[2/16, 9:24 PM] Cutie cutie pie: *BAƘIN HAURE....🐾🐾* {Greed for Money is the roots of all evils🫀} ```Bismillahir rahmanir Rahim *Alhamdulillahi Ubangiji ya nufa mun dawo a daidai wannan lokacin me tarin albarka. 15/12/2023 na fara, Ya Allah ka bani ikon isar da wannan sakon da na dauko Ya Allah ka bani damar sauke nauyin da na dauka, ina muku Fatan alkhairi Ga Jamilah Janafty wacce bata gajiya da dimbin alkharinta a gare ni da sauran marubuta baki ɗaya. Wannan labarin wani ɓangare na Labarin ya faru da gaske wani ɓangare kuma kwaskwarimar daliban ilimi ne.``` Sadaukarwa ga *BINTUN BATUL* Wannan labarin na kudi ne! BAARE GOLDEN EMPIRES. Niamey. Niger republic *02:30pm* Ta zubawa kofar yalwataccen ofishinta idanuwa, kamar kullum da rana zata fito har ta fadi ba tare da ta jira zuwan Yaranta ba, sai dai yau kamar har sun wuce ka'idar lokacin da suke zuwa mata, wayar landline da ke gefenta tayi kara. Ɗauka tayi cikin sanyi ta saka a kunnenta. "Assalamu alaikum!" Ta faɗa cikin sassanyar murya wanda yake cike da dattako. "Ina magana da Chairwoman ne na BA'ARE GOLDEN EMPIRES?" "Eh" ta amsa zuciyarta na rawa, domin daga jin harshen da aka mata magana tasan daga nigeria ce, domin da harshen turanci ne. "Yawwa Ma'am Captain MJ Mamman Ba'are ya ce a gaya miki ba zai samu zuwa ba, har..." "Ok ba damuwa!" Ta faɗa cikin sauri da wani raunanen murya, idanunta cike suke da kwallar bakinciki, idan tace bata ji dadin rashin ganin MJ ba tayi karya. Yau shekara shida kenan rabon da ta saka shi a idanun, MJ ba yaro bane balle a ce sai an tuna mishi nauyin da ya rataya akanshi na iyaye, sauke ajiyar zuciya tayi lokacin da aka kirata a wayarta ta ɗauka harshenta yayi nauyi. Amma a zuciyarta addu'a take mishi, a duk inda yake Allah ya kare mata shi. "Madame ga Amaan Mamman Ba'are yana son shigowa." "Ya shigo!" Ta faɗa tana dauke kwallar da yake idanunta da wani tissue. Da sallama ya shigo hannunshi dauke da wayar iPhone 14pro. "Barka da rana Hajiya!" Ya faɗa yana kai wayar kunnenshi. "Barka dai Amaan Mamman Ba'are!" D'aga mata hannu yayi, ta kura mishi idanu. A hankali ta kai hannunta kan wata sandar ƙarfen gold, kafin ya ankara ta make hannun da sandar ta watsa mishi harara. "Auch Hajiya, waya me muhimmanci nake son yi?" Ya katse kiran yana kallonta, tare da tura baki. "Fisabilillahi Hajiya daga na dan yi miki alamar ina zuwa sai ki make min hannu?" "Allah ya shiryaku! Ka gaya min wacce uwar ce zata yarda ka mata haka?" "Tow Hajiya me nayi?" Ya tambaye ta kamar zai yi ihu, wayarta ce ta kuma kara, ta dauka. "Madame ga Aryan Mamman Ba'are yana son ganinki." "Ya shigo!" Ta faɗa tana kallon agogon hannunta, can kuwa sai gashi dogo sambal kamar Amaan Mamman Ba'are, Kyakyawan buzu sak da dan uwanshi, niman wuri yayi ya zauna yana gaida ta a sanyayye. "Sannu Hajiya ya aiki?" "Alhamdulillahi, ya takwarata da Nabeeha?" "Suna lafiya!" "Hajiya shine ni baki tambaye ni ba, wato don an tsane ni. Ko Yarana ba za'a tambaya ba!" "Da kazo ka bani damar tambayarka?" "Amma Hajiya fisabilillahi waya nake fa" "Wayar tafi ni muhimmanci ne?" Shiru yayi yana sunkuyar da kai kasa, shi har ga Allah Hajiya bata mishi gentle, gashi wannan dan iskan Yaron yana zuwa ta wani tsaya tarairayarshi. "Hajiya kin yi waya da Hamma MJ?" Murmushin takaici tayi, ta ce mishi. "Aryan MJ ba zai sami zuwa ba" "Amma Hajiya kuri'ar mu ba zata wadatar ba, dole sai da Hamma, ko zan tafi Port Harcourt din ne?" "Kasan idan na cika matsawa gudu zai sake yi, daga Port Harcourt zuwa wata ƙasa kyale shi." "Tow Hajiya idan yaki zuwa ki basu abinda suke so mana, tunda shi aikinshi yana gaba da kome" " Wani lokaci idan kayi magana, kamar baka san zaman aji ba, anya Hajiya ba asarar kudin tara kika yi ba?" Inji Aryan Mamman Ba'are, "Hajiya ki gaya mishi ya fita hanyata, ba da shi nake ba. Dake nake ina ruwanshi da ni." Lumshe idanun tayi ta bude akanshi, idan da sabo ta saba da halin Amaan, wani lokaci idan yayi abu kamar ba ita ta haife shi ba, idan ta tuna past ɗinta sai ta ga kaman da gayya yake mata wani abu, domin yasan duk yakin da take yi ai domin su ne baki daya, ko makiyinta bata fatan ya ga irin rayuwar da tayi balle masoyinta ko ɗan da ta haifa, amma halin Amaan ya zame mata kamar jinin jikinta ne, yana ganin kamar tafi son Yan uwanshi akan shi, bayan shi bai san bakiɗayansu kaunarsu take ba, tana damuwa da MJ ne ba don kome ba, sai don rashin lafiyarshi. Shi kuma Amaan gabbo ne bai da hankali sam, yayinda Aryan ya kasance mai matukar hakuri amma bai iya faɗa ba, Majeed shine daidai da su, hatta Hajiya Turai kakarsu shakkarshi take, kaf Ba'are estate babu dodo sama da Majeed. "ba zan sallama musu tsinke daga kamfanin nan ba, duk abinda kaga ya faru dama can rubutaccen al'amari ne. Yaushe ka samu duniyar da har ka manta da asalinka? Ka manta nayi aikin tuwo-tuwo domin ka rayu?" Dafe goshi Aryan Mamman Ba'are yayi hawaye na zuba mishi, wasu abubuwan akan idanunsu wasu abubuwan kuma kafin a haife su, past din Hajiya yana da alaka da nisan da MJ yayi. Har ya koma Nigeria da zama duk da dama can Nigeria ita ce inda suka rayu, daidai lokacin da suke buƙatar taimako. "Hajiya a kara kiranshi saura kwana biyar, idan ta kama naje zan tafi har inda yake." Girgiza kai tayi ta ce mishi. "ina tsoron rasa shi a karo na biyu." "Kada ki damu nayi miki alkawarin zamu dawo cikin amincin Allah." "Hmm! Da ka hutar da kafarka, gayen da aka ce yazo Babanmu yana gabbar mutuwa bai zo ba..." Maka mishi ƙarfen tayi a kan gwiwarshi. "Kana hauka ne?" "Hajiya sai nayi shiru? Fisabilillahi nayi shiru fa? Tow nayi shiru." Zata kuma magana Aryan Mamman Ba'are ya ce mata. "Hajiya ya isa haka, kada ki damu zai zo." Mikewa tayi ta dauki tap ɗinta da duk wasu abubuwanta na aiki. Har zata tafi sai ta zauna kamar an ce ta ɗan duka kanta kasa, ta ga wani abu kamar mayen karfe, cirewa tayi tana kallon abun kafin ta saki murmushi ta ce. "Aryan ka ajiye min wannan a wurinka." Karba yayi yana kallon ikon Allah, kafin ya ce mata. "Hajiya na fasa?" "A'a kabar shi." Amsar kayan hannunta yayi, suka nufi waje, a hankali daga Office din sai gaishe su ma'aikatan kamfanin suke, tana amsawa da kai. Sai da suka fito ta tsaya tana kallon yadda ginin kamfanin yake, kafin ta sauke ajiyar zuciya. Burinta bai wuce Yaranta baki daya su rike kamfanin ba, amma MJ yaki bata haɗinka. Lashe bakinta tayi ta nufi inda motar Aryan take ta shiga, cikin Fushi Amaan ya ja Motarshi ya fita. "Kwantar min da kujerar nan na gaji." Ta faɗa tana me lumshe idanunta, only God knows duk abinda yake faruwa, amma ita ba zata ce yaushe kan Yaranta ya rabu haka ba, sannan ba zata ce ita ce silar fadawar matsalar su ba, tasan da babu da ba dadi haka suka taso, cikin tsannanin bakinciki da bakin zalinci da mugunta da bakar talauci na tsananin tashin hankali.. Kuma a haka ta rike yaran suka kai inda suka kai, amma yau sakamakon da take gani shine na tarwatsewar Yaranta. Bayan gwagwarmayar rayuwar da ta sha, haka bai isa ba sai ta kara amsar wani Punishment, bayan wanda ta gani bai isa ba, ace yau yaranta kamar zasu kashe junansu. Tsayawa suka yi a traffic Jam, kamar an ce ta bude idanu ta hango Sajjid Mamman Ba'are, tare da wasu turawa suna gaisawa. "Me Sajjid Mamman Ba'are yake yi anan?" Kallon wurin Aryan yayi kafin yayi tsaki, ya ce mata. "waye ya sani? Sharrin da yake cikin duhun BA'ARE GOLDEN EMPIRES Allah kadai ya sani." Ya faɗa yana kara jan motar bayan an basu damar wucewa kwantar da kai tayi tana zare glass din idanunta. "Duk abinda yake faruwa a rubuce yake, amma kuma mutane sun rufe idanunsu kamar basu gani,bayan sun san kome." "Hajiya yakin nan ba iya ke daya ba ce, har da Hamma MJ, shine kashin yakin." Da wannan suka isa unguwar da suke zama, inda kana gani kasan ba iya su kaɗai ke rayuwa a unguwar ba. ~~~ Port Harcourt *Nigeria Naval barracck* _09:30 pm_ Ruwa ake tun safe, har zuwa yanzu ba a daina ruwan ba. Kallon yan tsintsiyar hannuna nayi a karon farko ina me hadiye yawun tsoro, yau na isa na komawa Addah hannu rabbana ne? Ai yau daga ni har dangin Uwata sai munci zagin da ba zai kare ba, sosa kaina nayi ina kokarin niman hanyar da zan fita. Don haka nayi ta bin layi da gida-gida, domin ya fitar dani barracck din nan wai ma meye ya kawo ni nan? Tambayar da nayiwa kaina kenan, haka na cigaba da bin duhu ina buya, ina jin gara na fake na kwana anan, tow wannan jikar na jikina fa? Wani munafikin sanyi na ji ya shige ni, da sauri na kara makalewa da jikin bangon gidan da nake. Sai dai kash, ban gama nazarin me zanyi ba, naji hayaniyar mutanen sojan nan. "Innalillahi'wa'inna'ilaihi'raji'un;" na furta a hankali, da sauri na cire takalmina na bazama da gudu, kasancewar ana ruwa. Can naji an hura wusir, kafin kace me sojojin area din sun fito da manya-manyan torchlight ɗin su, ƙaddara ce ko tsautsayi. Kawai dai nasan nazo wani kofar gida, amma daukata aka yi ko janyo ni aka yi ban sani ba, sai dai nasan na buɗe baki zanyi ihu, naji kamar an cusa min wani abu a cikin bakina, tare da ganin wani duhu ya mamaye ganina. Ma'ana gidan baki daya a cikin duhu babu alamar haske ko tafin hannun baka iya gani, amma zan iya cewa fatalwar da ya ɗauke ni, yasan kome na gidan tunda gashi nan har ya kai ni dakin da babu kome sai duhu, ina ji ya bude wani abu ya cilla ni cikinshi. Sannan ya dauki abu ya rufa min gami da danne dakin. "Idan kika sake kika yi motsi suna zuwa harbeki zasuyi." Ya faɗa min da irin turancin da ake yawan yi a garin patakwal, hawaye ne ya zubo min, ina ji daga can nesa ana buga kofar gidan, bugawa kamar za a b'alle kofar. Can ina iya jiyo hayaniyar mutanen sojan nan. "Oga ya ce meku wuna search any where akwai yaron hausa da ya dauko daga waje, ya gudu." "Ok ku shiga ku duba!" "Kambu!" Wato ma zai bar su ne, me yasa ya dauko ni? Jin ana buruntu yasa na kara k'amk'ame jikina, na rantse na gudu daga nan tabbas zai yi wahala na kara komawa wurin Addah, takum zan koma naje wurin Baffana yafi min wannan bakar wahalar. Ba zato ba tsammani kawai naji ana buga inda nake ciki, wani irin dauke wuta nayi domin nasan shi kenan kwanana ya ƙare. "Oga mu bude nan?" Ban ji me ya ce ba, but naji suna bashi hakuri. "Oga kayi hakuri! Kayi hakuri." Suka yi ta bashi hakuri, sannan suka fita daga cikin gidan. Ajiyar zuciya ya sauke, sannan ya dawo dakin yana mamakin yadda wasu daga cikin ƙabilar Hausawa su ka lalace da son abin duniya, yanzu yar wannan yarinyar me zata yiwa namiji? Bubbuga abin yayi tare da bude abin, ya haska min fuskata na kare da hannu bibbiyu, "fito!" Ya faɗa da wata irin murya mai dadin gaske, cire hannu nayi a fuska, tare da kara leka fuskarshi, abin haushi bana ganin fuskarshi. "Fito!" Ya kuma fada min da muryar, da sauri na mike tare da kallonshi. "ban iya fitowa ai!" Shiru yayi, ya juya kamar zai fita kawai sai ji nayi, kamar an dakume wuyata, anyi sama da ni. "Kambu kashe ni zaka yi?" Cilla ni yayi can gefe guda, na zube a kasa "Kum!!" *Wai me yasa sojoji kuka cika mugunta ne?* Na tambayi zuciyata, fita yayi ya bar ni a dakin, na takure wuri guda, Addah tana can tana barci ni ta watso rayuwata gabbar mutuwa. Hasken da na hango yasa na kara k'amk'ame jikina, ya shigo da ƙatuwar bargo ya watsa min, sannan ya kuma fita. Can sai gashi da wasu kaya ya watsa min, zama nayi a cikin duhun. Domin na lura akwai amana a tsakaninshi da duhu. Mikewa nayi na cire kayan jikina, har na sauya kayan, sannan na dauki bargon na lullube jikina, na cigaba da zama a wurin, domin ko wancan da na gudu daga wurin shi. Sai da ya bari na fara barci, kawai naji ya fara min wani abu na daban, rintsa idanuna nayi, tsoro nake kada sai na fara barci shima ya biyo daren. Commodore Magaji Abba Chindo. Cirko-cirko Yaranshi suka yi, jikinsu a matukar sanyayye. Shi kuwa yana tsaye a saman barandar kofar gidanshi, sai bunka hayaki yake. Busa sigari yake tare da lumshe idanun, a duniya yana son kwanciya da Yara kananu, musamman wanda shi yake fara bude su da kanshi, haka yasa baki daya yake jinshi kamar mara lafiya. Ya saka buri akan yarinyar nan, amma shegiya sai da ta gudu. Hadiye yawu yayi, bayan ya kashe sigarin. " Kun duba gidan wancan dan cirani?" "Yes Sir, mun duba." Dukar karfen da yake tsaye yayi yana faɗin. "Taya zata bar barracck din nan? Sannan a wannan lokacin da ake tsuga ruwa? Kai ku bi min gida -gida har gidajenku!" "Yes Sir;" Suka fada baki daya, sannan suka juya tare da barin kofar gidan. Daya biyu yarinyar nan tana hannun wancan dan kutumar uba, bai san me yasa gayen yake mishi kallon banza ba. Koma ciki yayi ya dauko ledar ruwa, ya nufi gidan, dukar kofar da aka yi ne yasa shi jan tsaki, ya fito daga cikin dakinshi da yake kallon arewa da kofar. "Yes!" Ya faɗa yana tsaye a jikin kofar. "Ka bude!" Aka gaya mishi da karfi. Bude kofar yayi ta tsaya a jikin kofar. "Meye?" "B,,.. uba ne!" Commodore Magaji Abba Chindo ya faɗa a fusace. "Ok nawa kenan?" Ya tambaye shi, yana haska kasa. "Ka bani hanya na shiga na dauki kayana." Hannunshi ya kai kunne ya ce mishi. "Magana kake?" "B..,, Uba nake?" "Ok kayi ta yi!" Ya juya zai shiga tare da rufe kofar, yayi maza ya kai mishi tokare, sai da ya fadi, torchlight ya fadi can. Mikewa yayi yana faɗin "An shiga tsakaninmu, ka kama gabanka domin xan iya kiran Admiral" ya fada cikin sanyin murya wanda zai tabbatar maka da baya son hayaniya ko faɗa. "Wallahi ka sake baka fito min da ajiyata ba, sai na ga bayanka idan muka hau teku " "Kai ne bakon mutuwa, amma ni babu irin mutuwar da ban gani ba. Please zaka iya fita." "Kai Son of bitch, sai na kashe ka." Wannan ihun yasa na kara k'amk'ame jikina, tabbas na jefa mutimin nan cikin masifa. Kara k'amk'ame jikina nayi na cusa kaina a tsakanin cinyoyina. Sake kofar da aka yi yasa na razana sai da na mike. Can naji alamar an rufe kofar, ina jin takunshi har ya bude wani kofar ya rufe, ajiyar zuciya na sauke a hankali, ina jin kamar na fito na gudu amma me zan taras a gaba yasa na kara rungume bargon da ya bani. Haka na raba dare har lokacin, ina zaune kamar mara gaskiya duk tsawon dare nan ban bari raina na rintsa ba, tsoro nake ji kada na kwanta ya farmake ni. A hankali ruwan ya tsagaita, garin yayi wani irin sanyi me dadi da shiga jiki. Wanda ya haifar min da jin matsananciyar barci, na kwanta a wurin. .... 3:30am "Don Allah kayi hakuri Alhaji, wallahi ba zan kuma ba. In sha Allah zan yi kokari, Alhaji don Allah ka dube Yarana kada ka ci mutuncina a kan idansu." Kamar walkiya haka yake hango abin, a zahiri kuma kuka yake har da shasheka, yana surutu. Ina barci nayi ta jin kuka da shashekar mutum, "shikenan an kama ni" na fada zubur ina mikewa. Ganin babu kowa yasa naji wani irin tsoro ya kara kamani, mikewa nayi ina jin kukan yana kara ta'azzara. Fitowa nayi daga bakin kofar, na nufi hanyar da nake jiyo kukan. Walkiya aka yi naji kamar hantar cikina zata fita, yayyafin da aka aka fara yasa na ji kamar na juya tare da komawa dakin da ya ajiye ni. Amma ina ƙaddara ko Hatsari ya kai ni inda ba zan manta ba. Walkiyar da aka kara tare da tsawar da ta cika ko ina, yasa na kama handle kofar na tura, ina shiga na ga dakin har tafi nawa duhu. Gurnani da nishin da ake yasa naji kamar kafaffuna ba zasu dauke ni ba, juyawa nayi domin na koma inda na fito domin ta nan kaɗai zan tsira da rayuwata, sai dai tunda na shigo dakin na rasa ta ina na shigo, garin laluben hanya nayi ciki tare da karo da gadon, kifawa nayi bisa gadon akan mutum. Ji nayi an cafko ni tare da shake min wuya, ina ƙoƙarin kwace kaina amma ina, baki daya ya zuba min karfinshi. Ya danne ni da karfin tsiya, bubuga gado nake ina kokarin kwatar kaina, amma ina. Wani walkiya aka yi, me haɗe da tsawa. Shi ya bashi damar hango wata yar ƙaramar wukar da take kasar pillow da yake kwance. Bayan ya zame rigar da yake jikina dama kuma rigarshi ce. Yan matasan dukiyar fulanin da suka fara fitowa suka bayyana, domin tsirara ya min tare da ɗaukar wukar yana kokarin bude ta daga gidanta, gefe daya yana kara kutsa kai tsakanin cinyoyina. "Innalillahi'wa'inna'ilaihi'raji'un!" Iya abinda na iya faɗa kenan, da ƙaramar muryar da tayi kama da mai shirin mutuwa, azabar da ta ratsa ni lokaci guda........ *Gamu nan mun dawo* 1/3/2024... #Mai_Dambu [2/16, 9:24 PM] Cutie cutie pie: *BAƘIN HAURE....🐾🐾* {Greed for Money is the roots of all evils🫀} Arewabooks:maidambu41 Wattpad:Mai_Dambu Mallakar:Mai_Dambu *002* _Ban zan yi tafiya mai nisa ba, ba tare da na tsaya na miki fatan Alkhairi Hannatu Idris Allah ya shiga cikin lamarinki, ya saka da alkhairi na gode sosai_ Operation Anaconda *** A daidai lokacin da nake tsammanin mutuwata, ta zo gare ni domin nasan abubuwa dayawa sun faru a cikinsu har da rashin ganawa da mahaifiyata, wanda tana raye amma bamu san a wata duniyar take ba, iya hakan idan aka barshi a rayuwata na azabtu da rashin Uwa, nasan duk laifin na Baffa ne da Addah at least ya dace a gaya min inda mahaifiyata take. Soka min wukar a gefen cikina, yayi dai-dai da dawowata daga duniyar tunani da mafarkin zahirin da nake bayan na ga mutuwa. Sake caka min wukar yayi cikin tashin hankali ina kara jin abin da yake fada. "Sai na kashe ka, idan ka kuma tab'a min Mamana!" Ya kara d'aga wukar zai soka min kamar wanda aka mishi wani abu, haka ya zube a jikina. Azaba da rad'ad'i yasa na kasa aikata kome, ina kwance kasarshi da alamun suma yayi domin ina jin dan bugun zuciyarshi. A hankali na tattara karfin da yaymin saura na tunkud'e shi gefe can, ina jin yadda jinin yake zuba. Ga zafi gashi yana zuwa da sauri da dumi, a hankali na fara sauka daga bisa gadon sai dai na kasa, komawa nayi ina jin wata iriyar azaba ga zufa da gajiya me haɗe da jiri kamar xan yi aman kayan cikina. Haka na koma tare da kame wurin ina kwance, nayi ta kokarin niman wani abu na rufe ciwon. Na rasa a wurin lalube na tabo fuskarshi. "Tashi ka taimaka min kada na mutu,ka tashi don Allah zan mutu ka ji." Na fada ina jijjiga kafadarshi. Kamar a mafarki yayi ta jin muryata, haka yasa shi bude manya idanunshi da suke cike da barci, "Tashi ka taimaki rayuwata mutuwa zan yi." Na fada da asalin karamar muryata. Ina jin wani uban tsallen da ya buga, yasa ni ƙara ware idanuna, ina nishi idanuna a rufe naga kamar an haska fuskata. Bude idanuwan da zan yi hasken wuta ya gauraya dakin, sai dai abin mamaki shine bana gani sai dishi-dishi. Lumshe idanu nayi a hankali naji kamar barci ne ko wani abu ne yake faruwa da ni, na dai san ban kuma fahimtar duniyar da nake ba. Wani irin rikicewa yayi wanda yasa shi gaba-daya rud'ewa, wayarshi da yake gefen gadonshi ya dauka, tare da duba lokaci. "Innalillahi'wa'inna'ilaihi'raji'un!" Ya iya furtawa domin kuwa yasan yayi abinda ya dame shi, ya kuma rasa wanda zai kira ya gaya mishi halin da yake ciki. Sake wucewa yayi ban daki ya kalli wandon shi bai ga alamar manhood ɗinsa tayi wani abu ba, amma kuma hannunshi kaca-kaca da jini. *Doctor Umaima!* Abin da zuciyarshi ta ambato kenan, da sauri ya fito tare da ɗaukar wayarshi. Jikinshi na rawa ya kirata. "Assalamu alaikum!" Ya faɗa ta d'aya bangarenta. Ina bai samu arzikin amsa mata ba ya jifa mata tambayar. "Kina asibiti ne?" "Yes ina Night ne!" "Alhamdulillahi! Umamai don Allah ina cikin tashin hankali ne, na yi attempt kisan kai. Please ki taimaka min gani nan." "Ya Rahaman,tayah hakan ta faru?" "Ba lokaci gani nan." Ya faɗa mata, sannan ya koma kan gadon ya dauki wani towel ya daure inda jinin yake zuba, sannan ya dauko zanin gado ya nad'e ta da shi, kafin ya kuma ɗaukar bargo ya dunkule ta a cikin, sannan ya dauke ta, ya nufi hanyar waje, ta falonshi ya shiga gareji. Ya ajiye ta bayan motar, ya koma ya dauko key, yana zuwa ya bude a cikin motar ya sakata, ya koma ya gyara dakin shi tas, yana jin zuciyarshi kamar zata buga, yasan halin Commodore Magaji Abba Chindo, yana samun labarin ya kashe yarinyar kwanar shi ya ƙare. Haka yasa shi kara rud'ewa domin wannan aikin shi ne farincikin shi, shine kome na shi idan ya sake ya rasa shi tabbas sai yayi matukar danasani. Haka ya gama goge dakin ya saka kome a wancan dakin duhu, sannan ya nufi gareji a lokacin Dr Umaima ta kira shi ya kai sau uku, yana shiga motar ya kirata. "On my way!" Ya kashe ya kunna motar sannan ya fito ya bude get din, ya koma ya fitar da motar, sannan ya sake dawowa ya rufe get din ta ciki ya koma ta fito ta kofar gidan. Har ga Allah ya tsani kanshi, wannan lokacin ya dace ya rabu da wannan laluran, amma ina kamar kara cusa mishi abin ake, kara ji yayi ya tsani ahalin shi idan aka cire Hajiya. Itace har abada ba zai tsaneta ba, tunanin shi ne ya katse lokacin da ya iso bakin get din fita. Ya nuna ID card ɗinshi, haska motar suka yi, sannan suna ga normal bargo ne. "Oga ina zaka?" "Zan shiga clinic ne an kira ni." "Ok Oga kayan cikin motar nan fa?" "Idan na gama aiki xan kwanta ne, bargo na ne." "Ok ku bude mishi kofar!" Haka suka bude mishi kofar, ya fita yana sauke ajiyar zuciya. Da gudu ya nufi titi tare da ɗaukar hanyar asalin cikin barrack din, yadda yake gudu kadai zai tabbatar maka, yana biyayya ne ga zuciyarshi da take bugawa. Koda ya isa asibitin dake d'an tafiya ne ya raba su, yana isa bakin get din aka tsare shi, mika musu ID card ɗinshi yayi, suka bude mishi domin sun san likita ne, kuma babba, yadda yake tukin har ya isa bakin Asibitin zai saka ka gane Allah kaɗai ya kawo bawan Allah nan asibitin. Yana shiga harabar asibitin Dr Umaima da wasu Nurse biyu suka fito, zasu amshi mara lafiyar, suka ga ya bude motar ya dauko ƙunshin bargo. "Jeed Ina mara lafiyar?" "Ba lokaci mu wuce ciki " ya dauki bargon suka wuce cikin asibitin. Kai tsaye emergency room ya wuce da ita. Ya kwantr da ita a saman gadonsu na marasa lafiya. Sannan aka shiga bude ta, har aka bude ta gaba-daya. Har lokacin jini yake zuba. "Innalillahi'wa'inna'ilaihi'raji'un! Tana zubda jini" Doctor Umaima ta faɗa da sauri tana danne wurin. "Ki taimaka min kada ta mutu." "Kayi wani abu, a tsayar da jinin nan, a shiga da ita tiyata." Cikin abinda bai wuce minti ashirin ba,suka nemi yin tiyatar . "We need blood?" "Innalillahi'wa'inna'ilaihi'raji'un!;babu a bank ne?" "Ban sani ba!" Da sauri Nurse Biodun ta bude blood bank, ta ce musu ."Daya ne ba zai wadatar ba." "Za a samu mutane a lab?" "Bana tunanin sun tashi,saboda aikin su ba dare ba rana ne." Da sassarfa ya fita ya nufi can wurin lab din, ko minti talatin ba ayi ba, ya isa sun rufe da kyar aka samu wanda yake kwana a wurin. "Duba jini na, group O+ ne" Ciro wayarshi yayi ya kira Doctor Umaima. "Leda nawa ake so?" "Ina ga hudu zai yi, don yanzu na samu an tsayar da jinin." "Ok ki kokarta gani nan zuwa." Ya faɗa, kallon mutumin yayi, bai mishi magana ba, ya dauki duk wani abun bukata, ya fara aikinshi, cikin ikon Allah dake mutumin yasan shi, kuma yana tambayar shi, sannan yana duba medical records dinshi a computer ɗinshi, sai gashi Allah ya takaita da sai anyi ta tests. Aka dibi leda daya, can aka kuma diban na biyu, a lokacin aka barshi ya huta. Kiran Doctor Umaima ya shigo mishi lokacin ana diban na uku. Cikin tsananin gajiya ya ɗauka. "Saura leda daya, a zo a karbi sauran" " Captain!" "I'm okay!" Ya faɗa cikin karfin hali, can kuwa sai ga nurse da wani soja, aka zo aka amsa. Yana isa wurinta ta ce mishi. "Baka saka hannu ba a Matsayin." "Umaima rayuwar yarinyar ne mai muhimmanci, ba saka hannuna ba." "Ok" Haka suka shiga da ita aiki, yana kwance ana diban jinin karshen. Wurin karfe biyar na Asuba ya fito a hankali yana jin jiri na dibanshi. Dakyar ya isa emergency room. Zama yayi a kujerar da ke cikin dakin, jin kiran Sallah yasa shi nufar masallaci, yana sallah a nan ya kwanta domin wani irin jiri da zazzaɓi yaje ji. Karfe shida na safe Doctor Umaima ta fito, a matukar gajiye domin babu inda baya ciwo a jikinta. Sannan aka turo yarinyar a gadon marasa lafiya. Aka kaita ward, wucewa daki tayi ta gabatar da sallar asuba, sannan ta shiga hada kayanta. Tana kokarin kiran wayarshi amma ba a dauka ba. Sai da ta cire kayan jikinta sannan ta wuce dakin da aka kwantar da yarinyar, bata ga wani fuskarta sosai ba, ta juya ta fita wurin seven ta bar asibitin. Yana barci a cikin asibitin yaji kiran da wayarshi keyi, kamar a tsakiyar kanshi. Bude idanu yayi da suka yi wani irin fari da ja. Yasa a kunne. "Sir kana ina ne? Za atafi teku." Wani irin jiri ne ya kwashi Idanunshi ya ce. "Ok gani nan" kashe wayar yayi ya sauke ajiyar zuciya, kafin ya hada karfinshi wuri guda, ya tashi tare da ɗaukar kome na shi ya fita daga Masallacin domin yasan team lead ɗinsu Commodore Magaji Abba ne, haka yasa ya boye ciwonshi domin ya san halinshi sarai, and yaso ya kuma ganin yarinyar nan, haka ya kwashi motarshi a guje. Sai community dinsu na sojoji. Yana isa a daddafe ya shigar da motarshi, sannan ya wuce kitchen ya haɗa tea me kauri ya sha, kafin wani lokaci ya fara zufa kamar me. Wanka ya shiga yayi sannan ya kimtsa ya fito daga gidan ya turawa Doctor Umamai kudi tare da short Note. *Yarinyar nan idan ta farka please ki bata wannan! Thank you da abinda kika min!* Daga haka ya fita bayan ya dauki duk wani object na aikinsu. Operation Anaconda plan. Kai tsaye headquarters dinsu ya nufa, anan ya hadu da Commodore Magaji Abba Chindo, kanshi ya sunkuye yana kallon kasa. "Kun san abin da ya tara mu, mun samu labarin za a fitar da mai ta ruwa. Aikinku shi ne ku dakushe yunkurin yan tada kayar baya shine aikinmu,mu mazaje ne a fagen yaki idan kunso idan kun koma cikin matayenku tow ku daura zanin matayenku,kune kuka sani ba mu ba ku ajiye personal emotion dinku domin dakile aikin yan ta'adda. Muna da Kyakyawar yakinin duk wani sojan kasar nan yana tsaye ne domin bawa al'umma kariya da taimakon gaggawa. Yan kasa ne kaɗai zasu fahimci yadda tasirin kishin kasa yake kun ji ko? Kada wani yayi harbi idan muka kama su, aikin mu shine mu kawo su headquarter ba kashe su ba, domin suma fararen hula ne." "Yes Sir!" Suka fada da karfi. Sannan suka wuce inda aka ajiye mota, suka shiga shi kam bai wani damu da ya shiga gaba ba, yafi damuwa da baya, haka wani sub-Lieutenant ya bude mishi gaban mota ya shiga, har zai zauna Magaji Abba Chindo ya zo daidai kunnen shi. "I hope kayi ban kwana da danginka! Domin bana fatar ka dawo a raye." D'ago kai yayi yana murmushi, ya ce mishi. "Kai ne bakon mutuwa!" Ya faɗa yana murmushi. "Wannan murmushin sai ya zame maka mutuwa." Yar dariya yayi ya ce mishi. "Ban sani ba, idan akan aikin da kasan idan na bari ba zai kare ni da kome ba, domin kuwa hmm!" "Domin me? Kai da aka watsar da kai." Juyawa yayi ya kalli MAC. A fusace yake amma kuma baya jin zai yarda su yi faɗa. Sai ya dauke kanshi yana me kallon gefen driver. "Muje ko!" Wato daga cikin abin da Allah ya hore mishi iya sarrafa fushinsa. Zai yi wahala ka ga tunzurar shi, idan kuwa ya tunzura yana zame mishi mugun yanayi ne mai matukar tsoratarwa, shi yasa baya son fushi baya son fada, baya son hayaniya, yana ajiye kanshi da yanayin shi a wani aji na musamman. Fushinsa ba haka kawai yake yin shi ba. Maganar Magaji bai dauke ta a bakin kome ba. Har suka bar headquarter suka nufi bakin ruwa. A ka'idar operation Anaconda, kome suka hadu da shi, lakwame shi zasu yi amma daga abinda Commodore Magaji Abba Chindo ya a gaya musu ba a basu damar harbi ba, ba a basu damar kome ba sai dai dakile fashin da za ayi, a motarsu na tafiya kai tsaye ya kira Admiral shugabansu. "Sir wannan mission din yana da matukar hatsari, idan muka samu kanmu cikin tarkon makiya ya zamu yi? Kasan masu wannan aikin suna dauke da miyagun makamai, sir a bamu damar kare kanmu da rayuwarmu don Allah a tura wannan sakon zuwa ga Oga!" Admiral duk da ba musulmi ba ne, yana matukar ganin girmanshi, musamman yadda yake da jajjircewar aiki, daukar kasada a kan kowani aiki. Infact shi yana cikin SISA, wato (special intelligent Soldier Agent) sannan ya ajiye haka a matsayin personal life din Yaron, ko wannan operation Anaconda plan din yana cikin sojojin da suka kirkirota musamman yakin south south. Sannan asalin labarin daga bakinshi suka jiyo shi, haka yasa suka kara bincike aka tabbatar za a fita da mai ta teku. Shi yasa aka tura su. "Ku kare kanku, idan kuka faɗa tarko!" "Yes Sir!" Commodore Magaji Abba Chindo, kiran wasu sojoji guda uku, ya umarce su da su je har gidan da ya dauko yarinyar nan, su ci uban Uwarsu, kada su d'aga mata kafa. ** Unguwar hausawa. Koda yake ana kiran unguwar ce da sunan unguwar hausawa, amma a zagaye yake da Musulmai da kiristoci, musamman inyamurai. Tun karfe shida na safe ya dace a ce an dawo da ita, amma shiru har karfe takwas. "Ada wetin happen? I see you dey pass up and down, shebi your Ethiopia girl neva come back?" Inji wata Beyarabiya, cikin takaici da bakinciki Adda ta ce. "Bise kyale ni da yar iska haihuwar asara, me aka yi da haihuwar bakinciki, shad'ari ya haifa mana irin masifa, kaf cikin al'ummar fulani babu miyagun iri kamar anagamba." Ta faɗa tana watsa hannu. Fitowar wata budurwa daga wani daki tana yatsina fuska ta ce mata. "Addah hala irin masifa bata dawo ba ko? Kowa na fitowa bariki arziki ita wannan a barikin ma tsiya da masifa take kara janyowa kanta. Kuma wallahi sojan nan bai da mutumci, ba lallai ya saka condom ba, a tsarinshi baya saka condom. Shi yasa lokacin da ya tab'a daukar Ummi ta dawo tana ta mita, domin tace bata da infection dan shegiya ya zuba mata, mugu. Tow gashi ya dauki Zahrah." Kwafa tayi tana faɗin."ai ni ban ga amfanin haihuwar Zahrah ba, shegiyar yarinya ta dauko bakin jinin Uwarta. Ke kan ai Munaisah kyanki jarinki gaki tabarkallah, ita waccan yar iskar." Fitowar wasu yan mata da kayan barci, yasa tana kallonsu. "Zully kin tashi?" Dauke kai tayi kamar bata gansu ba, ta koma dakin ta dauko brush da marclean, ta kuma fitowa. Bakin magudanar ruwan ta tsuguna tana wanke bakinta. "Zulaihah hala laifin tura Zahrah kwanan waje ko?" Nan ma bata tanka mata ba. "Daurawa kai jaraba, wai tana jin haushin abin da ya faru ne?" "Munaisah babu ruwanki da ni, domin zan ci mutuncin ki." Inji Zully din. Kumshe dariya tayi tana faɗin. "Bani na kar zomon ba, yau wata yarinya zata sha wutsiya gatar gato!" A fusace Zulaihah ta wuce bata kula su ba, sauran yan matan suna mata dariya, domin a duniya rayuwar Zulaihah idan za a ce ta bada shi domin ta kare Zahrah zata bada. Ta tsani irin rayuwar da mahaifiyar take daura yan mata a kai, suma dake son abin duniya da kwadayi yasa suna bada jikinsu me daraja, suna fadawa bariki. Tashi Addah tayi ta nufi banɗaki ta kama ruwa, sannan ta fito domin ka'idar kiran wayar Mahaifin Zahrah karfe goma na safe, ji tayi kamar zuciyarta zata buga domin karfe goma saura. Wannan wacce irin masifa ce Zahra zata cillata cikinshi? Tunda take kawo yara babu wacce ta tab'a wuce shida na safe bata dawo gida ba, sai Zahrah. Abin karyawa suka yi baki daya taliya da mai da yaji, sai Zulaihah da ta fasa kwai da sadine ta soya da yar attarugu da tumatiri sai albasa, ta shiga daki ta ajiye musu tasan idan ba wani lalura ba, babu yadda zaayi Zahrah ta kai wannan lokacin, idanunta yana kan wayarta, duk wani motsin lokaci tafiya yake da sautin bugun zuciyarta. A hankali ta kara rike wayar, goma tana cikawa wayar Addah tana kara. Jikinta na rawa ta fado dakin. "Zulaihah ban san me zan gayawa Shad'ari ba, don Allah taimaka ki mishi karya wallahi nayi danasanin turata." Amsar wayar tayi cikin sanyin murya ta ce. "ina kwana Kawu?" "Lafiya lau Zulaiha, ya kwananku da na Addah?" "Lafiya lau Kawu!" "Ina kawarki?" "Baffa yau makaranta sun tura su, wani nazari sai nan da kwana uku zasu dawo in sha Allah." "Tow Masha Allah, Ubangiji ya dawo da su lafiya, Zulaihah don Allah ki kula da Zahrah kin san yadda take bata ji, sai anyi da gaske." Murmushi tayi tana faɗin. "Kawu Indai akan gaskiya ne, ba zan gushe bata goyan baya ba, har sai na koma ga Allah." "Allah ya muku albarka!" "Amin Ya Allah, Kawu har yanzu babu labarin Ammynmu ne?" Shiru yayi kafin ya ce mata. "Na tafi har ye'ude ban samu wani labarinsu ba." "Allah sarki Ubangiji ya bayyana ta!" "Amin Ya Allah, ya Munaisah ita ko wayar ba zata yi da ni ba ne?" "Bari na mika mata." Ta mike zuwa waje, ta mikawa Munaisah. "Baffanku!" Amsar wayar tayi ta saka a kunnenta. "Barka dai Baffa." "Hmm! Ke Wato sai na nime arzikin magana dake, amma ina jin kina kiran Innarki ko?" "Kayi hakuri Baffa!" Ta fada tana wani had'e rai, Indai zata yi waya da shi tow bata sake jiki tayi wayar kamar yadda take da innarta...... #thedambuje [2/16, 9:24 PM] Cutie cutie pie: *BAƘIN HAURE....🐾🐾* {Greed for Money is the roots of all evils🫀} Arewabooks:maidambu41 Wattpad:Mai_Dambu Mallakar:Mai_Dambu *003* *Zahrah* Lumshe idanuwa na nayi ina kallon dakin da nake, gari ya waye garai sake lumshe su nayi na kara tabbatar da inda nake, amma wani ikon Allah na kara fahimtar ashe ba lahira aka kai ni ba, a duniya nake, tashi na fara kokarin yi aka ce min. "Ke ki kula da ciwon jikinki mana." Kasake nayi jin mutum ce ke min magana ba daya daga cikin Mala'ikun da suka zare rayuwata ba, bani da karfi ko kaɗan don haka na ce mata. "Don Allah ban mutu ba ne?" Juyowa tayi ta kalle ni,sannan ta ce min. "Kina da number yan uwanki?" Dafe goshina nayi ina tuna na bar wayata a dakin wancan dan iskan. "Baki ji ba ne?" Sake kallonta nayi na fara fada mata number Zully."Zero eight zero....."har karshen number, kiran layin matar tayi. Aka ce ana amfani da wayar. "Don Allah kira min wannan number." "Zero seven zero..." Lokacin da ta kira wayar ta shiga, an dauka sai dai ihun da ake yi yasa ta kura min idanu. "Ke ungo wayar kiji abinda yake faruwa." Ta mika min, ihu da kuka tare da jin alamar ana musu wani abu yasa na mike gabakidaya, nasan wasu zasu ce hala ban san halin da nake ciki ba ne? Ganin na mike a hankali har na tsaya da kafaffuna, matar ta ce min. "Amma baki da hankali?" Murmushin wahala nayi domin ciwon kamar yanzu aka ji min, zafi da azaba sun ishe ni. "Eh ni mahaukaciya ce akan dangina!" Eh sune raunina, "ina zaki yanzu?" Matar ta tambaye ni, "zan tafi gida wani abu yana faruwa, idan naje in sha Allah zan dawo don Allah ki bar ni na fita." "Zai shafi aikina ne!"ta faɗa tana kallon yadda damuwa ta bayyana ƙarara akan fuskata. Amsar wayar tayi ta koma gefe tayo kira, maganar da bai wuce second talatin ba, ta dawo ta mika min wayar tana faɗin. "Jira Doctor tazo." "Ok" na fada ina kallon agogon ward din, wato wani ikon Allah jiran Doctor da nayi ji nake kamar rayuwata nake jiran yadda xa ayi da ita, domin ban san iya adadin bugun zuciyar da nake ji ba, can har na hakura zan mike, sai ga wata kyakkyawar matashiya ta d'andasa wanka kamar wata fure. "Sannu yan mata ya jikin naki?" Ta tambaye ni,tana kai hannun ta saman rigata ta d'aga. "Pretty good!" Ta faɗa, "Sisi ta kira ni ta ce min,kina son zuwa gida." "Eh!" Na faɗa ina kallon ƙasa, "ok wacce unguwa kenan?" Domin bata yi tsammanin ina jin Hausa ba, balle a kai ga wani yare. A'a tunaninta ai daga irin cotonou ko Togo, ko Mali,na fito ko irin yan ciranin Ethiopia nan, Yes haka skin dina yake kasancewar ni ba fara ba ce, amma ina da wani irin dogon fuska da siririn hanci, idanuna manya ne dara-dara. Ni ba wata dogowa ba ce, domin yar siririya nake, sai dai fa ina da cikar halitta musamman kirji da kugu, a yanzu da nake shekaru sha shida a duniya, ina ji kamar na kama duk abinda ake bukata, sai dai halin irin na rayuwa yasa na faɗa ƙaddarar rayuwa. "Wacce unguwa kike? Sannan me yasa zaki tafi yanzu bayan baki warke ba?" Kallonta nayi na ce mata. "Ina unguwar hausawa!" Na bata amsa cikin tararadin yadda zata dauki unguwar da na fito. "Ke Bahaushiya ce?" Hadiya yawu nayi,tare da girgixa kai. Kallona tayi kafin ta ce min. "Fulani?" Da idanu na amsa mata, ina lumshe su, gyada kai tayi tana faɗin. "Jiya an kawo ki cikin mawuyacin hali, bamu jima da miki aiki ba, kice zaki tafi?" "Dangina suna cikin wani yanayi!" Na fada kamar zan yi kuka nace mata. "Ni dai zan dawo kuma haka na gaya mata, don Allah ku bar ni naje naga halin da suke ciki." Kallona tayi kafin ta ce da harshen Hausa, "kina son ciwonki kada ya warke ne?" Murmushi nayi kafin na ce mata. "Babu abin da xai samu ciwo na, kawai dai ina son ki kai ni na gansu, don Allah." Na fada mata da hausa. "shi kenan muje!" Ta fita zuwa waje can sai gata da kaya, ta mika min, haka na saka kayan na shiga bin bayanta a hankali, har na isa inda motarta take, wani soja ne ya bude min kofar ita kuma ta shiga baya, suka rufe min motar muka bar asibitin. "Amma me had'aki dashi?" "Wa kenan?" Juyawa tayi tana kallona. "Wanda ya kawo ki?" Hadiye yawu nayi, kafin na ce mata "babu" domin ban san yadda zan mata bayani ta fahimta ba. Har muka fita daga barrack din, ita kanta tunani take a ranta. Yaushe Captain ya fara bin mata? Tasan a iya rayuwarta bata tab'a kama shi da mugun abu ba, kuma har yau babu wanda zai zo ya ce maka mace tana gabanshi. A hankali ta maida kanta nazarin yadda ya ji mata ciwo, gabakidaya kanta ya daure ciwon yana bukatar nazari. Har muka bar barrack, hankalina baya jikina sai da naga mun dauki hanyar unguwar da muke zama, na ji kamar an kuma cilla ni cikin wata sabuwar bala'i "ya zanyi da addah idan ta san na dawo babu kudi sai ciwo." Juyawa tayi tana kallona, ni a tunani na a zuciyata nayi maganar sai na fahimci ashe ba da zuciyata nayi ba, a zahiri nayi. "Zata dake ki ne?" Idanuna ne suka cika da kwalla na ce mata. "Idan duka ne da sauki, mahaifiyata ita ce zata sha zagi." Cikin yanayin dan son ta sha cikina ta ce. "Dama ba mahaifiyarki ba ce?" _Fatimah na hore ki, ki zama me takatsantsan ɗa abin da zai fito daga bakinki. Addah yar Uwata ce kada kuskurenta yasa ki saka duniya ta zargeta._ Hadiye maganar nayi kamar ban tab'a furta koda kalma daya ne ba, kaina a sunkuye muka isa kofar gidan da an yi bala'in cika. Kafin muyi parking motar sojoji ta bar unguwar tana kara da ihun a bata hanya, sai da suka wuce muka samu damar parking, a hankali mutanen suka ragu kowa ya kama gabanshi. Hango Munaisah sun rufe Addah da mutane suke daukarta a waya, da sauri na fara kokarin bude motar, Doctor ta ce min. "Baki da lafiya fa, ki kula da lafiyarki mana." Sauka nayi daga motar a hankali, bayan itama ta fito, ban tsaya jin abinda zata ce min ba, wallahi na zura da gudu."Addah" cikin wani irin yanayi me dauke da kallon kiyayya, tsana, takaici, bakinciki, Addah ke kallona."Zahra'u na gode da abinda kika saka aka min. Zahra'u saboda nace mu mori juna ki bada gishiri a baki manda shine zaki wulakanta ni? Zahra'u duk wani abinda nake bawa Ubanku da mishi kome nan nake sayarwa a bani kudi na tura mishi abinci, na bi maza a Saudiya don na ciyar da Ubanku. Duk yan uwanki suna kyautata min Zahrah kece kawai kika zaɓi kuntatta min. In sha Allah ki rubuta ki ajiye kamar yadda kika saka aka tozarta ni, wallahi sai na d'and'ana miki." "Hajiya kafin ki fara shan alwashi yana da kyau, ki san me ya samu Zahran domin daga asibiti muke; taurin kai da tunda ta kira taji ihun ku, taki kwanciya a ka'idar aikin sai nan da gobe xata fara sauka a gado,amma ta tawo ganin halin da kuke ci!" Ta d'aga mata cikina, inda mutumin duhu ya caka min wuka. Takaici yasa Doctor ta koma motar ta ciro kudi a jakarta,ta kalle ni. "Gashi wannan kudinki ne,wannan kuma ƙatin shiga asibitin ne. Ina fatan zaki dawo a duba lafiyarki" "Zan dawo"na fada mata, ina sunkuyar da kaina. Har ta juya zata tafi nace mata. "Baki gaya min sunanki ba" "Doctor Umaima Amin Minjibir." Daga haka ta juya zuwa motarsu, suka bar ni a tsaye. "Ke Zulaihah kamo hannunta ku shiga daga ciki, kafin matar nan ta dawo ta maida mata kudin,kin san halin zahararriyar kawarki " Gabakidaya Addah ta manta da shegen dukar da aka mata, kun san wacece Addah? Addah ta musamman ce a duniyar kaunar kudi, Ya Allah ka mana tsari da irin soyayyar kudin Addah. A haka kuma duk duniya babu me moranta sama da Baffansu Ummi,baffan mu yana dai rike da dabbobinta ne domin babu yadda ya iya da jarabar Addah. Idan nace zan fara baku labarin kauna da soyayyar da Allah ya daurama Addah kan kudi, sai ku ce karya nake domin haka ba zai faru ba. Addah saboda son kudi. Ta tafi har Saudiya tayi aikin tuwo tuwo.Addah ta zauna a garin lagos tayi harkar tuwo tuwo, kuma kada ku ce iya tuwo tuwon ne fa, A'a har da d'aga buje ana yi babu laifi. Jan hannuna yasa na dawo duniyar tunanin halin Addah, Matar nan kamar Ba ita aka daka ba. Haka muka shiga cikin gidan, Ummi tana gyara gidan. "Shegiya kin zame mana bala'i da masifa, ban san wacce irin ƙaddara ce tasa adda." "Ke kyaleta! Sannu Zahrah sannu yar nan, ke Zulaihah saka min ruwa na gasa jikina." Ta zube kan taburma tana matsar kwalla, kafin na koma can gefe rike da bunch na yan dubu dubu har biyu. Hadiya yawu tayi ganin yadda nake rike dashi. Zulaihah har zata wuce, ta dawo ta amshi kudin ta mika mata ɗaya. "ai kowa yasan g**ndi kika sayar kika ciyar da Kawu shad'ari, duk cikin mu babu yarinyar da fita daya ta dawo miki da dubu dari biyu, sai yar baiwa me kafar sa'a don haka ga dubu dari nan ki warware gajiya, daga yau Kawu shad'ari kudin yar baiwa zai ci, muje Zahrah kici abinci mu koma asibiti. Ina rokon Allah kada yasa ki yi karkon kifi daga ruwa zuwa wuta. Duk me hankali ya ga ciwon nan yasan kin tsallake siraɗin rayuwa da mutuwa " Da sauri Adda ta wawuri dubu darinta,tana washe baki. "Kema dai Zahra hala taurin kai kika mishi,ya burm.. ke daya waye ya turo sojoji suka min shegen duka?" Dariya Zulaihah tayi ta ce "Ai kuwa gajarabul din da ya dauke ta mana ko Zahra?" Bakina ya mutu murus Allah ya horewa Zulaihah baiwar predict duk abinda tayi hasashenshi sai ya tabbata haka. Tsakin Munaisah muka ji, ta juya tana me faɗin. "A gama boye-boye sabo da kaza bai hana a yankata." Ta faɗa tana nufar dakin mu, haka muka bita muka bar Ummi a wurin Addah. Lokacin da muka shiga dakin. Zulaihah ta haɗa min tea, "Zahrah kin gudu a hannun gayen nan ko?" "Eh zuzu!" Na fadi haka, ina kiranta da Zuzu saboda jin dadin sunan, Zulaihah ta girme ni, don kusan sa'ar Munaisah ce, a ƙalla zasu kai shekaru ashirin a duniya. "Zahra'u! Ina kara baki shawara kada ki zama bolar da kowa zai zuba shararshi akai." Na gode na sha tea din kaɗan, sannan ta shirya ya kwashi kayan mu kala uku nata uku nawa uku. Muka fito tana rike da hannuna. Sai lokacin na ga jini yana zuba. "Zuzu mutuwa zan yi?" Na tambayeta, Addah ta fito ta sha kwalliya kamar wata yar tsanar roba, domin bakin nan har da jan baki,ta kalle ni "za a koma asibitin ne?" Gyada kai nayi, murmushi tayi sannan ta ce mana."tow ita Zulaihah da zata bi ki can, ta manta tana da kwastamomi ne?" "Zan tura miki dubu talatin ta account ɗinki!" Kallonmu tayi kafin ta ce mana, "Anya Yaran nan baku cin junanku? Wannan shakuwar tayi yawa ku gaya min gaskiya me yasa kuke zartas da hukuncin junanku. Idan kuna cin juna ne na sani domin a bani kasona domin banga amfanin tara munafukai irinku, kuna cutata ba. " "Yanzu addah don Allah wani yace miki, muna soyayyar jinsi ba zaki ji wani iri b?"wani tsalle tayi ta koma gefe can,"Kambu wallahi bani jin kome,kawai kudin daki zaki kara min na saka a muku shamaki da gulmar su Munaisah an kashe boss." "Allah ya shirya ki Adda" inji Zulaihah muka fita, har waje ta biyo mu, muka tari taxi muka gaya mishi inda zai kai mu,kamar ba zai amince ba, sai kuma ya ce muje. Haka muka tafi har zuwa asibitin,kamar zan yi hauka domin kuwa ciwon ya taso ni a gaba. Haka muka isa har asibitin aka karbi katin, muka shiga. Dr Umaima. Tun dawowarsu bata wuce gida ba, domin yadda Zahrah ta arta aguje tasan sai an dawo da ita dole, don haka bata da wani aiki amma ta kasa tafiya, tana ji kamar akwai abinda take son ta sani dangane da yarinyar, tana asibitin har awa biyu. Aranta tana jin kamar ta tafi, amma Ƙwaƙwalwarta na gaya mata zata zo, haka ta cigaba da tsayuwa har minti ashirin ya wuce idanunta yana kan wayar,minti takwas yazo zai wuce shima daidai babban hannu ya daura kan minti na tara, siririn hannu ya wuce kan taran kenan,taji dirin motarsu, ajiyar zuciya ta sauke tana tsaye idanunta na kan kofar. ....... Dakyar nake jan numfashi, domin zuwa yanzu na fahimci akwai dalilin da yasa jinin yake zuba, muna isa har bakin kofar Emergency,ya tsaya Zuzu ta fito da ni. Muka shiga cikin asibitin. "Kun dawo?" Ta tambaye mu! "Eh Aunty, gashi jini yana ta zuba." "Gudun da ta arta lokacin da muka isa ya haifar mata da zubda jinin" ta fada tana rike ni na kwanta, Zuzu ta fita tare da biyan mai motar kuɗinshi, ta dawo anan aka wuce wani daki dani, Zuzu tana zaune cikin tararradin mai zai faru. *** Addah tana fita bata tsaya ko ina ba, sai gidan Malam Sammani wani dan arewa ne,da yake harkan malunta irin masu duban nan, kallonta yayi yana shafa gemunshi. "Zahra'u!" Ya kara zana sunanta a kasa, ya saki ƙasaitacciyar murmushi."yarinyar nan yar baiwa ce kamar yadda Yarki ta ce, tauraronta karfin tsiya ne da shi, domin ta gaji haka daga Uwarta,da kin barta da dan uwanki da ba karamin arziki zai yi ba, sai dai ƙaddarar da kika kirkira da hannunki ya shiga tsakaninku da arziki, sai dai kici a jikin yarsu. Wato yarinyar nan jiya tauraronta ya hadu da wani raunannen tauraro, kuma Qaddarar da ba a san me zata haifar ba gobe ta shata tsakaninsu. Ban san me zai faru gobe ba, amma tafiyar ƙaddara tana nan da riskanku baki ɗaya. Idan kina son zaman lafiya ki bi yarinyar nan zaki huta kowa zai huta, bayan ita babu wacce zata iya mallakar arziki domin duk inda ta shiga sai ta had'a arziki." "Allah gafarta Malam, ina da mafarki akan Zulaihah ita fa?" Share ƙasar yayi sannan ya rubuta sunan Zulaihah. Dariya yayi sannan ya ce mata. "kamar yadda baiwa take a gaban Uwar gijiyarta haka Yarki take a gabanta" "Don Allah Malam duba min na sauran. " Murmushi yayi ya ce mata. "Sunansu;" "Munaisah!" Rubuta sunanta yayi yasannan ya kalli Addah. "Lallai kin hada masifar da ba zaki iya kashe ta ba, sai Allah babu kome a tare da ita sai bautar da zaku mata, amma.kuma zaki dan huta a jikinta kamar yadda kike hutawa a yanzu." "Ummi fa?" Rubuta itama sunanta yayi, sannan ya ce mata. "Ita wannan igiyar ruwa ce, duk inda ruwa ya jata bi zata yi. " "Malam kace Zahrah zata...." Rubuta sunan Zahrah yayi ya cika tiren, yana murmushi ya ce mata. "Har ki mutu ba zaki daina cin arzikin ta ba" "Malam kana nufin babu wanda zai." Hannunshi ya kai kirjinshi, "na gama aikina indai ba so kike nai miki karya ba,kuma duk inda zaki je babu wanda zai gaya miki wani abun da ya wuce haka, idan aka gaya miki akasin haka karya aka miki wallahi." Kudi ta ajiye mishi, ya girgiza kai ya ce mata."Ni yau bani bukatar kudi, can kasa nake son na rage gajiyata." Wani irin malolon bakinciki ne ya cika Addah, ta ce mishi "tow Malam" haka ta cire kayanta, suka kwanta a dan farin buzun malam na aiki, bayan ya rufe kofar, ai kuwa yazo bai wani mata wasa ko wani abu ba,. malam kamar jaki haka ya zo mata, yana sama da kasa akanta, surfeta yake yana zuba mata rashin mutunci, ta hanyar saduwa da ita kamar wata bebin roba, Addah ta ci azaba a hannun malam kamar ba gobe. *** Operation Anaconda plan. Suna isa bakin ruwa suka shiga cikin jirgin, kowa ya ajiye kayanshi ban da Captain da ya nufi inda matukar jirgin suke, ya fito da Map na inda zasu ya shimfida akan wani table. "Likitan soja, Captain akan ruwa." Murmushi yayi ya cigaba da warware taswirar, sannan ya fito ya sarawa Commodore Magaji Abba Chindo ya ce mishi. "Ko zaka zo ka duba taswirar!". Kafin ya rufe baki Magaji Abba Chindo ya kai mishi naushi, da sauri ya rike hannunshi. "Please Sir kazo ka duba abinda na ce maka." "Idan naki fa " "Shi kenan!" Ya fada yana wucewa, "Guys idan Captain ya dake ni zan bishi sau da kafa, idan kuma na dake shi,kada na kuma ganinshi ya hauro kan ruwa sannan zai zama driver na." "Commodore!!!!" Wasu daga cikin sojojin suka fara kiran sunayensu, wasu na cewa. "Captain!!!" "Look ni bana son faɗa!" "Sai kayi sai kayi!!!" Dama a cikin sojojin akwai waɗanda suke bayan Commodore, wasu kuma suna bayan Captain, na farko yana da matuƙar kamun kai,.yana da nutsuwa da sanin ya kamata, sannan duk inda suka shiga lokacin sallah yana yi zai gabatar da sallah. Babu ruwanshi da hassada ko kyashi,gashi mutum ne mai yawan alkhairi da kyauta, bai da girman kai baki ɗaya, haka Allah yayi shi, abu daya mutane suka sani shi ne, akwai kauna da amana a tsakaninshi da duhu. "Indai kai ba shege bane, ka zo ka gwada mana mazantakarka, matukar ba cin kanka kake a cikin duhun nan ba, ka zo nan, ka gaya mana shin hannunka domin aiki da sarrafa bindiga take zaune, idan kuma domin mulmula doguwar tsokar da take tsakanin cinyoyinka.." Dariya aka kwashe ban da sauran sojojin da suke tare da Captain, suna masifar jin haushin Commodore,amma babu yadda suka iya, sai dai a wannan karon alamar dai maganar tayi tasiri..... #thedambuje [2/16, 9:24 PM] Cutie cutie pie: *BAƘIN HAURE....🐾🐾* {Greed for Money is the roots of all evils🫀} Arewabooks:maidambu41 Wattpad:Mai_Dambu Mallakar:Mai_Dambu *ZINARIYAR MACE⚡* *Wai shin 'yar'uwa menene matsalarki? zubewar nono, ko kuma rashin kwankwason juyawa a falo maigida ya shiririce ya manta da tibi da matan tictok, menene matsalarki ne? rashin ni'ima ko kuma mugun sanyin da ya yi miki katutu, shin rashin taushin fata ne ko kuma kuraje da tabbani, ko bala'in ramar da ta addabeki kuma babu rashin ci ba rashin sha a gidan auranki, gwaigwayewar gashi ce matsalarki ko kuma kaushi da faso na tafin kafa da bushewar fata, kina bukatar fatarki ta yi glowing kalarki ta fita kuraje su mutu, ko kuma kina bukatar azababbun turaruka da humra tare da turarukan wuta. Na san dai kuna da yawa matan da tumbi ya yi musu karan tsaye ina nufin ya katse muku hanzarin yi wa maigida gwalli da muskuce-muskuce a falo😃 Nesa fa ta zo kusa AL-KUTUBIYYA ISLAMIC MEDICINE sun tanadar muku da nau'in magungunan da suke magance kowace irin matsala da izinin Allah. Babban burinmu shine sha'ani na aure ya inganta a samu daidaito. Muna da.* Na gyaran nono. Na sanyi. Dilka tare da hadin sabulu. Duk Wani nau'in maganin mata. Humra turarukan wuta perfumes, original miski tahra 3in1, ciccibi budurwar kaza. Had'addun supplement irin wad'anda ba su da matsala. Maganin Sliming wato narka tumbi. Abubuwan da muke sayarwa suna da yawa, kuma babu asarar dukiya. Muna garin kano kuma muna tura kayanmu kowane gari fad'in Najeria da Nijar har ma da kasashemn ketare. Kai tsaye a tuntu'bemu ta lambobin wayarmu domin karin bayani. *08089965176* *07084653262* *004* *Captain* Juyawa yayi ya kalli Magaji Abba Chindo da yake mishi dariya, idan ya sake suka yi faɗa. Tow yau ba zai iya samun nutsuwa ba, don haka ya saki dan ƙaramin murmushi ya ce mishi. "Sai a ka yi rashin dace, ni mata-maza, bana haɗa jikina da yan maza, musamman waɗanda basu dauki aikata sabo illa ba." Daga haka ya juya abinshi, shiru wurin ya ɗauka, abin ya bawa Magaji Abba Chindo dariya, amma da ya nutsu sai ya fahimci da gaske Captain magana ya gaya mishi. Mikewa yayi zuwa ciki jirgin don da suna daga waje ne. "Kai magana ka gaya min?" Murmushi Captain ya yi sannan ya ce mishi. "Kaga ni bana son tashin hankali, kayi hakuri ba magana na gaya maka ba." Kurawa juna ido suka yi, sannan ya fauce Map din hannun Captain ya yaga gida biyu. "Naga yadda...!" Kafin ya rufe baki Captain ya zabga mishi marin da sai da ya daina gani. D'ago shi yayi ya ce mishi. "Kada ka sake wani yaji wannan labarin domin zai maka dariya, kada ka kuma aikata abin da kayi. Ni idan kaci zarafina zan yafe maka. Amma idan ka taba aikina zan baka sakamakon da yafi haka. " Wato marin nan, ya shiga Magaji domin kuwa hakorin shi na wannan bangaren har yana girgiza. Sauran matuka jirgin duk hankalinsu na kan aikinsu, babu ruwan su kuma haka da Captain yayi shi ne zaman lafiya, don haka, A hankali ya juya tare da fita daga dakin, Captain ya gyara takardan, bayan Mr Oke ya mika mishi salatep, ya gyara suna hira sama sama. Lokacin sallah yana yi suka fita baki ɗaya, musamman Domin a yi sallah wanda Captain ne ya jasu, sannan aka ɗauko abinci da wasu daga cikin sojojin suka dafa, mika mishi aka yi ya kalli agogon ya ce musu. " Na koshi!" Haka suka kyale shi, ya tashi tare da ɗaukar abin hango wasu abubuwan, yana me duba gabansu. Komawa ciki yayi ya dauki wata waya,ya shiga duba sakon. _Sir mutanen nan basa gudanar da kome sai dare yayi,hankalin kowa ya koma tsoron dare. Kada ku shigo da rana domin zasu gudu_ mai da wayar yayi ya ajiye, taya zai yi facing Commodore? Haka ya daure ya fita ya zauna a gabanshi. "Yallabai!" Cikin wani irin yanayi Commodore yake kallon Captain kamar ya shake dan banza amma yanzu ya fahimci gayen ya wuce tunaninshi. Mari daya yayi mishi, hakorinshi yake girgiza ina kuma da sun daku, tow kuwa kareraya shi zai yi ya tara dan iska a gefe kenan? "Meye?" "Inda zamu shiga basa kome da rana, sai dare." "Tow me kake so nayi?" Ya faɗa yana nad'e hannunshi a kirji. "Ina ga a tsaya nan, sai mu duba nisan kafar ruwan, idan nisan ba yawa sai muyi musu shigar dare." "A matsayinka na wa?" A hankali yayi kasa da kanshi kafin ya ce. "A matsayina na soja, kuma shugaban rukunin sojojin da suke aikin sirri, mataimakin ka. Na bada shawara kuma na fita." Ya faɗa yana me mikewa daga gaban Magaji ya nufi dakin iko. Jikin Magaji ne yayi sanyi, kudirinshi shine a kashe Captain a wannan lokacin, kuma ba zai fasa ba. Don haka ya mike tare da fito da sabon tsarin da ya sauya, a ka'idar zuwansu nan. Shi ne shi zai jagoranci wasu daga cikin Yaranshi su isa har inda ake zaton abin, amma son zuciya irin nashi, sai ya kalli Captain ya ce mishi. "Kai da team dinka zaku tafi inda ake badakalar, ni da team dina zamu zauna a nan. Domin ba za a rasa wanda zai iya kawo farmaki ba, idan kuma ba a samu ba kunyi nasara, ga fireworks sai ku sanar da mu." "Amma Sir wannan abin babu tsari, taya kana shugaban sojojin kuma kace Captain zai jagoranci wasu daga cikin mu, kuma mutumin da bai tab'a rike bindiga ba, aikinshi kawai sanin meke faruwa." "Shi namiji ne, idan har ya cika namiji ya jagorancin tafiyar." "Na amince " ya faɗa tare da ware wasu daga team ɗinshi. "Zamu tafi in sha Allah hakkina ne, na bawa rayuwarku kariya,ku yarda da ni in sha Allah zan mai daku cikin iyalanku lafiya." "Mun amince " suka fada, sannan ya shiga musu bayani tare da tara su a cikin wurin tukin jirgin, yana nuna musu yadda tafiyar zata kasance. *** Addah Kallon Addah mutumin yayi ya ce mata. "Ki kula da zuciyarki kada ki aikata abin da zai dame ki, ita yarinyar babu ruwanta." Kasa magana tayi can ta daure ta ce mishi. "Yanzu haka 'yata zata kasance? Babu wani cigaban rayuwa sai ta karuwanci? Karshenta." "Ba farinciki da nutsuwa ake nima ba?" Ya tambayeta yana gyara zaman wandonshi, domin yana matukar jin dadi Adda tana cikin mata na musamman da yake mu'amala da su. Murmushi yayi yana faɗin, " A gaskiya bakya tsufa " dauke kai tayi ta gyara jikinta, sannan ta dauki jakarta ta bar dakin, tana fita waje ta sauke ajiyar zuciya, tana jin wata iriyar tsanar Zahra. Duk inda zata aiki akan zahrah sai ta bada kanta bata san me yasa haka ba, yarinyar ta shiga ruyuwarta ita da take tutiyar ta samu hannun jari, ashe bala'i ta daukowa kanta. Hadiye bakinciki tayi ta shiga kasuwa tayi sayayya. Sannan ta dawo gida ta mikawa Ummi wata leda, ta ce mata. "Ki girka mata wake da hantar mu kai mata asibiti!" "Tow ai basu bamu kati ba" "eh idan kuka isa ku kira Zulaihah." "Hmmm!" Inji Munaisah, ta cigaba da gyaran farcenta, domin tana son zuwa saloon a mata fixing farce. "ina son zuwa saloon dai, domin farce na da kaina yayi datti." Da Ace Munaisah ta san halin da Adda take ciki ba zata fara fadar ita zata saloon ba, dauke idanun tai kanta ta wuce ɗakinta. Sai da tayi wanka ta cire roban condom din mata ta wurga cikin masai din, sannan ta wanke gabanta tass. Sannan ta gyara ta fito, Adda ta san darajar gyaran jiki, shi yasa take gyara jikinta. Duk da abin da take yi be dace ba, amma kuma ita ta dauki haka a matsayin wata hanya ta samun kudi cikin sauki, Aiki take amma a zahirin gaskiya gangan jikinta ke jagorantar aikin, amma zuciyarta da kwakwalwarta basa bata haɗin kai, baki daya ta kashe rayuwarta domin yau ta samu riba, tana son ace yau ta zama wata hamshakiya, amma wani ikon Allah rayuwarta da na Yarta ne a lalace, wanda take ganin ta maida ita baya an gaya mata ba zata iya kome da ƙaddarar ta ba, "hmmm!" Ta fada tana kallon tilin kayan da ta sauke daga wardrobe ɗinta, tana mamakin me yasa meta da wannan aikin? Lallai ya kamata ta mike wannan lamarin sai kace an saka mata hannu. Jin muryar yan matan da suke mata aikin abinci suka shigo gidan yasakata mikewa "Ina Zahrah take?" Jin murya Shamsiyah yasata fitowa daga cikin ɗakinta tana kallonsu. "Tana asibiti ba lafiya." Daga haka ta nuna musu kome da kome da ta sayo, sannan ta wuce ɗakinta ta kwashe kayan. Wurin karfe daya na rana Zulaihah ta kirata. "Wai Addah ba za a kawo mana abinci ba ne?" Runtse idanuwan ta tayi kafin ta lailayo wata uwar ashar ta maka mata, "babban.....,,, ubannki! Ba za a kawo ba kina da abinda zaki fada ne? Shegiya mara mutunci." "Addah dubu dari aka baƙi, idan ba zaki d'aga kafa ba, ki dawo min da kudin mu maza, dawo da saba'in xan baki talatin din." Kamar ta fasa ihu tayi shiru, kafin ta ce mata. "Bana son iskanci, nace ba za a kawo muku ba ne? An jima za a kawo muku." Ta fada a fusace, "Adda ihu kike mana fa?" Inji Zulaihah. "Yanzu don Allah na ce muku ba zan kawo ba ne, ku yi hakuri me da me kuke bukata?" "Yawwa a hada mana da kofi biyu, kayan tea flask da kuma special abinci dare da rana. A kula da mu kamar baki Hajiya Addah." "Shi kenan za a kawo muku." Wannan shine asalin dole kanwar naki. Haka suka kashe wayar, kowa najin babu dad'i ita Addah tana ganin kamar Zulaihah bata kyauta mata, ita kuma Zulaihah tana haka ne domin huce takaicin Mahaifiyarta. *** *Zahrah* Ruwa aka sanya min, bayan an kara duba min ciwon, shi ne aka fito dani, yanzu dai sun saka min ruwa da wasu allurai. Ina jin wayar Zulaihah da Addah, a hankali barci yayi gaba da ni. Ban farka ba, sai wurin karfe uku, na samu Munaisah da Ummi suna hira sama-sama. Zulaihah bata dakin, kallonsu nayi kafin na ce musu. "Kunzo ne?" Domin ban kawo a raina zasu zo ba. Kallona suka yi kafin suka ce min. "Eh amma ke taya aka yi ana yin abun arziki ta kasa ke taya kika kare da gefen cikinki?" Shiru nayi ban ce musu kome ba, shigowar Zulaihah da Dr Umaima yasa ni kallonsu ina kakaro murmushi. Ganin su Ummi da Munaisah sai Dr ta kara yarda wani lokaci halittar kyau da hasken fata bala'i ne, domin kuwa Munaisah hancinta da huji, kunnenta kuwa har saman kunnen a makale suke da barima har da na gwal. Sannan ta kara kallonsu ganin yadda suke wani, iyayi yasa ta sha jinin jikinta waɗannan yan matan sun fini wayewa da gogewa a bariki, ni din kamar sabuwar yankar rake ce, shi yasa har nake gadon asibiti tow ko da ta koma gida ta ji kaninta yana bata labarin ai gida gida, Magaji Abba Chindo ya sa aka yi ta niman wata yarinya da ya dauko daga cikin gari. Kallona tayi tana mamakin anya ba ni ba ce? Duba min ciwon tayi tana faɗin. "Kin yi sallah kuwa?" Girgiza kai nayi. "me yasa kike wasa da sallah.". Kura mata idanu nayi kafin na bude baki ta daura da cewa. "Sallah tana kare mutum daga aikata alfasha, idan har kika kiyayye sallah, a duniyar nan babu wanda ya isa ya cutar da ke, sai dai abin da Allah ya rubuta xai same ki." "Na gode zan kula, bana wasa da sallah amma daga faruwar wannan al'amarin nayi wasa da sallah har subhi da zuhur sun wuce ni" Murmushi tayi sannan ta juya tana kallon Zulaihah. "Idan kika hada mata tea, tayi sallah ko a zaune ne sai ta sha rabin kofi." "Abinci fa, domin gashi an kawo." "Sai jibi saboda tumbin ta ya tabu, tasha tea din idan babu abinda ya faru, zata iya cin abincin." "Shi kenan" ta faɗa tana hada tea din, sannan ta fita daga cikin ɗakin, haka Zulaihah ta rike ni har ban daki ta taimaka min nayi alola, sannan na dawo dakin na gabatar da subhi da zuhur, ina idarwa na amshi tea na sha, ciwon ciki ne ya sako ni gaba, kamar zan mutu kiranta Zuzu tayi suka shigo dakin. Wuce dani wurin scanning aka yi, aka min anan suka ga ɗinkin cikin bai yi da kyau ba, akwai buƙatar a sake min wani aikin yau. Alluran rage zafi tayi min, sannan suka wuce aka fara shirin, a lokacin Adda ta kira su Ummi tana faɗa akan me basu dawo ba, suka gaya mata ai aikin aka kuma shiga dani, babu shiri Addah ta nufo asibitin, domin abin ya bata tsoro kada garin niman duniyarta, na rasa rayuwata. Bata san amsar da zata bawa Shad'ari ba. Haka kuwa ta iso a gigice, tana tsaye har aka fito dani. A galabaice jikinta yayi matukar sanyi, ita tsoro take ji kada na mutu, haka suka bi ni har dakina, "Likita ya aikin?" "In sha Allah an dace, dama na farko munyi shi tare da bin raunin ne, amma na yanzu mun yi shi ne da bin duk inda yake ciwon." "Hmm! Kuma nawa ake bukata? Domin akwai kudi a hannunsu." Kura mata idanu Umaima tayi kafin ta ce mata. "Allah sarki, ai Captain ya biya kome babu abinda ake bukata duk kudin da za a cire a insurance ɗinshi za a cira." "Kai madalla." Murmushi Addah ta sake tana faɗin. "Don Allah ko zaki taya ni amsar kudin hannunsu, ki ce musu akwai wani abu da za a saya." "Hajiya anya kece kika haifi yaran nan?" "Kai haba daya Kyakyawar me dogon hanci da dogon gashi, ita ce na haifa. Ita kuma mara lafiyar da wancan me doguwar riga ruwan toka ubansu daya kanina ya haife su, ita kuma daya fara tas din can itama yar Kani nace, Zahrah ce ta dauki duhun fatar Uwarta ai kin gansu nan." Gaba Doctor Umaima tayi ta barta a nan tana surutu, haka kawai take jin Addah bata mata ba, Indai zaka kawo Yara ka daura su kan wani yanayi mara daɗi, meye ribarta? Itama Adda dakin da aka kwantar dani ta shigo, tana tsaye sai yamutsa fuska take tana faɗin. "Ita dai wannan shegiyar ta san hanyar b'adda kudi loko-loko, ban da iskanci da wulakancin taya zaki kare a gadon asibiti akan ciwon da bai taka kara ya karya ba, mtsew." Ta ja tsaki tana isa bakin gadon yarinyar nan yar bala'i, a ranta domin kuwa ta ga yadda ran kowa yake a b'ace idan ta cika mita kan yanayin da ake ciki. "Tow ai ku muje ko, tunda an yi aikin a sa'a" ta fada tana barin dakin, haka suka bi bayanta ban da Zulaihah da take zaune, ta saka ni a gaba tana kuka. "Ya Allah kai ka jarabce mu Ubangiji ka tashi kafadar Zahrah." Ta cigaba da kukanta, har aka yi sallar la'asar tayi sannan ta koma ta zauna. Shigowa Dr Umaima tayi tana faɗin. "Kuka ya isa haka, ki ci abinci." "Ba zan iya ci ba, bayan Zahrah tana kwance." Shiru suka yi, sannan Dr ta ce mata. "Matar nan Mamarki ce?" Rintse idanunta tayi tana jin kamar an watsa mata ruwan zafi a jikinta, don dai Allah ya ƙaddara zata zo a tsagin addah ne amma da ba zata tab'a yarda a ce Addah mahaifiyarta ce ba. "Eh Mamata ce." "Allah sarki naga kuna kama sosai." "Eh haka mutane ke faɗa muna kama da Adda, shi yasa duk lokacin da wani ya ganni sai ya tambayeta ko ya tambaye ni." Daga haka tayi shiru itama Dr Umaima bata zake sai ta san kome akanta ba, amma zucuyarta ta kwadaitu da son sanin wacece Ni? ★★ Tarkon makiya Bayan an yi sallar Isha, da ya jagorance su, yayi musu addu'a. Sannan ya mike tare da kallon sauran abokan shi da suke su bakwai ne, sauran kaso masu girman suna tare da Commodore Magaji Abba Chindo, murmushi yayi sannan ya dauko kayan aiki, yana kuma da kayan da zasu saka idan zasu faɗa cikin ruwa. "John ko zaka zauna anan ne naji kace matarka ta kusan haihuwa." Daukar kayanshi yayi yana sakawa, "Cab ai nayi Imani da Allah, amma gara na mutu a filin yaki da ace ina nan, ina jiran dawowarku." Ya fada yana saka rigar ruwanshi domin ana iska don har tana kad'a jirgin ruwansu. "Ammar kai ma ko zaka zauna ne, kace rabonka da Misau tun haihuwar Anam, saboda inda zamu mutanen suna dauke da miyagun makamai." "Hmm! Fatana kada Kasata ta mance da 'ya ta." "Kana nufin zaka bi ni kenan!" Haka yayi ta rokonsu da su hakura da bin shi, amma ina baki daya suka nace, sai sun bishi anan ne suke ta hira da zasu tafi wurin karfe tara na dare, ya dauke su zuwa wurin Commodore. "Zamu tafi Sir! Dayawa sun daura hakkin kula da rayuwarsu akanka da kuma ni, Sir sun yarda da kai ne suka gwammaci su zauna da kai, Sir hakkin mu ne mu kare kasarmu da mutanen da suke karkashin kulawarmu. Please Sir gasu nan" Har ya gama maganar Magaji Abba Chindo,bai ce mishi cikanka ba domin kuwa baya fatan ya bude baki yayi magana, Babban burin shi Captain yana barin jirginsu yan tada kayar baya su yi musu daga-daga da namar su, shi yasa da ya ce ya tafi,ya fara bin sauran yana gaya musu ai fa Captain da suke ganin zasu bi, bai da lafiya da zaran an fara harbe-harbe cutarshi zata motsa. Muna cikin zamani ne da son kai yayi mana katutu, kowa son ranshi yake haka yasa baki daya suka janye bin bayan Captain. Kuma an gayawa Captain amma kuma bai ce kome ba, domin bai dauki haka a matsayin wani abu me muhimmanci ba. Yasan Commodore Magaji Abba Chindo yana jin haushinsa, amma kuma bai kawo a ranshi kiyayyar zata girmama haka ba, sai dai ya ce Allah ya kyauta. Haka suka bar wurin da jirgin yake da wasu kananun jiragen ruwan, masu colour din navy blue. Haka suka shiga tafiya daidai an fara ruwan sama me karfin gaske. Haka suka yi ta tsala gudu, a nan Jirgin aikinsu, suna barin wurin aka shiga shagali da hidima, dama kafin dare sai da Commodore ya tura wasu matasan sojoji biyu suka kwasu musu yan mata, aka shiga shagali. Haka yasa yaki barin Captain zama domin, yasan matuƙar yana nan ba zai bari ayi shagalin ba, asalin sun manta da aiki suka zo yi, haka yasa suka yi ta shagali ga shi ana ta ruwa kamar da bakin kwarya. ---- A bangaren Captain da mutanen shi, ba karamin gudu suke ba, kasancewar takun yana jan jirginsu, karshe shi ya amshi tukin, ya kalli John ya ce mishi. "Da matukar hatsari fadawarku ruwan nan, a daidai wannan lokacin don haka tunda ana ruwa ku kashe fitilar goshinku, zamu isa har jikin jirgin." "Ok Sir" shi ya fara kashe wutar nashi sauran mutane bakwan suka kashe nasu. A hankali suka yi ta tafiya, har suka isa wurin babban jirgin da yake dauke manya cantainers, zuwa kasashen waje. Tsayawa suka yi kusa da jirgin, sannan suka harba abin da zai rike su idan suka sauka daga cikin jirginsu. Hakance kuwa ta faru duk su bakwai suka shiga cikin ruwan bayan sun daure kugunsu da wata igiya, sannan suka fara hawa jikin jirgin har suka shiga saman jirgin. Babu kowa, Captain shi ya musu jagora, har cikin jirgin inda ya fahimci za a fara kwasar man saura wani lokaci kadan, don haka suka samu maboya suka boye, tare da samun bayanai akan kari. Sun kai wurin karfe sha biyu kafin aka fara aikin kawo danyen man fetur din, don haka sai da suka samu damar musu kawanya, kafin suka bude wuta a sama, dole yan daban suka yarda makamansu, domin abin ya basu mamaki, "dama sojojin da aka kaiwa hari daban ne da waɗannan sojojin?" Inji Shugaban yan daban. "Captain ka ji sun kai hari jirginmu......... Waye zai mutu? Waye zai rayu follow my golden Pen. #Thedambuje [2/16, 9:24 PM] Cutie cutie pie: *BAƘIN HAURE....🐾🐾* {Greed for Money is the roots of all evils🫀} Arewabooks:maidambu41 Wattpad:Mai_Dambu Mallakar:Mai_Dambu *ZINARIYAR MACE⚡* *Wai shin 'yar'uwa menene matsalarki? zubewar nono, ko kuma rashin kwankwason juyawa a falo maigida ya shiririce ya manta da tibi da matan tictok, menene matsalarki ne? rashin ni'ima ko kuma mugun sanyin da ya yi miki katutu, shin rashin taushin fata ne ko kuma kuraje da tabbani, ko bala'in ramar da ta addabeki kuma babu rashin ci ba rashin sha a gidan auranki, gwaigwayewar gashi ce matsalarki ko kuma kaushi da faso na tafin kafa da bushewar fata, kina bukatar fatarki ta yi glowing kalarki ta fita kuraje su mutu, ko kuma kina bukatar azababbun turaruka da humra tare da turarukan wuta. Na san dai kuna da yawa matan da tumbi ya yi musu karan tsaye ina nufin ya katse muku hanzarin yi wa maigida gwalli da muskuce-muskuce a falo😃 Nesa fa ta zo kusa AL-KUTUBIYYA ISLAMIC MEDICINE sun tanadar muku da nau'in magungunan da suke magance kowace irin matsala da izinin Allah. Babban burinmu shine sha'ani na aure ya inganta a samu daidaito. Muna da.* Na gyaran nono. Na sanyi. Dilka tare da hadin sabulu. Duk Wani nau'in maganin mata. Humra turarukan wuta perfumes, original miski tahra 3in1, ciccibi budurwar kaza. Had'addun supplement irin wad'anda ba su da matsala. Maganin Sliming wato narka tumbi. Abubuwan da muke sayarwa suna da yawa, kuma babu asarar dukiya. Muna garin kano kuma muna tura kayanmu kowane gari fad'in Najeria da Nijar har ma da kasashemn ketare. Kai tsaye a tuntu'bemu ta lambobin wayarmu domin karin bayani. *08089965176* *07084653262* *005* "Captain mai zamu yi?" Shiru yayi yana kallon yan tadda daya bayan daya. "Sir me zamu yi?" A hankali ya saka hannunshi ya ballo tear gas, tare cilla musu, sannan suka ƙare fuskokin su, ai kuwa sai ga hayaki fuuuuu, haka yasa shi shiga cikin hayakin tare da kama su sannan suka daure su baki daya, kafin ya mike yana faɗin. "John zaka tsaya anan, kai dasu Ammar, duk wanda ya motsa ku sakar miishi wuta ko waye shi?" "Ok Sir!" Sai da ya karkasa su sannan ya sauko ruwa ya nufi inda jirginsu yaƙe na aiki. Sosai yayi shirin tunkarar asalin jirginsu da aka kaiwa hari. Koda ya isa ya samu babu kowa a cikin jirgin sai wasu mutane biyu, da suka jikata sosai. Durkusawa yayi a gabansu. "Me ya faru?" Cikin azaba da Harbin da aka mishi ya fara bashi labarin. "Muna cikin shagali bayan tafiyarku sai kawai muka kaji ƙaran harbi, ashe yan fashin tekun ne suka mana tarko." A hankali ya mike tsaye duk da ruwan da ake yi, dafe kanshi yayi ya koma cikin jirgin mutum daya ne a cikin matuƙan ya tsira shima yadda ya fada don ya shiga ban dakin kasa Allah ya kubutar dashi. "Yanzu ka juya da jirgin zuwa headquarter zan tawo da sauran mutanen." Ya fadi haka yana fita daga jirgin, a hannun dayan mutumin ya samu takarda. Amsa yayi yana dubawa, *Mun ji labarin baka tab'a fita operation ka fadi ba, so wannan karon ka zo ka amshi yan uwanka sannan ka sakar min mutane na, ko na kashe Commodore.* "Zaku wuce headquarter zan tawo da wancan jirgin." Ya fita da sauri ya koma asalin jirgin yan fashin tekun, tsoron shi daya kada suma tarko aka musu. Koda ya isa ya same su, ajiyar zuciya ya sauke sannan ya saka aka karkato kan jirgin, baki daya suka nufi headquarter ɗinsu,. Suna isa dama labarin ya isa an kaiwa jirginsu hari har an sace wasu sojojin. Yana isa da wadanda aka harba, asibiti aka wuce da su. Admiral da kanshi ya zo inda aka ajiye jirgin. A lokacin karfe biyu na dare, "Sir!" Ya sarawa Admiral. "Aiki yayi kyau, yanzu wani hali Magaji yake ciki tare da sauran abokan aikinku." "Umarni nake jira mu sake sabon shiri." Captain ya faɗa yana sarawa. "Zan duba lamarin yau, amma tabbas dole a kai musu ɗauki." Mika mishi takardar da aka ajiye musu yayi. Shiru Admiral yayi yana kallon takardar. "zan tura yau kafin gobe zan nema maka _permission_ " "Ok Sir!" Ya sara mishi, sannan suka bar wurin aka wuce da mutanen da suka kamo, lokacin da ya shiga barrack din baki daya labarin ya karad'e cikin barrack din, waɗanda mazajensu suke hannun hankalinsu ya tashi, waɗanda mazajensu suke asibiti, a daren wasu suka yi ta wucewa, su kuma suna tafiya a mota. "Yallabai wannan abin da ya faru, da damu zai faru Allah ya tsare mu." Gyada kai yayi yana kallon hanya, kofar gidanshi aka sauke shi, kasancewar shi ne babba a cikinsu. Sai da ya fito ya ce musu. "Kada ku manta ku kula da kanku. Idan sun gama zamu tafi gobe ko jibi." "Ok Sir!" Sannan ya ce musu. "Ku kula da iyalinku." Ya wuce ciki da sauri, yana shiga ya sauke ajiyar zuciya bayan ya shiga da sallama, a ka'idar wannan operation din ba a fita da waya, daga nesa ya hango wayarshi yana haske, a matuƙar gajiye ya isa wurin. *Brother* ya gani baro-baro a saman screen din wayar, a hankali yayi picking yana sakawa wayar a kunnen shi. "Baka yi barci ba?" "Taya zan yi barci bayan wurinka na zo." "Ka koma, ina da abinda zan yi nan da kwana biyar." "Ai na gama nawa kawai, ka shirya." Brother ya gaya mishi. Dafe goshi yayi yana sosawa ya ce mishi. "Ka koma inda ka fito, don Allah." "Babu inda zan tafi." Yana fadar haka ya kashe wayar. Zama yayi jikinshi da matukar damuwa. *Zahrah* Muna kwance muka ji kar'ar motar daukar marasa lafiya. Kafin wani lokaci asibitin ya cika da hayaniyar mutane. Har kusan karfe hudu na asuba, can sai ga Dr Umaima ita da wasu Nurses su uku. "Baku yi barci ba?" Girgza kai nayi nace mata. "Eh Aunty, amma lafiya?" "Sojojin mu ne suka hadu da tsautsayi, Sisi kira mana Captain aikin nan ba zan yi ni daya, sannan ki haɗa da Mrs Kayode hutun ya ƙare." A hankali ta tawo kaina. "Nasan kuna da hankali, please ku kula da kanku sannan kada ku ce wani abu." Gyad'a kai nayi nace mata. "tow Aunty Umaimah." Fita suka yi, can kuwa muka kara jin hayaniyarsu ya karu, Zuzu kan duk abin da ake tana ta barci, sai da na gaji na tashi zaune ina yatsina fuska. Suna fita basu wani ɗauki wani lokaci ba, suka yi ta kiran wayar likitocinsu. Haka suka halarta kafin wani lokaci sun fara aiki, kafin karfe shida na safe, sun fito daga aikin. "Captain ko zaka kwanta ne?" Ta tambaye shi cikin kulawa, domin Allah ya jarabceta da kaunarshi, amma shi babu haka a ranshi. Gyada mata kai yayi, ko bude idanunshi baya iyawa balle yasan inda yake jefa kafarshi, haka ta juya itama ta bar sauran aikin a hannun Mrs Kayode ta tafi gida. Dama mun yi da Zuzu karfe shida zata wuce ko shida saura domin tun fitar Dr Umaima, itama ta farka ta leko mana abinda yake faruwa. Har tayo saurayi a cikin sojojin. Shi yace zai kai ta gida, muna idar da sallar asuba, ya zo suka tafi ni wani barci me karfi ya dauke ni. Ko don mun raba dare bamu yi barci ba ne. Haka nayi ta barci kamar me, yana shigowa ko don ya gaji ne, kawai yana shigowa ya kwanta. Tuni barci yayi gaba da shi, duk da yana son yin sallar asuba, amma ina barci me nauyi yayi gaba da shi. Wani ikon Allah dukkan mu biyu babu wanda ya fahimci halin da dayan mu yake ciki. Har wurin sha biyu lokacin Nurse tazo duba ni, anan ta same mu kwance ya tattara ni ya cusa cikin jikinshi ni kuma kamar mage na kwanta kwayam kamar mage, ko yanayin ba mamaki ko dumin da muka ji daga junanmu ya haifar mana da barci me nauyi, ganin haka ta juya tana me barin dakin, Dr Umaima ta kira ta gaya mata. Ai babu shiri sai gata a asibitin, tana isowa Zuzu tana isowa itama. Kallon juna suka yi, kafin Dr Umaima ta ɗan bata rai tana faɗin. "Ki jira ina zuwa."tana faɗin haka ta shigo, a hankali ta tashe shi, kaina yana kirjinshi, hannunshi dukkan biyu ya zagaye ni dasu. Sake tab'a shi tayi ya buɗe ido dakyar yana kallon ta. "Kafin ka dawo hankalinka ya kamata ka san inda kake." Kallonta yayi, sannan ya kalli inda nake kwance. Bai ga fuskata ba, amma baki daya yaji lissafinshi ya fara aiki kamar wanda ya aikata wani mugun aiki, ya ware manyan idanunshi ya kafeta da shi. "Su waye a waje?" Sanin ko ta fusata ba zai dame shi ba. Ta ce "babu sosai." A hankali ya zare jikinshi a nawa, kafin ya saka kafarshi cikin takalminshi, yana kallonta. "Baka duba ciwon ba, sau biyu aka yi aikin fa." Cikin kamewa da nuna kamar bai aikata kome ba, "Good!" Ya saka kai ya fita. "Karfe nawa?" Agogon hannunta ta kalla ta ce. "12:30" "innalillahi'wa'inna'ilaihi'raji'un! Ban yi sallah asuba ba." "Sai dai sallah safe." Inji Dr Umaima. Da dan sauri ya bar ward din, dama dabi'arshi ce matukar yayi aikin dare tow ba makawa sai ya shiga daki daya yayi barci, a gidanshi baya iya barci kwana yake yana mafarki. Koda ya fita motarshi ya faɗa, da gudu yana shiga ya bata wuta, kan lokaci ya isa gidan, a kofar gidan ya taradda motar bmw, sai da ya tura motar gefen gidan,a kasar bishiyar lim, yayi parking da sauri ya fito tare da kallon inda motar take. Bai ga alamar da wani ba, haka ya wuce motar ba tare da ya kalli inda motar take ba, ya shiga kokarin buɗe kofar gidanshi, a hankali yaga kofar a buɗe yaƙe. "Emmanuel yazo aiki kenan?" Ya tambayi kanshi,cikin gidan ya shiga tare zubawa wanda yake zaune idanuwa. Dauke wuta yayi tabbas a duniya an rena shi. Wucewa yayi a gaggauce ya nufi dakinshi. "Na ga kayan jini, na san baka fara kisan kai ba, balle na ce ka fara amma na wanke Yaronka bai sani ba, domin ya same ni a kofar inajiranka." Bai ce mishi cikanka ba, ya wuce dakin yayi wanka da alola yazo ya gabatar da sallar asuba, sannan ya hada da zuhur. Shima bakon zuhur din yayi sannan ya wuce kitchen. Abinci ya dafa musu mai kyau sai kamshi yake, a hankali ya nufi falo da abincin, ya ajiye nashi sannan ya wuce da na Captain ɗin ya ajiye mishi a gabanshi. "Kaci nasan kana nan kana wasa da cikinka, ga aikinka aikin hatsari ne." "Me yasa baka jin magana?" Ya tambaye shi yana kallonshi. "Ni kuma? Ai idan akwai mara yafiya da rashin jin magana kai ne dai baka jin shi, kai a dadin ranka ne ka bar mahaifiyarmu tana kuka tana gayawa Allah yaushe zaka dawo gare ta? Ya Majeed duk abinda ya wuce ya wuce, a barshi ya wuce ban ga amfanin datse alaƙar da kayi ba." "Aryan ka koma kace baka ganni ba." "Zan koma amma ka sani na gama abin da ya kawo ni, gashi ka duba." Ya ajiye mishi takardar izinin tafiya da Captain Majeed Mamman Ba'are, kuma Doctor a wani bangaren. "Akan me zaka min haka?" "Muna da Kyakyawar alaƙar kasuwanci da kamfanonin mu da mahukuntan Nigeria, don haka kai tsaye daga sama na liko da kai kasa, don haka sun baka hutun wata guda." "Kasan hatsarin da abokan aikina suke ciki?" Ya fada a fusace, "bai kai hatsarin da BA'ARE GOLDEN EMPIRES yake ciki ba, sai ka zab'a saura kwana uku zaben, su kuma abokanka, zai dauki sati kafin su fito domin sun bada zabin a sake musu kayansu ko su kashe su. Na gama hada maka kayanka." Ya fada yana ƙoƙarin barin dakin yana faɗin. "Akan shegen aikin da albashinsa bai wuce a sayawa karen gidan mu abinci ba, kazo zaka kare rayuwarka akanshi." Shiru yayi yana kallon abincin, tabbas abubuwa dayawa sun faru. Amma kuma ba zai tab'a yarda ya rike musu kome ba, zai dawo bakin aikinshi. Kamshin abincin yasa shi jin wani irin yunwa, da sauri ya fara ci, shigowar Aryan Ba'are yasa shi d'ago kai yana kallon shi, zama yayi a gaban Aryan Mamman Ba'are, murmushi suka yiwa juna, zama yayi ya juye abincin kan na Captain Majeed, suka fara ci hawaye na zuba daga idanun Aryan Mamman Ba'are, diban abincin yayi a cokali ya mikawa Majeed din, amsa yayi yana kallon shi, "kayi hakuri saura kwana huɗu ne ba uku ba, na fahimci yadda kake son aikinka." "Ba kome." Ya diba shima ya bawa Aryan Mamman Ba'are, amsa yayi yana ci, d'aga kai Captain yayi yana maida kwallarshi. "Kayi hakuri!" "Ai ba fushi nake ba, kawai dukiyar wancan mutumin ne bana son alaƙa da shi, don Allah ka." "Ba dukiyar shi bane yanzu, dukiyarmu ce wanda naka da kaki amfani da shi yafi karfin tunanin kowa. Duk hannun jarinka sun fi na kowa yawa,.kaga yawan kudinka." A hankali ya bude baki zai magana Aryan Mamman Ba'are ya cusa mishi abincin a baki, dole ya ci. "Maganar aurenka ma Hajiya tana son lallai ka koma ayi maganar aurenka." "Ni bana son." Tura mishi abincin yaƙe yana murmushi, karfi da yaji Aryan ya hana shi magana, kuma yayi shiru ya ci abincin tass, sannan ya bude mishi ruwa ya sha, sannan ya mike yana kallon shi. "Me ya faru? Naga jini a zanin gado da sauransu." "Ba kome fa." "Nasan baka fara bin mata ba, amma wannan sarkar fa." Shiru yayi yana kallon Aryan. "Ban san me ya faru ba, kawai dai." "Amma kuma." Girgza kai yayi, Aryan ya san halin ba zai tab'a magana ba. A hankali ya mike ya dauki wayarshi, ya kira Admiral. Sun jima suna magana, sannan ya koma cikin dakinshi can sai gashi dauke da kayan aiki. "Zan tafi kwana biyu in sha Allah zan yi." "Nayi alkawarin maida mata kai gida, zan zauna har zuwa ranar." "Shi kenan!" Ya faɗa ya fita daga cikin gidan. *Asibitin!* Wato yana tashi daga gadon, ina bude kanana idanuwa na da suke cike da barci. "tashi" inji Zuzu. "Ke wani irin dumi naji, shi yasa nayi ta barci." Murmushi tayi min sannan ta ce. "Zahrah kin san dumin da kika ji?" Girgiza kai nayi ina kallonta, dariya tayi min sannan ta ce min. "Dumin wani Kyakkyawan soja kika ji, ke dama ana samun Kyawawa ne a sojoji?" "Ke!" Na ware idanuna, ina shafa jikina. "Da fatan bai min kome ba?" Na fada ina zare idanu. "Namiji fa?" Gimtse fuska tayi tana hararata, "Sai hakuri domin ya b'arar miki da darajarki sai dai mu taru mu kwashe." "Ke Zulai!" Na san a duniya ta tsani na kirata da Zulai tun muna yara, don haka ina cewa zulai ta ce. "Zan ci mutuncinki banza babu abinda yayi miki." "Allah ya huci zuciyarki." Daga haka na rufe bakina. Ban daki ta shiga ta haɗa min ruwan zafi,.na shiga na kama ruwa sannan na fito da alola. Abin sallah ta shimfida min nayi sallar, asuba da zuhur ina istigfari,domin nayi laifi me girma na wasa da sallah, koda na idar addu'a nayi sosai sannan na tashi zuwa bakin gadon. A hankali nake jin wani irin kamshi yana tashi me matukar dad'i da sanyi, ware ido nayi ina kallon Zuzu. "Zuzu kamshi me nake ji?" Kamshi kuma?" Gyad'a kai nayi ina kallonta. Itama ni take kallo, dube dube muka shiga yi, a hankali Zuzu ta d'aga pillow da yake gadon, wani ƙaramin hanky ne yake wannan azabebben kamshi. "Mtsew ji abin da yake kamshi." Na ja tsaki, ina kokarin gyara zama, fari ne kal a hankali na warware. Gefen zanen wani babban gida ne kamar masarauta gashi nan kamar castle. An rubuta BGE. "Mene ne ma'anar wanan kalamar?" Na tambayi Zuzu. "Adda mai tuwo tuwo!" Ta fada min hankalinta kwance. "Amma dai ke dai anyi yar banzar Y'a." "Tow shi kenan sunanshi Fadimah Zahrah Buba Shad'ari." "Bana son b.... uba." "Na waye? Nawa ko naki ko najin dadin bakinki?" Abinci ta saka min kaɗan, duk da dama aikin ai ba wani aiki na tashin hankali ba ne, a hankali nake kurbar shayi, ina kallonta. "Zuzu!" "Na'am!" Ta amsa tana kallona. "Kinyi alƙawari ba zamu tab'a cutar da juna ba?" Na mika mata hannuna, "Me yasa kika bukaci haka?" Ta tambaye ni, murmushi nayi ina kai abinci bakina, a hankali na d'ago kai ina kallonta. "Ban sani ba, amma kuma nasan dai wata rana zamu iya cin amanar juna." Amsar kofin hannu na tayi da plate ɗin,ta ajiye, a duk lokacin da tayi haka nasan me take nufi. "kin san an min aiki." Na faɗa idanuna rau-rau. "Mtsew! Kin ci sa'ar ciwon jikinki da kin sha mamaki." Dariya nayi mata, sannan na cigaba da karyawa ta, har na gama ta balla min maganin da na gani ta Ciro a lock din gadon ta mika min. Da ruwan tea na sha ina son tmbayarta Addah amma nasan halinta bai zama dole ta bani amsa ba. "Ya Addah take?" "Lafiya lau!" Kallon fuskarta nayi naga kamar a dakile. "Wani abu ya faru ne?" "A'a." Ta fada tana leka wayarta, kawai na sha jinin jikina haka kawai Zuzu ba zata sauya ba. Sai na share kawai ban ce mata kome ba. Tuna abin da ya faru a komawarta gida yasa baki daya, ranta ya kara b'aci da maganar Zahrh Lokacin da ta koma gida, ta samu Addah tayi bakon wani mutum, tunda ta gansu a dakin Addah tasan mutumin ba na alkhairi ba ne, duk da ba yau din ya fara zuwa ba, sai dai kuma zuwan shi na yau kamar niman shi aka yi, shi din d'an bori ne. Haka yayi ta tsalle yana ihu, kafin can ya fara gyatsa. Ya fashe da dariya, yana nuna Addah da hannu. "Tabbas baki da arziki a jikinta a yanzu, sai gaba zaki ci arzikinta sama da yadda kika zata. Ƙaddara ta hadata da shi, maza ki nisanta ta daga wannan duniyar zuwa wata duniyar, domin kuwa kika sake suka kuma haduwa ba zaki kara morarta ba har abada." "Nazimu ya zanyi? Ita Zulaihah bata da gobe ne?" Ta faɗa a hankali. Gyatsa ya sake yana dariya. "Gobenta yana manne da yarinyar da take asibiti." A dame ta kalli Nazimu ta ce mishi. "sauran yan matan fa?" "Hmmmm! Itace inuwarsu." "Babu yadda za ayi a mallake min ita?" Shafa gemunshi yayi ya ce mata."ba zan iya wannan aikin ba,lokaci na zuba da zaki amfana da rashin haka, idan aka mallaka miki ita ba zaki tab'a samun biyan bukata ba." "Nazimu kace na dauketa daga nan?" Gyad'a kai yayi yana gyatsa. "In sha Allah wani sati zamu wuce Taraba!" "Dakyau. Ki nisantatta da nan domin zai bincikota."yana gama fadar haka ya fara kwara amai, nan Addah ta fito ta gaya musu zasu tafi Taraba, shiru kowa yayi a cikinsu. "Addah kinsan muna zuwa za a fara maganar munki aure fa." "Ba zamu wuce kwanaki uku ba, tunda zamu bi motar dauko shanu ne,iya kwanakin da zamu yi uku ne, idan kuma kuna son zama anan shi kenan " "A'a zan tafi naga Yakumbo na kwana biyu ban ganta ba."inji Ummi, "Nima zan je na ga Nenne na!...... #Thedambuje [2/16, 9:24 PM] Cutie cutie pie: *BAƘIN HAURE....🐾🐾* {Greed for Money is the roots of all evils🫀} Arewabooks:maidambu41 Wattpad:Mai_Dambu Mallakar:Mai_Dambu *ZINARIYAR MACE⚡* *Wai shin 'yar'uwa menene matsalarki? zubewar nono, ko kuma rashin kwankwason juyawa a falo maigida ya shiririce ya manta da tibi da matan tictok, menene matsalarki ne? rashin ni'ima ko kuma mugun sanyin da ya yi miki katutu, shin rashin taushin fata ne ko kuma kuraje da tabbani, ko bala'in ramar da ta addabeki kuma babu rashin ci ba rashin sha a gidan auranki, gwaigwayewar gashi ce matsalarki ko kuma kaushi da faso na tafin kafa da bushewar fata, kina bukatar fatarki ta yi glowing kalarki ta fita kuraje su mutu, ko kuma kina bukatar azababbun turaruka da humra tare da turarukan wuta. Na san dai kuna da yawa matan da tumbi ya yi musu karan tsaye ina nufin ya katse muku hanzarin yi wa maigida gwalli da muskuce-muskuce a falo😃 Nesa fa ta zo kusa AL-KUTUBIYYA ISLAMIC MEDICINE sun tanadar muku da nau'in magungunan da suke magance kowace irin matsala da izinin Allah. Babban burinmu shine sha'ani na aure ya inganta a samu daidaito. Muna da.* Na gyaran nono. Na sanyi. Dilka tare da hadin sabulu. Duk Wani nau'in maganin mata. Humra turarukan wuta perfumes, original miski tahra 3in1, ciccibi budurwar kaza. Had'addun supplement irin wad'anda ba su da matsala. Maganin Sliming wato narka tumbi. Abubuwan da muke sayarwa suna da yawa, kuma babu asarar dukiya. Muna garin kano kuma muna tura kayanmu kowane gari fad'in Najeria da Nijar har ma da kasashemn ketare. Kai tsaye a tuntu'bemu ta lambobin wayarmu domin karin bayani. *08089965176* *07084653262* *006* Juyawa tayi ta kalli Zulaihah,kafin ta ce mata. "Baki da ra'ayi ne mu barki anan?" Murmushi tayi iyakarshi lebbenta. Ta ce mata. "Ina da ra'ayin idan na tafi nima ba zan dawo ba, aure zan yi domin na samu mijin aure " dariya Addah tayi sannan ta ce mata. "Ta yaro kyau take bata karko, Allah ya kai mu zulai." Har ta juya zata tafi ta ce mata. "Ki sani matukar muka tafi kika zauna a can, duniya sai ta san me kike aikatawa balle mijin da nake da yakinin shi kike hari." "Addah barazana kike min?" Itama ta mike tsaye, tana kallon Addah. "Kashedi nake miki, kuma idan na miki barazanar ai ba laifi ba ne. Saboda ai da kome nawa kika kawo haka, sannan idan nace zan miki barazana ba laifi ba ne." sannan ta juya ga Ummi ta ce mata. "Ko nayi laifi a cikin wannan maganar?" Girgza mata kai suka yi, domin Allah ya zuba musu shakkar Addah idan ka cire Zulaihah, da sam bata shakkarta, ɗakinta ta koma ta kalli Nazimu. Kamar zata fashe da kuka. "Yarki bata da matsala, halayyarku ce da bambanci, ita ba zata iya abin da kike yi ba, domin tana da kirki da nutsuwa shi yasa halayyarsu da jininsu ya hadu da Yarinyar can, don haka ina baki shawara da kada ki sake, ki takura Yarki domin duniya ki sarara mata." Gyad'a kai tayi tana faɗin. "Itama tana da farin jini fa." "Eh mana, amma kuma kila yawan takurar da kike mata zaisa ta iya rabuwa dake na har abada." Dafe kirji tayi tare da cewa. "Don Annabi?" Wannan ne karon farko da Addah ta kira sunan Annabi Muhammad Sallallahu alaihi Wasallama,domin ba dabi'arta ba ne kiran sunan Allah. Yadda Nazimu yayi kasa da murya yasa ta nutsuwa tana sauraron shi, sannan can yana gamawa ya mike ya fita, Munaisah ta shiga dakin ta gyara, "Ya gaya min maganar chef yace wai yau ki saka wannan turaren zaki samu alkhairi sosai a wurin shi." "Kai Addah ni ai mota nake son ya saya min." "Banza sakarya motar kaniya, idan kika samu kudi saniya zaki saya da shi a fara ajiye miki." "Kuma haka yayi fa, Addah ya batun Zahrah?" Tsaki tayi tana tab'e baki, zata tafi can ta hadu da wancan dan iskan Yaron, su kare kalau ni ina zargin anya Yaron nan bai gama lalata Zahrah da take jin ba zata iya wani abu sai da shi ba." Addah ta faɗa tana kallon Munaisah, "Uban waye ya sani, shegiya munafika ni ban son tayi aure domin haka zai saka a samu a gaba da munki aure sai zaman bariki." Shiru Addah tayi tana kallon Munaisah ta sake murmushi ta ce mata. "Da ni kuke zancen, ki bar kome a hannu!" Daidai shigowar Zulaiha. "Wa makaru wa makrallahi wallahu khairar makiri." Tana fadar haka Addah ta zuba mata idanu, "zan tafi asibiti." "Allah ya tsare." Juyawa tayi ta fita, amma ranta soye yake... "Ke tunanin me kike yi ne haka?" Tab'e baki tayi tana faɗin. "Babu kome!" Ta fada tana kallon wayar. Ba zan iya ganinta cikin wani yanayi na Kyaleta ba, don haka na ce mata. "Zuzuna gaya min!" A hankali ta d'ago kai tana kallona kafin hawaye ya zubo mata."Zahrah kin ji dadinki,tunda kike baki tab'a zina ba, sannan baki tab'a yarda kin lalata tarbiyyar da Kawu shad'ari ya miki ba, Zahrah wani sakayya zan bawa mijin da ya aure ni?" A hankali ta fashe da kuka, sosai tana yi tana karawa. "Kada ki manta Allah xai baki mijin da zai kauna ce ki a duk yadda kike, kin ga yanzu da kin yarda kin amince kin koma diplomar nan, ai da yanzu saura watanni zamu gama, na gaya miki ba zina yake bada abinci ba, a'a yarda da Allah, Zulaihah kin bi na Addah kina lalata gobenki, bayan su mazan abin da yake jikinki suke bi idan suka gama dake zasu gudu." "Ya zanyi?" Ta fada cikin kuka, tana kara jin tsanar kanta. "Kiyi hakuri kawai." Na fada mata, a hankali ta warware min tafiyarmu taraba, amma kuma tana jin addah tana kulla min sharri. Murmushi nayi na ce mata. "duk abinda Addah zatayi, ba zata hana Allah ikon shi ba, don haka ta gama abin da zata yi saura ta barwa Allah ikonsa." Daga haka muka cigaba da hirarmu. ** Kwana biyu mai kyau aka yi ana bata kashi a tsakanin, Captain da yan tada kayar baya, kafin aka fitar da su Commodore Magaji Abba, wanda yaci bakar wahala. Sannan sojojin ruwa da na kasa suka kame sauran yan tawayen aka tafi da su, a daren ya dawo gida a gajiye anyi anyi ya tsaya a asibiti amma ina, domin shima akwai rauni a jikinshi, yana shiga ya samu Aryan yana kwance a falon. Wucewa dakinshi yayi ya nufi ban daki ya shiga cire kayanshi, yana gamawa ya ga inda aka harbe shi biyu saboda bullet proof da ya saka ne basu ji mishi rauni ba, wanka yayi ya fito ya sha magani, ya sauke salolin da yake kanshi. Sannan ya fito ya hada tea ya sha, kafin ya dawo daki ya kashe wutar gidan baki daya, akwai yarda da Amana a tsakaninsu da duhu. Karfe biyar na asuba ya farka, ya nufi ban daki yayi wanka da alola ya fito falon suka yi sallah,a lokacin an fara ruwan sama. Kitchen Aryan Mamman Ba'are ya wuce ya hada musu abin karyawa. "Kasan yau zamu bar garin nan." "Eh! Amma ai ana ruwa." Kallonshi Aryan yayi kafin ya ce mishi. "Zamu wuce Enugu a can muke da jirgi zuwa kano." Haka ya zauna ya ci abinci, suna hira sama-sama. "Ya Amaan?" Tab'e baki yayi yana faɗin." Yana nan." Daga haka dukkansu babu wanda ya kara cewa Uffan. Har suka gama, Aryan ya shiga dakin Majeed yayi wanka ya shirya sannan ya zo ya kwashi kayansu, yafita da su. "kana nufin kwana biyu da kayi baka fita ko ina ba?" Tab'e baki yayi irin abin ya zame mishi jiki ya ce mishi. "Ina zan leka? Gari kullum ruwa, da nasan haka ne, ai da na tawo da Sanayah!" Shiru yayi yana kallon yadda yake shirya kome. Bayan ya gama shima ya koma ya shirya tsaf cikin Kananun kaya, suka rufe gidan bayan ya kwashe kayan abincin ya rubutawa Emmanuel, yayi amfani da shi. Sai da suka fara zuwa headquarter yayi sign sannan ya leka asibiti ya duba Magaji Abba Chindo, da yake zaune ana wanke mishi ciwon shi, zama yayi bayan an gama nurse din suka fita ya amshi sauran kayan aikin ya cigaba da gyara mishi ciwon. "Ba na son na kuma maimaita maka abin da ya wuce, amma zan gaya maka gaskiya yarinyar nan da ka saka a bi sawunta ni na taimaka mata, ba don kome ba sai don na kubutar da kai daga sharrin zina. Nasan kayi nisa amma ka gwada barin shi zaka fahimci abin da nake nufi. Ni zan wuce ƙasarmu, ka sani ba wai bamu da inda zan yi aiki ba ne, sai dai wannan karon idan na tafi ba zan dawo ba,na bar maka ƙasarku na koma aiki a babban headquarter Naval na French." Daga haka ya mike zai fita daga cikin dakin. " tow sai me? Bayan sai da na zama nakasashe zaka gaya min na daina zina? Sun kashe min gaba wadancan karnukan." "Zina ya janyo maka haka." Daga haka ya juya ya fita, bai samu Dr Umaima ba, sako ya bar mata tare da tura mata kuɗi, sannan ya fita daga asibitin suka bar garin ma baki daya. *** Ranar da na cika kwana shida, aka sallame, Doctor Umaima tazo tare da mika min jaka. "Gashi akwai ticket na jirgi zuwa Yola, daga can zaki samu motar taraba. Don Allah ki koma gaban Iyayenki ga wannan kuɗin inji Captain ya ce a baki kuma yana bada hakuri da abinda ya faru. Shima ba a son ranshi ba ne." Murmushi na sakar mata, ina faɗin. "Duk wannan kuɗin?" "Akwai matsala ne?" Girgiza kai nayi, sannan na ce mata. "Ko zamu je banki a tura min kuɗin." "Wani bank ne?" "Ecow bank!" "Me yasa sai bank din?" Saboda idan na koma zan tafi niman Mamana ne ne a Kamaru.". "ok muje!" "Gaskiya kin yi dabara, yadda Adda ta shirya wulakanci tana ganin kudin nan zata raba ki da su." Murmushi nayi na wuce muka fita, da taimakon Aunty Umaimah muka tura kudin account dina, sannan suka sa ni lallai sai na yi welcome back din layina. Bayan nayi na sayi wata yar ƙaramar wayar bani da buri akan babbar waya. Haka yasa nake rayuwata da yar karamar waya abina. Lokacin da muka zo gida, na samu su Addah sun gama shirin tafiya. Koda na gaya musu ni jirgi zan bi sai suka yi shiru, Zulaihah itama ta kira wani sugar daddy dinta ya tura mata kudin ticket, sai gashi baki ɗaya sun biya har da Addah da Ummi. A daren muka bar garin fatakwal. Muka wuce garin Yola. Mun isa wurin ƙarfe daya na dare, don haka muka kwana a masallacin da yake cikin airport din, gari na wayewa muka fito tare shiga kasuwa muka yi sayayyar tsaraba, sannan muka dauki hanyar taraba. A hankali muke tafiya, hankalina yana kan wayar hannuna, na turawa Sabiru sakon gamu nan muna hanya, amma shiru bai dawo min da ansa ba. "Ya dai Zahrah?" Tsaki nayi ina yatsina fuska."Sabiru bai kira ni ba." Juyawa Addah tayi tana kallonmu, fuskarta dauke da murmushi. "Allah ya sa ba halin yan maza zai miki ba." Shiru nayi ban iya magana ba, amma tabbas akwai wani abu a kasa, haka kawai Sabiru baya kin daukar kirana ko sakona ya gani. Wai ma kun san wacece Ni? Fadimah Zahrah Buba Shad'ari, shine cikakken sunana. Mahaifina Bafulatanin taraba ne daga karamar hukumar Takum. Gari ne da ya hada makiyaya da manoma. Alhaji Shu'aibu Jauro shine kakanmu dattijon arziki, mutumin kirki da babu biyun shi, Allah ya mishi rahama. Domin ya rasu tun ina da shekara shida a duniya, amma ba zan manta alkhairinshi ba. Addah ita ce Babbar yarshi, kuma kangararriya mara jin magana. Wato ana cewa albasa batayi halin ruwa ba, hakan ce ta faru da Addah domin bata dauko halin iyayenta ba dukka biyu, sai Baffa'm wanda shine d'a na biyu da yake bin Addah, mutum ne me hakuri kawaici da Dattaku. Baffa'm yasan darajar kanshi da rayuwarshi. Mutum ne da yake da ilimin addini sosai, sai dai bai samu halin yin ilimin boko ba, sai ya saka a ranshi matukar yana raye Yaranshi sai sun yi karatun boko, wani abin haushi. Nenne Matarshi kuma uwargidansa, babu ruwan ta domin har wurin ardo ta kai Baffa'm don yace sai yaranshi sun yi boko. Haka ya hakura dake yana tafiya da shanu cirani, musamman yankin Gyambu da yake da yalwataccen yanayi me kyau, yana zuwa yayi watanni sannan ya dawo da su. A irin wannan tafiyar ne ya hadu da Mamana domin tafiyar ta kaishi har kamaru, a can ya aurota ya kawota. Lokacin Munaisah tana da shekaru biyu a duniya. Tunda Baffa'm ya auri Mamana, mutanen gidan suka sakata a gaba, wai ita Rumada ce wato bayin fulani, duk da kana ganin Mamana kasan yar babban gida ce, domin duk rugar mu babu macen da take sanye da zinari a kunne sai ita, sannan take gaya min ina Yarinya su Mahaifinsu kana cika shekaru goma a duniya kake fara zuwa aikin hajji, daga nan duk Shekara kana tafiya Umara. Wannan yasa duk yan gidansu suka je aikin Hajji. Baffa Modibo shine ke bin Baffa'm, sai dai mutum ne mara kirki,haka yasa har da shi a cikin masu musgunawa Mamana. Haka tayi ta rayuwa a kuntacce, a lokacin da aka haife ni kuncin yayi yawa, domin a lokacin Addah sun dawo da Mijinta ya saketa, haka ta zo ta saka Mamana a gaba da fitina da tashin hankali. Har zuwa lokacin da ta samu wata kawarta ta kawo mata ziyara daga kano suka tafi tare da Addah, ashe tafiyarta Kano Saudiya ta tafi. Wato mu yan gidanmu Allah ya zuba mana baiwar kyau, sai ma dai nice da nake da duhun fatar Mamana. Haka yasa yan gidanmu suke yawan min ba'a. Bayan tafiyar Addah Baban Zulaihah yaso ɗaukarta, amma Kakanmu Alhajijo yace ba zai dauketa ba, sai ta kai shekaru bakwai a duniya. Haka muka taso da Zulaihah duk da ta girme.ni, haka Mamana ta haɗa mu ta riƙe. Tunda Addah tabar Nijeriya ta isa Saudiya, take tukaranci da rashin jin magna, har dai ta samu yadda take so. A nan kuwa ba zance me ya faru ba, domin a lokacin ban wuce shekaru Biyar ba, aka nime Mamana aka rasa, sama da kasa ta b'ace, wannan al'amarin ya daki babana da Alhajijo a lokacin ya kwanta jinyar da tazama ajalin sa,, haka muka zama marayun dole ni da Zulaihah. A lokacin Baffa'm ya saka ni makaranta, kuma cikin ikon Allah sai Ubangiji ya min baiwa na daukar karatu, domin ina da shekarun goma a duniya na gama primary school. Na shiga secondry school, a gurin a saka sunana a registered din yan jss one aka saka a na yan jss two, haka Baffa ya cika musu kudi domin shi mutum ne mai son yaga kayi abinda yake so. Ina da yayu maza biyu, Babangida da Habibu, sai Munaisah take bin Habibu. Sai ni nake bin Munaisah, sai Kuluwa take bina, sannan Dizah burin Baffa'm akan mu yayi yawa amma haka Nenne ta kashe mishi burin akan Yaranshi,ni ce kawai yake da iko dani, shi yasa ina shiga jss3 a shekaru goma sha daya na kara riƙe wuta, koda muka shiga Ss1 bana wasa, ina shiga ss2 na nime Baffa'm ya biya min waec da neco, sanin ina kokari yasa shi biya min ikon Allah sai gashi da muka yi jarabawar naci, duk da bani da shekaru amma ina da dan tsawon kafa. Sannan ni siririya ce sosai. Kamar mamata haka nake. A shekarar da na gama secondary Hajiya Addah ta dawo, ganin mu yasa ta fara shiri akanmu, sannan a gefe guda kuwa burinta ya kusan cika, don haka ta kwana biyu ta sayi shanu ta bawa baffanmu, ta koma ashe a Lagos take da aka kore hausawa masu tuwo-tuwo shi ne ta dawo fatakwal. Ganin mu kawai yasa tana komawa tayi gaggarumin shiri, tana zuwa ta dauko Ummi da Munaisah,suka zo watansu biyar suka dawo. Ni da Zulaihah da zasu koma aka tawo damu,a lokacin Baffa'm ya bani takarduna,nayi kokarin niman cigaba domin ta gaya mishi zan koma makaranta. Da muka zo kuwa kudin da ya bani taso kwacewa ni kuwa na ce ta mai dani gida baki ɗaya shekaruna sha huɗu, ina da wayewa ta ilimi,domin saura izu goma na sauke Kur'ani mai girma. Wannan dalilin yasa addah nima min, diploma a bangaren ilimin lissafi, kuma dama Allah ya min baiwar iya lissafi. Har yan canji suna kirana na taya su aikin lissafi idan ban tafi makaranta ba, a hankali Addah tayi ta fito da asalin kalarta akan lallai mu bi maza, ni kuwa naki na sha duka da wahala, ga azabtarwa yunwa kada ku manta wannan shafa ce domin a gidan Ubana ma na horu da rashin abinci, Zulaihah ce aka samu kanta, domin ba zata iya jurewa ba, haka na samu number din baffa na gaya mishi, shi ne yasani na hada shi da wani iyamurin gefen gidan Addah yana turo min kuɗin makaranta da na abinci. Yayarshi ce babu yadda ya iya da ita idan yayi magana zata ce ya mata rashin kunya,haka yasa ya zuba mata ido. Kullum zai kira yaji ina nan ko na tafi, baya kira a wayata sai wayar addah. Kudin da take samu a wurin su Ummi da Munaisah da Zulaihah,da shi take turawa gida ana saya mata dabbobi, gashi bata gajiya da kai karana na mata kaza nayi kaza. Ya kira ya min nasiha, domin ban tab'a boye mishi abinda take son nayi ba, shima kuma yace naji tsoron Allah yana gani na idan ni bana ganinshi. Haka muka cigaba da rayuwa, gashi har na zama cikakkiyar budurwa, domin ban wuce shekaru goma sha shida ba, haka yasa maza rawar jiki a kaina, amma naki Ba su fuska, sai ranar da ƙaddara ta haɗa ni da mutumin nan da ya soka min wuka,koda yake shegen iyayi na ya kai ni. A daren da abin zai faru wannan sojan yazo wurin Tuwon mu ya matsawa Addah ta barshi ya dauke ni, amma taki domin ya tab'a daukar Ummi bayan ya kwana da ita ya mata dukar kawo wuka ya korota. Sai da ya zuba mata kudi, sannan ta barni muka tafi, daga na bishi na amso kudi ya tafi da ni. Koda ya kawo ni, da farko bai nuna damuwa akan yana son wani abu ba, sai da na je na kwanta ina nazarin yadda zan fita ya shigo min tsirara, ai kuwa garin na kwaci kaina na bude mishi wani abu can, ai kuwa ya fadi can, da haka na gudu, daga nan na hadu da Aminin duhu. ....... Biyar na yamma muka isa taraba, daga nan kuma muka dauki shatar mota har har zuwa Takum kai ba zan fadi yadda farinciki yake wanze akan fuskar mu ba, amma tabbas mun yi kewar garin mu, ai kuwa bamu isa ba, sai dare shima ba cikin gari ya shigo damu ba. "Driver ai da ka kaimu sai mu kara maka kuɗi." "Gaskiya Hajiya ba zan iya barin takum ba, ina ma zaku?" "Jenuwa" shiru yayi kafin ya ce mana.."zaku ƙara min dubu ashirin?" "Eh zamu kara maka!"inji Zulaihah domin ta kagu ta isa gidan. Gyara tsayuwa yayi ya ce mana."tow muje!" Haka ya cigaba da tukin har muka isa garin mu, dake shigar dare muka yi, har kofar gida ya kai mu ya sauke mu, sannan ya juya abinshi.... #thedambuje [2/16, 9:24 PM] Cutie cutie pie: *BAƘIN HAURE....🐾🐾* {Greed for Money is the roots of all evils🫀} Arewabooks:maidambu41 Wattpad:Mai_Dambu Mallakar:Mai_Dambu *007* Tunda muka sauke kayanmu naji bakiɗaya wani irin sanyi ya lullube ni, sanyin dadi domin babu inda ya fi mahaifarka, haka na karewa garin kallo cikin wani irin tsananin so da kauna. Buga kofar rugar mu muka yi muryoyin mu na tashin sallama, Baffan Ummi ya fara fitowa yana faɗin. "Ikon Allah Hajiya Addah kece a garin mu a daren nan?" "Eh Modibo gani nan jenuwa babu shiri. Bari mu shiga mu huta." "A'a bari a taso Lantana ta dama muku fura." "Barshi Modibo bari mu huta haka." "Tow madalla, ku huta lafiya." Ya juya zuwa bangarensu, mu kuwa ni da Zuzu tsohon dakin Mamana muka shige domin dama babu kome sai tsohon gadonta da tarkacen da ake zubawa a dakin, haka muka kwana a gajiye, dake Allah ya taimaka duk mun yi kasaru a Yola sallah Magariba ma sai da muka yi a hanya. Wani abu da ya dame ni, shine na kasa barci haka nayi ta juyi har asuba ta gabato, daga nan na tashi nayi sallar Isha da na asuba, sai lokacin barci me nauyi ya ɗauke ni. Cikin wani irin yanayi mara daɗi, nake barcin nan, make min cinya aka yi na bude idanuna. "Ya?" "Kawu na kiranmu." "Karfe nawa yanzu?" "Tara da rabi." Tashi nayi ta mika min kofi da dafafen madara."sha ki hada da magani sai mu tafi." Yatsina fuska nayi domin bana son shan madara, haka Allah yayi ni bana son madara idan ba dole ba, haka kuwa na sha, ina tsaki sannan na mike muka fito zuwa dakin Baffa'm, bayan na sha kayan sanyi. Koda muka isa yana bakin kofarshi yana zuba ma Yaran Baffa Modibo shayinsa. D'ago kai yayi ya kalle ni sannan ya saki murmushi, yana faɗin . "Innawuro sai yanzu kika farka?" "Eh Baffa." "Zulaihah kema shigo." Haka muka shiga dakinshi, zama muka yi ga dadi da dumi. "Kun iso lafiya?" "Alhamdulillahi, mun same muku lafiya?" "Masha Allah, Alhamdulillahi. Ya jikin naki?" Sai a lokacin fuskarshi ta sauya kaɗan. Zuba min Idanu yayi kafin ya gyara zama ya kira sunana. "Fadimah Zahrah!" Gabana ne ya fadi, na kalle shi kafin nayi kasa da kaina. "Na'am!" "Idan aure kike so, me yasa baki gaya min ba?" Girgiza kai nayi, a hankali ya shiga min nasiha, Baffa'm yana da matukar hakuri da sanyin hali, haka yasa ba zaka tab'a jin shi yana faɗa da wani ba. Sai da ya gama ya zuba mana idanu yana son jin me zamu ce. "Kawu shad'ari!" Kallon Zulaihah yayi zata magana na rike hannunta. "Meye kike son hana ni magana?" "Ya wuce, a barshi ya wuce har gaban Ubangiji ya wuce." "Kawu laifi ne don ta kare kanta daga dattin zina? Yar uwarka azzaluma ce, bata da imani." "Kuyi hakuri nasan Allah yana tare da ku, kuma me yasa baku gaya min zaku zo ba? Garin jenuwa babu lafiya, ai da ban barku kunzo ba. Muma zaman dar-dar muke." "Lafiya kawu?" "Lafiyar kenan, sai dai wasu daga cikin yan uwa Makiyaya kuma abin da na fahimta baƙin haure aka samu suka shiga gonar mutanen suka musu barna sannan suka kashe musu mutane kusan goma. Haɗe da yiwa matansu fyade, tun ranar juma'a suke son daukar fansa, hukumar tsaro suka shiga cikin lamarin, yanzu haka babu dad'i garin baki daya, shi yasa nake son idan da hali gobe ku bar garin nan." "Baffa'm na dawo kenan fa." Kura min idanu yayi na wasu dakikai kafin ya ce min. "Kiyi hakuri ki koma can, idan kin samu miji maza ki kirani ki gaya min." "Baffa'm Sabiru fa?" Kaina a sunkuye."Allah bai nufa shi ne abokin rayuwarki ba, yayi aure suna jalingo da Matarshi da yake yana aiki a can." Wani irin sanyi ya shige ni daga waje har cikin jikina, na hadiye wani irin yawu me daci. "Baffa." Kura min idanu yayi sannan ya ce min. " Allah yana sane dake, ga wannan takardun, ki tabbatar kin nime Mahaifiyarki, domin duk inda take tana cike da kewarki." "Baffa'm me yasa ka bani?" Na tambaye shi lokacin wani irin sanyi da zazzaɓin sun rufe ni. "Akwai rayuwa akwai mutuwa idan na kasance araye zan tayaki nimanta, idan muka bana raye zaki tsayawa kanki, Zulaihah ku rike amanar juna,kada ku sake wani abu ya raba tsakaninku, ita duniyar ba kome sai rud'i da karya, ba kome zaka bashi damar fushi ba, na horeku da zumunci, kuma duk abinda Addah zata muku, kada ku sake ku yi fushi Allah yana tare da masu hakuri." Nasihar Baffa'm yake mana, sai da ya gama sannan ya shiga tsokanarmu. "Kun tuna kuna yara kuke damben wace ce zata sha furar Alhajijo." Ya dauki wani allon karfe, ya shiga rubutu yana kallona. "wannan zamanin dole ka nimawa kanka mafita, idan ba haka ba, sharrin zamani sai ya hada da zuri'arka." "Haka ne Kawu " murmushi yayi sannan ya cigaba da rubutun,yana jan mu da hira har ya gama ya wanke a kwanon shan, ya dauko wani saiwa ya jefa yana faɗin. "ku dai rike gaskiya da Amana, ban da cuta da cinAmana, zalunci bai da tsawo domin idan alkadarin ya karye sai an tozarta." "Haka ne!" Suka ci gaba da hirarsu da Zalaihah ina jin su, har ya gama.ya bawa kowacce ta sha. "Idan kun fita ku bawa Ummi da Munaisah, su sha." "In sha Allah!" Muka fada, "Baffa'm rubutun me ka bamu?" Murmushi yayi ya ce min. "Tsarin jiki ne?" Gyada kai nayi, har zan fita ya ce min. "Innawuro!" Juyawa nayi, "zo nan!" Komawa nayi na zauna, bude wani ƙunshin takarda yayi ya mika min. "Ina ta ajiyewa kafin aurenki, ki saka a wannan abin me kama da lalita, wata rana zai miki amfani kada yunwa ko talauci ya sa ki.aikata Zina don Allah ki rufa min asiri kinji. Duk inda zaki kada ki zauna babu sana'a wannan gwal ce na Mahaifiyarki."gyad'a Kai nayi, a hankali na mike ina mishi godiya, har zan fita ya mika min wasu leda. "Shi wannan abubuwan masu mahimmanci ne, na yaran Harirah ne nasan..." Burr muka ga shigowar Nenne, fisge ledar tayi, "wato ga yar so, ni kuma nawa yaran da baka so su mutu da bakinciki da yunwa bani. Ai keda ganin uwarki sai a lahira." "Harirah kenan. Allah ya bamu sa'a." Daga haka na fita na barsu, tana saukewa Baffa'm tijara. Ni kan cikin gidan na nufa duk da wani irin zazzaɓin da nake ji, bai hanani zuwa sassan Baffa Modibo na gaishe su ba,har dama-dama Yakumbo bata da matsala, sai Amaryarta ce ma Bama shiri. Yakumbo wacce sunanta Sarai tana da yara hudu, Shu'aibu shine babba yana yola a can yake karatu shine yaron da ya fita Zakka a bangaren Baffa Modibo. Sai Jamilu yana nan domin yayi aure yana garin takum, sai Sa'idu kafin Ummi. Amaryar Baffa Modibo kuwa, tana da Yara kusan shida duk maza ne, sannan irin haihuwar nan na kunika. Yaran kamar kwarkwata. Aminu shine babba, sai Zakaria, Amadu, Adamu, Abdullahi, Abubakar dan karaminsu, wucewa dakin mu nayi na kwanta, ina ganin Zuzu tana dafa mana abinci,domin doya ce take dafawa zata mana miyar kwai. Zulaihah akwai kokari domin duk inda zata, tafi da gidanka take yi, har indomie tazo mana da shi, ga kifin gwangwani irin me Mai din nan. Tana gama dafa doyar take bani labarin yadda tayi da ruwan rubutu,ta ce min. "ke nabasu suka ki sha, ai kuwa na sha rabi na bar miki rabi." Ni dai bance mata kala ba, na cigaba da kwanciyar da nake, domin idan na bude baki zan yi magana kuka ne zai kwace min. Haka na dauki lalita ta, ina kallo. "Zahrah ya dai?" Idanuwa na da suka cika da kwalla na kalleta."Ashe Sabiru yayi aure bai gaya min ba?" "Mtsew sai kace autan maza." A hankali na fashe da kuka, ina jin wani irin abu yana taso min, kamar kukan nan saka ni ake yi, har sai da nayi na gaji, tana kallona taci abinci ta koshi, ta mike ta daura ruwan zafi, ta fita tayi wanka sannan ta shirya zuwa gidan Babanta, koda ta je can faɗa yayi mata me yasa zata zo, gari ba lafiya. Hakuri ta bashi tare da mishi zancen ta hadu da wani tana son ta turo shi,ta kira saurayin ta hada su, sukayi magana ta roki Babanta kada ya bari Addah ta sani. Ya mata alƙawarin ba zata sani ba. *** Karfe biyar ina wurin dabobbi, ina taya Baffa'm tatsar madara. Wayarshi tayi ƙara dauka yayi yana me sallama. " Alhaji Abubakar ko?" "Eh ni ne?" "Okay ko zaka fita kai da wani naka, domin mun samu labarin za a." "Anan aka haife mu, anan muka girma bamu da inda yafi nan, sai dai mu mutu, Yallabai mun gaya musu, bamu ne muka musu barna ba, taya zamu cigaba da amsar laifin da bana mu ba, a matsayinku na jami'an tsaro hakkinku ne kula da rayuka da dukiyoyin mu." "Shi kenan, kada kace ban sanar maka ba, na gaya maka gaskiya kuma ba a bamu umarnin kare kowa ba, don Allah ka fita daga cikin Jenuwa." "Shi kenan!" Baffa'm ya faɗa yana kallona, taya zai fara. Haka ya wuce ni ya saka aka kira mishi sauran mutanen rugar ya gaya musu abin da yaƙe faruwa. Shiru suka yi kafin aka samu wasu tsagera suka kama dariya."Baffayo kana nufin Mu bar rugarmu saboda kada mu mutu? Kusan kai ma kana da shanun nan,don haka babu inda zamu ai wannan maganar karya ce wallahi babu wani! Harin da za a kawo mana, da alamu tsufa ya fara kama baffayo." Kiri-kiri matasan nan suka ƙaryata shi, haka yasa shi komawa gida da tarin takaici da bakinciki. Koda ya dawo ana kiraye-kirayaen sallar Magariba, a masallaci ma yayi magana dayawa suka karya tashi sai yayi shiru, koda ya dawo bayan isha muna cin abincin, ya shalenta abin yake faruwa a cikin gidan, Babangida ya ce mishi. "Baffa taya zasu kiraka su gaya maka, kawai dai wannan zance ne. "Bai fito ya ƙaryata baffa ba, amma maganarshi sak ce da ta sauran mutanen, ban san me yasa ba ko don a gabana aka yi wayar sai naji zuciyata tayi sanyi, kuma wani irin tsoro da fargaba, ya shige ni Zulaihah ma ta shiga haɗa duk wani abu me muhimmanci akan mu bar garin cikin daren nan, amma wani abin mamaki kana naka, Allah yana nashi, wurin karfe tara na dare, muka dinga jin ƙarar harbe-harbe, hankalin Baffanmu ya tashi, yana shigowa dakinmu ya ce min.."taso Fadimah." Tashi nayi a rikice ya cewa Zulaihah. "Kema tawo!" Dakinshi ya wuce damu," kada ku sake ku fito matukar bani na bude muku kofar ba, da izinin Allah babu abinda zai faru." Ashe ya tafi har dakin Nenne ya kwaso yaranshi, Yar matan nan tace ta adana Yaranta, domin mugun nufinsa ya janyo wannan tashin hankalin,da bai fada ba ai da babu abinda zai faru. Bai mata magana ba ya dawo duk inda ya nime su bude kofar ya kwaso yaran sunki,.haka yasa shi dawowa ya dauki addarshi ya tsaya a kofar gidanmu. Ban tab'a shiga tashin hankali irin na yau ba,domin kuwa kana d'aga kai zaka ga yadda garin yayi jajjur da wuta da hayaki. Baka jin kome sai karar bindigu da kukan dabbobi. Ban san me yasa idan wani abu ya faru mutane ke huce takaicinsu akan shanu ba, shanu suna da daraja a rayuwar Bafulatani, domin zai iya hakura da rayuwarshi akan dabbarshi, amma mutane basu ganewa. A cikin yan dakikai nayi wannan nazarin, "Tau!" Muka ji kar'ar harbi kamar a cikin gidan anan aka yi,kuma babu karya a cikin gidan aka yi. "Malam Buba yau addarka ba zata amfane ka, da kome ba, domin kafin ka kai sara mun tashe ka aiki." Jijjiga kofar nayi ina hango Baffa'm a kwance, domin sun haska mishi katon torchlight dinsu mai shegen haske, Baffa'm a kwance jini na zuba ta gefen cikinshi. "Kai ku shiga ku fito mana da yaran da suke cikin gidan, matan ku ware mana manya da kanana, mazan a musu yankan raggo a gaban Malam Buba da yace basu ne suka mana barna ba." Inji mutumin, "tow;" dakyar Baffa'm ya mike yana rike kafar mutumin. "Don Allah dan ladi kada ka cutar dasu, wallahi bamu bane. Akan me zamu cutar da zaman da muka yi na amana da ku?" Shure Baffa'm suka yi tare da take mishi wurin ciwon, suna murtsukawa. Haka suka fito da kowa na gidan, har da Baffa Modibo. Babangida da Habibu. Sa'idu da su Aminu. Dukar kofar da nayi yaja hankalinsu ba zan iya ganin wannan cin mutuncin ba, gara na mutu da Mahaifina. "Aiho boye wasu kuka yi?" Ya dokawa Baffa'm gindin bindigarshi akan ciwon, "ku balla kofar ku fito da su." Haka suka nufi kofar da gudu Baffa'm ya tashi yana me tare kofar. "Ku min kome na yarda, don Allah ku kyale mata da yaran basu yi kome ba." Rufe shi da duka suka yi, tare da janshi daga kofar dakin suka ɓalle kofar, tare da finciko mu. Suka yi waje damu. Ganin suna dukar Baffa'm babu me cetonshi na nufe shi, tare da fara ture su, haka aka fisgo ni suka bugani da kasa, tashi nayi da rarrafe kafin na isa sun mishi wani irin duka tare da cin zarafinshi suka tube mishi suturarshi. Rike gashin kaina mutumin yayi yana dariya. "Ke me baba ko? Maza jeki, Malam Buba idan kana son mu kyaleka dole sai ka amince kayi tarayya da Yaranka mata. Su kuma Yara mazan su kwanta da iyayensu Mata ko kuma mu,mu kwanta da su." Suka fada suna dariya irin abin ya musu dad'i. "Ku kashe ni ba zan iya ba, ba zan iya kallon wannan kazantar ba." "Ashe? Tow kai daure min hannun mazan a musu yankan raggo su kuma matan ku ware min yan matan manya kuma su raba su." Har zuwa wannan lokacin yana rike da gashin kaina. "Dan Ladi kada kayi abin da zai dame ka, don Allah kada kaci zarafin Musulunci mana, addinin Kirista bai baka damar cin zarafin mata da yara ba." Amma mutanen nan suna dariya suka d'ago Babangida. "Kaje ka kwanta da uwarka kacita kamar yadda namiji yake cin Matarshi a gadon auren, kada ka biyewa Ubanku ba zai tab'a barin ku tsira ba, kana gamawa ga kofa ka fita ba zamu tab'a ka ba." Kusan yadda dan Adam yake da buri, kuma a ran Babangida gani yake idan ya aikata haka zasu barshi ya rayu, Baffa'm yasan yaudara ce kawai. Rike hannun Babangida yayi ya ce mishi. "Idan ka sake ka aikata haka, zasu kashe ka Allah ya saka hijabi a tsakaninku har abada ba zasu kasance a shimfidarka ba, Mahaifiyarka da yan uwanka, haramtattu ne a gare ka. Don haka kada ..." Dauke kan Babangida suka yi da harbi, sai gashi a jikin Baffa'm. Wani irin ajiyar zuciya Baffa'm ya sauke ya ce musu."Gara ku kashe mu da ku kasance kuna saka mu,aikata barna." Wurgar da ni Mutumin yayi na na rarrafa wurin Baffa'm, na mika mishi kayanshi. Ina durkushe a gabanshi. "In sha Allah duk tsanani yana tare da sauki, kada wani abu ya baƙi tsoro gwagwarmayar...." Sake mishi harbi suka yi a gadon bayanshi. Ya fadi a jikina. "Kada tsoron mutuwa yasa ki ki tserewa da zaki rayu. Kiyi iya yinki Allah yana tare da mai gaskiya da takawa." Wani Harbin suka yi mishi sai da jin ya wanke min fuska. Har lokacin bai cika ba, babban burin shi yaga mun tsira ba tare da sun ci zarafin mu ba. Janyo shi suka yi, akan idanuna kamar wata gaula ina kallonsu, suka shiga bude mishi wuta har sai da ya daina shure shure yana kalmar shahada, ban san ya aka yi ba amma ihu da karar harbe-harbe nake ji amma ban san me yake faruwa ba..haka suka yi ta bin Yaran nan suna harbinsu har da Baffa Modibo, akan idanun Nenne suka kashe mata Yaranta maza biyu, Yakumbo Sa'idu, Amaryar Baffa Modibo kuwa a wurin ta samu tab'in hankali domin kuwa ganin jinin yaranta yasa ta kama dariya. Bayan sun kashe mazan baki ɗaya, haka suka yi ta bin iyayenmu mata suna kwanciya dasu, ko nace Fyade. Hawwa'u da Hadiza kan, ko taron da mazan suka musu ne, amma ban san kome ba, sai da naji an rufe mu da duka ni da zalaihah. Ni dai naji kamar an suka min wani abu ban kuma sanin kome ba. Bayan sun gama ta'aadacinsu, suka sakawa gidan wuta, kafin wani lokaci rugar mu ta zama makabarta domin babu inda babu gawarwaki. Sannan yadda suka tozarta mu haka suka bar mu a wulakance. Bayan tafiyarsu Addah da duk rashin imaninta yau sai da tayi kuka, Ita ta tashi da gudu tana shiga dakinta ta Ciro kaya tana daukar zanuwa da zanin gado, ita da Yakumbo. Dukkan iyayen nan kana ganin yadda suke abu kasan karfin zuciiya ne domin Nenne da suka mata wulakancin bata iya tashi ba, haka aka yi ta lullube gawarwakin da sauran mu, ita kan Amaryar Baffa Modibo, bayan sun gama mata fyaden, kasheta suka yi sannan suka barta a wurin. Zama Addah tayi a gaban gawar kannenta ta fashe da kuka. Sai lokacin kuka ya zo mata, har gari ya waye sai lokacin yan agajin gaggawa suka kawo mana taimakon gaggawa. Aka wuce damu asibiti sai dai kuma babu gado domin kuwa asibitin cike yake. Wani abin da nake son ku sani, Taraba tana kudu da kasar Kamaru, sannan koda aka bamu taimakon babu wani abu, tura mu camp na yan gudun hijira aka yi, muna zuwa can,aka ce babu wuri dole aka hada mu da hukumar gudun hijira aka mana takardu aka wuce da mu Kamaru.... This is the beginning.....300₦.. #thedambuje [2/16, 9:24 PM] Cutie cutie pie: *BAƘIN HAURE....🐾🐾* {Greed for Money is the roots of all evils🫀} Arewabooks:maidambu41 Wattpad:Mai_Dambu Mallakar:Mai_Dambu *Wato jiya an yi kuka, hmm ayi hakuri na kara bada hakuri. Abin labarin a sannu 😍 wannan naku ne masu bibiyata. Allah ya saka da alkhairi 😍❤️🫀🌹 na ji dadin comments dinku na jiya ya tashi kaina su Auntys and mommies har da niman kari 🤣😹 Na gode sosai* *008* Saboda azabar ciwo da muke fama da shi, bama fahimtar juna ko me yake faruwa, iyayen mu mata kawai zaka kalla ka fahimci suna cikin wani yanayi amma gudun kada su sare a gaban idanuwan Yaransu yasa suke fakar idanunmu suna kuka. A haka muka isa har Kamaru tafiyar kwana biyu, Adamawan Kamaru aka kai mu, anan babban camp na yan gudun hijira yaƙe. Sai da muka je asalin headquarter aka mana takardu, sannan aka wuce da mu asibitin da yaƙe asalin garin, anan aka shiga bamu taimakon gaggawa. **** *Niamey: Niger republic* Ranar zaben. Wato wannan ranar abu biyu za a gabatar na farko yadda suka shirya idan har suka fi su Aryan Mamman Ba'are yawan vote. To zasu amshe BA'ARE GOLDEN EMPIRES daga hannunsu Hajiya da Yaranta, na farko kenan, na biyu zasu sayarwa mutanen kasashen waje, sannan su zare hannun jarin Hajiya da Yaranta. Sai dai wannan lokacin al'amarin daga ita har Yaranta sun sadakar musamman da suka ga Aryan Mamman Ba'are ya dawo babu Majeed, sai jikinta yayi sanyi a matsayinta na Uwa ya zata yi? Hawaye ne ya zubo mata tana kallon Aryan Mamman Ba'are. Tasowa yayi ya mika mata hanky yana faɗin. "Kukan me kike yi?" "Na hango faduwarmu ne, burinsu idan muka fadi hatta gidan BA'ARE housing estate zamu bari, duk wani abu da ya shafi BA'ARE zamu bari." Dariya yayi yana faɗin."haka muke so sannan a wannan karon za a sake gwanjon kome har da estate kenan?" Ya fada yana mikewa daga inda ya zauna ya koma wurin shi, masu hannun jari da matsayi a board din kamfanonin BA'ARE mineral oil and gas, amma babban al'amarin da wannan rikicin yana kan GOLDEN EMPIRES ne. Hajiya Nana ita ce a sawun gaba, sai Hajiya Tani da d'anta Sajjid Mamman Ba'are, sai Hajiya Rabi Mamman Ba'are, sai Hajiya Fauziya Mamman Ba'are, can sai ga Hajiya Harirah Mamman Ba'are, dukkansu da yaransu mata da maza. Dukkansu nan babu wacce za a nuna mata takarda ta karanta, kawai kishin jahilci ake yi, Hajiya Sa'adatu Mamman Ba'are, ita ce Hajiya mahaifiyarsu Captain. Kuma ita ce Amaryar Alhaji Mamman Ba'are,sannan ita ce take da Yara maza uku cif. Su Majeed suna da yayu mata manya, amma kusan da yake akwai kishi da hauka yasa kowa yake rayuwarsa a inda yaƙe. Idan ka cire Hajiya Harirah da take da abin bata yarda ta kashe kanta da kishi ba, domin sai da ta nime ilimi, saboda ta fahimci wani abu da sauran suka gaza fahimta. Can Alhaji Haladu Abdul Majid Ba'are sai Alhaji Kamilu Abdul Majid ba'are, kafin Hajiya Hadiza Abdul Majid ba'are. A bangaren Hajiya Sa'adatu Mamman Ba'are, Akwai Amaan Mamman Ba'are, sai Aryan Mamman Ba'are, sai Jamilah Mamman Ba'are, sai Aneesah ita ce auta. A hankali wurin yayi ta cika, kuma a wannan zaman babu bare amma kuma wani abin mamaki shine zuwan wasu daga cikin turawa da yan siyasar da Sajjid Mamman Ba'are ya gayyato, ya tashi ya taro su. Har wurin Nana suka gaishe ta. Kafin suka gaida kowa sannan suka koma wurin zamansu, Abdul Majid dan Hadiza Abdul Majid ba'are, ya mike tare da nufar wurin Hajiya suka gaisa. "Hajiya Abdul Jeed ba zai zo bane?" Idanunta da suka cika da kwalla ta ce mishi. "Ban sani ba, na dai tura Aryan bai ce min kome ba." "Lallai Jeed dole ya bayyana anan. Domin an shirya makirci na bala'in fitar hankali." Duk wahala da ta sha, da iya azabar da ta sha, wai karshe abin da ta samu shine ya tsonewa kowa ido. Suna da nasu amma ita nata da na Yaranta ya tsone musu ido. Hajiya Hadiza Ba'are watsawa danta Abdul Majid harara tayi, ita kan bata san wani irin d'a ta haifa ba, ko a gidan Ubansu haka yake makalewa ya'yan kishiyoyinta yana basu kulawa kamar wani son shi suke. Komawa wurin zamanshi yayi yaki yarda ya kalli Hajiyarsu, da Nanah kakarsu kenan. Kanshi yana can bakin kofar aka fara taron tare da zab'en ra'ayi akan matsayin BA'ARE GOLDEN EMPIRES. Abin dai ba a cewa kome. Haka aka fara voting, jikin Yaran Hajiya yayi sanyi ban da Amaan Mamman Ba'are, dan shi dama yasan haka zata faru, kuma shi yana tare da su, babu me kaso mafi girma da yawa a kamfanonin kamar Majid, don haka gara ayi uwar watsi kowa ya rasa, Aryan Mamman Ba'are kuwa ko a jikinshi domin bai tashi ya kada kuri'ar shi ba, kallon shi Alkalin yayi ya ce mishi. "Malam Aryan Mamman Ba'are, shin baka ga kowa ya kada kuri'a ba ne?" D'ago kai yayi yana yak'e ya ce mishi. "Alkali kayi shiru yanzu zan kundume wasar domin uban gayya ya bayyana." Ya cigaba da danna wayarshi alamar game yake yi, "Malam Aryan kuri'arka ake jira fa." "Ba iya nawa ba, har da na wancan da yake tsaye a bakin kofar." Ya nuna musu Majid Mamman Ba'are sanye da kayan turang. Shadda ce skyblue, yasha babban riga da takalmi halfcover, kanshi sanye da rawani ya rufe fuskarshi da ita, yadda yake tafiya kasan cikakken jarumi ne. Mikewa Aryan Mamman Ba'are yayi ya tafi can bayan kujerar da aka ware babba kuma an lullube shi da mayafi, Hajiya ya dace ta zauna a wurin amma saboda fitina ta hakura, sai gashi Aryan ya janye lulluben da aka mata, sannan ya jata baya, Majid Mamman Ba'are ya isa wurin y zauna, dukkansu sai da suka mike tsaye. Yadda ya zauna sai da ya jingina da kujerar sannan ya aza kafa d'aya kan ɗaya, ya janye mayafin da yake fuskarshi. Yana bin ilahirin mutanen wurin da rikitaccen Idanuwan shi me dauke da wutar takaici da b'acin rai. "Amma taya dan iskan Yaron nan ya dawo?" Cikin kwafa Hajiya Tani tayi magana tana kallon Majid da ya daura daya kan ɗaya, yana sakin wani murmushi yana kallon Aryan da ya koma wurinshi da zama. "Alkali Bismillah!" Inji Aryan ya faɗa yana murmushi. "Tow Malam Aryan kuri'arka da ta Abdul Majid Mamman Ba'are ya rage, akan sikeli" hannu ya kai aljuhun rigar shi ya Ciro wasu zinarai manya guda uku, sai na shi daya yana zuwa ya saka nashi, yana kallon kowa a wurin sannan ya saka daya na Majid Mamman Ba'are, tuni hannun ya rinjayi daya hannun cikin tsokana da niman magana ya ce. "Alkali idan na saka sauran biyu ina cewa Ba zaku ce nayi son kai ba?" "Baka da matsala Malam Aryan" cikin wani irin juyi ya ajiye dayan, sai ga shi bakidaya ya rinjaye gefen. Kafin d'aga dayan sama ya ce musu. "Kun ganshi nan kuri'ar Majid Mamman Ba'are na karshe kenan!" Ya ajiye . Shiru wurin ya ɗauka. Babu wanda ya kawo Majid zai bayyana, balle a kawo zancen kuri'arshi, sannan babu wanda ya kawo wannan al'amarin haka shi daya kuri'arshi daya ta mutane goma ce ukun baki daya ta mutane talatin ne, domin kuwa asalin zinarin na Alhaji Mamman Ba'are ne, da kanshi ya ajiye wasiyya har kotu aka kai banki aka ajiye, asalima ba a kasar ya ajiye ba. Sai aka zo rabon gado aka gani. Ya narka ta zuwa na Majid Mamman Ba'are kuma ya saka sunanshi a jikin zinarin. "Kuri'ar Hajiya Sa'adatu da Yaranta sune masu rinjaye, sannan suna da damar fadin yadda suke so ayi da BA'ARE GOLDEN EMPIRES." A hankali Aryan ya mike ya ce. "Alkali dama ai idan aka yi rinjaye a kan mu gwanjon kamfanin za ayi ko?" Kallon Alhaji Haladu Ba'are da Sajjid Mamman Ba'are alkali yayi, suma kura mishi idanu suka yi. "Alkali ni nake magana ba Sajjid tani ba, ba Haladu Ba'are ba, Aryan Mamman Ba'are yake magana." "Eh Malam Aryan." "Kawai a saka a kasuwa!" Ya fada yana me komawa wurin zamanshi ya daura daya bisa ɗaya. Ajiyar zuciya Alkali yayi ya fara karanto ka'idodin sayar da kayan. "Doka ta farko waɗanda suka fadi basu da hurumi akan kamfanin dole suyi hakuri da duk abin da zasu ji ko zasu gani. Doka ta biyu idan aka sayar ga duk wanda ya saya hurumin shine cire sunayen wasu da baya ra'ayi a board meeting, doka ta uku iya waɗanda suka saya suke da ikon tafiyar da kamfanonin baki ɗaya." Wannan shine shirinsu idan Majid Mamman Ba'are bai zo ba,tow abin da za ayi kenan. Mikewa Aryan Mamman Ba'are yayi ya mikawa alkali kudin da aka sakawa kamfanonin. Hajiya tasan ba wayonta bane, ba Kuma iyawarta ba ne kawai wata falala ce daga rabbul alamin, ya bata yara maza biyu masu matuƙar zuciya da son cigaban juna. D'aga takardar kudin alkali yayi, nokewa kowa yayi babu wanda yayi kuskuren tashi domin kuwa basu da kwatar kudin da aka nima balle rabi. Haka yasa Majid Mamman Ba'are mika hannu. "Na saya!" Shine dama me hannun jarin da ya wuce misali. Yana fadar haka ya mike, tare da barin taron. "Alkali kaji ya saya, ko akwai wanda zai ja ne?" "Babu Malam Aryan!" A hankali ya taka gaban kujerar Hajiya Tani ya zuba mata ido. "kun shirya wasa, ba tare da kun san waye dan wasan ba, ya dawo har na tsawon lokacin da ya dibawa kanshi." Daga nan ya nufi wurin Hajiya ya daukar mata jaka, suka nufi hanya Jamilah da Aneesah suna biye da su. Lokacin da Amaan ya isa wurin Nanah kasa magana yayi. "Munafiki ba kace mana Aryan bai same shi ba? Ko dama munafurci ne yasa kazo don kasan sirrinmu!" "Nana!" Alhaji Haladu ya kira sunanta, "shima bai san kome ba, babu babban shaidanin kamar Aryan yaron nan " "Wai ku yaushe zaku daina faɗa akan abin da ba naku ba? Dukiyar nan da bakin Ya Mamman ya mallakawa Sa'adatu da Yaranta, musamman Majid don Allah ku kyale su mana." "Ai kai ban san wani irin haihuwa nayi ba, baki daya baka da kishi da kishin yan uwanka, ban da jaraba irin ta Mamman ai shi kenan." Hajiya Tani bata ce kome ba, domin dama ba zata tab'a cewa ba, amma zuwan Abdul Majid Mamman Ba'are ya kashe mata kasuwa, domin duk burinta ya lalace. Juyawa tayi ta futa bata musu magana ba, ta nufi hanyar waje ita da d'anta. "Hajiya!" Hannu ta d'aga mishi. A waje suka same su, musamman Aryan."Hajjaju! Ki kara shiri da kyau." "Kana wasa da rayuwarka." Inji Sajjid Mamman Ba'are. Ai kamar jira ake Sajjid ya fadi haka sai ga Press sun shiga daukar hotonshi a bakin kofar kamfanin. "Taron da aka shirya domin ruguza kamfanonin BA'ARE, ya tashi cikin wani irin juyin juya halin, domin kuwa ana cigaba da taron Majid Mamman Ba'are ya bayyana sannan ya saye kamfanin da kaso daya na cikin dukiyar shi, abin da ba a saba gani ba domin duk taron da ake Majid bai tab'a halartar taron ba, amma wannan karon ya tawo cikin ban mamaki " can wani dan jaridar ya amsa da cewa. "A wani abin da ba a san mafarin shi ba, Sajjid Dan wurin Hajiya Tani da ta likawa Marigayi Mamman Ba'are, yayiwa Aryan Mamman Ba'are barazana da rayuwarshi." Jikin Hajiya Tani ne ya dauki rawa, ta juya tana kallon Sajjid da ake ta daukar shi, da sauri ta fada cikin Motarsu, suna shiga ta juya a fusace . "Ina ruwanka da shi? Idan ma wani abu ya maka sai ka yi shiru meye na tanka mishi? Ga ka nan kato amma tunaninka na Yara ne, bakasan ka girme shi ba ne? Amma ya iya nutsuwa ya shirya kome cikin dadin rai. Ka koya daga gare shi." Rintsa idanun yayi yana jin kamar ya fita ta rufe su da duka. "Kai mishi barazana da rayuwarshi? Kasan ko ciwon kai yayi kai ne, idan mun koma gida kayi gaggawar kiran yan jarida ka wanke kanka." "In sha Allah " "Na gaya maka, hatta tari idan kayi duniya zata fassara shi da wata manufa ce, baka gane ba, kana kokarin lalata min shiri na." Hajiya da Yaranta baki daya wucewa gida suka yi, Majid da daman ya rigasu barin wurin taron, sun same shi a dakin shi na Asali , yana kwance. Dakin duhu kamar kullum. "me yasa kake son zama cikin duhu?" Tashi yayi zaune yana kunna wutar da yake gefen gadonshi. "Hajiya ina jin dadin haka ne, domin yana tuno min da wasu abubuwan da suka wuce." Murmushi tayi tana kallonshi ya kara girma, ya nutsu ba kamar lokacin baya ba. Ya zama cikakken namiji me cikar halitta, sadauki da duk inda ake nimanshi ya kai. "Abdul Majid maganar aure fa?" Gabanshi ne ya fadi, ya kurawa ƙasa idanu. Akwai wani abu da yake rufewa a zuciyarshi baya jin zai iya aure. "Hajiya!" Ya kira sunanta muryar shi tana rawa. "Hajiya auren nan dole ne?" "Dole ne Majid! Dole kayi aure domin haka ne zai saka ka kara zama cikakken mutum ka zama magidanci." "Hajiya." "Akwai yar kawata babanta abokin cinikin mu ne, kaje an jima da yamma ka ganta." "Hajiya!" "Bana son musu, ai na maka adalci rabonka da kasar nan." Mikewa tayi tare da fita daga dakin. Sai da ta isa bakin kofar ta juya ta ce mishi. "Ka fahimci gatar da zan maka amma ban maka dole ba." Gyada kai yayi yana jin kamar ya fasa ihu. Hajiya tana fita falon ta Salamatu me aikinta tace "Hajiya akwai baki a falon kasa ." Kura mata idanuwa tayi ta ce mata. "Su waye?" Cikin girmamawa ta ce mata. Hajiya Nana da Hajiya Hadiza!" "Muje!" Tsayawa Salamatu tayi Hajiya ta shiga gaba, har falon kasa suna zuwa suka same su a hakimce. Niman wuri tayi ta zauna tana gaishe su. "Ina Abdul din yake?" Inji Hajiya Nana. "Yana sama!" Kwafa tayi ta ce mata. "Wato har ya kai da ya mai da mutane yan iska ko? Sai yazo gari ya ki zuwa gaishe da Hajiya." Murmushi Hajiya tay ta ce musu. "Na ga dai Abdul Majid Mamman Ba'are, d'ana ne kin manta ne Hajiya Hadiza? Da kika ce Yaransu Hajiya Rabi da Fauziya sune Yaranki, Yaran da suka fito daga jikina Yayan bariki ne, yanzu kuma da wacce kuke tafe?" Kurawa Hajiya idanu suka yi, Nana ta ce. "Bana son munafurci, kiyiwa jikana magana yazo har gida ya..." "Tunda kika kasa hakuri kika zo takalata da faɗa, kin san dai baki isa na zo har gidanki ba." Ya fada yana gyara hannun rigarshi. Kallonshi tayi wannan yaro yana bata tsoro har cikin ruhinta. Hadiye yawu tayi tana kauda kanta domin tana matuƙar tsoronshi. Zama yayi ya kalli Hajiya Hadiza ya ce mata Mama Barka dai." Tab'e baki tayi ta ce mishi. "Barka." "Yanzu Alhaji sai kazo garin nan baka zo ka duba ni ba.? Fisabilillahi." Ta fada kamar zata fashe da kuka..... #thedambuje [2/16, 9:24 PM] Cutie cutie pie: *BAƘIN HAURE....🐾🐾* {Greed for Money is the roots of all evils🫀} Arewabooks:maidambu41 Wattpad:Mai_Dambu Mallakar:Mai_Dambu *009* Tamke fuska yayi yana kallonta, domin ba zai tab'a mantawa da izayar da matar nan ta bashi ba, cikin muryar shi mara daɗi ya ce mata. "Nana kin ajiye ni ne da zan zo na duba ki?" Shiru tayi tana kallonshi kamar zata mutu, idan ta ga yana nuna mata kiyayya haka. "Alhaji ina laifin Nana don ta damu da kai?" Mikewa yayi bai basu amsa ba, musamman ita Hajiya Hadiza da ya tsani ta mishi magana. "Kyale shi ai Uwarshi tana gani yake wulakantani." Murmushi Hajiya tayi tana faɗin. "kin sha gaya min idan kina magana da ahalinki na daina shiga cikin maganar, kuskure ne don na zab'i yin shiru akan na magantu?" Cikin borin kunya ta ce mata. "Hmmm! Haka dai kika ce, amma ni yaushe na ce ki daina shiga cikin ahalina. Yanzu dai nazo ne maganar kamfanonin nan, da fatan dai ba za a cire min hannun jarina ba ko?" "Ni babu ruwana ki same shi." "Tow ta nan kika bullo min Sa'adatu?" A gajiye da halin Nana Hajiya ta ce mata. "Nana meye nawa a cikin wannan lamarin? Yaran nan jikokin ki ne, sannan kuma." "Kawai dai ki ce mana Yaranki sun fi karfinki, amma taya akan wannan yar maganar zaki ce wai babu ruwanki salon munafurci da nunawa kamar ba ruwanki." Inji Hadiza Abdul Majid ba'are, "Hadiza kin ga babu ruwanki da sha'aninmu, tsakanin Nana da Jikokin ta gata ga su ina ruwana?" Ta fada tana kallonsu, kwana biyu da suka wuce har cikin gidan suka biyo ta suka ci mata mutunci har da mata gorin a caca aka aurota, haka duk bai isa ba Nana ta gaya mata cewa ta zuba idanu tayi kallo hatta wannan gidan da take ciki sai ta fice daga cikinshi, sai gashi Allah ya raba gardama ya kawo mata shi cikin sauki, don haka ba zata lamunci rainin hankali ba. "Hmm! Nana tashi muje!" Inji Hadiza, haka suka fito a harabar gidan suka same su, a ran Hajiya Hadiza ta ce. *Shaidanun biyu* kallon Nana Aryan yayi, ita hankalinta yana kan hannun Captain yana goge wata sabuwar bindiga. "Captain ni dai ka nima min lasisin rike bindiga!" "Munafiki algungumi uban me zaka yi da bindiga?" Juyawa yayi ya kalli Nana. "Hajjaju laifin me na miki? Uwar Mamman Ba'are!" Ya tambaye ta, yana wasa da katon lion dog ɗinshi. "Uwarka Sa'adatu gata can a sama." Juyawa yayi ya sumbaci hannun shi ya wurga mata. "Ta iya haihuwa tunda ta haifi Abdul Majid Mamman Ba'are, ta haifi Aryan Mamman Ba'are ba, Uwar Jamilah da Aneesah, Babar Amaan Mamman Ba'are, akwai saura ne?" Ya tambaye ta, cike da takaici ta ce mishi. "munafikin banza." "Da nayi miki me?" "Kai dai wutarka dabance." Sam baya son hayaniya, don haka ya d'anna kunamar ya sake harbi a iska, shiru wurin ya dauka. Musamman Hajiya Nana da ta ji kamar zuciyarta ya harba, kafin su farga daga ita har yarta sun gudu baka ganin alamarsu, sojojin da aka bawa Captain ɗin suka shigo a guje. "Sir!" Murmushi yayi ya musu alamar su tafi da hannunshi. Kar'ar harbin Majid Mamman Ba'are, ya karad'e ilahirin gidan baki daya, wanda yasa kowa ya sha jinin jikinshi, lallai Majid ya iso, Gidan Alhaji Kamilu Abdul Majid ba'are, kuwa tab'e baki yayi ya ce. "Kowa ya sayi rariya yasan zata yi yoyo, ai na gaya musu, babu ruwansu da Yaran Sa'adatu amma suka ki, gashi nan sun takalo mana jaraba." Ya fada yana shan tea a hankali, "ni kuwa sai nake ganin kamar da gayya aka takalota." Kallon Matarshi yayi, kafin ya ce mata. "eh da gayya ce mana, tayi abu ko Yaranta suyi su zama masu laifi ake so." "Amma me yasa suke haka ne?" "Saboda dukiyar Mamman ya raba biyu ya basu rabi, rabi aka yi rabon gado da ita." "Allah ya kyauta!" "Kin yi waya da Maisarah?" "Eh mun yi waya, amma tace min idan suka samu hutu zata zo." Shiru yayi yana kara jin ba dad'i. Kowa a duniya yana farinciki da nutsuwa idan yana tare da ahalinshi, amma shi a nashi ɓangaren dole ya hakura da Maisarah ta koma wurin dangin Mamanta da suke labenon, tunda a can ya auro ta,kuma ba karamin son Yaransu suke ba. Sai dai tun bayan Mutuwar Mamman Ba'are yarinyar taki zama a wurinshi. "Ina Jamal?" " Ya tafi wurin kallo!." Gidan Hajiya Tani. Cikin matsanancin b'acin rai take kallon Sajjid Mamman Ba'are, "kasan yadda na ɓata lokaci akan ka samu damar shiga cikin dukiyar Mamman Ba'are?" Girgiza kai yayi yana durkushe a gabanta. "Kiyi hakuri Hajiya!" "Idan ka kuma bani hakuri sai na tsine maka." Ta fada ranta yana suya, "sai da na gaya maka ba zan dauki kuskure ba, kace babu matsala Amaan zai bamu hadin kai, amma sai gashi daga kai har shi kun fad'i." Kasa magana yayi domin yana matukar tsoron kada yayi magana ta tsine mishi. "Yanzu kana da hanyar da zaka iya dawo min da asarar da nayi?" Girgiza kai yayi, tayi kwafa sannan tacigaba da cewa. "Dake kai lissafinka baya ja, shine ka bude shegen bakinka zaka mishi barazana da rayuwarshi!" "Na tuba Hajiya!" Ɗaukar glass cup tayi ta jefe shi sai da ya tasa mishi goshi, jini ya shiga zuba a Kyakyawar fuskarshi. "Ka sake bani hakuri sai na illataka!" Jini da yake zuba yasa shi rike wurin. "Ɓace min da gani." Mikewa yayi ya nufi dakinshi,ya shiga kallon kanshi a mirror din dakinshi. Wayarshi ce tayi ƙara. Dauka yayi ya ce. "Na'am!" Cizon fatar bakinshi yayi ya ce. "Ban san asara ba, kayan nan Libya zaa shiga da su, ka gayawa Guru ya binciko min duk inda Jaguwa yake a tsakanin sahara da dazuzzukar Kamaru da Nijeriya, idan kuka sake na fita farauta ba zai muku kyau ba." Ya kashe wayar yana me jifa da ita, asara biyu yayi yau baki daya bai tab'a shiga damuwa irin ta yau ba, ban daki ya wuce ya wanke fuskarshi da jikinshi, sannan ya bude first aid kit ya gyara goshinsa. Yana gamawa ya fito yana tsane jikinshi, ya ji harbin bindigar Majid. Datse fatar bakinshi yayi da hakorinshi sai da ya fara jini. Ya sake bakinshi a hankali, yana jin Idanunshi yana cika da kwalla. Idan yana raye sai ya ga bayan Majid, ya raya a ranshi yana me kara tabbatarwa kanshi, sannan ya shirya cikin kananun kaya, ya dauki madubi ya saka domin ta rufe mishi inda aka jefe shi. A falon ya sami Hajiya Fauziya, tana kasa da murya ta ce. "Wato ban san yadda aka yi wancan dan iskan Yaron ya dawo ba, amma tabbas ita Uwarshi abin ya mata dad'i." "Zan fita." Dauke kai tayi tana faɗin. "Hm!" Daga haka ta juya ga Hajiya Fauziya. "Me kika ce?" Cikin tuntuben harshe ta ce mata. "Naga alamar babu nasara." A fusace Hajiya Tani ta watsa mata harara. "Kika ce me?" Hadiye yawu tayi ta ce mata. "Dama nace wannan karon mun fadi ya zamu yi?" Tab'e baki tayi tana faɗin. "Ya kuwa zamu yi? Ku je kuyi shawarar makomarku bamu ba." A zunkud'e tace mata. "Ban gane ba?" Gyara zama Hajiya Tani tayi ta ce mata. "Dama da an samu nasara kamar yadda na gaya miki, kina da kaso saba'in cikin dari, ni zan tashi da talatin kuma gashi ya dawo." Cikin tsannanin takaici Hajiya Fauziya ta sauke kanta kasa, "Ban san ta inda aka samu matsalar nan ba, amma tabbas akwai wani abu." "Idan ma akwai ya dace ki sani kece me yara mata baki daya, gara Rabi tana da Lukman, Harirah tana da Sharif ke fa? Babu ko daya sai Yara mata, kuma kin san koda yau gwanjon kayan ba'are aka yi kasonku bai wuce kason Aryan ba, kai ina ba ma zai kai kason Aryan ba. Duk da yadda muka yi dake na cewa zaki tsayawa Sajjid a wurin sai gashi har aka tashi baki yi kome ba, yanzu zaki zo kice min wani abu." Tana gama fadar haka, ta mike tana me barin Hajiya Fauziya a wurin. A hankali ta fita ta bar gidan, tana me jin takaici me yasa Majid ya dawo daidai wannan lokacin. Alhaji Haladu. Tunda ya shiga yake safa da marwa, kana ganinshi kasan lissafi ya kwace masa. Matarshi kuma me bashi shawara ta musamman ta zauna tana kallonshi. "Abban Afiyyah ban ga dalilin d'aga hankalin nan naka ba, ai ja da baya sai raggo, taya zamu zuba idanu Sa'adatu ta ci bulus bayan ka manta a caca aka ciyo ta." Cikin takaici ya zuba mata idanu, ya ce mata "taya zan manta bayan dan uwana ya ciyo ta ne a caca,a lokacin da yake ƙishirwar d'a namiji a lokacin ya saka kudinshi aka ci kawunta." Murmushi tayi tana kara jin haka shine abinda take bukata,bata kaunar Sa'adatu ta cigaba, amma dole haka zata hakura. Shigowar Hajiya Fauziya kamar an watsota daga sama, yasa baki dayansu suka razana. "Ke lafiya?" "Ina lafiya kuwa." Ta fada tana gyara zama, "ya zamu yi Haladu?" Gyara zama yayi ya ce mata. "ya kuwa zamu ban da mu nime wata hanyar?" "Kamar ya wata hanyar?" Gyara zama yayi yana faɗin. "Dole zamu marawa Tani baya, sai mu san me za ayi kuma." "Kana ganin marawa Tani baya shine mafita?" Inji Hajiya Turai Matarshi. "Eh mana shine mafita, domin ita ba zata watsar da ra'ayinmu ba" Dariya tayi tana faɗin. "Lallai fa, tow Tani itama hanyar niman shiga take kan dukiyar Yaran Sa'adatu, idan kuka mara mata baya zata iya juya muku baya, idan kuka nime naku na kanku kowa zai kasance a ankare. " Shiru suka yi kafin kuma suka ce mata. "Bamu fahimci inda kika dosa ba?" A hankali ta gyara zamanta ta warware musu fahimtarta, sannan ta kara musu kwarin gwiwa da cewa dole su kasance masu mika kai domin idan baka iya kama barawo ba tow shi zai kama ka." Nan suka yi na'am da shawara ta, har Hajiya Fauziya ta fita, Hajiya Turai ta cewa Mijinta. "Bari na gaya maka gaskiya, matar nan munafuka ce ka sani nima kuma na sani, so abin da zan gaya maka. Zata tafi wurin Hajiya Tani da zancen nan, kai ka fara kiran tani ka gaya mata abin da ka yanke. Sai na gaya maka yadda zamu yi" Ai kuwa kamar yadda ta fada haka ya kira Tani, ya gaya mata kome da kuma yankar bayan da Hajiya Fauziya ta mata, sannan suka dauki laifin kacokan suka daura mata, ita ce ta kawo musu zancen a shiga malamai. Jin shi Hajiya Tani take, sai da ya gama ta ce mishi. "Zan duba al'amarin" Ta kashe wayar, murmushi Hajiya Turai tayi ta ce mishi. "Ka shirya zuwa bayan Magariba ka tafi gidan Hajiya Sa'adatu ka yi sulhu da ita. Idan ta lalace maka anan a can zaka fita" Kurawa Matarshi idanu yayi tunda yake bai tab'a zata shaidaniya ce har haka ba. Take ya sake murmushi yana faɗin. "Lallai Hajiya ke duniya ce." Murmushi tayi tana faɗin "taya ba zan kasance haka ba, ina tare da dai ga makiya sun rufa maka baya ta ko ina, ai lahu a gare ni na tsaya maka, don haka kada ka ji kome mijina." *** Wurin karfe biyar na yamma Hajiya Sa'adatu tana kan abin sallah, tana lazimi Nabeeha matar Aryan ta shigo hannunta dauke da katon tire, bayan ta Aryan ne dauke da Kwando, "Assalamu alaikum Barka da maraice Hajajju." Sallamewa tayi tana kallonsu fuskarta dauke da murmushi ta ce musu. "Amin wa'alaikumus Salam, barkanku mutanen kirki." Gyara zama tayi tana faɗin. "Nawa ne ko na Hammanku?" Dariya sukayi. "Hajiya naki da nashi ne, muka ce bari a kawo mishi, duk da ban gaya mata da wuri ba." " Hajiya kinji ba yaki gaya min zai tawo da hamma kawai sai gashi nan yazo da zancen akwai bako." Nabeeha ta faɗa tana tura baki. "Baka kyauta ba, maza jeka dakinshi ka taso min shi." "Tow Hajiya." Haka ya fita zuwa dakin Majid din da yake kwance, ya lullube kanshi da mayafi, dakin ya bada wani irin duhu. Kunna wutar dakin Aryan yayi, ya hango shi zaune ya jingina da allon gadon. Amma kanshi a lullube yake. "Baka da lafiya ne?" Janye lulluben yayi yana kallon Aryan. Dauke kai yayi yana me sake lullube kanshi. "Kazo falon Hajiya da yake sama Please." "Me zan yi?" A yanayin rayuwarshi matukar ba'a wurin aiki ba,baka tab'a ganin fara'arshi, tashi yayi ya sauka daga gadon ya nufi ban daki. Sai da ya gama uzurinshi ya fito ya saka hula a kanshi ya fita. Zuwa falon hajiya domin sun fito daga ɗakinta, yana shiga ya same su a kan kafet sun baza abinci. "Matar Aryan ce ta maka abinci." "Nagode sosai!" Ya fada yana gyara zamanshi a kafet ɗin, Aryan ya zuba mishi yana jan shi da hira. "Amma shirun da Hajiya Tani tayi babu magana a kasa?" "Allah yana sane kuma yafi mu sanin abinda yake zukatansu." Inji Hajiya, tana cin abincin itama don ta lura Majid yaki cin ko loma daya ne, har yau yana shakkar cin abincin kowa, domin rufawa rayuwarshi asiri yasa ban da girkin Hajiya kai ko tea bai yadda ya ci wani abu daga wani wurin ba. Shi yasa a duniyarshi yake shakkar kaidin mace. Saboda kaf duniya babu wanda yasan cewa sanadin jinyar Mahaifinsu guba ce. A hankali ya tura abincin yana murmushi. "Bana son abincin da aka saka citta da tarfarnuwa, domin ina da allergy." Sanin ba zai ci bane Aryan yayi maza y kare dan uwanshi. "Wayyo kayi hakuri, na manta na gayawa pretty baka cin citta da tarfarnuwa." Murmushi yayi ya mike, karshe abincin da bai ci ba kenan. Kuma ai Hajiya tasan ba zai ci ba. Ita tana ganin har yau Majid bai warke ba, pretend yake kamar mai lafiya amma a zahirin gaskiya bai da lafiya. Shi yasa take son yayi aure ko zai samu wacce zata jure matsalarshi, "Kiyi hakuri haka yake, baya cin citta da tarfarnuwa ne, tun yana Yaro." Itama Hajiya ta fadi haka, shi kuwa gogan naku yana shiga dakin drower yaja ya Ciro kudi me yawan gaske, ya fito daga dakinshi kenan suka hadu da Amaan Mamman Ba'are,. Kallon kallo suka yiwa juna kafin kowa ya kame kanshi, akwai wannan rigimar na sako da sako, amma ita Hajiya bata taɓa kawowa al'amarin zai lalace har girman yaranta ba, a zahirin gaskiya tsanar da Amaan yakewa Majid tayi yawa da har sai da kowa yayi magana. Wani irin tsana ce irin na matukar na samu dama sai naga bayanka. Amma a bangaren Majid babu wannan tsanar kawai shi mutum ne da yasan ciwon kanshi da darajar kanshi,. Sannan bai kullaci Amaan har haka ba. Kamar yadda shi ya kullace shi, reni ne baya so kuma ya fahimci Amaan yana da reni da son abin duniya. Kiyayyar tasu ta faro ne daga lokacin da Alhaji Mamman Ba'are, ya bar wasiyya akan cirewa kuri'arshi ya gadarwa Majid, sannan ko a halin jinya yadda Alhaji Mamman Ba'are yake ta rokon a nimo mishi Majid ya roke shi gafara kada ya mutu da hakkinshi ya kara tunzura dayawan mutanen dake jikinshi, bawan Allah nan har ya mutu da rokon a kira mishi Majid, don Allah ya yafe mishi. Duk da akwai hakkin iyaye akan Yaransu, haka akwai hakkin Yara akan iyayensu, wannan al'amarin ya tab'a zuciyar kowa na jikin Mamman Ba'are musamman Hajiya Nana wacce idan taji yana cewa Majid ba zaka zo ba, Majid kana ina ne? Majid zan mutu ban ga fuskarka ba. Majid nasan na cuce ka, Majid kazo. Shi yasa bayan kome da ya warewa Majid, akwai wasu takardun da ya bawa abokinshi. Wanda babu wanda ya sani daga Hajiya sai Abokinshi Alhaji Abubakar Abzin, shima shahararren dan kasuwa ne da yake garin marad'i, kuma wani ikon Allah Alhaji Abubakar Abzin bai tab'a takowa zuwa Niamey ba, idan abubuwa suka shiga gaban Hajiya wurinshi take zuwa. Yanzu ma tunaninta kafin hutun Majid ya ƙare zata kai shi garin marad'i, su gana. Wannan shine shirinta. Sai da Majid ya jira Amaan ya shiga dakin, sannan shima ya shiga ya mikawa Hajiya kudin tare da mata magana da idanu, ta bawa Nabeeha. "Barka Hammayo." Inji Salaha matar Amaan, "Barka!" Ya fada a hankali, idan baka saka kunne ba, ba zaka ji me yace ba. Shigowar yara uku suna ihu, yasa shi juyawa. Sai wani guda daya da yake bakin kofar shiga falon Hajiya. "Appa kaga Shuraim ya dake mu ko?" Yaran suka nufi wurin Amaan, mikewa Amaan yayi tare da nufar Shuraim ɗin. Shima Aryan har zai mike Majid ya kalle shi, a fusace ya koma ya zauna yana kwafa. "Kai wato munafurcin da ka gada daga wurin wancan dan iskan Yaron shine zaka fara." Ya rike kunnen Yaron. Amadadin yaron ya fasa ihu, sai ga Amaan yana fasa ihu, babu wanda ya san me ya faru, sai yaron ne kawai ya san me ya faru. Daukarshi Majid yayi suka fita. "Daada taka mishi kafa kayi ko?" Ya rad'a mishi a kunne. "A'a" "Daada Allah yana kona me karya inji Ummina." Dakinshi ya shiga da shi, ya Ciro katon kwalin chocolate, ya mika mishi sannan ya kara dauko dayar ya ce mishi. "muje!" Haka ya riko hannunshi har falon Hajiya suka koma, zama yayi ya kira sauran Yaran, Yaran Amaan dake duk mata ne, tasowa suka yi duk da harara su da Amaan yake, haka suka tawo wurin Majid ya ajiye su a gefensu. Sannna ya mikawa yar karamar yar Aryan hannu da sauri ta taso. Ya ajiye ta" Kai Ayyan ka sammata a naka, Anum da Widad zan basu anan." "A baco na Yaya!" Injin yarinyar. "Bushrah!" Babanta ya daka mata tsawa. D'ago kai Majid yayi ya watsa mishi harara. "Tow shi kenan tunda baki son na Yaya Anum a san mata?" Gyada kai tayi, ya bude musu kwalin ya ciro chocolate din ta ce mishi. "Dada a bacon na Anunu." Ta maida hannunta baya. Hajiya kuwa me zata yi ban da dariya ta ce mishi. " Ai yadda ka bawa sa'anta kwali itama haka zaka dauko mata kwali domin bata yarda a raba kansu da yan uwanta." "Uwata taso muje." Ya dauki su Anum ya zaunar dasu a saman kujerar ya dauki Bushrah har dakinshi ya dauko mata nata, tun da ya bata, ta fara bashi labarin da Allah ya gani bai fahimci Yaren ba, har suka isa falon, bashi labarin take. "Ja'ira mara kunya, dole ki bashi labari anya takwara haka zamu yi dake." "Jiya babu luwana dake, ban baki cokulet dina ba " ta zauna ta yaga kwalin. Ya zube dukka. "Dada ashe min!" Wato ya kwashe mata, "abawa jiya." Ai kuwa Hajiya ta wafta ta ce. "Sai dai kada abawa gobe, amma jiya kan zan sha." Haka aka yi ta hira har wani lokaci kafin lokacin magariba tayi duk suka tashi zuwa Masallaci.. *Sansanin gudun hijira* #thedambuje [2/16, 9:24 PM] Cutie cutie pie: *BAƘIN HAURE....🐾🐾* {Greed for Money is the roots of all evils🫀} Arewabooks:maidambu41 Wattpad:Mai_Dambu Mallakar:Mai_Dambu *010* *Sansanin Yan gudun hijira* Adamawan Kamaru. Abu na farko da muka fara fuskanta a camp din, shine rashin matsuguni da kuma kayan amfani, wai a haka dai an kawo mu nan saboda akwai inda zamu zauna, sai dai tunda aka yasar damu a asibitin wanda ba laifi an gwada mana kulawa da duk wani abun da ya dace, sai dai kuma babu wanda ya kuma zuwa da zancen ga yadda zamu yi, kwanan mu goma duk da haka mun samu lafiya daidai gwargwado. Idan ka cire Nenne da Yakumbo lantana da kullum jininsu yake hawa. Ita kan Yakumbo idan ta zauna sai ajiyar zuciya tana kiran sunan Sa'idu. "Ayya ayya akan idanuna suka kashe min shi. Ko tausayin rai basu ji ba, suka kashe min Abubakar yaron da bai gama koshi da nono ba." Sai ta fashe da kuka, ita kan Nenne bata hummm bata hmmm, hasalima tsayuwa mai kyau bata iyawa, domin a bakin Munaisah nake ji wai an mata ɗinki ciki da waje, sakamakon yadda suka mata kaca-kaca. Ashe wani lokacin kuka ma rahama ce, har yau ina son nayi kuka amma ko da wasa ban zubda hawaye ba, sai dai idan na tuna mutuwar Baffa'm sai naji har zuciyata tana wani irin bugawa, can kuma naji kirjina yana min ciwo, dole sai na kwanta. Lokacin da likita yazo na gaya mishi, kura min idanu yayi kafin ya ce min. "Kina son ki mutu ne da kuruciyarki? Me yasa kike tuna abin da ya faru?" Sunkuyar da kai nayi, ina wasa da yatsun hannuna. "Zan bada test a miki, kada ki sake na ga wani abu domin zan na miki allura kullum." Murmushi nayi nace mishi. "Ni." "Ke ke! Meye?" "Ina son nayi kuka ne?" Kura min idanu yayi kafin ya ce min. "shi kuka yana zuwa ne idan lokacin bukatar shi yazo, lokaci na zuwa zaki yi kuka kin ji." Gyada mishi kai nayi, ina faɗin. "Nagode!" "Ba kome yar fillo!" Daga haka na fito daga office din, na fita daga cikin asibitin can harabar asibitin na nufa na tsaya ina shakar kamshin ƙasa, domin ina son na samu nutsuwa. Idan nace ina jin dadin rayuwa nayi karya, ko dariyar da nake a dole nake yin shi ba wai yana kaiwa zuciyata ba ne. "Nan kika fito?" Juyawa nayi na kalli Addah ko daga ina take oho. "Hmm!" Nace mata, gyara tsayuwa tayi domin itama har yanzu bata gama jin dadin jikinta ba. "Zahra babu wani abu ne, kin ga saboda Lantana da Matar Babanki anki sallamar mu, balle har mu samu damar barin asibitin nan." Shiru nayi ina nazarin wace irin zuciya ce da Addah haka. "Naji Zulaihah tana cewa akwai wani abu a wurinki." Sai lokacin na samu zarafin mata magana. "Zuzu ba zata gaya miki akwai wani abu a hannuna ba, sai dai idan Munaisah ta gaya miki." Na fadi haka ina kallonta, sai kuma ta fara kame-kame. "Yauwa ashe." "Addah don Allah bana son damuwa, ki je kice ta baki kudin ki kyale ni." "Hmmm! Ai kin san dai zuzunki ba zata tab'a bani wani abu ba." Ta fada tana hararata, na ga karfin hali a wurin Adda. Haka ta taso ni a gaba, har dakin da aka kwantar damu, na nufi wurin Zuzu nace mata. "Bani jakar nan" a hankali ta d'ago kai ta kalle ni, bari na gaya muku wani abu dukar da aka mana ya haifarwa Zuzu rashin ji da kunnenta daya. Bata ji sosai sai ka mata magana da karfi, ni kuma bana son na sabar mata da yawan magana da karfi. "Me zaki yi da shi?" Ta tambaye ni, tana kallon Addah da ta haɗe rai ita kada ma ta sakata a cikin lissafin ita ta turo ni. Itama kuwa Zuzun tawa haɗe rai tayi ta ce da ƙarfi. "Ban san inda yake ba." Tunda ta fadi haka nasan wallahi ba zata bada ba, kuma duk abin da za ayi sai dai ayi amma ba zata tab'a bada jakar ba. "Ai kin ga irinta, waye ya gaya miki ana mu'amala da irin Zulaihah da tana da jin ta ma ya aka kare balle ta rasa jin." Juyawa nayi na kalli Munaisah tana matsa kafar Nenne, Ummi tana kwance gefen Yakumbo. Ni daya ce bani da uwa anan, ita me uwar ma bata samu tausayi da jin kai ba. "Addah lalurar Zuzu ba siya tayi ba, sannan likitocin kwakwala da kunne sun ce zata dawo da jin ta kamar baya, matukar tana amsar magani, me yasa kike mata gorin ji? Idan tausayi da jin kai bai shiga tsakaninku ba, Addah kada tsangwama da hantara ya shiga tsakaninku domin wata rana ita ce zata tsaya miki." Daga haka na koma wurin Munaisah na ce mata. "Ya jikin Nenne?" Idanunta da suka yi bullu-bullu sakamakon kukan da take yi ta ce min. "Jikin Nenne kara zafi yake, gashi yau bakiɗaya bata ko magana." Wani irin tausayi ne ya cika min zuciya, na ce mata. " Bari na je na ga Dr Moses!" Haka na fita, a hanya na hadu da Nurse rabeka, "yar fillo ina zaki?" "Yawwa Aunty Nurse zo ki duba min Mamanmu." Ba musu ta bi bayana har dakin mu, tana shiga ta fara dubata da sauransu. Kallona tayi ta ce min. "Yar fillo bari na kira Dr Moses!" Haka kuwa ta fita can sai ga su tare da wasu likitoci biyu, haka suka dubata sannan suka saka Nurse Rabeka da Nurse Ali suka dauketa a keken marasa lafiya aka fita da ita, haka muka bi bayansu. Har wani wuri can da aka rubuta ICU da manyan harufa. A wurin muka tsaya aka shiga da ita, tunda muka tsaya a wurin Munaisah ta fashe da kuka, kuka take tana faɗin."me yasa? Me yasa sai mu? An kashe mana iyayenmu, anci zarafin mu da iyayenmu, an kona mana dukiyarmu da muhallinmu me yasa gwamnati ta zama makauniya?" Rungumeta nayi, ina buga bayanta. "Zahrah Nenne kawai ta rage min sai ke, Zahrah idan wani abu ya samu Nenne ba zan tab'a yafewa Gwamnatin Nigeria ba, ko ina ka shiga kome mugun aikin da aka yi, zaka ji ance Fulani me yasa aka tsane mu? Kowa yasan bafulani daga kiwo sai sayar da madara yake, amma a yau duk wani aikin ta'addanci zaki ji sunan bafulani ni ne, me yasa Zahrah me muka yi? Zahrah bamu da yanci anan mu da bakin haure daya ne, babu tausayi, babu tausassawa, babu." Rufe mata baki nayi. "Kowane bawa da yadda rayuwa take zuwa mishi, idan muka kalli yadda tazo mana, sai mu amshe ta da hannu bibbiyu, kada mu zama masu son rai, shi Ubangiji bai tab'a jarabtar bawa akan baya sonshi ba, yana jarabtarshi ne gwargwadon karfin imaninshi. Ki cigaba da addu'a Allah ya bata lafiya.". Wato ko Munaisah yar gata ce, tunda ga Mahaifiyarta a raye, ni fa? Gani a kasar su mahaifiyata, amma ban san ta inda zan fara nemanta ba. Haka na hadiyi tawa damuwar, domin ba lokacin bayyana tawa bace, haka na cigaba da zama da ita, domin Addah bata biyo mu ba, Zulaihah kuwa bata iya tafiya saboda kafarta da aka mata dauri. Ta samu tsagewar kashi, muna zaune a wurin har suka fito, mikewa nayi na nufe su. "Ya jikin Mamanmu?" "Da sauki!" Dr Moses ya faɗa, yana kallon yadda muke raba idanu. "zamu iya ganinta?" Girgiza min kai yayi yana faɗin. "tana ƙarƙashin kulawar computer ne." Sabon kuka Munaisah ta fashe da shi, tana rike kirjinta. "Wayyo Allah na, Wayyo Allah Nennena. Don Allah ku barni na ganta." Girgiza kai yayi yana faɗin. "zaku kanta amma ba yanzu ba, sai ko zuwa gobe." Rufe bakina nayi, cikin rudani ina kallonshi. Ita kuwa Munaisah kuka take me tab'a rai, baki ɗaya na rasa ina zan saka kaina. "Yar fillo kada ki damu fa, zata ji sauki kawai an dora ta akan kulawar computer ne, ki cewa Fulani ta daina kuka haka. Nenne zata ji sauki." Gyada kai nayi, ina kallon Munaisah, haka suka tafi suka bar mu a wurin. Dakyar naja ta muka koma dakinmu, sallah muka yi. Abincin da ake rabawa na asibitin aka kawo mana, ban iya cin ko loma daya ba, haka Munaisah itama bata iya ci ba. Muna idar da sallar Isha, na mike xan fita Munaisah ma ta biyo ni haka Zulaihah ma ta ce mana. "Ku jira ni." Ummi da take jikin Yakumbo ta ce mana. "Zahrah akwai maganar da Yakumbo tace zata gaya miki don Allah." Kallonsu Zuzu nayi nace musu. "Kuje ina zuwa." Zuwa nayi na zauna a gefen Yakumbo. "Gani Yakumbo!" "Zahra'u!" "Na'am!" Ga Ummi nan na baki amanarta. Ta shiga lallubar hannuna, kallon Ummi nayi da ta dauke kai, tana share hawayen da yake zuba mata. "Sis yaushe yakumbo ta daina gani." Murmushin karfin hali tayi ta ce min. "Zahra'u, don Allah ki taimaka min ki maida Ummi Yola wurin Dan Malam, ina tsoron kada na mutu rayuwar Ummi ta lalace." Wato sai na rasa ya zan kwatanta halin da nake ciki, shin zan fadi ne na mutu ko kuma zan fita ne nace a bude zuciyata a ciro min shi a rage damuwar mutane da yake cike a bar min tawa. Ajiyar zuciya na sauke sannan na rike hannunta. "In sha Allah, zan cika alkawarin da na daukar miki." Itama rike hannuna tayi da kyau ta ce min "Ki yafewa Nenne, don Allah ki yafe mana, don Allah ki yafe mana ko zamu samu rahamar Allah." A wannan lokacin ina son nayi kuka ko zan rage nauyin da yake zuciyata, amma ina zuciyata sai kara zafi take tana kara taurarewa, ina ga ba mamaki an sauya min zuciyata daga tsoka zuwa dutse. A hankali na zubawa Yakumbo idanu. "Duk abinda ya wuce ya wuce abar shi har a wurin Ubangiji ya wuce." Na fada ina kokarin barin dakin, "Kina nufin kin yafe mana?" "Har a gaban Ubangiji bana fatar haka ya tsayar damu a kan wannan abin, na yafe maku." "Ki bari na gaya miki abin da muka aikata mana!" Juyawa nayi na koma wurinta, na saka hannu na rufe mata bakinta. "Nace na yafe, kuma ko kin gaya min ba zai sauya kome ba, sai ma lalata kome da zai yi. Ina fatan nima Ubangiji ya yafe min laifin da nayi mishi ya rufa min asiri, ba ya tona min ba. Yakumbo abar maganar Allah ya baku lafiya." Rike hannuna tayi tana faɗin. "Lallai Allah ya albarkaci rayuwar Aminatu a duk inda take, ta haifi daya tamkar da dubu. Zahra'u Alfarma daya zaki min, ina son na mutu a wurin dan Malam." Kallonsu nayi kafin nace mata. "Yakumbo in sha Allah za a maidake wurinshi." Daga haka na fita, ICU na nufa, a hanya na tsaya tare da jingina da bango,na rasa me ke min dadi, sai da nayi nazari kafin na wuce wurin su Zuzu. "Sai yanzu?" "Eh!" Na fada ina me zama a gefen Munaisah. "Zuzu Yakumbo tana son komawa gida, ko muma mu koma ne?" Gyada kai tayi kafin ta ce min. "idan mun koma wurin waye zamu zauna?" "Wurin Ya Dan Malam mana!" Na fada mata, ina kallon reaction ɗinta. "Hmm! Shima nima yake, ba laifi idan kin saka su Yakumbo a motar, amma har ga Allah na yafe Nigeria, domin nasan sun kashe min har mahaifina." Ta fada tana kallon kofar icu ɗin. Kaina a kasa ban kuma magana ba, har dare ya fara yi na riko hannun Munaisah. "Sister taso muje." "A haka xan bar Nenne a nan? Idan wani abu ya same ta fa." Girgiza kai nayi sannan na riko hannunta, "Muje babu abinda zai faru, in sha Allah." Daga haka muka juya zuwa dakin mu, dukkansu sun kwanta nice kawai nake zaune, ga Addah da bata zama haka kawai ta tsiro da yawo, ina zaune a wurin har wani lokaci na tashi na shiga ban daki nayi alola na fito na shimfida dan kwallin kaina na fara sallah. Sallar nafilla nayi ta jerawa, ina rokon Allah ya yafewa iyayenmu da suka rigamu zuwa gareshi, ya musu rahama. Ni kuma Allah ya bayyana min mahaifiyata. Su Nenne kuma Allah ya basu lafiya. Haka na cigaba da sallah har wurin karfe biyu, a lokacin Addah ta shigo. Gadonta ta nufa ta kwanta. "Addah ke daya ce me lafiya a tsakaninsu Yakumbo, amma Addah kin ki bamu lokacinki sai ki tafi yawo ba zaki dawo ba, sai dare ya raba." "Tow Zahrah sai ki rufe ni da duka, dake an ce miki yawon banza nake tafiya ba." Ban kara ce mata uffan ba, ina jin Zuzu tana kwafa, idan na fahimta idanunta biyu. Kawai ba zata yi magana ba ne, haka na kwana, kusan kamar nurse domin ina jikin Munaisah ina kula da Yakumbo. Wannan al'amarin ba karamin tab'a rayuwata da lafiyata yake ba, da gari ya waye bayan mun yi sallar asuba, sai ga wasu mutane uku, biyu maza daya mace. "Zamu mai daku sansanin gudun hijira ne, domin mun samu labarin yadda wasunku suke fita yawon dare." Dukkanmu Addah muka zubawa idanu. Matar nan tayi mirsisi da idanunta, ta nuna ni. "Ga yar iskar da take bin maza, nayi fadar nayi maganar na gaji." Wato wani irin razana muka shiga, domin babu wanda ya kawo Addah zata iya min sharri, ni kuwa banyi mamaki ba, domin fiye da haka idan akace zata min wallahi zan yarda, matukar Hajiya Addah ce kaɗan da aikinta, amma kuma abin da tab'a rai. "Tow koma waye, zamu tafi da ku." "Addah ki fara gina wutarki kafin ki tafi lahira." Inji Zuzu, sake bude baki tayi zata kara magana. Na rufe mata baki saboda ko Munaisah da muke tare itama bata ce kome ba, hakan yasa na gane ni ce bare a cikinsu, dukkansu abu daya ne. Haka na shiga haɗa kayanmu. "Muna jiranku." "Ranki shi dade, akwai yar Uwata da bata da lafiya an kaita ICU ko zan zauna a jikinta?" "Ba zaki zauna a jikin kowa ba, domin kuwa kika zauna a nan ba jinyar zaki yi ba, yawonki zaki shiga yi." Inji Zuzu. Haka suka fita, ko ya aka yi sai ga Nurse Ali da Rabeka. "Yar fillo, ga wannan katin yanzu na amsa miki keda yar Uwarki. Koda zaku fito daga camp zuwa nan tow ku tabbatar kun rike wannan katin, sannan Fulani zata tsaya tunda Mamarta ce, ke idan an jima yayi sai kizo ki canjeta. inji Doctor Moses." Ba alfahari ba, haduwa da mutanen kwarai a jinina yake, duk inda na shiga sai na hadu da mutanen arziki, haka muka fito baki ɗaya, a lokacin da zamu bar Asibitin Dr Moses yaga Yakumbo ya dubata da kyau, sannan ya bamu magani akan muna bata idan ya kare muzo da ita taga likita. Gyada mishi kai nayi, muka tafi inda Nenne take, dake zamu bar Munaisah a wurin. Rike hannunta nayi. "Don Allah ki kula kin ji." Gyada min kai tayi, ban san wani irin zuciya nake da shi ba, ni fa bana iya rike ka idan kayi min, ina ji a raina babu amfanin rike mutum araina domin haka ba zai amfane ni da kome ba, sai ciwon rai. Ni kuma bana son hassada da kyashi ya shiga, zuciyata saboda kai. Haka muka isa camp din, cikin wani irin yanayi, muna isa Office din shugaban da yake kula da camp din aka kai mu, aka saka sunanmu, da inda muka fito da dalilin fitowarmu. Ana gamawa muka fito daga office din, Mutanen da suka kawo mu, suka raka mu har wani tanti, shiga muka yi baki dayanmu. Ba laifi cikin a rufe yake kasar kuma an lailaye shi da leda, alamar waɗanda suka zauna a cikin tantin suna da tsafta. Zubewa muka yi, daya matar ta ce min. "Fillo zamu je ki fara dauko muku kayan shimfidarku." Gyada kai nayi, muka fita da ita,haka nayi ta jido kayanmu. Har da kayan Abincin. Cikin sakin fuska matar ta ce min. "Akwai kayan abinci ku nawa ne?" "Mu bakwai ne." Na fada a sanyayye. "To shi kenan kai kayan ki dawo." "Amma me yasa za a bamu danyen abinci?" Murmushi tayi tace min. "Danyen abinci shine zamu iya baku, idan muka ce dafaffe ne, a wurin bayarwa aka fara dambe sai an zubda abinciin baki daya." "Subhanalillahi!" Na fada ina ɗaukar katifa da ta daura min, har tantin mu ga nisa. Ina kaiwa na kuma juyowa zan koma muka hadu da wata yarinya. Itama budurwa ce. "Barka mai kyau!" Murmushi nayi mata sannan na ce mata. "Ai kema mai kyau ce." Juya idanu tayi, "Hmm!" Ai ban tsaya bin nata ba, na wuce abina domin ina da abin yi. Tass na kwaso kayan har da kayan abinci, ina tsaye ina haki Zuzu ta ce min. "Yanzu ya zamu yi idan aka fara ruwan sama?" Juyawa nayi na kalleta. "Kamar ya?" "Wurin girki. "Ok na fahimta. Kamar an wurgo ta,ta shigo cikin ba sallama. "Batun girki kuke? Akwai inda ake sayar da itaccen da gawayi, har gas akwai me sayarwa." Ta fada tana rangwad'i da yauki. Da fulatanci Zuzu ta ce min "Zahra a ina kuka kwaso mana Zee yauki?" "Ande!" Ita kuwa sai yauki take, wato ko Allah ya shirya zuzu. "Dukkanku masu kyau ne, wow." "Yanzu ya zamu yi kenan mu sayi gawayi kawai domin zai fi gas din nan, ko?" Na tambayi Zuzu. "Tow ya zamu yi da kudin nan na naija ne da" "ai duk suna amsa, kasancewar garin nan yana kusa da boda, zaku iya sayayyarku da shima." "Mun gode amma meye sunanki?" ."Aina'u suna na!" Gyada kai mukayi, muna kallonta kafin Zuzu ta ce . "Kina da kyau!" Ai kuwa kamar an kunna radiyo, ta fara zuba. "Zahra'u dauke kawarki ta rakaki, ku nimo mana abinda zamu ci bamu isa da surutun ta ba." Inji Addah ta faɗa da fulatanci, haka na jata muka tafi har inda zamu sayi kome,, dake a cikin kayan da aka bamu har da kayan miyar gwangwani kifin gwangwani, da sauran tarkacen irinsu garin kunu, shinkafar ci da ta tuwo garin madara, burabisko, mangyad'a da man ja, magi ma ban tab'a ganin irinshi ba, sai a wurinsu, haka muka siya har da tukunyar hannu da kwanuka. Anan wurin take cewa. "idan ba zaku yi amfani da kayanku ba, ku bamu zamu baku kuɗi." Murmushi nayi mata nace mata. "Bamu koshin da zamu sayar da abinci ba, ki jira idan mun koshi zamu kawo mu sayar." ........ 08130269641 *Mai_Dambu* [2/16, 9:24 PM] Cutie cutie pie: *BAƘIN HAURE....🐾🐾* {Greed for Money is the roots of all evils🫀} Arewabooks:maidambu41 Wattpad:Mai_Dambu Mallakar:Mai_Dambu *011* Bige hannuna Aina'u tayi cikin rangwad'a ta ce min. "Ba a fadar haka, Uwar mugu bata lamuntar cika baki" sannan ta kalli matar cikin fara'a ta ce mata. "Uwar mugu muna neman yafiyarki domin bakuwa ce daga Nijeriya bata san kome akan gurin nan ba." Murmushi matar tayi tana kallona cikin wani irin kallo kafin ta juya ga Aina'u tana murmushi ta ce mata. "Ya sunanta?" Cikin kad'adi irin na wanda ya saba ta ce mata. "Zahra!" Rike baki Uwar mugu tayi tana cewa. "Mai Babbar suna kenan, kun ga uwata takaina, maza ku je babu komai ai Uwata ce bata laifi." Aina'u kamar ta zube kasa, tayi ta godiya har da cewa. "In sha Allah zaki same ta mai biyayya." Idanunta kyam a kaina, ni kuwa ko dar ban ji ba, domin matar asalima kawai bata kwanta min a rai ba, haka muka bar wurin ko inda take ban kuma kalla ba, babbar mace ce amma yanayinta zaka kalla kasan bata da mutunci. "Amma matar nan bata da mutunci ko?" Da sauri Aina'u ta rufe min baki, ta juya tana kara gaida matar, wacce da na juya na kalleta ni take kallo."Uwar mugu bata da matsala, kuma bata da abokin tarayya a cikin sansanin gudun hijirar nan, mace ce da tasan kan duniya idan taso zata iya janyowa a Kore ki, ko kuma a kwace muku kayan abinci. Tana da Yaro ɗaya baya cikin sansanin nan, yana tafiya farauta ne, sai dare ya ke shigowa. Matar tana da matuƙar hatsari idan ka nuna mata kai ma dan duniya ne, idan kuma ka bita a hankali zata iya sakawa kowa ya kaunace ka, idan ka nuna mata baka da mutunci zata iya sakawa a tsane ka. Uwar mugu mace ce da take hada mutum da mutane masu arziki na wajen nan. Nima ba karamin arziki na samu a ta sanadinta ba." Ware idanu nayi na kalli Aina'u, "yanzu Aina'u harkokin bin maza ta dauraki a kai?" Murmushi tayi irin bai dame ta ba, ta ce min. "Kai ji wata magana sai kace wani saɓo nayi, ai wannan rayuwar idan baka iya d'aga kafa ba, ba zaka huta ba, abincin da aka baku kin zata zai kai wata ne? Bari ki ji, daga zarar kun kai sati biyu nan ne idanku zai raina fata." Baki daya naji hankalina ya tashi, bamu rabu da bukar ba an haifi Habu, wato mun yi gudun gara mun tadda zago. Ban kuma magana ba, haka dai na barta tayi ta surutu domin ban san me take fada ba, haka muka isa, na ajiye kayan na shiga daki na samu wata mata suna ta hira. "Laaa Mamata itama tazo kenan." Ta shigo, "Tumba!" Ta kira sunanta. "Na'am Aina'u." Zama tayi a jikinta tana murmushi. "Kin samu kawa daga zuwa kenan?" Mamar ta tambayeta. Juya idanu tayi tana faɗin. "Eh Tumba." "Dama Yarki ce?" Gyara zama tayi tana murmushi ta ce mata. "Y'ata ce, na tafi Saudiya na barta ina dawowa rikicin boko haram ya koro mu nan Kamaru." Shiru tayi kanta na kasa kafin ta ce. "Sai da muka yi kwana talatin a hannun Yan boko haram, suna gana mana azaba, ga cin zarafi da fyade." Ta rungume Aina'u, itama yarinyar k'amk'ame Mamarta tayi, alamar har yau idan suka tuno abin yana musu zafi da ciwo. "Sun ci zarafinmu." Mikewa nayi na fita waje, kallon sama nayi domin bana son hawayen da ya taru a idanuwa na su zubo. "ku shiga da kayan ciki domin za a sace." D'ago kai nayi muka yi ido biyu da shi. Security ne domin naga sanye yaƙe da Uniform. "Tow!" Nace mishi. Na shiga da kayan cikin tantin mu, "Aina'u a ina zan samo ruwa?" Mikewa zumbur tayi tana faɗin. "Muje!" Ta dauki daya daga cikin langar da ta sani na saya. Muka fito ban ga mutumin ba, haka muka ratsa ta dakinsu, da mutane a ciki. Guga ta dauka, dakin ban da warin sigari baka jin kome. Kafin ta dauki gugar daya daga cikin mazan dakin ya fisgota. Tana dariya ta ce mishi. "Meye haka, Faruq?" Da sauri nayi baya, na tsaya a waje, ina jin mazan dakin suna ta dariya, har da ita ganin xata bata min lokaci na juya na bar wurin, haka kawai naji jikina yana bani kamar ana bina, juyawa nayi naga mutumin dazun ne. Mutanen da na gani a dakin suma irin kayan jikinsu ɗaya, tsayawa nayi naga ko zai wuce, abin mamaki sai naga ya tsaya. A hankali wani sabon tsoro ya kamani na juya . "Me kake so?" ."raka ki kawai zan yi, don naga kina da nutsuwa. " Ya tawo ya amshi bokitin hannuna, yayi gaba ina bayanshi, har bakin inda zamu d'ibi ruwan. Kallona yayi ya ce min."Idan muka karasa wurin zaki iya ganin maza suna wanka, zaki iya ganin su babu kaya?" Sunkuyar da kai nayi na juya bayana, ilahirin jikina rawa yake, "bana fatan kara ganin wani babu kaya" na juya kamar zan fashe da kuka. Abin da ya faru yana dawo min, a hankali naji kirjina yana min ciwo, ban san tafiyarshi ba, sai ga shi nan dauke da bokitin da jarkar ruwan, haka muka tawo, ina share hawayen da yake zuba min. "Idan zaki dauki shawarata, ki hakura da tarayya da yarinyar nan, sannan idan dare yayi ki kula da kanki da yan uwanki." "Wani abu yana faruwa ne?" Murmushi yayi irin wanda yafi kuka ciwo, ya ce min."ki kula da kanki." Sai lokacin na hango Aina'u tana rungume da wani mutumin. Tana hango ni ta ture shi, ta iso wurina. "Balali meye haɗinka da Kawata?" Bai tanka mata ba, ya saka ni gaba muka wuce ta, shiru tayi har taga wucewar mu, sannan ta biyo mu, a bakin kofar tantin mu, muka hadu da Zuzu ta fito da wutar tana gani na, ta ce. "Zahra'u hala kin mai damu kazar turawa zaki saka mana wuta a daki?" Murmushi nayi nace mata. "matar Babban sakataren gwamnati yi hakuri bari na mai da shi waje, kada ki narke domin da kitse aka yi ki " na ajiye ruwan ina kallonshi. "Na gode Yayana " na fadi haka ina jin kwalla yana cika min idanu. "Ni ne da godiya, amma bana son yaya nan". Zuba ruwa a tunkuyar zuzu tayi, tana faɗin. "Love at first sight!" "Yes haka ne, yar uwa." Ita kan aikinta ta cigaba da yi, dakyar na sallame shi ya tafi. Yana tafiya Aina'u tana zuwa. "Zahrah kin ga mutumin nan dan iska ne, kada ki bashi fuska." Kallonta nayi na wasu dakikai, kafin na ce mata. "Na gode." Tow me zance mata? Ni dai nasan idan karuwanci bai zama abincina ba, ba zai tab'a zame min guba ba, tunda mutanen da suke zagaye da ni kusan ƙaddararsu ta haɗa da wannan sana'ar. Ganin naki kulata, ta ja ta zauna domin na fahimci abincin take bukata, don haka Zuzu tayi uwa tayi makarbiya, ta tsaya kan abincin, ganin nima bani da katabus akan abincin ta koma tantinsu, domin yadda Zuzu ta haɗe rai ko ni a dakile take amsa min magana, don haka tana gama abincin, ta zuba kwanon asibiti sannan ta zuba mana a wani kwano, muka hadu har da Addah muka ci. Alhamdulillahi ba laifi mun tashi komad'a, sallah muka yi, sannan na shirya tare da kwanon abincin ni da Zuzu muka nufi Asibitin, ba a hana mu fita ba, amma sai da muka bi kofar uwar mugu, haka Balali ya gaya min ya ce na gaya mata zamu tafi asibiti. Lokacin da muka isa tantinta wanda yafi na kowa kyau, domin kamar gida yake, buga mata kofa muka yi, ta ce. "Waye?" "Zahra'u ce." "Shigo abinki!" Bude kofar nayi na tura kaina da sallama, dakin sai warin wiwi yake, durkusawa nayi na ce mata. "zamu tafi duba Mamana a asibiti ni sai gobe zan dawo, yayata zata dawo da yar Uwata." "Ai naji labarin Yadikonki ce, mahaifiyarki yar kasar nan ce, baki son a nima miki ita ne?" Idanuna ne suka cika da kwalla muryata a sanyayye na ce mata. "ba a bukata, waɗanda suke wani hali nake son su samu lafiya tukun nan." "Sai kin dawo, ga abinci ko zaki ci." Da sauri na ce mata. "A'a na gode!" Na mike na fito, Zuzu da Balali suna waje, ina fitowa ya kalle ni. " Me yasa kace mu gaya mata?" "Domin ina son ki samu kusanci da ita, yadda babu me iya tunkararki da mugun nufi, idan har kika iya kiyaye abin da bata so, cinnaka bai isa ya cijeki bata saka an ga bayanshi ba." "Amma ya naji ɗakinta yana warin wiwi?" Murmushi yayi yana faɗin, "muje zaki fahimci wani abu nan gaba." Da muka fito mun haɗu da wasu zafafan motoci guda biyar, mutanen da suke jikin motar dauke suke da manyan bindigu. "Tambayarki ga amsarta." Shiru nayi ban san dame zan lissafa abinda nake son ganewa ba, haka muka isa bakin hanya ya saka mu a mota, ya dawo. "Zahrah bayan tafiyarki diban ruwa, matar nan dai Addah ta bata labarin mu, sannan ta amince zata shiga sana'arta." "Yanzu don Allah ita Addah meye abin burgewa a wannan sana'ar? Gaskiya gara na mutu da nayi wannan sana'ar." Murmushin takaici tayi ta ce mata. "gara ke, kina da taurin kai, ni Addah tana cewa zata tsine min nake amincewa. Ki godewa Allah babu wani mai mugun nufi a rayuwarki." Ta fada tana kuka, rike hannunta nayi ina faɗin. "Ya isa haka!" Itama rike hannuna tayi tana wani irin kuka, wanda na fahimci ba kukan abin da yake faruwa damu ba ne, akwai wani abu a ranta. "Zahra'u Alfarma nake nima daya tal?" Rike hannunta nayi, hannuna ta ja cikin rigarta, ta daura a saman cikinta. A razane na cire hannun ina toshe baki. "Idan ya rayu, zan so ki rike a matsayin naki don Allah bana son ya bata min gobe na. Idan na mutu ki rike shi har abada." Wani irin rawa jikina ya dauka, ban taɓa kawowa a raina haka zai faru da Zuzu ba, "Me yasa kika bukaci haka?" "Babu wanda ya sani sai ke, don Allah." A daidai isar mu asibitin, sauka nayi na bashi canjin da Balali ya bamu. Koda muka isa asibitin Munaisah tayi kuka har ta godewa Allah. Tana ganinmu ta faɗa jikina, tana kuka tana faɗin. "tun tafiyarku sai tashi abin yake ana ta niman wanda zai nimo ki, tana son ganinki." Bubbuga bayanta nayi, na ce mata. "Ya isa!" Dakyar ta daina kuka na ajiye mata abinci, ta fara ci zata cire hannu na cigaba da bata, tana ci tana kallona. "Kiyi hakuri.!" Ta ce min, ni na saba da wannan kalmar bata wani hana ni sakat, haka ta ci abincin sosai, sannan na tafi inda zan sauya kayana, na nufi dakin da Yadikko take, an zuba mata na'ura kanta da kirjinta. Ina zuwa na rike hannunta. Kafin na shafa kanta bude idanu tayi tana kallona. Hawaye ne yake zuba mata, ta rike hannuna da babu kome. Ina murmushin karfin hali nace mata. "In sha Allah zaki tashi kin ji Nenne na, zaki tashi da kafarki da karfinki." Kallona kawai take har na wani lokaci, kafin Munaisah da Zuzu suka shigo. Kallonmu tayi tana kallonmu bakidaya, "bari na rakasu," na janye rikon da tayi min, na tafi na rakasu. "Balali yana jiranku zai kai ku har har tantin in sha Allah." "Tow shi kenan!" Haka suka hau mota na dawo dakin Nenne, ina rike da hannunta, tunda ta bude idanu ta ganni, ta lumshe idanunta, wato ko? Wannan yanayin Allah kadai yake da ikon jarabtarka a zauna lafiya. Nenne tana cikin wani irin yanayi, domin kuwa tasan kai ne akanta amma babu bakin magana. Can kuma zuzu ta fado min a rai. *Yaushe tayi cikin?* Wannan shi ne tambayar da nayiwa kaina, kuma nasan bani da me bani amsar sai ita, haka yasa nayi shiru, ina nazarin wannan al'amarin da tashin hankali yaƙe. Kwana nayi a zaune ban rintsa ba, ina sakawa da kwancewa, sannan Zuzu ta bani abin cikinta. Ashe Uwa tana kyauta da d'anta tun kafin ya shaki iskar Yanci? Amma me yasa Zuzu tayi haka? Me yasa tayi shiru bata fada ba? Ko tana tsoron kada Addah ta ce ta zubar ne?¹ tunda haka ya tab'a faruwa da Shamsiyah tasa dole sai da ta zubar da cikin hankalinta ya kwanta. Ajiyar zuciya na sauke idan har Addah zata iya sakawa a zubda na bare tabbas zama bai kama ni ba, dole mu bawa cikin kariya. Ajiyar zuciya na sauke ina jin kamar na sauke rabin damuwar da yake damuna. Kiran sallah ya fahimtar dani ashe kwana zaune nayi. Haka na fito zuwa Masallaci, acan nayi sallar asuba, sannan na koma ciki. Karfe tara da rabi, sai ga likitocin da suke dubata. Suka gama dubata sannan suka fito babu wanda ya ce min kome, bayan tafiyarsu ne Zuzu ta kawo mana abincin,"Ina Munaisah? Kina fama da kanki zaki zo nan?" Murmushi tayi tace min. "Kuma sai na zauna kowa yasan ina da Yaron ciki?" Gyara zama nayi na fara cin abincin da kunun da ta kawo min. Ina sha ina kallonta, "Zahrah don Allah bar kallona haka." Sai na dauke kai kamar ban ji me ta ce ba, na cigaba da cin abincin na. "me yasa baki gaya min kina da ciki ba?" "Saboda kin koya min kome ya same ni, na adana shi sirrina ne ba na kowa da kowa ba, har kwanan gobe baki gaya min yadda aka yi kika samu yankar cikin ba, amma na tayaki boye mutumin da kuka kwanta gado daya a asibiti. Addah tasan da wannan zancen ai sunanki." Murmushi nayi ina kallonta. "Zuzu kenan, kina tsammanin wani hujja ce don na ki gaya miki yadda aka yi na yanke a cikina? Ban sanshi ba, ban san yadda aka yi ya taimaka min ba, ban kuma San me yasa ya yanke ni ba, abu daya na sani Allah ya kubutar da ni daga hannun Azzalumi ne ya wurga ni rayuwarshi. Haka ya ishe ki ko kina buƙatar wani karin bayanin?" "Shi mutumin da ya kwanta dake a dakin asibiti fa?" Kura mata idanu nayi, baki daya sai naji abincin ya fita kaina. Na rufe a hankali nace mata. "Ki raya duk abinda yake ranki haka shine daidai." Na fada mata ina murmushin takaici. Mikewa nayi ina karkade hannuna. "Zahra'u kina boye min abubuwa dayawa, sai dai nice uwar baki uwar magana, nayi ta gaya miki sirrina." "Me kike so nayi miki? Ni nasan ban boye miki kome ba, kuma iya gaskiyar kenan na gaya miki me kike so bayan haka?" Shiru tayi tana kallona, kafin tayi kasa da murya ta ce min. "Ina wannan lokacin da muka hadu da wani dan Yola ya zo seminar?" Gyad'a mata kai nayi, a ranar da ya zo cin tuwo ya roke ni na bishi, koda muka je bai yarda mun wuce masaukinshi ba, tambaya ta yayi asibiti muka je, a daren ya kai ni wurin likita aka duba lafiyata, da nashi domin yace baya son yayi mu'amala da macen da take dauke da wata lalura shi asalima Haihuwa yake nima, Allah ya bai bashi ba. Kuma yana da mata huɗu babu wacce Allah ya nufeta da haihuwa. Bayan an gama mana ne muka wuce masauki, kusan dukkan kwanakin da muka yi da shi. Ba zan iya mantawa ba, duk da sabon Allah ne amma kuma abubuwan da suka faru ba masu mantawa bane, bayan ya gama kwanakin shi zai tafi ne ya bani number shi akan idan wani abu ya taso na gaya mishi sannan ya roke ni da cewa kada na bi wani namiji na tsawon wata uku. Ban tab'a haduwa da wanda yake zuba min kuɗi kamar hauka irinshi ba, haka nayi ta bawa Addah kudi ina tafiya na kwana a hotel gudun kada tace na bi wani namijin, wata biyu da tafiyarshi ne na fahimci ina da ciki, na tura mishi sakon da kwanaki da test da aka min, kin san wani ikon Allah sakon ya same shi dai-dai zai bar kasa ne, amma a ranar ya turo min kuɗi da duk wani abun bikata, ya kuma roke ni naje gida na gayawa Baffa zai zo niman aurena. Tun lokacin na rasa yadda zan gayawa Addah, har cikin ya shiga wata hudu,ina boye mata kwatsam sai ga abin da ya faru nan muka tawo jenuwa, ashe Allah bai nufa zamu sake ganawa da shi ba ne." Ta fada cikin wani irin kuka, kasa magana nayi ina kallonta, kafin na d'ago kai.... #Thedambuje [2/16, 9:24 PM] Cutie cutie pie: *BAƘIN HAURE....🐾🐾* {Greed for Money is the roots of all evils🫀} Arewabooks:maidambu41 Wattpad:Mai_Dambu Mallakar:Mai_Dambu *012* Wani lokaci kana iya ganin abu amma don a zauna lafiya zaka iya makancesa sai a zauna lafiya, ba tare da an cutar da juna ba. Kusan hakan ne ya faru idan da ace na d'ago kai na kalli abinda Addah take min sai nace hakkina ya kama Zuzu amma idan na duba yadda itama zuzun Addah ba kyaleta tayi ba, sai naga ashe ba kome bane don tayi min wani abin, tunda 'yar da ta haifa ma bata kyale ba. Irinsu Addah a cikin al'umma masifa ce matukar zaka nemo kudi tow bata da matsala da kai, kaunarta da kudi yasa bata jin ko dar, zata iya aikata kome matukar zata samu kuɗi, babu abinda ya dame ta. "Kin yi shiru!" Ta faɗa tana share kwallar da yake zubo mata. "Tow Zully me zance? Ina ga a gayawa Addah maganar cikin ki, domin bana son na samu matsala da Addah." Mikewa tayi kamar maganar da nayi ya bata haushi, ta juya zata bar wurin na sha gabanta."Ban fadi haka saboda na b'ata miki rai ba, amma idan kin ji haushi kiyi hakuri kin ji " hawaye ne ya zubo mata, tana min wani irin kallo me cike da tausayi, tsarguwa nayi na juya baya. "Zan mutu ne?" "Ki min alƙawarin ba zaki barshi yayi maraici ba." Rufe mata baki nayi ina faɗin. "Kina saka zuciyata wani irin bugawa, don Allah ki rufa min asiri, bani da kowa sai ke." Cire hannuna tayi ta daura bisa cikin ta ce min. "Sai wannan kina da wannan, in sha Allah zan zauna a gefenki." Komawa muka yi wurin zaman muka zauna. "Me yasa ranar da Baffa zai baki addu'a baki gaya mishi ba?" Hawaye ya zubo mata, ta share tana faɗin. "idan na gaya mishi zai tsani yar uwarshi a tsarina bana son a tsane ta da wuri, na fison sai na mutu za a tsane..." Rufe mata baki nayi ina faɗin. "Duk lalacewarta mahaifiyarki ce, kada don abin da take yasa zaki so duniya ta zage ta, kiyi hakuri wata rana sai labari." Kamar zata ce wani abu sai kuma tayi shiru, "kin ci abinci ma kuwa?" "Na koshi!" "A'a Maman Unborn zauna kici idan bai isheki ba, a karo miki." "Ni fruit nake so." Shafa fuskata nayi, sannan na juya na fita kasancewar gari ne masu yalwar ya'yan itace, ban sha wuya ba asalima ina zuwa wurin na samu Doctor Andrew zai saya sai ya biya mana kudin, duk da ban so ba, amma haka na amsa ina mishi godiya, na kawo mata, yadda take yasa na zuba mata idanu. Da alamu ranta yana son ya'yan itacen domin yadda take ci kamar tana ci da wani. Murmushi nayi nace mata. "My heart yana son abincin da kike ci." Girgza kai tayi tana faɗin. "Mace ce!" "Are you sure?" Gyad'a kai tayi tana faɗin. "Na rasa ma me zance, ke bakya tsoron wani abu ya faru ne?" Dariya nayi tare da mika na ce mata. "Bana tsoron kome, yaushe Munaisah zata zo, barci nake ji bakidaya jikina ciwo yaƙe." "Zata zo maybe sai yamma!" Numfashi na sauke, tare da cewa. "Ai kuwa da ta min bidi'a domin wallahi barci nake ji." Karbar zancen tayi tana faɗin. "Eh tow Allah yasa ta zo ɗin." Haka muka cigaba da zama har rana tayi, hakura da abincin da ta kawo min nayi na barta ta ci, dama kuma Zuzu bata da ciki ma, ci gareta kamar gara balle kuma an samu kari, haka yasa nake yawan kallonta domin burge ni take, muna zaune sai ga Nurse Ali da takeaway, ya mika min yana faɗin. "InJi Doctor Moses." "Kace mishi Allah ya saka da alkhairi." "Zai ji!" Ya zubawa Zuzu idanu, kafin ya ce mata. "Me yasa baki fara awo ba?" Dauke kai tayi tana faɗin. "Bana bukata." Mai da hankalin shi kaina yayi ya ce min. "Ki mata magana wallahi bata kula da kanta balle cikin jikinta. Na tsani taurin kai idan ma baki son cikin waye ya aike ki wurin uban cikin?" Yadda yake masifa sai duk muka zuba mishi idanu, can na harbo jirgin shi. "Tow kayi hakuri!" Kura mata idanu yayi, yaga ta dauke takeaway da ya kawo tana ci, juyawa yayi ya bar wurin. "Dan iska da kugu kamar na sauro, ya wani tsaya kamar ubana yana min masifa, bai san takaicin da yake bani ba, wai ya tsaya sai masifa yake daga ganin shi nan ba wani kuzari ne da shi ba, a gado." Rufe mata baki nayi ina faɗin. "Don Allah ban da yasasshiyar magana domin ina da ajiya a jikinki." Ture hannuna tayi. "bana son bu....." Maza na danne bakin. "Tarbiyya daga ciki ake farawa, yanzu ne lokacin da zaki fara dora mishi tarbiyyar da kike so, don Allah ban da zagi ko fushi." Kura min idanu tayi, "yanzu duk abin da nayi sai ya ɗauka?" "In sha Allah!" "Tow ya zan yi?" "Ki yawaita ambaton Allah da azkar, yawan addu'a zai taimaka wurin haihuwar salihar mace." "Ban sani ba ko zamu gana da Babyn don Allah kada ki bari addah ta rab'e ta. Domin kuwa tana rab'arta yarinyar zata tashi a matsayin karuwa." Ta fada idanunta jawur. *** Sansanin Yan gudun hijira. Kallon Addah Uwar mugu tayi, tana kara kallon sauran yan matan. Murmushi tayi ta ce musu. "Ni Zahrah nake so, domin har na gayawa mutane na samun sabuwar yankan rake." Gyara zama Addah tayi tana kallon Uwar mugu, cikin tsananin takaici ta ce mata. "Yarinyata Zulaihah zata iya abin da kike so." Girgiza kai tayi tana faɗin. "Dukkansu sun san maza, sana'ata akwai hatsari ina son yarinyar da maza basu bude mata idanu da kofa ba ne, don haka." "Idan ma sayar Zulaihah zaki yi zan sayar miki da ita." A razane su Ummi da Munaisah suka kalli Addah. Baki sake tare da son tabbatarwa shin Addah ce ko ba ita ba ce. "zan sayar miki da ita, suma ki ɗauke su a aikin." Hadiye yawu Ummi tayi tana faɗin. "A'a ni dai na tuba." Zabga mata mari Addah tayi sai da ta durkushe. "Idan har zan sayar da diyar cikina dan Ubanki gaya min me zan yi da ku? Don haka babu fashi." "Ni dai na amince." Kallonsu Uwar mugu tayi ta ce mata. "Tow kada ku damu, ku koma an jima za a azo a duba lafiyarku,domin sana'ar mu bama son kasada a cikinta. Sannan daga nan.har sauran iyakokin mutanen mu ne, kuma a cikin gidan nan kowa na wane, naji kince kin tuba ko?" Ta nuna Ummi, sannan ta saki murmushi, "ba zan miki dole sai kin shiga ba, amma mahaifiyarki ko kuma shi kenan." Jikin Ummi ne ya dauki wani irin rawa, tare da zubewa a wurin tana me rarrafawa har gaban Uwar mugu. "Na amince, don Allah kada wani abu ya same ta." Ta fada tana kuka. Shigowar da aka yi yasa duk suka mike banda Ummi da take durkushe tana kuka, "Hajajju a ina kika samo flowers masu kyau haka!" Ya fada yana gyara zaman facemask din fuskarshi. "Sannu da zuwa ranka shi dade." Sannan ta juya tana kallon Addah . "Ke ki tafi ki bar su." Juyawa Addah tayi, ta bar su a wurin. "Hajajju a taimaka min nayi wanka, ina son tausa." "An gama!" Ta kalli Munaisah domin ta lura Allah ya daura mata itama son abin duniya. "Ki shige cikin dakin nan akwai duk abin da ake bukata ban da musu." Gyada kai tayi tana faɗin. "Tow!" "Ke !" Ya kira ta, tashi tayi ya kalli Uwar mugu da take tsaye. "Bana son naga kyawawan mata na kuka, Hajajju ki ce tayi shiru.". "kinji kiyi shiru" dunkule hannun yayi yana bubbaga kafadarshi. "Kafata ciwo yake min, ko zaki min tausa." Kallon Uwar mugu da take tsaye tayi ta mata alama, da sauri ta mike ta nufi kafadarshi. "Yallabai da akwai wani abu ne?" "Dilla ya arce da kayan dawa." Ya fada yana daura kafarshi a saman stool din da ta ajiye mishi. "Garin k'ak'a naga dai har da Giwaye a dawa." "Ambaliyar ruwa aka yi, kusan kowa yasan yadda ruwan yayi barna ba kowa yake iya tsira zuwa tudu ba." "Amma kuwa dilla har ya manta yadda kura ta kawo mishi cabka ya tsere." "Magana ake miki ta ambaliyar ruwa." "Eh kuma haka ne, gaskiya ba kowa yake tsira daga ambaliyar ruwa ba, sai wanda Allah ya so ceta." Kallonta yayi yana kara nazarin yadda take tsaye, "duk wani sansani nasan inda yake zuwa, amma ban same shi ba. Hajajju kece kawai nasan akwai alaƙar wasa da dariya a tsakaninku." Wani ware idanu tayi tana dafe kirji. "Na shiga uku." Ta zube a kan gwiwarta. "Don Allah ka rufa min asiri." Lumshe gajiyayyun idanunshi yayi yana kara jin wani irin gajiya me tattare da kasala cikin wani yanayi me dauke da sanyi ya ce mata. "Na gaya miki, ta inda aka hau ta nan za a sauka matukar nayi idanu biyu da shi, tow lahira zata yi bako." Ya fada daidai fitowar Munaisah daga dakin. "An gama hada maka ruwan." Inji Uwar Mugu, "Hmm! Ina aina'u?" "Bata san zaka zo ba" ta bashi amsa muryarta na rawa, mikewa yayi a hankali yana kallon Yan matan ya ce musu. "Su waɗan nan daga ina suke?" "Hmmm! Yan gudun hijira ne!" "Yayi kyau, amma ina da rani ga damina ya gangamo ban san yadda zan yi ba, domin ina tsoron kada kwarin wake su bata min ruwa." "Hmmm! Ina ga matukar sanyi da tsawa bazasu b'ata maka ba, mai zai hana ayi aurensu zuwa bad'i da damina sai a haife su." "Hajjaju ba zai sai bad'i da damina ba. A k'ak'ar bana ma matukar yan matan nan suna da hankali sai mu game da su." "Mai zai hana? Kyawawan mata ai abin so ne." "Eh amma ba dukkansu ba, akwai wacce kai kanka kasan ba a yi ta don tsalle ba, anyi ta ne domin adana a cikin gida. Idan na wannan tabbas daukar ta zan yi na kaita wata duniyar ta rayu domin ni da Yarana." Cikin murmushi ta ce mishi. "Akwai irin flower da na ajiye maka, amma nasan zaka bukata ka je kayi wanka." Mikewa yayi yana tangad'i. Har dakin yana rike da hannunsu har bandakin, hawaye ke zuba daga idanun Ummi domin ita bata ga wani cigaba daga wannan kazamar rayuwar ba, haka suka mishi wanka tsaf sannan suka dauki towel da suka ga a cikin wardrobe. "Ku nawa ne kuka zo sansanin nan? Ba a min karya." Ya faɗa yana kallon Ummi da take share hawayenta, a hankali ta bashi labarin su nawa ne. "Ina sauran yan matan?" "Suna asibiti." Ta bashi amsa tana share hawayen. "Dukkanku karuwa kenan?" Girgiza kai tayi ta ce. "A'a iyayen mu ba karuwa ba ne, Yayar mahaifinmu ce, sai Zahrah itama bata taɓa yadda da kowa ba. Bata son sana'ar." Murmushi yayi yana kallon yadda take kuka, "Gaya min yanzu mene yasa kike kuka?" "Mahaifiyata ba lafiya, sannan ta ce kada na kara aikata wani abu. Wallahi na tuba." Ta fada tana zubewa akan gwiwarta. Shiru yayi sannan ya ce mata. "Yanzu ita Mamanki tana nan kenan?" Ya kalli Munaisah da take tsaye. "Eh!" Mikewa yayi, cikakken namiji me Kyakyawar sura, ya dauki mayafinshi ya lullube mata kai, ya kalle ta sosai. "Kina ji na!" Ya faɗa yana kallon Munaisah. "Kada naji ko na gani, domin idan aka ci amanata ina iya kashe mutum. Da munafuki gara barawo." Ya fada mata yana tab'a kanta," jeki babu wanda zai dakatar dake." Da sauri ta juya zata fita, ya ce mata. "baki ji ba, ki nutsu sosai." Gyada kai tayi tana fita, a hankali ya budewa Munaisah hannu."ke ina Mamanki." "Tana asibiti da Zahrah da Zulaihah." Shafa bayanta yayi ya ce mata. "Me yasa baki je ba." Sake shiga jikinshi tayi tana k'amk'ame shi, domin tun wanda aka mata a rikicin jenuwa bata kara hada hanya da namiji ba, amma ganin Bako yasa baki daya tana jin kamar ta cinye shi. "Kina nan mahaifiyarki tana tare da yar uwarki!" A hankali take lasar kirjinshi zuwa wuyarshi. "Ina girmama uwa me yasa?" Bakinta ta kai habbarshi, tana wani lasar bakin kamar ta samu alewa, a hankali ya kunce towel din kugunshi ya d'auketa suka faɗa gadon, gefen gadon ya kai hannunshi ya ciro golden ring a cikin aljuhun wandonshi. Yana romancing da ita yana kara saka kayanshi, yana gama sakawa cak ya d'auketa ya dora ta, bisa bishiyar dogon Yaronshi. Hannunshi dukkan biyu a kirjinta, ita kuwa sai aikin gaske take, ko tunawa da abinda ya faru bata yi ba, damuwarta kawai taji namiji a jikinta. Shi kuwa sai da ya kure mata lissafi domin ya jima shima bai hadu da Shaidaniyar yarinya irinta ba, don haka sun jima suna cinye juna. ---A lokacin da Ummi tazo fita kallonta uwar mugu tayi,tana son tayi magana amma sai tayi shiru, har ta bar wurin Uwar mugun ta wuce tantinsu, da sauri sauri. Tana isa ta cusa kai kenan, idanunta ya sauka akan Addah zata shake mata uwa, da wani karfi ta bangaje Addah ta fadi can. Ta shiga dukarta kamar Allah ya aikota. Dake yarinya ce kuma da sauran kuruciya a tare da ita, da kuma a fusace take da Addah haka ta rufe idanunta tayi ta dukar Addah. Ganin da gaske zata kashe ta yasa ta saka ihu da kururuwa tana niman ceto. Amma ina zuciyar Ummi ta kai iya wuya, domin ta gama sarewa matukar basu nan Addah kashe mata uwa zata yi, tunda ta iya sayar da Yarta Uban waye ba zata kawar don cimma manufarta ba, Ihun Addah yasa mutane suka farga aka kawo mata dauki. "Ke ba Babarki ba ce!" Aka shiga d'aga ta dakyar. "Da wannan ta haife ni gara ban zo duniya ba, in sha Allah Addah mushe sai yafi ki daraja." Ta fada tana kuka me ciwo, ta d'ago kai tana kallon yadda kowa yake bata laifi. "Wannan da haihuwarki gara b'arinki, sam baki cancanci zama uwa ba, Allah ya isa tsakanina da ke, Addah In sha Allah lahiranki sai tafi duniyarki muni." Ta fada cikin kuka domin bata san wani level zata ajiye Addah ba, domin matar bata buƙatar addu'a sai Addu'ar iftila'i da masifa da jafa'i. Sai da Uwar Mugu ta shigo ta zubawa Addah idanu. Kafin ta ce. "Me ya had'aki da ita?" "Eyeee! Hmm kawai don." "Karya take zuwa nayi ma same ta, zata kashe min Yakumbo." Harara Uwar mugu ta watsa mata tana faɗin. "Ka da na kuma jin makamancin haka." "Naji Hajiya haka ba zai kuma faruwa ba," inji Addah da kumburaren bakinta, kallon Ummi tayi ta ce mata. "Kema wannan ya zama na karshe ki kula da Mamanki. A wannan duniyar mutane na iya kome saboda kuɗi kiyi tunani dakyau... #money #evilalive #trueordare #mai_dambuje [2/16, 9:24 PM] Cutie cutie pie: *BAƘIN HAURE....🐾🐾* {Greed for Money is the roots of all evils🫀} Arewabooks:maidambu41 Wattpad:Mai_Dambu Mallakar:Mai_Dambu *Ni ban san me Adda tayi aka tsane ba, salon ku saka mata ido da baki ta lalace 😹😡✊🏻🤔 da alamu Adda tana girgiza ku😹 mutuniyar kirki saura ku ji ban dadi 😡😹🤣* ___________________________________________ ```Assalamu alaikum barkanmu da warhaka da fatan kuna cikin koshin lafiya, karku manta da wannan Kamfani mai albarka mai kawo muku kayan bukata cikin sauki da Aminci da Inganci. Wato TA RASULU MULTIPURPOSE. YA SAKE DAWO MUKU DA KAYAN NAN MASU ARMASHI DA DANDANON KOWACCE MACE TAURARUWA CE. _______________________ MARKADADDIYAR GYAD'A HADADDEN KAYAN SHAYI GARIN KOSAI NA TAFI DA GIDANKA. GARIN TUWO GARIN KUNU YAR ASALI CURRY ME DADI SPICES TYME YAJIN DADDAWA ME KYAU GARIN DAN WAKE JAN YAJI MAI DAD'I... _____________________ BUGU DA KARI MUN TANADAR MUKU DA KAYAN FITAR SALLAH DA NA SHAGALIN SUNA DA BUKUKUWA. ATAMFOFI, LESHINA, MATERIAL, SHADODDI, YADUDDUKA NA MAZA DA NA MATA, JAKKUNA DA TAKALMA. WANI ABIN SAI KUN ZO TA RASULU MULTIPURPOSE DOMIN KASHE KWARKWATAN IDANU. ZAKU IYA TUNTUƁARMU A WADANNAN NUMBOBIN.. 08086639163 - 09030168590.... MUNA DAKON SAYAN DAI-DAI KO SARI.....``` *013* "Babu abin da kudi basu saka mutum ya aikata, rayuwar mahaifiyarki ko kuma ki wayi gari babu labarinta shine gaskiyar da zan gaya miki." Daga haka ta juya ga Addah, "Ba kowa yake da hakurin da zai ga kina shirin lalata mishi goben shi ya iya hakuri ba, don haka sai a kula." Daga haka ta fice a dakin, ita kuma Ummi ta koma gaban Mamanta, tana shafa fuskarta hawaye na zuba mata, a duniya idan akwai abin da ta tsana shi ne ka tab'a mata Yakumbo, haka yasa ta kece da kuka me ban tausayi, gani take kamar duk abin da ya faru Addah ce sababi domin da bata yi shawarar kawo Zahrah Taraba ba, da basu faɗa wannan bala'in ba, bakiɗaya ta tattara laifin kacokan ta aza bisa kan Addah, tsanarta da wani sabon kiyayyar Addah take ji, a hankali ta juya tana kallon Addah kafin ta ce mata. "In sha Allah sai na gayawa Zulaihah kin sayar da ita, sannan abinda baki sani ba, Zulaihah ciki ne da ita, don haka ki saka a ranki bakin ciki da goyon shege yana wuyarki. Mu dai duk lalacewar da muka yi bamu daukowa iyayenmu shege ba, kinci ribar bariki da hujja." Ta fada tana sakin wata dariya me daukar hankali ta cigaba da cewa. "Ni dake shege ka fasa, idan baki ga bayana ba, ni sai naga naki wallahil azim ki ajiye a ranki daga yau na fara farautar rayuwarki. Ba iya ke ba, hatta ta Zulaihah sai na saka ta tsane ki sama da yadda kike tsammani." Cikin da Ummi ta faɗa mata, bai bata mamaki ba. Kamar yadda take ji take gani zata rasa Zulaihah. Murmushi tayi ta ce mata. "Ai ciki na san da shi, sai me? Kuma ki saka a ranki cikin ya kusan b'arewa matukar ina raye. Na gama magana sayar da ita zan yi idan ma suna sonta da cikin jikinta shi kenan, idan har zan sayar da d'iyar cikina Wacece ke da bazan iya cusawa a tashin hankali ba? bakya gaba na domin ina da abin da ya fiki daraja." Shigowar Munaisah ta kura musu idanu, "ba sai kin zuga Zulaihah ba, Addah sayar da ita kika yi ra?" Ta tambayi Addah dafe da goshinta, "Addah na zata duk abin da zamu yi miki akan kuɗi iyalinmu da mu kanmu mun tsira." Dariya Ummi tayi, ta ce mata. "Baki san wani abu ba, tow ina kallon lokacin da Addah ta danne Nenne har dai da ta shiga wannan halin." Cakume wuyar Ummi Addah tayi. "Munafiki algunguma me nayi miki?" "Addah ba zamu kara miki biyayya ba ne, na gaya miki kuma sai na rabaki da duk me shirin yimiki biyayya." Ummi ta faɗa tana dariya. "Domin idan ta kashe iyayenmu, bamu da kowa bayan ita, zata saka mu lallai mu amshi ƙaddarar da bata rubuce cikin littafin mu, wallahi ina gaya miki sai na ga bayanki" "Ummi kina tsammanin don kin gaya min Addah tayi yunkurin kashe Nenne zan yi mamaki ne? A wannan takin ni kaina na samu damar zan kawar da Nenne domin matukar tana raye ba zan samu yadda nake so ba, don haka ki ajiye a ranki mutuwarta shi ne tashina." Wani abu ne ya tsaya a ran Ummi wato, ita ta ma lura duk wanda ya zauna da Addah sai ya zama mara mutunci, fisabilillahi uwar da ta haife ka, zaka nuna bata da amfani a rayuwarka. Komawa jikin Yakumbo tayi, tana jin kamar ta goyata su gudu, domin kuwa tana hango rashin imaninsu kada ta matsa jikin Mamanta a kashe mata uwa. Tana jin yadda suke shewa da ihu, kudi suke kirgawa tun daga lokacin bata tashi a gaban Yakumbo ba, sai da taji sallamar Zalaihah. Sai lokacin kunya ta kamata, tabbas bata kyauta ba amma kuma babu wanda zai so a tab'a mishi uwa. Abin da ya fara fitowa bakin Zulaihah shi ne. "Addah hatsari kika yi ne?" Ta tambayi Addah hankalinta a tashe. Kallon Ummi Addah tayi, ta fashe da kuka tana nuna Ummi. "Ban gane ba, kina nuna Ummi gware kuka yi da ita?" Girgza kai tayi ta fara magana. "Kashi ta bani." Juyawa Zulaihah tayi ta kalli Ummi, bata ce mata kome ba, ta wuce ta zauna tana nishi. "Ashe dama zulai har zaki yi ciki ba zaki gaya min ba?" Da sauri ta kalli Ummi, eh Ummi tasan da cikin, kallon Addah tayi kafin ta ce mata. "Ina son cikina ne, domin ba don naci abinci na same shi ba, domin ina son Ubangiji ya gafarta min ta sanadin cikin." "Shi yasa Uwar da ta haife ki, ta sayar da ke ba." Inji Ummi, sannan ta cigaba daga inda take cewa. "Babu wanda zai yarda yana ji yana gani don biyan bukatar wani a kashe mishi Uwa, kama wannan tsohuwar kilakin nayi zata kashe min mahaifiya, kuskure ne don na kare rayuwar Mahaifiyata? Nayi laifi kenan?" Girgza mata kai Zulaihah tayi, tana jin zuciyarta kamar zata buga, ta kalli Addah . Gyara zama Ummin ta kara yi ta ce mata. "Ta sayar da ke. Idan kina da yadda zaki yi kafin su bukaci ɗaukarki da cikin jikinki sai ki sani." Daga haka ta mike ta suri gwangwani. "Zan tafi sallah ga Yakumbo, idan wani abu ya same ta, Addah ce." Daga haka ta fita daga tantin, Zuzu kan bata ce kome ba,.domin kuwa tasan idan tayi magana ba mamaki zucuyarta ta buga, haka ta zauna shiru har Ummi ta dawo. "Ki duba tana raye?" Zuzu ta tambayeta.b'ata Yakumbo Ummi tayi ta cewa Zuzu. "Eh tana raye." A hankali ta juya ta fara sallah, tana idarwa ta fara addu'a a lokacin Munaisah da Addah suka fice a dakin, ita kuwa ta cigaba da musu munanan addu'a da tsinuwa. Duk wanda ya jefa rayuwarta cikin hatsari. "Ya isa haka, kada garin fushi ki jefa rayuwarmu cikin tsinuwa. Tunda Yakumbo tana raye, ki saka idanu akanta. Kuskure daya kika min, na bayyana zancen cikin jikina ko Zahra sai yau na gaya mata. Addah kuwa ba zan yi mamaki ba, idan ta nuna bata san da zancen cikin ba, ai ba laifi ba ne, to amma kada ki kara min haka." Itama Ummin cikin kuka ta ce mata. "Wallahi na gaji ne da halin Addah, a can idan ta ce ta dauki nauyin mu da na iyayenmu ba laifi amma a wannan lokacin da muke, cikin tsaka me wuya ta ce zata saka mu, karuwanci ai babu kanta sannan haka bai ishe ta ba, sai da na kamata zata kashe min Uwa, gaya min Zalaihah me ya dace nayi?" "Kare mahaifiyarki;" inji Zuzu, "Gaya min ta ina nayi kuskure? Akan addah wani irin bala'in rayuwa ne ban gani ba? Kafin na waye a harkan sai da aka zubda min ciki sau uku, ya take son nayi? A haka ta haɗa ni da mutumin da ya goga min infection da kyar na rabu da ciwon. Haka kawai sai ta nime kashe min uwa? Duk abin da nayi fama da shi addah bata bani kudin magani ba, ni daya nayi fama da kaina. Allah ba zai tab'a barin addah ba, domin daga duniya zata ga sakamakon abinda ta aikata. Wallahi nayi dasananin abin da na aikata, Zuzu akan idonku aka keta alfarmar Mahaifiyata, aka keta nawa maza sun fi shida akan Yakumbo, Zuzu Gaya min har zan ji wani d'a namiji ya burge ni? Gaya min anya akwai adalci a cikin wannan yanayin? Mahaifiyata fa suka lalatawa farinciki bayan sun kashe kannena da mahaifina da kowa nawa. Zuzu me Addah take so nayi? Bayan na gama ganin masifa da idanuna zata bukaci na kara hada shimfida da wani d'a namiji, tsoro nake ji Zuzu ina tsoron Allah kada ya kona ni." Rungume juna suka yi. "Babu wanda zai kuma saka ki dole, koda bana nan kada ki gayawa Zahrah kome ki barta ta fahimci abinda ya faru da kanta, kada ki gaya mata don Allah." "Wallahi ba zan iya ba, matukar na ganta cikin wani yanayi zan gaya mata. Amma zuzu me yasa kike gaya min haka?" Murmushi tayi tace mata. "Ba kome kawai dai na gaya miki ne kada ki gaya mata kome." Suna zaune addah suka shigo da kayan ciye-ciye, itama Zuzu ledar da tazo da shi, ta bude suka ci abincin da Ummi. Sai da ta gama cin abincin, ta kalli Munaisah. "Ita baiwarki da kika bari a can Asibitin me kike nufi?" Kallon Addah tayi, tana son tayi magana amma ganin har lokacin Zuzu bata yi magana ba, yasa Addah kasa da kanta. "Zaki tashi ko sai naci Bu..... Ubanki." Inji Zuzu tana mikewa. "Doluwa jaka!" Mikewa Munaisah tayi kamar zata mutu, ta dauki kayanta. Itama zuzun ta mike tana bayan Munaisah, tana kare mata zagin kare dangi, har asibitin don masifa Zuzu ta kawo ta, ina zaune kamar wata mara galihu, sai ga su nan mikewa nayi ina kallon yadda Munaisah take share kwalla. Domin a duke zasu daku da Zuzu, amma kuma Zuzu irin mutanan ne masu matukar kwarjini domin yar bala'i ce. "Meye na kuka?" "Rabu da shegiya ba zata zo ba, wai har tana kuka yar iska Uwarki ce, ba Uwarta ba." Girgiza kai nayi na cewa Zuzu. "Tunda bata son zama ta koma, ke mu kwana dake." "Wallahi ba zata koma ba, idan ta koma ma wurin wani shegen zata kwana." Sake baki nayi ina kallonta, "wurin wani shegen zata kwana?" "Wallahi na rantse miki da Allah, kwana zata yi a wani wurin." Mikewa nayi ina karkad'e jikina na ce mata. "Ok sai ki zauna. Ai kin san yadda ake kome ke muje!" Daga haka muka bar asibitin, raina yana b'aci. "Kin san Ummi da Addah sunyi faɗa?" "Ina zan sani, tunda ina asibiti." Murmushi tayi tace min. "Hmmm! Allah abin tsoro rayuwa abin tsoro, yau wai Ummi ce take gaya min Addah ta sakata aiakata abubuwa masu kazanta, yanzu ta tuba ta bi Allah ba zata kuma bin maza ba, asalima tsoron mazan take " "Alhamdulillahi Allah ya amshi addu'ata, akanta kenan, tunda gashi nan tana faɗin ta tuba." Murmushin karfin hali tayi ta fara bani labarin yadda aka yi, ware idanu nayi ina mamakin yadda ta iya dauke kai kamar babu abinda ya faru. "Me yasa baki damu ba?" "Kawai ba zan tab'a damuwa ba, domin kare rayuwar Mahaifiyarta tayi, kuma ko kashe addah tayi bata da wani hukuncin." "Amma!" Rike hannuna tayi tana faɗin. "Addah tayi kurakurai, kada haka ya zama abin da zaki bi bayanta, barta da halinta bata ga kome ba." Ta fada tana sauke ajiyar zuciya. Ban san me yasa haka yake faruwa ba, amma nasan Addah tana da kaso mafi girma na lalacewar rayuwar Ummi, lokacin da muka isa da Balali muka haɗu tunda ya ganni yake murna, sama sama na gaishe su, muka wuce koda muka isa kallona Ummi tayi ta ce mana."me yasa kuka bar ta a can Asibitin?." "Mahaifiyarta ce duk abinda ta gadama tayi, rayuwar Nenne yana hannunta, ta ce ko ta samu damar kawar da ita, zata yi ga damar nan na bata na dauko Zahrah da ta tare mata damar." Inji Zuzu tana dafa kafadana. "Ban gane ba?" "Ba zaki gane ba." Hadiye yawu nayi wato idan na fahimta akwai abin da ake boye min, kura musu idanu nayi da na fahimci basu son na fahimci kome, sai na zauna ina faɗin . "Yau baku mana abinci ba ne?" "Tun tafiyarki jiya babu wanda ya kara abinci sai Zuzu." Inji Ummi, mikewa nayi na dauki sauran kayan abincin, na fara kokarin daurawa, sai ga Uwar Mugu da wasu matasa uku, kallonta nayi kafin na mike ina son nayi magana. "Ina Munaisah?" Tana asibiti wurin Mamarta. "Me yasa bata zo ta gaya min ba?" Daga ciki zuzu ta leko tana faɗin. "Bata zo ba, domin can ya dace da ita ba nan ba." "Ke waye ya saka ki?" Daya saurayin zai shiga cikin tantin na tare shi, "wai meye haka ne?" Na tambaye ta. "Kyale su ku tawo da Aina'u " haka suka wuce ina kallonsu, juyowa Uwar mugu tayi tana kallona, fuskarta a sake. Ta bar wurin a can kuwa tana shiga dakinta, ta ce . "Yallabai yarinyar tana asibiti wurin jinyar Mamarta, amma na saka a kawo min Aina'u." Gyad'a kai yayi yana kallon wayar hannunshi. "Me yasa bata gaya min Uwarta bata da lafiya ba?" "Afwa Yallabai." Haka aka tawo da Aina'u da ta cab'a kwalliya kamar zata wurin gasar kyau. ★★★ Niamey. Niger republic *Familyn BA'ARE* Alhaji Muhammad Dan Ba'are, su ɗin dangi suke da Ibrahim Khalil Dan Ba'are (na cikin Bororoji) kakansu daya, kasancewar sun jima da barin agadaz, haka yasa su sai suke amfani da Ba'are zalla, yayin da Khalil yake amfani da Dan Ba'are.(zaku iya bincikar Bororoji duk da ban fito da nasabarsu ba, amma labarin BAƘIN HAURE da Bororoji yana da nasaba da juna) Alhaji Muhammad Dan Ba'are, ya baro gida agadaz domin karatun addinin Muslunci, ba don kome ba sai don yadda Mahaifinsu yake fifita wasu ɓangaren na gidan da su, shine d'a na farko a gidan, sai Alhaji Ibrahim Dan Ba'are d'a na biyu, sai Hajiya Latifa, Mahaifiyar Mohan. Kasancewar su dakinsu Ibrahim sun maida hankalinsu akan karatun boko, yayinda Mamman Ba'are yaki boko ko kadan, haka yasa shi ganin ai ana fifita yaran dakinsu Ibrahim, mahaifiyasu an maida ta kamar saniyar ware. Dalilin haka ya bar gida, ya tafi karatu a can ya hadu da wani abokanshi. Suka wuce kasar mali. A can suka shiga harkar hako ma'adinai, har na tsawon shekaru biyu, ana haka wata rana, kasa ta rubta musu sai da suka kwashe wata goma sha huɗu, kafin aka fito dasu, a kasar nan shi daya ya rayu sun kai su goma sha takwas da suka shiga amma shi daya ya rayu, a lokacin da aka kai labarin Mutuwarshi, Nana sai da ta kwanta jinya da tsanar kishiyarta Hajiya Balaraba, da ganin kamar ita ta mata hanyar da d'anta ya mutu, gaba da kiyayya me zafi suka kara ruruwa a Familyn Dan Ba'are dalilin da yasa suka bar garin agadaz kenan. Shi kuma a can ya rayu cikin amincin Allah, domin a tsawon watanni nan. A ramin nan da suke hako kuza, a nan yayi katarin haduwa da dutsen zinari, haka yayi ta hak'a, bai fasa ba Abinci sai beraye su yake kamawa ya buga gwal da kuza, wuta ta kama, ya gasa beran da ya kama. Ruwa yana samun shi ne ta wata jijiyar bishiya da ta ratsa karkashin kasa. Haka yayi ta rayuwa, kwatsam sai ga shi ana tono, inda cikin hukuncin Allah aka tono da shi, ya tara dukiya me yawan gaske sannan aka fito dashi. Wannan abin ya bawa kowa mamaki, asibiti aka wuce da shi yayi sati biyu aka sallame shi, tare da kayanshi baki daya da ya hako a rami. Aka dawo da shi Nijar, Aka karrama shi gwamnati ta bashi babban gida da fili anan Niamey. Sannan gwamnatin ƙasar ta nemi ya sayar mata da abinda ya zo da su, ya sayar da kadan domin ya gina dukiyarshi saboda kusan rayuwarshi ya saka a hatsari ya samo dukiyar nan. Kad'an da ya sayar din nan, da ita ya cigaba da gina katafaren kamfanin zinari, har ya kuma haɗa gwiwa da kasar Mali ana shigo mishi da zinari, a lokacin bai wani karatun boko ba, amma kuma ya san kan lissafin kome, sai da ya samu shekaru uku da dawowarsa ya tafi ya nimo Danginshi. Ganinshi cikin wadata da nutsuwa yasa suka ta murna, har agadaz ya je domin an san ya mutu dole yaje ya nuna kanshi dan su san yana raye. Yana zuwa Kanin mahaifiyar shi ya bashi auren Yarshi, Rabi duk da bai so ba amma haka ya amshi auren, domin yana niman macen da tayi karatun boko wacce zai ciccibeta ya dorata akan dukiyarsu, haka aka sha biki. Tana shiga a burin shi tana fara haihuwar namiji, zai gina rayuwar yaron ta hanyar bashi ilimi me yawa da zai rike dukiyarsu. Sai dai kash tana fara haihuwa ta haifi mace, haka ya kara auro Fauziya itama tana shigowa mata ta fara haifa masa, haka ya hakura ya cigaba da kula da yaran da basu ilimi sai dai iyayen basu wani damu da ilimin ba, ana haka ya hadu da Harirah yar secondry haka yayi ta mata hidima, har ta gama itama dai ba wani abin kuzo ku gani ta yi ba,haka ya aureta. Alhaji Mamman Ba'are, yana da wata dabi'a ita ce cacca, dake yana yawan shiga libya, a nan ya haɗu da Alhaji Nasiru Wodabbe shima rikakken dan cacca ne. "Yau gidan nan yayi baki,ga Alhaji Nasiru Wodabbe gefe guda Alhaji Mamman Ba'are, yau wasan sai tafi koda yaushe armashi da karsashi" domin kowa yasan kowannensu gwani ne a harkar cacca. "Idan nayi nasara akanka Ba'are me zaka bani?" Murmushi Mamman Ba'are yayi ya ce mishi. "Wodabbe idan kayi nasara a kaina, ka kwashe kome har da kayan jikina. Idan nayi nasara akanka kuwa zan bika har garin na dauke shanayenka!" "Na yarda!" Inji Nasiru Wodabbe, shima kuma Mamman Ba'are ya ce mishi."na amince." Aka shiga buga cacca kamar da wasa, Nasiru Wodabbe ya shiga nasara akan Mamman Ba'are, har dai da ya cinye shi kome hatta wandon jikinshi sai da ya saka a cacca. "Mamman Ba'are kwashe kayanka, idan ka haifu namiji ka saka kamfaninka " kurawa Alhaji Nasiru Wodabbe idanu yayi, kamar ya zagi Uwarshi. "Zan saka amma ka sani idan nayi nasara ba zan maka da wasa ba." "Na amince," saka kamfanin yayi cikin murna da kwarewa Nasiru Wodabbe ya fara buga wasa, tun a zagaye na farko ya fahimci kamfanin Ba'are GOLDEN EMPIRES ba sa'ar sa bane, domin a wasan farko Ba'are ya dawo da kayanshi wasa na biyu ya dawo da kome hatta zobensa na azurfa sai da ya dawo da ita. Murmushin yaƙe yayi suka cigaba da wasa, aka cinye kome cikin takaici ya ce mishi. "Na saka yar Yayana Sa'adatu." Shiru Mamman Ba'are yayi yana kallon Nasiru Wodabbe,"Me yasa baka saka yarka ba sai yar dan uwanka." "Da ina da Y'ar ba zan saka Sa'adatu ba, domin darajarta tafi karfin dan cacca irinka,na gaya maka." Tab'e baki Mamman Ba'are yayi yana dariya,"bari na gaya maka ko gwal ce da kanta, bata fi karfin dan cacca irina ba sai ma tausayinta da naji da ta samu Baffa irinka." Cikin fushi Nasiru Wodabbe ya kara buga wasan hannunshi, cikin rashin sa'a ya fadi Mamman Ba'are yana bugawa sai gashi yayi Nasara, "Na sameta kana da wani abu da zaka fanshe ta?" Idanunshi ne ya kad'a jajjur. "Kai tsinanne yarinyar da babu ruwanta, yarinyar da gwamnati dauki nauyinta saboda kasancewarta hazika, me ilimin addini da na boko, shine zaka samu a banza ba zan baka ita ba, ni na sakata a cacca amma ka fara ketare ni kafin ka isa gare ta." "Ba zan ketare ka ba, yadda ka saka ta a cacca haka zaka bani ita har da kome nata." Shi kanshi Alhaji Mamman Ba'are, bai tab'a zatan Allah zai bashi irin macen da yake so ba, sai da ya buga kamfanin shi na gwal a cacan sai gashi Allah ya bashi ita a lokacin da bai zata ba. Kafin wani lokaci rikici ya barke a tsakaninsu, sai ga manyan maza da bawa hammata iska, dakyar aka raba su domin har jami'an tsaro sun shiga lamarin, Alhaji Mamman Ba'are da yaga samu zai ga rashi ya daka tsalle ya ce ai ta zama tashi tunda wasa aka buga, wasa gaske dai yaki karbar kome ita Sa'a kawai yake so. Ganin haka yasa Alhaji Nasiru Wodabbe ya amince da shawarar da aka bashi a office din yan sanda aka daura auren Sa'adatu Aliyu Wodabbe da Alhaji Mamman Ba'are, a Office din yan sanda, da sadakinta aka bashi yana ji yana gani Alhaji Mamman Ba'are ya wuce tare da ɗaukar yan rakiya har gidan Nasiru Wodabbe, ganin kamar Mamman Ba'are bai da hankali yasa shi isa gidan kafin su isa, yana shiga kamar wanda aka wurgo shi, dama a Libya yake da zama da Matarshi da yar rokonshi. Sakamakon wani karamin abin da bai kai ya kawo ba, ya baro kasarshi. "Sa'ade ki yafe min, na miki rashin adalci. Kiyi hakuri in sha Allah gobe zaki yi dariya." Ya fada yana dauke kanshi ya kalli Matarshi, Raliyah. "shiryata za a zo ɗaukarta na aurar da ita " "ka me?" Ta tambaye shi jikinta yana rawa. "Eh na gaya miki na aurar da ita, ina ga ai da Hausa na fada ba larabci ko fillanci ba." "Amma me yasa? Kasan Lamido yana can yana jiranta." "Haka Allah ya nufa ita ba matar shi ba ce." Ya dawo kan Sa'aden ya riko hannunta. "Kinsan ba zan tab'a cutar dake ba ko?" Gyada kai tayi kanta a sunkuye. "Tow kiyi hakuri kin ji." Ya fada yana Hadiye kukan da ya zo mishi, haka ya hada har da kome nata, ya tsaya Raliya ta shiryata......... (Hmmmmmmmm ku bi alkalamin ƙaddara) #Mai_Dambu [2/16, 9:24 PM] Cutie cutie pie: *BAƘIN HAURE....🐾🐾* {Greed for Money is the roots of all evils🫀} Arewabooks:maidambu41 Wattpad:Mai_Dambu Mallakar:Mai_Dambu Assalamu alaikum barkanmu da warhaka da fatan kuna cikin koshin lafiya, karku manta da wannan Kamfani mai albarka mai kawo muku kayan bukata cikin sauki da Aminci da Inganci. Wato TA RASULU MULTIPURPOSE. YA SAKE DAWO MUKU DA KAYAN NAN MASU ARMASHI DA DANDANON KOWACCE MACE TAURARUWA CE. _______________________ MARKADADDIYAR GYAD'A HADADDEN KAYAN SHAYI GARIN KOSAI NA TAFI DA GIDANKA. GARIN TUWO GARIN KUNU YAR ASALI CURRY ME DADI SPICES TYME YAJIN DADDAWA ME KYAU GARIN DAN WAKE JAN YAJI MAI DAD'I... _____________________ BUGU DA KARI MUN TANADAR MUKU DA KAYAN FITAR SALLAH DA NA SHAGALIN SUNA DA BUKUKUWA. ATAMFOFI, LESHINA, MATERIAL, SHADODDI, YADUDDUKA NA MAZA DA NA MATA, JAKKUNA DA TAKALMA. WANI ABIN SAI KUN ZO TA RASULU MULTIPURPOSE DOMIN KASHE KWARKWATAN IDANU. ZAKU IYA TUNTUƁARMU A WADANNAN NUMBOBIN.. 08086639163 - 09030168590.... MUNA DAKON SAYAN DAI-DAI KO SARI..... *014* Tana fito da ita ya kalli yarinyar, kafin ya riko hannunta har waje. Ya ja Alhaji Mamman Ba'are gefe. "Gata nan, ka da ka duba lalacewar da nayi ka hukunta ta da shi, wallahi billahil azim mahaifinta shahararren Malami ne kuma attajiri ne, soyayyar da take min tun tana yarinya yasa ni tawowa da ita yawon bariki, Sa'adatu bata rasa kome ba, hatta abinda zata ci Ubanta ya tanada mata, wallahi rashin ji ya sani fitowa da ita, Ba'are don Allah kada ka cutar da ita babu ruwanta." Duk da zuciyarshi ta motsa akan yadda ya mishi da farko amma kuma yadda yake gaya mishi inda yarinyar ta fito sai yake ganin kamar bai mata adalci ba, amma halin Nasiru Wodabbe yasa shi jin ko kad'an baya tausayin yarinyar domin baki daya bata wuce shekaru goma sha shida ba, haka ya kad'e babbar rigarshi ya ce mishi. "Nasiha kake min ko me? Ka sani babu abinda ya dame ni, daga yau har zuwa ranar da zan gama amfani da ita a caca na ciyo ta." "Na roke ka kada ka cutar da ita, don Allah. Ita bata maka kome ba ni nayi laifi." Ya fada yana niman durkusa mishi. "Abbati kada ka durkusa mishi, Indai akaina ne wallahi bana tsoron duk abinda zai faru kuma bana fatan naga hawayenka. Duk abinda kayi a kaina Abbati daya ne, ba zaka tab'a cutar dani ba." Cikin wani irin tashin hankali ya riko hannunta. "Ba zaki fahimci me na aikata ba, sai dai duk rintsi kada ki manta da Allah." "Ke muje, na gaji da wannan wasan kwaikwayon naku, sai kace uban wani ne yasaka shi saka ki a caca." Haka Alhaji Mamman Ba'are ya sako ta a gaba har inda motarshi take. A lokacin yana da wani aboki wanda suka taso tun suna agadaz daga baya shi da iyayenshi suka koma marad'i da zama. Wato Alhaji Abubakar Abzin. Duk da shi yayi karatun boko, can marad'i yayi tunanin kai Sa'adatu domin a can zata fi sakewa. Haka kuwa ya faru domin daga Libya kai tsaye marad'i ya wuce da ita, a lokacin da Alhaji Abubakar Abzin ya ganshi da ita, ya sha mamaki amma sai ya nuna ba wani abu bane, domin yasan kulafuncin niman haihuwar d'a Namiji da yake, bai kai burin shi na niman mace mai ilimi ba, sai gashi ya samo yarinya karama me ilimi da nutsuwa. Bayan sun kebe da Alhaji Mamman ya labarta mishi duk abinda ya faru. Sannan ya mika mishi takardunta, ya duba sosai ya ce mishi. "Kai ne dan boko, duba min ta ina yarinyar nan zata tayani rike kamfani na?" Ya tambaye shi yana leken takardar. Gyaran murya yayi kafin ya ce mishi. "Yarinyar bata da matsalar kome, sai dai tana da fahimta ta bangaren kimiyya, idan da a zabinta zaka tambaya ba zai wuce ta ce zata karanci likitanci ko unguwarzoma. " "Tow ina niman wanda zai rike min kamfani ina zan barta ta tafi asibiti, duba dai da kyau." Ture takardar Alhaji Abubakar Abzin yayi ya ce mishi. "Maganar gaskiya, idan har kana son ta zama yadda kake so, dole sai ka nisantatta da wannan rayuwar, ka kaita wani wurin ta rayu tayi karatu. Domin idan tana cikin matanka da danginka kishi da damuwa ba zai barta ba, sannan ita ce karama kowa zai zo mata da fitina da baƙin kishi. Don Allah ka nisantatta da gidanka ban ce kada ka kaita ba, zaka iya kaita amma kuma dole ka rabata da su. Domin kuwa matuƙar tana cikinsu ba zata yi karatun ba, kuma ba zata baka abin da kake so ba, karshe ta haifa maka yaran da kake so babu ilimin da kake bukata, zaɓi yana gare ka." Ya faɗa mishi yana gyara zaman shi, ajiyar zuciya ya sauke kafin ya ce mishi. "Kana nufin na dauketa daga cikin gidan kenan?" "Duk yadda yayi maka." "Shi kenan zan d'auketa amma ina zan kaita?" "Nigeria, kano idan ka kaita can in sha Allah zata dawo maka da abinda baka zata ba." Shiru yayi kafin ya sauke ajiyar zuciya, "ya zan yi da Nana?" Shiru Alhaji Abubakar Abzin yayi kafin ya ce mishi. "Nana ka ɗauke kai akan wani abun da take amma batun yarinyar nan ka tsaya kai da fata ka bata ilimi idan ba haka ba, gidanka duk jahilai za a ayi ta haifa maka. Karshe ga hanyar da za a ci abinci amma kuma babu damar cin abinci, sai dai a kashe kamfanin a zauna a haka. Amma a ƙalla aka samu mace daya da maza biyu zasu jagoranci kome da yardar Allah." "Shi kenan in sha Allah haka za ayi." Ba don Allah ya bashi aboki na gari ba, tabbas Alhaji Mamman ba'are haka zai kaita cikin iyalinshi babu wani tsari ko plan. Sannan Alhaji Abubakar Abzin ya kara mishi kwarin gwiwa na ya tsaya akanta kai da fata, domin yasan Mahaifiyarshi ba karamar shu'umar mace ba ce, idan bata son mutum. Sannan yana son yadda yarinyar take da nutsuwa koda Allah zai bata haihuwa da Alhaji Mamman Ba'are, ya kasance Yaran sun fita daban. A wannan takin Amaryar Alhaji Mamman Ba'are ita ce mace mara yara dayawa, amma daga Rabi har Fauziya, a ƙalla suna da yara kowaccen su shida zuwa bakwai , domin gidan gasar haihuwa ake kamar yadda suke hango iyakar kokarin mijinsu. Sannan Nana ta kara musu zafin kishinsu, ta hanyar gasa musu magana da cewa "Ni duk macen da bata haifa min jika namiji ba, ai tayi a banza tunda mace bata gadon arziki." Wannan ya kara musu kwarin gwiwa daukar ciki suna haihuwar yara rututu, don ma Uban yana tsaye akan Yaran. A gefe guda ga kannenshi da suke hararar dukiyar, wanda ya sani sarai kawai dauke kai yake akan su, fatanshi kada ya bar duniya bai samu wanda zai rike kamfanin ba. Haka ya tawo Niamey da Sa'adatu. Asalin Bafulatana, kana ganinta kasan Bafulatana ce kasancewarta doguwa sirirya. Ga kyau ga farar fata gata da wata irin kunya da kamun kai. Haka yasa Alhaji Mamman Ba'are, kware mata daga yan kwanakin da suka yi a hanya, ya fahimci yarinyar mace ce guda, haka yasa yayi ta nan nan da ita har suka iso gida. Sannan itama bata takura kanta ba, tunda tasan ba zata iya sauya ƙaddarar da ta same ta ba. Haka suka isa kantamemen gidan alfarma. Wanda ya gaji da haduwa kamar ba gobe, suka shiga cikin gidan motar tayi parking ya fito itama ta fito. Cikin gidan ya nufa da ita, tana baya yana gaba duk inda ya wuce gaisuwa ake mika mishi har ya nufi falon Nana, zama yayi a saman daya daga cikin kujerun falorn, ita kuma Sa'aden ta zauna a kasa, kanta a kasa. "Ka dawo Mai Babban suna, ya hanya ya kasuwar?" "Alhamdulillahi! Kasuwa tayi albarka tunda har da mata na samu." Ya fada yana dauke kai yana kallon Sa'adatu. Kalman Alhaji Abubakar Abzin yana dawowa mishi. "Don Allah kada ka zubar mata da mutunci ta hanyar gayawa mutanen gidanka a caca ka samo ta." "Ban gane ba?" Ta tambaye shi.da alamar bata ganen ba, gyara zama yayi ya gaya mata kome amma ya roketa da don Allah kada sauran matanshi su sani, Sa'adatu a caca ya samota. Kuskuren shi kenan bayan Alhaji Abubakar Abzin ya roke shi, shi kuma yana tunanin Nana Uwa ce da zata iya rufa mishi asiri, sai dai yayi kuskuren domin Nana bata cikin irin wadannan iyayen. Kiri-kiri ta shafawa idanunta toka, ta shiga bala'i da hayagagga. Akan me zai auro mata mugun iri, maza ya fice mata da ita daga gida, kada bala'i ya fado musu cikin dukiyarshi mai tsafta. Fadar Nana da ihunta yasa matan gidan sanin Alhaji Mamman Ba'are ya karo aure kuma matar Nana bata yi na'am da ita ba. Haka sukayi ta bala'i a gidan, ya wuce da Sa'adatu bangarenshi, ya zuba mata idanu. "Kiyi hakuri laifina ne, da ban gaya mata ba da haka bai faru ba." Dake tana da hakuri haka ta sunkuyar da kai ta ce mishi. "Ba kome Uwa ce bata laifi." Wannan abin da tayi ya kara mishi kaunarta da bai san lokacin da ya faɗa ba, Haka zaman gidan ya kasance, idan ta fita tsakar gida, Hajiya Rabi da Yaranta su rufeta da duka, koda kasheta zasu yi idan Nana ta fito cewa take. "shegiya jinin matsiyata, Ubanta da tsiya ya masa katutu a caca ya sakata. Ku kashe banza da haihuwar su gara mutuwarsu." Harirah wacce ta kasance itama yar babban gida ce, sannan Yayanta babban lauya ne, yasa take iya shiga fadar Sa'adatu, sau biyu tana kwatarta a hannun Hajiya Rabi da Yaranta. Sun mata dukar kawo wuka, ta suma ta ce musu. "Wallahi idan yarinyar nan ta mutu sai na gayawa Yayana ya nima mata hakkinta kuma daurin rai da rai za a muku kun san dokar Nijar ai." Jin haka yasa suka rage dukanta, aMma hantara da wulakanci ayi abinci a hanata. Karshe ma sai wanda yaran suka jagwalgwala shi za su bata, ga bakar magana idan ta bukaci wani abu. Shi Alhaji Mamman Ba'are bai san me ke faruwa ba, domin bata tab'a gaya mishi halin da take ciki ba, amma kuma tana matukar cutuwa, sai Harirah ce ta gaya mishi abin da suke mata, ta ce mishi. "Idan baka yarda ba, ka tafi ka dawo idanunka ya gane maka, nima don ina gidan ne aka rage dukanta amma matukar bana gidan tow sai abin da ya karu " Haka ya kwana cikin mamaki, domin koda ya tambaye ta, shiru tayi mishi kanta sunkuye tana wasa da yatsunta. Washe gari da safe, suka fita daga shi har Harirah. Lokacin har Sa'adatu ta fito tana share gidan, Yar Hajiya Rabi Babban wacce bata wuce shekaru goma ba, ta zo wucewa ita Sa'adatu bata sani ba, ta zuba mata shara. Ai kuwa yarinyar ta daddage ta zuba mata dundu a baya, tana ihu. ""Mama Mama kin ga wannan matsiyaciyar da aka auro a caca ta zuba min shara ta b'ata min safa ta." Dama Hajiya rabi tana cike da ita Harirah ta hana a casata, sai gata ta fito da wani murtikekken bulala. Ta rufe Sa'adatu da duka, tana yi yaranta suna yi. Fitowa Hajiya Fauziya tayi tana faɗin. "Shegiya sai kace Mayya idan an gama dukarki wanke -wanke na yana jiranki." Tasan ana dukarta ne babu halin amsa mata, haka ta shige kitchen ta dibo ruwan zafi zata watsa mata sai ga Alhaji Mamman Ba'are da Harirah. "Ka gani ba? Ruwan zafi zata watsa mata bayan sun gama dukarta. Alhaji kaji tsoron Allah Ubangiji ba zai barka ba, kasan zaka kawo ta cikin masifa ka auro ta ka mai da ita wurin danginta." "Rabi da Fauziya. Na baku nan da minti ashirin ku bar min gidana, idan kuwa na dawo na.same ku wallahi sai na sake ku.". Ya nufi Sa'adatu ya dauketa suka nufi ciki. Goge mata fuska yayi yana son yayi Magana amma ya kasa magana. "Shirya mu bar ƙasar." "Ina zaka kai ni? Wurin Abbati? Ko wurin Baffana?" Ta tambaye shi cikin kuka. "Wani wuri da zaki rayu babu faɗa babu tsangwama." "Tow." Haka ta shirya kayanta sannan suka fito a lokacin Nana ta fito tana kallonshi. "Ban gane ba, ina zaka kaita?" "Idan Uwar da ta haife ni, ta gaza taimaka min waye zai taimaka min? Nana ke kika basu damar cutar min da Mata? Nana gani na da kika yi a raye yasa kike cutar da abinda nake so? Nana zan nisantatta da ku ne domin Harirah ta gayawa dan uwanta na auro mace na kawo Matana suna son kashe ta, kotu zata turo min sammaci sai ki san abin da zaki ce musu."daga haka ya riko hannun Sa'adatu suka bar gidan, Marad'i ya wuce da ita suka kwana biyu, a wannan kwana biyun ne, ya mai da ita cikakkiyar mace, cikin alfahari da samun mace irinta, dama an gama.mata kome na makarantar, da shi da Alhaji Abubakar Abzin suka tawo da lta garin kano, inda ya tsaya sai da yaga ta fara karatu. Don kusan watan shi biyu kafin ya fara shirin dawowa nijar ya rike hannunta. "Kinsan dalili na na kawo ki nan, kin san kudirina na kawo ki nan. Don Allah kiyi karatu sosai, kiyi abin da ya kawo ki zan na zuwa lokaci zuwa lokaci ina duba ki." Gyada kai tayi, Washi gari motar shi tazo ta dauke shi, haka ya barta cikin kewa da rashin sabo, ta fara karatu a BUK, a tsangayar tattalin arzikin kasa da kasuwanci. Yarinya me kwazo da hazaka. Wata ukun farko da fara karatun, kaf tsangayar suka san tana ja,. Ai kuwa shima Alhaji Mamman Ba'are da suka zo da Alhaji Abubakar Abzin, ya ga sakamakon da ta fara samu ya fahimci yarinyar guruwa ce, domin samun irinta a cikin Yaranka ba karamin arziki ba ne. Haka yayi ta dora Alhaji Mamman Ba'are a kan hanya, yadda zai na kyautatta mata. Har ta samu shekara daya a lokacin ne ta samu cikin Abdul Majid. Cikin tsananin zafin laulayi haka ta haɗa karatu da laulayi tana tsoron kada ta samu matsala ya ce tana wasa, a lokacin ta shiga aji biyu. Haka yazo ya samu tana fama da laulayi ga shi suna tsakiyar semester, kanta yayi zafi duk da wannan yanayin bai gaza gaya mata kudirinshi ba, har ya gama kwanakinshi zai tafi ya ce mata. "Idan mace kika haife zan barki ki kara haifar daya, su zama biyu kema ki samu abokan hira, don Allah ya azurtani da Yara mata sun kai goma sha bakwai ga na cikinki ga na cikin Rabi da Fauziya. Don haka kina haifan biyu zan kai ki a cire mahaifar ki huta kinji." Gyada mishi kai tayi tana jin duk abinda ya ce, domin ita ba zata tab'a bijire mishi ba, shi din kamar waliyi ne a gare ta, haka yasa ta ke daukar duk wani abin da ya ce da muhimmanci. A hankali ya shafa kanta yana rungumeta. Abu daya yasa yake sonta, ilimi da kokarinta. Kuma yaranta zasu banbanta da Yaransu rabi haka yasa yake kara jin dadin ganinta tana kara mishi biyayya. ** Ya dawo da su Hajiya Rabi, suka nime saka Harirah gaba, danginta suka ce basu san da zancen ba, kada su fara saka yarsu a gaba ba yarda zasu yi ba. Haka ba karamin ja mata mutunci yayi ba. Bayan shekara daya ne Alhaji Nasiru Wodabbe da Mahaifin ta suka zo mata da kayan aurenta, kayan alfarma na yar gata, da wasu daga cikin yan uwan Mamanta,. Dake Alhaji Mamman Ba'are har kasarsu ya tafi ya je suka ganshi ya tabbatar musu tana lafiya, sai gashi sun kawo mata kayan aurenta da duk abinda ake na al'adar kasar nijar. Shima ganin ya auri yar babban gida, basu bar kasar ba, sai da ya ajiye musu kayan auren da ake a cikin kayan har da zinari babba tukwaicin budurcinta..... #past #entangled #revals #lovers #Dambuje😹 [2/16, 9:24 PM] Cutie cutie pie: *BAƘIN HAURE....🐾🐾* {Greed for Money is the roots of all evils🫀} Arewabooks:maidambu41 Wattpad:Mai_Dambu Mallakar:Mai_Dambu _🙄 Wai page biyu kuke so, Yasin kuyi maneji mana😿 masoyan Addaririya_ Assalamu alaikum barkanmu da warhaka da fatan kuna cikin koshin lafiya, karku manta da wannan Kamfani mai albarka mai kawo muku kayan bukata cikin sauki da Aminci da Inganci. Wato TA RASULU MULTIPURPOSE. YA SAKE DAWO MUKU DA KAYAN NAN MASU ARMASHI DA DANDANON KOWACCE MACE TAURARUWA CE. _______________________ MARKADADDIYAR GYAD'A HADADDEN KAYAN SHAYI GARIN KOSAI NA TAFI DA GIDANKA. GARIN TUWO GARIN KUNU YAR ASALI CURRY ME DADI SPICES TYME YAJIN DADDAWA ME KYAU GARIN DAN WAKE JAN YAJI MAI DAD'I... _____________________ BUGU DA KARI MUN TANADAR MUKU DA KAYAN FITAR SALLAH DA NA SHAGALIN SUNA DA BUKUKUWA. ATAMFOFI, LESHINA, MATERIAL, SHADODDI, YADUDDUKA NA MAZA DA NA MATA, JAKKUNA DA TAKALMA. WANI ABIN SAI KUN ZO TA RASULU MULTIPURPOSE DOMIN KASHE KWARKWATAN IDANU. ZAKU IYA TUNTUƁARMU A WADANNAN NUMBOBIN.. 08086639163 - 09030168590.... MUNA DAKON SAYAN DAI-DAI KO SARI..... *015* A bangaren Nana ta dai sassauta kiyayyar ta ne don, iyayen Sa'adatu babu wanda ya isa ya kawo musu raini sannan daga mazan dangin har matan kana ganinsu kaga wadanda suka san ciwon kansu, ga wanka da matan suka yi na arziki zaka fahimci sun tashi cikin arziki da wadata domin gwala-gwalan da sukayi kwalliya da su, bayan tafiyarsu ne ya fara ginin part din Sa'adatu ya zuba mata kome nata, da zai tafi wurinta ya dauko mata yan kunnenta babban set da karami ya kai mata, A lokacin da laulayi nata yayi sauki kenan, haka ta rike shi da daraja, bai gayawa kowa Sa'adatu tana da ciki ba, amma yadda yake lissafin zata haihu bayan sun gama jarabawa zai kaita wurin danginta ta zauna sai tayi arba'in ya dawo da ita. Haka kuwa aka yi domin suna gama jarabawa, ya zo ya zauna ko zata haihu amma ina shiru haka.yasa shi daukarta suka tafi kasar Iyayenta. Lokacin da ta ganta a cikin danginta. Ranar kwana tayi tana kuka tana jin wani irin son danginta..ga iyayenta ga Abbati sai shiga da fita yake yana kawo mata abinci da ta ce tana so. Shi kanshi Alhaji Mamman Ba'are sai da yaji wani iri domin kuwa yarinyar ba tsarar shi ba ce, don Abbati ya nuna mishi wanda aka so ta aura, yaro ne Matashi amma haka ƙaddara da rabo ya shiga tsakani. Ranar da suka isa a daren ranar ta haifi d'anta namiji, babu wanda yasan tana nakuda, tsabar kunya da wauta. Yafendo mahaifiyarta tana dakin Mallam mahaifinsu, suna sallar nafilla da mallam wanda suke kiran shi Babaji, taji kukan jariri, bata yarda kunnenta ya jiyo mata ba, sai can ta kara jin kukan. Ai sallama tayi ta nufi dakin ta, anan ta samu Sa'adatu da Kanwarta Kabo, an rasa wanda zai yi wani abu, sun saka Baby a gaba. Dariya abin ya bata ta ce. "Danejo jaririn kuka kasa a gaba. Keda kabo shine baku fita kun kira Sumai ba?" Tana jingine da gadon, tana sauke ajiyar zuciya. Bata ce kome ba, itama Yafendo fita tayi ta kira Sumai, Uwargidanta kenan, ita tazo ta gyara Babyn tsaf, ta wanke Sa'adatu a lokacin, sannan suka saka turaren wuta, domin ita Sumai fulanin chad ce, tana harkar turaren wuta. Kafin wani lokaci gidan ya cika da kamshi, Sa'adatu ana kiranta danejo, Babaji yana kiranta da Hajiya. Kasancewar sunan Mahaifiyarshi ce kuma Hajiyar ce da gasken gaske. Da asuba aka gayawa Alhaji Mamman Ba'are, Hajiya ta haihu.don da fari bai fahimci wacece Hajiya ba, sai da Alhaji Nasiru Wodabbe ya zauna ya mishi bayani, sai ya gane ya kuma ce musu. "In sha Allah Hajiyarta za a kirata.". Haka ya fita Masallaci, ya shiga gidan don ance mishi ta haihu amma basu gaya mishi me ta haifa ba, sai da ya shiga Sumai take murmushin farinciki ta ce mishi. "An samu da namiji, ango ba cefane." Zubewa yayi a kasa ya zuba sujudul shukur, kafin ya fashe da kuka, aka mika mishi Yaron, jikinshi yana rawa ya fito da yaron har gaban Babaji, ya ce mishi."ka saka mishi sunanka." Murmushi Babaji yayi ya amshi yaron ya mishi huɗuba, a madadin yasaka mishi Aliyu, sai ya saka mishi Abdul Majid. Ya mika mishi. "Gashi nan Abdul Majid, kukan ya isa haka. In sha Allah zai zame maka fitila a duk wani Mabudin alkhairinka." "Mallam baka saka sunanka ba?" Ya faɗa hawaye na zuba mishi. "Suna na ba shine mai muhimmanci ba, sunan da zai zame mishi alkhairi ake bukata." Malam yaji dadin wannan kara da Alhaji Mamman Ba'are ya mishi, shi kan kuka yake tayi, don gani yake kamar ba dan shi bane, har asibiti aka kai Yaron aka duba lafiyarshi. Sannan suka dawo kwanan shi biyar ya dawo Nijar ya gayawa Nana ai Sa'adatu ta haihu, bata wani damu can ba, sai da ya ce mata namiji ta haifa shine bayan suna suka je ita da Hadiza da Harirah. Ba karamar hidima aka musu ba, duk iskancin Nana da wulakanci sai da ta rena kanta, domin tazo inda ake magana ta arziki wato kudi kumbar susa. Domin su suka je Barka, sai gashi sun dawo da kayan arziki niki-niki. Madadin haka ya janyowa Sa'adatu farinjini sai tsanarta ya kara cika zuciyar Hadiza da Nana, ita kan Harirah tun farkon ganin Sa'adatu da hakorin hajji jikinta ya bata daga babban gida ta fito, shi yasa bata wani takurawa kanta wurin kishi me zafi ba. Watansu guda suka dawo kano da kaya niki -niki, suka cigaba da zuwa makaranta. Da dattijuwar da tazo da ita daga garinsu me suna Inno, ita tayi ta renon Abdul Majid har suka yi arba'in da wasu satika sannan Inno ta koma ita kuma ta cigaba da karatunta, sai da suka yi wata hudu sannan suka tafi marad'i, kwanansu uku suka wuce Niamey. Wayyo rawar kai a gurin Alhaji Mamman Ba'are ba acewa kome, haka tayi musu sati Uku. Don zasu koma makaranta kuma har cikin azumi suna karatu. Haka da zata dawo Alhaji Mamman Ba'are yayi ta mata hidima. Har suka dawo, kaunar da yake nuna musu ya janyo mata bakin jini, haka suka yi ta jigilar karatu ga danginta daga garinsu ana yawan mata aike, lokacin da Abdul Majid ya cika shekaru biyu, suka tafi Umara da shi, Abbati ya biya mata da Abdul Majid. Lokacin sun samu hutu koda suka dawo, Nijar suka sauka a can ta huta domin lokacin zata shiga aji hudu ne, ga zata tafi IT, wannan zuwan ta fahimci kamar bayan son ganinta har ta gama hutun zata koma, ya zo domin sau biyu suka hadu, da zata koma ya mata kome, ya ce kada ta kuma zuwa Nijar. Tunda ta dawo bai kuma waiwayonta ba, Allah ya so Abbati baya wasa da zuwa ganinta duk bayan wata uku, bata taɓa gaya mishi tana cikin matsi ba, ba kayan abinci shima Abbati idan yace zai zo Mahaifinta zai cika mota da kayan abinci akawo mata . Sannan Yafendo tana turo mata da kayan sayarwa turaren wuta da wasu abubuwan da babu anan, haka yasa ta samu damar tsayawa da kafarta. A can Nijar kuwa, Alhaji Mamman ne ya hadu da wata mata sun haɗu tun a lokacin zuwan shi Mali, sun dan tab'a soyayya sai gashi ta kuma dawowa rayuwarshi,. Bayan da ta fahimci ta kare mata, tun da suka hadu ta kara jan ra'ayinshi suka fara soyayyar bariki, kuma dama can yar barikin ce shima ba zai ce ba yar barikin bace domin bai san.yadda aka yi ya fada tarkonta ba. Tunda ta dawo rayuwarsa tayi bincike a cikin matansa wacece yafi so, a binciken ta gano Sa'adatu da danta. Anan ta fara shige da fice, sai da ta cire mishi su a ranshi, sannan ta aza mishi kiyayyar Abdul Majid, idan ya ga yaron kamar zai kashe shi. Don haka yace kada ta kuma zuwa gare shi, don yaron. ----- Bayan ta gama IT, ta koma makaranta Allah ya taimaka akwai kudi a hannunta dasu ta biya kudin makaranta, ta cigaba da karatu, suna cikin karshen zangon da zasu gama makaranta, yazo a lokacin Abdul Majid bai wuce shakara biyu da rabi ba. Da murnar yaron ya tawo gare shi, Alhaji Mamman yasa kafa yayi kwallo da Yaron, tana wanka ta ji ihun Abdul Majid, da sauri ta fito daga ban daki, ganin Alhaji Mamman Ba'are ya rufe yaron da duka, yasa ta isa wurin ta dauke shi, tana faɗin. "Yaron da babu ruwanshi me yayi da zafi?" Kame gashin kanta yayi ya rufeta da duka, har da kwallo da ita, wulakancin da yayi mata Allah kaɗai ya sani, ya kuma jan ta har cikin ɗakin, haka Abdul Majid ya tafi bakin kofar yana buga kofar yana kiran sunanta "Hajiya!" Yana buga kofar, Alhaji Mamman Ba'are kuwa, ya kwana biyu bai tab'ata ba, haka yayi ta sukuwa akanta kamar ya samu jaka. Yana gamawa ya tashi yayi wanka ya gyara jikinshi, ya saka aka sauke musu abincin yayi tafiyarshi, Bai kara waiwayarta ba, sai bayan sun gama exam ana batun zuwa bautar ƙasa, ya samu tana fama da laulayi, lissafi yayi kafin ya sakata gaba suka je asibiti aka duba lafiyarta, sannan suka dawo ya kuma rufe Majid da duka, ya kara saka mata doka. Tana gama bautar ƙasa Masters zata wuce. Haka yasa suka zama kamar bayi, a wannan zuwan da yayi har da Hajiya Tani da ya mai da ita yar gida. Amma idanuna Harirah yana kanta, domin bata yarda da ita ba, koda tayi magana akan hakan sai da suka kwashi yan kallo. Tana ji tana gani Tani ta samu damar k'amk'ame kome a cikin gidan. Wato tani wata irin Shaidaniyar mace ce, da ta gallabi kanta da duk wanda yake kusa da ita. Musamman ta kananaye kowa har da kannenshi da Nana, babu wanda ya isa ya d'aga mata murya. Domin idan kayi magana Alhaji Mamman Ba'are zai ce ka fita ka bar mishi gida, haka yasa kowa ya sha jinin jikinshi. Kowa ya rufawa kansa asiri, kuma ai wargi wuri yake samu. Akwai wani lokaci da Hajiya Rabi ta rufe ta da duka, ai kuwa Alhaji Mamman Ba'are yana shigowa ya samu Tani a inda Hajiya Rabi ta dake ta, babu bin ba'asi ya rufe Hajiya Rabi da duka, sannan ya kwaso mata kaya ya watsa a waje, da guzirin sakinta. Wannan abin ya tashi hankalin mutanen gidan, domin saura igiya daya a tsakaninsu, haka sai da aka yi da gaske ya dawo da ita, ya kuma kafa mata doka, tun daga ranar Tani take zuba mulki kuma babu wanda ya isa magana, sannan itama Tani tasan cewa yana biye mata amma mafi yawan hirarsu zai sako sunan Sa'adatu. Hankalinta a tashe ta nufi wurin Malaminta ya rufe mishi baki da zuciyarshi. *** A Kano tayi bautar ƙasa, kasancewar Abbati yazo, tana gamawa ta wuce kasarsu a can ta haifi Amaan aka turawa Alhaji Mamman Ba'are sakon haihuwarta, dake a can kamfanin labarin ya same shi, Kuma dayake aikin bai shafi jaririn ba cikin farinciki ya tsayar da dan aiken ya bashi sako ya kai musu, amma shi dai bai taka har can ba, har tayi arba'in ta koma Kano. Dan abin da taxo da shi suka cigaba da rayuwa, bai kuma zuwa ba sai da Amaan ya cika wata takwas, ya turo Alhaji Abubakar Abzin, ya kara biya mata masters ta cigaba da karatu, haka tayi ta fama da Yara biyu ga karatu, koda Alhaji Abubakar Abzin bai zo ba, akwai mutumin da yake kawo mata sako. Lokacin Abdul Majid yana da shekara uku da rabi, Amaan yana da shekara daya da rabi, domin har ta yaye shi. Sai ga Alhaji Mamman Ba'are da Tani dauke da d'anta karami da ta haifa bata jima ba, kuma abin mamaki shi kanshi Alhaji Mamman Ba'are ya kasa cewa kome akan dan na farko shi bai ce dansa ba ne, sannan kuma bai ki yaron ba, a wannan zuwa da yayi, rayuwar Abdul ta fara fuskantar matsala, abin da ya kawo haka, shine tunda suka zo gidan suka saka shi a gaba da duka, na safe daban na rana daban, idan suka mishi wannan dukar, zasu saka shi a daki a rufe shi, a manta da shi ita kanta Sa'adatu bata da ikon ciro shi, idan ta ciro shi kuwa Tani ta sakata a gaba da masifa sai kace ita ta haife ta, idan Alhaji Mamman Ba'are ya dawo kuma ta gaya mishi ya rufe ta da duka, ita uwar a wahale yaron a wahale. A hankali Abdul Majid ya zama kamar dolo matukar Alhaji da Tani suna gidan zai na wani irin sizing kamar zai suma. Tsoro da firgici na Uban ya kara cika zuciyar Yaron, satin su hudu suka bar gidan, shine ya dawo daidai amma kuma sai ya xama ko sauti yaji mai karfi, zai zabura yana niman inda zai boye kanshi. Gashi zama da mutane bai saka ta saki jiki da kowa ba, haka yasa bata mu'amala da kowa. Wani zuwan Mahaifinta taron Malamai na Afirka, yazo ya ganshi bai tsaya ba, ya dauke shi zuwa gidan Sheikh Muhammad Taj Kalarawi, ya ajiye mishi Yaron yana faɗin. " Malam Muhammad ka kalli yaron nan kamar akwai sihiri ko?" "Ikon Allah yanzu dan wannan yaron aka yiwa asiri haka?" Murmushi Sheik Aliyu Wodabbe yayi ya dauki Yaron. "Idan anyi ne don a ga bayan shi, in sha Allah ba zasu ga bayan shi ba. Sai ya zame musu gaggarabadau.." ya dauke yaron yana murmushi, "Alaraini kayi hakuri kada ka mai da musu sharrinsu." "Ni ban musu ba, kuma ba zasu min na kyale ba. Kasan waye ni kuma kasan daga ƙabilar fulanin da na fito, wallahi ba zan bari ba." "Don darajar Ubangiji kayi hakuri amma shi ka tsare shi." Huci yake kafin ya sab'a yaron zai fita Sheikh Muhammad Taj Kalarawi, ya ce mishi. "Kawo shi!" Mikamai yaron yayi, sannan ya tafi ya koma wurin Sa'adatu. Ya tambaye ta meke faruwa da Yaron, amma bata ce kome ba sai kuka. Haka yasa shi fahimtar tana da damuwa amma ba zata fada ba, sati biyu ya yi a garin tare da tsayawa akan Yaron. Wannan zuwan ya zame musu alkhairi, domin kuwa har makaranta aka saka yaron, bayan tafiyarshi Alhaji Mamman yazo da Tani. Hmmm ganin yaron yana makaranta da nutsuwa. Hankalinta ya tashi a wannan lokacin da ta saka mishi kahon zuka, domin kuwa duka take mishi wani lokaci idan zai tafi makarantar domin har gida ake zuwa daukar shi, amma zata hana a kai shi, duk da Sa'adatu tana son mata magana tsoron abinda zai je ya dawo yasa take rintsa idanunta. Bata taɓa hanawa ba, sai sau daya tana laulayin cikin Aryan da aka zo za a dauke shi, Tani ta hana. Kasa hakuri tayi ta ce mata. "Gaskiya ba zai yiwu ba, ya tafi makaranta domin ba zai zama ya rasa nutsuwa ba, a gida bai huta ba sannan a can inda zai huta kice ba zashi ba, wannan ba yi bane ." Ta kamo danta ta fi da shi. Tana komawa cikin gidan Tani ta saka sakatar gidan zata rufeta da duka, ita dai bata san me ya faru ba, sai dai kawai an balle kofar gidan ne aka d'aga daga kan Tani da ta suma. Koda Alhaji Mamman Ba'are ya zo don yaji labarin abinda ya faru, shima tsorata yayi da Yanayin Sa'ade, don haka ya tattara kayan Tani da d'anta. Bai kuma takowa gidan ba, har ta haifi Aryan ita da kanta tayi mishi huɗuba. Haka tayi ta rayuwa can wurin danginta kamar sun manta da ita, haka shima bangaren mijinta ya manta da ita, sai da ta kai dole ta cire Abdul Majid a makaranta. Dake makarantar Sheikh Muhammad Taj Kalarawi ne,. Ya daina ganin yaron domin Allah ya daura mishi son Abdul din, wani ikon Allah sai kamar an dakatar da shi da zuwa duba su. Haka ya watsar da tunaninsu.. yara uku babu abin da zasu ci, don haka kawai ta fita ta fara aikatau, tana wanke-wanke da abinci, a bakin titi, karshe ma karatun da take ne ya tsaya, akwai wani karamci da kanawa suke dashi, kasancewarta bakuwa kuma daliba, ganin bata zuwa aka tashi wasu daga cikin dalibai suka nimo labarinta, haka yasa makarantar B.U.K suka dauki nauyin sauran lokacin da ya rage mata, wannan karamcin da suka. Mata yasa bata iya mantawa da su ba, sannan daliban tsangayar suka hada mata kudi ta kama sana'a a cikin gidan, ba sai ta fita ba. A bangaren yaranta ta saka su a wata makarantar gwamnati. Haka suka ta rayuwa da dadi ba dad'i. Har suka gama ta cigaba da xama a Kano, a hankali ta rungume Yaranta, ta cigaba da sana'a idan suka cinye jarin, sai ta nemi aikatau a gidan mutane. Abdul Majid tun yana primary yake da kokari, sai dai daga lokacin da aka mishi tsawa, zai birkice ya koma kamar dolo, haka yasa wani lokaci yake hakura da makarantar ya zauna a gida. Akwai gidan da take aiki, Yaron gidan ya nimeta da lalata, ita kanta bata sani ba. Sai da ta ganta a Office din yan sanda, an rufeta, tayi tayi ta musu bayani amma ina sharri aka mata, haka ta bar Yaranta a gida ,babu kowa sai Allah, tayi kuka tayi bakinciki har cewa take ita da ganin wannan rayuwar da mutuwa tayi ya fi mata, akan wannan rayuwar domin tana cikin tasku. Tun safe da Yaran suka karya har rana bata dawo ba, har dare babu labarinta, haka Abdul Majid yake goyan Aryan idan ya gaji ya sauke shi. Kwana suka yi babu kowa a gidan sunyi kuka har sun yi shiru. Washi gari da safe suka tashi babu Mamansu. Har rana bata dawo ba, dalilin da yasa Abdul Majid ya fita bakin shagon unguwar kenan ya sato bread,. Babu wanda ya lura da halin da suke ciki. Haka aka rufe shi da duka yana rungume da bread din, yaki sakewa sai dukan shi ake yi, makocin sune ya ga ana ta dukar shi, shine ya karbe shi. An farfasa mishi jiki. Mutumin da yake lura da shige da ficen su, yaga yau bai ga Mamansu ba. "Abdul Ina Mamanku?" Yana sheshekar kuka ya ce bata dawo ba, har lokacin yana rungume da bread din,. "Me yasa ka daukar musu bread." "Aryan da Amaan yunwa suke ji Hajiya bata dawo ba." Jikin mutanen da suka dake shi ne yayi sanyi. "Nawa ne kudin bread din?" "Dari ce!" Biyan kudin yayi ya saka yaron a gaba har gida, "ina mamarku take aiki?" "Ta can ne?" "Tow ka jira ni ina zuwa." "Tow!" Gidan shi ya koma ya amso musu kunu da dumammen tuwo, ya kawo musu Aryan da Amaan suka ci sai da suka kusan cinyewa sannan suka koshi, Aryan ya koma ya kwanta sannan Abdul Majid yaci kadan ya bar musu, yadda Mamansu take yi ta ci kadan ta bar musu sauran.... ~~~~~~~~~~~~~~ ```Shahararu goma aduniyan kayan mata wato m zee kamshi kayan mata kenan inakuke matan kwairai manyan Mata fah bamuna mataba Mata masu aji Wanda tasan kanta agidan mijinta kozokuyi gyara masu kyau da inganci Wanda zaisa oga nishadi yasashi farinciki atare dake kayanmu wane yaro sai uban yaro kinsha zumar makalemata dare daya wanka goma wanan set ne na kayan kwairai akwai fati budurwa mumuna da aeki Dan miyau malaka to shu,Umar Zuma zumar kiba gari kiba Zuma me lakani ningi tsumin lahaula hadin miski ba ahira dawando garin me kabara kasa ruwa sama ruwa wanan magani ba ,a magana magani sanyi mekyu maza da Mata ci da kaza ci da cicibin vlp yan shila ci da kifi nama kayan sakiba na gida danawaje munadakaya kala kala fani kamshi munada shu uwar humra namu ba irin nasubane akwai turare 24 hr turare kabasa Dana gida masu Dadi gakyau ga kamshi 08063845136``` #Mai_Dambuje. [2/17, 5:06 PM] Cutie cutie pie: *BAƘIN HAURE....🐾🐾* {Greed for Money is the roots of all evils🫀} Arewabooks:maidambu41 Wattpad:Mai_Dambu Mallakar:Mai_Dambu *016* Mutumin nan bai yi kasa a gwiwa wurin neman Mutanen unguwar tare da mai unguwa, ya zauna a tsakiyarsu ya ce musu. "Akwai matar nan yar kasar Nijar, tow gaskiya a da ina ganin mijinta yana zuwa, amma a yanzu an dauki shekara biyu ban ga mijin yazo ba, sanan ita kuma tana yawan fita aikatau domin ina yawan ganinta ta fita da sassafe ta dawo da la'asar lis, tow kada na kaiku da nisa Matar nan dai jiya bata kwana a gida ba, sannan ku yi nazarin idan mune ya zamu ji? Sannan yarinya ce domin bata kai talatin ba, don Allah ku duba lamarin." "Hmmm! Waye ya sani ko yawon bin maza ta tafi." Inji wani mutum a wurin, tsawa limamin unguwar yayi mishi. "Mene ne hujjarka?" Sunkuyar da kai yayi, kafin liman ya ce. "A yanzu muje gidan, ko akwai yaron da zai fada mana inda take zuwa aiki." Haka suka mike bakiɗayansu, suka tafi har gidan, sun samu Aryan yayi kashi ya b'ata jikinshi. Haka Mutumin farko ya kira Matarshi ta wanke su, sannan ta dauko musu kayan Yaranta, suka kasa sannan ta riko hannun Abdul Majid suka fito. "Abdul Majid!" "Hmmm!" Ya fada yana komawa gefe, domin har yau yana fama da rashin sakewa. "Kasan gidan da Mamanku take zuwa aiki?" Gyada kai yayi. "Ok Maman Luba tafi da sauran, bari ya kai mu inda take zuwa aiki." Haka suka saka Abdul Majid a gaba, har gidan dake tana zuwa da shi yana taimaka mata da Aryan yana wasa da shi, koda suka zo gidan babu wanda ya yarda yayi musu maganar Sa'adatu, sannan babu wanda ya kula su, sai da yan unguwar suke gayawa musu ai tun jiya da hantsi yan sanda suka tafi da ita office dinsu. Ba karamin kaduwa suka yi ba, domin kuwa har an rasa me magana, haka suka mai da Abdul gida, sannan wasu suka wuce kasuwa, wasu kuma suka hakura da kasuwa suka nufi Office din yan sanda nimanta. Musamman Baban Luba mutumin nan yayi halacci musamman da yake makocinta, haka suka yi ta yawo kafin Allah ya gajarce musu wahala, suka same ta goshin Magariba a wani Office din yan sanda. A lokacin da suka je a bada belinta, kin sauraronsu aka yi, da suka nace aka kawo laifin da ake tuhumarta da shi na sata da yunkurin kisan kai. Shiru kowa yayi kafin, suka roki a basu ita tana da Yara kanana. Amma aka hana su, sai dai sun fito da ita, suka ga ko tsayuwa bata iyawa ga yunwa ga tashin hankali, haka Baban Luba ya tafi ya sayo mata tuwo hannu baka hannu kwarya haka take cin abincin. Tana ci a lokacin hankalinta ya dawo jikinta, duk yadda suka so jin me ya faru, kunya da zurfin ciki ya hanata magana. Haka suka maida ita hankalin kowa ya tashi, sai da aka mai data ta zauna tayi ta kuka tana jin me yasa ta kasa magana. Haka ta kwana kuka. Washi gari.. Gidan mutumin da take aiki suka je, dakyar da sannu sannu aka bawa mutumin hakuri sannan ya janye karar domin yace kotu ce zata raba su da ita, daga taimako zata kashe musu d'a da sata. Su dai tunda aka janye karar, suka yi godiya suka bar gidan. A can office din yan sanda, aka bada belinta, aka dawo da ita gida, Baban Luba shi ya fita can sai gashi da kayan abinci, ya kawo mata da dafaffen har da Yaranta. "Idan kina da matsala ki yi magana da Maman Luba, Allah ya tsare na gaba." "Allah ya biya maka bukatarka na alkhairi, na gode." Ta fada tana kuka, haka ya bar gidan, sai da tayi wanka tare da sauke sallolin danke kanta, ta samu wuri ta zauna ta sakawa yaran abinci, suka ci banda Abdul Majid da yake manne a jikinta, yana kallon yadda take sharar kwalla. "Hajiya kici abinci man." Ya faɗa kamar zai fashe da kuka. "Na koshi Alhaji!" Ganin taki ci yasa shima yaki ci. Yadda ta ga rana haka ta ga dare, Washi gari ta tafi har gidan Baban Luba tayi godiya, sannan ta ce mishi. "Ina son zan fita da yaran, ga gidan." Kafin Baban Luba yayi magana Maman Luba ta yi maza ta karɓe zancen. "Ina zaki kuma?" "Ina son zuwa nijar ne, shine nake son fita muyi Bara ko za a samu kudin mota." Ta fada cikin matsanancin kunya, "Bara?" Suka hada baki, "ki je gida ki shirya gobe in sha Allah sai ku tafi, yau zan samu abokina Hamisu bazabarme na gaya mishi akwai fasinjar marad'i ko?" Gyada kai tayi, ya jinjjina kai ta koma gida, haka ta dawo gida, bayan fitar shi ta koma gidan ta cewa Maman Luba."idan kina da aiki kawo na rage miki." "A'a Maman Abdul barshi." "Don Allah kawo ko wanki ne." Haka matar ta fito da wankin. Kafin azahar ta gama wanki, kuma kayan sun fita tass, ta shanya mata sannan ta basu abinci suka dawo gida, ita kan Maman Luba wani irin son Sa'adatu take, shi yasa take tsananin tausayinta. Tasan yarinya ce. Da dare Luba ta kawo musu abinci har gida, washe gari da sassafe makocinsu ya sakata a gaba, bayan ya gayawa me unguwa da liman, aka kaita tasha sannan suka bata guzuri me yawa, ta baro Kano zuwa marad'i. A lokacin da ta isa ta samu Alhaji Abubakar Abzin, baya gari a gidan ta zauna na tsawon sati daya, kafin ya dawo. Duk da tazo wurin shi da damuwa amma kuma tana ganinshi sai ta kasa fadar kome, ta koma kuka. Yana rike da hannun Abdul Majid, yake tambayarshi sai ya kalli Mamansu kafin yake magana, amma yaki fadar abin da ya faru. "Hajiya baki ce kome ba, sai kuka." Girgiza kai kawai tayi. Haka ya mike ya ce ta koma can wurin uwargidansa tunda dama a can ta sauka, Mutumin kirki, Washi gari ya tashi wani yaron shi ya je har Kano aka duba mutumin da ake bashi aika ya kai mata, ashe ya rasu, sannan dan aikan ya tafi har unguwarsu, anan yaji labarin abin da ya faru, kwana biyu tsakani sai gashi nan ya dawo da bayani, Alhaji Abubakar Abzin ya yi shiru. Sannan ya kira ta. "Me ya faru har aka rufe ki na tsawon kwana biyu?" Kanta a sunkuye ta ce mishi. "Babu kome Abba." Don a haife ya haifeta. "Shi kenan, amma Mamman yana zuwa?" Hawaye ne suka zubo mata, ta girgiza kai. "Shi kenan." Haka ya fita a ranar ya bar marad'i, wato koda ya isa Niamey. Faɗa suka shiga yi shida Alhaji Mamman kamar zasu yi doke-doke, kafin suka dawo Alhaji Abubakar Abzin ya gaya mishi halin da iyalinshi suke ciki. "fisabilillahi yara maza har uku fa, gasu nan duk da rashin kulawa amma yaran sun samu tarbiyya kaji tsoron Allah kafin ya tsayar da kai." "Naji zan zo amma gaskiya Ya fada kuma sai yayi shiru, kafin yayi kwafa. Kwanan Alhaji Abubakar Abzin daya, suka juyo tare. Cikin farinciki yaran suka ga Babansu, sai dai Majid ya koma jikin Hajiya ya lafe, saboda kallon tsanar da Alhaji Mamman yake mishi. Tambayoyi har da takardun ta, duk ta bashi sannan ya kalleta cikin isa ya ce mata. "gobe zaki koma Kano, ki sani ban baki damar kiyi karatu don jin dadinki ba, ban tara dukiya don yaranki su ji dadi ba, na tara su ne, don amfanin gobensu. Dole ki jajirce ki kuma koyi boye damuwarki, sannan kiyi hakuri da abinda kike da shi. Wannan shine abin da zan gaya miki ". "Mun gode sosai hakan ma" ta faɗa muryarta a raunane. "Kada ki kuma kawo karana." "Allah ya huci zuciyarka, in sha Allah haka ba zai kuma faruwa ba." Haka ya kwashi Amaan da Aryan, ya tafi da su yawo, sai dare ya dawo dasu. Duk abinda ya kawo musu haka yace kada ya bawa Abdul, amma abin ka da Uwa. Sai da sauran suka yi barci ta tashe shi ta bashi ya ci, sannan ya kwanta. Tausayin Abdul take ji, gani take kamar tana da laifi wurin duk abinda ya same shi. A hankali take shafa kanshi har barci ya dauke shi, tana zaune a wurin Alhaji Abubakar ya shigo ya cewa Matarshi ta turata wurin Mijinta, haka ta shirya ta tafi, za a iya cewa wannan karon rabo ya kawo ta, domin kuwa washi gari ya juya ya koma ya bar kome nasu a hannun Alhaji Abubakar Abzin. Ita kuwa a ranar ta dawo kano da tsaraba me yawan gaske. Ta kaiwa gidansu Baban Luba, sannan ta kai na gidan Mai unguwa da Liman, don sune iyayenta. Bayan tafiyarta da binciken da Alhaji Abubakar Abzin yayi, ya ji gaskiyar abinda ya faru. Ai kuwa ya maka mutumin da yasa aka rufeta a kotu, rikici babba aka yi ta yi kamar me, sai da dattawan unguwarsu suka saka baki, haka ya sama mata yanci, suna dawowa ranar Monday aka zo aka kwashe Abdul da Amaan suka tafi makaranta. Ba laifi zuwa yanzu ta samu dan nutsuwa, tana dan sana'a kuma abincinsu yana nan. *** A can kuwa Tani tana zuba mulkinta yadda take so, bata yarda ta kuma cewa tana son zuwa ganin halin da Sa'adatu take ciki ba, domin tsoron abinda ya faru kada ya kuma faruwa, haka ta zauna tana zuba musu isa da mallaka. Sannan a gefe guda ta mallake Nana sai yadda tayi da ita, kuma bata da katabus sai Abinda Tani ta ce, ana haka ta saka Alhaji Mamman a gaba ya saka mata danta Sajjid a makaranta tare da gaya mishi duk abinda yake so Sajjid zai mishi, ba sai ya damu da Abdul ba, fatanta kawai ya saka Sajjid a cikin Yaranshi. Amma mutumin nan yaki kula zancen. Idan ta dauko zancen zai ce mata yaji kawai don ta rabu dashi amma a ranshi baya jin zai yarda ya amshi Sajjid domin ba jininshi ba ne. Haka tayi ta kokarin lallai sai yaron, ya zama wani abu kai babu wanda ya isa yayi mishi fada balle tsawa. Ga rashin kunya da fitsara. **** Tunda suka dawo ta fara laulayin cikin Jamilah don ma babu wani wahala, amma kuma tana yawan kwanciya. Saidai da sauki,haka taci gaba da rayuwa har Allah ya sauketa lafiya, ta samu yarta mace, Kyakyawa da ita, haka yasa ta saka sunan Yafendo Jamilah. A lokacin ba laifi abinci da sakon yana samunta, haka tayi ta renon Jamila, amma ta turawa Alhaji Abubakar Abzin sakon ta haihu, shi kuma ya turawa Alhaji Mamman Ba'are, bai bi ta kanta ba, sai bayan shekaru biyu, rabon Anisah ya kaishi Kano, a lokacin Abdul Majid ya kusan gama primary, a wannan zuwan da yayi ne. Ya kama yaron ya mishi mugun dukar da ya suma saboda kawai an kawo kararshi wai ya dauki kudin wani me shago, ya mishi wannan dukar, ya tura shi gidan horar da kangararun Yara,. Wani abin tashin hankali ya dauke Hajiya da sauran Yaran suka koma Niamey. Suka bar Abdul Majid, da yayi fama da jinya ga cutarwar yan gidan, duk wanda ya fika ƙarfi zai zalunce ka, sannan yara ne masu banbancin hali, har da marasa jin magana masu luwadi, sai dai tunda suka barshi Hajiya ta bar amanarshi a hannun Maman Luba. Tana can amma addu'arta bai daina sauka a kanshi ba, Sai da ya kwashe shekaru goma har ya zama kaman dan gida, anan ya gama primary school da secondry school, yayi jarabawar shiga jami'a, ƙoƙarinshi yasa shi samu tallafin karatu a wurin gwamnatin Kano, anan ya tsaya ya karanci bangaren likitanci, tsawon wannan lokacin, Hajiya tana marad'i, tunda Alhaji Mamman ya zubasu yayi tafiyarshi, Alhaji Abubakar Abzin shine kome nasu, har ta haihu. Dukkan Yaran sun san Majid amma Anisah bata san shi ba, sai labarinshi. Zamanshi a gidan horan Yara, ya kara maida shi wani irin mutum mai murdadden hali, sannan baya hmm baya Humm. Dole yasa yake zama a cikin aji, amma baya son hayaniyar mutane ko kaɗan. Idan dare yayi kuwa baya barci domin idan ya fara barci zai ta mafarkin Babansu yana dukar Hajiya. Haka xai bude idanu, sau biyu yana faduwa a aji, a duk ranar da yayi mafarkin tow zai fadi ya suma sai washe gari don bai samun isasshen barci. Ganin haka zai shafi karatunsa, yasa shi fara ganin likitan kwakwalwa, aka fara duba shi, domin har dawanau aka tura shi. Lokacin da suka samu hutu, ya shirya ya tafi marad'i da tambaya da kwatance yaje gidan Alhaji Abubakar Abzin, Aryan yana kofar gidansu na maradin ya hango Abdul ba zai manta da shi ba, da gudu ya tafi ya rungume shi." Hammayo;" murmushi yayi ya kara rike shi suka nufi cikin gidan, ya kawo musu tsarabar Kano. Hajiya da ta ganshi, juya baya tayi tana kuka. Murmushi yayi bai ce mata kome ba. Ya zauna kanshi a sunkuye. Haka ta shiga daki Jamilah ta fito ta ce. "Hammayo kai ne" ta zauna a kusa dashi tana washe baki . "Yafendo kin zama yan mata " "sai buhun rashin mutunci." "Hammayo kaga Hamma Aryan ko?" Tashi yayi ya shiga dakin Hajiya, ya same ta a can kuryar dakin tana kuka. Zama yayi gabanta. "Hajiya ko daidai da rana daya ban manta daku ba." "Amma ai na manta da kai!" "Hajiya nasha mafarkin kina sallah kina min addu'a da wannan na yarda a zuciyarki ina tare dake." "Alhaji baka yi fushi ba?" Girgiza kai yayi yana murmushi. "Hajiya kina karkashin mijinki, a kaina ba zaki kashe auren da na bude idanu na gani ba." Hawaye ne ya zubo mata danta dan kimanin shekaru goma sha takwas. "Gobe zamu je Niamey." "Hmm! Allah ya kai mu!" Ya fada. Haka ya fita ta kawo mishi abinci, kannen suka zagaye shi, suna bashi labari can sai ga Anisah ta shigo tana kuka."Hajiya!" "Na'am Auta." "Hajiya Hamma Amaan ya kwace sauran canjin." "Allah ya shirya min ku baki daya." Ta amshi sakon, ta ajiye a kitchen. "Hajiya Ina hamma Aryan?" "Suna cikin daki Hammayonku ya dawo." Da sauri ta shiga Dakin, ta d'aga labule. Kura mishi idanu tayi idanunta cike da kwalla. "Hammayo!' bude mata hannu yayi, da sauri ta isa gareshi tana kuka. "Hammayo ban sanka ba, amma Hamma Aryan kullum sai ya bani labarinka." Murmushi yayi yana kallon Aryan. "Ya ce miki ina sat.." rufe mishi baki Aryan yayi. "Alkhairi nake gaya mata, yarinya ce bata san sharri ba please." "Hamma Amaan yake gaya min wai sat..." Rufe mata baki Jamilah tayi. "Ke dai akwai bakin allatsine, idan kika bi na wancan sakaran sai an daure ki igiya tayi saura." Domin daga Jamilah har Aryan basu shiri da Amaan,.kamar wuta da auduga. Mikewa yayi suka tafi masallaci, suna dawowa suka samu Hajiya tana kokarin tuka tuwo.. "Hajiya bani na miki?" "Yau.girkin maza zamu ci?" Ta tambaye shi, "zamana a gidan Horon kangararrun Yara, yasa na rike bangaren girki har gasar girki muke " ya faɗa a sanyayye, Duk da cikin raha yake maganar amma fuskarshi bata nuna haka ba, yanayinshi babu yabo babu fallasa, suna zaune ya tuke tuwon ya kwashe tas, yana gamawa wata mata ta shigo kawo kar'ar Amaan. "Maman Jamilah ina jin kunyarki, ki jawa danki kunne wallahi ya fita harkata da yarinya ta." "Kiyi hakuri;" shine abinda Hajiya ta faɗa, sannan matar ta fita tana zage-zage. Can kafin magariba sai ga Amaan, ya shigo yana zage zage da rashin kunya. Kallon Abdul yayi ya ce mishi. "Barawo ka dawo ne?" "Hammayo muje masallaci!" Inji Aryan, domin a cike yake da Amaan babu ranar da zata waye ba a kawo ƙarar shi ba, "Kai dan shegiya da kai nayi?" Wani irin mari Abdul ya kifa mishi, a wurin ya zube yana nishi, "kayi yadda kake so, idan kaso ka fadi abinda yayi maka. Amma ka sake ka zagi wani cikinsu sai na cire ma hakori." "Hajiya kina ganin barawon danki zai kashe ni." Alola yayi ta wuce daki, shima ya wuce dakin. A masallaci Aryan yake bashi labarin abinda yake faruwa, sannan wani abin tashin hankalin shine duk bayan wata biyu Hajiya xata kwashe su har Niamey, su je can ayi ta wulakanta su ana ganawa Hajiya azaba da masifa. Lashe baki yayi yana jin daci a ranshi, haka sukayi sallah sai bayan Isha suka dawo, tun a kofar gidan suke jin muryar Jamilah, Hajiya tana gefe bata yi magana ba ta xuba musu idanu Amaan sai dukanta yake. A fusace Aryan ya nufi Amaan Majid ya rike shi, "sake ta!" "Idan naki fa?" "Aryan wuce da hajiya ɗakinta!" Ai dama ganin hajiya a wurin zai saka ya kyale shi, sai gashi cikin fushi ya kai mishi wani irin duka a kafa, dauke wuta yayi wato Majid zama gidan horon nan ya koyar da shi mugunta sala sala. Targad'a shi yayi ya ce mishi. "Kafin ka warke ka fara fita zaka fahimci muhimmancinsu, idan ma baka horu ba, akwai hanya dayawa da zaka nutsu." Haka ya wuce da ita daki, yana faɗin. "Kin mishi rashin kunya ne?" "A'a Hammayo, kiranta yayi tana sallah shine tana idarwa ta fita ya kama dukanta da hajiya tai magana yace babu ruwanta." Cizon fatar bakinshi yayi yana jin tafasa a ranshi, a daren Aryan ya gyara dakinsu, da Inda Hammayo zai kwana. Haka suka kwana suna hira, sai asuba suka yi barci.. wurin karfe goma motar kai su Niamey tazo, suka tafi sai cika Amaan yake yana batsewa. Har suka isa gidan, wanda daga kofar gidan zaka fahimci ana sha'ani ne. Lokacin da suka isa gidan, ba laifi ana ta hada-hada, falon Alhaji Mamman suka nufa suka gaishe shi sama sama ya amsa. "Kai me yasa meka?" "Ba Barawon can bane ya dawo ya targad'a min kafa ba." "Waye barawo!" "Abdul Majid!" Wanda ya shigo falon, mikewa Alhaji Mamman yayi ya ce. "Sa'a me yasa kika kawo min shi gidana!" Juyawa yayi ya bar falon. Ai kuwa garin bashi hakuri ya rufeta da duka, har waje. Wannan abin ko a jikin Amaan domin shi gani yake Hajiya ta rabasu da jin dadin gidan Ubansu ta kawo su wata duniya suna wahala. Shi yasa duk abinda Alhaji Mamman zai mata baya tausayinta ko kaɗan. Da gudu Anisah ta fita waje, "Hammayo kazo Alhaji xai kashe Hajiya." Sun saba duk lokacin suka zo haka xai mata duka a gaban jama'a. Amma na yau ya wuce tunaninsu domin biki ake yi a gidan, kuma ga mutane babu wanda ya damu sai ma tsayawa da suka yi suna kallon abin. Haka ya ratsa taron ya shiga. Ya rike hannun Alhaji Mamman Ba'are da yake zuba mata duka. "Ya isa haka!" D'ago kai yayi yana mamakin waye ya isa ya dakatar dashi daga dukar Sa'adatu. "Ya isa haka Alhaji Mamman Ba'are!" Ya sake hannun shi yana kallon cikin idanunshi. "ya isa haka nace!" Ya fada yana me dago kai yana kallon Hajiya Nana. " Na rantse da Allah,duk ranar da danki ya kuma d'aga hannu ya tab'a min Uwa, sai na hauro sama na bugaki da kasa daga saman zan wurgo ki billahi azim, Uwa bata fi Uwa ba duk sunansu Uwa." Ya faɗa yana d'ago Hajiya. ""Kai waye ya baka damar shigo mana gida?" Inji Sajjid Mamman Ba'are, cikin wani irin fushi, ya juya ga Sajjid wanda ganin idanun Abdul ya bashi tsoro. Ƙwayar idanunshi a fusace yake fushinsa daga zuciya take kunno kai ga idanunshi, kamilalliyar fuskar shi bata nuna fushin ba.. "Kace me?" Hadiye yawu yayi, ya juya ga Alhaji Mamman Ba'are zai magana Hajiya ta ce mishi. "Kul ka kara magana!" "Hajiya idan ya kuma dukanki sai kashe shi, Nana kin ji me nace." Ya fada da karfi, juyo shi hajiya tayi ta watsa mishi mari, ta kuma marin shi. Jikinshi ya hau cira kamar zai tashi sama. "Ban doraka akan haka ba,me yasa zaka min haka?" Inji Hajiyar tana kuka."Mahaifinka ne me yasa zaka mishi haka a gaban jama'a?" Zube gwiwarta tayi ta ja hannun Majid din, sai yaki. "Ki cewa danki ya fita na tsame shi cikin zuri'ata." "Haka yayi ai dama kafin yau ni ba danka bane." "Ba zai fita ba, rashin kunyar da yayi sai Uwarshi ta biya akan idanunshi." Jin Nana tana saukowa. A fusace yayi kanta tare da tsare ta da idanunsa masu Bala'in ban tsoro. Da gudu Hajiya ta rufe shi da duka, "ka bar tashin hankalin nan, ka koma inda ka fito na roke ka, don Allah na roke ka ka tafi ka yi nisa da mu na yafe maka zuwan." Juyawa yayi zai tafi Nana ta dauki sandarta ta shiga bugawa Hajiya, "Hammayo tana dukan Hajiya" bai ce kome ba, ya nufi falon Alhaji Mamman ya ce mishi. "Ka fita ka jawa Mamarka kunne ko na kona gidan nan baki ɗaya wallahi billahi azim." Ya fada a haukace, zuwa yanzu shi kanshi Alhaji Mamman Ba'are tsoron Majid ya darsu a zuciyarshi. Ganin yadda ya fita da gudu, inda motar gidan take ya nufa, ya cire rigarshi ya bude wurin tanki, ya saka rigar sai da ya jike da fetur, ya Ciro yana watsawa a kan kome na gidan, "Hajiya kyale ta don Allah." Alhaji Mamman Ba'are ya fada, sannan ta tsaya tana hakki. "Me yasa ka dakatar dani?" "Saboda d'anta zai aikata kome don mahaifiyarshi." "Kenan idan aka dake ta zai dau mataki?" "Zai aikata kome.ma". Ya faɗa yana kallon yadda Majid din ya d'ago Hajiya suka dauki kayansu, suka nufi gidan. " Ita da Yaranta su zauna a gidan shi ya bar magana gidan mu!" Inji Nana domin ta shirya sai Hajiya ta biya abinda Abdul Majid ya aikata musu. Suna da kudi suna da karfi, Majid ba xai zubda musu kimarsu ba. Don haka suka hana Hajiya tafiya, suka sakata a gaba. Shima Majid din kin tafiya yayi yana tsaye a kofar gidan, yana jiran ganin ko Aryan ne, suna can Alhaji Mamman yasa Hajiya a gaba da cin mutuncin, har aka gama bikin cikin kuka take, karshe ma turawa maradi yayi aka rufe gidan wai kada Majid ya tafi can ya zauna. Shi kuwa rubuta wasika yayi ya bada aka kaiwa Hajiya da ban hakuri, Bayan tafiyarshi da wata biyu, Alhaji Mamman ya yanke mata rabin wahala ya sakata a gaba ta fara zuwa aikin kamfaninshi. Da iliminta da kokarinta ta fara aiki inda ta fahimci wasu na azurta kansu da dukiyarshi, don haka ta fara aikin binciken anan ta gano har da hannun Alhaji Haladu da Kamilu. Ta mika mishi duk wani abinda ta tattara, sannan ya ce mata. "Ki saka Yaranki a gaba su koma makaranta, naji ance wancan dan mahaukaciyar, likitanci yake karantawa. Tow sai ya cigaba amma ya sani ko ya gama karatun anan zai yi aiki xa a fara gina mishi asibiti." Zuwa yanzu baya shakkar mutuwa dama abinda yake so ya samu, Yaran hajiya zasu iya tsaya mata, duk da yasan yayi kuskure amma a yanzu yana da damar barin mata kome domin shima yanzu ya san girma ya cimma shi. Majid da y koma sai da yayi jinya, a haka yake karatu, bayan wata uku aka kawo shi har marad'i, don bai san waye akanshi ba, abu daya yake faɗa sai na kashe ka idan ka tab'a min Mamata. Hajiya bata iya ganinshi a wannan halin ba, kamar an mata bushara ta wuce da shi wurin danginta,. A can ya zauna har ya samu lafiya sannan aka yi cuku-cuku ya dawo nan da karatu, amma abin ya zame mishi cutar damuwa dan mental health ɗinshi ya tabu, don ma Kakanshi yana tsaye akanshi da sauran dangin Mamarshi haka yasa shi ya boye yadda yake shan wahala, ya cigaba da karatunshi.... Bayan shekaru bakwai..... #Dambuje [2/18, 11:33 AM] Cutie cutie pie: *BAƘIN HAURE....🐾🐾* {Greed for Money is the roots of all evils🫀} Arewabooks:maidambu41 Wattpad:Mai_Dambu Mallakar:Mai_Dambu *017* Bayan shekaru bakwai. Duk da wannan shekarun zaka dauka Hajiya ta huta daga jidalin dangin Alhaji Mamman Ba'are, amma ina domin bala'in ya kara hauhawa ne bayan Alhaji Mamman Ba'are ya nad'ata sabuwar shugabar kamfanin ya sauke wanda yake kai ya dorata, ai kuwa sai gashi fitina ta kunno kai, daga kamfanin har gida bata da sukuni. A lokacin ko barci neman gagararta yake, wata irin wahala take sha da kamfanin Mamman Ba'are, gashi yadda ta tsaya ba ƙaramin bunƙasa kamfanin tayi ba, domin idan har kana son gane yadda kamfanin ya cigaba tow ka shiga office dinta, ita da Aryan suke tsara duk wani cigaba dake Allah ya taimaka shi mutum ne mai kwazo kamar Abdul sai gashi ya hada karatu da aikin da yake taya mahaifiyarshi, duk da wannan jigilar bai hana idan ta koma Nana ta sauko ta shiga gaya mata magana marasa dadi ba, ana cewa idan duka yayi yawa na kai ake karewa tow ita Hajiya baki daya da ta ko ina kare dukan take, sannan Yaranta tsayawa tayi akansu, domin idan ba haka tayi ba Yaran so ake a lalata mata rayuwarsu. A cikin shekaru bakwai din nan, suka tafi bikin gama makarantar Abdul Majid, wanda kana ganinshi kaga babban mutum, sai dai har yau yana nan babu sakewa kamar baya, ga shi nan dai amma yanayinshi zai nuna maka yadda yake jin babu dad'i a cikin mutane. Haka aka gama a hanyarsu ta komawa gida ne, Hajiya ta amshi takardarshi. "First class, Alhaji ka fito da shi amma baka farinciki." Yake yayi ya ce mata. "Ya Amaan yake?" Ajiyar zuciya tayi tana kallon Aryan da Jamilah da kowannensu yayi tsaki. "Yana lafiya." Ta fada tana son ta manta da abinda Amaan din yake mata. "Hammayo yaushe zaka dawo gida?" Shafa kan Anisah yayi yana faɗin. "Zan dawo." "Ka dawo ko Hamma Amaan zai daina saka Hajiya magana, shi ba karatun ba, shi ba aiki yake ba. Sai dai kullum a bashi kuɗi. Hajiya tayi magana har ta gaji " Bai ce mata kome ba, shi dai ba zai je Nijar ba, wallahi ko a kai za a kai shi ba zai je ba. "Hmm tayi hakuri ta cigaba da addu'a." "Ba zaka dawo gida ba!" Shiru yayi bai ce mata kome ba, zata kuma Magana Aryan ya ce mata. "Nisah ya isa haka, Hammayo ya gaji." Ya faɗa yana kallon Abdul Majid din, dake su sun iya turanci duk haka suka juya harshen turanci. A hankali Aryan yake tambayarshi me yasa ba zai dawo gida ba. "Kawai ba kome, zan tafi karatun sanin makaman aiki a Nijeriya ne " "Amma.". "bana son hayaniya don Allah." Hajiya tasan halin Yaranta, kowa da irin nashi hakurin, amma hakurin Majid daban ne, haka fushinsa daban ne kuma zai iya hakura da kome musamman idan akwai wulakanci da cin mutuncin. Haka suka iso gida, Innarsu kanwar Hajiya wato Kabo wacce aurenta ya mutu take gida dauke da karamar yarta mai suna Zaytoonah. Yarinyar suna shiri sosai da shi, yana shiga ta tare shi da kyaututtuka masu yawan gaske. Tana murmushi ta ce mishi." Hammana ina tayaka murnar kammala karatun ka!" Amsa yayi yana faɗin. "Na gode dear!" Daga haka suka wuce ta tsaya tana kallon Aryan da yake mata dariya. "Hamma Aryan dariyarka kamar gwalo kake min" "Tow Allah ya baƙi hakuri, ina Nabeeha?" Murmushi tayi ta ce mishi. "Ka bani cin hanci dai na kira maka ita." "Ok idan na shawo miki kan shi fa?" Murmushi tayi ta ce mishi. "Karya kenan domin kuwa zuciyarshi da kiyayya ta ginu, duk macen da zata samu damar kutsa kai cikin zuciyarshi mace mai Sa'a ce, mu shiga ciki zankirata." Shi kan Aryan tausayinta yake ji, duk da ba bata wuce sha uku ba, yarinyar tana da hankali da nutsuwa, kuma kowa yana musu kwadayin zama ma'aurata, domin ahalin Sheikh Aliyu Wodabbe, suna da nutsuwa da hankali uwa uba Ilimi idan Yaro yayi magana ba zaka dauka shi yayi ba, domin an samar mishi nutsuwa tuntuni. Bayan isha Nabeeha tazo suka sha hira, sannan ya rakata bangarensu, waye zai ce wannan haɗin bai mishi ba? Ai babu kaf gidan domin soyayyar da sukewa Sa'a na musamman ne, shi yasa suka dorawa Abdul Majid wata irin kauna. Bayan sati suka koma Nijar, suka cigaba da abinda yake gabansu. Shi kuma Abdul ya gama abinda zai yi ya dawo Nijeriya domin a can Nsukka yayi course ɗin shi na likitanci, wani ikon Allah sai gashi ya dace. Ana yaye shi aka tura shi asibitin Malam Aminu Kano, anan ya fara Internship ɗinshi. Yana tsaka da aikin ne aka fara diban sojojin sama. Yayi join amma suka ki amsarshi. Saboda wasu takardun shi, sau uku yana gwadawa amma baya samu karshe sai suka makale a bayan matsalarshi na cewa idan ya shiga damuwa zai iya kawo musu matsala a yanayin mental health din shi. Haka ya hakura da sojan sama, yayi apply na kasa shima ya makara, haka ya hakura wata shekara kamar wanda aka ingiza shi ya cika sojan ruwa, wani ikon Allah yana tura takadunshi, suka yi approved. Amma a lokacin suka bukaci suga iyayenshi, kamar ba zai je Nijar ba. Amma haka ya tafi wurin Alhaji Abubakar Abzin, ya gaya mishi. Shiru yayi sannan ya ce mishi. "Dole Mamman ya tsaya maka." "A'a ni bana bukatar taimakon shi, kawai kai ai ka wadatar." "A'a dole ya ga matsayin da ka taka, duk da nasan wata rana haka zai faru dole a bashi matsayinshi na uba." Haka Alhaji Abubakar Abzin ya tawo har Niamey, ya gayawa Alhaji Mamman Ba'are abinda yake faruwa. "Amma har na kusan gama.aikin asibitin yaron nan zai dauko wani zance?" Ya fada a harzuke, wai ma girma ya cimma shi. "Baka da iko akan karatun shi, lokacin da nake gaya maka ka janyo danka a jiki ki kayi, yanzu kuwa ya tsaya da kafaffunshi kace ya dawo jikinka, shi wancan da kake hidima dashi har yau babu cigaba jikinka ne?" Shiru yayi, Alhaji Abubakar Abzin ya mishi tass, haka yasa bayan kwanaki ya tawo har kano shi da Hajiya, duk yadda Hajiya taso ta janyo ra'ayinshi ya dawo ga asibiti ki yayi ya ce mata. "Babu dukiyata a cikin asibitin, ni nawa zan nima don Allah ki kyale ni na cika mafarkina." Alhaji Mamman Ba'are yana jin shi, amma bai ce kome ba dukiyarshi ce wato Majid yake kyama? Wani irin kuskure yayi ne haka? Lallai Majid shine magajin GOLDEN EMPIRES, shi daya zai rike da zuciya daya domin babu buri ko kwadayi a ranshi. "Zan biya ka miliyan goma duk wata kazo ka taya mahaifiyarka aiki." Juyawa yayi ya kalli Alhaji Mamman Ba'are, ya saki murmushi ya ce mishi. "A'a bana bukata na gode." "Abdul Majid ka manta da kome, ka dawo zan bar maka kamfanin BA'ARE GOLDEN EMPIRES " juyar da kai yayi yana murmushi. "Da kake gabar mutuwa ko? Hmmm wallahi idan na cire ahalina mahaifiyata da yan uwana har duniya ta nad'e bana fatan had'a alaka da dukiyarka, rayuwarka ka saka ka nimo dukiyarka nima rayuwata zan saka na nimo tawa. Hajiya ki gayawa Mijinki ya daina shiga rayuwata." Daga haka ya mike, ya nufi can wurin da aka saka water dispenser, ya dibi ruwan ya sha, sannan akan lokacin aka ce su shiga, koda suka shiga cikin dakin. Suka tattauna a lokacin da ake gaya musu sharudan aikin da sauransu, sannan sunan da yake jikin takardunshi yasa masu daukar sojoji a matakin farko yasa yake son ganin da gaske ne shi ɗin, family mahukuntan kasar nijar ne. Takaici yasa Majid cewa. "Sir ban nemi aiki a matsayin dan Mamman Ba'are ba, na nima ne a matsayina na dan Nijeriya kuma farar hula, bani da alaka da nijar." Juyawa hajiya tayi ta rufe mishi baki. "Me yasa baka jin magana ne?" Kwafa yayi cikin fushi ya ce. "Na fasa aikin ma." Ya juya zai fita, Alhaji Mamman Ba'are ya ce mishi. "Asibiti ko kamfani ina zaka yi aiki da su." A fusace ya juya zai magana Hajiya ta tsinke shi da mari, rike kunci yayi yana kallonta. "Wannan rayuwarka ce, va zan maka dole ka san daidai ba, amma ba zan matsa maka kayi aiki a ko daya daga cikin kamfanin Ba'are ba, ka tsaya akan ra'ayinka anji kai jinin ba'are ne, so what? Duniyarka zaka gina sai kayi fushi da damarka? Waye kai? Oya wuce kayi sign kai ba bawa bane, mutum ne mai ra'ayin kanshi don haka ka tafi aikinka Allah ya baka sa'a." Haka yasa shi amsar kome cikin dadin rai, Hajiya tana tare da shi bayan sun fito, Alhaji Mamman Ba'are ya ce mata. "kin nuna min bani da iko da d'ana kenan?" "Me yasa lokacin da yake bukatarka baka damu da shi ba? Sai yanzu da kasan iya shi zai iya rike sauran abubuwanka. Nima ajiye maka aikinka zan yi na gaji zan koma wurin dangina." A matukar tsorace yake kallonta, bayan Majid ya fito. "Kina nufin zaki juya min baya kenan?" "Hajiya muje!" Uffan bata ce mishi ba, haka suka tafi gidan da yake haya shi kuma Alhaji Mamman Ba'are ya wuce hotel, tunda ya isa can ya fadi rike da gefen kirjinshi, a kayanshi aka samu passport dinshi da hoton Majid da wasu abubuwan, haka aka wuce da shi asibiti. Sannan a nan suka shiga niman Abdul Majid a cikin asibitin, dakyar duka samo shi, koda ya zo kanshi bai wani girgiza ba, kawai dai ya tsaya duba wasu daga cikin tests din da aka bashi, anan suka yi magana da daya daga cikin likitocin. Ya ce mishi."Doctor kasan ya auna arziki?" Sosa kanshi yayi yana kallon Likita. "Ban gane ba?" "Hmm guba ne a cikin jininshi, wanda yayi yawan da." "Bar zancen haka, Allah ya bashi lafiya." Daga haka yaki yarda ya amince da sauran bayanan amma tabbas yasan abin da Alhaji Mamman Ba'are ya shuka shi ne zai girba. Ya je har gidan shi ya tawo da Hajiya ko ita bai yarda ya gaya mata ba, sai a bakin likitan taji. Wani irin tsoro ya cika mata zuciya. Tow Yaranta da suke can waye zai kare mata su. "kina tunanin su Anisah da Jamilah ko? Ai su ba za a musu kome ba, koda za'a yi sai don a kuntatta miki ta hanyar niman wani abu, amma ba wai don tab'a ki ba." Kwanan shi uku aka sallame shi, suka wuce nijar. Tunda suka koma jikin Alhaji Mamman Ba'are ya ki,asalima jinya ya kwanta inda aka kwantar da shi asibitin da ya ginawa Majid a can yake kwance. A hankali jinya tayi jinya domin ya kai sama da shekaru biyu a kwance, har wannan lokacin bakin shi bai daina kiran Majid ba, yazo ya yafe mishi. Dakyar Hajiya ta samo shi A Lagos yazo ya ganshi a ranar da yazo yake gayawa Lauyan shi. "Kuri'ata na barwa Abdul Majid Mamman Ba'are, akwai wasu kamfanoni na guda uku da asibiti duk da sunan Majid Mamman Ba'are na ajiye su, lauya ka rubuta a matsayin wasiyyar da na bari, Abdul Majid Mamman Ba'are, ka yafe min." Dauke kai yayi yana latsa wayarshi ya ce mishi. "ai ban kullace ka ba, don haka Allah ya baka lafiya " daga wannan ranar Majid ya bar Nijar dama kwana uku aka bashi, ya bar musu kome nasu kai ko ruwan gidansu baya sha, sannan ya gayawa Hajiya matukar ba ita zata yi girki ba, kada ta sake Yaran su ci abinci daga wani waje don kashe su za ayi. Daga lagos tura shi cotonou aka yi, a lokacin jikin Alhaji Mamman Ba'are ya kara rikicewa sannan ana ta nimanshi, a lokacin yana can teku Hajiya tayi sintiri ya kai sau uku. Babu labarinshi. Bata jima da dawowa ba, Allah ya amshi rayuwar Alhaji Mamman Ba'are, ya rasu ya bar wani irin tukekken rikici, domin bayan rasuwarsa, yan uwanshi da Hajiya Tani suka ce da kason su a cikin dukiyarshi.. sannan wasu suna jin haushin Majid domin gani suke saboda son da Alhaji Mamman Ba'are yake mishi ya mutu domin an ki fadar asalin abin da ya kashe Mamman Ba'are. Ana cikin wannan tashin hankalin har aka kai shi makwancinsa ana rikici. Bayan anyi Addu'ar bakwai sannan aka fara batun gado, domin sai da aka kira Alhaji Abubakar Abzin, sannan aka fara rabon matanshi da suka mishi takaba aka ware musu nasu, sannan aka koma kan Yaranshi mata da maza aka raba, wasa wasa sai ga Hajiya ta tashi da wani irin kaso saboda ita Yaranta maza ne, sai Hajiya Rabi da itama ta samu ba laifi amma ina gani ake kamar da gayya aka tulawa Hajiya Sa'adatu. A hankali Lauya ya fitar da kuri'ar kowa ya bashi, da sunanshi sannan ya cire na Alhaji Mamman Ba'are ya ajiye a gabansu. Wannan na Abdul Majid Mamman Abdul Majid ba'are ne, har aka gama raba kome ba a kira sunan Tani ba, nan tayi tsalle ta ce musu. "Shi Sajjid bai da kaso ne?" "Saurin me kike? Akwai kamfanin da take shigo da man fetur kasar nan, ita ce Alhaji Mamman ba'are ya bashi gashi nan." Ya tura mata. "Ban gane ba asibiti da mattan man fetur da ya gina fa?" "Mallakar Majid Mamman Ba'are ne?" Sakin baki tayi tana kallon kowa. "Sajjid shima fa jinin shi ne." "Ta ina ya zama jininsa? Mamman Ba'are yana da yara talatin da biyar, biyar din kai sune Yaran Sa'adatu, sauran ashirin Yaran, Rabi, Fauziya, Harirah. Yaran rabi goma sha daya, Hajiya Fauziya goma sha biyu, ashirin da uku sun tafi, Yaran Harirah bakwai da dan karami auta. Lissafi ya fito?" "Eh!" "Tow bamu ji labarin ya kuma aure ba, domin ko Sa'adatu da ya aureta ya faɗa ke kuma a ina kuka yi auren?" "Bai gaya muku Ni dadiron shi ba ne?" "Eh koma meye Muslunci ba zata bawa danki gadon shi ba, domin duk wanda suka ci gado ya halatta a gare su." "Ban gane ba?" "Su aure ya basu uba, ke kuma dadiro kuka yi aka same shi, ba dan shi ba ne danki ne ke ɗaya " Wani irin abu taji ya dake ta, tun daga ranar ta hana kanta sukuni ta saka masifa da bala'i a ranta, ta hada kai da wannan ta hada kai da wannan burinsu ace za a sake raba gadon, sannan har bincikan jini sai da taso a ciro gawar Alhaji Mamman Ba'are ayi domin a halatta Sajjid Mamman Ba'are akan dan shi ne Amma abu yaci tura. Don haka ta samu mutanen gidan ta basu shawarar saka hannun jari a kamfanin idan kudinsu yafi na Hajiya da Yaranta yawa, sai su kwace kamfanin. Haka aka yi har Nana da take kan gangara ta zuba hannun jarinta.dukda dai tsufa ba shine mutuwa ba. Dake ana bada na Abdul Majid Hajiya ta zuba nashi bakiɗaya, sannan kamfanin sa biyu ana aiki ana tura kuɗin, asibiti ma haka, duk bayan wata sai ayi rigima a board meeting. Dakyar ake shayo kan rigimar, bayan shekara daya da rasuwa Alhaji Mamman Ba'are Aryan yayi aure ya auro Nabeeha, aka sha biki a lokacin Nana ta ce kada Hajiya ta kuma shiga harkar jikokinta har ta yanke hukunci bata gaya mata ba, ita da aka ciyo a caca. Dake sun san Aryan bai da kunya, tass yaje har sama wurin Nana yace mata. "Hammayo bai wurgo ki ba, wallahi kika kuma shiga harkarmu sai na turo ki daga sama." Ya janyota har bakin matakalar. "Sake ni mara mutunci, idan kace na fita Harkar uwarka zan fita ba sai ka kashe ni ba." Tun daga lokacin suka samu salama. *** Bayan shekaru biyu da rasuwar Alhaji Mamman Ba'are, kamar wanda aka mishi kiranye, kuma ai kusan haka ne domin Hajiya ta hana idanunta barci akan Yaranta. Addu'a ba dare ba rana ga kome ta samu amma kuma kan Yaranta a watse, sannan a wannan lokacin ita ce me yara kanana, sannan tana cikin wani irin tashin hankali Sajjid ya saka Anisah a gaba. Ta rasa me yake nufi da ita, tayi mishi magana ya ce ta sa a dakatar da shi, da ta gayawa Amaan budar bakinshi ya ce mata. "Hajiya ki saka idanu akan Yaranki mata, kada kina can kina niman kudi da barci wasu su lalata musu rayuwa " sai da ta shiga tsakaninsu domin dambe suka so yi da Aryan abin ya mishi ciwo. Wata laraba kwatsam sai ga Majid, lokacin Sajjid ya biyo Anisah wacce ta fito wanka daga ita sai towel, tana ihun niman ceto sai dariya ake mata, shi kuma da abokanshi sai ihu suke. Ranar da kayan shi na aiki ya shigo yaga yadda Sajjid yake kokarin jan towel din. Jan get din gidan yayi ya rufe, sannan ya dauki wani dutse ya jefi Sajjid din sai da ya fadi can gefe. Juyawa tayi ta hango Hammayo, da gudu ta rike towel din ta nufe shi. Rungumeta yayi yana faɗin. "ya isa haka." Ya janye ta, tare da cire rigar jikinshi na kakin soja ya saka mata. "Wuce part din Hajiya!" A tsorace ta wuce, wato ba zaka san soja wala imani ba, sai da bawan Allah nan ya rufe idanu yayi ta zane su da duk abinda ya zo hannunshi. Ya kwabe Sajjid zigidir ya mishi dukar kawo wuka, Hajiya Tani zubewa tayi tana faɗin. "Idan ka kyale shi wallahi ba zai kuma kulata ba." "Tani ni bana son ya daina kulata, don Allah ya kulata ni zan kula da lamarinshi." "Nana ki bashi hakuri don Allah ya yafe mishi ba zai kuma ba." Wato dukar da Majid yayiwa Sajjid yasa baki daya kowa ya shafawa kanshi ruwan sanyi, domin Hajiya ta haifi zaki, shima kuma Sajjid ko ba a ce mishi ya fita harkarta ba, ba zai kuma shiga harkar nata ba. Don haka ya rufawa kanshi asiri bayan ya kyale shi, ya koma part dinsu, ya same ta ta saka kaya. Tana takure a wuri guda sai kuka take. "Me yasa baki tafi makaranta ba?" "Bani da lafiya ne!" "Kina da saurayi?" Gyada kai tayi, "Jamilah fa?" Tana da shi." "Kice mishi yazo ya samu Alhaji ayi magana" domin bai san Alhaji ya rasu ba, kuka ta kara sosai sannan ta gaya masa Alhaji ya rasu ana niman shekaru uku kenan. Jikin shi yayi sanyi. Amma kuma sai bai nuna ba, sakata yayi a gaba suka tafi kamfanin, a can suka bude farinciki, bai gayawa Hajiya kome ba domin ya gargad'eta kada ta faɗa. Daga kamfani gida suka dawo da ake gaya masa abubuwan da aka bar mishi. "Ni dai na yafe dukiyar Mamman Ba'are" "Baka isa ba!" Haka suka dawo gidan. Kallon gidan yayi sannan ya cewa Aryan. "Gidan a warewa kowa wurinshi baka san me wani yake yi ba haka zai saka kowa ya zauna lafiya babu saka ido ko cin zarafi. A cikin dukiyar da ya bari a ware part din hajiya a zagaye shi ina son ayi aikin nan da kwanaki arba'in." "Tow ina Hajiyar zata?" "Zata wuce garinsu, hutu na samu na wata biyu, don haka tafiya zamu yi sannan ka samu me niman Jamilah da Aneesah, su nufi Agadaz, su nime aurensu." A gaban Hajiya aka yi kome, wani abu da Hajiya tayi ta karawa kanta kima shine, dangin Alhaji Mamman Ba'are, bata yarda ta ki su ba, binsu take har inda suke take takai har Hajiya Latifah mahaifiyar Mohan(Bororoji) tana zumunci da ita, sannan yana zuwa wurin Hajiya Umamata mahaifiyar Khalil Dan Ba'are,. Haka yasa suka tura su wurin Ibrahim Dan Ba'are, mahaifin Khalil Dan Ba'are. Bayan masu niman auren sun gabatar da kome daga can, Aka kira Aryan aka gaya mishi an kai har da sadaki, ya ce tow ya gayawa Abdul Majid. Daga nan garinsu Hajiya. Basu bi tanka Amaan ba, suka yi tafiyarsu domin Hajiya ta gaya mishi, ya ce ba zai je ko ina ba, wato Amaan shine matsalar dakin Hajiya munafiki. Duk da uzurin da Hajiya take mishi baya gani. Watan su daya da rabi suka dawo an gama gyaran gidan har an zuba kome na gidan, daga cikin gidan zaka shiga asalin cikin gidan baki daya, shi dai Majid ya ware layinsu baki ɗaya don abin da yake faruwa babu wanda ya shiga musu. Bai bar kasar ba sai da aka yi bikin kannenshi, sannan ya saka Aryan ya dawo da Matarshi kusa da Hajiya inda shima ya cire flat me kyau aka mata, suka zauna lokacin tana goyan d'anta Abdul. Tunda ya bar kasar bai kuma waiwayonta ba, tsawon shekaru shida. A wannan shekarun babu ranar da Hajiya ba zata tafi niman shi ba, ko tasa a nima mata shi ba, sai gashi wannan karon Aryan ya dauko mata shi a kai. Wannan shine labarin Hajiya da Yaranta. ------------- Mu dawo labari. ------------- Sansanin Yan gudun hijira.. Wato kun san meke faruwa a cikin sansanin gudun hijirar da muke kuwa? Hmmm wato wani murdadden al'amari ne, adamawan Kamaru tana iyaka da Nijeriya da nijar ta yamma, sannan ana smuggling na kwayoyi safara da yara da mata, wasu ana tura su cikin kamarun, wasu kuma a tura kasashen Afrika da turai. Sannan babban wani abun mamaki ta hannun Uwar mugu ake wannan aikin, sannan asalin miyagun kwayoyi da makamai, ana shigowa da sune ta nan ana shiga da shi Nijeriya da nijar. ---- Kwana muka yi muna hira da Zuzu da Ummi Addah bata dawo ba, sai wurin asuba ta dawo tana kuka wiwi. "Addah lafiya!"shigowa da Munaisah aka ayi dakin kamar bata da lafiya ko taci duka. "Allah yayiwa Nenne rasuwa?" Tashi zaune mukayi. Murmushi Ummi tayi ta ce mata. "Hankalinku ya kwanta " "Me kike nufi? Babu kowa a wurinta sai Munaisah naje domin na tayata zama ne!" "Ya isa Addah" inji Zuzu, wallahi duk sun saka ni cikin duhu. "ina gawar?" "Tana can ana mata sutura" nida Zuzu muka fita, Ummi ta kalli Munaisah ta ce mata. "Daga nan karatun daya ce har birnin lantsandaal, kin biyewa Addah kun kashe Mahaifiyarki, ki rubuta ki ajiye. Addah sai ta ci amanarki wallahi kuwa sai ta saka ki kuka lokacin babu Zahra da zuzu, matukar zata sayar da Yarta ke din banza ce ba zata iya miki butulci ba. Na tausaya miki matuka gayya." Tun bayan an yi jana'izar aka kaita makwancinta, da zamu koma Balali ya kirani ya ce min."don Allah ina son magana dake." "Ok me ya faru?" "Ki saka idanu akan matar da take dakinku da ita wancan me cikin." Hadiye yawu nayi, na ce mishi. "Lafiya kace haka?" "Kiyi hakuri anan sansanin tunda wancan gayen yazo tow wallahi numfashin ki ma da zai saya tow tabbas zai saya ya samu kuɗi." "Me zan iya yi?" D'ago kai yayi ya ce min. "Jeki zan baki sako!" Haka na juya na tafi sai lokacin na lura ashe Uwar mugu ya gani. A hankali muka hadu da ita ta ce min. " Me yake gaya miki?" Murmushi nayi nace mata. "Ta'aziya yake min." "Bayan nan bai ce wani abu?" Girgiza kai nayi nace mata. "Haba bai ce kome ba!" "Zahra'u kenan! Mu shiga ki karya." Girgiza mata kai nayi ina faɗin. "A'a na koshi." "Muje mana, ko an gaya miki wani abu ne?" Ganin tana son daura zarginta akan Balali yasa ni binta har dakinta, muka zauna ta shiga zuba min abinci da kayan ciye-ciye. Duk abinda ta zuba min sai da na raba biyu tana kallona, tana gamawa na ce mata. "Muci tare." "Kin xata zan saka miki guba ce?" Girgiza kai nayi nace mata."ko daya kawai muci tare wannan zan kaiwa Zuzuna." "Tow muci" haka muka ci tare da ita, sannan na mike ta kara min abincin. "Kina da wani irin kyau, kiyi amfani da kyan nan mana." Girgiza kai nayi nace mata. "ai kyauwa na muni ne ga wancan abin" "Kina son zuzu ko????????? " 🤔🙄Me ya kawo irin wannan tambayar... Jama'a me uwar Mugu take nufi. #Thedambuje [2/19, 12:21 PM] Cutie cutie pie: *BAƘIN HAURE....🐾🐾* {Greed for Money is the roots of all evils🫀} Arewabooks:maidambu41 Wattpad:Mai_Dambu Mallakar:Mai_Dambu Assalamu alaikum barkanmu da warhaka da fatan kuna cikin koshin lafiya, karku manta da wannan Kamfani mai albarka mai kawo muku kayan bukata cikin sauki da Aminci da Inganci. Wato TA RASULU MULTIPURPOSE. YA SAKE DAWO MUKU DA KAYAN NAN MASU ARMASHI DA DANDANON KOWACCE MACE TAURARUWA CE. _______________________ MARKADADDIYAR GYAD'A HADADDEN KAYAN SHAYI GARIN KOSAI NA TAFI DA GIDANKA. GARIN TUWO GARIN KUNU YAR ASALI CURRY ME DADI SPICES TYME YAJIN DADDAWA ME KYAU GARIN DAN WAKE JAN YAJI MAI DAD'I... _____________________ BUGU DA KARI MUN TANADAR MUKU DA KAYAN FITAR SALLAH DA NA SHAGALIN SUNA DA BUKUKUWA. ATAMFOFI, LESHINA, MATERIAL, SHADODDI, YADUDDUKA NA MAZA DA NA MATA, JAKKUNA DA TAKALMA. WANI ABIN SAI KUN ZO TA RASULU MULTIPURPOSE DOMIN KASHE KWARKWATAN IDANU. ZAKU IYA TUNTUƁARMU A WADANNAN NUMBOBIN.. 08086639163 - 09030168590.... MUNA DAKON SAYAN DAI-DAI KO SARI..... *018* "Na'am me kike ce?" Na kalleta cikin son fahimtar me take nufi, murmushi tayi tana kallona. "Kawai naga yadda kike damuwa da ita ce ko mahaifiyarta bata damu da ita haka ba, kin ga wannan wuri da kike kowa ta kanshi yake, ki ajiye wata Zuzu ki kama Harkar gabanki yafi miki." "Ban damu da ko waye bai damu da zuzu ba, amma ni a raina na damu da zuzu. Sannan ba zan dauki wani ya dora ni akan hanyar da ba zata bulle min ba,, idan Addah ta gadama ta kula da rayuwar Yarta idan bata gadama ba, ta barta tai yadda take so. Ke da ita baku isa tilasta ni yin abin da ban shirya ba, idan kuma kina ganin zaki iya Bismillah. Har karshen rayuwata ba zan daina tsayawa a bayan zuzu ba kin ji na gaya miki sai ki san nayi." Daga haka na juya tare da barin mata dakin ko abincin ban dauka ba. "Abincin da kika bar min fa?" Ban juyo ba, na ce mata. "Kece idan baki ci ba zaki mutu, ni kuwa ko banci ba zan rayu matukar Allah shine rayayyen nan da baya mutuwa." Sannan na sa kai zan fita, ta kuma ce min. "Kada ki d'aga kafarki domin zan iya aikata kome." Juyawa nayi na kalle ta dariya nayi nace mata. "Ni ban san tsoro ba, ki gaya min taya zan san tsoro bayan akan idona aka kashe min dangina? Gaya min tsawarki bai wuce haushin dan kwaikwayo ba. Ni gurnanin fitar rai naji kin ga kenan babu abin da zai bani tsoro bayan nasan ina raye ne ko na mutu don Allah, ko a kashe ni don niman duniya." Daga haka na bar mata gidan, Yana kwance yana jin duk abinda suke fada, a ina aka samu yarinya me zuciya haka, Aina'u ya kalla da take ta sharar bacci, ya mike zaune yana mika, kirjinshi cike da gargasa ya dauki dogon wandonshi ya saka. Ya fito inda Uwar mugu take zaune tana mamakin maganganun Zahrah. " A ina kika samo jar wuya haka?" "Yan gudun hijira ne da suka taso daga Nijeriya, za akai su sansanin gudun hijirar hadin gwiwa da na Nijeriya yaranmu suka karkato mana da su nan, Yaran jiya da ka gani duk daga can suke." Shafa kanshi yayi yana faɗin. "Yarinyar ta iya jefa citta a bakin mutane, ban tab'a jin yarinyar da ta gaya miki gaskiya haka ba." Sosa kanta tayi tana murmushi ta ce mishi. "Eh ai bata da kunya ko kaɗan. Haka yar Ubanta take fama da ita, taurin kai ne da ita kamar arnan dutse." "Nawa aka samu domin ina son wucewa da shi kafin lokaci ya kure min." Sunkuyar da kai tayi tana faɗin. "Ba a wani samu dayawa ba, amma zaka iya zuwa wurin ajiyar zaka ga iya wanda muka samu." Gyada kai yayi yana faɗin. "Duk bayan wata shida nake zuwa amma ace iya wanda na samu kenan? Babu waɗanda suke jinya ne?" Kasa tayi da murya tana faɗin. "Allah ya baka hakuri, akwai Aina'u anan!" Shiru yayi kafin ya ce mata. "A nemo min nan da sati xan wuce na gaya miki." "In sha Allah, amma akwai yaron nan Balali da Dilla ya kawo mana shi, yana son ballo mana ruwa." "Ki saka a kawo min shi naji hujjarshi na lalata min dagiya ta." "Yarinyar da ta fita suna tare." "Nace a dauko min shi, ita kuma a tadata tabar min daki kafin fushina ya sauka har kanta." Da sauri ta nufi dakin ta tada ta, suka fito domin idan ya fadi haka rashin Imanin shi ya motsa kenan. Tana fita ta nufi kofar da su Balali suke aiki, ta ce. "Ku rufe kofar nan." " Tow!" A take suka rufe ta ce musu."ku kama min dan iskan cen ku kaiwa yallabai." Bai gudu ba, ya tsaya suka kama shi har gidanta, ajiye shi aka yi gaban shi. Kanshi a sunkuye. "Kai me ya haɗaka da yan matan da suke wannan sansanin?" "Ayi hakuri yallabai ba zan sake ba." "Hmmmm ba zaka sake kula su ba ko ba zaka sake wani abu ya fita daga bakin ka ba." "Dukka biyu yallabai." Gyada kai yayi yana faɗin. "Idanuna yana kanka, nan da sati biyu zan bar nan ka sake wani abu ya faru." Wata ƙatuwar wuka ya ciro, yana wasa da ita kafin ya ce mishi. "Da shi zan kashe ka." "In sha Allah, ba zaka kara kama ni da wani laifi ba." Haka ya bada hakuri sannan aka kyale shi, wani abin mamaki murmushi mutumin yayi bayan ya fita. "Me yasa baka kashe shi ba?" "Akwai abin da na karanta shi me dabi'ar Dilla ne bada hakuri akan kuskure wanda ya aikata da wanda bai aikata ba, wannan yaron dila ne. Kin san dai wannan wurin an gina shine da ra'ayin mutane mabanbanta, shi kin san aikinshi da abinda yake so, ni kin san aikina da abinda nake so, idan na ce zan kashe shi. Zan lalata goma daya bata gyaru ba, madadin na kama shi sai nayi rashin sa'a. Dilla baya shan ruwa haka kawai sai da wutsiyar shi, idan har zai ajiye wani abu nashi tow duk yadda akayi ina iya jiyo kamshinsa domin yana nan kaɗan damu." "Kana nufin yana kusa kenan?" "Kin san waye Dilla?" Girgiza kai tayi ya ce mata. "Dilla ita ce dabbar da bata kwana a ko ina sai a tsakiyar busashen ganye, domin ko fara ne ya fada kan ganyen zata farka, Dilla bata kamuwa ta dadi sai da tarko. Don haka maharba basu iya kamata sai sun saka mata tarko." "Tarko kuma?" "Eh tarko ita ba a kamata da nama, ko abinci duk abinda tasan baya samuwa a daji bata cin shi, tarkon dilla na musamman ne domin raga ake watsa mata." "Na gamsu Yallabai, amma taya zamu iya kama shi?" "Ai shi baya buƙatar tarko."."ban fahimta ba?" Mikewa yayi ya nufi dakin, ya watsa ruwa ya fito yana me zama ya ci abinci, bai kara magana ba kuma ita Uwar mugu tana son jin shirin Yallabai akan Dilla ne, tasan su basa shiri amma kuma bata zata al'amarin zai kai har haka ba. ----- Lokacin da na iso tantin mu, tsayawa nayi a waje ina jin shewar Munaisah da Addah, d'aga labulen nayi muka yi ido biyu da ita, gimtse dariyar tayi tana faɗin. "Allah sarki Nennena." " Ba sai kin yi min wasan kwaikwayo ba!" Na fada ina kallonta, shiru tayi tana kallona. "Wacce ta tsare miki gaba ta tafi, sai me? Daga nan sai ki daura daga inda aka tsaya." Na fahimci abu daya, daga Addah har Munaisah babu ruwansu matukar kudi zai zo musu wallahi zasu bada kome suka mallaka, kai hatta rayuwarsu da zasu iya sallama ta, tow kuwa zasu samu kudi da ita. Sannan wani abin mamaki shine kudin nan gashi nan amma ban san me suke da su ba, zuzu tana kwance nace mata. "Yan mata kina jin yunwa ko?" "Jiranki nake ai ki zo kaina, Zahra'u yunwa nake ji." Mikewa nayi na hada wuta, sannan na yan yanka kayan miya, na soya shi sama sama." "Zahra'u a saka kifi!" Duba wurin kayan nayi naga babu kifi."Zuzu bari na amso mana kifin!" Na karbi jakar kudina na dauki abinda nake da bukata, na fito waje. Gidan Uwar mugu na nufa, har na isa ban hadu da kowa ba, sannan kowani tanti shiru ya dauka, buga kofar nayi, ta bude. "Zahra'u me ya dawo dake?" "Kifi nazo saya." " Kin ga kuwa jiya da daddare Addah ta kawo min shi na bata kuɗi!" "Ta kyautawa kanta!" Na mika mata kudin iya wanda nake so, ina jin Muryar shi me cike da Amo ya ce mata. "A maida mata wanda aka kawo a sayar a hada mata da kayan abincin." "An gama Yallabai!" "Kuma kada ki sake ki kara amsar kayan kowa inji ni!". "Tow yallabai, maza ki mishi godiya." Ta ce min, "iya na kudina nazo saya." Na fada ina juya fuskata. "Ba zaki mishi godiya ba!" "Ni ba rokonshi nayi ba, shi yayi niyya kuma nace bana so dole ne?" Na fada Ina kallonta. "Yallabai!" "Bata abin da take so!" Ya fada yana me juyowa yana kallona, nima kallonshi nayi na dauke kaina. Ban san yadda zan muku bayanin yadda yake ba, amma Kyakyawa ne dai-dai misali, sannan yana da sura irinta sadaukan maza. Amma abu daya da kwakwalwata taki mantawa shine yanayin surar Aminin duhu, har yau ina jin haka a raina. Domin kirjinshi a wani murde yake, tsokokin da suka cika kwanjin shi kadai abin burgewa ne. Dafe kaina nayi sakamakon jin kaina yana wani irin kuwwa. Sai yau na tuna da shi sosai, duk da zuciyata bata samu zarafin hasasho min shi ba, sai yau. "Baki da lafiya ne?" D'ago kai nayi na kalle shi, kafin na dauke kai ina amsar kayan hannunshi. "Mai kyau!" Ya faɗa kamar rad'a. Juyawa nayi na bar wurin, ko ina da kyau Allah ya min tsari da hada shirgi da wannan abin kamar dodo. "Amma kada ki sake fitowa, domin tsarina ne." Shiru nayi ban ce kome ba, domin kuwa ba zan iya cewa komen ba, don naga yadda sansanin yayi kamar an yi shara. Haka yana nufin yana da karfin faɗa aji, ina isa tantin mu na ce musu. "Ashe yau ba a fita?" Sai lokacin Addah ta ce min. "Eh an gaya min jiya doka ce idan yana nan ba a fita." "Kuma Adda sai kika barta ta fita?" Zuzu ta mike dakyar cikin takaici. "Waye ya sani ko an shirya haka ne don a dauke Zahra din tunda yanzu anyi walkiya kowa yasan kowa." "Allah ya tsare mana ita." Inji Zuzu, ina ga cikin nan ya karawa Zuzu masifa, domin faɗa tayi ta cigaba da yi, tana hararar Addah. "Na gaya miki ban da fada." "Ke kyale ni nayi magana, me aka yi aka yi son zuciya." "Tow Allah ya baki hakuri!" Daga haka na tafasa mana taliyar da miya, na zubama kowa zan zauna uwar mugu ta shigo ita da Balali. Ajiye mana kayan yayi ya juya ya fita. "Daga yau kada wani ya kara kawo mana kayan Abincinsa." "Hmmmm!" "Inji yallabai ne, ba inji ba!" "Tow ai bin na gaba bin Allah, ina zamu samu wannan kayan dadin naga har da madara." "Na Zahra'u ce, ba na ku bane." "Ikon Allah Zahrah an fara dan waken zaga ye ne?" "Ita ba haka take ba, domin har yau bata dagula kuruciyarta da sabon Allah ba " inji Ummi tana tattara kayan, wato na fahimci a dakinmu akwai wani irin yaƙi dake tsakanin Ummi da Addah, tsakanin Adda da Zuzu, sai suka saka ni a tsakiya, duk yadda aka kawo min duka zasu kare min, "kinji dadi Zahra sai ki saka idanu akan yan uwanki. Domin kada su kawo mana hayaniya." Ta fada tana kallon Zuzu da Ummi da Munaisah da addah, ban san me yasa take yawan gaya min haka ba. "Na yarda da yan uwana, don haka ba zan sakawa kowa idanu ba. Kawai duk abinda kika ga ya faru tun can rubutacciyar al'amari ne." "Gaskiya kan!" Inji Addah tana kasa da kanta, domin wani lokaci idan addah tayi wani abu yadda kasan mutuniyar kirki. Fita tayi ta barmu a wurin, na zauna naci abinci nima, Haka muka ci muka koshi,bamu fita ba sai can yamma da aka ce mana zamu iya fita wanka, Zuzu da Ummi da Addah suka tafi, ya rage daga ni sai Munaisah, yadda bata ce min kome ba nima kuma ban saka ran xan yi mata magana ba, yadda take rayuwarta cikin nutsuwarta ba zaka ce uwarta ta mutu a ranar ba, domin ta warware kamar ba ita ba. Lashe bakina nayi ina gyarawa Yakumbo kwanciyar ta. "Zahra'u!" Na juya a hankali ina kallonta. A hankali ta matso kusa dani. "Don Allah idan kin samu damar fita daga nan, ki nemi wannan number please Zahrah." Cike da Mamaki nake kallonta. "Murmushi tayi tana faɗin. "Zan fita mana, zan tafi nesa dake idan ina ganinki zan iya aikata mugun abu akan ki. A wannan wurin ba uwa ba d'a, kowa ta kanshi yake kuma zaka iya aikata kome saboda kuɗi. Fatana daya ki fita daga nan sansanin domin ba sansani ba ne, wuri ne na biyan buƙatar kai." Baki daya sai ta kara min rud'ani, sama da wanda nake ciki ina muka kawo kanmu? Ina muke raye? "Munaisah me yasa ba zaki min bayani a nutse na fahimta ba?" "Idan na miki ma ba zaki gane ba!" Muna zaune a wurin har su Addah suka dawo, Nima da ita muka fita, muka je wurin wankan, baki daya sai na kasa wanka na saba sai dare nake wanka,.don haka na juya ina faɗin. "Ke bani iya wanka sai dare yayi." "Tow ai shikenan, ki je abinki." Haka na dawo na barta a hanya na hadu da Aina'u. "Naji ance yallabai ya tura miki da abinci, tow wallahi na rantse da Allah ba zan dauka ba, itama wancan me kama da zabiyar sai naci B... Ubanta, domin ba zata kwace min masoyi ba, shegu Mayun kudi. Ki saka idanu ki ga abinda zai faru." Rab'ewa nayi na wuce ina xan iya da haushin ta, don haka na koma tanti na kwanta. "Baki yi wankan ba!" "Wurin cike yake da mutane ba zan iya wanka a gabansu ba." "Kuma dai!" Inji Addah. Haka na kwanta muka yi ta hira har lokacin sallah yayi, sai lokacin Munaisah ta dawo. Kusan ma rikota akayi . "Me ya faru?" "Ita da Aina'u suka yi faɗa suka fada wuri me zurfi, ita kan ba a same ta ba. Sai Munaisah aka samu." Hadiye yawu nayi cike da tsoro domin nasan karshen mu yazo. Ihun Tumba muka ji tana faɗin. "Wayyo Allah na, kun kashe min fitilar dake haska min gabana wayyo Allah ka dawo min da Yarinya ta. Me tayi muku." Yadda take ihu yasa kowa jikinshi yayi sanyi. "Me ya haɗa ku?" Kuka ta saka tana faɗin. "Ita ta tura ni wurin zurfi, kuma wallahi ban san cewa idan muka fada ba zata iya fitowa ba. Wallahi ban kashe ta ba" "Hakkin uwa wasa ne?" "Ummi ki daina kawo maganar Nennena a cikin wannan yanayin, don Allah." Bakiɗaya sai na rasa bakin magana, d'ago kai nayi naga Addah tana murmushi, ban san me take nufi ba, amma tabbas murmushin mugunta ce zallah. "Addah me akayi kike murmushi?" Na tambaye ta, ganin yadda ta firgita. Sauran ma duk suka zuba mata idanu ta ce mana. "Ni kuma? Akan me zan yi farin ciki da abinda ya faru." Bata rufe baki ba, sai ga wasu manyan karti, sun zo sun ɗauki Munaisah. "Wallahi bani na kashe ta ba." Haka suka tafi da ita, wurin Uwar mugu na tafi ina.buga mata kofa dakyar ta bude, zubewa nayi akan gwiwata. "Na yarda ki saka ni na aikata kome don Allah ban da Munaisah. " Na fada cikin matsanancin damuwa da tashin hankalin. Ƙarar fitar wasu manyan motoci irin na gidan yari Uwar mugu ta ce min. "Ai na gaya miki, ki kula da danginki. Me kike so ki sani? Ta amshi kudinta ta kuma kai inda ya dace, idan da rabo zaku ƙara ganawa, don sun tafi da yallabai." "Sun tafi kin ga motar da ta fita sune, ba yau yaso tafiya ba, amma saboda samun dami akala yasa shi tafiya. Ki kula da mai cikin nan, domin idanun Addah kada ya tsaya akanta." Ji nayi kamar an hura min wuta a kirjina, dakyar na mike na nufi tantin mu, ina shiga na zube a wurin suma nayi mutuwa nayi Allah masani. Ni dai gani nan domin sai da gari yayi haske na farka, a hankali na tashi zaune babu sallar Magariba da Isha, ga ta asuban ban samu ba. Tashi zaune nayi ina kallon dakin, Zuzu ce zaune sai Ummi da take jikin Yakumbo, tashi nayi da gaske na kalli wurin Munaisah babu ita babu labarinta. "Bata dawo ba ko?" "Kiyi sallah ki ci abinci, babu abinda yasan inda aka kaita addah ma tun jiya ta fita bata dawo ba." Inji Zuzu. "Zuzu ki kula da Addah." Mika min ruwa tayi, na fita nayi alola na dawo nayi salolin da suke kaina. "Ina son nayi kuka Zuzu." "Ai kuka rahama ce idan kin samu kiyi Zahra'una." Kasa magana nayi ina kallon yadda kome ya lalace mana, "zuzu cikinki wata shida ko?" Juyawa tayi ta kalle ni, sannan ta gyada kai tana ajiye min abinci. "Ga kunu nan ki sha." Wasa wasa tafiya da Munaisah ya xama.kamar tarihi domin babu ita babu labarinta babu labarin b'atar Aina'u abin da ya kusan tab'a kan Tumba kenan,. Addah kuwa facaka take da kudi son ranta. A hankali lokaci yayi ta tafiya sama da yadda ba'a tunani, wata biyu kenan da tafiya da da Munaisah tana raye kuwa? Ta mutu ne?Allah shi kadai ya barwa kasan sani. Muna cikin wata na biyu cib da tafiyarsu, haihuwa ta tasowa Zuzu da yamma haka aka nufi asibitin da yaƙe cikin sansanin, da ni da Addah haka muka isa asibitin da ita, tun yamma take abu ɗaya. Ina jin muryarta har na daina jin muryarta. Hankalina ya tashi domin uwar mugu tazo har sau biyu ana faɗin bata haihu ba. Sai yanzu naji ban yarda da kowa ba har Addah itama ban yarda da ita ba, ina tsaye Balali yazo ya ke tambayata. "Ya take?". "Alhamdulillahi tana ciki." Shiru yayi kafin ya ce min. "ban san waye ya dace ki taimakawa ba, uwar ko jaririn tana haihuwa zan muku wani abu da zaku bar nan ku tafi can ku rayu nan ba zasu barku ba. Yawan abincin da kuke ci yawan rayuwarku da kuke wasa dasu hatta kanki kada ki yarda da shi."......... Shahararu goma aduniyan kayan mata wato m zee kamshi kayan mata kenan inakuke matan kwairai manyan Mata fah bamuna mataba Mata masu aji Wanda tasan kanta agidan mijinta kozokuyi gyara masu kyau da inganci Wanda zaisa oga nishadi yasashi farinciki atare dake kayanmu wane yaro sai uban yaro kinsha zumar makalemata dare daya wanka goma wanan set ne na kayan kwairai akwai fati budurwa mumuna da aeki Dan miyau malaka to shu,Umar Zuma zumar kiba gari kiba Zuma me lakani ningi tsumin lahaula hadin miski ba ahira dawando garin me kabara kasa ruwa sama ruwa wanan magani ba ,a magana magani sanyi mekyu maza da Mata ci da kaza ci da cicibin vlp yan shila ci da kifi nama kayan sakiba na gida danawaje munadakaya kala kala fani kamshi munada shu uwar humra namu ba irin nasubane akwai turare 24 hr turare kabasa Dana gida masu Dadi gakyau ga kamshi 08063845136 (Wash na gaji wallahi!) #thedambuje [2/20, 4:26 PM] Cutie cutie pie: *BAƘIN HAURE....🐾🐾* {Greed for Money is the roots of all evils🫀} Arewabooks:maidambu41 Wattpad:Mai_Dambu Mallakar:Mai_Dambu Assalamu alaikum barkanmu da warhaka da fatan kuna cikin koshin lafiya, karku manta da wannan Kamfani mai albarka mai kawo muku kayan bukata cikin sauki da Aminci da Inganci. Wato TA RASULU MULTIPURPOSE. YA SAKE DAWO MUKU DA KAYAN NAN MASU ARMASHI DA DANDANON KOWACCE MACE TAURARUWA CE. _______________________ MARKADADDIYAR GYAD'A HADADDEN KAYAN SHAYI GARIN KOSAI NA TAFI DA GIDANKA. GARIN TUWO GARIN KUNU YAR ASALI CURRY ME DADI SPICES TYME YAJIN DADDAWA ME KYAU GARIN DAN WAKE JAN YAJI MAI DAD'I... _____________________ BUGU DA KARI MUN TANADAR MUKU DA KAYAN FITAR SALLAH DA NA SHAGALIN SUNA DA BUKUKUWA. ATAMFOFI, LESHINA, MATERIAL, SHADODDI, YADUDDUKA NA MAZA DA NA MATA, JAKKUNA DA TAKALMA. WANI ABIN SAI KUN ZO TA RASULU MULTIPURPOSE DOMIN KASHE KWARKWATAN IDANU. ZAKU IYA TUNTUƁARMU A WADANNAN NUMBOBIN.. 08086639163 - 09030168590.... MUNA DAKON SAYAN DAI-DAI KO SARI..... *019* _Wani lokaci kana son ace farin ciki da nutsuwa sun wanzu a bisa fuskarka. Sai dai kuma bai zama dole sai haka ya faru ba, matuƙar zaka yi fafutukar rayuwa da mutuwa tow dole kayi adabo da dariya sai dai wani sauyin idan tazo maka babu yadda ka iya_ Cikin farinciki muka shiga rige-rigen shiga dakin, ana shiryata. "Ku bamu waje!" Malaman jinya suka ce. "A'a Zahra'u zo nan!" Yadda tayi kiran suna na yasa na isa wurinta, "dauke ta!" "Wai macen ce da gaske!" Na fada cikin zumud'i ban lura da halin da take ciki ba. "Mace ce Zahra'u, kada ki manta da alƙawarin mu." Ta faɗa hawaye na zubo mata. "Zuzu kada ki fadi haka, ai alƙawari gaskiya ce ba zan tab'a barin amanar da na dauka ba" kallon juna muka yi, naga zufa na karyo mata, "Zuzu kina lafiya!" Kallon Addah tayi tana murmushi. "Ki ajiye a ranki ko inuwar Y'ata kika rab'a sai bala'i da masifa sun zagaye ki." Juyawa nayi ina kallon Addah da babu wani ko dar a fuskarta sai murmushi. "Allah ya baki lafiya Zulai!" Yunkurin tashi take amma ta kasa, haka ta kalle ni hawaye na zuba mata ta ce min . "Ki bar sansanin nan, don Allah ko don abin da na haifa ki tafi wani wurin ki rayu don Allah." Hadiye yawun bakina nayi ina kallonta, "Maman Baby ina zan tafi?" "Ki je ko ina kawai ki tafi inda zata rayu don Allah, idan ba haka ba ita da Ummi kasa ku zasu yi a tire." Juyawa nayi ina kallon Addah jikina kamar mazari. "Ko da yake ba zaki gane illar da matar nan tayi ba ko? Tow shi kenan don Allah ki tafi kada ki ajiye Babyn tafi da ita ki kawo min ruwan zafi." "Ba zaku bani Babyn ba?" Addah ta tambaye mu, kamar zata yi kuka ta ce mana. "Kuna zargina tun ba yau ba. Ni fa na haife ki, na dauki renon cikinki amma bakya raga min." "Zahra'u ajiye min Babyn nan a kusa dani, ki taimaka min na tashi zaune."haka na saka mata babyn a gefenta na d'aga ta zaune tana kallon Addah ba zan iya gane kallon kiyayya ce ko tausayi ba, amma tabbas kallon yana da nasaba da b'acin rai. "Dauki yar ki tafi ina jiranki yunwa nake ji " wannan shine karon farko da Zulaihah ta nime na basu wuri a tarihin rayauwarmu da ita, duk abinda zata fada ko tayi kai tsaye take yi a gabana. Ina fita ta ce mata. "Me kike so bayan rayuwata" zama tayi tana washe mata baki. "Ki bani rikon Yarki ba zan neman kudi da ita ba." Murmushi tayi tana kallon Addah. "Ko jikina kunne ne ba zan yarda ba, na haramta miki ita koda." "Zulaihah kenan, idan na gayawa Zahra ce kin ta bata maganin zubar ruwan nono ya zaku kwashe? Ko na gaya mata cewa da bariki zaki shiga niman kudi ya zata ɗauka?" Wani irin rawa jikin Zulaihah ya ɗauka, tana kallon addah hawaye na zuba mata. "Addah me yasa zaki min haka? Me yasa karfi da yaji kike son lalata rayuwar Zahrah? Meye tayi miki? Na zata idan wani zai dauko wuka domin ya kashe zahran ke me kare ta ne ashe ke ce kike dab'a mata wuka ta baya me yasa sai ita? Gaskiya Allah ba zai barki ba, hakkin mu ya ishe ki duniya da lahira." "Yarki zaki bani!" "Har abada ba zan baki Y'ata ba, Zahra ce zata riketa. Na san Ummi zata gaya mata gaskiya amma na fi son koda zata tsane ni ke ta fara tsanarki na har abada." "Ai kuwa zata bani ita domin na sayar da ita, kamar yadda na sayar da ke har mahaifanki domin kada ki sake haihuwa." "Addaaaah" ta kira sunan da karfi, "me na miki?" "Baki min kome ba, Yarki zaki bani." "Kin dauki kasonki Yarinya ko bayan raina ne diyar Zahra ce, don haka duk abinda zaki yi kiyi." Tafa hannunta tayi, sai ga wasu kartin maza sun shigo, haka suka kama Zuzu suka mata allura sannan suka kyaleta. A hankali ta kalli Addah, "da ke da Ummi kun sayar da Munaisah, bayan kun kashe Nenne. Yau ni kika sayar Addah matukar na rayu wallahi sai na farauce ki kamar yadda mafarauci ke farautar dabba." Harshen ta ne yayi mata nauyi daga nan bata kara magana ba, tana kallo suka rufa mata farin mayafi. --- Lokacin da na isa tantin mu, dauke da Babyn sai da Ummi ta mike tana leka yarinyar. "Yarinya tafi Zuzu kyau!" "Wallahi kuwa!" Na fada, ina mika mata babyn. "Ummi Khair!" D'ago kai tayi tana kallona. Idanunmu ya haɗe da juna. "Me kuke aikatawa da Addah?" Murmushi tayi a hankali ta juya min baya, tana fadin. "Addah dai ni ina yi ne domin kare rayuwar mahaifiyata, duk lokacin da zata dauka zan so ta rayu koda ba zata yi magana ba, ba zata motsa ba ina son mahaifiyata." "Ina kuka kai Munaisah?" "Munaisah ta fiki gata, ta tafi inda zata samu nutsuwa ne, matukar tana tare da ke zata iya daukar zugar Addah ta kashe ki." "Ummi ban gane ba?" "Ba zaki gane ba, amma anan inda muke rayuwa ba zata yiwu ba sai da cin amana, sai da zalunci, sai da cutarwa ko ita Zuzu ai ta cutar dake ta hanyar da ba zaki tab'a yafe mata ba. Shi yasa don ki yafe mata idan kika samu labarin ta baki yarta ba zaki ji labarin nan kusa ba, kina da sauran lokaci ki je ki ji daga bakinta me ta aikata miki, Mother Teresa!" Ta fada tana mika min babyn, sake rungumar Babyn nayi zan fita. "Zuciyarki tana da kyau sosai Zahrah, kina da adalci sosai shi yasa ba zan iya cutar dake ba, amma kowa kika ga baki ganshi ba adalci yayiwa kanshi domin akan kuɗi zasu aikata kome infact har dani zan iya kome abu daya yasa na kasa cutar dake Yakumbo", ta kalleta tana murmushi. "Amma idan ta nice yadda ake bani kudi domin na sayar da kowa kina nufin ba zan iya ba ne? Yakumbo ta yarda da cewa wata rana ke haske ce ga rayuwata." Kunsan me ake kira da gudun ceton rai? Shi nake son nayi ko zan cimma manufarsu a kaina, don haka na sa kai na fita da gudu domin titsiye Zuzu ta gaya min wacce irin cutarwa tayi min, gabana faduwa yake ina ji kamar ana mai dani baya, duk yunkurin gudun da nake hakan amma ina kome ya lalace daga lokacin da na bar Zuzu. Koda na isa na samu an fito da gawarta ne. Haki nake ina kallon Addah kafin na kalli gawar zuzu. Da sauri na nufi kan gawar, rike ni Addah tayi tare da faɗin. "Mutane nawa ne kike son su mutu domin ki? Me yasa lallai sai kowa ya sadaukar da rayuwarshi domin ki? Me yasa lallai sai kowa ya rasa ranshi dominki? Zahra'u na rasa Y'ata dominki don haka ki bani jikata." Kasa magana nayi ina jin jikina yana rawa. "Ad.....!" "Dan uwana ya rasa rayuwarshi domin ke? Na rasa zuri'ata domin ke? Na rasa kowa don ke. Anya Zahrah ke mutum ce? Yanzu ma na rasa Zulaihah saboda ke." Kai na ne ya fara sarawa a hankali na isa gaban Zulaihah. "Ki tashi ki gaya mata ba don ni kika mutu ba, gaya mata ban san kome akan kowa ba. Me yasa?" Na fada da karfi, "Me yasa na zama masifa ga ahalina?" Na fada da karfi ban san yadda aka yi ba, kuka ne ya kwace min kuka nake wanda tunda nake a rayuwata ban tab'a jin shi ba. Kuka nake cikin tsannanin takaici da b'acin rai. Kiri-kiri Addah ta daura min alhakin mutuwar Zulaihah. "Taso muje!" Uwar mugu ta riko hannuna, ina tafiya ina kuka har tantinta. Murmushi tayi tana zaune tana kallon yadda nake kuka. "Da Alamu kukanki ba yau kika tara shi ba. Don haka kiyi abinki, kiyi ko zaki samu nutsuwa." Nayi kuka har sai da Babyn ta fara kukan niman abinci, nan hankalina ya dawo jikina. Na dauke ta cikin rawan jiki zan fita ta ce min. "Ga madarar jarirai nan ki bata!" Ta ajiye min formula na yara, karba nayi xan fita ta ce min. "Ki daina kukan haka, zab'an rayuwar suka yi, ke kuma kina da sa'a shi yasa ba zaki gane ba." A fusace na ce mata. "Shi yasa kuke bibiyarmu kuna hada mu faɗa da tsanar juna? Me muka yi muku haka?" Na tambaye ta hawaye na zubo min, "ba fa haka ba ne?" "Haka ne mana, haka ne mana me yasa tun fil azal baku gaya mana cewa nan sansanin mutuwa ce ba ta yan gudun hijira ba? Ki sani kunyi kuskure in sha Allah karshen ku yazo wallahi azim sai Allah ya wargaza wannan wurin ki saka idanu ki kalli yadda kome zai zama tarihi." Na juya na fita ko madarar ban dauka ba, muna zuwa tantin na samu Ummi tana barci. Zama nayi bayan nayi sallama da disasshen muryata, na zauna ina son nayi magana amma bakinciki ya hanani, bamu kara jin duriyar Addah ba. Zama nayi na fashe da kuka yarinyar ma kuka take. "Ki bata nono idan ta ja ruwa zai sauka." Na kalli Ummi a mamakance. "Kin tuna kunun da Zulaihah take baki?" Kafin ta karasa na dakatar da ita. "Ba sai kin gaya min ba, zuciyata ciwo take." A hankali na bude nonon zan saka mata ta ce min."dakata!" Tashi tayi ta dauko wani garin magani ta zuba a wani bojuwa ta wanke nonon dashi, sannan ta ce min. "Bata." A hankali na saka mata nonon a baki, sai da tayi ta niman bakin nonon kafin ta fara alamar tana jan ruwa. Kuka ne ya kara kwace min ina ji kamar xan mutu kafin rana ta sake bud'ewa. Wani irin ciwo nake ji mai zafi a kirjina. Ban san yaushe xan daina kuka ba. Haka na rungumeta har ta fara jan ruwan. Wato kunun da Zuzu take bani maganin kawo ruwan nono ne? Wani irin murmushi ne ya kwace min ba na kome ba sai na bakinciki, ina ji ina gani kowa ya mai da ni sakarya ko nace sokuwa. Sun mai dani doluwa. Munaisah ta tafi Zuzu ta tafi. Haka na cigaba da zama har aka kira sallah na tashi nayi, sannan na saka yarinyar a gaba ina kallonta. "Zahra'u ba amata wanka ba" "eh " na fada, tashi tayi ta haɗa ruwan zafi, yana zafi ta dauko bawo ta fara mata wanka, tana yi tana kallon yadda yarinyar take nishi wato rashin wanka yasa jikinta yayi tsami. Ina tuna abin da ya faru zan sake kuka musamman idan na tuna mutuwar Baffa sai naji kamar zuciyata zata fito don ciwo da zafi. "Zahrah kukan ya isa haka man" " duk tsawon wannan lokacin Zuzu wato har ta san yadda zata bani abu naci domin na biya mata buƙatar ta? Ummi me yasa kuka min haka?" Murmushi tayi tana fadin "tow me yasa ba zamu miki haka ba? Ke fa mahaifiyarki yar babban gida ce, Zahrah ke fa kina da sa'a wallahi." "Wani irin sa'a!" Na fada da karfi me yasa suke cewa ina da sa'a, Sa'a ko masifa. "Da ciwo idan ka fahimci wanda ka yarda da shi ya ci amanarka. Zuzu bata mutu ba tana raye sai dai kece yadace ki mutu ki bar wannan duniyar idan ba haka ba bakincikin addah ya ishe ki, Addah tayi alkawarin sai ta hana ƙaddarar sa'arki bayyana, ta kuma rantse ko zata muku sai ta yanke duk wanda zai bude miki fukafiki domin ki tserewa ukubar ta." "Me na mata? Me na tsare mata." "Ba zata tab'a morarki a yanzu ba, ita kuma idan ba zata more ki ba, ba zata barki ki huta ba, sannan Yarta da ta haifa ta zaɓe ki sama da ita gayan kin san yadda take ji kuwa? Kin san ciwon da take ji kuwa? Shi yasa idan aka kawo mata tayin kudi take karba don ke, don ta ga baya ki kafin ki samu daukakar da ake gaya mata zaki yi, Zahra daga zuwan mu nan hotunanki kawai manyan mutane suka saka kudi akanki, ita kuma Uwar mugu bata tilastawa mutum karbar Kudi sai da ra'ayinka, kaf sansanin nan kece kawai Uwar mugu take sararawa. Muna ji muna gani mun zama kamar saniyar ware ba tare da kin sani ba. Sau uku ana saka caca akanki kawai, amma Allah yake tseratar dake. Muna cikin duniyar da ko yaya kudi ya shigo yafi dan uwanka gaya min laifi ne don kowa ya bar jikinki bayan kowa ya san cewa matukar kika rabe shi ba zai cigaba ba, sai dai ya manne a jikinki dukkansu biyu sun haye saboda ke. Mun fito jini daya, amma nasararki ko yaya mutum ya ambaci sunanki a cikin abu sai yayi Sa'a ki fara niman mafaka kafin a fahimci karfin tauraronki, kafin Addah ta yi bincike na fara kafin Addah ta kai sunanki wurin Malamai Zahra ni na fara. Tauraronki ko a sararin samaniya ne ƙarfin shi yafi na sauran. Don haka ki kula da inda zaki rayu duk wanda ya fahimci haka tow ba ke ba, hatta Baby rayuwarta zata zama abin tausayi ne." Wani uban ihu na fasa ina kuka ina faɗin. "Ni tsinuwa ce? Bani da albarka ne?" Hawaye ne ya zubo mata. "Ko daya baki da alaka da tsinuwa" "Bakar ƙaddara ce dani?" "Haskenki ne yayi yawa, idan har tafiya ta kama ki da mutane dayawa zaki gane haka, mu nan baki dayan mu hassadarki muke." Ta Fada min ido da ido. Wato jin wannan kalmar yasa ni baki daya na dauke wuta sai hawaye. Kunsan yadda na shiga rud'ani, me yasa ban gane hakan ba? Me yasa na rufe idanuna ban san inda nake rayuwa ba? Bata kuma bi ta kaina ba. Haka ta mata wanka tass, sannan ta dauki wani ruwa mai dumi ta fara gasa mata cibiya, sai ga yarinya kafin a gama tayi barci. Kayan da nake ta ajiyar shi na haihuwa shi na dauko na shiga dubawa na mikawa Ummi da take gasa mata cibiya da garwashi, mika min ita tayi bayan ta gama mata, amsarta nayi na saka mata kaya tayi kyau kuwa. Sannan na gyara wurin kwanciya muka kwanta, amma barci ya gagare ni . Haka na raba dare ina gadinmu baki daya, domin gani nake matukar na kwanta zan wayi gari Babu Baby, haka na kwana ina kuka. Wurin asuba na fara jin barci, baby kuwa barci take abinta, tashi nayi na gabatar da sallah, Ummi ma haka. **** Niamey. Wurin motsa jiki ya nufa, yana motsa jikinshi, kamar daga sama abin ya fado mishi. Ajiye ƙarfen yayi ya dauki wayarshi bayan ya dauki ruwa ya sha, kan wayar ya shiga ya fara niman cantact din mutanen naija, da gudu aka bangaje shi wayar ta fadi can. Cike da Mamaki ya juya yana kallon waye haka. Kyakyawar yarinya ce tsaye rike da kugunta wata mata tana me shigowa wurin tana faɗin. "Feeyah ki tsaya kawai na duba wallahi babu wani jimawa." Sunkuyawa yayi ya dauki wayarshi. "Hammayo!" Bai saurari kiran da tayi ba, yayi ficewarshi yana kallon yadda fuskar wayar ta zama damage, karamin tsaki yayi. "Bazai yi aiki ba?!" Dayan ta tambayeta, murmushi tayi mai sanyi. "Zai yi aiki mana saka idanu kiyi kallo!" Shi kan fashewar wayar ta sha mishi kai, yana fitowa falon ya samu Hajiya ya zauna yana kallon tv Aryan yayi matashi da cinyar Hajiya. "Kai dai an yi katon banza." Ya fada yana cilla mishi wayar. "Hammana me yasamu wayar kuma?" Tsaki yayi ya cigaba da kallon tv, sai ga yan matan sun fito kamar munafukai. "Mune muka fasa mishi wayar." Ta fada kamar zata fashe da kuka. "Haukar banza kenan, Afiyyah wani irin wawanci ne haka?" Aryan ya tambaye ta a fusace, "kayi hakuri Hamma Aryan!" "Kai ya isa" ya faɗa yana musu alama su tafi da hannu. "Mun gode sosai Hammayo!" Shiru yayi yana kallon tv. Suna fita Aryan yayi tsaki yana kallon Majid da yake kara kallon tv, "Hajiya kin ji labarin haihuwar Zaytoonah!" Aryan ya faɗa yana kallon yadda fuskar Majid din bai wani sauya ba, asalima ko a jikinshi. "Kasan labarin rasuwar mahaifinta ya kidimata shine ta haihu lokacin bai yi ba." "Ayya Allah ya jikanshi." "Amin!" Hajiya ta faɗa, "kuma naga laifin Inna tako, yarinyar nan tun tana yar mitsitsiya take son ganin Babanta, amma taki fisabilillahi." Juyawa suka yi suka tsare shi da idanu. Majid sai Allah sai yayi magana kamar bashi ya faɗa ba, "kasan hakan ne?" Juyowa yayi yana kallon Aryan kafin ya daura kafa daya kan daya. "Zamana a can tayi ta bin Inna tako amma taki karshe da na Uzra mata, kwad'a min mari tayi." Ya fada yana me shafa fuskarsa, don baya manta ranar da ta tsinka mishi mari kamar a film. Kura mishi idanu Hajiya tayi tana son jin karin bayani. "Hajiya ni ma ban wani san kome ba, kawai dai abin da na sani Inna Tako tayi fama da lalurar gushewar hankali kafin ta warke amma ta manta da kome." "Ikon Allah!" Mikewa yayi zai nufi dakin shi. "Gobe zamu marad'i." "Allah ya kai mu." Yana barin falon Amaan Mamman Ba'are yana shigowa a gajiye, zama yayi yana kallon Hajiya. "Lafiya Mai martaba?" Sosa kanshi yayi yana faɗin. "Hajiya dama." Mikewa Aryan yayi zai bar falon domin ya barsu kada yaji abin da zai rufe Amaan din da duka. "Ina jinka!" "Aron kudi zaki bani katin bankina Amirah ta karya." "Ina kudadenka suke?" Ta tambaye shi. Sosa kai yayi yana kallonta kamar zai fasa ihu. "Ina kudinka suke? Ni ba baiwarka ba ce kamata yayi a ce na huta sai dai na maka hidima saboda baka da kunya........ (Pool Zahrah 🥲😔) Shahararu goma aduniyan kayan mata wato m zee kamshi kayan mata kenan inakuke matan kwairai manyan Mata fah bamuna mataba Mata masu aji Wanda tasan kanta agidan mijinta kozokuyi gyara masu kyau da inganci Wanda zaisa oga nishadi yasashi farinciki atare dake kayanmu wane yaro sai uban yaro kinsha zumar makalemata dare daya wanka goma wanan set ne na kayan kwairai akwai fati budurwa mumuna da aeki Dan miyau malaka to shu,Umar Zuma zumar kiba gari kiba Zuma me lakani ningi tsumin lahaula hadin miski ba ahira dawando garin me kabara kasa ruwa sama ruwa wanan magani ba ,a magana magani sanyi mekyu maza da Mata ci da kaza ci da cicibin vlp yan shila ci da kifi nama kayan sakiba na gida danawaje munadakaya kala kala fani kamshi munada shu uwar humra namu ba irin nasubane akwai turare 24 hr turare kabasa Dana gida masu Dadi gakyau ga kamshi 08063845136 #Mai_Dambu [2/21, 5:17 PM] Cutie cutie pie: *BAƘIN HAURE....🐾🐾* {Greed for Money is the roots of all evils🫀} Arewabooks:maidambu41 Wattpad:Mai_Dambu Mallakar:Mai_Dambu _😡😏 A fusace da b'acin rai a fuskana nake cewa ya ishe ku🤣🙄 Cin mutuncin Addaririya kuje ta yafe muku✊🏻 tace ku daina bin ta da tsinuwa 😔🥲😂zata shiryu_ Assalamu alaikum barkanmu da warhaka da fatan kuna cikin koshin lafiya, karku manta da wannan Kamfani mai albarka mai kawo muku kayan bukata cikin sauki da Aminci da Inganci. Wato TA RASULU MULTIPURPOSE. YA SAKE DAWO MUKU DA KAYAN NAN MASU ARMASHI DA DANDANON KOWACCE MACE TAURARUWA CE. _______________________ MARKADADDIYAR GYAD'A HADADDEN KAYAN SHAYI GARIN KOSAI NA TAFI DA GIDANKA. GARIN TUWO GARIN KUNU YAR ASALI CURRY ME DADI SPICES TYME YAJIN DADDAWA ME KYAU GARIN DAN WAKE JAN YAJI MAI DAD'I... _____________________ BUGU DA KARI MUN TANADAR MUKU DA KAYAN FITAR SALLAH DA NA SHAGALIN SUNA DA BUKUKUWA. ATAMFOFI, LESHINA, MATERIAL, SHADODDI, YADUDDUKA NA MAZA DA NA MATA, JAKKUNA DA TAKALMA. WANI ABIN SAI KUN ZO TA RASULU MULTIPURPOSE DOMIN KASHE KWARKWATAN IDANU. ZAKU IYA TUNTUƁARMU A WADANNAN NUMBOBIN.. 08086639163 - 09030168590.... MUNA DAKON SAYAN DAI-DAI KO SARI..... *020* "Kai ko kunya baka ji ne? Ace kome nice zan maka. Dukkansu hudu kokari suke su kyautata min amma kai dayake baka da lissafi ka kwaso jiki kamar fulawar da aka watsa mata yeast kazo na baka kudina ko Amaan Mamman Ba'are." Wata irin kunya ce ta kama shi, "Hajiya don Allah." Tsuke fuska tayi tana harararshi. "Kowacce uwa tana iya kokarinta akan Yaranta, sannan iya kokarin da nake akan ku ko da ace aiki aka sani baku isa biyana ladar ba, domin iya ƙoƙarina nayi kuma ina kan yi, Amaan ni na haifeka amma ni nake kuka akanka kannenka ban yi kuka akansu ba, sai kai." Murmushin takaici tayi tana kallonshi kafin ta cigaba da cewa. "Su waɗanda ka ke kai musu sirrinmu basu baka kudine? Mara zuciya wanda lissafinshi daban da na kowa. " Yadda take fada har wajen gidan kowa yana jin ta, tabbas Hajiya ta fusata kuma takai bango. Robar ruwa Aryan ya fito da shi ya mika mata, ta amsa tana me kai bakinta. "Zaka iya tafiya Mr Mamman Ba'are!" Yau ko yar borin kunyar nan da yake yi na takalar Aryan bai yi ba. "Daga yau kada na kuma ganinka a kamfani bayan mun tashi, sannan wannan Bluetooth da ka saka musu shine na cire kwanankin baya. Amaan ka fita idanu ko na sallama musu kai." Subul subul ya fita, yadda kuka san (Gfresh Al-Ameen Kano state material, haka Amaan Mamman Ba'are yake🤣) haka ya fice abin shi, a harabar gidan ya hadu da Majid da Yaran Aryan suna wasa, sai ihu suke yana tayasu. Tsayawa yayi yana kallon yadda suke wasa cikin jin dadi da nutsuwa, me xai yi ya samawa Matarshi nutsuwa ne. Ba zai iya rayuwa babu ita ba, haka yasa shi juyawa ya fita kai tsaye bai tsaya ba sai can wajen gari, gidan Sajjid Mamman Ba'are. Ya shiga cikin gidan a harabar gidan ya ga motarshi tabbas yana gidan, zai shiga masu tsaron gidan suka hana shi dole ya zauna a harabar gidan ya jira shi. Har zuwa wani lokaci kafin Sajjid din ya fito da gajeren wando da yar singlet. Ya tsaya yana kallon Amaan Mamman Ba'are. Kafin suka kwashe da dariya tare da rungumar junansu. "Nayi kewarka Baby na!' inji Sajjid, "Nima haka My love!" *** camp *Idan har akwai wanda zai ci amanarka tow kada ka damu kowa, koda zasu haɗu baki daya su ci amanarka matukar ka yarda da Allah magana ta kare, amma wanda ka bawa yarda ya ci amanarka sai kaji kamar zaka mutu, zuciyarka ba zata yi jimirin daukar kowacce nauyi ba. Ina jin wani irin ciwo me zafi* Bude idanuna nayi ga babu kowa a cikin tantin mu, daga ni sai Baby. Kayan Addah ma babu babu kayansu Ummi, wani kar'ar fashewar abu naji, kafin na fara jin Ihun mutane da kukan Yara yana kusanto ni. Ƙarar harbe-harbe yana kusanto inda nake, bansan ya aka yi ba amma sai ganin tantin mu ya kama da wuta nayi, haka na sunkuci Baby na fita da gudu, kamar yadda kowa yake gudu haka nima nake gudu, gudun da ban san inda muke jefa kafar mu ba,mu dai gamu nan ana kad'a mu kamar wasu awakai. Mun yi tafiya me nisan gaske a cikin daji, babu ci babu sha tun daga wayewar gari har rana ta faɗi, sannan baka san waye a kusa da kai ba, shima kuma don rud'ani ba zai ce ya san waye kai ba, sai yau na kara jin kamar da mutuwa nayi da abinda Zuzu da sauran Yan uwana suka min,amma me yasa zuciyata taki yarda Zuzu zata yaudare ni. Duban Babyn nayi naga bata motsi. "Wayyo Allah na, Yarinyata bata motsi jama'a ku taimaka min kada ta mutu!" Ihun da nayi ta musu kenan ina cika musu kunne, hasko min torchlight aka yi na runtuma da gudu kamar mahaukaciya, na ce musu."ku duba min ta mutu ne!?" Na fada ina ihu. "Ke ki nutsu!" Aka daka min tsawa, amma ina baki daya kamar wacce aka toshe min kwakwala, haka nayi ta musu ihu da rokon su duba min yarinyar ko ta mutu. Can hasken wani dakin da aka kafa shi a dajin ya kunnu, fitowa yayi sanye da jallabiya. "Yallabai ka tafi zamu magance matsalar!" Yana zuwa ya amshi Babyn. Sannan ya juya da ita, "ina xaka da ita? Ina zaka kaimin Baby na! Bani ita ta mutu ne?" Fisgo ni yayi ya tura ni dakin tare da rage hasken dakin, dumin dakin ya kara sani shiga hankalina. Daukar wani torchlight yayi yana haskata, kafin yayi magana cikin wata irin murya me sanyi, duk da Muryar shi da take da matuƙar sanyi da dad'i haka bai saka na fahimci cewa dani yake magana ba, sai da ya kuma haska min torlight ɗin na ce mishi. "Kace ta mutu?" Ajiye fitilar yayi ya ce."yaushe aka haifeta?" "Jiya!" "Ina Mamanta?" "Gani nan!" Na nuna miishi kaina,kamar bai yarda da ba sai kuma ya koma kan yarinyar ya ce min. "Yaushe rabonta da shan nono?" "Jiya da daddare!" "Zo ki bata!" Ya faɗa min yana mika min ita, burina Baby ta rayu. Ciro mata nonon nayi na saka mata a baki bata amsa ba. "Bata karba ba" janyo wani kofi yayi ya matsa jikin wani irin murhu, ya kara kofin kafin wani lokaci yayi dumi, janye kofin yayi ya mika min yana faɗin. "Taimaka min ya huce!" Haka nayi ta hurawa har ya huce, sannan ya amsa ya saka mata a baki ruwan ya fara shiga bakinta, tana fara sha kuwa sai gashi ta kware, d'agota yayi yana shafa bayanta sakin baki nayi ina kallonsu, sai da ya gama dubata ya bani ita, na saka mata nono ai kuwa ta rike da sauri, zafin da ya ratsa bakin nonon da kaina yasa ni sakin yar ƙaramar ƙara. Bai kalle ni ba, amma kuma ya juya baya ya kwanta abinshi, har ta gama sha ya ce min. "idan kin fita kice Ado ya kai ki wurin Uwar mugu zata kula daku. A mata wanka a nad'e ta kafin gobe!" Fita nayi a bakin kofar na samu Ado. "Muje!" Ya ce min, har wurin Uwar mugu ya kaini, ya gaya mata sakonshi. A daren ya kafa mana tanti shi da wasu mazan, uwar mugu wanka tayiwa baby ta kara bata madara. "Ina Addah da Ummi?" Murmushi tayi ta ce min. "Suna lafiya a cikin wannan yanayin, sun zata kin mutu ne." Mika min ruwan zafi tayi na sha a hankali, har na gama sannan wani irin barci yayi gaba damu, daukar Baby tayi ta kai mishi. "Kika ce Nawwas ya sayar da uwar Jaririya?" Cikin tsannanin biyayya ta ce mishi. "Eh Sarki a dawa Sarki sarari. Ba iya uwar yarinyar ba, wannan bakar al'adar shin nan, ta sayar sassan jikin dan Adam yana nan bai daina ba, sannan akwai kanwar Babanta da take da bala'in son kudi." "Uwar yarinyar tana raye kenan?" "Eh amma an fitar da ita tun yammacin shekaranjiya."shiru yayi yana kallon Babyn. "Nawas babu imani a cikin lamarinshi." "Ba laifinshi bane kakar yarinyar ta bukaci haka." "Je ku kwanta." ------ Tafiya muke cikin koriyar ciyawa, ina gaba rike da Baby ina mata dariya, sai ji nayi kamar an hand'akani cikin wani rami me duhuwar gaske wanda bana iya hango farkon ramin ga Baby tana ta callara kara. "Ki rayu a wurin." Cikin wani irin kuka na ce. "Wurin akwai duhu bana ganin Baby." "Ki zauna a wurin haske zai zo miki." "Taimako!!!!" Da wannan Ihun taimakon na farka, naga Baby har an mata wanka an kara nad'e ta, babu kowa a dakin sai abinci da aka ajiye min, tashi nayi na fito waje. Naga an zubawa kofar tantina idanu ga mutane kowa ka gani a firgice yake. "Gimbiya ke ake jira!" Addah ta faɗa tana hararata. "Addah!" "A'a gatari ko guduma." Ta fada tana juya min.baya, Allah ya gani ina da rauni wurin Ibada, alola nayi na wuce ciki na gabatar da sallar da yake kaina sannan nayi na asuban yau da garin ya gama haske tas, sannan na koma dakin na goyi Baby a tsaye naci abincin na rikema addah sauran, don nasan bata samu kamar wannan ba, lokacin da na fito aka nad'e tantin, wato tunda na nufi wurin Addah na fahimci matar nan bata da mutunci, mika mata abincin nayi ta fauce. A can gabanmu na hango Ummi ban kula ta Addah ba, na tafi na same ta. "me yasa kika tafi kika barni." "Ba gashi kin same ni ba!" "Amma;" gyara goyon Yakumbo tayi tana me cigaba da tafiya, kafa babu takalmi sai lokacin na fahimci nima haka nake tafiya,ga tarin kayoyi. Kamar wasu shanu haka muke ratsa tafiyar cikin dazuzzuka da kwazazzabai. Babu abinci babu ruwa, "Ummi ko zaki kawo yakumbo ki rike min Baby!" A gajiye ta ce min. "Eh!" Haka na bata yar ni kuma na amshi Yakumbo, muka cigaba da tafiya muna ratsa hamada da kwazazzabai. Sai da yamma tayi likis aka tsaya, na ajiye Yakumbo, hawaye na zuba min domin Baby kuka take, tun daga taimakon farko da na samu ban kuma samu ba. Haka nayi ta jigila da Baby dakyar muka yi sallah, kuma baki daya haɗawa muka yi, Abin tambaya anan ina za a kai mu? Babu me amsar tambayar nan, sai dai a cikin tawagar maza naji ana bayanin wasu sun mutu. A hankali naji wani abu ya tokare min kirjina, ruwa da yar karamar busashen gurasa aka bimu da ita, mukaci muna lashe hannu, domin dai bai Ishe mu ba. Haka muka kwana cikin wani irin sanyi, muna tsaka da barci wata ta fasa ihu. "Wayyo Allah maciji ya sare ni!" Tashi kowa yayi zaune, aka fara haska torchlight, sai gashi nan wuluk, ya kara fasa kai zai kai wani saran daya daga cikin mutanen da suka fito ya samu ya harbe shi, sai da ya fasa mishi kai, matar ma bata haura minti biyar ba, ta fara shure-shure kumfa yana futa bakinta, kafin wani lokaci ta ce ga garinku. Cikin tsananin tsoro muka kara tattara kanmu wuri guda, haka aka bar gawar domin muna farkawa nan bamu kara kwanciya ba, sai tafiya haka muka yi ta ƙeta daji da kurmi. Lokaci zuwa lokaci uwar mugu tana amsar Baby ta gyarata, ta kawo min ita na bata Nono, sannan ta wuce da ita wurin Mutumin da ban kara ganin fuskar shi ba, haka aka cigaba da tafiya mutanen da muka tawo wasu suna mutuwa, wasu idan aka gaji a nan za abarka a cigaba da tafiya, babu tausayi babu imani, kowa ta kanshi yake sannan a wannan tafiyar akan abinci sai mutum ya kashe ka har lahira, wani abun da na fahimta wannan yanayin ya haifar mana da matukar yunwa, fushi, rashin imani, babu tausayi ko jin kai. Akan idanunka mutum zai fadi yana niman taimako, amma haka zaka tsallake shi kayi tafiyarka, idan aka zo rabon abinci kuwa tow sai an hada da bulala ko bakin bindiga, sai a nutsu a raba lafiya. Idan ka tsaya janjani wani zai fauce abunda aka baka, kuma ya ci kenan. A wannan lokacin babu abinda muka zama sai kamar zombies, domin idan ka bawa mutum haushi matukar babu masu lura a kusa zai shake maka wuya agaban mutane kuma babu ruwan kowa, godiyar Allah da Uwar Mugu tana bawa Baby madara, da asirina ya tonu. Domin wani irin bala'in yunwa da gajiya nake ji, gashi haka muke karbe-karbe da Yakumbo. A wannan tafiya wani lokaci Uwar mugu ta dauke yarinyar ba zata kawo ta ba, don ta ga wahalar ta mana yawa. Yau satin mu biyu muna tafiya a daji, babu me kuzari ko hankali a cikinmu, "Zahra!" "Na'am" "Yakumbo ta kara min nauyi ko zaki taimaka na sauke ta." "Tow." Na maida Baby baya, ina me gyara goyanta. Bayan na gyara na koma bayan Ummi, ina rukota ta koma jikina, ko ba agaya min mutuwa ba, zuwa yanzu na santa na san yadda take, na san yadda take daukar na kusa dani. "Khairat!" "Yakumbo ta rasu ko?" Tambayar da tayi min kenan, "eh Ummul Khair!" "Kuma itama yarda ita za ayi kamar sauran?" Kura mata idanu nayi, a hankali muka kwantar da ita, ana ta wuce mu. "Don Allah ki min wannan alfarmar, nasan mun ha'ince ki ki duba girman zumunci kada a yar da ita;" ta faɗa tana wani irin kuka me cin rai, nima hawaye ne yake zubo min wani na bin wani. Tashi nayi da gudu, ina ratsa mutane har na isa wurin babbar motar da take dauke da shugabansu, daukar dutse nayi na jefe motar, kusan babu wanda ya dakatar dani. Sai yan bindigar, sake tsinta wani dutsen nayi na kara bugawa motar, dole suka tsaya naje har gaban motar na tsaya. Hawaye na zuba min. "Ke kina son mutuwa ne?" "Gaya min inda mutuwar take naje na rungumeta, na kuma tambaye ta mai yasa tuntuni bata zo min ba, bayan dakonta nake ba dare ba rana." Na fada hawaye na zuba min. "Matsa ko mu bi ta kanki!" "Babu inda zani!" Na fada ina kara tsayawa dakyau. Daga cikin motar ake tambayarsu lafiya. "Yarinyar nan me jaririya ce, ta tsare mana hanya." "Me ya samu jaririyar!" Ya fada a gajiye, "bamu sani ba Yallabai bari a tambaye ta." Fitowa suka yi. "Ke bama son hauka, bamu hanya, wuce shi nayi na nufi inda ya fito na bude nace musu. "Ku gayawa mai gidanku Babata ta rasu ba za a yar min da gawarta ba ya fito ya sallaceta." "Zahra'u!" Muryar Uwar mugu ya ratsa kunne na, "kina hauka ne" "Daga turu na fito Uwar mugu, kuma wallahi idan baku mata sutura ba, sai kun ga tashin hankali da masifa da bala'i." Don dole aka tsayar da tafiyar, domin yadda na shafawa idanuna toka kowa yasan ba zan tab'a barin abin da na saka kaina ba, "Yallabai kayi hakuri." Hannu ya d'aga mata, "ina Babarki!" Nuna mishi can inda Ummi take durkushe tana risgar kuka nayi. Ban tsaya tantance waye shi ko fuskar shi ba, na dai san ya fito kuma ina gaba yana baya har zuwa inda gawar Yakumbo take, durkusawa yayi yana kallon yadda muka sakata a gaba, ni kan hawaye nake sharewa bana kuka. Shar-shar. "Uwar mugu ku mata sutura a sallace ta " ya fada yana barin wurin, "Addah da Tumba kuzo a gyara ta.", Haka suka gyara ta aka kafa musu mayafi suka mata wanka aka mata sutura tare da sallatarta. Sannan aka binne ta a dan can gefe da hanyar da muke, ina tsaye na kalli Ummi da take kuka, ina ga gara tayi kukan da ace bata yi ba, zai zama mata ciwo. Haka aka yi ta tafiya ana barin mu a ciki kuwa har da Addah, "Ummi muje kada mu rasa yadda zamu je." Sai da ta ƙara jimawa kafin ta mike, muka nufi hanya. Tana tafiya tana kuka, har suka mana nisa sosai sai ƙurarsu muke hangowa. "Ummi mu hanzarta mana!" Na fada ina diba a guje, kamar wacce aka sa mana gasar tsire. Gudu sosai muka yi, sai da muka yi da gaske sannan muka kamo su. Sauke Baby nayi naji tana shakuwa. Nono na saka mata a baki muna tafiya ina bata har muka isa cikin tawagar sannan abin dariya abin tashin hankali babu wanda ya ce mana ga inda zamu, kawai tafiya muke kamar wasu shanu. Tsayawa aka yi baki daya, suka juyo mana. "Ina son ku sani wannan karon kuna tsaka da rayuwa da mutuwa, anan inda zamu shiga ana samun guguwar sahara, sannan akwai kunamar sahara masu matukar hatsari, don haka ku kula wani lokaci idan ta kama zamu iya kwana a cikin saharan." Wannan masifar dame yayi kama? Na fada a raina, ina kara rungumar Babyna. Bakina dauke da ayatul kursiyu, haka muka shiga saharar zuciyata wata irin bugawa take, domin kuwa wani tsoron ne ya shigeni. Haka muka cigaba da tafiya sai da muka shiga tsakiyar mun bar inda muka fito da tazara me yawan gaske, sannan bamu isa inda zamu wuce ba,wata irin guguwa ta taso da wani azazzben karfi, tayi ta watsi da mutane. Ihu kawai kake ji tare da kukan Yara da mata. A take muka kara rikicewa, gashi ko gabanka baka gani, sannan wani abin da ya kara gigita mu shine yadda mutane ke fad'awa cikin sahara, wato idan guguwar ta kawo sura sai kasar ta zuke mutum. Na zata iya fim ake irin wannan abin sai gashi yau a kan idanuna ina ji ina gani mutuwa a cikin sahara tana kara kusanto mu, har wannan lokacin ina rungume da Baby, ban san me ya faru ba kawai sai ji nayi kamar....... Shahararu goma aduniyan kayan mata wato m zee kamshi kayan mata kenan inakuke matan kwairai manyan Mata fah bamuna mataba Mata masu aji Wanda tasan kanta agidan mijinta kozokuyi gyara masu kyau da inganci Wanda zaisa oga nishadi yasashi farinciki atare dake kayanmu wane yaro sai uban yaro kinsha zumar makalemata dare daya wanka goma wanan set ne na kayan kwairai akwai fati budurwa mumuna da aeki Dan miyau malaka to shu,Umar Zuma zumar kiba gari kiba Zuma me lakani ningi tsumin lahaula hadin miski ba ahira dawando garin me kabara kasa ruwa sama ruwa wanan magani ba ,a magana magani sanyi mekyu maza da Mata ci da kaza ci da cicibin vlp yan shila ci da kifi nama kayan sakiba na gida danawaje munadakaya kala kala fani kamshi munada shu uwar humra namu ba irin nasubane akwai turare 24 hr turare kabasa Dana gida masu Dadi gakyau ga kamshi 08063845136 🙄🤔 Hala Zahrah ko Baby daya zai mutu kafin a fita a sahara.....🥳🫀 #Mai_Dambu [2/22, 11:31 AM] Cutie cutie pie: *BAƘIN HAURE....🐾🐾* {Greed for Money is the roots of all evils🫀} Arewabooks:maidambu41 Wattpad:Mai_Dambu Mallakar:Mai_Dambu Assalamu alaikum barkanmu da warhaka da fatan kuna cikin koshin lafiya, karku manta da wannan Kamfani mai albarka mai kawo muku kayan bukata cikin sauki da Aminci da Inganci. Wato TA RASULU MULTIPURPOSE. YA SAKE DAWO MUKU DA KAYAN NAN MASU ARMASHI DA DANDANON KOWACCE MACE TAURARUWA CE. _______________________ MARKADADDIYAR GYAD'A HADADDEN KAYAN SHAYI GARIN KOSAI NA TAFI DA GIDANKA. GARIN TUWO GARIN KUNU YAR ASALI CURRY ME DADI SPICES TYME YAJIN DADDAWA ME KYAU GARIN DAN WAKE JAN YAJI MAI DAD'I... _____________________ BUGU DA KARI MUN TANADAR MUKU DA KAYAN FITAR SALLAH DA NA SHAGALIN SUNA DA BUKUKUWA. ATAMFOFI, LESHINA, MATERIAL, SHADODDI, YADUDDUKA NA MAZA DA NA MATA, JAKKUNA DA TAKALMA. WANI ABIN SAI KUN ZO TA RASULU MULTIPURPOSE DOMIN KASHE KWARKWATAN IDANU. ZAKU IYA TUNTUƁARMU A WADANNAN NUMBOBIN.. 08086639163 - 09030168590.... MUNA DAKON SAYAN DAI-DAI KO SARI..... *021* Ni dai ba zancen ga abinda ya faru ba, sai da gari yayi haske sannan muka fahimci dayawanmu, sun b'ata a sahara. Shafa baby nayi na ganta a bayana har lokacin, ajiyar zuciya na sauke tare da fara niman hanyar fita, a hankali nake tafiya ina niman Ummi ashe guguwar tayi gaba da ita can, mune yan baya da abin ya fi ritsawa da mu, don haka a hankali muka yi ta bayyana daya bayan daya, muka isa inda suke jiran mu, kafin wani lokaci mun sake haduwa sai dai ba dukkanmu aka kuma haduwa ba, wasu sun bace wasu kuma sai gawarwakinsu. Da sassarfa uwar mugu ta amshi Baby. "Da fatan babu abinda ya same ta?" Girgza kai nayi ina son tambayarta Addah. "Duk suna lafiya, karfin tsayawarmu anan kece, domin Yallabai yace ba zai bar nan ba, sai an samo mishi ke da Baby." Ta cigaba da duba yarinyar har wurin shi, amsarta yayi ya hure mata fuska saboda yan kuran da suke fuskarta. Haka muka cigaba da tafiya har sai da muka ji babu dad'i, domin wasu sun tafi, bamu tsaya ba sai da rana ta faɗi, a wani ƙaramin gari, tun kafin mu shiga garin na fahimci mutanen garin suna maraba da zuwanshi, garin dauke yake da kabilu biyu, hausa da fulani, domin ga alamu sune suka kafa garin. Sannan kowa ka gani yana da abin yi, ma'ana Babu wanda zaka gani yana zaune haka. Gaishe shi ake yana amsawa har muka bar cikin kauyen muka kara nausa daji, anan ne na fa kara yarda Allah daya gari Banban. Dajin da muka nufa gona ce ni nace lambu, babu irin shukar da babu a cikinshi, sannan akwai cigaban zamani. Lokacin da muka isa wucewa damu aka yi wasu gidajen da suke zagaye da wani gida can, gaba da gidanshi. Yanayin gidan kamar irin dakunan kwanan dalibai ne, gado da katifa har da bargo. Kwanciya muka yi barci yayi gaba damu. *** Niamey. Suna kwance wuri guda, hannunsu sarkafe da juna. Kana ganinsu kasan lovers ne na gayawa yan gari. "My heart meke damunka?" "Hmmm! Kudi naje hajiya ta bani ta hanani, raina a b'aci na zo nan." Shafa kanshi Sajjid yayi yana faɗin. "Kamar nawa?" Mikewa yayi yana faɗin. "A'a ka barshi zan tafi na sayar da motata." "Kana dani kace zaka sayar da motarka, baka yarda ina sonka ba ne? Kasan yadda iyayenmu suke gaba da juna amma kake tsammanin zan iya rayuwa babu kai? Ko wancan mutumin gidanku ba zan tab'a yafe mishi ba." "Idan na yafewa kowa, Majid ba zan yafe mishi ba, sai na saka shi biyan abinda ya aikata." Sai da Sajjid ya gama hasala Amaan Mamman Ba'are, sannan ya dauki kudi masu yawan gaske, ya bashi ya kai hannu fuskarshi. "Kayi hakuri nasan Aryan da Majid yan uwanka ne, amma ina matuƙar jin haushinsu, ina ta kokarin koyawa kaina dauke kai akansu amma na kasa. Ka gafarce ni." Sajjid ya faɗa kamar zaiyi kuka, a rikice Amaan ya rungume shi. "Zan taya ka lallubar hanyar da zamu ga bayansu." "Allah!" "Da gaske zan iya kome matukar zaka yi farinciki." Murmushi Sajjid yayi yana faɗin. "Ban yarda ba, don na baka kudi kake fadar haka." Mai da mishi kudin yayi yana faɗin. "Bana bukatar kuɗinka, lokaci zai nuna maka ina sonka ne don Allah ko kudinka." Murmushi Sajjid yayi yana juya idanu ya ce mishi. "Dauka ka tafi nasan kana sona ne don Allah, wasa nake maka." Ya fada yana cusa mishi kudin tare da mishi chakulkuli. Dariya suka saka bakiɗayansu. Sai da suka yi wanka sannan Sajjid ya raka Amaan har wurin Motarshi ya bar gidan, kiran Mahaifiyarshi yayi yana faɗin. "Jakin yaron nan ya faɗa fa!" Ajiyar zuciya Tani tayi ta ce mishi. "Ban yarda zai iya mana wani aiki ba, ka dawo haka ina son ganinka." "An gama!" Ya fada yana shafa ciwon da yake goshinsa. "Kada ka dauki lokaci." "Tow." Ajiye wayar yayi yana hararar shi, tabbas idan ya samu hali sai Hajiya Tani ta biya abinda ta aikata, ba ita ta haife shi ba ko ita ta halicce shi sai ya mata abinda ba zata manta da shi ba, kuma yanzu ma zai cigaba da mata biyayya. Tun yana Yaro take azabtar da rayuwarshi har girmanshi bai huta ba, yanzu ma don yana da abu me muhimmanci ne ya barta take raye. Yasan duk wannan fadi tashin da yake ba don kanshi yake ba, iya ita kanta yake mata, sannan shu'umar mace ce ta gaske da ba zata iya daukar rainin hankali ba, yasan ita ce ta haife shi, amma baya tunanin zata iya d'aga mishi kafa, idan ya mata kuskure shi yasa a duk lokacin da yayi kuskure da girman shi sai ta illata shi. Shi kuma a nashi tunanin yayi girman da dole ta daina dukarshi, domin yau da gobe ya wuce wasa, sannan ba zai cigaba da zuba mata idanu tana dukar shi ba. -- Washe gari. Hajiya ta hada kan Iyalanta zuwa Marad'i, har da Amaan yana Motarshi a baya, Hajiya da su Aryan suna mota daya, sai hira ake kamar yadda suka saba ana zolayar juna, Aryan ke tuka motar, shi yana zaune a gefen Aryan din, idanunshi rufe. *Ka taimaka min kada na mutu!* Bude idanunshi yayi yana kallon gefen hanya, tare da juyowa yana kallon su Hajiya da suke dariyar Widad, ta dage sai magana take tana mita. "Ya dai Hammayo?" "Babu kome." Tabbas yaji muryarta, amma kuma yasan don ya damu kanshi jiya da niman Umaimah bai samu number ta ba, asalima jiya har da mafarkin abinda ya faru, yana son ganin likitan da yake mishi therapy, lumshe idanun yayi cikin wata irin gajiya, domin baki daya yana jin wani sabon yanayi na kara kusanto shi, kara jingina yayi da motar, ya shafa fuskar wayar shi da aka sauya mata screen. A hankali ya gwada kiran Ammar. Ai kuwa yana shiga ya ƙara bude manyan idanunshi masu kyau da sheki. "Ammar ka nimo min number da zan samu Umaima." "Ok Sir ya kake ya hutun naka." "Alhamdulillahi! Sir sai muka ji labarin ba zaka dawo ba. Sir" "Zamu yi magana an jima;" ya fada yana kashe wayar. "Wai da gaske ba zaka koma Nijeriya ba?" Inji Aryan, "I ba zan koma ba " ya faɗa yana kauda kanshi,karar da wayarshi tayi ya sa shi duba screen din wayar. Shiga kan message din yayi ya tura mishi. "Thanks!" Sannan ya danna number, can sai gashi ta shiga. "Ya yarinyar nan take?" "Eyeeeee!" Bakiɗaya suka zuba mishi idanun suna jiran abin da zai fada, "ok please ki bincika ina son sanin yadda take." "Amma ya kamata kayi min sallama sannan ka gaishe ni!" "Kin ga bani da." "Yes nasan baka da lokacin gaisuwa. Nima na bincika last month an ce an samu crisis a garinsu." Cikin wani tsuke fuska ya ce mata. "I don't care Koda ace garin babu kowa, ki nima min information akanta. Domin ina son sanin yadda take ne." "But niman abu kake sai nake jin babu dad'i kamar kana saka ni lallai sai na maka abinda." "Ok taimaka min" ya faɗa a gajiye da kuma son maganar ya ƙare. "Shi kenan zan bincika in sha Allah." A hankali ya sauke wayar daga kunnenshi yana me fatan Allah yasa ba mutuwa tayi ta sanadin abinda ya farun nan ba, domin bai san me zai ce ba. Zufa ne ya shiga karyo mishi Aryan da Hajiya kuwa sun tsare shi da idanun suna son ƙarin bayani. Juyawa yayi ya ga yadda suka saki baki. "Wacece ita?" "Aaaah ba fa wani abu ba ne, kawai na mata treatment ne a gidana." Daga haka ya ja bakin shi shiru , duk yadda suka so yayi magana gum yayi da bakinshi. Zurfin ciki irin na Abdul Majid ai ya b'aci, ita kan Hajiya tayi mamakin yadda aka yi ya bukaci jin labarin wata. Tasan duk inda yake rayuwa bata taɓa jin labarin mace a tare da shi ba, duk da taso hada shi aure da Yar Kanwarta wato Zaytoonah, amma al'amarin yaƙi yiwuwa asalima tunda tayi mishi maganar aure bai kara yarda ya bada fuska ba, har suka isa marad'i bai ce uffan ba, itama bata kuma yarda tayi magana ba, sai da suka isa Gidan Alhaji Abubakar Abzin, dake ya tashi daga tsohuwar unguwar da suka san shi. Aryan kadai yasan unguwar da suka koma. Sun same shi a gida, Hajiya na bayan Aryan ita da matar Aryan da Yaranshi, Majid yana mota yana waya. Suka shiga cikin gidan, yana kallon Amaan Mamman Ba'are ya fito tare da Matarshi, da Yaranshi sai lokacin ya bude motar shima ya fito suka kalli juna. "Hammayo ina wuni!!" "Lafiya!" Ya faɗa, don ya lura matar Amaan bata da nutsuwa da tarbiyya, yaran ma gasu nan kamar su kamar uwarsu, an musu shigar diban albarka. Dauke kai Amaan yayi, hala yana jiran Majid ya gaishe shi. "Daada ina kwana!" Inji Amir. Daukar Yaron Majid yayi, yana ce mishi. "Lafiya lau Amir Ba'are." "Daada kafi Abbanmu kyau, kuma ka fishi kirki." Murmushi yayi yana kallon Amaan din. "Baya daukarka ne?" Girgiza kai yayi yana faɗin "Daada kana dariya shi kuma baya dariya." Murmushi ne ya kwace mishi yana kara rike Yaron, da sallama suka shiga babban falon gidan. "Daada nima ka ɗauke ni." Inji little Abdul. Ajiye Amir yayi ya dauke shi yana dariya. "Abdul Majid kannenka sun maka wayo kaga sun tara zuri'a saura kai." Murmushi Iya tayi tana kallon Abdul Majid, ta nuna shi da sandarta tana faɗin. "In sha Allah, Matarshi da uku-uku zata cika mishi iyali." Murmushi ne ya subucewa Hajiya, ta ce mishi. "Allahummah Amin, Iyah Allah ya yarda." Ta fada tana kallon Majid da yasa fuskar shanu. Wasa da hannun Abdul yake. "Captain Allah ya kawo mana kai kenan " murmushi yayi yana me sunkuyar da kanshi, "Eh Abba!" Kura mishi idanu Alhaji Abubakar Abzin yayi kafin ya ce. "Allah ya jikan Mamman da rahama! Ya yafe mishi kurakuransa." "Allahummah Amin" suka fada baki daya,. Abincin da aka kawo musu, suka ci bayan an basu wuri. Bayan sun gama Hajiya suka shiga cikin gidan yan mazan suka nufi masallaci, basu dawo ba sai da aka yi la'asar sannan suka shigo, anan aka kara gaisawa sannan aka bude shafin hira. Kafin, suna hirar karamin D'an Alhaji Abubakar Abzin ya shigo. Mahdi Abubakar Abzin, sosa kai yayi yana faɗin. "Abba kayi hakuri don Allah." "Taya zan cigaba da barinka a matsayin lauyana? Dole na nemo wani da zai cika min alƙawari." "Ka kara hakuri dai Abba! Nifa ba zance ka biya ni ba, duk Lauyan da zaka dauka sai ka biya shi kudi me yawa." Daure fuska Alhaji yaji ya ce mishi. "idan har bukata zata biya ai shikenan babu matsala sai inbiya, amma meye amfanin badi ba rai? Meye amfanin ka tunda bana biyanka jeka ka ajiye min aikina." "Alhaji ni zan nima maka wani lauyan." "Bana so ai Ni ba makaho ba ne." "Allah ya huci zuciyarka." Ya zauna yana dauko wasu jakakkuna ya ajiye, waya Alhaji Abubakar Abzin ya dauka yayi magana. Kafin ya ajiye. "Lauyan Mamman yana zuwa." Kallon shi Hajiya tayi sannan ta ce mishi. "Abba ban gane ba!" Kallon Majid yayi kafin ya ce mata. "Majid zan bawa hakkinshi sanadin rayuwa da mutuwa, sannan ga shi nan ya bukaci na yi mishi wani aiki." Sunkuyar da kai Majid yayi, yana murmushin farinciki, yau Allah ya kwace shi daga tarkon Hajiya. Can Lauyan yazo, "Malam Sulaiman!" Murmushi yayi yana faɗin. "Na'am Soja marmari daga nesa." Kallon Aryan yayi ya Banka mishi harara. Murmushi yayi ya ce. "Ba zaka gane yadda rayuwa da mutuwa take ba, shi yasa kake min kallon munafiki." Gyaran murya Alhaji yayi sannan ya bude taron da Addu'a, kafin ya ciro wasu takardu ya mikawa Mahdi. Shi kuma ya mikawa Lauyar Mamman Ba'are, shi kuma ya mikawa Majid, ya amsa yana kallon Alhaji Abubakar Abzin, "takardun ka ne, tun lokacin da aka haifeka Mamman ya bude maka kamfani anan da katsina." Sunkuyar da kai yayi yana kallon kasa, "Alhaji Mamman Ba'are bai kyauta ba, amma kuma ya rayu da boye kaunarka domin kada a kassaraka. Ke kanki ni nace ya nisanta ki da iyalinshi domin nasan cewa zaki zame mishi alkhairi." Mikewa Aryan yayi ya ce."ku dakata!" Ya nufi Amaan, kamar wani dan sanda haka ya shiga caje shi ya fitar da kome daga waya har agogon hannunshi, da zobe hatta botir din kirjinshi, a hankali wani abu ya fado. "Hmm!" Hajiya tace tana kallon Amaan cike da takaici, haka Aryan ya fitar kome. "Ko zaki bani sarkar wuyarki?" Hajiya ta mikawa Matar Amaan hannu. "Tow" ganin yadda suka tsareta da idanun. Haka ta mika musu harda agogo da dan kunnenta. Aka fita da shi waje, "Amaan baka da kunya. Baka da kunya baka da kunya ba zan maka baki ba amma ina rokon Allah ya shirye ka." Ko tari bai yi ba, "Abba ka cigaba." Gyara zama yayi yana kallon Amaan cike da takaici. "wancan takardun naka ne, wannan kyauta ce bayan an haifeka ya samu alkhairi mai yawan gaske, haka yasa ya cire wanan ya ce na baka naka ne, Hajiya Abdul Majid ya nemi na baki wannan takardur kiyi hakuri ki fahince shi." Amsa tayi ta ga takardar sallama ce daga aiki. Kallonshi tayi tana faɗin. "Ban san me yasa ka yanke haka ba, amma nasan kana da hujja me karfi." "Aryan zai rike matsayinki na Chairwoman zai zama Chairman na kamfanin Ba'are, Anisah zata rike matsayin CEO!" Kallon Abdul Majid suka yi, sunkuyar da kai yayi yasan sarai irin kallon da Aryan yake mishi. "Amaan zai rike board director. Sa'adatu kin girma da zaki hakura da wannan gwagwarmayar, Abdul Majid ya bukaci haka domin ki huta." "Abba shi fa?" Kallonta yayi yana son fadar mata abin da Abdul Majid din ya yanke amma yana shakkar yadda zata dauka. Mahdi ya ce mata. "Zai tafi karatu ne jami'ar sojoji da yake kasar Afrika ta Kudu." Ji tayi harshen ta ya mata nauyi da tayi magana, tana son tayi magana amma ta kasa tilas tayi shiru tana kallon Majid, "kin san me yasa bai bawa Jamilah wani matsayi ba? Saboda ga takardar asibitin shi zata rike matsayin shugaban asibitin. Amaan Mamman Ba'are zai rike matsayinshi ne baki daya." Ajiyar zuciya Hajiya take saukewa a kai akai, cikin Murmushi Lauya yace. "idan Hajiya ta ce zata bawa Aryan matsayinta sai an sakata gaba da magana amma da mai gayya me aiki ya daura wanda yake so zai yi wuya a samu matsala." "Wallahi haka ne!" Suka fada bakinsu a haɗe. "Abba Alhaji ya gama abin da ranshi yake so, nima ina niman izinin nayi wanda raina yake so!" Murmushi Alhaji Abubakar Abzin yayi yana faɗin. "Kiyi yadda kike so!" "Aure nake son yayi, kuma na zab'a mishi yarinyar da zai Aura............. Shahararu goma aduniyan kayan mata wato m zee kamshi kayan mata kenan inakuke matan kwairai manyan Mata fah bamuna mataba Mata masu aji Wanda tasan kanta agidan mijinta kozokuyi gyara masu kyau da inganci Wanda zaisa oga nishadi yasashi farinciki atare dake kayanmu wane yaro sai uban yaro kinsha zumar makalemata dare daya wanka goma wanan set ne na kayan kwairai akwai fati budurwa mumuna da aeki Dan miyau malaka to shu,Umar Zuma zumar kiba gari kiba Zuma me lakani ningi tsumin lahaula hadin miski ba ahira dawando garin me kabara kasa ruwa sama ruwa wanan magani ba ,a magana magani sanyi mekyu maza da Mata ci da kaza ci da cicibin vlp yan shila ci da kifi nama kayan sakiba na gida danawaje munadakaya kala kala fani kamshi munada shu uwar humra namu ba irin nasubane akwai turare 24 hr turare kabasa Dana gida masu Dadi gakyau ga kamshi 08063845136 #Mai_Dambu [2/23, 4:28 PM] Cutie cutie pie: *BAƘIN HAURE....🐾🐾* {Greed for Money is the roots of all evils🫀} Arewabooks:maidambu41 Wattpad:Mai_Dambu Mallakar:Mai_Dambu *022* "AURE!!" ya furta da karfi, yana me toshe bakinshi. "Eh aure zaka yi, aure nace zaka yi ko ba zaka yi min biyayya ba ne?" Idanuwanshi suka yi jawur ya kalli Aryan da Mahdi, mikewa Aryan yayi ya cewa Nabeeha. "Tashi muje cikin gida." Shima Amaan tashi yayi da Matarshi, domin kuwa ya fahimci maganar ta manya ce. Yadda fuskar Majid ya koma kamar zai nufi filin yaki, yasa kowa ya mike suka fita daga falon. "Hajiya ba zan iya aure ba." Cikin fushi ta ce mishi. "Wacce karyan kake tunanin zaka min kuma? Duk duniya kowa gani yake nice na rike maka kan maciji kake wasa da jelarshi, karewa har cewa ake ina zaune zaka kwaso min abin kunya duk wannan bai isa ka fahimci yadda nake rayuwa akanku bane? Majid ina son rayuwa ina son farinciki, amma na zabi na zauna da ku domin kuyi farinciki. Domin ku rayu cikin salama sannan ku zame min ribar hakurina na zauna daku, Ashe ban cancanci ka kyautata min ta hanyar yin auren ba?" Ta fada muryarta na rawa, kanshi a matukar sunkuye duk maganar da take yasan gaskiya ce kuma duk abinda ta faɗa gaskiya ne, amma kuma shi ba zai iya faɗa mata cewa bai da lafiya ba, ba zai iya cewa ga halin da ya tsinci kanshi ba, sai dai a shekarun baya . A banɗakin gidan horan yara marasa jin magana, wannan tashin hankalin ya same shi. Jikinshi ya tafi baya da wani amfani sai fitsari, bata wani motsin sai dai yayi fitsari kawai. Sannan yanayin rayuwarsa bai bashi damar kallon wata mace da sunan soyayya ba, ya kasa sakin jiki ya yi soyayya domin idan ya ce zai yi soyayya me zai bawa mace? Saduwa tana daga cikin shika -shikan aure, shi tashi tazugen bazata iya amfanar shi ba balle wata. Sannan har yau baya jin zuciyarshi tana da wata shauki akan mace, abin da ya sani ko aiki ne ya haɗasu da mata yana tsayawa yaga sun yi nasara, haka yasa Umaima ta makale mishi. "Kuna gani ina magana ya bawa iska ajiyata? Abdul Majid ba zan kunshi bakin cikin mahaifinku na kunshi naka ba." Mikewa yayi zuwa gabanta. "Hajiya ki min uzuri, don Allah." "Na maka uzuri fa kace min? Na hana kaina farinciki na gina ku shine zan maka uzuri? Gaya min Meye matsalarka?" Hadiye yawu yayi yana kallon yadda take cikin b'acin rai. "Hajiya duk matar da zaki aura min, karshe wahala zata sha, domin idan ta zauna dani." "Maza kake so kenan?" Inji Alhaji Abubakar Abzin, da sauri ya juya kanshi yana kallon Alhaji Abubakar Abzin, idanunshi har wani shekin kwalla yake tsabar tashin hankali. "Abba da ace zan so mazan da nayi farinciki,tunda a karshe dai na fahimci inda zuciyata take amma abin bakinciki babu maza da matan da suke iya burge ni ko shiga rayuwata. Duk wanda na zauna da shi don aiki ne da wani halin rayuwa" "Ita yarinyar da kace a nimo maka fa?" Hajiya ta kara watsa mishi tambaya. "Yarinyar nan hatsari ne ya had'a mu, domin na bugeta da motana ne, kuma nayi mata jinya Hajiya ki fahimta auren idan nayi karshe." "Abba ka zama shaidana idan Abdul Majid bai yi aure ba, tow kuwa sai dai ya zab'a ya hakura ya ajiye aikin shi ya zauna anan." Da sauri ya kalleta yana jin kamar kanshi zai buɗe wani irin sara mishi yake yana jin jiri. Harshensa yayi wani irin nauyi, so yake ya fada musu ba zai iya rike mace har ya mata kome ba, haka yasa shi jin wani irin jiri-jiri kafin ya ankara duhu ya mamaye mishi idanu, haka ya zube a gaban Hajiya a sume. Sai gashi ita tafi kowa shiga damuwa. Salatinta ya shigo da Amaan, da yake makale. Lauya Sulaiman ya watsa mishi ruwa yana kwance jikin Alhaji Abubakar Abzin da ya rike shi yana tofa mishi addu'a. "Ba zance lallai kada kiyi yadda kike so ba, amma yana da kyau mu hakura da al'amarin auren nan." Wani irin kuka ne ya kwacewa Hajiya tayi ta yi ta kuma yi, muryarta yana rawa ta ce. "Abba don Allah kada ka hana ni yimishi aure, domin kuwa ina matuƙar son yayi aure. Duk wannan shiri ne." "Ba shiri bane, tun ranar da Mamman ya gaya min ya bar shi a gidan horan kangararun Yara, ban kara yarda na zauna ba. Lokaci zuwa lokacin ina kai ziyara naji halin da yake ciki. Yaron nan ya sha wahalar rayuwa, idan kika ji abinda ya same shi ba zaki kara barci ba. Don Allah ki kyale shi ki mishi fatan Allah ya bashi lafiya." Wani irin sanyi ta ji ya lullubeta, bata taɓa kawowa da gaske bai da lafiyan ba, domin a tunaninta zai tsarewa auren da zata kakaba mishi ne, amma kuma anya zata yarda da su? Tunda ya iya ajiye mata takardar sallama, babu abinda ba zai aikata ba don kada Alhaji Abubakar Abzin yaga kamar tana da bala'in taurin kai ta share hawayenta, amma a kasan ranta sai anyi auren nan ko zai mutu ne idan aka yi auren don ubanshi ba zata yarda ta ganshi haka babu aure ba, don haka ta dauke kai tana share hawayen da yake zubo mata. Ganin yadda yake barci yasa baki daya aka yi shiru, babu wanda ya kara tada zancen. Asalima kowa tausayin Hajiya suke ji hatta Amaan da yake ganin duk wani abinda ya faru da laifin Hajiya tun farko. "Tow ki daina kuka mana, ba gamu a raye ba, idan mutuwa aka ce zai yi ai kowa ya huta." Juyawa Aryan yayi yana kallon shi. "Dadina da kai baka boye waye kai? Gab'o kawai." "Kai waye gab'o." Ya taso a fusace. "Idan bakincikin Mamman Ba'are bai kashe ni ba, bakincikin abin da kuke aikatawa ya isa ya kai ni kabarina, don Allah ku bari." Ta fada tana kuka. "Hmmm Alhaji meye kuskurena akan Yaran nan? Jama'a su jefe ni, suma su koma gefe suyi dariya, Alhaji idan nace maka bana jin dadin rayuwata zaka dauka rashin godiyar Allah ne ko? Tow wallahi bana jin dadin rayuwata." Ta fada tana kuka, "sun mai dani mahaukaciya, basa jin magana ta, basa son junansu kamar su kashe kansu suke ji don Allah ya ake son nayi?" Baki daya sai jikin kowa yayi sanyi. "Alhaji da zaka Duba zuciyata, Yarana ne a cikinta,, ina son su hade kansu ina son na gansu cikin farinciki. Ina son nayi alfahari da haihuwarsu, sai dai idan na cire maka Aryan da sauransu, Amaan zai kashe ni. Bakincikin shi zai kai ni lahira ban shirya ba. Amaan ya zame min wake daya me kona gari." Yadda take kukan kawai xai saka kaji kamar ka tayata. "Ban san meye nayi mishi na kuskure ba, ya tsani yan uwanshi mata da maza ba, Alhaji Abubakar na hakura da kome na zauna da mutumin da ya haife ni kasan ba karamin al'amari ba ne. Mace ta zauna da namijin da tasan bata sonshi. Kuma ta zauna akan babu yadda zata nime hakkinta. Alhaji amsar ƙaddarata da nayi hannu bibbiyu shine laifina ko zama da nayi nai ta haihuwarsu!" Yadda Hajiya take kuka yasa bakiɗaya tashin hankalin da suke ciki ya nunku. "Idan da ace Amaan yana da adalci ba zai tab'a had'akai da makiyana ba, nawa zasu bashi? Nawa suke da shi? Bana son nadama tazo mishi bayan ya haɗakai dasu sun kashe ni." Yadda take kuka yasa Majid ya tashi da matsanancin ciwon kai, wanda yasan baya raba daya biyu jininshi ne ya hau. Hajiya bata fasa fadar abin da yake damunta ba, tana ganin idan bata fada ba, tabbas kafin su koma Niamey ta mutu, shi yasa ta hakura ta fadi abinda yake damunta ko zata samu sauki. Kuma bata fasa fitar da abinda yake ranta ba, domin taji sauki kuma Allah ya taimaka tana faɗa tana jin kamar ana zare mata k'ayar da yake ranta, ruwa Aryan ya mika mata, ta amsa ta sha sannan ta sauke ajiyar zuciya. "Allah kagani na fita hakkinsu, saura su ya rage su futa nawa." "Kiyi hakuri Hajiya, Indai aure kike so nayi zan yi in sha Allah." Inji Majid yana dafe kanshi, "A'a Majid kayi yadda kake so, ba sai kayi auren ba, tunda baka da lafiya." Ta fada tana share hawayen da yake zubo mata, "Aryan don Allah kai ni, asibiti kada na fadi don zan iya samun shanyewar b'arin jiki." Ya fada kamar zai fadi, da sauri ya tare shi, suka bar falon Hajiya tana me bin su da idanu, don a tunaninta shirinsu ne suyi wasa da hankalinta. Sai da ta ga sun tafi baki daya, sai Amaan kaɗai ya rage, yana son ya hada rigima. "Ba wani ciwon da yake damunshi, kawai renin hankali. Fisabilillahi Hajiya kina ji kina gani wai board director aka bani?" Sai kuma yayi kasa da murya yana faɗin. "Hajiya Chairman bai yiwa Aryan girma ba? Ki ga fa Yaro ne? Sannan."da "Duk da Yaro ne bai saka dukiyarshi gaba ya lalata ba, har yau bai tab'a kaso biyar na dukiyar shi ba, kai ina naka dukiyar? Wai me kake yi da kudinka?" Shiru yayi yana kallon yadda take tsare shi da idanu. "Wato Hajiya " "ya isa haka! Kada ka kara kawo min sukar kowa sannan da na san board director za'a a baka wallahi da sai na hana a baka, domin ba zai yiwu a dauki jahili a bashi abin da ba zai iya rikewa ba " "Allah ya baƙi hakuri Hajiya, naga kamar ranki ya b'aci " "Hakuri shi ya kashe Uwar jaki." Yadda tayi maganar yasa shi kame kanshi kada Hajiya ta kara fusata. ---- A can Asibitin kuwa, Mahdi shi ya musu jagora aka kwantar dashi bayan an saka mishi ruwa. Likitan da ya duba shi ya fito yana kallonsu kafin ya ce su same shi a office ɗinshi. Bayan sun shiga ya zauna yana ta rubuce-rubuce. Kafin ya d'ago kai domin har Aryan ya gundura da zaman ya ce musu. "Gaskiya jininshi ya hau, don Allah a bashi lokaci ya huta, idan kuma yana da mata tow a dan janyeta daga gare shi, a nisanta shi da hayaniyar mutane." "In sha Allah!" Suka faɗa, kafin ya ci-gaba da cewa. "zamu sallame shi nan da kwanaki uku, domin jikinshi yana ƙarƙashin kulawa ne. In sha Allah zuwa nan da wani lokaci zamu sallame shi." Haka suka yi ta godiya, sannan suka fito. "Hajiya Sa'adatu tayi hakuri da maganar auren nan, Yaron nan yana buƙatar nutsuwa." "Abba me yasa ba zai yi auren ba?" Kallon shi suka yi ta window, Alhaji Abubakar Abzin yana tuna ranar da ya kai mishi ziyara da yadda aka fito dashi baya iya tafiya. Sai riko shi aka yi. Idanunshi ne ya cika da kwalla. "Ya hadu da hatsari ne, bayan an kai shi gidan horon, Yaran da suka fi karfinshi suka mishi duka tare da doke mishi gabanshi. Wanda sanadin haka gaban ya mutu." Rufe baki Aryan yayi da karfi jikinshi yana rawa, hawaye na zuba mishi kamar mace haka yake kuka yana kallon dan uwanshi. "Hammayo ba xai tab'a zama da mace ba kenan?" "Gashi nan dai, bamu sani ba ko Ubangiji zai yi ikonshi, amma Abdul Majid yana cikin jarabawa." A hankali ya fashe da kuka, yana jin wani irin tausayin dan uwanshi. "Innalillahi'wa'inna'ilaihi'raji'un! Ubangiji mun gode!" Ya fada Aryan akwai karyayen zuciya, haka yake ga saurin kuka kamar mace, gani yake kamar dan uwansa zai mutu da damuwar lalurar. Shi yasa yake nisanta kanshi da mutane, baya yarda ya zauna da kowa rayuwarshi cikin duhu, akwai wani irin shakuwa tsakaninshi da duhu tun yana Yaro, gashi ya girma da wannan trauma ɗin. A rayuwar Abdul Majid bai san soyayya ba, bai samu soyayya ba, ita kanta Hajiya ta haifi Majid ne amma bata damu da damuwarshi kamar yadda ta damu kanta da yayi aure ba. Duk laifin abinda ya same su, laifin Alhaji Abbati ne, da bai saka Hajiya a cikin caca ba da babu yadda zata hadu da mahaifinsu ya kashe rayuwar dan uwanshi haka,. Sai yanzu yake fahimtar me yasa Majid ya tsani dukiyar Mamman ba'are, asalin don a gina duniya da dukiyar aka lalata musu rayuwarsu. Cikin shashekar kuka yake faɗin. "Saboda hab'aka dukiyarshi ya lalata rayuwar wanda babu ruwanshi." "Asibiti muke kayi hakuri ka bar wannan zancen." Haka suka cigaba da zama har wani lokaci kafin Alhaji Abubakar da lauya suka bar asibitin tare da Mahdi,. Suka tawo da Hajiya tare da abinci, mika mata kome Aryan yayi sannan ya koma gefe yana kallonta, ajiye takardar tayi ta zauna tana kallon Majid. A hankali hawaye yake zuba mata, wannan wacce irin rayuwa ce? Me yasa kome yake zuwa mata haka? Me yasa daga wannan sai wannan? Shin anya bata yi wani laifi Ba tare da ta saninta ba. Su da suka zo da zimmar kwana ɗaya, sai gashi sun kare da dibar kwanaki har sama da biyar, a na shida aka sallami Majid din, ba laifi ya ɗan samu sauƙi. Kuma dama yanayinshi ba mai yawan walwala bane, sai abin ya kara yawa. Ita kanta Hajiya ta damu sosai kamar ta cire ciwon. Haka suka tawo Niamey zuciyarta babu dad'i. Lokacin da suka isa gidan A tsakar gida suka hadu da Nanah, tana jin rigima. "Ya zamu yi da wannan tsohuwar?" A hankali ya fito yana tafiya, kamar ba zai taka kasa ba, saboda rashin karfi da kuzari. "Kai Alhaji!" Ta fada tana mikewa tare da dogara sanda har inda yake ta ce mishi. "wallahi ka sake ka mutu sai Allah ya mana hisabi. Kai ma mutuwa zaka yi?" Ta faɗa, yadda tayi maganar zaka fahimci bata cikin nutsuwarta. "Munafukan can ne suka kaika zasu kashe min kai ko?" Kasa magana yayi yana kallon yadda take fada. "Nana likita yace a barshi ya huta." "Muje daga yau ni zan yi jinyar shi " duk da bata kaunarsu amma a lokacin da takira Hajiya take fadan ba zasu dawo bane, an barta kamar ba a damu da ita ba, gashi kayan abincinta ya kare, babu nama babu kome Haladu da Kamilu sunki saya mata, me take nufi na dauke mata Aryan shi ko zata mishi meye baya fasa saya mata kayan abincin. Shi ne ta bata hakuri da gaya mata ai Majid bai da lafiya ne, bata san lokacin da ta rikice ba, tayi ta sumbatu tare da dorawa Hajiya laifin abinda ya faru gani take kamar Hajiya ta kaishi aka mishi wani abu, sannan ga Amaan da dama can tasan munafuki ne. "Ina gaya maka kada ka sake kana yarda da mutane, domin kuwa wasu ba imani a cikin zuciyarsu. Sun sayar da imanin su ga duniya, Gara ka yi nisa da su domin kada a wayi gari babu magajin Abdul Majid ba'are. Sannan kasaka ayi ta maka addu'a da saukar Alqur'ani domin nasan makiya ba zasu Barka haka ba, li'ilafi aniyar kowa ta bishi daga yau har Sa'a ban yarda da ita ba. Domin dankareren dukiyarka yawa ce da ita a tow zamani na masu iya kashe mutum, waye ya sani ko shima Muhammad kashe shi aka yi!" Zama yayi a daya daga cikin sofa, yana haki yana kallon agogon hannun shi. "Nana zan huta kiyi shiru." "Alhaji duk abinda kace ai shi zan yi." Ta zauna tana kaskantar da kanta tana faɗin. "Ahtow nayi shiru, amma ina ga hatta Salamatu ban yarda da ita ba, waye ya sani ko har da ita ake shirya maka kitimurmura." "Nana jeki gida, an jima zan shigo duba baki." Ya fada yana daure fuska, domin idan ba haka yayi ba, ba zata kyale shi ba. Sannan ya san halinta sarai sai ta kara mishi wani sabon ciwon kan. "Tow Allah ya baka lafiya, zan damo maka kunu na kawo maka." Yasan sarai idan yace mata ba zai sha ba, zata yi tsammanin bai yarda da ita ba ne. Haka yasa shi rufe idanunshi ya d'aga mata kai, domin kuwa baki daya bayan son magana. "Sa'adatu ki saka idanu akan shi domin ba zan yardaba idan wani abu ya same shi." Ta futa tana faɗin. "A kula da shi don wallahi zan iya shiga kotu da kowa." Tana fita ya kalli Hajiya ya ce mata. "don Allah a gyara min dakina." Daga haka ya juya musu baya, don baya son magana, Hajiya da kanta ta wuce dakin, ta gyara baki daya, sannan ta fito tana faɗin. "Na gyara maka" dakyar ya mike ya haura sama, koda ya shiga kashe wutar dakin yayi ya kwanta. A hankali labarin matsayin da Abdul Majid ya bawa su Aryan ya zagaye cikin gidan, bakiɗaya suka taru a falon Nana suna mitar abin da ya faru, da akan me Majid zai yanke hukuncin babu shawara da su, musamman su da suke Yan uwan Babanshi. Yadda ake masifar Nana ta zuba musu idanu, can da suka ishe ta mike tana faɗin. "Yayi yadda yake so kamfanin nasu ne ba na wasu ba. Don Allah ku sakar musu mara na gaji da fitinarku, kada na kuma jin wata magana." Ta wuce dakinta bata kuma kula su ba, haka ta shiga ta bar su nan suna mita. Wannan fitinar ta dame ta, kowa yasaka musu idanu. Kowa ya saka buri akan abinda ba na shi ba, sannan baki daya kowa burinshi ya mallaki abin da yafi na dan uwanshi, a kan wannan zasu iya kashe junansu akan abin da ba nasu ba, *** *Zahrah* Bana ce rayuwa tana da sauki a wurin Uwa irina ba, domin baki daya na susuce akan Babyna, zamowa uwa ba abu ne mai sauki ba. Haka na nakoma kome kamar mahaukaciya, bana barci da zarar naji motsinta duk barcin da nake na daina Kenan xan tashi daga barci har sai ta koma, wani abin da na kasa sabawa da shi, shi ne, da zarar na saka abinci a gaba Baby zata fara kuka, ba zata kuma shiru ba sai na hakura da abincin............ #Mai_Dambuje [2/24, 2:51 PM] Cutie cutie pie: *BAƘIN HAURE....🐾🐾* {Greed for Money is the roots of all evils🫀} Arewabooks:maidambu41 Wattpad:Mai_Dambu Mallakar:Mai_Dambu _Hodjam Fire to fire Fitilar hikayar Dambuje, BAƘIN HAURE comments. Wannan Pagen na kune yan arzikinsssssssss zaku sheke min dariyata 🥳🥰 Irin wannan comments a kwana a hantse sai Kyakyawa 😏 Baby Aminatu sai tasha Baloon din nan fa 🤣😂Baby bata mutuwa fa sai hakuri_ Assalamu alaikum barkanmu da warhaka da fatan kuna cikin koshin lafiya, karku manta da wannan Kamfani mai albarka mai kawo muku kayan bukata cikin sauki da Aminci da Inganci. Wato TA RASULU MULTIPURPOSE. YA SAKE DAWO MUKU DA KAYAN NAN MASU ARMASHI DA DANDANON KOWACCE MACE TAURARUWA CE. _______________________ MARKADADDIYAR GYAD'A HADADDEN KAYAN SHAYI GARIN KOSAI NA TAFI DA GIDANKA. GARIN TUWO GARIN KUNU YAR ASALI CURRY ME DADI SPICES TYME YAJIN DADDAWA ME KYAU GARIN DAN WAKE JAN YAJI MAI DAD'I... _____________________ BUGU DA KARI MUN TANADAR MUKU DA KAYAN FITAR SALLAH DA NA SHAGALIN SUNA DA BUKUKUWA. ATAMFOFI, LESHINA, MATERIAL, SHADODDI, YADUDDUKA NA MAZA DA NA MATA, JAKKUNA DA TAKALMA. WANI ABIN SAI KUN ZO TA RASULU MULTIPURPOSE DOMIN KASHE KWARKWATAN IDANU. ZAKU IYA TUNTUƁARMU A WADANNAN NUMBOBIN.. 08086639163 - 09030168590.... MUNA DAKON SAYAN DAI-DAI KO SARI..... *023* Ko don na taso a tsakar gidanmu ne, ban tashi gaban Uwa ba, ban san yadda Uwa take handling yara kmr Babyna ba, akwai wani abu da na fahimta da zarar gari ya waye zata wuni barci, sai dare garinta zai waye duk da haka bai hana da zarar na saka abinci a gabana zata bude idanunta ta fara rigima ba, sannan baki daya a girman dakin da muke babu me iya tunanin ya taimaka min, Ummi da Addah kowa harkar gabanshi yake, sannan basu da lokacin da zasu tsaya lallai sai sun taya ni kula da yarinyar. Bakidaya sai na kasa sabawa, da zarar dare yayi zan goyata ina yawo da ita har daren yayi nisa tayi barci. Na kwanta da ita a bayana, sannan zamu yi barci idan kuma sanyi ya dame ta hana kowa barci take, haka zasu yi ta tsaki suna mita. Gari na wayewa kowa zai kama gabanshi. Suna tafiya suna mita, ban tab'a fushi akan hakan ba. Yazeed Hamir. Asalinshi dan kasar aljeria ne, mahaifinshi babban attajiri ne sannan Basarake ne a babba a kasar , kuma Balaraben aljeria. Suna da kudi sosai sai dai shi Yazid ya lalata rayuwarshi ta hanyar shaye-shaye. Mutum ne da bai da yawan magana ko hayaniya, sannan akan abinda ya shafi sayar da kwayoyi baya da wasa. Domin ya bar ƙasarshi ta haihuwa ne yazo wannan wurin ya kafa inda zai na fitar da shu'uman kayan maye yana rabawa tsakanin kasashen Afrika. Shaidani ne na gayawa Sarkin gari, yana da wani irin sirrin da duk inda ya shiga sai ya fitar da kaya, zai yi wuya ya shiga wuri bai fitar da kayanshi ba, sai dai yana da rauni sosai matarsa da Yaran shi, biyu dukkansu mata ne yana matukar kaunarsu. Yazid ya bar gidansu ne tun yana shekaru ashirin da biyar a duniya, domin yana da matukar kiyayya da sarauta, domin a sanadin mulkin da za'abawa Babanshi Mahaifiyarshi ta rasa rayuwarta kuma dama ana ta faɗan cewa ya sadaukar da ita ne ga mulkin shi, shi yasa ranar da ya fara jin labarin ya sami mahaifinshi da maganar, ƙaryatawa yayi shi kuma ya ce matuƙar ya tabbatar da haka sai ya bar mishi kasar da kome yaje yayi rayuwarshi,. Dake akwai mutanen da basu son Babanshi, sai suka yi amfani da haka suka tabbatar da cewa sadaukar da Amiratul Aminat aka yi, duk yadda Uban yaso mishi bayani amma yaƙi fahimta. Don haka ya saka kafa ya bar kasar da dukiyarshi a lokacin ya gama karatunshi a bangaren had'a magunguna. Wannan abin yayi matukar yiwa mahaifinshi ciwo, har kwanan gobe yana zuba idon ganin shi, Yazid yana matukar tausayin mata da Yara, akan mahaifiyarshi ya kara jin tausayin Yaya mata, kuma wani abin da yake kara saka shi tausayinta, ita sikila ce. Sai akayi dace shi bai da shi, haka yasa yake son Reshmah kamar zai haukace da ta fara haihuwa ma bai tab'a ce mata ga zab'in shi ba, sunan da takeso take sakawa. Tozali da yayi da Zahrah yaji duniya bai tab'a tausayi da son wata Y'a mace ba kamar ta, sannan baki daya sansanin da suka zauna mutanen Yazid ne, hatta Uwar mugu dalilin da yasa Nawwas yazo nimanshi wurinta kenan, sai gashi kuma Nawwas din jin kamar Yazid din yana zuwa yasa shi guduwa da yan matan. Matarshi itama balarabiya ce, Reshmah mace ce mai tsananin kishi da saurin fushi, sannan shima Yazid yana matukar kiyayye abinda zai saka kishinta ya fito har ayi tunanin wani abu. A wannan dajin idan kana son ka fita sai ka je an saka maka wasu kwayoyin da zaka masa safara da shi idan ka sha zaka je a cire maka, sannan kayi tafiyarka daga nan ka samu yanci, ba kuma zai barka ba domin abin shi kamar da siddabaru domin ko ka bar dajin ka manta kenan. Ba zaka kara tunawa ba, da haka Yazid yafi karfin abokan gabanshi, domin yana fito da kayanshi ta kowace fuskar ya sayar a waje. Lokacin da muka zo garin ina cikin waɗanda aka rabawa aikin shara da goge gogen gidanshi, idan har Matarshi ta rigashi tashi hatta bango sai na goge, sannan babu ruwanta da ina da baby ko bani da Babyn, matar nan yar bala'i ce. Kafin Yazid ya fito na gama kome na bar gidan. Sai yamma kuma na koma. Ban san me yasa ba ko yana sane da yadda matarshi take saka ni a gaba da fitinar aiki, ranar ina zaune a kofar gidan da muke sai gashi ya zo ina jijjiga Baby. "Babyn Zahran bata yi barci ba ne?" Juyawa nayi zan yi magana domin ban zata shi ba ne. Sunkuyar da kai nayi na ce mishi. "Yallabai kai ne?" Na fada ina jijjiga ta, ajiye wata jakar takarda yayi ya ce min. "Kawo min ita." A hankali na mika mishi ita har hannunmu yana gogan juna. Da sauri na janye nawa hannun, shi kuma ya cigaba da kallona. Yana me kallon inda kwanon abincina yake, na bude zan ci ta fara rigima. "Ki ajiye abincin anjima sai ki ci ga wannan ki ci." Ya nuna min jakar da idanunshi. Sai gashi na rikice baki daya, domin ina jin yadda yake bina da idanu, ban saba ba sai nake ganin kamar ba zan iya tsayawa da kafata ba. Jingina nayi na dauki jakar na bude, madara ce a kwalba sai gassashen nama, hadiye yawu nayi duk da ba laifi tunda muka zo ba laifi abincin mu yana da kyau, sannan a wadace muke samu. A hanya muka fuskanci matsala amma tunda muka zo abincinmu babu laifi. A hankali na fara bude takardar da ya nad'e namar, kamshinsa kawai yasa na hadiye yawu yafi sau goma. Na d'ago kai naga yana hidimar baby da sauri na fara ci, ban sani ba ko yana kallona domin ganin nama yasa ni jin duk wata yunwar da nake ji na tsawon watanni bakwai ta dawo min sabo fil, "ki ci a hankali." D'ago kai nayi naga Babyn yake wasa da ita, goge bakina nayi na cigaba da cin namar, har na koshi. "Zan tafi!" "Allah ya saka da alkhairi." Na faɗa ina sunkuyar da kai, koda su Addah suka dawo a gajiye, idanunta ya sauka akan jakar takardan, dauka tayi zata buɗe Ummi ta fauce. "Dalla bani." Dama kuma na rage musu ne, ganin kowannensu ya samu ba zai bawa dan uwanshi ba. Yasa na amsa. "Idan kuka yi hakuri na ku ne, idan kun yi faɗa ma naku ne." Na fada ina ciro musu na mika musu, faucewa suka yi suna jan tsaki. "Wani dan iskan kika samu ya kawo miki?" Inji Addah, ban bata amsa ba na gyara mana kwanciyarmu da Baby. Washi gari da na shiga gidan aiki naga Matarshi sai hawa da sauka take, har na gama aiki zan fita ya fito dauke da Yarshi. Murmushi yayi min na sunkuyar da kaina, na fita da sauri. A harabar gidan naga alamar zasu fita ne, haka yasa na bar gidan domin yau bata min kakale-kakale ba, asalima kamar sauri suke. Ina dawowa nayiwa baby wanka. Sannan muka kwanta bayan mun karya. 12:30pm, Ji nayi kamar ana tsaye a kaina a hankali na bude idona, ya sauka akanshi yana bakin gadon Ummi yana latsa wayarshi, da dan sauri na tashi zaune ina kallonshi. "Yau Baby bata yi rikici ba kenan?" Ya ajiye min irin jakar jiya. "Wai ya sunan Babyn?" Tiririn da nake ji na kamshi yasa ni rikicewa domin yunwa nake ji, kuma sai karfe biyu za a kawo mana abinci. "Ban mata suna ba, baby muke kiranta." "Ya sunan Mamanta?" D'ago kai nayi ina kallon shi, kawai sai ya cika min idanu. Sunkuyar da kai nayi ina faɗin. " Zulaiha!" Na zabi na fadi haka ne domin ya min kwarjini. "Ok bani ita!" A hankali na mika mishi ita, kamar mai tunani sai kuma ya ce min. "Hmmm! Ba zan saka mata sunan Uwarta ba, domin zata iya gadon halinta." "Ka saka mata sunan Addah." "Ita criminal ce zata tashi da shaidancinta." "Tow ka saka mata sunan Mamana!" "Ya sunan yake?" "Aminatu!" Murmushi yayi ya ce "sunan Kakata ce da tasoni sama da kanta." Ya fada yana shafa kan Babyn yana me mata huduba. "Maman Aminatu!" Murmushi nayi, tare da Mikewa zan karbeta ya ce min. "Ci abinci" ba musu na zauna na ci grill fish da chips a gefenshi. Sai da na gama ci ya mike, ya ajiye min yarinyar. Ya tafi, lokacin sallah yayi na mike na wuce ban daki nayi alola sannan.na dawo nayi sallah, sannan muka kara kwanciyarmu, domin kifin akwai maiko. A hankali wata irin shakuwa da bansan daga inda ya samo asali ba, ta shiga tskanina da Yallabai Yazid, da farko sau daya yake zuwa, daga baya ya koma yana zuwa sau biyu. Da rana da kuma Yamma, a hankali idan yazo shirya Baby Aminatu, Addah kamar zata rufe ni da duka da taji sunan har da Min Allah ya isa, bata yafe ba don na saka sunan Mamana. Da yamma idan ya zo ɗaukarmu yake muna zaga cikin garin, gonarshi da lambun shi har da gidan dabbobin shi. Yau ma haka ya saka ni a gaba, bayan ya kawo min wata doguwar riga da mayafinta. Muka shiga wani yanki ta Cikin gonar, mun yi dogon tafiya kafin ya kawo mu wani wuri a ƙarƙashin ƙasa, ya ce min. "Kin ga wannan wuraren? Akwai kofar da xasu fitar da ke har wani kauye, daga nan zaki wuce bodar Nijeriya da nijar ne da yake dole kaina, mu nan muna yankin River Benin ne. "Ban gane ba?" Zama yayi yana kara murmushi ya buɗe kofar ya shiga shi da Babyn sannan ya mika min hannu na rike shi na sauko. "Kina da saurayi?" "Na'am?" Na ce mishi, ina kallon shi. Murmushi yayi min sannan muka cigaba da tafiya. "Nace kina da saurayi?" Ya juyo yana kallona." Zare idanuwa na fara, da wasa da ya bakin mayafina. A hankali yake takowa na juya bayana naga ko wani abu yasa yake biyo ni, sai naga haka kawai koda na juya ya matso kusa dani sosai. "Baki da saurayin ne?" Hadiye yawu nayi na gyada kai na, a hankali ya sunkuyo da kanshi a tunanina sumbatar bakina zai yi, da sauri na kawar da kaina. A hankali ya kai hannunshi gefen wuyata ta wurin mayafina ya kad'e min gizo-gizon da yake kaina. "Ki kula." Ya fada yana kallon kwaron. Hadiye yawun bakina nayi ina kara jin kamar zan saki fitsari. --- Cikin larabcin da bai gama rike bakinta ba, Addah ta kara gyara zamanta ta ce mata. "Idan nayi miki karya, ki saka a kashe ni a binne gawata, amma yarinyar da Yallabai yake fita da ita yata ce, kuma zaki iya zuwa gidan mu, ki ga irin kyawawan kyaututtukar da yake kawo mata." Mikewa tayi tana faɗin. "Muje!" Haka Addah ta mike jikinta yana rawa ta ce mata. "Tow!" Suka tawo har gidan, wato ita Yazid zai ci amanarta. Ita zai tsallaka yana bin karuwa da ta gama yawon karuwancin kafin ta fado hannunshi, bata kara sarewa namiji ba dan goyo da zani ba ne, sai da ta ga katon akwatin kayan da ya kawowa uwar da yar, ciwon bakinta tayi sannan ta juya ta fita cikin nutsuwa Addah kuwa murna kamar zata daka tsalle. Haka Reshmah ta koma gida, ta zauna tana tunanin me zai faru, me zata aikata da zai bawa Yazid tsoro ita ba kalar Matar da zai ci amana bane . Bai isa ya ci amanarta ba. ---Sai dare muka dawo tun a hanya aka tare shi, ana gaya mishi abin da ya faru cikin wani irin yare, murmushi yayi ya ce musu. "Suwa laula!" (Shi kenan naji) kallonshi nayi domin ban tab'a zatan yana jin wani harshe bayan Hausa da larabci ba. "Wani yare ne haka?" Murmushi yayi ya ce min. "Harshen darsa, yana da saukin amfani.". "zan koya!" "Zaki iya kuwa?" "Hmm!" Haka ya rako ni gidan sai da na shiga ya ce min. " Za a kawo miki abinci." "Tow na gode!" Daura yatsar hannunshi yayi a baki ya ce min. "Shiiii" hadiye yawu nayi. "Kada ki b'ata min alakata da godiya." "Shi kenan!" Haka ya bani Babyn muka shiga cikin gidan, yana fita yayi waya aka kawo min abinci, muna kwance aka buga kofar kallona Addah tayi na mike na bude kofar na amso abincin na fara ci, tashi tayi zata saka hannu Ummi da take gefen gadona ta doke hannun da wani sanda, sai da kashin hannun yayi ƙara. "Kika sake wani abu ya shiga bakinki sai na shakeki har lahira munafukar banza." Daga haka bata ci ba na kalli ummi ta dauke kai. "Me yasa kika hanata!" "Ba zata ci ba wallahi." Shiru nayi ina kallon Addah da ta koma ta kwanta. Ban kuma musu magana ba, sai da zan fita Addah ta ce min. "Bani Aminatu na taya ki goyanta." "Ba zata baki ba, duk abinda zai faru sai dai ya faru!" Inji Ummi. Fita muka yi, nima na nufi gidan Yallabai. A falon kasa na same ta a hankali naji jikina ya bani akwai matsala. Haka na wuce na fara aiki har na gama. Tana zaune sai da na gama zan fita ta ce min. "Ke jira ni!" Daidai shima yana saukowa daga sama, kenan ta shiga kitchen, kamar ya san nufinta, tana fitowa kawai ta watsa min soyayyen mangyad'a da ta dauko a fry pan. Rumfa yayi min ta zuba mishi a bayanshi, bata san lokacin da ta saki fry pan din ba, "Yazid!" Ta kwalla mishi kira, bude idanu yayi a kaina."Yallabai!" Na kira sunanshi. "Jeki gida lafiya ta lau." "Yallabai bayanka fa?" "Ba kome, jeki" Ya fada min da wata irin murya, da sauri na fita tana rufe da fuskarta tsoro ya kamata, hadiye yawu tayi tana kallonshi. "Me kike nufi?" Jikinta ne ya fara rawa, "don Allah kayi hakuri." Jan iskar bakinshi yayi ya yaga rigar tare da zama a bakin kujerar falon, da gudu ta fita ta kira Aseem ta gaya mishi, shi ya tafi har wurin likitan ya tawo dashi, suna shiga suka same shi a falon. "Garin yaya?" "Nice na zuba mishi ba da gangan ba." Bai ce uffan ba har likitan da Aseem suka yi ta cire mishi rigar da ya hadu da fatar bayanshi, ya zuba mata idanu. Cikin wani irin Imagining da Zahrah zata zubawa man gyadar nan a fuska. Sai lokacin ya iya bude baki ya ce Mata. "Nufinki Zeehra zaki zubawa?" Zubewa tayi tare da rufe fuskarta ta fashe da kuka. "Kayi hakuri sharrin iblis ne." Ta fada tana shasshekar kuka, haka ya cigaba da kallonta tana kuka. Yana wondering yadda zuciyarta ta mutu da tunanin ta nakasa mace yar uwarta, murmushi ya saki a hankali yana kallonta. "Sultan kayi hakuri don Allah!" Ta fada tana waiwayen bayanta. "Aseem!" Da rarrafe ta kama kafarshi. "Don Allah ka rufa min asiri Sultan kishinka ne ya saka na aikata haka, Sultan ba zan kara ba." " A bata abinci dare da rana, ta zauna a wurin sai na warke." Fashewa tayi da kuka kamar ranta zai fita, "Sultan afuwa!" "Aseem!!" Zubewa yayi akan gwiwarshi. "Uwar Yaranka ce, kuma mace mai daraja a gare ka, kasan haka kuma kai da kanka ka gaya mana babu mace mai darajasama da Reshmah." "Zeehrah tana da daraja, darajarta me girma ne!" Ya fada yana kauda kai. "Matar da nake aure idan bata ji magana ta ba nawa zata ji? Idan wani abu ne ya had'ata da yarinyar waye zata tinkara? Dole sai ni, wato shine aka gaya mata xata kona musu yar mutane. Idan ta lalata mata fuska fa? Fisabilillahi ace mangyad'a zata zuba a fuskar Zeehrah... #Mai_Dambu [2/25, 7:57 PM] Cutie cutie pie: *BAƘIN HAURE....🐾🐾* {Greed for Money is the roots of all evils🫀} Arewabooks:maidambu41 Wattpad:Mai_Dambu Mallakar:Mai_Dambu *Muna da stone Veils da plain,sai hular Yara, masu kyau akwai veil na Yaran shima.* *024* Kallon Aseem yayi kafin ya ce masa. "Ka fice min da ita ko kuma na had'a da kai." Haka ya saka Reshmah a gaba ya wuce da ita wani gidan da aka ware domin hukunta duk wanda ya ja da Yazid, gidan kamar gidan yari yake, sannan a cikin gidan akwai masu kula da kowa kawai ba zaka fita ba,ba zaka iya kome ba kana zaune a daki guda ga kome amma kuma takure kake. Ya kaita can wani daki da yafi kowanne kyau, "Aseem don Allah ka roke shi." "In sha Allah." Ya fada, yana me barin dakin, kuka ta fashe da shi a ranta tana kara shan alwashi sai ta wulakanta Zahrah matukar ta fito. ----- Tun da nake a rayuwata ban taɓa cin karo da irin wannan abin ba, domin kuwa ban zaci mangyad'a mai zafi zata watsa min ba, dafe goshina nayi ina mamakin kishinta. Ina zaune har su Addah suka dawo. Muna zaune ana cin abinci kawai muka ga mutanen Yallabai sun shigo cikin dakin, basu yi magana ba suka dauke ni. Zasu fita dani nace musu. "Ina da karamin goyo don Allah ku bar ni na dauke ta." Haka suka fita dani, dariya Addah takamayi tana cin abinci."Allah yasa su mata abinda ya wuce tunaninta." "Kenan ke ce kika hada mata rigimar?" "Eh nice!" Ummi bata kuma magana ba, tana mamakin Addah. Da suka wuce dani can wajen garin suka ajiye ni a gabanshi. "Kuje!" Kaina yana sunkuye. "Ke meye ya haɗa ki da Sultan?" Da sauri na d'ago kaina ina kallonshi, fuskarshi a rufe sai idanun shi kawai nake gani. Sake daka min tsawa yayi, na fashe da kuka, musamman da ya fidda wuka tsirararta. " Ban san shi ba." Na fada ina ja da baya, "Meye alakarki da Yazid?" Wani irin curewa yayan hanjina suka yi, jikina ya dauki wani bala'in rawa, na ja da baya ina girgiza kai. "Ba zaki gaya min ba kenan?" Ya kara daka min tsawa, kuka na saka mishi me karfi ina faɗin. "wallahi babu kome." "Ok tashi ki gudu" da sauri na mike tare da diba a guje, sai dai ko wurin ban bari ba, na ci birki sakamakon kartin mazan da na gani sun tare ko ina. hankali na a matukar tashe na waiga na ga sun zagaye ni. "Daga yau kada na kara jin labarin kin hadu da shi ko kin shiga gidan, idan kuma kika kara sakewa kuka hadu ko?" Ya fisgo ni tare da yaga min riga har kasa, kare kirjina nayi ya saka kafa ya tokare ni sai da na fadi. Ba a tab'a tozarta ni irin na yau ba, domin yana tsaye a kaina ya cire gabanshi ya shiga sakar min fitsari a kaina, sauran suka kwashe da dariya. "Wannan wasa ne, wanda zan miki ba fitsari ba ne, tsakanin cinyoyinki zan raba, nayi sukuwa a akanki yadda zaki ji rad'ad'in haka a ranki, naji labarin baki tab'a karo da namiji ba." Ya maida abin shi ya matsa a kaina, ya d'ago kaina ya dinga marina. Sai da naji kamar fuskar bata jikina, na karshe ne ya mare ni akan idanuna. "na tsane ki daga yadda Sultan yake zubar da kimarshi akanki." Suna gamawa suka watse daga wurin aka bar ni babu kowa. Haka na mike a hankali naji wani abu ya cika min zuciya na kasa kuka, har na kusa shiga gida, tun kafin na isa gidan nake jin Ihun Baby. Har na isa babu wanda ya kulata asalima a duhu suke. Banɗaki na Wuce ina ta kwara ruwa, ina wanke jikina sai da na wanke ko ina sannan na koma dakin. Na dauke ta tare da rungumarta ina sheshekar kuka, daga Addah har Ummi babu wanda ya ce min, nayi shiru a hankali barci ya dauke ni, ga ciwon da idanuna suke domin ina ga da wani abu ya mare ni ba da hannu ba. Sai asuba na tashi nayi alola nayi sallah, ina idarwa na juya na kwanta sai dai kamar yadda nake saka raina zan yi barci, ashe abin ba haka ba ne,. Wasu kartin maza ne suka kuma zuwa suka tafi da ni wannan karon ina ganinsu na dauki Babyna muka tafi, tun daga ranar ban kuma zama ko na minti biyar ba tare ina aiki ba, wahalace ta karu min kamar na mutu na huta, haka nake fama da aiki babu dare babu rana, sannan abinci sau biyu ake bani sai yanzu na fahimci akwai iyakata akwai iyakar wasu, Yazid iyakar wasu ne, shi din duniyar wasu ne da zarar na sake wani abu ya kara had'a ni da shi tabbas zan iya fuskantar mutuwa. Haka yasa nake addu'a ba dare ba rana, ina gayawa Ubangiji ya kawo min mafita da karshen wannan halin da nake ciki. ----- A bangaren Yazid babu ranar da ba zai tambaye su Zeehrah ba, an kai mata abinci Ya Baby take, babban burinshi ciwonshi ya warke ya tafi ya ganta, domin baya iya fita ko waje ne, yana cikin gida yana fama da ciwon. Akwai wani abu da dayawanmu mata bamu gane ba, shine idan har namiji ya lakato batun dating da wata mace mafi alkhairi mu kyale shi, mu zuba mishi idanu. Idan kuwa muka ce zamu yi magana. Tow kuwa ya dinga abun da zai b'ata mana rai. Gashi ko sati ba ayi ba, Aseem da Sharif suka saka dakyar ya fito Reshmah, amma abin da tayi ya tab'a zuciyarshi, sannan ba karamin hakuri da juriya yake da shi ba, domin da mace ce aka watsa mata mai da ba karamin jinya zata yi ba. Amma dake akwai kulawa kwanciyar hankali da nutsuwa kuma ana mishi kome ko wurin had'a magungunan shi baya fita anan ake mishi kome, tun ranar da abin ya faru Reshmah bata kwana a gidan da akai ta ba, amma kuma zaman babu dad'i. A wannan daren da sukayi abin da ya faru duk shirinsu ne. Ita da Yaranta shi Aseem yana tare da Yazid babu abin da ya sani. *** Niamey. Tunda farko da ace ta san matsalar nan na shi tabbas ko zata rasa rayuwarta ba zata tab'a barin shi da ciwon ba, "Hajiya!" Salamatu ta kira sunanta. "Na'am!" Ta amsa a sanyayye, "Shayin yayi sanyi." "Tow!" A hankali ta dauki kofin ta kurba kana ta d'ago kai tana kallon Salamatu. "Hmmm! Alhaji ya tashi ne?" "Eh yana dakin motsa jiki." Ajiyar zuciya ta sauke, sannan ta ce mata. "Shi kenan jeki." Juyawa tayi zata fita Hajiya ta ce Mata. "Salamatu Aryan fa?" "Tun dazun ya shigo suna tare da bakon Marad'i." Murmushi tayi sannan ta ce mata. "Shi kenan na gode." Tana fita magani ta dauka ta sha, sannan ta dan kishingid'a tana kallon gefe guda. Wani irin sakaci tayi da rayuwar Majid ya lalace haka. Hawayen da ta gaza tare shi yake zuba mata, tana jin kamar tadau ciwon a jikinshi ta dorawa kanta, bata son ta ce bata yafewa Alhaji Mamman Ba'are ba, amma tabbas shi ya lalata mata nata rayuwar da har haka ya shafi na wanda bai ji ba bai gani ba. Yadda take kuka kamar karamar yarinya, domin Majid yana matukar bata tausayi, idan ta cire Matsalar Amaan tow Majid ya sauke kaso mai nauyi a zucuyarta. Bakiɗaya ta rasa inda zata saka hakkin Majid domin abin da ya same shi kamar laifinta ne, da bata yarda ta bi Alhaji Mamman Ba'are a lokacin ba tow da wannan abin bai same shi ba. --- Amaan Mamman Ba'are. Kallon juna suka yi, kamar zasu cinye juna kafin murmushi ya kwace mishi ya ce mishi. "Ban yarda da abin da kake faɗa ba." Lumshe idanunshi yayi ya bude a kan fuskar Sajjid. "Baka yarda ba kenan?" Dariya Amaan ya saka yana faɗin. "Lallai kuwa, hmm dukiyarshi bata da wani amfani tunda babu me ci haka zata yi ta habbaka yadda zamu san me zamu yi mishi." "Hmm! Ban yarda Abdul Majid bai da lafiya ba. Na fi yarda da cewa bai da ra'ayin aure amma ace bai da lafiya ai maganar kawai tatsuniya ce." Mikewa Amaan yayi yana faɗin. "Zan tafi idan lokacin da ka sani sai ka tsaya muyi magana." Sajjid bai ce mishi kome ba, har ya bar gidan. Wani irin murmushi Sajjid din yayi, ya kira Mahaifiyarshi ya gaya mata, shiru tayi, yanzu ne ya dace ta tashi ayi ta ta kare ko kuma ayi ta kasa. Idan Majid bai da lafiya kason shi Hajiya da Yan uwanshi ne zasu more tunda mutuwa zai yi a wurin aikinshi. "Mutuwar Abdul Majid Mamman Ba'are baya hannuna, amma nasan dukiyarshi zata iya dawowa hannunmu idan har aka bi a sannu. Kana jiye mana abin da zai kai Sa'adatu lahira." "Ba iya shi ba, akwai labarin da nake son nasani amma yaki gaya min. Ina son idan na samu labarin zan gaya miki." "Wane labari ne haka?" "Ya ce min a sanadin haka aka kai, Majid gidan kangararun Yara, domin fitar da Hajiya tayi. A wannan ranar shi ya saka Majid ya fara sace-sace har aka kai shi gidan horar. Idan ya tuna abin yana jin tsanar Hajiya." "Kai haka ya ce? Lallai nayi babban kamu. Tow kada ka sake ya fahimci cewa kana son jin lallai ya baka labarin, zan cigaba da aikina anan da kanshi zai baka labarin." "Shi kenan, amma ni gaskiya na gaji da wannan harkar." Shiru tayi ta ce mishi. "Na dan lokaci ne, ka saka idanu yadda zan tarwatsa Sa'adatu." "Yawwa Hajajju sabuwar Chairwoman ba BA'ARE GOLDEN EMPIRES!" Murmushi ta saki ya sauke wayar yana faɗin. "Hajiya Tani, kifi na ganinki mai jar koma. Ina harinki kina harin Hajiya Sa'adatu." --- Hajiya Tani. Jikinta ne ya bata ana tsaye a falonta, ta kashe wayar ta fito, ganin Hajiya Fauziya Mamman Ba'are yasa ta sha jinin jikinta kamar babu abinda ya faru ta kakaro murmushi ta ce mata. "Kina son wani abu ne?" Girgiza kai tayi ta ce mata. "Naji kin ambaci sunan Sa'adatu ne akwai abinda ya faru ne?" Wani sirrintaciyar murmushi tayi tana faɗin. "Hajiya Fauziya taya zan yarda na gaya miki gaskiya, bayan kema idan kin samu yakata zaki yi." "Haba wani yakarki? Kawai gaya min zan taimaka miki da yad'a shi." " Ba yad'awa ba ne, so nake ki saka ya Haladu yabawa Abdul Majid auren Afiyyah." "Kina ganin haka mafita ne?" Girgza kai Tani tayi tana faɗin. "Haka shine zai bamu damar fitar da abinda kike son faɗa." "Akwai labari kenan!" Murmushi Tani tayi tana faɗin. "Mai girgixawa." Daga haka suka fita, kamar yadda suke son sanin me ya janyowa Majid ya samu wannan matsalar duk yadda aka yi Hajiya tana da wani dark secret da take boyewa idan haka ne kuwa tow tabbas Hajiya ta kusan mutuwa. ---- Kure volume na radio Nana tayi tana niman gidan rediyon Faransa, tana ƙara ware idanun. Bubbuga radio tayi tana tsaki. "Mtsew, ƙarfen nasara babu tabbas yanzu wannan raidiyon wai batiri yake nima." "Assalamu alaikum!" "Waye nan?" Ta amsa cikin masifa tana mikewa. "Nana Fauziya ce!" "Kin kashe maganar bashin da Mulaika taci?" Wani shiru Hajiya Fauziya tayi kafin ta ce. "Ayya Nana daga zuwa gaishe ki sai ki gwale ni." "Ahtow ai gaskiya na faɗa, ko kunyar Harirah baki ji, tana tattalin dukiyar Yaranta babu ruwanta iya shi ne a gabanta, ke baki da aiki sai bin malamai da munafunci, wallahi ina rabaki da wutar jahannama." Ta fada mata tana wani zumburo baki. "Wai Hajiya na hango wani abu da ba kowa ya hango ba, shine nace duk da babu wanda yake kallona da idon rahama." Tayi shiru gashi Allah ya jarabci Nana da bala'in son jin gulma don haka tayi kwalkwal da idanunta. "Ina jinki bana son munafurci zaki fara magana kiyi shiru." "Hmmmm Nana ai ban san yadda zaki ɗauki maganar ba, shi yasa na kasa faɗa miki." Inji Hajiya Fauziya.. Wani galla mata harara Nana tayi ta ce mata. "Kin san na tsani a zo bani labari a tsaya ana kame-kame uwar me idanunki ya hango wanda nawa idanun bai hango ba?" "Hmmm Hajiya naga Maisarah tana wurin dangin Mamanta, kuma kin ga zata fi dacewa da Alhaji shine nace mai zai hana a hada Maisarah da shi." Ware manyan idanunta Nana tayi kafin ta ce mata. "Amma Fauziya Allah ya miki albarka, ina na tab'a tunanin hakan." "Amma Hajiya wani hanzari ba gudu ba, ko za a hada shi da Afiyyah ne?" B'ata rai Nana tayi tana faɗin. "wannan yar banza da shegen kugu kamar an zargawa biri igiya babu abinda zai hadata da bawan Allah tunda ai shi mutumin kirki ne, yarinyar nan ranar wasu irin kaya ta saka tana tafiya ina ganin jikinta Allah na tuba ita da Sajjidu kullum suna makale da juna kamar kadangaru ita dai wancan ko zuwa tayi kowa yasan iyayen Uwarta mutanen kirki ne, Turai kuma babu wanda bai san shaidaniya ba ce." Hadiye yawu Hajiya Fauziya tayi domin kawo bambancin Maisarah da Afiyyah a fili take. "Amma Nana don Allah kada kice nice na ce ya auri Maisarah, don kinsan Alhaji Karami zai kullace ni." Galla mata harara tayi tana faɗin. "Babu wanda ya isa Miki haka domin sai naci uwatai, ke da kika hada alkhairi sai na watsa miki kasa a idanun. Tashi ki je amma ki daina munafurci domin ba abun arziki ba ne " "Shi kenan Hajiya naji sannan Hajiya kin ji labarin Aryan shine sabon shugaban Kamfani ba Abdul Majid ba!" Sake Radio din hannunta tayi ya fadi kasa ta ce. "Ke dai had'a husuma ya zame miki jini ko? Ina zaki aikata abin arziki amma munafurci ya saka ki sabule ladar ki. Taya Majid zai bawa wancan kodadden bawan shugabancin ai sai dai Sa'adatu ta cigaba da rikewa har ya gama yawon sojancinshi." "Hmmmm! Wallahi kuwa Nana ki tambayi Sa'adatun idan karya na miki ranar Monday zasu tabbatar da shi, sannan ya rabawa yan dakinsu matsayi ko kara bai raba mana ba." "Lallai wato shine suke niman kashe shi, idan bai basu shugabancin kamfanin ba, kuma babu babban munafukar kamar Sa'adatu domin ta munafurce ni. Da ta gaya min da na saka Haladu ko Kamilu dayansu ya rike kamfanin abin gado ne da ba za abawa wani ya rike ba. Yau idan ban ci mutuncin Sa'adatu ba, shegiya Uwata ta haifan." Ta tashi don masifa a juye ta saka hijab dinta, ta nufi hanyar waje, Hajiya Fauziya tana dariya a ranta. Har kofar Hajiya ta rakota, sannan tayi tafiyarta ita daya ta jefi tsuntsu biyu da dutse daya, ta juya lamarin maganar auren Afiyyah da Majid, an maida maganar kan Maisarah da Majid, yanzu zata sake hada wani rigimar tsakanin Nana da Afiyyah, sannan ta nuna babu ruwanta a zancen kamar bata sani ba. A fusace Nana tana bala'i ta shiga falon Hajiya, suna falon har da Majid kuma fa tun farko an zo an gaya mata ta ce babu ruwan kowa kamfanin sune amma yanzu da jaraba take cinta tazo sauke jaraba. Kallo daya yayi mata, ta koma daya daga cikin sofar falon ta zauna. " Sai wiki-wiki take da idanuws. "Barka da yammaci Nana " " yawwa Sa'adatu!" Ta fada a dakile. "Nana ya kike?" Inji Aryan yana cika bakinshi da kankana. "Kundun Ubanka mara mutunci, Abdul Majid kaga yadda yake min gaisuwar yan tasha." "Haushin kaza huce kan dami, Nana kowa yasan kin shigo da jaraba ne, don haka ba zaki fara a kaina ba." "Alhaji kai kake daure mishi gindi yake min rashin kunya, don kawai na damu da ku? Fisabillahi Alhaji kaf gidan nan a rasa waye zaka bawa shugabancin kamfani sai wannan me kama da zabiya?" Sai kuma ta kama share hawaye tana faɗin. "Yanzu Sa'adatu da saninki Alhaji ya dauki jagorancin nan ya bawa Aryan wannan mara kunyar yaron ni dai ban amince ba." Ta fada tana yatsina fuska. Mika mata bowl din fruit din da Hajiya da kanta ta haɗawa Majid yayi. "Sha." A hankali ta dauka tana sha, ta ce mishi. "Duk gidan nan babu wanda ya kaika mutuncin da Alkhairi." "Sha kawai Hajiya!" Haka ta sha, bata gama sha ba Aryan ya tawo da gasashen namar kaza ya ajiye a gaban Majid. Kallonshi tayi tana son ta hango iyakar muguntarshi. "Nana me kike son gani a fuskar." Hadiye yawu tayi tana faɗin. "Lamari na duniya akan abin duniya sai a iya kashe mutum, kai Alhaji ina fatan ba barazana yayi maka ba ko?" Ta fada tana kallon Majid din, "to naga ga Yan uwan Ubanka, ka tsallake su ka bawa mara kunya kamfani." Ganin Majid yana cin namar shi babu abinda ya ce mata, yasa ta ci-gaba da cewa. "Shi namar ka tabbatar da cewa babu guba a cikinshi?" Cak ya tsaya da taunar namar, yana me kallon Aryan ɗin, "Kika ce me?" "Hmm nace ka tabbatar babu guba." "Ai tun a ya'yan itacen da kika sha nake tsammanin ya na zuba gubar yadda kike tunani." Harararshi tayi tana faɗin. "Gubar zaka zuba ka fada min? Sa'adatu ki gayawa wannan futsararen dan naki ya daina shiga harkata da Alhaji " "Tunda tare kika ganmu haka zaki bar mu, sannan da kike cewa a hana ni babu abinda zaisa a hana ni sai kiyi kuma." Ya fada a fusace zai bar falon, "dawo ka zauna." Inji Majid ita kan Hajiya babu ruwanta. "Tow fisabilillahi zata zo tana irin wannan maganar, idan wani bai yarda ba wani ai zai yarda." "Koma ka zauna " Zama yayi yana huci kamar zai fashe da kuka,"Nana asalin abinda ya kawo ki, akan kamfanin da na bawa Aryan ne ko? Dama can Aryan shine Magajin Mamman Ba'are,, Ni aikina yana da muhimmanci, idan nace xan riƙe kamfanin ba za a samu abin da ake so ba, Nana ni soja ne kawai abinda na sani na koma bakin iyakar kasa ko ruwa na kare al'umma, domin wannan aka haife ni." "Tow me yasa ba zaka bawa yan uwan Babanka ba." "Kowa ya nemo na shi dukiyar Mamman Ba'are na Yaran Mamman ba'are ne, don haka kada na kuma jin haka idan ba haka ba, sai na saka an bincika min ke da laifin yunkurin hada husuma." Ya ciro bindigarshi ya ajiye a gabanta.. #Dambujeeeeeee🥳 [2/26, 7:37 PM] Cutie cutie pie: *BAƘIN HAURE....🐾🐾* {Greed for Money is the roots of all evils🫀} Arewabooks:maidambu41 Wattpad:Mai_Dambu Mallakar:Mai_Dambu *025* "Daga yau kada na kara jin kin ce wani abu akan Aryan, ko me kuwa idanunki ya gani ko kunnuwarki suka ji, babu ruwanki da Yan uwana. Ba zaki raba ni da shi ba ko ina raye ko bana raye Aryan shine Magajin Mamman Ba'are, kin fahimta bani da shakikin da ya kai shi. Sannan ni ba d'anki ba ne da zaki tsara ko ki saka mishi idanu akan abinda yake, Waccan da kika ce ba zaki amshe ta a surukarki ba ita ke da ikon saka ni ta hana ni. " Jikinta yayi matukar sanyi, tabbas a duk lokacin da zai yi magana yana gaya mata ba ita ta haife shi ba, Sa'adatu ce ta haife shi. Kafin ta gama tunanin abin da yake gaya mata, ya kara dukarta da wasu kalaman masu zafi da ciwo. "Kamfani namu ne, kuma ni na saka Hajiya tayi murabus. Domin a cigaba daga inda ta tsaya Hajiya ni da kika ganni ina son mahaifiyata, kuma ina son ganin ta huta idan kina son mu zauna lafiya da ke, ki fita hanyarta idan ba haka ba duk abinda ya fito bakina sai na gaya miki. Ba iya ke ba duk wanda ya ƙara shiga harkarmu sai na kure mishi lissafinshi. And ki tattara kafarki, ki koma inda kike zaune bangaren Sa'adatu na Yaranta ne babu wanda ya isa kara zuwa ya shiga tsakanin Yaranta. Da kika ce tana ganin abin da nake aiakatawa tana gani, kema kina ganin lokacin da d'anki yake wulakantata kin iya dakatar da shi?" "Majid!" Hajiya ta kira sunanshi, domin bata son abin da zai d'aga mishi ciwonshi, su shiga damuwa. "Hajiya kada ki damu, ita ta manta lokacin da take fadar cewa a kuntata miki ko zan bi hanyar da suke so, bayan da saninta d'anta ya haramta min ganin Mahaifiyata, ta manta da saninta danta ya nisanta ni da kowa nawa, yanzu Nana don bakya tsoron Allah kin zo zaki hada ni faɗa da dan uwana, ki tashi tun muna girmama juna ki fita kafin raina ya b'aci mu samu matsala." Bai gama rufe baki ba,Nana ta mike a hankali zata fita Aryan ya ce mata. "ki gyara hijabinki." "Tow!" Ta fada tana gyara zaman hijab din, har zata fita ta juya tana kallon Abdul Majid da yake cin naman a nutse. "Ka yafe min abin da nayi maka, nasan na cutar daku amma don Allah a wurinku nake samun damar yin yadda naso don Allah ka yafe min." Ta sharce hawayen da yake zubo mata, sannan ta fita tana kukan sarari da na zuci. "Baka kyauta ba, da baka gaya mata haka ba." Murmushi yayi ya cigaba da cin abincin shi, "Hajiya idan ba haka yayi mata ba, Nana bata da kirki haka kawai xata mai dani abin zargi." Inji Aryan yana cika bakinshi da namar gaban Abdul. Harara ya watsa mishi yana faɗin. "Kaje kaci naka mana." Da sauri ya wafci namar yana faɗin. "Ba zan iya cin nawa ba, naka zanci gaskiya wannan gashin yafi nawa dad'i." Lokacin da Nana ta koma taci kuka har ta godewa Allah, tana me kara ganin laifinta ne duk kiyayyar da Yaran Hajiya suka nuna mata laifinta ne. Kamata yayi ace su taso sama da sauran jikokinta tunda ba karamin dadi taji da aka haifi Abdul Majid ba, amma daga baya kawai ta tsane su idan ta tuna cewa a caca aka ciyo uwarsu sai ta ga kamar sun zo da wani irin gurbataccen jini mara kyau da amfani. *** Zahrah. Wata na guda ina nan bana kome sai aikin noma, idan na koma dakinmu kuwa idan na kwanta dakyar nake barci, abincin da nake ci baya isa ta Sannan duk tsawon wannan lokacin, ana kawo min abin da Yallabai yake kawo min, Addah take amsa tana cinyewa ko Ummi bata sani ba, ranar da dubunta ya cika, ranar ya fara fita domin ya warke kamar bashi ba, da kanshi ya kawo min abincin sannan itama Reshmah bata san cewa zai futa har ya nimo ni ba, tunaninta ai abinda ya faru zai saka mishi shakkar nima ta ne, sai dai shi namiji ne da yake da ra'ayin kanshi, babu wanda ya isa ya sauya mishi. Lokacin da ya zo ya zauna yana jiran na dawo har dare yayi yana zaune a wurin karewa da wayar da suke amfani da shi a dan kauyen, ya kira Aseem ya kawo mishi abin sallah, a wurin suka yi sallah suna hira, tunda ya zo Addah ta leko ta ganshi tsoro ya kama ta, yana tsaye a wurin mamaki ne yake kara kama shi ya cewa Aseem ." Kuma kai ne kake kawo mata abincin?" "A'a Ghadafi ne!" Gyada kai yayi. Har aka yi sallah Isha ban dawo ba yasa aka tara kowa. "Ghadafi ita kake kawowa abincin?" "Eh Sultan" ya fada yana kallon Adda. Dafe kirji tayi tana kallon shi. Zuba mata idanu yayi, ya cewa Aseem. "Ita wannan ita ce ta je ta gayawa Reshmah ina fita da Zeehrah!" A fusace Aseem ya mike, "kyale ta ku tambayeta." Fito da Addah aka yi ta zube akan gwiwarta. "Ina kike kai abincin da ake kawo miki " "ina bata ne!" Ta fada bakinta yana rawa. "Karya take Sultan, cinyewa take kullum aka kawo, sannan Zahrah yau ce bata dawo da wuri ba, tana can lambun wiwi tana noma a wurin.." Sakin baki yayi yana jin kamar a mafarki yake jin labarin inda Zahrah take. Bai ce uffan ba ya mike tare da barin wurin. Aseem yana take mishi baya, ita kuma Addah tana zaune a wurin da wasu masu gadinsu. "Ummi Allah ya tsine miki albarka." "Ash, Addah babu abinda zai same ni domin kuwa tsinuwar da Zuzu take miki a duk lokacin da wani ya kwanta da ita ya ishe ki zuwa lahira lokacinki bai yi ba, Addah da na haifi ɗan da xan tura shi karuwanci gara na kare rayuwata babu d'a babu jika in gaya miki, Munaisah ma da muka yi raba dai-dai akanta. Hakkin Uwarta da ta bari kika kashe mata ne. Bari na gaya miki wallahi ba zan barki ki karasa cutar da Zahra ba, muna nan sai na saka an illataki kafin mu bar nan wallahi." Shiru Addah tayi tana tsoron abin da zai kuma faruwa. ---- Yau kan babu abincin da aka kawo min, nayi noman har na kasa domin idan na sunkuya sai na fara jin amai, yunkurin aman yasa karfina ya ƙare, har rana ta fadi ina kwance a wurin, ita kanta Baby kamar bata da lafiya, jikinta yayi zafi rau. Haka yasa na kwanta a wurin daga nan ban kuma sanin kome ba, domin duhu ya lullube gani na. Kamar daga can nesa nake jin ana kiran sunana, dakyar na bude idanu kamar shi na gani, na saba yin mafarkin yana zuwa ya ce gashi ya samu lafiya ya dawo kenan, sai na kara lumshe idanuna. Har tsawon kwanaki biyu, ban san waye a kaina ba, a wannan kwananki biyu Baby ta murmure kamar ba ita ba, nice ulcer ta min mugun kamu, saboda babu abinci me kyau. Sannan jinin jikina yayi kasa bani da wadataccen jini. Don haka ya bada na shi aka saka min, na cigaba da samun kulawa har rana ta uku sannan na farka. Ina ganinshi na zuba mishi ido. "Zeehrah ya jikin?" " Da sauki" "Allah ya baƙi lafiya!" Daga haka na lumshe idanuwa na, haka ya gama zama har ya gaji ban ce mishi cikanka ba. Asalima koyawa kaina fita harkar shi nake son nayi kamar yadda suke bukata, don haka na fita hanyar shi ban kuma shiga rayuwarshi, washe gari da aka kawo min Baby tayi bul-bul da ita gwanin ban sha'awa. "Maa Yallabai ya ce kada ki kara bata nono tana shan madara." Yarinyar da bata wuce wata uku ba. Kamar tasan abin da nake tunani a raina, sai gashi ta ce min."Eh akwai madarar da zai mata,kema Dr ya ce zai bada magani a baki." Ban ji dadi ba, amma kuma zaman mu a asibitin ya sani murmurewa nima. Sai dai idan yazo bana mishi magna, haka idan yazo yayi ta magana juya mishi baya nake, haka nurse ta kawo min maganin da zan fara sha, rabin maganin na gyaran jiki ne da SUPPLEMENT na islamic. Ban taɓa zatan akwaisu ba, haka nayi ta sha har aka sallame ni, da na koma dakinmu a lokacin ne na fahimci Addah har lokacin bata dawo ba, sannan an sauke min aikin da nake yi, bana aikin fari balle baki, ina nan daga na tsoma biyar sai na wanke goma. Kwanana biyu ina barci na dora Baby a cikina ya shigo ya d'aga ta. Bude idanu nayi ina kallonshi, kafin na juyar da kaina. "Zeehrah wai me na miki ne?" "Baka min kome ba, kai ne dai nayi maka laifi" "Ban gane ba?" "Ok zaka gane!" Na fada ina kokarin sauka daga gadon, rike hannu yayi yana faɗin."kiyi hakuri ki gaya min laifina." Girgiza kai nayi nace mishi. "Wallahi baka min laifin kome ba, kawai bana son kana zuwa inda nake ne don Allah." Yadda nayi maganar yasa shi kallona. "Meye ya faru?" " A hankali na zare hannuna cikin na shi, a kundin ƙaddarata ba zan tab'a cike shi ba tare da na ambaci Yazid ba, domin shine mutum na farko da ya tare min masifar matarshi. Hakazalika ba zan tab'a rufe labarina ba tare da gayawa duniya waye shiga gare ni ba, ya min alkhairin da babu wanda yayi min, ƙaddarata rubutacciyar al'amari ce da ba zata tab'a shallake ni ba tare da na bayyanawa duniya girmansa da darajarshi ba." "Ki gaya min meye nayi miki da baki son na tsaya a hanyarki." Yadda yayi maganar cikin Rarrashi yasani fashewa da kuka idan na tuna abinda mutanen nan suka min sai naji kamar zan mutu, da b'acin rai. Rufe idanuna nayi gam naki kallonshi, a hankali na had'a kaina da gwiwa ina wani irin kuka na takaici da bakinciki. Cizon bakinshi yayi ya ce min "me kike so?" D'ago jajjayen idanuna nayi ina kallonshi kafin na ce mishi. "Kawai ka rabu da ni." "Ba zan iya ba. domin lokacin da zuciyata ta had'e dake bata yi shawara da ni ba, ni kuma bana jin a raina zan iya rabuwa dake don kawai kin ce na rabu dake, kiyi tunani da kyau." "Babu inda zan yi tunanin kawai ka rabu da ni!" Na faɗa cikin kuka. "Fadimatul Zahra'u, ni fa akan abinda nake so babu abin da ba zan aikata ba. Gaya min me aka miki kike kuka haka.". "ni yaushe nace maka anyi min wani abu, don Allah ka rufa asiri kada ka ja min sabon masifa, kawai ka tafi ka bar ni, idan da hali ka kore ni daga rayuwarka." Rike hannuna yayi yana kallon kantar hannuna, kafin ya ce min."su waɗanda suka miki barazana zasu miki wani abu har suke bautar dake baki gaya musu kina da Sultan Yazid Hamir ba ne?" "Kai ba iyakata ba ne, su kuma kai ne iyakarsu, ina da tawa rayuwar a wani wurin don Allah ka yi hakuri ka barni." Na fada da ƙarfi. Shigowa Aseem yayi d'aga mishi hannu yayi alamar ya tafi ya ce min. "Sun miki barazanar zasu kashe ki ko? Ko sun miki barazanar zasu maki fyade ne? Kai ko sun Miki..." Wani irin zabura nayi tare da kame jikina, da yake rawa sakamakon hada'a idanu da nayi da mutimin da kullum sai ya min kashedi akan Yallabai. Bin inda nake kallo yayi da idanu yaga na sunkuyar da kaina ina kara tattare rigar jikina ina faɗin."don Allah ka tafi kaji ka rabu dani." Kusan ban san fuskar shi ba, amma da safe idan na fita ina yawan had'a idanu da shi, haka yasa na karanci kwayar idanuwanshi, ko bai magana ba, nasan shine . "Darda!" Ya kira sunanshi, "Na'am Sultan!". Wani irin tsalle nayi na koma ƙasar gadon, domin shi din ne fuskarshi da Muryar shi ya tabbatar min da shine, na kame jikina da yake rawa na ce. "Don Allah ka tafi, ka tafi bana son ganinka wallahi bana kaunar ganinka ka rufa min asiri da halin da na shiga." Na fada cikin matsanancin kuka da ihu. Ganin haka ya sashi barin dakin asibitin. Darda ya bi bayanshi. "Aseem ka saka Darda ya gaya maka me suka yiwa Zeehrah!" "Wallahi Sultan Amiratul ta saka mu, mu mata barazana." Shiru yayi yana zare Idanu, ai yasan matuƙar bai magana ba shine a ruwa. Don haka yayi magana da wuri, koda suka isa gidan yarin. Zubewa Darda yayi ya lissafo mishi wadanda suke da hannu a cikin abin da suka mata. Duk a ka tawo dasu. "Me kuka mata?" Da kanshi yayi tambayar. Jikinsu na rawa suka nuna Darda. "Shi yace zai mata fyade bayan ya mata fitsari kai." Ware manyan idanunshi yayi yana tuno yadda tayi ta kame jikinta. "Abin da ka aikata kenan?" Inji Aseem. "Tuba nake a yafe min ba zan kuma ba. Wallahi saka ni aka yi, ba zan kara ba " murmushi yayi sannan ya ce mishi. "ka yanke mishi hukunci daidai da laifinshi. "Sultan ka yafe masa, ba zai kuma ba." "Ita yarinyar bata da gata ko? Babu wanda ya damu da ita tunda uwarta da Ubanta sun watsota duniya basu san dajararta ba ko? Gaya min abin da yayi mata akwai adalci a cikin shi, itama mutum ce fa. " "Bai kyauta ba " "Aseem ina son Yarinyar shi yasa bana kaunar kukanta, idan har ban bata tsaro da kulawa ba, taya zan ji da abinda yake raina " Haka ya mike yana faɗin. "Ka hukunta shi nace." Ya fita, gidansa ya wuce yabar shi ya samu Reshmah. Share ta yayi bai kuma kulata ba, domin idan yayi magana zata kuma fitar da hanyar da zata kuntattawa Zeehrah. Lokaci yayi da zai koma aljeria. Dama rabon ya hadu da ita yasa ya kasa komawa, a yanzu kuwa babu wanda ya isa ya shiga tsakaninsu koda kuwa mutuwa ce sai dai ta dauke su tare. Haka ya gama tsara yadda zai tafi da komin shi Addah kuwa, sakawa yayi aka mata duka, har sai da suka tab'a mata lafiyar idanunta ɗaya. Koda aka dawo da ita kallo ɗaya Ummi ta mata ta ce mata, "Kina tsammanin daga nan zaki kara samun sukuni ne? Kamar yadda kika saka rayuwar wacce bata ji ba bata gani ba a gaba haka zaki rasa kome naki." Addah bata yi Magana ba, sai dai dukarta da tab'a mata idanu ya kara haifar mata da bala'in tsanar Zahrah. Sai ta ga bayan Zahrah, sannan abinda ta fahimta Yazid niman kuɗinshi ba don ya cutar da kowa ba ne, niman kuɗinshi akan kanshi yake daukar kasada, ba kamar wancan mutumin da yake sayan Sassan dan Adam tare da sayan yan mata domin karuwanci ba. *** Sati biyu nayi sannan na dawo, a lokacin naga idanun Addah yayi wani bala'in girma gashi jini ya kwanta a cikinshi. "Addah baki je asibiti ba?" "Na je asibiti kika tambaye ni? Nace na je asibiti fa? Sai na illata rayuwarki Zahra matukar ina numfashi." "Baki illatata ba ma an kashe miki idanu, idan kika lakace ta sai dai lahira tayi bako." "Ban yi dake ba!" "Dama baki isa kiyi dani ba Addah." "Mara kunya kawai " "Marasa kunyar suna dayawa!" "Addah ki kyaleta muyi maganar idanunki." "Kinci Ubanki shegiya munafika." "Kayya da ina nufinki da sharri da kullum kaina zai tsaya, amma dake zuciyata daya ba zan iya nufarki da sharri ba." Na gaya mata, domin zuwa yanzu addah ta fara isata, ban san yadda zan yi da itaba amma na gaji da halin ta, "idan kina son idanunki,ki shirya gobe ki ga likita." D'ago kai tayi tana kallona, "Annamimiya kina min haka ne don na yafe miki!" Inji ta. "Idan kin so kada ki yafe min Addah wallahi babu abinda zai tsaya, bakya gabana asalima tausayi kike bani, daga lokacin da ƙaddarar Allah ta rabamu wallahi billahi azim sai kin yi fatar da ina tare da ke. Ba zan ce Hakkina yayi ta bibiyarki ba, amma nasan zaki so ina tare dake domin ni daya ce kawai. Zan tsaya a gefenki ki tuna da kin haifi Zuzuna, sannan ba zance nayafe muku ba daga ke har ita sai ranar da muka hadu ta gaya min dalilinta na cutar dani babu hujja. Idan yayi miki muje a duba idanun idan bai miki ba, ki zauna da shi Allah ya baƙi lafiya." Daga haka na kyaleta ina zan iya da bakin hali, bakiɗaya bata kanta take ba, hanyar da zata cutar dani kawai take nima sai kace na tare mata wani abu. *** Niamey. "Alhaji gaya min ina ke maka ciwon?" Kasa d'ago kai yayi ya kalleta. Kuma yayi shiru kamar baya wurin. "Kace jibi zaka tafi ko? Idan ka tafi zaka ga likita a can ko?" Duk ta uzirawa kanta, gani take kamar laifinta ne da sakacinta. "Alhaji" can kasan makoshinsa ya ce . "Hajiya lafiyata lau." "Ina lafiya mm, zan zo na ganka." "Assalamu alaikum!" Afiyyah ta shigo cikin nutsuwa domin duk rawar kanta da iyayinta, tana shakkar Majid da Aryan. "Wa'alaikimus Salam!" Hajiya ta amsa tana kallonta cikin kulawa. "Hajiya wai kizo keda Hammayo inji Nana!" "Tow shikenan ki ce mata gamu nan!" A hankali ta fita cikin wani irin taku me tab'a zuciyar yan maza, tunda ta shigo kallo daya yayi mata bai kuma kallon ko inuwarta ba, harkar gabanshi ya ishe shi. "Muje Alhaji." Me yasa Nana ta kira su bayan abinda ya faru kwanakin baya bata kuma shiga harkar su ba. Tashi yayi ya haura sama ya sako wasu kayan shadda ce skyblue, anyi mata ɗinki yar shara. Ta cikin rigar wata farar riga ya saka me dogon hannu, sai hular da ya saka ta amshi fatarshi sosai. Turaren pure oud ya fesa, bakiɗaya dakin ya hargitse da kamshinsa me dad'i...... #Mai_Dambu [2/27, 10:56 AM] Cutie cutie pie: *BAƘIN HAURE....🐾🐾* {Greed for Money is the roots of all evils🫀} Arewabooks:maidambu41 Wattpad:Mai_Dambu Mallakar:Mai_Dambu ```Hajiya ga kaya nan Masha Allah, Available price Huluna da Mayafai, da na yara sai Wanda ranko yakeso gasunan kala kala, Hajiya muna dasu ba iya hulana da Mayafai ba, har da shadodin na fitar sallah, Hajiya domin hutar dake da fitar dake kunya na tanadi yadda ba zaku sha wahalar yawo kasuwa a cikin azumi ba, don haka kafin kishiyarki tazo ta sata au 🤣😹😂 kafin kishiyarki tazo ta saya na tayiwa mijinku shakara gara kizo ki sata au 😔🤣😹 baki ya saba gara kizo ki saya, barauniyar gida, kai Sarauniyar gida 😂😹 atow kayana na Uwaren gida da na Amare ne``` *TUNTUBE WANNAN NUMBER 08130269641* *026* Yadda ya karya hula zaka rantse cikakken bahaushe ne, amma yanayin fatarshi zai nuna maka cewa bai da alaka da hausawa. Lokacin da ya fito daga dakin shi, Hajiya tana kallonshi daga kasa, kamilalliyar fuskar shi, me cike da kamewa ta kalla sannan ta shiga tasbihi ga Allah madaukakin sarki. "Ya Allah ka tsare min bawan nan naka." Ta fada tana cigaba da tasbihi har ya iso inda take, takalmin kafarshi kawai abin dubawa ne. Haka ya wuce ta suka fita tana bayan shi yana gabanta, sai da suka isa wurin kofar ya bude mata, sannan suka shiga bangaren Nana, haka suka iske falon a cike, gaban Hajiya ne ya fadi, tunda ta gan su tasan Babu alkhairi a wannan zaman nasu, don haka ta shiga da addu'a a bakinta. "Assalamu alaikum jama'a, Barkanku dai." "Wa'alaikimun Salam, barkanki Sa'adatu." Yadda suka amsa mata, yasa jikinta ya kara bata akwai wani abu. Zama tayi a daya daga cikin kujerar falon, Shi kuma ya zauna a kasar kafarta. Sai da aka yi gaishe gaishe hankalinshi yana kan wayarshi. Kafin aka bude taron da addu'a. Shiru falon ya ɗauka aka rasa wanda zai fara magana, Hajiya Fauziya ta ce. "Nana kinyi shiru abin arziki ya tara mu ba na tsiya ba" "Eh wallahi fa, dama Sa'adatu." D'ago kai Hajiya tayi tana kallon Nana, baki daya sai ta cika mata idanu. "Na'am Nana!" "Hmmm dama dama!" "Dama me Nana?" "Wai cewa nayi a cikin yan matan gidan nan ya duba daya ya zab'a." "Ai shine maganar? Tow ai Nana na gaya miki tsakaninku ne na Familyn Ba'are, ni a caca aka ciyo ni gaki ga Majid din Allah ya baku sa'a." "Ashe akwai babban Al'amari Hajiya shine baku gayyace ni ba?" Inji Aryan yana shigowa falon, yadda yake tafiya zaka tabbatar da iskanci yake ji A ranshi. Domin kuwa bai kawo haka ba, shi dai yana shiga gidan ya ga basu nan, har zai fita yake tambayar Lawe yake gaya mashi ya fito ban daki ya ga fitarsu ta kofar Nana. Zama yayi a stool bakinciki ne ya kama Nana, tasan da babu Aryan zata iya rarrashin Majid,. Amma da Aryan yazo ko ta kulla sai ya kunce mata. "Alhajina Maisarah ko Afiyyah." Ajiye wayar shi yayi yana kallon yadda ta ririta fuska. Alamar tana son kada ya bata kunya. "Ni ba zan aure su ba, matar da zan aura Hajiyata ce zata nima min, sannan Nana na gaya miki ki daina shiga harkana baki ji ko." "A'a Alhaji!" Ta faɗa tana ware idanun tana kallon yadda ya saka hannu a cikin aljuhun rigar shi. Tasan bindigarshi zai ciro "Alhaji Fauziya uwar munafukai ce ta ce na had'aka aure da Maisarah da Afiyyah, wallahi ba tunanina ba ne, tunaninta ne." "Hajiya tashi muje!" Ya fada yana mikewa, "Kenan idan baka amshi auren nan ba yana nufin kai ba cikakken namiji ba ne? Ko dai baka da lafiya ana boye mana ne, aeeeeh da alamu mutumin hotiho ne, babu karfin da zai raxana mace, koda yake kai idan aka baka mace karshe a shiga hakkinta aikin sojan shi ya kamace ka." Inji Sajjid da ya fito tare da Amaan. "Idan hakan ce zata saka ya zama cikakken namiji, tow ba zai amshi auren ba. " Inji Hajiya ta juya tana kallon Tani. "Da alamu bata gaya maka cewa shi aure da Yaron ciki aure darajarsu ba daya ba ne, shi dan aure yana da wata isa da kamala da duk inda ya shiga sai an girmama shi domin iyayenshi sun san cewa ba zasu b'ata mishi gobenshi ba, duk da a caca aka ciyo ni, ban yi zaman dandi ba, zaman aure nayi na haifi kyawawan irin da babu irinsu." Sannan ta juya ga Amaan da yake zare idanu. Takawa tayi har inda yake ta ce mishi. "Kayi kokari muje!" Ta fada tana jin kamar ta fashe da kuka, ita kuma shi ne jarabawar ta, ace yaro baka isa kayi kome ba sai ya gayawa kowa. Kowa ma abokan gabanka waɗanda basu da buri sai ganin bayanka. "Hajiya ni fa ban gaya musu kome ba." Bata ce mishi cikanka ba, har suka isa falonta. Sakin hannunshi tayi ta zube a kujerar , tana kallonshi ranta a b'ace yake kuma abinda zuciyarta ke son faɗa zai iya saka ya kara lalacewa sama da yanzu, "Hajiya na rantse da Allah, ban fadi kome ba." "Gaskiya baka fadi kome ba, sharri aka maka ko? Taya wancan tsinannen ya san matsalarshi? Wato kai dai ina ga baka da banbanci da jaki, domin kwanyarka bata daukar lissafi." "Meeting din da za ayi gobe ka soke sunanshi a cikin board director." Inji hajiya ta kara kallon Aryan, "akai shi matsayin karamin ma'aikaci kamar kowa jahilcinshi ba zai bashi damar aiki ba." "A'a Hajiya, tsanar da Amaan yayi min ni ba zan tab'a mishi ba, tayiyu shi yana da dalilinsa, amma ni bani da hujjar tsanarshi. Don haka ki kyale shi a matsayinsa, haka da yayi min yana kara min son shine, domin akwai wani abu da yake boyewa sama da tsanar da yayi min ba iya tsana ce take fitowa daga kalamanshi ba, har da kauna da bai san yana min ba. Shi yasa nake mishi uziri.". Ya faɗa, kafin ya wuce dakinshi, rufe kofar dakin yayi ya jingina a jikin kofar. Yana jin kamar ya fashe da kuka, me yasa shi yake jin ciwo sama da kowa? Me yasa yake jin zafin haka? Da yana da wata hanya da ya nisanta kanshi da kasar nan bakiɗaya. Bayan barin Majid falon, Hajiya ta kalle shi, "ka ji dadinka wallahi, Allah ya shirye ka" tsaki Aryan yayi ya bar falon, hatta Matarshi sai da ta fahimci ranshi ya b'aci, don har dare bai da walwala. Sai lokutan sallah yake fito da shi, bakiɗaya sai ya tsangwame kanshi. Da dare Hajiya da kanta ta kai mishi ruwan tea, yana cikin duhun shi na fama dama tasan za ayi haka, "tashi ka sha ruwan zafi!" Tashi yayi zaune, ya amshi kofin tana tsaye akanshi ya sha ya ajiye kofin a gefen gadonshi, "Zaka yi aure!" Da sauri ya d'ago kai. "Eh zaka yi aure koda kuwa babu wani tarayya, idan kayi auren ka tafi da matarka." "Hajiya!" "Maisarah ta bar gidan nan tun kafin rasuwar Babanku, Sannan mahaifiyarta kawai take mu'amala da ita, sau biyu muna haduwa a Saudiya, tana son yin magana amma tana ganin Mahaifiyarta zata yi shiru mu gaisa." "Hajiya idan ta san ba zan mata..." "Kada ka damu, dazun na kira Hajiya Sanah na tambaye ta, ko tana da saurayi ne? Ta ce babu hankalina ya fi kwanciya da Maisarah domin Afiyyah suna tare da Sajjid, duk abinda zai haɗaka da Tani ina avoiding ɗinshi." "Hajiya!" "Kada ka ce min kome!"ta faɗa tana barin dakin, zuwa yanzu Hajiya tana son fitar da wani abin da ba kowa ya sani ba, daga ita sai Majid dangane da Mutuwar Mamman Ba'are, idan har tayi hi jack points, tow ba makawa zata iya saka wanda yayi kisan motsi. Duk da bata san meye ake shiryawa ba, sai dai tafi tunanin ana shirin da bata san ta inda xa a fito mata ba. *** Monday. A yau monday akwai batutuwa da yawa da ake son aiwatarwa a kamfanonin BA'ARE GOLDEN EMPIRES, sai dai wani abin da ya tab'a zuciyar al'umma shine tashi da samun labarin mutuwar babban manajan kamfanin. Daga Hajiya har yaranta hankalinsu a tashe yake, kuma abin tambayar anan shi ne, waye ya kashe shi? Shin kashe kansa yayi ne? Tow akan me? Majid kan kin saka kanshi yayi cikin maganar, kuma bai da niyyar haka kuma har Hajiya ta fahimci haka, shi yasa ta tsaya ita da Aryan suka yi ta shige da fice. A cikin kwanaki uku sun jigata, jinin Hajiya hawa yake yana sauka, dole Aneesah ta tsaya a gefen Aryan, ga sintirin yan sanda a kwanakin. Sai da aka kwashi sati daya ana abu ɗaya, karshe tafiyar Majid da bai samu yayi ba kenan, ya kara niman excuse. A cikin sati biyu da yin abin, aka ga wasu mutane haka kawai suka rufe Kamfanin. Tsawon awa takwas aka dauka, kafin aka bude kamfanin kamar babu abinda ya faru. Washi gari. Aka kai sakamakon office din Aryan suna tattaunawa da Majid da ya kawo mishi, "Yallabai gashi nan, sakamakon binciken da muka yi." Ya mikawa Aryan kallon Majid yayi kafin ya dauke kai, yana amsar takardan. Mikawa Majid yayi ya ajiye, yana kurbar coffee. "Mun gode!" Sannan mutumin ya fita, zama Aryan yayi ya fara bude takardar, mikawa Majid yayi, "ban fahimci abinda suke nufi ba." A hankali ya amsa yana faɗin. "Kiran da yayi kafin faruwar lamarin, sai sakon da aka turo mishi aka goge na barazana, sannan a daren da abin zai faru kamar bibiyar shi aka yi. Ka duba ka gani" "Wannan number kamar na san ta." "Amaan Mamman Ba'are!" Majid ya faɗa, tare da ajiye kofin. "Kada ka ce min!" Aryan ya faɗa yana zare idanu waje, "Tow yanzu ni da kai muna nan taya zan sani bayan an bar masu bincike sun yi aikinsu, ace abu sati daya a matsayinka na Chairman ka gaza yi, ok zan tafi tunda kome ya fito zan bar kasar nan yau. Amma kafin nan ka fara duba number na farko kafin na Amaan Mamman Ba'are." Saka number yayi a wayarshi, "Haladu Abdul Majid ba'are." Ya furta. Sai daya number kan babu baya ma amfani alamar an daina amfani da shi. "Don Allah ka tsaya a kammala binciken!" Aryan ya faɗa, shiru yayi bai ce mishi kome ba, har suka fita daga Office din. "Office dinka ko!" Sai kuma yayi shiru bai kara magana ba, har suka isa gida kafin su kara mika sakamakon ga yan sanda sai da suka ritsa Amaan. "Me Manaja yayi ka kashe shi?" "Ni kuma?" Ya fada a razane, "a ranar da zai mutu ka kira shi!" Majid ya faɗa yana kallon Aryan. Kamar ba da Amaan yake magana ba sannan ya cigaba da cewa. "Kunyi waya da shi na tsawon minti ashirin, wanda har Muryar ka ta fito." "Idan ka tsane ni, sai ka min sharri." Aryan zai magana ya dakatar da shi. "Kyale shi, ina daidai da shi." Ciro wayarshi yayi a cikin aljuhun riganshi, ya kunna. _Kada ka sake ka bawa Aryan wannan files din Sajjid idan ka sake ka bashi sai na kashe ka na gaya maka_ "Ina fatan ka fahimci wannan Muryar?" Shiru yayi yana kallonsu. "Bani na kashe shi ba wallahi." "Eh kowa ya sani ba kai ne ka kashe shi ba, amma me yasa ka faɗa zaka kashe shi?" "Tow ai barazana nayi mishi!" "Barazana da mutuwa?" *Yallabai Amaan nasan meke faruwa tsakaninka da Sajjid ni dai ba zan baka ba, amma ina maka fatan shirya idan kai me shiryuwa ne, idan ba zaka shiryu ba Ubangiji ya gaggauta kashe ka, amma ba zan bada Files din nan ba* "Hammayo akwai wani abu da Amaan yake aikatawa tunda har irin wannan addu'ar ya fito bakin Manaja, mutumin kirki ne, ya kai sama da shekaru ashirin da biyar yana aiki a kamfanin mu." Inji Aryan, shiru Majid yayi yana nazarin yadda zai shawo matsalar, kafin ya tafi amma tabbas akwai gaggarumar matsala. "Kai da Sajjid kun kashe bawan Allah kenan? Domin da alamu ya ga kuna aikata wani abu ya dauke files din." "Wallahi a ranar ban shiga kamfani ba, asalima ban san yadda aka yi ya mutu ba." "Shi kenan! Aryan riko shi muje da shi, zan tabbatar da yayi magana in sha Allah." Inji Majid. Riko Amaan Aryan yayi suka fita daga gidan suka nufi inda motarsu take, Turus suka yi.. *** Zahrah Raba ni dasu Addah da Yallabai Yazid yayi ya fi kome, saka min nutsuwa sannan an bani mai taya ni reno, bani da aiki sai karatu, domin a yanayin yadda muke yau da gobe har ya san na fara karatu na bari. Don haka da kanshi yake gaya min. "Zaki koma makaranta." Murmushi nayi na ce mishi. "Yaushe? A wata duniyar? Wannan duk mafarki ne." Na fada ina kokarin mikewa. "Da gaske zaki koma makaranta domin ki karanci tattalin arzikin kasa, ta haka zaki samu aiki me kyau ki gina kanki ba tare da wani ya sayi abu me daraja a tare dake ba, naso da ina da hali ba zaki kara zama a kasan wani ba. Sannan ba zaki kara yadda ki mu'amalanci waccan kanwar Baban taki ba. Akwai wani abu da kike dashi kin kasa fahimtar haka, sai dai nan gaba zaki gane haka. Amma kiyi karatu sosai domin ta haka zaki zama Madam Zahra babban akawun kamfani." Don haka na kara maida hankalina sosai, sannan da kanshi ya nima min wani cikin mutanen shi,yana koya min yadda ake amfani da laptop, rayuwata da ta baby tana cikin kwanciyar hankali, sannan bani da Matsalar kome, sai ta cigaba da kula da Baby da karatu na. itama Baby tayi katuwa bul bul da ita tayi kyau. ---- Wata na biyu ban saka Addah a idona ba, yau da ya shigo da yake sai ya jima bai shigo ba, "ina son zuwa ganin Addah." "Hmmm! Tow." Ya fada yana kallon yadda nake shiri, yan uwanka yan uwanka ne komai muninsu, haka ya raka ni yana rike da Baby da take niman wata biyar, yadda na gansu babu wahala a tare da su, sannan suna cikin nutsuwa. Kamar na fashe da kuka haka na isa gare su, na mikawa kowacce jakarta da na kawo musu. Ganin yana tsaye yasa Addah kame bakinta. "Naji daɗin ganinku, Addah ya idanunki?" "Kina farinciki ne don ba zan kara gani da shi ba ko?" "Ko daya Addah, ya kamata ki daina tsanata." "Saboda ke na rasa Y'ata." "Addah don Allah ki daina faɗar haka, idan don nice ya kamata ki gane na amshi hukuncina da rikon Yarta." "Idan ina raye sai na saka yar ta kashe ki, wallahi sai na saka ta wulakanta ki." Murmushi nayi ina wasa da hannuna, "zan yi fatan ki kai wannan lokacin sannan ni kuma zan yi ƙoƙarin naga na daurata a kan layina, in sha Allah, sai kin sha mamaki ba zan hana ki ita ba, amma kuma sai kin yi tunanin anya jininki ce." Hmm Addah kenan, bari mugani Ni da ita waye zai yi sa'ar cika burinshi ni zan nemi taimakon Allah ya taya ni, rikon Allah ya kare min ita da zuciyarta. Cikin fushin da ban san ina da ita ba, na kalli Ummi na ce mata. "Ummi zan tafi." Na kalli Addah, na ce mata. "Ki ajiye hakan ni dake Allah ya bawa mai rabo sa'a!" Na fita yana kallon yadda muke magana da fulatanci ya fahimci faɗa muke da harshen mu, don haka yayi ta kallon yadda nake magana, ina fitowa na share kwallar da zai zubo min, na amshi yarinyar ina jin wani irin kuka ya kwace min, domin kuwa ina jin tsoron kada Addah ta sake raba ni da wani abu mai daraja....... ```Shahararrun goma aduniyan kayan mata wato m zee kamshi kayan mata kenan inakuke matan kwairai manyan Mata fah bamuna mataba Mata masu aji Wanda tasan kanta agidan mijinta kozokuyi gyara masu kyau da inganci Wanda zaisa oga nishadi yasashi farinciki atare dake kayanmu wane yaro sai uban yaro kinsha zumar makalemata dare daya wanka goma wanan set ne na kayan kwairai akwai fati budurwa mumuna da aeki Dan miyau malaka to shu,Umar Zuma zumar kiba gari kiba Zuma me lakani ningi tsumin lahaula hadin miski ba ahira dawando garin me kabara kasa ruwa sama ruwa wanan magani ba ,a magana magani sanyi mekyu maza da Mata ci da kaza ci da cicibin vlp yan shila ci da kifi nama kayan sakiba na gida danawaje munadakaya kala kala fani kamshi munada shu uwar humra namu ba irin nasubane akwai turare 24 hr turare kabasa Dana gida masu Dadi gakyau ga kamshi 08063845136 KADA KU MANTA KAMAR KOWACCE WATA Wannan akwai Promon Azumi me kike jira ne* #Mai_Dambu [2/29, 7:47 PM] Cutie cutie pie: *BAƘIN HAURE....🐾🐾* {Greed for Money is the roots of all evils🫀} Arewabooks:maidambu41 Wattpad:Mai_Dambu Mallakar:Mai_Dambu ```Hajiya ga kaya nan Masha Allah, Available price Huluna da Mayafai, da na yara sai Wanda ranko yakeso gasunan kala kala, Hajiya muna dasu ba iya hulana da Mayafai ba, har da shadodin na fitar sallah, Hajiya domin hutar dake da fitar dake kunya na tanadi yadda ba zaku sha wahalar yawo kasuwa a cikin azumi ba, don haka kafin kishiyarki tazo ta sata au 🤣😹😂 kafin kishiyarki tazo ta saya na tayiwa mijinku shakara gara kizo ki sata au 😔🤣😹 baki ya saba gara kizo ki saya, barauniyar gida, kai Sarauniyar gida 😂😹 atow kayana na Uwaren gida da na Amare ne``` *TUNTUBE WANNAN NUMBER 08130269641* Hular Yara Mayafai Dogayen riguna Hijabai Takalma Kayan Yara ATAMFOFI Laces SHADODDI Materials Sayan na gari mai da kudi gida..... Wannan page din na kune. Hajiya Sa'adatu wato Ambassador Auntyna Addah gashi nan kun zungud'o ni nayi muku posting....😍🥰 Nagode sosai da kulawarku... In sha Allah sai Talata ina da uzuri me girma 🌹🥰😍 *027* Duk wanda Allah ya jarrabe shi da fitinar Addah, tabbas ya gamu da jarabawa, kamar dai ni da ta addabi rayuwata, amma ban iya daukar mataki ko na mata wani abu ba, na barta da Allah da kuma halinta, in sha Allah Ubangiji shi yasan yadda zai yi da ita. Bayan fita ta, Ummi ta fisge kayan da na kawo musu, "bani nan, ke da bakya kaunarta, taya zaki ci abin hannunta bani ko babu komai Na ci tudu biyu." Ta fada tana buɗe ledar. "Ki bani kayana tunda kema ta baki naki." Inji Addah kamar zata yi kuka. "Wallahi ba zan baki ba." Inji Ummi. Cikin bakinciki da abin da Ummi take mata, ta ce mata. "Allah ya isa ban yafe ba." ke ai mu zamu miki Allah ya isa bamu yafe ba, tunda kika lalata mana rayuwa, kuma muka cigaba da zama dake ai kin san mun yi hakuri, oya wuce tsohuwar banza kawai." Ta haɗa da abinda na kawo mata, ta cinye har da na Addah. Haka yanayin ya cigaba da tafiya, Ummi tana zuwa kuma ina jin labarin yadda suke zaune da halin Addah, murmushi nayi domin Allah ya tsamo ni daga cikin masifar Addah babu dalilin komawa cikinshi, matar Yallabai Yazid ma ta gama jarabararta ta kyale ni, har cewa take ya ajiye karuwa yana abin da yaso da ni, kuma Ni tsakani na da shi bai tab'a min kallon wani abu ba, asalima y'ata yake dauka, idan tana hannuna ya amshe ta, ko ma bata hannuna zai dauketa. A iya zaman da nayi da shi ko da wasa bai tab'a yunkurin yi min wani abu ba, idan akwai abinda yake son ya gani shine na zama mai tsayuwa da kafarta, wannan shi ne mutum na farko da ya tsaya min, sannan zuwa yanzu na san yana rike dasu Addah ne domin ni, ba don haka ba da sun bar mishi yankinshi,. Tow nice karfin zamansu. Ko ranar da ta b'ata min rai shi ya ce min. "Ke ni zan Kore su, na gaji da ganin suna kuntata miki. Gara su baki wuri ki huta." Girgiza masa kai nayi ina faɗin. "Ko daya, kawai nafi son na gansu a tare dani. Ko babu komai nasan wata rana zasu min adalci." Wato idan rana ta fito tafin hannun bai isa kare ta ba, wannan shine adadin abinda zan fada domin Addah tun kafin a haife ni take adawa da mahaifiyata, da aka haife ni kuma dole ta hakura da abin da take mata, sai dai babban abunda yake min ciwo mahaifiyata da ban san dalilin da yasa ta manta dani ba, nasan dai duk inda take zata so da ina tare da ita, A hankali kome yake tafiya tare da zama tarihi, kusan shekara daya da rabi kenan, da barin mu Nijeriya, sannan muna wannan ma'aikatar sarrafa maganin Yazid, zuwa yanzu na kara fahimtar abin da suke aikatawa, musamman da ya fahimci yadda nake da baiwar ilimi, haka yake sakani duk wani lissafin Kudi ko wani abu, a gefe guda kuwa Babyna tana yawo ko ina, domin tana tafiya dagwai-dagwai abin ta, duk wanda ya ganta zai dauka ta shekara biyu, nan kuwa shekara daya ne da yan watannin. Yarinyar Kyakyawar gaske ce, don ma ina boyeta, idan na kalleta sai naga bata kama da Zuzu,babu abinda zaka gani kace tana kama da Zuzu sai kwayar idonta. --- Kallon Addah yayi cikin fushi da b'acin rai ya ce mata. "Na gaya miki, zata tafi karatu , iya abinda nazo gaya miki kenan ke kuma da yarki na shirya yadda zaku tafi sansanin gudun hijira da yake Agadaz OIM,." Kura mishi ido daya tayi sannan ta ce mishi. "Na gaya maka ka saye ta, domin matukar ina raye zan amshi kudin wani." Shiru yayi yana mamakin taurin kan Addah, kafin ya ce mata. "In sha Allah ba zaku tab'a haduwa ba." Sannan ya juya ya bar gidan, Ina zaune na ga ya shigo har dakin ina aiki da laptop. Rike hannuna yayi yana faɗin. "Nasan wata rana zaki tambaye ni dalilin da yasa na kawo ku nan." Ya fada yana hada kayanmu. "Lafiya?" Cusa kayan yayi ya tattara kome nawa, "Idan muna raye ki ajiye a ranki zan neme ki." Ya ciro wata sarkar da yake wuyarshi ya saka min. Sai da muka bar yankin gaba daya yakaini wannan underground tunnels din. "Me yasa zan tafi ban yi sallama da dangina ba." "Ka Min bayani ina zan tafi." Haka ya cigaba da tafiya har na tsawon awa biyu, sannan muka fito bakin tunnels din, ya kai ni har zuwa inda wata mota take ya ce. "Aseem ka kaita iyakar inda ka ajiye su Reshmah, zan zo idan damar haka ta samu, motar Ansar zai kaita har inda zata zauna. Ka fahimta ko?" "Eh Sultan na fahimta." Haka ya saka baby a motar, sannan ya janyo ni, ya rungume ni. "Ina son na gaya miki a kurarren lokaci, ina kaunarki." Ya sumbaci goshina sannan ya saka ni cikin motar. "A'a Yazid!" Ban san me ya min ba, sai dai na zube a jikinshi ban kuma sanin kome ba, haka ya gyara min kwanciya. "Na gode Aseem." Daga haka ya koma cikin tunnels din. Tsawon awa biyar ina sume, sai da muka isa iyakar da yace da shi. yasa shi yayyafa min ruwa, ina farkawa na zubawa inda muke ido. "Sannu, ga motar Ansar nan." "Don Allah ina yallabai Yazid?" "Kiyi hakuri nasan shi namijin duniya ne, yadda ya ƙare iyalinshi haka ya ƙare ki, don haka kiyi karatu yadda zai yi alfahari dake. Ki kula da Amirah sugrah."haka yake kiran Baby. Kuka nasaka ya kwashe kayan mu ya saka a cikin motar Ansar ɗin., daga nan ya tada motar muka bar wurin, sai da muka kwana muka wuni, kafin muka isa Marad'i. A wata unguwar masu hali ya kai mu, ya kai ni har cikin gidan. Babu abinda babu a cikin gidan, sannan ya mika min wata jaka. "Gashi wannan duk wani abun da kike bukata yana cikin nan, sannan ina kara baki hakuri da ta'aziyar rashin da kuka kuma yi, domin a lokacin da kuka iso labari ya zo min Yallabai Yazid da yan uwanki, sun rasu." Ji nayi kamar duniyar tana juya min, daga nan ban kuma sanin kome ba, na zube a wurin, kwana biyu ina kwance a gadon asibiti babu kowa sai nurse da likitocin da suke kaiwa da komowa, sai wata mata da take dauke da Baby. Kunsan yadda nake cikin tashin hankali? Babu Addah babu Ummi, babu kowa sai Allah sai baby!" "Sannu Allah ya baki lafiya." Kallonta nayi na lumshe idanuwana, ina son kara haska fuskarshi, a wannan yanayin ya ce min yana sona. A wannan ranar kome ya kara sauyawa. Wata kaddara wata rayuwa, wata duniyar, kome ya tafi kamar bai faru ba. Da taimakon Matar nan nayi wanka na gyara jikina nazo na sauke ibadar da yake kaina. Ruwan zafi ta haɗa min na sha, ina kallon Baby da tayi barci, turo kofar aka yi likita ne da nurse. Suka gama duba ni, zasu fita nace musu. "Ku sallame ni " "Jikinki da saura." Inji likitan, "A'a zan karasa a gida don Allah ku sallame ni." Haka suka bani sallame, muka fito Matar nan ita ta nimo mana abin hawa muka nufi gida, har cikin gidan muka shiga. A daya daga cikin kujerun falorn na kwanta, "Maman Amirah sugrah, zan turo yarinyata, tazo ku kwana domin ba zan barku ku kadai ba." Gyada mata kai nayi, ta fita can sai gata da wasu yan mata uku. "Assalamu alaikum!". "wa'alaikimus Salam!" Na amsa muryarta a ciki ciki, "Maman Amirah sugrah, ga Barakatu zata kwana anan, sauran sun zo miki ya jiki ne." "Ayya na gode." Na fada a hankali, "muna BQ dinki ne." "A cikin gidan nan kuke?" Gyada min kai tayi. Sallamar wani magidanci ne yasa suka mike tare da amsa mishi, ya shigo muka gaisa. "Shine maigidana, yana kula da gidan nan." "Na gode!" Na fada. "Ya Jikinki?" "Da sauki Baba na gode sosai." Daga haka suka watse aka bar ni da Barakatu, ina kwance kamar ruwa ya cinye ni. A hankali na mike na nufi hanyar kitchen, nayi ta bincike, akwai kome babu abinda Yazid bai saka min ba, wasu kayan abincin zasu shekara uku hudu, zama nayi na fashe da kuka, sai da nayi me isata. Duk abincin da ya dace gasu nan, freezer biyu ne a kitchen din, da na bude daya cike yake da nama na kaza da na saniya, ga kifi da turkey. Taliya na dauka da kayan miya Barakatu ta shigo taga ina ciro kayan abincin, ta tayani na kunna gas, muka yi jallof da busashen kifi, ita ta karasa na koma daki nayi sallar Magariba, nayiwa baby wanka, ban fito ba sai bayan Isha. Abincin ta kwashe min, na ce ta zuba ta ci, ni kadan na saka saboda Baby ne ma, haka ta dauki nata zata fita nace ta kara musu, idan ta je kada ta damu zan iya kwana. Sai da safe ta min na rufe gidan Baby na gama cin abincin ta, na wanke mata baki da jiki, muka shige daki. Kwanciyarta tayi jikina, ina shafa bayanta. Har barci ya dauke ta, baki daya rayuwata nake tunawa tun daga ranar da narasa mahaifiyata, har zuwa mutuwar Baffa'm ya dawo min haka nayi kuka har na godewa Allah, tashi nayi nasha magani na hada da alola nayi sallar nafilla, sannan na jima ina addu'a da rokon sauki a cikin al'amarina... A hankali na kwanta barci ya dauke ni, haka na kwana cikin mafarkai marasa kai da fasali.. Kiran sallar farko, ya tashe ni na mike kan kafata, na fara addu'a bayan nayi alola nazo na gabatar da sallar nafilla, sannan na dan jira lokacin shiga sallar inata yan tasbihi na, har lokacin danaji ankabbara sallah, nayi, ina idarwa na zauna ina azkar, me zan yi wanda ya wuce ibada daga rayuwar da na fad'o cikin Ni'ima da wadata, addu'ar da nake mishi yafi na kowa, domin ya bani abubuwa dayawa da na rasa, ya bani abin da zan tsaya da kafata. Hawaye ne ya zubo min, lokacin da na tuna da kalamanshi. *Idan ana son kiyi karatu dole a dauke miki, nauyin cikinki da na bukatar yau da kullum, shi yasa nake son kafin ki fara karatu na nima miki abin da ba zaki nima a wani wurin ba, so samu ne a mallaka miki kuɗi kamar misalin miliyan goma, sannan duk wata akwai wanda zai na kawo miki abinci da kayan masarufi, sutura duk bayan wata uku ana sabunta miki. Baki da ƙishirwa baki da yunwa, baki da buƙatar kuɗi, kin ga kenan babu ke babu niman taimakon wani kato balle ya tab'a min martabarki. Domin wallahi kika sake wani ya tab'a min alfarmata sai na kashe shi na kashe ki, na kashe kaina.* Hawaye ne ya zubo min, duk ya cika min kome. Amma ya tafi ya barni ya tafi ya bar ni da ciwon da ya dasa min a ranar da zamu rabu. *Dole ki zama kamar namiji, domin rayuwar nan kowa rauninki zai kokarin gani, idan kuma kika sake aka fitar da rauni babu wanda zai mutuntata ki, ba ina nufin ki zama mafadaciya ba, amma ki tsaya kada wasu su kara rena ki kamar yadda yan uwanki suka rena min ke, ki zama mace me tsayawa kanta, yadda Ummina zata tashi ba ta ga Ammynta tana kuka ba.* Share hawaye nayi na saka a raina daga yau babu wanda zai saka ni kuka. *** The other side. Yazid ya sake fitar dasu Addah da Ummi a ranar, ya ce mata. "Ba zaku kara ganin Zeehrah ba, sannan itama ba zata nime ku ba domin na saka a gaya mata kun mutu, inda za a kai ku zasu baku kome sannan zasu koyar daku yadda zaku kama kanku. Ummi Zeehrah ta gaya min cewa Mamarki tace ki koma wurin Yayanki, zaku koyo sana'a na tsawon shekara daya, ki cikawa Mamarki burinta, ga wannan matukar kika koma Nigeria, ki je duk bankin da yayi miki, ki amshi wannan Zeehrah tace na miki wannan kyautar " fashewa tayi da kuka, "Duk cutar da muka mata bai hana ta saka a kyautatta mana ba, Ya Allah na tuba ka yafe min, idan kun sake haduwa ka nima min yafiyarta " Haka suka rabu, duk sun watse bayan barinsu garin Nawwas ya shigo da mutanenshi, aka shiga wani irin fada a tsakaninsu, har tsawon kwanaki goma sha, a wannan fadar harbi biyu aka mishi a kafarshi. Amma Allah ya bashi sa'a sun kore mutanen nawwas, shima Nawwas din guduwa yayi, da nashi raunin. Amma Yazid an dauke shi a jirgi me tashin angulu aka wuce dashi Algers dama burin mahaifinsa kenan ya dawo a raye ko a kowani yanayi, sannan zai amshe shi. Domin shine next king in sha Allah. *** Niamey. Yanzu shekara daya da wani abu kenan, Majid tunda ya samu aka fitar da masu hannu a kisar Manajan kamfaninsu, ya wuce south Africa. Sau biyu Aryan ya tafi wurinshi na farko shi da Yara da Hajiya dasu Jamilah da Aneesah, na biyu kuma ne daga shi sai Mahdi, suka ga inda yaƙe. Koda yake sai su wuni basu ganshi ba, bayan karatu yana aiki a ruwa bai da ma isasshen lokacin zaman gida, haka yasa a zuwansu na farko suka same shi available. Yanzu kuwa ba sosai ba. Bayan sun dawo ma ba laifi rigimar cikin gidansu, yana nan babu abinda ya sauya, sai dai tun da aka gano Sajjid yana da hannu a kisan Manaja Hajiya Tani ta kame kanta, sannan shima Amaan Mamman Ba'are, ya nutsu sai dai Tani bata karaya ba. Domin tasan matukar tana raye sai ta raba Abdul Majid da duk abinda yake da shi. Sai ta dasawa Hajiya bakincikin da ba zata manta da ita ba. Koda yake tun bayan abinda ya faru, hankalin Amaan ya dawo jikinshi, domin ya lura ba don Hajiya ba wannan daren da su Majid suka fita dashi da babu abinda ba zasu mishi ba, haka yasa ya dawo hankalinshi ya fadi abinda ya faru, amma bai gaya musu dalilin da yasa suka kashe Manaja ba, wanda yasan a haka idan ya fada Hajiya faduwa zata yi ta mutu, sannan ya daina zuwa wurin Sajjid din, domin kuwa yana tsoron kada asirinsu ya tonu. Yana aiki yaji wayarshi na kara, dauka yayi ya saka a kunne. "Lover boy!" Gabanshi ne ya fadi. Domin kwanan nan yana fama da ciwon ciki, tsoron abin da zai ji yasa shi kin zuwa asibitin. "Sajjid ya kake?" "Lau kai kawai nake son gani." Kasa yayi da murya yana faɗin. "Sajjid na daina wallahi bani da lafiya, ciwon ciki yake damuna. Sannan bana iya rike bayan gari don Allah ka bar wannan harkallan na daina!" "Karya kenan, domin na saba da kai kuma.bayan kai bana jin akwai wani da na saba da shi. Zaka zo ne ko sai na turawa tsohuwarka videon mu......⁉️ ```Shahararrun goma aduniyan kayan mata wato m zee kamshi kayan mata kenan inakuke matan kwairai manyan Mata fah bamuna mataba Mata masu aji Wanda tasan kanta agidan mijinta kozokuyi gyara masu kyau da inganci Wanda zaisa oga nishadi yasashi farinciki atare dake kayanmu wane yaro sai uban yaro kinsha zumar makalemata dare daya wanka goma wanan set ne na kayan kwairai akwai fati budurwa mumuna da aeki Dan miyau malaka to shu,Umar Zuma zumar kiba gari kiba Zuma me lakani ningi tsumin lahaula hadin miski ba ahira dawando garin me kabara kasa ruwa sama ruwa wanan magani ba ,a magana magani sanyi mekyu maza da Mata ci da kaza ci da cicibin vlp yan shila ci da kifi nama kayan sakiba na gida danawaje munadakaya kala kala fani kamshi munada shu uwar humra namu ba irin nasubane akwai turare 24 hr turare kabasa Dana gida masu Dadi gakyau ga kamshi 08063845136 KADA KU MANTA KAMAR KOWACCE WATA Wannan akwai Promon Azumi me kike jira ne* #Mai_Dambuje........ [3/3, 4:56 PM] Cutie cutie pie: *BAƘIN HAURE....🐾🐾* {Greed for Money is the roots of all evils🫀} Arewabooks:maidambu41 Wattpad:Mai_Dambu Mallakar:Mai_Dambu ```Hajiya ga kaya nan Masha Allah, Available price Huluna da Mayafai, da na yara sai Wanda ranko yakeso gasunan kala kala, Hajiya muna dasu ba iya hulana da Mayafai ba, har da shadodin na fitar sallah, Hajiya domin hutar dake da fitar dake kunya na tanadi yadda ba zaku sha wahalar yawo kasuwa a cikin azumi ba, don haka kafin kishiyarki tazo ta sata au 🤣😹😂 kafin kishiyarki tazo ta saya na tayiwa mijinku shakara gara kizo ki sata au 😔🤣😹 baki ya saba gara kizo ki saya, barauniyar gida, kai Sarauniyar gida 😂😹 atow kayana na Uwaren gida da na Amare ne``` *TUNTUBE WANNAN NUMBER 08130269641* Laces ATAMFOFI SHADODDI Materials Kayan yara Veils Huluna....etc *028* A rikicewa Amaan ya ce . "Sajjid me nayi maka da zafi haka? Nace na daina sai ka kyale ni dole ne sai nayi yadda kake so?" Dariya Sajjid yayi yana faɗin. "Wai tow lokacin da ka saka muka fara baka san cewa haka zai faru bane?" Zufa ne ya shiga karyo mishi, jikinshin na rawa ya mike tsaye. Duk ya rikice. "Sajjid don Allah ka saurare ni!" "Kit ya kashe wayarshi." Kiran wayar sajjid din yakara yi, amma yaki dauka karshe ma kashe wayar yayi, hannu Amaan yadors a kai kamar ya fasa ihu, ya rasa yadda zai yi da ranshi. Turo kofar da aka yi yasa shi d'ago kai da sauri yana kallon Aryan da yazo tambayarshi. Amma da yake yana cikin tashin hankali, bai iya sauraran Aryan din ba, ya bangaje shi ya fita yana kallon agogon hannun shi. Sake kiran layin Sajjid yayi ya ce mishi. "Don Allah ka rufa min asiri gani nan zuwa." "Ba zan rufa maka asiri ba, kawai ka san yadda zaka yi idan ba haka ba. Hmmm!" Sajjid ya faɗa yana kashe wayar. Kamar zai saki fitsari a wandon shi haka yake ji, don dole ya ja motar shi da gudu, Aryan yana kallonshi ta office. "Me ya same shi?" Ya tambayi kanshi yana me kare kankance idanunshi. Kafin ya sauke ajiyar zuciya. ------ Har inda Sajjid yake boye kanshi ya isa domin ya sani, amma yaki faɗa kuma yasan ana niman sajjid ɗin. Lokacin da ya shiga cikin gidan, Sajjid yana tare da wasu mutane. Amma koda Amaan din ya isa zubewa yayi akan gwiwarshi, a gaban Sajjid din. Dariya suka saka tare da kallon yadda yake durkushe a gabansu. "Don Allah ka rufa min asiri, ka gaya min duk abinda kake so." Kallonshi Sajjid yayi yana juya kofin wine na hannun shi. "Bana bukatar kome, ya cikin naka?" Kamar ya fashe da kuka ya ce mishi. "Da sauki.", "Ka wuce zuwa asibiti duk abinda aka rubuta ka gaya min." Kasa yayi da kai yana kallon kasa, kafin ya ce. "Idan na tafi asibiti za a iya ganina, sannan mutane zasu ta yawo damu. Ina son fita Najeriya ne naga likita a can." "Shi kenan jeka!" Girgza kai yayi yana faɗin. "Ba zan iya zuwa ba, sai da yardarka da izininka zan tafi." Tashi Sajjid yayi ya nufi inda Amaan yake zaune, shima ya zauna yana kurbar wine din shi ya ce masa. "Idan haka ne kafin ka tafi asibiti bakidayanmu sai mun more ka." A razane Amaan ya zame zaune daga durkushen da yake, ya zubawa Sajjid idanu. "Wallahi idan kuka min zan sha wahala, don Allah ka rufa min asiri." Tab'e baki Sajjid yayi yana faɗin. "Idan kana tsammanin zaka sha ne, tashi ka je amma ka tanadi amsar da zaka bawa danginka da press!" Ya fada yana d'aga kafadarshi. Wani abu ne ya tsayawa Amaan a rai, ya kasa cewa Uffan domin Sajjid ya kashe shi. "Na gaya maka bani da lafiya, da ace ina da lafiya da zan maka yadda kake so, amma yanzu bani da lafiya." "Tashi ka tafi dan uwarka, maza fita min a gida dan shegiya!" Kasa motsawa yayi yana zaune a wurin, Sajjid ya cigaba da zagin shi, karshe da yaji haushi daukar kwalba yayi ya wurgawa Amaan a goshinsa sai da ya fasa mishi goshi, duk da haka Amaan bai motsa ba, yana durkushe a wurin, "ka fita min a gida kafin na kashe dan iska irinka." A hankali Amaan ya mike yana dafe da goshinsa ya fita, yana shiga motarshi ya saka tissues yana goge jinin. Haka ya gama ya fita sai da ya bar unguwar ya kifa kanshi a kan sitiyerin motar, ya saki wata irin ajiyar zuciya. Bai san makomarshi ba, matukar Sajjid ya saki videon da yake kokarin sakewa bai san yadda zai fuskanci Hajiya ba, ciwon cikin ne ya murde shi, taka motar yayi da gudun bala'i. Bayan fitar shi, daya daga cikin mutanen Sajjid ya ce mishi. "Me yasa ka kyale shi." Murmushi yayi yana me busa sigari hayaki na tashi sama. "Ina da shiri ne, ka tab'a ganin yadda aka jefi tsuntsu uku da dutse daya?" Girgiza kai suka yi, ya saki murmushi yadda yayi mishi, "ina kan shiri na, kuma ina shirya abin da zai min kyau ne, idan har nayi nasara sauke da tsuntsaye uku lokaci guda bana jin duniya zata waiwaye ni, domin kuwa na shirya tsaf." Ya fada yana kurbar wine din. "Bamu fahimci abinda kake nufi ba." "Zaku fahimta amma yanzu ku fara kai mana, mutanen mu ma'aikatan yadda suna shiga cikin aikinmu zai tafi daidai da lissafinmu." "Ban gane me kake nufi ba!" Inji daya mutumin. Gyara zama Sajjid yayi sannan ya dauko abin wasan chased ya saka yan statue din guda uku, sannan ya ce musu. "Kamar haka nake nufi." "Au min fahimta yanzu." "Bayan nan akwai abin da nake so ya gaya min. " Ya fada yana murmushi, "idan ya gaya min dole na saka kome akan inda ya dace, domin ina son bazata." "Amma kai shege ne, yawwa ya batun dila ne? Kwaro ya kawo mana manyan kaya, kuma kayan nan har mun wuce da su. Scotland da France." "Hmm! Haka Julie take gaya min, Kwaro bai tab'a kawo kaya masu kyan wanan kayan ba, musamman na bayan yafi kowanne kyau. Gaskiya labarin ya min dad'i." Lashe baki daya mutumin yayi, yana faɗin. "kuma abin dad'i, irin wanda Mr Williams yake so, ya turo kuɗin aka ce, naso da an bani kayan na gyara kaina kafin a saka kasuwa, karshe duniya ce zata fara morar kayan kafin kai ka samu ragowar yan iska." *** Wasu takardun da Aryan ya kaiwa Hajiya take dubawa, hankalinta ya tafi sosai ga takardun aka yi sallama, sai da ya kara yi a karo na biyu Hajiya ta amsa tana faɗin ."Barka da shigowa Alhaji kai ne da kanka?" Zama Alhaji Haladu yayi yana kallon takardun gabanta, ya saki murmushi yana ce mata. "Duk da kin sauka, har yanzu baki huta ba?" "A'a ina duba abubuwa masu muhimmanci ne, sannan sauka nayi ba barin aikin nayi ba. A matsayin Uwa nake taya shi aiki sannan yana da damar ya bani aiki a kamfanin domin na kara taya shi da wasu abubuwan." "Gaskiya ne amma kuma ai kin wuce lokacin da." Kara kallonshi tayi kafin ta ce mishi. "Na wuce lokacin me?" Dariyar renin hankali yayi ya ce mata. "haba yaushe zaki daina goya su?" Zare medical glass ɗinta tayi tana murmushi. "Idan ban goya su ba wa zan goya? Wa nake da shi da zan goya idan basu ba? Sune dole na, kuma karfina sune suka sani tsayawa da kafaffuna idan ban tsaya musu ba, gaya min waye zan tsayawa?" Gyad'a kai yayi yana faɗin . "Tow Allah ya kyauta, tunda kin mai dasu rauninki." Gyara zama tayi ta ce mishi. "Su ba raunina ba ne, nice nan rauninsu domin tari kawai zan yi su dakatar da abinda yake ransu." "Au tow kice babu wanda ya isa ya tab'a ki, ba tare da sun matsa ba." Ranta ne ya fara b'aci. "Idan babu abin arzikin da ya kawo ka, zaka iya tafiya ina da abin yi." "Tow Allah ya huci zuciyarki don naga ranki ya fara b'aci dama na kawo takardun Afiyyah ce." Gyara zama tayi tana faɗin. "Au ashe bani ɗaya bace nake son Yaran? Kenan idan har haka ne tow wallahi ka sake gaya min sai na sab'a maka, ko dan uwanka aure ya bashi damar tozartani ba wai don ya isa ba, kuma ko yanzu ba za a sake maimaita abin da ya faru ba, don haka ka sami Amaan Mamman Ba'are, shine yake da alhakin daukar ma'aikata ba ni ko Aryan ko Aneesah ba." Shiru yayi yana kallon yadda ta maida hankalinta kan aikin gabanta, "tow babu yar wata alfarmar da zan samu ne?" Juyawa tayi ta kalle shi, "ok ajiye a can" ta nuna mishi inda ya dace ya ajiye takardun, ta cigaba da aikinta. "Mun gode Allah ya saka da alkhairi." Ya fada mata, bata amsa ba illa aikin da yake gabanta da take yi, kuma ai tasan yana zaune. "Sa'adatu baki da burin aure ne? Da sauranki har yanzu idan har mutum ya nutsu zai dauka Majid da Amaan da yan uwansu kannenki ne, sannan a wannan lokacin da kike da sauran kuruciyarki aure ya dace dake ba wani abu ba." "Idan ka gama bayaninka, zaka iya tafiya." Ta ce mishi tana cigaba da aikinta. "Ina dai kara tuna miki, zama haka ba naki ba ne idan da hali ki bawa wani dama ya goge miki tabon da Mamman ba'are ya miki." Murmushin da bai kai zuci ba, tayi tana faɗin. "Kuma da yake an gaya maka namiji ne a gabana ko? Idan har wannan tunanin shine a ranka tow ka cire ni bana tunanin wani namiji, don Allah tashi ka fita." Mikewa yayi yana murmushi. "Nasan zaki so kiyi tunani ina jiran duk abinda kika yanke." "Kana son naci mutincinka ne? Ka fita ka bar min gidana." Ta fada a fusace, shigowar Amaan bai hana shi magana ba. "Kina da sauran damarki, a matsayinki na mace mai lafiya da jini a jika don haka ina kara baki shawara ki yi tunani da kyau. A shirye nake na wanke miki zuciyarki." Cikin wani irin fushi Amaan ya cakumi wuyarshi. "Wallahi sai na karya wuyarka, kai na rantse ka kara cewa kana son Hajiya, sai na kashe ka." Ya janyo shi kiiiiii kamar kayan wanki, ya watsa a waje yana faɗin. "Na rantse Hajiya ta fi ƙarfinka na sake ganin, kiraren sawunka sai na ballaka." Ya fada yana hayagaga, Amaan kishi yake taya Ubanshi. Domin baya kaunar Hajiya ta kebe da wani. Musamman lokacin da ta amshi kamfanin idan tayi baƙi masu saka hannun jari, tow bake-bake yake zuwa yayi yana kallon ko zata mika musu hannu su gaisa, duk da mugun halinshi yana matukar kishin Ubanshi sannan abinda ya faru a kuruciyarsu da Hajiya yana nan a memory din shi bai manta ba, haka yasa baki daya yake kara jin haushin ganin Hajiya da wani namiji, domin bayan faruwar lamarin abin da wasu suke ta faɗa yasa shi cikin rud'ani haka yasa wani lokaci yake ganin, yunwa da wahala.yasa Hajiya aikata wancan abin. "Kai meye haka?" Hajiya ta tambaye shi tana watsa mishi harara. "Hajiya cewa yayi fa." "Sai me? Zama zan tayi? Ba zan yi aure ba kenan?" Ware idanu yayi cike da takaici. "Aure kamar ya? Fisabilillahi Hajiya da tsufarki, ki ce aure zaki yi? Ke Hajiya haka ya dace dake?" Sakin baki tayi tana kallon shi cikin mamaki da takaici. "Kasan ni ba mutum ba ce da zaka ce aure xan yi. Sannu isasshe jikan mallaka'u, aure zanyi kuma na gaya maka idan kaso kada na ƙara ganin kafarka a gidana." "Wallahi kika yi aure sai na kashe shi, haka kawai don janyo mana abin kunya da magana kice aure zaki yi, Hajiya idan kin manta abinda ya faru wallahi ban manta ba, ba zaki tab'a aure ba, domin cin amana ne, taya zaki..." Kura mishi idanu tayi tana son jin me zai ce. "ban fahimce ka ba, meye na manta da ku baku manta ba?" Hadiye yawu yayi ganin yadda ta kura mishi idanu. "Babu kome." "Da kome mana, Amaan idan da babu kome mai zai kawo wancan maganar, shi yasa kake min rashin kunya da fitsara? Akan wancan abin da ya faru kake had'a kai da mutanen da suke bi na da sharri." Murmushi tayi mai sauti tana kallon yadda yake zufa, ga goshinsa da ya sha bandegi. "Kada ka damu, su din zasu maka abin da na kasa maka, amma ka sani duk lokacin da ta kwabe maka bana fatan haka , amma a lokacin zan iya barrata kaina da kai har abada. Ga takardu can ka dauka na Afiyyah zata yi aiki a kamfanin mu." "Hmm!" Ya fada yana jin wani irin ciwon ciki, da tsoron abin da zai je ya dawo tabbas idan hakan ta faru kwananshi ya ƙare. Da sauri ya haura sama da gudu dakin Majid Mamman Ba'are ya wuce da sauri ya faɗa ban daki, sai da ya katsiye abinda yake cikinshi, ga wani irin ciwon cikin da yake damunshi wanda ya saka shi kasa gane kanshi. Dakyar ya daure wandon shi ya fito yana nishi, koda ya sauko kasa, takardun ya dauka ya fita bai cewa Hajiya kome ba. Itama tana son yi mishi magana amma da yake ya bata haushi sai tayi banza da shi. Dakyar ya bar gidan Hajiya, don dole ya nufi wani kanti, ya sayi wasu bakaken kaya yasaka. Sannan ya nufi wani asibiti. Dakyar yaga likitan, a lokacin wani sabon ciwon cikin ya kara turnike shi kamar zai mutu, haka likitan ya mishi scanning. Yana ganin yadda sperm ya dankare a cikin wurin kashinsa, shi yasa yake jin ciwon ciki. "Alhaji wannan abin da nake gani, matukar aka cigaba da yin shi zai haifar maka da Cancer cikin makasayarka, sannan idan ma baka yi fama da Cancer ba, karshe zai zama tsutsa ya cinye maka duburanka, idan da hali tunda Allah ya ce kada ayi shi haramun ne, tow a barshi wannan shine nasihar da zan maka." Idanunshi cike da kwalla ya ce mishi. "Likita ka raba ni da shi, don Allah nayi alkawarin ba zan kuma aikatawa ba." "Tow zan daura ka akan magani, na tsawo kwanaki sannan idan muka tara shi wuri guda sai, a maka aiki a cire amma ka kula gaskiya domin zaka iya rasa lafiyarka sannan idan ka cigaba zaka iya kamuwa da wasu cututtukan da babu magani sai mutuwa." Tashi zaune yayi ya rike hannun likitan, kamar yaro karami ya ce mishi. "Likita na daina don Allah ka taimaka min bana iya rike kashi ma." "Shiga ga ban daki, kayi." Haka ya shiga da gudu, tausayin Amaan din ne ya kama shi. Can da Amaan din ya fito ya zauna yana dafe goshinsa ya ce mishi. "ka kula sosai sannan idan mun yi aikin na cikinka zamu duba wurin muga ko zamu iya aikinshi." "Ba zaku iya bane?" Girgza kai likitan yayi yana cire handglove din hannun shi yana faɗin. "A'a ba haka ba ne, wurin yana da matukar hatsari ne matukar aka tab'a wurin ya samu matsala tow kai baka isa ka rayu lafiya ba, zamu duba yiwuwar dubaka ko mu turaka wani asibiti." "Innalillahi'wa'inna'ilaihi'raji'un! Allah na tuba don Allah likita kayi wani abu." "Ban ce ba zamu iya ba, shi makasaya yana cikin wuri me matukar muhimmanci da hatsari da zarar an tab'a shi zai yi wuya mutum ya kara morar kanshi." Cikin kaduwa Amaan ya kalli likitan. "Ka min bayani yadda zan fahimta don Allah." "Zan maka bayani ai, shi idan aka maka aikin matukar bai yi kyau ba tow ba kai babu rayuwa saida famfas zaka kare rayuwarka kamar yaro karami da ake goyo ne. Kullum duwawunka cikin kunzugu." Wani azababben rawa jikin Amaan ya dauka. "Likita babu wata hanya ce?" "Gaskiya babu tabbas, koda akwai kuwa." Jikinshi ne ya dauki wani irin rawa, kamar zai saki fitsari a wandonshi. Kuma shima likitan yayi amfani da waɗannan kalaman ne domin ya barranta shi daga wancan barnar domin idan ya mishi aikin zai iya komawa aikata abin da yake amma idan ya bashi tsoro dole ya hakura daga aikata shirmen domin wannan masifar da ta fad'o wannan zamanin ba karamar bala'i ba ce. Don haka ya cigaba da razana shi, har sai da yaji nadamar aikata haka yazo mishi, sannan likitan ya rubuta mishi magani, ya tafi. Koda ya sayi maganin gida ya wuce, a falo ya samu Matarshi. "Amaan ina son kudi?" "Ki kyale ni bani da lafiya don Allah." Ya fada mata yana wucewa. "Wallahi sai ka bani, kana board director ace baka da kudi uban me kake yi a kamfanin?" Juyawa yayi ya kalleta kamar zai buɗe baki yayi magana sai kuma yayi shiru, ya haura sama ya shiga dakinshi sai da ya rufe kofar ya nufi gefen gadon shi ya dauko kudi me yawan gaske ya fito. Kai mata yayi sannan ya juya zuwa dakinshi, kanshi kamar zai tsage haka yake ji. Lokacin da ya shiga dakin ya rufe kofar shi kwanciya yayi kafin ya tashi ya sha magani da fresh milki, kafin ya koma ya kwanta yana ji kamar ana tsatsagar zuciyarshi. Bai san dalilin fadawar shi wannan yanayin ba, amma tabbas bala'in da ya fada baya fatan wani ya kara faɗawa, babban abin da yake kara tsorata shi ranar da Hajiya zata gane me yake aikatawa ranar kashin shi ya bushe, wani irin tsoro ne ya kara mamaye ilahirin lungu da sako, na cikin zuciyarshi. Tabbas ranar zai bukaci mutuwarshi da ganin wannan ranar. ----- Aryan. Har aka tashi aiki bai ga Amaan ba, don haka daga wurin aiki ko gida bai shiga ba, ya nufi wurin Hajiya haka ya zame musu al'ada tunda dama suna zuwa da safe sannan da rana suna zuwa wurin aikinta, yanzu da ta daina aikin wurinta suke fara zuwa kafin su tafi wurin matansu. Da sallama ya shiga falon tana lazimi. Zama yayi sannan ya jira ta gama, kafin ta kalle shi. "Ya aiki?" "Alhamdulillahi!" Ya faɗa yana kallonta tv. "Da magana ne?" "Matsayin Aneesah yayi mata nauyi, ita matar wani ce, mai zai hana a bawa wani wanda muka yarda da amanarshi da nagartar shi. " Kallonshi tayi kafin tayi shiru na wasu dakikai ta numfasa sannan ta ce mishi. "Ina ga a bawa Abdul Majid dan Hadiza." Murmushi yayi ya ce mata. "Hajiya nayi tunanin haka, sannan idan kin lura sam ko cusa kanshi baya yi a cikin harkar gidan nan. Shi yake damun Hammayo amma shi Hammayo ko a jikinshi. Shi ya fi dacewa da xama CEO na kamfanin BA'ARE GOLDEN EMPIRES." "Kuma idan aka bashi a bazata Uwarshi zata sha mamaki, duk makaman yakinta zata zubar, sannan rigimar da yake tashi akan kamfanin zai yi sauki " inji Hajiya. "Tabbas nima na amince da haka, amma hajiya Amaan ya shigo kuwa?" Tab'e baki tayi tana faɗin. "Ya shigo." "Tow shi kenan" ya faɗa yana me mikewa. "A gaida Nabeeha da takwara. Da dan Daada." *** Agadaz OIM : Organisation International pour Les iMigrations office din yan gudun hijira suke kai takardun su ne domin a basu damar zama a cikin camp din oim yana under African countries ne, domin duk wasu ƙasashen Afrika da suke makotaka da Nijar suna turo mutanensu, domin akwai hulɗar zaman lafiya a tsakaninsu. Sannan akwai kyakkyawar fahimta idan har kasa ta turo dan gudun hijira Nijar zata mishi duk wani abin da ya dace har ta mai da shi zuwa ga gwamnatin ƙasarshi sannan da abin yi me kyau, don haka *OIM* yana kasar Nijar a cikin jahohi biyu na ƙasar, kusan kullum na duniya Addah da Ummi sai sun tafi office din amma kuma babu sa'a, domin yawan yan gudun hijirar da suke zuwa don niman a basu agaji. Yau ma kamar kullum bayan sun bi dogon layi, Adda da idanunta daya da ya samu matsala take ƙare shi, wani jami'in wurin ya zo wucewa ya ganta ana ƙoƙarin ture ta a layin, ya ce musu. "Sannu Inna muje ke daya ce?" Ummi da take bayanta tayi maza ta ce mishi. "A'a oga tare da ita muke ina mata jagora." "Amma ai ke ya dace ki tsaya a bayanta ba a gaba ya dace ki tsaya bs." Cikin gajiya da turereniyar da ake mata ta ce mishi. "Shi kenan oga." Ta faɗa tana komawa gaban Addah. "A'a muje a duba takardunku, domin ba a son me ciwon idanu yana tsayawa a rana." "Mun gode fa " suka bi bayanshi har cikin office din, mutane sai surutu suke, suna zuwa aka duba takardunsu, Asalima stamp na Hukumar tsaro ne a jikin takardar. Ba ajima ba aka sallame su aka tura su camp, wato OIM camp shine ake kiranshi da aljannar yan gudun hijira. Duk wani abu da zaka bukata na rayuwa a cikin camp din an tanadar maka, kulawar da ake bawa yan gudun hijiran ko yan kasar basu samu, domin babu abinda ba a musu. Ana kyautata musu, sannan kome nasu ana basu. Daga zuwan su aka wuce da Addah Clinic da yake cikin camp din aka fara duba matsalar idanuhta. Ita kan cewa take. "Ku barshi zai tsiyaye da kanshi, ai idanun ya mutu." Ta fada cike da takaici, duk ranar da ta haɗu da Zahrah sai ta mata abinda ba zata manta ba, sai ta mata sanadin da ta sake komawa zero daga Add din da Yazid din ya sama mata, matukar tana numfashi sai ta saka mata Fargaba da tashin hankali a ranta, zata cigaba da zaman jiranta har ranar da zata bayyana. Ko a cikin Uwarta ya kaita sai ta zakulota ta rama abin da tayi mata, ba zata kyale ta ba. Haka tayi ta kintsa mugun nufin da yake ranta. Haka suka gama dubata, sannan suka sallame ta. Da magungunan masu yawan gaske. *** Marad'i........... #Mai_Dambulaaaaaaaaaaa [3/4, 9:14 PM] Cutie cutie pie: *BAƘIN HAURE....🐾🐾* {Greed for Money is the roots of all evils🫀} Arewabooks:maidambu41 Wattpad:Mai_Dambu Mallakar:Mai_Dambu *029* Bahaushe yayi gaskiya da ya ce d'an uwa rigar k'aya, kabarshi a jikinka ya soke ka. Ka cire shi duniya ta zage ka. Ban fadi haka don kome ba, sai yadda nake cike da kewar Addah da Ummi, musamman Zuzu da ban san wata duniya take ba, ina matuƙar son ganin Zuzu ta gaya min meye nayi mata haka? Me yasa tayi min haka? Me yasa ta ha'ince ni? Kowacce rayuwa tafe take da kalubale. Sai dai a wannan lokacin na fahimci girma da muhimmancin nisantar su Addah. Sannan akwai wani abu daya da na kasa sabawa shi, wato tunanin Yazid, na kasa yarda ya mutu domin zuciya ta bata bani damar amsar labarin Mutuwarshi ba, sannan haka su Addah bana fatan ace suma sun mutu domin ciwon zai min yawwa. Yau ya kamata na fara zuwa makaranta, amma bani da karsashi da nutsuwar zuwa, zuciya ta a rufe take wani irin yanayi nake ji mara daɗi, haka yasa na cigaba da kwanciyar da nake har zuwa wani lokaci. Karfe tara na fada ban daki, na dad'e sosai sannan na fito daure da towel, a hankali idanuna ya sauka kan Baby da ta farka, gadon na nufa ina faɗin. "Kin tashi ne?" Na d'auketa a kafadata, zuwa banɗaki na mata wanka sannan na daurata akan karamin poo mikewa tayi tana ihu, "yi hakuri zauna kiyi " ai kamar na zage ta, haka yasa dole na.hakura muka fito na shirya ta cikin wata riga da wando, pink da purple. Sai farin hular Amnas, da nasaka mata, na shafe ta da turare mai daɗi da sanyi, Yallabai Yazid ya koya min amfani da turare dan zaman da nayi da shi, ko wannan gidan haka ne domin gaban mirror akwai turaruka kala kala wasu ma ban taba jin sunansu ba. Hadiye yawu nayi ina jin kwalla na cika min idanu. Mikewa nayi na nufi sip dinmu na bude, karamin drowe din jikin siff din,bra ne da pants ɗinsu, a hankali na cire wasu farare kalkal, na saka a saman gadon na koma na bude asalin wurin kayana. Wata doguwar riga na ciro, da mayafinshi da hular da zata dace da shi. A hankali na saka bra din da pant, sannan na saka wani gajeran wando, iya gwiwa kafin na saka gown din. Wanda aka rubuta Amnas collection, na saka a hankali, kallon kaina nayi a madubi fuskata tayi kyau, ba laifi sai dai kana kallon kwayar idanuna zaka fahimci ina cike da damuwa. Murmushi nayi na tattara gashin kaina,.na saka bam na daure shi tsaf, sannan na nufi inda mayafinshi yake na lullube, bugun kofar dakin aka yi na ce. "Shigo." Ina gyara jakar da zan fita da shi, ta shigo. "Tante!" Cikin kulawa na amsa mata. "Na'am Barakatu?" "InJi Babanmu wai na gaya miki, mai kaiki makaranta ya jima da zuwa." "Ok gani nan zuwa!" Na mike ina.gyara zaman mayafina, tare da saka jaka a kafadar, na nufi wurin turare na shafa, sannan na fito ina dauke da baby, dake bata da rikici, mikawa Barakatu ita nayi na koma daki na d'aga towel din na shanya sannaan na dauki kudi a cikin drower gadon, na zuba a jakar ko da zan bukaci nayi wani abu, ina gamawa na dauko flat shoe na saka, sannan na fito bayan na rufe dakin, na dauki kayan abincin baby na kai musu, da wasu kayanta kala biyu da Pampers. "Maman Barakatu zan tafi ga Baby Amirah sugrah!" "Allah ya dawo dake lafiya, sai kin dawo." "Yawwa, Barakatu idan ban dawo ba, ki dafa mana shinkafa akwai sauran miyar nan ki zuba muku ku bar min sauran." "Tow Tante!" Ta fada, da sauri na fito daga wurinsu na nufi hanyar waje. Tun kafin na isa driver ya fito ya bude min kofar baya, na shiga na zauna. "na gode! Nace mashi" Sannan ya shigo muka bar gidan, kwantar da kaina nayi a jikin kujerar, ina ji na kamar wata sabuwar halitta, wacce aka sauya mata duniyarta, tabbas an sauya min duniyata amma kuma ina dangina da zuri'ata suke? Buɗe idanu nayi, ina shaƙar kamshin turaren motar, kafin na dan zubawa gefen hanya idanu. Bani da kowa bani da kome, daga ni sai Baby haka zan rayu cikin kaɗaici, cizon fatar bakina nayi ina mai da kwallar da ke shirin zubo min. Haka muka isa makarantar, na kasa barin zuciyata ta huta, muna isa ya Fito ya bude min kofar, sannan ya amshi jakar hannuna. Har Office din Dean na Mariama Abacha University marad'i ya kai ni. Koda muka shiga office din, Dean din bata nan, don haka muka zauna har ta dawo. Cikin girmamawa mutumin ya gaishe ta cikin harshen French, ya mata bayani. "Tow shi kenan, zan duba bari na kira shugaban tsangayarsu." Ta fada da hausa, jin tana hausa sai naji kamar ina cikin dangina ne. Domin wani lokaci idan kana jin wani harshe aka zo ana yin irin shi, zaka ji kamar dangi kuke da mutum,haka yasa na zuba mata idanu ita kanta hausar da take cikin gayu da kwarewa, kamar irin ban ma san yadda zan yi bayani ba, amma tabbas na tsinci dami a kala. "Muje Madame!" "Ok!" Na furta a hankali, haka muka fito daga cikin office din zuwa department ɗinmu na Yan economic, duk wasu abubuwan da ya dace duk muka kammala a yau, sannan ya kalle ni cikin girmamawa ya ce min. "Madame daga yau bani zan kara zuwa ba, akwai wanda xai rika zuwa yana kawo ki, sannan asabar da lahadi zai zo ya kaiki wurin koyon tukin motar, wannan shine inda zan tsaya. Idan na tafi da motar wanda zai cigaba zai dawo da ita." "Da gaske Yazid ya mutu?" Bai kalle ni ba, kuma nasan ba lallai ba ne ya kalle ni tunda iya kan aikinshi yake, ina ji ina gani ya ja motar ya bar makarantar. Hawaye ne ya zubo min, tabbas ba mutuwa akewa kuka ba, sabo ita ce akewa kuka kuma yanzu da na saba da shi, ya tafi ya barni da ciwo a rayuwata. Haka na share hawayen da ya zubo min, sannan na nufi hall din da zamu na daukar lecture na zauna, bamu da yawa a cikin hall din haka ya tabbatar min da cewa course ɗin mu bai da farinjini. Eh bai da farinjini domin ba kowa yake yin shi ba, ko ni naso da accounting dina da nafara tun farko na karanta da na samu damar cigaba daga inda na tsaya, amma wancan takardun ma Yazid cewa yayi basu dace dani ba. Ina zaune malami ya shigo ya gama bayaninshi, masu maida hankali suna maida hankali mu kuma, muna ta baza idanu, sai bayan fitar shi na sauke ajiyar zuciya. Wunin ranar ban da Masallaci ban je ko ina ba, asalima ni yanzu ban son sakewa da mutane, gudun kada wani abu ya taso a san Asalina ayi min gori ko cin mutuncin. Haka yasa ana tashi na tafi inda aka ajiye motar dazun naga motar, tun kafin na isa ya taso da sauri kamar zai kwanta na bi ta kanshi, ya amshi jakar hannuna, ya bude min baya na shiga, sannan ya ajiye jakar a kujerar gaba, sannan muka bar makarantar. Koda muka isa a matukar gajiye na isa, na samu Baby Amirah sugrah tana ta ihu, amsarta nayi ina faɗin. "Me ya same ta?" "Faduwa tayi dan zaki dawo nan!" A hankali idanuna ya sauka kan hannunta da yayi jajjur, "toh ba kome." Na wuce da ita falo, ina rungume da ita. Sai kuka take kamar zata tsaga gidan, na rasa me ke min dad'i. Haka na bata ruwa tasha, ta faɗa kirjina tana sauke ajiyar zuciya. "Mirah me aka miki?" Sake k'amk'ame ni tayi, tana sauke ajiyar zuciya. Dakyar na samu damar shiga kitchen na duba Barakatu ta gama abinci, na zauna naci na bata amma taki ci, kafin ayi Magariba jikinta yadau zafi kamar wuta rau. Haka na daure nayi sallah, sannan na fito ina gayawa Baban Barakatu zan kaita asibiti. "A'a da dai kin koma, za azo a dauke ki." Haka na dawo can kuwa sai ga drivern da ya dawo da ni, yazo muka je asibiti aka duba hannun ashe tsagewar kashi ne, domin ta fadi akan hannun ne. Haka aka daure hannun muka dawo gida da lodin magunguna muna dawowa Mamansu Barakatu tazo tayi ta bani hakuri. Ni na rasa hakurin na meye? Naga dai tsautsayi yana kan kowa, don haka na fahimci wani abu, babu yadda zaka yi ka daurawa wani nauyinka, don kawai wani dalili. Haka yasa da muka kwana washe gari da kaina nayi abin karyawa, da duk wani abin da ya dace, sannan na ajiye na mata wanka, na shiryata. Bayan na gama shiri cikin nutsuwa da cikar kamala, na fito ina rungume da ita. "Hajiya zaki tafi da ita ne?" "Eh idan ta warke zan barta domin ko na tafi ba xan samu nutsuwar karatu ba." "Shi kenan a dawo Lafiya, Allah ya bata lafiya." "Amin Ya Allah." Daga haka na wuce mota, muka bar gidan. "Madame ko za a akaita gidan renon yara ne, kada ta raba miki hankali." "Ba kome zan iya." Haka muka isa har makarantar, wani abin mamaki shine tana ganin baƙin fuska ta ware, kowa ta gani Ba, wai ita Baba. Haka muka shiga aji, tayi ta yawo dake tana tafiya, ganin bandeji a hannunta yasa kowa ya ganta sai ya tambayeta. Ita kuma tayi mishi gwaranci. Lokacin da malama ta shigo nan ta ɗauke ta. Ta fara mana darasi, kafin wani lokaci tayi barci. "Ina Mamanta?" Mikewa nayi na je na amsheta. "Jikinta kamar da zazzaɓi, ki bata magani." "Tow na gode!" Na wuce da ita, na zauna muka cigaba da darasi, ta fara goma ta gama sha biyu, sai karfe biyu zuwa biyar haka muka wuni. Koda ta farka magani na bata da abincinta, wasa ta cigaba da yi, har muka taso. Haka na cigaba da tafiya da ita har aka warware hannun, na sakata a daycare. Ba lallai kowa ya fahimce ni ba, amma nasan har ga Allah shi daycare makaranta ne, su kuma Barakatu, ba zan daura musu dawainiyyar bari-bari ba, haka yasa na yanke shawarar sakata, amma nasan ran Mamansu ya b'aci,. Sai dai ban wani damu ba. Domin yanzu ba da bane da damuwar wani zai hana ni nutsuwa, sannan a gefe guda ina tsoron kada wata rana Uwarta ta bayyana taga yarta ta nakasa ta ce ban rike amanar da ta bani ba, gashi na nakas ta mata yarta. Watana biyu da fara karatu aka fara shirin azumi, nayi farinciki sosai amma kuma sai nake ganin kamar ba wani farinciki da karsashi, dake ina koyon tukin mota kuma mutumin ya gaya min bayan sallah ba xai cigaba da ajiye ni a school ba, iya wa'adin shi ya ƙare, na takura kaina sai na koyi mota. Domin ni sai abin yazo min banbanrakwai. Haka na cigaba da zuwa koda aka fara azumi ina makarantar aka kawo min duk wani abin bukata, "baban Barakatu basu gaya maka daga ina suke ba?" "Gaskiya basu fada ba, kawai ajiye min kayan suka yi suka tafi." "Shi kenan!" Na bude kofar ya shigar min da shi store, sannan na wuce daki ina nazarin waye da wannan dawainiyyar. *In sha Allah, ba zaki sake kuka don yunwa ko wurin kwana ba, duk wani abu sai dai ki bawa wani. Nayi alƙawarin ko bayan raina ba zaki wulakanta ba, zan tsaya miki idan ina raye. Haka koda na mutu sunana zai cigaba da baki duk wani abin da zaki roka, a tab'a kimarki ba, ba zan tab'a barin ki rasa shi ba.* Zubewa nayi akan gwiwata na fashe da kuka, wata irin rayuwa nake yi ne? Da farko mutumin da ya taimaka min ya kubutar dani a hannun wancan azzalumin, babu shi babu labarinshi, na ganshi ma nayi mishi godiya babu dama, Aunty Umaimah ma, ban san inda zan same ta ba. Shima wanda nake farin cikin na same shi, baya nan baya nan ya tafi "innalillahi'wa'inna'ilaihi'raji'un, me yasa mutanen kirki suke fita a rayuwata lokacin da nake tsannanin bukatarsu???????????? #Mai_Dambu ```Hajiya ga kaya nan Masha Allah, Available price Huluna da Mayafai, da na yara sai Wanda ranko yakeso gasunan kala kala, Hajiya muna dasu ba iya hulana da Mayafai ba, har da shadodin na fitar sallah, Hajiya domin hutar dake da fitar dake kunya na tanadi yadda ba zaku sha wahalar yawo kasuwa a cikin azumi ba, don haka kafin kishiyarki tazo ta sata au 🤣😹😂 kafin kishiyarki tazo ta saya na tayiwa mijinku shakara gara kizo ki sata au 😔🤣😹 baki ya saba gara kizo ki saya, barauniyar gida, kai Sarauniyar gida 😂😹 atow kayana na Uwaren gida da na Amare ne``` *TUNTUBE WANNAN NUMBER 08130269641* Laces ATAMFOFI SHADODDI Materials Kayan yara Veils Huluna....etc [3/6, 8:07 PM] Cutie cutie pie: *BAƘIN HAURE....🐾🐾* {Greed for Money is the roots of all evils🫀} Arewabooks:maidambu41 Wattpad:Mai_Dambu Mallakar:Mai_Dambu *030* Haka nayi ta kuka ina jin kamar bani da sa'a shi yasa mutanen kirki suke barina, nayi kukana na godewa Allah. "Ma....ma!" Naji Muryar Baby Amirah sugrah, bude idanuna nayi a kan fuskarta, da sauri ta tako zuwa wurina, bude mata hannu nayi ina jin sabon kaunarta. "Ta kira ni Mama!" Na fada da karfi wanda yasa na kara k'ank'ame ta a jikina. "Amirah sugrah, nice Mama?" Sai ga hawaye ashe haka uwa take ji? Ranar da d'anta ya kirata Mama, ashe haka abin yake da dad'i,. Sai ga hawaye shar da duminsu, wannan irin bazatar da Amirah tayi min da tab'a zuciya yake, sai na rasa kukan farinciki nake ko na bakinciki, bakiɗaya rayuwata ta kuma sake samun wani nauyin daga wanda na amsa, domin amsa sunan uwa ba karamin al'amari bane, balle irina da nasan dayawa suna son sanin wacece ni, kuma na fahimci haka a makaranta musamman idan aka ga yadda nake makale da ita, a cikin aji. Sai ya kasance kowa son sanin wacece ni yake meye alakata da Yarinyar da nake dauke da ita. Sai dai na barwa zuciyata wannan aikin ba zan fara buɗe cikina da zuciya ta ga kowa ba, komai alakata da kai balle kuma na fahimci idan har mutane suka ji ina turanci, sai na zama kamar wata criminal domin yadda yan Nigeria muka b'ata kanmu ba mazan ba matan. Mikewa nayi na nufi store na ware kayan cikin kitchen din na fito da shi, sannan na nufi hanyar waje, na kira baraka ta dauka musu, ina shiga na samu suna aikin abincin buda baki. "Tante baki bar aikin da za ayi miki ba." "Assalamu alaikum! Amma ai na fara sallama ko?" Murmushi tayi tana sosa kai. "Wa'alaikis salam, Amirah tunda kika fadi tante ta raba mu dake!" Inji Zainab mai bin Baraka tana amsar Amirah. Murmushi nayi nace mata. "ba haka bane, kawai idan na barta ba zan iya nutsuwa ba, amma ai yanzu ma gamu a gida." "Sannu Maman Amirah!" Murmushi nayi, ina mai rusunawa na gaida ta. "Yawwa Maman baraka, ya zafin nan ya niyya kuma?" "Alhamdulillahi, ya makaranta." "Masha Allah, sai godiyar Allah." Na fada ina zama, "Nace baki bar abin da za'ayi miki ba?" Murmushi nayi nace mata, "Maman baraka, jiya aka fara azumi yau biyu babu wani abin tashin hankali, yanzu aka fara kuma ina ji ba zamu cigaba da zuwa makaranta ba, domin nan da sati biyu zamu dawo gida hutu sai bayan sallah." "Ayya amma da kina barin aikin, domin a rage miki kafin ki dawo." Murmushi nayi ina kallon yadda suke ta shirin buɗa baki, "yawwa Baraka, ke da Zainab ko zaku dauko kayan abinci yana kofar kitchen." Kallon Mamansu tai, kafin ta kalle ni. "Maman Amirah!!!" "Kuje ku dauko." Hadiye yawu tayi tana son magana amma naki mata magana, sai kallon garin kunun da zasu yi. Ina zaune bayan fitarsu sai ga Babansu. "Wai ayi haka?" Murmushi nayi, a karon farko na kara samun wasu ahalin me ya kai haka dad'i. Haka suka fito da kayan abincin, muna da shinkafa da na bude tun zuwa na, sannan na basu buhu guda, taliya, makaroni, na dibar musu sugar sai madara da na ware musu da Ovaltine. An karo min nama da kifi, na basu daga cikin wanda nake da shi. A hankali naga hawaye a idanun bayin Allahn nan, yana zuba sai naji kamar an sauya ni, domin ban basu don su min kuka ba, na basu ne don niman lada. Haka suka yi ta min Addu'a. Tashi nayi na bar musu Amirah don taki biyo ni , haka na dawo na shiga aiki, dankali na fere sannan na zuba mishi ruwa, na koma daki nayi sallar la'asar don nayi azahar a makaranta. Ina idarwa na shiga soya tare da gyara kaza nayi mana farfesu mai dankaren kamshi, na koya ne a wurin Zuzu, sannan na daura jallof din taliya, dake gas ce cikin lokaci ƙalilan na gama, na wuce ban daki nayi wanka na sauya zuwa doguwar rigar material me laushi da taushi na Amnas collection da hula me kyau, body mist na shafa oil ɗinshi. Na nufi hanyar falon na zauna ina kallon agogo karfe shida da minti uku, ina zaune a wurin har da minti ashirin, na mike na fito da kome falon na jera, sannan na wuce dakina na dauro alwala, na fito ina azkar da salatin Annabi Muhammad Sallallahu alaihi Wasallama, ina zaune har aka kira sallah, a lokacin Baraka da Zainab suka kawo min kunun tsamiya da kosai, ba karamin dad'i naji ba, haka na nuna musu abincin da na zuba suka ɗauka suna godiya. Kunun da kosai naci, na koma daki da Amirah nayi sallah, ban fito ba sai da nayi sallar Isha da tarawee, sannan na fito na saka hand out a gabana, ina karatu ga Abincin wurin, ina ci ina karatun. Daga nan ina jin Radion Baban baraka, da yake sauraren Malam Jafar Mahmoud Adam, haka kawai naji ina son rike waya, ina tow tawa take? Sai lokacin na tuna na bar kome a can garin. "Gobe in sha Allah, idan na fita zan nime waya domin na gaji da shirun nan, ni ba Ma'abociyar kallo ba, balle nace zan yi kallo kawai dai nasan ina son jin Radio kasancewar Baffa'm yana ji, sannan Alhajijo shima yana yawan sauraren Radio. Haka na tashi abincin da na zuba, tare da farfesu. Har wurin karfe sha biyu, na mike zuwa daki na sauya kaya, tare da alola na fara sallah, sai wurin karfe biyu na idar na kwanta. Akwai wata dabi'ar da nasan na koya a bayan zuwana garin nan shine kuka kafin nayi barci, haka na ci kuka na koshi, sannan barci yayi gaba da ni. *** South Africa. Tunda aka fara azumi yau biyu ga wata, lumshe luhu-luhun idanunshi yayi yana kara bude su, jin wayarshi tana kara. Bai bude ido ba, ya dauka Sannan ya saka a kunne. "Yes.!" "Ubangiji ya shirye ka." A hankali ya tashi zaune yana kallon gefen gadonshi, ya kunna wutar dakin yana jin wani yanayi don bai saba ganin haske a dakinshi ba. Tattaro nutsuwarshi yayi ya ce mata. "Hajiya Barka da shan ruwa." "Hmmm Barka dai Alhaji, ya Ibada?" "Alhamdulillahi!" "Ina rokon arzikin kazo kayi hutu a gida." "Hajiya!" Ya kirata, "Na gama magana na baka nan da kwana biyu, idan ka sake aka yi azumi biyar baka zo ba, Abdul Majid na barwa sojoji kai. Kai ka saka ni a damuwa dan uwanka ya saka ni a kunci gaya min ya zanyi? Na maka uzuri tunda baka da lafiya, ina son farinciki da nutsuwa na zaɓe ku sama da farinciki na, idan na isa ka taho idan ban isa ba, ka sha zamanka Allah ya baka sa'a!" Kit ta kashe wayar, kut da wani tsalle ya dira a gadon, ya nufi inda kayanshi suke,. Ya shiga zubawa a wata Kyakyawar Luggage, yana gamawa. Ya koma ya zauna tare da kiran Aryan. Sai da wayar ta kusan katsewa sannan ya dauka, Muryar shi a shake ya ce mishi. "Hammayo lafiya?" Yarrrrr yaji kamar wani abu yana yawo a tsakiyar kanshi. "Sorry zamu yi magana gobe, ina hanya." "Haba? Ubangiji ya kawo ka." "Amin Ya Allah!" Ya katse kiran, domin shi ba yaro ba ne, yana jin Muryar Nabeeha. A hankali ya ajiye wayar bakiɗaya yana jin shi kamar bai cancanci rayuwa ba, kowa na cikin farinciki da iyalinsa, amma banda shi. Rufe fuska yayi da tafukan hannunshi yana jin wani abu yana tsaya mishi a rai. Kusan shekara daya da rabi kenan, Umaimah ta kasa samo yarinyar da ya yanketa, yana tsoron kada sanadin wannan yankar ta mutu, domin yasan yadda irin wannan yanka yake, bakiɗaya jin shi yake sama-sama da zaran ya tuno da abinda ya faru. Sai yaji kamar yana da hannu a cikin abin da ya samu yarinyar tunda Umaima ta gaya mishi sun koma garinsu har anyi faɗa sun tashi amma taji labarin kamar faɗar da aka yi ya shafe ta, ko mutuwa tayi shi bai ma iya tuna abin ba, amma tabbas yaji Umaimah tana faɗin anyi faɗa a garinsu ga abinda ya faru, wani takurarren numfashi ya fesar, yana jin kamar bai kyautawa kanshi ba, na rashin ganin fuskar yarinyar amma ya rike muryarta, har a kwanan gobe ba zai manta da sassanyar murya mara amo da kwaramniya ba, shi fatan ma ya ga fuskarta ko sau daya ne, amma ina sai yanzu ne ma yake danasanin domin Umaima da ta gaya mishi, ita ce suka yi barci da ita a gado daya, a ranar da suka zo aikin ceto rayuwar sojojinsu, shafa kanshi yayi cikin tsananin damuwa da takaicin halin ko in kular shi, amma kuma a gefe guda sai yake ganin bai ga dalilin tunawa da ita ba. Meye hadinshi da ita? Meye matsalarshi da ita? Sam baya jin yana da wata alaƙa da zai saka shi tuaninta. *** Yahunde. Cameroon, Shashekar kuka take tana jin kamar zuciyarta zata buga, domin wani irin tukikin tashin hankali take ji a ranta, tana jin wani azazzben zafi da ciwo a ranta, ita kanta bata san iya adadin lokacin da ta dauka a gaban Mahaifinsu ba, kukan yayi yawa da yasa Yafendo tashi zuwa ɗakinta Sumee ce ta kasa hakuri ta ce mishi. "Ayya Ayya Datti haka zaka cigaba da kallonta, tana kuka abu biyu ta rasa fa, ta rasa miji da Yarta ai ba zaka zuba mata idanu har haka ba." Yalwataccen murmushi ya saki, yana faɗin. "Bilkisu idan har Nafisah bata fahimce ni ba, ai ke ya dace ki fahimce ni. Iya su biyu mata Allah ya bani a tsakanin Ya'ya maza, Allah sai ya albarkaci rayuwarsu da jarabawa, idan ban gode mishi ba, me zan iya yi ? Alhamdulillahi Allah ya basu ikon cinye jarabawarsu." Ya fada yana murmushin karfin hali, domin izuwa yanzu yasan yayi kuskure, ahalinshi sun yi kuskure da ya shafi bayansu. Kuskuren da yayi ba karamin kuskure ba ne, yayi watsi da Amanar da Allah ya bashi, ya watsar da Yaran dan uwanshi sannan ya rungume kashi. A ina zai ga Isma'il da Aminatu? Ta haka zai gyara kuskuren da yake bibiyar Yaranshi mata da jikokinshi. Ace Yaranshi mata biyu, a wulakance ake aurar dasu, sannan mazajen su azabtar dasu da Yaransu. "Tashi ki tafi Allah ya kara miki hakuri da dangana, Ubangiji ya mata rahama, sannan ki rungumi Zaytoonah domin tana jin zafin hanata ganin mahaifinta, wannan ma wani jan aiki ne da dole sai kin yi da gaske. Allah ya kara miki hakuri." "Baffayo." Sai kuma tayi shiru kafin ta fashe da wani irin kuka, "Sai hakuri idan har ka yi hakuri, akwai riba da fa'ida." Mikewa tai ta nufi cikin gidan, tana kuka har dakin Yafendo. D'ago kai Zaytoonah tayi tana kallon yadda take rusur kuka. Kauda kai tayi bata jin tausayinta ko kad'an, ta roke ta ta bata hakuri ta ce ta yanke mata kome, ita dai ta barta taje ta ga mahaifinta da Yayarta, amma taki sai yanzu zata yi wani kuka. Ita kuma da bata san shi ba fa? Ita da bata ji duminshi ba fa? Hmmm ita kukan dadi take tunda gata da nata iyayen ita kuma tayi mata asarar rashin ganin Ubanta. Ita yanzu ta tsani kowa ma banda Babynta, domin ba zata iya tsanar Babynta ba, tana son abinta kuma ba zata rabata da mahaifinta ba, domin ita nata rayuwar ta zama incomplete, tunda ta rasa inuwar uba, hatta zaman aure ya haramta a gare ta, domin abinda ya kashe mata aure har da gorin rashin uba. Haka kawai ta ja... "Zaytoonah!" Mikewa tayi tare da ɗaukar yarta zata bar dakin. "Ki tsane ni babu laifi amma, idan kika nisance ni mutuwa zan yi. Da kewar shi xan ji ko da rashin yar Uwarki? Zaytoonah ina cikin wani yanayi da ban san mafarinsa ba, balle karshensa..... #Mai_Dambu ```Hajiya ga kaya nan Masha Allah, Available price Huluna da Mayafai, da na yara sai Wanda ranko yakeso gasunan kala kala, Hajiya muna dasu ba iya hulana da Mayafai ba, har da shadodin na fitar sallah, Hajiya domin hutar dake da fitar dake kunya na tanadi yadda ba zaku sha wahalar yawo kasuwa a cikin azumi ba, don haka kafin kishiyarki tazo ta sata au 🤣😹😂 kafin kishiyarki tazo ta saya na tayiwa mijinku shakara gara kizo ki sata au 😔🤣😹 baki ya saba gara kizo ki saya, barauniyar gida, kai Sarauniyar gida 😂😹 atow kayana na Uwaren gida da na Amare ne``` *TUNTUBE WANNAN NUMBER 08130269641* Laces ATAMFOFI SHADODDI Materials Kayan yara Veils Huluna....etc [3/7, 10:49 AM] Cutie cutie pie: *BAƘIN HAURE....🐾🐾* {Greed for Money is the roots of all evils🫀} Arewabooks:maidambu41 Wattpad:Mai_Dambu Mallakar:Mai_Dambu *031* "Ni a sanina ban ki shi ba, tunda nice na kawo shi nace ina son shi, ashe don haka ya faru uziri ya dace ayi min ba fushi da b'acin rai ba." Ta fada tana kuka sannan ta cigaba da cewa. "Na amshi kuskure na." Juyawa Zaytoonah tayi ta koma gareta, ta zauna tana me dora mata Baby Zahra a saman cinyarta."Ammy ki daina kuka, don Allah." Ta fada tana jan hancinta. "Dole nayi kuka, yar uwarki ta rasu baku gana ba, mahaifinku ma haka duk laifina ne." "Bana jin Didi ta rasu, baffanmu kan jikina ya bani baya raye, amma Didi fa ina jinta a raina sosai da sosai." Rungume su tayi tana faɗin, "duk inda take, tana cikin kariyar Ubangiji, Allah zai shiga lamarinta a ko ina take." Wato idan har aka samu irin ahalin Sheikh Aliyu Wodabbe, zai yi wahala wata fitina ta sauko ba tare da an samu warakar shi ba, tun da suka ji labarin mutuwar Baban Zaytoonah, hankalin kowa ya tashi haka yasa Zaytoonah rikice musu, tare da nisanta kanta da Mahaifinta, duk da kowa yaso mata bayani amma taki fahimta. Haka yasa taje har gaban Sheikh Aliyu Wodabbe, ta ce ita ya mata lamuni zata bar gidan ta tafi neman danginta da suka rage a duniya. Shine ya kira Aminatu da Yafendo da Sumeye, Zaytoonah tana zaune a wurin. "Na kira ku ne, domin Zaytoon tana son ta tafi neman ahalinta." Da sauri Ammynta ta d'ago kai tana kallonta cikin wani irin rawan jiki tace mata. "Ba dai tafiya zaki yi ki bar ni ba?" Girgiza kai tayi tana kara faɗin. "Kiyi hakuri nayi laifi wallahi nayi laifi, nasan nayi laifi tunda kike shirin gudu na, don Allah kiyi hakuri. Amma kada ki tafi kiyi hakuri na had'aki da Manzon Allah Sallallahu alaihi Wasallama." Kwalla ne masu zafi suka shiga zubo mata, tana kallon yadda mahaifiyarta take kuka da dukkanin zuciyarta, mikewa tayi ta bar wurin, haka yasa Yafendo bin ta dakin. Kuka ta saka tana kara jin zafin Ammyn har Hamma tasa ya roke ta, duk shirin da suke da Hamma sai da ta mishi rashin mutunci, amma yanzu ta zauna tana mata wani kuka mara hujja. "Idan kin shirya ki gaya min, akwai kanwata da muke Yayan mata a Yola, tana aure a can idan kika tafi zasu tayaki niman sauran danginki. Amma kafin nan bari na gaya miki wani abu. Da ace Allah bai nufa an ga Aminatu da wuri ba, ta wuce wani wurin da lalurar gushewar hankali ga kuma cikinki, tow kuwa ba makawa bamu san abinda zai faru ba, imma da tun lokacin kin mutu ke da ita, ki godewa Allah tunda har kika taso an tab'a miki gorin yar mahaukaciya? Tow hauka tuburan Aminatu tayi, da ta warke kuwa ko da wasa bata kaunar ka tambaye ta, bayanta ki godewa Allah da mari kika sha a duk lokacin da kika tambayi bayanta. Saka ran mahaifinki zai biyo sawunta yasa Malam dakatar da ita har na tsawon shekaru Domin tsakaninki da yar Uwarki, tazarar me yawa ce. Ba zance kiyi hakuri ba domin an zalunce ki, amma a matsayina na mahaifiyar Aminatu dole na kare mutuncinta da rayuwarta, tana kuka ne don ta rasa abubuwa masu muhimmanci a rayuwarta, sannan tana shirin rasa ki a karo na uku. Ke baki jin tsoron kukan da take yi wata rana yarki ta saka ki?" Da sauri ta d'ago kai tana kallon yafendo bakinta yana rawa ta ce. "Yafendo!" "Mahaifiya ce ita, bai dace a saka ta kuka har haka ba, hakan zai tab'a rayuwarta da lafiyarta." Daga haka ta bar dakin, har ta kai bakin kofar ta ce. "Ba fata nayi miki ba, kina da damar yin fushi da kuka da fada, da ihu amma ki sani itama an mata uzuri domin ba laifinta ba ne, haka Allah ya shirya lamarinshi da ace mutum yasan abinda goben shi zata bayar da zai gyara wanda yake ganin ya dace da shi, ki yi hakuri na baki hakuri ne a matsayina na mahaifiyar Aminatu. Ba a matsayin kakarki ba ki dauka a wani wurin aka miki kuskure to ina mai kara baki hakuri." Daga haka ta bar dakin, tabbas Yafendo ta tsayawa yarta at least ta nunawa Jikarta itama tana son Yarta, ba zata sake damuwa ya cutar mata da Aminatu ba, kamar yadda tana ji tana gani aka hanata akan Yar uwar Aminatu. Wannan abubuwan yasa Zaytoonah, hakuri da mata uzuri, amma bakiɗaya bata jin dadin rayuwarta. "Ammyn ina son tafiya Nijar na cigaba da karatu a can!" Ta fada tana kallon Ammynta. "Indai haka zai saka ki farinciki na amince, zan kira Dadah na gaya mata, sai ki tafi can Allah yasa haka shine mafi alkhairi." "Amin Ammyna, in sha Allah zan binciko mana inda Didi take." Inji Zaytoonah. "A'a kada ki wahalar da kanki, in sha Allah zata zo gare mu." Cikin shashekar kuka ta ce mata. "Muma dole mu neme ta, ba zamu jira sai tazo ba." "Hmmm kin dai ce tana raye ne, amma yadda nasan rigimar su da mutanen garin nan zai yi wahala idan bata mutu ba." "Wallahi tana raye tana raye na rantse da Allah." Haka suka yi ta kuka a tsakaninsu. Har bayan an sha ruwa Malam ya kirasu ya musu nasiha da addu'ar idan Zahra tana raye Allah ya bayyanata, idan ta mutu Allah ya mata rahama." Haka suka yi ta addu'a, sannan suka tashi. Duk da dai zuciyoyinsu babu dad'i amma kuma haka bai hana su sakin ransu ba, domin kuwa kowa yana jin ciwon abin da ya faru. Musamman Ammyn gani take kamar da wata a kasa, haka kawai ba zata samu lalurar gushewar hankali ba, sannan daga baya, taji kamar zata mutu idan aka tambaye ta, me ya faru ko ina mijinta yake. Wannan abin ya sakata cikin damuwa, bayan sunyi sahur, Ta kira Yayarta ta gaya mata, cikin farinciki da murna ta ce tazo tana bukatar abokiyar hira. Sannan ta gaya mata dalilin zuwan Zaytoonah karatu zata yi, Itama ta karfafa mata gwiwar haka, dake Allah ya taimaka dukkansu suna da abun yi domin itama Aminatu koyarwa take a nan Jami'ar Cameroon. - South Africa. Sai da aka kai ruwa rana, kafin suka bashi hutu tun zuwan shi bai matsa ko nan da can ba, yana makale da aikinsa, sannan da ya nemi hutu kin bashi suka yi, sai da ya koma ya rubuta musu ajiye aiki. Da shugabansu ya gani a fusace ya yaga takardar. "kana da hankali kuwa? Kasan yadda muke alfahari da kai da zaka so ajiye aikinka?" Kusan soja da bala'i da masifa da ihu, shi dai bai ce kome ba yayi shiru yana sauraren Commander ɗinsu. Har ya gama sannan ya dauko wata takarda, ya rubuta mishi an bashi hutun sati biyu. "Sir mahaifiyata ba zata fahimce ni ba, sannan ina son a bani koda wata daya ne, nasan is too hard na samu wannan kwanakin. Amma idan na ajiye aikin zata fahimci ita din abar girmamawa ce." Dake Commander din Muslimi ne kuma dan arewancin Nijeriya, murmushi yayi ya ce mishi. "Abdul Majid Mamman Ba'are, nasan waye kai Chairman guda da yake gudun matsayinsa. Sai dai an haife ka ne domin ka zama soja, ba wai kayi aiki da sojoji ba, zan baka wata gudan amma ka sani can kujerar da kake gudu, zata bibiye ka a duk inda kake matukar kana raye. Kasa yayi da kanshi yana kallon takalminshi da bai daura igiyar ba, "mahaifiyarka tana son ka rike matsayinka ne, domin hankalinta zai fi kwanciya. Sai dai ba abu me sauki bane a wurinka. Kayi imani da hawa saman teku domin aikinka, ka dauki kamfanin a matsayin teku ne, ta gaya min kome akanka da kuma kamfanoninku." Bai ce mishi uffan ba, yasan halin shi sarai ko abokan aikinshi ba karamin mita suke akan wannan halin nashi na rashin magana ba, har kawo ƙararshi suke amma babu abinda ya sauya, wani irin murdadden hali ne dashi, yaki sabo da kowa aikin shi kawai yake baya kula kowa baya harka da kowa baya shiga harkar kowa, ina ka fito aiki ina zaka aiki. Haka yasa ko irin yan matan nan babu me shiga sabgar shi, domin sun tabbatar da cewa shi din ba daidai ba ne, kuma bai da lokacin mace. "Shi kenan Allah ya tsare, ka dawo lafiya." Salute yayi sannan ya dauki takardar, ya nufi hanyar waje, yana kallon agogon hannunshi. Sam bai dauki rayuwarshi da zafi ko fadi ba, asalima ya ajiye kanshi inda yake ganin nan Allah ya ajiye shi, bai tab'a nuna fad'in rai ko kuma nuna cewa shi din wani ba ne, yasan yana da dukiya me yawan gaske, amma haka bai tab'a damunshi ba, asalima shi yafi saka kanshi a matsayin kananan mutanen da suka taso cikin talauci da wahalar rayuwa. Wannan yasa baya jin girman kai ko wani abu, meye a rayuwar da wata rana mutuwa zaka yi, sannan magana ce babu wanda ya isa saka.shi, shi bai saka kowa lallai dole a kula shi ba, kuma baya jin lallai dole sai yayi magana duk wanda yaji haushi to ya daukarwa kanshi dala ba gammo ne. Daga headquarter ɗinsu, airport ya wuce dama da shirinsa ya fito, ba zai sake a kai azumi na biyar bai sha ruwa a gaban Hajiya ba, domin yana tsoron Allah yana tsoron fushin Hajiya, don haka yana zuwa bai samu jirgin nijar ba, sai na Algers ya samu, bai wani b'ata lokaci ba ya biya yana jin yana isa nan da awa biyu, zai samu na nijar tunda yasan basu rabuwa da masu shiga da fita a kasar, haka yasa shi bawa zuciyarshi hakan. Bayan wani lokaci jirginsu ya tashi, bayan awa biyu suka sauka a Algers, yana zaune a inda zasu jira jirgin nijar. Wata Kyakyawar budurwa, tazo ta zauna a wurin murya kasa-kasa take faɗin. "Ni zanzo ne kawai amma ba wai don ina da ra'ayin haka ba, don bana kaunar abinda ya haɗa ni da BA'ARE family." Da wutsiyar idanu ya kalleta. Tab'e baki yayi tare da kauda kanshi, ashe akwai masu tsanar BA'ARE family ba shi daya ba ne. Kiran fasinjoji nijar yasa suka mike baki daya, wani abin mamaki shine sit dinsu kusan wuri guda, zama tayi tana faɗin. "Mame sai nazo, ni dai bana son zuwa kika kira ni, Allah ya gani ba zan sauka ba, meye a cikin wannan gidn ban da masifa da hakkin Hajiyarsu Aryan kada ki biyewa Appa domin zai kai ki ya baro ki ne, nafiki sanin waye shi. " Ta kashe wayar tana jan tsaki, kauda kai yayi tare da saka facemask ɗinshi, baya jin zai iya hayaniyar yarinyar nan, ban da yasayi kujerar da ya koma VIP. Wuraren biyar da rabi suka isa nijar, bayan sun isa ne suka yi ta fitowa. Aryan da yazo daukar Majid din ya hangota. "Maisarah!" Tawowa wurinshi tayi, tana murmushi. "Ya Aryan kazo dauka ta ne?" Watsa mata harara yayi yana faɗin. "Hammayo dai!" Ya nuna mata shi, da yake bayanta. A hankali ta juya tana kallonshi baki sake. "Dama tare muka zauna shine bai nuna min ya sanni ba?" Murmushi Aryan yayi yana amsar jakar Majid. "Barka da hanya, muje na ajiye ku baki daya." Haka ta fito tana jan jakarta, shi sikagon ana jan nashi, yana isa wurin motar ya bude baya ya shiga, tsayawa tayi tana kallonshi. "Shiga gaba!" Haka ta shiga tana mamakin duk gaishe shi da Aryan yayi bai amsa ba, sai dai buga bayan shi da yayi, wannan irin lifestyle din yana matukar burgeta, ta madubin gefenta take kallonshi, ya wani zauna like king yayi crossing leg, hannunshi dukkan biyu ya baza su kamar wani wanda yake kan karagar mulki. He look like king . "Ya Aryan!" Ta kira sunanshi a hankali, "hmm!" Ya ce mata. "Amma Hammayo yana da nasaba da sarauta ko?" Gyara zaman madubin gaban yayi yana kallon Majid din da yayi wanann zaman, murmushi yayi yana faɗin. "Me kika gani Maisah?" "Hmm! Zamanshi da halinshi." "Masarautar Agadaz, itace babban tushen nasabarsa " duk abinda suke fada yana jin su, kawai amsawa ce bai da niyya kuma ba zai amsar ba koda yana da niyya. Shi yarinyar ta cika rawan kai, shi yasa ba zai magana ba. Haka sukayi ta hirarsu tana kara kallonshi a madubin gefenta, tana jin wani abu yana cika mata kai da ruhinta, a karon farko da ta haɗu da irin namijin da take fata, ita kan zuwa nijar ya mata rana.. har suka isa Aryan ya sauketa a gidansu, sannan ya wuce da Majid. "Hammayo kayi kasuwa wallahi, kaga har yanzu bata shiga gida ba, gaskiya wannan karon zamu sha biki bayan sallah." Bai ce mishi uffan ba, suka shiga cikin gidan su, ajiyar zuciya ya sauke tare da kai hannu ya bude kofar, ya saka kafarshi ya fito a hankali, yana jin kamar bashi ba. Haka ya nufi cikin gidan bayan ya cire facemask, ana gaishe shi. Amsawa yake da kai kawai. Har ya isa falon Hajiya tana zaune Amaan yana kwance a saman Kujeran, dama ga azumi ga rashin lafiya da yake boye musu. Cikin kulawa da wani irin idanu Majid ya zuba mishi ido yana karantar shi, tabbas Amaan bai da lafiya domin har fatarshi tayi duhu, amma sanin ba wani shiri suke ba, yasa shi yin fuskar shanu ya wuce gaban hajiya yana faɗin. "Gani nan nazo Hajiya." "Kaje ka sauke ibadar da yake kanka." Mikewa yayi ya wuce dakinshi, bai fito ba sai da aka fara kiran sallah ya sauko a hankali, ya samu duk sun hadu a falon ana addu'a, zama yayi aka yi da shi sannan ya dauki dabino da ruwan dumi ya sha, sannan ya koma gefe yana sha yana kallon Amaan da yake rike cikinshi. Suna gamawa suka wuce masallaci, Hajiya tayi nata sallah a gida, bayan sun fito suka dawo aka cigaba da buda baki. "Amaan baka da lafiya ne?" Da sauri ya kalli Majid. "Eh amma da sauki domin anyi min aikin basir ne." "Allah ya baka lafiya." "Amin ai da sauki yanzu." Inji Hajiya, "fatarshi tayi duhu kai ma ka gani ko Hamma?" Hadiye yawu Majid yayi yana diban farfesu. "Duhu sosai." Ya fada yana cigaba da cin abincinsa. "Ba fa kome lafiya ta lau, bana jin kome wallahi."."Eh ku ci abinci kawai." Haka suka cigaba da cin abincin, har suka gama sannan Amaan ya wuce dakinshi da yake falon Hajiya. Da idanu Majid ya bishi. "Ai kusan wata biyu kenan da samun matsala da Matarshi, ta kwashe Yaranta." "Allah ya kyauta." Iya abin da ya iya faɗa kenan domin ba zai iya magana ba, sai da yaci abinci ya koshi, suka tafi sallah Isha da taraweeh, sannan suka dawo aka zauna ana hira. Ya lura da Amaan din da yake yan zabure zabure, yana kallon wayarshi. A hankali ya dauke kai. Kamar bai ganshi ba. Shima latsa wayarshi yake. "Assalamu alaikum!" "Wa'alaikimun Salam, Maisah kece a gari?" Murmushi tayi tana faɗin. "Hjiya tare da Hamma muka zo ai!" Juyawa tayi tana kallonsu. "Kin ga basu gaya min ba." Shigowa tayi ta gaishe su sannan ta zubawa Majid idanu da yake ta latse-latse waya kamar baya wurin. "Hajiya kin sha ruwa lafiya?" "Lafiya lau, da fatan kin iso lafiya." "Alhamdulillahi," a hankali ta Ciro wata yar ƙaramar camera recorder. Hajiya tuntuni ina tason na baki wannan abin amma Allah bai nufa ba, don Allah ki ajiye a wurinki. Wata rana zai miki amfani, amma yanzu ba zai miki amfani ba, ki dai ajiye kawai." "Tow maisah." Sai lokacin ya d'ago kai yana kallonta. "Kun leka Nana kuwa?" Mikewa yayi ya nufi hanyar sama, Aryan ma ya nufi hanyar waje. "Allah ya shirye ku?" "Amin Ya Allah!" Inji Maisarah. "Ke zomu je na kai ki gida." "Tow!" Har zata mike ta rike hannun Hajiya. "Koda kin ji labarin wani abu ya biyo baya, tow ki sani saboda wannan Camerar ce, don Allah ki adana shi da kyau." Ajiyar zuciya Hajiya ta sauke tana faɗin. "In sha Allah babu abinda zai faru." Haka ta mata sallama ta bar falon, ita kuma Hajiya ta bi Majid dakinshi, ta kai mishi, tare da cewa. "Yarinyar ba yau take nuna min da wani abu ba, rayuwarta na cikin hatsari a yau ba gobe ba, nake son ka amince ka aureta. A daren nan ba sai gobe ba......... #Mai_Dambu [3/9, 6:39 PM] Cutie cutie pie: *BAƘIN HAURE....🐾🐾* {Greed for Money is the roots of all evils🫀} Arewabooks:maidambu41 Wattpad:Mai_Dambu Mallakar:Mai_Dambu *032* Sakin baki yayi yana kallonta kafin ya tattaro nutsuwarshi da abin da zai gaya mata Hajiya ta bar dakin bakiɗaya yanzu shi me zai cewa Hajiya? fisabilillahi Hajiya bata mishi gentle ba, shi fa auren familyn Ba'are gani yake kamar shiga lahira ne babu guziri, yo da guzirin ma ya aka kare balle ka shiga babu abin da zaka kare kanka. Yasan wani tarko ne ba wani abu ba ne,uban waye zai kashe ta a wannan lokacin da kowa yake ibada. Gyara kwanciyarshi yayi kamar ba zai tashi ba, can kuma ya mike tare da sauka ya saka takalman ya nufi hanyar waje. A falo ya samu Hajiya tana waya. Fita yayi yana kallon yadda garin yake, hannunshi sakale a cikin aljuhun wandonshi. A hanyar shi ta shiga gidan ya had'u da Aryan da yake dawowa daga rakiyarta. "Ina zaka Hammayo?" Sosa wuyar shi yayi yana kallon Aryan ɗin. "A irin wannan yanayin me yasa baka wuce gidanka ba?" "Na raka maisarah gida ne, domin wurin ya cika duhu kuma mace ce ta dauki kasadar fita a wannan lokacin. Tana bukatar wanda zai rakata gida." "Hmm!" Ya faɗa suka wuce zuwa gida, zama suka yi a harabar gidan. "Hamma kamar akwai abinda yake damunka?" Girgiza kai yayi, yana kallon sama. "Ban san me yasa hajiya take jan wasu abubuwan ba? Nafi Hajiya son nayi aure, amma kuma a haka na lura kamar bata yarda bani da lafiya ba ne, idan na auri Maisarah me zan mata? Sannan abin da nake boyewa zata iya cutuwa idan tasan halin da nake ciki." Ya fadi haka a hankali, shi kanshi Aryan sai yake ganin kamar sa'a yayi da Hamman shi yake gaya mishi irin wannan al'amarin, wanda kowa yasan halinshi da boye abinda yake ranshi. "Wayyo Allah taimako!" Suka ji Ihun Maman Maisarah, kallon juna suka yi, kafin su shiga Mamarta suka samu tana ihu. Shiga cikin gidan suka yi har da ita, dakin yarinyar ta nuna musu. Kur suka mata, aka rasa me bakin magana. "Don Allah ku taimaka min, kada ta mutu." Da sauri Aryan ya wuce kitchen dinsu, ya dauko wuka ya yanke igiyar da ta daure wuyarta da shi. Fita da ita aka yi, a lokacin su Nana sun iso. "Lafiya?" Yanzu Aryan ya rakota muka gaisa, da yake taje gaida Hajiya Sa'adatu, shine bayan tafiyarshi, naga an kirata a wayarta, ta dauka ban san me aka gaya mata ba, amma naga ta fita zuwa tsakar gida, daga nan ban bi ta kanta ba, ashe igiyar shanya ta dauko ta rataye kanta." "Kun yi ja'ira yar banza, waye ya gaya mata mutuwa shine mafita, me ma aka mata da zata kashe kanta, bayan ni ban mutu ba, ku kaita asibiti." Kallon Aryan Majid yayi, cikin wani irin yanayi da baya son ya zarge shi. Amma sai ya dauke kai kamar bai damu ba, haka suka tafi asibiti suna zuwa aka karbesu kusan kwana suka yi akanta, kafin wurin karfe biyar na Asuba likitocin suka fito daga cikin dakin da take. "Ya take ciki?" "Alhamdulillahi zamu ce, sai dai bakiɗaya ko zata rayu bai zama dole ta mori kanta ba." "Akan me?" "Saboda kashin da yake haɗe da bayanta, da spinal code dinta ya karye." "Innalillahi'wa'inna'ilaihi'raji'un, me yasa na kiraki? Kin rayu cikin firgici da tsoron kada a kashe ki, yau gashi ke baki mutu ba. Ke baki rayu ba." Mamanta ta faɗa cikin kuka da danasanin abinda ya faru, domin da tasan haka zai faru ba zata so Maisarah tazo ba, haka yasa ta cigaba da kukanta har gari ya waye, wannan faruwar lamarin ya kara saka tashin hankali a zuciyar mutane, musamman yan cikin gidan. Abin da yafi hurting ran mutane, shi ne a daren Aryan ne ya kaita gida, haka yasa baki daya ya shiga yanayin zargi da tuhuma. Karfin imani da tawali'u yasa Aryan bai haukace ba, amma sai da ta kai ya zauna yana kuka kamar karamin yaro a gaban Hajiya. Shi kanshi Majid tausayin Aryan din yaƙe ji amma baya son maganar gaskiya shi daya ne abin zargi a cikin gidan. Domin shine ya ganta na karshe kafin faruwar lamarin. Amma kuma maganar gaskiya bazasu ce shi ya aikata ba, sannan ba zasu ce bashi ba ne. Dole bincike ne zai tabbatar da haka. Ba karamar girgiza Alhaji Kamilu yayi ba, domin bai tab'a kawowa hakan zai faru ba. Sai dai da Hajiya tayi mishi maganar binciken abin da ya faru. "Wani bincike kuma? Babu wani binciken da za'a yi, domin nasan ƙarshe a cikin gidan nan aka samu wanda yayi wannan aika-aikan." "Ai gara a bincikan hakan zai saka mu daina zargin Aryan domin kowa yaji ta hadu da Aryan abin da yake ayyanawa a ranshi akwai wani kudiri ko wani abu na daban." "Na sani, sai dai hakan ba zai haifar mana da d'a mai ido ba, Allah ya bata lafiya kawai." Ya fada yana kara jin wani irin d'aci a ranshi domin Allah ya gani yaji zafin al'amarin, sannan duk wanda yayi wannan aika-aikan yasan abinda yake yi, shi yasa yayi amfani da rakota da Aryan yayi da zuwanta gidan Hajiya. Ajiyar zuciya Hajiya ta sauke, sannan ta ce mishi. "Shi kenan, tunda baka son binciken Allah ya bata lafiya. " Ta fada tana mikewa, tare da leka dakin Maisarah da take cikin Unconscious. *Idan wani abu ya fito bayan kawo miki wannan Cameran tow tabbas abin da yake ciki babban al'amari.* Wani irin zufa ne yake zubowa Hajiya, duk abinda yarinyar nan ta gani ba karamin al'amari ba ne, haka yasa ta nufi gida zuciyarta na wani irin zillo. *** Zahra A matukar gajiye na dawo, dake Allah ya taimake ni Amirah sugrah tana wurinsu, ina shigowa aka kawo ta, yarinyar nan taki zama, "kuje da ita kawai, na gaji gajiya zata kara min." "Tow Tante!" Suka fita da ita, ina kwance a wurin har wurin biyar, tashi nayi na nufi kitchen. Dama tun safe na surfa wake tare da dafa kwai, wanke-wanke na shiga yi, ina gamawa na zuba mishi kayan miya. Na zauna na markad'a shi. Ina tsaye har yayi laushi na juye ina nazarin nayi ta manja ko mangyad'a. Karshe haka nayi ta mangyad'a, na zuba kwai da kifi. Sannan na duba geron da na bawa Barakatu ta surfa min, na dauka na wanke shi tass. Sannan na zuba ruwa na watsa gefen. Bude frij nayi, na dauko yogot na ciro na ajiye. Na gyara alala ta na ɗora bisa wuta, sannan na koma daki nayi wanka. Na saka kayan shan iska, na fito nazo na dama kunun garin kunun da ruwan tsamiya na. Har kunun yayi min yadda nake so, na ajiye shi na daura shinkafa jallof, na cigaba da aiki. Ina haɗawa na dawo na kunna tv, na fara kallon tafsirin Malam Awwal Albani Zaria. Gyara kwanciya nayi ina kallon, sai da naji kamshin alalen ya cika min hanci naje na sauke, kusan uku suka fashe. Haka na ajiye na gama haɗa kome na fito dashi a faranti. Ina ajiyewa ana kiran sallah, komawa daki nayi na dauko jakata na tuna akwai fruit da na sayo. Haka na fito da dabino naci, na sha ruwa. Ban tashi a wurin ba, suka dawo min da Amirah, tayi barci kwantar da ita nayi na mika musu nasu abincin. Ina faɗin, "ku gaida min Mamanku." "Mun gode sosai!" .... Bayan nayi sallar Magariba da Isha da su tarawee,, na kwanta a falon. Har na fara barci sama sama, naji kukan Amirah dakin nashiga na cire mata kayan jikinta, na mata wanka na sauya mata na barci. Sannan na dawo dakin bayan nayi wanka da alola, na kwanta barci me nauyi ya ɗauke ni. Washe gari na tashi da wuri da yake Muna da test. Da wuri na wuce ban dawo ba, sai karfe biyu a gida nayi sallah. Haka aka azumi yayi ta tafiya, rayuwar da dadi babu dad'i, ban rasa ci ko sha ba. Amma sai nake ganin kamar daular tayi min yawa, ina matuƙar son da ko wani ne a cikin dangina na gansu, su dandani dadin da nake ciki sai dai.nasan kamar yadda Allah ya halicci wuta da ruwa basu gamuwa, haka nasan matukar muka hadu sai mun yi abin kunya, haka yasa ta wani bangaren nake ganin kamar nauyi aka sauke min akan Addah, gefe guda kuma ina jin kamar ban kyauta ba, ba dadi mutuwar mutanen da kasani. Amma kuma mutuwar Addah shine samun sukuni na da Amirah. Kwanciyar hankali da nutsuwa ya shige ni, sannan wani abin da ya kara bani mamaki ashe tun fil azal ina da kalar fata mai kyau, domin kuwa nayi fesh kamar bani ba. A makaranta ma gani na da Amirah yasa mutane dayawa sun shafa min lafiya, domin daga malamai har dalibai farkon zuwana sun fara matsa min da gaisuwa. Ni kuma na iya dauke kai bana kula kowa harkar gabana ta ishe ni. Saura kwanaki uku mu samu hutu, wani malami ba a department ɗinmu yake ba, amma bakiɗaya idanunshi yana kaina duk da bana son kula shi. Amma haka yake saka a kirani, Ni kuwa idan naje bana magana sai na tsaya mishi a kai. Yau ban shigo ba sai karfe goma, ina shiga department ɗinmu na ganshi dauke kai nayi kamar ban ganshi ba, koda na kusan wucewa ya ce min. "Zahra Buba!" Juyawa nayi nace mishi."Ni!" Tasowa yayi daga inda yake zaune ya ce min."Bayan ke akwai wata Zahra Buba ce?" Share shi nayi naki magana. "Ok! Dama akan yanayin gari ne ya kike?" "Bashi ya kawo ni ba." Na fada ina karawa gaba. "Ai naji labarin baki da miji zaman kanki kike." "Ina baka shawara da ka kiyaye kanka da bin rayuwar wasu, bin rayuwata kamar wasa da wuta ce." "Ai na zata wasa da mutuwa ce." Murmushi nayi na ce mishi. "Ban yi wannan wayewar ba, amma ka tsaya a matsayinka." "Ok zaki gani, wallahi matukar kika yi wasa sai na baki mamaki." "Ina mai baka shawara kada ka bani mamaki, kayi harkar gabanka nayi tawa." "Mtsew dani kike zancen." Ban kula shi ba, na wuce aji abina na gama abinda nake muka fito. Bayan nan aka sanar da mu dawowa makaranta sallah da kwana biyar. Haka muka bar makarantar, zuciya ta tayi min dad'i. Ba karamin dadi ba fa. A wurin ajiye motoci na ganshi, sai da gabana ya fadi. Sai da na isa jikin motar ya wani fisgo ni. Fitowa Badar yayi ya zagayo ban san me yayi mishi ba, sai dai naga ya sake ni da sauri. "Madame shiga gani nan zuwa." Shiga motar nayi babu musu. "Kayi hankali ba kowane abinci ake ci don koshi ba, akwai abincin da a madadin yayi maka dad'i, guba ce domin kashe ka zai yi. Nasan labarin kowa a cikin makarantar nan. Hmmm kace me?" "Ban ce kome ba!" "Yayi kyau, ko a hanya ka ganta ka kiyaye abin da zai saka ku had'a idanu. Ni nayi maka da sauki idan da wani ne tuni ya tashi kanka." Daga haka ya juya wurin motar ya shiga ya bar shi a nan tsaye, nima nayi mamakin me yasa yayi laushi lokaci guda, haka muka bar makarantar. Alhamdulillahi Yazid ya kare min mutuncina da kimata, yadda yayi alƙawarin. Abin ya tab'a ni da yasani kuka ban sani ba, baya raye amma babu wanda ya isa ya min barazana a kyale shi. "Meye alakarka da Yazid?" Juyawa yayi ya kalle ni, kafin ya cigaba da tuki. "Sultan zaki ce, idan ba Sultan ba. Ba zan iya baki amsar tambayarki ba." Ya fada yana cigaba da tukin, "Sultan kuma?" Na kuma tambayarshi, bai bani amsar ba domin har mun iso gidan. "Sultan! Waye Sultan Yazid?" Murmushi yayi sannan ya ce. "Mun iso gidanki..... ```Hajiya ga kaya nan Masha Allah, Available da saukin price Huluna da Mayafai,na manya da na yara sai Wanda ranku yakeso gasunan kala kala, Hajiya muna dasu ba iya hulana da Mayafai ba, har da shaddodi na fitar sallah, Hajiya domin hutar dake da fitar dake kunya mun tanadi yadda ba zaku sha wahalar yawo kasuwa a cikin azumi ba, don haka kafin kishiyarki tazo ta sata au 🤣😹😂 kafin kishiyarki tazo ta saya tayiwa mijinku shakara gara kizo ki sata au 😔🤣😹 baki ya saba gara kizo ki saya, barauniyar gida, kai Sarauniyar gida 😂😹 atow kayanmu na Uwayen gida da Amare ne``` *TUNTUBi WANNAN NUMBER 08130269641* Leshi ATAMFOFI SHADDODI Materials Kayan yara Veils Huluna....etc #Mai_Dambu... *BAƘIN HAURE....🐾🐾* {Greed for Money is the roots of all evils🫀} Arewabooks:maidambu41 Wattpad:Mai_Dambu Mallakar:Mai_Dambu Sorry Dearest yau babu editing 🥰❤️. *033* Jikina a matuƙar mace na fito daga motar, "Waye shi?" "D'a ne ga sarki Hamir Julaibi na kasar Algeria!" Bakina na rufe, jikina ya dauki wani irin rawa. "Me?" "Na gaya miki gaskiya." Juyawa nayi tare da barin motar, ina shiga falon na zube kamar wata matacciya, domin kuwa Yazid yana kashe ni da Mamaki,idan nace ban jijiga ba kayi karya. Ban san lokacin da kuka ya kwace min ba, tashi nayi da gudu zuwa dakina na shiga banɗaki na bude ruwa a kaina, zama nayi can gefen can banɗaki. Yadda na ke kuka ni kaina ban san akan me yasa nake kuka ba? Kukan me nake yi? Kukan ya boye min waye shi? Ya cutar dani ta hanyar boye min kanshi. Ban iya tsinanawa kaina kome ba, har aka sha ruwa tea nasha, sai kunu da kosai da na sha, da dare yayi na ta fasa indomi da kwai, na koma gefe ina ci ina hawaye. Da asuba kuwa sahur nayi da tea kawai. Washi gari wuni nayi kamar mara lafiya, ban kara wani walwala ba domin na sha mamaki. *** Tunda aka kawo shi asibitin, suke ta fama da lafiyarshi. Domin hankalin kowa ya tashi yadda yake duhu da fama da rama. Shafa kanshi Aryan yayi cikin tausayi. "Amaan" bude ido yayi yana kallon Aryan ɗin da yake kara shafa kanshi. "Me ke damunka?" Yana son magana amma babu bakin magana, haka kawai aka same shi a tsakar dakinshi yashe kamar matacce, haka yasa suka kwaso shi zuwa asibiti sai dai ko da suka zo an bincikar lafiyarshi ne. Tunda Majid ya ganshi yasan bai da lafiya boyewa yake, a binciken da suke ne aka gano aikin da aka mishi na cikin, Jamilah ta fito daga Lab rike da wasu takardun tana faɗin. "Hamma babu aikin basir. Akwai abin da Amaan yake boye muku wallahi." Amsar takardun Majid yayi suka wuce office dinta, shiru tayi tana kallon shi kafin ta bude baki zata yi magana ya ce mata. "Allah ya kyauta meye a cikin test din jininshi?" "Sakamakon bai fito ba" ta faɗa a hankali tana wasa da pen din hannunta. A nutse yake kara kallon takardun hannunshi, yana jin kamar ya fasa ihu ne ko kuka. Mikewa yayi ya nufi dakin Amaan. Yana shiga ya samu Aryan yana rike da hannun Amaan din. Shi kanshi bai san irin kallon da yakewa Amaan din ba, shin tausayi ne ko takaici ne? Domin bai kawo lalacewar shi zata kawo har haka ba. Dakyar ya bude baki ya ce mishi. "Tun yaushe ka fara...." Turo kofar da aka yi yasa shi shiru ya zubawa Hajiya idanu, "Majid meke damun Amaan din ne?" "Ciwon ciki ne, tare da borin jini!" "Ban gane ba." Hajiya ta fada a rikice, "Hajiya zaki gane, bari a gama bincike." Inji Aryan yana kallon Amaan, shigowar Jamilah yasa Majid suka kara fita, nan suka kara rikicewa kamar zasu tashi sama, domin ciwon sanyi ya shige shi sannan jikinshi zai iya daukar kowani mahaukacin ciwo matukar ba a kula ba. Haka yasa bakiɗaya Majid ya shiga wani irin d'imuwa da tashin hankali. Duk Familyn Ba'are babu wanda zai zo ba, domin Amaan bai da wani matsala da su, dake wawa ne yana shiri da kowa, haka yasa aka yi ta zuwa gaishe shi. Bakiɗaya ruwan kan Majid ya kone, taya zai gayawa Hajiya Amaan luwadi yake bai san da wata kalamai zai iya gaya mata ba, kallon Jamilah yayi yana faɗin. "Kada ki sake Hajiya ta ji labarin halin da yake ciki. Ki bari zan ji da kome." Numfashi ta ja tana kallon shi kafin ta daure ta ce mishi. "Hamma" "kada ki damu zamu yi magana da Aryan." Ya furta tana lashe bakinshi da ta bushe. A hankali ya a nufi hanyar waje, yana nazarin abinda zai fadawa Aryan domin bakiɗaya ya tattara damuwar ya azawa kanshi. Don yasan matuƙar Aryan da Hajiya taji sai zuciyarta ta kusan bugawa, ya kuma san idan aka gayawa Aryan kamar an gayawa Hajiya ce. Murmushi Hajiya Tani tayi tana kallon, videon Amaan tana faɗin. "Wannan lokacin ya dace na tashi kan Sa'ah." Shan ruwa da yake gaban shi Sajid yayi yana faɗin. "Hajiya Sa'adatu ta kare mata, dole ta biya abin da ta saya." Suka fada suna dariya, "Meye tsakaninka da Afiyyah?" Ware idanu yayi yana fadin. "Ba wani abu fa, chill out muke da ita kuma nasan an dauke ta aiki a kamfanin Ba'are." "Lallai kwanyarka bata ja Sajjid, taya zaka fara wannan aikin." D'aga kwalba yayi yana faɗin. "Bana kuskuren harkalla, duk abin zan yi Hajiya da tsari a cikinshi. Yarinyar ita ce Bingo dina, tana sona ina bata abinda take so. Sannan zan san yadda zata matsa jikin Chairman din kamfanin yadda zan basu mamaki." Murmushi Tani tayi tana faɗin. "Yaro yaro, ni na gama shirina saura ja jira tashin bom." Ta fada tana dariya, tare da barin falon. Da sauri ya bi bayanta yana faɗin. "Hajiyata me kika shirya?" "Lokacin da zai faru zan gaya maka, domin ni kome nawa da tsari bana faɗar tsarina kada a samu matsala. " Hura iskar bakinshi yayi yana faɗin. "Ni dai ki gaya min shirinki, domin kuwa ba mamaki na tayaki." Tsayawa tayi ta kalle ta kirashi da yatsu biyu, yana matsowa ta rike kunnenshi ta gaya mishi wata magana, murmushi ya sake. "Hajiya wacce irin Shaidaniyar tunani ne haka?" jan kunnen shi tayi tana faɗin. "Ba zan tab'a yarda wani ya san wacece ni sannan, ya dawo ya soke ni a baya ba, sun wanda ya sake ya ci amanata sai na mai da rayuwarshi abin kwatance yadda kowa sai yaso yaji me mutum yayi min haka." "A'a sam haka ba zai taba faruwa ba, ai kowa ya kwana lafiya shi yaso." Hajiya kam hankalinta yana kan Amaan, bakiɗayansu babu wanda yake zaune, azumin ma suna yi ne amma bakiɗaya hankalinsu yana can. A ranar da ya cika sati daya a asibitin aka sallame shi, domin ya d'aga musu hankali lallai a sallame shi. Hakan ya faru ne wani zuwan da Sajjid yayi mishi cikin daren rana na biyar ya, yana kwance ya shigo mishi don a sanin Amaan dai Majid yake zaune da shi amma bai san ya aka yi Sajjd ya shigo dakin ba. "Kana ta barci, ina can ina kewarka." Cikin tsananin tsoro Amaan ya ce mishi. "Sajjid wai ni daya ne kawai da ba zaka kyale ni ba? Ka kyale rayuwata kayi naka rayuwar." Dariya ya saka mishi yana faɗin. "Amaan ba zan kyale ba, idan ka kuskura ka haura kwana goma a cikin asibitin nan, tabbas ward din mata nan zai zama wurin kwanciyar tsohuwarka. Domin ina ƙishirwanka, sannan ka duba wayarka zaka ga kayatattun hotunan da videon debe kewa" Haka Sajjid ya saka kai ya bar dakin, sanadin haka yasa Amaan d'aga musu hankali sai an sallame shi. Sannan wani abin da ya kara tashin hankalinshi, yadda Sajjid ya tabbatar mishi matukar bai koma ruwa ba, sai kowa yasan abinda yake faruwa a tsakaninsu. Asalin rashin lafiyan Amaan yana da nasaba da Sajjid, domin kuwa lokacin da aka mishi aiki tsakani da Allah ya daina wanna shashancin, ya mugun kame kanshi. Sai dai kuma gefe guda Sajjid ya haɗe kai da matar Amaan, inda suke sharholiyansu. Ranar da aka kai na farko ya dawo gida, ya ga motar Sajjid cikin azama ya shiga cikin gidan. Koda ya shiga bai same kowa a falo ba, haka.yasa ya wuce dakin shi, abin takaici da bakinciki. Zuwa yayi ya samu Matarshi da Sajjid suna tsulla tsiyarsu. Kuma abin bakinciki babu tsoro ko dar a tare da ita. Shi idan yana son hakkinshi sai ya biya asalima sai tayi ta jan shi a kasa, ya zuba mata kudi . Gashi a karon iska akan Idanunshi, Sajjid yana more ta. "Na zata duk abin da kace nayi zan yi ba zaka wuce gona da iri ba, ashe har matar aurena kake hakewa." Basu fasa ba, karshe da bakinciki ya fita a dakin yana tari, tare da ciwon ciki tunda ya koma ruwa baya ganewa kanshi, gashi kullum idan suka yi akwai wani ruwa da Sajjid yake bashi ko yana so baya so sai ya sha ruwan tun daga wannan lokacin fatarshi ta fara duhu. Dalilin da yasa ya bar mata gidan kenan ya koma gidan Hajiya har ya fara rashin lafiya, tayi tayi ta same shi ya koma gida amma fir yaki da zata dame shi ya tura mata sakinta, haka yasa bakiɗaya Sajjid ta shiga takaici, na farko yana amfani da Amaan yasan motsi Aryan. Na biyu yana da abin da yake son sani daga bakin Amaan. Sai akayi dace ranar da ya nemi ya ji dalilin sake, Matarshi. Suna haduwa ya saka mishi kwaya a ruwa ya bugar da shi, anan ya ji labarin abinda ya faru a lokacin suna Kano, kofa ya farka abin da ya faru akan shi ya dawo mishi kai, rokon Sajjid yake amma ina Sajjd tsalleke shi yayi yana faɗin. "Kada na kuma ganinka, idan na ganka sai na gayawa duniya wacece Uwarka, anya kuwa kai dan halak? Idan har kai dan halak ne ba zan kuma ganin kazamar fuskarka ba." Daga haka suka rabu wannan abin ya saka Amaan tsoro da faduwar gaba, sannan wani abin tashin hankali yadda Hajiya zata ji yana luwadi, yayi kuka yayi kuka amma babu abinda ya sauya domin dai bayan kwana biyu Sajjid bai kyale shi ba, cigaba yayi da matsa masa lamba, tare da amsar kudin shi har a gadon asibitin da yazo, lallai Amaan ya kwaso takardun dukiyar Majid ne. Shi yasa ya zo mishi tare da bashi wasu zabin abubuwa uku. Na farko ko ya kawo mishi takardun Abdul Majid Mamman Ba'are. Na biyu ko ya turawa Hajiya videon nan, na uku ko ya gayawa Duniya Tsohuwar Chairwoman na BA'ARE GOLDEN EMPIRES, karuwa ce da aka kamata har aka rufeta yana da shaidun da abin ya faru da su, kuma zai gayawa duniya cewa bakincikin haka yasa Mamman Ba'are mutuwa, karin tashin hankali shi ne yana kalubalantar Aryan da Jamilah da Aneesah ba jinin Mamman Ba'are. Sai ya zab'a a cikin wannan yanayin. Amaan sai a yayi fatar da mutuwa yayi da Rayuwar da ya jefa kanshi, yayi kuka yayi bakinciki a duniyar nan yaji kamar ya mutu ma, amma yasan darajar rayuwa, yasan matuƙar Hajiya taji abin da yasa shi zama haka zata tsane shi, zata cire shi cikin Yaranta,. Hajiya zata yi alawadai da shi. Haka yasa bakiɗaya yaki zama gidan Hajiya. Haka ya dawo gidanshi, Ana gobe sallah Majid suka je gidan suka same shi, a daki kamar mayye. "Wai lafiyarka zaka bar inda kake samun kulawa ka dawo nan da zama?" Kallo daya Majid yayi mishi ya fahimci yana cikin tashin hankali, daurewa kawai. "Amaan Mamman Ba'are!" Yaji muryan Majid ya ratsa kunnen shi. "Meke damunka? Kasan dai nasan abin da kake boyewa." Kuka ya fashe da shi, har jikinshi yana rawa, a hankali wayarshi tayi kara. Yana dubawa ya dauka har jikin shi yana rawa ya ce mishi. "Meye?" "Ina gargadinka da ka iya bakinka." "Tow naji." Kashe wayar yayi yana mikewa yana faɗin. "Muje babu abinda yake damuna." "Shi yasa daga waya zaka ware kamar babu wani abu?" Inji Aryan. "Kyale shi, yana kara cilla kansa cikin tashin hankali." Daga haka suka fita, sai mita Aryan yaƙe, haka suka nufi gidan Hajiya. Anan suka yi shirin sallah. *** Tun ana jibi sallah, na dauki su Barakatu muka je saloon. Aka mana lalle da wanke kai. Sannan muka dawo, ana gobe sallah, kuwa munyi cin-cin da cake, donuts. Saboda gas ɗina Babba ne. Ranar sallah muka shirya aka zo aka dauke mu zuwa masallacin idi. Bayan an sauko idi, muka dawo gida muka cigaba da bikin sallah. Ni kan ina gida su Baraka da Amirah sun tafi, yawon sallah. *** Za a iya kiran yau da ranar sallah, amma a zahirin gaskiya ranar yau tana cikin wasu irin ranakun da Majid Mamman Ba'are ba zai manta ba, domin ana sauko sallah idi. Labarin rasuwar Maisarah ya karad'e cikin gidan bakiɗaya, kafin a ce wani abu. Ana cikin wannan jimamin, aka sake videon Amaan Mamman Ba'are, a internet bakiɗaya, Hajiya bata sani ba sai da ta shiga gidan rasuwa taga yadda ake kallonta ana cewa. "Eh danta ne na biyu."bata ce kome ba, sai da ta isa dakin Maman Maisarah zata isa wurin gawarta, Hajiya Turai ta ce mata. "Sa'a da alamu tarbiyyar Amaan ya sha bambam da na su Majid waye ya sani ko dukkansu daya ne." "Ban gane ba? Wacce irin magana ne haka " "Sa'a ai kina da waya ki duba mana, waye ya sani, Yayanki dai bamu yarda Yayan Mamman Ba'are ba ne." Zata yi magana Hajiya Tani ya ce mata. "Duba wayarki da bada amsa karamar mara kunya." A hankali ta duba wayarta dake datar a rufe take bata ga kome ba. "Sa'adatun me make ji? Dama Mamman yasan kina bin maza a can Kanon ya dawo dake nan innalillahi'wa'inna'ilaihi'raji'un, Wayyo Allah na." Bakiɗaya maganganunsu ya kara gigita Hajiya, bata san me suke nufi ba. Sai da Anisah ta kirata tana faɗin . "Wayyo Allah na, Hajiya su Hammayo sun mutu..... ********Barkan yan uwa masu kamshin furanya, ni dai anan xan tsaya sai Allah ya kai mu bayan sallah. Sannan ku saka ni cikin addu'arku Hajji nan ko Umara Ya hayyun Ya Kayyum ya kiramu duk me niyyar Alkhairi Assalamu alaikum da sauran free page's In sha Allah.... Kada ku manta 300N ne babu yawa 🥰😍🌹 Allah ya amshi ibadarmu Ramadan Kareem 🫀🥰😍🌹 #Mai_Dambujebuje🥰❤️🥳🫀 [4/13, 4:03 PM] Cutie cutie pie: *BAƘIN HAURE....🐾🐾* {Greed for Money is the roots of all evils🫀} Arewabooks:maidambu41 Wattpad:Mai_Dambu Mallakar:Mai_Dambu 😹 Appy sallah ina jiran goran sallah na🙄 034 Wani irin dauke wuta Hajiya tayi, bakiɗaya kanta ya shiga juya mata, wani irin lumshe idanu tayi tana ganin duhu yana mamaye mata ilahirin ganinta, kamar daga sama ta tsinci bakinta da faɗin."Alhamdulillahi innalillahi'wa'inna'ilaihi'raji'un, Alhamdulillahi." Ta shiga faɗa da sauri da sauri, amadadin gigita da tashin hankali sai Allah ya saukar mata nutsuwa. Kwalla ne suka cika mata idanu, kafin ta shanye su ta hanyar sakin murmushin da yafi kama da yaƙe. Bata ce musu cikanku ba, ta nufi dakin Maman Maisarah ta ce mata. "Allah ya ƙara miki hakuri, nima yanzu na samu labarin hatsarinsu Amaan." Tana fadar haka ta juya ta bar kofar dakin, a falon kuwa ganin yadda lokaci guda nutsuwa ya dawo mata, ya b'ata ran Tani domin ita so take lallai sai ta ga kukan Sa'adatu, bata kaunar yadda take wani nunawa kamar babu abinda yake damunta. Bayan tasan cikin ranta tana cikin tashin hankali, cikin takaici da bakinciki ta ce mata. "Ikon Allah, ko shima Amaan din ba d'an Mamman Ba'are ba ne?" "Tassss!" Hajiya ta dauke ta da mari, wanda yasa kowa na wurin shiga hankalinshi hatta Nana da take zaune. "Akul ki lalata min nasabar Yarana da Mamman Ba'are, nayi shiru tsawon shekaru talatin da wani abu, ba wai ban iya magana ba ne ko tsayawa kai na ne ba zan iya ba, na zab'i shiru shine mafi alkhairi. Tare da saka ran wata rana zaki gane kuskurenki." Murmushi Hajiya tayi tana faɗin. "Kamar yadda kika san kome akan kowa, nima haka na hana idanuna barci domin nasan wacece ke." Matsawa sosai Hajiya tayi tana mai kasa da murya ta ce mata. "Idanun duniya yana kanki, domin na samu asalin waye Sajjid Mamman Ba'are, tare da labarin kawar da ta kashe kawar.." dabas Tani tayi tana kallon Hajiya baki sake, murmushi Hajiya tayi tana me juyawa bata kuma magana ba, don dama karfin hali take kawai, don ita kaɗai tasan yanayin da take ciki, zuciyarta tayi mata wani nauyi, ji take kamar zata mutu. Salati da taslimi take, tana fita a gigice ta faɗa cikin motar da take jiranta, tana shiga ta dafe goshinta, "wani asibiti suke?" Ta fada da wata irin marayar murya, wanda yake gab da sakin kuka, haka suka nufi asibitin Ba'are hospital. Tunda Hajiya ta shiga asibitin, niman wuri tayi ta zauna tana kallon yadda mutane ke kaiwa da komowa, bakiɗaya basirarta ta tsaya cak, a zahirin gaskiya inda suke ya dace ta nima, amma kuma sai gashi tana kallon kome da idanun zuci, lokaci guda jin ta da ganinta suka tsaya cak. A can emergency room kuwa, ana ta ƙoƙarin a ceto rayuwar Jamilah Mamman Ba'are, tare da Aryan Mamman Ba'are. Wanda yake kansu kuwa Majid ne, aikin yake da zuciyarshi da rayuwarshi bakiɗaya, wani irin narkewa zuciyarshi take, musamman da yayi ido biyu da yan uwanshi, akwai wani abun da ya bashi mamaki ya aka yi hakan ya faru? Ace Aryan da Amaan da Jamilah sun yi hatsari a lokaci guda, ya aka yi haka ya kasance? Yana gama aikin tare da taimakon wasu likitocin da Nurse, ya fito daga dakin yana zare safar hannunshi, Hajiya ya hango a can gefe zaune. Da sauri ya cire facemask, ya nufe ta da sauri, yana tab'a kafadarta tana tafiya bakiɗaya ta kwanta, "Hajiya!" Ya kira sunanta da karfi, abinda ya ja hankalin mutanen cikin wurin kansu kenan, wasu daga cikin nurse na asibitin da suka san Hajiya, sune suka turo abin daukar mara lafiya ya d'aura ta akai. Kome na kan Majid ya tsaya cak, bai gama fita daga mamakin hatsarinsu Amaan ba, ya kuma katari da sumar Hajiya. A wannan karon ya gaza taimaka mata, Dr Najib ne ya tsaya akan Hajiya. Bayan ya gama aka turata daya daga cikin dakunan VIP domin yadda jininta ya hau bata son hayaniya bata son ganin duk abinda zai sake d'aga mata hankali. Zama Majid yayi yana kallon yadda ta koma duk saboda su, shi kan bai san inda zai cusa ranshi ba, amma har ga Allah ya gaji da tashin hankalin da yake faruwa a cikin gidansu. Yana tsaye aka sakawa hajiya bututun zukar numfashi, don alamar hawan da jininta yayi ya tab'a mata zuciya, shi yasa suka saka mata oxygen din, ko zai taimaka mata wurin zukar numfashinta, fitowa yayi daga dakin ya tsaya yana sauke numfashi. Sakatariyar Hajiya wato Salamatu, tana tsaye jingine da bangon dakin, kamar zata yi kuka. "Ya Hajiya da jikinta?" "Da sauki" ya furta a sanyayye, "Alhaji me ya faru ne?" D'ago farareen idanunshi yayi, ya zuba mata. Kafin ya sauke gwauron numfashi, lashe bakinshi yayi yana faɗin. "Ban san kome ba." Ya faɗa yana kallon ƙasa, "Amma taya haka ya faru?" Inji Salamatu, bakiɗaya hankalinshi baya tare da shi, sama sama ya tsinkaye muryan Anisah. Tana ihu kamar mahaukaciya, d'ago kai yayi ya zuba mata idanu, a hankali ta rage sautin kukanta. Daga nan ya maida hankalin shi kan nazarin shi. Bayan awa guda, hankalin mutane ya koma kansu Familyn Ba'are, musamman labarin Amaan da abin da ya faru, kafin kace kwabo an shiga rubuce rubuce akansu da nuna su, kamar wutar daji labarin ya karad'e ko ina, sai da ta kai babu wanda yake shiga asibitin da sunan Familyn Ba'are, sannan wani abin mamaki yadda yan jarida suke ta zarya asibitin. Karfe sha biyu na dare, Aryan ya farka cikin tsannanin ciwo da wahala. "Hammayo!" Ya kira sunan Majid. Kallon Aryan yayi yana duba na'urar da yake kanshi. "Anisah tana cikin tarkon Shaidaniyar Tani." Bai kula shi ba, domin gani yake kamar magagin ciwo ne. "Hammayo ka bincika Anisah." Jan allura yayi ya mishi a cikin drip ɗinshi. Rike hannun Majid, "Na rantse da Allah, tana cikin damuwa kayi wani abu." Daga haka barci yayi gaba da shi. *Anisha kuma?* Ya faɗa a ranshi, a hankali ya fito yana jin wani tashin sense. Bai tab'a ganin tashin hankali irin wannan ba. A hankali ya fita tare da nufar office din da bai tab'a shiga ba, ya zauna yana me jin kamar ya fasa ihu. Wayarshi ya ciro yana saka a kunne. "Kayi tracking number Anisah ina jiranka." Kashe wayarshi yayi yana nazarin irin matakin da zai dauka. ----- Marad'i Bikin sallah, anyi shi cikin farinciki duk da bani da kowa a marad'i, amma kuma Maman Barakatu da Yaranta, sun saka ni farinciki. Haka muka kwashe wunin ranar muna yawo,koda muka dawo sallah muka yi. Akwai wani abu da na fahimta a rayuwa, shine duk inda zaka shiga matukar naka yana tare da kai zaka ji kamar ka samu duk wani farincikin da kake nima, haka nake ji a duk lokacin da na kalli Amirah sugrah, uwa uba Yazid da ya maida ni mutum, bawan Allahn nan ban san da me zan saka mishi ba. Bawan Allahn nan yayi hidima dani ko nace yana hidima da ni, domin taimakon da yayi min hár abada nake jin babu wanda zai min irin shi. Bugun kofar falon da nake kwance ya katse min tunanina, tashi nayi naga Barakatu ne da Amirah. "Wai zata zo wurinki ne har da kukanta." "Mirah me yasa kike da halin rashin kirki, tow ai sai ki shigo." Da sauri ta miko min hannu na amshe ta. "Tante kiyi hakuri, kawai bata son nisa dake ne." "Kyaleta kiuya ce kawai, amma ina wani nisa sai tazo ai." Haka na amshe ta, Barakatu itama ta shigo muka zauna. "Mama" ta kira sunana, tana rike hannuna, "Ko kina jin yunwa ne?" Kallonmu Barakatu tayi, kuma na bata abinci taki ci fa." "Yau tana jin rikici ne." Haka na wuce kitchen na hada mata shayi na kawo mata, ta fara sha tana gamawa kamar wasa yarinyar nan ta koma gefe sai barci. "Halin Amirah sai ke Tante kada ki ce ban bata abinci ba, amma taki ci." Ta fada tana mita, ita nan Amirah ta bata takaici, tashi nayi na kawo mana abincin na ajiye mana, "Ga abinci." "Ni kan ba zan ci ba, tunda aka yi na jiya naci nayi ta yawon ban daki, na haƙura kunu nake ta sha kawai." "Da dai kin ci abincin." Na fada mata, tura baki tayi tana mikewa, "ina gaya miki, cikina baya son abinci yanzu sai dai ki hada min shayin Amirah shi kan zan sha." "Lallai cikin nan naki, kwadayayye ne tow ki shiga kitchen ki haɗa." Dariya ta saka tana tafiya, "Tante na gode, Allah a koshe nake kawai zolaye ce." Tana faɗar haka ta bar falon, ajiyar zuciya na sauke, sau dayawa rowa yana rage kima, kyauta kuwa yana kara daraja da girma. Da nace mata ba zan bata ba, da ba zata ji dadi ba amma da nace taje ta haɗa gashi don kanta tace a'a, kuma abin da na lura kamar tarbiyyar mahaifiyarsu ce. Yaran basu da kwadayi, sannan duk abin da zan basu basa rawar jiki a kai, asalima tsoron karba suke kada iyayensu, su musu faɗa kaga inda ake tarbiyya da adalci, a wannan zamanin da son kai da son zuciya, wani yaron baka isa ka shiga gidansu ba, idan ka shiga ma yayi ta maka rashin kunya iyayenshi na dariya wai ai yaro ne, wani kuma kana zuwa da shi wani wurin yayi ta kunyata ka kenan, duk ƙoƙarinka akanshi kuwa, irin wadan nan Yaran iyayensu ba karamin kokari suke wurin tarbiyyar su ba, sai dai muce Allah ya shirya mana zuri'a amma Iyaye na kokari akan Yaransu, domin wata zaki sha mamaki idan da zaka ga yadda take fama da Yaran. Ban haifa ba, amma bana jin zan yiwa Amirah irin rikon uwar wani, saboda Amirah tawa ce ni ɗaya na. Shi yasa nake sonta da dukkan zuciyata, kuma bana jin har abada wani zai fini son Amirah, koda kuwa uwarta ne, sai dai ta gaya min ita ta haifi Yarta amma ba zata gaya min soyayyar yarinyar ba. Daukarta nayi zuwa banɗaki na mata wanka, sannan na sauya mata kaya, kafin na fito ni ma na nime ruwan zafi na zubawa cikina da yake cike, ina tsaye rike da kofin a jikin window. Saboda iskar da ake yi, nake tsaye a wurin. "Ko wani hali Zuzu take ciki? Wani hali Munaisah take ciki ina suke yanzu?" "Taya zan fara nimo su? Ina zan shiga ina zan fara nimansu?" Waɗannan sune manyan damuwata, ta ina zan nimo Yan uwana an samu shekara daya da wani abu kenan amma babu labarinsu. Jikina yaki amsar sun mutu yadda wani bangare na zuciyata take gayamin, nafi jin a jikina suna raye, a duk inda suke a fadin duniya sai na nimo su, "Amma taya?" Ajiye kofin hannuna nayi, kafin na cusa hannu a cikin sumar kaina. Taya zan nemo su? Ta ina zan fara? Babu shakka ina cikin damuwa. Allah ya kawo min mafita,. Amma dole na binciko yan uwana. *Mahaifiyarki fa?* Gabana ne ya fadi wanda yasa kofin hannuna faduwa niman wuri nayi na zauna, ina kallon duhun wajen. Mahaifiyata ya kamata na fara nemowa amma ta ina? Hawaye ne suka zubo min wanda ban san zan iya kukan ba, kuka nake sosai kamar raina zai fita domin ina cikin wani irin kewa, ina kewar Mahaifiyata sosai. Sai da nayi kuka me yawan gaske, sannan na mike zuwa ban daki nayi wanka nazo na kwanta a gefen Amirah. *** Niamey Wannan sallah bata zo da alkhairi ba, lokacin da Majid ya saka bayanan da aka turo mishi akan Anisah, sai da jikinshi yayi sanyi. Duba agogon hannun shi yayi ya mike tare da ɗaukar keyn mota. Bai tsaya ba sai gidan Anisah, kiran mijinta yayi ya ɗauka. "Gani a kofar gidanka." "Tow gani." Can dai gashi ya zo ya buɗe, cikin gidan suka shiga. "Ina Anisah?" "Tana dakinta taki bude mana kofa da yara." "Muje!" Gaba mijinta yayi Majid yana bayanshi har kofar ɗakinta. "Anisah! Bude min kofar Abdul Majid Mamman Ba'are ne." "Hammayo!" Ta kira sunanshi da karfi, "Na'am Autar Hajiya bude min na shigo." Ya faɗa da tausassshen murya. Kuka ta saka sosai, "Ka tafi idan suka san kazo zasu cutar da kowa don Allah." "Babu wanda zasu cutar miki da shi, fito ina tare dake." "A'a Hamma!" "Bana ce ki yarda da ni ba, kin san halin da Amaan da Jamilah suke ciki kuwa? Tow kowani lokaci mutuwa zasu yi, Aryan ya farka dazun nan kin ga yanzu dare yayi. Bude min kofar don Allah." Rufe bakinta tayi tana kuka kamar ranta zai fita. "Ki kunna wayarki, ki duba abin da yake faruwa. Idan har kika san baki da hannu a cikin wannan abin da ake fada tow ina jiranki A falonki." Mikewa yayi ya bar kofar ɗakinta ya dawo falon, a can dakin tayi kuka har ta godewa Allah, kunna wayar tayi tana ganin sakwannin mutane. *A yau muka samu labarin hatsarin da Yaran marigayi Mamman Ba'are suka yi, wanda aka ce daya daga cikin Yaran yake da hannu a cikinshi* *An saki faife videon Amaan Mamman Ba'are wata majiya tace yar uwarshi tana da hannu wurin sakin faifen videon domin kada ya kalubalence ta akan mukamin shi da aka karba aka bata* sake wayar tayi da karfi, ta fito da gudu. "Wallahi Hamma ban san kome ba, na rantse da Allah ban san kome ba." "Nutsu ki gaya min me ya faru?" Ya faɗa yana kallon mijinta, da ya mike tare da nufar kitchen ya kawo mata ruwa. Amsa Majid yayi ya bude mata, domin ya lura a firgice take, sai da ya sha ruwan sannan ya mika mata, da sauri ta amsa ta sha dayawan gaske. Sannan ta sauke Ajiyar zuciya. "Mutuwar Babban sakataren kamfanin Alhaji Ahmed Ya'u, yana da nasaba da Sajjid Mamman Ba'are da Amaan, abin da ya faru a ranar da zai mutu. Amaan yaje Office din shi akan ya saka mishi hannu ya cire wani kudi ya turawa Sajjid yayi amfani da shi, amma Alhaji Ahmed Ya'u yaki, ya ce mishi ya je ya nimo amincewar hajiya ko Aryan ko kai." Haka yasa suka yi sa'in'sa, har ya kira Aryan bai same shi ba." Shiru tayi tana share hawayen da suke zubo mata. "Bayan nan abin da ya faru shine aikin da ya sha kan Alhaji Ahmed yasa bai tafi gida da wuri ba, har aka shiga aka kashe shi ga abinda na samu lokacin da nake binciken Office ɗin shi." Wani dan karamin recorder, ta miƙawa Majid, tun da naji haka na sake saka idanu akan Amaan domin tun da aka bani matsayin nan yake turo min sakon na ajiye mukamina ko ya min rashin mutuncin. Da ya ishe ni ne na kunna mishi recorder din yaji da kunnen shi, ashe na kai kaina ga halaka domin Sajjid yaji labarin ina da shaidar abin da suka aikata. Tun daga wannan ranar ban kuma barci ba, da fari turo min sakon waya ake na za a kashe ni idan ban sake bawa Amaan bayanan ba, na ki kula su daga baya sai aka fara min barazana da Rayuwar Yarana da Mijina. Bakiɗaya na rasa me ke min dad'i. Bansan ya aka yi ba Aryan ya san da zancen ba, sai gashi dukkansu sun tawo suka ce min zasu tawo har da kai, ashe kafin su tawo Aryan ya kira Sajjid sun yi faɗa har da sa'in'sa Hammayo shine suka turo mota biyu suka buge su. Sannan suka sake faifen videon Amaan, bayan sun tilasta min na kira Hajiya na gaya mata kun mutu. Wallahi Hammayo ba da gangan nayi ba, Hammayo Yarana suka ce zasu kashe kamar yadda suka buge su Aryan. "Me yasa baki gaya min ba?" Inji Mijinta. "Su'ad ba zaka iya kome a kai ba, babban al'amari ne da mu kan mu, dole muke yakin sunkuru, lokaci yayi da zan ajiye aikina na soja, na tsaya akan Dangina. Idan ba haka ba, ina can za a shafe min yan uwa da dangi" "Amma Majid"! "Akwai jami'an tsaro, sun zagaye gidan nan babu wanda ya isa ya kuma muku abin da zai d'aga muku hankali. Yaranki kuwa ki kyale su, ba zasu iya miki kome ba. Idan ya kuma kiranki kice ni Abdul Majid Mamman Ba'are idan ya cika namiji ya kira ni." A razane ta kalle shi, share mata hawayen fuskarta yayi yana murmushi ya ce. "Eh ni na gaya miki haka." Sannan ya mike tare da barin falon. "Su'ad ka saka idanu a kanta, ka tabbatar tayi barci." Daga haka ya musu sai da safe, ya fito ya samu sojoji a harabar gidan, "ku saka idanu akan ko tsintsu ne, idan ya zo giftawa ku sake mishi wuta." "Sir!" Barin gidan yayi. Hajiya Tani tana tsaka da barci, hasken da ya cika dakin yasa ta bude idanunta. Majid ta gani zaune, a razane ta mike tare da cewa. "Uban me ya kawo ka." "Ba kome sai dai kashedi nazo nayi miki, domin nasan zaki fi dauka sama da yadda kowa zai dauka, d'anki yana wasa da wuta, amma bai san wuta yake wasa da shi ba." Zama yayi a bakin gadon. "Ki ja mishi kunne, idan ya sake aka kama.shi ko tow a gidan Yari zai mutu, domin laifuffukan shi da yawa, sannan idan ya fahimci cewa Raihana ce ta haife shi ba Tani ba, akwai ." Da sauri ta sauka akan gadon ta zube a kasa, "Don Allah ka gaya min me kake so?" Ta tambaye shi jikinta yana rawa. Mikewa yayi yana zaga dakin. "Me zance miki nake so, ai yaci ace kin gane me nake so." "In sha Allah ba zan kuma barin shi ya shiga cikin al'amarinkaba, ba iya kai ba hatta yan uwanka." "Tani kina da lissafi" Bakiɗaya ta girgiza domin abu ne da bata kawo wani mahaluki zai san wacece ita ba, sai gashi an canko wacece ita. "Ki kula kowane yana....... *Barka da sallah, ina jiran goran sallah na😹🥰😍😿😹* 300₦ 0016341139 unity bank zahra'u yahaya Ali Katin MTN 400 +2347035133148 or 08130269641..... #Mai_Dambu ce [4/16, 8:16 PM] Cutie cutie pie: *BAƘIN HAURE....🐾🐾* {Greed for Money is the roots of all evils🫀} Arewabooks:maidambu41 Wattpad:Mai_Dambu Mallakar:Mai_Dambu *Alhamdulillahi na gode sosai, marubuta da makaranta Allah ya saka da alkhairi, musamman yan grp din Fitilar hikayar Dambuje, Allah ya bada lada naga kira da sakonnin ku. Allah ya karo dubun zumunci, Ubangiji ya jikan dukkan yan uwa musulmai da suke faɗin duniya, tare da iyayenmu bakiɗaya... Allahumma Amin* 035 _Yau kan babu editing 🥰_ Nad'e hannunshi yayi a kirji, yana kallonta yadda take gurfane a gabanshi. "Ba xance kada ki hana shi ba, amma tabbas nayi ido biyu da shi, sai dai Uwarshi ta kara haifar wani koda yake ina zao ganta. Amma ki saka idanu akan shi domin." Sake hannunshi yayi ya nufi kofar fita yana faɗin. "Duk yadda kika so, kiyi amma inuwar Ba'are da al'ummar gidan kada na kuma ganinku." Daga haka ya bar mata dakin da gidan bakidaya. Wani irin zufa ke karyo mata, yana fita da gudu ta mike ta ɗauki goran ruwan da yake gefen gadonta, sai da ta shanye goran bakiɗaya, sannan ta ajiye. Zirga zirga ta fara a cikin dakin tana jin kamar tayi ta kurma ihu, Hajiya Sa'a ta gaya mata magana akan haka, yanzu ma Majid ya kara gaya mata, haka yaná nufin sun san kome akanta, ita ce dai bata san kome akansu ba, wanda ta sani ma na bogi ne domin sune suka san wacece ita. Hannu ta saka a kai, kafin ta koma ta zauna tana jin kamar ta tattara yan abin da take da shi ta gudu, domin zuwa yanzu da Majid yasan Sajjid ba dan Mamman ba'are ba ne, zai fi mata kyau tayi ta gudun hijira. Ai na Majid wasa ne akan na Sajjid don binne ta zai yi da ranta, matukar yaji wani labari mara daɗi akan waye shi, cikinta ne yayi wani irin murdewa a daddafe ta shiga toilet. Bata san ya aka yi ba, sai g kashi shaaaa cikinta ya tsinke. Wato Majid bala'i ne, idan ta sake wani abu ya kara had'a su. Binne kanta zata yi da ranta kafin Majid ya zo gare ta, don na Majid me sauki. Koda ta fito daga ban dakin, a daddafe ta nime wuri ta zauna. Can cikin ya kuma murdeta, da sauri ta shiga banɗakin ta zauna akan wurin kashin. A lokacin da ya bar gidan Tani, a hankali yake jin wani irin abu yana yawo a kanshi, har wani nutsuwa yake ji, Hajiya Tani ba ita daya ba ce akwai wasu a bayanta. Bari ya ga iya gudun Tani domin idan akwai wani a bayanta dole zai fito, don haka ya tab'a spot point. Lokacin da ya isa asibitin Hajiya tana barci, zama yayi na wani lokaci kafin ya mike ya nufi Office ɗinshi, bude drowe office din yayi ya ciro abin sallah da jallabiya, murmushi yayi domin yasan aikin Jami'ah da Aryan ne, sune zasu nishi haka. Ban daki ya shiga yayi alola, ya fito ya shimfida abin sallah, tun ya fara sallah nan karfe uku bai tsaya ba sai da Masallacin asibitin aka kusan shiga sallah, ya sallame ya nufi masallaci. Bayan an idar da sallah ya zauna yana addu'a, sai da rana ta fito sannan ya wuce asibitin. Anan ya samu Anisah da Salamatu sun shigo. "Hammayo!" Ta kira sunanshi, bude mata gefen hannunshi yayi ta isa wurin tana kuka kamar ranta zai fita. "Hamma kayi hakuri." "Shiiii!" "Duk laifina ne, da na fada maka haka da bai faru ba." "Ya isa haka, kin yi barci kuwa?" Ya tambaye ta cikin kulawa, "Nayi su'ad ya saka ni nayi barci." Murmushi yayi ya ce mata. "Good girl, muje ki bani abinci naci don naga basket a hannun Mama Salamatu." Ya faɗi haka don ya kwantar mata da hankali. Har dakin da Hajiya take suka shiga, "ina zuwa ko" ya faɗa yana nufar dakinsu Aryan a can ya samu Matarshi tana ta kuka. "Ya isa haka, ya farka fa bari na duba shi." Ya faɗa yana shiga dakin,duba shi yayi yaga lafiya lau barci yake, bai tashe shi ba ya nufi wurin Amaan, ya shafa kanshi tausayin shi ya masifar cika mishi zuciya, duk da rashin jituwa da yake tsakaninsu, haka bai tab'a damunshi ba, domin yasan wata rana zai gane gaskiya, duba karin wurin yayi yana me saka mishi wani ruwan. Sannan ya wuce kan Aryan da yake ta motsi. A hankali ya isa kanshi, ya cigaba da dube-dube har ya farka. "Welcome back Mr Mamman Ba'are." "Anisah fa?" Tab'e baki Majid yayi, sannan ya ce mishi."Na zata matarka da Yaranka zaka tambaya." "Wani hali kanwata take ciki?" "Ina zan sani tunda ina tsaye akanku." "Hamma kasan bala'in da na gani jiya." "Ina zan sani ragon maza." Ya faɗa yana murmushi, d'ago shi yayi ya zauna. "Hamma!" "Guduma!" Ya faɗa yana murmushi, don ya gaji da maganar Aryan. "Hamma Abdul Majid." "Anisah tana lafiya, wurin Hajiya matarka tana waje bari ta shigo." Ajiyar zuciya ya sauke, "Manyan mota biyu suka tasamu a gaba, Hamma dole na firgita." "Allah ya kiyayye na gaba." Ya faɗa yana ƙara duba shi. "Ina ke maka ciwo yanzu?" Ya tambaye. "Hakarkarina ke ciwo." Matsawa yayi ya d'aga mishi hannunshi, da sauri ya riko hannun Majid, "Hamma bari kawai." Sake hannun yayi yana dauki wani littafi yayi rubutu, sannan ya ce mishi. "Motar ya doke ku ne?" "Tsakiyarsu suka saka mu, wallahi ban san yadda aka yi aka ciro mu a ciki ba." "Anjima zaa zo a kaika x-ray, mu ga wurin " inji Majid, juyawa Aryan yayi yana kallon Amaan, "bai farka ba ko?" Ya tambaye shi idanunshi cike da kwalla. "Ba shi ne matsalata ba, Jamilah tana da ciki, kuma har yanzu bata farka ba." Shiru ne ya gifta a dakin, dukkansu babu me kuzarin magana, fita yayi ya nufi ICU, inda aka kwantar da Jamilah. Yana shiga yaga yadda kome yake tafiya a cikin na'urar da aka saka mata, amma ya kasa tabuka kome dake ya samu wasu drs akanta, sai ya zama kamar dan kallo, haka ya juyo daga dakin ya gagara yin kome, a bakin kofar ya samu Mijinta, dasu Nanah. "Ya jikin nata?" Kallon kayan jikinshi yayi kafin ya ce mata. "Da sauki." "Kace anan kake zaune?" "Eh!" "Ayya to dama ina babu wanda ya mutu?" Banza ya bawa ajiyarta, ya cigaba da tafiya. "Kai kurma ne ina magana kayi banza dani." Uffan bai ce ba. " Yau ga lalacewar duniya, kai yanzu ina magana kayi banza dani don kaga na tako inda kake? Yanzu don." "Me kika ce ne?" Ya juya yana me tambayarta da sigar renin hankali. "Uwarka Sa'adatu da ta haifi ɗan karuwi." Murmushi yayi tare da cigaba da tafiya, tana kuwa bin shi, tana zagin shi. Sai kallonsu ake shi kuwa ko a jikinshi. Yana isa kofar office din shi ya ce mata. "Idan kin gama jarabararki, na gode sai ko wuce gida domin na fito na same ki wallahi ni kaɗai nasan me zan dirka miki a asibitin nan." Ware idanu tayi tana faɗin "yanzu don baka da imani sai kayi min wani abu? Tambayarka nake sai kayi min wani abu!" Hango wata nurse yayi ya ce mata. "Ki kawo min babban sirinjin allura tare da maganin nan, yanzu." "Ke dan uwarki kika kawo wani abu, sai na saka an kore ki a asibitin nan, kafira me kama da fatalwa. Kai kuma zamu gamu da juna, mara mutunci dan banza me kama da gwaggon biri " Murmushi yayi ya rufe kofar shi, domin yasan Nana da dan banza tsoro, kuma bai zama dole ta kuma dawowa ba, murmushi yayi shi kaɗai, har ya gama sauya kaya. Ya fito dakin Hajiya, ya samu ta farka sai kuka Anisah take Nana sai surutu take ta musu da sababi. Safar hannu ya saka tare da haɗa kayan aikin ya cire ruwan daya kusan karewa, ya saka wani sannan ya zuba mata allura a ciki. Yana kallon yadda take kallonshi kamar irin ta farka daga cutar makanta, ya sani tana mamakin yadda aka yi babu abin da ya same shi. Sai da ya gama sannan ya dawo gabanta ya riko hannunta, ya saka a fuskarshi."Hajiyana nine Majid Mamman Ba'are gani nan lafiyana lau, ki kwantar da hankalinki." Murmushi me had'e da hawaye ta sake tana kallonshi har barci yayi nasarar gaba da ita. "Nana muje na kai ki gida kinji." Kallonshi tayi a kaikaice irin zata kafta mishi rashin mutunci. Yadda ya saka fuskar sojojin tuni hankalinta ya dawo jikinta, "hmmm muje!" Ta ce tana shirin mita. "Nisah kema idan ba da motarki kika zo ba, zo muje na ajiye ki kada na kuma ganinki tunda kuka zaki na mana asibitin. " "Don Allah kayi hakuri ba zan kuma, na daina kukan." Ta fada tana k'amk'ame jikinta alamar ba zata fito ba, "ok muje ki ga jikin Aryan da Amaan." Mikewa tayi suka fita, har dakin a lokacin Aryan yana Sallah, yana idar da sallah. "Hamma Aryan?" Ajiyar zuciya ya sauke. "Ya jikinka?" Ta fada tana kuka, "Ya isa Auta, ba gashi naji sauki ba. Bar kuka ina fatan babu abinda ya same miki ko?" Girgixa mishi kai tayi tana share hawayen da yake zuba mata. "Bari na kai matar nan gida " "kaga matar nan a kofar dakinka, ni ba matar nan ba ce." Ta fada tana wani dauke kai, ita fa gara mata ma Majid da wannan me kalar zabiyar haushi yaƙe bata, balla mishi harara tayi. "Don kana gadara da Alhaji yana tsaye sai ka kashe min jikoki, dan banza me kama da mutanen boye." "Muje!" Majid ya faɗa mata, domin ya lura jaraba take nima. "Aikin banza kishiya da shashasha, da ka kafe ni da idanun kamar na mayu kurwana kur, idan ma ka kirkiro hatsarin ne don su mutu kaci kasonsu kayi karya, ina sane daku munafunkin banza munafikin wofi." Maganar Nana tayiwa Aryan tsauri amma kuma sai yayi murmushi ya ce mata. "Ai ke zan fara turawa lahira, domin na gaji wannan gwal din wuyarki." Wani dafe kirji tayi, tana nuna shi tare da kallon Majid. "Kaji ba, yana shirye shiryen turani lahira bayan ban ga matarka ba, dan bakin ciki wannan sarkan na matar Alhaji ne ko mutuwa nayi bata cikin gadona." "Ai kuwa ki saka idanu sai kin garzaya barzahu bari a sallame ni, domin zan fara aikatar da aikina ne akanki." "Wallahi baka isa ba, sai kotu da yan sanda sun shiga tsakaninmu, na rantse da Allah ba zan yarda ba, ko tuntube nayi Alhaji kai zaka nimo min lauya domin Ariyan ya shirya kisan kai, ya ga baya tow na rantse da Allah sai nayi fatalwa ko na mutu na kwaci hakkina." "La fatalwa ma zaki zama?" "Kwarai don ba barin hakkin jinina zan yi ba." Ta fada tana hura hanci kamar ta doka mishi sandan hannunta. "Tsuhuwa lokacinki yayi, sai a fara shiri kafin na zo." "Alhaji kana jin shi ko." "Muje ki daina biye mishi, cinnaka Aryan ba zai kashe ba, balle dan mutum nayi mishi wannan shaidar tun daga duniya har lahira ba zai kashe wani ba." "Au hatsarin da ya ja musu fa?" "Muje a hankali zaki fahimci abin da yake faruwa." Haka ya fita da ita, " Nabeeha wai zan iya kashe ..." Hannu ta saka mishi a baki, "Tsakanin harshe da hakori ana samun sab'ani, haka tsakanin mutum da mutum ana samu, Aryan ban kowa a duniyarka ba, sai adalcinka har abada ba zaka b'ata hannunka da jinin kowa ba in sha Allah." Ta fada tana kuka, tana son Mijinta kuma bata ji a ranta zata zarge shi ba. "Idan Hamma!" "Hamma Aryan, itama Nana gurbata mata tunani ake da zancen banza, muji da halin da Amaan da Jamilah suke ciki." Shiru dakin ya dauka, babu wanda ya kuma magana, sannan Mijin Jamilah da dangin shi suna asibitin, hatsarinsu yasa videon Amaan ya mutu, sai aka koma labarin hatsarin domin abin ya faru ne da safen jiya, kuma kowa ya ga yadda abubuwan suka faru, sai aka shiga yayyata videon hatsarin da yadda abin ya faru, sama da labarin Hajiya da Amaan. Wannan al'amarin ya faru cikin kwana ɗaya, sai ya zama kome ya tafi kamar bai faru ba, don haka Majid shima yayi amfani da nashi kwarewar yasa aka binciko mishi wanda ya sake videon Amaan. Ai kuwa gayen yaci uban dokar sojoji. * Tunda Majid ya bar Tani a ɗakinta har gari ya waye bata fito ba, koda Hajiya Fauziya tazo gidan a daki ta same ta, don ta kawo mata tsegumi ganin halin da take ciki yasa, bata iya bata labarin ba. Domin ta same ta ta birkita dakin tana niman abu. "Tani lafiya?" "Lafiyan kenan wayata nake nima." Kallonta Hajiya Fauziya tayi baki sake ta ce mata. "Ban gane wyaarki ba, wanene a gefen gadonki?" Juyawa tayi ta ganshi ta ce mata. "Ikon Allah, ban san yana wurin ba." Ta dauka da sauri har yana kokarin faɗuwa a hannunta, ta shiga kiran Sajjid.. "Dauka mana." Katse kiran aka yi ta kuma kiranshi, sai da tayi bugu uku sannan aka ɗauka a make ya ce mata. "Dalla me zan miki?" "Idan kana cikin Niamey tow ka gaggauta barin garin nan, Majid na gaya maka Majid. Wallahi kafin wayewar gari nayi kashi ya kai sau goma maza ka bar garin nan ka kashe wayarka kada ka kunna sai nan da wata uku na gaya maka kada ka dawo Nijar " "Babu inda zanje, ina garin nan wallahi." "Na gaya maka kamar kare zai kashe ka, domin ko ya kashe ka babu abinda zai faru, ya fika gata ya fika kome ka kyale kome ka bar garin nan daga baya zamu yi magana don Allah." Ta fada a raunane, "Ni dai ban ji dadi ba, kawai zan tafi ne ba don ina da ra'ayi ba." "Jeka don Allah da kuma ni." Kit ya kashe wayar yana mita. Itama zama tayi dabas da malmalan duwawunta tayi da kasa, a hankali ta sauke ajiyar zuciya me nauyi domin sai yanzu taji abu ya wuce mata, d'ago kai tayi a matuƙar gajiye ta kalli Hajiya Fauziya. "Uwar me kika zo yi?" "Hmmm! Hmm dama na gaya miki Aryan ya farfaɗo sannan an kama kama mutanen da suka yi ta." "Je ki don Allah domin kin zama tauraruwa mai wutsiya, ganinki babu alkhairi domin nasan sharri ke tafe dake, don haka tafi wanda nake ciki ma ya ishe ni wallahi." "Hmmm daga abin arziki, amma tunda bakya son na gaya miki shi kenan." Ta juya tana jin haushi kamar zata rufe Hajiya Tani da duka, don tazo da mugun labarin cewa an kama yaron da suka saka aiki. Don ba iya Sajjid yake mocking Amaan da yan uwanshi ba, har da taimakonsu....... *Kuyi hakuri babu yawa* *₦300* 08130269641 #Mai_Dambu ce.... [4/17, 8:10 PM] Cutie cutie pie: *BAƘIN HAURE....🐾🐾* {Greed for Money is the roots of all evils🫀} Arewabooks:maidambu41 Wattpad:Mai_Dambu Mallakar:Mai_Dambu 036 Tuntube Nana ta yi zata fad'i, Majid ya tare ta . "Innalillahi kaga ni ba? Ka ga ni ba tun ban bar asibitin ba ya fara ƙoƙarin ganin bayana." Shi dai bai ce mata uffan ba, har suka isa wurin Motarshi. Bude mata yayi ta shiga. Don jaraba glass ɗinta ma sai da ya kusa faɗuwa ta riko ta saka a juye, da wutsiyar idanu Majid ya kalle ta. Yana tab'e baki har suka bar Asibitin. "Hajiya!" Ya kira sunanta, bayan ya zare glass ɗinta ya saka mata shi. "Na'am Alhajin Allah." Murmushi yayi cike da takaici, domin tun fil azal ya dace su samu wannan soyayyar amma basu samu ba, sai rana tsaka. "Ka kira sunana kuma kayi shiru, ni bana son haka idan ka san ba magana zaka yi ba ka daina min haka, sai a kira mutum ya dauka wani abin arziki zai samu amma ayi shiru, ai wannan wulakanci ne." Bai ce mata cikanki ba har suka iso gida, zata fita taji kofar motar a rufe. Fito da yar karamar bindiga yayi ya ajiye, zare idanu tayi waje. "Hmm Alhaji me zaka yi da bindigarka haka?" Gyara zama yayi yana faɗin. "Duk wanda ya gaya miki labarin abin da ya faru, tow ki kirani ki tambaye ni kinji ko? Kada na kuma jin kina zargin wani kina jina?" "Alhajin Allah, da akan wannan zaka min kashedi ai ba sai ka rike bindigarka ba, kawai ce min Nana kada na kuma jin kin zargi kowa, zan ce maka Allah ya huci zuciyarka bawan Allah ba zan kuma ba." A ranshi yana jin dadin yadda take saurin razana, da hawa hanya. Idan da wata ne hayaniya zata mishi. "Kin ga dai ni ban ce kome ba, kawai abin da nake so zan saka miki lambata kawai ki gaya min kome ya faru zan baki amsa." Ya dauko wayarshi ya kunna mata videon abinda yake faruwa na hatsarin, taga dai ba Aryan din bane ma yake tukin Jamilah take tukin. "Hmmm! Amma fauziya tsinanniya ce, ita ta kawo min labarin Aryan ya tafi ya watsa min jikoki a titi mota tabi ta kansu." Lumshe idanun yayi ya ce mata. "Je ki kinji Matar ƙarfen daga ke ba ƙari." "Alhajin Allah ka maida bindigar nan." "Tow matar ƙarfe." Ya ajiye shi a asusun motarshi. "Hmmmm. Alhajin Allah yaushe zaka saya min nama." "Jeki za a kawo miki." "Alhajin Allah baka saka min wayarka a wayata ba." Ya karbi wayarta da yake makale a wuyarta har da igiya domin cire mishi tayi, yayi abinda zai yi ya mika mata. Layin sai tarin bashi. "Taya kika ci bashi haka?" "Ina zan sani tunda Yar gidan Hafiza ɗaukar wayar take, ba dare ba rana matukar na ajiye zata ɗauka." Hafiza stepsister ɗinshi ce, yarta tazo hutu. Ciro kuɗi yayi ya mika mata, "Ga Barka da sallah ɗinki." "Allah ya kara bud'i, na gode sosai." Ya bude mata motar ta fita, ya juya ya bar gidan bata shiga gida ba, sai da ta daina hango Motarshi ta shiga gida. "Nana Oyoyo ya masu jikin?" Kuru tayiwa Hajiya Fauziya, kafin ta ce mata. "Ke dai Allah ya tsine gulma da munafurci da yake kokon ranki, munafuka Annamimiya. Kika saka ni zargin dan marayan Allah da yake kwance cikin jinya, kai fauziya ke tsinanniya ce wutar munafukai ya tabbata akanki. Munafuka makira. Allah ya isa min shi yasa Rabi take burge ni bata shiga harkar kowa amma ke kullum munafurci yana cin gindinki." Tass ta wanke Hajiya Fauziya da kanta a kasa, ai Nana ta iya tozarci idan ka sake ka takaleta a gaban uban Kowa zata wanke ka kai din banza ina ruwanta tunda kai ka tab'ata. Asibiti kuwa sai yamma can Amaan ya farka, Jamilah ce dai sai du'a'i domin hankalin kowa ya tashi ya dace ace ta farka amma al'amarin ya ci tura. Haka yasa likitoci suke kanta ba dare ba rana. Hajiya ta farka itama, sai dai babu wanda ya bata labarin halin da Jamilah take ciki, ko lokacin da Amaan ya shigo dakin dakatar da Majid tayi ta hanyar juya musu baya. "Ya tafi bana son ganinshi." Alama Majid yayi mishi da hannu suka fita. Ƙoƙarin danne hawayen da suke son zubo mata tayi domin bata son tayi mishi kuka, idan tayi mishi kuka, bata san wacce irin rayuwa kuma zai yi ba, sai tayi ƙoƙarin danne abin a ranta, "Kiyi kukanki amma ba da nufinmu ba, kiyi jininki zai sauka sosai. Kiyi kuka ba ragwanta bane jarumta ce, rago shi yake ihun, jarumi hawaye yake zubarwa domin ya samu sauki a zuciyarshi. Hajiya bature ya ce "courage doesn't mean you don't get afraid, courage means that you don't let fear stop you," kiyi kukanki Ummina, kiyi kuka idan baki ba zai dame ki har karshen mu, ba iya shi ba hatta mu rashin kukan zai haifar da abubuwa dayawa." Zama yayi a gabanta yana murmusa mata ya ce. "Kina nufin Allah ba zai jarabce mu bane? Idan bai jarabce ki ba, Ummina ki binciki girman alakarki da Allah, domin shi baya jarabtar kowa sai wanda yake da kusanci da shi. Hajiya Ummina, Allah baya duban marasa nima a wurinshi sai masu nima, kada ki ce Allah bai amshi addu'arki ba ne, a'a ya amsa yana son ya ga girman hakurinki ne, Ummina Allah baya waiwayar waɗanda suka manta da shi, yana waiwayar masu ambaton shi ne. Ya amshi addu'arki na neman shiriya akan Yaranki, ya tab'aki ne don yaga hakurinki idan kika yi hakuri ya kara miki alkhairi akan haka. Hajiya Ummina kiyi hakuri domin rabonmu yake wahalar dake, Allah ya nufa ta hanyar mu zaki ta haduwa da kalubalen rayuwa. A madadin Yan uwana bakiɗaya muke nimawa Amaan Mamman Ba'are, yafiyarki da albarkanki." A hankali ta saki kuka me sauti, yau Majid ya tunatar da ita Allah, a wannan halin da take ciki. "Ki godewa Allah da aka farga da lalurar shi idan kuma da gawarsa aka samu da wannan labarin fa? Hajiya akwai abinda kai a wurinka babban al'amari ne, amma a wurin Allah karamin al'amari ne." Dafe kirjinta tayi, tana kuka har da shasheka."Kiyi kukan ki samu sauki Hajiyata, domin da haka ne ba zan tab'a yarda hawan jini ya sake tab'a min ke ba, amma idan kika yi shiru zuciyarki zata yi sauki tunanin da zaki ta ajiyewa domin ganin ya zaki yi, zasu tafi shaidan da miyagun mutane ba zasu same ki ba, domin kin rigada kin cire." "Ba zan iya cire abin da na gani akan Amaan ba, ji nake kamar ba zan yafewa kaina ba." Ta fada tana kuka, "Zaki iya fa, amfanin kukan kenan ya sauke min kaso me yawa na damuwarki, kuma ba gazawa ba ce, amma tabbas zaki manta idan kika tuna inda Amaan yake raye, Hajiyata har da laifinki wurin barin Amaan ya faɗa wannan halin." D'ago kai tayi tana kallonshi. "Wallahi da gaske nake gaya miki, domin amman yana bijire miki ba shi yake nufin ki kyale shi yayi yadda yakeso ba, na sani dukkanmu kece kika haife mu, amma samuwar ɗayanmu yana iya shafe halin kowannen mu da yake ciki, Hajiya tun ranar ƙari kika bar tubani, domin da kin tsaya akan Amaan da haka bai faru ba, bakiɗaya kina tunanin idan kika takura mishi zai kauce ta wata hanyar bayan kyale shi, shi ne fadawar shi halaka, Hajiya wani hanzari ba gudu ba, ni kina son nayi aure. Amma baki san me yake damuna ba, Hajiya idan xan yi auren na su macen da nake so, karshe xan iya zama me karkon kifi daga ruwa zuwa wuta. Hajiya idan har da gaske ke Uwa ce, yanzu ya dace ki tsaya akan Amaan ba kyale shi ya rayu babu wani a kusa da shi ba." "Duk ƙoƙarina akanku dama na gaza ne?" Murmushin karfin hali yayi mata, ya ce mata. "Har kwanan gobe ba zan kiraki raguwar Uwa ba, domin duk inda ake bukatar uwa jaruma kin kai wurin, sai yan kura-kurai da ba za a rasa ba, amma ai kin yi ƙoƙari domin zaki iya lashe kambun uwa ta musamman a duniya." Majid yayi maganar da yasa jikinta yayi sanyi, don bata taɓa kawowa gazawarta akan Amaan shi ya haifar mishi da lalacewar shi ba, yasa tayi shiru sanin ya kara mata aiki yasa shi fita ya sayo mata magani har da me saka barci, ya b'alla mata ta sha. "Tabbas nice na taimaka mishi wurin lalacewa, domin a lokacin gani nake idan ban barshi yayi yadda yake so ba, zai iya lalacewa." "Yanzu ai mun rufe wannan chapter ɗin ko Hajiyata." Ya zauna yana kallonta, ɗaukar wayarshi yayi yana danne-danne. Shiru yayi domin yana son tayi shiru ta kwanta. Kuma hakan ce ta faru, da ta gama yan nazarinta, kafin ta kwanta barci yayi gaba da ita. Ajiyar zuciya ya sauke ya kara karfin ac din dakin sannan ya nufi jikin windown dakin ya tsaya yana kallon waje. Dole ne a gare shi ya fuskanci kowacce matsala. Wayarshi ce tayi kara ya dauka, "Majid Mamman Ba'are, na ga sakonka. Allah yasa haka shine mafi alkhairi, kuma ka dauki matakin da ya dace. Kasa da duniya ba zasu manta da alkhairinka ba." "Na gode Sir" ya faɗa, haka suka yi sallama, yana jin wani sabon nutsuwa yana saukar mishi ya ajiye aikin soja ya huta. Yanzu dama biyu gare shi ya tsaya asibiti ko ya karbi kamfaninsu. Sai dai wani abu da yake ganin zai fi mishi, zaman asibiti domin akwai abinda yake tuna mishi military section. Murmushi yayi yana jin wannan shine mafarin farincikin shi. Sai da aka sallami Hajiya da Aryan, amma Amaan yana cigaba da jinya. Domin har zuwa lokacin ana kan zancen mishi tiyata ne, don duburarshi dole aiki za ayi mishi. Manyan likitocin da suka kware akan tiyata, har da shi Majid a ciki suka jagoranci tiyatar farko, domin zama yana shirin gagararshi. Koda akayi aikin farko za a iya cewa an samu nasara, tunda har an samu yana iya zama tare da yin bayan gari da kanshi. Jamilah ce dai da alamu sai yadda Ubangiji yayi da ita, a wannan yanayin Zaytoonah da Mamarta suka zo, har da Yafendo. • Camp. Wato al'amarin Addah sai a hankali, domin kuwa idonta ya lalace. Duk yadda aka so a gyara amma abin ya ci tura, a duk lokacin da Addah ta kalli idanunta, ta kuma tuna cewa saboda Zahra idanunta ya lalace, tana kara jin matukar tana raye Zahrah tana raye sai ta rusota daga sama, sai tayi kaca-kaca da duk wata daukakar Zahra. Jin za a shigo dakin tayi maza ta boye madubinta, bayan Ummi ta rigada ta gani. "Kina kallon idanunki ne?" Ummi ta tambayeta babu wani abu a ranta, amma dake tana kallon kamar izgilanci Ummi zata mata, ita kuma zuciyarta daya tayi maganar. "Kina min dariya ne don na rasa idanuna ɗaya? Ai ba ayiwa ƙaddarar wani dariya yau gare ni gobe ga wani." "Ke dai kika sani, abin da yake zuciyarki kike faɗa, amma ya daga tambayarki kawai zaki hau surutu kamar wacce aka zaga." "Shegiya munafika, algunguma." "Eh na yarda amma ban kai ki ba, makashiya me sayar da Yarta domin duniya da abin cikinta" "Ni kika zaga karuwa kawai, wacce ta zubda cikin shege." "Kanku ake ji, farka da makaho." "Lalatacciya mazinaciya." "Duk abinda muka aikata ai laifinki ne, domin kece kika aika mu, bari ki ji ko jahannama zan shiga ina fatan Ubangiji yasa tare dake ne, gani ga ke. Ina kallonki kina kallona." "Tsinanniya muguwa, in sha Allah ba zan shiga cikin jahannama ba." Addah ta faɗa tana mikewa, Ummi ta ce mata. " Kika sake hannunki ya tab'a ni sai na miki shegen duka, idan kina ganin wasa ne Bismillah." Ta fada tana mikewa a fusace tana watsawa Addah harara. "Ni nace zan dake ki ne? Kawai don kin ga na tashi sai ki fusata." Lokaci guda tayi sanyi, domin tasan Ummi bugun kato zata mata. • Wata biyu da sallah, karatu yayi zafi domin kuwa, gashi bani da lokacin kaina sai na karatu zuwa yanzu babu wani da yake tare da ni sai su Maman Barakatu, a wurinsu Amira take zaune, idan na dawo haka zan huta na shiga cikin gidansu. Dake motar da ake kai ni makaranta sun bar min ita, ni kuma kunya nake ji na ja motar. Ina kwance kamar ruwa ya cinye ni, nifa sai yanzu na gano raguwa ce ta gaske. Domin kuwa idan na dawo nayi sallah na kwashi abinci, to nan nake bajewa, habawa bana iya tabuka kome kai Allah na gode talaka bai iya samun wuri ba, sai na baje nayi ta nishi dai-dai kamar wata tsohuwar akuya. • Duk yadda Hajiya taso danne abin, kasa rike zuciyarta tayi. Domin ganin har Yafendo a Nijar yasa zuciyarta laushi ta shiga fesar da abinda yake ranta, tana faɗa tana kuka. "Wannan sirrin Yaranki ne, ko kin gaya mana sai dai mu baki hakuri kamar yadda Abdul Majid ya gaya miki, kin bar Amaan don yana nunama Majid kiyayya kike gudun kada wani ya sani ya yi amfani da hakan ba? Tow ga shi nan yadda aka wayi gari, Wa garin ya waya? Addah na sha gaya miki duk abinda ya faru dake ba laifin kowa ba ne, laifinki ne akan Yaranki ya dace ki tsaya. Don Allah kada ki kara barin haka ya faru." Cikin shashekar kuka ta ce mata. "Har yau baki ji labarin batula ba ko?" Murmushin karfin hali tayi tana faɗin. "Ta rasu fa, ni kan.har nayi mata addu'a Allah ya mata rahama." Amma!"Ni kuma ina ji a jikina Batula tana raye, kamar tana kusa damu." "Kawai kina jin haka ne don kin saka hakan a ran ki ne amma ni nasan bata raye." "Ammi don Allah rike min, Mimi." Ta mika mata Yarta zata fita, "ina zaki?" "Zan tafi wurin Hamma Abdul a can asibiti." "Hmm! Ki dauki yarinyarki me shegen kukan tsiya." Inji Mamanta, "barta ba zata yi kuka ba." Da sauri ta fita bata ma tsaya ba. "Zaytoonah tana son Majid sosai." "Bana jin akwai bukatar ayi wannan zancen, domin kowannensu ƙaddarar shi daban." Inji Yafendo tana shigowa. "Yafendo ko don zumuncinmu!" Inji Hajiya. "Malam ya gaya min cewa duk yadda muke son, su had'a kansu haka ba zai yiwu ba. Domin kuwa kowa da ƙaddarar shi da rabonshi" "Kuma ai babu adalci ace Majid ya auri bazawara da Yarinyarta a duba dai." Inji Maman Zaytoonah, "kada na kuma jin irin wannan zancen." Inji Hajiya. Dariya Yafendo tayi domin tana jin dadin yadda suke tsayawa junansu. A can asibitin kuwa, dama da gayya Majid yaki komawa gida, don idan ya koma suka yi idanu biyu da Zaytoon ba barin shi zata yi ya huta ba, shi yasa shima ya hana kanshi komawa gidan..... 300₦ 0016341139 unity bank zahra'u yahaya Ali Katin MTN 400 #Mai_Dambu ce. [4/19, 4:22 PM] Cutie cutie pie: *BAƘIN HAURE....🐾🐾* {Greed for Money is the roots of all evils🫀} Arewabooks:maidambu41 Wattpad:Mai_Dambu Mallakar:Mai_Dambu *037* *Aunty Nuratu Salihu Abba⁩ gaisuwarki ta musamman ce. 😹 Tare da Team Hajiya Tani ikon God 🤣* A harabar gidan suka hadu da Nana, kallon uku saura kwata Nana tayi mata, kafin ta dauke kai kamar ba zata amsa gaisuwar da take mata ba, kafin ta amsa ta ce mata. "Ina zaki haka?" Tana hura hanci. Zuciyar Zaytoonah daya ta ce mata. "Wurin Hammayo zan je a asibiti." Ta mikawa Driven food flask, wani haɗe fuska. "Ce miki yayi yana jin yunwa?" Ta fada tana wani haɗe rai, "A'a kawai nayi mishi irin abincin da yake so ne." "Au ya gaya miki ba'a bashi abincin da yake so ne?" Gajiya da Jarabar Nana Zaytoonah tayi ta wuce zata shiga mota, Nana tayi bake-bake. "Wallahi bakya shiga ki je wurin shi." Fitowar Aryan tare da Nabeeha suka samu ana rigima, ita kan Zaytoonah zuba mata idanu take, sai masifa Nana take. "Kai Ariyan wannan yarinyar me kama da muciya da zanin me take nufi da Alhajin Allah?" Juyawa yayi ya gama duba ko ina bai ga me kama da abinda ta siffanta ba ya ce mata. "Wa kenan?" Ya tambaye ta, zubura baki tayi tare da zunden Zaytoonah da idanunta suka kawo kwalla, juya fulatanci yayi ya ce mata, "shiga mota ki tafi zan ji da ita.". "Wallahi wuta balbal ko kabarin mutum yana ci da wuta ba zan yafe ba, da zagin da aka min." Wuce ta Zaytoonah tayi ta shiga motar, kafin Nana ta fahimci abinda suke nufi motar ta bar gidan, kallon Aryan tayi baƙi sake. "Idan baka yi haka ba ai ba zaka tabbata ka sha nonon Fulani ba, kuma zan kira Alhajin Allah na gaya mishi domin nayi alkawarin bani cin amanarshi." Garin masifa har madubinta ya fadi, dauka tayi tana faɗin. "Allah ya isa Annabin Allah ya isa, kuma duk wanda ya sake ya likawa jikana bazawara ban yafe ba, Allah bai yafe ba, Annabin Allah bai yafe ba." Ta dauki madubin ta saka shi a juye. Wayarta ta lalluba ta shiga dankara kira. "Halo Alhajin Allah " "bashi bane Haladu ne Nana." Kashe kiran tayi ta kuma lallubar wani number. "Halo Alhajin Allah." "Nana Halima ce fa!" "Yau naga tijara Alhajin Allah nake nima." Ta kuma kashe kiran, ta wuce gidanta, tana kiran Driventa"Salele!" Da sauri ya iso. "Kira min Alhajin Allah." Tunda ta fadi Alhajin Allah yasan Majid ne, don haka.ya kira mata shi ya mika mata wayar. "Gashi nan Nana." Karba tayi wayar ma a juye ta saka a kunnenta. "Halo Alhajin Allah, kasan ba zan cuce ba kuma ba zan ci amanarka ba." "Eh Nana!" "Tow ga wannan doguwar yarinyar nan, me kama da fatalwa tana kawo maka abinci. Ban san me ta kawo maka ba, na dai gaya maka gaskiya a tow ba zan iya cin amana ba." "Na gode Nana!" .... A asibitin kuwa tun kafin su isa, Nana ta fesa mishi zuwan Zaytoonah, don haka ya shige Office ɗinshi yana shiryawa domin tana zuwa zasu fita. Bayan son wani ya san akwai wacce take bibiyar shi yanzu a fara yayata shi. Lokacin da Zaytoonah ta iso ne take raba idanu, tana nimanshi. "Yan mata!" Ya kira sunan, juyawa tayi tana tura baki, "cutie cutie pie zaka ce." "Ok muje!" Ya amshi basket din Hannunta, ya mata jagora har dakin da aka kwantar da Jamilah, "Hamma ya cikinta?" "Lafiya lau, baby girl ce kin ga yadda take, girma kuwa." Ya nuna mata wani computer da yake kula da cikin Jamilah. "Allah ya bata lafiya!" "Amin Ya Allah." Daga nan suka nufo wurin Amaan , anan suka sha hira kamar ba gobe, sai dare ya sakata a mota ta dawo gida. Bayan wata biyu, an sallame Amaan har lokacin Jamilah bata farka ba,abin har ya fara kashe jikin kowa, shima Majid ba karamin matsanancin damuwa ya shiga ba. Haka yasa suka fara tunanin ko a fita da ita waje ne. A bangaren Zaytoonah kuwa an nima sama mata Makarantar Jinya a nan Niamey, inda ta fara da taimakon Nabeeha. Tun faruwar Al'amarin su Amaan ba a kara jin motsin ko Hajiya Tani, amma kuma sai dai lokaci zuwa lokaci ana samu abu marasa dadi da suke faruwa, a tsakanin Kamfaninsu da kuma wasu abubuwan. Hakan yasa Majid ya ɗan fara bibiyar kamfanin da taimakon Aryan wanda ya amshi matsayin Anisah, suka koma bakin aiki gadan-gadan. Ya ajiye aikin asibiti idan ya dawo da dare sai ya leka asibitin. Duk da bai cewa Hajiya ya koma kamfani ba, sai dai haka ya mata dad'i domin addu'a da ta dad'e tana yi ne Allah ya amsa mata. Lokacin da bata zata ba kuma abin daɗin aiki biyu yake dubawa ko bai je kamfani ba, yana asibiti kuma da alamu aikin asibitin yana so ne har cikin ranshi, shi yasa ya ke lekawa idan ya samu lokaci. Amma bakiɗaya aikin bai da lokacin na asibitin. A binciken da yayi na kamfanin yasa, aka shiga sallamar mutane musamman masu aikin bangaren tattalin arzikin kamfanin, don ya gano har dasu a cikin masu yi musu zagon kasa, sannan suna cikin masu yayyata wasu abubuwan, haka yasa bakiɗaya yaƙi yarda da kowa, aka sallame wasu aka kuma d'ebi wasu, a bangaren Jamilah kuwa sosai likitocin suka tsaya akanta, har Allah ya d'aga kafadarta bayan wata biyu tana sume, ba karamin farinciki Hajiya tayi ba, don su Yafendo sun koma da Maman Zaytoonah, aka barta a nan Nijar, sannan a bangaren Zaytoonah ba karamin haukar son Majid take ba, su kansu yan uwanshi, sun bata goyan baya, sannan haka yasa take shige mishi. Sai dai kamar yadda ya gayawa Hajiya gaskiya duk da bai fito ya ce yana da zabin ranshi ba, amma ya ce mata shi a kanwa ya dauke ta, ba a macen da zai aura ba. Shima din sai da a bakin Aryan da Amaan suka gayawa Hajiya, domin haka ya faru ne ranar babban sallah suna aikin Nama, ta kawo musu gasashen namar da ta gasa, don ana yankar ta tsaya akan Aryan ya diba mata, ta kawo kitchen tayi mishi denderu. Ta kai mishi koda ya amsa ce mata yayi. "Ya Allah ya bawa Zaytoon miji na gari." Hararanshi tayi tana tura baki, ta ce mishi. "Mimi bata da dady sai kai." "Eh dama ai ni ne dadynta." Murmushi tayi ta wuce, "Hamma yarinyar nan tana sonka, me kake nufi da Allah ya bata miji na gari." Tab'e baki yayi yana faɗin. "Ita dasu Anisah kallo daya nake musu, bana ajiyeta a tsarin matan da aka halitta daga hakarkarina." "Abdul kana nufin cewa." Lumshe idanunshi yayi ya bude akan wayarshi, da Umaima take kira, kashe kiran yayi ya kirata da kan shi. "Barka da sallah ya kike?" "Abdul Majid Mamman Ba'are!" Yarrr tsigar jikinshi ya mike, ya amsa a sanyayye. "Na'am Umaima minjibir." Ya amsa yana jiran yaji me zata ce. "A gida a can na fitar da miji, ni kuma ban ga wanda ya dace da ni ba sai, please Majid kada ka yi rejected dina." Iska ya ja yana jin shashekar kukanta. "Kiyi hakuri, Allah ya baƙi wanda ya fini, amma babu aure a lissafina." "Please Majid, kazo gidan mu ka gaya musu zai aure ni amma ba yanzu ba, wallahi zan jiraka." Ta fada tana kuka, "A'a ba zan yaudari kowa ba, ni namiji ne da zan amsa suna a ko ina namiji, ba zan yaudari yar kowa ba balle har akai Allah ya kama ni. Ni ba Basimpe ba ne ɓalle na yaudare ki, kiyi hakuri nasan akwai waɗanda suke sonki baki basu fuska ba ne, kuma zasu fini sonki." "Majid wallahi kai kaɗai nake so, don Allah kada ka min haka, idan ma Zahra kake jira ta mutu." "Zahrah!" Ya ambata a hankali, kafin ya sake murmushi yana faɗin. "Ni ban santa ba, abin da na sani na gaya miki gaskiya babu shirin aure a tsarina. Idan zaki yi hakuri kiyi hakuri. Akwai wanda na san shi jiranki yake kuma zai rike ki da Amana da gaskiya amma ni idan na aure ki, zan miki rashin adalci." "Majid ka gaya min baka sona." "Idan na boye miki, ai babu armashi shi yasa nake gaya miki gaskiya kawai a wuce wurin." "Allah ya isa rejected dina da kayi, in sha Allah sai kasha wahalar so kamar yadda nake sha akanka, kuma ba zaka tab'a haduwa da Zahrah ba har abada." Murmushi yayi yana kara rarrashinta, ita kuwa sai zaginshi take yi, amma shi murmushi yake yana bata hakuri, nuna mata muhimmancin hakurin dai da zata yi, ta samu wanda yake sonta ba wanda take so ba, ba karamin rigima tayi mishi ba, shi kuwa bai fasa rarrashinta ba. "Majid me kake boye min? Yarinyar da ka kwanta da ita a asibiti kake tunanin zata dawo gare ka?" "Umaima! Ina son ki gane cewa ni babu wani shauki a raina. Sannan bana jin akwai bukatar haka. Mace hmm ba a haifi matar Majid ba." Wani uban ihu ta saka tana faɗin. "Karya ne Majid, karya kake wallahi yarinyar nan ita ce a ranka. Idan ita ce Majid ka kwallafa rai akanta, baka mana adalci ba wallahi." Shafa yar kasumbar shi yayi yana faɗin. "Ko daya yarinyar da ban san yanayin fuskarta ya yake ba? Yarinyar da ko cikin dubu na ganta ba zan gane ta ba." "Jininka ne a jikinta, zaka gane ta wata rana idan tana raye, amma yarinyar nan bata min adalci ba." Dakyar ya rabu da ita, Amaan ya zuba mata idanu, shi kan Aryan bai yi mamaki ba domin kuwa ya sha jin yana waya tare da cewa. A bincika mishi sansanin gudun hijira, ko za a dace. Amma shiru sanin cewa baya son magana kuma.idan ka tambaye shi bai zama dole ya baka amsa ba, yasa shi jan bakinshi yayi shiru. "Kai mata suna da matsala haka masu yan mata suke fama." "Kai dai ka ji dadinka munafuki, kana da wacce take binka tana sonka amma dake kayi zubi da munafukai kayi shiru ka bar, Zaytoon tana wahala wacce me karfin ikon ce ta shammaci zuciyarka." "Ba a haife ta ba." Inji Aryan yana kunshe dariyarshi. "Lokacin sai kuyi niman budurwa daya da Affan ko?" Dan gidan Aryan inji Amaan. Mur yasha kamar bashi ba, domin bai cika son su tasa shi gaba da tsokana ba, don haka ya haɗe rai ya cigaba da aiki, tun daga wannan ranar bai kuma ce musu kala ba, sai da Hajiya ta tuntube su akan lamarin Zaytoonah da Majid din ne suke gaya mata yadda suka yi da shi, karshe bata sare ba har daki ta same shi yana aiki a can kuryan dakinshi inda aka saka table da kome da kome, ta ja stool ta zauna tana kallon shi. Tunda yaga yadda take mishi kallon tuhuma yasan Hajiya yau no mercy. "Umaimah Ashe ta kira ka akan ka aure ta kaki?" "Hajiya idan na ajiye mace zata bukaci abubuwa dayawa, babu wacce zata fahimci yadda nake ji idan ba wacce take da sanin yadda rayu take ba." "Majid yaushe ka fara magana." Shiru yayi bai ce mata kome ba, "Majid ban yarda da kai ba, ka ajiye maganar baka da lafiya ni nasan lafiyarka lau, aure nake son naka yi " Shiru yayi bai ce mata cikanki ba, balle har ta yi tsammanin zai bata amsa. Ta cigaba da fada kamar zata mare shi. "Na rantse da Allah, ka fitar da mace ko ni nayi nawa ikon akanka....... 300₦ 0016341139 unity bank zahra'u yahaya Ali Katin MTN 400 07035133148 #Mai_Dambu ce [4/20, 9:07 PM] Cutie cutie pie: *BAƘIN HAURE....🐾🐾* {Greed for Money is the roots of all evils🫀} Arewabooks:maidambu41 Wattpad:Mai_Dambu Mallakar:Mai_Dambu *038* *🙄Kawayen Tani ina gaisuwa, Kawata Ambassador tare da Mamarsu Anam da Anum, da kanwata Labilah Lalan Mummy 🤣😹 How market dole gayen nan yayi aure ko muyi mishi forcing marriage 😹😂* Yadda take ta fada har Amaan da yake falon kasa sai da ya hauro sama, ya ga yadda take fada Majid din bai ce mata kome ba, amma ya kasa ci-gaba da aikinshi kanshi a sunkuye, haka yasa Amaan yayi maza ya riko hannunta yana faɗin. "Me yasa ba zaki mishi addu'a ba? Me yasa kike wargaza aikinki akan mu? Me yasa ba zaki yi hakuri ki ta nima mishi zabin alkhairi ba? Hajiya Maisarah cewa tayi tana son Majid aka kashe ta har lahira, gaya min yar waye zaki janyo cikin wannan tashin hankalin? Gaya min waye zai bawa Majid yar shi bayan ansan gidan nan akan mallakarka ma niman rayuwarka ake, Hajiya ya isa haka, idan Majid yana da lafiya lokaci ne zai gwada mana haka, idan bai da lafiya lokaci ne zai gwada mana, so kike su kashe shi da bakinciki idan aka san bai da lafiyar da zai rike mace, Haba Hajiya haba haba Hajiya. Gaggawar ta meye ne? Lokaci yana zuwa da Majid zai ajiye mace har da Yara don Allah ki shafawa ranki ruwan sanyi idan ba so kike zuciyarki ta samu matsala ba " A wannan lokacin ba karamar damuwa Majid ya shiga ba, shi yasa da ya samu damar kasuwanci a kasar Poland bai yi wasa da damar ba, haka ya dauki kome na shi ya tafi, da taimakon Amaan wanda suka tafi tare ya samu yaga likitan da ya daura shi akan Magani, domin Amaan ya mishi hanya, shege Amaan tunda ya ga ya kusan mutuwa, ya koma jikin yan uwanshi, sannan har kwanan gobe babu wanda ya ce mishi me ya faru a baya, domin sun san ƙaddara kuma zata iya fadawa kan kowa. Hajiya ba son shi ba ne don Allah ki sassauta mishi, Hajiya ni da nayi auren ba haduwa nayi da makirar mace ba, yaran da nake alfaharin nawa ne ba Yarana ba ne, Yaran Sajjid ne Hajiya me ya fi haka Muni? Hajiya Aure lokaci ne idan har Allah bai nufa zai yi yanzu ba, duk abinda zaki yi ba zai yi ba, don haka Hajiya ki kyale shi ya jira lokacinsa yayi. Kowane mutum da iyakar ƙaddarar shi, shi nashi ƙaddarar da sauran ta. " Mikewa Majid yayi ya dauki kayan zuwa asibitin shi ya bar dakin. "Ka gani ba, wai yayi fushi." "Da bai tattara ya gudu ya bar kasar ba, shi ne zamu ce da sauki." Zama tayi bakin gadon Majid ɗin. "Kana nufin sai ya gudu?" "Tsaf sai ya gudu tunda kin ce auren dole zaki mishi." "Kai Amaan ni sa'arka ce da xaka ce zai gudu don zan mishi auren dole." "Wallahi Hajiya idan da can baya ne tafiyar shi zai yi " Shiru tayi bata kuma magana ba, ta mike suka fita, "Amaan ka saka idanu akan shi kaji don Allah kada ya gudu." "Bayan ya ajiye aikin sojan zai gudu ina? Babu inda zai je kawai ya tafi asibiti ne." Hajiyar zuciya ta sauke tana jin wani sauki a ranta ba ta kuma yarda tayi zancen auren ba, gudun kada ya fece. Ashe shi kan Majid ba asibiti ya wuce ba, gidan Nana ya wuce a can ya kwana. Domin baya jin zai ji dadi ranshi, shi yasa ya dawo gidan, yana shiga falon Nana ya hadu da Afiyyah. Sakin baki tayi don bata zaci zai zo gidan ba, sannan wani abin da ya kara rud'ata yadda take zaune daga ita sai bom short da yar shimi, haka mutumin nan ya wuce ta bai d'aga idanu ya kalli inda take ba, ya wuce dakin Nana kai tsaye. "Ke bana ce ki tafi gidanku ba, sai ki tawo nan domin zuwa yawon darenki, ki hana ni barci ina zaman lafiya ta, ki fita kafin nazo na maka miki sanda." "Ba ita ba ce" ya faɗa yana nufar daya daga cikin kujerun hutun ɗakinta ya zauna, ya cire agogon hannun shi, ya kalle ta. "Bani pillow dinki ɗaya." Tashi tayi jikinta yana rawa ta mika mishi, sannan ta dawo ta dauki bargo, ta ajiye mishi tsantsar mamaki ya hana ta magana. bude botiran rigar shi yayi ya kwanta. Yana sauke ajiyar zuciya, don har zuwa lokacin zuciyarshi zafi take mishi. A nan ya bar Nana baki sake, bai yi barci da wuri ba, domin maganar da Nana take yi ita da Afiyyah da ta ce ta bar mata gida ko ta gayawa Majid din yawon ta zubar take fita. Haka yasa ya fahimci yarinyar tana zuwa wurin Nana da sunan kwana amma yawonta take zuwa, yanzu haka file din yarinyar yana office ɗinshi akan za a dauke ta aiki, amma bai saka hannu ba, asuban fari Nana ta farka ta hango shi kan Abin sallah. "Lallai Alhajin Allah da kokari kake, ahto wani shegen ya isa cutar ka, bayan Allah da Mala'ikun da suke tare da kai, yana idar da nafilla aka kira sallar asuba, ya tafi masallaci. Daga nan da aka idar da sallah, ya juya cikin gidansu, a falon kasa ya samu Hajiya tana zaune, ta kafe kofar gidan da idanu, tasan bai tafi asibiti ba tunda keyn Motarshi na falo, haka yasa hankalinta yaki kwanciya bata samu barci ba, idanuwanta sun yi jawur. Zama yayi a kujerar kusa da ita ya ce mata. "Ina kwana Hajiya." "Sannu Majid. A ina ka kwana?" Kafin yayi Magana Aryan ya ce mata. "Hajiya don Allah me yasa kike haka ne? Tun jiya kin hana kowa barci Bayan kece kika fara tado abin da yasa shi barin gidan don Allah Hajiya ki yi hakuri mana." "Ba zan yi ba, nace ba zan yi hakurin ba." "Kyale ta, ai dama tunda naga Alhajin Allah yazo wurina ya kwana na kwana da sanin akwai dalili, yanzu ma na ga bai dawo ba nace bari na biyo sahu , ashe masifarki ce ta motsa kika hana shi barci, anya Sa'adatu? Wallahi kika sake wani abu ya same jikana kotun duniya ce zata raba bani da ke, haba don Allah duk abin da yaron nan yake bakya gani, tow kashe shi ki huta idan ya mutu kece da asara, ina cewa barin aikin shi yayi don ya tsayawa dan daudunki shine kike niman hallaka min jika wallahi baki isa ba, sai kotu ta raba ni dake Sa'adatu domin ba zan kara ganin wani gawar ba." Ganin yadda Nana take shiga ba nan take fita ba, anan take gayamata . Ai ga abinda Alhaji Haladu ya ce akan yarshi Afiyyah amma ita tana tare da Alhajin Allah duk abin da yake so shi take so, ba zata mishi dole ba, duk son Hajiya da yayi aure, jin Afiyyah za a nemi haɗasu tuni tayi saranda ta ce ita ta yafe auren Allah ya bashi mace ta gari. Haka yasa Majid ya samu ƙwarya kwaryar zaman lafiya da Hajiya, don Nana tana tare da shi. Bai san me ya sauya Nana ba, amma a zahirin gaskiya baya tunanin bindigarshi ce tayi tasiri. Tashi yayi ya haura dakinshi ya shirya ya fito cikin wani American suit Navy colour, don yau ya tuna da bakin daga ne, ya fito sanye da farin glass, yayi mishi kyau, duba agogon falon yayi yaga karfe takwas saura, an kawo abin karyawa daga gidan Aryan, ga wanda Zaytoonah ta haɗa musu, zama yayi ganin an bazawa Nana tana ci, ya zauna kusa da ita ya fara ci a cikin nata, dake Allah ya taimaka Nana tana da tsafta, idan ka cire abin da tayi mace ce me matukar tsafta da gyaran jiki, Murmushi tayi tana ci da shi, "Hamma kai zaka ajiye ni yau a makaranta don Allah." Ta fada tana miƙewa, "Salele zai kai ki, ni bana son gulma haba don Allah idan ba munafurci ba, taya za'ayi ki maida min jika direba, idan ba munafurci aka hada don a cuce min shi ba." "Nana kanwata ce fa." "Hmmm! Na dai ji wannan." Da gangan Nana ta hana shi tashi, sai zai mike ta kawo mishi wani labari mara kan gado, ita nan don kada ya dauki Zaytoonah. Karshe Aryan yana shigowa Zaytoonah ta mike. "Hamma Aryan muje ka ajiye ni school." Ta fada fuskarta a had'e, "oho dai sai dai ariyan din ya kai ki, amma ban da jikallena ba." Don bakinciki sai da Zaytoon ta ji kwalla yana zubo mata, a gurguje Aryan ya sallami Hajiya da take kallon rigimar Nana da Zaytoonah. "Nana me yasa kike mata haka?" Ya tambayeta. "Haka kawai zata mai da kai bawanta." Ta fada tana zumburo baki , "Nana ai duk namiji bawan mace ce, matukar ya san ciwon kanshi. Koda bai bautawa Matarshi ba, dole zai bautawa kanwarshi da Yarshi, Nana Zaytoonah marainiya ce, sannan ta baro Cameroon tazo nan domin mu, ina ga ita ai kamar jikarki ce." "Ni ba jikata ba ce." Ta faɗa tana wani b'ata rai. "Na ji ba jikarki ba ce, shi kenan ki daina ci mata fuska akan idanuna, na roke ki." "Haba Alhajin Allah, sai ka roke ni ne? Kawai kace min Nana ki daina sai na daina, meye a cikin idanu banda ruwa." Daga haka ya kashe bakin Nana, daga nan ya mike ya musu sai ya dawo. • Hidimar kasuwancin ne ya kai su, har Poland don ba karamin ci-gaba za a samu ba, don haka sai yayi amfani da wannan damar tare da ganin likita, wanda yayi nasarar gano matsalarshi, sannan ya ɗaura shi akan magani. Kwanakin shi goma sha daya, gobara ta kama wani part na kamfanin BA'ARE GOLDEN EMPIRES. • Zahrah Buba. Karatun da ya sako ni gaba, yasa bani da lokacin kowa sai na kaina. Sai wani dan ajinmu me suna Sauban yana da matukar kirki. Yau ma daga dakin karatu muka fito, ya ce min. "Fatimah zaki iya tafiya don ni zan shiga cikin makaranta, kuma kin ga yamma tayi." "Haka ne, sai gobe kawai." Anan muka yi sallama na wuce gida, a bakin get din makaranta na hadu da wasu yan department ɗinmu, dauke kai nayi domin daya daga cikinsu mai suna Abdullahi ya saka min idanu, Abdullahi yana masters ne amma irin yaran nan ne marasa jin magana, a bakin Sauban nake jin babanshi mai kudine kuma dan siyasa ne, haka yasa yake yadda yake so, duk da wannan abin bai taɓa burge ni ba, domin ni karatu ya kawo ni ba shashancin ba, kodon na cikawa Yazid alkawarin shi,zan tsaya nayi karatu. Har na tsayar da abin hawa, iskanci da rainin hankali Abdullahi yake min, ina shiga na sauke ajiyar zuciya. Ina jin wani abu yana sauka a raina, don ba ƙaramin abu ba ne, Abdullahi ya kunyata mace a gaban jama'a. Haka yasa Sauban ya gaya min nayi a hankali da shi. Sannan ganin yadda ake shakkarshi yasa shi jin shi wani jan wuya ne. Mun hadu ne ana sallah layya saura kwana biyar lokacin da aka bada hutu, ranar da mota na shiga makarantar, nazo zan fita kawai ya tare hanya, kuma ya hana kowa fita, haka muka zauna a cikin makaranta har sai da Den na makarantar ta fito da kanta, shine ya bada hanya amma tabbas bamu ji da dadi ba, domin bai da mutunci. Haka yasa yana bada hanya muka fita, ina cikin waɗanda suka fita da mugun gudu, tow ko me ya gani ya ke bibiyar rayuwata oho, ya dai turo min wani yaro na bawa Yaron hakuri akan cewa ni matar aure ce, mijina yana nan. Amma mutumin nan bai kyale ni ba, sai ma kara adabbar rayuwata yake, don ko da aka dawo hutun sallah, bai daina bibiyata ba. Zuwa yanzu kan sai hamdala kome yana zuwa min Cikin sauki da nasara. Bayan ya turo yaron sai da ya kuma tare Sauban da maganar banza, haka yasa Sauban ya gaya min abin da yake nufi, shi damuwar shi na zama budurwar shi na wucin gadi, sai kace wacce bata san ciwon kanta ba, don Allah ya zanyi?.... *Kuyi hakuri muna fama da rashin wuta.......* 300₦ 0016341139 unity bank zahra'u yahaya Ali Katin MTN 400, 07035133148 #Mai_Dambu ce [4/21, 7:33 PM] Cutie cutie pie: *BAƘIN HAURE....🐾🐾* {Greed for Money is the roots of all evils🫀} Arewabooks:maidambu41 Wattpad:Mai_Dambu Mallakar:Mai_Dambu *039* *Wannan shafin domin ki Maman Husnah 😍🥰❤️* Ban yarda nayi wani abun da zai janyo shi jikina ba, domin kuwa cikin shigar kamala da mutunci nake, sannan a yadda nake jin labarin abin da ya faru a can baya. Babu dad'i domin idan yarinya bata yi mishi ba, a gaban jama'a zai kunyatata, sannan yayi mata sanadin barin makarantar, ni idan na bar makarantar ina zan ni? Waye zai tsaya min. A hankali naji zuciyata tana gaya min Allah yana sane da lamarina ban da Allah waye ya raba ni da fitinar Addah? Ban da Allah waye zai min nisan kwana har yau na zo nan, nasan ko a mafarki ba xan tab'a kawo kaina nan ba, amma sai ga shi Allah ya kawo ni, ya saka min da wasu abubuwan da ban roka ba, Tuna wannan abin da nayi yasa na fara niman agajin Allah, akan Abdullahi don bana son dalilin da zai saka a ce min nima wani abu mara dadi ya faru da ni a makaranta. Haka yasa na yawaita addua, ba dare ba rana, yawan addu'a yawan sab'ani da nisan da ke tsakanin mu, haka yasa kowa yake kallon kamar ya kasa min kome, ni nasan Allah ne ya shiga tsakanina da shi, ba iyawata ba ne kuma ba wai don nafi kowa ba ne, a'a Allah ne yaso haka. Haka lokaci yayi ta tafiya har muka kammala aji daya, muka shiga biyu abin ba wuya fa. Koda yake kana naka Allah yana na shi, na Allah shi ne gaskiya amma tabbas rayuwarmu karewa take, a lokacin Amira tana da shekaru biyu a duniya, ga ta da farin jini, haka yasa nake kara boye ta gudun kada bakin jama'a ya tasirantu akanta, don idan baki yayi yawa akan Yaro ana iya samu nakasu, sosai na ke boye ta. Nima Babba ban da ina saka Hijab da dogayen riguna dayawa cewa suke ni somalians ce, domin yanayin fata ta da jikina. Koda nace musu fulani ce ni ba yarda suke ba, na sha gaya musu ni Daga Nigeria nake amma sai su ce eh ai haka kowa ma yake boye Asalinsa. Haka yasa bakiɗaya nake jan bakina nayi shiru ina kallon ikon Allah • Somewhere in south Carolina. Babban gidan rawa ne, da yake tashin sautittuka. Dauke take da tire izuwa gaban wasu gungun matasa, maza da mata. Ajiye musu tiren tayi tana cire kofi nan glass din kan tiren. Sanye take da farin shirt da top akan rigar, sai skirt iya gwiwarta. Cikakkiyar bafulatana Zulaihah tsaye ta tufke kanta, da yake sanye da katon Black bam. Sannan ta ɗauki tiren zata juya, wani matashi a cikin matasan ya mari mazaunanta, bata kula shi ba haka ta wuce inda suke ɗaukar kayan, ta tsaya. "Zully ya dai?" Murmushi tayi sannan ta ce mata. "Ba kome Ra'if." Ta faɗa tana shafa bracelet din hannunta. "Ko kin tuna da Baby da Zeehrah ne?" Juyawa tayi tare da washe hakori, "Eh kusan haka ne, amma a yanzu basu ne a tunani na ba, yadda zan bar wannan aikin nake." Murmushi yayi ya karkad'a haɗin da yake sannan ya ce mata. "Dala talatin ake biyanki duk sati biyu, sannan kina sane da cewa Mr Williams ba zai kyale ki ba sai kin biya shi dukkan kuɗin shi da ya saka akanki sannan zai barki ki tafi, bazan baki shawarar sabawa Allah ba, amma ki nemi yadda zaki yi, ki biya shi kudin shi in sha Allah akwai aikin da ya fi na shi." Murmushi me ciwo tayi, tana wasa da bracelet din hannunta, kafin wasu gungun mata suka shigo, suka ce ayi musu hadi na musamman a kai musu, ita ta kai musu. Yau club ɗin yayi wani irin cikar da ba cika yi ba, saboda bikin auren jinsi da aka yi maza sun auri maza mata sun auri mata , yayinda wasu masu jinsin biyu suka auri yan uwansu. Abin ba a cewa kome shi yasa club ɗin ya cika makil, babban burinta shine, ta fita kafin wani lokaci domin ana cika club ɗin xa a rufe kofar kuma haka yana nufin babu abinda ba zaa yi ba. Kallon agogon bangon club ɗin tayi, karfe biyu saura, kamar lokacin ake cin kasuwar rana, don haka ta cewa. "Ra'if zan tafi, yau gidan nan babu masaka tsinke, kuma abin da zai biyo baya, babu kyau." "Ok ki shiga office din Mr Ardor Kiyi sign." "Na gode." Da sauri ta wuce tana kallon agogon domin tasan Mr Williams yana can yana jiranta, idan ta kara koda minti ɗaya ne, sai ya ci mutuncinta, sannan ya wulakantata a gaban jama'a. Sauya kaya tayi zuwa doguwar riga, sannan ta yane kanta da mayafi, kafin ta wuce office din Mr Ardor tayi knocking, gurnanin shi ta ji haka yasa ta ce mishi. "Sir nazo Sign ne." "Shigo kiyi zully " shiga tayi zuciyarta na dukar uku uku. Kin kallon inda suke tayi ta wuce tayi sign, ta fita da sauri cikin d'aga murya ya ce "crazy bitch." Ita kan da gudu ta bar club ɗin, ta nufi wurin Bus stop. Tana tsaye har na wani lokaci kafin ta samu taxi zuwa gida, ina shiga na sauke ajiyar zuciya. "Ke yar Afrika ce?" "Eh!" Ta fada tana kallon gefen hanya, wani irin kewar Zahrah da Babynta take, don ba karamin wahala ta sha ba. Don ma Allah ya taimaka, bata yi karuwanci ba amma kuma duk wani abinda yake da alaka da assha a wurin take zaune, Mr Williams shine wanda ya saye ta a wurin wani dan kasar Japan, Hararu James. A wurin Hararu James ta fara aiki a bar din club ɗin. Mr Williams irin kazaman masu kudin nan ne, amma gurgu ne akan keke yake yawo, yana da yan mata kamar hauka, amma matsalar shi guda daya ne, a tsotse mishi taliyarshi. Tunda shi dai ba iya abin arziki zai yi ba, amma kuma zai mika musu ita kamar abin wasan Yara, sannan a duniya babu wanda yake addaba kamar Zuzu, domin ta fisu iya sarrafa abin. Idan ta makara kuwa haka zai rufeta a daki yasa Yaranshi yan mata su mata duka, tunda ta fahimci cewa akan haka suke dukanta yasa ta ƙoƙarin kiyayye abin da zai ja mata duka, kafin kace me har sun isa gidan, ta biya kudin motar ta nufi cikin gidan da sauri tana sauke ajiyar zuciya ko waya ba a bata damar rikewa ba, balle har ta nime wani nata, a farkon zuwanta har kula da aladu sai da tayi a wani gidan gona, tayi aiki na tsawon wata shida tunda aka fahimci ba zata iya aikin karuwanci ba, domin bayan haihuwarta take zubar da jini, babu namijin da ya isa ya kusanci inda take da sunan lalata, ba tare da zaren sadarwar shi ta tsaya ba, haka yasa suka camfeta da cewa yanayin kyanta da surarta ba mamaki tana daga cikin godness, haka yasa bakiɗaya kowa yake tsoronta sai Mr Williams kawai da yake jin dadin ta tsotse shi. Kwabe kayanta tayi ta shiga dakinshi, yana kallon yadda ta shigo mishi murmushi yayi yana faɗin. "Good girl, tawo nan." Hawaye ne ya cika mata idanu, tana ji aranta Allah ya bi mata hakkinta kamar yadda Addah ta watsar mata da rayuwa. Sai da tayi mishi kamar yadda take mishi sannan ta fito ta wuce ɗakinsu tayi wanka tare da alola tayi sallah, • Tunda ya dawo daga Poland bai kuma wani tafiya mai nisa ba, asalima Aryan yake wakiltawa akan kowani tafiya, shi kuma da Amaan suna jikin kamfanin domin, sau daya suka hadu da Hajiya Tani a wata kwanciyar Nana asibiti, wai ta shiga ban daki ta zame ta faɗi, shine ta buge kugunta. Ai kuwa ta saka rikici kugunta ya ɓalle, aka yi aka yi ta nunawa mutane taki. Majid yana zuwa ta shiga nishi tana matsar kwalla. "Alhajin Allah, ka shiga tsakanina da afiya ta fita daga gidana. Tunda ba tare Mamman ya bar mana gadon shi ba, kaga yadda na karya kuguna yarinyar nan zuba min ruwa tayi na zame gashi nan ko tafiya bana iyawa." "Sannu Nana, ina ga zan sayo miki magani." "Wallahi ba zan yarda ba, ina wancan yarinya har daukarta kayi zuwa asibiti da bata da lafiya."shiru yayi yana kallon yadda take kirkiro tashin hankali, saboda ya kula da Zaytoon da tayi fama da matsanancin rashin lafiya. "Amma ita ai da kafarta ." "Yo idan ba an shiga tsakaninmu ba, uban waye ya ce maka bani takawa da kafata?" "Amma Nana cewa kika yi kin karye?" "Dalla can annamimi kwarin wake, na gaya maka bani zuwa ne ko kace na tashi na kasa ta shi ne? Ni fa bana son hada husuma na lura da kai Allah ya hore maka baiwar munafurci, Alhajin Allah muje asibitin ka ji." "Nana idan muka je, ganinki za ayi kawai mu dawo amma ba zasu baki gado ba." Inji Majid. Komawa tayi gefe tana matsar kwalla, hawayen gulma yana zubo mata. "Ai shikenan sai ka tafi ka sayo min maganin ai nasan don ka kulla ce ni ne, sa'a ba zata tab'a barinka ka kula da ni ba, ai na sani don akan abinda ya faru ne shekarun baya ko Allah yana yafe mana balle kai Alhajin Allah " "Nana nifa bance ba zan Kai ki asibiti ba,tashi muje." Ya faɗa yana ƙoƙarin danne takaicin da yake cin shi idan Nana tana wannan borin, ya lura ko Yaranta bata yiwa wannan fi'ilin sai shi da ta gama renawa hankali. "Yawwa dan albarka ai nasan sa'a bata yi haihuwar banza ba." Haka ta mike, ya shiga gaba suka tafi asibiti. Tun kafin ya ga likitan kowa ta gani sai ta gaya mata ai jikanta ne ya kawo ta ganin likita don ta faɗi, Yaron nan dan albarka ne, yadda ya damu da ita ai ba karamin abu ba ne, ita bata so zuwa ba amma shi ya matsa lallai dole sai tazo, gashi nan.dai tazo. Yana jinta haka ya share yaki yar da ya bata fuska kada ta disga shi (😹🤣😂 Nana ikon Allah) da ya gaji da surutunta, wani daki aka kaita ya ce mata. "Nana wallahi kiyi shiru ki zauna lafiya domin maganarki tayi yawa, kika kara magana wallahi zan saka su karya kugunki kowa ya huta." Hannu ta kai bakinta ta rufe kamar yadda ake saka Yara su yi shiru. Haka tayi jinyar nan lafiya lau, don ma sai ta ga Majid zata fara narkewa, sannan duk wanda bai zo ya gaishe ta, in sha Allah kiranshi take awaya ta zungura mishi zagi me tsalle sa bakar magana, tare da cewa ko mutuwa tayi banda gayyatar su kan gawarta. Haka tasa Majid ya kira Aryan ta zage shi tas, sannan ta ce mishi. "Kuma na gaya maka ko mutuwa nayi kada na ganka kan gawata, don bana bukatar almura irinka." Dariya yayi yana faɗin. "kice kin kawo min kanki asibiti." "Alhajin Allah, sallame ni wannan bakin munafikin yana zuwa ban san me yake nufi da ni ba." "Nana baki warke ba, gara kiyi jinyarki kada wani abu ya faru ace wani abu ya same ki." "Kai babu abinda xai faru kawai ka sallame ni na gaya maka." Haka ya sallame ta, suka.dawo gida sannan zaman asibitin jidali ne fa, duk wanda xai je gaida ta, da ledar shi na kunshin nama, ko cooler da farfesu. Wannan abin ya matukar takurawa rayuwar Nana, ga shi Zaytoonah itama duk zuwa da katon kular farfesu. Idan tazo Nana tayi ta watsa mata harara a fakaice, don tana ganin kamar da gayya take leka Majid. Wannan bibikon da Zaytoonah take yiwa Majid yasa aka fara kananun magana da cewa ai suna soyayya ne, shi kuma har ga Allah babu wannan batun, abin da yasa Ita Zaytoonah jin kamar ta mallaki Majid din, ta shiga wani kaf-kaf da shi. • Alhamdulillahi... Shekaru hudu, a wannan zangon karatun manyan kamfanoni da ma'aikatu sun turo takardun daukar ɗalibai masu hazaka. A cikin wannan yanayin daya daga cikin BA'ARE GOLDEN EMPIRES suka turo mataimakin Chairman dinsu........ Saura daya na gama Book one! 300₦ 0016341139 unity bank zahra'u yahaya Ali Katin MTN 400 #Mai_Dambu ce [4/22, 8:49 PM] Queen BeeBee: *BAƘIN HAURE....🐾🐾* {Greed for Money is the roots of all evils🫀} Arewabooks:maidambu41 Wattpad:Mai_Dambu Mallakar:Mai_Dambu *040* _Karshen littafi na ɗaya!_ A ranar da kamfanin Ba'are suka zo, sun yi amfani da score din mu na kowace semester ne, haka yasa ina zaune aka kira sunana, kamar wacce aka tsikarawa allura haka na mike ina zare idanu, "Ni Zahra Abubakar?" "Eh ke." Mikewa nayi tare da bin bayan masinjan Den, a hankali nake tafiya ina tattare hijab dina, har Office ɗinta. Lokacin da muka isa ni daya na shiga office din, manyan mutane ne a cikin office din idanuwansu ya dawo kaina,kunya kamar na nitse a kasa, "Shigo ki zauna!" Aka ce min, haka na samu wuri na zauna ina zare idanu. "Zahra Abubakar." Gyada kai nayi, kafin suka cigaba da tattaunawar su, "Za'a a tura ki kamfanin Ba'are, kuma dama muna neman kwararru akan kasuwanci da kuma tattalin arziki, shin wacce gudummawar zaki bawa kamfanonin mu." Zufa ce ta karyo min muryata na rawa na ce musu, "Zan yi iya kokarina domin na bada iya gudummawar da zan iya, wannan shine kawai abin da zance." "Bakya da wani fata ne ga cigaban Kamfanin?" Murmushi nayi sannan nace musu, "Fatana zai tsaya ne akan abinda ya kai ni, na gama lafiya na dawo makaranta lafiya" Kallon juna suka yi kafin suka ce min. "Kafin yau kin tab'a aiki da wani kamfani?" "A'a ban tab'a ba, wannan shi ne karon farko da zan fara." Shiru suka yi sannan suka ce min. "Idan har muka ga kwarewarki zamu dauke ki aikin dindindin." "Ina me farincikin jin haka, ni kuma xan yi iya kokarina akan aikin." "Allah ya bada sa'a." "Amin na gode!" Na fada ina mikewa, bakiɗaya sai naji babu wani shakka a raina, domin kuwa wani irin nauyi ne da aka sauke min nake ji, haka yasa na wuce aji. Fitowa ta na hadu da Kashim daya daga cikin abokan Abdullahi, kamar maye duk da ya gama makarantar amma ya mai da makarantar gidan Ubanshi, "Kizo ga Sauban can mota ta buge shi." Amadadin na wuce aji sai na tsinci kaina da faɗin. "Innalillahi'wa'inna'ilaihirraji'un, garin yaya yanzu na fita na barshi a aji fa." "Eh " yayi gaba ina bin shi a baya, abin mamaki mu da zamu bi cikin mutane sai gashi ya kusa ta cikin lungun makaranta, ganin haka yasa na juya tare da cewa. "Ba zan bi ka ba, idan ma turo ka aka yi." Na juya tare da tattara hijab dina zan zuba gudu. Saka min kafa aka yi, ban san yaushe yazo wurin ba. "Kin zata zaki shigo tarkona ki gudu ne? Bayan na gama tsara yadda zan kamaki, shine zaki gudu." Murmushin takaici nayi nace mishi. "Sam babu tsoron zaka min kome, domin ba zaka iya ba. Kana tsammanin kai har zaka razana ni na razana?" Mikewa nayi tare da cigaba da cewa. "Zan tafi kuma babu abinda zaka iya min, don ba xaka iya dakatar da ni ba. Abdullahi ba tsoronka yasa nake gudunka ba, ko daya ni bana gudun sharrinka. Tunda Allah ya kare ni daga ta'addancin da aka yi mana, bana jin akwai wanda ya isa ya min wani abu. Sannan izuwa yanzu na koyi tsayawa kaina." Takawa nayi gabanshi ina yar dariya na ce mishi. "Gata tayi maka yawa, jin dadi sun lullube ka. Bani amsar waɗannan tambayoyin nawa, ya zaka ji idan aka kashe mahaifinka akan idanunka? Ba ni amsar nan ya zuciyarka zata dauki ayiwa ahalinka fyade kana gani amma babu yadda ka iya?" Hawaye ne ya zubo min, na haɗiye kukana na ce mishi. "Ya zaka ji idan wad'anda ka yarda dasu, suka ci amanarka ya zaka yi? Duk wannan ciwon da aka jiwa zuciyata bai saka na juya da baya don tsoro ba, shine kai akan yar kudirin da bai wuce kayi minti ashirin kai minti biyar ma, kai ji mana gaya min a wannan lokacin da na dawo daga mutuwar ce zaka razana ni har na razana? Gaya min? ni da har mutuwa nayi na dawo don na cimma abin da nake bukata baka san yadda rayuwa take ba shi yasa idan kaci ka koshi, baka da burin da ya wuce ka wulakanta mata irina masu kima da daraja, bana faɗa kuma bana son faɗa,amma abinda kake so ka gani a idanuna har abada babu kuma ba zaka tab'a samu ba, domin gata da jin dadi sun saka kullum lissafinka na dabbobi ne, da kana lissafi irin na zakuna mace ba ta gabanka sai abin da kasa a gaba ,don haka b'ace min a gaba, duk ranar da ka samu amsar tambayoyina ka zo ni zan baka damar yin yadda kaso da ni.." daga haka na juya na barshi sake da baki, shi yasa aka ce ko wani mutum da fahimtar da yakewa kowa shi nashi fahimtar Mijinta ya watsar da ita, shi yasa zai maye gurbin shi duk yadda yaso ya b'ata mata lokaci da rayuwa, yanzu ya fahimci ashe bai san meye rayuwa karan kansa ba. Wauta da hauka yake domin da yasan darajar rayuwa ba zai tsaya bata lokaci haka ba, A hankali ya juya yana bin bayanta da idanu,shin me rayuwarshi ta amfanar mishi? Me gatan da ya ke da ita tayi mishi? Babu kodaya, a kodayaushe burinshi ya sami kintsatsiyar yarinyar ya lalata mata suna don basu cancanci shiga jami'a ba ko me? A rayuwarshi ko rashin kunya yaga mace take yi tsanarta yake domin yana ganin ta gama lalacewa babban burinshi ya lalata goben kamilalliyar mace, domin yasan dama wasunsu ba karatun ya kawo su ba, lalacewa ce ta kawo su makaranta. Da farko ganin Zahra ya kwadaitu da ita ne saboda wani irin dirin da take da shi, haka yasa shi matukar bukatar yayi nasara akanta. "Boss ko muyi mata daukar amarya ne?" "Kai duk maganar da tayi bai shiga jikinka ba ne?" Inji daya daga cikin abokan Abdullahi, "Ya ne?" "A 'a tunda yake wata ta tab'a mishi irin wannan maganar? Don haka yarinyar nan ta tuna min da abinda na rasa, ban san hakkin yan matan da muka lalata ba, kaga tafiya ta Allah na tuba." Haka ya tafi ya bar su, kafin kace me sauran biyun sun gudu sun bar Abdullahi a tsaye shi ɗaya kamar gunki. *Ni kan tunda na bar wurin, sai naji hawaye masu yawa suna zubo min,* nasan ba wayo na bane ko iyawata ba, kawai ikon Allah ne da buwayarshi. Aji na koma na dauki Jakata, na fita zuwa gida. Haka na wuni suku-suku. Sam na manta da batun zuwa aiki kamfani. • Niamey Cikin bala'i ta nufi cikin gidan Hajiya, tun daga bakin kofa take kwala mishi kira. "Alhajin Allah, Alhajin Allah,!!" Barci yake amma haka ya farka tare zuro kofar shi daga gado, ya gaji da fitinar Nana wallahi kamar ya gudu ya bar garin. "Alhajin Allah!" Ta kuma kwala mishi kira. "Nana Barka da zuwa " "Yawwa ba wurinki nazo ba" ta fadawa Hajiya tana baza hanci ita nan tazo wurin jikanta. Kasancewar yau Asabar yana hutun karshen mako, amma haka Hajiya Nana ta zo kawo mishi rigima. "Sa'adatu ina Alhajin Allah." "Yana dakin shi." "Au sai na roke ki ne zaki kira min shi?" Gyaran murya yayi daga bayanta. Washe baki tayi tana faɗin. "Dan arziki irin albarka, kun ga d'an da aka haifa tsiya tana barci, bata farka ba balle ta ganka. Alhajin Allah dan maliki me had'arin CFA, Hmmmm" ta kuma ce cikin sigar gulma da ya kawo ta. Zama yayi yana fuskarta ta tare da hamma yana mika. "Assalamu alaikum!" Muryar Aryan da Zaytoonah ya ratsa falon, juyawa tayi ta wani turbune fuska irin bata yi maraba da zuwan su ba. "Alhajin Allah, magana ce ta kawo ni. A tow ni dai tunda na ziyarci garin Manzon Allah Sallallahu alaihi Wasallama, na dawo rakiyar munafukai da yan tsugudidi, sannan nayi alkawarin agaban Uban fatsima ba zan kara cin amanarka ba, tunda dai Umaran kai ne ka biya min ko?" Gyada kai yayi yana kallon Zaytoonah da take narke mishi, salon fitina kala kala, Zaytoonah ta sani, duk da surutun da ake na cewa suna soyayya bai tab'a cewa kome ba, amma yana damuwa da ita, domin bai da abokiya na kusa kamarta, a lokacin zamanshi a kamaru, ita ce abokiyar hirarshi. "Hamma!" Bude shanyayyun idanunshi yayi akanta domin yadda take mishin nan, baya ya iya daukar abin, tausayin ya kasa koyawa kanshi sonta yake ji. "Ke bana son karuwanci, kin zo kin wani min bake-bake ke gaki nan yar bala'i. Wallahi gaban kika taras,ke har kin isa ki saka min jika a gaba? Haka kawai ban da karuwanci kin wani zo kina wani hamma a'a gatari ne, da ke da munafikin da yake zugaki wallahi sai na sha dammara mu doku. Kunji min munafukar yarinya wani hammmmma, a'a gatari ne Sa'a zo ki dauke min wannan me shigen fatalwar a gaba, nazo ganawa da jikana kin wani fito sai kace an daurawa cokali zani, wani hamma." "Gaskiya Nana baki kyautawa." "Dalla can ka rufe min baki, ka wani zo da dogon wuya kamar autar amale, wallahi ahir dinka Ariyan na gaya maka ka fita idanuna domin nasan munafurcin da yake cin ka, algungumi da kai kamar tukunyar mayu." Zuba tagumi Majid yayi yana kallon Nana tana faɗa akanshi. "Ina jinki Nana." "Raina ma ya b'aci duk na manta abin da nazo gaya maka, haba don Allah ayi duk gidan sa'a ba mutane na gari sai kai, duk mutanen banza aka haɗa, alawadan naka ya lalace." "Hmm! Muje na rakaki." "A'a zan tafi da kafata." "Tow muje na saya miki nama mana Nanata." Washe baki tayi tana faɗin, "ke dai Sa'a kin iya farar haihuwa, kin ga d'a nagari, rabona da naci Nama tun bayan mutuwar Mamman." (🤣😹😂🥲😭 Nana bata tsoron ilahi) "Tun mutuwar Abba rabonki da nama kika ce fa?" Inji Amaan da ya shigo gidan, "Eh karya nayi Alhajin Allah?" Share ta yayi ya wuce dakin shi ya dauko key, "Nana kina jin tsoron Allah a cikin lamarinki, ban da tada husuma wai rabonta da cin nama tun mutuwar Abba." Ai kuwa Nana tayi caraf ta fasa ihu, tare da zama a wurin dirshan tana kuka. Tsaki Majid yayi, ya lura sam idan akwai waɗanda suka fi Nana fitina Aryan da Amaan ne, "Wai meye haka ne Aryan, Amaan kai da kake babu." Inji Hajiya, "Hajiya kyale wannan tsohuwar bata da aiki sai fitina, wallahi duk ta saka Abdul a gaba sai kace danta, tayi kukan jini mana." Saukowar Majid ne yasa ta sake karkace kai tana kuka. "Tashi muje Nanata." Mikewa tayi tana faɗin. "Kaji abinda suke gaya min.," "Allah ya shirya su." Ya faɗa suka fita, yawo yayi ta yi da ita tana bashi labarin gulmar shi da aka yi a dakin Hajiya Rabi, da kuma wani abin da bata fahimta ba, shine ta ce mishi. "Mun gama da daya shima Ubanta mun hana shi magana." "Inji waye Nanata?" "Hmmm! Inji Balaraba yar gidan Rabi. Kasan bin malamai take ko boka ya ganta ya barta anan ta hadu da wanda yasa mijinta ya sake ta shima ya aure ta,a tow mutum idan ranshi mugun nufi ne ai ya gani akwaryar shi. Kai dai a bar kaza cikin gashinta, domin da tarhona tana magana da ta gaya maka, tsinanniyar yarinyar nan ashe ita ta kai Tani wurin bokan da ya shiga tsakanin Sa'adatu da Mamman. Bayan dukar Sa'adatun da suke yi lokacin da mahaifinka ya aure ta, nasan nayi laifi amma wallahi na tuba." Ta fada tana kuka bayan ta cika nama a bakinta, jikinshi tsuma yake yi ta ce mishi. "Sannan naji suna cewa ai tunda kwan ya fashe Amaan ya samu lafiya babu abin da zai iya cutar da shi. Kwan me suke nufi?" "Nana ina zan sani?" "Na gode sosai Nana!" Daga nan ya wuce da ita, gida suna isa ya kira Sheikh Aliyu Wodabbe a waya. Bayan sun gaisa ya gaya mishi maganar da yaji a bakin Nana. Murmushi Dattijon yayi sannan ya ce mishi. "Kada ka damu kamar yadda muka fara, a hankali kome zai fito maka." "Baffayo Hajiya gani take kamar da gayya nake." Dariya Dattijon yayi sannan ya ce mishi. "Lokaci na zuwa ai, kada ka damu zan muku aike insha Allah kai da yan uwanka." "Na gode sosai Allah ya kara lafiya da nisan kwana." "Amin Ya Allah, Ubangiji ya kawo maka sauki da mafita." Daga nan suka yi sallama, dama abin da yasa shi shiru kenan, amma akwai abin da yake son fahimta, waye suka hana shi magana? Akwai wani a cikin gidansu da aka hana shi magana ne? Tunanin shi ya gama yawo bai hango waye ba, amma tabbas tunda yaji yasan akwai magana. Haka ya tattara ya ajiye kome a gefe, sannan ya shiga harkar gabanshi. Amaan ya same shi da maganar zuwan dalibai uku da zasu yi aiki a kamfanin, bai tsaya ya saurare shi ba, sai dai wani abokin Amaan din da aka dora akan aikin me suna Dan larai. Dan larai dai dan daudu ne, tun ranar juma'a Amaan yake bin shi akan ya saka hannu ya ce shi dai ba zai ɗauke shi aiki ba, har ranar Monday da suka fito zasu aiki yake tuna mishi. "Dan larai dai zai zo don Allah ka ɗauke shi aiki." "Idan na dauke shi, Afiyyah kai zaka dauke ta." "Kai ni bana son fitina don Allah ka ɗauke su, yanzu baba Haladu ya ji cewa ina da hannu akan daukarta aiki sai naji magana." "Shi kenan, zan duba takardunsu sannan idan basu min aiki a cikin wata goma ba, zan Kore su." "Eh na yarda." Haka kuwa suka isa kamfanin suka shiga meeting, sannan aka tattauna akan ɗaukar ma'aikata akwai daliban tattalin arziki da zasu zo, wannan abin ya musu dadi domin tun koran wasu ma'aikatan ba a kuma dibar ma'aikata ba, sai wannan karon. • Tun ranar da nayiwa Abdullahi tass, ban kuma ganin shi ba, amma tabbas nasan zai dawo, sannan a gefe guda yadda ake kawo min maganar kamfanin BA'ARE GOLDEN EMPIRES, yasa jikina yayi sanyi domin Allah ya gani bana son tashin hankali, gashi ance bakiɗaya Yaran tsohuwar Chairwoman na kamfanin anan suke aiki. Wannan abin ya dame ni gashi saura kwanaki ne mu tafi. Ina ta tunanin idan zan tafi dole zan tafi da Amirah don ba zan iya zirga-zirga tsakanin Niamey da Marad'i ba. Wannan abin ya sani jin wani irin damuwa, domin bana son nisa da gida kuma tow ya zanyi. Haka muka cigaba da karatu har aka yi jarabawa, daga wannan hutun ba zamu kara dawowa ba, sai bayan wata shida idan muka dawo zamu dauki wata tara kafin mu gama makarantar gaba daya.. • Algers A hankali ya fito rike da sandarshi, yana takawa a hankali sanye yake da kaya irin na sarakai. Kyakkyawar balaraben Algeria. "Sultan" murmushi yayi ya ce mishi. "Zuwa yanzu ta daina kuka don kada a cutar da ita ko?" "Sai dai kewa da kaɗaici yasa har yau taki yarda da kowa." "Na kusan bayyana a gareta, na kusan na mallaki abinda nake tunanin nawa ne." • "Majid ya kamata ka ajiye maganar lalurar nan ka fuskanci rayuwarka. Kayi auren ko za a dace." Murmushi yayi yana rike da Mug din Black tea,yana kurba. "Na kusan isa ga wacce take manne da duniyata, rayuwata da farincikina yana tare da na ta, na kusan isa gare ta, a da can baya ina jin kamar tana kara nisanta da ni, amma, a yanzu ina jin kamar duk bugun dakika kara kusantowa take gare ni...................... Tofah ! Da wa za'a yi ne? Dan sarki ko mai kudin ba'are😘 Kodayake jarumi Sajjid ma yana cikin yan gasar 💃💃💃💃💃💃🤣🤣 Anan book one ya kare sai Allah ya had'a mu a book 2 domin jin yadda za a kayya... Taku har kullum. RamlatManga Mai_Dambu. 300₦ 0016341139 unity bank zahra'u yahaya Ali Katin MTN 400 #Mai_Dambu ce BOOK TWO [5/29, 07:47] Hlm: BHB241 "Kana nufin matarka tana kusa kenan?" Murmushi yayi yana faɗin,a da can hasashe nake amma a yanzu na tabbatar da tana kusa dani, tana dab da ni sama da yadda nake jin tazarar sama da kasa." Murmushi ne me kayatarwa ya kwace a fuskar shi. "Amma wacece haka me sa'a?" Lumshe idanunshi yayi yana faɗin. "Kawai Imagining ne, amma babu wacce zata auri yar uwarta mace." Yana fadar haka ya mike kamar bashi ya gama murmushi ba, domin baki daya, sai ya tsume musamman da aka yi knocking kofar office din, Afiyyah ce sanye da wani irin suit riga da wando pink, bakiɗaya surarta a bayyane yaƙe. "Hammani ga report din da ka sani na maka."ta faɗa tana ajiyewa akan table din gabanshi. Dauke kai yayi yana wani haɗe fuska, domin mutum yana iya hango tsakankanin kirjinta, ajiyewa tayi cikin salo da jan hankali, Mahdi Abubakar Abzin yana lura da shi, murmushi yayi yana bin ta da wutsiyar idanu, har ta fita ya ce. "Ba'are yarinyar nan ta haɗu fa." "Ka je gare ta mana." Ya faɗa yana bude files din, kwankwasa kofar aka yi, "shigo!" Mahdi ya faɗa. A hankali ya zuro kafarshi da yake sanye da hill sheo na gucci, hannun shi sakale da jaka shima na gucci, fuskar shi ta sha fenti, gashin dokin nan har gadon baya. "Assalamu alaikum!" Ya faɗa yana kareraya kamar maciji. Kunshe dariya Mahdi yayi yana kallon ikon Allah. "Sannu sir ga report din da kace na kawo maka, kayi hakuri bana nan ne wancan satin." Ya faɗa yana ajiyewa. "Saurayi ya kake?" Washe baki Mahdi yayi ya ce . "Lafiya lau ya sunanka?" Tuni ya haɗe rai, ya ce mishi. "Sunana Sahiba." Gyaran murya Majid yayi da sauri ya fita kamar kugunshi zata karye,. Wato asalin ko Sahiba duk wanda ya san James brown wannan shahararren dan daudun nan. Gashi kamar one haka yaƙe. Amma don jaraba ya daurawa kanshi masifar daudanci. "Ba'are a ina ka samu 2sim?" Ya tambaye shi cikin dariya da tsokana. Banza Majid yayi mishi don baya kaunar abin da zai saka shi maganar dan daudun nan, "Gaye ko kana cikin ne da Sahiba?" "Idan na zage ka ba zaka ji haushi ba?" Dariya Mahdi ya saka mishi, irin na niman faɗa, "oh kodai shine bugun zuciyarka?" "Idan ban ci ubanka ba Allah ya min albarka " "Zan gayawa Hajiya, kayi budurwa saurayi budurwa.". "na rantse da Allah sai na ci ubanka." "Oho dai sai na gaya mata." Haka Mahdi yayita zolayar shi yana dariya. • Ranar talata na shigo garin Niamey, a gajiye likis domin ban san kan garin ba, kuma ba karya Niamey babban alkarya ce, sannan naji daɗin yadda Maman Barakatu suka bani shawarar na fara zuwa naga yanayin wurin kafin na zo da Amirah ba don haka ba,da na shiga uku, don koda na isa sai da nayi ta yawo, kafin na isa babban office dinsu, ina isa aka ce sun tashi haka yasa dole na nemi masauki, na kwana, washegari da safe na isa kamfanin. Sanye nake da doguwar Jallabiya, sai mayafin da na rufe jikina ruf, ta cikin mayafin na saka hula me kyau da ta dauke sumar kai na, ina tsaye akai ta budewa ma'aikatan kamfanin get suna shigowa ni kaina nayi mamakin uban sammakon da nayi, amma kuma ai ban yi a banza ba, tunda ina zaune wurin karfe tara aka kira ni. A bakin kofar shiga naga an rubuta CEO Aryan Mamman Ba'are. Buga kofar nayi, "shigo!" Aka ce min. A hankali na tura kofar bakina yana me dauke da sallama. "Wa'alaikimun Salam." Ya amsa min, cikin sakin fuska. Kujera ya nuna min, na zauna. "Ina kwana yallabai?" "Lafiya!" Ya ce min hankalinshi yana kan aikin gabansa. "Daga Jami'ar marad'i ko?" "Eh" ya d'ago kai yana me kallona, yadda nake takure. "Tow gashi nan, kije office din AG na maaikantan zai had'aki da Admin, ban sani ba ko zaki bukaci ganin Store amma ga dai takardu nan ki mika musu." "Na gode sosai." Na mika mishi nawa takardun da na kawo, na mike zan fita ya ce min. "Fadime Abubakar?" "A'a Fatima Abubakar dai." Shiru yayi domin dai abin da yake gani a gaban computer din shi daban, wanda ta faɗa daban. "Maybe an samu matsala ne daga makarantarku nake tunani." "Hmm!" Haka na fito na nufi waje,. ina duba takardun, a ina aka samu matsala. A hankali nake dubawa, ji nayi an wani bangaje ni sai da takardun suka watse a ƙasa. Shima waya yake wayar ta fadi can, "Kayi hakuri don Allah, kayi hakuri don Allah." Haka nayi ta nanatawa, ban ma san waye ba, amma kuma kaina kamar zai tab'a kasa, haka na dauko wayar na mika mishi, na kwashe takardun na mike, yana tsaye har zuwa lokacin bai tafi ba, a hankali na juya kaina a sunkuye na ce mishi. "Don Allah kayi hakuri, ni bakuwa ce a cikin maaikantan nan." Juyawa yayi ya tafi bai jira na gama mishi bayani ba, wucewa nayi na nufi inda aka tura ni, amma na jima ina yawo kafin na hadu da wani mutumin ya kai ni office din Admin. "Assalamu alaikum!" Bai ji ni ba ne, ko wani abu yake ban sani ba, sake shiga cikin office din nayi can ciki naji ana magana a hankali. "Hajiya na gaya miki, babu wani motsi sai dai idan da wani abu zan miki magana, amma a yanzu babu motsin da Yara ukun suka yi." Ja da baya nayi kamar xan fita na ji ya ce. "Kada ki manta wutan da kika umarce ni na saka, har yau mayen sojan nan yana bincike a kai, don ma nayi ƙoƙarin kauda hankalinshi a kai." Shiru yayi ya ce mata. "Shi kenan kawai ki saka Aljan yayi kome mana, ai nasan zai so yin haka." Ya faɗa yana kara kasa da murya, tow meye nawa na sauraron abin da ake, a hankali na fito na tsaya a bakin kofar. Ina tsaye a wurin ban shiga ba, kunnena basu daina amsa kuwa da abin da ya faɗa na karshe ba, sai na tsinci tsoro a cikin kalaman shi, kamar zan juya na koma sai na fasa, ina tsaye haka mutane suka yi ta wucewa, sai na je kamar zan buga kofar sai na fasa, kada yayi tsammanin na ji yo sirrinshi, haka yasa na kasa kome, na kashe minti ashirin a tsaye, "Baki shiga ba ne?" Naji Muryar mutumin da ya turo ni, jikina ne ya dauki rawa kamar wacce ta aikata wani, "Lafiya?" Ya tambaye ni, "a'a babu kome, kawai zan tafi ne nayi sallama ba a amsa ba." Na fada zan juya, "dawo mu shiga i think yana ciki." Ya wuce gaba bai gama jin me zance ba, ya shiga office din yana d'aga murya. "Hamza!" Ya kwalla mishi kira, "Na'am yallabai Aryan" ya fito yana sharce zufan da yake ta karyo mishi. "Ya na turo bakuwa a bata, key din estate tayi sallama baka amsa ba?" "Kayi hakuri waya nake, daga gida gyatumata ba lafiya, ban ji ba kuma." Ya juya yana kallona, cikin wani irin murdewar ciki na ce mishi da sauri. "Nayi sallama da buga kofa baka amsa ba, amma ban shigo ba." Wani zuba min idanu yayi, sai da CEO ya ce mishi. "Ka amshi takardunta daga nan ka kaita Office din Amaan, za tasaka hannu." Ya faɗa yana me fita, ji nayi kamar ya barni cikin mutuwa, "kin kai minti nawa a wajen?" "Ban wuce minti biyar ba." Sauke ajiyar zuciya yayi cikin fara'a ya ce min. "Kin san mutumin da yake da abubuwa dayawa dole ya zama me yawan sabgogi." "Eh haka ne!" Na fada, ina kallon kasa domin wani irin tsoro yake bani, haka ya gama ya mika min key nasa hannu zan amsa ya mai da hannunshi. "Kina da kyau." Ji nayi kamar zan mutu, mika min key din yayi yana faɗin. "Muje ko." Haka ya sako ni a gaba, har Office din da aka ce ya kawo ni, ina shiga na samu office din da mutane, "Hamza bakuwa muka yi?" Ya tambaye shi, cikin kulawa. "Eh yallabai yanzu mai gida Aryan ya turo min ita." Mikewa yayi cikin kulawa da fara'a kamar wanda ya tab'a gani na, ya wuce da ni cikin office din shi, ya ce min. "Zauna ina zuwa." Ya ajiye min ruwa da lemo, ya fito ya gama.musu bayani, sannan ya shigo office din. Wuce ni yayi wurin zaman shi, yana kallon File dina da yake laptop din shi. "Fatimah Abubakar?" Ya kira sunana. "Na'am!" Na mike, girgixa kai yayi ya ce. "A'a kawai na kira sunan ne, daga marad'i ko?" "Eh!" "Anani fulfube?" "Na'am" na ce mishi. Dariya yayi yana faɗin. "Kin yi magana da Fulani ne, kuma ga shi abin da aka rubuta a personal information ɗinki kenan." Daga haka ya gama cike-ciken shi ya ce min. " Zamu yi aiki dake a bangaren tattalin arzikin kamfanin nan, idan kina da wani abu na cigaba kiyi kokarin fito min da shi mu gina kamfanin nan." "In sha Allah." Daga haka na mike ya ce min. "Ki dauki abin shan ki mana" "A'a na gode." Dauka yayi ya saka min a cikin wani leda, ya rako ni har waje, ƙara wayarshi tayi ya ce. "Yawwa Abdul na turo maka sako, sannan ga ɗaliban nan." "Allah ya yaye maka, shi kenan." Ya faɗa yana kashe wayar, wani babban hall ya tura ni, inda da alama anan ake aikin duk wani data information na kamfanin, sai ɓangaren masu zanen zinari, abubuwan dai gasu nan. A hankali muka wuce wannan hall din, wani babban falo muka shiga, su kuma asalin aikinsu akan tattalin arzikin kamfanin ne, wata kujera ya nuna min. " Anan zaki zauna." "Na gode sosai!" "Idan kina bukatar wani abu, ki min magana." Haka ya juya ya fita, sannan wani abu da na fahimta ana mugun ganin girmansa,ko ina muka wuce girmama shi ake. "Kass!" Naji karar chew gum. Juyawa nayi naga ashe dan daudu ne. Yadda na kalle shi sau daya na cigaba da aikina. "Ya da kallona ko idon ya miki yawa ne, kwakulo daya mu raba, ana bikin dan zakara biri abokin ango su mage ne yan mata." Ya faɗa yana murguda baki, *mamaki baya karewa* Na fada a raina domin na fahimci wai habaici yake min. Ban kuma kallon shi ba, don na gano bai da mutunci ko kaɗan. Karfe biyu naga ana ta fita, ashe wurin cin abinci suka nufa, ni ban sani ba na zauna a office din, sai ga mutumin da ya kawo ni office din. "Baki fito ba, da fatan lafiya dai?" Murmushi nayi ina faɗin. "Lafiya lau. Ina son nayi sallah kafin naci abinci ne." "Ko na saka a kawo miki ne?" "A'a yallabai zan je da kaina." "Tow shi kenan, muje na kai ki masallaci." "Tow!" Na rufe computer din, na mike tare da bin bayanshi. Sai kallonmu ake, ni dai haka kawai Allah ya haɗa jini na da nashi, nakuma ji ina son shi a matsayin dan uwana. Har can masallacin ya raka ni, shima ya wuce bangaren maza. Bayan na idar shima ya fito, amsar jakar bayana yayi ya yana faɗin. "Kawo na rike miki kanwata." "Tow " na mika mishi, wurin abinci muka wuce, wasu naci suka fito sallah, a lokacin an watse, zama nayi, na yi shiru, masu tambayar me za'a zuba maka suka zo, na duba abinda xan iya ci,na faɗa shi kuwa ganye ne sai tea da short cake. "Don Allah ko zaka taimaka min da wayarka." Mika min yayi na amsa, "Ba'are shine password din!" Ina sakawa ya nuna min ba daidai ba, tura mishi nayi na ce mishi. "Yaki budewa." Amsa yayi yana faɗin. "Kina tsoron kada ki shiga wani wuri ne?" Bude min yayi ya mika min, ganin xan bawa kaina wahala na karanto mishi number, amsa yayi ya saka min sannan ya kira yana me mika min. "Assalamu alaikum! Baraka ina Mamanku?" "Laaaa Tente kece?" Murmushi nayi nace mata, "Eh!" "Mama ga tente." Mikawa Maman wayar tayi muka gaisa, sannan ta ce min."kin isa lafiya dai ko? Ya aikin da inda kika je?" "Alhamdulillahi, wurin zama aka bani yanzu zan tafi domin nags yanayin wurin, idan yaso wani sati sai nazo na dauke ta." "Allah sarki, muna kewarki." "Nima haka Ina Amirah sugrah?" "Gata nan!" "My heart kina lafiya!" Ba hmm balle humm, haka take ba baki sai wayon azaba, haka na gama hira da ita, na ma manta wayar aro ce, bai ce min kome ba sai da na gama don kaina na bashi wayar a kunya ce. "Kayi hakuri na cinye maka kati ko?" "Idan baki gama.wayar ba, ki cigaba kanwata ce ke ai." "Na gode sosai na gama" "Tow maza ki ci abinci."cikin farin cikin waya da Amirah na ce na koshi ma, mikewa yayi ya amsa min cake da donuts, meatpie da samosa. Sai kayan sanyi a cikin jakar kamfanin. "Muje na saka a kai ki estate dinku, ki gyara gidan." "Na gode sai dawainiyya kake dani.". "Ni yayanki ne babu bukatar min godiya " Haka muka fito ya kai ni na dauki kome na, sannan da zamu tafi ya ce min. "Kina da waya kuwa?" "Eh ina da shi amma ta b'aci ne." "Account fa?" "Ina da shi, amma ban rike number ba." "Allah ya kyauta, ki nemo saboda kudin da kamfani zata na biyanki." "Tow;" na fada muka tafi gidan da mutumin. .... "Sannu uban yan kwashe- kwashe." "Yawwa uban yan mugun hali ba banza Nana take cin mutuncinka ba.". "Amma me yasa ka wani biye mata, sai gulmar ku ake har a whatsp." Dariya yayi yana zama tare da faɗin. "kawai naji ina son na kula da ita ne, kamar yadda nake kula Anisah da Jamilah da Zaytoonah. Yarinyar tana da nutsuwa kaga yadda take nan, wallahi ko waya babu a hannunta." "Waye ya damu?" Inji Aryan, "Ni na damu, domin daga ganin tana da Yarta da ba sa tare." "Kana nufin yarinyar nan tana da Y'a?" "Tow meye a ciki?" "Babu amma naga." "Ka duba da kyau ba yarinyar ba ce fa, ka kara kallonta kawai jikin ne dai irin model." "Hmm ba sa'ide har ka gano haka." "Don ma a kanwa na dauke ta, da a ce a macen aure na dauke ta, kaf -kaf zan yi da ita domin kamfanin nan cike yake da tuzurgwauro." "Amma dai ba da Hammayo kake ba?" "Kai dai ka sani, wallahi don ban faɗa ba." "Ka fadi gaskiya ma idan Hammayo ya zo." "Ko Gatari ba" Ya faɗa yana dariya, a haka suka wuce office dinsu. ..... Gidan da aka kai ni apartment ne babban, sannan kowane da daki biyu da banɗaki da kitchen, sai yar baranda a bayan apartment din, domin gidan sama ne mai dauke da hawa dari da wani abu. Akwai gado da kome a cikin gidan...... 300₦ 0016341139 unity bank zahra'u yahaya Ali Katin MTN 400 or +234 703 513 3148 #Mai_Dambu ce [5/29, 07:47] Hlm: BHB242 A hankali nayi ta bin gidan da kallo, yo wannan idan mutum bai wasa ba sai ya manta da waye shi ko me ya kawo shi, haka yasa na gyara inda xan zauna daki daya da falon. Ina ga ko don suna yawan saukar da baki ne yasa oho,amma gidan kome ba laifi. Ina gama gyara cikin dakin aka kwankwasa min kofa. Fitowa nayi daidai ana kiran sallar la'asar, bude kofar nayi ina kallon wasu Mutane su uku dauke da kayan abinci. "Kanwata ni na kawo miki don nasan dole zaki bukaci abinci." Wani lokaci haka kawai sai Allah ya haɗa ka da masu taimakonka. "Sannunku!" Na fada ina basu hanya, haka suka shigo min da kayan Abincin, duk wani abinda zan buƙata. "Ki saki jikinki, kamar kina gida, nan ma kamar gida ne " a karo na biyu da aka mu'amalance ni a matsayina na yar adam. "Allah ya biya maka bukatarka na alkhairi." "Amin kanwata." Mutanen na gama shigar da kayan suka juya tare da barin dakin, "tow zan tafi, bakya bukatar da wani abu ne?" Girgixa mishi kai nayi, ina faɗin."Alhamdulillahi kome ya yi Allah ya saka da alkhairi." "Tow sai an jima." Yana fita na rufe kofar dakina, na yi alola da sallah. Ina idarwa na kwanta ina jin yunwa tashi nayi, naga har da takeaway sai robar fura da nono. A hankali na fara sha ina godiya ga Allah da ya haɗa ni da mutumin kirki,haka na sha na koshi naci jollop din shinkafar ciki wanda yaji hanta da nama, daya takeaway din rabin kaza. Sai ga hawaye, ai dole ranar Asabar na tafi na tawo da Amirah. Ba zan iya cin wannan abin arzikin ni daya ba, amma kuma ya xanyi da ita? Dole na duba koda daycare ne na sakata. Da dare ina kwance aka buga min kofa, daga ciki na ce "waye ?" "In ji Yallabai Amaan ya ce a kawo miki abinci." Bude kofar nayi na amshi abincin, na koma na rufe. Zama nayi tuwon shinkafa miyar kuka wanda tunda nake ban tab'a ganin yadda aka raya miya haka ba, bayan kamshin daddawa. Nama aka dake ta a miyar. Sai gudar tsokar nama da manshanun nguru, wanda kana ci kana jin kamshinsa. Yawuna ne ya tsinke, na zauna na saka malmalan tuwo biyu, na fara ci man shanu nan har bayan hannuna. Ina ci ina santi. "Allah ka sakawa Ya Amaan da alkhairi." Wato sai gani na tashi malmalan nan biyu, na kuma dinfari na uku. Daukar daya daga cikin goran da aka saka a cikin basket din nayi na bude tsumi ne, da ya sha kayan kamshin wanda shuwa suke ce mishi ardif, wasu suke ce mishi pito. Yaji kayan kamshi, kamar haka domin kana sha kana jin kamshinsu. 1. Pineapple 2. Cloves 3. Mint leaf 4. Ginger 5. Tamarinds flavor 6. Tamarinds 7. Cinnamon stick ( optional), tass na shanye har da neman kari, ban yi kasa a gwiwa ba na shanye daya goran wanda shima zobo ne, kai jama'a wasu matan Allah ya halicce su ne domin sarrafa maiwa zuwa dawa. Ban daki na shiga nayi brush na dawo na saka littafan da yake gabana, ina yi ina hamma man shanu ya fara ratsa ni, ban yi aune ba sai barci, a falon na kwana. Washi gari. Kitchen Amaan ya nufa bayan ya dawo daga masallaci, "Hajiya idan zaki hada abin karyawa a hada har da na bakuwa kamar na jiya." "Yaushe ka zama Uban Teresa?" Juyawa yayi yana kallon Majid da yayi maganar, "Ba haka ba ne, kawai ina jin yarinya ne a raina." "Idan kana sonta sai ayi wani abu?" "A'a Hajiya ba soyayya ba ce, fiyye da soyayya nake mata, bana jinta don na aure ta. Akwai wani abu a tattare da ita idan ka saka idanu akanta, zaka hango maraici da kaɗaici. Sannan rayuwata nayi kuskure dayawa ina jin kamar idan na kyautatta mata Allah zai kankare min wasu daga cikin zunubai na. Rayuwar duniyar ma guda nawa ce?" Wannan kalmar da ya rufe maganar shi da ita yasa jikin Hajiya mutuwa. "Wani irin kalamai ne haka Aliyu?" "Hajiya kina tsoron kada na mutu ne?" "Ko ba mutuwa ba, da farar safe zaka dakushewa Alhajin Allah sa'arshi. Kaga Amaan ka fita idanuna na rufe, ban da zancen banza dan kaniyarka yaushe ka isa mutuwar? Ko ni nan da saura na balle kai, mara mutunci na sake jin ka ambaci mutuwa, sai na zabga maka mari kada ka ganka kato kayi tsammanin zan kyale ka, wallahi sai na ci damara muyi dambe." Inji Nana ta mike tana cin dammara, "kuma sai kiyi dambe da shi?" Inji Aryan da ya shigo, domin Majid ya bar musu falon. "Dan banza me mugun nufi, ban da rashin sanin ciwon kai ana zaune kalau, zaka kira min mugun nufi, mutuwa ban da dole waye zai so ta, idan ma don ni kake kiranta tow ahir dinka futsararen banza." "Allah ya baƙi lafiya, da nisan kwana tunda bakya kaunar mutuwa." "Sa'a ki jawa d'anki kunne wallahi ya fita idanuna ko, hukuma ta shiga tsakanina da shi." "Nana me yayi zafi da za a saka hukuma." "Nanata tawo ki kyale su don Allah." Inji Majid da yake sama a tsaye. "Yawwa Alhajin Allah, fari me farar aniya akawali kak'i musayar, Bijimin sa me bawa raguna da awakai tsoro, gaishe ka Namijin duniya daga kanka kallo ya ƙare." Duk da Hajiya wannan bai dame ta ba, amma yau jin kirarin Nana sai ya shafe mata duk wani kunci da damuwa da take ji akan Majid, kirarin ya dace dashi, sau dayawa tana son ace tayi mishi kirarin amma yau da Nana ta yi mishi sai ta ji kamar fansarta tayi da wani abu me daraja, wani abun sai ranar da ta ganshi da farar shaddar aure, ranar bata san me zata yi ba, bata san wani farincikin zata shiga ba, duk ranar da Majid yayi aure. "Nana dole yau na sayo miki kilishi, da wannan uban kirarin da kika yiwa Zakin Hajiya." Washe baki tayi tana faɗin. "Yawwa Aliyu Haidar, na san zaka saya ai basu boloko ba." Ta fada tana hararar Aryan. "Oho dai shima don ki yabe shi ne, amma ai ba don Allah zai saya miki ba. Idan kin dage na saya miki zan saya miki amma da sharadi?" "Sharadin ya wuce ka saka min guba na mutu." Ta fada tana hararar shi, tare da haurawa sama, har falon Majid ta shiga. Tunda take bata taɓa sanin Majid yana da matsalar zama cikin duhu ba, sai yau domin falon shi kawai ta shiga ta ga ko ina duhu. "Alhajin Allah!" Kunna hasken falon yayi, ajiyar zuciya ta sauke tana fadin ya kome na falonka me duhu?" Murmushi yayi ya ce mata. "Ba kome!" Shiru yayi yana me bude mata wata jakar bagco, kunshin takarda ne kato, a hankali ya warware kafin sai ga jarida da maiko-maiko. Kilishi ne sai kamshi yaƙe. "Naki ne wannan Hajiya." "Anya Alhajin Allah, baka sangarta ni ba?" "Idan ban sangarta ki ba, waye zan sangarta." Ya tura mata kilishin, sauka tayi daga kujerar ta zauna a kasa,ta fara ɓantara tana ci hankalinta a kwance, don ba karamin dadi take ji ba, yadda Abdul Majid ya damu da ita, shi kuwa yana yin haka ne don nasihar Hajiya akanshi, kullum bashi hakuri take da nuna mishi muhimmancin hakurin da suka yi yau ga Nana ko Yaranta bata kulawa kamarshi. Sannan shi daya ne yake iya juyata cikin ruwan sanyi a zauna lafiya. "Alhajin Allah, akwai wani abu ne a tsakaninka da Afiyyah?" "A'a!" Ya ce mata. "Yo ai nasan za ayi haka, da dai Ariyan ta ce zan ce ai haka ne don idanunshi a tsatsaye suke kamar na bazawari don ma baya saka kwalli." Ta fada tana wani haɗe rai. "Assalamu alaikum!" Turus Zaytoonah tayi don bata zata Nana tana sama ba. "Zaytoon ya dai?" "Umma ce ta ce na kawo maka." "Mtsew! Asaran fage fallin daki, mace bata isa mace ba, sai naji ance namiji yake bibiyarta." "Nanata meye haka?" Yau kan Nana ta cika Zaytoonah cikin fushi ta ce mata. "Idan kin so akan Hammayo ki aure shi ki huta da min habaicin da kike. Ban da rashin girma kina da jikokin amma kike saka min ido da magana." "Zaytoon!" Ya daka mata tsawa, "kina da hankali kuwa?" "Bani da shi akanka ba ni da shi, ban san inda yake ba. Tun zuwana garin nan matar nan take gaya min magana ban kulata ba, dadin abin kai ne nace ina so ba wani ba, ita da ta gagara tsayawa akan jikokinta suka lalace shi ne zata bude baki tana gaya min magana? Meye ne ban sani ba, sai yanzu da ka zama na mora zata Ishe ni da kinibibi. Indai don kin ga ina gidan jikokin ki ne, kike gaya min magana Nana zan bar gidan kuma in sha Allah sai Allah ya saka min." Ta juya tare da barin falon, har ta isa waje ta tsaya cikin kuka ta ce mata. "Ki gane duk abinda kike yi ba burge kowa kike ba, suna biye miki ne saboda sun tsotsi tarbiyya da nagarta ne, sannan ki gaya min a addinin musulunci a ina aka ce mace idan ta ga namiji tana so kada ta faɗa mishi. Ki saka idanu akan Afiyyah da take gabanki ba ni...." "Get out!" Ya daka mata tsawar da har akasa ana jin su. Kallon shi tayi cikin fushi ta ce mishi. "Ba iya falonka ba, hatta gidanku zan bar muku. Ku zauna da masoyanku." Ta juya da gudu ta sauka daga sama, zuwa falon kasa bata saurari abin da Amaan da Aryan suke fada ba. Ta wuce dakinta, ta shiga had'a kayanta duk abinda suke yi Hajiya tana ji bata ce uffan ba. Asalima bata son shiga rigimar da ta hada har da Nana ne. "Nana kin ga abin da yasa nace miki bana son kina gayawa Zaytoonah magana ko? " Ya faɗa ranshi a b'ace. Ita kanta Nana jikinta yayi sanyi, domin bata taɓa kawowa yarinyar zata mata rashin kunya haka ba, sai gashi ta silleta tass sannan ta fita wani irin kunya ne ya kama Nana ta mike dakyar da sandarta ta nufi waje. A kasa ta taraddasu Aryan suna hiranru. Kamar munafuka haka ta bar gidan. Babu wanda ya damu da hakan, tana fita sai ga Zaytoonah da akwatinta dauke da goyon Yarta. "Ke ina zaki?" Inji Aryan, "Zan koma Kamaru ne akwai wani abu ne?" Ta fada a fusace. Saukowa yayi yana, mika mata hannu tayi banza da shi, bayanta ya je ya amshi goyan Mimi. "Ki tafi gaba da Kamaru if you want, babu me dakatar dake kin ji ko." Jan akwatin tayi kiiiiiii, "da dai kinyi hakuri Nana ba fasa halinta zata yi ba, kamar yadda take da baki kema sai ki koyawa kanki kwatar kanki ba ta rashin kunya ba, ban ji dadin yadda kika gaya mata magana ba, ko babu kome kakarmu ce. Idan da akwai wanda yafi wahala da Nana Majid ne, kuma har yau shi yake ɗaukar wahalarta da fitinarta, kin ga ko Yaranta ta damu da su?" "Amaan kyaleta don Allah ta tafi." Inji Aryan da yake cike da takaici. "Matar nan ba don ina da hakuri ba, da babu dalilin da zai saka na kyaleta cewa tayi duk abinda ya faru ni ne nake kokarin kashe yan uwana, waye zai ji wannan abin bai zarge ni ba, gara ki hakura idan tayi miki babu rashin." Make kanshi Hajiya tayi, ta bi na Amaan ta make. Ita kan Mimi ta ga Babanta sai ta kwanta luff a kirjinshi. "Ku da zaku mata fadar rashin kunyar da tayi, shine kuke gaya mata yadda zata ji da Nana?" "Kyale su Hajiya na!" Inji Majid yana amsar akwatinta ya wuce dakinta da shi. "Ki bishi ku daidai ta kanku." Cikin kuka da bori ta zauna a falon tana kuka, can ta mike ta nufi dakin. "Wai da Yaji zaki yi?" Share shi tayi zata wuce ya ce mata. "Nana kakata, ke kanwata ce ina son ki fahimci wani abu, ni Abdul Majid ban ajiye ki don ina sonki ba, ke kanwata ce idan kika samu wanda ya fini ki aure shi." A gigice ta juya tana kallonshi....... 300₦ 0016341139 unity bank zahra'u yahaya Ali Katin MTN 400 +2347035133148 #Mai_Dambu ce [5/29, 07:47] Hlm: BHB243 Kura mishi idanu tayi kuka ya kwace mata, tana kallonshi. "Hammayo da kaunarka na taso, na kasa zama da Baban Mimi ne don ina kaunarka. " "Kiyi hakuri!" Ya furta a hankali, sannan ya ajiye mata Mimi. "Tun fil azal babu wannan batun a raina, amatsayin kanwata na dauke ki idan nace zan yi shiru kamar yaudararki nayi, Ni bana cikin jerin mazajen da zasu yaudari mace, sannan idan na yaudareki meye ribata? Ban tab'a kaunarki da aure ba, soyayyar zumunci da kasancewarki kanwata kuma abokiyata nake yi maki." "Hamma Abdul ina sonka." Zauna da ita yayi tare da durkusawa a gabanta. "Ni ban ce bana sonki ba, kaunar aure ne bana yi miki, ni na gaya miki gaskiya tsakanina da Ubangijin da ya halicce ni." "Hammayo." "Shiiii! Na gaya miki gaskiya." Kura mishi idanu tayi tana faɗin. "Ina sonka." Miƙewa yayi ya bar dakin. "Kiyi duk yadda kike so, amma Allah ya gani my heart belong to someone." Ya faɗa mata cikin kwarin gwiwa da yarda da kanshi. Eh gaskiya ne zuciyarshi mallakar wata ce, ba ita ba. A da yayi kokarin tsayawa akan lalurar shi, ba tare da ya yarda cewa zuciyarshi wata yake jira ba, amma a shekara daya zuwa biyu ya yarda zuciyarshi wata take jira, sannan bai taɓa kawowa a ranshi yana jiran wata ba ce, sai wannan lokacin da duk yadda ya hadu da mata a wurin mu'amalar kasuwanci, da sauransu. Amma jiya yaji wani irin al'amari me karfin gaske. Wucewa yayi ita kuma Zaytoonah ta fito da gudu zuwa wurin Hajiya. Tana kuka tare da rike hannunta. "Ummati wai Hammayo yana da wacce yake so, Ummati ya ce min zuciyarshi mallakar wata mace ce. Ummati saboda shi nake raye, don Allah Ummati ni ko a Kwarkwarah ne ya aure ni." Ta fada tana zubewa a kasa, tare da rusa kuka kamar ranta zai fita. "Tow ki mutu kawai muci gumba idan yaso sai ki zama fatalwa ki addabi rayuwar yarinyar da yake so. Wai ma tsaya Majid ne ya gaya miki yana son wata?" Ya faɗa yana bushewa da dariya, "Hajiya gaskiya danki ya girma ayiriri Dan Majid zai yi aure, kara faɗa breaker ya kusa aure kara faɗa breaker ya kusa aure." Takaici ne ya ishi Hajiya ta maka mishi ludayin miya. "Kai dai kayi girman kawai." Dariya yayi ya nufi dakinshi yayi wanka ya shirya cikin danye boyel, ya fito ya nufi kitchen ya dauki basket din abinci ya fito da sauri, domin dukkansu mota daya suke fita da shi, tunda suka yi hatsarin nan. Ga Jamilah har ta haifi d'anta namiji da ta sakawa Amaan takwara suna kiranshi da Ajwaad. Aryan ya rigasu fitowa sai shi Amaan da basket."yaushe ka koma dan makaranta?" Aryan ya tambaye shi cikin zolaya. "A'a ni bokon ne bakiɗaya." "Allah ya huci zuciyar Imam Aliyu." A fusace Amaan ya ce mishi. "Bana son iskanci, yau kuma da renin hankali ka tashi." "Ni ba dan iska ba ne." Ya faɗa yana dariya. Fitowar Majid fuskar nan a haɗe kamar hadari dan watan Agusta. Ya wuce gaban motar ya zauna Amaan ya shiga baya, Aryan ya koma gefen mai zaman banza ya zauna. Da wani uban gudu ya ja motar suka bar gidan, yana tuki yana tsaki har suka iso kamfanin, sauka Amaan yayi yana dariya. Ciki ya wuce tare da bude wayarshi yana dubawa. Fara'ar fuskarshi.ce ta dauke. A hankali ya mai da wayar aljuhun wandonshi, bai kuma dubawa Asalima farincikin da yake yi ya dauke, haka ya wuce office ɗin, musamman bangarensu, yana shiga ya hangota tsaye tana tsaye. "Kanwata!" Juyawa nayi ina kallon shi fuskarshi babu walwala. Murmushi nayi mishi."Ina kwana Ya Amaan." Lafiya lau, ya bakunta?" "Alhamdulillahi!" Ya mika min kwandon abincin. " "Baka gajiya ne da dawainiyya?" Na fada ina kallonshi. Zama yayi yana faɗin. "da fatan kin huce gajiyar jiya." Ya faɗa yana kauda wancan maganar da tayi. "Alhamdulillahi!" "Akwai laptop na kamfanin nan, an jima za a baki naki da tap." "Na gode!" "Sannan ga wannan takardun ki duba kudadden da kamfani ta ke kashewa ne, a duk wata, ban sani ba ko kina da abin da zaki iya a matsayinki na daliban tattalin arziki." Amsa nayi ina me cewa. "In sha Allah zan duba." Na amsa, ina dubawa tare da kallonshi kamar baya cikin nutsuwa. "Ya Amaan akwai wani abu ne?" "A'a, ina abubuwan da na tambaye ki?" Bude jakar da nake yawo da shi nayi, don na makarantar ne, na cire takardun na mika mishi. "Wai wayarki lalacewa tayi ne?" "Hmm! Yarinya ce ta saka a ruwa." Na fada kamar bana son magana. Don ina tsoron kada ya dauka ni mutuniyar banza ce, don duk wanda nace ina da yarinya kallon ta ina na same ta ake fara min. "Kin barta a wurin su Umminki ne?" Gyada kai nayi, ina faɗin. "Eh!" "Amma ya kamata ki kawo ta kusa dake, yau kunyi waya kuwa?" "A'a" na faɗa ina duba takardun da ya bani. "Tow gashi nan ki kirasu, sai ki karya bari naje Office din Majid." Ya ajiye min wayar ya fita, yana futa ko minti daya bai ba, aka turo mishi sako, daidai xan yi kiran kenan. *Ka turo min da Cefa miliyan goma, ko kuma na saki videon da na tura maka.* Sake shigowa videon yayi kamar wacce aka saka na bude nayi Clicking kan videon, wani irin zabura nayi tare da sake wayar a kasa. Da sauri na bi wayar na kashe videon. Jikina yana rawa na ajiye mishi wayarshi na koma kan aikina, wani irin kyamarshi nake ji, abincin da ya kawo min ko kallo basu ishe ni ba, domin hoton fuskar shi baro-baro. Jikina ya dauki rawa hala shi yasa yake rawan jiki a kaina. Haka na tattara takardun da ya bani na bar office, ina futa na fara amai. Sai da nayi sosai, sannan na tafi can karkashin bishiya na zauna ina sauke numfashi. ........ Wunin ranar aiki kawai na nazarin ayyukan kamfaninsu nake, koda aka tashi kin yarda mu hadu nayi da wuri na koma gida, na ajiye mishi yar karamar short not nace mishi. *Allah ya saka da alkhairi, kayi hakuri cikina yana ciwo ban ci kome ba, wayar ma na barta cikin basket din* ........... A lokacin da ya ga sakona, jikinshi har rawa yake, ya dauki abincin ya kaiwa masu tsaron kamfanin. Kamar mara lafiya haka ya dawo gida, abincin dare bai ci ba. Washi gari ma haka yasa aka yi abinci amma wani ikon Allah koda ya isa yau bai ganta ba, abin ya dame shi ko itama wani ya gaya mata waye shi ne? Baya alaka da kowa a kamfanin sai yan uwanshi, haka yasa kowa yake shakkar mishi wani abu, domin Majid da Aryan ba zasu kyale ka ba.. Haka kawai tunda na saka kaina nazarin abin da suke, sai na yanke alaƙar haduwarmu, haka yasa naji sauki sai dai inda gizo ke saka, dayawan ma'aikatan kamfanin nasu shiga harka na, wasu ma wani irin kallo suke min, wato irin ga yar iskan nan. Wannan abin ya min ciwo haka yasa nake lallaba rayuwata, sati na zagayowa na tafi Marad'i ranar Asabar ranar Lahadi da yamma muka dawo, abin mamaki a bakin kofar dakina na same shi, fuskarshi tayi wani irin fari. A dan razane na kalle shi. "Kin ga videon ko?" Ya tambaye ni, hawaye na zuba a Idanunshi. "A'a ni ban ga kome ba" "baby zo nan!" Da sauri ta isa gare shi, ya d'auketa. Sannan ya matsa min na bude kofar, shiga dakin yayi nima na shiga tare da barin kofar a bude. "Ya sunanki?" "Amira" ta faɗa, zama nayi na wuce kitchen. Shi kuma ya juya ya fita da ita can ba jimawa sai gasu dauke da kayan abinci niki-niki. "ba sai kinyi girki ba." Gabakidaya a takure nake, har addau nake ya bar gidan na samu iska na shaka."kafin ki hukuntani kanwata ki saurari me zance." "Don Allah ka tafi zamu yi magana, gobe." Yadda yaga na takure wuri guda yasa shi cewa. "Ba zan tab'a cutar dake ba, tunda na ganki naji kamar wajibi ne a kaina na taimaka miki, amma idan bakya bukata ba zan miki dole ba. Sannan ga yadda wannan kada ki sake tafiya baki sanar ba, domin muna aiki Asabar da Lahadi department ɗinmu." Ya saka kai ya fita, ina ga yadda yake share hawaye sai naji bakiɗaya ban kyauta ba, ai da na saurare shi naji meke tafe da shi amma na kasa bashi wannan damar. Haka na kwana abincin da muka zo da shi naci, wanda ya kawo mana na ajiye shi, washe gari monday na tashi da azumi, ita kuma na mata dumame, muka fita aiki da ita, awurin masu gadin kamfanin na ajiyeta na shiga. Lokacin da suka shigo kamfanin ya hango Amirah, sauka yayi ya nufi wurin Masu gadin ya ce mata. "Mirah!" Ya mika mata hannu da sauri ta nufe shi. "Ina Mamanki?" "Tana can!"ta nuna mishi cikin kamfanin. "Ok muje yawo?" Girgza mishi kai tayi tana fadin. "Mami zata yi fushi." Riko hannunta yayi suka shiga kamfanin, dama Majid da Aryan tuni sun shige basu san me yake yi ba, sai da ya tafi office ɗin Majid da ita. "Uban Teresa yar wa ka samu?" "Yar yarinyar nan Fadima Abubakar." "Yawwa kai ne ka bata takardun kamfani?" "Eh!" "Haba ko da naji, yau da asuba naga wani analyzing da aka yi akan kudin da ake kashewa a kamfanin. Sannan naga kai tsaye board ta tura fa." "Eh ni na bata kome." Ya faɗa cikin Murmushi. "Ban tsaya dubawa ba, na rufe na shiga wanka, yana rungume da yarinyar yake kallon Laptop din Aryan da yake magana, Majid yana sauraronsu. "Ranar Alhamis na bata fa, yau monday har ta cire abubuwan da ake yi da kudi babu gaira babu dalili, idan har sanin makaman aiki tazo a matsayinta na daliba, ina ga mai xai hana a dauke ta aiki dindindin." Abin da suka fara dubawa, kudin da ake kashewa akan abinci a duk wata, ya haura abincin da ake yi duk watan, don haka idan aka rage kudin aka saka akan ma'aikatan kamfanin zasu fi mora sama da abincin da ba wani cinye shi ake ba, sannan ma'aikatan da suke haya a wasu wuraren kamata yayi a basu damar zama a cikin gidajen estate din, ba wai sai ma'aikatan hucin gadi ba, sannan kamata yayi daga kan masu tsaron kamfanin har zuwa masu aiki a cikin kamfanin, a hada masu damar insurance card, yadda ko ina zasu ba sai sun nime tallafin kome ba, akan lafiyarsu. Sannan kamfanin ya kamata ya duba iyalan waɗanda albashinsu bai.da yawa a kara ma su, sannan a wancan kudin abincin ya kamata a yi wani asusun da zai taimakawa marasa karfin cikinsu. Idan har kamfanin tana samun riba duk shekara tow ya kamata ma'aikatansu, su fahimci aiki sannan asabar da lahadi, a ajiye shi ya zama ranakun hutu ga al'adar kowani ma'aikaci na duniya. Yadda suke karanta rubutun sai da Aryan yace musu. "Yarinyar nan ba iya kamfanin nan ba, bakiɗaya kamfanin BA'ARE GOLDEN EMPIRES a samo mata office da team din da zasu jagoranci wannan baiwar ni " "Nayi rejected din rubutunta, kada a sake a board members su gani, a goge shi." Inji Majid ya faɗa yana mikewa, "sannan ka mai da mata da yarta, ta tafi gida an dakatar da ita don zuwa da yarinyar da tayi, wani sati ta dawo ta kuma rubuto sakon ban hakuri abisa kutse da tayiwa kamfani." "Ni ne na bata duk abinda tayi, ba wani ba don Allah kada ka tab'a min kanwata." "Kanwarka?" Inji Majid. "Eh "inji Amaan. "Tow idan na ce bana buƙatarta a kamfanin fa." "Hamma!" Hannu ya d'aga musu. "Ta tafi idan kuka kara magana sai na Kore ta. Kuma na lalata takardunta." "Wannan rashin imani ne." Inji Amaan, yana zama tare da rike bayanshi da yake mishi ciwo, yadda Majid ya fita a office din haka Aryan ya fita, shima rike hannun Amirah yayi suka fita. A harabar kamfanin suka same ni, ina tsaye wurin masu tsaron. "Mami!" Ta tsunko da gudu, bude mata hannu nayi, Ya Amaan na zuwa na gaishe shi. "Ki koma gida da Mirah, wannan satin ku yi shi tare sai mu duba makaranta zuwa Monday ta fara." Ya faɗa yana nuna min mota, shiga nayi. ...... 300₦ 0016341139 unity bank zahra'u yahaya Ali Katin MTN 400 +2347035133148 #Mai_Dambu ce [5/29, 07:47] Hlm: BHB244 Ni dai na koma gida, sannan sauran ranakun ban je aiki ba. Duk da ina gudun Ya Amaan. Amma kuma akwai gaskiyar da na kasa yarda na tsaya na ji, sai da nayi kwana uku a gida, sai naji na takura kamar an daure ni. Amirah da Ya Amaan ya sakata makaranta, ana zuwa ɗaukarta kuma a dawo da ita. Tana dawowa na shirya bayan la'asar muka tafi yawo, haka yasa muka dawo wurin Magariba, na samu yana tsaye shida dan uwanshi. Shima naga kamar bai da yawan sakewa ba kamar Ya Amaan ba. "Ba!" Amirah ta kira sunanshi. Mika mata hannu yayi ta isa wurin shi. "Ba me yasa baka zo ba? Yau ma jini ya fito a bakinka ne?" Cikin shashantar da zancen ya ce mata "ga sweet ɗinki." "Fadima ya zaman gida?" Sai kunya ta kama ni na gaishe su, "yawwa naga kamar ba zai miki magana ba, ko zaki bani laptop da tap din?" "Ok bari na kawo." Amma kuma wallahi ban ji dadin haka ba, amma.kuma ba Yadda na iya tunda na kamfani ne. Haka na shiga na kawo musu, ina kallo ya shiga motar ya fito da manyan kwalaye ya mika mata, ni kuma ya mika min wani kwalin. "Na rigada nayi niyya, don haka ga wannan Hp ne." "Hmmm!" Nace xan mishi musu, zuba min idanu yayi sai ya cika min ido, haka na amsa ina godiya. Ina gani ya tafi ni kuma muka wuce ciki. Ban san me yasa yake yi min hidima har haka ba, sannan Ni dai na kasa sakin jiki da shi. Domin lamarin abin da na gani dole ya bani tsoro, sannan kuma da hujja ta na kare kaina da mu'amala da shi. Ranar Lahadi ina zaune sai gashi nan, ya zo yana ta haki. Bayan na bude mishi kofar ya shiga kallon juna muka yi, fuskata a daure, zama yayi ya ce min. "You hate me?" Zuba mishi idanu nayi kafin na ce mishi. "Ni." "Zahra kin tsane ni!" "Ni ba haka nake nufi ba, alakata da kai wani sai ya dauka nima haka nake don Allah ka tafi ka daina shiga rayuwarmu." "Tun ranar da na ganki a marad'i kina magana da yaron nan, da yadda kika tsaya domin kare kanki. Naji a jikina na samu kanwa. Zahrah" "Dama kace ka sanni shi yasa kake bibiyata." "Ba iya ke ba, hatta inda kike zaune na sani na san baki da kowa a marad'i da nan Nijar. Amma ba ina nufin na wulakantaki ba ne. Kawai naji a raina akwai wata nasaba da take haɗe a tsakaninmu." Zama yayi ya fara magana a hankali, yana yi yana rike hancinsa. Ni da nake tsaye sai gani a zaune, ina sheshekar kuka. "Majid yafi mu wahala, tun yana Yaro rayuwarshi ta lalace, sannan yana nan domin shine Chairman na kamfaninmu. Wannan kaɗan daga cikin labarinmu kenan, ban sani ba ko zaki yarda dani amma ki sani na gaya miki gaskiya, don na lura babu me gaya miki gaskiya a kaina, kowa abin da yayi mishi yake gaya miki." Hawayen da suke zubowa kamar famfo yasa ni kasa magana, "Yanzu daga ina kake?" Ajiyar zuciya ya sauke ba a san na fito ba, shine wasu suka biyo ni." Kura mishi idanu nayi, "Me yasa kake wasa da rayuwarka?" "Saboda na goge videon da kika gani ne, eh na aikata abin da kika gani, amma wallahi dare daya na tsinci kaina da son bin maza, tun daga ranar na zama haka. Amma tunda aka min aikin na daina tunda dama ba dabi'ata ba ce. Ki yarda dani." "Yanzu ka kira Aryan yazo ya dauke ka." "A'a xan koma da kaina." "Allah ba zaka bar gidan nan ba, sai da wani naka." Haka muka shiga rigima, dakyar ya kira Chairman. Ko minti biyar ba ayi ba ya ce maza ya fito yana jiranshi. Bayan tafiyarshi da dare muna barci aka yi ta buga min kofa, tashi nayi ban kunna wuta ba. Na nufi bakin kofar na ce. "Waye?" "Ki bude kofar." "A'a waye dai." "Dazun Amaan Mamman Ba'are yazo, kuma nasan da abin da ya gaya miki." "Ni?" "Ki bude ko mu fasa kanki da bindiga." Wani irin rudewa cikina yayi, na juya dakina da gudu, na rufe kofar. Ihun su da buge buge yasa na kara kame Amira hawaye na zuba min. Can naji wani irin kaara daga nan ban kuma jin kome ba, sai na ihun mutane, kai naga tashin hankali a rayuwata. Sai gashi duk abinda suka faru suna yawo a cikin idanuna kuka na saka ina kallon ikon Allah. Har wurin asuba kafin na daina jin ihu da kakari. Washegari tun asuba yan sanda suka buga min kofa, ga bindigarsu, alamarsu uku ne, ga yadda aka jasu a wurin bayan an ji musu ciwo. "Ko kin san me ya faru?" Girgixa kai nayi, don ina matuƙar tsoro. "Baki ce kome ba." Kuka na saka musu, ina jin kamar zuciyata zata buga. "Ban san kome ba." "Ku kyaleta." Aka fada musu, daga bayansu. Shiga dakin nayi na had'a kayanmu zan bar garin nan, ban ga dalilin zamana a zo a kashe mu a banza ba, haka na hada kayanmu na fito. "Zahra ina zaki?" "Marad'i mana, zan je a sauya min wani wurin." "Kina tsammanin zasu daina bibiyarki ne? Meye Amaan ya gaya miki?" Kallonshi nayi, dogo ne, kamar wani Superman. Yanayinshi kamar Lee dong wook, ga tsawo ga jiki, irin na zaratan sojoji. Haɗiye yawu nayi tare da yin baya, ana cewa ina da tsawo wallahi ina ganin shi sai naga ashe ni yar tsako ce, domin ya ninka ni tsawo, a tsakanin hannunshi nake tsaye. Daure fuska yayi yana faɗin. "Magana nake kina kallona." "Ni dai zan tafi!" Na fada kasa -kasa. "Allah ya tsare." Ya fada yana barin falon. Kamar an wurgo shi ya shigo falon, ganin ina jan kwatinmu ya rike "Zahra." "Me yasa ka jefa rayuwata a hatsari?" "Kiyi hakuri ban san zasu biyo ni har wurin ki ba." "Shine ka saka kowa yake tambayata, meye ka gaya min?" Idanunshi ne ya kad'a jajjur. "Kiyi hakuri, amma kin ga mutanen ne?" Girgixa kai nayi ina shashekar kuka, "tow ina suke ga kayansu nan, amma babu alamarsu." "Ban gane ba?" "Eh kowa a cikin apartment din nan, sun tabbatar da zuwan su wurinki. Amma kuma ance babu su, an ji muryoyin su sai dai babu su babu labarinsu." Zubewa nayi a kasa, na fasa ihu domin haka shine ya dace dani. Tun daga ranar aka saka tsaro a apartment din, tare da sanin fitana da dawowa ta. • "Hajiya kice ya rabu da yar mutane, domin kuwa zai jefa rayuwarta a cikin hatsari ko Hamma." Inji Aryan, kura mishi idanu Hajiya tayi yadda yayi shiru, alamar akwai abinda yake damunshi. "Amaan!" "Na'am Hajiya." "Kana son yarinyar ne?" Girgza mata kai yayi, "Tow ka kyale musu yar mutane, kada ka cilla ta cikin wahala." "Hajiya ni taimakonta nake son yi, sannan ni." A zuciye Majid ya bar musu falon, "Dawo nan Alhaji " kamar ba zai dawo ba, ya dawo ya zauna yana me saurarenta. "Tun wancan satin da ta fidda rahoton nan, na ce ya dakatar da ita, domin shi kanshi jagwal din yake ciki bai fita ba, zai saka yar mutane." Ya faɗa da fushi, don yasan dayawan makiyansu, suna board ne shi yasa yake ganin gara ya dakatar da ita. Shi yasa ya goge rubutun da tayi, ya kuma bada hakuri. Sannan ya san a bangaren abincin kamfanin sun ji babu dad'i. Baya so a fahimci cewa zai shiga rigimar da bata da farko ɓalle karshe, hidimar kamfanin ya barwa kanshi ne. Sannan tun fil azal abin da tayi, shima yana tsarinshi, amma fito na fito da partner na kamfanin kamar yaƙin duniya na uku ne. Shi yasa ya zuba idanu yana aikinshi ba tare da ya tab'a su ba. Haka suka yiwa Amaan caa, da fada wanda shi yasan cewa a wannan ɓangaren Zahra ce zata iya futar da abinda yake boyewa, koda yake ai bai yi mamaki ba. Tashi yayi ya nufi dakinshi, ya shiga ban daki ya cire kayanshi. Zama yayi akan wata ƙaramar po, a hankali yake nishi tare da rike cikinshi. Tattaunawar da suka yi da Zahra ne ya dawo mishi. _Eh ni dan luwadi ne, amma a da can nayi ba yanzu ba. Zahra ina son na gaya miki gaskiya mahaifiyarmu ta sha wahala da mahaifinmu, bayan nan kuma na fada wannan harkar a lokacin da na tsani dan uwana Majid. Zahra a yanzu akwai wasu da suke min barazanar zasu kashe ni a cikin kamfaninmu suke. Don Allah ko da kin ji labarin mutuwata ki gayawa Majid waɗanda suke da hannu a cikin mutuwa. Sannan rahoton da kika fitar, Majid ya ce kada ki kara shigar da kanki cikin lamarin kamfanin kiyi abin da ya kawo ki. Zahra ga wannan ki bawa Majid ko Aryan. Ki tabbatar ya shiga hannunsu_ Kallon shi tayi cikin tsananin tsoro ta ce mishi. *Me yasa sai ni?* Dariya yayi har yana tari ya ce mata. _Saboda bakiɗaya kamfanin mutum daya sukewa aiki! Ba a karkashin Majid suke ba umarnin Sajjid suke bi, domin ya saye su bakiɗaya._ *Meye?* Ta faɗa tana zare idanu. _Kiyi ƙoƙarin, gano yawan masu aiki da Sajjid na fitar da manyan cikinsu gashi nan a ciki sauran kuma zaki iya zakulo su._ Ajiyar zuciya ya sauke tare da Mikewa, sai kuma ya durkusa yana ta aman jini. Ya sani ya jefa rayuwarta cikin hatsari, amma zata iya taimaka mishi. Sai da ya gama ya mike. Irin wannan azabar Alhaji Mamman Ba'are yayi ta ji, lokacin da aka yi ta zuba mishi guba yana ci, da ajali ya zo yayi ta kashin jini, Maisarah da bata san hawa ba. Bata san sauka ba itama an kashe ta hanyar karya mata wuya. Shine na ukun da yasan waye yaƙe bibiyar gidan. Yasan Sajjid da Tani ba su ne matsalar Familyn ba, asalin masu fitinar Familyn yan cikin gidan nan ne. Sannan abin da yasa suke wannan fitinar don gadonsu yafi nasu yawa ne, sannan sai wasu daga gefe can. Zubar da kashin jinin yayi ya wanke banɗakin da maganin kamshi, sannan ya fito ya wuce gado yaji ruf da ciki. _Zahra idan na mutu, na sansu zasu iya cewa kashe kaina nayi a'a Zahra ba kashe kaina ba ne. Ayi binciken gawata da kyau nasan ni na kai kaina, amma ban kawo a kaina cewa masifa na cilla kaina ba, Zahra a cikin gidan mu ne amma akwai dodonnin da idanun basu ganinsu kema ina jin kwarin gwiwa ne yasa na gaya miki._ Magani ya ɓalla ya sha, sannan ya gyara kwanciyarshi barci me nauyi yayi gaba da shi. • Kwana biyu da faruwar al'amarin. Ranar na futa aiki a inda muke hawa motar da zata kai ni makarantar su Amirah, naga wasu mutane biyu. Tsoro ne ya kama ni na matsa can ina rike da Amirah. Mota na zuwa na shiga da sauri. Ina shiga cikin na zauna kafin mu tashi naga daya daga cikinsu ya zo zai shiga motar. Wani mutum ya bangaje shi ya fadi, sannan shi ya shiga motar har makarantar babu wanda yayi wani motsi, ina sauka mutumin ya sauka, ya wuce nashi hanyar sai da na ajiye Amirah, a lokacin wani irin tsoro ya kamani. "Maman Amirah sugrah!" Juyawa nayi naga abin mamaki. "Aseem." Rufe bakina nayi, ina kallonshi. A hankali na durkusa a wurin na fáshe da kuka. "Akhi!" "Na'am ina Sultan?" Shiru yayi yana kallona, "tashi muje." Ya nuna min motar da ya zo da ita, mikewa nayi na bi bayanshi. Har cikin motar na shiga ya ja ni muna tafiya ina kuka. "Naga kamar a firgici kike?" "Ina cikin damuwa, Sultan kadai zai iya tsaya min yana ina?" Murmushi yayi ya ce min. "Tabbas idan yana tare da ke ba zai iya barin wani abu ya cutar da ke ba, don haka babu wanda ya isa cutar dake." 300₦ 0016341139 unity bank zahra'u yahaya Ali Katin MTN 400 #Mai_Dambu ce [5/29, 07:47] Hlm: BHB245 Ajiyar zuciya na sauke lokacin da ya kawo ni kamfanin ya juya tare da ciro wata jaka. "Gashi nan, waya ce da duk abinda kike buƙata. Ga wannan ki saka a hannunki duk abin da zai faru ki danna wannan abin in sha Allah, duk inda kike Allah zai kawo miki ɗauki." Murmushi nayi nace mishi. "Da gaske?" "In sha Allah, wannan ma ki sakawa Amirah." "Ina farin ciki." Na fada ina kallon abubuwan, "bari na shiga." "Zan dauko miki Amirah xan kawo ta nan." "Hmm ko zaka tafi da ita wasa, don basu son Yara a kamfanin." "Saboda ƙurar dalma ce ba don yaran, sannan kema kina amfani da wannan facemask din." Amsa nayi ina faɗin."Na gode sosai." Sannan na fita a motar, na nufi get din kamfanin. Ina shiga na nufi department ɗinmu. Ina shiga na samu baki dayan three brothers suna tsaye, kamar munafuka haka na wuce zuwa table dina na zauna. "Ba a koya miki gaisuwa ba ne?" inji Aryan, shiru nayi ina wiki-wiki da idanu. "Ina kwana." "Rike gaisuwarki." Haɗiye yawu nayi, ina jin suna magana da fulatanci. a raina nace munafukai hala sun dauka kowa kidahumi ne, sai da suka gama dube-duben su sannan suka fita. "Sun zo sun ishe mu da gulma, dama an san Fulani da gulma." Inji dan daudun nan. Bance musu kome ba, har aka tashi. Na rufawa kaina asiri, na daina cin abinci a cikin kamfanin. Zuwan Aseem ya sani samun nutsuwa, sannan babu wanda ya kara min barazana, sai dai a wurin aikin ne babu sauki, ina zaune a za a tula min aiki kamar jaka. Tun ya Amaan yana zuwa ya bani hakuri, har ya daina nasan hana shi suka yi. A hankali na fara sabawa da aikinsu, ga shi ba hutu Asabar da Lahadi aiki. Don ko ban je ba, za'a kirani na je. A hankali na samu wata uku ni da Yarinyata mun nutsu, ana haka aka samu hutun ranar maaikata na duniya, muka wuce marad'i da Aseem, a can muka kwana uku, sannan muka dawo Niamey, ai a ranar da na dawo na sha masifar Mr Aryan kamar zai doke ni. Da na gaji ne na ce mishi. "Bafa aiki nake yi ba? Kune kuka gayyace ni nazo na san makaman aiki, akan me kuma za ahana ni rayuwata? Ban matsawa kowa ya zauna dani ba, kafin nazo nan ina raye don na bar nan ba ya nufin zan mutu ne. Tun kafin ayi uwar me sabulu balbale take da farinta." Na fada ina ajiye musu file dinsu na kamfani. Na juya zan fita Aryan din ya ce min. "Kina nufin kina da inda yafi nan ne? Ko kina da inda zaki zauna hankali kwance." "Kana mun barazana ne da rayuwata?" Na juya na kalle shi, "Zahrah ya isa haka." "A'a bai isa ba, bai isa ba barni na gaya mishi abin da yake ganin zai zame min kamar dole." "Ki ajiye aikin ki bar mana office ɗinmu." Naji Muryar shi kamar daga sama. Dariya suka bani. "Tow tunda na bar office dinku zan tafi lahira a kafa kenan ba." Na fada ina barin office din. Ko a jikina. A cikin wata uku na gyara musu kasuwancinsu ta hanyar d'aga darajar hannun jarinsu ta hanyar da ni kai na ban zata ba, sannan a cikin wannan yanayin, akwai mutanen da zasu zo domin saka hannun jarinsu don kawai rate na kamfanin GOLDEN EMPIRES yana tafiya, shine zasu min kinibibi. Na ajiye musu aikin. Ina fita na kira Aseem, na gaya mishi abinda ya faru. "Gani nan zuwa kin ji" ina tsaye a bakin kofar, Amaan ya iso da sauri. "Me yasa zaki min haka?" "Me yasa ba zan maka haka ba, halitta ta kuka yi da ba zan rayu ba sai da ku? Gaya min ko ce muku aka yi ina raye ne don ku? Ni fa bani da isasshen lokacin da zan na zama kuna juya ni kamar wata trouser dinku." "Amma kin san aikin da muka yi dake, yana bukatar taimakon ki. Da taimakonki muke kokarin bunkasa kamfaninmu ki ce zaki ajiye aikinki. Please ba don ni ba ba don halinmu ba, ki dawo." "Ba zan dawo ba." Daidai parking din Aseem, na shiga motar hankalina kwance. Daga can office ɗinshi yana kallon kome, yarinyar dan nutsuwa tana da shi, kawai ba xai yiwu tana abin da ranta yake so ba, idan har tana haka makiyan kamfanin zasu iya amfani da hakan. "Hamma anya Amaan ba son yarinyar yake ba?" "Shi ya sani idan ma sonta yake waye ya damu?" "Hmm! Tun ranar da aka kai mata harin nan, wannan mutumin ya bayyana kawai ban yarda da yarinyar bane." "Humm!" Ya faɗa yana kallon yadda Amaan ya dawo Office. Tun ranar da abin ya faru, ya fahimci wani abu, akwai wani abu a tattare da yarinyar na farko shine akwai wanda yake kare ta, sama da yadda take rayuwa. Don koda ya sa mutanen shi su bincika sun dai gano daga marad'i har zuwa Niamey akwai wanda suke bibiyarta, sannan kome na rayuwa bata bukatar shi daga wani, kome mata ake ana kawo mata. "Waye shi?" Ya furta da karfi, don ya zata a ranshi yake magana. "wa kenan?" "Idan baka manta ba, mutanen da suka bi bayan Amaan suka isa wurin an batar dasu. Sannan case din an kashe shi daga wurin yan sanda. Ba tare da sanin yarinyar ba, don an hana a bincike ta." "Eh Hamma haka ne." "Akwai wani babban inuwa a saman kanta,na rasa waye shi?" "Ka rasa waye shi?" "Eh na rasa, ina gudun alakarta da kamfanin yasa a cutar da ita." "Tabbas Hamma kowa na kamfanin nan aiki yake yi, ita kuma ta shiga jikin Amaan lokaci guda haka yana nufin ake bibiyar rayuwarta. Tow ya zamu yi?" "Kyale ta!" "A dawo da ita dai!" Don ya fahimci abin da yake son faɗa kenan. "A'a barta ta tafi tunda ita ta zab'a haka." "Bammmmm!" Aka bude kofar. "Munafukai algungumai, ba zata bar aikin nan ba kuma wani shegen ya kara mata rashin mutunci."tari ne ya turnike shi, har ya fadi a kasa, jini ta kunne da hancinsa, ta ko ina fita yake. "Kai Amaan!" Inji Majid yana me rungumar shi, da sauri ya ciccibe shi suka fita daga kamfanin, motar kamfanin na kai agajin gaggawa aka dauko, suka nufi asibiti. A can aka amshe shi, aka shiga bashi taimakon gaggawa. Har dare suna asibiti babu wanda yayi tunanin Hajiya. Sai da Jamilah ta kirata ta ce tazo asibitin, ganin halin da Amaan yake ciki yasata jin kamar zuciyarta ne zata buga. "Aliyu meke damunka?" Ta fada tana jin wani irin kuka, tabbas Amaan yana ganin jarabawa, haka ta fito tana kuka me ban tausayi. "Aryan me ya same shi!" "Hmm" ya ce kafin ya bata labarin abin da ya faru, kafin ya kai aya ta ce musu. "Anya yan adam ne ku? Don ta kara kwanaki uku sai ya zama kuskuren da za a Kore ta? Na zata ko makiyi Aliyu ya kawo ya ce zai zauna da shi , ku masu taya shi zama da shi ne ashe kanku kuka sani? Ni zan dawo da yarinyar." Ta juya tare da barin Asibitin, don ita Hajiya a tunaninta Amaan son Zahrah yake, don haka ta saka Aryan din a gaba har apartment din Zahra. Akwai wani abun da Allah shi kadai yake haɗawa, lokacin da Hajiya ta ga Zahra sakin baki tayi tana kallonta. "Ya sunanki?" "Fatimah Abubakar!" Murmushi Hajiya tayi duk hankalinta a tashe, amma sai tayi ƙoƙarin kwantar da hankalinta. "Amaan ya fadi bayan barinki aiki yana cen asibitin kwance sai abinda hali yayi." Rufe bakina nayi ina jin hawaye na zuba min. _Zahra guba ce a jikina nasan ba tsawon rai zan yi ba, idan na mutu ki tsaya a gefen ahalina_ "Yana wani asibitin?" Murmushi Hajiyar tayi tana faɗin. "Ko zamu tafi ne?" Kasa nayi da kaina, don ta cika min idanu, haka na dauko Amirah muka fita, ita a farko ta zata irin a wurin shiriritan shi ya tsinto ni, yake ta wannn hidimar dani, sai da take tambayata matakin karatu, da sauransu sannan ta fahimci ai ni ba watsatssiya ba ce, da kamun kaina sai dai gani na da yarinya yana dukar duk wanda yaji yarinya ta ce. Haka muka isa asibitin, a bakin kofar shiga asibitin muka hadu da Chairman, sai muzurai yake gashi bai da irin fuskar da zaka kawo mishi raini, don ko fadar da muka yi da Aryan muka yi, ba da shi ba shi ce min yayi na bar kamfanin. Kuma ban iya ja da shi ba, don kwarjinin shi kamar wanda ya tafi filin yaƙi. Allah sarki ko ina wannan sojan, na tuna shima dai duk da a duhu ne zai kai haka tsawo. Haɗe rai yayi a raina nace. *Wannan mutum da alamu zai yi mugun hali, ji yadda yake bata rai kamar ya ga kashi* Tuni muka wuce cikin asibitin har dakin Amaan din, hmm masu kudi suna jin daɗinsu, a lokacin da muka shiga wai ashe ya farka bayan fitar Hajiya. "Final ga ta nan!" Kunya ce ta kama ni. "Kyakyawar gaske kuwa, kai Aliyu don uwaka a ina ka samu kyakkyawar mace, wannan ai da Alhajin Allah ta dace, kun ga wata doguwar halitta kamar matar gidan Aljannah. Gaskiya Sa'adatu ki gayawa Aliyu ya nemi sa'ar shi wannan ai idan aka hada ta da Alhajin Allah zasu zama wata da zahara, don zasu haskaka alkhairi da duniya." Inji tsohuwar da na lura rigima ya gama cinye ranta. "Ban da zalama irinta Aliyu ai yarinyar nan da Alhajin Allah ta dace ba shi ba, don haka wallahi na gaya miki ki gaya mishi ya nime wata mace ba dai wannan ba." "Nana babu wata mace da zai nima, ita yace yana son gani ba wata ba. Babana ya jikinka?" "Da sauki Hajiya,amma Zahra ba budurwata ba ce, kanwata ce kamar su Jamilah." "Ban gane ba?" Mika min hannu yayi, na nufe shi. Murmushi yayi min sannan ya ce min. "idan har na tashi, ki gaya min me kike so na baki, domin na saka rayuwarki cikin hatsari." "Lafiyarka tafi min kome, Allah ya tashi kafadunka." Na faɗa mishi hawaye na zubo min. "Kina kuka ne don na gaza ko?" Girgza kai nayi ina share hawayen fuskata. "Kai ne mutum na biyu da ba zan manta da alkhairinshi ba. Ina zuwa ka amshi ni hannu bibbiyu. Taya ba zan yi kuka ba kowane mutum da ta shi ƙaddarar naka ƙaddarar iya boyewa ahalinka lalurar ka sai da yaci lakarka. Ya Amaan, kai mutumin kirki ne wanda yayi kokarin sadaukar da rayuwarshi domin ahalinshi. Duk da ban gaya maka kome a kaina ba, daga gani na kace kana min kallon wacce take cikin kaɗaici. " Kuka ya kwace min, "ina niman yafiyarka lokacin da na gaza fahimtar ka, ban san kai waliyi ba ne sai yanxu, ka gaya min me kake so nayi maka daga yau har zuwa karshen rayuwata." "Babu kome!" Ya faɗa min yana murmusa min, "Babu kome fatana ki rike min Hajiya kamar ke ta haifa bamu ba, ki kula min da Hajiya kamar ke ta haifa." Kukana ne ya tsananta domin a yau na samu dan uwa, na kara samun uwa wannan shine dadi kan dadi kunama ta harbi gyambo. Ga Uwa ga dan uwa, "A yau da ka kirani a matsayin yar uwa ka kara min da kyautar uwa, sai nake jin kamar nafi kowa dace a samun dan uwa irinka...... 300₦ 0016341139 unity bank zahra'u yahaya Ali Katin MTN 400 07035133148 #Mai_Dambu ce [5/29, 07:47] Hlm: BHB246 "Kai mutumin kirki ne da duniya bata dadaka da kasa ba, kowane mutum da ƙaddarar sa. Ka tashi don Allah." Na faɗa mishi ina hawaye. Dariya ya fara yana tari. "Hajiya nifa ko yau na mutu bani da haufi." "Shiiii! Cuta ba mutuwa ba ce, haka zalika wuya bata kisa, da tana kisa da yau bana nan a zaune. Zakarar da Allah ya nufa da cara." Fuuuu tsohuwar nan ta fita, ban damu ba na goge hawayen fuskata. -- "Alhajin Allah, yarinyar nan waye Ubanta? Ni dai da kai ta dace ba da wancan karuwin ba." Ware idanu yayi yana faɗin. "Nana ni kuma?" Girgza kai yayi yana faɗin. "Never," "Kai ni ban san neba ba, da kai dai ta dace domin nasan...." Bai saurare ta ba, ya wuce dakin. "Allah ya baka..." Damkar hannuna aka yi na juya, ina shakar kamshin turaren shi. Sauvage doir, sarawa kaina yayi ina jin wani abu kamar an jona min wutar lantarki. "Tashi!" Kamar wanda ya bani rufe baki, haka na mike tare da bin shi kamar raƙumi da amale "Ka sake ka fitar da ita daga dakin nan, furucin da zai fito bakina zai iya shafar rayuwarka." Ba iya shi ba, hatta ni taka burki nayi tare da juyawa na zuba mishi idanu. Ina jin kaina kamar zai rabe biyu, numfashi na ne ya shiga hawa da sauka. Na fara niman shi da kyar da kyar, domin ji nake kamar numfashina zai bar jikina, ko Hajiyar ta fahimci haka ne ta zo ta rungume ni ta baya."Hajiya!" Ya kira sunanta a raunane, "Na gaya maka daga kalamai na." Tsit wurin yayi, "koma ki zauna ki dauka nan cikin yan uwanki kike raye, babu me miki ko kallon banza ne." Ta cire hannunshi cikin nawa. "Amma Hajiya." Ruwa ta bani na sha. Ina tari. "A'a Baffayo, kana son yarinyar nan a kusa da kai. Taya zan nisanta ka da ita? Ni kuma ina son ko ba zaka tashi ba naji kana magana kamar kowa, shima arziki ne zauna Yarinya ya ma sunanki." "Fatimah Abubakar." Murmushi Hajiya tayi hawaye na zubo mata. Daga yadda take daurewa kawai ya sa ni tuno labarin da ya bani irin wahalar da Hajiya tasha da mutane, tausayin ahalin ta yakara ninkuwa a rai. "Zahrah ki bi Hajiya ku je gida ku kwana." Girgiza kai nayi ina faɗin. "Zan kwana a tare da kai, sai dai a tafi da Amirah." "Akwai sauro kuma kin ga kuma..." "Allah na gode maka da babu dodo ko?" Dariya yayi, sannan na ce mishi. "Ya kamata ka rage nauyin da yake ranka, kayi barci ka huta." Daukar Amirah Aryan yayi da ta fara barci. Ni da hajiya muka zauna a asibitin can sai ga Chairman da bargo, matashin kai. Da sauran abin bukata. Mikewa nayi zan amsa ya wuce ya ajiye. "Hajiya xan kwana a waje." "Tow!" Haka muka kwana muna hira sama-sama, kafin barci ya dauke mu. Ina zaune a kujerar dakin nayi barci Bayan na lullube kafata da bargo. ...... Wani irin duhu garin yayi gani cikin sahara, na rasa inda xan dosa. Ji nayi an rike hannuna ana ja na da sauri. Haka na bi wannan hannun, har muka shiga haske. "Yazid!" Na furta lokacin da na ganshi. Murmushi yayi min sannan ya riko hannuna muka ci gaba da tafiya, bamu yi nisa ba, muka hadu da Chairman da wasu mata har da Hajiya tare da su Addah da Munaisah. Da sauri na nufe su suka juya min baya, na ƙara sauri zan nufe su. Wani farin dattijo ya rike ni. Ya nufi daki da ni. "Idan kika yi hakuri zasu biyo ki, kada ki bisu domin zasu sake nasarar raba ki da kome da kike da shi." Buga kofar dakin aka yi Chairman da Yazid suka shigo kamar wasu zakuna. "Duk wanda kika zab'a, Allah yana tare dake, amma shi wannan idan kika zab'e shi tsugune bata kare ba..." Bude idanu nayi daidai lokacin da xan kalli inda ya nuna min. Hakin da nake yi ne ya sa dole ya shigo dakin, yana kallona. Cilla min goran ruwa yayi ya fita, a hankali na bude ruwan na sha, na shiga ban daki nayi alola. Dakyar na samo abin sallah. Na tada sallar dare. Sai da na idar sannan na dora da addu'a, kafin na mike na koma wurin Kujerar.. .... Yana zaune yana aiki da laptop ɗinshi, yaji kamar ana numfashi sama-sama, shi ya zata ma Amaan ne yasa shi leka dakin sai dai yana shiga ya ganta a kan kujera. Tana juya kanta. Fita yayi ya dauko goran ruwan da ya ajiye don aikinshi. Yana shiga ya samu ta farka. Cilla mata goran yayi ya fita. Haka kawai yake jin wani strang feel ganinta, a duk lokacin da yayi ido biyu da ita yana jin abin yana yawo a jininshi da jikinshi. Cigaba yayi da aikinshi. Washe gari. Da safe sai ga Amirah, rungume juna muka yi. "Mami ina kika je?" Ta tambaye ni da fulatanci. "Ba bai da lafiya ina wurin shi." "Kina jin fulatanci dama?" Juya idanu nayi ina cewa. "Eh ni Fulanin Bauchi ce." Na tsinci kaina da fadar haka, "ikon Allah." "Ai kuwa gashi nan kin yi." "Mami Ba bai tashi ba ne?" "A'a Ba bai tashi ba, muje gida Uncle yana jiranki." "Fatimah, baban Yarki ya rasu ne?" Inji Aryan, haɗiye yawu nayi zan bashi amsa Hajiya ta make kanshi tare da faɗin. "Kada ku tsannanta bincike." Ba iya ni ba, sai gashi kowa a wurin zuciyarshi tayi sanyi, gida Aryan ya ce zai kawo ni, muna fita muka hadu da Aseem, da gudu Amirah ta nufe shi ya cillata sama. "Yan matan Uncle muje a shirya ko." Ya kalle ni. " Amma kin yi kwanan zaune ne?" Murmushi nayi ina girgza kai. Tare da hamma. "Ni soyayya kike yi ne da mara lafiyar?" Yadda yayi min mganar yasa na kara kallonshi domin babu wasa a cikin maganarshi. "A'a" "Amma ai ba danginki ba ne?" Kallon shi nayi a karo na biyu cike da mamaki. "Me ya kawo wannan tuhumar haka?" "Saboda tsaron lafiyarki da rayuwarki na kai na ne." "Hm!" Na faɗa, ai ba zan kuma cewa kome ba, kuma ban ga laifinshi ba. "Yazid yana raye?" "Kice Sultan da girmamawa." Ya faɗa min had'e rai nayi ban kuma magana ba, domin nasan idan na kara magana masifa zan yi, amadadin ya kai ni gidan da na sani wata unguwa naga ya kai ni na daban, "tun jiya na tattara miki kayanki, suna nan na saka an gyara gidan ki shiga ki duba." Yar karamar unguwa ce da aka yi gidajen estate. Masu bala'in kyau da ɗaukar hankali. A hankali na fito tare da nufar gidan, fitowa yayi ya bude min gidan, yana min bayani sam bana fahimtar shi, har sai da ya kira sunan siyamah. Na kalli kofar babbar mace ce. "Na'am." Ta amsa cikin girmamawa. "Ga Amirah sugrah, a shirya ta na kaita makaranta. Amirah ga Nannynki." Haka ya mikawa matar, ni dai ban ce kome ba. "Idan kin shirya zan zo na kai ki kamfanin ko asibitin." "Asibiti." Na fada ina kallonshi. "Wai don Allah duk wannan na meye ne?" "Nima Umarni aka bani." "Waye Yazid ko?" "Ki ambaci sunanshi da girmamawa." "Anki a ambata." Na fada a masifance. Daga haka na wuce dakin da ya nuna min, kayan haushi kome na dakin cream colour da coffee. Yayi kyau har wall ɗin. Wanka nayi na shimfida abin sallah, nayi sallar walaha. Ban tashi a wurin ba sai wurin karfe goma, kitchen na wuce na ga Siyamah, wake na zuba na fara aiki kamar yadda nake da can baya, na dafa wake da kifi, sai kwai da na dafa na zuba a waken. Dake ya kawo min kayan abinci na, na wancan gidan. Ina gamawa na bar Siyamah ta sauke min, ta juye min. Wanka nayi na saka doguwar riga, na yane kaina da mayafi, mai kawai na shafa da hoda tare da kwalli. Hula na saka a cikin mayafin don gashina yaki bari mayafin ya zauna. Ina gamawa ya kai ni har asibitin, sannan ya ce min. "Yaushe zan zo daukarki?" "Karfe biyar tunda Siyamah tana tare da Amirah." "Shi kenan." Ya faɗa yana me barin Asibitin. A bakin kofar asibitin muka hadu da Chairman, kai jama'a mutumin nan ya iya tsare gida, kallo daya nayi mishi yana sanye da suit black colour, ana cewa dan adam bai cika goma ba, a idanuna Chairman ya kai 💯 percent, yana tafiya bindin shi yana biye da shi, sau daya na kalle su na kauda kaina. Har bakin kofar muka isa, dake suna gabana ban san me ya gayawa security din bakin kofar ba, naga suna kallona. Ina zuwa suka amshi basket ɗin, abincin suka buɗe. "Ki ci?" Kallonsu nayi su kan har sun shiga cikin dakin. "Ban gane ba?" "Ki ci umarni ne aka bamu." Cokalin da na zo da shi a cikin basket din na dauka tare da juya abincin na diba na ci, hawaye ne ya zubo min ban san me yasa yake min haka ba, sai da naci sau uku. Sannan na ajiye ina kallonsu. "Ok ki shiga amma ba da abincin ba." "Ban gane ba!" "Haka akace mana, kada kishiga da Abincin." "Tow." Na fada ina shiga dakin babu kome, bakina da sallama. Ina shiga muka had'a idanu da shi, wani irin tsanarshi nake ji yana taso min, "ina wuni Hajiya." Na durkusa har kasa na gaishe ta."lafiya lau Fatimah, ya gajiyar kwanan zaune?" "Alhamdulillahi, ya me jikin dai?" "Jiki da sauki, yanzu yayi barci ma." "Allah ya bashi lafiya." Sannan na juya na gaida sauran matan dakin, wanda nake ganin kamar kannen shi ne. A dakile suka amsa min, ban kula su ba. "Zahrah!" Ya kira sunana."Na'am!" Na amsa ina isa inda yake. "Ina ta jiran abincinki ne fa" juyawa nayi na kalli Chairman da ya hana ni shigowa da Abincin. "Zaka ci ne?" "Eh Zahrah." Juyawa nayi na fita, na samu har lokacin abincin yana wurin, dauka.nayi zan shiga suka so hanawa, Aryan da ya biyo bayana ya ce musu. "Ku kyale ta." "Tow!" Haka na shiga dakin da abincin na ajiye. "Dama kin zo da abinci ne?" "Eh security din kofar dakin nan suke dubawa ko an saka wani abu a ciki." "Ayya ai bani da haufi zaki saka wani abu ..." "Hajiya mutum mugun icce " d'ago kai nayi na kalle shi ya watsa min harara. Dauke kai nayi ina jin zafin haka ba yadda na iya, ina bude abincin kamshin ya cika ko ina. "Lallai ke yar Nigeria ce." Murmushi nayi na zuba mishi abincin, sannan Chairman ya d'aga shi zaune yana mishi magna kasa kasa. Shi kuwa dariya yake yana faɗin. "sai kayi ƙoƙari." Hajiya na mikawa flat din ta fara zata bashi. "Ki bawa Zahra ta bani dai." Tsaki daya cikin matan dakin tayi, sannan ta mike zata fita."Anisah meye haka?" "Waye ya sani ko a harkar banzan shi da ya saba ya kwaso kara da kiya shi." Kallonta nayi sai bance kome ba, na cigaba da bashi abincin, turo kofar dakin aka yi wata budurwa ce, me sanyin murya ta shigo, d'ago kai nayi ina kallonta. Ban da akan idanuna Munaisah ta bar camp ba, da zan iya rantsuwa Munaisah ce a gabana. Jikina kamar an jona min wuta, haka nayi ta bashi har ya koshi. "A ina kuka samo sadaka yalla?" Inji Yarinyar. "Wani irin magana ne haka?" "Eh tow laifi ne don naso sanin a ina aka kwaso mana iri." "Kanwata ce!" "Au sai yanzu na gane ma'anar sunan Uba Teresa da Hamma Abdul yake faɗa, ashe kalandangi aka samu mana. Yarinya taga dan beauty an makalewa." "Matsalata dake baki iya tauna magana ba, daga dabi'arka ake fahimtar daga inda ka fito." Inji Hajiya. "Hajiya gaskiya ta faɗa, mata dubu nawa suke." "Amma ai naga ita me maganar bata kai, Zahrah kamun kai ba, Zahrah tazo nan ne don ni na kirata. Sannan ita ba ballagaza ba ce, irin wasu matan da suke bin namiji suna so yana musu wulakanci. Zahrah first class ce bata bukatar sai tabi namiji ya sota, ita maza suke bi don taso su. Kun fahimci karatun ko na karo muku aya?"inji Amaan din, ganin zasu samu matsala akai na, na mike tare da cewa. "Ya Amaan Allah ya baka lafiya, zan tafi daukar Amirah a makaranta. Hajiya Allah ya bashi lafiya." "Amin Zahrah." Na saka kai zan fita. "Karuwai ai basu da maraba da macizai, Hajiya idan." Idanuna ne suka cika da kwalla na ce mata. "Ke mace ce, kuma wata rana uwa, kada ki kara jifar wata da irin wannan kalaman.... 300₦ 0016341139 unity bank zahra'u yahaya Ali Katin MTN 400 #Mai_Dambu ce [5/29, 07:47] Hlm: BHB247 Tun daga lokacin na fahimci daga Hajiya, sai jarababbiyar tsohuwar nan suke masifar kaunata, sai wata da babu ruwanta da ayi da kar ayi, amma kuma sauran kiri-kiri suke kirana da yar iska me bin maza, na makalewa dan uwansu. Wani lokacin idan naje asibitin sai su hana ni shiga, haka yasa na hakura da zuwa tare da kame kaina, tunda ba dole ba ne. Sannan nayi apply wani kamfanin, a nan cikin Niamey na bar musu nasu kamfanin, don na fahimci ko wasu basu kashe ni ba, takaicin Ba'are family ya isa ya kashe ni, ina komawa wancan kamfanin sai gashi Allah ya taimaka na samu mataimakiyar shugaban tsare-tsaren tattalin arzikin kasa, kuma abin da na fahimta nazo a daidai lokacin da suke bukata ta, sai gashi na samu kawaye da Abokai, haka yasa naji kamar an tsamo ni daga wuta zuwa Aljanna. *** Poland embassy. A hankali take taku kamar me tausayin kasa, idan har jiki da kuɗi suna biyan bukata a tsawon shekarun nan hudu tana jin babu wanda ba zata yi gogayya da shi ba,kai tsaye ta wuce office din jakadan Nijeriya, wanda haka yasa aka bude mata cikin nutsuwa ta zauna. "Munaisah Abubakar Takum." Kura mishi shanyayyun idanunta tayi ta ce mishi. "Ina son visa zuwa Nijar." "Amma." Ya kalleta tare da lashe bakin shi. "Ba zan baka ko sisi ba, haka kuma ba zan baka jikina ba, domin na fahimci baka da lissafi wallahi." "Amma kuma me yasa ba zaki gane yadda rayuwar nan take ba, shi fa kome bani gishiri na baki manda ne?" Wayarta ta dauka ta kira wani layi. "Baby!" "Me kike so?" "Wai sai na bashi " "Waye haka?" Mika mishi wayar tayi, Mikewa mutumin yayi yana faɗin. "Afwan Sir ban san yarinyarka ba ce. An bata kome yau zata bar Poland " Yana gamawa ya kashe wayan yana faɗin. "Shegiya kice bujenki na wasan manya ne." Tabe baki tayi, tana faɗin. "Zan je na dawo ba zama zan yi ba, don ina da mara lafiya." Ta juya ta kwashe kayanta ta yi waje. "Duk da ban yi karatu ba, bana jin xan kare rayuwata a wulakance." Ta fada tana tafiya a nutse, domin wani buri da take da shi ba zata iya give up ba, taya zata ganshi kuma ya zame mata haramiyanta. Murmushi tayi zuwa yanzu ta daina bariki. Mr Paul kawai take tare da shi, shima saboda yana masifar jin dadinta ne, yasa bata rabu da shi ba kuma.yana zuba mata kuɗi. Hatta kudin fansar kanta shi ya bata, ya kuma bude mata manya manyan store na kasuwanci a Poland din. Kuma ya hanata mu'amala da kowa, ya mata abubuwa dayawa. Mr Paul yana cikin manyan attajirai kuma yan kasuwan kasar, shi yasa yake manne da ita. Babban abinda yake so a tare da ita shine ta amince ta aure shi amma kafira taki, haka ya faru ne shekaru biyu da suka hadu da wani wanda ya dace da tsarinta, sannan musulmi kuma dan kasar Afrika ba irin mr Paul da yake kirista ba. Duk yadda taso cire lamarin, abin ya ci tura don ta saka a ranta sai ta mu'amalanci Abdul Majid Mamman Ba'are, don ya mata kuma ko yana da mata ko bai da mata sai ta saka ya aure ta, ta kware a yaudara da iya bibiyar namiji, sai dai har yau idan ta tuna da Zahrah tana jin kamar bata mata adalci ba, sannan itama Zahrar tayi mata laifi da ta bata amana bata cika mata ba, sai dai ita ta koma koda yake ta ji labarin abin da ya faru na tasar sansanin da wani yayi, tasan inda Zuzu take amma bata jin zata iya taimaka mata, domin ta rama abin da Addah tayi masu na lalata musu rayuwa da tayi. *** Baya bata kaɗan, ashe tunda na daina zuwa, Hajiya da Aryan sun yi ta nima na domin har marad'i suka je, aka ce na turo a sauya min wuri amma bana nan, naji labarin ne a bakin Aseem. Bakiɗaya rayuwata ne ta sauya domin kome zan yi ina da masu tsaya min, shi yasa ban wani ji zafin rabuwa da su Ya Amaan ba. Ranar juma'a mun taso aiki, na dawo gida na ji gidan shiru. "Siyamah ina Amirah." "Wai an zo an dauke ta." Ban san lokacin da na mike ba. Kai ban san na fito waje ba, sai da ta biyo ni, bakiɗaya na manta Amaan shi ya sakata a makarantar, kuma da can yana daukota. Ai kuwa kafin wani lokaci na birkice na birkitawa kaina lissafi. Nida Aseem muka tafi makarantar, Allah da ikon shi, muna zuwa aka fara bincike da shigarsu da fitarsu sai ga shi nan, lokacin da yazo ɗaukarta. Wani irin sanyi naji. "Kun gane shi? Sannan shine ya fara kawota ai makarantar shi yasa ba a hana shi daukarta ba." "Kuyi hakuri." Inji Aseem har da yan matan hawaye, haka muka nufi gidansu. Koda muka isa a harabar gidan muka ga yara sun cika, alamun ana wani hidima ne. Shiga cikin gidan nayi, har falon Hajiya. Yarinyar tana gefe can da alamu tayi kuka har ta gaji. "sugrah!" Na ambaci sunanta. Da sauri ta mike tare da nufo ni da gudu, bude mata hannu nayi ta faɗa kirjina. Dariya yaran suka yi, da suke falon daidai fitowar yarinyar asibitin. "Mami muje gida."ta faɗa tana kuka har da shashekar kuka, alamar tayi kukan sosai tun kafin nazo. "Waye ya tab'aki?" A hankali ta bude cinyarta, ja fatar wurin yayi tana me faɗin. "Muje Mami." "Waye ya kona ki!" Na fada da karfin tsiya, ina son Amirah, bana kaunar wani abu ya same ta. Runtsa idanunta tayi taki budewa. "Ni ce wani abu zaki iya?" Na d'ago kai tare da binta da idanu. Bakina ya kasa furta kome, nufarta nayi na kifeta da mari, tare da riko jelar gashinta. "Wallahi kinci albarkacin Amaan, idan ba haka ba da sai na koya miki hankali." Na hankade ta, na wuce. Tare da ɗaukar Yarinyata,muka bar gidan. "Akan me zaki kona mata yarinya?" Inji Aryan da yake saukowa daga wurin Majid."akan me ba zan konata ba, tunda tazo birthday din Mimi ta kwace kawayen Mimi." "Mimin da bata wuce shekaru biyu ba, har tasan kawaye ne? Ke munafuka me bin namiji ya sota, ai wallahi keda Alhajin Allah sai dai ki ga ni daga nesa, munafuka algunguma, ina ke kika ce Aliyu ya dauko miki yarta zaku yi kafircinku shine bari ki toya mata Y'a algunguma idan ma kina haka ne don kada ta samu matsuguni tow annamimiya ta samu domin fadima bata da miji sai Alhajin Allah, doguwar mace ba." "Ni kam Nana me na tsare miki ne?" "Au zagina zaki yi? Waye bai san kaso aurenki kika yi ba, sakarya me kama da gwanki me rangwangwan." Cin mutuncin da Nana tayi mata Allah kadai ya sani, Hajiya ma ta gaji da halinta, haka yasa taki kula su, ai kuwa tayi kuka sosai ita kuwa Nana ta sako Aryan a gaba ya kaita gidan Zahrah. ... Mu daga nan asibiti muka kaita, aka saka mata magani, sanan muka koma gida, a kofar gidan na ga Aryan din da tsohuwar nan. "Zahra'u kiyi hakuri kin ji, wallahi ban ji dadi ba ban san abinda ya faru ba kenan, ai in sha Allah ita da Alhajin Allah sai dai taga ana yi. Me yasa kika daina zuwa wurin Yayanki bayan kinsan ba lafiya ne da shi? Dalilin da yasa ya biya makaranta ya dauko yar jikalle kenan, kiyi hakuri ina baki hakuri da abinda aka miki." "Hajiya ba kome ya wuce ai, don Allah ki ce kada ya kuma.daukarta ba tare da izini na ba, hankalina ya tashi." "Haka ba zai kuma faruwa ba, kin ji." "Fadime me yasa kika bar kamfani " "Ya kake so nayi? IT nazo yi, tunda members na kamfani sunce basu bukata na me zan.yi?" "Shi kuma asibitin fa?" Murmushin takaici nayi, sannan nace mishi. "CEO Aryan Mamman Ba'are, akan idanunka Chairman yasa aka duba abincin da na kawo ko? Sannan akan idanunka sisters dinka sukayi ta bullshit dina, me kake son nayi? Nazo asibitin sun ce kada a kuma barina na shiga gaya min dole ne ni a gare ku." Hawaye ne ya zubo min, "Ni na iya manejin rayuwa, ko babu Ya Amaan ina iya rayuwa na gode." "Su waye suka saka hana ki shiga kamfanin gaya min naje naci kundugurin ubansu." "A'a Hajiya ya wuce wallahi." Haka na shige na barsu a wurin, ai da suka koma gida Nana tayi ta bala'i kamar zata yi dambe. Haka lokaci yayi ta tafiya har na gama IT na, na koma makaranta muka doshi Final year , tunda muka dawo babu abinda ya kuma faruwa sai alkhairi. • Wannan shine karo na biyu da taso ganin shi babu hali, a cikin wata shida. Amma yau da alamu har ta samu shiga. Tana zaune ya shigo, sanye take da doguwar rigar abaya, lokacin da ya shiga office din ya zuba mata idanu, shi kanshi ya shiga wani irin rud'ani don ya zata Zaytoonah ce. "Barka dai Mr Mamman Ba'are, ina farin cikin samun ganawa da kai." "Hmm!" Ya zauna yana jin wani abu yana yawo akanshi. "A cikin wata shida yau Allah ya bani damar ganinka," zama yayi a table dinsa yana kallonta. "Nazo ne akan abinda zamu iya cimma idan ka amince." "Hmm!" "Ina sonka da aure." "Zan gaya miki gaskiya, ni ba zan aure ki ba." "Akan me yasa?" "Don my heart belong to somebody else." "Kada ka saka nayi kisan kai." "Ba zaki iya kome ba, domin Allah yana kare ta a duk inda take " "Kana ja da ni kenan." "Munaisah Abubakar Takum, na jahar taraba da yake Nigeria. Kina da kasuwancinki a Poland bayan kin shiga ta haramtacciyar hanya, sannan kina zaman dadiro da Paul wanda yake son aurenki. " Tafi ta kama tana faɗin. "Lallai na yarda kai na musamman ne." "A haka ba xan auri macen da ta kasa rike kimarta da rayuwarta ba. Kada na kara ganinki a kasar nan." "Sai na binciko yarinyar nan da kake so na aikata lahira." "Ina miki fatan alkhairi." "Kana wasa dani." Wayar Office din ya dauka yayi magana sai ga security suka yi waje da ita. Mikewa yayi yana kallon yadda take masifa. _"Tashi ka taimaka min kada na mutu,ka tashi don Allah zan mutu ka ji._ "yummmy" yaji wani abu yana yawo a jikinshi. A ina zai ganta? Ya ganta shin tana raye ne ko ta mutu. Amma me yasa yake jin wani irin abu akan Fadima? Shafa kanshi yayi idan har wancan yarinyar da a wancan daren tayi faffutukar kare mutuncinta, zata amince tabbas zai aure ta, domin yadda tayi ta gudun ceton mutuncinta ba wai don ta rasa yadda za tayi ba ne, a'a irinsu ƙalilan ne acikin mutane, da duniyar nan akan yarinyar da bata wuce shekaru sha tara ba, ya amma a yanzu yasan zata bawa ashirin da wani abu baya, murmushi yayi yana shafa kanshi lokacin da ya kwanta da ita a asibiti, murmushi yayi yana ji a ranshi tabbas ita ce zata. Iya hakuri da shi ba zai tab'a give up. Zai nemeta ba zai hakura ba. Wayar shi ya ciro ya gwada kiran Umaimah. "Hmmm!" Ya ce mata yana ahafa kanshi. "Ka kira ni ne ka ce min hummmm?" "Dr yarinyar nan fa?" Ya tambaye ta, yana murmushi. "Ka kira ni ka gaya min bakar magana ne?" "Idan na gaya miki fara ci zaki yi?" "Ok sai an jima." "Kin ga labarin yarinyan nake nima?" "Ka je garinsu mana." "Akwai tazarar da yake tsakaninmu ba zai hana ni nimanta ba." "Hmmm, sai ka nimeta ai." "Shugaba." Kashe wyaar yayi don ya fahimci haushinsa take ji, kuma ba zata tab'a tsayawa ta saurare shi ba... A hankali ya wuce waje hannun shi a cikin aljanuh wandonshi, duk inda ya wuce gaida shi ake har ya fito inda motarshi take ya shiga.... 300₦ 0016341139 unity bank zahra'u yahaya Ali Katin MTN 400 07035133148 or 08130269641 #Mai_Dambu ce [5/29, 07:47] Hlm: BHB248 A hankali ya malala hancin motar har ya fita waje, yana fita kuwa ya ga motar Munaisah tana bin bayanshi har ya bar area din kamfanin bata daina bin shi ba, don haka yana isa gidansu kafin ta shiga ya saka kada a bari wani ya shigo gidan, haka yasa koda ya shiga tazo babu wanda ya kulata, dake tana ganin kamar kowa mayen kudi ne, har da fito da kudi ko zasu. Barta ta shiga amma suka bawa banza ajiyarta, ganin haka ta tsaya ko wani zai zo fita ta samu damar shiga gidan, amma babu hali. Haka tayi ta bibiyar shi da rayuwarshi, sannan ta saka a gefe guda ana bibiyar shi, da duk wani motsinshi akan idanunta. Yana sane amma ya share kamar bai san meke faruwa ba, sai da suka samu kusan wata biyu ana haka, ranar yasa aka binciko mishi ita, ya zuba mata idanu. "Na miki gargadi amma kin ki ji ko? Na ce kada na ganki a inda nake amma kamar na b'ata lokacina ne, kada na kara ganinki wannan shine kashedina dake, idan ba haka ba zamu samu matsala da ke, idan na kuma jin labarin kin saka wasu kananun karnukar da kika sa suke bina, zan shafe labarinsu bana son fitina. Sannan ni ba zan aureki ba, kai koda wasa ba xan yi mu'amala dake akan harkar banza ba, na baki shawara kada na kara ganinki. Abin da xan yi na gaba shi ne zan ɗauki matakin da zan baki mamaki" Yadda yayi maganar yasa ya fahimtar da ita shi din ba kamar sauran mutane ba ne, yana da kwarjini da cika idanu, kanta a sunkuye ta ce. "Don Allah ba zaka aure ni ba?" Kura mata idanu yayi kafin ya dora kafa daya kan daya ya ce mata. "Na gaya miki gaskiya ne ko na barki da halinki lokaci ya gaya miki." Hawaye ne y zubo mata tana jan kuka a hankali. "Ina sonka tsakani da Allah, da farko nazo ne ko zaka tayani, amma sai na fahimci kai baka cikin irin wadannan mazajen, amma ba zan tab'a give up ba. Sai dai kamar yadda kace zan nisance ka. Haka ba yana nufin zan rabu da kai ba ne har abada, ina nan akan bakana har sai ka juyo gare ni." Bai ce mata uffan ba, haka ya mike ya bar inda aka haɗa su." Ya biya kudin abin da ta sha, yana barin wurin ta fashe da kuka, sosai tayi kuka sannan ta saka sunglass ta fito daga gidan cin abincin. Motar da take kula da zirga-zirganta, ta buga tare da fadar ya kaita hotel. Can ya kaita ta kira yaran da ta saka suke mata aiki ta saka su daina bibiyar Majid din, amma ta basu wani aikin saka idanu akan wata mace da yake tare da ita. Sannan a daren ranar ta bar kasar abinta bayan ta tula musu kuɗi. • Zaman da nayi a Ba'are Company yasa ni kara sanin abubuwan akan tattalin arzikin kasa da na duniya, haka yasani nutsuwa na rubuta project me kyau ta yadda zan zama zakarar gwajin dafi. Buga kofar falo akayi "Na'am waye?" "Baƙo daga Niamey." Rufe bakina nayi tare da shiga daki da gudu na dauko hijab har kasa, na fito da gudu na buɗe kofar. "Hamma Amaan!" Murmushi yayi me haɗe da dariya. "Dubeta a cikin hijab sai ta dace da Mar'atus saliha, bani hanya na wuce." Ba shi hanya nayi ya shiga, ina dariya. "Kai Masha Allah, ashe anan kike raye shi yasa kika rena abin da GOLDEN EMPIRES suke baki." Kallon Laptop din gabana yayi yana faɗin. "Ya Salam, apple laptop." Ya faɗa yana daukar laptop din, wuce kitchen nayi na kawo mishi ruwa da kayan motsa baki, sannan na koma na had'a mishi abinci na kawo mishi wayar shi ce tayi kara,.naga ya rubuta. *Captain* dauka yayi ya saka a hand free. "Soja ya dai?" "Ina kake yanzu?" Dariya yayi ya ce mishi. "Ina marad'i tare da kanwata." "Kai Amaan baka jin magana, ita yarinyar nan ko mayya ce sai haka, kuma ka zauna a gidan gani nan zuwa kada ka sake ka bar garin nan." "Tana jin ka kana kiranta mayya, babu adalci fa." "Tsuk!" Ya ja tsaki tare da kashe wayar, murmushi nayi tare da zama a gabanshi. "Ka sha hanya ci abinci." "Ba zan ci ba, ina Amirah?" "Sun tafi islamiyya." "Masha Allah!" Ya fara cin jollop din cus-cus da nayi, wanda yaji kayan kamshi da na lambu. "Ko zaki yi min alfarmar yin abinci ga wancan international tuzurun?" Don kada yace ina da bakin hali yasa nayi shiru amma nasan halin Chairman ba lallai ya ci kome ba."tow!" Haka na wuce na fara aiki muna hira sama-sama, ina da miya da kome, grill kifi nayi. Sannan na dafa white rice with coconut da vegetables, miya kuma na fitar da shi a frij kafin su zo nasan zai narke. Sannan na fito na wuce dakina, nayi wanka tare da gyara jikina na fito muka cigaba da hira. "Kina da plan ne idan kika gama karatunki?" "Eh ina da plan A&B plan A zan koma Nigeria na bar wani abu zan koma, idan ban samu damar haka ba, zan koma plan B zan nime aiki anan marad'i." "Ga Alfarma ina nima a gare ki, offer na sama miki, daga kamfaninmu. Na zama sakatariyar Chairman."ware idanu nayi, tare da cewa. "A'a Ya... Hamma Amaan." "Zaki iya mana, alfarma nazo nima kina da baiwar da zaki iya cimma abubuwa dayawa, Majid yana bukatar taimakon wanda yasan harkar tattalin arziki da cinikayya, ke kuma tattalin arzikin da cinikayya kika karanta, idan har muka dauke ki aiki a kamfanin, zaki taimaka sosai." Gyara zama yayi bayan ya cika bakinshi da cus-cus, ya ce ."nasan zaki yi mamaki, Hajiya tana da sakatariyarta, Mama Salamatu shi kuma a lokacin shi yaki yarda da kowa gani yake kamar za a iya cutar da wani na shi, soja ne shi kuma likita Aryan kuma injiniya ne, dukkan mu idan kika cire Hajiya kowa da abin da yake so,kin ga har yau kamfanin na kwan gaba kwan baya, please ki taimaka ki amshi wannan offer din please " ya faɗa kamar zai yi kuka. Mikewa nayi zuwa kitchen na sauke abinci, na juye tare da zubawa a kula na dawo, ina murna na rabu da fitina ashe fitinar nan na bibiyata. Zama nayi a sanyayye na ce mishi. "Hamma!" "Don soyayyarki da Annabi ki amsa, don Allah, don darajar iyayenki." Hawaye ne ya zubo min. "Abin da yasa board da Sajjid suna kokarin tasawa dole su zasu bada sakatariyar ta gefensu, ni kuma da Hajiya mun shirya niman haka daga gare ki. Kina jin turanci, sannan nasan Faransancinki ma ba laifi, duk inda kika shiga a duniya zaki yi gogayya da takwarorinki don Allah, nasan munakisar da ake shiryawa amma idan na faɗa rayuwarsu Majid ce a hatsari, kuma ke kin san da haka, ƙoƙarinki shine ki fitar da kamfanin kunya. Nasan is too hard for you, amma zaki iya You can do it." Haɗiye yawu nayi, tare da sunkuyar da kai babu wanda ya tab'a niman wani abu naki, "Hamma, kasan Chairman ya tsane ni." "Wannan matsalarshi ce, aikinki kawai ki tsaya akan abin da zaki yi, ni kuma zan sha kan kome dan banza me taurin kan tsiya, idan haka soja yake da taurin kai Future child dina ba su yi soja ba." Ya faɗa yana dariya. Kafin ya shiga rarrashina, yana bani baki yana kara tabbatar min ni alkhairi ce tunda ya ganni. - Zuwa karfe shida na yamma suka iso shida bindinsa, murmushi a fuskata na amshi Aryan, lokacin da suka shigo falon sun samu Amaan yana cin dan wake shi da Amirah da take mishi hira. "Ku zauna kun tsaya kamar a bakin daga." "Kai bana son iskanci tashi zamu yi mu bar garin nan." "Bayan kunci abinci ba" ya faɗa yana kara zuba dan wakenshi a cikinsa. "Waye zai ci abincin." Inji Chairman, gyaran murya Aryan yayi yana faɗin. " Ta wannan bangaren gaskiya ba zan iya bin ra'ayinka ba, a zubo min." Haka na kawo abinci na shirya musu, Aryan yaci abin shi, har da cewa. "Idan da hali a zuba min dan wake na, a takeaway nayi gida da shi, shinkafar ta cika min cikina." "Tow!" Haka na dauko wata kyakkyawar kula na zuba mishi, tare da kayan makulashe, ana kiran sallah suka mike. "Zan tafi, ina kara tuna miki girman alƙawarin da kika ɗauka." Gyada kai nayi bance kome ba, saboda irin kallon da Chairman yake min har cikin jikina nake jin kallon irin kallon tsana da b'acin rai da fushi ne. Duk sun fita ya rage sai shi, fisgo hijab dina yayi yana huci. Jikina ne ya fara kyarma, na sunkuyar da kai kasa. "Laaa Mami Uncle yana miki kallon kud'a." Sake ni yayi yana me nufarta. "Ina Babanki?" Da sauri na janye ta, ina shiga gabanshi. "Don Allah kada ka saka mata sunan da bata san da shi ba a baki, don Allah kada kasa ta tambaye ni kome don Allah." Murmushi yayi yana mikewa yana kallona daga sama har kasa, "kada ta tambaye ki Babanta?" Hawaye ne ya zubo min. "Amma na had'aka da Allah ko?" "Tow ki fita daga harkar Amaan, duk kudin da yake samu yana spend din shi ne akanki ko? Me kike bashi yake...." Ban san ya aka yi ba, sai dai na tsinci kaina da hankade shi ina me jin takaici na ce mishi. "Out!" Na daka mishi tsawa. Ware idanu yayi yana kallo na, nace! Kayi sa'a ban yanke ka da mari ba, shine kawai." Na nuna mishi waje, ya fita sannan na bi bayan shi. "Ki fita hanyar Dangina!" Banza nayi da shi domin bani da lokacin shi.har wurin motar na raka su sai na tuna ina da Dambu nacewa Hamma Amaan. "Don Allah minti biyar!" Na shiga cikin gidan da sauri na kawo musu bokiti biyu, na mika mishi da yake gaba ban bawa Amaan ko Aryan ba, shi na cusawa. "Hamma Aryan a kaiwa Nana daya, Hajiya daya." "Sannu da ƙoƙari, mun gode." Daga Ni har shi hararar juna muke, har suka bar gidan. "Ni sa'arta ne da zata zuba min kayan a jikina!" Ya faɗa yana hararar Aryan. "Tow Hammayo ya zata yi. Kawo na ajiye maka." Garin mikawa Aryan dambun ya buɗe, kamshin ya daki hancinsa. Wani irin yunwa ne ya taso mishi. Muzurai ya fara yi yana jin uwar hanjin shi tana murdawa. Mikawa yayi tare da kamewa shi nan, kamammen mutum, amma ina dama can dan almajiri yace. Iya yunwa bata da hankali, iya yunwa taci mutum tara, haka Majid yayi ta muzurai yana haɗiye yawu. "Idan ka kai mu airport, zamu tsaya muci abinci." "Ni dai na.koshi, dambun Hajiya zan ci." Inji Amaan, "nima ga danwake na ya ishe ni." Shiru yayi bai ce kome ba har suka isa airport, soft drink. Ya sha amma bai ji kome ba, fakar idanun Amaan yayi da suka wuce sallah, ya dumbuli dambu ya cika a bakinshi ya haɗiye dakyar, ya kara dumbular wani zai kai baki aka ce mishi. "Mr Mamman Ba'are, kaci a hankali zan yi kamar ban ganka ba." Kunya ce ta kama shi ya haɗiye da kyar, kamar ya bude kasa ya boye kan shi, Aryan ya koma can wurin sallah, yana dariyar Majid. Dakyar ya lallaba kunyar shi yaje yayi sallah, sannan suka bar marad'i yaki yarda ya kalle su, sai dariya suke suna hirar su kamar basu san da shi ba. "Aryan kaci dambun nan ne?" "Eh!" Ya faɗa yana kauda kai, don yasan Majid ba zai tab'a cewa kome ba. Sai da suka iso gida, Aryan ya bawa Amaan labarin abin da ya faru, ai kuwa suka kwashe da dariya har da ta fawa. Tsarguwa Majid yayi ya buga tsaki tare da haurawa sama, yasan ba mutumci ne da su ba, ai kuwa yana haurawa suka fashe da dariya....... 300₦ 0016341139 unity bank zahra'u yahaya Ali Katin MTN 400 07035133148 or 08130269641 #Mai_Dambu ce [5/29, 07:47] Hlm: BHB249 _AUNTY UMMIE DAI AUNTY DAI, TAYA ZANCE NAFI SON YAN AREWA DAKU ❤️😭🙄 INNALILLAHI'WA'INNA'ILAIHI'RAJI'UN_ Dariyar su yasa Hajiya nishadi domin ta bude idanu ta kalli yaranta cikin farin ciki shima arziki ne, ba za ta tab'a manta wannan lokacin ba,haka yasa take murmushi. "Gulmar waye kuke?" Dariyar suka sake fashewa da shi, Amaan ya ce. "Mutum idan junarshi munafurci ne, ai zai gani a kwalarshi. Ina dalili kaci abinci ka tsaya sanabe, karshe ka kare da ɗaukar abu kana ci a boye." "Bana cike da munaurci, kun zauna kuna gulmar shi idan ba tsoron ba kuyi a gabanshi mana!" Watsewa suka yi suna dariya don yau ba karya Majid ya saka su dariya. Haka suka tafi washe gari. Karfe biyu na rana, Anisah da suka kulle kansu a matsayin o gidan suna hira da Hajiya take tambayarta. "Hajiya naji board members suna maganar samar da sakatariyar ga Hammayo kuma baki ce kome ba" Murmushi Hajiya tayi tana faɗin, "Duk abinda suka yi daya ne." Ware idanu tayi tana faɗin. "Hajiya amma kuma haka za a bar su." "Wa kike so a kawo?" "A kawo me hankali namiji da zai iya fahimtar Hammayo." "Meye Hammayonki ya karanta?" "Medicine!" "Wani aiki yayi?" "Soja!" "Yana da kwarewa ne a aikin kamfani?" Ta girgiza kai. "Masha Allah, me yasa kika ci mutuncin Fadime?" Tsuru-tsuru tayi tana wulli-wulli da idanu, kai Hajiya ta iya kai hari. "Ba ki bani amsa ba?" "Hmm!" Anisah ta faɗa. "A jami'ar da take tana jan ragamar ajin ne a matsayi na biyu, ana saka tsammanin idan ta gama zata fito a first class, kina tsammanin kawai haka take kara zube? Ni a kaina ma fatan da sonta Amaan yake da ni zan tsaya mishi ya aureta, shine don rashin kunya da rashin mutunci kika yi ta cin zarafinta a kamfanin ko? Ai kome ya dawo har kunnena." Ta kunna wayar hannun ta, ta nuna mata. Ranar da suka ci Mutuncin Zahra a kamfanin lokacin da ta je cin abinci, suka watsa mata abinci ajiki sannan suka zage ta har da cewa me bin maza, magana iri da kala, ita kuwa bata ce kome ba. Har suka gama. Don wani irin girmansu da jinsu take a zuciyarta. Tana jin kamar idan ta rama zata iya yin abin kunya ne yasa bata rama ba, kuma ta yanke hukuncin barin kamfanin. "Baki ji kunya ba? Kin ci mutuncinta a madadin ta rama, ta wuce bata ce miki uffan ba. Ke har wani alfahari zaki yi da dukiyar Ba'are me hana barci. Tashi ki bani wuri." Tashi tayi kamar munafuka, tana share hawaye don Hajiya bata saba yimasu faɗa ba, amma yau da Hajiya tayi mata fada sai take ji kamar zane ta, take don shagwab'a haka ta fito tana kuka, a bakin kofar fita suka hadu da Nana. "Uwar algungumai me aka miki kike kuka?" Ta tambaye ta fuskarta a had'e, dake wawuya ce ta shiga bawa Nana labarin har da kiran Zahrah mayya bata rufe baki ba, Nana ta tsinke ta da Mari, "Yar bakinciki, shine kike tsammanin zan goyi bayanki Allah sarki Zara haka don ubanki na gaya miki sai na ci ubanki akan Yarinyar da nake Addu'a Alhajin Allah ya auro min ita." Yadda Nana take bala'i sai da Anisah tayi danasanin gayawa Nana, ita a tunaninta Nana zata bi bayanta su zage Zahrah sai akayi rashin dace Reshe ya juye da mujiya. Haka ta bar gidan tana kuka wiwi. Tare da kiran Hammayo ta gaya mishi rarrashinta yayi suka rabu lafiya. Falon Hajiya Nana ta shiga tana haki. "Sa'adatu me kuke nufi da Alhajin Allah da Zahrah matar wata." "Hajiya ya kike so na ce miki." "Ya kuwa zaki ce min, bayan yanzu naji wannan me kama da mujiyar tana faɗin wai ta tozarta Yar baiwa Zahra." "Nana kin ga yarinyar nan, aiki tazo yi bamu san asalinta ba. Shakuwa ce irin ta" "Jini! Yarinyar nan ina jinta kamar Jamilah, yanayinta da sanyin halinta yana min kamar da uwar Jarabibiyar Yarki, kanwarki Aminatu." Gaban Hajiya ne ya fadi, wannan maganar Nana ya tab'ata. Sai yanzu ta kara gano yanayin yarinyar. "Allah sarki kama ce!" Ta fada a fisge, don ita kaɗai tasan me take ji, Nana dai ta gama mitarta ta fita, a hankali Hajiya ta dafe kanta tana jin wani irin yanayi. Har wani jiri -jiri yake ɗaukarta. • Wasu lokutan ana iya amfani da kai don cimma wasu abubuwan, wani lokaci kuma sai ka ga wani abun yazo maka kamar sauyin yanayi. Haka yasa na tsaya da addu'a akan zabin Allah maɗaukakin sarki. Haka na mika lamarina ga Allah, domin ina matuƙar son Allah ya shiga lamarina, nasan shi ne mai kowa mai kome, har azumi nake domin facing Mr Chairman don Allah ya gani bana son fitinar shi. ShiYasa nake ta addu'a Allah ya bani hakurin zama da shi. Haka muka fuskanci final exam dinmu, wanda daga shi bana jin zan kuma dawowa makaranta sai karbar result. Haka muka yi ta fama har muka gama, bayan na gama na shirya Amirah na gayawa Aseem a waya, ya shirya min tafiya Nigeria. Tunda na fara shiri ba kama hannun yaro, domin har taraba nake son zuwa na duba Ummi ko ta iso gidan Ya Babangida. Haka muka kwashe kwanaki muna shiri kafin ranar wata Asabar muka bar marad'i, ni kan ma tafiyar mota naso muyi yaki ya nima min ticket, muka bi jirgi. A Kano muka sauka, daga nan na sake sayan ticket din yola. Lokacin da muka isa jikina yayi laushi, hotel muka wuce muka kwana domin ba zan ɗauki Yarinyar mutane izuwa taraba a dare ba, na daina wannan tafiyar ƙaddarar, washegari muka shirya cikin riga da wando rigar pink wando blue, sai bam da na sakawa Amira ni kuma na daura farin abaya, sannan na wuce na riko suitcase ɗinmu muka fito, Amirah tana rike da teddy bear dinta, gashi na mata kalaba, an jera bead a kitson. A hankali na bude kofar, ta fita da gudu yarinyar tayi kyau so much domin idan ka kalleta sai kaji a ranka tayi maka, haka na fito na ja musu kofa, ashe ita tana fita da gudu ta iso babban falonsu tana d'aga min hannu, d'aga mata hannu nayi nima, ina murmushi. Wayata ce tayi ƙara na duba kafin na d'ago naji ana faɗin. "Subhanalillahi. Baki ji ciwo ba ko?" Kallonshi tayi ta juya tana kallona, dariya tayi tana faɗin. "Daady ban ji ba." Ta mike zata kara gudun ya rikota, murmushi yayi yana faɗin. "Me kike so?" Isowa nayi nace mishi. "Kayi hakuri tayi maka barna ko?" Mikewa yayi yana faɗin. "Yarki ce?" Gyada kai nayi ina faɗin. "eh Amirah!" Daukarta yayi yana faɗin. "Princess ko!" Gyada kai tayi, zuwan wasu mutane guda uku, daya ya ce mishi. "Yallabai Madam ce da Magajiyar Lamido?" A hankali ya juya yana kallona, "A'a princess buge juna muka yi yanzun nan, na zata ma ta ji ciwo ne." "Ban ji ba Daady." Murmushi yayi ya ajiye ta yana faɗin. "Gaskiya Malama ki kula da ita, ina sonta kamar tsokar da take kirjina." Ya faɗa yana shafa kanta, "yarrrrr!" Naji wani irin abu ya taso min, "in sha Allah zan kula da ita." Na fada hannunshi ya saka a cikin aljuhu ya ciro wani kati ya mika min, sannan ya dubi daya daga cikin mutanen shi. "Ka buɗe aljihun motar nan ka bawa princess bunch na dubu dari biyu ta sha chocolate." "A'a yayi mata yawa mun gode ma" "A'a nayi mata kyauta ne as my own kada ki dawo min da shi. burina Allah ya bani kamarta ma, amma Allah ya bani ya amsa tare da uwar ma." Ya faɗa cikin yanayin damuwa yana sumbatar goshinta. "Bani number ki." "Mu baki ne daga Nijar, zan baka Number nan da na can." Na mika mishi wayar. Haka ya saka ya kira ni, "ki saka Su'od Khabir Lamido.." Murmushi nayi na saka SK Lamido, ina faɗin. "Amirah ki cewa Daady zaki tafi " "Daady zan tafi!" Ta rungume shi tare da sumbatar goshinsa, dariya yayi yana faɗin. "Zan yi kewarki." "Nima Daady!" Haka muka rabu waɗanda basu yi niyyar rabuwa ba, har wurin mota ya raka mu ya bata kuɗi me yawa, ya saka aka.kai mu tasha. Haka muka bar Yola cikin wani irin kewa, kamar me Yarinyar nan Amirah abu abu ba sai ta ce Daady, abu ba abu ba Daady gata da farin jini kowa ya ganta sai yayi magana, ina tofa mata addu'a. Lokacin da muka isa taraba gidan Yaya Babangida muka fara nima dakyar na samu gidan shi. Ranar kwana muka yi muna kuka, da nake basu labarin abinda ya faru kowa sai da ya sha mamaki, da nazo ba da labarin Zulaihah da yadda ta tafi bamu gana ba, yayi min ciwo, ama ban gaya musu yarinyar gabana Yar ta ce ba, . "Ban san inda take ba, kuma ko da na sani ban san me zance mata ba, domin ta tafi ta bar ni da kewa, Alhamdulillahi na rayu a nijar cikin farinciki." Na basu labari amma ban basu labarin abinda ya faru damu da abinda Addah tayi mana ba. Haka na kwana da farinciki, washe gari tun kafin ka tashi na samu an gama mana kome yau gani cikin gatanmu. Naji dadi sosai. Bayan nayi wanka na saka riga da zani na karya kallabi, ina zaune aka kawo min abin karyawa, shima Yaya Babangidan yana fama da rayuwa ga iyali nan matan shi biyu. Lokacin da ya gaya min Ummie bata dawo ba, na kadu sosai domin nasan tace zata dawo no matter how. Hawaye ne ya zubo min don tausayin Yakumbo da ta nemi na dawo mata da ita gaban Yayanta, haka na wuni suku-suku da yamma ya ke gaya min can jenuwa, babu yan uwa don haka babu amfanin zuwa. "Dangin Mamana ba su zo ba?" Girgiza kai yayi min. "Babu wanda yazo sai dai Baffa'm ya gaya min cewa Mamanki yar Marwa ce. Yar babban gidane kakanki yana nan a raye yana koyarwa." Hawaye ne ya kuma zubo min,wannan shine karfin dawowata Taraba amma babu wani nasara. "Zan nime ta in sha Allah" na fada amma tabbas ina cikin damuwa sosai. Kudin da SK Lamido ya bani shi na ɗauka na bawa Ya Babangida ya sayi kayan abinci, hmmm ko kunsan bawan Allah nan amadadin ya sayi abinci, sai gashi ya buge da karo aure. Satina daya na bar garin, kullum waya muke da SK Lamido musamman shi da Amirah, idan suna hira kamar wanda suka saba da juna na tsawon shekaru. Lokacin da nace zan dawo ya turo min da kudi, wai nayi tsaraba haka na yi ta mishi godiya. Zan dawo Nijar tare da fatan Ummie da Addah zasu dawo nasan Allah zai hada mu. Haka na tawo da tsaraba har da madara aka dafa min na tawo yola, daga nan muka tsaya SK Lamido da Amirah suka yi sallama, da kaya niki-niki haka muka tawo a jirgin Kano, da yamma jirgin nijar ya cilla mu marad'i. Kai jama'a nayi kewar garin nan mutanen Nijar akwai amana, nagarta da aminci irin na mutanen da. Bayan mun iso ne na kira Sk Lamido da layina na nan Nijar, sannan na kira Ya Amaan na ce mishi. "Zan saka maka kindurmo aje a amsa a tasha." "Wow kin tafi Nigeria kenan!" Ya faɗa, "eh, jiya na dawo." Sama sama.muka yi magana sannan muka kashe wayar, washe gari na kai jakar tasha, bayan yayi kankara aka wuce da shi Niamey. Lokacin da ya isa ya kira ni, tare da cewa. "Bakauyiya da kina Whatsp da kin ga yadda kowa yake sha." Dariya nayi kawai nace miishi. "Hmm! Ni bana son damuwa ne." Na fada ina dariya, * Amaan bai gayawa Majid cewa daga Zahrah ba ne, a'a kawai saka Hajiya yayi ta musu dambun gero wai na a kawo mishi kinda...... Majid the king of dramatic 🙄 300₦ 0016341139 unity bank zahra'u yahaya Ali Katin MTN 400 #Mai_Dambu ce [5/29, 07:47] Hlm: BHB250 Lokacin da aka dama furar har asibiti Amaan ya kai musu shi da Zaytoona, suka sha har da santi, shi dai bai ce kome ba sai dariya da yake yi. "Amaan babu kari ne?" "Yana gida idan ka dawo sai ka sha." "Tow me yasa ka kawo min kad'an?" Harararshi Amaan yayi yana faɗin. "Kuma ajiye ni kayi da zan na maka hidimar kawo maka abinci?" Banza yayi da shi. "Maganar gaskiya kinda din nan ya min dad'i." "Ai fa!" Ya faɗa yana kunshe dariya, haka ya zauna har Majid din ya gama suka dawo gida, ya nufi kitchen din Hajiya yana dube-duben kinda. "Ai ba sai ka duba ba, bari na duba maka." Haka ya dauko mishi, Hajiya ta kara gyara kindirmon har da kwakwa da dabino, mutuminku yasha tass abincin da bai ci ba kenan, ya kuma diba ya kaiwa Nana, kallonshi tayi tana faɗin. "Ai Aliyu ya kawo ashe yarinyar nan yar arziki ce?" Zama yayi yana ajiye mata kofin da kunshin kilishin da ya sayo mata. Fuskar shi dauke da son jin karin bayani yake kallonta. "Yarinyar nan dai da Aliyu yake tare da ita, ta marad'i nan." Ta shiga mishi bayani, ai Zahra ce ta dawo daga Bauchi ta kawo musu kindirmon. Wani irin abu ne ya tokare mishi kirji, ya mike fuuuuuu ya nufi gidan Hajiya. "Ka ji da shi dai Gulmamme!" Nana ta ja kunshin kilishin ta fara ci abinta, tana kurbar fura me sanyi ina zata iya da takaicin Majid, don ta lura babu babban dan hassada irin Majid, ita bata ga wani illa akan yarinyar nan me dan karen kirki ba. Tsaki tayi daidai shigowar Hajiya Hadiza, "Hajiya Nana." Wani haɗe rai Nana tayi tana faɗin. "Wannan dai mugun hali ne da mugun abu, taya zaki tawo babu labari." "Ayya Nana don nazo ganinki!" "Ina Abdul Majidu, ina son abin duniya ya rufe mishi idanu, a tow ga Alhajin Allah nan baya gajiya da hidima da ni." "In sha Allah zai yi hidima dake."ta faɗa tana rarrashinta. • A can gidan Hajiya kuwa,Majid yana shiga ya kurawa Amaan idanu. "Wato kai da hannunka zaka ciyar dani guba." "Innalillahi'wa'inna'ilaihi'raji'un! Nana ta gaya maka ne?" Ya tambaye shi yana zaro idanu, cire takalminshi yayi zai bi Amaan da gudu ai kuwa ya koma bayan Hajiya ya tsaya. "Lafiya!?" Ta tambaye su, "Hajiya Fisabillahi har ni Amaan zai bawa abu." "Wani abu ya baka?" "Da yanzu na mutu fa." "Ban gane da ka mutu fa?" "Hajiya wai don Zahrah ta kawo min, kinda mun sha har na kai mishi asibiti shine yaji labarin a wurin wancan tsohuwar yazo yake jaraba." "Yanzu akan kasha furar kake ihu." "Hajiya na zauna a cikin hausawa da fulani yarinyar nan mayya ce." Ya ce ba tare da ya fahimci me zai fada ba. "Kana nufin ta lashe kurwan mu kenan." Yarda takalminshi yayi yana me barin falon ya ce musu waye ya sani, idan ma kun dauko abin da ya dame ku, can zata kare muku." Ya wuce cike da takaici, Hajiya da Amaan da Aryan suka kwashe mishi da dariya, sake hawa yayi kamar yeast. Don dama haushi ya ishe shi. "Hajiya idan ya gano ita ce sakatariyarshi ya za'a yi da shi?" "Ba zai tab'a bijirewa umarni na ba." Murmushi da farinciki suka yi, ana saka ran za ayi board meeting next month, haka Hajiya take jin zata ja zarenta da kyau. Sai dai kuma ba haka abin yake ba, kamar yadda take da karfin gaske akan kamfanin suma masu hannun jari a kamfanin suna da yadda za su yi, musamman da Tani suka sake kulla wani makirci akan wannan gabar, ai sun san Majid bai da experience akan tafiyar da kamfanin idan suka yi nasarar sako sakatariyarshi daga ɓangaren members na kamfanin. Duk wanda aka hada shi da ita zata zame mishi alakakai. Wannan abin sun yi ne a tsakaninsu, amma sun jima suna kullawa a gaban Amaan, shi yasa Shekara ɗaya da aka dauko maganar sakatariya ya zauna ya gayawa Hajiya shirin Sajjd da wasu membobin kamfanin. Idan har shirinsu ya tafi yadda ya dace, ba makawa Majid zai shiga tashin hankali. Domin zasu yi amfani boycott suyi ta Blackmailing Majid har sai ya yarda ba zai iya ba. Wannan yasa da kanta tayi ta bin manyan jami'oin ƙasar tana bibiyar dalibai masu hazaka, har ta samu Zahrah tare da taimakon Hajiya Zainabu Isma'il Wodabbe. Ta hada ta da Zahra sannan bayan sun ga Zahra basu mata magana ba, shine ta tura Amaan, shi kuma yaje bai san shirin Hajiya ba ya dauko Zahra don kanshi. Sai ya kasance daga shi har Hajiya buri daya suke da shi akan kamfanin, kuma lokacin da aka kawota da aikin da tayi ya kawowa Hajiya tare da bata shawarar ko zasu dauki Zahrah a matsayin sakatariyar Majid, duk da itama da nata gudunmawar amma kuma sai.ta biye mishi don kada ya fahimci itama tana ƙoƙarin taimakon Majid, ta bar mishi yayi na shi ƙoƙarin. Lokacin da zai tafi wurin Zahrah a marad'i, sai da ya kuma gaya mata da takardar daukar aikin kuma ta goya mishi baya, ya je wurin Zahran haka yasa shi kara jin lallai yana da abin da zai yi. Murmushi Hajiya tayi a karo na babu adadi. "Kuyi ƙoƙarin tunzura shi yace baya buƙatarta tunda kun ga yadda yake a birkice." • Muna waya da SK Lamido, sosai har yake gaya min zai zo nijar wurin Princess. Don dama ya gaya min akwai aikin da zai kawo shi, amma sai ya fara sauka a Niamey kan yazo mana, nay matuƙar jin dadi don ko ba kome kai ma kana da masu zuwa gare ka. Don ko bayan dawowata Ya Babangida ya ce zai zo amma sai ya samu kudi, na ce mishi idan zai zo ya gaya min kawai na tura mishi kudin zuwa. A wannan rayuwar me ya fi maka dad'i kai da danginka da al'ummar Musulmi da suke yin ka. Haka na sha zaman gida, a lokacin na gama kome, kirana aka yi a makaranta, abubuwa dai har da bikin gama makaranta suka shirya mana. Kasa da sati biyu. Haka yasa muka yi ta shiri,babu kama hannun yaro. Kaina ya dauki zafi bana gane kome sannan babu wanda nake da shi da zai taya ni, na gayawa Ya Babangida halin da nake ciki, a lokacin ya ce zai zo da Amaryarshi, ba karamin murna nayi ba. Haka dake bikin ya rage kwana uku, SK Lamido yazo ai tunda yazo Amirah ta makale mishi, shi kenan na samu hutu na turawa Hamma Amaan sakon bikin gama makaranta, a kan lokaci ya gaya min zasu zo. Haka kuwa ranar bikin duk mun tafi makaranta, Amirah tana wurin Sk Amaan da Hajiya sun zo, uban yan girman kai bai zo ba, abin burgewa har da tsohuwa Nana. Har wurinsu naje na gaida su. "Fadime ya baƙi yi kwalliyar zamanin nan ba?" Ya Babangida da suka gaisa, na gabatar musu da shi a matsayin babban Yayana. Hango Amirah Amaan yayi ya bude baki. Sauka tayi da sauri ta tawo wurina ya dauke ta, dressing ɗinmu iri daya. Don rigima ta saka na saya mata yadin aka dinka mata, har da hular da ta saka. Haka farin code lace din da yake jikina riga da skirt, ita kuma aka yi mata short gown da shi, ba karamin kyau yayi mata ba. "Yar nan, amma kin yi kyau ina ta Addu'a akan Alhajin Allah. Ina ga sai na hada da Umara domin Alhajin Allah kamar an saka mishi hannu akan lamarin aure." "Nana lokaci ne aure da mutuwa, da haihuwa idan lokacinsu yayi sai ki ga anyi?" Haka muka koma rumfa, ni na koma wurin mu,inda muke zaune aka fara gabatarwa har zuwa kan yadda aka kafa makarantar da kome da kome, kafin aka fara kiran department da ɗaliban da suka yi kokari, department ɗinmu ne na uku, ban yi tsammanin za a kira ni ba, sai jin nayi Fatima Abubakar, wani yarrrrr naji wato ni. Kallona aka fara yi lokacin da na mike, na nufi inda pro din yake ya mika min shaidar kammala jami'a, da matsayin First class, wani irin kuka ne ya kwace min sannan manyan kamfanonin irinsu GOLDEN EMPIRES da wasu kamfani suna son na saka musu hannu zasu dauke ni aiki. Sannan batun shaidar halin da Kyakyawar fata da nutsuwa da kamun kai na same shi, haka nayi ta samun kyauta a wurin mutane. Bayan an tashi taro aka yi ta hotuna, ina tsaye Abdullahi yazo, bayan mun gaisa ya mika min wani katon kwando. "Ina taya ki murna, ina Baby Mirah." Nuna mishi ita nayi a wurin SK, shi kuma na shi ƙaddarar kenan ya saka Amirah a gaba su yi ta hira sai ka dauka abin arziki suke fada nan kuwa shiririta ce zalla. Haka aka gama taro. Aka watse Yan Niamey suka koma washe gari Ya Babangida da SK suka bar marad'i, nima kuma saboda rokon da Amaan yayi min na saka hannu zan fara aiki da su, na nemi Aseem ban same shi ba, gidan da ya saya min na Niamey na tattara kayana na koma can, nan din na barwa su Maman Barakatu,da muka sha kuka kamar me. Don shakuwa na kuma gaya mata don Allah idan suna son abu kada ta boye min ta gaya min. In sha Allah idan bai fi karfina ba zan yi. Lokacin da muka dawo Niamey, na samu Siyamah tazo don haka na kwantar da hankalina, na sha barcina da na farka na samu tayiwa Amirah wanka da kome, har Amaan yazo ya kaita makaranta. Sai da na kwashe sati biyu kafin na shirya cikin natsuwa da kamala na nufi hanyar office,sai dai koda naje na samu ana ta bata kashi na bala'i akan me yasa Hajiya munafurce shi ta bawa wata aiki. Nan aka yi ta bala'i, Ni kan office din Aryan na wuce na zauna domin sun san da zuwa na. Ina shiga na samu Jamilah sama -sama muka gaisa, na cigaba da wasa da wayata ina temper running. A fusace Majid ya shigo office din, ya kura min idanu. "me kika zo yi?" Ganin Jamilah a Office din na mike cikin girmamawa, na ce mishi. "Ni ce zan fara aiki a matsayin sakatariyarka." Kura min idanu yayi kafin ya tako gabana. "Nayi miki alkawarin sakawa ki gudu da kafarki." "Allah ya nuna mana." Na fada cikin girmamawa. A fusace ya fita, kallona Jamilah tayi tana faɗin. "Kiyi hakuri, sannan kiyi aikin da Hajiya zata yi alfahari dake, ki tsaya ki cikawa Amaan yardar da yayi dake. Don Allah kada ki bawa wani damar cutar da ahalin da suka yarda dake." "In sha Allah!" Na fada ina kokarin sunkuyar da kai na, "Hamma Abdul Majid yana da kirki, yana da hakuri idan kika gane kanshi zaku zauna lafiya, rashin kirkin da yake yi na dan lokaci ne, idan aka kwana biyu zai sauko da kanshi." Jin ta nake, ita ce hala bata san halin shi ba, amma ni nasan wannan dan bala'in ba zai sauko nan kusa ba, mutum kamar wani muzuru, sai yayi ta niman jaraba kamar akan shi aka fara jidali, ai wannan sunan shi dan balaja'u. Haka tayi ta bani hakuri, har su Amaan da Aryan suka shigo. "Wow kin yi kyau muje na kaiki Office dinki." mikewa nayi muka fito, har Office ɗin Chairman ina bakin kofar office din shi, ina iya hango shi Hajiya tana shafa kanshi, ya lumshe idanunshi, murmushi Aryan yayi yana faɗin. "Kai wannan gayen babu asalin dan takife irinshi, kalli yadda yake wani mashar mashar kaman jikakken zakara." Ai kuwa suka kwashe da dariya. Haka suka gama shakiyancinsu, sannan suka fita da zasu fita ne Amaan yake gaya min. "Zan turo miki dan larai, bai da matsala amma ki kula domin idan yaji haushi yana faɗin zai daku da mutum ne." Murmusa mishi nayi tare da faɗin. "In sha Allah ba zamu samu matsala da shi ba." Ya saka kai ya fita, ina murmushi. Can Hajiya ta fito, mikewa nayi tare da gaida ta. "Ina kwana Hajiya." "Lafiya lau Daughter, ina yar jikata." "Tana lafiya." Na fito daga wurin Kujerar na amshi jakarta. "Allah ya miki albarka, ga Majid nan na bar miki amana, sannan ke mace ce tunda kika iya tarbiyyar Yarinya irin Amirah sugrah, har kowa yana son ɗaukarta. Nasan zaki iya tarbiyyarta min da wancan kasungurmin tuzurgwauro....(Anya babu lauje cikin nad'i a Maganar Hajiya...... 300₦ 0016341139 unity bank zahra'u yahaya Ali Katin MTN 400 0813269641 #Mai_Dambu ce [5/29, 07:47] Hlm: BHB251 Jikina ne ya dauki rawa, tare da kallonta baki sake. "Zaki iya na sani zaki iya, shi ysa nake jin ki a raina." "Idan kuma ban iya ba fa? Idan na kasa na fadi fa?" "Ba zan tab'a zarginki ba, don nasan kin yi ƙoƙari kuma kin yi iya bakin ƙoƙarinki." Hawaye ne ya ciko min,"Kada ki sare ta hanyar zubda hawaye, nasan zaki iya fa." Gyada kai nayi har na rakata, na dawo na zauna ina kallonshi ya juya kujerar shi. Bakiɗaya sai naji na muzanta, haka na zauna yinin ranar babu abinda aka yi, har aka tashi. Washe gari. Da wuri na iso aikin, inda na samu ayyuka da uban yawa. Haka na nasa kaina a gaba da taimakon Aryan na rage aikin, sannan da aka tashi ya ga na ciro yar karamar flaks da cooler abinci na fara ci. "Babu tayi ne?" Diba nayi na bashi sauran, muna cikin ci Hamma Amaan ya kawo wasu files zai shiga office din ya hango Aryan yana cin abinci cikin takaici ya ce mishi. "Kai dai kayi girman banza, ajiye mata abincinta." "Sai kayi kuma!" Haka ya lullube Aryan da faɗa, ganinsu tsaye bakiɗaya yasa shi lekowa yana haɗe rai. "Meye haka?" Mikewa nayi ina goge bakina. "Kayi hakuri sir, kana bukatar wani abu ne?" Zuba min idanu yayi kafin ya ce. "Aikin zama ki tara maza kika zo yi?" Fitowa nayi daga inda nake na tafi bakin kofar na tsaya. "Kayi hakuri Sir!" Tsaki yayi ya shige ciki sake baki suka yi, suna kallon na shiga office ɗin, tunda na shiga nake tsaye, bai ce min ga aiki ba, shi bai kore ni ba. A fusace Amaan ya nufi Office din, "idan baka son tayi aiki da kai yayi kyau, amma batun ka shanyata ai ita mace ce mai rauni. Zaka iya shanya Jamilah ko Anisah, har tsawon mintuna?" "Ka bar kiran Yan uwana masu kamun kai. Hira tazo yi da maza ko aiki?" "Ok idan na fahimta mune baka son mu kulata ok that's fine, amma ka sani idan kasan yadda rana ta fito kasan inda zata fadi ne? Kayi kokarin ganin mu'amalar ka da kowa tayi kyau akwai ranar da kana bin kowa don muradinka zasu juya maka baya. Muje Zahra." Girgiza mishi kai nayi tare fa faɗin. "Na gode!" Haka ya ajiye takardun ya fita, shima Aryan ya shigo cikin Yarensu na buzaye yayi mishi magana, banza yayi mishi. Haka ya fita bai kula ni ba, bai kula kowa ba har aka tashi. Na d'aga kafata na kasa, zama nayi a wurin ina nishi. B'acin rai da tsanarshi suka kara cika ni, haka ya fita ya bar ni a Office din, Dan Larai ne ya shigo office din kawo abu ya ganni ina kokarin tashi. "Zahra'u lafiya?" Haɗiye yawu nayi nace mishi. "Babu kome taimaka min na tashi." Haka ya riko hannuna na tashi, har na fita na kira driven da yake zirga-zirga da ni, a hankali na isa har wurin shi na shiga. Kuka ne yake taso min, amma naki yi har sai da na isa gida, ina shiga dakina na fada ban daki na fashe da kuka, haka nayita kuka karshe hada sallah nayi bayan na fito, tsanar shi ba zai amfane ni da kome ba. Amma don tsana a duniya babu wanda na tsana irinshi. A wurin da nayi sallah a wurin nayi barci, sai dare na farka nayi sallar Magariba da Isha, sannan nasha magani da tea na kwanta, Siyamah tana tare da Amira. Haka muka yi ta gwagwarmaya da Majid, cutarwa irinta bakin mugu babu wanda bai sani ba, har ta kai yana iya saka ni nayi ta yawo a kamfanin wai na kai wasu takardu, sai da takai kafafuwa na har wani irin ciwo suke ban tab'a fushi ba, amma ina yawan kuka domin a gaban kowa disgani yake. Watana uku a wannan yanayin Allah ya kawo min Yazid, kunsan yadda abin yake ne? Idan kana son ka fahimci lamarin shine kayi tafiya a cikin tsananin zafin rana a sahara, kai baka fita ba kai baka cimma tafiyar ba, ga zafin rana ga rashin ruwa kawai sai a fara ruwan sama me karfi a saharar nan,haka Yazid ya zame min. Ranar mun taso ina takawa da kyar ashe sun yi baƙin larabawa daga Algers. Na fito daga elevator. Muka yi kicibis da shi, shi da su Aryan da Amaan. Sun gama meeting ne suka fito. "Zeehrah!" Kunne na ne ya fara shuuuu, na juya abinka da wanda ya gaji ya kuma cire tsammanin ganin wanda ya sani. Kallonshi nayi kafin naji kamar kifi ne duhuwa ne ya kwashe ni, ban san yadda aka yi ba, ni dai Bayan wasu lokuta na farka, na ganshi zaune yana kallona. "kin farka?" Juyar da kaina nayi na fashe da kuka, ina jin kamar raina zai fita. "Kiyi hakuri dominki nazo akan me yasa zaki yi fushi da ni." Sauka kayi daga gadon, tare da niman kayana. Tashi yayi naji ya bani wani irin warm hug, ta bayana "kiyi hakuri kin ji nayi kuskure ni ne ba wani ba ne kuma ba fatalwa ba ne, don Allah kada ki azabtar da ni da fushin ki." Yadda nake kukan ya sashi saki na ya zaunar da ni sannan ya shiga ban daki ya hada min ruwan wanka ya fito yana mai faɗin tashi likita ya ce kina aiki fiye da kima, ke mace ce jikinki baya buƙatar wahala. Ban dakin na nufa, shi kuma ya fita, ina shiga da minti biyar sai aka buga kofar ban dakin. "Karba!" Ya mika min kaya na amsa, na yi wanka na shirya sannan na fito da alolana. Abun sallah ya shinfida min ina fitowa nayi sallah da yake kaina, sannan na fara ƙoƙarin kwanciya. "a'a ci abinci." Haka ya zuba min abinci ya zauna yana bani a hankali. Turo kofar dakin aka yi Amirah ce da Siyamah. "Marhaba ya Sultan Yazid." "Sannu da kokari Siyamah, aikinki yana kyau." Shigowa da gudu Amirah tayi ta rungume shi. "Abihna shi ne ka daina zuwa ko?" Kallonshi nayi ya rike kunnenta yana magana dariya tayi, suka tafa. Ni ya cigaba da bawa Abinci."Abihna Mami ta koma Baby." "Eh she always look like baby ai."tura baki nayi ina faɗin. "Ba zaka daina tsokana ta ba ko?" "Tow Allah ya baƙi hakuri." Shigowar su Hajiya ya sa na d'ago kai.har da shi ma. "Ahh bude baki." Ya damu da ni a gaban kowa zai iya bani kulawa, haka ya saka min tsokar nama, ina rufe bakina. "Baki san likita yace kina skipping abinci ba ko? Kina wasa da cikinki idan ciwon gyambon ciki ya kamaki mu na jikinki mune a wahale oya bude min na zuba miki abincin." Ya faɗa yana kara zuba min, Amirah da take bayan shi ta ce mishi. "Abina idan bata ci ba, ayi mata irin yadda, Ma Siyamah take min, sai ta ce min idan ban ci ba,akwai dodo da zai zo ya duba cikina idan babu abinci ya kai ni duniyarsu, sai naci abinci cikina yayi kato." Dariya yayi ya juya yana kallonsu Hajiya, "Barkanku da zuwa." "Zahrah ya jikinki!" "Inji Amaan, cikin tsananin kulawa, "da sauki." Mikewa yayi ya ce min. "Girl maza ki karasa abincin nan, kafin na dawo." Ya dauki sandarshi yana dogarawa, wani irin tausayinshi ne ya cika min rai. Haka ya fita ya bamu wuri, da yazo fita daga cikin dakin ne suka yiwa junansu wani irin kallo, kafin ya ficce daga dakin. Tambayar ya jikina suka yi, Hajiya take tambaya na. "Me ya faru?" Aryan ya ce mata, "tana aiki sama da tunanin me tunani, bata hutu ga ciwon kafa da take fama da shi." Kallonshi Majid yayi cikin fushi ya ce mishi. "Hammayo ai gaskiya na fada, kawai don son kai da mugunta da ba zaka iyawa wani dan uwanka ba, kana yiwa yar mutane, ni a bangaren zalinci bana goyan bayanka, akan haka kahana Amaan zuwa Office dinka adalci kake yi ko zalinci, ko ina a cikin kamfanin kowa yasan kai azzalumi ne, baka da sani akan kasuwanci bai dace ka zalinci kowa ba, amma kai ita ce abar zalincinka." Yana gama fadar haka ya fita, Amaan ma ya fita ya rage daga ni sai Hajiya. "Kiyi hakuri kin ji." "Ba kome Hajiya." Na fada ina murmushi. Shigowar Yazid ya mika min takardar sallama, "sannunku an sallame ki, kuma sun ce ki huta ko na tsawon wata guda ne, jinin jikinki ya dawo." "Tow aikin fa." "Karatun da kika yi, ba yana nufin ki zama baiwa ba ne, idan kina so idan kin dawo hutu zaki duba aikin idan kuma bakya so, kina dawowa ki ajiye musu aikinsu babu dole." Kasa magana Hajiya tayi, fuskarta ya nuna tashin hankalinta, amma ya xan yi haka na mike tare da kokarin hada kayana. "Babu bukatar kiyi kome." Shi ya shirya min kayana, ya cewa Hajiya. "Ita mace abar tausayawa ce, ba laifi idan ace aikinta take yi, amma Hajiya Zahrah ba talauci yasata amsar aikinku ba, ita kanta bata bukatar kome daga gare ku. Idan yar Uwarshi aka yiwa haka hala sai ya kusan mutuwa." Sannan ya riko hannuna muka bar asibitin, Hajiya. Kallon Majid tayi, da ya rasa meke mishi dad'i. Shi bai ga wani kuskuren da yayi ba, amma kowa yake blaming din shi da kuskuren yarinyar can. Hajiya bata ce mishi cikanka ba,amma ta zuba mishi idanu wannan abin da ya faru sai da Hajiya tayi ta fama da rashin lafiya,. musamman jininta yayi mugun hawa, bata magana balle a ce ta rage wani abu a ranta ranar da ya dame ta da tambayar meke damunta, sai da yayi danasanin tambayar, domin kifa hannunshi yayi a fuskarshi. Hajiya tayi mishi magana ɗaya."idan ka sake yarinyar nan ta subuce daga kamfanin nan, asarar da zamu tafka sai ka rasa inda zaka saka ranka. Mune masu kaso 90, tow ka je ka duba Baitul Malin kamfanin Yan uwanka sun kwashe kaso da rabin dukiyarsu don gudun kada Amaan ya faɗa kan nasu don ya gurguntan duniyarka. Idan har zata iya bada lokacinta domin aikinta ina ga baka bukatar ƙarin haske.." • Sajjid "Goga kaji labarin Yazid yana nan kasar kuwa?"shaƙar hodar iblis yayi yana faɗin. "Koma meye sai na kashe dan iska." Murmusa mishi Nawwas yayi ya ce mishi. "Akwai yarinyar da nake nima, ga hotonta nayi maka alkhairi me yawan gaske. Ina son ka biya ni da wannan alkhairin, ka nimo min ita." Duba hoton yayi Zahrah ce sakatariyar Majid. "Amma kai dan iska ne, Ita yarinyar nan tana wurin Majid da muke Uba daya kuma nima na yake ruwa Ajallo, shi kuma Yazid kasan kanwar mu bata jike." Nuna mishi hannun yayi dungulmi ya ce mishi.."idan har akwai gaskiya a abotar mu, ba zaka ji dadin ganina da wannan abin ba ko?" "Don Allah boye zan san yadda zan kawo maka. Amma me xaka mata?" "Budurwa ce cikakkiya, ina son kafin wani ya fara saninta ni na shanye wannan romon farkon." Dariya Sajjid yayi yana faɗin. "Zaka bani bayan?""kai dai kazami ne, me zaka ji a wurin kazanta?" "Koma me ina son a bani wannan damar." "Zan shirya kome cikin nutsuwa." • Tunda muka shigo gidan, na fahimci lallai Yazid babban mutum ne, domin bakiɗaya unguwar security ne, kuma duk sun yayyame unguwar bakiɗaya baka isa wucewa ba sai da dalili. Cikin gidan muka shiga na sake wanka muka ci abinci, a daren ranar muka bar Niamey. Barci nayi ta yi a jirgi, Umara ya kai ni nayi ibada tsawon sati biyu ina ibada. Bayan mun gama muka wuce Dubai anan muka gama kwanakin mu, sannan muka wuce Nigeria inda muka tafi har Taraba, a Yola muka hadu da SK Lamido, dakyar Yazid ya bashi aron Amira mu kuma muka wuce taraba kwanan mu biyar bayan ya cika Yaya Babangida da alkhairi. Kai bawan nan akwai Alkhairi. Gidan SK Lamido muka sauka aka mana tarban arziki, bayan sun cika mu da hidima. Mamar Sk Lamido har da kukanta don zamu tafi. "Idan tayi hutu xan kawo miki ita Umma." Inji Yazid nasan shi kaifi daya ne, idan ya fada ba zai sauya ba. Daga nan jirgin da muke tafiyar da ita na shine marad'i muka wuce. [5/29, 07:47] Hlm: BHB252 Kwanan mu biyar a can muka dawo Niamey, nayi wani kiba har da kumatu, ni kaina na san na sauya. Sai da yayi min sati biyu bayan yawon da muka yi, ya ce zai tafi ya zuba min idanu. "Zahra, akwai mafarkin da na fahimta baki cimma ba, shi yasa ba zan kawo bukatata gare ki ba. Amma idan har kin cimma ina jiranki, ni me kaunarki ne a kodayaushe. Aikin nan idan bai zama dole ba, ki hakura da shi amma ba zan tilasta miki lallai ki bari ba, don nasan kina da burinki akan aikin."abin da yasa ya fadi haka a tafiyar da muka yi yaga yadda nake sayayyar littafan da suka shafi kasuwanci, haka ya sa shi fahimtar ina son aikina. "A'a..." Sumbatar goshina yayi yana faɗin. "Na sani wani cikin kamfanin ya nemi alfarma ba!" Kura mishi idanu nayi, "Jeki kwanta." Haka na mike na nufi dakin, har yanzu jin dumin bakinshi nake a goshina, murmushi nayi, washe gari da safe ya shirya na rakashi airport suka tafi kafin na dawo bakin aikina, ban san ya gaya musu zan dawo ba, ina shiga kamfanin naga an karbe ni da farinciki godiya nayi na wuce elevator, ina shiga Chairman shima yana zuwa komawa gefe nayi na makure bance kome ba. Har muka isa office ina baya yana gaba, "Oyoyo kawaciya!" Murmushi nayi don na lura dan larai dan iska ne sai ya ce zai rungume ni. Zama nayi a kujerar Office din na fara dube dube. Can aka kira layin office din dan larai yadauka ya kalle ni. "Kiranki ne." Dauka nayi. "Shigo!" Ya faɗa, gabana ne ya fadi. _Kada Chairman dinku ya zame miki dodo babu abinda zai miki, ba zai kuma wahalar dake ba, ki nutsu ki daina rawar jiki akan kowa. Kinji ko* murmushi nayi na ciro hoton da muka yi a Dubai na saka a dest dina, na nufi Office din Chairman. Ina shiga na gaishe shi, bai amsa ba bai kuma d'ago kai ba, *A duk lokacin da ya kiraki kika ga bai da lokacinki, to ki bar office din* kallon agogon hannuna nayi naga lokaci har naci minti biyar. Bance mishi cikanka ba sai jin sawun takalmina yayi zan fita. "Ni na sallame ki?" "Ina kiyaye rayuwata da lafiyata, idan na nakasa kamfaninka bata yi asara ba, Yata da mijina ne zasu yi asarata." Na saka kai zan fita ya ce min. "Ok kice wannan dan kwayar ya zuga ki kenan?" "Duk da shi dan kwaya ne, ya kula da ni kamar yar Adam, innocent kuwa suna kula ni ne kamar dabbobin da suke kiwo." "Zahrah;" ya daka min tsawa, ko kaɗan ban razana ba, "kika ce me?" "Sir idan akwai takura sai na bar aikin ba zaka saka ni a gaba kamar baiwa ba." Na faɗa ina kallon shi don tsanar da na mishi ya gani ba tsoron shi nake ji ba. Kome ya tuna ya ce. "Amma da kika yi tafiyar haka ake dawowa babu sanarwar kin san asarar da muka yi kuwa?" "Dake ni baiwa ce shi yasa ba zan san.asarar da kuka yi ba, sannan ai ko baka sani ba naga staff sun yi welcome din dawowata." Na fada.. "Ki je wurin Aryan ya baki bayanai akwai baki daga lokacin, kamfaninmu yana dab da durkushewa." "Allah ya kiyaye na gaba." Na fada ina barin office ɗin, yayi hakuri tare da rarrashinkansa ne don Hajiya ta kafa mishi sharadi da sai ya kure mata hadda." Koda yake dawowa ta, bai saka na samu hutu ba, amma kuma iskancin Mr Chairman ne bana dauka, duk yadda yaso na dauka naki yana min xan tsayar mishi ta hanyar zan bar aikin babu dole haka yasa shi rage zafin kai ba wai don ya daina ba, a'a sai dun kawai yana niman nasara da biyan buƙatar kamfaninsu. Bani mantawa Hajiya ta bani wani aikin binciken da na gano Amaan yana fitar da makudan kudade a kamfanin duk wasu kwanaki, lokacin da na tura mata ta ga sakamakon sai da tayi kuka, haka yasa take ta bani hakuri ta email dina na dawo kamfanin. Alhamdulilahi daga cikin abin da ya faru Hajiya ta sayar da manyan kadarorinta, ta zuba kudin a kamfanin, haka yasa ni da kaina na bashi shawarar a saka kamfanin a tsarin manhajar play store. Kuma alhamdulillahi, take muka bayyana kudirinmu na duk inda kake a duniya zaka sayi gwal kuma yazo maka. Sannan an rage ma'aikatan da basu da amfani, domin a farfaɗo da tattalin arzikin kamfanin, mun samu nasarar cire ma'aikatan bogi, sai gashi wannan karon manyan kamfanonin sun fara zuwa ana zuba hannun Jari, kai a cikin wata shida kacal ni kaina nasan nayi macen ƙoƙari. Wannan aikin da muka yi yasa shi bamu hutun sati daya. Muna dawowa hutu ya shirya mana tafiya india seminar. Kuskuren da nayi ban gayawa Yazid ba, har muka bar kasar nabar Amira wurin Siyamah da Baraka da tazo karatu. Kwanan mu biyu, a Delhi na fito motsa jiki, don na je wurin ina fitowa na gansu zaune kowannensu sai muzurai yake. Mika min ruwa Yazid yayi cikin kulawa ya ce min. "Shine baki gaya min ba.""kayi hakuri kasan sha'anin aiki." Na fada ina kokarin zama,"idan kun gama seminar ku ina jiranki muje yawo!" "Ok" na fada ina tashi na wuce dakina, kallon juna suka yi, kowannensu yana jin haushi musamman Majid da yake ganin iskancin Mr Yazid ya fara wuce iyaka. Bayan na shirya muka tafi seminar, bamu dawo ba sai karfe biyar, abinci naci da sallah,.muka shiga zaga India ba karamin fusata Majid yayi ba, amma haka yayi hakuri. Ya kira Hajiya ya gaya mata abin da ya faru. "Fisabilillahi Hajiya aiki muka zo yi ko yawo?" "Mijinta ne don haka baka isa raba su ba." Wannan korafin ya mata dad'i, ko babu kome zuwan Yazid zai saka shi hankali. Mukan mun sha yawo, sannan ya kashe min kudi kamar hauka, sai dare muka dawo. Yana ganin kayan da ke jikina ba shi na futa da shi ba, ya biyo ni. Bayan na fito wanka ina goge kaina, ya buga kofar nace. "Shigo" don na saka kaya, kuma ina goge gashin kaina ne. Lokacin da ya shigo yaga ina ta goge gashin kura min idanu yayi. "Ba zan hana ki bin shi ba, amma don Allah kada ki zubar min da mutunci." Ya fada yana kallon yadda nake ta goge gashin. "Idan mijinki ne,.ku fadawa duniya amma haka." "Ban gane ba?" Rufe kofar yayi yana dafe goshinsa, ya kwafsa. Yana fita abun ya bani dariya, na kwanta abuna nayi barci Bayan nayi waya da Siyamah da Baraka da Amirah, kashe wutar dakin nayi muka fara waya da Yazid. Ina dariya, akwai abubuwan da ba zan manta ba, yau nayi su kallo a cinema, na tafi wuraren tarihi, Har barci yayi gaba dani, da safe ina tashi na nufi banɗaki nayi wanka da alola da sallah, na samu an kawo min abin karyawa, naci kadan domin Yazid ya gaya min yau zamu karya tare. A dakin na bar mishi kome nayi tafiya ta bayan na ajiye mishi yar ƙaramar note, don na san sai sha biyu zamu shiga seminar. Don haka na tafi muka karya da Yazid a wurin cin abinci na alfarma. Lokacin da Majid ya je duba ta ya samu ta ajiye mishi yar note. *zan dawo kafin mu shiga mun fita da Sultan* Bai ce kome ba amma abin yana kona mishi rai, bai wani nuna a fuskarshi ba juyawa yayi ya fita, karyawan da bai yi ba kenan. A daddafe aka gama seminar ni da Yazid kamar kada mu rabu, tunda muka bar Delhi yake dan jana da hira na ga ni ba fahimta nake ba, barci nayi na bar shi. Sai dare muka isa Abu Dhabi, ko awa bamu yi ba muka wuce Nijar, a gajiye suka.kai ni gida, tunda nayi salolin kaina barci yayi gaba da ni. Tunda ya lura da bana ta, ta shi, aikina da Yazid ne a gabana yasa shi shafa min lafiya. Na kuma kara mai da hankali kan abinda nake yi, wasa wasa wata irin shakuwa ta kullu a tsakanina Yazid, wanda haka kawai zai zo nijar, duk lokacin da yazo sai naga sauyi daga Chairman. Don da wuri nake tashi, kafin shekaru daya kamfanin ya farfaɗo tare da kara bude rassa haka yasa na zama busy, ga yawan baƙin da muke yi a kai akai. Sanadin Amirah SK Lamido ya saka hannun jari a kamfanin Ba'are, sama sama suke mutunci da Chairman don ma yana da kirki shima yasa Chairman yake kula shi. A hankali na fahimci duk namijin da yake tare da ni, Chairman haushinsa yake ji haka ya faru ne sakamakon wata tafiyar da muka yi Nigeria, aka yi taron tattalin arzikin kasa ta nahiyar Afirka, inda aka gayyaci har yan kasuwa da attajiran African. A lokacin da muka hadu da wani saurayi, ya rako Babanshi gayen nan yayi ta rawar kafa akaina. Bayan an yi taron na kwana uku, gayen nan sai da ya kashe min kudi a ranar da zamu rabu kiri -kiri Chairman ya gaya masa akan idanuna. "Ka daina wahalar da kanka matata ce." "Ke Matarshi ce?" Bakina sake nake kallon shi. Kafin na samu damar cewa wani abu, Har mun shiga jirgi ya ce. "Ya ishe ki tara samari haka, SK Lamido, Yazid yake ko Ziyad ne oho, ga Amaan maza nawa zaki aura?" Tura baki nayi ina faɗin. "Tow kai meye matsalar ka, ni burina na tara maza ashirin kowa kuma yana sona " "Hm, haukar banza dai." Ya faɗa yana kallona, haka muka dawo Niamey, sai mita nake har gida suka ajiye ni na shige ko.sai da safe bance ba. *** Camp "Allah ya gani na gama gajiya zan koma Nijeriya idan kin so kada ki tafi ki zauna anan, amma ni zan koma gida wurin Yayana." Inji Ummi tana faɗa dai-dai lokacin da take haɗa kayanta, domin karshen wata zasu bar camp amma Addah take niman su kara rasa damarsu na barin kasar. Ita kan Ummi ta rantse ba zata kara zama a Nijar ba, idan ita zata zauna ba laifi amma ita zata koma wurin ahalinta. "Ina haka ne don ke!" "Karya kike Addah ba don ni kike ba, don kanki kike." Daga haka ta bar dakin. Zuwa yanzu ya dace ace ta san yadda kome yake tafiya, musamman Zulaihah da ita ta dace yanzu ta dauki alhakin kula da ita amma ba hali ko ta koma Nijeriya, babu me kula da ita sama da Zulaihah da Zahrah. • Ban san yadda kome yake zuwa min ba, amma Alhamdulilahi zan iya cewa Yazid tsaye yake a kaina, kasancewar Chairman yau yake kara shekarun haihuwar shi, a gidansu. Duk da ban wani damu na je ba, amma haka Amaan ya takura min, na dauki Siyamah da Baraka, d Amirah muka saya mishi abin da zamu bashi kyauta raka ni suka yi suma na saya musu. Muna dawowa gidan na ajiye su, "Mami zan bi ki." Shiru nayi kafin Nace musu. "Mujenku dukkan ku." Ai kuwa da sauri suka shiga, Ajiyar zuciya Siyamah tayi. "Wani abu ne?" "A'a!" "Ma ki taka motar kamar ana bibiyar mu ne!" Kan uban can, da gudu na fisgi motar. Kamar xan tashi sama. Sai da muka gama gudu, har mun isa gidansu, suka sha kaina tare da harbin tayar motar mu, "Ma! Ki tsaya." Ta fada tana kallon yadda na rud'e. Tura kujerar motar tayi naga ta ciro bindiga, tsoro ta bani."ku kwanta" ta fada da karfi ta sauke gilashin motar nan, ta fara sakar masu harbi kan me uwa da wa bi, ban tab'a ganin tashin hankali ba irin na yau. Rike hannunta nayi . "Bar harbin, ni suka zo dauka shi yasa basu harbe ki ba." Na fada ina kallonta, don tun fara harbin tartsatsi wutar motar na hango fuskar........ 300₦ 0016341139 unity bank zahra'u yahaya Ali Katin MTN 400 #Mai_Dambu ce [5/29, 07:47] Hlm: BHB253 Tabbas ko a cikin dubu Nawwas ba zan tab'a mance fuskar shi ba, haka yasa na dakatar da ita domin kuwa idan ta fusata shi ba zai tab'a kyale mu ba, duk sai ya hallaka mu. Anyi Y'a kwance uwa kwance kenan. Bude motar yayi ya fito yana zukar tab'a. Ya iso har gefen driver ya kwankwasa min glass, yana murmushi sauke glass din nayi ina me tausayin kaina. "Fatimah nan kika dawo?" Hawaye ne ya zubo min. "Nan Yazid ya kawo ki, sai gashi bai iya boye min ke ba, kin samu rayuwa me kyau kin manta da danginki." Ni dai ban iya magana ba, sai dai shiru murmushi yayi sannan ya cigaba da cewa. "Haka ma yayi ai,fito muje Gimbiyata." Ba musu na saka hannu zan fita Siyamah ta rike ni. "Sultan zai yi fushi idan ya ga ina raye ke kuma bakya nan." Murmusa mata nayi na ce mata. "Ki gaya mishi nasan zai zo ba zai miki kome ba." Haka na fito daga motar ya rike sigari da daya hannu me lafiyar. Shi kuma dungulmin ya saka a bayana ya nufi cikin motar da ni."Maminah ku kai ni Mamina." Inji Amirah. "Wow Yar wurin Zuzu kenan? A dauko min ita." Cikin tsananin tsoro na ce mishi, "kayi hakuri kada ka cutar da ita bata da laifi ni ce mai laifi." "Har yau kina nan da son naki, koda yake ba laifi ba ne, kaso naka." Haka ya saka ni a motar, tunda muka isa na kifa kaina, ina wani irin kuka, kafin Yazid yazo daga Algers na mutu murus, shi wancan sikagon ba wani abu zai iya min ba, haka yasa nake ganin Allah yasa wannan tafiyar ta zama ajalina na gaji da abubuwan da suke faruwa da ni. "Ya isa ba kuka zaki yi ba." Ya fada min, ban iya kula shi ba, kuka na cigaba da yi. ... Siyamah a daren ta kira Yazid, ta gaya mishi abin da ya faru ta dauka har da number motar da suka dauki Zahrah. Kiran Office din Embassy na Algers da yake nan nijar yayi ya shaida musu. Tare da hoton Zahrah, ya ce lallai ayi wani abu kafin ya iso dake mutum ne mai matsayi da kuma girmamawa sai gashi jakadar Algeria a nijar ya samu damar tura sako ga primemininester, kafin wani lokaci an kafa dokar bincike ko ina a fadainrgarin. * Ana cikin Birthday party sai raba idanu Majid yake yasan tabbas zata zo, haka yasa shi sankankancewa. Shiru da yaji ne yasa shi damuwa yana kallon kowa, Umaima da suka zo nasu harkar lafiya, yau tana can tana kallonshi kamar a dame yake. Da sauri Amaan da Aryan suka shigo Aryan yana rike Amaan, yana kwacewa. Mika mishi tap din hannun shi yayi yana faɗin. "Sajjid ya sace Fadima." Shigowar Motar yan sanda gidan ne, yasa hankalin kowa ya koma kansu. Nan suka iso har gaban Majid, tare da mika mishi hannu. "Yallabai kana da labarin an sace sakatariyarka?" Zufa ne ya shiga yanko mishi, tare da kura musu idanu. Amsar tap din yayi ya ga hotonta da motar da aka sace ta. "Wannan motar mallakar Iyalin Mamman Ba'are ne ko?" "Eh na gode sosai, kuyi iya ƙoƙarinku mu ma zamu tuntube ku idan wani abu ya taso." Karfin hali ne yasa shi yin magana, amma ba wai yana da zuciyar magana ba ne, kallon Aryan yayi ya ce mishi. "Tunda wasu abubuwan ke faruwa baka tab'a gaya min kome akan motar da aka sace ba, Aryan me kake kokarin aikatawa?" "Me zan aikata wanda zai tab'a kimar gidan nan, motar nan an sace ta kusan shekaru biyu kenan, yau nima nayi mamakin ganin shi." "Aryan ka sayar da motar ne?" Haɗiye yawu yayi tare da sunkuyar da kai ƙasa. "Bani da zaɓi ne, na bawa Sajjid koyar." "Me yasa ka bashi motar da ni kaina hukumar tsaro ne suka ba ni." "Barazana suka min na daukar Abdul Majid shi yasa na basu motar." "Me yasa baka gaya min ba?" Shiru yayi ya sunkuyar da kanshi. "Bana zarginka amma ka sake na zarge ka, garin nan sai yayi mana kaɗan." Hankalin kowa ya tashi, kafin wani lokaci an fara ture-turen hoton Zahrah. Ita kan Hajiya kasa magana tayi, har suka shiga cikin gidan, Umaimah ta amshi wayar Jamilah tana kallon Zahrah duk da ta sauya amma ba zata mance fuskarta ba. "Captain dama ka samo Zahrah Buba ce?" Cak ya tsaya da hawa Step. "Yes ita ce Yarinyar da kake nima, yarinyar da bata jininka, ita ce dai a tare da kai." Iska ne ya cika mishi huhun shi, ya kasa gaba balle baya, ya kasa motsin arziki. Akwai wani abu da yake ji na daya muryarta na biyu wani irin abu yake ji a jininshi a duk lokacin ya ganta bai tab'a zata jininshi da yake yawo a jikinta ne yake saka shi jin kamar ya santa da jimawa ba. Kasa magana yayi ya kai minti ashirin a tsaye kafin ya wuce dakinshi, ya zube a saman gadon, wannan shine an bata goma daya bata gyaru ba. Zumbur ya mike tare da nufar kofar fita daga gidan. "Ina zaka Hamma akan wannan karuwar yarinyar zaka b'ata lokacinka ne?" Juyawa yayi a fusace ya buga mata harara, tare da wani irin kallon tsana da takaici. " Kika sake kiranta karuwa sai na fasa miki baki, sakarya kawai." Yayi ficewar shi, gidan Tani ya shiga ya samu zata fita daga gidan kenan. Zuwa yayi ya bude motar ya zauna yana murmushi. "Da alamu ba ki ja kunnen d'anki ba?" "Ban san kome akan satar Yarinyar ba." "Ki kira shi a duk inda yake ya saki yarinyar, ko ya fadi inda zan dauke ta. Amma ki gaya mishi ya mika kanshi ga hukuma domin zai samu sassauci ni idan na same shi sai dai Raihana ta haifi wani." Tani bata yi wasa da Kalaman Majid ba, a take ta kira Sajjid. "Don Allah ka sake mishi sakatariyarshi." "Ni ina ruwa na, yaje ya samu wanda ya sace mishi ita." Wayar shi da yake hannun shi ya tura sako office din bincike, tuni aka gano inda Sajjid din yaƙe. "Ka dawo mishi da ita domin motar nan ta kace, ka dawo da ita kafin kome ya tonu." "Sai kuyi!" Fita Majid yayi a motar, ya nufi cikin gidan su yana waya. Ya nufi cikin gidan su ya samu ana ta nanata abu daya, haka yasa shi wucewa sai kuka Zaytoonah take tare da cewa. "Sai ka gaya min meye nayi maka baka sona?" Banza yayi da ita tare da bin shi da gudu, bai kulata ba don yasan cewa bai da lokacinta. "Wallahi sai ka gaya min." Kura mata idanu yayi kafin ya ce mata. "Bana sonki,ban tab'a kaunarki ba. Ban tab'a jin ko dai-dai rana daya na so ki ba ni kanwa na dauke ki ai na gaya miki tuntuni zuciyata na wata ce. Tow akan me xan damu kaina na lallai sai na gaya miki karya ki je ki nemi wanda ya miki amma ni bani da lokacinki." "Me yasa ka koya min sonka?" "Munafuka an tab'a so dole ne yau naga danyen jaraba. Baya sonki sai me? Yau naga jaraba, hehehe Alhajin Allah don dai ka hana ni saka maka baki ne .maganar ka amma tun yaushe na gano Ariyan kasungurmin munafuki ne, dan iska idanu kamar matsatsaku." Shi kan fita yayi tare da amsar wayar, "Alhamdulilahi" ya furta. "Nana an kama jikanki wanda ya bada motar da aka sace ta. Ina zuwa." Bakiɗaya kwana zaune aka yi, Hajiya kallon Aryan take haka matarshi kuka take tana faɗin. "Me yasa ka rusa yardan da nayi maka. Aryan me yasa ka zubar min da kimana bayan ban maka kome ba. Yan uwanka sun yarda da kai amma ka lalata wannan yardan, idan har zaka iya munafuntar yan uwanka tabbas zaka iya kashe ni har da Yarana." Ta fada tana kuka, Hajiya kuwa tasan waye Aryan ba zai tab'a yin haka ba tare da dalili ba. Ta jima da sanin yana boye mata wani abu, amma bata kawo a ranta cewa wannan abin ne ba. "Yanzu ka kyauta kenan." Mikewa yayi a fusace ya mari Amaan. Sai da falon yayi tsit ya kuma d'ago hannu zai kai marin Hajiya ta ce mishi. "Kyale shi haka." • Yazid . A daren ya bar ƙasarshi don yasan babu nisa da nijar amma a haka sai asuba Suka shigo garin, koda ya iso abu daya ne shine basu agogon hannunshi da ya ce musu. "akwai agogo a hannunta matukar yana hannunta za a iya gano inda take." Wasa wasa sai gashi an samu inda take, suna hanyar Libya da Nijar. Haka yasa shi tashin jirgi. Tun tafiyar da yayi ya saya musu agogon iri daya, sannan aka sawa agogon tracking. Haka yasa shi gaya mata kada ta ajiye shi ya zama yana jikinta ko wani lokaci bacci ne kawai zai rabata da agogon. Ya kuma san zata yi hakan. Sannan da Nawwas yasan da agogon ba zai yarda ya bar kasar da ita ba. Soji da yan sanda suka dauki hanyar, yayinda Majid da yan sanda suka bisu Yazid kan da yar ƙaramar jirgin sama aka dauke shi, ana bin inda suke. Da fari Nawwas yaso yayi lalata da Zahrah kawai ya sauya ra'ayinsa don kada a samu matsala, tuni ya tura hotonta akan manhajar su, yan iskan attajiran turawan nan na gani suka ce tayi musu aka fara saka kudi a kanta, haka yasa shi tattara kudi me yawa gara ya sayar da ita kowa ya huta, ya saka Yazid b'acin rai. Haka yasa shi nufar Libya daga can ya bi teku da ita dake akwai kayan safarar shi. Cikin minti arba'in da wani abu aka same shi. Yana kan iyakar zai fita da ita, garin bincikar motar da suke fita ya tsaya bin layi, har Yazid suka iso. Lokacin da ya gansu ne ya san ba makawa sai sun kama shi. "Waye ya tsaya miki?" Ya fada bayan ya damke gashin kaina. "Allah mana, ban da Allah waye zai tsaya min?" Murmushi yayi sannan ya ce min. "Idan na kashe ki ke daya, ban ci raba akan wancan dan iska ba amma idan na kashe ku dukkanku ku biyun fa?" Kewaye motar aka yi tare da bindiga aka ce ya fito daga motar, haka muka fito bayan ya saka min bindiga a kaina. Ganin Yazid yasa ni fashewa da kuka domin gari ya waye yayi haske. "Kina lafiya?" Gyada kai nayi. "Ku kyale ni na tafi sai na baku ita." Sosa kan shi Yazid yayi da bindiga. "Matsalar da aka samu shine ni ban san wannan Yaren ba." Ya faɗa yana kallon Nawwas. "Zahra kina lafiya inji Majid!" Gyada kai nayi mishi. "Wow Majid Mamman Ba'are. Tow waye zai bada rayuwar shi na kyale ta?" "Ni" inji Majid, mamaki abin ya bani. "Gabata ba akanka ba ne, akan Yazid ne sai dai idan zan kashe Zahra." Ganin ya b'ata musu lokaci, yasa wani cikin yan sanda da yake bayan shi ya harbi hannun da ya rike bindigar, can ya fadi, da sauri Yazid ya finciko ni, hawaye ne ya zubo min lokacin da ya rungume ni yana shafa bayana. "Akwai nakiya a jikina." Harbin Nawwas aka yi wanda ya fadi bai, ko shura ba, Majid Mamman Ba'are yayi haka. "Kada ki damu zan cire miki shi, kin gama zaman Nijar muje na kai ki wurin danginki ya isa haka." "Nakiyar fa?" Na tambaye shi ina kuka, "Zan cire miki." Haka ya janye ni ya shiga duba nakiyar, a hankali ya cire min nakiyar ya wullar can, wani irin ƙara ne ya tashi wanda ya dauke min jina da gani na. A hankali na zube a jikinshi, runtsa idanu Majid yayi yana jin wani irin abu a ranshi, zafi yake ji da wani irin ciwo me tattare da danasanin abinda ya aikata. Tabbas yayi kuskuren kuntatta mata. 300₦ 0016341139 unity bank zahra'u yahaya Ali Katin MTN 400 #Mai_Dambu ce [5/29, 07:47] Hlm: BHB254 Haka suka nufi Niamey tare da gawar Nawwas, cikin tsananin farinciki domin Yazid gani yake kamar Allah yana son shi da rahama ne yasa shi samun damar tare Nawwas. A private jet din da aka kawo shi a ita aka mai dasu, don alfahari da ya yiwa Majid tayin tafiya banza yayi da shi tare da nunawa ba zai shiga ba, haka suka nufi ababen hawansu kowannensu kishi yana cika shi, Yazid yana ganin shi yafi cancanta da Zahrah yayin da Majid yake ganin shi ya dace da ita domin ya jima yana nimanta ruwa Ajalo, haka yasa kowannensu yake jin yafi karfin ya tsaya ayi mishi alfarma. Lokacin da Yazid ya isa asibitin a lokacin yayi Sallah, Majid tun kafin a same su yabi jam'in sojojin da suke taya shi nimanta. A lokacin da suka iso wurin karfe goma na safe, gida ya wuce yana me nufar dakinshi. Rufe kofa yayi domin ba zai iya magana ba, a wannan lokacin. Ko sallar azahar da la'asar a dakin yayi, sai la'asar likis ya fito yana kallon gidan musamman Aryan da ya zube a gabanshi. "Na cancanci mutuwa, ka kashe ni da hannunka kawai." "Ni bana kisa, sai dai ka cire yarda da nayi maka." "Alhajin Allah bar shi munafiki ina kishiyar tawa, an same ta?" Lashe bakinshi yayi yana jin wani irin rauni a hankali ya ce mata. "An same ta, Nanata." Yadda yayi maganar yasa Hajiya kallonshi kowa yasan Majid da juriya da karfin halin amma yadda yake maganar zai tabbatar maka akwai abin da yake damun shi." "Hajiya xan koma asibitin." "A dawo Lafiya!" Haka ya fita bai ce kome ba, don ko da ya iso asibitin. Likitoci na kanta, ana ta dubata har lokacin bata farka ba, abin ya dame shi kwarai. Abin da ya fahimta Yazid yana da goyan baya domin likitocin da suke zuwa da fita kwararrun likitoci ne daga babban asibitin Niamey. Haka yasa shi jin wani irin karaya, Indai ita ce yarinyar da yake fatan samu , wannan gayen ya gama gina kanshi a zuciyarta. Haka yasa shi jin ba zai iya ba, har ya tashi zai tafi wata zuciyar ta ce mishi. "Lusari katon sikago, haka zaka gudu ka bar macen da kake so? Waye ya gaya maka ana gudu, ka dauki salon shi ka kyautatta mata sama da shi, ina zaka sakarai." Dawowa yayi ya zauna har likitoci suka fito daga dakin, shima ya shiga tana kwance numfashinta da bututun iska take ja, sai da ya zauna yana kallonta, murmushi yayi yana kallon bakin tsiwar nan" Yana zaune yana kallonta, Yazid ya shigo kallon juna suka yi, kafin Yazid ya juya baya yana zama a gefen gadon. A hankali yana waya cikin wani irin isa da mugun gadara, abin ya motsa halin da mulkin ya motsa haka yasa yake jin wani irin isa a ranshi. "Duk yadda suka gadama su yi, ba zan dawo ba sai lokacin da na gama abinda naje Aseem ka gaya musu inji.". Jin hakan yasa Majid gane da mutanen gidansu yake, bayan ya gama wayar ya ja tsaki tare da kwafa. Wannan abin ya kara harzuka Majid ya bar dakin, tab'e baki yayi dama ai babu wanda ya gayyace ka ya faɗa a ranshi. A dakin ya kwana yana tsaronta, yadda zaka fahimci Yazid yayi masifar nisa a kan Zahra, nisar da baya sauraron kowa sai kanshi, wani irin tsaftataccen so yake mata me dauke da kauna zalla, babu duba jinsi babu duba kabilar da ta fito, babu duba waye Ubanta waye danginta, soyayya yake mata irin na ko daga sama kika fado haka nake sonki, Yazid ya san inda su Addah suke amma saboda kada wani ya d'aga mata hankali yasa shi hakura da kawo su inda take, Yazid ya binciko inda dangin Mamanta suke don har ya je da kanshi don sai da ya ji kome a bakin Babangida, burin shi ta sauke abin da take jira ne ya kaita wurin Mamanta amma gashi nan wancan dan shegiyar ya lalata mishi kome, saboda tsaro ko bakin kofa bai fita ba, dakin da take akwai karamin firji tashi yayi ya dauko abin sha, ya zauna yana sha yana latse latsen wayarshi. Hoton shi da ita ne a india, sun yi kyau sosai, murmushi yayi yana kallon yadda take fama da na'ura kanta. Haka ya kwana a kanta, yayinda Majid ya tafi gidanta ya dauki Amirah da Barakatu, iya su ya samu duk da akwai tsaro a gidan amma a firgice suke, gidan Jamilah ya kaisu yasan Zaytoonah zata iya saka su a gaba, ba musu aka basu dakin. "Hamma yarinyar." Kallonta yayi a hankali ya ce mata. "wacce?" "Yar Zahrar bayan rabuwa ku ne ta haife ta?" A hankali ya zuba mata idanu, "Umaimah ta gaya miki abin da ya faru ne?" "Wa Zaytoonah da Anisah ta gayawa,Ashe karuwanci suke a fatakwal din?" Kura mata idanu yayi kafin ya ce mata. "Tayi kama da karuwa ne da kike ganinta?" Jin irin amsar da ya bata yasata rike bakinta. "A'a, ai.nana tace ko Magajiyar karuwai ne haka take sonta." Murmushi yayi ya mike tare da nufar waje, "ki kula da ita don na yarda dake ne na kawo su." Daga haka ya fice, yana mamakin yadda Umaimah tayi irin wannan maganar a daren ya kirata, yayi ta masifa har da cewa bata da sirri kome dai ta faɗa ne, ta ji ko a gidan karuwai Zahra ta fito yana bukatarta haka, shi ita yake bukata ba virgin ba. (Karya kake munafuki 😭🙄🤣 Ja'iri zai raba masoya) Koda ya iso gida yaki yarda ya nufi part dinsu, wurin Nana ya wuce ya samu tana sauraren Radio. Kwanciya yayi a dogon kujeranta. "Ya jikin Zahra'u, Allah sarki baiwar Allah ashe har kashe ta ka kusan yi?" Kwanciya yayi ya juya mata baya. "Ina magana Alhajin Allah kayi banza da ni?" Ta fada tana kashe radio din, tashi yayi yana faɗin "kina min magana amma kin kunna Radio Nana da naki zan ji ko da raido" "Allah ya baka hakuri Alhajin Allah, dama nace ko zaka san yadda zakayi ne, ni dai ina son yarinyar domin dai ina hango alkhairi a tare da ku, ban damu ba ko a gidan karuwai take." Murmushi yayi yana faɗin. "Shi yasa nake sonki Nana." "Hmm ayi sha'ani kawai, wani irin kiyayya ce ban nunawa Uwarku ba? Yau waye yake rike da ni, wallahi Mamman bai tsane ka ba, raba ku aka yi domin irin tanadin da yayi maka a kanshi Allah ne kaɗai ya sani. Don Allah kada wasu su saka ka kauce hanya akan yarinyar nan." Murmusa mata yayi ya kwanta abin shi, ai baya jin akwai me dakatar da shi tunda Nana ta ce ya nime ta, ya nime ta kawai. Barci yayi a falon Nana, tana gama zamanta ta wuce dakinta. **Bayan sallar asuba, ya wuce wurin Hajiya a falo ya same ta tana lazimi. Zama yayi har ta yi sallama, suka gaisa jin bata ce kome ba, yasa shi mikewa zai haura ta ce mishi. "Ina ga kada ka fara dauko maganar sakatariya, idan da a wani wurin ce ka hadu da ita ba laifi, amma a ji karuwanci suke abin zai tab'a zuri'a har duniya ta tashi, ba wai kinta nake ba. Amma ina son kayi mata adalci kada abin da ya same ni ya same ta." Ban da Hajiya ce ke wannan maganar , da wani ne sai ya san yayi magana. "Na san lafiyarka lau, ita kake jira ba, ka nimo wata macen. Idan har ni na haife ka." Murmushi yayi sannan ya ce mata. "Zahran da a yanzu ma bana jin na isa namijin da xan tsaya a gabanta, Hajiya kina ganin karya na miki da bani da lafiya ko?" Ya faɗa yana jin wani irin bakinciki yana cika shi. "Wanda yake tsaye kan Zahrah, cikakken namiji ne kuma Basarake ne wanda yake da kome, don haka ban isa na tari Zahra da labarin nine wanda ƙaddara ta haɗa mu can baya ba, taya zata kalle ni ma. Hajiya ga number likitan da nake gani idan baki gamsu ba, ki shirya muje na ga likita ni koda na samu Zahrah son kai na zai iya janyowa mu rabu. Kin ga babu damar auren wata mace balle Zahrah kenan." Hawaye ne ya zubo mata, shima don yana namiji ne, a hankali ya ce mata. "Ina ta ƙoƙarin na fitar da abin da yake raina akanta, amma a yanzu na hakura da kome." Ya faɗa yana nufar hanyar dakinshi, idan har Hajiya bata fahimce shi ba, waye zai fahince shi Nana ta fahimci halin da yake ciki, amma Hajiya ta kasa fahimtar haka. Da wannan ya shirya ya bar gidan. Wasa wasa sai da ya zama ko a kamfanin babu wanda yake ganin shi baya zama bakiɗaya, amma yana zuwa asibitin sosai don har lokacin bata farka ba, abin da ya fahimta Yazid baya farinciki da zuwan shi, bakiɗaya sai ya rasa inda zai saka ranshi yaji dad'i. Sai dai bai tab'a yarda ya nuna gazawar shi ba, amma kuma a haka kishi suke da juna, idan Majid din ya zo baya damuwa da likitocin da suke wurin, zai dauki kome yayi ta dubawa, yana tambayar su yanayinta, a satinta daya ne su Hajiya da Aryan da Nana suka zo ganinta a lokacin suka ganshi sanye da kayan aiki na asibitin shi da wasu likitocin an fito da ita daga dakin za a kaita hoton domin yadda bakiɗaya ta ki farfaɗowa shi Majid yana ganin kamar akwai wani abu da ya buge kanta. Haka yasa yayi tunanin mata hoton kanta, a wannan bangaren Yazid bai mishi katsalandan ba, amma kuma ya nuna idan wani abu ya faru sai ya maka shi kotu. Bai kula shi ba, haka suka fita da ita anan Hajiya ta ga dan gudun hijiranta, suka tafi aka mata hoton, babu wani abu da ya sami kanta. Kiran Umaimah yayi suka tattauna da ita, don haka aka nimo likitan zuciya, anan suka fahimci zuciyarta ne bata bugawa yadda ya dace, don haka za ayi aikin zuciyar suke tunanin. "Bana tunanin aikin zuciyar shine mafita, ku kyaleta akwai." "Wannan wani irin shirme ne kake fad'a?" Inji Majid, yake kallon Yazid, cikin fushi shima Yazid din ya ce.."Shirme akwai wanda ya kaika ne? Ka barta na ce ba za a mata aikin ba." "Aiki ya zama dole domin na amshi case dinta." Ai kuwa suka shiga sa'in'sa akan ita majinyaciyar. Duk yadda Umaimah taso raba su kowannensu ya hau dokin zuciya. Can nake ji kamar ana min rad'a, ga wani kararrawan da nake jin yana bugawa a kaina. Bude idanu nayi ina kokarin tashi na ga Yazid da Chairman ne, kamar zasu cinye juna. A hankali jina ya dawo daidai. "Kai baka isa ba" inji Yazid, "Na isa domin aiki za a mata." Inji Chairman. "Waye zai ayiwa aikin?" Na fada a hankali, kallona suka yi ganin ina kallonsu. "Zahrah!!!" Suka kira suna na lokaci guda. "Kin farka." Yazid ya faɗa, kokarin tashi nake amma Chairman ya ce min. "Koma ki kwanta na duba ki." "Ya zaka ce haka, ta farka zata tashi." Inji Yazid, "A kan aikina nake, idan ka shiga rayuwarta ce a hatsari, daga farkawar ta ba a bukatar ta zauna sai mun duba lafiyarta." A hankali yake aikin shi yana tambayata ina bashi amsa, kafin ya zare na'urar da suke kaina, ya ce min. "Kanki yana miki ciwo?" "A'a da dai dazun na ji kan kamar ana buga min kararrawa?" "Ok yanzu fa?" "Babu?" A hankali ya wuce ya bude min labule da window ɗinkin iska me dad'i da sanyi ya shigo dakin. "Ki kula da kanki, za a kawo abinci da magani ki sha akan lokaci." Fita yayi daga dakin. "Ya jikin naki?""Da sauki," na fada dama can Umaima tunda suka fara ta bar dakin tayi tayi su rabu sun ki. Abinci aka kawo min na ci a hankali, na sha magani, sannan nurse biyu da Aunty Umaimah suka taimaka min nayi wanka da sallah. 300₦ 0016341139 unity bank zahra'u yahaya Ali Katin MTN 400 #Mai_Dambu ce [5/29, 07:47] Hlm: BHB255 Alhamdulilahi sauki yana ta samuwa, domin kuwa har asibitin sau biyu Nana tana zuwa, idan tazo babu abin da take bani sai labarin Rayuwar Majid da Hajiya, ni dai ban tambaye ta ba, kuma bana jin akwai wani abu da yake tsakaninmu da ya wuce aikin kamfani. Amaan a asibitin yake wuni haka ma Aryan yana zuwa akai-akai don kawai muyi hira, haka Hajiya tazo ita da Zaytoonah. Sai dai daga yadda take min kallon kamar taga abin kyama yasa ni fahimtar saboda mazan gidansu ne, ba laifi Hajiya tayi min alkhairi kuma a duk zuwanta sai tazo min da abinci, haka yasa nake jin dadin haka. Sai dai kuma akwai wani abu da nake fahimta daga gare ta. Wanda iya fahimta ta ce ban san me ye ba, sai bayan da aka sallame ni mutane sun yi sauki tazo har gidan. Ni da Baraka muka yi ta mata hidima, kafin ta ce min. "Ya isa haka." Dawowa nayi na zauna, tana murmushi ta ce min. "Wani abu nake so na sani." "Akwai alaƙar soyayya ne a tsakaninku da Abdul Majid?" Girgixa mata kai nayi, ajiyar zuciya na sauke, kafin na ce mata. "Babu!" "Kece kika haifi Amirah?" A wannan karon tambayar tayi min tsauri, bakiɗaya sai na rud'e, bakina yana rawa na ce mata. "Eh...a!" "Eh ko a'a!" Yadda ta tsare ni da idanun na samu kaina da cewa. "Eh!" "Waye ubanta? Ko Majid ne?" Wani irin rawa jikina ya dauka, na kasa bata wannan amsar. "Umaima ta gaya mana, cewa Majid ya kai ki wurinta tayi miki jinya?" "Waye Majid Hajiya?" Na tambaye ta ina daura hannuna a baki. "Barikin sojan sama na Fatakwal sojan da ya dauke ki awannan daren Majid ne ko?" Kamar an buga min guduma haka naji kalaman Hajiya, sake rudewa nayi kamar xan tashi zaune na ce mata. "Chairman Majid shine sojan....." "Eh soja ne, kafin ya ajiye aikinsa ya rike kamfanin mu. Meye alakarku? Amirah yar shi ce?" Wasu irin hawaye ne ya shiga zuba min ina jin kamar na haɗiye zuciyata na huta. "Yar shi ce ko." "Ba yarshi ba ce." Na bata amsa cikin wani irin kuka. "Zata kuma magana nayi maza na ce mata. "Hajiya ya isa haka, babu wani alaka a tsakanina da shi sai na aiki bayan nan ban san kome akan shi ba, idan akwai bukatar na ajiye aikin kamfahinku ma zan ajiye amma don Allah kada haka yasa ku sheganta min Yarinyata." Daga haka na bar falon zuwa dakina, har bakin kofar ta iso. "Ba zan sheganta miki Y'a ba Zahra amma ina son sanin wacece ke? Sannan meye alakarku da Yazid, ni uwa ce da take kokarin tsayawa d'anta, nazo nan ne domin nima Majid soyayyarki ba nazo na cutar dake ba ne, amma kiyi hakuri. Ban san yadda zuri'ata zata yi alfahari dani ba, amma macen da aka ciyota a caca bata cancanci tayi farinciki ba ne? Ko macen da aka samota a bariki bata dace da farinciki ba ne. Bana son tarihi ya maimaita kanshi ne." Ni dai ina dakin a bakin gado, kuka nake mara sauti Hajiya kuwa tana ta magana ne, har na daina jin maganarta na fito na samu ta ajiye min karamar takarda. _Kiyi hakuri amma ina son kiyi farinciki ne bana son daga baya kiyi kuka da ni. Ina tsoron kada shigowar ki zuriyarta a sake samun wata victim._ Yaga takardan nayi abuna, lokacin da Yazid ya zo ya so ya gano wani abu amma naki, kwanan shi goma sha daya ya koma garinsu. Nima sai da nayi sati Uku na koma wurin aikina. A lokacin dayawa sun min ya jiki,wani abu da na kara fahimta, shine kusancina da Chairman. Yanzu ba karamin kulawa yake ba ni ba, ina zaune zai min odar abinci. Wani lokaci kuma zai Ajiye aikin ya ce min. "Zo muje wani aikin." Muna fita gidan cin abinci ne, tun kafin mu shiga zai saka a sallame kowa. Haka yasa bakiɗaya nake jina a takure. A wannan takin ne akazo aka yi ta kama wasu daga cikin ma'aikatan kamfanin ana sallamarsu. Koda yake zan iya cewa ta wani fuskar da sauki wasu abubuwan. Ranar da ya ishe ni da kinibibi ne, ina aiki kawai ya fito da keyn mota. "Zo ki raka ni?" "Babu inda zani ina aiki." "Ba jimawa zamu yi ba." "Na ce ba xan je ba Please." "Na mana odar abinci?" "Bana bukata!" Kura min idanu yayi kafin ya ce min. "Ok me kike so?" Ajiye aikin nayi kafin na ce mishi. "Don Allah ka rabu da ni." Kamar haka bai mishi dad'i ba ya ce min. "Na bata miki rai ne?" "Nace maka don Allah." "Tow shi kenan " ya faɗa tare da fita, bayan kamar minti ashirin, sai ga shi ma'aikata na ta fita, "lafiya dan Larai." "Wai yau an dakatar da aiki ne sai gobe." Tashi nayi ina ajiye aikin, na fita nima tare da jakata. Ina jin wani irin dadi da nutsuwa. "Zamu iya fita yanzu?" Ganin mutane basu gama barin kamfanin ba, yasa ban tsinka shi a gabansu ba. Don haka na yi banza da shi muka fito na shiga motar. "Gida zaka kai ni." "Ok Madame Zahrah." Daga haka muka wuce zuwa gidan, sai so yake ya min magana amma naki, muna isa gida na wuce ciki shi ma ya biyo ni. Daki na wuce na zauna tare da ɗaukar wayata, kiran Sk Lamido na gani na dauka muka fara magana da shi, kafin na fito na samu yana wasa da Amirah, mika mata waya nayi. "Ga Daady!" ai kuwa ta amsa tana murna. Kallon shi nayi ina faɗin. "Me yasa baka tafi ba?" "Ina jiranki ne ki bani abinci." "Ni ce xan baka abinci na baka guba? Ko ka manta irin kallon da kake min ne?" Na tambaye shi ina tsare gida, "eh ko yanzu a bani gubar zan ci. Idan na mutu a hannunki ba zan yi bakinciki ba tunda nasan a wurin Khamila na mutu." Sake hade rai nayi kafin nace mishi. "Gobe kace muna da tafiya zuwa damagaram ko? Amma meye ya kawo wannan abin kuma?" Mikewa yayi yana faɗin. "Tow Allah ya kai mu goben." Dauke kai nayi tare da wuce shi har zai fita na ce mishi. "Idan ka kuma zuwa gidana ka zauna ba da iznina ba, zamu samu matsala." Murmushi yayi ya fita yana faɗin. "Tow Ma!" Ya fita, babban burin shi ganinta cikin farinciki yafi komai yi mi shi dadi, yarinyar da ya jima yana fatan gani ashe ita ce yake ta zubawa tijara.. A ranar mun wuni cikin farinciki, har yar ƙaramar party muka yi,da yamma muka fita zuwa yawo sai dare muka dawo ai kuwa ina dawowa Yazid ya kira ni yana mita. "An ce min wancan bishiyar kukar yazo, sannan kin fita yawo. Ni fa bana son yana zuwa min wurinki." "Ji shi kamar ba basarake ba, ko kunya baka ji ba, na ji ba zan kuma barin shi zuwa ba. Gobe zamu je damagaram," hayaniyar da naji ta wayar yasa ni kashe wyaar baki daya. Muka ci tuwo miyar kuka. Sannan muka yi hira, kafin muka kwanta. A hankali nake tafiya a cikin duhu, "Mamina! Mamina!! Zo ki dauke ni Maminah!!" Juyawa nayi naga babu kowa sai duhu a hankali na kira sunanta. "Aminatu!" Ina waige-waige. Can na hangota a kasar haske tana kuka tare da mika min hannu, nufarta nayi naga wani wawakeken rami, Nawwas yana rike da hannunta yana tafiya da ita. "Nawwas!" Juyawa yayi ya min wannan murmushin da ya zauna a cikin kwayar idanuna. Zumbur na farka kaina yayi wani irin sarawa har sai da jini ya zubo min a hancina. Juyawa nayi naga tana ta barci, ban daki na shiga na rike hancina, ina wanke shi. Ina gamawa nayi alola na fito nayi sallah,kusan har asuba ina zaune a wurin ina rokon Allah ya kawo min kome cikin sauki, bayan na idar da sallah ne,.na wuce nayi wanka na tashe ta. Na mata wanka na gyara mata jiki muka fito bayan tayi sallah, tazo taci abinci. Sannan muka wuce zuwa makaranta baraka ma ta shirya muka fita da ita dukkansu na ajiye su a makaranta, sannan na wuce office,.ina shiga Chairman yana jirana. "Baki yi barci ba jiya?" Banza nayi da shi, daukar jakar shi nayi muka bar kamfanin. Kaina sai wani irin sarawa yake kamar nace na fasa tafiyar amma babu hali, tunda muka nufi airport din naga manyan motar Bus. Mata ne suke ta fitowa suna shiga cikin airport din. Haka muka shiga aka ce jirginmu ba zai tashi ba, sai an sallame waɗan nan yan gudun hijiran, wani daki aka kai mu muka zauna. ..."Ke Ummi kin ga kamar Zahra." Koda ta juya bata ga kowa ba, "ban ga kowa ba." "Yanzu ta shiga da wani Kyakyawar Bature." "Hala don bakya son tafiyar ne kike tunanin kin ga Zahra." Shiru Addah tayi don tasan Ummi ƙaryatata zata yi. Don haka tayi shiru. Ina zaune aka kira ni, Yazid ne don haka na fara waya a dakin, kura min idanu da yayi yasa ni fita daga dakin na bar cikin airport din,.na samu wuri na xauna muna ta hira, sosai har da kyalkyalewata. Sosai muke hira fa, abin gwanin ban sha'awa. Ina gamawa na juya na koma ciki. "Ke Ummi kin ganta fa!" Ta nuna mata bayan Zahrah. Tsaki Ummi tayi tana faɗin. "Kama ce kawai amma babu wata Zahrah anan" ita Addah ko cikin dubu ta ga Zahra zata gane ta amma Ummi sai Musa mata take haka yasa tayi shiru tana kallon ikon Allah. Ina shiga ya kalli agogon hannun shi, "minti ashirin fa, fisabilillahi idan da adalci wannan lokacin yayi tsawo dayawa. Ki gayawa dan kwaryan nan ya daina kira a lokacin aiki bana so." Ya mike ya fita abin shi yana mita, wannan mutum da mita yake, haka ma Yazid mita na rasa gane kan wannan al'amarin kowa mita sai kace Yara. Bayan fitar shi na cigaba da duba, makasudin zuwan mu damagaram, ina dubawa ina tura sakon ta Email din shi, har lokacin bai shigo ba, ina cikin yi naji gabana ya fadi. A hankali kalaman Baffa'm yake dawo min raina kamar a mafarki. _Ki yiwa zumuncin hidima_ iska ne ya cika min bakina da hancina, dakyar nake jan numfashi, Allah ya taimaka sai gashi ya shigo dakin. Da sauri ya mika min ruwa na Sha. Na dafe kaina ina jin wani irin sarawan da yake yi, ga faduwar gaba da nake ji, d'ago kai nayi yaga jini na bin hancina. Mika min hanky yayi na tare jinin hancina. Kiran waya yayi yana faɗin. "An janye meeting din nan, zuwa wani sati." Sannan ya kashe wayar. "Muje asibiti." Girgiza mishi kai nayi, xan yi magana kamar wacce aka cika min bakina da abu haka na zube kasa, ina aman gudan jini. Durkusawa yayi a gabana ya janyo ni a jikinshi. "Zahrah baki da lafiya ne?" Sai da ya bani ruwa na sha, sannan ya d'ago ni na zauna da kyau yana min fifita. "Ina ke miki ciwo?" "Babu ." "Ina ke miki ciwo?" Ya faɗa min da karfi, "kirjina da kaina!" "Zahrah kina yawan tunani ko? And da alamu baki yi barci ba jiya. Tashi mu tafi asibiti." "Chairman " "a'a Chairwoman! Oya tashi." "Ciwo ne fa daga Allah kawai zan ji sauki." Riko ni yayi a hankali ya kwashi kayan muka bar dakin, a hankali yake tafiya dani, har muka iso inda yan gudun hijiran suke dab zamu fita naji an kira sunana da muryan da ko A barci na tashi ba zan manta da shi ba "Zahra'u........... 300₦ 0016341139 unity bank zahra'u yahaya Ali Katin MTN 400 #Mai_Dambu ce [5/29, 07:47] Hlm: BHB256 Ji nayi numfashina kamar ya bar gangar jikina, daganan wasu abubuwan ban sani ba sannan ban san ya aka yi muka zo asibiti ba, sai farkawa da nayi rike da kaina. Dube -dube na shiga yi yana kallona. "Kina niman su ne?" Lumshe idanu nayi tare da ware su akanshi. Tabe baki yayi yana faɗin. "Suna can hukumar shige da fice na kasar nan, na ce a ajiye min su."lallai ina son ganinsu." Na fada jiki ba kwari, kuma na kasa tashi. Wani irin kallo yayi min kafin ya ce min. "A haka zaki je wurinsu? A haka zaki ki gansu? Don't fool yourself, kin san ba zan barki a wannan lokacin ki fita ba oya koma ki kwanta." Ya saka safar hannu, tare da ɗaukar allura ya fasa ya ja ruwan ya saka a cikin wani kwalbar magani, "don Allah kada ka min allura." "Idan ban yi miki allura ba me kike so nayi miki?" "Ni bana so." Jijjiga kwalbar yayi sannan ya ja ruwan cikin kwalbar yayi min allurar, "baka da imani, duk yadda naso kada ka min allurar sai da kayi, ita wanna matar Yayar Babana ce, ita wannan ta kusa da ita Ummi yar uwata ce, ina son na gansu gashi ka min allura taya zan gansu wannan ba yi ba ne. Bana son wahalar da zuciyata ta sha, bana fatan wani ya sha irinshi. Na tashi ban san Mamana sosai ba, ta tafi ta bar ni. Na gama Secondry aka tura ni wurin Addah a river, a can ne zan yi karuwanci na ci abinci......" Yarrrrr yaji kamar an zare mishi laka, ya kura mata idanu. Bakiɗaya tausayi take bashi yanayin ta irin na mutanen nan ne masu matukar hakuri, da son nasu. "Allah ya baƙi hakuri sleeping beauty." Ya faɗa yana murmushi, yana shafa kanshi. Daukar wayar shi yayi, "Waɗannan mutane biyun please a kawo su Ba'are guest house." Daga haka ya koma ya zauna, yana zaune yaji kar'ar vibret na waya. Duba jakarta yayi ya ciro wayar, "My King!" Wani yatsina fuska yayi yana wani kyabe baki kamar ya ga kashi. Kashe wayar yayi bakiɗaya, tare da jan tsaki. "Tsuk!" Ya cigaba da zamanshi. Ya tsani gayen nan. ** Yazid. Ganin kiran da yayi bata dauka ba, yasa shi kiran mutanen shi, ya tambaye su. "Ina Zahrah?" "Ta tafi damagaram." "A'a bata da lafiya." Domin jikinshi ya bashi bata da lafiya, tashi yayi yana zaga office din shi kafin can ya kira pilot ya ce. "A shirya zuwa Nijar!" Shiga dakin da yake sauya kaya yayi ya fito, ya shirya tare da barin office din shi na cikin fadar masarautar. Ana ganin fitowar shi aka dauko Motarshi. Ya shiga biyo shi manyan masu mukaman fadar suka yi. "Sultan ka manta yau ne." "Na har baya da kura." Ya faɗa yana zuge glass din motar, shi kan ya gaji da wannan masifar mulkin yana son yayi rayuwa cikin yanci da walwala. Suna isa inda jirgin masarautar yake ya fito, ya shiga tare da barin masarautar shi bai son hayaniya shi yasa ya zabi rayuwarshi. Yana isa ko minti biyar ba ayi ba, suka bar fadar, shi ya tsani damuwa, yana shiga ya lumshe idanunshi, tafiyar awa uku, ta kai su kasancewar jirgin karama ce, haka yasa koda suka isa kai tsaye a airport ya fara baza nimanta, wani ikon Allah anan ya samu ganinsu Addah domin akwai cctv, haka yasa shi jin wani irin takaici,ganin yadda Majid ya tsaya aka ciro su cikin layi ya saka hannu. Wannan bakincikin da me yayi kama, Majid yasan bala'in Addah ba ne. Haka ya juya tare da nufar Ba'are Clinic, yana shiga kamar sun san da zuwan shi aka mishi jagora har dakin da take, yana shiga ya samu tana barcin magani. * "Bawan Allah ina zahra'u take?" Zama yayi ya kura musu idanu, sanin cewa babu wasa a fuskar shi yasa Addah shan jinin jikinta. "Tana lafiya! Idan ta ganku zaku koma garin ku, kafin na san yadda zaku sake haduwa." "Haka yafi a yadda take cikin wannan yanayin, kada ka saka lallai mu zauna domin gawarta za a iya samu." "Ke dai munafuka ce." Inji Addah take gaywa Ummi. "Ke kuma babban Shaidaniya." Ganin zasu fara faɗa, ya tashi ya bar musu gidan, lokacin da ya dawo asibiti ya samu Yazid yayi daidai yana aiki da tap ɗin shi. "Waye ya baka iznin shigowa asibitin nan?" Ko kallonshi bai yi ba ya ce mishi. "Matata Sultanah Zeehrah." "Karya kake!" Tabe baki yayi yana faɗin. "Ni tun fil azal ban iya hayaniya ba, domin ba a koya min ba, don haka ka daina min ihu." Ya fada yana cigaba da abinda yake yi, duk yadda Majid yaso suyi rigima abin ya ci tura, shi Yazid yasan da haka amma a tsarin shi ba zai tab'a faɗa da namiji akan mace ba, idan tasu ta haɗa su dai zasu yi amma ban da akan mace. Fadar kenan kyautatawa macen idan ka isa kayi fiye da abin da nayi, wato gasa. Zama yayi sai lokacin sallah duk suka fita, basu dawo ba sai bayan isha, Yazid ne ya fara shigowa ya samu na bude idanu, tura kofar da yayi na juya ina kallon shi. Mika mishi hannu nayi, ya iso wurin da nake. Yana rike da hannun. "Wanda ya mutu yana dawowa ne?" "A'a Zeehrah!" "Me yasa ka min karyar su Addah sun mutu?" Hada hannuna da kaina yayi ya rungume ni. "Kiyi hakuri!" Lumshe idanun nayi ina faɗin. "Me yasa baka gaya min suna raye ba?" "Saboda ko na gaya miki suna raye a kullum matar nan cusa miki bakinciki zata yi." "Sai meye?" "Sai me? Sai na gaya miki gaskiya bana kaunar ganin wani abu ya same ki, bayan nan babu." "Kodan ka saye ni ne?" Na fada ina cire kaina daga kirjinshi. "Duk yadda kika ce Zeehrah daya ne." Kuka na saka mishi, ya kuma rungume ni, yana shafa bayana. Tun ina yi da karfi har nayi shiru. Yana tsaye a bakin kofar yana kallon yadda take kuka, kamar wanda aka zabura, ji yayi kamar wani abu ya motsa a tsakanin cinyarshi, wanda ya haɗa da marar shi da yayi wani irin kullewa, da sauri ya ajiye abin hannun shi ya bar kofar, a daddafe ya koma gida, yana shiga cikin gidan bai tsaya ko ina ba, sai dakin shi ban daki ya wuce yayi ta kwararawa kanshi ruwa. Yana sauke Ajiyar zuciya. Kafin yaji dama-dama. Daki ya dawo ya kwanta yana nishi. A hankali wayar shi ya dauka ya kira likitanshi. "Dr" "Na'am Mr Mamman lafiya?" "Dr wani abu naji ya harba amma ban san meye ba." "Thank God, wannan al'amarin yayi kyau, ya kake ji?" Nan ya gaya mishi abin da ya faru. Shiru likitan yayi kafin ya ce mishi. "Ko ita ce yarinyar da kuka hadu shekaru biyar baya?" "Eh ita ce." Murmusa mishi yayi sannan ya ce mishi. "Kana bukatar yarinyar a rayuwarka, idan baka manta ba a lokacin kayi yunkurin mata fyade amma ka kasa saboda wancan trauma din, yanzu kuma ya motsa ne saboda ka ganta da wani ka isa gare ta, abubuwa dayawa zasu sauya." Tabbas rayuwar shi zata fara gyaruwa kenan, haka yasa shi godiya tare da kwanciya a wurin, ya rasa farinciki zai yi ko bakinciki. A nan yake kwance har barci ya kwashe shi. ... Rigimar da muka yi da Yazid ba karama ba ce, haka yasa har ya kira nurse suka min allurar barci, haushinsa na boye min inda su addah suke ya sani jin ba dad'i. Washe gari. Karfe sha daya na farka, Addah na fara karo da ita, ban ganshi a dakin ba. Kallon addah nayi da kyau naji gabana ya fad'i babu ido daya, tayi wani irin baƙi. "Zahra kin farka." "Eh Ummi, ko zaki kira min nurse ta cire roban nan nayi wanka da sallah" "Tow!" Ta fita. "Sannu yar duniya mage taji kulkuli, kin yi shan dandan uwa kud'a a jikin gyambo. A lokacin da nake tunanin nawa Yar rayuwarta ya lalace ashe ke taki rayuwar kyau tayi har ana ina-ina dake yar gwal." "Addah zaki fara jidalinki ko?" Inji Ummi da ta shigo da nurse. Cire min ruwan tayi, da taimakon Ummi tayi wanka tare da alola. Sannan na fito zuwa waje. Sai jifana da harara Addah take kamar ta ga kashi. Bayan na idar da sallah, na cewa Ummi. "Babu wani abun ci ne yunwa nake ji." Haɗa min tea tayi na sha na koshi, ina ajiye kofin Yazid ya shigo shi da Amirah da take ta rikici, tana ganina ta faɗa kaina da gudu. "My heart, sannu kin ji " "Mamina ina kika shiga?" "Zahra Yar wajen Zula...." "A'a yar Zeehrah ce." Ya fada yana hararar Addah da ta bude baki zata yi magana."Mamina su waye wannan?" Ya nuna min su, "wancan mama ce, wannan kuma Ummanki ce." "Hmm! Bana son wancan Mamanki, tsoro take ba ni." "Akul na kuma jin haka," dake ban saba mata fada ba, kuma bana mata tsawa. Da sauri ta juya wurinshi, ta fashe da kuka. "Dole ne sai taso ta? Ai ba dole ba ne." Shigowar Majid yasa samu zubawa kofar idanu shi da Nana ne, yana rike da kwandon abinci. "Ayya wannan yarinyar kina ganin Jarabawa, sannu Allah ya baƙi ikon cinyewa Alhajin Allah kawo abincin nan taci." Ta fada tana kallon yan dakin, kafin ta sauke idanunta akan Yazid. "Wai wannan baturen shi zaki aura ne?" Ta tambaye ni, murmushi nayi nace mata. "Nana zauna, ke ce da rana tsaka nan!" Na kauda zancenta. Zama tayi tana kallon Addah. "Wannan me kama da yan alaziyi wahidi din fa?" Dole idan ka ga Addah kayi tunanin yan bara ne ko irin masu bin yawon gidajen mutane maula. "Gwaggona ce." Na fada cike da kunya, "Ai!" Addah tayi baki, ta lalace babu wannan kyan da yake rud'ata. Babu jikin nan me kyau da haiba shi yasa kowa ya ganta, sai yayi min magana. Abinci ne mai rai da motsa zuciya. "Ina Amaan ne?" Na tambayi Nana, tab'e baki tayi tana faɗin. "Ai bai da lafiya ne." "Subhanalillahi Ubangiji ya bashi lafiya." Tabbas na jima ban ga Amaan ba, na zata ko Majid ne ya hana shi zuwa nima kuma ban tambayi rashin ganin shi ba. Ajiyar zuciya na sauke lokacin da ta zuba min jollop din taliya da yaji kayan hadi har da nama. "Ummi muci mu biyu." Zama tayi bayan ta wanke hanunta, sannan aka zubawa Addah. Kallon agogon hannun shi yayi ya ce mana. "Babu wani isashen lokaci su ci mu tafi." Yazid da yake bakin gadon ya dauke kai, yana faɗin. "Idan da kasan gubar da yake cikin wancan me ido ɗayan ba zaka sake su hadu da Zahra ba, ai nasan inda suke na san yadda zasu hadu, amma naki hada su. Dake kai kanka baya ja shine bari ka haɗa su? Ka sani wannan ba kome ka haɗa ba, sabon tashin hankalin ka budewa Zahra duk yadda kake tsammanin zaka kare rayuwar Zahra baka kai ni ba, amma haka na kyale wancan hatsabibiyar matan, don haka kafin wani lokaci ka nisanta su da Zahrah." Ya faɗa da harshen French, duk da bana ji sosai amma na tsinci wasu abubuwan, kura mishi idanu nayi, ya fada a hankali. "Ko ita wannan yarinyar da zaran na fahimci damunki zata yi zan rabata dake balle kuma su." Muna gama ci, Ummi ta ce min. "Kika ce ya Babangida yana jalingo?" Gyada kai nayi ina murmushi."anya ba xan biku ba." "Ance zuciyarki ce take da matsala, idan kika bimu wasu zasu iya kashe ki, babban farincikina. Duk tsawon shekaru baki manta da gida ba, kin tafi gare su." Tari nayi na ce mata. "Na je ne don naga ko kin koma, amma yanzu zan kira wani daga can, zai kai ki har wurinshi, ban cika alkawarin Yakumbo ba, ina fatan Allah kada ya kamani da rashin cika alkawari." "Ko daya, da kika nisance mu ba ga rayuwarki tayi kyau ba, kin je Har Takum?" "Takum?" Majid ya tambaya yana kallonmu. Dariya Yazid yayi yana faɗin. "Kada ka sake ka ambaci sunan wancan yar iskar, kafin ka kara lalata kome, kyale kowa zai bayyana don kanshi." "Kasan garin mu ne?" Na kalle shi, "A'a lokacin da kika koma na tura har can ne." "Ai ho!" Ya faɗa, haka kawai nake zargin Yazid. "Me kake nufi da yayi shiru?" "Ni kada ki saka min jakar tsana, don na lura haushina kike ji." Ya faɗa yana dariya.... 300₦ 0016341139 unity bank zahra'u yahaya Ali Katin MTN 400 8130269641 #Mai_Dambu ce [5/29, 07:47] Hlm: BHB257 Sakin baki nayi cikin takaici na ce mishi. "Nayi maka kama da mahaukaciya ce?" Gabana ya dawo ya zauna, "Wane mutum inji mutuwa, Ina sonki!" Ya faɗa da karfi yadda kowa a dakin sai da yaji, a diririce na d'ago kai ina kallon yan dakin musamman Majid da yayi wani irin kalar tausayi. "Wannan wani irin zance ne?" " Da gaske ina sonki Zahra naga idan ban yi kome akan idanun kowa ba za a iya samun matsala." Riko hannuna yayi yana faɗin. "Babu abinda ya dame ni, a gaban kowa zan bayyana abin da nake so, ki amshi soyayyata da hannu bibbiyu." Ya faɗa yana kallon Majid da wutsiyar idanu. Ko ni kaina da naga yana satar kallon Majid, haka satar kallon Majid nake balle shi da ga abin da yake nufi. "Muje." Ya faɗa da wats irin murya da na san ta b'acin rai ne zalla, mikewa nayi ina kallon Addah da nasan da magana a bakinta. Matsawa nayi tare da faɗin. "Addah in sha Allah karshen wata zan zo na ganki." "Ni zaki gani? Tow kada ki tako inda nake ba tare da Zulaihah ba, sannan ki bani yarta na tafi da ita." Da sauri na dawo da Amira bayana. "A'a ba zan baki Amirah ba, ba zan iya ba duk inda Zuzu take zan nimo miki ita, amma don Allah kada ki raba ni da Amirah." Na rungume Yarinyata, don ina ga mutuwa ce kawai zata raba mu da juna. "Ba zata nimo miki yarinyar da ke kika sayar da kanki ba "dan ja baya Addah tayi tana kallon Yazid, "wannan tsakaninmu ne na zumunci idan kana shiga Allah zai saka mana " dariya yayi yana faɗin. "Zumunci? Daga yau ba zaki kuma ganinta ba, balle har ayi zancen zumunci." Ya faɗa da yanayinshi mai matukar razanarwa ba zaka dauka shi ne ya gama dariya ba, haka suka fita ina kallonsu, "ko a cikin dangi bana fatan Yarana su farka su ga irin wannan matar." "Hmm!" Na fada ina rungumar Amirah, sake shigowa Ummi tayi tana faɗin. "Zahra baki bani number shi ba?" "Zai zo ya dauke ku a Abuja, sannan zai kai ku har jalingo!" Inji Yazid, "Na gode sosai Zahra, Allah ya tabbatar da alkhairi mu sha bikin ku." "Ke;" na fada da karfi, da gudu ta fita. Haka ya tsaya yana min dariya, tura baki nayi ina faɗin. "Ni dai ka daina min dariya." "Nayi ɗin! Na tura wurin Babangida ne, ina tsoron kada na rasa ki." "Abhna Mamina tana irin abin da nake yi " "Ai yarinta na damun Yan matana." Ya faɗa yana zungure min goshi, "wallahi ka daina bana so." "Sai kiyi." Idan har farin ciki da saka mutum shine ke warkar da mutum, tabbas Yazid ya san kan yadda zai shawo min kome nayi dariya, haka muka wuni a tare da juna. Bayan ya tabbatar sun bar kasar shi da Nana, ta ce mishi. "Wancan baturen santa yake ko?" Bai bata amsa ba, ya cigaba da tukin shi. "Hmm! Alhajin Allah sanyi kayi da lamarinta. Idan har mutum yana son abu nace mishi yake tare da cusa kanshi har sai ya samu, ba wai kana baya-baya da abin ba, Yarinyar nan ina jin alkhairori masu yawa a kanta, amma kake wasarere da ita. Gaskiya ka cire zurfin ciki ka fuskance ta ku fahimci juna." Har suka isa gida Nana bata daina,bashi shawara ba don har ga Allah tana son shi Da Zahra a duk lokacin da ta kalle su sai ta ga kamar an halicce su don juna ne, kowannensu yana da tashi baiwar da da yanayi. Sai da ya rakata sannan ya fito ta ce mishi. "Sau daya tak ake samun dama, idan aka rasa har abada an rasa kenan, kayi amfani da damar da kake da ita ka sakata farin ciki da nuna mata zaka iya kome dominta, idan kayi haka tabbas zaka samu kyakkyawar dangantaka daga gare ta." Daga haka ta wuce dakinta. Ya kai minti biyar a tsaye kafin ya wuce ya samu suna hira a falon. Zaytoona tana waya da Mamanta. Wucewa sama zai yi Hajiya ta ce mishi. "Ya Zahra da jiki?" "Lafiya lau!" Amaan da yake kwance a wurin ya ce mishi. "Majid da sauki sosai?" "Eh da sauki kai! Don zasu iya sallamarta ma an jima, ya wuce, tashi Amaan yayi ya bi bayanshi, ya same shi cikin duhun dakin,yana kwance. Kunna wutar dakin yayi yana faɗin."Abdul Majid!" Juyawa yayi yana kallon shi. Kafin ya lumshe idanunshi. "Me yasa ka dawo daga asibitin?" "Saurayinta yana tare da ita!" "Tow amma ai." "Kasan dai babu kyau nima a cikin nima? Sannan." Yadda Amaan ya kafe shi da idanun yasa yin shi shiru, yana nazarin abin da zai fada. "Suna son junansu har haka ne?" "Yadda yake sonta bana jin a raina zan iya mata wannan son, yadda yake kaf -kaf da ita bana tunanin ina da wannan jimirin yin haka. Yarinyar tana bukatar nutsuwa da kulawa ina tsoron kada na kawo ta wannan gidan ta kuma samun matsala da kowa. Balle ma zai yi wuya ta amshi tayi na, nasan nayi kuskure amma ba zata amshi soyayya ta ba." "Wani irin soyayya yake mata?" "Kulawa bata lokaci, haka kawai zai iya barin abin da yake ya taso ya zo domin ta, duk yadda naso na samu kusanci da ita, ya kanenayeta bata iya kwakkwaran motsi ba tare da ya ce mata me kike so bs." "Ni kuwa sai nake ganin wannan damar na ka ne malam sikagon, idan aka sallameta ka bata hutu na wata guda,sauran kuma sai muga yadda zamu yi." "Hmmmm ba xaka gane ba ne." "Zan gane mana!" Ya faɗa yana kallon Majid din, shigowar Aryan ya saka su a gaba yana basu labarin yadda kome yake tafiya, don haka da dare suka shirya zasu shiga Asibitin. Domin karfafa mishi gwiwa. Abin gwanin dad'i. Haka aka yi da zasu kai abincin dare, Majid jikinshi a sabule suka isa, har dakin. Muna cin abinci da Baraka Amirah tana cinyarshi, suka shigo kallonsu yayi sau daya ya dauke kai. "Assalamu alaikum! Sannunku!" "Yawwa sannunku Hamma Amaan, ya jikinka?" "Ai kin bari na zauna sai ki tambaye ni." "Afwan!" Suka zauna a kafet, sama sama suka gaisa da Yazid, da ya ga ana hira sama sama. Ya ce min. "Little bird bari na tafi, ina ga wani sati ko ta sama zan zo ki shirya zaki tafi kamaru." "Tow Allah ya kai mu!" Har zai tafi sai kuma ya dawo ya zo har inda nake ya ɗan duka kaɗan ya sumbaci goshina."zan yi kewarki." "Na gode sosai!" Na fada ina murmushi. "Abhna nifa!" Ta nuna mishi goshinta. "Hmm!" Itama ya bata kiss din, mikewa nayi na bi bayanshi. Har waje inda security din shi suke jiran shi. Hannuna ya rike. "Shi Chairman dinkun nan, ya fa takura min." "Kayi hakuri!" "Tow nayi, amma gaskiya ya dame ni." "Ayi hakuri!" "Matata idan muka je Kamaru zan roke su a bani aurenki, kin ji." "Hm" na ce. "Me yasa?" "A'a ina son koda xan yi aure, na yi kokarin niman Maman Amirah, domin ta nima mata Babanta. Ban san me zai faru ba amma tabbas yana da kyau na nima mata Babanta." "Ni ban isa ba ne sai an nima mata wani abu?" Murmushi nayi tare da faɗin. "Ka isa har ka zarta." Dakyar muka yi sallama na koma dakin na zauna, ina shiga dakin na samu ana ta hira, zama nayi a bakin gado. "Ga abinci Zahra." "Na koshi wallahi, Sultan ya mana odar abinci." "Hm! Ba zata ci ba, tunda ba shi ne ya ce ta ci ba." Kallon shi nayi cikin takaici nace mishi. "kamar ya?" "Ku tashi mu tafi!" "Wani irin mu tashi mu tafi, ke Barakatu ko? Ke da Amirah kuzo ku raka ni" Amaan ya kwashe su har da Aryan,suna fita na mike ina gyara dakin, ban san dalilin da yasa nake jin a matukar takure ba, idan na juya sai naga idanunshi a kaina, daga karshe sai da na juya kawai na ganshi a bayana, a hankali na ja da baya ina son tambayarshi. "Lafiya?" "Lau!" Ya faɗa yana kallon yadda nake ja da baya. "Ni babu abinda xan miki, kawai ina mamakin yadda. Kike kasa fahimtar." Kura mishi idanu nayi nace mishi. "Don Allah ka matsa min, bana son haka."na faɗa tare da matsawa zan bar inda yake. Fisgo ni yayi ta baya tare da k'amk'ame ni. "Please! Calm down!" Ya faɗa, a karo na biyu da naji sautin bugun zuciyar shi, wanda ya tunomin da wancan daren da ya taimaka min a cikin duhu, yana wani irin bugawa. "Ki saurare ni kin ji yadda yake bugawa." Hawaye ne ya shiga zuba a idanuna. "Na sha wahalar nimanki, na san ban kyauta ba,.amma tabbas ban yi haka don ki tozarta ba, ban yi haka don na bata miki lokaci ba, na nime miki sama da kasa ban ganki ba, na yi ƙoƙarin bin kauyika da sansanonin gudun hijira a nima min ke amma babu me kama da ke. Ni nasan da na juya ko sau daya ne na ga fuskarki tabbas da zaki zama abin tunawa a rayuwata. Sai dai kash ban yi haka ba a gado daya mun kwanta ban duba wacece ba." A hankali ya kai hannunshi inda ya soka min wuka, "Ki bani damar kankare abubuwa a ranki a cikin shi har da wannan ciwon, idan kika duba lamarina zan kasance adali a tare dake." Daga haka ya sake ni, ya fita daga dakin ni kuma na koma bakin gado na zauna ina me sakin kuka a hankali, ina jin bugun zuciyar a kunnena da zuciyata. "Me yasa? Me yasa sai yanzu ? Me yasa sai yanzu xan shiga yakin masoya." Na fada ina kuka, Yazid ya faɗa min shi kuma ya gaya min me yasa, haka ya fita ya bar ni na yi kuka har na godewa Allah, bakiɗaya sai naji kamar na tsani kaina, koda su Baraka suka dawo, ina kwance suka zo da kayan ciye-ciye, ban kalli abin da suka zo da su ba da suka dame ni nace musu su kwanta ko su koma gida. Yadda na ga rana haka na ga dare, na kasa barci na kasa motsin kirki, karshe tashi nayi na shiga ban daki nayi Alola, ina ga bani da abinda ya wuce na gayawa Allah matsalata. Kafin wani lokaci na ji sauƙin kome kamar babu abinda ya addabi zuciyata. Washe gari. Nayi ta barci har yazo ya duba ni, yadda yaki yarda ya kalle ni haka nima naki yarda na kalle shi haka shima sai gashi mun zama surukan juna, ganin haka yasa ni mikewa na fara tattara kayana,ina haɗawa Barakatu ta shigo tana faɗin. "Tante da kanki zauna na hada kayan." Haka ta haɗa kayan muka fito, dake ta kai Amirah makaranta. ** Addah dai sun isa najeriya lafiya, amma babban burinta bai wuce yadda zata samu damar ganin ko wayar da zata na kiran Zahrah ba. Haka yasa koda ta iso jalingo bata yi wani farinciki na gata a cikin danginta ba, kawai abin da ta fara yi binciken me Zahra take musu me ake kawo.musu daga Zahra. Shi kuwa Babangida zuciya daya yake bata labarin, jin yadda Babangida yake bata labarin yasa Ummi ta ce mishi. " Da dai kayi shiru, domin duk abin da xaka faɗa ba zai taba burge Addah ba." "Zaki min rashin mutuncin da kika saba ko? Haka ta saka ni a gaba da rashin kunya da rashin mutunci!" Yadda tayi ta fadar abin da Ummi take mata yasa Babangida hawa kan Ummi da fada, kamar zai dake ta. "Indai Addah da kanka zaka bukaci ta bar gidanka. Ita tauraruwa mai wutsiya ce." Bai saurare ta ba, don gani yake kamar sharri takewa Addah. ** Rayuwa dai ta cigaba da tafiya kamar yadda muke hasashe, ina kuma tsaka mai wuya, domin kuwa Yazid baya sati daya biyu zai zo Majid kuma ya kankane min rayuwa kowannensu lallai ala tilas sai na bayyana ina sonshi. Na Majid ma yafi na kowa yawa, domin hatta abokan aikina ya hana ni magana dasu Hatta Dan Larai sai da ya kira shi ya mishi kashedin kada ya kuma ganin shi da ni, shi kuma Ɗan Larai ya zata saransa na kai, sai gashi..... 300₦ 0016341139 unity bank zahra'u yahaya Ali Katin MTN 400 8130269641 #Mai_Dambu ce [5/29, 07:47] Hlm: BHB258 Sai gashi ya zo kaina yana min tijara, har fa da kirana munafuka don naga ya fini samun damar zama a kamfanin idan na kara mishi munafinci sai mub daku. "Da wa zamu daku?" "Da ni mana." Ya faɗa yana murguda min baki, akwai yanayin da idan fitina ta taso gara ka nime tsari da shi, yadda ya tsaya yana min tijara yasa ban kula shi ba, nayi kasa da kaina har ya gama ya bar kaina, duk abin da muke Majid yana kallonmu, sai bayan mun tafi sallah na gan shi da Dan Larai. Da farko yadda yake girgiza ya sani fahimtar rigima yake yi da dan larai amma daga yadda naga ya sha mur tuni dan larai ya nutsu yana bada hakuri. Bayan mun koma ya biyo ni inda nake ya tsaya a kaina, ban d'ago kai ba kuma ban damu da lallai nayi magana ba. "Kina da lokaci ne mu fita" "ina da bako daga Algers!" Daga haka na ja bakina shiru. "Wai shi bai da mafada ne?" Ban ce mishi cikanka ba, domin bana son magana. "Gaskiya ya kamata ki fahimci me kike ciki?" "Saboda a yanzu ban fahimci me nake ciki ba ko? Ko qkwai wani abu da ake son na fahimta ne ban sani ba?" Na tambaye shi idanuna akan shi. "Baki bani amsar bukatatta a gare ki ba?" Kashe laptop din da nayi tare da ɗaukar wayata na nufi hanyar waje. "Ba sai na baka amsar ba, don tuni zuciyata tayi, nisan zangon akan wanda kansa." Fadar haka yasa gabana faɗuwa, har sai da ya tambaye ni. "Lafiya kuwa?" "Lau!" Na faɗa ina jin wani irin kuka kamar xan yi shi amma ina zuciyata tayi wani irin narkewa, Shiru yayi kamar ya bini, amma ina na shiga elevator, daga kamfani makarantarsu Amirah na wuce, ina zuwa suna tashi, na tsaya a jikin motana, a wurin yau nake saka ran fitowarta har aka fara watsewa, haka kawai sai naji kamar na fashe da kuka, amma ina a hankali sai naji zuciyata kamar an karfafa mata, ina tsaye har mallamai suka fito a lokacin ne na nufe su. "Amirah bata fito ba, ban ganta ba?" "Kamar Ya? Ai kuwa tazo yau." Tashin hankali wacce ba a sa mata rana, hawaye ne ya fara ƙoƙarin kwace min, nan aka shiga bincike tun karfe uku har aka yi la'asar, aka kira yan sanda babu Amirah. Suka saka ni kiran gida ko an dauke ta babu wanda ban kira ba, hatta Amaan na.kira kafin wani lokaci duk sun hadu a kaina. A hankali duk sunzo babu wani wanda bai zo ba, amma ina Babu Amirah babu me kama da ita, nayi kuka har na godewa Allah. Idan ka kalle ni zaka zata jinya nayi, domin nayi kuka har na godewa Allah na, bana iya dogon magana, bakiɗaya tausayin kaina nake ji, har zuwa dare babu labarin ko za a iya turo sakon ana son ba biya biya wani abu a karbeta. Dare nayi aka ce mu koma gida, amma ina kasa mikewa nayi, ya d'ago ni ina kuka. "Don Allah ka nimo min ita!" "In sha Allah" Haka ya ɗauke ni muka nufi gida, a ranar kwana nayi a zaune, washi gari da safe kuwa ina mikewa na yanki jiki na faɗi. Haka aka kai ni asibiti, lokacin da na farka na ga kowa kaina babu Amirah. "Ina Aminatu?" "Kiyi hakuri ana kan nimanta." Ji nayi dakin yana juya min. Suma nayi ta musu ga jini na da yayi azabar hawa, haka yasa naji kamar zan mutu. A cikin kwana biyu, na zama kamar mahaukaciya. Da na fahimci suma da kuka ba zai min ba, wurin asuba na fita daga asibitin, na tafi makarantar na zauna, ina kallon kofar makarantar. Haka yasa har gari ya waye kowa sai gani na yake. "Fadima me yasa kike haka ne?" D'ago kai nayi ina faɗin. "ban sani ba, ko rayuwata ce tazo karshe amma babu inda zani sai naga Yarinyata." "Fadima tashi." Inji Aryan. "Babu inda zaki Aryan, yarinyata ina zan je? Ba zan iya tafiya ba." Na fada ina share hawaye, dakyar ya d'aga ni daidai zuwan Majid. "Me yasa baki jin magana? Me yasa ba zaki sakawa zuciyarki sallama ba." Durkusawa nayi kasa, ina tsuguno har ya gaji ganin zan tara musu mutane, yasa shi d'aga cak, ya saka ni a mota. "Kiyi hakuri da rayuwa." Ya faɗa min kasar kunnena. Yadda nake ihu tare da ƙoƙarin kwace kaina. "Ka kyale ni, ku nimo min Yarinyata wayyo Allah Aminatu." Cusa ni cikin motar yayi, ya ja muka bar makarantar. Ba karamin fama na sha ba, muna isa asibitin har lokacin babu wani labarin. Karfe biyu daidai na rana, sai ga Yazid. Lokacin da ya iso yaji labarin, makarantar ya nufa anan, a kasa da awa biyu da rabi sai ga labari ya fito. Ina kwance ya shigo dakin, ina ganin shi na fashe da kuka. "Ya isa haka." Yana zuwa na tashi, daura kaina nayi a kafadarshi. "Wacece kika tura makarantar ta dauke ta?" Hawaye ne ya zubo min ina faɗin. "waye xan tura? Ban tura kowa ba." Shafa bayana yayi. "Ki kwantar da hankalinki." Kuka nake tare da jin kirjina yana zafi. "Ina ji kamar zan mutu." "Ba zaki mutu ba." Ya faɗa yana matsa hannuna, "me yasa aka dauke Amirah?" "Saboda wacce take da bukatar ta ne ta dauke ta. Ya kamata ki cire wadannan mutanen a rayuwarki, domin basu kaunarki kuma basu son wani abu da zasu saka miki don farinciki sai bakinciki." Ya faɗa, "Yazid" "meye? Iya gaskiya kike so na gaya miki ko me?" Shigowar Majid yasa shi dauke kai. "Zahrah an samu wacce ta dauke ta." Da sauri na ce mishi. "Wacece?" Nuna min hoton yayi a kan tap din shi. "Ji nayi kamar xan fado, ban san lokacin da numfashina yake hawa da sauka kamar me asthma. Allura ya dauka ya ja ruwan tare da haɗawa da sauri ya danna min, kowa nayi xan fadi Yazid ya tare ni. "Sam baka da lissafi, gaka kamar me tausayi da hankali taya zaka nuna mata irin wannan abin ?" "Malam babu ruwanka da ni." Tsaki Yazid yayi yana faɗin. "A wannan lokacin kowa ya zama mahaukacin karfi da yaji, ita yarinyar da aka dauka kasan wace ce ta dauke ta?" Kallon Yazid yayi da alamun son karin bayani. "tsuk" ya ja tsaki sannan ya mike ya kwantar da Zahrah. Yana faɗin. "Duk son gwaninta, ba ta haka zaka gaya mata ba." "Kada ka gaya min magana!" Inji Majid, "A'a gaskiya xan gaya maka, daga da su baku da banbanci. Na san abin da nake yi, tun da naso na samu Uwar yarinyar ce ta dauke ta, amma ba ta hanyar da ya dace ba kana da abin da zaka iya ne? Wannan matsalar Zahra ce zata iya magance shi, mu yan taya ta ne ba yan kashe mata gwiwa ba." Daga haka ya saka kai ya fita, haka suka cigaba da bin duk inda zasu samu Amirah, sai dare aka samu wani suitcase a kofar asibiti. Aka rubuta a saman akwatin. Zuwa ga Zahra ke daya zaki bude akwatin. Hukumar asibitin da yan sanda ne suna taru. Babu wanda yayi yunkurin budewa,Har masu bincikar bom sai da aka kawo, ina zaune Yazid ta shigo dakin. Cire min ruwan yayi, sannan ya mika min hijab muka fita, yana rike da hannuna. Don tun da na farka bana hmm-hmm bana yi, ina cikin d'imuwa. Gaban jakar ya ajiye ni, ina gani na fahimci sakon Zuzu ce. Jikina ne ya dauki rawa, na kalle shi kamar xan yi kuka na girgiza mishi kai. "Babu abinda zai faru." Inji Majid, sai na kai hannuna zan maida baya, daga karshe dukkansu biyu suka rike hannuna na bude jakar, Amirah ce kwance a cikin shi, rungume da Bunny Bunny, da sauri na d'ago ta tana barci me nauyi. A jikin rigar ta aka saka. *Am sorry na bata maganin barci ne, amma na gode Yarinya ta girma. Yawwa akwai daya suitcase din a kofar gidanki* ciro yarinyar nayi Nurse suka amsheta. *Don Allah kada ki ni footage dina, idan kika yi haka zan ji babu dad'i. Kuma zan amshe Y'ata wallahi" " A kashe case din anan." Dariya Yazid yayi yana faɗin. "Tow kun ji me kara ta janye." "Amma Zahra criminal case ne." Inji Majid, "And so what? Duk abinda nawa yayi min ina iya rufa masa asiri, koda kuwa tawa rayuwar yake bukata, ina hakura na bashi akwai wani abu ne?" Wannan maganar ya mishi zafi, a binka da tsohon soja tuni ya daka zuciya ya bar wurin. Yazid dariya abin ya bashi, haka ya sa shi riko hannunta, yadda Yazid yasan Zahrah sam baya jin zafi dayawa akan Majid yana shige mata,don billahi azim tsaf zata kunce maka kome. Haka yasa shi riko hannunta har dakin da aka kwantar da Amirah, suna tsaye. Bana ce ina cikin farin ciki ba, amma yau ganin sakon Zulaihah ya fama min ciwo dayawa, na kasa kome sai hawaye, har likita ya fito ya ke gayawa Yazid da sauki sun rage kaifin maganin, a daren barcina ragagge ne domin kuwa ina rufe idanuna zan ji kamar za a dauke ta, Allah ya taimaka Yazid na tare dani, yana rike da hannuna. "Kiyi hakuri kin ji." "Nayi wani abu da bai dace ba ko?" "A'a sai dai soyayyar yan uwanki ta rufe miki idanu." "Ya zan yi?" Na tambaye shi, "ki hukunta su haka zai saka su fahimci lallai kina da fushi." Murmusa mishi nayi, kafin na ce mishi. "Ba zan iya ba, ba zan tab'a ba idan ayi haka na zama mara hakuri, duk abinda zumunci yayi min ba zai saka na saka wuka na datse alakata dasu ba." "Ina sonki!" Yau kalmar tafi koda yaushe dukan zuciyata, na tsayar da kome nawa da wannan fitinar gara na auri Yazid. Saboda ya bani farinciki sama da kome ya saka ni dariya kma zai cigaba da saka ni dariya. "Zan tafi Marwa kan yanzu da Amirah. Kai kuma ka tafi wurin Ya Babangida kuyi magana, zaman Nijar ya kare idan kuka tsayar da magana ina marwa!" Jan hancina yayi yana faɗin. " Na jima da jiran wannan ranar. Yau gashi Allah ya kawo min." Ya faɗa yana murmushi. Nima sunkuyar da kai nayi ina wasa da yatsuna. Haka muka kwana a wurin masallaci ya wuce ni ma a dakin Amirah nayi sallah, bayan na idarwa na wuce dakina, na hada tea na sha na hadawa Amirah na kawo, tana barci har lokacin. Ina rungume da ita. Barci ya fara fisgana har nayi me nauyin, sai ji nayi ana shafa kaina. "Zahra!" Bude idanu nayi dakyar amma ina barci yaci karfina. "Na gode sosai, naga Amirah sugrah. Amma ina son Y'ata na kasa barci without aamirah, nasan ke adila ce kuma zaki bani Y'ata sannan ki gaya min nawa kika kashe zan biya amma ki bani Y'ata don Allah nima ina son naji dumin ta As a mother." So nake na bude idanuna, amma.nasaka ina son na tashi amma na kasa, abu daya na sani na k'amk'ame Amirah, a hankali barci yayi awon gaba da ni. Ina ga mafarki nake. Ban tashi ba sai dare, a lokacin hankalin Kowa ya tashi,don a gwada jinina da aka yi ne aka tabbatar akwai sinadarin bugawar a ciki,a hankali na bude idanu. "Alhamdulilahi ta farka!" "Tun yaushe nake barci?" "Tun five na safe." Kokarin tashi nayi na kasa, don har lokacin babu karfi a jikina. "Me ya faru?" Na kuma tambayarsu. "Kwantar da hankalinki babu abinda ya faru." Nifa na zata mafarkin zuzu nayi, sai da aka tabbatar min an samu abin maye a ruwan tea da nasha, ware idanu nayi tare da dafe goshina. Dakyar na tashi na shiga ban daki nayi Alola da wanka zan fito naga dan takarda a jikin allon madubin banɗakin. *Ba mafarki kike ba, da gaske ina son Y'ata nice na saka miki abin maye a ruwan tea ɗinki." A hankali na zare takardan na yi plushing dinsa.... 300₦ 0016341139 unity bank zahra'u yahaya Ali Katin MTN 400 #Mai_Dambu ce [5/29, 07:47] Hlm: BHB259 Ina fitowa na samu an shimfida min abun sallah, sai da nayi sallah sannan nayi addu'a, abincin da Yazid ya Kawo min naci. "Babu yadda zan bar garin nan kafin nan da jibi?" "Akwai mana." "Don Allah a kai ni Marwa!" Na fada cikin tsananin kad'uwa, murmushi yayi yana faɗin. "In sha Allah daren gobe zaki bar garin nan, amma ki fara ajiye musu aikinsu." "Tow! Yanzun nan." Na fada jikina yana rawa don bakiɗaya hankalina baya jikina, rike kafada ta yayi yana faɗin. "nutsu" na fashe mishi da kuka na ce mishi. "ya zanyi? Yan uwana sune matsalata." "Kece kika mai da su matsalarki." Cikin kuka nace. "Kamar ya? Taya na mai dasu matsalata? Taya zan ." "Zaki iya mana, ki kwantar da hankali sannan ki nutsu ki saka a ranki zaki tafi kuma zuzu ba zata kuma zuwa wurinki ba." "Zata zo wurin Yarta." "Ba zata kuma ba." ... Dakyar ya rarrashe ni, sannan na rubuta takardar barin aiki. Abin da ya faru... A ranar da Nawwas ya ɗauke ta, a ranar ya ga Amirah. Kuma dama suna tab'a juna da Zuzu,akan ya nima mata inda Zahra take da Babynta. Sai gashi ya ganta don haka ya tura mata da hoton yarinyar domin kuwa ya jima yana bibiyar yarinyar da makaranta da ko ina da suke, tunda ya tura mata Zuzu ta d'aga hankalinta. A ranar da tazo a ranar Zahrah ta hadu da su Addah tana airport din, sannan ta je har asibitin tana bibiyarsu. Lokacin da aka sallame su, ma tana ganinta babban burinta shine yarta, kuma ta ganta amma tana son lallai ta amshi abinta ta koma U.S don ba zata iya rayuwa a nan Afrika ba, ta saba da rayuwar can har ta gina kanta da Yarta. Don haka ta je makarantar daidai anyi break ta samu damar fitar da yarinyar daga makarantar, kuma dalilin yadda aka yi ta dauke ta, don kwallonsu Amirah ya fito waje ne, ita kuma tazo dauka, shine ta ce mata."zo gashi a mota ta!" Da gudu yarinyar ta shiga, tana shiga ita kuma ta rufe motar ta fisgeta da gudu. "Ina za muje?" "Zan kai ki wurin Maminki ne?" Ta mika mata Bunny Bunny, wanda ta shaka mata iskar da ya sumar da ita. Daga hakan ta wuce da ita wani gidan da Nawwas ya ajiye mata, tun da ta kai yarinyar ta farka bata da wani aiki sai kuka bata cin abinci a tsawon kwanaki biyu nan, yarinyar bata barci duk yadda Zuzu taso ta daina damuwa, amma taki don haka ta rasa yadda zata yi da ita. Kawai ta dura mata maganin mura, ta sayo mata kaya kamar hauka, amma haka Yarinyar nan taki kulawa ita Maminta kawai, ganin ga Zahra a can asibiti haka yasa ta hakura ta kai mata ita asibitin ta ajiye ta, sannan ta kai sauran kayan gidan Zahra. .............. A lokacin da aka sallame ni muka dawo gida, a daren na tura takardar barina aiki, da sassafe sai ga Majid. Yadda yake buga kofar gidan yasa ni fitowa waje, na bude kofar kamar zai fada kaina ya shigo. "Me yasa?" "Aure zan yi kuma na ajiye aikin zan bar kasar, zan koma ƙasata." Na faɗa mishi cikin magagin barci da na farka,"Zahrah!" Naji Muryar Hajiya. "Na'am!" Na ce ina kallonta, "zauna mu yi magana." Zama nayi a hankali ina kallonta. "Abdul ya ce min kin ajiye aiki. Wani abu aka miki barazana ne?" "A'a kawai zan tafi garinmu ne, sannan zan yi aure a algeria ne." "Aure!" Ta tambaye ni a mamakance, wato tayi mamaki. "Kina nufin kin samu mijin aure ne?" Murmushi nayi nace mata, "Hajiya mace bata rasa mijin aure, sai dai idan lokacinta bai yi ba." "Majid din fa?" "Ban gane ba?" "Yana sonki?" "Hajiya kin manta yadda kika bukata ne?" "Don Allah ki...." "A'a Chairwoman, ba ayiwa mace dole kuma taya zata auri mutumin da bata sonshi. " Inji Yazid. Ya faɗa yana shigowa daga bakin kofar. Cin kwalarshi Majid yayi. "Kai meye haka?" Inji Yazid yana cire hannun Majid a wuyarshi, "Ni namiji ne sai da na share fagen fama kafin na samu Zahrah don haka ba zan yi faɗa da kai ba, a gaban matata." Sake wuyar Yazid yayi yana me barin gidan, "Idan kudi kike so." "Hajiya an wuce wurin, kiyi hakuri."na faɗa ina me juyawa zuwa dakina, sai yanzu nake iya tuna abin da ta gaya min, ban da ina ganin girmanta da yau na gaya mata magana, amma ina tana da wani irin girma a idanuna wanda ba zan iya mata fitsara ba, na kira Iyayen Barakatu na gaya musu zan tafi garin mu suka ce ai su Barakatu tawa ce duk inda naso nayi da ita don haka na gayawa Yazid shiga da fita yayi ina karyawa sai gashi da wasu takardun. "Marwa zan kai ki da kaina." Haka muka shirya cikin shigar alfarma muka bar gidan sannan muka wuce kasuwa muka yi sayayya. Kafin mukayi ta yawo sai dare muka wuce airport. Karfe bakwai muka bar Nijar, sai da na sauke ajiyar zuciya. Domin nasan nayi nisa da Zuzu, sai dai ina ji a raina kamar na gwada son kai. Kallon shi nayi ina faɗin. "Amma banso kai na ba ko? Yarinyar nan ban rabata da uwarta ba ko?" Jan hancina yayi yana faɗin. "Duk ranar da na mallake ki, a ranar zan gaya miki me kika yi amma yanzu ban da amsar baki." Juyar da kaina nayi, "Yawwa nayi magana da Babangida, ya ce idan naje Marwa zai zo shima sati me zuwa sai na tura magabatana, su zo nima min." Kashe min idanu yayi. Tunda maganar aure ya shigo na fahimci Yazid kwarkwar ne. Kasa yayi da kanshi ya rad'a min magana a kunnne rufe bakina nayi da kunnen duka. Haka yayi ta zuba min rashin kunya, kamar nayi kuka,.har muka isa da asuban fari. A airport din muka karasa kwana ya ce min. "Yanzu don Allah idan da kin zama matata ba sai dai ki lullube ni da bargon kauna ba." "Kai ka sani wallahi" na fada ina sauya wurin zama, zama yayi a kusa dani yana dariya. "Allah bargon kaunarki zaki lullube ni." "Yazid ka fita idanuna dama haka kake?" " Eh wallahi har na wuce haka, baki san wani abu ba, nifa..." Wucewa wurin sallah nayi na bar shi awurin yana min dariya, haka kawai yake jin nishadi a ranshi. Sai da gari yayi haske muka dauki motar Marwa. A ranar naji kamar anyi min bushara da aljanna, haka muna tafe ina share hawayen farinciki. Sai da muka isa a wani babban gida me haɗe da masallaci, a kofar gidan manyan maza ke karatu gabanshi kadan yara ne suke karatun suma. Kallona yayi yana faɗin. "wancan shi ya haifi Mamanki, Sheikh Aliyu Wodabbe." Hawaye ne ya zubo min. "Share hawayenki kin ji." A hankali ya fito tare da bude min kofar, Barakatu da Amira da suke gaba suka fito, wani irin kuka ne ya kwace min ina rike da rigar Yazid. "Ya isa haka bana son kukan nan." D'ago kai yayi ya zuba mana idanu, hannu ya d'aga ya fara addu'a, suma almajiran suka d'aga tuni aka tashi. A hankali ya mike tare da dogara sandarshi har inda muke. "Fatimah Batula!" Wani irin kuka ne ya kara zuwa min, "Sannu da zuwa, sannu da kokari Mai martaba, ka cika dan halak. Kayi abinda ya dace." Daga haka ya wuce damu cikin gida. "Fendo? Sume yau ga kishiyarku tazo gare ku." "Maza a kira min Aminatu ga Qurratul-Ayn dinta ta zo." Kafin kace me an cika falon Malam, tare da kiraye-kirayen waya,Yazid kuwa kamar su goya shi. A ranar dai muka rabu da shi, don tunda ya fita bai dawo ba, Baraka da Amirah ma ban kuma ganinsu ba, gani ga kakata sun gayawa dangi da yan uwa,washe gari da sassafe ina barci naji ana shafa kaina. Bude idanu nayi na ganta na zata Hajiya ce sai na lura ita bata kai Hajiya girma ba, murmushi da hawaye cabe-cabe a idanunta, tashi zaune nayi a hankali na ce mata. "Mama!" Rungume ni tayi, tana kuka ina kuka. "Kiyi hakuri Kiyi hakuri na tafi ban ce kome ba" "Babu kome Mamana." Haka muka yi ta kuka, har dare ina dakin can aka kawo min Amirah. "Yarki ce? Kin yi aure ne?" Girgixa kai nayi na ce mata. "Eh Y'ata ce amma bani na haife ta ba." Ina lura da hawayen da ta sauke har suna gudu. Haka muka ci kuka muka godewa Allah. Bayan kwana ɗaya, aka ce baki daga Nijar zasu zo haka kawai naji gabana yana faduwa, wurin karfe biyar muna falon da Yazid da yayi kewata, muna zancen mu na masoya, ya ce min.."na gayawa Malam ina sonki kuma kin ce na fito har mun yi magana da Babangida, amma Malam bai ce min kome ba sai murmushi da yayi min ina cikin damuwa." "Kada ka damu..." Ban karasa abinda zance ba, naga Majid a kanmu. Murmushi yayi yana faɗin. "Ashe kanwata ce nake tare da ita, sakatariya maza ki haɗawa Yayanki Tea." Banza na bawa Ajiyarshi, Yazid ya mike yana saka hannu a cikin aljuhun wandonshi na rako shi waje, "Zahrah ina ganin kamar ba zan same ki ba." "Kada ka ce haka." "Majid;" ya faɗa da sanyin murya, "ina sonka, ina kaunarka yau zan gaya maka ina sonka." Na fada cikin matsanancin kuka, shafa sajenshi yayi yana faɗin. "ranar da aka kai min ke ba zan barki ki huta ba." Rufe idanu nayi tare da juyawa da gudu, yana dariya. Wato lokacin da suka iso ganin Aamirah da Baraka a falon Goggo Sume haka yasa suka san nice bakuwar, shi kuwa uban rawan kai ya zata daga ni sai malam ne yana zuwa ya ga ni da Yazid ne, shine bari ya zuba min iyayi. Shi gashi nan zanzalale kaudadde. Lokacin da na koma zauren zan shiga cikin gidan ta zauren ya ce min. "Ni da shi waye yafi wani a wurinki?" Daidai malam zai shigo zauren. "Sake ni na wuce." "Ba zan sake ki ba, ki gaya min meye ya fini da shi? Ni fa dan uwanki ne? A Yanzu da kika gano dangantakar mu ba zaki kauna ce ni ba?" "Ko ɗaya, kai matsayin da na.baka Yayana ne shi kuma matsayin da na bashi abokin rayuwata ne, idan na aureka me zan kira auren da shi? Auren dole ko na tausayi? Ko auren tilastawa? Ka gane ni ina son Yazid ne ko babu kome kayi min wani alkhairin da ba xan manta da shi ba, amma Yazid yafi cancanta a rayuwata." "Zahra ni dan uwanki ne?" "A bangaren auratayya ana ajiye dangantaka ayi batun auratayya ni shi nake so!" "Zahra ina sonki!" "Kayi hakuri!" Na faɗa tare da juyawa na fita daga zauren, juyawa yayi ya kalli Malam. "Ina sonta, Malamijo!" "Koda ƙaddarar ku daya, zan nime Allah ya bata wanda yafi kwanta mata, ita mace ba a mata dole, idan ka iya bakinka da kokarin niman yardar ta Allah ya taimaka, idan kuma taki duk da ƙaddara ɗaya ce, zan bata wanda take so." Hankalin Majid ya sake tashi, sai.dai yanayin yadda ya rayu yasa bai da wani hanyar da zai tankwarani, Malamijo yasan abinda yake faruwa, sauran yan gidan babu wanda ya sani asalima a gaban kowa lafiya lau, amma ni da shi bamu ga maciji.........300₦ 0016341139 unity bank zahra'u yahaya Ali Katin MTN 400 #Mai_Dambu ce [5/29, 07:47] Hlm: BHB260 A wannan duniyar babu abinda bazai baka mamaki ba, wai Hajiya take kula dani a matsayin nata, haka Anisah da Zaytoonah. Kallonsu nake kawai. Da suka matsa min na daina zama a cikinsu gara Jamilah da Amaan, idan ka ga ina Dariya tow daga kakannina sai Jamilah da Amaan, sai ko Yazid, kiri-kiri na nuna musu bana tare da su. Kwana biyu da zuwana, muna cin abinci Nura dan kawun mu Musa ya shigo yana kallona ya ce min. "Zahra balarabenki yana kiranki a waje." Tsame hannuna nayi. "Yanzu Zahra haka xaki auri balaraben nan ga dan uwanki." Juyawa nayi na bankawa Anisah kallo. "Karuwarce zata auri dan uwanki? Karuwarce zata zauna da dan uwanki. Ko kin manta kwadayin kudi ya kawo ni kamfaninku?" Ina fadar haka na wuce abuna, na fita ban kuma shiga dakin ba, na je na same shi ya gaya min cewa. "Yana son ya tafi, ana niman shi ne!" "Sai yaushe zaka dawo?" "Zan dawo in sha Allah, ni dai ki kula min da kanki. Zahrah ina son na roke ki wata alfarma." Ya faɗa yana kallon yadda nake murmushi na ce mishi. "Allah yasa zan iya maka alfarmar nan!" "Idan ban dawo ba, kada ki jira ni." A hargitse na zuba mishi idanu. "Me kake nufi?" "Ina nufin idan ban dawo ba, kada ki jira ni?" "Me yasa nayi maka wani laifi ne?" Na tambaye shi. "Ko daya, sai dai ina sonki ne.!" Ya faɗa yana murmushi, kafin ya cigaba da cewa. "Kin tambaye ni akan abin da kika yiwa Zulaihah akwai rashin adalci a ciki ko?" Idanuna da suka kad'a jajjur, na zuba mishi.."Tabbas akwai son zuciya a cikinshi. Shakuwa gaskiya ce amma dauko mata Y'a da kika yi kin so kanki. Ita tafi ki son zuciya, ta fiki sonkai a duk inda gaskiya take mu gayawa juna shine cikon zaman lafiya, idan Zuzu tazo ki hakura da Aamirah ki bata yarta, ba zata kuma cutar dake ba sannan kuma tare da mahaifiyarki kada ki ce zaki saka arai a kan wadancan yan uwanki, ki zauna da mahaifiyarki zaki samu nutsuwa, zata zo zata biyo yarta kada ki sake ki saka yarinyar a ranki har ta fahimci ita ce matsalarki, ki basu yarsu wani lokaci muna hakura da abubuwan da muke so ne sai a zauna lafiya, kada ki ce zaki ajiye kome don Amira, idan kika yi hakuri zaki haifi kamar Amina zaki haifa zaki haifa abinki." "Da alamu idan ka tafi ba zaka dawo ba?" Dariya yayi min yana faɗin zan dawo mana, idan ban dawo ba kada ki jira ni." "Zan jiraka har karshen rayuwata." Rufe min baki yayi da hannun shi, "Zan dawo. Sannan ki dauke ni a matsayin Yayanki dan uwanki, me share miki kuka?" "A'a ban yarda ba!" Na fada da ƙarfi, juyawa yayi ya bar zauren, zama nayi a wurin na fáshe da kuka, ta asalin babban kofa ya shiga gidan yayi musu sallama, sannan ya fita kamar ance na leka. Na gansu tare da Majid suna tafawa har da hira. Abin su har da dariya. Ban ji me suke fada ba sai gani nayi Majid ya rike kunnen shi. Lallai wato ni zasu yi wa dan waken zagaye. Juyawa nayi rai a b'ace. "Me yasa ba zaki hakura da shi ba?" Kallon Mamana nayi, kafin na fashe da kuka. "Yayi min halacci." "Duk da haka zuciyarki bata samu wanda kike so ba ne, Yazid yayi miki halacci, domin har abada ba zaki samu na biyun shi ba, adali me adalci da tausayi. Ba banza ya zama Sultan ba." "Mama ina sonshi." Riko hannuna tayi, ta ja ni zuwa waje sannan ta bude mota ta saka ni, muka bar gidan a idanun Majid. "Muje waje ki sha iska, nayi kewarki." Haka muka ta zaga gari kafin ta kawo ni, wani lambu. "Kyautata miki da Yazid yayi babu wanda ya isa ya ce bai cancanci aurenki ba, domin yayi miki abin da muma bamu miki ba. Abisa ala'adar mahaifinmu idan mace ta haɗa maza biyu, kuma suna sonta yana iya basu addu'a duk wanda yayi addu'ar aka dace zai zo mishi da zancen aurenki ne, Lokacin da muka hadu da mahaifinku ina da wanda nake son zan aura. Haka Babanku yayi ta bibiyar rayuwata, amma naki kula shi. A lokacin da yazo akwai dan Yayan Yafendo da muke soyayya. Haka Malamijo ya basu addu'ar, me haɗe da niman zabin Allah. Ina ji ina gani suka yi addu'ar, kwana biyu Abbas yazo ya ce ya janyewa Mahaifinku, shi yana da wata rayuwa na daban zai tafi domin cimma ta." Hawaye ne ya zubo mata,tayi murmushi. "Allah ya gani bana son Abubakar, amma haka suka tasani a gaba na aure shi, da fari muna zaune anan, ya ce zai koma garinsu bayan na haife ki. Kin ga yan gidan mu babu wanda bai tafi aikin hajji ba, gata na duniya na samu..amma da Allah ya ƙaddara sai gashi na auri makiyayi wanda bai san fari a zamani ba sai dai addini kan babu laifi don yana da ilimin addini sosai. Koda nazo cikin gidan sai na fahimci dangin shi basu farinciki da ni, haka na zauna idan na cire miki Mahaifinsu babu wanda ya dauke ni mutum, amma Alhamdulilahi tunda wanda ya kawo ni yana sona, haka na cigaba da zama har zuwa lokacin da na bar gidan da laluran gushewar hankali, Allah ya takaita min wahala, daga can gida na dawo a hanyar dawowa na hadu da wadanda suka san Malamijo, sai dai na sha azaba domin wata na takwas ina tafiya da kafa, ga tsohon ciki. Haka na dawo gida aka min jinya, kafin na haifi Zaytoonah. " Hawaye ta share bayan ya cire glass ɗinta, "Bayan nan ban kuma yarda na ambaci sunan Abubakar ba, domin a gidan nasan Addah ta tsane ni, sannan ta sha alwashin sai ta ga bayanki, na jima da fahimtar bata sona ita da sauran matan gidan, amma wannan ba dalilin ba ne da zan kullace ta, domin haka ta tsani Babanku kamar me, duk da yana mata bauta amma gani take kamar aurena yasa shi juya mata baya, don ta sha cewa ya sake ni. Amma yaki ban zargi kowa da yayi min wani abu ba, Amma nasan an zalunce ni matuka gaya." Share hawaye nayi ina wasa da mayafin hannuna. "Malamijo yana son duk wacce zai mata aure ta kasance mai biyayya." Na yarda ya zab'a min miji, amma Mama ban da Majid." Na fada ina shashekar kuka. "Shima bai ce zai zab'a miki Majid ba, idan kuma Majid yana cikin kaddararki haka zaki hakura da shi." "Na hakura kika ce? Mutanen da basu san darajar rayuwa mutum ba, Mama har Hajiya sai da tace na rabu da Majid me zan yi da su?" "Duk da haka me yasa kika tawo da yar da ba naki ba? Kin gagara rabuwa da mutanen da suka tsane ki sai waɗanda." "Mama kada ki ce min kina tare da Hajiya?" "Ba haka ba ne, ba zan tayaki faɗa don kawai an b'ata miki ba, amma zan tashe ki daga barcin da kike kuma ba zan miki dole ba. Amma ki raba kanki da su Addah don rayuwarki suke nima." Kuka na fashe da shi tare fa faɗin. " Wasiyyar Baffana ne fa!" "Idan ma me nene ya kamata ki ajiye kiyi fama da kanki, a wannan fagen ba naki ba ne, ki barsu shi ma bai iya da dangin shi ba balle ke." "Mama kina nufin!" "Idan kin mutu saboda, ina da Zaytoonah. Kuma ba zan fasa farincikina saboda ke ba, idan kin so ki rungume su ai ba wani abu ba ne waye ya damu, ban san wahalarki ba abu ɗaya na sani idan wani abu ya same ki, wallahi tsakanina da ke sannu. Domin ba zan manta da azabar da na sha ba, kuma idan Zulaihah tazo ki bata yarta, Babu kira babu abin da zai ci gawayi. Kema ki wanke kanki daga kallon da ake miki, muje." Idan nace Mama itama tabi layin su Yazid ban yi mamaki ba, haka muka dawo na shiga dakin Yafendo tana zaune, Aamirah tana gefenta tana tashan zuma. Zama nayi a gefensu ban san lokacin da na fashe da kuka ba, wani irin kuka nake wanda yasa Yafendo murmushi. "Kiyi hakuri a bata yarta don ko kin hanata, ba zaki tab'a farin ciki ba sannan alaƙarku ba zai dawo ba, amma idan kika bata zaki rayu cikin farin ciki. Allah ya sakawa Yazid da alkhairi. Jiya mun jima da shi." Dattijuwa me tarin ilimin addini da sanin rayuwa tayi ta min nasiha har Mama ta shigo, Hajiya kam ko da ta shigo kasa magana tayi. "Mama zan maida ta, amma don Allah kada ki min auren dole." Murmusa min tayi tana faɗin. "ba zan tab'a miki dole ba, har abada babu dole a cikin gidan nan domin an daina." Da wannan naji sauki a raina. * Zuzu Kamar tayi hauka, lokacin da taji labarin Zahra sun bar nijar da ita. Bata kwana a Nijar ba, ta nufi Nigeria don dama akwai nata da Addah. Akwai wani al'amarin da sai ka gama shirinsa, sai Allah ya lalata maka kome. Zuzu tayi niyyar sai ta binciko inda Zahra take, bayan ta gama yiwa Addah tijara. Sai dai bayan ta isa Kano, daga Kano suka hau jirgi zuwa Yola, a wannan yanayin al'amarin Allah ya shigo, domin shima bai tab'a saka ranshi zai ganta ba. Yana waya da wani abokin cinikayyar shi, kawai ya ganta kamar saukar aradu. Sake wayar yayi kamar wani gaula, ya bita da idanun zata fita daga airport din, da wani irin azama yayi kanta da sassarfa. "Zulaihah!" Ya fada da dan ƙarfi. Juyawa tayi tana kallonshi, jikinta ne ya dauki rawa. Ta rufe bakinta tana jin wani irin hawaye na zuba mata, karasowa yayi yana haki, abin ka da jiki duk madara. "Ina kika shiga?" Kallon shi tayi tana ƙara tuna abin da ya kawota, juyawa tayi ta cigaba da tafiyarta. "Zuzu!" Kamar zata tsaya sai kuma ta cigaba da tafiyarta. Biyo ta yayi tare da riko hannunta, cikin wani irin fushi ta fisge hannunshi. "Kada ka sake tab'a ni, na gaya maka." "Ina abin da kika haifa?" Ya tambaye ta, cikin wani irin yanayi. "Ka bani ajiyar ciki ne? Malam ban sanka ba, bani hanya na wuce." "Ki saurare ni!" "Sai kayi kuma!" Fitar da ya fasa kenan, kallonta yayi gata da wani irin shiga kamar irin yan iskan yan matan nan, hujin kunnenta kusan biyar. Ga hanci, wuyarta kuwa wani dan iskar abin wuya ne baki. "Muje na kai ki Taraba." "Ka ga nayi maka kama da yarinyar arziki ne?" "Haka na same ta, a shekarun baya nasan haka nasota, haka na raba dare da ita muka raya dareraki masu yawan gaske. Nasan kina sona!" "Karya ne, bana sonka kada ka sake damuna." Rungume ta yayi ta baya, "kiyi hakuri Uwar Yarana." Wani irin kuka ne ya kwace mata. Riko hannunta yayi suka tafi wurin Motarshi, bude mata aka yi ya sakata. Ta cigaba da kuka wiwi. Haka yayi ta rarrashinta, a ranar tafiyar shi zuwa China ne amma haka ya hakura, ya nufi Taraba da ita. Lokacin da suka isa ya samu gidan ana ta rikici. Tsakanin Addah da Matan Babangida wani irin kunya ya rufe Zuzu. "Yaushe zaki girma? Yaushe zaki daina abin Kunya?" Ta fada da karfi, rikota yayi yana faɗin. " Ki kula Soulmate!" Cikin wani irin kuka ta ce. "Gaya min meye addah take so?" Ta janyo jakarta ta tura mishi. "Aiki na ne da nayi da jikina da rayuwata." Cikin wani irin kuka ta ce. "Sayar dani kika yi fa? Sayar da yar cikinki, saboda hassada da kyashin. Yau ga Zahra tana cikin farinciki da dangin Mamanta. Zahra tana rike da yar da kika raba ni da ita, ina son naga Y'ata abu ya gagara." Ta durkusa a wurin tana kuka. "Zamana a U.s ban da wulakantacen rayuwa me nayi? Nice rawa a gidan rawa tsirara, Ni ce gamsar da wani tsoho...." "Kome kika yi a duniya, ina sonki a haka ya isa haka. Ina sonki a haka ko da kuwa kece Magajiyar karuwai, Lamido yana sonki yana kallonki a matsayin Uwar Aamirah!" Indai Zahra da take rike da Amirah ita ce Zahrah da take fada.... 300₦ 0016341139 unity bank zahra'u yahaya Ali Katin MTN 400 #Mai_Dambu ce [5/29, 07:47] Hlm: BHB261 "Zahra ta Nijar ce Yarinyar take wurinta?" Ya kuma tambayarta domin ya tabbatar. Cikin kuka ta gyada mishi kai, cikin shashekar kuka ta ce masa. "Taya zaka ji idan mahaifiyarka ta kasance kamar Addah ya zaka ji? Tsananin son kudi da abin duniya ya zaka ji?" Cikin wani irin kuka ta zauna dabas ta ce mishi. "Ita ta haife ni, ita tace na bi namiji, na kwana da maza na kawo mata kudi a hakan na hadu da kai." Takasa tsayar da kukanta tana kallonshi. "Still kana nan akan bakanka, kana son tarayya da Ni haka?" Murmusa mata yayi yana faɗin. "Ina sonki!" "Tow mutuwa xan yi!? Mutuwa zan yi da bakincikinta da halin da nake ciki, wannan matar gara na mutu na bar mata duniyar bakiɗaya na gaji da halinta. Wayyo Allah na." Ta fada tana ihu da birgima, hauka da rikici babu wanda bata yi ba, haka tayi ta rigima da rikici. "Idan kudi ne gashi nan tayi ta ci har ta mutu, amma ta bar min rayuwata na samu taslima na gaji na gaji da azabar Adda da masifarta." Idanun Adda kirmisisi tana kyallara daya tana kallon Zuzu, ina ruwanta ta ce mata. "Ina ruwana jan kudina zan yi ke kika ji wurin" haka ta ja a kwatin duniya sabuwa, shi kuma Sk Lamido ya fitar da zuzu daga gidan da take ta Ajiyar zuciya. A tow abun kunya bai dame Addah ba, a gidan ma hada husuma tayi tare da gulma wai Amaryar Babangida tana yin asiri tana zubawa a cikin abinci, ta gayawa Uwargidan, shine Ita uwar gidan ta samu Amaryar da fada, da habaici da Ummi ta ga haka ta fahimci Addah ce ta haɗa husumar shine ta saka su a gaba aka mai da magana anan suka kira Addah aka fara tone-tone. Kai Addah masifa ce. • Yazid ya tafi ya barni da kunci da b'acin rai. Wanda ya ja min na tsani kowa da kome. Hajiya tayi juyin duniyar nan na dawo jikinta amma naki, domin idan na tuna abin da ya faru sai naji bana son shiga harkar kowa kuma bana son ganin kowa. Satinsu daya suka bar Marwa, ni kuma na bi Mamana Duola, a nan na ƙara samun wata irin nutsuwa da saukin warware wasu abubuwan. A hankali Mama take jana a jiki tare da nuna min kome, kai Uwa na da dadi. Wayyo Allah na wannan abin da take min ne yasa na ji lallai zuwa yanzu tafi ni gaskiya, kuma maganar zuzu xan kirata na bata yarta. Haka na nimo Ya Babangida na kira shi. "Yaya Babangida ina son zuwa amma a Yola please!" "Tow in sha Allah." "Zan turo maka kudin abin hawa." "Kada ki damu, amma gaskiya Addah ta dame ni." "Hmmm!" Na fada ina jin wani irin zafi a raina, kafin na ce mishi. "Ba zaka gane wacece ita ba, sai gaba kaɗan." Na fada mishi sannan muka yi sallama. Tun daga lokacin na fara hada mata kayanta. Dakin Mama na shiga na zauna. "Ya dai Batul?" "Mama zan iya rabuwa da Amira kuwa?" "Me zai hana kuwa? Zaki iya mana." Haɗiye kukan da ya taso min nayi. "Ina son yarinyar domin na...." Sai na kasa fada mata kome, "kin shayar da ita ko?" Gyada kai nayi, "halin Babanku ya miki yawa." Ta fada tana miko min wasu dogayen riguna. "Duba sun miki kyau?" Tashi nayi ina gwadawa. "Ya miki kyau sosai, akwai takalmi da jaka a cikin wardrobe ki duba kalar da kike so." Haka na bude na dauki kalar da suka min na rufe mata, "me zaki kaiwa babangidan?" "Babu don xan tura mishi kuɗi" "Idan kina da wani abin bukata ki gaya min." "Babu Mama!" A cikin kwanaki goma, bayan na turawa yaya Babangida kudin ya tafi na nufi Nigeria. • A Yola kuwa Sk Lamido ya gayawa Mahaifiyarshi abin da ya faru, sai da tayi kuka don farinciki. Sannan ta tsaya mishi tsayin daka sai ya auri muradin shi, haka yan uwanshi kamar su tafi Cameroon su dauko Amirah kowa sonta yake. Haka matan shi, bai boye musu ba sannan ya sake daya ya bata dukiya me yawan gaske ya ce zai auri Zulaihah. Sai dai har lokacin Zuzu taki bashi fuska don ma ta kwantar da hankalinta ya ce mata ta shirya su tafi Marwa. Tace a'a ta fasa zuwa domin da kunya ta samu Zahrah ta ce ta bata yarta bayan wahalar da ta sha akan yarinyar wanda tayi ma Allah ya yafe mata. Wannan abin da ya faru sai da ya kira Majid ya bashi address din Zahra a can douala, amma sai da ya gaya masa abin da zasu yi nan ya gaya mishi shima zai zo Nigeria ɗin, sai su tafi tare, kiran Zuzu yayi ya gaya mata, ita kuma ta gayawa Babangida ya ce musu ai zata zo yola zata sauka ba zata shigo Taraba ba. Hankalin Addah ya tashi, don taji har da Majid a bakin Ummi take jin matsayin su Majid. Don haka ta shiga dakin su ta cewa Zuzu. "Da Lamido da Majid din nan waye ya fi wani?" Ita Zuzu bata kawo kome a ranta ta ce. "Shi fa kamfanin gwala-gwalai ne da shi, zaki hada me shigo da gwala-gwalai? Lamido aikin shi shigo da gwala-gwalai ne shi kuma Majid Mamman Ba'are kera gwala-gwalai suke." "Kenan shi Majid din yafi Lamido arziki?" "Hmm! Nesa ba kusa ba." "Tab" ta faɗa tare da juyawa ta bar dakin,. Can ta kuma shigowa tana faɗin. "Kina nufin zaki auri Lamido ne ba tare da kin fi Zahra ba? Ki san yadda zaki yi" "Ai Zahra ba Majid take so ba, Sarki take so wani dan kasan Algeria." "Yazid kike nufi?" "Eh shi naji wai!" "Sarki da Sarkin da Majid wanene yafi wani?" "Ban sani ba!" Zuzu ta faɗa mata domin ta fara bata haushi. "Ki gaya min!" Ta fada da karfi. Har idonta daya da babu yana tsaftsafo da jini. "Dukkansu masu kudi ne, shi kenan!" "Ko zan yi yawo tsirarar Zahrah ba zata tab'a.jin daɗin rayuwa ba." Ta fada tana fita daga cikin dakin, "ki kiyayye dai" inji Zuzu. .... Ranar Laraba na iso Yola, Ni da Baraka da Amirah, muka iso cikin farin ciki. Abin mamaki sai ga Majid kamar an turo shi. Kame kaina nayi ina dauke kai, motar.da aka zo daukata har da shi, a ranar muka wuce Taraba duk da ban so zuwa ba. Domin na so na bawa Yaya Babangida yar ta na juya, dole suka min muka tafi. Lokacin da muka isa yan uwa da mutanen gidan sukay ta zuwa wurina. Sanyin halina da nutsuwata yana mugun janyo min mutane, haka yasa har yaran gidan suka baibaye ni. Raba musu kayan tsaraba nayi, sannan na wuce dakin Amaryar Yaya Babangida na kwanta domin a nan xan zauna kafin na tafi jibi. Addah ta ji haushi da ban sauka ta kashe ni da magana ba,da dare ina zaune aka kawo min kayan ciye-ciye wai na Amirah. Zuzu kuwa tunda aka ce nazo bata yarda ta fito ba, sai na share kamar ban san tana nan ba, da na dauki kayan ciye-ciyen na bayar suka raba, washi gari da safe Alhamis na tashi da azumi a bakina. Na shiga har dakin kowa na gaishe su, sannan na wuce dakin su Addah. Tana karyawa muka shiga da su Amirah, komawa bayana Yarinyar tayi taga Zuzu wacce ta kasa dauke idanunta a kaina. "Ina kwana addah?" "Da ban kwana ba zaki ganni a zaune?" Murmushi nayi nace. "tow sannu!" Ban yi aune ba kawai sai ji nayi ta tofa min yawun bakinta tare da watsa min kunu a fuska, d'aga kaina nayi sama domin har Aamirah ta fashe da kuka. "Addah kenan, sara da sassaka baya hana gamji toho!" Daga haka na wuce abina, ban kulata ba.. "Karuwa me bin maza woooo ashawo!" Daidai shigowar Majid da Sk Lamido. Dariya nayi lokacin da naji Zuzu ta amsa mata da cewa. "Ai kuwa Zahra ta dace domin ba ta dauko abin magana ba, ke kuwa gaya min meyee ban yi ba? Gata nan dai ribar da na samu,.kin yi? Kin ciyar dani da kudin yi, kuma kin sani nayi ina ga kawai a wuce dake layin masu lalurar hauka yafi kyau." Cikin wani irin fusata tayo kan Zuzu. "Kada muyi abin kunya, domin ga Baban Aamirah!" Inji Zuzu, "Baban Aamirah yaci cin abu kaxan uban shi, Allah ya isa idan ya auren min ke, ni karuwanci zaki min don shi na haifeki,.Kiyi ki samo min kuɗi." "Kudin! Kudi kika ce Addah? Addah kashe ni kawai ki kashe ni na huta." Ta fada kamar zata mutu. " Zata yi magana na ce mata. "Ashe yawon da kika yi a duniya bai saka kin dauki darasi ba? Na zata ba zaki damu da Addah ba.." "Kai-kai -kai!" Kafin ta kawo min duka da wani katako me kusa. Majid ya rike yana faɗin. "Ba zaki daina ba? Ba zaki daina yunkurin cutar da ita ba ko? Kin ga Yazid ya kyale ki ko? Wallahi kika kuma wannan haukar sai na.saka a tura ki gidan mahaukata yadda zaki yi haukar da hujja!" Yadda ya koma sojan, yasa ta tsorata domin ya bata tsoro ba iya ita ba hatta mu sai da kowa ya razana. "Ka kaita can, barin addah a cikin al'umma bala'i ne." Ta fada tana haki, daga zuwa yanzu bata san yadda take ji ba, don kusan mutuwa take ji kamar Yanzu -yanzu. A hankali ta juya zata shiga dakin, duhu ne ya lullube ganinta ta zube a wurin, hankalin mu ya tashi muka yi kanta. Tare da nufarta da gudu. Ai kuwa ban san lokacin da na fasa ihu ba, "Zuzu don Allah ku duba min ita." Yadda na birkice da sauri suka dauke ta a jikina aka fitar da ita, na juya na kalli .... 300₦ 0016341139 unity bank zahra'u yahaya Ali Katin MTN 400 #Mai_Dambu ce 300₦ [5/29, 07:47] Hlm: BHB262 "Sannu Addah kin ji dadinki, Yarki daya tak zaki kashe saboda duniya idan Zulaihah ta mutu sai ki zuba ruwa a kasa kisha, ban san ke wacce irin uwa ba ce? Son kanki yayi miki yawa, idan har kudi kike nima Addah kiyi ta nima amma ki sani idan Zuzu ta mutu sai na saka an daure min ke, wallahil azim!" Daga haka na juya na bar gidan domin na gaji da halin Addah, wannan mugun halin nata yayi yawa. Na saka Baraka da Amirah a gaba muka bar gidan. Kiran Yaya Babangida nayi na tambaye su suna wane asibiti, ya fadamin haka muka nufi asibitin. Koda mukaje sosai ake dubata, ina zaune sai hawaye ke zubo min. "Amma matar nan bata da hankali ne ko?" "Da hankalinta tsabar mugun hali ne." Na gaya mishi, ina share hawayen da yake zubo min, "Ba iya Zuzu ba hatta Mama sai da ta sha wahala a hannunta, duk wanda yake inda Addah take sai ya sha azaba, don haka kada kayi mamakin abin da take yi domin kuwa zata aikata." Haka ya saka ni a gaba muka yi ta hira, koda yake ba wata hira ba ce, amma kamar dama yake nima irin wannan muyi magana, Aamirah kam sk Lamido ya dauke ta, ko ya lura Majid din yana son magana da ni ne oho, a yau na gaya mishi abubuwan da suka faru tun daga Fatakwal har zuwa yawon da nayi, rintse idanun shi yayi tare da dunkule hannun shi."Kina son zaman nan ko zaki tafi?" "Zan tafi idan ta farka." "Me yasa da muka hadu baki gane ni ba?" "Taya zan gane ka? Bayan ni kaina ba gane kome nake ba, fatana na gudu daga masifar mutumin nan." "Na zata baki da yarda ne?" "Ina da yarda amma ba akan kowa ba." Na fada ina mikewa,.kusan kwana muka yi a asibitin, kafin ta farka kallona tayi. "Baki tafi ba?" Girgixa mata kai nayi "ina xan je? Bayan baki da lafiya." "Nayi kuskuren da na saka ki a damuwa, Aamirah bata da uwar da ta wuce ki,.ki tafi da ita ni nasan...." "Dangin Babanki suna Gombe a kumo, na san idan kika je can kome zai zo da sauki. Idan kuma zaki bini kamaru ne ba kome muje." "Zahra zan bi ki" ta faɗa hawaye na zubo mata, rungume ta nayi ina shafa bayanta. "Zahra na gaji, so nake na mutu na huta., Hawaye ya cigaba da kwaranya daga idanuna. "Muna tare Aamirah tana bukatar kanne daga wurinki da wurina." Na faɗa ina kuka. Murmushi Majid yayi yana shafa kanshi. "Tayi kukan mutane, nata kukan ta shanye shi kamar ba kuka ba. Haka yasa shi jin ta ƙara samun matsayi a zuciyarshi. Bayan sallar asuba, aka kawo mota muka wuce Gombe, karfe biyu muka shiga garin Gombe kafin muka wuce nafada, wurin karfe biyar muka isa garin su Babanta, lokacin da suka ganta ba karamin farinciki suka yi ba, ranar mun sha kindirmo kamar me, kwanan mu uku saboda jikinta Majid ya saka mu a gaba har Kamaru, inda SK Lamido ya ce zai kawo Aamirah, tunda muka isa ake zirga-zirga akan Zuzu. Da gaske bata da lafiya, domin zuciyar ta kamar zata buga, saboda masifar Addah. Haka ta cigaba da jinya, har Allah ya bata lafiya satinta daya. Hmm ko kunsan Majid tattarowa yayi ya dawo gidanmu da zama, Zuzu kuwa idan ta ganshi tayi ta dariya tana faɗin. "Wai Hamma Majid ba zaka koma nijar ba ne?" "Zuzu babu ruwanki da ni." Yake fada yana kallona. Ni ban kawo don ni yake zaune ba, kawai dai na ga yana zaune a gidan ne wurin kanwar Mamanshi. Watan shi biyu da zuwa Zaytoonah tazo. Da farko na zata kamar zata sake don ina yar uwarta ne, a'a sai daga baya na gane ba haka ba ne, harkar gabanta daban tazo yi, ina ban daki na fahimci haka domin tazo tana ta rusa kuka, kuma bata zata ina ban dakin ba, ko nace basu san ina ciki ba. "Kiri-kiri kina nuna min kin tsane ni,ita farincikin da kike bata Allah kaɗai ya sani, ni kuma kin barni a can" "Tow ki dawo nan sai na hada Ku na baku farincikin ba shikenan ba!" Inji Mamanmu. "Tow ki mishi magana." Ta fada da kuka, "Mahaifina bai tab'a zartas da hukunci nace ga abin da yayi min ba,.ya sha gaya min babu alaƙar aure a tsakaninki da shi don haka ni ba zan mishi magana ba, domin ya gaya min gaskiya.baya sonki." "Mama Babu adalci cikin wannan al'amarin." "Duk abinda kike so ki faɗa." "Ita da ta gama yawon Duniya za a dauki mutumin kirki....." Tass ta tsinka mata mari, "Akan me? Me tayi miki? Haka kawai zaki tsane ta ai an gaya min abinda kikayi ta mata a nijar wallahi kika sake wani abu ya haɗa ku sai na sab'a miki." Ta fada tana nuna mata waje,.fita tayi da gudu tana kuka,tabbas abin akwai ciwo. Duk da ban san akan me suke Maganar ba, amma a hankali na bude kofar na fito. "Mama me tayi kika dake ta? Me yasa zaki dake ta?" Ita aka mara ni nake kuka wiwi. "Fita ki bani wuri sakarya mara zuciya." Haka na fita na shiga dakin mu, Zuzu da take saka jan farce a yatsun Aamirah na kalla harkar gabanta take ga Zaytoonah na kuka. "Zay!" Riko ni tayi, "kyaleta tayi abin ta, kowa ya debo da zafi bakin shi." "Kanwata ce fa!" "Sai me? Kashin awaki kukayi kuka fito shegen shisshigin da yake ja miki bakin jini da tozarci." Ta riko hannuna, zamu fita ta juya tana faɗin. "Daga yanzu ba zan kara barin wani dan kutumar uba ya tab'a Zahra ba, sai na rotse mishi kai da kwalba." Ta fada tana jan tsaki, kamar munafuka haka muka bar dakin. "Me yasa kika mata haka?" "Dalla can, ke kenan kina mutuwa kan kowa babu me mutuwa akanki." Haka muka bar cikin gidan. Muka tafi wajen gida Inda Majid yake zaune da SK Lamido da yazo yau da safe. Hira suke sosai kamar sun shekara dari a tare saboda kawai Majid ya gano babu alaƙar kome a tsakanin mu shi baban Amirah ne kuma mutumin Zuzu. Abun da ya sa Zuzu ta yiwa Zaytoonah haka, ba kome bane daren jiya suna waya da SK Lamido, sai ta ji ana kuka falo, lokacin Zahrah tayi barci. Shine ta fito taga ita da Majid ne ta zube a gaban shi tana kuka, da rokon ya aure ta wallahi tana son shi ta fi Zahra tasan yadda zata kula da shi wannan abin yabawa Zuzu haushi, ta buga tsaki kawai ta wuce abinta. Wannan abin ya tsayawa Zuzu a rai don gani take kamar cin amana ce aka yiwa Zahrah. Shine fa da safe ta tashi da haushin Zaytoonah koda ta shigo da kuka kasa mata magana tayi, tare da cewa" wallahi kika sake Zahra ta ji wannan labarin sai kin yi danasanin haka." Daga nan bata kuma bi ta kanta ba, don ta lura yarinyar yar iska ce, ga cin kai kiri -kiri. Haka yasa bakiɗaya ta ɗauki wannan matakin, ai tasan Zahra zata iya barin kome akan yan uwanta, a yanzu Majid din shukar yardar shi yake son yi shegiya zata musu wasarere. Haka muka bar gidan sai dare muka dawo ana sallar Magariba, muna shigowa Mama muka samu a falo, ta bini da idanuwa. "Ina Majid?" Tab'e baki nayi zan yi magana Zuzu ta ce mata. "Suna tare da Uncle din Aamirah!" Don a kan idanuna cewa take Baban Aamirah Uncle. "Tow kuyi sallah, tuwo miyar kuka nayi." "Sannu da kokari!" Na ce mata, muka wuce dakinmu, kwanciya Zuzu tayi tana faɗin. "Washi amma Hamma Majid, dan kurewa soyayya maleji ne, don Allah ki ga yadda ya tare ki da zaki zame?" "Ko ba soyayya ba."na fada ina shiga ban daki. "Wallahi yana sonki." "Mtsss" na ja tsaki ina yin abinda ya kai ni, ina fitowa ta ce. "Omo gayen nan ya saka mace a daki, yayi ta lafta mata bulala sai tayi bul-bul da ita." Tana lashe baki. "Zuzu yaushe kika zama yar iska ban sani ba?" Fari ta min da idanuwa Allah yaso Baraka da Amirah suna falo suna tasu sallah akwai ban daki a falo. "Ke akwai Zaytoonah fa." "Ina ruwana, ni dake nake, nifa da akwai makarantar koyan rashin kunya da cire kunya Allah sai na saka ki, kiyi karatun d'aga kafa." "Allahu Akbar!" Na tada kabbar ta fara sallah, dariya ta kwashe da shi. Sannan ta wuce banɗakin tayi Alola tazo gefena ta tsaya itama ta fara sallah. A hankali muka idar, ina addu'a itama ta fara addu'a, har da hawaye nasan damuwarta kusan a tare muka shafa. "SK Lamido ya koma Nafada fa." "Allah sarki,ba dai abin yazo ba." "Tow gamu nan, Baffana ya ce ya hada shi da ni ya tambaye ni na turo shi. Zahra yana da mata fa!" "Kuma sai Allah ya nufa kece zai samu albarka a cikinki, Allah ya tabbatar." "Ba zan iya zama da kishiyoyi ba, na gaya mishi gaskiya!" "Zaki iya mana, kin ga Mamanshi tana sonki. Yan uwanshi tun kafin su ganki su san Aamirah yar shi ce suke sonta suke hidima da ita, ina ga lokaci yayi da zaki samu kwanciyar hankali dan familyn mutanen kirki ne." "Ina matuƙar tsoro ne." Ta fada tana kallona. "Zuzun da na sani bata da tsoro!" "Karya ne naci uban duka a America." "A nan babu me dukarki sai dai." Na kwashe da dariya, haka muka fito muka bar Zaytoonah adakin, Majid na samu a falon, suna maganar komawar shi cikin yan kwanakin, har na saka abinci na koma dakin na samu sai kuka take. "Zaytoona tashi muje!" Na janyota, kawai yarinyar nan ta wanka min mari, sai da naji shi har tsakiyar raina. Dama ashe da na tashi na shigo Mama ta biyo ni, ban tab'a ganin fushin irin nata ba, yadda tayi ta rufeta da duka. Kamar zata kashe ta yasa na fasa ihu. "Wayyo Allah don Allah ku zo!" Da gudu Majid ya shigo, dakyar ya rabata da Zaytoonah wacce tsoro ya kamata kamar zata mutu, bata tab'a dukarta ba tunda ta haife ta kamar kwai haka ta rene ta. Zama nayi ina kuka a wurin Mama sai huci take. "Wallahi kallon banza kika mata, sai na tsiyayar miki da ruwan idanuwa,.balle mari hannunki kuwa ban balla shi ba sai kunya." Kuka take har da birgima tana wayyo hannunta, gara ta mutu ta huta. "Tsuk sai me idan kin mutu? Dama kin dami kowa gara ki mutu me irin halin Addah!" Inji Zuzu tana jan hannuna zuwa waje, don Majid yaja hannun Mama sun fita, ranar naga tashin hankali. A daren a dakin Mama na kwana, don cikin dare sai da aka saka min ruwa, da asuba ina farkawa Mama na samu tana rike da hannuna me karin ruwan, "sannu kin ji!" Murmushi nayi mata. "Mama ya Zaytoonah din?" "Basu jima da barin garin nan ba" tashi nayi zaune "ki kula da ciwonki." "Mama me yasa ta tafi babu sallama!" "Hmm eh gara ta tafi." Sai da ruwan ya kare na shiga ban daki nayi Alola nazo nayi sallah, sannan na kwanta. Ina sauke ajiyar zuciya. • A hanya dama Marwa zai kaita daga can su wuce Nijar, yana gaba tana baya driver da xai kai su yana gefe. "Hamma Abdul Majid ka gaya min ni ko ita?" Banza yayi da ita, tayi ta magana amma bai ce mata cikanki ba, kuka tayi ta musu babu wanda ya kulata har suka bar garin daoula, bata daina kuka ba kuma bata ji a ranta ta daina kukan ba, "Ka gaya min da ni da Zahra wacece kake so?" Juyawa yayi yana faɗin. "Yanzu naji magana ai na gaya miki tun farko ina sonta, ke na gaya miki bana sonki." "Kace baka sona? Ni ka gayawa baka sona? Tow shi kenan dukkanmu mu rasa kowa ya huta." Kawai ta saka dan kwalinta ta shake wuyar driven, tukin ya kwace hannunshi, ya faɗa daya titin, kafin Majid yayi wani yunkuri tuni trela tayi kwallo........😹😹🤣 Jinin Addah yana yawo a jikin Zaytoonah... 300₦ 0016341139 unity bank zahra'u yahaya Ali Katin MTN 400 #Mai_Dambu ce [5/29, 07:47] Hlm: BHB263 Wani irin juyi motar tayi a tsakiyar titin ga babu haske a garin, salati Driver da Majid suke, ita kan tunda ta bugu bata kara motsi ba, can gefen hanya motar ta hantsila. Mai motar da ya buge su ne ya tsaya shi da Yaranshi, suka fita aka firfito da su Majid aka kai su gefen hanya, kafin aka kira motar asibitin, abin mamaki ja'ira bayan buguwa ko kwarzane bata ji ba, amma Majid da drivan sun jikata, ba ma kamar Majid, domin kwalba sai da ta yaga mishi baya, haka yasa aka shiga dashi aiki da gaggawa. Kafin wani lokaci labarin ya isa kunnen Mama Aminatu da Zahrah. - Yadda muka gansu cikin wani hali ya girgiza ni, haka yasa bakiɗaya na shiga wani irin yanayi domin ji nake kamar ba ni ba, bana son naga wani nawa cikin wani hali,. A lokacin da muka shiga dakin Zaytoonah tana barci amma bakinta bai daina fadar magana ba. "Sai ka zab'a ni ko ita, ko kuma kowa ya rasa ka." Abin da tayi ta faɗa kenan, takaici ya kama Mama zata nufi kan Zaytoonah na riketa. "Kyale ta, tana cikin wani hali bata san waye a kanta ba, don Allah barta." "Hmmm!" Ta faɗa da damuwa a ranta, "Me zancewa Dadah idan ta fahimci Zaytoonah ce tayi sanadin hatsarin tunda ga abinda take fada " Nima rasa abin faɗa nayi haka muka ci gaba da zama har ta farka. Tana ganina ta fashe da kuka. "Ina Hamma Abdul Majid!" "Yana dakin shi." "Don Allah idan bai mutu ba, ki bar min shi mana!" A fusace Mama tayi kanta. Na sha gabanta. "Me kike nufi?" "Na taso da soyayyar shi amma shi tun da ya ganki ya juyawa soyayyata baya." "Dama saboda shi kika mare ni?" Cikin kuka ta ce min. "Eh don Allah ki bar min shi don Allah." "Waye ya gaya miki muna soyayya ne da shi?" "Ko baki son Majid na rantse da Allah sai kin aure shi, ke babu wanda ya isa ya raba ki da Majid, ita kuma ko zata mutu babu ita babu Majid har duniya ta nad'e." "Mama ni Yazid nake so!" "Ba Yazid ba ko waye wallahi ba zaki aure shi ba, idan har na isa dake ba zaki aure kowa ba sai Majid!" Daga haka ta koma dakin Majid din ya farka, shima kuma da sauki. Bayan fitar ta Zaytoonah ta sauko daga gado har da riƙe kafata tana kuka. "Don Allah ki saka baki ta bar ni na auri Majid!" "Tashi idan har Majid ne kamar kin same shi." Na fada mata,domin har ga Allah bana son shi, asalima bana jin shi a raina. Haka yasa na ga babu amfanin tsayawa batawa juna lokaci. Kafin wani lokaci yan'uwa da abokan arziki sun taru, Ni dai tunda ya farka na koma gida, nayi abinci ashe bayan na dawo yake tambayarsu ina nake, aka ce ina gida ban sani ba sai da Mama ta kira ni wai nayi maza na tawo Majid yana nima na. Haka na gama girkin na tafi asibitin don na bar Zuzu a can, ina shiga harabar asibitin muka hadu da Hajiya. "Sannunku da zuwa." Cikin farinciki da sakewa ta riko basket din Hannuna tana faɗin. "Yawwa sannu Binta. Kawai sai aka bar ni da yake sunan yayi min banbarakwai. "Ya Hanya!" "Alhamdulilahi, sannunku da kokari sannu Allah ya shiga lamarinku. Ubangiji ya duba al'amarin nan ya dawwamar da shi, albarkacin nabiyun rahamati!" "Amin!" Muka shiga cikin asibitin tare, ina shiga Zuzu ta rungume ni cikin farinciki da jin dadi. "Ina jin wani irin farinciki ne!" Wucewa nayi na shiga dakin, na samu ana ta hira. Kafe ni yayi da idanunshi, lokaci guda na takura kamar yadda yake bina da tsumammun Idanunshi masu dan karen kaifi da tasiri. "Ya jikin?" Na fada ina kumbura baki, Kin amsa min yayi,Malamijo ya ce min. "Da sauki Amarya, ya kike ya kika ji da haukar kanwarki?" Sake fuska nayi zuciyata daya, na ce mishi. "Ai haukarta da dalili take, kuma shine dalilin haukar nata. Idan har ana son tayi hankali a bata shi sai a zauna lafiya tunda kowa yasan tana son shi, babu amfanin tsayawa bata lokaci,idan ya warke sai a daura musu aure." Kallona suke baki daya, babu wanda ya ce min cikanki, murmushi Malamijo yayi ya ce min. "Idan Allah bai ƙaddara ita matar shi ba ce fa?" "Amma kullum cikin addu'a muke,Allah ya kawo mana ƙaddarar da zamu iya amsar ta. Idan aka saka musu albarka auren zai zauna." "An daura mishi aure da matar da yake so, ruwanta ne tayi biyayya ko kuma tayi akasin haka." "Ba sai ya aure ta a na biyu ba,don Allah Malam tana cikin wani hali shi kawai take so." Shiru dakin ya dauka Goggo Sume ta riko hannuna ta kai ni har gaban gadon Majid. "Zauna Fadime!" Zama nayi domin na kasa magana. "Idan kika duba lamarin me sauki ne, amma ki nutsu da kyau zan gaya miki wani labarin da bai zama dole ya miki kyau ba." "Hmm!" Na ce ina kallon Mama da take antaya min harara. "Jiya da dare Aminatu ta nime a daura aurenki da Majid..." Iya abinda na ji kenan sauran ban san yadda aka yi ba, ashe tuni na suma musu a wurin shi da kanshi ya sauka yana jinyar shi ya gyara min kwanciya tare zama ya zuba min idanu. Har likita da nurse suka shigo aka fara duba lafiyata. Maganar ne kamar saukar aradu wallahi. Sai da na kwana uku a yadda Zuzu ta gaya min wai ai basu zata zan farka ba, lokacin da na farka kuwa abu daya na faɗa, wanda ya dagula lissafin kowa har da shi Majid ɗin. "wallahi bana sonshi ban tab'a son shi ba. Don Allah ku raba ni da shi." Kura min idanu yayi yana kallona kafin ya ce min. "Kiyi hakuri kin ji." "Ba zan yi hakuri ba, kai ne bana so kai ne bana kauna, bana kaunar zama da kai" a yadda nake kuka da ihu yasa shi daukar alluran barci ya dankara min. "Allah zai saka min. Ka kyale ni nace ka kyale ni, bana son haka." A hankali barci yayi gaba da ni. Allah ya takaita duk borin babu kowa a dakin, haka na kwana uku a cikin wannan yanayin ranar ta hudu na farka babu bori da rikici. Bai kula ni ba ya wuce ban daki yayi abinda zai yi ya fito sanye da wani wando. Kallon dakin nayi naga kamar an canza mana dakinmu. Dauke kai nayi ina kokarin sauka a gadon ya karaso ya tare ni na fada a jikinshi, ni a tunanina karfi ne da ni, sai gani na kasa ture shi, ina huci ina tutture shi amma ina ya kasa motsawa kuka na saka mishi, a hankali ya zuba min idanu." Tow ya isa haka, wuce toilet kiyi abin da zaki yi " haka na mike ya matsa min, ina saka kafafuwa ta a kasa, na yanki jiki zan fadi ya kuma tare ni. "You see!" Ture hannun shi nayi cikin tsiwar da ban san ina da ita ba."kyale ni nace bana sonka!" Murmushi yayi ya bani hanya da rarrafe na nufi hanyar ban dakin, ganin yadda nake tafiya kaɗan na huta, sai ji nayi anyi sama da ni. Ban dakin ya kai ni, nayi wanka na gyara jikina, sai lokacin na samu karfin jikina na fito ina jin wani irin karfi ba me yawa ba. Abin sallah ya ajiye min na fara sallah, sai da na sauke wanda ake bina kafin na shiga addu'a wanda rabin addu'a duk akan ya sake ni ne, Allah yasa ya sake ni ma. ** Daren da Zaytoonah ta mare ni, a daren Mama ta gayawa Malam, a daren ta roke shi a daura auren. Majid da Zahra haka zai saka Zaytoonah ta huta da tashin hankalin lallai sai ta auri Majid. Suna gama waya Ya kira Babangida, ya gaya mishi domin shi kamar Uba yake a wurin Zahrar. Ai kuwa ya bashi hakuri ya ce kada ya gayawa Zahrah da Zulaihah Addah ce ta gamu da yan fashi a hanyarta na barin garin, suka mata dukan mutuwa don taki basu kudin al'amarin kamar wacce aka mata cune. Dukan da suka mata ne ya tab'a kugunta don kamar sun karya mata kugu, bayan sun kwace kudin. Asalin ba wani wurin zata ba, an bata labarin wani boka ne, a can Benue shine xata ya raba Zahra da duk wani farincikin rayuwa ya dasa mata bakin ciki har ta mutu, ya saka mata bakinciki ta rasa kowa a duniyarta danginta kowa ya gujeta, Zuzu kuma ta zama under control dinta, sai yadda tayi da ita, tasan a yadda taken nan ba karamin cin kudin maza zasu yi ba. Haba sai gashi ba a je ko ina ba, Allah ya wargaza shirinta, ya hada ta da su da'u. Suka wulantata suka kwace kudin shine aka kawota asibiti akayi ta yayatata a gidan radiyo. Shine Babangida ya ji aka duba aka ga ita din ce, haka yasa shi jin tausayinta, yasan addah ba ƙaramar Shaidaniyar mace ba ce. Dalilin da yasa bai nemi zuwa auren Zahra ba kenan, washe gari aka daura auren bayan sallar asuba, Malamijo ya sanar mishi ya ce ayi duk abinda ya dace kada a jira shi. .... A asibitin da Addah take kuwa tunda ta farka ta ganta a gadon asibiti bata san lokacin da ta fashe da kuka ba,domin wannan ba shine tsarinta ba, wannan baya cikin shirinta, sai gata a gadon asibitin, tana tunowa zata fashe da kuka, kamar ranta zai fita, sau biyu tana yunkurin tashi tana kasawa, shigowar Ummi ta kalleta tana faɗin. "Karshen sharri ya kare, babu kafafun zuwa kulla shi, Zahra ta zama matar Abdul Majid Mamman Ba'are, shugaban kamfanin Ba'are golden EMPIRES, saura ki mutu." "Ummi, don ku nake kome!" Ta fada cikin matsanancin kuka, "fadi gaskiya Addah, keda iskancinki.har Saudiya kina tsammanin Allah zai barki da hakkin mu ne? Don haka bari na tuna miki, yadda kika lalata.mana alaka da Zahra yau da alamun Zahra ta zama bishiyar gamji, Allah ya wanke ta ya bata miji daidai da hakurinta, mu kuma kin saka ana mana kallon karuwai, Yarki daya tal zaki kashe ta tir da halinki Addah. Yanzu ma naji labarin SK Lamido wai zai tura danginsa su tambayo mishi auren Zulaihah idan naso sai na lalata auren amma.nasan idan nayi hakan a dadinki tunda karuwa kike son ta zama ba zan tab'a mata sanadin lalacewar rayuwarta ba, amma ke zan yi fatar ki dawamma a nan, kashi a kwance fitsari a kwance. Kuma babu me miki jinya sai ni kamar yadda kika kashe Innar Munaisah har yau babu labarin Munaisah haka zan zauna nayi ta gana miki azaba na dare daban na safe daban yadda zaki gane cewa Allah da girma yaƙe, kin cuci mutane." Haka tayi ta gaya mata magana tana cusa mata bakin ciki da takaici, haka yasa Addah fashewa da sabon kuka, dakyar Ummi ta bar dakin, kuma ta saka a ranta sai ta muzantawa Addah zata ji sauki a ranta. • Duk yadda nake bore mutumin nan yaki kula ni, domin har barazana nayi zan sha guba na mutu. "Idan kin mutu ai da aurena kika mutu, kuma muje gaban Allah nace a min hisabi dake!" "Wallahi sha zanyi" na fada cikin kuka da takaici. "wace irin guba kike so ta ganye ko ta dabbobi wanda ake sakawa bera da jab'a xan nemo miki?" "Wallahi ka daina tsokanata;" "Tow! Na daina!" Haka na cigaba da kukana, ina jin bakinciki kamar ya kar ni. Haka yayi ta manna min hauka ya ce min. "Za a sallame mu cikin satin nan, zaki Najeriya ayi wani buki ne ko zaki zauna a nan?" "Ni na gaya maka gaskiya bana sonka" kura min idanu yayi alamar maganar tana mishi zafi ...... 300₦ 0016341139 unity bank zahra'u yahaya Ali Katin MTN 400 #Mai_Dambu ce [5/29, 07:47] Hlm: BHB264 Murmushi yayi min,irin wanda ake kira yake sannan ya wuce abin shi. Yana gama shiryawa ya bar min dakin, sauya kaya nayi, ina zaune Mama da Zuzu suka shigo dakin sai Amirah da tayi tsalle ta faɗa kaina, ina dariya. "Darling zaki karya ni fa." "Ai bata da hankali meye haka?" Lafewa tayi a jikina na zabgawa Zuzu harara. "Bana son mugun hali" "Idan kun gama ga abincinki nikan zan tafi, Zulaihah ki tabbatar taci abinci fa" "In sha Allah Mama!" Ta fada tana kallon yadda nake tura baki. "Ni gaskiya ki saka shi ya rabu dani, na yarda ko mahaukaci..." Buge min baki tayi, tare da cewa. "Sai na fasa bakin rashin kunyar nan;" inji Zuzu kenan, "Kan Uban can, marin bakina kika yi fa." "Allah ya miki albarka, Zulaihah bari naje na dawo." "Ki dawo lafiya Mamanmu!" Kuka na saka Mama ta fita tana dariya, sun mai dani mahaukaciya, sai manna min hauka zuzu take. "Ban da mahaukaciyar baban lagaje haba Allah ya baƙi hadadden gaye irin Majid ki ce zaki mana bakinciki ai sai yayar uban mutum." Ban san lokacin da kuka ya kwace min ba, atoh ni dai na zama a koke. Tun daga lokacin sai rigima ya k'aru shi kan shi ya rasa yadda zai yi dani, tunda na lura idan nayi a gabansu basa damuwa, sai na addabi rayuwarshi da fitina, har aka sallame ni kwananmu daya aka kawo ni marwa tunda muka zo, aka shiga gyara mana jiki ni da Zuzu, shi kuma ya wuce nijar, ashe tun zuwansu Hajiya aka tafi da Zaytoonah. Tana can tana hauka da tashin hankali, waye ya damu da ita, sai dai ta haɗu da Nana tayi mata wankin babban bargo. Haka aka yi ta gyara min jiki, har tsawon kwanaki duk da bana so amma haka suka matsa min da gyaran nan, tsawon wata guda ana min gyaran jiki duk sati sai mama tazo duba ni. Sati na hudu ne taso lallai muje ayi min sayayyar aure. Amma fir naki da ta dame ni na fashe da kuka. Da Zuzu suka tafi, ni suka bar ni gida, haka suka yi ta sayayya kusan wata biyu suka dauka ana sayayya, ashe akwai gidan Majid din anan Marwa, gidan yana bayan na malam, anan akayi min jere. Su Baraka da Aamirah suna cikin Alkhairi dumu-dumu, domin sun fi kowa farincikin auren da zan yi, haka suka gama jere sati daya muka wuce Nigeria a can aka yi biki da Shagali har angon yazo da shi da Aryan da Amaan, daga nan aka kawo ni Nijar aka cigaba da bikin ranar da aka yi dinner a ranar Yazid yazo. Naci kuka kamar raina zai fita, haka aka gama bikin da zai tafi ya bani kyautatta masu yawan gaske. Sannan ya bar garin, ba zan manta da Yazid a rayuwata ba, yayi min halaccin da babu wanda yayi min ya mai dani mutum ya kuma sayamin farinciki da walwala. Zuzu da take makale dani, don ta ji labarin jinyar Addah yarinyar nan bata zauna ba, karshe Ummi ta ce mata ta je abinta zata cigaba da kula da ita, nan kuwa azaba take gana mata. Kamar kowacce amarya haka aka kai ni gida na, inda ya gaji da haduwa. Bayan tafiyar kowa ina zaune ni daya aka shigo gidan kamar an diro daga sama. Kallon juna muka yi kafin nace mata. "Ki fahimce ni Zaytoonah." Dariya tayi kafin ta ce min. "Da kenan mai cin amana ashe rufe ni kuka yi keda Mamanki." "Zaytoona wallahi ban san kome ba." Dake bata da kunya zuwa tayi zata kara tsinka min mari, na rike hannunta. "Ya isa haka don Allah." Na fada da karfi wanda ban san ina da muryar ba. "Ni ban nufe ki da sharri ba, asalima tunda na ganki naga jinina. Amma babu batun cin amana a tare da ni, wallahi Malam da mama suka yi wannan aikin ko shi Majid bai san da haka ba, sai dai kiyi hakuri na miki alƙawarin dole zan rabu da shi ya aure ki, koda kuwa da mutuwata aurenki zai tabbata a tare da shi." Na fada mata ina kallon yadda ta sauko, domin ina son naga tayi farin ciki sosai. Ita ɗaya ce cikinmu ɗaya idan ban bata abin da take so ba na rasa ta fa? Gara na saka ya sake ni sai ya aure ta Indai da gaske yana sona. Haka nayi ta rarrashinta kafin ta juya ta fita, bayan fitar ta da wani lokaci Amaan da Aryan suka rako shi, ban da zolaya babu abinda suka yi sannan suka fita, zama nayi ina faɗin wallahi sai ya sake ni. Har ya dawo zai zauna kusa dani na mike, ina banka mishi harara. Share ni yayi ya fita daga dakin, ban kara ganin shi ba sai da na kwanta cikin barci naji kamar an k'ank'ame ni. "me ya kawo Aamirah nan kuma? Mirah ta matsa ki bani wuri kin takura ni." "Shiiii!" Aka fada min, gyara kwanciya yayi tare da k'ank'ame ni. "Kambu!". Na fada da ƙarfi, ina ture shi da sauri na diro daga gadon, na wuce can kuryar gadon, "dawo ki kwanta abinki!" Haka ya sauka tare da ɗaukar pillow ya bar min dakin, na cigaba da barcina har gari ya waye. Nayi sallah da wanka na sauya kaya sannan na koma na cigaba da barci. Shigowa yayi ya samu ina barci cikin salama, mutumin nan baya jiran kanshi ko yaga barci yayi gaba da ni ne sai ji nayi kamar ana d'aga min rigana sama. Buɗe ido nayi na ganshi a kaina, ban san lokacin da na fasa ihu ba. Tare da ture shi ya fadi can, na kare kirjina. "Me zaka min?" Na tambaye shi ina harararshi. "Sadakina zan gani." Da gudu na fada ban daki, ban kuma fitowa ba har ya fita, ina dalili, zai kawo min iyayi. Tun daga ranar muka shiga wasan buya da shi,ranar da na cika sati biyu ya ajiye min takardar komawa aiki, nayi ta mita don ban so komawa ba, haka ranar na wuni sukuku. Washe gari zai fita kusan tare muka fita, sai uban dokokin da ya labta min, Ni ce hijab har kasa, kai na gaji da azabar da Majid yake bani na kare mutuncin aurena ba kaɗan ba ne shi yasa bana gajiya da zabga mishi harara a cikin nikab din da ya kankama min. Ina kallonshi yadda ya mike yana waya, kafin can na ga ya fito daga office, wurin Aryan ya nufa can sai gashi ya sake fitowa Aryan ya biyo shi, suka fita bai tsaya ba har suka fita ya zo ya same ni. "Don Allah kada ki tafi wani wurin ko ban dawo ba, ki shiga office dina ki rufe kanki." "Hmm!" Ya saka kai ya fita, haka na gama kome har wurin karfe biyar na yamma. Kallon wayar dake gabana nayi. Ashe abin da ya faru Amaan ake tunanin an sace shi, tun safe aka samu wayar shi a bakin wani gidan mai, har zuwa lokacin babu labarinsa, anyi anyi a san inda yake babu labarin shi. Sai wurin karfe shida ina zaune a office Majid din ya kuma shigowa. "Na zata kin tafi ne taso muje gida." Tashi nayi na bishi, a bakin Majid naji labarin abin da ya faru. Murmushi yayi yana faɗin. "Ya za ayi tow?" Kiran Majid din aka yi da wata number. "Wa ke magana?" "Ku sake Sajjid ko kuma matar kusa da kai, ta mutu bayan an kashe Amaan Mamman Ba'are." Dube -dube Majid ya fara, a ka ce mishi. "Kada ka damu kanka da niman wanda yake bibiyarku, ina sane da kai kaji Muryar Amaan!" "Majid kada ka saurare su." Duka aka kai mishi y fasa ihu. "Shi kenan ku bani nan da awa ashirin da huɗu,." Kashe wayar suka yi, a hankali ya zuba min ido yana kallona, "Muje na ajiye ki a gida?" A hankali naji wani irin tashin hankali, ya kamani. "Kai ina zaka?" Murmushi yayi yana furzar da iskar bakinshi. "zan tafi wani wuri ne!" "A'a babu inda zaka, muje gidan kawai a kira yan sanda." "Akwai abubuwa da ba a bukatar yan sanda a cikinsu." Kallon shi nayi baki sake, cikin wani irin tsoro da tashin hankali nake ji kamar zuciyata zata buga. Lokacin da muka isa gidan, hankalin kowa ya tashi. Kiran Aryan yayi zasu fita na rike hannunsa. "Ina jin tsoro." Na fada kamar zanyi kuka, "ki tsaya a wurin Hajiya da Nana babu abinda zai faru kin ji ko." Jikina ne ya yi sanyi na zauna a gaban Hajiya ina me buga tagumi. ...... Tunda suka fita ya cigaba da tuki, "ranar na tambaye ka dalilin da yasa ka bawa Sajjid. Ban maka magana ba, sannan tun bayan barin Zahra kamfani na ga ana ta fitar da wasu kudaden Aryan me kake son kayi" a yau ya gaji da halin da aka jefa Amaan, gara ya fito fili ya gaya masa ko zai huta shima.. "Amaan bai da lafiya sosai, kuma idan aka ce sai anyi mishi magani babu maganin shi, haka yasa duk wayewar garin duniya ake sayan allurar kudin da ya kai nera dubu dari uku, wanda yasan maganin Sajjid ne. A wurin shi muke sayan maganin wallahi Allah daya ne, ban yi kome don na cutar da kowa ba, sai dai jiki da jinin Amaan yana fama da matsanancin rashin lafiya, sannan a kullum ana sayan nama kilo biyar ana cusa mishi a mazaunan shi yadda zai samu saukin wasu abubuwan. Yasan motar tana da amfani yasa ni na bashi. Idan ina son lafiyar Amaan" Shiru yayi yana kallon Aryan"Me yasa baka gaya min ba?" "Amaan ya ce kada mu gaya maka." Ya faɗa cikin kuka da tashin hankali, wannan ita ce masifar da suke ciki yasan Amaan ya jangwalo musu. Haka Majid suka isa har gidan yarin da aka rufe Sajjid. Koda aka fito da shi, samun kanshi yayi da kwashewa da dariya. "Me kuka zo nima?" "Sajjid ban zo niman kome a wurinka ba, akan me xan matsa sai na nemi wani abu?" Majid ya faɗa, sannan ya mike yana dariya shima. "Kai fito da file din da na baka." A hankali ya fito da shi. "Na san kayi boko. Ko xaka Duba mana ka gani?" A hankali ya bude file din yana kallon Majid. Gwaje-gwajen jini ne, tare da Mikewa yana faɗin. "Karya ne wallahi." "Mamanka tana raye, ka gaya min waye ya turo aka ɗauki Amaan, kasan yadda nake son irin wannan wasan kuwa? Kai ne baka sani ba, amma ai na kware a wurin wannan wasan." "Majid!" "Na'am rayuwar ka kake so ko na yan dakinku?" Murmushi yayi yana faɗin. "Rayuwata bata da amfani matukar yan uwana basu da nutsuwa." "Ka tafi abinka amma karya kake kace ni b jinin Mamman Ba'are ba ne." "Wai tow ai inda matsalar take shine ban san wannan Yaren ba, sai dai da alamun Tani bata gaya maka gaskiya ba, Tani ba ita ba ce." "Karya kake min!" Ya faɗa da ƙarfi tare da juyawa zai bar dakin ganawar. "Idan ka shirya ganin gaskiya zan turo maka da kome amma ka sani, idan wani abu ya sami Amaan, sai na saka an batar min da Mamanka yadda ba zaku gana ba." Cak ya tsaya kafin ya juyo yana faɗin, "Indai Tani ba ita ta haife ni me yasa ta kawo ni gidanku?" "Saboda tana da wani burin cimmawa a cikin gidanmu." Cikin takaici ya ce mishi. "Baka fahimci bayan rasuwar Maisarah hauhawan darajar kamfanin Ba'are ba ne? Sannan bayan mutuwar Mamman Ba'are Aryan baka ga yadda kamfanin darajarta tayi sama ba ne? Idan har tabbas zaka kare yan uwanka, dole sai anyi ta zubda jini waɗanda basu ji ba basu gani ba, ni gidan yarin yafi min waje, domin idan na fito bai zama dole a bar ni na rayu ba, musamman yau da kazo har nan da kanka. Nasan rayuwata tana cikin hatsari."........300₦ 0016341139 unity bank zahra'u yahaya Ali Katin MTN 400 #Mai_Dambu ce [5/29, 07:47] Hlm: BHB265 "Me kake nufi?" Murmushi yayi ya ce mishi. "Ba ku ne kuke yin yadda kuke so a kamfanin Ba'are ba, juya ku ake sannan kasuwarku tana hannun wasu tsirarun mutane, an gane cewa ko daya daga cikinku ya rike kamfanin za a samu biyan bukata, shi yasa aka hana ku nutsuwa balle kusan meke damunku, naji ance ka auri sakatariyarka. Idan da hali ka rabata da aikin kamfanin domin kamfanin gwal din nan kamar tsinuwa ce ga duk wanda ya fahimci meke tafiya a kamfanin." Shiru duk suka yi sai kuma.ya kwashe da dariya yana faɗin."Ku sani shigar daku nayi.". Murmushi Majid yayi yana faɗin. "Na sanka na san halinka, kuma nasan ba zaka gaya mana waye a bayanka ba, amma ka sani kana da damar niman alfarma ni kuma nayi maka alƙawarin yimaka!" "Ni dai ka kula min da mahaifiyata idan ka min haka ka gama min kome." "Ni kuma na maka alƙawarin kula da Mamanka!" Haka suka fita wato zama bai same shi ba, karbar tukin Majid din Aryan yayi yana kallon yadda kan Majid din ya dauki zafi, haka suka dawo gida na ga duk ya sauya kamar bashi ba, domin suku-suku ya koma kamar kazar da kwai ya fashe mata a ciki. Bakiɗaya sai naji zuciyata bata da sukuni, kamar akwai abinda yake damunshi, haka na bishi har dakinshi, kwanciya yayi da kayan shi ko motsi bai iya yi ba, ni na cire mishi takalmi da safar na d'ago ina kallon shi. "Baka yi sallah ba." Tashi yayi ya zauna yana kallona. "Ya zanyi?" Murmushi nayi tare da cewa. "ka gayawa Allah shi ne mafita." Mikewa yayi na tsaya a bayanshi na cire mishi jacket din shi na amsa, na kai drower ɗin na ajiye ya wuce ban daki yayi Alola an rigada an yi sallar Magariba, abin sallah na shimfida mishi. Fita nayi daga dakin shi na nufi falo. A nan na samu Zaytoonah ta zo gabana ne ya fadi, "Zaytoon!" "Cin amana ko? Bayan kin yi min alƙawarin rabuwa da shi, shi ne, kike makale mishi?" "Zaytoona ko mahaukaci yana son kulawa balle Majid da halin da yake ciki, ya kike so nayi? So kike na barshi a cikin damuwa wallahi idan kika dame ni zan gayawa mutane kowa ya san halin da muke ciki." "Karya kike wallahi Zahra kada ki ga muna ciki daya, zan iya kashe ki akan Majid nima ina son shi koda kuwa mutuwa zaki yi, ba zan bar miki Majid ba wallahi." "Idan kin fasa baki haifu yar halak ba." Ta saka kai ta fita, nima na rasa me ke mun dad'i. Bani da wani dangi bayan Zaytoonah ita ce ciki dayana, yanzu akan Namiji muna samun matsala da ita idan wasu ne da yanzu na bar musu Majid, da sauri na bi bayanta, na same ta a a falona ta juyo tana min dariya. "Zaytoona ki tsaya muyi magana." "Ba maganar da zamu yi, tunda ai baki so muyi shi ba." Ina saka kafata naji kamar abu ya kwashe ni zan fadi, tare ni aka yi wanda bana tantamar Majid ne. "Liquid kika zuba mata? Waye ya baƙi izinin shigo min gidana?" Girgiza kai ta shiga yi ya kara daka mata tsawa sai da ta zube, kafin ya taka har inda take ya shure ta da kafa sai da tayi dungure sau biyu. zai kuma na rike shi. "Don Allah ka kyaleta,mu ji da abinda yake damunmu taya Amaan zai kubuta." Riko hannuna yayi muka koma sama, "da ban zo ba haka zata buga ki da kasa, me yasa ba zaki iya faɗa don kare kanki ba." Zazzare idanu nayi kafin nace mishi. "Kawai ba zan iya fadar da Zaytoonah ba " harara ya watsa min yana me niman wuri ya zauna, yana sauke ajiyar zuciya. "Babu wani abun tab'awa ne?" "Me kake so?" "Everything special!" Daure fuska nayi bayan na fahimci inda Idanunshi suka tsaya cak. Dauke kai nayi tare da cewa. "Akwai abinci idan kana so!" "Hm a bani na ci!" Haka na wuce na sauka kasa, ma hada mishi abincin na haura sama, sai da na tsaya ya ci ya koshi sannan, na kwashe kwanukan shi kuma ya shiga wanka, kusan daren raba shi yayi yana bincike, Ni kan tuni na wuce dakina. Na kwanta nayi barci, Washe gari tun asuba na tashi da aiki domin waina ce da miyar taushe. Koda ya tafi masallaci ya dawo ya samu ina ta aikin, ina gamawa na nufi daki sai da na gama kwabe kayana na daura towel, zan shiga kitchen naji bawan Allah nan ya yi sama da ni. "Innalillahi'wa'inna'ilaihi'raji'un, don Allah sake ni sake ni." "Alhamdulillahi sun saki Amaan yana asibiti. Sajjid kuma bai da lafiya." Ajiyar zuciya na sauke tare da faɗin. "Alhamdulilahi Alhamdulilahi Alhamdulilahi, amma sauke ni sai na taya ka murna." Mai dani kan gado yayi tare da jan towel din sama, na rike hannunsa. "Bani da tsarki." "Ni ina da shi." Ya fisge towel din, tunda aka tabbatar da an daura mishi aurenta, tun daga lokacin, yake jin wani abu na taso mishi daga tsakiyar kanshi yana zuwa kan marar shi zai ji abin ta harba haɗe da bugun zuciya me karfin gaske, har sai ya rintsa idanun shi, hannu bibbiyu ya kai tare da cike na Fulanin da suka dauki hankalinshi. Wani irin murza yake tare da matsasu. Kamar wanda ya samu aikin tausa. Da sauri na mike ya mai dani. "Kusan shekaru 40 ban san yadda kayan mace suke ba, don Allah kada ki hana ni jin kayana." "Amma Zaytoonah tana sonka." "Hmmm! Matsalarta ce ni bani da matsala da ita." "Amma don Allah ka bari ba yanzu ba, ban shirya wannan abin ba." "Ni ma haka, ina son na fara koya ne naji yadda kowa yake jin dadi idan yana tare da Matarshi. Ina son naji daɗin da kowa ke ji ba zan miki kome ba, ki bar ni ko wasa dake nayi, na rantse ba zan miki dole ba." Yadda jikina ya dauki rawa, haka yasa shi tsayawa cak. "Ni ba yaro ba ne, idan kina son sai na jira mun yi soyayya ne ai zan kara tsufa, ki bari na gwada yanzu kin ji!" Zufar da yake yanko min ne yasa shi wasa da kirjina, yana yi yana shafa kaina. Ban sani ba ko yana kallon porn videos ne ko kawai yawan shekaru da rashin aure yasa shi sanin kan kome, amma Majid ya bani tsoro, ganin yana kara razana ni nayi maza na ture shi na sauka daga gadon na fada banɗaki, na rufe. Ban shirya ba, wallahi ban san me nake ji a kanshi ba, na dai san bana son shi don haka ba zan bashi alfarmarta ba. Shi a tunanin shi ko nayi wata rayuwar ce nake tsoron kada ya gane, da wannan ya dasa ayar tambaya, ga Magajiyar shi da take ta harbawa, shi tunda yayi hatsarin nan yake hango samuwar lafiyar shi, don wani sa'in sai ya saka wando uku yake ganin nutsuwar Magajiyarshi. Haka yasa shi kiran likitanshi ya gaya mishi, shi kuma ya tura shi ya ga likitan a nan Nijar, ai kuwa aka.gano ita dai magajiya ta dawo daidai babban burinta ta ci abinci kamar kowa, a yanzu ma da Zahrah ta gudu ambaliyar da take yi na madarar sha'awa har ya ba'ci, haka yasa shi kwafa idan har haka ne shi bai ga abin gudu ba, wallahi." Yanayin mu haka ya cigaba da tafiya, tsakanina da Majid wasan buya, tunda yaci Uban Zaytoonah ta shafa min lafiya. Bata kuma damuna ba, sai dai a duk inda ya ganni sai ya ma matse ni yayi ta kiss dina, tare da matse duk wani gidan laushi, musamman mazaunaina suna cin kaniyarsu cewa yake kamar yana tab'a auduga. Ni har ya fara isata. • Addah kan sai a hankali, ganin idanun Zuzu yasa Ummi ta kyale Addah, lokacin da ta amshi kula da Addah ba karamar wahala take sha ba, ga babu kudi ita kuma ganin akwai yarda da soyayya a tsakaninsu ita da SK Lamido yasa taki yarda ta tambaye shi kudi, tunda duk zamansu A Kamaru Mahaifiyar Zahra ce take kula da su, sannan da gayya ta tawo da Aamirah, Baraka tana Kamaru wurin Maman Zahra sannan kuma tana karatu a can tunda iyayen yarinyar sun bawa Zahra. Suma har da su a bikin Zahra, ba karamin dadi suka ji ba. Haka da zasu tafi shatara na arziki aka musu. Sannan suka koma gida. Rasa waye zata kira ta roke shi, domin na magani ma ya aka kare, Ummi ce mai yin kome itama kuma yanzu da ta dawo dole tana bukatar taimakon wani. Jan wayarta tayi ta shiga niman number Zahra, yana shiga ta ce mata. "Zahra!" Yadda ta kira sunan zaka yi kuka, "Zuzu kina son kudi ko?" Sai ta fashe da kuka, kamar ranta zai fita. "Zuzu idan ba abinki ba, waye ba zai taimakawa danginshi ba? Ni nasan wacece ke, ba don kanki ko Amira kika nima ba, don Addah ne don haka ki kwantar da hankalinki Zahran da kika sani bata sauya ba, ni din ce wallahi " Tura mata kudi tayi kusan dubu dari uku da hamsin, ranar sai da Zuzu tayi kukan bakinciki. Haka ta cigaba da rayuwa, domin Yaya Babangida yana bakin ƙoƙarin shi, Matanshi ne basu kula su, sannan har da Ummi ita zuzu bata yi mamaki ba, sai dai tasan halin Addah ne ya janyo ake mata haka, SK Lamido shima tunda ya samu yazo sau biyu ya ga Amirah ya tafi da ita tayi sati biyu a wurinsu da zai dawo ne ya zo musu da kayan masarufi dayawan gaske. Yana son Zuzu kuma aurenta yake son yi, sai dai wani sabon tashin hankalin da ya kunno mishi yasa shi zubawa sarautar Allah idanu, domin an samu wani munafiki ya bada labarin Abinda Addah tayi wanda shi ya tab'a kome nasu har da Alaƙarsu, shine dangin Babanshi suka ce ba su shiga lamarin ba, shi kuma yayi alƙawarin matukar basu shiga maganarshi ba, wallahi za ayi ta haihuwar yayan gaba da Fatiha, dalilin da yasa Mamanshi cewa tunda ya fadi haka bai da hakuri tow bata yafe mishi ba, matukar ya auri Zuzu. Ya gayawa Babangida amma ya roki ya bar maganar a tsakaninsu na Maza, amma abin da ciwo, a duk lokacin da Aka mata haibaici sai taji kamar ta mutu, ba ita tayi wani abin ba, amma tana biyan zunubin Addah da hannunta tayi kuka tayi danasanin dawowarta. Wata rana bayan bikin Zahra da wata biyu, Aamirah tana ta mata rikici ta kira mata Maminta, wannan rikicin yasa Zuzu rarrashinta har tayi shiru. Ta fito tsakar gida sai taji Ummi tana faɗin. "wallahi iyayenshi sun hana shi aurenta, sun ce ba zasu dauki masifa su kai zuri'arsu ba, domin dai an buga karuwanci. Itama ai karuwancin tayi zamanta a kasar wajen waye bai sani ba, ribar barikin gata nan a bayanta." Har wani yanga take ita gata nan yar gwal ta samu me kuɗi." Ranar Zuzu kwana tayi bata rintsa ba, Washe gari ta bar gidan da Yarta suka shiga niman gidan haya dakyar ta samu wani safe cantaints, dubu dari, haka ta shiga ta gyara ko ina a ranar ta kuma kiran Zahrah ta gaya mata kome, ta kuma turo mata da kudi kusan miliyan uku, ta shiga gyaran gidan, can da ta gaji suka koma, ta samu addah ta bata jikinta haka ta gyara mata jikinta, sannan ta gyara dakin ta shiga kwashe kayansu tana kaiwa ita da Amirah suna gamawa suka dauki addah, a tsakar gida suka hadu. "Ina zaku Zuzu?" "Zan kaita asibiti ne." "Ok a dawo Lafiya!" Tunda suka saka kafa suka bar gidan, basu dawo ba sai dare tazo ta kwashe sauran kayan, sai da zata fita ne ta samu Yaya Babangida ta ce mishi. "Yaya Nagode sosai da kula da Addah da kayi, na gode sosai Ummi na gode sosai, amma ki sani shi rayuwa bata da tabbas. Bana fatan ki ji ciwon da nake ji, amma nasan wata rana sai labari, ko babu kome nayi riba da barikin tunda Aamirah bata rasa Uban da zai tsaya mata ba, Akwai mahaifinta, Akwai Yazid, Akwai Sk Lamido da nasan cewa an hana shi aurena da na hakura tuni......... 300₦ 0016341139 unity bank zahra'u yahaya Ali Katin MTN 400 #Mai_Dambu ce [5/29, 07:47] Hlm: BHB266 "Ba alfahari ba, nasan nafi gaban a wulakanta ni, sannan tunda ya Amshi Amirah a tashi. Ai ko bai aure ni ba ya gama min kome balle kuma nasan Allah ba zai tab'a wulakanta ni ba, ko ya kama ni da laifin da Addah tayiwa wasu, nasan akwai hakki amma bana fatan ya fada kaina, ko ya faɗa kaina zan godewa Allah da ya halicce ni, Alhamdulillahi a duk yadda yaso yayi dani na gode mishi, ina kara godiya da yayi Zahrah me zuciyar musulmai da alkhairi da bata hada alkhairi da sharri. Yaya Babangida na gode sosai da dawainiyyar da kayi mana." Daga haka ta saka kai ta bar musu gidan, "tow waye ya damu, don ta ga an damu da ita ne daga fadar gaskiya Allah ya bamu hakuri mu da Aaddah ta lalatawa rayuwa." "Ummi me kuka gaya mata? Shin ba nace kuyi shiru kada ku gaya mata maganar fasa nimanta ba?" Ya fada a matukar harzuke. "Tow ni me nayi daga fadar gaskiya sai ya zama laifi." Mikewa yayi tare da fusata kamar zai daketa, haka yasa ta koma ɗakinta tana kuka ita yayi mata faɗa, ita kan Zuzu ta bar gidan da Yarta, bata nunawa Addah ga abinda ya faru ba, Ita dai ta cigaba da jinyarta, tana kuma kaita asibiti. Haka yasa koda SK Lamido yazo, gidan Babangida ya nufa, a can ya samu bata nan, sun tattauna da Babangida wanda kunya ya kama shi,. Shima SK Lamido nimanta yayi dakyar ya samu wayarta, daga nan ya tafi, lokacin da ya zo gidan bata nuna mishi ga abinda ya faru ba, duk wata kulawa ta bashi. Ya dauki Aamirah suka fita sai dare ya dawo da ita. "Kiyi hakuri da abinda ya faru." Murmushi tayi tana faɗin. "Me kenan?" Yadda ta tambaye shi, sai ya sashi jin kunya ba na wasa ba. "Da ban gaya miki ba sai ji kika yi a wani wurin." "Normal" ta faɗa. "Ina son na amshi Amirah ne domin ina son ganinta a tsakanin mu." "Lafiya lau, don gata kayi mata." Shiru yayi yana kallon yadda take amsa mishi magana kai tsaye, "Amirah je ki kwanta zan gayawa Auntyn ki wani abu" Tashi Yarinyar tayi tana faɗin. "Sai da safe Uncle, Aunty sai da safe." Ta shige ɗakinsu da uwarta. Tana tashi ya kashe wutar falon. Damketa yayi yana faɗin. "sunki bani damar na aureki, ai basu hana ni zazzaga miki diyoyina ba." "Wannan shine karya don ba zaka cigaba da lalata min suna ba, ana zagina a matsayin mara kirki, ana zagin Uwata ba." Ta fada cikin matsanancin kuka, "Na ji shi kenan ki yarda za a daura auren mu wani sati." "Ni ba zan aure ka ba, kaje can wurin danginka su baka mace." Rigima sosai suka yi da zuzu kafin ya fita ya bar gidan, asuban fari ya bar Taraba sai Gombe, har da kukanshi yana rokon iyayen zuzu su aura mishi ita, kamar yayi hauka sai da yan uwan Babanta suka kirata, suka tambayeta ko ta amince, tana kuka haka ta amince idan ma bata amince ba, ba zai barta ba, suna gama wayar ta kira Zahrah tana kuka take gaya mata. Itama shawarar da ta bata kenan, har gara bikin Zahra anyi hidima nata babu wanda yaji labarin ma. Tunda aka daura auren, ta shiga dakin Addah ta ce mata. "Kina kwance yau Allah ya tabbatar na auri Kabir Lamido, don haka ina ƙara godiya ga Allah da yayi min wannan Ni'imar don ba zan lalace kamar yadda kika so ba, a kullum ina miki fatan shiriya." Daga haka ta bar dakin, ta cigaba da kula da kanta. Babu abinda zata yi ta faɗa, sai da Zahrah ta kirata ta ce maza ta nemi wurin gyaran jiki ga nata gudunmawar, ta gayawa Majid shima ya turo mata. ••• Babban Asibitin Poland. Rike take da hannun Nenne, cikin kulawa tana murmushi. "Sannu Nenne cuta ba mutuwa ba." "Ina zahra'u?" "Tana can tayi aure." "Yaushe?" Hawaye ne ya zubowa Munaisah. "Wata biyu kenan ana cikin na uku." "Ke fa?" Inji Nenne, "ni wanda muke tare ba bakin fata ba ne, Bature ne." "A'a ki auri bakin fata ƙabilarki." "Babu kabilana da zai aure ni." "Allah ya zab'a mana mafi alkhairi!" "Amin Ya Allah." Flash back. Babu yadda Addah bata so Munaisah ta kashe Nenne ba, dake da gaske Munaisah da mugun son abin duniya amma bata tab'a jin zata iya kashe wani saboda duniya ba, sai ga Addah ta ce mata ta kashe uwar da ta haife ta, haka yasa ta samu Nurse din da yake son Zuzu ta bashi duk kudin da addah ta bata na kanta, ta bashi tace ya taimaka mata ya kula da Nenne, Zahrah zata zo in sha Allah. Sannan ta tafi, a lokacin ba karamar wahala ta sha ba, domin har wasu sassan jikin Nenne an sayar, don haka aka dauki wata gawar aka basu, shi kuma ya ci gaba da kula da Nenne, haka ya samu labarin an d'aga sansanin, yayi bakinciki sosai don haka bai kuma jin labarin su ba, sai bayan Shekara guda, lokacin ta hadu da Baturen da suke tare. Kawai ta kira Nurse din ta tambaye shi Zahra tazo sai da suka yi fada kafin ya gaya mata gaskiyar abin da ya faru babu bata lokaci tazo wurin Mahaifiyarta. Ganin halin da Mamanta take ciki ya kazanta, yasa ta nimawa Mamanta takardar barin kasar. A lokacin tasamu mahaukatan kudi, don haka ta dauki Nenne zuwa Poland a can ta cigaba da jinyarta har zuwa yanzu. Ita kanta bata zata Nenne zata tashi ba, sai gashi Allah ya d'aga kafadarta. Don haka ta ci buri a ranta zata dawo Nijeriya, zaman kasar wajen ya isa, sai da ta hada kome nata sannan ta samu Paul da zancen zata koma Nijeriya, shi ya mata duk wani cuku-cuku ta bar kasar da Mahaifiyarta, bayan ta ajiye mishi sakon kada ya nime ta, zata fara sabon rayuwa sabon yanayi sannan yaje gidan marayun da suke zuwa akwai yarinyar da aka saka mata suna Zahrah ya amsheta Yar shi ce da ita, suka haifa bata son duniya ta sani ne, kuma bata son ta koma da ita cikin danginta yasa ta ajiye yarinyar a wurin, ya barta haka don Allah. Yaji takaici don yana sonta ne. Amma da yaji sunan Yarsu da gudu ya tafi gidan ya samu yarinyar tana da shekaru uku a duniya, lokacin da ya je har ana shirin adopt ɗinta, ya amshi yar shi, yana kukan farinciki.ita kuma dalilin ta nakin yarinyar bata san yadda zata fuskanci Nenne da lamarin Yarinyar ba, bata san yadda zata dauki batun ba, domin tana ganin idan taji haihuwa tayi da kafiri mutuwa zata yi kwananta bai kare ba. Da wannan ta rufe shafin Paul da Yarshi. *** Zuwa yanzu Majid ya gama rena min hankali, ban isa nayi wani kwakwaran motsi ba, sai dai naji anyi sama da ni kamar wata yar tsana, gashi wani ikon Allah yadda nayi wani azababben kiba zaka rantse da Allah wani abu nake samu kawai kwanciyar hankali da na samu ne. Ina gyara kayan drower ɗin shi, shi kuma yana banɗaki, ina an kare d shi. Ganin wani hotonshi da wasu sojoji yasa ni shagalta da kallon, kawai sai ji nayi anyi sama dani. "Don Allah sauke ni." Na fada kamar zanyi kuka. Fadawa gadon muka yi, wannan gado ba don anyi shi da karfi ba, ina ga da karyewa zai yi wallahi. Haka ya juyo kaina. "Kasan me?" Bakinshi ya haɗa da nawa, na kasa magana duk ƙoƙarina da na kwaci kaina, amma na kasa sai na hakura na bar shi ya sakankance kafin na shammaci shi na gudu abina, murmushi yayi mai ciwo . Ya fara gajiya da iskancin Zahra, sai ya zuba mata idanu. Ya shirya ya fita, wurin Hajiya ya wuce yayi mata hira, kafin ya wuce bangaren Nana, yana shiga ya kwanta rubda ciki. "Alhajin Allah lafiya kuwa? Ya Zahra matar wata?" Ta fada tana kallon shi. "Alhajin Allah meke damunka?" Shiru yayi yana mitsi-mitsi da idanunshi. "Nana aure xan kara?" "Kaci gidanku, yaushe kayi auren da zaka kara auren dan kaniyarka." "Nana ki barni nayi auren Zahrah kashe ni zata yi." Ya fada yana kara rubda cikin. Gwalalo idanu waje tayi tare da dukar kirjinta, ai mayafi a hannu ta bar gidan, murmushin mugunta yayi yasan Nana ba zata kyale ta ba. Ina tsaka da kwashe abinci, kawai naji an banko min kofar kitchen. "Zahrah ashe ke ba yar arziki ba ce? Na zata ke yar arziki ce da zaki bar Alhajin Allah a cikin mawuyacin hali, Anya akwai Allah a cikin lamarinki?" Yadda matar nan take shiga ba nan take futa ba, ihu da bala'i naji shi idanuna har ya cika da kwalla. Sai da naji hawaye na zuba min, "haba Zahra da hankalinki kike gudun mijinki a shimfida? Na zata wani ya gaya min karyata shi zan yi, Zahra idan Alhajin Allah bai samu nutsuwa dake ba, taya zai zama cikakken namiji me murya ɗaya? Don Allah ki cire kome ki rufa mishi asiri. Sai ya zama cikakken namiji, yana tare da makiya ba dare ba rana, idan har ya rasa tallafawarki makiya ba zasu barshi ba, sai sun yi nasara akan shi, da ace lokacin da Sa'adatu ta auri Mamman na bata irin wannan goyan bayan akan Mamman da yanzu wani labarin ake ba wannan ba. Don Allah ki taimaka Alhajin Allah ya zama namiji kamar sauran mazan " Wato da Majid da Kakarshi, basu da kirki, amma kuma yadda take nuna min ta damu da jikanta yasa ni bata mamaki. A bangaren Hajiya zan iya cewa bani da matsala da ita, domin duk wani abin cigaba da kyautatawa tana min, sannan tunda aka sako Amaan kusan a wurina yake cin abinci, sannan ga Nabeeha yar kawunmu matar Aryan, kusan a tare muke kai abinci. Akwai wata irin girmama juna da muke a tsakaninmu wanda haka ya haifar mana da kyakkyawar alaka. Yaranta a wurina suke zama idan suka dawo makaranta, sai Jamilah muna shiri sosai amma Anisah tana tare da Zaytoonah kamar munafukai. Nana tana fita na wuce na karasa kwashe abinci, bayan ta bar gidan ya shigo yana marairaicewa. Kamar xan yi kuka yadda yazo min, haka ya tsaya muka gama kome na sauya kaya na kai nasu Hajiya sannan na dawo, na wuce daki nayi wanka. Bayan na gama wanka na fito na samu yana dakin, doguwar riga ya mika min. Shima shiri yayi ya wuce wurin drower na ya dauki abun da zai dauka ya ja.hannuna muka bar gidan, kai tsaye muka bar garin Niamey. Ina kallon shi mun yi sallah la'asar da Magariba a garin Kano, daga nan muka wuce yola. Anan muka kwana washi gari ya dauki shatar mota muka kama.hanyar gembu. Wuri ne me kyau da Natural air kasancewar gari ne dajin Allah, sai ci-gaba da aka kawo garin, mun sauka a masaukin baki, Sai da muka huce gajiya sosai sannan ya fito dani muka yi ta yawo, yankin kamar ba a cikin Nigeria yake ba, kasancewar yanayinsu yayi daban da yanayinmu. Sai sallah yake dawo damu, da dare aka kawo mana abinci, me rai da lafiya sai kayan fruit da aka kawo min na sha har na gaji, bayan sallar isha kuma muka yi sallah nafilla. Kafin nan sai da yayi min tambayoyi sosai akan Addini na bashi amsa, Wannan daren me cike da tarihi, Majid ya koya min abubuwa dayawa har lokacin ban iya cewa ga abinda nake ji a kanshi ba, sai dai ni kaina nasan naji jiki naji yadda kowacce mace take ji, naji abinda ba kowacce mace take iya ji ba, matukar bata rike kanta ba, shima da zuciya daya ya zo min sai dai yadda abubuwan suka faru, yasa shi rufe idanun shi yayi yadda ranshi yake so dani wanda ya sani jin na fasa auren. Koda yake kowacce macen kirkin tana alfahari da wannan daren...... 300₦ 0016341139 unity bank zahra'u yahaya Ali Katin MTN 400 #Mai_Dambu ce [5/29, 07:47] Hlm: BHB267 Mutumin nan bai da imani, tausayinshi ƙalilan ne bai duba halin da nake ciki na rashin sanin kan abun ba, ya farmin da abu daya, tun karfe sha daya na dare sai gamu har wurin sha biyu da wani abu, kuka na ke wiwi kamar raina zai fita, yasha yakushi , duk na mishi bai ji ba, shagalin shi yake a wannan daren Majid ya dasa min tsoro da shakkar shi, wallahi bana jin akwai abin da zai saka na mishi rashin kunya ko wata tsiwa. "Don Allah kayi hakuri, nabi Allah na bika." "Ba zan iya ba! Na kasa." Fashewa da kuka nayi ina ƙoƙarin ture shi, amma mutumin nan bai bar ni ba, sai da yayi yadda yake so, ina ganin shi ya mirgina daga gadon ya fadi, a kasar dakin ya kwanta rub da ciki. Zazzaɓi me karfi ne ya rufe ni, hakan shima zazzaɓin ne ya rufe shi, bakiɗaya sai aka rasa me kula da wani. Sai goshin asuba barci yayi gaba dani, shi kuma ya mike tare da lullube ni, sannan ya shiga banɗaki ruwan zafi ya hada yayi wanka, sannan ya fito daure da towel ya zuba min idanu, haka kawai zai barwa wani kato ajiyar Allah, bayan yasan Allah yayi halitta a wurin, ai ko karen hauka ne ya cije shi, ya nemi magani ya sha ya warke. Kaf duniya babu wanda ya isa nuna mishi tattalin mace (Nace karya kake dan talakawa 😏😹Crown Prince Maina da ya iya ririta kwaila ya fika, a tow karewa dai kenan shi da kwaila tace ya tafi kogi ya kamo mata kifi mai rai zata yi wasa da shi, kuma ya kamo crown Prince guda fa, ahto balle kai da ka auri uwar mata) Sallah yayi ya shiga zuba addu'a a aurensu da neman albarka yayi addu'a sosai har da yaran da zasu haifa, bai barsu ba sai da yayi dogon addu'a a kansu, sannan ya mike ya kwanta a bayanta, ya rungume ta yana shakar kamshin turarenta, "Tashi kiyi sallar asuba." Kara manne kaina nayi a pillow din na cigaba da barci ina jin sanyi sama-sama, ya kara min magana a lokacin na bude idanu da kyar. Bani da kuzarin da zan iya tashi haka yasa na cigaba da kwanciya. Can sai ji nayi ya dauke ni cak, yayi ban daki da ni. Ni kuwa fir naki bude idanu na, ganin haka yasa shi hada min ruwan zafi, sai ji nayi an saka ni ciki, wata mikewa nayi tare da ware idanu. "Don Allah fitar dani!" Danna ni cikin ruwan yayi da karfi, na fashe da kuka kamar raina zai fita. Haka bawan Allah nan ya gasa ni, nayi laushi tass. Bude min gaban rigarshi yayi yana nuna min tabon cizon da nayi mishi, ya kai bakinshi kunne na. "Zan barshi ba zan bari ya b'ace ba, domin wannan shine tambarin samun kyauta daga Mace ta gari!" Rintsa idanu nayi tare da fashe mishi da kuka, fita yayi ya bar ni nayi wankan tsarki nazo na samu ya shimfida min kome, sannan na fara gabatar da sallah, sannan na yi addu'a na koma gadon na kwanta, mika min mug yayi, na karba na sha tea me zafi da paracetamol, sannan na koma na kwanta. Ai kuwa ya ta da ni zaune na zauna. "Cikinki zai kumbura waye ya sani ko wasan jiya na zuba an dagwai-dagwai iyalan Baba!" Majid bai da kunya, ture shi nayi na kwanta ya bi bayana muka kwanta. Haka muka yi barci tare da jin dadin ranar domin sai karfe biyu muka farka, wanka na shiga zanyi. Kawai sai ga katon nan ya biyo ni. "Innalillahi'wa'inna'ilaihi'raji'un me zan gani!" Na fada tare da rufe idanuna da hannu. Cirewa yayi ya bude mana ruwa akanmu. "Bari na jira ka gama." "Sunnah Manzon Allah Sallallahu alaihi Wasallama kike gudu? Yayi wanka da Nana A'ishah a kwarmi daya, please ki bari nayi koyi da shi." Kamar wacce aka zare min laka, haka na tsaya. Ruwan na sauka akan mu ya dauki soso ya cude ni, sannan ya mika min haka na cuda shi, amma akwai inda ko me zayi sai dai yayi naki tab'awa, amma shi kan ba lokacin wurin ɓare wasu abubuwan duk sun faru kuma suna kan faruwa. Haka muka fito a manne da juna ni kan kunya ta kusan kashe ni, amma shi ko a jikinshi. Shafa mai ya tsaya min sannan nima na taimaka mishi ya shafa muka shirya cikin kananun kaya, shi ya fito min da wata riga an rubuta Queen shi kuma nashi an rubuta King (Dan talakawa ina kasamo rigar Prince Maina 😭 sata Majid ka fara? Tow Allah shi yaye maka.) Haka muka ta zaga wannan hadadden tsauni, da dare muna dawowa yaga ina dan dingishi, muna shiga ya cire min kayana, ya sani na kwanta ya fara duba ni. "Sannu bari na duba wurin ko?" "Me zaka min?" "No dubawa zanyi kawai!" Rintsa idanu nayi ina jin shi yana duba wurin kafin ya tashi ya dauko kayan aiki, tashi zaune nayi nace mishi. "Malam lafiyata lau." "Eh haka kowane mara lafiya yake faɗa, lafiyan shi lau. Ki nutsu ba zan miki wani abu da zai tab'a lafiyarki ba, tafiyarki ce nake son na gyara miki shi."."A'a bana so." "Zan kashe zafin da allura please ki tsaya na gyara miki." Yadda yake lallabani dakyar na amince ya min allurar da ɗinkin, yana gamawa ya dauke ni har ban dakin ya taimaka min nayi Alola ya shimfida min abin sallah, nayi a zaune. Duk wani abin da xan yi na tab'a lafiyata sai da ya raba ni da shi. Hatta cire kayana, a wannan kwanankin sai da ya koya min abubuwan da ba zan iya boyewa kaina ba, na farko ya koya min tunanin shi. Haka zai jani har wani wurin ya zauna yana karatu ni kuma ya dora kafafuna a cinyarshi. Ko kuma ya zauna na kwantar da kaina, hannun shi yana cikin rigana. "Nayi addu'a na roki Allah, ya bayyana min ke. Tun ranar da kika fara aiki naji Muryar ki,. Amma nayi ta kokwanto kece bake ba ce, haka nayi ta nazarin yaushe zan ganki. Ashe kina tare da ni kina kusa da ni, Zahra na san ban kyauta miki ba, amma a lokacin haushi nake ji idan na ganki da wasu musamman Amaan, bansan me yasa nake jin haushin duk wanda zai miki magana ba, ganinki da Yazid ya sani jin kamar xan mutu, dan iska ya hanani sakewa da yar budurwa Kodayake a lokacin gani nake babu abin da bai hadaku ba, musamman idan naga Amirah sai nake ɗauka ai yarku ce. Ke nifa ba karamin takaici kuka kunsa min ba, dan iska abu na samunki zan ga yazo ai sai ya bar min filin ya kanenaye ki ya hanaki sakat ya hana zuciyata samun ki. Ai Umaima ta kyau ta min." Sumbatar bakina yayi, na kai hannu bibbiyu na rike fuskarshi. Muka shiga wata duniya ta daban, sai da naga tafiyar zata yi nisa na ture shi. "A'a ina da ciwo." Dariya yayi min yana jan hancina. "Na sani yau kwana uku kenan nima ba zan yi wani abin da zai fama mana ba." Share shi nayi ina jin kunyarsa, "Yarinya ki saki jiki, muyi shagali atoh ni ina son shagali." Haka muka kasance sauran kwanakin, farantawa juna muke kawai. Ranar da muka cika sati, da yamma yana aiki na kwanta a bayanshi. "Angon Nana da Nana!" Ture laptop din yayi yana faɗin. "Nana da Nana karama da magana a bakin nan." Murmushi nayi nace mishi. "Eh muna najeriya, me zai hana mu karasa muga zuzu da Addah!" Haɗe rai yayi yana faɗin. "Salon muje ta saka ki kuka!" "Ba zan yi kuka ba!" Dakyar ya amince ya bar ni, sannan muka kara kwana biyu, wayewar na biyun ne ya kuma murzani son ranshi. Kamar zan yi hauka domin abin ya kara dawowa kamar sabo, kuka nayi ta mishi ina mita. Lallabani yayi ya jani muka bar garin, karfe sha daya muka bar garin, bamu shiga taraba ba sai karfe biyar na yamma. Agajiye, yana lura da yadda nake dan kame jikin, haka yasa shi tambaya ta. "Har yau yana ciwo ne?" Girgiza kai nayi nace mishi. "A'a zazzaɓi kawai nake ji." "Allah ya baƙi lafiya!" Ya fada cikin matsanancin damuwa, har muka isa gidan Yaya Babangida, cire jacket din shi yayi ya saka min, yana faɗin. "Ina ga sanyin can da kika kwaso da kuma sanyin nan, tunda kin ga anyi ruwa." "Eh!" Na fada ina fitowa daga motar, sumbatar goshina yayi kafin ya sake ni muka fito da kayanmu, cikin gidan muka shiga ya sallame drivern ina shiga naga Munaisah a tsaye, tana magana da wani yare. Yar banza cillar da wayar tayi ta fasa ihu. "Zahra!" Ta fada da karfi. Rungume juna muka yi, ta fashe da kuka. Nima kuka nake. "Mu shiga Nenne tana ciki " "bata mutu ba?" Na tambaye ta, ina juyawa domin amsa sallamar Majid da ya shigo gidan. "Sannu da zuwa Abdul Majid Mamman Ba'are, Chairman na BA'ARE GOLDEN EMPIRES!" "Yawwa Munaisah Abubakar Takum, mai kamfanin kayan kwalliyar mata " Kallonshi nayi na kalle ta, nifa tunda Zaytoonah ta gaya min ba zata bar min Majid ba, na fahimci kowa ma zaka iya kishin mijinka akanshi. Tsakiyarsu na shiga ina blush. "Yaushe aka san juna?" Na fada ina kare shi. Kasa yayi da kanshi. "Kina kishin kato ne?" "Dole nayi kishinka katona!" Na fada ina zare idanu. "Don Allah stop childish, ko mutuwa kika yi ai Majid ya haramta min, balle kina numfashi, ai ana barin halak don kunya. Yes naso ya aure ni amma Daga baya na fahimci shi din is belong to you. Oya matsa min mu gaisa da in-law na " Ta fada tana mika mishi hamnu, buge hannun nayi nace mata. "Ke bafa zaki mana yahudanci ba, wallahi ba zai baki hannun ba." "Ok muyi hugging mana!"."Kan bu... Uban can ke ! Zan zage ki wallahi, kai kuma wuce sai na nime ka." Haba me zasu yi ban da dariya, wato ni suka mannawa hauka, gaisawa yayi da yan gidan har da Nenne da take wheelchair, sannan ya ajiye musu kuɗi me yawa , na rako shi waje. A tsakar gidan muka rungume juna. "Zan dawo anjima Baby me zaki bani?" Murmushi nayi mishi nace . "Ka dawo da wuri don zan baka dadi ni dumi nake so, sanyi ya dame ni!" Kallona yayi ga rigar sanyi har da nashi, ga safar hannu ga ta kafa. Kaina lullube da mayafin abaya. "Ok Nur zan mana booking din masauki." "Yawwa katona ni da Nana da Hajiya." Dariya yayi yana jan hancina, mikewa nayi na sumbaci bakinshi, rike harshena yayi mun jima har aka fara yayyafi, ya sake ni ya fita. Dakin na koma muka kara gaisawa, sai niman bargo nake. "Munai! Bani bargon can,.kunna min room heater." Na shige cikin bargon sama-sama muka gaisa dasu, jin dumi yasa barci yayi gaba da ni. "Yau ga ni ga Zahrah ga Ummi, ina Zuzu?" Cikin barci na bude idanu. "Ku kira shegiya tayi aure ai." "Haba?" "Bata gaya muku ba ne? Sati Uku kenan anyi auren da sati daya muka tawo gembu satin mu biyu kenan muka zo nan" Ai kuwa suka fara magana. "Ku cewa shegiya ta tawo min da yarinyata ba xan bar mata ba." Barci yayi gaba dani, Munaisah zata kuma magana Nenne ta ce mata. "Barta tayi barci, Allah ya bata lafiya ya raba lafiya." Ita tun da taga ta Shigo tana niman wurin dumi, ta fahimci shigar ciki ne, domin haka Aminatu tayi lokacin cikin da suka korata da shi, tayi ta bin hantsi da duk inda aka hura wuta, ko ta shige dakin Malam wato Baffa'm, idan kuma ta shige ɗakinta har wuta take kaiwa, tayi ta niman bargo tana rufawa da shi. Hawaye ne ya zubo mata, waya Ummi ta dauka ta kira Zuzu sama sama suka gaisa don tunda ta bar gidan zumuncin ya yanke.... 300₦ 0016341139 unity bank zahra'u yahaya Ali Katin MTN 400 #Mai_Dambu ce [5/29, 07:47] Hlm: BHB268 "Dama Zahra ce ta ce na gaya miki, sun zo amma tana barci kamar bata jin dadi ne, idan da hali Kizo mata da Princess." "In sha Allah!" Ta kashe wayar, tana kallon Munaisah. "Abin gwanin ban sha'awa, dukkanmu mun haɗu. Don Allah Nenne ku roka min Zulaihah ta yafe min na cutar da ita gashi Allah da yaga zuciyarta har anyi aurenta da Baban Aamirah." Kukanta ya tashe ni, na tashi zaune ina jan bargo. "Sadiq dan Babangida ya shigo min da wasu manyan ledoji shi da wasu Yara, bude jakar nayi naga kayan kwadayi ne. *I forgot to tell you I love you, and now a said I love you* Murmushi nayi na bude ɗaya ledar me zafi. Roasted chicken ne. "Ki ci sosai, ina sonki." Ya rubuta a jikin takardar. Bude Jakata nayi na dauki yar karamar memo na rubuta mishi. "Ina sonka sosai, Allah ya tashe ka cikin Asahabul kahfi " Da gudu yaran suka fita. "Wannan shiririnta fa?" Kaji uku ne a ciki na mika musu biyu da rabi, na dauki rabi, yaran da suka kawo aka basu, sai da naci na koshi sannan nayi sallolin da ke kaina na kuma kwanciya sai barci. "Allah ya hada Zahra da aiki!" Wurin shida da rabi Zuzu ta shigo, dake ana ruwa. "Barci har ana kiran sallah." Tashi nayi na kalli Aamirah ta sha kyau ga kibar da tayi. Tashi nayi na bude mata hannu, ta shiga da sauri har tana tuntube. "I miss you Mami!" Rungume ta nayi ina faɗin. "Me too love!" Mikawa Zuzu hannu nayi, ina fadin. "Annurin amarci ba wasa ba." "Kema kin ga yadda kika yi kiba?" "Hmmm ina kiba anan" na mike tare da nufar waje nayi Alola na dawo dakin nayi sallah, itama ta gaya min tayi sallah a gida. Abinci ta kawo mana, tuwon semo miyar kuka ya ji kayan kamshi ga nama. Ga pepper meat da tayi. Sai manshanun. "Sannu zuzu!" Dibawa mijina nayi, na karbi wayarta na saka number shi naga ta saka Abban Aamirah, kira daya ya dauka. "Auntyn Aamirah!" "A'a Uwar Amirah ce, ga abinci kazo kaci kada ya huce." "Tow uwar Aamirah da sauran yara!" Haka yazo na kai har falon yaya Babangida na ajiye ya zauna muka ci tare, shiga jikinshi nayi ina faɗin. "Sanyi nake ji!" "Muje ma sauki!" "Idan muka gama hira sai mu ajiye Zuzu, mu wuce masaukin ko?" "Duk yadda kika ce matar kirki" Sumbatar bakinshi nayi, shi kuma ya rungume ni dakyar muka rabu. Ya tafi ni kuma na kwashe kayan, na koma wurinsu.aka bude shafin hira kamar me, duk wannan hirar ta rayuwar baya ce babu wanda ya sako Addah, domin mutunta Zuzu. Itama bata da yadda ta iya da Mahaifiyarta kuma bata da wacce ta fita. Haka muka yi ta hira har sha biyu saura aka zo kiranmu, haka muka fita ina dauke da Aamirah. A motar na kwantar da ita, ya kai su har gida, na shiga naga Addah tana barci. "Zan tafi amma gobe anan zamu wuni." "Na gode sosai Zahra!" Murmushi nayi muka fita, ta rako mu, wato dakyar muka isa dakinmu domin daukata yayi yana faɗin. "Yau nasan kin gaji muje nayi miki tausa." "Sauke ni na shiga da kafata ." "A'a muje dai na kai ki!" "Aishi kenan!" Na fada ina lumshe idanuna. A daren dai a gajiye nake, amma labarin daren me tsayawa a rai ne, domin barcin mu ƙalilan ne. Sai goshin asuba muka yi barci. Bamu tashi ba sai karfe goma domin mun makara, haka muka yi sallah a kurarren lokaci. Duk jikina ciwo yake duk da yau na ce zan fita amma dumin dakin ya hanani fita ko waje. Haka yasa shima makale min tunda na karya, sai naji dakin yana bani wani irin yanayi na musamman gashi ga dumin dakin, duk ya haukata min lissafi. Bamu bar masaukin ba sai karfe biyu na rana, ya kai ni gidan Zuzu. Yaga Addah a zaune an daura ta a kan wheelchair, an saka mata belt ya riƙe ta. Kunyar Zuzu yasa shi bai ce mata kome ba. haka ya tafi ya bar mu muka sha hira wurin karfe uku sai ga Ummi da Munaisah. "Jar Uban can, gidan nan ya min!" Inji Munaisah tana bin ko ina da Zuzu ta zuba interior design masu kyau, "amma kayan nan akwai Turkiyya ko?" "Eh uwar dakina, amma bani na saya ba, Hamma ya turo min,.kayan kitchen Mama daga doula ta aiko min kamar naki, lokacin da muke sayayya naga kome biyu take saya, ashe nawa ne. Ki shiga har kitchen din wasu na zuba su a can gidanshi na Yola domin gado biyu yayi min daya nasaka anan, daya nace akai cen kuma na rigada na saka kayan kitchen din da na saya shine nace a kai min can Yola." Yadda take maganar sai take karya min zuciya. "Zahra na gode!" "Allah ya shirya min ke!" Haka muka yi ta hira anan zuzu take bamu labarin Zahra yarta. Rike baki nayi na zuba mata dundun makafi a bayanta. "Wallahi ba zaki bar mishi ba, dole a dauko mana ita." Murmushi me ciwo tayi tana faɗin. "ba zai bani ba, sai dai idan zan aure shi. Ni kuma bana son aurenshi ina son nayi auren a cikin dangina yan uwa da abokan arziki." Haka muka ta jajantawa juna, kafin muka dawo case din Zuzu da Ummi, dakyar muka shawo kan Zuzu ta yafe mata, muka ci gaba da hirar mu sallah ke d'aga mu nice nayi abincin dare muka ci muka gyara dakin Addah wacce bakinta yake karkace ta ce min "Allah ya tsine miki albarka, la'annniya munafuka,. Kin saka yaran da suke samo min kuɗi sun daina, karshenki ba zai yi kyau ba." "Ayya Aaddah karshe me kyau gata har da cikin dan Sunnah." Dafe cikin nayi ina kallon Munaisah, "Yes ciki ne dake, sabo ma don Allah wannan turmusan a rage domin suna har nijar, zamu je ina dalili. Dan albarka kenan. Idan namiji ne Mamman Ba'are za a saka mishi ko? Idan mace ce Aunty Aminah za a samu!" Kunya ce ta sani fita daga dakin. Haka na zama kamar munafuka can nace musu. "Kai saura kwana uku nayi period!" "Ko maita kika ci wallahi baki period din nan sai kin haifi Mamman Abdul Majid Mamman Ba'are!" Inji Ummi, suka yi ta cakalata da magana kunya ta hanani magana. Haka yazo ya dauke ni da zamu tafi Munaisah bata da mutumci. "Mr Mamman Ba'are, ayi hakuri da wasan d'aga kafa, kada garin zungura a zunguro min Little Mamman Ba'are." Kifa kaina nayi ina faɗin. "Yarinyar nan ta zama bayahudiya." "Tow Miss Buba takum, za a kiyaye." Har muka isa sai kallona yaƙe har muka shiga daki yau ma hanani tafiya yayi, da dare kuwa lallabani yayi, akayi kome a takaice. Bayan ya huta ya ce min. "Idan har cikin ne tow zan kai ki Kamaru ina tsoron kada tashin hankalin gidan Mamman Ba'are ya shafi uwa da cikinta." "Kyalesu karya suke babu ciki!" Na fada ina shigewa jikinshi saboda sanyin da kafafuwa ta sukayi. Nan muka sake bude wata sharholiyar. Haka muka kwana, da safe na tashi da morning sick. Sai da ya saka min drip, domin zazzaɓi ne har da amai. Fita yayi ya sayo kayan magani ya saka min drip, sai wurin karfe biyu na farka, tunda na tashi nayi sallah, sannan na koma na kwanta. Innalillahi'wa'inna'ilaihi'raji'un ashe haka laulayi yaƙe? Bawan Allahn nan haka yayi ta rawar kafa a kaina, ya kira Hajiya ya gaya mata, ta ce ya mai dani gida, kwana uku aka mai dani gida wurin Hajiya. Kullum ina kwance a dakin Hajiya, gashi a lokacin ya jarabtu da son lallai sai ya tab'a ni, haka zai fakaici idanun Hajiya ya sakawa dakin Key, sai yayi yadda yake so da ni yake kyale ni. Da yamma abin ya ciyo shi, yazo ya samu Nana a dakin tayi bake-bake tana mitan. "Alhajin Allah taya zaka barta a dakin Sa'a matar da itama bata kula da kanta ba balle majinyaciyar da take dauke da karamin cikinka? Gaskiya ka mai da ta dakinka idan ta kama ma na dawo nan da zaman jinya xan yi." "A'a Nana!" Ya faɗa yana kallona, nasan kalar mijin da Allah ya bani, shi yasa na mike a hankali nace mishi. "Muje kaci abinci!" Tausayina da kaunata na gani a idanunshi. Haka muka tafi har zuwa falon na dibi abinci muka haura sama, tun daga ranar jinyar kasa ya kare domin na ga yana takura don haka na bashi duk wats kulawar da ya dace, sannan na rungume mijina hannu bibbiyu. Ana haka Mama tazo, naga hidima daga kakanni na da Mamanmu tsayayyar mace ce da bata son wasa, ita tayi ta gaya min yadda xan kula da shi, muna falon Hajiya kafafuna na kan cinyarshi yana matsa min, don bana iya zama sai kwanciya. Tunda muka dawo Zaytoonah bata taɓa tambaya ta ya jiki ba, haka zata wuce abinta tana harkar gabanta. Shigowa tayi ta samu yana matsa min kafa. Ta gaida kowa amma ko inda nake bata kalla ba, "Mama kina nan ne?" "Eh!" Babu wanda ya ce mata cikanki. Shigowa Nana tayi da katon kula. Ta bude min kamshin farfesun kan rago tashi nayi zan zauna ya rike ni. "Sannu kin ji!" Haɗiye yawu nayi dadin abin duk wannan ciwon baya hanani cin abu, zuba min Mama tayi, ya tashi ya kawo min ruwa. Sai da na sha Nana ta ce. "Hajiya Aminatu don Allah ku kawowa Zahrah da a bin cikinta maganin kambun baka da na idanu, da rubutun tsari kada a shammace mu a nakasa mana yaro kafin yazo duniya." "Nana an kawo mata, tana sha kullum kuma nasan tana addu'a akan cikinta da azkar." "Assalamu Alaikum!" "Wa'alaikimun Salam," Amaan wanda ya kara zubewa bai da lafiya gayen nan haka muka yi ta hira sama sama, ina gama sha barci yayi gaba da ni, ya gyara min kwanciya, "Ka maida ta sama kawai." Daukata yayi bayan ya cire min drip din, muka wuce sama, sai da ya kwantar dani ya dawo ya dauki drip din ya wuce da shi sama. Kwanciya yayi a bayana muka yi barci tare, kwanan Mama goma ta koma gida cikin farin ciki da jin dadi, haka abubuwan suka cigaba da tafiya. Idan ka ganni zaka dauka mutuwa zan yi tsabar laulayi. Wata na biyu da dawowa Zuzu da Munaisah suka zo, tun daga haduwar Munaisah da Zaytoonah, Munaisah ta ce mata. "Ke zo nan dan Ubanki!" "Kin Sanni?" "Zahra sa'arki ce? Zanci bu... Ubanki yar iska da kike ganin mutane kina dauke kai, me kika taka? Me kika sani na rayuwa shegiya har kin isa ki jera kafada da Zahrah, kika sake na bar garin nan baki zuwa kullum kina gaida Zahra sai na miki diban albarka." Yadda ta ga Munaisah bata da mutunci yasa bata mata fitsara ba, ke Munaisah har da cewa. "Shegiya don kinyi aure sai ki nuna mata rashin kunya." Ashe bayan ta gama a gabana, ta kuma sakata a gaba tayi mata tass kuma tace wallahi wani abu ya samu cikin jikina sai ta daure ta, kada taga suna uba daya zata rufeta har igiya yayi saura. Tsoron haka yasa ta cire kudirinta na ganin Bayana. Kai jama'a. Satinsu daya na warware kamar bani ba, muka je marad'i bikin Zainab kanwar Baraka,. Dake da Majid muka je Munaisah tana nan ita da Zuzu, kawai Mahdi Abubakar Abzin ya ga Munaisah, tuni ya susucew, ita kuwa sai fada take yana faɗin me zan yi da shi, dube shi fa da uwar wuya a wurin. Mu kan me za mu yi banda dariya. 300₦ 0016341139 unity bank zahra'u yahaya Ali Katin MTN 400 #Mai_Dambu ce [5/29, 07:47] Hlm: BHB269 Da gaske ta dauki fushi ita Mahdi ya mata dogo, ita ta saba saurayinta na baya katon namiji ne, iskanci kala kala haka tayi ta mana har aka gama bikin. Muka dawo su Kuma suka wuce naija daga can. Munafuka ashe ya bita sun hade kai, sai da ta kira ni muna waya take ce min." Kashe don Allah Babyn baby yana kirana." "Waye muka samu babyn baby?" Dariya ta saka min tana rokon na kashe kiran na kashe. ** A can Yola kuwa zuzu tana sauka Sk Lamido ya wuce da su gidanshi. Ashe gagarumin tashin hankali aka yi a family wanda ya zakulo wani alamarin da ba a san da shi ba, Maman Sk Lamido ashe ba ita ya haife shi ba, dan kishiya ne ta rike domin sai da rigimar auren ya fito Yaranta suka ce ai ta so kanta taya xata hana shi auren wacce yake so duk matanshi ita ta saka ya aura, karshe daga can garin Numan dangin mahaifiyarshi suka ji labari suka yi tsalle suka ce basu san da haka ba, ya ga matar da Allah ya haɗa halittarsu zata ce bata ji ba, ko don ba ita ta haife shi ba? Kuma ita tunaninta idan ya fara haihuwa bai zama dole ya kula da su ba, sai daga baya yake fitar da wahalar da ya sha a hannunta, abin yana tsaye a ranshi. Amma kamar an rufe mishi baki, dangin mahaifiyarshi suka dauki Zuzu da Yarta aka tafi garin Mamarshi aka sha biki, anan ya hadu da yayun shi da suke ciki daya, amma ba uba daya ba, anan ya fahimci Hajiya ta raba shi da kowa ne don kanta. Bikin da aka yi dangin Uwa suka nuna mishi kara, aka yiwa Aamirah hidima kamar zasu maidata ciki. Ga wani cikin da Zuzu ta samu. Hajiya bata hakura ba sai da tazo har numam ta gaya musu wacece Zuzu suka ce sun yarda suna sonta sirkarsu. Dake itama Zuzun taga Rayuwa kama dangin shi tayi ta rike gam, kayanta da na shi da na Aamirah ta saka suka barwa dangin Mamanshi wasu kayansu sabi ne dal, wayyo Allah sai gashi an hada mata kwaryar tsaraba, kifi, dafaffen madara, man shanu, kayan miya kayan lambu. Da Hajiya uwar goyan shi tayi magana akan rayuwar Zuzu cewa suka yi.. "Ba kome, ai Aminatu ta tabbatar mana da Lamido shi ya fara ta'adin uwarta tunda gani ya kori ji." Wannan abin ya kara rufe bakinta, amarya da ango da yarsu suka bar dangi cikin so da kauna, haka suka dawo Yola,aka bude sabon amarci kamar a cinye juna, wannan al'amarin yafi kome dad'i, kuma shima yadda ta rike danginshi haka ya dauko Aaddah ya ware mata part har da yan aikinta, ga wani cikin a gaba don ma laulayin me sauki ne kawai abu kad'an bata so. Haka suka yi ta rayuwarsu, ya kwashe su suka tafi Umara daga can suka tafi China aka.akayi sayayyar kayan haihuwa, sai da ta fara yi ma Zahrah sannan tayi nata, sai kayan kitchen da ta sayawa Munaisah da Ummi. Aka kawo duk da Ummi har lokacin bata samu miji ba, amma kuma duk abinda ta saya har da ita. Shima mijin lokaci ne da sauran. ** Duk da ban tab'a daukar ciki ba, sai yanzu a yanzu na fahimci dalilin da yasa Zuzu ta ce na bata yarta, domin wata soyayyar sai uwa da d'anta. Tunda Munaisah ta ci Uban Zaytoonah na samu sauki Aunty sama Aunty kasa. Ga uwa uba duk wani aiki sai dai na samu tayi min. Kallona tayi tare da yanka min kankana ina sha. Ta ce min. "Ashe duk abinda ya faru baki tab'a gayawa kowa irin wahalar da kika sha da su Munaisah ba." Ina tauna na ciro kwallon na ajiye ina faɗin. "Ba kowane lokaci ake tanka rikicin dangi ba, kayi iya yinka kada ka sake zumunci ya nime hakkin shi a wurinka a ranar gobe kiyama, a gaban Allah." "Me yasa kike da hakuri akan naki?" Dariya nayi ina kallon yadda take share hawaye. "Saboda bayan su bani da wasu dangin, su din sune dole na, kuma kwarin gwiwata. Idan na rasa tallafi daga gare su ni ba kome ba ce." "Aunty Zahra kina rike da ni ko?" Ta fada tana kuka. "A'a bana rike dake, amma nasan har abada ba zan bar miki Majid ba, domin ni aka yi shi." "Ni kuwa kin ga zan karo mata uku russss kwailaye kuwa!" Wurga mishi filo nayi ina faɗin. "kwailaye for my foot shoes." Dariya yayi yana faɗin. "Yarinya kwailaye masu kananun!" Kura mishi idanu nayi, ina nuna mishi Zaytoonah. Zuwa bayanta yayi ya toshe mata kunne. Dafe goshi nayi na ce mishi. "Wallahi Bawan Allah yana jinka kana fadar batsa shima zai ɗauka." "Ayi haka na fasa, ke, tafi wurin Hajiya mijin yarta ya dawo atow maza mai tumbi duba lamarin mijinki" ya fada yana bude kofa. "Maza sai da safe kada a kuma zuwa sai na fita." Juyawa yayi ya ganni a bayanshi. "Me yasa xaka tab'a ta? Kasan yadda na.ji kuwa?" Na fashe da kuka, ina dukan kirjinshi. "Ji nayi kamar xan mutu. "Yarinyar nan ko mutuwa kika yi wallahi ba xan tab'a aurenta ba, ni idan na mutu zan so ki rayu da kowa amma ban da jinina wato kannena, don Allah ina tayaki kishin kanmu a kanwa na dauke ta." Tunda ya fahimci kishina yake takatsantsan dani, Nima kuma sai na sayi wata irin girma na azawa kaina, bana wasan kannen miji da yan uwanshi, kuma sun fahimci haka sai suka bi bayan Baraka tante sama tante kasa, yan uwanshi da suke uba daya suma suka shiga girmamani musamman Ya'yan Harira. Yayunshi kuwa ido suke bina da shi, gani da tsayi sai cikina ya kara min cika da wani irin girma,.kafin wani lokaci cikin wata biyar ya fito, a lokacin aka yi bikin Munaisah mun sha shagali anan Ummi suka hadu da Abdul B, dan gidan Hajiya Hadiza Mamman Ba'are, da fari taso tayi bori Nana tayi tsalle tace ya ga mata, haka aka saka bikin bayan na haihu za ayi. Bayan kome ya lafa, ya dube ni a hankali ina sauke ajiyar zuciya. "Zahra!" "Na'am! Sojana!" Shafa fuskata yayi yana faɗin. "Ina sonki matar soja." Kwanciya nayi a kirjinshi ina dariya, magana yake son yayi amma ya kasa fada. Ya kuma kasa cewa kome. "Ina son na rakaki lebo room!" Mintsinin shi nayi ina faɗin.." kaga labor room a kanka!" Shafa cikin yayi, yana dariya. "Allah ka daina razana ni." "Da aka yi me? Kawai dai baki yarda da kanki bane, cewa zan yi miki oya push!" Ture shi nayi ina faɗin. "kyale ni da fushin." "Zan tafi Mali maganar wasu golden dinmu da suka makale." "A'a babu inda zaka, ka tura wasu dai." "Nafi son zuwa da kaina, ba zan wuce two weeks ba baby girl." Idanuna ne suka cika da kwalla, na ce mishi. "Allah ya gani ba da son raina xaka tafi ba " na fashe da kuka, kusan raba dare muka yi ina kuka yana rarrashina, har da murmushinsa. Washe gari na tashi na taya shi shiri, haka ya tafi office ya bawa Aryan rikon kamfanin. Sannan ya dawo gida ya haɗa kayanshi. Haka kawai jikina yabani na duba wurin kayan sojojin shi na samu babu kodaya. Bin shi nayi falon shi. "Na ga kayan Army dinka babu ko daya." Dafe goshi yayi yana faɗin. "Oh sorry love na kwashe nayi kyauta da su ne." Ya zo ya kanenaye ni yana zuba min kauna, kamar me. Haka muka raka shi har airport, Nana har da kukanta. "Alhajin Allah yadda ka bani amanar Magaji ba zaka ji kunyar dawowa ka same mu lafiya lau ba." Kallon Hajiya yayi yana faɗin. "Gobe a wuce da ita Kamaru, a can zata haihu haka na gayawa Mama." "Ba sati biyu kace zaka yi ba." "Eh mana, amma ki haihu a gaban Mama yana da muhimmanci." "Kaifa? Cewa kayi zaka raka ni lebo room a ko wane yanayi kuma zaka kace a kai ni wurin Mama? Gaya min akwai abinda kake boye min ne?" Juya baya Hajiya tayi ta bar mu, amma itama hawaye take sharewa. Aryan ma barin wurin yayi shida Nana Amaan ne ya bari daga baya, ganin xan birkice mishi ya sumbaci goshina. "Ba zan jima ba, zan dawo in sha Allah." Duk yadda naso ya gaya min gaskiya yaki, Mijina ne da na.mishi wani irin sani lokaci kalilan na san fushinsa na san dariyarshi, sai da aka fara kiran sunayen su ya kara sallama da kowa, nima ya tsaya ya rungume ni, sannan ya juya ya tafi. Kasa kuka nayi na zuba mishi idanu, hawaye na zuba min kamar famfo. Dafe cikina nayi da yayi mugun nauyi, mutumin nan ko tausaya min bai yi ba, haka ya tafi ko waiwayawa bai yi ba, da yasan yadda yake a rayuwata ba zai min haka ba. Kuka nayi ta yi da karfi tare da ihu da sauri Nana tazo ta ja hannuna, muka bar airport din Da na shiga mota kuwa kuka nake tsakanina da Allah kamar raina zai fita, har muka iso gidan kuka nake........ *Kuyi hakuri ba yawa* 300₦ 0016341139 unity bank zahra'u yahaya Ali Katin MTN 400 #Mai_Dambu ce [5/29, 07:47] Hlm: BHB270 Kwanaki goma da suka wuce, tun bayan dawowar mu daga biki, ina kwance yake gaya min." Yan mata zan yi baƙi ko zasu samu abinci a kai musu office ɗina." Kallonshi nayi kafin kace mishi. "Me yasa ba zasu zo nan ba?" Karamin murmushi yayi ya ce "min sojojin ne zan bari su shigo min cikin gidana." Zumbur na tashi zaune tare da zuba mishi idanu. "Amma wasa kake min ko?" "Ban gane wasa nake miki ba? Zan miki wasa ne don jin dadina?" Ya faɗa yana gyara zaman tie ɗinshi. Cikin fushi na mike zan fita ya riko ni. "Wani abu aka miki mara daɗi ko bakin ne bakya son zuwansu?" Ban san me yasa na tsani harkar sojojin ba, kawai na fashe da kuka. Na gaya mishi. "Ni harkar sojojin ne bana so, kuma bana sha'awar kayi." Shiru yayi kafin ya ce min. "Ok idan na fahimta bakya son hidimar soja kawai na zauna a matsayin civilian?" Gyada kai nayi, murmushi yayi sannan ya ce min. "Shi kenan dama sun zo min Allah sanya alkhairi ne, amma tunda bakya so a yi abincin a kai musu." Gyada mishi kai nayi, ina nufar hanyar kitchen, shi kuma ya fito yana kallon yadda nake tura baki. "Allah ya huci Maman Mamman Abdul Majid Mamman Ba'are." Watsa mishi harara nayi, na ci-gaba da aikina, shigowa Zaytoonah tayi ta gaishe shi cikin girmamawa sannan ta ce min. "Girki zaki yi?" "Eh baki zai yi anjima za a kai office din shi." Zuwa yayi ya rungume ni ta baya. "Madam ayi musu kome special." Kwantar da kai nayi a jikinshi, ina dariya. "Na ji amma sake ni kada na sangarce na ce na fasa!" Da sauri ya fita, mikawa Zaytoonah aya nayi ta wanke, yana tsaye yana sani magana. Kai hannu yayi zai tab'a min danyen kazar da na Ciro na dauki muciya na ce mishi. "Oya muje ko na ma ka maka!" Zaytoona sai dariya take min tare da gyara tafiyar shi wai yana koyan yadda nake tafiya. "Allah na ganinka ai!" "Tow Aunty Zahra!" Ya faɗa yana sauka a step din. "Zaka dawo ka same ni." "Zan wuce wurin Uwargida Nana!" Share shi nayi ina me cewa. "Takaici bai tashi gaya min aikin ba sai yanzu." "Ba mamaki shima da safe nan suka mishi magana." Haka na cigaba da aikina, ina kallon yadda take min aikin itama, tana wanke ayar ta rege, nasata ta nika min, ni kuma na wanke shinkafar tuwo na saka a cikin tunkuya, na duba fridge na debo kayan miyar ganye. Na bata ta gyara min ni kuma na dauki zallar kayan miya na raba biyu, na nika sannan na sake daura jollop din cus-cus wanda ya ji kayan lambu, na zuba musu sai dan meat pie da yar cake, kafin karfe biyu da rabi, mun kulla tuwo a leda, muka saka a manyan kulolina. Idan ina wani aikin ita karbar wani aikin take. "Assalamu alaikum, mutanen sama me ake ta mana ne gida ya bude da kamshi." Inji Anisah, wacce nayi imanin tana cikin masu zuga Zaytoonah, ganin yadda taki daukar zugarta yasa ta dawo jikina. Dauke kai Zaytoonah tayi tana cigaba da aikinta. "Auta ya kike?" "Hmmm lafiya lau, Aunty Zahra." Ta fada tana kallon yadda nake shirya kome a cikin basket. "Babu tab'i ne?" "Nan aka fi auki!" Inji Zaytoonah. "Koma me mutum ya fada nan dai gidan Ubana ne." Ko ta manta cewa cikin mu daya da ubanmu ɗaya. Kafin na bude baki nayi magana sai jin Muryar Amaan muka yi yana faɗin. "Wannan wani irin jahilci ne? Ke wata irin mahaukaciya ce wawuya kawai." Shiru tayi tasan halin shi mutuncin shi kaɗan ne a da can, shi yasa bata amsa ba da wani ne ramawa zata yi. "Kyale ta Amaan, idan ta gama rashin kunyarta ta bar min part dina." A fusace ta bar part din, Ni kuwa ban san lokacin da zafin rai ya kwashe ni na bita ba. Suna kirana amma ko kula su banyi ba, na sauka kasa na samu tana fadawa Hajiya wai mun mata rashin mutunci. Hajiya ta ce. "Karya ne wannan zancen da Zaytoonah kika ce xan yarda ban da Zahra sai dai idan akwai abinda kika mata." Ina sauka na zauna ina haki. Fulatanci na juyawa Hajiya don sau dayawa muna sakewa muyi, yadda nake hakin yasa jikin Hajiya yayi sanyi na ce mata tabbas Zaytoonah zata bar gidan, amma ba don maganar Anisah ba. Don takaici girkin da ba a kare da ni ba kenan, Zaytoonah ta karasa don ba zan iya komawa sama ba. Ina zaune suka sauko da kome har da Na Hajiya da Nana aka kai mata Amaan ya wuce da na Office, anan nayi sallar Isha, tow tun da ya dawo na fahimci yana cikin damuwa, lokaci guda na ga ya je ya saka kayan sojojinshi a gaba, cikin jin haushi don ni yanzu abu kad'an yake harzuka ni, kuma da yake likita ne sai baya biye ni. Haka na gama kallon shi na juya na bar mishi dakin shi na tafi nawa, ina zaune don na kasa barci sai gashi nan. "Lady lafiya kika dawo?" "Amma kasan haduwar kaddara ce a barikinku?" Zama yayi a kusa dani. "Na sani!" "Kasan nasan cewa saboda ni wannan mutumin yayi ta bibiyarka?" A hankali na fashe da kuka me cin rai. "Ban ga laifinka ba, amma aikin soja na tsane shi." Rungume kaina yayi yana shafa bayana. "Kiyi hakuri ba zan koma aikin soja ba, ina kallon kayan ne." Haka ya gama rarrashina, sannan ya bude wani babi na daban yana daura min karatunsa me saukin dauka da wuyar aiwatarwa. Wannan shine abin da ya faru, na kara fashewa da kuka, a lokacin da naji Nana tana faɗin , "suma sojojin nan munafukai ne, akan me zasu ce yazo ya taimaka musu da wani aiki tunda sun san ya bar aikin sojan!" Wani irin kuka na fasa ina rike cikina. "Wato yaudarata yayi ya ce min ya bar aikin soja ashe ba haka ba ne." Nayi ta surutu, haka muka isa gida a daren ranar a asibiti na kwana, har da drip aka saka min. Kwana biyu ina jinya, Zaytoonah ce a kaina, Mama tazo da kanta kamar yadda ya ce a kai ni. Sai gashi tazo. "Ke baki da hakuri ne?" Kallonta nayi sai ga hawaye. Fada ta shiga min kafin tayi kasa da murya alamar rarrashin. "Kiyi hakuri, bukatar haka ce ta taso, ya sha gaya min yadda yake son ki haihu a hannunshi, idan kika saka damuwa a ranki zai tab'a cikin jikinki." Kwanan mu biyu muka koma Marwa domin itama ta ajiye aiki, tana yar business din nan na zamani, kuma ta ce bata ga wani abun da take nima ba don ta samu, ina yawan jin haka daga gare ta. Sai da muka yi sati biyu me kyau kafin muka fara samun shi a waya, ranar da ya kira ni, nayi kuka kamar zan bi shi ta wayar. Daga nan kuma yayi ta bani baki, kafin nayi shiru. "Yawwa ko ke fa, ina baby na?" "Lafiyanta lau!" "Mace ce aka gaya miki?" "Naga kafi karkata akan namiji ne." "Duk wanda Allah ya bani ina so." "Hm!" Ya faɗa yana cigaba da niman fitina ta, a sati biyun nan ji nake kamar nayi hauka. "yauwa yaushe xaka dawo?" "Da sauran lokaci." "Gaskiya ka dawo na haihu a gabanka!" "Naji zan zo ki haihu a gabana." "Shi kenan zan zo na haihu a gabanki yayi!"ya faɗa yana murmushi. Sai da yaji alamar zan yi barci ya kashe wayar, haka washe gari ya kira sai da ta kai kullum zai kira yaji ya muke, Alhamdulillahi duk wata damuwata ta kau, Aryan yaƙe rike da kamfaninsu,wanda Hajiya take bayan shi tana nuna mishi kome, sannan ganin yadda yake tafiyar da kome yasa Hajiya kara tabbatar da cewa Aryan zai rike kamfanin sama da Majid, don haka masu kawo musu matsala, sai suka ja da baya. Sannan dayawansu gani suke kamar Majid yana bibiyarsu. *** Ina Kamaru sai ga Zuzu da Ummi, sai da suka huta na zuba mata idanu ina shafa kan Amirah da take wasa da wayata. "Ina kika bar min Aaddah?" Murmushi tayi tana faɗin. "Tana gida, tare da masu kula da lafiyarta." "Allah sarki Aaddah na." "Tana nan tana fade-fade mun so zuwa da Munaisah Mahdi ya hanata zuwa." "Wai tun ba a shiga daga cikin ba ma kenan." "Wallahi kuwa!" Kiranta muka yi na ce mata. "Munafika cewa kika yi ya cika tsawo siriri ne, ke kin hadu da samudawan maza ko?" Dariya ta saka tana faɗin. "Eh sai me?" "Sai na gaya miki kin zama munafuka." "Eh tunda fir'auna zai danne ni a kasar wuta, Zahra zan dura miki Ashar." "Na nawa kuma, bayan kin zage ni sai ga Ummi da Zuzu da fatan lafiya suka baro ku?" "Lau Zahrah sun zo ganin Baby ne!" Haka muka gaisa, sannan muka yi sallama. Ni kaina nasan naji dadin zuwansu satinsu biyu suka koma bayan zuzu ta ajiye min kayan da ta sayo min. Nayi ta murna, Hajiya ma satin da ya wuce ta aiko min da kayan Baby Jamilah ma haka, Aryan kudi yake turo min a cikin wata guda da tafiyarshi. Amaan duk sati daya zai tura min kudi shima, duk da nasan bai da shi sosai amma yana kokari. A hankali muka share wata biyu, a lokacin cikina ya shiga wata bakwai, a lokacin ba karamar buƙatarshi nake ba. Haka zan ta kuka ina jin tsanar aikin soja, ban san yadda matan suke handling wasu damuwar ba, amma ni tabbas na shiga matsanancin damuwa. Tun muna samun shi awaya, har ta kai bamu samunshi, sai ya kusan sati biyu bai kira ba, ko na kira baya shiga. Ashe a lokacin sun hau teku ne. Wannan abin ya d'aga min hankali domin ban saba ba, ban tab'a shiga irin wannan yanayin ba, sai gashi jini na hawa yaƙe kamar hauka, domin na saka damuwa a raina, dalilin da yasa Hajiya tazo ta ganni har take bani labarin abubuwan da suka faru a baya, sai naga babu amfanin d'aga hankalina domin itama kamar bata son zuwan shi amma babu yadda ta iya tunda abin ita suka fara tuntub'a. Abin da ya faru kuwa kamar yadda ta gaya min, yan fashin teku ne suka sace wasu turawan biritania, sannan anyi anyi su sake su sun ki, karshe shugaban yan fashin ya ce matukar ana son ya sake mutanen dole a nemo Majid, domin Majid ya mishi sanadin da ba zai manta ba, sannan a yadda Hajiya ta faɗa ko a wurin aikin Majid yana da tarin makiya da masu jin haushinsa, haka yasa ni jin kamar abu zai fito daga cikina,. Nace mata."Hajiya me yasa kika bar shi ya tafi? Idan da na sani wallahi ba zan tab'a yarda ba, wannan ai ba inda zai je ba ne." Muryar Mama ne ya katse min kukan da zan yi. "Tow ayu, so miji." Tura baki nayi ina faɗin. "fisabilillahi an san mutanen nan ba son shi suke ba, a tura min dan uwa salon su kashe min shi ko su nakasa shi wallahi ba zan yarda ba." "Ba yarda zakiyi ba? Tow sai ki bishi karshen rashin yarda." Inji Yafendo, "Ni dai Yafendo ki daina shiga maganata, ke ba ga mijinki a tare dake ba, ko an tura shi wani wurin ne?" "Zahra ban san rashin kunya, yaushe kika fara son Majid ɗin da kike mana rashin mutunci akan shi " ai kuwa na fashe da kuka, cike da takaici domin dai akan gaskiya ta nake magana kuma dole nayi magana akan me za a tura min miji wata uwa duniya da sunan ceto basu da sojoji ne da sai shi, don an maida min miji iliya dan mai karfi. 300₦ 0016341139 unity bank zahra'u yahaya Ali Katin MTN 400 #Mai_Dambu ce [5/29, 07:47] Hlm: BHB271 Ita kan Yafendo sai dariya take tana faɗin. "Eh Malamijo yana tare dani, idan kin ji haushi ki bi shi mana mara kunya." Ai kuwa na kara cika kamar balloon nace mata. "da shi shugaban sojojin da shugaban Najeriyar wallahi wani abu ya samu mijina sai na ja musu Allah ya isa " na tashi ina tafiya da kyar domin daurewa da marata tayi, ina faɗin. "duk me hannu cikin raba ni da mijina, shima Allah ka kashe shi kowa ya huta don yana ceto rayuwar waɗancan mutane za a takurawa rayuwar mu, kuma ban yafe ba haka kawai mutum yana raka ni awo anyi min bakincikin zuwa awo da shi don wulakanci babu maza ne a Nijeriya sai an zo nijar. tow ban yafe ba." Tashi Mama zata yi Hajiya ta rike ta. "Barta tayi abinta da zafi, bana fatan tayi yadda nayi bana fatan ta ji zafin rabuwa da shi, in sha Allah zai dawo gare ta " haka kawai sun dauke min mijina Allah ya isa, na fada a raina domin ban yafe ba, Haka Hajiya tayi ta rarrashina, Mama kuwa kamar bakinciki ya kashe ta, domin gani take da gayya nake wasu abubuwan. Idan ma da gayya ce ai ina da gaskiya Allah ya isa min na fada ban yafe ba, kullum idan naji kewar shi sai na musu Allah ya isa min ban yafe ba, kullum sai na musu. Hajiya sai da tayi wata guda na shiga na takwas, sannan ta bar Kamaru. Kafin na haihu ta ce min zata dawo, da kuka muka rabu, idan Mama ta kalle ni kamar ta zane ni. Ni kuwa ko a jikina. Wani lokacin sai ta kyale ni nayi ta rigima da Goggo Sume, ba zata iya min ba, haka nayi ta turawa ga cikin ya kara girma, har tsoron cikin nake domin idan yafi haka girma, ban san ta inda zai fito ba. Shi yasa kullum sai na yiwa Mama mita. "Ayya Mama ni cikin nan tsoro yake bani duba fa, idan yana motsi har fitsari nake yi!" "Haka kowa yake yi, ayi hakuri ayi ta lallabawa shima ibada ne." Haka yasa nayi shiru ban kuma cewa kome ba, tunda ta gaya min ibada ne na rungume kaina da rayuwata. *** Tun da ya isa south Africa, suka dunguma, zuwa Nigeria, a can aka shiga tattaunawa tare da saka, bayan ya saka uniform din shi. "Ba'are me ka sani akan yan fashin tekun nan?" Shiru yayi kafin ya sauke ajiyar zuciya. "Idan har wadanda muka kama shekarun baya ne, tow nasan suna gidan yari. Idan kuma wasu ne tow ba makawa masu nima na sun sanni kuma ni din suke nima, domin idan ba ni ba ne da tuni sun kashe mutanen." Ya faɗa yana kallon board sannan ya cigaba da cewa. "Idan har yadda nake hasashe ne, tow dole a bani team dina da muka yi aiki da su shekaru shida da suka wuce, ina son a tara min su yadda zasu taimaka min yadda zamu yi aikin." "A kira su duk inda suke nan da kwana uku." Tunda daga wannan meeting, da farko yana kiran gida amma tunda team din shi suka haɗu kawai ya datse kiran gida suka shiga aiki, a haka suka tafi har maboyan yan fashin tekun, ba karamin aiki suka yi ba, shi yasa ba a jin labarin shi sai da ya kwashe wata biyu, a na uku ne yayi kokarin kiran gida a san ko lafiya tunda ya bar mace da tsohon ciki. Ranar da ya kira ta ɗauka kukan da take yi ne ya kashe mishi jiki. "Fatuna, kiyi hakuri in sha Allah ina kammalawa zan dawo kin ji, ki shafa min kan babbar mace." "Amma me yasa baka kira ni ba?" D'aga kai sama yayi yana murmushi ya ce mata. "Saboda bana son na kasa aikina." "Don Allah ka dawo tsoro nake ji, kada su cutar min da kai, don Allah ka dawo ka ji." "Zan dawo in sha Allah." "Amma kayi min alƙawarin tare zamu shiga dakin haihuwa don Allah ka cika min." Murmushi yayi yana faɗin. "Nayi alƙawarin haka, idan Allah ya nufa xan dawo, idan kuma ta Allah ta kasance kada ki yi kuka.". Fashewa da kuka tayi tana faɗin. "Allah ya tsinewa wanda ya kirkiro zuwan ka Nigeria, haka kawai basu nime ka ba sai da nake cikin tsannanin buƙatar ka, kasan yadda nake son kasancewa da kai kuwa. Wallahi Allah ya isa min." Dama da yar guntun tsiwa ya hadu da rikicin ciki ai kuwa tayi ta kuka da Allah ya isa bata yafe ba. Dakyar ya shawo kanta sannan ya roketa da kada ta manta ta saka shi cikin addu'arta, domin gagarumin aiki ne a gabanshi. Kuma yau zasu fita aikin don haka su tabbatar sun mishi addu'a. Yadda take wani irin kuka ya sa shi kashe wayar domin yasan ba zai iya jure kukanta ba, Zahra wata irin jigo ce a rayuwarshi ba iya ita ba, duk wanda yake tare da shi yana amfana da kasancewar Zahra a tare da shi don haka yasa shi kashe kiran, a daren ranar suka hau jirgin ruwa zuwa inda barayin suke. Wani abun da Majid ya kasa ganewa, yadda ga zaratan sojoji amma ba a nime su ba sai shi, kuma abin da Zahra ta koka mishi kenan, amma bai ce kome ba, babu wani abin da yake iya juyawa ko ya sauya ƙaddara. Wacce addu'a take iya sauya akalarta, musamman wanda ya yarda da Allah ya kuma miƙa lamarinshi ga Allah sai kome yazo da sauki. Haka abin yake domin jikinshi a mace zasu tafi yake jin wani iri don haka ya ce a tsaya. Tsayawa suka yi ya kalli Yaranshi mafi kusanci da shi sannan ya ce musu. "Ni zan tafi sannan ku bi diddigina ta nan, ban san yawan su ba, amma idan naje zan tabbatar da yawansu shi yasa xan tafi, kuyi kokarin ganin motsina ta nan!" Hikimar shi koda yaje wani abu ya faru tow ba zai kasadar janyo su a cutar da su ba, shi kuma yasan idan baya raye Zahra da Yarshi zasu samu kulawar dangi da na abokan arziki, kuma ya bar dukiya me yawan gaske da zasu kula da kansu. Shi yasa da abokan aikin suka fita ya ce musu. Suyi kokarin ganin sun san inda yake ya bazama bin location din da barayin suke. Wannan ita ake kira tafiyar ƙaddara, wanda cikin shi babu guziri babu kome sai wani ikon Allah da sa rai. Haka ya damki hanyar tare da matukin jirgin. Kuma yana da yakinin tunda suka ce shi suke nima tabbas shi din ne babu makawa, gara yaje can ya ga me yasa idan ma ya mutu ya mutu ne a matsayin jarumi ba rago ba. Kuma abin alfahari ga ƙasarshi da kasar Nijeriya. *** Zuwa yanzu cikina ya shiga wata tara, rabona da shi wata uku cif da kwanaki haka yasa hankalina ya kara tashi, ga tsananin kewar shi da begen shi,. Abin ka da sabon shiga kullum sai nayi mita nayi kuma Allah ya isa ban yafe ba. Dake yau Laraba ne ina zaune a tsakar gida, an shimfida min tabarma, sai mita nake yi ina cin.taliya da mai da yaji wanda aka min miyar jajjagen tattasai sai yajin da yake gefena. Ga ruwan zafin tea da na'ana da nake kurba, "Ni kan tun daga ranar da kuka yi waya da Abdul ya kuma kira kuwa?" Kamar zan yi kuka nace mata. "Bai kira ba, na gwada layin baya shiga." Na d'aga kofin zan kai bakina, naji wani wata faduwar gaba, sai da na sake kofin ina faɗin. "Innalillahi'wa'inna'ilaihi'raji'un! Allah na tuba ka yafe min,Allah na tuba, Allah na tuba. Subhanalillahi walhamdulillahi Allahu Akbar!" Na fashe da wani irin kuka, wanda tunda nake ban tab'a jin nayi irin shi ba, kuka nake ga duk me saurarona yaji kukan.yasan na gigita ne bana lafiya ba. Kafin kace me Mama da take shanya kayana a igiya ta zuba min ido , Goggo Sume da Yafendo suka yi min cirko-cirko. Malamijo suka kira ya tsaya a kaina ya shiga min addu'a, yasa aka bashi ruwa yana tofa min, Goggo Sume tana shafa min. Kafin wani lokaci na fara ajiyar zuciya. Can barci yayi gaba da ni, ina ajiyar zuciya. Tunda na kwanta nake mafarkin shi yna murmushi, yana faɗin. "Ki tashi ki min addu'a, ina bukatar addu'a. Kinji tashi ki min addu'a ina bukatar addu'a." Ko minti ashirin ban yi ba na farka a razane, ina faɗin. "Don Allah kuyi mishi addu'a ya ce yana bukatar addu'a." Ganin yadda na birkice yasa Malamijo saka Yayansu Mama Alhaji Ahmed da yazo gidan ya kira Hajiya, kafin wani lokaci labarin halin da ake ciki ya iso mana, wayyo Allah raxanar da na shiga ya haifar min da sarkewar hakori domin har na fara tattauna harshe na, "Ku bani cokali innalillahi'wa'inna'ilaihi'raji'un!" Haka aka saka tsumma aka naɗe a jikin cokalin aka tusa min a bakina, sannan aka dauke ni don har na fara zubar da ruwan haihuwa. Aka nufi asibiti da ni. "Innalillahi'wa'inna'ilaihi'raji'un! Tashin hankalin da ba saka mishi rana, yarinyar nan taji halin da mijinta yake ciki a jikinta ne Ya Allah na tuba, Ya Allah nayi kuskuren inazan ga Isma'il da Yar Uwarshi!" Haka Malamijo yake fada yana nanatawa, kuka yake sosai, duk abinda ya faru ga zuri'arsa gani yake kamar har da abin da yayi na kuruciya ya zalunci yaran dan uwanshi ya barsu. Haka aka kai ni asibiti ana shiga da ni. Aka ce aiki Kawu Ahmed ya saka hannu aka debi jininshi aka saka min, zuwan wani babban likita yasa kowa ya shiga gaishe shi yana ganin Zahra ya ce musu. "Yarka ce Amadu?" "A'a Madobi yar Aminatu ne da dan Sa'a yake aure, tow yau aka samu labarin mijin an kashe shi shine ta shiga tashin hankali." "Maza a wuce da ita ayi mata aikin!" Kafin kace kwabo an wuce da Zahrah aka shiga da ita aikin kafin awa biyu har an fito da ita, da katuwar Yarsu gwanin ban sha'awa, a cikin wannan yanayin aka.fito da ita aka wuce da ita dakin hutu..... 300₦ 0016341139 unity bank zahra'u yahaya Ali Katin MTN 400 #Mai_Dambu ce [5/29, 07:48] Hlm: BHB272 Duk yadda al'amarin yake ya wuce tunanin mutane, domin kuwa an nemi Majid sama da kasa an rasa, gashi nan sun ga location din da ya nufa amma daga baya babu shi babu labarin shi. Wurin sati daya da faruwar al'amarin, haka gamayyar sojojin ƙasa da ƙasa suka tafi har inda aka ga al'amarin yana nan, babu shi babu labarinsa, sai dai sun samu turawan lafiyarsu lau. Sannan suka dawo da su. A bakin su suka ji labarin abin da ya faru. A lokacin da aka kama su, burin shugaban barayin a kawo mishi Abdul Majid, ko a mace ko a raye. Sannan suka ce idan aka kawo zasu sake su. Duk da cewa basa tunanin Majid din zai zo amma kuma wani ikon Allah, sai ga shi nan ya taso ya zo, tunda ya fara tunkararsu sai abin ya zama kamar an san da zuwan shi. Tuni suka zagaye shi tare da cewa. "Ka ajiye kayan aikinka, kai kawai muke so." Lumshe idanunshi yayi ya ajiye kome ban da abin dauka, sannan aka wuce da shi can wurin da aka daure turawan, kafin su karasa zuwa aka fitar da su aka saka ya cire kayanshi, suka bashi wani sannan suka dauke shi a jirgin ruwa bayan sun rufe mishi fuska baturen yake cewa duk abin da yake faruwa idanunsu a rufe, haka suka tafi suka bar su a wurin, duk da sun cire rai za a kawo musu ɗauki sai gashi nan anzo. Hankalin kowa ya tashi musamman da suka ce basu san inda aka wuce da shi ba, sannan babu labarin inda yake, duk yadda ake tunanin al'amarin ya wuce tunanin me tunani. Sannan kuma babu wanda yake da sanin yana raye ne ko yana mace, tun ana boyewa ahalin shi har aka fada musu gaskiya ba'a san inda yake ba, gara Hajiya tayi matukar hakuri sannan ta bukaci gwamnatin kasar Nijar ta shiga lamarin Majid yana rike da kamfanin su da matar shi da tsohon ciki, yadda Hajiya ta fito tayi magana ne yasa aka saurari al'amarin tare da mai da hankali akan al'amarin Majid, Nana kuwa tayi suma ya kai bakwai an kashe mata jika, tana farfaɗowa zata ce musu ya labarin Alhajin Allah, kafin su bata amsa ta kuma sumewa, haka abin ya kasance mai dan kwarin gwiwa kenan Amaan. Da shi aka zo Nijeriya, don bakiɗaya hankalin kowa a tashe yake. A can inda suka sace shi kuwa, Commodore Magaji Chindo ne da wasu Yaranshi suka dauke shi, asalima ba iya su ba, har da wasu manyan sojojin, don ba ƙaramin haushi Majid yake basu ba, akwai wani janar ne lokacin yana ganin yadda Chief of Army yake kula da al'amarin Majid, yasa suka tsangwame shi, sai gashi ya samu matsayin shugaban bataliyar sojojin ruwa shi yasa suka shirya daukar fansar su, musamman Magaji Chindo da yake nan babu abin da ya raba shi da mace tunda ba amfani da kayan aikinshi ba. A hankali aka tsananta bincike a cikin tawagar Nijar har da Mohan Muhammad Mamman d'a ga tsohon shugaban kasar Nijar, shugaban kwamandan Rundunar sojojin Nijar bakiɗaya, sannan akwai mataimakin shi Ibrahim Ibrahim Khalil dan Ba'are. Wannan gamayyar sojojin nijar sun tashi kan mutane, ana haka sai ga rundunar kungiyar sojojin Baihak Salahudeen AbdulMutallab Hatim wato Saraki, wanda ya kasance Kani ne ga Muhammad Maina, kuma abokin Majid wanda suka yi wani karatun horarwa a kasar busuwana, akan tattalin arzikin kasa da kasa. Kara iya kara mutuncin iya mutumci. Ana cikin wannan yanayin ba ayi zato ba, sai ga tsohon dilar kwayoyin nan wato Sultan Yazid Hamir na kasar Algeriya, ya kawowa tsohon kishiyin shi taimako ba don kowa ba, sai don Zahrah wacce yake mata kallon kanwarshi. Waɗannan zaratan mazan sun zauna tare da tattaunawa. Tare da binciken kwafkwaf duk yadda ake tunanin ba zasu kai labari ba, sai ga mazaje sun zakulo inda yake da taimakon network din da yake cikin ruwan. Wanda manyan jeragen ruwan suke amfani da shi, tare da wayar da ake amsawa daga tekun zuwa gari, cikin wani irin sarrafa computer Dan Ba'are ya ce. "Abin hari hana waya da wani, ku binciko mana shashin sadarwa." (Idan baku manta ba, Dan Ba'are a cikin Bororoji, yaƙe kuma akwai dangantaka me karfi a tsakaninsu da su Majid. ) Ai kuwa tuni layin glob suka tambayar anan headquarters su ake wayar tuni aka fara bin address din da suka turo abin mamaki sai gashi Office din shugaban rundunar sojojin suka samu nasarar isa, yana waya hankalin shi a tashe bai rufe kofar ba, yana faɗin. " Magaji ka rufa min asiri, ka dawo da shi domin idanun duniya yana kanmu." Shiga office din Mohan da Salahudeen Saraki suka yi tare da cewa. "Idan Magaji ya haifu dan halak ya kashe Majid don Allah!" Suka kwace wayar tare da kama shi Mr Bukola, kafin wani lokaci har an binciko inda su Magaji suke aka musu wani irin shiri sojoji ta saka da ta ruwa aka tura musu men at work. Za iya cewa an samu nasarar kama Magaji, sai dai tsugune bata kare ba, domin babu Majid babu labarinsa. Abin tambaya anan ina Majid? Ina suka kai majid? Haka suka yi ta niman shi babu labarinshi. Duk wahalar da Magaji ya sha yaƙi fadar inda Majid yake, dole aka tattara kayan Majid, suka dawo da shi domin Magaji ya gaya musu kafin su zo ya faɗa ruwa, wanda Mohan ya tabbatar karya ce. Ko kashe shi za ayi ba zai fadi gaskiya ba. Haka suka hado kayanshi har Nijar, aka bama Hajiya, wacce tayi kuka har ta godewa Allah. A hankali aka yi zaman makoki, domin kuwa an gaya musu ya mutu. ** A hankali na bude idanuna, bayan wasu kwanaki da bansan adadinsu ba, sannan bakina yayi min nauyi kallon dakin nayi kafin na shafa cikina naji wayam, yunkurin tashi nayi aka rike ni. "Ina Ya Abdul yake?" "Kiyi a hankali, domin jikinki da ciwo." Komawa nayi na kwanta, da taimakon Jamilah da Mama na tashi zaune bayan likita ya duba ni, aka ce aiki yayi kyau. Sannan aka cigaba da bani kulawa, sai dai yadda basu ce min ga halin da ake ciki ba, haka ban kuma tambayar su ba. Har kwana shida, sannan aka sallame mu,. Lokacin da muka isa gida, a ranar nayi kuka kamar raina zai fita, ina son Majid so na hakika, Majid yana da kirki da adalci ba wai don ina Matarshi ba. A'a gaskiya daya ce duk abinda nake so shi yakan fini son abin ne ma, ba karamin gata ya nuna min ba, ya koya min yadda zan so shi shi daya babu sirki, idan na kalli Babyna sai naji wani irin kaunarta da tausayinta zata tashi marainiya babu uba. Bayan wasu kwanaki Hajiya tazo, a yadda naga Hajiya na fahimci tana kewar d'anta sama da ni, don haka na tattara soyayyar da nake mishi na shiga bawa Hajiya kulawa, duk da halin da nake ciki, sai na sakata taci abinci ta sha magani don ta kwanta a asibiti suka gaya min. Watan mu biyu, da Hajiya zata koma Mama ta bani shawarar ko xan bita na zauna da ita don ta saka rai a kan Jikarta. Sa'adatu muna kiranta da Alfah, duk wanda ya ga yarinyar nan wani irin so yake mata, Zaytoonah kamar tafi sonta da yarta Mimi, sai muka raba na rungume Mimi ita ta rungumi Alfah. Zuzu,Ummi, Munaisah ya Babangida sun zo min ta'aziya da kuma barka. Watan mu uku cif lokacin har mun koma Nijar Zuzu ta haihu Hajiya da kanta ta shirya min tafiya da Zaytoonah da Barakatu, Yazid kuwa baya sati biyu yazo ganin Alfah. Haka yasa yarinya ta samu wani irin gata . Bayan dawowarmu daga Nijeriya,. Ranar da yamma ina zaune aka ce nayi baki. Ashe sun zo har sau biyu ina Najeriya. Fita nayi na shigo su Dean ɗinmu na Makaranta da wata mata , mai matukar izza da takama duk da ba wata babba va ce domin ko ta girme ni da kadan ne, fuskata cike da fara'a na ce musu. "Mu shiga ciki ko, Barka da zuwa, "Yawwa Zahra ya hakuri kuma?" Inji Dean ɗinmu. "Alhamdulillahi!" Muka shiga falon Hajiya, cikin girmamawa suka gaida Hajiya, tana murmushi ta ce. "Kamar na san fuskarki." "Eh matar tsohon shugaban alkalai ba!" "Zainab Umar Ja'e ko ? Mrs Isma'il Wodabbe." "Eh muna tare da shi ma, dake Maimuna Mijinta yana cikin tawagar Nijar da suka tafi niman Majid ɗin " "Allah sarki, don Allah ya shigo zaman waje kuma." "Kece Maimunar?" Murmushi tayi fararen hakorant suka bayyana, a raina nace tsarki ya tabbata ga Allah madaukakin sarki. Sai da tayi murmushi naga zahirin kyau a tare da baiwar Allahn nan, mika musu Babyn Hajiya tayi na wuce kitchen na samu Zaytoonah tana ta haɗa musu kayan kwalama, muka kamo tare, daidai shigowar baban mijin dean. Na zata malamijo ne har nace . "Tsohon nan da gajen..." Sai nayi shiru ina zare idanu, duk da malamijo bai kaishi duhun fata ba, amma kamarsu ta b'aci. Abin tab'awan muka ajiye ina kallonshi. "Yarinya kin san me kama da ni ne?" Gyad'a kai nayi. "Ikon Allah waye haka!" "Mahaifina ne, Sheikh Aliyu Wodabbe." Shiru yayi kan shi a sunkuye, ya rasa me zai ce sai mikewa yayi ya ce. "Zainab idan kun gama ku same ni a waje." "Hamma Ila!" Hajiya ta kira sunanshi. "Baka yi kuskure ba, kuma duk abin da kayi dai dai ne, amma duk abinda ya faru Malamijo yana can yana nimanka kai da Kabo, don Allah ka manta da kome wallahi iya jarabawar da muka gani ma ya ishe mu idan ka tafi hakkinku zai ta bibiyar rayuwar ahalinmu, ka duba ka gani da kuruciyarta ta rasa Mijinta, ta rasa abubuwa dayawa amma na mijinta yafi kome tsayawa a ranmu. Ga jinjirar nan ta rasa Ubanta saboda hakkinku. Don Allah kayi hakuri ka janye Allah ya bi maku hakkinku wallahi muna ganin Jarabawa " "Kayi hakuri mana baban Almamoon, idan kace ba zaka yafe ba, Allah ma muna mishi laifi ya yafe mana balle mutum, kayi hakuri a fahimci abu ɗaya. Ni beenazir ta gaya min wai danginsu Khalil ne ashe duk ta ko ina dangine, haba shi yasa da muka hadu naji ina son Zahrah ina Yarki me rikici." "Tana wurin iyayenta!" Na fada ina share kwalla, "Maimuna ko zaku bamu wuri ne?" Da sauri na mike itama sai da ta gama yangarta, ta mike muka haura sama, falona na kaita ta zubawa hotonmu idanu. "Kun dace!" Hawaye ne ya zubo min, kaina a sunkuye. Nace mata. "Eh haka kullum nake faɗa, amma a yanzu ya tafi ya bar ni, ba tare da ya ce min ya tafi ba." "Tow ki bishi mana!" Ta faɗa min, (wato dai yar baka hali na nan ko) murmushi nayi mata. "Ina jiran mutuwar ce, domin nasan ba zan mori kaina ba, kuma babu me morata, tunda jigon rayuwata ya tafi!" Jin haka yasa tayi shiru, shigowa dakin Zaytoonah tayi da Alfah. Ta mika min Yar. "Bata abincinta" "yau aikin rana ake?" "Eh mana " Sannan ta fita, kallona Maimunan take kafin ta ce min. "Ashe kin san Mami Makarantar da nayi shi kika yi." "Eh" na bata amsa ita gani take tafi kowa miskilanci, sai na nuna mata ni bani da shi amma ina da wata irin dabi'a tsakanina da kai eh ko a'a, ai kuwa haka muka zauna can ta mike zata fita. "Mu yan uwa ne, don haka next idan muka hadu mu tarbi juna as familie!" "Hmm!" Nace mata, muka sauka na shiga dakin da kayanmu yake na zuba mata turare da da atamfofi kala biyu nata daya na Dean daya. Muna zuwa suka mike, har waje Hajiya ta rakasu, ni kuma aka yi ta shigo min da kayan baby masu yawan gaske har na rasa bakin godiya,bayan tafiyar su Hajiya ke gaya min nasabar da yake tsakanin mu yi...... [5/29, 07:48] Hlm: BHB273 Banyi mamakin haka ba, domin ina yawan jin Malamijo yana fadar waye Kawu ila sai gashi ta sanadin b'atar Majid ya haɗa dangin wuri guda musamman kawu ila, wani abu da na sani a kasar Nijar shine duk wani dan kasar Indai a ƙasar yake zaka same shi da girmama zumunci da kawaici, uwa Uba yarda da kowa. Akwai tarin albarka a rayuwarsu domin mutane da suke da halayyar zamantakewa tun zamanin baya, wannan yasa na ji Majid ya kara shiga rayuwata ta kowacce fuska. Sannan mu'amalarsu da kowa akwai son Barka. Mutane daga ko ina na zuwa min jaje, da ta'aziya sannan a bangaren Munaisah d'aga aurenta aka yi tace ba zata iya biki babu ni ba, domin mijin da ta samu ta sanadina ta same shi don haka ba zata yi aure ba, kuma naji mugun dadi ashe haka yan uwa suke da dad'i? Sai nake ganin kamar duk wanda zai ce bai dace da yan uwa ba, hakuri ne bai yi ba, idan kayi hakuri kai da kanka zaka ce ashe haka dangi suke. Bana jin daidai da rana d'aya zan iya murmushi ni kaina nasan na sauya fiye da lissafin mai tunina, a duniya bana jin zan iya sakewa nayi farinciki, rashin Majid ya sauya min dabi'ata. Alhamdulillahi domin duk da haka na san ya gyara min rayuwata sama da tunani na. Watan mu biyu na matsa aka yi bikin Munaisah domin Mahdi yayi min kira ya kai sau dubu, zuwa kuwa har Hajiya ta gane wurina yake zuwa domin aurenshi. Tunda na mata magana tuni ta amince aka fara shiri. Ranar da na shiga dakinshi ina gyarawa domin abisa ala'adar da na koyawa kaina kullum sai na shiga na gyara dakin. Don ji nake cikin kowane yanayi zai dawo gare ni, haka yasa nake gyaran dakin kada ya zo ya samu da kazanta. Ina cikin aikin na sharo datti a kasan gadon ni dai nasan ni daya nake shiga dakin,, sannan babu wanda yake zuwa sai ni, wasu takardu ne a hankali na sharo tare da bude su. Abin mamakin shine yadda ya ajiye min sakon auren Munaisah wato gudummawarshi. Ai kuwa bana manta lokacin da aka saka bikin sai bayan na haihu na tab'a shigowa na samu yana abu ina bude kofar ya wurga kasar gado dama shi ne? Na tambaya a raina. Zama nayi na fashe da wani irin kuka, me yasa ya tafi ya barni. Me yasa? Ko tausayina baya ji yayi tafiyarshi. Hajiya jin shiru shiru yasata haurawa da Alfah. Ganin dakinshi a bude ta turo kofar ganin yadda nake kuka yasa ta tsaya turus. Na rungume takardu, bata yi min magana ba, ta ajiye min yarinyar a gabana ta fita. Ita kanta Hajiya tasan majid danta ne, amma bata kawo Zahra zata so irin wannan yanayin ba, domin tasan tana da hakuri da juriya. Amma kuka ya karya mata zuciya, haka yasa ta fara wani tunanin amma bata jin zai zama kwalliya ga ita Zahran. Bayan na gyara dakin a wurin muka wuni,don ko kasa ban sauko ba kayan daki ya saya mata da kayan kitchen kamar yadda yayiwa Zuzu, da sakon ya ajiye min kudi a drower din shi, da katin bankin shi na dauka nayi amfani da shi ga abin da xan haifa bayan wanda ya bar min, ni kaina ina da tarin kudi sai dare muka sauko bayan mun yi wanka mun sauya kaya, na samu Anisah tazo tana ta kumbure-kumbure, Hajiya da Zaytoonah sai lissafi suke. "Sannunku ukhty lissafin me kuke yi ne?" Murmushi tayi wanda ya kara fitar da kamaninta da Munaisah ta ce. "Addah Baban Mimi ne hajiyar shi ta ce ya dawo dani." Rike Bakina nayi ina faɗin. "Amma kinsan zamu tafi naija bikin Aunty Munai ko?" Dariya tayi tana faɗin. "Eh na sani mana, shi yasa Yaya Babangida ya ce za a maida auren a lokacin nata, amma kuma tarewa sai bayan sallah." Sai lokacin na juya ga Anisah "ke kuma fa?" Cikin rashin mutunci ta ce min. "Ina kin ganni kika share ni, waye ya sani ko farar kafa gare ki, har ya shafi dan uwanmu." Kallona Zaytoonah tayi don na hanata magana idan Anisah tana haukarta, babu ruwanta. Dauke kai nayi na ce mata. "Sai dai bakar kafa, sannan idan kika cigaba da takura min gidan nan sai kin daina zuwa." "Wannan haka yake, saboda ta hana Mijinta sakat don zai ƙara aure shine take jin haushin kowa." D'aga kafadata nayi ina faɗin. "Beb zubo min abinci, kowa ya kwaso da zafi bakinshi. Auren yanzu ma ka lallaba ya aka kare bare kuma kayi tawaye? Idan kina ganin kashe auren shine mafita sai ki gwada yi amma ki sani kowa rai ya amfana baya ga me shine." Na fada ina cin jollop din taliya da aka yi na dare wanda yaji namar rago, ganin ni da Hajiya babu wanda ya sha bakinta yasa ta mike ta wuce dakin Hajiya, nasan xamanta da Zaytoonah babu lafiya don haka na ce Zaytoonah muje mu kwana a saman, don a banza zasu yi ta gayawa juna magana. Haka muka kwana ina tambayar Zaytoonah me take bukata na kayan daki, dariya tayi tana faɗin. "Idan lokacin yayi xan gaya miki." Tsaki nayi na ce mata. "Allah ya taro min ke!" Haka na dauketa daga kasa ta dawo sama, domin daga alamu Anisah auren ta balle, ta dawo zata yi mana iyayi. Aryan ya samu Mijinta ya ce ya gaji, don haka ta zauna a gidan ta ji, ba ayiwa mutum dariya amma Zaytoonah sai da tayi da nake mata fada kuka ta saka min tana gaya min yadda take zuwa har asibitinsu tana cin mutuncinta. Murmushi nayi nace mata. "Ita motar gawa ba ayi mata dariya, idan bai dauke ka ba, wata rana zai dauki ubanka. Don tayi miki gorin mutuwar aure kanta tayiwa ni banga abin tashin hankali ba." Cikin shashekar kuka ta ke gaya min. "Shi yasa nace Baban Mimi ya dawo mu gyara aurenmu." "Dama kece kika bukaci ya dawo?" "Aunty na nuna mata nima mijina yana jirana tunda yaki auren kowacce mace." "Mamarshi fa!" "Kinsan shine ɗan auta a gidansu, da ta tada bori ya bar gidan shine ta kirani wai nasan inda yake? Ni kuma dake nasan yadda suke son shi na ce ta kwantar da hankalinta zai dawo na nime shi ta daya layin shi nayi ta rarrashinsa, dakyar ya koma gida suka yi mishi tambayar duniyar nan dakyar ya ce musu shi ni yake son na dawo." "Shine da safe hajiyarshi ta kirani take rokona na yafe mata, domin albarkacin Mimi na dawo wurin Babanta. Aunty me yafi haka dadi, ai kuwa nace mata ni ba zan dawo su wulakanta ni akan abin da ya faru ba, matar nan tayi tsalle tace wallahi ko karen gidan bai isa ya min haushi ba, ai dama tsakanin mata da miji duk wanda ya shiga shine munafiki, haka matar nan tayi ta rokona na dawo nace ta samu Mama suyi magana. " "Hmmm, sannu Zaytoona!" Na fada mata wato har ta gyara aurenta cikin ruwan sanyi, dariya ta yi tana faɗin. "Matar na tuba bata rasa miji,. Sannan akwai wani abu da ba a gane ba, shi auren ɗan auta yana da dad'i, idan yana sonka all over kowa yana sonka, idan baya sonka tow hatta karen gidan haushi zai maka. Ina dalili ga inda zan mike kafa nayi ta rashin jina ana tattlina ina zan yarda da zagegeduwa." Wato yan matan yanzu wasun su, sun gane yadda zasu gyara aurensu. "Kin kyauta amma ni ba zan iya abinda kika yi ba, wallahi da kunya." Kura min idanu tayi kafin ta ce min. "Allah matar Hamma Majid, ina cewa kika yi bakya sonshi." "Ke tafi can, kin san daga inda muka fara soyayyar mu? A duniya babu mutumin da na sani da kaunar duhu kamar Baban Alfah. Har cewa nake Aminin duhu." A hankali na kai hannu gefen cikina ina shafa wurin na kalleta. "wannan ita ce tambarin haduwarmu, daga nan ya bani jininshi. Ke kina da lovestory irin namu?". Girgiza kai tayi tana dariya ta ce min. "Wai love story manya, ni ma zance auta ya zo mu kafa namu Titanic din don na lura lamarin na soyayya ne!" "Zaytoonah kin raina ni!" "Taya zan raina ki, nima irin soyayyarku nake son koya." "Ai ba zaki iya ba" na tashi na tafi ban daki nayi Alola, na kan raba dare ina sallah tare da niman Allah ya dawo min da shi a duk inda yaƙe. Nasan bani da tsimi bani da dabara, amma iya wannan ita ce dabarata . Itama ganin ina sallah itama ta fara muna yi tare. Al'amarin Ubangiji ba wani abu ba ne da yake bukatar gaggawa, hakuri juriya, naci da nima a wurinshi. Nasan ban isa in dawo da mamaci ba, amma nayi imani da Allah da Majid ya mutu babu yadda za ayi jikina bai bani ba, kamar yadda aka ce ba a ga ko gawarshi ba. Haka nayi ta fafutukar ganin na tsaya da kafata, ta hanyar rokon Allah. Allah sarki Nana har kullum tana zuwa tayi min hira, da sayawa Alfah kayan zak'i. Ni kuma na dauke abinda Majid yaƙe mata, na shiga saya mata nama, duk sati. Ba wai ina da mahaukacin kudi ba ne, amma nasan Majid ya bar min hanyar samun kuɗi, domin albashinsa da hannayen jarin shi ta account dina yake shiga, shi yasa nake samun kuɗi kamar yadda ba a zata ba. Sannan Hajiya da Aryan suna kaina, idan wani abu ya taso kafin na maida hankali nayi sun min, ga Yazid da shima baya kasa a gwiwa bai zo ya duba ni ba. Haka dai na lura da yawan tambayar da yake min akan bani da ra'ayin aure ne, tuni nake shiga b'acin rai, na haɗe rai kamar bani ba dole ya daina min wannan tambayar renin hankalin. Amma ba karamin hidima yake mana ba. Don ko da lokacin bikin Munaisah yazo,muka tafi aka yi shagalin biki a can muka dawo marad'i, anan da ga marad'i kuwa maza suka min caa, don ma mun haɗu da Aryan shi ya tsare min aurena kuma ba wai shigar banza nayi ba, kawai farin jini ne zan ce ko fitina irinta mazan zamani. Haka aka gama bikin muka dawo gida bayan mun kaita gidan ta da yake jekadir. An sha biki ba na wasa ba. Daga nan muka dawo gida, a matukar gajiye. Bayan bikin da sati biyu aka fara azumi, tunda aka fara Ibada ban tab'a fashin dare daya ko wuni daya ba, abincin sadaka Nana da kanta take rabawa, na yarda Majid shine zuciyar gidan, domin da baya nan hatta masu faɗa akan dukiya kowa damuwa yayi, duk bala'in yan uwanshi da suke uba daya sai da takai su da kansu suna begen shi bayan ya mutu.. sannan wani abin da na rasa fahimta Abdul B tunda Mamarshi ta hana shi niman Munaisah Mahdi na zuwa ta amshe shi sai ya zama yaki ya kuma mai da hankali akan aure. Ni nasan tunda na mika al'amarina ga oga kwata-kwata, nayi imani ba zan ji kunya ba, a goman karshe kuwa sai da Hajiya tayi ta min fada, wai na takura kaina da yawan ibada, a lokacin murmushi nake yi domin na san ibadar ce abin da ya dace dani, kuma Alhamdulilahi na samu sauki da sukunin da nake jin rashinsa a raina. Naji wata irin nutsuwa da babu irinta, haka muka sha bikin sallah, bayan sauke azumi, sallah da sati biyu Zuzu ta haihu daidai za mu tafi Kamaru. Ai babu shiri muka wuce Nigeria, anyi bikin suna da ban tab'a ganin irinsa ba, sai da naji hawaye ya zuba min domin bikin sunan yazo da wani irin bazata, sunan Yaron da ta haifa Abdulmajid, basu faɗa min ba sai da muka zo wurin walimar naga Abdulmajid, nayi. [5/29, 07:48] Hlm: BHB274 Wai na rasa me zance, kuma sai nayi ta kuka Allah yaso tun basu fadi sunan da zasu saka ba, na yi akwati biyu. Na kayan uwar da yaron Zuzu ce fa, a duniya idan ban yiwa Zuzu hidima ba wa zan ma wa? Danginsu na Numan sun zo, ni da ita muka yi ta musu hidima. Sannan duk wanda yazo a cikin dangin Mamanshi sai da muka ware musu turamen atamfa chiganvy me kyan da tarkacen suna domin saniya da raguna biyu ya yanka, daya rago na dangin Mamanshi, daya rago na mai jego. Saniya kuma aka cire na wurin hajiya uwar rikon shi da dangin Babanshi, sauran muka saka a hidima. Mun sha hidima sosai kamar me kafin muka nutsu na kara bata shawarar ta kula da dangin mahaifiyarshi ba sai sun bukaci wani abu ba, idan da hali ta saka yayi musu, ai yiwa kanta ne da yarta da. Kuma taji dadin hakan da nace mata. Sati daya muka wuce kamaru bikin Zaytoonah koda yake shegiya ta ce kome ni ce. Haka muka yi hidimar dangin mijinta har da sabon kayan aure ita da yarta, wannan lamarin ya min dad'i. Wato tunda na ga Mamata naki komawa Nijar, ni da Alfah wacce yanzu take kokarin tashi tsaye wata goma, Hajiya tayi waya ta kira Malamijo amma naki dawowa, ina ganin kiranta zan fara dariya kawai. Yau ma muna aikin dambun tafiya ta kira na dauka ina dariya. "Hajiyata!" "Don Allah ku dawo wallahi babu kowa a gidan?" "Hajiya ina Anisah?" "Ke tafi can, wacce kuma haka dalla ki kawo min alfa!" Inji Nana tana mita, "Yanzu banda Allah ya nufa Alhajin Allah ya haifa min Alfa ya zan yi? Ina sai dai nayi ta bada labarinshi ana ƙaryata ni, Zahra'u ban san lokacin da kika zama munafika ba, don Allah ki kawo min yar y'ata." "In sha Allah Hajiya Nana matar Abdul Majid Mamman Ba'are, matar ƙarfen Majidu angon Nana da Nana!" Sai ta fashe da kuka wiwi. "Allah ya miki Albarka, kin saka ni jin kewar Alhajin Allah" Murmushi nayi ina faɗin . "In sha Allah duk inda yake yana cikin Amincin Allah kuma zai dawo gare mu!" Haka muka gama wayar ina jin kwalla na cika min idanu. "Ki cigaba da addu'a, kada ki saka ran ba zai dawo ba." Murmushi nayi ina kallon Mama, "Mama nasan Allah yana tare damu, kuma shi yafi mu sanin gaibu. Don haka ba xan tab'a kauce hanyar da ba tashi ba, na san ina cikin damuwa da kewarshi, matsayin mijina ba matsayin dan uwana ba, hakikanin gaskiya ina kewar shi." Na fada muryata na rawa, a hankali na fashe da kuka. Don nasan ina matuƙar son ganinshi, sannan idan nace bana buƙatarshi nayi karya, barin aikin dambun nayi na koma gefe ina sharbar kuka, murmushi Mama tayi tana faɗin. "Allah yana gani bana jin dadin ganinki a haka, ki cire damuwar Baban Alfah a ranki, ki fara tsayuwa da kafarki. Kudin da ya tara wata rana zai kare amma idan kika tashi kina nima Allah zai dafa miki, sannan damuwar zata zo miki da sauki duk wanda kika gani a wannan lokacin kokari yake ya tsaya da kanshi ko aikin kamfanin ki koma zaki ji sauki da sassauci , a ranki." Akwai wani sirrin da Allah ya bawa Uwa, wanda duk duniya babu na biyunta, kuma nasan Mama tana cikin Wadannan iyayen, Mama bata barmu haka ba don mun girma muna da aure ai mun san ciwon kanmu a'a ita kanta ta gaya min na yawaita mika lamarina ga Allah, sannan ta gaya min duk halin da nake ciki kada na manta nayi wanda ya fi shi zafi da muni, sannan bata bar mu hakaba sadaka da azkar tana yi akanmu mu biyu, don na mata magana kwanaki ta ce ai ita babu wani damuwar namiji a ranta sannan ita ai ba zata zama damuwa ga Addini ba, tunda Muslunci ya bata damar idan ba zata yi aure ba ta kame kanta tayi ta ibada ta zaɓi wannan mazahabar, sannan idan zata yi aure mai mata zata aura, na farko Matarshi idan bata da hakuri ta hana ta sakat, idan ta samu mara mutunci ya sakata a gaba akan dan abinda take, dake ta karanci dabi'un dan adam, shi yasa ta zabi kula da Yaranta. Haka ya kara min kaunarta, domin ta hakura da farincikinta don mu kada wasu su raba mata hankali, kuma na san har da tsoron fitinar abun da ya faru lokacin aurenta da Baffa'm. Shi ne gaskiyar maganar da zan iya faɗa. Bayan kwanaki tara, muka bar kasar Kamaru zuwa Nijar, tare da alƙawarin daukar shawarar da ta bani, ina dawowa farinciki kamar me, kwana na sha daya da dawowa aka yi layya, yawon sallah muka je har marad'i, na samu Munaisah tana laulayi, ita ke tambayata Addah. "Tana nan lafiya sai godiyar Ubangiji Kawai amma Adda tana cikin jarabawa, Allah ya bata lafiya." Da gaske ganin Adda yasani kin tunota, Addah ta wani irin malkwadewa kamar wacce tayi hatsari. Yawu na zuba ga wuyarta yayi wani irin karkacewa kai ni wallahi sai na ga kamar an sauya mata halitta ne. Kuma tana magana sai dai bai fita sosai burinta bai wuce ta samu yadda zata cutar damu ba. Dukkanmu munyi aure Ummi ce bata yi ba,sannan Nenne taji sauki har tana takawa Munaisah ta saya mata gida babba ta zuba yan haya da masu kula da ita, atow hidima takewa Mamanta kamar ba gobe sannan tana kashe mata kudi kamar me, Munaisah tana da kudi domin ko sarkokinta kawai masu yawan gaske ne, balle kuma tsabar garin kudi ga shagunanta A yola da Taraba,naji tana cewa wa ma zata bude wasu shaguna a abuja da Lagos, domin sun hada gwiwa da mijin Zuzu. Wanda yasa zuzun itama ta zuba kudi suka shiga juyawa. A lokacin na ce musu sun munafurce ni, budar bakin Mijin zuzu cewa yayi ko mutuwa Majid yayi ya bar abinda yarshi da ƴaƴanta zasu mora, balle ana maganar Chairwoman na Ba'are. Harararshi nayi lokacin, kuma zuwana ma Munaisah ta kara gaya min. Bayan dawowarmu na nutsu wuri guda, na fara zuwa aikin kamfanin inda aka bani Office din Majid, sai dai abin da na fahimta kamar ana tab'a kayan Majid na Office din, wasu abubuwan an bincika su. Sannan yanayin dai ba yabo ba fallasa, ni da Aryan muka kara mike kafa da gaske muna aikin da ya dace. Shekara daya ya wuce ranar Birthday din,Alfah ranar naji ya kara nisa ga zuciyata, lallai Majid yayi nisa a gare ni. Haka nayi ta fadi tashi muna aikin muna fama a lokacin aka sake tasa kamfanin a gaba, wannan karon mun yi nasara, an yi haka da sati daya, gobara ta kama a bangaren Hajiya Rabi da Yaranta. Domin ba iya mu kaɗai muka tashi ba, hatta a can Kamaru sun tashi tsaye, sai ga gobara ta lashe duk wani abin da Rabi ta tara ita da Yaranta, karshe basu tsira da kome ba, sai kayan barcin da yake jikinsu. Bayan wannan babbar yayarsu Majid, tayi tafiya tana dawowa suka kwantsama wani mummunan hatsari, a shekarar ba a tab'a samun ribar da aka samu a wannan lokacin ba, sai gashi riba kamar hauka wanda yaja nasa aka yi karin albashi, a yadda abin yake faruwa yasa Hajiya kiran gida tana kuka ban san me ya faru ba amma hajiya ta kasa barci domin irin yanayin yana.bata tsoro ko Rayuwar Majid bata ji haka ba. Ni kaina a yan kwanakin wasu miyagun mafarkai nake, wanda yasa ni fara tsoron na saka hakarkarina a katifa, domin take zan fara mugun mafarki, a ko ina idan na dan kwanta barci me dan ƙarfi ya dauke ni mafarkin wai ga wani mutum yana tona rami, sai kasa ta rubta ta rufe shi, can aka zo aka bude shi sai ga jini yana zuba da gwala-gwalai. Mama na kira na gaya mata, ita ta gayawa Malamijo, shiru yayi kafin ya ce mata. Ta min nasiha nayi hakuri da duk abin da zai faru kada ta gaya min, haka na kwantar da hankalina, sai dai bayan kwana biyu na fara mafarkin Majid yana son zuwa gamu cikin tashin hankali. Majid yazo ya mika min hannu. Amma Aryan yana kuka kada na tafi na tsaya, har da rungume ni ta baya, kada na tafi na barshi. Ina ganin wani mutum ya kama Aryan ya danne shi, sai da ya daina motsi, yana nufo ni Majid yana isowa inda nake ya rungume ni. Anan na farka. Da safe na gayawa Hajiya a saya min rago, a yanka a gyara ayi abinci a dafa a kai sadaka. Idan kuma abincin zai bata lokaci a saka namar a leda, da danyen abinci a saka jaka uku, a raba sadaka. Bayan na fito na ga Nana ta fito rike da sandarta. "Uwargida a wurin Abdulmajid da Abdul Majid Yaro." Yake ta min ta zuba min idanu kafin ta ce min. "Ina mafarki da Alhajin Allah yana tafe, sai dai kamar wata fitinar da take tafe a gabanshi. Na saka yau ayi min yanka zanyi sadaka" "Na gayawa Mamana nima, ina wannan mafarkin nace ayi min saukar Alqur'ani, zan yi sadaka an jima za a kawo ragon!" "Tow ayi ta saniya mana;" "Kuyi magana da Hajiya kawai " Ni da Nana muka yarda Majid yana raye, amma kowa gani yake mun zare wai abu kusan shekaru biyu amma muna da yakinin yana raye. Da sauri na tafi wurin Aryan na shiga motar ina gaishe shi. "Lafiya Baban Amir." Na cigaba da danna wayata. "Fadime?" "Na'am" na amsa ban kalle shi ba. "Tunda shekara biyu kenan har da watanni me zai hana mu tattauna a tsakaninmu, sai na maye gurbin shi." A wani fusace na kalle shi, "sau nawa ina gaya maka kada ka sake min irin wannan maganar? Tow bari na gaya maka koda ace zan shekara dubu ne babu Majid wallahi na fi karfin na had'a makwanci da Yayanka sannan na hada da kai, ni babban gora ce sai magogin ƙarfe." Na juyar da kaina ban kuma kallon inda yake ba, Aryan tunda Majid ya samu shekara daya ya fara min wani irin abubuwa, tun bana kulawa har na fahimci so yake ya nuna min shi ɗan akuya ne. Allah na tuba ko mutuwa Majid yayi na ga gawarshi ai na shafawa kaina lafiya balle ban ga gawar Mijina ba zan kama zancen wani namiji tun da aka rasa shi ni maza ma kallon mata nake masu wallahi duk yadda Yazid yake sona amma fir naki, sannan abin da ya kara min kwarin gwiwa Majid zai dawo shine Yariman Baihak Crown Prince Maina da yazo kamfaninmu ya bani shawarar kada na damu da rayuwar wasu na gina tawa domin mijina, yasan jarumi ne a ta kowace fuskar kuma zai zo gare ni, sannan na ga yar karamar Matarshi wacce yake haukar so yarinya ce karama don bata wuce sa'arsu Barakatu ba, sai kinibibi take kamar zata shige jikinshi. Shi kuma shashasha sai rudewa yake, wato larabawa basu da kai akan matar da suke so sai bayan fitar shi ta nutsu tana rufe fuskarta. "Aunty Zahra ki bar min kallo haka!" "Ba dole nayi miki ba, kin mai da magajin Baihak kwarkwar." "Sirrin kwailantaka ce" sakin baki nayi ina kallon ta, ta sake murmushi da yanzun zance ya shiga gari ya nimo min dawo, kafin na rufe baki zai tafi, ai shi yasa bama daukar las a wurin miji, ita head girl tana can ta bamu wuri mu darji amarci" "Ya isa haka.ban ce ki baro min magana ba!".....🤣 (Ni dai na san I dey take las, domin akwai wani sirri a jikin kwailayen mata don Allah me yasa Zahra ta hana kwaila baro zance 🙄🤣😂😏 Ni bana son hassada) 300₦ 0016341139 unity bank zahra'u yahaya Ali Katin MTN 400 #Mai_Dambu ce [5/29, 07:48] Hlm: BHB275 Kai jama'a yarinya sai kace Radio, gata yar banza ba wasu shekaru ne da ita ba, yadda na had'e rai yasa ta nutsu daga ganinta yar kauye ce. Hankalina yana kan aiki ta ce min. "Mijinki yana raye?" A zabure na zuba mata idanu, bakina yana rawa. "Me yasa zaki d'aga min hankali?" Na fada kamar xan yi kuka. Ina ji a jikina yana raye amma ban san dalilin da yasa nake bin rinjayen abin da mutane suke fada ba. "Wallahi mijinki yana raye, kuma bai yi nisa da nan da kike ba, sai dai a inda yake ne gaskiya ban sani ba, amma ke bakya jin motsinshi a ranki? Bakya jin kamar yana tare dake ?" Juyawa tayi ta kalli kofar shigowa, murmushi tayi ta nufo ni tana me mika min hannu. "Idan har kin yarda da mutane masu baiwar gane-gane tow ki amshi wannan zoben. Duk me hannu a boye mijinki zai na gudunki. Ki dauke danginki daga Hajiya, Alfah Amaan, Jamilah da Anisah. Su tafi wani hutun Allah zai baki Sa'a amma Aryan ya xama yana gefenki, Aryan mutumin kirki ne bai miki maganar yana son maye gurbin dan uwanshi don ya tsani dan uwanshi ba, a'a yayi haka ne don rage miki kaɗaici da kewar Dan uwanshi. Yasa yake bayyana miki sakon zuciyarshi. Ba mutumin banza ba ne." Ta riko hannuna ta saka min zoben, sannan ta juya tana kallon kofar, shigowa tana murmushi ta ce. "Alahan wassalan ya Habibi da'im!" Haɗiye yawu nayi ban tab'a ganin tashin hankali irin na yau ba, da sassarfa hade da kuruciya me haɗe da sakalci ta isa jikinshi, rungume shi tayi tana murmushi. "Sauran canji ne a jikina ba sai kin sace su ba." Dariya suka saka tare da min sallama. Raka su na fito nayi naga Aryan shima ya fito. "ina fatan baki mata sane ba?" "Kai haba ai abar tausayawa ce, munafukai suna dayawa a cikin kamfaninsu. Amma ita zata kawo karshen rikicin kamfanin ta hanyar fitar da bara gurbin kamfanin!" Janye jiki tayi ta nufe ni. "Ki kama wancan dan iskan da yake leke ta window ki fara da shi." Da wutsiyar idanu na kalli Admin. "Na gode haka suka shiga motarsu suka bar kamfanin." "Shi abokin Hammayo ne sun yi course akan kasuwanci ne." "Allah sarki! Ka shiryawa su Hajiya tafiya Umara ita da su Jamilah kowa da kowa. Har da matarka da Yaranka har da Amaan! Ka shirya musu kamar tafiya yawo ƙasashe uku!" "Tow an gama yan mata!" Haɗe rai nayi, na juya zuwa cikin office ɗina. Ina shiga na dauki jakata na fito ina kallon Admin. D'ago kai nayi na kalli Admin da sauri ya boye kanshi, na wuce abuna Amaan da zai tafi gida muka tafi tare. Anan na bar Aryan ina shiga da gudu Alfah ta zo ta rungume ni. "Ina sonki love!" Na fada ina sumbatar goshinta. "Hmm! Yar nan ya aiki?" ,"Alhamdulillahi Nanan Alhajin Allah, nace a kawo miki kilishi gobe in sha Allah" "Allah ya miki albarka!" Ta fada tana share hawayen da ya cika mata idanu. "Ya Allah idan Alhajin Allah yana raye Allah ka bayyana shi idan baya raye Ubangiji ko gawarshi ka bayyana mana!" "Amin Nana!" Na wuce daki na zube a gado ina ajiyar zuciya. Top din jikina na cire na kwanta ban yi yunkurin cire skirt din jikina ba. Haurowa gadon tayi ta kwanta akan ruwan cikina tana mita. "Love me kike so " "Haji kuka " Amira tayi baki da wuri amma alfah babu baki sai gwaranci me sifirin, "me ya same ta?" Wayyo Allah na, da ta buga min wani gwarancin bansan yadda aka yi na tashi zaune ba. "Haka aka yi? Babban magana magajin gari da kiran wambai, tow jeki gani nan zuwa." Tana fita na tashi na cire skirt daga ni sai dan gajeran wando, na cire shirt din rigar ya rage daga bom short sai transparent bra, sannan na wuce ban daki nayi wanka na fito, sallah nayi domin nayi alola, sannan na fito falo, shinkafa da miyar bindin sa aka yi, sai coslow na zauna ina ci ina jin hirar Hajiya da Amaan, shigowar Aryan yasa muka bada hankalinmu kanshi. "Hajiya an shirya muku tafiya hutu har Kamaru ma." Juyowa tayi ta kalle ni. "Me kike nufi?" "Zaku tafi nan da kwana uku, dukkanku." "Ke fa?" "Ina da aiki!" Na fada ina cigaba da cin abincina. Ai kuwa Nana ta fashe da kuka ai babu abinda ya fi haka dad'i. Ina cin abincin na ce mata. "Nana ke da zaki tafi aikin umara sai ki mishi addu'a a can!" "Haka ne yar nan" Ta fada tana goge kwallarta. Da na gama na wuce sama, dakin da yake motsa jiki na shiga na dan kunna walking, don abincin da naci ya ragu don bana son kiba, haka yasa na samu damar yawan motsa jikina. Kuma tun haihuwar Alfah na fahimci cewa tumbi na ba zai koma daidai ba, sai na rage shi. Ina cikin haka ne Alfah ta shigo itama ta fara nata, ina yi tana min surutu, wasa ta fara a cikin dakin can kamar an ce ta tab'a inda aka saka mirror sai ga kofa ta bude. "Ma!" Dake haka take kirana, zuba mata idanu nayi tana kallon kofar, nima bin kofar nayi da ido, muka tsaya kallon kofar, da sauri na koma na rufe kofar shigowa, sannan na riko hannunta muka shiga cikin dakin. Kunna wutar dakin nayi ina kallon ko ina na dakin, lalube aka rufe wani jikin wani bango ina zuwa na ga hotunan mutane ne. Dake ina yawan nuna mata hoton shi, tana ganin shi ta fara tsalle. "Daada." Rufe mata baki nayi, na ji wani motsi me karfi, "welcome to Abdul Majid Mamman Ba'are, secret room service." Katon tv ne ya bayyana, sai ga shi hotunan mashigar kamfanin ne ko ina kai tun daga gidan nan har zuwa wajen garin nan bakiɗaya. Wasu takardun na gani na juya a hankali ina kallon hotunan wurin. "Waye ya kashe Mamman Ba'are da Maysara?" Hoton Sajjid don dama ban san shi ba, sai da ya saka sunan a kasa, Tani na santa. Tana can kamar mahaukaciya. Kawu Haladu, Kawu Kamilu, Hajiya Hadiza,. yaya Umma. Yaya Ikilima, Yaya Saratu. Hajiya Harirah. Admin, Commodore Magaji Chindo, Mr Bukola, A hankali na fara bude takardun. _Koda wata rana zaki shigo nan, ki saka idanu da kyau ki kuma nimo wanda yake da gaskiya ya taya ki wannan yakin._ _Zasu iya tab'a iyalina, domin ban san karfin su ba, amma nasan idan kika nemi Taimakon Yazid zai taya ki wannan yaƙin!_ Wata takardar na kuma dubawa na ga ya saka. _Zabi daya na dauka sadaukar da rayuwata domin naki da na yan uwana, ki kula da abin cikinki_ Kuka na saka a hankali ina jin wani irin tausayinshi dama yasan haka zai faru ne? Bai gaya min ba. Fitowa nayi na dauki wayata na shiga na dauki videon kome na fito na kira Yazid yana ganin kirana ya kashe ya kirani. Kuka na saka mishi tare da kashe wayar. Sake kirana yayi na shiga mishi bayanin abinda na gani, sannan na tura mishi videon. "Na jima da sanin haka don ya turo min, ya ce bai san lokacin da zaki iya fahimtar haka ba, yanzu ya ake ciki?" "Mijina yana raye!" "Taya zamu tabbatar da haka." "Hanyar bibiyar Admin!" "Baki da matsala, yanzu wani sati xan shigo." "Na gode." Fitowa nayi a dakin na wuce zuwa dakinmu muka ci kuka muka more, sannan na shiga shirya kayan Alfah. Dole mijina ya dawo gare ni, amma kafin nan sai na fara gayawa Allah. Washe gari na tashi da azumin niman biyan buƙata. Na kuma saka ana sadaka, har su Hajiya suka bar garin ban daina ba, karshe na cewa Aryan . "Zan koma hotel da zama, Yazid zai zo wani sati." Don ban gaya mishi ba, sai dai barina gidan zuwa hotel din ya saka shi zargin wani abu. Amma na share shi don bana son ya gano kome sai Yazid ya zo, kwana na hudu Yazid ya zo a ranar na bude mishi kome, zuba min idanu yayi yana faɗin. "Me yasa baki gaya min ba?" "Kawai babu kome!" Nasan yaji haushi amma ya zan yi nima haka nake ji, daga nan muka shiga shiri, na farko shine saka Admin a tarkona yana ganina zai fara zufa, kamar yaga abin tsoro. Kafin nan Alhaji Kamilu da yake zuwa domin ganin yadda kamfanin yake tafiya, shima baya son haduwa da ni, Wannan yasa lokaci guda Yazid ya kawo shawarar rufe kamfanin na tsawon wata guda, haka kuwa aka yi tare da rufe kamfanin da mashigar kudin kamfanin, a cikin kwana biyu rak aka fara bibiyar Aryan, ya kira ni ya gaya min nace mishi. "Ba kai ba kwanan gida dawo hotel." A gefe guda kuwa Admin muka kama yana ganin mu ya bude bakinshi. "Don Allah ki min rai, wallahi kina bani tsoro ne, idan na ganki kamar na ga mutuwa ta." A hankali nake murza zoben, zubewa yayi a kasa, yana jin wani irin abu a ranshi. "Ina kuka kai min mijina?" "Yana can gidan ajiye kayan da suka lalace." Juyawa muka yi ni da su Aryan muka fita, gidan ajiye kayayyakin muka nufa, a lokacin aka fara bin motarmu da gudun gaske. Mun isa gidan babu kowa, muna shiga aka rufe get din, har cikin store din muka shiga, anan na fara hango Majid zaune. "Kada ki isa wurin" cak na tsaya ina kallonsu. "Mijina ne!" Na isa da gudu. "Zahra!" Ya faɗa a hankali. "Me yasa kika zo ke daya?" "Bani daya ba ne!" Na fada da wani irin kaduwa. "Ai haka kawai ba zasu baku damar zuwa nan ba, tarko suka shirya muka, kuka fada" "Soja muma da namu shirin!" Matsawa suka yi aka shiga dirowa ta sama, a hankali na rufe fuskarshi, jami'an tsaro ne, suka mana kawanya, a hankali naji wani abu me karfi da sauri ya wuce ta kunne na, wanda yasa sani jin wani irin abu kamar an girgiza ƙwaƙwalwa ta, daga nan ban kuma sanin kome ba. Jin karar harbin yasa Jami'an tsaro suka yi ta dauki ba dad'i, kafin daga bisani aka tsayar da harbe -harbe, a lokacin aka lura da harbin Aryan da aka yi fita da shi aka yi, a daren aka tafi har gida aka kama Alhaji Kamilu da Haladu, Zahra da Aryan aka wuce dasu asibiti, har da shi Majid ɗin da bai da karfi a jikinshi. Sai dai ana kai shi asibiti, aka duba shi Yazid ya nemi su bashi takardun Majid din, ya wuce da shi Algers domin yace mishi. "yadda ka kare kamar kudin guziri gara ka tafi wani wurin kayi jinya idan kayi a gabanta zata kuma shiga wani yanayi sama da baya. Aryan an samu an ceto rayuwarshi dakyar, amma Zahra kan sai a hankali domin wannan harsashin da ya wuce ta kunnenta yasa kunnen ya daina aiki baki daya, saboda karfin gudun shi. Kwanan Aryan biyu ya warke tare da mai da hankali akan jinyar Zahra suna waya da Yazid har yana hada shi da Abdul Majid, sai dai a tsawon shekaru biyu ya koma kamar bashi ba, tsabar azabar da suka mishi. Sai da na kwashe sama da kwanaki goma sha biyar kafin na farka, kamar a.mafarki nayi ta kallon kowa, ina ganin bakinsu yana motsi amma bana gane me suke cewa sai na juya da daya kunnen nake gane musu. Aryan ne ya gaya min na rasa kunnena daya, wannan abin ya dake ni wanda ban san lokacin da na fashe da kuka ba, dama ai idan baka mutu ba, ba a gama maka halitta ba....... 300₦ 0016341139 unity bank zahra'u yahaya Ali Katin MTN 400 #Mai_Dambu ce [5/29, 07:48] Hlm: BHB276 Wani irin tashin hankali na shiga, cikin d'aga murya don gani nake kamar baya jina. "A haka zan rayu babu kunne ɗaya?" Na tambaye shi, turo kofar dakin da Mama tayi yasa ni sa ke fashewa da kuka ina fadin. "Bana ji da kunne ɗaya, na kurmance." Ita kanta na hango hakuri da juriya a kwayar idanunta, na ga tarin ban hakuri da lamuni fuskarta. Rike hannuna tayi tare da fadin. "Ba dashi Allah ya halicce ki ba, tunda samu kika yi dare daya zai dawo " ta faɗa tana rungume ni, nima kuka nake tare da surutai Shafa bayana take, ita kan ta gaji wallahi gara Majid idan ya warke ayi ta da wajewa, damuwar tayi yawa, ya sakar mata Yarta tunda Aryan ya kira ya fadi halin da ake ciki ya Allah ne da rayuwa, ta ji kamar da ita ce ciwon ya same ta, ba Zahra Yarinyar da bata ji dadin rayuwa ba, tun tashinta. Kamata yayi a ce Zahrah ta san farinciki da jin dadi, amma daga wannan matsalar sai wannan. "Mama!" Na kira sunanta. "Ina ihu ko?" Hawayen da take dannewa ne ya zubo mata. "Zahra baki ihu, sai ma magana a hankali." Rike hannunta nayi ina jin kuka yana zuwa. "Shin kina nufin Allah ba zai jarabce ki ba ne? Ko kina son Allah ya fahimci kin butulce mishi ne? Don Allah ki daina kuka ki mikawa Allah lamarinki, yana sane da ke. " Nasiha da ban hakuri babu wanda bata min ba, rarrashi da kulawa babu wanda na rasa, domin nuna min tayi kaf duniya babu irina. Babu kamata, a daren ranar Hajiya da Nana suka iso, fadi take. "Wani tsinannen ne ya boye min Alhajin Allah, Allah ka tsine mishi albarka." Haka Alfah da tazo ta ganni ina hawaye, ba zan ji sweet voice dinta me cike da gwaranci da kunne duka biyun ba, sai na fashe da wani irin kuka ina me rungumar ta. Sai ya kasance kowa tsoron komawa gida yake don kada su dawo ace musu na mutu ko an sace ni, sannan wani abin da ya kara b'ata min rashin Majid wato nayi wannan sadaukarwa ne don shi amma sai ya tsallake ya tafi nashi sabgar. A cikin wannan yanayin labari ya zo mana, an kama Hajiya Turai. Da laifin kashe Maysara ita da Alhaji Haladu, abin tausayi kuma suka saka dan uwansu Alhaji Kamilu a cikin tashin hankali tsamo-tsamo. Wani abin kuma shine niman Tani da aka yi ta gudu,sai daga baya aka samu labarin ta mika kanta ga yan sanda tace gara su hukuntatta kafin Sajjid ya ji labarin abin da tayi mishi don ba ita ta haife shi ba, da ita da yan uwan Alhaji Mamman Ba'are, wato Haladu da Kamilu suka shayar da shi guba ya mutu, amma ita ba ta kashe Maisarah ba. A hankali duk wani sharri yayi ta fitowa, hatta sakawa Hajiya Rabi da Yaranta wuta ,sune domin kada a samu matsala wurin tona musu asiri bayan dukkansu family suka had'a kai a dauke Majid, kuma aka yarda sai daga Baya Hajiya Rabi ta ce tana tsoron tsinuwar Nana da kullum take yiwa duk me hannu a cikin rayuwar Majid. Wato yarinyar nan matar Maina ta zame min alkhairi, zuwanta ya zame min alkhairi. Ta gaya min ni daya zan iya dawo da mijina gare ni, sai gashi ya faru. Kwanan mu biyu, a asibiti aka sallame mu, don ma Nana bata da lafiya idan ta ga abinda Yaranta suka aikata, sai ta ji kamar ta mutu. Tayi kuka kamar ranta zai fita, amma haka ta ce ba ta zama a gidanta. "Atow na sani ko nima kashe ni zasu yi, tunda akan dukiya suka kashe junansu." Haka muka tare da ita a gidanmu baki daya, Amaan da Majid suka wuce Algers, don tunda abin ya faru sun ji ban yi maganar shi ba, ko da naji ana maganar shi sai nayi pretend kamar ban.ji ba, haka yasa suka tafi duk tsiya ya dawo yayi jinya a gidan yafi yana wata duniya. Kamar yadda suka tafi haka suka dawo yaki biyo su, wannan abin ya kara harzuka ni wato don na nakasa yasa ba zai dawo ba, wannan abin yasa ran Mama ya kara b'aci,. musamman da ta kamani ina kuka da rubutu a wani ƙaramin littafi. _Dama duk wata soyayyar da bata gaskiya ba haka take? Da gaske Love is gone_ faɗa tayi ta min tare da cewa na cire shi a raina yayi duk yadda yake so, dama lafiyata yake buqata tunda bani da shi bata ga amfanin zamana a nan ba. Rike hannunta nayi na ce mata. "A'a Mama ki bari yazo ya gaya min hujjar shi na tafiya idan lafiyata yake so kwana ɗaya ba zan kara ba, zan tafi kiyi hakuri kin ji." "Na gaya miki gaskiya ba zan iya kallon yana wulakanta ki ba, akan me zai tsallaka ya bar ki bayan don..."."Don Allah nayi Mamana, kada Hajiya ta ji ki." Na fada ina zaunar da ita, ita uwa akan danta wata irin dabba ce da bata iya sauraron kowa sai dantan nan, uwa wata irin duniya ce da bata gane kome matukar akan danta ne. (Amma ba kowacce ba) A hankali na samu hankalin Mama ya kwanta,yau muke saka tsammanin Majid, gobe ne har ta gaji ta bar Nijar Majid bai dawo ba, sannan ta ce nayi ƙoƙarin nazo naga likitan kunne, ganin har lokacin bai dawo ba, yasa na gayawa Hajiya zan tafi Kamaru. Ban san sunyi rigima da Mama ba, sai dai naga tsoro da tashin hankali a cikin idanunta ƙarara, "Kin gaji da zama ne? Zahra don Allah kiyi hakuri kada ki gaji da Majid." Girgixa mata kai nayi na ce mata. "Ban san uxirinshi ba, amma nasan zai dawo zan tafi ne don naga likitan kunne." Hawaye ne ya zubo mata, "Da ina son ya dawo ne sai a kaiki asibitin kunne da yake Baihak." Murmushi nayi nace mata. "Hajiya da an barshi nayi kewar Zaytoonah ne xan tafi." Ganin takasa shawo kaina, ta ce min. "Shi kenan za a shirya miki tafiya nan da kwana uku." "Tow na gode. Allah ya kara lafiya da nisan kwana." A yadda nake jin tana kallona sai nake jin kamar na rasa duk wani abin da nake dashi, sai nake jin wani irin tausayi a raina, don haka ina shiga dakin na fara kuka, shigowar Alfah yasa ni share idanuna dake ina mata turanci da fulatanci, Aryan suna mata Buzanci da Faransanci, da turanci ta ce min. "Ma kina kuka ne?" Kallon bakinta nayi na fahimci me take nufi, sai da tazo kunnen da nake ji ta kara maimaita min, wannan wacce irin rayuwa ce. Murmushi nayi mata nace mata. "A'a abu ne ya faɗa idanuna." "Ayya soli!" Ta fada da tsamin turancinta, haka na rungume ta muka zauna a dakin. Hajiya Bayan Zahra ta bar falon, kiran Number da aka bata na dakin Majid tayi suna gaisawa yana dauka ta ce mishi. "Idan har ka sake ta saka kafa, ta bar Nijar yadda naga ran Aminatu ya ba'ci wallahi billahi azim ba zaka samu Zahrah ba, duk rintsi ka dawo wurin matarka kada ka sake ka kara wani lokaci ba ka dawo ba, domin ina jin kunyar yarinyar da ta nakasa domin ka, sannan ka dawo kana can ka zauna yau wata biyu kenan ana niman na uku." Kafin ta Kashe wayar , tana faɗin. "Ka dawo kada ka rasa matar rufin asiri,da haka na jajurce akan mahaifinku da ban san yadda xan zama ba, ita da ta tsaya akanka zaka tozarta? Anya Majid kana kaunar Allah!" Ta faɗa tana mita don haushi ya kamata, ya bata haushin kaniyarsu shi da likitan. Haka tayi ta faɗa. ** A can kuwa babu shiri ya fara hada kayanshi. Shigowar Yazid yana kallonshi. "Ya da shiri?" "Zahra zata tafi ta barni." Murmushi Yazid yayi yana faɗin. "haba dai." "Wallahi mamarta tana da matukar zafi, yadda kasan volcano haka take, kai lokacin da ta bani auren Zahrah kada ka ga yadda ya tsayar min, yanzu kuwa tace idan ba zan iya xama da Yarta ba, na sako mata,don ni ne ɗan Zainab mahaukaciya da zan saki Zahra, ai ko Shawara wani ya bani sai inda karfina ya kare, balle kuma babu ɗaya kanwar biyu zan koma jibi zan koma gida na gaya maka " Fir Majid ya ki zama, don babu wanda ya gaya mishi ga halin da take ciki an dai gaya mishi tayi rashin lafiya ne, kuma dalilin da zai saka Zahra tafiya bai dawo ba, dalili ne babba, don haka ya tattara ya ce zai zo shekaru uku ba wasa ba ne da wasu malamai zasu zauna zasu ce babu aurensu. Haka yasa gara ya tattara ya koma gareta. ** Bayan kwana biyu, sauran kwana ɗaya tafiyata, Duk yadda nake son sakewa, sai nake yawan fuskantar kamar ana min dariya, ko ana nuna ni, haka ya faru ne a hidimar da ake yi a familyn har su Maimuna da mijinta da abokin Mijinta da kanwarta. Jikina rawa yake saboda ban san taron na meye bane, sai dai duk yadda na juya sai na ga ana dariya da karfi, haka yasa na sulale zuwa dakina. Zauna dama haka nakasassu ke jin wani iri? Ina zaune a dakin Anisah da wata kawarta suka shigo wai sun zo min jajje. Ina tab'a wayata suka shigo ban ji sallamarsu ba, sai ganinsu nayi a kaina. "Ya zaku shigo babu sallama?" Dariya tayi tana faɗin. "Kiyi magana a hankali, kina magana kamar da mutanen waje kike yi. Mun yi sallama baki ji da kunne me lafiyar ba ne? Au ashe fa kin kurmance." Kura mata idanu nayi sai na saki murmushi, sannan na ce mata a hankali. "Idan kasan farkon ka, tsakiyarka ya dace ka ji tsoron isa, domin karshenka mutuwa ce. Ni ta sanadin aure da kuma yaki akan mijina idan kin ji haushi ki zama sarauniya a dangi ta hanyar tsayawa mijinki, ba korarriya da kishiyar da zata zo ta koro ki ba " kome ya ja hankalinta suka fita da gudu,ban sani ba amma tabbas taji d'acin maganata,. Da gudu Amaan ya shigo ya riko hannuna muka fita da sauri. Har kasa ya sauko dani an zagaye shi bakiɗaya sai raba idanu yaƙe, yana zaune a tsakiyar falon. A hankali naja na tsaya tare da kwace rikon da yayi min zai kai ni gare shi. Zubawa juna idanu muka yi, a sannu a hankali na janye nawa idanu daga gare shi nayi kasa da kai, ina wasa da yatsuna. Hannun Alfah naji cikin nawa tana kallon yadda hawaye yake zubo min. "Ma!" Ta jijjiga hannuna. Daga kai nayi sama ina shanye hawayena, kafin na sauko da kan naji ya bani wani irin hugging da ban zata daga gare shi ba. Wani irin kuka nake me ciwo da zafi,kuka nake me cin rai da kowa a falon sai da ya taya ni, kuka nake na farin ciki da bakin ciki da suka hadu lokaci guda suka min dabaibayi, kukan sanin cewa bani da wani amfani a duniyar Majid sai dai ya min alfarmar zama da ni, kukan sanin cewan na rasa ji na da kunne ɗaya na har abada. Kuka nake na tausayin yadda zai ta magana shi daya kafin naji na bashi amsa, kukan yadda Alfah zata yi ta jin haushi idan tayi magana ban amsa mata ba, kukan yadda al'umma zata yi ta kallona a nakashe. "Ya isa haka Matar arziki." Ya faɗa tare da niman wuri ya zauna sannan ya ajiye ni kusa da shi, Alfah tana zaune a cinyarsa. Ajiyar zuciya ya sauke yana kallon kowa a falon. "Sannu ku da zullumin b'atar da nayi, ko nace sace ni da suka yi." Sai da ya sauke numfashi ya bude gefen cikinshi dinki ne kato, ya ce mana. "Wannan shi ne abin da suka fara min bayan na shiga hannunsu, wuka aka soka min sai da ya fito ta bayana. Baffa Haladu ya mon wannan aikin a ranar da suka dauke ni." Kallon Amaan yayi ya cigaba da cewa. "Sun nime Amaan ya kashe yan gidan ko su kashe shi, amma bawan Allah nan ya ce musu sai dai su kashe shi dama shi bai da wani amfani tunda ba amfani zai yi ba, yau fari gobe tsumma, daga nan sun san yadda muke da Aryan basu tab'a tuntubar shi ba, sai da suka saka ya bada motar ta hanyar maganin da ake amsa a hannun Sajjid ina yiwa Amaan. Haka suka cigaba da barazana ga yan uwana, basu tab'a min barazana ba, sai ranar da suka kama turawan nan.... 300₦ 0016341139 unity bank zahra'u yahaya Ali Katin MTN 400 #Mai_Dambu ce [5/29, 07:48] Hlm: BHB277 A ranar suka turo min da sakon na kawo kaina, ko kuma su kashe turawan. Duk yadda na shirya su faɗa tarkona abin ya ci tura, sannan suka tabbatar min asibitin da nake kai Zahra waye ya san iya adadin mutanen da suke cikin asibitin wanda nasu ne. Ga yan uwana ga matar da nake aure, taya zan bar wani ya cutar min da abin da yake cikinta bayan yadda ta kwallafa rai a kan cikinta. Shi yasa na zabi tafiya na basu rayuwata don na tambaye su idan wani abu suke so zan basu har dukiyar da nake da ita, suka gaya min su rayuwata kawai suke bukata. Ya zan yi? Zan ce ina son rayuwata ne don na rayu Dangina kowa ya mutu? Idan na tuna na bar Zahra da ciki sai na ga kamar zata kuma haihuwar wani Yaron da zai zama kamar ni, nasan Zahra zata kula da Hajiya zata kula da kowa, sannan zata bawa kowa farincikin da ya dace. Haka yasa na tafi, tsawon lokacin da aka dauka ana nima na, an rigada an shigo dani nijar, duk abinda ake suna kallon kowa. Har haihuwar Alfah sai da aka kawo min labarin. " Shiru yayi cikin takaici da damuwa kafin ya cigaba da cewa. "Iya zaman da nayi nasan yadda Zahra take da kwazo, nayi addu'a Allah yasa Zahra ta san inda ma ajiyar bayanan komai. Amma ina zaune shekara daya ya wuce aka kawo min hoton Alfah, da ta cika shekaru biyu ma haka, tun da aka shiga na uku na fahimci cewa koda na mutu ahalina suna cikin nutsuwa da Amincin Allah. Ban kawo Zahra zata zo nima na ba, sai a daren da suka gaya min an rufe kamfani kuma nasan duk ranar da aka rufe tow nima na za ayi, ko kuma sun san inda nake." A hankali ya cigaba da gaya mana abubuwan al'ajabi, wanda muka sani da wanda bamu sani ba, da dalilin shi na tafiya Algers jinya, duk da na ji dadi amma kuma maganar da Anisah tayi yasa kowa ya shiga damuwa, musamman ni da na san yadda nayi na sulale a falon. "Ai yanzu kan sai kayi hakuri,amma zama da kurma ba sauki kana maganar sirri na waje na jin ka, idan kuma ka samu lafiya kana da halin kara aure." " Ke me yasa naki mijin da zai kara aure baki yi hakurin zama ba? Alhamdulillahi ita ko yanzu yakara aure ba zai samu mace irin Zahra ba, ba karya ba ne mu abin a cikin jininmu na Fulani yake, hakurinmu da kawaici yasa duk buzaye suka kanenaye rayuwarmu, don sun fahimci baya gamu babu wata mace me iya shanye ƙaddarar mijinta." Inji Benazir, ta mike tare da nufar hanyar da Zahrah ta bi. "Allah ya kyauta, ana sara ana duban bakin gatari." Inji Maimuna. Ta bi bayan Benazir, ina zaune a bakin gadona naga Benazir ta shigo. Kallonta nayi ina murmushi. Zama tayi tana kallona. "Kiyi hakuri!" Murmushi nayi ina faɗin. "Kai ba kome jarabawa ta ce" "Koma dai me nene kiyi hakuri." Ta rike hannuna tana faɗin. "kin yi nasarar, zama a zuciyarshi babu macen da zata samu gurbin zama a ranshi bayan ke, amma kada laifin wasu ya shafe shi." Shigowar Maimuna yasa ni kallonta. Itama aka baje hirar a kitchen dina nayi musu girki ko nace muka yi, baki daya. Sakin baki Maimuna take ita da Beenazir, "Kin shiga makarantar koyan girki ne?" Dariya nayi tare da faɗin. "mun yi sana'ar tuwo -tuwo." Na juye denderun kazar da muka yi, jollop din taliya ce sai tuwon semo miyar kuka, aka yi ta fita da shi. Miyar kukan da taji namar rago da kayan kamshi. Kunun aya da tsumi da yaji kayan kamshi, haka muka yi ta fita da shi, ana gamawa muka shiga daki, na samu sun ciro min kayan da zan saka. Nayi wanka na fito Beenazir ta gyara min fuska da kwalliya light, sannan na shirya suma na cire musu sababin kayan aurena, musamman abayar. Suka saka bayan sun shirya muka fito tare, muka samu yar iskar mara kunya tana tsaye Hajiya ta hanata tab'a kayan abincin don shegiya sai ta ce zata tab'a. Haka muka yi serving din kowa sai lokacin na fahimci baya falon, "Zahrah ki zuba mishi zuwa dakinshi." Inji Dean ɗinmu, kunya ce ta kama ni Maimunari ta hada kome ta mika min, na haura sama. Na kai mishi ya fito wanka yana goge gashin kanshi ga Alfah akan gadon shi tana wasa da tap ɗin shi. Kallonta nayi na ajiye kayan na dauke ta tare da kunna mata wakar Bunny. Na ce mata. "Love maza kaiwa hajiya da Nana su kunna miki." "Da intafi!" Kallonmu yayi ina jiran naji me zai ce sai zuwa yayi daidai bayana, ya ce mata." Ki je ina zuwa!" Da gudu ta fita, kasa d'agowa nayi. Yana kuma tsaye a hankali na d'ago bayana yana gogan nashi, yarrrrr naji abu yana yawo a jikina. Jin hannunshi nayi a saman cikina tare da cewa. "Ayi hakuri!" Haɗiye yawu nayi, tare da janye jikina ina rarraba idanu. "Ga abincinka nan!" Na fada xan fita, riko hannuna yayi tare da dawo dani ya rungume ni. "Ki kalle ni mana." A hankali na zame jikina na bar shi tsaye, a wurin cike da tarin mamaki na, na dawo dakina. Zama nayi hawaye na zuba min me zafi har wani lokaci kafin na tashi zan shiga ban daki ya shigo, kallon juna muka yi. Ajiye abincin yayi yazo ya zauna kusa dani. "Yunwa nake ji." Ya faɗa yana kallon yadda nake ƙoƙarin kauda kaina. "Baki yi farincikin dawowata ba ko?" Shiru nayi ban ce kome ba, sa ke magana yayi na kalli bakinshi kafin na juya da kunnen da nake ji na ce mishi "ka faɗa min me kace?" Na fada da karfi. Juyawa nayi naga yana kallona Idanunshi jajjur. "Zahrah baki ji ne da kunne ɗaya." Murmushi nayi ina wasa da yatsun hannuna. Abin da nake son ya fahimta kenan kuma ya fahimta, fita yayi daga dakin na bishi da idanun, ban kuma futa ba sai da su Maimuna suka zo min sallama, muka fita na raka su bayan na sake diba musu kaya a cikin laida, Mami sai fada take min bakya gajiya ne ga sabon abayar ga kaya kuma, murmushi nayi nace mata. "Idan ba naka ba waye zaka yiwa hidima baka gaji ba ai sai naka." "Allah ya zaunar da ku lafiya!" Murmushi nayi ina faɗin "Amin" bayan tafiyarsu na koma cikin gida muka baje dasu Baraka muka ci abinci. "Maman Amirah, ina son zuwa gida Zainabu ta haihu." "Me ta samu?" "mace yarinyar nan ta cika haihuwa, fisabilillahi Aunty tasan." Dakuwa nayi mata, ina faɗin. "Kaniyarki kema baki fi karfin Allah ya jarabce ki ba, don ta haihu sai ta zama me laifi." Tura baki tayi tana faɗin. "Allah laifina kike gani kawai." Girgiza kai nayi ina kallonta, Baraka ta zame min wata sanyin idaniyar, a duk lokacin da na kalleta sai naji ina kara kaunarta, shi yasa nake burin Yazid ya aure ta ita da iyayenta su fita a rayuwar da suke ciki duk da suna da rufin asiri, Baban yana aiki a kamfanin Mahdi mijin Munaisah. Bayan sati guda baki ta ko ina sai zuwa suke har da Zaytoona da yaranta biyu, Ummi da ta kusan aure itama tazo, Munaisah da nata Yaron, Zuzu na ma haka farinciki iya farin ciki. Muna cikin wannan farin cikin Mutumin da xai auri Ummi ya kira ya gaya mata ya fasa yaji ance ta tab'a karuwanci a baya, tayi kuka nayi kuka dukkanmu mun yi kuka,, shi yasa nace ta zauna da mu anan babu amfanin zuwa Nigeria kada ta zama abin nunawa. Addah yadda zuzu take gaya min, ta koma kamar wata halitta. Amma bakinta yana nan radau kamar ba ita bace a nad'e. Zuwan Malamijo da Alhaji Abubakar Abzin, yasa gidan ya kara cika. Allah yaso tunda ya dawo babu abinda ya tab'a hadamu zuwan dattawan nan da Ya Babangida,aka sake daura aurena da Majid, tunda a shari'ance yana kasar kuma yana sane da ya sake ni ne da sauki amma Nima ban yi wani auren ba, wanda ba a san inda yake bane da ya shekara hudu babu aure, amma yana raye ina raye kuma yana kusa damu a Muslunce wata hudu ya dace a kashe auren. Daura auren ya yayyafa wutar da yake cin ran Mama sannan kiri-kiri ta saka ni a gaba muka bar nijar, wai ta tafi yi min jinya ai shima da ya tsallaka ya tafi bai yi tunanina ba. Ina son Mamana, wallahi babu ruwanta kankaro min mutunci take ta ko wace fuskar, Bayan mun isa Kamaru naga likitan kunne an bani abin jin magana, sannan muka dawo, ina ganin ta hada dilke ta saka ni a gaba tana gyara min jiki. "Munafuka, kina nunawa babu ruwanki, nan kuwa nasan har kuka ke yi kina jin haushin na raba ki da mijinki. Ja'ira ya tafi tsawon shekaru uku, kina tsammanin baya son dadi ne, wurin za a kara gyarawa mutuncinki ya cika idanunshi. Ya gane ke daban ce a cikin mata, na lura har wani hura min hanci kike to na ga bakaloji." Tana fadar tana zungure min goshi, ni dai ban ce mata cikanki ba, sai dariyar da nake mata, wato gyaran da tayi min wallahi har wani ji nake iska na shiga jikina, ko ina na jin shi nake zam-zam kamar bani ba, a sati biyu na yi kyau na ciko ta ko ina, a ranar da na cika sati Uku a ranar ya diro ranar juma'a, ina can gidan lalle, an gyara mana bangaren mu. Sai kamshi yake daga gidan lalle da suke har saloon aka min, ko ina na jikina Masha Allah jiki duk Madara. Muna dawowa, na hango shi tsaye jikin motar Malam, yana waya ya saka wani farin yadi na maza har ina iya hango farin singlet din cikin. Dauke kai nayi na zo xan wuce ya ce min. "Fulani ba magana ne?" Murmushi nayi nace mishi. "Barka da hanya baban Alfah!" Na wuce abina, bina yayi da idanun yana fadin."ji mana." Tsayawa nayi ina kallon gabana, jikina rawa yake, kasa ƙasa yace "Kinyi kyau sosai." Ya durkusa a gabana, abu ya ciro a cikin aljuhun shi ya saka min kamar sarka. "Ina son ganin mace da sarkar kafa, kuma nasan yadda ƙafafuwan nan sukaji lalle zai yi kyau." Murmushi nayi mishi, sannan na wuce cikin ban ce uffan ba, lokacin da na shiga cikin gidan Mama kallona tayi yana biye dani. "Ya kake binta!" "Amma Inna mata ta ce?" "Allah ko?" Ta tambaye shi tana d'aga mishi gira. "Yaushe muka fara wannan wasan!" Yadda tayi maganar babu wasa yasa nima na kalleta. "Ya za ayi wasu daga cikin yan uwanka basu son kurma bayan nasan ba haka na baka Zahrah ba, ya xa ayi domin nima ba zan yarda a kuntatta mata ba! Kamar yadda kaima danginka basu so a kuntatta maka, Ina son Zahrah kuma ba zan bari a mata wani abin ba, Tow ya zamu yi don naga wasu suna ganin kamar ta zame maka lalura zaka yi maneji da ita ne kawai." (Ya kuke ganin abin da Mama Amina take shirin yi zai haifar da d'a me ido ko yayya?") 300₦ 0016341139 unity bank zahra'u yahaya Ali Katin MTN 400 #Mai_Dambu ce [5/29, 07:48] Hlm: BHB278 Sakin baki nayi ina kallon baiwar Allahn nan, kafin na ce. "Mama!" A wani fusace ta juyo min, jikina ya dauki rawa kar-kar domin bata taɓa min ko kallon banza ba, "ki b'ace min da gani kafin na mugun saɓa miki!" Da sauri na bar falon, yadda naga fuskarta babu wani sassauci. Yadda take cika tana batsewa ya kara saka Majid rud'ani da tashin hankali. "Inna fisabilillahi." "Ungo nan kaniyarka" ta masa dakuwa da hannu bibbiyu. "Kaci kaniyarka." Ta fada da karfi, kafin ta gyara zama ta ce mishi. "na fasa baka Zahra, maza maza ba yau ba. Ba gobe ba don gobe ta Allah ce maza ka yanko min takardar ta, idan kanwa ce zan jika abata." " A kidime ya mike jikin shi yana rawa, "wallahi ba zan iya ba, gara a kashe ni akan na saki Zahra!" "Tow kuwa sai dai ka mutu, wato har ana tuna maka ta kurmance akwai mata masu ji. Akan waye ta samu lalurar?" Kamar an saka mishi shocking, kamar zai yi hauka fir Mama ta ki kula shi ta ce mishi. "Na rantse da Allah ba zan baka Zahra ba, sai an hadu family idan kana ganin wasa ne Bismillah ina ku Yayan Idanu ne, Ya Sa'a bata iya tsawata.muku? Tow b'ace min da gani ka fita ka bar min gidan Ubana, kamar yadda Anisah ta ce gidan Mamman Ba'are gidan Ubanta ne fita kabar min gidan Ubana duk lokacin da kayi arzikin gidan kanka danginka suka san darajar Y'ata zan zauna da kai." Har ta wuce ta juya a fusace ta ce mishi. "na fasa zaman family wallahi kada na kara ganinka a wurin Y'ata ka saketa domin na mata mijin da zai zauna da ita da kurmanta maza nan da 48hrs ka kawo min sakinta." Kaf gidan babu wanda ya goyi Bayan Majid domin duk abinda ya faru, Barakatu ta gayawa Mama ashe ni ban sani ba, Cidi aka hada ni da ita, ni ina zaune da ita tsakanina da Allah ashe ita aikin Mama take, ban sani ba. Dakyar na danne fushin da yake raina, amma Mama ta bani mamaki koda yake Zaytoonah munafuka ta ce min ganinta nake haka, ko Hajiya bata tab'a marin Majid ba amma Mama ta watsa mishi mari. Ina zaune har dare sannan ta shigo inda nake matar nan bata kalla ba. Tayi uzurinta ita da Jikarta suka kwanta suna hira tana bata labari da tatsuniya da hirar duniya kafin naji yarinyar tayi shiru, ina jin tana mata addu'a ta tofa mata. Ina zaune kan Sallaaya ta ce min. "Na b'ata miki rai ko? Na batawa mijinki rai ko?" Gyara zama nayi tare da cusa kaina tsakanin cinyoyina. Hmmm na zata rarrashina zata yi tare da bani hakuri, a'a bata yi haka ba, bata kuma ji a ranta tayi hakan ba sai ce min tayi. "Don Uban mutum idan ya fasa jin haushina na karci hancin uwar Mutum;" ta faɗa tana tsare gida saboda yadda na d'ago da sauri ta kuma sake hada rai. "Eh na fada din, kuma wallahi ko da wasa naji an ganki da Majid sai na ci ubanki don uwarki, mara zuciya da rashin sanin ciwon kai idan ba rashin sanin ciwon kai ba, ina ke ina jin haushina. Ke ki mutu akan kowa ke ba zaki samu me sumewa akanki ba, kuma kika min kuka na tashi na ci Uwarki." Wani irin tsoro ne ya kama ni, na ja bargo na gyara wurin kwanciya na kwanta, ina ajiyar zuciya. Har barci ya dauke ni. Kafin tayi wannan borin, sai da ta samu iyayensu da Yayunta manya uku ta gaya musu halin da ake ciki, ta ce musu idan bata tsayawa Zahra ba, abubuwan zasu yi yawa ga rashin kunne ga cin zarafi a gaban kowa kuma Sa'adatu bata ce kome ba shi ma Majid bai yi magana ba, ta ce ba zata iya ba, ba zata kashe musu aure ba. Amma don Allah a kyaleta ta taya Zahra, da Uban Zahra yana raye ba zai barta haka ba. Wannan yasa kowa ya goyi bayan Mama. Kuma ba karya babu b'ata lokaci, ta hana ni ganin Majid ko tsakar gida bana fita, abinci ma daki ake kawo min, wani lokaci ina jin Muryar shi da Yarshi amma babu yadda na iya nasan yayi kewata domin kuwa a yadda yake bawa Yafendo da Goggo Sume hakuri suna yab'a mishi magana zai baka tausayi, idan Mama bata nan.zama nake naci kuka na wanke idanuna. Wasa wasa tun yana bin kakanninmu har ya fara sarewa, Malamijo da ya samu da maganar murmushi yayi ya ce mishi. "Kasan Manzon Allah Sallallahu alaihi Wasallama ya tsayawa Yarshi Nana Fadimah da mijinta Sayyiduna Ali zai auro yar wurin Abujahal ? Yace bai yarda ba, kamar yadda Nana Fadimah bata yarda ba shima.bai yarda a yiwa Yarshi kishiya ba, kasan sayyadi Ali bai kara wata matar ba sai bayan mutuwar Nana Fadimah Allah ya kara mata yarda. Don haka ina bayan Aminatu tayi duk yadda take so, Yarta ce mu tayata zamu yi." Haka ya tafi gidan Kawu Gidado, shima kiri-kiri ya ce "ai Aminatu tana kan Daidai shima uwarsa ta tsaya mishi balle marainiya da bata da uba bata da kowa don bata da arziki ba yana nufin bata da me tsaya mata bane, Ummi, Kai babu wadanda basu zo ba har zuzu da Mijinta. Family ya hadu bakiɗaya. Ranar Alhamis muka fara amsar baki har ranar asabar, ranar Lahadi aka fara meeting. Kafin a fara meeting din sai da aka so raba raini tsakanin Munaisah da Anisah da Zuzu. Suka nime dukarta saboda habaicin da take yada min. Na cewa. "An samu wuri ana zuba iskanci, dadin abu dan uwana aure zai kara mace me ji da magana a hankali." Shine suka mike tare da rufe ta da duka, na shiga tsakaninsu, ture ni tayi na hada kai da cabinet na kitchen, hayaniyarsu ya janyo hankulan mutanen gidan aka shigo da sauri ana tambayarta. "Waɗan nan yan iskan karuwan ne zasu shiga tsakani na da Zahra don kawai ina..." Kifa mata mari Mama tayi sai da ta gigice, bata kuma dawowa hayyacinta ba, ta ƙara kifa mata wani tana fadin. "Yaran nawa zaki jifa da kalmar karuwanci?" Matar Kawu Gidado ta riƙeta. "Haba Amina fadar yara ne." "Bu... Ubanta, don ubanta ni zata kawowa rashin mutunci. Shegiya ta kasa zaman gidan mijinta zata saka yara a gaba, naji karuwai ne baki ga zaman gidan Aurensu suke ba jaka jahila." "Amina wani irin magana ce haka, zaki zauna kina cin mutuncin Anisah akan Yara...." Fusace Mama ta juya tana kallon Hajiya da ta kasa karasa maganar bakinta. Wai idan kasan na fada baka san na maidawa ba, wani irin tashin hankalin da ba a tab'a yin shi ba, domin Ni kan daki na wuce na rufe kaina, Majid rike kanshi yayi kamar ya fasa ihu. Sai da Yafendo da Goggo Sume suka daka musu tsawa, kafin Baba karami ya shigo yana kallonsu. "Baku ji kunya ba? Kuna cece ku ce akan yaranku." Wani irin kuka Hajiya ta fashe da shi tana faɗin. "A kodayaushe Amina ce me gaskiya nice mara gaskiya." Malamijo ya ce mata. "Dole tayi gaskiya kina ganin Yarki tana kuskure baki tsawata mata, ko an gaya miki bamu ji irin abinda Anisah take yiwa Zahra ba ne? Don haka ga Yaranki nan ki saka Abdul Majid ya saki Zahrah ai da nasan da wannan tashin hankalin da ban kara mai da mishi ita ba, Mun ji Zahra kurma ce kuma karuwa ce, Zahra ina babu iddarshi a kanki? Maza sake ta yau ba gobe ba za a daura mata aure da Yazid." Wani irin rikicewa Majid yayi ya mike tsabar ya kidime, fadi yaƙe. "Shi kenan sun kashe ni, sun gama da rayuwata." "Ko mutuwa zaka yi ba zan koma ba, ba zan koma.ba ka zauna da danginka, bani da kunne yan uwana karuwai ne, ka rike nagartattun danginka, yarinyar da take tsakaninmu idan baka yarda da yarka ba ce itama zan rike amma ba dai gidanka ba." Na fada bayan na fito dakin sannan na koma, ina jinsu tunda na koma kuka nake. "Shi kenan,ta kwana gidan sauki oya sa shi ya saketa." Zubewa yayi a kan gwiwarshi a falon babu wanda bai bawa tausayi ba. Har itama Mama sai da ta dauke kanta. Babu abinda Majid zai nima ta hana shi, amma yau bata jin zata bashi Zahra ta sauki. "Innani, gaya min waye kike so na kashe zan kashe idan zaki bani Zahra. Innani gaya min waye kike so na b'atar da shi zan yi haka idan zaki bani Zahra. Innani ga shi wannan shine takardun duk wani abin da na mallaka idan zaki bani Zahra na bar miki ko da dako zan rike Zahra zata daura zanin da matar shugaban kasa zata daura. Innani gashi wannan bindigar tawa ce, ki kashe ni idan har zaki bar min Zahra a rayuwata na amince." Ya ajiye mata kome, sannan ya tafi gaban Hajiya da jikinta yayi mugun sanyi ya ce. "Tana yi ne domin yarta, tana yi ne domin darajar Yarta, zo ki bata hakuri zata hakura, idan bata hakura ba idan na tafi sai dai a dawo muku da gawata." Gaban Alhaji Isma'il ya koma, "Kawu na kawo ka ne domin ka nima min alfarmar Mama ta bani yarta me daraja, Kawu kada .ka zama dan kallo mana." Rarrafawa yayi gaban Nana wacce tun da aka fara take share hawayen takaici. "Nana kukan kawai zaki yi Nana kuka kawai zaki min, Nana ba zaki bata hakuri ba, Goggo Sume Yafendo. Wai me yasa ban mutu ba" ya faɗa yana kallon kofar dakin. "Yarinyar ce ni take cewa ba zata zauna da ni ba, idan kowa ya guje ban cancanci ki guje ni don laifinsu ba. Zahra ki gaya min me zanyi don farincikinki?" Ina dakin sai kuka nake, Ya bude baki zai magana aka ji Muryar Mama tana faɗin. "Ba zan hana ka Zahra ba, ba zan saka ka kashe kowa ba, kuma ba zan so ka rabu da kowa ba, sai dai sharadi." Da wani irin sauri ya isa gabanta. "Kwashe kayanka, kafin nayi ra'ayin sauya tsarin." "Kiyi hakuri don Allah, Aminatu ki bashi damar zama da Zahrah wallahi billahi azim ba zan sake wani ya muzanta mata ba, na rantse da Allah." Inji Hajiya nan aka shiga bata hakuri tana ji sai da aka gama ta ce musu. "Zahra ba zata zauna gidan Mamman ba'are ba,. kasancewar ina da wasu Yaran zasu zo wurinta, bana son su zo a musu gorin arziki. Na biyu babu Abdulmajid ba kara aure, sai ranar da Zahrah ta mutu, idan yaso a ranar ya kara aure. Na uku duk wanda ya kuma zagar min Ya ko Yarana kotu zata shiga tsakaninmu,. Ga wanann takardan yarjejeniyar ce sannan Abdul Majid zai biya miliyan dari biyar kudin diyyar rasa kunnen Yata da kuma ci mata fuskar da ake yi, sannan zai ɗauke ta zuwa jinyar kunne. Bayan nan na gama magana idan ya muku fine idan bai muku ba, a sako min ita." Ta fada irin ko a jikinta, take aka bata goyan bayan, jiki na rawa ya shiga ware kudin ta wayar shi da wasu kadarorinshi ya kalli Mama ya mika mata ya ce. "haka yayi?" Yadda jikin shi yake rawa yasa ta riko hannunshi tare da kwala min kira. "Ban yi haka don kwadayin kudinka ba, nayi ne a san darajar Y'ata, sannan kada na kuma ganin Anisah a inda Zahrah take idan ba haka ba, sai kotu ta raba mu." Fitowa nayi ta galla min harara. "Munafuka,ga mijinki nan kudin diyyar kunnenki nace miliyan dari biyar." "Mama yayi mishi yawa, miliyan goma ma ta isa, idan aka duba girman zumuncin." "Uwaki da zumunci ni kan Aminatu hala babu zuciya a kirjin wannan yar taki anya ba sace miki Y'a aka yi ba? Yarinya bata da kishin kanta." A hankali akayi ta bata hakuri, Ana rarrashina da ita tare da mana nasiha, ita kuma Anisah Kawu Isma'il yayi alƙawarin daureta idan ta kuma shiga sabgata. Kai an sha drama sannan suka juya kan Hajiya da nuna mata tarbiyyarta sakarci ne ba tarbiyya ba, Anisah tana son fin karfinta. yadda aka mata tass yasa ta ce Anisah ba zata bita nijar ba, ta zauna anan Kamaru, Bayan nan aka rufe da addu'a, sai dai me kuma zai faru, Majid yana mikewa ya yanki jiki ya fadi....... Tsugune bata kare ba.. 300₦ 0016341139 unity bank zahra'u yahaya Ali Katin MTN 400. #Mai_Dambu ce [5/29, 07:48] Hlm: BH79 Kamar wacce aka dasa ni nake kallonshi kwance, ashe kuka rahama ce dadi yake sa ayi . Ban san wacce duniya nake ciki ba domin tun ina jin salatin mutane har ta kai nima na daina ji da gani na zube a wurin. Dukkan mu biyu naji labarin an kai mu asibiti, a yadda Zaytoonah take gaya min damuwa tayi mishi yawa, domin ni na farka da yammacin washe gari. Shi kuwa naji ance har yanzu bai farka ba, domin kuwa a gajiye yake. Tunda na sauke sallaolin dake kaina, na wuce dakinshi nake zaune ina azkar da salatin Annabi, haka na cigaba da du'a'i sallah da abinci yake tadani har tsawon kwanaki uku, a rana ta hudu bawan Allahn nan da na cire rai ya farka. Dama abisa ala'adar da na dauka kullum zan daura kaina a kirjinshi, naji ko yana raye, idan kuma bai min ba, zan tab'a hancin shi da gefen wuyarshi. Ashe tun ina gyangyadi ya farka, yana kallona kamar a mafarki nake jin kamar ana kallona, bude idanu nayi ya lumshe idanunshi, tashi nayi na fara yan dube -dube, can sai da na gama nakan sumbaci bakinshi. A hankali na kai bakina kan nashi zan sumbata kawai naji ya cafke bakina, ban san lokacin da na daka tsalle ba, na koma bakin kofar. Hannunshi ya kai saman bakinshi. "Zaki yi disvirgin din balagaggen bakina Allah sarki bawan Allah." Ya shafa bakinshi. Tura baki nayi hawaye na zuba min na ce mishi. "Fisabilillahi idan da ina da ciki ne fa? Ba asara zaka ja min ba wannan wane irin abun ne haka!" Kura min idanu yayi yana faɗin. "Zo ki cire min waɗannan monitor din." Na isa kanshi ina taya shi cirewa aka turo kofar, fisgo ni yayi na fada kanshi, muka leka kofar a tare. Su Hajiya, Mama, Nana Zaytoonah. Da sauran dangi. "Alhajin Allah!" Inji Nana, "Ke dai ba zaki hutar da ranki akan Hammayo ba?" Inji Zaytoonah. Da sauri na sauka akan gadon, ina me nufar banɗaki na hada mishi ruwan zafi, kasancewar ana sanyi. Sai da aka gama mishi ya jiki ya shiga ban dakin yayi wanka, na isa bakin kofar bandakin na buga amma yaki budewa, ganin haka Nana ta ce. "Tow tow zamar uwar me muke musu, Alhajin Allah bude tazo ta wanke maka bayanka." Wayyo Allah wata irin kunya ce ta kama ni, take na diririce kafin na gama dawowa nutsuwa sun gudu abinsu, suka ajiye kayan Abincin da sukazo da su. "Nasan sun gudu oya rufo kofar kizo kiyi aikin lada." "A'a ni nayi wanka na" "Tow rufe kofar" ban ki jin nashi ba, na rufe kofar, juyawar da zan yi na ganshi tsaye daga shi sai yar gajeran wando. Kunya ce ta kama ni na juya, sai ji nayi ya riko ni. Ba zance kome akan lamarin ba, sai dai da na biye shi da ya ajiye min kunyata cikin asibiti sai dai ni ina da kunya kuma kunyata tana da mutunci. A daren ranar aka sallame shi, gidanmu da yake jikin gidansu Mama muka tare, ni a nawa tunanin za a ce bai da lafiya, amma ina ban da Majid, a daren sai da na hada da magiya wai ba zai kyale ni ba, sai ya rama abin da na mishi, a dai takaice ya min dakar sakwarar shege. Har asuba ya manne min yana makale da ni, sai da yaji za a shiga sallah ya janye daga jikina ya shiga ban daki yayi wanka da alola ya tafi masallaci, nima wanka nayi da Alola na gabatar da sallah, ina azkar ya shigo min. Nan ma naga yana niman kafi shayi, rudewa nayi kamar zan yi kuka, amma babu yadda na iya, haka na bashi damar ya zane ni son ranshi. Kafin ya janyo ni muka yi barci. Sauran kwanakin da suka biyo baya, har su Nana sun tafi, Anisah ma Mama tace ba zata zauna mata ba, ta tafi Hajiya ta gyara kayanta da ta lalata. Tun daga ranar muka bude wani babin soyayya da kaunar juna, nayi kyau nayi kiba. Fata ta kuwa har wani glowing take saboda nutsuwa da kwanciyar hankali, watan mu guda,.na fara wani irin jin sanyi idan ya fita office zan gudu wurin Mama, nayi ta nad'e kaina da buya a cikin dumi tunda ta ga haka tace min ciki nake da shi,.na tura mata baki. Labarin cikin yazo min da ban mamaki domin a lokacin take gaya min ai ya ce mu da Nijar sai sallah da wata hidima, zai zauna a kamaru dama can nan ne mazauninshi, kasa magana nayi ta ce min. "Dan kwali yaja hula ko!" Kifa kaina nayi a cinyarta har barci ya dauke ni. A can Nijar ma dake sun tafi da Alfah,wani irin riko Hajiya take mata kamar ta maida ta ciki itama yarinyar tana son Hajiya da Nana.. Sai da cikina ya shiga wata shida, kafin Malamijo ya dauki hakkin su Alhaji Isma'il Wodabbe ya kira yazo ya amsa ya bashi hakuri ya kai shi har gidan gonarsu, ya ce dukiyar mahaifinsu ne, shi da kanwar shi wacce har lokacin bata sauko daga fushin da tayi ba.(wato Innar Almamoon 🤣😂😹) Bayan ya koma Nijar ya taso Inna har Kamaru, a lokacin da suka hadu kuka tayi ta yi,tana faɗin. "Kiri-kiri ka Kore mu ka bamu Iya adadin shanu goma sha biyar kace na yafe maka" "Uwata kiyi hakuri, ki yafe min nima zuri'ata ta samu zaman lafiya da nutsuwa." Ya bata labarin abinda ya faru, ta share hawayenta, ta ce ta yafe kwanansu biyar suka koma. Jamilah da su Hajiya da Nana suna ta son ganina haka yasa Majid ya shirya min tafiya shi kan aikin asibiti ya rike shi, haka na tafi ni daya na. Akan sati biyu zan yi musu, ina zuwa kuwa na tafi har marad'i. A can na kira Yazid na mishi maganar aure, idan yana da sha'awa. Bai min musu ba, ya amshi Barakatu amma yace zai zo su daidaita. Naje gidan Munaisah itama ta yaye d'anta, sai rigima yake mata tana ta lissafi, .kwana ɗaya nayi a gidanta don naga ta dauko Nenne. Ina cikin sati na cewa Aryan ya shirya min komawa gida, abin ya basu mamaki kwanana takwas kawai na ce eh gida zan koma, na kuwa dauko mana Nana da take fama da rikicin tsufa wai na hana Alhajin Allah kiranta. Nace matukar shine matsalarta muje ta zauna a wurin shi. Lokacin da muka zo tana ganinshi ta ware, haka na cigaba da jan cikina ina turawa har ya isa watan haihuwa, wani babban rashin da muka yi ana shirin saka ranar Baraka, Allah yayiwa Amaan Mamman Ba'are rasuwa. A nan Kamaru Ashe sun zo shi da Hajiya domin daga airport asibiti suka wuce. Ni ban sani ba, domin kwana biyu ina fama da nakudar tsaitsaye, duk da ba nan Majid ya karanta ba, amma ya kira wata incharge na asibitinsu ita ta nuna mishi kome ta kuma gaya mishi yadda zai min idan lokacin yayi, ranar da suka zo yana aikin dare, don ya tafi ya bar ni kwance a dakin Mama don tun da na fara haka su Nana suka ce a kawo ni cikinsu na zauna. Haka na kwana ina fama, ashe sun ji labarin rasuwar domin a cikin gidan aka dawo da shi,ina jin sautin kukan Hajiya na fito na ji Mama tana faɗin. "Ba kuka zaki yi ba, jinya ya kare kamar yadda yayi fatan ya mutu a hannun dan uwanshi, ya cika a hannunsa." "Waye ya mutu?" Na tambaye ta, ina dafe bayana. "Amaan!" A hankali naji wani abu ya zubo min, na durkusa a kan gwiwata daidai shigowar Majid da dark green uniform.na likitoci. Da sassarfa ya iso gabana ya rungume. "Sannu Flower push!" Wani irin azabar da ta ciyo ni, ban san lokacin da na damke shi na manna mishi cizo ba, sai ji nayi kamar an b'antare abu a jikina ya sauka kasa bakiɗaya. Sake nishin na kuma yi wani ya sake durowa. "Thank You God for everything, thank you flower." Haka Goggo Sume ta amshi Yaran, ni kuma ya gyara min jikina ya kai ni ban daki, sai da ya kwashe min kome na cikina, musamman jini me saka ciwon ciki, ya haɗa ruwa da kanshi ya min wanka ya dauki pant da pad ya saka min,. Sannan ya samu Yafendo ta dama min kunu da zafinshi yace na sha ya saka min ruwa, sannan ya gyara min kwanciya bayan ya saka min allurar barci, sumbarta bakina yayi ya fita, ya koma.kan hidimar gawar. Ana gama shirya gawar aka fita da ita, ya dawo ya sake kayanshi suka tafi makabarta, wato a lokacin da wasu suke kuka a lokacin wani yake dariya, bayan an gama wanke Yaran. Mama ta ce musu. "Aliyu ya tafi daren jiya, yau da safe Aliyu ya dawo, Allah ya rayaka." Haka kowa jikinshi yayi sanyi, bayan dawowarsu daga makabarta, ya zo yayiwa Yaran Huduba, ban kawo zai saka sunan Mama ba kasancewar ina da Aamirah. Sai gashi ya musu huduba, Aliyu da Aminatu. Mutanen Nijar sun zo ta'aziyar da barka, Allah ya takaita, ba suna. Haka muka yi zaman makoki ni kuwa nayi kyau abuna. Zaman jego ba karamin dadi naji ba, Doctor yana shigowa muyi hira korar shi Mama take, kwananmu talatin da biyar, ya cewa Mma."Innani don Allah ta koma ɗakinta." Hajiya tana jin mu dake rasuwar Amaan bai barta ba. Watan mu biyar muka je Nijar sallar azumi, daga can muka wuce Nijeriya. Lokacin da muka je kan Addah wacce take kallona. "Zulaihah mijinta yana kasan mijinki, Munaisah mijinta yana kasan naki. Ummi bata yi aure ba. Ke wacce irin mayya ce." "Itama zata yi aure wanda yace zai auri Munaisah Allah bai yi ba, Abdul Majid shi yake son Ummi har an gama magana. Akwai sauran abu ne?" "Wato da aka gaya min na zata karya ne, ke Shaidaniya ce a cikin siffar mutane." Addah ta shiga ihu da tonawa kanta asiri, wannan bakin cikin yasa Zuzu ta kaita gidan Mahaukata, ta ce zata na zuwa dubata. Addah bata mutu ba, amma taga yadda Allah ya daukaka ni ya kuma daukaka rayuwata. Mijina kuma abokin rayuwata yana girmama kome nawa, wacce ta tsaya min mahaifiyata. Anyi bikin Barakatu da Yazid bikin da aka sha hidima da ni da Majid muka tsaya a hidimar a matsayin iyayenta, yadda Majid yayi ta kafa sharudda na san ko bikin Alfah da Aminatu ne sai haka, mun kaita gidan mijinta da yake cike da sarauta, sai dai kuma na bata hakuri. Sannan muka dawo, koda yake watan Oktoba aka yi bikin sai gashi sun zo a watan Fabrairu, na sha mamaki da Yazidu yake kaf-kaf da ita ko me zata yi yana faɗin. Tayi a hankali tasan bata da karfi, a bakin Mama nake jin labarin ciki ne da ita, don ni ta dauke ni a matsayin uwa ce bata sakewa ta gaya min kome, kuma yadda na ganta nasan babu matsala, sai da nayi kukan farinciki iyayenta har Kamaru suka zo kamar zasu kwanta na bi ta kansu. Suka gayamin wai mijinta ya saya musu gida a Kamaru su zauna kusa dani, wani irin farinciki nake ji, kome na kalla sai naga ya zame min 100 percent. Anyi bikin Ummi da Abdulmajid dan Hajiya Hadiza Mamman Ba'are, wacce ta sauko domin Aryan ya sauya wa kowa matsayi dan daga karshe Kamfanin Majid na Marad'i ya rike shi Abdul Majid din Hajiya Hadiza. Sai daga baya kowa yake faɗin Ashe Majid waliyin Allah ne, Aryan tun mutuwar Amaan ya zama karkace aiki kawai da ibada da kula da dangi da Matarshi. Matan Alhaji Mamman Ba'are, Aryan ya maida kowacce garin iyayenta ya saya musu gida madadin na Niamey. Gidan kuwa Hajiya tace a sayar kawai ko a maida makarantar Amaan and Mamman Ba'are Memorial Islamic college. Domin ta haka ne za a cigaba da tunawa da bayin Allahn nan. Har yau Anisah bata yi aure ba, kuma bata da ma niyyar yi da ta fara bin kawaye, Aryan ya mata mugun duka. Kafin ta nutsu Allah ka shirya mu tafarkin addinin Muslunci. Ummi ma suna maradi, dukkansu an sha gwagwarmayar rayuwa, sannan an kuma dawo ana morar arzikin da Allah ya tsaga mana, wato Zina bata da wata amfani. Duk yadda ka ɗauke ta ba hanyar arziki ba ne, gashi dai dukkansu babu wacce ba ta tab'a rayuwa ba, amma dake Allah ya dubi tubarsu sai ya basu mazaje na gari. Nasihata ga mata da matasa, zina bata da fa'ida. Sannan a cikin.maza dubu dakyar ake samun ƙalilan da suke sonka domin Allah, kada rayuwar Zuzu ko Munaisah ya burge ki wallahi babu riba a cikinsa. Ga dai karshen Addah bata mutu ba, bata fasa ganin cigaban Zahra ba. *** Ranar muna hira da Majid nake bashi labarin yar Munaisah, tashi yayi yana kallona. "Zahra kuma kika bar yar a hannun Paul?" "Tow ya zan yi?"kwanciyarmu muka yi nazata maganar ta kare, bayan sati biyu ya ce na shirya zamu yi tafiya, amma na ajiye yan biyu."salon ka kara dura min ciki!" Murmushi yayi min kawai. Bayan kwanaki muka bar Kamaru sai gamu a Poland, kai tsaye gidan Paul ya kaimu ashe an san juna, anan muka samu kyakkyawar tarbar. Amma babu Paul sai yan aiki wai ya mutu bayan tafiyar Munaisah sai yarinyar da aka bar mata tarin dukiya kamar hauka. Lokacin da ta ganni, da gudu ta faɗa jikina. "Kece Mamana?" Hawaye ne ya zubo min, muna zaune sai ga lauyoyinta dama wai jiran wani daga cikin dangin mahaifiyarta ake, Babanta ya ce a damkata ga danginta, yarinya yar shekaru takwas. Kuka nake na saka hannu da kome, muka tattaro abinda zamu iya kwananmu biyar muka dawo Kamaru nace lallai Zuzu tazo ina son ganinta. Jin haka suka tattaro ita da Mijinta, ta manta da rayuwar Yarta baki ɗaya. Ta amshi sabuwar ƙaddararta, lokacin da muka zauna nasaka aka kira min Lilly, sai da uwar ta zubda hawaye domin babu abinda ya fi jini ƙarfi, na mika mata takardun yarinyar da kome na dukiyarta. Na tura mata dukiyar. Dawo min da shi tayi. "Ko a lahira, zan amsa sunan Uwar Fatima ne, amma ki saka a ranki ba tawa ba ce taki ce, kada ki sake ki gaya mata cewa nice na haifeta. Zahrah taki ce ba tawa ba. Idan da nasan don haka kika kira ni da ban zo ba, ai na gaya mata ke ce mamarta ni Yayarki ce ina zuwa gareta a madadinki, hatta waɗannan abin ba nawa ba ne naki ne." Wannan wacce irin rayuwa ce? Haka Munaisah ta bar min yar, ko dukiyar bata waiwaya ba. Haka na kama Yaran duk na rungumesu. Haka na cigaba da rayuwa,. ina zaune kawai sai ga Amirah ta dawo min. Baraka ma d'anta namiji ta yaye ta kuma dauko magana. Haka Ummi itama tana haihuwa ina ga Arba'in kawai tayi ta kuma dauko magana, Ni ce dai daga guda biyun nan ban kara ba. Sai rike na wasu. Daga baya dan renin hankalin yake gaya min shi ne yake family plan, nace yayiwa kanshi. Haka muka cigaba da tafiya, Hajiya ma ta dawo gida ta zauna ina kula da su. *** Bayan shekaru masu yawa, ina rungume da jikata yar wurin Zahra, da ta haifa da wani dan majilsa. Don Allah yakara bunƙasa Majid, ya gina asibitinshi shima. Amirah da Zahra suna aiki anan dukkansu nurse ne, Alhamdulilahi domin naci ribar hakuri, kuma Dukansu na aurar da su, sai Alfah da take karantar likitanci itama, naji Uban yana cewa Abdul Majid Aryan Mamman Ba'are ya mata miji Nijar can zata. Mimin Zaytoonah ma tana wurina. ** Ina zaune ya shigo na ajiye Amnah, na amshi jakarshi. "Barka da dawowa litikan zuciyata, sojan rayuwata. Chairman din duniyata ya aikin dai?" "Alhamdulilahi ki kira Zahrah ta amshi yarta yau zamu wuce Baihak za ayi nadin sarautar Maina, ban isa da Abin kunya ba." "Da gaske?" "Yes of course" Raka shi nayi zuwa dakinshi yayi wanka na bashi abinci yaci, sannan na fara ciro kayanshi da nawa da zamuyi tafiyar da su. ina gamawa na kira Zahrah. Ina gaya mata ta fara rikici kamar zata fasa ihu. "Mami don Allah ina xan.kai yarinyar nan wallahi yayeta zan yi ko na kaita wurin Umma Zuzu!" "Kaniyarki nima haka na yi fama da ku ni daya, oya kizo ki amshe ta sati zamu yi mu dawo." "Mami!" Kashe wayar nayi domin Yarana sun san lagona, yanzu sai su sauya min lissafi. Da dare suka zo suka dauki Yarsu. Gida na kuwa na barshi a wurin su Mama da Hajiya. Na bar Amina da Aliyu. ** Mun sha shagali na bikin nadin sarautar, sai a lokacin muka kebe da Yarinyar nan, ta kai ni bangaren Uwargidanta, wacce na yabada da hankalinta da kirkinta kwarai da gaske, Yanzu King Muhammad Maina yana da irin wannan matar ya auro fagal. na fada a raina. "Aunty Zahra ni ba fagal ba ce " rike bakina nayi, ta juyo tana kallona. "Kada ki gayawa Ya Majid ya karanci abinda yake ranki, domin zai gayawa Maina shi kuma zai cire rai da zan dawwama a rayuwarshi." Ta fada tana kyafkyafta idanu. "In sha Allah, Queen!" Na fahimci kowacce rayuwa da Y'a mace zata yi tana yin shine akan abu uku, Na farko Mijinta, na biyu Yaranta na uku domin kanta, abin da na fahimta kenan akan Queen, yaranta kyawawan gaske suna zagaye da ita domin wani irin so take musu, ina ganin tana share hawayen da yake zubo mata. "Me yasa kike kuka?" "Nasan ba xan yi nisan kwana ba ne, a koda yaushe mutuwa tana kara kusanto ni. Gashi wannan shine labarina The Last Empress" Amsa nayi ina rarrashinta, tare da saka mata iklasi da Tauhidi abin da na fahimci ya yi rauni a rayuwarta kenan. Na nuna mata ikon Allah ta hanyar bata labarina, sai gashi ta ware sannan wani abu da na fahimta tsoron kada wani abu ya faru da ita ta zama wata iri. Haka muka bar kasar muka dawo tun a jirgin nake son karanta labarin amma Ya hanani, muna isa gida bayan an huta mun nutsu kanshi yana cinyata, na bude farkon babin. "Bakar wata!" "Ke tsaya bana son labarin ban tsoro muje ki min tausa.." "Kayiwa kanka ba zan baka labarin ba nan gaba in sha Allah." Cak yayi sama dani zai wuce dani daki, Aliyu ya ce. "Ikon Allah na zata kun tsufa baku soyayya ashe, shi yasa kuka kore mu, tow sai an jima Ram Layla." "Yawwa Romeo dan sa'ido, me leken sirrin mutane!" Da gudu ya fita dan kimanin shekaru sha tara, shi da Aminah. Bayan shekara daya nayi bikin Alfah, ta tafi Nijar Aminatu kuwa Jikan su Mama ya ce yana sonta aka sha baki Sharhabil. Sai dan autana wai ce mishi suke dan hauka. Wata biyu da bikin, Allah yayiwa Nana rasuwa a hannun Alhajin Allahn ta, tsakanin Nana da Malamijo sati goma sha daya, ya rasu shima. A rasuwar ne muka sake haduwa Familyn Wodabbe aka yi hoton Familyn bakiɗaya. Addah kuwa tana can bata mutu ba, amma Allah ya daura mata jinya har da rubewar gaba sakamakon Cancer da ta kama. Muna yawan tattaunawa da Majid akan matsalarta. Nima ta bangaren lalurar kunnena sai godiya, na hakura domin har sau biyu ana min aika babu ji sai da wannan karamin abin jin. Haka daman rayuwa take, ba kome kake samu dukan ba, tunda na samu farinciki shi me sauki ne, Daman ai farkona na gani abin damuwar me zai faru a tsakiyar Alhamdulillahi Allah yasa mu cika da imani... Alhamdulilahi anan na kawo karshen bakin haure, wanda abinda ake nufi da sunan yan gudun hijira. Na gode sosai da bibiyar labarin da kuka yi.. sai mun hadu a ( the La empress) wanda zai zo maku a free in Sha Allah..... 300₦ 0016341139 unity bank zahra'u yahaya Ali Katin MTN 400 #Mai_Dambu ce.