(1)Ahaji bishir ya kosa ya isa gidansa don kai wannan albishir.haka nan MIMI ta kosa matuka dad din nata ya dawo don ta sanar da shi labarin masoyinta khalil.momy nafisa kuwa tana cikin damuwa,tana ta tufka da warwara a kan yadda zata hada fitina tsakanin MIMI da mahaifinta. A haka alhajin ya iso gidan,cikin doki.tun daga shigowarsa falon yake zuga kiran nafisa!nafisa ta fito cikin sauri tana cewa, "Alhaji ga ni.lafiya kake ta kira na?"ya ce,"Lafiya lau. sai alheri." Ta amshi jakar hannusa da hularsa da malum-malum. "Mu je ciki ki ji albishir!"Gabanta ya fadi. wani sabon kasuwancin ne? ya ce,"wannan duk ya wuce nan.sai da suka zauna,sannan ya ce,"Abbas, ashe MIMI yake so?"Gaban momy ya fadi. ya ci gaba da cewa, "gaskiya na yi murna sosai.burina zai cika."ta yi dan yake,ta ce,gaskiya kam, da abin zai yiwu,zaa yi murna."Ya ce,"me zai hana shi yiwuwa?daina fadin haka. Nafisa ta ce,dazun take sanar da ni cewa saurayinta zai zo daga kaduna gaishe mu. ya zaro ido yana kallon ta.ya ce, wane ne shi?wannan ba gaskiya ba ne.lnda MIMI tana da wani saurayi,nine mutum na farko da zan fara sani,domin kin san babu wani abu da take boye min.ba ta da aboki ko kawar da ta fi ni. Nafisa ta ce,haka ne, amma jiya tayi min zancen. da alamu kuma tana son sa sosai.ya daga hannun, alamun dakatarwa.sannan ya sa kai ya fita daga dakin.kai tsaye saman MIMI ya nufa.tana kwance a kan kujerarta,catin suke yi da khalil,tana ba shi labarin halin da take cikin na damuwa.shi ma duk hankalinsa ya tashi.a sama ta ji muryar dad yana cewa, uwata tashi zaune da sauri!tana fadin dad ka dawo ne?ban sani ba,ai da na sauko. Ya zauna kusa da ita.yau ina cikin farin ciki ne MIMI.burina zai cika.ya kama hannunta,kin san na dade ina addu'ar ALLAH ya kawo miki mijin da zai kula da ke ko?gabanta ya fadi,ta ce,"eh dad."ya ce,"to ga abbas dan gidan minista. mahaifinsa yake sanar da ni tsananin son da abbas din ke miki..... [01/10 9:45 pm] Abdul: STEP (2)Wannan lamarin ya zo a daidai da burina na hada surukunta da minista. zai kawo ci gaban kasuwancina,musamman ta fannin man fetur." Ta ce,"Dad akwai matsala.shi abbas din ai mun gama magana da shi."Ya ce,"Wace irin matsala kuma?"Ta ce,"Dad,ya zo ya ce yana so na.na fada masa ina da wanda nake so.lokaci mai tsawo muna tare da shi. dad ya kama in bar shi in koma wa abbas?"kallon ta kawai alhaji ke yi.bai fara jin haushinta ba don yana sa ran zai shawo kanta.ya ce,"Za ki iya barin sa,tunda bai nemi aurenki ba.sannan ban zaci zaki boye min komai ba.wai kina tare da saurayi tsawon lokaci ban sani ba.to ina son ki ajiye batun wani saurayi.ki natsu kin ji mamana?" Ta yi shiru,ranta bace, lndanunta sun soma kawo kwalla.ya daga fuskarta, "mene ne abin kuka?murna za ki yi.ALLAH yayi miki zabi na gari."Ta ce,cikin kuka,"Dad ba na son sa ne. ai ni khalil nake so.zai zo yau ka gan shi.lrin mijin da zuciyata take so kenan." Ya daga murya,"MIMI zo lokacin da zan ce ina son abu,ke kuma ba kya so?mun fara jayayya kenan?"Yanzu kam kuka sosai take yi"Dad ba haka bane,amma bai dace a tsananta min in so shi ba.kar ka damu zan kira abbas din in sake tuna masa cewa ba na son sa." Saukar mari ta ji fau! a fuskarta.ya ce,"ba ki isa ba!" A fusace ya nufi fita.ta rike kumatu tana kuka sosai.momy da ke labe ta sauka da gudu,jin alamun zai taho.cikin dakinta ta shiga.lallai tana cikin farin ciki.bari ta je ta kara wa wutar kananzir. Ta fito ta nufi dakin alhajin,tamkar bata san komai ba.ta yi sallama, alhajin ya amsa a ciki,yana ta zirga-zirga a cikin dakin nasa.cikin alaye ta nufe shi,"Lafiya alhaji?Me ya faru?"Ya kalle ta,"MIMI wai take nema ta tona min asiri.bakina da na uban dan nan na ce,na basu yarinyar nan,amma in zo mata da batun,ta ce,bata san zancen ba?"Nafisa ta zaro ido,tare da dafa kirji,"in ji MIMIN?"Momy nafisa ta ce,"aa wasa take yi,kana ji ko alhaji?kiyayyar mace bata wani tasiri,sai dai in ba a yi auren ba. [01/10 9:45 pm] Abdul: STEP (3)Ku tsai da rana. kafin ta kammala makaranta ku daura musu aure.bikin kwa yi in ta gama karatun."Ya ce,"Kina ganin hakan zai yiwu?"ta ce, sosai kuwa.ldan ta san cewa da akwai igiyar wani a kanta,dole ta rabu da kowa.ya ce,"Ke ma kin kawo shawara.amma zan so ki je ki dan kara bata shawara. ko don gatan da na nuna mata,ya kamata ta yi min biyayya."momy ta ce bari in je.amma kafin in tafi, za a hada maka ruwan wankan ne,ko abincin za ka fara ci?"Ya ce bana bukatar ko daya.ya zauna bakin gado,"bari in kira sauda,ko zan samu natsuwa."ranta ya dan sosu,amma ta danne. bari to in je gurin MIMI din.ka ce da ita ina gai da ta." Kuka sosai ta samu MIMI tana yi.don haka ta shiga lallashinta da cewa ta yi shiru,su yi magana.ta zo ne don sama mata mafita. bayan MIMI ta share hawayenta ne,momy nafisa ta ce,ki ce masa ya turo iyayensa,shi khalil din. kila in alhaji ya ga magabatansa sun zo ya hakura. cikin disasshiyar murya ta ce,momy bana fada miki ba karatu yake yi?lyayensa,yanzu baza su saurare shi da batun aure ba.da ma mun bar shi a kan sai mun gama karatu ne.momy nafisa ta yi shiru tana tunanin mafita.MIMI ta kama mata hannun,don ALLAH momy ki fada min yaya zan yi? Ta rungumo ta,kwantar da hankalin ki MIMI.wannan karamin abu ne,kuma kin san dad dinki yana son duk abin da kike so.shawarar da zan baki ita ce,ki tsaya a kan raayinki na cewa khalil ki ke so.zai hakura. amma in kika bi raayinsa,ba za ki ji dadin zaman auren wanda ba ki so ba. MIMI ta ce,to ni bana son dad ya ce ban ji maganarsa ba.ta ce,kar ki damu da haka.yanzun nan daga dakinsa nake.ya ce in ya ga kin dage zai hakura. MIMI ta sauke ajiyar zuciya, sannan ta ce, shi kenan zan tsaya a kan raayina.momy nafisa ta ce,duk runtsi ki ce baki son abbas.MIMI ta ce, "shi kenan." Alhaji kam, hajiya sauda ya kira yana labarta mata komai daya faru,tun daga burinsa har zuwa yanzu.ya ce,ina son ki kira ta ki yi mata fada,ta bar batun wani yaro....... [01/10 9:45 pm] Abdul: STEP (4)Ta tsaya ga wanda ni na zaba mata. hajiya sauda ta ce,alhaji ba zan shiga zancenku ba,kai da lelenka.abu daya kawai nake ganin zan iya.shi ne zan kira ta in bata shawara. ya ce ban gane ba zaki shiga zancenmu ba. ta ce alhaji ke nan.yanzu ne da ta kwabe muku ka san da ni?lna uwarta mai son ta wadda aka canza mata da ni,saboda ni ina takura mata ta yi abin da ya kamata?shawara kawai zan ba ta ta yi maka biyayya,amma ba wai in takura mata ba.ldan ta ki yarda,sai ka yi mata abin da take so,kamar yadda ka sabar mata tun tana karama.shiru ya yi,ya kasa magana.sai kuma ya kashe wayar. momy nafisa ta same shi cikin damuwa, yana ta tattauna maganganun hajiya sauda a cikin zuciyarsa.ta zauna kusa da shi.alhaji nayi maga da MIMI.ya kalle ta cikin sauri,ta amince? "MIMI ta ki sam alhaji.kuka take ta yi.da na tsananta mata da lallashi,da nuna mata cewa ta yi maka biyayya, sai ta ce min don na ga bani na haife ta ba.ln dani na haife ta ba zan so a yi mata auren dole ba.ya ce haka ta fada?kenan tana da daurin gindin mahaifiyar tata?domin da na kira ta a kan ta yi mata fada,ce min ta yi ita shawara zata iya ba ta, ba fada ba. Momy nafisa,cikin jin dadi ta ce,amma hajiya sauda ba ta kyauta ma kanta ba.ta yaya za ta hana 'yarka ta yi maka biyayya?"ya ce,shi ne abin mamakin amma zan gwada musu su duka cewa ba su isa ba."ta ce, "abin da ya kamata kenan da ma ku zauna kai da minista ku sa lokacin auren sati uku ko hudu,ku daura kawai,ka wuce gurin kamar yadda na fada maka.ya ce, gobe za mu tattauna da shi.amma MIMI ba ta isa ta ja min asara ba.ta lelo ta koma min kenan. lta kuwa hajiya sauda, wadda ba ta san komai ba, sai da alhaji ya fada mata, amma ita ma yanzun laifin ya shafe ta,ta kira MIMI. can kasa-kasa ta ji muryar MIMI ta amsa sallamar hajiyar.hajiya ta ce"ba ki da lafiya ne?"MIMI ta soma kuka,dad ne wai sai na auri dan minista,kuma ni bana son sa."Hajiya sauda ta ce,ni dai in na isa in fada miki ki ji,to ki bi zancen mahaifinki, [01/10 9:45 pm] Abdul: STEP (5)Ki auri wanda yake so.yanzu ke wannan ba abin kunyarki bane,saura 'yan uwanki su ji kina takaddama da ubanku? mutumin da ya nuna miki gata,ya yi miki duk abin da ki ke so,ya nesanta ki da duk wani abu da zai bata miki rai.MIMI na zaci ko wuta babanki ya hura ya ce,ki shiga,za ki shiga ba tare da kin tsaya dogon nazari ba.ashe ba kya yi masa son da yake yi miki. ki yi tunani sosai,kuma ki yi abin da ya dace.shawarata kenan."Ba tare da ta ji uzurin MIMIN ba ta kashe wayar. Alhaji lawal ya kawo sadakin zainabu dubu dari kamar yadda lnnarta ta fada musu.kuma an kawo akwatuna,an kuma sa ranar bikin sati biyu.zainabu na ta kuka kuma har gidan su mahmood ta je ta fada masa,ta kuma bukaci ya bata wayar don ALLAH,ta kira lsmail.ya ce mata ai kawai taje tabi maganar iyayenta.lsmail ba abinda zai iya tunda an rigaya an yi mata miji.shi ba ya so ma lsmail din yaji zance ma haka ta tafi ba tare da ta cika burinta ba.lsmail kuma duk kwanakin sai yayi ta fama da muggan mafarkai marasa kai.ln ya kira mahmud,sai ya ce masa kowa lafiya.tun kwanaki da yayi waya da zainabu, mahmud bai sake hada su ba.ln ya ce masa don ALLAH ya je gun ta za su yi waya,sai ya ce masa ba lokaci.daga karshe har ya ji haushi,ya ce,na daina cewa ka kai mata wayarka.da na dawo zan sai mata in huta. mahmud ya ce,ka taimake ni,don ba a son raina nake zuwa ba.lsmail ya kashe wayarsa cikin takaici. kusan kwanaki uku,in lsmail ya shiga gidan don koyar da MIMI,har lokaci ya cika bata fitowa,don haka sai ya kuduri niyyar yau in alhaji ya dawo zai sanar da shi. haka kuwa bayan sun yi sallar isha.sai ya sanar da alhajin.alhaji ya ce zai yi mata magana.ln ma bata fito ba kar ka damu.ka ci gaba da koyar da kannenta. lsmail ya ce shi ke nan.alhaji ya ce in ta fito kuma,to don ALLAH ka dinga yi mata nasiha.ka ji ko?lsmail ya ce,insha ALLAH. momy nafisa ita da naima sun kulle kansu a dakin momy tana sanar da na'imar yaddaa tsarin da ta yi yake tafiya yadda take so. [01/10 9:45 pm] Abdul: STEP (6)Ta ce an kusa zuwa gurin kar ki damu. na'ima yanzu fa har hajiya sauda,alhaji haushin ta yake ji.ya zaci ita ce ke zuga MIMI.shekaran jiya MIMIN ke fada min wai hajiyar saudar ta ce lallai ta bi zabin alhaji.na ce mata MIMI kin san dai sai dai mahaifiyarki ta gwada min ta haife ki,amma ba ta kai ni son ki ba ko?MIMI ta ce eh.na ce to ki yi duk abin da na ce,lta kin ga bata yi boko ba,ba lallai ta san 'yancin kanta ba,bare naki. MIMI ta ce haka ne.nan da nan na zuge ta.sai da na goge dan tunanin da ta soma yi na danganar da uwar ta sa ta yi."Na'ima ta ce momy ai na ji dadi.yanzu dad ya fi kula mu a kanta.momi ta ce shegiya ba,ni ma na dan ji tsai,a yi nan dad dina,a yi can dad dina,ta kwaikwayi muryar MIMIN,suka kwashe da dariya.na'ima ta ce,to ba ki ganin dad zai iya daura musu auren,ni kuma fa? tunda kin ce masa kawai su sa rana.momy ta ce,ina so ne a yi mai yiwuwa ne a gama.shi ya sa nake son a sa rana.ke dai duk abin da na ce ki yi,to ki yi kokari ki aikata.na'ima ta ce,"an gama." Alhaji akilu da alhaji bishir suna zaune cikin ofishin alhaji bishir din,su zabi haduwa a nan ne don su tattauna batun auren yaransu.alhaji bishir ya ce,ka san ja'irar yarinyar nan wai ina fada mata sai take neman yi min gardama."haba dai?!"in ji alhaji akilu.alhaji bishir ya ce,"ALLAH kuwa.amma na san duk iyayi ne na yaran nan."alhaji akilu ya ce,ka san mata ba mamaki tana zaton mu ne muka hada su,ba shi ne ya gan ta ya ce yana so ba.ka bar ta kawai.da zaran an yi kiyayyar mace bata dorewa.sai dai in ba ta samu kula ba. Cikin jin dadi,alhaji bishir ya ce na gode daka fahimci hakan.yanzu wane lokaci kake ganin za musa? alhaji akilu ya ce kar mu ja abin;mu yi mu wuce gurin. ni ma haja na gani,in ji alhaji bishir.mafi sauki mu saka sati uku ko hudu.alhaji akilu ya ce,mu bar shi hudun.don naji mata suna cewa za a fita dubai ko chaina hado kayan auren.shi kuma angon ya soma gyaran gidan nan nawa na asokoro. [01/10 9:45 pm] Abdul: STEP (7)Alhaji bishir ya ce, ka fasa sai da shi ke nan? ya ce,ba dole in fasa ba, tunda abbas ya dage gidan yake so?gidan yayi masa girma,amma shi wai tsarin gidan yayi masa.alhaji bishir ya ce,to a bar masa. ALLAH ya sa hakan ya fi alheri.alhaji akilu ya ce. amina.zan turo waliyyan nasa,kanina da alhaji sa'idu abokina za su zo.alhaji bishir ya ce,babu matsala. ni ma zan yi wa nawa kanin da kuma alhaji kabiru magana.yaushe ne za su zo?alhaji akilu ya ce cikin satin nan.za dai muyi waya. bayan sun gama tsarinsu ne suka koma batun kasuwancinsu. Abu kamar wasa,zance ya soma nuna,don an kawo sadaki.kuma momy nafisa da wata kawarta sun shaki kudi gurin alhaji sun nufi dubai siyayyar kayan kicin, ta zage kuma tana ta zabar masu kyau da tsada,domin tana fatan su rikide su zama na na'ima. Tafiyarsu da kwana biyu,sai ga khalil da mahaifiyarsa har gidan su MIMI.yadda abin ya faru kuwa,hajiya amina ta ga danta ya shiga damuwa da tashin hankali ta rasa gane kansa,sai ta tsare shi a daki don ya fada mata damuwarsa.ta yi ta lallashin sa da nuna masa cewa,ita ce ta fi dacewa da ta san matsalasa,kuma ta magance masa,in har za ta iya.jin haka ya sa shi koro mata komai.ba ta yi kasa a guiwa ba ta sanar da mahaifansa wanda hankalinsa yake kan siyasa. nunawa yayi wannan ba damuwarsa ba ce damuwarsa kawai khalil ya yi karatu ba tare da zabin da ya wuce bai wa dan nata hakuri,gami da shawarar tsayawa kan karatunsa.amma cikin kwanakin sai ga yaro kwance warwas,ba ci ba sha,duk ya fita hayyacinsa. ba arziki ta taso shi zuwa abujan don rokon a bar masoyan su ci gaba da soyayyarsu har zuwa lokacin da za su hattama karatunsu,sai a daura musu aure. na'ima da ke falo ita ce ta amshi bakuncin nasu. suka gaisa.ta ce,kun zo gurin momy ce?ga shi ba ta nan.hajiya amina ta ce, mahaifinku fa?na'ima ta ce, yanzun nan ya fita.khalil ya ce MIMI fa?na'ima ta ce tana samanta;in kira ta ne? hajiya amina ta ce,eh.kudundune take cikin bargo.yau tun safe zazzabi ke jikinta. [01/10 9:45 pm] Abdul: STEP (8)Na'ima ta yi sallama,ta shiga ta sami MIMI.baki aka yi.sun ce in kira ki.ta ce daga ina?ki ce su hawo,ba zan iya sauka ba.na'ima ta raka su har falon MIMI,ta ce,sis ga su nan.MIMI ta yunkura za ta tashi,ta kasa.ta ce,tambaye su na'ima,daga ina?ba zan iya tashi ba.na'ima ta tambaye su.sai ko hajiya amina ta mike mu je kawai,in yi mata bayani. Ta zauna bakin gado,ta kamo hannun MIMI,yata ni ce mahaifiyar khalil.da sauri, MIMI ta tashi zaune.sannu da zuwa momy.wa ya nuna miki gidan nan?ta ce, ga shi nan a falo,tare muke. da sauri MIMI ta sauko daga gadon don tabbatar wa idanunta khalil dinta ne kuwa?sabbin hawaye suka soma zubo mata.ta je ta zauna a kujerar da ke kusa da shi.cikin damuwa ya ce, dubi yadda kika rame,don ALLAH MIMI ki yi hakuri.ga momy na nan na kawo ta za ta yi magana da momy dinku ko dad. MIMI cikin kuka ta ce,ba zai saurare ku ba.don sun yi nisa da shirin aura min abbas.hajiya amina ta dafa bayan MIMI.bayan ta zauna a hannun kujerar da take,sai ta ce,kar ki damu 'yata.yaya za a yi in gan shi?MIMI ta ce bari in gwada kiran sa ko zai daga,don yanzu bai damu da daga kirana ba, Sai a kira na biyu,sannan ya daga me ya faru MIMI? abin da ya soma tambayar ta ke nan,bayan ya daga wayar.ta soma kame-kame am,am da ma wannan ne, baki ne suke son ganin ka. Hajiya amina ta amshi wayar,sannu da kokari alhaji.ya ce,yawwa,wace ce?ta ce,sunana hajiya amina daga kaduna.kuma ni ce mahaifiyar khalil saurayi MIMI,wanda take so. Haushi ya kama alhaji bishir,amma sai ya danne, ya ce,to lafiya?ta ce,na zo ne ina son ganin ka don mu yi magana a kan yaran nan. ya ce,babu bukatar wata magana domin na riga na ba da ta.yanzun haka nan da sati uku ne bikin.don ALLAH ki bawa dan naki hakuri.ta ce,amma alhaji kana sane cewa ba ta so ko?ya ce,ba damuwata ba ne,kuma ke ma ba damuwarki ba ce.ln kin zo nemawa danki aure ne, tuni ya kamata ki yi haka ba yanzu ba.yanzu kam kun makara.na gode.sai an jima.ya kashe wayar. [01/10 9:45 pm] Abdul: STEP (9)Ta yi shiru,ta rasa me zata ce wa yaran,ga shi sun tsare ta da idanu.ta ce,ku hakura kawai.tashi khalil mu tafi.MIMI ki bi zabin iyayenki.sai kawai ta ga sun soma kuka su duka biyu.MIMI ta riko hannunta, don ALLAH momy ku gudu da ni.ba zan iya rayuwa babu khalil ba.zan mutu,don ALLAH.momy ta ce,ba zai yiwu ba 'yar nan rufa min asiri. shi ma ya ce,momy don ALLAH mu tafi da ita. uwar ta kalle shi,lallai ba ka da hankali.ta dafa kafadar MIMI,ki yi hakuri 'yata.mu yi addua ALLAH yayi mana zabi na gari.har kasa MIMI ta biyo su da kuka,har gurin motarsu.maaikatan gidan wadanda ba su san me yake faruwa ba,sai kallon MIMI suke yi.sun fi zaton mutuwa ce aka yi gagaruma.fatansu allah ya sa ba maigidan ba ne domin gudun tarwatsewar aikinsu. Na'ima ce ta kama ta suka nufi cikin falon kasa.ta zauna ta ci gaba da kuka, na'ima tana bata hakuri. daidai lokacin lsmail ya shigo falon,don lokacin karatun sa ne da yara.ganin MIMI cikin halin da take ciki, har zai koma sai ya tambayi na'ima,lafiya dai ko?banza ta yi da shi cikin salon wulakanci.ya dan yi jim,can ya ce,baiwar ALLAH kuka bai taba zama mafita ga bawan da musiba ta auka masa ba. ldan kina da bukata zan ba ki maganin damuwa da yaye bakin ciki.kila ma ki cimma burinki.duk ba su tanka shi ba har ya fice. MIMI ta fi saa guda tana kuka har kanta ya soma ciwo.na'ima ta yi lallashi ta gaji,don haka ta kira momy nafisa ta fada mata abin da yake faruwa.momy ta yi ta kiran MIMI bata dauka ba,da yake tana kasa, wayar kuma na sama.sai da ta soma jin jiri.ta mike ta nufi saman.ta jima a kwance kafin ta ji rurinta. cikin sauri ta dauka. tunaninta khalil ne,ashe momy ce.ta dauka, muryarta can kasa,ta ce, momy'momy ta ce,na'ima ta fada min komai.lna so ki kwantar da hankalinki.na fada miki baza ki auri abbas ba.ta soma kuka,kin yi min alkawari momy?ta ce,ko rantsuwa nayi miki,ba zan yi kaffara ba.don haka nayi miki alkawari.lna dai sake fada miki,ki tsaya a kan raayinki.ta ce,shi ke nan momy. [01/10 9:45 pm] Abdul: STEP (10)MIMI tana tsaye a windonta na falo,wanda yake kallon boys quaters da kuma lambun gidan. fararen tantabarunta take kallo masu yawa,wadanda dad ya sai mata tun shekaru da dama da ta ce tana so.hamsin ya sai mata, amma yanzu sun fi guda dubu,duk da cin su da suke yi.ta tuna ta yi kwanki rabonta da zuba musu abincinsu.sai masu aiki ke ba su.duk da kayan barci ke jikin ta,haka ta sauka. na'ima tana cewa ina zaki? ta ce,zan duba tantabaruna ne.tunda aka soma matsalolin nan ban je gurin su ba.ta kicin ta bi zuwa barandar baya,inda nan abincinsu yake.ta diba ta watsa musu.duk da ba safiya bace,yanzun lokacin da ta saba watsa musu,sai ta ga suna nan da yawa. har ta yi mamakin hakan, domin da rana suna fita. Kamar an ce waiga,sai ta hango malam lsmail yana shanya a gefensu.da alama ya wanke kananan kayansa na ciki ne.take zantukansa suka fado mata. in kina bukata zan baki maganin yaye damuwa da bakin ciki.kila ma har ki cimma burinki.lna ya san tana da wani buri? kodayake shi malami ne, kuma ta ji ana fadin malamai suna yin magani.ta tuna mina kawarta ta taba ba ta labarin cewa kishiyar mamansu ta yi wa babansu magani,sai abin da ta ce.a fili ta ce,zan nemi taimakon malamin nan, amma ta yaya zan yi masa magana? Da wannan tunanin ta hau samanta.ta jima kafin ta yanke shawarar kiran na'ima.bayan ta daga ne,ta ce,ina son ki je ki amso min lambar malam din nan mai koya mana karatu.na'ima ta dan yatsina,ba ki san ba na son zuwa boys quaters ba sam.bari in tura polina.MIMI ta ce,aa ki sa malam hamisu kawai ya amso miki ki kawo min.ta ce,ok. Na'ima ta amshi wayar MIMI da ke hannunta ta saka mata lambar lsmail,ta yi mata saving da malam.ta mika mata.MIMI ta ce,aje kawai.har na'ima za ta fita, sai kuma ta dawo.sis wai me zaki yi da lambarsa? MIMI ta kalle ta,ki je kawai. kar ki damu sai kin san dalili.tun fitar na'ima,MIMI take tufka da warwara a kan kiran malam lsmail.ln ta kira shi me zata ce masa?kuma yaya ma zai dauki zancen nata. [01/10 9:45 pm] Abdul: STEP (11)Kuma yaya ma zai dauki zancen nata? wanan tunanin shi ne ya dauke ta har zuwa karfe takwas din dare,wanda har lokacin ba ta tsai da matsaya ba. Sallamar mahaifinta ne ya zaburar da ita cewa an bude kofar.ta waiwayo,ta dube shi.kwanaki kusan hudu ba ta sa shi a ido ba, domin yana fushi da ita. cikin in-ina ta amsa sallamar, ta dinga kallon sa cike da kewa.ya zauna kusa da ita.cikin sigar lallashi ya ce,uwata ta kaina.ta dube shi,dad na yi kewarka.don ALLAH ka yi hakuri a kan abin da na yi. ya ce,kar ki damu.kina ji na MIMI,ki tashi ki je ga abbas can ya zo don ku tsara irin shagalin bikin da kuke so lokacin bikinku,ku zabi kasashen da za ku tafi shakatawa. MIMI ta yi shiru tana tunani,kamar ta amince,sai kuma ta tuno zance momy nafisa da ta ce duk runtsi ta tsaya a kan raayinta.don haka sai ta ce,dad don ALLAH ka taimake ni. wallahi dad ba na son shi. ya ce,"what?! lna cewa mun gama wannan maganar.ya rike kansa yana tunanin yadda zai bullo mata.can ya saki ya dube ta cikin lalama.MIMI ki yi nazari da kyau.tunda kika fito cikin mahaifiyarki nake dawainiya da ke.na fifita ki cikin 'ya'yana.na yi miki dukkan gata.MIMI zan tambaye ki,na taba neman wani abu gurinki? ta ce,dad,ni ba ni da komai da za ka nema.ni ma da kai nake takama. ya ce,to yau ina neman alfarmarki,ki taimake ni ki min biyayya,ki auri abbas.ta ga kamar zai sauko ya runsuna mata.sai ta yi sauri ta ce,na amince dad.ta soma kuka wi-wi.ya rungume ta.na gode 'yata. ni da ma na san irin son da kike mini ba za ki ba ni kunya ba.daina kuka.ki share hawayenki.ki je ku yi magana.ln kun gama,ni ma ina son mu yi magana da ke.za mu je store din wani abokina ki zabi kalolin gadon da kike so.gidanki dakunan barci shida ne; gaba dayansu zan zuba miki gadaje na alfarma 'yan dubai da chaina da lndiya. zan nuna miki wata mota da na yiwo miki oda.ba ta karaso ba.amma hotonta yana cikin laptop dina don ki yi yawon amarci in kun dawo.... [01/10 9:45 pm] Abdul: STEP (12)Shakatawa tashi maza ki je kin ji MIMI. MIMI ta mike cikin kasala ta nufi dakinta.mayafi kawai ta dauko,suka jera da mahaifinta har kofar falon baki ya raka ta.sai da ta shiga sannan ya dawo. Ta zauna kujeri biyu tsakaninta da abbas.ya mike ya dawo wadda suke daf da juna ya zauna. sabon kuka ta soma.abbas ya ce,haba MIMI,wai ta ina ALLAH ya rage ni ne da kike ta ki na har haka?ta dago ta dube shi,"Ya rage ka ta soyayyata.abbas don ALLAH ka taimaka min ka rabu da ni.khalil kadai nake so.ya tausasa murya,MIMI ki ba ni dama ni ma in nuna miki kalar tawa soyayyar. na yi miki alkawarin zan koya miki sona har sai kin manta cewa an taba halittar wani da namiji a doran duniya in ba ni ba. Ta ci gaba da kukanta.ya ci gaba da fadin,gobe karfe goma zan zo mu fita.ki fada ma kawarki amina, zan zo da abokaina don mu duba guraren da za mu yi shagalinmu.me da me kike son mu yi?ni dai ina son dinner. Ta ja tsaki,don ALLAH ka bar ni,ka shiga tsakani na da mahaifina.ya ce,kin kasa yi masa biyayya ne MIMI?me zai sa ba zaki yi wa mahaifinki sakayyar son da yayi miki ba?ta mike,zan je in kwanta,kaina ciwo yake.ya ce,ba ki ba ni amsa ba.MIMI ta ce,ba ni da amsar da zan ba ka.amma ka sani in ka matsa cewa sai ka aure ni,nadama da dana sani sune karshen lamarin. shi ma ya mike, ban damu da su ba MIMI, saboda ban taba sanin su ba.kada ki manta gobe karfe goma za mu zo. fatana za mu same ki da kawarki.suka fito a jere.ta ce,ban taba ganin mutum mai son kai irin ka ba.ya ce, ban taba ganin mara tausayi irin ki ba.ko barci fa bana yi.amma ban damu sosai ba,da kin zama a gefena,zan rama duk barcin da na ci bashi.tsaki ta ja,har yanzu ban taba hasashen hakan ba.ko cikin mafarki aurenmu ba zai kasance ba,na yi ma kaina alkawari.daidai lokacin suka iso babba falon,ya runsuna ya yi wa dad bankwana tare da sanar da shi cewa gobe za su fita don duba guraren da ya dace su yi bikinsu.dad ya ce ba damuwa,sai ka zo.ya kalli MIMI wadda ke shirin... [01/10 9:45 pm] Abdul: STEP (13)Ya kalli MIMI wadda ke shirin yin samanta ya ce,ki taka masa mana zuwa gurin mota.ba ta yi gardama ba, suka fita. Ya dube ta, nawa kika sa in auren ya kasance?ta ce,in har auren nan ya kasance,na yi maka alkawarin halaka kaina.ya waigo ya dube ta,ni kuma nayi miki alkawarin hana hakan faruwa.sannan zan yi kokarin ganin mun samu 'yan biyu a haihuwarmu ta farko.rasa me za ta ce ta yi,sai ta ja tsaki,ta koma ciki tana jin shi yana cewa,mu kwana lafiya. Dad ya ce,zo uwata zo ki ji.ya bude laptop dinsa ya dinga nuna mata kalolin kayan kicin din da momy nafisa ta siya ta turo masa ya gani.ya ce,suna da kyau, sun yi miki?cikin kosawa ta ce,eh.ya nuna mata motarta.motar ta ja hankalinta don ta shekara mai zuwa ce,amma ga shi an sai mata cikin wannan shekarar.ya ce,bari ki ga fa irin gadaje da abokina ya turo min.su ma sai kin zaba. Ta kalle su,ta kalli dad, sun yi yawa.ya ce kar ki damu uwata.zan yi miki duk abin da kike so.zan kashe ko nawa ne gurin auren nan ba tare da jin cewa na yi asara ba.ribar mai daya in aka bani kwangilarsa,zan ribanya dukkan kudin da na kashe. MIMI ta mike.zan sha magani dad,zan kwanta ne. ya ce,to je ki kwanta.ya fada miki za ku fita karfe goma ko?ta ce,eh.ya ce,to sai ku je har da na'ima.ta ce,to.A sama MIMI ke ta nazarin abubuwa.zuciyarta ta fi aminta cewa ta bi umurnin mahaifinta.dubi duk daular da yake shirya mata. gaskiya bai kamata ta bari a ji su ba.ita da mahaifinta.hakuri shi ne kurum mafitarta.za ta huce haushinta a kan abbas ne kurum,wanda ya dage cewa sai ya aure ta. Har ta kwanta da nufin barci,sai agogonta ya buga sha daya.kallon agogon ya zo daidai da ringin din wayarta.khalil ne.gabanta ya fadi.shi da take tunanin shafe babinsa,amma ba ta iya share shi,don haka ta daga.cikin sanyin murya ta ce,dear,ina ka shiga na kasa samun ka a waya?ya ce,na yi kokarin na hakura da ke ne,shi ya sa na kashe wayata,sai na ga ashe ba zan iya ba.zan mutu MIMI.don ALLAH ki fada min yaya za mu yi." [01/10 9:45 pm] Abdul: ya soma kuka. itama kukan ta soma yi. sai kuma ta tuna da batun malam Isma'il. da sauri ta CE, yauwa Khalil zanyi wa malam din nan magana, ko zai bamu magani. ya ce AI ba irin shine masu yin maga ni ba. ta ce bari kaji abin da ya CE min... nan ta fada masa yadda sukayi. ya CE, OK, ki kirashi yanzu. sai dai ina so ki Sani ba mu da ishashen lokaci, sabo da kullum kwanakin aurenki kara matsowa yake. ta CE, to bari in kira shi. zan fada maka duk yadda m kayi. ba tare da wani dogon nazari ba, mm ta soma kiran Layin Isma'il. ya gama shafa'i da wururi kenan, yana kwance kan doguwar dar dumar, duk hankalin shi ya koma katsina, gani yake kamar akwai abin da mahamud yake boye masa. yana ganin cikin satin nan zai koma gida...karshen wata yayi mashi nisa, duk da saura kwanaki takwas watan ya kare... Ringing din wayar Sa ne ya katse masa tunani. cikin sauri ya duba, bai San lambar ba, amma yadda yaga numbobin ya San cewa na musan man ne. ya daga tare da sallama, yar siririyar murya CE, ta amsa da helo! ya sake yin sallama, ta CE, ni ce mm. ya CE, baki amsa sallamata ba..." [01/10 9:45 pm] Abdul: Wanda ya kasance ba ya qmsa sallama wajibi ne a cikin addini. cikin kosawa ta amsa, sanan Tace, kasan dalilin kiranka..? ya CE, a a...Tace, ka CE, zaka bani maganin bakin ciki da, yaye damuwa. sanan kace, zan iya cimma buri na. Isma'il yayi dan murmushi, amkar yana gaban ta, sanan ya CE, kwarai kuwa...ta CE, to don Allah ka tai maka min ina cikin damuwa, mahaifi nane .yace, dakata! ba sai naji damuwar ki ba, ko abin da kike ciki ba, sanan zan taimaka maki. ta ce , nasani malam. INA so be kawai in fada maka, kila zaka tausaya min cikin gaggawa.. ya CE, Allah ne me taimako. tun da kin zabi ki fada min, INA sauraron ki.." ta CE, dady nane zai yi Mun auren dole...INA kuma da Wanda nake so. wlh mlm ni dashi Muna cikin wani hali. shine muke son mafita. Isma'il yace, mafita dai ita CE komawa ga Allah. Zaki: ya tashi cikin dare..?...ta CE, zan iya ko mai mlm don in cin ma buri na. ya CE ki tashi karfe ukun dare kiyi alwala, kiyi sallah raka'a biyu ko sama da haka. [01/10 9:45 pm] Abdul: ki fada wa Allah da muwarki. in sha Allahu Allah zai yaye maki halin da kike ciki. sanan ki yawaita zikirin Allah da karatun Alkur'ani mai girma. ba wai sai can cincikin Alkur'ani ba, ko kanan surorine kiyi ta karanta su, Zaki sami waraka. Mimi dai shiru, tayi, yana magana ita tana kuwa tana tunanin ta daban...to, shi wanan malamin da yake cewa tayi sallah, baya ganin cewa da ba ta damu da yin sallah ba, yanzu da matsala ya sameta, sai kuma ta wai wayi sallar...?...tam kar ya shiga zuciyar, ta, ya CE, kar ki dubi yawan zunubin ki, matsawar kika t ba, Allah zai yafe maki kurakuran ki sanan, yana da kyau kiyi adu'ar istihara, wato Neman zabin Allah kafin kikyi zabin mahaifin ki. ta CE, to malam AI ni ban iya ba...duk abin da ka CE min inyi din nan bansan ta inda zan fara ba... ya CE, in kin amince sai in koya maki yadda zakiyi. ta CE, to, amma ka bari zan kiraka. Khalil, ta kira, ta fada masa ko mai.." [01/10 9:45 pm] Abdul: ki fada wa Allah da muwarki. in sha Allahu Allah zai yaye maki halin da kike ciki. sanan ki yawaita zikirin Allah da karatun Alkur'ani mai girma. ba wai sai can cincikin Alkur'ani ba, ko kanan surorine kiyi ta karanta su, Zaki sami waraka. Mimi dai shiru, tayi, yana magana ita tana kuwa tana tunanin ta daban...to, shi wanan malamin da yake cewa tayi sallah, baya ganin cewa da ba ta damu da yin sallah ba, yanzu da matsala ya sameta, sai kuma ta wai wayi sallar...?...tam kar ya shiga zuciyar, ta, ya CE, kar ki dubi yawan zunubin ki, matsawar kika t ba, Allah zai yafe maki kurakuran ki sanan, yana da kyau kiyi adu'ar istihara, wato Neman zabin Allah kafin kikyi zabin mahaifin ki. ta CE, to malam AI ni ban iya ba...duk abin da ka CE min inyi din nan bansan ta inda zan fara ba... ya CE, in kin amince sai in koya maki yadda zakiyi. ta CE, to, amma ka bari zan kiraka. Khalil, ta kira, ta fada masa ko mai.." [01/10 9:45 pm] Abdul: Shi ya sa kike son shi,to ki ba abbas dama ki ga irin tasa.MIMI ta ce,ke yanzu za ki so a raba ki da faisal?ta ce,aa. amma in ta kama zan iya sadaukarwa.ina nufin dad dinki ya cancanci sadaukar da soyayyarki don ki faranta masa rai. MIMI ta ce,na yi yunkurin haka,amma na kasadon haka yanzu mu tsai da shawara ta karshe,ni da khalil.kuma ita ce mafita. mina ta ce,me kuka yanke? MIMI ta ce,kar ki damu,ba sai kin ji ba.suna yin zantukan nan ne a inda suka kebe kansu lokacin da abbas da abokansa suka je gurin manajan hall din da su mina suka ce yayi musu. Duk komai mina da na'ima suka zaba,MIMI ko kallon su ba ta yi.sai kusan daya saura suka nufi gidan da za su zauna.ba su da nisa da gidan iyayen mina. sai murna take yi,wai za ta dinga zuwa a kai,a kai,ga shi gidan ya burge ta.ko MIMI ta yaba gidan a zuciyarta,amma ba ta nuna ba. abbas ya zo kusa da ita,dear ya kika ga gidan naki?saman nan naki ne ke daya,falulluka uku,duk naki ne.da na lura kina son zama a sama,shi ya sa kike abar so kamar tsuntsaye.MIMI ta kau da kai,ina jin yunwa,don haka zan je gida.ya ce,bari mu je gurin cin abinci,mu ci mana. ta ce,aa ba na cin abincin ko'ina,ba komai nake ci ba. ya ce,shi ke nan bari mu fara kai mina ko?ba ta kanka ba ta nufi fita. sun fara sauke mina wadda take ta yaba wa abbas,har MIMI ta soma jin haushinta,ya sauke abokansa gidan cin abinci, ya ce bari ya kai ta gida ya dawo,zai same su a nan.duk zantukan da yake mata tun sad da suka taho ba ta tanka shi ba,har suka zo gidan,yana yi mata magana,ba ta tanka shi ba. ta sauka ta nufi ciki. ko da ya koma,abokansa korafi suka yi masa a kanta.munir ya ce,don tana da kyau sai ta hada da iskanci?don wannan ya wuce jan aji,tana kallon mu sai ka ce ta ga kashi.ya ce,ku yi hakuri abokaina.tana cikin fushi ne,amma lokaci kadan za ku ce tafi kowa kirki a nan gaba.dariya suka yi masa,don sun gane yayi nisa a soyayya. [01/10 9:45 pm] Abdul: Isma'il yana murna zai soma cusa tauhidi a zuciyar MIMI,ya tanaji abubuwan da zai fada mata don kara cusa mata ALLAH a cikin lamurranta.ya yi ta jiran kiranta,amma shiru.bayan laasar sun fita shi da direban yara,hamisu ke nan, don in an aike shi ko zai kai yara wani gurin,lsma'il kan bi shi don ganin gari.ya kosa su dawo don ya kira ta.haka kuwa aka yi.suna dawowa ya shiga daki,sai da ya zauna tsakiyar katifa ya nemi layinta ya kira.gab da za ta tsinke,ta daga.ya yi sallama.a kagare ta amsa.ya ce,ya ranki ya dade na ji shiru ne?ta ce,malam ka bar shi kawai.mun canza dabara. khalil ya ce naka zai ci lokaci.lsma'il cikin sauri ya ce,amma nawa shi ne mai tabbas,ln kin yi sabanin abin da na fada miki,karshe ki yi nadama.ba lalle ba ne adduarki ta dauki lokaci, domin ALLAH mai jin kan bayinsa ne.ba ki da wata dabara sabanin yi masa biyayya.ta yi jim,ta ce,don ALLAH ka bar shi kawai malam.sai ta yi tsaki.ta kuma kashe wayarta. Ta ko'ina abubuwa sun dauki zafi,domin ko can katsina tuni an daura auren zainab da alhaji lawal.an kuma kai ta gidan.matansa uku ga yara nan kwatsam. gidan bene ne hawa daya. dakinsa ne a saman,sai matarsa ta ukun,sai kuma dakin zainabu.a kasa matansa biyu ne da 'ya'yansu da kuma 'ya'yan wasu matan da suka fita. tunda aka kai zainabu take cikin kuka.bayan kowa ya kama gabansa,ta tashi ta datse dakin alhaji lawal ya taho misalin karfe sha daya da tsarabar kazarsa da abin sha.ya murda kofar amarya,ya ji ta gam.ya yi ta bugawa tamkar zai balla kofar ta ki budewa.ba zainabu ba,ina zaton duk matan gidan suna jin irin zagin da yake surfa wa amaryar tasa.fadi yake,ni zaki kawo wa rainin wayo don ubanki?yar matsiyata, ba za ki bude ba?ln kika bari na balla kofar nan na shigo,sai na karairaya ki,ko in sa a daure iyayenki har sai su biya ni abin da na kashe.lta dai zainabu jikinta sai bari yake yi,tana ta kuka.alhaji cikin takaici ya nufi dakin matarsa ta ukun ya sauke mata wahalar da ya debo ta magungunan da ya dankara. [01/10 9:45 pm] Abdul: Zainabu har goman safe ba ta bude kofa ba.sai da ya bar gidan,uwargidan ta zo ta buga,ta ce,bude yarinya ni ce,shi ya fita. matar ta shiga dakin,tana kallon zainabu cikin tausayi,ta ce,ALLAH sarki, ashe yarinya ce karama.ke ko me ya kai ki auren alhaji?cikin kuka,zainabu ta ce dole aka yi min.kudi ya nuna wa iyayenalna da wanda nake so,yake so na.ta ce,amma iyayenki ba su bincika ba ne?ta ce ni fa ban san komai a kan auren nan ba.ta ce,kai iyaye da yawa suna yin kuskure.da zara sun ga kudi,sai su tura 'ya'yayensu kawai,babu bincike. zainabu cikin tsoro, ta ce don allah hajiya me yake yi?ta ce,ba komai,kar ki damu.shawarar da zan ba ki,kar ki sake rufe masa kofa.duk abin da ya ce,ki yi,kar ki ke yi masa gardama hakan zai fi miki alheri,ke da iyayenki.ln kuma kin ki,to zai tozarta ku gaba dayanku. zainabu cikin kuka ta ce,na shiga uku!hajiya to ke 'yar uwarsa ce?aa,ni ce matarsa ta farko.ya aure ni tun bashi da ko kwabo. 'yayana goma da shi. zainab ta zaro ido,dama yaransa goma ya boye min?ta ce,nawa ke nan kadai 'ya'yansa ashirin da biyar,banda masu ciki uku. zainab ta ce ban gane ba. matar alhaji ta ce,matan da ya saka goma cif.ta karshen tana da ciki.sai sauran matansa biyu,duk suna da ciki.zainabu ta sake rushewa da kuka,tare da cewa,ita dai za ta gudu. matar ta ce kar ki fara!zai sa a kama iyayenki,kuma ba zai sake su ba sai ran da ya ji an ce an ganki,kin dawo dakinsa, ta mike, bari in sa a kawo miki abin kari. zainabu ba ta ce aa ba,dm tana jin yunwa,rabonta da abinci tun jiya da safe.koko ne da kosai,duk sun huce,yarinyar da ta kawo za ta kusan saarta.zainabu dai haka ta tuttura. da rana lnna yalwa ta zo, aminiyar lnnarsu ce.zainbu cikin kuka ta fada mata komai.lnna yalwa,ta ce,da allah can, duk karya ta fada miki,kika kama.kishiya ce har za ta ce miki ga laifin miji,ki hau kai?zainabu ta ce,lnna yalwa gaske ne.ga shi nan jiya sai zagi na yake yi dana rufe masa kofar.jiya fa na zo gidan.ln da mutunci bai dace yayi hakan ba. [01/10 9:45 pm] Abdul: Laifinki ne.yaya zaki rufe masa kofa?lna kika taba jin haka? bayan tafiyar lnna yalwa,ba jimawa yaran gidan suka cika mata daki, wanda gado ne kurum wanda alhaji ya sa mai kyau ne,amma da gani ba sabo ba ne.wadda ya aura nan dakin yake kawo ta.ln za ta tafi kuma ta bar masa gadonsa. ya shigo tana sallar magariba.ya zauna bakin gado,yana ta huci,sai ka ce kumurcin maciji.tsoro da fargaba suka hana ta idar da sallar.sai yi take tana sallamewa.ta sallame ta sake mikewa.ya finciko ta, ni za ki zo mawa da salon salla?magariba dai rakaa uku ce.kuma nafilar da na sani bayan magariba rakaa biyu ce,amma ke da na shigo kike ta zabga salla ko?cikin tsoro da kuka ta ce,aa baba ba haka ba ne. baba?ya tambaye ta,cikin fushi.kuka ta ci gaba da yi. ya kashe ta da mari,nine babanki?to,bari in nuna miki cewa ni mijinki ne,ba ubanki ba! da karfinsa ya yi amfani,ya raba ta da tufafinta,ya jefa ta kan gadon.duk 'yan gida da yara suna jin ihunta.da ma ya yi mata nata shiri na musamman.don kansa ya bar ta,ba don rokon da take masa ba,ko don wahalar da ta sha.ya bar ta yashe ba kulawa bare tausayawa,ya nufi dakinsa. haka ta kwanta babu barci sai kuka take yi.ya fita da wuri,don haka hajiya lndo ce uwargidansa ta zo ta duba ta,ta dafa ruwan zafi ta taimaka mata,ta ba ta abin kari.tsawon sati guda da yayi a dakinta bai raga mata ko sassauta mata ba.haike mata kurum yake yi.don haka ta sha azaba.tsoronsa da tsanarsa sun dasu cikin zuciyarta. khalil ya yi nasarar goge dan imanin MIMI da dan tauhidin da lsma'il ya soma cusa mata.ya zuwa 'yan kwanakin da suka biyo baya,sun yi nisa cikin tsarin yadda za su gudu.ko yanzu da suke yin waya fada mata yake yi,ta nuna cewa ta amince sai daf da auren sai su gudu.suna da bukatar kudi kafin ranar.ya ce,zan dauki sarkar mamana in kai kasuwa in sai da,sbd dad dinmu ba shi da kudi a gida sbd siyasarsa din nan.MIMI ta ce,kai baka da naka kudin ne?ya ce,account dina babu kudi,bai fi dubu ashirin ba.dad baya zuba mana kudi. [01/10 9:45 pm] Abdul: (2)Dad baya zuba mana kudi sosai yanzu saboda siyasa.ta ce,ka bar shi,ina da kudi a cikin karamin account dina.kamar nawa za mu rike?ya ce,muna bukatar kudi sosai,sbd za mu kama guri mai kyau ne a wani state din wanda ba za su yi tunanin za mu je ba.MIMI ta ce,ok,ka samo,ni ma zan samo,sai mu hada.ya ce,shi ke nan sai mun yi waya. bayan sun yi bankwana ta soma tunanin yadda za ta kwashe duk wani abu nata mai amfani.matsalarta daya.kudinta masu yawa suna cikin babban account dinta.ln kuma ta taba dole ne mahaifinta ya ji alat. Momy nafisa an dawo daga dubai,'yan gidansu abbas sun kawo kayan lefe.ran hajiya sauda ya baci da yadda alhaji ya nuna mata.matsayinta na wadda ta haifi MIMI ya kyautu a bata hakkinta ko da na shawara ne,amma alhai yayi mata dif,tunda ta ce baza ta shiga lamarinsa da MIMI ba,ita 'yar ba da shawara ce.bata fadi hakan da wata manufa ba, sai dai nuna ma alhaji kurensa,amma ya dauka da zafi,don haka ta lashi takobi ita da yaranta babu inda za su je,domin auren abba a nan katsina aka yi shi,na MIMI in baza a kawo nan ba,to su je can su yi kayansu. biki saura kwana goma MIMI ta yi wanka,ciki sauri ta zura doguwar rigarta atamfa,sai dan bakin karamin mayafi. takalmi mara tudu ta saka,ta kwashi katinta na ATM daga jakarta da take zuwa banki,ta zuba su cikin jakarta da takan je saloom,ta ra aya takar.ta kwashi wayoyinta.tana sauka kasa,momy zata hawo saman ta ce,aa sai ina haka MIMI? ta ce,za ta je saloon.na'ima ta ce yayi wuri sis.saura kwana goma biki fa?MIMI ta tabe baki,ke kika san da wani biki,ni kam ban san da shi ba. momy nafisa ta ce,ki zo ga tela,zai gan ki sbd dinkunan kayan biki,kin ki zuwa ki ga kayan ki.MIMI ta ce.momy har da ke a wannan maganar bayan kin san komai?ni fa ba son shi nake yi ba.momy ta sassauta murya,yanzun dai ki bi ni kawai.ln lokacin da za ki ce wa alhaji baki son abbas yayi,zan sanar da ke ki tubure kawai.a ran MIMI ta ce,ke ma baki san namu shirin ba.a fili ta ce, [01/10 9:45 pm] Abdul: (3)A fili ta ce,shi ke nan momy.tela ya gwada MIMI sosai.kafin ta fice,makullin motar momy ta dauka ta fita.lta ta ja motar zuwa bankinta na karamin asusunta,inda ta kwashe kudinta kaf.ta nufi babban asusun da ke wani bankin daban,ta dibi dubu dari biyu.za ta kara sai kiran dad ya shigo.ta daga ya ce,MIMI kina ina ne?ta ce, ina banki ne.dad ya ce,yaya kika taba wannan account din MIMI?ta ce,dad ba ni da kudi ne,kuma zan yi gyaran jikina ne.ya kalli alhaji akilu,ya ce,shi ke nan ya isa,ki bari zan ba ki kudi. kar ki kuma cira daga wannan account din,ina son yi miki wani tsari ne da kudin.za ki yi kasuwanci kina daga gida,kuma na manyan kudi kin gane?MIMI ta ce,eh dad ba zan kara cirewa ba.ya ce,shi ke nan. alhaji bishir cikin dariya ya ce,ka ji 'yar kwal uba? wai tana fadin bata so,amma ta zo tana dibar kudi wai za ta yi gyaran jiki.suka sa dariya.alhaji akilu ya ce,me na fada maka?kiyayyar mata ba ta zuwa ko'ina.amma shi ma abbas din ai shi ya dace ya ba ta kudin gyaran jikin. alhaji bishir ya ce,ai ita da shi duk daya ne.ka rabu da shi,zan ba ta.alhaji akilu ya kira layin abbas.bayan ya dauka,ya ce abbas ya baka bai wa amaryarka kudin gyaran jiki ba?abbas ya ce,dad ta ki ba ni damar in san abin da take bukata ne.amma zan ba ta anjima. ya ce,shi ke nan ka je ka ba ta.ka lallabe ta,ka san yarinya ce.abbas ya ce, insha allah dad. MIMI gida ta wuce ta adana kudinta da duk abin da ya kamata ta tafi da su,amma banda kaya. lsma'il ya dangana har zuwa ranar ashirin da tara da alhaji bishir ya yi musu albashi.duk da kin karatun da MIMI ta yi,bai sa alhaji canzawa daga dubu darin da ya alkawarta zai ba shi ba.lsma'il yayi ta juya kudin a cikin dakinsa,yana farin ciki.sam bai taba rika su ba a hannunsa ko na wani ma bare nasa.lalle goben nan sai katsina,ya je ya biya kudin gaisuwa,ya hada kayan sa rana,ya sai ma zainabu waya,yayi alheri,yayi sabbin dinkuna,yana ta baje burinsa.nan ya kira mahmud ya sanar da shi cewa gobe yana tafe. [01/10 9:45 pm] Abdul: (4)Tun dare yake ta shirin sa,washegari ya kira hajiya sauda ya fada mata cewa yau yana son zuwa gida ya ga 'yan uwa.ta ce ba laifi,sai ka iso.ln ka zo kuma don allah ina neman ka.ya ce babu matsala.sai dai ina son don allah ki sanar da alhaji sbd ban san lokacin da zai fito ba.ta ce,ya ba ka albashi dai ko?ya ce, wallahi ya ba ni.ki yi min godiya.ta ce,to zan sanar da shi yanzun nan. ba a yi minti talatin ba, sai ga hamisu direba ya ce lsma'il ya je in ji alhaji.a falo ya same shi.ya zauna,ya gai da alhajin cikin girmamawa.alhaji ya ce, sauda ta kira ni,ta sanar da ni cewa zaka je gida yau. haka ne?ya ce,eh alhaji.lna son in je in ga 'yan uwa ne. alhaji ya ce,da fatan ba mu takura maka ba ko?ina nufin ka ji dadin zama da mu?lsma'il ya ce,na ji dadi sosai.alhaji ya ce,to ina fatan za ka dawo.lsma'il ya ce,eh to,na ji ana cewa za a yi wa wadda na zo in koyar da ita aure,shi ne ban sani ba ko hakan yana nufin ni ma na gama aikina ke nan?alhaji yayi murmushi,ai in na lura ita din bata yin karatun,amma kannenta suna yin karatun. kana yi mana salla.ga yaran nan suna yin karatu sosai,suna yin salla a kan lokaci.wannan ya fi min komai.yanzun ma da ka ce zaka je gida din,na kira ka ne in ji ko kwana nawa za ka yi?lsma'il ya ce,to ina ganin dai zan yi kamar sati daya.alhaji ya ce,har sati daya?na zaci baza ka wuce kwana uku ko biyu ba.har me zaka yi haka?lsma'il ya ce,eh to ina so dai za a sa ranar aurena ne tukuna.alhaji yayi 'yar dariya,oho haka ne?to ba damuwa.allah yasa alheri.ya laluba aljihunsa,dubu biyar ya kara masa.ga wannan kayi kudin mota.ka amshi lambata gurin sauda.ln ya so in ka tashi kira na.sai ka kira ni kai tsaye,ba sai ka bita gurin hajiya sauda ba.lsma'il ya ce,to na gode sosai. bayanan fitarsa ne momy nafisa ta ce,na lura yaron nan yayi maka ko?alhaji ya ce yana da hankali sosai.lna son mutum haka.har gareji, hamisu direba ya kai lsma'il,bayan yayi sallama da dukkan maaikata gidan. [01/10 9:45 pm] Abdul: (5)Kowa yayi kewarsa, damuwarsu kar ya dade ko ya ma ki dawowa. shida na yamma daidai ya isa gida.matasan da suke zama a gindin bishiyar da ke kofar gidansu suna nan zaune kamar yadda suka saba.hirar ta kwallo ce sai ta siyasa.dukkansu sun juyo suna yi wa lsma'il sannu da isowa,bayan dayansu ya sanar da su cewa ga lsma'il nan ya dawo.ya isa gurinsu ya babba su hannu suka gaisa.suna ta yi masa murna da samu aiki a abuja. wasunsu har suna cewa.ustaz ka ga yadda ka yi kyau kuwa?gaskiya abuja ta amshe ka! shi dai godiya yayi musu,ya shige gida.kai tsaye cikin gidan ya shige.matan gidan suna ta haramar sauke girki, sallamarsa suka ji.fatu ce ta soma ganin sa.cikin irin faraar da bata taba yi masa ba ta ce,ga yan abuja,ga yan abuja!nan dai aka yi ta masa sannu da zuwa.ya amsa cikin jin dadi da mamakin fatu.a wata zuciyar ya ce,kila don dai ta daina ganin sa ne. dakin lnna ya shiga ya gaishe ta,sanan ya mika mata tsarabarsu.ya tashi ya koma dakinsa ya bude,yayi kakkabe-kakkabe a gurguje,sbd lokacin salla ya kusa.ya shimfida katifarsa,ya dauki bokitin ruwa wankansa ya kulle kofar da makulli,ya nufi cikin don yin wanka.da ya dawo,yayi alwala ya zura jallabiyarsa ya sake kulle kofa ya nufi masallacin kusa da su. bayan idar da sallar ya dawo ya zauna ya kasafta kudinsa,ya adana sauran ya canza kaya tare da fesa turarurruka masu kamshi.ya yi kyau matuka cikin shadda mai ruwan toka,ya murza hula.ya kosa ya ga zainabu,ga shi tunda ya shigo garin katsina yake ta neman layin mahmud. cikin nishadi yake takawa,duk da lokaci bayan lokaci gabansa yana faduwa.sam ba ya ganin nisan gidan su zainabu daga nasu gidan.a kafarsa ya taka.har ya je kofar gidan,sai kuma ya tuna bai zo mata da tsaraba ba.don haka ya juya,ya tare dan acaba ya hau,sai wani shago ya je inda ya siyo mata waya ta naira dubu biyar.ya sake komawa kofar gidan.kamar an turo shi,sai ga kanin zainabu.kafin lsma'il yayi masa magana har ya juya da gudu ya koma ciki.a ran lsma'il ya ce, [01/10 9:45 pm] Abdul: (6)Yawwa kira ta,kai ma ka zo ka dan ja wani abu.kwarai idanunsa suka kosa su ga fitowarta.cikin duhun zauren ya ga alamun fitowar mutum.a zatonsa zainabunsa ce,har da gyara tsayuwa. muryar mahaifiyarta ya ji daga sama tana cewa,sannu malam lsma'il da zuwa.cikin faraa ya ce,yawwa lnna. cikin girmamawa ya gai da ta.ta amsa.ta ci gaba da cewa,sai ka samu labarin zainabu ta yi aure ko?ledar wayar da ke hannunsa ta subuce,ta fadi a kasa.cikin in-ina ya ce,mene kika ce lnna?ta ce,zainabu ta yi aure.allah ya sa ba rabonka ba ce.kodayake laifinka ne. tunda baka kawo ko da sallama ba.lsma'il ya ce, inna don allah kar kiyi min haka.da shirina na zo.sai an sa bikinmu zan koma.ta ce assha!ai ka bar shiri tun rani yaro.tana gidan alhaji lawan.ba tare da jiran sake ji daga gare shi ba ta koma ciki. lsma'il ya tsuguna,ya dauki wayarsa jiki babu karfi,zuciyar na tafarfasa,ya nufi gidan yaya amina.da kyar ya kai. sai ganin mutum ta yi babu ko sallama.kan tabarmar da ya gani a shimfide ya zube zaune tare da dora kansa a guiwowinsa.cikin fargaba ta ce,lsma'il lafiya?ta tambaye shi fiye da sau biyar,ya dago kai da kyar ya ce,lafiya lau.ta ce ina fa lafiya,dube ka fa?me ke maka ciwo?ya girgiza kai, babu. ya sake dosa kansa a kan hannuwansa wadanda suke sarkafe a guiwowinsa.ya ce,yaya ashe zainabu ta yi aure?ta ce,au da ma damuwar ke nan?ta sake tausasa murya,ka yi hakuri.allah ya rubuta cewa zainabu ba matarka ba ce.nan ta shaida masa abin da ta ji game da auren. ya ce,mahmud bai kyauta min ba.me zai sa muna waya,amma yaki sanar da ni?ni na san da a ce ina nan ba yadda za a yi a raba ni da ita.sam mahmud bai cika alkawari ba,kuma bai rike min amana ba.yaya amina ta ce kar ka ga laifinsa,domin a boye duk aka yi komai.sai daurin aure aka ji.lsma'il ya sauke ajiyar zuciya,wasu zafafan hawaye suka zubo kan kumatunsa.ta ce,haba don allah lsma'il,sai ka ce ba namiji ba?kamar baka da ilimi.ka fa san komai mukaddari ne.ka yi hakuri,zainabu ba rabonka ba ce. [01/10 9:45 pm] Abdul: (7)Allah zai baka wadda ta fi ta komai.lsma'il ya ce,shi ke nan yaya na gode.ya ciro dubu uku daga aljihunsa, ga wannan yaya.ta amsa tana fadin, har da kudi haka.ya ce,ba yawa.lna ganin gobe ma zan juya kawai,da ma da kyar alhajin ya bari na taho. ta ce,haba dai ka dan kwana biyu mana?ya ce,aa ba zan iya zama a garin nan ba,ina tuna zainabu.lna bukatar cire ta daga raina. ya mike a kasalance,ya dauki ledar wayarsa ya ce,to ni sai na dawo.ta ce, ba zaka biyo ba gobe ke nan?ya ce sammako zan yi. da kyar ya isa gida.tunda ya bude kofarsa ya fada kan katifa,bayan rufe kofar ya soma kuka.shi kansa bai san yana tsananin son zainabu haka ba sai da ya rasa ta.ya yi kuka sosai,ya dangana,ya fita cikin dare yayi alwala.gurin allah ya yi ta kai kukansa.bukatarsa allah ya cire masa son zainabu,ya ba shi dangana ya sada shi da mafi alheri. daga bisani ya dauki alkurani,yana karantawa. Kafin wani lokaci,salama ta sauka a zuciyarsa.sai da yayi sallar asubahi,ya soma jin barci. yana dawowa daga masallaci ya kwanta.ba shi ya farka ba sai goma saura. shi ma kwankwasa kofarsa aka yi ya farka.ya tashi da kyar ya zare sakatar.mahmud ne,don haka ya dawo ya zauna. mahmud ya shigo,shi ma ya zauna. lsma'il ya ba shi hannu suka gaisa.ya ce,na yi ta kiran wayarka a kashe. mahmud ya gyara zama.ina sane na kashe,domin bana so ka rike ni a ranka.na san dai zuwa yanzu kaji komai.lsma'il ya tsura ma bakin kofa ido,kamar mai kallon wani abu a gurin. mahmud ya ce,ka yi hakuri allah ya kaddara ba matarka ba ce.lsma'il ya ce,duk da haka mahmud,kai ma na ga laifinka.me zai sa ba ka kira ni ka fada min ba?na tabbata zainabu dole aka yi mata,don tana so na.mahmud ya ce,fada maka ba zai kare ka da komai ba.a lokacin da na samu labarin kwana kadan suka rage a daura aure. amma ka yi min afuwa.lsma'il ya ce,ni yanzu zan shirya in koma abuja.malam yana nan kuwa?mahmud ya ce,yana nan.na dai bar shi a gida. haba dai ka ce yau za ka koma?ya ce.tun jiya katsina ta fita daga raina. [01/10 9:45 pm] Abdul: (8)Mahmud ya ce,allah yasa hakan shine mafi alheri.amma ya kamata ka dan yi kwana biyu.lsma'il ya ce,in na zauna babu abin da zan yi.da a ce na san da wannan matsalar.lallai da ba zan zo ba.mahmud ya ce,shi ke nan allah ya kai ka lafiya.ko wanka lsmail bai yi ba,ya hada nasa-ya-nasa ya shiga cikin gida yin sallama.fatu ta ce, lsma'il sai ka ji batun auren zainabu.bai san lokacin da murmushi ya sauka a fuskarsa ba.ya ce,zainabu ta yi aure.fatana allah ya bata zaman lafiya.fatu ta yi 'yar dariya,ka dangana ke nan?bai tanka ta ba,ya wuce abinsa dakin lnna.ya shiga ya sanar mata cewa zai koma,ya kawo dubu biyu ya bata.ta amsa tana godiya.ta ce ko ka hadu da yan uwanka?ya ce mun gaisa da asuba a masallaci,amma ga wannan ki basu.ya mika mata dubu uku.ta ce,an gode.allah ya saka da alkhairan.sai kuma kaji wannan yarinyar da kake nema ta yi aure ko?ya ce eh na ji lnna.allah bai yi dani ba.ta ce,duk da haka ma sun so yaudararka ne.ka je ka amshi duk abin da ka san cewa naka ne,lna nufin wanda ka bata.ka kuma lssafa kudin da ka bata, tallar nan duk a amso su,ya ce,lnna a bar wannan maganar kawai.ban bata don in karba ba.ya mike,ya fito,ta ce,to shi kenan allah ya tsare hanya.nan su ma matan gidan ya basu dubu daya,ya dauki jakarsa. Bayan ya ba mahmud dubu biyu,mahmud ya ce, kudin mene ne?ya ce,kudin albashina mana.dana yi niyyar gabatar da abubuwan aurena har zuwa a sa rana.amma tunda babu zancen,gara in yi alheri in samu lada. mahmud ya ce,na gode sosai.gidan su mahmud suka je,inda ya ba malam dubu uku.ya goya shi a mashin dinsa.har za su wuce tasha,ya ce,kodayake ka kai ni gidan alhaji bishir in gaisa da hajiya sauda.sai da suka je kofar gidan,ya kira layin hajiyar ya ce mata ga shi a waje,ta turo abdullahi suka shiga tare.lsmail bai boye mata komai ba game da MIMI na kin karatu ba.ya sanar da ita halin da yake ciki.ta ce,ba komai kar ya damu da batun MIMI tunda aure za ta yi.yanzu ya koma ya ci gaba da abin da yake yi,a kan zainabu kuma tace kar ya damu, [01/10 9:45 pm] Abdul: (9)Kila ita din ba alheri ba ce a gare shi.ta ce,in da zai yarda ma da ya koma makaranta don zurfafa iliminsa gaba daya a fannin bokon da kuma lslamiyyar ya ce,shi ma tunaninsa ke nan a yanzu suka yi bankwana,bayan ta ba shi wani turare mai kamshi.ya fito mahmud ya kai shi tasha.bai samu motar abuja kai tsaye ba,don haka sai ya hau ta kaduna. suka miki hanya,zuciyarsa da rauni,bai san lokacin da zai warke ba. hajiyar mardiyya,matar alhaji lsa mani,abokin alhaji bishir ita ce ke kwada sallama a falon hajiya sauda.hasina ce ta fito daga dakinsu ta ce,sannu da zuwa maman su nabila.ta ce,yawwa hasina,hajiya fa?ta ce,bari in duba ta.nan hajiyar mardiyya ta zauna kan kajera.hasina ta fito ta ce, tana wanka ne.hajiya mardiyya ta mike,bari in shiga cikin dakin.kawaye ne sosai,har yanzu ba su yada juna ba,don sun fi mazan nasu zumunci,har da matar alhaji kabiru,hajiya ramatu, abokansa na tun ana talakawa. kan gado ta zauna tana 'yan dube-dube. ke kullum aka zo dakinki kal,sai ka ce amarya.daidai lokacin ta fito tana cewa, me kika ce?hajiya mardiyya ta maimaita.sauda ta yi dariya,to ni ke gyra dakina da kaina.ku ko kun fi son na 'yan aiki.ta ce,to meye aikinsu in ba shara da wanke-wanke ba?sauda ta ce,ku dinga duba masu. kullum ina fada muku,suna yi kuna dubawa,kuma gyara musu. hajiya mardiyya ta ce,ke ni zuwa na yi in ji dalili ko kuma laifin da nai miki baki fada min biki ba,sai dai in ji a gurin alhaji.hajiya sauda ta yi tsaki,kin san allah,ban san komai a kan bikin nan ba.ke in takaice miki,yanzu alhaji fushi yake yi da ni.hajiya mardiyya ta ce,a kan me?ta ce,kin san bata son auren,shi ke so.ya kira ni wai in tursasa mata ta yi abin da yake so.sai na nuna masa cewa ba ruwana, yanzu ne aka san da ni?to ni shawara zan ba ta,tursasawa ba.kar ki dada,kar ki raga.daga wannan shine laifina.wai ni ce ke zuga ta.har yau bai sake ce min kala a kan bikin ba.na'ima take fada wa su hasana ta waya wai nafisa ta je dubai siyan kaya.an kawo lefe,an yi kaza,an yi kaza. [01/10 9:45 pm] Abdul: (10)Hajiyar mardiyya ta ce, amma alhaji bai kyauta ba. ko da keke zuga ta.ai kamata yayi ya baki hakkinki na haihuwa.sauda ta ce,ni ma dai shi na gani. don haka nasa musu ido.ya maki zuwa garin nan sam. ko kira waya yayi.sai ya yi ta wani dake-dake yana magana a cije. hajiya mardiyya ta ce, amma da kin yi masa magana da kanki,ki yi masa bayanin nufinki don ki amshi ragamar auren 'yarki. sauda ta ce,kin san allah ba zan kula auren nan ba.kuma ba zan taba yi masa magana a kan wai ya fahimci ban zuga MIMI ba.mu je a na zuga tan.ita ma ba halin kirki gare ta ba.so nake su gane kurensu,dukkansu shi da ita.mardiyya ta ce,shi ke nan,allah ya kai mu.mu dai za muje biki.ln abuja din ne,in nan ne ma dai duk da mu za a yi,allah ya taimaka, in ji hajiya sauda. Ana saura sati daya bikin ne,alhaji bishir ya zo katsina.bai ko sanar da zuwansa ba.barcin rana take yi lokacin da ya iso. yaran suka yi masa sannu da zuwa.kai tsaye ya nufi dakinsa,ya bude ya shiga.ya zuba jakar hannunsa da hularsa zuwa wayarsa a kan kujera. shi kuma ya zauna a bakin gado.hasna ce ta shiga dakin hajiya sauda ta tashe ta,tana sanar mata zuwan dady.ta sha mamaki sosai, domin sai ya sanar kafin ya isa.ta kalli husna,shi ne ya ce ki kira ni?husna ta ce,aa ya shiga dakinsa ne kawai.sauda ta ce,to je ki ina zuwa.har ta mai da kanta ta kwanta,a zuciyarta ta ce tunda da abin da ya zo gidan ke nan ba za ta kula shi ba.amma sai wata zuciyar ta ce, mijinki ne kina kasansa ki je. ta same shi yana cire safar kafarsa.ta yi sallama, ta shiga.daga bakin kofa ta tsaya tana fadin,sannu da zuwa.alhaji a ciki ya amsa da cewa yawwa.ta zauna a hannun kujera,na ji mamaki,ba ka ce min kana zuwa ba,kamar yadda ka saba.ya dago ya dube ta laifi ne?ta lumshe ido,cikin takaici ta ce,aa babu laifi.ta mike tsaye,me kake bukata?ina nufin abin da zaka ci ko sha?ya mike, alhamdulillah ba na bukatar ko daya.ta ce,har wanka?ya dan yi tsaki,kin ga na yi datti ne?ta kautar da kai gefe. [01/10 10:34 pm] Abdul: (12)Ameen.me kuke bukata a cikin bikin ke da yaranki? ta ce,ba ma bukatar komai bikin da ba a nan za a yi shi ba.mu ma fa yan gayyata ne.ya ce,ba na son kina fadin haka.ba za kuyi ashoben ba?ta ce,aa ba za mu yi ba.ya ce,don me?ta ce,ba za mu samu dinki ba kar ka damu.ya ce,shi ke nan.ya kwana,washegari ya wuce malumfashi.ya koma abuja saura kwana biyar biki.kuma ranar ne aka yi jeren amarya a gidan angonta. lsma'il ya isa abuja yammacin magariba. maigadi da ya soma ganin sa ya sha mamaki.ya ce, malam kai ne ka dawo?ya ce,ni ne daga kiran sallar lsha'i ne,alhaji ya bukaci ganin lsmail a kebe.bayan sun gaisa ne alhaji ke tambayar lsma'il lafiya ya dawo da wuri?lsmil bai boye masa komai ba.ya fada masa abin da aka yi masa,ya ji ya tsanin garin katsina.alhaji ya ce, kar ka damu.allah yasa haka ne mafi alheri a gare ka.lsmail ya ce,amin na gode [01/10 10:34 pm] Abdul: (11)Ta yi dan huci,ta mike. har ta kai bakin kofa,ta kasa jurewa,ta dawo,alhaji wai laifin me na yi maka da duk ka canza min.ya kalle ta,baki san kin yi laifin ba ko?ta ce,wallahi ban sani ba.ka sanar da ni mana.ba sai in baka hakuri ba.ya ce, ban zaci zan ce ki yi abu ba,amma ki ce min ba za kiyi ba.ni ne na ce kiyi wa MIMI fada kan ta bi zabin da nayi,amma kika ce min ba za kiyi ba,karshe ma sai kika zuga ta ta katse shi,na zuga ta kuma?ln ji ta ne ta ce na zuga ta?shawara na ce zan bata,kuma na bata. ka tambaye ta wace irin shawara na bata?zan yi mamaki sosai in ka ce ka mance halina.a tunanina mun kai matsayin da zaka san abin da zan iya da kuma wanda ba zan iya ba.don ni yanzun zan iya rubuta kundi a kan halayyarka.haka kuma in an fadi wanda ba za ka iya ba,zan ce sam baza ka iya yin haka ba.kansa yana kasa,yayi shiru,domin ya san cewa gaskiya ta fada.can ya dago kai,me kika ce mata?ta mike ta koma kusa da shi.bayan ta dauki wayarsa ta soma latso lambobin ta kai kan lambar MIMI ta dannan kira,ta latsa handsfree sai da ta soma ringing ta mika masa,ina son ka tambaye ta,mu ji.kafin ya ce,aa,har MIMI ta daga,muryarta ta ratso,inda ta ce,hello dad.ya ce,MIMI,in tambaye ki?ta ce, eh dad.ya ce,me mamarki ta fada miki game da auren abbas?ta ce,wace maman,momy nafisa?ya ce, mahaifiyarki.ta tura baki,dad cewa fa tayi wai in hakura in bi abin da kake so,ko don irin kaunar daka nuna min.wai shawara ta bani.ya ce,shi ke nan. yana kashe wayar sauda ta mike.ya kamo hannunta, kar ki yi fushi matata,ki yi hakuri,na fahimce ki.bai-bai ta dan yi jim,ta ce,shi ke nan ya wuce.ya ce,to zauna muyi maganar auren MIMI.ta ce bani da ta cewa game da auren MIMI,face allah ya bada zaman lafiya. yanzu ka hakura zaka ci abincin?ya girgiza kai,aa sai in kin zauna.ta lumshe ido, ta zauna.ya ce,ni ma na yi miki laifi ban fada miki komai ba.yau saura kwana bakwai.kuma za a yi bikin ne a can abuja.sauda ta ce,babu damuwa. allah ya sa a yi lafiya.ya ce ameen. [01/10 10:34 pm] Abdul: (13)Washe gari saura kwana hudu biki,amarya ta sha gyara jiki,ita da na'ima.duk abin da aka yi mata,an yi wa na'ima.mai gyara ta musammam momy nafisa ta dauko.an zuba musu zanen lalle har ba za ka iya bambance amarya ba.kawayen MIMI su mina suna ta kai koma don ganin shirye-shiryensu sun kayatar.yammacin laraba za su yi family night. na'ima tayi zaton zuwan 'yan katsina,amma shiru. MIMI bata damu ba,don ta san ita ba zama za tayi ba. rashin zuwansu ma zai fi mata.a ranar alhamis kuwa za su yi 'mothers day, wanda momy nafisa ta shirya.kuma a ranar ne MIMI suka shirya guduwa,ita da khalil dinta.amma momy nafisa a nata tsarin sai daren jumaa,in an dawo daga kumbo,an yi kamu ke nan sai ta sa MIMI ta tubure.daga nan sai ta tura na'ima ta ce wa dad din su ita ta yarda a daura da ita. An yi mothers day lafiya an tashi ana ta daukar hotuna,MIMI ta daga wayarta ta kira khalil ta ce su zo,shi da wani abokinsa kamar za ta yi magana da wani ta fita wajen hall din ta nufe su.da mota suke,don haka ta shige.kai tsaye gidan su MIMI suka koma.babu kowa,duk ana gurin biki,amma dad yana nan.da ta dauko jakarta za ta sauko sai ta ji shi yana waya.tana fitowa ta ji ashe a falonsa yake,amma daf da babban falon nasu. sai ta yi sanda ta fice.da gudu ta ja mota suka tafi. Ta dubi khalil,yanzu ina muka nufa?ya ce,kaduna. don in muka ce za mu kwana a abuja,da safe za a kama mu.haka cikin dare nan suk dauko hanyar kaduna,gudu suke yi sosai. ga shi lokacin sanyi.ga MIMI ba ta son sanyi,kuma kayan jikinta irin na amare ne,ba na dumi ba.ta kudundune duk da cewa khalil ya cire t-shirt din sa ya bata ta dora a kan kayan jikinta.shi kuma ya zauna da singileti.zuciyar MIMI ta kasa natsuwa,wani gefen yana fada mata cewa ba ta kyauta ba,za ta yi nadama,ta kunyata mahaifinta.wata zuciyar kuma tana zuga ta da cewa ke ki tafi kina kan daidai.alamarin dai ga shi nan. [01/10 10:34 pm] Abdul: (15)Amma da yaje daki na musamman suka kama,sam ba ya fitowa ko kofar daki.duk abin da suke so sadau ke zuwa ya sai musu.su kuwa su momy nafisa ba su ankare ba,suna can suna ta hidimar ganin kowa ya samu abinci. a zatonsu tana can suna hotuna da kawayensu sai lokacin da na'ima ta zo tana cewa momy ina sis MIMI?ga abbas sun zo da abokansa.nan fa aka shiga neman amarya,ba ta babu dalilinta.hankula suka tashi. nan dai biki ya kare.momy nafisa kuka wi-wi.nan ta kira alhaji bishir tana fada masa cewa MIMI ta zo gida?ya ce babu wanda ya zo gidan nan.shi ma zuwansa ke nan.daidai lokacin da suke yin wayar da a ce ya waiwayo da zai ga MIMI,tunda gilashi ne ya raba falonsu da nasa. Ta ce masa,to MIMI dai an neme ta an rasa ta,ko kasa ko sama.har zuwa sha biyun dare ana ci gaba da neman ta lungu da sako, banda wayoyi da ake ta yi don ji gurin abokanen arziki. matuka hankalin alhaji ya tashi sosai.alhaji akilu ya kira shi yana jajanta masa. ya ce,amma alhaji bishir da ma yarinyar nan ba ta hakura ba?alhaji bishir ya ce,ta hakura mana.ga shi ana ta biki.sai yau a ce ta gudu?alhaji akilu ya ce,baka ganin ko yaron da suke yin soyayyar ne ya zo ya sace ta?alhaji bishir ya ce, komai zai iya faruwa.amma bari mu gani zuwa da safe.alhaji akilu ya ce,in ko ya tabbata yaron nan sace ta yayi,lallai babu abin da zai hana shi zaman gidan yari.ka ga halin da abbas yake ciki kuwa?ya ce,ko ni ma ba zan kyale iyayansa ba bare shi,tunda daga gani ba da yardarta ya sace ta ba, domin bata bar wani sako ba,ba ta dauki komai na sawarta ba.alhaji akilu ya ce,kun kira lambarta?ya ce tana ta ringing ba ta daga ba.kusan karfe dayan dare alhaji bishir ya kira hajiya sauda tana barci,ta dauka, tana fadin,alhaji lafiya?ya ce ina fa lafiya,an sace MIMI.ta diro daga kan gado.an sace MIMI kuma?ya bata labarin komai hajiya sauda ta ce,ko dai guduwa suka yi tare da saurayin nata?ya ce, bana tunanin haka,ta nuna min ta hakura.kuma sun shirya komai da mijinta, har kudi ta cire a account din ta don gyaran jiki. [01/10 10:34 pm] Abdul: (14)Dayan dare suka shigo garin kaduna.sadau abokinsa shi ne ya kawo shawarar su shiga cikin wata unguwa su nemi otal,kar su kama na bakin hanya.ta titin kagoro suka shiga,inda suka sami wani otal suka kama.MIMI ta ce su kama mata dakinta daban khalil ya ce,dear za ki iya kwana ke kadai?ta ce,eh mana kar ka damu.ta yae,shi ke nan. daki biyu suka kama a sama.khalil ya kalli sadau bayan sun kwanta,abokina ina kake ganin ya dace mu je?sadau ya ce,gobe ku shiga motar sakkwato ko zamfara.ba za a yi tunanin za ku je can ba.khalil ya ce,ni da lagos na so mu tafi,mu boye kamar na sati daya.sadau ya ce,kai banza ne.wane sati daya.ai in ni kai sai na dinke yarinyar za mu fito. yadda dole za a aura min ita.khalil ya tashi zaune,ban gane ba.sadau ya ce,ina nufin,yayi kwatance da hannunsa da cikinsa.khalil ya ce allah ya sawwake.ba ni da niyyar in cutar da MIMI zan barin mu yi halastaccen aure da ita. sadau ya ce,ka ji matsalarka.a shawarwarin da na baka,wacce ce aka samu matsala?na ce ka sai da gwal din mom dinka,mun sai da na ce ka dauke ta ku gudu.ba ga shi ka yi nasara ba?khalil ya ce,ban dauke ta da niyyar aikata wani abu ba,sai don in fid da ta daga auren wani na.kai dai naka da safe ka kai mu garejin mota mu tafi.kai kuma koma gidanku mun gode. MIMI kuwa ta kasa barci, sai juyi take yi.wayarta tana,silent,amma tana kallon kira.da wani ya yanke,wani zai shigo da farko ta ki dubawa,amma daga baya sai ta duba.kiran dad dinta ne da momy nafisa har da su na'ima. kuka take ta tayi tare da tausayin mahaifinta.ji take kamar ta daga ta ce su zo su dauke ta,kuma ta amince za ta auri wanda suke so.amma sai shaidaniyar zuciyarta ta kangare,ta kuma hana ta aiwatar da hakan.da zazzabi ta farka tare da ciwon kai mai tsanani,don haka sai batun tafiya ya fasu.sun fita suka sayo mata doguwar riga da hijabi ta saka,suka dauke ta zuwa asibitin biba.gado likita ya bata,don tana cikin damuwa.hankalin khalil ya kara tashi, tsoron sa kar wanda ya san shi ya gan shi burinsa su bar kaduna, [01/10 10:34 pm] Abdul: (16)Ba ta dauki komai ba. hajiya sauda ta ce,allah ya kyauta.amma a zuciyarta tafi yarda cewa MIMI kudi ta diba suka gudu.ta ce to yanzu wane mataki ka dauka?ya ce,mun sanar da yan sanda,gobe za mu je kaduna gidan iyayensa. hajiya sauda ta ce,to ku kuwa hada da addua. bayan sun yi sallama da kansa ya taka gefen masu masu aiki ya kwankwasa kofar dakin lsma'il ya yi sallama ya amsa,don lokacin yana ta juyi cikin damuwar rashin masoyiyarsa zainabu.jin muryar alhaji ya bude kofar cikin fargaba.ya ce.alhaji lafiya?ya ce baka ji abin da yake faruwa bane?lsma'il ya ce,ban ji ba alhaji.a zatosa ma barayi ne suka shigo gidan.alhaji ya ce mu shiga daga ciki.a tsakiyar dakin suka yi cirko-cirko. alhaji ya ce,malam lsmail a gurin shagalin biki aka sace MIMI.aka sace MIMI?lsma'il ya maimaita.alhaji abbas ya ce,na zo gurin ka ne ina son a taya mu da addua kafin gobe in samu malamina saboda ya duba min inda suka boye ta.lsmail ya ce,allah ya kyauta,ya kuma bayyana ta sai dai alhaji baka tunanin ko sun gudu ne? alhji ya ce,bana tsammani, tunda bata bar wata alama da za ta nuna hakan ba.ba ta dauki kaya ba.lsmail ya ce haka ne.shi ke nan insha allah zan taya da addua. ikon allah a gabana suka hau mota alhaji da zasu tafi. to ni dama muna yin isha'i,na yi shafa'i nake shiga in kwanta da wuri saboda ina tashi cikin dare. alhaji ya ce,to bari mu je mu yi sauraro.lsma'il ya ce allah ya jishe mu alheri. bayan fitar alhaji,lsmail yayi ta mamakin MIMI.tabbas sun gudu ne,tunda ta fada masa cewa sun samu mafita,ya kira layinta,yayi ta ringing har ya tsinke.haka yayi ta kira har ya gaji.alhji kam yana tafe yana tunanin maganar lsmail haka sauda ta ce ko sun gudu ne.shi ma gashi ya ce hakan.momy nafisa ya samu ta zabga ta tagumi bakin gadonsa.ya dafa ta,kar ki damu nafisa za a gan ta.ni damuwata ma da sauda ta ce ko dai guduwa suka yi haka ma malaminta ya fada min yanzu.sai dai ina shakku don na san MIMI baza ta guje ni ba ta bi wani sakarai. [01/10 10:34 pm] Abdul: (17)Momy nafisa ta ce,haba ba za ta gudu ba.don ta tabbatar da ya zai yi in gudun ta yi,sai ta ce,ko ta gudu ma,ai dole ta dawo.ya ce,me kika?ya mike cikin tashin hankali,ya ce kuskure mafi girma da MIMI za tayi shi ne ta guje ni.kin ji na rantse miki,in MIMI guduwa ta yi ta kunyata ni,to ni kuma sai na yi mata abin da ba za ta manta da ni ba wannan alkawarina ne. tunda asubahi momy nafisa ta shiga dakin na'ima ta ce,tashi ki ji,ga fa dama ta samu.na'ima ta gyagije daga barci.ta ce wannan gudun na MIMI yayi matukar zuwa mana a daidai.yanzun abu daya ya rage mana.shi ne dad dinku ya san cewa tana sane ta bar gida.na'ima ta ce,in ya sani mene ne?nan momy ta sanar da ita alwashin da ya ci,ta ce,kuma tabbas MIMI ba sace ta aka yi ba. ga shi na yi ta kiran ta bata daga ba.amma zan ci gaba da kira.ln ta daga zan sa ta fada wa alhaji cewa ta gudu ne.safiyar ranar lsmail yana masallaci zaune,alhaji ya fito zai fita.ya nufe shi ya gai da shi cikin girmamawa.ya dada jajanta masa.alhaji yayi godiya.lsmail ya ce,sai dai jiya na yi mantuwa.sai bayan ka tafi na tuna.alhaji ya ce,ta me?ya ce,alhaji duba haramun ne a musulunci.akwai inda yake zama shirka ma.wato mutum ya fita daga musuluci.alhaji ya ce, istihara ce ai za a yi malam lsma'l ya ce,alhji ai istihara kai ne zaka yi da kanka,ba wani ne zai yi maka ba, kamar yadda wasu malaman suke cewa don su ci kudinku.alhaji ya ce, shi ke nan.ana jira na.ln na dawo zamu yi maganar. bayan ya koma daki ne ya ga kiran hajiya sauda. nan take ya kira ta.cikin girmamawa.ya gaishe ta,ya jajanta mata abin da ya faru.ta ce,lsma'il na kira ne ina son a taya ni da adduar allah ya tsare yarinyar nan, don ina zaton guduwa ta yi tare da yaro nan.lsmil ya ce,ina yi hajiya ni mana fi zaton sun gudu ne.ta ce,ina amfanin gatan da ya nuna mata.ai da ma kuskure ne mutum ya gina dansa a kan cewa duk abin da yake so sai ya samu.gara ka nuna wa yaro cewa akwai kuma kaddara.amma sam ita ba ta san wannan ba.duk abin da take so zai mata. [01/10 10:34 pm] Abdul: (18)To yaya yanzu ba za ta turbure ya bata wanda take so ba?lsmail ya ce, haka ne.a ransa ya ce da ma hausawa sun ce,ka sa danka kuka kafin yasa ka a fili ya ce,allah zai saukaka mana lamarin da yardarsa. hajiya sauda ta ce,allah ya sa.abbas kuwa shi ma cikin tashin hankali yake.a nasa zaton an sace ta ne,tunda ya ga gab da bikin ta saki jiki.da alamu ta yarda za ta aure shi.cikin mutunci ta amshi kudin gyara jikin da ya kai mata.ranar da aka yi family night sun yi ta hotuna tare.a ce an sace ta.ko dai masu yin garkuwa da dan adam ne?alhaji akilu ya ce kar ka damu.ln ma sune zamu ba da ko nawa ne don su sake ta. Alhaji bishir ya sanar da duk masu kofofin sadarwa don neman ta,ko in ce cigiyarta.da kamfanin layin MTN aka gane cewa tana kaduna,don haka can suka dosa.kwamishinan yan sanda na kaduna shi ne ya kira mahaifin khalil ya sanar da shi cewa ga iyayen yarinyar da dansa ya gudu da ita sun zo.bai yi kasa a guiwa ba ya iso gidan kwamishinan,sun tattauna da mahaifin khalil,ya ba su hakuri,tare da tabbatar musu cewa dansa khalil ya gudu tare da yarsu.ya fada wa kwamishina cewa in ya zo a kama shi kamun barawo don ya dauke sarkar mahaifiyarsa. Daidai lokacin MIMI ta daga wayar momy nafisa, bayan momy ta tura mata message cewa ta daga su yi magana,ta san dai tana tare da ita a kan komai, bayan khalil ya karanta,sai ya ce,MIMI momy nafisa ce, ki daga wayarta.na san za ta taimaka mana.ta tashi zaune ana yi mata karin ruwa.ta daga.cikin sauri momy nafisa ta ce, MIMI kuna ina ne yanzu?ta ce momy yaya dad?wane hali yake ciki?ta ce,dad dinki yana cikin matsananciyar damuwa.yana tunanin ko an kashe ki ne,ko an sace ki.kuma sun ce za su daura aurenki gobe,ko gawarki aka gani dai abbas ne mijinki.don haka ki rubuto masa text cewa kin gudu ne,don ba ki son abbas.ke ba za ki dawo ba har sai ya amice zai baki khalil.kin ji ko,ki yi haka yanzu.na san zai ce ki dawo.cikin kuka MIMI ta ce,ni fa na soma yin nadama momy.zan hakura ne kawai in auri abbas. [01/10 10:34 pm] Abdul: (19)Wallahi ina jin tausayin dad dina.momy nafisa ta ce,aa ki yi abin da nace. 'yan gidan su abbas din ma da suke ta zagin ki,wai kin bi namiji.wa ya san abin da za kuje ku yi?MIMI tana kuka tace shi ke nan zan yi momy.ta ce,yanzu nan za ki yi,MIMI tana kuka tace to Suna cikin yin musabaha don yin sallama message din MIMI ya shiga wayar dad dinsu.bai yi kasa a guiwa ba,ya bude ya soma karantawa kamar haka: Ka yafe ni dad in na bata maka.na yi kokari in yi maka biyayya,amma na kasa.ba na jin zan iya zama da abbas a matsayin mijina.zan dawo gida,in ka amince zaka bani wanda nake so.ya dago ya kalli alhaji lsa,wanda dashi suka zo kaduna,ya ce,ka gani ko? karbi ka karanta.ka gani guduwa suka yi ba sace ta yayi ba.ni kuma zan nuna mata cewa ta yi mummunan kuskure. Da kyar alhaji bishir ya kai cikin gida saboda ciwon kai.amma kafin ya kai tsakiyar falo,tuni ya zube kasa.sabon alamari ke nan wanda yata da hankalin mutan gidan.nan da nan aka yi asibiti da shi.ya farfado,inda aka tabbatar masa jininsa ya hau sosai. an gano yana da ciwon sugar.cikin abin da bai fi minti talatin ba,dukkan iyalansa sun samu labari kuka sosai hajiya sauda ta yi domin ta san MIMI ce silar komai. karfe sha daya momy nafisa ta kira na'ima ta ce,ga lokacinki fa yayi daga yanzu zuwa da safe.na'ima ta ce,shi kenan momy ya farka ne?ta ce,eh in ya farka yana tambaya ta wai ga shi gobe daurin aure.bai san yadda zai yi ba.na dai lallaba shi.ki shirya zan fita in sa hamisu direba ya dauko ki,don shi ya kawo su kawunku da suka zo biki.tana fitowa ta leka ta ce ma hamisu ya je ya dauko na'ima.alhaji lsa ya ce ta yi me da daren nan? momy nafisa ta ce,kuka take yi sosai.kuma ta ce tana da magana da shi,cikin kuka na'ima ta shigo dakin momy ta rungume ta,yi shiru mana.ai jikin da sauki. kalle shi har ya farka. Ta isa gurin sa,dad ta kama hannunsa.dad kar ka damu ni na amince in har abbas yana so na.gobe a daura auren da ni.wallahi dad bana son in rasa ka.ya yunkura zai tashi. [01/10 10:34 pm] Abdul: (20)Momy ta rike shi.ya jingina,ya kama hannuwan na'ima,da gaske kina son abbas?ta ce,ni ban san so ba dad.amma zan koye shi a gidan abbas.zan so shi in ya zama miji gare ni.alhaji bishir ya rumgume ta.na gode yata.allah yayi miki albarka.ya kalli momy ta ce,na ji.allah yayi miki albarka.kar ka damu,ka kira alhaji akilu din.bai san ma akwai matsalar bai san kana asibiti ba.ln ya zo sai ku tattauna.ya ce,haka ne. ke ma din allah yai miki albarka.momy nafisa ta ce, amin.ya ce,leka ki kira min alhaji lsa. nan suka shigo,ya sanar da su abin da naima ta ce,suka yi ta sa mata albarka alhaji ya ce,to kowa ya koma gida,insha allah,biki babu fashi.momy ta ce,alhamdulillahi ga shi da ma yan biki sun cika gidan,yan masari da yan malumfashi.hajiya binta da ma bata taho ba,tana shirin zuwa ta ji labarin batar amaryar,don haka ta dakata.yanzu kuma sai ga labarin ciwon alhajin don haka dole gobe sai abuja. A daren,alhaji bishir ya sanar da alhaji akilu komai. da yake kowannensu ba damuwar 'ya'yan bane,su dai hada surukuntar ne kawai don cimma burinsu.ba tare da neman shawarar abbas ba,ya amince da auren na'ima sai da asubahi bayan sun dawo sallah yake sanar da abbas din canjin da aka samu.nan take abbas ya ce, shi sam bai so na'ima alhaji akilu ya ce,ba damuwata ka so ta ba.ln aure ya dauru burina ya cika.ka aure ta in ya so daga baya ka auri wadda kake so.abbas ya ce,MIMI nake so.ln kuma ina auren kanwarta yaya zan yi in aure ta?ya kawo iyaka wuya,cikin fada yake cewa,kai ma za ka yi min irin abin da 'yar alhaji bishir ta yi masa ne?to bari ka ji. ba zan dauki rainin wayo ba.kawai kayi abin da nace. dukkan su ai mata ne.abin da waccan ke dashi,ma tana dashi.yanzu an daina auren soyayya,sai auren me zan samu.ka gane?na fada maka nasarar da zan samu ta hulda da alhaji bishir so kake sai ka ja min asara ne?abbas ya ce,shi ke nan dady,na yarda har da hawaye ya bar gurin.a dakinsa kuwa yaci kuka sosai domin ya kallafa rai a kan MIMI. [01/10 10:34 pm] Abdul: (22)Ba ki zo bada 'yata ta bata,amma da jin an ce mijinki babu lafiya,kin debo yara kun taho.sauda ta ce, shi ne dole na,yarki,ai ba dole na ba ce.suka gaisa ta ce,ina muktar?hajiya sauda ta ce,mun yi ta jiran sa bai karaso ba.na ce mu tafi,ya zo.sauda ta isa gurin mijinta ta zauna daf da shi.ya kama hannunta.har kin zo? ta ce,jiya ban yi barci sosai ba,amma yadda na ga jikin naka,alhamdulillah.ya ce, ashe ina da ciwon sugar ne.kwanaki kina ce min duk na rame.sugar?sauda ta tambaye shi.ya ce,tabbas har ya soma yi min yawa. yanzu dai likita ya dora ni kan magani da dokoki da kuma abincikan da zan kiyaye.hawaye suka zubo a idon sauda.ya dafa ta,aa kar ki yi kuka sauda,insha allah zan warware,ta ce, allah ya baka lafiya.ya ce, amin.ya kalli abba,ina takwarana?abba ya ce, suna gida.za su zo da mamansa.alhji ya ce,madallah,allah yayi maku albarka.kun ji abin da MIMI ta yi min ko?ya dinga kallon su da dai-dai,ya dan sunkuyar da kai.na san har da hakkinku.lna mai baku hakuri.abba ya ce,haba dady babu komai.allah ya ba ka lafiya.sauda ta ce,to yanzu ya ake ciki?ya ce, na me fa?ta ce na bikin ya ce,na'ima za a daura da ita.ya kalli abdulkarim ya nuna masa wayarsa.miko min wayar can.ya miko masa.ya bata,bude ki ga sakon da yarinyar nan ta turo min.hajiya sauda ta kammala karantawa cikin kuka.ta ce,alhaji ba zan gaji da fada maka,laifinka ne kai da nafisa ba.kun gina ta a kan yi mata duk abin da take so.ya kamo hannuwanta,na yarda laifina ne.nafisa ta biye min ne don ganin haka nake so. abba ya ce,to dady ka ce ta dawo mana.ln yaso ka bata shi wanda take so din,tunda na'ima zata auri wanda ba ta so din. ya kalli abba,ba canji ke nan.zan ci gaba da yi mata abin da take so ke nan?ai yadda ba ta yi min abin da nake so ba,haka nan ba zan taba yi mata wanda take so ba ai ta yar da wannan gatan da kanta.lta ma zan mata abin da ba za ta manta ba,kamar yadda ni ma ba zan manta da abin da ta yi min ba. hajiya sauda ta ce,yanzu a ina take?oho!in ji alhaji. [01/10 10:34 pm] Abdul: (21)Suna idar da sallar asubahi lsmail ya ce wa hamisu direban yara,don allah kai mu asibiti mu duba alhaji.har da kanin alhaji da 'ya'yansa mata suka tafi tare.sun samu alhaji yana salla.don haka suka zauna momy nafisa ce ta kwana a gurinsa.lta ma tana sallar ne.bayan sun idar ta leka ta ce.ku shigo mana.suka shiga suka gai da shi.ya ce. na samu sauki.nan da karfe bakwai zan koma gida.a ci gaba da biki kun ji na'ima ta share min hawaye ko? lsmail da bai san kan maganar ba,sai ya kalli alhaji daidai lokacin da kanin alhajin ke cewa,mun ji zata auri shi yaron da waccan ja'irar ta gudu domin sa.yanzu ai sai ta dawo.alhaji ya ce,ta dawo ina?ai ko ta dawo,ita ma sai nayi mata abin da ta yi min.suka ce hakuri dai za a yi.lsmail yayi wa alhaji addua.suka ce za su koma. alhaji ya ce,malam lsmail na gode.sai na zo. suna komawa gida lsmail ya kira layin hajiya sauda.har sau biyu bata daga ba.don haka ya bari. yana gugar kayansa,sai ga kiran ta.ya daga suka gaisa. ya ce,kin samu labarin ciwon alhaji?ta ce tun jiya.yanzu maga mu nan ni da yara za mu biyo jirgin karfe takwas.yaya jikin nasa?ya ce,da sauki.ta ce,an ji labarin MIMI?ya ce, eh to,na ji dai an ce tunda ta yi masa text ne cewa ba za ta dawo ba sai in zai yi mata abin da take so,shi ne ya fadi.amma yanzu na'ima ta yarda za ta auri wanda MIMI ba ta so. hajiya sauda ta ce,oh ni saude!allah ya shirya wannan yarinyar.shi ke nan sai mun iso. bakwai da rabi alhaji ya iso gidansa,jamaa sai shigowa suke.yayi wanka,ya karya.ya sha magani,ya dan kwanta kafin tara.daurin auren sai karfe biyu,in an idar da salla a babban masallacin abuja.tara saura hajiya sauda da abba da abdulkarim da su hasana da usaina suka shigo.na'ima ta rungume su hasanan,ta gai da hajiya ta ce,lna momy taku?ta ce,tana dakin dad.dukkan su suka shiga.ya tashi barci suna magana da nafisa momy nafisa ta ce,oyoyo, sannun ku da zuwa.nan yaran suka gai da ta,suka nufi gurin dadynsu.lta kuma ta ci gaba da yi wa hajiya sauda mita. [01/10 10:34 pm] Abdul: (23)Jiya dai an ce suna kaduna.hajiya sauda ta ce, allah ya kauta.daidai lokacin wayarsa ta yi ringing,momy nafisa ta shigo tana cewa, alhaji kana da baki. Duk tare suka fito.hajiya sauda da su hasana saman MIMI suka nufa saboda gidan da mutane.har an soma cin abinci dangin momy nafisa sun fi yawa. usaina ta kalli hajiya sauda bayan sun zauna,hajiya ki kira ta mana a waya,ki ce ta dawo.ni na ga na'ima kamar tana murna da hakan.ta ja mu tana nuna mana lefen sis MIMI,wai nata ne.ga mota can a gare ji,an zuba dukiya a gidanta. abdulkarim ya ce,ai ni na yi murna da faruwar hakan.shi dad din yanzu yayi nadama ai.abba ya ce,ni zan zo ma in ma koma ne fa hajiya.don ba zan kwana abuja ba. gaskiya tunda ya samu sauki,ga shi ma sai bikinsu suke yi.sai ga masu aiki da kulolin abinci,wai a kawo musu.hasana ta tashi ta shige dakin barcin MIMI. usaina ta biyo ta.hasana ta kalli usaina,gaskiya sis MIMI bata duba wa kanta ba. kalli fa dakinta.dubi duk nan bangaren ta ne,ya fi ko'ina kyau a gidan nan,amma ta kasa yi wa dad biyayya. allah ta ban kunya.usai ta ce,ai ga shi nan na'ima ta yi abin da ita ta kasa.na san ko moy nafisa za ta iya sa ta ko don su birge dad. Hasana ta ciro wayarta, mu gwada kira mu gani ko za ta daga.nan suka soma kiran layinta.yana ta ruri yana tsinkewa,ba ta daga ba.daidai lokacin MIMI tana gado asibiti kwance. damuwa ce ta sa take jin ta babu wani sauki.duk wanda ya kira,tana kallon kisansa.yanzu haka tana kallon lambar usaina, hawaye suka soma zubo mata.yaran da bata damu da su ba,ashe suna son ta.lta yanzu tana jira ne ta ji kira momy nafisa don ta san matsayin da take.ln dad dinta ya yarda,kai ko bai yarda ba,yadda take jin zuciyarta za ta koma gida ne kawai.khalil ya dauki wayar bayan ya ji shigowar sako.ya ce,sako ne dear.ki duba ko momy din ce ko?cikin sauri ta amshi wayar.usaina ta gani.har ta ajiye wayar sai kuma ta bude.ga abin da usaina ta ce: [01/10 10:34 pm] Abdul: (24)SIS MIMI DON ALLAH KI DAWO DAD BA LAFIYA YA FADI SABODA JIN CEWA KIN GUDU NE,BA SACE KI AKA YI BA.ANJIMA ZA A DAURA AUREN NA'IMA DA ABBAS. Ihun da MIMI ta yi ne yasa khalil mikewa. tambayar ta yake yi,me ya faru?cikin kuka take fadin, dad ba shi da lafiya.ni zan koma gida ne kawai.khalil hankalinsa ya tashi.ya shiga lallashin ta.ki yi hakuri mana dear.za mu koma ai.amma bari su neme mu.ta ce,ba ni wayata.bari in kira dad din.ya ce,aa kar ki kira shi tsaya ki ji.MIMI ta tsaya tana kallon sa ya ce,ki kira su usaina din kiji komai daga bakinsu.nan suka kira layin.hasana ce ta daga wayar:MIMI cikin kuka ta ce, usaina!hasana ta ce,ni ce ba usaina ba ce,ta ce,yanzu wane hali dad yake ciki?hasana ta ce ya ji sauki,babu laifi,amma ya kwana a asibiti ne.ya ji zafin sakon da kika turo masa cewa kin tafi saboda wani.usaina ta amshi wayar tana cewa,sis MIMI ki dawo kawai zai fi miki. dad ya ce,ba zai damu daki dawo ko kar ki dawo ba, don na'ima ta gama fitar da shi kunya,ta amince anjima za a daura aurenta da abbas.MIMI ta kasa magana kuka kurum take yi.suka nufi hajiya da wayar usaina ta ce.ga sis MIMI tana jin lokacin da hajiya take fadi me za a yi mata don ga ta a waya?abin da ya kamata ta yi ta kasa.don haka bani da lokacin sauraron ta.ubanta ma da ya nuna mata so,ta yi masa butulci, bare wani.da allah kashe wayarki!hasana ta katse wayar.kuka sosai MIMI dinga yi tun khalil yana bata hakuri,har yayi shiru ya tsaya yana kallon ta.sai da ta gaji don kanta,ta kalli khalil ni zan koma gida.ta sauka ta soma duba jakarta.zan koma gida khalil in yi wa dad dina biyayya. amma har abada ka sani ina son ka a cikin zuciyata. ya ce,ki tsaya ki ji sauki mana.ba a sallame mu ba.ta ce,ba na bukatar sai na samu sauki zan tafi.ka zo ka kai ni gurin da zan hau mota.tana daukar jakarta,ya nufi ofishin likitan,ya sanar da shi cewa wai tana son ta tafi.lokacin da likitan ya fito,ta kai harabar asibitin.suka sha gabanta, [01/10 10:34 pm] Abdul: (25)Khalil ya ce,MIMI ki saurari likitan mana.ta ce, likita ka yi min afuwa, awanni suka rage a daura min aure.ka san cewa guduwa nayi?babana ya fadi sbd na gudu.likita ya ce,na ji zaki koma,amma ki bari ki gama karbar allura. MIMI ta ce,bari in tafi.na yi nadama sosai da na bijire wa mahaifina.zan koma in ba da hakuri,in nemi ya yafe min.ya aurar da ni ga ko waye yake so. Dole likitan ya ce,ka bar ta ta tafi kawai.ba shi da zabi,dole ya koma ya dauko tasa jakar suka je titin bypas don samun motar zuwa abuja.suna cikin motar ne ta sake kiran usaina,karfe nawa za a daura auren?ta ce,bayan azahar ne a babban masallaci.mu ma hajiya ta ce,da an gama daure aure za mu koma gida.ta ce,shi ke nan sai na iso.ta kalli khalil,ina za ka tsaya?ya ce zan je har gaba mahaifinki, yayi yadda ya ga dama da ni.amma na gama hango mutuwata,in har na rasa ki. ta kalli agogo,yanzu sha biyu da wani abu,kana ganin har za mu je abuja ba a daura da na'ima ba?ya ce zan fi kowa so in hakan ta kasance.ki yi adduar allah ya sa ni ne mijinki.daya saura alhaji ya shigo gidan don shirin zuwa masallaci ko kuma in ce gurin daurin aure.daidai lokacin ne kuma hajiya binta ta shigo,ita da yaranta. mamakinta da tunaninta alhaji ya rasu ne?ko an ga amaryar ana ci gaba da biki,shi yana asibiti?ta ga harabar gida an zuba kujeri da rumfuna,ga mutane da yara.suka shiga falo.nan ma duk jamaa.dakin nafisa hajiya bintar ta nufa.cike da manyan kawayenta,tana zaune a gaban madubi,ta yo wanka ana yi mata kwalliya.hajiya binta ta ce,nafisa wai biki ake yi ne?ta mike da sauri,sannun ku da zuwa kun iso?eh,kin san tafiyar mota,tun bakwai muka fito.ban gane ba,wai bikin ake yi ne?eh bikin na'ima.cikin mamaki, hajiya binta ta ce,na'ima kuma?momy nafisa ta karaso gurin ta cikin murmushi,eh,kin san MIMI ta gudu.shi ne na'ima ta zabi ta fitar da mahaifinta kunya. hajiya binta ta ce,to shi alhajin wane asibiti yake?ta ce,ya shigo yana gefensa,zai yi wanka. [01/10 10:34 pm] Abdul: (26)Tun jiya aka sallamo shi.yana jin na'ima ta yi wannan furucin,sai ya gyare.wata daga cikin matan da ke zaune a kan gadon ta ce,yarinya ai ta share wa ubanta hawaye. wata ta ce,ai ko ta yi saa jiya maigidana ke ba ni labarin irin gudummawar da abokan kasuwancin alhaji suka yi ta ba amarya. babban dan kasuwan nan wanda yafi kowa shahara a afrika an ce zunzurutun kudi miliyan ashiri ya ba da, banda motoci.hajiya binta dai ta ce,bari in duba alhaji. momy nafisa ta ce,to ki duba shi.yawwa hajiya sauda ma suna saman MIMI to kawai hajiya binta ta ce, ta nufi sasan alhajin,cikin al'ajabi.gani take yi momy nafisa murna take yi da aure ya juye a kan 'yarta. Ta kalli yaranta ku hau saman sis MIMI,hajiya sauda tana nan.da farko har za su noke,don suna tsoron MIMI,tunda bata kula su.amma jin cewa sauda tana nan,sai suka nufi saman cikin murna.suna son hajiya don in sun zo hutu ba sa son tafiya.ta iya tafiyar da yara sosai. Ta samu alhaji ya fito wanka,ya ce,aa ku ma kun iso?ta ce,eh,alhamdulillah sam ban zaci zan samu jikinka haka ba.na ji an ce sugar,mene ne mene ne.ya ce,da sauki.da ma karin damuwar kunyar da MIMI ta so ta ba ni ce,sai kuma na'ima ta zo ta tare matsalar.yanzu dai burina a daura auren nan.zan koma asibiti,likita ya duba ni yadda ya kamata.ta ce allah ya sawwake.to,yanzu mene ne labarin MIMI? ya kalle ta.bayan ya gama saka wando,yana tura singiletinsa,ba ni da labarinta, kuma bana bukatar in sani.hajiya sauda sun zo da su abba.lna zaton suna saman.hajiya binta ta ce,to bari in ji gurinsu.ta samu su abba za su fito.nan suka tsaya suka gaisa.suka ce bari su fita su yi salla.ln an daura aure za su wuce.hajiya binta ta ce,wai ni hajiya yaya lamarin ya zama haka?ba kya tunanin cewa nafisa ta san komai a kan gudun MIMI ko bijirewarta?ba na tunani,in ji hajiya sauda.ba na zargi a kan abin da ban ji ban gani ba.abin da na sani kawai alhaji shi ne silar komai.haka nan kullum ina cikin adduar allah ya shirya MIMI.ya bata miji na gari. [01/10 10:34 pm] Abdul: (27)Ban yi fushi ba ko da aurenta bai kasance da dan gidan minista ba.kila ba alherinta.hajiya binta ta ce, haka ne allah zai amshi adduarki,domin bakin mahaifiya yana da karfi a kan yara.hajiya sauda ta kalli usaina wadda ke dube-dube a kan kwamfutar MIMI,ta ce,ku sa wa yaran nan abinci ga shi nan.hasana ta sa wa hajiya binta.hajiya binta ta ce,ni duk damuwata ta a ba na jin yunwa.sauda ta ce,damuwar me,bayan ga jikin mijinmu da sauki? hajiya binta ta ce,batan MIMI ai abin tunani ne.ko kusa,in ji hajiya sauda,guduwa ta yi,ba bata ta yi ba.kin ga kwanukan da su abba da abdulkarim suka ci?cewa suka yi tunda jikin dadynsu da sauki a sa musu abinci su ci.ni ce ma ban riga na ci ba.na fi son abu mai ruwa da safe,mai kuma dumi kamar shayi.hajiya binta ta ce,ya fi dadi ai hasana sa min wainar allah ya rufa asiri.suka ce amin. Duk da gudun da motar da su MIMI suka shiga take yi,gani take yi kamar ba gudu ba.ba ta taba shiga motar haya ba tunda aka haife ta sai yau.bugu da kari bata taba shan wahala ba a rayuwarta tunda take kamar wannan lokacin da ta bar gidan iyayenta.shiru da ta yi daga zaune abubuwan da take lissafawa ke nan.duk da tsananin son da take yi wa khalil ba ta jin za ta sake barin gida,ba tare da yardar mahaifinta ba.abin nufi ba tare da sun yi mata aure ba.cikin haka ne ta ji mutanen cikin motar suna salati,wadansu kuma wadanda ba musulmi ba suna ambatar abin da suka yi lmani da shi.ta zaro idanu,lokacin da ta ga motar ta su ta saki hanya, sosai ta firgita,ta soma fadin wayyo allah!daf da wani rami motar tasu ta tsaya cak.wai ashe taya ce ta fashe,tana duniyar tunani,bata ji kara ba.babu wanda ya zaci motar nan za ta tsaya.motoci suka tsaya ana ta yi musu allah ya kyauta.hankalin MIMI ya sake tashi.har aka canza taya jikinta bai daina bari ba.haka nan duk lallashin da khalil ke yi mata bata daina kuka ba.shi kansa yayi dana sani sosai na tahowa da ita.da kyar ma ta yarda ta sake shiga motar suka nufi hanya.karfe biyu daidai aka daura auren. [01/10 10:34 pm] Abdul: (28)Karfe biyu daidai,aka daura auren na'ima da abbas.daurin auren mai dimbin tarihi irin manyan mutanen da suka halarci gurin.babbar matsalar angon yaki halartar daurin auren,yana gida kwance,lta kuwa na'ima suna can gidan yayar mommy nafisa suna cashewa da makadan da suka dauko.sun koma can ne wai kar a ce suna murna da auren ya koma kan na'ima.wani karin abin aushin ma na'ima ita da abbas din ba su taba yin magana ko da ta waya ba. kuma daga momy har na'ima ba su taba tunanin cewa wannan wata matsala mai zaman kanta ba ce.uku saura tasi din da suka dauka shata ta karyo kwanar layinsu.kasancewar layin baya fita,sai ta tsargu da ganin motocin da aka ajiye a layin,ga mutane ta ce,me ke faruwa?ba dai dady ya mutu ba?dan tasi din ya ce,gaskiya ina zaton ba mutuwa ba ce,sai dai biki.ta ga nisan su karasa har kofar gidan,don haka ta ce,tsaya ina zuwa.yana tsayawa ta dauki jakarta,ta zura da gudu.kofar gidansu duk jamaa.gate dinsu a bude.tana shiga da malam lsma'il ta soma yin ido hudu. mutane ba su gane ta sosai ba,saboda ita ba maabociyar saka hijabi ba ce.lsma'il ya ce,daga ina kike?ta ce,me ake yi a nan gidan?ya ce,auren na'ima ta zaro ido,an daura da na'ima?ya ce,tabbas!sai ta juya,yana cewa ke!za ta fita ke nan su abba da abdulkarim za su shigo don yin sallama da hajiya sauda don basu so su kai wannan lokacin ba a abuja.dad ne ya tsare su,wai sai an gama daurin aure.yana ta nuna su ga abokansa, wadanda a da MIMI suka sani,basu san ma yana da wasu yaran ba.sai abokansa na tun farko irin su alhaji lsa.abdulkarim ne ya gane ta,don abba ne a gaba,amma bai kalli fuskarta ba,kuma hijabin da ta sa ya kara boye ta.da karfi abdulkarim ya rike hijabinta,har ta dan gota shi.ya jawo ta ya falla mata mari.sai da ta ga wani haske,ya ce,gidan uban wa za ki koma?ta tsala ihu,wanda ya janyo hankalin duk mutanen da suke harabar gidan.lsmail ya iso gurin yana cewa a yi mata hakuri.abba ya ce, haka shi ne daidai da ita. suka iza keyarta tana kuka, suna rankwashin ta,gami da zagi. [01/10 10:34 pm] Abdul: (29)Momy nafisa ta fito da gudu,domin wata kawarta ce zata tafi gida,sun yi sallama.amma tana fitowa ta ga MIMI a hannun su abba.sai ta koma da gudu ta sanarwa momy nafisa cewa ga fa MIMI.da farko momy nafisa idanu ta zaro,tana cewa,na shiga uku!me zai sa yarinyar nan ta dawo yanzu?sai yarta ta ce,kar ki damu tayi ta dawowa.an riga an daura aure.momy nafisa ta ce, kuma fa haka ne.bari in fita in ga yadda wannan fim din zai kare.suka sa dariya gami da shewa,ita da kawayenta.ta kalli wata hajiya nana,ba ni wayata!ga ta nan kusa da ke in sanar da ubanta.ln ya zo fim din zai fi dadi kallo. shine nan ta fito da gudu.a daf da hawa sama ne ta iso ta rungume MIMI ta fashe da kukan karya.lna kika shiga ne yata?me ya sa kika yi haka?abdulkarim ya ce,momy sake ta mu je sama.sake komawa za ta yi.abba cikin fushi ya ce,ki wuce mu je mana!don shi yana jin haushin momy nafisa ta taimaka gurin lalacewar MIMI.momy nafisa ta sake ta suka iza keyarta zuwa sama. abdulkarim yana rike da jakarta.momy nafisa cikin kukan ta kira alhajin ya ce? tana sheshekar karya ta ce,ka zo gida,ga MIMI nan ta dawo su abba suna ta dukan ta ya ce,haka shi ne daidai.na gode musu.ya kashe wayarsa. hajiya sauda tana inda take zaune ba ta tashi ba tunda ta yi sallar azahar sai ko ga MIMI ta shigo da gudu.a gaban hajiya sauda suka yi mata duka.dama kowannensu yana da haushinta.hajiya binta ce ta kwace ta.ko kallo bata ishi hajiya sauda ba,bare ta yi magana.hasana da usaina sun yi jungum-jungum cikin tausaya mata ta rakube gefen kujera tana ta kuka. abba ya ce,wawiya mara hankali kin bata sunanki a duniya.kin zubar da mutuncin kaki.abdulkarim ya ce,sosai kuwa,duk yarinyar da ta gudu ta bar gidan iyayenta,ai sunanta yar lska.hajiya binta ta ce, gaskiya baki kyauta ma kanki ba MIMI.ba ki yi wa mahaifinki adalci ba lrin son da alhaji ya nuna miki,ln kina da hankali,ko wuta ya hura ya ce MIMI shiga,ba za ki yi tsalle ki shiga ba,bare aure? [01/10 10:34 pm] Abdul: (30)Sai lokacin hajiya sauda ta yi magana,ta ce. ai shi yasa haihuwa ma da yawa take da dadi.ln wani ya saka kuka wani sai ya share maka hawaye.na'ima ta kai yar albarka.allah ya bata zama lafiya a gidana,ke kuma sai ki zauna mu gani,wanda kika bijire mawa din kika watsa masa kasa a ido,kika so ki kunyata shi zai ci gaba da jiyar dake dadi,gami da nuna miki kauna kamar da. Daidai lokacin alhaji ya shigo yana cewa,ba ta da mazauni a gidana.ta zo ta fita ta ko inda ta fito.na sallamawa duniya ita!hajiya binta ta ce,haba alhaji wannan ma ai ba mai yiwuwa ba ne.ka yi mata afuwa,ta yi kuskure.alhaji ya isa gabanta,ke khadija!na ce ki zo ki bar gidana!sunan uwata kika ci,ni uwata ta dade da mutuwa.don haka yadda kika yi min abin da ba zan manta ba.haka nan ke ma zan yi miki abin da ba za ki manta ba.MIMI ta mike ta zo gabansa tana kuka a tsugune,dad don allah ka yafe min.wallahi dad na yarda na dawo,zan auri duk wanda kake so.dad ya ce,me abbas zai yi da ke a halin yanzun?kin je kin kwana da wani ki zo ki ce kin yarda!cikin tashin hankali MIMI ta ce,wallahi ban kwana da wani ba.na rantse maka dad! hajiya sauda duk dauriyarta ba ta san lokacin da ta soma zubar da hawaye ba.su usaina suka je jikinta suna bata hakuri. abba ya ce,daddy to kawai ka daura mata aure da shi wanda ta bi din mana.dad ya sake daga murya,har abada wallahi!ba zata aure shi ba.yadda bata yi min abin da nake so ba,ita ma har abada ba zan taba yi mata wanda take so ba. momy nafisa ta shigo tana kuka,tana ba alhaji hakuri. ya ce,na yi rantsuwa,yau dole yarinyar nan ta bar gidana,ko da ita kadai na haifa.yarana ashiri da biyu. don na rasa ita kadai bana jin cewa nayi asara. Hajiya binta ta ce shi ke nan za mu wuce da ita gidana can malumfashi.ya ce,gidanki ko gidana?can ma gidana ne,don haka ba ta ba shi.ta gama cin arzikina,don ko gidan mahaifiyarta na yi mata tsakani da shi.abba ya lumshe ido,yana tunanin dad ya tsaurara da yawa.don haka ya ce, [01/10 10:34 pm] Abdul: (31)Dad shi ke nan bari mu wuce da ita,in tafi da ita gidana.alhaji bishir ya girgiza kai,ban lamunta ba.ln kuma ka yi hakan ba zan yafe maka ba.ka sa min idanu kaga irin hukucin da zan yi mata.hajiya binta ta ce,don allah alhaji ni dai kar ka ce zaka kore ta a gidanka,ka ji?momy nafisa ta shigo cikin kuka tana cewa,don allah alhaji kayi hakuri,ka yafe mata,tunda na'ima ta riga ta auri abbas din sai a bar zancen.MIMI ta zo tayi shirin komawa makaranta.cikin zafin rai,ya waiwayo,wace makarantar?nafisa za ki sa in tafka miki ashariya!ya nuna MIMI,wannan yarinya don ubanta ta gama boko a gidana,ta je tayi zaman aure.yau din nan zan aurar da ita ko ma ga uban wane ne.bana son kowa ya ce,min uffan.a kalle ni da hukuncin da zan yanke duk inda na bada ta da sunan aure.na gindaya allah ya isa ga duk wani ahalina da ya je,ko na sani ko ban sani ba.sai lokacin hajiya sauda ta daga ido ta kalle shi,duk da halin MIMI,amma da da mahaifi sai allah.ta ce,alhaji kana ganim wannan hukuncin bai yi tsauri ba?a fusace ya kalle ta,bana bukatar ki sa bakinki a cikin lamari,kamar yadda tun farko kika ce ba ruwanki ke yar shawara ce.to don allah ina son shawarar ma ki bar ta.kina da kima sosai a idona bana son mu fara abin da bamu yi a da ba.za ta yi magana.abdulkarim yayi mata alama da hannu wai ta yi shiru.don haka sai ta kulle bakinta.shi kuma alhajin ya fita yana fadin zata gane ba ta da wayo. Hajiya sauda ta kalli MIMI maganinki ke nan!hajiya binta ta ce,ni fa ina zargin cewa MIMI shigo-shigo ba zurfi aka yi mata. momy nafisa ta ce,me kike nufi?ke nan ni na sata bijirewa mahaifinta?hajiya binta ta ce,komai zai iya faruwa.yaran da suka tashi a karkashin tarbiyyarki me zai sa na'ima ta lankwasu, amma MIMI ta kasa lankwasuwa?hajiya sauda ta ce,ku bar zance nan.laifi dai duk na MIMI ne.ban ji haushin alhaji ba,duk hukuncin da ya yanke mata.da ta tsaya a kan bata so,sai ya fi mata a kan gudun da tayi.wa ya san abin da ya faru a gudun da ta yi?MIMI ta ce,hajiya ku yarda da abin da zan ce [01/10 10:34 pm] Abdul: (32)Na rantse muku babu wani abu da ya faru da ni.ni kadai na kwana a dakin da na sauka.abba ya ce,kin dai cuci kanki da kika sa kafa kika bar gidan mahaifinki,kika bi wani kato. kuma duk sunan da aka kira ki da shi dole ki amsa. abdulkarim ya ce.alhakinmu ne yasa ta yi wa alhajin haka.don haka ni duk mai zai mata ba zan ji haushi ba.usaina bata ce,yaya ni kuma a nawa ganin tunda wannan ne karo na farko da sis MIMI ta soma saba masa da ya yafe mata,sai in ta kara.momy nafisa ta ce,yawwa usaina,abin da ni ma nake so ke nan. shi kuwa alhaji ya fita ne da niyyar ba ta duk wanda ya ci karo da shi.babu abin da ta fi tsana a duniya kamar talaka,don haka za ta dandana rayuwar talauci.har zai fita gate,sai idanunsa suka hango lsmail yana alawala,tamkar an tsai da shi ne,ya tsaya cak, yana kallon lsmail.sai ya tuna ta taba furta masa cewa ta tsani lsmail. murmushin takaici ya yi,ya ce,malam lsmail yana kan wanke kafafu,ya dago da azama ya karasa,ya mike cikin girmamawa yake cewa,alhaji barka da arziki.na ga MIMI ta dawo.alhaji yayi yake,tare da cewa,barka ka dai.wato malam lsmail kamar kai ne kake fada min an aurawa budurwarka wani ko?lsmail sam baya ko son tuna lamarin don haka sai ya ce,ni ne alhaji,amma na dangana.haka allah ya hukunta.alhaji ya ce,wane ne wakilinka wanda zai amsar maka aure?gaban lsmail ya fadi,cikin in-ina ya ce,alhaji ban gane ba.ka ce mene ne?ya ce,kar ka damu,in mu i sallar laasar ka samu ko baba maigadi ne ka wakita shi ya amsar maka aure.kar ka ji mamaki hausawa suna cewa wani hani ga allah baiwa ne.sai kawai alhaji ya wuce ya bar lsmail tsaye,zuciyarsa cike da tambayoyi,amma bai san wa zai amsa su ba. Maigadi da hamisu suka nufo lsmail suna cewa, malam lokaci fa,baka yi kiran salla ba.maigadi ya ce,kodayake alhaji ne ya tsai da shi ko?lsmail ya ce,ku ji alhaji wai in samu wanda zan wakilta ya amsar min aure,wai ko kai. su ma suka cika da mamaki.hamisu ya ce,ko cikin yan aikin gidan ne tunda ya san kayi rashin budurwarka? [01/10 10:34 pm] Abdul: (33)Isma'il ya ce,ni don na riga nayi fushi da soyayya, don ma kar in ce na daina yin ta ne,a ce na dauka da zafi.hamisu ya ce,tunda ya zabe ka zai yi maka alkhairi kar ka ce aa,ka yi shiru.lsmail ya ce,ba zan iya musu da shi ba,dana yi tun tuni.ku taya ni adduar allah yasa in ci jarabawar don ina cikin gwaji.suka ce,amin allah ya sa ka ci. bayan sun idar da salla,alhaji ma ba a nan yayi sallar ba.kamar minti goma,sai ga alhaji da abokansa hudu da kuma kaninsa kawu shafiu wanda daki lsmail yake kwana tunda suka zo bikin.nan alhaji ya ciro naira dubu talatin,ya mika wa maigadi.sadakin malam lsmail ne.ga wanda zai ba da auren nan,ya nuna kaninsa cikin masallaci suka koma,inda aka daura auren KHADIJA DA ISMA'iI duk ba su yi saurin dago wace ce khadija ba,saboda sunan MIMI ya boye.sun fito suna tambayar juna,alhaji kuma da kaninsa suka shiga gida. daki lsmail ya shiga yana kai-komo a fili ya ce,kaddara ta kawo ni abuja.ya dauko wayarsa yana ta zufa,ya kira mahmud ya sanar da shi komai.cikin murna ya ce, allah ya sanya alherh.lsmail ya ce,ba na son wulakanci jaje ya kamata ka yi min ba murna ba.mahmud ya ce bari in sanar da malam, in kuma je gida yaya amina in fada mata.lsmail ya ce,ni damuwata ko daki ban kama haya ba ban san ma yaya zan yi ba.amma komai ake ciki zamu yi waya.alhaji kam da ya shiga ciki,shi da dan uwansa kai tsaye suka wuce saman MIMI,inda su hajiya sauda suke.alhaji ya ce,mika wa binta sadakin, duk suka zura ido,hajiya sauda salla take yi,amma sai da ta ji kamar ta fadi.momy nafisa da ke biye da su alhajin don tana falon kasa da baki suka shigo,ta ce,wane ne mijin alhaji?ya ce,zai shigo ai lna take MIMI?hasana ta ce,ta shiga cikin tana wanka.ya ce,to in ta gama ku fada mata ta shirya maza-maza alhajin ya sake sauka ya bar su nan cirko-cirko shi ma dan uwan ya basu kudin,ya fice. [01/10 10:34 pm] Abdul: (34)MIMI tana fitowa wanka,hasana tana shiga dakin ta ce,in ji dad ya ce ki shirya.MIMI ta zaro idanu, zuwa ina?hasana dai ta ce,haka dai ya ce,amma ban sani ba.riga doguwa ta zura ta zauna bakin gado tare da yin tagumi.hajiya sauda ta idar da salla ta zabga tagumi,tana hawaye,lalle alhaji.jim kadan ya sake hawowa, wai ina su abba ne?usaina ce ta iya cewa,sun tafi tun dazun.sun ce za su je suyi salla su wuce.ya sake sauka ya fita.hamisu ya samu a bakin gate,ya ce, malam hamisu ga shi ka je ka cika tankin motarka.don allah ka zo ka kai amaryar katsina.lna shi lsmail din yake ne?hamisu ya ce,yana dakinsa.ya ce,to ka je ka ce masa na ce ya shirya kayansa,ya zo ina nemansa.yan kayansa da ma basu da yawa,ya tattara su,ya zuba a jaka,ya fito ya tsaya a wajen su maigadi,shi kuma hamisu ya tafi siyan mai. Alhaji ya sake fitowa ya yafito lsma'il da hannu. lsmail ya nufi alhaji cikin faduwar gaba yana cewa,kaddara da ta same ni,allah ka duba min.ya isa gurin alhajin.ya ce,biyo ni. suka ratsa falon.har yanzu da mutane,amma sun ragu ba kamar dazun ba. matakala alhaji ya soma takawa,shi ma ya bi shi.ya waiwayo ya yi masa alama da kai. suna shiga alhaji ya kalli usaina, kira min MIMI.hajiya binta ta ce,alhaji wai me kake nufi ne?momy nafisa ta ce,kana nufin wannan ne mijin? usaina ta shiga ta same su da hasana ta ce,sis MIMI dad yana kira.da sauri ta mike,kanta babu dan kwali,ta fito a firgice.duk zatonta zai ce ta koma gidan mamanta ko gidan hajiya binta.tana fito ta kalle shi,ga ni dad.ya ce,ki shirya ga mijinki nan za ku wuce.ta zaro ido,tare da fadin dad me ka ce?na shiga uku!dan da nan sai kururuwa,ta zube kasa.su hajiya binta suka nufe ta, suka daga ta suna salati. Momy nafisa tana fadin sam alhaji ba zai yiwu ba. tsaki ya ja,kar ki bata min rai nafisa.ku yayyafa mata ruwa ta farfado da wuri.ku hada mata komai nata, katsina ba nan ba ce.ya kalli lsmail,wanda tsabar firgici ya hana shi magana, ya ce,kai kuma daga yau na sallame ka daga aiki. [01/10 10:34 pm] Abdul: (36)Kuka MIMI ta saka. momy nafisa ta shiga cewa, ai ni kuma na shiga uku,watan kuma nawa ne tunda na'ima ta auri abbas, amma ia na ga dai ita MIMIN ba son shi take yi ba. ta ja tsaki,ta fice fuu.su hasana ne suka shiga shirya wa MIMI kayanta na sawa da irin abin da ya danganci na karatu.tana ta kuka alhajin ya sake sawowa lokacin hamisu ya dawo.ya shiga har dakin MIMI ya ce,ta ba shi katinan ATM duka.ta ba shi tana kuka tana rokon sa.ya amshi duk wani abu da ya danganci dukiya. gwalagwalanta kuma hajiya sauda ta amsa. hasan suka ce hajiya da kin bar mata.ta ce,duk ku rufe min baki.suturun MIMI ma ba duka suka dibu ba.an dai cika duk akwatunanta. takalma da kayan shafa duk an diba.sai lokacin ta tuna da wayarta.jakarta kuma da kudi,ta kalli hasan, ina jakata?hasana ta fita falo ta dauko mata.sai ta tura ta cikin wata jakar bayan ta cire wayarta wada take a silent.miss call din khalil ya fi hamsin.kuka ta soma.a zuciyarta ta raya yanzun kam babu makawa za su gudu. Haha aka yi ta fita da kayan MIMI ana zubawa a bayan mota da kuma bayan boot.lta kuwa banda kuka,babu abin da take yi. hajiya binta ta yafa mata mayafi.dad da kansa ya tasa ta har mota.duk 'yan bikin sun fito sun yi cirko-cirko suna kallo.ya ce,ko da sunan wasa ba na bukatar sake ganin ki a gidana har sai in ni na bukaci ganin ki.ya dubi lsmail,kai ma ina kara ja maka kunne ka kula,don na san sai ta ce za ta gudu.ya ce,insha allahu alhaji,har motar za ta tashi,sai ga hajiya binta da gudu da kudin sadakin ta damka wa MIMI,ga shi an manta ne.MIMI ta amsa don ta san tana bukatar kudin. motar babba ce,cikin ta da boot dinta duk kaya ne,sai gurin da mutum biyu za su zauna,MIMI ta zauna,lsmail yana gaba tamkar zai saka ihu bakin ciki.alhajin ya sake zuwa kusa da shi,na ga duk ka damu.yanzun mene ne babbar matsalarka? lsmail ya dube shi da sauri,babbar matsalata ita ce inda zan ajiye ta.ya ce, ba kuna da gida ba?ya ce, muna da shi,amma dakina a soro yake.alhaji ya ce,kar ka damu,ka ajiye ta a nan....! [01/10 10:34 pm] Abdul: (37)Ya ce,shi ke nan alhaji na gode.tunda suka taso MIMI kuka take yi har suka yi nisa.lsmail sai dai ya waiwaya ya kalle ta,ya kasa yi mata magana. tsakani da allah shi tsoron ta ma yake yi yanzun. hamisu direba ya ce,ka bata magana mana.ai sai ka lallashe ta.lsmail ya ce bar ta kawai ta yi ni kaina ji nake tamkar in saka kuka wallahi.hamisu ya saki dariya,ya ce wane irin kuka kuma?kai ko yau da wanda ya kai ka farin ciki? tsaki ya saki,ya ce,yau sai dai in daidaita ta da ranar da mahaifiyata ta mutu. hankalin MIMI ba ya tare da su don haka ba ta san me suke fadi ba.ta ciro wayarta,ta cire ta a silent. layin khalil ta soma kira.a ringing na biyu ya daga cikin sauri ya ce,MIMI kina ina?ta ce ka san wani abu ne?ya ce,aa ta ce yanzu muna hanyar katsina.ka shigo motar katsina ka biyo mu,zan ta yi maka kwatance.za mu bar garin nan.ya ce,shi ke nan.ln ban samu ta katsina ba,za hau motar kaduna.ln na sauka komai dare zan hau ta kaduna.ln ban samu ba,zan je gidanmu,ko a boye ne in dauki mota.ta ce,kar ka je gida a gan ka.ba zan so su tsare ka ba.abubuwa da yawa sun faru zuwa na gida.na yi danasani matuka, amma in mun hadu za kaji.don allah ka yi alkawarin za ka zo?ya ce,in biye da ke,kar ki damu.ta ki fada masa cewa an daura mata aure ne.kar ta kashe masa guiwar zuwa gurinta. Su kuwa su hajiya sauda nan take suka soma shirin tafiya su ma.hasana da usaina suka zazzabi kaya cikin kayan MIMI,suka fito.sam hajiya sauda bata bi ta kan alhaji ba,ta ce, su tafi kawai ko a motar haya ne.momy nafisa dai ta biyo su tana don allah su kwana. hajiya binta dama ko sallama ba ta yi wa nafisa ba.sauda ce ta tsaya yin sallama.nan take ta dauki waya ta soma kiran alhaji.ya daga ta ce masa,ga fa su hajiya sauda nan za su wai tafi gareji su hau mota.nan da nan ya kira hajiya sauda wai su jira karfe shida zai yi musu booking din jirgi.ta ce, wa hajiya binta,ba komai mu jira.ai shi mijinmu ne.dole mu ji maganarsa.hajiya binta ta ce,shi ke nan. [01/10 10:34 pm] Abdul: [7/27, 11:10] A~PROF: (38)Shida daidai suka nufi katsina a jirgi.su kuwa su na'ima daidai lokaci suka dawo gida don za a kai ta gidan miji.nan fa aka turo motoci don daukar amarya. an dauke ta zuwa gidanta da ke asokoro.jamaa sun yaba gidan.ga motocinta guda biyu,daya na lefe,daya ta gurin dad dinsu. kawayenta da yan uwa sai murna suke yi mata.karfe tara daidai abokan ango suka rako shi zuwa dakin amarya.ango abbas wanda yake jin yau tamkar ranar mutuwarsa ba ranar aure ba,ya zauna a falon yana kallon su usman suna yi da kawayen na'ima.shi haushi ma suke ba shi kwarai.ya kosa su gama shirmensu su tafi don ya gaji,barci yake ji. suna tafiya,ya nufi sama inda nan ne dakinsa da komansa yake yayi kwanciyarsa,ya bar amarya tana ta jira sa.duk da azabar daurin dankwalin kanta ke yi mata,shiru da ta ji yayi yawa,shi ne ya sa ta tashi tana lekawa har sha biyu.sai lokacin ta kira momy nafisa.lta ma lokacin tana dakin dad,wanda ke kwance jiki babu dadi.ta daga wayar ta ce,na'ima yaya ne?na'ima ta ce,momy ban gan shi ya shigo ba.tunda ya tafi raka abokai.ta ce ki duba dakinsa mana.na'ima ta ce,ai ban san ina ne dakin nasa ba.ta ce,ki duba mana,ke da gidanki.ni ina nan gurin dad dinku ne, jikinsa babu dadi sam. na'ima ta ce to a gai da shi. Daga nan ta soma neman dakin maigidan. ta binciko dakin mijin,sai dai yana kulle.ta kwankwasa sau uku,yayi magana cikin dakewar murya,waye a nan?ta ce,ni ce.ya ce,ke ce wa?ta ce,na'ima.ya ja dogon tsaki,don allah bar nan gurin.waye ya neme ki da za ki zo ki ta da ni daga barci?ta yi tsuru cikin fargaba.ta ce,yi hakuri,ina jin tsoron dakin ne.ya ce,ina ruwana da tsoronki.da ma abin da kike sone kara taba min kofa.dole ta juya,ta sauka ta koma dakin cikin firgici ta kulle,ta sake kiran wayar momy a kashe.sai ta hakura ta kwanta. Zainabu tana kasa inda kicin dinsu yake, tana ta kici-kicin dora katuwar tukunyar da suke dafa abinci.mudu takwas suke dafawa in shinkafa ce suna yin tazarce ne daga rana har dare.ln tuwo ne, [7/27, 11:11] A~PROF: (39)Suna tuke mudu hudu ko hudu da rabi.tana hada ice,alhajin ya shigo.sallamar sa kawai ta ji,gabanta ya fadi take ta soma kuka,don ta san abin da ya maido shi gida,ci gaba ta yi da aikint uwargida wadda suke ce mata maman bishira ta ce,zainabu ki je mana ga alhaji can ya dawo.ta kalle ta cikin raunanniyar murya ta ce,wallahi na gaji.lnnar su bishira don allah ki bashi hakuri.ta katse zancen, sakamakon kira da ya kwala mata.ke zainabu,ni saanki ne,kina kallo na shigo kin tsaya?mama bishira ta ce,je ki zan sa miki hannu.laure da ke wanki wadda ita ce ta biyu ta ce,kwadayi mabudin wahala.zainabu ta shiga dakin tana ja baya,tana fadin sannu da zuwa.ya ce,rike sannunki,ba na so.sai da na kira ki,za ki zo?ta ce, ina sanwa ne,da ma zan zo.ya ce,to mu je!ai kin san abin da ya kawo ni ko?ba ta da zabi face mika wuya. shi sam bai san wani wasanni ba.auka wa iyalinsa kurum yake yi.ln ya cimma burinsa sai ya kakkabe jikinsa ya tashi. Rayuwar zainabu a gidan alhaji lawal,abin tausayi ne.ga girka babbar tukunya,abin da bata saba ba,ga fama da wannan miji,uwa uba ga su laure. suke dame ta da nuna kishinsu a kanta.don haka in ba girkinta ba ne, ba ta saukowa,sai in su laure ba sa nan.wani lokacin kuma in yarasu sun shiga dakinta su yi ta wasa ta biye musu. amma duk wanda ya san ta kallo daya zai yi mata ya san cewa ta rame.ta yi baki,kyawunta da cikar budurcin da ta soma,duk komai yayi lakwasa. cikin haka ne wata rana kannanta suka zo.ganin ta suka yi cikin yanayin suka je suka sanar da lnnarsu. washgari sai ga ta salati ta zabga tare da fadin na shiga uku ni.yasu zainabu kin yi ciwo ne?ta ce,aa ta soma kuka,wallahi innarmu na gaji da zaman gidan nan.mutumin nan bashi da imani,don allah ki tafi da ni.kullum sai ya zazzage ni.ga matansa biyu kullum sai su yi ta min habai ci tun ban gane da ni suke yi ba, har na gane.lnna ta ce,duk wadda ta yi miki ki rama ai zamansa suke yi,ke ma haka.to ki fada masa mana. sallamar maman bishira ce,ta katse su.ta shigo suka gaisa [01/10 10:34 pm] Abdul: (40)Zainabu ta ce,lnna wannan ce uwargidansa,ita dai tana taimaka min sosai. lnna ta ce,na gode baiwar allah,amma su sauran ta ce,suna yi mata habaici.na ce to ba zan lamunci wannan ba.sai in zo in same su har nan don ba ni da hakuri.maman bishira ta ce,ita zainabu yarinta ke damun ta.lnda tana da wayo,za ta ke masa faran-faran,ta daina jin tsoronsa. to da su kansu ba za su soma yi mata haka ba.tsoro za suji kar ta fada masa.kafin wani lokaci za ta dan samu abin da ta samu.amma ita sai raki da tsoro.nan suka yi ta shirya mata yadda wai a ta yi masa.jinsu kawai take yi, ba ta jin za ta iya kallon alhaji da wata kauna ko birgewa.lta dai kullum zuciyarta tana gurin dan kyakkyawan farin saurayinta lsma'il. Ismail shi da hamisu direba suna jin MIMI duk wayar da take yi,don tana yin maganarta kai tsaye ne,ba tare da wani noke-noke ba.a nata ganin wannan malam lsmail din shi ne wa har da za ta ji shakkar sa.ya san dai ita ba saar aurensa ba ce.ln ma ya ce zai kalle ta a matsayin mata zai bata wa kansa lokaci ne.shi kuwa lokacin fargaba ne ya sake dabaibaye zuciyarsa.tabbas shi rin guduwa take yi,ba ta zo zama ba.tambayar da yake yi wa kansa,yaya ke nan?yaya zai yi,ta nina zai bullo wa lamarin?a filin ya ce,allah da kai na dogara. ya ciro waya ya sake neman mahmud.bayan a dauka ya amsa sallamar, sai ya soma zolayar sa,ango,ango!ya ce don allah ka bar fada min kalmar.da ma zan sanar da kai ne cewa muna hanya. yanzu haka mun kusa kaduna.za dai mu iso dare yayi ne.don allah ina son ka dan tsaya a dakina,mu same ka a nan.ya ce ba damuwa.sai ma in dan share kafin ku iso.cikin zolaya mahmud yayi zancan.tsaki isma'il ya ja,ya canza harshe zuwa larabci, inda yake fada wa mahmud cewa MIMI din nan aka bashi fa tare da sanar da shi halin damuwar da yake ciki da duk yadda abin ya faru a takaice.sai dai bai ja sunan MIMIN ba.ya yi masa misali ne yadda zai gane.bayan sun yi sallama ne hamisu ya ce,ka san allah malam in kana larabanci kyau kake kara yi mi kamar. [01/10 10:34 pm] Abdul: (41)Balaraben da ma amma ku fulani ne ko?yayi murmushi tare da fadin ta wurin uwa ba.da yake lsama'il saurayi ne kyakkyawa sosai,sak ya debo mahaifiyarsu wadda ta kasance fulanin daura.ga shi da tsafta sosai,ga ilimin addini.na zamanin ma yana kan nema,don duk biyun yake da burin ya hada.yana da tsare gida sosai.amma akwai farin jinin jamaa.duk inda ya shiga mutane suna son sa.kodayake halayyar shi ta janyo don yana da son jamaa da son yi wa jamaa nasiha.ba ya ganin kuskure yayi shiru.ko ina ya shiga da wuya ya bar gurin bai samu wanda ya amshi lambarsa ba ya ce za mu dinga gaisuwa.tare da haka sam ba ya son raini ko cin mutunci ko wulakanci.yam mata da dama suna son sa,musamman dalibai.sai dai ba ya bada fuska, kasancewar ba abin da yake kai shi makaranta ke nan ba.zainabu ya soma so amma ga yadda rayuwa take canzawa,abu ya juye,ya je abuja neman kudin aure,ya dawo da mata.takwas daidai suka shigo kaduna.lsmail ya ce lallai su tsaya su yi salla. hamisu ya rada masa cewa kar mu fita ta gudu. lsmail ya ce,ka rufe motar mana,ka je ka yi.ln ka idar ni ma sai in je in yi.daga nan suka dauki hanyar katsina.jefi-jeri lsmail yana jin MIMI tana tambayar khalil sun kusa kaduna. sha biyu da minti goma suka shiga katsina,lokacin khalil ya kira MIMI wai bai sami motar katsina ba.sai dai ya sauka a kaduna. kuma ya je gida, mahaifinsa ya yi tafiya,don haka kai tsaye ya wuce gurin hajiyarsu don ya san za ta hakura ba,sai ya bata gold dinta.ya ce da safe zai kaita gurin wanda ya saida mawa.da haka ta yi ta yi masa fada da nasiha. ba ta san shi ba abin da ya dawo da shi gida ke nan ba.ya dawo ne don ya dauki mota.ya san ta da barcin safe.don haka sai da ya karya ya fita ya duba lafiyar motar,ya koma dakinta ya ci saar ganin makullin motar tata a kan madubi.ya fita ya dauki motar.maigadi ya ce,ina za ka?ya ce,hajiya ce ta aike ni in sha mata mai.sai bayan ya zo zariya ya tsaya ya sha mai.yayi tambayar ina zai bi in za shi katsina?aka nuna masa wata mota aka ce ya bi ta. [01/10 10:34 pm] Abdul: (42)Sha biyu da minti goma suka shiga katsina,lokacin khalil ya kira MIMI wai bai sami motar katsina ba.sai dai ya sauka a kaduna. kuma ya je gida,mahaifinsa yayi tafiya,don haka kai tsaye ya wuce gurin hajiyasu don ya san za ta tausaya masa.ya ba ta hakuri,ta ce baza ta hakura ba.sai ya bata gold dinta.ya ce da safe zai kaita gurin wanda ya saida mawa.da haka ta yi ta yi masa fada da nasiha.ba ta san shi ba abin da ya dawo da shi gida ke nan ba.ya dawo ne don ya dauki mota.ya san ta da barcin safe.don haka sai da ya karya ya fita ya duba lafiyar motar,ya koma dakinta ya ci saa ganin makullin motar tata a kan madubi.ya fita ya dauki motar maigadi ya ce,ina za ka?ya ce,hajiya ce ta aike ni in sha mata mai.sai bayan ya zo zariya ya tsaya ya sha mai yayi tambayar ina zai bi in za shi katsina?aka nuna masa wata mota aka ce yabi ta.lokacin ne kuma ya kira MIMI ya fada mata ya taso daga zariya.su kuwa yadda suka yi jiya,suna isa katsina hamisu ya ce,to yanzu kai ne zaka yi ta mana kwatance har gidanku.haka kuwa aka yi. unguwar shiru.kowa ya rufe gidansa,tunda lokacin sha biyu ta wuce,ga kuma yanayin sanyi.lsmail ne ya fita ya je ya turra kofar gidansu,don ya san bata rufuwa da sakata.mahmud ya bude kofar dakin lsmail ya fito.kana ciki ke nan? mahmud ya mika masa hannu tare da fadin gaskiya kun sha hanya. lsmail ya ce,to bari mu kwaso mata kayanta.suka fito.tare da wayarsa yayi amfani ya haska,ya bude murfin gefen da MIMI take zaune ya ce,ki fito.ba ta yi musu ba.ta sauko.sai dai tana saukowa ta toshe hanci,ya haska mata har ta shiga zuren gidan.ya nuna mata dakin.ki shiga nan.a fili ta ce,tafdi!ta shiga tana kallo ko'ina na dakin ta ce,na yarda dad ba ya kauna ta sam.ko tantabaruna dakinsu yafi wannan.lsmail dai ya juya. jiki a sanyaye ya nufi waje.suka soma shigo da kayanta.can ta rakube da bango a kan katifar,tana sake kallon ko'ina a yatsine, hawaye na ta zuba daga idanunta,tana kara karfafa wa kanta cewa lallai gudu shi ne abin da ya halasta ta yi. [01/10 10:34 pm] Abdul: (43)A wannan gidan,a wannan dakin za ta yi rayuwar aure?suka gama shigo da tulin jakunkunanta da kayan takalmanta,suka loda su a gefe.lsma'il ya ce. mahmud kuje da hamisu ya kwana gurinka.da safe zai dauki hanya.mahmud ya ce,ba damuwa.mahmud ya kalle ta,to amarya,an iso lafiya?da sauri ta dago idanunta ta balla masa harara,tare da jan dogo tsaki,ta ci gaba da latsa wayarta.haka suka fice.lsmail ya raka su mota, suka shiga suka tafi.shi kuma ya dawo ya dauki buta ya fita waje yayi alwala ya shigo ya ra sakata.duk da yana ta addua,gaban sa bai daina faduwa ba.yayi shafa'i,ya daga tsohuwar akwatinsa ya dauko bargo ya kalle ta,ga abin rufa.ta yi masa hararar sama da kasa,ta ce,tunda dai ka ji ban ce maka komai ba.to ka gode wa allah.amma kar ka sake ka kara yi min magana.ka ga na yi kama da tsumman bargonka ne?lsmail ba ya daukar raini sam don haka ya ce,za ki iya ce masa tsumma,amma naki sabon ina yake?kar ki cuci kanki,ki amsa ki rufa don ana sanyi sosai.ta yi masa wata harara irin ta sama da kasa,ta ce,kar ka zata wai an daura maka aure dani, shi ke yake ba da damar in zama matarka.ya ce,na nawa kuma?sai dai in kar a kara,amma aikin gama ya gama.ta ce,ai ba bisa yardata aka yi ba,don haka babu aure.yayi yar dariya,yadda kika ce ba.amma aure daram, musulunci ya kulla shi.kuma nine kadai zan iya warware shi ta hanyar saki.ta ce,to maza ka warware shi.don ni da gari ya waye zan kama gabana.ya ce,da hakan za ta yiwu tun daga abuja zan yi hakan.sai dai kash na riga da na yiwa mahaifiyarki alkawari.ta daga murya,kai ni yanzu ba ni da wata mahaifiya,ban da iyaye,ban da kowa. mahaifiyar da tana zaune aka gama cin zarafina.ban ji haushinta sosai ba,dama can na san ba wai tana so na bane.don haka zan fi son in tafi inda babu wanda zai ji labarina. ya sake mika mata bargon,ki rufa,sanyi yayi yawa.ta ce,ka bar shi in ya so sanyin ya zama ajalina.lsmail ya ce,ni ma dana huta da tunanin nan. [01/10 10:35 pm] Abdul: (44)Ta kalle shi sannan ta ja dogon tsaki.tabarma ya shimfida.bata bude sosai ba, don dama gurin da ya rage bai fi gurin salla ba.ya dauko wani zanin gado ya shimfida,ya dauki filo daya ya saka.tunaninsa daya,duk tsananin sanyi,shi ba maabocin yin barci da kaya ba ne,sai dai ya rufa.har ya kamanta haka,dole ya tashi ya cire riga,ya kwanta da dogon wando.lta dai tana inda take rakube,iyaka dai kau da kanta tare da tabe baki.sama-sama yake yin barcin saboda ba ya kwanciyar kasa har ya zuwa lokacin da ya saba tashi don yin nafilfili.ya yi mika,ya saka rigarsa ya waiwaya ya kalle ta,ta takure,kanta yana cinyarta, wayar ta fadi can gefe.da alamu sanyi sosai take ji.ya daga akwatinsa ya ciro malumalun dinsa a goge,tana ta kamshin turaren da yake sawa a kayansa,ya lallaba,ya rufa mata.ya fita don yo alwala. ko da ya dawo ta zame ta kwanta,ta kankame filo,ko fuskar ta ba a gani.yayi sallarsa,ya gabatar da adduoinsa ga mahalicci.abin da yafi alheri kawai yake ta roka tsakanin sa da MIMI.ya sake kwanciya yana fuskantar inda take kwance.bai iya ci gaba da barci ba,sai hasashen me zai faru gobe da jibi?lna zai samu kudin da zai ci da ita irin cimar da take ci?lna zai samu kudin irin tufaein take sawa zuwa kayan shafanta wanda a gabansa ta ce dubu dari albashinsa shine kudin kayan safanta.a haka har asubhi tayi.ya kulle dakin ta baya,ya tafi masallaci.a can suka hadu da yan uwansa,wato yayyinsa maza,suka gaisa. suka yi masa murna mahmud ya zo ya fada musu cewa maigidansa ya ba shi yarinya.ya ce haka ne.babba ya ce.amma ai mu ne ya kamata mu zama wakikanka duk lalacewarmu.lsmail ya gano sun dauki zafi ne,don haka ya fada musu yadda abin ya taso amma duk da haka cewa kurum suka yi,allah yasa alheri ba don sun yarda ba.daga nan gidan yaya amina ya wuce.idar da sallarta ke nan yayi sallama,ta amsa,suka gaisa. cikin murna ta ce,sai ga labari mai dadi.ya ce,uhum yaya ke nan.ta ce,mene ne uhum,kun zo da amaryar ne?ya ce,eh,tana dakina.amma matsalar ba ta so na. [01/10 10:35 pm] Abdul: (45)Ni ma sam bana son ta ko da wasa.nan dai ya fada mata komai.ta ce.to allah dai ya daidaita ku.ka tashi ka je kar ta farka.yanzu to me zaka bata na kari?ya ce,sai dai na je na ji daga bakinta,don ban san da me za ta karya ba.nan suka yi sallama ya nufi gida.kai tsaye cikin gida ya wuce,fatu tana kicin ya ce mata ina kwana?ta dago ta dube shi,aa yan abuja ne?sai muka ji aure.na ce kila dai don mu bamu da zanin zuwa abuja ne.yayi dan murmushi ya wuce.saura suka fito su ma dai ya gaishe su,amma sai sakin magana suke yi.dakin lnna ya shiga tana kwance,ga rushi a gabanta,ya zauna ya gai da ta.ta ce,sai kuma mamuda abokinka ya zo mana da labarin aure.ya ce,eh.abin allah ya kawo shi kafin a yi shiri.ya ce,to allah ya ba da zaman lafiya.mu da har muna cewa kila ka canza dangi ne.ya ce ba haka ba ne.ni ma abin ya zo min ne ba shiri.tana ciki ai tana barci.ta ce,to kuma a nan dakin za ku zauna?ya ce,eh,to sai dai yau zuwa gobe za mu fara neman daki.ya mike,bari in gani ko ta farka. ya sa makulli ya bude dakin.har lokacin bata tashi ba.ya kira mahmud yana tambayar sa ko hamisu ya tashi?ya ce tunda suka yi salla ya koma.ya bar shine ya dan warware gajiya tunda hanya zai kara bi. sai karfe goma da kwata,lokacin tuni lsamail yayi wanka,yayi shirinsa cikin shada mai ruwa siminti.yayi kyau yana ta kamshi.ta farka,mika tayi ta yi tsaki.ya ce,ai kamata yayi ki yi adduar tashi daga barci,ba tsaki ba.yanzu da kin bude ido kin gan ki a kabari fa?ta tashi zaune,da sai na fi murna fiye da in gan ni a dakin nan.da sauri ta shiga neman wayarta.ta dauka ta soma kiran layin khalil,ya katse.ya kira ta, lokacin ne yake fada mata ya taso daga zariya.ta ce, shi ke nan zamu yi ta waya har ka iso.ya ce,shi ke nan,sai na iso din. lsmail ya ce,wai da wa kike ta yin waya ne?ta harare shi,na ce ka daina yin min magana ko?ya ce,to ki tashi ki yi salla.ta harare shi,ta ja tsaki,ba zan yi ba.ya ce kina fashin salla ne?ta mike tsaye cikin mamakin wuce gona da irin. [01/10 10:35 pm] Abdul: (46)Na mutum,ta ce,cikin daga murya,zo ka matse ni ka duba ka ji ko?ta zare idanu a karshen maganarta. ya mike,mai da wukar.me za ki ci?ta sake hararar sa,kai har ka mallaki abin da za ka iya ciyar da ni?ta sauka daga kan katifar ta nufi jakarta wadda ta sa jakarta mai kudi a ciki.ta ciro ta zo zata zauna,sai ta ga malum-malum dinsa,ta sa kafa ta ture.ya ce,oho dai ta yi miki amfani. ba ta kula shi ba ta kwance kudin sadakin da aka bata a gefen gyalenta,ta zuba a cikin jakar,ta dauko karamin akwaiti cikin jerin akwatunanta,ta bude akwatunan tana zabar kayan da za ta sa.yawanci kananan kaya ta diba.ta bude wata jakar ta dauki kayan ciki da na shafa,sai takalmi daya ta saka jakarta mai kudi,ta rufe.ta sauka daga kan katifar.ya ce,wai ke ko fitsari ba ki ji ne,duk sanyin nan da ake yi?ta ja tsaki,ban ga gurin da zan iya tsugunawa ba.ya ce,mu shiga cikin gidan.daga nan sai ki gai da lnnata.tunda ya ambaci fitsari,sai ta ji ya matse ta har kamar zai zuba.shiru ta yi,sai ya dauko buta,mu je in raka ki.ta dauki mayafinta ta dan yafa.suka fito zaure a share fes.don tun kafin ya shiga wanka ya share.suna shiga tsakar gida,matan gidan suna ta aikace-aikacensu.ta sa gefen mayafinta ta rufe hancinta.ya ce,ki gai da su mana.ta zabga masa harara,ta ce,nuna min toilet ni kam.ya nuna mata,ta shiga da kyar ta yi yin fitsari saboda zarni da kuma rashi inda zata tsugunna.ba ta taba ganin irin wannan ban dakin ba,don ko na kauyen su dad da ta tsani shiga yafi wannan kyau.ta fito duk ta bata kafafunta.sai da ta fito ne take ta wanke kafarta,tana zubar da miyau.cikin sauri ta bar tsakar gidan.sai da ta je soro ta sauke numfashi ta soma kuka.matan gida suka yi ta kallon kallo.fatu ta ce,salo da yayi,wai kaza ta ji shikar dare.lsmail ya ce,ku yi hakuri ba laifinta ba ne,ba ta saba da ganin haka ba.suka sa dariya,gami da shewa,to a kai ta inda ta saba,ln ji fatu. shi dai fita yayi ya bar su suna ta habaici da kananan zagi. [01/10 10:35 pm] Abdul: (47)Ta shiga cikindakin ta dauki wayarta ta soma kiran khalil.ya ce,mun kusa ki ba ni minti talatin.gudu nake yi sosai,kin ji dear ta ce,to inda nake ne ko dakin karen gidanmu ya fi shi.ran lsmail a bace,ya ce karya kike yi.lna sake fada miki karya kike yi.ta ce,dakin karenmu akwai tayils,na fa? ya ce,dakina akwai alkurani da littattafan addini.ke nan dakina yafi naki ma,duk kyawunsa.ta sake bin dakin da kallo,tana tabe baki.ta ce,tsayawa yin musu da kai bata lokaci ne. ta sake mikewa ta zage wani zif din akwati ta ciro muhimman takardunuta,ta zage jakar da za ta tafi da ita ta zuba.ta zauna ta yi tagumi,jifa-jifa tana duba agogo,shi kuma ya kasa ya tsare ya ga inda za ta. Na'ima amarya kuwa an yi barci sama-sama a gidan abbas sai takwas ta farka ta zauna zugum a bakin gado.ta dauki wayarta ta soma kiran layin momy.momy tana dagawa ta ce,na'ima an tashi lafiya?bata jira amsa ba,ta ci gaba da cewa,da dinku jikinsa fa ya tashi kamar yadda na ce miki jiya.yanzun haka mun koma asibiti.ki fada wa maigidanki.na'ima ta ce to kawai don ta san babu damar ta yi korafi a cikin wannan halin.wanka ta shiga,ta yo alwala.ta dan fi MIMI tunda ita takan yi sallah ko da dai ba kullum ba.ta zo ta yi kwallaiya,ta bude wardrobe dinta ta ciro sabuwar jallabiya mai shegen kyau ta saka,ta yafa mayafinta irin yadda MIMI ke yi,ta fesa turarruka,ta saka lallausan silifas na zaman gida,ta nufi sama abbas.ta jima a tsaye bakin kafar tana tunanin bugawa.can dai ta daure ta murda kofar,sai ta ji ta a kulle.daga ciki ta ji an ce waye?ta dan yi shiru tare da zaro ido.a sanyaye ta ce,ni ce.a lokacin ya riga ya zo zai bude kofar ya ga ko wane ne.duk da haka bai fasa ba,sai ya bude.ganin ta sai ya bar kofar a bude.ta shiga da alama wanka ya fito don ga rigar wankan a jikinsa. a hannunsa akwai karamin tawul,yana goge kansa.ta tsuguna har kasa,ina kwana?ya bata rai ya kau da kai lafiya.ta ce,da ma momu ce ta yi min waya wai dad dina ba shi da lafiya.an mai da shi asibiti. [01/10 10:35 pm] Abdul: (48)Ya waiwayo ya kalle ta,irin kallon kashi din nan,to me zan yi masa?ln za ki je.ga ki ga hanya,amma ni bani da lokaci.kin gane?ta mike a sanyaye.har ta kai bakin kofa sai kuma ta waiwayowa,am na ce me zan dafa?ya sake waiwayowa,bana bukata. ranta ya dan sosu.ta mike ta nufi dakinta tana kuka. Bakin gado ta zauna, lallai za ta shiga matsala babba.da ma abbas bai amshe ta ba?shi ne ya amince ya aure ta don kawai yayi mata wulakanci?haka ta yi ta kuka.ko kayarwa bata yi ba har kusan karfe biyu,sai ga kannen momy,su anty rukayya.suka ce lafiya ke kuma kike kuka?anty jamila ta ce,wawiya mana,yanzu an daina wannan abin dan.kin yi daren farko a gidan miji,kiyi ta wani kuka.ta ce,ba haka bane.ta fada musu komai ta ce,ya san bai yarda ba tun farko ba sai ya ce,aa ba.sai yanzu ne zai fara yi min wulakanci?anty rukayya ta ce,ke dai sakarya ce.don wannan za ki yi kuka.ki saurare mu kiji.tunda daga ke sai shi a gidan,abu ne mai sauki ki ja raayinsa.anty jamila ta ce,ina kananan kayan nan da momy dinku ta siyo miki daga dubai?ta ce,suna cikin akwatunan da kuka zo da su.ta nuno shi,ga su can. suka je suka bude.suka ce yawwa ki gwada mu gani.ta yi ta gwadawa suna tafa mata,tare da koya mata kalolin sanya su yadda za ta ja raayinsa.ba su bar gidan ba sai da suka tabbatar da haddace duk abin da suka koya mata.ba su jima da fita ba,sai ga dangin abbas da masu aiki an kawo mata.da dattijiya da mana yarinyar dai yarinyar gwari ce,sannan ta kuko namiji.karfe tara na dare na'ima ta yi wanka sosai,ta yi gayu kamar yadda suka ce maties din ta suka ce.ta saka rigar da suka zuba mata wadda ita ce ta dace da ita a wannan dace.hannu din rigar gare ta.shi ma kulle shi aka yi kirjinta a waje.tsawo rigar bai kai guiwa ba.ta kama gashinta a tsakiyar kanta,ta yi wanka da turarurruka masu daukar hankali.ta soma rihasal din yadda za ta shiga dakin da yadda za ta tunkare shi da duk abin da suka ce ta yi.sai da ta tabbatar zata iya ta nufi saman abbas, duk da tana fargabar kar ya gwasale ta. [01/10 10:35 pm] Abdul: (49)Ita kuwa MIMI kamar karfe shabiyu sai ga kiran khalil.ta daga ya ce,kina ji na?ta ce eh.ya ce,na iso.ta mike ta bude jaka lsmail suna tsane da mahmud a kofar gida suna tattaunawa a kan inda zai nemi dakin yanzun nan hamisu direba ya wuce bayan ya kawo mahmud sun yi sallama ya lsmail ya ce masa godiya,mahmud yana cewa,mu je mu samu malam.mahaifina kayi mai bayani,lna zaton akwai daki a gidansa na kofar guga amma can bayan gari ne,ba mutane sosai a gurin.gidan dai mutane biyu ne,amma daki uku ne ciki da falo.lsmail ya ce,to da ma ina da kudin nan.mahmud ya ce,ka san ma ba zai amshi kudinka ba. fatanmu allah yasa bai riga ya ba wai ba.rufe bakin mahmud ke nan,lsmail ya ce,amin...bai karasa ba,sai ga MIMI ta fito sanye da riga da wando damammu,sai dan mayafi da ta rataya shi kamar yadda take yi tana janye da dan akwatinta.da sauri ya nufo ta,ina za ki je?ta kalle shi sama da kasa,ta ja tsaki,ta tsallaka kwata.ya kalli gurin zaman yan majalisar kofar gidansu ba su fito ba rana.mahmud ya ce,bar ta mu bita a baya. haka kuwa tana tafe suna bin ta.sai ta tare dan acaba ta hau.su ma suka hau suna hangenta tana waya har zuwa garejin mota.tana tsayawa suka tsaya ta ciro kudi ta ba dan acaba,su ma haka.ta nufi wata mota.kafin su tsallaka su isa ga motar har sun tashe ta.lsmail ya shiga tashin hankali sosai.ya ce, mahmud barin ta za mu yi ta tafi?na yiwa mahaifiyarta alkawari. mahmud ya ce,zo mu dauki mai gulf din can ya bisu.sun nufi gurin sai suka ga hamisu direba ana sa masa fasinjan abuja.lsmail ya ce,aa me kuma ka tsaya yi?ya ce,lodin abuja zan yi,in dan kara na mai,ln samu na batarwa.lsmail ya ce,sauke sumu bi su MIMI,ta gudu ga su can sun dauki hanyar kaduna. [01/10 10:35 pm] Abdul: (50)Nan da nan hamisu ya sauke su,lsmail ya shiga gaba,mahmud ya shiga baya.duk da halin da lsmail yake ciki bai hana shi ya yi wa hamisu direba nasiha ba.ya ce,hamisu tsakani da allah ban zaci kana cikin direbobi masu cin amanar iyayengidansu ba.sam bai dace ka yi lodi ba tare da izinin maigidanka ba.haramun ka ci.ai gara ka ce min in kara maka na mai.amma wannan cin amana ne.ya baka amana ne fa.ko ya san kana yi?hamisu ya ce,wai!ln alhaji ya ji ai na shiga uku. lsmail ya ce,ka gani ko?yana biyan ka hakkinka.hamisu ya ce, lnsha allah na daina.daga yanzun ba zan kara ba. Da yake hamisu gudu yake yi,sun hango su,har sun kusa zuwa daf da jun. MIMI ce ta gane motar gidansu.ta ce,ana bin mu. waccan motar gidanmu ce. nan suka kara gudu.gudun nasu yayi yawa.allah dai ya tsare...karan da suka ji shi ne ya tabbatar musu da cewa taya ce ta fashe ta su MIMI. daga inda suke suna hangen yadda motar take tuntsira gudi-gudi a kan titi.gaba dayansu suka hau salati.hamisu na cewa taya ta fashe shi. kuma ya taka burki.hankalin lsmail ya yi mugun tashi.suna isa gurin,motar tana tsayawa bayan ta tokari bishiya.suka fito suka nufi gurin.motoci suka tsaitsaya ana ta kokarin ciro su.duk jikin lsmail bari yake yi.wasu na cewa tun dana ga tukin da yaron nan yake yi na san zai yi wuya basu fadi ba. Nan zan dan huta.sai mun hadu a kashi na uku don jin shin su MIMI za su rayu?ln sun rayu,yaya zamansu zai kasance?wai na'ima ta ci nasara da ta hau saman abbas?mene ne labarin zainabu? Taku Halimarku K Mashi. sai na ji ku a 08081165107. lna jiran shawara ko korafi.