure domin Matarsa ta ishe sa, yasa His Excel... Ya Aurawa yaron sa Aliyu Aishatul Humaira ɗiyar abokin nasa ta shiga matsayin ta Biyu domin lokacin an daɗe da Aura masa Yasmeen. Daga nan ne kuma ƙannen ta maza biyu da mace guda ya fita dasu Austaraliya suna karatu shi ne ita ma Mahaifiyar tasu ta ce zata bisu kawai can ɗin ta ci gaba da kula da tarbiyyar yaran ta, dama kuma bata da kowa. Ba da ɓata lokaci ba His Excel... Ya amince aka shirya Komai, mahaifiyar Humaira da ƙannen ta suka wuce Austaraliya. Yayin da Humaira take gidan Aliyu matsayin matar sa ta Biyu.... *WANNAN KE NAN. IN BRIEFLY!!!* *PRESENT.!!!!* *ANEESERH* *💥Aneeserh Just The Beginning.*💥 *Story $ Writing By:*✍️📚 *N $ N.* *🔥💫Nanameera $ Nainarh KD.🔥💫* *Ep-Fourteen* Da sassafe ta tashi ta shirya ta saka kayanta amma kuma batasan mene ne abunda zatayi ba dan kwata-kwata tsoron sauka ƙasa take, tana nan zaune har kusan ƙarfe sha ɗaya ganin babu wanda yazo nemanta kuma ga yunwa data fara damunta yasa ta mike jiki babu ƙwari ta sauko duk ta koma asalin Aneeserh nta marainiya, zaune ta samesu suna taɓa hira wani matashin mutumne wanda aƙalla bazai shige shekarun G.A ba kuma sosai suke kama dashi kana gani ko ba'a faɗa maka ba kasan ɗan'uwansa ne, murmushi Khaleepa ya sakar mata yana kallonta ta sunkuyar da kanta ahankali ta ce "Ina kwana?" Da fara'arsa y ce" lpylao sannunki" Shuru ta yi dan bai sake cemata komai ba kuma har sannan ko kallonta Aliyu bai yiba bare tayi tunanin zai kulata ganin haka yasa Khaleepa ya ce" zauna manaa Aneeserh" batayi musu ba dan daman ta gaji ta tsayuwar ta zauna ɗan nesa dasu sai asannan G.A ya ce" tashi kije ki karɓi abinci" ya yi maganar batare ya kalli inda take ba, jiki babu ƙwari Aneeserh ta miƙe ta tafi duk sai ta baka tausayi bayan ta shiga kitchen ɗin Khaleepa ya ce "Gaskiya kada kace zakayi treating ɗinta hka coz batada laifi kuma ance a warware auren so dan Allah kamar yanda Daddy ya faɗa ka kula da'ita kaji" harararsa ya yi ya ce" ai sai ka sani na kula da itan ko ni nace su auran min ita? Me zanyi da wannan ƙaramar yarinyar" murmushi Khaleepa ya yi ya ce" kawai dan bakason auran yarinya ne amma ni banga aibun wannan yarinyar ba she's cute kuma ga hankali wlh ƙarshema tafi waɗannan gantafalfallun matan naka amfani" tsaki Aliyu ya yi sannan ya ce" kai ka sani" daidai nan Aneeserh ta fito hannunta riƙe da plate sai ɗan mug ɗin tea tana rarraba idanu dan ganin inda zata zauna bata damesu ba, ganin haka yasa Khaleepa ya ce" zo ki zauna mana Aneeserh" ok ta ce sannan ta dawo wajen da take da ta zauna tana ɗan satar kallon G.A ta fara cin abinci ahankali dan ba daban yunwar da takeji ba da haƙura zatayi. Yesmeen ce ta fito tana kallonsu ta ce" sannuku da hutawa" "yawwa" suka amsa mata kallon Aliyu ta yi ta ce "Wai dear wannan yarinyar fa naga kuna kama?" Shuru Aliyu ya yi mata dan yasan halin surutunta, kwaɓe fuska ta yi ta ce" i'm.asking you" "Ajiya aka bani ita kuma matata ce so becarefull" dafe ƙirjijta ta yi tana kallonsa baki buɗe ta ce" what!?" Miƙewa ya yi dan daman yasan ita ce zata kawo masa ruɗani ya ce "Abinda kikaji na faɗa haka maganar take babu ruwanki da ita ok?" Yana gama faɗin haka ya kalli Aneeserh wacce tayi shuru sai kallonsu take ya ce" tashi ki koma ɗaki" batayi musu ba ta tashi ta wuce shikuma ya yi hakane saboda yasan halin Yesmeen ɗin, banda huci babu abinda take harma wannan ƙaramar yarinyar zai aura wato tunda su sun gaza bari asake sabon zubi tana wannan tunanin bata lurada sanda suka fita daga parlon ba saida ta ɗago zata yi masa magana taga wayam basu nan kwafa tayi sannan ta haye sama. Aneeserh kam nan parlon ta zauna tagama cin abincinta dan daman ta takura zama tare dasu ɗin, bugun ƙofar da tajine yasa ta kalli ƙofar amma bata yi tunanin buɗewa ba, sosai Yesmen take bugun ƙofar zuwa sannan kuma Aneeserh ta fara tsorata da bugun kawai ta kifa kanta a cinyoyinta ta fashe da wani irin raunataccen kuka, duk rashin iyaye shine abinda ya jefata cikin irin wannan rayuwar kwata-kwata bata ganin zamanta dasu Excel matsayin cigaba musamman ma zamanta gidan G.A tabbas akwai wata ƙaddarar data kawota cikin irin wannan gidan kuma matsayin matar gidan, wani irin mahaukacin bugu Yesmeen takewa ƙofar duk Aneeserh ta ruɗe hakan yasa ta miƙe jikinta na rawa ta ƙarasa bakin ƙofar tana sake tabbatar da ita ake bugawa. Kwafa kawai ta yi sannan ta bar ƙofar ɗakin ganin ba'a buɗe ba. Kai tsaye company ɗinsa na motoci suka shige bayan sun shiga cikin office ɗin Khaleepa ya ce" yanzu ya zakayi da yarinyar?" jingina ya yi da kujera ya ce" zuwa ta kammala karatunta zata zauna wajena tana ƙarasawa zan mayar masa da'ita dan ni babu abinda zanyi da yarinyar kamarta dan da nayi aure da wuri toh da tabbas na haifi kamarta" Tuntsirewa ya yi da dariya harda buga table ya ce" ai mace bata kaɗan wlh tuni zata saka ka fita hayyacinka" tsaki Aliyu ya yi ya ce" banza mahaukaci kawai" "E, naji wlh shawara ka gwadata ka gani amma tayi ƙarama da yawa kar ashiga haƙƙinta" Tsaki G.A ya yi sannan ya ɓalle water bootle ya fara sha, saida ya kusa shanyewa sannan ya ajiye yana yin gyatsa ya ce "Alhamdulillah, kai kuma na dawo kanka wlh koda desire zai kashe ni babu abinda zanyi da wannan yarinyar ni kallon ƴa nake mata bawai matata ba" Girgiza kai Khaleepa ya yi ya ce" Allah ya bamu rai da lafiya" "Ameen" Sai kusan 10pm sannan convey ɗinsa suka shigo, ajiyar zuciya ta sauke sannan ta bar jikin benen ta koma ɗaki. Babu kowa a parlon ya shigo kai tsaye ya shiga vip part ɗinsa wanda ko matan nasa babu wacce ta taɓa shiga shi kaɗai yake mu'amala awajen, yana gama shirin baccinsa ya fito cikin wasu pyjamas farare ƙal sunyi matuƙar amsar jikinsa musamman yadda duk wata hallita ta jikinsa ta fito ana gani tar,kai tsaye apartment ɗin ya nufa bai tsaya wani bugu ba ya saka key ya buɗe ɗakin. Bata cikin parlon hakan yasa ya shige cikin bedroom ɗin. Zaune ya tararda ita tayi tagumi kana gani kasan cikin damuwa take sosai, dafata ya yi tayi saurin kallonsa tana bude idanuwanta, "Kukan me kika yi?" Sunkuyar da kanta ƙasa tayi bata ce komai ba ya ce" keee i'm talking to a daft?" girgiza masa kai tayi ta ce "Dan Allah dan Annabi Abba ka mayar dani wajen Mommy banson zama anan" Numfasawa ya yi sannan ya ce" wani abun akayi miki?" Girgiza masa kai ta yi ya ce" then banason rigimar banza kin ci abinci?" Girgiza masa kai tayi nanma ya ce" why?" "Banajin yunwa kuma ni banason shinkafa" Sakar baki ya yi yana kallonta jin irin nata rainin hankalin ya ce" sai ki kwana da yunwa" daga haka ya juya ya fita a ɗakin. Kwanciya tayi kan gadon ta sake fashewa da kuka dan Allah ya gani tana jin yunwa kuma batason cin shinkafar shiyasa ma bata ciba, rumtse idonta ta yi jin yadda yake murɗa mata saboda rashin sabo da zama da yunwa tana wannan halin har Bacci ya yi awon gaba da ita. 𝐀𝐍𝐄𝐄𝐄𝐒𝐄𝐑𝐇. *_𝐄𝐩.Fifteenth_* *💥Aneeserh Just The Beginning.*💥 *Story $ Writing By:*✍️📚 *N $ N.* *🔥💫Nanameera $ Nainarh KD.🔥💫* *_𝐄𝐩.Fifteenth_* 𝐖𝐀𝐒𝐇𝐄 𝐆𝐀𝐑𝐈. 𝐀𝐑𝐎𝐔𝐍𝐃 6:50𝐀𝐌. A hankali ta tura ƙofar Bedroom ɗin ta shiga, bakinta ɗauke da sallama ƙasa ƙasa ba tare da ta jira an amsa sallamar ba, ta cusa kanta ta shiga cikin Bedroom ɗin gaba ɗaya. Zaune ta hangota saman Stool na Dress Mirror tana fuskantar Mirror da alama bata daɗe da fitowa daga bathroom ba domin bathrobe ne sanye a jikin ta. "Wa'alaiki Salam lafiya dai na ganki a ɗakina da wannan sassafiyar ina fatan dai lafiya?." Safeena ta faɗa Hakan ba tare da ta juya ta kalla Yasmeen da ta shiga Bedroom ɗin ba. "No, akwai dalilin zuwa na, domin haka kawai bazan shigo Bedroom ɗin ki ba har sai da Dalili." "Okay Tohm Ina sauraren ki." Zama gefan Bed tayi tana Gyaran murya ta ce. "Wai baki da labarin abin da yake faruwa ne a gidan nan?." "Kamar ya ya ke nan, kiyimin Bayani yadda zan gane Please idan kuma ba haka ba ga hanya nan ni banason gulma wallahi da kike gani na ." "Dalla Malama kema ai kinsan bana gulma ɗin, kawai dama faɗa miki zan yi wancan Yarinyar Aneeserh take ko wacece to matar Aliyu ce ba ƙanwar sa ba. Yes na faɗa Miki ne saboda idan baki sani ba ma ki sani Aha." Yasmeen ta ƙari sa maganar tana kuma lura da yadda Safeena ta zaro ido cike da mamaki na maganganun ta ga dukkan alamu dai batasan da maganar ba sai wannan lokacin. Murmushin gefan fuska Yasmeen tayi tana karkaɗa ƙafa ba tare da ta ce komai ba, yayin da Safeena ta kasa taɓu ka komai, kawai dai ta zuba ma ta ido ne tana kallo. *ANEESERH P.O.V.* Tun Bacci da ya ɗauke ta jiya da dare ba ita ta kuma farkawa ba har sai safiyar yau da ta kasance Jumma'a sannan kuma kwanakin ta na biyu ke nan a gidan General Aliyu Yayan ta kuma Mijinta. Zama ta ci gaba da yi saman Sallaya tun bayan idar da Sallahr Asuba da tayi, sannan tayi azkhar nata kamar Kullum. Tanajin yadda cikin ta ke faman ƙugi na yunwa amma ta kasa ta tashi balle ta nemawa kanta abin da zata saka a bakin sallati sai faman zare ido take yi tana ƙara tabbatar wa da lokacin period nata kwanakin sun kusa shiga tunda take a Rayuwarta sau ɗaya ta taɓa yi kuma baizo ma ta, ta sauƙi ba domin sosai tasha Azaba, shiyasa har batasan tunawa da lokacin domin ita kaɗai tasan kalar wahalar da ta sha na ciwon mara. "Wayyo ni Aneeserh ya ya zan yi da rayuwata ke na?." Tayi ma kanta tambayar da babu mai bata amsa. Shiru tayi yayin da take sauraren bugun zuciyarta cikin Rashin abin yi daurewa kawai tayi sannan ta miƙe tsaye da dabara, folded na sallayar tayi sannan ta mayar da shi ma'ajin sa ba tare da ta cire hijabin Sallahr dake jikinta ba ta kama hanya, murɗa handle ɗin ƙofar tayi sannan ta buɗe ta fita gaban ta bai dena bugawa ba. "Ke Aneeserh kike ko, come here." A firgice ta juya tana kallon saitin wurin da ta jiyo Muryarsa mai cike da amo da ya yi ma ta magana. Taɓe baki tayi cike shagwaɓa kamar mai shirin fashewa da kuka ta fara tafiya a hankali har ta ƙari sa Dining Room ɗin taja tunga ta tsaya yayin Mutanen dake Dining ɗin suka bita da kallo. Sosai Humaira take ɓoye dariya domin lamarin sosai yake bata dariyar wai wannan 'yar halittar dake gaban su ita ce Mata ta huɗu a wurin mijin su G.A. lallai kam da alama iyayenta sun gaji da ita ne Tabbas, ta ayyana hakan a ranta tana kuma kumshe dariya. Yayin da banda ido babu abin da Safeena take bin Aneeserh da shi. Ita kuwa hamshaƙiya Yasmeen zuba mata ido kawai tayi tana so taga ta yadda Yarinyar zata moru ƙarama da ita ban da abin iyayen Aliyu ma abin da su suka kasa ne wannan kucakar zatayi, qwafa kawai taja cike da takaici.😒 "Hey you, how are you feeling today?." Cikin rawar baki kaɗan ta amsa masa da faɗin. "Am Okay Abba na."🤨 Da mamaki matan Aliyu suka kalleta jin sunan da ta kira sa da shi, sai dai babu wacca ta iya cewa komai, Murmushi kaɗan da bai bayyana ba, ya yi domin yana lura da Reacted na kowa, mayar da kallon sa ya kuma yi kan Aneeserh sannan ya ce. "No, you're not okay, kinji abinci ne?." "A'a, ban ci ba." Ta basa. amsa. "Okay, bakiji abinci ba amma kince kina lafiya ko, ya yi miki kyau, zauna anan?." Ya yi maganar yana ma ta nuni da kujerar dake gefansa. Zama tayi a ɗar ɗar sannan ta fara buɗe food flasks dake jere a Dining ɗin tana neman abin da zai yi ma cikin ta daidai. Ta gefan ido yake kallon ta sai dai bai kuma cewa komai ba. Haka ma sauran matan sa dake wurin. Ita dama Aneeserh yanzu ba surutu take so sosai ba, mayar da hankali tayi wurin cin abincin ta bil-haƙi. 𝐀𝐑𝐎𝐔𝐍𝐃 10:30 𝐀𝐌 Gajiya da zaman palon da tayi ne tsuru da ita yasa ta miƙe tsaye tana kallon sa ta ce. "Abba na, na gaji zan koma Bedroom ɗina." Ba tare da ya juya ya kalle ta ba, ya amsa ma ta da faɗin. "Okay take care." Bata ce komai ba ta juya ta koma zuwa Bedroom ɗin ta dama a takure take tun lokacin da ta kammala Breakfast nata taso ta koma Bedroom ɗin amma ya hanata da faɗin ta zauna a Palon tare da su nan ne yake faɗa ma ta kaɗan daga cikin tsarukan Gidan nasa, wai duk sati Ranar Jumma'a ke nan kamar yau, haka ake yi ba ya fita Office ko wani wurin sai dai zuwa Masallaci, bayan ya dawo kuwa yana gida tare da matan sa a Palo suna fira idan akwai mai wata maganar ma sai tayi anan, ita dai Aneeserh amsa masa kawai tayi a lokacin badan ta gama fahimtar abin da yake faɗa ma ta ba. Domin bata hayyacinta sama sama takejin ciwon mara na taso ma ta sai dai ta daure. Tana shiga Bedroom nata ta garƙame da key, zama tayi gefan Bed idanunta na kallon ƙasa yayin da fara lulawa Duniyar tunani, Allah Sarki Baiwar Allah sosai takejin kewar Hajiya Aisha Mommy har dama His Excel. Uncle nata sai dai kewar iyayenta ya shanye wannan, shawara kawai ta yanke akan zata sama G.A da maganar ya taimaka ya sai ma ta waya ko dan ta dinga gaisawa da Mommy. *IN BRIEFLY.* Haka dai Rayuwar Aneeserh ta ci gaba da kasancewa a gidan General Aliyu Yayanta kuma miji a gare ta, cikin matan sa masu mabanbanta halaye, tsakanin ta dasu sai dai ido domin ko gaishesu ma da take yi da farko zuwa yanzu ta dena domin ta fahimci ba ƙaunar ta suke yi ba, tsakanin ta da uban gayyar wato G.A Gaisuwa kaɗai ke haɗasu wasu lokutan ma saita kwana ta wuni bata gansa ba, sai dai lokaci bayan lokaci Khaleepa yana kawo ma ta ziyara kuma sosai takejin daɗin hakan musamman ma lokacin da ya zo da matar sa har da Yaron sa ƙarami. Ta gefe guda kuwa duk yadda taso akan ta sama Aliyu da Maganar ya sai ma ta wayar kasawa tayi domin mugun tsoron sa takeji ga mugun kwarjini da yake ma ta, cikin sati guda da zuwan ta Kano komai ya kammala na komawar ta school cikin Iko da nufar Ubangiji Aneeserh ta fara zuwa School Driver yake kaita ya dawo da ita.... *💥Aneeserh Just The Beginning.*💥 *Story $ Writing By:*✍️📚 *N $ N.* *🔥💫Nanameera $ Nainarh KD.🔥💫* *ANEESERH* *💥Aneeserh Just The Beginning.*💥 *Story $ Writing By:*✍️📚 *N $ N.* *🔥💫Nanameera $ Nainarh KD.🔥💫* *Ep-Sixteen* Da sauri tashige ɗakinta tana riƙe mararta saboda wani azababben ciwo da take mata, kwanciya tayi ƙasan carpet ta baje kamar wata gawa hankali kuma ta fara kuka tana sake riƙeta dan ji take kamar ranar mutuwarta ce tazo "Wayyo Ummina!! Wayyo Abbana!! Wayyo Yayana wlh mutuwa zanyi wayyo Allah cikina na shiga uku zan mutu" Abinda Aneeserh ke furtawa kenan tana sake rushewa da kuka har lokacin sallar magrib ya yi tana nan ta kasa tashi. Fitowa ya yi dan tafiya masallaci kamar wanda aka yiwa dole ya ƙarasa jikin ƙofar apartment ɗin nata, tura ƙofar ya yi bakinsa ɗauke da sallama yana ƙarewa ɗakin kallo. Hangota ya yi kwance daga gefe kamar wata matacciya da mamaki ya ƙarasa yana kallonta dan batasanma ya shigowa ba "Keeee!" A firgice ta ɗaga kai ta kalleshi sai kuma ta sake fashewa da sabon kuka tana miƙo masa hannunta ta ce" Abbana ka taimakeni zan mutu cikina zai cire" ɗagota ya yi ya jinginata ƙirjinsa yana kallon fuskarta wacce duk ta kwaɓa da kuka ya ce" lafiya?" cikin kuka ta ce "cikina ne yake ciwo zan mutu kuma" girgiza kansa ya yi danshi a ganinsa shirmene irin nata wanda ta saba ya miƙe yana kallinta ya ce" tashi tsaye" kwaɓe fuska ta yi zata fashe da kuka ya ce" idan kika yimin kuka sai na zaneki, tashi nace" kujera ta kama ahankali kamar wata mai ciki ta miƙe kallon inda ta tashi ya yi kafin ya yi mata magana ta tafi tayi baya luuuuuu kafin ta ƙarasa ƙasa ya riƙeta yana kallonta bai ɗauka period take ba dan shi iya zatonsa ma tayi ƙarama da period, rasa yanda zai yi da ita ya yi gashi lokacin sallah na shigewa tsaki ya yi sannan ya ɗauketa kamar Baby ya shige Bathroom ɗin da ita, saida ya yi mata wanka lokacin ta farfaɗo ya bata kaya da pad ta saka sannan ta sake kwanciya. Fita ya yi ya koma wani ɗaki wanda yake kamar chemist ya ɗauko allura da drip ya fito, a hanya Yesmen ta ganshi tana kallon abin hannunsa ya ratsa ta gefenta ya yi wucewarsa dan yasan yanzu saita saka shi magana har sannan Aneeserh na kwance sai kuka take ya shiga ɗakin wata kyakyawar tsawa ya daka mata ya ce "Kimin shiru shashasha kawai ko yau kika fara haila da zaki dameni" haɗiye kukanta ta yi saboda yanda ta tsorata da tsawar gashi dai Allah shine shaidarta akan irin ciwon da takeji amma shi ko ajikinsa bazaka taɓa cewa yarinyar ta raɓeshi ba ko sau ɗaya bai cemata sannu ba har ya gama ɗaura mata drip ɗin da allurar, ita kanta ta yi mamakin irin dauriyar da tayi har ya yi mata allura batayi kuka ba ya kwashe kayansa ya yi waje lokacin kusan ƙarfe 7:06 dole ya koma ɗakinsa ya yi sallar acan. Wajejen ƙarfe goma ya shigo domin cire mata drip kwance ya tarar da ita har sannan kuma bata daina kukanba tsaki yayi sannan ya zauna gefen gadon yana kallonta ya ce" miƙe zaune" bata yi musu ba ta kama fuskar gadon ta miƙe zaune ta jingina da jikin gadon miƙe mata plate ɗin hannunsa ya yi ya ce"ci" batayi musu ba ta karbi abinci ta buɗe Jallof rice ce sai peppersoup ɗin offals da aka watsa akai sai kaza kusan rabi, kallon abincin ta tsaya yi ya ce" kee jiranki fa nake" ahankali ta fara ɗiban abincin tana kaiwa bakinta ko loma uku batayi ba ta kauda kanta tana ajiyewa kan bedside drawer ɗin, wani banzan kallo ya yi mata ya ce" i'm play with you?" girgiza masa kai tayi kafin ya sake magana ta fara yunƙurin amai, da mamaki yake kallonta dan bai gane wannan abun nata ba bai kai ga taɓuka komai ba ta fara kwarara masa amai anan inda take Shuru G.A ya yi yana kallon ikon Allah har ta gama aman sannan ya kaita banɗaki ta wanke bakinta ya gyara wajen, wani zazzaɓine ya rufeta jikinta ya fara kakkarwa ya ce"fita muje" bin bayansa ta yi suka fita daga ɗakin Bedroom ɗinsa ya shiga ya ɗauko car key ɗinsa sannan ya yi gaba tana biye dashi abaya har suka isa parking lot ɗin gidan, guards ne suka taso ya ɗaga masu hannun ya buɗe mata motar ta shiga sannan shima ya zagaya ya shiga ya bar gidan... Sakin labulen tayi sannan tayi kwafa wato har zai fara nuna musu banbanci a tsakaninsu wlh kam da sake ta furta aranta sannan ta koma ta kwanta, sai kusan ƙarfe 11pm sannna suka dawo gidan lokacin har bacci ya ɗauketa dalilin allurar da likita ya yi mata, a hannunsa ya ɗauketa tamkar wata Baby ya ashiga cikin gidan, zaune ya samu Safeena da Yeemen suna hira amma bazaka ce ga hirar da suke ba, kallo ɗaya ya yi musu ya shige ciki suka bisa da kallo baki sake saida ya haye sama sannan Yeesmen ta ce "Kin gani ko wlh ya mayar damu ƴar iska" Taɓe baki Safeena ta yi bata ce koma ba. Master bedroom ɗinsa ya shige da ita ya kwantar da ita kan haɗaɗɗan royal bed ɗin nasa na alfarma karo na farko kenan da wani ya kwanta akai bashi ba. Aneeserh bata farkaba sai wajen ƙarfe 3:30am lokacin yana zaune kan dadduma bayan ya idar da salloloinsa, zama ta yi tana kallonsa har ya gama sannna ya kalleta ya ce" lafiya?" girgiza masa kai ta yi ya ce" ya yi sauƙi marar?" hawayene ya zubo fuskarta ta ce" zafi ya kemin Abba" tasowa ya yi ya zo wajenta ya tsaya yana kallonta ganin duk ta rame daga yammaci zuwa sannan "Ki kwanta zai saida duka" "Fitsari zan yi Abba" Kama hannunta ya yi ya kaita banɗakin sannan ya fito tana gamawa ta fito ta sake kwanciya nan da nan bacci ya ƙara ɗauketa. *Washe Gari.* Kallonta ya yi har ta karaso ta tsuguna ta gaishesa sannan ta ce" Abba zan tafi makaranta" "kinji sauƙi?" gyaɗa masa kai tayi ya ce" toh zauna ki fara breakfast sannan" zama ta yi kan kujera sannan ya miƙo mata plate mai ɗauke da soyayyen kwai sai chips agefe "Ki saka sugar kaɗan" gyaɗa masa kai ta yi sannan ya cigaba da cin abincinsa ɓakinciki ne yasa ta miƙe fuuuu ta bar wajen ya bita da kallo sannan ya taɓe baki. Tana gama cin abincin ta kalleshi ta ce"Abba nagama" ɗago kansa ya yi daga kan wayar hannunsa y ce" kije ki kwanta zuwa gobe sai ki tafi makarantar" hawayene ya kawo idonta ta ce" dan Allah Abba ina son naje please" girgiza mata kai ya yi zata sake magana ya ɗaga mata hannu yana nuna mata hanyar ɗaki ya ce" je ki" tashi tayi jiki asanyaye ta koma part ɗinta Tana shiga ta zauna kan kujera ta fashe da kuka sai da ta yi mai isarta sannan ta kwanta nan da nan bacci ya yi awon gaba da ita. **** Tsaki ya yi ya ce" nifa ba haka nake ba Khaleepa wlh bazan iya haƙura na zauna da wannan yarinyar ba ai yazama abun kunya kenan duk abokai na su dinga ganinta ace matata ce ko?" Murmushi Khaleepa ya yi ya ce" shikenan tunda haka ka zaɓa amma idan nine kai haƙura zanyi na tabbata akwai abinda su Daddy suka hango wanda kai baka hangoshi ba" ɗaga kafaɗa ya yi ya ce" ni wannan bai dameni ba kawai banason abu banaso period" Da gudu Sabeer ya tawo ya rungumeshi, ɗaga shi sama ya yi yana dariya ya ce" my boyy ka ɓuya" dariya Sabeer ya yi ya ce" ba Daddy bane yaƙi kawoni kullum idan nayi masa magana sai yace sai anyi hutun school" kallonsa Aliyu ya yi ya harareshi ya ce"rabu dashi yau ko yana so ko baya so sai muntafi tare" murmushi ɗauke afuskar kyakkyawan yaron ya ce" thank you Abba" Fashewa ta yi da sabon kuka ganin irin yanda jinin jikinta ke tafiya abanza ita bata taɓa irin haka ba arayuwarta, tayi amfani da pad aƙalla guda biyu daga dare zuwa yanzu duk ta zuge ta rame. Ana idarda sallar magriba suka shigo gidan da kallo Sabeer ya bi duk matannasa yana ganin Humaira ya tafi da gudu ya rungumeta murmushi ta yi ta ce" oyoyo Love sai yau?" " wlh Aunty sai yau Abba ya tawo dani da Dad ya hanani" ok ta ce sannan ta riƙe hannunsa suka shige part ɗinta shikuma ya haye sama. Har ya yi gaba sai kuma ya dawo ya buɗe ɗakin ya shiga, durƙushe ya tarar da ita gefen gado "Wai ke har yanzu baki ji sauƙi ba?" Hawaye na gangarowa kan kuncinta ta ce. "Ciwo yake min sosai Abba." Tsaki ya yi sannan ya juya ya fita dan ɗauko ma ta magani. https://chat.whatsapp.com/J3EAYvZGXUxKkXHsRRvrpS _Innocent Girl_ *ANEESERH.* BY AMEENAH I IBRAHEEM (Nanameera) And KHADEEJARTH SABI'U YAHYAH (Nainarh KD) *EP_Seventeen.* *IN BRIEFLY.* Haka dai Rayuwar Aneeserh Baiwar Allah ta ci gaba da kasancewa a cikin gidan General Aliyu Yayan ta kuma Mijinta da take kiransa da Abbanta a koda yaushe kuma ta ɗauke sa a matsayin hakan. Ta ci gaba gudanar da Rayuwarta a cikin gidan tare da matansa uku kuma wacce halinta ya bambanta dana 'yar uwarta kaf cikinsu Yasmeen ce take mugu mugun takurawa Aneeserh cikin zamanta a gidan, tsakaninta da Humaira sai dai kallo dan bata cika zama a gidan ba ma tana fita Office. Yayin da ita kuma Safeena babu ruwanta da kowa sai dai taci tasha ta kwanta a palo ta yi kallo tahau online aikin ta ke nan a kullum ko girki ma ba ita keyi ba 'yar aiki take yi ma ta duk Ranar da ya kasance ita ke da girkin. Aneeserh ta ci gaba da zuwa school nata tana fafata Karatu Yayin gefe guda kusan duk sati sau uku zuwa huɗu take waya da su Mommy da Uncle nata His Excel... *Wannan Ke Nan...* *Abuja, Nijeriya.* Da mamaki ta kuma kallonsa a karo na biyu da jin abin da ya kuma faɗa cike da takaicin raina ma ta da yakeon yi ta ce. "Saima suna na kuma Kaduna State nake ni ce make-up artist ta Gidan Hajiya Aisha nake yiwa aiki kuma ni ba 'yar aiki bace domin duk wata Dubu ɗari Biyar nake ɗauka a matsayin salary nawa, kaga ko nafi ƙarfin 'yar aiki, sannan kuma ni ba Yarinya bace domin shekaruna Ashirin da Biyar ehee." Tayi tana murguɗa masa baki kaɗan domin ta lura wannan mutumin akwai rainin wayo da yawa akan mai ma zai kama ya kira ta da 'yar aiki kuma Yarinya ai ba za ta lamun ta ba shiyasa ta saki jiki ta yi masa bayani idan ya fahimta ruwansa. Kama Hanya ta yi zata bar wurin sai dai a bazata taji ya riƙo hannunta ko kafin ta yi wani yunkurin ya janyo ta zuwa cikin Garden. "Wayyo Hajiya Aisha zoki taimakeni wayyo ni kwartt....."😳 Cikin sauri ya kai hannunsa ya toshe ma ta baki cikin zaro ido da Magana ƙasa ƙasa ya ce. "Ke baki da hankali ko wato ni ne ma zaki kira da kwartt......"🤨 Shiru ya yi ba tare da ya ƙari sa ba. "Ni ka sakeni, ka ƙari sa faɗa mana in ba hakan ba mai zai sa ƙaton gardi kamar ka mara mata ka janyo budurwa kamar Ni cikin nan wurin." "Bazan sake ki ba ɗin." Kuka ta saka masa ta ce. "Saboda me?." Murmushi ya yi yana ɗan sassauta riƙon da ya yi ma ta ya ce. "Ko ki nutsu da kyau na faɗa Miki abin da ke Zuciyata ko kuma mu ci gaba da kasancewa a haka muga wanda zai gaji." Sanin halinsa da ta yine da kuma tuna cewa Hajiya Aisha tana neman ta domin zuwa anjima zata fita zuwa wurin taron auren wata ɗiyar ƙawarta kuma ita ce zata ma ta make-up kamar kullum yasa Saima ta sauke ajiyar zuciya sannan ta ce. "To na nutsu ai." "Good Girl." Ya faɗa sannan ya umarce ta da ta zauna. Tana zumɓura baki ta zauna saman ɗaya daga cikin Chairs na hutawa dake garden ɗin, sannan shima ya zauna gefanta kaɗan. "Ki Aure ni." Ya faɗa lokaci guda kuma babu alamar da wasa ya yi maganar a gare ta. Kallon amma dai baka cikin hayyacinka take bin sa da shi tsaban mamaki ma ta kasa ta ce masa Komai. Da sauri ta miƙe tsaye har tana tuntuɓe ta fi ce daga Garden ɗin ko waigen sa ba tayi ba, yayin da ya bita da kallo yana lumshe ido. Yarinyar tanason wahalar da zuciyarsa gashi baisan ya nema abu ya rasa ba a Duniya tun tasowarsa har izuwa yanzu. "Saima lafiya kuwa kika shigo kamar wacce aka koro?." Tana sauke haki na gudun da tayi ta zauna a sofa tana faɗin. "Babu Komai Her Excellency kawai dai na ɗan tsorata ne sakamakon ganin snake da nayi a garden gashi kuma ya gudu." Ta faɗa hakan ba tare da ta kalla Hajiya Aisha ɗin ba dan gudun karta ganota. "Ayya, snake kuma zuwa anjima zan saka securities su duba bai kamata ana samun irin su a Garden ba." "Ai gaskiya kam ya kamata a gaggauta dubawa a fitarda shi daga Gidan nan domin hatsari ne ga 'yan mata iri na." Tayi maganar tana ɗauke idanunta akan Jay da shigowar sa Palon ke nan. "Akan menene ake magana haka naji ana cewa a fita da shi?." Juyawa Hajiya Aisha tayi tana kallon sa da mamaki ta ce. "Jay! Yaushe kuma ka shigo Gidan dama kana Nijeriya?." Ta jero masa tambayoyin lokacin da yake zama saman Sofa 2 sieter ya kalleta sannan ya bata amsa da faɗin. "Yanzu Yanzu na shigo fatan na sameku lafiya?." Ya ƙari sa maganar yana kashewa Saima da ta saki baki tana kallon sa ido. "Ah Hajiya Ina ga kizo mu fara make-up ɗin tun yanzu lokaci fa yana ja." Saima tayi maganar lokacin da Hajiya Aisha ta buɗe baki da niyyar ta yi masa wata maganar. Ajiyar zuciya Hajiya Aisha ta sauke ta ce. "Dama ai kece kika tsaya jan lokacin yanzu tunda kin shigo sai a yi kawai." *Kano, Nijeriya.* Watannin Aneeserh Biyu ke nan a Garin Kano zuwa yanzu sosai ta saba da Khaleepa da kuma Matarsa Hafsat da Yaron su. Zamanta da G.A kuwa ba'a ce komai ba, domin sai ta kwana biyu ma basu haɗu da shi ba sai dai idan taji tanason magana da su Hajiya Aisha ne shi ne zata nemesa da maganar, idan yaga dama ya bata wayar ta kirasu su gaisa, wasu lokutan kuwa idan yanajin tsiya hana ta yake yi sai dai taci kuka ta gode Allah. Zuwa lokacin Yasmeen ta fara saukowa akan kishin da take gwadawa akan Aneeserh gane cewa da tayi da gaske Aneeserh bata gaban mijinta General Aliyu, zuwa lokacin tunaninta ya koma ne akan yadda zata raba sa da gaba ɗaya matan nasa cikin sauƙi ba tare da Asirin ta ya tuno ba.😳🙄 Humaira kuwa ta ɓangaren ta sosai suke shiri ita da Mahaifiyar ta akan yadda zasu sace wasu files na wurin aikin sa masu matuƙar muhimmanci a wurin Aliyu wanda akan hakan ne kaɗai Burinsu zai cika. Safeena kuwa wannan 'yar daɗi Miji ce duk abin da Aliyu yakeso ita ma shi take so, haka ma abin da yaso tofa wannan abun baya burgeta sam, shiyasa shima yake ji da ita bata da Hayaniya bata da gulma barta da son jiki kawai da rashin iya girki. A cikin wannan taƙin ne Aliyu ya yi tafiya zuwa ƙasar Paris sannan bai faɗa musu ga adadin kwanakin da zai yi ba, sannan kuma da Safeena ya tafi kuma Hakan ba ƙaramin fusatar da zuciyar Yasmeen ya yi ba, kawai daurewa ta yi ta nema ƙawayen ta Sabeera da Suhaila domin su bata shawara. Aneeserh sanye take cikin Riga Top white Mai gajeren hannu sai kuma wando jeans crazy white and black color ta ɗaure dogon gashin kanta da ribbon tayi packing ɗin sa a tsakiyar kanta ba tare da ta saka hula ba, fitowarta ke nan daga Garden hannunta ɗauke da guava da alama bishiya ta hau ta tsinko. Murmushi tayi hango Umaru mai bawa flower's Ruwa da tayi, kaf cikin ma'aikatan gidan tafi shaƙuwa da shi, sakamakon sunan Yayan ta Umar da yake da. Cikin sauri ta ƙari sa wurin sa cikin washe baki ta ce. "Barka dai Yayana aiki kaketa sha ne haka kawo na tayaka bawa flower's ɗin Ruwan." Tayi maganar tana ƙoƙarin karɓar abin bawa flower's ɗin Ruwan dake hannunsa. Kallon ta ya yi yana Murmushi ya ce. "A'a dai ƙanwata na huta ce ki fa, kije ki ci guava da kyau ki barni da aikina anan." Murmushi tayi tana faɗin. "Kai Yaya Umar to shikenan na tafi sai anjima." Tayi maganar tana juyawa domin shiga cikin palon gidan, sai dai jin ta yi karo da Mutum ne ta bugi faffaɗan ƙirjin sa, yasa ta ɗa go kanta da sauri cikin zare ido take kallon mutumin dake gaban ta.... *ANEESERH* *Ep-18* Da sauri tayi baya tana kallonsa tayi zilli gidi-zilli gidi da'ita batareda yace komai ba ya kama hannunta ya hau figarta har cikin gidan, tsabar yanda ta tsorata ko kuka ta kasayi yana zuwa ya yi wurgi da'ita a parlon yana mata Wani mugun kallo, tsayawa sukai suna kallonsa dan ce musu ya yi wajen Khaleepa zashi, hannunsa yasa ya ɗagota batayi auneba taji ya wanketa da wani kyakkyawan mari dan har saida taga stars a fuskarta, kasa yin kuka tayi ta koma baya tana riƙeda kuncinta tana sakin ajiyar zuciya cikeda bala'i yake cewa "Wato ke mara hankali ko?, ke ga mahaukaciya ko?, ba kisan mene ne yake miki ciwo ba uban wane ya baki damar fita daga cikin parlon nan har kitafi kina hira da maid?" Shuru Aneeserh tayi dan sai a sannan tagane laifin data aikata jikinta sai rawa yake "I'm talking to a daft?" A tsawace ya yi maganar dan duk saida suka tsorata yanda idanunsa suka sauya kala shine zai nuna maka irin ɓacin ran da yake ciki, kwafa ya yi sannan ya kalleta ya ce" na fuskanci ke yanzu kika fara iya naki haukan to zanyi maganin duk rashin hankalin da kike famada wlh idan baki nutsu ba ruwa sai kin gagara sha cikin kwanciyar hankali a gidan nan shashasha mara hankali kawai" yana gama faɗin haka ya juya ya yi fitarsa. Sai a sannan ta fashe da wani irin kuka tana shafo fuskarta domin ita tunaninta fuskar fashewa tayi da kallo suka bita kowacce ta kama gabanta dakyar Aneeserh taja jiki ta haye sama tana riƙe da fuskarta Kallonsa Khaleepa ya yi ya ce "G.A what's wrong with you naga ranka a ɓace?" kwafa Aliyu ya yi bai ce komai ba kuma daman yasan ba lallai ya magantuba, murmushi ya yi ya ce" kodai kaida ƴar rainon taka ne?" tsaki ya yi ya ce" kasan Allah nan bada jimawa ba zan mayarda yarinyar nan dan idan ina ganinta tana yimin wani abu wallahi wataran saidai a ɗauki gawarta sabida yanda nakejin haushinta bataji ko kaɗan yarinya kamar sheɗaniya" girgiza kai Khaleepa ya yi ya ce "Dan Allah ka dinga sakawa zuciyarka haƙuri i know zamada yarinya akwai ƙalubale amma tunda har ta dawo wajen naka kuma bazata ƙara kwanakin da tayi abaya ba dan Allah kayi haƙuri yanzu fa third term suka shiga kwata-kwata four months akeyi kuma yanzu sunyi 2months kaga idan kayi haƙuri nan bada jimawa ba zata koma hannun Daddy ta cigaba da rayuwarta karka manta yarinyar nan marainiyace kuma batada wasu shekaru dole sai kana haƙuri" Furzar da iskar bakinsa ya yi ya ce" bazaka gane bane bakasan halinta bane dan badakai take zaune ba wlh inaga da tuni ka koreta saboda halinta" murmushi Khaleepa ya yi ya ce" ni ka kawomin ita mu zauna tare" harararsa ya yi ya ce" ba haka nake ba" Tanajin ana kiran sallar magrib amma ta kasa tashi tayi sallah saboda wani zazzaɓi ya rufeta jikinta sai rawa yake dakyar ta lallaɓa ta mike lokacin anfara kiran isha'i tana dafe kanta saboda wani ciwo da yake mata ta shiga banɗakin, a daddafe ta idar da sallar ta jingina da jikin gado ta rushe da wani irin kuka mai tsuma zuciya tabbas rashin iyaye masifane bata taɓa tunanin haka zata kasance da rayuwarta ba bata taɓa tsammanin rabuda da iyayenta a wannan lokacin ba sannan ta ɗauka matsalar ta kau bayan ta hadu da His excellency ashe sannan ne matsalar zata fara tana zaune nan har kusan ƙarfe 9pm lokacin yunwa ta fara damunta ga kuma tsoronda take ji karta sauka taje ta tarar da G.A yana ƙasan dan taji sanda ya dawo gidan. Daga ƙarshe haƙura tayi da abincin ta linke daddumar ta ajiye sannan ta kalli fuskarta jikin dreesing mirror ɗin dake maƙale a ɗakin sosai fuskarta ta yi wani Ja ta kumbura duk shaidar yatsu akanta taɓa fuskar ta yi hawaye na zirarowa kan kuncinta ta tafi ta kwanta tana lumshe ido wasu zafafan hawaye suka shiga sakko mata haka har bacci ɓarawo ya saceta. Da safe bayan tagama shirin makarantarta ta sauka dukda yanda take jin jikinta babu daɗi, gabantane ya faɗi ganinsa da tayi zaune kan kujera yana operating laptop Safeena na zaune gefensa dakyar ta ƙarasa sakkowa tana tafiya kamar mara gaskiya har takai bakin ƙofar "Keeeee!" Da sauri ta juyo ta kalleshi taga ya kafeta da ido ta sunkuyar da kanta tana wasada fingers ɗinta har batasan sanda ya iso gabanta ba hucin mutum kawai taji tana ɗaga kai suka haɗa ido dauke nata tayi dan ko san ganinsa batayi, kallaonta ya shiga yi from head to toe ya kalli fuskarta dukda ta sace amma shaidar tafin hannunsa tana nan raɗau a fuskar "Ina kika shirya zuwa?" Tambayar da ya yi mata kenan yana kafeta da ido, sunkuyar da kanta ta yi ta ce "Makaranta zani" Harararta ya yi ya ce" zoki shige ciki" ya faɗi maganar yana nuna mata hanyar parlon hawayene ya taru a idonta ta ce" dan Allah Abba yau test zamuyi kuma idan banyi ba malamin bazai sake yimin ba" "Oh really?" Sauri gyada masa kai ta yi ya ce" idan kika kuskura na ƙirga uku kina tsaye anan wlh sai ranki yayi mugun ɓaci shashasha kawai" tana riƙe bakinta gudun kada tayi kuka tashige cikin parlon da gudu ta koma sama tana zuwa ta waɗa kan gadon ta fashe da wani matsananincin kuka. "Ina Aneeserh?" "Tana bacci Mommy idan ta tashi zan kiraki sai ku gaisa" ok Mommy ta ce sannan sukai sallama. Ajiyar zuciya ya sauke dan bayason ko kaɗan aga gazawarsa wajen rikon yarinyar har sanda zai maida ita. Murmushi Yesmeen ta yi ta ce" wai dear yaushe zaka mayar musu da ƴar su?" kallonta ya yi sai kuma ya ce "Daman akanki take bansani ba?" Murmushi ta yi ta ce" kawai tambaya nayi yallaɓai" "Tom babu ruwanki ko yaushe zan mayar daita koma anan zata ƙari rayuwarta" saurin kallonsa ta yi ta ce" Allah ya baka haƙuri mai da wuƙar". Sai azhar sannan ta farka tayi wanka ta gabatar da sallah shiryawa ta yi cikin wata atampa super holland green da adon baƙi ta ɗaura ɗankwalinta tayi kyau abinta amma kwata-kwata zuciyarta babu annuri. Zaune ta tarar dasu kamar dole sai an zauna atare saida ta kalli gefenta sannan taga G.A zaune ya tankwashe ƙafa ana ajiye abincin kala-kala gabansa, tsayawa tayi tana kallonsu da mamaki dan ita bata taɓa ganin wannan abun ba tashi sukai suma suka zauna kusada shi kowacce ta ɗauki plate ta zuba abinci, kallonta ya yi yaga ta juya zata koma sama ya ce "Aneeserh!" Juyowa ta yi ta kalleshi sai kuma ta ƙaraso gabansa ta tsuguna kanta ƙasa "zauna kici abinci" Kallonsa ta yi sai kuma ta ce"naƙoshi Abba" wani kallo ya yi mata daya sanya ta shiga nutsuwarta ya ce "Zauna nace" bata kuma musu ba ta zauna daga gefe tana bin kowa da kallo haka kawai taji abincin na saka mata tashin zuciya musaman naman da tayi ido biyu da, Abincin ya zuba mata yana kallon fuskarta ya ce"oyha take it" karɓa tayi amma batayi yunƙirin ciba ta ajiye gefenta ta cigaba da kallonsu saida ya gama cin abincin sannan ya kalleta yaga ko taba abincin bata yi ba "Keee, ni sa'an wasanki ne?" Girgiza masa kai tayi ya dauki abincin yana kallonta ya ce "Open your mouth" Sauke idanunta ta yi sai kuma ta buɗe bakin nata a hankali ya zuba mata abincin domin shi duk abunda zaku yi dashi baya lamuntar zama da yunwa dole sai kaci abinci. Haka ya cigaba da feeding ɗinta har ta ƙoshi dukda yanda zuciyarta ke tashi bata nuna masa ba saida suka gama ci, da gudu ta ƙarasa toilet bayan tashiga parlon tana zuwa ta hau kwara wani irin amai, duk abunda taci saida ta amayar dashi a hakama kamar ta amayar da hanjin cikinta saida tagama aman sannan ta zauna banɗakin tana sauke numfashi dakyar ta tashi ta wanke bakinta sannan ta fito daga banɗakin tana dafe bango saboda kanta dake juya mata. Tana shiga bedroom din ta kwanta nan da nan bacci ya dauketa. Har akayi sallar magriba bata fito ba kuma babu alamun tana ɗakin, shigowa ya yi bakinsa dauke da sallama yana kallonta da mamaki ganinta kwance tana bacci da alama ma batasan anyi sallah ba, tsaki ya yi sannaan ya ƙarasa gabanta ya taɓata ya ce "Aneeserh!! Aneeserh" Kasancewar batada nauyin bacci yasa tayi saurin buɗe idanunta nata murtsikesu harararta ya yi ya ce "Bakida hankali ko?, bakisan lokacin da zaki kwanta bacci ba ko?" Kalle-kalle ta shiga yi sai asannan tagane dare yayi ita kanta mamaki ta shiga yi domin baccin rana ba ɗabi'arta bace amma yanzu ta rasa meyasa take kwanciya kowane lokaci kuma bacci ya ɗauketa bai sake cewa komai ba ya juya ya fita ita kuma ta tashi ta shige banɗaki. Tana fitowa ta gabatar da sallar magriba tana jiran ayi isha'i, wata sabuwar yunwa taji ta ziyarceta dukda daman yau yini tayi bataci komai ba dan da safe bata ciba da rana kuma tayi amansa gashi kaf duniya babu abinda take sha'awar taci ji take komai ma ta tsaneshi kuma yunwar ta fara damunta. Kifa kanta tayi tsakanin cinyoyinta ta fashe da wani kuka na baƙin ciki kenan abincima bata isa ta ciba wannan wace irin ƙaddarace?, sallar isha'in da batayi ba kenan bacci ya sake awon gaba da ita.. *Aneeserh the begining of the manifestation* *Written by N^N* *Nanameera & Nainarh.* *ANEESERH.* *EP_Nineteenth.* BY: N^N🤙 "One Month! One Month kaɗai suka rage mana ko mu nemo waɗanan files mu damƙa musu, ko kuma muyi rashin nasara mu rasa gaba ɗaya Dukiyar da take shirin zama namu." Shiru tayi tana sauraren abin da take faɗa, har sai da taji ita ma tayi shirun alamar dai ta kammala sannan ta sauke ajiyar zuciya ta ce. "Nifa ban gane miki ba sam, yanzu kina nufin na saka rayuwata a wala-wala ta hanyar shiga Bedroom ɗin Aliyu domin ɗauko files.. an ya ke uwa ta gari ce kuwa, wato baki damu ba idan Aliyu ya kamani ke nan ko, wai shin ita Dukiyar nan na abin da suka yi alkawarin bamu?..... Kai a barshi a komai ya tafi normal na ɗauko files na damƙa miki ke kuma kin basu, ke nan wanene zai kasance dukiyar tana hannunsa ke nan kiyimin Bayani ko kuma na rusa Komai ta hanyar kin ɗaukowa sannan ki sani na bincika nasan inda suke kawai ɗaukowa ne bazan yi ba." Cike da tsaban takaici take sauraren abin da Ɗiyar nata take faɗa har sai ita ma takai a ya sannan a fusace ta ce. "Amma dai kin cika shashasha wacca batasan menene take yi ba wato ma kinsan inda suke tsayin kwanakin nan amma shi ne kikaƙi ɗaukowa ki kawo a kai musu mu sama kuɗaɗen nan, na gama fahimtar komai zuwa yanzu na fahimci ina ne kika dosa wato Hassada kikemin na abin da zan samu daga biliyoyin kuɗaɗen da zamu samu idan muka damƙa musu wannan files ɗin, an ya kuwa keɗin 'yata ce da na sani kece kuwa anya ba kin fara son General Aliyu ba ne?." Dafe kanta tayi ita fa batasan takura a rayuwarta komai da take yi sai tayi ra'a sam ta tsani naci wallahi. "Na fasa."! "Kin fasa me?."!! Ta tambaya da sauri tana Gyara riƙon da tayi ma wayar cike da faɗuwar gaba ta ci gaba da cewa. "Ke Humaira karfa muyi haka dake domin ƙarshen abin nan bazai ma kowa kyau ba muddun kika ce kin fasa dauko files ɗin nan...."! Katseta tayi da faɗi a fusace. "Yes haka nake nufi na fasa ɗaukowa kiyi abin da zakiyi akai sannan da kike magana akan ƙarshen abin bazai yi kyau baz kece zata kwaɓe ma domin ni ina cikin kariyar Aliyu da kalma ɗaya tak zan yi amfani koda ya gane gaskiya ya kasa aikata Komai a gareni Simple ina faɗa masa Ina ɗauke da cikin sa, ma kaɗai ya wadatar." A gigice irin na fusata da kalaman ɗiyar tata, ta miƙe tsaye har wayar tana ƙoƙarin faɗuwa daga hannunta bakinta har kumfa take fitar wa cike da Bala'i ta ce. "Ke Humaira amma yau na tabbatar da kin cika mara ƙwaƙwalwa ki saka Ido a yau ba sai gobe ba zan saka a shigo har cikin Gidan a gaban shi Aliyun yana ji yana gani za'a ɗauki waɗanan files a tahomin dasu har nan Austaraliya. Tabbas na lura kin fara manta Wacece ni..." "A'a ina ga kece dai kika manta Wacece Humaira da alama kin manta da basira ta da shawara ta aka yi amfani wurin kashe mai Gidan ki da muke pretending a matsayin shi ne mahaifina bacin cewa ni ɗin ɗiyar shege ce ke kanki da kika haifeni bakisan wanene ubana ba...."😳 Shiru tayi tana shafa kanta tare da furzar da iska daga bakinta idanunta a rumshe da alama abin yana damun zuciyarta sai dai tana ƙoƙarin dannewa. "Ina saka Ido domin ganin ta yadda wasan naki zaki ɓullo ina jiran zuwan Gaggan 'yan ta'adda na Duniya domin ɗaukar waɗannan files." Tana fitar da huci cikin ɓacin rai ita ma ta bata amsa da faɗin. "Ki saka Ido zan baki mamaki zan kuma nuna Miki na daɗe cikin Duniyar ta'addan ci ba'akan kashe mijina da ba shi ne farau ba na fara ta'addan ci ba kuma ba zai zama ƙarau ba." "Ina jira kuwa..." Tayi maganar tare da katse kiran ƙitt...... Banda huci babu abin da take fitarwa tana tuna kalaman mahaifiyar nata Zazzafar iska ta kuma fitarwa sannan ta zura wayar In her Trouser pocket, p-cap dake kanta ta Gyara ta sauko da shi ta rufe fuskarta sannan ta ɗauki face mask ta saka, zura hannayenta tayi cikin Aljihun rigar sanyi dake jikinta bayan ta saka wasu Boots na ma ta a ƙafafunta, fitowa tayi daga Bedroom ɗin, kamar yadda tayi tsammani babu kowa a palo dama kuma Aliyu ya fita shi da Safeena. Direct Master Room nasa na musamman da babu mai shiga kaf cikin su sai shi ɗaya ta shiga. Ta fara lalube laluben ta inda zata ɗauko su domin ta ɗan shiga confusing saboda bata gansu a wurin da ta san suke ba, lokaci guda garin neman files ɗin tayi kaca kaca da Room ɗin har takai ga ta cire mask dake fuskarta ba tare da ta sani ba. Tana ci gaba da neman ta wurin da suke. A hankali yakai hannu domin buɗe ƙofar da key. Ya yi mamaki gwarai jin ƙofar da ya yi a buɗe, silently ya fara takawa yana shiga Room ɗin yayin da yake ƙare masa kallo da mamaki ganin wasu muhimman files zube a ƙasa.... A firgice ta juya gaba ɗayanta jin alamun taku kuma coridor da take ake tunkarowa gadan gadan...... "Na shiga uku na Mommy ki taimakamin Aliyu ya kashe ni, na shiga uku na Ni Yasmeen Mommy ciki! Ciki Yarinyar can take da shi, wayyo ni Yasmeen zuciyata zata buga Mommy ji nake kamar na kashe ta Aliyu bai kyauta min." A firgice ta miƙe tsaye daga zaunen da take jin yadda ɗiyar nata take kuka tare da kiran ta shiga uku. "Ke Yasmeen wai menene yake faruwa, kiyimin Bayani yadda zan fahimta Please menene ya faru da Aliyu?." Cikin sheshsheƙar kuka hawaye kace kace Yasmeen ta ci gaba da faɗin. "Mommy Aliyu ne...." "Aliyu ya yi me??." Ta tambaye ta jin ta kasa Ƙarisawa, da kyar ta iya saita nutsuwar ta tana fyace hanci ta ce. "Ciki Aliyu ya yi ma wancan kucakar Yarinyar Mommy bazan iya jurewa ba domin dana bari wata ta haifawa Aliyu yaro bani ba, gwara na ƙona gidan nan gaba ɗaya mu mutu har da shi Aliyun domin hakan zai fi min da ganin Ranar da wata mace ba Ni ba zata haihu tare da Aliyu zama da kishiyoyi ma da ya ya na haƙura balle azo ga batun haihuwa." Ɗifff wutar jikinta ya dakata da jin abin da Yasmeen ke faɗi da kyar ta iya tambayar ta. "Yasmeen wai ciki na haihuwa kike nufin Aneeserh take da shi?....." Cikin baƙin ciki da sake jin wani kukan yana zuwa ma ta ta ce. "Eh Mommy Aliyu yaci amana ta ya yiwa Yarinyar cikinsa ciki...."😳 "Alhamdulillah. Madallah da faruwar haka daga ƙarshe dai Her Excellency da His Excel... Zasu sama jika nan kusa, gaskiya ya kamata a ce Ni ce zan fara sanar da su wannan kyakkyawar albishir." Ɗifff kuka da jan macina tare da Ruwan Bala'i da Yasmeen keyi ya dakata chakk sakamakon jin abin da mahaifiyar nata take faɗa. Cikin rashin yarda da abin ta buɗe baki da kyar ta iya cewa. "Mommy Hamdala ma kikeyi bayan faɗa miki wannan mummunar labari da nayi?..." "E, mana Hamdala nayi kuma zan ci gaba da yi sannan ba tare da ɓata lokaci ba zan sanar da His Excel wannan Kyakykywar Labarin..." "Ba zai yiwu ba. No! No way!! Bazan taɓa yarda ba, saina kashe ta tabbas yau ɗin nan sai na hallaka Aneeserh da ita da yaron dake cikin ta su mutu gaba ɗaya. Sai dai duk abin da zai biyo baya ya daɗe bai faru ba komai ta fanjama..." Yasmeen tayi maganar a fusace tare da cilli da wayar gefe guda tana fitar da huci gadan gadan ta nufa kofar fita daga Bedroom ɗin. "Hello! Hello!! Hello Yasmeen!!! Na roƙeki da ki dakata kada kiyi wannan mummunar aikin domin ƙarshen ba zai mana kyau ba daga mu iyayen ki har ke..." Shiru tayi sakamakon gane Yasmeen ta daɗe da katse kiran da tayi dafe kanta tayi cike da damuwa tare da tashin hankali cikin rashin abin yi... Daɓas taja da baya tare da zama irin na 'yan bori saman Bed ɗin tana tuna kalami da taji Yasmeen ke faɗa tuna maganar Yasmeen ɗin na ƙarshe da take ikirarin hallaka Aneeserh ne yasa ta miƙe tsaye cikin sauri ta ɗauko Wayarta ƙoƙarin kiran lambar Aliyu take ta faman yi sai dai kuma a kashe ta gwada ta gwada har ta gaji, cikin sauri ta fito daga Bedroom ɗin nata da sauri ta nufa hanyar Bedroom ɗin Aneeserh dake Up ɗin domin tanada tabbacin nane Yasmeen ta nufa ko'a mutu ko ai rai..... *ANEESERH.* *EP.20.* *END OF BOOK ONE.* *AFTER SOME HOUR'S.* Ji ya yi gaba ɗaya ji da ganinsa kamar ba daidai suke ba. Kara kallon Doctor dake kwararo masa bayani kawai yake yi cike da al'ajabi da rashin abin faɗa, da kyar ya iya saita kalaman bakinsa ta hanyar faɗin. "Pregnancy and Aneeserh ita ce ke ɗauke da shi tsawon three Months ba tare da na sani ba ikon Allah ke nan that's very amazing, Masha Allah tabbas godiya ta tabbata ga Ubangiji maɗaukakin sarki da ya bani ikon ganin wannan kyakkyawar Ranar a Rayuwata.." Maganar ya yi tare da miƙe wa tsaye daga inda yake, saitawa ya yi sannan ya yi sujadar shukur yana daɗa miƙa godiya ga Ubangiji. Da kallo Doctor tare da Khaleepa suka bisa Yayin da Khaleepa yake baki a sake cike da ruɗani da kuma sarkakiya da wannan lamarin ya je fa sa. *Few minutes later.* Fitowarsu ke nan daga harabar hospital ɗin Khaleepa ya kallesa da kyau yana nazari tare da imagine chakwakiyar dake gaban su. "Aliyu wai da gaske ne Aneeserh Yarinyar da kake raino ce da juna biyu tsawon three Months wannan lamarin fa akwai ruɗani yanzu baka tunanin irin hukuncin da His Excel... Zai yanke idan ya sama wannan Labarin?." Dakatawa da tafiyar ya yi, yana shafa sumar kansa ya jingina da motar su bayan sun suka ƙari sa wurin da take a fa ke. "Tabbas ina tunanin abin da zai biyo baya idan Daddy ya sama labari sai dai bani da zaɓi ne." Jinjina kai Khaleepa ya yi da jin amsar da ya basa. Yana shirin ƙara furta wani wani abu wayar G.A tayi ƙarar shigowar kira. Picking ya yi ba tare da ya ce komai ba. Yayin da Khaleepa ya zuba masa ido. Annashuwar dake ɗauke saman fuskar sa ne ta ɗauke ɗifff. Baya ya yi kamar wanda juwa ya ɗiba yana mai kallon wayar hannun nasa tare da nazarin kalaman da Doctor yake faɗa masa sam ya rasa a wani matakin zai ajiye su. Da sauri Khaleepa ya ƙari sa wurin sa tare da riƙo sa yana tambayar sa abin da ke faruwa. Kallon Khaleepa yake yi kamar yau ce Ranar da ya fara Ganin sa. "Wai Aliyu menene yake faruwa ne, me aka faɗa maka ne da ya saka ka shiga wannan yanayin lokaci guda?." Khaleepa ya tambaya yana mai fata ba abin da yake zargi ne ya faru ba. "Khaleepa, Safeena ce.. Safeena..."! "E, Safeena menene ya faru da ita ɗin menene Doctor yace akan lamarin ta?." Cikin fitar hayyaci ya kalla Khaleepa kamar yadda shima ɗin shi ne yake kalla. "Safeena ta rasu sanadin daɓa ma ta wuƙa da Yasmeen tayi.... Na rantse ba zan bar Yasmeen ba tun da har ta kashe rai nima sai na kasheta kowa ya huta ai kishi ba hauka ba ne." Ya yi maganar a fusace tare da nufar mota domin buɗewa sai dai dakakkiyar murya mai cike da amo ce da ta daki dodon kunnen sa cikin tsawa yasa shi dakatawa chakk.... "Ina ne zakaje kuma menene abin da zakayi?." Chak ya dakata ba tare da ya iya buɗe motar Ba, bare ya shiga yayin da salon bugun zuciyar sa ya ƙaru fiye da baya. A firgice Khaleepa ya juya domin ganin wanda ya yi maganar da kuma son tabbatar da zargin sa akan Muryar da yake ji. "His Excellency Oh Allah komai ya caɓe." Ya yi maganar cike da tashin hankali yana kallon yadda His Excel... Yake bin Aliyu da wani mugun kallo na ka ci amana. "Ta ina?." Shiru Aliyu ya yi ba tare da ya ce komai ba kuma bai cire hannunsa saman murfin motar Ba. A fusace His Excel.. ya kuma daka masa tsawa da faɗin.. "Nace ta ina ne ko baka ji nane?." Da kyar ya iya harhaɗo kalaman bakisan ta hanyar faɗin. "Please Daddy zan yi maka Bayani Please.."! "Au ba zaka faɗa min tana ina ba ke nan?." Ganin lamarin yana neman ya yi tsauri ne yasa Khaleepa ya yi saurin tarar Daddy daga ƙoƙarin ƙari sawa wurin Aliyu da yake yi gadan gadan. "Ayya. His Excellency kayi haƙuri Aneeserh tana lafiya tana ciki ta sama Bacci ne And ita kuma Safeena Allah Ubangiji da ya halicce ta kuma yafimu son ta ya karɓa abin sa sanadin 'yar hatsaniya da ta shiga tsakanin ta da Yasmeen. Safeena tana ƙoƙarin kare Aneeserh shi ne cikin rashin sani Yasmeen ta daɓawa Safeena ɗin wuƙa a ciki yanzu haka ma tana Headquarter. Please Daddy ina mai haƙuri a duka waɗan nan abubuwan babu hannun Aliyu ko laifinsa..." Shiru His Excellency ya yi da alama ba ƙaramin taɓasa maganganun Khaleepa suka yi ba, lokaci guda ya ɗimauce tare da shiga tashin hankali da jin wannan mummunar labarin ke nan dai da gasken Iyalin Yaron sa sun tarwatse. Yayin da cikin sauri ko tsayawa kuma sauraren abin da Khaleepa zai kuma faɗa Hajiya A'isha batayi ba, tun lokacin da ya faɗa Address na Ward da Aneeserh take ta nufa ciki Saima da suka taho tare tana mara ma ta Baya... *END OF BOOK ONE.* BY: N^N🤙 _Am nace ba Innocent Girl Reader's daga nan fa Book 1 da yake free ya ƙare. Zamu shiga Book 2 is Paid book kamar yadda aka faɗa da farko so duk masu buƙatar ci gaba da karantawa sai ku biya kuɗin 500₦ ne kacal karku bari a baku labari fa kuma dai kun san ya ya tafiyar take Aneeserh 🔥💃💖👑_ ______ *Account Name: Hauwa lawan.* *Account Number: 9086030007.* *Bank Name: Opay digital service.* *Sannan sai ki turo evidence of payment ta waɗan nan Countacts_08081129487 or 0908 603 0007 via WhatsApp Only* ___________________✍️🔥🔥🔥🔥🔥🔥🔥🔥🔥🔥