[11/7, 11:23 AM] maryamsuleiman48@gmail.co: MAIMOON BY Maman Maama 1 Bismillahir Rahmanir Rahim Episode One : The Beginning of the Beginning Shin ta ina zan fara ne, in fara ta haduwa ta da Ibrahim ne ko kuma ta haduwa ta da Sultan? Ko kuma in fara da baku tarihi na ni kaina? Sunana Maimuna Muhammad Dikko. An haifeni kuma na tashi garin Abuja, Nigeria. Mahaifina Alhaji Muhammad Dikko bafulatanin garin 'yalleman ne dake jahar Jigawa. Garin 'yalleman garin Fulani ne kyawawan gaske wadanda kuma Allah yayi musu arziki sosai har suka watsu a duk fadin Nigeria, musamman garin Lagos da port hercourt tunda yawancin arzikin su na chanjin kudi ne. Mahaifina bai bi family tradition ba saboda shi ya kasance dan boko ne. Yayi primary school dinsa a nan garin 'yalleman tamkar sauran 'yan uwansa amma saboda hazakarsa sai head master dinsu ya bawa mahaifinsa Alh Lawan Dikko shawarar in dai da hali gwara a tura shi kasar waje Dan ya fi samun karatu mai kyau. Da yake kakan mu mai hali ne tun a wancan lokacin, sai ya tattara makuden kudade ya dauko yaro ya tafi dashi Lagos, da taimakon 'yan uwansu da suke can aka samar wa Muhammad biza zuwa England inda a can ne aka samar masa admission a makarantar Gifted International College inda ya fara karatunsa na secondary school.Duk bayan shekara ake basu hutun session, Muhammad yakan zo Nigeria ya ga iyayensa da 'yanuwansa ya koma, shi kuma Alh Lawan duk sanda Muhammad zai koma sai ya hada kudade masu yawa ya bashi saboda harkar registration da kuma bukatunsa na yau da kullum. Mahaifiyar Muhammad ma Hajiya Adama ba'a barta a baya ba domin tana iya kacin kokarinta dan har shanun ta na gado take sawa a sayar mata a boye bada sanin mai gidanta ba ta tattara kudi ta bawa Muhammad. Kwanci tashi har Allah yasa ya gama sec sch dinsa kuma a take ya samu scholarship na karatu a Oxford University inda ya karanci business administration saboda burinsa na ganin ya gama karatu ya dawo gida yana taimakawa mahaifinsa a harkar kasuwancinsa. Daga lokacin ne ya gayawa mahaifansa cewa babu zancen biyan kudin makaranta kuma tunda yanzu he is on scholarship, amma duk da haka Alh Lawan yakan aika masa da kudade dan ya biya bukatunsa. A lokacin da ya gama first degree dinsa ne ya dawo gida da niyyar cika burinsa na karbar garkar business din mahaifinsa amma hakan bai samu ba saboda rigimar data barke a familyn su inda kishiyar mamansa wacce ake kira da Hajja tayi tsalle ta dire tace sam ba zata sabu ba bindiga a ruwa. A cewar ta duk wahalar da aka sha da makudan kudaden da aka kashe akan karatunsa sannan ya dawo kuma yace zai karbi dukiyar gida? Ta kara da cewa" inace cewa a kayi shi mai kwakwalwa ne ba zai yi kasuwanci ba karatu zai yi, sai da aka gama kashe kudi a karatun nasa sannan kuma zai zo yace zai yi kasuwancin to ba'a isa ba wallahi, suma sauran yaran gidan ai 'ya'yane". Da wannan Muhammad ya tattara ya koma England ya dora karatun masters dinsa, yana gamawa ya wuce pH D. Bayan ya gama ne kuma ya karbi aikin lecturing a makarantar. Shekarunsa biyar yana lecturing a Oxford aka bashi award na professorship. A shekarar ne kuma mahaifansa suka dage akan lallai ya dawo Nigeria yayi settling down kaman sauran 'yan uwansa. Saboda gogewarsa a harkar ilimin kasuwanci da mu'amala da kasashen waje yasa yana dawowa Nigeria government din wancan lokacin ta bashi mukamin ambassador. Kasar da aka fara turashi itace makociyar mu, Niger. Wannan kenan; Mahaifiyata Hajiya Fatima wadda ake kira da Bintou, buzuwa ce ta asali, mutuniyar kasar Niger ce. Mahaifinta ya rasu run tana yarinya kuma dama it's kadai Allah ya bawa mahaifanta. Mahaifiyarta wacce sunanta aka saka min (Maimoon) ita ce ke kula da ita da karatunta har ta kammala sec sch dinta. Anan suka fara chuku chukun turo ta Nigeria dan tayi jamia anan amma saboda rashin hanya da rashin abun hannu sai abun ya gagara. A nan ne Allah ya hada su da mahaifina lokacin yana matsayin ambassador na Nigeria a Niger. Farko tausayinta ya fara ji da sha'awar yadda take da son karatu, daga baya kuma sai soyayya ta fara shiga tsakanin su duk ya cewa ya girme mata sosai. Dama kuma a lokacin Inna (haj. Adama) ta takura masa akan maganar aure dan haka bai samu matsala ba akayi aure ya taho da ita Nigeria ya ajiye ta a gidanmu dake Abuja unguwar Aso drive inda har yau anan muke da zama. [11/7, 11:24 AM] maryamsuleiman48@gmail.co: MAIMOON BY Maman Maama 2 Episode Two: Meet my Family Gidan mu katon gida ne saboda sanda daddy ya gina shi yayi niyyar dauko iyayensa ya dawo dasu Abuja amma Baffa (Alh Lawan) yace sam shi bazai bar 'yalleman ba, wannan ya saka daddy ya tsantsara musu gida a can wanda duk da kudin da 'yan garin suke ji dashi sai da gidan ya zama abin kallo. Sannan ya kawo ma'aikata ya zuba musu tundaga kan masu shara har zuwa kuku. Saboda yace lokaci yayi suma da zasu huta, kuma duk abinda yayi inna sai yayi wa Hajja. Ai kuwa suna hutawar dan babu abinda suke yi illa su ci su koshi su kwanta, kuma duk shekara sai sunje aikin hajji, sannan al'adar daddy ce duk sanda aka turashi wata kasa a matsayin ambassador sai ya debe mu munje munyi wata daya har su Baffa da Inna saboda yana so mu samu wayewa irin ta zamani amma yace ba zamu rayu a can ba saboda tarbiyya. Mu biyar Allah ya bawa mahaifanmu, uku maza; ya Lawan, ya Habeeb sai Faruk, biyu mata; Hafsat da Ni. Ya Lawan ne babba sai ya Habeeb, sai Hafsat sannan Ni sai dan autan mu Faruk. Da yake mommy kwanika tayi sai ya zama babu tazara sosai a tsakanin mu, dukkan mu a shekaru bakwai ta haifemu sai kuma haihuwar ta tsaya mata, daddy kuma yace mun ishe shi fatan shi Allah yayi mana albarka. Zo gidan mu kaga kyau, saboda mix ne aka samu na Fulani da Buzaye, dan haka in ka ganmu sai ka kasa tantance wanne kabila ne mu, tundaga ma zan mu har matan mu haka muke dan sauda yawa inna takan aiko mana da rubutu tace maganin baki. Ni maimunatu wadda ake kira da maimoon kamar yadda ake kiran wacce aka saka min sunanta wato maternal grandmother dina, nice ta hudu a gidan mu, nice kuma auta a mata. Fara ce ni tas, fatata mai sheki silkin Fulani da Buzaye, ina da tsaho amma ba sosai ba, fuskata oval shape ce mai dauke da dara-daran idanu kwantattu masu yalwataccen eye lashes, girata kamar an zana min ita. Hancina dai-dai misali, lips dina sirara masu kalar pink mai haske, gashin kaina mai cikane kuma mai tsaho, Wanda yazo har kan kafadu na. Ina da dimples a both chicks dina masu lotsawa koda magana nakeyi ballantana kuma ace nayi murmushi. A gidan mu muna magana da daddy n mu da fulfulde, mommy da buzanci, sannan a tsakanin mu muna magana da English, a school ma English dinne dan haka sai kuma tashi babu Hausa sosai sai dai muji a gurin neighbours ko kuma in munyi 'yan aiki hausawa. Duk a cikin 'yan'uwana na fisu surutu dan ya Walid parrot yake ce min tun ina yarinya, da yake shi ba mai son magana bane, kullum sai yayi ta korata yana cemin parrot, ni kuwa duk abinda na gani sai na tambaya, in ba'a bani amsa bama in yi ta tambayar har sai an bani amsa sai in sake tambayar wani abun daban. Tun sanda na shiga kindergarten daddy ya fahimci duk cikin 'ya'yansa nafi daukan kwakwalwarsa duk da suma sauran ba baya bane wajen karatu. Tun daga lokacin sai yake biyemin inyi tayi tambayoyi yana amsamin har ya zamanto mun shaku sosai fiye da yadda muka shaku da mommy. Mommy n mu wacce a yanzu lawyer ce takance ko ita zan gada ne in zama lawyer saboda yawan tambayoyi na. Ina shiga basic school na zama tauraruwa, ga kyau, ga kokari, ga surutu mai shiga rai. Sai ya zama kowa yana ji dani a school din. Bani da fada sam- sam, kuma ina da tsoro, ko juniors dina nayi wa wani abu by mistake sai in basu hakuri saboda ina bala'in lallaba jikina. A basic school na samu nickname din MOON saboda shape din fuskata da bright dimpled smile dina, ga kuma yanayin sunana MAIMOON. Wasa wasa sunana har ya fara bata in ba'a register din makaranta ba. Moon kowa yake kira na dashi. Kasancewar mommy n mu ita kadai ce a gurin mahaifiyarta (daada) yasa ta dauko ta ta dawo da ita Nigeria cikin gidan mu, akayi mata part dinta a kusa da part din su inna, mu kuma sai ya zamanto bamu da gurin hira sai gurinta tunda Allah bai bata haihuwa da yawa ba sai kuma ya dora mata son mu. Kullum tana cikin kula damu, kunshi da kitso a kan mu ni da Hafsat baya tsufa sai an sake wani, duk da muna da gashi amma kullum kanmu a kitse yake ganin sha'awa. All comments and suggestions are welcome. It is just beginning. [11/7, 11:25 AM] maryamsuleiman48@gmail.co: MAIMOON BY Maman Maama 3 Episode Three: Loved by All Shekara daya Hafsat ta bani don haka aji daya ta fini da shi amma ka ganmu sa ka dauka ta bani shekaru da masu yawa saboda ni Allah yayi min karamin jiki, babu tsaho babu kiba sai dan karan surutu, ita kuma Hafsat bata da magana sosai amma akwai sa ido da bin kwakwkwafi, don haka duk abinda nayi tana gani na kuma muna zuwa gida zata gayawa mommy ko daada, inda ita kuma mommy zata hauni da fada, da yake mommy n mu tana da zafi, wannan shi yake kawo yawan sabani a tsakani na da Hafsat. Babban aboki na shine ya Habeeb wanda surutun mu da son karatun mu yazo daya dashi, kullum in mun dawo daga school ina dakinsa, idan an bamu homework shi yake koyamin, shi yake kawomin novels wani lokacin ma in kwanta a cinyarsa yana karanta min. Faruk kuwa dan auta kullum yana gurin daada dan a can ma dakinsa yake in ka ganshi a part din mu to daddy ne yazo gari. I na basic 4 Hafsat ta na 5 muka zana common entrance a tare kuma duk mukaci. Babu yadda mommy ba tayi ba akan daddy ya fita damu waje muyi karatu yaki, yace tarbiya tana da wahala a kasashen waje ko da kuwa kasashen larabawa ne, musamman tarbiyyar 'ya'ya mata. Yayi believing cewa makarantun kasarmu a good enough. Ba tare da bata lokaci ba aka sakamu a secondary school tare da Hafsat, wannan ba karamin bata ma Hafsat rai yayi ba dan ranar har kuka tayi su daddy na yi mata dariya wai zatayi set daya da kanwarta. Ni kuwa sai na bata hakuri na yi mata alkhawarin idan anzo promotional exam zan ki yin kokari yadda za'ayi mini repeating ita kuma ta wuce. Mommy ba karamin takaicin tafiyar mu tayi ba musamman ma da yake boarding school ce, ana gone zamu tafi na ganta a kitchen tana kuka tana soya mana miyar tankwa, anan na tsareta da tambayoyi taki kulani balle ta bani amsa sai daga bata ta jawoni ta rungume tana ci gaba da kukan ta. Ranar tafiyar mu kuwa mommy cewa tayi ba zata rakamu ba amma da muna zo tafiya da kyar daddy da daada suka banbare mu daga jikinta dan cewa tayi mun fasa karatun, Daddy kuwa sai dariya yake yi mata, ni kuwa zuciya ta fes ina ta murna abinda. A lokacin shekarata goma amma in ka ganni zakayi tunanin banfi shekara bakwai ba. Ana kaimu makaranta akayi admitting din mu, Daddy ya roki principal din mu cewa ta bamu daki daya ni da Hafsat saboda yana son Hafsat ta rinka kula dani. Haka kuwa akayi, aka bamu daki daya, gado daya, ni ina sama ita tana kasa, class din mu ma daya, seat dina yana gaban nata. Amma muna zuwa class Hafsat ta chanja seat ta koma can baya wai dan kada a ganmu a tare a gane ni kanwar tace.Amman duk da haka duk teacher din da ya shigo in ya ganni a gaba in yaje bays kuma yaga Hafsat sai ya tambaye ta "is she your sister" ya nuno ni, ita kuwa Hafsat sai bakin ciki ya kamata. Daga baya wai ta tsiri saka nikab tana rufe fuskarta dan kar aga kamannin mu. A makarantar mu muna da masu yi mana komai tun daga kan shara, wanki, guga, wankin toilet da sauran su. Mu dai bamu kawai shine muyi karatu. Ai kuwa Moon an samu abinyi, nan na zage na kama karatu baji ba gani, kullum ina library sai dai in fito inyi sallah in ci abinci in koma. Da daddare kuma bana karatu sai bacci, saboda ni din gwanar bacci ce, tun inayin sallahr isha'i zan kwanta har sai assuba zan tashi inyi sallah. Daga nan sai mu tafi islamiyya wacce mukeyi daga assuba zuwa 7. Sannan muzo muyi wanka muyi breakfast a dinning hall sai mu wuce class sai 10:30 mu fito break a kawo mana snacks da drinks, wani lokacin kuma farfesu ba kifi ko naman rago da bread mu ci mu koma class. Sai 1:30 muke tashi daga class mu je mosque muyi sallah sai mu shuga dinning hall muyi lunch sannan mu wuce hostel. Daga nan sai inyi wanna in saka evening wears dina in koma class area in shiga library bana fitowa sai 6:00 sannan zan koma hostel in yi magrib, daga nan zan saka Hafsat a gaba da surutu tare da sauran 'yan dakinmu. Sau da yawa inna dameta sai ta saka ear piece a kunnen ta ta rabu dani, amma haka bazai hana ni yin magana taba. Ban damu ko tana jina ko bata jina ba. Hafsat duk ta rame saboda ita 'Yar hutu ce gaskiya. Kuma da gaske tana missing gida, kullum bata con abinci sai race babu dadi, ni kuwa sai in hada da nata da nawa in cinye babu abinda ya dame ni, as long as akwai books a library to bani da matsala. Duk karshen wata mommy da daddy sai sunzo mana, in ya na gari, ranar visiting day su kawo mana kayan sosai drinks, chocolates, biscuits amma banda kayan abinci kuma banda kudi, haka rule din makarantar yake. Mommy tana damuwa idan taga yadda Hafsat ta rame, in ta tambayeta dalili sai ta saka mata kuka tace ita gida zata tafi, ni kuwa sai inyi ta kallon ta ina mamakin wai ita menene matsalar ta, saboda ni dadi make ji tamkar an saka ni a aljanna. Daddy ya lura da yadda nake jin dadin school kuma ya bani kwarin gwuiwa tare da bani study tips yadda zan fi gane karatu sosai. Sai ya zama na da teacher ya fara mana topic inna shiga library sai na san almost everything da topic din ya kunsa, in na shiga aji kuwa na fara zabgawa teacher tambayoyi har sai yace min ya isa haka. Teachers din mu are very qualified dan haka bana samun matsala dasu, suna encouraging dina most of the times kuma suna jin dadin koyar dani. Ban dade a school din ba na yi suna, kowa ya san Moon, daga staff har students kuma da yawan su suna sona saboda duk wanda na gani sai na yi masa magana kuma duk 'yan class din mu kawayena ne banda Hafsat. A class din mu wadda bata iya wani homework ba guri na suke zuwa in koya musu, sam bani da kyashi kuma bani da rowa, wannan shi ya karomin farin jini. Sai da mukayi hutun first term sannan nasan cewa na yi missing gida, ina shiga gidan da gudu naje na rungume mommy ina hawaye, ina ganin yaya Habeeb na saki mommy na tafi gurinsa da gudu, shima da saurinsa ya tare ni tare da rungume ni a jikinsa kamar zayyi kukan shima. Dama ya Walid shine ya dauko mu. A cikin satin da muka zo gida mommy ta shirya mana tafiya Russia gurin daddy, lokacin yana can, daada kadai muka bari a gidan da masu aiki. Munji dadin holiday n sosai, duk da sanyin kasar amma munyi enjoying kanmu tare da family n mu. Hafsat ta ware dan har 'Yar kiba tayi abinta. Bayan hutun mu ya kare ne akasha drama, dan ba Hafsat kadai ba ni kaina cewa na yi bazan koma ba sai dai a mayar damu day school. Mommy kuwa ta goya mana baya. A dole Daddy ya dauko hutu ya taho Nigeria tare damu, sai da ya kai mu har school. Kamar yadda kowa yayi tsammani ni ce na dauki first position, Hafsat kuma second. Daddy yayi murna sosai ya saka mana albarka sannan ya kara karfafa mana guiwa akan karatun mu. A haka muna rabu dashi yana muna hawaye shi kuma yana mana blowing kisses. Thank u all for following MAIMOON. I hope u enjoyed this. Next episode coming up tomorrow insha Allah. [11/7, 11:25 AM] maryamsuleiman48@gmail.co: MAIMOON BY Maman Maama 4 Episode Four: Moon's Sister Kwanci tashi har muka gama J.S 1. Sanda za muyi sessional examination ban manta da alkawarin da nayiwa Hafsat ba, dan haka da akazo exams sai inta amsa questions wrongly, wata kuma sai inyi jagwalgwalo yadda ba zai karantu ba, wata question din ma sai in barta blank inyi submitting. Na daina zuwa library sam -sam sai dai in kwanta inyi ta baccina. Rannan ina bacci da yamma Hafsat ta dawo daga karatu, ta daka min duka a cinya na tashi a zumbur a tsorace, ta hade rai sosai ta kalleni tace " what is wrong with u?" Na tsura mata ina mamakin nuna caring dinta. Ta taba jikina kamar mai testing temperature dina race "are u sick?" Na girgiza mata kai. "U are behaving strangely this past few days, what is wrong with u? Ta sake tambaya ta tana me tsareni da manyan idanunta, na hadiye yawun tsoro nace mata " am OK, am just too sleepy these days" race "but u know we have exams tomorrow morning right?" Nave mata "I have already read enough before the exams sister, don't worry, I will be OK" na yi murmushin tsokana na kuma ce mata " when did u start caring? This is so unlike u? Tayi murmushi itama tare da bude dan karamin bed side fridge dinmu, ta dauko lemo ta zauna a gefen gadon ta sannan ta kalleni tana yamutsa fuska tace " gobe ma rana ce and besides, I just asked to know what to tell dad in case something happened. U can do as u wish for all I care" Daga haka ta bude drink dinta ta fara sha. Babu wanda yasan me make aikatawa a exams hall ba, har sai da mukayi hutu, muna 'yalleman principal dinmu ta kira dad a waya ta gaya masa cewa something is wrong, malamai sun kawo mata complaint a kaina cewa duk na fadi papers dina kuma daga gani ansan intentionally nayi. Muna zaune a dakin inna, ina kwance a cinyar inna ina zuba mata shagaba ita kuma Hafsat tana kan kujera tana karatun wani novel, sai ga daddy ya shigo. Daga ganinsa nasan cewa something is wrong, nan take cikina ya bada kululu saboda nasan abinda na aikata aschool. Ya zauna a nutse ya gaida inna sannan mu kuma muka gaishe shi duka. Direct ya juyo yana kallona da serious voice yace min" Maimoon mai yasa kika kayar da kanki a exams? " nan na fara inda inda, nace "am..I ..am sorry daddy, dan Allah kar ka dakeni wallahi bazan karaba?" Hafsat ta ajiye littafin hannunta tana kallon daddy cike da mamaki. Inna ta jawoni jikin ta tana bubbuga bayana a hankali tana tambayar daddy me ya faru cikin harshen fulatanci. Inda shi kuma ya kwashe duk yadda sukayi da principal din mu ya gaya mata, ya kara da cewa " ni ba dukanta zanyi ba. I just want to know why tayi hakan cos principal dinsu tana suggesting a mayar da ita school ta sake re-writing duk papers dinta. Cikin muryar lallami inna ta kalleni tace" memu? Me yasa kika aikata hakan? Ke meson karatu kuma kikayi haka?" Na juya na kalli Hafsat ina hawaye, ita kuma ta harare ni tare da cewa " karki kalleni, I did my best inga kinyi karatu kika cemin u have read enough before exams" ta kalli daddy tace masa " dad kullum bacci take yi bata karatu, innayi mata magana tayi min rashin kunya, God is my witness, I tried my best" tana gama fadin haka ta koma tayi kwanciyar ta. Nan na lura kowa ni take kallo ana jiran amsata. Ni abinda ya bani mamaki shine yadda suka manta da alkawarin da nayiwa Hafsat farkon sakamu a makaranta. Daddy yaga bani da niyyar magana sai ya fara lalllabani da cewa " I know u Moon, nasan koda baki yi karatu ba zaki iya cin exams dinki, and your principal said what u did looks intentional. I just want to know why " "I did it for Hafsat" nace a hankali, " I want her to get ahead of me, I promised her zanyi repeating js1, I was just keeping my promise " shiru dakin yayi kowa yana saurarena, cikin kuka naci gaba da cewa" Hafsat ba ta sona, bata son kasancewarmu a aji daya, she is always sad and lonely saboda duk ajinmu kawayena ne ita kuma bata son ta zama friend dina, I just want her to be happy ". A lokacin su mommy suka shigo falon ita da yaya Walid da Faruk, kallo ta bimu dashi daya bayan daya sannan ta zauna tana tambayar daddy menene yake faruwa, shiru yayi bai amsa mata ba sai inna ce ta fada mata brief abinda ya faru. A take mommy ta day zafi, daga ni har Hafsat din ta hada ta wanke mu tas. Dama tasan halin Hafsat amma bata dauka har a school bata kulani ba. "She is your only sister, me yasa ba zaki so ta ba? Me yayi miki a rayuwa?" Ta juyo kaina " and you little mouse, ta yaya zakiyi ki yi asarar shekara guda ta rayuwar ki just saboda kina so ki raba class da 'Yar uwarki, why didn't you tell me or your father about what is happening so that we can do something about it, we can put u in separate schools or something. Mommy fada take yi kamar zata ari baki har sai da daddy ya koma shine mai bata hakuri, ita mommy takaicinta shine wai ace "ya'yanta mata su biyu kadai da Allah ya bata kuma ace wai basa jituwa. If we didn't look after each other, who will look after us? Sai da kowa yayi shiru sannan daddy ya fara magana: " tun farko dama nasan basa shiri? Kuma me Hafsat kece fitinanniya. Wannan shine dalilin da yasa na kaiku boarding kuma bace a sakaku a class daya daki daya. Nayi tunanin in sun zauna tare a inda basu da kowa zasu hada kansu, banyi tunanin hakan da nayi zai kara wa Hafsat jin zafin Moon ba. Kuma Ku sani wannan ba zai saka in raba muku school ba. Yanzu abinda za'ayi shine, me Hafsat Ina so ki fada min menene matsalarki da moon?" Da kamar ba zata yi magana ba sai kuma ta dago kanta ta share hawayenta fara magana a hankali " daddy ni bansan me nayi wa mutane ba, kowa yafi son moon, hatta Ku kai da mommy, daada, inna, baffa, yaya habeeb har faruk kowa moon yake so, komai aka tashi yi moon za'ace kuma bayan nice babba. Daddy ko waya kayo sai kace a baka moon kafin kace a baka ni even though I am the eldest" hawaye ne yake zuba a fuskar ta sosai " a school, teachers dinmu kowa itace tashi haka friends, at school fa ana referring to me as Moon's Sister as if am her shadow or some supporting actress. I am tired of all this dad, I want to get away from her, i want to start shining on my own, not shining in her light. I never know what she plan, I didn't even think she can do something like this for me. I didn't asked her to do it and now u are already blaming me for it. Kuka take yi sodai yanzu, ni kuwa sai na tashi naje na rungume ta muna kukan tare ina kuma rarrashinta. Saboda ni bana so inga mutum tana kuma ballanta ne Hafsat. Murmushi Daddy yayi yace" duk naji complaints dinki Hafsat, kuma inaso ki sani, daga ni har mom dinku baku da banbanci ke da moon a gurinmu. Abinda baki fahimta ba shine halinku ba daya bane ke da moon, moon ta Fiji son mutane, ke kina da saurin fishi, kullum kina daki to waye zai biki daki ya kulaki. For example, yanzu tunda muka zo garin nan baki fita ba, inajin mom dinku tana yi miki fada dazu, duk kawunnanki da gwaggwanninki babu wanda kika je kika gaisar. Amma moon duk taje, wasu ma twice taje musu. So tell me, why won't they ask of moon first than u? Duk sanda bans kasar nan Moon kullum sai ta kirani a phone din mom dinku amma ke sai in na nemeki. In kina so mutane su so ki to kema dole ne ki so mutane" nan dai daddy ya yi mana fada sosai. Ni kuma daddy yace min as punishment for what I did, bazan sake exams dina ba, tunda yasan in aka hada first, second and third term scores dina aka day average to bazan yi repeating ba. Inna ma yayi mana fada sosai akan zumunci da kaunar juna kuma da alama fadan ya shige mu Dan tun kafin muyi resuming school na fara ganin chanji daga Hafsat. Watch out for the next episode tomorrow insha Allah. Thanks [11/7, 11:26 AM] maryamsuleiman48@gmail.co: MAIMOON BY Maman Maama 5 Episode five: The Strangers Bayan shekara uku Haka rayuwa ta cigaba da kasance mana cikin jindadi da gata. Daddy yana ta samun ci gaba, yana ci gaba da harkar ambassadorship dinsa kuma yana visiting lecturer a Oxford. Ya Walid ya kammala sec sch dinsa inda Daddy ya tura shi Oxford yake karatun degree dinsa a fannin engineering. Ya Habeeb yana ss3, Hafsat dani kuma muna ss2. Yaune second day of resumption kuma kamar yadda al'adar school din take, yaune ake gabatar da speech and prize giving. Mommy, ya Habeeb, daada da Faruk duk sunzo mana, suna zaune a gurinsu na musamman a side din parents. Ni da Hafsat da babbar kawata Amira munyi kwalliyar mu dai dai misali, muka fito gurin taron. Abinda ya bamu mamaki shine ganin wadansu mutane su biyar da kayan NYSC a jikinsu a zaune a bakin hall din taron. Tsayawa nayi ina kallonsu da mamaki saboda tunda muke a school din ba'a taba daukan coppers sunyi service anan ba, ko teachers din ma ba kowa ake turowa ba, sai very qualified teachers wadanda suka san me sukeyi. A hankali na furta " this doesn't look good " amma ga mamaki na sai naga duk sun juyo suna kallon mu alamar sunji abinda na fada. Kunya ce ta kamani, yayinda Hafsat ta tabe baki tace" I guess there is a first time for everything " tana fadin haka tayi gaba tare da fizgar hannuna, babu shiri ni da Amira muka bita a baya. A yanzu kam Hafsat zan iya cewa ta zama budurwa, dan inka ganta ba zaka ce she is just fifteen years ba, ni kuma lokacin ina fourteen amma still bani da girman jiki sai tsaho shima ba sosai ba. Hafsat kuwa masha Allah, dan koni da nake mace wani lokacin tsayawa nakeyi inyi ta kallonta. Fatarta bata kai tawa haske ba amma fa a murje take tana daukan ido, ga laushi. Hancinta yafi nawa tsaho kamar yadda fuskarta ma tafi tawa tsawo. Idanuwanta dara dara farare tas, bakinta mai dan fadi wanda yake dauke da full lips shi kansa abin kallo ne. Kirjinta a chike yake taf haka hips dinta wanda yasa dole mommy ta dinka mata dogayen hijabs saboda in tana tafiya gaba daya jikin ta rawa yake yi. Hafsat mai class ce sosai, ba kowa take yiwa magana ba ballantana kaga dariyarta, amma in tayi dariya wani one sided dimple ne da ita ga kuma jerarrun hakora farare tas abin sha'awa. Ni kuwa mostly English wears nake Takawa saboda nafi feeling comfortable a cikin su. Kuma babu mai yi min magana saboda bani da komai a jiki na sai kyan fuska, wannan kuwa mutane da yawa sukance nafi Hafsat amma ni kam ban yarda ba, a ganina yawan murmushi na ne yasa ake ganin kyau na. Saboda shi murmushi ado ne musamman a gurin mace. Muna shiga hall din gurin su mommy muka je muka gaishesu sannan muka je muka gaida Maman Amira muka tafi seats dinmu muka zazzauna, saboda an kusa fara taron. Kamar yadda aka saba, bayan bude taro da addu'ah sai aka fara gabatar da jawabai. Hafsat ta dauko novel dinta ta dora akan chinyarta ta fara karantawa ni kuma nayi tagumi da hannu bibbiyu ina sauraren speeches din daki daki. Sai da aka gama sannan aka kirawo passing head girl ta gabatar da farewell speech on behalf of the graduands. Lokacin har kuka nayi saboda tunanin shi kenan bazan sake ganin suba. Hafsat kuwa bama tasan me akeyi ba, sai da taji ina sheshahekar kuka sannan ta dago kanta ta kalleni ta kalli stage sai kuma tayi tsaki ta cigaba da karatun ta. Sai da aka fara rabon gifts sannan ta dago kanta ta rufe littafin da take karantawa ta mayar da hankalinta kan stage. A kayi ta kiran mutane ana basu gifts sannan aka zo kan set din mu. Kamar duk shekara, ni aka bawa overall san nan Hafsat second. Sai da aka gama rabon gifts sannan senior master ya hau kan stage ya fara announcement " I know all of u notice some strangers wearing strange clothes here" akayi dariya gaba daya, yaci gaba da cewa" they are NYSC members, they are sent here because the are the best in their various fields. The NYSC board wants this school to start participating in the scheme, that is why they sent this coppers to work with us. I hope you students will give them your maximum cooperation " daga nan sai ya fara kiran su daya bayan daya suna gabatar da kansu tare da fadin subjects din da zasu ke dauka da kuma classes din da zasu dauka. Tunda suka fara naji gabana yana faduwa, haka kawai naji jikina yana bani cewa something not so good is going to happen. Ina cikin haka naji wani daga cikinsu yace" my name is Ibrahim Adeniran Oluwaseun, from Ibadan. I will be taking SS2 mathematics and geography. Innalillahi wa inna ilaihir rajiun shine abinda nayi ta maimaitawa a zuciyata. Ji nayi tamkar an juya min dukkan plans dina na rayuwa ta. Mathematics is my best subject, maths teacher din mu is my best teacher, yaya za'ayi a chanja min teacher a hada ni da inexperienced copper? Ji nayi tamkar inbi su mommy mu koma gida saboda ji nayi gaba daya makarantar ta fita daga kaina. Ban kuma fahimtar me ake ciki ba saiji nayi ana hayaniya alamar an tashi daga taron. Cikin sanyin jiki na dauki gifts dina na tafi gurin mommy na kai mata, haka ma Hafsat. Mommy tana gani na tasan something is wrong, tana tambaya ta kuwa na fara yi mata bayani. Mommy akwai daukan zafi dan haka nan da nan ta jamu sai office din senior master ta fara yi masa bayani akan cewa tun da muna senior class bai kamata a dauki subject as important as mathematics a bawa copper ba, kamata yayi ace an bar coppers a junior classes. Murmushi yayi tare da cewa " na fahimci complaints dinki Ma, kuma insha Allah in ya fara daukan su in har sunga akwai problem, ina encouraging dinsu su zo su yi complaining. But first they need to give him a chance. We will all need a chance one day in our lives, one way or another". Da haka muka fito daga office din, mommy tana encouraging din mu akan as soon as muka ga bama gane teaching dinsa mu zo muyi complain. In ba'a dau mataki ba in tazo mana visiting mu gaya mata, in yaso sai tayi wa daddy magana yazo da kansa yayi solving issue din. Watch out for episode six tomorrow. It has began. Love you all [11/7, 11:26 AM] maryamsuleiman48@gmail.co: MAIMOON BY Maman Maama 6 Episode six: The Challenge Nidai har ga Allah wannan hukuncin baiyi min dadi ba, saboda haka kawai naji raina baya son copper dinnan, he is too young to teach us a ganina. Hafsat kuwa sai na lura babu abinda ya dame ta. Da nayi mata magana sai cewa tayi "laa ni ban wani damu bafa, musamman akan geography, wancan teacher din ya fiya bayar da note, kin san ni kuma bana son note" (Yar Hutu). Unlucky for me, washe gari muna da geography. Tun safe naji raina ya baci dan ma bashine first period ba,sai munyi biology sannan zamuyi shi. Tom teacher din biology yana gama yi mana sai ya bamu assignment, yana fita sai na dauko assignment dina na fara sai naji hayaniya a class anata leka window. Na tambayi Amira nace "menene wai ake wannan leken" sai tayi dariya tace " wannan yaron ne ya taho zai koya mana geography" nayi tsaki nace "zai koya musu dai" na ci gaba da zanen da nakeyi na digestive system dan shine assignment din da biology teacher ya bayar. Hafsat naji tace "sabon shiga, ko dan late coming dinnan ma abar mutane su huta baza'ayi ba". Tana gama fada yana shigowa kuma na tabbatar cewa yaji abinda tace, dariya ce ta kubce min ganin yadda Hafsat ta wani maze kamar ba ita ce tayi maganar ba. Ina kallonsa ta gefen ido na. Ya cire uniform din NYSC ya saka personal shirt da wando amma ya dora p-cap din NYSC din a kansa. Ban wani kalleshi sosai ba na maida hankali na akan zanen da nake yi. Ya jima a tsaye yana kallon mu daya bayan daya sannan a hankali yace "don't u guys know how to greet? Duk class din muka mike a tare, tare da cewa " good morning sir" ya jima yana binmu da kallo sannan yace "sit down" inajin Hafsat a hankali tace "finally" Nayi murmushi na zauna tare da ci gaba da zane na. Takowa yayi a hankali yazo gabana ya tsaya yace "why are u laughing?" Na dago kaina na kalle shi ido cikin ido nace " I am not laughing sir, I was smiling". "Hmm" shine abinda yace sannan ya kunna board, da yake smart board muke amfani dashi. Ya saka flash drive dinsa na nemo slides din da zai yi mana ranar ya kunna. Ni kuma ina ganin haka na cigaba da zane na. Inajinsa yace "our topic for today is rocks and their origin". Sannan yayi tambaya "who knows what this is?" Ban dago kaina ba ballantana inga abinda yake tambaya akai saboda ina expecting wani a ajin ya bada amsa, amma ga mamaki na sai naji shiru babu wanda yayi magana. Jikina ne ya bani ana kallona, na daga kai sai na ganshi a tsaye a kaina "miss smiler, we are trying to have a class here" yace min " can you please, out of the goodness of your heart, tell me what this is?". Ya fada yana nuna board, araina nace lallai wannan mutumin ya raina min hankali. Ya dan bude ido yace "the picture is displayed on the board, miss smiler, not here" ya sake fada yana nuna kansa. Dariya najiyo kasa-kasa daga bayana sannan na fahinci cewa kallonsa nake tayi. A hankali na janye idona daga kansa. Kallo daya nayi wa hoton black shiny stone din da yayi displaying a board, na dauke kaina. Na mai da dubana kan assignment dina tare da daukan pencil dina na cigaba da zanen da nake yi. A hankali nayi magana nace " that's obsidian sir". Shi kansa da yake kusa dani baiji abinda nace ba, dan haka ya sunkuyo da kansa yace "can you PLEASE, raise your voice a little bit?" Take naji raina na sake baci. "PLEASE" Ya sake cewa da muryar challenge. Dariya na sake ji saga baya na. Ni kuma har lokacin zane na nakeyi. Har ya juya zai koma gurin board sai na daga murya ta nace " That is Obsidian " Chak naga ya tsaya sannan a hankali ya dawo inda nake zaune ina zane na yace. "Tell me more" murmushi nayi sannnan na fara kwararo masa bayani tun daga kan yadda earth core take da yadda rocks suke melting su zama lava, yadda mantle da crust suke budewa har lava din ta fito earth surface. Daga nan na koma kan bayanin different types of cooling and solidification na lava din yadda yake producing different kinds of rocks. Sannan na dawo kan shi obsidian din, cooling process din da yake forming dinshi, dalilin da yasa yake black and shiny, composition dinsa, life span dinsa da amfanin sa a gurin mutane. Nafi 30minutes ina magana kuma at the same time ina cigaba da drawing dina. Tunda na fara magana ajin yayi tsit babu wanda yayi magana har na gama. Gamawa ta yayi dai dai da gama drawing dina. Sai da na karewa drawing dina kallo na tabbatar na gama sannan na dago kaina na kalle shi ido cikin ido tare da cewa " Is there anything more you want to know, SIR?" Na fadi kalmar sir din nima cikin challenge. Sai da wajen 30sec ta wuce sannan ya iya magana yace "wow, that is very correct. No, there is nothing more. U have said it all". Kamar hadin baki, yana gama fadin haka aka buga bell din break. Books din mu duk muka rufe muka fice daga class din. Sai da mukayi nisa sannan na juyo na kallo class din mu naga yana nan a tsaye a inda muka barshi ya saka hannayensa cikin aljihun wandon sa yana kallon kasa. "He must be feeling like an idiot" na fada ina murmushi. Amira tace " Ai kin wanke mana shi tas, I wonder ta yaya zai yi facing din mu tomorrow morning for maths" Hafsat tace "and they said I am the cruel one". Dariya muka yi muka tafa ni da ita, nace "ai ba cruelty bane, he asked me a question and I answered him. He then asked me to tell him more, so I told him more" wata kawarmu Hasiya tayi joining din mu tace "baki da kirki Moon. You told him more and more. By the way, how do u know so much? Ni dai nasan ba'ayi mana duk wannan a aji ba" Nayi murmushi nace mata a cikin holiday na karanta, nasan za muyi shi a wannan term din. Nayi forming note a kan shi, in kina so kizo ki karba ki copying " tayi min godiya ta wuce. Amira tace "Tabdi ai ni babu abinda zai saka inyi karatu a cikin hutu, hutu fa akace, we are suppose to huta a cikin hutu" I hope u will enjoy this. See u guys tomorrow. [11/7, 11:27 AM] maryamsuleiman48@gmail.co: MAIMOON BY Maman Maama 7 Episode Seven: The Thin Tall Man Washe gari first period muke da mathematics. Dan haka tunda na shirya nayi breakfast sai na dauki jotterta, calculator, sannan na duba syllabus naga abinda ya kamata muyi yau sannan na fice sai library. Ina zuwa na tarar librarian din ma zuwanta kenan. Ko gama cleaning library din ba'ayi ba. Na samu guri na jira har suka gama sannan na shiga. Miss Martha, librarian din mu ta tambayeni ya akayi banje class ba, na amsa mata da cewa teacher din mu bayanan kuma inada assignment da nake so in karasa. Ina shiga mathematics section na wuce, na debo textbooks din calculus har uku sannan na samu secluded guri na zauna na fara calculations dina hankalina a kwance. Saboda ina ganin a haka sai nafi ganewa akan ace wannan yaron ne zai koya min. Double period ce damu dan haka a lissafina zaiyi one hour 20min. Ina yi ina duba agogon hannuna har naga one hour ta wuce saura 20mins kenan. Hankali na gaba daya yana kan calculations dina saboda sosai nake jin dadin product rule din da nake yi a lokacin. Ji nayi tamkar ana kallona, da sauri na dago kaina tare da cire earpiece din kunnena. Ido muka hada dashi ga mamaki na sai naga ya sakar min murmushi. Daga dukkan alama ya jima yana kallona. Nayi saurin dauke kaina tare da sunkuyar da ido na kasa ina mamakin ganin shi a nan bayan nasan ya kamata ace yana class dinmu yana koya musu maths. "Mind if I join" ya fada cikin muryarsa mai sanyi. Ba tare da na sake kallonsa ba na ce "no". Kujerar kusa dani ya ja ya zauna. Ta ke naji na shaki kamshin sa. Na dan matsar da kujera ta kadan saboda kafadan shi da naji yana taba tawa. A hankali ya fara yi min magana wanda na tabbatar da ace da akwai mutun a kusa dani bazai ji me yake cewa ba. " Why aren't you in class" "am sorry" na fada a takaice. "Sorry for what" ya fada tare da adjusting kujerar sa yadda zai fuskance ni sosai, na kara jan kujerata baya sannan nace "for not attending your class". Murmushi mai sauti yayi sannan yace" it is not my class, it is OUR class, we are all suppose to be participating in it". Yayi shiru sannan ya kara da cewa " by the way, we miss u in class today. The class was exciting though, but I thought it would have been more exciting if u were there. So I asked of u and was told to check the library. And here u are. So, why are u here?" Ya tambaya yana kallon cikin idona. Na dauke kaina ina inda inda cike da jin kunyar abinda nayi. Ya saka hannunsa ya juyo da fuskata gare shi muke kallon juna, cikin muryar rada ya ce min "you think I am not good enough to teach you, right?" Kunya ce ta kamani, nayi sauri na kwace fuska ta daga hannunsa, nasa hannaye na na rufe idona cikin kunya nace masa "no" da dan karfi. Ga mamakina sai kawai naji ya kama dariya nima bansan sanda na fara dariyar ba. Sai da muka dena dariyar sannan ya dauki jotter din da take gabana tare da cewa " let's see what you have been doing for the past one hour" ban ce masa komai ba. Sai da ya gama studying abubuwan da nayi sannan yace " wow, we were in class tying to solve some few problems while you are here already done with the term. Na zaro ido nace "am not done with the term sir, am not even close" ya rungume hannayensa a kirjinsa, abinda na lura cewa dabi'ar sa ce. Yace " you are special, do you know that? Nayi sauri nace " no sir, am not. Kawai dai ina da son karatu ne" na fada ina kokarin kare kaina. Kallona kawai ya tsaya yana yi chike da rashin fahimta. Sai a lokacin na kalleshi sosai. Ba bahaushe bane. Na sunkuyar da kaina. "What tribe are you?" Ya tambaye ni cikin sanyin murya wadda itama by now na fahimci hakan yanayinsa ne. "Fulani" nace ina wasa da 'yan yatsuna. Yace " but what you just spoke is Hausa, right?". Nace "yes" yace " so u are Hausa Fulani " na girgiza kaina alamar a'a. Bai sake min wata tambayar ba. Can ya ce " I am yaroba. I am from Ibadan, Oyo state. My name is Ibrahim Adeniran Oluwaseun. Will you do me the honor of been my friend? " ya miko min hannunsa alamar shaking. Na gado kaina na sake kallonsa. Fatarsa ba mai haske nace kamar tawa ba kuma baka bace ( wankan tarwada). Dogo ne sosai sannan siriri ne dan bashi da kiba sam amma kuma straight bayansa yake tsahonsa bai sa ya rankwafa ba. Yana da doguwar fuska da dogon hanci da yalwataccen gashin gira. Bakinsa mai dan fadi ne mai dauke da siraren lips wadanda a yanzu suke dauke da murmushi. Fuskarsa tana zagaye da siririn saje da dan karamin gemu a habarsa. Fararen glasses be sanye a idonsa wadanda suke lumsassu kamar na maijin bacci. A hankali na sauke ajiyar zuciya tare da cewa " I am Fulani from Jigawa State. My name is Maimoon Muhammad Dikko. Yes, I will like to be your friend and I am sorry for missing OUR class today" " it is OK friend" ya fada yana sauke hannunsa ganin bani da niyyar shaking dinsa. Agogo hannuna na kalla, ga mamakina sai naga next period har tayi nisa. Da sauri na mike ina harhada takarduna hankalina duk ya tashi. Shima ya mike tare da daukan jotter da nayi calculations yace 'I will look this calculations over if you don't mind" "no problem" nace ina sauri duk hankalina yayi class. A bakin kofa ya sameni ina signing out. Ina fita ya biyo baya na, sai a lokacin na sake lura da tsahonsa, dan gabaki daya na a kirjinsa na tsaya. "See u tomorrow" na fada bayan mun fita daga libraryn. "See u in CLASS tomorrow" yace yana jaddada Kalmar class din. Da sauri nayi gaba dan bana so ya cigaba da bata min lokaci tunda already nayi latti a class din English. Ina shiga Aunty grace ta fara tuhumata akan daga ina nake, inda ni kuma na bata amsa da cewa ina library ina assignment ban san cewa har lokaci ya wuce da yawa ba. Saida aka fita break sannan na tambayi Hafsat ya akayi a lokacin maths. Ta be baki tayi tace "ina ruwanki, ke da kikayi tafiyarki kika barmu da wannan dogon mutumin" nace "sorry tare da langwabar dakai, ta harare ni ta dauke kai alamar har yanzu fushi takeyi. " is he good? " na tambayeta. Kamar ba zatayi magana ba sai kuma tace "you will find out tomorrow, we have him double period da safe" " oh my God Moon, he is so good, ban taba enjoying mathematics irin na yau ba, I really did enjoy it. Wato dalla-dalla yake bin komai kuma sai ya tabbatar kowa ya gane sannan zai yi gaba. Gaskiya Moon kinyi missing " inji Hasiya wacce ta dawo kusa da desk dina fuskar ta kamar gonar auduga. Na mike tsaye na dubi sauran 'yan class nace "OK people, tomorrow, I will give the Thin Tall Man a chance" "Thin Tall Man?" suka kusan hada baki. Nace "yes" matter of factly, "baku ga yadda yake bane? I think the name fits him perfectly". Dariya ajin ya dauka gaba daya, inda ni kuma na bawa Hafsat hannu muka kashe muna kyalkyala dariya. Amira na hango ta gefen idona fuskarta dauke da bacin rai. Thank you all for the support. Ina fatan zaku cigaba da bin labarin Maimoon. [11/7, 11:27 AM] maryamsuleiman48@gmail.co: MAIMOON By Maman Maama 8 Episode Eight: The New Imam Muna hostel da daddare Amira tazo dakin mu ta sameni nayi wanka ina shirin yin bacci, ta zauna a bakin gadona. Da yake yanzu mun zama seniors ba bunks ne damu ba. Still dakin mu daya da Hafsat da wadansu Christians su biyu Naomi da Abigail. Mu hudu ne a dakin mai dauke da gado hudu, lockers hudu da kujerun karatu kowacce da table dinta guda hudu, sai fridge guda biyu. Dakin babu tarkace da yawa da yake Hafsat akwai tsafta kuma duk ta fimu girman jiki hakan yasa ta zama kamar Senior din mu. Babu wanda ya isa yayi kazanta. In kaga Hafsat tana bamu order sai ka dauka ba class din mu daya ba. Muna da toilet din mu guda daya a dakin wanda muke sharing mu hudun, kuma kullum twice cleaners suke zuwa su wanke mana shi duk da ba wani datti yake yi ba. Masifar Hafsat ma ba zata barmu muyi kazantar ba. Ina tsaye ina kallon fuskata a mudubin jikin locker din Abigail Amira ta shigo dakin sanye da dogon hijab har kasa tare da sallama. Ina ganinta nasan har ta kwanta ta taso. Ta cikin mudubin nake kallonta har ta zauna a kan gadona tace "kai Moon wannan bargon naki da laushi yake, wannan inna kwanta a kansa ai ba zan iya tashi daga bacci ba" na juyo ina fuskantar ta nace ' ko kina so in bar miki ne, u can take it if you want. Ina da wani" da sauri tace " a'a wannan ai sai in kasa tashi sallah asuba" muka yi dariya baki daya. Hafsat dake kwance kan gadonta tana karanta novel tace "Amira wai da gaske yasaiyadin mu ya tafi umrah?" Amira tace "eh wallahi Hafsat, shine ma maganar da nazo muyi. Ya tafi umrah, sai nan da at least a month zai dawo. Na taho na zauna kusa da Amira nace " to fa, yanzu me ake ciki kenan Amira? Waye zai ke janmu sallah kuma wa zai ke yi mana dori? Amira a lokacin itace mosque prefect dan haka duk wasu bayanai akan harkar addini a gurinta a ke samu. Tace "senior master dai yace they will find a solution. Maybe da assuba in muka je sallah zamu ga new face" na dafe kai nace "oh God, I don't like these changes da muke samu wallahi" Amira ta gyara zama tace "change is sometimes good Moon. Dama maganar da nazo muyi kenan, karki damu kanki da wadanna changes din har su zo suyi affecting dinki negatively, please Moon, give the change a chance, ki daure, you might even like it. Bana so gobe idan munje masjid kinga new imam ki yi loosing interest akan karatun ki. Kinga kun kusa sauka ke da Hafsat. Kada kizo karatun ki ya koma baya kuma. Muka kalli juna nida Hafsa wacce yayi her usual side looped smile tare da whispering "she likes you" na tashi daga dan kashingidar da nayi nace "I like you too Amira. Kuma insha Allah babu abinda zai samu karatu na, besides, I have u". Amira tayi sauka tun kafin tazo school din. Shi yasa run muna jss ni da Hafsat muke daukan karatu a gurinta. Tana dariya ta mike tana cewa "ni din bayan in muna karatun wasa kike yi. Da haka ta mike tare da wishing din mu good night, tayi sallama dasu Abigail sannan ta tafi dakinsu Ajiyar zuciya nayi nayi rigingine ina tunano abubuwan da suka faru a ranar. Na fahimci cewa abinda nayi ban kyauta ba. Ya kamata in bawa Thin Tall Man chance kamar yadda Amira ta fada kafin in ce bana son teaching dinsa. Abinda nayi na kin shiga class dinsa is very wrong, za'a iya furnishing dina akan hakan. Amma duk da haka bai nuna min bacin ransa ba sai ma neman sulhu da yayi dani. Kafin inyi bacci ranar sai da nayi alkawarin insha Allahu gobe zanyi making up for my mistakes. Washegari kuwa kamar yadda muka yi tsammani hakane ya faru. Mukaji muryar diff liman yana jan sallah. Muka yi joining har aka idar sannan muka tafi class din da ake mana islamiyya. Muna zazzaune muna bitar karatun mu na baya sai gashi ya shigo ajin. Duk da cewa akwai duhun assuba amma class din tar yake da fluorescent light wacce take a kunne. Kallonsa na tsaya yi cikin mamaki. It is the thin tall man. Jallabiya ce a jikin sa ash color sai bakin dogon wando da bakar hula a kansa. Idonsa babu glasses. Ya shigo ya rufe kofar tare da jingina a jikinta, ya ringume hannayensa a kirjisa tamkar mai jin sanyi. Daya bayan daya ya ringa binmu da kallo har idonsa ya kawo kaina, muna hada ido nayi saurin sunkuyar da ido na kasa. Gyaran murya yayi na dago kaina kawai sai naga ya yi min murmushi nima kuma sai na samu kaina da yi masa murmushi. Na sake sunkuyar da kaina kasa a karo na biyu. Ya sake yin gyaran murya tare da cewa "I was asked by the senior master to guide you through your Islamic studies before your mu'allim returns from his pilgrimage" ya tako a hankali ya jingina da jikin board yana facing din mu sannan ya cigaba da cewa "I don't know how you guys do it, do u have a class monitor or something?" Duk muka amsa masa da "yes" sannan ya bukaci da ta tashi tayi masa bayanin yadda tsarin karatun mu yake. Nan Amira ta tashi cikin nutsuwa ta fara yi masa bayani dalla dalla tare da nuna masa time table din mu. Yana sauraronta attentively yana gyada kai alamar fahimta. Sai da ta gama sannan yace " with your permission, I will like to make some changes. Instead of group progression I will like it to be individual so that we will carry everyone along. Because of the time factor, we will add night classes to the early morning ones so that we will have enough time. I will discuss this with your Senior master to see if its OK to have the night classes". Ya zagayo gabana ya dauki alqur'anin da yake bude a gaba na ya duba inda muka tsaya sannan ya mayar ya ajiye yace " I don't think we can start today, the time has already run out, we will insha Allah start tomorrow. Maassalam to u all" duk ajin suka amsa masa da "bissalam" banda ni wacce haka kawai naji na zama uncomportable saboda tsayawar da yayi a kusa da seat dina. Duk iskar da zan shaka sai na shaki kamshin jikinsa da scent din after shave dinsa. [11/7, 11:28 AM] maryamsuleiman48@gmail.co: MAIMOON By Maman Maama 9 Episode Nine: Give Me a Chance Geography lecture din da muka yi was very interesting. Sai yanzu na fahimci abinda Hasiya take nufi lokacin da tace yana bin komai dalla-dalla. He makes sure He carries everybody along. Yana making references da abubuwan da na fada rannan yana kara buda su dayi mana bayani using simple terms wanda ko the most stupidest person zai gane. Anan na kara fahimtar cewa shi mutum ne mai tsantsar nutsuwa, komai nasa a hankali yake yinsa. He is very gentle, bashi da hayaniya sam. Toward the end of the class sai ya bamu classwork, kowa ya rubuta abinda ya fahimta a game da topic din yau for 10mins. Kowa ya dauko takarda ya fara rubutu, ni kuma na duba takarduna na rasa fullscap sheet, sai na juyo gurin Hafsat nayi mata alama da hannu akan ta bani paper, take mutuniyar tawa sai ta makale kafada tare da murguda baki. Takaici ya ishe ni gashi time yana tafiya. Sai na juya gurin Amira. Kafin Amira ta fallo min sai naga an ajiye min paper a gaba na, na daga kai na kalleshi na ce "thank you sir" ya amsa da "don't mention, what are friends for" tare da yi min irin kallon nan na 'kin tuna'. Nayi murmushi nima na fara rubutu. Ga mamaki na sai na ganshi ya zauna akan desk dina kusa da takardar da nake rubutu a ciki. Lokaci daya wannan special kamshin nasa ya ziyarci hancina, naji wani iri a jiki na tun daga kaina har zuwa yatsun kafata, nan tubutun ya gagareni dan duk ideas dina guduwa sukayi suka barni na kasa hada koda cikakken sentence ne. Na saba jin masculine scent a wajan su ya Walid but it never have this effect on me, nashi is like special, it tells me that he is very much male. Na zama very uncomportable har absentmindedly na fara fidgeting da kasan hijab dina. A hankali ya sunkuyo da kansa sai tin kunnena, unexpectedly naji yayi min magana a kunne yace "am I making you uncomportable?" Ya fada in a very low whisper. A firgice na dago kaina sai ga idona tsaf cikin nasa with his face few inches from mine. In that instance da muka hada ido dashi, everything froze, me, him, time, the class and even my heartbeat. Ido na ya rufe bana ganin komai, kunne na ya toshe bana jin komai. A cikin wadannan seconds din (or maybe minutes, I don't know), babu abinda yayi existing a duniya ta sai shi, only him. Fuskarsa kadai nake gani, kamshinsa kadai nake shaka. Apart from him komai ya zama blank. A hankali na fara jin muryar Hafsat tana cewa " sir, sir, sir" sai muryar kuma ta fara karfi sannan ta zama tamkar kara a kunnena. Nayi blinking once, twice sai a sannan common sense dina ya fara dawo wa, sai a sannan na fahimci abinda ya faru. We have been staring at each other for a while (I don't know for how long). Take naji tamkar kasa ta tsage in shige ciki, na dauke fuskata da sauri zuwa daya side din. Sannan na lura cewa kusan duk 'yan class din mu suke kallo. Hafsat naji ta sake cewa "sir" da karfi, daga jin muryar ta nasan cewa she is really angry. Yau na san na shiga uku. What is happening to me? What just happened? Murya can kasa naji yace " yes, what is it?" "I am through sir" " through with what?" Ya tambaya har yanzu muryarsa bata dawo dai dai ba kuma clearly kansa ma bai dawo dai dai ba. "Through with the class work sir, you gave us classwork, remember?" Ta fada tamkar mai shirin tashi zama, "ohhh" shine abinda kawai yace yana shafa kansa. Sai kuma ya mike ya kama hanyar fita yana cewa "keep it with u. I will collect it tomorrow" daga haka ya fice ba tare da ya juyo ba, ba kuma tare da ya dauki glasses din sa, handset da papers dinsa da ya ajiye akan podium ba. Yana fita Hafsat ta zagayo gaba na tare da saka duk hannayenta biyu ta rike kugunta ta na kallona fuskarnan filled with fury ta fara yi min masifa " were u flirting with the thin tall man ko idona ne yake min karya" na bita da kallo ina mamakin mai take nufi, I still don't fully understand what happened, ni ina ganin kamar stroke na samu, for all I know I could be sick or something " answer me" ta sake doka min tsawa. Kafin in bata amsa teacher din mu na physics ya shigo, a dole Hafsat ta zauna tare da zagaya hannun ta a wuyanta alamar I will kill you. Muka gaishe shi, ya amsa da fara'arsa, ni dai duk jikina a sanyaye. Bayan mun zauna ne ya kalleni yace "Moon, what is wrong with u?" Hafsat nayi sauri tace " help me ask her oo". Da yake teacher din mai barkwanci ne Sai yayi dariya yace " maybe the geography was so boring, worry not my dear, I will cheer you up with physics " akayi dariya gaba daya. Sai a lokacin ya lura da kayan kan podium, yace " clearly, the geography was boring to the teacher also, he forget his his things. Do u guys chase him out? " aka sake dariya gaba daya tare da cewa "no, sir" yace " OK, to brighten up our Moon, let's send her on an errand to return this to the runaway teacher " na sauri nace "I rather not" ina jin Hafsat a bayana tana cewa "good for you" Yace " why not?" Sai kuma na kasa bashi amsa. Amira ta yi sauri tace "let me take it to him, sir" amma sai ya dage akan lallai ni zanje, a cewar sa it will help clear my head. Ba yadda zanyi dole na karba na fita, ni yanzu bansan ma inda zan same shiba. Na dau hanyar staffroom. Na shiga naga bayanan, sai naga another copper a zaune yana marking some papers, na gaishe shi tare da tambayar whereabout of Mr Ibrahim, ya dago kansa ya kalleni tun daga kasa har sama with devilish smile on his face tare da cewa " hello beauty, why are u looking for him? Na hade raina nace "is he around?" Ganin na bata rai sai ya zama serious yace "he is not around, but I can take message for him. My name is victor, Ibrahim and I share the same room" " OK " nace " please give this to him, he left them in our class ". Nace tare da ajiye kayan a gabansa. Na juya na fita, in my mind ina godiya ga Allah da bayanan. Kaina a kasa ina tafiya naji nayi karo da mutum. Nayi sauri na matsa. Bana bukatar in kalli fuskarsa, kamshin da naji ya gamsr dani cewa shine. Cikin in ina nace "I brought your things" " OK , thanks " ya bani amsa a takaice. Nayi sauri nace " I was asked to do so by our physics teacher " OK ya sake cewa. Nayi gaba inajin haushin kaina, mai yasa nayi masa magana. Sai kuma naji ya kira sunana" Maimunatu" ban amsa ba kuma ban tsaya ba. Ya biyo ni da sauri yasha gaba na. Ga mamakina sai naga ya kama hannuna, nayi sauri nayi dago kaina na kalleshi, fuskarsa babu murmushin da na saba gani a ciki. Na bude baki na zance ya cika ni sai naji ya saka min wani abu a hannuna yace "this is for u" daga haka ya saki hannuna ya juya ya tafi. Na sauke idona a kan abinda yake hannuna sai naga ashe jotter tace da ya karba a library, a front page kusa da inda na rubuta sunana naga ya rubuta PLEASE, GIVE ME A CHANCE Ina taya duk masoya MAIMOON murnar ganin Arafat day. Allah yasa muyi eid lafiya Ameen. Aci nama lafiya [11/7, 11:28 AM] maryamsuleiman48@gmail.co: MAIMOON By Maman Maama 9 Episode Nine: Give Me a Chance Geography lecture din da muka yi was very interesting. Sai yanzu na fahimci abinda Hasiya take nufi lokacin da tace yana bin komai dalla-dalla. He makes sure He carries everybody along. Yana making references da abubuwan da na fada rannan yana kara buda su dayi mana bayani using simple terms wanda ko the most stupidest person zai gane. Anan na kara fahimtar cewa shi mutum ne mai tsantsar nutsuwa, komai nasa a hankali yake yinsa. He is very gentle, bashi da hayaniya sam. Toward the end of the class sai ya bamu classwork, kowa ya rubuta abinda ya fahimta a game da topic din yau for 10mins. Kowa ya dauko takarda ya fara rubutu, ni kuma na duba takarduna na rasa fullscap sheet, sai na juyo gurin Hafsat nayi mata alama da hannu akan ta bani paper, take mutuniyar tawa sai ta makale kafada tare da murguda baki. Takaici ya ishe ni gashi time yana tafiya. Sai na juya gurin Amira. Kafin Amira ta fallo min sai naga an ajiye min paper a gaba na, na daga kai na kalleshi na ce "thank you sir" ya amsa da "don't mention, what are friends for" tare da yi min irin kallon nan na 'kin tuna'. Nayi murmushi nima na fara rubutu. Ga mamaki na sai na ganshi ya zauna akan desk dina kusa da takardar da nake rubutu a ciki. Lokaci daya wannan special kamshin nasa ya ziyarci hancina, naji wani iri a jiki na tun daga kaina har zuwa yatsun kafata, nan tubutun ya gagareni dan duk ideas dina guduwa sukayi suka barni na kasa hada koda cikakken sentence ne. Na saba jin masculine scent a wajan su ya Walid but it never have this effect on me, nashi is like special, it tells me that he is very much male. Na zama very uncomportable har absentmindedly na fara fidgeting da kasan hijab dina. A hankali ya sunkuyo da kansa sai tin kunnena, unexpectedly naji yayi min magana a kunne yace "am I making you uncomportable?" Ya fada in a very low whisper. A firgice na dago kaina sai ga idona tsaf cikin nasa with his face few inches from mine. In that instance da muka hada ido dashi, everything froze, me, him, time, the class and even my heartbeat. Ido na ya rufe bana ganin komai, kunne na ya toshe bana jin komai. A cikin wadannan seconds din (or maybe minutes, I don't know), babu abinda yayi existing a duniya ta sai shi, only him. Fuskarsa kadai nake gani, kamshinsa kadai nake shaka. Apart from him komai ya zama blank. A hankali na fara jin muryar Hafsat tana cewa " sir, sir, sir" sai muryar kuma ta fara karfi sannan ta zama tamkar kara a kunnena. Nayi blinking once, twice sai a sannan common sense dina ya fara dawo wa, sai a sannan na fahimci abinda ya faru. We have been staring at each other for a while (I don't know for how long). Take naji tamkar kasa ta tsage in shige ciki, na dauke fuskata da sauri zuwa daya side din. Sannan na lura cewa kusan duk 'yan class din mu suke kallo. Hafsat naji ta sake cewa "sir" da karfi, daga jin muryar ta nasan cewa she is really angry. Yau na san na shiga uku. What is happening to me? What just happened? Murya can kasa naji yace " yes, what is it?" "I am through sir" " through with what?" Ya tambaya har yanzu muryarsa bata dawo dai dai ba kuma clearly kansa ma bai dawo dai dai ba. "Through with the class work sir, you gave us classwork, remember?" Ta fada tamkar mai shirin tashi zama, "ohhh" shine abinda kawai yace yana shafa kansa. Sai kuma ya mike ya kama hanyar fita yana cewa "keep it with u. I will collect it tomorrow" daga haka ya fice ba tare da ya juyo ba, ba kuma tare da ya dauki glasses din sa, handset da papers dinsa da ya ajiye akan podium ba. Yana fita Hafsat ta zagayo gaba na tare da saka duk hannayenta biyu ta rike kugunta ta na kallona fuskarnan filled with fury ta fara yi min masifa " were u flirting with the thin tall man ko idona ne yake min karya" na bita da kallo ina mamakin mai take nufi, I still don't fully understand what happened, ni ina ganin kamar stroke na samu, for all I know I could be sick or something " answer me" ta sake doka min tsawa. Kafin in bata amsa teacher din mu na physics ya shigo, a dole Hafsat ta zauna tare da zagaya hannun ta a wuyanta alamar I will kill you. Muka gaishe shi, ya amsa da fara'arsa, ni dai duk jikina a sanyaye. Bayan mun zauna ne ya kalleni yace "Moon, what is wrong with u?" Hafsat nayi sauri tace " help me ask her oo". Da yake teacher din mai barkwanci ne Sai yayi dariya yace " maybe the geography was so boring, worry not my dear, I will cheer you up with physics " akayi dariya gaba daya. Sai a lokacin ya lura da kayan kan podium, yace " clearly, the geography was boring to the teacher also, he forget his his things. Do u guys chase him out? " aka sake dariya gaba daya tare da cewa "no, sir" yace " OK, to brighten up our Moon, let's send her on an errand to return this to the runaway teacher " na sauri nace "I rather not" ina jin Hafsat a bayana tana cewa "good for you" Yace " why not?" Sai kuma na kasa bashi amsa. Amira ta yi sauri tace "let me take it to him, sir" amma sai ya dage akan lallai ni zanje, a cewar sa it will help clear my head. Ba yadda zanyi dole na karba na fita, ni yanzu bansan ma inda zan same shiba. Na dau hanyar staffroom. Na shiga naga bayanan, sai naga another copper a zaune yana marking some papers, na gaishe shi tare da tambayar whereabout of Mr Ibrahim, ya dago kansa ya kalleni tun daga kasa har sama with devilish smile on his face tare da cewa " hello beauty, why are u looking for him? Na hade raina nace "is he around?" Ganin na bata rai sai ya zama serious yace "he is not around, but I can take message for him. My name is victor, Ibrahim and I share the same room" " OK " nace " please give this to him, he left them in our class ". Nace tare da ajiye kayan a gabansa. Na juya na fita, in my mind ina godiya ga Allah da bayanan. Kaina a kasa ina tafiya naji nayi karo da mutum. Nayi sauri na matsa. Bana bukatar in kalli fuskarsa, kamshin da naji ya gamsr dani cewa shine. Cikin in ina nace "I brought your things" " OK , thanks " ya bani amsa a takaice. Nayi sauri nace " I was asked to do so by our physics teacher " OK ya sake cewa. Nayi gaba inajin haushin kaina, mai yasa nayi masa magana. Sai kuma naji ya kira sunana" Maimunatu" ban amsa ba kuma ban tsaya ba. Ya biyo ni da sauri yasha gaba na. Ga mamakina sai naga ya kama hannuna, nayi sauri nayi dago kaina na kalleshi, fuskarsa babu murmushin da na saba gani a ciki. Na bude baki na zance ya cika ni sai naji ya saka min wani abu a hannuna yace "this is for u" daga haka ya saki hannuna ya juya ya tafi. Na sauke idona a kan abinda yake hannuna sai naga ashe jotter tace da ya karba a library, a front page kusa da inda na rubuta sunana naga ya rubuta PLEASE, GIVE ME A CHANCE Ina taya duk masoya MAIMOON murnar ganin Arafat day. Allah yasa muyi eid lafiya Ameen. Aci nama lafiya [11/7, 11:29 AM] maryamsuleiman48@gmail.co: MAIMOON By Maman Maama 11 Episode Eleven : The Protector "You are a smart one, you must know something" kafin in bashi amsa naji Hafsat tama kwalla min kira daga class. Na juya na juya na ganta a kofar ajin ita da teacher din mu. "Good lord" Ibrahim ya fada tare da matsawa daga kusa dani sannan yace "please meet me in the library after school, please come" da haka ya juya ya fara tafiya, sai da yayi nisa sannan ya fahimci hanyar hostel yake tafiya, sannan ya juya kuma ya dau hanyar staff room. Ni kuma na koma class. Ina zuwa kofar class teacher fin mu ya fara tambayata me nayi wa copper din can. Nace masa babu komai. "But he seems agitated, are you sure you are not in trouble with him?" " i am not sure sir, i have no idea what he was talking about" na amsa masa frankly. Ya jima yana kallona kuma ya fahimci iyakacin gaskiya ta nake fada masa, ya girgiza kanshi a hankali yace "just be careful Moon, if u ever feel like he is crossing the line with you, just report to me or any other senior staff" nace masa tom. Har aka tashi daga school ban yanke shawarar ko zanje library gurin Ibrahim ba. Saida akayi ringing bell sannan na tuna cewa ban yanke shawara ba. Kamar Hafsat tasan tunanin da nakeyi sai naga ta zauna a kusa dani, na juyo na kalli fuskarta naga babu wasa a cikin ta. In a serious tone tace min "me yace miki dazu? " na gane maganar da take yi kuma ga mamaki na sai na samu kaina da fada mata gaskiyar yadda mukayi da Ibrahim. Ta girgiza kanta alamar gamsuwa tace "i expect as much. Babu inda zakije, yau a hostel zakiyi karatun ma ko class ba, zaki zo ba ballantana library. Green snake under green grass kawai. Sumi sumi dashi kamar wani na Allah. Ni dama duk ustazan nan bana yadda dasu..... ". Duk da nasan Hafsat tana kokarin protecting dina ne amma sai na samu kaina da jin haushin maganganun da take fada akan Ibrahim. Na dakatar da ita nace "bafa wani abun ba yace min ba Hafsat, he just asked me to meet him in the library. It might be totally different from what you are thinking. Please Hafsat ki bar ni inje inji abinda zai ce" nayi ta lallaba Hafsat amma taki bari na inje. Haka ta tusa keyata har hostel. Ranar haka na wuni jikina da zuciya ta babu dadi. Ina tunanin ban kyauta ba dana barshi yana jira na, kuma deep inside me ina son inje din saboda insan me yake so dani, nima kuma in wanke duk wani kokwanto dake zuciya ta a game dashi. Amma Hafsat ta kasa ta tsare ta hanani sakat. Washegari da assuba ina tashi gaba na yake ta faduwa saboda nasan yau dai dole zamu hadu da Ibrahim a islamiyya. Hafsat ta hade ranta sosai ta kora min warning akan koya yimin magana kar in kulashi. A haka muka je masallaci mukayi sallah sannnan muka tafi islamiyya. Muna zama sai gashi ya shigo. Na kasa daga kaina in kalleshi har muka gaishe shi duk ya ajin. Kawai sai ganin sa nayi ya zo ya tsaya a gaban seat dina yace "maimunatu" na daga kaina a hankali na kalleshi, bacin ran da na gani a idonsa shi yasa nayi saurin saukar da idona kasa ba tare da na amsa kiran da yayi min ba. "Maimunatu am talking to you " ya sake cewa cikin tsawa-tsawa. Jikina ya fara karkarwa saboda tsoro, nace "am sorry sir " "sorry for what? I clearly asked you to meet me after school yesterday but you didn't. Why? " kawai sai naji hawaye yana zubo min, sai na fara sheshshekar kuka, ni dama akwai saurin kuka. Tsayawa kawai yayi yana kallona da mamaki sannan yace "why are you crying? For God's sake I only asked you a question" cikin fada yake min magana. Wani kukan na sake rushewa dashi, ni babu abinda bana so a rayuwata irin a yimin tsawa ko fada. Shi bai san cewa fadan da yake yi min shi ne ya ke sakani kuka ba. Hafsat ce tace masa "she was sick sir, that's why she didn't meet you in the library " duk da kukan da nake yi sai da nayi mamakin yadda Hafsat ta shirga masa karya. Kuma na gane motive din ta, so take yace min in tafi hostel tun da bani da lafiya. Ya sunkuyo dai dai fuskar ta sannan cikin sanyin murya yace min "are u sick? Na girgiza kaina. "Do u want to go back to hostel? " na sake girgiza kaina alamar a'a. "OK stop crying for God's sake, or else I will have to send you back to hostel" ya fada da dan karfi wanda hakan yasaka na sake rushewa da wani kukan. Tsaki yayi sannan yace "OK, that's it, u are going back to hostel" yana fadin haka Hafsat ta mike tare da kamoni kamar wata marar lafiya. Ya dakatar da ita tare da cewa "where are you going to? " nan ta kama inda inda tana kokarin yi masa bayanin cewa rakani hostel zatayi. Shi kuma ya ce mata tunda nace lfy ta kalau ta barni inyi tafiya ta ni kadai ita kuma tayi karatun ta. Ta koma ta zauna tana zumburar baki, ni kuma na kama hanyar fita. Ina tajin surutan mutane a ajin nidai nayi tafiya ta. Na dan yi nisa da class din kenan naji takun mutun yana bina, ina juyawa na ganshi a kusa dani ya kamo hannuna ya jani da sauri zuwa wani class da babu kowa ya rufe ajin tare da tare bakin kofar. Duk wannan ya faru ne cikin seconds. Wani kukan na sake saka masa ina rokon sa "please let me go, i will never disobey you again, please let me go" kallona kawai yake cikin mamakin yadda nake ta rusa kuka. Ya rungume hannayensa a kirjinsa sannan yace " do you want me to let you go? " na gyada masa kai "then stop crying like a baby, for God's sake I just walk out of my class just to talk to u. Why are you crying? What have I done to u? " nayi shiru ina sheshshekar kuka, ya sake maimaita tambayarsa " did i do u anything wrong ". "You are shouting at me" na amsa ina kara sautin kuka na. Dariya ya fara yi kasa kasa yana girgiza kansa ni kuma dariyar ta kara bani haushi, yaya bayan yayi min tsawa ina kuka kuma zai saka ni a gaba yana min dariya? Dan haka sai na rufe fuskata da hannayena biyu na kara rushewa da kuka. Ya tako a hankali ya tsaya agaba na sannan ya sunkuyo kansa dai dai kunne na yadda har inajin saukar munfashinsa a wuya na yace "I am sorry for shouting at you. I promise to never do it again " na bude fuskata na turo baki ina goge hawayena da bayan hannuna. Ya chiro handkerchief a miko min, nasa hannu na karba na karasa goge fuskata dashi, sannan na daga kaina na kalleshi naga yana kallona yana murmushi. "OK cry cry baby, tell me why didn't you come to the library yesterday? " na kalli windon class din naga gari ya fara haske sannan na tuna cewa ya baro students suna jiran sa zai yi musu dori. Na kalle shi naga ni kawai yake kallo yana murmushi daga dukkan alama ya manta da 'yan class din da suke jiransa. Nace masa "we, will talk about that later, now your students are waiting for u, time is running out " ya danyi frowning face dinshi alamar tunani sannan yace "good lord! I totally forgot about them." Ya shafa gashin kanshi sannan yace "just PROMISE that we will talk tomorrow " na ce "not tomorrow sir, we will talk on Monday " yace "why not tomorrow? " Nace "I don't want to be taking time from our Islamic class time. I will talk to u on Monday if u promise that you will not talk to me during our Islamic class " yayi shiru yana kallona sannan yace "OK I promise "nayi murmushi nace masa OK. Daganan na bude kofar class din na fita na koma hostel. Yayi keeping promise dinsa kuwa dan bai kuma yi min magana a islamiyya ba, karatu kawai mukeyi dashi mu tashi. Ranar monday muna da class dinsa kuma nasan dole zai ce min mu hadu a library after school. Yana shigowa bayan mun gaishe shi sai ya dauko wata 'yar jotter ya rike yace yau discussion za'ayi, zaike mana tambayoyi muna amsawa. Kawai sai ya taho kan desk dina ya zauna kuma ya juyo yana facing dina kuma yana facing sauran 'yan class din, tunda a front row nake. Nayi sauri na kalleshi sai ya sakar min murmushi, na sunkuyar da kaina kasa duk naji na takura. Yana ta questions dinsa sauran 'yan class suna amsawa amma ni ban san ma me suke yi ba, saboda yadda yake zaune gab dani kuma duk numfashin dana shaka saina ji kamshinsa. Na rasa inda zan sa kaina. Chan ya ce min "Maimunatu are u OK " sai da na dan firgita kadan saboda nayi nisa a cikin tunani, na manta ma a ina nake. Nace"yes sir, i am alright " "are u sure" Hafsat ce tace " I am sorry sir, but dont you think you are making her uncomfortable? " gaba daya ajin akayi shiru yace mata "what makes you think I am making her uncomfortable? She is not complaining, is she? " ta kalle shi ido cikin ido tace "i know she is uncomfortable because she is my little sister " "ohhh" shine abinda Ibrahim yace sannan ya juyo ya kalleni ya sake komawa ya kalleta kamar mai comparing din mu, yayin da ita kuma ta tsare shi da ido. Like, comment and share [11/7, 11:29 AM] maryamsuleiman48@gmail.co: MAIMOON By Maman Maama 12 Episode Twelve : This is Me Note: duk maganar da akeyi da Ibrahim da turanci akeyi, amma zamu keyi da hausa saboda a samu sauki fahimta. Ayi karatu lfy "Da gaske sisters ne su? " ya fada yana kallon sauran 'yan ajin. Duk ajin ya dauka "eh sir sisters ne, baka ga suna kama ba? " ya sake kallon mu yana girgiza kai, "ni ban ga kama ba" Hafsat ta kara kulewa ta hade rai sosai, shi kuma sai ya kalleta yayi dariya yace " ok Big Sister, kiyi hakuri na takura ma kanwarki. In babu damuwa to in dawo desk dinki mana maimakon nata? " Hafsat ta bude baki tana kallonsa da mamaki, sannan tayi sauri tace "a'a yi zamanka anan" yayi dariya sosai har habarsa ta lotsa sannan yace "dama nasan zaki ce haka, nima kuma nafi son zama anan" nidai duk ina jinsu bance komai ba. Sai da period dinsa ta fita sannan yace min "kar ki manta alkawarin mu, ni kadai nasan abinda zanyi miki in kika yi min irin ta rannan" da haka ya fita daga ajin. Yana fita Hafsat ta jawo kujerar ta kusa da tawa tace " alkawarin me mutumin nan yake magana akai? Yaushe kuka hadu har kika yi masa alkawari ba tare da nasa ni ba? " na kalleta nace " wani lokacin Hafsat ina mamakin mutane in suka ce na fiki surutu, sa idonki yayi yawa Hafsat " nan Hafsat ta kuma kuluwa tace " au haka ma zaki ce ko? Duk abinda nakeyi fa dan ke nakeyi. Mutumin nan daga ganin sa ba mutumin kirki bane, bana son kowacce irin alaka a tsakanin ku. I am trying to protect you" nace " ni kuwa Hafsat kina bani mamaki duk sanda kika ce Ibrahim ba mutumin kirki bane ba, how do you know? Kin san kullum daddy yana ce mana never judge a book by it's cover, ba dai dai bane ba kawai ki yanke hukunci akan mutum ba tare da kin fahimce shi ba" tace "OK kina so ki gayamin cewa ke kina so ki fahimce shi kenan ko? " nace mata "exactly " Amira ta taso tazo gurin mu tace "pls guys not here, zamuyi maganar in munje hostel" Hafsat ta cigaba da balbalin fada ni kuma na tashi kawai na fita daga class din. Kan veranda na zauna ina tunanin yadda zan bullowa wannan lamarin, nasan Hafsat akan gaskiyarta take fada, duk da ina da karancin shekaru amma na gane duk abubuwan da Ibrahim yake min da duk kwana kwanar sa nasan inda ya dosa. Kuma ni kaina basai wani yayi min fada ba nasan nayi kankanta da zuwa inda ya dosa. Abu na biyu kuma Ibrahim bayarabe ne, ni kuma bafulatana bana jin tarayyar mu dashi zatayi kyau. Murmushi nayi sanda na lissafo fuskar mommy inta samu labarin ina dating yaroba guy. Amma koma menene zai kasance yau zamu zauna muyi magana da Ibrahim, zan bukaci ya fada min duk abinda yake zuciyar sa ni kuma zanyi masa bayanin cewa abin ba me yiyuwa bane. Ina so mu samu maslaha a tsakanin mu. Da aka tashi bayan munyi sallah munci abinci Amira ta jamu dakin su tana so ta daidaita tsakanin mu da Hafsat. Na zauna a nutse na yiwa Amira bayanin abinda yasa nake son muyi magana da Ibrahim. Muna ta maganar mu Hafsat tayi banza ta rabu damu, saida Amira tace mata "baki ce komai ba Big Sister" ta fadi big sister din da tsokana, irin yadda Ibrahim ya ce mata dazu a class. Ta juyo ta kallemu tana yamutsa fuska tace "She can do as she wants, ni dai tasan cewa komai tayi kamar tayi a gaban mommy ne dan wallahi sai na gaya mata" Amira tace "Haba Hafsat pls let her go, inta dawo zata gaya mana duk abinda sukayi dashi daga nan za muyi shawarar me zatayi next" Dakyar Amira ta lallaba Hafsat ta barni na tafi da sharadin cewa duk abinda yace min zanzo in gaya mata. Naje nayi wanka na shirya a tsanake, dama ni ko a gida ba kwalliya nake ba ballantana a school na saka hostel wears dina, har na nada vail dina sai kuma na chire na dauko dogon hijab din Hafsat na saka. Ina fita na nufi library, tun daga nesa na hangoshi a zaune a side din library din da table a gabansa dauke da littattafai, amma kuma ba karatun yakeyi ba waya yake dannawa. Na karasa da sallama, ya dago kai ya kalleni da murmushi a fuskarsa, daga gani ya dade a zaune a gurin. Ya nuna min kujerara kusa dashi yayi min nuni da in zauna. Maimakon in zauna a kusa dashi din kamar yadda ya bukata saina dauki kujerar na zagaya daya side din na zauna ina fuskantarsa. Ban gaishe shiba nace masa "am here, what do you want ?" Ya sake yin murmushi yace min good evening ma'am" sai kuma naji kunya ban gaishe shiba nace "good evening sir" ya cire glasses din idonsa yana murza idon yace "har na fara tunanin bazaki zo ba, na dauka yau ma Hafsat ta hana ki zuwa" na kalleshi da mamaki nace "ya akayi kasan ita ta hanani zuwa rannan? " yace "da ban sani ba, sai dazu data cemin ita sister dinki ce sannan na fahimci ita ta hana ki zuwa" muka yi shiru baki daya na wani lokaci sannan ya cigaba da magana a hankali " am sorry for shiga rayuwarki da nayi kwana biyu. Nima bansan mai yake hawa kaina ba tun zuwa na makarantar nan, ina so ki fahimci cewa bani da wani mugun nufi a kanki sai alkhairi insha Allah. Tun ranar da kika amsa question dina a class naji kin burgeni, bayan na fita daga ajin ku na je staff room nayi tambaya akan ki anan na fahimci cewa you are a genius " nayi saurin katse shi nace "am not a genius " yayi dariya yace "research ya nuna cewa babu genius din da ya taba yarda cewa shi genius ne" ban bashi amsaba na sunkuyar da kaina kasa. Ya cigaba da cewa "tun daga nan na zama interested akan ki, lokacin ne nayi miki offering friendship. Kuma ina saka ran babu wani abu da zai rusha friendship din mu" ya sake yin shiru kamar ya gama magana sai kuma yace "ita zuciya tana da wahalar fassarawa, na kasa fahimtar me zuciya ta take nufi dake. Kullum sai inji ina so in ganki, inna ganki kuma sai inji bana so mu rabu, in ban ganki ba kuma sai inji na rasa farin ciki na" ya sake yin shiru yana shafa gashin kansa. "What do you want from me? " na sake tambayar sa a karo na biyu. Ya yi tagumi da hannayensa duk biyun ya sauke lumsassun idanuwansa a kaina sannan cikin muryar rada yace " ina so ki kara kahuri dani mu cigaba da friendship din mu, nasan wannan feeling din da nake ji akanki zai wuce wata rana. Ina so please kiyi tolerating dina for the time being. In kina ignoring dina zan iya aikata wani abun da ba dai dai ba". Duk bayanin da yake yi ina jinsa kuma ina analyzing duk maganganun sa. Na bude baki zanyi magana kenan sai ya daga min hannu ya dakatar dani yace "kar kice komai yanzu, ki bari sai kinje hostel kinyi tunani akai tukunna. Ina so mu cigaba da zama a friends but i have feelings for you. Nace masa to zanje inyi tunanin kamar yadda yace. Muka danyi shiru na wani lokaci sannan ya ce " kafin kiyi tunanin amma ina so in dan baki brief labari na saboda ki fahimceni sosai. Kamar yadda na sanar dake ni bayarabe ne full blood. A yanzu shekaruna ashirin da biyar da haihuwa. Mahaifina ya rasu tun ina five years old. Nine babbar a gurin parents dina, sai kanne na mata su biyu. Bayan rasuwar mahaifina mamana ta sake aure ta haifi maza su biyu. Step father dina babban malamine a garin Ibadan, a gurinsa na koyi karatu sosai. Ya rike mu ni da sisters dina tamkar shi ya haifemu dan idan ba gaya maka akayi ba ba zaka san ba shine baban mu ba. Daga mamana har step father dina basu yi wani karatun boko sosai ba, baban mu dai yana dan taba kasuwanci kadan sai kuma islamiyya da yake koyarwa a unguwar mu, dan haka mu ba masu arziki bane sosai sai rufin asiri dai dai gwargwado. Allah ya bani kwakwalwar karatu na arabi da boko, wannan yasa baban mu ya sakani a makarantar kudi dan insamu ilimi mai kyau kuma Alhamdulillah na samu. Duk kudin babanmu akan karatuna yake karewa, sauran siblings dina duk a makarantun government suke, a cewar baba ni zan kula dasu inna samu aiki. Bayan na gama secondary school ne na samu na fara aikin teaching a wata primary school dake unguwar mu. Shekara ta uku ina teaching ina samun salary na baba yace lallai saina koma makaranta nayi degree, Allah ya taimakeni na samu admission a university of Ibadan nayi degree na a fannin mathematics. Na samu kyakykyawan sakamako na fita da first class shine NYSC suka zabe ni aka turo ni nan". [11/7, 11:30 AM] maryamsuleiman48@gmail.co: MAIMOON By Maman Maama 13 Episode Thirteen : This is Me 2 Ya dakata yana kallona da murmushi a fuskarsa yace "now, tell me about yourself" nayi shiru ina tunanin mai zance mishi, sai na tuno da maganar daddy da yake ce mana (if someone tells you about their misfortunes, don't tell them about your blessings, it will makes them feel worse) Dan haka sai na samu kaina da gaya masa cewa mu fulani ne daga 'yalleman jigawa state. Muna zaune a abuja, babana yana aiki da gwamnati, mu biyar ne a gidan mu etc. Ban gaya masa wanne aikin daddy yake ba ballantana ya fahimci cewa mu masu arziki ne. Wannan shine babban kuskurena na farko. Sai da nayi shiru sannan na dago kaina muka hada ido sai naga yayi dariya a hankali yace "is that all? " nace masa "yes, that's all" yayi shiru sannan yace "OK, koma dai menene baki gaya min ba zan sani ne a nan gaba, kinsan a hankali kake sanin mutum, halayensa, likes and dislikes etc. Yanzu dai tell me, from what we discussed, what do you understand about me? " nayi shiru ina kallonsa for sometime, sai kuma wani tunani ya fado min a raina kawai sai na kana dariya, yana kallona shima da dariya a fuskarsa yace "what? Menene ya baki dariya?" nace "it's nothing really, a funny though just crossed my mind" yace "OK, share with me, let's laugh together" na nutsu a hankali nace "this is going to hurt a little, duk sanda naji an ambaci sunan yaroba, the first thing that came to my mind is fat, short, people masu katon ciki, kuma masifaffu, most of them Christians. So when u asked me what i learnt about u i realised that what i learnt is not about only u, it is about people in general. Mutane da yawa yanda ake kallon su ba haka suke ba. You for example, are neither fat not short, bansani ba dai ko kana da masifa, and u definitely are not a Christian. Ban taba sanin cewa akwai handsome yarobas ba" murmushi naji yana yi mai sauti, na dago kai muka hada ido sannan na fahimci abinda na fada, indirectly na gaya masa yana da kyau, kunya naji ta rufeni kamar inyi tsuntsuwa in tashi daga gurin. Nayi sauri nace cikin in ina "i did not meant to say you are handsome, i mean you are amm..you are.. I mean" ya katse ni da cewa "i understand, and thank you so much, i really appreciate it" dariya yake yi sosai, yayinda ni kuma na rufe fuska ta da hannayena biyu, sai da ya gama dariyarsa sannan yace "and you my dear are very, very beautiful. You are the most beautiful intelligent girl I have ever seen in my life. Akan maganar yaroba kuma ina tabbatar miki cewa ba gaskiya bace, we have fat, thin, short and tall people among us kamar kowanne tribe, akan maganar addini kuma, more than 60% na yaroba are muslims kuma we are very religious. Kin ga kamar ni for example, both bangaren uwa da uba na bamu da Christian ko daya. Kuma let me tell you something, ni tunda nake ban taba shiga north ba, dan haka duk sanda aka ce fulani abinda yake zuwa mind dina shine illiterate mutanen daji masu kiwon shanu" dariya mukayi gaba ki dayan mu sannan nace masa "duk family na babu masu kiwon shanu" muka sake yin dariya sannan yace "now we all know better " Muna haka alarm yayi beefing a wayarsa, ya duba yace "time for asr prayer" Muka mike a tare muka yi shirin alwala. Bayan munyi sallah a masallaci na riga shi dawowa inda muke zaune, na bude textbook din maths a cikin littattafan da ya dora akan table din na fara karantawa, sai gashi yazo sai ya dauko notebook dinsa ya nuna min note din da yayi forming na abinda zamuyi this week a maths. Nan muka zauna yana ta koya min har magrib sannan mukayi sallah na tafi hostel shi kuma ya tafi staff quaters. Ina shiga hostel dakin su amira na tafi muka zauna tare har lokacin islamiyya yayi, muna ta hira da ita amma ga mamaki na bata tambayeni game da Ibrahim ba, har sai da muka zo tafiya islamiyya sannan nace mata "Amira baki tambayeni yadda muka yi da Thin Tall Man ba? " sai ta ce "nasan ai zaki bani labari ne when you are good and rready" naji dadi har cikin raina. Amira is such a good friend to me, bata damu da sai na gaya mata komai ba, kuma duk sanda nake bukatar shawara she ia there for me. A islamiyya muka hadu da Hafsat amma ko kallo na bata yi ba. Ibrahim ma bai yi min magana ba sai dai duk sanda muka hada ido sai yayi min murmushi kuma nima haka kawai sai na sami kaina da mayar masa. Da muka tashi nima banbi takan Hafsat ba nayi tafiyata daki nayi wanka na kwanta. Ina jinta ta shigo tana shirin kwanciya su naomi suna yi mata magana tayi banza ta rabu dasu. Ni dai ina kwance amma na kasa bacci ina ta lissafin abubuwan da suka faru a ranar. Alaka ta da Ibrahim tana neman kawo matsala tsakani na da Hafsa kuma bana jin dadin hakan saboda no matter what, blood is thicker than water. Duk duniya bayan iyayena bani da sama da Hafsat. Amma Hafsat tana da matsala, idan na bata dama zata ce zata ke controlling dina ne akan komai, bawai akan Ibrahim kadai ba. Dan haka na yanke shawarar ko menene zai faru bazan bata damar controlling dina ba. A bangaren Ibrahim kuma though yayi admitting cewa he has feelings for me, amma baiyi magana akan soyayyaba dan haka na yanke shawarar zan ci gaba da kulashi kamar yadda ya bukata amma da zarar naga yana kokarin wuce gona da iri zan taka masa burki, and so help me God. A dan fahimtar da nayi masa na fahimci cewa shi mutun ne mai ilimi, dan haka nayi alkawarin zan mori ilmin sa, zan ke koyan karatu a gurin sa, in that way duk kanin mu zamu ke gaining kuma relationship din mu ba zai zama suspicious a makarantar ba. Da wadannan shawarwarin bacci ya dauke ni. Like, comment and share [11/7, 11:31 AM] maryamsuleiman48@gmail.co: MAIMOON By Maman Maama 14 Episode Fourteen : The Limit Washegari tun kafin assuba na tashi nayi wanka na saka uniform dina, assuba tana yi na tafi masallachi nayi sallah daga nan na wuce islamiyya. Nayi haka ne saboda bana son muyi rigima da Hafsat. Har muka fara karatu Hafsat bata zo ba. Amira ta tambayeni ina Hafsat na daga mata kafada alamar I don't know, har aka tashi daga islamiyya babu Hafsat babu labarinta, sai na ringa jin babu dadi a raina, what if she is sick? Na taho na barta. Ana tashi na kira Amira nace mata please tayi checking on Hafsat, ni class zan wuce bana son komawa hostel, tace min ba problem. Ina yin breakfast na wuce class na zauna ina karatu na har aka fara zuwa class. Karatu nake amma duk hankali na yana kan masu shigowa ina jiran inga shigowarta. Can sai gata ta shigo fuskarnan babu alamar fara'a, tana zama na mike na tafi wajenta nace "Hafsat lafiyar ki kuwa yau ban ganki a islamiyya ba?" Tayi min kallon sama da kasa tace "what is it with you idan banje islamiyya ba? Ko zaki saka shi yayi min bulalar fashi ne?" Nayi murmushi nace "that settled it, dama ina ao insan lafiyar ki, na fahimci kuma lafiyar ki kalau" na koma nayi zama na. Ina zama sai ta mike ta kama jan seat dinta sai da ta kai shi can row din baya sannan tayi zamanta. Sam bana jin dadin abubuwan da Hafsat take yi amma kuma bana son in bata chance din da zata ke controlling rayuwata. Farko Ibrahim ya fara kulata yana tsokanar ta da big sister amma sai ya lura cewa bata so dan haka ya rabu da ita. Rannan muna karatu ya tambayeni "how is your sister" nayi mamakin tambayar amma na maze nace "she is fine" he snickered kafin yace "she hates me" na ajiye rubutun da nake yi nace "no, she does not hate you, she has always been like that dama, believe me, sometimes I feel like she hates me too" daga nan bai sake yi min maganar Hafsat ba. Bayan munyi wata daya da fara term din su mommy suka zo mana visiting. Tun da aka kira mu gaba na yake faduwa dan bansan me Hafsat zata kulla min a gurin mommy ba. Muna tafiya zamu je gurinsu na matsa kusa da Hafsat nace mata "what are you planning to tell mommy? " ta kalleni da murmushin mugunta tace " that's my business, me kike ci na baka na zuba? " na hadiye yawun tsoro cikina ya kulle kamar zanyi zawo a wando amma na daure na cigaba da binta a baya kamar munafuka. Muna zuwa visitors room sai muka tarar da daada da faruk, nan da nan na manta da damuwar da nake ciki na fada kan cinyar daada ina murnar ganinta, Hafsat ma tazo ta rungume ta muna ta dariya daada tace da yaren buzanci "kai ni karku ji min ciwo, ku baku san kun zama 'yan mata bane" nace mata "haba daada, ina abin yake? Sai dai ki gaya wa Hafsat bani ba" Hafsat kuma tace "ai komai girman da zanyi bazan daina hawa cinyar kiba daada" muka sake yin dariya. Faruk yana zaune yana kallon mu nace "autan mommy ko magana babu?" Yace "au kuna gani na? Na dauka ai ni invisible ne tunda babu wacce ta kula ni a cikin ku" nan kuma muka tafi da gudu a tare muka rungume shi yana turemu wai yayi fushi. Hafsat ce tace daada wai ina mommy n ne? Daada tace "muna zuwa principal dinku ta kira ta" nan take wani gumi ya karyo min, tunda muka shigo ban ga mommy ba na dauka bata samu damar zuwa ba har hamkali na ya kwanta. Nayi saroro har wani daci nake ji a baki na. Hafsat ta dafa ni tace "yayane moon? Ko bakya murnar ganin mommy ne? " na ture hannunta na koma kusa da daada ina tambayar ta su ya Habeeb. Muna cikin haka sai ga messenger daga principal's office wai ana kiran mu nida Hafsat. Muka tashi muka tafi, nice a gaba Hafsat tana bina. Ina tura kofar office din naga mommy a zaune a kujerar gaban table din pc daga can gefe kuma Ibrahim ne a zaune yayi folding arms dinsa yana kallon mommy. Sandarewa nayi a gurin na kasa motsi, komai nawa ya tsaya hatta bugun zuciya ta. Hafsat naji tana fadin in matsa in bata guri ta shigo tunda ni bazan shiga ba. Sai a sannan lumfashi na ya dawo si kuma zuciyata ta fara bugawa da karfi, dacin da nake ji a baki na ya karu, Hafsat ta karewa office din kallo sannan tazo dai dai kunnena tace min "whatever goes up must come down" tana yi min murmushin mugunta ta shige ciki da sallam. Ba yadda zanyi dole na bita a baya. Ga mamaki na sai naga mommy ta juyo da fara'a sosai a fuskar ta ta mike tsaye ta buda hannayenta tare da cewa "come here my darlings" ban san sanda na manta da komai ba na fada jikin mommy ina murna. Ta rungume mu sosai a jikinta na wani lokaci sannan ta sake mu, muka gaisheta, muka gaida pc sannan na juya na gaida Ibrahim. Hafsat ko kallon inda yake bata yi ba mommy kuma bata lura ba dan suna magana da pc a lokacin. Sun jima suna magana amma ni hankali na ya tafi akan tunanin dalilin wannan kiran da akayi mana kuma gashi an kira Ibrahim shima, lokaci lokaci inna daga ido na sai mu hada ido da Ibrahim sai ya sakar min murmushi amma ni kam ranar bani da damar mayar masa dan gaba daya hankali na a tashe yake. Sai da suka gama hirar su sannan mommy tace " I am very proud of you Moon. Tun ina gida aka aika min da report na yadda karatunki yake progressing, naji dadi sosai. PC ta gaya min cewa ashe kun dai daita da sabon copper din da da kike complaining akansa, tace yanzu har extra lessons yake yi miki kuma kina samun cigaba sosai" bani ba hatta Hafsat sakin baki mukayi muna kallon mommy na juya na kalli Ibrahim shima sai naga bakin ya saki yana kallon ta" principal ce tayi dariya tace "au mamaki kukeyi yadda nasan kuna yin extra lessons? This is my school, I know everything going on in it. Ina da security da suke zagayawa koda yaushe, kuma kullum sai sun kawo min report cewa sun ganku kuna karatu a gaban library, sai na fara tambayar teachers din ku akan performance din moon kuma suka tabbatarmin da cewa she is doing much better than before. Dan haka na rubuta report na aika gidan ku" Mommy ta juya tana kallon Ibrahim tace masa " bawan Allah, thank you so much. I really appreciate what you are doing. Kuma ina so in nemi favor a gurin ka akan ka hada da Hafsat please. I know she can be annoying sometimes but please bear with her. Zanyi making arrangements zamuke baka allowance duk wata" Ibrahim ya kalleni, he looks compused. Ya chire glasses dinsa sannan yace "Thank you so much maam for the offer but it is not what you are thinking. Actually I am not giving maimunatu any extra lessons. In fact she teaches me sometimes, kawai muna karatu ne tare. She is very intelligent and always ahead of her class so we are both benefitting. There is no need for any allowance Maam because I am gaining as well. As for Hafsat, it will be my pleasure " ya karasa yana kallon Hafsat da murmushi ita kuma da dauke kanta sai da mommy ta harare ta sannan tace masa " thank you sir". Ya amsa da you are welcome. Mommy ma tayi masa godiya sosai sannan ya fita. Daga nan muma mukayi sallama da pc muka koma gurin su daada Hafsat tana ta zumburar baki reshe ya juye da mujiya. Ita dai bata da wani evidence da zata nuna wa mommy cewa soyayya muke da Ibrahim tunda report ya nuna cewa karatu muke yi. Nan mommy ta saka Hafsat a gaba da fada cewa lallai itama ta ringa fita muna karatun tare da ita, tace min duk sanda bata fita ba in gayawa principal nace mata to, nace mata to sannan na faki idon Hafsat nayi mata gwalo. Bayan su mommy sun tafi muka aika da kayan da suka kawo mana muka koma class. Luckly muna da period din Ibrahim. Ya shigo muka fara maths to question din da muke yi jiya munyi ta da daddare ni da shi. Muna cikin yi sai muka kakare sai yace min " maimunatu check your jotter and see how we got the answer yesterday " yana fadan haka Hafsat tana daga baya sai ji muka yi taja wani dogon tsaki. Tsit ajin yayi. Ibrahim yayi folding hannunsa a kirjinsa yace " who did that?" Kowa yayi shiru, ni nasan Hafsat ce amma nayi shiru nima. Ya sake cewa "who did that?" Fuskarsa ta nuna tsananin bacin rai wanda ban taba gani a tare da shi ba. Ga mamaki na sai kawai naji Hafsat tace masa"I am" duk ajin aka juya ana kallonta, fuskarta babu alamar tsoro ko fargaba. Kallonsa kawai takeyi ido cikin ido. Yace mata "walk out of my class and never come in in my period " bata ce komai ba babu sorry sir babu komai ta fice" ni kaina abin ya daure min kai, wai Hafsat wacce irin mutum ce ita? Da kansa yazo ya karbi jotter din hannuna muka cigaba da calculation din mu amma ni duk hankali na yana kan Hafsat. Muna nan kawai sai ga senior master nan sun taho tare da Hafsat, ya shigo ya kira Ibrahim suka fita waje. Ni dai gaba na sai faduwa yake yi kamar in bisu inji me suke cewa. Can sai ga su sun shigo har da Hafsat. Ga mamakina sai naji senior master yace mata tayi kneel down a gaban class. Hafsat tayi nan ya fara yi mata fada ta inda yake shiga ba tanan yake fita ba, wai dama staff da yawa suna kawo masa complain akan rashin kunyar Hafsat yana basu hakuri amma yau da kanta taje tayi reporting an kore ta a aji bayan ita tayi masa rashin kunya. Nan yace lallai sai ta bawa Ibrahim hakuri. A ciki ciki ta bashi hakurin yace ta dada da karfi taki. Ya dauko yawarsa ya kira discipline master. Ina jin haka na fara kuka amma Hafsat ko a jikinta. Ibrahim yace its OK shi ba sai ta bashi hakuri ba, amma senior master yace ai badan shiba ne, hakkin makaranta ne ta koya mata tarbiyya. Ni dai na kifa kaina a kan seat dina ina ta kuka na. Ina jinsu suka fara dukanta. Tun tana daurewa har saida ta fara kuka, na manta rabon da inga Hafsat tayi kuka, sannan suka kyaleta, kuma suka cewa da Ibrahim inyaga dama ya barta ta zauna in baiga dama ba kuma ya koreta. Ina jinsa ya tsaya a gabana yana kiran sunana nayi banza na rabu dashi sai ya ajiye min jotter ta ya juya ya fita daga class din, na tashi na tafi gurin Hafsat ina taba ta ta ture ni, nan naga hannunta duk ya farfashe yana jini [11/7, 11:31 AM] maryamsuleiman48@gmail.co: MAIMOON By Maman Maama 16 Episode Sixteen: Blood is Thicker than Water. Da kyar na samu na lallaba hafsat ta koma seat dinta ta zauna. Har aka tashi muka koma Hostel bata yiwa kowa magana ba. Tunda taje hostel ta kwanta take kuka har lokacin islamiyya bata fito daga daki ba, ni kuma ban zauna bata hakuri ba amma sam ranar ban fita gurin Ibrahim ba. Da dare yayi saina samu kaina da kin zuwa islamiyya. Nasan ba Ibrahim ne ya daki Hafsat ba amma still ina ganin duk a sanadin alakata da shi ne komai ya faru. Sai da na gama shiri zan kwanta sannan nazo kan gadon Hafsat na zauna na fara yi mata magana da harshen fulatanci. "Hafsat nasan yadda kike ji a ranki yanzu, kina jin tamkar duniya duka ta juya miki baya amma ina so ki sani ba haka bane. Ita duniya tana zuwa maka ne a yanda ka dauke ta, inka dauke ta da zafi to babu shakka zata zo maka da zafi. Ina so ki san cewa ni bani da komai a raina a game dake sai alkhairi, bana miki fatan komai sai na alkhairi, ban taba rukon ki a raina ba kuma kema ina rokon yafiyar ki idan na taba yi miki wani abu. Please Hafsat tunda muke ban taba neman alfarma a gurinki ba, dan Allah wata alfarma nake nema as a sister, idan kika yi min wannan nayi alkawarin bazan sake rokon wani abu a gurinki ba, please ina so komai ya wuce dan Allah kiyi abinda mommy tace, kizo muke yin karatu tare da Ibrahim, I assure you you will like him. Please sister just give us a chance" duk maganganun da nake bata cemin komai ba amma ni na tabbatar tana jina. Na tashi naje na kwanta nayi adduoi nayi bacci. Washegari ma duk mu biyun bamu je islamiyya ba, nayi wanka ina saka uniform sai ga Hafsat ta fito daga wanka ta bude fridge ta dauko fresh milk tana sha sai ta miko min tace "do you want some?" Nayi murmushi na karba nace mata "thank you" daga nan muka shirya muka fita class tare. Tun daga lokacin muka daidaita da Hafsat, muka koma yin alamuran mu kamar da. Hafsat ta fara zuwa gurin karatun mu da Ibrahim sai dai ba kullum ba, in taje su kan danyi magana kadan ba sosai ba. Shakuwa ce sosai take shiga tsakanina da Ibrahim. Kullum muna tare tun daga 3pm har magrib. Kofar library ya zama permanent gurin zaman mu. Abin mamaki shine, kusan duk interest din mu daya; a duk subject nafi son maths shima haka, sport din da nake yi shi ne basketball kawai ranar sport shima sai na ganshi a gurin basketball, duk kanin mu muna da fara'a da surutu kuma bamu da fada. Kullum in aka tashi daga class Ibrahim sai ya rakani har bakin hostel, haka zalika in aka tashi daga islamiyya ta dare ko ta assuba sai ya rakoni har sai na shiga hostel sannan zai koma. Tun ana min surutu ina damuwa har na saba. Zan iya cewa kusan komai na Ibrahim na sani, duk wani abu da yayi idan bama tare in muka hadu sai ya bani labari. Rannan muna zaune a gurin zaman mu sai sister dinsa ta kira shi a waya, ya dauka suka fara hira da yarabanci, ni sai abin ya bani dariya saboda ban taba jin yana yarabanci ba dan har manta wa nake yi shi yaroba ne, daga dukkan alama fada yake mata. Sai da suka gama sannan ya miko min yace mu gaisa, na karba tare da yi mata sallama ta amsa min da accent din yaroba. Muka gaisa babu yabo babu fallasa na mika masa wayar sukayi sallama ya kashe. Nace masa "what is her name?" Yace "Maryam" na sake tambaya "how old is she?" Yace "23" sai a lokacin na sake realising age gap din da yake tsakanina da Ibrahim. Nan yake bani labarin cewa maganar auren ta ne ya taso, ta kawo miji step father dinsu baiyi approving ba shine take so shi Ibrahim din ya shiga cikin maganar shi kuma yaki. Anan na fahimci cewa Ibrahim yana mugun yiwa step father dinsa biyayya like shi yake da final say a duk abinda ya shafesu. Ibrahim sam ba mai yawan abokai bane dan ban taba ganinsa ko jin sa yana waya da wani aboki ba. Rannan mun tashi daga islamiyya. Nace " why aren't you going into town? Yace "I have nothing to do in town, ni ban san kowa a garin nan ba, school din nan ta bani gurin zama a cikin quarters, tana bani abinci kullum" ya tsaya da tafiya ya juyo yana kallona "and you are here also, so mai zai kaini cikin gari?" Nayi murmushi naji dadi har cikin raina nace "amma tunda har kazo Abuja, why not baza kayi using this chance ba ka ga gari, it is a very nice town, besides, u never know wa zaka hadu dashi a cikin garin. Ka sani ko kayi budurwa. Dariya yayi sosai yana kallona da lumsassun idanuwansa, ya langwabe kai gefe kamar mai shirin yin shagwaba yace "ni nayi kankanta da yin budurwa. Baki ganin ni yaro ne" yadda yayi maganar ne ya bani dariya nima nace "yaro a ina? I thought 25years kake? To in bakayi budurwa ba sai ka fara furfura tukunna? Ya kalleni da serious look yace "Allah da gaske nake bani da budurwa, sai later, da nace sai na gama service amma yanzu ina tunanin anya zan iya jira kuwa? In na tsaya wasa zuciya ta zata iya fitowa daga kirjina" yadda yake maganar a hankali da yanayin da yake kallona yasa naji tsigar jikina tana tashi. Banyi aune ba sai ji nayi Amira ta kama hannuna tana jana gefe tare da cewa "to love birds, times up, goodnight sir, sleep tight " da sauri da sauri take jana muna tafiya hostel ni kuwa har yanzu ido na a kansa suke shima kuma ni yake kallo, sai da muka je bakin gate din hostel sannan naga yayi min alamun 😘 nayi sauri na dauke kaina ban kuma kallon inda yake ba. Muna shiga hostel Amira ta jani gefe "what are you doing Moon? Kinga kallon da yake miki kuwa? Shaidan fa is real komai iliminsa kema kuma komai kame kanki da saka hijabin ki ba guarantee bane na cewa shaidan ba zai yi nasara akan ku ba" raina ya baci da accusation din Amira nace mata "Amira mutumin nan fa ba saurayina bane, we are just friends, sannan kuma bama kebewa mu kadai ni dashi, kullum a waje muke inda kowa zai gan mu" tace "ni ban taba ganin inda saurayi da budurwa za'a keyin friendship ba, you are deceiving yourselves, ko makaho ya shafa fuskokin ku yasan cewa something is there" nace "saurayi da budurwa kika ce. He maybe saurayi amma ni ba budurwa bace" tayi min kallon sama da kasa tace "oh ke 'yar jaririyace kenan ko? Ji nake yanzu haka ma period kike yi? Wanne girma kuma zakiyi nan gaba bayan already hormones din adolescent sun fara aiki a jikin ki. You are a woman now whether you are full breasted or not, dole akwai attraction tsakanin ki da shi" nayi sauri nace mata "am not attracted to him" tace "really? " tayi tafiyarta ta barni. Ya kamata a ringa yin sharhi dan insan cewa ana fahimta. Suggestions and criticisms are also welcome. Lots of love [11/7, 11:34 AM] maryamsuleiman48@gmail.co: MAIMOON By Maman Maama 17 Episode Seventeen : The Letter Har na karasa dakin mu ina tunanin maganganun Amira. Tabbas duk abinda ta fada gaskiyane. I know my biology and I know I am in adolescent stage. But am I really attracted to Ibrahim? It is not as if we are in love or anything amma kuma do i even know what love is? Am I ready for this? Har na kwanta ina ta lissafi a raina. Soyayya da Ibrahim ba abu ne me yiwuwa ba. Wata tafiya ce mai tsaho. Family na, family n shi, everyone will be against us. Hatta Hafsat ta saurara masa ne yanzu saboda nace mata ba soyayya tsakani na dashi. But i know what I am feeling. Ba zance ina son shi ba saboda ban san menene son ba. Amma nasan ina son kasancewa tare dashi, yana sani dariya, kuma duk sanda bana tare dashi inajin kamar ina missing wani abu. Is this love 💟? Ni na san ba zan iya yiwa Hafsat wannan tambayar ba in ba so nake in tsokano tsuliyar dodo ba. Tambayar da nake yiwa kaina itace: if abinda nake ji shine love din, am I willing to take the chance for him? And more important, is he willing to take the chance for me? Tun daga lokacin sai na samu kaina da yin baya baya da Ibrahim. Bana barin mu hada ido dashi sam, in ya taho zai rako ni kuma nakan jawo Amira mu tafi tare, ita ma kuma Amiran ba ta ki saboda ta fahimci maganar da tayi min rannan ne ta saka nake gyarawa. Kullum in muna tafiya kuma maganar mu bata wuce ta karatu ko labari gida. Muna haka har muka fara exams komai ya koma serious, Amira ma tayi joining karatun mu, kullum tare muke karatu mu uku shi kuma Ibrahim in mun gama sai ya dunga yi mana questions muna amsawa. Ana gobe zamu yi hutu mun fito daga Exam sai Ibrahim yayi kirana, muka tafi ni da Amira. Muna zuwa muka tarar dashi yana waya gida da yarabanci. Amira da sunkuyo dai dai kunnena tana dariya, kawai sai na samu kaina da jin haushin ta. Sai da ya gama wayar sannan ya kallemu yace "so u guys are going home tomorrow, right?" Amira tace "yessir" yayi dariya yace "oh su Amira harda saurin amsawa ko? Wato kin gaji da ganin mu ko? Dadinta dai muma gidan zamu tafi muma mu huta" sai a sannan nayi magana nace "are u going home also" ya kalleni da seriousness yace "yes, i am going tomorrow, there is nothing for me to do here in kun tafi" na hadiye wani kululu da ya tsaya min a wuya na nace a hankali "ok". Mukayi shiru for sometimes sannan yace "i will see you guys tomorrow before you go" Amira ce kawai ta bashi amsa da ok sir. Daganan muka tafi hostel. Duk jikina a sanyaye nake shirin tafiya, tamkar wacce ta tashi daga jinya haka nake ji na. Washegari tun a assembly ground nake ware ido ko zan ganshi amma babu shi babu alamarsa. Gashi wannan abun da ya tsaya min a makogwaro na har yanzu yaki wucewa. Wajen karfe goma aka bude get motoci suka fara shigowa. Hafsat sai ware ido take tana neman motar gidan mu ni kuwa adduah nake yi a raina kar suzo yanzu sai na ganshi. Muna cikin haka na hango motar mu tana shigowa, na lura Hafsat bata ganta ba sai nayi sauri nace mata "Hafsat zan danje toilet kafin azo daukan mu" batare data kalli inda nake ba tace "ok" na juya da sauri nayi hanyar classes ina ta waige waigen ko zan ganshi, har naje get din hostel ban banshi ba, kuma na tarar har an rufe get din dan haka na juyo, hawaye naji mai zafi yana tahowa daga kirjina amma naki na barshi ya karaso idona saboda kar a gani a tambayeni dalilinsa. Ina tafiya kaina a kasa naji an kama hannuna an jani da sauri cikin wani class, da sauri na kwace hannuna ina neman hanyar gudu sannan naji wannan mayataccen kamshin nasa ya ziyarci hancina, na juyo da sauri muka hada ido. Ya saka complete kaki na NYSC a jikin sa, p-cap din ya juya ta tana kallon bayansa, da wata katuwar school bag a goye a bayansa. Fuskarsa babu murmushi. Mun jima muna kallon juna sannan nace"i thought ka tafi" ya hadiye yawu adams apple dinsa ya motsa sannan yace "I am sorry, an kira mu meeting ne tun safe, i was really pissed na dauka bazan same ki ba" naji dadin maganarsa har cikin raina, take naji wannan kululun da ya tsaya min a wuya ya narke yana tafiya. Nayi murmushi nima nace "I was afraid ka tafi without saying goodbye" ya matso gaf dani yanda har muna iya jin lumfashin juna, sa saka hannayensa biyu ya ruko fuskata idonsa cikin nawa yace "I will never" a can kasan zuciya ta nake jin tana min warning cewa in kwace fuskata daga hannunsa in matsa daga kusa dashi amma jikina yaki yayi responding, na kasa koda dauke ido daga cikin nasa ballantana in matsa. A hankali ya sauke idonsa daga ido na zuwa kan lips dina sannan ya fara sauko da fuskarsa zuwa ta wa. I was screaming at myself from the inside, nasan what he was about to do, nasan kuma it is wrong but I failed to stop him. Kamar wanda akayi wa shocking sai kuma yayi baya da sauri sannan ya juwa min baya yana furta "A'uzubillahi minash shaidanir rajim" sannan ba tare da ya kalleni ba yace "go maimunatu, just go" sai a sannan naji jikina da dawo dai dai, da sauri na bude kofar class din na futa jikina yana ta rawa. Ina fita na hango Hafsat tana tahowa daga hanyar hostel, daga dukkan alama ni take nema, gurinta na tafi da sauri ina kiran ta. A tare muka karasa gurin motar mu Ya Walid yana ta fada wai na bata masa lokaci, ni kuwa hankali na har lokacin bai gama dawowa jikina ba. Muna shiga mota sai ga Amira da sauri tana tsayar damu. Muna tsayawa ta bani wani littafi wai inji Ibrahim. Wani novel dinsa ne Sands of time. Abin mamakin shine ni ban ce masa ina so ba, asali ma ni ba ma'abociyar karatun novel bace. Na karba na saka a hand bag dina muka yi sallama da amira muka tafi. Kafin muje gida har na ware, Ya Walid yana gaya mana su Inna sun zo tare da Amina (wata cousin din mu sa'a ta a 'yalleman) dan haka muna zuwa gida da murnar mu muka tafi gurin mommy, daddy baya kasar a lokacin, muka tarar an shirya mana abinciccika iri iri, nan muka hadu gaba daya a falon su inna har daada muna cin abinci muna hirar yaushe gamo, Ya Walid yayi tayi mana hotuna saboda washegari zai tafi England hutun sa ya kare. Gaskiya ba abinda yafi Family dadi. Kowa yabar gida gida ya barshi. Har dare muna tare ana ta hira, ga mamakina Hafsat bata yi zancen Ibrahim ba. Sai mommy ce ma tace " Hafsat kina zuwa extra lessons din kuwa?" Hafsat tace "Eh, mommy ina zuwa" mommy tace "good, saboda bana son Moon take zama ita kadai tare da wannan malamin naku, kuma bana son in hana ta saboda naga tana benefitting" sai a sannan na gane manufar mommy ta hada mu da Hafsat, lallai ance abinda babba ya hango yaro ko ya hau dutsen dala ba zai hango ba. Sai da dare yayi sannan muka koma part din mu. Na hada ruwan wanka na shiga tub sannan na fara lissafa abubuwan da suka faru. Tabbas maganar da Amira ta gayamin gaskiya ce. Shaidan yana iya shiga tsakanin 'yan uwa ciki daya ma ballan tana mu. Kuma tabbas I am attracted to Ibrahim kamar yadda ta fada, tunda gashi dazu ya kusa kissing dina kuma ban hana shi ba. I am weak. Zuciya ta is too soft. Ko zan cigaba da alaka da Ibrahim sai na dage sosai. Daganan na tuna da littafinsa a cikin hand bag dina. Bayan na fito daga wanka da shirya cikin riga da wando na bacci sai na dauko littafin na kwanta ina dubawa kawai sai naga takarda ta fado. Ina dauka naji kanshin turarensa a jiki, na bude naga rubutun sa kamar haka. MAIMUNATU I CAN NO LONGER STOP MYSELF FROM SAYING THIS, BELIEVE ME I TRIED. MAIMUNATU I LOVE YOU. I NEVER KNOW WHAT LOVE FEELS LIKE BUT I AM 100% SURE THAT THIS IS IT. I AM NOT SURE IF YOU FEEL ABOUT ME AS I FEEL ABOUT YOU. PLEASE MAIMUNATU, IF MY ANSWER IS NO, CALL THE NUMBER AT THE END OF THIS LETTER JUST SAY NO, THEN I WILL ASK FOR TRANSFER BEFORE YOU RESUME. I CAN'T KEEP SEEING YOU KNOWING YOU WON'T BE MINE. YOURS IN LOVE IBRAHIM An zo gurin, will Moon say yes knowing the consequences or will she say no knowing she will never see him again? [11/7, 11:34 AM] maryamsuleiman48@gmail.co: MAIMOON By Maman Maama 18 Episode Eighteen : The Reply Na jima ina karanta takardar hannuna ina maimaitawa. Amma Ibrahim baka yi min adalci ba, yanzu me kake so ince maka? Yes or No? Ni dai nasan koda wasa bazan tunkari Hafsat da sunan neman shawara ba. Na saka karanta takardar kamar me saka ran ganin ganin chanji a rubutun. Tabbas handwriting dinsa ne, kuma kamshin turarensa ne. Na kai ido na kan number daya rubuta a kasan takardar lokaci daya na haddace ta. Na ninke takardar na mayar cikin littafin, a lokacin Hafsat ta shigo tana hamma, ta kalleni tace " kasa, a gidan ma sai kinyi baccin wuri" nayi dariya ban bata amsa ba saboda I am not in the mood. Ina kallonta tana shirin wanka na dauko littafin Ibrahim na fara karantawa saboda nasan sa idon Hafsa, tana shiga wanka na rufe littafin na saka a kasan filona na kwanta akai. Har ta fito ta shirya ta kwanta banyi bacci ba ina ta sakawa da warwarewa. What should I do? Ni nasan ina son Ibrahim har cikin rai na, wannan bani da tantama akai, amma nasan abu ne mai wahala kasancewar mu tare. Bani da problem da daddy sai mommy nake ji, kallo daya idan tayi min sai na gwammace ban taba ganin Ibrahim ba, Inna da baffa da kawunnai na na 'yalleman zasu iya haka rami su binne ni akan su barni in auri Ibrahim. Ina son family na fiye da komai dan haka maganar inbijire musu ma bata taso ba. A daya side din kuma inna cewa Ibrahim no nasan ba wasa yake yi ba akan maganar barin school din mu, kuma bazan sake ganin saba har abada sai dai wani ikon Allah. Anya zuciya ta zata iya daukan haka kuwa? Anya zan iya ci gaba da rayuwa ba tare da shi ba kuwa? What should I do? A haka bacci barawo ya dauke ni. Cikin bacci nayi mafarki wai gashi muna tafiya da family na a mota a nata hira ana dariya sai naga Ibrahim yana tafiya a kasa shi kadai, sai yayi mun murmushi nima nayi masa, mun wuce shi kenan sai ya fara bin mu da gudu yana kirana a haka har muka yi nisa na daina ganinsa. Na farka a firgice ina addu'ah. Na jima a zaune ina ta maimaitawa a raina cewa 'it is only a dream, you will see him again". Ina tashi na daga pillow na na dauko letter dinsa na je na bude locker din textbooks din mu na saka ta acikin wani biology textbook na mayar na rufe. Hutun sam banji dadinsa ba, kona saki raina da na tuno da takardar da take cikin locker dina sai inji gaba na ya fadi. Rannan na fito daga wanka ina shirya wa kawai na kalli mudubi sai na fara wondering what happenned to me? Yaushe har nayi girman da zan fara tunanin soyayya? Yaushe daada ta daina goyani? Ni ba shekaru ba ni ba girman jiki ba amma na dora wa kaina wahala? Na tuno daddy da yadda zai zama disappointed in yaji labarin abinda yake faruwa. Da wannan tunanin na saka kayana direct na tafi part din daada, luckily na tarar tana bacci, banyi wata wata ba na dau wayarta na saka number din Ibrahim. Sai da ta kusa katsewa sannan ya dauka yace "hello" da muryar bacci. Dif duka nepar jikina ta dauke na tsaya sororo da waya a kunnena na kasa magana. Ya sake cewa "hello, who is there?" Still na kasa magana kuma na kasa kashe wayar. Ina jinsa yayi tsaki yana kunkuni kasa kasa ya kashe wayar. Na durkushe a kasa ina jin haushin kaina. What has Ibrahim done to me? I can't even say no to him. Tun daga ranar ban sake gwada kiransaba kuma har hutun mu ya kare banyi making decision ba. Ranar da zamu koma haka kawai naji ni kamar marar lafiya, mommy duk ta dauka bana son komawa ne har tana yi min fada. Kamar tasan abinda yake raina tace "Moon zaku cigaba da lessons din da wannan copper din?" Na kalleta truthfully nace "I don't know mommy" tace "ok in zaku cigaba ki tabbatar kuna zuwa tare da Hafsat, I don't want you staying alone with him" na sunkuyar da kaina kasa nace "ok mommy". Da haka mukayi sallama muka tafi. Motar mu tana packing na hangoshi a jikin staff room, ya jingina da jikin katanga ya rungume hannayensa a kirjinsa, idonsa akan inda motoci suke ajiye students. Muna fitowa Hafsat ta matso kusa dani tace "wow, he can't wait to see you Moon, can he?" Nayi banza na rabu da ita ina fito da bags din mu, na sake matsowa tace "au ba zaki bani answer ba? Ko saina fada da karfi ya Habeeb yaji? Maybe they can even be friends" na ajiye jakar hannuna nace mata "what exactly do you want to know?" Ta tsare ni da ido tace "is it going to be a Yes or a No?" Nan take naji daci a bakina, so Hafsat ta karanta letter din Ibrahim kenan, amma ban taba ganin mutum mai sa ido a rayuwata irin Hafsat ba. Na tsaya kawai ina kallonta ita kuma tana yi min murmushin mugunta. Ya Habeeb ya zagayo yace "Hey, zaku fara fadan tun kafin in tafi ko?" Hafsat tace "No, yaya Habeeb ba fada muke ba, we are just catching up akan harkar makaranta" Ya Habeeb ya kalleni yace "is she maltreating you, I know Hafsat can be bossy at times" na kalle shi kawai sai naji kwalla tazo min, na rungume shi sai kuka, nayi kuka na mai isata sannan na sake shi, sai a lokacin na lura ashe fada ya ke yiwa Hafsat ita kuma sai rantse rantse take yi cewa sharri nake yi mata babu abinda tayi min. Su duk basu san me yake damuna ba. Ina gama share hawayena na dauki handbag dina na wuce hostel. Ina zuwa hostel ko gado na ban gyara ba na dauko wani pink handkerchief dina mai ratsin purple, na duba locker dina da dauko permanent marker na zauna nayi rubutu a jikin handkerchief din na barshi ya bushe sannan na ninke na fita daga hostel din da sauri. Hanyar staff room na nufa ina tafiya ina share kwalla a ido na, a hanya muka hadu da Hafsat ta fara yi min bala'in na taho na barta da daukan kaya, ban kula ta ba na wuce na bini da kallo. Ina shiga staff room na ganshi yana arranging desk dinsa ya dago da sauri yana kallona, ya taho kamar zaiyi min magana na wuce shi na ajiye handkerchief din hannuna a kan desk dinsa na juya na fita. Ina kallonsa yayi sauri ya dauki handkerchief din sai naga murmushi ya baiyana a fuskarsa. Abinda na rubuta masa shine "I DON'T KNOW WHAT THE FUTURE HOLDS, BUT I WANT TO FIND OUT WITH YOU" na juya na koma hostel. Washe gari muna shiga class naga students a tsaye a gaban board suna karanta wani abu, na buda su na shiga, rubutun Ibrahim ne akan board "THEN I WILL BE THE HAPPIEST MAN ON EARTH" na juya naje nayi zamana a seat dina. Ina zama sai ga Hafsat ta zo ta tsaya a gaba na tace "then it is a yes" na kalleta cikin ido nace "yes, it is" Wow, then the battle has begun. [11/7, 11:35 AM] maryamsuleiman48@gmail.co: MAIMOON By Maman Maama 19 Episode Nineteen : What's Next? Hafsat ta tsaya saroro tana kallona. Sannan ta sunkuyo saitin fuskata tace "yanzu ke Moon kina ganin har kinyi girman da zaki fara soyayya? Har kina ganin kin isa ki yanke wa kanki hukunci? Har kina ganin kin san menene dai dai menene ba dai dai ba?" I was ready for her dan haka ko gezau banyi ba nace "7 years ago, sanda nace inna girma ina so in zama neorosurgeon murna kuka yi ta tayani kuna cewa nayi making right decision, ta yaya kuma yanzu zaki ce min ban isa in making decisions ba? I know what I am doing I just need u to support me please" Tayi min wani kallon wulakanci tace "lallai yau na tabbatar baki da hankali Moon" tayi tafiyar ta ta zauna. Nayi shiru ina tunani, lallai Hafsat bata gama sanina ba har yau. Mutane da yawa suna cewa I am a genius, amma ni ban yarda ba, na san dai ina da brains kuma I am going to use it here. Tabbas nasan ina son Ibrahim amma hakan bazai sa in barshi yayi meddling with my life ba. Dole zanyi mana katanga tsakani na dashi. I said yes to him saboda bana son ya bar makarantar kamar yadda yayi threatening amma hakan ba yana nufin I will let him romance me ba. In dai har yana sona zai jira ni har in gama sec sch sannan we will see what will happen. Na gama tsara komai yadda nake so ya kasance. Abu na farko shine; ba zan ke bari muna kebewa ni da shi ba alone. Dan haka ana yin break na tashi a class nayi announcing cewa ina gayyatar duk wanda yake da ra'ayi zamu ke karatu tare. Kusan rabin class din suka ce suna so, nan muka zauna muka tsara timetable ta karatu, kullum da akwai subject din da zamukeyi, za muke fara wa 3pm mu gama 6pm. Nayi inviting duk class din ne saboda nasan kullum dole wani zai zo, baza mu kasance daga ni sai Ibrahim ba. Abu na biyu da nayi shine na fito da duk textbooks dina na jefa akan desk dina yadda babu yadda za'ayi mutun ya zauna akai, no more sitting on the desk tactic. Iyakacin sa sai dai ya tsaya a gaban board ya gama abinsa ya fita. The next thing da nayi shine ana tashi a school na tafi gurin HOD na Islamic studies na kai masa complain cewa ina so a raba mana class din islamiyya ni da Hafsat, ina so a mayar dani B class. Da kyar na samu ya amince shima saboda muna mutunci dashi sosai tun jss1. Nasan in Ibrahim ya fahimci abinda nayi he will be mad but I am ready for him. Ai kuwa sanda ya fahinci na chanja class a islamiyya he was furious. Muna zaune muna karatu a new class dina sai gashi ya shigo ya bawa yasaiyadin mu hannu suka gaisa sannan yace "I will like to see one of your students please" nasan ni yake nema amma sai naki dago kaina na dukufa ina karatu, ya sayyadin yace masa "kadan yi hakuri in ba emmergency bane yanzu muna karatu in mungama sai tazo" Ibrahim yayi masa godiya ya fita. Sai da naga saura less than ten minutes mu tashi kuma na riga na biya karatu na sai na tambayi yasayyadi nace zan je toilet, yace min ai it is almost time inna tafi inyi zamana kawai, dama haka nake so dan haka na dauki books dina sai hostel. Hafsat tana zuwa ta fara tuhumata akan menene yasa na chanja class nace mata its none of her business. Ranar da Ibrahim yazo mana maths yaga na cika gaba na da texbooks, kawai ya tsaya yana kallona ni kuwa na dauke kaina kamar ban san yana yi ba. Duk yadda yaso in kula shi naki yarda har period dinsa ta fita, yazo ya tsaya a gabana yace "see me immediately after school" nace "yes sir" amma ko kadan banyi niyyar zuwa ba. Da yamma muka shirya wajan mu biyar muka fita karatu. Muna zuwa muka yi arranging chairs muka samo wani babban table muka saka, mun fara karatu kenan sai ga wasu ma sunzo, haka muka hadu wajan mu goma, muka shiga library muka karbo aron books da syllabus din term din muna tsara yadda zamu fara karatun sai ga Ibrahim. Tsayawa yayi yana kallon mu fuskarsa cike da mamaki. Yayi kwalliyarsa da sabuwar shadda sai, kamshi yake yi. Ya jingina da jikin library ya rungume hannayensa a kirjinsa ya zubo min ido, kallo daya nayi masa na dauke kai naci gaba da abinda nake yi. Amira ta taba ni tace "mutumin ki fa ke yake nema" nace mata "I know" na cigaba da karatu na, can ta sake cewa "duk wannan kwalliyar fa ke akayi wa" na sake ce wa "I know" taga dai bani da niyyar kulata ta rabu dani, ita Amira bata san zafin da nakeji a raina ba, I missed him alot amma still I want to be strong, na leka ta saman littafina ina kallon shi naga ya dauko wayar sa yana dannawa, nan na samu damar kare masa kallo. Sabuwar shaddar sa kalar ash mai haske ta sha dinkin tazarce da aiki kalar ash mai duhu, hular sa da takalmin sa duk ash mai duhu ne, fatar sa tayi tas. Ina kallonsa kawai sai tsintar ido na nayi acikin nasa, nayi sauri na dauke kaina. Sai kuma ya taso ya karaso inda muke, ina jinsa yana tsokanar Hafsat wai taje gida ta kara kiba, ga mamaki na sai naji ta kulashi tace shima yaje gida ya kara fari, ya dawo kusa da Amira yace mai ta kawo masa daga gida. Kusan saida yayi wa kowa magana a gurin amma banda ni, nima kuma bance masa komai ba. Washegari muna cikin class sai gashi yazo yace da teacher din mu zai karbi sako a guri na. Ina jin haka nayi sauri nace "I gave Mr Victor to give to you" ya tsaya yana kallona, ni dashi duk munsan babu wani sako da zai karba a gurina, can yace "OK thanks" ya fita fuskarsa babu alamar annashuwa. Ranar da daddare muna zuwa islamiyya naga 'yan A class suna komawa hostel, na tambayi dalili sai suka ce yasayyadinsu yace baya jin dadi bazai samu damar zuwa ba. Kusan 3 weeks muna haka da Ibrahim, he was so frustrated nima haka, har na fara tunanin anya zan iya kuwa? I am not as strong as I thought I was. San da mukayi wata daya daddy yazo mana visiting tare da yaya Walid, naji dadin visit dinsu saboda I was in need of little love, kuma na samu sosai a gurin daddy, mun dade muna hira kafin su tafi. A ranar da daddare bayan mun tashi daga islamiyya sai yasaiyadin mu tsayar dani akan maganar saukar mu, by the time da muka gama magana dashi almost kowa ya tafi, shima yana fitowa yayi tafiyarsa, nan naji tsoro ya kama ni, ina tafiya ina waige waige. Kamar daga sama naji an fincikeni an hada da jikin katanga, na takarkare iyakacin karfi na zan yi ihu aka toshe bakina da hannu. Duhu ne gurin dan haka na kasa ganin fuskar wanda ya rike ni, jikina sai karkarwa yake yi kamar mazari. A hankali na fara nutsuwa sai a lokacin naji kamshin sa. A bangare daya na zuciya ta naji dadi cewa ba barayon mutane bane ko dan yankan kai, a daya bangaren kuma wani tsoron ne ya shige ni, what is he going to do to me? Nan na fara kokarin kwace kaina daga hannunsa amma maimakon ya sake ni sai ya saka duk kannin jiki sa ya matse ni a jikin bango, na saka hannayena duka biyun na tattara karfina ina tura kirjinsa amma ko motsi baiyi ba, kawai sai na saka kuka, na kifa fuskata akan kirjinsa ina ta kuka na, a hankali a sunkuyo fuskarsa dai dai kunnena yace min "why do you say yes?, tunda kinsan ba kya sona mai yasa kika ce min you want to walk the path to the future with me? Why are you playing with me? Do you have any idea what you are doing to me?" Ya jera min tambayoyin da nasan ba zan iya amsa masa su ba, yasa hannu yana kokarin dago fuskata amma fir naki yarda, ya hakura ya rabu dani, ya sake cewa "ni kawai so nake in san me yasa kika amsa min bayan kinsan bakya sona, kina gaya min zan barki kiyi tafiyarki. You don't love me, right?" A hankali na girgiza kaina, ya saka hannayensa biyu ya dago kaina yana kallon cikin ido na yace "look into my eyes and tell me you love me" wasa ma kenan, na dauke ido na daga cikin nasa nace "I can't" "you can't what" "say it" "say what" "the L word" daga kirjinsa naji sound din dariya amma bata fito bakinsa ba. "Then why are you avoiding me" nan ma shiru babu amsa "are you ashamed to be seen with me?" Nayi sauri nace "No" "please just tell me why" sai da na dauki some seconds sannan na fara magana "I am just not ready for this, bana so in bata rayuwa ta, ina so in kara girma, at least in gama sec sch, am sorry ban gaya maka haka ba, i just don't want you to go" ya sake dago fuskata yace "look at me, I will never mess up your life, never. I love you and I will wait for you to be ready, no matter how long, kawai ina so in tabbatar cewa kina sona kema" sai kuma ya danyi dariya kadan "but tunda kin kasa fadar L word a gaba na dole in hakura da gyada kan" kunya ce ta kara kamani na cigaba da kokarin ture shi yana dariya, na hakura na barshi, sai da ya gama dariyarsa sannan ya sake rage murya yace "I missed you, please ki daina min abinda kike min, please ko yaya ne kike bani lokacin ki, I promise I will behave, bazan kuma yi miki maganar L ba, please ki daina share ni, I will loose my mind, ki gaya min duk abinda ba kya so zan daina, I promise" ina jinsa kuma inajin maganar sa har cikin raina, a hankali nace "ka daina tabani, babu kyau" ina rufe bakina ya shika ni yace "done, I will never touch you again" muka yi shiru for sometimes, nace "zan tafi, dare yayi" yace "ok, I will see you tomorrow in class" [11/7, 11:35 AM] maryamsuleiman48@gmail.co: MAIMOON By Maman Maama 20 Episode Twenty : The Goodbye Ibrahim ya cika alkawarinsa, mun bar soyayyar mu very low, ban da occasional smiles babu wani abu da zai nuna maka cewa akwai wani abu a tsakanin mu. Har muka gama second term muka koma third term. Muna shirye shiryen rubuta qualifying exams ne rannan a class ake zancen in mun tafi hutu baza mu dawo mu tarar da coppers ba, sai dai maybe mu tarar an kawo wasu. Sam na manta cewa shekara daya ake yi ana service, nan take naji kaina yana juyawa. Amma Ibrahim bai taba min wannan maganar ba, dole in zauna inyi tunani. Wato shi nufinsa sai dai kawai in mun dawo in neme shi in rasa ko? Amma dai bara in ga gudun ruwansa tukun. Wasa wasa har saura one week muyi hutu Ibrahim bai ce min komai ba. Ranar akayi taro akan shirye shiryen saukar alqur'ani da zamu yi, an saka ranar hutu ranar za'ayi bikin sauka. Duk an tura wa iyayen mu IV. Ana cikin taron ina kallon Ibrahim yana ta kallona yana yimin murmushi amma na hade rai naki mayar masa. Hafsat sa ido tana lura dashi tace min "yau da alama tsimin ya tashi" nayi banza na rabu da ita. Ana tashi daga taron ya taho gurin mu yace min " I want to see you, please" nace masa "OK, ai gani ko" ya sunkuyo saitin fuskata yace "alone" daga haka ya juya ya fice daga hall din. A raina nace lallai wannan mutumin, amma bance komai a fili ba saboda su Hafsat 'yan bani na iya 😎..Bayan sa nabi na tarar dashi a staff room a zaune shi kadai saboda duk malaman are busy. Ya nuna min kujera na zauna ina ta shan kanshi ni lallai fishi nake yi. Yace "wai wannan fushin na menene Maimunatu?" Na kara tsuke fuskata ina turo baki, dariya ma abin ya bashi yace "ni dai bansan abinda nayi ba, duk dokokin da aka kafa min ina binsu, to me nayi ne ni Ibrahim?" Na kalle shi da fada nace "sai yaushe kake planning zaka gaya min in ka tafi gida ba dawowa zakayi ba?" Nan take murmushin fuskarsa ya bace. Ya taso ya dawo kusa dani ya zauna yace "maimunatu ina so muyi maganar amma so nake in tsaida tsayayyiyar magana tukun" nace "bangane ba" yace "bana son komawa Ibadan, ina son in nemi aiki anan ko cikin abuja ko school dinnan, inda dai zan ringa ganin ki. To nayi wa principal dinku maganar inda akwai vacancy inaso amma bata bani amsa ba tukun, to ni tunda nazo ba shiga cikin gari nake yi ba sosai sai last two weeks muka fara zuwa da victor muna raba CV din mu. In har na samu job a Abuja zan dawo nan da zama saboda ke, in ban samu ba kuma babu yadda zanyi maimunatu dole in koma Ibadan" naji dadin maganar sa har cikin raina, cewa zai iya dawo wa Abuja da zama saboda ni alhalin family dinsa suna Ibadan. Nace "amma familyn ka fa? Don't you want to go back to them" yace "family na ina zuwa ganin su ai duk weekend. Bature yace home is where the heart is, and u are my heart maimunatu. I want to be with you" na sunkuyar da kaina kasa ina lissafin maganar sa. Tabbas ina son zamansa a abuja saboda bana son yayi nisa dani amma kuma family dinsa fa? Nayi musu adalci? Amma kuma ta wani bangaren samun aikin sa a abuja ai cigaban sane, duk da bansan salaryn sa na Ibadan ba amma nasan nan nan sai yafi na can. Wata idea ce tazo min raina kuma nayi alkawarin zanyi trying. Muna zaune wasu staff suka shigo suna kallon mu, sai kawai naji ban damu ba. It doesn't matter tunda barin school din ma zaiyi. Tun daga ranar kullum muna tare da Ibrahim gani nake kamar in muka rabu bazan sake ganin saba, shi kuma kullum yana assuring dina da cewa koda bai samu aiki a abuja ba to kullum zai ke zama a hanyar zuwa gurina. Ana saura kwana biyu hutu mun fito daga exams muna zaune akan veranda ni da Ibrahim muna ta hirar mu muna dariya, yanzu ban damu kowa ya ganmu tare ba tunda it's almost over. Sai nake tambayar shi maganar auren sister dinshi Hadiza, yace "Hadiza ta jama kanta ai, yanzu wani cousin din mu za'a aura mata kuma bata so, data hakura da wancan ta fito da wani da shikenan ai" na sunkuyar da kaina nace "do u think it is easy?" Yace "what?" Nace "idan kana son wata kuma parents dinka suka ce no, do u think it will be that easy ka hakura da ita ka samu wata?' Yanzu ya fahimci cewa ba maganar Hadiza nake yi ba, ina magana ne akan abunda zamu iya fuskanta anan gaba. Yayi shiru bai ce min komai ba, har nayi tunanin ba zai amsa ba sai kuma yace "they will not say no. Maganar Hadiza is different, wanda take so ba mutumin kirki bane. They only need to get to know you zasu soki sosai" nayi murmushi a raina ina cewa naka mai sauki ne Ibrahim nawa nake ji, a fili kuma sai nace "idan kuma basu soni ba fa?" Yace "they will" na sake cewa "what if they don't?" Kamar wanda aka mintsina sai ya mike tsaye yace "dan Allah ki bar maganar nan, we will cross that bridge when we come to it " a raina nace Allah ya bamu ikon tsallake wa lafiya. Dama da akwai plan din da nake shiryawa na abinda zanyi. Na jawo school bag dinsa da ya ajiye a tsakanin mu na bude na fara yi masa bincike, ya dawo ya zauna yana cewa "me kike nema a jakar tawa kuma" nace "wasikar budurwar ka nake nema" yayi dariya yace "ai ba"a nan zaki samu ba, kin ganta a nan" ya fada yana zaro pink and purple handkerchief dina daga aljihunsa. Nasa hannu na rufe fuskata ina dariya nace "kai yanzu ajiye shi kai?" Yace "eh mana, kuma ajjiyarsa zanyi tayi as a reminder" nayi shiru ban bashi amsa ba, yace "seriously, what are u looking for a jaka ta?" Nace "CV dinka nake nema" yace "me zakiyi da CV dina" nace "ajiyewa zanyi nima as a reminder" yayi dariya yana karbe jakarsa daga hannuna. Nace masa "da gaske so nake in ajiye duk sanda na tashi rubuta CV sai in duba taka" ya jima yana kallona da alama bai yarda da bayani na ba sai kuma ya daga kafada ya dauko ya miko min, na karba nace "nace thank you " "you are welcome" Ranar hutu daga ni har shi kamar marasa lafiya muka zama, tun da sassafe na fito muna tare dashi har akayi assembly aka fara shigo wa daukan students. Yace min "kina da number dana baki" nace "yes" yace "you can call me anytime" nace "to" duk mun rasa kalaman da zamuyi sallama dasu kawai dai muna enjoying company din each other. Ina ta addu'ah a raina Allah yasa kar azo daukan mu da wuri sai na hango motar gidan mu tana shigowa, gaba na ne ya fadi saboda naga motar mommy ce sabuwar benz dinta, bana son Ibrahim ya ga motar tunda har yanzu bai san gidan mu muna da kudi sosai ba. Nace "ga daddyn mu chan yazo, would you like to meet him?" Nan da nan naga fuskarsa ta chanza alamar tsoro, yace "no, not now" dama nasan haka zaice shi yasa na gayyace shi din. Yace "look at me " na daga kai ina kallon cikin idonsa da yayi kalar tausayi, yace "please in kinje gida call me, da akwai abubuwa da nake so in gaya miki" nace masa to amma still ya kasa tafiya nima kuma na kasa tafiya, sai ga Hafsat nan tazo tana kirana, dole na dauke ido na daga cikin nasa na dau hanyar gate ina hadiye kuka na. Ina jiyo shi yana bawa Hafsat amana ta, ga mamakina sai naji ta biye masa har da dariya. I am very sleepy yau, in kunga typing errors kuyi hakuri [11/7, 11:36 AM] maryamsuleiman48@gmail.co: MAIMOON By Maman Maama 21 Episode Twenty one : The New Job Bayan mun koma gida da sati daya daddy ya zo. Ranar duk mun hadu a main falo muna kallo, ina kwance a cinyar mommy tana yi min tsifa, Hafsat kuma suna playing chess ita da Ya Habeeb wanda yanzu ya gama SSCE dinsa yana jiran result, da Faruk. Ya Walid ne kadai baya nan tunda su basu samu hutu ba. News aka fara daddy ya karo volume muma duk sai hankalin mu ya karkata akan TV din. Titi aka nuno chike da hold off ana ta hayaniya can gaba kuma wasu motoci ne guda biyu suka yi crossing suka rufe titin ruf babu hanyar wucewa. A kusa da motocin kuma wasu samari ne sun takarkare suna ta jubgar junansu kamar Allah ne ya aiko su. Camera tayi zooming fuskokinsu ga mamakina sai naga daya daga cikin su dariya yake yi shi kamar game ne abin a gurinsa, dayan kuma sai huci yake yi da alama dariyar dayan ce take kara kular dashi kuma daga dukkan alama me dariyar yafi shi karfi. Daddy ne yayi gyaran murya yace "Habeeb wannan ba Sultan ba ne?" Ya Habeeb ya dan kalli TV yace "Hmm shine fa daddy, yana nan sai abinda ya kara gaba" mommy tace "ai dan baka zama sosai ne, mu yanzu ai mun saba da labarai akan Sultan, kusan kullum zancen kenan. Ni na rasa wanne irin yaro ne wannan. Daga yau a kama shi da drunk driving, gobe fada akan titi ya kama yaran mutane yayi ta jubga, jibi kuma sai kaji ance yaje yayi terrorizing unguwa. Kuma wai an rasa mai daukan mataki akan sa, wannan wacce irin rayuwa ce" daddy yace "ba laifin sa bane, laifin maimartaba ne. Ni bansan yaushe ya chanza hali ba, mutum ne shi mai zafi sanda muna makaranta" da sauri muka hada baki ni da Hafsat "daddy dama sarki abokin kane" yayi dariya yace "ba abokina bane, kawai dai munyi makaranta tare, department din mu daya dashi a Oxford, first degree da second, amma ba abokina bane, tunda ni talaka ne a lokacin su kuma 'ya'yan masu kudi ne. Muna haduwa dai in za'ayi taron Nigerian students. Ni lokacin tsoro yake bani, wato kato ne gashi baki ga zafin zuciya" duk mu ka kwashe da dariya. Ya Habeeb yace "ah bara mu je mu siyo alkyabba, ai ni daga yau na zama dan sarauta tunda babana sunyi makaranta daya da sarki" nan ma dariyar muka same yi, bayan anyi shiru daddy ya shigaba da cewa "bayan mun gama masters ne, munyi applying for PhD sai na daina ganin sa, na tambaya akace sun dan samu problem ne da babansa akan yarinyar da yake so, shine uban ya chire shi yace a daina karatun. Nasan yarinyar dan ina yawan ganin su tare, balarabiya ce, I can remember in na gansu har dariya nake yi, shi bakikkirin ita fara tas, kyakykyawa ce sosai" muka yi dariya ganin yadda mommy ta turo baki kamar yarinya. Na juya na sake kallon screen din TV naga police sun zo scene din an raba fadan, wanda aka kira da Sultan ya kama police guda daya da kokawa sai da suka taru akan sa sannan suka saka masa ankwa, He was still grinning. Anan camera ta tsayar da hotonsa, reporter ta fara lissafo irin crimes dinsa amma da an kama shi za'a sake shi saboda dan sarki ne. Na kura masa ido ina kallonsa. Kyakykyawa ne first class, kana ganin sa kaga half caste, fatar sa golden brown mai kwalli da daukar ido. Idanun sa dara dara farare tas, hankinsa kamar an auna da fuskarsa, lips dinsa tamkar ya shafa jan baki. Bashi da tsaho sosai amma fa a murde yake dan sai da police uku suka hadu sannan suka iya rike shi. Na dauke kaina ina aiyana yadda rayuwar sa take. What is his story? Kawai na samu kaina da tambayar daddy "daddy to an yi auran?" Yace "auran wa?" "Auran balarabiyar, naga wannan kamar halfcast ne" daddy yayi shiru yana kallon hoton sultan a TV sannan yace "gaskiya I can't say ko anyi auran ko ba'ayi ba" mommy tace " anya kuwa anyi? Dan na taba shiga fadar amma matar sarkin da na gani bahaushiya ce, and she is far from being beautiful, kuma na lura Sultan din dan ta ne dan lokacin tana ta fada wai an tafi dauko shi daga airport da wrong car, specifically ya fada yace ga motar da yake so a dauko shi amma aka ki. Gaskiya ina ganin kamar itace ta bata sultan" daddy ya girgiza kai yace "Allah ya kyauta". Washe gari da sassafe na tashi, na shiga kitchen naga cook din mu tana ta kokarin hada breakfast. Pancakes na yi irin yadda naga mommy tana yiwa dadday, na hada masa coffee shima irin yadda yake so. Na hada da cup da komai akan tray na hau saman daddy. A balcony dinsa nagan shi kamar yadda nayi tsammani. Yana zaune yana karatun news paper. Na durkusa na gaishe shi sannan na koma falonsa na dauko stool na dawo na dora masa tray din da na kawo akai. Na zauna a kasa a gefen sa. Sai da ya fara shan coffee dinsa sannan yace "ya akayi ne maimunatu?" Na sunkuyar da kaina na kasa magana. Ya ajiye cup din hannunsa ya bani dukkan attention dinsa yace "You know I can do anything for you, in dai bai sabawa addini ba, just say it and it will be done" a hankali na fara magana "daddy ba akai na bane" "OK, akan waye?" "Dama wani copper ne a makarantarmu" sai kuma nayi shiru "ina jinki" "dama wani copper ne a makarantar mu, to sun gama service dinsu wannan watan, to daddy mun saba dashi sosai kuma yana taimaka mana sosai, gashi soon zamu fara SSCE" na sake yin shiru kirjina yana bugawa, saboda is simple amma baya tolerating nonsense, bai ce komai ba amma ni yake kallo, naci gaba "daddy so nake yi ko zaka saka baki a bashi aiki a school din mu" yayi shiru yana cigaba da shan coffee dinsa, na daga kaina naga idonsa yana kaina, da alama studying dina yake yi. Can ya nisa yace "maimunatu shi copper din shi yace miki yana son aiki a school din ku?" Nayi sauri nace "eh daddy shi yace yana so" "kuma yace ki nema masa?" Na girgiza kaina, " yace dai yayi wa pc din mu magana in da akwai vacancy yana so" "then that's all, in suna da vacancy, in he is as good as you said he is, za su bashi ba sai nayi magana ba" nayi shiru kuma naki tashi daga durkushen da nake, daddy yace "menene qualifications dinsa?" Nayi sauri na zaro CV din Ibrahim dana boye a jikin rigata, daddy ya karba da mamaki a fuskarsa yace " How did you get his CV?" Nan fa ido na ya raina fa ta, idonsa har yanzu a kaina yake kuma ni kaina nasan nayi alamar rashin gaskiya. Ya sake tambaya "Maimunatu how did you get his CV?" Nace " He just mentioned it in class cewa yana neman aiki a school din mu, to rannan na ari book dinsa sai naga CV din a ciki shine nayi tunanin in kawo maka ko zaka taimaka masa" na fada bakina yana rawa, a nutse daddy yace min "you are lying" wani daci naji a cikin bakina, nan danan zuciyata ta fara bugawa a cikin makogwaro na. "What tribe is he?" A sanyaye nace "he is a Muslim dad" yace "OK, naji musulmine, what tribe is he" can kasan makoshina nace "yaroba" kalmar yaroban kamar wani garwashi naji ta a bakina. Daddy ya ninke takardar dana bashi ya ajiye sannan yace "Hafsat ta tashi?" Nace "a'a" yace " tashi ki tafi, in Hafsat ta tashk ki turo min ita" jiki a sanyaye na tashi na koma saman mu. Ina shiga toilet na shiga na rufe kaina, nan da nan hawayen da nake rikewa suka fara zuba. I was a fool to think I can fool daddy. Shikenan tawa ta kare, yanzu da Hafsat taje zai tambayeta ita kuma zata gaya masa gaskiya, shikenan mommy tana zuwa zai gaya mata ita kuma zata sakani a turmi da daka. Hafsat ce tayi knocking kofar tana jira na, na wanke fuskata na fito ina sussunne fuska. Tana kallona tace "kuka kuma da sassafen nan?" Nayi banza na rabu da ita. Sai da ta fito tana saka kaya na gaya mata kiran daddy, ta zura hijab dinta zata fita na sha gabanta nan da nan wani kukan ya taho min tace "lafiyar ki kuwa Moon?" Cikin kuka nace "Hafsat please, akan maganar Ibrahim daddy zai tambaye ki, dan Allah kar kice komai" tana kallona da mamaki tace "saboda me?" Tambayar ta ta bani mamaki nima, ban gane saboda me ba? Ita ai tasan saboda menene. Tacigaba da cewa "bakya ganin cewa it will be easier for you both in aka gayawa daddy in za'ayi yace eh in kuma baza'ayi ba yace a'a? The longer kuka jira the more painful it will be in aka hana ku aure, ni bazan ce da daddy komai ba, it is not my call, amma shawara ce nake baki" daga haka ta juya tayi tafiyar ta. Sam Hafsat bata gaya min yadda suka yi da daddy ba kuma shima bai ce min komai ba. Washegari muna breakfast daddy yace min "Moon na duba takardun copper din ku, naga yana da first class a maths kuma yana da experience a teaching, zan kira PC dinku in suna da vacancy zanyi endorsing dinsa" daga haka bai kuma cewa komai ba, Hafsat ta mintsine ni a bom bom nayi kara muka saka dariya muna godewa daddy. Mommy ta tsaya tana kallon mu tace "maganar me kuke yi ne?" Hafsat ce tayi mata bayani, mommy tace "ok, wanda kuke extra lessons dashi?" Nace mata "eh" tace "OK, Allah ya sanya alkhairi, adaiyi hankali, the youth of nowadays are not to be trusted" daddy ya kalleta yace "extra lessons kuma?" Nan mommy ta bashi labarin yadda suka yi da pc din mu. Daddy ya kallemu da serious face yace "I want the extra lessons to stop, in zai maku lesson yayi fixing kuyi a class da sauran dalibai, bana son any special treatment a tsakanin ku, da banyi niyyar ne ma masa aikin ba sai da Hafsat tace min shi ya roke ku a class akan duk wacce tasan baban ta zai iya samar masa aiki ta kai masa takardunsa" nayi sauri na kalli Hafsat ita kuma ta daga kafada. Har cikin raina banji dadin abinda Hafsat ta gayawa daddy ba, Ibrahim is a very proud person amma ta ce wai shi ya roke mu mu samar masa aiki. Daddy ya cigaba da cewa "zan taimaka masa ne saboda bana son in discouraging dinku akan taimako, amma no strings will be attached, shi yasa zance da pc din kar ta gaya masa baban ku ne, saboda bana son wani special something. Allah yayi muku albarka baki daya" muka ce amin. Kamar yadda al'adar makarantar mu take, duk second day na first term ake yin speech and prize giving. Wannan session din ma haka. Muna shiga hall na tuna cewa shekara guda kenan da haduwa ta da Ibrahim. Muka gaida su mommy muka zauna. Yana shigowa idona ya sauka akan sa, ya saka complete yaroba attire har wannan hular tasu. Ina binsa da kallo har ya zauna a side din baki. Muna ta karbar gift duk gift din da za'a bani sai na kalleshi shi kuma sai yayi min 👍 har aka tashi. Ban je gurinsa ba na wuce gurin su mommy muka basu gifts din mu suka tafi gida. Ina komawa hall din naga students sun zagaye shi ana ta tambayarsa me ya dawo dashi. Na tsaya daga gefe kawai ina kallonsa. Yana gani na ta taso ya kara so inda nake bakinsa har kunne. Sai kuma muka rasa abin cewa "you didn't call me" yace yana dan bata fuska, na rufe tawa fuskar nace "sorry". Muka sake yin shiru nace "ashe baka manta yau speech and prize giving ba" yace "I wouldn't miss it for the world, ko da kuwa da rarrafe zan taho" nayi dariya nace "thank You". Can ya sake cewa "I also wanted to tell you, principal din ku tace next week inzo interview, wai wani ambassador ne ya nema min aikin, bansan ko waye ba" na kirkiro mamakin karya nace "congratulations, amma naji dadi sosai" shima yace min "thank You " sannan yace "by the way, Happy Anniversary to Us" na saka hijab dina na rufe fuskata na tafi na bar shi a gurin. How do you guys enjoy this episode? [11/7, 11:37 AM] maryamsuleiman48@gmail.co: MAIMOON By Maman Maama 22 Episode Twenty Two : Amira Ibrahim ya kawo mana kaya babu lefi, kayan tea, biscuits, cosmetics da drinks. It must have cost him dukkan albashinsa. Yazo yayi interview din, kuma bayan wata daya aka aika masa da offer dinsa har ibadan. A week after that, ya tattaro ta dawo abuja. An bashi gida a staff quarters. Nan take ya fara siyayyar kayan gida, kusan komai ya saya sai ya gayamin ni kuma sai in gaya masa menene next abinda ya kamata ya saya. I wanted to help him with money amma nasan ba zai karba ba, kuma bama nason yasan financial status din family na. Farko sai aka bashi ss2 shi kuma ya dage lallai baya so shi ss3 yake so, a cewar sa ya saba damu tunda mu ya dauka sanda yana service. Sai da kyar suka bashi SS3 din, ranar bakinsa har kunne yana murna yazo yake gaya mana, sannan kuma an bashi sports master. Yanzu kam da yawa daga 'yan ajin mu sun san alaka ta da Ibrahim tunda sam yanzu baya boye abinda yake ranshi, ni ce dai nake dan ja da baya.A haka har muka yi hutun first term. A cikin hutun abubuwa da yawa sun faru, na farko Allah yayi wa baban Amira rasuwa. Asalin su Amira 'yan kano ne, baban ta babban mutum ne sosai, yana da manyan 'ya'ya a kano sai aiki ya mayar dashi Abuja, ita kuma uwargidansa tace sam ba zata koma Abuja da zama ba tunda ta tara iyali a kano. Nan 'yan'uwansa suka hada musu auren zumunci da maman Amira ya taho da ita Abuja. Amira ce kadai 'ya a tsakanin su tunda shekarunsa sunja sosai. Sam 'yan uwan Amira babu wanda ya damu da ita balle mahaifiyarta, dan haka sai mutuwar tayi musu zafi sosai. Maman Amira bata san komai na dukiyar baba ba sai gidan da suke ciki a abuja, duk harkokinsa da manyan 'ya'yansa yake yi. Matarsa ta kano ta dage lallai sai a sayar da gidan na Abuja a hada kudin da sauran dukiyar sa ta kano sannan a raba gadon. Ita kuma maman Amira bata son sayar da gidan saboda bata son tashi daga abuja tunda nan ta saba dashi, daga ita har Amira. Mommy ce tayi tsayin daka akan maganar tunda ita lawyer ce har sai da taga an bar musu gidan a matsayin gadonsu, bayan gidan kuwa babu abinda suka tsira dashi, hatta motar da maman take hawa sai da aka karbe. Maman Amira sec sch kadai tayi, dan haka babu zancen neman aiki, ga Amira ita ko sec din bata gama ba. Mommy ce ta biya wa Amira school fees na second and third term sannan ta biya mata kudin SSCE din da zamu yi nan bada jimawa ba. Muna komawa pc tayi taron Muslim students ta sanar mana cewa akwai musabaka da federal government take shiryawa, ance a bada daliba guda daya da zatayi representing din school din mu, dan haka mu zaba a tsakanin mu wa muke ganin zata iya. Nan take muka zabi Amira, kuma tace ta yarda zatayi, muna ta murna sai pc tace zata hada ta da malami guda daya wanda za su ke yin tilawa tare kafin likacin musabakar. Muka tashi daga taron muna ta yiwa amira murna. Da daddare after islamiyya sai Ibrahim yace da Amira ta tsaya yana son ganinta, inajin haka nasan shi akace yayi coaching dinta. Amira ta ja hannuna muka tsaya tare. Sai da aka gama tafiya sannan yazo yace mata "congratulations Amira, naji abin alkhairi, Allah ya bada sa'a" muka ce amin. Nan suka fara tsara yadda zasuke karatun ni kuma ina jinsu ina dan bada tawa shawarar. A karshe suka yanke shawarar zasu keyi daga magrib zuwa isha. Haka kuwa akayi, kullum in munyi sallar magrib sai Amira ta zauna a masallaci tare da Ibrahim har sai munzo sallah isha tukunna mu tafi ialamiyya tare. A bangare na kuma lokaci daya girma razo min, ni kaina bansan yaushe ba sai gani nayi kayana duk sunyi min kadan. Kirjina kullum kara chika yake haka hips dina, har saida nakai ga komawa aron kayan Hafsat ina sakawa ita kuma tace sam ba zata yiwu ba sai dai in aika gida akawo min wasu kayan. Ina aika wa kuwa sai ga kaya akwati guda duk size din Hafsat kuma dana saka sai naga duk sunyi min dai dai. Wata ranar sport muka saka sport wears kamar yadda muka saba muka fita. Ni dama basketball nake yi tun jss1 haka Ibrahim ma, duk ranar sport tare muke yi dashi kuma ya iya sosai saboda yana da tsaho. Ina zuwa na tarar dashi already a field da wadansu staff su biyu tare da students wadanda mostly 'yan kallo ne. Ban yi wata wata ba na shiga muka fara bugawa, amma sai na lura Ibrahim hankalinsa sam baya kam ball din, duk ya zama distracted, ya kasa scoring ko kwallo daya, gashi anaso ayi mana game, nan na tafi gurinsa da niyyar in tambayeshi mai yake damunsa sai na lura gaba daya ransa a bace yake. Ina zuwa kusa dashi sai kawai naga ya chire jacket din daya daura a kugunsa ya kama kokawar saka min, na kwace daga hannunsa cikin fada nace "what is wrong with you?" ya dora min jacket din akan kirjina yace "just go and play table tennis or snooker, ai ba sai lallai kinyi basketball din ba" raina naji ya fara baci, nace "saboda me? Kullum ba basketball din nake playing ba? Dan me yau zaka ce wai inje inyi snooker bayan kai ne ma kake bata mana game din" wani kallo da yayi wa kirjina yasa naji kafafuwana duk sun sage, kallon kawai yayi min na gane ma'anar me yake nufi, wata kunya ce naji kamar zan narke a gurin. Bai ce min komai ba ya juya ya bar field din. Daga baya na naji wasu sababbin coppers suna cewa "wannan Ibrahim din dan bakin ciki ne wallahi" wani hawayen takaici naji yana taho min, nayi sauri na mayar dashi. Da sauri sauri na zura jacket din Ibrahim na bar gurin. Ina jin wata tana kwalla min kira na rabu da ita. Can kasan wata bishiya na hango hafsat tana zaune akan kujera da novel a hannunta tana karantawa, ta dora kafa daya kan daya. Itama sport wears din ne a jikin ta amma tayi rolling farin vail har saman kirjinta. Na tsaya a gabanta nace "why didn't you tell me?" Ta kalleni da rashin fahimta tace "tell you what?" Na zauna kusa da ita nace "ba za kiyi min fada kice kayan jikina are showing ba, kika barni na fito mutane suna kallona?" Dariya tayi ni kuma na kara kuluwa, sannan tace "kusan shekaru biyu da suka wuce na taba fada miki magana akan Ibrahim sai kika ce min you are old enough to make decisions for yourself, to dan me yanzu kuma zan yi miki magana, tunda you are not blind. Yanzu ai kin dauki darasi ko?" Na kara bata rai bance mata komai ba. Kamar daga sama naji yana cewa "barka da hutawa big sister" duk muka kalleshi Hafsat tana dariya tace "ni fa bana son big sister dinnan, sai inji duk tsufa ya kamani" suka yi dariyar su su kadai. Ya zauna kusa dani naja kujera ta na matsa yace min "am sorry, bai kamata inyi miki magana a cikin mutane ba, amma bazan iya hakura mutane suna kallonki ba" Hafsat tayi gyaran murya tace "Hello, ina nan fa" ya kalleta yace "in ba zaki tashi ba to ki toshe kunnuwanki" ni dai bance musu komai ba dan duk haushi suke bani. Tun daga ranar na koma saka dogon hijab irin na Hafsat, 'yan sport din mu kuwa tun suna nemana har suka hakura. Muna gab da fara SSCE Amira tace min sun daina karatu da Ibrahim. Na tambayeta dalili tace babu komai kawai tana ganin ta iya duk abinda ya kamata ta iya. Washe gari muna class aka kira ta a staff room, shiru shiru bata dawl ba sai na tashi na bi bayanta. A hanya muka hadu da ita. Abinda na gani a fuskarta ya bani tsoro, na tambayeta "Amira lafiya, ko a gida ne wani abu ya faru?" Wani kallo ta yi min wanda naji tamkar ta doka min guduma aka, cikin sarkewar murya tace "me kika biyo ni kiyi min kuma, nace na fasa karatun dashi ba shikenan ba? To yanzu na fasa musabakar ma gaba daya, kije kiyi na bar miki, besides you are the golden one ai, you are so perfect that you must have everything that you want. You can have him, you can have the musabaka and everything else" ta bangaje ni da kafadar ta ta wuce. Ni sam ban gabe ina maganganun Amira suka dosa ba dan ni a iya sanina banyi mata komai ba. Tana tafiya sai naga Ibrahim ya fito daga office din PC muka hada ido ya girgiza min kai alamar kar inyi magana ya tafi. Tunda muka shiga class Amira ta kifa kanta a desk take kuka, kowa ya tambayeta sai tace babu komai. Hafsat tace a rabu da ita, dama tun mutuwar babanta she has not being herself maybe mutuwar ta tuna. Ana tashi Ibrahim yazo ya kira ni ya tambayeni ko zan iya yin musabakar? Da mamaki nace masa "Amira fa" yace "tace ta fasa" na tambayeshi dalili yace bai sani ba. Muna zuwa hostel nayi wa Hafsat bayanin duk abinda ya faru. Tayi shiru sannan tace "Are u sure babu wani abun a tsakanin su?" Naji maganar ta kamar kibiya a zuciyata amma sai na maze nace "wani abu kamar me fa?" Ta kalleni da nutsuwa tace "Amira ba haka take ba, in har ta gaya miki wadannan maganganu to da akwai dalili, kuma they have been spending a lot of time together lately, maybe something happened". Maganar Hafsat ta shige ni kuma nayi niyyar zan samu Ibrahim inji daga bakinsa. Dama yanzu mun daina lectures sai dai revisions ko kuma muyi ta tutorial. Dan haka muna zuwa class na tafi staff room na cewa Ibrahim ina son ganin sa. Mu ka fito tare muna tafiya, direct na tambayeshi nace "Me ya hada ka da Amira?" Ya tsaya yana kallona yace " bangane ba, wani abun tace nace mata" nan na fada masa duk maganganun da Amira ta gaya min, yayi shiru bai ce komai ba. Direct na sake tambayar sa "is Amira in love with you?" Yace da sauri "what? Me yasa zaki fadi haka" na sake cewa "are you in love with Amira?" Da karfi yace "hell no!!" Nayi shiru saboda naga yana son yayi min ihu a cikin mutane. Sai da muka jima a tsaye muna kallon kallo sannan ya fara magana "OK, na jima da sanin cewa amira tana so na, tana dannewa saboda she is your friend, ni ma kuma ban taba nuna mata na sani ba, but I know the signs. Yanzu da muka fara karatu da ita sai ya fara zama worst har bata concentrating akan karatun sai dai tayi ta tambata things about me and other stuffs, to sai nayi suggesting cewa mu gayyato ki kizo muke yin karatun tare, shine taji haushi tace ta fasa karatun, na gaya wa pc kuma shine tace ta fasa musabakar gabadaya, sai dai ke kiyi tunda nace dake nake so muyi karatu" tun daya fara maganar nake sauraron shi ina jin wani daci yana taso min a baki na, ji nayi kamar in rufe shi da duka, amma dana kalleshi sai naga iyakacin gaskiyarsa yake fada min. Na juya da sauri zan bar gurin ya kamo hannuna, wani mugun kallo na jefa masa nan da nan ya sake ni nayi gaba. Ina jinsa yace "maimunatu 🙏please " [11/7, 11:37 AM] maryamsuleiman48@gmail.co: MAIMOON By Maman Maama 23 Episode Twenty Three : Efisowa This is going to be a long episode, it will deserve more comments, don't you think so? Ina zuwa class Hafsat ta taso take tambayata "well, what did he said?" Na kalleta da jajayen ido nace "it's none of your business" ta jima tsaye a kaina sannan ta daga kafada tace "OK, in tayi tsami maji" da ace ana sayar da maganin sa ido da saina sayo na bawa Hafsat. Two days suka wuce, zuciya ta fara sanyi amma har yanzu ban huce ba. Ibrahim duk ya gama rikicewa saboda silent treatment da nake bashi. Amira kuma ta ja baya da komai, ta zama wata irin silent ba ta yiwa kowa magana, musamman ma ni. On the third day muna aji a zaune sai ga Ibrahim nan yazo, ya taho direct gurina ya tsaya a gabana yace da karfi yadda kowa a class din zaiji "nace miki I don't love her, what more do you want from me?" Gabadaya ajin kowa yayi shiru yana kallon mu ballantana su Hafsat sa ido. Nayi kasa da murya nace "what are you doing?" Ya kara daga murya yace "am telling everyone bana son ta ni ke nake so, ke kadai nake so" Wata jamila tace "sir wacece? A ajin nan take? Cewa tayi tana sonka?" Na dan saci kallon amira sai naga ta juya ma class din baya tana kallon waje, sai kawai naji zuciya ta ta karye, na dauki wani katon textbook na fara dukan Ibrahim da shi ina korar sa waje, amma yaki tafiya yace lallai saina fada masa cewa maganar ta wuce sannan zai fita, su kuwa 'yan aji sai kara tambayarsa suke ya basu labari. Da naga dai Ibrahim da gaske yake so yake yayi wa Amira tonon silili sai nace masa na yarda, maganar ta wuce, yace "kinyi alkawarin ba zaki kara tayar da maganar ba?" Nace "I promise" sannan ya juya ya fita. Yana fita Hafsat tace "well3, dama nace in tayi tsami zanji, 'yan class din nan duk mai son yaji wacece yazo in gaya masa" nan da nan duk suka tafi gurin Hafsat, na kalli Amira naga alamar tsoro a fuskarta, nayi sauri naje gurin Hafsat nace "Hafsat dan Allah ki bar maganar nan" tace "sai kinyi min alkawarin daga yau anti Hafsat zaki ke ce min" nace "done, anti Hafsat from today". Sai da muka je hostel sannan Hafsat tace "ni daga ke har Amira kun bani mamaki wallahi, ni banga abin so a jikin wannan dogon mutumin ba" nayi dariya kawai ba rabu da ita, amma maganar ta ta tsaya min a rai. A lokuta da dama mutum ba shi yake zabar wanda zuciyarsa zata so ba, kawai haka kawai zakaji kana son mutum, wani lokacin kuma daga kaga mutum sai kaji baka son sa, ba tare da yayi maka komai ba. Kamar yadda lokaci daya na ji zuciya ta tana son Ibrahim duk da irin banbancin da yake tsakanin mu, babu wani dalili da zance saboda abu kaza nake sonsa, kawai dai nasan ina son sa. Da nayi considering Amira sai naga itama haka ne a wurinta, kawai taji tana sonsa ne amma saboda kusancina da ita ya saka ta boye a ranta har sai yanzu da suke spending time together sannan ta fara nuna masa, it must be hard on her, especially yanzu da yayi declaring a gaban kowa cewa baya sonta, sannan gashi gandantakar mu ta shekaru kusan shida tana so ta baci saboda kawai ta kasa controlling zuciyar ta. She deserves a break from me. Ina yin wanka na shirya sai na tafi dakinsu Amira, na tarar da ita a kwance idonta a rufe kamar mai bacci amma kana ganinta kasan ba baccin take yi ba. Na daka mata duka a cinya nace "sleepy heads, ki tashi mu tafi karatu" ta bude idonta tana kallona da mamaki. Ita tasan na sani. A hankali tace "bana jin dadi ne" nace "yeah right, in kika fita zaki warke" a haka na takura ta tayi wanka muka fita. Tun daga nan muka cigaba da kawancen mu da Amira, amma duk abinda muke yi da Ibrahim yazo gurin zata tashi, ni ma kuma bana cewa ta tsaya saboda ta ciki na ciki daurewa kawai nake yi. Soyayya sabowa muke shimfidawa da Ibrahim. Gani nake tunda na shiga SS3 ai I am old enough, shima kuma dama kiris yake jira. Sam Ibrahim baya kunyar nuna min soyayya ko a gaban waye ma kuwa, ni dai duk sai kunya ta rufe ni. Rannan a class ya zo yana cewa wai ya kasa bacci jiya kawai sai yaji muryata yake so yaji, wai saura kadan ya taho hostel, su kuma 'yan ajin sai su biye masa suyi ta tsokana ta, inna ga sun dame ni sai in tashi in bar musu ajin. Anan nake so inja hankalin iyayen yara musamman 'yan mata akan mu kula da tarbiyyar 'ya'yan mu. Yanzu makarantu sun baci, da yawa malamai suna soyayya da daliban su mata. Kuma da yawa daga cikin su basa nufin alkhairi, musamman a boarding schools. Kuma school management suna basa kula tunda shi kansa principal din ko vice ba zai rasa budurwa ba, musamman a private school inda yaran suke da budaddan ido. Mu tabbatar mun bawa yaran mu tarbiyya sannan kullum muke yi musu addu'ah dan babu abinda yafi addu'ah iyaye kariya a gurin 'ya'yansu. Allah yayi wa zuri'ar mu albarka baki daya. Rannan muna a gaban chemistry lab muna duba past questions and answers na WAEC sai muka hango Ibrahim da wasu mata su biyu a gaban staff room, Hasiya ce ta taba ni tace "kinga mutumin ki can, ko suwa ya samu kuma" ina dubawa naga mata ne su biyu da kaya a hannun daya, dayar daga gani babbar macece dayar kuma budurwa, budurwar da hijab matar kuma da babban mayafi, sun jima a tsaye suna magana sai naga ya karbi kayan hannun budurwar ya wuce gaba suna binsa a baya suka tafi staff quarters. Har dare ban kuma ganinsa ba kuma ina ta tunanin ko su waye wadan nan? Washe gari da safe sai gashi yazo yace min inzo, muna fita waje sai yace "there is someone here that wants to see you" gaba na ya fadi nace "who?" Yace "my mother" nan da nan naji wani tashin hankali yazo min, he wants me to meet his mother, this is serious. To ni yanzu da wacce fuskar zan je mata? Kuma me zance mata? Nace masa "Ibrahim am sorry, I can't" ya bata fuska yace "why can't you?" Nace "tsoro nake ji" dariya yayi yace "tsoron me kuma? Bata cin mutane, besides tare zamu je, just ku gaisa shikenan" na kalli kayan jikina, uniform ne a wanke a goge, hijab dina ya rufe har bom2 dina, fuskata babu kwalliya, dama ba kwalliyar nake yi ba. Na sake kallonsa har yanzu da dariya a fuskarsa. Yace "you look great, let's go" yana fadin haka ya shige gaba, na bishi a baya kamar wadda kwai ya fashewa a ciki. Direct visitors room muka je, ya dan tsaya yana kallona yace "are u ready" na girgiza kaina alamar no, yayi dariya kawai ya bude kofar da sallama. Nima nayi sallama na shiga. Su biyu ne kamar jiya da babba da karama. Ina kallon babbar nasan ita ta haifi Ibrahim sai dai bata kaishi tsaho ba, karamar kuma sam basa kama dan ta fishi hasken fata sosai, dan da kadan zan nuna mata fari, sai dai ita fuskarta duk kuraje yayin da tawa take tas. Kana ganin maman su Ibrahim kaga typical yaroba woman. Da daurin zanin ta akan riga, da goggoron akan ta. Ibrahim ya zauna a kusa da ita ni kuma na durkusa daga nesa a kasa na gaisheta da turanci. Ta amsa min amma daga gani turancin na isar ta yayi ba. A raina nace oho dai ni ba iya yarabanci nayi ba sai dai mu tsaya daga gaisuwar. Na gaishe da dayar tunda daga ganinta nasan ta girme ni. Ta amsa tana dariya, na dago kai sai naga Ibrahim ne yake hararar ta, ya wani dora kafa daya akan daya. Maman su kuwa idonta yana kaina. Sai da muka dan jima a haka sannan Ibrahim yace "Maimunatu this is my mother, and that girl over there is my sister" da saurin ta tace "his step sister" na dago kai na kalleta sai naga idonta a kansa, bansan dalili ba sai naji hankali na bai kwanta ba da kallon da take masa. Mamansu naji ta fara magana da gurbataccen turancinta "kullum na kira Ibrahim zancen sa Maimunatu tace kaza maimunatu tayi kaza, inna yi masa complain akan baya zuwa mana weekend sai yace ai muna karatu da Maimunatu sun kusa fara exams, kullum zancen kenan, shine nace bara inzo inga maimunatun nan dai da ido na" naja hijab dina na rufe fuskata, inaji tana masa magana da yarabanci, naji dai tace fulani a ciki, sai naji yace "mu fa yaroba ba'a wani kunyar suruka, in zaki bude ido ki bude, dan duk randa kika haihu ita zata yi miki wanka" na kara dunkule wa a guri daya a raina ina cewa kai Ibrahim mai ya kawo zancen haihuwa kuma? Gaba daya suka yi dariya. 'Yar budurwar ce tayi magana tace "let me introduce myself properly, ni step sister dinsa ce, ma'ana babana ne mijin mamansa, sunana Efisowa amma zaki iya kira na Efi, nazo in taya shi assessing sabida nasan ba iya zabe yayi ba. Dama tunda naji mama tace Fulani nace sai nazo nagani da kaina, gashi kuma naga kinyi kankanta da yawa" Ibrahim yace mata "shut off" sannan yayi mata magana da yarabanci itama ta mayar masa, sai maman tayi musu magana duk sukayi shiru. A hankali maman tace min "ina parents dinki?" Nace mata "suna cikin garin abuja" tace "ku 'yan Abuja ne" nace "'yan jigawa ne mu" kawai sai naji matar tayi min, yadda take magana a hankali irin maganar Ibrahim. Efi ce dai hankali na bai kwanta da ita ba, duk na damu ganin ta kasa dauke idonta daga kan Ibrahim. Ibrahim ne yace zai mayar dani class dan muna karatu, Efi ta sake yin magana da yarabanci shi kuma ya sake ce mata shut off maman tayi tsaki tana kallon efi alamar warning. Tunda muka fito bamu yi magana ba sai da muka dan yi nisa sannan yace "how do you like my mother" nace "she is OK, you look like her but taller" yace "no, she always say da baban mu nake kama" Har nayi tunanin kar in tambayeshi akan efi amma sai zuciya ta ta kasa jurewa, nace "Your sister doesn't like me" yayi dariya yace "yours doesn't like me either" nima nayi dariya sannan nace "but this is different, i feel like there is some tension between you two" yayi shiru bai bani amsa ba, wannan ya tabbatar min da zargina. Nan take naji raina yana kuna. Sai da muka kusa zuwa class sannan yace "koma menene da a tsakanina da efi is over tun tuni, abinda yake tsakanin mu sam bashi da dangantaka da efi. A mincewar mama da baba kawai nake bukata. Please Maimunatu don't screw this thing off. Mama tazo takanas saboda ta ganki, please show her your best behavior yadda in taje zata bawa baba labari shima zai yaba dake, please don't let Efi get in your head, that is exactly what she wants" muna zuwa gaban class din mu nayi shigewa ta ba tare da nace masa komai ba. Har na zauna yana tsaye a gaban class din ya rungume hannayensa fuskarsa da alamar damuwa. Bayan na zauna sai nayi tunanin ban kyauta wa Ibrahim ba, kuma gaskiya ya fada cewa this is our chance, ya kamata inyi kokari inyi probing to his mother cewa I am good enough, inna bari kishin Efi ya shiga raina tun yanzu to ina da problem. Anan zan tsaya inja hankalin 'yammata har ma da matan auren, idan mace ta nuna tana son mijin ki, musamman idan shi mijin ko saurayin baya son ta, don't make an enemy out of her, ki jata a jikin ki kiyi mata kirki sosai, make sure duk sanda saurayin ko mijin yake around kun nuna mata irin soyayyar da kuke yiwa junan ku, ita da kanta zata ji kunya ta ja baya, amma idan kika kama fishi da fada kamar kina tura shi gurinta ne. Ke kuma budurwa da kike neman miji, kar kiga wata da nata kiyi sha'awa kice lallai sai kin raba. In dai har soyayyar tsakani da Allah yake yi mata to ba zasu rabu bafa. Washe gari da yamma muna kofar library da Amira da wasu kawayen mu sai ga Ibrahim sun taho gurin mu shida Efi, tun daga nesa nake kallon yadda take ta shishshige masa, gaba daya kowa ya tsaya yana kallon su har suka kara so. Kallo daya nayi masa nasan ransa a bace yake. Suna zuwa yayi introducing dinta generally, sannan yace "she said she wants to look around the school" nayi sauri nace "she is welcome" tare da miko mata hannu, ta kalle ni sannan ta kalli Ibrahim kamar me neman izni shi kuma ya dauke kansa ya juya ya tafi, tayi masa magana da yarabanci bai amsa mata ba, ya saka hannayensa a aljihun wandon sa yayi tafiyarsa. Yana tafiya na fara yi mata hira, nayi mata introducing duk friends dina da suke gurin. Amira ko kallon ta bata yi ba. Daga nan nace tazo in showing her around, tun daga classes, labs, kitchen, dining hall duk sai da na kaita, sannan na kaita hostel. Hafsat tana kwance muka shiga, ta bimu da kallo, sannan tace min da fulatanci "wannan kuma a ina kika samota?" Na amsa mata da turanci "she is Ibrahim's step sister" sannan na kalli Efi nace "this is my Sister, Hafsat" Efi tace "oh my God she is so beautiful, nice to meet you" ta mika wa Hafsat hannu, kirikiri Hafsat ta ki bata hannu tace da fulatanci "ni bazan taba hannunki ba, kurwata kur" nayi dariya, Efi tace "what did she said?" Nace mata cewa tayi "ai kin fita kyau ma" nan da nan ta washe baki tace "thank u" Hafsat ta harare ni. Nan da nan Efi ta fara santin dakin mu, wai wannan ai ko a gida sai haka, ita in tana nan ai ba zata so ayi hutu bama. Nan da nan na chika mata gabanta da kayan chiye2 muka zauna muka yi ta hira, tana bani labarin gidan su. Amma ni bance mata komai ba akan namu gidan. Har akayi sallar magrib muna tare can sai Ibrahim ya kira ta yace ta fito su koma gida, haka kawai sai na samu kaina da jin babu dadi saboda ya kira ta a waya. Na dauko wani set din toiletries na mu na dove na saka mata a keda na bata. Tayi ta mamaki wai ina student har nake kyautar kaya? Washe gari Ibrahim yace min zasu tafi, na hado sweets da biscuits madu yawa a leda na boye a hijab dina saboda 'yan sa ido, yazo ya kira ni muyi sallama da mama. Ina shiga na gaishe ta, ta amsa min da sakakkiyar fuska sosai tayi min fada akan karatu, naji dadi har raina, na dauko leda ta na bata nace a kaiwa Abdullahi da Abdulrahman, kananan kannen Ibrahim. Taki karba na ajiye mata a gabanta na tafi. Da daddare Ibrahim yazo yana ta fada wai me yasa na kashe kudi na sayo kaya? In ina son in basu basai inyi masa magana shi ya sayo musu ba? Shi ya dauka siyowa nayi. Bayan kwana biyu sai gashi da kaya niki niki ya kawo min. Sanda muka fara SSCE kullum in mun shiga exam Ibrahim zai zauna a kofar hall din ya jira ni, har sai na fito ya tambayeni ya paper sannan zai tafi. A lokacin ya koya min jin kida, zai kunna slow music ya saka ear piece a kunne daya ni ma in saka kunne daya muna ji tare. Shakuwa ce sosai kullum take kara shiga tsakanin mu. Har tararradin ranar da zamu gama paper nake yi. A week to gama papers din mu PC ta kira ni tace federal government ta aiko a bada sunan best student za' a biya mata scholarship zuwa university of her choice. Dan haka tana sanar min cewa sunana zasu bayar. Nayi shiru ina tunani. I don't need the scholarship, daddy zai iya biya min karatu zuwa kowacce kasa nake so. Scholarship is meant for bright students din da iyayensu ba zasu iya biya musu school fees ba. Kawai sai Amira ta fado min a rai. Nan take nace da pc na barwa Amira, asaka sunan ta instead of sunana. PC ta nuna bata ji dadi ba, I am the best student that they ever had a school din. Nace mata to tayi contacting daddy ta sanar masa, duk abinda yace shikenan. Ana gobe zamu yi graduating Ibrahim ya kira ni yace zamuyi magana. Muna zama na lura he is serious. Yace "Maimunatu in kunje gida ina so zanzo in nemi iznin neman auren ki a gurin daddyn ku" zuciya ta ta buga da karfi na kalle yace "yes, ina so in samu permission dinsu saboda insan in da na dosa, just pray for us" I hope you enjoy this episode. Put on your seat belts because the next episode is going to blow u away. Pray for the love birds 💏 [11/7, 11:38 AM] maryamsuleiman48@gmail.co: MAIMOON By Maman Maama 23 Episode Twenty Three : Efisowa This is going to be a long episode, it will deserve more comments, don't you think so? Ina zuwa class Hafsat ta taso take tambayata "well, what did he said?" Na kalleta da jajayen ido nace "it's none of your business" ta jima tsaye a kaina sannan ta daga kafada tace "OK, in tayi tsami maji" da ace ana sayar da maganin sa ido da saina sayo na bawa Hafsat. Two days suka wuce, zuciya ta fara sanyi amma har yanzu ban huce ba. Ibrahim duk ya gama rikicewa saboda silent treatment da nake bashi. Amira kuma ta ja baya da komai, ta zama wata irin silent ba ta yiwa kowa magana, musamman ma ni. On the third day muna aji a zaune sai ga Ibrahim nan yazo, ya taho direct gurina ya tsaya a gabana yace da karfi yadda kowa a class din zaiji "nace miki I don't love her, what more do you want from me?" Gabadaya ajin kowa yayi shiru yana kallon mu ballantana su Hafsat sa ido. Nayi kasa da murya nace "what are you doing?" Ya kara daga murya yace "am telling everyone bana son ta ni ke nake so, ke kadai nake so" Wata jamila tace "sir wacece? A ajin nan take? Cewa tayi tana sonka?" Na dan saci kallon amira sai naga ta juya ma class din baya tana kallon waje, sai kawai naji zuciya ta ta karye, na dauki wani katon textbook na fara dukan Ibrahim da shi ina korar sa waje, amma yaki tafiya yace lallai saina fada masa cewa maganar ta wuce sannan zai fita, su kuwa 'yan aji sai kara tambayarsa suke ya basu labari. Da naga dai Ibrahim da gaske yake so yake yayi wa Amira tonon silili sai nace masa na yarda, maganar ta wuce, yace "kinyi alkawarin ba zaki kara tayar da maganar ba?" Nace "I promise" sannan ya juya ya fita. Yana fita Hafsat tace "well3, dama nace in tayi tsami zanji, 'yan class din nan duk mai son yaji wacece yazo in gaya masa" nan da nan duk suka tafi gurin Hafsat, na kalli Amira naga alamar tsoro a fuskarta, nayi sauri naje gurin Hafsat nace "Hafsat dan Allah ki bar maganar nan" tace "sai kinyi min alkawarin daga yau anti Hafsat zaki ke ce min" nace "done, anti Hafsat from today". Sai da muka je hostel sannan Hafsat tace "ni daga ke har Amira kun bani mamaki wallahi, ni banga abin so a jikin wannan dogon mutumin ba" nayi dariya kawai ba rabu da ita, amma maganar ta ta tsaya min a rai. A lokuta da dama mutum ba shi yake zabar wanda zuciyarsa zata so ba, kawai haka kawai zakaji kana son mutum, wani lokacin kuma daga kaga mutum sai kaji baka son sa, ba tare da yayi maka komai ba. Kamar yadda lokaci daya na ji zuciya ta tana son Ibrahim duk da irin banbancin da yake tsakanin mu, babu wani dalili da zance saboda abu kaza nake sonsa, kawai dai nasan ina son sa. Da nayi considering Amira sai naga itama haka ne a wurinta, kawai taji tana sonsa ne amma saboda kusancina da ita ya saka ta boye a ranta har sai yanzu da suke spending time together sannan ta fara nuna masa, it must be hard on her, especially yanzu da yayi declaring a gaban kowa cewa baya sonta, sannan gashi gandantakar mu ta shekaru kusan shida tana so ta baci saboda kawai ta kasa controlling zuciyar ta. She deserves a break from me. Ina yin wanka na shirya sai na tafi dakinsu Amira, na tarar da ita a kwance idonta a rufe kamar mai bacci amma kana ganinta kasan ba baccin take yi ba. Na daka mata duka a cinya nace "sleepy heads, ki tashi mu tafi karatu" ta bude idonta tana kallona da mamaki. Ita tasan na sani. A hankali tace "bana jin dadi ne" nace "yeah right, in kika fita zaki warke" a haka na takura ta tayi wanka muka fita. Tun daga nan muka cigaba da kawancen mu da Amira, amma duk abinda muke yi da Ibrahim yazo gurin zata tashi, ni ma kuma bana cewa ta tsaya saboda ta ciki na ciki daurewa kawai nake yi. Soyayya sabowa muke shimfidawa da Ibrahim. Gani nake tunda na shiga SS3 ai I am old enough, shima kuma dama kiris yake jira. Sam Ibrahim baya kunyar nuna min soyayya ko a gaban waye ma kuwa, ni dai duk sai kunya ta rufe ni. Rannan a class ya zo yana cewa wai ya kasa bacci jiya kawai sai yaji muryata yake so yaji, wai saura kadan ya taho hostel, su kuma 'yan ajin sai su biye masa suyi ta tsokana ta, inna ga sun dame ni sai in tashi in bar musu ajin. Anan nake so inja hankalin iyayen yara musamman 'yan mata akan mu kula da tarbiyyar 'ya'yan mu. Yanzu makarantu sun baci, da yawa malamai suna soyayya da daliban su mata. Kuma da yawa daga cikin su basa nufin alkhairi, musamman a boarding schools. Kuma school management suna basa kula tunda shi kansa principal din ko vice ba zai rasa budurwa ba, musamman a private school inda yaran suke da budaddan ido. Mu tabbatar mun bawa yaran mu tarbiyya sannan kullum muke yi musu addu'ah dan babu abinda yafi addu'ah iyaye kariya a gurin 'ya'yansu. Allah yayi wa zuri'ar mu albarka baki daya. Rannan muna a gaban chemistry lab muna duba past questions and answers na WAEC sai muka hango Ibrahim da wasu mata su biyu a gaban staff room, Hasiya ce ta taba ni tace "kinga mutumin ki can, ko suwa ya samu kuma" ina dubawa naga mata ne su biyu da kaya a hannun daya, dayar daga gani babbar macece dayar kuma budurwa, budurwar da hijab matar kuma da babban mayafi, sun jima a tsaye suna magana sai naga ya karbi kayan hannun budurwar ya wuce gaba suna binsa a baya suka tafi staff quarters. Har dare ban kuma ganinsa ba kuma ina ta tunanin ko su waye wadan nan? Washe gari da safe sai gashi yazo yace min inzo, muna fita waje sai yace "there is someone here that wants to see you" gaba na ya fadi nace "who?" Yace "my mother" nan da nan naji wani tashin hankali yazo min, he wants me to meet his mother, this is serious. To ni yanzu da wacce fuskar zan je mata? Kuma me zance mata? Nace masa "Ibrahim am sorry, I can't" ya bata fuska yace "why can't you?" Nace "tsoro nake ji" dariya yayi yace "tsoron me kuma? Bata cin mutane, besides tare zamu je, just ku gaisa shikenan" na kalli kayan jikina, uniform ne a wanke a goge, hijab dina ya rufe har bom2 dina, fuskata babu kwalliya, dama ba kwalliyar nake yi ba. Na sake kallonsa har yanzu da dariya a fuskarsa. Yace "you look great, let's go" yana fadin haka ya shige gaba, na bishi a baya kamar wadda kwai ya fashewa a ciki. Direct visitors room muka je, ya dan tsaya yana kallona yace "are u ready" na girgiza kaina alamar no, yayi dariya kawai ya bude kofar da sallama. Nima nayi sallama na shiga. Su biyu ne kamar jiya da babba da karama. Ina kallon babbar nasan ita ta haifi Ibrahim sai dai bata kaishi tsaho ba, karamar kuma sam basa kama dan ta fishi hasken fata sosai, dan da kadan zan nuna mata fari, sai dai ita fuskarta duk kuraje yayin da tawa take tas. Kana ganin maman su Ibrahim kaga typical yaroba woman. Da daurin zanin ta akan riga, da goggoron akan ta. Ibrahim ya zauna a kusa da ita ni kuma na durkusa daga nesa a kasa na gaisheta da turanci. Ta amsa min amma daga gani turancin na isar ta yayi ba. A raina nace oho dai ni ba iya yarabanci nayi ba sai dai mu tsaya daga gaisuwar. Na gaishe da dayar tunda daga ganinta nasan ta girme ni. Ta amsa tana dariya, na dago kai sai naga Ibrahim ne yake hararar ta, ya wani dora kafa daya akan daya. Maman su kuwa idonta yana kaina. Sai da muka dan jima a haka sannan Ibrahim yace "Maimunatu this is my mother, and that girl over there is my sister" da saurin ta tace "his step sister" na dago kai na kalleta sai naga idonta a kansa, bansan dalili ba sai naji hankali na bai kwanta ba da kallon da take masa. Mamansu naji ta fara magana da gurbataccen turancinta "kullum na kira Ibrahim zancen sa Maimunatu tace kaza maimunatu tayi kaza, inna yi masa complain akan baya zuwa mana weekend sai yace ai muna karatu da Maimunatu sun kusa fara exams, kullum zancen kenan, shine nace bara inzo inga maimunatun nan dai da ido na" naja hijab dina na rufe fuskata, inaji tana masa magana da yarabanci, naji dai tace fulani a ciki, sai naji yace "mu fa yaroba ba'a wani kunyar suruka, in zaki bude ido ki bude, dan duk randa kika haihu ita zata yi miki wanka" na kara dunkule wa a guri daya a raina ina cewa kai Ibrahim mai ya kawo zancen haihuwa kuma? Gaba daya suka yi dariya. 'Yar budurwar ce tayi magana tace "let me introduce myself properly, ni step sister dinsa ce, ma'ana babana ne mijin mamansa, sunana Efisowa amma zaki iya kira na Efi, nazo in taya shi assessing sabida nasan ba iya zabe yayi ba. Dama tunda naji mama tace Fulani nace sai nazo nagani da kaina, gashi kuma naga kinyi kankanta da yawa" Ibrahim yace mata "shut off" sannan yayi mata magana da yarabanci itama ta mayar masa, sai maman tayi musu magana duk sukayi shiru. A hankali maman tace min "ina parents dinki?" Nace mata "suna cikin garin abuja" tace "ku 'yan Abuja ne" nace "'yan jigawa ne mu" kawai sai naji matar tayi min, yadda take magana a hankali irin maganar Ibrahim. Efi ce dai hankali na bai kwanta da ita ba, duk na damu ganin ta kasa dauke idonta daga kan Ibrahim. Ibrahim ne yace zai mayar dani class dan muna karatu, Efi ta sake yin magana da yarabanci shi kuma ya sake ce mata shut off maman tayi tsaki tana kallon efi alamar warning. Tunda muka fito bamu yi magana ba sai da muka dan yi nisa sannan yace "how do you like my mother" nace "she is OK, you look like her but taller" yace "no, she always say da baban mu nake kama" Har nayi tunanin kar in tambayeshi akan efi amma sai zuciya ta ta kasa jurewa, nace "Your sister doesn't like me" yayi dariya yace "yours doesn't like me either" nima nayi dariya sannan nace "but this is different, i feel like there is some tension between you two" yayi shiru bai bani amsa ba, wannan ya tabbatar min da zargina. Nan take naji raina yana kuna. Sai da muka kusa zuwa class sannan yace "koma menene da a tsakanina da efi is over tun tuni, abinda yake tsakanin mu sam bashi da dangantaka da efi. A mincewar mama da baba kawai nake bukata. Please Maimunatu don't screw this thing off. Mama tazo takanas saboda ta ganki, please show her your best behavior yadda in taje zata bawa baba labari shima zai yaba dake, please don't let Efi get in your head, that is exactly what she wants" muna zuwa gaban class din mu nayi shigewa ta ba tare da nace masa komai ba. Har na zauna yana tsaye a gaban class din ya rungume hannayensa fuskarsa da alamar damuwa. Bayan na zauna sai nayi tunanin ban kyauta wa Ibrahim ba, kuma gaskiya ya fada cewa this is our chance, ya kamata inyi kokari inyi probing to his mother cewa I am good enough, inna bari kishin Efi ya shiga raina tun yanzu to ina da problem. Anan zan tsaya inja hankalin 'yammata har ma da matan auren, idan mace ta nuna tana son mijin ki, musamman idan shi mijin ko saurayin baya son ta, don't make an enemy out of her, ki jata a jikin ki kiyi mata kirki sosai, make sure duk sanda saurayin ko mijin yake around kun nuna mata irin soyayyar da kuke yiwa junan ku, ita da kanta zata ji kunya ta ja baya, amma idan kika kama fishi da fada kamar kina tura shi gurinta ne. Ke kuma budurwa da kike neman miji, kar kiga wata da nata kiyi sha'awa kice lallai sai kin raba. In dai har soyayyar tsakani da Allah yake yi mata to ba zasu rabu bafa. Washe gari da yamma muna kofar library da Amira da wasu kawayen mu sai ga Ibrahim sun taho gurin mu shida Efi, tun daga nesa nake kallon yadda take ta shishshige masa, gaba daya kowa ya tsaya yana kallon su har suka kara so. Kallo daya nayi masa nasan ransa a bace yake. Suna zuwa yayi introducing dinta generally, sannan yace "she said she wants to look around the school" nayi sauri nace "she is welcome" tare da miko mata hannu, ta kalle ni sannan ta kalli Ibrahim kamar me neman izni shi kuma ya dauke kansa ya juya ya tafi, tayi masa magana da yarabanci bai amsa mata ba, ya saka hannayensa a aljihun wandon sa yayi tafiyarsa. Yana tafiya na fara yi mata hira, nayi mata introducing duk friends dina da suke gurin. Amira ko kallon ta bata yi ba. Daga nan nace tazo in showing her around, tun daga classes, labs, kitchen, dining hall duk sai da na kaita, sannan na kaita hostel. Hafsat tana kwance muka shiga, ta bimu da kallo, sannan tace min da fulatanci "wannan kuma a ina kika samota?" Na amsa mata da turanci "she is Ibrahim's step sister" sannan na kalli Efi nace "this is my Sister, Hafsat" Efi tace "oh my God she is so beautiful, nice to meet you" ta mika wa Hafsat hannu, kirikiri Hafsat ta ki bata hannu tace da fulatanci "ni bazan taba hannunki ba, kurwata kur" nayi dariya, Efi tace "what did she said?" Nace mata cewa tayi "ai kin fita kyau ma" nan da nan ta washe baki tace "thank u" Hafsat ta harare ni. Nan da nan Efi ta fara santin dakin mu, wai wannan ai ko a gida sai haka, ita in tana nan ai ba zata so ayi hutu bama. Nan da nan na chika mata gabanta da kayan chiye2 muka zauna muka yi ta hira, tana bani labarin gidan su. Amma ni bance mata komai ba akan namu gidan. Har akayi sallar magrib muna tare can sai Ibrahim ya kira ta yace ta fito su koma gida, haka kawai sai na samu kaina da jin babu dadi saboda ya kira ta a waya. Na dauko wani set din toiletries na mu na dove na saka mata a keda na bata. Tayi ta mamaki wai ina student har nake kyautar kaya? Washe gari Ibrahim yace min zasu tafi, na hado sweets da biscuits madu yawa a leda na boye a hijab dina saboda 'yan sa ido, yazo ya kira ni muyi sallama da mama. Ina shiga na gaishe ta, ta amsa min da sakakkiyar fuska sosai tayi min fada akan karatu, naji dadi har raina, na dauko leda ta na bata nace a kaiwa Abdullahi da Abdulrahman, kananan kannen Ibrahim. Taki karba na ajiye mata a gabanta na tafi. Da daddare Ibrahim yazo yana ta fada wai me yasa na kashe kudi na sayo kaya? In ina son in basu basai inyi masa magana shi ya sayo musu ba? Shi ya dauka siyowa nayi. Bayan kwana biyu sai gashi da kaya niki niki ya kawo min. Sanda muka fara SSCE kullum in mun shiga exam Ibrahim zai zauna a kofar hall din ya jira ni, har sai na fito ya tambayeni ya paper sannan zai tafi. A lokacin ya koya min jin kida, zai kunna slow music ya saka ear piece a kunne daya ni ma in saka kunne daya muna ji tare. Shakuwa ce sosai kullum take kara shiga tsakanin mu. Har tararradin ranar da zamu gama paper nake yi. A week to gama papers din mu PC ta kira ni tace federal government ta aiko a bada sunan best student za' a biya mata scholarship zuwa university of her choice. Dan haka tana sanar min cewa sunana zasu bayar. Nayi shiru ina tunani. I don't need the scholarship, daddy zai iya biya min karatu zuwa kowacce kasa nake so. Scholarship is meant for bright students din da iyayensu ba zasu iya biya musu school fees ba. Kawai sai Amira ta fado min a rai. Nan take nace da pc na barwa Amira, asaka sunan ta instead of sunana. PC ta nuna bata ji dadi ba, I am the best student that they ever had a school din. Nace mata to tayi contacting daddy ta sanar masa, duk abinda yace shikenan. Ana gobe zamu yi graduating Ibrahim ya kira ni yace zamuyi magana. Muna zama na lura he is serious. Yace "Maimunatu in kunje gida ina so zanzo in nemi iznin neman auren ki a gurin daddyn ku" zuciya ta ta buga da karfi na kalle yace "yes, ina so in samu permission dinsu saboda insan in da na dosa, just pray for us" I hope you enjoy this episode. Put on your seat belts because the next episode is going to blow u away. Pray for the love birds 💏 [11/7, 11:39 AM] maryamsuleiman48@gmail.co: MAIMOON By Maman Maama 34 Episode Twenty Four : The Break up 💔 Alright this is another long episode, nayi deciding zan ke yi da yawa ne saboda we have a long way to go. Na yi shiru na zuba mishi idanu kamar yadda shima ya zuba min. Can ya dan yi murmushi yace "are you scared?" Na gyada kaina alamar eh. Yayi dariya yace "I am scared too, amma dole muyi haka, saboda inaso in kun koma gida in ke zuwa gurin ki kuma kinga bazan ke zuwa bada iznin daddy ba, it's not right" na sunkuyar da kaina nace Allah ya kai mu. Washe gari har mukamuka fitar da kayan mu bakin gate banga Ibrahim ba, mun dawo hostel muna sallama da mutane sai gashi yazo bakin gate, daga ganin sa nasan cewa he is not OK. Hafsat ce ta tambaye shi "sir, baka da lafiya ne?" Yace mata "wallahi kwana nayi da zazzabi" nan Hafsat ta saka shi a gaba da tsokana wai dan zamu tafi ne, nima kaina zazzabin nake ji. Muka je bakin gate yace shi ba zai karasa ba, wai ko wanka bai yi ba baya son ya shiga gurin mutane. Nan Hafsat ta barmu ta karasa gate. Tana tafiya ya matso kusa dani yace a hankali "so, finally dai zaki tafi ki barni" nace "ba kace zaka ke zuwa ba" yace "ba dole in zo ba, dan ke fa nake zaune a garin nan, only for you, yanzu ma tunanin yadda zanke yin spending days with out you nake yi." Nace masa "ai zamu ke yin waya" yace "bayan ke baki da waya? Kuma in kinje gidan bakya kirana da wata wayar" nace "ai zan kira ka yanzu" "ban yarda ba, ki bani number mommy kawai" "laa to in ka kira ta me zaka ce mata?' "Sai ince mata son in law dinta ne" nayi dariya, a raina nace lallai wannan bai san wacece mommy ba. A fili kuma nace "Allah da gaske nake zan kira ka" ya marairaice fuska "yanzu tafiya zaki yi ki barni?" Nayi dariya ganin yadda yayi da fuskarsa, yace "au dariya ma kike yi min ko? Duk sanda daddy ya bani permission kullum sai nazo" nace "Allah ya kaimu lokacin" Hafsat naji tana kwala min kira, naga tana dago min hannu, nasan anzo daukar mu kenan. Naki tafiya, sai gata tazo tace in ba zaki tafi ba zanyi tafiya ta wallahi, na kalle ta na dauke kai. Sai tace au kuka zakuyi? Bani phone dinka inyi muku hoton tarihi, kawai sai ya fito da phone din ya mika mata, ta karba ta bude camera ta dauke mu. Na dan kwantar da kaina a kafadarsa shi kuma ya juyo da kansa yana kallona. Hoton yayi kyau sosai. Daga haka Hafsat ta figi hannuna muka tafi, ina jinshi a hankali yace "Maimunatu" amma ban juyo ba ballantana in amsa masa. Muna zuwa gida muka tarar daddy da mommy sun shirya mana surprise party na graduation, duk kowa yana nan har neighbours an gayyato, ga cake kato da hotunan mu a jiki ni da Hafsat. Nan da nan muka chanja kaya zuwa dogayen rigunan da mommy ta bamu as gift din ta, ta Hafsat pink tawa red. Munyi kyau ba kadan ba, mommy tayi mana light make up. Muka fito muka yanka cake tare da daukar hotuna, nan take naji duk na manta da wani rabuwa da Ibrahim. Muna gamawa daddy ya kawo mana nashi gift din. Muna unwrapping muka ga wayoyi ne sababbi fil kirar Samsung galaxy edge ta Hafsat pink tawa red. Ai ji nayi kamar daddy ya saka ni a aljanna. Muka rungume shi muna murna tare da cewa "thank you daddy". Bayan an tashi daga party muka dawo main palo muka dasa sabuwar hira, muna ta basu labarin makaranta su kuma suna bamu labarin abubuwan da suka faro sanda bama nan. Hafiz ya samu admission shima a Oxford inda zai karanci accounting. Anan daddy yake ce min sunyi waya da PC din mu akan scholarship dina, "is that what you really want" nace eh, yace "to shikenan zance a bata din, Allah yasa haka ya zamar miki sadaqatujjariya" nace "amin daddy" nan ya kara yi mana nasiha akan tausayawa na kasa damu da duk wanda muka ga yana bukatar taimako, wanda duk ya taimaki wani Allah zai taimake shi. Muna komawa daki da daddare mu ka dauko wayoyin mu muka kunna, dama already an saka mana sim cards a ciki. Hafsat ta dauko address book din da muka karbi numbers din friends din mu ta fara saving a wayar ta, ni kuma number da nake so inyi saving tana cikin kaina. Na zauna nayi dialing, bugu daya ya dauka, sai kuma na kasa magana, yayi ta hello3 can yace "maimunatu talk now, ko so kike zuciya ta ta buga ne" da mamaki nace "ya akayi kasan ni ce?" Yayi dariya yace "nasan babu wanda zai kira ni yayi shiru, wato wayo zaki yi min ko? Ke kina jin murya ta amma ni kinyi min rowar taki ko?" Nace "a'a ba haka bane ba fa. Dama so nake ince maka daddy ya saya min waya" da sauri yace "haba? Amma daddy ya gama yi min komai" nace "ya jikin naka?" Yace "na warke yanzu tunda naji muryarki" na lumshe ido na ina jin dadin kalamansa. Dama Ibrahim da magana a hankali balle kuma ana tsara budurwa a waya. Na kwanta lamo a kan gado na rungume pillow, ina ganin Hafsat tana harara ta ni kuma na murguda mata baki. Kalamai Ibrahim yayi ta tsaro min wadanda nake jin su har 'yan yatsun kafata. A haka har bacci ya dauke ni. Da assuba karar waya ta tashe ni, da kyar na bude ido na na duba naga number Ibrahim, tunda banyi saving ba. Ina dagawa yace "a tashi ayi sallah sleepy head" cikin bacci nace "na tashi ai" yace "aa, ban yarda ba, ki shiga toilet ki kunna ruwa inji tikunna" na tashi na shiga toilet na daga sink sannan ya kashe wayar. Haka rayuwa tacigaba da kasance mana ni da Ibrahim, kullum muna makale a waya. Wannan yasa na rage zaman falo sai bedroom. Da naji mommy ta taho kuwa sai in kashe wayar. Babu abinda Ibrahim bai tsara min ba, ya gama tsara mana rayuwar mu kaf, tun daga design din gidan da zamu zauna, 'ya'yan da zamu haifa, yace duk so yake su yi kama dani amma mazan suyi tsahon sa. Ni dai sai dai inyi dariya ko ince masa to. Wani lokacin yakan sakj layi ya koma bedroom secrets ni kuma da naji haka sai in kashe wayar. Munyi three weeks da dawowa Ibrahim yace yana son zuwa, yana son in gaya masa ranar da zai samu daddy a gida. Na gaya masa yace to in jira shi. Ranar da zaizo tun safe na tashi da mutuwar jiki. Muka yi waya da Ibrahim na ce masa ya bari sai yamma tunda yanzu daddy baya gida. Nayi masa text din address. Allah ya soni mommy tana office tun safe, dan haka na shiga kitchen na gaya wa cook abinda nake so ta hada min zanyi bako. Tana dariya take tsokana ta "it is about time, ya kamata mu fara ganin samari a gidan nan" nima nayi dariya nace "asma'u ba fa saurayi na bane, just nace miki zanyi bako sai kice saurayi?" Ta tabe baki tace "ai ku 'yan boko haka kuke, sai kuce baku isa aure ba" da naga dai magana take nema sai na fice na bata guri, dan banajin dadi sosai. Nayi wanka na na saka wata blue din atamfa mai pink flowers, riga da skirt, na gyara fuskata da powder da wet lips, na fesa turaruka na masu dadin kamshi. Hafsat tana kwance tana kallona tace "finally yau zai zo gidannan, I salute his courage" na ce mata "shut your mouth, saidinawa masu bacci da ido daya" na fita na kira wani daga cikin yaran gidan nace ya saka min kujeru a garden. Na dawo falo na zauna nayi folding hannuna zuciyata tana bugawa. Har five daddy bai dawo ba, Ibrahim bai zo ba. Hafsat ta sauko tana kallona tace "you look pale moon, relax" nace mata "baki san mai nake ji ba Hafsat" waya ta ce tayi kara na duba naga Ibrahim ne, na dauka yace "Am here, ina gate, your security won't let me in" tun daga muryarsa na gane he is somehow not happy" nayi sauri na dauki gale na pink na fita, ina jin Hafsat tana cewa "good luck". Ina fita wani security ya karaso guri na yana min bayanin wani yazo gurina, nace masa su bude masa gate, nima na yi hanyar gate din da sauri. Yana shigowa wani security ya zo da bomb detector yana shafa masa, da sauri na daga masa hannu nayi masa alama da ya matsa daga gurin. Na karasa da sauri ina kakaro murmushi, shima murmushin yayi min da side daya, da alamar bacin rai a fuskarsa. Complete yaroba attire ya saka. Riga bubu three quater da wando mai fadi, sai hula da aka dinka da yadin shaddar, ya lankwasa hular zuwa side din fuskarsa. Nayi masa sannu da zuwa na wuce gaba da dan sauri shi kuma ya biyo bayana. Kamar daga sama naji ance "hey!! Where are u going?" Na juyo naga chief security din gidan ne yake wa Ibrahim tsawa. Zuciya ta naji ta buga da karfi. Na juyo a fusace na kama yi masa masifa shi kuma yana bani hakuri cewa bai san tare muke ba. Yadda yake kallon Ibrahim kadai zaka gane assessing kayan jikin sa yake yi. Banyi aune ba sai ji nayi gate ya bude, lokaci daya Royce Rossey din daddy ta danno kai harabar gidan. Ji nayi kamar kafata ba zata dauke ni ba, ni kame kam a gurin da nake haka ma Ibrahim. A hankali motar take gangarowa har tazo dai dai saitin mu sannan glass din ya fara sauka kasa. Innalillahi wa inna ilaihir raji'un kawai nake ambata a zuciya ta dan bakina bazai iya furta komai ba. Fuskar daddy ce ta baiyana cike da kwarjini da kyau da kasaita irin na fulani. A hankali ya chire glass din idonsa yana kallona sannan ya mayar da kallonsa kan Ibrahim. Daga ni har Ibrahim babu wanda yace komai. Ya mayar da glass din idonsa sannan glass din motar shima yayi sama a hankali har ya rufe sannan motar ta mirgina tayi gaba. Ajiyar zuciya mai karfi na sauke, sannan na fara jin wanj sanyi yana shigata alamar zazzabi. Na juya na kalli Ibrahim wanda har yanzu motar yake kallo. Nasan idan ba a movie ba Ibrahim bai taba ganin RR ba, dan very few people ne suke da ita a Nigeria. Nace masa "let's go" amma bai motsa ba. A hankali yace "I guess that is your father, the man I am suppose to meet today" kaina a kasa nace yes. Da haka na juya na nufi hanyar garden. Sai da nayi nisa sannan ya biyo bayana muka karasa tare. Muna zuwa na nuna masa kujera amma sai ya tsaya ya fara safa da marwa. Ni dai na zauna na zuba masa ido. Dan kansa kuma yazo ya zauna yace "why didn't you tell me" nace "me fa?" Ya kalleni bacin rai karara a fuskarsa yace "you clearly know what" nace "me kaso ace na gaya maka? Cewa babana ambassador ne? Muna da katon gida mai cike da securities?" Ya katse ni da cewa "hell yes!! Exactly like that, da kin gaya min haka da nasan mai zan fuskanta ai" nace "it doesn't change anything" yace "it changes everything, ni maimunatun da na sani is a simple daliba, wannan kuwa is a princess living in a castle guided by a bunch of dragons" ta gefen ido na na hango driver yana fito da motar yaya Walid daga garage, da alama fita zai yi. Na dawo da hankali na kan Ibrahim nace masa "I am still me" ya mike tsaye ya cigaba ba safa da marwa "ta yaya kike tsammanin mutun kamar ni zaije gurin mutun kamar babanki yace masa yana neman auren 'yarsa? Daya kalleni abinda zai gani shine some stupid yaroba parasite da zaiyi feeding on his daughter, he will take one look at me and ask his security to throw me out" zafin zuciyata naji ya karo, na mike tsaye ni ma "don't talk about my father that way, baka san shiba, ba haka yake ba. Don't judge him without knowing him" gani yayi da gaske raina ya baci, sai ya tsaya yace "am sorry maimunatu, am just not myself" na zauna shima ya zauna. Ta gefen idona na hango Ya Walid ya fito daga gida ya nufi motarsa. A cikin zuciya ta nake cewa "karka juyo, karka juyo" amma kamar wanda na takarkare na kwalla masa kira sai gani nayi ya juyo din kuwa, ya dan dakata yana kallon mu, har da saka hannunsa ya kare hasken rana. Har ya bude kofar motarsa sai kuma ya rufe ya sake kallon inda muke, na kalli Ibrahim naga shima shi yake kallo. Kawai sai naga ya nufo inda muke zaune. Innalillahi wa inna ilaihir rajiun kawai nake ta maimaitawa a raina. Ibrahim yace "I guess this is your brother" nace "yes". Duk gidan mu Ya Walid ya fi mu hasken fata, fari ne tas dan har yalo fatarsa take yi. A kyau kuwa ba daga nan ba. Dan gayu ne na ajin karshe, ballantana kuma yau kamar fitar musamman za'ayi. Shirt da wando a jikinsa 'yan gaske, kansa babu hula sai gyaran da gashin sa ya sha sai daukan ido yake, takalminsa da agogon hannunsa kadai abin kallo ne. Ya karaso gurin mu idonsa a kaina, sannan ya kalli Ibrahim da alamar tambaya a fuskarsa. Ya bawa Ibrahim hannu suka gaisa. Da fulatanci ya ce min "Moon a inda za'a kare kenan?" Na bata fuska yayi dariya, sannan yace da turanci "idan mommy ta dawo kice mata na fita" sai a lokacin na tuno cewa mommy tana iya shigowa a kowanne lokaci. Na gyada masa kai kawai. Ya juya yayi taku biyu sai yayi juyi 180 ya dawo yace "baki yi introducing din mu ba kuma" nayi murmushin yake nace "Ibrahim wannan shine yaya Walid, babban yayan mu, Ya Walid wannan shine Ibrahim my.... " Ibrahim yayi sauri yace "her former teacher" nayi sauri na kalleshi amma sai naga bani yake kallo ba. Ya Walid ya dan jinjina kai yana dan turo baki, sai kuma ya juya zai tafi, two steps ya sake tsayawa a raina nace "oh dear God, what now" ya juyo fuskarsa da alamar tambaya ya sake kallon Ibrahim sannan yace min da turanci "Ohh ko shine wanda kwanan baya kika sa daddy ya samo wa aiki?" Zuciya ta naji ta bug sau biyu a tare sai kuma ta tsaya chak, jini yayi draining daga fuskata. Ya Walid ya lura da chanzawar yanayi na sai ya daga kafada yace "what did I said?" Daga haka ya juya ya nufi motarsa kirar Ferrari wacce ba'a dadr da saya masa ba. Ta bata wuta, ya kunna kida ya figa a guje a fice. Tunda ya bar gurin babu wanda yayi magana a tsakanin mu. Can Ibrahim yace "you really are a genius maimunatu, you played me like a fool, and like the fool I am I am madly in love with you. What a foolish fool am I" a hankali nace "I am sorry" ya sake mikewa, "sorry? Do u just say u are sorry? Wato kina ganin bazan iya samarwa kaina aiki ba shine kika je ki ka gayawa daddy ya samomin?" Nima na mike tsaye "ni bance ba zaka iya samarwa kanka aiki ba, ka riga ka kai takardunka ka nemi aikin ka da kanka... " ya katse ni yace "amma ni da ke munsan da baiyi magana ba baza'a bani ba" yayi shiru sannan ya cigaba "PC tace min wani ambassador ne yayi endorsing dina, I should have known, amma da yake I am a fool sai na karba ina murna" magana yake yi da karfi cikin bacin rai. Out of no where naga chief security yazo gurin "ma'am is this man bothering you?" ban san sanda na rufe shi da masifa ba nace idan bai bar gurin ba saina saka ya bar aiki. Bashiri ya bar gurin. Na sake cewa da Ibrahim "am sorry, ban dauka ranka zai baci har haka ba, naga kana son aikin kuma I didn't want to loose you. I love you" na fada ba tare da realizing cewa na fadi L word ba. Murmushi Ibrahim yayi sannan a hankali yace "and I love you too, only too much" ya karaso inda nake tsaye ya saka hannayensa biyu ya riko fuskata yana kallon jajayen idanuna, ya cigaba da cewa "I am going maimunatu, zan dawo in ga daddy amma sai na zama worthy of u, sai na zama worthy of meeting your daddy, sai na zama someone da zaki nuna wa family dinki. Please wait for me, I will come back for you, I promise you" i dona a cikin nasa nace "you are already worthy enough to me" ya dora lips dinsa akan goshina for what seems like eternity sannan ya juya bayansa ya kama hanyar gate. Kamar hadin baki sai ruwan sama ya tsuge. Ina tsaye ina kallonsa har ya isa bakin gate sai kuma na tafi da gudu na shiga gida, direct sama na hau, na wuce dakin mu na bude kofar balcony na fita na hangoshi ya fita daga get din ya dau hanyar fita daga quarters din, hannayensa a cikin aljihun rigarsa, yana tafiya a hankali yayin da ruwan sama ya ke sauka a kansa. Anan zan dakata inja hankalin samari da 'yan mata a harkar neman aure, in kaga budurwa kana sonta itama tana sonka, in dai har kana da halin yin aure, ma'ana kana da aiki ko sana'a wadda kasan zai iya rike ku to kar kace sai kayi kudi zakayi aure, hakan bashi da ma'ana. Maybe baka da rabon yin kudin. Maybe arzikin ka is linked with her. Fadin ubangiji ne cewa kowacce rai da arzikinta take zuwa duniya, idan baka da arziki sai kaga a sanadiyyar auren da kayi, ko haihuwar da matarka tayi Allah ya baku arziki. Kuma abinda mutanen mu har yanzu bamu gane ba shine, idan kayi aure baka da arziki, kukazo kukayi arzikin tare da matarka to kun fi mutunta juna, ku sha wahala tare kuji dadi tare. Indai har yrinya tace tana sonka, indai har soyayyar Allah da annabi take maka to bata damu da kudinka ko rashin kudinka ba. Wannan wait for me shiriritar bata da ma'ana, kana can kana neman kudin wani zaizo wanda ya fika komai kuma she may fall in love with him, kaga kayi losing kenan, biyu babu. Next thing da nake so inyi magana akansa, duk da dai sai a next chapter za'a fi fahimtata sosai shine akan judging mutun ba tare da kasan sa ba. Never judge a book by its cover. Yawancin mutane suna da kirki, no matter the tribe, you just need to know them. Masu kudi da masu sarauta, in kaga wulakanci a tare dasu mostly daga gurin na kasansu ne ba daga su bane. You just need to take a deep breath and talk to them... Next thing shine secrets in a relationship. In kuna so relationship din ku ya dore, never ever keep a secret from each other, never lie to each other. Ga 'yammata da samarin da suke tsoron relationship dinsu ba zai dore ba saboda banbancin yare, ko social status, do u try to make it work ko kuma a boye kuke yi? Just take a deep breath ku tunkari iyayenku da maganar, it may turn out easier than you imagine. Ita zuciya an halicceta da son wanda yake kyautata mata, ko wanne kabila ne shi, indai har zai juri kyautatawa iyayenki, yana nuna musu best behavior dinsa, ke kuma kullum kina nuna musu how much you love him, insha Allahu zaku ga chanji a gurinsu. But most importantly pray. [11/7, 11:40 AM] maryamsuleiman48@gmail.co: MAIMOON By Maman Maama 25 Episode Twenty Five: The Heartbreak 💔 Ibrahim has broke many hearts yesterday, especially Moon's. Na cigaba da kallonsa har ya bace min da gani. Feshin ruwan saman da akeyi yana dukan fuskata amma sam ban damu dashi ba. Zuciya ta tana kuna amma hawaye yaki zuwa ido na balle inji dadi. Motsin mutun naji a baya na, nasan ko wace dan haka ban juya ba. Sai da ta lulluba min towel sannan nasan duk jiki na ya jike da ruwa. A hankali ta jani muka shiga daki ta rufe kofar balcony din. Na zauna a kan stool ina goge ruwan jikina ita kuma ta zauna a gefen gado tana kallona. Tace "what happened Moon?" Na dago kaina na kalleta da busassun idanu na nace "He is gone" "gone?" "Yes, He was mistreated by our security, He saw Daddy and....... Ya walid yazo ya gaya masa cewa daddy ne ya samo masa aiki, he then lost it" Hafsat ta saki hannuna ta rufe bakinta da hannayenta. "Oh my God, me yace kuma" nan na bata labarin duk abinda ya gudana tsakanin mu. Tayi shiru na wani lokaci sannan tace "Moon am so sorry, I really am, amma dama nasan alakar ki dashi ba mai dorewa bace. You are too different from each other. Banbancin da yake tsakanin ku kamar banbancin da yake tsakanin maiduguri ne da lagos, ba zasu taba haduwa ba" na kalleta da murmushin takaici a fuskata nace "you are wrong my dear sister, we are more alike than we are different. Na farko duk kanin mu mutane ne, sannan kuma Africans, must importantly kuma Muslims. As muslims kuma munsan we are all equal a gurin Allah, babu wanda yafi wani sai wanda yafi tsoron Allah. Banbancin da kuke gani a tsakanin mu banbancin kabila ne. Ni a ganina kabilar mutum ba komai bace illar yarensa da al'adunsa. Yanzu misali ke wacce yare ce?" Ta kalleni da mamaki tace "fulani mana" nace "eh, babanki fulani ne amma mamanki buzuwa ce, meaning you are not full blood fulani. Yare yana nufin language, yanzu misali ni, ina jin fulatanci, buzanci, turanci, larabci da hausa. To wanne yare ce ni kenan? Yanzu fulani nawa kika sani wadanda suke full blood fulani amma basu iya fulatancin ba? Wani ko zo bai sani da fulatanci ba amma yana ikirarin shi bafulatani ne. It doesn't make sense to me. In nayi maganar al'ada kuma is much worse than yare, dukkan kabilun Nigeria mun aje al'adun mu a gefe mun dauko na wadansu daban munayi. Then how are we different from each other? Yanzu ke da kika ce ke bafulatana ce duk cikin suturar ki babu ta fulani, babu abinda kika sani na daga al'adar fulani, we are even lucky mun iya yaren ma. This all doesn't make sense to me. Yanzu na tabbata idan aka kawo miki wani bafulatanin wanda bai iya fulatanci ba, aka kawo miki igbo ko yaroba wanda ya iya turanci sai ki fi communicating da igbon ko yaroban akan fulanin" duk maganar da nake Hafsat tayi shiru tana kallona da alamar tana fahimta ta. Can ta nisa tace "Ok, yanzu what will you do?" Na kalleta for some seconds nace "That, my dear sister is what I don't know" Sati guda kenan chif da zuwan Ibrahim amma har yanzu ban ji sassauci a zafin da zuciya ta keyi min ba, kuma har yanzu ban yanke shawarar menene abinyi next ba. Ina kwance main palo akan kujera, Hafsat tana zaune a gaba na, mommy tana can gefe tana operating system din ta. Waya ta nayi dialing na saka a kunne na "the number you are trying to call is currently switched off, please try again later, thank you" naji wadannan kalmomin ya kai sau dari a cikin satin nan, amma na kasa hakura in daina trying. Na ajiye yawar na lumshe ido na. Muryar Ya Habeeb naji ya shigo da sallama, ya gaida mommy ya zauna kujerar kusa dani. Na dan kalle shi, yayi min murmushi, ban mayar masa ba, na sake mayar da idona na rufe. Wajan five minutes muna zaune a haka babu wanda yayi magana. Can Ya Habeeb yayi tsaki yace "wai menene yake faruwa a gidan nan ne? Duk komai ya zama so dull kwana biyun nan, ni na gaji gaskiya" mommy tayi ajiyar zuciya tace "I don't know Habibi, ni kaina abin ya ishe ni wallahi, dazu nake cewa ko da yamma fita zamuyi ne mu dan zaga gari? Duk gidan babu dadi" Hafsat tace "au wai ku baku san me yake faruwa ba?" Ya Habeeb yace "menene yake faruwa" tace "we are having a lunar eclipse" mommy tace "what? Me kike nufi?" Hafsat tace "our Moob is no longer bright" duk suka juyo suka kalleni. Ya Habeeb yace "tabbas, duk ta zama wata iri kwana biyun nan" mommy tace "ko abincin kirki bata ci fa, kullum na tambayeta ko bata da lafiya sai tace min ita lafiyar ta kalau" duk ina jin abinda suke cewa amma na kasa tanka musu. Daddy ne ya shigo ya Walid yana binsa a baya. Muka tashi gaba daya muka gaishe shi. Ya amsa mana da fara'arsa kamar yadda ya saba. Ya zauna sannan yace "dama ina son ganin ku gaba dayan ku, to tunda gaku kun hadu shikenan sai muyi maganar" mommy ta rufe system dinta ta dawo kusa da daddy ta zauna, mu kuma duk muka sauka kasa muka zauna a gabansu. Daddy ya fara magana da cewa "maganar da nake son inyi muku akan Hafsatu ne da Maimunatu. Tunda Allah yasa kun gama secondary school, ina son in san plan din ku for the future. Aure kuke so kuyi ko kuma karatu kuke son yi?" Muka juya muka kalli juna ni da Hafsat, saboda bamu taba tsammanin wannan tambayar daga gare shi ba, mun riga mun yi zeroing mind din mu cewa karatu zaice muyi, la'akari da irin zurfin ilminsa sannan yayun mu suna gama sec sch suke wucewa university. Mommy ma ta saki baki tana kallonsa tace "aure? Aure fa kace Dear?" Ya kalleta da murmushi yace "yes, aure" ta nuna mu da hannu tace yanzu wadannan 'yan babies din za'ayiwa aure?" Dariya sosai daddy yayi yace "kwarai da gaske. Babu wacce zan matsawa a cikin su ince tayi aure, amma duk wacce tace min aure ta ke so to babu shakka auren zanyi mata. It's very wrong abinda mutanen mu suke yi yanzu na cewa ba zasuyi wa 'ya'yansu aure ta sai sunyi karatu mai zurfi. Hakan bashi da ma'ana. Indai har yarinya ta isa aure, ta samu miji, kuma tace tana son auren to abu mafi a'ala shine ayi mata auren. In ba haka ba ka shiga hakkin 'yarka kuma in Allah bai kare taba to zaka jefa ta a halaka" mommy ta tabe baki tace "ni dai 'ya'yana basu isa aure ba" daddy yace "cikin su wacece bata period" duk palon kowa yayi shiru, ya cigaba da cewa "shekara nawa nana Aisha ta tare a gidan annabi SAW? Duk abinda annabi yayi a rayuwarsa yayi ne saboda yana so mu kwaikwayeshi, su Westerners din da muke kwaikwayo basa yiwa 'ya'yansu aure da wuri amma ai basa hana 'ya'yansu tare wa a gidan samari ko? Mu tunda addinin mu ya hana hakan mai yasa ba za muyiwa yaranmu aure in sun isa ba?" Mommy ta sauke ajiyar zuciya ta karya murya tace "amma dear karatun fa?" Daddy yace "aure ai baya hana karatu, su kansu mazan yanzu ai sun waye basa hana matan su karatu. Yanzu misali, Prof Rukayyatu Ahmad Rufa'i tana sec sch akayi mata aure amma sai da takai har matsayin professor. Dan haka indai har mazajen su sun amince to za suyi karatu har sai inda suka gaji" yayi shiru for some time. Kamar daga sama yace "Moon ina saurayin nan naki yaroba?" Da sauri na dago kai na na kalle shi sannan na kalli mommy wacce itama shi take kallo da sakakken baki. Ya cigaba da cewa "yes, I know. Tun sanda kika sa na nemar masa aiki nasan there is something between you two. Na yi miki gargadi akansa ne saboda malamin ki ne a boarding school, babu idon mu a kanku, amma nasan in har da gaske yake son ki zai biyo ki gida, kuma naga ya biyo ki din. I thought zai zo ya ganni ranar sai kuma naga bai zo ba, sai na saka a raina cewar he is not ready" mommy ta fara girgiza kanta tana maimaita "no, no, no, not my daughter, not Moon" daddy ya cigaba da cewa "I know your mother will throw her tantrum, but I can handle her" mommy tayi sauri tace "inna da baffa ma ba za su yarda ba, Moon din za'a aura wa bayarabe? Dama munafikin copper dinnan ashe bana Allah bane?" Daddy ya kalleta with serious face yace "menene matsalarki da shi" tayi sauri tace "bayarabe fa kace? Wannan kadai bai isa matsala ba?" Daddy yace "indai har yana sallah, yana da asali, mutumin kirki ne, kuma yana da halin rike mata shikenan. Wannan shine abinda addini ya gindaya mana akan in zamu zaba wa yayan mu mazaje, addini baice mana mu duba kabila ko yare ba" mommy wacce by now ranta ya gama baci tace "I am not looking forward to having yaroba grandchildren, can u even imagine that?" Daddy ya kashingida akan kujerar da yake kwance yace "kinga shikenan sun huta idan ana tribal crisis" Ya Habeeb yayi dariya mommy ta harare shi. Daddy ya kalleni yace seriously"tell him in da gaske yake yazo ya same ni muyi magana dashi, in kuma bada gaske yake ba kar ya sake zuwa gidan nan" ni dai bance komai ba. Ya juya kan Hafsat yace "Hafsat ke kuma fa? Karatu ko aure?" Hafsat ta gyara zama tace "daddy ni dai nafi son karatu" yace "shikenan, Alhamdulillah. Along the line in kina karatun in kinji kina son auren kuma Allah ya kawo mijin shikenan sai kiyi kayanki" Ya Habeeb ya zunguri Hafsat "to dama ba dole kiyi karatu ba, tunda babu mashinshini?" Ta juya ta murguda masa baki, yace "kinga tsiyar ai, rashin kunyar kima ai bazata bar samarin su zo ba" duk akayi dariya banda mommy. Daddy yace "shikenan, kowa ya tafi harkokinsa, next week zamu sake yin magana" da sauri na mike, dama kaman akan kaya nake zaune. Na hau saman mu, ina shiga daki naji tafiyar Hafsat a baya na. Ta shigo ta rufe kofa. Lokacin ina cire kaya na tace "now what?" Nace "now, my dear sister, I am going to look for him" da haka na shiga wanka. Ina wanka ina tunanin abubuwan da suka faru. Look what Ibrahim almost cost us. The Idiot. Na fada a fili. He don't know daddy amma after one look at him yayi deciding ba zai saurare shi ba. The Fool. Har da wani tafiya wai sai yayi kudi zai dawo, ko ina ruwan daddy da kudinsa? The Idiot. Na fito daga wanka na zura doguwar riga nayi rolling vail. Hafsat naga ta yafa mayafi. Nan muka fita tare. A falon mommy muka same ta a zaune ita kadai har yanzu ranta a bace yake. Ta bimu da kallo. Hafsat tace "mommy zamu danje unguwa mu dawo" wani mugun kallo mommy tayi mata tace "wato dan ance za'ayi muku aure shine zaku fara yawo kuma? Ko neman mazajen zakuje yi?" Hafsat tace "mommy gidan su Amira fa zamu je" "oh zakuje ku bata labarin za'ayi muku aure ko?" Mu kayi shiru bamu ce komai ba. Ta kalle ni tace "Maimuna ki kiyaye ni wallahi, ki fita daga ido na in rufe, ko da wasa na sake jin maganar wannan bayaraben wallahi sai kin san bani da dadi" na makale daga bayan Hafsat. A raina nace "oh mommy, da kinsan yadda nake jin bayaraben nan a raina da baki ce haka ba" mun jima a tsaye sannan tace "kar ku kai magrib" daga nan ta tashi ta shige bedroom dinta. Muna fita driver ya dauko motar da ake kaimu unguwa. Wani security ya zo ya shiga seat din gaba, take nace masa ya fita. After what happend ba zanje gurin Ibrahim da security ba. Mu ka shiga baya Hafsat tace da driver ya kaimu former school din mu. Muna zuwa staff room muka wuce. Muna shiga seat dinsa na kalla. Lokaci daya na sandare a inda nake tsaye. Babu shi babu alamar sa. Babu komai akan desk dinsa. Not even a single paper. Babu kowa a staff room din sai wani malami guda daya. Hafsat ta karasa gurinsa ta gaishe shi, yace "well3, didn't expect to see you soon" Hafsat tace "sir, malam Ibrahim fa?" Ya maida kallonsa kaina yace "you didn't know? He is gone. He quite his job five days ago, babu wanda yasan mai ya faru, yayi rashin lafiya for two days aka kwantar dashi a clinic, yana fitowa ya rubuta resignation, a day after that ya kwashe kayansa kaf ya koma ibadan" sama sama naji Hafsat tana masa godiya, naji ta zo ta kama hannuna tana ja na, naji ta sakani a mota ta rufe kofar ta zagaya ta shiga daya side din. Driver ya ja muka tafi. He is gone, He is really gone. Ban taba tambayarsa address dinsa ba. Ban taba tambayarsa phone number din wani nasa ba. Abinda na sani kawai shine a ibadan yake, where in ibadan I don't know. Hanyar da Ibadan take ma bansani ba. Ina jin driver din mu yayi horn mai gadi ya bude masa get muka shiga gida. Muna fitowa sai ga mai gadi nan ya taho da saurin sa yana yi min magana. "Mai sunan Daada" duk muka tsaya. Ya zo gurina yace "mai sunan daada kinga na manta wallahi sai yanzu dana ganki. Kwanaku hudu da suka wuce wani yazo ya bani sako yace in baki, yana ta jaddada min kar in manta kinga kuwa sai da na manta din, kinsan tsufa sai a hankali" a nutse nace masa "ina sakon yake?" Da gudu ya sake komawa dakinsa sai gashi da wata brown envelope a hannunsa. Hafsat ce ta karba ta gode masa. Ta bare seal din ta saka hannu a ciki sai gashi ta fito da CD a hannunt. A jikin CD din an rubuta da marker I LOVE YOU. Tsaf na gane rubutun sa. Hafsat ta shiga gida ni kuma na koma motar da muka fito, na zauna a seat din gaba na kunna radio na zura CD din hannuna sannan na danna play. A hankali wakar ta fara tashi.. ...... I don't know when am coming back. I will be gone for a little while, but I will keep myself for me and you, I will be back for you. I don't know what the future will brings, but I will want you to be with me. I will hope and pray make you wait for me, cos I will come back for you, darling You are my life, you are my prize, and I went to the finish line. You will be always on my mind. I will be so far away, promise you will wait for me, I will think of you everyday, my love. I may not come today, but I will be with you again. I will pray for you everyday, My Love.......... I will think of you tonight, cos I no dey by your side, just for a little while, but know that am alright, and I will see you soon, make you wait for me my dear Na runtse idona, sannan for the first time tun tafiyarsa, hawaye suka gangaro kan kuncina [11/7, 11:40 AM] maryamsuleiman48@gmail.co: MAIMOON By Maman Maama 26 Episode Twenty Six : The Eclipse Kuka nayi sosai ni kadai babu mai rarrashina. Saida nayi na gaji dan kaina nayi shiru. Na kashe radion na chire CD din na fito daga motar. Ta kofar baya na shiga gidan saboda bana son ganin kowa. Direct saman mu na hau na shiga daki na turo kofa. Na zauna a kan gado ina kallon rubutun jikin CD din. I LOVE YOU. Nasan Ibrahim yana sona but how much? Ni a tunani na in kana son mutum zaka so ka kasance tare dashi, ya kamata ace komai runtsi komai tsanani ace muna tare, we can face anything together. Amma yanzu ya tafi, ya kuma kashe wayarsa ma'ana baya son magana da ni, sannan kuma yace min I love you?. What kind of love is this?. Na jawo kafafuwa na na dora akan gadon da dunkule a guri daya. I wish sanda ya fara cewa yana sona nace masa no, da ban saba dashi ba ballantana har inyi kewarsa. Da yanzu bana jin radadin da nake ji a zuciya ta. Na saka hannuna na jawo bargo na kudunduna. Wa yace da Ibrahim na damu da kudinsa ko rashin kudinsa? As long as we are together, that's the only thing I want. A hankali na mayar da idanuna na rufe. Kaina ne yake bala'in sara min, idanuwa na sunyi min nauyi. Da kyar na motsa ido na ina son in bude su amma na kasa. Muryar mommy naji can nesa tana cewa "Moon3" na motsa bakina amma na kasa magana. Can nesa naji daada tana to fa min adduoi sai kuma naji kukan mommy kasa-kasa. To ita mommy mai ya sakata kuka? Ko har yanzu zancen da daddy yayi mana ne a ranta? Ita kuma daada me ya kawo ta dakin mu? Ita da bata shigowa part din mu in har daddy yana nan. Na tattaro dukkan karfina na bude ido na dan in tabbatar me yake faruwa. Ga mamakina sai naga dakin ya chanza min, ya koma kamar dakin asibiti, ga ledar ruwa nan a sakale a kusa da gadon da nake kuma daga dukkan alama ni ake karawa ruwan saboda igiyar hannuna ta shiga. Mommy tana zaune akan kujera a kusa dani ta jingina kanta a jikin daada wacce take tsaye a kusa da ita tana lallashinta. Dama mommy ta saba, in dai wani a cikin mu bashi da lafiya to ta ringa kuka kenan har sai ya warke. Na kalli daya side din gadon. Hafsat ce a zaune a zabga tagumi fuskar ta da alamar damuwa. To da gaske ni ce bani da lafiyar kenan tunda nice a kwance. A hankali na furta "mommy" ta dago jajayen idanuwanta ta kalleni sannan ta kalli daada wacce itama ni take kallo. Gaba daya suka karaso kusa dani mommy ta rike hannuna mai dauke da drip. Nace "mommy wai bani da lafiya ne?"da sauri mommy tace "lafiyar ki kalau my daughter, kawai zazzabi ne kike yi, maybe ma malaria ce" mommy bata iya karya ba dan haka tana fada na gane ba haka bane. Hafsat ta fita sai gasu sun dawo tare da likita. Dan matashin saurayi ne haka dogo marar kiba. Ina ganin sa gaba na ya fadi. Ibrahim. This is not Ibrahim. Ibrahim is gone. Na rintse idona kaina yana cigaba da sara wa. Doctor din ya auna ni yace "zan sake yi mata allurar bacci saboda ciwon kan, kar a tasheta sai ta tashi da kanta, in ta tashi sai mu sake gwada jinin nata mu gani in ya sauka" what? Me likitan nan yake nufi in jini na ya sauka? Yaushe ya hau ballantana ya sauka? Shigar allura naji a cinyar hannuna daga nan kuma shikenan. Sanda na sake bude ido na mommy na sake gani a zaune a inda take, amma ta chanza kaya, fuskarta harda kwalliya. Da sauri tazo kusa dani ta zauna tana murmushi. "Sannu Moon, ya jikin naki?" Nima nayi mata murmushi nace "da sauki mommy" ta dauki wayarta tana waya, daga alama Ya Walid ta kira, naji tana ce masa na farka su shigo. Ba'a jima ba sai gasu complete har daddy. Duk sunyi kwalliya kuma kowa da murmushi a fuskarsa. Nan da nan dakin ya hargitse da hayaniya kowa a cikin su na kokarin jawo attention dina zuwa wajensa. Daddy ne ya, dauko wata sabuwar system kirar apple, red colour, yace "surprise!!" Ya miko min, na tashi zaune da sauri, ciwon kan ya ragu sosai, na karba ina godiya, yace "get well soon sunshine" sannan yayi min kiss a goshina, the same spot da Ibrahim yayi min ranar da zamu rabu. Ya Habeeb ya tabe fuska kamar mai shagwaba yace "gaskiya nima bara in zo in fara rashin lafiya tunda har gift ake bawa mutun in bashi da lafiya" gaba daya suka yi dariya, nima nayi murmushi. Mommy ta dauko wayarta ta zagayo ta bayana tace "selfie" nan da nan duk suka taho kowa yana zuro guskarsa, faruk har da hawowa kan gadon da nake ya kwanta a jikina. Mommy ta nuna min hoton tace "look moon, duk ke kika chinye hoton" na karbi wayar na duba, sam banyi kyau ba, bakina duk a bushe, fuskata tayi fari tas kamar babu jini, gashina duk a tarwatse ga idona ya fada ciki kamar nayi sati a kwance. Na kalle su daya bayan daya duk suna min murmushi, na gane me sukeyi, they are trying to cheer me up saboda jini na daya hau ya sauka. They love me so much and I love them too. They mean more to me than Ibrahim ever will. Har dare suna nan. Anan duk suka ci abincin dare. Sai lokacin na fahimci kwana na biyu a asibitin. Mommy da kanta tayi min wanka da ruwa mai zafi dan inji karfin jikina, ta shafa min mai ta chanza min kaya, ta bani kunun gyada mai zafi ta saka dole sai da na shanye cup daya. Sosai naji dadin jikina. Mommy ce ta kwana a gurina. Da daddare ta saka ni duk saida na rama sallolin da ake bina sanda nake bacci. Washegari da safe doctor yazo ya auna ni yace jinin ya sauka sosai, zasu rikeni zuwa yamma su gani, in bai kuma hawa ba sai su sallameni. Bayan an sallame ni mun koma gida ma haka ce ta kasance, dan mommy dawowa tayi dakin mu muke kwana tare. Tace barin mu da take yi mu kadai ne ya saka nake tunani har jini na ya hau. Daddy kuma kullum sai ya shigo kafin ya fita, in ya dawo ma sai ya shigo. Kwana na biyu a gida na warke sosai, babu ciwon kan sam kuma tunanin ma ya ragu, dan sam ba'a barina ni kadai. A week after that daddy ya sake kiran mu palonsa. Muna zuwa muka tarar dashi da mommy a zaune, ya Walid da Ya Habeeb ma duk suna zaune a kasa. Muna zama sai ga Faruk shima ya shigo. Ya Walid yayi mana addu'a muka shafa. Daddy yayi gyaran murya yace "kamar yadda na gaya muku wancan zaman cewa zan neme ku bayan sati daya, rashin lafiyar moon ce ta saka har muka yi delaying zaman. Yanzu ina son in gaya miki wani abu moon, ba fa matsa miki nayi nace sai kinyi aure ba, ra'ayinki nake so inji. Kuma gashi naga har yau shi wanda nayi miki magana akansa bai zo ba, kuma ko a asibiti ban ganshi ba. Ina so inji kunyi magana dashi ne? Nayi shiru can na dago kaina nace a nutse "daddy munyi magana dashi amma na fahinci cewa he is not serious akan maganar, dan haka nima na yanke shawarar zan fara karatu na first kafin inyi aure" murmushi ne ya bayyana a fuskar mommy tace "Alhamdulillah, kafin ki gama karatu kuma insha Allah kin samu wani" ni dai na sauke kaina kasa bance komai ba. Daddy yace "to Alhamdulillah, hakan ma yayi, Allah yasa haka shi yafi alkhairi. That been said, ni da mommyn ku mun yanke shawara, tunda Walid da Habibi suna karatu a England, ga Hafsat da Moon suma sunce karatu zasuyi, to zamu tattara gabaki daya zamu koma England da zama. Dama tunda nazo nake ta chuku2n yadda za'ayi min transfer daga kasar da nake yanzu zuwa England kuma Alhamdulillah jiya aka tabbatar min da samuwar transfer di ta, mommyn ku kuwa ta rubuta leave of absence a office dinta har sai ranar da Allah ya sa muka dawo Nigeria. Faruk shi kuma tunda saura shekara daya ya kammala sec school zamu barshi anan shi da daada har sai ya kammala tukun sai ya bi mu can" tunda ya fara maganar komawa England gaba daya palon ya hargitse, kowa murna. Ni ina zaune kawai ina kallonsu suna ta tsalle suna rungume juna, at the same time ina assessing maganar daddy. Tsam na zame jikina na bar palon na hau saman mu, kofar balcony na bude na fita waje na kama railers ina kallon exact gurin da naga Ibrahim last. Dear Ibrahim, when are you coming back? Dole na san sai na bar Nigeria. Tunani na anan shine, what if Ibrahim ya dawo ya tarar bana kasar? Ta yaya zaiyi contacting dina? Na zauna na danyi tunani kadan sai na dauko takarda da biro na fara rubutu kamar haka: Dearest Ibrahim I may not be around when you come back. Please give the man who gave you this letter your new phone number and I will call you. I miss you Maimunatu. Na ninke takardar na saka a envelope nayi sealing. Sai da naga babu mutane a compound din gidan sannan na fita na tafi gurin baba Habu mai gadi. Tun da daddy ya gina gidannan ya saka baba Habu gadi kuma har yau shine yake bude gate da rufewa. Ina zuwa na ganshi a zaune a kan benci shi kadai. Na zauna a gefensa na gaishe shi, ya amsa min da fara'arsa. Nace "baba yanzu kuwa zaka iya gane wanda ya kawo maka sako rannan yace ka bani?" Da saurinsa yace "sosai ma kuwa. Ai ina da mantuwa amma kuma ina da gane mutane" na dauko takardar hannuna na mika masa nace "baba dan Allah gashi, duk sanda yazo in bana nan ka bashi kace injini, zai baka sako ka bani. Baba dan Allah kar ka manta" ya kalleni da alamar tambaya a fuskarsa amma ya daure ya ce "in sha Allah mai sunan daada, kar kiji komai" nayi masa godiya na koma cikin gida. Shirye shirye akeyi sosai na komawar mu England, daddy yace yana so mu je 'yalleman muyi musu sati daya kafin mu tafi, duk da dai zamu ke zuwa Nigeria in mun sami hutu. Kafin tafiyar mu sai ga sako daga former school din mu ana gayyatar mu taron speech and prize giving day da graduation party da school ta shiryawa 'yan set din mu. Hafsat tana ta murna ni kuma nace bazanje ba. Mommy tayi tayi dani inje saboda da akwai awards da za'a bani kuma ko ba komai ai zanga friends dina za muyi sallama tunda ba lallai mu kuma haduwa da wadansu ba, ga pics da video da za'ayi na tarihi. Hafsat kamar zatayi kuka tana roko na akan inje amma naki nace har yanzu bana jin dadin jikina. Su basu san abinda yasa naki zuwa ba. I don't want to bring back the memories, which is exactly what will happen idan naje. Ina kallo Hafsat taci kalliya kamar ba gobe ta tafi, na bata sakon ta gaishe min da kowa kuma ta karbo min gift dina. Suna tafiya na koma balcony na zauna ina kallon hanyar da Ibrahim yabi. We made so many plans for our graduation party. Ibrahim cewa yayi zai yi mana anko ni da shi mu saka ranar. Nayi murmushin takaici ina tausayin Hafsat akan irin tambayoyin da zata sha a gurin 'yan ajin mu in sunga babu ni babu shi. Haka staff ma, dan kusan kowa yasan abinda yake tsakanina dashi. Na sake yin wani murmushin dana tuno yau shine exactly two years da haduwa ta dashi. Yanzu gashi mun rabu kuma ko hotonsa bani da shi, amma ina da permanent picture dinsa a zuciya ta. A hankali na furta a fili "Happy Anniversary Ibrahim [11/7, 11:41 AM] maryamsuleiman48@gmail.co: MAIMOON By Maman Maama 27 Episode Twenty Seven: A Step Further Away Basu dawo ba sai daf da Magrib. Suka dawo da kaya niki niki. Hafsat ta zauna tana bani labari kamar zata ari baki "gaskiya Moon kin yi missing, kowa yazo kuma kowa sai ya tambaye ki" nayi murmushi kawai, a raina ina cewa Hafsat ba za ki gane ba. A lokacin ne mommy take cemin an bawa Amira scholarship award dina, na tambayi Hafsat nace "ya Amira tayi kuwa da aka bata?" Hafsat ta tabe baki tace "kema kinsan ya tayi ai, she first said it is a mistake, sai da pc ta kira su ita da maman ta tayi musu bayani cewa it is a gift from you, baki ga maman ba har da hawaye tana yi wa mommy godiya. Ni fa banji dadi ba Moon, you are too soft wallahi, wai duk abinda yarinyar nan tayi miki amma shine zaki wani bar mata scholarship award dinki" mommy ta dan bata rai tace "me Amiran tayi wa Moon?" Hafsat tayi sauri tace "it is nothing mommy, wani small girl issue ne kuma munyi solving tun a school" daga gani kasan mommy ba ta yarda da bayanin Hafsat ba, kawai dai tayi shiru ne. Nan suka dauko min gifts dina suka nuna min. Duk a ciki guda biyu sunfi birgeni, na farko medal din da school ta bani, na glass ne me kauri, a ciki anyi rubutu da golden colour kamar haka: Award of Excellency To Maimoon Muhammad Dikko For being the most talented student this school has ever had. Na biyu kuma students ne suka bani, shi kuma da wood suka hada shi, a tsakiya sun yi zanen moon, a kasa kuma suka rubuta: Thank you Moon for brightening our lives. We will forever miss u. Kawai sai naji hawaye a ido na. Hafsat ta dauko wayarta ta nuna min video da 'yan set din mu suka yi suka ce a nuna min. Duk sunyi kwalliya kuma they are all laughing and talking at the same time. "Moon ashe baki da lafiya? We miss you today, kinga gifts dinki?...... " ina dariya kuma ina hawaye at the same time, can wata a videon tace "Moon shine kika rike mana uncle kika hana shi zuwa ko? Hafsat tace yana can yana jinyar ki, ki gaishe ki kice we miss him also" na kalli Hafsat ita kuma ta daga kafada. Wato karya tayi musu tace muna tare da Ibrahim shi yasa basu ganshi ba. Class monitor din mu Hamidda ta hada min take away na duk abinda aka ci a gurin party da handwritten note na get well soon. A ranar da daddare sai ga Amira da mamanta sunzo yimin godiya har gida, mommy ta kaisu gurin daddy shi ma suka yi masa godiya. Daga nan muka tafi dakinmu muna hira, anan muka ba ta labarin tafiyar mu England, yanda tayi da fuskarta kamar zatayi kuka. Nace mata "Amira ni ina ganin ki cike Oxford kawai sai mu tafi tare, kinga sai ki zauna a gidan mu muke zuwa makaranta tare" ta girgiza kanta idonta fal kwalla tace "I can't. Mama bata da kowa a garin nan sai ni. Bazan iya barin Nigeria in barta ita kadai ba. University of Abuja zan saka saboda in zauna a gida. I wish you guys best of luck in England, in kun je please ku kira ni saboda in samu number dinku ta can" nace mata "insha Allah, you will be among the first ones da zan kira" Haka muka yi ta hira har sai da suka zo tafiya. Casually ta tambayeni "ya labarin uncle din mu kuwa? Naga shima baije partyn mu ba" na kalleta sai ta sunkuyar da kai. Hafsat ce ta gaya mata yayi directly "yayi resigning daga aikin sa ya koma Ibadan" ina kallon fuskarta ta chanza kala lokaci daya "but you are in contact right?" Hafsat tayi sauri tace "What is it to you, in suna fa contact?" Na dakatar da Hafsat da naga ta fara daukan zafi, nan na bawa Amira labarin duk abinda ya faru, na kara da cewa "I believe He will come back like he promised" Hafsat ta ja tsaki tace "wahala da rai" tun daga nan Amira bata kara cewa komai ba har suka tafi" Washegari muka tafi "yalleman, satin mu guda acan kamar yadda daddy yace. Amina cousin din mu da muke kusan sa'anni sati daya na bata, ta dage lallai sai ta bimu England da kyar daddy ya lallabata yace ta bari in ta gama sec sch za'a mayar da ita can. Mun shaku da Amina sosai dan bayan Hafsat, ita ce kamar second sister dina, bayan kasancewar mu sa'anni, muna kama da ita, dan idan naje 'yalleman cemin ake yi Hassanar Amina. Muna dawowa Abuja muka fara shirin tafiya England. Muka yi sallama ta duk makota, muka hada hada personal kayayyakin mu, duk da dai daddy yace kar mu dauki kayan sawa tunda zamu ke zuwa Nigeria, in mun je can ma sayi wadansu. Duk da cewa na zama busy a kwanakin nan amma komai nakeyi sai inji irin feeling dinnan da mutun yake ji idan ya manta baiyi wani abu mai muhimmanci ba. Ibrahim is always there tugging at my mind. Ranar da zamu tafi muka su Faruk da daada suka raka mu airport, faruk har da kukansa muna ta tsokanarsa. Muka shiga jirgi, mommy tana kusa da daddy, ya Walid da Hafsat, ni da Ya Habeeb. Jirgin mu yana tashi na kalli window, ina kallon Nigeria a hankali gajimare yana rufe ta tana bacewa. "Goodbye Ibrahim". Na fada a hankali knowing now I am a step further away from him. Na saka earpiece, na lumshe ido na na jingina kaina a jikin headrest din seat dina yayin da jirgin mu ya cigaba da lulukawa sararin samaniya. This journey is like a transition in my life [11/7, 11:41 AM] maryamsuleiman48@gmail.co: MAIMOON By Maman Maama 28 Episode Twenty Eight : University of Oxford Karfe dayan dare jirgin mu ya sauka a birnin London. Tuni motoci masu dauke da tutar Nigeria masu fenti kalar kayan sojojin Nigeria suna jiran mu. Muna sauka suka dauke mu sai embassy. A cikin embassy din anan gidan da zamu zauna yake. Gate daya ne zaka shiga, sai ka wuce offices din su daddy sannan sai gidan, sai kuma gidajen sauran manyan staff na embassy din. Gidan katon gaske ne, dan kusan girman su daya da gidan mu na Abuja with exception of part din su inna da na daada. Amma wannan gidan yafi wancan haduwa, it makes me wonder dama Nigeria muna da irin wannan arzikin? Ko dan kawai muyi show up ne a duniya a dauka babu talauci a Nigeria? Wato rayuwa a Nigeria kamar kashin dankali ce, manya su suke danne kanana. Komai a gidan computerized ne, ko wacce kofa sai tayi detecting finger print sannan zata bude, dan haka dole a daren akayi uploading finger prints din mu. Part din mu ni da Hafsat kowa da dakinsa, falo daya, kitchen daya amma mommy tace sam sai dai mu rufe daki daya mu zauna tare, kitchen din ma tace a rufe, mu ringa zuwa main dining room muna cin abinci tare dasu. Mommy da daddy part din su daya, ya Walid da ya Habeeb ma haka. Sai kuma main palo wanda yayi connecting duk parts din. Washegari da yamma muka fita shopping muka siyo kayan amfanin mu kaf, tun daga kan sutura, toiletries, cosmetics da sauran tarkace. Daddy tun yana biyan cash har ya dawo using credit card, daga baya yace "kai yaran nan so kuke kuga gudun ruwa na ko? To ya isa haka" mommy tana yi masa dariya tace "kai fa kace kar su taho da komai zaka saya musu anan, duk wanda ya sayi rariya kuwa ai yasan zata zubar da ruwa" ni da Hafsat dogayen riguna mommy ta sa muka dauka saboda zuwa makaranta, tace bata son shigar english wear, kar muga muna England muce muma mun zama turawa, mun dauki english wears din dai amma saboda sakawa a gida. Mun sayo sababbin sim cards muka saka a wayoyin mu muka cire na Nigeria muka ajiye. Nan muka fara kiran 'yan'uwa da abokan arziki muna basu numbers din mu. Kamar yadda nayi alkawari, Amira tana daga cikin na farkon dana kira. A week after zuwan mu England aka fara maganar school din mu, ni dama daddy yasan me nake so, neurology, Hafsat aka tambayeta tace itama medicine din take so bangaren gynecology. Har daddy yace mu tafi sai nace "daddy, ina so kuma in dau some courses on psychology" yayi shiru kafin yace "anya Moon abin ba zai yi miki yawa ba? Medicine is not easy on it's own sannan kice zaki kara da wani abun kuma?" Nayi shiru bance komai ba, yace "OK, I will see what I can do, normally ba'a barin students su dau courses out of their field, amma tunda psychology is some how related to medicine zan nema miki" nayi godiya muka tashi muka tafi. Muna zuwa falon mu Hafsat ta fara tambayata "ke kuwa me yasa kike son yin psychology?" Nace "I want to know exactly what people are thinking, I want to be able to tell if someone is lying or not" tayi shiru sannan tace "is this about Ibrahim?" Nace "partly, yes" Tunda muka koma England,duk sati sai na kira baba Habu maigadin mu na Abuja na tambayeshi ko Ibrahim yazo? Kuma duk sati amsar daya ce "bai zo ba tukun" rannan ina kiran sa kafin inyi magana yace "mai sunan daada" gaba na ya fadi nace "na'am baba" yace "indai har da gaske yana sonki zaizo, ni kuma in yazo zan bashi sakonki kuma zan kira ki in gaya miki yazo har in baki shi ma ku gaisa, idan kin ga bai zo ba, to ba son gaskiya yake miki ba ko kuma Allah bai kaddara alakar da take tsakanin ku mai dorewa ce ba, ki kwantar da hankalin ki, ki manta da batun sa, kiyi karatun ki" jikina naji duk yayi sanyi, kirjina yayi nauyi, nasan gaskiya baba Habu ya gaya min amma anya kuwa zan iya? Murya a sanyaye nace "nagode baba" daga nan ya kashe wayar. Mun kama karatu sosai. Ita kanta makarantar abar kallo ce, dan zan iya cewa gari guda ce, with its ancient buildings, kowanne faculty kamar unguwa guda ne, dan saida daddy ya bamu maps yace muke tafiya dashi saboda kar mu bata. School of medicine duka muke ni da Hafsat, kuma first year komai tare za'ayi mana tunda kamar introductory courses ne, daga third semester kuma zuwa sixth kowa zai dauki individual courses din field dinsa, shekara ta hudu da ta biyar kuma zamuyi clinicals, kamar practical kenan inda zamu tafi asibitoci muna koyon aiki a gurin kwararrun likitoci, shekara ta shida kuma project. Tsarin makarantar tsari ne me kyau, lecturers dinsu sunsan me sukeyi, ga kayan aiki nan kamar banza, a raina nace dole a kira ta da second best university in the world. Tunda muka fara lectures kawai sai naji nayi loosing interest a karatun, sam bana gane me akeyi. Ina shiga lecture hall zan tafi seat din baya in zauna in yi ta sake sake a raina ina tuno rayuwar sec sch din mu, sai inji gaba daya hankali na ya koma Nigeria. Sometimes sai inke ganin kamar a class din mu muke, Ibrahim zai iya shigowa anytime. Wani lokacin kuma sai inji kamar kamshin turarensa sai inyi ta waige waige. Duk sanda wani yazo yana son yayi min magana sai inji kamar Ibrahim yana kallona da lumsassun idanuwansa. It is like he is watching me. Sau da yawa in mun shiga lectures sai in kwanta inyi ta bacci har sai an gama sannan Hafsat ta tashe ni. Hafsat tayi fadan, tayi nasihar amma ina, sai da tace zata gayawa mommy bacci nake a class sannan na daina baccin amma still attention dina baya gurina. It is a million miles away. Only time da nake zama inji lecture sai a psychology courses dina. In homework aka bayar sai dai Hafsat tayi mana, kullum tayi ta min gori tana yimin bala'i amma bazan yi ba. It is as if spirit dina na karatu is gone. A haka muka gama first semester, lokacin exams ma da kyar Hafsat ta tirsasa ni na danyi karatu tana koyamin wasu abubuwan. Hutun da aka bamu babu yawa dan haka daddy yace ba zamu je Nigeria ba, ranar har zazzabi nayi, mommy ta ga ciwona yana kokarin tashi ta kwashe mu muka tafi yawo banda daddy sai security daya hada mu dasu. Mune gari gari, duk garin da muka je sai mu samu hotel mu kwana, mune zuwa kallon London bridge, mune har Scotland da Wales. Na saki raina sosai nayi enjoying time dina. Hutun mu yana karewa muka dawo gida. Muka cigaba da zuwa makaranta. Har yanzu bani da kawa ko aboki, in fact da yawa daga 'yan ajin mu basu sanni ba, wadanda duka sanni ma suna referring to me as Hafsat's sister, dan basu san suna na ba. It is like am afraid to get attached. Duk abinda akeyi daddy bai sani ba, tunda basu kafe result ba sunce sai at the end of the session. Mommy kuma tunda a gida ina nuna bani da wani problem itama bata taba tunanin ina da problem a karatuna ba. Ni dai kullum lissafin sanda zamu yi hutun session nake yi, dan wannan karon nayi alkawarin bincike zanyi sosai sai na nemo Ibrahim na gaya masa daddy yace bai damu ko wanne kabila ne shi ba, bai kuma damu da cewa he is not wealthy ba, gani nake yi hakan ne kawai zai saka ni in maida hankali na akan karatu na. Second semester tana karewa aka fitar da result na both semesters din. Tunda Hafsat ta gayamin gaba na yake faduwa, nasan ban aikata abin kirki ba. Allah Allah nake mu tafi Nigeria kafin daddy yaga result dina in yaso in mun dawo ayi wacce za'ayi. Adduah ta bata karbu ba dan washegarin da aka kafe result muna main palo muna kallo sai mommy ta kira Hafsat tace muzo daddy yana kiran mu. Muna shiga palon su na san daddy yaga result dina. Bantaba ganin bacin rai a fuskarsa irin na ranar ba. Muna zama su yaya Walid suka shigo da fara'arsu, ganin yanayin fuskar daddy suma suka shiga taitayinsu. Muna zama ya jeho min takardar hannunsa yace "pick it up" hannu na rawa na dauka, yace "bude ki karanta a fili inji" nan na bude na fara karanta sakamakona. Tun daga first semester har second bani da B ballantana A. Mostly C ne har da D. Nan daddy ya fara fada, ta inda yake shiga ba tanan yake fita ba, tun ina daurewa har na fara kuka. Yayi min wankin babban bargo mommy ta dora a inda ya tsaya. Su bakin cikin su shine sunsan ina da kokarin kawai karatun ne suke ganin banyi niyyar yi ba. Nan daddy yace dole ayi punishing dina akan abinda na aikata. Yace "punishment dinki shine, no holiday for you. Zaki zauna ke kadai a England ba zamu tafi dake Nigeria ba. Use the time to think about what you have done to your life. Sannan kiyi karatu so that you can catch up a inda aka barki a baya" daga haka ya mike ya shige cikin bedroom dinsa ya turo kofa [11/7, 11:42 AM] maryamsuleiman48@gmail.co: MAIMOON By Maman Maama 29 Episode Twenty Nine: The Message Kowa a palon yayi shiru, hatta ni da nake kuka nayi shiru ina assessing me daddy yace. It then dawn on me suddenly cewa yana nufin bazan je Nigeria ba. Ai kuwa da gudu na mike na nufi kofar dakinsa ina kuka ina "daddy dan girman Allah kayi hakuri, daddy na tuba please" amma ko motsin sa banji ba, nan na durkushe a gurin ina faman gumurzun kuka. Hafsat ce tazo ta kamani ta mayar dani falo. Na zauna a kasa na kifa kaina a cinyoyina ina cigaba da kuka. Hafsat tace "mommy please do something" mommy wacce itama daga dukkan alamu hukuncin na daddy ya bata mamaki, tayj ajjiyar zuciya tace "yayi fushi sosai, and she deserves to be punished" ya Walid yayi sauri yace "amma mommy kunsan fa yarinyar nan ba lafiya ce ta ishe taba, ta yaya za'ace mu tafi mu barta ita kadai thousands of miles away? Ni dai mommy idan daddy yaki yarda a tafi da ita zan zauna anan nima, kice masa ina harkar wani project and I need to stay in town" mommy ta harare shi tace "kana tunanin he will buy that, duk harkar karatunku babu abinda bai sani ba, yasan cewa babu wani project da kake yi" ya Habeeb yace "at least mommy try something, ba za a bar maganar nan kawai ace shikenan ba" ni daj duk ina jinsu bance komai ba, kuma ban daina kuka ba. Mommy ta mike tace "ina zuwa" sai da naji mommy ta shiga dakin daddy sannan na dago kaina ina goge hawayena. Tun muna yara nasan sau da yawa mu na cewa mommy tana da magic, duk sanda ka tambayi daddy wani abu yace no, to in ka samu mommy tace yes, daga ta shiga dakin daddy ta fito shikenan sai kaji shima yace yes din. A lokacin yarinta sai muke cewa magic ne take yi masa. Mun jima a zaune ba wanda yake yin magana, ni dai in banda sunayen Allah babu abinda nake kira "please God intervene, bana jin zuciya ta zata iya daukan wannan hukuncin" it has already been a year rabo na da Nigeria, da Ibrahim, i just want to know if he is ok. Bude kofar mommy ne ya dawo dani daga tunani na. Fuskarta kawai na kalla nasan cewa wannan magic din baiyi nasara ba. Tana zama na rarrafa gurinta na dora kaina a chinyar ta na cigaba da rusa kuka na. Bata rarrashe ni ba ta fara magana. "Moon, you will be left behind. Zaki zauna kiyi karatu for two months, zai shiga makaranta ya karbo miki textbooks na courses din da kuka yi last session wadanda zaki karanta. Kowanne textbook zaki rubuta formal report akansa in mun dawo zaki wa daddyn ki submitting shi kuma zai kai department din ku with hope zaku kara miki grades dinki. Za'a bar securities, you are not to leave this building har sai mun dawo, za'a bar miki david, chief bodyguard din daddy, duk abinda kike so a cikin gari ki gaya masa zai siyo miki. Cooks da sauran servants duk zasu zauna suna kula da ke da gida. Za'a dauko miki nurse din da zata ke zuwa tana kwana dake, kuma zata ke gwada bp dinki three times aday. A clinic din embassy take" ta juya wajan ya Walid tace "bai yarda da zaman ka ba anan. Saboda bai yarda ya barku daga kai sai moon ba. Nima kuma ban yarda ba" tana gama fadin haka ta mike ta shige daki. Knowing mommy, nasan kuka zata je tayi. Haka abin ya kasance, textbooks kwali biyu daddy ya lode min wai duk ni zan karanta. Ina kallon su suna ta shirye shiryen tafiya banda ni. Da assuba jirgin su zai tashi dan haka tun cikin dare su ka tashi suna ta wanka da shiryawa. Inajin Hafsat ta na shiryawa nayi banza da ita nayi kamar bacci nake yi. Ta zo ta tsaya a gaban gadon da nake tace, "Moon I am going" na kalle ta kawai bance mata komai ba. Ta sha bakaken kaya da wani bakin glass a fuskar ta. Nasan ta saka glass din ne sano da kar inga kukan ta, she is too proud to let me see her tears. Tunda aka haife ni muke tare da Hafsat, bana jin mun taba sati daya ba tare ba. Yanzu gashi zamuyi two months ba tare ba. Tace "zan yi iyakacin kokarina inga na samo miki news" na gane maganar da take yi, a hankali nace "thank you" daga haka ta juya ta fita tare da rufe ko fa. Ina nan dai a kwance naji anyi knocking kofar sannan aka bude a hankali. Kamshin turaren daddy naji nayi sauri na rufe idona. Ya jima a tsaye yana kallona sannan naji ya hawo gadon yayi kissing dina a goshi sai kuma naji ya sauka ya rufe kofa. Hawaye naji yana zuba daga idona masu zafi. Next ya Habeeb ne yazo da dariyar sa yana ta tsokana ta wai daddy so yake na zama prof kafin su dawo. Sai da ya fahimci cewa am not in the mood for wasa sannan ya rabu dani sai ga mommy nan ta shigo itama, complete ta gama shiryawa dan harda handbag dinta a hannunta. Ina ganin ta naje na rungume ta ina cewa "mommy dan Allah kice daddy ya bar ki su su tafi" ta girgiza kanta tace "kema kinsan hakan ba zai yiwu ba, kiyi abinda yace miki shine mafi alkhairi a gareki, kinsan dan yana sonki yayi hakan ba wai dan yana kinki ba, in mun barki ba karatu ai bamuyi miki gata ba. Kuma yace in dai har ba kici 70% a report din da zaki rubuta ba to next holiday ma ba zaki je ba. Take care of yourself, do as u are instructed and you will be fine" daga nan tayi min kiss a cheek dina ta fita. Na durkushe a gurin zuciyata tana yimin zafi, ina jin tashin motar su amma na kasa lekawa har suka tafi. Tunda suka tafi ko palo ban leka ba har bayan magrib. Ina kwance a kan gado sai dai in tashi inyi sallah in kuma komawa in kwanta. Bayan magrib ne naji ana knocking kofar bedroom din, da sauri na tashi ina tunanin ko daddy ya chanza shawara an bar wani a cikinsu. Ina bude kofar naga wata mata da kayan nurses a jikin ta tana murmushi tace "good evening, my name is... " kafin ta karasa nace cikin tsawa "go away" tare da banko kofar na rufe. Sai wajan karfe goma na bude dakin na fito shima azababbiyar yunwa ce ta dameni, ina fitowa naga abinci a jere akan center table din palon, na wuce na bude fridge na dauko fresh milk na koma daki. Washegari da sassafe yunwa ta addabeni na fito palon na sake ganin breakfast a ajjiye, naje na zauna na fara hada tea, ina cikin sha naji an bude kofar extra dakin da yake kusa da nawa, wannan nurse din ta jiya ce ta fito, kallo daya na yi mata na dauke kai, tazo inda nake tace min "good morning, my name is Victoria, your father asked me to take care of you" nace " OK " ba tare da na kalle ta ba. Har ta juya zata tafi sai kuma naji babu dadi a raina tunda ni ban iya wulakanta mutane ba, kuma ba laifin ta bane aka tafi aka barni ba, na kira ta nace "zo muci abinci" tace ok, tazo mukayi breakfast tare, sannan ta gwada bp na tayi recording, daga nan ta fice ta tafi office dinta. 12 ta dawo da sake gwada bp na ta fita, ina nan dai zaune ni kadai kuma naki bude kwalin books din ballantana in fara karatu, har six din yamma, sai ga Victoria ta shigo tace "I have gift for you" sai ta dauko wadansu CDs na movies har guda biyar ta miko min, tace "since you don't have interest in reading book, i thought maybe you will like watching movies" na karba nayi mata godiya sosai. Nan da nan na fara kallon movies din. Duk kannin su akan likitanci ne, suna koyar da harkar medicine amma a cikin labari, ranar kwana nayi banyi bacci ba ina kallo, sosai naji interest dina yana dawowa akan karatu. Washegari nace ta kawo min wadansu films din, da rana kuwa da zata zo sai gasu ta karo min wasu, sam bata takura min akan inyi karatu ba amma tana ta gayamin amfanin karatun da, dadinsa. As a doctor zaka zama kana saving life din mutane, babu wani feeling din da yafi, dadi akan ace someone is alive because of you. Da yamma ta dawo tace inzo mu fita yawo, muka fita muka zagaya cikin embassy din, duk wanda muka hadu dashi sai sun gaisa sai ta gaya masa ko ni wacece. Ina kallon David yana bin mu duk inda mukayi. Five days muna tare da Victoria, da yake bani da wahalar sabo nan da nan muka saba. Har yanzu dai ban fara karatu ba amma sosai ina jin son karatun a raina, kuma bp dina is great. Ranar kwana na biyar din ina daki ina kallon daya daga cikin movies din da victoria take kallo sai na ji kamar motsi a main palo, gaba na ya fadi tunda nasan sai 12 Victoria take zuwa. Na tashi a hankali na dan bude kofar palon mu na leka, kawai sai ganin daada nayi a tsaye tana ta kalle kalle, can kuma sai ta takarkare ta rangada sallama "salamu alaikum" ai bansan sanda na fita da gudu na rungume ta ba, kafin in gama recovering daga shock din ganin daada a palo sai ga Faruk da Amina sun shigo suna jan akwatinan su. Nan na saki daada na je na rungume su a tare, har da kwallar murna a ido na. Sai da muka gama murnar ganin juna sannan daada take gaya min cewa ai bayan su mommy sunje Nigeria ta tuburewa daddy lallai idan bai bar su daada sun taho wajena ba to ita zata dawo. Inna kuwa tana jin labarin abinda ya faru tace lallai ya kira David ya gaya masa ya sako ni a next plight in taho gida, shine yace mata ai ya zai turo su daada su zauna a gurina. Ita kuma Amina tana jin labarin tafiya England tace lallai sai ta biyo su tunda dama daddy yayi mata alkawari, Shine suka taho tare. Naji dadin zuwansu sosai, nan da nan na qara warwarewa, daada ta dage tana ta yimin nigerian dishes da nake missing. Faruk kuwa kullum sai ya fita yawo shi da David, wata rana Amina ta bisu wata rana kuma tayi zamanta. Zuwan su daada bai hana Victoria zuwa ba, ta daina kwana dai amma kullum sai tazo sau biyu ta gwada jinina kuma munyi hira wanda mostly akan harkar karatu ne da kuma harkar medicine. A lokaci daya sai naji hankali na ya karkata a gurin karatu, na zauna na ributa timetable wacce zata bani damar yin karatu for 5hours kullum. Part dinsu daddy nake zuwa inyi karatuna yadda babu wanda zai dameni. Nayi browsing yadda ake rubuta study report, nan take na fara rubutawa. Sai da su daddy suka yi wata biyu chip a Nigeria sannan suka dawo, ni kuma a lokacin na karantu sosai dan banajin ko Hafsat zata gaya min sanin abubuwan da aka yi mana. Na hada report dina tsaf na kai bedroom din daddy tare da apology letter ina bashi hakurin abin da nayi, da kuma alkawarin bazan sake yi ba. Ranar da zasu dawo gabadaya muka tafi airport muka taro su, murna a gurina kamar ranar sallah, saboda ba karamin missing din su nayi ba. Ban tambayi Hafsat ko ta samu labarin Ibrahim ba ita ma kuma bata cemin komai ba. Satin su daya da dawowa muka koma school, yanzu an raba mu da Hafsat kowa ya koma bangarensa, amma a yanzu kam Alhamdulillah ina gane karatu na sosai, in an shiga lecture ina zama a gaba kuma ina bada attention dina sosai, kuma sai naji karatun babu wahala tunda duk basic abubuwa na iya su. A ranar wata Thursday, na riga Hafsat dawowa ina zaune a main palo ni da mommy da Amina sai ga wani security yazo yayi knocking kofa, naje na bude masa sai na ganshi tare da wani mutun. Muka gaisa dasu sai mutumin yace "I have a mail from Nigeria for miss Hafsat" nace masa "bata nan amma zan karba mata" nan ya bani wasu takardu nayi signing sannan ya miko min sakon. Brown envelope ce babba, na shafa ta sai naji kamar takardu ne a ciki. Na koma palo nace da mommy sako aka kawo wa Hafsat amma ban fada mata daga Nigeria bane, hankalinta yana kan kallo dan haka bata kalleni ba, na wuce na shiga part din mu, na ajiye sakon akan bedside table na zauna akan gado, haka kawai sai naji zuciya ta tana ayyana min in bude in ga menene a ciki, can nayi tsaki a raina nace in Hafsat ce aka kawo min sako babu abinda zai hana ta budewa taga menene, dan haka zuciya ta daya na dauko na bare seal din na zazzage contents din akan gado. Wata irin bugawa kirjina yayi saida na dukushe a gurin. I think this is the longest episode so far. Ko me sakon Hafsat ya qunsa? Me ma i don't know 😝 [11/7, 11:43 AM] maryamsuleiman48@gmail.co: MAIMOON By Maman Maama 30 Episode Thirty : The Final Blow A hankali na mike na koma kan gadon na zauna ina bin contents din da kallo. Hotuna ne wajan kala ashirin, sai takardu anyi binding dinsu kamar wani project report. Na fara daukan hotunan daya bayan daya ina kalla. Kaina kamar wacce aka shafe min memory na gaba daya, kwakwalwata ta kasa assessing abinda idanu na suke gani. Hoton farko dana fara dauka hoton Ibrahim ne, yana tsaye a kusa da wani masallaci da sallaya a hannunsa, fuskarsa da alamar bacin rai a tare dashi. Na kurawa fuskarsa ido, komai yana nan kamar yadda nasan shi sai duhu da fatar sa tayi, next photo shi dinne dai akan kujera a kofar wani gida a kusa da wani dattijon mutun bayarabe, daga dukkan alamu serious magana suke kuma basu san an dauki hoton ba. Haka nayi ta bin hotunan ina kalla, duk shi ne a ciki, wani shi kadai wani kuma shi da mutane. Na ajiye hoton hannuna kenan idanu na suka gane min wani kati, na dauka a hankali ina karantawa word by word. Join us in person or in prayer to celebrate the wedding matrimony of our children : Ibrahim Adeni Oluwaseun And Efisowa Olabesi Adebayo Na duba date din naga about 3 weeks ago. Ido na kafa akan sunan sa kamar mai hopping mistake ne zai automatic correcting kansa, amma ina, it is real, it has happened. And there is nothing I can do about it. Na ajiye card din na dauki sauran pictures din. Wedding pictures ne, picturing Ibrahim and Efi. She is exactly how I remember her, kawai dai ta yi kwalliyar amare ta rufe kurajen fuskarta. Wani hoto na dauka daga shi sai ita da katon cake a gabansu. Sun sha kwalliya. Ita ta saka farar wedding gown mai dogon hannu shi kuma ya saka wata sabuwar shadda dark brown ta sha aiki. Na kalli fuskokin su gaba daya suna dariya. Fuskarsa tana dauke da tsantsar farin ciki. Na kasa daina kallon hoton. Kofar dakin naji an banko an shigo da sauri. Ban dago kaina ba amma nasan Hafsat ce saboda kamshin turaren ta da naji. Ta karaso da sauri tana cewa "ina saqo na da akace an....... " bata qarasa maganar taba saboda abinda ta gani. Ta tsaya a bakin gadon tana kallon tarkacen da suke kai. A hankali tasa hannu ta dauki IV din sai naga ta yarda shi ta rufe bakinta da hannunta. Na kalli fuskarta naga kamar wadda idanuwanta zasu fado kasa saboda mamaki. Bata cemin komai ba ta fara kallon hotunan da sauri sauri. Na ajiye hoton hannuna na mike na fara cire kayana. Har a lokacin ba zance ga abinda zuciyata take ji ba. Na daura towel zan shi ga toilet naji Hafsat ta kira sunana a hankali "Moon am so sorry, da na san abinda za'a kawo min kenan da ban saka private investigator ya nemo shi. I thought in kika ji labarin halin da yake ciki zaki nutsu ki koma normal life din ki" bance mata komai ba nayi hanyar toilet, ta sake cewa "moon please let's talk about this" na juyo da sauri nace mata "ba abinda kika yi min Hafsat, in fact I am so grateful naga wannan sakon. I just need to be alone for a while" daga haka na shige toilet. Shower na kunna na shiga ciki nayi zaman dirshen ruwan yana zuba a kaina. So karya yayi min sanda yace min zai dawo, dama bashi da niyyar dawowa. Shekara daya kawai. He got married to Efi. Amma ai cemin yayi baya son Efi, ko duk a cikin karerayin daya shirya min ne. Har hawan jini na samu da yarintata saboda shi, nayi watsi da karatuna saboda tunaninsa amma dame zai saka min ? He got married. Married for God's sake. Zafin da nakeji a zuciya ta yayi yawan da hawaye yaki zuwa idanu na. Ruwa mai sanyi ne yake sauka a jiki na amma zafi nake ji kamar ana hura wuta a kirjina. What hurt me the most is the fact that he looks happy. He is happy ya auri Efi. Maybe idan aka ambaci suna na sai ya yi tunani kafin ya tuno ni. Maybe I am just one of the others. Kuka nake so inyi amma hawayen yaki zuwa. Why Ibrahim? Why do you choose me as one of your victims? Na tashi na kashe shower na goge jikina da towel na daura wani na fita. Hafsat tana nan a inda na barta, ta gama kallon hotunan tana karanta report din. Na shafa mai, na dauko wani wando skin tight 3 quater na saka, na dauko riga itama 3 quater, daga sama ta matse ni daga kasa ta bude na saka. Kananan kalba ce a kaina, na tattare su nayi packing dinsu a tsakiyar kaina suka zubo kan kafaduna. Na dauko turare na feshe jikina dashi. Ban kalli Hafsat ba ballantana pictures din da suke gabanta. Har na yi unlucking kofa na kama handle zan bude Hafsat ta yi min magana "what are you going to do?" Na tsaya amma ban juyo ba. Ta sake cewa "look, a cikin report din nan an nuna cewa takura masa akayi ya aure ta, babanta shine ya rike su shida sisters dinsa tun rasuwar babansu, kuma shine ya matsa masa sai da ya aure ta, in fact yana lagos akayi daurin auren ma kawai kiransa akayi yazo akayi biki" kallonta kawai na ke yi fuskata babu expression, na saki kofar na jingina a jikinta na rungume hannuna a kirjina, kamar yadda Ibrahim yake yi, a hankali nace "does that change the fact that he is married?" A hankali tace "no. I just thought it will make you feel better. Look ni ban damu da Ibrahim ba, in fact I don't even like him. Baki da lafiya already bana son wani abin ya kuma samunki a kansa. Please just read this for yourself" na juya na sake kama handle din kofar sannan na juyo da kaina na kalleta nace " I am a psychologist my dear sister, I don't read words written on some pages, I read people, I read minds and this man... " na dawo cikin dakin da sauri na dauki hoton Ibrahim da Efi suna dariya, na cigaba da cewa "this man here is happy, and that's all that I need to know". Na juya na fice daga dakin. Kitchen na shiga na tarar da cook tana ta aikin dinner, na dauki vegetables na fara yankawa sai ga mommy ta shigo ta tsaya tana kallona saboda ni bamai son girki bace, sam bana shiga kitchen in ba dole ba. Kit na yanke hannuna da wuka, da sauri mommy tazo zata rike hannuna na ja da baya na fice daga kitchen din, ina jin ta tana kirana na bude kofar main palo na fita hannuna yana jini. Har na dau hanyar gate sai na tuna kayan jikina yadda suke sai na dawo na koma cikin palo, ina jin Amina tana yimin magana itama na rabu da ita. Sam bana so ayi min magana. Extra dakin da yake part din mu na shiga, na shiga toilet na wanke ciwon hannuna, na daure shi da handkerchief. Har dare ina dakin ban fito ba kuma har lokacin hawaye bai zubo a idona ba. Nayi sallar magrib da isha, Hafsat ta kawo min abinci tace ta gayawa mommy bana jin dadi, nace mata na gode. Na kwanta amma bacci ya gagari idona sai juyi kawai nake yi. Cikin dare naga ba bacci babu labarinsa, na tashi nayi alwala nazo na fara sallah. Ni kaina bansan raka'a nawa nayi a ranar ba, kuma duk sujjada sai na roki Allah ya chire min Ibrahim daga raina. Har aka yi sallar asuba, nayi sallah na zauna ina azkar anan bacci ya dauke ni. Mommy ta shigo ta dubani taji jikina yayi zafi, nan ta kama fadan me yasa na kwanta ni kadai? Nan da nan aka kirawo Victoria, tana gwada jini na kuwa tace ya hau. Dama nasan haka zata kasance saboda yadda nake jin wani azababben ciwon kai. Mommy ta saka ni a gaba akan lallai sai na gaya mata menene matsala ta amma nayi shiru, fada take kamar zata ari baki. Ni dai na samu akayi min allurar bacci nayi kwanciyata. Ranar wuni nayi a gida ban je school ba. Washe gari Saturday tun safe nace da daddy ina son zuwa bakin ruwa (beach), ya barni saboda yana ganin fresh air zata taimaka min, amma yace mu tafi tare da Hafsat da Amina. Ban so haka ba saboda so nake in zauna inyi tunani. Muna zuwa bance musu qala ba na dau handbag dina nayi gaba, sai da na samu gurin da babu kowa sannan na zauna a kasa ina kallon ruwan. When was the last time I had a serious conversation with myself? Me ya faru da ni ne? Ina wannan yarinyar 'yar makaranta who is loved by all? Na tuna da medal din da school din mu ta bani, to the most talented student the school has ever had. Ina dreams dina na zama likita in bude private hospital a Nigeria in ringa taimakawa marasa karfi wadanda ba zasu iya zuwa kasar waje ba? My life was so peaceful before kuma ina so ta koma kamar da. Indai har ina so in koma kamar da i have to let go of Ibrahim. Tabbas ya samu guri a zuciyata yadda bazan taba iya goge shi ba, amma zan iya tura shi baya yadda bazan ke tuno shi ba. Tabbas wani barin na zuciyata is 100% sure cewa Ibrahim yana so na amma mai yasa yayi aure? Nasan maganar Hafsat zata iya zama gaskiya cewa takura masa akayi amma still ya kamata ace ya neme ni ya gayamin abinda ya faru, na bar masa sako a gida kuma nasan da yaje da baba Habu ya kira ni ya gaya min. Tunda har bai neme ni ba yana nufin yayi accepting auren kenan, he looks happy in the wedding picture. Duk da ya taba gayamin cewa baya son Efi amma tana da chance din da zata juyo hankalinsa kanta a matsayinta na matarsa. Duk da bani da shekaru da yawa amma nasan maza suna da one weakness, Sex, cikina naji ya hargitsa wani amai ya taso min, sex, kusan wata guda kenan da auren, they might have already done it by now. Da sauri na tashi na fara kwarara amai, Allah ya soni babu kowa a gurin, sai da na gama amai na sannan hawaye ya zo idona, na zauna na saka kaina a tsakanin cinyoyi na nayi kukana mai isata sannan na tashi, naje bakin ruwa na wanke fuskata da bakina. Na dauko handbag dina na bude na fito da hotunan da takardun da aka kawo wa Hafsat, daya bayan daya na ringa jefasu cikin ruwan suna tafiya, ina kallansu suna tafiya a saman ruwa sannan suka fara nutsewa kasan ruwa. Na dauko waya ta na goge numbersa da na ke ta faman ajjiya, na shiga messages duk na goge messages dinsa da na kasa gogewa da, na saka hannu a handbag din na sake sauko letter dinsa, first letter din da ya fara rubutomin, na bude na sake karantawa sannan itama na jefa ta ruwa, abu na karshe shine CD din daya aiko min, na dauko ina kallon rubutunsa da yayi da permanent marker a jikin CD din, I LOVE YOU, a hankali nace I love you too Ibrahim but I must let you go, na jefa cd din shi ma cikin ruwan [11/7, 11:43 AM] maryamsuleiman48@gmail.co: MAIMOON By Maman Maama 31 Episode Thirty One: Let it go Ina kallon cdn ya jima yana floating sannan ya nutse. Na dauke kaina na koma hanyar inda na baro su Hafsat. Tun daga nesa na hango alamar abinci suke ci, sun shimfida blanket suna zaune akansa. Na karasa da sauri nace "ina fatan dai baku cinye sandwich din nan ba" Amina ta kalleni da mamaki tace "au da jira kike yi mu rage miki? Kinga na hannuna shi ne na karshe, sai dai kisha fruits" ban yi wata wata ba na kwace na hannunnata na tura gabaki daya a baki na, ai kuwa ta taso kaina lallai sai ta kwace, suka hadu ita da hafsat suka danne ni, Hafsat ta kama yi min chakulkuli ina dariya Amina ta kwakule sandwich din daga bakina, sai kuma ta jefar dashi a kasa tace "ew, duk ta saka yawu a ciki" Hafsat ta daga ni tana karkade jikinta saboda dan squeezing da kayanta suka yi, na faki idonta na damko kasa cikin hannuna na watsa mata ta cikin wuyan rigarta. Tsayawa kawai tayi tana kallona cike da takaici, Hafsat da shegiyar tsafta, kuma na tabbatar kasar ta shiga har cikin brazier ta. Ta ma rasa me zata ce min duk masifar ta. Sai kawai ta juya baya tana karkade rigarta ni kuma na cigaba da kyalkyala mata dariyar mugunta, banyi aune ba kawai sai jin kasa nayi a fuskata, har cikin baki na dana bude ina dariya. Nan take wani fadan ya kuma rinchabewa kowa yana watsawa kowa kasa. Kasa har cikin gashin mu ranar sai da ta shiga. Sai late evening ranar muka bar beach din gabaki dayan mu munyi kacha kacha. Muna shiga palo mommy ta mike "what in God's name happened" Hafsat ta nuna ni tace "ita ce ta fara" mommy ta juyo da dubanta kaina, kafin tayi magana na yi sauri nace "aga wanda zai fara zuwa toilet" nan muka dau gudu muka yi dakin mu muka bar mommy da sakakken baki. Tun daga ranar na mayar da hankali na wajan gyara rayuwata, daga naji Ibrahim ya fado min araina sai in fara wani abin da zai dauke hankali na. Addu'ah kuwa kullum sai na yita. Lecturers din mu sunyi marking report din da na rubuta sun turo wa daddy, ya kira ni naje na same shi a zaune shida mommy ya miko min takardar hannun sa yace "karanta a fili inji" na bude hannuna yana rawa na fara karantawa, As da Bs ne duk, ko C babu, na ajiye takardar na rufe bakina ina dariya, daddy shima dariyar yake yi yace "ashe zaki iya, da wato ganin dama ne bakiyi ba ko?" Mommy tace "Moon ai tamkar mai aljanu take, yau fari gobe baki, ni kaina ban san inda ta sa gabanta ba" daddy yace "at least she is doing good yanzu" ya juyo ya kalleni yace "Moon, ina so in cigaba da ganin irin wannan result din, bana son wannan mood swings din naki. Kina da kokari, kiyi amfani da brain din ki yanzu da kike da chance" nace "nagode daddy, insha Allah abinda ya faru a baya ba zai kuma faruwa ba". Yanzu a makaranta bama tare da Hafsat, dan haka kowa harkar gabansa yake. Amma hakan bai yi affecting dina ba kamar yadda nayi tsammani, na mayar da hankali na sosai akan karatu na, nan da nan na fara sabawa da mutane, lecturers duk sun sanni saboda ni ina da saurin shiga ran mutane. Turawa, blacks da sauran kabilu duk kowa nawa ne, maza da mata. I am very serious akan karatu but I am not boring, I am very friendly. Rannan muna zaune a daki muna ta shirin kwanciya bacci, sai muka ji knocking a bakin kofa, Amina tace "waye?" Yaya Habeeb yace "ni ne, I am coming in" Hafsat tace "don't come in, we are naked" kawai ya bude kofar ya shigo yana dariya. Hafsat tayi sauri ta ja bargo ta rufe cinyoyinta, Ya habeeb yayi dariya yace "yanzu Hafsat ni kike wani rufe jiki dan na shigo daki? Da yaushe kika gama shan dummy?" Hafsat ta murguda masa baki tace "i was doing you a favor da nace kar ka shigo, now you are doom for life" yana kallonta yace "bangane ba" tace "yanzu ka shigo kaga tsiraicin mu, zaka fara tunanin duk mata irin mu ne, zaka yi ta searching ka kasa samun kamar mu at the end zaka kare da auri saki" duk muka saki baki muna kallon ta ya Habeeb cikin mamaki yace "Hafsat yanzu rashin kunyar ki dama har ta kai wannan stage din? Do you even think you are beautiful? No wonder har yau baki taba yin saurayi ba" Hafsat tace "Na dauka cewa kayi yaushe muka girma, kuma yanzu kana maganar har yanzu banyi saurayi ba, ashe mun girman kenan" rasa amsar da zai bata yayi, ya juya ya fice. Ni dai ina tsaye da towel a jiki na, Amina tace "Hafsat mai yasa kika yi masa rashin kunya" Hafsat tace "Na gaya masa kar ya shigo, specifically na gaya masa cewa we are naked amma ya shigo, nima banji dadi ba da nayi masa rashin kunya amma so nake yasan cewa we are matured enough yanzu, it is not right ya ke shigo mana daki anyhow" maganar Hafsat tayi zafi amma she is right. Ko 'yan biyu ne ku karewar brother and sister da akwai privacy da kowa acikin ku yake bukata. Samari bai dace su ke shiga dakin 'yammata ba, haka zalika suna 'yammata bai dace su ke shiga dakin samari ba, in dai har bada wani uziri ba. Sai da muka gama second year din mu sannan na samu zuwa Nigeria. Kawai sai naji bana wani murnar zuwa saboda dama wanda nake saka ran zan gani a Nigeria yanzu na tabbatar is no longer mine. Da muka je Nigeria sai muka zama abin kallo a gurin mutane saboda yadda muka zama, ni kaina nasan a cikin wadannan shekaru biyun ba karamin chanji na samu ba, fata ta wani mugun laushi da santsi, nayi kyar kiba ta komai ya cika yayi bulbul, ga kuma uwa uba wayewa, dadin mu daya mommyn mu is very strict, bata son shigar banza, dan haka koda English wear mu ka saka to sai mun rufe jikin mu, bama taba fita waje da matsatstsun kaya. Samari kuwa tun a makaranta har a gida haka muke ta fama dasu, daga ni har Hafsat har Amina babu wacce take kula samari, dan ni a England zobe na saya na saka a ring finger dina, duk wanda yazo naga yana kokarin ya fara nuna min soyayya sai in nuna masa zoben in ce "am married" duk da dai wadansu suna fahimtar karya nake yi amma dole su hakura tinda babu yadda zasu yi dani. Muna zuwa Nigeria ma abinda ya faru da mu kenan, dan ma samarin nan suna dan jin tsoron tunkarar mu amma duk da haka da akwai masu courage, in sunzo nakan tsaya in basu hakuri ince anyi mana miji, Hafsat kuwa ko kwallon inda suke bata yi balle ta kulasu. Rannan Amina tace "ni kam Hafsat zan ga saurayin ki a duniyar nan" nace "gaskiya kam, duk wanda Hafsat ta bude baki tace tana so to ya kamata azo kallonsa" bata kulamu ba saboda in miskilancin Hafsat ya tashi mu din ma bamu ishe ta kallo ba. Satin mu biyu a Abuja muka tafi 'yalleman. Murna a gurin su inna ba'a magana. Tana ganin mu tace "lah, England din ce haka? Anya ba za abar karatun nan ba kuwa? Kar kuzo wata rana mu kasa gane ku saboda kun zama irin 'yan can" na rungume ta nace "we miss you too innarmu, in mun tashi tafiya next time tare zamu tafi dake saboda kullum kike ganin mu dan karki manta mu" ta rungume ni itama tana cewa "na ki wayon, salon mu tafi da baffa ki kwace min shi da wannan kyan ka kike yi kullum bayan ni tsofewa nake yi" Amina tace "kai inna, ai kamar ku daya ke da Moon" Naji dadin zuwan mu 'yalleman dan ba kara min missing din su nayi ba. Nan da nan fara bin 'yan'uwan mu gida gida ina gaishe su kuma kowa sai na kai masa kayan tsaraba, har kayan da na siyo musu suka kare na fara diban kayan mu ina rabarwa. Nan take samari kuwa su kace dawa Allah ya hada su ba da ni ba, babu shiri na koma daki kusa da Hafsat na zauna na daina fita, amma duk da haka ban tsira ba saboda har gida ake aiko wa wai ana sallama da maimuna, Hafsat tana ta yi min dariya wai wa ya aike ni futa yawo a garinnnan. Rannan muna zaune a compound din gidan sai daddy ya shigo zai gaishe da mutan gidan kamar yadda ya saba. Inna ta aika ni na dauko masa carpet a cikin gida aka shimfida masa, duk ya gaishe su mu kuma muka gaishe shi. Sai Hajja tace "ni kuwa muhammadu ina son magana da kai, da Adama naso muyi magana da ita amma sai nayi tunanin kar ta ce bakin ciki nake yi wa jikokinta" ina jin haka nasan maganar mu zatayi masa. Daddy yace "to hajja ina jinki" tace "anya muhammadu yaran nan ba za kayi masu aure haka ba? Yanzu ka debi yara mata ka tafi dasu kasar waje wai da sunan karatu? Wanne karatu mace zatayi wanda ya wuce na dakin aure? Ni dai a shawara ta ka dawo dasu nan, ga 'yan'uwansu nan sai a hada su auren zumunci, ga nuraddeen nan shima in karatun ne ai yayi, ya gama degree dinsa a BUK, ga balarabe, ga manniru duk babu abinda suka rasa. Ni tsoro yaran nan suke bani musamman wannan tsagerar" ta fada tana nuna Hafsat, "yanzu ma tana mana kallon wulakanci ballantana nan gaba in tafi haka? Ai cewa zata yi bata taba ganin mu ba" daddy yayi ajiyar zuciya yace "to hajja, ni ban taba tunanin hana su aure ba, ko yau suka fito da miji aure zanyi musu" Hajja tayi sauri tace "yo ai indai wadannan ne ba zasu fito da miji ba, ai indai ana so ayi wa wadannan aure to sai dai a fito musu da miji" daddy ya sake cewa "shikenan Hajja, yanzu abinda za'ayi ki kira su samarin ki ce su zo suyi magana da su Hafsat din, indai sun fahimci juna a tsakanin su to na miki alkawarin baza mu bar garin nan ba sai da auren su aka". Chapdi, lallai da rabon Hafsat zata saka wa garin wuta gaba daya. Lol. I love you all. Thanks for following [11/7, 11:44 AM] maryamsuleiman48@gmail.co: MAIMOON By Maman Maama 32 Episode Thirty Two : Munnir Daddy yana gama fadin haka ya mike yayi musu sallama ya fita. Gurin kowa yayi shiru banda Hajja dake ta sambatun ta ita kadai. "Yauwa, yanzu na ji magana, amma abar yara suna so sufi karfin mutane? Yanzu kuwa zan kira 'yan samarin nan duk abinda suke yi su bari su taho gida, azo ayi ta ta kare" tsam mommy ta mike ta shige dakin da muke sauka in munzo, Hafsat ta tashi ta bita a baya, nan Hajja ta sake daukan magana "zasu je suyi kulle kullen yadda za'a fasa, ai kuwa wannan maganar kamar anyi ta an gama ne, yo gida bai koshi ba a bawa jeji?" Duk abinda take yi inna bata tanka ta ba, aikin gabanta kawai take yi. Sai da na gama taya inna juye furar da ta dama a jug na kai kitchen na saka a fridge sannan na shiga dakin mu. Dariya naji tana neman kubucemin saboda ganin yadda akayi upside down da dakin, duk su biyun sun dage suna ta loda kayan mu a akwatinan mu, wadansu kayan ma ba'a ninke suke ba haka ake watsa su. Mommy idonta ya kada yayi jawur, Hafsat kuma fuskarta kamar an aiko mata da mutuwa. Bance musu komai ba suma haka, na samu guri na zauna na zuba wa sarautar Allah ido, nan da nan mommy ta bani aikin kwashe kayan kwalliyar mu da underwears din mu. Muna cikin aikin da bansan na menene ba sai ga inna ta shigo, da mamaki take bin mu da kallo "yanzu Bintou shine kika tisa 'ya'ya a gaba kuke hada kaya zaku gudu?" Maganar guduwar da inna tayi shi ya saka dariyar da nake kunshewa ta fito, Hafsat ta bini da uwar harara hamkar idanunta zasu fado. Mommy ta yar da rigar da take ninkewa ta zauna dabas a bakin gado tace "inna yanzu zama zanyi a yiwa yaran nan auren dole, dududu nawa suke? Girman jiki ne fa kawai dasu amma ba wani shekarun kirki ne dasu ba ballantana ace sunyi kwantai za'a raba wa 'yan'uwa, wai Nuraddeen, har da Mannirun da baya ganin kowa da gashi" inna tace "ke waya ce miki za'ayi musu auren dole? Ya kike abu ne kamar ba kisan halin mijin kiba? Ni dai abinda kunne na ya jiye min yace shine 'za'ayi auren in dai har yaran sun amince a junansu' to menene kuma abin tashin hankali a ciki. Ke kinsan waye Muhammadu, kinsan babu yadda za'ayi yayi wa 'ya'yansa auren dole, amma yanzu kina diban su kuka gudu cewa zai yi ba kya son 'yan'uwansa. Ki zauna kiyi musu addu'ar zabin alkhairi shi yafi miki" tana fadin haka ta juya ta fice daga dakin. In matsala irin wannan ta samu mutun, musamman harkar ta aure, rigima, koke-koke da tuburewa iyaye ba shine zai samar da maslaha ba, abinyi shine ka bisu a yadda suka zo maka sannan daga baya sai ka same su, ko ka samu wani wanda suke jin maganar sa kayi masa bayanin cewa kaifa baka son hadin nan. Sannan abu mafi muhimman ci shine ka yawaita addu'ah, wani baya taba auren matar wani kamar yadda wani baya taba haihuwar dan wani, rayuwar mu gaba daya a rubuce take duk abinda Allah ya rubuta sai ya faru da kai to babu tsimi babu dabara, addu'ah kadai ita ce maganin masifa. In Allah ya rubuta something bad zai faru da kai in kana yawaita addu'ar neman mafi alkhairi sai Allah ya goge ya rubuta maka something better. Mommy ta fasa tafiya amma daga ganinta kasan ranta a bace yake, Hafsat ta kara hade gida, ni kuwa harkar gaba na nake yi saboda na yarda cewa daddy ba zai taba aura min wanda bana so ba, duk wanda yazo yace yana sona all what I have to do is in ce bana son sa, kalas. Nuraddeen ne ya fara zuwa, very cheerful and nice guy. A falon inna ya same mu, kallo daya Hafsat tayi masa ta tashi ta shige daki, ni kuwa harda durkusawa ta ina gaishe shi, ya amsa min da fara'arsa yana tambayata labarin England da rayuwar makaranta, nan na zauna na tankwashe kafata na ringa kwararo masa labari yana dariya, shima ya fara bani labarin BUK da irin wahalar da suka sha ina ta mamakin banbancin makarantun mu na gida da kuma na waje. Sai da muka gama hirar mu ya tashi ya daga labulen cikin daki yace "Hafsat ke kuwa ko gaisawa ai kya fito muyi, ni ba cewa zanyi ina son ki ba dan kin fi karfina, in ma zaban zanyi sai dai Moon ita ce mutuniyar kirki, to amma ita kuma na dauke ta kamar kanwa ta" ina jiyo inna tana yi mata fada sannan ta fito ta gaishe shi tana kirkiro murmushin karya. Har ya juya zai fita sai yace "kun taba zuwa hadejia kuwa?" Muka girgiza kai a tare, yace "ku shirya to gobe tunda ina gari sai muje yawo ku gano fadar sarkin mu, kuga river hadejia" da murna ta nace "Allah ya kaimu, mungode Allah ya bar zumunci" daga haka ya juya ya fita, Hafsat tabi bayansa da harara. Yana fita ta kama kunnena ta rike "maza ki zauna kiyi ta wangale musu baki, in aka aura miki daya ni ko gidanki bazan ke zuwa ba" . Washegari kuwa mukaje hadejia da yaya Walid, nuraddeen da kuma mu uku har Amina. Munyi yawo sosai a garin, ya nuna mana duk guraren tarihi, hatta Hafsat ta ware muna ta hirar mu ta zumunci, a hanyar dawowa ne yake bamu labarin budurwarsa 'yar kano, tana karatu a BUK, bai kai maganar gurin iyaye ba saboda yana so sai ta kammala tukun. Hafsat tana jin haka ta sake warewa tana yi masa hira. Da zamu dawo gida ya sayo mana balangu mai uban yawa. Har zamu shiga gida sai ya kirani na dawo, seriousness na gani a fuskar sa nima na nutsu, yace "naji Hajja tace ta kira munnir shima, in yazo kar ki yadda ki sakar, masa fuska, bashi da kirki ko kadan kuma bashi da kunya" na gyada masa kai da sauri alamar na fahimta, daga haka na shige gida. Balarabe bai zo ba, sai yayo waya ta wayar inna wai shi ba zai samu damar zuwa 'yalleman ba sai dai a turo masa hotunan mu ta waya ya zaba. Nan inna ta haushi da bala'i "an gaya maka su atamfofi ne da zaka wani ce a turo maka hotuna ka zaba, aikin banza, ai ba neman kai muke yi dasu ba" ta inda take shiga bata nan take fita ba. Mommy tace "good riddance" nima kaina sai da maganar tasa ta bani haushi, lallai ma wannan mutumin, me ya dauke mune? Duk hajja ce ta jawo mana wannan wulakancin. Shi ogan bai zo ba sai ana ya gobe zamu tafi, muna dakin inna Hafsat ta shigo tana bata fuska tace "wannan dan iskan ne yazo, I was hoping ba zai zo ba, ganinsa ma kawai yayi spoiling mood dina ballantana yin magana dashi" mommy tana jin haka tace "wai munnir din ne yazo?" Hafsat tace "eh shi fa, yana dakin hajja" mommy ta watsomin wani kallo tace "behave your self" bata ce da Hafsat komai ba saboda tasan halin abarta. Duk muna bedroom din mu ya shigo palon, tun daga daki muka jiyo kamshin turarensa. Hafsat ta kwanta taja bargo. Ina jinsu suna gaisawa da mommy da inna, yana tsokanar inna wai kullum kara kyau take ko ita zai zaba ne. A raina nace "oh ni 'yar nan, me hajja ta mayar damu ne? Kashin dankali?" Naji inna ta kalla mana kira wai muzo mu gaishe shi. Na dauki mayafi na na yafa na kalli Hafsat naga ta rufe ido. Ina fita palon mommy ta tashi ta shige daki tana harara ta, inna ma tace bara taje kitchen ta duba abinci. Kallo daya nayi masa na fahimci abinda Nuraddeen yake nufi da yace inyi a hankali dashi. Kallo daya nayi masa naji sam bai yi min ba. Tun daga sama yake kallona har kasa. Inna tana rufe kofa yace "damn, wai mafarki nake yi ne ko gaske ne Moon ce ta zama haka? Ni da hajja ta kira ni ina mita za'a hada ni da 'yar tsakuwa ashe kin zama dakwalwar kaza?" Binshi kawai nake da kallo, wannan me yake nufi ne? Sai a lokacin nayi nadamar saka mayafi ba hijab ba. Ya nuna min kan handle din kujerar da yake kai yace "come sit with me" lallai wannan duk inda nake tunanin sa ya wuce nan. Na tafi kujerar da take opposite dinsa na zauna ina gyara lullubi na. Tsam naga ya taso ya dawo handle din kujera ta ya zauna yana cewa "meye kuma na wannan uban lullubin, ni da nazo in ganki kuma in kika rufe me zan gani kenan?" Ya fada yana kokarin sauke min lullubi na. Na mike tsaye ina kallonsa. Kyakykyawa ne ba karya, dan gayu ne na azo a gani, haihuwa da rainon legas. Baban su shine babba a gurin baffa, kuma shi yake kula da business din baffa a lagos. Acan aka haifesu duk, kuma acan suka girma. Bafulatani ne gaba da baya. Ya riko gefen rigata "ina zaki je kuma ko gaisawa ba mu yi ba?" Na kalleshi a raina nace "yau dole in dauki page a cikin littafin Hafsat" na watsa masa wata hararar da bansan na iya taba, nace "don't you dare try to touch me again, in kana so mu gaisa ka koma kujerar da ka taso daga kai, in ba haka ba bazan kara second daya anan ba" ya mike yana wani shagwabe fuska yace "i can't help it wallahi, you are so beautiful" na wuce na zauna tare da hade girar sama da ta kasa irin yadda Hafsat take yi nace "ina wuni" cikin wata irin murya yace min "lafiya lau sweetheart, ya England? Nima nace "lafiya" a ta kaice. Daga nan ya fara min labarin irin kudin da yake samu, sabuwar motar da ya saya, irin yadda yake shanawa a lagos, ni dai duk ina jinsa, sai da na gaji na mike nace "bara in kirawo maka Hafsat", shima ya mike tare da cewa "there is no need, I have already made my choice" daga nan ya ajiye rafar 'yan dubu dubu akan santa table, ya sakar min wani kasalallen murmushi ya fice. [11/7, 11:45 AM] maryamsuleiman48@gmail.co: MAIMOON By Maman Maama 32 Episode Thirty Two : Mahdi Na jima a tsaye ina kallon kofar da ya rufe bayan ya fita, me wannan mutumin yake nufi ne? Ni wannan ko a kafa aka daura min shi ai na gwammata in dau wuka in datse kafar in huta. Na zauna akan kujera na dafe kaina da hannayena. Dear Ibrahim, is this our destiny? Sai kuma naji haushin kaina, why am I even thinking of Ibrahim now. Me yasa har yanzu na kasa cire shi daga raina? Shekara biyu kenan rabona dashi, shekara daya kuma da yin aurensa, maybe har sun haihu by now. Jiki ba karfi na tashi na shiga daki na kwanta kusa da Hafsat. Tun muna yara dama ni bana son munnir, sam bai yi mun ba, ballantana yanzu da ya kara habaka, I must be strong, I must pray hard, in nemi zabin Allah kuma nasan Allah ba zai zabar min munnir a matsayin miji na ba. Ina nan kwance inna ta shigo take cewa waye ya ajiye kudi a palo? Nace "mata munnir ne" ta ajiye akan dressing mirror sannan ta fara yi mana fadan mun kwanta da la'asar bayan munsan babu kyau. A ranar da daddare har nayi bacci na fara jin hayaniya sama-sama, na farka sai naji a compound ake yi, na tashi da sauri na fita palo sai naga Hafsat a tsaye a bakin window tana lekawa, na karasa kusa da ita ina tambayar ta "lafiya" ta yi min alama da inyi shiru. Nan muka cigaba da leke tare. Hajja ce take balbalin fada "ai ba haka mukayi dashi ba, ce min yayi ba zasu tafi ba sai an daura aure, kuma yanzu kawai sai ace min wai gobe zasu wuce?" Baffa yace "kai muhammadu mai yasa kayi mata alkawarin da kasan ba zaka iya cikawa ba?" Daddy yace "baffa ni abinda nace shine, in har an samu fahimtar juna a tsakanin yaran to baza mu bar garin nan ba sai an daura aure, kuma ai daga zuwan manniru yau ba za ace har sun fahimci juna shida maimuna ba, abinda nake gani shine kar ayi gaggawar auren nan ya zama an bata zumunci maimakon a gyara shi, a bari idan yaran sun daidaita tsakanin su shikenan" hajja ta katse shi da cewa "yo yaushe zasu daidaita tsakanin su bayan zaka dauke yarinyar ku tafi? Ai in ma so ake su daidaita sai a bar yarinyar anan yadda zasuke ganin juna" kawu Aliyu yace "hajja rayinyar nan fa karatu take yi, ya za'ayi a raba ta da karatun ta? Daga manniru har maimuna 'ya'yan mu ne, ba za mu so mu tauye wa wani hakkinsa ba, tunda yarinyar nan tace bata son shi a rabu da ita, hajja zamani fa ya chanja, yanzu da da ba daya bane, idan da anyiwa yara aure ba tare da son ransu ba suna hakura yaran yanzu zasu zo su bata mana zumuncin mune. Maimuna yarinya ce mai hankali wallahi, Manniru ba shi da kunya sam, kuma ya girme mata nesa ba kusa ba, ni dai baffa ina ganin in akayi wannan hadin an tauyewa yarinyar nan hakkinta kuma zata iya ta kullace mu har abada" a raina nace "God bless uncle Aliyu, Allah ya baka abinda kake so duniya da lahira" na jingina kaina wanda already ya dau zafi a jikin Hafsat ina cigaba da sauraron mahawarar da zata iya chanza rayuwata gabadaya. Baffa naji ya fara magana "kai manniru kana son auren maimuna kace ko?" Nayi sauri na leqa window, munnir na gani a zaune a gefen hajja, murya kasa kasa yace "eh baffa" baffa yace "to shikenan, na baka damar ka cigaba da neman auren ta daga yau har zuwa ranar da zata gama karatun ta, idan kafin nan ta amince tana sonka shikenan" da sauri munnir yace "baffa shekara uku kenan fa nan gaba" tas, naji saukar mari daga hannun uncle Aliyu zuwa fuskar Munnir, inajin Hafsat tana dariya kasa2, nan uncle Aliyu ya rufe shi da fada "baffan kake musawa magana? Rashin kunyar taka takai har haka?" Baffa yace "rabu dashi Ali, idan ba zai jira ba ya nemo wata a aura masa, ni na gama magana" daga nan ya mike yayi hanyar part dinsa. Nan gurin ya hargitse kowa yana fadin albarkacin bakinsa, kuma daga dukkan alama fiye da rabin mutanen gurin basa bayan wannan hadin saboda duk suna yabon halayena tare da kushe da Allah wadaran halayen munnir, inna sam bata cewa komai, hajja kuwa sai kumfar baki take har da cewa duk sanda mukayi kwantai kar a kawo mata. Munnir kuwa tun daga inda nake nake hango yadda ya murtuke fuska yana bin kawunnan mu da mugun kallo. Washe gari tun assuba muka fara wanka muna fitar da akwatinan mu, inna ta zo ta saka mu a gaba da nasiha "ku kyautata addinin ku, ku bi iyayenku, ku tsarkake zuciyar ku daga mugun nufi akan kowa, in kuka yi haka Allah ba zai munana rayuwar ku ba, kullum in za kuyi addu"a ku nemi zabin Allah, kar kuce 'Allah ka bani kaza ko Allah ka yi min kaza' gwara kuce 'Allah ka zaba min mafi alkhairi a duk al'amurana'. Ku yawaita karatun alqur'ani dan shi kariya ne, musamman ayatulkursiyu, ku mayar da ita tamkar babbar kawarku kullum ta kasance a bakin ku, in zaku kwanta bacci kuyi alwala, na tabbatar muku in kuka rike wannan duk wani mugun nufi na mutun, aljani ko shaidani ba zai same ku ba". Kiri2 sanda mukaje yiwa Hajja sallama taki kulamu, haka muka taso muka fito, Hafsat tace a hankali "kinyi wa kanki" muna fita waje naga nuraddeen tare dasu ya Walid, muka gaishe su muka wuce. Na shiga gaba Hafsat ta zauna a baya tunda tare zasu zauna da mommy, ba tare da Amina zamu tafi ba, saita karasa hutunta anan zata same mu a Abuja, ya Walid ne zai tuka mu. Ina zama sai ga nuraddeen yazo yana tsokana ta "amaryar yayan mu" sai na samu kaina da daure fuskata, yayi dariya yace "congratulations though, naji yadda aka kare maganar jiya" nayi masa murmushi nace na gode, ya juya yace "gashi nan yazo sallama bara insan inda dare yayi min" sai da ya matsa sannan na hango munnir yana tahowa inda motar mu take, sai a lokacin nayi nadamar fito war mu da wuri, da munsani mun jira mommy dan nasan duk rashin kunyarsa ba zai yi a gaban mommy ba dan zata iya kwakkwada masa mari. Na yi sauri na dauko wani katon bakin glass na saka wanda ya kusa rufe rabin fuskata, yana karaso wa na daga glass din motar, ga mamakina sai naga ya zagayo ta side din driver, ya shigo ya rufe kofar, daga dukkan alama bai san da Hafsat a motar ba, na dauke kaina tamkar ban san ya shigo ba, murya can kasa yace "ba gaisuwa" nayi banza na rabu dashi, ya sake cewa "shine kika ce da kawu ambassador ba kya so na ko?" A zahirin gaskiya ni daddy bai tambayeni ba, asali ma bamu taba maganar dashi ba, nasan ya fadi haka ne saboda shima baya son wannan hadin. Ji yayi bani da niyyar cewa komai ya sake cewa "ina so ki sani, yanzu na fara sonki, kuma zan cigaba da bin wannan tsohon har sai ya amince da maganar nan dan ni yadda nake jinki bazan iya jiran 3 years ba" still no reply from me, na juya kaina ma ina kallon daya side din, kawai sai jin hannunsa nayi a fuskata yana kokarin juyo dani in kalle shi, Hafsat tana daga baya tace "hey, don't" a tsorace ya juya ya kalleta, duk da ban juya ba na tabbatar harararsa take yi, yace "hey, yaushe kika shigo?" Tace "tun kafin ka shigo, naji komai" yace "sa'ido fa babu kyau, musamman a harkar miji da mata" Hafsat tace "not even in your dreams". Suna cikin haka mommy ta fito, da sauri ya juyo gurina yana min blowing kiss tare da cewa "sai munyi waya" ya fice, a tare mukayi tsaki ni da Hafsat. Yana fita gurin mommy ya tafi ya durkusa yana gaisheta, Hafsat tace "chusa kai ba kwarjini" mommy ta amsa masa fuskarta a sake sannan ta karaso mota. Su daddy ma duk suka shiga motar su shida ya Habeeb da faruk, sai motar security a gaba, muka tafi. Tun daga ranar har muka koma England kullum sai munnir ya kira ni a waya, na rasa a gurin wanda ya samu numberta, muna komawa England muka koma school. Shakara daya tazo ta wuce muna ta karatu, har shekarar ta wuce babu Ibrahim babu labarinsa, munnir kuwa har yau yaki hakura duk da maimaita masa da nake yi kullum cewa bana son sa. Amira ma muna da contact da ita tana ci gaba da karatun ta a abuja. An tura mu clinicals, daddy ya saka aka tura mu asibiti daya da Hafsat amma ita tana bangaren gynecology ni ina neurology, Amina ma an samar mata admission ita da faruk sun fara karatu, yaya Walid ya gama, ya Habeeb kuma yana project dinsa. Na koyi abubuwa da dama a asibitin nan, anan na kara sanin irin baiwar da Allah yayi wa bil adama, naga yadda ake bare kan mutun ayi masa aiki a kwakwalwa sannan a mayar a rufe, na koyi yadda ake yin hemisphecrotomy inda ake chire rabin kwakwalwar mutun a bar masa rabi kuma ya tashi lafiya lau. Na koyi abubuwa da yawa wadanda nake sa ran zan dawo Nigeria in yi. A asibiti na hadu da Mahdi. Nasha ganinsa amma bamu taba magana ba saboda ba daga school daya muka zo ba dan haka ban sanshi ba. Rannan mun fito daga wata theatre ina zaune ina hutawa kawai sai naji anyi min sallama, na daga kaina sai na ganshi, na amsa masa cikin mamakin accent din hausa da naji a bakin sa. Fari ne tas, irin farin da har jaja yake yi kamar in ka taba jini zai fito, kirar jikinsa dai dai misali, komai nasa kamar shi yayi wa kansa, sam bai yi kama da hausawa ba. Ban gama mamaki ba sai ji nayi yace "sunana Mahdi Datti Sufyan, daga university of Michigan, ni dan garin kano ne, unguwar gwauron dutse. Naga kamar kema 'yar Nigeria ce ko?" Sai a lokacin hankali na ya dawo kaina, sannan na fahimci cewa na bude baki ina kallon sa, nayi sauri na rufe bakina nace "wait Datti Sufyan? The name sounds familiar" yayi dariyar data bayyana kyawawan jerarrun hakoransa yace "yah... My father is kind of famous in kano" ya zauna a kusa dani yace "baki gaya min sunan kiba amma" na sake tattaro hankali na nace "sunana Maimoon Muhammad Dikko, I am Nigerian also, I.." Ya katseni "ambassador MD?" Nace "kasanshi ne?" Yace "yeah..... Da akwai sanda baba yazo ya kaini embassy gurinsa, yace in ringa zuwa ina gaishe shi, amma kinsan halin students ban taba zuwa ba. So you are his daughter?" Na gyada kai ina murmushi, yace "nice to meet you Maimoon" nace "nice to meet you too Mahdi" #ga masu complain cewa Moon bata da kamun kai, ina tuna mana cewa akwai mutane in reality da suke exactly kamarta wadanda sam basu iya bata rai ba, suna da faran faran da saurin sabo da mutane, yawancin su kuma suna da mugun kirki. Hakan ba yana nufin basu da kamun kai ba, kawai nature dinsu ce haka, kuma yawanci mutane suna son su. Fara'a ita take jawo mutane, su kuma mutane rahama ne# Thank and I love you all. [11/7, 11:47 AM] maryamsuleiman48@gmail.co: MAIMOON By Maman Maama 33 Episode Thirty Three: Zayed Tun daga ranar mahdi ya zama best friend dina, in har ina cikin asibiti to muna tare dashi, rannan muna zaune dashi nace "dan Allah Mahdi in tambayeka" ya cire glasses dinsa yana kallona yace "ina jinki" nace "dan Allah da gaske kai bahaushe ne? I mean biologically?" Straight yace min "no, babana adopting dina yayi" da sauri nace "yes!! I knew it" dariya yayi sosai har yana buga kafa sannan yace "wasa fa nake miki, serious ni bahaushe ne, why do you doubt it?" Sai naji kunya kuma nace "kawai dai ba kayi kama da hausawa ba" yayi shiru sannan yace "my mother was shuwa arab, ni kadai ta haifa Allah yayi mata rasuwa, so.... I am different duk a family, wannan shi yasa na taho kasar waje karatu, I want to feel like I belong, a gida kullum kamar alien nake ji na a cikin siblings dina" na sunkuyar da kaina inajin ba dadi, ace ka zama kamar bare a cikin 'yan'uwanka babu dadi, nace "am sorry about your mom, am sorry I asked you" yayi murmushi yace "chill, ba komai, it is better that you know". Har gida na kai Mahdi ya gaishe da daddy, take daddy ya gane shi kuma yayi masa fada akan baya zuwa yana gaishe shi. Karatun mu muke yi sosai gar muka gama first year din mu a clinical, sanda muka je hutu gida kamar za'a chinye mu danyu, babu shiri daddy ya sako mu a jirgi muka dawo England. Munir da ya ganni kamar zai yi hauka, lallai ai shi baffa yayi masa alkawarin aure na. Inna da daada ma yanzu sun fara mita, a cewarsu ya kamata by now ace muna da tsayayyun samarin da muna gama makaranta sai aure. Four years kenan rabona da Ibrahim, tabbas har yanzu ina jinsa a raina amma sosai na rage tunaninsa. Sometimes na kan yi lissafin ko me yake yi yanzu? Sai kuma in yi sauri in kawar da tunanin saboda bana son in dawo wa da kaina aiki baya. Sai da muka shiga final year din clinical sannan na fara fahimtar cewa Mahdi is gradually falling in love with me. Yawan kira na a waya, kullum da weekend yana hanyar embassy gurina, ga yawan compliment, duk kayan da na saka sai yace nayi kyau, ko kuma yayi ta kallona a sace in mun hada ido ya yi sauri a dauke kai. He is really a nice guy and I really don't want to hurt him, amma sam ni bana jin sonsa a raina, I like him, but I don't love him. Rannan muna daki da Hafsat da Amina, sai Amina ta dau waya ta tana ganin pictures kawai sai taga hotona da Mahdi. Tace "wow, moon wannan gayen fa?, gaskiya ya hadu ba karya" nace "wa kenan?" Ta juyo min screen din naga Mahdi nace "ohh, he is my friend, sunan sa Mahdi" tace "wait, don't tell me bahaushe ne" nace "dan kano ma kuwa, kanon ma cikin badala" ta bude baki tana kallona da mamaki sannan ta sake kallonsa, sai kuma tayi murmushi tace "something is really cooking here, wannan din za ki ce min wani friend din ki? Mu dai a fada mana ba sai tayi tsami ba" nayi dariya nace "am serious, we are just friends" tace "then something is definitely wrong with you, anya kuwa kina da lafiya, anya kuwa female hormones estrogen and progesterone suna aiki a jikin ki kuwa?" Nayi dariya kawai na share maganar ta, amma kuwa maganar ta tsaya min a rai, ba maganar Mahdi ba, maza in general, sam bani da interest a kan su, sam bana jin wani feeling idan naga wani namiji me kyau ko kuma in muna tare da wani namiji ballantana Mahdi wanda jinsa nake kamar Hafsa. Na tuna sanda muna tare da Ibrahim yadda nake jin attraction a tsakanin mu, why is it now gone? Yanzu dana kara girma ma ya kamata ace libido na ya karu amma it's like I have none. Na zauna ina lissafo Mahdi, komai bashi is perfect, sai kawai naji a raina ina comparing dinsa da Ibrahim. Mahdi is far more handsome than Ibrahim, more educated, more richer, his family is well known, kuma a kyawun dabi'a ma ban taba kama Mahdi da hali marar kyau ba, dan tunda muke bai taba taba ni ba. Amma why is it that in na tuna shi bana jin komai amma in na tuna Ibrahim nake jin pang a zuciyata, why must love be so cruel? Da haka na yanke shawarar cewa i must do something about Mahdi tun kafin inyi hurting dinsa. Rannan yazo gida gurina kawai sai nace masa "ni kuwa Mahdi baka taba fada min wacce irin mata kake son aure ba" kamar wanda na sosa masa inda yake yi masa kaikayi nan ya fara lissafo min duk siffofi na da halaye na yana murmushi, yace duk sune abinda yake bukata a gurin matarsa. Ji nayi kamar hawaye zai zubomin dan na tabbatar da cewa she is head over heal in love with me. Sai da ya gama tsarinsa sannan yace "ke kuma fa" na kakalo murmushi nace "OK, inason namiji baki, kakkarfa, mai ilmi, mai addini.. " ya katseni yace "baki kuma? Why?" Na sake yin wani murmushin nace "tun ina yarinya haka kawai sai nake ganin kamar dark color is for men and fair color is for women, to har girma na sai ya kasance I am more attracted to darker men then fair men" murmushin fuskarsa naga yana subucewa, nayi sauri nace da alamar mamaki "oh God am so sorry Mahdi, you are very handsome the way you are, it's just my short coming and it's not as if you are in love with me, right? Na tambayeshi zuciyata na bugawa, ya sunkuyar da kansa kasa sannan ya girgiza kai yace "you are right, i just find it weird cewa ba kya son maza farare" ya hadiye wani abu a makogwaronsa yace "bara in tafi, see you tomorrow " bayan ya tafi na jima a gurin a zaune, I hated hurting him amma it's better this way, na dafe kaina nace "ohh Ibrahim, what have you done to me? Kai kana can kayi auren ka ni kuma I can't even have a boyfriend" Tun daga ranar muka koma 'yar wasan buya da Mahdi, duk sai naji na takura saboda ban saba da haka ba. Cikin 'yan kwanaki naga Hafsat ta fara zama mysterious, nasan da abinda take boyewa amma na kyale ta nace in tayi tsami maji. Rannan kuwa na dawo daga asibiti kawai sai na hango ta a mota ita da wani, can nesa da gate din gidan mu, na saka driver ya sauke ni a gate, ni ma yau sai na gwada mata sa'do irin wanda take yi wa mutane. Ina karasa wa kuwa na tabbatar ita din ce da wani, harara ta watso min, na dauke ido na daga kanta na kalli wanda suke tare, ai bansan sanda na bude ido, baki, hanci kai har da kunne ina kallonsa ba. Dariya yake yimin wholeheartedly sannan yace "so, the beautiful one is here" Hafsat tace min da fulatanci "to rufe bakin haka" na mayar da bakina kuwa na rufe, nace mata nima da fulatanci "kamar balarabe nake gani?" Bata bani amsa ba ta shareni. Tabbas sanda nace duk saurayin da Hafsat tace tana so to azo a ganshi da gaske nake, amma sam banyi tsammanin irin wannan ba. Balarabe ne, kuma daga ganin shi full blood balarabe ne, ga gayu da cikar kamala irin na larabawa, zai kai around thirty something years. Fuskarsa cike da kyau da annuri irinna larabawa. Yasa hannu ya bude min kofar baya yace cikin kyakykyawan turancin sa "shigo, waje akwai zafi sosai" ba musu na zagaya na zauna. Ina zama yace "my name is Zayed, and i am going to be your brother in law insha Allah" na ce excitedly "Ameen, sunana... " ya katse ni "Maimunatu, ana ce miki Moon, shekara daya Hafsat ta baki and you are her only sister... " nan yayi ta bani labari akaina har abubuwan da nake so da wanda bana so, nace " ya akayi ka sani?" Ya kalli Hafsat yace "kullum sai anyi min hirar ki, Moon this, Moon that, kullum maganar kenan, inama zan samu asoni kamar yadda ake sanki" Hafsat ta dafe kanta tace "ohh God, am out of here" na bude motar sannan tace min, "to parrot, in kin gama surutun ki shigo gida" ko kallon sa bata yi ba ta rufe kofar ta kama hanyar gida. Tana tafiya nima na fito, amma maimakon inyi hanyar gida nima sai na zagayo na dawo seat din gaba in da ta tashi na zauna, nan muka kama hira dashi, na fahimci shima yana da surutu da tsokana. Ya gaya min cewa shi mutumin saudi arabia ne, aiki ne ya kawo shi England, shine director na pediatric department na asibitin da muke clinical, wato ogan Hafsat ne, be taba aure ba saboda be taba ganin wacce tayi masa completely ba sai akan Hafsat. Nan nima nace masa "kasan kuwa Hafsat bata taba saurayi ba, ko da kuwa saurayin wasa ne" yace "really?, please bani labarin ta? Nan na gyara zama na fara kwararo masa labarin Hafsat tun muna yara, muna nan har aka kira sallar magrib, sam bai gaji da hirar ba nima kuma ban gaji ba, a karshe nace masa "the bottom line is, she is very annoying but she is the best sister that I could ever ask for" Tun daga ranar kullum Zayed yazo sai ya neme ni munyi hira, tun Hafsat tana tashi in nazo har ta hakura take zama. Na fahimci cewa suna matukar san junan su kuma ni a idona sunyi bala'in dacewa. Zayed yayi min a matsayin brother in law. Muna kokarin gama clinical din mu ne rannan da weekend naga Hafsat kamar hankalinta a tashe, nayi niyyar in rabu da ita sai kuma dai na kasa, na tambayeta, har ta shareni sai kuma ta dawo kusa dani ta zauna. Tace "Zayed ne zai zo ya gaishe da daddy yau" nan da nan na washe baki na da murna nace "Allah?, to kuma menene abin bata ran ke da zakiyi murna" tace "I am scared moon, gani nake kamar za'a samu matsala, and I really love Zayed you know" sosai na gane yadda take ji saboda nima na taba kasancewa a irin exact position din ta, nan na shiga lallabata ina cewa "daddy ba zai taba kin someone like Zayed ba". Wajen yamma yazo, Hafsat kasa fita tayi dan gabaki daya jikin ta karkarwa yake yi. Sai ni na fita na shigo dashi main palo sannan naje na gayawa daddy yayi bako a palo, sai da daddyn ya fito sannan na tashi na dawo daki, akan sallaya na tarar da Hafsat tana ta faman jan charbi, har dariya taso ta bani amma na dake, kawai na tuno ranar da Ibrahim yazo gidan mu a Abuja yadda securities suka ringa maltreating dinsa, Zayed kuwa yanzu yana zuwa har wani bashi guri suke yi suna gaishe shi, a raina nace rayuwa kenan, if you have money you have everything. Muna nan zaman jiran sakamako ni har na fara bacci naji Hafsat tana kiran sunana, na tashi na hango ta akusa da window, nima naje na leka, Zayed, daddy da ya Walid muka hango suna tafiya hanyar gate, daga ganin yadda suke cikin nishadi kasan an samu nasara, Zayed bakinsa har kunne. Hafsat ta rungume ni itama tana murna, kawai sak naji kwalla a idona. Inama Ibrahim ne muma hakan ta kasance damu. Su daddy basu jima da dawowa cikin gida ba ya kirani a waya yace muzo ni da Hafsat. Hafsat duk kunya ta ishe ta. Muna zuwa kuwa kowa ya fara tsokanarta wai ta dauko balarabe dan take yin aikin Hajji da umra a free. Sai da akayi shiru sannan daddy yace " Hafsat naga sakon ki, kuma ni dai a ra'ayina ni da mommyn ki munyi na'am da zabin ki. Amma na gaya masa in kun gama wannan session din zamu je Nigeria sai ya saka time ya turo magabatan sa sune 'yalleman su gaida baffa da kawunnan ki, su zasu bada auren ki bani ba, suma kuma ina saran insha Allah ba za'a samu matsala dasu ba. Allah ya sanya alkhairi" gaba daya muka ce "Ameen" ya Walid ya kalleni yace "saura ke" nayi sauri na sunkuyar da kaina. Daddy yace "eh Maimunatu saura ke. Ya kuke ciki ne da wannan farin yaron dan Datti Sufyan?" Nayi sauri na dago kaina nace cikin in ina "ba.. ba komai daddy" yace "bangane babu komai ba, dama ba saurayin ki bane?" Na girgiza kaina, yace " to maimunatu, kinsan dai akwai maganar Munnir har yanzu, kuma ni Allah ya sani bana son hadin ku da munnir, amma babu yadda zanyi indai har baki fito da miji ba kafin nan kafin ku kammala karatunku" Mommy tayi ajiyar zuciya tace "ni na rasa gane kan Moon wallahi, kamar wadda take gudun samarin, who would have thought Hafsat zata riga Moon samun miji [11/7, 11:48 AM] maryamsuleiman48@gmail.co: MAIMOON By Maman Maama 34 Episode Thirty Four : Back to Square One Daddy ya tashi ya shige daki. Yana shiga Hafsat ta mike ta fada cinyar mommy ita kuma ta rungume ta suna dariya, nima dariyar nake yi amma ta yaqe ce, maganar daddy ce take yi min yawo aka, tabbas nasan munir bashi da niyyar hakura, kuma nasan in har na gama school bani da wani sauran excuse, ballantana yanzu idan iyayen Zayed suka je neman auren Hafsat kowa kuma hankalinsa dawo wa kaina zaiyi. Ina cikin wannan lissafin naji maganar mommy wacce ta sake daga min hankali "ai naji yace ma indai har su baffan sun amince acikin hutun nan naku yake so ayi komai a gama, in yaso kya karasa project dinki a gidan sa, kinga nan da baifi wata biyar ko shida ba za'a gama komai" Hafsat ta boye fuskar ta a cinyar mommy wai ita kunya, su yaya Habeeb suna ta tsokanarta da amarya, ni kuwa, shock din maganar ne ya daskarar dani a inda nake zaune, mommy ta kara da cewa "ni dai kam ni aka tasa a tsaye, lokacin yayi min kadan gaskiya, saboda ni plan dina shine nan da kamar shekara biyu masu zuwa, so nayi yadda kuka taso tare ke da moon in hada ku rana daya in aurar daku shikenan" I have heard enough, na mike zuciya ta tayi min nauyi na kama hanyar fita, ina jiyo su suna ta making plans, mommy ta kira daada tana gaya mata. Ina fita part dinmu na shiga, sai kuma na rasa me zan dauka, sai kawai na dauki hijab dina na saka na kama hanyar gate. Ni kaina bansan inda zani ba, I just want to get away for a while. Baifi saura wata biyu ya rage mana muyi hutu ba, muna yin hutu zamu tafi Nigeria. Allah ne kadai yasan irin abinda zan fuskanta a can. Dan jiki na yana bani baffa zai iya cewa a hada aure na dana Hafsat, da zarar nace bani da saurayi kuwa za'a ce ai ga munnir nan yana ta zaman jira. Allah ya gani bazan iya auran munnir ba. I despise him. To ko Mahdi zan lallaba ne? But I don't love him and I will end up hurting him. Ya Ilahi. Ina fita gate na hango motar Zayed a gurin da yake tsayawa in yazo gurin Hafsat. Na juya na fara tafiya in opposite direction, ina jinsa yana horn kuma nasan dani yake amma naki juyowa. Ban ankara ba sai ganin mota nayi a gaba na, yayi winding glass din motar ya kalle ni da murmushi a fuskar sa "beautiful one ina zaki je ne haka ke kadai kuma a kafa?" Nayi niyyar inyi banza in rabu dashi tunda duk shi ya ja min daya dauko maganar auren Hafsat amma kuma sai na kasa, it is not in my nature wulakanta mutane. Na karasa kusa da motar sa nace "nan baya zan je ba nisa" daga yadda yake kallona nasan bai yarda da maganata ba, ya bude kofar motar yace "shigo in kai ki" na danyi jim sai kuma na shiga. Ina zama yace "What is wrong" kawai sai jin hawaye nayi yana zubo min, nayi sauri na rufe fuskata da hannuna na fara kuka. Ya gyara packing din motar ya zauna, bai ce min komai ba, bai kuma rarrasheni ba, sai da nayi kuka na me isa ta sannan na dube fuskata ina goge idona da hannuna, ya miko min box din tissues, sannan ya sake tambayata "what's wrong?" Nan take na fara bashi labarin tun farkon haduwar mu da Ibrahim, aikin da na saka daddy ya samo masa, graduation din mu, yadda ta kasance ranar da yazo gidan mu da tafiyarsa, dawowarmu England da labarin aurensa,na kara da cewa "har yau babu shi babu labarinsa, he might be dead for all I know. Amma na kasa chire shi daga raina, na rage tunaninsa amma na kasa mantawa dashi, I can't fall in love again" sannan sai na bashi labarin Munnir, na kuma bashi labarin Mahdi. Na kara da cewa "yanzu muna zuwa Nigeria aka fara maganar ku da Hafsat, shikenan hankalin kowa zai dawo kaina, ko dai in fito da miji, which I don't have, ko kuma a aura min Munnir, who I don't love". Nayi shiru idona a lumshe ina sauraren yadda zuciyata take bugawa. Zayed yayi gyaran murya yace "do u want the truth?" Ba tare da na kalle shi ba na gyada kaina. A hankali yace "He is not coming back" na juyo da sauri na kalleshi ya gyada min kai tare da maimaitawa "he is not coming back" na dauke kaina na daina kallonsa, yacigaba da cewa "he left because he weak and unsure of himself, yes, sanda ya tafi maybe yana da niyyar dawowa sanda yaji he is strong enough, auren sa ya kara rage chances dinsa of coming back to you saboda matarsa zata yi iya kokarinta wajan janye hankalinsa daga kanki, da zarar ta haihu kuma shikenan hankalinsa zai kara karkata kan 'ya'yansa. After almost five years kuwa his chance of coming back to you is zero percent. Dole ki saka a zuciyarki kuma ki yadda da fact that he is not coming back. Abu na farko kenan. Abu na biyu shine, dole kiyi opening heart dinki for another man. Love at first sight is very rear dan haka idan guy yace yana sonki kamata yayi ki bashi chance, get to know him sannan zaki san cewa you can love him or not. You are very young and very beautiful Moon, your life is just starting, kar ki bar wani can da maybe ya manta dake yayi ruining happiness dinki. Open your heart to both Munnir and Mahadi and whoever else comes your way. Kina jina Moon?" Na gyada kaina yayinda wasu siraran hawaye suka biyo kuncina. Ya cigaba "daga duk kan stories dinki da nake ji a gun Hafsat, na fahimci cewa you have a good heart, mutane like you, I mean people with good heart sun fi kowa facing challenges a rayuwa akan harkar aure, kasuwanci da sauran al'amuran rayuwa saboda Allah yana testing din su yaga how good they are saboda He is saving something good for them" Idan kana ta samun matsala a rayuwa, kuma ka tabbatar baka da hakkin kowa akan ka, ka tabbatar kana bin iyayenka kuma kana da zuciya mai kyau wacce babu hassada babu ganin kyashi babu kwadayi ko zalunci a ciki, to ka tabbatar cewa jarabawa ce daga Allah kuma in har kaci jarabawarka to sakamakon ka zai zamo something very good aduniya da kuma lahira. Allah ya bamu dacewa, Ameen. Tunda muka yi magana da Zayed sai naji tamkar an sauke min wani nauyi daga kaina, maybe dama I needed someone to talk to. Naji na samu confidence na facing ko menene yake tahowa gareni ko da kuwa auren munnir ne. Kafin mu rabu ranar sai da ya saka nayi masa alkawarin duk halin da nake ciki zan ke zuwa ina gaya masa. Ina zuwa asibiti na samu Mahdi bace masa ni fa bana jin dadin yadda muke yi yanzu, ina so mu koma kamar da, ya nuna min cewa komai ya wuce, nan muka cigaba da al'amuran mu kamar da. A gida kuwa mommy sai shirye shirye take yi, daddy kuma yayi waya Nigerian embassy da ke UAE ya basu information din Zayed ya saka suyi masa bincike akan sa da family dinsa. Hafsat da Zayed kuwa sun dage sai diga soyayya suke kamar zasu chinye juna, inna gan su sai inyi ta sha'awarsu, both gentle, kuma Hafsat duk rashin kunyar ta in suna tare sai inga tayi laushi, dan ko harara ta zata yi sai taga baya kallonta tukun. Mun kallama clinicals din mu an sallamemu daga asibiti muka koma school, inda acan ne aka bamu project topics wanda kowa ake so ya kammala acikin shekara daya. A bangaren psychology da nake yi ne coordinator din mu ta bani wani strange topic. Abinda tace shine "kowanne mutum yana da sides guda biyu, da akwai side din da yake in the light da akwai kuma side din da yake inda dark. Shi light side din shine wanda mutum yake nunawa kowa yana gani, ma'ana, dabi'unsa da kowa ya san sa dasu. Shi kuma dark side din shine wanda mutun yake boyewa, ma'ana, dabi'unsa wadanda ba kowa ne ya sansa dasu ba. Wannan side din shi ta kira da shadow, kowa yana dashi amma ba'a ganin sa sai mutun ya fito cikin haske. Naturally da akwai mutanen da suke iya boye dark side dinsu yadda babu wanda yake gani, even if you are a psychologist you have to look very deep kafin ka gani. Compused? Kar ku damu kawai dai an bani project a psychology. Task dina shine in samo irin wadannan mutanen in binciko shadow side dinsu, ba tare da sunsan ina bincike akan su ba. Hint din da ta bani shine, most of them are attention seekers, saboda suna son su nunawa mutane light side dinsu yadda ba za a ga shadow side din su ba. Don't worry, zaku gane later. Da haka muka tattara ina mu ina mu sai Naija. Muna zuwa Nigeria kamar yadda aka tsara haka ce ta kasance, an bawa su Zayed rana kuma sunzo, a Abuja suka sauka daga nan daddy zai saka a raka su 'yalleman. Babu yadda daddy bai yi dasu ba akan su sauka a gidan mu amma suka ki, suka sauka a hotel. Shi kuwa Zayed dama direct nan ya taho, ko kunya baya ji, ya sauka a dakin ya Walid, nan Hafsat aka hau hidimar yi masa girki kala-kala. Kwanan su daya a Abuja suka tafi 'yalleman da ya Walid da wadansu abokan daddy su biyu. Ranar da suka tafi Hafsat kwana akayi ana sallah. Washegari Amira tazo muka hadu muka saka Hafsat a gaba da tsokana. Nayi mamaki da naji Amira ko mentioning Ibrahim bata yi ba. Zuwa wajen la'asar Zayed ya kirani a waya yace "congratulations, I am going to be your brother inlaw in the next two months" nan na yar da wayar ina ihu, Amira da Amina suka biye min Hafsat kuwa ta shige toilet ta rufe kanta [11/7, 2:24 PM] maryamsuleiman48@gmail.co: MAIMOON By Maman Maama 35 Episode Thirty Five : When Destiny Calls. Shirye2 ake yi sosai na bikin Hafsat, tun ana saura sati biyu gidan mu ya fara cika, mutanen Niger sunzo sun sauka a part din daada. Amira kusan kullum sai ta zo mun yi namu plans din, ita kuwa Hafsat ba abinda ya dame ta na shirin biki, soyayyarta kawai take zubawa. Zayed ya kira ni ya tambaye ni yadda al'adar mu take na harkar biki, nayi masa bayani dai dai misali, nan ya saka ni na yi gaya masa size din kayan Hafsat dan yasan ita ba fada zata yi ba. Duk wanda yazo gidan sai yace "dama tare aka hada da Moon da shikenan an huta" araina sai ince "in kun kawo min mijin ba sai kuyi min auren ba". Mommy ta zage dantse sai siyayya take yiwa Hafsat kamar babu gobe, kayan fitar biki akwati set guda mommy tayi mata, nima kai na da ba amarya ba na sha kaya har sai da na gode Allah. Mun tsara mu kawaye za muyi bridal shower da dinner, mommy zasu yi kamu, kunshi da mother's evening, daga nan kuma sai ayi daurin aure. Familyn Zayed suma sun shirya bridal welcome dinner wacce za'ayi a can England in an kai amarya. Tun maganganun mutane basa damuna akan Hafsat zatayi aure ta barni har suka fara damuna, ga hidimomi sunyi min yawa, ga surutun mutane. To rob salt to my wound sai ga Munnir nan yazo tun biki saura sati daya. Ina daki ya kira ni naki dauka, sai ya kira Amina, ina jinsu suna magana sannan tace min "Moon angonki yazo" ji nayi kamar ta watsa min ruwan zafi, nace "in kin gaji da ganin sa babu aure ke ba sai ki aure shi ba" tayi dariya tace "mai da wukar, ni 'yar aike ce. Allah da gaske nake yace kije yana compound" nayi tsaki na gyara kwanciyata a raina nace "ai gidan ba bakonsa bane, kuma shi ba makaho bane" shikenan kuma yanzu mutane zasu kara takura min, shima kuma zai kara takura min, duk burin da naci na bikin nan bana jin zan ji dadinsa, na sake tsaki na ja bargo ina neman bacci amma yaki zuwa. Tun sanda mukayi magana da Zayed nake kokarin inga ko yaya ne na saka son Munnir a raina amma na kasa, tun ina yarinya bana son sa duk abinda yayi haushi yake bani, He is so arrogant and selfish. A hankali bacci ya fara dauka na. Kamar daga sama naji ance "out all of you" nayi sauri na bude ido na saboda naji muryar tayi kama data munnir. Na mike zaune da sauri kawai na ganshi a tsaye a tsakiyar dakin yana korar Amina da Amira. Ina ma Hafsat tana nan dan nasan bazata fita ba. Da sauri na fara neman abinda zan rufe jikina dashi, suna fita yayi locking kofa lokacin na samo hijab ina kokarin saka wa, cikin taku biyu ya karaso inda nake ya warce hijab din yana tsareni da ido, cikin gadara yace "dan baki da kunya shine na kira ki kika ki dauka, na aiko ace kizo kika ki zuwa ko? Who the hell do you think you are? Kin manta akwai alkawarin aure na a kanki? Badan wannan stupid uncle Aliyun ya hana ba da tare baffa yace ayi dana Hafsat, ni dai Allah ma ya sani ana shiga hakkina" na tattaro duk bravery dina nace "to in an shiga hakkin ka ka nemi wata matar ka aura mana? Ko ni kadai ce mace a duniya? Ba lallai ba dole kayi hanyar ka inyi tawa" yana kallona da mamaki yace "me yasa ba kya sona wai" direct nace "baka yi min ba" maimakon yaji haushi kamar yadda nayi tsammani sai naga yana murmushin mugunta "don't worry, I will surely change that duk ranar da aka kai min ke, you will begin to like me then" ya fada yana lasar lebensa, nayi sauri na dauke ido na daga kansa ina kallon kasa, ji nayi bai sake magana ba na dago na kalleshi, idansa na gani kyar akan kirjina, ba shiri na mike nayi hanyar toilet, kafin in karasa naji ya kamoni ya hada da jikin bango ya hada jikina da nasa, na zazzaro idanuwa cikin tsoro yayi sauri ya saka hannu ya toshe bakina, a kunne na ya rada min "ko yanzu ya kamata in fara making changes din ne? Kinga dole ki aure ni tunda ba wanda zai karbi second" Sai kuma ya maida kallonsa akan abinda ya tsokane masa ido yana murmushin mugunta ya fara kokarin dora fuskarsa akan saman kirjina daya fito ta wuyan rigata, hannun daya toshe bakina dashi na gantsarawa cizo, babu shiri ya bude min baki, na dage da duk karfin da Allah ya hore min na kwalla ihu, da sauri ya sake ni ya ja baya yana kalle2, na kuma dage wa nace "daadddyy, moommmyy, Haafsaaat,... " kafin in kai karshe ya bude kofar ya fice da saurinsa. Nan na durkushe jiki na yana ta karkarwa. Da yake kofofin gidan sound proof ne sai ya kasance babu wanda yaji ihu na, ni kadai nasan abinda ya faru. How can I marry a man like that?. Ranar Wednesday ita ta kama ranar da za'a fara biki, ranar ce ake yin kunshi da bridal shower, Thursday za'ayi mother's eve da kamu, friday su Zayed za su zo shi da friends dinsa za muyi dinner, Saturday da safe za'a daura aure daga nan za'a tafi a akai amarya. Amarya kam tasha gyara ciki da waje, from head to toe, nima kuwa banda gyaran cikin, duk wani gyara da akayiwa Hafsat na waje to anyi min nima, dan haka jin mu muke yi on top of the world. Tun safe 'yan yalleman suka fara zuwa, duk wadanda suka zo sai sun bata min rai "amaryar Manniru, amaryar Manniru" duk sai inji farin cikin da nake ciki ya kau, dan ma dai ni ba mai iya bacin rai bace. Tun safe masu kunshi suka zo duk aka fito compound din gidan ana ta kunshi, ja da baki, Amarya aka fara yiwa nata sannan mu, sannan sauran mutane. Anata hidimar kunshi har yamma sannan mu kuma muka fara hidimar bridal shower din mu. Abin ya tsaru sosai domin Amira akwai iya tsari, amarya tayi kyau a cikin gown lemon green ta rike pink roses an dora mata pink crown akanta, mu kuma duk munsa gown light pink da light green din jaka da takalmi. Ana tsaka da hidima naji karar waya ta ina dubawa naga uncle Aliyu. Gaba na ya fadi, na koma can gefe inda babu haya niya na dauka na gaishe shi, ya amsa min cikin kulawa sannan yace "Maimunatu tunda aka kawo zancen maganar auren Hafsat gabadaya gida ya hargitse akan maganar auren ki kema, Hajja ta dage akan lallai sai an hada anyi auren ku tare" numfashina ne gaba daya yake neman daukewa, jiri naji yana dibana, "ya Allah" na furta a hankali, yace "ki kwantar da hankalinki, na samu na shawo kan baffa, nayi masa bayanin cewa ita Hafsat mijinta acan England din yake da zama, ke kuma in akayi miki aure za'a dora miki nauyin aure ne har tsahon shekara guda kafin ki tare da mijinki. Na samu ya yarda sai next year in kin gama project din ki" wata ajiyar zuciya na sauke wacce karfinta sai da yasa na durkushe a gurin, ya cigaba da cewa "Moon kar ki bani kunya don Allah, kinga na kara nema miki lokaci, ki daure kafin lokacin ki ya cika ki fito da mijin aure, kin san halin munnir ba sai na gaya miki ba, Munnir ya wuce duk inda kike tsammani, daga ni har yaya Ambassador bama son hadin nan amma in har kika gama makaranta ba tare da wani tsayayye ba to dole mu bari a aura miki shi". Gaba daya naji taron ya fita daga kaina, muka yi sallama dashi na koma gurin taro amma sam hankali na baya jiki na. Na tsaya kusa da Hafsat kenan muna yin pictures naji hayaniya ta karu, ina juyowa naga Munnir ya doso inda muke fuskarsa dauke da wannan murmushin nasa da yake karamin tsanarsa. Ideally maza basa zuwa bridal shower saboda kayan da ake sakawa masu bayyana jiki ne, to shi in banda iskancinsa mai ya kawo shi? Yana zuwa kusa dani ya bude rafar yan 1000 yana watsa min, ya gama abinsa yace "kinyi kyau, my darling" sannan ya juya ya fita yana wani takun bada fadi wai shi yana ganin ya hadu. Wani tukuki naji a raina saboda ganin duk gurin ni ake kallo daga masu dariya kasa kasa sai masu rada a tsakanin su. A hankali na janye jikina na shige cikin gida. Direct dakin mu na shiga na zauna bakin gado na rufe fuskata da hannayena "Ya Allah, ka bani yadda zan yakice wannan bawan naka daga gareni, Allah ka kawo min mafita. Ina haka naji hayaniya ana hawowa, cousins din mu ne wajan su biyar suka shigo, ciki har da kannen munnir su biyu, suna shigowa Nusaiba tace "Maimuna ta Munniru, Maimuna ta Munniru" nan take sauran suka dauka suma. Da ace ina da bindiga zan iya harbe su amma su sunki su gane. Na juya da nufin fita kenan aka bude kofar, Amira ce tare da wasu daga cikin kawayen mu na sec sch, suna shigowa Hasiya tace "Moon wai da gaske wannan mutumin zaki aura wai? Ina uncle Ibrahim?" Na juya ba tare da nace mata komai ba, har na kai kofar toilet ta sake cewa "Moon ina Ibrahim?" Na murda kofar toilet din na shiga na rufe. Finally, i am alone. Direct shower na shiga na kunna da complete kaya a jiki na har takalmi na ban cire ba, la lumshe ido na ina addu'a a zuciyata "ya Allah ka bani ikon cin wannan jarabawar, Ya Allah idan wannan shine zabinka a gareni ka bani karfin zuciyar dauka, Allah kaine Allah, Allah kayi min jagora zuwa inda yake mafi alkhairi a gareni" nan na fara amfato sunayen Allah, ban fito daga shower dinba sai da na gama su duka 99 din. Ina fitowa na cire kayan jikina na daura rob na koma dakin, har yanzu a cike yake ana ta hayaniya, kayana na diba na koma toilet, doguwar riga ce ta atamfa purple da white, rigar ta kama jikina daga sama, daga kasa ta bude sosai, ban daura dankwali ba na dauko farin veil na yi rolling, na fesa turare. Ji nayi gaba daya zaman gidan ya ishe ni it is like everyone is against me. Sama sama mukayi magana da mutanen dakin na fice, falo ma a cike yake, compound ma duk samari ne da 'yan mata ana ta tadi, addu'ah nake tayi a raina Allah yasa kar Munnir ya ganni, can na hangoshi ya ritsa wata yarinya amma ban gane fuskar taba, ni dai na wuce da sauri nayi gate, sai ranar nayi nadamar ya akayi ban koyi mota ba, na duba agogon waya ta naga 9:00pm. Ina ta tafiya har na isa bakin titi na tari taxi nace ya kaini Hilton. Ni kaina bansan dalilin da yasa nace akaini can ba. Muna zuwa na zarce restaurant dinsu na samu guri acan wata corner na zauna. Waiter tazo ta kawo min menu nace ta kawo tea kadai. Banfi minti goma da zama ba ya shigo gurin. Yana fitowa daga revolving doors din ya tsaya yana kalle kalle. Kallo daya nayi masa nasan tabbas nasan wannan fuskar, amma na kasa tuna a ina nasan shi. To ko a England ne? Yana tsayawa naga securities out of nowhere sun bayyana a gurin, amma basu ce masa komai ba, they just look ready. Na cigaba da kallonsa daga inda nake zaune, a half breed, half african half something else. Gashin kansa a hargitse kamar wanda ya tashi daga bacci, rigarsa tayi squeezing, body hug ce wadda ta kama jikinsa sosai ta fito da kakkarfan kirjinsa, damatsensa da suke a bayyane a mummurde suke kamar wanda yake wrestling kullum (who knows?). Bashi da tsaho sosai amma ba za'a ce masa gajere ba. Ya saka hannunsa a cikin gashinsa yana dan sosawa kamar mai tunanin wani abu hakan yasa muscle dinsa yayi flexing, nayi sauri na dauke kaina, zuciya ta naji tana bugawa. Who is this? I know him but where? Wow, gaskiya yau nayi typing da yawa. Somebody give me a cookie. Lol. [11/7, 2:25 PM] maryamsuleiman48@gmail.co: MAIMOON By Maman Maama 36 EpisodeThirtySix: Interesting Na sake daga ido na na kalle shi naga still yana tsaye a inda yake, sai dai ya saka hannayensa a aljihun wandonsa yana karewa gurin kallo, as if he owns the place. Securities ne masu sanye da kaya masu tambarin Hilton suke ta kara shigowa cikin restaurant din, sai a sannan na lura cewa kusan rabin mutanen gurin shi suke kallo amma shi daga dukkan alamu bai ma san anayi ba. Banyi tsammani ba kawai sai ganin idonsa nayi cikin nawa, nayi sauri na dauke kaina na wayance da daukan kofin tea na da ya kusa sandarewa na kurba. A lokacin ne naji wani security a kusa da inda nake zaune yana yin waya "oga mutumin ka ne fa ya shigo yanzu, eh shi kadai ne yallabai, gamu nan duk mun shigo ciki muna observing dinsa in case ko zai yi halin nasa. Ok sir" na tabbatar akan mutumin da ya shigo yanzu ake waya, interesting, so you are a trouble maker. Na sake kallon inda yake tsaye sai naga kamar wanda na kira shi, ya juyo direct ya taho wajan table dina. Nayi sauri na dauki cokali na fara juya tea dina duk da cewa babu abinda na kara a ciki, zuciya ta kamar ta fito waje, na shiga uku, kodai mutumin nan baya son kallo ne kuma yaga ina ta kallonsa shine zaizo ya kwada min mari? Na kasa daga ido na ballantana in tabbatar gurin nawa ya taho. "Assalamu Alaikum" a firgice ba dago kaina na kuwa ganshi a tsaye a gaba na. Duk yadda naso in hana kaina kallonsa amma na kasa dauke ido na daga fuskarsa. Fatarsa chocolate ce mai haske, misali ace ka hada coffee ka zuba masa ishashshiyar madara, tas take cike da alamar kulawa da jin dadi. Tunda nake ban taba ganin idanu masu kyau irin nasa ba, farare ne tas masu maiko, bakin ciki kuma ba baki bane ba, light brown ne, wannan ne ya kara tabbatar min da cewa ya hada jinsi da fararen fata. Girarsa mai yalwar gashi ce, lips dinsa jajawur tamkar ya shafa jan baki mai turuwa. Fuskarsa ba mai tsaho bace ba kuma bata cika fadi ba, tana zagaye da kwantaccen saje wanda ya sha gyara. Gashin kansa a hargitse, amma daga gani kasan ba gashin hausawa bane. Finally na dauke ido na daga kansa na cigaba da aikin juya tea din da yake gabana. Can kasan makoshi na amsa masa "Amin wa alaika as salam" yace "mind if I join?" Mind If I join? Wani ya taba gayamin exactly wadannan words din. Ibrahim, a library, maganar da muka fara yi daga ni sai shi ranar da naki zuwa class dinsa. Na kirkiro murmushi, at least ba mari na yazo yayi ba, nace "bismillah, zauna babu wani abu" sai da ya zauna sannan na tuna cewa har yanzu fa juya tea nake yi. Na dauki kofin na cigaba da sha, da shi da ruwan fanfo basu da maraba sai sugar. Na dan saci kallonsa ta saman kofin hannuna kawai sai muka hada ido shima yana kallona, a tare muka yi sauri muka dauke kai. Ya danyi gyaran murya yace "so.. Me zaki ci?" Na nuna masa kofin hannuna nace "tea nake sha" ya wani bata fuska kamar abin kyankyami yace "tea? Are you telling me kin baro gida kin taho nan dan ki sha tea? In fact restaurant din nan ma basu iya tea mai kyau ba, what is so special about it?" A takaice nace masa "bana jin yinwa ne shi yasa" wani murmushi yayi wanda sai da naji shi har kafafuwa na yace "in kika ga abinda zanci yanzu, dole ki ji yinwa" daga nan ya daga murya yadda nima kaina sai da na dan tsorata "Wai babu waiters ne a gurin nan?" Ya dawo da dubansa kaina yana murmushi mischievously. Wait, I know that smile, sai yanzu na tuna a inda na san sh, a tv, suna fada shi da wani mutun akan titi police suka zo suka yi arresting dinsa. Dan sarkin Abuja, Sultan, yes, haka naji ya Walid ya ce sunansa, a real big time trouble maker, no wonder daga shigowarsa gurin aka cika gurin da securities. Wait, hakan yana nufin ina zaune a table daya da criminal kenan? Ta gefen idona naga securities guda biyu sun zo gefen mu sun tsaya, sannan sai ga wata waitress nan tazo da sauri ta kawo masa menu ta ajiye a gabansa, daga ganin ta kasan a tsorace take, nima ta ajiye min a gaba na, na daga mata hannu alamar bana bukata, bai dago kai ba yana duba menu din gabansa yace "don't worry, I will order for you. Please don't say no" bance komai ba har ya gama bada order dinsa ta tafi. Ya sauke ajiyar zuciya yace "Allah yasa kar su dade, dan yunwa nake ji sosai kuma bana so kice zaki tafi ba tare da kinci abinda nayi miki order ba" ni dai bance komai ba kawai na cigaba da shan tea dina wanda by now ya tashi daga ruwan fanfo ya koma ruwan fridge. Na ajiye kofin nayi signal na akawo min bill zan tafi, fuska sosai ya bata yana cewa "dan Allah karki tafi" waitress ta taho zaka kawo min bill yayi mata wani kallon banza ba shiri ta koma da sassarfa. Yau na ga ta kaina ni Maimunatu. Na kalleshi with serious note nace "serious tafiya nake so inyi, dare yayi kuma a gida ba'a san na fito ba" ya gyada kai alamar gamsuwa sannan ya sake daga murya "waiter!!" Sai gata ta dawo har tana sassarfa, yace "na fasa cin abinda nayi order, just bring us something simple, a fried rice with chicken perhaps" tace "but sir, already an fara shirya maka wancan order din" ba tare da ya kalleta ba yace "i don't care, bring us fried rice and be very quick about it" har tayi gaba ya sake daga murya "make sure the chicken is not burnt" dariya yake yi kasa2 yace "tsaya kiga wani abu" wayarsa ya zaro ya fara magana da dan karfi "yah Amir kana ina ne? Ina Hilton wallahi yunwa nake ji gashi suna wasting time dina sun wani sa securities sun tsatstsaya a kaina, eh mana, in dai basu kawo min order ta in the next two minutes ba, kuma basu janye securities dinsu ba to abinda zanyi musu sai yafi na last week, kasan halina ai" daga haka ya kashe wayar yana mischievous smile dinsa. Daya bayan daya securities din suka ringa fita, hatta mutanen gurin gani nayi suna tashi suna fita, dariya yayi yace "now a person can eat in peace, amma idan mutane in yayi yawa ma ai mutun ba zai iya cin abinci ba" a raina nace au kasan ana kallonka ashe. Da sauri waitress din tazo tayi serving din mu, babu musu na kama cin abinci na dama nima din ina dan jin yunwar dan in ana taro sam bana iya cin abinci. Daga dukkan alama kuwa yunwar yake ji dan da gaske yake cin abincinsa. Sai da yaci kusan rabi sannan ya fara magana "kinsan har nayi bacci kawai na farka naji ina jin yunwa? Nasan cikin gida babu abinda zan samu sai tuwo shi yasa na taho nan. Amir ya tafi yawo ya barni, i don't like coming out alone. I hate being alone" a raina nace wannan surutu ne dashi kenan. Ya sake cewa "what's bothering you?" Na kalleshi na dan bata rai nace "me ka gani?" Ya danyi murmushi "a girl all alone in a restaurant, tana shan tea, it is either you are trying to getaway from something or you are or you are waiting for someone" sai kuma ya ajiye spoon din hannunsa ya bude manyan idanuwansa a kaina "ko ni kike jira dama? Maybe we are destine to meet here, har nayi bacci fa na tashi na fito na taho nan, ke kuma only God knows what you were doing kika fito ke kadai kika taho nan" ni ma na ajiye spoon din hannuna ina jin jina maganarsa. He is not my type, too rough for me. Na girgiza kaina nace "it is just a coincidence, i just wanted to be alone shi yasa nazo nan" yayi kasa da murya kamar me rada yace "let me tell you a secret, am a magician, kina gaya min abinda yake damun ki zaki nemi duk matsalolinki ki rasa" yadda yayi maganar ne yasa dariya ta kubuce min, shima dariyar yayi wadda tasa maikon idonsa yayi kyalli, kyawawan hakoransa suka bayyana, shima kallona yake yadda nake dariyar. Sai da muka gama dariyar mu sannan ya sake cewa a hankali "there you go, yanzu kinga ai kinyi dariya har naga dimples din ki" kunya naji na rufe fuskata shi kuma ya cigaba da dariya "wani ya taba gaya miki cewa you are very beautiful? Very unique?" Na bude fuska ta a hankali nace "thank you" har yanzu fuskar tawa yake kallo. Na mike a hankali nace "thank you for the food and the talk" da sauri nayi hanyar fita, yace "wait" ban tsaya ba kuma ban waigo ba, na bude kofa na fice, ina jinshi yana kwalla wa waiter kira. Sai da na fito sannan na tuna cewa ba da mota nazo ba. Na duba agogon hannuna naga after 11.oh God Allah yasa ba'a neme ni a gida ba. Tun daga bakin titin na jiyo karar cin taya, jikina ya bani shine zai fito kuma na tabbatar nema na yake yi, oh God me yasa banzo da mota ba? Da sauri na kama tafiya ina rufe fuskata da mayafi na, ai kuwa banyi wani nisa ba naji an ci taya a gefena, ban kalleshi ba na cigaba da tafiya ta, ya bude motar ya fito ya sha gabana yana dariya "thank God bada mota kika zo ba da tuni kin gudu, wow, na tsorata da yawa fa" na dago kai na kalleshi, sai yanzu na kara ganin kakkarfan jikin shi. Ya cigaba "ko sunan ki fa baki gaya min ba, and after seeing your face kina tunanin zan iya bacci with out knowing your name?" Direct na bashi amsa "Sunana Hafsat" "I always like the name Hafsat, muje in sauke ki a gida ko?" na girgiza kaina nace "thank you, amma ni ba zan shiga motar ka ba, I don't know you" yace "sunana Sultan, shikenan?" Na sake girgiza kaina. Ya fahimci dai da gaske bazan shiga motar saba sai yace "to dan Allah ki bani address dinki mana" ba musu na bashi address din gidan su Amira, bakinsa har kunne yana dariya yace "ok, saura phone number" ya miko min phone dinsa na karba na saka masa tsohuwar number din Ibrahim da na haddace. Nishadi yake sosai yana jin dadi. Ya tarar min taxi na shiga sannan yazo window yace "it is very nice meeting you Hafsat, i will call you in na je gida" nace masa "ok, nice meeting you too Sultan" Ga mamaki na sai na samu kaina da waiwayensa bayan motar mu ta ja, yana tsaye yana kallon motar mu ya saka hannayensa a aljihun wandonsa. Sai kawai naji tamkar na bar wani part of me with him. Na runtse ido na "ya ilahi, sultan is not my type, he is a rogue" amma me yasa sanda muke tare dashi naji for the first time na manta da Ibrahim? A lokacin da muka yi dariya ni da shi na manta da duk wadansu problems dina dana fito na bari a gida. Yanzu kam nasan ba lallai ne mu sake haduwa dashi ba, amma kuma nasan bazan taba mantawa da fuskarsa ba. How do you guys like Sultan? Masoyan Ibrahim ga rival anyi muku. [11/7, 2:26 PM] maryamsuleiman48@gmail.co: MAIMOON By Maman Maama 37 Episode Thirty Seven : The Dinner Gaskiya kalamai ba zasu fayyace muku jin dadi na ba akan yadda labarin nan ya samu karbuwa. Nagode Allah ya bar kauna. Masoyan Ibrahim kar ku bani kunya mana tun yanzu. Lol Zaku ga changin yanayin rubutun labarin, nayi haka ne dan a samu fahimta sosai. I hope zakuyi enjoying sabon tsarin. Much love from maman maama 💖 Ya jima yana kallon motar har ta bace. Sannan ya juya ya shiga motar sa ya figa a guje ya dau hanyar palace. Yau dama sam bai yi niyyar fita daga gida ba. Tun daga nesa ya danne horn din motar sa, dama ya saba kullum abinda yake yi kenan, kowa sai yasan sultan ya shigo, ko mutun yayi bacci sai ya tashi. Yana shiga direct part dinsa ya wuce yayi packing a inda yake ajiye motocinsa. Direct bedroom ya nufa, yana shiga ya kalli kansa a cikin mirror sai ya bata rai yana kallon squeezed rigar sa "damn" ya fada kan gado da kayan sa complete har takalmi. Ya lumshe idonsa yana tuno every detail na fuskarta, it is like brain dinsa tayi automatically saving hotonta. "Hafsat" ya furta a hankali. Tunda yake bai taba yin serious budurwa ba, 'yammatan da yake haduwa dasu duk club girls ne da zasu yi rawa tare and that's all. Shi ba manemin mata bane sam, he consider it dirty. Ya dauko wayarsa ya dubo number dinta da yayi saving yana murmushi a ransa yana yabawa kansa dabarar da yayi na karbar number dinta maimakon shi ya bata tashi, dan yasan ba lallai ne ta kira shi ba. Ko ta karasa gida yanzu? No, unguwar da ta yi masa kwatance tana da dan nisa, bara ya bari a dan kara jima wa tukun. Ya ajiye wayar tare da gyara kwanciya. Har after 12 yana kwance a haka kuma baiyi bacci ba, ya sake dauko wayar yayi dialing "The number you are trying to call is currently switched off, please try again later" "damn you MTN" ya fada tare da jan tsaki. A cikin daren ya kira number takai sau goma amma still switch off ake gaya masa, maybe charge dinta ne ya kare, ya fada a ransa, amma baiji dadin haka ba saboda yana son ko yayane ya sake jin muryarta kafin yayi bacci. Washegari tunda yayi sallar asuba yake zaune yana kallon agogo, jira kawai yake yi yaga gari yayi haske ya kira ta. 8:00 ya sake dialing number ta amma still switched off. Damn it, kar dai ace wrong number ta bashi, in haka ne kuwa to tabbas address din ma wrong ta bashi. Ya mike da sauri ya shiga wanka, nan da nan yayi ya fito. Duk gayun sa yau da sauri ya shirya cikin usual body hug kayansa, yana fitowa ko kallon bayin da suke zazzaune a falo da abincin da aka shirya masa a dining table bai yi ba ya fice. Agogon hannunsa ya duba yaga karfe goma, yasan tunda Takawa yana gari to duk mutan gidan suna falonsa yanzu. Shima direct can ya wuce, duk masu gaishe shi a hanya babu wanda ya kula, yana shiga yaga Takawa a zaune a kan shimfidar da ake masa ta cin abinci a tsakiyar palon, Hajiya tana kusa dashi daga hannun dama Abbas kuma daga hannun hagu, daga gefe kuma saratu ce da Fa'iza. Daga dukkan alamu hira suke suna dariya har Takawan, shigowar Sultan ce tasa Takawa ya hade girar sama data kasa tamkar bai taba dariya ba, Sultan ya karasa gabansa ya durkusa "barka da assuba" bai samu amsa ba kuma dama bai sa ran zai samu ba, ya mike ya koma kusa da Hajiya ya zauna tare da dora kansa akan kafadarta, ta sa hannu tana shafa gashin kansa a hankali "yaron kirki yau kuma da wuri aka tashi haka? Ko wani gurin za'a je ne" ya girgiza kai yace "no Hajiyata, part din Amir zan shiga nace bara in shigo in gaisheku" Abbas yace "yaya Sultan barka da assuba" sultan ya kirkiro murmushi yace "Abbas, ya kake?" Su saratu ma duk suka gaishe shi daga nan sai kowa yayi shiru. Sultan ya danyi jim a zaune sai kuma ya mike yace "Hajiyata bara inje" tace "to yaron kirki, a dawo lafiya" ya karasa gaban Takawa ya sake durkusawa "a huta lafiya" nan ma babu amsa. Sai da ya fita ya turo kofa sannan yaji muryar Takawa sun cigaba da maganar da suke yi da Abbas. Ya runtse idonsa zuciyarsa tana masa zafi sannan kuma ya saka hannayensa a aljihunsa yayi gaba. Kamar yadda yayi tsammani, rashe rashe ya tarar da Amir yana ta shirgar bacci, Allah ne kadai yasan jiya karfe nawa ya kwanta bacci dan tunda yace Solomon ya zo gari to yasan sai sun raba dare a club. Tsaki yaja ya daddaka masa duka a cinya "kai tashi daga baccin nan haka" Amir ya bude ido cikin bacci yana kallon sa, "what happened naga har ka shirya, ko ta samu ne?" Sultan yace "eh ta samu, babban samu ma kuwa" nan sultan ya zauna ya bashi labarin haduwar su da Moon da yadda wayarta bata shiga, tunda ya fara maganar Amir kawai kallonsa yake yi, sai da ya gama sannan yace "in baka shawara abokina? Kawai kaje kayi ta addu'a dan kuwa ina da tabbacin gamo kayi da aljana" dariya sosai Sultan yayi sannan Amir yace "to in ba aljana ba Sultan ni ban taba ganin ka damu da wata mace ba, daga jiya zuwa yau har kabi ka tayar da hankalinka akanta, tunda har ta baka wrong number ai bata yi da kai ne" Sultan yayi sauri yace "a'a, raka ni zakayi address din mu gani, maybe wayar ta samu problem ne" Amir yace "wai kana nufin yanzu? Haba rankai dade, duk matsuwarka ai ka bari yamma tayi zuwa dare ko? Saboda tsabar kai sabon shiga ne, ka hadu da yarinya jiya da daddare sannan kawai yau da safe kaje gidansu" Sultan ya fada kan gadon kusa da Amir ya lumshe idonsa, a hankali yace "baka san yadda nake ji bane Amir, ba zaka gane ba" Moon Tun dana tashi da assuba ban koma bacci ba, muna ta hidimar kamu da mother's eve da za'ayi yau. Sam na manta da wani Sultan duk da jiya da daddare da kyar nayj bacci ina ta tuna abubuwan da suka faru a tsakanin mu. Anyi taro lafiya an gama lafiya babu wata matsala sai rigimar da akayi da Hafsat akan ita fa lallai ba za'a zuba mata nono aka ba, sai da aka rirriketa kamar mai aljanu sannan aka zuba mata, dan muguntar hajja kwarya guda ta juye mata. Mu dai muna ta dariya. Hajja ta juyo tace min "in naki yazo wanka zanyi miki dashi" Munir kam ya zamar min tamkar jela, cikin mata ko cikin maza duk inda nayi sai ya bini kuma sai yayi maganar da zata sa a gane akwai wani abu a tsakanin mu. Washegari da wuri jirgin su Zayed ya sauka shida abokan sa guda biyar, sai Waliyansa su uku. A ranar ne kuma zamuyi dinner da daddare, Zayed ya kawo mana kayan da zamu saka ni da Hafsat, dogayen riguna ne masu kyau, wadanda kuma suka rufe mana jikin mu ruf, iri daya ni nida ita sai dai banbancin color, ta Hafsat golden tawa cream. Ni samun wannan rigar yasa duk na manta da dinkin mu a gurin tailor ni da Amira wanda da muka yi niyyar zamuyi anko ni da ita. Ban tuna ba sai da muna shiryawa ta kira ni tace gata nan zuwa. Ai kuwa ina gaya mata ai ban karbo ba ni na samu wasu kayan ta hau bala'i daga karshe ta kashe wayar gaba daya. Nima nasan ban kyauta mata ba amma abubuwa ne suka yi min yawa shi yasa. Har muka gama shiryawa muka tafi Amira bata zo ba, nayi ta kiran wayarta kuma bata dauka, a karshe na hakura na rabu da ita. Sultan A hankali suke bin address din har suka zo gidan. Suna yin packing Amir yace "to munzo, now what?" Sultan ya dan sosa kansa yace "ya akeyi in anzo gurin budurwa?" Amir yayi tsaki yace "ideally kiranta zakayi a waya, to tunda kai baka da number dinta sai ka nemi yaro ka tura shi ya kirata" Sultan ya bude kofar mota ya fito yana ta zagaye ya rasa dan aike, sai da kyar ya samu wani yaro yace masa ya shiga yace ana kiran Hafsat, can yaron ya dawo yace "wai ance babu Hafsat anan gidan" ya juya suka dubi juna shida Amir, Amir ya kyalkyale da dariya yace "sai kazo mu tafi ai, yau dai ka barni inyi bacci tunda ka tabbatar yarinyar nan tayi playing dinka" sultan ya juyo jiki ba kwari ya shiga mota, har zaiyi mata key sai kuma ya dakata yana tunani, can yace "no, bazan hakura ba, tunda har tayi min kwatancen nan gidan to inhar ba gidan su bane ba to gidan 'yan'uwansu ne, ko kuma gidan su kawarta, yes, zan jira inga wanda zai fito daga gidan in tambayeshi ko ya santa" Amir binsa yake da kallo har ya gama sannan yace "you are not serious are you? Kana nufin zama zamuyi tayi a gurin nan har sai wata ta fito mun tambayeta? What if babu wanda ya fito har gobe?" Sultan yace "then I will wait har gobe, in kaga ba zaka jira ba kayi tafiyarka ban hana kaba" tsaki Amir ya sake yi ya kwantar da kujera tare da kunna kida, Sultan kuwa ya fito ya jingina da jikin motar idonsa na kan gidan. Shiru2 har wajan awa daya babu alamar wani zai fito, kuma unguwar shiru babu motsin mutane ballantana su nemi wani information. Amir har yayi baccinsa amma sultan yana tsaye kamar soja. Wannan shine kadai link din da yasan zai same ta dan haka ba zai yi wasa da wannan damar ba. Can kawai yaji motsi daga ciki, sannan yaga an bude karamar kofar gate din. Wata budurwa ce ta fito, doguwa, baka kyakykyawa. Taci kwalliya irin ta kure adaka dinnan, daga gani kasan gidan biki zata je. Suna hada ido da sultan ta danyi baya alamar tsorata sannan kuma ta maze ta rufe kofar tana gyara mayafin ta. Sultan ya karasa kusa da ita yace "Assalamu Alaikum" ta juyo ta watsa masa harara tace "alaikassam, ya akayi" kut, wannan badan information yake nema a gurin taba da sai ya babballata. Ya daure yace "please, wata ce ta bani address din nan gidan tace gidan su ne, sunan ta Hafsat" Amira ta sake yi masa kallon wulakanci tace "ko wacece karya tayi maka, nan babu Hafsat, oyo san inda dare yayi maka" lallai wannan yarinyar bata san hali ba. Daga bayansu suka ji ance "Hey, who do you think you are ana miki magana kina yiwa mutane rashin kunya, da wata mummunar fuskar ki anan, ko ki bashi amsar tambayarsa ko kuma wallahi.. " ta katse shi "ko kuma me Amir? Zaka dake ni ne?" Mamaki ne ya ishe shi yadda ta san sunan shi kuma ta mayar masa da magana ba tsoro. Har ta juya zata tafi Sultan ya sake binta "please, ko cikin kawayenki babu wadda kike tunanin zata bada address dinki?" Kamar ba zata kula shi ba sai kuma ta juyo fuskarta da murmushin mugunta tace "ya kamanninta yake?" Da sauri sultan yace "fara, fulani, very beautiful, tana da dimples manya guda biyu" murmushin mugunta Amira ta sake yi, Amir ya karaso yace "so? Do you know her or not" ba tare data kalleshi ba tace "shut off" Amir ji yayi kamar ya gaggaura mata mari, ko ba yau ba sai ya koya wa yarinyar nan hankali. Ta kalli sultan tace "na gane ta, yanzu ma tana gurin bikin da zanje" wata ajjiyar zuciya Sultan yayi yace "to shigo mota mana mu tafi" ta girgiza kanta tace "no way zan shiga motar ku, Allah ya raba gatari da saran shuka, in kuna son ganinta ku biyo ni" daga haka ta juya tayi gaba. Da sauri sultan ya koma mota ya tayar yana ta yiwa Amir horn dan yayi sauri ya shigo, Amir kuwa bakin ciki ne ya cika shi, wai ba zata shiga motar su ba, wacece ita?. Haka suka yi ta bin Amira a baya har ta fita titi ta samu taxi ta shiga, suka cigaba da bin taxi din har Sheraton. Amir yayi tsaki yace "maimakon kawai tace mana Sheraton, sai ta saka muka ringa binta a baya kamar wasu yaranta. Wannan budurwar taka should better be worth this in ba haka ba akanka zan huce" Sultan yace "believe me, she is worth morethan this" suna fitowa Amira tayi musu nuni da hall din da ake taron tayi shigewar ta ta barsu. Moon A matsayina na kanwa kuma babbar kawar amarya nice na ke zaune a kusa da ita a high table, sai Zayed da babban abokin sa Hamad. Ana cikin tsakiyar taron na hango Amira ta shigo, sai da ta gama shawaginta suna gaisawa da mutane sannan ta karaso high table, nan nayi introducing dinta a gurin su Zayed sannan muka dauki hotuna. Sai da muka gama sannan tazo dai dai kunnena tace "I brought a gift for you. Saboda bari na da kikayi babu kayan sawa yau" har ta juya kamar zata tafi nace mata "what gift?" Tace "Sultan, yana bakin kofa" nayi sauri na kalli hanyar shigowa, ga mamaki na kuwa sai naga masu gadin kofar suna ta hayaniya, har mutane sun fara tsayawa kallo. "Damn you Amira" [11/7, 2:26 PM] maryamsuleiman48@gmail.co: MAIMOON By Maman Maama 38 Episode Thirty Eight : The Shadow Gaba nane ya fadi da muka hada ido da munnir wanda ya kasa ya tsare yana kallon duk wanda zai yi min magana. Na tabbatar sultan yana shigowa zai hangoni tunda ina kan high table, yana gani na kuwa zai taho, Allah ne kuma kadai yasan abinda zai faru tsakanin sa da Munnir. Na rada wa Hafsat "two minutes, ina zuwa" ta yi sauri ta rike hannuna alamar bata so in tafi in barta, nayi mata alamar yanzu zan dawo. Cikin friends din mu na dan shiga, ina kallon munnir ta gefen idona yana bina da kallo, sai da na tabbatar baya gani na sannan nayi hanyar gate da sauri. Ina zuwa kuwa na ga Sultan ya dunkule hannunsa ya naushi wani mai gadi, nan na nan jini ya fara fita ta hanci ta baki, maybe ma hakori ya fita, wanwar gayen ya fadi a kasa yana gunjin azaba, sultan ya durkusa kusa dashi, na dauka ma hakuri zai bashi, sai naga ya goge jinin daya bata masa hannu a jikin rigar gayen, ya mike tsaye yace "who is next?, dan rainin hankali har ni zanzo ince zan shiga guri ku ce min card admit ne, da card din da admit din duk naci uwarsu gaba daya" da sauri na karaso gurin cikin fada nace "what the hell are you doing" sai a lokacin ya ganni, hannu duk biyun ya saka a cikin gashinsa tare da cewa "shit" na durkusa gurin mai gadin da aka daka wanda har yanzu ya kasa tashi, da sauri sauran guards din suka karaso suka kamashi suka tafi, na mike ina kallon sultan daya kasa hada ido dani nace "what are you doing here?" Ya karaso kusa dani yace "am sorry" sai a lokacin na lura da wanda suke tare, zasuyi kusan tsaho daya da sultan amma bazan tantance kibar saba saboda uban kayan daya loda a jikinsa duk kuwa da yanayin zafin da ake ciki, kansa yasha kwal kwal amma kuma ya bar saje a fuskarsa. Kallo daya nayi masa na maida kallona kan sultan wanda yasha kwalliya dan daga gani wannan shigar ta musammance. Har yanzu ya kasa magana ni kuma na bata rai na tsare shi da ido. Abokinsa ne ce "so, kece Hafsat kenan, kwana biyu wannan sunan har acikin bacci kiransa yake" sai a lokacin na tuno cewa ashe fa ce masa nayi sunana Hafsat. Na sake cewa "uhum, ina jinka, me ya kawoka nan?" Ya sake hargitsa gashin kansa sannan yace "I just wanted to see you ne, please, number da kika bani bata shiga, shine naje address din shima na tarar wrong ne da kyar yarinyar gidan ta kawo munan" nace "OK, ka ganni zaka iya tafiya yanzu" ina fadin haka na juya zan koma ciki, da sauri yasha gaba na, fuskarsa kamar wani abin tausayi "please kar ki koma" nace "serious, bani da lokaci, biki muke yi, na tabbatar yanzu ma nema na akeyi a ciki" da sauri yace "OK, at least ki gaya min sunanki na gaskiya, ki bani number dinki ta gaskiya" ya saka idonsa cikin nawa pleadingly, kawai sai naji na daina jin haushinsa, ya danyi murmushi tare da cewa "pretty please" na danyi murmushi nima kadan. Abokinsa ne yace "OK, lokacin introducing dina yayi" daga ni har sultan babu wanda ya kalleshi, sam ya kasa dauke idonsa daga cikin nawa, ni na fara dauke kaina nace "i really must go inside" yace " OK, sunanki na gaskiya" nace "Maimunatu" ya dauko wayarsa yace " phone number?" Har na fara fada masa sai ya dakatar dani yana karkada hannunsa "not again, an sha ni na warke" ya miko min hannunsa "bani wayarki" na gane me yake nufi dan haka nima nayi dariya tare da mika masa wayar, ya karba ya saka number dinsa yayi dialing, da kiran ya shiga wayarsa sai da ya dauka ya tabbatar shine sannan ya kashe ya miko min waya ta. Ina karba naga an bude kofar hall din an fito, a tsorace na waiga, yaya Habeeb na gani a tsaye yana kallon mu ni da Sultan, sai kuma ya koma ya maida kofar ya rufe. A sauke ajiyar zuciya nace "zan koma kaga already ana nemana" ya gyada kai yace "it is OK, nagode sosai, and please don't block my number" nayi murmushi nace "I won't" na juya na kama hanyar komawa ciki, naji abokin sultan yana cewa "hey, bakayi introducing din mu ba fa" sultan yace "shut up Amir". Tunda na koma na cigaba da activities dina har aka tashi ban kuma tunawa da wani sultan ba ballantana his troubles, bayan an tashi munje gida duk mun sallami friends din mu, zamu hau samanmu kenan sai yaya Habeeb ya kira ni, na juya na koma duk jikina a gajiye, so nake kawai in ganni a kwance. Ina zuwa naga ya bata fuska yace "dazu dawa na ganki a gurin dinner" sai a lokacin na tuno da wani sultan. Nayi ajjiyar zuciya nace "Sultan ne, dan sarkin Abuja" yace "nasan ko shi waye, kece baki san sultan ba shi yasa har kika tsaya dashi. Duk inda kike tunanin sa ya wuce nan. In ana zancen top criminals a Abuja sunan sultan yana daga layin farko" nace "ya Habibi babu komai fa a tsakanin mu, naga cewa idan ban kula shi ba zai iya tayar da rigima a gurin shi yasa na kulashi, but I know he is a trouble maker and all.. " ya Habeeb ya katseni "trouble maker? He is not just a trouble maker Moon, he is a drunk" ji nayi tamkar ya Habeeb ya watsamin ruwan zafi a fuska, a drunk? Har naje dakin mu jikina a sanyaye yake, can kuma nace a raina, me yasa na damu, it is not as if na damu dashi. Direct toilet na shiga na yi wanka nayi shirin bacci, ina fitowa na ga Hafsat har tayi bacci, nima na kwanta nayi addu'ah. A drunk, but how, me yasa ya zabi wannan rayuwar? Me yasa ya zabi abokai irin su Amir? Dan manyan mutane kamarsa, dan Sarki, sarkin ma na federal capital, how can he be what he is? Me yasa iyayensa ba zasu dau mataki a kansa ba? Waya ta naju tayi kara, na dauka na duba screen "my Sultan" naga an rubuta, nayi murmushi, wato haka yayi saving number dinsa a waya ta kenan. Na ajiye ta na barta tayi ta ringing dinta har ta katse, wani kiran ya shigo sannan wani. A drunk, na maimaita a raina. Take na yanke shawarar in dauki wayar in gaya masa cewa bani da interest a kansa yayi hakuri. Tana fara wani ringing din na dauka "Assalamu Alaikum" naji yace. Assalamu Alaikum, peace be unto you. Wannan itace kalmar daya fara fada min ranar da muka hadu a Hilton. Mutane nawa ne a cikin mutanen kirki suke sallama idan sun kira ko an kira su a waya. Mostly hello ko hi ake cewa wanda ba dai dai bane, amma shi a matsayinsa na known criminal me yasa yake yi min sallama. Ko hakan yana nufin some part of him is good?. Wannan kalmomi na Assalamu Alaikum da Sultan yace min sune suka sa na fasa yanke alakar ta dashi. I feel like I want to know him better. "Assalamu Alaikum" ya sake maimaitawa, sai a lokacin na samu damar amsa masa "ameen, wa alaika assalam" ya sauke ajiyar zuciyar da sai da naji daga cikin wayar, "sorry I kept calling, ina so ne ko yaya in danji muryarki kafin nayi bacci" nayi shiru babu amsa, yace "ya taron? Da fatan baki gaji da yawa ba" nace "gajiya kam akwaita, sai godiyar Allah" "sorry" na danyi murmushi saboda yadda ya furta kalmar sorry din, ya sake cewa "am really sorry akan abinda ya faru dazu, I came to your party uninvited kuma na yi creating commotion, I just can't hold my temper ne most of the times" nace "it is OK, ya wuce, Allah ya kiyaye gaba" "Ameen, thank you for understanding" kasa2 naji suna magana da wani, nace "kai da waye ne?" Da muryar dariya yace "Amir ne, wai koya min zance zaiyi, wai ni ban iya ba" nace " He is funny" yace "yes he is, bari in barki ki huta kin gaji ko? Na gode da daukan waya ta da kika yi, you have no idea how much it means to me" na runtse ido na inajin kalamansa har cikin raina. Nace "good night" yace "fi amanillah" daga nan ya kashe wayar. Na kara runtse idanuna ina jin wani abu yana min yawo a jikina. Na jima banji irin wannan feeling din ba, tun rabo na da Ibrahim. Nayi tsaki na gyara kwanciya ta, ya kamata in nutsu in san me nake yi especially after warning din da yaya Habeeb yayi min cewa sultan is a drunk, but he didn't look or sound drunk to me. Oh dear God, don't let me fall in love with a wrong guy again. Not again. Da kyar na samu bacci ya dauke ni. Washegari tun safe aka tafi "yalleman daurin aure, mu dai muna abuja muna ta shirye shiryen kai amarya, Zayed ya dage shi lallai babu zancen wani kafi ko gara, su a al'adarsu in kayi aure mata kawai za'a kai maka, shi wai a gurinsa abin kunya ne aga ana shigar da kaya gidansa wai daga gidan surukansa, dan haka daddy ya hada kudin duk da yayi niyyar yiwa Hafsat kayan daki ya saka mata a account dinta yace inta ga dama tayi jari dasu, in bata ga dama ba kuma ta kashe kayanta, kudin kayan gara kuma ya saya wa Zayed dalleliyar mota ya bashi a matsayin wedding gift. Tunda akayo mana waya an daura aure Hafsat take kuka tamkar wacce aka yiwa auren dole, sanda muka zo tafiya airport kuwa cewa tayi ta fasa auren ta shige daki ta rufe kanta, sai da daddy yazo da kansa sannan ta bude kofar. A hanyar zuwa airport na duba waya ta naga 5 missed calls daga sultan da message guda daya "please in kin samu chance call me" sai na samu kaina dayi masa reply cewa yanzu zamu tafi England, in naje zan kira shi da number ta ta can. Masha Allah, gidan Hafsat ya tsaru iya tsaruwa, tsayawa bayanin gidan bata lokaci ne, likita matar likita, ina kallon gidan ina tunanin cewa some people are so lucky in life, komai yana zuwa musu da sauki. Embassy muka sauka, anan zamu yi kwana biyu sannan mu dawo Nigeria. Ranar da muka baro Hafsat a gidan miji kwana nayi ina juyi, Allah sarki 'yaruwata shi kenan an shiga layin manya. Sai kawai na samu kaina da imagining what will it feel like, ga mamakina kuma a imagination din nawa sai naga Sultan with his muscular body, red lips and shiny brown eyes maimakon Ibrahim da nake gani duk sanda nayi irin wannan tunanin. Nayi sauri na kawar da tunanin daga raina tare da sake sabuwar addu'a amma still babu bacci. Nayi tsaki na jawo wayata na duba time, 12:30am, a Nigeria zai zama around 8:30am kenan. Nayi dialing number dinsa, bugu daya ya dauka kamar mai jira. "Assalamu Alaikum" na amsa masa, sannan yace "God, saura kadan in running mad, ban taba jin haka a rayuwa ta ba, what have you done to me woman?" A raina nace kai zanyi wa wannan tambayar ai, a fili kuma cewa nayi "haba dai, da girman ka?" Yayi dariya yace "nima na dauka am strong, sai yanzu nake ganewa ashe shayi ma ruwa ne" hmm kawai nace, yace "to ya hanya? Ya kuma amarya" nace "lafiya lau, mun kaita mun baro ta, gobe zamu huta jibi mu dawo insha Allah" yace "so, tell me about yourself" nan na bashi labari na in brief, abinda ya shafi family na da karatu na, ko kadan banyi mishi zancen Ibrahim ba, shima ya fara bani labari da cewa "well, as unbelievable as it may sound, babana shine sarkin Abuja, ni ne first born sai Abbas, Saratu sannan fa'iza, nayi primary a Abuja, sec da university duk nayi su a USA. Na karanci architecture first and second degree. I have many friends but Amir shine babban abokina, he is like a brother to me" daga nan yayi shiru, a hankali nace "what about your mother?" Yayi shiru kamar ba zai magana ba, can yace "I don't know who my mother is" duk da ta cikin waya ne sai da na fahimci irin zafin da maganar da ya fada tayi masa a ransa. Ba wai besan babarsa ba, a'a bai ma san wacece babarsa ba. [11/7, 2:27 PM] maryamsuleiman48@gmail.co: MAIMOON By Maman Maama 39 Episode Thirty Nine : The Shadow 2 Jinjina ta musamman ga masoya Ibrahim. Lallai kun chika masoyan gaskiya da kuka rike soyayya har tsahon shekara biyar. Ina kuma baku hakuri dangane da jin shiru akansa, na tsara labarin ne a haka saboda in kara masa armashi yadda zaku fi jin dadinsa, amma insha Allahu nan ba da dadewa ba zamu ji labarin Ibrahim. Jinjina ta musamman again ga masoya Sultan tunda har kuke son sa duk da kasancewar sa bad boy wannan itace soyayya ta gaskiya, kaso mutum ba dan halinsa ba. 💖 you loads Nayi shiru maganar tana sinking a raina, sannan nace "bangane ba, how comes?" Shima shirun yayi kamar baiji abinda nace ba, munfi minti biyu a haka, ina jiyo saukar numfashinsa ta cikin wayar, can yace "can we please not talk about this? In fact yanzu nasan dare yayi sosai a England, gwara in barki kiyi bacci haka ko?" Na gane waccan maganar ce baya son yi amma nasan bani da right din da zan matsa masa dan haka nima ba bar maganar "OK, good night then" "fi amanillah" na jima bayan munyi sallama ina lissafin maganar sa, me yake nufi? What is his story? Washe gari tun safe nake baccin gajiya har zuhur sannan inna ta tashe ni nayi sallah naci abinci na sake komawa wani baccin. Sai la'asar sannan na tashi nayi wanka na shirya dan zamu je gidan Hafsat muyi mata sallama tunda gobe da safe zamu koma Nigeria. A gidan Hafsat ne su inna da gwoggo rabi babar su nuraddeen suka yi ta yiwa Hafsat nasiha akan zaman gidan miji, nima na zauna naji kuma na karu sosai, bayan sun tashi suna kara zagaya gidan ne na saka Hafsat a gaba da tsokana wai sai ta gaya min abinda ya faru jiya bayan mun tafi, harara tayi ta watsa min daga karshe tace "wai ke yaushe na fara wasa dake ne? In auren kike so ki fada yanzu zaki ganku a gidan munir" wata harara nima na watsa mata, dan ni har mantawa nake yi da wani munir a duniya, dariya itama tayi min tunda ta kashe min baki. Sai da muka zo tafiya kuma sannan ta fara kuka, babu kunya Zayed ya kama rarrashinta a gaban su inna, sum2 suka fice ina ta yi musu dariya. Kaya sosai maman Zayed ta bamu muka tafi dashi. Washegari da safe muka dawo Nigeria. Duk 'yan biki kuma kowa ya watse sai fatan Allah ya sanya alkhairi. Sai da aka gama watsewa sannan na fara missing Hafsat, gashi Amina ma bata nan ta bi mutanen 'yalleman zata karasa hutun ta acan. Duk gidan ya gundire ni sam babu dadi. Sultan kuwa kullum sai ya kirani a waya, yayi2 in barshi yazo gidan mu naki, saboda ina tsoron abinda zaije ya zo. A raina nasan ya kamata in dakatar da Sultan amma zuciya ta taki barina in yi haka, sosai nake jinsa a raina, dan wani lokacin ma ni da kaina nake kiransa a waya. Ranar da mukayi sati daya da dawowa daga England na tambayi mommy cewa ina so inje gidan su Amira in wuni acan sai dare zan dawo tunda na gaji da zama ni kadai, babu musu mommy ta barni tace driver ya kaini da daddaren sai ya koma ya daukoni. Na shirya cikin riga da skirt na jar atamfa mai adon fari da baki, na yafa farin mayafi, da farin takalmi, na debi wayoyina muka tafi. Muna cikin tafiya munbi ta wata siririyar hanya sai muka tarar da go slow, gurin ya chunkushe mutane sai hayaniya suke yi, nayi mamaki saboda normally gurin babu traffic, driver nane ya fita ya tambaya sai ya dawo yace min wai wani ne yayi blocking hanyar yace yau babu mai wucewa ta nan, sai dai mu koma baya sai mubi ta wata hanyar. Nayi shiru ina tunani, sai na dauko waya ta na kira number din sultan, ya dauka nace masa "kana ina?" Dariya yayi yace "na fita unguwa ne kuma sai na tsaya neman rigima" bance komai ba na kashe wayar nace da drivern ya zauna ina zuwa, na fita na kutsa ta cikin mutane har inda problem din yake, katuwar Jeep Dodge na gani anyi crossing dinta akan titin yadda ta rufe titin completely, duk glasses dinta a tinted dan haka bana hango wanda yake cikin motar, mutane sai hayaniya suke, wani naji yana cewa "to tunda ba zai dauke ba ba sai a kira masa 'yan sanda ba, in yafi karfin mu ai baifi karfin hukuma ba" wani kuma yace "to in an kira 'yansandan ma ya za suyi dashi? In sun kama shima ba zai awa daya ba za'a sake shi, su kansu yanzu sun gaji da kama Sultan" a raina nace da gaske shi din ne. Number motar na duba naga "SULTAN 3" na karasa kusa da motar, inajin wani daga bayana yana cewa "'yan mata kiyi a hankali fa, wannan mutumin is very dangerous". Na karasa dai dai windown driver nayi knocking a hankali, da sauri ya sauke glass din fuskarsa ta bayyana dauke da murmushin mamaki "Hey, me kike yi anan?" Na daura hannayena akan windown nayi tagumi nace "unguwa zanje kuma an tare min hanya" ya kalli dandazon mutanen da suka taru a gefe sannan yace "lallai kice dara taci gida kenan" nayi dariya nace "dama ai hausawa sunce in zaka gina ramin mugunta ka gina shi gajere, yanzu kaga nice na rufta ciki" shima dariyar yayi yace "da fatan baki balla kafa ba" wani daga bayana yace "baiwar Allah dama kin rabu dashi, wannan mutumin bai san magiya ba, gashi nan an kira police zasu zo suyi mana maganin sa" Sultan ya leko da kansa yace "kafin suzo suyi magani na ni bara inzo inyi maganin ka, dan rainin hankali kawai" ya bude kofar motar ya fito da sauri, sai kuma ya kalleni ya ga yadda na hade rai sai ya koma yana cewa "kaci sa'a, amma na gane fuskarka, zamu hadu wata rana" ni kawai kallonsa nake yi da mamaki, shi babu abinda ya dame shi wai dan mutane suna zaginsa, kamar ma wani enjoying kansa yake yi. Yasa hannu ya bude min kofar kusa dashi yace "shigo in kaiki unguwar" na yi jim ina tunani, anya kuwa in shiga motar Sultan? Anya mutunci nane? Besides ba wani sanin halinshi nayi ba, kuma duk a halayensa da ake gaya min babu wani na kirki. Na sake kallonsa naga shima ni yake kallo pleadingly, oh God, kawai sai na zagaya na shiga. Mutumin da suke fada da Sultan ya saki baki yana kallon mu, ina kallon sultan ya mika hannunsa ta window yayi masa alamar fuck you. Daga nan ya daga windown ya tayar da motar muka tafi. Wani daddadan kamshi ne a cikin motar, irin kamshin nan da yake sa mutum ya lumshe idonsa, da gaske sultan dan gayu ne dan cikin motar tsaf yake, kujerun an lullube su da wani tattausan bargo wanda shi kansa kamshin yake yi. Shi kansa Sultan din gani nayi ya kara yi min kyau da kwarjini, yauma kamar kullum rigarsa body hug ce data kama jikinsa sosai amma yau 3 quarter wando ne a jikinsa, gashin kansa a hargize yake kamar kullum. A 20 yake tafiya da motar kuma gaba daya ba titi yake kallo ba ni yake kallo, har sai da naji kunya na rufe fuskata da mayafina. Motoci sai horn suke yi mana daga baya, duk wanda yazo wucewa kuwa sai yayi bala'i amma sultan ko kallonsu baya yi hankalinsa gaba daya yana kaina. Nace "wai wannan kallon na menene kuma" "duk sanda na ganki sai inga kamar kara kyau kike yi" kamar nima ince masa shima haka sai kuma dai nayi shiru nace "thank you" yace "ina zakije ne?" Sai yanzu na tuna na bar driver da mota a baya, da sauri na dauko waya ta na kira shi nace na tafi, ya danje yawo kadan sai ya koma gida yace ya kaini. A muryarsa naji alamar baiji dadin abin ba amma kuma babu yadda zaiyi. Mun danyi tafiya kadan nace "why do you do it?" Yace " me fa?" Nace "why do you block the road?" Kafin ya bani amsa wani ya danne horn a bayanmu sannan ya zo ya wuce mu a guje yana cewa "malam in ba zaka wuce ba ka bawa mutane hanya su wuce" Sultan yayi dariya yace "that's why" nima dariyar nayi nace "to kai me yasa ba zakayi saurin ba, kana tafiya a cikin abuja a 20 bayan kasan kowa a garin nan sauri yake" ya wani kwantar da kujera kashingida yace "sauri va gurin zuwa ba" da sauri nace "dan Allah ka rufa min asiri ka tashi, ya za'ayi mutum yana driving kuma ya kwanta" sai da yayi dariya sosai sannan ya tashi zaune, ni kuwa duk na rude, yana tashi wani ya yi masa dakuwa daga waje, ai kuwa ya sauke glass sukayi ta zage2 sannan muka wuce. Sai a lokacin na gaya masa inda zanje, yace "OK, inda kika tura mu rannan ko?" Muka yi dariya gaba daya. Muna tafiya a hanya ne yake tambayata me yasa nake yawo da driver? Nace masa "ban iya driving ba" yayi ta min dariya yana tsokana ta wai abin kunya kamata ban iya driving ba, yace "in kin yarda sai in koya miki" nace "not now, sai na gama school tukunna" yace "OK, Allah ya kaimu" mun danyi nisa na sake tambayarsa "yanzu dazu da kayi blocking hanya da mai martaba yazo wucewa fa?" Yace "kinsan kuwa hakan ta taba faruwa" na ware ido nace "haba? Ya akayi kuma?" Yace "kamar yadda nayi dazu, na rufe hanya nace ba shiga ba fita, na rufe glasses din mota na kunna AC na kwantar da kujera ta nayi kwanciyata, mutane suna ta hayaniyarsu da zage2n su, kawai sai ga Takawa nan ni ban sani ba, yana zuwa yaga an tsaya ya tambaya lafiya aka ce ai hanya a rufe take, yace aje a gano me ya faru, aka koma akace masa ai nine na rufe hanya da motata" yayi shiru, nace "me yace kuma?" Yace "dogarai ya aiko yace su farfasa motar su fito da ni suyi min duka su jani a kasa su kaini gida" na rufe baki na ina mamaki nace "ya salam, sunyi din kuma?" Wani murmushi ya jefa min yace "sun fasa mota alright, amma none of them will dare to touch me, duk wanda ya taba ni kuwa sai na kwantar dashi a asibiti kuma ya bar aikin sa kenan" nayi shiru ina jimamin maganar, it seems like there is crisis between the father and the son, does it has to do with Sultan not knowing who his mother is? Ina so in sake tambaya kuma bana so yaga kamar ina bi masa kwakwkwafi. Mun danyi gaba kadan sai naga ya sake hanya yabi wata hanyar daban, nayi sauri nace "ba nan ce hanyar ba fa" bai kalleni ba yace "eh na sani, sayar dake zanje inyi" nayi shiru yace "kinga kuwa zakiyi tsada" ni dai bance masa komai ba, sai a lokacin na fara lissafin babu wanda yasan tare da wa na fita, shi kansa driver din da muka fito dashi baiga sanda na shiga motar sultan ba, what if ya sace ni? Ina kallon shi ta gefen ido na yana min dariyar yadda na takure a gefe daya ina rarraba ido. Wata unguwa muka shiga irin unguwar talakawan nan, a raina nace me yake kawo sultan irin wannan unguwar kuma? I really hope he is not doing drugs kuma? Can gefe ya samu yayi packing yace "please two minutes dan Allah zanje in karbo sako" na gyada masa kai amma a raina ina cewa zaka je ka karbo drugs dinka dai. Ina kallonsa ya fita ya saka hannayensa a aljihu yana tafiya ya shige wani loko. Da sauri na dauko waya ta na kira Amira, "Amira gani na taho amma ba'a motar gida ba, ina motar sultan, in case in na bata a gurinshi zaku neme ni" na kashe wayar ina rarraba ido. Ta mirror na hango wani mutum yana tahowa wajen motar daga opposite direction din inda Sultan ya tafi, magidanci ne zaikai kamar 45 years, ta side din driver yazo yayi knocking, ina sauke glass din ya fara kokarin durkusawa zai yi gaisuwa sai kuma yaga babu kowa a gurin. Na gaishe shi ya leko ya amsa cikin sakin fuska sannan yace "yallaban baya ciki ashe" nace "ya fita, wai zai karbi sako" ya girgiza kai yace "zai kawo sako dai, tun dazu mukayi waya yace gashi nan zuwa da naji shiru shine na dan fita" sai kawai naji ina son in san sakon menene zai kawo. Nace "sakon menene zai kawo?" Yace "kudin makarantar yara ne, kinsan an kusa komawa sabon session, to nayi masa list na school fees, kudin books da uniform tunda akwai sababbin dauka to shine yace zai kawo min yau" kaina naji ya toshe nace "yara? Wadanna yaran kuma" yace "yaran unguwannin nan mana, ai duk shi yake musu komai na makaranta, mu kam ba abinda zamu ce masa sai sam barka dan da yawa mutanen da suke zaune a unguwannin nan shi yake ciyar dasu, ya ciyar damu ya biya wa yaran mu kudin makaranta ya samarwa matasan mu aikin yi. Kinga wannan sabuwar orphanage din daya gina duk nan unguwar yazo ya dauki ma'aikata maza da mata" cikin cushewar kai nace "orphanage? Sultan din ne ya gina orphanage?" Yayi alamar rufe bakinsa yace "ai na dauka tunda kuna tare kin sani, ai baya so a sani, da nasan vaki sani ba da bazan gaya miki ba" nayi sauri nace "dan Allah baba gayamin, wallahi bazan ce kai ka gayamin ba" ya gyara tsayuwa da alama yana da surutu, ya ce "ai wannan ta biyu ce, waccan babbar ma ta cikin gari ai shi ya gina ta sai mutane suke cewa dan majalissa ne shi kuma sai ya samu dan majalissar yace yace shine yayi. Ai duk unguwannin nan na marasa karfi yana da representative da yake gaya masa duk bukatun mutane kuma in dai an fada to zai bayar, in dai har maganar kudi ce to mukam sai godiya" nayi shiru ina jinjina maganar a cikin raina. Nayi wa mutumin godiya ya tafi hanyar da naga sultan yayi, har Sultan ya dawo ina jinjina maganar mutumin nan a raina. Yana zuwa ya shiga muka tafi yace "sorry na barki kina jira" kai kawai na gyada masa, yace "are you OK? Naga kin chanza?" Nan na kirkiri murmushi nace masa ba komai, bai yarda ba dai yace "bayan na tafi wani yazo nemana?" Na girgiza kai nace "babu wanda yazo nemanka" ina ganin fuskarsa ta chanza alamar yaji dadi. Dole na ware nima dan kar ya fahimci wani abu har muka je gidan su Amira. Tun 10:30 na baro gida amma banje gidan su Amira ba sai 1:30, kamar wacce na tafi kano. Muna yin packing Amira ta fito da sauri kamar dama a bakin gate take. Sultan ya tsatstsare ni da ido wai lallai sai na yarda yazo a maida ni gida. Amira tana bude kofar ta finciki hannuna "fito daga motar nan" Sultan yana dariya yace "check her from head to toe, ban ciri komai ba" ita dai bata kula shi ba sai jana take ni kuma naki fitowa. Sultan yace "please yaushe zan zo in dauke ki" Nace "after magrib" yayi murmushi yace "thank you" na juya zan fita muka hada ido da Amira wacce ta saki baki da hanci tana kallona. [11/7, 2:27 PM] maryamsuleiman48@gmail.co: MAIMOON By Maman Maama 40 Episode Forty :TheShadow 3 Tunda muka shiga gida Amira take min bala'i. Ni dai kawai dariya nake mata. "Yanzu kinsan kuwa duk wanda ya ganki a motar sultan irin kallon da zaiyi miki? Kin san ma kuwa waye Sultan? Mutumin nan ko magana bai kamata ace ta hada ku dashi ba ballantana har ki shiga motar sa. Yanzu ma tukunna, ina kukaje da kuka dade haka baku karaso ba?" Na harare ta nace "gidan sa ya kaini. Ina ruwanki da inda muka je?" Muka shiga dakin mamanta muka gaisheta sannan muka koma dakin ta. Nan fa ta saka ni a gaba da nasiha, ita lallai gani take shiga motar Sultan din da nayi tamkar wani katon zunubi na aikata. Tace "Yanzu Allah ne kadai yasan irin maganganun da ya gaya miki, duk sai yaje ya hure miki kunne anzo an kasa gane kanki. Ki rufa mana asiri Moon ki rabu da Sultan dinnan" Nace "Saboda me?" Tace "saboda me? Yanzu har tambaya kike yi saboda me? Just look at him zaki gane saboda me. He is a criminal for God's sake. He is spoilt rotten. A gangster. A rogue. A drunk. Duk wadannan dalilan basu ishe ki ba?" Murmushi kawai nake yi ina kallon yadda ta dage tana ta bayani. Nace "yanzu in tambayeki, ya akayi kika san Sultan is a drunk?" Tace "duk garinnan waye bai san dan shaye2 bane? sau nawa ana ganinsa yana yawo a gari a buge" nace "yanzu ke kin taba ganinsa yana shan giya?" Tace "ni ban taba ganin sa ba amma.. " na daga mata hannu nace "amma me? Annabi da kansa ya hana yada jita jita, abinda baka tabbatar ba kar ka fada musamman akan alfasha" Amira ta saki baki tana kallona kamar zata yi kuka tace "are you truly depending him?" Nace "ba wai goyon bayan Sultan nake yi ba, ina goyon bayan gaskiya ne" ta sake matsowa kusa dani desperately tace "yanzu ki duba kiga irin abokansa, ki kalli wannan shegen Amir din ki gani. Kin san kuwa sunan gang dinsu? Gang Bang they call themselves. Gang din 'ya'yan manya ne wadanda suka fi karfin karfin iyayensu. Abuja, kano, kaduna, legos da duk sauran manyan states na Nigeria an sansu, Sultan da Amir sune 'yan Abuja. Moon duk wanda yake cikin gang dinnan is a known criminal kawai dai dan babu yadda za'ayi dasu ne shi yasa. Kinsan kuwa kwanan baya suka yi gang raping wata yarinya a Nassarawa state?" Ji nayi tamkar ta chaka min mashi a kirjina, amma na daure nace "ke a ina kikaji wannan labarin?" Ta daga kafada tace "a radio, a television, a social media, a newspaper ko ina zancen akeyi" nace "ita yarinyarce tace su su kayi raping dinta" tace "eh mana, anyi hira da ita har a gidan radio" na sake cewa "ita yarinyar ce tace da wane da wane da Sultan suka yi raping dinta?" Tace "just because his name wasn't mentioned doesn't mean he didn't do it" na girgiza kai na kawai ina kallonta, tace "Moon kar ki bari son da kike masa ya rufe miki ido ki kasa ganin gaskiya. Dududu yaushe kika sanshi da har zaki tunanin kinsan shi fiye da sauran jama'a? Duk abinda nake gaya miki kamar yana shiga ta wannan kunnen ne yana fita ta wancan. Already har ya riga ya hure miki kunne" ta mike a fusace ta dauko laptop dinta ta ajiye min agaba na tace "in baki yarda dani ba check for yourself, ki duba internet zaki fahimci waye Sultan" daga nan ta fice ta barni a dakin. Na jima ina kallon laptop din ina jimamin abinda bincike na zai gano min. Can na dauka na kunna direct na shiga goggle, nayi typing sultan sai naga amsoshi da yawa wadanda ba sa dangantaka da abinda nake nema. Na goge nayi typing sultan Abuja prince. Nan da nan kuwa naga an watso min hotunan Sultan, wadansu a kasarnan wasu a kasar waje. Duk hotunan babu ko guda daya da yake da manyan kaya a jikin sa, babu kuma ko guda daya da yake tare da babansa. Nayi typing criminal record dinsa, nan ma naga rubutu da hotuna da yawa, can ya daki wancan, nan yayi trashing wancan shagon, yayi causing traffic jam, duk dai labarin daya ne. Nayi shiru ina karanta labaran daya bayan daya, sai wani tunani yazo min, duk cikin labaran banji ance yayi sata ba, banji fashi da makami ba, banji kisan kai ba kuma banji labarin yarinyar ta Amira ta fada ba, asali ma duk hotu an nasa babu inda na ganshi da mace, duk tare da maza ne masu shiga irin tasa. Wani hotonsa ne ya dauki hankali na nayi zooming, Sultan ne fuskarsa dauke da murmushi, rike a hannunsa kwalbar giya ce a daga ta alamar cheers. Na runtse idona ina jin zafi a kirjina. So it's true, yana shan giya. Hawaye naji yana kokarin zubo min na yi sauri na mayar dashi. Nayi typing emir of Abuja, nan ma hotuna na gani ba adadi na mai martaba sarki kuma kusan duk hoton yana tare da second son dinsa Abbas, cikin kima da daraja da kwarjini irin na sarauta, mostly a gurin saukar karatu ko bude masallaci ko musabakar alqurani. Nayi zooming wani hoton mai martaba, kana ganinsa kasan shi ya haifi sultan, idonsu, girarsu da shape din fuskarsu iri daya. Na koma nayi searching prince Abbas, nayi ta bincike amma na kasa ganin single fault nasa, he is like a perfect son, komai tare suke yi da mai martaba, duk inda mai martaba zaije tare suke zuwa. Can naga wank hotonsu shida sultan a america gurin graduation din sultan na masters. Nayi shiru ina tunani, mutane criminals irin sultan basa karatu, most of them da wahala suke gama sec sch, amma sultan masters ne dashi kuma a babban field like architecture. What is happening? What am I missing? What are u sultan? A gurin manyan mutane da masu kudi shi criminal ne, a gurin talakawa da sauran marasa karfi shi hero ne. Wanne dalili ne zai saka mutumin kirki ya mayar da kansa mutumin banza a idon mutane. Har zan rufe laptop din sai na fasa nayi typing the gang bang. Ai kuwa naga rubutu sosai a kansu, Amira tayi gaskiya dan daga 'ya'yan tsofaffin shugabannin kasa sai 'ya'yan gwamnoni da manyan masu kudi, a cikin list din naga an rubuta "the drunk prince of abuja" duk da basu fada ba nasan sultan suke nufi. Na rufe laptop din na kwanta ina tunani. Why will Sultan want people to think he is a bad guy while in reality he is good, very good. Yau kusan 3 hours nayi a motar sa daga ni sai shi amma ko da wasa bai kai hannunsa jikina ba kuma baiyi min wata magana da zata nuna cewa dan iska bane. Dear God, what do I do now. Inanan a kwance Amira tazo ta kawo mana abinci har yanzu fushi take yi dani ita wai lallai naki jin maganar ta. Da kyar na samu na bata hakuri nace tayi min addu'a insha Allah komai zai warware. Muna nan muna ta hira har magrib sai Sultan ya kira ni yace min gashi nan zuwa, tun daga nan Amira ta cigaba da bata fuska, naje zanyi sallama da mama tace min "Maimunatu wai me yake damun kawarki ne?" Nace "mama me ya faru? " tace "sam taki kula samari ballantana har ayi maganar fitar da miji, ta gama degree dinta, tayi service, me kuma yayi saura? Ni na gaji da surutun da iyayenta suke yi min wallahi, ni babu miji ita babu miji amma ita sam bata damu ba, shi wanda naga tana nacewa da ya fara zuwa kamar gaske kuma yanzu shiru, ni ko waya ma yanzu banji suna ji ba, idan ba aurenta zai yi ba sai ta rabu dashi ta samu wani" na kalli Amira da alamarr tambaya saboda ban gane maganar da mama take yi ba, Amira ta daga kafada irin oho din nan, nan dai na bawa mama hakuri nace zamuyi maganar da Amira. Muna fita na tambayeta "wanene mama take magana akansa" ta dauke kai tace "nima bansani bafa, ita dai kawai ta damu sai nayi aure ne kuma ai shi aure lokaci ne, idan mijin baizo ba ni zan auri kaina ne?" Jikina ya bani da akwai abinda Amira take boyewa amma sai na rabu da ita, na san in tana son in sani zata gayamin ne da kanta. Muna zuwa wajen motar Sultan Amira ta rike hannuna tayi masa knocking, ya sauke glass yasha wani bakin glasses a fuskarsa, Amira ta hade rai sosai tace "gata nan na kawo ta, kuma ka sani wallahi duk abinda ya same ta hukuma ba zata bar ka ba" Sultan ya dan sauke glasses din idonsa kadan yana kallonta ta saman glasses din, sai kuma yayi dariya yace "Thank you Mah, zan bi duk kanin umarnin ki" ina jin Amira tana ta kunkuni tana cewa "banza mai kyan dan miciji kawai" ni dai ina ta kunshe dariya ta naje na shiga muka tafi. Kamar yadda ya kawoni a 20 komawar ma a 20 muke tafiya. Ya chanza wanka yasaka riga mai dogon hannu amma kuma sai ya nannade hannun rigar zuwa gwiwar hannu. Wani irin cikar halitta da kyau ne yake bayyana a jikinsa. Kawai sai ji nayi yace "are you checking me out?" Naji wata kunya ta kama ni saboda bansan yana kallona ba. Yayi dariya yace "Thank you for appreciating me" nayi sauri nace "I didn't" yace "OK ni bara inyi appreciating dinki. Kinga kina da kyau sosai da sosai, kina da komai da yakamata ace mace tana dashi. Sannan kina da nutsuwa sosai da kamun kai. Ga ilimi, you are a potential doctor at a very young age, and that's wow. Zan iya cewa babu abinda kika nema kika rasa. Ina so ko yaya ne kiyi sharing abinda kike dashi with me" ya danyi shiru ni kuma bance komai ba, sai ya cigaba "nasan ni ba kowa bane ba, I am nobody and I have nothing, na san kinfi karfina nesa ba kusa ba kuma nasan abinda nake so in fada kamar selfish ne, amma kuma tun ranar da na fara ganin ki na kasa samun sukuni na zuciya na kasa controlling kaina. I want to spend the rest of my life with you" na lumshe idona na kwantar da kaina akan headrest din kujerar inajin sonsa yana kara huda kirjina. A lokacin Ibrahim cewa nayi idan mommy ta sani zata saka ni a turmi ta daka ni ta mayar dani gari, wannan karon kuwa inajin in ta sani sala sala zatayi da nama na tayi kilishi ta cinye, lol. Sorry guys, abubuwa ne suka danyi min yawa shi yasa baku jini jiya ba. [11/7, 2:27 PM] maryamsuleiman48@gmail.co: MAIMOON By Maman Maama 41 Episode Forty One : This is Me 3 Jin bance komai ba yasa Sultan yayi ajjiyar zuciya yace "am sorry, maybe it sounded like an insult to you. Allah ya baki hakuri. Kawai dai na fada ne saboda ni bana iya rike abu a raina. I don't deserve you, I know. Kawai dai na dauka for once maybe zan zama lucky" na kalleshi ina girgiza kaina nace "am not saying no Sultan, am just not saying yes. Duk wannan abin yayi sauri da yawa, babu dade da haduwa ba. I don't know you and you don't know me" ya cire glasses din idonsa ya dora akan dash board yace "look ba fa cewa nayi zan turo iyayena ba ko something like that ba, am just asking for your permission to love you" nace "na sani, amma still, indai har soyayya ce dole a kafa ta akan yarda da juna da aminci. Kafin in ce ina sonka ko bana sonka dole sai na sanka first. Sultan I don't even know your real name, babu abinda na sani a tare da kai" guri ya samu a gefen titi yayi packing ya juyo yana kallona sosai, yace "saboda rannan kin tambayeni about my mother shi yasa kike cewa haka ko?" Nace "well, yes, na gaya maka almost everything a kaina amma kai ka kasa gaya min komai, ta yaya kake so in fara relationship da kai ba tare da nasan komai a kanka ba?" Yace "I didn't tell you anything about my mother because I don't know" ya buga hannunsa akan steering alamar ransa ya fara baci. Nayi shiru bance komai ba ina gudun kara bata masa rai. Mun jima a zaune sai ya fara magana "Sunana na gaskiya Abbakar Sadiq Abdallah, for some unknown reason babana ya saka min sunansa, a game da mahaifiyata kuma bansan komai akanta ba, it is as if she didn't exist,babu wanda yake maganar ta, abinda na sani kadai shine sunanta, shima kuma a jikin birth certificate dina na gani. Tun tasowa ta a gidan kakana na taso, kakana wanda ya haifi mahaifina lokacin shine sarki ba Takawa ba. Duk duniya zan iya cewa daga shi sai Amir zan iya nunawa ince wadannan suna sona dan soyayyar da ya nuna min sanda yana da rai ko 'ya'yansa baya nuna wa haka. Tun ina yaro nasan Takawa shine babana amma kuma tun a lokacin nasan baya sona, dan ina tuna lokacin da in yazo gidan zan kama rigarsa in rike ina kuka shi kuma yana ture ni har sai na fadi sannan yayi tafiyarsa. Kakana lokacin shi zai daukeni yayi ta rarrashina. Gata kam a lokacin na gani, duk abinda nake so shi za'a yi min, babu wanda ya isa yayi min tsawa ko fada koda kuwa Yaya ce (yaya itace kakata wacce ta haifi babana), dan haka na taso a sangarce, babu mai sani babu mai hana ni, wani lokacin sai in zauna inyi ta kuka ince ni gurin mommy na da daddy na zanje ko wanne yaro yana gurin iyayensa banda ni, a irin wadannan lokutan ne marigayi sarki ya dauke ni ya kaini orphanage ya nuna min yaran gurin yace 'kaga wadannan yaran su basu san uwarsu ba basu san ubansu ba, basu san kowa a dangin su ba, kai kuma kasan babanka, kasanni ni kakanka, kasan dukkan danginka na gurin babanka to kamata yayi ka godewa Allah', a orphanage din na hadu da Amir" na kalleshi da sauri ya gyada min kai "yes, Amir is an orphan. Babarsa tana haihuwarsa ta dauke shi daga shi har mahaifarsa ko cibiya bata yanke masa ba ta ajiye shi a kofar orphanage ta gudu. Kakana shi ya rada masa sunansa Abdallah shine ake ce masa Amir. Sanda yake kaini orphanage ya hada ni da shi, tun a lokacin muke abota da yake shima fitinanne ne iri na, daga baya in zamu taho sai yayi ta kuka yace sai ya bi mu, sai kawai kakana yayi adopting dinsa ya saka mu a makaranta tare, komai tare muke yi dashi har yau. Lokacin da kakana ya rasu ne rayuwata ta chanza gaba daya, I was ten years old then, nayi ta kuka akayi ta rarrashi na naki hakura, Takawa yana zuwa ya kama ni ya daure min hannu da baki na ya saka ni a dakina ya rufe kofar. Haka na kwana ina kukan zuci babu bakin yin kukan ga uban dauri da nasha, sai washe sannan ya aiko aka kunce ni kuma yace in na sake kuka sai ya kuma daureni. Daga ranar nasan na rasa soyayya a rayuwata. Hankali na bai kuma tashi ba sai da aka nada babana sarki, ya dauko iyalansa wadanda ko saninsu banyi ba tunda baya bari inje gidansa ya dawo palace. Ni na riga na saba duk abinda nake so shi zanyi, tun da ya dawo gidan kuwa sai ya zamana duk abinda nayi no matter how small ba zai yi min fada ko nasihaba sai dai ya saka dogaran sa suyi ta dukana, wani lokacin har Amir za'a hada a daka koda kuwa ni kadai nayi laifin. Daga lokacin muka fara koyon fada ni da Amir, in an saka a dake mu sai ya zamana suna dukan mu muna ramawa. Bayan na karasa primary school, Rannan na tambayi Yaya nace dan Allah ta saka a kaini gurin babata sai tace min itama bata san inda take ba, na tambayeta ko ta san dalilin da yasa iyayena duka rabu? Sai tace min saboda ayi protecting family name. Lokacin ina yarinta ban fahimci maganar ta sosai ba. Lokacin Takawa ya sai wata sabuwar mota kawai sai na dauki fenti na shiga garage dinsa na rubuta 'fuck the family name, I want my mother', nasan abinda na aikata dan haka naje na shirya, na saka duwatsun wuta a cikin safa ta na hada da hannuna wanda na daure da karamin towel na daure, neman kawai wanda zan huce temper ta akansa nake yi, ai kuwa sai dashi an turo wani dogari mai tsautsayi akan ya zo ya dake ni, da na dage na fara naushinsa da hannuna mai duwatsun nan har sai da naga baya motsi, haka aka kwashe shi sai asibiti. Washe gari takawa ya kirawo ni yace "tunda ni ka gagare ni zan tura ka inda za'a koya maka hankali" shikenan abinda yace min, babu Sultan me yasa kayi haka? Babu Sultan ya kamata ka dena haka. Kawai ya saka mu a jirgi ni da Amir sai lagos, gidan kangararru. Wasu iyayen suna ganin gidan kangararru a matsayin gidan da zai gyara musu 'ya'yansu basu san cewa kara kangarar da yara yake yi ba. Sanda ya kaimu na tambayeshi 'why?' Amsar da ya bani shine 'to protect the family name'. Babu abinda ban koya a gidan nan ba, babu abinda ban iya ba, acan na hadu da most of the gang bangs, iyayensu sun kasa basu tarbiyya sun turo su nan. Shekarar mu biyu acan uncle dina galadima yaje a fito damu, yana kawomu gida Takawa kallo daya yayi mana yace ba'a gidan sa ba, a lokacin ne Hajiya ta kira ni dakinta ta ce min zata saka a kaini America a saka ni a makaranta amma sai na mata alkawarin bazan dawo Nigeria ba zanyi zama na acan. Ni a lokacin gani nake yi me zai dawo dani Nigeria tunda babu wani abu da na bari anan, nobody wants me, not even my mother. Sai a lokacin naga birth certificate dina da sunanta a jiki 'Khairat Abdallah' da signature dinta, sai a lokacin nasan cewa a america aka haife ni, dan haka ina zuwa America asibitin da aka haife ni na fara zuwa ina bincike ko zan samu wani information akanta amma ban samu komai ba. Takawa ya saya min gida ya saya min mota ya cika min account dina da kudi. Babu wanda yayi tsammanin zamuyi karatu da gaske ni kuwa na dage da karatu kawai saboda ina sa ran maybe in nayi karatu he will love me, na gama sec sch na shiga jami'a amma ko sau daya bai je ya ganni ba, sai dai duk kudin da nake so zai aika min. San da na gama first degree dina na shigo jirgi na zo Nigeria na kawo masa certificate dina ya karba ya duba, abinda yace min shine "good for you" daga nan ya jefo min takardata, alokacin ne na fahimci cewa ba wai halina ne baya so ba ni din ne baya so, Hajiya tace min ina alkawarinta nacewa bazan dawo Nigeria ba? Dan haka na tattara na koma America na koma makaranta. A lokacin nayi hankali sosai kuma na fahimci cewa duk abinda ya faru a rayuwata ya faru ne saboda babana yana so yayi protecting his family name, ni kuma na sha alwashin sai na bata family name din nasa da yake ji dash, duk tsiya dai shi ya haife ni kuma duk abinda nayi dole sunan nasa da yake ji dashi za'a ambata. Ina zuwa Nigeria hajiya ta fara tambayar alkawarin mu and I told her to fuck off, nasan abinda take so, bata so na a kusa da sarauta saboda tana son abbas yayi sarauta ita kuma bata san sarauta is the last thing on my mind ba, dan haka na fara bribing dinta cewa in dai har tana bani goyon baya ina yin duk abinda nake so to I will leave Abbas alone yayi ta sarautarsa. Aikina na architecture yana kawo min kudi sosai, dan haka a yanzu bana bukatar kudin Takawa dan duk abubuwan da nake yi da kudina nakeyi, yanzu ba zai sa a dakeni ba kuma babu yadda zaiyi dani dan haka sai ya koma ignoring dina, nuna wa yake yi kamar bai san dani a duniyar ba amma nasan cewa sakonni na suna isa gurinsa sosai" ya juyo ya kalleni fuskarsa dauke da wani murmushin dana kasa gane kansa yace "to Maimunatu, I opened up to you, babu wanda na taba zama mukayi irin wannan maganar dashi bayan Amir sai ke. This is me. Yanzu zaki iya yin making decisions dinki yes or no" yana gama fadar haka ya mayar da glasses dinsa ya tayar da motar. Har muka je gida babu wanda ya sake cewa komai. Ni a gurina kaina ne ya kulle, I need to digest duk maganganun Sultan kafin inyi fully understanding din labarinsa. Yana packing nayi masa godiya, kai kawai ya daga min na fita. Sai bayan na gama da kowa nayi sallah nayi wanka na kwanta sannan na fara rewinding duk maganganun sultan ina reviewing dinsu. Duk abinda yake yi yana yi ne dan ya bata sunan family dinsa saboda yana ganin basa sonsa kuma sune sanadiyyar gurbacewar rayuwarsa. Yanzu na fahimci dalilin soyayyarsa da yara da taimaka musu ta hanyar gina orphanage da saka su a makaranta, saboda yasan ciwon rashin samun kulawa daga iyaye, yasan maraici duk da shi ba maraya bane. And suddenly I know what sultan wants, what he needs, LOVE. Na dauki waya ta na duba time na lissafa naga rana ce yanzu a England, nayi dialing number din supervisor na, yana dagawa nace "sir I think I found the subject for my research project" *what do you guys think is more important, Family or Family name?* [11/7, 2:28 PM] maryamsuleiman48@gmail.co: MAIMOON By Maman Maama Episode Forty Two : Born for This Sultan ya jima a zaune a cikin motar bayan fitar Moon, shikenan ta faru ta kare, haushin kansa gaba daya yake ji, menene dalilin da yasa ya gayawa Moon labarinsa, yanzu ya tabbatar she will say NO to him, babu wacce zata so ta hada zuri'a dashi. Wannan shine dalilin da tun tuni ya kasa yin budurwa saboda baya jin zuciyarsa zata iya daukan rejection daga budurwa kuma, plan dinsa shine yazo Nigeria yayi destroying name din familyn sa sai ya koma America ya cigaba da rayuwa acan. A plan dinsa babu budurwa ballantana aure, saboda yasan aure zai ruguza masa plan dinsa ne tunda in yayi aure dole zai haihu kuma 'ya'yansa will still bare family name din da yake yaki da. Out of nowhere Moon ta shigo rayuwarsa, kallo daya yayi mata and he is hooked for life dan yanzu baya jin zai iya rayuwa babu ita wanda hakan yasan wani babban yaki ne ya dauko. Yasan babanta sosai, Ambassador M D, a very well respected man, tsakanin sa da ambassador MD tamkar hanyar jirgi ne da ta mota. Koda ace yayi convincing Moon baya jin zasu iya convincing babanta. Babansa kuwa yasan ba zai shiga maganar ba ballantana a duba darajarsa a bashi ita. Ya runtse idanunsa yana jin zafi a zuciyarsa. She means the world to him, he can't loose her. Ya tayar da motar ya fara tafiya. Yayi mamakin kansa dazu, he don't normally talk about himself amma kawai ya zauna ya saki baki yayi ta zuba mata magana kamar wadda tayi masa asiri, yanzu ya yarda da ake cewa Love is the strongest magic of all. Ya tabbatar cewa yau ba zai yi bacci ba. Ko da yaje gida ya kwanta ma juyi yayi tayi akan gado amma ya kasa bacci. Sanda baccin ya dauke shi kuwa mafarkai yayi tayi na rayuwarsa a baya. Sai wajen assuba sannan a samu bacci mai dadi. Cikin bacci yaji wayarsa tana kara, da magagin bacci ya dauka ya saka a kunnensa ba tare da ya buda number ba "Assalamu Alaikum" yaji ance "wa alaika assalam, a tashi daga baccin nan haka assuba tayi" tuni yaji baccin ya watstsake, ya duba screen din wayar da sauri, Love, ya sake mayarwa kunnen sa yaji an sake cewa "in baka tashi ba zan kashe in sake kiranka har sai ka tashi" a hankali ya furta "Love, is that you?" Daga cikin wayar yaji sautin murmushinta ya lumshe idonsa yana hango fuskarta da dimples dinta, tace "yes it is me, ka tashi kayi sallah assuba tayi" still idanunsa a lumshe ya ce "then you are not dumping me, right?" ta danyi shiru inda bugun zuciyarsa ya karu sannan tace "no Sultan, am not dumping you". Bai san sanda wani murmushi ya bayyana a fuskarsa ba yaji tamkar an cire shi daga ukuba an saka shi a Ni'ima, murya can kasa yace "thank you, i will never let you down". Na ajiye wayar ina bin screen din wayar da kallo, nasan na debo babban aiki but I can't stop myself, I feel like I was born for this. Jiya na jima banyi bacci ba kuma na yanke shawarwari da yawa, na farko zanyi accepting soyayyar Sultan dan nima ina son shi kuma ina so in chanza masa rayuwarsa in fito da kyawawan halayensa kowa yasan ko waye real sultan, zan bashi abinda ya rasa a rayuwarsa tun kuruciya, soyayya, zan bashi something to care for, me. Zan nuna masa cewa akwai wanda ya damu dashi kuma zan fahimtar dashi cewa idan har bai gyara rayuwarsa ba zai rasa ni. Matsalata daya shine yadda zanyi family na suyi accepting Sultan a matsayin mijina. Daddy na is soft as well as hard, dole in ina son in gabatar da Sultan a gurinsa sai na nemi soft spot dinsa which for now I don't know. Mommy is as hard as steel dan haka bansan ta wanne barin zan shigar mata da sultan ba, wannan dalilin ne ya saka na yanke shawarar zan cigaba da ganin sultan a boye sannan sai in nemi chance dina kuma inyi ta addu'a. Addu'ar ita na tashi nayi da daddaren nayi istikara na nemi zabin Allah, akan sallaya ta anan nayi bacci kuma ina farkawa da assuba Sultan ne ya fara fado min a rai na shi yasa na kira shi na tashe shi yayi sallah. Tun daga ranar muka dinke ni da sultan, kullum muna tare dashi a waya dan har komawa nayi saka ear piece saboda bazan yi ta rike wayar a hannuna ba. Wani lokacin muna zaune a falo da 'yan gidan mu muna hira at the same time kuma muna waya dashi. Duk sun san cewa nayi sabon saurayi amma basu san ko waye ba saboda bana yadda in kira sunansa a gabansu. In muna so mu hadu kuwa sai in kirkiri fita unguwa, ko ince zanje kasuwa ko gidan kawaye, sai muyi plan din inda zamu hadu dana fito sai in sallami driver na ince ya tafi yawo in na gama zan kira shi, daga nan sai sultan yazo ya dauke ni. Ni kaina nasan abinda nake yi ba dai dai bane amma na kasa samun wata mafitar. A haka har hutun mu ya kare muka fara shirin komawa england. Ranar da na gaya wa Sultan abinda yace shine "kice tafiya England ta kama ni kenan" nace "ban gane ba?" Yace "wai kina nufin zan zauna a Nigeria ke kina England bana ganin ki? You dey craze? Ai bana jin zan iya sati daya ban ganki ba" dariya nayi sosai nace "Sultan aikin ka fa?" Yace "Daga can ma zan iya yi. To in kin tafi ai tunani ma ba zai barni in yi aikin sosai ba" kuma nasan har zuciyarsa yake wannan maganar, yes Sultan loves me that much, wani lokacin har zama nake inyi tunanin me zaj faru in aka ce za'a raba mu? Ni nasan cewa duk ranar da Daddy da mommy suka ce in bar Sultan to kuwa zan barshi har abada duk kuwa da son da nake masa saboda ban taba yi musu gardama ba kuma bana fatan inyi musu, ina son iyayena sama da komai kuma zan rabu da Sultan in sunce in barshi koda kuwa sansa zai zama ajali na. Ana gobe zamu tafi Amira tazo zamuyi sallama nan na bata labarin cewa sultan fa bin mu zai yi. Tace "bangane ba, daki za'a bashi a gidanku ya zauna?" Nayi dariya nace "ke Amira, da akwai gidan babansa acan, anan zai zauna" ta bata rai tace "ni dai Moon Allah ya gani bana son ki da Sultan wallahi, this is a very dangerous game you are playing. Ita behavior is contagious, idan ke baki chanza shi ba shi zai chanza ki tunda ya fiki taurin zuciya plus kina son shi da yawa. He is handsome na sani, but He is as handsome as sin. Duk wani abin zunubi zaki ga kyakykyawa ne, very tempting, dole sai ka kai zuciya nesa zaka hana kanka" nayi shiru ina lissafa maganar ta, but i know what I feel for Sultan is not lust, it is love. Bayan munje England ma haka ce ta kasance, kullum muna tare da Sultan a makaranta dan komawa yayi kamar shima student din ne. Kullum in muna tare sai nasan yadda nayi nayi masa nasiha ta sigar lumana, ina nuna masa this is right and this is wrong, amma ga mamaki na sai naga in aya na fara janyo masa sai ya karasa min, in hadisi na dauko sai ya gayamin wani irinsa, wato yana sane da duk abinda yake yi kenan. Abinda na kara fahimta a dangane dashi shine yana da zuciya, muguwar zuciya ma, wannan shi ya saka ya ke da fada, dan a makaranta kullum ina cikin rabon fada da Sultan. Allah yaso makarantar tana da girma shi yasa har yanzu siblings dina basu san da zaman sultan ba. Sannan kuma Sultan yana da mugun kishi dan ko kallona wani namiji yayi indai kallon bai gamshe shi ba yanzu zakuji kansa, ni har dariya yake bani dan ni mai mutane ce kowa nawa ne babu mace babu namiji. Haduwar su ta farko da Mahdi nayi introducing dinsu suka gaisa kamar gaske sai bayan mahdi ya tafi sannan Sultan ya bata rai yace "I don't like him" nace "saboda me? He is nice and shine best friend dina a school dinnan" ya tsare ni da ido yace "amma kin san yana sonki" na sunkuyar da kaina nace "yes, but I don't love him, I love you". Sau da yawa sai in samu kaina da comparing Sultan da Ibrahim. Sam basu da alaka, kamanninsu sun sha ban ban, yayinda Ibrahim yake da sanyi Sultan kuma zafi ne dashi, Ibrahim ustaz ne sultan is the total opposite of ustaz, amma abinda yake bani mamaki shine lokacin da muna tare da ibrahim har rigima mukayi dashi akan taba ni duk da kuwa lokacin ina kwaila amma sultan ko da wasa bai taba kai hannun sa jikina ba. Situation din da muke ciki da Sultan is exactly wanda muka kasance da Ibrahim, yadda yake bina duk inda na tafi, yadda yake sona kamar ya cinye ni, da kuma yadda duk nake boye su daga gurin iyayena. They are totally different but exactly the same. A hankali ina ganin chanji a halayen Sultan, yana behaving kansa especially if I am around. Kuma har yau ban taba ganin shi a buge ba kuma na kasa tambayar sa saboda bansan yadda zai dauki maganar ba, amma nasan ko da yana shan giya to ba sosai ba saboda shi dan giya ko yayane sai an gane shi. Shakuwa ce sosai take kara shiga tsakanin mu kuma Sultan is an open guy, komai nasa yana gayamin saboda koda yaushe yana gayamin shi baya son secret. Rannan muna zaune a school yace min "tell me Love, akwai wani guy da ya kamata in san da zamansa? Ina nufin akwai wani da kuke tare kafin ni ko akwai wani da yake sonki bayan ni? I want to know" nayi shiru ina auna maganar sa, bana jin zan iya gaya masa labarin Ibrahim, there is no need saboda by now na tabbatar cewa Ibrahim ba zai dawo ba, nace "actually there is one guy, sunanshi munir" nan na gaya masa labarin munir da alkawarin baffa nayi mana aure in na gama makaranta ba tare da miji ba. Sultan ya saka hannu a cikin gashinsa yana hargitsawa, dabi'ar dana lura yana yi duk sanda wani abu ya taba zuciyarsa, shi yasa kullum gashinsa yake a hargitse. Na saka ido na a cikin nasa nace "wannan shi yasa nake son ka nutsu yadda zan kaika gida kafin in gama project dina" ya bata fuska yace "am trying, really trying, but this is me, I can't just change over night" naga maganar tana so ta bata masa rai sai na chanja topic din nace masa "to kai fa? Any girl that I should know of?" Nan take murmushi ya yi replacing damuwar sa yace "No, not Sultan. Ban taba son wata ba sai ke though akwai yarinyar da take sona, Khulsum, kanwar Hajiya ce. Farkon dawowa ta Nigeria na tarar da ita a gida, she is a good cook ni kuma I love food sai take yi min girki kullum then I realized tana da hidden agenda sai nayi ending alakar mu, she might still be in love with me duk da dai mun dade bamu hadu ba" na gyada kaina nace "it's OK" amma cikin raina na dan ji babu dadi especially inda yace ta iya girki, in akwai abinda ban iya ba a rayuwata girki ne, lol. Bayan kwana biyu nayi deciding zan kai Sultan gidan Hafsat su gaisa. Tun safe na kira ta na gaya mata zanzo kuma zan kawo bako, sannan na gaya mata cewa I also want him to meet Zayed. Da yake ranar Weekend ce sai na gaya wa mommy zanje gidan Hafsat tace a dawo lafiya, dama mun gama plan din inda zamu hadu da sultan dan haka muna fita da driver na gaya masa inda zai kaini, muna zuwa na tarar already Sultan yana jira na dan haka nayi changin mota. Tare muka shiga palon Hafsat da sallama. Suka amsa a tare ita da Zayed. Idan sunyi mamakin ganin Sultan to sun boye dan sam banga alama a fuskar su ba. Muka zauna mu hudu muka yi ta hira, nayi ta sha'awar Hafsat da Zayed, yadda suke abubuwansu, Arabic din Hafsat ya gyaru sosai dan dashi suke magana da Zayed. Zayed yayi ta yiwa Sultan tambayoyi shi kuma yana amsawa truthfully, saboda gaskiya Sultan ba shi da karya ko kadan, bashi da boye2, duk abinda ka tambayeshi zai gaya maka, either ka karba ko ka bari. Tare mu kaci abincin rana bayan munyi sallar Zuhr, daga nan su Sultan suka fita suka barmu. Na kalli Hafsat nace "so... Fadi abinda yake ranki" tace "he loves you, that's for sure. But he is Sultan, kinsan sunan da yayi a Nigeria babu inda babu labarinsa da labarin takadirancin sa. Kema kanki kinsan cewa kin debo da zafi Moon. Kuma na tabbatar cewa har yanzu a gida ba'a san da maganar sa ba ko an sani?" na girgiza kaina, ta cigaba da cewa "you are making the same mistake as you do with Ibrahim. Bana so ki shiga da yawa kamar yadda kika shiga son Ibrahim kuma abin yazo baiyiwu ba kika zo kika shiga wani hali" nace "so nake inga na chanja shi kafin in kaishi gida, He is a good guy, kawai dai ya riga yayi wa kansa ado ne da bakin fenti, I want to have a chance dazan yi presenting dinsa as the good guy he is" Hafsat ta girgiza kanta tace "you may not have that chance, kawai kisa rana ki kai shi, in yes, yes in no, no, shikenan an wuce gurin" ita Hafsat bata fahimci cewa no dinne zuciya ta ba zata iya dauka ba, bayan heart break din dana samu akan Ibrahim bana jin zan iya daukar wani heart break din na rabuwa da sultan. Ina so inyi ta jan lokaci for as long as possible saboda bana son rabu da shi. A hanyar mu ta komawa gida sultan ya lura da changin yanayi na ya tambayeni "me ya faru?" Na girgiza kaina nace "babu komai" ya saka hannunsa a gashin sa yace "she doesn't like me ko?" Nace "no ba haka bane wallahi, ta nuna min ya kamata in kaika gida gurin daddy ni kuma am not ready yanzu" ya hade rai yace "why not? ni am ready, ke kawai nake jira ki kirawo ni" na kalle shi naga da gaske yake babu wasa, he is strong, very strong, stronger than Ibrahim, dan nasan Sultan ba zai taba guduwa ya barni ba, ba zai taba rabuwa dani ba sai dai ni in rabu dashi, wannan kuma shine abinda nake tsoro, tunda Sultan yazo duniya yake shan wahala mutane suke juya masa baya da nuna masa kiyayya, bansan abinda zai faru dashi ba in nima iyayena suka tilastamin na rabu dashi. Nayi nisa sosai a harkar project dina dan kadan ya rage min in kammala, haka zalika project dina na psychology ma, wanda kachokam akan Sultan nake rubuta shi, ina ware light side dinsa wato behaviors dinsa da mutane suka sani da kuma shadow side dinsa wato behavior dinsa da yake buyewa, wadanda sune hakayensa masu kyau, anan na fahimci cewa halayen Sultan masu kyau sun ninka marasa kyau dan kusan rabin halayensa marasa kyau shaci fadi ne, rabin abubuwan da ake cewa yayi bai yi ba, wadansu abubuwan ma shi yake kirkira ya ce yayi saboda ya kara wa kansa tabo, gashi yanzu tabon shi zai iya jawowa a hana shi aure na. Dama hausawa sunce rana goma ta barawo rana daya ta mai kaya, rannan muna tafiya a makaranta ni da sultan wani bature dan ajinmu ya tsayar dani muna magana, Sultan duk ya gama kulewa sai faman taje kansa yake da hannunsa. Can dai ya gaji yazo ya taba Jack ta baya, ya juyo sultan yace masa "ita wannan da ka sakata a gaba kana kallonta kana mata surutu tayi kama da uwarka ne?" Jack ya bishi da kallo bai san me yace ba, Sultan ya sake cewa "Uwarka nace, shege da fuska kamar danyen kosai" ni dai ina ta kunshe dariyar da take neman kwacemin, kawai kamar daga sama sai ganin yaya Habeeb nayi a gurin yana kallona da mamaki, nan take dariyar ta tafi zuciya ta ta fara lugude a kirjina. Na gaishe shi sannan Sultan shima ya lura dashi ya bashi hannu suka gaisa, bai kuma cemin komai ba ya wuce warsa ya tafi. Tun daga lokacin ban kuma samun walwala ba har na koma gida, nasan yaya Habeeb ya taba kora min warning akan sultan kuma a lokacin nace masa babu komai a tsakanin mu to yanzu gashi ya kuma ganin mu tare kuma a England bama a Nigeria ba. Har dare ina ta sake saken amsar da zan bashi in ya tambayeni. Ina shirin kwanciya kuwa sai ga kiransa a waya, na dauka yace "ki same ni a palo" daga nan ya kashe. Na riga na gama shirya abinda zan gaya masa dan haka da confidence dina na fita gurinsa. Wani mugun kallo yake bina dashi har na zauna yace "me yake yi a garin nan kuma a Oxford kuma a tare dake?" Nayi gyaran murya nace "yaya Habibi" ya katseni "don't yaya Habibi me, ki gaya min gaskiya in ba haka ba straight daga nan sai gurin mommy zan kai ki" nace "yaya Habeeb kasan ina yin psychology, to an bani project topic" kaf na bashi labarin project dina da yadda na lura characters din sultan sun dace da project din nawa nace "to abinda yasa nake tare dashi kenan, idan ban jawoshi a jikina ba bazan iya studying dinsa yadda ya kamata ba. Amma da zarar na kammala aiki na a kansa zan yi masa kafa" naga kamar bayani na bai gamshe shiba na tashi na dauko laptop dina ba bude masa aikin da nake yi akan sultan ya karanta, sai a lokacin naga yayi ajjiyar zuciya yace "OK, but you have to be very careful, guy din is very dangerous" daga nan ya tafi ya barni ina tunani. Anya kuwa abinda nayi dai dai ne? Shi kanshi project din da nake rubutawa har yanzu ban gaya wa Sultan ina rubuta shi ba, gashi kuma nayi wa yayana karya akansa, Sultan ya sha gayamin cewa baya son secret. Amma in banyi haka ba menene a binyi. Kullum ina cikin feeling guilty saboda karyar da nake tayi ina boye boye. Dole in nemi mafita. Na yanke shawarar zan daina ganin sultan har sai na samu solution, time is running out. Bani da abinyi a school wannan week din dan haka nayi zamana gida naki fita, wayar duniyar nan sultan yayi min amma naki fitowa nace masa bana jin dadi, wani lokacin sai yayi kamar yayi fushi amma ana jimawa zai kara kirana. Ranar Friday sati guda kenan bamu hadu ba, muna palon mu ni da Amina muna kallo har after 12, daga nan na fara jin bacci nayi mata sallama zanjr in kwanta tunda yanzu mun raba daki ita tana spare dakin part din mu. Ina bude kofar dakina naji kamshin Sultan, nayi sauri na mayar da kofar na rufe ina wara ido, aikuwa ga mamakina shi dinne a tsaye a bakin window. Da sauri na na saka lock a jikin kofar na juyo na rasa ma me zance masa "Sultan how do you get in here" ya nuna min taga, nace "amma duk security din gidan nan ta ya akayi ka wuce get na farko dana biyu, ka zagayo baya, taya akayi ma kasan waccece window na" devilish smile yayi kafin yace "baki san waye Sultan ba har yanzu" lallai sultan ya wuce duk inda nake tunani, tsalle yayo daga inda yake ya fada kan gado na kamar wani karamin yaro, sai da katakon gadon ya amsa, ni maimunatu yau na shiga uku katon gardi akan gadona, yanzu idan mommy ta shigo gurina fa? Ko Amina? Ta yaya zan fara yi musu bayani? Na tabbatar in aka zo aka kama Sultan a dakina to babu wani bayani da zanyi wa daddy ya aura min shi kuma. Nace "Sultan dan Allah ka tafi, this is very dangerous wallahi, idan wani ya ganka fa?" Bai bani amsa ba sai jawo bargo na yayi yana shanshanawa yana wani lumshe ido "hmmmmm I so much miss kamshin ki wallahi" ikon Allah sai kallo, anya sultan kansa daya kuwa. Sai a lokacin na kalli kayan jikina, riga da wando ne na bacci, Allah ya soni dogaye ne sai dai linon ne masu bin jiki. Nayi sauri na dauki hijab din sallata dogo har kasa na saka na bata rai nace "Sultan ka fitar min a daki" ya mike shima ya hade rai ya zo sai tin fuskata yace "if not?" Na kara bata fuska nace "zan danna button din alarm mintu biyu yayi yawa security zasu cika dakin nan har daddy da mommy na" ya kawo fuskarsa dai dai tawa yace "then go ahead and do it" mamaki ne ya cika ni na saki baki ina kallonsa shi kuma ya tsare ni da ido, can yace "nasan ba zaki iya ba because you love me too" murmushin mugunta ya sake yi min sannan ya koma ya yi adungure akan gadona. Ya gyara kwaciya tare da bubbuga gadon yace "zo ki kwanta" na watsa masa harara, yayi dariya yace "I will not touch in abinda kike gudu kenan, ni kaina kishin kaina nake yi akan ki, I can't bring myself to touch you. Zuwa nayi in ganki kuma muyi hira. Me yasa kika ce min baki da lafiya bayan kuma lafiyar ki kalau" na tabe baki nace "in kana son muyi magana ka fitar min daga daki gobe sai mu hadu muyi magana" shima tabe bakin yayi yace "OK then, sai da safe" daga haka ya gyara kwanciya yaja bargo ya lulluba, da sauri na karasa bakin gadon "sultan ka tashi ka fita don Allah" rokonsa nake tayi amma kamar ba dashi nake ba dan ko motsi bai yi ba, idansa a rufe amma nasan bai yi bacci ba. Na tsaya kawai ina kallonsa. Ina bin kowanne feature na fuskarsa da kallo, ban taba kare masa kallo irin haka ba, naga yadda akayi trimming sajensa yayi kyau sosai da yadda sajen ya kwalta akan fatar sa daga dukkan alama zai yi laushi, ji nayi a raina kamar in kai hannu in taba, nayi sauri na mike tsaye na bar gurin na koma bakin kofa ina tunanin abinyi, inna ce zan koma palo in kwanta that means kofar dakin zata zama a bude kenan and I can't take that risk, wani zai iya shigowa yaga sultan, and I can't take the risk of sleeping with sultan saboda I don't trust him and I definitely don't trust myself akansa. Muryarsa naji yace "in kin gama lissafin ki kashe fitila saboda bana iya bacci da haske" wato idonsa biyu ma ashe. Kofar ban daki na bude na shiga ina lissafin ko anan zan kwana ne? Kai gaskiya bazan iya kwana a toilet ba, nayo alwala na fito, ina fitowa na tarar har ya kashe fitilar ya koma yayi kwanciyarsa. Na dauki pillow na koma can bakin kofa na ajiye. Windows din dakin na rufe nayi locking ta ciki sannan na karo karfin AC. Na dauko wani bargon naje inda pillow na yake na shimfida rabi sannan na kwanta na kudunduna ba hijab din jikina sannan na sake lulluba da sauran rabin bargon. Oh ni Maimunatu naga ta kaina, yau zan kwana da gardi a dakina. *wannan dai kam har da arias nayi muku, I love you guys so much. Stay blessed. * [11/7, 2:28 PM] maryamsuleiman48@gmail.co: MAIMOON By Maman Maama EpisodeFortyThree: America Na jima sam babu bacci a idona, yanzu mai zan ce wa daddy idan ya kamani da katoton namiji a dakina? Wato sultan shi bai san bari ba ko? Babu ruwan shi da what is right and what is wrong shi dai kawai in zuciyarsa ta raya masa yayi abu shikenan sai yayi kayansa babu ruwansa da consequences. Kunnuwa na baza ina sauraron ko zanji motsi, ko motsin Sultan ko motsin wani daga waje amma shiru banji komai ba, a haka har bacci barawo ya dauke ni. Dai dai sanda na saba tashi kafin assuba na farka, jikina duk sai ciwo yake yi sakamakon kwana a kasa da kuma takurewar da nayi a guri daya. Nayi mika ina addu'ar tashi daga bacci, Sultan ne ya fado min a raina nayi sauri na mike na kalli gadon. Babu shi babu alamunsa, babu alamun ma mutum ya kwana a gadon saboda gadon a gyare yake tsaf, to ko mafarki nayi ne? Kai ba mafarki bane tabbas Sultan ya shigo dakina jiya da daddare, na karasa gaban gadon sannan naka rose flower a ajjiye a saman wata farar takarda, na dauka na bude na karanta "na dade banyi bacci mai dadi irin na jiya ba, thanks for the night" da sauri na yayyaga takarda gaba na yana faduwa, yanzu idan wani ya karanta wannan ai sai yayi tunanin wani abu, lallai sultan, da ace bangani ba na tafi school mommy ko wani ya shigo ya ga wannan takardar kuma fa? Rose flower din na dauka na kai hancina na shanshana ina lumshe ido, kamshinta har cikin kwakwalwata da zuciya ta, na tafi da baya na fada akan gadon irin yadda yayi jiya, gadon naji gabaki daya kamshin sa yake yi. Sultan is special, he took a special place in my heart. Ina gama shiryawa na fita palo muka yi breakfast da duk family din. Ana yi ana hira amma ni kam hankali na har yanzu ba'a kwance yake ba ina tsoron ko wani yaga sanda Sultan ya hau window na ko kuma anga fitarsa, har muka gama breakfast shiru babu wata magana mai kama da wannan, sai a lokacin na fara sakewa ina dariya. Daddy yace "Moon supervisor din ki ya aiko min da takarda akan project dinki. Yace da akwai wani experiment da zaki yi amma sai kinje John Hopkins hospital ko?" Ni fargabar Sultan ma ta saka na manta da wannan maganar nace "eh daddy, dama ina son inyi maka maganar bansan ya za'ayi ba" mommy ta ajiye spoon din hannunta tace "john Hopkins? Wai kuna nufin America?" Nace "yes mommy" nan da nan mommy ta fara daukar zafi tana girgiza kanta "wanne irin experiment ne ba za kiyi shi a duk girman UK ba sai kinje USA? Wa kika sani a america ma tukunna? Gaskiya dear kayi magana a chanza mata wani experiment din, ai a ko ina ana substitute, gaskiya ni ban yarda kije America ba" daddy kawai kallonta yake yana murmushi ita kuma murmushin nasa ne yake kara kular da ita. Yace "babu abinda zai same ta in taje america, it will be an experience to her, kuma abinda na fahimta shine ba ita kadai bace suna da dan yawan su za'a tura daga makaranta, dan haka in sunje tare zasu yi komai su dawo tare. Shi asibitin John Hopkins shine number one a duniya a harkar neurology dan haka zuwanta can din yana da muhimmanci sosai" mommy dai har yanzu kai take girgizawa alamar bata gamsu ba, daddy ya kuma cewa "look, shi kansa director na pediatric neurology department na assibitin is a friend of mine, Benjamin Carson, kafin su tafi zanyi masa waya, in hada shi da ita, mutumin kirki ne sosai, shi da matarsa Candy, idan ba kya son ta zauna a cikin students sai taje gidansu ta zauna acan, na tabbatar zai kula da ita sosai. Mutum ne mai dimbin ilmi dan yana daga cikin top knowledgeable mutane na America" Ina bada shawarar duk wanda ya samu dama ya sayi littattafan Ben Carson, Gifted Hands da Think Big, akwai tarin ilmi sosai a cikin su. Nan dai daddy ya dauko wayarsa yayi wa Ben waya yayi masa bayanin zuwana da irin aikin da zamu yi ya kuma roki dan Allah ya sa idonsa a kaina. Da yake weekend ne shima Ben din yana gida sai bawa matarsa suka gaisa da mommy. Har suka gama wayar dai mommy bata saki fuskarta ba. Daddy yana fita ta saka ni a gaba da tambaya, tare da su wa zamuje? Kwana nawa zamuyi? Nace mata "6-8 weeks" nan ta kara tayar da hankalinta, nace mata "mommy ba gashi nan daddy yace a gidan uncle Ben zan zauna ba? Tunda shine shugaban gurin nan kinga tare zamu ke zuwa asibitin in mun gama abinda zamuyi mu dawo gida tare" mommy tace "Moon mutanen nan fa ba musulmai bane ba, in fact they are very devoted christians, bana son kije gidansu suna kira miki jesus da yesu, kuma duk gidan nasan sun rarrataya cross, malaikum rahama ba zasu shiga ba gashi kema kuma kina ciki" nace "to mommy in hankalinki bai kwanta ba ki barni kawai in zauna a lodge din da za'a bamu, a cikin quaters din asibitin ne, kuma kowa nashi daban ne, mom trust me" ta dan saki fuskar ta kadan sannan tayi tsaki tace "ni dai da zaku fasa tafiyar nan da sai hankali na yafi kwanciya" nayi ajjiyar zuciya a raina nace "nima da zamu fasa tafiyar da sai hankali na yafi kwanciya" tun sanda aka yi mana maganar tafiyar nake tunanin yadda zata kasance, akai na bani da matsala, problem dina Sultan ne, dole in gaya masa zancen tafiyar kuma I am 90% sure sai ya bini, and that's my problem, bana son ya bini, especially after ziyarar da ya kawo min jiya a cikin gidan mu ma kenan wanda yake cike da security ballantana in na tafi wata duniyar ba daddy ba mommy. Ban gaya wa sultan zancen tafiyar ba sai ana gobe zamu tafi, a tunanina ai in lokaci ya kure ba zai samu chance din bina ba, bawai inason rabuwa dashi bane a'a sam bana jin dadin yadda nake wa iyayena karya akansa sannan kuma har yanzu na kasa samun courage din zuwar musu da maganarsa. Tun da naje school muna tare dashi har aka zo daukana amma na kasa yi mishi maganar, sai bayan nazo gida nayi shirin kwanciya sannan na kira shi a waya, ya dauka da sallama kamar yadda ya saba, na amsa masa sannan yace "are you already missing me, love" nadan yi dariya sannan nace "magana nake so muyi, be serious please" yace "ina jinki" na dan sassauta murya nace "kana ji, dama wani dan course ne daga makaranta aka tura mu zamuyi a US, to gobe zamu tafi insha Allah, shine dama na ke so in gaya maka tun dazu a school kuma na kasa" shiru bai ce komai ba, na cigaba "Sultan dan Allah kar kayi fushi, ina taso in gaya maka wallahi tun tuni bansan yadda zaka dauki maganar ba, ba wani dadewa za muyi sosai ba, please say something" murya a duskure yace "for how long zaku kasance a can din?" Na yi shiru kalmomin sunyi min nauyi, sai da ya maimaita tambayarsa sannan nace "6-8weeks akace mana" nayi sauri na kara da cewa "amma ba lallai ne mu kai hakan ba, da mun gama zamu dawo" shiru bai ce komai ba amma ina jiyo numfashinsa ta wayar, sai da na gaji na kira sunansa "Sultan?" Yace "yaushe zaku tafi" nan ma amsar tawa ba mai dadi bace "gobe" ya maimaita "gobe?" Na daga kaina kamar yana kallona, "wato kina nufin dazu da muka rabu bye bye kika yi min kenan sai nan da wata biyu?" Na danyi dariyar yake nace "wata biyu ne fa kawai Sultan, kuma ai kullum zamu ke yin waya, kuma dana kammala wata biyun nan na gama project dina sai in rubuta report in yi submitting.... " kawai ji nayi ya katse wayar, na tsaya ina kallon wayar a hannuna, sultan dan rigima, text na rubuta masa da kalamai masu dadi cikin sigar bada hakuri na tura masa, shiru2 babu reply, lallai da gaske fishin yake yi, bamu taba fada da sultan ba, bai taba yin fushi dani ba, sai naji rai na duk babu dadi. Washe gari 12 jirgin mu zai tashi dan haka da wuri na tashi na kaya na da zan tafi dasu, bini2 sai in duba waya ta amma babu missed call babu message from sultan. Kudi sosai daddy ya bani kuma ya kira uncle Ben ya sake tuna masa yau ne fa zuwa na. Mommy har lokacin cewa take yi ita fa sam hankalinta bai kwanta da zancen tafiyar nan tawa ba, nima kuma haka, duk jina nake yi jiki a sanyaye ko dan ban taba yin tafiya mai nisa on my own ba. Gaba dayan su ne suka raka ni airport har mommy, har na shiga jirgi ina ta kiran Sultan amma yaki dagawa, duk sai naji kamar in fito ince na fasa tafiyar dan dai kawai babu yadda zanyi ne. Kira after kira nake ta jera wa Sultan kafin passengers su gama shigowa amma still no answer, na kashe wayar na jefa a jakata, hankali na duk ya tashi, anya kuwa nima zan iya jure wadannan satittikan ba tare da sultan ba? Especially in ya cigaba da kin daukan wayata. Muka sassaka seat belt din mu jirgi ya tashi, wani dan tsohon bature ne a kusa dani dan haka muna gaisawa na gyara kwanciyar kujera ta na saka earpiece ina jin karatu na lumshe ido na ina so inyi bacci ko Allah zai sa zuciya ta tayi sanyi. Nasan dole Sultan zai sakko dan kansa dan haka nayi alkawarin ko mun sauka bazan kira shi ba har sai ya kira ni da kansa. Jiki nane ya bani kamar ana kallona, to shi wannan tsohon menene nashi na kallon mutane kuma? Su turawa fa sam basu da kunya wallahi. Mayafi na naja na rufe fuskata ba tare da na dube ido na ba, ji nayi ansa hannu an bude fuskar tawa, da sauri na bude ido na zanyi bala'i amma se me? Sultan na gani zaune a kusa dani yana kunshe dariya "do you miss me, Love?" Na rasa dariya zanyi ko kuka, mamaki da takaici duk suka rufe ni shi kuwa dariya sosai ya ke yi, na dauki magazine din kusa dani na fara dukansa aka da ita, ya saka hannayensa ya kare yana cigaba da dariya, can dai na lura mutane da yawa a jirgin mu suke kallo, nayi sauri na ajiye magazine din hannauna na maze kamar bani ce nake yi ba. Sai da ya gama dariyarsa sannan ya juyo, "kin dauka fushi nayi ko?" Nayi banza na rabu dashi, ya cigaba da "ni na isa inyi fushi dake? Ai kin wuce wannan gurin. New York is not England. Bazan iya barinki ki tafi ke kadai ba, jiya bayan munyi waya na kira airport na tambayi wanne jirgin ne zai tafi America yau kuma karfe nawa zai tafi, sai kawai nayi booking na shirya kayana" nace masa "ya akayi ka samu visa daga jiya zuwa yau?" "Visa kuma? Legally ni dan America ne acan aka haife ni, i don't need a visa to go there" what a fool i have been, shaf na manta da wannan tsarin, na kasa tantancewa farin ciki nayi da zuwan Sultan ko bakin ciki. Earpiece dina guda daya ya cira ya saka a nasa kunnen shima ya kwantar da kujerar sa a haka muka yi bacci tare. Bamu farka ba sai da aka fara announcing jirgin mu zai sauka sannan muka tashi muka saka seatbelts din mu. Direct asibitin muka tafi, muna zuwa muka hadu da sauran students aka bamu keys din dakunan da zamu zauna sannan aka fara zagayawa damu za'a nuna mana duk inda muke bukatar sani, Sultan yazo ya ce in bashi key dina ba musu na mika masa ya tafi. Ina kallon yadda sauran students din suke kallona da alamar tambaya, a raina nace ina ruwanku? Mahdi ya dawo kusa dani yace "so..... I have seen you found your dark skinned man, Allah ya bar kauna" nasan magana yake gayamin dan haka na dauke kaina nace "amin" sai kuma yace "are you guys like living together kenan?" Na kalle shi ya hade rai nace "what do you mean?" Yace "naga ya biyo ki nan, kuma gashi har da wani karbar key din dakinki ya tafi zai shiga, ni dai a sani na ba'a gayyacemu daurin aure ba ballantana muce ai mijinki ne" na katse shi nace "dakata ya isa haka, kaya na ne da na zo dasu a cikin motar daya dauko mana shata daga airport, shima kuma da kayan sa a ciki, ya karbi key dina ne saboda ya sauke min kaya na ya tafi ya kai nasa masaukinsa. I don't even know me yasa nake maka bayani cos I owe no one an explanation" daga nan nayi gaba na barshi. Sai kuma naji a raina babu dadi saboda gaskiya ya fada min, sultan ba muharramina bane he have no business da shiga dakina. Bayan mun gama duk zagayen mu, a gajiye muka koma lodge din mu, one bedrooms ne a jere kowanne da number a jikinsa. Na duba nawa na tarar da a bude an dan saya kofar, a hankali na tura ne leka kaina ina sallama, babu amsa, na shiga ciki nace "sultan" nan ma shiru babu motsi, na sauke ajiyar zuciya sannan na kare wa dakin kallo, an gyara shi tas sai kamshin freshner yake yi, sabon bedsheet din da nazo dashi ne akan gadon tare da bargo, wato Sultan har kayana ya bincika ya dauko kenan ko? Shi sam baisan ma'anar boundary ba. Ya share dakin tas yayi mopping ya gyara gadon ya jera min kaya na a chest of drawers da suke dakin, ina dubawa naga har underwears ya saka su a drawer daban, kunyar duniya ta isheni yau Sultan yaga panties dina da braziers dina. Na duba toilet naga shima a gyare tas yana ta kamshi, sai a lokacin na lura har da karamin carpet ya siyo ya saka a gaban gadon. Tun ba yau ba nasan Sultan yana da tsafta sosai dan har mamakin tsaftar sa nake inna lura da irin yadda ya taso, koda yake ita tsafta a jinin mutum take, dan wani zakaga gidan su masu tsafta ne amma shi a kansa kazami ne. Komawa nayi nayi locking kofar, kayan jikina na chire na shiga wanka na tarar har kayan wanka na ya jera min a toilet din, na fito na shirya cikin riga buba na gyara gashina nayi packing a tsakiya kamar yadda nake yawan yi in ina gida, na fesa turaruka na sannan na saka hijab na fara ramuwar sallolin da ake bina. Ina idarwa naji anyi knocking nace "am coming" kafin in karasa kawai naga an bude kofa an shigo, na tsaya ina bin shi da kallon mamaki ganin key a hannunsa, wato spare key din dakin ya zare ya tafi dashi, as if dakin namu ne mu biyu, na hade rai sosai na rike kugu ina kallonsa, shi kuma yana murmushi, Allah yaso ma ban cire hijab din da nayi sallah dashi ba, "wannan bata ran kuma fa? Ni na kasa banbance yaushe kika fi kyau, in kin bata rai ko kuma in kina dariya" na kare daure fuska na ce "me yasa ka daukar min kex din dakina? Kasan hakan ai ba dai dai bane in kazo gurina sai ka kira ni a waya in fita in same ka ba wai ka shigo min daki ba" yi yayi kamar bada shi nake ba ya karaso dakin ya ajiye ledojin abincin da suke hannunsa sannan ya zauna a bakin gadk yana cewa "wash na gaji da yawa" na kara masa wata hararar nace "malam sauko min daga gadona, kuma ma waye ya baka damar ka bude min kaya? Kasan dai kayan mata sirri ne ko?" Ya sake share ni ya sauko yana bude ledar abincin da akayi sealing dinsa a cikin dan babban container, sai lemuka wanda ban taba ganin irin suba masu sanyi ya ajiye a gefe "malama in zaki zo muci abinci kizo, in kika tsaya iyayi kinsan ni bana wasa da abinci zan chinye ne in barki" daga haka yasa cokali ya fara cin abincinsa, ina kallonshi yana wani lankwasar da wuya yana lumshe ido nima naji yawuna ya tsinke kuma dama yunwa nake ji da gaske, a hankali na tafi kamar wadda ake jana da magnet naje na zauna na dauki cokali na fara ci dadin abincin yana ratsani, sai da muka kusa cin rabin abincin babu wanda yace wa kowa komai, can dai naji babu dadi tunda ni ban iya shiru ba nace "thank you for.... " na nuna dakin da hannuna, ya ajiye spoon din hannunsa yace "you are welcome" na ce "a ina zaka sauka ne kai?" Yana murmushi ya nuna kan gadon, na harare shi yayi dariya yace "relax 'yammata, garin mu fa kika zo, i have a house here duk da dai yanzu da akwai wadansu friends dina a ciki amma acan zan sauka" na gyada kaina alamar gamsuwa, a haka muka gama cin abincin mu yana ta yi min hida, nayi mamakin yawan abincin da naci, da zan sja drink din sai da na duba ingredients dinsa, ina kallon sultan yana yi min dariya na harare shi kawai bance komai ba. Yana gama wa "nace to atashi kuma asan nayi, sai da safe" ya mike yace "ba sai kin kore ni ba nima dama baccin nake ji" har ya kai bakin kofa nace "bani spare key dina" ya jiyo yace "na karfi ne, in kina da karfi ki kwata" I don't know why inna fara typing bana son tsayawa sai daga baya in ga ashe nayi da yawa. Ya kamata mu koma yi kadan kadan ko? [11/7, 2:28 PM] maryamsuleiman48@gmail.co: MAIMOON By Maman Maama Episode forty four : America 2 Yana gama fadin haka ya ficewarsa ya barni. Naje nayi locking kofar amma a raina ina cewa wannan ai bonono ne rufe kofa da barawo. Na dawo na kyara inda muka ci abinci sannan nayi shirin kwanciya, ranar sam na kasa bacci saboda rashin sabo da sabon gurin, kawai na tashi nayi alwala na yita salloli ina rokon Allah ya bani karfin zuciyar da zan iya controlling Sultan shi kuma Allah ya shirya min shi, na tuno da maganar Amira da tace am too soft and Sultan is too hard, in dai har ina so in gyara masa rayuwarsa dole nima in zama hard amma how? I have been soft tunda nazo duniya how can I be hard kuma yanzu?. Washegari muka fara aikin da ya kawo mu tukuru, aikin shine koyon yadda ake raba twins din da aka haifa a hade ta ka, yadda kowanne daga cikin su zai rayu. Kullum wuni muke yi a lab sai yamma likis sannan zamu dawo, kuma kullum muna dawowa zan tarar da abinci Sultan ya ajiye min, wani lokacin ma har da ruwan zafin wanka, sai yanzu na fahimci dalilin da yasa ya dauki spare key dina kuma inajin dadin yadda yake kula dani sosai, saboda badan shiba gaskiya zaman zai yi min wahala sosai, fita siyan abinci kawai sai ya isheni. Wani abin mamakin shine duk da cewa ni kadai nake zaune yanzu amma Sultan har yau bai taba kai hannunsa jikina ba, ko wani abu zai bani baya barin hannayen mu su hadu, na jinjina masa ta nan gurin sosai dan ba ko wanne namiji ne zai iya haka ba, wani lokacin har tunani nake "to ko he is not attracted to me?" Amma kuma in na kalli idonsa ina gani a ciki, wani lokaci har bana son hada ido dashi saboda irin abubuwan da nake karantowa a ciki, abinka da psychologist, lol. Watan mu daya a America wani aiki ya taso wa Sultan wanda ba zai iya yi tanan ba sai lallai yaje Nigeria, ji nayi kamar zanyi kuka har sai da ya gane yace to ya fasa tafiyar sannan na hakura. Kafin ya tafi sai da ya bada order a restaurant din da yake siyo mana abinci cewa kullum zasu ringa kawomin safe, rana, dare babu fashi. Yana tafiya muka dinke a waya, kudin da Sultan ya kashe a saka credit daga tafiyarsa zuwa dawowarsa Allah ne kadai yasan yawan su, koda yaushe muna tare a waya sai dai in zanyi waya da 'yan gida ince masa ya kashe kuma shima ana jimawa zai sake kira. Satinsa biyu acan ya dawo amma ji nayi kamar yayi wata biyu. Yana dawowa ya shiga lodo min siyayya yana ajiye min wai tsarabar da zan kaiwa 'yan gidan mu, nace "Sultan wannan uban kayan ya zanyi in tafi dasu?" Yace "shipping dinsu zanyi miki ai" na sake cewa "to yanzu in naje dasu gida ince da mommy a ina na samu kudin saye?" Na danyi tunani kadan sannan yace "tell her you won the lottery or something" kawai na saki baki ina kallonsa, shi a ganinsa wannan is a total excuse, shi bai saba in yayi abu a tuhume shi ba dan haka bashi da idea yadda za'a yi wa iyaye karya. Haka yayi ta lodo kaya yana jibgewa. Sati daya ya rage mana mu dawo England, duk ayyuka sun yi mana sauki dan kusan zan iya cewa mun kammala, ana koya mana ne yadda za'a kula da twins din ana monitoring dinsu har su warware. Sai lokacin sultan ya samu damar fita dani yawon ganin gari, ai kuwa nasha gararamba lungu da sako na New York sai da ya shiga dani. A lokacin ne ya kaini gidan sa ya nuna min. Tun sanda yace min can zamu je na kudurta a raina cewa bazan shiga ba, muna zuwa yayi packing ya zagayo ya bude min kofa naki fitowa, ya tsaya yana kallona "ko sai na fito dake ne?" Nace "no kawai dai bazan shiga bane" in yayi mamaki ma ya boye bai nuna min ba yace "ohh really? Duk zirga2 da nake yi gurinki ke ko shiga ki saka min albarka a gida na baza kiyi ba? Thanks a lot" wani barin na zuciyata yace min, he is trying to control you, don't give in, na daga kafada nace "sorry, kawai dai naga kamar shiga gidan ka is way ahead of limit" shima kafadar ya daga yace "if you think so, amma matsalata guda daya ce, what I plan is in munzo nan zan barki anan zanje wani guri in karbo sako a gurin wani wanda gobe zai bar gari gobe kuma gurin da zamu hadu is no place for a lady especially lady din da ba zata iya shiga gidan fiancé dinta ba" na daga masa hannu nace "technically kai ba fiancé na bane yet" yayi murmushi tare da jingina da jikin motar yace "OK, yanzu ya kike so ayi?" Na kalleshi ya langwabar da kai side daya, na dauke kai a zuciyata ina cewa, don't fall for that, ya sake zagayo wa ta side din dana mayar da fuskata yace "na rasa me yasa har yanzu kin ki trusting dina, if I want something da tuni na karba, you are too precious for that, I just want you to see my house, nan shine inda na zauna for thirteen years, tun ina twelve years nake rayuwa a gidannan har na kai twenty five years" ba fito daga motar ina karewa gidan kallo, madaidaici ne, sama da kasa, da veranda a kofar gidan, gaba daya gidan a kewaye yake da flowers masu kyau. A hankali na tambayeshi "amma kai kadai ka zauna a gidan tun farkon zuwanka? Ina nufin girki da kula da gida" ya daga kafada yace "farkon zuwan mu akwai house help da driver da suke zuwa kullum, daga baya muka kore su muke kayan mu da kanmu, fifteen years na fara driving, Amir ya iya girku sosai, so we managed" na runtse ido na ina jin zafi a raina, sultan tun yana karamin yaro yake zaman kansa kuma a lalatacciyar kasa kamar America. Sultan ne ya dawo dani daga tunani na yace "look in baki yarda dani ba ga key ki bude ki shiga ki rufe kanki, just look around in na dawo sai mu tafi" ba kalleshi da tuhuma nace "how do I know baka da spare key?" Dariya yayi sosai yace "Wallahi bani da spare key, kinji na rantse miki dai" na karbi key din ina kunkuni na matsa baya, ya rufe kofar ya zagaya seat din driver ya shiga ya kunna motar yace "in kin shiga sama zaki hau, kasan anan friend dina yake zama, amma nace masa zamuzo dan haka ya fita" na gyada masa kai sai kuma ya tsaya yana kallona, na daga masa kafada alamar what? Yace "this is New York not Abuja, ki shiga ciki kiyi locking kofar sannan sai in tafi" Na turo baki na juya ina kallonsa yana yi min dariya har na shige cikin gidan na rufe kofa sannan ya tayar da motar ya tafi. Kallo daya na yiwa palon kasa na hau sama. Ina shiga wani katon hoton Sultan ba gani hannunsa rike da guitar fuskarsa da murmushi, akwai yarinta sosai a fuskarsa, na karasa gaban hoton ina kallonsa, na daga hannu a hankali na shafa fuskarsa ina jin wani sabon sonsa a raina, na shiga uku ni Maimunatu ya zanyi duk sanda aka raba ni da Sultan? Ba wani tarkace a palon amma kamar yadda nayi tsammani tas yake ko digon datti babu a ciki, na cigaba da kallon pictures din jikin bango, duk yawancin su shi da Amir ne, wani suna yara wani sun dan girma, gaskiya Allah ne kadai yasan shakuwar da take tsakanin Sultan da Amir. Wanj hoto ne ya dauki hankali na, Sultan ne da school uniform ana bashi gift a makaranta, gashin kansa a hargitse kamar wanda ya dawo daga filin dambe. So you are brilliant also. Na shiga bedroom dinsa naga gado ne kawai sai sif din kayan sa, na bude sif din a raina ina cewa kaima ai bude min kayana kake yi. Anan na saku baki ina kallo, sets din kaya ne sunfi karfin a kirgasu, a jere neatly, takalma, undies, p-caps abin ba'a magana. A raina nace dan gayu. Na koma kitchen naga babu kayan abinci amma akwai kayan electronics iri iri. Gaba na ne ya fadi da naga fridge, ko zan ga giya a ciki, a hankali na bude fridge din kamar mai taba wuta, na duba kaf banga alcoholic drink ba, na sauke ajjiyar zuciya na dauko orange juice na dawo palo na zauna ina sha. Kamar daga sama naji ance "hello" a tsorace na juya saboda nasan nayi lucking kofa, wani black American na gani kansa ya sha kitso kamar wata budurwa a tsaye a bakin kofar palon. Na mike tsaye a tsorace ina kallonsa. Sosai naga shima ya tsorata yace da American English "Sorry, na dauka kun tafi shi yasa na dawo kuma banga mota ba sai kuma naga sama a bude, na dauka ya manta bai yi locking bane. Am so sorry, please karki fada masa" ajjiyar zuciya na sauke nace masa "babu komai" har ya juya zai tafi sai kawai wani tunani ya fado min a raina, this is my chance to know more about sultan. Da sauri nace masa "wait, at least tun da ka shigo ai ya kamata mu gaisa ko?" Da fara'ar sa ya dawo amma yana dan rarraba ido, daga dukkan alama Sultan ya kora masa warning akan zuwana. Na nuna masa kujera ya zauna nace "my name is Maimoon" yace "I know, sultan talk about nothing else" ya miko min hannunsa yace "I am Steve " nayi ignoring hannun daya miko min nace "so how long do you know Sultan?" Yace "as long as I can remember" na gyada kai nace "to yanzu misali in aka tambaye ka is he good, bad or in between me zaka ce " mamaki ne ya bayyana a fuskarsa yace "Sultan is more than good, he is the best person dana sani a rayuwata, duk wanda ya gaya miki wani abu bayan wannan karya yake yi. Ba dan Sultan va da yanzu ina cikin hoods ina trading drugs, he saw me through sec sch and college, bani kadai ba muna da yawa wadanda sultan ne uban mu a garin nan, cinmu, shan mu, suturar mu duk Sultan ne. Da akwai sanda za'a aiko masa da kudin makaranta daga gida sai ya dauka ya biya mana kudin makarantar mu sai ya aika gida yace kudin sun bata ko sun kare, muna kallo daddynsa zai aiko har gida azo a kama shi a rufe a cell, wani lokacin sai yayi sati sannan a fito dashi. Saboda Sultan ya ciyar damu ya koyi playing guitar, zai dauka ya tafi market square yayi playing ana bashi kudi in ya tara yazo ya siyo mana kayan abinci. Daga baya ya koyi art, sai yaje ya zana mutum ya biya shi kudi yazo ya raba wa mabukata. He once told me saboda orphans yake karatu, duk kudin da zai samu akansu zai karar, in dai yana da rai babu dan da zai yi kukan rashin gata" hawaye naji yana kokarin tahomin nayi sauri na mayar dashi, nace "naji ance kuma yana yin drugs da alcohol" ya bata rai sosai yace "drugs? No, not Sultan, he hates drugs, ko bashi da lafiya sai anyi da gaske yake shan kwaya ballantana haka kawai" na gyada kaina nace "alcohol?" Ya dauke idon sa daga nawa ya kalli gefe, he then shifted from one leg to another, as a psychologist, tin kafin yayi magana nasan amsar da zai bayar, a hankali yace "sometimes, but only when he is frustrated" nayi shiru na kasa yi masa wata tambayar kuma, ya cigaba da magana "he has a bad temper you know, yana da zuciya sosai, wani lokacin in ransa ya baci gaba dayan mu sai jikin mu ya gaya mana, it is his way of releasing his temper, baya harkar mata sam dan babu wanda zai ce ya taba ganin budurwar Sultan duk kuwa da 'yammatan da suke binsa kamar jela cos he is handsome you know and girl fall for his kind but baya kula su" ni dai kawai sauraronsa nake yi ina saving duk maganganunsa a kaina. Nan ya zauna yake ta zuba min labarai na rayuwar Sultan a America, wani inyi dariya wani kuma inji kamar zanyi hawaye. Muna haka mukaji tsayuwar mota, ya tsorata sosai ya mike yana leka window, dariya sosai abin ya bani, wato they respect and fear him at the same time. Nace masa "relax, ba shigowa zai yi ba" ya kalle ni yace "why? shida gidansa?" Nace "nice nace karya shigo" ina kallon sultan ya dauko wayarsa ya kira ni yace in fito mu tafi. Daga gidan bamu koma John Hopkins ba park ya kaini, muka zauna akan bench muka sha ice cream, anan nake tambayarsa "dama kana playing guitar baka taba min naji ba?" Ya danyi murmushi yace "kinga pictures dina kenan. Yes, ina playing guitar da, amma tunda na koma Nigeria na daina, one day zan yi miki kiji" sai gab da magrib sannan ya mayar dani, muna tsayawa yace 'akwai inda nake so in kaiki in an jima please, ki shirya zan zo around 8pm" serious tone din da yayi maganar dashi ne ya saka ni ban masa musu ba. 8 pm dai dai yazo ya kira ni a waya yace in fito, nayi shigar doguwa riga budaddiya, nayi rolling babban veil daya rufe min jikina sosai. Tunda na fito ya dora idonsa a kaina tamkar ba dazu muka rabu ba, nazo gabansa na tsaya nayi gyaran murya "kallon ya ishe ka haka malam" with seriousness yace "hace I ever told you you are beautiful?" Na juya idona nace "only a million times" yace "to bara in kara daya akai, you are very beautiful" yadda yake kallona yasa na rufe fuskata da hannuna nace "thank you" sai da muka yi tafiya ta kusan 30minutes duk da dai ba gudu yake ba, Sultan naturally baya gudu a mota, sannan muka zo inda zamuje. Kallo daya nayi wa gurin na fahimci ina ne, Club, na juyo na kalleshi da bacin rai nace "am not going in there" yace "ba wai na kawo ki nan gurin bane saboda naga kin dace da gurin, na kawo ki ne saboda ina son in nuna miki wani abu kuma inaso in gaya miki wata magana, na kawo ki nan ne saboda ina ganin in kika gani da idonki zaki fi gane manufata" ni dai kawai jinsa nake dan ni banga me zan gani ko ji a club ba amma yadda naga alamar babu wasa a fuskarsa ya saka na fita na bishi. Muna zuwa kofar gurin naga masu gadi sun fara gaishe shi, da sauri suka bude mana kofa, ana budewa naji wata hayaniya da karar kida da warin sigari, ga fitilu masu kala suna kawowa da daukewa. Tsoro ne ya shiga zuciya ta, na shiga uku ni Maimunatu yau ina na kawo kaina? Amma curiosity ya hana ni komawa da baya. Banyi tsammani ba kawai naji hannun sultan a jiki na, abinda bai taba aikawata ba, nayi sauri na ture shi ya sake kamoni yace "stay still, a guri irin wannan someone will just grab a beauty like you daga nan kuma babu babu wanda zai sake jin labarinki" bansan sanda na makalkale hannunsa ba, ina jinsa yana mun dariya ni dai ban kula shi ba, a raina ina cewa kai da kasan haka gurin yake ka kawoni? Wani mutun da nake tunanin ogan gurin ne yazo yana gaishe da sultan kamar zai cinyeshi, daga nan ya buda mana hanya muka bi ta cikin mutanen da kyar muka wuce har muka wuce stage muka zo wani gurin da babu mutane sosai, sai a lokacin na saki hannun Sultan, ya kalleni yana dariya na harare shi. Daga ganin gurin VIP section ne dan kujeru ne masu kyau a gurin, na samu kujera na zauna Sultan ya jawo kujerar kusa dani ya zauna shima, nan take aka cika gabanmu da kwalabe, kallo daya nayi musu na gane menene, na kalli Sultan da alamar tuhuma sai a lokacin ya lura da abinda aka kawo, da sauri yayi wa attendant din daya kawo magana da wani yare da ban gane ba, kafin minti daya an kwashe su an kawo wadansu, still nace ba zan shaba. Nace "sultan what are we doing here?" Ya sake matsowa ya saka idonsa a cikin nawa ya fara magana "Maimoon na kawo ki nan ne saboda ina so inyi miki bayani akan abinda kike ta yi min magana akai. Change. This place is where I practically grew up, kullum for over ten years anan nake raba dare, this people are my family, su kadai na sani a rayuwata" yana magana yana nuna cikin chunkoson mutanen club din, nima na bisu da kallo, irin mutanen da ake kira da ghettos, niggas da babu abinda suka sani sai shaye2, clubbing da crime. Wannan ita ce rayuwar da Sultan ya kasance a ciki for 15 years, it is a miracle ma that he is what he is. Na juyo da idona kansa ya gyafa min kai ya cigaba "farkon zuwana America daga ni sai Amir ne kawai, bamu san kowa ba, sai daga baya muka fara friends, a lokacin na lura kusan 50% na Africans da suke zaune a america basu da muhalli, basu da gata ga kuma tsananin talauci, rana daya na kori driver na na kori house maid dina na debo mutun goma na kawo gidana, daga nan supplies suka fara yi mana kadan saboda kudin da ake aiko mana dashi kawai nawa ne ni da amir, nan muka fara shiga trouble na kudi dan haka dole na fara improvising, ina playing guitar ina kuma making drawings for money, lokacin ban wuce 15 years ba. Kin san duk inda aka tara mutane irin wadannan to dole akwai matsala, my house was always in chaos but I held on, I felt like they are my responsibilities, lokuta da yawa one of them will get in trouble with the police sai in fito ince ni ne, cos nasan babana zai aiko ayi bail dina amma su in sun shiga sun shiga kenan" na gyada kaina murya can kasa nace "I know" yace "what?" Nan na bashi labarin haduwata da Steve a gidansa da duk labaran da ya bani, bai ce komai ba kawai ya sunkuyar da kansa, na cigaba da cewa "I also know about the orphanages" mamaki ne karara ya baiyana a fuskarsa yace "who told you that" nan na bashi labarin haduwa ta da wannan mutumin ranar dana fara shiga motar sa, na tambayeshi " amma me yasa baka son mutane su san cewa kai ka gina?" Ya shafa kansa yace "saboda badan mutane nayi ba, na dora wa kaina alhakin kula da duk wasu yaran da basu da galihu as long as I am alive kuma abinda nake archiving kenan with the orphanage, in dai har yaran sun samu muhalli, abinci, sutura, ilimi da kuma little bit of love, shikenan abinda nake bukata not people's praises" na bude baki zanyi magana yace "damn it, wannan ba shine abinda ya kawo mu nan ba, na kawo ki nan ne saboda ina so in gaya miki cewa I want to change, I want to be the person you want me to be but it will take time, i can't just change overnight, it is not possible, amma nayi miki alkawarin I will always give you my best, amma ina so kema kiyi mini wani alkawari" ya kamo hannayena duk biyun ya rike a cikin nasa, na kalli fuskarsa ina son in karanta idonsa amma emotions din da na gani sunyi yawa, yace "promise me that you will never let go of me, no matter what" hawayen da bansan sanda na fara su ba naji suna bin kunchi na, anya zan iya yi maka wannan alkawarin Sultan? A hankali nace "I promise I will also give you my best" murmushi yayi yace "thank you" sai kuma yace "I have a little something for you" ya saka hannu a aljihu ya dauko wani dan karamin box ya bude, zobe ne a jiki na diamond, a samansa anyi shape din moon, na bude baki kawai ina kallonsa, ya kamo left hand dina ya saka min a ring finger dina, sai kuma kawai ya tsaya yana kallon finger din, nima na kalla naga zoben yayi min kyau sosai kamar an gwada kafin ayi shi. Ya dago kansa yana wata dariya mai kama da sheshshekar kuka, ni ma dariyar nake yi, yace "yayi miki kyau sosai, ashe na fadi size dai dai" na karbe hannuna ganin bashi da niyyar cikawa. Mutumin daya shigo damu gurin ne naga ya zo gurin mu da wata katuwar guitar a hannunsa ya mika wa Sultan yana masa magana excitedly da wani yare, ya karba yana dariya yace min "wai sun yi missing kida na, suna so inyi musu" da sauri nace masa "nima ina so" ya jima yana kallona sannan yace "then I will play for you" daga haka ya mike tsaye, nan take naga an zagaye gurin kowa na nutsu. Daga ganin yadda ya rataya guitar kasan gwani ne. Idansa cikin nawa ya fara playing guitar yana kuma waka a hankali. What will I do without your smart mouth. Drawing Me in and You kicking Me out. You got my head spinning, no kidding I can't pin down. What's going on in that beautiful mind, Am on your magical mystery ride, And am so dizzy, don't know what hit me, but I will be alright. My head is under water but am breathing fine. You're beautiful and am out of my mind. Cos all of me, loves all of you. Love your curves and all your edges, All your perfect imperfections, Give your all to me, I will give my all to you. You're my end and my beginning, Even when I loose am winning, I will give you all of me, and you will give me all of you, of you Our cards are on the table and we are both showing hearts, Risking it although it is hard. Cos all of me loves all of you.............. How many times do I have to tell you, Even when you are frowning you are beautiful too, Even if the world keeps beating you down I will be around through every mood. You're my downfall, you're my muse, my worse distraction, my rhythm and blue, Can't stop singing it is ringing in my head for you..... Cos all of Me loves all You. [11/7, 2:29 PM] maryamsuleiman48@gmail.co: MAIMOON By Maman Maama Episode Forty Five : The Rush Sai around 11pm muka bar club din, muna tafiya a hankali kamar yadda ya saba, ya tambaye ni "so, anything you want to ask me?" Na danyi shiru for some seconds sannan nace "why do you join the gang bang?" Sai da yayi dariya sannan yace "ke baki ji yadda sunan yake ba? It sounds dangerous, duk wanda aka ce dan wani gang ne mutane zasu ke tsoronsa, tsoro kuma yana kara wa mutum kwarjini, irin bad boy dinnan" nayi dariya nima nace "kai kuma burinka shine mutane suce maka bad boy right?" Yayi shiru bai ce komai ba, sai ya chanza maganar yace "waye ya baki labarin gang bang?" Nace "Amira, she told me about the rape case" ga mamaki na sai naga yana dariya, yace "dama wannan Amirar daga ganinta zatayi surutu da tsegumi" na hade rai nace "ba abin dariya bane ba ai, how can you get involved with those kind of people? Duk wandanda zasu hadu suyi raping yarinya karama kamata yayi ka nisanta kanka dasu ba wai ka kirasu friends ba" ya daina dariyar yace "no body raped anybody fa, it is all politics. Shi yaron da akayi case din akansa Daniel, lokacin babansa yana takarar governor a Nassarawa. Yarinyar da ake magana akanta tsohuwar budurwarsa ce fa, dama sun saba harkarsu kuma she is not a girl dan banbancinta da karuwa kawai dan ita a gaban iyayenta take, she knows duk sunayen friends din Daniel, lucky for me bata san ni ba, kawai rana daya aka zo aka bawa iyayenta kudi da ita kudi suka ce wai Daniel da friends dinsa sun zo har gida sunyi raping dinta" na katse shi nace "maybe kai a yadda kaji labarin kenan, mutane irin su fa babu abinda basa iya aikatawa" shima ya katse ni yace "OK, she mentioned Amir's name, kuma ranar da tace abin ya faru tare muka wuni muka kwana da Amir, sai dai in a cikin bacci yayi raping din nata. Abubuwa da yawa yadda ake bada labarin su ba haka suke ba, kawai ke dai believe what you see, duk wani abinda wani ya gaya miki kar kiyi believing" Sai da yayi packing sannan na lura how late it is, few minutes to one, ni da a gida nake na isa in kai karfe goma ma a waje? Sai kawai naji guilty feeling. Ya zagayo ya bude min kofa na fito muka yi sallama sannan ya koma mota amma yaki tafiya, nasan sai yaga na shiga gida zai tafi dan haka na tafi na fara kokarin bude kofa, ji nayi kamar ana kallona, na waiga baya da sauri sai naga Mahdi can nesa damu a gurin flowers, duk da cewa gurin da akwai duhu amma hasken fatarsa ya tona masa asiri. Ban nuna na ganshi ba saboda Sultan will not take it lightly, na bude kofa na shiga nayi waving at Sultan sannan na rufe. Da jikin kofar na jingina zuciya ta tana bugawa, is Mahdi stalking me? Mahdi yasan daddy na kuma yana sona dan haka yana kishin mu'amala ta da Sultan, nasan babu abinda zai hana shi zuwa ya bawa daddy labarin Sultan. Menene abinyi yanzu? To ko zuwa zanyi in same shi muyi magana ta fuskantar juna? Zuciya ta naji duk babu dadi, na mike na shiga toilet nayi wanka nayi alwala, nazo nayi shirin kwanciya, ina kwanciya na fara lissafin abubuwan da suka fari yau ina rewinding dinsu daya bayan daya ina kara fahimta, yau na sake fahimtar abubuwa da yawa akan sultan, kuma naji dadin mafi yawa daga abubuwan dana fahimta. Na dago hannuna daya saka min ring ina kalla. Wani nishadi naji yana shigata, kawai na fara murmushi ni kadai like an idiot. Kwanci tashi har muka kammala duk abubuwan da suka kawo mu America muka fara shirye2n komawa England. Ana gobe zamu tafi Sultan ya kuma dauka na yawo, wannan karan cewa yayi zai nuna min abubuwan da yake yi for fun sanda yana America. Farko race track muka je kallon car race. Daga nan muka tafi bayan gari wajen wani ranch yace mu hau dokuna, ni kam ban iya hawa ba dan haka sai na dauko camera nake yi masa video. Sosai ya burgeni yadda ya iya sukuwa a doki danni har tsoro yake bani dan gani nake kamar zai fado, shi kuwa kamar wadda nake kara zuga shi har mike wa tsaye yake yi, yadda iska take diban gashin dokin tana wasa dashi haka take diban na Sultan shi ma. A mota ma bayan mun bar gurin videon na cigaba da yi masa yana ta tsokana ta wai ni matsoraciya ce nace na yarda din. Daga nan yace "I want to show you one last thing kafin in mayar dake gida" tafiya muka sake yi mai nisa sannan muka zo gurin wasu duwatsu, sam babu mutane a gurin, muka fara hawa wani dutse mai tsaho dan ni kam da kyar na kai duk na gaji. Muna zuwa na kunna camera ta na cigaba da video, ya nuna min gurin da zan tsaya shi kuma ya koma baya, sai da yayi kusan rabin dutsen sannan ya kwallo min magana yace "get ready" ni dai bansan me zai yi ba kuma, nayi zooming dinsa ta camerar naga ya cire shirt din jikinsa ya bar singlet kadai, ya durkusa kamar me shirin gudu, kar dai Sultan yace min da gudu zai hawo dutsen nan, ina kallon fuskarsa yayi taking deep breaths sannan ya fara hawowa a guje, wow , shine kadai abinda na iya fada, na saki baki ina kallonsa ta screen din camerar, dukkan jikinsa a mummurde yake musamman yanzu da ya cire rigarsa, yadda muscles dinsa suke rippling ne ya saka nayi sauri na runtse idona, I shouldn't be looking at this kamar yadda I shouldn't be doing abubuwa da yawa da nake yi. Iskar gudunsa kawai naji tazo ta wuce ni sannan na bude ido na naga ya doshi clip din dutsen kuma bashi da niyyar tsayawa, yana zuwa karshe naga ya doka tsalle ya fada. Zuciya ta ce naji kamar ta fado kasa, a rikice na yadda camerar hannuna na tafi inda ya fada da gudu ina kiran sunan sa. Ina zuwa karshen dutsen na leka kasa tare da durkutsewa a gurin. Sultan na hango a cikin ruwa yana kyalkyala min dariya. Ashe ruwa ne a gurin ni dai har lokacin kirjina bai daina bugawa ba. Ina kallonsa ya fito daga ruwan yana yi min magana amma bana jin me yake cewa saboda nisan gurin. Har ya zagayo ya kuma hawowa kan dutsen ina zaune a gurin, naga ya chanja kaya daga alama dama ya taho da wadansu a mota. Yana zuwa na mike tsaye nace masa "don't ever do that again" na wuce nayi tafiya ta na barshi. Shi sam bai damu da rayuwarsa ba. Har muka koma gida ina fushi akan tsoron daya bani, ranar da wuri muka koma saboda in karasa shirin tafiya gobe, already an sallame mu, wadansu ma sun tafi tun yau amma mu jirgin gobe Sultan yayi mana booking, nayi waya da 'yan gida na gaya musu gobe zan dawo. Tun dare na gama hada kayana kaf, sai wadanda zan saka goben na bari a waje. Sai da na gama shiryawa kaf sannan naci abinci nayi shirin kwanciya na kwanta. Ina kwanciya na dauko camera ta ina kallon pictures da videos din dana yi mana ni da Sultan ina ta murmushi. Text dinsa ne ya shigo waya ta, na dauka na karanta " I want you to know that these past few days are the happiest days of my life " nayi replying "me too" Har bacci ya fara daukata na tuna bansan time din da jirgin mu zai tashi ba, na kira Sultan wanda naji kamar cikin bacci yake magana yace min 10am. Da assuba na tashi nayi sallah naga babu abinda zanyi tunda na kammala duk shiri na dan haka na saka alarm 8:30am nasan one hour ta ishe ni in shirya, kafin 30min kuma munje airport. Dan haka na koma baccina. Kamar cikin bacci naji waya ta tana ringing da tone din Sultan, na duba agogo naga 7am, ne wannan mutumin yake so kuma? Zai hanani bacci kuma a jirgi ma ba lallai ne ya barni inyi baccin ba. Na juya na cigaba da bacci na. Waya ta ce ta sake ringing, Sultan again, na danyi karamin tsaki ba dauka. Da sauri yake magana "kiyi sauri ki shirya, jiya nayi mistake flight din mu ba 10 bane 8 ne" ai ban karasa jin maganar ba naji baccin ya wartsake, na mike da sauri ina kallon dakin dan in tabbatar ban manta komai ba, na cire kayana da sauri na daura bath robe na shiga toilet. Cikin shower na shiga na sakar wa kaina ruwa, sai a lokacin na fahimci har yanzu jikina ciwo yake saboda hawan dutsen da muka yi jiya. Na jima ina jin dadin zubar ruwan a jikina sannan na tuna cewa sauri fa nake yi, na kashe shower da dauko shower gel na fara shafawa a jikina har na hada kumfa a jikina. Sultan Bayan yayi sallar asuba yaji sam ya kasa bacci, yayi ta juyi yana ta lissafe2, ji yake kamar kar su koma England, duk da acan ma yana ganinta amma ba kamar nan ba, lokaci yayi daya kamata suyi taking next step a relationship dinsu, he is ready, amma ita har yanzu yaga kamar tana tsoro kuma baiyi blaming dinta ba, her family is a very decent family shi kuma he is what he is. Ya mike tsaye yana karasa hada kayansa, akan bed side ya ga flight tickets dinsu ya dauka yana dubawa "shit" 8am ya gani "shit" ya akayi yayi wannan mistake din? Yanzu yasan da wahala su samu flight din nan tunda sai yaje ya dauko ta sannan su tafi airport. Ya dauko wayarsa ya yi dialing number dinta, no answer, damn it yanzu haka ma bacci ta ke yi, ya duba agogo, 7:05, ya sake kiranta sai da ta kusa katsewa sannan ta dauka, da sauri ya fara mata bayani ta amsa in alarm ta kashe wayar, good at least yasan zata shirya kafin ya karaso, da sauri shima ya shirya ya dauki jakarsa ya fita yana waya da Steve. Gudu yayi ta tsalawa a mota yana ta addu'ar Allah yasa ta gama shiryawa. 7:30 yayi packing ya dau waya yana kiranta, ni answer, Good Lord, yarinyar nan ina ta shiga ne? Ya fita da sauri ya bude apartment din nata ya shiga, babu kowa a dakin sai jakarta a ajjiye, babu motsi a toilet, to ko ta fita waje ne? Har ya yi hanyar fita sai kuma ya dawo ya kama handle din toilet yaji shi a bude, on impulse, kawai ya tura kofar ya bude, a lokacin ne ya ganta, and his world froze. Moon Sai da na tabbatar na gama hada kumfa a jikina sannan na kai hannuna zan kunna shower, a lokacin naji kamar motsi a dakin, kar dai ace har Sultan yazo, gaba na ne ya fadi da na tuna a bude nabar kofar toilet din, wani side na zuciya ta yace min ya za ayi ya neme ki a toilet? Ina murda shower din naji karar bude kofa, a razane na juyo, a take idona ya fada cikin nasa, and I froze for some seconds. Wani irin adrenaline rush ne yazo min wanda har sai da naji daci a bakina, da wani irin sauri na mika hannuna da niyar daukar bath robe dina amma kafin hannuna ya kai kan robe din naji an rike su, a firgice na kalle shi dan bansan ya akayi ya taho daga bakin kofa ba har zuwa inda nake saboda akwai yar tazara tsakani. Abinda na gani a idonsa shi ya kara tsorata ni, lust ne, the kind of which I have never seen. "Sultan look at me, Sultan No, No" amma sam sultan ba fuskata yake kalloba, he is looking at something else, wannan Sultan din ba wanda na sani bane, idansa ya chanza daga light brown ya koma black, na fara kokarin kwace hannuna wanda hakan yasa ya hada ni da jikinsa ya rike gam, duk kumfar da take jikina ya goge ta a kayansa, na sake gwada yi masa magana "Sultan me kake son aikatawa ne haka, Sultan ka dawo cikin hayyacinka dan Allah" tashin hankalin da nake ciki yafi karfin hawaye, sai a lokacin yayi magana "please please please only now, only today" daga haka ya hade bakin mu guri daya ya fara kissing dina fiercely. Ji nayi komai ya tsaya min, dukkan emotions din da nake gani a idon sultan su yake zuba min, his sadness, loneliness, anger and his love for me. And I find myself responding back. Daga ni har shi karkarwa muke yi tamkar wadanda ake karkadawa. Babu abinda muke yi sai ajjiyar zuciya one after the other. I feel my senses slipping away from me. A lokacin da za'a tambayeni sunana ma ban sani ba. Hannun Sultan daya ya zagaye kuguna dashi ya matseni a jikinsa daya hannun kuma yana yawo dashi a jikina yana shafa duk inda hannunsa zai iya kaiwa. Allah ne kadai yasan time din da muka dauka a haka dan ni dai kam ban sani ba. Ajiyar zuciya Sultan ya sake yi wacce tayi vibrating a jikinsa gaba daya, a lokacin naji pulsing daga kasansa, wannan shi ya fara dawo min da sense dina, what in God's name is happening? What the hell are we doing? Another pulsing followed. Dukkan senses dina sun dawo kuma yanzu. What have I gotten myself into. Na fara tunanin daddy da mommy, idan suna kallona yanzu mai zasu ce min. Duk tarbiyyar da suka bani. Duk da cewa muna rayuwar kasar waje amma mommy ta bamu tarbiyyar da ko a family muna daga cikin wadanda ake yabawa. And all of it will be for nothing in the next few minutes. Na janye hannuna daga wuyansa na tattaro dukkan karfina na tura shi baya, inda ace dutse na tura to iyakacin response din da zan samu kenan. Na kara gwada tureshi ina kokarin raba bakina da nasa. Still no response. Ya raba bakina da nasa yace "please please don't fight" naji abinda yace kuma na gane me yake nufi. Karfina dana Sultan tamkar a gwada karfin kaza ne dana doki, lol, in dai har nace zan gwada masa karfi to shima dole zai saka min nasa karfin kuma in dai yasa min karfi to kashina ya bushe dan fata fata zai yi dani. Mafita ta daya ce itace inyi using brain dina, fata na daya ne Allah yasa kwakwalwar tawa tana aiki dan sosai jikina yake karbar sakonnin Sultan. Nabi toilet din da kallo a hankali, na hango kofa a gefen inda muke, a hankali na fara tafiya da baya yayinda Sultan shi kuma ya biyoni tamkar magnet har sai da bayana ya hadu da bangon toilet din kusa da kofa, ina jin sultan ya sauke wata ajjiyar zuciyar da na kuma jinta a kasa tare da kara matse jikinsa a nawa. Ta gefen idona na karewa kofar kallo, naga hook din da ake rataye towel a jikin kofar, good, very good. A hankali na saka hannuna a kan handle din kofar na murda, naji dadi da kofar bata yi kara ba duk da ma ko tayi ba lallai ne sultan yaji ba, na bude kofar kadan sannan na saka hannuna ta waje na rike handle din waje, na dakata ina jiran chance dina kuma ina addu'ar Allah yasa kada jikina yayi giving up kafin in samu chance din, ban jima ba kuwa sai ga chance dina ya fado, Sultan ya chire bakinsa daga nawa ya dago kansa da niyyar mayar dashi wani gurin daban. Na bude kofar da dukkanin karfina. Lissafina yayi dai dai dan hanger towel din ta samu Sultan a gefen kansa. Gaf. Da sauri ya sakeni ya rike kansa da hannu biyu. Next second a waje yayi min, ina fita na rufo kofar tare da murda key din sau biyu. A bakin toilet din na durkushe ina karkarwa, har yanzu na kasa tantance takamaimai me ya faru. I feel lower than the lowest rat, I feel cheaper than a common prostitute. Sai a lokacin sannan wani kuka yazo min wanda ban taba irinsa ba a rayuwata. # This chapter is for you in kinsan kina bin saurayi ba tare da sanin iyayenki ba. This chapter is for you in kinsan ba zaki iya cewa saurayinki a'a ba duk inda yace ki bishi zaki bishi. This chapter is for you in kinsan kina barin maza ko da kuwa ba samarinki ba suna shiga har dakinki. Ba fata nake miki ba amma zaki iya fuskantar abinda yafi na Moon, ba lallai ne ki zama as smart as she is ba, ba kuma lallai ne ki iya controlling jikin ki kamar yadda tayi controlling na ta ba. Sannan kuma ba lallai ne ya zamanto saurayin naki yana sonki kamar yadda Sultan yake son Moon ba. Zai same ki ne a banza kuma daga ranar ba lallai ne ya kara kallon ki ba. Allah ya raba mu da aikata aikin da zamuyi nadama har karshen rayuwar mu Allahumma Ameen. [11/7, 2:29 PM] maryamsuleiman48@gmail.co: MAIMOON By Maman Maama Episode Forty Six : The Repentance Gaba daya jikina karkarwa yake yi saboda irin kukan da na keyi, ba me sound sosai bane sosai amma irin wanda karfinsa yake jijjiga jikin mutun din nan ne. What just happened to us? Ji nayi na tsani kaina gaba daya saboda ina ganin duk abinda ya faru laifina ne. I shouldn't have let Sultan come to America with me tunda nasan ni kadai ce ba kowa a tare dani. Daya biyoni din ma I should have stand my ground in nuna masa limit dinsa. Amma na barshi kusan komai tare muke yi, shi ba muharramina ba sannan ga strong attraction da yake a tsakanin mu. Na tuna lokacin da ya fara cewa yana sona, cemin yayi he has nothing yana so inyi sharing what I have with him. Nothing din da yace bayana nufin kudi ba, yana nufin many things da yayi lacking including tarbiyya, amma maimakon inyi sharing tarbiyyata with him sai na biye masa muka zama marassa tarbiyyar gaba daya. Na tuno maganar Amira da take cemin ita character is contagious, idan ni ban gyara shiba shi zai iya lalata ni, gashi kuwa ta tabbata, ni nasan abubuwan da na aikata zuwana America ko a mafarki akace min zan aikata something like that zance karya ne. Ni nasan wannan abinda ya faru dani har da alhakin iyaye na a ciki. Sunyi iyakacin kokarinsu gurin bani tarbiyya amma nake cin amanar su ina bin Sultan, na tuno abinda na ke yi a abuja da England, sai inyi wa mommy karyar zanje unguwa mu fito da driver sai inyi ditching drivern in bi sultan, instead of in yace min inzo muje yawo in ce masa a'a in yana son gani na yazo ya same ni a gidan mu. Na tuna irin kallon da colleagues dina suke min tinda muka zo America suka ganni tare da Sultan, a lokacin sam ban damu ba, gani nake what people think about me doesn't matter, tunda kullum abinda sultan yake ce min kenan, na manta cewa ita shedar mutane itace shaidar da take bin mutun har kabarinsa. Nan tunanin mutuwa yazo min. Yanzu da zan mutu na tabbatar wuta zanje, annabi saw cewa yayi damu 'kada ku kusanci zina' amma ni exactly opposite abinda yace min nayi. Nan take wani irin tsoron Allah ya fara shigata, kukana ya tsananta, cikin kukan na fara kiran astagfirullah, astagfirullah har sai da murya ta da dashe ni kaina bana jin me nake cewa. Wani sanyi naji yana ratsani sannan na tuna har yanzu babu kaya a jikina, bedsheet din kan gadon na jawo na kudinduna ina karkarwa, a hankali naji na daina jin sanyin, kukan ma ya tsaya sai ajjiyar zuciya. Na sa hannuna na shafa fuskata ina goge hawayena, anan na taba lips dina da suka kumbura, tun da na mallaki hankali na babu wani namijin daya taba koda rike hannuna ne, but Sultan has kissed me today kuma wannan ba shine abinda nafi regretting ba kamar the fact that I kissed him back. I should have control myself but I didn't, I am too weak, too soft. Na kalli hannuna naga zoben da Sultan ya bani last week. Sai a lokacin na tuna dashi a toilet, duk da abinda ya faru sai naji ina wondering is he OK? Ba motsi sam a toilet din, what if I hit him too hard? Na mike a hankali na dauki kayana dana ajiye na fara sakawa, sai a lokacin na tuna cewa na saba kumfa a jikina ban dauraye ba, na kalli jikina naga babu kumfa babu alamarta. Na saka kayana ba tare da ko mai na shafa a jikina ba, turare ma sai dai yayi hakuri yau kam. A madubi na kalli fuskata naga tayi fari tas tamkar babu jini. Idona ya kumbura sosai saboda kukan da nayi, na dauko glass a cikin handbag dina na saka, na tuna Sultan ne ya saya mana rannan iri daya ni dashi. A kwatina kawai naja nayi gaba, har nakai bakin kofa sai na tsaya ina kallon kofar toilet, har yanzu babu motsi a ciki, na karasa gurin na zare key din daga jikin kofar na tsugunna a hankali na tura shi ta kasan kofar. Still banji motsi ba. Hankali na naji bai kwanta ba, na leka ta keyhole, a zaune na ganshi ya jingina da bango yana facing kofar, idonsa a lumshe, side din fuskarsa daya da jini alamar karfen yaji masa ciwo, na jima ina kallonsa sannan na lura kirjinsa yana dagawa alamar numfashi, sai a lokacin na lura cewa kayan jikinsa complete suke har da takalmi da agogo, sai dai yanzu gaba daya kayan sun jike da kumfar jikina. Ba abinda ya zo gurina yayi kenan ba, zuwa yayi ya kaini airport, he has been good, more than good, how did this happened. Na sake masa one last look sannan na bude kofar apartment din na fita. Na duba agogo naga 12:30, yaushe time ya wuce har haka? Sai da anje gate din hospital din sannan na samu taxi nace ta kaini airport, ina zuwa na sake sayan wani sabon ticket for the next flight to England. Wanda suka ce min sai 6 na yamma zai tashi, I will wait, dan da in koma apartment dina gwara in kwana anan ina jira. Waiting room dinsu na shiga na zauna, na tuna ko breakfast banyi ba amma na share. Ina zaune har lokacin sallar Zuhr yayi na tashi na shiga toilet nayo alwala na dauko potable sallaya ta mai hade da compass na shimfida can gefe na tayar da sallah, sai da nakai sujjadar karshe inda anan na saba gabatar da adduoi na amma yau na kasa addu'ar komai, am a sinner, ta yaya zan roki Allah bukatuna bayan na saba masa, sai kuka, da kyar na dago daga sujjadar na kammala sallar sannan na dinkule a kan sallayar na cigaba da kuka na. Anan na wuni ko ruwa na kasa sha, ina ganin missed calls din mommy, nasan sunje daukana basu ganni ba, bazan iya magana ba shi yasa ban dauka ba. Karfe 6 jirgin mu ya tashi, na zauna a seat dina temperature ta tana hawa, flight attendant na kira nayi requesting a bani bargo, haka na kudunduna ina ta juya zoben sultan a hannuna. Is he OK? Ko ya fito daga toilet din? Duk da abinda ya faru tsakanin mu amma sam har yanzu banji haushinsa ba, nafi jin haushin kaina. Ina nan a kwance har jirgin mu ya sauka around 11:30 na dare, na kunna waya ta na fita reception na kwanta na kudunduna a cikin hijab dina ina karkarwa. Bana son zuwa gida sam saboda gani nake kamar abinda na aikata yana rubuce a goshina ina zuwa gida zasu gane. Number din Hafsat nayi dialing tana dauka nace "Hafsat ina airport bani da lafiya, dan Allah ku zo ku dauke ni" da sauri ta amsa jin yanayin muryata. Ba'afi 20 minutes ba sai gasu ita da Zayed, Hafsat tana taba jikina tace asibiti, Zayed yace "No, mu kaita gida kawai tasha magani ta kwanta, zuwa gobe in babu sauki sai a kaita asibitin" sai da muka je gidan Hafsat sannan ta kira mommy ta gaya mata gani nan a gidansu babu lafiya, nan da nan mommy ta daga hankalinta tace zuwa zatayi ta ganni da kyar daddy ya hana ta yace ta bari sai da safe, tunda daga Zayed har Hafsat duk likitoci ne yasan zasu kula dani. Magunguna zayed ya bani na sha sannan Hafsat ta dama min oats shima na sha, gana nan suka tafi suka barni suka ce in kwanta inyi bacci. Suna fita na tashi na shiga toilet nayo alwala na gabatar da sallah Magrib da Isha, sannan na zauna na fara jero salloli a duk sujjada ina kuka ina neman gafarar Allah, kawai sai na samu kaina da yiwa sultan adduah. Na tuno da maganar da Steve ya gayamin lokacin da na tambayeshi ko sultan yana shan giya, he said only when he is frustrated, yanzu kuwa nasan sultan is as frustrated as frustration goes. Sai da aka fara kiran sallar asuba Hafsat ta shigo da niyyar tashina sai ta ganni already akan sallaya sai ta koma. Sai da na idar da Sallah asuba sannan na kwanta, ji nayi kamar an dauke min wani nauyi daga kaina. A take bacci yayi awon gaba dani. Aduk sanda bawa ya aikata laifi, babban abinda ubangiji yake so shine bawa ya tuba, taubatan nasuha, ka tuba da niyyar ba zaka sake aikata laifin irin wannan ba. Shi Allah mai gafara ne kuma mai rahama. In dai har ka tuba ga Allah, kai kanka ba sai an gaya maka cewa tubanka ya karbu ba, ajikin ka zakaji, saboda shi zunubi nauyi ne dashi, zakaji kunchi a zuciyar ka amma da zarar ka tuba zakaji kunchin ya yaye. Allah yasa mu dace. Sultan Jinsa yake kamar wanda yake yawo a gajimare, bai taba jin feeling irin wannan ba saboda bai taba bin wannan hanyar ba. Ji yake yi kamar ya bar duniyar nan mai cike da kuncin rayuwa ya kama hanyar wata mai cike da soyayya, gaba yake kara yi ko waiwaye baya yi burinsa kawai ya isa destination dinsa. Kamar daga sama yaji saukar karfe a gefen kansa. Ba shiri ya sake ta, ba wai zafin dukan yaji ba a'a it took him by surprise ne kawai, irin ba zato ba tsammani din nan. Ya rike gurin yana tunanin me ya faru, next thing da yaji shine karar rufe kofa. Sai a lokacin ya bude idonsa, ga mamakinsa sai ya ganshi a tsaye a toilet, toilet din apartment din Moon. "What the hell am I doing here" ya kalli kayan jiki sa yaga duk sun jike da ruwa, what happened, shi dai yasan ya taho da sauri zai dauki Moon zasu tafi airport, ya tuno ya shigo dakin yana nemanta, ya tuno sanda ya murda kofar toilet din, he remember seeing her. He then remember everything. Wani irin jiri yaji ya taso masa yayi baya ya hadu da jikin bango sannan ya durkushe a gurin. Innalillahi wa inna ilaihir rajiun. What have I done? A hankali ya fara jiyo saurin kukanta daga cikin dakin, jin kukan yake yi tamkar saukar ruwan kibiyoyi a kirjinsa. Ya runtse idonsa yana fatan Allah ya dauki ransa anan. Abu daya ne zai hana shi kashe kansa ayau, saboda yasan duk wanda ya kashe kansa wuta zashi, shi kuma yana da burin samun lahirar sa, tunda bai samu farinciki a duniya ba ko Allah zai nufe shi da rahama ya samu lahira. Sai da ya hadu da ita sannan ya fara tunanin maybe zai iya samun farin ciki a duniyar ma, amma yanzu after doing what he did, he knows that he lost his dunya sai dai kuma lahirar. Tun farko yasan cewa he is playing with fire, saboda yadda yake jinta is beyond explanation, amma gani yake ai zai iya daurewa, saboda yana ganin tunda bai taba aikatawa ba bai san dadin abun ba, yana ganin he can control himself, sai yanzu ya gane cewa ashe shayi ma ruwa ne. Har yanzu kukan take yi har muryarta ta dashe. Da ace wani ne ya sakata kukan nan da sai inda karfinsa ya kare amma gashi shi da kansa ya saka ta kuka kuma ko rarrashinta ba zai iya ba saboda baya jin zai kuma iya hada ido da ita. A hankali ya furta "am a monster" . Jin dadinsa kawai shine the things stopped halfway, da ace yayi destroying dinta completely da baisan yadda zai yi da ransa ba. "I should have know that I will never amount to anything good, iyayena ma sunyi abandoning dina saboda sunsan cewa am a monster" a take ya fara nadamar saninta a rayuwarsa, da basu hadu ba da shikenan something like this ba zai taba faruwa da ita ba, she is the most decent girl daya taba sani a rayuwarsa. Now she is crying because him. Ta daina kukan yanzu amma yasan kukan fili ta daina na zuci kuwa zata cigaba dayi har abada. Yana jinta tana shiryawa, tafiya zatayi, yana so ya sake ganinta, one last look, amma yasan ba zai iya ba, abinda yayi mata is unforgivable, ya jingina kansa a jikin bango tare da runtse idonsa. Ya jima a haka kafin yaji an bude kofar apartment din sannan aka rufe, she is gone, gone from his life. A hankali ya mike daga inda yake zaune a karasa gaban mirror yana kallon fuskarsa, jinin da yake fuskarsa har ya bushe. Bai damu da shi ba dan haushin kansa yake ji sosai, ya dunkule hannu ya naushi reflection dinsa, mirron ya tarwatse duk ya yanke shi a hannu "fuck" ba fada yana karkada hannunsa saboda da gaske yaji zafin buguwar. Ya kunna fanfo ya wanke hannun sannan ya wanke fuskarsa. A kasa yaga robe dinta, ya tuna sanda ya kwace ta daga hannunta, ya sunkuya ya dauka ya cusa fuskarsa a ciki yana shakar kamshinta, ya jima a haka sannan ya rataya robe din a ruyansa yayi hanyar kofa, ya murda handle din yaji a rufe, damn, wato he was as bad as sai da ta rufe shi a toilet, I am truly a monster, ya sake fada a hankali. Yayi bending yana studying lock din, sannan ya ciro belt din jikinsa ya zare pin din ya dan lankwasa shi kadan ya zura a keyhole din, bai jima ba ya bude kofar, tun yana yaro ya iya bude locks saboda tsabar yawan rufe shi da ake yi a daki. A Lagos kuwa hatta locks masu pins sai da ya koyi yadda ake budesu. Sai da ya jawo kofar sannan yaga key din a ajjiye a kasan kofar, wani abu yaji ya tokare shi a kirji, she loves him so much, tayi locking dinsa amma kuma sai ta ajjiye masa key saboda ya bude kansa, bayan duk abinda yayi mata, she loves him and that hurts him alot, he let her down bayan kuma shi yayi mata alkawari yace "I will never let you down " . Yasa kai ya fita ya kalli dakin yaga babu abinda ta dauka sai jakar kayanta, hatta kayan da ta chire suna kan gado. Yayi deciding he will have to come back later ya hada mata sauran kayanta ya aika mata dasu, da kayan da ya saya mata na tsaraba, amma shi kam yasan bazai kuma iya hada ido da ita ba. Moon Sai wajen 12 na tashi daga bacci, shima kuma yunwa ce ta tashe ni, a hankali na tashi zaune. Abubuwan duk da suka faru suna nan tas a raina amma kuma fes nake jin zuciya ta, na bude kofa na fita palo, mommy na gani zaune ita da Hafsat, sai a lokacin na lura da kibar da Hafsat tayi, she is pregnant, mommy ta tashi da sauri ta karaso inda nake "Moon ya jikin naki? Kinga yadda kika rame kuwa? It is my fault, dana sani na biki American nan in yaso ko hotel sai mu kama mu zauna har ki gama, zaman kadaici ne ya saka miki ciwon ba komai ba" na danyi murmushi a raina nace "I was never alone mom, but you will never know" na rungume ta ina jin dadi har cikin raina, mother is above everyone. Har wajen Zuhr mommy tana nan, sun sani a gaba ina ta basu labarin America da abubuwan da na koya, amma ko da wasa banyi mentioning sunan Sultan ba. Sai da daddy yayi ta kira sannam mommy ta tafi, ni kuma nace sai gobe zan dawo gida. A raina ina son magana da Hafsat ne. Sai da daddare muna bedroom din Hafsat sannan nace mata ina son magana da ita, ta samu guri ta zauna ta bani attention dinta, tiryan tiryan na fara fara bata labarin bina da sultan yayi america har abinda ya faru jiya ban boye mata komai ba, sai da na kai karshe sannan na sauke idona kasa nayi shiru. Saukar mari naji a kunci na na hagu, naji zafin marin sosai a raina nace "I deserve it " wani marin na kuma ji a kuncin dama, wannan karon har sai da kwalla ta kawo a idona, da sauri Hafsat ta mike ta fita, ni nasan kuka zata je tayi. Follow my New Group #MamanMaamaNovels [11/7, 2:30 PM] maryamsuleiman48@gmail.co: MAIMOON By Maman Maama Episode Forty Seven : Amir Na jima ina shafa fuskata dan da gaske marin ya shige ni. I deserve it. I deserved everything that happened to me. Bawai na gaya wa Hafsat abinda ya faru bane dan tayi min fada ko wani abu ba, na gaya mata ne saboda ta bani shawara akan abinda ya kamata inyi yanzu. Hausawa sunce mai neman shawara sirri sa baya rufuwa amma kuma aikinsa baya baci. Na jima anan a zaune ina ta lissafe lissafe a raina, ina juya zoben Sultan a hannuna. I desperately want to know how he is, amma kuma bazan iya kiransa ba. Nasan kuma shima yana son yaji daga gareni, amma ba zai iya kirana ba. I just want someone to act as intermediary. Har nayi shirin kwanciya na kwanta babu Hafsat babu labarinta. A raina nace tayi fushi dani. Da safe na tashi na yi wanka na shirya sannan na fita, a kitchen na same ta ita da maid dinta suna hada breakfast, ko kallon inda nake bata yi ba har suka gama aikin ina zaune ina kallonsu, suka shirya dining sannan ta tafi yin wanka. Naje na zauna nayi serving kaina ina cikin ci sai ga Zayed nan, daga yadda yake yi min magana na fahimci cewa Hafsat bata gaya masa maganar da mukayi ba, wannan yana daga cikin dalilan da yasa na iya gaya mata, baza ta gaya wa kowa ba. Muna breakfast muna hira sai gata ta fito kamar amarya, tun kafin ta karaso Zayed ya mike ya taro ta suka fara zuba soyayya ni dai ina ta kallonsu. Ko wata rana ni ma zan samu wannan farin cikin? Da sauri sauri ya gama ya shirya ya fita asibiti. Nan muka zauna awkwardly ni da Hafsat, maid dinta tana cleaning table din. Can dai tace "yanzu how do I even know you are intact?" Na harare ta nace "ko in bude miki ki gani?" tayi ajjiyar zuciya tace "yanzu me kike so daga gareni" nace "so nake ki bani shawarar abinda ya kamata inyi" ta bude baki da mamaki tace "yanzu ke har sai na baki shawara? Kina nufin kice min da akwai sauran alaka a tsakanin ku? After what he did to you?" Na sunkuyar da kaina a hankali nace "I love him" tace "you are crazy" a raina nace "maybe I am" can ta sake cewa "yanzu in na baki shawarar ki rabu dashi, zaki rabu dashi?" Na girgiza kaina va tare dana kalleta ba. A fusace tace "then what do you want from me?" Na dan jawo kujera ta kusa da ita nace "yanzu so nake in san ta wacce hanya zamu yi moving forward, abinda ya faru ya riga ya faru, it is in the past. Amma matsalar itace bansan ta yadda zamuyi communicating da shi ba, I can't call him and he can't call me. So nake at least in baki number dinsa ki kira shi kuyi magana, at least to know how he is doing. He is a really good guy, he is not what people think he is. I don't want abinda ya faru tsakanin mu yayi affecting dinsa negatively. Please Hafsat" na gama kamar zanyi mata kuka, amma banga alamar tausayi sam a fuskar ta ba, sai ma tsabagen mamaki na da take yi, cikin mamaki tace "You want me to call him? In kira shi ince masa me for God's sake? Thank you for trying to rape my sister kike so ince masa ko me?" Na dakatar da ita da sauri nace "He did not try to rape me, what happened wasn't entirely his fault, ni ma da laifi na a ciki" kafin in karasa ta mike da sauri kamar wadda ta manta wani abu, taje bakin kofar palo ta bude kofa ta juyo tana kallo na cike da tsantsar takaici tace "get out of my house" banyi mata musu ba na koma bedroom dinta na jayo akwatina wanda dama ko bude shi banyi ba kayan ta nake sakawa, nazo na fice daga ni har ita babu wanda ya kalli wani. Ina fita na tari taxi nace ya kaini Nigerian embassy. Ina zuwa gida zan iya cewa kusan na manta da komai saboda farin cikin ganin family na. Sai wani ji dani suke yi kamar zasu goyani. Kwana na biyu na warware sosai ina ta harkoki na amma ta ciki na ciki dan dai dai da second daya ban manta da Sultan ba. I terrible miss him. Kullum zan budo number dinsa a waya ta inyi ta kallonta. Duk sanda kuwa naji kira ya shigo waya ta sai naji gabana ya fadi ina tunanin ko shine amma shiru makatau. Last seen dinsa a Whatsaap shine a day to barowa ta America. One week ya wuce, two weeks ma haka. Ni kadai nasan yadda nake ji a zuciya ta tunda babu wanda zan gaya wa in ji dadi. Har aka yi mana fixing ranar defence na project din mu. Meaning mun gama karatu kenan. Na zama busy sosai ina tsara yadda zan presenting project dina, neurology zan fara sannan a week later in yi psychology. Duk sanda tunanin Sultan ya dame ni sai in dauko waya ta inyi ta kallon pictures din mu, wani inyi kuka wani dariya. Ko na dauko waya ta zan kira shi sai in tuna abinda ya faru sai in kashe, kunyarsa nake ji sosai. Ana gobe zanyi defense dina daddy ya tara mu a palo yayi min addu'ah sosai ta samun nasara, dan it is not easy kayi facing professors komai ilimin ka kuwa. Alhamdulillah washegari nayi defense dina successfully na gama. Sosai akayi celebrating a gida amma ni sam hankali na ba'a kansu yake ba dan yau kam da gaske nayi missing sultan saboda kusan tare dashi muka rubuta project din. Ranar har Hafsat tazo gida ita da Zayed sun kawo min gifts. Sai da muka kebe ni da Hafsat sannan ta tambayeni "so... Do you call him?" Na girgiza kaina da sauri, sai kuma hawaye suka fara zuba nace "I can't" ta gyada kanta tace "He is stronger than you, he is suppose to call you first in dai har yana so ku dawo tare" na gyada kaina ina goge hawayena, sai kuma ta rungume ni tana dan bubbuga bayana a hankali, tace "be strong little sister, am sure God have something special for you" Ranar da daddare na dauki wayata da niyyar kiran Sultan ina ajiyewa ya kai sau goma, daga karshe dai na kashe wayar na jefa a cikin jaka na rufe. Har na kwanta kuma sai na tashi na dauko camera ta na kunna videos din da nayi mana ana gobe zan taho, wajen horse race da inda ya hau dutse a guje ya fada cikin ruwa. Kuka na zauna sosai nayi. Washegari muna zaune palo yaya Walid yace "Wai Moon ina saurayin nan naki da kuke yawan waya dashi? Tunda kika dawo daga America naji shi shiru" Mommy tayi sauri tace "kaima dai Walidi ka fada, nima naji shiru, kinsan dai almost karatunki ya kammala, daga miki kafar da baffa zai yi kawai shine idan ba'a gaya masa kin gama ba, shima kuma delay din da za'ayi kawai zuwa sanda result dinku zai fito ne. Gara kisan me kike ciki Moon. Nima kuma office din mu a Abuja sun fara damuna akan lallai ya kamata in koma aiki in ba haka ba sai dai inyi resigning, so nake muyi magana da daddyn ku kawai mu koma gida haka nan. Faruk ne kawai bai gama karatunsa ba shima kuma zai iya zama shi da daddyn ku zuwa sanda zai karasa" ina sauraronta ina lissafin in dai muka koma Nigeria to ni kam na kade har ganyena. Masifar Hajja da jarabar Munir kadai ta ishe ni. Su familyn mu gani suke yi kamar nayi girma da yawa, musamman yanzu dana gama karatun likita, gani suke ya za'ayi ace har na zama doctor babu aure bayan a zahirin gaskiya am just 22 years, 16 years na gama sec sch yanzu kuma after 6 years na gama first degree na. Har dare ina ta lissafin what to do. Na dauko report dina na psychology ina karantawa, it contains everything about Sultan, sai kawai naji ya kamata in dan kara masa armashi, kamar make-up. Na dan yi tunani kadan sai na mike na tafi part din su yaya walid, na debo kayan drawing dinsa na dawo dakina. I am not a good artist but I am going to try my best. Na zauna a nutse na fara zane, sai da na dauki 3 hours sannan na gama, na tafi palo na dauko fresh milk na dawo na zauna ina duba zanen da nayi. Sultan ne a tsaye, da sleeveless riga a jikinsa da three quaters wando. Ya zura hannayensa a aljihunsa ya dan juya kansa yana kallon side daya. Fuskarsa babu fara'a. Yayi kyau sosai kamanninsa sun fito dan duk wanda ya sanshi in yaga zanen zai gane shi. A jikinsa nayi rubuce rubuce akan behaviours din sa da mutane suka san shi dasu. The drunk, arrogant spoilt rotten prince. Daga bayansa sai na sake wani zanen something like his shadow, a jikinta kuma sai na yi rubutu kanana akan dukkan abubuwan da nayi learning na kyawawan halayensa, saboda yawan abubuwan da na rubuta har sai da gurin ya cika na rubuta etc. Kuma wadannan iyakacin abinda na sani ne kawai, dan na tabbatar da akwai wadanda ban sani ba. Na kalli zanen inajin wani dadi har cikin raina, ina ma mutane zasu ga wannan zanen nawa? Tabbas da sun so sultan kamar yadda nake son sa. I wish one day I will be able to show it to the world. Amma bazan yi hakan ba sai da amincewar Sultan. ( naso ace na iya zane dana zana muku. Lol ). Ranar da zanyi presenting ita ce kuma final day dina a Oxford. Tun safe na shiga makaranta ina ta practicing abinda zanyi. A ka'idar makarantar malamai kadai ake presenting to, duk sauran guest suna waje. Ana kira na na shiga na kafe zane na a jikin board. Tun daga yadda malaman suke kallon zanen nasan ya samu karbuwa, wannan shi ya kara min confidence. Katardun hannuna na ajiye a gefe, i don't need them, I am going to talk about Sultan and I know him like the back of my hands. Nan na fara kararo bayani akan rayuwarsa, yadda yake rayuwa with two personalities, as a hero and as a villain. Tun da na fara maganar murmushi ne a fuskata. Ina gamawa daya daga cikin lecturers din yace min "who is this man to you?" nace mishi "he is my boyfriend sir" gaba dayan su sai da sukayi murmushi. Ina fitowa da gudu na karasa gurin su mommy na rungume ta ina murna, nan muka ta daukan pictures dan har daddy yazo gurin duk suna waje. Muna cikin haka na hango motar Sultan, gaba na ne yayi wata irin faduwa, mutun na gani a tsaye a jikin ta yana kallon inda muke, Amir, nayi sauri na dauke kaina kamar ban ganshi ba amma kuma duk hankali na ya tafi gurinsa, ko tare suke da Sultan? Har muka gama yana nan a tsaye a inda yake, an kawo motoci zamu tafi nace musu "ku tafi kawai ni zan taho daga baya, akwai friends dina da nake so muyi sallama dasu" daddy ya kalleni da tsokana yace "friend ko boyfriend" na shagwabe fuska ina bubbuga kafa nace "daddy" yayi dariya yace "is alright, a driver will come back for you". Suna tafiya na juya na tafi gurin Amir. Nayi masa sallama, ya amsa fuskar sa da murmushi. Yana sanye da geans da sweater ya saka hannunsa a aljihun sweater kamar mai jin sanyi. Yace "can I talk to you for a minute?" Ya fada yana nuna cikin motar, Na girgiza kaina dan na fahimci shi kadai ne babu Sultan nace "akwai gurin zama a can, mu karasa sai mu zauna" ya daga kafada dan ya gane bazan shiga motar ba. Muka danyi tafiya kadan sannan muka karasa wata rumfa da akayi dan students, na jawo mana kujeru muka zauna. Sai a lokacin na kare masa kallo, baki ne amma very handsome, yana da manyan ido, fuskarsa irin mai natural murmushin nan ce. Na gaishe shi ya amsa. Sannan ya fara magana "kin ganni a England ko? Na rasa yadda zanyi muyi magana ne shi yasa dole na taho nan" nace da sauri "wait, kana nufin takanas ka taho daga Nigeria saboda kayi magana da ni?" Ya gyada kai yace "Sultan is my only family, I can do anything for him. I guess ya gaya miki labari na ko?" Na gyada kai, yace "you are very special to him you know, Sultan baya magana akan kansa amma daga dukkan alama kinsan komai akansa. Sultan mutum ne na musamman wanda ni kaina bazan iya kwatanta miki shi ba. Tunda ya hadu dake ya soma chanzawa. Ya daina shiga trouble, I was happy for him, very happy. But now...... " ya dago yana kallona, he looks very sad, ya ce "what happened?" Nace "bai yaga maka ba?" Ya girgiza kai yace "the fact that bai gaya min mai ya faru ba shi yafi daga min hankali. Bai taba boyemin wani abu ba. Amma yanzu all he keeps saying is that he is a monster, and that he is taking himself as far away from you as possible. Ranar da yace min zaku dawo England na kira shi sai yace min yayi missing flight, that something he never did, Sultan mutum ne mai kula da time, sai yace min kuma ke kin taho, daga nan na gane something is wrong saboda ba zai taba barin ki ki taho ke kadai ba, in ma missing flight dinne sai dai kuyi tare. Daga nan duk sanda na kira sai in tarar still yana America. Rannan Steve ya kira ni yace police sun kama sultan ya kwana a station, anan nake tambayar Steve me yake faruwa yace min everything is wrong, bai san me ya faru ba but yana ganin it has to do with you. Bayan an fito dashi daga station na kira nayi2 dashi ya gayamin me yake faruwa yaki. Yace he is never going back to Nigeria and he is also not coming to England. A america zai zauna. Tun daga nan na yi tunanin dole in neme ki, yaki ya bani number dinki and that your ugly faced friend itama taki bani. Things are going very badly for Sultan, dole na taho England gurin ki. I need your help" na runtse idona hawaye yana sauka akan kuncina. Yaci gaba da cewa "he is back on the bottle. Kin san rabonsa da alcohol?" Na girgiza kaina yace "tun ranar da kuka hadu a Hilton. Ranar sunyi rigima da Takawa as usual, he got drunk and I had to go out and leave him a gida, after he sober up shine ya fita kuka hadu. He told me that he got something better than alcohol, he said he got love" kuka nake yanzu sosai, ya cigaba "please Maimunatu dan girman Allah, call him" ya fada shima kaman zaiyi kukan, nace "but why should I be the one to call him? Mai yasa shi ba zai kira ni ba?" Yayi murmushi yace "because you are the light to his darkness" Follow my new group #mamanmaamanovels [11/7, 2:30 PM] maryamsuleiman48@gmail.co: MAIMOON By Maman Maama Episode Forty Eight : Awkward Ranar duk ban karasa ta da nishadi ba, today is my graduation day, I am suppose to be happy. Da naje gida ma yake kawai na ringa yi daga baya na tafi daki nace na gaji bacci zanyi. Na kwanta amma na kasa bacci. So Sultan thinks he is tough right? He thinks he can just give me up instead of facing me? Lets see how tough he can be. Wato ni nice soft one din shine Amir zai wani zo yace in kira shi ko? Na ga dai baccin ba zai yiwu ba na mike na fara abinda na saba duk sanda wani abu ya dameni ko wani al'amari ya shige min duhu, na tashi na fara gaya wa Allah. Nayi adduoi sosai akai na da kan Sultan ina nema mishi guidance na ubangiji. Sai a lokacin na fara wani tunani, addu'ar iyaye itace addua mafi inganci a gurin 'ya'ya, Sultan baya samun wannan, shi kansa ba lallai ne yana yiwa kansa da kansa addu'ar ba. Duk da dai adan zaman da nai dashi na lura baya barin sallah. Na gama adduoi na na kwanta akan sallayar nayi baccina. Da assuba na tashi nayi sallah, har na koma zan kwanta naji still raina babu dadi, na dauko waya ta a jaka na kunna na nemo number din Sultan nayi dialing, sai da ta kusa katsewa sannan ya dauka, amma bai ce komai ba, naji takaici ya kamani, why did I even called? Na katse kiran kaman zanyi kuka. Ina ajjiye wayar kiransa yana shigowa. I let it ring. Ya sake kira naki dagawa. Message ya shigo. "Answer the call please" nayi reply "why didn't you call me sai da na kira ka?" "Am sorry, please pick up the phone" wani kiran ya shigo, it has been a month rabona da Sultan, rabon da inji muryarsa. Na dauka tare da sallama. Ajjiyar zuciya naji ya sauke. An awkward moment followed. Nace "look, idan ba zaka yi magana ba zan ajjiye wayar" a hankali yace "how are you?" sai da naji muryarsa sannan na fahimci how much I have missed him. cikin rawar murya Nace "I missed you" ya dan jima sannan yace " I have more than missed you, i have no word for what I felt" "amma me yasa baka kira ni ba? It hurt me sosai, how can you just give me up just like that?" A nutse ya fara magana "you have no idea how much I love you, do you? Bawai nayi giving up on you bane, I am a bad person Moon, You are good, more than good, bana son in bata miki rayuwarki. Ina sonki son da zan iya rabuwa dake even if it kills me, in dai har zaki samu kyakykyawar rayuwa" na katse shi da muryar kuka nace "and who says I want a good life? Huhh? All I want is a life with you. Just tell me idan har kai ka daina sona ne kawai ka gayamin ka daina min wani boye2. You keep saying you are a bad boy, you can never be good in dai har kana tunanin you are bad" yadda na rufe shi da fada ne yasa yayi shiru ya kasa magana. Nima dana gama fada na nayi shiru. Sannan nace "when are you going back to Nigeria?" Yace "I have nothing to go back to Nigeria for" nace a hankali "you can come to England, you have me here, right? Besides, ina son kazo ka gaishe da daddy" ya danyi jim sannan yace "are you sure?" Nace "yes, am sure. Kai na zaba a matsayin mijina, whether you are good or bad, kai nake so" sosai magana ta ta taba zuciyar Sultan dan har a muryarsa naji, shi abinda ya cigaba da insisting shine wai am too good for him, baya so ya sake letting dina down. Daga karshe dai na gaya masa cewa nan da about a month zamu koma Nigeria kuma muna zuwa aure za'a yi min da Munir, whom I despise, dan haka zabi ya rage nasa, is either ya zauna a America ya cigaba da playing bad boy role dinsa ni kuma a aura min munir ko kuma ya dawo yayi facing daddy ya karbi aurena. Ina fadin haka na katse wayar, ko minti daya ba'a yi ba ya kira, na katse kiran na kashe wayar gaba daya. Na san na kunna masa wuta. Dole ya dawo cikin sense dinsa yasan abinyi. Ranar da yamma naje na samu mommy a dakin daddy tana gyara masa kaya. Na zauna a kusa da ita nace "Mommy wannan da kuke zance ke da yaya Walid rannan, sunansa Abbakar, dan garin Abuja ne, he is an architecture, iyayensa manyan mutane ne sosai a garin abuja. Ina son kiyi wa daddy maganar sa dan cikin satin nan na keso zaizo England ya gaishe da ku" mommy ta kalleni fuskarta kamar gonar auduga tace "kai Alhamdulillah, he is your final choice kenan ko?" Na gyada kai tace "Allah ya kawo shi lafiya" nace "Amin" har na mike sai kuma tace "Moon, kash, kinga har naso in manta, daddynku gobe zai yi tafiya, president ne ya tura shi wani summit a South Korea kuma zasu dan jima a can, dan yace ma maybe sai dai mu hadu a Nigeria tunda mu zamu tafi da wuri kinsan maganar bikin Nuraddeen ya tashi" na danyi jim ina jin babu dadi, dan da karfi na nazo so nake ayi wacce za'a yi a cikin satin nan a gama. Nace "OK, shikenan sa hadu da daddy a Nigeria, in yazo kawai sai ya gaishe ki ke" mommy tayi dariya, na tsaya ina kallonta dan ni banga abin dariya a cikin magana ta ba, tace "Moon kenan, ina kika taba ganin saurayi yazo ya gaishe da uwa?" Sai da ta fada sannan nima nayi dariyar abin, tace "kawai kice masa yayi zamansa a Nigeria za muzo mu same shi" nace "ai baya Nigeria yana America, dama munyi dashi ne zai biyo ta England sannan ya karasa Nigeria" mommy tace "babu wani abu ai, yazo kawai ku gaisa, in yaso sa hadu da daddyn ku a Nigeria" daga haka na koma part din mu ina lissafin ba haka naso ba ni kam. Amma Allah yasa jinkirin ya zamar mana alkhairi. Dan nasan ba karamin takaici zan sha ba a wajen bikin nuraddeen, a lokacin kowa zai san na gama makaranta. Sai da daddare na kunna wayata. Messages ne suka fara rige rigen shigowa waya ta, nace a raina 'waya gaya maka barno gabas take ne da, dan kaga ina wani lallabaka shine zakake daga min kai. Na fara karantawa "shine kika kashe wayar ko?" "Please karki kuma mentioning wani munir or else.... I don't even know what I will do" "OK, i will come, pick me up in the airport tomorrow morning" nayi murmushi a raina nace 'na gano lagonka ai yanzu, kishi. Amina ce ta shigo tanata kumbure2, nace "ke kuma ke da wa kike bata rai" tace "wai Nigeria zamu tafi bikin Nuraddeen, ni wallahi banson zuwa, ina zuwa gida yanzu zancen aure za'a fara yi min, duk an bi an saka min ido a gida kamar ni nafi kowa girma" dariya nayi sosai nace "that makes the two of us, at least ke ba'ayi miki mijin bama, ni yana nan an ajiye min dan haka bani da bakin cewa ai mijin ne bai zo ba" ta zauna a kusa dani tace "yanzu muyi shawara, ki lallaba mana mommy ta bar mu anan, sai mu zauna a gidan Hafsat su suyi tafiyarsu" na harare ta nace "you are joking, right? Mommy n ce zata tafi ta barmu a gidan Hafsat? Ai in mafarki kike ma yanzu ki farka" ta sake bata rai "to ni yanzu ya zanyi, ni ba samari nake yi ba kema kin sani, kuma ni gaskiya bana son a yi min auren family wallahi, ni nafi son in samu miji na da kaina wanda nake so shima kuma yake sona" murmushi nayi jin ta ambaci kalmar so, tace "this is not a laughing matter oo, ke ma fa ba son munir kike ba na sani" nace mata "wai waye yake maganar wani munir ne dan Allah? Akwai wanda zai zo kasar nan gobe, shine wanda zan aura, zan hada ku ku gaisa" tace "kina nufin baffa zai bari? Duk wannan zaman jiran naki da munir yayi?" Nace "matsalarsa ce kuma wannan, babu wanda ya matsa masa yace lallai sai ya jira, ni dai abinda na sani shine baffa yace in na gama karatu ban sami miji ba za'a hada ni da munir, to na samu, babu sauran maganar munir kuma". Sai da nazo kwanciya bacci sannan na kira sultan, bugu daya ya dauka nace "na dauka kayi fushi ai" yayi ajjiyar zuciya yace "ni na isa? Bayan kinsa yau na wuni da waya a hannuna saboda ina tsoron kar in ajiye ki kira ban gani ba" daga nan na bashi labarin cewa ba zai samu ganin daddy ba sai nan da kamar 3-4 weeks a Abuja. Muka gama plan din zuwansa gobe, ban ankara ba kawai sai gani nayi har karfe biyun dare tayi muna ta hira ba tare da lura da time ba. Washegari ya kira ni ya gaya min sun taso. Sai a lokacin naji gaba na yana faduwa, can I really face sultan? A wayar ma da yaya ballantana ido da ido. This is going to be very awkward. Nayi wa kaina alkawarin na daina munafuntar iyayena dan haka na tafi gurin mommy nace mata "Mommy Abdallah yau zai zo, kuma yace yana so inje in dauko shi a airport" tace "to shikenan ai babu wani abu, sai ki dauki driver ya kaiki. Allah ya sa albarka a ciki" nace "Ameen, nagode mommy" wannan shine abinda muka yi lacking da a relationship din mu, albarkar iyaye, ko da yaushe in iyayenka suna saka maka albarka to ba zaka taba tabewa ba. Na rasa inyi kwalliya ne ko kar inyi? Wanne kayan zan saka? Karshe dai na gayawa Amina nace dan Allah tazo ta rakani, ina ganin kamar in tare muke kunya ta sata yi sauki. Amina ce ta matsamin wai lallai sai nayi kwalliya, wai ai ba haka ake zuwa taryan saurayi ba, ita ta dauka wani sabon saurayi ne, bata san Sultan babu abinda bai sani nawa ba. 😂. Sai da na nemi Hijab din da yafi kowanne girma a cikin hijabai na sannan na saka. Tsaki Amina tayi tace "wallahi baki isa ba, koni da na girma a 'yalleman ba zan saka wannan hijab din inje gurin saurayi ba" ta dauko min gyale nima nace bata isa ba, a karshe dai wani hijab din na dauko wanda bai kai wancan girma ba na saka. Muka yiwa mommy sallama muka tafi. Karfe 12 jirgin su ya sauka. Ni dai tunda naji announcement na sunkuyar da kaina kasa. Can naji Amina tace "gashi nan ya taho" ban dago kaina ba nace mata "ya akayi kika san shine?" Tace "ko yadda yake kallonki ma ai dole a gane. Kai amma fa ya hadu, a ina kika samo shi? Dan Allah ki samo min irinsa nima". Sallamarsa ce ta hana ni karasa kai mata dukan da nayi niyya, ai babu shiri na juya baya na, ga mamaki na sai naji yana dariya, Amina ma ta biye masa suka yi tayi, yace "chafdi, kice akwai rigima kenan" Amina tace "ba karama ba kuwa, kaga kuma yadda ta zauna take ta koda min kai? Wai kyakykyawa, ga ilimi da hankali, shine ta dauko ni wai lallai sai nazo na ganka" dukan da nayi niyar yi mata dazu shina karasa yi mata yanzu, ta matsa daga kusa dani tana dariya, shi kuma ya matso har sai da naji dumin numfashinsa a jikina "please ki juyo mana in ga fuskarki, you have no idea how much I have missed you" ya ga bani da niyyar juyowa sai ya zagayo, ai muna hada ido nayi sauri na rufe fuskata da hannayena, nima kuma zuciya ta tana son ganin tasa fuskar daurewa kawai nake yi. Wayyo ni kam naga ta kaina. Dariya suke yi min sosai shida Amina. Lallai namiji bashi da kunya, wato shi ko a jikinsa ko? Da sauri nayi gaba na tafi gurin motoci, ina zuwa na shiga na zauna. Anan na samu damar kallonsa kafin su karaso, ya rame, ya tara gashi a fuskarsa but he still looks more handsome to me than duk mutanen da suke gurin. Suna tafiya shida Amina tana ta zuba masa zance, Allah ne kadai yasan yawan karerayin da take shirga masa. Suna karasowa ga mamaki na sai naga ya bude wa Amina gaba shi kuma ya shigo baya kusa dani. Ai kuwa na dunkule a guri daya kamar zan shige cikin kujerar, yana shigowa ya kalleni ya kyalkyale da dariya yace "Amina juyo kiga 'yar kauyen 'yalleman" tana juyowa tace "a'a wannan ai kauyancin ta ya wuce nan, maybe daga wata rugar da bamu sani ba ta taho" ni dai ina jin su bance komai ba. Can Sultan yace "kinsan Allah, ko ki ware daga wannan nannadewar da kikayi kamar macijiya ko kuma..... " sai kuma yayi shiru, na leko ta cikin hijab dina nace masa "ko kuma me?" Ya dauke kansa yace "zaki sani ne duk ranar da na kamaki" what? Me wannan mutumin yake nufi? Driver ne ya katse min tunani na yana tambayar ina zai kaimu. Nayi sauri nace masa "take us to the nearest saloon" Sultan ya kalleni yace "mai zakiyi a saloon kuma?" Nace "not me, you. You really need a haircut" yayi sauki ya shafa fuskarsa yace "damn" it is my turn to laugh now, dan haka nima na rama dariyar da yayi min, ya harare ni yace "how do I look?" Nace "terrible". Wani hadadden barbing saloon yayi wa driver kwatance, muka je ya shiga ciki ya bar mu a waje, nan Amina ta zagayo baya ta fara min barin hakora, "gaskiya gayen nan ya hadu, dan Allah dan ina ne?" Nace mata "Abuja" tace "gaskiya ni kam har yafi min kyau akan Zayed din Hafsat" nace "laa, wannan maganar kamar a kunnen Hafsat dan sai na gaya mata" yana fitowa naga ya koma sak Sultan dina, da murmushi a fuskarsa ya shigo yace "to yanzu fa?" Nace "like the Sultan I know" daga nan gidan Takawa inda Sultan yake sauka muka je, kiri2 yaki fita daga motar wai bai gama gani na ba. Sai da nace masa ina gayyatarsa dinner yau da daddare a gida sannan ya sauka. Muka tafi Amina tana ta santin sa, ni kuwa bata san haushi take bani ba. Dama saurin da muke dan mu samu muyi sallama da Daddy ne, muna zuwa kuwa muka tarar ana fito da kayansa, nan muka sake komawa airport muka rakashi, sai da ya bimu daya bayan daya yayi hugging din mu sannan ya tafi. Muna komawa gida na gayawa mommy Abbakar zai zo dinner da daddare, nan ta fara yi min mitar ban iya girki ba "idan da ace kinyi spending koda quarter of time din da kika yi spending kina karatu a kitchen, da yanzu kin zama chef. Amma ke ba zaki yi girki ba. To yanzu ni kike so inyi masa abincin? Go to the kitchen jare, a haka zaki koya ai" na bata fuska nace "mommy idan kuma abincin bai yi dadi ba fa?" Tace "matsalarki ce kuma wannan" na kara shagwabe fuska "please mommy" tace "zan yi masa amma ba dan ke ba, dan shi" a raina nace "oho dai". Ana magrib Sultan yazo, wa yaga gandoki, anan masjid din embassy yayi sallah sannan ya kira woni. Yaya Walid tare suka tafi da Daddy, yaya Habeeb kuwa tun last week yana Nigeria, sune abokan nuraddeen ana ta shirin biki, dan haka a palon su na sauki Sultan, wata kyalliyar amina ta kuma zama tayi min tana yi tana cewa "irin wadannan samarin in baka kwalliya yanzu sai wata ta kwace maka shi" ni kuwa jinta nake yi kawai dan nasan mai kwatar sultan a hannuna sai ta shirya, kuma sultan ba kwalliya ta yake so ba, ni yake so. Already mommy ta aika an shirya wa Sultan dining din palon, dan haka ina shiryawa kawai can na wuce. Ina shiga palon na hangoshi dare2 akan dining yana serving kansa a raina nace 'oh Sultan da abinci, at least dai ai ka bari azo ayi maka bismillah ko' ina shiga ya dago yana kallona yace "bismillah, zo muci abinci" shi ko kwalliyar da Amina ta zauna ta tsara min ma bai gani ba, shi ta cikinsa yake yi. Na zauna a kan kujerar da take facing dinsa na rafka tagumi ina kallonsa yana lodawa cikinsa abinci, no wonder yake so energetic, lallai akwai aiki a gabana. Sai da cikin sa ya fara cika sannan ya dago yana kallona, sai kuma ya dan saki baki yace "menene wannan a saman idonki?" Nace "it's called an eye shadow" yace "menene amfaninsa?" Nace "kwalliya" ya saki baki yana kallona, yace "Amina ce tayi miki ko?" Na gyada kai nace "I look terrible, right" yayi dariya yace "no my love, you look beautiful, with or without make up, you are always beautiful" nace "thank you" suddenly na jefe shi da tambayar da take raina tun sanda muka dauko shi daga airport. "Sultan, me yasa kake shan giya" lemon da yake bakinsa ya fesar kan dining din saboda kwarewar da yayi, wanda yake hannunsa kuma ya zame ya zube a kasa, ya dago dara daran idansa yana kallona da mamaki, sam bai san na san da wannan side din nasa ba. Follow my new group #mamanmaamanovels [11/7, 2:30 PM] maryamsuleiman48@gmail.co: MAIMOON By Maman Maama Episode Forty Nine : Ya Habeeb "What?" Ya tambaya da mamaki, ban maimaita tambayata ba sai ruwa dana zuba a cup na mika masa, bai karba ba, na ajiye a gabansa. Ya sake tambayata "me kika ce?" Na kalle shi cikin ido nace "cewa nayi me yasa kake shan giya" ya bata rai sosai yace "who told you that?" Nayi shiru ban kalle shi ba, can yace "damn it, it's Steve, isn't it?" Nace "tun kafin muyi magana da Steve na sani" ruwan dana ajiye masa ya dauka ya shanye sannan ya mike ya bar dining area din ya koma cikin palon, nima na mike na bi bayansa, na zauna kujerar kusa dashi. Jin bashi da niyyar yin magana yasa na sake cewa "baka ce komai ba fa?" Ya juyo yana facing dina ya wani bata rai yace "can we please just drop this? I really don't want to talk about it now" nima na bata rai nace "why not? Sai bayan anyi bikin mu tukunna zamuyi maganar? Look Sultan da ace zan rabu dakai saboda kana shan giya da tuni na rabu da kai, amma ba wai hakan yana nufin nayi na'am da dabi'ar ba, ina dai saka ran cewa zaka daina. Nayi maka maganar ne yanzu saboda naga har mun fara maganar zuwanka gurin daddy dan haka ya kamata duk wani personal issues din mu muyi solving" na dan yi shiru ina studying dinsa, he looks really disturbed, ya saka duk kan hannayensa a cikin gashin sa, na cigaba "nasan kusan 70% na troubles dinka with the police are related to your drinking habit, saboda fadar annabi ne cewa ita giya itace shugabar dukkan alkaba'i, zata iya saka mutum yayi sata, zina, har ma kisan kai. Sultan zanyi tolerating komai akan ka amma banda drunk husband, what if one day ka dawo a buge kayi min duka?" Da sauri ya kalloni yace "I will never hurt you" nace "you can't be sure, duk sanda kasha u will lost control of yourself, maybe ma ba zaka gane koni wacece ba" alamun bacin raine karara a fuskarsa yace "please ki daina wannan maganar mana, wai what has come over you ne today? Ke fa baki san komai akan maganar nan ba kuma banyi niyyar ki sani ba har abada, yadda kika dauki abin sam ba haka yake ba. Amma na miki alkawarin one day zamuyi maganar but not today. You have no idea what I was going through kafin in hadu dake, and you also have no idea how much I have changed bayan na hadu dake" nace "na yarda, i don't understand and I may never understand. Ni yanzu dai please so nake kayi min alkawari guda daya. Promise me that you will never touch alcohol again" ya jingina da jikin kujerar ya zubo min idanuwansa, a hankali yace "I will do anything for you" na girgiza kaina nace "and that's where you are wrong a duk changes din da kake kokarin yi tunda muka hadu, you are trying to change for me, what I want is for you to change for YOU. Ka gyara ba dan ni ba sai dan kanka, dan ka gyara tsakaninka da ubangijin ka. Idan Allah ya duba niyyar ka yaga cewa dan shi kake komarin gyara rayuwarka sai ya taimaka maka, amma idan ya ga cewa danni kake kokarin gyarawa sai ya barka dani ko kuma ma ya hana ka ni din gaba daya" sai yanzu naga tension din fuskarsa ya ragu, a hankali ya fara murmushi idonsa a cikin nawa yace "thank you for loving me so much. I love you too. Na miki alkawarin one day zamu zauna zan baki labari akan my drinking habit, yadda na fara da struggles din da nayi akai" na lumshe idona inajin tausayinsa a raina, oh dear sultan, what other dark secret are you hiding?" Ya sake langwabar da kai gefe yace "please mu bar maganar nan haka, OK? Dan Allah kiyi min murmushi in ga dimples dinki mana" na rufe fuskata da hannayena ina jin kunyar kallon da yake min. Daga nan muka bar maganar muka koma plans na rayuwar mu, dan yanzu gaba dayan mu munyi shirin taryan koma menene zai faru. Sultan ya yanke shawarar ba zai gaya wa babansa ba saboda yasan ba zai shiga maganar ba. Ya yanke shawarar samun uncle din shi Galadima, amma first sai ya fara ganawa da daddy na. Ni kuma na yanke shawarar samun uncle Aliyu in yi masa bayanin komai akan sultan, na yanke wannan shawarar ne saboda sanin halin daddy na, he is too smart, idan nace shi zan yiwa bayani har sai ya tono abinda bai kamata ya sani ba. Sai after ten sannan Sultan ya tafi. Ina shiga gida na tarar da mommy da Amina jigum jigum a palo sun saka uban kaya a gabansu, na karasa nima ina kallon kayan, kayan da sultan ya lodo min a America ne, dama yace zai yi shipping dinsu nan, ashe ya riga ya turo su shine yanzu ya aiko dasu cikin gida ba tare daya gaya min ba. Na samu guri na zauna ina lissafin ta ina zan fara bayani. Mommy ta ce "shi Abbakar din naki ce masa akayi in za'a zo zance tare da kayan lefe ake tahowa?" Daga ni har Amina dariya muka yi, nace "mommy kayan lefe kuma?" Tace "to in ba lefe ba wadannan uban kayan na menene? Ki kirawo shi tun kafin yayi nisa kice ya dawo ya dauki kayansa. Kema kinsan in daddyn ku yana nan ko da wasa babu wanda zai shigo masa da wadannan kayan cikin gidansa" na lankwasar da kai nace "mommy tsaraba ce fa ya taho min da ita daga America. Kuma yanzu idan na mayar masa shi namiji yaya zai yi da kayan mata? Kuma ba'a nan kasar ya saya ba ballan tana ya mayar musu" ta kalle ni tace "wato tare kuka hada plan din ku kenan. Ke kika ce ya sayo miki kenan?" Nayi dariya nace "wallahi mommy bani na roke shi ba, kuma ni bansan ma ya aiko da kayan nan cikin gidan nan ba, ko gaya min bai yi ba" ta sake kallon kayan tace "to yanzu ya kike so ayi dasu?" Amina ce tayi zumbur tace "ni dai bara in fara zaban rabona" nan ta baje kayan tana zaba, nace da mommy "kinga yanzu na huta da siyan kayan tsaraba in zamu tafi Nigeria" dama mommy ta san halina na kyauta, duk sanda zamu je Nigeria sai na kusan yiwa account dina tas saboda kowa sai na sai masa wani abu, tun daga kan tsofaffi zuwa kan jarirai, Hafsat har mamaki take yi yadda akayi nasan kowa a familyn mu duk kuwa da cewa ba tare muke ba. Tun daga ranar kullum anan gidan Sultan yake dinner kuma sosai muke kara shakuwa da juna ni dashi, ban taba tunanin cewa wani mutun zai iya yiwa wani irin son da muke yiwa juna ni da Sultan ba. Wani lokacin a gidan Hafsat muke haduwa amma sam yanzu na daina binshi yawo, ko zamu fita ma sai dai tare da Amina ko kuma da driver. A duk sanda muka hadu a gidan Hafsat in dai Zayed yana nan sai ya ta yiwa Sultan tambayoyi akan a ina yayi karatu kuma a ina yake aiki da dai sauransu. Ni har kunya nake ji tunda anyi tambayar nan ba sau daya ba ba sau biyu ba amma Sultan sam baya nuna damuwar sa sai dai yayi ta bashi amsa. Rannan dai bayan sultan ya fita sai Hafsat tace "Darling wai me yasa kake ta yiwa Sultan wadannan tambayoyin ne?" Zayed yace "wallahi na rasa dalili, kullum na ganshi sai inji tamkar na sanshi, kuma na rasa a inda na sanshi, sam babu wani guri da muka gadu dashi" Hafsat tace "kasan wadansu haka suke, kama ce kawai, maybe kasan wani mai kama dashi ne" Zayed ya girgiza kansa yace "I know him or someone that looks like him from somewhere, I just cant place my finger on it" . Kwanci tashi har lokacin bikin nuraddeen yazo. Nan muka shirya inamu2 sai Nigeria, Sultan ya riga mu yin gaba saboda wani aiki daya taso masa. Kwana biyu muka yi a Abuja muka wuce 'yalleman. Abinda nake tunani kuwa shi ya faru dani dan kowa muka hadu sai ya tambaye ni "yaushe ne naku bikin?" Ni dai kawai da dariya nake bin su. Munir kuwa kamar jela haka yake bina duk inda nayi, mutane kuwa da sun ganmu sai suce "our next amarya da ango" ni kuwa haushi kamar ya kashe ni. Kuma wai duk da muna tare amma haka nake ganin sa a gurin 'yammata, da karya da akuya kowa ya gani indai da skirt a jikinta to sai ya bita, sai dai in ya ganni ya maze kamar bashi bane ba. Sultan kuwa rikice min yayi wai lallai sai ya taho gurin bikin, a cewarsa ai shikenan sai ya gaida duk uncles dina kuma 'yan'uwana ma duk sai su gan shi, da kyar na hana shi, kuma nasan abinda yake damunsa shine yasan dole muna tare da munir, sau da yawa in muna waya in yaji muryar namiji sai ya tambayeni "waye wannan?" Sultan akwai kishi, ni har tsoro yake bani, na hana shi bina 'yalleman saboda bana son haduwarsu da munir dan ba za'a kwashe da dadi ba, na fison sai naje gurin iyayena formally kafin su hadu. Masha Allah anyi biki lafiya an gama lafiya, nayi ta yiwa 'yan'uwa rabon kaya kamar yadda na saba, nuraddeen ya gina gidansa mai kyau anan 'yalleman din inda nan zasu zauna shida amaryarsa, muna zuwa ganin gida kuwa na saba da amaryar dan itama mai son mutane ce, nan muka yi exchange din number. Ana gama biki uncle Aliyu ya kira ni palon waje, ni nasan kwanan zancen kuma na shirya. Ina shiga na ganshi shida uncle Rufa'i na gaishe su na zauna a kasa. Uncle Aliyu yace "maimunatu kinsan dalilin kiranki da nayi?" Na gyada kaina. Yace "to ya muke ciki?" Nace "Uncle da akwai wani, ina son kusa masa rana yazo ya gaishe ku. Na so ya gaida daddy tun a England amma kuma basu hadu ba, insha Allah daddy yana dawowa zai je ya same shi sai kuma yazo gurin ku kuma" Uncle Rufa'i yace "madalla, Allah ya sanya alkhairi. In yazo mun ganshi kuma zamu saka ayi bincike a kansa. Kin tabbatar shi kike so" na sunkuyar da kaina bance komai ba, yace "to Alhamdulillah. Shi kuma munir ya kuke ciki dashi?" Nace "Uncle shi Munir ai na riga na gaya masa, shi ne dai yaki hakura har yau. Ni dai uncle wannan din dai..... " yace "wannan din dai shi kike so?" Nayi shiru. Uncle Aliyu yace "kar ki damu Maimunatu, babu wanda zai miki auren dole, maganar munir zamu san yadda zamuyi da ita yadda ba za ta bata zumunci ba. Shi wannan da kike magana akansa ya sunan sa? A ina yake? Dan waye shi?" Nace "sunansa Abbakar Sadiq, A abuja yake" na danyi shiru sannan nace "dan sarkin Abuja ne" uncle rufa'i yace " ah, kice da princess muke magana" na rufe fuskata ina dariya. Uncle Aliyu yace "ban san 'ya'ya nawa ke ga maimartaba ba, amma nasan akwai wani dan sa fitinanne. Whatever dai ki kai shi gurin yaya ambassador din in ya dawo, tunda shi ya fini sanin kan Abujan. Allah yayi miki albarka" nace "Ameen, nagode uncle" . Bamu bar 'yalleman ba sai da su daddy da yaya Walid suka zo tukunna, kwanan su biyu sannan muka koma Abuja gaba daya. Ranar da muka koma a ranar Sultan ya zo. Duk gidan a hargitse yake saboda ana general cleaning da ake yi dan haka a mota naga Sultan. Ina shiga da sallama yace "look what you have done to me" na kalle shi sama da kasa nace "me nayi kuma?" Ya nuna min wuyansa, baki ga ramar da kika saka ni nayi ba" nayi dariya nace "ni banga wata rama da kayi ba Sultan, gashi nan kayi wani fresh da kai har da ajjiye tumbi" da sauri ya shafa cikinsa, ganin yana kokarin daga shirt dinsa nayi sauri na dauke kaina ina dariya, yace "please dan Allah tumbi nayi?" Nace "wasa nake maka fa" ya wani bata fuska "amma wannan ai mugun wasa ne, kinsan kuwa yadda bana son tumbi? Amma ke kinga yadda ki ka yi kiba kuwa? Dama ku fulanin nan haka kuke da wayo,sai ku tafi ruga kuje kuyi ta cin dadi,kuci kaji,kuci zabbi, kusha nono" nace "kuma muci kwai ba. Karka damu indai 'yalleman ce har sai ka gaji da zuwanta" daga nan muka koma hirar yaushe gamo, na bashi labarin yadda muka yi da uncle Aliyu, yace "daddy fa?" Nace "tare da shi muke yanzu, zan tunawa mommy ta gaya masa, sai ya baka rana ka zo" shi kuma ya bani labarin ya samu maigirma galadima da maganar, yaji dadi sosai kuma yace in dai ance ya turo iyayensa to yazo direct ya gaya masa, shi zai yi masa komai. It's like everything is falling in place, matsalata daya yadda zanyi convincing daddy ya karbi Sultan, amma shima na samu solution, project din da na rubuta akan sultan zan bashi, in yaki yadda kuma ince masa yayi bincike. Da daddare na samu mommy na tuna mata maganar Sultan nace ta gayawa daddy, tace zata gaya masa amma yace mata gobe zai koma England, da akwai wadansu takardu da zai cike amma ba zai dade ba zai dawo. Naji babu dadi amma we are ready to wait. Washegari tunda na tashi nake jin zuciya ta babu dadi. Irin feeling din da mutun yake ji idan something is wrong, nayi ta tunani ko zan tuno wani abu da nayi ba dai dai ba amma na kasa tunawa, sultan na kira na tambaye shi if he is alright, kuma daga muryarsa na gane bashi da wata matsala, jin yadda nake jin babu dadi yasa yace zai zo da yamma. Yamma nayi na shirya cikin doguwar riga purple mai ratsin pink nayi rolling pink veil, ina gama shiryawa sultan ya kira ni yace yazo, part din su ya Walid na saka aka bude masa ya shiga sannan na fita, ina shiga palon na tarar dashi ya bude fridge ya dauko drink yana sha, na tsaya ina kallonsa nace "wannan wanne irin bako ne? Daga zuwa zai bude wa masu daki fridge" ya juyo ya kalleni dan bai san ma na shigo ba, yace "waye bakon? Ni a gidan nan ai sai dai in sauki wadansu" na shiga na zauna tare da gaishe shi, ya amsa sannan ya zauna akan center table din gurin yana kallona, yace "so... What's the problem?" Nace "I don't know, kawai dai ina jin ba dadi ne, I just want to confirm if you are alright" yayi murmushin nuna jin dadin sa yace "am OK, I really am. Maybe akan tafiyar daddy ne kike feeling bad, tunda ba dade wa zaiyi ba ai babu problem ko?" Na kirkiro murmushi nayi masa. Nan ya zauna yake ta bani labarai da zasu saka ni farin ciki, in no time kuwa sai gani na ware ina dariya sosai. Yana cikin bani labarin Amir yayi wata budurwa kanuri sai kawai ji muka yi an bude kofar palon, a tare muka dago kai muka kalli kofa, ya Habeeb ne a tsaye, yadda muke kallon sa shima haka yake kallon mu, Sultan ya mike da murmushi ya doshe shi yana mika masa hannu, kallo daya yayi masa ya wuce shi ya karaso inda nake zaune a daskare, ya nuna sultan ya hannu yace "Moon me wannan yake yi a gidan nan?" Na bude baki amma na kasa cewa komai ganin yadda kamannin yaya Habeeb suka juye "I asked you a question, me wannan yake yi a gidan nan" murya na rawa nace "gurina yazo" na kalli sultan naga mixed expression a fuskarsa, na sake mayar da kallona kan yaya Habeeb wanda har yanzu ni yake kallo, yace "amma ya muka yi dake, you told me he is not your type that you are just using him for your project, ko? Rasa amsar da zan bashi nayi, na sake kallon Sultan, he is getting angry, nace "yaya Habeeb please don't do this" yace "don't do what? Ke fa kika cemin da kin gama using dinshi for the project zakiyi masa kafa, that's exactly what you told me, kuma yanzu kin gama so banga dalilin da yasa zaki cigaba da ganin sa ba, i see no reason why you should waste his time any longer" yana fadin haka ya juya ya koma gaban sultan ya tsaya yace "look man, this should be the last time da zan ganka tare da kanwata, you are not her type, ita da kanta ta fada, she was just using you for her project kuma ta gama, so ala raka taki gona" gaba ki daya kamannin sultan sun chanza, idonsa ya rikide ya zama jajawur, bai ce da yaya Habeeb komai ba sai ya karaso inda nake, da sauri na mike tsaye nace "Sultan listen to me, abinda ya fada ba haka bane, you of all people know I love you" ya Habeeb yace "bullshit" wani irin juyi sultan yayi ya danki wuyan ya Habeeb yayi baya dashi ya hada shi da bango, a zabure na karasa gurin na fara kokarin kwace yaya Habeeb nan da nan hawaye suka fara zuba a idona, hawayen da Sultan ya gani a idona ne yasa ya saki Ya Habeeb shi kuma duk da shakar da yasha amma bakinsa bai mutu ba, yace "kai kana tunanin kowa mahaukaci ne irinka? Waye kake ganin zai dauki 'yarsa ya baka?" Ya juyo kaina yace "ke kuma ki sani, am going straight to mommy" daga haka ya juya ya fice. Kujera na samu na zauna na rufe fuskata da hannayena ina kuka, ina jin Sultan ya kuma dawowa ya zauna akan center table din gaba na. Yace "Maimunatu me mutumin can yake cewa ne? Do you really told him cewa am not your type?" Na bude fuskata amma ban kalle shi cikin ido ba, ya sake cewa "what project was he talking about? Did you really write a project on me?" Nace "Sultan listen to me, duk yadda ka dauki maganar nan ba haka take ba... " ya katse ni "did you write a project on me? Yes or No" nace "yes, but... " da sauri ya mike yasa kafa ya daki kujerar kusa dani, nima na mike nace "Sultan ka saurare ni mana, I never meant to hurt you, ina taso in gaya maka ban san yadda zaka dauki maganar ba" ya juyo yana kallona, a hankali ya karaso inda nake tsaye, ya matso sosai har sai da ya hade goshin mu guri daya sannan cikin murya mai kama da rada yace "fuck you, and fuck your damn project" rintse idona kawai nayi hawaye yana zuba dan nasan babu abinda zan ce masa ya saurare ni. Ban bude idona ba sai da naji rufe kofar sa. Da sauri nabi bayan sa, kafin in fita daga palon har ya shiga motarsa ya tayar, a guje ya fincike ta dan Allah ne kadai ya taimaki mai gadin mu dan sauran kadan sultan yayi ciki dashi. Please appreciate this episode, you have no idea da yadda na yi muku typing dinsa. I know I kept you guys waiting but know that it hurt me more than it hurts you. Much love. [11/7, 2:30 PM] maryamsuleiman48@gmail.co: MAIMOON By Maman Maama Episode Fifty : Munir 2 Nabi motar da kallo har ta fice, ji kaina nake a cushe cos babu wani tunanin da yake tafiyar min dai dai. Kamar daga sama naji kara mai kama da accident din mota a waje, ko ba'a gaya min ba na san Sultan ne, bansan lokacin da naje bakin gate ba kawai nima gani na nayi a gurin, motar Sultan na gani ta daki bishiyar da take opposite din gidan mu, ji nayi tamkar zuciya ta ta fado kasa, ina ganin masu gadi suna tafiya gurin amma ni ji nayi kamar an daskarar dani, ga mamaki na sai naji ya yi wa motar key yayi reverse da ita tare da tarwatsa mutanen da suka tafi kayo masa dauki, gaba daya gaban motar yayi damage amma a haka ya sake figarta ya yau titi. Yana tafiya masu gadi suka fara surutu, 'wai yaron nan me yake kawoshi unguwar nan ne kwanannan? Kar fa yazo ya tattaka mana yara a banza kuma babu mai daukan mataki a kansa" ni dai jiki a sanyaye na koma gida. Sai da na kama hannun kofar shiga palo sannan na tuno da ya Habeeb da kuma alkawarinsa na gaya wa mommy. Ga mamaki na sai naji babu wani tsoro a zuciya ta, gwara a yi ta ta kare kowa ma ya huta, dan ni yanzu ban damu da kome za'ayi min ba, nafi damuwa da halin da Sultan yake ciki, I fear he might hurt himself, ni kuwa nasan ba za'a taba yimin wani physical damage ba. Na murda kofar na shiga da sallama, babu kowa a palon sai ya Habeeb, fuskarsa sam babu rahama a cikin ta, kallo daya nayi masa nayi hanyar kitchen, haushinsa nake ji sosai duk da cewa deep down nasan ba laifin sa bane ba laifi nane, he was only trying to protect me. A kitchen na samu Asma'u, cook din gidan nace "Ma'u ina mommy?" Tace "Mommy taje unguwa, lokacin kina gurin bakon ki, tace in gaya miki sai dare zata dawo" banji dadi ba cos I don't want to delay this any longer. Na sake fito wa na wuce ta gaban yaya Habeeb na hau stairs din part dina. Direct balcony na wuce na saka kujera na zauna. Kamar yau ne na tsaya a gurin nan ina kallon Ibrahim ya fita daga gidan nan ruwan sama yana dukansa. Can't believe it has already been six years. History is repeating it self today. Amma yanzu a shirye nake, I am no longer sixteen years old, I am twenty two. Yanzu ba yarinyar nan bace da ta gama secondary school, wannan double degree ne da ita a second best university in the world. Ba wai zama zan yi in jira abubuwa suke faruwa ba kamar yadda na zauna nayi ta jiran Ibrahim, this time I am going to make things happen. Tashi nayi na koma daki na dauko laptop dina na kunna, email na shiga na rubuta wa daddy sako kamar haka "please daddy check this out" sai nayi masa attaching da duk rubuce2n da nayi akan sultan, na tura masa. Nayi missing Hafsat, da at least in na gaya mata zan dan samu sassaucin radadin da ziciya ta take yi. Na dauko wayata nayi dialing number din sultan, matar mtn ce ta fara yi min bayanin is switched off. Wani murmushin takai ci nayi, exactly haka nayi ta kiran Ibrahim is switched off, it is funny sometimes yadda rayuwa take zuwa wa mutum. Wani tunani ne ya fado min, this is my chance na ganin sultan in tabbatar masa da cewa abinda ya dauka ba haka bane, and most importantly to find out if he is Ok. Dan nasan mommy tana shigowa gidan nan suka hadu da yaya Habeeb to ni da in kara fita sai wani ikon Allahn kuma. Kuma nasan duk bayanin da zan mata ba zata fahimta ba da taji bayanin abbakar din da nake gaya mata Sultan ne shikenan zata toshe kunnuwanta daga dukkan baya ni na. Amma still it will be better in ni na fara gaya mata. Na dauko waya ta nayi dialing number ta, ta dauka suna ta hayaniya a gurin tace "Moon ya akayi ina gurin taro ne, akwai wani abu ne?" Nace "mommy akwai maganar da nake so muyi ne" tace "am very busy yanzu, can't it wait sai na dawo?" Nace "Ok mommy, sai kin dawo din" na ajiye wayar a raina nace "why is everyone not available when I needed them the most?" Ina daki har aka kira magrib ina ta kiran sultan har yanzu switched off, in ma nace zan fita neman sa bansan inda zan same shi ba, to ko gidan su zanje? Tunda gidan babba ne maybe har in fito babu wanda zai san na shiga? Amma fa ni ban taba shiga palace ba, in naje ma bansan inda zan dosa ba. Na tashi nayi alwala nayi sallah na zauna ina adduoi na naji karar wayata, ban dauka ba sai da na kammala, na dauka baga bakuwar number, ina kokarin dialing wani kiran ya sake shigowa, na daga da sallama. "Maimunatu Amir ne, kina ina?' Ji nayi gaba daya yawun bakina ya kafe nace "Amir ina Sultan?" Ya sake cewa "kina ina?" Nace "ina gida, me yake faruwa?" Ya danyi shiru sannan yace "ina gida dazu wani friend din mu ya kirani yake gayamin yaga Sultan a bar, he seems to be injured, to shine naje gurin na same shi, he is injured kuma yaki tashi in kaishi asibiti" da sauri nace "how bad is it?" Yace "not that bad, kawai dai kafarsa ce, kuma tana bleeding har yanzu. Sultan taurin kai ne dashi, ban sani ba ko ke in kika yi mishi magana zai tashi, he has been drinking also" a raina nace "nasan za'a rina, an saci zanin mahaukaciya" ya katse min tunani na da cewa "can you come, please?" Na ce "of cause I will come. Kuna ina?" Yayi min kwatance, nace amma kuma fa ban iya driving ba, bana so kuma in dau driver, ko kuma zuwa zakayi ka dauke ni?" Yace "alright gani nan zuwa" tashi nayi da sauri na chanja kaya zuwa wani material simple doguwar riga, nayi rolling veil sai kuma na saka dogon jihab, na sauka kasa, yaya Habeeb ya tashi daga inda yake dazu ina jin masallaci ya tafi, na samu Asma'u tana shirya dining nace mata "Ma'u kinga kaina ne yake ciwo, na sha magani yanzu zan kwanta, please in mommy ta dawo ki gaya mata ina kwance banjin dadi" da sauri tazo ta dafa goshina, "oh oh, sannu mai sunan daada, gashi nan kuwa jikin ki ya fara zafi, Allah ya sawake" nace "Ameen" na koma kamar na hau sama sai nabi ta kofar baya na fita, ina fita Amir ya kirawo ni yace gashi ya zo, na zagaya ina buda securities, dama in daddy baya nan basu da yawa, guda biyu kawai na hango tare da baba Habu a can gefe a zaune, sai da na zagaya ta side din da ba zasu ganni ba sannan na shige seat din baya na durkusa a kasa yadda wanda yake waje in dai ba lekowa yayi ba ba zai ganni ba. Ina jin baba Habu yana tambayar Amir "har ka karbi sakon?" Shi kuma yace masa eh sannan muka fita. Sai da muka hau titi sannan na zauna sosai ina tambayar Amir "ya jikin Sultan" ya yi murmushi mai sauti yace "He is lucky to have you. Da sauki jikinsa, so nake kawai ya tashi in kaishi ayi dressing kafar kar ciwon ya zama infected kuma a tsayar da jinin" nayi shiru ina lissafi, wannan fitar da nayi ni kaina nasan I am playing a very dangerous game, saboda na bawa mommy damar yadda da duk abinda za'a gaya mata, amma kuma bazan iya barin Sultan ba alhalin yana bukata ta. Wani hotel muka shiga, sannan muka bi ta bayan building din muka tsaya a wani karamin packing space. Ga wanda bai san gurin ba zai dauka babu komai a gurin, amma sai naga mun doshi wata kofa, Amir yayi knocking wani ya leko ya kare mana kallo sannan ya bude muka shiga, wani dogon corridor muka bi muka sake shiga wata kofar sai gamu a wani katon guri. Ga mutane nan birjik kowa yana abinda yaga dama, kowa ka gani da kwalba da cup a hannunsa, wasu da 'yammata wasu kuma su kadai. Fitulun gurin duk dim ne marasa haske. Oh ni maimunatu wai yau nice a gidan giya? Lallai soyayya babu abinda bata sakawa. Tun kafin mu karasa inda yake na gane shi duk kuwa da juya bayansa da yayi yana kallon bango, light blue din wandonsa yayi staining da jini, a hankali na karasa na jawo kujerar kusa dashi na zauna. Da sauri ya juyo ya kalleni sai kuma ya dauki kofin gabansa ya shanye abinda yake ciki sannan yace a hankali "damn you Amir" ya janyo kwalbar da take gefensa ya sake cika kofinsa sannan yace ba tare da ya kalleni ba "what are you doing here, this is no place for a girl like you" nace "it is also no place for someone like you, dan kai nazo kuma na tabbatar ba zaka bari wani abu ya same ni ba" murmushi yayi me kama dana takaici sannan yace "what do you want?" Nace "first ina so in gaya maka cewa I love you, all of you, sannan na biyu ina so in gaya maka cewa wannan mutumin da yake zaune a gaba na yana shan alcohol is not sultan, it is what you think you are but it is not who you really are" yace "ta ya akayi kika sani? Kinfi ni sanin kaina ne? This is what I am, this is what I have always been" na girgiza kaina nace "no, ba haka bane, wannan shine abinda mutane suka saka ka mayar da kanka" ya danyi shiru sannan ya sake daga kofin gabansa yayi masa kurba daya yana yamutsa fuska. He looks calm, so peaceful, fuskarsa sam babu damuwa, muryarsa kuma a nutse yake magana. Sai da ya ajiye cup din sannan yace "kin san wani abu?, ranar da muka hadu dake na dauki alkawarin bazan taba barin kisan ina shan giya ba, ballantana har ki ganni ina sha" ya daga kafada yace "I was a fool, ban taba wishing for something na samu ba amma na saka ran cewa zan samu wannan wish din. Now here we are" na hadiye wani abu da ya tsaya min a makogwaro nace "wannan bai chanza komai ba a tsakanin mu, kamar yadda nake so abinda ya faru dazu kar ya kasance ya chanza wani abu a gurinka" ya juyo yana kallon cikin idona yace "idan da akwai wani abu da nake da tabbas dinsa a rayuwa shine I will love you, till my dying day. Amma nasan you are just another dream a gurina, and my dreams never come true" nace "wannan mafarkin zai tabbata Sultan, I will fight for us, amma ina bukatar kaima kayi fighting for us. Abinda zaka fara yanzu shine ka ajiye kwalbar hannunka, ka tashi muje a duba kafarka" bai ajiye dinba kuma bai tashin ba, har zan sake magana sai yace "me yasa baki gaya min zancen project dinki ba?" Na sunkuyar da kaina kasa na fara magana "lokacin da aka bani project din ban sanka ba, daga baya muka hadu dakai, ranar da ka fara kaini gidan su Amira muka biya ta wata unguwa har na samu labarin orphanages din da ka gina kuma kake running da kuma irin taimakon da kake wa marasa hali sai naga kafi fitting topic dina, a lokacin na fara rubutu na, I was already in love with you then, nayi tunanin yin rubutun akanka zai sa in kara fahimtar ka sosai, I never meant to hurt you. Ina ta so in gaya maka kullum but ina tsoron yadda zaka dauki abin. You are not an easy person, you easily lost your temper" ya dakatar dani yace "have I ever loose my temper with you?" Na girgiza kaina dan ko mugun kallo Sultan bai taba yi min ba. Na cigaba "tun ranar dinner din Hafsat da ka je Ya Habeeb ya gan mu tare yayi min warning kar ya sake gani na da kai, a lokacin nace masa 'u are not my type' saboda ni kaina a lokacin bansan zan so ka ba saboda a lokacin ban sanka ba. A England ma ya sake ganin mu a Oxford, he threatened me cewa zai gaya wa mommy kuma nasan in har ya gayawa mommy ba za'a barni in sake ganin ka ba. Na ce masa 'I was using you for my project' ne saboda in kara samar mana lokaci together" sai kuma na kasa ci gaba da maganar na rufe fuskata da hannuna ina hawaye sanin lokacin da na samar mana ya kare yau, dan maybe already mommy ta koma gida by now, maybe already sunyi magana da yaya Habeeb. Bai rarrashe ni ba sai ya sake kiran bartender ya karo masa wata kwalbar, yana ajiyewa na dauke na ture ta gefe nace "please Sultan me kake son yi ne? So kake ka kashe kanka?" Idanunsa sunyi jajur, amma abin mamaki banda jan idon babu wani abu da zai nuna maka cewa a buge yake, he seems totally in control of himself. Bai karba ba ya kara zama yace "rannan na miki alkawarin zan baki labarin yadda na far shan giya" ban amsa ba shima bai jira amsa ta ba ya cigaba da magana "ina da shekara goma kakana ya rasu, bayan an yi nadin sarauta babana, Hajiya da sauran siblings dina suka dawo palace, su kuma su yaya da sauran matan kakana sai akayi musu sababbin gini a bayan palace din suka koma can. Ina jin labarin tarewa a sabon waje na fara tattara kayana nima saboda nayi zaton dani za'a tafi, tunda dasu yaya na saba, ban saba da Hajiya da su Abbas ba. Amma ranar tarewa tana zuwa sai akace ban dani, wai Hajiya tace a barni saboda in saba da 'yan'uwana, nan na dasa rigima lallai ni ba zan zauna dasu ba. Sai da Yaya ta kirani ta zaunar dani tayi min bayanin cewa an ce in zauna ne saboda in saba da babana nima yake kula ni kamar yadda nake so, ina jin haka na fara murna nima zanyi family. Sai daga baya na fahimci ba haka bane, ba wai rashin sabo ne ya saka baya kulani ba a'a ni din ne baya so. Gaisuwata da safe baya amsawa, baya cin abinci dani kamar yadda yake ci da abbas, ko dariya yake dana zo gurin zai bata rai. A lokacin abinda ya fi komai bata min rai shine, kullum in zaije fada zai saka a shirya Abbas, a saka masa manyan kaya da rawani da alkyabba, su tafi tare, amma ni bai taba ko tunani zuwa dani ba. Kullum in aka dauki abbas aka barni sai na hargitsa gidan nan dan bacin rai, in farfasa glasses din windows da duk abinda tsaho na zai kai, next thing duka ne zai biyo baya, ko kuma a sakani a daki a kulle ni. In nayi buge2na na gaji sai in zauna in hada kai da gwuiwa inyi ta kuka, I am four years older than Abbas, ni a gani na ni ya kamata baban mu ya kai fada ba Abbas ba, duk sanda aka saka mishi kayan sai inyi ta sha'awa dan nawa wanda nake sakawa sanda kakana yana da rai ma duk Hajiya ta karbe ta bashi tace min sunyi min kadan za'a sayo min sababbi, har yau ba'a sayo min ba. Wata rana ina ta gursheken kukana Hajiya ta aiko akayi kirana dakinta, cikin bedroom dinta, ta tambaye ni tace in gaya mata me nake so, nace mata inaso babana ya soni kamar yadda yake son Abbas, tace min to zata bani maganin da zan ke sha wanda zai saka ya soni fiye da Abbas din ma. Ta dauko shi a kwanba ta zuba min a kofi tace in sha, na dauka da murna ta na shanye, babu dadi amma haka nasha saboda ina son Takawa ya soni, banji dadin taste din ba amma naji dadin feeling din da ya saka naji, zuciya ta naji tayi min dadi, babu bakin ciki ko bacin rai sam, sai wani nishadi da nake ji, I felt very calm and happy. Tun daga nan kullum sai ta aiko naje nasha, ni kuma ina jin dadin yadda nake ji in nasha din, daga baya ma sai ya zama ni nake zuwa da kaina in raina ya baci ince ta bani magani insha, tace min inyi mata alkawarin ba zan gayawa kowa ba ni kuma nayi mata. A hankali na fara zama less active, kullum sai bacci ko kuma in zauna inyi ta kallo ko tv game, wanda da ba halina bane cos I was very energetic child, Amir ne ya fara lura sai ya gayawa Hajiya yace akaini asibiti fa, bani da lafiya tace masa to amma yaga shiru ba'a kainin ba, hakan yasa ya shirya ya tafi gurin yaya ya gaya mata cewa bani da lafiya kuma anki kaini asibiti, babu shiri yaya ta taho cikin gida tazo ta tarar dani ina bacci, jikina babu zazzabi amma nayi weak babu karfin da ta sanni dashi da. Nan ta samu hajiya ta tambaye ta sai tace ai na samu kulawa ne da tarbiyya shi yasa na nutsu, ita kam yaya bata yadda ba saboda tasan yaro mai fitina daban yake da yaro quite, I was never quite and calm dan haka lokaci daya ba zan zama ba. Ta daukeni ta tafi dani gurinsu da sunan zanyi week end acan, kwana na daya na rikice musu suka rasa kaina, daga baya dai nace ni aje gurin Hajiya a karbo min magani na, nan yaya ta saka ni a gaba da tambayar wanne irin magani har dai na gaya mata. I was young then, ba zan iya tuna duk abubuwan da suka faru ba amma dai nasan an yi rigima sosai da yaya, ni dai rigima ta daya ce, a bani magani na. Hajiya ta daina bani, but I was already addicted to it. Ita kadai take calming dina down duk sanda nake tantrums dina. It still does. Duk sanda raina ya baci ita nake sha inji zuciya ta tayi sanyi. Ba abinda rannan kike cewa bane rannan, it doesn't make me do things, it calm me down and stop me from doing things. A lagos kuma su masu kula da mu su nake bribing su kawo min, wani lokacin ma da kansu suke bani saboda in nayi bacci shikenan sun huta da fitina ta. Sanda aka kaini America kuwa tamkar an bani ticket ne, hankali na kwance babu me cemin kar inyi. Sai da na shiga university sannan na fahimci tana hanani karatu, ni kuma a lokacin ina son karatu saboda in faranta ran babana. A lokacin na fara ragewa dan kaina, ya zama bana sha sai in na zama really frustrated yadda ba zan iya controlling anger dina ba. Bayan na hadi dake kuma I cut it down to zero, saboda in raina ya baci da munyi waya dake zan manta da bakin ciki na, I returned to it sanda muka rabu a America but tunda muka dawo ban kuma sha ba sai yau." yayi shiru yana kallon cup din hannunsa kamar mai studying dinsa. Na saka hannayena na juyo da fuskarsa gurina, still ban cika fuskar ba nace "alcohol doesn't give you calmness sultan, it makes you think it gives you calmness. Haka giya take, shi yasa take addiction ce, zata baka feeling din da kake so saboda ka cigaba da shan ta. Do you believe in destiny Sultan?" Bai bani amsa ba kallona kawai yake yi, nace "I know you do, I strongly believe that we are destined to be together. Zayed ya taba gaya min wata magana rannan wacce kuma na yarda da ita, yace people with good heart da suke suffering a rayuwa are destined for greatness, suffering din da suke yi is like a test da Allah yake musu dan yaga how good they are. Sultan I strongly believe that you are destined for something great" kallona kawai yake yi da jajayen idonsa, amsar daya bani itace "can I kiss you now?" a raina nace 'he is really drunk' a fili nace "no" ya daga kafada yace "OK" sai ya kifa kansa akan table din gabansa. It is time for me to get him out of here, na tabbata mommy ta dawo yanzu, hope dina kawai in taji bani da lafiya maybe ta bar maganar sai safe. Na fara waige waigen Amir wanda sai yanzu na tuna dashi, babu shi babu alamar sa, na bar waya ta a gida ballantana in kira shi, ina Amir when I need him the most? Na tambayi Sultan "ina wayarka?" Idonsa a rufe yace min "Amir" haka ne da ita muka yi waya da Amir. Nace "Sultan tashi mu tafi, am getting you out of here" ya dago kansa idonsa sun kara ja yace "can't stand" tashin hankali, ta yaya zan iya daga sultan, I really need to go back home kuma ba zan iya tafiya in bar sultan a haka ba. Dole somehow in fita dashi waje, fresh air zata danyi clearing head dinsa, daga nan sai in samar masa taxi a kaishi gida, nima kuma in nemi taxi zuwa gida. Na saka hannu a aljihunsa na dauko kudi, roll ne na 1000 notes, na dau guda biyu na mayar masa da sauran. "Sultan try standing up please" ya gwada, nasan kafarsa tayi tsami yanzu, da kyar ya dafa table din ya mike yana cije lebe, yanzu saura tafiya kuma, na a side din kafarsa mai ciwon na ce masa ya dafani mu tafi. Sai da muka fara tafiya sannan nayi nadama, he is very heavy, gashi duk ya sakar min jiki kaman ma naya sane. Sai na muka huta sau bixu kafin mu zo gate. Muna fita gate din na fara rarraba idon inda zanga taxi, nace "Sultan zan saka ka a taxi za'a kaika gida, inna je gida zan kira Amir in gaya masa ya kira doctor ya duba kafar ka sosai. Ana barin taxi ta shiga palace?" Uhmm kawai yace, good, tunda yana gane me nake cewa. Wata mota ce ta wuce mu har na fara daga hannu sai na lura ba taxi bace na sauke hannuna. Har tayi gaba sai tayo baya kuma, good, maybe it's Amir, tayi packing a gaban mu aka bude kofar da sauri aka fito. "Moon? Is that you?" Na saki baki ina kallon me maganar, Munir. Na kasa rufe baki na ballantana in yi magana. Ya karaso gaban mu, da sauri ya toshe hancinsa. "Moon waye wannan? Me kike yi a gurin nan da daddaren nan? Are u drunk?" Tambayoyin da ya jero min kenan. Sai a lokacin na fahimci what we looked like, kusan rabin sultan a jiki na yake, gaba dayansa warin giya yake dan haka nima warin nake, yadda muke tafiya kuma babu wanda zai ce ba'a buge muke ba gaba dayan mu. A hankali nace "listen Munir, this is not what you are thinking" Sultan naji daga gefena yace "Munir? " Hmm. Things seem to be going very badly for Moon. [11/7, 2:31 PM] maryamsuleiman48@gmail.co: MAIMOON By Maman maama Episode Fifty one : Mommy Nayi kokarin raba jikina dana Sultan wanda da kyar ya tsaya. Munir ya kara matsowa yana kare mana kallo, dogon hijab dina duk ya chukuikuye yayi squeezing yace "dama abinda kike aikata wa kenan shi yasa ko waya nayi miki ba kya dauka, haka ne fa ya saka na shirya na taho abujan da kaina dan inga me yake faruwa. Ashe abinda kike aikatawa kenan har ake yi min gorin baza 'a bani ke ba dan kin fini tarbiyya? Ina tarbiyyar take anan? I wish uncle Aliyu zai ganki a yanzu sai ya gane tsakani na dake wa ye marar tarbiyyar" da kyar na bude baki nace "Munir kar ka adar da batun da baka tabbatar ba, I was only trying to help him, shi kenan taimako kuma sai ya zama laifi?" Yace "waye shi? Menene tsakanin ki da shi?" Nace a fusace "what is your problem with that?" Sultan ne naji yace "I am her husband to be, ko kana da abinda zaka yi akai?" Wata harara Munir ya watsa masa yace "da masu hankali nake magana ba da bugaggu ba" da sauri Sultan ya yunkura zai kai masa duka nayi sauri na rike shi, nasan a yadda sultan yake a yanzu Munir duka zai yi masa dan gaba daya alcohol din ta zuke karfin sultan. A fusace Munir yace "cikashi kizo mu tafi" nace "am not leaving him here" da mamaki kawai ya tsaya yana kallona yama rasa me zai ce min. Wata taxi ce ta tsaya a gaban mu Amir ya fito da sauri ya karaso in da muke, yace "Moon ya akayi kuka fito nan, what if someone sees you?" Sai kuma ya juya ya kalli munir yace "waye wannan kuma?" Takaici bai barni na bashi amsa ba, nace "ina ka tafi? Dare yayi sosai, I needed to go home, ba zan iya tafiya in bar shi ba, babu wanda na sani a ciki ballan tana in nemi taimako, ina ka tafi?" Kamar zaiyi kuka yace "am so sorry Moon, na dauki motar da Sultan yayi accident da ita niyya ta in kaita gida sai in dawo in dauke shi a mota ta, na hadu da police a hanya sunga damage din da motar tayi suka tare ni suna ta yimin tambayoyi, sai da naje station nayi cike cike sannan suka barni na tafi, I thought zaki kira ni a waya ma, dan Allah kiyi hakuri" nace masa "ai babu waya a hannuna, wayar sultan kuma tana hannunka" ya kuma kallon munir da har yanzu yake tsaye yana sauraren mu yace "waye shi?" Da takaici nace "shine wanda akayi alkawarin za'a aura min a gida" Amir ya dora hannunsa aka yace "ya Salam, am so sorry Moon" Munir yace "are you guys done? Saboda na matsu muje gida inji bayanin da zaki yi musu" nace "ni ba zan shiga motar kaba, ai ba tare muka zo ba, kayi tafiyarka kawai" wani murmushin mugunta yayi sannan ya dauko wayarsa ya fara dannawa yace "in ba zaki shiga mota taba, bara in kira wanda dole ki shiga tasa" kafin inyi wani yunkuri naji yana cewa "Hello Walid kana ina? Guess wa na gani yanzu? Moon. Au dama nemanta kume yi? a buge na ganta a hannun wani gardi suna ta marisa a gefen titi. To shikenan in baka yarda ba kazo ka gani da idonka." Daga nan ya fada masa inda muke ya kashe wayar. Har yanzu murmushin nake yace min "mu zuba ni da ke mu gani, lets see idan gobe ba'a daura mana aure ba" Kaina naji yana wani irin juyawa, idona har wani dishi dishi nake gani. Wata zuciyar tace min in kwashi takalma na a hannuna in fita a guje, wata kuma tace min in dauki halin Sultan in rufe Munir da duka. Na juya na kalli Sultan idona cike da kwalla, daga ganin sa kasan zuciyarsa tafasa kawai take yi amma babu karfin yin wani abu akai, a raina nace 'daga yau zaka fara fahimtar illar shan giya'. Amir kam gaba daya hankalinsa ya tashi, da sauri sauri ya wuce ya shiga cikin hotel din can sai gashi ya dawo da motar sa. Ya bude kofa yazo zai kama Sultan amma sultan ya tubure yaki tafiya, nace "Sultan ku tafi gida kafin yaya walid yazo ya same ku" na juya gurin Amir nace "Amir ka kira doctor din palace sai ku hadu dashi a can ayi dressing kafar" Sultan ya rike hannuna yace cikin gaskararriyar murya "I am not leaving you here, gurin nan bashi da kyau, and am not leaving you tare da wannan mutumin" na rike hannunsa nima, a raina ina jin tamkar wannan shine gani na karshe da zan yi masa a rayuwata. Sam babu kwalla a idona nace "Sultan kayi min alkawarin ko ina nan ko bana nan wannan itace rana ta karshe da zaka kuma shan giya, kayi min alkawarin duk sanda ranka ya baci zaka rungumi alqur'ani not alcohol. Sultan please promise me that you will fight for us, bawai fada zaka yi ba, show people your true self wannan shi kadai zai saka a baka ni. Please sultan, ka manta da zancen destroying family name dinka, koda ba za kayi dan kanka ba, do it for me and for our unborn children, tunda in dai na aureka shi family name din naka shi ne dai sunan da zamu yi bearing ni da 'ya'yan mu" ya saki hannuna daya ya jawo ni jikinsa, ina jin yadda zuciyarsa take bugawa da karfi a kirjinsa, a kunne na ya rada min "please don't leave me, let's runaway together, let's go back to America" nayi kokarin kwace jikina ya kara rikeni "please, I can't live without you" na zame jikina ina girgiza kaina nace "no Sultan, guduwa ba shine solution ba, solution shine mu samu albarkar iyayen mu, in muka gudu ba zamu taba ganin dai dai ba a rayuwar mu" duk da irin son da nake wa Sultan, bazan taba iya guduwa daga gurin iyayena ba, duk da nasan irin abinda yake jira na a gida amma nasan abinda zan fuskanta inna gudu sai yafi wannan, ni ina ji a jikina cewa fitowar da nayi ba tare da sanin iyayena ba shi ya zawo komai ya kara chakude min. A ganina worse abu da 'ya zata yiwa iyayenta shine ta gudu ta barsu, duk duniya babu wanda yake son ki ko kuma wanda zai soki sama dasu, in kika gudu kika bar su kullum zasu zamo cikin tashin hankalin rashin sanin halin da kike ciki, wannan tashin hankalin nasu kuma ba karamin bala'i bane a gurin ki. Tun daga nesa na hango motar ya Walid ta shigo layin, Sultan ya kara rikon da yayi wa hannu na, na kalli Amir nace "take care of him please". Yana zuwa yayi packing ya fito yana bin mu da kallo daya bayan daya, idonsa ya sauka akan hannayen mu ni da sultan. Munir ya karasa gurinsa yana cewa "kaga ni ko? Yanzu ka yarda da abinda na gaya maka? A rungume take a jikinsa ma ganin ka ne ya saka ya sake ta" ya Walid bai ce masa komai ba ya karaso in da muke tsaye ni da sultan, kallo daya yayi wa Sultan ya dawo da kallonsa kaina, muna hada ido na sauke kaina kasa amma na kasa cika hannun Sultan. Wani wawan marin da ban taba tsammanin ya Walid zai min ba shi ya sakar min, sai da na dena gani for some seconds, taste din jini naji a bakina, ina dago kaina naga ya sake daga hannu zai kara min wani, na runtse idona ina jiran saukar marin, wannan karon nasan completely zan karasa makancewa. Jin marin bai karaso ba yasa na bude idona dan ganin abinda ya tare shi. Hannun Sultan na gani rike da na yaya Walid, ba zan iya kwatanta expression din fuskar saba, murya can cikin makogwaro yace "don't you dare hit her again" da dayan hannun ya Walid ya wanka wa Sultan shima na shi rabon, daga ganin marin nasan yafi nawa karfi dan sai da sultan yayi baya kamar zai fadi Amir ya rike shi, sannan yaya Walid ya nuna shi da hannunsa yace "an dake ta din, me zakayi akai?" A raina nace 'ayyah ya Walid, dan dai Sultan ba dai dai yake ba da yau sai ka kwanta a asibiti' ban dawo daga tunani na ba naji ya Walid ya damki gashina ta cikin hijab daga baya ya fara jana, wata azaba naji tamkar zan saki fitsari a wando, a haka ya jani har mota, inajin Sultan yana kwalla min kira amma zafin rikon da ya Walid yayi min ya hanani magana, kafin mu karasa mota Munir ya bude kofar baya, ya Walid ya watsa ni ciki tamkar kayan wanki ya mayar da kofa ya rufe, ina jinsa ya tada motar ya ja muka tafi. Sam babu hawaye a idona sai fuskata data kumbura side daya. Muna tafiya wayarsa tayi kara ya dauka yace "Hello mommy gamu nan mun taho, she is OK but sai munzo dai" Ina jinsa yayi horn aka bude mana gate muka shiga gida, yana packing ya zagayo ya bude kofar baya ya ya fito dani, he half drag me zuwa palo, muna shiga ya watsar dani flat a tsakiyar palon. Ban dago kaina ba ballanta na in san suwaye a palon. Muryar mommy naji tana magana a nutse tace "ka gayawa daddyn ku?" Ya Walid yace "a'a, naga yanzu a can cikin dare ne shi yasa na bari sai da safe tukun na" mommy tace "ka barshi, ni zan gaya masa" yace "Ok mommy" yadda take maganar a nutse ne ya bani mamaki sabida nayi zaton kafin muzo zan tarar ta hargitsa gidan gaba daya. Na dago kaina ina kare musu kallo, mommy tana tsaye a tsakiyar palon ta rungume hannayenta, daga can gefe daada a kan kujera tana ta sharbanen majina, Ya walid yana tsaye shima a kusa da mommy, ya Habeeb yana zaune daga bayana. Mommy ta kura min ido tana kallona sannan tace "kai ka dake ta ne?" Ya Walid yace "eh" sannan tace "Habibi kira David kace asa muna bukatar karin securities a gidan nan, kace masa nace munyi receiving threats, duk wanda suka ga zai hauro mana su harbe shi" wata muguwar faduwa gaba na yayi, na mike zaune daga kwancen da nake. Ta cigaba da magana tana zagaya palon, tace "ina da labarai da yawa akan yaron nan, he is capable of doing anything, nasan zai iya yayi attempting shigowa ya dauke ta. Yazo har gida ya dakar min da, sannan ya dawo yayi kidnapping yarinya ta, in ya sake dawowa for the third time ina da right din da zan saka a harbeshi in self defense" cikin rawar murya nace "mommy he did not kidnap me" marin da dazu yaya Walid bai karasa min ba shi yayi min yanzu, wannan karon kunnena ne naji ya dena ji, sanda na dawo hayyacina a kwance na ganni again. Daada ta kara sautin kukanta kamar ita aka mara. Sama sama naji mommy tana yiwa ya Walid fadan kar ya sake dukana, tace "duka is not a solution to kangararrun yara" kalmar kangararruce ta tsaya min a raina, wato nima yanzu na shiga layin kangararru kenan. Na kuma tashi na zauna ina jinsu suna ta plans na security, a raina nace 'indai sultan yayi niyyar shigowa gidan nan sai ya shigo, but I don't think he is coming, not today' Mommy ta kalleni tace "tashi ki tafi daki" na mike sum sum2 nayi hanyar stairs sai kuma tace "ah ah ah, bani wayoyinki" na nuna mata hannayena nace "ban fita dasu ba dama" tace "Habeeb bita ta baka ka kawo min, manyan wayoyinta guda biyu da karamar Nokia, da laptops dinta biyu, ta hado maka da ATM cards dinta guda biyu suma. Kayi locking kofar balcony dinta sannan in ka fito ka rufe kofar dakin daga waje ka taho min da keys din" mommy is surely harder than steel, tun ina yarinya nasan she is thorough a duk al'amuranta. Muna shiga daki na bawa yaya Habeeb duk abinda mommy tace, bai ce min komai ba ya rufe kofar balcony ya zare key din, ko kallo na baiyi ba ya kwashi kayan ya fita sannan yayi locking kofar daga waje. A gaban gado na durkushe fuskata tana min radadin marin da nasha. Na kusa kaina a tsakanin kafafu wana ina neman kuka amma yaki zuwa. Wani zafi nake yi a kirjina. Kamar yadda na saba duk sanda nake jin irin wannan yanayin sai na fara kiran sunayen Allah 99 a fili amma a hankali, kafin in kai karshe naji raina ya danyi sanyi. Hijab din jikina wanda gaba daya warin giya yake na cire na shiga toilet nayo alwala nazo na yi sallar isha sannan na dauko alqurani na na fara karantawa a hankali, wata nutsuwa ce take shigata a hankali, kamar some kind of assurance cewa everything is going to be alright. Sai da naji muryata ta fara dashewa sannan na rufe alqur'anin na kwanta a kusa dashi, na ki barin zuciyata tayi tunanin sultan saboda kaina ba zai iya dauka ba. A hankali bacci ya fara daukana. Ana kiran assuba na tashi na fara kawo nafiloli sannan da akayi assalatu nayi sallar assuba amma da nazo yin addu'ah sai na rasa me zance, what if Sultan ba shine alkhairi a gare ni ba, ko kuma nima ba nice alkhairi a gare shi ba? Dan haka kawai sai na yi addu'ar Allah ya bamu ikon cin dukkanin jarabawar da zai yi mana, ya bamu karfin zuciyar daukan ko menene zai taho mana kuma ya zaba mana mafi alkhairi a duniya da kuma lahira. Da gari ya waye ina kwance a gado naji an bude kofar dakin, nayi sauri na mike zaune, mommy ce ta shigo sai mai aiki a bayanta, a ajiye tray da abinci a ciki ta fita, na ce "mommy good morning" ba tare data kalleni ba tace "ki tashi ki ci abinci" daga haka ta fice tare da rufe kofar. Tunda nazo duniya yauce rana ta farko da na gaida mommy bata amsa ba, It feels really bad, wato haka Sultan yake ji kenan tunda yazo duniya. Ban kalli in da abincin yake ba na cigaba da kwanciyata har zuhr tayi. Ina zaune a kan sallaya aka sake bude kafar, wannn karon Asma'u ce, tajiye trayn hannunta ta kalli na safen da ko taba wa banyi ba. Tace "mai sunan daada ki ci abinci mana? Ya za'ayi mutun ya zauna babu abinci?, murmushi kawai nayi mata na cigaba da jan charbi na. Bata dade da fita ba aka sake bude kofar, wannan karon mommy ce ita kadai. Ta zauna akan bedside drower sannan tace "tashi kici abinci" banyi mata musu ba na dauko trayn ba bude na zuba abincin na fara ci, sam ji nake abincin babu taste amma haka nake hadiyewa da kyar, ina gama cin abincin ta dauke trayn ta fita ta rufe kofa. Sai da akayi la'asar sannan ta dawo, yanzu ma ina kan sallaya ta zauna akan bedside tace "zo nan" na mike naje gabanta na tsugunna, tace "tashi ki zauna a kan gado, ba musu na tashi na zauna ina kallon kasa tace "Maimoon ina so ki gaya min gaskiya, in kika yi min karya abinda zanyi miki sai yafi wanda nayi niyya" a hankali nace "to mommy" tace "tun yaushe kuke tare da Sultan?" Nace "tun bikin Hafsat" tace "shekara daya kenan?" Nace "eh" ta gyada kai tace "good, yaushe ne kuma ya fara koya miki shaye shaye?" Da sauri na dago kaina ina kallonta "mommy nice fa, Moon ce fa mommy" ta dauke kanta tace "I don't know you anymore, Moon din dana sani ba zata bi saurayi gidan giya ba, Moon din dana haifa na raina ba ita ce wannan a gaba na ba. Just answer the question" sai yanzu sannan hawaye suka zo idona, na rufe fuskata da hannayena ina kuka, ta sake cewa "just answer the question, tun yaushe yake kaiki bar?" Nace "wallahi mommy ban tana shan komai ba. In baki yarda ba kisa ayi min drug test" tace "OK, ina son ki gaya min komai and I mean everything da ya faru tsakanin ku" nan na fara bata labarin tun haduwar mu dashi a abuja har komawar mu England shima ya bi mu, sannan na bata labarin bina da yayi America da duk abinda ya mu kayi a can amma na cire labarin abinda ya faru ranar da zan dawo, oh no I can never tell her that, sannan na bata labarin dawowar mu Nigeria da plans din mu na kai maganar gaban iyayen mu, na gaya mata kuma abinda ya faru tsakanin su da yaya Habeeb da kuma bin Amir da nayi zuwa gurin sultan. Na kara da cewa "mother, he is not a bad person, he is a good person. Dan Allah ku tsaya ku fahimce shi" ta yi ajjiyar zuciya tace "you are not as smart as we all thought you are, moon he is playing you. Mutane irinsa abinda suke yi kenan, su samu yarinya kamarki su yaudare ta su bata mata rayuwa suyi dumping dinta. Tunanin ki bai taba baki cewa duk wadanda suke zuwa suke baki labari akansa shi ya ke turo su ba?" Na girgiza kaina nace "mother this is for real, wallahi da gaske ne, I trust him" ta mike tsaye tare da ajjiyar zuciya tace "Maimoon, you are no longer allowed to see or talk to Sultan in dai na isa dake" na fado daga kan gadon na rike kafafuwanta, ina kuka nace "Mommy kiyi min rai, mommy wallahi in kika raba ni dashi mutuwa zanyi, purnish me duk yadda kike so dan Allah karki raba mu" ta kwace kafarta taje bakin kofa tace "you really have no idea about your situation. Already munir yayi waya 'yalleman ya gaya musu abinda ya gani jiya, it is just a matter of time kafin baffa ya turo a bincika masa, so you really understand why I want you as far away from sultan as possible? He is who he is and you are who you are" ta bude kofa ta fita ta barni a durkushe a gurin. Innalillahi wa inna ilaihir rajiun. Allahumma ajirni fi musibati wa aklifni khairan min ha. I can only imagine yadda Hajja zatayi ta yawo da maganar nan. Allah ne kadai yasan irin karyar da munir ya kara akan abinda ya gani din. Na dafe kaina daya fara sara min. Washe gari da assuba mommy ta shigo da breakfast a hannunta ta saka ni a gaba na ci, sannan tace in tashi inyi wanka, naje naji na fito na tarar ta ajiye min kaya har da underwears akan gado tace in saka, a raina nace ina zamu je kuma da sassafen nan? Ni dai na shirya na zauna ina kallonta, ta kalleni cikin ido tace "you are going on a journey, ke da daada, ba za ku dawo ba har sai kin manta da Sultan" na durkushe a gabanta nan da nan na fara kuka ina rokonta, ko saurare na bata yi ba, tace it's for my own good, a karshe dai nace mata "mommy, ina son magana da daddy" tace "mun riga munyi maganar dashi, shine ma ya bada wannan shawarar" mommy is a bad liar, in dai tayi karya sai an gane, ina kallon fuskarta nasan daddy bai san maganar tafiyar nan ba. Zata tura ni wani gurin da Allah ne kadai yasan inane, ba tare da sanin daddy ba ballantana wani dan haka Allah ne kadai yasan ranar dawowata. Allah gani gare ka. When everything seems lost, always have hope. Have faith that God is planning something for you. Believe that God's plan is the best. [11/7, 2:31 PM] maryamsuleiman48@gmail.co: MAIMOON By Maman Maama Episode Fifty Two : The Journey Munir, ni mai nayi wa Munir a rayuwa? Kawai dan nace bana son sa? Ai ba yaudarar sa nayi ba, tun farko na gaya masa bana sonsa kuma ni ban saka shi lallai sai ya jirani ba shi yaga dama. Na gane mugun nufinsa so yake yayi ruining reputation dina yadda lallai koda na dage bana donsa sai iyayen mu sun tilasta min na aure shi. Ni kam ban masan me zanyi ba in aka aura min Munir. Ina nan a durkushe a gurin ina hawaye har ta dawo, daga bakin kofa ta tsaya tace "let's go" na kuma rike kafarta "mommy dan girman Allah ki bani wayata, wallahi ba sultan zan kira ba, mommy dan Allah ko Hafsat ki barni inyi magana da ita" ta hade rai tace "am not stupid Moon, ni na haife ki ba ke kika haife ni ba, in dai har zan baki waya menene amfanin kaiki wani gurin. Tunda har kika san ki fita daga gidan nan ki tafi gurin saurayi ai zaki iya komai moon. Moon daga bar fa aka dauko min ke kina warin giya. Moon kece fa har da daukar saurayi ku tafi wani kasar. Duk abinda nayi miki har kina da bakin rokona mercy. In dai har ni na haife kiba zaki kara ganin yaron nan ba har abada. Kuma in dai har ni lawyer ce sai na tabbatar yaron nan yayi jail time saboda ya zama darasi a gare shi da sauran masu hali irin nasa" sautin kukana na kara, tashin hankali na shine jin tace sai ta rufe sultan, sanin halin mommy i know she is not bragging. "Mommy kiyi min rai dan Allah karki taba Sultan, dan Allah ni kiyi min komai, laifi nane, ni naje gurinsa bashi yazo gurina ba, he needs help mommy not more suffering. He will loose himself completely idan ya rasa ni kuma aka rufe shi" ta karaso inda nake tana kallona, ni kuma na sunkuyar da idona kasa tace "did you have sex with him?" Na dora hannayena aka na rusa wani sabon kukan tace "answer me, did you? How many times?" Kuka kawai nake na kasa bata amsa, mommy ta riga tayi nisa duk abinda zance mata ba zata saurare ni ba. Tace "ba zaki amsamin ba sai na kira Walid ya nakasa min ke tukunna? Did you?" Na girgiza kaina da sauri "no mommy, never" ta jima tana kallona kafin tayi deciding gaskiya nake fada, tace "tashi mu tafi" nace "ban dau kaya ba ai" tace "no need, na hada miki already" na juyo na kare wa dakina kallo, sannan na fita ta biyo ni a baya. Babu kowa a palo, haka ta tisa keyata muka fita waje, daada na gani a tsaye gaban motar mommy, baya mommy ta saka na ta rufe kofar ta zagaya zata shiga drivers seat. Yaya Habeeb na hango ya fito daga part dinsu da gajeran wando da singlet, daga dukkan alama jogging zai fita, tsayawa yayi da sakakken baki yana kallon mu muna shiga mota, wannan shi ya tabbatar min da cewa suma basu san da wannan tafiyar ba, da sauri ya karaso "Moon ina zaku je" bani da amsar da zan bashi sai kawai na daga masa hannu alamar 'oho' ya karasa gurin mommy tun kafin ya karasa ta watsa masa harara, ya juyo ya sake kallo na sai kuma ya juya da sairi yana kwalla wa ya Walid kira, tun kafin ya shiga part din nasu mommy ta ja motar dan haka ya tsaya kawai yana kallon mu, munje gate na juyo naga ya Walid ya fito shima ya tsaya yana kallon mu fuskarsa dauke da mamaki. Titi babu kowa dan haka mommy ta ke kwarara gudu san ranta, ta gaban palace muka wuce, na kalli gate din ina lissafin ko Sultan yana ciki? Na lumshe idona knowing this is the closest I can get to him. Airport muka je, a raina nace kasar zamu bari kenan gaba daya. Muna zuwa muka fito muka shiga waiting room muka zauna, ni dai bance musu komai ba, sai da aka fara kiran flight naji an kira Niamey sai naga sun mike, zuciyata naji tayi min fari kal, dan dai Niamey ai bani da problem, wato mommy gidan su zata kaini kenan, ina zuwa zan karbi waya a gurin cousins dina na can in kira daddy in kira Sultan. Na mike da kwarin jikina, amma ban saku fuskata ba dan kar ta gane ban damu da zuwa Niamey ba. Wata jaka ta miko min tace "ga magungunan ki nan kullum zaki rinka shan dai dai" na duba naga magungunan hawan jini nane, watk mommy tasan sai jini na ya hau shine ta dauki precautions. Na rungume ta ina hawaye nace "am sorry I failed you mother" ta dan shafi bayana kadan sannan tace "it's ok, Allah ya kiyaye hanya" daganan ko fuskata bata kalla ba ta juya ta fice daga gurin. A jirgi hankali na a kwance muke tafiya, ni ce har da bacci, dan nasan 'yan Niamey sosai dan haka bani da matsala. I will come back to Nigeria in less than a week. Hmm 11 na safe a Niamey tayi mana, muka dauko kayan mu muka fito, muna fito wa na fara wara idon ganin motar da zata dauke mu, dan nasan duk sanda muka je Niamey wani cousin din mommy ne yake zuwa daukan mu, babu shi babu alamar sa. Taxi naga daada tana tsayarwa, na karasa gurinta naji suna magana da mai taxi din da yaren da ban sani ba, abinda na fahimta kawaj shine kudin da ya gaya mata, kudi ne masu yawan gaske, ya fito ya fara zuba kayan mu a mota, nace "daada ina zamuje ne?" Tace "zaki gani ne ai" nace "daada ko ma ina zamuje mu fara zuwa gidan su Ahmodou mana mu gaisa, kinga sai mu huta acan" bata kulani ba ta tura keyata cikin mota sannan itama ta shigo. Tun muna tafiya ina gane titunan da muke bi har muka fara shiga inda ban sani ba, daga baya muka dau hanyar barin gari, ni maimunatu na shiga uku, ina zamuje ne? Ni in banda Niamey ban taba zuwa wani gari a Niger ba, na sake cewa "daada ina zamu je ne?" Direct tace min "Tahoua" na kwantar da kaina a jikin window ina kallon jefi jefin bishiyoyi suna wucewa, Tahoua, nasan sunan garin amma a iyakacin sani na bamu da 'yan'uwa acan. Lallai mommy da gaske take, na danyi murmushin takaici nace a raina 'tace bazan dawo ba sai na manta da Sultan. Bata san sai da ya dauke ni shekara biyar ba kafin in chire Ibrahim daga raina ba? Sultan kuwa nasan kuwa nasan zan tafi dashi ne a raina zuwa kabari na' a haka bacci ya dauke ni, can naji daada tana tashina, na dauka munzo ashe tsayawa mukayi sallah, cikin sahara, dan gurin da muka tsaya ko 'yan bishiyoyin babu, ni dai a tsorace nayi sallar na koma mota. Bayan mun kuma daukan hanya daada ta dauko wata food warmer da soyayyun kaji a ciki ta hado min da ruwa da lemo ta miko min, na diba na zubawa drivern na mika masa. Ni lemon kawai nasha dan sam bakina babu taste. Sai bayan magrib muka isa Tahoua. It is worse than I imagine. Gidan da muka je gidan kasa ne rufin azara, cikin wata chakudaddiyar unguwa. Ji nayi gaba daya hankali na ya kuma tashi, yanzu mommy tana nufin anan zan zauna har sai ranar da ta waiwayoni? Muna shiga muka tarar da wata tsohuwa tana kirki a itace, da mamaki ta taso ta tari daada, suka rungume juna suna ta murna, ni dai 'yar kallo ce, ta kaimu wani daki mai dan girma wanda ko siminti babu sai kasa. Ta shimfida mana tabarmar karauni muka zauna na gaisheta tana kallona tace "tubarkallah, daada ina kika samo 'yar kyakykyawar yarinya haka?" Daada tace "diyar bintou ce fa" tace "hidijan, yanzu bintou ke da diya kamar wagga?" Daada tace "laa wagga ita atta hudu" matar tace "alqur'an daada wagga ya kamata a amra mata dan'uwa ta zamna a Niger" ina jika na mike nace "ina ne bandaki zan zagaya?" Matar ta taso ta rakani, shaddar kasa, na kasa tsugunnawa na fito nayi alwala nazo na tayar da Sallah. Ina yin sallar isha na shimfida zanina na kwanta na lulluba da hijab dina, ba bacci nake ba, so nake inji hirar su daada dan insan halin da nake ciki, ga mamakina ko zance na basu yiba, labarurrukan da kawai suke yi suna dariya. A cikin hirar naji daada tace ai akan hanya muke, tsayawa mukayi mu huta, Agadaz zamu je. Zumbur na mike daga kwancen da nake nace "Agadaz daada? Daada Agadaz fa karshen duniya kenan?" Cos haka muke cewa sanda muna yara. Daada ta harare ni tace "dama ba bacci kike ba ko?" Nace "dan Allah daada Agadaz zamu? Wa muke dashi a Agadaz? Mommy ma da kanta tace bata taba zuwa ba saboda nisan garin? Daada me laifi na har ya kai girman haka?" Sai kuma kuka. Ina jin matar tana ta yiwa daada tambayoyi amma bata ce mata komai ba, aka kawomin abinci naki ci, daada ta dauko min magani na ta bani tasa lallai sai da na sha. Ranar sam banyi bacci ba, ga gajiya ga tunani, da zarar baccin ya daukeni kuwa zanyi ta mafarke mafarke, most of them na Sultan ne kuma duk basu da dadi. Daga karshe dai na tashi zaunr na hade kai da gwuiwa nayi ta rera kuka na. Babu abinda ba zan iya bayarwa ba a lokacin dan insan halin da Sultan yake ciki. Ni kaina ina tsoron zuciyarsa. Sai ya hargitsa garin Abuja gaba daya. Sai gab da assuba sannan nayi bacci, cikin baccin naga sultan a cikin gidan mu yana bi daki daki yana nemana, yana bude dakin mommy ta dauko bindiga ta harbe shi. Na farka a tsorace ina ta jero adduoi. Naji ana kiran sallah na tashi nayo alwala nazo na fara nafiloli ina ta jero wa Sultan addua, ni ban damu da kaina ba, duk abinda mommy zatayi min nasan ba zata taba chuta ta ba, amma shi bashi da kowa sai Allah. Mommy lawyer ce, zata iya creating case against him wanda dole alkalin ya dauke kansa daga ganin cewa dan sarki ne ya rufe shi, babansa kuwa ko dan yatsa ba zai daga ba ballantana ya damu. Hope dina kadai shine daddy, shi kadai ne zai taka wa mommy burki. Amma bansan shi kuma yadda zai dauki al'amarin ba, saboda shi daddy baka ta ba gane inda ya sa gaba saboda kwarjinin sa. Ana yin assalatu na tashi daada sannan na tayar da sallar, na idar ina azkar naji tana gayawa matar ta aika a samo mana mota shata. Karfe shida muka shiga motar, kawar daada ta hado mu da kunu da kosai wai ma ci a hanya. Motar hilux ce saboda sahara. Muna baya ni da daada kayan mu kuma suna gaba tare da driver. Tun karfe shida muke tafiya har karfe uku na yamma sannan muka tsaya muka yi Sallar azahar da la'asar muka cigaba da tafiya. Lallai Agadaz akwai nisa, nayi baccin har na gaji, nayi tunanin har kaina yana neman bugawa. Ko bishiyoyin ma babu, inka leka ta window yashi kawai zakayi ta gani babu iyaka. Daada tayi tayi dani inci abinci naki ci. Rabona da abinci tun wanda mommy ta takura min naci ranar da zamu taho. Mun daga nesa na hango garin. Babban gari ne babu laifi amma ko irin 'yan kauyukan kan hanya din nan babu kawai sai dai ka ganshi a gabanka a tsakiyar sahara. Muna shiga garin daada ta gaya wa drivern in da zai tsaya, ya tsaya amma maimakon inga mun fito sai naga mun zauna a mota muna jira, can sai ga wata katuwar Jeep ash color ta tsaya a kusa damu, wani saurayi ne ya fito ya kara so windon da nake yace "baki daga Nigeria?" Hausar shi tas kamar dan kano. Na dauke kaina kamar ban ji shi ba dan ni kowa ma haushi yake bani. Daada ce ta amsa masa da murmushinta tace "eh mune, mustapha ne ko musbahu?" Yayi dariya yace mata "Mustapha ne daada" ya kalleni yace "Hafsat ko Moon" ya sake bawa iska ajjiyarsa. Daada ta kama fada ni bama abinda take cewa nake ji ba, ya bude min kofa shima yana magana amma bana gane me yake cewa. Ina fitowa daga motar jiri ya debe ni sai kasa. Da sauri ya zo zai rike ni na daga masa hannu nace "Don't touch me" ni na manta ma 'yan Niger basa turanci, amma ga mamakina sai naga ya ja baya yace "just trying to help" daada ta zagayo da sauri ta rike ni muka tashi tsaye, muna tashi kuwa nayi mata wanka da amai, babu komai a cikin aman nawa sai ruwa. Sama sama nake jinsu suna ta yi min sannu. Daada tana cewa "bata taba yin tafiya me nisa irin wannan ba ne shi yasa, kai wannan gari naku da nisa yake" ni dai aka sakani a mota na kwanta ina jin dadin sanyin ACn motar. Ina jin alamar muna tafiya amma babu damar in dago kai in kalli gari saboda jirin da nake ji. Naji horn kuma naji an bude gate, daganan naji mun tsaya. Daada ta riko ni muka fito tare, inajin saurayin yana yiwa wata yarinya French sai naga tazo ta kamani itama muka shiga cikin gidan. A palo suka kwantar dani akan doguwar kujera. Mustapha ya sake aiken yarinyar sai gata da cup din tea mai zafi ta kawomin, na karba nace "graciers" na ringa kurba a hankali har sai da na sanye. Sai a lokacin na samu idon kallon palon. Yana da girma kuma an cika shi da kayan alatu, daga dukkan alama mutanen gidan basu da matsalar kudi. Daada ta shigo daga alama sallah tayi. Mustapha shima ya shigo daga masallaci. Nan aka nuna min inda zanyi sallah na shiga nayi. Daki ne babba da katon gado da wardrobe a ciki, sai toilet shina babu lefi mai kyau. Kayan mu na gani a dakin, anan kenan zamu zauna. Ina idarwa yarinyar ta dawo tayi min alama da ana kira na. A palon na tarar dasu suna cin abinci, daada da wata mata da maza samari su uku. Na karasa na zauna daga dan nesa dasu. Matar ta dago ta kalleni fuskarta a hade babu murmushi. Na gane ta. Aunty Zaliha. Kawar mommy ce tun muna yara, gurin aikin su daya da mommy. Tana zuwa gidan mu muma kuma muna zuwa gidanta tare da mommy, muna secondary school mommy tace mana sun tashi daga Nigeria amma sam bamu san Niger suka dawo ba ballantana insaka ran ganinta a agadaz. Tana da yara maza uku. Twins, Mustapha da Musbahu, sai kuma gambon su Musaddiq. Musaddiq shine sa'an Hafsat su kuma twins din sa'annin yaya Walid ne. A hankali nace "aunty Zaliha?" Tace "eh nice dai, in kin manta ni ma ki tuna ni, kinsan cewa ni ba Fatima bace bana daukan nonsense. Kin bata wayonki wallahi Moon. Kin bani mamaki. Ni ba dan fatima bace ta gaya min ba zan iya rantsewa karya ake miki. Amma babu komai, zaki dawo hankalin ki ne. Ni na bawa Fatiman shawarar ta kawo ki nan gurina har sai komai ya daidaita tukun" kowa yayi shiru ni kam bakin ciki ne ya kamani jin itace ta bada shawarar rabani da Sultan da babana da 'yan'uwana, sai kuma ta cigaba "yarinya kamarki, me kika rasa ke kuwa a rayuwa, mai kika gani a gurin wannan kangararren yaron da bamu tabbatar ma da asalinsa ba? Kina da asalin ki, ilimi, tarbiyya, ga kyau, na tabbatar samari suna nan suna layi wadanda ko yau akace su fito zasu fito din, amma shine kika gwammace ki zibar mana da mutunci a gurin jama'a" fada take tayi da duk karfinta, ni kuma na sunkuyar da kaina kasa amma ta inda fadan nata yake shiga ta nan yake fita. Daada itama ta dauka suka yi tayi. Sai da sukayi mai isarsu sannan sukayi shiru. Wani daga cikin samarin ne ya zubo min abinci ya miko min, na karba tare da yi masa godiya. Aunty Zaliha tayi sauri tace "a'a, no friendliness of any kind. Duk wanda a cikin ku ya sake ya bata wayarsa ko da wasa ne sai na saba masa wallahi. I am dead serious. There is a very bad person a Nigeria da yake son bata rayuwarta, an kawo ta nan ne saboda a raba su. Duk wanda ya taimaka mata to ya sani cutar ta yayi. Did I make myself clear?" Duk suka amsa da yes. Sakani tayi a gaba sai da na chinye abincin da aka zubo min sannan na sha magani na tace inje in kwanta. Gaba daya jikina ciwo yake yi, ina zuwa nayi sallar isha nayi shirin bacci na kwanta. Bacci me nauyi ne ya daukeni, amma daga baya sai mafarkan suka fara dawowa, na farka na kuma kasa komawa. Daada tana gefena tana ta baccin ta, na tashi na shiga toilet nayo alwala nazo na saka goduwar riga ta na dauko al'qurani na na fara karan tawa, ina yi ina zubar da kwalla. Allah ka fini sanin halin da nake ciki, Allah ka fini sanin waye Sultan. Allah ka huci ran mommy da daddy. Allah ka bani dauriya da juriyar daukan duk wani abinda ka kaddara zai sane ni. Allah ka bawa Sultan hakuri na duk abinda ka kaddara masa. Allah ka zaba mana mafi alkhairi a rayuwar mu baki daya. Kwana daya ya wuce, na biyu ma haka, sati daya ya wuce na biyu ya biyo bayansa, wata daya yazo, haka wata biyu sannan wata na uku yazo shima. Ko bakin gate ban taba zuwa ba ballantana in fita waje. Daga daki sai palo. Kullum da alqurani na a hannuna dan yanzu shine babban abokina, it's the only thing that's keeping me sane. Ko da yaushe daada ko aunty Zaliha suna kallona, ni kam daga gaisuwa babu abinda nake kara cewa kowa. In an bani abinci inci, in an bani magani in sha. Samarin gidan kullum suna son kula ni amma babu hali saboda suna tsoron aunty zaliha sosai. Amma ina ganin tausayina a idon su. Wanda muke magana dashi kawai shine mijin Aunty Zaliha, kullum in ya ganni palo zai ta tsokanata wai bafulatanar daji tazo birni ko yawo bata zuwa saboda kyauyenci. Kullum sai ina jin aunty zaliha ko daada sai sunyi waya da mommy amma bata taba cewa a bani ba, ni kuma ban taba cewa zan karba ba. Rannan muna palo da aunty zaliha da Musbahu sai mommy ta kira suna magana ta tashi ta shiga daki dan kar inji me suke cewa, dama haka suke yi kullum. Tana shiga musbahu ya matso kusa dani yace "ya sunan sa?" A hankali nace "Sultan" when was the last time I called his name out loud? Yace "am sorry, I know what love feels like" a lokacin muka ji motsin aunty zaliha zata fito, yayi sauri ya matsa. Tana zuwa ta miko min waya "Fatima zata yi magana dake" na karba kawai ina kallon wayar, hannuna har rawa yake yi na saka a kunnena amma na kasa magana, can naji muryarta tace "Moon?" Wasu hawaye masu zafi suka zu bo min, banyi magana ba ta sake cewa " Moon banyi tunanin zaki dade haka ba, banyi tunanin abinda nayi planning zai dau lokaci ba" ta kuma yin shiru. A hankali nace "mommy ina daddy dasu ya Walid? Mommy in Hafsat ta haihu?" Ta jima bata yi magana ba, sanda tayi muryarta tayi alamar kuka, tace "duk lafiya lau suke, Hafsat bata haihu ba" desperately nace "mommy dan Allah ki bar ni ko waya ne inyi dasu" dif naji ta kashe, na saki wayar na rife fuskata da hannuna ina kuka. Jin muryar mommy ya daga min hankali sosai, gida kawai nake son zuwa. Aunty Zaliha ta dauke wayarta ta sake dialing number din mommy ta koma daki. Ina cikin kuka na naji an ajiye min wani abu a kan cinya ta, na dago kaina da sauri naga Musbahu yana min murmushi, na kalli cinya ta naga waya, a hankali yace "call him, but let it be our secret" gaba nane ya fadi sosai, shi kuma ya mike ya fice daga palon. Da sauri na dau wayar na saka a riga ta ina rarraba ido. I got a phone now, what do I do? Kar a kama ni kuma a kaini wani gurin da yake worse than here. Na tashi na shiga daki naga daada a kwance, nima na kwanta a gefenta na rufe idona kamar mai bacci ina ta lissafi a raina, menene yasa mommy kuka? Me ya faru a gidan? Me yasa tace abinda ta shirya is taking time? Ko dai wani abin ta saka aka yiwa Sultan kuma take regretting yanzu. Na shiga uku. Ina nan kwance har naji daada ta tashi ta shiga toilet, ta fito ta jima tana kallona sannan ta fita palo. Tana fita na mike na shiga toilet nayi locking kofar sannan na dauko wayar, babu security a jikin ta ya chire. Na shiga dialer da sauri na saka number din Sultan, na daga hannu zan dialing na kasa, what if something bad has happened to him? My heart can't take it, ya Ilahi. Sai kawai na goge number. Na saka number din daddy, ta gama ringing har ta katse bai dauka ba. Ya Allah. Na sake re-dialing ina lissafo sunayen Allah a ziciyata. Ringing na uku ya dauka "salamu Alaikum" a hankali nace "daddy" ya danyi shiru sai yace "Moon? Is that you?" Sai hawaye na kasa magana, yace "my God, Moon kiyi min magana mana, a ina kike? Ina Fatima ta kai min ke? Are you Ok?" Kuka ne yaci karfina nace "daddy ina Agadaz" yace "what? Agadaz fa kika ce? Yanzu Fatima cikin extreme saharar agadaz ta kai min yarinyar? To uban wa ta sani a agadaz din?" Nace "aunty Zaliha tsohuwar kawarta ta office dinsu" yace "Zaliha? Dama agadaz suka koma? Are they treating you well? Ko tabo na gani a jikin ki sai na dau mataki akai" nace "daddy am OK. Yaron gidan ne ya taimaka min da aron yawarsa. Please daddy kar asan shi ya bani" yace "don't worry about him, I will come and pick you up tomorrow. OK? Kar ki gayawa kowa kin kira ni, OK?" Na gyada kai kamar yana kallona. Har yanzu hawaye bai tsaya a ido na ba. A hankali nace "Daddy how is Sultan?" Godiya marar adadi ga duk masoyana masu bibiyar lafiyata, Alhamdulillah lafiyata kalau, biki ne dai muke yi shi yasa akaji shiru. Nagode Allah ya bar zumunci. Na samu labarin wadansu masoyan moon a whatsaap suna shirya riot dan kwato mata 'yancinta, haha, to sai ku shirya zuwa Agadaz, amma sai dai kuje ku kadai dan ni ban shirya zuwa sahara da zafin nan ba. Lol I love you all 💖 [11/7, 2:31 PM] maryamsuleiman48@gmail.co: MAIMOON By Maman Maama Episode Fifty Three : Daddy Yace "Don't worry about Sultan. Kar ki bari zaliha tasan kin kirani har sai na nemi contact da mijin ta, dashi zamuyi magana. Badan jirgi baya zuwa agadaz ba Moon da yau zanzo in dauke ki. Amma highest jibi. Ki kwantar da hankaliki kinji?" Na gyada kaina kamar yana kallona sannan nace "I miss you daddy" ya danyi shiru sannan yace "I miss you too, sunshine" daga haka ya kashe wayar. Nayi tunanin in kira Hafsat amma kuma sai na fasa kar ta gayawa mommy na kira ta. Na mayar da wayar cikin jaka ta na fito daga toilet din ina kalle kalle. Babu kowa a dakin. Na dan tsaya ina tunani, a raina nasan kiran daddy da nayi dai dai ne amma kuma duk da haka sai nake jin feeling kamar nayi ba dai dai ba. Na tsaya a gaban mirror, when was the last time dana kalli fuskata? Tunda muka zo na saka wani towel na rufe mirron dakin saboda bana son kallon fuskata. A hankali na bude, ni kaina sai da na tsorata, babu komai a fuskar sai katon hanci da idanuwa kamar na mujiya, dama haka idona yake? Lallai kiba ma rahama ce. Na kalli wuyana naga wani katon kashin da bansan ina dashi a gurin ba, amma kuma kirjina yana nan dam dam, ramar da nayi ma sai ta karawa girman su fitowa, a raina nace 'su basa ramewa ne?' Na mayar da mirror din na rufe na koma na kwanta. Ina kwance daada ta dawo tayo alwala tazo tayi sallah sannan ta tashe ni, har da dan magagi na kamar me baccin gaskiya sannan na mike na shiga toilet nayo alwala nazo nayi sallah ni ma, muka fita falo tare. Musbahu ne kadai a zaune yana kallo, daada ta zauna kusa dashi ya fara labarin film din da yake kalla, hankalinta gaba daya yana kam kallon na zaro wayar na ajiye a kusa dashi na koma gefe na zauna. Ina kallonsa ya dauka ya saka a aljihunsa ba tare daya kalleni ba. Muna zaune a palon har akayi magrib, anan muka yi sallah aka fara kawo abinci. Mun fara zubawa kenan mukaji shigowar abban su Mustapha, gaba na ne ya fadi saboda nasan ba yanzu yake dawowa ba, tun daga compound yake kwalla wa aunty zaliha kira, ta mike tsaye fuskarta da alamar tsorata, yana shigowa ya fara balbalin fada "Zaliha yanzu dama abinda kuke aikatawa kenan ke da Fatima? Kika ce min yarinyar nan hutu tazo yi gidan nan, dama ni ina mamakin tunda tazo ban taba ganin ta fita waje ba, ashe ita nan zaman prison take yi a gidana. Saboda tsabar rashin hankali ku raba yarinya da ubanta da 'yan'uwanta kawai dan saurayin da take so bai yi muku ba?" Kamar zatayi kuka tace "abban musaddiq dan giya ne fa" yace "to amma baku yi tunanin cewa baban ta shima yana da right na zaba mata miji ba? Ko ita Fatima tana ganin cewa tafi ambassador son ta ne? Yanzu kinga ni kinsa naji kunyar mutumin nan, mutumin kirki wallahi, sai da nayi tayi masa rantsuwa cewa babu hannuna a cikin maganar nan. Yanzu da wani ne da sai dai kawai inga 'yan sanda a gidana" ya zo gaba na ya sunkuya yace "Maimunatu kiyi hakuri kinji? Dana san halin da kike ciki da tuni na dau mataki a kai, babanki ya taho already, a daren yau zai sauka a Niamey dan da private jet dinsa ma ya taho, ni kuma ni zan kai ki Niamey da kaina. Ki tashi kije ki shirya" aunty zaliha ta ce da sauri "wai a yanzu zaku tafi?" Ya tashi yayi hanyar dakinsa yana harararta yace "in bamu tafi yanzu ba yaushe zamu isa can?" Yana shiga daki kowa yayi shiru a palon, na mike sum sum zan shiga daki aunty Zaliha ta danko hannuna fuskarta babu rahama tace "uban waye ya baki waya kika kirashi?" Nan da nan hawaye ya kawo idona saboda zafin rikon da tayi min, nace "ni bani na kirashi ba, bansan yadda akayi yasan ina nan ba" ta juya tana kallon 'ya'yanta har yanzu bata cika ni ba tace "cikin ku waye ya bata wayarsa?" Duk sukayi shiru, cikin tsawa tace "ba za'a bani amsa ba?" Nan suka kama rantse rantse banda musbahu da yake ta game dinsa kamar bai san me akeyi ba, tace "Mustapha kai ne ko? Dan na lura da yawan shishshige mata da kake yi?" Mustapha ya kama rantsuwar bashi bane, ko ta kan musbahu bata bi ba dan sam tunda nazo gidan baya kulani, shi dama ko a cikin 'yanuwansa bashi da harka sosai. Ta sake ni tana girgiza kai fuskarta kamar zatayi kuka "poor you, you have no idea what you have done. Sai kije ai, shi baban naki ya aura miki wanda yake so din. Duk abinda fatima tayi, she did it to protect you amma ke gani kike ta takura miki ne saboda bata son ki" ban gane mai take nufi da babana ya aura min wanda yake so ba, ni dai nasan daddy bai zaba min miji ba kuma shi da kansa ya fada cewa baya son Munir. Ta juya ta shigewarta daki, ina shiga daki daada ta biyo bayana, tana ta maganganun ta akan ban kyauta ba ni ko ko kulata banyi ba na dauki iya abinda zan iya dauka na ziba mana a akwatinan mu, sauran na barwa 'yan gidan. Ban bi ta kan daada ba na jayo akwatinan mu na kawo palo, lokacin already gari yayi duhu, abban su mustapha na gani yana cin abinci a palon, yace min "ina daada? Ku zo kuci abinci mu tafi dan kwana zamu yi a hanya" ba musu na zauna na zuba abinci na fara ci, sosai naci na koshi dan nasan wahalar da nasha sanda muka zo. Har muka gama babu aunty zaliha babu labarin ta, muna gamawa abba ya kira musaddiq ya saka mana kayan mu a mota sannan daada ta shiga dakin aunty zaliha nima na bita a baya, tana kwance a kan gado, suka yi sallama da daada nima na matsa kusa nace mata "zamu tafi" ko kallona bata yi ba, tayi fushi, na kara matsawa nace "aunty Zaliha zamu tafi" tace "Allah ya kiyaye hanya" daga haka bata sake cewa komai ba. A waje na samu daada a kusa da mota nima na tsaya, musbahu ne yazo yana murmushi yace min "so... Har taimakon gaggawa yazo kenan?" Nayi murmushi, yace "there you are, gashi har kina murmushi, abinda tunda kika zo banga kinyi ba" sai yanzu nima na tuna yaushe rabona da murmushi? A hankali nace "thank you" bai ce komai ba, daada ta kalleshi cike da zargi tace "kai ka bata wayarka ko" murmushi kawai yayi mata, ya miko min kati yace "call me when you get your phone back, and ki gaida Sultan. Adios for now Moon" nima nace masa "adios" lokacin abba ya fito da sauri ya shiga gaban motar driver dinsa ne zai tuka, mu kuma muna baya. Na kalli gidan ina jin a raina kamar wacce na bar prison na samu freedom. Tun kafin mu fita daga gari na kwanta nayi pillow da cinyar daada na fara bacci. Sai gab da assuba muka isa Tahoua, already abba ya kira wani abokinsa yace gamunan zuwa, dan haka muna zuwa can muka je, ni kam na jima banyi bacci mai dadin na yau ba, muna zuwa muka yi sallah muka huta muka yi breakfast. Karfe tara muka sake daukan hanyar Niamey, da yake hanyar me kyau ce kuma motar lafiyayya ce karfe biyu muka isa, daada ce ta ringa yi masa kwatance har muka zo gidan kawu sharu wanda yake yayane a gurin daada kuma a gidansa muke zama duk sanda muka zo Niamey. Muna packing naga manyan motoci da number din Nigerian embassy na Niamey nasan daddy yazo, da kyar na iya controlling kaina saboda excitement, amma ina shiga compound din gidan naga palon kawu a bude da takalman mutane a bakin kofar, bansan sanda na zubar da takalmana a gurin na shiga dakin a guje ina rarraba ido ina nemansa, yana ganina shima ya mike tsaye ya bude min hannunsa, ai kuwa a guje na karasa na shige ciki na kankame shi tare da sakin wani kuka mai ratsa zuciya. Sai da nayi kuka na na gama sannan ya raba ni da jikinsa yana kallon fuskata, fuskarsa sam babu fara'a, kallona yayi tayi sama da kasa kamar mai tabbatarwa babu abinda aka gutsira a jikina, sannan yace "are you OK?" Kaina kawai na gyada masa. Na juya ina kallon sauran mutanen dakin, sai a lokacin naga mommy, tana zaune a kan carpet ta harde kafafuwanta a guri daya,fuskarta tayi ja, akwai uncles dinta su biyu na gurin uwa dana guri uba, na saki daddy na tafi na fada kan cinyarta, bata cemin komai ba sai dan bubbuga bayana da take yi. Daada ta shigo tare da abba suka gaisa da mutanen gurin. Daddy ne ya soma fada, daga dukkan alamu dama fadan ya keyi kafin mu shigo yanzu cigaba yayi "ta nuna min ni ban isa ba. Ta dauke min yarinyar ba tare da sanina ba kuma nayi nayi ta gayamin inda take taki. Ko wanne laifin yarinyar tayi au kamata yayi ace an gayamin first sannan kuma sai mu hadu ni da ita musan irin hukuncin da zamu yi mata, amma a haka ai ta nuna min ban isa da 'yata va kenan" kawu sharu ne yace "tashi ki shiga cikin gidan Maimoon" daga dukkan alamu daddy ya manta ina gurin. Na tashi na shiga cikin gida amma jikina duk yayi sanyi. Tunda nake a rayuwata ban taba ganin mommy da daddy suna musu ba ballantana fada, dan ina da burin ace wata rana ni da mijina mu kasance tamkar mommy na da daddy na. Har daga cikin gidan ina iya jiyu muryar daddy yana fada, sam ba halinsa bane ba, dan da wahala kaga daddy yana fada, ballantana a gaban surukansa. Ji nayi gaba daya komawa Nigeriar ma ya fita daga kaina. Na zamanto dalilin samun matsala a tsakanin iyayena, kowa a cikin su is trying to put me first. Nasan duk abinda mommy tayi tayi ne dan tana ganin shine dai dai a gareni, amma ni abinda ban fahimta ba shine dalilin ta na kin gayawa daddy bayan kuma nasan komai tayi sai ta gaya masa. Ina nan kwance abin duniya ya ishe ni gwoggo Sa'a ta shigo tace in tashi inyi sallah inci abinci, bayan na gama ne ta tambayeni "Maimoon wai me ke faruwa ne tsakanin mommyn ki da daddyn ki?" A raina nace wannan tsegumi take so kenan, na daga mata kafada alamar bansani ba, daga nan bata sake cewa komai ba. Mommy suka shigo tare da daada, ko kallon inda nake bata yi ba ta shige toilet tayo alwala tazo ta tayar da sallah, daada tana ta 'yan mitocinta "ba shikenan ba, sai kije ai ya aura miki ko ma waye yaga dama, duk abinda ya fari kuma daga baya kar ki zo gurin mu, ki je can ku karata ke da baban naki" ni duk maganganun da take yi ban fahimci me take nufi ba dan haka kawai kallonta nake yi, mommy ta idar da sallah ta mike ta tsaya a bakin window tana kallon waje, muna haka sai ga dan aike daga waje "wai Maimoon tazo su tafi" na mike ina saka hijab dina nace "mommy ance mu fito" ta juyo ta kalleni tace "ance ki fito dai, ko kinji an ambaci sunana?" Na yar da hijab din hannuna na karasa kusa da ita nace cikin rawar murya "mommy ba tare zamu tafi ba?" Ta juya min baya tace "no, am going to stay here for a while, go with your father " na durkushe a gurin duk farin cikin komawa gida ya gushe daga zuciya ta, na rike kafarta nace "mommy ni bazan koma gida ba tare da ke ba, mommy dan Allah kiyi hakuri ki zo mu tafi, mommy in dai akan maganar Sultan ne zaku samu matsala da daddy wallahi ni na hakura da shi. Kun fiye min dubun sultan wallahi. Dan Allah mommy kiyi hakuri kice kin yafe min" kuka nake sosai. Ta dago ni ta rungume ni tace "ni na yafe miki tun tini Moon. I just wanted to clear the mess you created" nayi sauri nace "to in kin hakura kizo mu tafi gida tare" tace "that's not up to me, daddyn kine yayi fishi bani ba" na chika ta da sauri nasaka hijab dina na fita, a compound naga daddy tare dasi kawu, ina fitowa yace "taho da sauri mu tafi dare yana yi" ina zuwa na durkusa akan gwuiyoyina ina hawaye nace "daddy dan Allah kayi hakuri, wallahi ni na hakura da koma menene yasa kuka samu matsala da mommy, it's all my fault. Dan Allah kuyi hakuri mu koma gida gaba daya, ni ba zan iya rayuwa babu mommy ba kuma bazan iya babu kai ba" ya dago ni yace "it is not your fault Moon, kowa akwai destiny dinsa a rayuwa. Ita kuma mommyn ki ita tace tana son ta zauna anan for sometime, bani nace ta zauna ba, if you can get her to go with us then I will be more than happy" na koma ciki da sauri nace "mommy daddy yace ki zo mu tafi tare" tana kallona tace "shi ya gaya miki hakan?" Nace "eh" kafin ta sake magana kawu sharu ya shigo ya kama bambami "ya zaku ke wani abu ne kamar yara Fatima? Kece me laifi kuma kece mai fushi? Shi kenan kuma kinyi laifi sai kice ba za'a yi miki fada ba? Dan kin samu miji mai hakuri ko?" Ya juya kan daada A cigaba "duk kece kike daure mata gindi ai, kin barta sai abinda taga dama take yi, ai ba gata kike mata ba" sai da ya wanke su tass sannan yace mommy ta fito mu tafi. Fuu ta wuce ni tayi gaba, da sauri2 na bita a baya. Ina fita na kalli motoci guda biyu da suke jiran mu, a lokacin idanuna suka sauka akansa. Yana tsaye ya jingina da jikin mota, light brown eyes dinsa a kaina. Shadda ce doguwar riga da wando dark brown a jikinsa, kalar shaddar ta kara fito da uniqueness din fatarsa, hularsa da takalmin sa light brown kalar idonsa. Yawan sumar kansa ta saka hular bata shiga kan sosai ba. Ya cire hular ya saka hannu ya hargitsa gashin sa sannan ya mayar da hular still idonsa a kaina. Kafafuwana naji kamar ba zasu dauke ni ba, what is he doing here? Muryar daddy naji yana cewa "Sultan ina Walid din kuma ya tafi? Ku zo mu tafi mana, weather din sahara is unpredictable" [11/7, 2:32 PM] maryamsuleiman48@gmail.co: MAIMOON By Maman Maama Episode Fifty Four : Her Father's Daughter Hannu na saka na murza ido na, ni dai nasan ba bacci nake ba ballantana in yi tunanin ko mafarki nake, idonsa yana kaina kamar yadda nawa yake kansa. He looks different, but it is still him. Ya rame shima. Ban taba ganin sa da manyan kaya ba maybe shi yasa naga ya kara chanzawa, but God he looks more handsome than ever. Kamar in ruga da gudu in taba shi dan in tabbatar ba hallucination nake ba. Muryar daddy naji kamar daga sama yace "Sultan, da kai nake magana fa" yayi sauri ya dauke idonsa daga kaina tare da sunkuyar da kansa kasa yace "sorry daddy" sannan ya zaro wayarsa yayi dialing ya saka a kunne "kana ina ne? Daddy fa har ya fito, kayi sauri" ya kashe. Muryarsa ce, so it is really him. Ya bude wa daddy kofar baya, bayan daddy ya shiga ya gyara masa rigarsa sannan ya rufe. Yana rufe kofar ya juyo ya sake maida idonsa cikin nawa, with all my psychology amma a lokacin kasa reading dinsa nayi, so clouded. Daddy ne ya sauke glass dinsa yana kallon sultan sannan ya kalleni, wannan karon nice nayi saurin dauke idona na sunkuyar da kaina sannan kuma sumi sumi kamar munafuka na tafi motar da naga mommy ta shiga, na zauna a baya a kusa da ita. Ta window na cigaba da kallonsa duk da yanzu bana ganin fuskarsa, bamu jima ba naga yaya Walid ya taho da dan gudun sa ya shigo gaban motar da muke ciki, ina kallon sultan ya bude gaban motar da daddy yake ciki ya shiga. Tunda muka fara tafiya babu wanda yayi magana, can mommy tace a hankali "yana motar daddyn ku ko?" Ban fahimci me take nufi ba kuma nasan ba dani take magana ba shi yasa nayi shiru, ya Walid ne ya amsa "yes, mommy" tayi kwafa tare da dafe kanta. Ina son in tambaye su maganar wa suke yi saboda in tabbatar wanda na gani shi dinne dai ba wani ba, amma kuma bazan iya ba. Na runtse idona ina so in fahimci me yake faruwa. Wata na uku da sati biyu rabona da Nigeria amma ji nake kamar wadda nayi shekara daya. Me Sultan yake yi tare da daddy na? A iya sanina ko haduwa basu taba yi ba. Me ya faru bayan tafiya ta? Kafin Moon ta samu amsarta mu bara mu koma baya mu riga ta sani. Nigeria bayan tafiyar Moon Walid da Habeeb suka bi bayan motar mommy da kallo. Walid ya juyo ya kalli Habeeb yace "ina zasu je?" Habeeb ya daga kafada yace "oho, nima kawai ganin su nayi suna shiga mota" Walid ya kalli agogon hannunsa, 7 ma bata yi ba, where can they possibly go to at this hour? Jikin sa dai bai bashi dai dai ba. Yace "OK, mu jira su su dawo kawai" ya juya ya koma ciki. Sai around nine mommy ta shigo gidan ita kadai, babu Moon babu Daada, a palo ta same su suna breakfast, ta shige ciki, har ta shirya ta fito suna palon, ta zauna tana hada tea, Habeeb yace "mommy ina su Moon suka tafi ne da sassafe haka?" Ba tare data kalleshi ba tace "inda ka aike su nan suka tafi" daga nan babu wanda ya kuma cewa komai, daya bayan daya suka mike suka bar palon, tabi bayan su da harara. Tana gamawa ta shirya ta tafi office. Sai karfe biyar ta dawo, tana yin packing wayarta tana yin kara, ta duba screen din 'dear' tayi ajjiyar zuciya, tasan maganar dai, tun jiya maganar daya ce, tasan dole zatayi facing wannan challenge din but she is ready. Moon is weak, too soft, tun da aka haife ta haka take, she trust too much, love too much and gives her all in everything she do, she is her father's daughter, shima haka yake, dan haka ita mommy dole ta zama strength din su, ba zata taba barin wani ya yi taking advantage of her sweet daughter's innocence ya cuce ta ba, not that so called Sultan and not that stupid munir. Tasan plan din munir, so yake a tilastawa Moon ta aure shi, ita kam ba zata taba barin ayiwa 'yarta auren dole ba da mutun kamar munir ba, over her dead body, abinda yayi recently ya tabbatar mata da ba son Allah da annabi yake yiwa moon ba, idan da ace yana sonta da ko ita data haife ta ba zata san abinda ya gani ba. Kiran ya sake shigowa wayarta, tayi taking deep breath sannan ta dauka, 'salamu alaikum" da sauri ya amsa sannan yace "ina kika shiga ne haka? Wajen five missed calls?" Ta danyi murmushi tace "kasan aiki yayi min yawa tunda na dawo dinnan. Ina office sai yanzu na dawo gida. Ya kake?" Ya danyi murmushi "am fine mommyn kids, busy body, ya kuke?" "Lafiya lau, just missing you" "wai Moon har yanzu wayarce bata gyara ba? Tun shekaran jiya rabon da muyi magana da ita. Please in tana kusa bata wayar" ta shirya abinda zata ce masa dama "bata gida yanzu, kafin in fita dama tace zata je gidan su Amira, yanzu na tarar bata dawo ba, nima bana son rashin wayar tata amma tace she is taking a time off" ya tare ta "ba wani time off, tell her in ta dawo na turo mata kudi taje ta siyo wani wayar, and also tell her to call me ASAP" tayi dariya sosai tace "to daddy, an gama" shima dariyar yayi, suka dan taba soyayya kadan ta kashe. Ta jima tana kallon wayar, ta san halinsa akan son 'ya'yansa especially moon amma bata yi tsammanin zai tada hankalinsa da wuri haka ba. Ta gyara packing ta shiga gida. Karfe takwas na dare Munir ya shigo gidan, tunda yazo garin dama hotel ya kama, baya son zaman gidan saboda baya son asaka masa ido, gwara hotel yadda zaiyi abinda yaga dama. Yayi packing tare da dauko wayarsa yayi dialing number din Moon, switched off, ya tabe baki, shi ya rasa dalilin da yasa ya kasa hakura da yarinyar nan, tun ranar daya fara ganinta yasan cewa he must have her, no matter what. Duk da kiyayyarsa da yake gani a idonta amma yaki hakura, she don't love him, she thinks she is too good for him. Bai taba sanin yana da sa'a a rayuwa ba sai shekaran jiya da ya ganta a gaban hotel din daya sauka, ya fito da niyar zuwa neman abokiyar harka kawai ya ganta tare da wannan half breed drunk guy din. Ashe itama A ce bai sani ba? Who would have imagine that the so good daughter of the so good ambassador is a drunk slut? Yayi dariya, yaso ace ya dauki video yadda zai ji dadin nunawa dan afi yarda dashi. Ya bude motar ya fito ya nufi cikin gidan. A palo ya tararda Habeeb shi kadai yana kallo, tunda ya amsa sallamarsa bai kuma kallon saba. Ya dora kafa akan kujera yace "kai ba ka iya gaishe da mutane ba?" Habeeb ya waiwaya ya kare wa palon kallo sannan yace "suna ina mutanen? Ni banga kowa da zan gaisar ba ai" Maimakon munir yaji haushi sai ma murmushi da yayi yace "duk zaku gane kuren ku ne, kuna daga wa mutane hanci kuna ganin kamar kunfi kowa a family ko? Da sannu duk zaku gane kuren ku" ya samu guri ya zauna yace "ina gantalelliyar kanwar taka take? Ko yauma ta fice? Ya kamata kuyi gaggawar saka mata mari ko kuma ku miko min ita nan ni nasan maganin irin su" Habeeb ya mike yace "kaga malam zo ka fita mana a gida, Moon ba gantalalliya bace ba, kuma tafi karfin ka wallahi, kaje kayi ta fadan abinda zaka fada, idan mafadin magana wawane majiyinta ai ba wawa bane. Babu wanda baisan halinka a family ba kuma babu wanda baisan halin Moon ba, babu kuma wanda baisan cewa moon bata son kaba, so go ahead and continue telling the lies, you will end up looking like a fool" a fisace munir ya mike yana nuna Habeeb "kai dama rashin kunyar ka har ta kai haka? Ni zaka cewa makaryaci? Rufa mata asiri fa zanyi in aure ta, bayan abinda tayi wa kake tunanin zai auri ragowar wani?" Kyakykyawan mari Habeeb ya ajiye a fuskar munir, abinka da farar fuska take fuskar tayi ja. Wannan yayi dai dai da saukowar mommy daga sama, munir ya shaki kwalar habeeb ya fara duka, mommy tayi sauri ta danna security alarm, kafin minti daya wajan mutum biyar suka shigo, da kyar suka raba munir da habeeb kowa ya daku a cikin su, mommy tace "ku fita dashi, kar ku sake barinsa ya shigo gidan nan" munir yace "bazan sake zuwa ba sai kun neme ni da kanku, kuma nayi muku alkawarin sai kun neme ni, daga nan 'yalleman na nu fa" ya fincike daga hannun security din ya fice. Mommy ta zauna akan kujera tana dafe kanta da yake neman sara mata, tabbas gwara data dauke Moon daga gidan. Haka rayuwa ta cigaba da kasance musu har bayan kwana uku, a lokacin daddy is sure cewa something is wrong, tun Moon tana karama bata taba 24hours ba tare da ta yi masa waya ba in dai baya gari ballantana ace yau kwana biyar rabonsa daya yi magana da ita, tun mommy tana masa karya yana yadda har karyar tata ta kare in ya tambaye ta sai tayi shiru. Dole ya ajiye abinda duk yake gabansa ya tafi Nigeria. To him, his family is above everything, har aikinsa. Ya na kokarin handing over to his assistant kira ya shigo wayarsa daga Walid, ya daga da sallama sannan yace "ya akayi?" A hankali Walid yace "daddy you need to come home, something is wrong, Moon is missing" sai da ya jima yana assessing maganar a ransa sannan yace "what? Ban gane Moon is missing ba?" Walid ya bashi labarin duk abinda ya sani, sannan yace "Mommy ta dauke ta tun three days ago, mun tambayeta taki gaya mana inda ta kaita" daddy ya kasa cewa komai, not Moon, not my daughter, something must be wrong somewhere. Yace "OK, I will be home tomorrow, kar ka ce da mommyn ku komai, in nazo zanji duk abinda ake ciki" washegari kuwa ya sauka a abuja a private jet dinsa. Mommy kawai sai ganin shi tayi ya shigo palo, da sauri ta mike tsaye tana twisting fingers dinta, direct yace mata "ina Maimunatu?" Ta bashi amsa "she is safe" Sultan Bai taba regretting shan giya irin na ranar ba, yana kallo aka saka moon a mota aka tafi da ita amma ba zai iya yin komai ba saboda bashi da karfi, karfinsa shine babban abinda yake takama dashi, gani yake he is untouchable, amma yanzu gashi anyi touching something that is more precious to him than himself and he couldn't do anything. Da kyar Amir ya chusa shi a motarsa yaja suka nufi gida, babu abinda yake maimaitawa sai "I will kill him, I swear I will kill him" Amir dai bai ce masa komai ba, tun a hanya ya kira family doctor dinsu ya gaya masa su hadu a gida. Da kyar ya kama sultan ya shiga dashi part dinsa, direct bedroom ya kaishi ya kwantar dashi, lokacin jikinsa ya karasa saki gaba daya. Doctor yana zuwa ya duba kafar yaga bayan yankewa da yayi wanda sai anyi masa dinki, ankle dinsa ma ya goce, ya gama masa komai ya gyara masa kafar, yace kar ya taka kafar sai nan da 3days, ya bashi 3days bed rest, zai fita Amir ya kira shi gefe ya roke shi yayi wa Sultan allurar bacci dan yasan ba zai zauna ba, yana watstsake wa zai fita, ba musu doctor ya hada allurar, Sultan ya bude ido yana kallonsa yace "allurar menene kuma wannan?" Doc yace "pain reliever ce" kafin sultan yace wani abu yayi mishi ita. Tun kafin likitan ya fita sultan ya fahimci allurar me akayi masa, cikin magagi yace "I will kill you Amir, shine kasa akayi min allurar bacci ko? Bayan kana kallo yana dukan ta ko? Waya san me zaiyi mata in sunje gida, duk ni na jawo mata kuma sai na rama mata" Amir yana shafa kansa yace "Sultan brother dinta ne fa?" Sultan ya ture hannunsa yace "I don't care koma waye shi, he have no right to hit her" daga haka bacci ya dauke shi. Har gari ya waye sultan yana bacci, bashi ya tashi ba sai kusan azahar. Yana farka wa Moon ce a ranshi. Ya mike da sauri sannan yaji pain a kafarsa ya tuna ashe yaji ciwo. Ya zauna a bakin gado ya dafe kansa. Jiya baiyi sallah magrib ba baiyi isha ba, ga subh yau sannan zuhr ta taho, baya wasa da sallah, baya yin nafila dai dasu azkar amma baya barin farilla. Zuwa gurin Moon have to wait sai yayi sallah tukunna. Ya tashi yaji zafin ciwon kafarsa har cikin kansa, a hankali yake jan kafar ya shiga toilet, it annoys him, babu abinda ya tsana irin abinda zai takura shi ya hana shi activities dinsa. Ya fara sallolinsa a tsaye amma dole daga karshe a zaune ya karasa sanoda ciwo. Damn it, wannan kafar ba zata barshi yaje yaga moon ba. Yasan ba za'a barta ta fito ba dan haka plan dinsa shine ya haura ya shiga dakinta ta window kamar yadda ya taba yi a England. Dama ya riga ya lura inane dakin ta. Yaji haushin ta akan kin gaya masa zancen project dinta da tayi amma ya yafe mata, ba zai iya yi fushi da ita ba. Ya mike ya koma toilet ya hada ruwan wanka, ya fito yana shiryawa amir ya shigo tare da wata maid dauke da abinci, ta ajiye ta fita, shi ya manta ma da wani abu wai shi abinci, duk soyayyarsa da abinci kuwa, ashe gaba ma akwai gabanta. Amir ya zau a yana kallonsa yace "ya naga kana shiryawa? Ina zaka je kuma? Kasan doctor yace 3 days of bed rest ya baka ko?" Ba tare da sultan ya kalle shi ba yace "fuck the bed and fuck the rest" Amir bai hakura ba yace "at least kafin ka fita eat something, rabon ka da abinci tun jiya da rana" sultan ya sake cewa "fuck the food" ya dauki key din mota ya saka takalmansa yayi hanyar waje, Amir ya bishi da sauri yace "don't do this sultan, zaka saka yarinyar nan in more trouble than she already is" ya juyo ya nuna amir da key din hannunsa yace "fuck you" ya juya ya fice. Tafiyar da yayi zuwa packing space kadai ita ta tabbatar masa ba zai iya shiga dakin Moon yau ba, har gumi ya hada saboda ciwo, sai da ya zauna a mota ya huta sannan ya tayar da ita ya fita. Daga nesa da gidan yayi packing ya dauko wayarsa yayi dialing number dinta, shi kansa yasan ba zai samu ba dan ya san da ace da waya a hannunta da yanzu ta neme shi, duk three lines dinta are switched off, har layin ta na England sai da ya kira. Ya jefar da wayar akan seat din motar, sai yanzu yayi nadamar kin cin abincin da yayi, da at least ya dan samu karfi ko yayane. He is not going to give up, no, sultan never gives up. Ya tayar da motar ya karasa bakin gate din gidan yayi packing ya fito, ya karasa baking gate fin yayi knocking. Instead of maigadin daya saba gani, wani katon mutum ya gani ya bude kofar yana kallonsa yace "ya akayi?" He itch to punch the man in the face, ya dan kakaro murmushi yace "Moon tana gida kuwa?" Mutumin yace "what is it to you in tana gida?" Control3 sultan yake ta maimaitawa a ransa sannan yace "am... Ina son magana da ita ne" mutumin ya sake hade rai yace "she is not seeing anybody, so get lost" daga haka ya mayar da kofar ya rufe. Hannu sultan ya dunkule ya daki kofar dashi wishing ina ma dai mutumin ya daka da sai yafi hucewa. Ya koma mota kafarsa tana pulsing saboda zafi ya zauna yana tunanin abinyi. Yana hango balcony dinta a rufe. They are her family, yasan ba zasu yi harming dinta ba, he just need to see her dan ya tabbatar she is OK. A karshe ya yanke shawarar ya tafi gida for now, yayi jinyar kafarsa ya samu lafiya, karfinsa ya dawo, and then he is going to take her away, and no body will stop him. Kwana biyu yana kwance yana jinya, Amir ne mai kula dashi, kaf cikin gida babu wanda ya leko yace masa ya jiki duk kuwa da cewa Amir ya shiga ya fada musu. Yana bin ka'idojin likita sosai saboda yana so ya samu lafiya, on the fourth day ya shirya yau za'ayi ta kare dan har kayan sa ya zuba a mota, ya sayi flight tickets da sunan sa da nata zuwa America. Dare yana yi ya dau mota ya fita, ko Amir bai sani ba, yaje yayi packing a bayan gidan ya fito da kafa ya zagaya, yayi studying katangar da gate din sosai, ya lura akwai shocking saman katangar, gate din kuma yana hade da alarm. Windown dakin mai gadi yaje, a hankali yayi sliding glass din, ya leka dakin yaga babu kowa, daraf ya shige dakin, a ransa yayi tsaki yace 'mai gadi ya tafi yana gadin gate yabar dakinsa unguarded' silently ya fita ta kofa, ya hango mai gadi da securities biyu a bakin gate duna zaune suna hira. Ta cikin inuwar katangar gidan ya ringa bi yana tafiya saboda security light din da aka kunna ta haske gidan gaba daya, a haka har sai da yaje backyard kusa da boys quarters sannan ya koma jikin gidan, a hankali ya ringa neman back door har ya ganta, lock dinta is coded, dama yayi tunanin haka, ya dauko powder a aljihunsa ya hura akan lock din, a take ya gane numbers din 0258 yayi tunani kadan sai yayi murmushi, Moons birthday, a ransa yace 'they should have change it' ya danna da correct arrangement din 25-08, kofar ta bude ya shige ciki. A gaban stairs ya ganshi, bai jira komai ba ya hau, ya san a side din da dakinta yake dan haka nan yabi, yana ganin kofar ya gane itace saboda pink doormat daya gani, she is the only girl in the house, ya kama door knob din yaji a rufe, ya tsugunna yana studying keyhole din sannan ya dauko wani pin a aljihunsa ya zura a ciki, in less than a minute ya bude kofar ya shiga, wayarsa ya dauko ya kunna fitila yana haska dakin, babu kowa, gadon ma ko shimfida babu akai, a gurin ya durkushe, where is she? Haske ya ga ya gauraye dakin, ya dago kai da sauri half hoping to see her standing, mommy ce a tsaye a bakin kofa, da securities guda biyar a gefenta, yayi sauri ya mike tsaye, tace da securities din "take him away, ku kaishi station kuyi charging dinsa with assault, kidnapping and trespassing" ta juya tayi tafiyarta. Mamaki ne ya hana sultan motsawa har suka saka masa ankwa suka fita dashi, lallai mommy ta nuna masa ta fishi shekaru. Ranar a station ya kwana. Bai damu ba, tunanin sa daya shine ina Moon take. Washe gari da sassafe aka turo daga fada akayi bail dinsa, not because an damu dashi but to protect the family name, yana zuwa gida ya tarar da takardar sammaci a kotu, mommy ta kai shi kara, kuma a takardar ance ya sace Moon, dan haka ana tubumarsa daya fito da ita. Duk abinda yake na glass a part din Sultan ranar sai da ya fasa shi, duk ya jiwa hannunsa ciwo, sai da Amir ya kira galadima sannan ya samu kan sultan. Nan da nan Takawa ya fara neman yadda za'a samu alkalin da aka kaiwa karar a kashe maganar ba tare da yasan 'yar waye ma ake rigima akanta ba. Babu wanda ya kira sultan ya tambayeshi ba'asin mai ya faru ko kuma yayi masa fada. Bayan la'asar Amir ya kira masu gyara suna ta aimin gyaran part din Sultan, Sultan ya sulale ya fice daga gidan, gidan su Moon ya koma, gate din a bude yake kamar gidan a cike yake, yayi packing ya fito direct ya nufi gate din yana shiga David ya tso ya tare shi, David shine chief security din gidan, katon gaske ne dan Moon tun tana rayinya take tsoronsa, amma naushi daya Sultan yayi masa sai ga David akan gwuiwoyinsa yana kokarin dawo da numfashinsa, nan take sauran securities din sukayi kansa. Hayaniyar da suke yi ce ta jawo hankalin daddy wanda yake tsaye ya tsare mommy da ido bayan ta amsa masa da "she is safe" ya fita da sauri su Walid suna binsa a baya. Scene din da ya gani a compound dinsa ne yasa ya saki baki yana mamaki, already Sultan ya zubar da mutun uku a kasa, yana ganin daddyya fito ya gane shi dan yasha ganin pictures dinsa a wayat Moon, ya karaso gabansa da sauri, yana zuwa ya zube akan gwuiwarsa, yana haki yace "Sunana Abubakar Sadiq Abdallah, I am a drunk, I don't know who my mother is and my father hates me, na taba zama a gidan kangararru, I have a bad temper, I get in trouble most of the times and I have heavy criminal record with the police. Nazo ina neman auren 'yarka, Maimunatu" Hmmm. Lets see, a mazan gidan nan waye yake da courage din Sultan? [11/7, 2:32 PM] maryamsuleiman48@gmail.co: MAIMOON By Maman Maama Episode fifty five : Her Father's Daughter 2 Kowa a gurin sakin baki yayi yana kallon Sultan, hatta daddy rasa mai zaice masa yayi, ya jima yana kallon sa shi kuma Sultan ya sunkuyar da kansa kasa, a zuciyarsa yana wishing ina ma dai zai iya kuka, maybe in hawaye ya fito masa zai ji sanyi a zuciyarsa, wannan mutumin da yake tsaye a kansa is his only chance to happiness, idan yace yes to shi kam ya samu duk wani buri nasa na rayuwa, in yace no kuma tamkar a saka full stop ne a rayuwar sultan. Daddy ya sauke ajjiyar zuciya yace "wannan shine dalilin ka na shigo min gida ka tayar min da hayaniya? Wannan shine dalilinka na dukan securities dina?" Sultan ya kuma sunkuyar da kansa yana jin bugun zuciyarsa yana karuwa. Daddy yace "tambayarka nake yi fa?" Sultan ya dago kai ya kalli daddy da jajayen idanunsa yace "daddy ba zasu bar ni in ganka ba ne. And I must see you. Tun a England muka shirya da Moon za ta kawo ni gurinka, bamu samu dama ba, anan ma muka sake shirin zuwa ganin ka shima still bamu dace ba. This is the only way for me to see you" da mamaki daddy yace "ita moon dince ta amince maka kazo gurina ka nemi auren ta?" Sultan ya gyada kansa yace "yes daddy, kuma yanzu I don't even know where she is" daddy ya jinjina maganar a ransa, in dai har Moon ce ta turo shi gurinsa then she must have her reasons, maybe reasons dinta yana daga cikin dalilan da yasa mommy ta dauke ta. Ya juya ya kalli Walid a gefensa yace "Walid shigo dashi ciki" ya juya ya koma palo, walid ya bishi da kallon mamaki amma shi yasan bai isa yayi masa musu ba, yiwa iyaye musu baya daga cikin tarbiyyar da aka basu. Ya mika wa sultan hannu da niyar ya taimaka nasa ya tashi tsaye, sultan ya watsa masa harara ya mike a hankali yadda su biyu kadai zasu ji yace "zan dawo kanka ne" bai jira walid yayi masa jagora ba ya bi bayan daddy. Ya tarar palo babu kowa, da alama daddy sama ya hau, akan carpet ya zauna ya harde kafafunsa ya zabga tagumi. He is ready to wait to awa nawa ne, ko kwana nawa ne, indai har at last daddy zai saurare shi. Walid ya shigo ya samu guri can nesa da Sultan ya zauna, babu wanda yace wa kowa komai har daddy ya sauko, ya yi wanka ya chanza kaya sai kamshi yake, Sultan ya kalli kayan jikinsa, sun chukurkude saboda fadan da yayi da securities, babu abinda yake sai warin gumi, ya daga kafada bai damu ba. Daddy ya zauna akan kujera yana studying Sultan. He is a perfect mixture of his father and mother. Fuskarsa sak ta Khairat sai dai kawai shi namiji ne ita mace, sai kuma duhun fata da ya fita saboda yayi mix da duhun fatar babansa, kirar jikinsa kuma sak na babansa lokacin yana age dinsa. Daddy yana hango su a idonsa suna wayo tare ko'ina a Oxford. What has gone wrong tsakanin su? Yayi gyaran murya yace "bismillah malan Abubakar, fara daga farko, a ina ka hadu da 'yata kuma menene a tsakanin ku?" Sultan ya danyi shiru yana controlling emotions dinsa sannan ya fara bada labari, komai sai da ya fada wa daddy, da boye boyen da suke yi saboda tana tsoron kawo shi gida, rayuwar su a England da America, amma duk bluntness din sultan bai bada labarin toilet experience dinsu ba, ya bada labarin plans din da suka ringa hadawa na zuwa ganin daddy amma ana samun sabani, ya bada labarin matsalar da suka samu akan project dinta da fushin da yayi ya tafi bar ita kuma ta bi Amir ya kaita gurin shi, ganin da munir yayi musu da zuwan Walid. Sai da ya gama kaf sannan yace "dan Allah daddy kar ka raba mu wallahi mutuwa zanyi, I have no body a duniyar nan sai ita" daddy ya kalle shi a nutse yace "you look like your mother" Sultan ya dago kansa da sauri ya kalli daddy yana tunanin anya kunnen sa ba karya yayi masa ba, sam babu wasa a fuskar daddy, ya sake cewa "kamar ku daya, sai dai ta fika fari, ta fika kuma hankali da nutsuwa" da rarrafe sultan ya karaso gaban daddy ya rike kafarsa yace "you know my mother?" Daddy ya gyara zama yana kallonsa yace "ba sosai ba, dan bamu taba magana da ita ba, amma na san ta kuma ina ganin ka nasan dan ta ne kai. Oxford sukayi karatu ita da babanka, lokacin yana kamar ka. Baban ka was exactly like you, he was a rogue also. A gang leader na 'ya'yan masu kudi" daddy yayi murmushi yana tuno rayuwarsu ta makaranta yacigaba da cewa "ni lokacin dan talakawa ne dan haka bana cikin su, ina dai hangen su suna yawo da motoci a cikin makaranta. He was so energetic, so stubborn like you. Duk sanda na ganshi a TV yanzu sai inyi ta mamakin yadda akayi ya koma haka" sultan ya saki baki yana mamaki, bai taba tsammanin cewa da akwai wani abu na halayya daya dangantashi da babansa ba. A hankali yace da daddy, "please tell me about my mother" daddy yace "kamar yadda na gaya maka, ban santa sosai ba, nasan dai sunanta khairat, and i always say, she is the most beautiful woman I have ever seen. She is full blood Arab. Tana da nutsuwa sosai, kuma daga ganin ta daga babban gida ta fito. They were so much in love ita da Sadiq. I remember always thinking they look odd, ita so fair shi kuma so dark, ita gentle shi stubborn, ita Arab shi Hausa. Amma duk 'ya'yan masu kudi. Muna gama PhD suka bar Oxford, ni kuma na zauna na kama lecturing a can. Ban taba dauka sun rabu ba. Shi yasa nayi mamaki da kace min baka san mamanka ba, and you said something about your father hating you. Ban gane me kake nufi ba. Why will your father hate you?" Sultan ya girgiza kansa yace "nima ban sani ba fa" nan ya fara bawa daddy labarin rayuwarsa tun sanda yayi wayo har zuwa haduwarsa da Moon. Duk abin ya daure wa daddy kai. He needs time to think about it. Sultan ji yayi kamar zai hadiye daddy, tunda yake babu wanda ya taba bashi labarin mahaifiyarsa, he only know her name shima kuma a birth certificate dinsa ya gani, yanzu yasan she is Arab, yayi murmushi, he always have a thing for Arabs, duk da ba wai iya larabcin yayi ba amma duk sanda yayi sai aji kamar a bakinsa aka rada shi ashe its in his blood. Ina ma dai one day zai ganta? Sai kuma ya cire maganar daga ransa, tunda har ta iya cire shi daga jikinta ta ajiye shi ta tafi without a second look to shima dan me zai nemeta. Suna tare da daddy har magrib sannan suka je masjid tare suka yi sallah daga nan daddy yace masa "kaje gida sultan, give Walid your number, I will think about maganar ka and I will call you" daga haka ya shige gida, Sultan yaji babu dadi, he don't want to go home, to menene a gidan ma in yaje? Shi da daddy zai barshi ma anan gidan zai zauna, it will make him feel closer to Moon and also to his Mom. Tunda mommy taga Daddy ya shigo da Sultan palo ta hau sama ta shige bedroom din ta, this is exactly abinda yasa ta dauke moon, tasan halin daddy, he is soft hearted like moon, da mutum ya zauna ya tsara su ya nuna musu cewa shi abin tausayi ne shikenan. People are not to be trusted, especially people like sultan. Dan haka ta yanke shawarar ba zata gaya wa kowa inda Moon ta ke ba har sai daddy ya fahimci cewa Sultan is totally not to be trusted. A bangaren daddy kuwa bayan sun rabu da sultan ya hau samansa ya tarar da abinci sa a dining dinsa, an jera komai amma babu mommy a gurin, bata taba yi masa haka ba kullum tare suke cin abinci in dai yana gari dan haka abincin kadan yaci yaji ya koshi. Ya kira wayarta taki dauka, mata kenan, shi a ganinsa itace fa mai laifi, ita ta boye masa yarinya amma kuma itace mai yin fushi? Shi me yayi mata? Abu daya ya saka zai rabu da ita shine yasan babu yadda za'ayi tayi harming Moon dan haka kamar yadda tace she is safe ya yarda she is safe din. Maganganunsu da Sultan ya fara dawowa dasu baya yana bin su daya bayan daya, maganar farko daya kamata yayi looking into itace ta yadda Moon ta zabi Sultan har tace ya zo yaga babanta, yasan halin Moon kuma ya yadda da ita, in dai har tace ta zabi sultan than there is something about him da ta gani, something good. Ya shiga bedroom dinsa ya dauko laptop dinsa ya kunna, the first place da ake samun information ya shiga, internet, amma duk abinda ya gani akan Sultan are not good, but why will Moon choose him? Shi abinda ya gani ma zai iya cewa gwara Munir akan Sultan, ya girgiza kansa, hakkin ubane ya samo wa 'yarsa miji na gari, yes Sultan indai labarin daya bashi gaskiya ne to negligence ya jawo ya zama abinda ya zama, amma wannan ba zai saka shi kuma ya dauki 'yarsa ya bashi ba. Emails dinsa ya duba yaga sun taru, kwana biyun nan he was very busy baya samun duba mails dinsa. Ya tashi yaje yayi sallah isha ya dawo, daya bayan daya ya fara bin emails din yana karantawa, bai jima ba yazo kan nata, "please daddy look into this" ya duba date din ya ga ranar da tabi Sultan bar ne amma da safe, ya bude document din data yi attaching, it is an amazing write up akan sultan, ta fara da tarihinsa, almost duk labarin da sultan ya bashi sazu, tayi bayanin duk bad characters dinsa, so she knows duk mugayen halayensa amma ta zabe shi? Sai kuma ta fara wani bayanin da daddy bai gane ba, a totally different side of Sultan, tana bayanin wadansu halayen wanda babu wanda zaice sultan yana dasu, tana dauko kowanne mugun hali data fada a baya tana justifying abinda yasa ya zama haka, tayi bayani akan yadda yayi rayuwa a america da irin yawan mutanen da ya rike tun a lokacin da ya kamata shi kansa ace rike shi ake yi, she then mentioned the orphanages, anguwannin talakawa a Abuja da Sultan ya rike, he is a hero to them, mutanen da ya samarwa aiki, yaran da ya saka a makaranta, talakawan da yake ciyarwa kuma duk ba tare daya nemi ko da godiya ne daga gare su ba, tace "he told me that doing something good makes him feel good, and that's what he wants, not people's praises" a karshen rubutun kuma tace "I believe this character a good person, but this life conditions makes him look bad in his eyes and the eyes of other people, but deep inside him he is good, very good" Daddy ya zama speechless, ya rasa tunanin me zaiyi, internet ya koma ya fara searching abubuwan data fada akan sultan amma bai ga ko daya ba, me hakan yake nufi? Amma yasan 'yarsa, she will not lie like this, especially not to him, amma me yasa babu wanda yasan sultan da wadannan halayen data lissafa sai ita kadai? Sai kuma yayi tunanin halin mutane, they only see what's on the surface, dan haka kallo daya zasu yi wa Sultan suyi tagging dinsa as a bad person shi kenan kuma, su kuma wadanda yake good to mutane ne da basu da say a cikin al'umma, dadin dadawa kuma shi kansa sultan din bai yarda cewa shi mutumin kirki bane kuma he is set on anything da zai bata wa babansa suna. Sai da kan daddy ya fara ciwo sannan ya tashi ya je ya kwanta, har yanzu mommy bata zo ba, ya yanke shawarar he is going to ignore her for now, har sai ya gama binciken sa akan sultan. Washe gari sai 12 ya sauko saboda jiya bai yi wani baccin kirki ba. Kuma yau ma tunda ya tashi yake making phone calls na meeting din daya shirya, yana yin breakfast ya dauki Walid a mota suka fita. Farko court din da mommy ta shigar da kara ya fara zuwa yace an janye karar dama misunderstanding ne kuma an samu fahimta. Private investigators ya hada har mutum goma, task din su shine yana son sanin komai akan Sultan, komai, including labarin rabuwar iyayensa. Sun charging dinsa kudi da yawa amma money is nothing to daddy dan haka ya signing musu check, half now half kuma sai sun gama aikin. Exactly one week aka kawo masa report dinsa, ranar har gari ya waye bai runtsa ba, hatta school report din duk kanin makarantun da Sultan yayi sai da aka kawo wa daddy. Komai na Sultan sai da daddy ya sani har abubuwan da ita kanta Moon bata sani ba. Sanda ya karanta ainahin dalilin rabuwar iyayen Sultan sai da ya dafe kansa yace "ya Salaam" gari na wayewa ya kira Walid yace "ka kira Sultan kace ina son ganin sa da yamma" A bangaren sultan kuwa tun da ya bar gurin daddy gida ya koma ya shiga part dinsa ya kori kowa ya rufe kofa, he misses Moon sosai, dama zai samu ko muryarta yaji da yaji dadi, amma babu abinda zai yi dole ya jira kamar yadda daddy yace masa, tunda yace he will call then he will call din tunda baiyi kama da karamin mutun ba. Matsalar daya ce shine bai san abinda zai gaya masa in ya kira shi din ba, it will either be the end of his life or the beginning of his life. Jiran kuma anan za'a samu matsala, jira bashi da dadi ballantana ga mutum mai zuciya irin ta sultan. Kwana daya kawai duk yabi ya tayar da hankalinsa, he badly want a drink amma yana tsoron kar yasha daddy kuma ya kira shi, ko kuma ace moon tazo, ya tuna rokon da tayi masa akan kar yasha, menene ma abinda tace masa yayi instead? Ce masa tayi ya karanta alqurani. Ya tashi a hankali ya bude drawer da yake zuba books dinsa, anan yake aje alquranin sa tun wanda kakansa ya bashi, yana yawan daukoshi ya karkade ya mayar ya ajiye, karantawar ne dai baya yi. Ya dauko ya dawo kan gado ya zauna ya bude page din farko ya karanta fatiha. Ita kadai ya karanta yaji wani dadi a ransa, ya tuno sanda yana yaro a gurin kakansa wani lokacin tare suke karatu saboda kullum kakansa yana ce masa yana son yaji yana karatu saboda yadda yake lankwasa harshensa irin na larabawa. Ya ajiye al'quranin ya shiga toilet ya yo alwala ya zo ya shimfida sallaya yayi sallah raka'a biyu, sai kawai ya samu kansa da yin addu'a, abinda da ba yayi, ya roki Allah ya kawo haske a cikin rayuwarsa duniya da lahira, ya kuma yiwa Moon addu'a Allah ya kare ta a duk inda take sannan kuma Allah ya sa allkhairi a al'amuran su baki daya, daga nan ya jawo alquraninsa duk surorin saman sun bace masa duk da cewa da ya iya amma rashin karantawa yasa duk sun zube, na kasan dai ya iya su sosai saboda kullum yana karantawa a sallah. Nutsuwar da ya samu sai yaji tafi wacce yake samu idan yasa giya, ji yake kamar wani assurance na cewa everything will be OK. Tun daga ranar ya samu abinyi, baya zuwa ko ina yana daki sai dai a kawo masa abincinsa nan, kullum sai Amir ya shigo ya duba shi su dan taba hira ya fita, sosai Amir yaji dadin changin abokin nasa dan bai dauka zai taba zama calm akan rabuwarsu da Moon ba, Sultan ya bawa Amir labarin duk yadda sukayi da daddy nan suka hadu zaman jiran kiran daddy. Sai da akayi kwana takwas sannan kiran ya shigo, lokacin amir yana game da wayar Sultan, wayar ta fara ringing amir yace "wow, is this who I think it is?" Sultan ya kalli screen din yaga 'Walid' da sauri ya warce wayar ya daga da sallama, ba tare da Walid ya amsa ba yace "Daddy says to come after Asr" daga nan a katse wayar. Sultan ya jima yana kallon wayar a hannunsa, duk jiran da yake yi kuma sai yaji gabansa yana faduwa. Ya gayawa Amir abinda walid yace, ya tashi ya fara neman kayan sakawa, sai yau yayi nadamar rashin dinka manyan kayan da bayayi, da sam bai damu da duk irin shigar da yake yi ba amma yau sai yaji yana son yayi shigar kirki, da kyar ya samu kaya wadanda basu kama jikin sa ba. Amir yace zai rakashi, nan sultan ya kora masa warning kar ya saka matsatstsun kaya kuma ya tabbatar baya warin sigari, baki kawai Amir ya saki yana kallon Sultan, he is really changing, yace "since when did you care wanne kayan na saka?" Sultan ya bata rai yace "just do as I say kuma ka tabbatar ka cire wannan sarkar in ba haka ba bazan tafi da kai ba" Da yamma suka je gidan, a palon baki aka sauke su aka kawo musu drinks da snacks, sultan da baya barin abinci amma yau sai ya samu kansa da kasa cin komai, so yake kawai daddy yazo yaji abinda zai ce masa. Basu jima ba daddyn ya fito cikin shiga ta alfarma kamar kullum, yana shigowa suka mike tsaye duk har sai da ya zauna sannan suka zauna suma tare da gaishe sa, ya amsa ba yabo ba fallasa sannan ya kalli Amir yace "Amir ko?" Amir ya gyada kansa, haka kawai yaga daddyn yayi masa kwarjini. Shima daddy ya karanta labarinsa da duk abinda Sultan yayi masa. Ya jima yana kallon Sultan wanda ya sunkuyar da kansa yana jiran abinda zaice, can daddy ya bude baki yace "Sultan, zaka iya dawowa nan gidan ka zauna a gurina?" [11/7, 2:32 PM] maryamsuleiman48@gmail.co: MAIMOON By Maman Maama Episode Fifty Six : What You Sow Sultan ji yayi maganar wani iri, sam ba abinda yayi tsammani ba. Ya jima kansa a kasa kafin yace "daddy bansan me zance ba" daddy ya gyada kai yace "I understand. Kafin ince zan baka Moon ko ba zan baka ita ba, dole ina so inga how far you can change, dan haka nake son chanza maka environment zuwa gurina. Amma da akwai sharadi, indai har ka amince zaka dawo gidannan dole zaka bi sharuddan zaman gidan nan, na farko babu yawo, zaka iya fita iyakacin cikin gari amma in dai zaka bar gari sai na sani kuma sai na amince, a cikin garin ma duk inda kake in lokacin cin abinci yayi zaka dawo gida saboda tare muke cin abinci a gidannan breakfast lunch dinner duk tare muke ci, kuma duk inda kake 9pm tayi maka a gida, babu wayon dare. Sanna the most important thing, ba zanyi tolerating koda single drop of alcohol a gidan nan ba, kuma koda a waje kasha ba'a gidan nan ba zan sani kuma ni kadai nasan hukuncin da zan yanke maka. I also want a total change of friends daga gareka, Amir will still be your friend of cause amma shima in naga bashi da niyyar chanza hali dole zan raba ka dashi, ga Walid nan shine sabon friend dinka zan kuma gaya masa kar inji kuma kar in gani a tsakanin ku. Abu na gaba kuma gida na ba gidan 'yan dambe bane, ko da wasa kar inji ance ka daki wani a cikin 'yan aikin gidan nan, tsakanin ka dasu ya zama girmamawa da mutunta juna. Next thing is you will need a change of wardrobe, saboda kamar yadda nake yawo da Walid haka zan ke yawo da kai kuma ba zan ke shiga da kai cikin mutane da wannan shigar a jikin ka ba. Wadannan sune sharudai na, in kaga zaka iya yarda dasu then you are one step to getting Moon, in kuma kaga ba za ka iya ba shikenan sai ka chire ta a ranka Allah ya hada kowa da rabonsa" da sauri sultan ya dago yana kallon daddy wanda shi kuma ya dora kafa daya kan daya ya daiki jarida yana kokarin budewa, alamar ya gama magana kenan. Sultan wani iri yake jinsa, wani irin feeling mixed with kunya, tunda yake ba'a taba ce masa 'yi kaza ko kar kayi kaza ba' amma yau gashi daddy ya wanke shi tas kuma a matsayinsa na surukinsa to be. Da sauri Sultan yace "daddy na yarda, ni kam na yarda da duk sharudan" daddy ya ajiye jaridar yace "madallah da wannan hukunci, gobe da safe zanje fada da kaina zan nemi alfarmar dawowarka gidan nan a gurin mai martaba sarki" Sultan ya girgiza kai yace "ba zai ce komai ba, ba zai noticing ma bana gidan ba" daddy yace "whatever, hakkin sane a gaya masa, kuma ni da kaina zan gaya masa. Yadda muka yi dashi Walid zai kira ka ya gaya maka. You can go now" Sultan ya kasa tashi, shi maganar bata ishe shi ba, shi da za'ayi ta masa fada so yake yi, can ya dan taba Amir yayi masa rada "ask him ina Moon take" Amir ya dan yi gyaran murya yace "daddy ko zamu samu ganin Moon kuwa" ba tare da ya kallesu ba yace "you will see her when the time is right" still sultan bai tashi ba, he have one more question, ya matsa gaban daddy sosai yace a hankali "daddy, dan Allah a cikin informations din da kake dasu, I want to know, did my parents.... " sai kuma ya kasa karasa maganar, daddy ya ajiye takardar hannunsa sa yace "ina jinka" sultan ya hadiye yawu yace "did my parents marry before...... Did they marry kafin su haife ni?" Daddy ya jima yana kallonsa ya kasa magana, tausayin yake ji har cikin ransa, jin daddy bai yi magana ba yasa Sultan ya mike tare da cewa "thank you daddy, dama ina so ne kawai in sani, I always thought wannan shine dalilin da yasa babana baya sona" daga haka yayi hanyar fita, har ya kai bakin kofa daddy ya kira sunan sa, ya tsaya ba tare da ya juyo ba saboda wani irin zafi da yake ji a ransa, daddy yace "sultan iyayenka sunyi aure kafin su haife ka, you are a legitimate child, abinda ke tsakanin ka da babanka is totally different from haihuwarka" Hmmm Kamar yadda daddy ya fada haka ya aikata, washegari yaje fada akayi masa iso gaban mai martaba sarki, bai yi tsammanin zai gane shi ba amma sai yaga ya tare shi sosai da fara'a da wasa da dariya yace "Muhammad baka da kirki, ace kana garin nan da iyalinka amma ba ka zuwa mu gaisa? Kasan ni nauyi yayi min yawa bazan iya ziyarar abokanai ba" daddy yayi murmushi yace "Allah ya taimake ka ai ni ma ba zaman garin nake sosai ba, kuma in dai nazo to abubuwa sukan yi min yawa har sai na koma. Amma ayi min afuwa, in sha Allah zan ke lekowa lokaci zuwa lokaci" Har palon da yake barkar manyan bakin sa ya saka aka shiga da daddy, nan suka zauna gaba dayan su akan carpet suka fara hirar yaushe gamo da labarin karatun su da friends dinsu wadanda yanzu kowa ya kama gabansa. Daddy yayi mamaki sosai yadda yaga takawa ya zage sosai yana hira da dariya, saboda shi ya dauka maganar da zasuyi formally zasu yi ta maybe a gaban mutane ma, ashe dai Sadiq din is still the same person da ya sani kawai dai nauyi ne ya hau kansa yanzu. Anan suka zauna har aka kawo musu lunch sam daddy bai lura da yadda lokaci ya tura haka ba, he totally can't believe cewa wannan elegant mutumin shi yayi raising Sultan. Da kansa mai martaba yayi serving dinsu a plate daya suka ci, suna cikin ci Abbas ya shigo a nutse yazo ya gaishe su sosai sannan ya fada wa babansa sako cikin girmamawa ya fita. Daddy yayi noticing wani abu, Abbas totally baya kama da Sultan, ba zaka taba cewa 'yan uwa ne ba. Sai da suka gama sannan daddy ya gyara zama yace "Allah ya taimaki sarki magana ce ta kawo ni. Akan dan mu Sultan" daddy ya fada yana kallon fuskar takawa, abinda yayi tsammani kuwa shi ya tarar, just mentioning sunan sultan ya goge dukkan fara'ar dake fuskar takawa, komawa yayi kamar bai taba dariya ba. Yace "Wani abun yayi?" Daddy yace "babu abinda yayi ran sarki ya dade, ina neman alfarma ne in da hali ina so ya koma gida na da zama" Takawa yace "saboda me?" Daddy yace "ba wani abu kawai mun hadu da shine sai naga kusan sa'an yaron wajena ne walid shine sai naga ina sha'awar in hada su a gurina for sometimes, in ka amince of cause" Takawa yayi shiru yana shan lemon hannunsa, har daddy ya fitar da ran cewa ba zai yi magana ba sai kuma yace "you can do with him as you wish. Kawai dai ka tabbatar duk abinda ya aikata maka kai ka jawo mu babu hannun mu a ciki, kuma ka tabbatar duk abinda yayi kar ka danganta shi da mu" daga haka ya ajiye cup din hannunsa ya mike tsaye yace "in ka kammala da akwai servants a waje zasu raka ka motar ka. Na gode da ziyara Allah ya bar zumunci" Da yamma Sultan yaji wayar Walid da sakon sarki ya masa maganar daddy, Sultan sam ya kasa tantance me yakeji a ransa, few things dinsa ya dauka ban da kayan sawa tunda daddy yace baya son irin su. To shi yanzu ina zai iya saka wata shadda ko yadi ne kam. Bashi ma da tailor. Yana zuwa gidan ya tarar da walid da Habeeb suna jiransa a compound, direct part dinsu suka wuce dashi fuskokinsu babu yabo babu fallasa dan sukam sam basa murna da wannan hukuncin na daddy. Four bedrooms ne dama a part din, sai palo mai hade da dining duk da dai ba mafani suke da dining din ba sai dai in bakon da ba za'a shiga dashi main palo ba. Walid ya bawa sultan key din daki daya da kuma spare key din palon. Sultan ya bude dakin ya shiga, ba laifi yana da girma, da gado da dan karamin closet sannan sai toilet. Yana gama duba dakin ya fita yana tambayar ina masu share share aka nuna masa su yace "dan Allah aron kayan cleaning nake so" da mamaki suke kallonsa, suka ce "ai mu zamu gyara maka" ya girgiza kai yace "thank you, zanyi, ba wani abu" Sultan sam bai yarda wani ya gyara masa dakin saba saboda gani yake ba za'a taba yi masa dai dai ba, tunda ya fara aiki bai gama ba har magrib, sannan ya shiga toilet yayi wanka ya chanza kaya ya fito da sauri, yana fitowa yaji dad yana cewa a kirashi su tafi masallaci, tare suka yi sallah suka dawo gida, suna zuwa suka zarce main palo, shi dai Sultan duk wani iri yake jin sa, yana zuwa masallaci wani lokacin amma bai taba zuwa tare da mahaifinsa ba ballantana ace wai harda siblings. A palon suka tarar an jera abinci a dining amma sam babu mommy, basu yi magana ba saboda kwana biyun nan haka take yi, kuma daddy ma baya son su hadu da Sultan har sai yayi mata magana da kansa. Suka zazzauna a dining din suna kallon kallo, can daddy yace "Sultan ai sai kayi representing Moon, kayi serving din mu" nan da nan sultan ya washe baki har kunne, ance yayi representing Moon, ya mike har da nade hannayen riga ya fara lafta musu abinci, walid yayi dariya yace "wannan uban abincin duk kana tunanin zamu cinye?" Sultan yace "why not?" Sai da kowa ya rage nasa abincin amma sultan ya chinye nasa tas. Daddy ne ya fara tashi ya koma palo, sultan ne na karshen gamawa, nan ya fara kokarin kwashe kaya, Habeeb yace masa "ka bar shi fa, za'a kwashe ai" shi Sultan ya saba da yiwa kansa komai, tunda aka kaishi america shi yake yiwa kansa komai, daya dawo Nigeria ma haka. Ya karaso palon, har zai zauna sai kuma yaji ajikinsa kamar zai shiga hurumin da ba nasa ba, sai ya mike zai fita, yana jin ba dadi a ransa, daddy ya kira shi ya dawo ya zauna yace "ina maganar kayan sawa da muka yi da kai?" Sultan ya dan bata rai yace "daddy ni ban taba dinki ba, ban masan inda ake saida yadikan ba ballantana wani tailor, amma in na samu zanyi" daddy ya kalli walid yace "gobe ka kai shi gurin tailor din mu ya auna shi, sai kuma ku shiga kasuwa kuyi siyayya" sai kuma ya juya gurin sultan yace "zaka iya ci gaba da saka kananan kayan ka a gida, amma duk sanda zamu fita ina so in ganka da manyan kaya da hula" sultan ya shafa kansa, lallai akwai rigima kenan, shi kam rabon da ya saka traditional hula tun kakansa yana da rai. Daddy ya juya kan su walid yace "ga Sultan nan, ina so ku rike shi tamkar shima dana ne da baya gurin mu amma yanzu yazo, kar inji kar in gani a tsakanin ku" duk suka amsa. Daddy ya sake cewa da Sultan "yi min bayani akan yadda kake gudanar da aikin ka" nan sultan yayi masa bayanin yadda yake yi, daddy yace "abinda za ayi yanzu shine, head office zaka bude, ka dauki ma'aikata sosai, ka saka wa gurin suna yadda zaka ke samun contract sosai. Na duba ayyukan ka naga suna da kyau sosai dan haka nima zan kara yi maka advertising dan kake samun contract a projects din government. Ina ganin hakan shi zai kara rage kama yawo, in ka samu abinyi zaka fi zama a guri daya" sosai sultan yaji dadi, babu wanda ya taba bashi shawara akan me zaiyi da rayuwarsa ko aikinsa. Ji yake yi wata soyayyar daddy tana shigarsa. Daga nan suka fara hirar su abin sha'awa, a tsokani wannan2, har mamaki sultan yake dama haka family yake? Dama haka uba yake a cikin 'ya'yansa? Bayan sun tashi daga hirar sunyi sallah isha daddy ya hau saman su, dakin mommy ya shiga ya tura kofa, tana zaune tana aiki a computer, taji shigowarsa sarai amma bata dago ta kalleshi ba, a ransa yace 'wai ita menene problem dinta ne?' A bakin kofar ya tsaya yace "Fatima, ina so in sanar miki cewa Sultan ya dawo gidan nan da zama" zumbur ta mike har tana ball da system din gabanta ta karaso kua dashi da sauri tace "Sultan fa kace?" Sai kuma hawaye "haba dear, ya zaka dauko yaro kamarsa ka hada shi da yaran mu, so kake suma ya bata mana su kamar yadda ya so ya bata Moon? Dan Allah kayi hakuri idan purnishing dina kake dan na daukr Moon, wallahi zan dawo da ita, please ka kore shi daga gidan nan" daddy ya girgiza kansa yace "bazan taba korarsa ba sai dai in shine da kansa yace zai tafi, wanda bana jin zai ce haka, kuma badan kinyi min laifi bane yasa na kawo shi nan ba, a'a nayi haka ne dan naga wani chance ne na samun lada Allah ya dora akan cinyata, shi da na kowa ne, baka san wane ne zai ji kanka ba wata rana, kuma ita rayuwa duk abinda ka shuka shine zaka girba, ina so in shuka alkhairi yadda ko bayan raina zuri'ata zasu girbi alkhairi na. Ban gaya miki ba har sai da ya dawo saboda ina son kini zafin da naji nima sanda baki gayamin kin dauke moon ba har sai da kika aikata din. Yanzu bazan matsa miki cewa ki dawo da ita ba har sai na tabbatar da changes din da nake so in gani agurin sultan tukunna" daga haka ya juya yayi tafiyarsa. Mommy ji tayi gaba daya duniya tayi mata zafi, lallai daddy is even softer and weaker than she thought. Amma babu komai, ta tabbatar cewa Sultan will teach him a lesson. Ita kuma ba zata dawo da Moon ba har sai daddy ya yi learning lesson a gurin sultan tukunna. Cikin sati daya Sultan ya warware a gidan Ambassador MD. Ba laifi sun fara sabawa da su Walid, in da suke jinjina masa akan tsaftarsa dan gaba daya part dinsu ya chanza fasali kamar ba shi ba, har palon sai da yayi rearranging ya chanja labilaye da carpet. Daddy ya samo masa building din da zai bude head office dinsa, wanda ya fara dauka aiki shine Amir, tunda dama tare suke aikin su, nan da nan ya zama busy wajen gyaran gurin da interviewing maaikata, sai yanzu ya kuma gane abinda daddy yake nufi, dan in yana aiki sam mantawa yake yi da komai ballantana har yayi tunanin shan giya, ko a gida kuma har yanzu yana bin shawarar moon ta karatun Alqurani duk sanda ya ji yana son alcohol. Shi kansa yana jin chanji akansa, dan nutsuwarsa ta karu sosai. In dar har baya wajen aiki to suna tare da daddy, dan duk inda daddy zaije tare suke zuwa dashi da walid, har gurin manyan mutane, nan ya fara koyon saka manyan kaya da yadda ake gaishe da manyan mutane. Rannan har gurin president suka je, kuma he found it very interesting dan babu wanda yayi masa kallon wulakanci babu wani security daya hana shi shiga ballantana suyi rigima. Kuma wani abu da daddy yake yi shine, duk inda suka je sai ya gabatar da sultan a matsayin babban dan sarkin abuja, duk sai sultan yaji banbarakwai in yaga mutane suna bashi respect A gida kuma malami daddy ya dauko na karatun addini, bai ce saboda Sultan ya dauko ba sai yace yaga duk kowa a gidan ya watsar da islamiyya dan haka ga malami nan duk weekend zai ke zuwa za'ake karatu, har maaikatan gidan duk haduwa ake ana daukan karatu. Nan sultan yaga chance dinsa ya dauko alquranin sa ya fito, surorin daya manta nan duk suke bi suna tilawa tare da malam. A hankali karatunsa yake dawowa. In akayi dori ranar assabar ran lahadi kuma sai ayi tafsir, ko ayi karatin sauran littattafan addini, sai abin ya koma kamar discussion, kowa ya fadi abinda ya sani ayi masa gyara, in mutum yana da tambaya yayi. Sultan kam ya bude kunnuwansa sosai yana daukar karatu. Matsalar sultan yanzu daya ce, he terribly misses Moon. Kullum yana so ya tambayi daddy labarin ta amma baya so daddyn ya bata rai ko yaga gazawarsa. Kullum da daddare sai ya dauko bathrobe dinta daya dauka a toilet a america, da ita yake bacci yana jin kamshinta. Idan yana zaune shi kadai kuwa sai dai yayi ta kallon pictures dinsu da videos dinsu yana ta murmushi. She really is a Moon, her arrival in his life have brought light to his darkness. Ina ma iyayen mu zasu zama kaman daddy? Allahumma Ameen. [11/7, 2:33 PM] maryamsuleiman48@gmail.co: MAIMOON By Maman Maama Episode Fifty Seven : What You Sow 2 A 'yalleman kuwa tunda Munir yayi wa Hajja waya da sassafe ya hada mata karya da gaskiya ya gaya mata. Suna gama wayar ta fita daga part dinta ta tsaya a compound ta rafka wani uban salati "na shiga uku ni zuwaira yau wanne mugun labari zanji haka" a tare da baffa da inna suka fito daga part dinsa suna tambayarta "lfy? Me ya faru? Waye ya mutu?" Ita kuwa kuka take tana fyace majina da bakin zanin ta, "dama babu abinda ban fada ba aka ki daukan magana ta saboda bani na haifi muhammadu ba kuma shine dan gatan gidan nan, dama gata ai mugun abu ne, babu abinda yake haifarwa sai nadama. Wanda duk baiji bari ba ko ai zai ji oh'oh" inna tana jin zancen muhammadu ta ja da baya ta tsaya tana jiran taji alkaba'in da zai biyo baya. Baffa ma bari yayi sai da hajja ta gama sambatun ta sannan ya kuma tambayarta "me ya faru da muhammad din" Hajja ta duba taga duk yaran gida sun taru a compound suna sauraren abinda ake yi sannan tace "yaran nan babu yadda banyi ba akan ayi musu aure akaki, aka nuna min ban isa ba, to yanzu gashi nan abinda ake gudu ya faru. Manniru ne yayo min waya dazu hankalinsa a tashe, yace tunda yarinyar nan ta dawo kasar nan ta juya masa baya, in yaje gidan nasu sam ba'a barin shi ya ganta, in ya kira ta a waya bata dauka, to jiya da daddare wajan karfe daya ya fita neman abinci saboda yaje gidan sun hana shi abinci shi kuma yunwa ta dame shi, kawai yaga yarinyar nan a titin Allah tana yawo da dan skirt, ta sha giya tayi mankas ko tafiya bata iyayi sai wadansu maza ne suka rirriketa, shima kansa da kyar ya gane ta, kuma ya kira walid ya gaya masa, ashe sun riga sun san halin da yarinyar take ciki shi yasa basa barin ya ganta. Daya bisu gidan ya na tada maganar saboda ayi wa tubkar hanci sai walid da habibu suka taru suka yi masa dukan tsiya suka ce in dai ya sake ya fada wa mutane sai sun nakasa shi" wani irin jiri inna taji yana neman daukan ta, wannan wanne irin sharri ne munir ya shirya wa maimunatu? Palon ta ta koma ta zauna kanta yana bala'in sara mata, yaran gidan kuwa tunda suka gama jin abinda hajja tace suka fara fita daya bayan daya suna shiga makota kai rahoto, baffa kasa cewa komai yayi dan shima jirin ne yake dibansa, Ma'aruf dan autan hajja wanda kuma shi kadai ne ya rage a gidan ne yayi saurin dauko kujera ya zaunar da baffa. Sai da baffa ya mayar da numfashin sa sannan yace "hajja kin tabbatar munir ba karya yayi miki ba?" Hajja ta matso kusa dashi tace "yaya zaiyiwa yarinyar da yake so karya? Ita fa ya zaba ta zama uwar 'ya'yansa ta yaya zai yi mata sharri kuma? Ban taba ganin so na gaskiya irin wanda yaron nan yake yiwa yarinyar nan ba, duk da abinda ya gani da idanuwansa fa cewa yayi shi so yake ma a gaggauta auren ko Allah zai sa auren ya gyara ta" still zuciyar baffa taki yarda da maganganun hajja, yana kallon fuskar maimunatu a zuciyarsa, duk acikin jikokinsa yana son 'ya'yan muhammadu, kuma duk a 'ya'yan muhammadu maimunatu ta daban ce, ga tarbiyya, ga ladabi, ga fara'a, ga shiga ran mutane sannan uwa uba ga son 'yan'uwanta. Sam bata da girman kan wai babanta wani ne, duk sanda tazo sai ta zaga 'yan'uwa kai hatta 'yan aikin gidan nan kawayenta ne dan wani lokacin a cikin su zai ganta tana wasa. Hajja ta tankwashe kafar ta ta cigaba da zuba zance "ya gayamin ai ba laifin ta bane, wani yaro ta hadu dashi lalatacce shine ya bata ta, su kuma iyayen sun dauki son duniya sun dora mata shi yasa suka kasa raba su, dan ce musu tayi ko yanka ta za suyi ba zata rabu da yaron ba. Ni dai shawara ta shine, ka kira muhammadu ka gaya masa zama maza ya kawo mana yarinyar nan gurin mu, tana zuwa sai mu sata a lalle ayi auren nan kowa ya huta. Shi kuma wannan yaron da yace yaji ya gani zai aure ta a haka Allah yayi masa albarka" baffa da har yanzu kansa bai gama juya masa ba ya aika ma'aruf ya dauko masa wayarsa, amma maimakon ya kira muhammadu kamar yadda hajja tace, sai ya kira Aliyu, aliyu yana dauka ko gaisawa basu yi ba yace "Aliyu kaga abinda ka jawo mana ko? Taurin kanka ne ya hana ayi auren nan da yanzu duk wannan abin bai faru ba, to kasani ni babu ruwana, tunda kai ka jawo sai kasan yadda zakayi ka warware" yana kaiwa nan ya kashe wayar ya mike ya shige dakinsa, hajja ba haka taso ba dan tasan Aliyu sam ba zai taba goyon bayan munir ba, saboda kamar yadda take fada tace ya tsane shi saboda ba uwarsu daya da wanda ya haife shi ba. A bangaren inna kuwa tana shiga dakinta ta dauko wayarta ta kira mommy, sai da ta katse ta sake kira sannan mommy n ta dauka, itama ba tare da sun gaisa ba tace "Fatima me ya faru tsakanin manniru da maimunatu?" Cikin inda inda mommy tace "inna babu komai wani abu akace ya faru?" Inna ta bata rai sosai tace "Fatima dani fa kike magana ba da wani ba, cewa nayi me ya faru tsakanin munir da moon?" Mommy kuma sai kuka, sai da tayi me isarta sannan ta bawa inna labarin duk abinda ya faru a lokacin. Inna salati ta saka tace "amma fatima ya za'ayi ace yarinya tana tare da saurayi har tsahon shekara guda amma ke a matsayinki na mahaifiyarta baki sani ba?"Mommy tace "inna wallahi nasan tana tare da wani, amma bansan ko waye shi ba, da nasan yaron nan ne wallahi da tuni na raba su. Ita yarinyar nan kinsan halinta, har cikin zuciyarta gani take taimaka masa take yi" nan inna ta gaya mata duk abinda hajja take fada, mommy sai da ta sake wani kukan sannan tace "wallahi inna ba haka akai ba" kafin ta cigaba da magana inna ta katseta tace "na sani ai, ni nasan maimunatu, nasan abinda zata aikata da wanda ba zata yi ba. Yanzu dai zamu jira muji abinda baffa zai ce" Suna gama wayar uncle Aliyu yana kiran inna, saboda kiran da baffa yayi masa, tambayarta ya shiga yi akan menene ya faru, nan inna tayi masa bayani, nan take ransa ya baci yace sai ya babballa munir, da kyar inna ta lallabashi, maganar yaron da akace suna tare da moon kuma yace zaije har abujan yayi bincike yaji me ake ciki, saboda yasan da maganar yaron da moon tace masa tana so, tace masa dan sarki ne, kuma yasan akwai dan sarkin abuja tantiri. Da kadan da kadan magana take watsuwa ya a garin yalleman, amma ga mamakin hajja duk wanda aka gayawa maganar tun kafin a karasa ma yake cewa karya munir yake yi, da yawa daga cikin 'yanuwa cewa suke yi dan yaga har yanzu bata sonsa ne shi yasa zai yi mata sharri dan ayi mata dole, kowa yasan halin maimunatu kuma kowa yasan halin munir, shi halinka kuma shine jarinka, mutane kuma sune rahamarka. Shi yasa bature yake cewa 'it is good to be good' ni kuma nace 'it pays to be good' Uncle Aliyu bai samu zuwa abuja ba saboda aiyuka da suka yi masa yawa sai bayan sati biyu, yana zuwa baije gidan ba ya sauka a hotel, yaje unguwar a wayance yake tambayar mutane abinda suka sani tsakanin sultan da moon, amsoshin da yake samu sam basu yi masa dadi ba. A karshe dai ya kira ambassador inda shi kuma ya gaya masa ai yana gari ma. Da yamma yaje gidan, a compound ya tarar da ambassador tare da walid da kuma wani kyakykyawan yaro sun saka kaya iri daya shi da walid, har ya zauna yana kallon yaron dan sam bai san shi ba, suka gaishe shi tare shi da walid, uncle Aliyu ya dan tsokani walid sannan suka shiga gida. Sai a lokacin ya gaishe da yayan nasa, sannan yace "wannan yaron kuma fa yaya a ina ka samo shi?" Fuskar ambassador dauke da murmushi yace "Sultan sunan sa, shine babban dan mai martaba sarkin Abuja" da mamaki uncle Aliyu ya kalleshi yace "Sultan? Sultan din moon?" Daddy shima da mamaki yace "kasan shi ne?" Uncle aliyu yace "a'a bansan shi ba. Amma maganar sa ce ta kawo ni abuja. Sai dai kuma yadda ake gaya min labarinsa ba haka na ganshi ba" daddy ya gyada kai cikin gamsuwa yace "ai ba haka din yake ba, yanzu ne ya zama haka" nan ya fara bashi labarin sultan dalla dalla, a karshe yace "labarin yaron ne ya saka naji tausayinsa kuma nayi alkawarin gyara masa yaruwarsa" uncle Aliyu yanu tausayin rayuwar sultan sosai, amma duk da haka sai yace "gaskiya yaron abin tausayi ne, amma duk da haka yaya kana ganin ya dace mu dauki maimunati mu bawa yaron da yake da past kamar nashi?" Daddy ya gyara zama yace "shi aure wannan nufin Allah ne, yanzu ba maganar auren su ake ba tukunna, maganar chanzawa yaron yaruwa ake yi. Kuma ni sam ba domin maimunatu nake yi ba, ko da ace a yanzu sultan zai ce ya fasa auren moon to ba zan fasa ko daya daga cikin abubuwan da nayi niyyar yi masa ba". Suna cikin maganar sai ga sultan ya fito daga part dinsu, ya chanza wanka, yazo kusa da daddy ya durkusa yana shafa kansa yace "daddy zan dan fita" daddy yace "OK, Allah ya tsare. Make sure ka dawo kafin dinner" sultan yayi dariya yace "I won't miss it for the world" shima daddyn dariya yayi sanin halin sultan akan abinci, Sultan yayi wa uncle Aliyu sallama sannan ya fita. Har lokacin dinner uncle Aliyu yana nan, sosai yaji yana missing moon amma daddy yace kar ya kula mommy akan maganar ta, a dinner din duk su Habeeb har daddy suka saka sultan a gaba da tsokana shi kuwa ko a jikinsa sai zuba lomarsa yake yana kuma zuba surutu, sai dai in sun hada ido da uncle Aliyu ya dan sunkuyar da kai alamar kunya. Nan take uncle Aliyu yaji sultan ya shiga ransa saboda Sultan yana da shiga rai kamar Moon. Daga Abuja direct yalleman uncle Aliyu ya koma, ya samu baffa ya tabbatar masa da cewa duk maganganun Munir karya ne, yace masa kawai yayi mata sharri ne dan yana so a tirsasa ta ta aure shi. Ai kuwa da baffa ya tisa munir a gaba da fada kamar zai dake shi da kansa, dan har hajja sai da fadan ya shafe ta. Shi dai munir yasan ba duk maganar sa ce karya ba, akwai 'yar gaskiya a ciki, amma fur kowa yaki sauraronsa. Yana fita waje kuwa suka kwashi 'yan kallo da nuraddeen wanda tun da yaji maganar yace wallahi duk sanda munir ya shigo gari sai jikinsa ya gaya masa tunda yayi wa Moon sharri irin wannan. Kaikayi ya koma kan mashekiya. Wannan kenan; Sultan yana kwance a daki daddy ya kira shi, ya daga da sallama, daddy yace masa "Maza ka shirya ka fito zamu tafi Niger mu dauko Moon" rasa masar da zai bayar yayi dan ji yayi komai ya tsaya masa, sai da daddy yace "kaji abinda nace kuwa?" Da sauri yace "yes, daddy" ya mike yana tunanin anya yaji abinda yace din kuwa? Ya daiji kamar ance Niger kuma ance Moon, sai a lokacin tunanin shi ya dawo, Moon zadu je su dauko a Niger, what? It means yau zai ganta kenan? Wani tsalle yayi ya sauko daga kan gado ya fito palo yana neman walid dan yayi confirming maganar, yana fitowa walid yana shigowa da sauri, ya kalle shi yace "a haka zaka je dauko amaryar taka" Sultan ji yayi kamar kafafuwan sa ba zasu dauke shi ba, da gudu ya koma daki, sai kuma gashi ya sake fitowa da gudu yace wa walid "yau zamu dawo ko kwana zamu yi?" Walid ya duba agogonsa yace "sai dai mu kwana ai, it is already late, dan dai daddy ya matsa tafiyar nan ne amma da mun bari kawai sai da safe" Sultan bai ji karashen maganar ba ya koma dakin, ba'afi minti biyar ba sai gashi ya fito ya shirya da jaka a hannunsa, babu walid a palon dan haka ya fita waje ya saka kayansa a motar da zata kai su airport, ji yake kamar yaje ya chichchibo duk wanda za'ayi tafiyar dasu suzo su tafi, gani yake kamar duk suna sane suke lakaki. It seems like eternity kafin su mommy su fito, yana ganin ta yaji jikinsa yayi sanyi, bata taba yi masa magana ba kuma ko sun hadu a compound in ya gaishe ta bata amsawa, bai kuma taba ganin ta a palo ba shi kuma bai taba tambayar dalili ba. Yaji dadi da ba mota daya zasu shiga ba, shi da daddy, ita kuma da Walid. Sai gab da magrib suka je airport, private jet din daddy suka hau, kafin isha suka sauka a Niamey, aka kai su wani gida shi da walid suka sauka, shi dai kawai jira yake yi suje gurin moon, sai da zasu kwanta walid yake masa bayanin moon fa ba'a nan take ba, tana agadaz amma sun taho suna hanya, goben ma sai wajen azahar zasu karaso. Ranar sultan yadda yaga rana haka yaga dare, wani irin farin ciki yake ji da wani irin son Moon a ransa, sannan kuma da fargaba, what if yanzu kuma tace bata son shi? Tunda shi ya jawo mata duk wannan wahalar da ta sha, yasan tana cewa bata son shi kuma daddy zai kore shi daga gidansa. He will then be back to square one. Washegari tunda yayi breakfast yake zaune, gabansa ne kawai yake ta faduwa, sai can bayan azahar Walid ya shigo yana dariya, sultan yasan me zai ce masa "sun zo, baka je kayi mata oyoyo ba" Sultan ya zauna akan kujera yana rikr kansa, Walid yayi dariya yace "jarumtar kenan? Kar ka bani kunya mana, ni da na saka ran zaka fita a guje kaje ka ture daddy ka rungumeta?" Hararar sa kawai Sultan yayi dan shi kadai yasan me yake ji a ransa. Walid ya sake cewa "kaga ni na fita yawo, in ga kama ragwantar ka fita driver zai kaika inda suke, zan same ku a can" Sultan bai iya fita ba har sai da daddy ya kira shi a waya yace sun kusa gama wa fa, su zo su same su. Da sauri ya dan watsa ruwa ko zaiji garau, ya chanja kaya yana kallon kansa a mudubi, maybe ma cewa zata yi bai yi kyau ba, ya chire hular ya ajiye sai kuma ya sake dauka ya dora. Sai kuma yaji haushin kansa, me yasa yake nin tsoron wannan 'yar mitsitsiyar yarinyar ne. Koma me zata ce ta fada din. Ya fita aka kai shi can gidan, ya fito ya jingina da jikin mota yana jiran fitowar su, wayarsa ya dauko yana daddan nawa amma sam ba wai yasan abinda yake yi bane, ji yayi ana kallon sa, kuma har cikin jinin jikin sa yasan cewa itace kuma yasan daga wanne side take, a hankali ya daga kansa, cikin idonta ya tsinci nasa. Ya Allah. He had no idea how much he missed her sai da ya ganta. Karfin zuciya ne kawai ya saka ya tsaya a inda yake, ji yayi kamar yayi abinda walid yace, yaje ya rungume ta, amma kuma anya rungume budurwa a gidan surukai dai dai ne? Ta rame, sosai, Allah ne kadai yasan abinda zai yiwa wanda duk ya takura mata da zai ganshi. Sama sama yaji daddy yana magana amma bai fahimci me yake cewa ba, sai da ya sake maimaitawa sannan ya fahimta, wayarsa ya dauko ya kira walid ya gaya masa sakon daddy sannan ya bude wa daddyn kofa ya shiga ya rufe da sauri ya juyo inda take tsaye, Allah yasa bata bace ba, tana nan kuwa tamkar wadda aka dasa, cikin kwayar idonta ya kalla ya fahimci cewa he have nothing to fear, kujerar mulkinsa tana nan daram a zuciyarta. Da sauri ta bar gurin ta tafi daya motar ta shiga, sai bayan data shiga sannan ya lura daddy ya sauke glass din window dinsa yana kallon shi, ya shafa kansa da sauri yana sunkuyar da kai kamar munafiki sannan ya shiga gaban motar ya zauna. Walid ya karaso suka hau hanyar airport. [11/7, 2:33 PM] maryamsuleiman48@gmail.co: MAIMOON By Maman Maama Episode Fifty Eight : I Missed You Na lumshe idona ina addu'ar Allah yasa shi dinne ya gani ba wai gizo yake yi min ba, dan ganin nasa ya taba min wani guri a zuciya ta wanda bansan yadda zanyi ba idan ba shi bane. Muna zuwa airport muka fito, mommy ce ta fara shigewa jirgi, daddy ya tsaya suna sallama da mutane, sai lokacin na samu damar ganawa da yaya Walid dan a mota tsoron mommy ya hana ni magana, na rungume shi tsam a jikina ina ajjiyar zuciya "I missed you" ya rabani da jikinsa yace "I missed you too sweetie pie" ta gefen idona na hango sultan yana tahowa gurin da muke, kara kankame yaya Walid nayi ina runtse idona, 'Oh Allah, give me the strength kar inje inji kunya a gaban mutane' na kasa kallon inda yake dan nasan zan iya loosing control, muryarsa naji yana cewa "to cika ta haka, ai an gama oyoyon" shi dinne dai, dan muryar sa ce wannan. Ya walid ya dafa kafaduna da hannayensa duk biyun yace "anki din, sai ka bari in an daura muku auren sai kayi min iko akanta amma yanzu tawa ce. Ni ban taba ganin ma suruki marar kunya irin kaba sultan, babban wa ai uba ne, ni ne fa madaurin auren ta, inna ga dama sai ince bazan bayar ba" yaushe Sultan suka fara wasa da Ya Walid? Last time I check ya Walid ya mari sultan. Wata dariya sultan yayi yace "kayi kadan yaro, ni iya kacin sanina na girme ka, dan haka kai ya kamata ka ke yi min biyayya" ya walid ya kama hannuna muka tafi jirgi, har yanzu na kasa kallon sultan, sai da muka fara hawa steps din sannan na juyo ina tunanin kar mu tafi mu barshi, ina juyo wa muka hada ido, nayi sauri na dauke kaina. Chamber biyu ne da jirgin sai gurin pilots, daddy da mommy suna chamber din farko, mu kuma mu uku muna chamber ta biyu. Tunda na zauna har jirgin ya tashi ban daga kaina ba, duk jina nake a takure saboda idanuwan da sultan ya dora a kaina ko kiftawa baya yi. Ji nayi kallon yayi yawa na dan daga kaina kadan sai naga ashe ido hudu ne a kaina ba biyu ba, yau naga ta kaina zasu chinye ni danya. Ya walid yace "kin ganki kuwa? Wannan ai kece ifritu minal jinni. Wannan irin rama haka? Me Aunty Zaliha take miki?" Ni dai bance komai ba na rufe fuskata da hijab dina. Ina jin Sultan yana ce masa ya tashi ya koma gurin su Daddy, ya Walid yace "saboda me? Duk abinda zaka gaya mata ka gaya mata a gabana. Suma wadancan din couple ne, gwara ma ku ba aure ne da ku ba, babu wani abu da zakuyi wanda ba zan iya gani ba" su kayi ta maganganun su ina jinsu bance musu komai ba, shi Sultan yana ta insisting sai Walid ya tashi ya bamu guri shi kuma yaki. Nadan bude fuskata kadan na kallesu naga basa kallona sai na gyara zamana na bude fuskata sosai. A hankali nace ina kallon sultan "how is your leg?" Duk suka jiyo suna kallona da mamaki Sultan yace "What?" Na sake maimaitawa ina kallon kafarsa. Still bai gane mai nake nufi ba, nace "kafarka da kaji ciwo rannan, how is it?" Dariya yayi sosai, da alama yama manta da cewa yaji ciwon, yace "ta warke ai, tun tuni. Abinda ya kamata ki tambayeni shine how is my heart" ya Walid ya harare shi, ni kuma nayi murmushi ina sunkuyar da kai na kasa. Har muka sauka a Nigeria bamu samu munyi wata magana da Sultan ba, muna sauka muka tarar da motoci suna jiran mu, muka shiga sai gida. Tunda da na fito daga mota nake jin idanuwan sultan a kaina amma baki kallon inda yake da sauri na shige cikin gida. Ina shiga palo na tarar da yaran gida kowa sai murnar dawowa ta suke, nan na sha runguma har sai da jikina ya fara ciwo, da wayo na gudu na hau sama na shiga dakina, a gyare na tarar da dakin sai kamshi yake yi, na fada kan gado tare da lumshe idona, home sweet home, da sauri kuma na mike naje na bude window ina leken waje ko zan ganshi amma naga bayanan, to ko ya tafi gidan su? Toilet na shiga na kunna ruwa a tub na hada kumfa sosai, when was the last time I had a real bath? Na cire kayana na shiga ina sauke ajjiyar zuciya. Na lissafo irin wahalar da nasha, kuma duk akan Sultan amma yanzu wai gani gashi na kasa yi masa kwakwkwarar magana. Sai kuma na fara yiwa kaina tambayoyin me ya faru da bana nan? Ya akayi har su daddy suka karbi sultan har ya saba dasu sosai? Jin ana kiran sallar isha yasa na tuna ko magrib banyi ba, na dauraye jikina na fito, na bude kayana naga sunanan yadda na tafi na barsu sai dai daga alama an dan karkade su an sake gyaramin, na saka wasu riga da skirt ga mamaki na sai naga wuyan rigar yayi min yawa skirt din kuma yana zamewa, chafdi, gaskiya na rame da yawa, dole na saka doguwar riga nayi rolling mayafi na fita. Ina saukowa daga sama na tsaya da mamaki, Sultan again, dare dare a kan kujera a palo suna ta zabga musu da ya Habeeb, a tare suka juyo suka kalle ni, dif sultan ya dauke wuta ya daina magana, ya Habeeb kuma ya taso da sauri gurina yana cewa "welcome home, my parrot" nayi murmushi na karasa gurinsa, sai kuma ya rike hannuna yana kallon fuskata, dariya yayi yace "kinga yadda kika yi baki kuwa?" Na juya idona nace "tubarkallah, wannan yace da rame wannan yace nayi baki in ba so kuke ku chinye ni ba ai ya kamata ku kyaleni haka" daddy ne ya shigo Walid yana biye dashi a baya, duk muka gaishe da daddy ya hau sama, har lokacin sultan bai ce min komai ba sai kallo kamar zai chinye ni, dole na tashi na tafi kitchen na zauna ina kallon ana ta fita da kayan abinci, sai da naji daddy ya kuma saukowa sannan na kuma palon, still Sultan yana nan, muka tafi dining har dashi, sai kawai naga ya tashi yana serving din mu, what is happening ne ni maimunatu? Someone should start explaining. Har ya zuba min abincin kuma sai ya dauke ya sake karo min ba tare da ya kalleni ba yace "ki chinye wannan a karo miki wani" ji nayi duk suna dariya ni bansan dariyar me suke yi ba, daddy yace "yes, kina bukatar alot of food da kuma bacci ko kya yi kyan gani" a raina nace Daddy kaima harda kai ko? Allah ne kadai yasan shi kuma Sultan me zai ce min. Na dan fara cin abincin kamar bana so kuma sai naji taste din abincin ba zan iya resisting ba, nayi missing home da duk wani abu na home din, ya Habeeb yace "to 'yar agadaz, bamu labarin agadaz" na yi murmushi nace "sai dai in baka labarin anty Zaliha da samarin 'ya'yanta, dan su kadai na gani tunda naje agadaz din, ko kofar gate ban taba zuwa ba" nan aka koma hirar Niger da zafin garin, suna cewa zafin ne ya sakani baki. Tunda muke hirar Sultan baice mana komai ba abincinsa kawai yake ci, har ya gama yasha lemo ya mike tsaye, ina kallonsa muka hada ido nayi sauri na dauke kaina. Yace da Daddy "Daddy sai da safe" Daddy yace "Allah ya bamu alkhairi" ya dan jima a tsaye kuma sai ya tafi, naji bude kofar palo amma banji rufewa ba. Yaya habeeb ne ya fara taba ni yana nuna min hanyar waje, nayi kamar ban ganshi ba, ina jin yaya Walid yana yin dariya kasa kasa, sai kuma ya dan daga murya yace "na'am? Tana zuwa" sai ya ce a hankali "kamar naji sultan yana kiranki ko?" Shima yi nayi kamar bansan me yake yi ba amma fa ta ciki na ciki, a hankali Daddy yace "tashi kije" nace "yes Daddy" na mike a hankali kamar bana so nayi hanyar waje, amma fa a xuciya ta ji nake kamar in kwasa a guje. Ina zuwa kofar falon na ganta a bude, na fita na mayar da ita na rufe. Kafin inyi taku daya naji ni a jikin sa, duk da banga fuskarsaba amma nasan shine, na danyi kokarin raba jiki na da nashi amma ya rike ni tsam, nima kuma I need the hug, dan haka na kwantar da kaina, a tare muka sauke ajjiyar zuciya, ina jin bugawar zuciyar sa kamar a kirjina take bugawa, mun jima a haka sannan ya kawo bakinsa dai dai kunne na yace "I missed you" na kara narkewa a jikinsa dan ni inajin ba zan iya cewa ma i missed you din ba. Sai da hankali na ya fara dawowa jikina na tuna anytime wani, ko kuma ma Daddy da kansa zai iya bude kofar palon ya fito. Na dan zame daga jikinsa amma ina jin kamar na bar wani part of me a tare da shi. Yana kallona yace "come, let me show you something" yayi gaba na bishi a baya da sauri, naga yayi hanyar part din su ya Habeeb, ni dai binsa nake, ya bude kofar yayi min alama da in shiga, ina shiga naga gurin gaba daya ya chanza min, wani kamshi mai dadi yana tashi, kamshin Sultan, irin kamshin da kullum motarsa take yi kuma irin kamshin da naji a apartment dinsa na newyork, ya tsaya a bayana yace "welcome to my humble home" na juyo ina kallonsa da mamaki, ya jawo ni ya zaunar dani akan kujera shi kuma ya zauna a gaba na ya harde kafafuwansa yace 'I have a story to tell you" nan fa ya fara bani labarin abubuwan da sula faru tun tafiya ta, duk irin abubuwan da Daddy yayi masa, dawowarsa gidan mu hatta zancen sabon kamfaninsa daya bude sai da ya gayamin, nayi mamakin yadda al'amarin ya kasance sannan na jinjinawa Daddy na, na kuma gode wa Allah da samun uba na gari da nayi, dan iyaye na gari sune ginshikin rayuwar 'ya'ya, sannan kuma na kara imani da kuma godiya ga Allah, dan nasan duk abinda ya faru ya faru ne saboda karfin addu'ah. Ni kam babu abinda zance sai Alhamdulillah. Nan ni kuma na zauna na fara bashi labarin nima abinda ya faru dani tun sanda ya Walid ya dauko ni daga gurinsa, tafiyar mu niger da duk abinda ya faru acan har taimakon da musbahu yayi min na samu na kira daddy na. Nace "yanzu Mommy ce kadai matsala, ita ma kuma insha Allah zata sauko" na sauko daga kan kujerar nima nayi irin zaman da yayi na cigaba da bashi shawarwari akan sabon companyn sa, na bashi shawarar ya bude branch a New York tunda yana da mutane sosai acan, naga alamar yaji dadin shawarar, nan yace in zabarwa companyn suna wai dama ni yake ta jira in dawo in fadi sunan da nake so, nace zan zaba amma ba yanzu ba sai nayi tunani. Nan kuma na sake bashi shawarar yake zuwa palace yana gaishe da babanshi, ya dan bata fuska yace "why?" Nace "because he is your father" Ya Habeeb ne ya shigo palon, ya tsaya yana kallon mu da mamaki yace "wai ke har yanzu kina nan? Mu duk mun dauka kinyi bacci by now?" Na kalli wall clock din palon 12:49, da sauri na mike ina rufe bakina da hannu, na shiga uku, duk dariya suke min, Allah yasa Mommy bata shiga dakina ba, dan tunda muka dawo gidan ban kuma ganinta ba, kar in kara wani laifin akan wani. Ya Habeeb yace "soyayya dadi, wayo ku baku ma san lokacin ya tafi ba ko?" Da sauri nayi hanyar waje ina jin Sultan ya biyo bayana yana kirana, a bakin kofa na tsaya ya karaso ya miko min wani abu a leda, na kalle shi da alamar tambaya yace "it is a phone, ba zan iya hakura da jin muryar ki ba, dazu na siyo na yi miki charge dinta na saka miki sabon sim" na dan yi shiru amma kuma nima ina son muke wayar ai. Na karba nace "thank you" bai ce komai ba, na juya na cigaba da tafiya ya sake biyoni ya sha gabana yana tafiya da baya da baya yana kallona kamar wacce zan gudu, har muka je kofar palon mu, na kama handle din kofar yace a hankali "love" na juyo na kalleshi, a hankali ya sake cewa "thank you for loving me" bance komai ba sai murmushi da nayi, shima murmushin yayi min, and in that moment ji nayi duk hawalar da nasha is nothing, for him, I can do it all over again, ko da wacce tafi ta baya ce ma. A bangaren Mommy kuwa tunda suka dawo ta shiga dakinta ta rufe kofa, ta kwanta a kan gado zuciyarta tana yi mata zafi, mai yasa wai kowa ba zai fahimce ta ba? Wannan yaron ba yaron kirki bane, bai dace da Moon dinta ba, her perfect daughter deserves someone like her. Wannan yaron is too strong for her daughter, in anyi auren ma cin zalinta zai tayi yana lallabata ita kuma da raguwar zuciya tayi ta yafe masa. That's is ko da ace ya gyaru ma, in kuma bai shiryu ba yaje ya sha giyarsa yazo ya lakada mata dukan tsiya. Ta runtse idonta, bama zata iya tunanin 'yarta wani katon gardi yana dukanta ba. Ta tashi ta dan daga labule ta leka waje, shi ta fara gani akan mota tare da habibin ta, ta rasa wanne irin charm yayi using akan 'ya'yanta da mijinta, ita yanzu abin kunya ne ma kawayenta su shigo su ganshi a gidanta bayan duk irin maganganun da suke yi a office akansa, da akwai cases dinsa da yawa da ake kawo musu amma sai kuma azo a janye saboda iyayensa sun bata shi, ita ta kasa gane wanne irin so iyayensa suke masa da har suka barshi ya lalace haka, wannan ai ba soyayya bace. Ta shiga toilet tayi wanka ta fito tana shiryawa, wai har ita yau dear ya zauna ya wanke ta agaban iyayenta, abinda bai taba yi mata ba kuma duk akan wancan shegen ruwa biyun. Ta saka kayanta ta fita ta leka dakin Moon ta jita a bandaki tana wanka, ita kunyar 'yar tata ma take ji, me zata ce mata bayan tayi failing, yanzu ga yaron nan an kawo shi har gida yadda zaiji dadin lalata mata 'ya a gidan ubanta. Ta sauka kasa tana bada order abincin da za'a dafa, a kitchen din ta zauna kamar yadda ta saba akayi aikin abincin tare da ita, sai da ta tabbatar komai ya kammala sannan ta koma sama tace akawo mata nata sama, bata son wannan tsageran yaron ya shigo ya same ta a kasa, da wasu idanunsa a tsatstsaye irin na marasa kunya. Ta koma dakinta tayi sallolinta sannan ta jawo abincinta taci, duk abincin ma babu dadi, sam yanzu bata iya cin wani abin kirki, she is suppose to be downstairs with her family, kamata yayi ace tana can ta tabbatar Moon taci abinci ta ko shi. Amma sam dear yaki sauraronta, ita ba zata iya zama da yaron nan ba, shi kuma direct ya gaya mata shi fa ba zai kore shi daga gidan saba sai ranar da shi da kansa yace zai tafi. Kuma yaran ma babu wanda ya hawo yayi mata magana, irin Mommy mai yasa ba kya saukowa mu ci abinci tare? Ji tayi wani hawaye ya zu bo mata, ta goge tare da jawo wayarta ta duba time, safiya ce yanzu a England, tayi dialing number din Hafsat. Hafsat ta gama sallamar Zayed tana shirin shiga wanka taji shigar kira daga Mommy, ta zauna da kyar saboda nauyi da ta fara, ta daga da sallama. Mommy ta amsa da daskararriyar murya, suka gaisa sannan mommyn tace "Moon ta dawo gida" da yake tuntuni Hafsat tasan duk abinda yake faruwa, da sauri Hafsat tace "Haba? Tana ina? Dan Allah Mommy bata mu gaisa" Mommy tace "tana kasa tare da daddyn ku da brothers dinku, da kuma wannan yaron" Hafsat ta gane wa take nufi. Sun jima shiru sannan Mommy tace "Hafsat ke kinfi kowa sanin Moon, dan ina ganin kamar hatta ni da na haife ta kinfi ni sanin ta, please tell me, where did I go wrong a tarbiyyar dana bata? Me yasa tayi choosing ta bakantamin ta tozartani a cikin jama'a? Me yasa ta zabi sultan? Me yasa tun farkon ganin ta dashi ba ta fahimci cewa ba sa'an auren ta bane ba?" Hafsat ta danyi shiru sannan tace "Mommy kaddara ce, destiny, Sultan destiny din Moon ne haka itama Moon destiny din Sultan ce. Allah ya riga ya rubuta cewa sai sun hadu kuma sai hakan ta faru a tsakanin su. Mommy babu inda kikai wrong a tarbiyyar mu dan ba mu kadai ba duk wanda ya san mu yana yabawa da irin tarbiyyar da kika bamu, wannan shi yasa ko da yaushe muke kokarin mu zama perfect saboda kar muyi failing dinki, but no body is perfect. Duk abinda Moon tayi tayi shine because she is afraid of failing you Mommy. Sultan ba shine saurayin Moon na farko ba, tayi Ibrahim, she loved him so much amma haka tayi ta kumbiya2 saboda tasan ba lallai ne in ta kawo muku shi ku karbe shi ba, sanda tayi summoning courage kuma ta kawo shi gida shi kuma ya kasa summoning courage yayi facing Daddy. Sai da tayi spending five years kafin ta cire ran dawowarsa. So you understand why she is holding tightly unto Sultan. Shima haka tayi ta hiding dinsa daga gurinku saboda tasan shima ba zaku amince da shi ba. Tsoron da take yi na cewa zaku rabata dashi shi yasa take going behind your back take ganinsa. Na sha bata shawarar ta kai ku gurinsa but she kept saying she is waiting for the right time, she was afraid, afraid of not being the perfect girl you want her to be. So tayi ta dan gyara shi kafin ta kawo muku shi, amma sai gashi kun ganshi in his worst" tunda ta fara magana Mommy bata ce komai ba, sai da taji tayi shiru sannan tace "yanzu me kike ganin ya kamata inyi" Hafsat ta sake cewa "Mommy ni personally i don't like sultan, but tunda har Moon tayi falling for him, kuma Daddy ya dauko shi ya hada shi da 'ya'yansa gudan jininsa, suma kuma a cikin 'yan watanni har suka saba dashi then there must be something Good about him. Ni ina ganin Mommy give him a chance, you might even like him too" Bayan sun gama wayar Mommy ta jima a zaune tana digesting maganganun Hafsat, tasan Hafsat tsintar kalmomi tayi wajan yi mata bayani amma abinda take so ta gaya mata shine 'she is too strict' kuma tasan haka ne, takurawar ta da son su zama perfect ne ya saka Moon take zuwa gurin Sultan a boye. Yanzu badan Allah ya kare mata yarinyar bama da sai dai ta ganta da ciki ta rasa a ina sa samu. She was wrong before, but now she is going to correct her mistakes. Ta tashi ta kwashe kayan abincin da ta gama ci ta fita dasu kitchen, babu kowa a palon duk sun fita, ta koma daki ta sake wani wankan tayi shiri na musamman, she is going to take back her family. Tana jin Daddy yazo ya wuce ta gaban dakinta amma ko lekowa bai yi ba, sai da ta bari ya dan jima da shiga sannan ta bi bayansa. Tana shiga taga ya fito daga wanka da towel a jikin sa yana kokarin shiryawa, kallo daya yayi mata ya dauke kansa, ta zagayo gabansa ta dauko mansa ta fara kokarin shafa masa, ya ture ta ya matsa, ta ajjiye man ta dauko turarensa ta biyo shi inda yake kokarin saka pajamas dinsa ta karasa saka masa ta fara fesa masa turaren hannunta, ture ta ya sake yi ya tafi kan gado yana shirin kwanciya, ta saka hannayenta ta baya ta rungumo shi, ya chire hannun nata ya matsa. Ta shagwabe fuskar ta kamar zatayi kuka tace "am sorry fa" bai kula taba ya hau kan gadon, ta bi bayansa ta kwanta a kirjinsa tare da sauke ajjiyar zuciya, sun jima a haka sannan a hankali ya dora hannunsa a bayanta yana shafa ta kamar mage, ita kuma ta kara narkewa a jikin sa, can kasan makogwaronsa a furta "I miss you" [11/7, 2:33 PM] maryamsuleiman48@gmail.co: MAIMOON By Maman Maama Episode Fifty Eight : For You, Only You Yau har sai kun gaji da karatu. Happy weekend. 'Yan #teamibrahim ina jin duk abinda ake yi muku, believe me, i will surely reward your loyalty. Bature yace "he who laugh last....... Washegari da sassafe Sultan ya kira ni yace min ya tafi office, yana da meeting very early, dan haka nima ban tashi da wuri ba, ina jin Mommy kusan shigowarta uku tana dubani, sai kusan karfe 12 na tashi, shima kuma yunwa ce ta tashe ni, nayi wanka na shirya cikin wasu riga da skirt english wears tunda duk kayana sunyi min yawa yanzu, nayi packing gashina a tsakiyar kai na sauko kasa, a kitchen na samu su Mommy already suna aikin abincin lunch, na gaishe da Mommy ta amsa tana kallon kayan da na saka, na jawo kujera na zauna nace "Ma'u ki kawo min taimako, yunwa na ke ji" da sauri Asma'u ta ajiye aikin da take yi ta fara hado min tea, na karba na fara sha sannan ta zubo min farfesun naman ragon da suka gama hadawa ta hado min da bread, na karba ina ci ina santi, Mommy tace "aikin kenan, amma in akace kiyi garki ba zaki yi ba sai dai a girka ciki, ni ban taba ganin macen da bata son girki ba sai ke Moon" Furaira ta karba "kuma gashi gwanin nata gwanin abinci ne ba" a tare muka watsa mata harara ni da Mommy, tayi sauri taja bakinta tayi shiru, can Mommy tace "ke furaira ya akayi kikasan saurayinta ne?" Furaira tace "nima Mommy wallahi a gurin 'yan waje nake ji, shi yake gaya musu" a raina nace "zai aikata" Asma'u tace "kar ki damu mai sunan daada, duk sanda akayi bikin ki gidan ki zan koma inyi ta dafa miki abinci ke da mijin ki" nan itama ta karbi nata rabon hararar daga Mommy" sai da na gama cin abinci na sannan Mommy tace "ku bata suyar friend rice din nan tayi" na fara yarfe hannu ina kallon Mommy kaman zanyi kuka "Mommy wallahi kone wa zanyi, ni kuba ni in yanka muku wani abu, ni zafin wutar ne bana so" asma'u ta biye min "dama wannan jikin naki haka babu tsoka ina zaki iya juya shinkafa? Bara dai in baki ki hada fruit salad" nan na kama murna na zauna dishen a kasa na nade kafa, maryam tace "so take fa ta gudu, ai tana zuwa kitchen zata ce a bata yanka, daga nan zata yanke hannu sai kuma ta tashi ta fita shikenan ba zaki kara ganin taba sai akan dining" duk suka saka dariya, na bata rai nace "ke Maryam har zaki nuna min aiki da wuka? Da likita fa kike magana" daga nan sai na fara basu labarin yaddda muke buda kan mutun mu bude kwakwalwarsa mu yi masa aiki sannan mu mayar mu rufe, ban ankara ba ina ta surutu sai gani nayi ana juye fruit salad din a bowl, har an gama hadawa, na dauko cup aka zuba min na koma gefe na fara sha ina cigaba da labari na. Tsayuwar mota muka ji a waje, Mommy ta kalleni tace "madam ki je ki chanza wadannan kayan na jikin ki, dan wannan tsageran yaron bashi da linzami a gidan nan, har kitchen din nan zai iya shigowa" nace "Mommy kaya na duk sunyi min yawa ne wallahi" tace "to sai ki saka wadanda suka fi wadannan girma ko kuma ki saka dogon hijab" nace "yes Mommy" har zata fita tace "kar ki yadda fa inzo dining in tarar dake da kayan nan sai ranki ya baci" da sauri na mike na riga ta hawa saman. Sai da nayi alwala na saka dogon hijab dina bayi sallah sannan na dan gyara fuskata na sauka kasa, ya Habeeb na tarar a palo, na zauna muka fara hira sai da ga Daddy, ya Walid da Sultan sun dawo, daga gani daga masjid suke. Ko kallon inda Sultan yake banyi ba na gaishe da Daddy, duk da ina jin idanuwansa a kaina. Daddy ya fara yi mana zancen convocation din mu da za'a yi next week, kuma duk tare za'ayi har dasu Faruk. Nan muka kama murna. Saukowar Mommy ce ta katse mana hayaniyar mu, gaba daya muka juya muna kallonta, tasha ado tun daga sama har kasa, tayi kyau sosai dan bazaka kalleta ba kace ta haife ni ma ballantana ya Walid daya doshi 30 years. Tana zuwa ta gaishe da Daddy, su kuma duk suka gaishe ta har Sultan, ta amsa ba tare da ta kalle shi ba, sannan tace "ga abinci nan a dining" ta mike ta tafi, muma duk muka bi bayanta. Muna zama na tashi na fara zubawa kowa abinci, sakara ce da miyar vegetables, fried rice da hadin salad sai farfesun naman rago, sai kuma fruit salad. Kowa farfesu na fara zuba masa sannan kuma sai in tambaye ka me kake so a cikin sakwara da shinkafa sai in zuba maka, amma da nazo kan Sultan ban tambaye shi ba na xuba masa fried rice da salad da yawa amma na ciccire tumatir din cikin salad din, duk abinda nake yi idon kowa akaina yake, ina gamawa yace min "thank you" ban amsa masa ba na koma na zauna. Ya Habeeb ne ya kasa shiru yace "shi Sultan mai yasa ba'a tambaye shi abinda yake so ba? Idan kuma ransa yafi son sakwarar kuma fa?" A hankali nace "baya cin sakwara ai" ya Walid yace "wow, yanzu kai zama kayi kai ta lissafa mata abincin da kake so da wanda baka so?" Daddy yayi gyaran murya duk kowa yayi shiru. Ina lura da Sultan gaba daya a takure yake, kuma nasan ganin Mommy a gurin ne. Daddy ya cigaba da maganar zuwan mu England ita kuma Mommy ta gaya mana cewa in munje zamu taho tare da Hafsat saboda tana son tazo ta haihu a gida, nan muka kara yin wata murnar. Sultan ne ya fara tashi yace wa Daddy zai koma office saboda ya baro aiki sosai a can. Yana tafiya su Daddy da yaya Walid suka fara maganar irin cigaban da company n Sultan yake samu, yaya Habeeb yace "yanzu fa a cikin 'yan watanni har ya fara zancen sayan building din kusa dashi zai kara wasu offices din ya kara expanding din gurin. He is a real hustler. Baya zama sam, baya kuma gajiya da aiki" ni da Mommy kawai jin su muke bamu ce komai ba. Sai da suka gama sannan Mommy tace da ya Habeeb "kai da kake ta celebrating success din wani kai ina taka success din? Tunda aka samar maka aikin nan ka fara ni banga ko hula ka saya wa kanka ba, baka da aiki sai kashewa 'yammata kudi ko? Ka san Allah Habeeb ka fita daga ido na in rufe, kana ganin walid ya sayi filin sa yana kokarin fara gini amma kai ko ajikinka sai ana maganar wani ka iya cewa 'he is a real hustler' bayan kai yanzu da zan duba account dinka babu wani abin kirki a ciki" yadda kokayi maganar ya Habeeb ne saka mu muka yi dariya ni da ya Walid, ta juyo tana hararar ya Walid tace "kai kuma ka iya taya wani murna cewa budurwarsa tasan abinda yake so da wanda baya so amma kai kaki yin budurwar ballantana ka gaya mata kai me kake so din, you are not getting any younger fa, ya kamata kai ma ka san me kake ciki tun kafin hajja ta juyo kanka ta samar maka mata" na rufe bakina ina dariya ganin yadda ya Walid ya bata fuska, ta juyo kaina tace "ke kuma a ina kika samu wannan wayar ta hannun ki?" Cikina ne ya bada kululu, na fara in ina, tace "shine ya baki ko?" Na gyada kai, tace "ce masa akayi ba zamu iya saya miki waya bane ba? Ko kuma ke ce kika roke shi?" Nayi sauri na girgiza kaina tace "to ki tabbatar kin mayar masa da wayarsa, phones din ki suna dakina kije ki dauka, kuma kar ki sake karbar komai nasa" nace "yes Mommy" Daddy yace "saura ni" duk mukayi dariya banda Mommy, yace "to duk kin hada min kan yara kin musu fada ai gwara ki hada dani kawai" Haka rayuwa ta cigaba da tafiyar mana inda Sultan ya dage da aikinsa ni kuma na fara mayar da kiba ta. Kullum haka muke wuni makale a waya duk da cewa zai zo muyi lunch tare, dinner ma haka, kullum da daddare kuma muna tare a palon su ya Walid har sai Mommy ta kira ni ko kuma in su ya Habeeb sun kora ni gida. Ana gobe zamu tafi england aka dauko Amina daga 'yalleman. Tare duk muka tafi England a jirgin Daddy, a gidan Hafsat na sauka naga tayi nauyi sosai, Sultan ma ba kunya cewa yayi acan zai kwana, dole Zayed ya bude masa guest room din waje, ranar kusan raba dare mukayi hira, da zayed da sultan suka zauna hira har sai da muka gaji ni da Hafsat muka tafi muka kwanta muka barsu. Washegari da sassafe muka tashi muka fara shirin tafiya Oxford, wata tsadaddiyar doguwar riga Sultan ya aiko min da ita yace in saka, ai kuwa kamar an gwada ni dan das ta zauna a jiki na, Hafsat ta kalle ni ta tabe baki tace "to ba dole tayi miki dai dai ba tunda yasan size din komai, ni rashin kunyar ku har mamaki take bani, kun wani maze kamar babu abinda ya faru" na bata rai nace "kai Hafsat, ni kam da na sani ban gaya miki maganar nan ba, ni dashi har mun manta ma amma ke kin kasa mantawa, it is in the past, please move on" ta tabe baki tace "shine yace miki ya manta? An gaya miki duk wannan kallon naki da yake na banza ne? To gwara ma ki sani, bai manta ba, dan haka sai kibi a hankali dashi" ni dai ban kuma ce mata komai ba saboda bana so tayi spoiling mood dina for today. Na dora graduation gown akan doguwar rigar muka fita, sam na kasa hada ido da Sultan sai nake ganin kamar maganar da Hafsat ta fada gaskiya ne. Tun daga gidan Hafsat muka fara pictures, a dole na ware da Sultan muka yi ta pictures sannan muka tafi mkrt, muna zuwa suma 'yan gida suka zo nan guri ya hargitse muka tafi hall din taro, muna shiga muka tarar anyi displaying innovations na graduands, zanen Sultan na gani anyi enlarging dinsa a saka a wall din da take kallon mu, duk kan mu tsayawa mukayi muna kallon zanen, kowa yana cewa "kunga zanen sultan" "yayi kyau" "moon ke kika zana?" Ni dai duk ba wanda na bawa amsa, na juya na kalli sultan a gefe na naga ya saki baki yana kallon zanen, na kasa karanta expression dinsa, can ya juyo ya kalle ni yace "ke kika yi zanen nan?" Na kalle shi cikin ido nace "yes" ya kuma kallon zanen sannan ya sake juyowa yace "dama haka shape din kaina yake kamar mangaro?" Duk gurin kowa sai da yayi dariya nace "you are welcome, dan nasan thank you kake so ka ce" An gama taro lafiya duk muka karbi certificate din mu, I am now officially a neurologist and also a psychologist, Faruk da Amina ma duk sun karbi nasu, daga gurin taron gidan Hafsat muka zarce gaba daya inda Zayed da Hafsat suka shirya mana Walima. Washegari zamu koma Nigeria dan haka Hafsat already ta riga ta gama hada kayanta, Zayed sai bacin rai yake yi, ina jinsa yana gayawa sultan wai shi fa ba'a son ransa ba, kai Sultan maimakon ka bada hakuri sai cewa yayi "chafdi, ai kayi kokari ma, ni kam babu mai rabani da matata dan zata haihu" Hafsat tace "wato kar mu saka rai kenan ko?" Yace "gaskiya kam, kar ma ku saka rai ballantana in na hana kuji haushi" Washegari muka dawo Nigeria. Motar mu tana shigowa gate na hango mutane cirko2 a tsatstsaye. Da sauri muma muka karasa gurin muka fito. Wata arniyar picanto fara tas an nada mata ribbon alamar gift ce, a jikin plate dinta an rubuta 'Her Royal Highness' ina gani nasan aikin waye wannan, nayi ta nemansa ko sama ko kasa bayanan, a saman motar an ajiye card, na dauka na karanta 'it will be my pleasure if you will let me teach you how to drive' lallai sultan rigima yake so ya debo min a gidan nan. Daddy yana ganin motar shima ya gane aikin waye yace da walid "ina sultan?" Ya Walid yace "a hanya ya sauka bai karaso gida ba" Daddy yace "call him" yana zuwa Daddy ya mika mishi key din motar yace "not now. In zaka koya mata mota akwai motoci a gidan nan ku dauki duk wacce kuke so" Sultan ya dan bata fuska Daddy yace in serious voice "I said NO" dole sultan ya karbi key dinsa. Inaji ina kallo aka saka motar a garage aka rufe. A kasa aka gyara wa Hafsat daki saboda tace ba zata iya zirga2r hawa sama ba, nayi mamaki sosai yadda naga suna mu'amala da sultan, ta sake dashi sosai, Mommy ma naga yanzu tana dan kulashi kadan, har wani lokacin takan tambaye shi ya office ko kuma ta dan saka shi wani aiki. Shi kuma na lura yana jin nauyin ta sosai, dan in dai tana guri wata nutsuwa ta musamman yake yi. Kwanan mu biyar da dawowa rannan da safe bayan mun gama breakfast duk 'yan mazan sun tafi aiki sai ga Amira da mamanta sunzo, daga ganin fuskarta na san akwai matsala, a palo suka zauna tun kafin mu gaishe da mama ta fara fada "gata nan fatima na kawo miki ita maybe ke in kika yi mata magana zataji, Amira taki aure, na rasa me yake damun yarinyar nan, taki samarin ma ballantana har ta samu na aure. Ni na gaji, gwara in tattara in koma gida in yaso acan a samar mata miji a 'yan'uwanta" nan Mommy ta samu abinda take so, daga yiwa amira fada ta hada har dani tayi mana tas tace kuma tace ta bawa Amira 3 months in bata fitar da miji ba da kanta da kanta zata kaita kano gidansu a aura mata duk wanda yace yana so. Ni dai bance kala ba, maman Amira tace "wani shegen yaro ta hadu dashi ya hana ta kula kowa kuma shi yaki ya fito ayi maganar aure, na rasa yadda zan yi in raba ta dashi. Nan Mommy ta fara tambayar Amira wanda take so din ita sai ta aika a gaya masa idan bai shirya auren taba ya rabu da ita, tambayar duniyar nan Amira taki magana, duk fadan Mommy haka ta hakura ta kyale Amira. Muka tashi muka tafi dakin Hafsat muka zauna, nayi ta tambayar Amita problem din ta amma tace min ita babu abinda yake damunta tace " ita fa mama duk abinda take dauka ba haka bane ba, shi wanda take magana akansa fa ba saurayi na bane, a makaranta muka hadu, he is my friend kuma haka kawai sai inje in ce masa ya fito ya aure ni? Kullum threats dinta shine zata kaini kano dan tasan bana son can to ni ya zanyi? Idan miji bai zo ba ni zan auri kaina ne?" Sai naji tausayinta na rungume ta ina lallashinta, Hafsat ma ta bata hakuri, nan muka zauna hira na bata labarin duk abinda yake faruwa tsakani na da Sultan, na dauka zamuyi rigima akan maganar amma sai naga tayi murmushi tace "Allah ya sa hakan shi yafi alkhairi" gaba daya muka ce "ameen". Mama anan ta tafi tabar amira ta wuni a gurin mu tana bamu labarin aikin data samu a aso rock, da irin kudin fa take samu tana saving, yanzu basu da wani problem na matsalar kudi. Na danyi tunani nace " Amira ni kuwa ina ma zaki gwada Amir abokin Sultan, he is really nice...." Kafin in karasa ta katse ni "Allah ya sawake, ai kwantan nawa bai kai har haka ba, ke dai da kika ga zaki iya da sultan sai kije kiyi tayi" nayi dariya nace "idan kuma Allah yayi mijin ki ne fa?" Tace "ai Allah baya dora wa bawa abinda yasan ba zai iya ba" tare muka yi lunch da ita, Sultan yana ta tsokanar ta wai Amir yana gaisheta. Bayan la'asar ta shirya tafiya muka je zata yiwa Mommy sallama, nace "Mommy zan raka Amira gida" tace "to sai driver ya kai ku" na dan yi shiru nace "Mommy da Sultan ne yace zai kaimu" ta jima tana kallona ni kuma na sunkuyar da kai kasa sannan tace "a dawo lafiya" Na kira Sultan nace an bar mu gamu nan fitowa. A motar sa muka same shi already yana jiran mu, na shiga gaba Amira ta shiga baya muka tafi, yace "Amira wai yaushe ne bikin kawar ki ne?" Tace "wacce fa?" Yace "wacce ki ka fi damuwa da ita" tace "sai ranar da ka shirya ranar za'ayi" yace "to ai ni already a shirye nake" ina jinsu na rabu dasu nasan neman magana yake yi, naga ya chanza hanya na tambaye shi yace "Amir zamu dauko" da sauri Amira tace "What? Please ku sauke ni in hau taxi, I can't tolerate that man" duk dariya muke mata tace "am serious wallahi, he is so annoying" muna yin packing ya bude ya shiga baya, yana ganin Amira a ciki ya ja tsaki yace "damn it, wannan yarinyar me take yi a motar nan?" Dariya muka sake yi, ni drama dinsu dariya take bani. Daga nan naga mun kuma yin wata hanyar daban, this time banyi magana ba Sultan yace "I want to show you something" Bance komai ba har naga yayi packing a gaban wani katon building duk muka fito na daga kaina naga an rubuta a saman ginin 'MOON CONSTRUCTION AGENCY" na kalle shi da mamaki yace "to ba kin ki gayamin sunan da kike so ba, shi yasa na saka sunan da na fi so" muka shiga gurin suna nuna mana ko'ina suna kuma yi mana bayanin komai,gurin ya tsaru sosai, I trust sultan in dai ta gurin tsari ne, aikin architecture yayi suiting dinsa sosai. Daga nan muka tafi gidan su Amira, a can mukayi magrib sannan muka fito muka kai amir gida shima. Finally daga ni sai shi, nace masa "thank you for the name" yace "I only hope it will shine as bright as you" nayi murmushi. Yace "wai har yanzu Mommy ba ta ce miki komai ba?" Nace "akan me fa?" Ya nuna kansa sannan ya nuna ni yana mischievous smile dinsa. Na gane me yake nufi, na dan bata rai nace "ni ban san akan me kake magana ba" yace "common, how much longer do I have to wait ne wai. Ni aure na ke so seriously" na rufe baki ina dariya nace "kai Sultan, baka jin kunyata kake cemin aure kake so?" Yace "ke din zanji kunya? Ke fa zan aura kuma sai inji kunyarki? Please ki dan tambayi Mommy mana kiji me ake ciki" nace "kai ma wasa kake, me zan ce mata? Mommy yaushe za'ayi min aure?" Yace "exactly" na girgiza kai nace "sai dai kai kaje ka tambayi Daddy" yace "OK, wato ke kina nufin ba kya son auren kenan?" Nace "wai what has come over you ne yau?" A lokacin muka shigo gida, yayi packing amma be kashe motar ba yace "ai na riga ma gaya miki me yake damuna, aure nake so, ai nayi kokari, ya kamata a bani medal ma. Kinga yanxu abinda za'ayi, irin in kuna magana da Mommy sai kike gaya mata ga abinda kike so ayi da bikin ki, zata dauki haske ai sai tayi wa Daddy magana" nace "wai ni na ce maka ina son aure? Kai da kake son auren ba sai ka fada ba?" Ya juyo yana facing fina yace "look into my eyes kice ba kya son aure na" na ki kallonsa, yasa hannu zai juyo fuskata na kara matsawa, yace "kin gani ko? You want it too" na girgiza kaina nace "I don't want anything" yace cikin murya kasa kasa "then look into my eyes and tell me you don't want me" da sauri na bude kofar motar na fita, shima ya bude ya fito ya sha gabana "au guduwa zaki yi ko?" Nace "kafi karfina yau. Yau mood dinka is not for me" yace yana kallon cikin idona "I have always been in this mood, for you, only you. Kawai hakuri nake, please do something. Ni fa idan ba'ayi mana aure kwanan nan ba to akwai rigima." Dariya nake son yi amma shi fuskarsa so serious, can ya fara devilish smile dinsa sannan yace "laugh all you want, baby girl, my time will come, then I will do the laughing and you will do the crying" bansan sanda na daina dariyar ba, da sauri na nayi hanyar gida, ina jinsa yana kira na amma ko waiwayowa banyi ba. [11/7, 2:37 PM] maryamsuleiman48@gmail.co: MAIMOON By Maman Maama Episode Sixty : The Prince Sultan gaba daya ya rikice min, wai shi lallai sai na fada a gida cewa aure nake so, kaji mutum, kuma shi in nace masa ya fada sai yaki. Dole yanzu na fara rage doguwar hira dashi, a waya ma kuma sakin layi yake. Gaba daya ni yanzu lamarin sa tsoro yake bani, kuma gashi Daddy ko mentioning zancen mu baya yi, ballantana Mommy da ko maganar ma bata so ayi. Da yaga na fara gudunsa sai ya tsiyo da zancen driving lesson, Daddy ya gayawa, daddy kuma yace muke yi da yamma in ya taso daga office. Ni dai nasan ba wani abin arziki za'a koya min ba amma dai haka nake binsa muna fita, in muka je rabi lesson rabi hira. Rannan nace masa "to wai kai me yasa ba zaka je ka tambayi daddyn ba? Ai kun fi kusa dashi, ko kasa yaya Walid ya tambayar maka" yayi shiru yana kallona sannan yace "Daddy has done so much to me ne bana so inyi disappointing dinsa, bana so yaga gazawa ta ko kuma yayi tunanin dama abinda nake after kenan. Nafi so ace shi yayi min magana da kansa. Amma gaskiya na gaji da jira, I don't know how long zai taking kafin yayi min maganar" ya dan bata fuska yana kallona "ke ko ajikin ki ma wallahi, hankalinki kwance ke ko shekara za'ayi a haka babu ruwanki ko?" Nace "wa ya gaya maka haka?" Yace "to ai bakya nuna wa. At least kema ki dan ringa nuna min kina so mana, at least sai in san cewa the feeling is mutual ba wai ni kadai na ke abuna ba" nace "sultan komai fa da lokacin sa, musamman aure, in kaga anyi to lokaci ne yayi ba wai nuna ina so ko rashin nuna inaso bane zai sa ayi. Kai dai kayi ta addu'ah sai kaga komai yazo da sauki" Sosai muke ta shirye shiryen haihuwar Hafsat, takanas Mommy ta dauko wata midwife suke kwana tare saboda in case ko haihuwar zata zo da daddare. Hafsat kam duk tayi laushi, bata da aiki sai cin abinci sai da yamma inna tafi driving lesson dina ita kuma ta tafi strolling. Kaya kam har dai da aka ware daki guda ake zubawa dan kullum sai an siyo wani abu na baby an ajiye, in dare yayi kuwa bata zaman palo, tana daki makale da zayed a waya har sai tayi bacci. Ni kuma kullum da daddare bayan an gama dinner zamu zauna hira da Sultan, Mommy ta hana hirar palo tace muke zama a compound in da mutane za suke ganin mu, ni ma banyi mata musu ba saboda wannan Sultan din ba na da bane ba, shimq dana gaya masa abinda Mommy tace sai cewa yayi "yauwa, ai gwara ma muke zama inda Daddy zai ke ganin mu yana tunawa da maganar mu" Rannan ina gyaran kayana a daki kawai sai naga katin da musbahu ya bani a agadaz, shaf na manta dashi ma ni, dan adam kenan. Na dauka na saka number din nayi saving as 'musbahu ngr', sai bayan da nagama aikina kaf sai na dauko wayar na kira number dinsa, ya nayi masa sallama ya amsa yace "sai yau kika tina dani ko Moon?" Nace "lah ya akayi ka gane nice?" Yayi dariya yace "naga number din Nigeria kuma naji muryar mace, I have been expecting your call kuma shiru har na fitar da rai" nace "wallahi na rasa card dinne sai dazu na ganshi, ya su mustapha da sauran 'yan gidan?" Yace "lafiya lau. Ina Sultan?" Nace "au baka manta sunan sa ba?" Yace "It is kind of special ne shi yasa ban manta ba" muka dan taba hira na kashe na ajjiye wayar, ni sam ban kawo wani abu a raina ba sai da daddare muna tare da sultan ya karbi wayata yana kallon pictures din da mukayi dazu wajan koyon mota sai kawai naji an kira ni, na mika hannu ya ban wayata sai naga yanayin fuskarsa ya chanza, ya juyo min screen din na karanta 'musbahu ngr' wayar ta katse aka sake kira har ta sake katsewa bai bani ba kuma bai ce min komai ba. Can dai yace "why is he calling you?" A ina ma ya samu number dinki da zai kira ki" na bata rai nace "dazu na kira shi muka gaisa. Yace in nazo Nigeria in kira shi, tunda nazo kuma ban kira shi dinba saboda nama manta da maganar sa sai dazu" nan take naga yanayin fuskarsa ya chanza "ina ruwanki dashi to da zaki kira shi, yanzu gashi ya samu number dinki kuma har yana da guts din da zai kira ki yanzu da daddare" nace cikin lallashi "Sultan, gaisawa fa kadai muka yi, har tambayata kai sai da yayi, he means nothing, kuma ya taimakamin wallhi, badan shi ba maybe da har yanzu ina agadaz" Sultan yayi chuckling yace "he is fooling you, kuma zancen taimako ke fa kike gayamin kullum cewa komai yana da lokacinsa, dan haka tunda lokacin dawowar ki gida yayi dole sai kin dawo with or without his help" nayi shiru na rabu dashi tunda naga rigima yake ji da ita, jin nayi shiru sai ya cigaba " you called him yaji muryar ki, and now he is calling again saboda ya sake jin muryar ki. Ni da son raina ne in banda 'yan gidanku babu wanda zaki ke yiwa magana ballantana har wani kato yazo yace zai kula ki. Kamar yadda nake ban taba budurwa ba sai you and you are the last haka nake so kema tunda baki taba saurayi ba in zamanto the first and the last" gaba na ne ya fadi dana tuna cewa sultan fa har yanzu bai san labarin Ibrahim ba, nayi sauri na ture maganar daga raina nace there is no need for him to know, tunda dai what you don't know won't hurt you. Ya jefo min wayar kan chinyata yace "block him" na dauki wayar inajin zafin yadda ya dage yake fada akan abinda bai kai ya kawo ba, na mike tsaye nace "I won't block him, tinda ni ba butulu ba ce" da sauri ya mike tsaye shima, kamar zai ce wani abu kuma sai ya fasa, ya saka hannunsa a cikin gashinsa sai ya tafi kamar zaiyi hanyar gate kuma sai ya dawo sai da yazo daf dani ya tsaya, ke gezau banyi ba, ya kalleni cikin ido yace "in har naga kafarsa a gidan nan sai na babballashi wallahi" na hade rai nace " kai yanzu sai ka karya mutum dan ya kulani?" Yace "bazan san sanda zan karya shi ba ai, sai na ganshi a kasa sannan zan san me na aikata. So you better warn him" na juya ina kallonsa har ya fice a kafa daga gidan. Na sauke ajjiyar zuciya, lallai ina da aiki a gaba na, sultan zuciya, sultan kishi, dole sai yayi maganin wadannan abubuwan guda biyu sannan zamu zauna lafiya dashi. Na koma cikin gida, ban kira musbahu ba kuma banyi blocking dinsa ba, sai kuma naji babu dadi a raina, yau munyi fada da Sultan, amma nasan zai sauko na bashi nan da awa daya. Nayi shirin kwanciya na kwanta, bacci ya fara dauka na kenan naji wayar sultan, har ya sauko, nima yanzu zanyi nawa fushin. Na rabu dashi yayi ta kira na naki dauka, message ya shigo, ina dauka naa emoticon na kuka, ya rubuta 'am sorry love' nayi murmushi a raina nace 'iyakacin zuciyar kenan?' Kafin ya kuma kira na kira shi, bugu daya ya dauka har da sauke ajjiyar zuciya nayi shiru bance masa komai ba, sai na kuma jan aji tukunna. Cikin muryar shagwaba yace "to wai ba nace am sorry bane ba? Dan kinsan ba zan iya bacci banji muryarki ba ko?" Na sake yin shiru yace "please please please haba love, this is so cruel wallahi. Am sorry nayi miki fada, i don't want you talking to any man. Ina kishin ki sosai. Please kar kiyi fushi dani akan haka" a hankali nace "ni ba akan kayi min fada nake fushi ba" yace "to akan menene, tell me, koma menene zan daina" nace "akan baka yadda dani ba" ya danyi shiru sannan yace "bangane ban yarda dake ba" nace "all this while ya kamata ace kasan how much I love You, ba musbahu ba koma waye mu kayi waya dashi ko kuma ka gan mu tare dashi bai kamata ka bata ranka ba, ban san menene a cikin zuciyar musbahu ba amma nasan menene a cikin tawa, and that should be your only concern. Sultan bana ganin wani namiji a gaba na ko a bayana sai kai, my heart is for you, only you, to menene naka na tsayawa kana bata ranka akan nayi magana da wani wanda ba lallai in sake ganin sa ba" jin yayi shiru ya saka na kwalli wayar na dauka duk wannan tsarin da nake yi kiran ya katse, naga seconds suna reading na mayar da phone din kunne na nace a hankali "sultan?" Can kasan makogwaronsa naji yace "I must do something, I really must do something" cikin confusion nace "ban gane ba?" Yace "seriously na gaji da fadar kalmar I love you na kuma gaji da jin kalmar i love you. I want to start giving some actions and receiving some actions. Kalmomin sun kare, I am out of words to show you my love for you. I want to start really showing you my love. I want you" nace "sultan zan kashe wayata" yace "go ahead ki kashe din, ai dai naji muryar ki. Tun ina yaro, if I want something, I go for it, yanzu ma haka, I want you and I will come for You" na katse wayar da sauri, na kashe ta gaba daya. Da sauri na tashi na rufe windows dina da kofar balcony na dawo na zauna akan gado, amma a raina nasan in dai Sultan yayi niyyar shigowa daki na to sai ya shigo, but I don't think he is coming, he is not going to throw away duk abinda ya samu ba. Da safe yawa ta tana kashe dan haka bamu yi wayar da muka saba yi da safe ba kafin ya fita, bayan munyi breakfast na kira shi naji switched off, har aka zo lunch ban samu wayarsa ba, kuma bai zo cin abinci ba, daddy ya tambayi walid sai walid yace masa sunyi waya yace yau aiki yayi masa yawa ba zai zo ba. Muna gama cin abinci naje na hada masa basket guda na abinci na bawa driver nace ya kai masa office dinsa. Ga mamaki na sai ga drivern ya dawo yace wai ance yau baije office ba, suma nemansa suke yi. To ni maimunatu ina sultan ya tafi. Babu irin tunanin da banyi ba. Har akayi la'asar shiru. Ina kitchen ina zaune ina kallon su asma'u suna ta aiki, yau ko surutun ma bana musu, sai ga maryam ta shigo da sauri tace "kai kuxo ku gani yau baki akayi a gidan nan har da masu rawani da dogarai" da sauri na mike nabi bayansu muka leka ta tagar kitchen amma bama hangowa sosai, na dai hango jama'ar gidan mu sunyi chirko2 a gefe, muna cikin leke Mommy ta shigo kitchen din da sauri tace min "zo ki fita ki tafi daki" da sauri na fice ina jinta tana bada order abinda za'ayi. Dakin hafsat na shiga na tarar tana sana'ar tata ta bacci, na daga labulen window dinta na leka waje, jibga jibgan motoci na gani har guda biyu sai kuma mota mai kalar kayan dogarai, yaya Walid na gani da sauri yaje gurin motar farko ya bude kofar ya durkusa ya gaishe da wanda yake ciki sannan ya matsa ya badu guri suka fito, manyan mutane ne sun sha kayan alfarma na sarauta, duk ban san suba, naga sun tafi palon da Daddy yake saukar manyan bakin sa. Aka matsar da motar gefe aka matso da dayar, matane suka fiyo su biyu, daga ganin su kaga manyan mata, dogarai suka zagaye su har suka shigo kofar palo. Nayi sauri na koma bakin kofa nayi kneeling ina leke ta keyhole, Mommy da mutanen ta suna ta kai kawo a gurin bakin amma bana hango su sosai kuma bana jin me suke cewa. Na zauna anan na jingina da jikin kofar, na kara kiran wayar sultan switched off. Dazan kama matar nan mai cewa switched off a waya da Allah kadai zai raba ni da ita. Ina nan zaune naji kiran Mommy ya shigo, na dauka tace "kina ina ne?" Nace "ina dakin Hafsat" sai a lokacin Hafsat ta tashi ta ganni nayi tsuru2 ta tambaye ni menene na daga mata kafada. Mommy ta shigo tana kallona sannan tace "ki zo ki gaishe su" da sauri na bude kayan Hafsat ina neman kayan sakawa, Mommy tace "NO, kayan ki are OK, kawai ki dan gyara fuskarki sai ki samu babban mayafi ki saka" na shiga toilet da sauri na wanke fuskata, jikina sai rawa yake, inna kama sultan ni kadai nasan me zan yi masa, in less than five minutes na shirya Hafsat ma ta dan gyara muka fita. Tunda muka fita kaina yana kasa amma inajin idonsu a kaina, muka zauna daga can nesa muka gaishe su suka amsa mana da fara'ar su. Daya ta fara magana "Sultan bai kyauta mana ba wallahi, sam bai gaya mana maganar nan ba sai yau. Yanzu gashi ya saka munji kunya bamu kawo mata wani abin kirki ba" wata kuma tace "marar kunyar ba, ni yaushe rabon da in saka shi a idona, kawai sai gashi da sassafe yaje min kamar an koro shi, ni na dauka ma baya kasar" sai kuma ta dawo kaina "Maimunatu kalle ni kinji, ni ba surukar ki bace ba, ni kakar ki ce, Nani sunana, wannan kuma Yaya" ta nuna ta kusa da ita, "wannan ita ce surukarki, matar galadima ce" na kara sunkuyar da kaina ina murmushi, yaya tace "mu kadai muka zo yanzu saboda bai bamu lokaci ba, yace lallai sai munzo yau, mu zuwa muka yi mu ganki mu saka miki albarka sauran kuma magana ta maza ce" Matar galadima ita ma tayi mana addu'ah aka ce mu tashi mu koma. Ina shiga daki na zube a kan gado, gaba ki daya jikina rawa yake yi. Hafsat tace "wai kina nufin bai gaya miki zasu zo ba?" Na girgiza mata kai. Muna nan zaune har suka tafi sannan muka fito palo, kaya muka tarar a gaban Mommy akwati biyu, kayan kwalliya ne kawai dana gyaran jiki. Ina ta jiran inji anyi min wata magana shiru babu wanda yace min komai, har muka yi dinner da Daddy shima bai yi min magana ba. Sultan bai zo ba kuma babu wanda yayi maganar sa. Na gaji da zama na tashi na ce musu sai da safe na hau sama. Na kwanta amma sai juyi nake yi na kasa bacci, me hakan yake nufi? Babu abinda zuciya ta bata ayyana min ba kuma duk marasa dadi. A haka har bacci barawo ya dauke ni. Cikin bacci naji ana shafa fuskata a hankali, a tsorace na tashi ina rarraba ido, Sultan na gani a zaune a gaban gadona yana dariya, nayi sauri naja bargona lullube jikina duk da cewa dakin da akwai duhu. Nace "Sultan me kake yi anan ne? Na shiga uku, ka tashi ka fita, yanzu in Mommy ta shigo ta ganka fa?" Yana dariya ya saka hannu ya kunna bedside lamp, nayi sauri na kashe, nace "babu kaya fa a jikina dan Allah ka tashi ka fita" ya mike tsaye yace "OK, bara in juya bayana sai ki saka kayan sai in juyo muyi maganar" nace "kowacce magana ce ka bari mana sai da safe mayi, Sultan Mommy nake tsoro, in ta shigo ta ganka a dakina cikin dare me kake tunanin zata ce" ya zagaye gadon yaje bakin kofa yayi locking ya zare key din yace "problem solved" na sake cewa "me kake yi a dakina" yace "zuwa nayi inga amaryata" Hijab dina na nuna masa ya dauko min na saka sannan na fito daga bargon na zauna bakin gadon na kunna fitila. Gabana yazo ya zauna ya harde kafafuwansa yana kallona da murmushi, na bata rai, "shine ka kashe wayarka ko" yace "ramawa nayi, dan kiji yadda nake ji in kin kashe min waya" nace "amma dai at least ka gaya min plans dinka kafin ka aiwatar ko? We are suppose to be a team, kawai sai ganin baki mukayi bamu san da zuwan su ba" yace "I told you I must do something, kuma sanda na hada plan dina kin kashe wayar ki, da safe kuma na ai watar da plan dina. Tunda naga Daddy yaki cewa komai ni kuma bana so in tambayeshi shi yasa na je na gayawa galadima nace yazo ya nema min auren ki a gurin Daddy, munyi rigima dashi sosai kafin ya yarda yazo din, yace na daina zuwa gurinsa na zama dan kaina and all that, ni kuma abinda yasa na daina zuwa gurinsa saboda bana son cigaba da hada su rigima da Takawa, sanda nake zuwa gurinsa kullum sai Takawa yayi masa masifa akaina, so kawai sai na rabu dashi, ashe shi haushi na yake ji. Su kuma su yaya su suka gayyaci kansu, kawai galadima ne yace in je in gaya musu maganar shine sai suka ce lallai sai sunzo sungan ki, fitinannun tsofaffi kawai" ya mike tsaye yace "oh God yunwa nake ji wallahi" nace "to baka fada min ba kuma abinda akayi" ya daga gira daya yace "akayi me?" "Maganar da suka zo yi me akace?" Yace "yarinya tana so tana kaiwa kasuwa, bazan fada din ba sai kin bani abinci naci." Nace "dakai me kake yi ba kazo kaci abincin ba" yace "ina office wallahi ina zane" da mamaki nace "zanen me kuma cikin dare?" Yace "zanen gidan mu, I made all the plans, gobe za'a fara aiki" na saki baki ina kallonsa. Daga tsayen da yake straight ya fado kan gado, nayi sauri na mike nace "Sultan menene haka kuma, tashi min daga gado" yace "nace miki yunwa nake ji, ni bani da energy din tsayawa" nace "amma kana da energy din hawa katanga ka shigo wa mutane daki ta taga ba" ya tashi zaune "please ki samo min abinci inci, Allah yunwa nake ji" na tashi na dauki key na bude dakin, ina fiya na sake rufewa da key ta waje. Duk da saukowar da Mommy ta fara yi, na tabbatar in ta shiga dakina taga sultan a kwance a kan gado to koma menene aka shirya sai an warware shi, maganar aure ta tashi. Na duba kitchen naga duk an yi wanke wanke babu sauran abinci, a fridge na samo masa wata gasashshiyar kaza, na dumama ta a oven na hado masa da fresh milk na taho. Ina shiga daki naga agogo ya nuna 2:19. Ina shiga na kuma rufe kofar, yana kwance ya mike ya zauna ya harde kafa na ajiye masa a gabansa na shiga toilet na kuskure baki na na dawo, yana kallo na yace "menene na wani zuwa ki wanke baki?" Nace "tayaka ci zanyi" na hau gadon na zuba masa madarar na mika masa. Sai da ya fara ci sannan ya fara magana "Daddy yace 'yalleman za'a je, sunyi fixing jibi zamu je tare gurin baffa, shine zai ce ya bayar ko yace ya hana. Amma shi gurin Daddy yace ba matsala" nayi shiru bance komai ba, yace "hey, ya kamata ki bani tukwuici mana" nace "OK, me kake so in baka" yace "a hug will be very much appreciated" na harare shi nace "only in your dreams" yana murmushi yace "it happens only in my dreams now, it will happen in reality very soon" na sauko daga gadon nace "tashi ka fitar min daga daki" ya gyara zama yace "da ace zan yi miki wani abu baby girl, da tun sanda na shigo kina kwance kina ta sharar bacci a lokacin zan miki, so relax, i have waited for so long, saura kadan ya rage min" na zauna a kan bedside ina kallonsa har ya gama cin abincin sa ya tattare kayan sannan koma ya zauna ya dauko wata takarda ya warware yace "come let me show you something" na zauna kusa dashi, ya fara nuna min wani zane yace "this will be our home, anan zamu rayu muyi raising kids dinmu" ya fara min bayani dalla2, na jima da sanin cewa sultan ya kware a aikinsa amma sai yau na gani in reality, gidan ya tsaru iyakacin tsaruwa, kuma katon gaske ne, dan in baifi gidan mu girma ba to zasu yi kai daya. Sai da ya gama yi min bayanin gidan ya ninke takardar sannan yace "baki tambaye ni a ina za'a yi ginin ba?" Nace "a ina" yace "a palace. Nayi magana da galadima zai gayawa Takawa, ba cikin palace din bane ba, daga bayansa ne wani daji ne babu abinda ake yi da gurin, in ya yarda gobe zan aika ayi clearing gurin. Ta gate din palace din za'ake shiga sai kuma a zagaya baya" nayi mamaki sosai, ban taba tsammanin sultan zai yi tunanin zama a cikin palace ba, amma kuma sai na tuna cewa sarauta a jininsa take, yana sonta sosai, kawai dai yana basarwa ne saboda kar ya kara wa kansa bakin ciki, na tuna motar daya siyo min 'Her Royal Highness' it means deep down he is considering himself as 'His Royal Highness' kenan. Banyi masa maganar ba saboda bana son spoiling mood dinsa. Washegari kamar kullum ya fita da sassafe, sanda ya dawo lunch yake gaya min har ya aika za'a fara clearing din gurin, it means Takawa ya yarda kenan. Daga nan kuma yace galadima yana kiransa, bamu sake magana ba sai da daddare yace ba'a nan zai kwana ba saboda sa sassafe zasu tafi 'yalleman din, ta kano zasu biya su dauki uncle Aliyu shi zai raka su. Washe gari nayi wa Amira waya na gaya mata me yake faruwa sai gata nan tazo zata tayani zaman jira. Muna zaune sai ga message ya shigo min ta WhatsApp daga Sultan, hoto ne, ina budewa na saki baki ina kallonsa. Sultan ne, yaci ado da kayan sarauta, babbar riga, rawani, da alkyabba, maroon color da adon fari, rawanin kuma fari da adon maroon. Yayi kyau karshe, ban taba ganin sultan yayi kyau irin wannan ba, sarauta a jinin sa take, he is a real prince, a kasan hoton ya rubuta 'do u know this man?' Take na chanza dp dina na mayar hoton, sannan nayi masa reply, 'no, i have no idea who he is, but whoever he is tell him that I love him so much" yayi reply "ohh God, am jealous" sannan wani message din 'and I love you too" Gaskiya ina jin dadin sakonnin ku sosai, jiya nasha dariya musamman a WhatsApp, ansha rigima tsakanin #teamSultam da #teamIbrahim. Da fatan dai ba'aji ciwo ba lol. I love you guys alot, stay blessed. [11/7, 2:37 PM] maryamsuleiman48@gmail.co: MAIMOON By Maman Maama Episode Sixty One : Save the Date Afuwan nayi mistake gurin numbering episodes, nayi fifty eight guda biyu, so daya shine fifty nine, daga nan kuma sai sixty. A episode sixty kar kuji nace Sultan ya shiga dakin Moon ya kwanta a gado wata ta gayyato nata saurayin daki, duk abinda ya faru babu ruwan maman maama. Kai kuma saurayi kar kaji labarin sultan ya shiga dakin Moon ta taga kai ma ka kama katangar gidan su budurwarka ka haura, idan aka kamaka ba zan zo ceto ba, ehe. Remember, this is just a fiction. Wajan azahar su Sultan sukaje 'yalleman. Sun samu tarya sosai dan an sanar da baffa zancen zuwan su, kusan duk uncles din Moon su zo taryan manyan baki. Kofar gidan baffa kam cika yayi da mutanen gari da suka zo kallon sarki, a cewar su. Hakimai uku ne suka tafi tare da galadima, sultan kuma cousins dinsa guda biyu da amir ne suka raka shi. A palon baffa aka sauke su, aka gabatar da sultan, ya gaishe da baffa, baffa yana ta tsokanar sa, daga nan aka sallame su suka tafi gidan nuraddeen suka bar manya zasu yi magana a tsakanin su. A gidan nuradden suka ci abincin da akayi ta kawo musu kamar babu gobe, Sultan ya zauna yayi ta shan fura yana santi wai dama abinda Moon take sha kenan in tazo 'yalleman shine bata taba gayyatar sa ba. Nan da nan suka saba da nuraddeen, yana ta bashi labarin Moon sanda tana yarinya. Suna zaune Moon ta kira shi, nuraddeen ne ya dauka, "ke wato yau kadai din ma ba zaki bar mana shi ba ko? Sai kin dame mu da waya?" Tayi dariya "kai yaya, kira nayi fa in ce ya bani kai mu gaisa" yayi dariya "ni zaki yiwa yawo ko? Har da wani yaya sai kace da yayan kike ce min" suka yi dariya gaba daya sannan ya bawa sultan, tace "so...how are you?" Yayi murmushi yace "ke dai ki fadi gaskiya, kin kira kiji yadda nake ko kuma kin kira kiji me ake ciki?" Tayi dariya tace "yanxu shikenan bani da right din da zan kira ka? I just want to know ya kuka je" yace "lafiya lau muka zo love, and maganr kuma da kike so kiji ni ma ban sani ba, suna can suna maganganun su" tace "ni ba wannan ne yasa na kira ka ba, so nake inji ya akayi aka saka maka hular rawanin nan da wannan gashin na kanka?" yayi shiru bai bata amsa ba, ta fara dariya, tace "don't tell me aski aka yi maka" ya bata rai yace "don't laugh, give it a week, zai dawo ne. Besides, ba du aka aske ba ai" tace "can I see it?" Yace "never, ba zaki taba gani ba har sai ya dawo yadda yake" A wajen su baffa kuwa sosai suke ta shan hira abinsu, da yake baffa mutun ne mai barkwanci nan da nan bakin suka saki jiki da shi suke ta hira. Sai bayan sunci abinci sunyi sallah sannan galadima ya gabatar da maganar data kawo su, suna nemawa dansu Abbakar Sadiq Abdullahi auren Maimunatu Muhammad Dikko, daga nan ya aika aka shigo da wata jaka cike da kudi, aka ajiyewa uncle Aliyu aka bude, mint ne 'yan 1000, galadima yace "ga kudin aure nan, muna fatan zaku karba" kowa ya saki baki yana kallon kudin, uncle Aliyu ya kallu kudin da yasan zasuyi daga miliyan biyar zuwa sama, ya saka hannu ya dauki rafa guda biyu ya ajiye a gefen sa yace "mun gode sosai amma wannan ya isa, albarkar auren muke nema, wannan ma mun dauka ne saboda al'ada ne" Tafida ya matso zai yi magana, baffa yace "abinda zamu iya karba kenan. Tun sanda labarin yaron yazo mana na tura Aliyu yaje har Abujan yayi mana bincike akan yaron, kuma yace min ya gamsu da abinda ya samu, dan haka tunda shine waliyinta na yarda da maganarsa. Na bawa Abbakar Sadiq auren Maimunatu, Allah yayi musu albarka baki daya Allah kuma ya sanya alkhairi" gaba daya aka ce "Ameen" uncle Rufa'i yace "to sai maganar sa rana kuma, yaushe kuke ganin za'ayi?" Tafida yace "ni ina ganin kar aja kwanaki da yawa, matsalar dai kawai yaron bai kammala ginin sa ba, dan haka ina ganin a bashi wata biyu, insha Allah kafin nan ya kammala, ita ma amaryar kafin nan ta shirye2n hidimarsu ta al'ada" kowa yace "wannan yayi, Allah ya kaimu" daga nan nan akayi addu'ar neman alkhairi aka tashi. Sultan kam da aka gaya masa me aka yanke ji yayi kamar ya dora hannu aka yayi kuka. Tun a hanya yake mita "wai wata biyu, ko garin abuja zan gine gaba daya ai iyakacin kwanakin da za'a bani kenan, aikin ginin nawa da a cikin sati daya zan gama shi, aikina ne fa" Ahmad, cousin dinsa yace "why are you whining ne Sultan? Tunda ance an baka ba shikenan ba? Me kake yiwa sauri ne wai" Sultan kawai tsaki yayi yace a ransa 'ba zaku gane ba' A abuja kuwa kiran gaggawa Daddy ya samu daga fada, nan da nan ya tafi, yana zuwa mai martaba sarki ya nemi a basu guri zasu gana, yace "Muhammad dama abinda kake shiryawa kenan? Dama dalilin da yasa ka dauki yaron nan kenan" Daddy yace "Allah ya taimakeka sam ba haka bane, mayar da Sultan gida na daban da alakarsa da yarinyar wajena" Takawa yace "bakasan halin yaron nan ba labarinsa kakeji, duk inda tunanin ka ya kai to ya wuce gurin. Ina tausayawa yarinyar nan, she have no idea what she is in for. Ka taimaka mata ka janye maganar auren nan. Bana son abinda zai bata zumuncin da yake tsakanin mu. Nasamu labarin itin tarbiyyar da ka bawa 'ya'yanka, sam yarinyarka bata dace da yaron nan ba. He don't deserves her" Daddy yayi shiru yana tunanin amsar da zai bayar, sai yace "Allah ya taimake ka ni bani na hada yaran nan ba, hadin Allah ne, kuma magana ba'a hannu na take ba tunda tun dazu suka ce min har sun isa 'yalleman gurin baffa na, yanzu maganar tana hannun sa. Ni ina ganin mu zuba ido kuma muyi addu'ah mu ga zabin da Allah zai yi mana" Takawa yayi shiru kamar ba zai sake magana ba, sannan yace "mu dai mun gayama gaskiya, wanda bai ji bari ba kam tabbas zaiji hoho. Fatan mu shine duk abinda ya faru kar kazo gurin mu. Zaka iya tafiya" Daddy jiki duk ba kwari ya mike ya fito, har yaje gida yana lissafin lallai da akwai wani abu a tsakanin Sultan da babansa wanda duk bincikensa bai sani ba, koma dai menene, it is something big. Moon A dakin Hafsat muka zauna, hira kawai muke yi muna dariya abin mu, muna ta labarin Haihuwar Hafsat da irin shagalin da zamu yi ranar suna. Edd dinta ya riga yayi kawai haihuwa ake jira. Hira nake ina dariya amma can kasan raina ina tunanin abinda yake faruwa a 'yallemam. Muna cikin haka naji shigowar kiran Sultan, na daga ina kallon sunan jikin screen din 'my Sultan' na tuna ranar da yayi saving sunan da kansa a waya ta, ranar dinner din Hafsat, a lokacin ban taba tsammanin zan dauki kiran saba ko da ya kirani sai gashi yanzu ya zama tamkar wani sashe na jikina wanda ba zan iya rabuwa da shi ba. Yanzu gashi wai yana kirana ne ya gayamin an bashi aure na ko ba'a bashi ba, sai naji na kasa daukan wayar har ta katse, ya sake kira shima naki dauka. Amira tace "in ba zaki dauka ba bani shi nan, har wani Sultan akewa kunya? Baki san ance kunyar mara kunya asara bace" na mika mata wayar, tana karba aka sake kira, gani nayi ta taba rai ta dawo min da waya ta, na duba screen naga 'Amir" dariya nayi dan nasan drama dinsu da Amir na dauka, yace "wai kunyar amarcin ce za'a fara yi mana tun yanzu?" Nayi murmushi kawai bance komai ba, yace "gamu nan mun taho, amma na san sai dare zamu karaso Abuja, tell that your ugly friend ta shirya mana abinci dan anan zamu fara sauka" nayi kamar banji ba, na saka shi a hands free nace "me kace?" Yace "wannan kawar taki mummuna, bakar nan masifaffiya, kice mata ta dafa mana abinci kafin muzo" ai kuwa Amira ta warce wayar daga hannuna ta kama yi masa masifa "yanzu har kai zaka kalli wani ka kira shi da ugly? Anya kuwa kana kallon fuskar ka a mudubi kuwa? Duk baki na wallahi ni balarabiya ce akan ka" ni dai dariya nake yi Hafsat tana taya ni. Sai bayan isha suka zo, iyakacin samarin ne suka zo nan manya kowa ya kama gabansa, uncle Aliyu ma yazo ya taho da Amina wacce daga jin zancen biki ta rude ta hado kayan ta. A palon su Sultan suka sauka nan aka shiga hidimar kai musu abinci, sai da suka gama sukayi sallolinsu sannan muka je, ni da Amira da Amina. Muna shiga aka fara drama da Sultan dan fir yace babu wanda zai ga fuskata, ai an bashi ni yanzu dan haka i am no longer in tha market. Su Ahmad suka yi ta naci su kuma lallai sai sun ga fuskata tunda takabas dan su ganni suka zo, da kyar dai Sultan ya yadda na bude fuska ta, shima kuma ya kasa ya tsare yace babu dogon kallo, ni dai dariya kawai nake yi musu. Nan fa Amira da Amir suka dora daga inda suka tsaya, Amina ma da yake mai surutu ce sai ta shige cikin su suke tayi. A hankali sultan ya mike ya je bakin kofa sannan yayi min alama da in zo, tsam na zame na bishi ba tare da duk sun lura mun fita ba. Ina fita sai naga ya kama hanyar garden na bishi a baya. Akan kujera ya zauna nima na karasa na zauna a kusa dashi, ya juyo yana kallo na nayi sauri na sunkuyar da kaina kasa ina murmushi, dariya yayi sosai yace "wai ni kike jin kunya kuma? Tsafdi, lallai kin hadu da aiki" ni dai bance komai ba, ya kamo hannayena duk biyun yana kallon su, sannan a hankali ya shafa zoben sa da har yanzu yake makale a danyatsa na. Sannan yace "wata biyu suka ce, what if something happens a cikin watanni biyun? Na kalle shi naga ya sunkuyar da kansa yana kallon hannayen mu a hade, nace " Sultan, babu abinda zai faru kaji? Kullum muna addu'ar zabin alkhairi, tinda har Allah yasa suka ambaci wata biyu to sune mafi alkhairi a gare mu. What if da ace baffa cewa yayi NO? Ya zakayi kenan?" Ya dago da sauri yana kallon idona yace "then I will definitely be your patient, dan kwakwalwata zata iya bugawa" na same hannu na daga nasa na tallafo fuskarsa dasu ina kallon idonsa nace "babu abinda zai same ka, shi Allah baya taba dorawa bawansa abinda yasan ba zai iya ba" ya katse ni yace "then Allah ba zai raba mu bama, saboda yasan ba zan iya dauka ba" idonsa gaba daya ya chanza kala, nayi saurin chanza maganar nace "Askin ka yayi kyau" Hannu biyu ya saka ya rufe kan sa yace "ash, ya akayi na bari kika gani" nace "really yayi kyau, I like it" ba duk gashin aka aske ba, an rage masa tsaho dai, sai ya fi dacewa da sajen sa, fuskarsa kuma ta kara fitowa sosai. Ya shafa kan yace "thank You" sannan ya cigaba da magana "tom yanzu cikin two months din nan me za muyi?" Nace "kamar me fa?" Yace "to kill the time" nace "as usual, kai already ma ai aiki yayi maka yawa, ga office ga harkar gini, ni kuma I will just be here, waiting" yace "driving lessons din mu fa?" Nace "bayan ba wani abin kirki kake koya min ba, for over one month amma ace har yanzu ban iya driving ba" muna cikin haka muka ji muryar Amir "to in kun gama soyewa sai kuzo muyi sallama mu zamu tafi gida" na tashi ina dan jin kunya, muka fito muka tarar har sun dauko mota mukayi sallama suka tafi, Amir kuma ya dauko motar sultan guda daya, yana zuwa gurin mu nace "Amir dan Allah ga Amira nan ka kaita gida, kaga dare yayi sosai" a tare suke ce "what?" Ni da sultan sai dariya, sultan ya bata rai yace "gaskiya Amira in ba zaki shiga motar Amir ba to sai dai ki hau taxi, dan ni na gaji ba zan kai ki gida ba" Amir yace "to ni an gaya maka ban gaji bane? Ballantana wannan unguwar tasu mai shegen nisa, kuma ni ba ma nason a ganni da ita a mota a daukar ko budurwata ce, ai sai aji na ya zube" nan Amira ta hayayyako "Allah ya kiyaye min shiga motar ka, ni da in shiga motar ka ba gwara na tafi a kafa ba" yace "ai kuwa zaki tafi a kafar" har yaja mota sai kuma yayi reverse, yace "get in" kawai sai muka ga Amira ta zagaya ta bude ta shiga sun tafi, daga ni har sultan duk sakin baki muka yi muna kallon su, Sultan yace "munafukai, a hankali sai asirin ku ya tonu" Rayuwa ta koma normal, abubuwa suna tafiyar mana yadda muke so, sultan ya dukufa haikan akan aikin gininsa duk da kusan tare muke aikin dan dai ni bana fita field dinne amma komai tare muke tsara shi, komai za'a saka a gidan sai ya kawo min samples na zaba tukunna, ba karamin kudi yake narkar wa a aikin ba dan ni har mamakin inda Sultan yake samun kudi nake yi, gani nake kamar aikin sa ba zai shigo masa da wadannan uban kudaden ba. Rannan mun fita koyon mota sai yace min yana so zamu je wani guri. Hanyar barin gari naga mun dauka amma ban tambaye shi ina jamuje ba. Gani nayi yayi packing, na fito ina kallon gurin da muka zo, orphanage, a kafa muka shiga cikin building din. Babban guri ne sosai, ga dakunan yara, maza daban mata daban, ga gurin wasa, ga kitchen sannan ga offices din staff. Muna shiga ma'aikatan gurin suka fara gaishe mu da girmamawa sosai kamar zasu kwanta a kasa, ni har mamaki nake yi, idonsu kawai zaka kalla kaga tsantsar soyayyar sultan da kuma respect dinsa, ya fara tambaya "where are my kids?" Da sauri wata tace "suna playground suna wasa" muka tafi gurin, ina ta kallonsa naga wani excitement a fuskarsa, real love, ai kuwa muna shiga gurin wasan gaba daya rayan suka taho a guje wasu har suna faduwa suka rungume shi, sai da suka kai shi har kasa yana ta kyalkyala dariya, in ba tare da ni ba ban taba ganin sultan cikin wannan fara'ar ba, da kyar ya samu suka daga shi, ya zauna a zaune suka zagaye shi kowa yana kokarin bashi labari, ga mamakina duk yasan sunan kowa kuma yasan me yake ciki, ni sam bana fahimtar me suke cewa saboda yadda suke magana gaba dayan su a tare. Sai da suka dan numfasa sannan ya tashi ya kamo hannuna yace "na kawo muku bakuwa yau, Mommy zaku ke ce mata, she is going to be my wife" masu wayon cikin su suka kama murna marasa wayo kuma kawai suka tsaya suna kallona, har cikin dakunan su ya shiga dani na gani, ko wanne yaro da gadonsa sai 'yan kanana ne ake musu shimfida a kasa saboda kar su fado, gurin tsaf tsaf babu kazanta, ko wanne yaro da locker din kayansa, ga kuma inda suke cin abinci shima a tsaftace, muka shiga kitchen masu aikin girki suna ta gaishe mu, suka bashi list din abubuwan da suke bukata nan take ya bada kudin yace a saya, muka shiga dan karamin clinic dinsu shima ya nuna min sannan yace yana son ya dan yi musu 'yar karamar makaranta amma sai nan gaba tukunna, yanzu dai van ya saya musu ake kaisu kamaranta kullum ake dawo dasu. Har zamu tafi wani yaro yazo da gudu yana bata fuska yace "Daddy kace in ka dawo zaka kawo min bindiga kuma gashi ka dawo baka kawo min ba" Sultan ya sunkuya har kasa yana shafa kan yaron yace "sorry Halifa, na manta, amma gobe insha Allah zan bawa uncle Amir ya kawo maka" yayi masa kiss a goshi, yaron ya tafi yana ta murna. Ji nayi kwalla ta taru a idona, yanzu na fahimci inda sultan yake samun kudi, as long as kana kyautatawa mutane da dukiyarka, musamman marayu, to Allah zai yi ta ninka maka kofofin arzikin ka, abinda ka bayar sai Allah ya biya ka da dubun sa, mutum kamar sultan ba zai taba talauci ba. Muna shiga mota ya kama hannuna daya ya rike yake tuki da dayan hannun, babu wanda yace komai, can nace masa "da ka gayamin nan zamu zo at least ai da na taho musu da wani abu ko?" Yace "you are welcome, duk sanda kike son zuwa zan kawo ki" na sake yin shiru a raina ina mamakin mutum irin sultan. Tafiya muke a hankali kamar ba ma son zuwa gida, kowa da tunanin da yake yi, har yanzu kuma yana rike da hannuna, sai da muka yi nisa nace "Sultan ya kamata kaje gurin Takawa kuyi maganar bikin nan dashi" ba tare da ya kalleni ba yace "naje ai" da sauri na kalleshi ina mamakin ya akayi bai gaya min ba, packing yayi sannan yace "Abbas ne ya kira ni a waya ina office yace min inje Takawa yana kirana, da naje gurinsa na gaishe shi bai amsa ba, kin san me yace min?" Na girgiza kaina, yace "check book ya jeho min duk yayi signing pages din yace 'ka dauki duk adadin kudin da kake so kayi duk abinda kake so dashi, amma ina son ka fasa auren yarinyar nan, she doesn't deserve someone like you" yayi shiru fuskarsa tana nuna bacin ransa, a hankali na tambayeshi, "me kace masa kuma" ya daga kafada yace "na ajiye masa check book dinsa na ce masa bana bukatar kudinsa, abinda da nake nema daga gare shi ma yanxu bana bukatar sa" ya juyo yana kallona yace "all I wanted before is love, yanzu na samu daga gare ki, kowa ma yaje ya rike nasa, your love is enough for me" hawaye naji yana fitowa daga idona (is it possible to love someone so much that it makes you cry?) Ya saka hannu yana goge min hawayena yace "just promise me that you will never leave me [11/7, 2:37 PM] maryamsuleiman48@gmail.co: MAIMOON By Maman Maama Episode Sixty Two : The Manager Na kalli cikin idonsa nace "I will never leave you, dama parents dina kawai nake ji, tunda yanzu na samu go ahead din su babu abinda zai saka in rabu dakai" a hankali yanayin fuskarsa ya fara chanzawa daga bacin rai zuwa murmushin da ya saka nima na fara murmushi yace "then I don't need anybody else" Mun dau hanyar gida again naji wayata tana ringing, na daga naga Mommy, ina dauka tace "ya akayi har yanzu baku dawo ba? Ku zarto asibiti mun tafi da Hafsat yanzu tana labor" a rikice ta katse wayar ina kallon sultan nace "Hafsat....labor... Hospital" nan take Sultan ya gane abinda nake nufi ya juya kan mota muka tafi asibitin da Hafsat take antinatal. A hanya na dauko wayata ina neman number, sultan yace "wa zaki kira?" Nace "Zayed" yace "No, ki bari sai ta haihu tukunna" na mayar da wayar na ajiye. Muna zuwa da sauri na fita na bar sultan a mota, a waiting room na samu Mommy da Amina, Mommy tana ta faman jan charbi. Na samu guri nima na zauna. Ba'a jima ba aka leko aka ce wata a cikin mu ta shiga ta zauna da ita, da sauri na tashi na shiga. Zan iya cewa tare muka yi laborn da Hafsat, in tana kuka nima sai in kama kukan, in tana addu'ah in taya ta. A haka mukayi ta fama har dare ya raba, Sultan yana ta kira yana tambayar jikin Hafsat, a lokacin na kara jinjinawa mata da irin wahalar da suke sha a gurin haihuwa, a lokacin kuma na kara jin haushin duk matar da zata haihu ta dauki dan taje ta yar, kuma na kara tsanar duk dan da zai ki yiwa iyayensa biyayya. Hafsat ba ta haihu ba sai da alfijir ya fara keyowa, ta rike ni gam tamkar zata ballani sannan ta haifo kyakykyawar 'yarta mace, ana goge yarinyar na karbe ta na rungume ina jinsonta yana shiga zuciya ta, Hafsat ba kunya babu tsoron Allah tana samun kanta tace in bata 'yarta, har nurses din wajan sai da suka yi dariya. Na dora mata ita akan cinyarta ta fara shayar da ita (shayar da baby a wannan lokacin yana taimakawa wajen tsayar da jini da kuma saukin fitar mabiyya, kuma yana taimakawa jariri wajan saurin koyon shan nono da wuri kuma wannan ruwan nonon na farko yana da matukar amfani a gurin jariri). Gari yana wayewa aka fito dasu dakin hutu, nan fa dakin ya cika da 'yan ganin baby, ina ta Allah2 in kira Zayed ashe har Sultan ya riga ni, Mommy da Daddy sai rige rigen daukan baby suke, Hafsat kam cewa tayi ayi mata allurar bacci dan tana son hutawa, tayi kwanciyarta a ciki mu kuma muka taho daya dakin muna ta hayaniyar mu. Bayan azahar sultan ya kirani a waya, ina fita na tarar dashi a mota ya ce min "shigo" ba musu na shiga, naga ya tayar da mota, nace "ina zamuje?" Yace "gida zan kaiki kije ki huta, jiya baki yi bacci ba throughout" nasan gaskiya yake fada dan haka na kira Mommy nace mata zanje gida in anjima zan dawo, ina zuwa kuwa na tafi daki na na kwanta sai bacci, ban koma asibitin ba sai da daddare muka tafi tare dasu asma'u da suka dage sai sunje sun ga baby ba zasu jira su dawo gida ba, muna zuwa Zayed ya kira daddy yake gaya masa cewa ya samu delay din flight dinsa amma dan haka daddy yayi wa baby huduba da sunan Mommy, Fatima Zahra, Mommy kasa rufe baki tayi dan murnar an yi mata takwara, kowa sai murna har Hafsat taji dadi sosai, Daddy ya karbe ta yayi mata huduba ya miko min ita, Amina ce tace "to Hafsat yanzu me zamu ke ce mata kenan, tunda dai ai mu ba zamu kira ta da sunan ta ba" Hafsat ta daga kafada, sai gaba daya suka juyo suna kallona, ni aka barwa zabi kenan, na kalli babyn sosai ina ganin tsantsar kyawunta na larabawa, nayi murmushi nace "Khairat, we will call her Khairat" a tare Daddy da Sultan suka juyo suna kallona, nayi kamar bansan sun gane me nake nufi ba, Mommy tayi dariya tace "perfect, yayi sosai, Allah yasa ta zama sanadin alkhairi a gare mu baki daya" nan kowa yace "Ameen" Hafsat ma murmushi take da alama sunan itama yayi mata dadi, sultan bai yi magana ba sam, ni kuma ban kalle shi ba, sai daga baya na lura ya fice daga dakin. A mota na same shi ya kwantar da kujera ya rufe idonsa kamar mai bacci, na zauna kusa dashi nace "in bacci zakayi ka tafi gida mana" ba tare daya bude idonsa ba yace "why Khairat? Why do you want her when she doesn't want me?" Bance masa komai ba saboda babu abinda zance masa, jin nayi shiru ya saka ya bude idonsa yana kallona yace "yanzu zaki tafi gida ne?" Nace "a'a, anan zan kwana ai" yace "OK, but ki tabbata kinyi bacci sosai, kar ki biye wa little Khairat" nayi murmushi na fita, na tsaya nace "good night" yace "good night love". Washe gari da safe aka sallame mu muka koma gida, a ranar kuma Zayed yazo. Sati yana zagayowa akayi suna, anyi taro sosai, kayan barkan da Sultan ya hado in wani ya gani zai iya tunanin shi aka yiwa haihuwar. Ana gama hidimar suna Mommy ta juyo kaina, tace yawo ya kare, babu inda zan ke zuwa. Shirye shirye ake yi sosai, dan har gyaran gida Daddy yayi, Amira da Amir sune chairman da chairlady din committee n shirye shirye, Sultan yace shi big wedding yake so, a cewarsa it will be the biggest day of his life, dan haka dole yayi celebrating. Ni nafi so ace anyi komai kadan amma mutane sunfi karfi na, dan anko sai Amira ta fitar da kala biyar, wai kowanne event sai anyi masa nasa ankon, kawayen mu na secondary school duk sai da Amira ta je ta gayyato su, ni dai ban samu damar zuwa ba saboda Mommy ta hana ni fita sam. Takanas Mommy ta dauko wata mata daga maiduguri wai zata min gyaran jiki, ni dai kawai jinsu nake dan banga abinda za'a gyara a jikina ba. Ranar farko da matar tazo muka shiga daki da ita, ta shiga toilet ta hada wani ruwa a tub, tace in cire dukkan kayan jikina in shiga ciki sai nayi awa daya tukunna, ina jin haka na dau waya ta da ear piece na je na shiga na kwanta na kira Sultan lokacin yana office muke ta hirar mu, ban ma san sanda awa dayar ta wuce ba, sai ganin matar nayi ta dawo da wani soso a hannunta, na yiwa Sultan sallama nace mata "wannan soson fa?" Tace "dashi zanyi miki wanka yanzu da wannan sabulun" na bata rai nace "ni zaki yiwa wankan?" Tace "eh, ai wannan ruwan da kika shiga kamar jika ki nayi yanzu kuma zan chuda ki ki fita tas" ni dariya ma abin ya bani, wato ana nufin duk wankan da nake yi ba fita nake ba shine yanzu za'a yi min wani. Bana son in gwale matar nace mata "OK, bani soso da sabulun, ni zanyi wankan da kaina" tace "ai ba zaki iya da kanki ba, anfi so wani yayi miki saboda zaki fi fita" yau naga rigima, ni kam babu yadda za'ayi in zauna kamar wata jaririya ayi min wanka. Ganin na dage da gaske nake ba zata yi min ba yasa ta fita ta kirawo Mommy, Mommy tana zuwa ta karba tace ta bata ita zata yimin da kanta, ai kuwa kam nasha durza kamar za'a ciremin fata, ni gani nake duk wahalar da ni suke yi suma suna wahalar da kansu, ban tashi sanin bani da wayo ba sai da na fito na kalli kaina a mudubi, gani nayi kamar wadda aka cire min fata ta aka saka min wata, a hankali nasa danyatsa na taba jikina, wani laushi da santsi naji jikina yayi. Ina fitowa kuma aka hada wani kaskon turaren wuta aka saka na tsuguna akai, wani irin kamshi ne mai tsadadden dadi yake ratsani, bargo matar ta saka ta lullube ni, sai fuska ta ce kawai a waje, sai da nayi 30 minutes a haka. Bayan na tashi kuma ta dauko wani mai ta bani tace duk in daina amfani da mayuka na sai shi kadai har lokacin biki na, kuma tace in na tashi shafawa a duk jikina zan shafa. A haka muka rabu da ita tace bayan kwana uku zata sake dawowa ta sake yi min wani wankan da turaren. A raina nace wannan me kuke so in zama kafin lokacin bikin? Ta kara jaddada min kuma banda fita rana, sam ba'a son rana ta taba ni. Hafsat ma kanta ranar dana zauna a kusa da ita sai da ta rinka shanshanani tana cewa ya akayi ita ba'a yi mata irin wannan ba lokacin bikinta, amma tace in dai tayi arba'in itama sai anzo anyi mata. Ranar kam kin zuwa gurin sultan nayi saboda bana son ya saka ni a gaba da tambayar wanne turare na chanza, shima kuma da yake yanzu kullum a gajiye yake sai bai wani matsamin inje ba, a waya dai muka karaci hirar mu. A hankali komai na ginin sultan ya kammala, Hafsat da aunty Maryam kawar Mommy da gwoggo Aisha, matar uncle Aliyu ne suka je suka gano gidan saboda siyayyar kayan daki, tunda suka dawo suke santin kyau da tsarin gidan, Hafsat har dare zancen gidan nan take yi har sai da Mommy tace "ya ishe mu haka, munji yayi gida mai kyau, congratulations to him" sannan Hafsat tayi shiru. Har yanzu Mommy ba wani son sultan take yi sosai ba amma dai ba kamar da ba, duk da yanzu ta daina ce masa tsagera da sauran sunayen da take kiransa dasu amma har yanzu bata ambaton sunan sa, sai dai tace masa wannan yaron. Dama tun tuni ni da Sultan mun tsara colors din da muke so ayi furnishing ko wanne daki dashi, da colors din yayi amfani gurin tiling da fenti, dan haka na zauna na tsara wa Hafsat komai yadda nake so ita kuma ta gaya wa Mommy, a cikin sati daya akayi order komai aka kawo, masu interior decoration aka dauko suka je suka saka komai, suka kuma kara abinda suke ganin ya kamata su kara. Ni kaina nasan Daddy ya narkar da kudi a kaina. Tun ana saura sati uku biki aka gama shirya gidan tas aka rufe. Saboda tsabar gyaran da jikina yake samu gani nake yi kamar in aka tabani jini ne zai fito, fuskata har wani kalli take yi saboda tas din da tayi, idan na zauna a guri kuwa ko bayan na tashi kamshina yana nan. Dole na kara jan jikina daga gurin Sultan dan sosai yake nuna min kwalamarsa a fili, sau da yawa in yana zaune a kusa dani yayi ta shanshana ni har sai na tashi na gudu. Da kadan da kadan gida ya fara cika da mutane, daada ta iso da jama'ar niger, part dinta aka bude mata suka sauka a can, tana zuwa itama ta fara dura min tsumi, kullum da akwai abinda zata bani in sha, daga farko dariya nake yi mata dan ni gani nake duk wani maganin mata kawai fada ake yi, dan mu a likitance bamu san wannan ba, ban gane bani da wayo ba sai da na fara jin chanji a jikina, babu shiri na daina shan tsumin daada, inta bani sai inzo in ajiye a fridge in yi tafiya, data fahimci me nake yi ta tambaye ni dalili sai nace mata ta ajiye min in anyi bikin sai inke sha acan, sosai ta fahimci abinda nake nufi dan haka ta daina bani, sai da hado min su jaka guda kowanne da bayanin yadda zan yi amfani dashi ta bani tace in tafi dashi can, na karba nayi mata godiya, ni sai inta mamakin daada da Mommy, su da basa son sultan kuma me yasa suke yi tayi masa tanadi haka?. Saura sati biyu biki aka kawo kayan lefe, akwati set goma aka kawo,different colors, ni har kasa tsayawa nayi in kalla saboda kayan sunyi min yawa, duk kayan kuma Yaya ce tayi su, tace tata gudunmawar kenan, dan haka da Daddy ya saka sultan a gaba da fadan kayan sunyi yawa sai ya gaya masa yace shi ko dan kunne bai saya a ciki ba. Kaya ne masu tsada daga gani kasan cewa akwai class. Sarkokin gold akwatin su daban. Kuma komai size dina, daga gani kuma kasan babu abinda aka saya a Nigeria. 'Yan 'yalleman dama basu zoba sai ranar da aka kawo kayan, daga nan suma suka bude part din su inna suka baje tasu hajar. Hajja kam sai yada magana take tana kunkuni 'ai dama sai da jikina ya bani, kudi suka gani shi yasa suka hana yaron nan, duk abinda kuwa aka saka bidi'a a cikin sa ba zai yi albarka ba. Shima Allah ya bashi arzikin da yafi wannan kuma Allah ya bashi matar da ta fita" babu wanda ya kula ta haka ta gama sumbatunta. Inna kam tana zuwa ita tsarabar data kawomin shine na adduoi, tace "gidan sarauta zaki je dole kina bukatar tsari sosai, tsari daga sihiri, tsari daga mugun baki, tsari daga dukkan sharri na mutun kona aljan" ta babbani rubutu na sha, ta kuma koya min adduoin tsari sosai, sannan tayi min nasihu masu ratsa jiki akan kula da addini, tsarkake zuciya da iya mu'amala da mutane, tace as long as kana kula da addinin ka sosai, ka kuma tsarkake zuciyar ka baka nufin kowa da sharri to Allah ba zai taba bawa makiyinka nasara akan kaba. Shi kuma iya zama da mutane shi zai kara maka soyayyar miji ya kuma jawo maka soyayyar 'yan uwan miji. Naji dadin nasihohinta sosai, sai nake ganin kamar duk ita tafi kowa bani tsarabar gidan miji. Kamar yadda akayi bikin Hafsat haka nawa ma zai kasance, su Mommy sun shirya kunshi, kamu da mother's eve, su kuma su Amira da Amir 'yan committee sun shirya bridal shower, luncheon, dinner, sai walima for girls, and bachelor's night for the guys. Sai kuma ranar da aka kai amarya Amir ya shirya mana welcome party anan gidan mu da Sultan. Ni already jina nake a gajiye, I have no idea yaya zan iya duk wadannan events din. Har yanzu wasan buya muke yi da Siltan, dan sosai nake rikita masa lissafinsa in muka hadu, nima kuma tunda daada ta fara dura min tsumin ta na fara ja baya dashi. Yayi mitar har ya gaji, gashi gidan ya fara cika da mutane balllantana yace zai yi abinda ya saba ya shigo min daki cikin dare. Shima kuma yanzu ya dan fara ja da baya da zaman gidan saboda baki. Wani lokacin sai dare yake zuwa sai dai insa akai masa abinci office, da daddare kuma sai in aika masa dashi dakinsa. Ten Days To The D- Day Tun safe Amira tana gidan mu, sun hadu ita da Amina suna ta ware min kayan da zan saka a kowanne event, ni kallo kawai nake bin su dashi saboda already Sultan ya bada dinkunan mu ni dashi na kowanne event, anko zamu ke yi, wanda kuma na mata ne kadai shima ya dinka min abinda zan saka, hatta takalmi da jaka babu wanda bai saya ba, hotunan yake turomin ni kuma ina zaba, tunda yanzu mun zama mage da bera bama zama a guri daya. Sai da suka gama shan wahalar su sannan nace "kun gama?" Suka juyo suna kallona nace "to sai ku mayar min da kaya jikin akwati basu zan saka ba" na gaya musu tsarin mu da Sultan, Amira ta bata rai tace "kuma dan wulakanci shine kika barmu muke ta wahala, amma wannan akwai munafukar amarya, shine zaku ware ke da angonki ku tsara abinku ba zaku fada wa 'yan committee ba" nayi dariya nace "'yan committee manya, wai dan Allah me kuke cewa in kun zauna meeting din ne? Yarinyar nan babu abinda ba tace min akan Amir ba amma yanzu in ka gansu suna kus kus sai ka dauka they are lovers" ta kara bata rai tace "lovers fa kika ce? Allah ya tsari gatari da saran shuka, ni kuwa me zanyi da wannan? Dan Allah yanzu ke a ganin ki mun dace?" Nace "sosai kuwa" tace "to amma kuwa ya kamata kije ayi miki wankin ido" Amina dai dariya take yi tace "Moon kinga yadda kika koma kuwa? Shi yasa yanzu in dai kina guri Sultan ba sosai yake fahimtar magana in an yi masa ba. Oh Allah. My future husband where are you? Am waiting" dariya nayi sosai nace "to ke ki lallaba munir mana?" Ta zaro ido waje "a 'uzubillahi, kije ki wanke bakin ki please. Ai ni da kike gani sabo zan bare a leda. Munir shi kam in aka ce masa gwanjo ma ai an rufa masa asiri" ta jawo ni tazo dai dai kunnena tace cikin rada "gayamin, Sultan sabo ne ko tsoho" na ture ta ta fada kan gado, nace "you will never find out" Amira tace "ni fa har yanxu ban sayi gown din da zan saka ranar bridal shower ba, kowa ya gama shirin sa ban dani, bayan itama da akwai abubuwan da ban saya ba" nayi sauri na zauna kusa da ita nace "kinga kawata, kuje ke da Amina gurin Mommy ku lallabata ta barni in fita, sai muje in kaiki ki siyo, wallahi na gaji da zaman gidan nan. Tunda sunce rana ce basa so in shiga ai yau babu ranar ma" Amira tace "ni kinsan Mommy yanzu ba shiri muke yi da ita sosai ba, sai dai ko Amina" na juya gurin Amina nace "please yaya Amina, kije ki tambayar min" ta bata rai tace "to in kun fita me zaki siyo min?" Nace "duk abinda kike so" nan ta jera min uban list na abubuwan da take so in siyo mata, duk nace naji na yarda. Ta fita muka zauna zaman jira. Sai da tayi wajen minti talatin sannan ta dawo tana bata fuska, har na sare, sai kuma tayi dariya tace "an barki, amma ki saka dogon hijab da nikab" murna kamar in cinye Amina, dan ji nake gaba daya na tsani kaina saboda zaman gida. Na kira Sultan a waya na gaya masa zamu fita da Amira, yace "OK, in kun gama ki yi min magana, nima ina son zamu je wani guri" nayi shiru bance komai ba, yace "please say yes mana, yaushe rabon da in ganki wajan three days" nace "ina zamu je?" Yace "where it all began, ina so muje muci abinci a Hilton, anan na fara ganinki" kawai sai naji ba zan iya ce masa no ba, nace "OK" yana ta murna na kashe wayar. Da sauri na shirya muka fita, har wadanda suke palo basu gane ni ce na fita ba saboda na rufe fuskata, daya daga cikin motocin Sultan na gani na leka naga key a jiki kawai na shiga na tayar, Amira ta shiga muka tafi. A gate mai gadi kin budemin yayi sai da nayi magana yaji muryata sannan ya bude yana dariya. Wani supermarket tayi min kwatance, ni ban taba shigar sa bama ina dai ganinsa a hanya, ita ma tace bata taba zuwa ba an dai ce mata akwai kaya masu kyau a can. Muna zuwa muka yi packing, na chire nikab dina na ajiye a mota, muka shiga, karshen haduwa gurin ya hadu, kaya kam akwai su, ga shi komai a tsare, nan da nan Amira ta fara lodar kaya, ni kam ban sayi komai ba saboda babu abinda nake bukata, a wajen siyan gown tayi ta ruwan ido, nace "wallahi in ba zaki dauka ba zan tafi in barki, Sultan fa yace zamu hadu in anjima" ta tsaya ta saki baki tana kallona, tace "dama rakonin da kika yi na munafunci ne? Dama gurin sultan zaki tafi? Wallahi kinsan ba karamin aiki na bane yanzu in kira Mommy in gaya mata" nayi ta bata hakuri ina lallabata "ba wani gurin zamu je ba fa, abinci kawai zamuje muci a Hilton, kuma motar sa daban mota ta daban" tace ta hakura ba zata fada ba amma sai in barta ta gama siyayyar ta a hankali. Sai da ta gajiyar dani sosai sannan tace ta gama, muka tafi gurin biyan kudi. Da POS ta biya kudin, aka bamu receipt muka fito, muna shiga mota na dauko waya ta da niyyar kiran Sultan naji Amira tace da karfi "what?" Na juyo ina kallonta da waya a hannuna naga wayarta take dubawa, nace "ya akayi?" Ta nuna min screen din wayarta naga alert ne na siyayyar da tayi yanzu nace "menene?" Ta nuna min receipt din, ni har lokacin ban fahimci me take nufi ba, tace "duba ki gani, sun kara min 10k a cikin kudina" nayi ajjiyar zuciya nace "please Amira, let it go, wallahi na gaji" tace "wallahi bazan hakura ba sai sun biya ni kudina, haka kawai dubu goma a banza, zo muje sai sun biya ni kudina" kamar zanyi wa Amira kuka haka na fita na bita muka koma ciki. A gurin cashier ta fara masifar sai an biya ta kudinta "How can you guys be so incompetent, ku kara min kudi har dubi goma?" Cashier kaman zata yi kuka tana bawa Amira hakuri amma Amira ta shafa wa idonta toka tace sai an biya ta, ni dai ina ta kallon agogo naga har karfe biyar, nasan duk inda six tayi Mommy zata kira ni tace in dawo gida, kuma gaskiya bana son missing date din mu da sultan, na karasa gurin rigimar naji cashier din tana cewa da Amira "madam kudin sun riga sun shiga account din shagon nan, ba zamu iya fitar dashi ba sai dai ki dau wani abun na kudin ki" Amira tace "ni na gama siyan duk abinda nake so in saya, babu abinda zan dauka kuma, kawai kudi na kawai nake so a bani" cashier tace "I can't do that madam, only the manager can do that, sai dai in zaki yarda in kaiki gurinsa inyi masa bayani sai ya biya ki kudinki" naga tsoro karara akan fuskar cashier din, daga alama tana tsoron manager din, nace "Amira ki zo mu tafi, ni zan biya ki 10k dinki" tace "wallahi bazan tafi ba chafdi, nasan sauri kike ki tafi gurin Sultan, in ya kira ki bani shi in yi masa magana" ni dai duk raina a bace, tausayin cashier nake yi, mistake tayi muka maybe zata iya loosing job dinta akan haka, da har nayi deciding inyi tafiya ta in bar Amira su karata amma sai na sake tunanin maybe in na bisu gurin manager din zan iya bashi hakuri kar ya kori cashiet din. Sai da ta fara yin waya ta tabbatar yana office sannan tace muzo muje, ta shige gaba muna binta a baya, ta hau stair muka bita zuwa hawa na uku, da kyar na karasa ina ta haki, taje bakin kofar tayi knocking, aka yi magana daga ciki, ta bude tayi mana alamar mu jira a waje sannan ta shiga ciki, Amira kam ba zata jira ba dan haka ta tura kofar ta shige ciki, nima na zo kofar na tsaya. Cashier na hango tana ta kokarin yin bayani, muryarta sai rawa take yi, na dan shigo daga ciki dan in hango wannan manager da matar take tsoro haka. Ya dan juya side dinsa, dan haka banga idonsa ba, amma tsaf na gane shi. Familiar scent dinsa ne ya kara tabbatar min da cewa shine. Na kara taku daya cikin katon office din. He is still tall but no longer thin. Yayi kiba, jikinsa ya murje sosai, hakan sai ya bashi almost a giant frame. Doguwar fuskarsa ta cika, siririn sajensa ya kara fadi dan ya tafi da fadin da fiskarsa ta dan yi, dan karamin gemon da da yake dashi yanzu babu, meaning the ustaz part of him is gone. Amira naji tayi catching breath dinta very sharply. Fatarsa ta kara haske, tana kara nuna alamar hutun daya samu. He looks so different but still the same. Lokaci daya ya juyo ya kalleni idonsa ya fada cikin nawa dana bude ina kallonsa. His eyes look the same, babu abinda ya chanza. Suna nan a lumsassun idanun da nayi falling in love with all these years ago. Gabadaya yanayin fuskarsa ya chanza lokaci daya. Da sauri na juya na nufi kofa, bansan sanda ya sauko daga kan kujerar saba har ya zagayo table dinsa ba, ina dora hannuna akan doorknob naji nasa hannun akan nawa, ya jawo ni baya da karfi, cikin tsawa naji ya ce da cashier din data kawo mu "out" na fara kokarin kwace hannuna amma maimakon ya saki hannuna sai ya hada ni da kirjinsa ya matse. Na fara kokarin kwace wa amma sosai ya matse ni, kuka na saka sosai, still bai cika ni ba, ban san adadin tsahon lokacin da muka dauka a haka ba dan har sai da nayi kuka na na gaji dan kaina nayi shiru sannan ya sassauta rikon da yayi min. Ina kwacewa na rarumi wani file akan table dinsa na fara dukansa dashi, har sai da takardun ciki suka tarwatse sannan na kuma daukan wani na cigaba da dukansa ina cewa "why? Why? Why?" Bai hana ni ba har sai da dan kaina na gaji da dukansa na durkushe a gurin na sake wani sabon kukan. A hankali a durkusa a baya na yace "am sorry" na juyo a fusace nace "sorry? Abinda zaka ce kenan? Sorry?" ya sunkuyar da idonsa kasa yace "am sorry, i shouldn't have hug you like that, bai kamata in taba ki ba kina matar aure, am sorry i lost control of myself bayan ganin ki after all these years" na juyo da mamaki ina kallonsa dan ban fahimci me yake cewa ba nace "me kake nufi da matar aure kuma?" Yanayin yadda nayi tambayar yasa ya mike tsaye da saurinsa yana kallona gaba daya ya rude yace "ance min kinyi aure a shekarar da muka rabu, kwanan nan akace min kin haifi danki na uku" [11/7, 2:38 PM] maryamsuleiman48@gmail.co: MAIMOON By Maman Maama Episode Sixty Three : Amira 3 Cikin tsananin mamaki nace "what? Waye ya gaya maka haka" gani nayi yana kallon office din kamar me neman wani abu, nima na taya shi dubawa, sai a lokacin na tuna cewa tare da Amira muka shigo office din, babu ita babi alamar ta. A zuciye naga yayi hanyar kofa yana cewa "I will murder that bitch" jiri naji yana kokarin dibana, nayi sauri na zauna a kujera, nasan da za'a gwada jini na a lokacin za'a tarar ya hau, Amira, why? Me yasa zata yi min haka? I trusted her. Babu abinda banyi mata ba kuma babu abinda ba zan iya yi mata ba. Ina zaune rike da kaina Ibrahim ya dawo cikin office din idonsa kamar garwashin wuta, ya fara zagaye office din da alama jinin yarabawan ne ya motsa. "She told me lokacin da Daddy ya san alakar mu ya hada ki aure da wani cousin dinki a 'yalleman, she even showed me the wedding invitation, after a year ta turomin message tace kin haihu" sosai kaina yake juyawa dan sama sama nake jin maganar sa, lokaci daya kuma naji wani realisations yayi hitting dina, Hafsat, oh dear God no, not Hafsat, i can take betrayal from Amira but not from Hafsat, na juyo na kalleshi nace "kaima ance min kayi aure, ka auri Efi" ya tsaya a zagayen da yake yi, yazo ya tsugunna a gaba na, expression din fuskarsa na kalla naji wani dadi a raina, at least Hafsat gaskiya ta fada. Yace "yes, na auri efi shekara daya bayan rabuwar mu, amma ban karbi auren ta ba sai bayan da na samu labarin kinyi aure tukunna..." Na katse shi nace "and kawai daga Amira ta gaya maka nayi aure you just believe her, ba zaka bincika ba, ask around, ba zaka kira ni ba kayi confirming daga baki na ba" na danyi shiru ina controlling temper dina, sannan na cigaba "you switched off your phone, you didn't even call me, you just left without a second look" Ya mike tsaye ya koma ya zauna akan kujerar da take kallon tawa, har yanzu bai ce komai ba, na dago kai na kalleshi muka hada ido na mayar da ido na kasa, a hankali naji yace "kin chanza sosai, you look more beautiful, more beautiful than I kept imagining you would be" a hankali nima nace "it doesn't matter, abinda nake so kawai in sani shine 'why?' Dama tun farko bada gaske kake sona ba ko kuma bayan ka tafi ne ka chanza ra'ayi?" Ya kara jawo kujerar sa kusa da tawa yace "Maimunatu kema kinsan amsarki, I love You, more than life itself. Ki tsaya ki saurari labarin abinda ya faru bayan tafiya ta, ina tabbatar miki da cewa zaki yadda cewa it hurt me more than it hurts you. I was fooled by your friend, totally fooled" na sake dago ido ina kallon rinannun idanunsa da suke kaina. Nace "OK. Ina jinka, tell me, what happened" "Bayan na bar gidan ku a ranar nan, na koma makaranta, ina zuwa na kashe wayata na ajiye saboda nasan zaki kira ni, ni kuma a lokacin gani nake yi as long as ina jin muryar ki I cannot stay away from you. I thought i was strong, na dauka zan iya zama babu ke har sai na samu abinda nake nema, har sai nasan na isa in zo in nemi auren ki. I had your number in my memory, dan haka plan dina shine duk sanda naga cewa it's OK to return sai in kira ki. Ranar sam banyi bacci ba, washegari na tashi da rashin lafiyar da har sai da aka kwantar dani a clinic din school. Sati da daya ina jinya sannan na dan samu sauki nace su sallame ni, suna sallamata na shiga office din PC na bata takarda ta ta barin aiki, bana son duk sanda na tashi dawowa neman aurenki ya zamanyo ina jingine da babanki ne. Kayan da suke gidana duk na hada na sayar na dau jakar kayana na fita daga makarantar, gidanku na fara zuwa na bada sakon CD a gurin mai gadi sannan na wuce tasha, .nadabazan iya misalta miki yadda nake jin raina ba a lokacin maimunatu, ina jin haushinki a lokacin sabida kin gaya min gaskiya da kika yi kuma ina jin wani irin sanki a raina, sannan ga alhinin rabuwa dake kuma, ji nake kamar na chire wani bari na jikina na ajiye. I was tempted to call you then, na dauko waya ta na saka sim na kunna, sai kuma na sake kashewa na cire sim din na jefa shi ta window din motar. Kafin muje ibadan zazzabi ya sake rufe ni, da muka je sai mai motar ne ya karbi number din baba a wajena ya kira ya gaya musu halin da nake ciki, nan suka zo suka dauke ni sai asibiti, na jima shima ina rashin lafiya a can, hatta mama bata san abinda yake damuna ba ballantana su Hadiza, na gaya musu na ajiye aikina na Abuja, kawai dai sun fahimci cewa it has something to do with you. Bayan na samu lafiya an sallamoni sai na yanke shawarar tafiya Lagos, da akwai wani uncle dina a can wanda kudin inheritance din mu yake hannunsa yana business dashi, mama taso ace na zauna a ibadan na nemi wani aikin amma naki, gani nake aikin government babu abinda zai kawo min. Ina zuwa lagos uncle dina ya fara koyamin harkar business, cikin 'yan watanni na koya sosai, ya dauki kudaden mu gaba daya ya bani na fara nawa daban. Duk abinda nake yi kowacce rana, kowanne hour, kowanne minute kowanne second kina cikin raina maimunatu. A lokacin na fara trying kiran number dinki da sabuwar number ta, at least duk da cewa ina ganin lokacin dawowata bai yi ba amma ina so in san ya kike, amma ga mamakina your phone was switched off, kullum na kira a kashe, bani da number din kowa kuma a gidan ku sai taki. Tun a sannan na fara zama very frustrated. A haka har shekara ta kusa ta zagayo. Ban wani tara kudin kirki ba amma bazan iya jure zama babu ke ba, a dole na fara shirin tahowa Abuja in neme ki. Kamar hadin baki, ina zuwa ibadan baba ya shigar min da maganar auren Efi, a take nace masa a'a, wannan ba karamin bata ran mama yayi ba, saboda bata taba zaton zan iya cewa da baba a'a ba, tunda ban taba ce masa a'a ba. Ta fara fada baba yace a tambaye ni uzuri na, nan na gaya masa maganar ki, na nuna masa sosai irin yadda nake sonki, shi kuma ya goya min baya yace inzo abuja muyi magana da daddy in ya amince sai inzo in fada su kuma sai suje ayi maganar manya. Washegarin da muka yi maganar dashi na taho Abuja, har a lokacin wayarki bata shiga. Nazo unguwarku naga gidan ku babu alamar movement kamar wancan zuwam nawa, bana son wulakancin securities din ku dan haka na tsallaka gidan opposite dinku na tambayi me gadin kuna nan kuwa? Sai yace min ai kun tashi daga kasar ma gaba daya, sosai hankali na ya tashi, sai a lokacin na fahimci dalilin da yasa wayarku bata shiga. Bansan a gurin wa zan samu labarinki ba ballantana contact dinki. Na tuna da kawarki Amira itama a abuja take da zama kuma nasan tabbas zan samu labarinki a gurinta. Na tafi tsohuwar makarantar ku gurin principal na roke ta ta nemo min file din Amira, a ciki na samu address din gidan su, ina zuwa gidan su na aika a kirata aka cemin ta tafi makaranta, anan na zauna nayi ta jiranta har magrib sannan ta dawo. Sosai tayi mamakin ganina a kofar gidan su, kuma tayi murna sosai. Sai yanzu na fahimci dalilin murnar ta, ta dauka gurinta naje, ni na manta ma da cewa tana da wani feelings for me, na dauka tunda na gaya mata baki da baki cewa bana sonta shikenan magana zata wuce. Bayan mun gaisa ta kawo min ruwa nasha sai na gabatar mata da abinda ya kawo ni gurinta, cewa ina neman hanyar da zan same ki ne ko kuma number dinki. Abinda tace min shine 'au baka sani ba? Na dauka ta gaya maka ai' nace mata 'me fa?' Tace 'zancen auren ta mana, ai ranar da kaje gidan su Daddy n ta ya ganka, kana tafiya ya tambayeta waye kai ta gaya masa yace babu ita babu kai, shi ba zai bawa bayarabe 'yarsa ba, data takura ta daina cin abinci ta daina yiwa kowa magana sai ya dauke ta ya kaita 'yalleman, bata fi two weeks acan ba aka hada auren ta da wani cousin dinta a can' ji nayi tamkar ta zuba min fetur a jiki na ta kyatta a shana. She is your best friend, how can I not trust her words? Besides, nasan dama ba kowanne bafulatani ne zai yadda ya bawa bayarabe auren 'yarsa ba. Ganin irin yadda hankali na ya tashi ne yasa ta fara lallashina, tace in ban yarda ba zata kawo min sample din IV daurin aurenki kafin in bar gari. Ta gaya min cewa duk 'yan gidan ku suna England yanxu ke kuma kina 'yalleman. Anan ta karbi number ta da niyyar zata kawo min IV din. Daga gidan su Amira da kyar na samu taxi ta kaini hotel na kwana, ranar nayi kukan da ban taba yin irinsa ba a rayuwata, na tausaya miki na tausayawa kaina saboda ina ganin soyayyata ce ta jawo miki aka miki auren dole aka kaiki kauye aka katse miki karatun ki, alhalin ga 'yaruwarki can a England tana karatun ta. Washegari da ciwo na tashi dan ko fitowa ban iya yi ba har Amira tazo da yamma ta kawo min IV din, naga sunan ki da sunan wani Abdulaziz a matsayin mijin. Ganin ina kokarin in mutar mata a hannu yasa ta kira mai taxi suka kaini asibiti, a take aka kwantar dani dan sosai nake neman rasa numfashina. Kwana na uka a kwance Amira tana ta dawainiya dani, ranar dana warke nayi mata godiya nace zan tafi, amma dan Allah she should at least call you and let you know cewa I came back like I promised. Ina komawa ibadan na yiwa baba karya nace na samu Daddy yace yanzu kina karatu in bari sai kin gama tukunna. Mama tana gurin ashe ta gane karya nake yi. Rashin lafiyar ce dai bata barni ba dan tunda na koma ina kwance. Ban san ya akayi mama ta bincike kayana taga IV din da Amira ta bani ba. Bata ce min komai ba har na samu sauki na koma lagos. Ashe bayan na tafi ta nuna wa baba IVn ta gaya masa cewa yarinyar da nake so anyi mata aure, kuma wannan shine sanadin duk wannan ciwowwukan da nake. Ba tare da baba ya sake bi ta kaina ba ya yanke shawarar daura min aure da efi, a cewarsa macece kadai zata saka in manta da ke. Sam babu wanda ya gaya min labarin za'a yi min aure har aka daura ban sani ba, sai da uncle dina na Lagos ya je daurin auren ya dawo sannan ya kira ni ya gaya min, ranar naga tashin hankali, na gaya masa sunyi mistake, ni bana son efi ba zan iya zaman aure da ita ba dan a matsayin kanwa na dauke ta. Ya gaya min lallai in shirya in tafi ibadan inje ayi biki in taho da amaryata. A dole na shirya amma maimakon in tafi ibadan sai na zarto Abuja, direct gidan ku naje, wannan karon na tarar gidan da alamar mutane a cikin sa, ban shiga ba wannan karon a waje na tsaya sai da wani yaron gidan ya fito sannan na tambayeshi ko kina nan? Sai ya ce min ke baki zo ba, amma sauran mutan gidan sunzo, abinda na fahimta a lokacin shine mutan gidan sunzo daga England ke kuma baki zo ba tunda kina 'yalleman. Wannan shi ya goge min duk wani sauran doubts akan auren ki. Na tafi gidan su Amira, wannan karon a gida na same ta. Na gaya mata yadda mukayi da yaron gidan ku tace min eh ke kina 'yalleman, 'yan gidan ku ma sunzo suna ne saboda haihuwar da kika yi, har ta nuna min hoton babyn a wayarta. Ta gaya min cewa kunyi magana da ke kince mata in na sake zuwa ta ce min I should move on, ke kinyi moving on nima I should do the same thing. Zancen haihuwarki ba kara min tayar min da hankali ya kuma yi ba dan ina zuwa ibadan na zube wa mama a tsakar daki, mama hannu ta dora aka tana rusa kukan ta shiga uku danta zai mutu. Babane ya saka ni a gaba da nasiha da addu'a da fada har na dan samu na saki raina. Nan aka fara shirye shiryen biki. Sosai baba da mama suka kashe kudi a bikin nan a niyyarsu ta son suga sun faranta min rai. 'Yan uwana duk sun zo daga side din babana, side din baba da kuma side din mama, kowa was there to make me happy. Bana so in nuna musu kamar wahalar banza suke ji dan haka na ware sosai tamkar na karbi auren har aka yi biki aka gama. Bayan an gama biki ne mama tace mu tafi Lagos tare da efi sai nayi mata bayanin cewa bani da gida a lagos nima a gidan uncle dina nake, amma tunda a lokacin kudi suna shigo min sosai, inna koma Lagos zan sayi gida sai inzo in dauke ta, a haka muka rabu dasu na tafi Lagos. Na sayi gidan kamar yadda nace amma fir naki dauko efi. Nace ni bana son in ci zalinta kuma ni bazan iya zaman aure da ita ba. Sai da Efi ta shekara guda da aure akan ta amma tana zaman gida. Kwata kwata ma na daina zuwa ibadan saboda kar ayi min maganar tafiya da ita. Gashi arzikina kullum karuwa yake yi. Rannan kawai akayi min waya cewa baba babu lafiya, ba shiri na tafi ibadan, kwana na daya da zuwa Allah yayi masa rasuwa. A lokacin nasan mutuwar uba tunda sanda mahaifina ya mutu bani da wayo. Bayan komai ya lafa nace zan tafi, mama ta saka ni a gaba har da kukan ta akan lallai in tafi da matata, yanzu bata da kowa, ba uwa ba uba, ga mijin da dashi da babu duk daya, duk ta lalace ta fita daga haiyacinta. Kukan da mama tayi min ne ya saka na tafi lagos da efi". Muna zuwa lagos na kaita gidan uncle dina na kama gaba na, ban kuma komawa ta kanta ba. Muna yawan yin waya da Amira, nakan kira ta inji ya kike da su Hafsat, kullum tana ce min lafiya lau kuke, tace hankalinki a kwance yake yanzu baki da wani problem. Kullum tana min maganar ya kamata in ajiye maganar ki a gefe in san me nake ciki a rayuwa amma sam na kasa. Ina waya da ita ne saboda she was the closest thing i have to you. Rana daya kawai sai ga mama tazo Lagos, nan naga bacin rai a gurinta data fahimci abinda na aikata. Efi cewa tayi ta hakura da auren, ita a raba auren kawai duk son da take yi min ta hakura. Mama kuma tace ban isa ba tunda bani na haifi kaina ba. Dole efi ta dawo gidana ta tare. Mama ma anan ta zauna tare da mu ta saka mu a gaba" yayi shiru for the first time tunda ya fara magana. Na kalleshi naga yana kallon can gefe. Ya cigaba da cewa "a duk zaman da muka yi da efi bazan iya tuna ranar da na ganta cikin farin ciki a dalili na ba, ta samu gangar jiki na, amma zuciya ta da ruhina ni kaina basa tare da ni ballantana in bata. I kept blaming iyayen mu da suka hada auren duk da cewa sun san bana sonta. Ba kowanne namiji ne zai iya rayuwar aute da matar da baya so ba. Bamu dade tare ba ta samu ciki, cikin yana girma mama ta dauko ta suka dawo ibadan ni kuma nayi zamana a lagos. A ibadan ta haihu, anan kuma Allah ya karbi ranta a gurin haihuwa. Allah yaso zamuyi sallama nazo kawo musu kayan da mama tace in siya, ina xuwa ta fara labour na kaita asibiti, tana haihuwa jini ya balle mata wanda shine sanadin ta. Inda Allah ya taimake ni na nemi gafarar ta kafin ta mutu da nasan alhakin ta bazai taba barina ba. Bayan na koma lagos naji duk zaman garin ya ishe ni, da kadan na fara sayar da business dina ina dawowa nan garin, a hankali na gina wannan gurin na sayi gida sannan na dawo garin nan da zama. Bayan dawowa ta garin nan na fahimci cewa Amira still have something for me sai na yanke alakar dake tsakanin mu saboda ban taba jin son ta a raina ba, ban taba jin son kowacce mace a raina ba bayan ke. Ina yawan bin hanyar gidan ku with hope wai ko wata rana zan ganki koda kuwa daga nesa ne. Rannan kawai naje unguwar sai naga gate din gidan a bude, kamar ana biki a gidan. Nayi packing daga dan nesa ina jin dadin maybe zan ganki. Na kira Amira a waya nace mata nazo gidanku na tarar ana biki, sai tace min bikin Hafsat akeyi. Ta fito ta same ni tace ta gaya miki nazo kince please in tafi kar mijinki ya ganni, tace kince you are happy with your life and I should leave you alone" ya sake yin shiru yana kallona, fuskarsa tana nuna irin bacin ransa. Ya cigaba da cewa "tun daga ranar ban sake zuwa gidan ku ba. Nayi concentrating akan business dina. Amira tasan ina garin nan amma bata san me nake yi ba, she had no idea nan guri nane, dan haka da kuka zo bata taba tsammanin zata ganni anan ba" Tun da ya fara maganar nake hawaye har ya kammala, ya tashi ya je gurin water despenser ya debo ruwa a cup ya dawo ya miko min na karba na shanye ina jin dadin yadda sanyin ruwan yake sanyaya zuciyata. Maimakon ya zauna a kujerar daya tashi sai ya hau kan table din gabana ya zauna, exactly yadda yake yi sanda muna makaranta. Na dago kai na kalle shi, he was grinning from ear to ear. It is like nothing has changed, but yet, everything has changed. Involuntarily na kai hannuna kan zoben Sultan na fara wasa dashi. A hankali Ibrahim yace "it is alright now, we are together now" a hankali na far girgiza kaina hawayen fuskata yana karuwa, ya saka hannu zai dago fuskata na matsa baya. Nace "married or not married, ba dai dai bane kake taba ni ba, ka sani kuma" yayi dropping hannunsa a sides dinsa, yace "bani naki labarin inji, what have you been doing all these years" a hankali na fara magana nace "I waited for you, for five years, I waited" yace "six, almost seven" nace "I met someone after five years of waiting for you" nayi shiru ina kallon yadda yanayin fuskarsa ya fara chanzawa, yace "what? Who?" Nace "it doesn't matter who" ya sauko daga kan table din ya koma wajan ruwa, this time kansa ya zuba wa yasha, sannan ya tari wani ruwan ya zuba a kansa, ya juyo yana kallona da wani yanayin da bazan iya fassarawa ba, nayi sauri na dauke kaina dan ba zan iya juran kallonsa a haka ba. Yana daga tsayen yace "do you mean to tell me that you are in love with someone else?" Na yi shiru ina jinjina kalmar love, in nace love sai inga kamar na rage darajar what I feel for Sultan, it is more than love, na gyada kaina a hankali nace "yes" da sauri ya karaso gaba na ya durkusa "maimunatu please, please don't say that, zuciya ta zata iya bugawa please" na runtse idona ina jin zafi a raina, I hate to hurt him like this amma dole in gaya masa gaskiya, nace "I loved you, but not anymore" ya mike da sauri ya fara safa da marwa a office din yana cewa "you don't mean that, dan dai bana nan ne, you still love me, i know you do, I just need you to give me a chance in dawo miki da soyayyata" ya sake dawowa gaba na "maimunatu please ki sake bani chance" na sunkuyar da kaina ina kallon zoben Sultan a raina ina ayyanawa idan da ace sultan ya san inda nake kuma yasan tare da wa nake, zai iya harbo igwa ta tarwatsa building din gaba daya, a hankali na sake magana nace "there is no time, bikina saura kwana goma" da karfi yace "what?" Na gyada masa kai, ya sake mike wa ya buga hannun sa a table din yace "NO" da dan karfi. "No Maimunatu, destiny brought us together today. Da Allah baya so mu kasance tare da ba zai kawo ki office din nan yau ba. Da in zamu hadu ma sai da auren ki tukunna. Please call off the wedding" na girgiza kaina da sauri nace masa "not possible. I can't do that. Ko da ma ace bana son wanda zan aura ai bani nake bada kaina ba, an riga an bashi ni, an gama komai, bazan taba zuwa in ce bana son auren sa ba. It doesn't work like that" ya sake tsugunna wa kamar zai dora hannayensa a kan lap dina nayi sauri naja kujera ta baya, ya dora hannayen aka, sannan ya shafo fuskarsa. Idonsa ya sauka akan zoben sultan da nake ta aikin murzawa. Ka kalle ni yace "his ring?" Na gyada masa kai, ya sake cewa "who is he?" Na sake amsa masa "it doesn't matter" kamar amsar tambayar sa sai waya ta ta fara kara, a tare muka kalleta, 'my sultan' a hankali ya furta "sultan" ban dauki wayar ba saboda bazan iya yin magana da Sultan a yanzu ba, har ta gama ringing ta katse ya sake kira, nasan halin Sultan in yaso abu, bazai daina kira na ba har sai na dauka. Na mike tsaye, Ibrahim ma ya mike yace "please don't go" na kalle shi for some seconds sai na juya zan tafi, hijab dina ne ya jawo wani frame din hoto daga kan table din ya fado kasa, na durkusa a hankali na dauki hoton ina kallo, wata yarinya ce zata yi shekara uku a duniya, naga fuskar Efi a fuskarta amma idon Ibrahim, she looks very cute a cikin English wears tana murmushin da yake bayyana cleft chin dinta just like her father's. Nace "she is very beautiful" ya zagayo ta bayana yana kallon hoton yace "yes she is, just like the Moon I named her after" da sauri na juyo na kalleshi, yace "yes, sunan ki na saka mata, maimunatu, and I call her Moon" da sauri na hadiye kukan daya taho min, her mother died giving birth to her, but he named her after me. Daya frame din da yake kan table din na dauka, numfashina ne ya tsaya chak, hoton mu ne nida Ibrahim, duk bama dariya, fuska ta kamar zanyi kuka, yana tsaye a bayan class din mu ni ma ina tsaye a kusa dashi, na dan kwantar da kaina a kafadar sa shi kuma ya juyo kadan yana kallona. I remember sanda aka dauki hoton, Hafsat ce ta dauke mu da wayar ibrahim ranar da zamu bar makaranta. We were so young then, and so much in love. Na kalle shi da sauri naga yana murmushi, it is like nothing has changed, but yet, everything has changed. Na ajjiye pic din da sauri na yi hanyar waje ina jinsa yana cewa "maimunatu please" exactly yadda yake cewa in yana ya son ya lallabani in yi masa wani abu. Da bibbiyu nake hada stairs ina sauka, idona almost a rufe na fita na doshi motar sultan da nazo da ita, na bude na shiga nayi mata key, a lokacin na hango shi ya fito daga building din yana nemana. Nayi baya na fita daga packing lot din ina ganin sa ta mirror yana kallon motar, yayi noticing sunan da aka rubuta a gurin number "Sultan 2" . Sai da nayi nisa da building din sannan na sauka daga kan titi nayi packing, na kifa kaina akan steering na kama kuka, what hurt me the most is the fact that Amira can betray me like that. Sometimes, the person you trust the most will hurt you the most. Masoyan Maimoon ina gaishe ku baki daya, nima kuma ina sonku irin sosai dinnan. Ina ganin sakonnin ku ta WhatsApp da Facebook, masu bina private da masu turo wa ta group. Ina so ku fahimci abu biyu. Na farko Moon guda daya ce ba za'a raba ta a bawa kowa ba, dan haka dole wani ya samu kuma dole wani ya rasa. Dan haka at the end dole wani zai ga kamar ba'a kyauta masa ba. Abu na biyu kuma shine, tun kafin in fara rubuta labarin Maimoon na riga na tsara yadda zai kasance, yanzu kawai details din nake filling, kada wani yaga kamar labarin ina rubuta shine yadda zan farantawa wani. Idan kuka cigaba da bin Maimoon na tabbatar muku karshrn labarin zaiyi satisfying kowa insha Allah. Duk da dai ance shi dan adam ba'a iya masa. I so much love you all [11/7, 2:38 PM] maryamsuleiman48@gmail.co: MAIMOON By Maman Maama Episode Sixty Four : The Past and the Future Na jima a haka ina kuka mai tsuma zuciya, jikina har rawa yake yi. Why is my life almost so complicated, me yasa komai ni baya zuwa min da sauki. I hate hurting Ibrahim. Ya sha wahala sosai akan soyayyata, he deserves happiness from me now, but I can't give it to him because it is not mine, it belongs to somebody else. Ina jin wayata tana ta ringing, kira na wajan goma kenan, amma ba zan iya dauka ba saboda ba zan iya magana ba. Da zuciya ta da kaina gabaki daya sun toshe kaina sam babu wani abinda yake fahimta, abinda nake tunawa shine naga Ibrahim, kuma soyayyata da na gani a idonsa ta ninka wacce na san yana yi mini a da kafin mu rabu. A hankali na fara abinda na saba yi indai ina so in saisaita tunani na, na fara kiran sunayen Allah daya bayan daya idona a runtse, a hankali nutsuwa ta fara shigomin kuka na ya fara tsayawa. Na bude ido na ina kallon titi, gari ya fara duhu dan tini anyi sallar magrib. Na fara tunani straight. So Ibrahim did came back like he promised he would. Saura kwana goma bikina, bikina da Sultan. Ibrahim har yanzu yana so na, yana sona fiye da yadda ya soni a baya. But ya dawo rayuwata a little bit too late. My heart already belongs to another. I loved him before. Nayi masa son da a lokacin nake tunanin ba zan taba yiwa wani irin sa ba. But it is all gone now. Sultan ya cike dukkanin guraben da suke a zuciyata. Ibrahim Yace Allah ya hada mu ne a yau saboda we have a future together, in haka be kuwa to ba zabi na bane kenan. Even if da akwai sauran son Ibrahim a raina to yana can kasan zuciya ta wanda tono shi sai an dauki lokaci, and time is what we don't have. Even if an tono soyayyar Ibrahim a raina ta yaya zan iya facing iyayena ince musu na fasa auren Sultan wani kuma daban nake so? Komai sanyin Daddy na tabbatar sai naga bacin ransa ballantana Mommy da inajin sai ta kaini psychiatric hospital. I can't even imaging tunkarar Sultan da maganar wai na fasa aurensa saboda wani tsohon saurayina da muka rabu kusan seven years back. Duk wanda yaje ya gaya wa sultan wannan maganar will be committing suicide. I can't even imaging my life without Sultan. Choosing Sultan over Ibrahim is not a choice, it is a necessity. Kamar yadda Ibrahim ya fada hakane, God have reasons for everything He did. Tunda Allah ya hada mu yau to da akwai wani abu daya boye a cikin haduwar tamu, ko da kuwa ba aure bane. I just hope that whatever God has planned for us zai kawo happiness a rayuwar Ibrahim sannan kuma ba zai wargaza rayuwar ta da Sultan ba. Waya ta ta cigaba da ringing, na dauka ina kallon sunan sultan har ta katse, a cikin dictionary din sultan babu wata kalma wai ita giving up, he never gave up, yanzu kiran nan da ya ke yi min zai yi ta yi ne har sai na dauka ko kuma sai charging wayar ya kare. Na duba missed calls naga 23, amma 5 daga Mommy ne, sauran kuma nashi. Na fara tunanin abinda zance musu tunda duk cikin su babu wanda zan iya gayawa gaskiyar abinda ya faru yau. Mommy na fara kira, bugu daya ta dauka tace "ina kika shiga? Sai da nace muku fa kar ku kai magrib gashi har after seven baki dawo gida ba?" A nutse nace "Mommy mun dan samu matsala ne shagon, Amira ce suka dan samu sabani da wata cashier shine abin yayi delaying din mu, kuma nabar wayata a mota shi yasa ban san kuna ta kira na haka ba" ta dan rage fadan da take yi tace "to amma ai da ko wayar ita Amiran sai ki karba ki kira ki fada mana halin da kuke ciki, ni ba sai inzo da kaina ko in turo wani yaji matsalar da aka samu ba? Na kira wancan yaron ma yace shima yana ta kiranki baki dauka ba, duk kin tayar mana da hankali wallahi" na danyi murmushi a raina nace 'I love you too Mommy' nace "gani nan zuwa yanzu, zan kai Amira gida ne kawai in taho" da sauri tace "NO, duhu yayi kuma unguwar su Amira akwai nisa. Ku tsaya a inda kuke ki kira shi sai ya kai ki ya dawo dake gida" nace "yes mother" na kashe. Ina kashewa kiran Sultan yana shigowa, sai da nayi bismillah sannan na dauka, ina dauka yace "damn it, where have you been?" Cikin sanyin murya nace "am sorry Sultan, na manta waya ta ne a cikin mota, muna cikin wani supermarket ne kuma muka samu wata 'yar matsala, duk everything is Ok yanzu na kai Amira gida zan taho gida nima" kamar sun hada baki da Mommy yace "no, ki zauna bara inzo in dauko ki, dare yayi kuma hannunki bai yi kwari ba" nace "yes sir" ya sauke ajjiyar zuciyar da har sai da naji ta ta cikin wayar yace "you almost gave me a heart attack. Gaba na yana ta faduwa, kuma ina ta kiran wayarki tana ta ringing baki dauka ba. Please don't ever do this again in ba so kike zuciya ta ta buga in mutu ba" kalmar mutun da ya fada ce ta saka ni nayi murmushi nace "kar ka zama ragon maza mana, ko three hours fa ba muyi da waya ba" yace "anything can happen ai a cikin three hours din, kin san babu abinda ban aiyana a raina ba? Har sai da na hango ki a kasan tirela" nayi dariya, yanzu shikenan date din na mu ya wargaje? Har nayi musu waya nace suyi mana reserving table " nace "am sorry, in sha Allahu I will make it up to you. Yanzu Mommy tana can tana jirana in muka tafi fada zata yi. Insha Allahu zan lallabata ta sake bari na fita sai muje" ya shagwabe murya yace "baki ga kwalliyar da nayi miki ba fa" nayi murmushi nace "really?, show me, I want to see" yace "how?" Nace "kayi snapping picture ka turo min yanzu" yayi dariya yace "no, it is kind of special, in kina so ki gani sai dai kisan yadda zaki samar mana fita da wuri. Yanzu cirewa zanyi ma in boye" mukayi sallama yace gashi nan tahowa. Na tayar da mota, I have one stop to make, gidan su Amira. A hankali nake tuki sabida hasken fitulu da yake kashe min ido, addu'ah ta Allah ya kaini lafiya kuma Allah yasa kada Sultan ya riga ni zuwa. Cikin sa'a naje na tarar bai zo ba. Na debi kayan ta data siya ta bari a motar na shiga. Mama ce kadai a palo tana cin abinci, na gaishe ta ta amsa cikin kulawa tace "ya akayi kika zo da daddaren nan bayan dazu ta dawo daga gurinki itama?" Nace "wani sako na manta bance ta taho min dashi ba, kuma gobe zan yi amfani dashi" tace "da fatan dai ba ke kadai kika taho ba" nace "a'a kawo ni akayi" tace "kin ga yanzu tsayawarki ta shiga daki amma tunda ta dawo tana kwance a palon nan, tace bata jin dadine, ki shiga tana ciki" na mike na shiga dakin. Ina bude kofa ita kuma tana shigewa toilet. Na rufe kofar na karasa bakin toilet din na zauna a kasa. A hankali na fara magana "why? Me yasa kika yi min haka? Me tasa kika kasance me son kanki da yawa? Me nayi miki da nayi deserving wannan cin amanar daga gareki?" Shiru babu amsa. Na cigaba "ban taba koda jin labarin mutum marar imani marar tausayi irin ki ba. Nayi miki soyayya ta hakika amma ke ashe duk duniya babu wanda kika tsana irina. Amira babu abinda baki sani ba na wahalar da nasha akan soyayyar Ibrahim amma ashe ko sau daya baki taba tausaya min ba, maybe ma dariya kike min a bayan idona, Amira kina kallona a kan gadon asibiti amma ashe kina da maganin ciwo na kika boye kika hanani. To ki sani, ni babu abinda zan yi miki, na barki da Allah, kuma na tabbata Allah sai ya sakamin cin amana ta da kika yi. Kuma ki sani, kanki kika yiwa. Shi wanda kike claiming kina so shi yafi kowa wahala a cikin duk abinda ya faru, shine kuma still har yanzu a cikin wahalar bani ba. Kuma ki sani, duk da Allah ya kaddaro babu aure a tsakanina da Ibrahim to kema ba zaki same shi ba, saboda Ibrahim baya sonki kuma bai taba sonki ba, kuma ba zai taba sonki ba, especially yanzu daya gano gaskiyar makircin ki, he hates you and I hate you also. Kuma ina gargadinki da kiyi hankali da dosar inda yake saboda yace in dai ya ganki sai na lahira ya fiki jin dadi. Ina fatan zaki halarci bikina nan da kwana goma, ina so kizo saboda ki gani da idonki irin farin cikin da zan kasance a ciki, ina so ki gani da idonki irin sakayyar da Allah yayi min tun a duniya kafin muje can. Ga kayanki nan da kika bari a motar mijina" na mike tsaye, ina jiyo sheshshekar kukanta a cikin toilet na fice, nayi sallama da maman su na fita. Ina fita ana sauke Sultan a taxi. Da sauri ya fito yana bani hakurin ya dade, ya karbi key muka tafi. Muna daukan hanya, ga mamaki na sai naji yace "what's wrong?" Nace masa "me ka gani?" Yace "you look and sound different, kamar akwai wani abu a ranki" na tattaro dukkan charms dina nace "Hey, I am suppose to be the psychologist ba kai ba" yayi murmushi yace "kin san ance zama da madaukin kanwa" nace "to babu abinda yake damuna, kawai dai na gaji ne, kwana biyu bana fita kuma yau mun dan yi yawo, gashi ni nake driving" yace "sorry, kuma gaki dama da son jiki ko? Wannan duk sanda aka fara bikin nan bansan ya zaki ke yi ba" nayi dariya nace "ai wadansu events din skipping zan ringa yi, na gaya muku bana son big wedding kun dage sai anyi" yace "karki damu after the wedding zaki huta sosai, I will be there to help you rest" na harareshi duk da babi haske, dariyar mugunta yake min ban ce masa komai ba, yace "ya kika yi shiru?" Nace "oho maka, kai ka sani" Muna zuwa gida yace wai shi lallai sai dai mu zauna a mota muyi ta hira ba zan shiga gida ba, ni kuwa nasan dan dai gidan da akwai baki ne yasa har yanzu Mommy bata kuma kirana ba amma tana sane da cewa ban dawo ba. Da kyar na samu da lallabashi na gudu. Ina shiga bayan na gaishe da Mommy na tafi dakin Hafsat, kawai so nake in samu in gaya wa wani abin da yake raina ko na dan ji sanyi. Ina shiga na tarar tana lallaba little khairat, tayi min alama da inyi shiru, na rufe kofar na jingina da jikin kofar ina kallon su, sai da ta kwantar da ita sannan ta juyo tana kallona da murmushi tace "rigimammiya, wai ita lallai a jikina zata yi bacci ba zata kwanta ba" sai kuma ta kura min ido tace "lafiya na ganki kamar wacce aka koro?" Direct nace mata "I saw Ibrahim today" ta dan tsorata da maganar sai kuma tayi sauri tayi getting composure dinta tace "what? A ina? I really hope baki kula shi ba ko baki tsaya kin saurare shi ba" na karaso dakin na zauna a bakin gado ina kallon fuskar khairat da take ta baccin ta peacefully, nace "na tsaya na saurare shi, ba dan komai ba sai don ina son inji dalilin da yasa yayi abinda yayi" Hafsat ta watso min kallon tuhuma tace "and? I really don't like inda maganar ki take dosa Moon" nayi murmushi nace "inda kike tunani ba nan na dosa ba, I am not going back to Ibrahim, but he will always have a special place in my heart" daga nan na bata labarin duk abinda ya faru tsakanina da Ibrahim da Amira, bata ce komai ba har na kammala, ina gamawa naga ta mike ta na kokarin saka hijab, nace "ina zaki je?" Tace "I am going to kill that conniving bitch" nayi murmushi nace "shi yace zai kasheta ke kince zaki kasheta, a cikin ku bansan waye zai yi nasara ba amma nasan cewa koma me zakuyi mata ta riga ta aikata abinda ta aikata, kuma duk hukuncin da zaku dauka akanta ba zai dawo mana da hannun agogo baya ba, the past doesn't matter, what matters is the future. Ibrahim is my past, I have a great future to look forward to, I have Sultan" Hafsat ta yarda hijab din hannunta tazo ta rungume ni, I needed the hug, nima na rungume ta inajin zuciya ta tana sanyi a hankali. Mun jima a haka sannan ta sake ni tace "now, what are you going to do?" Nace mata "I don't know. Abinda na sani shine Ibrahim yana son in dakatar da bikina in bashi chance, which I told him I can't. Ya sha wahala akaina sosai kuma har yanzu yana sona, bana son inyi abinda zai kara masa bacin rai fiye da wanda yake ciki yanzu, kuma ni ba zan iya abinda yake so in yi ba. I don't know what to do. Na tabbatar kuma tunda har yanzu yasan bani da aure to zai zo gidan nan, it is a wonder ma da bai zo ba already, ina tsoron haduwar su da Sultan, Sultan is as unstable as a person can be, kuma bai san da labarin Ibrahim ba" Hafsat ta saki baki da mamaki tace "kina nufin baki gaya wa Sultan labarin Ibrahim ba?" Na daga kafada nace "ban taba tsammanin zan kuma haduwa da Ibrahim ba, so I thought there is no need in gaya masa, there is no point in tone tonen abinda yake a binne" ta kalleni da mamaki tace "Moon when will you stop keeping secrets? Duk abinda ya faru bakiyi learning lessons dinki ba. Kin boye wa iyayen mu Ibrahim, kin boye wa Ibrahim gaskiyar su waye iyayen mu, wannan shine asalin dalilin rabuwar ku da Ibrahim. Ki kazo kika boyewa iyayen mu Sultan sannan kika boyewa sultan zancen project dinki, akazo ba'a kare ta dadi ba. Yanzu kuma you are keeping Ibrahim a secret from Sultan? Again?" Nayi shiru ina jinjina maganarta a raina, she is right, nace "I guess it has all being my fault, it is because i have always been afraid of loosing those I love" tace "gaya wa Sultan labarim Ibrahim ba zai saka Sultan ya rabu dake ba. Kin gaya masa sai yafi bata masa rai akan gaya masa" nace "amma ba kya ganin yanzu it is late? In na gaya masa zai ga kamar dan mun hadu da Ibrahim dinne , ya dauka kamar dan ina son komawa gurin Ibrahim ne ko wani abu. Baki san halin Sultan ba, he is unpredictable, kullum gani yake kamar zan iya cewa na fasa aurensa, ko ya ya samu wani hint na wani abu ban san me zai aikata ba" Hafsat ta sake shiru sannan tace "what do you want to do?" Nace "so nake inyi iya kacin kokarina inga Sultan basu hadu da Ibrahim ba har bayan daurin aure, sannan sai in gaya masa, at least by then ya san dai na zama tasa already. Shi kuma Ibrahim ina so ya fahimceni ba tare da bacin rai ba" [11/7, 2:38 PM] maryamsuleiman48@gmail.co: MAIMOON By Maman Maama Episode Sixty Five : The Visitors Ina mika ta'aziyya a madadi na da sauran fans din Maimoon zuwa ga 'yar'uwar mu Nafisa Saleh, admin ta WhatsApp group din mu na mata, a bisa rashin yayanta da tayi sanadiyyar hatsarin mota, Allah yaji kansa ya gafartamasa, Allah ya yafeasa zunuban sa da namu baki daya. Allahumma Ameen. Nine Days to the D-Day Ban tashi da wuri ba saboda ban samu isheshshen bacci ba, kuma na tashi da ciwon kai. Amina da sauran cousins din mu na 'yalleman ne suka takura min da sututu a dakina dan haka na fito kan balcony na rufe kofar daga waje na zauna akan kujera ina jin dadin fresh air din gurin. Na jawo waya na kira Sultan, yana dagawa nace "hey busy body, ya kamata ka dauki leave ka samu ka huta, kar azo ana taro ka fadi ka hada mu da aikin dauko ka" yayi dariya yace "sai kace ke? An gaya miki kowa ma rago ne irin ki?" Nace "am serious, ya kamata ka huta" yace "alright amarya, yadda duk kika ce haka za'ayi. Besides, I need my energy for what is about to come" nayi kaman ban gane inda maganar sa ta dosa ba, nace "ina Amir?" Yace "baki bani amsa ta ba ai" nace "baka da amsa. Ina Amir?" Yace "OK, one day zaki buda baki sosai ki bani amsa. Amir ya dan fita, kina neman sa ne?" Nace "No, ka gaya masa kawai Amira bata jin dadi, so ya nemi Amina su cigaba da shirye shiryen da ita" ya dan yi shiru sannan yace "me ya sameta? I thought you guys were together jiya" nace "tun jiyan dama bata jin dadi, yau ta kira ni tace ba zata samu zuwa ba" muka yi sallama na kashe wayar, I feel bad duk sanda nayi wa Sultan karya, saboda shi baya min, baya taba boye min wani abu daya shafe shi. Amma ina jin tsoron gaya masa labarin Ibrahim. A ranar da yamma mai mun gyaran jiki ta zo mukayi, bayan mun gama tace min baza ta kuma dawowa ba sai ranar Saturday, wanda ita ce ranar daurin aure da kai amarya. Ta saka a ka fito mata da duk kayana da daddy ya dinka min wanda zan tafi dasu gidan sultan, dan babu abinda aka taba a lefe na duk already an kai su can ance in naje na dinka a can. Wani katon kasko ta hada turaren wuta take turare kayan nawa dashi, tace duk wankin da zan yi musu kamshin ba zai fita ba, ita shine nata gudunmawar bikin. Nayi mata godiya sosai. Ranar Tuesday za'a fara bikin, za'a fara ne da kunshi sannan da daddare a yi bridal shower, Wednesday za'a kamu da walima, Tuesday mother's eve da dinner, friday luncheon da daddary su sultan suyi bachelor's night dinsu, Saturday 12 na rana za'a daura aure da la'asar akai amarya, da daddare kuma za'ayi bridal welcome party wanda Amir ya shirya mana. Shikenan. Eight Days to.... Gidan kam a cike yake yanzu da mutane, daga maza har mata, munir bai zo ba kuma naji dadi, dan bana son yazo ya kara min wani tension din. Mamansa dai da sisters dinsa sunzo, suna zuwa suka ishe ni da iyayin suna so suga angon, nasan abinda suke nufi, so suke suga waye ya kasa yayansu, babu bata lokaci kuwa na hada su dashi, tunda suka ganshi suka yi kus, babu wacce ta sake magana a cikin su. Da yamma na fita balcony, nan ne gurin zama na yanzu indai ina son in jini ni kadai ko in ina son muyi waya da sultan. Na dafa railer na dauko wayata ina kokarin kiran sultan kawai ina daga ido na na hango shi, duk da cewa da akwai distance a tsakanin mu kuma gari ya fara duhu amma na gane shi, yayi packing dan nesa da gidan mu kadan yana tsaye ya jingina da jikin mota ya rungume hannayensa a kirjinsa. Wata irin muguwar faduwa gaba na yayi, Allah kenan, babu yadda baya juya lamarin sa, da akwai lokacin da kullum nake tsayawa a balcony din nan ina kallon waje hoping zan ganshi amma yau gashi ina kallonsa amma maimakon inji dadi sai faduwar gaba da ji. Allah ne kadai yasan dadewarsa a gurin, Allah ne kuma kadai yasan dawa yayi magana. Nasan Sultan dai bai dawo gida ba, baya zuwa yanzu sai dare yayi sosai saboda mutane. Kamar ance ya dago ido sai ga idonsa a cikin nawa, da sauri yayi kamar me shirin tahowa ni kuma nayi sauri naja da baya yanda zai daina ganina. Saboda faduwar gaba har daci nake ji a bakina, na shiga uku, na leka a hankali naga har yanzu balcony din yake kallo. Na koma daki da sauri na shiga toilet, sai da nayi calming down sannan na kira sultan. Yace "Hello love" nace "hey kana ina ne?" Yace "naje karbo mana sauran dinkunan mune. What's up?" Nace "babu komai. Kawai da ina so inji ya kake ne" yayi dariya yace "thanks love, ko in taho ne?" Nace "I would appreciate that amma kasan gidan yanda yake yanzu, ballantana yanzu da yamma" yace "right, nima daga nan zanje wajan Daniel ne yazo gari, so sai dare zan shigo gidan, hope ba za kiyi bacci ba kafin inzo" nace "yeah, bazan yi ba sai kazo, bye" muna gama wayar na koma na leka balcony naga har yanzu Ibrahim yana tsaye. Da sauri na sauka kasa dakin Hafsat na same tana shirya kayan khairat, tace "lafiya? Waye ya koro ki?" Nace "Hafsat Ibrahim ne yazo yana waje" tace "and? Kina nufin fita zakiyi gurin sa?" Nace "no, ke nake so kije" ta yatsina fuska tace "ni? Allah ya tsari gatari da saran shuka" nace "Dan Allah Hafsat kije kiyi masa magana, make him understand abinda yake so ba zai yiwu ba" tace "in baki shawara? Ki kira David ki hada shi da shi, nayi miki alkawarin ba zaki kara ganin sa ba" na girgiza kai da sauri, Hafsat ba zata fahimci abinda nake nufi ba, babu wanda zai fahimci situation dina sai wanda ya taba shiga irinsa. Ma zauna a bakin gadon ta nace "I don't want to hurt him, I don't want to hurt Sultan. Please help me" ta dan jima tana kallona sai kuma ta dauki hijab ta saka tace "amma kin san dama can ni ba shiri muke yi da shi ba, dan haka ba lallai ne yanzu ma mu fahimci juna ba" tana fita na koma sama da sauri na kuma shiga balcony, ya baro jikin motar ya dawo dai dai opposite din gidan mu, ina kallon Hafsat ta bude gate ta fita. Yana ganin ta yayi saurin karaso wa wajanta, bana hango su sosai yanzu, sun jima suna magana sannan daga baya naga ya juya ya tafi wajan motarsa, kafin ya bude motar ya sake juyowa ya kallo balcony din sannan ya shiga ya tafi. Na dawo daki na zauna ina sauke ajjiyar Zuciya, ina jin kuma babu dadi a cikin raina, but haka Allah ya tsara mana ni da shi, we are not destined to be together. Ina nan zaune har Hafsat ta shigo, ta jefo min wani complimentary card tace "gashi nan yace a baki, he is so hot headed sai da na kusa loosing temper dina, he believes hada ku aure akayi da Sultan, yace yaji labarin dan sarkin garin nan ne, shi a ganin sa kin yarda da auren ne saboda babu shi. Yayi yayi in bashi number dinki na hana shi shine ya bani card dinsa yace in baki ki kira shi, yace in baki kira shi ba zai sake dawowa gobe" ta zauna a kusa dani tace "Moon, ki kira Sultan ki gaya masa halinda kike ciki, he will know what to do" na girgiza kaina nace "Sultan will definitely hurt Ibrahim in na gaya masa" tace "to ki fada wa David ya hana shi zuwa gidan nan" nan ma na girgiza kai "securities will treat him badly and I don't want that" ta mike a fusace tace "to hada kayan ki ki kirashi yazo ya dauke ki ku gudu tare a fasa auren" ta fice a fusace ta bugu min kofa. Kwalla ce ta taru a idona ina jin zafi a raina. Na sunkuya na dauki card din nasa, kallo daya nayi wa number din na haddace ta na jefa card din a waste bin. Ina bukatar inyi addu'ar sosai in nemi Allah's guidance. Ranar kam da daddare haka na tashi nayi ta jero adduoi akan Allah ya fitar dani daga matsalar da nake ciki, Allah ya saka wa Ibrahim dangana ya fahimci cewa ni ba matar sa bace ba. Seven days.... Na tashi zucita ta fes kamar babu abinda yake damuna. Muna ta harkikin mu da 'yammata Amir ya aiko kiran Amina zasu je su gano venue din dinner. Muna zaune sai ga kungiya guda nan ta kawayen mu na sec sch, nan fa guri ya kuma hargitse wa, muna ta hira sai ga hasiya nan ta shigo daga baya, tana zuwa tace "guess wa na gani a waje yanzu?" Tun kafin ta fada nasan waye, nan take cikina ya kada tace "uncle Ibrahim" nan da nan suka kuma rude wa "yana ina?" "Moon dama kuna da contact dashi?" "Ko sallama yazo?" Duk ban basu amsa ba, hasiya tace "yana waje wallahi, ina ganin sa na gane shi, kunga yadda ya kara kyau kuwa? Ya goge sosai ya zama dan gayu fiye da yadda kuka san shi a baya" Walida tace "ke Hasiya, kina matar aure kike kallon wani ko? To wannan maganar kamar a kunnen abban Na'im" duk muka yi dariya tacigaba da cewa "da muka gaisa ma bai gane ni ba fa, wai yasan fuskar a cikin kawayen Moon amma ya kasa tuna sunan, sai da na gaya masa tukunna ya tuna. Yace yaji labarin bikin Moon shine yazo yayi mata Allah ya sanya alkhairi amma ya rasa wanda zai aika ya kirawo ta, nace masa in na shigo sai inyi mata magana sai yace kawai ma sauri yake yanzu in bashi number dinta zai kira ta, shine na bashi" hannu biyu na dora aka nace "kin bashi number ta fa kikace?" Ta kalle ni da mamakin yadda na rude tace "eh na bashi, Murna fa zaiyi miki shikenan, kuma ba'a daura ba ballantana kice kin zama matar wani ba zaki yi waya da wani ba" a raina nace "Hasiya had killed me" na tuna dramar da mukayi da Sultan akan musbahu ballantana Ibrahim. Duk abinda muke yi Hafsat tana jin mu baya tanka ba, sai kawai naji tace "'yan 'uwa ku matso in baku wani labari" duk suka juyo suna kallonta, tacigaba "kun tuna rannan a makaranta da Ibrahim yace wata a ajin mu tana sonsa amma shi baya sonta?" Duk suka ce eh, tace "a lokacin nace muku zan fada muku wacece amma moon ta hana, to yau zan fada muku kuma har ba bonus na labarin duk abinda tayi" da sauri nace "Hafsat no, please don't do this" bata jira abinda nake cewa ba ta kwashe labarin Amira kaf ta gaya musu" ta cigaba da cewa "sai shekaran jiya sannan Allah ya toni asirinta suka hadu a supermarket, kun ga ikon Allah ko? Da Allah ya tashi kamata ita da kanta ta kai Moon har office din Ibrahim" nan take gurin ya hargitse da hayaniya, daga masu dure2n ashar sai masu Allah wadaran halin Amira, Hafsat ta cigaba da cewa "na fada muku wannan ne saboda idan da akwai wacce take da saurayi to tayi musu katanga da Amira, mai miji ma haka, dan bamu san kan wanda zata koma ba kuma" Zulaihat ce dama masifaffiyar ciki ta mike tace "waye zai je gidan su Amira ya koya mata hankali?" Nan take duk suka mike har da Hafsat, dama ita tun shekaran jiya take son zuwa na hanata, na mike na sha gabansu, "dan Allah ku bar maganar nan, na riga na samu mijina wanda yafi Ibrahim a wajena ita kuma ta rasa Ibrahim din bashi kenan ba, shima Allah ya bashi matar data fini" ture ni sukayi gefe suna kumfar baki suka fice, Hafsat ce ta tsaya tana kallona tace "at least this will teach her a lesson tasan cewa tayi ba dai dai ba, amma in dai aka barta zata ga kamar taci riba ne ai, this will serve as a lesson to her da duk masu hali irin nata" ni dai anan na durkushe a bakin kofa ina hawaye, Amira was a good friend to me, she was my best friend for about 13 years, ni in ta nine ma zan so Ibrahim ya aure ta amma nasan ba zai aure ta din ba. Maman ta kuma kawar Mommy ce, naso rigimar mu ta tsaya a tsakanin mu bana so iyaye suji. Waya ta naji tana kara na duba, number din Ibrahim na gani, na san za'a rina dama, na ajiye ban dauka ba, ya cigana da kira kusan missed calls biyar sannan ya hakura, message naji ya shigo, shima ban dauka na karantaba. Sai can bayan la'asar sannan su Hafsat suka dawo suna ta dariya "dan Allah kuyi hakuri, ku bawa Moon hakuri dan Allah" wai haka Amira take cewa, kawai hawaye naji yana taho min, nace "da Amira ta raba mu da Ibrahim da kar ta raba mu, Allah ya riga ya kaddaro ba miji na bane ba" sukace "ke ai sanyin zuciya ne dake, da ace wani zai kashe ki ki sake dawo wa duniya ya baki hakuri cewa zaki yi kin hakura" sai kuma suka koma gulmar Ibrahim, "kin san har yanzu yana waje?" Nace "oho muku ku kuka sani" Hasiya tace "ni wallahi tausayinsa nake ji, Moon yana sonki da yawa wallahi" na harare ta nace "to bara in hada su shida Sultan in aura kawai". Hafsat ta gama tsara musu yadda events din bikin zai kasance sannan suka tafi suka barmu ni da Hafsat da Hamidda. Gab da magrib sai ga Amina ta shigo, fuskarta kamar gonar auduga, tana shigowa tayi tsalle ta fada kan gadon tana birgima. Muka bita da kallo da sakakken baki, sai da ta gama haukanta sannan tace "Albishirin ku" muka ce "goro" tace "at last yau wani yayi noticing cewa ni kyakykyawa ce" tsaki muka ja a tare ni da Hafsat, Hafsat tace "Allah ya shirye ki Amina" ta tashi zaune tace "am serious fa, anan waje muka hadu dashi bayan Amir ya sauke ni, ya taho da sauri yana yi min magana wai ya dauka ke ce" ta fada tana nuna ni, guiwata naji tayi sanyi na zauna akan stool, ta cigaba "ni ban san me yasa mutane suke hada kyakykyawar mace kamar ni da something like Moon ba, ni banga wani kama da muke yi ba" nayi dariya nace "shi yasa aka kasa noticing kyan naki ake noticing nawa" Hafsat tace "uhum, me yace miki kuma" ta cigaba "cewa yayi he is a friend of Moon, yaxo yana son ganin tane, daya ganni ya dauka itace shine ta taso. Yace muna kama sosai ko ni 'yar'uwarta ce, sai nace masa ni yayarta ce, shine yace shi Hafsat kadai ya sani yayarta, nace masa aini ba'a nan na taso ba a England na taso. Ya bani number sa yace in na shigo in kira shi sai in baki. Oh my God Moon ya hadu da yawa" na mike na shige toilet na rufe kaina, a fanfon sink na tara fuskata nabar ruwan yana ta zuba. Dai da naji numfashina yana neman daukewa sannan na cire kaina na goge fuskata da towel na koma dakin, ina shiga naga ta danna wayar ta ta miko min tace gashi, na jima ina kallonta sannan na karba, tace bara taje tayi sallah ta fita. Na zauna a bakin gado na saka wayar a kunne na naji already ya dauka, nace "assalamu alaikum" sai da ya sauke ajjiyar zuciya sannan ya amsa. Nayi shiru. Yace haka.u gaisuwa?" Nace "good afternoon" yace "yauwa ko ke fa, at least dai ai nayi deserving gaisuwa daga gare ki. Please Moon why are you doing this to us? Please don't punish me like this. Ba laifi na bane ba. I was led to believe kinyi aure. Kuma ko da hakan ma sonki bai ragu daga zuciyata ba sai ma karuwa da yayi. I know u love me too. I saw it in your eyes a office dina. You just have to tell Daddy cewa wanda kike so is here, a ajiye maganar wannan Sultan of a thing din" a hankali nace "Sultan is not my parents choice, he is mine. In fact daga farko ma parent dina basa sonsa nina matsa cewa shi nake so sannan suka yarda" yayi sauri yace "saboda bana nan ne yasa kika zabe shi Maimunatu. I am back now. Mun sha wahala Maimunatu kar kiyi mana haka. Abinda Hafsat tayi ta cewa kenan wai ke kika zabe shi. Whatever you think you feel for this man, believe me it is not love." Nace "Ibrahim, please don't make this harder than it already is. I know you are hurting and believe me, bana jin dadin haka sam. Amma abinda kake nema daga gare ni is just not possible. Ko da ace Sultan ba zabi na bane ba vazan iya tunkarar iyayena at the dying minute in ce musu na fasa auren nan ba. Ballantana ni na zabe shi. Put your self in his position, ace kana da budurwa kunyi maganar aure da ita, you went through alot together, kun sha wahala kuka yi convincing iyayen ku, an gama komai hatta jere anyi sai kuma few days to daurin auren ku sai tace ta fasa auren ka, how will that feel?" Yayi shiru for some seconds sannan yace "very bad" nace "good, to believe me it will feel more than very bad to Sultan, it will destroy him completely" yace "me yasa nasa zaifi na kowa zafi?" Nace "because he is kind of special" da sauri yace "ouch, that hurts" na danyi dariya nace "sorry" ya dan jima baiyi magana ba, sannan yace "do you think you will be happy with him?" A hankali nace "yes" muryarsa very deep with emotions yace "then I will be happy for you" wasu hawaye masu zafi naji sun taru a idona. Muka sake shiru sannan yace "Can I at least see you one last time?" Na danyi jim ina tunani, nace "not now, sultan zai iya zuwa anytime" yace "OK, I understand. Nagode for at least talking to me. Good night" ya katse wayar. Na ajiye ina jin zuciyata babu dadi. Six days to.... Duk an gama shirye shirye. 'Yammata ana ta rigima da tailors din da basu gama dinkuna ba, ni kam duk kayana sun kammala kuma suna dakin Sultan, nace ya barsu a can saboda cikin gidan duk a hargitse yake kar inzo in rasa wani abun ranar da nake bukatar sa. Wajan 12 na rana aka ce inzo nayi baki a palo, na sauko na ga 'yammata su uku a zaune, already an riga an cika musu gaban su da kayan ciye ciye, ban gane ko daya daga cikin su ba amma daga ganin su kasan 'ya'yan manya ne, biyu bakake daya fara, amma jikina ya bani cewa farin mai ne. Na zauna da murmushi na ce musu "sannun ku da zuwa" kallo kawai suka bini dashi sannan suka kalli juna, sai suka sake kallona, daya daga cikin su tace "Amaryar ta mu ce?" Na sake murmushi nace "sunana maimunatu" suka sake kallon juna sannan dayar tace "eh haka muka gani a jikin IV. Ita din ce kuwa. But you are younger than we expected. An ce mana medical doctor ce" nayi dariya nace "I am a neurologist and also a psychologist. Karatu ai ba shine shekaru ba, in dai ka fara da wuri shikenan" bakaken biyu suka yi dariya, daya tace "sunana Fa'iza, wannan kuma kanwata ce Saratu. Mu kannen ki ne" ban gane ba, tace "if you know you know" sai yanzu na fahimta, kannen sultan ne, he never talk about them kamar basu yi existing ba. Na kara fadin murmushi na nace "sai yau kuka tuna dani? Nayi fushi" saratu tace "sorry big sister, ba laifin mu bane, mu bamu san ma dake ba sai kawai IV aka kawo mana, ko ince sai IV muka gani, dan mu yaya Sultan ko gayyatar mu bai yi ba, maimakon ace mune masu gayyata ma amma sai a gari muke ji" nace "to kusha kurumin ku, har sai kun gayyaci wasu ma" suka yi dariya, nace "and who do we have here?" Na nuna wacce suka zo tare, fa'iza tace "antin mu ce, umma khulsum" ban nuna komai a fuskata ba nace "sannu da zuwa aunty" da alamar tsokana, ta bata rai tace "in kika ce min aunty ai sai ki mayar dani kamar tsohuwa" muka yi dariya. Bayan sun dan motsa bakin su na tafi dasu sama dakina, har bayan azahar suna nan, tare mukayi lunch dasu, kowa sai da na nuna masa kannan Sultan. Ina lura dasu suna ta kallon gidan, ni kuwa nasan ba 'ya'yan sarki ba, ko 'ya'yan waye karya suke su kushe mana gida. Tunda suka zo suke ta yi mini tambayoyi akan sultan, wai yana dariya kuwa? Har da tambayar is he romantic, nace sosai kuwa. Around 3pm aka zo aka dauke su, na hada musu kayan kyalliya masu tsada da turaruka na basu tare da katinan kowanne event na bikin. Na koma gida nayi wanka na shirya, nayi sallar la'asar aka sake cewa nayi bako kuma, na sako hijab dina na fito ni da Amina, a tsaye muka ganshi a jikin motar sa. Yayi kwalliya kamar babu gobe. Daga ganin sa kasan hutu ya zauna masa. Ina ganin da na gane shi. Abbas ne, muka karasa muka gaishe shi ya amsa yana tsokanar mu "wacce ce yayar tawa ne a ciki?" Na nuna Amina, yace "to tunda kika nuna ta ke ce" muka yi dariya yace "ya shirye shirye?" Amina tace "Alhamdulillah' nayi kokarin a kaishi palon su ya Habeeb amma yace sauri yake, yace karar Sultan ya kawo min, wai bai saka shi a cikin harkar bikin ba kwata kwata, shida ya kamata ace shi yake organizing bikin amma sai dai yake gani ana yin abubuwa babu shi, nayi masa alkawarin zanyi wa sultan magana akan hakan. Ya sake cewa " sai magana ta gaba, ina so in shirya masa hawan angwanci a matsayin wedding gift dina amma yace baya so, ni ban taba ganin inda akayi bikin dan sarki babu hawan angwanci ba" na jinjina maganar, nasan Sultan ba zai yi ba, tunda yake babansa bai taba hawan sallah dashi ba, kuma ko a magana ban taba jin yana maganar yin hawan angwanci ba, da yana so kuwa da zai ce zaiyi. Nace masa "insha Allah zanyi masa maganar shima, amma babu guarantee zai yi, in ba zai yi ba kawai ka rabu dashi", ya daga kafada yace "it's OK, ina son kuma cards saboda friends dina" na tura Amina ta dauko masa da yawa ta kawo masa. Shima muka yi sallama ya tafi. Da daddare Sultan bai samu zuwa gida da wuri ba saboda friends dinsa na America da suka zo, yana can nema musu masauki da entertaining dinsu, dan haka bamu hadu ba sai waya mukayi. Na gaya masa bakin da nayi yau da yadda muka yi dasu duk, yace "what? Munafukan yaran nan karya suke yi, babu abinda ban basu ba, su dai kawai tsegumi suka zo yi" nayi murmushi nace "it is OK ai. Tom Abbas kuma yace ka ki sakashi a organisers" yace "Abbas ba zai iya organising komai ba, bai san ni ba bai san me nake so da wanda bana so ba, role din Amir yake so in bashi kuma bazan bashi ba" nace "but at least involve him in something, tunda ya nuna yana so karka sace masa guiwa" yace "moon baki san halin yaron nan bane ba. But whatever, zan gaya wa Amir in da akwai wani abu ya bashi. Zancen hawan angwanci kuma bazan yi ba, I already told him bazanyi ba, he is trying me" jin ya fara daukan zafi nayi shiru, sai da naji ya huce nace "tell me something nice" daga muryar sa kadai nasan ya ware yace "what's nice without you. Sai yanxu nake nadama big wedding din nan, da na sani kawai daurin aure akayi aka kaimin amaryata" nace "tukunna ma, sai jibi in an fara ido zai raina fata" yace "ohh jibi za'a fara ko? Gaskiya ya kamata gobe ki san yadda zakiyi maganar date din nan. I really want to see you wallahi" nace "insha Allah tomorrow zamu fita. Kar ka manta da kwalliyar da ka yi min alkawari, I want to see it" yace "baki da problem. Thanks , Love" Gwara in tsaya anan, tomorrow ma dora. Have a pleasant night. [11/7, 2:39 PM] maryamsuleiman48@gmail.co: MAIMOON By Maman Maama Episode Sixty Six : The Wedding So...... The long awaited episode is here. Monday Washegari tun Mommy tana dakinta kafin ta fito naje na sameta, na gaisheta ta amsa. Sai kuma nayi shiru, ta kalleni tace "akwai abinda kike so ne?" Na danyi shiru ina tsoron kar ta hanani, tace "in ba zaki yi magana ba I have so many things to do" nace "Mommy dama zamu dan fita ne in an jima da Sultan" tace "in an jima kamar yaushe kenan?" Nace "kamar bayan magrib" tace "duk tsahon ranar nan bata ishe ku ku fita ba sai da daddare?" Nayi shiru a raina ina cewa 'shikenan, baza ta barni ba' tace "kun san dai gidan nan a cike yake da 'yan sa'ido da tsegumi bana don ku jawo mana wata maganar kuma" nace "to Mommy" tace "Allah ya kaimu, kuje, amma duk inda kukaje kar ku kai karfe goma" na ji wani dadi a raina, da sauri nace "thank you mother" ta harare ni, ni dai na tashi na fita tun kafin ta chanza ra'ayi. Bayan munyi break muka tafi saloon akayi mana gyaran gashi, kusan duk 'yammatan tare muka tafi har Hafsat, acan akayi mana manicure da pedicure, bamu dawo ba sai la'asar. Tun la'asar Sultan ya kira ni yace mu hadu acan. Naji haushin me ya saka ba zaizo ya dauke ni ba. Ina yin sallar magrib nayi wanka na dauko wani bakin material dina da aka dinka min a cikin kayan fitar biki na saka, riga da skirt ne anyi masa ado da golden, na gyara fuskata da light make up, ni kaina nayi mamakin irin kyan da nayi, na dauko golden mayafi karami nayi rolling, mayafin ya sauko ya rufe kirjina, na fesa turare na fita, dakin Mommy na fara shiga na ce mata na tafi, ta kalle ni sama da kasa tace "wannan mayafin yayi karami, ki daura dankwalin kayan sai ki saka babban mayafi, nace "yes mother" na koma dakina na dauko dan kwalin ina kallonsa, ni ban iya daurin dankwali ba shi yasa da wahala kagan ni da dankwali sai dai inyi rolling mayafi. Dole na nemo Amina, nan ta sakani a gaba wai sai ta kara min kwalliya wai wacce nayi tayi kadan, ta zauna ta tsara min kwalliya sannan tayi min daurin dankwalin shima, ina kallon kaina naga kamar ba ni ba, na juyo nace mata "Amina ba'a fara bikin ba fa, wannan kalliyar ai sai mutane suyi ta kallona" tace "to zauna kar mutane su kalle ki, ke da ba'a yi miki abin arziki" nace "thank you" ta kofar baya na fita, motar Mommy na gani a farko dan haka ita na shiga. Wajan 7:30 na isa Hilton, na kira sultan a waya yace "am sorry love, ki shiga nayi mana reserving table, gani nan zuwa, ki bani five minutes" na sake jin haushi nace "yanzu ni da nake mace ni zan je in jira ka? Maimakon ace already kana jira na acan?" Ji nayi bai wani damu da bacin raina ba yace "Sorry, yanzu ba zaki gane ba sai nazo tukunna" na kashe wayar ina tsaki a raina, na shiga ciki. Ina shiga naga wata waitress tazo ta tare ni ta tayi min jagora zuwa wani table a can corner din gurin, ga mamaki na sai naga the same table ne da muka zauna ranar da muka hadu. Na zauna akan the same seat din da na zauna ina kallon bakin kofa. A take na fahimci abinda sultan yake nufi, so yake abin yayi looking exactly kamar ranar da muka hadu, nayi murmushi, wannan shine dalilin da yasa yayi insisting in taho ni kadai kuma yace in shigo in jira shi, na kalli wajan naga babu abinda ya chanza. Ina zaune kawai naga waitress ta kawo min tea ta ajiye, na sake murmushi, wato ya tuno da tean da nake sha san da ya shigo. Na dauki tea din na fara kurba ina tina ranar, ranar bridal shower din Hafsat, Munir ya takura min, kawayen mu ma sun takura min da tambayar ina Ibrahim, I was so pissed up a lokacin na fito kawai na taho nan saboda ina son inji ni ni kadai, ashe destiny ne yake kirana. Na kai cup din tea din bakina zan kurba kenan na hangoshi ya shigo, kasa shan tean nayi na ajiye cup din tare da sakin baki ina kallonsa. Dark blue wandone a jikin sa three quarter da kuma light brown body hug short sleeved shirt, rigar tayi squeezing. Exactly kayan da suke jikin sa ranar da na fara ganin sa, gashin kansa a hargitse. Ya dan tsaya a bakin kofar yana karewa gurin kallo hannunsa a cikin aljihunsa. Tsayuwar da yayi exactly yadda na zana shi a project dina, except for murmushin da yake yi. Ya juyo ya kalli side din da nake zaune. Idon mu suka hadu, bansan sanda na mike tsaye daga zaman da nake ba. A hankali ya fara tahowa inda nake tsaye fuskarsa da murmushi, yace "Assalamu Alaikum" ban iya na amsa masa ba, yace "Mind if I join?" Sai a lokacin na rufe bakina na gyada masa kai ina dariya kasa kasa, maimakon ya zauna sai ya zagayo bayana ya rike min kujerata na zauna first sannan ya zagaya ya zauna a exact kujerar da ya zauna almost two years ago. Yana kallona yace "kinyi more than kyau, bama zan iya fassara yadda kike looking ba, kawai dai kinyi kyau" nayi dariya tare da dan shagwabe fuska nace "ba kai bane kace zakayi min special kwalliya shine nima kasa ni nayi kwalliya ashe kai abinda kake planning da ban" yayi dariya yace "kar dai kice kwalliya ta bata burge ki ba, da ita fa nazo na siye zuciyar ki" nace "waye yace maka a lokacin ka sayi zuciyata?" Yace "to yaushe na saya?" Na danyi tunani sannan Nace "nima ban sani ba. Kawai dai naga ta zama taka ce, ban masan sanda aka yi ciniki ba ballantana in san sanda na sayar maka" yace "hummm, ni kuma kinsan sanda kika sayi tawa? The first moment dana dora idona a kanki nasan cewa I am hooked for life, tun daga ranar kuma har yau ke kike controlling dinta" a lokacin aka fara serving din mu abinci, muka fara ci muna hira muna dariya, it's like mu kadai ne a duniyar, babu tunanin kowa babu tunanin komai a zukatan mu sai mu kadai. Yace "gwara fa ki samu kici abinci fa sosai, dan after today ba lallai bane ki samu damar cin decent meal ba kuma sai a gidan ki" nace "that goes also for you" yace "wa? Ni akwai wani abu da zai hanani cin abinci a kuwa? Amma nasan abinda zan ke yi miki in an fara bikin nan, kullum dura zan ke zuwa ina yi miki, kar azo a gama biki kuma ki kare da zuwa asibiti a bar ni da tagumi" na harare shi bance komai ba. Mun jima muna cin abinci sannan muka gama, ko bayan da muka gama ma aka gyara table din bamu tashi ba muka cigaba da hirar mu. Yana ta bani labarin friends dinsa da suka zo. A lokacin ne yake gaya min cewa 'yan gang bang duk sunzo, hotel daya duk suka kama suka sauka. Sai naji babu dadi, ni har na manta ma da zancen su, na dan bata rai, yace "what's wrong?" Nace "I thought ka rabu dasu, me suke yi kuma a bikin ka?" Yace "It's just biki kawai, kuma we have been friends shekara da shekaru, yanzu ba zai yiwu ace bikina yazo kawai sai dai suji labari ba" nace "why not? Ni dai sam bana son su wallahi, I don't want you with them" ya jawo kujerar sa kusa dani ya langwabar da kai yace "baby, I can't just send them away, babu dadi ai. Yaushe rabona dasu ma, yanzu fa duk mun girma kowa ya kama gabansa, in ba abu irin wannan ba bama haduwa. Yanzu kuma in aka gama bikin nan ba lallai ne mu kuma haduwa ba sai bikin wani kuma" na kalleshi cikin ido nace "ba zaka je bikin kowa ba" dariya yayi yace "yes ma'am, an gama. Please ki dan saki ranki mana" nayi murmushi yace "yauwa, ko ke fa" hannun da ya rike naji ya fara shafawa a hankali yana kallona, nayi sauri na kwace hannuna naja kujera ta baya, ina kallon fuskarsa yana so yayi dariya amma ya maze nace "wato tsokanata ma kake yi ko?" Ya dan bata fuska yace "ni din? Ni na isa in tsokane ki?" Nayi kwafa nace "as if I don't know you. Na san ka fa Sultan. Babu abinda ban sani naka ba" yace "really kin sanni?" Nace "yes, like the back of my hand. Na san ka ciki da bai" devilish smile dinsa ya fara, a take na fahimci so yake ya juya min magana ta, na bata rai, bai damu ba yace "yanzu da gaske kina nufin kinsan Sultan? Baby girl I let you know only what I want you to know. There is a part of me that you don't know, there is a part of me that even I don't know. Amma kar ki samu damuwa, we will soon explore that part very soon. But I think rannan mun dan buda page daya na wannan chapter din" ya sunkuyo saitin kunne na yace a hankali "In America" ji nayi tamkar kasar gurin ta tsage in shige ciki, wato abinda Hafsat ta fada gaskiya nr bai manta ba. Ina jinsa yana dariya kasa kasa ganin yadda fuskata tayi ja saboda kunya, ba tare da na kalle shi ba na saka hannu na dauki jaka ta na mike, yayi saurin rike hannuna na kwace na yi gaba da sauri kamar zan tashi sama. Da kyar na samu na dauko key din motar saboda yadda hannu na yake karkarwa. Ina bude motar yana karaso wa gurin "am sorry Love, ki tsaya in kaiki gida dare yayi" ban ko kalli inda yake ba na shiga motar zan rufe kofar ya rike yace "please ki bari in karki gida, I promise ko magana ba zan yi miki ba" har yanzu da akwai alamar dariya a muryar sa, ya zaiyi yayi wasa da wannan maganar? Amma kuma nasan ba iya tukin dare nayi ba kuma Mommy bata san ma na daukar mata mota ba dan duk a tunanin ta tare muka fita. Na fito na zagaya na shiga seat din baya na zauna, har yanzu dariya yake ya tayar da motar muka tafi. Har muka je gida ba wanda yayi magana. Muna packing na fito, ya fito shima ya sha gabana yace "thank you for today, I really had I great time" bai samu amsa ba na zagaye shi na shige gida. Seriously ni Sultan tsoro yake bani. Tuesday Yaune kunshi da bridal shower. Tun sassafe akayi shimfidu a compound, madu kunshi suka zo, ni kam sam bacci bai ishe ni ba haka aka taso ni wai lallai ta kaina za'a fara kunshin. Jan lalle aka fara yi min, ana fara wa 'yammata suka zagaye ni aka fara wakar gada ana tafi. Hannu da kafa duk akayi min, ni kaina lallen yayi min kyau musamman saboda gyaran da fata ta tasha. Ana gamawa nace Amina ta daukar min shi a hoto ta turawa Sultan, tana ta dariya nace tayi shiru kar mutane suji. Tana tura masa ya turo min reply din kisses. A baki Hafsat ta zauna taba bani abinci ina ci har na koshi. Nan akayi ba'ki shima akan jan. Ai fa nan take na fito amarya ta sak. Tsofaffi sai guda, 'yammata sai waka. Ana gama wa dani aka koma kan sauran 'yammata. Mai kunshin ce ta dawo gurina tace "bara inyi miki wani abu as my wedding gift" nace "me fa?" Tace "wait and see" riga ta ta daga tana min wani abu a kasan kafada ta, ni dai dariya nake yi har ta gama, Amina nasa ta dauko min hoton gurin in gani, ina dubawa naga wani design tayi da bakin lalle mai kyau, a tsakiya ta rubuta S & M. Yayi kyau sosai, nayi mata godiya. Sai wajen la'asar aka gama kunshin dan har su daada dai da aka yiwa, wai suma sai sunyi gayu,lol. Ni dai ana cire min nawa na tafi daki nayi wanka na shirya cikin wata doguwar riga ta ta lace orange color, tayi bala'in yi min kyau dan kana gani na ba sai an gaya maka ba kasan nice amaryar. Dakina a cike yake da 'yammata ana ta shirye shiryen bridal Shower, su Hafsat kuwa ana waje ana making arrangements na gurin da za'a yi event din. A garden din gidan mu za'ayi, decorators already sun shirya gurin sai dan abinda ba'a rasa ba. Ana sallar magrib mai kwalliya tazo, Fauziyya tace "to ina kayan da amaryar zata saka ne wai?" Amina ta tabe baki tace "oho, sai ku tambaye ta, nima ban sani ba" na kira sultan nace ya aiko min da kayan yau, duk suka saki baki suna kallona, Hamidda tace "wai kina nufin kayan da zaki saka suna gurin angon?" Nace "yep" basu karasa mamaki ba sai da Maryam ta shigo da kayan a 'yar karamar jaka, suka buda duna kallo, doguwar riga ce fara tas, mai hannun vest, wuyanta ya shiga ciki sosai both gaba da baya, sai wani dogon siririn veil mai kamar jela irin wanda ake nannadawa a wuya ash color, takalmi da jaka ta ma duk ash ne, suna fito da kayan sai ga brazier da pant a kasa, a tare suka saka salati, ni kaina sai da nayi dariya, suka juyo suna kallona nace "wallahi ban san ya siyo da underwears ba" Hasiya tace "amma wannan angon shine number one a marasa kunyar Nigeria" Amina tace "Ai in da akwai number zero to Sultan ne" Sai da nayi sallah sannan ta fara yi min, a kawayena har da masu recording kwalliyar a video. Na saka kayana sannan muka fita ta kofar baya gurin event din, muna zuwa Hafsat ta dora min crown a kaina sannan ta rataya min tag da aka rubuta 'Bride' a jikinsa. Ni nayi shigar fari tas sauran duk mutanen da suke gurin kuma sunyi shigar baki, kowa a ganni a ranar sai ya sake kallo. An saka securities sun tare hanyar garden din babu namijin da zai shiga. Gaskiya tun a ranar nasan ina da kawaye masha Allah, dan har wadanda ban saka ran zasu zo ba sun zo. Ina jin waya ta tana ta kara a cikin jaka kuma nasan Sultan ne amma naki dauka na rabu dashi. Aka kawo min cake dina shima fari da kwalliyar baki, Hafsat ta taya ni muka yanka, akayi ta pictures daga nan kuma aka fara dancewa. Muna ta enjoying kan mu bamu san lokaci yaja ba sai da Mommy ta aiko tace ya kamata a tashi haka tunda da akwai masu nisa, sannan muka duba time muka ga after 11. Mommy ta saka drivers din gidan suka yi ta jigilar kai mutane gida. A gajiye na shiga daki na fada kan gado duk jikina yana min ciwo. Gashi banyi sallar isha ba, wanka na fara yi sannan nayo alwala na fito nayi sallah sannan nayi shirin kwanciya. Sai da na kwanta sannan na dauko waya na kira sultan, yace "wato yau wannan matar kin manta dani ko?" Nace "ni na isa? Gurin da hayaniya in ma na dauka ba zaka jini ba" yace "to kuma shine ni ko a nuna min kwalliyar ko?" Nayi dariya nace "wannan kwalliyar ta yau tafi karfin idonka, ka bari zan ajiye maka pictures, randa duk ka kai matsayin gani sai in nuna maka" yayi ajjiyar zuciya yace "I can't wait" ban bashi amsa ba nace "good night Sultan" yace "fi amanillah" Wednesday Bacci nayi sosai da safe na huta, Sultan ne ya tashe ni da waya wai lallai yana son ganina kafin ya fita, da sauri sauri muka gaisa ya fita saboda mutane. Ranar anti Zaliha tazo, na gaisheta tace "Moon an samu abinda ake so ko? To baza muyi miki baki ba, Allah ya sanya alkhairi" sum sum na tashi na fice daga dakin. Rumfar motocin gidan aka gyara aka kwashe motocin gidan, anan za'ayi kamu. Ranar shigar atamfa nayi purple mai adon pink, sosai kalar atamfar ta kara haska fata ta, plain zani ne, na daura shi akan rigar, ana gama yi min kwalliya na shiga toilet na saka shower cap na rufe gashina tsaf da ita sannan aka daura min dankwali aka saka net aka rufe fuskata. Suna ta mamakin me yasa na saka shower cap a kaina ni kuwa nasan dalili. Nani ce tazo tare da mata da yawa daga fada. Dubu dari biyu suka ajiye da akwati guda na turaruka, sannan suka feshe ni da turare, daga nan aka bude fuskar amarya aka tayi min ruwan kudi, both dangin sultan da nawa. Sai da aka kusa gamawa sannan Hajja tazo tace sam kamu bai yi ba tunda ba'a zuba min nono ba, ai ni bafulatana ce dan haka da nono za'a kama ni. Kamar yadda tayi alkawarin sai tayi min wanka da nono haka tayi min, Mommy ta kule kamar zata yi kuka ni kuwa dariya ma nake yi abina, sai yanzu kawayena suka gane amfanin shower cap din dana saka. Ana gamawa direct toilet na shiga nayi wanka da special sabulu na, babu wani sauran karni daya rage a jikina. Bayan munyi sallar magrib kuma aka shirya tafiya walima. Doguwar riga na saka yellow mai adon golden stones, na saka jaka da takalmi suma golden, ina shiryawa na kira Sultan video call na nuna masa kwalliya ta, nan fa yace shi baiga dalilin da za'ace babu maza a walima ba, ai suma suna bukatar ayi musu wa'azin yadda zasu rike matan su, nace masa ai anayi amma suma du kadai banda mata, da kyar muka rabu wai bai gaji da ganina ba. A abuja national mosque akayi walimar, anyi wa'azi sosai da nasihohi masu ratsa jiki kuma duk akan zaman aure, da kuma sirrika na rike miji bisa sunna. Naji wa'azin sosai dan jikina gaba daya dai da yayi sanyi. Muna dawowa gida na tarar Sultan yana jira na waishi lallai bai gama ganin kwaiya ta a waya ba sai ya gani a fili. A mota muka zauna ya fito mana da fura da nono mai sanyi da tsire, muna ci muna hira, ni har na manta ma bikin mu ake yi dai da amina ta kira ni tace "kinsan dai in baki yi bacci ba zaki tashi da kumburaren ido, kuma kwalliyar ki ba zata yi kyau ba" a raina nace 'oh Amina ko passion design kika karanta sai haka' Hidimar bikin nan tayi yawa, na dauka zamu gama bikin mu a yau, gobe ma karasa insha Allah Masu cewa idan Sultan ya mutu ko kuma idan Sultan bai auri moon ba zasu daina karanta Maimoon, Ku sani ni bance wani zai mutu ba kuma bance ga wanda moon zata aura ba, You are all Welcome ku daina karantawa. Ko da mutum daya ne zai cigaba da karanta Maimoon ni kuma zan cigaba da rubutashi har sai na isar da sakon da nayi niyya. Have a pleasant morning, lots of love from Maman Maama. I hope ba zakuyi missing events din gobe ba. [11/7, 2:39 PM] maryamsuleiman48@gmail.co: MAINOON By Maman Maama Episode Sixty Seven : The Wedding 2 Thursday Tunda na tashi da assuba na koma na cigaba da baccina, cikin baccin naji kida na tashi kamar a tsakiyar kaina, na dauko pillow na dora a kaina na toshe kunnena amma a banza. Na mike a fusace ina mita "wai ba mother's eve aka ce ba? A bari sai evening din mana. Ni wallahi bacci bai ishe ni ba" Amina da ta fito daga wanka tana shiryawa tace "to ke da wa ya aike ki ki zauna hira da Sultan har karfe dayan dare? Dama ta yaya bacci zai ishe ki? Ai kawai hakura zaki yi ki tashi haka" na mike ina tsaki, na leka ta window na ga DJ ne ya baje kayan kidan sa a dai dai gaban tagar dakina. Na kara wani tsakin ina duba agogo, 11:30, kamar zan yi kuka nace "fi sabilillahi karfe goma sha daya za'a dasa min kida aka? Ni dai kam an shiga hakkina" Hafsat ta shigo cikin kwalliya tana kallona tace "wai yanxu kika tashi? Har Mommy tana cewa a kira ki ku gaisa da mutane?" Na kara bata rai na shige toilet. Ruwa na hada a tub na cire kayana na shiga na mayar da idona na rufe, take wani baccin ya sake dauke ni. Knocking kofar da akayi shiya farkar dani, ni ban ma san nayi baccin ba, muryar Mommy naji tana fada "uwar me kike yi a toilet din nan da har yanzu baki fito ba kin bar mutane suna ta jiranki?" Da sauri na tashi na kammala wankan ina mita a raina 'duk Sultan ne ya jawo min wallahi'. Ina fitowa na tarar mai kyalliyata tazo dan haka mai kawai na shafa na zauna muka fara, Hafsat ta shigo ta zauna tana feeding Khairat sai ga Mommy ta shigo itama, ta zauna akan bed side tana kallona tace "me ya hada ku da Amira?" Gaba nane ya fadi duk da dama nasan wannan tambayar tana nan zuwa, nayi shiru bance komai ba, ta sake cewa "fada kukayi ko?" Hafsat ce ta bata amsa tace "eh Mommy, fada suka yi" Mommy ta danyi shiru sannan tace "akan me?" Nan Hafsat ta zauna ta bawa Mommy labarin duk abinda ya faru, har ta gama Mommy bata ce komai ba. Sai da ta gama sannan Mommy tace "Maimoon3. Sau nawa na kira ki?" Murya can kasa nace "sai uku" tace "you are not to see that man again. Kinji ni ko baki ji ni ba?" Nace "Naji" ta kuma cewa "I am very serious in na sake jin maganar sa sai nayi mugun saba miki. Yanzu ace few days to daurin auren ki har kuma kina fada da best friend dinki a kan wani saurayi daban?" Nace "Mommy ni ba akan Ibrahim bane ba, akan tayi betraying dina ne, kuma ni ban hana ta zuwa gurin bikin nan ba, ita taga dama ta ki zuwa" Mommy tace "whatever, ni dai nace bana son sake jin maganar nan. Ok?" Nace "yes mother" tace "ita kuma Amira zata zo ta same ni ne, haka kawai akan wani saurayin da ko damuwa bai yi da ita ba zata watsar da rayuwarta kuma ta yi loosing best friend dinta" ta dauko wayarta tayi dialing ta fara magana "Hajiya salamatu lafiya kuwa? Jiya anyi kamu babu ke babu Amira yau ma kuma gashi har yanzu baku zo ba?" Ta danyi shiru tace "kani kuma? Me ya faru? Aa gaskiya ku dawo, please ko jirgi ku shigo ni zan biya ko baku samu mother's eve din ba ku sami dinner. Ok na gode sai kun zo din" ta kashe wayar ta fita. Da yamma akayi mother's eve, ranar naga gatan iyaye da 'yan'uwa, gidan taf ya cika da mutane kuma wai kowa saboda ni yazo, su fa'iza ma sunzo tare dasu akayi komai. Har magrib sannan aka watse. Sallah kawai mukayi kuma muka fara shirin tafiya dinner. Na aika aka karbo min kayan dinner a gurin Sultan naxo na sake wanka na dan kwanta na huta zuwa isha sannan na tashi nayi sallar isha aka fara shiryani. Yadi ne cotton cream color doguwar riga data kamani daga sama sannan ta bude sosai daga kasa, daga baya kuma tana jan kasa sosai kuma anyi mata adon stones masu kyalli, ta gaba kuma anyi mata aiki kalar golden brown. Head dina, jaka ta da takalmina duk golden brown ne da adon stones cream. An gyara min gashina ya sauko har saman bayana an jera masa stones cream color sannan aka tubke shi da golden brown ribbon. Ni kaina dana kalli kaina a madubi sai da nayi mamakin irin kyan da nayi, a zuciyata nayi tasbihi ina godewa Allah. Around 8:00pm muka isa hall din taron, already kowa ya shiga ya zauna amarya da ango ake jira. Sultan da tawagarsa ne suka fara shiga, aka saka musu kidan su aka gama cheering, sannan akace mu shigo, na juya na kalli tawagar kawayena duk sun saka ankon su na jan lace da yellow head, ga Hafsat a kusa dani ita kuma da yellow kace da jan head a matsayinta na maid of honour. A hankali muka fara tafiya, flower girls dina na gabana su biyar da fararen kayansu suna tafiya suna watsa flowers, sai ni da Hafsat na rikr hannunta kamar zan balla shi, sai kuma sauran kawayen mu a baya. An saka mana namu kidan da ban na musamman, muna shiga kowa a gurin ya mike tsaye muka fara tafiya akan red carpet din da aka shimfida mana direct zuwa high table. Straight idona ya shiga cikin nasa, a hankali na saki hannun Hafsat dana rike. Irin yadin jikina shine a jikin sa shima amma nashi color golden brown ne da aikin cream, wato kayansa kalar aikin kayana ne kayana kuma kalar aikin nasa. Yayi kyau sosai, for the first time ya gyara gashinsa ya kwantar dashi baya ya dora hularsa da tasha adon stones. Murmushin fuskarsa from ear to ear. Nima murmushin na mayar masa. Sultan bai iya jira mun karaso gurin sa ba ya sauko daga stage din ya taho gurin mu, nan take gurin ya dauki ihu da tafi, yazo ya miko min hannunsa na kama muka karasa high table tare. Sai da muka zauna sannan kowa ya zauna. Aka fara gabatar da addu'ar sannan aka fara programs. Anyi abubuwa da yawa, jokes, speeches da sauran su. Amina da Amir ne suka ce suna da surprise for us, nan suka fara displaying pictures din mu ni da sultan tun muna yara, Sultan dan lukuti abin dariya, har da picture dina da Pampers fuskata duk chocolate, aka cigaba da nuno mu muna girma har zuwa yanzu, akayi ta saka pictures din mu tare, da wadanda muka yi a America da na England da na nan. Abin yayi kyau sosai. Sultan yayi introducing dina to most if his friends da suka zo gurin including the gang bang, ina ganin su na ga basu yi min ba sam amma da dake nayi musu murmushi muka gaisa suka tsokane ni suka wuce. MC ne yace zamuyi playing game wanda zai nuna how much do we know each other. Handkerchiefs aka saka aka rufe mana idanun mu, sannan aka chire mana takalman mu, aka bani daya nawa daya nasa a kowanne hannu, shima aka bashi. Daga nan mc ya fara yi mana tambayoyi yace min in amsar Sultan ne sai in daga takalmin sultan in kuma Moon ne sai in daga takalmina. Ya fada wa Sultan ma the same thing. Daga nan ya fara jero mana tambayoyi kamar; waye yafi fara'a a cikin ku? Na daga takalmina, waye yafi tsafta? Na daga takalmin Sultan, who is the smartest? Na daga takalmina, who is the best cook? Na daga takalmin sultan, who love food the most, nan ma sultan na daga. Haka yayi ta mana tambayoyi ni dai ina amsawa amma bansan amsar da sultan yake bayarwa ba tunda idona a rufe yake. Ga mamaki na duk amsar dana bayar sai inji hall din ya dau ihu da tafi, anan na fahimci cewa the same answer muke bayarwa ni da sultan, it is like mind din mu tana working a tare, har mc ya gama tambayoyin daya rubuta ya koma karawa up head amma ba muyi missing ko answer daya ba. Gaba dayan mu dariya muke yi, we know our selves so much we are like two bodies with one soul. Finally, MC yace final questions, a cikin mu waye yafi son wani the most? Gaba daya gurin yayi shiru ana jiran amsar mu, muma kuma mukayi shiru din, sai daga baya a tare muka daga hannu, ni na daga takalmina ina nufin son da nake wa sultan yafi wanda yake min shi kuma ya daga nasa yana nufin son da yake min yafi wanda nake masa. Lol. Ai kuwa gaba daya hall din ya hargitse. MCn ma kasa magana yayi, sai daga baya yace "this means that the love is equal" daga baya aka bude mana idon mu. Bayan an nutsu aka kawo mana cake muka yanka. Akayi hotuna da family da friends Sai kuma aka ci abinci aka rufe taro da adduah. Friday A gajiye nake likis dan har saida nasha paracetamol sannan na danji dai dai, luncheon din da akayi is very brief and not as grand as dinner din jiya. Muna gurin luncheon din ne Amira tazo, ta zo guri na tace "hi" nima nace mata "hi" tace "kinyi kyau" nace "thank you" ina lura da sultan yana kallon mu ganin irin yadda muke magana casually amma bai ce komai ba, ta sauka ta tafi can wata corner ta zauna ita kadai saboda ba zata iya shiga cikin kawayen mu ba. Babu kyau baccin bayan la'asar amma ranar sai da nayi, muna zuwa gida nayi sallah kawai na kwanta na rufe kofa nace kar wanda ya tashe ni, ban farka ba sai ana kiran magrib sannan na tashi na bude kofa nayi sallah na kira sultan muka dan taba hira sannan na sauka kasa. Ji nake yi duk jikina babu dadi saboda ina tunanin yau ce rana ta ta karshe a gidan mu, duk sanda zanzo sai dai inzo a matsayin bakuwa. A kasa muka zauna gaba dayan mu tun daga kan daddy har faruk, suma kamar masu yi min farewell, anan mukayi dinner tare suna ta tsokana ta, sai da suka ga na fara musu kuka sannan suka rabu dani. Daddy da Mommy suka tashi suka tafi suka bar mu. Muna ta hira har sallar isha, su yaya walid suka fita mosque suka dawo, can nace musu "wai ku ba za kuje bachelor's night din bane" yaya Habeeb yace "Allah ya kiyaye. Wannan night din ai yafi karfin mu" ban gane me yake nufi ba nace "saboda me?" Ya walid yace "kin san menene bachelor's night ma kuwa?" Nace "I thought kawai it is just a funny guys' thing. Just to have fun" yace "exactly" nace "to menene laifi? Don't you want to have fun?" Yace "ya danganta da irin fun din da za ai having" nayi shiru ina kallonsa yace "look parrot, wadanda suka shirya wa Sultan bachelor's night dinsa are not my kind of people, dan haka yana yi min magana nace ba zamu je ba" Ban sake cewa komai ba nayi shiru ina tunani, su waye suka shirya masa? Take na samu amsata, the gang bang. Lokaci daya naji hankali na ya tashi. Tun da na dawo daga Niger ban kuma ganin sultan a buge ba, kuma bana jin ko a bayan idona yana sha duk da bamu taba maganar ba. Har karfe goma ina zaune a palon amma sam hankali na baya tare dani. Only God knows a ina sultan yake kuma me yake yi. Na tashi nayi musu sallama na tafi daki, na kira wayar sultan tana ta ringing babu answer. Ko da ace Sultan ya daina shan giya amma temptation fa? Musamman idan ya ga ana sha, ballantana nasan zasu iya bashi su ce sai yasha. A automatic redial na saka wayar na kuma saka ta a speaker na kwanta, kiran yana ta shiga har wajan 30minutes bai dauka ba, ina cikin haka Amina ta shigo, ta kalleni tace "ba dai Sultan kike kira ba? Ke ma kinsan kina bata lokacin ki da battery din wayarki ne a banza amma ba dauka zai yi ba" ina kallonta ta gama shirin kwanciya ta hawo kan gado ta kwanta, nace "Amina, what do you think maza sunayi a bachelor's night?" Tace "hmm, a England an taba bikin wani dan ajin mu, mazan suka shirya masa bachelor's night, washegari very few ne suka zo makaranta, saboda sauran all got drunk the other night ba zasu iya zuwa ba. Na tambayi wani a cikin su,why?, sai yace ai suna celebrating last day of freedom din su ne, in suka yi aure kamar they are bond to their wives babu sauran sakewa suyi abinda suke so. So duk abinda namiji yafi enjoying shi zai yi a daren, in mashayi ne in manemin mata ne sai yayi kayan sa one last time" tayi sauri tace "amma fa ba ina cewa abinda sultan yake yi kenan yanzu ba, it depends on mutun. Ke kinsan Sultan kinsan me zaiyi kinsan kuma menene ba zai yi ba" bance mata komai ba amma zuciyata in ban da zafi babu abinda take yi, har yanzu kira nake kuma har yanzu bai dauka ba. Ba'a jima ba Amina tayi baccinta ta barni, har na fitar da ran zai dauka kawai naji ya dauka, gurin da yake hayaniya ne kawai da kida yake tashi a gurin, yace "Hello, love, bakiyi bacci ba" nace "sultan where are you?" Yace "muna gidan Solomon, wani abu ne?" A hankali nace "Sultan I want you to come back home" yace "why? The party hasn't even started yet" ina jin wani a gurin yana cewa "chafdi, Sultan wannan amaryar taka in aka gama bikin nan ko kofar gida ba zata ke barin ka kana fitowa ba" duk suka kwashe da dariya, Sultan ya dan matsa daga gurin su yace "why?" Nace "ni kawai bana sonka da mutanen nan wallahi" yace "Moon, this is my party, saboda ni suka shirya shi. I can't just leave" naji wani abu ya tsaya min a makogwaro na. Kafin in san me zance masa wani a cikin su ya karbe wayar yace "look amarya, we are going to get your ango drunk today, he is even lucky he don't do women, amma shima in kika sake kiransa we will make him do it even if we have to tied him to the bed" Sultan ya warce yawar yana ce masa "fuck you" da sauri yace min "Moon" ban jira abinda zai kuma cewa ba na kashe wayata. Kafin in ajiye ta ya kira, ban dauka ba, ya sake kira na kuma share shi. Zafi nake ji sosai a raina. Sai da yayi five missed calls sannan ua hakura. Na runtse idona ina addu'ar Allah yasa in iya bacci amma sam babu bacci a idona. Ina tsakiyar tunani na naji wayata ta cigaba da kara, nayi niyyar in sake rabuwa dashi amma na daure na dauka, bance komai ba yace "kinyi fushi ko?" Naji inda yake babu hayaniya, amma duk da haka bance masa komai ba, ya sake cewa "gani a balcony dinki, ki bude min kofa" Let's stop here for today. I hope duk wacce take karanta littafin nan zata so saurayinta/mijinta kamar yadda Moon take son Sultan, duk wanda yake karantawa kuma shima zaiso budurwarsa/matarsa kamar yadda Sultan yake son Moon. Remembered, Love is the strongest magic of all. Stay loved. [11/7, 2:39 PM] maryamsuleiman48@gmail.co: MAIMOON By Maman Maama Episode Sixty Eight : The Wedding Night Na kashe wayar na mike da sauri na zura dogon hijab dina na bude kofar balcony. Yana tsaye ya jingina a jikin railer yana murmushi. Wandon jeans ne a jikin sa army green da farar singlet yayi stocking dinta a cikin wandon ya daure da belt, sai light green din top wadda ya balle duk maballayenta ya barta a bude, iskar da ake kadawa a gurin tana ta diban rigar tasa kamar zata chire ta. Na dan bata rai nace "Sultan me kake yi anan cikin daren nan" shima bata ran yayi yace "to tunda kin hanani zama acan ba sai in taho nan ba. Ni nasan kona kwanta yau ba zan iya bacci ba, ba gwara in taho nan ki tayani hira ba" naji dadi har raina dana fahimci ya bar gurin partyn saboda nace bana so, nasan it was a hard decision but a good one. Na jawo kofar na rufe saboda tinawa da nayi cewa Amina tana cikin dakin, na karaso inda yake na jingina da railer nima ina kallon kasa nace "thank you" yayi ajjiyar zuciya yace "I will never do any of those things da Daniel yake fada" nayi shiri ban ce komai ba, ya danyi dariya yace "they will kill me in suka kamani gobe da safe, dan duk cikin su babu wanda yasan na fito, sai daga baya zasu lura bana nan" ya dauko wayarsa a aljihu yayi switching off ya mayar aljihun sa. Ya kalleni ya fara murmushin muginta yace "but there is a price for everything, tunda kika hana ni kwana a gurin party na to yau a dakinki zan kwana" nima murmushin muguntar na mayar masa nace "bismillah, ina nuna kofa" babu musu yaje ya bude kofar, sai yayi sauri ya rufe ya dawo da baya, dariya nayi sosai nace "ka shiga mana, wallahi in ta fara ihu sai duk mutanen gidan nan sun tashi daga bacci" ya dan jima yana tunani sai kuma ya sake bude kofar, ina hango yadda Amina ta kudundune a cikin bargo tana baccinta, hannu ya saka ta bayan kofar ya zare key din jiki sannan ya mayar da kofar ya rufe yayi locking ta waje ya saka key din a aljihunsa yace "then we will sleep here" da mamaki nace "you are not serious are you?" Yace "sa ido kiyi kallo" daga haka ya tafi ya kwanta rigingine a kan carpet din da yake gurin. Tsayawa kawai nayi ina kallonshi naga yayi pillow da hannunshi ya rufe ido, gaba daya rigar ta bar jikinsa sai singlet din kawai. Nayi sauri na dauke kaina na daina kallonsa na koma ina analysing situation din, nayi tsaki a raina ina cewa 'Sultan, wannan fa shine baccina na karshe kafin aure a gidan mu amma ba zaka barni in kwanta a gado na ba'. A kwai security light sosai a compound din gidan amma duk waje suke haskawa, wannan ne ya kara wa balcony din duhu, ma'a na babu wanda zai hango mu daga waje amma mu zamu ke ganin su. Amma Amina da take daki zata iya farkawa kowanne lokaci taga bana nan. Already jikina ciwo yake min saboda gajiya amma kuma ace zan kwana akan carpet. Amma kuma gwara haka da ace Sultan ya kwana a gurin wadannan mutanen. Sai dai ni ban yarda inje kawai in kwanta a kusa da Sultan ba. Na zauna akan kujerar da take gurin na kudunduna a cikin hijab dina, kadan kadan nake kallon sultan har daga baya bacci ya dauke ni. Cikin bacci naji ana shafa lips dina, a hankali na bude idona da suka yi min nauyi saboda bacci, fuskar Sultan na gani dab da tawa yana kallon fuskata. A hankali tunani na ya fara dawowa, nayi sauri na mike zaune amma maimakon in ganni a kan kujerar dana kwanta sai na ganni a kasa a kan carpet nayi pillow da damtsen hannun Sultan. Na juya na kalli sultan naga ya chire rigarsa complete yayi pillow da ita sai singlet dinsa kawai. Nayi sauri na kalli nawa jikin naga hijab dina yana nan amma duk da haka ban yarda ba sai da nayi ta taba jikina wai ko zanji wani chanji. Duk abinda nake sultan kallona kawai yake yi yana dariya, sai da ya gama dariyar sa sannan yace "Don't worry yau ne ba gobe ba. And when I touch you ko tashi zaune ba zaki iya ba" na bata rai nace "wa yace ka dauko ni daga inda na kwanta? Ka hana ni kwanciya akan gado na kuma kan kujerar ma sai da ka raba ni da ita" ba tare dana jira amsar saba na mike tsaye ina kallon waje, I don't know the time but nasan assuba ta kusa, ya mike shima yana zuwa rigarsa ya karaso kusa dani yace "zanje in shirya, karfe shida zamu bar nan saboda muje akan lokaci" ban bashi amsa ba ya kara matsowa kusa dani yace "are you scared?" A hankali nace "yes" yace "me too. I am scared I might fail you as a husband. Na sani kamar yadda mutane suke ta fada min koda yaushe cewa I don't deserve you. Ni kaina bansan dalilin da yasa Allah ya bani ke ba, kin fi karfi na nesa ba kusa ba. Amma abinda na sani without doubt shine ke alkhairi ce a gare ni" ya riko fuskata da hannayensa yana kallon cikin idona yace "I promise you like I always did, I will never let you down. Abinda nake bukata daga gareki shine ki kara hakuri dani. I promise you you will never regret marrying me" na lunshe idona ina jin dadin maganganunsa sannan a hankali na bude ina kallonsa nace "kar kake cewa bakayi deserving dina ba sultan, you deserve more than me. Dan haka ni ya kamata inji tsoron kar inyi failing dinka, kar in gaza baka farin cikin da kayi deserving. And I promise you, I will never regret marrying you". Expression din fuskar sa is very clouded, irin yanayin da bana iya karantar sa, ya jawo ni da sauri ya rungume a jikinsa, ban hana shi ba, ya jima sannan ya sake ni ya kamo sannuna ya saka min key din kofar sannan ya haura railer ya juyo yana kallona yace "see you on the other side wife" daga nan ya dirga kasa. Ina kallonsa ya yi hanyar part dinsu da sauri. Na jima a tsaye a gurin ina kallon hanyar da yabi sannan na juya na shiga daki. Direct toilet na shiga nayo alwala nazo na fara sallali ina rokon Allah alkhairan da suke cikin auren nan da kuma tsari daga sharrukan da suke cikinsa, ban jima ba aka fara assalatu, na tashi na kawo raka'atainil fajri sannan na dora da subh. Ina idar wa Mommy ta shigo tace min "kizo inji Daddy n ku" na mike na bita a baya har part din Daddy, ina shiga na tarar dashi a zaune yana shan coffee, ya shirya tsaf daga dukkan alamu daga nan sai gurin daurin aure. Ba zauna a kasa na gaishe shi ya amsa mun fuskar sa a sake. Sai da ya gama shan coffee dinsa sannan ya fara min magana "maimunatu yau Allah yayi insha Allah nan da 'yan awanni zamu daura miki aure da Sultan wanda ke kika zabe shi da kanki mu kuma muka goya miki baya har Allah ya tabbatar mana da abin. To so far dai babu abinda zance sai Alhamdulillah. Na amince zan aura miki Sultan ne saboda abu biyu, na farko ina kwadayin ladan da zamu samu daga ni har ke in har burin mu ya cika na gyara rayuwarsa, abu na biyu kuma saboda tsananin sonki da naga yana yi, nasan wannan soyayyar zata iya saka shi yayi komai, wanda nake saka ran soyayyar ki zata iya saka shi ya chanza rayuwarsa. Auren Sultan da zakiyi tamkar jahadi ne. Duk abinda nayi a rayuwar sultan tamkar sharar fage ne akan wanda ke zaki cigaba dayi bayan auren ku. Sai kin dage sosai maimunatu. Nasan ke yarinya ce mai ibada amma ina so ki kara akan wacce kike yi da, ki dage da adduoi na neman tsari sannan ki tsarkake zuciyar ki daga dukkan sharri. In sha Allahu Allah yana tare da ke kuma bazai barki ki tabe ba. Ina son ki sani cewa dani da Mommy n ki muna tare dake 100% amma hakan ba yana nufin muna so mu san duk wani sabani daya shiga tsakanin ki da mijinki bane, duk abinda ya faru tsakanin ku mun fi son ya kasance ya tsaya a tsakanin ku, sai dai in har kinga yafi karfin ku sannan sai ki kawo mana shi mu kuma zamu yi iyakacin kokarin mu muga an samu maslaha a lamarin. Allah yayi miki albarka Allah, Allah ya baku zaman lafiya dake da mijinki" Mommy tace "Ameen" ya tashi yace "nina tafi" sai da suka fita shida Mommy sannan na lura cewa kuka nake yi ashe, ba goge hawayen idona ina jin alamar jikina yana daukan zafi kamar mai shirin fara zazzabi. Ina nan zaune har Mommy ta dawo daga rakiyar Daddy ta zauna kusa dani ta kamo hannayena tace "kuka kuma maimoon? Wa yace miki yanzu 'yammata suna kukan aure?" Nayi mamakin yadda Mommy take min magana a hankali cikin rarrashi babu fada, nan ta shiga yimin tata nasihar da kuma bani shawarwari akan harkar auratayya, na koma na kwanta akan cinyarta ina sauraronta kuma ina daukan duk abinda take gaya min. Muna a haka Hafsat ta shigo da khairat a hannunta suka hadu ita da Mommy suke ta kwantar min da hankali, Hafsat tana tsokanata da cewa "ke da zaki zauna ma a kusa da gida? Ko ihu kikayi da karfi Mommy zata jiyo ki" na dan yi murmushi kadan. Wayar Mommy tayi kara aka sanar mata mai gyaran jikina tazo, muka sauka kasa mukayi breakfast first sannan aka fara yimin kitso, dama na gaya mata ina son tayi min kitso shi yasa ma tazo da wuri. Kanana kitso ne irin na bare bari akayi min da kitson gaba da matar tayi masa wata tubka wacce ta rufe rabin ido na na hagu. Kowa yaga kitson nan sai sambarka. Bamu gama ba sai wajan sha daya da rabi. Ni dai duk hankali na baya kan wanda suke tare dani kallon agogo kawai nake yi gaba na yana faduwa, har daci nake ji a bakina. Ana gama yi mun kitson na sulale na gudu na tafi dakin daada, duk babu kowa a ciki dan duk suna part din mu, na shige cikin bedroom dinta na kwanta ina jin temperature dina tana kara hawa. 12:00 nayi na runtse ido na ina karanto duk adduoin da aka koya min a islamiyya. Around 12:30 na jiyo guda cikin gidan mu, gaba daya an dauki hayaniya. Nan take hawaye ya balle min. Kuka nake yi sosai amma ni kaina bansan dalilin kukan nawa ba. Shin na murnar na zama matar Sultan ne ko kuma na menene oho. Nasan ana can ana nemana a cikin gida dan ko waya ta ban taho da ita ba dan kar a kira ni. Suwaiba, wata 'yar uwar mu daga Niger ce ta shigo dakin ta ganni around 1:00 da sauri ta fita ina jinta tana bada sanarwar ai gani can a dakin daada. Kan kace kwabo dakin ya cika, tsofaffi da 'yammata sai tsokana ta suke wai azo aga amaryar zamani amma tana kuka, ni kam kamar kara zugani suke yi dan kuka na kawai nake yi bana sauraren su. Umma ce, babar Amina tazo ta fito dani tace su daina tsokana ta, ta shiga dani har dakina itama ta sakani a gaba da nasiha, Amina har da yimin video wai sai ta nuna wa Sultan dan yasan cewa ashe duk I love you din na karya ne bai kai zuci ba. Ina daukan waya ta naga 13 missed calls daga sultan, a raina nace "wasa ma kenan, kai da kaji muryata kuma ai sai dai acan" . Sallah kadai na samu nayi dan abinci ma kasa saka shi nayi a bakina, aunty zaliha ce ta saka ni a gaba da kyar na iya cin loma biyar nace na koshi. Mommy ta shigo ta kawo min magani na tace in sha, na karba ba musu na shanye. Idon Mommy kawai na kalla nasan itama kukan ta gama. Ina jin Hafsat tana kiran mutane su zo su ga hoton ango a waya, suna ta yaba kyan da yayi amma ni kam na kasa kalla. Daga baya naji suna waya da Hafsat tana gaya masa wai gani nan ina ta kuka, ta miko min naki karba sai ta saka shi a hands free "kiyi hakuri amaryata ki daina kuka, gani nan akan hanya, ina shigowa abuja zan zo in rarrasheki da kaina. Kuma duk wanda ya tsokane ki ki rubuta min sunan sa ni kadai nasan abinda zanyi masa" daga jin yadda yake maganar kasan shima dariyar yake yi, na karbe wayar na kashe, ni banga abin dariya ba dan ina kuka anyi min aure. Mai gyaran jiki na ta hada min ruwa tace inje in shiga, na shiga na kwanta ina lissafin shikenan fa, yau na taka wani stage na daban a rayuwaya, yau wani nauyi babba ya hau kaina, shi kenan na zama matar aure. Bayan an gama yi min wankan na shafe jikina da wannan man da ta bani na musamman, ta hada min turaren da nake tsugunnawa akai shima nayi. Muma gama wa da mai gyaran jiki mai kyalliya tazo muka fara, na gaya mata yau bana son heavy make up light zatayi min dan haka ba mu dade ba ta gama min. Yau shadda na saka fara tas da bakin aiki a jiki, komai da na saka fari ne. Irin shigar da Sultan yayi kenan ta daurin aure. Da dankwalin shaddar aka yi min gwaggwaro. Mommy ta shigo da wani dan karamin box a hannunta ta fito da complete set din sarkar gold, da kanta ta saka min, nan na kara fitowa tar dani. Ina yin sallar la'asar aka saka farin mayafina aka rufe ni ruf har fuska aka saukar dani kasa zuwa dakin Hafsat, karfe biyar 'yan daukan amarya suka zo, ai ina jin zuwansu na kankame Mommy na fara sabon kuka, itama biye min tayi muka yi ta rusa kukan mu, sai da wata kanwar daada tazo sannan ta kama yi wa Mommy fada. Yaya ce da kanta tazo dauka na, inna ce ta bayar dani ta danka hannuna a hannun yaya, ni dai idona a rufe, ji nayi an lullube ni da wani abu mai kauri yana wani kamshi na musamman, ashe alkyabba ce. Babu abinda nake ji sai guda ta ko ina. Haka ina ji ina gani aka fita dani daga gidan mu aka sakani a mota, da jiniya da komai aka tafi dani palace. Yaya da inna su suka saka ni a tsakiya. Tun da nake ban taba shiga palace ba sai yau. Kuma yau din ma fuska ta a rufe take dan haka babu abinda na gani. Cikin gida aka fara shiga dani direct part din Hajiya. Ina jin muryoyin su Fa'iza suna tsokana ta amma ban kula su ba. Da fara'a da komai Hajiya ta tarye mu. Duk da cewa fuska ta a rufe take amma na fahimci shima gidan a cike yake da mutane. A nan Umma kuma ta bawa Hajiya amana ta ita kuma tace ta karba. Sai da akayi sallar magrib sannan aka tafi dani gidana. Tafiyar kusan unguwa guda ce kafin gidan. Tun daga waje mutane suke kiran masha Allah, inna ta sakani nayi bismillah sannan na shiga da kafar dama. Direct cikin bedroom dina aka wuce dani, gidan gaba daya kamshi yake yi saboda tun safe Mommy ta aiko aka kara gyarashi aka saka fresheners a ko ina. Ko ina an bude a gidan saboda mutane su gani, part din Sultan ne kawai a rufe. A hankali mutane suka fara watsewa, iyayena duk suka zo sukayi min sallama suka tafi, daga karshe ya rage daga ni dai kawayena wadanda zasu zauna saboda partyn da za'ayi in an jima wanda kuma zai yi serving a matsayin siyan baki. Amina ce ta mintsine ni tace "to sun tafi, sai ki bude fuskar ai" sai da na leko na tabbatar babu wani babba a dakin sannan na bude idona. Hasiya tace "au ashe kukan ma harda na munafunci a ciki" na murguda mata baki nace "eh din" suka saka dariya. Zulaihat tace "Moon gidanki yayi kyau, masha Allah" nace mata "nagode" Hafsat tace "kunji rashin kunyar ko? Ki bar mu muyi godiyar mana". Anan muka yi sallar magrib da bamu samu munyi ba, ina cikin sallah naji wayata tana kara, Amina ta dauka tace "kunga daya marar kunyar ko? Ba karamin aikin Sultan bane yanzu yace an fasa partyn nan kowa ya tafi a bar masa amaryarsa" ta dauka ta gaya masa ina sallah sannan ta kashe. Ina idarwa nace "ke Amina waye ya baki damar yi min magana da mijina" duk suka kwashe da dariya. Hafsay tace "ina tausayawa angwayen nan yanzu fa dawowarsu daga 'yalleman kenan kuma zasu tarar da wata hidimar ta daban". Bayan munyi sallar isha muka shirya zuwa gurin partyn, a wajen swimming pool za ayi, gurin kato ne amma kuma a zagaye yake, dan madaidaicin swimming pool ne a gurin sai kuma kujeru da aka jejjera. An kawata gurin da fitulu masu color wanda yasa ruwan yake yi kamar shi ma different colors din ne. Kayan da na saka musamman Zayed yayi mana order dinsu daga saudiyya a matsayin wedding gift dinsa, kayan larabawa ne na mace dana namiji, kalar light blue mai kyalli. Nayi rolling mayafin yadda ya rufe rabin fuskata tunda ba'a saui baki ba. Sai da suka gaya mana sun iso sannan muka fita gurin partyn, kawayena a zagaye dani wai lallai babu mai gani na sai an biya kudi. Suka kaini kan kujerata suka zaunar dani. Hayaniyar da naji ne yasa na fahimci gurin a cike yake da maza abokanan Sultan, a raina nace 'sultan akwai kwashe kwashe shi kam' ina jinsu suna ta ciniki na sai kace wata kaza, har suka gama a take Solomon ya rubuta check ya bawa kawayena, sai da aka basu sannan suka matsa daga gabana na fito fili sosai. Ta cikin mayafina nake leken inda zanga Sultan, tunda aka daura ban ganshi ba, can na hangoshi a tsakiyar abokansa suna ta dariya, fuskarsa kamar gonar auduga, yayo kyau sosai da kayan sa irin nawa. Gurin gaba daya ya hargitse da samari da 'yammata, kusan rabin mutanen gurin a tsaye suke. Ina jiyo amir da sultan suna ta musu, Amir yace tunda an sayi baki sai a bude fuskata kowa ya ganni tunda purpose din taron kenan, a taryi amarya, Sultan kam yace sam babu mai gane masa fuskar mata, ai kowa ya ganni a dinner da luncheon. Ni dai ina zaune kamar gunki. Wani kamshi dana shaka be yasa zuciya ta ta tsaya ta daina bugawa for some seconds, sannan kuma ta fara bugawa da sauri, Hafsat da take zaune a kusa dani naji ta mike tace cikin muryar rada "what are you doing here?" Muryarsa naji yace "I have come for her" a razane na dago fuskata, Ibrahim na gani a tsaye a gabana, wani jiri naji yana neman daukana 'am I hallucinating?' Yawun bakina gaba daya ya kafe. Na kalli gurin da Sultan yake naga ya juyo yana kallon mu. Ji nayi kamar in tashi in fita daga gurin a guje saboda tsoro. Bakina ya kasa motsi ballantana inyi magana, inajin Hafsat tana masa bala'i murya kasa kasa "ka fita tun kafin su ganka, baka san an daura mata aure bane ba, there is nothing more between you two" maimakon ya fita din sai ya durkusa a gaba na, na kuma kallon Sultan da sauri naga gaba daya attention din su shida friends dinsa ya dawo kan mu. Fitsari ne kawai ban saka a wando na ba. Sama sama nake jin muryar Ibrahim yana magana "Maimunatu, nace miki na hakura ne saboda kince min you will be happy with him, a lokacin ban san wanene zaki aura ba, Maimunatu how can you marry someone like him? Is he blackmailing you or your family? Nasan ba dan kudinsa bane because you have all the money you need, kuma yanzu bayan binciken da nayi a kansa na tabbatar ba dan kina sonsa bane, saboda ni na sanki, nasan ba zaki taba son mutum mai hali irin nasa ba. Maimunatu nazo nan a yau, duk da nasan cewa ba lallai ne ya bar ni in fita daga gidan nan da raina ba amma am ready to die for you in dai har hakan zai kawo karshen wannan auren naki ne. I sacrifice my love so that you will be happy, but now after knowing you won't be happy I am willing to sacrifice myself so that you will be free" Tashin hankali ba'a saka masa rana. Poor Ibrahim. You have no idea what you have done. Hannuna naji ya kama ya saka min wani abu a ciki, sannan cikin rada yace "please Moon, run away" ta baya naga an finciki Ibrahim an mikar dashi tsaye, na daga kaina naga Solomon, kyakykyawan mari ya sauke a fuskar Ibrahim. Na mayar da dubana kan Sultan, kofin da yake hannunsa naga ya saki ya fadi kasa, sannan ya fara takowa a hankali idonsa yana kaina, na mike tsaye ina jiran karasowarsa, Hafsat ce tayi sauri tasha gabana, a raina nace "oh no my dear sister, Sultan will never hurt me" chak ya daga ta ya ajiye a gefe, na daga mayafina na karasa bude fuskata ina kallon cikin jajayen idanunsa. Bazan iya cigaba da kallon abinda nake gani a idon sultan ba dan haka na rufe nawa idon, ya dora goshinsa akan nawa yace cikin muryar rada "who is he?" Na kasa cewa komai, ya kara tambayata "who is he?" Da kyar na tattaro yawun bakina daya bushe a hankali nace "please sultan, not here" kamar baiji ni ba ya sake cewa "who is he" kafin in bashi amsa ya kama hannuna ya cire abinda Ibrahim ya saka min a ciki, na bude idona na kalli abin, shima shi yake kallo. Kallo daya nayi masa na gane menene, pink Handkerchief dina ne dana yiwa Ibrahim reply a jiki all those years ago. Sultan ya bude ya karanta rubutun jiki. "I don't know where the path to the future leads, but I want to find out with you" Hmm