Search
You have no alerts.

    496 Results in the "Hausa Novels" category


    • Rayuwa Da Gibi – Chapter Thirty-two Cover
      by Nadmin MASU ƁUKATAR A TALLATA MUSU HAJOJINSU ZA SU IYA TUNTUƁARMU TA LAMBOBIN 07045308523 MUN GODE "Salwa kuma Alhaji? Wani abu tayi?" Ahmad ya yi tambayar ne saboda a tunaninsa ciwon Kamal kaɗai ya isa ya gigita Alhaji. Me zai sa ya tuna da Salwa har ya nemi a taho da ita a lokaci mai mahimmanci irin wannan? Gwiwa a sage ya tambaye shi "Laifi tayi ko?" "Kai dai ka taho min da ita." Yana bashi wannan amsar ya gane ko ma mene ne ba abin wasa bane tunda lalura mai girma kamar ciwon ƙodar Kamal bai hana shi…
    • Rayuwa Da Gibi – Chapter Thirty-three Cover
      by Nadmin MASU ƁUKATAR A TALLATA MUSU HAJOJINSU ZA SU IYA TUNTUƁARMU TA LAMBOBIN 07045308523 MUN GODE Rashin walwala da kuzarin Taj har su ka idar da sallah yasa Hamdi wasu irin tunani marasa daɗi. Me tayi masa? Ko wani abu ne ya same shi? Ko kuwa wani abu yaji wanda bai yi masa daɗi ba? Idan sun haɗa ido sai ya yi murmushin da iyakarsa fatar baki. Cikin idanunsa fargaba take gani. Tayi zaton mata ko ace amare ne kaɗai su ke shiga yanayin tsoro a irin wannan dare. Ashe harda maza. Kai, amma bata zaton haka a…
    • Rayuwa Da Gibi – Chapter Thirty-four Cover
      by Nadmin MASU ƁUKATAR A TALLATA MUSU HAJOJINSU ZA SU IYA TUNTUƁARMU TA LAMBOBIN 07045308523 MUN GODE A cikin yanayin ciwo da gajiyar jiki Kamal ya buɗe idanu ya miƙa hannu zai ɗauki wayarsa. A gadon asibiti yake inda yake samun kulawa ta musamman. Da yake dokar asibitin ba a zaman jinya, shi kaɗai ne a ɗakin. Alhaji da su Ahmad suna hotel kusa da asibitin. Tafiyar just ƙafa ke kawo su. Tare dashi su ke wuni sai takwas na dare idan an buƙaci duka baƙi da masu ziyara su fita sannan su ke tafiya. Kwanaki…
    • Rayuwa Da Gibi – Chapter Thirty-five Cover
      by Nadmin MASU ƁUKATAR A TALLATA MUSU HAJOJINSU ZA SU IYA TUNTUƁARMU TA LAMBOBIN 07045308523 MUN GODE Saɓanin baƙin jiya da bata gama sabawa dasu ba, yau da yake Yaya Hajiyye da Firdaus ta zo sai Hamdi tayi saurin sakewa. Ga albishir ɗin tafiyar Yaya da ya sake faranta mata rai. Kitchen su ka shige da Firdaus suna ƙusƙus. A falo kuma Taj ne da Yaya Hajiyayye su ke tasu hirar. "Wai ka san Kubra tare su ka tafi da Alhaji? Ko ni kaɗai ce ban san da tafiyar ba?" "Bana son jin kowa na faɗin bai sani ba. Sai nayi…
    • Rayuwa Da Gibi – Chapter Twenty Cover
      by Nadmin MASU ƁUKATAR A TALLATA MUSU HAJOJINSU ZA SU IYA TUNTUƁARMU TA LAMBOBIN 07045308523 MUN GODE Bayan sallar asuba Taj ya kira Kamal domin su yi sallama. Jiya basu sami haɗuwa a gida ba. Ya yi ta waya shiru Kamal ɗin bai ɗauka ba. Wanka ya yi ya gama shiri da sauri ya sake duba wayar. Abin mamaki Kamal bai bi kiran nasa ba. Da wahala hakan ke faruwa. Jikinsa sai ya bashi ko ba ƙalau ba. Abba ƙaninsa ya kira ko tunawa da lokaci bai yi ba. "Happiness ya fito sallar asuba kuwa?" Abba ya ɗan wartsake idanu…
    • Rayuwa Da Gibi – Chapter Twenty-one Cover
      by Nadmin MASU ƁUKATAR A TALLATA MUSU HAJOJINSU ZA SU IYA TUNTUƁARMU TA LAMBOBIN 07045308523 MUN GODE Na ɗan taƙin lokaci ƙwaƙwalwarsa ta so ƙullewa har ma ya faɗi abin da bai yi niyya ba. Cikin sa'a sai ya tuno abin da ya tanadi faɗawa duk wanda ya ganshi a wannan yanayin. Murmushi ya yi mata sannan ya ɗaga hannuwa da ƙafafunsa yadda za ta gansu sosai. "Mene ne wannan Kamal? Me ya same ka kake irin wannan kumburin?" Ta ƙarasa inda yake tana tattaɓa shi. "Allergy ne Umma. A haka ma kumburin ya sauka…
    • Rayuwa Da Gibi – Chapter Twenty-two Cover
      by Nadmin MASU ƁUKATAR A TALLATA MUSU HAJOJINSU ZA SU IYA TUNTUƁARMU TA LAMBOBIN 07045308523 MUN GODE Da farko da taji ƙarar wayar cikin baccin da ya fara ɗaukarta tsorata tayi don ta manta da ita. Niyyarta ta barta ta gama sai ta kashe, ko waye ya kira da kansa. Ita ba mai son amsa wayar mutane bace. Wani kiran ne ya sake shigowa immediately bayan na farkon ya katse. Ta daure ta wartsake idanu ta kalli sunan mai kiran SALWA B. Wani irin tunani ne ya shiga karakaina a ƙoƙon ranta. Meye ma'anar B ɗin? Bichi,…
    • Rayuwa Da Gibi – Chapter Twenty-three Cover
      by Nadmin MASU ƁUKATAR A TALLATA MUSU HAJOJINSU ZA SU IYA TUNTUƁARMU TA LAMBOBIN 07045308523 MUN GODE Ko sakan 30 ba ayi ba tsakanin fitar Salwa da shigarsu ciki Taj ya turo gate ɗin. Kamal ya yi mamakin ganinsa tsaye daga waje. Shi kuwa yafito shi kawai yake da hannu. Cewa Hamdi ya yi ta ɗan jira shi. Ko kallon Taj ɗin bata yi ba domin ranta a ɓace yake. Bata son yanayin da take jin zuciyarta a ciki. So take ko dai taga dawowar Salwa ciki ko kuma ita tayi hanyar gidansu. Kafin Kamal ya ƙarasa gate ɗin sai…
    • Rayuwa Da Gibi – Chapter Twenty-four Cover
      by Nadmin MASU ƁUKATAR A TALLATA MUSU HAJOJINSU ZA SU IYA TUNTUƁARMU TA LAMBOBIN 07045308523 MUN GODE Har su ka ƙarasa gida idan sun kalli juna sai sun yi murmushi. Abin da ya ɗaurewa Hamdi kai shi ne yadda Taj har wani kawar da kai gefe yake irin na masu jin kunya. To ai ita ma kunyar take ji. Kuma ita ya dace ta dinga yin haka. Sai gashi kafin tayi yake yi. Gajiya tayi lokacin sun iso layinsu ta kalle shi. "Wai mene ne?" Gefe ya kaɗa kai yana wani rufe ido "Awwnnnnn, ni ki daina tambayata. Kin fi ni sanin ko…
    • Rayuwa Da Gibi – Chapter Twenty-five Cover
      by Nadmin MASU ƁUKATAR A TALLATA MUSU HAJOJINSU ZA SU IYA TUNTUƁARMU TA LAMBOBIN 07045308523 MUN GODE Lallai Alh. Mukhtar ɗinnan ya gamu da sharrin Mami shi ne abin da Alhaji ya fara rayawa a ransa bayan sun gama waya. Yadda ya dinga koro bayani akan irin son da ƴarsa take yiwa Taj da fatan amincewar Alhajin don ayi aurensu kai ka san kan ba ƙalau ba. Shi dai yana son ƴaƴansa, amma fa yana ganin babu ƴar da ta isa ta saka shi zubar da mutumci haka a gaban tsohon mijin matarsa. Irin waɗannan abubuwan ya…
    • Rayuwa Da Gibi – Chapter Twenty-six Cover
      by Nadmin MASU ƁUKATAR A TALLATA MUSU HAJOJINSU ZA SU IYA TUNTUƁARMU TA LAMBOBIN 07045308523 MUN GODE Taurin zuciya ya hana Hamdi kukan da sauti. Sai hawaye kawai da ajiyar zuciya. Ji take kamar ta buɗe ido ta ganta a gaban Yaya. Auren za ta ce ta fasa da gaske. Gashi dai zuciyarta tana ƙaunarsa. Ƙauna da son da har yanzu bata taɓa faɗa masa ba saboda kunya da jan aji na mata. Sai dai tayi abin da zai gane shi ɗin mai matsayi ne babba. Tana tanadin kalmominta masu tsada zuwa lokacin da za su kasance a…
    • Rayuwa Da Gibi – Chapter Twenty-seven Cover
      by Nadmin MASU ƁUKATAR A TALLATA MUSU HAJOJINSU ZA SU IYA TUNTUƁARMU TA LAMBOBIN 07045308523 MUN GODE Shirin fita zuwa wani katafaren wurin gyaran jiki da Amma ta biya kuma ta ce za ta turo direba ya ɗauki Hamdi kafin ƴan kawo lefe su iso take yi. Zee da ƙanwar Anti Labiba mai suna Fadila ne ƴan rakiya. Komai cikin mutuwar jiki take yinsa musamman da jiya bata sami isashshen bacci ba. Tayi ibada kuma tayi kuka sosai. Yawanci akan ce asiri birkita tunanin mutum yake yi har ya kasa gane taƙamaimai me yake…
    Note
    error: Content is protected !!