CANJIN RAYUWA (1) Hajiya saudat tana zaune kan sallayarta ta idar da sallar azahar tana istigfari, 'yar kimanin shekaru arba'in da bakwai zuwa da takwas,amma ba ta yi kama da shekarunta ba saboda kyan jikinta da kuma hutu.in an ce ka fadi shekarunta za ka iya cewa talatin da doriya,kyakyawa ce mai cikar mutunci. wayarta da ke gefe samfurin nokia tayi ruri, cikin natsuwa ta kai hannu ta dauka tare da kallon fuskar wayar. kamar yadda ta za ta, maigidan ne domin duk yinin yau ba ta samu kiransa ba.sallama ya yi,ta amsa cikin ladabi, sunanta ya kira ya ce,hajiya ki karbi bakuncin mu anjima. cikin taushin murya tace,shine ba ka fada mini ba tun safe? cikin lallashi ya ce,na yi ta neman layin ki bai samu ba, ta ce,da ka nemi ta su usaina,kila network ne domin waya ta kunne ta ke,ya dan murmusa,ba mamaki zan iso da yunwa fa,don haka a tarbe ni,ta yi 'yar dariya,wace irin yunwa?shi ma yayi 'yar dariyarsu ta manya,duk wata yunwa ta,da ita zan zo,ta ce, kar ka damu allah ya kawo ka lafiya,ya ce,amin. ki sa a yi wa uwata farfesun kifi tare za mu zo,take ta hade fuska, tamkar yana kallon ta,ta ce alhaji don allah kar ka zo min da mimi.ya ce,saboda me?ta ce,ka san komai, alhaji MIMI in ta zo gidan ba,ba maaikatan gidan ba.ta sani,na fada mata kar in sake ganinta a gidana matsawar ba ta canza halin ta ba,ba na bukatar ta.yayi shiru domin ranshi ya baci,kusan minti daya duk sun yi shiru. sannan ya ce,sauda, ba zan gaji da fada miki cewa ban jin dadin abinda kike yi wa MIMI ba gaskiya, zai fi kyau ki fito fili ki zage ni sai ya fi min sauki maimakon aibanta MIMI. allah! in ji hajiya saudatu,ta sake tausasa muryarta,ban san lokacin da za ka fahimce ni ba alhaji,amma kayi hakuri.in dai don mu zaka zo,to ka zo kai daya zan fi so haka.cikin dan zafi ya ce,sauda muna hanya kar ki manta da abincin ta na yau da kullum,ki fada ma duk 'yan gidan wanda bai son ganin ta zai iya barin gida har sai ta tafi, [01/10 12:45 pm] Abdul: STEP (2) sannan ya kashe wayarsa. ta dan ciji lebe tare da lumshe ido cikin takaici,ba ta da zabin da ya wuce yin abinda mijin ta ke so.a fili ta ce ni kan bana son zaman MIMI garin nan,na tsani halin ta,a ce yarinya karama a bar ta tana yin yadda ta ke so.ta mike tana nunke sallaya. Abdulkarim ya yi sallama, ta amsa fuskar ta daure,sannan ta yi tsaki, abdulkarim ya ce,lafiya hajiya?alhaji ne ya kira ni wai suna tafe shi da MIMI. abdulkarim ya ja tsaki,don jin ambaci sunan MIMI, sannan yace,ashe yanzu zan juya a kan sawuna mu gaisa kawai hajiya in sabi jaka ta,ai a wannan sati bani da darasi kamar yau,sai na sake dawo wa. hajiya sauda ta yi yar dariya tare da fadin haba abdul,ka taho tun daga zariya har katsina sannan ka ce mu gaisa kawai ka wuce saboda MIMI?ta ci gaba da fadin ba zai yiwu ba.dauki jakarka kawai ka wuce sashin ku,ka watsa ruwa.barin in sa mutuniyarka tabawa ta kawo maka abinci na san yanzu sun gama na rana.ya ce,ai ni bana son rainin wayonta ne hajiya,a ce yarinya karama kanwar bayanka ta zo tana kawo maka rainin wayo,ba dama ka yi magana.ni kuma kin sanni da zuciya sai in doke ta. hajiya tace,aa kar ka soma,ka san halin alhaji.ina fatan baka manta da yadda yayanka abbas suka kwashe ba,in ka tuna zungure mata kai kurum yayi,amma ta inda alhaji yake shiga bata nan yake fita ba.tsawon wata shida yaki ams gaisuwar abbas.sai da biki shi sannan alhaji ya sauko,shima sai da abokan abbas suka taro abokan alhajin aka hadu ana taba shi baki, sannan ya hakura da kyar da dokoki a kan 'yarsa. Abdulkarim yayi ajiyar zuciya cikin takaici,sannan ya ce,ban manta ba.hajiya shi yasa nace, zan koma,tace ka hakura da harkanta.yace, gaskiya alhaji ba yayi mana adalci,a ce cikin 'ya'yansa mu ishirin da biyu,amma ya zabi daya rak yace,ita ce star don kawai tana da sunan mahaifiyarsa.allah hajiya abin yana damu na, kanwarmu ce fa,amma ko shawara da ita sai abinda ta ce a family. hajiya sauda ta ce,ku yi ta hakuri, [01/10 12:45 pm] Abdul: STEP (3) Dadin abin ita dai ta mace ce,duk abinta ai dole ta yi aure ko? abdulkarim ya ce, tabdi, wannan 'yar jin kan?ya zauna a kujera, sannan ya ce,allah ya sa ta saurari wani.hajiya ta ce, ayya abdulkarim dole tayi aure. ba dai mace ba ce?shi kanshi zai so a bar masa ita a gabansa?abdul' ya yi 'yar dariya,sannan yace,kila ya ce mijin ya dinga biyo ta nan gidansa.hajiya ta ce, oho mishi su dai suka sani, suka yi 'yar dariya,ta ce ba su lokaci kawai.ni dai ina ta fada ma allah,ku da ma na haifa ciki daya kuna jin takaici da haushinta,bare wadanda ba ni ce na haife su ba.abdul ya mike tare da saba jakarsa,bari ni kan na isa dakinmu,hajiya ta ce, to ni ma bari in je babban kicin. hajiya sauda ta tafi gefen babban kicin,ka san cewar gidan babban gida ne mai tsari,tun daga waje za ka san cewa mamallakin gidan ya tara abin duniya ba kadan ba.ta isa babban kicin din,mata uku ta samu a ciki suna ta aiki,suka maido da hankalinsu gurinta tare da yin mata sannu da shigowa,ta amsa da sannunku da aiki cikin girmamawa,ta kalli tsohuwar cikinsu ta ce,baba tabawa me aka yi da rana?tsohuwar tace,taliya ce ke kan layi da rana,da dare kuma zamu yi tuwon masara da miyar danye kubewa,ga taliyar nan ma yanzu na sauke. hajiya tace to,a canza na dare a yi mana dan waken gari dawa sannan ayi shi da wuri.baba tabawa tace,maigida yana nan shigowa kenan?hajiya tace eh,suna tafe,suka hada baki guri cewa,allah ya kawo su lafiya.hajiya tace amin.sannan ta kalli jummai muna da kifin ruwa ko?jummai ta ce eh,hajiya ta ce yawwa ki dafa kadan kar ki cika yaji kuma kar ki sa tafannuwa. sannan ki kula kar ya dagargaje na MIMI ne. dukkan su suka hada baki gurin tambayar har da MIMI ne za a zo?jummai ta ce, allah ya fishe ni yin kuskure. hajiya tace kar ki damu, sannan abinda kawai zan fada maku in tazo,ku kawar da kai duk abinda za tayi kun ji ko?cikin karyayyar murya suka ce to shikenan,tabawa ta kalli jummai kar ki sa mata tafannuwa, [01/10 12:45 pm] Abdul: STEP (4) Wancan zuwan da ta yi maman sani daga sa tafannuwa shikenan ya zama sanadin korarta. jummai tace,zan kula insha allah. hajiya ta kalli ramma tace,da safe me muke da shi?ramma ta ce, shayi ne,hajiya tace,to a canza zuwa kosai da kunun gyada,ta ce to hajiya. tabawa tace akwai kafar safa ko wannan karon ba zaayi ma alhaji ba?hajiya tace,a dora zan dinga zuwa ina dubawa,na zata babu ne,tabawa mutumin ki fa yazo abdul,a kai masa abinci,ina magajiya?tabawa ta ce allah sarki abdul ne yazo zan kai masa ma da kaina maigida sukutum.hajiya ta juya tana dariya tare da fadin kowa ya duba abinda babu sai yazo ya fada min. Da kanta ta nufi wajen me wankinsu yana ta gugar kayan yara,ta ce masa ka je ka fadawa mai gadi da mai kula da fulawa cewa MIMI za tazo anjima,sannan yau direba ya same ni a falo.ta sake cewa,danladi na fada maku ne don ku kiyaye bana son ana korar min ku,danladi yace,zan fada masu.ya nufi gurin mai gadi,ya turo mata direba ya sanar da su zuwan MIMI nan suka dinga tattauna rashin mutuncin MIMI,ya same ta tana duba nono a cikin firiji.domin tasan aladan shi ta sha furan dare. Direba yayi sallama cikin girmamawa,hajiya ta amsa,ya gaida ta sannan yace,ga ni tace,malam yau da ma ina son sanar da kai ne,yau MIMI zata zo na san ba ka santa ba.amma ka samu labarinta?cikin in'ina yace eh naji gurin su danladi.tace to ka tafi filin jirgi tun misalin hudu da rabi,gara ka jira su,domin da jiran da suka yine wancan direban namu shine sanadiyyar korar shi da MIMI ta sa alhaji yayi.ya ce zan kiyaye insha allah. Tun hudu yau ya nufi filin jirgin,jiran zai fi masa sauki da haduwa da fushin MIMI. biyar da minti talatin suka iso,Alhaji bashir aliyu masari ya fito daga cikin jirgi,MIMI tana biye da shi, sanye cikin riga da wando masu kalar pink sun dame ta tsam.sai after diress baka mai sheki,sannan ta gaba an ratsa pink hakanan rigar ba ta kai kasa ba.don haka ana ganin wandonta, dan siririn mayafinta ba shi da girma, [01/10 12:45 pm] Abdul: STEP (5) Shima pink bai rufe dogon gashinta ba. Kafarta sanye cikin takalmi shima pink dinne,da ratsin baki marar tudu mai igiyoyi,purse din hannunta da wayoyin ta kirar nakia duk kalar pink ne.can sama goshinta zaka iya kallon wani katon gilashi irin wanda wayayyun 'yan mata masu jin kansu suke sakawa.da gudu yau ya nufe su domin duk da bai san MIMI ba ya san maigida na su.cikin ladabi ya yi masu sannu da zuwa,ya amshi jakar hannun alhaji, alhaji ne kawai ya amsa, MIMI kan ko kallon shi ba ta yi ba. ya bude kofofin motar sannan ya sa jakar alhaji a kujerar gaba,bayan sun fito daga filin yana hawa titi zai raraka da gudu,alhaji ya ce tafi a natsuwa MIMI bata son gudu,yau yace,to ranka ya dade. shi kanshi mai gadi a waje ya tsaya yana jiran zuwan su,yana hangosu da gudu ya nufi ciki ya wangale get din,kamar yanda MIMI ke so,don bata son jira.ko da direba ya tsaya ya bude masu sannan ya cire jakar ya bi bayan su MIMI ta kalli gidan sannan tace,Dad gidan nan yana son fenti yayi datti,ya yi 'yan kalle-kalle,yace,na lura da haka za a sabun ta shi da fenti.direban ya ajiye jakar a kujera sannan ya kalli alhaji Alhaji, na barku lafiya ya fita.Alhaji yaso ma kiran hajiyata-hajiyata,ta fito,dankwali a hannun ta,domin lokacin ta gama saka kayan,ta yi adonta cikin super kalar blue da ratsin yellow sai kamshin turare take yi. Ta kalli mijinta, sannu da zuwa alhaji,ya ce,yawwa sauda ta dubi MIMI wadda tunda suka shigo falo ta natsu saboda duk iya-shegenta tana tsoron uwarta,ta san hajiya sam bata daukar reni.ta dago ido cikin fargaba ta kalli mahaifiyarta sauda tace, sannu hajiya,ta amsa yawwa,ya mominku nafisa da kuma sauran kannenku?ta ce kowa lafiya,hajiya ta ce,masha allah,ta dauki hular alhaji da jakarsa da kuma malun-malun dinsa ta nufi dakinsa tana fadin za a hada ruwan wanka ko? aa rabona da abinci tun safe shima ba wani abinci na ci mai nauyi ba coffee ne,ta karasa dakin ta aje kayan hannunta ta fito tana fadin mu je Dining. [01/10 12:45 pm] Abdul: STEP (6) Hajiya ce ta janyo masa kujera ya zauna,ya kalli MIMI zauna mana uwata.ya mayar da kallon shi ga hajiya sauda, an yi mata farfesun kifin? hajiya ta kalli MIMI cikin daurewan fuska,sannan ta ce,an yi,MIMI ta turo baki tare da hada rai. hajiya tana zuba masu dan waken cikin plate tare da colslow,ta janyo wani plate din tana zuba masa farfesun kafar sa,ta tura gabansa tana fadin alhaji ba ka tambayi yaran gidan ba?ya kalle ta cikin 'yar zolaya yace,duk ganin ki ne ya mantar dani.ko da dai na san zuwa yanzu suna lslamiyya ko?ta ce eh,yau kam ma da murna suka fita,don na gaya masu cewa kana tafe,ya ce ga shi ban riko masu tsaraba ba.amma bari in sa direba ya sayo masu,ta ce aa zai fi kyau ka fita dasu don yaran nan basa samun kulawarka,kamar fa sam basu shaku da kai ba. Ya kalli MIMI wacce ta jibga tagumi,ya ce zan gani ko da lokacin,kin san fako a can ba samu zama nake yi ba.shiru tayi don ta san kome za tace ba fahimtar ta zai yi ba,ta jima tana yi mishi nacin cewa,ya dinga baiwa yaran ko da awa daya ne a cikin lokacinsa, amma sam ya ki.ko su da suke matansa basa ganin shi a kan lokaci,sai yayi wata ko sati uku in kuma yazo kwana biyu yake yi, nan guri ta ya kwana daya ya je malumfashi wajen hajiya binta ya kwana daya tunaninta ya katse lokacin da ta ji yana tambayar MIMI menene uwata?na ga duk kin bata ranki?ki ci kifinki mamana. ya kalli hajiya sauda ina kifinta?hajiya ta nuna kular da cokali,ga kular kifin nan gabanta?ta dauka mana ko a baki zan bata?MIMI ta sake tura baki tare da kallon mahaifiyarta,ni na koshi,hajiya sauda ta ce, karyarki dubu wallahi kin yi kadan ki ce a dafa miki abin, yanzu ki ce baza ki ci ba,saboda bakin raini ai na lura da ke tunda ku ka shigo gidan nan na san baki so zuwa ba, ko katsinar ce baki so zuwa ba oho miki, amma bakin ranki ya kare miki can. Sauda!alhaji ya katse ta tare da daga hannu, gaskiya ni bana son abinda ki keyi,a ce ke da 'yarki ta cikinki amma ba ki kaunarta?.... [01/10 12:46 pm] Abdul: STEP (7) Hajiya tace, ba kaunarta bane bana yi, halinta ne bana so.kuma in har ta ga mun zauna inuwa daya da ita to ta tabbatar ta canza halinta,in ko ba ta canza ba to sai dai ta nemi wata uwar ko da yake tana da ita ma. ya tausasa murya ai ba maganar fada bane, amma gaskiya ba zan iya kallo kina mata irin kalaman ba, kullum tana yi mini korafin ba ki sonta,ita in fada mata gaskiya ko dai bake ce ki ka haife ta ba?ya aje cokalin hannunshi,na rasa me take miki,ita dai ba ma a kasan nan take karatun ta ba.sai ta zo hutu irin haka,amma sam ba kya ko yin kewar ta. hajiya ta tsiyaya masa lemun abarba,wanda ta hada masa,a cikin kofi sannan ta tabe baki ta ce,halin ta kawai zata canza,in dai tana son soyayyata.yanzu baka kalli shigar da tayi ba? tun daga abuja ka sako ta gaba har katsina, kana mahaifinta ga shi kanta a waje,kayar jikinta duk sun dame ta,wai ita dole ta waye. ya kalli MIMI sannan ya kalli sauda, da dan murmushi,ina laifin kwalliyarta,ni ban ga aibun ta ba,haka 'yan mata matasa irin ta ke yi.ya kalli MIMI,ci kifin ki uwata kar ki damu kin ji?tsaki hajiya ta yi ta nufi dakinta.sai lokacin MIMI ta samu damar yin mita,kaga ko dad,sai da nace ka barni can in gama hutu na,ka ce aa sai na zo, ni daman na san hajiya ba za ta taba so na ba. Ta mike tsaye tare da kallon jikinta,shiga tafa, mene ne aibunta?ya kalle ta cikin sigar lallashi yace, ban ga laifi ba.ita hajiya wai sai tace,sai na saka hijabi da atamfa,ni kuma ba zan iya sa iri wannan kayan zafin ba.na yi karatu na waye ni ba irin su usaina ba ce kauyawa.yayi murmushi,shgwabarta tana burge shi.kallon ta ya ke yi tamkar 'yar shekara biyu. ya mike ya zagayo wajen ta ya dafa kafadarta,kar ki damu uwata.mamanki tana sonki,na san ta ga nafi damuwa da kene cikin 'ya'ya na,kin san don ita ce ta haife ki,shi ya sa fa.in da a ce kamar hajiya binta ce ko nafisa da tuni na sallame su,kin manta na taba kora hajiya binta saboda ke?ta ce na tuna Dad, [01/10 12:46 pm] Abdul: STEP (8)Ya ce to kar ki damu ina son mahaifiyarki ko da bata haifamin ke ba, bare ta haife ki. kina son a ce mahaifanki biyu ba su tare?ta ce ba zan so ba dad.amma ka yi mata magana ta daina matsa min,ya ce zan yi mata, amma ke ma ina son cikin kwana biyun nan ki canza kaya sawarki,ki rinka saka irin wadanda take so.ta ce zanyi in dai za ta bar ni in yi abinda na ke so,ya ce za ta barki mana kin ji,ki dai na kuka.ya yi ta lallashinta har ta daina kuka. suna cikin cin abinci hajiya ta sake fitowa daidai lokacin yara suka dawo daga lslamiyya da sallama suka shigo, ita ce ta amsa sallamar,husna da hasina ne a gaba,suka ce sannu da gida hajiya ta ce yawwa sannunku da dawowa yara na.ina sauran? kafin suba ta amsa sai ga su suna ta yin sallama,da hannu ta nuna masu gurin dining,ga dadin ku,suka nufi gurin suna gaida shi da daidaya.ya dafa kan husna da hasina, su ne kanana a gidan, yana ta amsa masu.MIMI ta hada rai ita ba ta son hayaniya. dady ya ce,ba ku gaida sista MIMI ba.suka kalle ta don suna tsoron ta,sannu yaya MIMI,cikin daure fuska ta ce,yawwa,na amsa duka ne ba sai kowanne ya gaishe ni daya bayan daya ba.hasana da usaina sune 'yan matan da suke bi MIMI a haihuwa.dad ya kale su ku shirya da kannen ku, yau yazo ya kai ku super market ku sayo tsarabarku, don ban riko komai ba, kowa ya je ya zabo abinda ranshi ke so. Yara suka shiga murna hasana da hussaina suka ce dad,mu kam ba zamu je ba.ya ce,saboda me?suka ce,muna da karatun hadda gobe,malamin mu zai zo, bin abdulrahaman.hajiya ta ce,tabbas ba ku da halin fita, in ba haka ba zaku sha dukan tsiya gurin shi.duka kuma?in ji dad dinsu,hajiya tace sun wuce duka kenan?karatu sai da zare ido.abdulkarim ya yi sallam, ya shigo falo suka amsa,ya iso gurin dadin shima ya gaida alhajin.MIMI tana ta chatin dinta ba ta dago kai ba,shima bai ko kalle ta ba. ya dubi su hasana ya ce, kun dawo?suka ce eh! yaya sannu da zuwa, dazun hajiya ta fada mana zuwan ka. mun je dakin ku kana wanka, [01/10 12:46 pm] Abdul: STEP (9) Kuma lokacin lslamiyya ya yi dole muka tafi.ya ce,na ji shigowar ai, ya ya zauna,usaina na fadin,lslamiyya lafiya,munyi murajaa ne yanzun. ya ce, kun kusa fara jarabawa kenan suka ce eh! hasana ta ce,yawwa yaya don allah ka amsar mana hadda in anjima mun yi magariba, gobe da safe muna da malamin gida bin abdulrahaman.abdulkarim cikin sigar tsokana ya ce, bani da lokaci,ku ce gobe zanyi kallon duka. usaina ta ce agaji yaya abdul, bulalarshi akwai zafi,suka sa dariya tare.ya ce,bari mu yi sallah sai in karbar maku,suka ce,yawwa yayanmu mun gode. MIMI daga wurin da take zaune tana jin su tana kuma kallon su,sai ta soma mita,ni na san duk 'yan gidan nan ba sa so na,dole kawai suke gani na,kalli yaya abdul,ko kallo na bai yi ba.alhaji yace,kai! abdulkrim,ya ce naam,ya zo ga ni dad.ya ce baka ga MIMI ba ne?ran abdulkarim ya baci,nan a take fuskarsa ta nuna,cikin wata murya marar dadi ya ce,na ganta mana dadi.shine ba za ka yi mata magana ba? Kafin ya yi magana hajiya ta amsa da cewa, in duniya da gaskiya ita da shi wanene gaba?shine ya kamata ya gaida ta,ko ita ce ya da ce ta gaishe shi?. alhaji ya ce,amma ita bakuwa ce.bayan haka kuma yaushe rabonsa da ganinta?a kalla ya nu na kewarsa gare ta ko?kan abdul yana kasa tamkar ya sa kuka don haushi da takaici.hajiya ta ce,bai gaishe ta din ba.tafi abinka abdulkarim,cikin sauri ya wuce.su hasana ma suka yi dakinsu ita ma hajiya ta juya zuwa dakinta,MIMI ta kalli dad,kawai mu koma kalli fa duk yanda suka watse suka barmu,ya dafa ta karki damu ina zuwa. baki gado hajiya sauda ta zauna ta zabga tagumi,wannan abin ya ci mata rai,a ce mutum kamar alhaji ya dinga irin wannan abu sai ka ce yaro.kirikiri yana gani garkiya sai ya runtse ido saboda son zuciya,bai san cewa haka zai sa kan 'ya'yansa ya rabu ba ne?sallamar shi ce ta katse ta,ta dago ta dube shi,shima ya iso ya zauna bakin gadon.haba hajiya ki sakarwa 'yarki fuska mana?ke ba abin faharin ki bane a ce nafi son 'yarki,duk cikin 'ya'ya na? [01/10 12:46 pm] Abdul: STEP (10) Ya kama hannunta cikin sigar lallashi ya ce,haba sauda kin fa san ina tsananin sonki, sonki ne fa ya shafe ta ko baki lura ba?ta daga ido ta kalle shi,ban musa ba,na san kana so na,amma ni burin na shine ka yi adalci tsakanin yaranka alhaji, ko don gudu rarrabuwar kansu. ya ce,menene na yi mata wanda ban yi masu ba?ta kalli cikin idon shi,ai ba za su kirgu ba,banda nuna tsantsar kulawa a fili, duk cikin yaranka wanene ka kai kasa wajen karatu bayan ita?to indan wannan ne,karatun na su na gida ya fina ta cin kudi sauda. umm, haka dai za ka ce,tunda kana son kare kanka,ya ce, ni dai ina neman alfarma ki sakar mata fuska ki dan ja ta a jikin ki har mu tafi.ta kalle shi,ta rasa me zata ce masa,sai kurum ta ce to. don tana son kawo karshen zancan, ya shafi kumatun ta,na gode,ya matso da bakin shi saitin kunnuwanta,ina son a kyuatata shimfida ta anjima. don na iso da muradin hakan. Ta sake murmushi tare da kallon shi,wai alhaji yaushe zaa girma ne?ta yi tambayar cikin sigar wasa. ya janyo ta jikin shi,wa ya ce miki ana girma da lada? sai dai in mutuwa ce ta dauka.suka sa dariya tare, daidai lokacin aka yi kiran sallar.suka mike, ta ce lokacin sallah yayi bari in fita 'yan mazan nan sai nayi fama sannan su wuce masallaci.tare suka fita ya nufi dakin shi,har lokacin MIMI tana zaune a falo.sai dai lokacin ta koma kan kujerar zaman mutum biyu tana ta chatin. alhaji ya nufe ta yana cewa,mamana kina hutawa ne?ba tare data dago ba,ta ce eh dady.ya ce da kyau.ya wuce dakinsa. hajiya sauda ta dube ta,ki tashi kiyi sallah,ta dago ta kalli hajiyar ta ga fuskarta a daure,ta zabga mata harara na ce,ki tashi ki yi sallah.tsam ta mike ta nufi dakin su usaina inda nan ne take sauka in ta zo,kayan tama cikin suke.sai dai ita bata sm hakan saboda a abuja sasanta dabam, amma a nan hajiya ta hana a yi mata dakinta dabam.ta sami su hasana suna sallah, ta fadi kan gado ta ci gaba da chatin dinta.ga al'ada alhaji in ya fita sallah, [01/10 12:46 pm] Abdul: STEP (11) Yakan kai sha biyu bai shigo gida ba zai yi ta gaisawa da mutane, abokai zuwa 'yanuwa suka ji cewa ya shigo gari.don haka ita ma hajiya bata fito ba sai bayan sallah isha,ta shiga daki alhaji don sake kalailai ce shi,tare da kunna turarukan kamshim daki,ta fitar ma da alhaji kayan barci,ta dama masa fura,ta nufi dakin yaranta don ta tabbatar suna cikin koshin lafiya.daki maza ta fara shiga, umar da aminu suna ta yin home work, abdullahi yana kwance kan gado, sadik yana buga game a tv. ta ce,sarkin game kai ka yi home work dinka? ya ce, eh nayi hajiya ta kalli abdullahi,kai fa bawan allah yau da wuri zaka yi barci kenan? ya tashi zaune kaina ke ciwo hajiya shi yasa ki kaji na ce dad ya bari sai gobe mu je super maket din.don ba zan iya kula da su ba. ta ce,ba sai kun yi haka ba,ya ce,kin shiga daki lokacin ta ce,to ka sha magani?ya ce eh!ta ce to allah ya sawwake,ya ce ameen.ta ce,sadik tashi ka kulle muku kofar ku sai da safe,suka ce,to ta ce,kar fa ku manta da yin addua lokacin barci,suka ce to.ta nufi dakin su husna da hasana da kuma zainab yar gidan hajiya binta, wace ta ki komawa wajen uwarta,tun lokacin da alhaji ya saki hajiya binta,ya kwaso yaran ya kawo su nan.hajiya sauda tace sam ba zai yiwu ba,lallai ya mayar da ita,ta rike kayanta. domin ita kanta ba zata sa araba ta da 'ya'yanta ba.shine da ya dawo da ita ya mayar mata da yaran amma ban da zainab,don kuwa ta kekashe ba9a ta bi su ba. lta ta fi son zama a nan, hajiya sauda ta rike ta,ta hada da 'ya'yanta guda goma sha biyu da ta haifa suka zama sha uku.su kam sun fara barci.don haka ta shigo ta yi masu addua tare da kulle masu kofar dakinsu. hasana suna zaune suna kara ma juna haddar alkur'ani mai girma, ita kuwa 'yar gwal,wato MIMI tana kishigide kan gado.tana ta chatin,kai tsaye gurinta hajiya ta nufa ta fisge wayar da sauri MIMI ta dubi wayar cikin bacin rai.tana ganin hajiya sai ta yi kasa da kai kamar munafuka,kin yi sallar ne? cikin tsawa ta ji maganar MIMI, [01/10 12:46 pm] Abdul: STEP (12)MIMI ta yi shiru, ta ce,ba ki ji niba ne?ta girgiza kai tare da fadin banyi ba. hajiya ta rufe ta da fada bangane ba kiyi ba? Anya ma kina yin sallar na kuwa? ta kalli hajiya cikin sauri tare da fadin ina yi mana,hajiya tace,karya ne kalli agogonki karfe nawa ne yanzu?da har zuwa yanzu baki yi ko sallar magariba ba bare lsha.in na lura musulunci ba ya birge ki,lslamiyya kin daina,duk wani abu da lslam yazo da shi,komi na addini kin mayar da shi kauyanci,ke ga 'yar boko ko?MIMI dai bata dago kai ba,hajiya ta ce,na san ko zaa kashe ki yanzu da kyar in zaki iya kawo mini fatiha cikakkiya. kin zauna kina ta danne-dannen waya,in ba ki sani ba ne gara ki sani,kina cutar kanki ne.rayuwar daki ka daukar wa kanki ba mai dorewa ba ce,don haka ba ta dace da ke ba.ki ta shi ki yi sallar yanzun nan, sakarya marar hankali. simi-simi MIMI ta tashi ta nufi bandaki,hajiya ta ce,tunda abin naki ya soma nisa haka,wayewar taki har ta kai ki da gudu salla,to nan gida za ki kare hutunki.ki dau karatu gurin malamin yaran nan,ki koyi salla tun da bani da tabbacin kin na yi.bari baban naku ya shigo,ta juya ta fita da wayar a hannunta.MIMI daga cikin bandaki,kuka wiwi ta dinga yi,ita kam baza ta iya zam har ta gama hutu cikin takurar ba. a silent hajiya ta saka wayar MIMI ta ja durowa ta jefa.MIMI tana kuka ta yi sallar,su hussaina suna kallonta,ta idar ta fada kan gado ta ci gaba da kuka.don ita amshe mata wayar da hajiya ta yi,ya fi bata mata rai fiye da fadan,don jin ta take tamkar an raba ta da ranta, sam bata nisa da wayarta. misalin shabiyu saura alhaji ya shigo,tuntuni yake ta neman layin 'yar lelanshi,amma sai tayi ta ruri har ta yanke ba a daga ba. hajiya ta shiga ta same shi tana cikin shirin barci,ya kalle ta da wayansa a hannu,MIMI fa?ta kalle shi,in kira maka ita ne?ya lura cikin gatse ta yi masa maganar,don haka sai ya ce,aa dama in ji ko ta yi barci ne,saboda ina ta kiran wayarta bata dauka ba.cikin jin haushi hajiya ta ce oho.. [01/10 12:46 pm] Abdul: STEP (13)Na zata ita ma nan zamu kwana tare don kar wani abu ya cinye ta. ya mike tare da kama hannunta,sauda kin canza sani na ba haka kike ba.yanzu kin zama mai saurin fushi.ta kalli fuskarsa,kai da 'yarka kuka canza ni.ya ja hannunta,to zo mu zauna in ji mai zan samu.ya basar da wancan zancen.ita ma sai ta biye masa da cewa,duk abinda kake so.ya tallabe fuskarta kin san mene ne sauda?ta girgiza kai kullum na kalli fuskarki.rana mai tarihi a guri na.hajiya sauda ta ce, ikon allah ni kan da a ce kalmar karatu ce,da sai in ce,tuni na haddace ta,tun muna da kananan shekaru. ya yi 'yar dariya ina jin dadin tuna baya,wani lokacin sai in ji tamkar in mai do lokaci.ta lumshe ido, ai alhaji kuruciya cike ta ke da shirme,in ta wuce sai ayi ta kewarta, [01/10 12:46 pm] Abdul: STEP (14)Ni kaina ina son tuna baya,rayuwa tana da sauri,duk da haka in muna tare,sai in rika jin kaina tamkar 'yar kasa da shekara ashirin.yayi dariya,a haka ni ke kallon ki sauda,kullum na kan ce, lokacin na sauri.ta kwantar da kanta a kafadarsa.allah ya kara mana tsaw rai da rayuwa mai amfani.a kunne ya rada mata amin.da ma an ce soyaya bata tsufa, sai dai masoya su tsufa, allah ka yi mana mai kyau. karfe bakwai alhaji bashir yana ta shiri cikin sauri,hajiya tana taimaka masa gurin saka kaya, rokonsa take yi ya dan sa wani abinci a bakinsa,ta ce don kai nasa a yi kunun gyada da kosai,saboda na san kana so.ya kalle ta,ta na saka masa liks a hannun riga ya ce,ki yi hakuri mata ta,ba komai,na yi alkawarin zan gana da wani mutum ne,wanda na fi wata guda ina neman damar ganinsa. ta ce,duk da haka ka karya zai fi.ya ce sai na dawo,domin in na samu damar da nike nema a gare shi,kasuwanci na zai ninka,in ko haka ta samu yaya kika gani?ta ce, umm! kai dai da ma kullum saurin ka bai wuce kasuwanci,a kasuwanci ina ne ba a sanka ba,duk fadin afirka ina ne sunanka bai kai ba! wane irin kudi ne baka mallaka ba kullum cikin samun riba ka ke. ta mika masa hularsa,me ya kamata ka nema kuma alhaji?yanzu baya ga aljanna? murmushi ya yi,ba tare da yaba ta amsar duk tambayoyin da ta jero masa ba.ta ci gaba, ni dai ba zan gaji da baka shawarar cewa,kamata yayi zuwa yanzu kayi murabus ka bar abba da mukhtar su jagoranci kasuwancinka.ya ce,ni kuma fa ta ce,ka zo mu zauna mu huta,mu karasa rayuwarmu,'yan kananan yaranmu su shaku da kai.ya saki dariya tare da cewa,sauda kenan.in ki ka fadi wata magana sai ki tuna mimi tadinmu na farko da ke.ta ce au!kana nufi maganar ma dana fada shirme ce?ya ce,kusan haka,kina cewa in bar ma su abba ragamar kasuwanci,ki na tsammanin za su yi jarumtar kasuwanci kamar ni? bai jira amsa ba,ya ci gaba da cewa,da ma MIMI ce babba,ko da tana mace na san za ta iya.amma su abba shirme kenan,shi yasa kika, [01/10 12:46 pm] Abdul: STEP (15)Ga ko shawara ce na fi son yi da ita koyaushe ta na bani shawara ta musamman yadda ake fadada kasuwanci a duniya ta cikin yanar gizo.su kuwa su abba bakin ku daya.kullum in takaita kasuwanci a iya gida nijeriya,ni kuma na wuce nan tuni. ta ce,ka fahimce ni ba muna cewa kar kayi kasuwanci da waje ba ne aa,ai bunkasar ka ta isa ka yi kasuwanci da waje.harkar shigo da magunguna ne muka ce ka daina,tunda ana yawan zargin kana shigo da haramtattun magunguna da kuma miyagun kwayoyi.ya gyara zaman hularsa,ya sa hannu ya shafi kumatun ta, ki ci gaba da yi min addua sauda,ke ce kurum ki ke fada min son ranki in ji ban ji haushi ba.ya cire takalminsa tana fesa masa turare ya ce,ban sani ba ko zamu gama tattaunawa da wuri ko ba zamu gama ba, amma ko yaya ne dai daga can zan wuce malumfashi. in duba su binta da yara sannan in kewayo gona ta, na jima ban leka ta ba.inda lokaci zan shiga masari can ma na jima ban je ba.kin ga sai na kwana kenan,gobe zan dawo in dauki uwata mu koma inda muka fi wayo.ta ce,allah ya tsare sai ka dawo din amma batun tafiya da MIMI ne nake tunani a kai.ya kalle ta, kamar yaya?ta ce,sai ka dawo dai allah ya tsare,ya dan tabe baki amin.suna fitowa falo yara suka nufo suna yi masu sannu da fitowa tare da gaishe shi,ya amsa da daidai,ya kalli usaina,MIMI fa?ta ce tana kwance dady,ya ce,shikenan zamu yi waya.hajiya ta raka shi har mota,ba sabon abu bane,haka ta saba tun suna da kuruciya.falo ya kacame,yaran suna ta karin kumallo,sai hayaniyarsu da karar kofuna.MIMI ta fito sanye ciki riga da wando masu dan kauri na barci. sauri ta ke yi,tare da fatan allah ya sa dad dinta bai fita ba,don ba za ta taba bari ya fita ya bar ta ba.ta iso gurin hajiya,fuskar ta babu annuri ta ce,ina kwana hajiya?ba tare da ta dube ta bata ce,lafiya lau.MIMI tayi tsaye shiru,tana son yin magana amma tana tsoro.hajiya ta dago ta dube ta,ga kayan shayi can a kan dining,na san ba kya shan kunu,ta ce tam!ehemm!da ma zan gaida dady ne,yana ciki ne? hajiya ta ce a'a. [01/10 12:46 pm] Abdul: STEP (16)Ya tafi malumfashi sai gobe zai dawo.MIMI ta zaro idanu yaya dady zai min haka ya tafi ya bar ni,ta kalli hajiya wanda ta soma watsa mata harara ta ce,hajiya don allah ina waya ta?hajiya ta ce,sai za ku tafi zan baki,don ni ba za kiyi mani chatin din naki ba a nan,ki karya ki je ki yi wanka,in malamin su hussai ya zo zaki bisu,ki je daukar karatu a gurinsa.ina sa ran ma alhaji ba zai tafi da ke ba,nan zai bar ki sai kin san addininki za ki tafi,ko da zaki cinye hutun ki a nan. cikin sauri MIMI ta koma daki cikin kuka sai da tayi me isarta ta shiga wanka,a fili kuwa fili kuwa fadi ta ke, allah ba zan zauna ba, shi ya sa na tsani zuwa katsinan nan.dolenta ta saka atamfa riga da siket,a cikin durowarta ta ciro don tana da kaya a nan gida, duk lokacin da aka yi wasu usaina sai an yi mata.ta shirya tsaf ta koma kan gado ta kwanta tana tunanin yadda za ta yi.amma ko ta halin kaka baza ta zauna cikin irin takurar ba.can ta hango wayar hasana kan durowar ta.cikin sauri ta tashi ta dauko,layin dad ta kira wanda ta san in ta kira zai dauka da sauri,cikin kuka ta soma magana,bayan ya daga dad kaga hajiya ta dauke min waya ta,kuma wai ba zan tafi ba,ni dai dad wallahi bazan zauna ba.ya ce,ya shiru uwata kar ki damu ba zan barki ba ni ma,yanzu me kike so?ta ce,phone di na,ya ce,shikenan zan ce ta ba ki,kin ci abinci?ta ce,aa ya ce,to kije ki ci zan sata baki wayarki kin ji? ta na zaune a kan dining ta hada shayi tana sha da cokali cikin hankali don ita sam bata da hanzari,tana kallo lokacin da hussaina ta kawo ma hajiya waya ta ce,dady ya kira,ta daga.ta na jin lokacin da hajiyar take cewa,tsaya kaji alhaji, sai kuma tayi shiru,da alama ya katse ta ne,ya hana ta magana,don taga hajiya tayi shiru,amma ranta a bace yake.sai kuma tace to alhaji naji zan bata, amma bana son chatin din nan data keyi.MIMI ta yi murna,a ranta tace dady na kenan,ta nufi daki da murna,alhaji ya ce,kar ki damu sauda,'yarki mai kamu kai ce.ita da kowa ya shaida ko saurayi ba. [01/10 12:46 pm] Abdul: STEP (17)Shi yasa nike dubawa don in samo mata miji wanda zai kimanta min ita,ya bata kulawa fiye da wanda take samu a guri na. [01/10 12:46 pm] Abdul: STEP (18)Hajiya ta ce umm!allah ya taimaka,ai ni dana zaci ma baza ka iya auradda ita ba(cikin gatse tayi maganar)ya ce,kash kin ji ki da wata magana kuma sauda,in ban aurar da ita ba ai kuma na cuce ta.ina maki kaga an taba haka?ke dai kiyi mana addua,ta ce,allah ya taimaka,kun gama ganawar ne?ya ce,eh,yanzu haka muna hanyar malumfashi sai na dawo ta ce,allah ya tsare,ka dawo lafiya,ya ce, amin,ga dai uwata nan amana naba ki,katse wayar yayi ba tare da ya jira jin amsa daga bakinta ba.ga zaton MIMI tana aje wayar alhaji zata zo taba ta tata,amma sai taji shiru. ta sake fitowa falo nufin ta kila hajiya ta ganta ta tuna,idan ta manta ne, amma sai taga hajiya ta ci gaba da lamuranta.yaran duk suka yi wanka suka fito,husna da hasina suka shiga falo da gudu suna cewa,ga malam nan yazo.ga mamakin MIMI sai ta ga duk yara sun rude, wasu sun dauko alkur'anin su suna karantawa da sauran littafai da yake masu.a ranta ta ce ni ko bari in ga wanene malamin ,kai har naji na tsane shi tun kafin in ganshi.a zaton ta nan zai shigo sai ta ga abdullahi da umar da aminu da sadik sun soma fitowa bayan dawowansu sai zainab da hasana da hussaina suka fita. hasina da husna kuma sun dukufa suna ta karbarma juna hadda,kafin a zo kansu.MIMI ta tabe baki tare da cewa,wahalar da kai,basu dade ba suka dawo.su hasana sun mike kenan hajiya ta fito daga daki ta ce,ke ma tashi kije, ta nuna MIMI ta hada rai,sai dai bata da damar yin musu,don babu alhajin da zai tare mata.hasana ta ce. yaya MIMI sai kin sako hijabi fa,ta banka harara,ban dauko ba,ina wasa da ke ne?in ki ka kara yi min magana sai na mare ki. suka yi shiru suka wuce,ta warware dan kwalin kayanta ta yafa,tana biye da su har falo baki,kafin su shiga sai da suka kara gyara hijabansu suka yi sallama suka shiga,ta tsaya tana mamaki wai malami ne suke yi ma bare-baren, malamin ma wai na lslamiyya,ita malami ko na boko bata dauke shi wani abu ba,face bawan ta mai ci a karkashin su.bare da ba zata iya, [01/10 12:46 pm] Abdul: STEP (20)Saboda ba son karatun ta ke yi ba.ka soma mata daga fatiha don ba na zaton ta iya,don allah malam lsmail kar kayi mata da sauki.lsmail ya ce, ba komai hajiya.amma ta saka hijabi ta ce,to ba komai bari in sasu hasana su kawo mata,in ta ki yi ka dake ta ko ka kira ni. hajiya ta fita shi kuma ya kai duban shi gare ta, MIMI ta cika tayi tam.ya na zama hasana tana shigowa da sallama,shine ya amsa,ta ce,yaya ga shi, harara ta watso mata,ta ki amsa,hasana ta aje a hannun kujeraq da take zaune ta fita. ya kalle ta,malama ki saka hijabinki mana,cikin sauri ta dago kai ta dube shi duban tsana mai tsanani,domin ba a taba ci mata mutunci kamar yau ba a gaban kaskantacce irin wannan.ba a taba rena mata wayo ba kamar yadda shi din ya yi mata,ya ganta sarai,amma ya ce,bai ganta ba.abin yayi mata ciwo fiye da abinda hajiya tayi mata.ta harare shi sama da kasa sannan taja tsaki, malam baya daukar reni,sabi da haka sai ya hada rai tare da rufe alkuranin shi. ta ce kai waye suna da ake kiranka? ina son ka sani na wuce ka rena min wayo kuma kai baka isa ka koya min karatu ba.ya daga hannu tare da katse ta da cewa ke.ba ki da ladabi ne? gaskiya ba tarbiyyar nan gidan ba ce,domin yaran gidan nan mazansu da matansu nayi shedar su guri ladabi game da sanin darajar mutane,ke ma ina yi maki nasiha ki canza.kuma ina son ki sani karatun nan in kin yi kin ma kanki ne bani ba,don haka ka da allah yasa ki yi,ya mike ya fita abinsa. yana jiyo tsakinta gami da cewa, talakan banza kana ci a karkashin mahaifi na ka nuna ni da yatsa,to bari ka gani lokacin barin ka aiki yayi.har ya tafi ya dawo ke ma dukiyar daki ke takama ba taki ba ce,ta mahaifin ki ce,ina son ki sani ba keki ka dauke ni aiki ba bare ki sallame ni.ba kuma maula nake zuwa yi a gidanku ba,ina son ki san wannan.kafin ta sake yin wata magana ya wuce ya barta cikin takaici,lallai sai nayi maganin sa,shine mutum na farko a tun tasowar ta da ya taba fada mata abinda ya ke so, [01/10 12:46 pm] Abdul: STEP (19)Face bawan ta mai ci a karkashin su.bare da baza ta iya bambamce shi da maigadi ko mai sharan gidansu,kosawa ma ta yi ta shiga ta gani wane gaja ne? ta jingina da kofar,sannan ta kai kallonta gurin shi,yana zaune kan kujeran zaman mutum daya sanye yake da jallabiya mai ruwan madara mai dogon hannu da maballi a hannu,tare da kwala a wuyarta.ga wani dan ado da zare mai ruwan kasa da aka yi a wuyar da hannun rigar,bata kai can kasa ba,irin dai shiga ta sunna,hular kanshi baka ce irin wanda ake kira minista. ya na rike da alkurani yana bude inda suke.su kuma su hussaina suna zaune a kasa kan kafet a gabanshi duk suna rike da alkuraninsu,MIMI ta tabe baki tare da harde hannuwanta a kirjinta,tana kare masu kallo.a ranta ta ce,tabdi,ai ba a yi mutumin da zai zo gidan ubanta ta zauna a kasa yana kan kujera ba.malam lsmail ya dago ya kalli bakin kofa da kyawawan idanunsa,duhun mutum ya gani,ya sa shi kallon gurin ya kalli MIMI da ke tsaye ta watso masa wani kallo da ba zai iya fassarashi ba.ya mayar da kanshi ga abinda yake yi.su hussaina suka ci gaba da kawo masa hadda yana yi masu 'yan gyare-gyare, suka kamalla,sannan suka soma sauran littafai. ta shiga ta zauna tare da daukan rimote ta kunna tv, ya dago ya dube ta, tamkar zai yi magana,amma sai ya fasa. ya san da gadara tazo, bayan su hussaina sun kamalla,sai hussaina tace, yaya kizo mun gama,ta kalle su cikin harara,ku fita mana, suka fita suka je suka sanar da hajiya ko mai.ita kam suna fita ta mike tana tafiyar nan tata, ta isa kan kujerar gefen shi ta zauna. ya dago ya dube ta,ya mike tare da tattara littafansa,ya nufi fita,a bakin kofa suka ci karo da hajiya zata shigo,ya dakata ta kara so suka gaisa,ta ce, har ka mata karatun?ya ce, wace kenan?ta ce, MIMI, bangan ta ba ai,hajiya ta ce aa ta shigo ciki falon, ta ce gata nan fa,ya dawo cikin falo,ok!wannan ce? na ganta amma ban zaci karatu za ayi mata ba.ita kuma bata fada min ba. hajiya ta ce,ai ba zata fada maka, [01/10 12:46 pm] Abdul: STEP (21)Kuma tana son ya zama na karshe, takaicinta ma talaka ne shi, ba wani isashshe ba. daf da zai fita daga cikin gidan,abdulkarim ya yi masa sallama,ya tsaya suka gaisa ta hanyar yin musabaha.ya ce,ai ina ta sallama baka ji ba,ya ce, na ga fuskar ka ba walwala ko yaran ne suka hada maka zafi?malam lsmail ya ce,ko kusa ai yaran gidan nan basu da matsala sam, sai dai wata bakuwa da hajiya ta ce a koya mata karatu,amma ba yar ta bace ko?abdulkarim ya sake matsowa kusa da shi,ya ce,ba dai MIMI ba? lsmil ya ce,kamar haka naji an kira ta,gaskiya saboda ita zan iya daina zuwa gidan nan in har zata dinga zuwa karatu.abdulkarim ya ce,kai mata nuna maka halinta kenan,don allah kayi hakuri zan fada ma hajiya, kuma ina zaton ma gobe zata tafi,lsmail ya ce, shikenan ba damuwa. suka yi sallama ya fita, abdulkarim ya nufi ciki kai tsaye zuwa falon hajiya, duk suna falon,MIMI kuma tana kujerar dining,ranta cinkushe,ya kalli hajiya,ke ki ka tura MIMI tayi karatu gurin lsmail,ta ce tayi masa rashin kunya ko? abdulkarim ya ce,ta yi masa kenan tunda ya ce, matsawar zata dinga zuwa gurinsa daukar karatu to kuwa zai daina koyar da yaran gidan nan. hajiya cikin fushi mai tsanani ta rufe MIMI da fada,ta ce,in kika sake na samu labarin kin yi sanadiyar koran malamin nan sai kin sha mamakin abinda zan yi miki,sai kin yi zaton ban sanki bama,sam bare ki tuna cewa nice na haife ki.don malamin nan ya fi min ke amfani,MIMI ta sa kuka,hajiya ta ci gaba,tunda na lura karatun ne baki so,to sai kin yishi,bari alhaji ya dawo nan zai barki sai nayi maganin abinda ke damun ki a cikin kanki. MIMI ta fada daki tana kuka. hajiya ta kira layin malam tana bashi hakuri a kan abinda MIMI tayi masa,yace babu komai ai yarinya ce. washegari misalin shadaya da rabi alhaji ya dawo.ya iso cike tam,ya ce,a ba MIMI wayanta, amma ba a bata ba.sai dai yadda ya samu hajiya rai bace kamar ma har kuka tayi,sai kuma ya juya da tambayar shi kanta yana son jin abinda ya same ta ciki, [01/10 12:46 pm] Abdul: STEP (22)Damuwa mai tsanani irin wanda bai taba gani a fuskarta ba,ta ce,ko kaji bazaka magance mun abinda ke damuna baya tausasa murya haba sauda yaya zaki ce haka?daga lokacin da muka zama maaurata shekara talatin da bakwai zuwa yanzu kin taba samun kanki cikin matsala ban taimaka miki ba?ta dube shi,karon na san bazaka...ya daga mata hannu dole ta dakata ya ce.amsa min kawai. ta ce,ban ce baka taimakamin ba alhaji,amma karon na san zai yi wuya, ya kama hannunta. matsalar kudi ce?ta ce,aa ni da yar gwal dinka ce MIMI,ta kalli fuskarsa yayi dan murmushi,ki ce abun me sauki ne,me ya faru?ta ce,ina son dai ka bar ta a nan saboda sam bata san komai kan addininta na musulunci ba. sallah har da kuka tayi,saboda allah a ce kamar MIMI shekararta nawa?amma bata yin sallah,malamin yaran nan lsmalil don ance taje ya koya mata karatu kurum, ta je tayi masa rashin mutumci. sannan ta toge tana jiran ka dawo ta ce ka kore shi.to bazan yarda ba,ita kanta ma dole ta zauna ya koya mata karatu,don baza ta koma bata yi tazama cikin jahilci, yayi shiru yana nazari.ya san dai komai za a yi bazai bar MIMI a gidan nan ba. ta ce,ai dama na san zai yi wuya ka bar MIMI nan,to ina son tunatar da kai iyaye abin tambaya ne game da kiwon da aka ba suna 'ya'ya a ranar gobe kiyama, ta mike ta fita abinta. ya fito falo.hussaina tana yin home work ya ce,ke ce da MIMI ta same ni a daki na.itama cikin kuka wiwi ta cewa dady,don allah ka kori malamin nan wallahi na tsane shi.tunda nake ba a taba yi mini abinda yayi min ba.ina son in nuna mi shi talaka ba komai bane a guri na.alhaji ya ce,uwata yi shiru ki daina kuka.zauna,ta zauna a kan kujera shi kuma yana bakin gado ya ce,MIMI ina son kibar batun koran yaron nan,domin mahaifiyarki mata zo min da zancen.ta bukaci in barki a nan ki kare hutun ki,domin ta lura baki cika son ibada c,kuma nima tunda baki son yin sallah bazan amince ba, domin abin yayi yawa kenan MIMI.don gaskiya mahaifiyarki tana da hujjar cewa in barki, [01/10 12:46 pm] Abdul: STEP (23)MIMI ta rude,dad don allah kar ka bar ni,ka san fa ba sa so na. ya ce,suna sonki na sani MIMI,in kin dan zauna zaku shaku ni ma ba a son raina zan barki ba.ta soma kuka wiwi tana fadin dady kawai ka ce ka daina so na,please dady kar ka barni ba zan zauna ba.ya dafa ta,shikenan naji ki yi shiru zan tafi dake,amma kin san dole sai ta bata rai ko?ta ce,dad in mun tafi zata huce,ya ce aa dole mu sunkuyar da kai mu tafi da yardar ta.ta yi shiru tana tunani,ya katse tada cewa, dole mu samu wani malami wanda zai dinga koya miki karatu,don ni maba zan so a ce 'ya ta mai kyau kamarki,bata san komai a cikin addininta ba take wata dabara ta fado wa MIMI ta ce,dady me zai sa bazaka daukar min wannan malamin ba? ya kalle ta,ke kika ce kin tsane shi zaki ce a daukar miki shi?ta kirkiro murmushi,dady naga yanda hajiya ke son karatun shi ne.sai naga in shine zata fi saurin yarda in tafi.yayi 'yar dariya me wayo kawai,to zan shawarce ta,amma zaki yi karatun ko?don na sanki duk abinda kika ce kin tsana,tabbas kina nufin abinda kika fada,ta ce,zan yi dady.ya girgiza kafadarta cikin jinjinawa 'ya ta.kira min mahaifiyarkin in lallaba ta ta amince ina so ki bata hakuri a bisa laifukan da take tuhumarki, ta ce,to dady zan bata,sannan ta fita. ta sami hajiya tana jera kayanta na sawa a cikin wadirof.bayan sallamar da ta yi hajiya ta amsa ta kasa cewa komai,ita kuwa hajiya dama bata waiwayoba kuma bata fasa abinda take yiba.ta dai san MIMI ce,bayan shudewar mintunan da basu kai uku ba,sai MIMI ta soma magana cikin in'ina ta ce,emm,da mazan ce ne hajiya don allah kiyi hakuri in sha allahu ba zan sake ba.kuma zan rika yin sallah ta a kan lokaci.hajiya ta ajiye kayan dake hannunta ta dauko zata saka a cikin durowar ta zauna a bakin gado.da hannu ta kira MIMI alamun tazo,ta ce,zauna kusa dani,MIMI ta zauna. hajiya ta tausasa murya ta kalli MIMI ta ce,ina son ki sani ba ina nuna miki kuskuren ki don wani abu bane,face don rayuwarki, [01/10 12:46 pm] Abdul: STEP (24)Tayi kyau,ba ina cewa ki yi sallah don ni ba ne,aa don kanki ne kiyi don allah.malamai suna fada mana cewa sallah ita ce abu ta farko da za a fara binciken aikin bawa in ya mutu.in tayi kyau ana sa ran sauran ayyukan sa zasu yi kyau.sallah ita ce abinda ta raba tsakanin musulmi da kafiri. lta ce ta raba mutum da dadda,sallah ba abin wasa ba ce,ki kiyaye.ki zubar da duk dabiun banza nan da kikeyi na yahudawa da nasara,wanda kike zaton na wayewa ne,to ina son ki sani ba wayewa ba ce,duk wata wayewa ta duniya da lahira addininmu na musulunci yazo da shi wancan kuwa da kika ka dauka bata ne,mu hausawa da mu ke da alada mai kyau wadda bata ci karo da addini ba.ina me yi miki nasiha da ki daina irin shigar ta kafirai,ki kama suturar ki ta aladarki da addininki,ki dauka ke da kowa duk daya ne,ba don allah yafi sonki ba ne ya sa ki ka fito a guri mahaifinki mai tarin arziki,ki muamakanci kowa kamar yadda addininki ya zana. kan MIMI kasa,kwarai ta kosa ta gama wadannan zantukan da ita sam bata ma fahimtar hajiyar.yaya ma allah yaba ta ubanta, hajiya ta ce,kar ta yi gadara?tayi dai murmushi a ranta ta ce,tab wannan ma kuskure ne,ta daga ta kalli hajiyar,dad ya ce,ki je. hajiya ta mike tsaye tare da dafa kafadar MIMI naji dadi da kika gane kuskurenki.kuma in kin canza zan nuna miki kauna irin ta 'ya da mahaifiya, murmushi MIMI tayi,wanda ita kadai ta san maanar shi, hajiyar ta fita tare da cewa karasa jera min kayan nan cikin word durop tana fita MIMI tayi dariya irin wadda ta fi yi idan taga mugunta,a fili ta ce,ka ji hajiya wai da talaka da mai kudi wai duk daya ne,ta ina suka hadu?ai bambamcin ma a bayyane yake.ai talaka wahalalle ne bayin mu ne,ita hajiya dai kawai bata waye ba ne,take irin maganar. shi kuma wawa sakaran malamin allah yasa ya yarda ya bini zuwa abuja, sai na taka shi,na ja shi,na tozarta shi,sai ya gane ya taba MIMI.lta kuwa hajiya da dadin rai ta fita dakin,na ta a zaton ta 'yarta ta soma hawa hanya, [01/10 12:46 pm] Abdul: STEP (25)Tunda har ta soma ba da hakuri,abinda bata taba yi ba a tsawon rayuwarta.watau tayi laifi ta bayar da hakur,gani ta ke yi ta kaskanta. da sallama hajiya ta shiga dakin yana zaune kan kujera,yana duba jaridar leadership.ta zauna a hannun kujerar ga ni alhaji. ya kalle ta,kin san dai tafiya zan yiki ka koma dakin kika share ni ko?ya ci gaba,ni gaskiya wannan zuwa ba samu wa maraba sosai ba kamar baya.ta yi yar dariya,sai dana ce,kar kazo da MIMI,ai amma ka ki,duk ita ce ta yi ta dama min lissafi.ya ce,to naji shikenan,ai tunda nima nayi mata fada wasa da sallah,ta daina in sha allahu, don haka ma nike so ki taimaka kiba mu aron malamin nan na yaranki tunda naji kina yabon shi gurin kwazo da jaruntar koyar da yara,in ya so sai ki samo masu wani. hajiya ta ce,tabdi,ai ba zai yiwu ba,sai dai in a samo maku wani,ya ce.saboda me?bafa da koyarwan gidan nan kadai ya dogara ba.malami ne a makarantaru,ina zaton akwai gidajen da yake koyarwa.ka bar ta kawai ta karasa hutu a nan,na san kafin ta koma nan da wata biyu ta samu abinda ta samu.ya kama hannunta ina son ki kira shi fiye da abinda yake samu.ta ce,in har ya amince kana ganin zata yi karatun a can? ya dan matse hannunta, kar ki damu sauda zata yi,ta ce,shikenan zan kira shi,sai dai ban so ba zai bar yara na,ni dai suna karatu sosai a gurin shi. hajiya sauda ta kira malam lsmail ta ce masa don allah in yana da lokaci yazo maigida yana son ganin shi.ko yarinyar nan ce ta kai karar shi,kuma yasan halin masu kudin nan da jarabar son yaran tsiya. ta katse mishi tunani da cewa,kar ka damu alheri ne,bari ma dai in fada maka,a takaice so yake ya dauke ka zuwa abuja saboda yarinyar nan,ka dinga koya mata karatu da kannen ta na can.don allah zan roke ka kar ka ce aa, saboda nasan zai biya ka da kyau.kuma nima zaka taimake ni.ya ce,hajiya gaskiya yarinyar nan da kyar in zata bayar da hadin kai a kan karatu,ga ayyuka na a nan.ta ce,ka dai zo din a yi magana a zaune ko? [01/10 12:46 pm] Abdul: STEP (26)Ya ce,to shikenan in na yi wanka yanzu zan taho. sai da ya bita gidan su mahamuda abokin shi,ya isa yayi sallama mahamud ya amsa tare da cewa,dan halak!sauri nake in zo gidanku yanzu,ashe kana tafe,ya ce,lafiya dai zaka zo?mahamuda ya ce,lafiya lau,takardun nan ne na manta,wanda headmaster ya baka kayi makin na dalibai. ya ce,shaf! na manta,ko dana zo gida fa ban tuna ba.suka fito tare ya ce,in bazaka fita ba mahamud mashin dinka zan ara,zan je gidan bashir masari.mahamud ya ce,to ka sauke ni bakin kasuwa?ya ce,to ka san me zai kaini?ya ce,aa lsmail ya ce,hajiya ce ta kira ni, wai tana son in koma abuja in koyar da wannan mara kunyar da nake baka labari jiya.wai tasan zan sami kudi.mahamud ya ce, kawai kaje,kar ka manta da tarin bukatun ka wadanda kudi kawai suke so.lsmail ya ce,ina sane, matsalar kawai bana jin zan dauki rainin yarinyar ko da suna taka kudi.mahamud ya ce,ka dai je kaji in abin zai yiwu,amma dari bisa dari na baka goyon baya. A falon baki abdulkarim yayi wa lsmail jagora,ya shiga ya sanar da hajiya cewa ga malamin yaran nan tare da alhaji.suka jera zuwa falon bakin ya gaida su cikin mutumci da sanin ya kamata,hajiya ce ta gabatar ma malam lsmail bukatar,yayi shiru.alhaji ya ce,kar ka damu nasa kana koyarwa a gurare dabam-dabam ba da gidan na kadai ka dogara ba.ina son ka hada abinda kake samu a kowane wata ka fada min.in har zaka amince ni kuma zan ninka maka kudi abu daya dai da zan roke ka shine ka tabbatar yarinyar nan ta iya karatu. hajiya ta ce,ka dinga yi mata nasiha ka tsoratar da ita.alhaji ya daga mata hannu,wata irin tsoratarwa kuma?karatu dai ta ce, shikenan karatu ai ya hada komai.lsmail dai yan jinsu kanshi a sunkuye lissafi yake tsakanin amincewa ko akasinta,can alhaji ya katse mishi tunani da cewa, me ka ce?ya dago ya dube shi da nufin cewa aa,sai mutuncin hajiya da kwarji ninsu ya hana shi fadin haka,sai ya bige da cewa,a bani lokaci domin sai na sanar da gidajen dani ke koyar da 'yayansu. [01/10 12:46 pm] Abdul: STEP (27)Na rubuta takardan barin aiki a lslamiyyar dani ke koyarwa. alhaji ya ce,yanzu dai a takaice ka yarda kenan?lsmail ya ce,na yarda,sai dai in fara watan gobe.alhaji ya ce, shikenan,nawa kake samu duk wata?hajiya ta ce,ai sai ya je yayi lissafi ko malam lsmail?ya ce,eh! haka ne.alhaji ya ce,kana da mata ne?ya girgiza kai tare da cewa aa,ina dai nema.alhaji ya ce,to shikenan,hajiya gaki nan,za ji komai gare ki.amma kafin haka zan so in san wanene lsmail?ya dago ya kalli alhaji,hajiya ta ce,wannan kaidar shi ce in dai zai dauki mutum aiki a karkashin sa,sai ya san wani abu daga tarihinsa,ko da kadan ne. lsmail ya ce,haka ne. lsmail bin abdulrahaman shine suna da aka fi kira na.mahaifina malam abdulrahaman ya rasu tun ina jss2,haifaffen nan katsina ne,dan kauyen 'yargoje.amma shi yayi gidansa a nan kofar soro.hakanan mahaifiyata ta rasu wata shida bayan rasuwar mahaifina,mu biyu ne 'ya'yanta.kasancewar tana da ciwon sikila tana shan wahala a guri haihuwa ta hakura tun daga kaina,sai aka tsaida mata,ciwon shine yayi sanadiyyar mutuwarta. kafin haka dama bata jin dadin zama da abokiyar zamanta lnna,wacce ita ce uwargida.lrin mata nan ne masu kishin tsiya,yaranta goma sha daya,kuma duk su ne manya damu,bakwai duk maza ne,sai mata hudu,kuma duk suna raye,daga cikin yaran nata, manya guda uku suna zaune a gidan yanzu haka da matansu da 'ya'yansu. dama an raba mana gado, ni na samu daki a soro,ita kuma yata dake aure a kofar soro sai aka bata wani dan fili karami dake jikin dakina ta kofar gida. lsmail ya dago ya kalli su hajiya,ku yi hakuri ina fada maku ba.nima ban san dalilin da zuciyata amince in sanar daku abinda bana son ina tunawa bama.hajiya ta ce,kar ka damu ci gaba.tunda na rasa iyayena haka na taso bana jin dadin kowa a gidamu,tun daga yayyina har ya zuwa mahaifiyarsu, babu mai biya min kudin makaranta.yaya amina kuwa,ita ma ba mai karfi take aure ba.ga yara tana dasu har biyar.don tsakani na da ita akwai tazara ta, [01/10 12:46 pm] Abdul: STEP (28)Don tsakani na da ita akwai tazara ta gurin haihuwa,mijinta ne ya kai ni wajen koyon gyaran TV,da yake ina son karatu sosai,sai na mayar da hankali har na iya,da dan abinda nake samu na biya kudin makaranta. lslamiyya kuwa akwai mahaifin abokina malam aminu shine malaminmu na lslamiyya,shi ya dauki nauyi karatu na lslamiyyata.da ya lura ina son karatu lokacin dana kammala sakandire di nada saukar alkur'ani.haka kuma mahaifin mahamud shi ya tsaya min na samu shiga mutawassid wato js1 na lslamiyya tare da dansa mahamud.koda yake ya ce min makarantar tana da tsada,ta yaran masu hali ce,ya roki mai makarantar ya rage masa biyu bisa biyar na kudin. amma fa akwai karatu,malaman kwararu ne,makarantar reshen ta yana madina.sukan bayar da tallafi ga dalibai guda uku da suka zama zakaru a matakin difloma,don yin karatun digiri a jamiar madina.wannan yasa na zage dantsen karatu bana wasa ba.duk da karancin shekaru na malam aminu shine ya sake yimin hanyar koyarwa a wani gida,saboda in dinga samun na siyan littatafai.hakanan ina koyarwa a lslamiyyar shi wanda muka yi sauka. da wannan ne nake tallafe da rayuwata.har na kammala shekaru shida na sanawiyya,lokacin ne na samu koyarwa a nan gidan, wanda malam lsa mai makarantar mu yayi min tayi,ya ce min yaran a makarantar sa suke karatu, 'ya'yan bashir masari ne,in zan koyar dasu.ban yin gardama ba,don ina son ci gaba da difilomata a nan makarantaarmu eh-mukhtar,yau wata biyu da kammala difiloma,ta kuma nayi nasarar zuwa na uku a ajinmu,sai dai kash makarantar daza muje a madina mutum biyu ta bukata,don haka bana ciki.sai dai ko wani lokaci zasu iya neman na uku,ina burin in karanta larabci ko kuma tafsir. amma a yanzu ina da haddar sittin,ina da haddar hadisai da dama.na san tauhidi da fikihu daidai gwargwado. malamai da dama suna jinjina ma kwakwalwata. malam aminu mahaifin mahamuda yana yin tafsiri da azumi a babban masallacin unguwarmu,sau da yawa nine, [01/10 12:46 pm] Abdul: STEP (29)Malam aminu mahaifin mahamud yana yin tafsiri da azumi a babban masallacin unguwarmu,sau da yawa nine nake ja masa baki. kuma zuwa yanzu shekara ta ashirin da bakwai. ya kalli su hajiya wadanda suka yi shiru suma saurare.ya ce,shine tarihin lsmail bin abdulrahaman.alhaji ya ce, shikenan zaka iya tafiya duk yadda kuka yi zanji gurin hajiya.kuwa tausayin lsmail ya cika ta,ta ce,zan iya tambayarka?ya ce,eh zaki iya.ta ce a fannin boko fa,daga sakandire ka tsaya?ya ce,eh,amma yanzu na zana jamb domin karanta zama ban samu wancan damar ba.hajiya ta ce,ALLAH ya taimaka ya bayar da saa,zan baka 'yar shawara ka dinga ziyartan malamai don neman karin ilimi,ya ce,ina zuwa hajiya, duk asubahi ina daukar karatu.ta ce,ALLAH ya taimaka alhaji ya ciro kudi daga aljuhunsa ya mika masa,ga shi ka hau mota.ya ce,ba komai alhaji da mashin nazo ka barshi,hajiya ta ce,ka amsa sai ka sha mai. sai na ganka,ka sanar dasu. ya amsa tare da yin godiya suka yi sallam.lsmail ya buga mashin kai tsaye gidan su mahamud ya nufa don ya kai masa mashin dinsa.kuma ya gana da mahaifin mahamud,su kuma sake tataunawa a kan batun tafiyarsa abuja.cikin saa yana tsayawa mahamud yana fitowa cikin faraa,suka nufi juna lsmail ya ce,sai ka ce dama kana jiran isowa ta?mahamud ya ce,wai inna ke son alayyahu,duk ga yaran sun tafi islamiyya,suka yi musabaha tare da gaisawa,lsmail ya ce,to hau muje a mashin mana muje mu amso mata,sai da suka je suka dawo suka zauna a dakalin kofar gidan. lsmail ya kalli mahamud,ka san cewa na kasa samun natsuwa da batun zuwa abujan nan?ga shi naje da nufin ince aa ba zanyi ba, amma ban san kadarar data sana amsa ba.duk sai suka yi min kwarjini na kasa kin amincewa. mahamud ya ce,in ka ce haka ka ban mamaki,kai dana sani dakakke mara tsoro,naga ko a nan a lslamiyya da muke koyarwa duk yaran masu da shi din ne,amma shakkar ka sauke yi lsmail ya ce,baza ka gane ba,ita fa yarinyar ina zaton irin, [01/10 12:46 pm] Abdul: STEP (30)Tabararrun nan ne ko da ban sani ba dai,amma na ga alamar kamar uban bai so a takura mata,ga ta da alamun ta tsani talaka bata dauke shi wani abu ba,ni kuma duk sun san hali na,bana son raini.shi yasa bana raina mutane,dalili kenan dana keta tunanin ya ya koyarwar tamu zata kasance?mahamud ya ce, shawarata a nan kawai ka aje duk wani waswasi kai dai ka amshi kudinka ka cika burinka. ka tuna da karatun da muke son yi,kai ko yau jamiar madina suka kira kaza ka bukaci kudi.ga yarinyar nan daka dauki son duniya ka dora mata, zainaba,kar ka manta da abinda mahaifiyarta ta ce,sadakin 'yarta dubu dari, akwatin 'yarta me shida ne,lsmail ya ce,da na tuna abubuwan nike jin cewa ya kamata in jajirce in je,yanzu dai malam nake son gani in nemi shawararsa. da ya amince zan kara samun kwarin gwiwa.haka kuwa yana unguwar har aka yi lshai, lokacin ne lsmail ya samu magana da malam,yayi masa bayanin komai,malam ya bashi goyon baya tare da karfafa masa gwiwa, cikin farin ciki ya nufi gidasu dakinsa da ke soro ya bude ya shiga ya kunna wuta haske ya gauraye dakin,ya zauna bakin katifarsa ya cire hularsa da agogo tare kuma da wayarsa ya dora a teburin da ke gefen katifar mai dauke da tarin littafai,ya ciro kudin da alhaji ya ba shi,da ma ya ba mahamud dari biyar daga ciki.ya dauko wani littafi wanda a cikinsa ya ke ajiyar kudi ya dora su a kan kudin da yake ciki,ya mayar da su ya rufe,ya mayar dashi a mazauninsa.ya dan kwanta rigin-gine gurin zainaba yake son zuwa don zuciyarsa ta matsu da son ganinta,amma yana jin jikinsa ya gaji.wayarsa ta soma ruri,yana daukowa ya ga hajiya ce. ya daga tare da sallama ta amsa ya gaida ta.ta ce, ka yi hakuri na kira ka cikin dare.ya ce,ba komai hajiya. ni mana so in kira ki,sai naga bari dai in bari sai da safe.ta ce daman na kira kane in sanar da kai cewa alhaji sun tafi dazun da mimi,ina son don mu karkare maganar ina son in sanar da shi.ka fada min albashinka,yaushe kuma za a kai, [01/10 12:46 pm] Abdul: STEP (31)Yaushe kuma za a kai ka abujan?saboda ku soma karatun da wuri.lsmail ya gyara zama,hajiya batun albashi dai ni ba zan iya cewa ga shi ba,ta ce yauwa ni ma bana son ka ce ma shi kaza ne. don alhaji in mutum yana son ya ce moriyar shi to ya biyo shi ta haka,zan fada mishi cewa ka ce duk abinda ya ga yayi,na san zai nemi shawarata.ni kuma na san abinda zan ce masa.labarinka daka bamu a jiya na tausaya maka, kuma na tabbatar kana bukatar taimako,yanzu ka yi magana da malamin naku?ya ce,eh?gobe zan je gidajen da nake koyarwa in sanar da su.ko zuwa jibi sai mu tafi abuja din.ta ce shikenan lsmail sai ka zo jibin,ya ce to na gode, hajiya ta ce ba komai. sun yi sallama hajiya tana ji a zuciyarta lsmail tamkar danta.washegari kamar yadda ya alkawarta ya sanar da duk wanda ya kamata cewa,gobe zai yi tafiya zuwa abuja,ya sanar dasu zainaba kadai ta rage masa ya je su yi sallama. da yamma laasar ya shirya zuwa gurin mahamud don ya raka shi zuwa gurin abar son sa,su yi sallama.yana isa lslamiyyar da suke koyarwa ya samu mahamud ya fito daga ajin da yake.bayan sun gaisa lsmail ya ce mu je ka raka ni gidan su zainab in duba ta da jiki,daga nan in yi sallama da ita.ko ta zo lslamiyya?mahamud ya bata fuska,gaskiya lsmail ka je kawai.ka ga ba a ma ta shi ba.ya ce amma ka fito ajin ai,wai me yasa ne ko yaushe idan na ce muje gidan su zainab sai ka be min aa?yau dai dolenka mu je,kuma gurin ka zanbar amanar ta. mahamud ya ce,mu je dai, amma ba ruwa na da wata batun amana.suka jera a hanya ya kalli mahamud,ban san me yasa kuke jin haushin yarinyar nan ba.haka yaya amina kullun sai ta yi min korafi. mahamud ya ce,ai ban boye maka dalilin ba.yarinyar tana da karancin tarbiya,sannan 'yar mace ce.ga shi uwar ta dora dogon buri a kanta. lsmail ya ce in fadi maka ni ba wata matsala ba ce a guri na.ni dai ina sonta don allah ita ma tana so na. ln ta zo hannu na ba sai yadda na yi da ita ba? mahamud ya ce,haka kake fada. [01/10 12:46 pm] Abdul: STEP (32)Mahamud ya ce, haka kake fada.suna isa kofar gidan suka aiki wani yaro ya kira ta.ya fito ya ce an aike ta,lsmail ya ce jikin yayi sauki kenan,ya kalli yaron,je ka ce nesa ne ta je,ko kusa ne mu jira ta?yaron ya koma,lsmail ya kalli mahamud,in nesa ne sai mu tafi mu dawo da daddare.mahamud ya ce ka dawo dai ni kan bazan zo ba.yaro ya iso tare da cewa da nisa,suna juyawa da niyyar tafiya. sai ga ta dauke da tire goro,ta tsaya cikin daburcewa irin ta marasa gaskiya.sam ba ta tsammaci zuwan su ba.don bai cika zuwa da yamma ba.ran mahamud ya yi matukar baci.duk da irin yarjejeniyar da muka yi?da ma karya ne lafiyarki lau,ki ka dain zuwa lslamiyya? zainab cikin in-ina ta ce,dama gidan wata tsohuwa kadai na kai, amma bana zuwa talla.ya ce,karya kike yi,in mutum daya zaki kaima wa,ya ya baki sa a leda ba?sai ki dora tire a kai,bayan kuma na fada miki babu abinda nafi tsana irin in ganki da wannan tiren a kai. kuma na fada na sake fada,bana son talla.kun dora min dari uku kullum, na yarda,kuma ina baku,shine zaki munafunce ni?ta sassauta murya ta ce,ka yi hakuri,ya ce,ke malama ba wani hakuri jeki yi min sallama da innarki,don bazan tafi in bar baya da kura ba.ta nufi ciki tsaki mahamud yayi,ya ce kalli irin gidan daza ka nemi aure. a ce uwar daza tayi wa yayanka tarbiya?wai kyan take birge ka ko me? lsmail ya ce,don ALLAH mahamud ka bar ni in ji da abu daya.kalli wulakancin, sama da wata takwas duk sati biyu sai naba su dubu biyu da dari daya ko dari uku.ko da ba zan ci ba, ba zan sha ba,sai na basu kudin nan.don kawai ta daina talla,ashe suna nan suna yaudara ta ne. mahamud ya be duk kai ka so,yaran mata gasu nan a fadin garin katsina masu tarbiyya da ilimi,ka kau da kai a gurin su,na san dai ka san cewa,in ba nema wa 'ya'ya uwa ta gari.lsmail ya ce,baza ka gane ba,ina yiwa yarinyar wani mugun so ne,ba zan iya rabuwa da ita ba.mahamud ya daga kafadunsa guda biyu tare da fadin ruwan ka. [01/10 12:46 pm] Abdul: STEP (32)Daidai lokacin zainab ta sake fitowa ta ce, shigo daga soro,nan suka tsugunguna.lta ma innar ta tsuguna.suka gaishe ta,lsmail ya soma magana cikin fushi,inna nazo ne nayi wa zainab sallam zan tafi abuja.sai kuma na ganta da tiren goro,bayan na san mun jima da wuce maganar talla.eh.nina ce ta zaga da goro tunda tun shekaranjiya ya kamata ka aiko da kudin amma shiru. lsmail ya sake shakar takaici,ciki sauri ya ce,amma inna ko na sati biyu na tara ina badawa ko? ya ci gaba gaskiya bai kamata a saba mun kaida ba.inna in na bar gari sai yaya kenan,bai da be fa a saba mun alkawari ba. lnna ta dago ta dube shi, aikin gwamnati ka samu a can abujan?ya dube ta,ya sunkuyar da kai ya ce,aa koyarwa ce.ta ja tsaki ta ce,ana nan dai.ta mike ya ce,inna zan bata kudin ta kawo,ni dai roko na kada ta dinga daukar tallar nan. ina hijaban dana dinka mata ne,yau na ganta da gyale?ta daga masa hannu,dakata kai lsmail,ba fa ka bada sadakin zainab bane daza kayi ta sa mani dokoki iri-iri a kan 'yata,kuma bazan gaji da fada maka cewa ba zan bayar da 'yata inda zata sha wuya ba,kamar yadda ni na sha wahalar talaucin ubansu.'yata tana da kyau, baza maida ta baya ba. lsmail ya mike shi dama mahamud tuni ya kai waje. ranshi ful takaici,zuciyarsa tana tafasa. zainab dake cikin gida kusa da soro ta leko cikin damuwa ta ce,innarmu don ALLAH ki daina wannan zancen,wai ke kullum in zaki yi magana sai kin sako babanmu?lsmail yasa hannu cikin aljihu,zainab zo in baki sako,innar ta koma cikin gida.zainab ta kalle shi,malama don allah kayi hakuri,ya ce,zainab ni dai rokon da zan miki,don ALLAH ki rike min amana. ya sake yin kasa da murya,kin dai san ina sonki ko?ta kalle shi da manyan idanunta na sani malam.to ki kula min da kanki,yasa hannu cikin aljihu ya ciro dubu uku,ki cire kudin sati, sai ki rike saura.in na dawo zan saya miki waya saboda mu rinka gaisawa, zan turo iyayena.ta ce,to nima zan fi son ka turo din,don allah kayi kokari ka dan yi kudi ko. [01/10 12:46 pm] Abdul: STEP (33)Da ba masu yawa bane,saboda innarmu ta daina yi maka haka. ya ce,kar ki damu shi arziki na allah ne yana bayar da shi ga wanda ya so kuma a lokacin da ya so.muna rokon shi ya bamu na halas,ta ce amin.yawwa a gidanku wace ce fatu?ya ce,me ya faru?ya tattara hankalinsa gurinta,sun hadu ne a gidan wani biki can kofar marusa,shine take cewa innarmu wai kar ta yadda ka aure ni,wai wuya zan sha baka da komai,sai dan daki daya daka gada a zaure.baka da aiki,sai kalallahu,kala rasulu.lsmail ya lunshe ido na dan lokaci, ya bude tare da furzar da huci mai zafi.ya ce,zainab don ALLAH ki toshe kunnuwanki,wadannan abubuwan duk kafin in mallake ki ne.da zarar kin zama mata ta,dole kowa ya zura mana ido.ta ce to shikenan amma wace ce fatu din?ya ce,matar wa na ce,kar ya dame ki,ni zan tafi ta ce to shikenan. sai yaushe?ya ce,sai dai na zo, don sai naje naga yanayin gurin,har ya kai bakin kofa ta ce,malam don allah kar ka manta ka samo kudin. bai iya cewa komai ba.ta shiga cikin gida shi kuma ya je ya samu mahamud suka wuce.mahamud ya kasa yin shiru,suna tafe ya ce, lsmail don ALLAH dubi irin wulakancin,don ALLAH ka yi zuciya ka bar mata yarinyar ta.lsmail ya ce,hmm ka san na sha yunkurin yin haka,amma sai in samu kaina cikin tashin hankali,ban san lokacin da na soma son ta ba.ka yi hakuri mahamud ban ki batunka ba,abin ya wuce duk yanda kake tunani.kai dai ka gode ma ALLAH tun da baka da matsala da iyayen rabia. mahamud ya ce,ko da ina da matsala da su bazan dauki haka ba,sai in bar su da yarsu.kaima ina mamakin duk zuciyar da kake da ita,ya dafa mahamud kar kaji komai,ka sa ni cikin adduarka. mahamud ya ce,ka binciki asalinsu?lsmail ya ce,yaya amina ce ta binciko,ranar take gayamin wai ubansu bakano ne.dan wani kauye wai shi kurje keya.ita kuma uwar 'yar ruma ce,can wajen safana.ya auro ta lokacin yana da abin hannunsa.'ya'yansu shida maza uku mata uku,maza ne manya mata kuwa zainb ce babba,tunda arzikinsa ya karye sai buga-buga sai ta raina shi. [01/10 12:46 pm] Abdul: STEP (34)Sai ta raina shi, 'ya'yan ma suka raina shi,sai abinda ta ce.ta dauki dogon buri ta dora a zainab,don kuwa ta ga yarinyar tana da kyau,ita sam ba za ta ba talaka ba. sannan yaran babu tarbiya babu karatu sai talla.maza kuwa daga kwandasto sai kwasan bola,sai karamin su mai sayar da rake.ka ji bayanin da yaya amina ta yi min. mahamud ya ce,tabdijan kuma ka ji ka gani?lsmail ya ce,to yaya zan yi?ba ni da zabin da ya wuce aurenta.buri na shine in ta zama tawa zan tsaya mata ta yi karatu duka biyu.mahamud ya ce,ALLAH ya taimake ka. bayan sallar lsha suka yi sallama da mahamud kan cewa sai gobe in sun hadu, kafin lsmail din ya tafi gida, gidan yaya amina ya nufa, a tsakar gida ya same su ita da yara suna cin abinci. nan yaran suka shiga yi masa sannu da zuwa.ya ciro naira dari ya ba sadam babban,je ka sayo maku biskit,ya ruga da gudu yana murna,yaya amina ta ce,ba ka gajiya ne?haba dai.ta ce aisha dauko ma kawunku tabarma.bayan sun gaisa sai yake sanar da ita batun tafiyarsa abuja.ta ce, gaskiya na yi murna.ALLAH ya sa alheri ne ya kira ka abujan.lsmail ya ce,amin yaya ina son in na dawo in tura gidan su zainab.yaya ta ce,umm!kai dai kana son wannan zainb din yayi dan murmushi,ku taya ni da addua ALLAH ya sa haka shine mafi alhari.ta ce.umm to amin,sun jima suna hira sannan suka yi bankwana ya tafi.yana shiga gida ya kunna wayarsa ya shiga soro su ya ciro makulli dakin ya bude.ya dubi makunnin wutar ya kunna haske ya wadace dakin ya shiga.ya dauki buta ya fita zuwa cikin gida don zagawa ban daki.a tsakiyar gidan matan yayyin sa ne da 'ya'yansu suke ta hira,ya yi sallama suka amsa yayi masu sannunku ya wuce.don shi dama tsakaninsu bai wuce haka ba,sai da ya fito bandakin sannan ya nufi dakin inna,ya yi sallama tana ta gyangyadi.sallamar shi ce ta tashe ta,ya shiga ya gaida ta,ta amsa tare da cewa kananan?ya ce eh na shigo da safe ki na bandaki. ta ce,haka dai ka ce,indai nina haife ka ai don ina bandaki ka jira ni.yayi dan murmushi, [01/10 12:46 pm] Abdul: STEP (35)Zuwa yanzun ya saba da halin inna.ya daina jin haushin maganganun da take fada masa marasa dadi.dama zan sanar da ke ne gobe in ALLAH ya kaimu zan tafi abuja.ta ce habuja?kai ko me zaka yi a habuja?ya ce,koyarwa na samu a wani gida zan dinga koyar da yaran gidan ta tashi tsaye,can kuma ka kutsa,lallai ba shakka,ya mike,ya jima da sanin inna zai yi wuya tayi masa adduar ALLAH ya sa alheri. ya fito yasa takalmi tare da daukar butarsa.tun kafin ya bar tsakar gida yana jinta tana cewa kunji mutan gidan nan,samail ya samu koyarwa a habuja,ya fadawa mazajenku?fatu ce ta soma magana,lallai ba shakka,ya fadawa mazajenmu su a su wa?ke ma don kar a ce dai bai fada bane,kala bai ce ba ya wuce dakinsa. Da safe sai da ya shirya tsaf,sannan yayi wa yayyansa maza sallama,su kam sun yi masa ALLAH ya sa a dace.gidan su mahamud ya nufa.yayi sallama da malam aminu mahaifin mahamud sannan suka nufi gidan hajiya sauda.mahamud ya goya shi a mashin,kuma sun yi shawara a kan mahamud zai ci gaba da koyar da su hussaina. A waya ya kira hajiya ya fadi mata ya iso,ta sa ya shigo,kar ya damu ai shima tamkar shi dan gida ne.suka shigo falon baki nan ta same su,ya gabatar mata da mahamud,bayan sun gaisa ta kuma kara rokonsa a kan ya tsaya mata sosai a kan MIMI,duk lokacin data yi yunkuri ko barazanar koran shi,to ya kira ta.ta ce nasan aiki ne na baka mai wahala,amma kamar jihadi ne,ya ce,na yi miki alkawarin zan tsaya a kanta kamar kanwa ta,zan jure saboda ALLAH da kuma halaccin da ki kai mun.ya'u direba ne zai kai shi,sai da motar ta tashi sannan mahamud ya buga mashin cikin kewa.suna tafe suna labari shi da ya'u cewa yayi,gaskiya ina yi maka jajena kan wannan aiki,gara in yi aikin kwasar kashi don na tsani wulakanci,lsmail ya ce,hmm ni fa gani nake kamar wata kaddar tasa zan je koyar da yarinyar nan. wata zuciya kuma tana fada mini ALLAH zai taimake ka.ina tunawa ni NAMIJI ne,sai inga to wai meye ne abin tsoro. [01/10 12:46 pm] Abdul: STEP (36)Ya'u ya ce,ba za ka gane ba,ai ubanta zata sa ya tozarta ka.ga zagin wulakanci,lsmail ya ce, ALLAH ta zage ni sai na mare ta.ya'u don dariya sai da motar tayi kamar zata sullube masa.ya ce gaskiya kar kayi wannan kuskuren, lsmail ya ce,nanne kaduna? ya'u ya ce,eh amma ba garin kaduna ba ce zariya ce,nan dama baka taba zuwa ba?kai ni ina zaton sokoto kawai muka taba zuwa yin gasar karatu lokacin ina SS1.ya'u ya ce gaskiya ni ban zata ba,in na kalle ka sai ka ce ka taba fita kasashen duniya. lsmail ya ce,ni kifin rijiya ne ban san ko in ba.in mun zo kaduna ka nuna min ina jin labarin garin ina son zuwa. ya'u ya ce,shike nan za nuna maka,tun daga na yake nuna masa garuruwa har suka isa kaduna.ya ce, bari in bi da kai ta cikin garin maimakon by pass tunda kana son ganin garin. shikenan lsmail sai kalle-kalle ya ke yi.ya ce,garin ya birge ni.amma duk a zato na ya fi haka,yadda sunan kaduna ya cika ko ina.ya'u ya ce,zaman garin yana da dadi saboda ba su shiga harkan abinda bai shafe su ba.lsmail ya ce,wani ya taba bani labarin garin 'yan karya ne ko?ya'u ya ce eh, to ni ma dai haka na ji ana cewa,to muna da 'yan'uwa. suna zuwa katsina gurin innarmu,mu ma mukan zo,ba wasu masu karfi ba ne,amma komai za su yi sai inga suna son yin wanda yafi karfinsu,ni ma sai na amince 'yan karya ne.amma daga baya lokacin ina yin tuki a nan kaduna a wata unguwa wai ita unguwa rimi sai na gane ba wai karyace da su ba,yin hakan a jinin 'yan kaduna ne yake.ka gane malam lsmail? su mutane ne masu son yin komai me kyau,kuma basu da kyashin sayan duk abinda ransu ke so,ko da kudinsu kenan idan za a aje maka dan kaduna mai dubu dari biyar,da dan wani gari mai milyan biyar,za ka ce dan kadunan ne mai milyan biyar,wancan mai dubu dari biyar.lsmail ya ce na gane,in ko haka ne sun burgeni.saboda ni mai irin raayi na kenan,arziki na ALLAH ne,in na samu zanyi abinda nake so da halas di na.haka suka yi ta labarin 'yan kaduna har suka kai abuja garin manya. [01/10 12:47 pm] Abdul: STEP (37)Shi kam a ranshi 'yan kaduna sun yi mashi, yana son mutane masu test,wadanda ba komai ne ya yi masu ba. Tafkeken gida ne na gani na fada,tunda suka doshi gidan lsmail ke mamaki sai ka ce fadar shugaban kasa,duk yadda yake kisima gidan a rashi ya wuce nan,tun kafin su shiga ma kenan.su na shiga sai ya ga ma kamar wata sabuwar duniya ce,wannan mutumin wane irin kudi ya mallaka?lsmail ke tambayar kanshi. dama tun kafin su kara so ya kira hajiya ya fada mata cewa sun iso unguwar,ita kuma ta kira momi nafisa ta sanar da ita.lsmail ya na jingine jikin mota,wani matashi ya iso wurinsa ya ce,wai wanene malam lsmail?ya ce,ni ne. ya ce,to zo mu je,ya kalli ya'u direba zo muje, ya ce,a'a,ni dama aiki na shine na kawo ka,kuma na kawo ka,yanzu zan juya.lsmail ya bashi hannu suka yi sallama bayan gidan suka nufa inda suka nufa gefen yara, suka je ya bude wani daki, an ce ka shiga nan.lsmail ya kalle shi,ba mu gaisa ba?ya mika masa hannu suka gaisa.ya ce,suna na lsmail,kai fa?ya ce hamisu, kuma nine direban yaran gidan nan.ga daki na nan kusa da na ka,mu biyu ne a cikin dakin,ni da me share-share,game da kula da fulawoyi.lsmail ya ce, ALLAH ya sa mu amfani juna,hamisu ya ce,amin. lsmail ya shiga yana kallon dakin tamkar ba dakin masu aiki ba,hamisu ya ce,ai kurar dakin ba ta yi yawa ba,don kanin momi bai yi sati da tafiya ba,da cikin dakin yake.lsmail ya ce,kurar ba tada yawa ma kenan,amma duk da haka bari in dan kakkabe,ya shiga ciki sosai,hamisu ya ce,in zaka yi sallah ga bandaki nan.lsmail ya ce,tunda muka taso,duk inda sallah ta same mu,sai mu tsaya muyi ta.ya ce, shikenan baka da wani nauyi a kan ka.lsmail ya gyara daki mai dauke da katifa katuwa,sai duruwar ajiye kaya,sai kuma dan teburi a gefan katifar. hamisu ya ce,bari in sa a sanar da momi cewa ka iso,kuma naba ka masauki, yanzu saura abinci. kusan minti ta latin da fitar hamisu,sai ga wani kuma dauke da plate a rufe da cokali da kuma ruwa.suka gaisa, [01/10 12:47 pm] Abdul: STEP (37)Kusan minti ta latin da fatar hamisu,sai ga wani kuma dauke da plate a rufe da cokali da kuma ruwa.suka gaisa,sannan ya ce,ga abincin ka.shi ma nan haka lsmail din ya sake gabatar masa da kansa, suna na lsmail kai fa?ya ce, suna na jabiru,kuma nine mai dafa abincin rana da dare,lsmail ya bashi hannu suka gaisa.bayan fitan sa ne ya bude plate din abincin, dafa dukan shinkafa ne,ta ji kifi da alayyahu,ya ci ya koshi,ya sha ruwa ya koshi.daga nan barci ya sace shi, saboda gajiya bai taba yin doguwar tafiya kamar haka ba daga katsina zuwa abuja. can da ya farka ya kalli agogo,sai ya ga lokacin sallah ya karato,nan da nan ya tashi yayi alwala,ya fito waje bakin gate don ya ga karamin masallaci a gurin. hamisu yana zaune kusa da maigadi suna hira,yayi masu sallama,suka amsa. ya ce,hamisu ina ladani ya kira mana sallah lokaci yayi, hamisu ya ce,ba a fa kiran sallah a masallacin nan,sai dai kawai kowa yayi alwalarsa ya shiga yayi sallah.lsmail ya ce,saboda me?hamisu ya ce,ni dai haka na tarar suna yi,to ai duka-duka mu uku ne ke yin sallar,ni da maigadi da mai shara.ko maigidan ba kullun yake sallah a cikin masallacin ba,ya fi yi a cikin gida.yaron sa namiji daya. ya kai shekara shabiyu, amma ko shi ba a turo shi. lsmail ya ce,ko ku uku za ku iya jam'i,don haka ni kam zan kira sallah. lsmail ya shiga ya ga da abin magana da komai,yana kwada kiran sallah daidai lokacin motar alhaji bashir tana kunno kai ko da direban ya tsaya bai fito ba,sai da ya ji karshen kiran sallah,muryar tamkar balaraben saudiyya. maimakon ya shiga gida sai ya samu kansa da nufar masallaci,gurin da aka tanada don alwalla,nan ya je ya tattara hannu rigarsa ya soma alwalla.su hamisu suka tsaya suna kallonsa, nan dai lsmail yaja su sallah,hamisu yayi masu ladanci,sai dai alhaji shi kadai ya tsaya a sahunsa. suna idarwa suka fito, lsmail ya gaida alhaji,ya nuna masa jin dadinsa da sallar da ya kira har suka yi jam'i.lsmail ya ce. [01/10 12:47 pm] Abdul: STEP (38)Ismail ya ce,alhaji zan yi wata magana,amma in na bata maka rai ka yi hakuri,amma hakki ne a kaina in sanar da kai.bai kamata ka tsaya ba a sahu ba,duk da cewa mu din masu nema a karkashin ka ne,amma gurin allah ba bu bambamci,musamman gurin sallah.sahu dole ne,na san alhaji ya sani.tuni kawai na yi masa,alhaji ya ce.na gode ba komai,sannan ya nufi cikin gida. sai karfe tara na dare, kuku ya sake kawo masu abinci,da ya karba sai ya fito,ya samu hamisu shi ma yana cin nasa,ya aje ya ce, me zai hana mu rinka ci tare?hamisu ya ce,ba damuwa bisimillah.suna ci hamisu ya ce,na ji mamaki da na ga kana magana da maigidan nan,wai me ka ce masa ne?lsmail ya ce,wata magana wanda bai dace in fito na fada ba,a takaice kuskure ne nayi masa tuni, hamisu ya ce tabdi,gaskiya ka yi saa,ai maigidan na mu mafadaci ne na gaske. wanda bai son a shiga huruminsa,kuma yana da wata yarinya mara mutunci,wanda kowa ke tsoron ta,hatta matan gida. sai dai gaskiya yana biyan kudi da tsoka,shi ya saka ga na jure,ni ne direban yaran gidan,don haka na fi kowa wulakanta. lsmail ya ce,na san ta,kuma ni malaminta ne,na zo in koya mata karatun addini. hamisu ya dago ya kalle shi,yayi dan murmushi, lallai ina mai baka shawara,ka nemo duk wani hakuri da kau da kai,ka kara a kan wanda kake da shi.lsmail ya yi 'yar dariya,ya ce,ta taba yi maka?ya ce,to da wanda ta raina ma iri na? ban san iya sau nawa ta zuba min miyau a fuska ba.banda kalaman cin mutunci.lsmail ya ce,kai kuma sai ka tsaya kana kallonta?hamisu ya ce,ya ya zan yi,tunda ina so,dubu talatin yake biya na a wata,ba ko'ina zan samu haka ba.lsmail ya ce,sannu da kokari,amma ni kam ba zan dauki wulakancin nan ba.sun jima yana ba shi labara,kafin suka yi sallama. haka da asubahi ya kwada kiran sallar farko, MIMI wacce lokacin ta yi sallama da kalil dinta wanda suke chatin tun misalin taran dare,ta bude idanunta tana jin sabon lamari a gidansu.ta tashi ta sauko daga kan gado,ta kunna wutar dakin na ta, [01/10 12:47 pm] Abdul: STEP (39)Sannan ta nufi windo,ta yaye labule tana kallon masallacin,wanda dama saitin windon nata yake.tabbas masallacin nan ne,to wane ne wannan da karfi hali?lta tunda ta ta so bata taba jin an kira sallah a masallacin nan ba.ta koma ta kwanta ta saki tsaki.za ta ga mai wannan kokarin na hana mutane barci.ta fara barci ta ji an sake kiran sallar,aka shiga masallaci aka yi sallah,ba ita ta samu barci ba sai da aka idar da sallah. don haka bata farka ba sai shabiyu,ta yi mika tare da hamma,ta silalo kafarta kasa kan lallausar kafet. tamkar sarauniya ta ke jan taku har zuwa bandakinta, wanda aka tsara shi da kalar pink,kalar da take bala'in so,bandakin da yafi na kowa tsaruwa a gidan, hatta mahaifinta.ta shiga bahonta,bayan ta cika shi da ruwan dumi,sama da awa daya ta dauka a wanka,ta fito.gurin shafarta daya ne da kayan sawanta, bata cika yin kyale-kyale a fuska ba, hoda kadai sai jambaki bayan mai,amma tsadarsu ta ishi talaka jari. ta saka wando baki irin mai kama jikin nan,da riga ja,ta ja dogon gashinta ta kama shi da bakin ribbon. ta soma wanka da turaruka.ta nufi gadonta ta dauki wayarta tana dubawa,miss call kusan goma dadin ta,da na dear khalil,dana hajiya guda biyu. bakin gadonta zaune tana kiran layin dadinta,ya daga tare da cewa uwata ya ya aka yi?cikin shagwaba da muryarta din nan wanda ke fid da sauti a hankali cikin salo ta ce, dad na ga miss call din ka ne fa?ya ce,uwata har na fita baki tashi ba,lafiyarki kalau ko?ta ce,eh dad,emm yawwa dad wane ne jiya cikin dare ya hana ni barci da kiran sallah?ya ce, malaminki ne,gabanta ya yi bala'in faduwa ta ce,dad shine da zuwansa zai canza mana tsarin gidanmu?mene ne nufinsa da haka?ya ce,babu komai MIMI,kin san malamai da son masallaci,yau ni mana samu yin sallar asuba a kan lokaci,sannan makwabtanmu sun shigo mun yi sallar tare da su.ta ce kash dad,yanzu gidanmu gurin tara mutane kenan? ya ce,kar ki damu musuluncin kenan,ina fata za ki sauko domin daukar karatu. [01/10 12:47 pm] Abdul: STEP (40)Gurin malamin na ki.kuyi amfani da falon baki, ko falo na ki ke so?ta ce,aa dad ya tsaya can falon baki,ba falon ka ba,da wannan bakauyiyar kafar tashi.ya ce,shikenan tunda naima tana gida ita mata soma karatun,in su ahmad sun dawo da yamma sai yayi masu,ta ce,shikenan dad,bari in kira hajiya naga ta kirani.ya ce,ok nima yanzu muka gama waya,ki ce ina gaida ta.cikin fargaba ta kira mahaifiyarta,hajiya ta daga cikin lallausar murya ta yi sallama,MIMI ta amsa tare da cewa,ina ki ka bar waya?ta ce,ina barci yanzu nayi wanka sai naga miss cal dinki.hajiya ta ce,na zaci kin fita gurin karatu ne?ta ce,hajiya ban san ma ya zo ba sai yanzu dad ke fada. ln na yi break zan yi yanzu,hajiya ta ce,ki maida hankali saboda ki san abinda zaki bauta ma ALLAH mahaliccin ki.suna yin sallama kiran kalil ya shigo sai da yayi daf da tsinkewa ta daga,wannan wani raayinta ne.ta ce, hello dear ya aka yi?ya ce,ba komai ina son in ji muryar ki ne?yanzu ki ka tashi?ta ce, fh,yaya hutu?ya ce,ga shi muna yi,don ALLAH ina son in zo gidanku wannan karon,ina jin tsoro kamar zan rasa ki,kar ka damu dear na fada maka don juna aka yi mu,ina jin haka a jiki na. ya ce, lovely har yanzu ban yi mafarkin haka ba ina ganin sai zancen ya je gurin manyanmu.ta yi 'yar dariya, ka san fa dad naka ba zai yarda ka yi aure yanzu ba, ni kuma in dad dina ya ganka guri na kila ya ce,zai min aure,ka ga sai matsala ta samu. ya ce,na fahimce ki,ba na son na sha wahala a aurenki kamar yadda na sha kafin na samu amincewar soyayarki na garu.ta yi 'yar dariya cikin salon maganarta ta ce,dear ka manta da haka,bari na karya,ya ce,to shikenan sai in mun hadu online ta ce,tam.cikin tafiyarta tamkar mai tausayin kasa take saukowa daga benenta,wanda ita kadai ce a sama ta ke mallakin kato falo da dakuna uku.daya dakin barcinta daya kayan karatun ta,tun daga computer zuwa kasa, dayan kuwa rufe yake duk da cewa shima da komai a cikinsa. [01/10 12:47 pm] Abdul: STEP (41)Momi nafisa tana zaune tana kallon fim a cikin tafkeken tv dake manne a bangon falon.ta waiwayo,kin fito MIMI?ta kalle ta,na fito momi an tashi lafiya?ta ce,lafiya lau, dadinku yayi ta kiran ki baki fitoba,ta yatsi na fuska,mai kiran sallar cikin dare nan ne ya hana ni barci.momi ta ce,ai malaminki ne,na ga dad dinki ya yaba da hakan.ta ce,na lura da haka a wayar da muka yi dazun. ta isa gurin karin ta hada shayi tana sha,ta dubi mahaifiyar tasu naima fa?ta ce,tana dakinta,ta dauki wayarta dake kusa da ita,ta soma kiran layin na'ima,tana dagawa MIMI ta ce,sis zo mana,naima ta fito cikin riga mai gajeran hannu da wandon jins damamme,kanta ita ma babu dankwali,ta kama gashinta da ribbo blue. ta ce,sis gani,MIMI ta daga fararen idanuwanta ta kalli na'ima cikin harshen turanci suka fi yin magana.ta ce,ki je gurin folina a kicin ki gani ko ta gasa kifin,ta ce,sis mu je snacks store mana mu ci, MIMI ta harare ta,ki yi abinda nasa ki mana,ta daga hannu,alamun ban hakuri ta rinka fadin sorry. folina ta zo,ta shirya wa MIMI gasashen kifi tare da gasashen biredi,tana gamawa ta kalli naima ina son a kira mini malamin da yazo jiya,amma ban san yaya zan yi ba,don ba za kije ba,amma ki duba in kin ga direban ku,ko wani dai ya kira shi,ta ce tam sis. lokacin da hamisu ya sanar da lsmail cewa ya je ciki ana neman sa,sai ya ce,sai mun yi sallah tukuna. don yanzu zan kira.bayan sun idar sannan ya ce,ma hamisu ya yi masa jagora zuwa cikin gidan. barandar kofar falon,nan suka danna 'yar wata danja,jim kadan aka bude. naima ce ta kalle su irin kallon da wasu 'ya'yan masu da shi suke yi wa masu yi masu hidima.ta ce, wane ne malamin?hamisu ya nuna lsmail wanda ke tsaye sanye cikin yadi mara nauyi,hularsa ta dace da yadin wandonsa a dage irin na ahalil sunna. ta kalle shi sama da kasa, ta ce,ina zuwa.kamar minti biyu ta dawo ta ce,sis ta ce,ka shigo,ya shiga dankareren falo wanda tsarin saya wuce duk tananin lsmail ga sanyi AC [01/10 12:47 pm] Abdul: STEP (42)AC ko ta ina.ta waiwayo ta ganshi tsaye, ka bi ni mana,ya ci gaba da binta cikin zuciyar shi yana addu'ar ALLAH ya tsare shi daga sharrin da ke cikin gidan,alherin dake ciki ALLAH ya sada shi da shi. wata kofa suka shigo inda suka iske wani falon madaidaici,shima ya tsaru ta ce,ka jira ta a nan. kusan minti biyar,sannan MIMI ta shigo falon ba tare da sallama ba,rashin sallama yana kona ran lsmail,don haka bai ko kalle ta ba.ta zauna tana kallon fuskar wayarta,ta fi minti biyar chatin ta ke yi da kalil dinta,labarin karfin halin malamin take ba kalil.ta ce, ni da zai ci a gurin ubana, amma ni yake jira in ji da shi,kalil ya ce,kin san talaka da girman kai.ta dago ido ta kalli lsmail wanda ya bude ALKUR'ANI yana karantawa a zuciyarsa.ta ce,hamm mai neman taimako baya girman kai. ya dago ya kalle ta,kafin in ce komai zan soma yi miki nasiha,da saka hijabi don suturta jikin ki. ki koyi sallama yayin da ki ka zo gurin mutane,abu na uku,ba neman taimako na zo ba,ke nazo in taimaka ma wa,don haka yanzu sai ki dauko littafi mu fara daga huruful ija'iyya.ta ce,ba ka isa ka ce za ka taimake ni ba,don baka da komai,kuma ba zanyi sallamar ba,ba zan rufe jikin ba.ln baka sani ba,barin in fada maka,na sa a kawo ka nan gidan ne saboda in tozarta ka,in nuna maka kai kaskantacce ne.ya ce,don na miki wane laifi?ta ce,kai ne mutum na farko dana taba yin sa-in-sa da shi.wanda ya taba kallon cikin ido na ya fada min magana,kuma ina son ka zama na karshe,wannan shine laifin ka.lsmail ya ce, yanzu dai za ki yi karatun ko a'a?ta ce,na ce ba zanyi ba,ya mike tare da kwashe takardunsa.ta ce,ban sallame ka ba,yayi tafiyarsa ya bar ta zaune. MIMI ta bi shi da kallo cikin mamaki,shi wannan dame yake takama,har da baya jin shakka ta,kamar yadda sauran jamaa suke ji?ya san wace ce ni kuwa?ya san wane ne ubana? Ba wani ba ne uban MIMI fa ce alhaji bashir,dan asalin masari ne,karamar hukumar kafur jihar katsina. mahaifiyarsa 'yar dabai ce,su shabiyu ta haifa, [01/10 12:47 pm] Abdul: STEP (43)Amma yanzu saura su biyar,bakwai sun rasu,mahaifiyarsu ta rasu lokacin ya kammala sakandire,yayyin shi. mata uku ne,sai namiji daya dake bin shi,rakiya da basira a malumfashi suke aure, saratu kuma tana cikin kafur,malam aliyu mahaifinsu ya sake yin aure. inda matar ta kasance mai son kanta game da son zuciyarta.wannan yasa ya bar masari,ya soma shiga cikin garin katsina don neman abin kanshi, maimakon noma da suke taya mahaifinsu,shi da shafi'u kaninsa. ya yi sana'o'i kala-kala, tun daga kan kwandastan mota har zuwa dako,daga bisani ya soma bin wasu abokansa guda biyu da suka kama shago daya su uku,da lsa mani da kabiru naalla suna harkan dabbobi. tun yana karba yana saidawa ya cire ribarsa,har ya zo ya samu jarin kansa. sannu a hankali suka yi zangonsu na dabbobi, lokaci bayan lokaci yana zuwa masari ziyartar danginsa da mahaifinsa kuma yana yi masu alheri. kaninsa shafiu har yayi aure matarsa ta haihu,don haka mahaifinsa da yayyansa kullun burinsu yayi aure.wani zuwa da yayi har mahaifinsa yana cewa,ga 'ya'yan 'yan'uwansa ya zo ya auri daya daga cikinsu,sai bishir din ya ce,yayi hakuri,shi ba ya shaawar auren zumunta,amma duk lokacin da ya ga wanda ta yi masa,to zai yi aure,amma a yanzu neman kudinsa ya sa a gaba. ranar wata jumaa lsa mani ya tare shi yana sauri za shi masallaci ya ce masa,bashir ga wadansu shanu can zaa saida su a rugar fulani nan mashi.bashir ya ce,har mashi?gaskiya da kyar zan je,lsa mani ya ce,za ka samu alheri mutumi na,don jiya na dawo tafiya,ka sani da na saye su,amma ka daure mu je in ka dawo masallaci.hardon gar ne ke son zuwa aikin hajji,shine zai cikon kudi.bashir ya ce,ni dai masallaci na nufa ga shi ina jinjina zuwa mashin nan,lsa ya ce,mu je dai masallacin nan tare ma kawai,da zanje na karfe biyu ne,in ya so daga can sai mu wuce.a masallaci suka hadu da kabiru na'allah,inda suka nufi mashi dukkan su. [01/10 12:47 pm] Abdul: STEP (44)Sun je rugar fulani,inda suka shiga garke shanu don duba shanu.ya nuna masu,aka shiga ciniki, an daidaita kuma bashir yayi alwashin kawo kudi gobe,saboda kudi suna banki.suna cikin sallama ne idon bashir suka kai kan wasu 'yan kwailoli guda biyu,sun dawo daga tallar nono,dayar ya kure da ido, 'yar similmila ta yi masa kyau,sai da ta bace ma idanunsa,ya bar kallonta.har lsa mani ya gane,bayan sun bar gurin ya ce,bashir kana ta kallon 'yar mutane saboda me?kar dai ka ce min son wata kake yi daga cikinsu?bashir ya ce laifi ne yin hakan?lsa ya ce,aa ban ce ba,sai dai ka bani dariya kawai,duk 'yan matan da ke cikin garin katsina? ka rasa wanda za ka zaba sai wadanan 'yan ruga mitsi-mitsi da su?kabiru na'allah ya ce,in dai fulanin nan nema,ba su son baiwa bare 'ya'yaansu.bashir ya ce,ku yi min addua in rabo na ce za su bani,don gaskiya na ga wacce nake so.suka sa mishi dariya. Abin ya wuce da tunanin bashir,domin ranar da tunanin 'yar fulani ya kwana,ya kosa ya je su kai kudin shanu,don haka tun tara ya shirya ya nufi banki ya ciro kudi,daga nan suka nufi mashi. ko da suka isa burinsa ya ga yarinyar da ta hana rayuwarsa sakat, har suka bayar da kudin shanun suna kokarin zuba su a mota,amma bai ga giccin wani da ba.ya kama mota zai hau sai ya hango ta tana kada nono cikin dan kuttunsu da suke cire mai,da sauri ya fasa shiga motar ya nufi gurinta. sallama yayi mata ta dago a firgice ta ji abin kamar daga sama,ganin mutum sai ta amsa cikin dariya. ya ce,'yan mata ya ya sunanki? ta kalle shi ta ce, suna na?ta kau da kai,ta ci gaba da abinda ta keyi.lsa ya kwada masa kira daga nesa,bashir ka zo mu tafi mana,bashir gani ya ke idan fa ya tafi ya bar damarsa,ya ma rasa ta kenan,shi damuwa.don haka da ya ga abinda zai dame shi,nan da nan zai yi maganin abin,in har zai iya, musamman in na kudi ne, tunda yanzu ba laifi yana samu. sake komawa yayi ya sa aka yi masa sallama da ardo,wanda ya tafi don ya adana kudinsa.kabir yazo gurinsa, [01/10 12:47 pm] Abdul: STEP (45)Zo mu je in ya so mu sake dawo wa,bashir ya ce,ba a haka da ni,ka san ni in ina son abu,zan yi duk abinda zan iya in kuna sauri kuyi gaba zan zo.kabiru ya gane fusata ta sa bashir fadin haka,sai yayi dariya,ya yafito lsa mani da hannu, suka zosu ukun suna jiran fitowar ardo. ya ce,da muna daki daya da ku,duk ku kayi aure ku ka barni,dole ku yi min dariya.duk yadda suka dauki lamarin da zafi gurin ardo,maana ba sauki sai suka ga akasin haka.ardo yana da ilimin addini,ya fahimce su,kuma yayi masu bayanin cewa lallai sun yi dace,domin har an bayar da ita,sai wanda aka baiwa din ALLAH yayi masa rasuwa wata biyu kenan. ya kara da cewa,in yana son ta ta amince ya nemi soyayyarta,in ta amince gurin shi babu wata matsala.kwana biyu tsakani bashir ya sake yi wa rugar fulanin tsinke,cikin ado aljihu dam da kudi.lsa mani yasa shi yin tsarabar sarka da 'yan kunne,wai mutanan ruga suna son abin ado mai kyalkyali.bai samu ardo a gida ba sai babban dansa jabiru.sun gaisa inda yayi masa bayanin cewa,ardo ya je cikin gari maganar tafiyarsa aikin hajji.sai dai yayi wa jabiru alheri,ya ce, masa yana son ganin bengel,kamar yadda ya ji ardo ya ambata rannan. sai jabiru ya ce,oh!sauda? ai saudatu sunanta,ardo kadai ke fada mata bengel, na gode bari in turo ta,domin yanzu zasu fita tallar nono.yana tsugune sauda ta isko shi,tana sanye da koriyar atamfa da kuma farin mayafi mai kyalli.duk da fuskarta babu walwala farin ciki gurin bashir ba ya misaltuwa.ta tsuguna can nesa da shi,ta gaishe shi,ba tare da wata kwana-kwana ba ya ce, saudatu kina so na?rufe fuska ta yi da gefen mayafinta ta ce,ardo ba za ya bada ni ga wanda ba bafulatani ba.ta yi magana cikin hausar da bata goge ba.ya ce,kar ki damu ardo ya san da zuwa na,ya amince in nemi soyayarki. saudatu yarinya ce ba za ta wuce sha uku-sha hudu ba,sai kyau tamkar balarabiya.ta ce,in na amince me zai faru?ya ce, aure ne zai faru,ya fada cikin kwaikwayon muryarta, ya lura akwai kuruciya, [01/10 12:47 pm] Abdul: STEP (46)Gurin yarinyar.ta ce,kamar ya ya?yanzu da na amince sai a kama aure? ya yi dariya,to me za a jira?zan turo iyaye na su gana da naki,zan bayar da sadaki da duk abinda kuke yi na al'ada,sai a daura mana aure.ta sake kallon shi,sai me daga nan?ya ce, a kai ki gida na,ta ce,ina?ya ce,cikin gari,ta ce daga nan sai me?kuma me zanyi a gidanka?ko kaima kana da shanun ne da zan dinga tatsar nono ina kaiwa kasuwarku.ya ce,aa abinci kawai za ki dafa min,sai in kin haifa min yara ki kula min da su.ta rufe fuska,zan tafi ya ce,haba da sauri haka muna hira mai dadi? ya ce,saada ce ke jira na za mu je talla.ya ce,wace ce saade?ta ce,'yar'uwa ta ce, kanmu daya,ya ce,tare zaayi maku aure?ta ce,ni kan zan tafi ta fada tare da rufe fuskarta.ya ce, ba na son tallar nan,ta ce,ni kan ina son zuwa talla,don naga kasuwa,kai kam,me ya sa baka so?ya ce,ina tsoron kar wani ya kwace min ke.ya ciro tsarabar sarka cikin gidanta ya ce,ga wannan,ta amsa da murna. tana godiya.ya sake fiddo da sabbin kudi 'yan naira goma-goma ta yi ta godiya ya ce,mata zai dawo jummaa ta ce,sai ka zo,cikin abinda bai fi wata daya ba ya mallaki zuciyar 'yar fullo.lyaye sun shiga, inda aka tsayar da rana,sai ardo ya dawo daga aikin hajji.su biyu aka hada bikinsu da saade,ita an kai ta wata rugar fulani da ke kusa da su.lta kuma saudatu can masari aka yi da ita,inda mahaifinsu ya ba su daki. satinsa guda ya koma katsina,a nan tudun wada ya nemi daki,ya koma ya dauko ta,ya saka ta lslamiyya saboda ya lura tana da karancin ilimin addini.ta kasa fahimtar cewa shi din fa mijinta ne,fa di take,yadikko,ta ce, ka da ta bari namiji ya taba ta,balle ma jikinta,ita kan ba 'yar iska ba ce. sai da ya lura ta saka hankalinta a karatu,kuma tana fahimta,sai ya samu malamin ya sanar da shi matsalarsu,nan malamin ya cire minti biyar kullum yana yin nasiha ga dukkan dalibansa don akwai me irin matsalar addini bai rufe komai ba,don haka bayani filla-filla ya dinga yi masu ya yin. [01/10 12:47 pm] Abdul: STEP (47)Nasihar.sauda ta fahimci komai,kuma ta mika wuya ga mijinta game da neman gafarar sa,lokacin watannin su goma da aure, shi kam yayi ta ji da ita tare da kara son ta tamkar ya ba ta kamshi. sunyi shekara uku,kafin ta samu cikin farko,ta sauka lafiya danta namiji, ya ce,sunan mahaifinsa aliyu,suna kiran sa abba, kullum kara son saude ya ke yi,saboda biyayyanta da ladabi.a wannan lokacin mahaifinta ardo ajalinsa ya sauka,sun shiga tashin hankali,domin damuwarta ta tayar da hankalinsu sosai.tana nan a rugarsu har ta yi sati biyu da kyar ya lallabe ta suka dawo. Bayan iyayensu sun fita takaba,sai aka yi masu rabon gado,sauda ta samu shanu tara da raguna, saboda su biyu ne a gurin ardo,bashir ya ce,ta ba shi aronsu ya saida,zai fadada kasuwancinsa,in komai ya daidaita zai maido mata da shannunta ko kuma kudinsu. amma ta je ta yi shawara da yadikkonta,yadikko ta ce,ki ba shi,in kin san zai ba ki.sauda ta ce zai ba ni,ta ce,to ki ba shi,sauda ta tattara komai da ta mallaka ta damka ma mijinta. ALLAH ya sama abin albarka,inda kasuwanci ya bunkasa ya fadada ta hanyar bude manyan shagunan kayan masarufi, kayan abinci,shaddoji da zannuwa,ba a fi shekara ba ya soma fita irin su kwatano,togo da dai sauransu.kafin shekara biyu ya fara shiga china da dubai.ln ya sayo kaya sai ya raba ma 'yan kasuwa. daidai lokacin ne ta sake haihuwar danta na biyu,inda aka rada masa muktar.bayan ta yaye,shine suka je aikin hajji,shine ya biya masu ita da shi,da wata shekara ta zagayo kuma ya biya wa mahaifinsa. shekara daya ya bude kamfanin kansa da ake sarrafa robobi da katifu. shekarar ne ta sake haihuwar danta na uku,aka sa ma shi suna abdulkarim. lokacine ya soma nuna mata maitarsa ta son 'ya mace.ya ce,sauda ban taba fada miki ba tun cikin abba na ke son 'ya mace.ln kina da ciki koyaushe ina cikin addua,ta ce,mu ci gaba da adduar ALLAH ya bamu 'ya mace amin.sai in sa mata suna khadija,suna mahaifiya ta ce, [01/10 12:47 pm] Abdul: STEP (48)ALLAH ya bamu masu albarka.abdulkarim ya shiga shekaru uku,amma ba ta samu wani ciki ba,lokacin ne alhaji bashir ya hadu da hajiya binta a saudiyya, bazawara ce,mijinta ya mutu,ya bar mata dukiya, amma bata taba haihuwa ba.a girme zata girme sauda,a boye suka yi ta soyayya,don ya rasa yadda zai yi ya fada ma sauda,sam baya son bacin ranta.wani dare bayan sun gama muamalarsu ta ma'aurata,sai ya rike hannunta yana me sake jaddada mata cewa sonta daban yake a cikin zuciyarsa.matuka take jin dadi a duk lokacin da ya yi irin wadannan kalaman,ta ce,ai tuni ta san haka,kuma ta yarda da wannan.ta kuma fada masa cewa,ba fa sama da shi a rayuwarta,amma in an cire yadikkota.ya yi murmushi sannan ya ce,kin san aure mukaddari ne ga kowane bawa ko?ba tare data fahimta ba ta ce hakane. ya ce,zan kara aure,da farko ta dauka wasa ne, amma jin yadda ya kuke yana ta zayyana mata inda suka hadu,da inda maganar ta tsaya a halin yanzu,sai ta mike cikin fushi ta nufi dakinta.kishi kenan,kumallon mata,rigima sosai suka yi har ta bukaci kudinta.ba da bata lokaci ba ya maido mata,sannan ta dauki matakin kaurace masa,ya yi ta lallabarta amma ta ki.ta kai kudinta gidansu,inda za a sai mata filaye da shanu.wannan ne karo na farko da ya taba kai karanta gurin kannin mahaifinta.har gida baffa ya zo yayi mata fada da nasiha,ta ci kukanta ta hakura doke. An yi biki inda aka kawo amarya sabon gida daya gina masu a sabuwar unguwa.katon gida mai tsari,sai da zama ya soma yin nisa,a nan saudatu ta gane lallai mijinta ya fi son ta.don haka ta saki ranta ta zauna da su zuciya daya. cikin wannan zaman ne ta samu cikin MIMI,haihuwar MIMI ta zo masa cikin nasarori,randa aka haife ta, rannan ya bude kamfaninsa na fulawa a kano.da ya dawo ya ga 'ya mace kyakyawa,mai kama da abar son shi wato mahaifiyarta,yayi murna tamkar ya hadiye 'yar. Yayi walima gagaruma, inda aka rinka sanarwa a jarida,gidan rediyo da talabijin,sabon abu,saudatu ta ga sabon abu kamar na fari. [01/10 12:47 pm] Abdul: STEP (49)Wani abinda ya fi bata al'ajabi,tuni ya amshi renon jaririyar tamkar ba zai fita ba.ya na burge ta har ta soma jin haushi, domin baya kula da ita yanzu kamar da koyaushe uwarsa MIMI,wai shi sam baya son jin kukanta,duk lokacin da yaji kukanta,ya dinga fada kenan,ita kuma ga shegen kuka.sannu-sannu MIMI ta soma girma, sai ta shiga yi ma kowa kuya sai dady,lokacin zama take yi.amma in dady yana gida ko hajiya sauda bata amincewa ta dauke ta.hakanan zai iya barin kowa da komai ya lallasheta,in har tana kukan rigima.haka ta taso cikin mugun gata da rigima ga shagwaba,abin da ta ce,shi zaayi,su abba har suka soma jin haushinta, yayyanta kenan.domin kirikiri zata yi laifin da ya kamata a zane ta,amma sai a ce ko kallon banza ba zaayi mata ba.da aka tashi sanya ta a makaranta,sai aka sanya ta a wadda tafi ta kowane yaro tsada a gidan,makarantar da duk wani mai ji da kansa a katsina nan yake kai 'ya'yansa.sai wani babban abin takaici a gurin hajiya sauda yadda kirkir MIMI ta ki lslamiyya. Da ta dage sai an sa MIMI,hakan ya hakura aka sa ta,in ta je bata komai sai kuka da birgima,rannan wani malami ya dan dake ta,saboda ta ki yin shiru kuma ta ki zama ta kage a tsaye,ai ko ya gane kurensa,domin 'yan sanda alhaji bashir ya kirawo wa malamin.lokacin da MIMI ta sanar da shi cewa malaminsu ya duke ta,'yan sanda suka rufe shi,ya ce a rama wa 'yarsa dukan da yayi mata,domin shine mutum na farko daya soma dukn ta.hajiya sauda ta yi bakin ciki matuka,haka nan ita ce taje ta yi belin malamin tare daba shi hakuri.tun daga lokacin ta kawo idanu ta zuba wa mijinta da 'yarsa,ya ce ta daina zuwa lslamiyya,wai sauda ta dinga koya mata a gida,ai ita da ilimi. sauda ta ce,ai ba zai yiwu ba,a ce baza tayi lslamiyya ba,yaushe za ta san kanta bare addinita.sai ya ce,ai ita mace ce,in ta iya na sallah tunda ba waazi za tayi ba,ba limanci zata yi ba ya ishe ta.sauda ta ce,ai kuwa a dai rayu cikin jahilci. [01/10 12:47 pm] Abdul: STEP (50)Tun daga lokacin MIMI bata kara lslamiyya ba, hajiya sauda sai ta dauki matakin tsare ta da bulala tana koya mata,in ta kiya sai ta zane ta.a kan haka suka yi rikici,wai bata son MIMI,shi ko sai ya dauki matakin tafiya da ita duk inda za shi.ta zama tamkar jaka,shi ke kai ta boko ya kuma dauko ta,ko da yana ofishinsa ne,lokacin tashi yayi zai bar komai ya je ya dauko ta.ta na gurinsa,sai zai bar ofis sannan sun koma gida tare.ln ko za shi wata kasa ko wata jihar,to fa zai kashe mata makaranta,tan gefen damansa. hajiya binta tana matukar bakin cikin abinda MIMI ke yi,tamkar ta kashe yarinyar ta ke ji.cikin haka sauda ta haifi 'yan biyu duk mata,hasana da husaina,ta yi murna sosai,tana zaton tunda ga wasu yara mata 'yan biyu ma abin shaawa,to lallai mijin na ta zai rage son MIMI,za su ture mata gwamnati ko ta samu ta yi mata tarbiyyar da ta dace,amma me?sai yana cewa,MIMI fa dabam take,da duk wasu 'ya'ya da ya haifa baya da kuma wanda zai haifa nan gaba. haka hajiya sauda ta kawo ido ta zuba masu, wai sai data kai MIMI ba ta maimaita kayan sawa,sai in ta yi raayi,ci-banza-ci-wofi shine abincinta.amma ba wai abincin kirki ba,wanda aka dafa ba,haka hajiya sauda ta yi ta haihuwarta a kai-a-kai,ta yi abdullahi sai ameen,sannan umar da sadik,a jere ta yi ta haihuwarsu,amma har lokacin MIMI ita ce ta gaba goshi.lokacin da hajiya sauda ta samu cikin husna, lokacin ne ita ma hajiya binta ta samu nata rabon. sauda tayi mata murna sosai ita mata yi farin ciki matuka.kasan cewar wannan ne farko da zata ga kwanta aduniya,lokacin data haihu an samu mace aka sa mata zainab,kishin MIMI yasa suke yawan rigima da mijin,ita wai dole sai yaji da 'yarta kamar yadda ya keji da MIMI. A wannan lokacin ne ya gina wani katafaren gidan gona a malumfashi,kuma ya gina wani gida a cikin garin malumfashi don haka sai sauda ta bashi shawarar ya maida daya daga cikinsu can tsakanin ita da hajiya binta,don ita kan bata son rigima ta gaji da takalarta fada da binta ke yi kan, [01/10 12:47 pm] Abdul: STEP (51)MIM.ya yarda kuma ya dauki hajiya binta ya maida ta malumfashi, bayan husna,sai cikin hasina shima bata yaye husna bata same shi.wani sabon al'amari,wata jumaa sauda tana daki kwance guraren shadaya na rana,sai jummai mai yi mata aiki ta yi sallama ta ce, hajiya kin yi bakuwa.ta fito taga mace wayayya kuma gogaggiyar 'yar boko,daga ganinta kuma 'yar masu hali ce,ko kuma mijinta mai hali ne.sauda ta ba ta mazauni, ta sa aka kawo masu abin sha.suka gaisa,sauda ta ce, sai dai bangane ki ba fa? bakuwar ta ce,suna na nafisa kuma daga abuja na zo nan,na san cewa ba ki sanni ba.amma ni sai ta dan yi shiru,sauda dai ta ji gabanta yana ta faduwa. cikin zakuwa,ta ce,ina jinki?bakuwar ta ce,za kiyi mamaki idan na ce miki ni matar mijinki ce?gaban sauda ya fadi cikin daga murya ta ce,me ki ka ce? bakuwa ta ce,ni matar alhaji bashir ce maigidan nan.jikin sauda ya soma bari ta ce,karya ki ke yi, mijina ba zai yi aure ba tare dana sani ba wallahi. Nafisa ta daga mata hannu tare da cewa kar ki rantse,domin mun yi aure da shi shekaru bakwai kenan.ta nuna babba daga cikin yaranta ita ce na'ima kuma ita ce 'yarmu ta fari.sai wannan sunan ta suhaila,sai kuma wannan karamin ahmad.na'ima sa'ar abdullahi ce danki,kuma inda MIMI 'yarki tana nan zata shaida miki,domin ita kadai kawai ta sanni,ta san yara na a duk lokacin da alhaji ya je abuja MIMI tana zama a hannu na ne. Na dade ina son ya kawo ni in ganku iyalinshi,ku sanni amma yaki sai ya ce, zai kawo ni,sannan wai baya son ki tada hankalinki, ni kuma naga cewa akwai mutuwa.shi yasa tunda ya sanar dani zai tafi china ni kuma na dauri aniyar zuwa mu gana daku saboda halin rayuwa.hajiya sauda jinta kawai take yi tamkar a cikin mafarki.sai da ta lallashi zuciyarta sannan ta ce,shikenan ba komi.ku jira shi a nan in ya dawo sai ku tafi,nafisa ta ce,ni ma haka ne kudurina,ina son a nuna muga dangi,sauda ta ce, babu damuwa.kwanan su biyu,ALLAH yayi wa mahaifin alhaji bashir rasuwa a masari, [01/10 12:47 pm] Abdul: STEP (54)Kwana su biyu, ALLAH yayi wa mahaifin alhaji bashir rasuwa a masari,da ma bashi da lafiya har misira an fita da shi,amma da yake jikin tsufa sai a hankali.nan suka tattara suka nufi masari, shima dole ya bar komai ya nufo gida,shi da 'yar lelensa MIMI,bayan an natsu hajiya sauda ta gabatar da nafisa ga dangin mijin na su.nan suka yita surutu bai kyauta ba,bai kyauta ba, wasu kuma suce giyar kudi ce.lta kam sauda cewa ta yi,ni haushi na daya,mene ne na kin fada mani,wa zai hana shi aure?kuma da ya ki kawo ta,inda ta ALLAH ta kasance a kanshi ta zo da yara ta ce ita matarsa ce za a yarda cikin sauki? lta kuwa hajiya binta zagewa tayi tana ta tsula rashin mutumci duk da cewa gidan mutuwa ne, karara ta nu na kishinta. Shima duk da yana cikin ciwon mutuwa,ya girgiza da samu nafisa a gidan, sam bai so ba.dole ya hakura ya jure masifar da hajiya binta ta dinga yi masa son ranta,ta fada ma shi maganganu.lta kuma sauda bata ce komai ba,sai rashin yin maganarta yafi daga mashi hankali fiye da masifar da hajiya binta ta keyi.sai da aka yi bakwai sannan kowa ya watse suka koma gidajensu. Daga nan yasa aka maida nafisa abuja,shi ma ya nufi katsina. Har cikin daki ya samu sauda tana shirya yaranta zasu tafi lslamiyya,sai da suka tafi sannan ya zauna kusa da ita ya ce,sauda na san nayi miki laifi,don ALLAH ina son ki yafe min, dama kullum cikin tunanin zuwa wannan ranar nake yi.ta kalle shi laifin me?ya kasa bata amsa,ta tabe baki baka yi min laifin komai ba.ya ce,ai nina san nayi laifi,ki fahimce ni,sam banyi da nufi ba. Tunanin halin da zaki shiga ne ya hana nina fada miki,saboda naga yadda muka yita samun matsala a lokacin auren hajiya binta,ni kuma bana son bacin ranki sam.ta ce,umm!ni yanzu lamuranka babu ruwa na da su,ya ce,don me kika ce haka?ta ce,na zata ni da kai duk daya ne,ko mutuwa zanyi don kishi ai ka fada min in ya so in mutu.kuma bayan kayi ma,ai sai ka fada min.ya ce,to nayi kuskure, [01/10 12:47 pm] Abdul: STEP (55)Ai lokacin auren ne yazo babu shiri don ALLAH bari in fada miki yadda abin ya faru. Lokacin ina son sayan wasu filaye a cikin garin abuja,saboda ina son fara harkan gine-gine ina saidawa,to mahaifinta shine shugaba a maaikatar filaye, da safiyo,ni da lauya na muka je gidansa don ganawa ta musamman kamar yadda ya bukata, shine na ganta,amma har ga ALLAH ba sonta nake yi ba.don in samu saukin wannan harkan shi yasa na nuna ina sonta,kuma alhamdulillahi sai ya bani ita. su alhaji lsa mani ne suka amsar min aurenta, ban zaci zamu dade a cikin auren ba,domin nayi ne na wani lokaci,amma sai mutuncin mahaifinta,da yanda ya sakar min nake samun alherin filaye,shi yasa na hakura.abinda yasa ta kara shiga raina shine yadda take son MIMI sosai har ma wani lokaci ina cewa a ce ita ce mahaifiyar MIMI,domin bata takura mata.hajiya sauda ta ce,wato ita MIMI har da ita a munafunta ta,yayi mata kyau.ya ce,kar ki ga laifin ta,ta ce,kaima ba cewa nayi kayi laifi ba cewa,na yi don me ka boye min?ai aure ba laifi bane,na isa in hana ka yi? ya ce,ba zan kara ba,ta ce, nan gaba in zaka cike ta hudu na roke ka,ka sanar damu.ya ce,ai na gama sauda.ta ce,uhum,haka dai ka ce,ni yanzu na daina yarda da kai.ya shiga lallashinta da fada mata maganganu,tsakanin mata da miji sai ALLAH,nan dai suka sasanta tamkar basu taba samun matsala ba,har ranta tabar abin a kaddara. Tun da ya samu sauda da sauran danginsa suka san da nafisa,sai yaga bashi da matsala,tuni yake son ajiye MIMI a gurin nafisa amma babu hali saboda ina zai ce ya kaita? amma yanzu ga dama ta samu,tuni ya tattara ta ya maida ta,MIMI mata yi murna da hakan,don ta san momy nafisa na sonta. lokacin da za su tafi kalma daya ta fada mishi,alhaji tunda kana ganin zaman MIMI a can yafi guri na,to babu matsala,amma ina son kasan cewa,duk iyayen da basu sa dansu kuka ba, to wata rana sai dan ya sasu kuka ya ce,wannan kuma irin naki tunanin kenan,ni dai zan maida 'yata inda za ta samu 'yanci ta kuma huta. [01/10 12:47 pm] Abdul: STEP (56)Lallai MIMI 'yargatace,domin a dankararren gidan da ya gina a abuja maitama,an tsara gidan sama ne hawa daya,amma saman na MIMI ne kowa yana kasa,dakin baccin ta komai pink don shine kalar data fiso.dayan dakin kayan karatun ta ne a ciki,shi kuma dayan an gyara shi an rufe.lokacin shekaranta goma kacal, momy nafisa tana yin iya yinta don ganin ta danne zuciyarta ta kauda kanta ga abinda alhaji ke yi ma MIMI,ba don komai ba,sai don ta samu shiga da kuma abin duniya da yake sakar mata.amma a badini bata son MIMI,bata kamar tana sonta,kullum burinta yanda zata shiga tsakanin su,don ko makaranta da zai sata wanda 'ya'yan jiga-jiga abuja ke zuwa yasata wata rana za shi katsina shi da MIMI ya ce bari su fara zuwa malumfashi don ya gasu hajiya binta,ya kuma ga gonarsa su wuce, tunda binta ta ganshi da MIMI ta hade rai,lokacin wayoyin hannu basu yi yawa ba,sai ta ga MIMI da dankareriyar waya mafi tsada a wannan lokacin.sai binta ta bata rai ta shiga jero zantuka marasa dadin ji,tana fadin ma alhaji cewa ya cika son kai,ba shi da hakki ya bambanta MIMI da 'ya'yansa nan fa ranshi ya baci an tabo rabin zuciyarsa ya ce,duk abin da zata yi,ta yi mishi don shine ya auro ta,amma ta cire sunan MIMI a bakinta, nan fa suka yi kaca-kaca abin har ya kai su da yi mata saki daya,ya tattara yaranta guda uku suka wuce katsina. Ran sauda ya baci matuka,ta duddungure MIMI a gabansa,ya dai daure fuska amma bai yi magana ba,ta matsa mishi lallai sai ya dawo da hajiya binta,ta ta sashi gaba suka je biko, bayan binta ta dawo ne ta zo kwasar 'ya'yanta amma sai zainab taki binta,saboda suna yin wasa dasu husna,ta yi-ta yi,yarinyar ta ki dole ta hakura ta barta. bayan husna hajiya sauda ta sake haihuwar hasina wadda ta zame mata auta, don ta sha wahala a haihuwar tamkar bazata tashi ba,sai da aka yi maka aiki,alhaji ya firgita sosai don haka ya ce da likita ayi masa taimako a tsaida haihuwar.hajiya binta ta kara biyu najaatu da fadila su biyar kenan. [01/10 12:47 pm] Abdul: STEP (57)Momy nafisa ita ma ta kara biyu mas'ud da aisha.bayan MIMI ta kammala secondary ta ce da alhaji bishir mahaifinta, daddy ni fa nafi son in fita waje america ko england ko spain.ya ce ba matsala ta zabi duk wadda take so, ya sayi hannun jari da sunanta,banda kamfanin da ya bude duk wata ribar tana shiga asusunta,sai da ya gama komai sannan ya samu sauda da batun har yana kara fada mata cewa zata fita karatu waje,hajiya sauda ta ce duk bata yarda ba,sun yi rigima sosai dole ta kyale shi. Shi kuma jin ta kushe kasashen turawa,sai ya ba MIMI shawara ya ce ta tafi dubai,tunda can garin larabawa ne,da kyar MIMI ta yarda ta tafi don yin karatun law,zabin ta shine ta zama lauya,amma in a son mahaifinta ne tayi karatu a kan kasuwanci, don ya dora ta a kan alamuransa.abba ya gama digree dinsa a kan mass com,ya samu aiki a banki,ya na kaduna,kuma ya auri samira wadda suka hadu a a ABU zariya, mahaifinta shine ambasadan najeriya a Egypt.su na da yaro daya, wanda suka sa mishi sunan alhajin suna kiran shi ta karshe,don karatun shi mai tsawo ne,likita ne fannin magunguna.shima abdulkarim shekarar shi ta karshe yake,engineering ya ke karantawa.lta kuma MIMI ta cinye shekarar farko ne ta zo hutu,za ta shiga ta biyu,wannan shine asalin su MIMI. Tunda lsmail ya koma dakinsa yake mamakin MIMI,har me ta dauki kanta da take wani ji da kanta haka?shi kam ba maula yazo ba,don haka baya zaton zai kaskantar da kanshi,ya kira layin mahmud suka gaisa,mahmud yana tsokanarsa,da cewa mutanan abuja garin daula,lsmail ya ce,gaskiya duk da ban fita cikin garin ba a gidan da nike kadai na tabbatar cewa akwai daula.mahmood ya ce,ai mutumin nan ya shahara,to yaya kuka yi da yarinyar nan?lsmail ya ce,kai dai bari,nan ya sanar da shi duk yanda suka yi,mahmud ya ce kar ka ce zaka yi zuciya,ka natsu ka danne zuciyar ka in ta shiryu zaka samu lada.sannan ga mahaifiyar ta, ko don ita ya kamata ka jure.lsmail ya ce shikenan, amma fa sai dai mu zuba. [01/10 12:47 pm] Abdul: STEP (58)Tunda lsmail ya koma dakinsa yake mamakin MIMI,har me ta dauki kanta da take wani ji da kanta haka?shi kam ba maula ya zo ba,don haka ba ya zaton zai kaskantar da kanshi,ya kira layin mahmud suka gaisa, mahmud yana tsokanarsa, da cewa mutanan abuja garin daula,lsmail ya ce, gaskiya duk da ban fita cikin garin ba a gidan da nike kadai na tabbatar cewa akwai daula. mahmood ya ce,ai mutumin nan ya shahara to ya ya kuka yi da yarinyar nan? lsmail ya ce,kai dai bari,nan ya sanar da shi duk yanda suka yi,mahmud ya ce kar ka ce zaka yi zuciya,ka natsu ka danne zuciyar ka in ta shiryu zaka samu lada sannan ga mahaifiyar ta,ko don ita ya kamata ka jure. lsmail ya ce shikenan,amma fa sai dai mu zuba. lta kuwa gimbiyar,wato MIMI,sintiri ta dinga yi a falon tana nazarin wannan mutumin wane irin hukuncin ya kamata ta yanke masa?wata zuciyar ta ce, don kin kore shi,ai ba ki rama ba,kin shirya me zaki ce ma hajiya?kar ki manta dai data gargade ki sosai sannan aka turo min ki shi.a fili ta ce,to me zan mi shi in huce?ta kalli wayarta, yawwa bari in kira mina dakingari. Bakin gadonta ta shiga, bedroom ta zauna,mina ta daga tare da fadin khadija masari ya?MIMI ta ce,lafiya dakingari,kin san mene ne? (ta ci gaba)mom di ta ce in fada miki ta dage sai wani malami ya koya min karatun islamiyya.mina ta ce,mene ne laifi?MIMI ta ce, dan rainin wayo ne,kinga yanda yake son nuna min iyaka ta?nan ta kwashe komai ta fada mata,mina ta ce,kin san me zaki yi masa? MIMI ta ce,aa,mina ta ce,in dad din ki ya dawo ki sa a kira shi,sai ki ce kina son a ware lokacin karatun ku minti talatin ko awa daya,yanda dai kika zaba, kinga ba zai taba tashi daga gurin karatun ba sai lokaci ya cika,MIMI ta ce, yawwa kin kawo shawara, kin ga sai in yi masa duk cin mutumcin da naso na tsawon lokacin,kuma dolen shi ya tsaya ya saurare ni, mina ta ce,in kin ga zai wuce gona da iri,ki mari fuskarsa,suka sa dariya ta ce,kin san ba na son taba jikin talakawa, [01/10 12:47 pm] Abdul: STEP (59)Amma zan tsirta mishi yawu,mina ta ce,haka yayi. yaya khalil dinki? oshshh!kin tabo rabin rayuwata,yana lafiya,ya ya faisal dinki?mina ta ce,sun gama hutunsu ya koma jiya, ta ci gaba da cewa,ina mamakin irin son da kike yi wa khalil dinki,kamar ba ki tsane shi ba,MIMI ta ce,kin san me mina?can dama ina son khalil tun lokacin da na soma ganin shi,na ja aji na ne kawai.mina ta ce,don ALLAH da gaske?MIMI ta ce,ALLAH kuwa,mina ta ce,kin iya jan aji kuwa to, shikenan in kunyi waya ki ce,ina gaida shi,MIMI ta ce, zai ji.bayan sun yi sallam ta shiga nazarin mau'du'in wulakancin da ya kamata ta dinga yiwa malami. Tara daidai lokacin cin abincin su na dare kenan,ta sauko da 'yar jar doguwar rigarta da kadan ta wuce gwiwarta,kamar kullum ta yi ado da gashin kanta,kowa ya hau kan teburin,tuni yara sun soma ci ma,sai da ta isa kusa da mahaifinta ta gaida shi, sannan ta dawo gurin zamanta ta kalli momi nafisa,mommy kin dawo?ta ce,ai ban dade ba MIMI,alhajin ya ce,ina kika je?ta ce,gidan hajiya adama na je,in duba masu takalma,ta dawo daga lngila.MIMI ta ce,kin samo mana?ta ce,duk kina da shigen su,ke kuma na san baki son duk wani abin ki ya zama gama gari.amma ta ce,wasu kayan na zuwa. MIMI ta ce,mommy ki bar shi ma kawai.takalma sun min yawa,akwai wadanda har yau ban sa su ba.na'ima ta ce,sis ina wadanda ki ka ce za ki ba ni?MIMI ta ce,ki tuna min da safe,ALLAH ya sa suyi miki,ke da katon kafar nan na ki,duka suka sa dariya. Alhaji ya ce,MIMI ke komai na ki daidai aka yi maki,kuma mai kyau,kalmar ta soki zuciyar momy nafisa ta ce,duk dai dan adam tara yake bai cika goma ba,ya ce,me ki ke nufi?ta maida abin wasa. ahaji na gani ne koyaushe sai ka wasa mamarka cikin dariya tayi maganar,shima cikin dariya ya ce,kin ga laifina kenan. Ya kalli MIMI,uwata ci abinci mana,ta zuba farfesun kaza ta soma ci tana yi,tana chating,bayan sun gama ne,alhajin ke ce ma MIMI zai yi bako ranar lahadi,ina so ayi masa tarba ta musamman, [01/10 12:47 pm] Abdul: STEP (60)Nan zamu yi diner da shi,inda zai zo da iyalansa,sai na fi yin murna. mommy nafisa ta ce wane ne?ya ce alhaji akilu bala, ministan man fetur,MIMI ta kalli mahaifinta,dad,ka samu ganawa da shi kenan,ya ce,uwata ai yanzu mun zama abokai tamkar tare muka taso.shi yasa na gayyace shi don ya ga iyalaina,MIMI ta ce dad insha ALLAH za mu tarbe su.kiran hajiya sauda ya katse shi,ya daga bayan sun gaisa ta ce,ya binciki MIMI ko ta yi karatun,ya ce,ki daina damun kanki sauda,za ta yi,suka ci gaba da maganarsu,jin haka ne bayan ya gama wayar ya mike daga kujerar ya nufi dakin shi,MIMI ta ce.amma dad dama ina so muyi magana a kan malamin nan.lna son a tsaida lokacin da zan dauka,don koya min karatu,ya ce kamar ya ya?ta ce,dad yau karatun minti hudu ya yi min,ya ce, ok na gane,da safe zan neme shi mu yi magana.ta ce,ok dad ni ma zan fito da wuri don a yi komai a gaba na ya ce,to bari in shiga ciki,ta ce tam,dad ni ma zan koma sama ne sai da safe ya ce,ALLAH ya kaimu. lsmail yana tsaye bakin kofar falon,tunda ya danna baa bude ba,kusan minti biyu,ya sake dannawa sai lokacin aka bude,daga ganinta 'yar aiki ce,kuma ba musulma ba ce,ta ce kaine malam?ya ce eh,ni ne,ta ce, ka shigo,a nan cikin falo ya same su dukkan su,ya kalli alhaji cikin girmamawa ya gaida shi,sannan ya gaida mommy nafisa,ya ce gani alhaji,malam hamisu ya ce,kana nema na. Alhaji ya nuna masa kujera zaka iya zama a kan kujera,MIMI ta kalle shi da gefen ido,aa dad kar ka bashi damar zama a kan kujera,ya kalle ta,saboda me?ta ce,dad bai kai matsayin ba,shi mabukaci ne a gurin mu,ta kalle shi, zauna a kan kafet,ya danne zuciyarsa,babu damuwa in maganar ba mai tsawo ba ce zan iya tsayawa alhaji,alhajin ya ce,kar ka damu zauna a kan kafet din abin ya bawa lsmail mamaki,amma sai ya zauna saboda alhajin ne ya bukaci hakan.ransa ya ce, lallai dama an ce karshen zamani baiwa zata haifi uwar gijiyarta. [01/10 12:47 pm] Abdul: STEP (61)Muryar alhajin ta katse shi,malam wanene ma sunanka?ya ce lsmail, alhaji ya amshe da cewa, yawwa lsmail,MIMI ce ta bukaci ka sa lokacin da za ku dinga yin karatu,da kuma tsawo lokacin da za ka dauka gurin yin karatun. lsmail ya ce hakan yana da kyau,wane lokaci ne ta tsaida?alhajin ya kalle ta, uwata wane lokacin ki kafi so ya koyar da ke?ta dan yatsina baki sannan ta kalli damfareren agogonsu a jikin bango kirar dubai,ta ce, kamar sha daya sai ya dinga zuwa don kada ya ce sai an aika a kira shi,ni bana son jira,nafi son a jira ni.lsmail ya yi dan murmushi a ransa ya ce,son kai, amma a fili sai ya ce,to mu tashi nawa?ta kalle shi sama da kasa.tsawon awa daya za mu yi gurin karatun.lsmail ya kalli alhaji, ba damuwa kullum zan zauna karfe shadaya mu tashi sha biyu kenan.ba lallai hakan ba ta katse shi. zaka iya zuwa misalin sha daya ya zama ban sauko ba,kai dai in ka zo shadaya daga lokacin dana sauko, daga saman na zo gurin karatu shine zaa dauki awa daya,lsmail yayi murmushin takaici,babu laifi matsawar lokacin sallar azahar ba zai shigo ba,alhaji ya ce,sai batun albashi,hajiya ta ce min ka ce duk abinda aka baka,lsmail ya ce haka ne. alhaji ya ce,aa zai fi kyau ka fada,lsmail ya ce,alhaji me karantarwa ladan shi yana gurin ALLAH,abinda zaa ba mu kyautatawa ce,alhaji ya ce,to da kana samu dubu hamsin a wata?lsmail ya ce,aa gaskiya basu kai ba,ya ce,to zan dinga baka dari. da sauri lsmail ya kalle shi, sai MIMI ta fashe da dariya kudin sayan kayan kwalliya na kenan fa,ta kalli na'ima, dubi yanda ya rude,ashe ni ma zan iya biyan shi da kaina,alhaji ya ce,ka iya tafiya,sai lokacin ya yi.lsmail ya ce to,tare da mikewa, ransa bace ya fita,lallai yarinyar nan 'yar wulakanci ce,anya kuwa zai jure?. Alhaji ya kalli MIMI,uwata ki daina irin wannan a gaban mutum.ta kalle shi,dad wallahi duk duniya ba wanda na tsana kamar shi,na'ima ta ce,shine to zai dinga yi miki karatu?ta ce, eh,amma na tsane shi,ta ce to mu fa karatun mu yaushe ne sis? [01/10 12:47 pm] Abdul: STEP (62)MIMI ta ce,ku kan sai karshen sati.alhajin ya mike cikin murmushi bari na fita,mommy nafisa wadda kallo ya daukar mata hankali,ta mike don yi masa rakiya,ya shafi kumatun MIMI ki yi min addua uwata, ta ce,sai ka dawo dad ALLAH ya baka saa,na'ima ta ce,sai ka dawo dad,ya ce,yawwa na'ima. mommy nafisa ta zauna a kan kujerar madubi tana kallon na'ima wadda ta fada kan gado ta yi ruf da ciki,ta ce,na'ima taso ki ji,ki taso mana na'imata,ta dago fuskarta da jurwayen hawaye,ta ce,mommy dad ba ya so na,komai sis MIMI, ni kam na gaji.nafisa ta ce. amma me nike fada miki kullum?ba ke kadai ba ce yake yima haka,ku duka ne, amma nayi miki alkawarin sai ya so ki fiye da MIMI. na'ima ta soma kuka,na gaji da jin haka mommy,sai yaushe ne haka zata faru?mommy nafisa ta tashi ta koma bakin gado ta zauna,ta janyo na'ima zuwa jikinta,kar ki damu,mu bi a hankali da sannu za ki zama 'yar gaban goshi. akwai shirin da na jima ina shiryawa,na'ima ta kalle ta da gaske?mommy nafisa ta ce,kar ki yi shakka.ta share hawayanta,shikenan zan so in yi kamar abinda take yi,ko kuma fiye suka sa dariya. Shadaya daidai lsmaik ya shiga cikin falon,bayan me aikin ta zo ta bude,na'ima ce kadai a falo tana kallon fim din india,ya ce,ki fada mata nazo,ta yi mishi kallon banza,ba ta ce, in kazo ka jira ta bane?ga falon da kuka zauna can a jiya,zaka iya jiranta a ciki.ya nufi falon ransa bace,anya rayuwar gidan nan zata yiwun masa?mintinsa goma shabiyu,sannan ya soma da jin kamshin turaren ta,gabansa ya fadi,ta ja kofar wadda ta kasance ta gilashi,kallo daya ta yi masa yana sanye da jallabiyya fara sal,ya yi kyau matuka,ta tabe baki,ta zauna shima ya kalle ta kamar koyaushe shigarta babu tsari,ya kauda kai,ya ce,ta ina za mu fara?ta daga wayarta ta sa a kunne,hello dear ka tashi lafiya?ta dai yi jim,ok zamu yi waya anjima,yanzu ina tare da talakan nan ne,sai kuma tasa dariya,khalil kenan sai anjima din.ta kalli lsmail me ka ke fada?ya ce,ta ina zamu fara? [01/10 12:47 pm] Abdul: STEP (63)Yanda ya kafa mata ido hadi da hade ranshi,sai ta ji yayi mata kwarjini,ba za ta iya kallon shi ba,yayi da zata yi masa rashin mutunci,ta kauda idanunta gefe,ko ta ina ka fara mana,ka tsare ni da idanunka,yayi dan murmushin takaici,ya ce,to zamu fara daga huruful hija'iyya,alifun kenan.ta dube shi da sauri tun ina 'yar nursery na yi wannan, yanzun kam university nike, don haka sai ka koya min karatun da yayi daidai da ajina,lsmail ya ce,zan so in baki shawara,dul me neman ilimi ko bana addini ba zai fi kyau ya zama me biyayya da saukar da kai, girman kai ba ya kai mutum ga gaci. ta daga mishi hannu,baa dauke ka don ka bani shawara ba,an kawo ka ne kurum ka koya min karatu. ya ce,to bari mu fara daga fatiha sai mu shiga bakara zuwa kasa ko?ta tabe baki,ina jin ka,ya ce,zan karanta miki kamar sau uku,sai ke ma kiyi.tunda ya soma karatun danna wayarta ma take yi,ya gama ya dube ta,yanzu sai ki karanto fatihar in ji ke ma daga nan sai in dora miki daga bakara aya biyar-biyar zamu dinga yi duk kwana biyu sau biyu a sati sauran kwanakin kuma sai mu saka fikihu,hadisi da tauhidi.ta ce,me kake fada ne?ni fa duk ban jika ba,ya ce,karatun na ce kiyi,ta harare shi,yanzu fa ka ce, sai ka fara sannan zanyi ya daga murya,kina nufin baki ji karatun da nayi ba?ta ce,shine gaskiya,da kayi ai da naji,ya rufe kur'anin cikin takaici,ya zuba ma kafet din kasan idanu, shi kam ya gaji.ta katse mashi tunani,a banza zaa ba ka dubu dari?ya ce,in na fasa koyarwar fa?ta ce,ka rasa,zan fin son ma ka ce ka fasa,don ni dole idanu na suke kallon fuskar ka,kuma bana son in kore ka saboda hajiya zata yi min fada,amma in ka tafi da kan ka shikenan. [01/10 12:47 pm] Abdul: STEP (64)Ya ce,yanzun zan kira hajiyar in fada mata komai,gabanta ya fadi,ta yi shiru cikin fargaba. ya ce,zan fada mata komai don kar ta zarge ni,ta ce,bari in riga ka fada mata,ga mamakinsa sai ya ga ta saka wayarta a handsfree ta kuma kira layin hajiyar,ba ta jima tana ringing ba ta daga.sun gaisa ta ce,ya ya kuwa karatun ki na yi?ta ce eh! hajiya yanzu haka ina kan yin karatun,na kira ne nayi miki godiya,ki yi wa malamin godiya in kun yi waya,don ina fahimtar karatunsa,ta ce,ai lsmail yana da himma ALLAH ya taimaka,ta ce amin,suka yi sallama. ta kalle shi,ka gane nufi na?na san yanzun dai za ka ji nauyin ce mata bana karatu,tunda na ce ina fahimtarka,ka ga kenan sai ka nemi dalilin ka na kin koyar da ni da zaka yi,yayi banza da ita ya ci gaba da kallo agogo minti goma da suka rage sun yi mishi nisa,sai da ya ga saura minti biyu,ya kalle ta, tana ta chatin,ya ce,ki yi amfani da lokacin ki tun kina da kuruciyarki,ki nemi sanin addininki sannan ki bauta ma ubangijinki kafin lokaci ya kure miki.ta ce,kai har ka samu sake da yawa irin haka ne?ganin ka ka kai ka dinga fada min magana son ranka ne?ya yi murmushi,in kin gaji da kallon kyakyawar fuskata zan tafi,don lokaci ya cika, kin san lokaci baya jira. Ta mike tsaye,shima ya mike tare da kwasar littafansa,ta ce,har wani kyau ne da kai? [01/10 12:47 pm] Abdul: STEP (65)Dube ka,ya ce, sosai kuwa,don na san nafi ki nesa ba kusa ba.ta ce, karya kake yi,na sha jin mutane suna gulmar kyau na,ban da wadanda suke fada a gabana.ya yi 'yar dariya,da son ya cusa mata takaici,sanna ya ce,ina zaton suna tsoron ki ne,ko jin nauyin ki,ki je ki roki masu fada maki cewa kina da kyau su fada maki tsakani da ALLAH.ya kalli agogo,kash har na kara minti biyu,ya face,kafin ta kai ga cewa wani abu, ranshi kar,ya san cewa ya guma mata.don ya san mata ko basu da kyau,sun tsani a fada,shi kuma yayi ne kawai don shakar da ita,bai yi nisa ba,ya ji ta saka kuka,sauri ya kara ya fice daga gefen na su. Mommy nafisa ta fito da sauri jin kukan MIMI, abinda ta dade bata ji ba, ta ce, mene ne?MIMI ta ce, mommy kalle ni sosai da gaske bani da kyau? mommy ta ce,in ji wane makahon?MIMI cikin shagwaba ta ce,wancan talakan malamin mana, mommy nafisa ta ce,barshi kawai karya yake,MIMI ta ce,bari dad ya dawo dole ne malamin nan yayi kwanan cell,mommy ta ce,ki share shi ne kawai, hajiya sauda ba za ta ji dadi ba,in har ki ka kai shi gurin 'yan sanda. MIMI ta yi samanta cikin matsananciyar damuwa,kai tsaye dakin ta ta wuce,sai gaban madubin ta na jikin sif dinta,don shine zai nuna mata siffarta tun daga sama har kasa,ta dinga juya kowane gefen ta tana kallo,zantukan malamin suna yi mata yawo a cikin kai.ki je ki roki masu fada maki cewa kina da kyau,su fada maki tsakani da ALLAH,wadannan kalaman sun sa ta a cikin rudani,ta dauki wayarta,ta kira layin na'ima,bayan ta daga ta ce, ki je ki ce ma hamisu direba zamu fita,na'ima ta ce to sis,ni ma zan bi ki,cikin tsawa ta ta ce,aa ki je aike na kawai. gidan su amina dakingari ta nufa,mina ta yi mamakin ganin MIMI ba ko sanarwa,bayan sun shiga daki,MIMI cikin kuka ta ce, mina don ALLAH ki fada mun gaskiya tsakani da ALLAH.mina ta dafe kirji,me ya faru MIMI?MIMI ta ce,ni dai ki fada min,ina da kyau?,mina ta ce,ko makaho ya shafa,MIMI ya san kina da kyau sosai ma. [01/10 12:47 pm] Abdul: STEP (66)Wai duk me ya kawo wannan tambayar? MIMI ta ce,hum!wannan malamin ne talakan banza nan dai,MIMI ta sanar da ita yanda suka yi.mina ta yi tsaki,na zata ma wani na kirki ne ya ce miki haka,ya fada ne kawai don ya baki haushi.ke to me zai dame ki tunda ba khalil ba ne ya ce baki da kyau!ln duniya za a taru a ce baki da kyau, na tabbata khalil ba zai ce ba. MIMI ta sauke ajiyar zuciya,ta isa gaban madubin mina tana kallon kanta,ta ce,mina cewa fa yayi kawai ana dai jin tsoro na ne ake cewa ina da kyau,mina ta zo ta dafata, kar ki ruda kanki MIMI,dube ki fa doguwa fara sal ga gashi har baya,idanuwanki masu haske.MIMI hatta hakoranki abin birgewa ne, so kar ki damu kanki.MIMI ta dauko wayarta ta soma kiran layin khalil,ta zauna daidai lokacin da ya daga ta ce,zan tambayeka wani abu,ka fada min gaskiya.ya ce,ina jin ki,ta ce,kana so na?ya tausasa murya,haba khadija wannan tambayar ai kin dade da sanin amsarta,amma in kina son in sake maimaita mi ke ne, sai in ce ina sonki,ina sonki sosai fiye da yanda ni ke son kaina,ta ce,saboda me kake so na khalil?ya ce, abubuwa da dama khadija, amma daga ciki akwai halinki da kuma kyawunki, MIMI ta ce,hali na kuma? khalil ko dai gaskiya ne mutane basa son fada min gaskiya?ban taba jin wanda ya yabi hali na ba, daga daddy na sai mommy nafisa,sai kai yanzun,ta kashe wayar,hawaye na zuba mata. Mina ta ce,MIMI kin cika son sama kanki damuwa, wani banza talala ya rikitaki duk ki damu kanki,ki dawo hankalinki mana? wayarta ta soma ringing ta duba ta ga khalil ne ta jefar da wayar.mina ta ce,shi kuma me ya shafe shi? MIMI ta ce,tsakanin da ALLAH mina kin taba jin wanda ya ce,ina da hali mai kyau?hatta mahaifiyata kullum fada take yi min in gyara hali na. ke ma in na yi wani abu,kina ce min irin hakin nan ba shi da kyau,amma yanzu khalik yana min wai yana sona don hali na. maganar malamin nan ta zama gaskiya,kenan masu cewa ina da kyau basu fada min gaskiya. [01/10 12:47 pm] Abdul: STEP (67)Mina ta ce,oh my god,don ALLAH ki daga wayar khalil,in kowa zai ce halinki ba kyau,khalil ba zai gani ba,don so yana hana ganin laifi,ka da ki dama ma kanki lissafi,shawara ta ki kori malamin nan ki huta mana.MIMI ta ce,kina nufin khalil iyaka gaskiyar shi ya fada min?mina ta ce kina dai karatun englis novel na soyayya dama baki fahimtar komai?MIMI ta yi shiru tana nazari,can ta yi ajiyar zuciya,ta dauko wayarta daidai lokacin khalil ya sake kira.wanda ba ta san ko kira nawa kenan ba.ta daga muryarta tana rawa ya ce,khadija fada min gaskiya nayi miki wani laifi ne?ta ce,aa na i ka ce kana so na don hali na,ni kuma kullum kowa ce min yake ba ni da hali,fada min gaskiya.ya ce,ni halayen ki sun mini,ko da ba su yi ma kowa a duniya ba,zan iya yin komai a kan sonki,ki yi min izini in zo abuja mu yi magana a cikin tsanaki.ta ce,na fada maka dad dina bazai so ya ga ina hira da saurayi bai san lokacin da muka hadu ba,ka bari na bashi labarin ka,sai ka zo ku gana.ya ce,ko wani guri daban sai mu je, in na zo sai mu yi maganar kin ji?don ALLAH dama ina son ganin ki,ta yi shiru.can ta ce shikenan,gobe ka zo, amma zan turo maka address din gidan su mina sai mu hadu a can,ya ce, shikenan sai kin turo,ki kwantar da hankalin ki kin ji?ta ce,babu komai. mina ta riko mata hannu, kar ki damu da sauraran shi,ki kore shi kawai.MIMI ta ce,bani da damar yin haka, don dazun na kara daure kaina na fada ma hajiya cewa ina jin dadin karatunsa ina fahimta,in na ce a kore shi bisa ga wane dalili?mina ta ce,kin hadu da alakakai,ta tashi,bari in je gida,duk da haka zan nemi shawarar mommy nafisa a kan shi.lokacin da ta iso gidan mommy nafisa, mommy nafisa suna dakin na'ima suna tattaunawa a kan matsalarsu,wato MIMI, mommy ta ce,na'ima ai na ji dadin zuwan malamin nan,saboda na jima ina son in ga ran yarinyar a bace,sai dai ni bani da damar in bata mata.na'ima ta ce,don ALLAH mommy kar ki bari ta kore shi,ai ni ya birgeni da yake mata abinda take yi wa mutane. [01/10 12:47 pm] Abdul: STEP (68)Kira da take yi wa mommymomy shine ya sa ta yin sauri ta fito daga daki,ta ce,ya ya ne MIMI,kin dawo?ta ce,eh,ni mommy kina ganin ba zaifi kyau in kori malamin nan ba? mommy ta ce,a'a bana son hajiya sauda ta zarge ni,don haka kiyi hakuri 'ya ta, bari in sa folina ta kira shi,in gargadeshi,don kada ya ci gaba da fada miki magana,ta ce,shikenan, amma ina son a yi mashi fadan a gabana don ya san ni ba sa'ar shi ba ce. Haka kuwa folina 'yar aiki ta kira lsmail,a gaban MIMI tayi mi shi gargadin kar ya kara cewa ba ta da kyau.ya ce,lnsha ALLAHU, ko ba komai dai lsmail ya ji dadin bata mata ran da yayi. A katsina kuma kwana biyu da tafiyar lsmail zainabu ta soma yin tallar ta,kuma a ranar ne ta hadu da wani alhaji,babban mutum ne a shekaru haka kuma a aljihu.direban shi ya tura ya tsaida ita,ya tambayi sunanta da kuma gidansu,ba ta boye ba don mahaifiyarta ta shirya mata cewa,ta saurari duk wanda ya zo,tunda lsmail ba ya gari,a nan ma za su samu kudin siyan mata kayan kicin.zainabu tana son lsmail sosai,don haka ta yarda tana son ta ji ana yin zancan auran su.alhajin ya zo da dare kuma ya tura uwar da kanta ta dinga gyarawa zainabu kwalliya har zaure ta rako ta, tamkar ta bi ta wajen a yi hirar da ita,tunda 'yar ta ba ta labari,ta ji a jikinta cewa irin wanda ta ke so ne ya zo.alhajin yaji dadin fitowar zainabu,don yarinyar ta yi masa,ya ce mata auranta zai yi,shi sunansa alhaji lawal,ta ce,ta yarda,da zai tafi nan ya cika su da kudi masu dama,wanda suka sa mahaifiyar rawa,ta kuma yarda cewa 'yarta ta samu miji. washegari da safe lsmail ya kira mahmud ya roke shi don ALLAH ya kaima zainabu wayarsa, don yana son su gaisa yaji muryarta,mahmud ya ce,shi fa ba ya son yaje ne a raina mishi wayo.lsmail yayi ta rokon shi,da kyar ya yarda,ya ce,zai je da yamma.suna gama waya ya mike ya debi takardu don zuwa cikin gida koyar da 'yar mulki,sunan da ya fi kiran ta kenan in zai yi maganar ta da hamisu direba. [01/10 12:47 pm] Abdul: STEP (69)Ta fi minti talatin sannan ta fito,tunda ya ga hakan ya san yau akwai matsalar da ta fi ta kullum. ALKUR'ANI da ma yake karantawa tun kafin ta zo, ta kalli inda yake,ta ja tsaki ta zauna,ya kai aya sannan ya dube ta barka da shigowa fatan kina lafiya? ta zaro ido,ba ruwanka da lafiya ta,ko kai likita ne? bai ce komai ba,amma idanunsa suna kallon ta,ta ja tsaki tare da fadin aikin banza shishigi kawai.ya ce, ki na ji na ko?yau ba neman fada nike yi ba,don ALLAH ki tsaya mu yi karatun nan shine ya kawo ni garin nan,ni na roke ki kin ji?ta ce bazan yi ba,ya ce, to zan kira mahaifiyarki in fada mata gaskiyar komai, sannan ni kuma in tafi abina,na soma gajiya da zama haka.ta ce,zan so haka,na fi kowa son ka tafi don na tsani kallon fuskar ka,amma bai kamata in barka ka tafi haka nan ba,ya kamata ni ma in yi maka abinda ba zaka mance ba.kamar yanda kaine mutum na farko da ka soma cusa min bakin cikin da bazan manta da shi ba.ba a taba bata min rai ba tunda ni ke sai kai,ya yi shiru,don shi ya gaji da wannan wasan kwaikwayon,ya ce,to in na baki hakuri fa?ta ce,ka rike kar ka bani don bazan karba ba,ka barni in rama. ya ce,ba laifi,daga nan yayi banza da ita,sai kuma ya mike tare da kwasar littafansa,ta ce,na sallame ka ne?lokacin ka bai cika ba,ya ce,ba amfanin zaman,tunda ba karatun zaayi ba ya ta fi abinsa. yana zuwa dakin shi ya kira hajiya sauda da nufin ya fada mata komai,suna gaisuwa sai ta soma yi masa godiya har ya kasa fada mata,suka yi sallama, ya kwanta yana tunanin abin yi.haka suka yi ta yi har ranar lahadi,wacce ta kasance ranar da alhaji bishir zai amshi bakuncin sabon abokinsa,ministan man fetur.karfe takwas zai zo,amma tun shida an hana kowa sakat a gidan.girki an yi shi yafi kala goma,ban da nau'in kayan sha na kanti,ga busassu tun daga kan goro dabino,kayan marmari ma gasu na kala-kala.takwas zai iso gidan, don haja zuwa lokacin kowa na ta shiri.ya kira alhaji bishir ya ce,alhajin ALLAH zan zo fa da nawa iyalan ne. [01/10 12:47 pm] Abdul: STEP (70)Alhaji bishir ya ce,na yi murna sosai,ina yi maku maraba. Ya fito daga dakinsa yana kiran nafisa,ta fito cikin sauri tana cewa,sun iso ne?ya ce,aa da iyalansa zai zo,ta ce,ALLAH ya kawo su lafiya.cikin azama ta shiga dakin na'ima ta same ta tana yin kwalliya, sai ta ce,yawwa na'ima ki yi gayu sosai,da iyalansa zai zo,inda namiji kiyi kokari ki ja raayin shi,ta haka ne za ki samu shiga gurin dadinku.zai so ki fiye da MIMI,na'ima ta ce,ya fada ne?mommy nafisa ta ce,aa ba ya fada bane,kin san yana son zama kut-da-kut shi da minista,in surukanta ta shiga tsakanin su yaya kike gani?na'ima cikin murna ta ce,zan yi kokari, amma in shi kanshi ne mommy ai yayi tsufa. ALLAH ya sa yana da yara maza mommy,nafisa ta ce,ina ruwanki da tsufansa?daura shi zaki yi a wuya?kudin muke bukata, ballantana a ce kin haihu,randa duk ba shi mu sha gado,ga gata gurin dadinku,na'ima ta ce,lnsha ALLAH za ta yi hakan. MIMI tana daki tana shirin ta,ita ba gwanar shafa abubuwa rakwacan ba ce,amma man ta da hodar ta zuwa turare tsadarsu ta isa.jambaki kurum ta shafa pink ta saka riga da wando damammu bakake a sama ta dora pink din shimin kayan ta zo mata gwiwa,ta tattare gashin kanta zuwa gefe ta kama shi da pink din ribom kasa-kasa,ta fesa turaranta na yau da kullum,don ta fi son turarukan arabia,takalmin ta flat baki mai ratsin pink. ta dauki wayarta daidai lokacin da wayar ta soma ringin,ta daga dad ya ce, uwata sauko sun iso,ta ce to daddy.lokacin da ta sauko falon kasan babu kowa,sun tafi tarbo bakin, bata bisu ba,sai ta samu kujera ta kame.suka shigo da sallama,ta tashi ta nufe su,matar minista ce suka shigo tare da mommy nafisa,sannan su alhaji bishir din,sai wani saurayi sannan na'ima da wata budurwa saar MIMI,sannan kananan suka shigo tare da su ahmad.kan kujerun fakon alhaji suka zauna,sun gaisa inda suka gabatar da junansu,ko in ce alhaji akilu ya gabatar da iyalansa.ya nuna uwar,ga madam dina hajiya bilkisu,sai yaro na na farko abbas. [01/10 12:47 pm] Abdul: STEP (71)Ga shi nan ina ta fama ya yi aure yaki.ya gama karatunsa,yanzun yana aiki da central bank ne,alhaji bishir ya ce,ya kamata kam a yi aure.abba zai shekara talatin ko?alhaji akilu ya ce,talatin din ce kuwa,alhaji bishir ya ce,saan abba kenan dana na fari.shi kam yayi aure har sun yi min takwara, alhaji akilu ya ce,ka gani ko abinda ni ke buri kenan in ga 'ya'yan.alhaji bishir ya ce,ka kokarta ka ji dana? abba cikin murumushi ya ce,lnsha ALLAHU. ya nuna ta mace,waccen kuma aisha ce tana shekarar ta ta farko a jami'a ta kasar ghana,sai samira da azima da jamil duk 'yan primary ne da j.s.s. alhaji bishir ya ce,masha ALLAH,ALLAH yayi masu albarka.kai ba su da yawa ni yara na ishirin da biyu, mata na uku,alhaji akilu yayi 'yar dariya,ku manya ne, amma hakan yayi kyau, dama ka yi kokari ka cike, suka dariya,alhaji bishir ya ce,mu yi tare,kai ta biyu sai a yi rana daya.suka kalli matan wadanda suma dariyar suke har suna hada baki gurin fadin ku yi ta yi mana,ga dai yaranku nan,sun girma.bayan sun gama gabatar da iyalansu sun dan yi wasa da dariya, sai kuma mommy nafisa ta ce,ya kamata mu je dining, nan fa aka hau kan teburin cin abincin. MIMI ta kalli na'ima cikin maganar nan ta ta a hankali ta ce,ki lura tun daga kan aisha zuwa kasa ni zan ji da su daddies, mommies da brother abbas.yanda tayi maganar, iyayen suka sa dariya,haka ta yi ta zuba masu sai da kowa ya ce,yayi,ita ma na'ima ta kula da na ta gefen.bayan an kammala aka koma kan kujeru, MIMI da ba son hayaniya take yi ba,sai ta kama hannun aisha zo mu je sama na.haka yayi wa mommy nafisa dadi,har ma ta dauki wayarta ta tura ma na'ima messege,inda ta ce,ga dama nan ta samu,ki lura da abbas kuma ki ja hankalinsa.a sama,aisha sai santin falon MIMI take yi, MIMI ta kai ta ko'ina a saman ta,ta ce,gaskiya MIMI kin ji dadi,ke kam 'yar gata ce,duk nan ke daya?a ina ki ke karatu?MIMI ta ce,dubai,ai in fada maki aisha dad yana ji da ni fiye da zaton ki,duk abinda ni ke son. [01/10 12:47 pm] Abdul: STEP (72)A sama,aisha sai santin falon MIMI ta kai ta ko'ina a saman ta,ta ce, gaskiya MIMI kin ji dadi,ke kam 'yar gata ce,duk nan ke daya?a ina kike karatu? MIMI ta ce,dubai,ai in fada maki aisha dad yana ji dani fiye da zaton ki,duk abinda ni ke so yana yi min.can kasa kuwa mommy nafisa ta ja hajiya bilkisu zuwa dakinta,alhazan su ma tasu hirar suke yi,kananan kuma sun bar falon alhajin sun nufi na su,suna gaban damfareriyar talabijin din falon suna buga game, Na'ima ta koma kusa da abbas wanda ke ta latsa wayar shi ta ce bros ya kokari,ya kalle ta, alhamdulillah,ya makaranta? ta ce,ai yanzu ina gida ne ban fara zuwa makaranta ba,ina son in je wajen ni ma,amma dadinmu ya ce, ko abuja ba zan bari ba.ya ce,kila kina rawar kai ne,ta ce,aa raayinsa ne haka,sai kuma ta canza maganar da cewa in ga phone din ka bros,ya mika mata ga shi. ta yi ta shiga nan fita nan ta dinga kallon hotunan shi lokacin yana karatu a waje, ya birge ta sosai.ta ce,ka hade fa bros,ya ce,na gode,ta saka lambar wayarta ta ce.ga lamba ta nan,in maka saving din ta, ya ce,eh,ta ce,kana da me irin suna na?ya ce,aa ta saka sunan,ta yi saving din ta shi.kamar daga sama sai taji ya ce,sa min ta sister din ki,mene ne sunanta na gaskiya?ta ce,khadija,ya ce,ok sa min lambarta,da ta tashi,sai ta canza lamba daya ta mi shi saving ta ce,in kun tafi sai yaushe?ya ce,ku ya kamata ku kawo mana ziyara ai,ta ce,haka ne,za mu zo,muryar alhaji akilu bala ta katse su. Goma tayi ku tashi mu tafi,alhaji bishir ya ce,tun yanzu?to sai mun zo muma, alhaji akilu ya ce,abinda zance kenan muna jiran zuwan ku,amma da rana za ku zo mana ko?alhaji bishir ya ce,in ka samu lokaci ka sanar da ni sai muzo,ya kalli na'ima,je gurin mominku ki ce su fito, alhaji akilu ya ce,ka san mata da kus-kus.sun fito inda mommy nafisa ta cika hajiya bilkisu da kayan mata,alhaji bishir ya cika yaran da kudi,na'ima kuwa abbas tayi wa kyautar turaruka masu kamshi,ita kuma MIMI kawarta aisha ta yi ma kyautar irin kaya jikinta. [01/10 12:47 pm] Abdul: STEP (73)Da takalmi da kuma turare,sannan suka yi canjen number,alhaji bishir ne ya kira MIMI ya ce,su sauko,abbas ya kosa ya sake ganin MIMI don komai na ta yayi masa,kuma ita ce yake ganin zai zaba ta zama matarsa,tunda suka fito yake sake kallonta zuciyarsa tana kara kuranta ta.sun raka su har bakin mota katuwa jeep, direba yana ciki yana jiransu,aisha ta rungume MIMI sis sai naji ki,MIMI ta ce,yawwa sis aisha sai kin ji ni. Tunda suka koma gida, abbas ke kiran layin da na'ima ta sa mi shi na MIMI, wani ke dagawa,duk ya damu sai kai kawo yake yi a gefen nasa,ji yake yi tamkar ya nufi gidan su MIMI ya fada mata ya na sonta. a gidan alhaji bishir kuwa bayan sun yi bankwana da juna kowa ya shiga makwancinsa, dad da momi sun shiga nasu makwancin,sai take ce masa,alhaji na ga kamar na'ima da abbas sun aminta da juna,ya ajiye rigarsa da ya dauka da niyyar sawa ta bacci ya ce,haba!!ta ce,(cikin dariya) da gaske kuwa,har canjin number ta ce min sunyi.ya kamo hannunta nafisa ALLAH yasa haka ta tabbata da sai nafi kowa murna.da na'ima ta ga aure gata,ina son mu hada surukanta sosai,ta haka zan zama na gaba a cikin masu yin dillancin man fetur,buri na in zama na daya mommy nafisa ta ce,kar ka damu,zan kula maka da wannan alakar tasu,lnsha ALLAHU har a kai ga yin auran,ya rungume ta,ke kanki kyautar ki daban ce,suka sa dariya. Abbas ya samu aisha a cikin falon su,ya sami waje kusa da ita ya zauna ya ce.sis don ALLAH ba,ta ce ina jin ka,ya ce lamba za ki bani,ta kalle shi,ta wa?ya ce kawarki,ta sa dariya, wacce kenan?ya ce.ta gidan da muka kai ziyara mana,na ga kun kulle.aisha ta ce,ok,MIMI ko lallai ka samu 'yar gaye,ka ga gefenta kuwa?ta shiga ba shi labari.yana sauraronta zuciyarsa tana kara fari.ta bashi number ya koma sasan shi.sai dai abin takaici ya kira ta kusa so biyar amma ba ta daga ba. abinda bai sani ba.MIMI bata daga number din da bata sani ba,don haka tana kallon wayar tana yi tana katsewa. [01/10 12:47 pm] Abdul: STEP (74)Sake komawa ya yi hankali tashe gurin aisha yana tuhumarta cewa bata bashi lamba daidai ba.ta ce,bari in kira ta da layi na,a ringin na hudu ta daga ta ce,hello sis aisha ya ya aka yi?lafiya lau in ji ta,bros ne yayi ta kira baki daga ba,shine ya zo ya tare ni wai na bashi number ba daidai ba.ta ce ok dama shine?ayya ban sani ba tsari na shine bana daga bakuwar number, amma zan yi saving dinta yanzun nan,ta ce to zai kira ki,MIMI ta ce babu damuwa ya kira kawai. Sasan shi ya sake komawa,sanna ya kira ta,sun gaisa bai tsaya bata lokaci ba ya ce,MIMI kin tafi da dukkan tunani na,tun da na ganki naji gaba daya na birkice,ke ce matar dasu dad su ka ce in nemo, lokacin da suke min maganar aure,ke kawai nike kallo a amaryar.MIMI ta yi shiru tana jinsa,sai da ya kai aya sannan ta ce kayi hakuri da abinda zan ce yaya abbas.gaskiya ina da wanda ni ke so sosai,ban san adadin son da muke yi wa juna ba.don ALLAH kayi hakuri saboda gudun faruwar haka na bar falon don na lura da yawa satar kallon da ka ke min,amma ina me yi maka adduar samun wadda tafi ni.sannan zan baka shawara ga kanwata na'ima,bata tare da kowa, kuma tana da hankali,ya katse ta,ki bani lokaci in zo muyi maganar daga zaune. ta ce kowane lokaci ina gida,ya ce,in zo yanzun?ta ce a!haba dai mu barshi gobe.sannan sharadi kar ka zo da batun so na kazo da batun kanwata,yayi 'yar dariya,sai dai in na zo din,ta ce shikenan. Misalin shadaya lsmail ya nufi gurin karatunsa kamar kullum,ya jira sannan ta fito,haka nan ya bude kur'ani yana karantawa kamar yadda ya tsara.ya gama ya kalle ta,gaskiya ya kamata yau ki karanto in ji,ko kina rikewa tunda kin ga mun kammala shafi biyu na suratul bakara,sai ji amma a ce kullum ni zanyi karatu,ke kina danna waya don ban sa ran cewa kina ji ba.ta ce,in fahimta,ko kar in fahimta ya shafi albashinka?don haka kayi kawai ina jin ka dama aya biyar yake yi kullum,don haka ya karanto mata ko daya gama ya dago ya kale ta daidai lokacin.. [01/10 12:47 pm] Abdul: STEP (75)Wayarta ta yi ringing,ta daga tare da cewa,brother abbas,ya na'am gani nazo fa,ta ce,ok ka shiga mana,na'ima tana nan a falo ka ce ta kawo ka falon baki na ciki.ya ce, ok to,lsmail ya kalli agogo abin haushi yanzun shadaya da rabi saura minti talatin. Bako yayi sallama lsmail ne ya amsa da ya shigo,sai ya mika wa lsmail hannu.shi ma ya miko masa kenan za su gaisa MIMI ta ce,aa yaya abbas,kar ka hada hannu da shi,abbas ya dakata sannan ya kalle ta lafiya?ta nuna ma shi gurin zaman,zauna kawai,lsmail ya bude kur'anin shi ya ci gaba da karantawa a zuciya,sai dai kunnansa yana gurinsu.ta ce,dan aiki na ne,kana dan minista zaka hada hannu da talaka? ni da zai koya min karatu ma na ki ya ji karatu na don bai kai matsayin ba, sai kai ka hada hannu da shi,kodayake mu bar zancan shi,ka iso lafiya?ya ce,lafiya lau,da farko ai na zaci shine na musamman din naki,ta ce,shishshhh haba mana abbas ka cuce ni,daka hada khalil da wannan,don ALLAH ka bani hakuri don ka cuce ni.abbas ya ce,to shikenan yi hakuri,amma so ba shi da haka,kuma wannan din ban ga laifinsa ba,ta ce zan hau sama in kana irin wannan zancen,ka yi abinda ya kawo ka. Abbas ya ce,ok na san jan ajin ku ne na mata shi ya sa kika ce min kina da wani,kar ki damu da jan aji don kina da ajinkin MIMI.tun ranar da muka zo ban kara sukuni ba don ALLAH ki duba ni.ta ce,yaya abbas don ALLAH ka bar zancen nan,ni da khalil mun fi shekara daya muna tare, shi yasa tun jiya na ce kar ka zo da batun nan,ka zo in ba ka kanwata na'ima.ba laifi in ka ce mu zama abokai,mu dinga ba juna shawara,ya ce,MIMI ni dai ke ni ke so,ta sa yatsan ta a kan lebenta ta ce shhhh, don ALLAH bar zancan,ka amince da batuna, bari ka ga na'ima,tana da kyau kuma ga hankali. Kafin ya ce komai ta danna kiran layin na'ima,ba ri ka ganta da kyau,na'ima daidai lokacin tana dakin momi cikin damuwa tun zuwan abbas da ta nuna mashi falon baki kamar yadda MIMI ta umurce ta. dakin momy nafisa... [01/10 12:47 pm] Abdul: STEP (76)Momy ta ce dama na san zai zo,na'ima ta ce,ai gurin sis MIMI yazo. gaban momy ya fadi ta maimaita cewa,gurin MIMI? na'ima ta ce,suna ma falon baki,momy ta yi shiru tana tunani,can ta ce,ni wai yaya zanyi da wannan shegiyar MIMI?wayar MIMI ce ta katse su ta dubi momy,ga MIMI tana kira na,momy ta ce,daga muji,MIMI ta ce,sis na'ima ki kawo ma bros abbas abin sha ta ce,ok gani nan.ta kalli momy,wai in kai masa abin sha,ta ce maza je ki kai masa,har ta fita,ta kwalo mata kira,zo na'ima ta ciro wani turare a jerin turarukanta ta fesa mata sosai,ta ce,je ki ko babanku na fesa turaran nan yana sa shi nishadi.a falo ta ajiye dan kwalin kanta,a ranta tana fadin in gashi ne ni ma akwai. Da sallama ta shiga falon,nan ma lsmail ne ya amsa,wanda ke zaune yana jin komai,ta shiga ta aje,sannan ta sake gaida shi,MIMI ta ce,zuba masa a kofi na'ima ta zuba,sannan ta ba shi a hannu ya amsa yana ta kallonta,sai da ta tafi sannan ya ce,MIMI kuna da bambamci da yawa, kyau kuma ba irin daya bane,ina son ki don ALLAH. MIMI ta ce,in baka amince da na'ima ba to ka tafi ka nemi wata,na yi haka ne don na san iyayanmu za su yi murna.ya ce,ni da ke zasu yi murna,ta ce,to abinda ya yi ni,shi yayi na'ima,ya mike,ke da ita akwai bambamci,zan tafi amma fa ban hakura ba. Ismail dariya yayi ta yi a daki tare da tausaya ma abbas,don ya san menene so,in ya tuna zainabun shi, kila ma in ya ci wata daya sai ya je katsina ya ganta, ya sai mata waya don ya dinga jin muryarta kowane lokaci. MIMI tana cikin damuwa,sam ba za ta so zancan nan ya kai gurin dady ba,domin zai so hakan. tun bayan tafiyar abbas MIMI take sake-sake. momy ta hau sama ta sami MIMI tana ta tunani ta ce, na'ima ta ce min abbas ya zo gurinki,MIMI ta bata rai,ya zo ne ya dama min lissafi momy,wai sona yake yi.gaban momy ya fadi,ta dan zaro ido,sai kuma ta wayance,mene ne,to ki amince kawai.MIMI ta ce, gaskiya momy ina da wanda ni ke so,momy ta ce,haba da gaske?ta ce, ALLAH,sunan shi khalil.. [01/10 12:47 pm] Abdul: STEP (77)Khalil,su 'yan kaduna ne,baban shine dan takarar da aka tsayar a jihar kaduna zai yi takarar gwamna.sunan mahaifisa usman kaura,haifaffan zariya ne.momy ta ce,to shawarar da zan ba ki ki yi saurin sanar da dadinku kafin shi ya sanar da na shi mahaifin. MIMI ta rike hannun momy,don ALLAH momy ki taimake ni ki fada min yanda zan fada masa. momy ta ce,kar ki damu in ya dawo ki same shi ki fada masa,inda hali ma ki ce da yaron ya zo ya gaida shi.MIMI ta ce,ai tsoro na kar dad ya ce masa ya turo iyayansa,to shi kuma karatu yake yi,gidansu ba za a yi masa aure yanzu ba,sai ya fara aiki.momy ta ce,ba damuwa don wannan kin san dadinku bai son damuwarki,ba zai takuraki ba.MIMI ta dan ji sanyi a ranta,ta kuma yarda duk abinda take so, shi mahaifin ta ke so. Abbas ya zauna kusa da mahaifinsa alhaji akilu bala ya ce,daddy na ga irin matar da ni ke so.ya tattaro hankalinsa ga dan nasa,'yar gidan waye? abbas ya sunkuyar da kai, gidan da muka je ziyara, gidan alhaji bishir masari. alhaji akilu ya dafa kafar danshi,yaro kayi abinda nake so,ka san buri na?mu zama surukai da shi,abbas ya ce,saboda me daddy? ya ce,saboda siyasa ta abbas,duk dan siyasa yana son hulda ya mutum mai jamaa.alhaji bishir babban dan kasuwa ne yana da mutane fiye da zato ka, lokacin da ya bukaci hulda da ni sai da na bincika,ka taimaka ka samo min soyayyar 'yarsa mu zama surukai.yana tare da mutanan da in suka goya min baya zai yi wuya ban dare kujerar shuganbancin kasar nan ba.abbas ya ce, na yi mata magana ta ce tana da wanda take so, amma ina zaton jan aji ne, don ALLAH kayi wa mahaifin ta magana. babbar na ke so,alhaji akilu ya ce,kar ka damu yanzu zan kira shi. Sun gaisa da alhaji bishir ya ce,ka samu hutu kenan mu kawo ziyaran,alhaji akilu ya ce,danka ne nan ya fiti ne ni wai tun da mun ce yayi aure,shi 'yar uwarsa yake so MIMI,tunda muka kawo ziyarar nan ya kasa sukuni.alhaji bishir cikin matukar murna ya ce,masha ALLAH....... [01/10 12:47 pm] Abdul: (78) ka fada masa kar ya damu, mimi ta zama ta shi don na bashi. nan Alh akilu ya hau godiya cikin murna, Abbas cikin murna ya rungume mahaifin sa. Alh bashir ya kosa ya iso gida don yayi Albishir ga mimi da momi nafisa, lallai burin shi zai cika. Alh lawal ya kalle direban shi, yarin yar nan ba zata bamu hadin kai ba, dan haka kayi min sallama da maman ta. haka kuwa ya rangada sallama, kaninta ya leko ya ce, yauwa ka ce Alh yana sallama da maman ku, yaron yace inannar mu...? ya ce, eh, ka ce inji Alh lawal. ba da jimawa ba, innar su zainabu ta fito, tamkar marokiya, haka take tayiwa Alh barka da zuwan ka ka iso lafiya, sannu sannu. ya fito ta durkusa bari a yi shin fida a zaure, ta mike ta koma cikin gida da gudu. daga gani Alh wanan yar raka yarima ce a sha kida, suka yi dariya tamkar ba direba da uban gida ba. to direba za a kirashi ko kawali, tunda shi ne me kawo ma Alh mata. suna zaune a kan tabarma a zaure, Alh ya ce, inna na zone akan maganar aure, zainabu taki bani hadinkai in turo manya ns, sai fada min take tana da wanda zata aura. inna ta cefke zancen da cewa, karya ne bata da shi, ka turo kawai, ya ce, to na gode. ya ajeye daurin yan dari biyar-biyar, inna ga wanan kyaci goro, kuma zan turo manya na gobe, bana son bikin ya wuce sati uku. ta ce, ai kuma lokacin bamu shirya ba, Alh kasan sai min nemi na gado. ya ce, ina da ko mai inna, mata na ce ina so, kuma ita za a bani ba tarkacen kaya ba. ta ce, to shike nan, in gobe kake so a daura bare nan da sati uku. tirkashi!!! ku biyuni a kashi na biyu don jin yadda zata kaya. taku halima k/mashi. ina sauraran ku,08081165107 dan shawara ko kuma korafi na gode....""