489 Results in the "Hausa Novels" category
-
Chapter
Bakar Ayah – Chapter Three
Saida taje daff da inda su Hajiya Zeena suke tsaye ta riƙe kanta tareda fara layin ƙaryah. Lylah ce ta kulada ita tace. "Lubna kema kuwa lafiya,naga sai layi kikeyi?" "Uhm kaina ne nake jinsa kaman zai fashe,bana jin daɗinsa ko kaɗan" "Toh ta tafi gida mana,dama waye ya riƙeta,ni nayi mamaki ma danaga tazo wajennan" Hajiya Zeena ta faɗa tana binta da harara. Itama ta wata fuskar ramawa tayi,tareda yimusu sallama tabar wajen,shikuwa uban gayyar dama yayi fushi da ita jiya. Dan haka ko kallon ta bayyi… -
Chapter
Bakar Ayah – Chapter Thirty-two
Hamma Hajiya zeenah tayi tareda kallon muruje wanda yakai karshen labarin dayake basun. Kuɗi ta ciro daga cikin purse ɗinta ta miƙamasa tareda yimasa godiyah. "Mun gode da wannan labarin daka bamu,koba komai yanzu munsan mai yake wakana,mu bari mutafi gida,yamma tayi bazamu hau cikin jejin yanzu ba" Zaro ido muruje yayi tareda cewa. "Hajiyah wai har yanzu baki haƙura da zuwa wajenta ba,bazan tambayi mai kike nema ba a wajenta,nagode ni bari na tafi" Fita muruje yayi daga cikin motar yakama… -
Muryar wani mutum taji daga bayanta yana cewa. "Ku shiga ciki ku ɗauresu,sannan ku zubaminsu a bayan mota,karku manta da ɗauremusu fuskokinsu" "Okay toh" Mutane guda biyune suka shigo motar tareda ɗaure musu hannayensu da igiyoyi,bakin kyalle aka saka a fuskokinsu,daga aka tasa ƙeyarsu zuwa cikin wata motar. "Maza kai toro jawo motar tasu ku tafi,zamu miƙasune ga itah,sai sun faɗi dalilin dayasa suke nemanta,sannan kuma wanene ya aikosu" Daga haka su Hajiya zeenah basu sakejin komai ba sai gungurawar…
-
Chapter
Bakar Ayah – Chapter Thirty-one
"Uhm karki ce mai yasa na tambayeki,amma menene haka kike nema a wajen wannan yarinyar,abinfah ya wuce yanda kike zato. Bayan bacewarta daga garinnan komai yafara tafiyah normal,saidai kuma mahaifiyar ta inna Danejo bata manta da batan ƴar ta ba,dakuma mummunan zagin da ake binta dashi. Hakanne yasa abin yafara damunta da kaɗan kaɗan,ga kuma dama ciki mai wahalarwa. Ba a tashi sanin mai ya faru ba har saida tazo haihuwa matsala ta tashi gadan gadan. A nanne mlm Ahmadu ya kaita asibiti amma tagagara… -
Chapter
Bakar Ayah – Chapter Thirty-four
Wani yarone ya shogo gidan da takarda a hannunsa cikin envolope,Innar iyani ya fara gaisarwa,wacce take zuzzuba abinci a kwanuka. "Uhm dama watace ta aikoni gidannan wai nabawa Hajiya zeenah abinnan" Iyani tanajin haka tayi saurin karbar takardar tareda cewa. "Wacece matar,tana waje har yanzu?" "Tasaka nikaf,tana bani takardar tajuyah ta tafi" "To shikenan jega an gide,bari dama zan kaimata abin karyawa saina tafi mata dashi" "Wani kallon mai kuke ƙullawa innartata tabita dashi,ganin bazai kaitaba ta… -
Chapter
Bakar Ayah – Chapter Thirty
Sauri take tayi cikin duhun dare,da alama fitsarine ya kamata sosai. Tazo daidai hanyar shiga banɗakin taga alamar wulagawar mutum a sashen goje. Ƙiftawa ido tayi tasake ƙiftawa,dan zaton ko aljani tagani,saidai kuma ta kawar ta hakan a ranta ta wuce banɗakin. Bayan tafito harta nufi ɗakinsu saikuma tashi alamar motsi a sashen kumadu. "To waye ne yashige sashen goje,shekara biyu kenan yadaina kawo mata,tunda kowa yasan babu abinda zai iya yi musu,to waye kuma a sashennasa?" Harzata shiga ɗakin kuma… -
Chapter
Bakar Ayah – Chapter Thirteen
Babu 'bata lokaci daneji ta shirya domin su tafi asibitin,har sannan Bombee na hannun mahaifinta,motsi kaɗan idan tayi ya leƙata,gani yake tamkar ƙwai ne a hannunsa,zai iya fashewa a kowanne lokaci. Ƙosawa yayi darashin shiryawar tata da sauri,dukkuwa da yanda take iya ƙoƙarinta wajen yin saurin,gani yake kaman jinkirinta a lokacin wani abun zai iya faruwa. Fitowa sukayi daga ɗakin tareda yiwa Inna laari sallama kana suka kama hanyar asibitin a mashin ɗinsa. Yana tafiyah yana waiwayen ƴar… -
Chapter
Bakar Ayah – Chapter Ten
Har suka fito daga cikin gidan su bombin babu wanda yacewa wani komai,saboda ɗumbin abin mamakin da suka gani. Magana suka ji a gefensu,suna waigawa suka ga ashe saurayin daya rakosu gidanne,yana jingine a bakin motar tasu. "Sannunku da fitowa,na tabbatar masu samu amsar abinda kukaje nemaba" "Taya kasan hakan,ko shiyasa ka tsaya kana jiran mufito,kenan kasan inda take?" "Eh to nasani bankuma sani ba,kunsan ance ba'a aikin banza,zan nuna muku hanyar dazaku bi ku sameta dai. Amma daman batun ku tsaya cikin… -
Chapter
Bakar Ayah – Chapter Sixteen
Saka ƙafa yayi yaƙara takata a ƙasa haɗeda cije baki. "Faɗamin ina so ki amsa cewar ke mayyace,baƙar mayyah babu abinda ya dace dake sai duka dakuma hantara,kar ma ki sake gigi cigaba da zama a ajinmu. Kunkoroki munyi miki komai amma kinƙi barin ajinmu ko,saboda ki nuna mana halinki na mayu,to idan muka koma gobe naganki a cikin ajinmu sai dakaki" "Zulaiha ce taƙarisa faɗin hakan,ƙanwar bello abokin sule. Da Bombee a primary 5 A take,saboda yanda suka maidata kaman jakarsu,yasa mlm Ahmadu yaroƙi… -
Chapter
Bakar Ayah – Chapter Six
"Saki kuma ummah?" "Eh saki haka nace,ko baka jiba kurmane kai nasake maimaita maka,ka rubuta sakinta ka bata tabar gidannan,bana sonta a cikin gidannan" Yawu ya haɗiya mai nauyi kafin yakai hannunsa zuwa kan takardar,tambayoyine suka fara kwaranya a cikin ƙwaƙwalwarsa,meyasa sai shine,meyasa komai shikaɗai zai dunga faruwa dashi? Daga ya fita cikin wanann ifila'in sai kuma yasake shiga wani. Koyaushe shidai bazai daina fita daga chaƙwakiyar mata oho. Biro ya ɗauka tareda takardar baya ya dawo daga… -
Chapter
Bakar Ayah – Chapter Seventeen
Jikinta sanyi kalau tashiga cikin ɗakin su Bombee,domin batasan mai zata ganewa idonta ba,saidai duk da hakan tana fatan Allah yasa karta ga abinda zuciyarta take raya mata. Labulen ɗakin ta ɗauke ta rataye ,hasken rana yashiga ɗakin,domin yabawa ɗakin ishashshen hasken dazata ganta dakyau. A kwance take ta rufe idonta kaman mai bacci,saidai kana gani kasan ba baccin take ba. "Bombee" "Na'am ta amsa a dake" Shuru Daneji tayi kaman mai nazari kafin ta zauna a kusada ita. "Shin menene ya farune kika… -
Chapter
Bakar Ayah – Chapter Seven
_________________________ GEMBU babban garine dayake Tsibirin MAMBILA a Sardauna local government dake jihar Taraba a nigeria. Shine gari na karshe daga nan sai a shiga ƙasar camaroo,hakan nw yasa ya zamo gari mai tarin ƙabilu da kuma tarun yaruka,kama daga irin su Bummi wanda sune manyan ƙabilun garin,sanann kuma akwai Mbubo, Ngebu,Fulani. Wannan sune mafiya yawan mutane da ake samu a yankin,saikuma sauran mutane kaman su Igobo,Hausa,da yaruba,dama wasu daga cikin ƙasar camaroo,wanda mafiyansu… - Previous 1 … 27 28 29 30 Next
