Search
You have no alerts.

    492 Results in the "Hausa Novels" category


    • Rayuwa Da Gibi – Chapter Seventeen Cover
      by Nadmin MASU ƁUKATAR A TALLATA MUSU HAJOJINSU ZA SU IYA TUNTUƁARMU TA LAMBOBIN 07045308523 MUN GODE Kallon da Abba ya yiwa Taj na tsantsar ƙauna da girmamawa ne bayan ya gama mamaki. Ya miƙe tsaye ya kama hannun daman Taj da hannayensa biyu. "A duniya bayan iyayena da matata da kuma ƴan uwana da ba su guje ni ba da kuma ƙalilan cikin abokai, kai ne mutum na farko da jini bai haɗamu ba amma kullum burinka ka sanya farinciki a rayuwata." Kamal samun kansa ya yi da girgiza kai saboda tsoron kada ya amince da…
    • Rayuwa Da Gibi – Chapter Eighteen Cover
      by Nadmin MASU ƁUKATAR A TALLATA MUSU HAJOJINSU ZA SU IYA TUNTUƁARMU TA LAMBOBIN 07045308523 MUN GODE "Ayyyyyyiririiiiiiiii. Allah mungode maKa. Hajiya Jinjin uwargidan Habibu namu asa goshiia ƙasa a miƙa godiya ga Sarkin sarakuna. Allah Ya kwashe miki ƴan matanki a sa'a guda. Wannan farar juma'a ta amare uku ce rigis. Sai a saurari zuwan ƴan dugwi dugwi iyalan Baba." Ba kowa bane da wannan aiki sai Ƴar Ficika daga soron gidan. Yana gama magana kuma yaransa su ka amshe guɗar su na yi. Yaya fitowa tayi daga…
    • Rayuwa Da Gibi – Chapter Nineteen Cover
      by Nadmin MASU ƁUKATAR A TALLATA MUSU HAJOJINSU ZA SU IYA TUNTUƁARMU TA LAMBOBIN 07045308523 MUN GODE Snacks lodi guda jere akan trays Zahra da Salwa su ka dinga shiga dasu falo. Komai da zafinsa saboda yanzu aka soya. Sai sassanyan zoɓo da kunun aya sun sha ƙanƙara a cikin jugs. "Zahra mun tayar dake tsaye ba notice ko? Da ba ki wahalar da kan ki ba. Yanzu mu ke shirin watsewa." Cewar Ya Zulaiha. Zahra tayi murmushi "ko yaya dai ya kamata ku ci. Abinci na so ɗorawa sai Salwa ta bani shawarar sayen frozen…
    • Rayuwa Da Gibi – Chapter Twenty Cover
      by Nadmin MASU ƁUKATAR A TALLATA MUSU HAJOJINSU ZA SU IYA TUNTUƁARMU TA LAMBOBIN 07045308523 MUN GODE Bayan sallar asuba Taj ya kira Kamal domin su yi sallama. Jiya basu sami haɗuwa a gida ba. Ya yi ta waya shiru Kamal ɗin bai ɗauka ba. Wanka ya yi ya gama shiri da sauri ya sake duba wayar. Abin mamaki Kamal bai bi kiran nasa ba. Da wahala hakan ke faruwa. Jikinsa sai ya bashi ko ba ƙalau ba. Abba ƙaninsa ya kira ko tunawa da lokaci bai yi ba. "Happiness ya fito sallar asuba kuwa?" Abba ya ɗan wartsake idanu…
    • Rayuwa Da Gibi – Chapter Four Cover
      by Nadmin MASU ƁUKATAR A TALLATA MUSU HAJOJINSU ZA SU IYA TUNTUƁARMU TA LAMBOBIN 07045308523 MUN GODE Auren Habibu da Jinjin ba na son zuciya bane kamar yadda ƴaƴansu suke hasashe. Yar mahaifinsu da suka fi ɗorawa alhakin saboda sunanta da Zee tace wato Anti Zinatu ma ba laifinta bane. Abu ne na karamci da sanin darajar wanda ya kiyaye taka darajar. Aure ne na zumunci domin kuwa kamar yadda Iyaa da Baba Maje suka fito daga zuri'a ɗaya su ma iyayensu mata shaƙiƙan juna ne. Mahaifiyar Habibu ita ce babba. Tayi…
    • Rayuwa Da Gibi – Chapter Six Cover
      by Nadmin MASU ƁUKATAR A TALLATA MUSU HAJOJINSU ZA SU IYA TUNTUƁARMU TA LAMBOBIN 07045308523 MUN GODE "Alhaji..." "Zan saɓa maka." Ba yadda ya iya. Cikin minti shabiyar ya sama musu tasi su huɗu suka kama hanya. Mama da Inna ba su san me ake ciki ba. Shi kuwa Alhaji tunda yaga sunan makarantar a bakin gate jikinsa ya soma tsuma. Ahmad dai jikinsa duk ya mutu. Ya yi kiran Taj ɗin da su ka shiga bai ɗauka ba. Da tambaya su ka ƙarasa wurin da ake gasar inda mutane su ka yi dafifi kamar ƙudaje. Basu wani sha…
    • Rayuwa Da Gibi – Chapter Seven Cover
      by Nadmin MASU ƁUKATAR A TALLATA MUSU HAJOJINSU ZA SU IYA TUNTUƁARMU TA LAMBOBIN 07045308523 MUN GODE Kyakkyawan envelop Yaya Babba ya miƙawa Alhaji ya kuma bishi da kallo a tsanake don son karantar yanayinsa. Kamar yadda ya yi tsammani duk wani annuri da walwalar da yake tare da ita a farkon zamansu tsaf ya kau. Duhun da yake zuciyarsa ya sami damar nuna kansa a fuskar. Disappointment ɗinsa akan Taj ya kashe masa jiki da zai yi magana. "Kawo maka ya yi?" Da Yaya Babba ya gyaɗa kai sai ya ce "to me yake…
    • Rayuwa Da Gibi – Chapter Eight Cover
      by Nadmin MASU ƁUKATAR A TALLATA MUSU HAJOJINSU ZA SU IYA TUNTUƁARMU TA LAMBOBIN 07045308523 MUN GODE Ummi dai baje kolin rashin mutumcinta tayi akan Hamdi har ya kasance sauran ɗalibai suna samun sararawa. Kowanne aiki Hamdi, kowacce bola da shara ma ita ɗin dai take nema. Wanki harda na su pant ita take mata. Su ɗebo ruwa da kwafar note dama tuni ta daina saka wasu. Kuma ko da wasa Hamdi bata taɓa faɗin wata kalmar neman sauƙi ba. Komai Ummi ta ce 'to' ce amsar. Ita dai burinta ta bar makarantar ba tare da…
    • Rayuwa Da Gibi – Chapter Nine Cover
      by Nadmin MASU ƁUKATAR A TALLATA MUSU HAJOJINSU ZA SU IYA TUNTUƁARMU TA LAMBOBIN 07045308523 MUN GODE Zazzaɓin gaske ne ya kama Ummi tun bayan ta saurari wayar Vice principal da mahaifinta. Aikin gama ya riga ya gama. Bayan ya ajiye wayar wani irin kallo ya yi mata ya jinjina ƙarfin halinta. Sannan ya ƙara tabbatarwa mace abar tsoro ce komai ƙanƙantarta. "Wannan mutumin shi ne mahaifinki Ummi?" Kai a ƙasa ta ce "eh." "Wanda yake zuwa kuma ya kuke da shi? Kuma me yasa ki ka zaɓi faɗin gaskiya yanzu?" Shiru…
    • Rayuwa Da Gibi – Chapter Ten Cover
      by Nadmin MASU ƁUKATAR A TALLATA MUSU HAJOJINSU ZA SU IYA TUNTUƁARMU TA LAMBOBIN 07045308523 MUN GODE Irin kukan da Iyaa tayi bayan jin tsiyar da Ummi take shukawa dole ya bawa mutum tausayi. Bayan an kai ruwa rana a station ɗin da su ka je Baba Maje ya gane duk inda yake tunanin Ummi ta wuce nan. Fitina da gagara ta ƴan matanci kam tana bugawa a bayan idonsa. Ya sake yarda ba a shaidar ɗan yau. Ba don da bakinta ta amsa laifukanta ba da ya yi rantsuwar sharri ake yi mata. Ummin da ya sani daban. Wadda ya dawo…
    • Rayuwa Da Gibi – Chapter Eleven Cover
      by Nadmin MASU ƁUKATAR A TALLATA MUSU HAJOJINSU ZA SU IYA TUNTUƁARMU TA LAMBOBIN 07045308523 MUN GODE Numfashi ta sake saukewa a hankali bayan ta karɓi loudspeaker ɗin sannan ta rufe ido ta buɗe da sunan Allah. Da ido ta lalubo Taj wanda har ga Allah tayi matuƙar mamaki da ta iya gano shi a cikin mutane. Bata sani ba ko hakan yana da alaƙa da sahun gaba da ya dawo ya tsaya a jikin ƙarfen canopy bayan kusan kowa a zaune yake. Ya yi mata murmushi gami da gyaɗa kai kamar mai bata damar yin magana. Mantawa…
    • Rayuwa Da Gibi – Chapter Twelve Cover
      by Nadmin MASU ƁUKATAR A TALLATA MUSU HAJOJINSU ZA SU IYA TUNTUƁARMU TA LAMBOBIN 07045308523 MUN GODE Yadda ya gaisa da kowa da zai wuce haka ya tsaya su ka yi musabaha da wanda ya rako su. Sannan ya ɗagawa Taj da Kamal hannu yana ɗan ranƙwafawa kamar yadda ya gaisa da sauran mutanen da su ka gani. "Ƴan samari barkanku dai. Ya sanyi sanyi? Ya ayyuka? To Allah Ya yi jagora." Ya dubi mutumin da da ya yi mu su rakiyar ya ce "na barku lafiya." "Dakata Mal. Habibu. Waɗannan fa kai su ke nema." Tsayuwa ya yi ya…
    Note
    error: Content is protected !!