You have no alerts.

    507 Results in the "Hausa Novels" category


    • Kura a Rumbu – Chapter Forty-five Cover
      by Maryam Farouk (Ummu Maheer) ALHAMDULILLAH Mun gama biki lafiya nagode da fatan Alkhairi. "Dan girman Allah Anty Amina kiyi mun wannan alfarmar, wlh nayi duk dabarata amma taƙi saurarona, idan naje gidan bata fitowa haka idan na kira wayarta bata amsawa. Ɗazu da safe suka zo ba dan na kulle gidan ta ciki ba ma da tuni sun kwashe kaya. Ke shaida ce ina son Halima duk abinda kuma ya faru sharrin shaiɗan ne da kuma Hajja amma wlh ba a son raina bane" ya faɗa bayan da ya tsayar da Anty Amina a ƙofar gida. Kallonsa ta ringayi har ya…
    • Kura a Rumbu – Chapter Forty-six Cover
      by Maryam Farouk (Ummu Maheer) "Kar kice haka mana Halima. Ke da na san ki jaruma shine zaki bari daga sama wata ta zo ta ƙwace miki miji kuma ki sakar mata? Haba mana dan Allah karki bani kunya. Na san abinda ya aikata miki dole kiji zafi ba ke ba hatta Hajja dake goyon bayansa a ko da yaushe a wannan karon tana adawa da auren nan dan wlh ba dan mun tausheta ba rantsuwa tayi akan sai ya saki yarinyar ba zata tare ba. Mu muka yi ta bata haƙuri saboda a ganina bai kamata ace a gyara ɓarna da ɓarna ba, ubangiji ya rigada ya ƙaddara…
    • Kura a Rumbu – Chapter Fifty-eight Cover
      by Maryam Farouk (Ummu Maheer) HALIMA Cike da haushin Dr Salman na koma gida ranar Juma'ar, haka nan ya san banda mu zasuyi meeting ɗin amma ba'a gaya mana ba saida muka rigada muka je tukunna sannan babu damar tafiya haka mukayi zaman banza har sha biyu kafin muka tashi. Dama-dama da na ji na samu nayi clearance ɗina kafin na wuce gida. Bayan sallahr magriba Anty Labiba tace mu shirya muje gidan Uncle Mudassir yaronsa na biyu Khalil ya faɗi ɗazu da safe ya samu karaya, muna shirin fita Mama ta kirata tana tambayarta yaushe zamuje…
    • Kura a Rumbu – Chapter Fifty-nine Cover
      by Maryam Farouk (Ummu Maheer) Sai dana tabbatar ya fice daga building ɗin gaba ɗaya kafin na fita daga office ɗin ina kalle-kalle kamar mara gaskiya, ganin babu kowa ya saka na shige Elevator da sauri, a reception na haɗu da Juwairiyya ta kalleni fuska ba yabo ba fallasa kafin tace "Ina kika tafi tun ɗazu?" Wucewa nayi ba tareda na bata amsa ba ta sake cewa "Dr Sulaiman yana neman ki?" Na amsa da "Toh" ba tareda na tsaya ba na fita. A can kan hanya ya tarar dani, fuska ba annuri ya sauke glass yana kallona kafin ya ce "Get in".…
    • Kura a Rumbu – Chapter Sixty Cover
      by Maryam Farouk (Ummu Maheer) Ranar da Bilal ya kwana bakwai a Asibiti aka sallame shi sai Hajja wacce tun zuwan Fadila jikinta ya sake rikicewa sauƙin data fara samu komai yaja baya bata da aiki sai kuka da Allah ya isa ga Ahlan da tace ya yaudaresu ya auri autarta yaje yana azabtar mata da ita. Ganin jikin Bilal yayi sauƙi sai abinda ba za'a rasa ba ya saka aka sallameshi bayan likita ya ja masa kunne sosai akan kulawa da lafiyarsa. Sosai Zulaiha ke tsaye a kansa tana kulawa dashi, yanda Bilal yayi wani sanyi ƙalau lokaci ɗaya…
    • Son Rai – Chapter Sixteen Cover
      by Aysha A Bagudo "Yayinda a hankali suka sakarwa junansu murmushi mai tsuma zuciya da aikawa ruhi wani sako na daba . " lokaci day'a kuma murmushin yesmin ya koma kuka cikin sanyin murya mai cike da kuka ta soma magana "why D ? "Me yasa ka min haka ? " Me yasa kayi nisa da rayuwata alhalin kasan zuciyata bazata iya d'aukar rad'adin hakan ba ? " lumshe idanunshi yayi saboda wani irin yanayi daya tsinci kanshi na zallar shaukinta , muryarsa a kasalance yace "Kiyi hakuri yesmin di nah , Ni kaina ban so tafiyar nan ba,…
    • Son Rai – Chapter Eighteen Cover
      by Aysha A Bagudo Bayan sun gaisa da abban yesmin , Dr Jamil ya d'an saurara ,yaji ko yesmin zata gaishe shi kamar Koda yaushe . amman yaji tayi shiru taki cewa komai ,hakan ne yasa shi maido hankalinsa da idanunshi har ma da natsuwarsa inda take zaune kusa da mahaifinta ,ya tsura mata idanunshi masu matukar kyau da tasiri a jikinta har ma da zuciyarta .... "Zuciyar ce ta dinga dokawa da mugun karfi , sakamakon idanunshi da take jin yana yawo a sansar jikinta, cikin wani irin yanayi na bugawar zuciya ta d'ago kanta ta…
    • Son Rai – Chapter Six Cover
      by Aysha A Bagudo *MASU ƁUKATAR A TALLATA MUSU HAJOJINSU ZA SU IYA TUNTUƁARMU TA LAMBOBIN 07045308523 MUN GODE* . ....Ita kuwa yesmin ta'ba kofar bathroom din , da akayi, yayi mugu mugun hargitsa mata 'kwal'kwaluwa ,har ta saki k'ara mara sauti batare da tasan tayi hakan ba, jikinta na sake d'aukar kyarma, dan daman tana manne da jikin kofar ne ,ta manne kunnenta tana sauraran tautaunawarsu , daki daki komai ke shiga kunnenta tun daga kan maganar jakarta da mahaifinta yayi har zuwa Sauran maganganun ... A matukar…
    • Son Rai – Chapter Eleven Cover
      by Aysha A Bagudo ... A hankali ya k'ai bak'insa daidai saitin Kunnenta ya soma rad'a mata magana Cikin Sanyayyiyar muryan shi mai tsananin kashe mata jiki, da tsuma zuciyarta . "Yesmin...... bazan i'ya abinda kike tunani ba a halin yanzu da zuciyata take cikin garari da tashi hankali ,bama haka ba har a cikin zuciyata bana so wani abu ya sake Shiga tsakanina dake..... nayi nadama har a cikin Zuciyata, Nayi nadama! nayi nadama!!! " bana son wata halaka ta sake shiga tsakani na dake matukar baki kasance mallakina ba…
    • Son Rai – Chapter Fourteen Cover
      by Aysha A Bagudo Tsura mata ido abbanta yayi yana kallonta kawai kafin daga baya ya sauke naunayen ajiyar zuciya yace " transfer ya samu zuwa borno state ,me ne ne Kika shiga damuwa da tashin hankali ? Kanta kawai ta shiga girgiza masa zuciyarta na wani irin dokawa da karfin gaske ," "to ki zauna kici abinci " komawa tayi ta zauna jagwab kamar yadda ya bata umarni ,sai dai kallo day'a zaka mata kasan cewar tana cikin damuwa da tashin hankali yayinda tuni idanunta suka kad'a sukayi ja ,ta lumshe idanunta dan ita…
    • Son Rai – Chapter Fifteen Cover
      by Aysha A Bagudo ....Yesmin na zaune ta zuba uban tagumi ,sai hawaye ke gangarowa bisa kuncinta , gabad'aya abun duniya ya isheta, duk ta rasa hanyar da zata bi ta had'u da Dr Jamil dinta ,bata san gurin Wanda zata samu cikekken address inda yake a maiduguri ba ,har mahaifinta ta tambaya cikin wayo da dabara ,shima yace " bai sani ba " me zatayi da address din ? Kame kame ta dinga yi masa daga karahe sukayi sallama " "damuwar da take ciki tasa karatu gagararta , tunanin barkatai kawai take ,Wanda ita kanta ta kasa…
    • Son Rai – Chapter Seventeen Cover
      by Aysha A Bagudo "Cak yesmin taja ta tsaya ta kasa cigaba da tafiyar da take , ta tsaya kawai tana kallon shigowar motarsa ,har sanda motar ta k'arasa shigowa harabar gidan , ta nufi inda aka tanada domin ajiye motoci, bata d'auke idanunta a kan motar ba ,yayinda faruk shima ya ja ya tsaya, ya kasa barinta, yana jiran ta motsa su k'arasa shiga cikin gidan . Shi kuwa Dr jamil bak'aramin tashin hankali da hargitsi zuciyarsa ta shiga a lokaci ba, saboda ganin da yayi musu ,duk da shi da kanshi ya bawa zuciyarta…
    Note
    error: Content is protected !!