489 Results in the "Hausa Novels" category
-
Blog
KANWAR MATATA
*🦜 _Matar Sayyadee_ _Wattpad @Matar_Sayyadee_ _K’anwar Matata ba kirkirarren labari bane! Sai da na samu yarda da aminta sannan na soma rubuta shi. Dan haka idan yayi shige da naki irin labarin, arashi aka samu. Sannan ina gargad’i da babbar murya, ban yarda a juya min labari ta ko wani siga ba, ba tare da izini na ba ko kuma a d’aura min…
-
Story
Ajiya A Duhu
……..Sosai ciwon kai yay ma Maanal rijib a wannan yinin isowarsu Abuja, shima kuma AA ɗin zuwa yamma dole aka saka masa drip ma, dan sam baya jin wani ƙarfin jikinsa. Har cikin dare ba’a gama saka masa ruwan ba dan kusan leda uku ne. Dole Fawzan ya kwana tare da shi bisa umarnin Abah. Oum taso yin magana amma tai shiru, dan ita… -
Chapter
Bakar Ayah – Chapter Thirty-four
Wani yarone ya shogo gidan da takarda a hannunsa cikin envolope,Innar iyani ya fara gaisarwa,wacce take zuzzuba abinci a kwanuka. "Uhm dama watace ta aikoni gidannan wai nabawa Hajiya zeenah abinnan" Iyani tanajin haka tayi saurin karbar takardar tareda cewa. "Wacece matar,tana waje har yanzu?" "Tasaka nikaf,tana bani takardar tajuyah ta tafi" "To shikenan jega an gide,bari dama zan kaimata abin karyawa saina tafi mata dashi" "Wani kallon mai kuke ƙullawa innartata tabita dashi,ganin bazai kaitaba ta… -
Chapter
Bakar Ayah – Chapter Twenty-two
Kwatancen da mai masarar ya gwada mata tabi tiryan tiryan har ta samu kanta a ƙofar gidan su goje. Tsayawa tayi a bakin dangar gidan ta riƙe kunkumi tana kallon gidan. "Hmm wai nan gidan baba yakeson nazo na zauna na ƙare rayuwata,nida nakeda burin fita daga nahiyar nan,shine zanzo wannan wajen na zauna,lallai baba yanzu na tabbatar ya rainamin hankali ba kaɗan ba,shi bayyi zaman irin gunnan ba saini Bombee?" Maganar ce daga bazata kaita ba,dan haka kawai tasaka kai cikin gidansu goje babu ko… -
Ana gama ɗaura auren yaji wani nauyi ya sauƙa a ransa,duk da cewar ba haka yaso auren yar tasa yazo ba,amma kuma yaji daɗi ganin ya aurar da ita kafin tagama fin ƙarfinsa. Yaso tayi karatu tazama wani abu a wannan rayuwa saboda takare kanta,amma kuma kana naka Allah yana nasa,inaga wannan shine tata kaddarar ba wacce yake zata mata ba,fatansa shine allah yabasu zaman lafiya da mijinnata. A ranar kuma Daneji ta haɗu abun bazata,wanda bazata ta'ba mantawa ba. Shatu ce tayi mata magana daga ɗaki kan…
-
Chapter
Bakar Ayah – Chapter Twenty-four
Bugun ƙofar da ake ne yafarkar da ita daga baccin gajiyar daya ɗauketa. A hankali take buɗe idonta har ta waresu akan rufin ɗakin,wanda aka haɗa da zare da kuma jarida. Tashi tayi ta zauna a tsakiyar gafon tareda yin wata kyakykyawar hamma,kaman wanda ta shekara bataci komai ba. Kallon gabas da yamma kudu da arewa tayiwa ɗakin,ta tabbatar dai ita kadaice ta kwana a ɗakin kenan,angonnata bai shigoba da alama,to mai yahanashi zuwa ta faɗa a ranta,ganin hakan zai bata mata lokacin yasa ta bar ma… -
Chapter
Bakar Ayah – Chapter Twenty-five
Sauƙe ajiyar zuciya tayi ganin ashe akwai ƙaramin wando a cikin dogon daya cire,saidai kuma an gudu ba'a tsira ba,gani tayi wandonnasa yana ɗagawa kaman wani abune yake motsi a cikinsa. Dariyah ya kece dai ta ganin inda idonnata ya sauƙa,wato kan hajiyar sa. "Hhhh ƙwaila kenan,tun ba akai ga komai ba harkin fara karayah,ima tsiwar taki da aka bani labari toh,ki shiryah yanzu zanyi miki abinda nake wa sauran ƴaƴa wanda kike ji da kunnenki a gari. Naji dama ance kinzo gidannan neman sanin wayeni… -
Chapter
Bakar Ayah – Chapter Twenty-six
Dukkansu sakin ajiyar zuciya sukayi na takaicin sakarcin Bombee ɗin,saidai babu yadda zasuyi ba laifinta bane,tunda kowa yasan ita yarinya ce,sannan a yanda take da kasada,da kuma yanda goje ya farmaketa,koma waye iya abinda zayyi kenan. Malm Ahmadu bashida zabi illah ya ɗora kusan dukkan laifin a kansa,tunda shine ya aurarta batareda tasan komai ba. Shiryawa yayi shida su jauro suka nufi asibitin,domin ganin jikinsa tanan kuma zasu wuce police station akan case ɗin. Bombee kuwa ganin kowa ya dauke… -
Bayan shekara biyu............. Kyakykyawa kana farar budurwace sanye da riga da wando farare,tayi ɗamara da wani jan ƙyalle a mulmulallen kunkuminta wanda yabaje yabada siffar mata masu cikakken diri,saidai daga ganin jikin kasan ana yawan motsashi,dan a tsikeyake tsama. Juyi take tayi gaba tayi baya da sanda a hannunta,wanda take tafiyar dashi a iska cike da bajinta da kuma ƙwarewa. Tayi kaman sa'a guda tana yi,amma batada alamar dainawa ko nuna gajiyarwata. Sai can kaman da daƙiƙa uku ta tsayah…
-
Miƙewa tayi gwiwa a sabule jin abinda innar tata tafaɗa. Hanyar waje tafita kanta a sunkuye,tana jiyo maganar mutane a bakin kofar gidan,wanda tuk yawancin maganar ta ne da abin tirrr da Allah wadai datayi. Sauri take tayi nesa da maganganun,dan ba komai suke kara mata ba sai dake daskarar mata da zuciya,maimakon suyi tasiri wajen saka zuciyar laushi. Sai dare yaraba tukunna tashigo gidannasu,sassafe kuwa kafin kowa yatashi ta fice a gidan. A gari taji labarin an kai mahaifinta asibiti jininsa ya…
-
Chapter
Bakar Ayah – Chapter Twenty-nine
A hankali take bude idanuwanta wanda sukayi mata nauyi tamkar anɗora mata dutsi akai. Saurin yunƙurawa tayi zata tashi,amma saitaji jikinta tamkar an ɗaɗɗauresu da wasu boyayyun zarurruka. Ɗakin haskene dashi amma bana hasken rana ba ko kuma fitila,sai na tsabar farin fentin cikin ɗakin. Alamar motsi tafaraji a kanta,a hankali take daga kannata harta sauƙeshi akan fankar datake wainawa tana bawa ɗakin wadatacciyar iska. Baki tasake cikeda mamaki ,dan tunda take bata taba kallon waje mai irin haka… -
Chapter
Bakar Ayah – Chapter Thirty
Sauri take tayi cikin duhun dare,da alama fitsarine ya kamata sosai. Tazo daidai hanyar shiga banɗakin taga alamar wulagawar mutum a sashen goje. Ƙiftawa ido tayi tasake ƙiftawa,dan zaton ko aljani tagani,saidai kuma ta kawar ta hakan a ranta ta wuce banɗakin. Bayan tafito harta nufi ɗakinsu saikuma tashi alamar motsi a sashen kumadu. "To waye ne yashige sashen goje,shekara biyu kenan yadaina kawo mata,tunda kowa yasan babu abinda zai iya yi musu,to waye kuma a sashennasa?" Harzata shiga ɗakin kuma… - Previous 1 … 8 9 10 … 29 Next
