489 Results in the "Hausa Novels" category
-
Ina zaune a falon har Baba Jummai ta gama haɗa kayan ta tana kukan da nake ji kamar na tashi na shaƙe mata wuya idan ya so ta yi mai dalili. Ni da ta ke neman ta kashewa aure ai ni ce da kuka ba ita ba, akan na ce ta tafi tun da ita ta janyo ni ma aka ce na tafin shi ne ta fasa kuka wai na mata rashin kunya tana ƙoƙarin kare mun mutunchi na watsa mata ƙasa a ido. Ta shi na yi na goya Al'amin bayan da ta fito da jakar ta daga ɗaki ina kallon ta na ce "Kuma wlh karki gayawa kowa abin da ya faru, kawai…-
247.6 K • Completed
-
-
Na ɗauka da wasa Mama take yi sai washe gari da safe bayan mun yi wanka na koma rage baccin da ban yi ba cikin dare saboda Kukan Al'amin ban jima da kwanciya ba Zainab ta tashe ni akan Mama tana kira na. A falon Abba na same ta, muka sake gaisawa sai Abba ya ce "Mamanku ta ce mijin ki yayi tafiya ko?" Ba tare da na kalle shi ba na amsa haɗi da gyaɗa masa kai dan haka kawai kuma kunyar Abban na ke ji yanzu, ni dai jiki na bai bani aka Baba Jummai bata basu labarin abin da ya faru ba yanda kuma suka mun…-
247.6 K • Completed
-
-
HALIMA Yanda naga rana haka naga dare, sai naji ashe ma jiya baccin daɗi nayi yaune nake ganin asalin baƙin dare. Sai da aka idar da sallar asuba kafin na samu bacci ya fizgeni, sai dai ban wani yi nisa ba na farka sakamakon kiran suna na da nake ta ji anayi. Na tashi zaune daƙyar ina matse ido haɗi da dafe gefen kaina da nake ji kamar zai faɗo saboda ciwo. Mama na tsaye ta ce "Hala kin manta abinda Abbanku ya faɗa miki shiyasa kika shantake kina bacci har ƙarfe tara". Gabana ya yanke ya faɗi,…-
247.6 K • Completed
-
-
Kafin na kai masa wayar ta yanke dan haka da na bashi ajiye ta ya yi ya cigaba da cin abincin ba tare da ya duba wanene ya kira ba. Duk yanda na so na mayar da hankali na kan Al'amin dake ƙananun rigima sai na kasa ƙarshe kawai na goya shi na yi tsaye ina kallon Bilal da ke cin abinci wayar sa na ƙara alamar shigowar wani kiran amma be amsa ba. Kamar me tsoron magana na ce masa "Ana kiran ka a waya fa" ya ɗago ya kalle ni kafin ya ɗaga wayar ya karata a kunnen sa lokaci ɗaya yana miƙewa tsaye.…-
247.6 K • Completed
-
-
"Ashe baka da mutunchi kai mutumin banza ne ban sani ba? Ban taɓa zaton haka kake ba, ashe abinda kake aikatawa kenan a bayan idon mu kana can kana zubar mana da mutunchi kana tozarta kanka; matan banza kake bi Bilal?" Ya dafe in da ta mare shi ba tareda ya bari sun haɗa ido ba ya ce "Ni wlh ba wasu mata da nake bi Hajja sharri kawai suka mun". Wani marin ta sake kai masa ya goce ta ce "Yanzu kake da bakin kare kanka kenan? Ni zaka kalla ka ce sharri ake maka saboda ka raina ni mai ya sa a gabansa baka…-
247.6 K • Completed
-
-
Abinda ya fi tsaya mun a rai yanda duk sanda zamuyi magana sai ya ce ya san ina son sa, kenan shi baya so na kuma yana ɗaukata wawuya saboda ina sonsa dole na jure duk wani abu da zan fuskanta daga gare shi ko me? "Dan Allah karki ce Aa Halims ki taimaka mu haɗu kada ki bari mahassada suyi galaba akanmu" ya sake faɗa cikin marairaice kamar zai fashe mun da kuka. Cikin dakiyar da na aro na azawa kaina na ce "Ka sameni a gidan Anty Labiba bayan Magriba" "Gidan Anty Labiba kuma?" Ya faɗa kamar a ɗan…-
247.6 K • Completed
-
-
Chapter
Kura a Rumbu – Chapter Fifty
Turus yayi yana bin falon da kallo zuciyarsa tana ƙara gudu, shiga yayi ciki da kyau har sannan yana ƙoƙarin gane abinda yake faruwa. Ƙofar ɗakin Halima ya tura, nan ya tarar da gurin shima tamkar falon babu ko tsinke anyi shara da alama ma har mopping akayi. Sakin ƙofar yayi ya matsa ya buɗe ta ɗayan ɗakin da yake mazaunin nasa; a nan ne ya tarar da kaya zube a ƙasa wanda kallo ɗaya ya musu ya fahimci nasa ne. Ɓacin rai haɗi da baƙin ciki suka kamashi lokaci ɗaya, fita yayi daga nan ya…-
247.6 K • Completed
-
-
Chapter
Kura a Rumbu – Chapter Fifty-two
Kwana yayi yana tunanin yanda akayi Zulaiha ta yaudareshi, tsayin shekarun da suke tare ace bai taɓa tunani ko hasashen tana da wani hali na daban bayan wanda ya santa da shi ba. Yaran da talauci da matsin rayuwar da suka tashi a ciki ya saka basuda kataɓus ko a cikin unguwa ɗaiɗaikun mutane ne suke mu'amala da su balle makaranta. Shigar sa cikin rayuwarsu ne ya kawo musu ɗauki har suka samu yanci dukda hakan kuma suna gabatar da rayuwarsu ne cikin takatsantsan dan ya sha tambayarta mai yasa bai taɓa…-
247.6 K • Completed
-
-
Madallah da mutane masu karamci. Nagode ƙwarai dagaske, ina lafiya wani aiki ne ya ɗauke ni tsayin kwanaki amma Alhamdulillah mun kammala na kuma gode ƙwarai da haƙurinku ina fatan har mu kammala babu wani uzuri da zai sake gifta mana 🙏🏽🙏🏽🙏🏽 *KURA A RUMBU littafin kuɗi ne 800, yake mai jira nayi posting ki fitar kiji tsoron Allah dakw da wacce take jira ki turo ta karanta a bati ku guji haƙƙin komai ƙanƙantarsa. Duk wacce ta shirya sauke nauyi ta tura mun kuɗi na a asususun…-
247.6 K • Completed
-
-
Jinyar stitches ɗin Zulaiha ta saka Bilal baya fita ko ina idan ba masallaci ba, duk ayyukan gidan shi yakeyi, sannan ya kula da ita a ɗan taƙin lokacin kuma ya ɗan fara samun nutsuwa daga tsoron sababbin halayen da ya ringa gani a gurinta tun bayan da aka ɗaura musu aure. Ranar data kwana uku ƙanwar Ummansu Anty Habi taje gidan ta kai mata gamje gamjen magunguna da ta ce na Aljanun da suke shafarta ne. Shi ya ringa jigilar dafa mata na wanka safe yamma kuma ya hura mata coal tayi turare, maganin na…-
247.6 K • Completed
-
-
Ko da ya koma gida daƙyar tunanin yanda Hajja zata karɓi zancen auren daya ɗaura ba tareda saninta ba ya danne waswasin da zuciyarsa ta dasa masa akan Zulaiha. Wayarsa ma kashewa ya sakeyi bayan daya shiga gida bai kuma kunnata ba sai washe gari gurin ƙarfe goma bayan daya shirya zuwa gidan Hajjan in da daga can kuma yake so ya biya gurin Halima. A tsakar gida ya tarar da Hajja tareda Fadila suna duba kayan da kallo ɗaya ya musu ya fahimci daga gurin Jalilah suka fito dan yanzu ta lalata Hajjan da…-
247.6 K • Completed
-
-
Tarin missed calls ɗin da ya gani daga Alhaji Lawan mutumin daya siya gidan Jalilah a hannunsa ya tabbatar masa da ba lafiya ba, a maimakon ya kira Alhaji Lawan ɗin kai tsaye sai ya fara kiran Nasir domin shi yayi hanyar cinikin. "Yanzu nake shirin kiranka dama; kana ina?" Nasir ya faɗa bayan daya amsa wayar Bilal ya ce "Mai ya faru naga mutumin nan daya siya gida a hannuna yana ta kirana a waya ban lura ba sai yanzu?" "Shiyasa na ce kana ina? Akwai matsala gaskiya" Nasir ya bashi amsa. Bilal ya…-
247.6 K • Completed
-
- Previous 1 … 15 16 17 … 31 Next
