MIJIN FATEEMAH SHORT STORY NA MARYAM AHMAD [ OUM SULTAN] BISMILLAH Ɗaga wayar ya yi ta re da faɗin who call me? Daga can bangaren tace nice fattun kace... Gyara zama ya yi yace ok Ina wani abu ne yanzu anjima zan kira ki, ki kulamin da kanki Please. Murmushin taƙaici ta yi a zuciyar ta ta na mai cewa shi wannan sai yaushe zai ri ƙa ba ni lokaci na ne? Ba ayi auren ba ya na min haka ƙila idan muka yi auren ma bazai ri ƙa kwana gida ba. taɓa ta ƙawarta ta yi ta ce" Fateema Mai ya ce maki ne" Maifa zaice kinsan shi da ba aiki muhimmanci ni wallahi nagaji da wannan hali da "Annur ke nuna min ace shi komi aiki aiki" barshi kawai nuratu ta yi tace "Fateema tun yanzu ki tsaya ki karanci mijin da zaki aura kada azo ku ta samun saɓani ba daɗi fa". Fira suka ci-gaba dayi. Noking a kayi masa umarnin ya bayar aka shigo tace' sir ga wani case a kawo yanzu wai yaron ne ya ma wata yarinya ciki. Da sauri ya miƙe yace what ?? so ana samun wannan abu fa ya yi yawa fita su ka yi zuwa wajan wanda suka kawo ƙara uwar yarinyar sai kuka take tana riƙe da ita yace sannun ku mai ke faruwa ne? Faɗa masa suka yi, inda yasa aka ɗauki rahoto 'alƙawarin yi masu ya yi zai ƙwamuso shi yau in Sha Allah, asibiti aka wuce da ita... Yara ya sa don yin bincike, angano wanda ya mata ciki inda aka yanke mai hukunci mai sauri.. kamar kullum yau ma tun da ta tashi take jiran kiran shi amma shiru tayi alƙawarin baza ta kira shi ba ko da za a kwana uku bai kira ba, wajan 11am sai ga kiran shi dariya tayi hadi da farin ciki ta ɗauka tare da faɗin hello baby! Ajiyar zuciya ce ya yi don wani sanyi yaji a ransa ya ce "baby barka da rana". Babyn nawa ya aikin ina fata kana cikin koshin lafiya. Ya ce alhamdulilahi sai ƙewar ki da nake, ina fata kema kina kewa ta? Murmushi tayi tace niko keyin kewarka baka bani Lokaci na kai kullum aiki aiki nafara gajiya ni wallahi.. Sorry Kinsan fa bikin auren mu nan da 3month ne fa, kidaina ɗaga hankalin keda zamu dawo zama gu ɗaya tare ma zamu ri ƙa fita aiki kina so ko? Ta amsa da ehhh my baby. ................... Bayan kwanaki Shirin tarbar baƙo take yi duk wani abinda tasan ya na so sai da ta girka masa 'ɗan matsagaicin gidan mai ɗauke da ɗaku na biyu sai bayi da Kitchen share ya ke kwallal ya sha siminti lailayaiyye tana shiga ɗaki, sai ga kiran shi yana kofar gida iso ta yi masa zuwa ɗakin Inna su gama gaisawa ne suka koma ɗakin "Fateema shinfiɗa masa ta barma tayi inda tai Mai iso ga abincin sa" Yace shagali na duk wannan Ni ɗaya? Murmushi ta yi ma sa ta re da yin fa ri da ido, a duk duniya ba'abinda ke tafiya da " Annur irin fa rin da ta ke ma sa ya ce my baby Bari na maki hoto. Gyara zama tayi ya bata ƙyaras har sau biyu nuna mata ya yi ta ce to nidai kaci abincin bari naga hotunan wayar ka"! Saurin amshe wayar ya yi ya ce" haba dai ina ce tare za mu ci kema kici sai na kunna mana film ma. Mamaki ne ya ka ma ta ko dai akwai a bin da ya ke boye ma ta ne wanda ba ya so ta ga ni rigima ta sa mai ita ala dole sai ya ba ta ko da za ta ci abincin cin ya ce "my Teemah na ba wai wani abu ne bani so ki ga ni ba a'a kawai ki ba ri mu ga ma cin abinci sannan" Fara ci su kayi inda yake bata a baki... WAYE ANNUR Malam Nura da Binta sune iyayen "Mustapha da Umar inda suka. Taso cikin gata da kulawa ta musamman shi Umar ya karanci fannin Dr ne sai Mustapha yana fannin kasuwanci ne, sun taso cikin kwanciyar hankali da kulawa ta iyayen su' don Mallam Nura har almajirai gare shi da yake koya masu karatu" Shekarar Mustapha 45 ya auri "hajara shi kuma Umar ya auri Wata nurse, bayan shekaru da dama Allah ya azurta Mustapha da samun ɗa namiji yaci sunan malam amma ana kiran da annur haka rayuwa taci gaba da tafiya da daɗi ba daɗi..... Wata rana "Dr ya ɗibe su a mota don ziyartar ƴan uwa suka yi hatsari. Baba da inna Umar da matar shi suka rasu da matar Mustapha ba karamin gigita Mustapha ya yi ba daga shi sai mai sunan malam maraici su ka shiga dashi har annur, sai a hankali suka saba da rayuwa makarantar kuɗi yasa shi yana ganewa sosai" Can ne suka hadu da "Fateema mahaifin ta ya rasu anan ne suka sha ƙu sosai ba mai jin kan su har suka gama makaranta suna tare"! inda annur ya je ma "dady da aure ya ke so amma fafur ya hana shi dole sai ya yi karatun ɗan sanda badan ranshi yaso ba ya hakura da auren sai nan gaba"... Back to story A na ta shirye shiryen biki ka'in da na in inda biki sauran kwana 15 farin ciki sosai ko wane bangan gare ke yi ta bangaren "Annur sai samun girma yake daga wajan aikin su inda yanzu za a ƙara karrama shi bisa jajir cewa wajan kama ƴan kunar baƙin wake, kiran wayar shi ne ya sa shi tashi daga barci cikin muryar irin ta masu barci ya ce'' baby yanzu zo in Sha Allah" Tsara yadda bikin zai gudana suke, a tsarin "annur ba wata bidi'a da za a yi amma Fateema taki amincewa da hakan har sai da ta samu ya amince sannan aka kama firar love" Alhamdulilahi yau saura 2 days a ɗaura aure kuma daidai yake da kammala bikin saukar Qur'anin a makarantar su "Fateema ita farin ciki ta kowane bangare ga mijin ta ya zama d.p.o duk a ranar daurin aure dai' yau ya kama Friday Arabian nights suka yi inda aka sha kayan larabawa an sha walima ba kaɗan ba Gida ya cika da ƴan biki ana ta sha gali karfe biyu da rabi aka daura auren ANNUR MUSTAPHA DA AMARYAR SA FATEEMAH HABIB a kan sadaki Naira dubu dari biyu da hamsin lakadan ba ajalan ba, karfe hudu aka fara saukar Qur'ani inda Fateema ta karanta bakara cikin Muryar ta mai daɗin sauraro sun kammala karfe 7pm zuwa ta 8pm ka kai amarya ɗakin ta..... *ALHAMDULILAHI ALHAMDULILAHI ALLAH NAGODE MAKA DA ƘASA NA GAMA LAFIYA*