Search
You have no alerts.

    Dingishin Kwado

    Bismillahir Rahamanin Rahim.

    1
    Shimfi’da

    *Karfe d’aya da rabi na talatainin dare a garin Katsina. Ruwa ake tafkawa tamkar da bakin kwarya. Garin ya yi sanyi. Baka jin komai sai zubar ruwan sama babu kakkautawa. Jefi jefi hasken walkiya na haska sararin samaniya.
    A daidai wannan lokacin da galibin mutane suke kwance suna barci cikin salama da nutsuwar zuciya a dalilin yadda garin ya dauki sanyi mai dad’i.
    Ni kuwa kwance nake gefen gadona hawaye d’aya na bin d’aya. Zuciyata ta kai makurar wajen nauyi akan al’amarin mijina. Na tashi na yi zaune na k’ara hasken fitilar gefen gadona(dim light).
    Na zuba masa ido ina masa kallo mai tsananin gaske. Ga shi nan dogo sambal. Fari tas kuma kyakkwan gaske.
    Duk inda ake neman namiji mai cikar halitta ya kai. Mijine na nunawa sa’a. Irin mijin da duk macen da ta ganshi sai ta ce wow. Domin hatta yanayin jikinsa tamkar ya zaba. Ba siriri ba ne, ba shi kuma da jiki. Komai na halittarsa tamkar da kansa ya yi. Mafi yawa k’awayena suna mini kallon na tafka sa’a. Idan kuwa muka yi hoto aka ga ni. An dinga fad’in kallon wannan mijin na ki kad’ai ya isa ya wanke miki zuciya.
    Hawayen idona ya sake yawaita a dalilin yadda tausayin kaina ya kama ni. Ni da kaina nasan kyawunsa ne abin da na gina aurena a kai. Cikin jerin abubuwa guda hudu da Annabi ya ce a duba a yayin aure.
    Annabi addinin mutum ya horemu mu fara dubawa. Ni kuwa sai na fara duba kyau, kyau ma iya na siffa na bi, ban nazarci na zuciya ba. Na shafe shekaru ina kuka sosai. Kukan kaico, kukan nadama. Amma a yau kukan ya BANBANTA da na baya. Domin kukan da nake yi a yanzu na kewa ne, na tsantsar bukatar a kad’aice da ni ne.
    Yanayin zafi da damina yana matukar sanya y’aya’ mata a cikin sha’awa mai yawa, yayin da maza tasu sha’awar tafi tsananta da sanyi.
    Na tsananta tunanin watanni da na kwashe a rataye. To a rataye mana, domin a baki ne nake matar aure. Yau watanni takwas kenan wani abu na auratayya bai gitta a tsakaninmu ba. A shekarun baya idan wani ya fad’a mini zamu shiga irin wannan yanayin ni da Baban Amrah zan musanta ne, na kuma ga beken mutum tare da jefa shi sahun y’an adawarmu.
    Sai gashi yau da gobe ta kawo mu wani irin bigire da muke rayuwa cikin wani mawuyacin hali kamar ba soyayya ce ta hada mu ba. Tamkar ba mune muka so juna ba. Na sani, shima ya sani a ka’idar shari’a mace ta kan yi hak’urin rashin namiji ne na watanni hudu matukar ba aure ne bata da shi ba.
    Amma a wannan zamanin da muke ciki mazaje na rataye matayensu na tsawon shekaru basu take su ba. Ba kuma sa jin d’ar ko tsoron had’arin da suke jefa mataye a ciki.
    Ni da kaina a yau tsoron Ubangiji ne zai sa na hadiye abin da nake ji a gangar jikina. Ba dan nasan hukuncin wacce ta yi zina da aurenta ba, da tuni na afka mata, tunda mazan wajen suna ganin k’uruciyata sabanin nawa mijin kallon na yi masa tsufa yake yi mini.
    Mata da yawa sun halaka a dalilin wannan matsalar. Maza sun yi sanadin jefa matan aure a cikin masifar zina da aurensu. Musulunci ya kange mace daga kowacce irin mu’amala da namijin da ba muharraminta ba. Mijinta kad’ai aka lamunce ta yi huld’a da shi kaitsaye. Hatta muharraminta ma akwai geji a mu’amala.
    To amma mazan yau loakcin yin hira da matansu ma basu da shi. Zai yini a wajen neman kud’insa. Idan ya dawo gida kuwa wayarsa ce abar hirarsa. Mace zata yiwa namiji magana, zai amsa mata hankalinsa na kan wayar hannunsa.
    Mace zata yi girki, ta yi kwalliya, ba za’a mata kallon rahama ba, har a gane irin kyaun da ta yi, bare a yabe ta ta ji dad’i.
    Ni kam tuni na cirewa kaina wannan damuwar. Na daina yin kwalliya saboda shi, na daina yin girki don ya yaba. Ina yinsu ne don iyalina. Ina yinsu dan kaina.
    Tuni na fita daga wannan matsalar tunda na gane bazan samu yadda nake so ba, sai na hak’ura nake yin dukkan abin da ya zame mini wajibi a matsayin ibada. Ibada kuwa yinta kake yi çike da juriya da addu’ar a karba.
    Abin da na kasa cirewa a raina daya ne, al’amarin shimfi’da.
    Juriyata ta tasamma karewa, hakan kuma na da nasaba da kasancewar jinine a jikina ba mai ba. Sannan halitta ce ban isa na zare sha’awa a tare da ni ba.
    Na mika hannu na zaro tissue din da take ajiye a gefen gadon.
    Na hau gogewa. Na dinga ambato Hasbunallahu wa ni’imal wakil a fili, na jima har na fara samun nutsuwa a tare da ni.
    Na jima ina tunanin na yi abin da zuciya take azalzalata ko kuwa na cigaba da jarumtar da nake yi.
    Cikin k’arfin hali da na zuciya na matsa kusa da shi, na kwanta na rungume shi ainun.
    Na sanya hannu na fara shafar sumarsa a hankali cikin nutsuwa da son na kunna shi.
    Tsawon lokaci ina ta shafarsa a wurare daban daban amma bawan Allah ya yi funfurufus tamkar da bulo alhalin na tabbatar idonsa biyu.
    Murya na rawa na ce “Baban Amrah shekaranjiya fa da bakinka ka ce sai yau”.
    Murya babu amo ya ce “To na sake d’agawa sai jibi idan na ji dad’in jikina, gabadaya ba ni da lafiya ba moruwa zan yi ba”.
    Yana rufe baki wani irin mololon abu ya tokare mini ya ninka nauyin da kirjina ya yi.
    Na kasa kukan. Na kuma kasa kwanciya.
    Fiye da shudewar awa guda ina zaune cikin kaduwar wulakancin da yake tata mini tamkar wacce aka bashi ni akan dole.
    Wai duk mata ne idan sun haihu, zama ya fara nisa sosai suke fuskantar wulakanci da tozarcin namiji ko kuwa ni ce kawai?
    Jiya na cika shekaru talatin da biyar da haihuwa.
    Amrah da itace babbar diyata tana da shekaru goma sha hudu.
    Sai k’aninta Faruk mai shekaru sha 12, sai kuma k’aramarsu Farha mai shekaru biyar.
    Shekaru biyu kenan da sake tsanantar lamarin. Na kuma hakkake ba zai daina ba, domin kullum da kalar wanda zai yi mini. Har ta kai jallin fargaba nake mu zauna inuwa d’aya da shi.
    Duk yadda na debe kunya na sake nemansa, amma ga abin da ya sake fad’a mini tamkar wancan karon.
    Wanne irin zalunci ne haka da k’etare iyakokin shari’a?
    Ganin zan yi asara biyu. Sai kawai na mike na doro alwallah na hau nafila ina tsananta addu’ar a kare ni daga afkawa b’arna.
    Ina kan sallaya aka yi kiran assalatu. Sai lokacin ya yi mik’a ya tashi ya zauna.
    Ni kuwa na mike na sake tada sallah dan yin raatainin fijir.
    Da k’yar ya yunkura ya shige bayi.
    Ya fito ya yi nafila sannan yasa ya kai ya fice uffan bai ce mini ba.
    Da na ji masallaci sun tada sallah sai nima na mike na yi tawa sallar cikin kankan da kai.
    Na riga na saba da zama kan sallaya har rana ta keto.
    Sannan na mayar da nafila sai kuma na fita kicin na saka ido akan y’an aiki.
    Dankalin turawa na bawa Alti mai aikin abinci umarnin ferewa da soyawa.
    Yayin da na hau hidimar dama kunu tsamiya. Amma da lemon tsami zan yi.
    Ita kuwa Alawiyya tana hidimar gyara falo da goge shi, tare da taimkawa Farha a shiryawa.
    Kafin bakwai na safe mun kammala komai an shirya abincin kan dining.
    Dukkan yaranmu sun shirya cikin uniform. Amrah ce makarantar ta daban yayin da Faruk da farha suke makaranta daya.
    Cikin walwala muke karyawar tamkar bamu da damuwa.
    Tare muka fita, shi ya wuce da Amrah yayin da ni na wuce da Faruk da Farha makarantarsu tunda Farha ma a pri 1 take yayin da Faruk yake a sakandire.(Js2)
    Har bakin gate din makarantar na kai su, suka fita suna fad’in “Thank you Mahmah! A dawo lafiya”.
    Na amsa ameen my dearies a yi karatu lafiya “.
    Cikin nutsuwa nake tukin har na isa cikin jami’ar Umaru Musa Y’ar addu’a(Umyu).
    Na adana motar a inda aka tanada. Na fito cikin nutsuwa na nufi ofishina da yake a tsangayar kimiyya da fasaha.
    K’ananun ma’aikatu sai gaisuwa suke miko mini cikin girmamawa, ina amsa musu cikin sakin fuska tare da mututantawa.
    Da Bismillahi na zauna akan kujera.
    Na ajiye jakar hannuna, da na siya a Egypt wajen *Umm Aslan&Asalah Egyptian Items* tare da fito da wayata. Na kalli agogon da yake daure a hannuna na ga saura mintina goma sha biyar na fara bada darasi.
    Na fito da ruwan faro daga fridge. Ba wani sanyi tabbacin yanzu aka saka da aka yi sharar office din.
    Na dauki abubuwan da zan bukata na fita zuwa hall din da zan bada darasin pharmacology.
    Duk inda na gitta dalibai maza da mata idanuwansu na kaina. Ni kuwa ina ta maimata addu’ar “Waallahu yas’muka minan nasi. Domin kaucewa kaifin idanuwansu. Sau tari akan kunne zan ji yaran matan suna fad’in “wannan mata ta had’u, ta morewa rayuwar duniya, komai ta hada, asali, kyau, ilimi, kudi, miji mai kyau, kyawawan y’aya’ ga lafiya.
    Ita kam mun rasa menene gibinta a rayuwar nan da ake cewa mutum tara yake bai cika goma ba.
    Ni kuwa murmushi kawai nake yi domin dukkan abin da suka lissafa hakane. Sai dai tawayar da na ke fama da ita, itace mafi munin tawayar da za’a jarrabi mace irina da shi.
    Hatta wasu cikin danginaa irin wannan kallon suke mini duk da kuwa kafatalin mazan sisters dina sun fi nawa mijin kudi amma kowa kallon the most peaceful marriage ake yiwa aurena
    Amma deep inside ni nasan abin da nake fuskanta. Ni kad’ai nasan gashin k’umar da mijina yake yi mini.
    Mafi yawa kuma haka mata irina suke fuskantar kalubale daban daban.
    Amma na riga na yi imani komai yana tafiya ne bisa ikon Allah.
    Ba komai kake so kake samu ba, mutum kuwa bai samun yadda yake so matukar a cikin wannan duniyar ne da babu cikakken jin dad’i a cikinta.
    Cikin nutsuwa na isa d’akin da zan gabatar da darasin. Na yi musu cikin gogewa da saukakken kuma gangariyar turanci.

    Cikin abin da yake debe mini kewa har da koyarwa da nake yi.
    Yana cikin abin da yake samar mini da nutsuwa na manta damuwowin da nake kwana na yini a cikinsu.
    Yau har yamma ina cikin makaranta dan haka na biya na dauko yara tunda suma sai after biyar suke tashi a ciki suke islamiya.
    Tun kafin na yi horn maigadi y a bude mini katafaren gate din gidan namu.
    Kafin na kammala tsayar da motar ya fito yana danne danne wayar da ya zame masa ka’ida da dabi’a.
    Yadda yaran suke masa hugging suna fad’in “We are back Dady, sannu da gida”.
    Suka shige da gudu, nima haka ya karaso ya rungume ni tare da karbar jakar hannuna yana fad’in “Welcome dear”.
    Na amsa da murmushi da ce wa “Thank you!
    Tare muka shiga cikin katafaren falon.
    Kaitsaye dakina muka nufa. Ya shiga taya ni cire tufafin jikina.
    Abin wuya ya cire mini. Ya zuge zif din doguwar rigar atamfar da take jikina. Wanda dinkin ya yi matukar zauna mini tamkar y’ar shekaru talatin.
    Na yi saura daga ni sai bra da pant da siket.
    A maimakon ya tsikari kirjina kamar yadda aladarsa take sai kawai ya koma gefen gadon ya kishingide tare da mayar da hankalinsa kan wayar da ta sake zame mini tashin hankali a rayuwar aurena.
    Na sake yin jarumtar mazewa na shiga wanka.
    Har na fito na shirya bai ankara ba, don kuwa ya riga da ya yi nisa a sabon shafin da ya bude.
    Duk yadda na so na cigaba da jarumtar cigaba da kawar da kai akan lamarin wayarsa abin ya ci tura.
    Dan haka na fara tunanin lokacin da zan shammace shi na dauka. Tabbas sai idan yana barci cikin dare. Domin yana cikin jerin mutane masu nauyin barci.
    Haka duk tsananin rudani da tashin hankali baya hana shi barci.
    Ba jimawa suka fice zuwa masallaci shi da Faruk.
    Gabadayanmu da yara muna falo, maimakon ace muna hira cikin farin ciki da walwala.
    Amma kowa da wayarsa a hannu yana nausawa cikin yanar gizo.
    Ogan nafi zaton chart yake yi da wacce take birkita shi. Ni kuwa ina cikin group din mu na old girls muna tattauna yadda taron reunion din da zamu yi zai kasance.
    Amrah kuwa bincike take yi tana aikin gida akan wani darasi da aka yi musu a makaranta aka kuma basu aikin gida a kai.
    Yayin da Faruk yake yin game. Farha kuwa hankalinta na kan tafkekiyar allon talabijin din tana kallon katoon.
    Na ajiye tawa wayar ina nazarinmu gabadaya. Jikina ya yi sanyi yadda waya take lashe mana dukkan lokutanmu. A shekarun baya a lokacin da yaranmu suke kananu sosai waya bata shiga jikinmu irin haka ba. Amma a yanzu mafi yawan mutanan wannan karnin sun fi girmama sha’anin waya fiye da komai.
    Na saki ajiyar zuciya na ce “Daddy, Amrah, Faruk, Farha dinner is ready”.
    Na mik’e na nufi dining din. D’ayan bayan d’aya suka biyo ni har muka hallara.
    Kowa da kansa ya yi serving kansa as usual.
    Mun ringa mun saba da rashin magana idan ana cin abinci dan haka ba a jin komai sai karo tsakanin tangaran da tsokali.
    Mun kammala aka fara kiran Isha. Dan haka muka hau haramar yin sallah, yayin da Daddy da Faruk suka sake ficewa zuwa masallaci kamar yadda suka saba.
    **
    Dare ya yi nisa. Na mirgina na tab’a shi na tabbatar ya yi nisa. Sai kawai na lallaba na zaro wayarsa da take karkashin filonsa.
    Jikina na bari na fice zuwa falo bayan na mayar da tawa wayar gurbin da na zare tasa.
    Na zauna a bakin kujera, na fara kokarin cire password din, na rubuta sunana da babban bak’i BILKISU amma bata bude mini ba. Na sake rubuta Bili nan ma bata bude ba.
    Kaina ya kulle yaushe ya canja? Na tambayi kaina a rude.
    Na yi jim ina nazarin me zan saka ta bude mini domin ina jin tsoron kada na cike adadin da zata ki buduwa gabadaya.
    Da zullimi na rubuta B Funtua nan ma bai bude ba. Cikin sa’a na sake rubuta Faruku Sm sai ta budu.

    0 Comments

    Heads up! Your comment will be invisible to other guests and subscribers (except for replies), including you after a grace period.
    Note
    error: Content is protected !!