489 Results in the "Hausa Novels" category
-
Ina zaune a falon har Baba Jummai ta gama haɗa kayan ta tana kukan da nake ji kamar na tashi na shaƙe mata wuya idan ya so ta yi mai dalili. Ni da ta ke neman ta kashewa aure ai ni ce da kuka ba ita ba, akan na ce ta tafi tun da ita ta janyo ni ma aka ce na tafin shi ne ta fasa kuka wai na mata rashin kunya tana ƙoƙarin kare mun mutunchi na watsa mata ƙasa a ido. Ta shi na yi na goya Al'amin bayan da ta fito da jakar ta daga ɗaki ina kallon ta na ce "Kuma wlh karki gayawa kowa abin da ya faru, kawai…-
247.6 K • Completed
-
-
Ko ba'a faɗa mun ba na san da wahala idan jini na bai hau ba, daƙyar na lallaɓa Al'amin ya yi shiru na goya shi kafin na fita samawa Bilal abin da zai ci. Bamu da komai da zai ciyu da safe ban da taliya. Ita na yi jollof da sauran miyar da ta rage na dafa masa baƙin shayi. Ya ringa kallon abincin kamar wanda na aje wa mugun abu kafin cikin faɗa faɗa ya shiga tambayar babu nama a gidan ne da zan dafa masa tsurar taliya ko me? Haka na koma na ɗebo masa naman ina ajiyewa ya sake balbale ni da wata…-
247.6 K • Completed
-
-
Na ɗauka da wasa Mama take yi sai washe gari da safe bayan mun yi wanka na koma rage baccin da ban yi ba cikin dare saboda Kukan Al'amin ban jima da kwanciya ba Zainab ta tashe ni akan Mama tana kira na. A falon Abba na same ta, muka sake gaisawa sai Abba ya ce "Mamanku ta ce mijin ki yayi tafiya ko?" Ba tare da na kalle shi ba na amsa haɗi da gyaɗa masa kai dan haka kawai kuma kunyar Abban na ke ji yanzu, ni dai jiki na bai bani aka Baba Jummai bata basu labarin abin da ya faru ba yanda kuma suka mun…-
247.6 K • Completed
-
-
Washe gari da wuri na fara haɗa kayan mu dan komawa gidan Anty Labiba duk da jirgin dare su Mama zasu bi amma da wuri nake so na tafi can ɗin dan ko rakiya ba zan tsaya yi musu ba. Gaba ɗaya raina babu daɗi na tashi, na ɗauka Bilal zai sake kira na daga baya ko kuma da asuba amma shiru. Ina zuge akwatin kaya na Zainab ta shigo ta ce mun na zo na yi baƙi, na ɗora mayafin doguwar rigar yadin jiki na ina ƙoƙarin kawar da ɓacin ran dake kwance akan fuskata na fita falon. Turus na yi a bakin ƙofa…-
247.6 K • Completed
-
-
Kafin na kai masa wayar ta yanke dan haka da na bashi ajiye ta ya yi ya cigaba da cin abincin ba tare da ya duba wanene ya kira ba. Duk yanda na so na mayar da hankali na kan Al'amin dake ƙananun rigima sai na kasa ƙarshe kawai na goya shi na yi tsaye ina kallon Bilal da ke cin abinci wayar sa na ƙara alamar shigowar wani kiran amma be amsa ba. Kamar me tsoron magana na ce masa "Ana kiran ka a waya fa" ya ɗago ya kalle ni kafin ya ɗaga wayar ya karata a kunnen sa lokaci ɗaya yana miƙewa tsaye.…-
247.6 K • Completed
-
-
Chapter
Kura a Rumbu – Chapter Thirty
Watan Al'amin goma sha takwas na yaye shi a kuma watan na samu wani cikin wanda ko kusa Bilal bai yi maraba da samuwar sa ba. "Wai dama bakiyi komai na tsarin Iyali ba? Ni na zata hankalin ki zai baki da kiyi ba sai an tuna miki ba, kina kallon yanda abubuwa duke tafiya kuma kawai zaki kama ki wani sake yin ciki. To ni dai gaskiya ban so haka ba" Abun da ya faɗa kenan lokacin da na shaida masa ina da cikin. Gaba ɗaya sai na rasa yanda zan fassara maganganun sa. Fassara ta kai tsaye dai na san yana nufin…-
247.6 K • Completed
-
-
Chapter
Kura a Rumbu – Chapter Fifteen
Ban tanka masa ba na shiga tattare kayan dake ajiye dana gama kuma na wuce ɗakina na kwanta, nayi mamakin ganin ya biyo ni, nayi lamo a kan gado ina sauraren sa har ya gama uzure uzurensa na bacci kafin ya kwanta a baya na tare da jana jikin sa yana cewa "Nasan ba bacci kike yi ba juyo na baki barka da sallah" nayi masa banza duk yanda yake ya mutsani da son se na biye masa na dake daya gaji ya sake ni ina jin sa yana tsaki har baccin gaske ya ɗauke ni. Washe gari nayi zaton ze cigaba da fushin amma naga…-
247.6 K • Completed
-
-
Chapter
Kura a Rumbu – Chapter Sixteen
*Nayi kuskuren rubutu a page 13, ajizanci ne, abinda ke raina daban abinda alƙalamina ya rubuta daban. Ina fatan zaku mun uzuri* Na ringa juya zancen Farisa a raina bayan ta tafi har sanda Bilal ya dawo sau biyu ina buɗe baki da niyyar tambayar sa gaskiyar abin da ta faɗa mun se na kasa daga ƙarshe na tattara zancen na watsar har ina ganin baike na dana yarda da maganar tata har na saka a raina. Ta ya ma haka zata yuwu? Kawai dai haɗa guri ne irin na Farisa amma kuma idan tayi ƙarya ta ƙulla abu…-
247.6 K • Completed
-
-
Chapter
Kura a Rumbu – Chapter One
"Malam idan kaje ƊAN ALJANNAH zan sauka" na faɗa ina nunowa me Adaidaitan da muke ciki saitin in da ze ajiye ni, bayan daya gama daidaita parking na sauka ba tareda na kalli Hansa'u data kalli ɗaya ɓangaren ba nace "Da ace kuturwa Allah yayi ni se inji haushi dan kince ba zaki tayani aiki ba, dake ko babu ke bazan rasa wanda zasu rufamun asiri ba" na faɗa ina miƙawa me Adaidaita ɗari biyar. Bata tankamun ba na juya ba tareda na amsa tambayar da me mashin ɗin yake mun ba akan iya kuɗi na ze ɗauka…-
247.6 K • Completed
-
-
Chapter
Kura a Rumbu – Chapter Seventeen
Be ko saurari tayin abincin da na masa ba ya fice daga gidan bayan yayi wanka yana sake jaddada mun Fadila ta bar gidan kafin ya dawo, bayan fitar sa na shiga gyara falon da tayi mun kaca kaca da shi dan tun shigowar Bilal ɗin ta koma ɗaki na in da na sauketa. Na tabbatar taji banbamin da yakeyi tun da ba a hankali yayi maganar da ze fita ba, na ɗauka daya fitan zata tuntuɓe ni da zancen amma shiru se ma dawowa falo da tayi zata sake tarwatsa gurin na dakatar da ita ta hanyar ce mata ba nisa yayi ba…-
247.6 K • Completed
-
-
Chapter
Kura a Rumbu – Chapter Two
*MASU ƁUKATAR A TALLATA MUSU HAJOJINSU ZA SU IYA TUNTUƁARMU TA LAMBOBIN 07045308523 MUN GODE* Washe gari daƙyar na yakice bacci nayi shirin makaranta, ina gama karatu Bilal ya kirani har gurin ƙarfe ɗaya muna hira kafin ya barni na kwanta dama ga gajiyar dana kwaso a makaranta jiyan na ɗora data girki sannan dana dawo gidan ma ban zauna ba na tarar anyi fenti a ɗakina gaba ɗaya an hargitsamun kaya seda na gyara su sannan na kwanta. Shaf na manta da munyi faɗa da Hansa'u jiya na zauna jiran zuwanta…-
247.6 K • Completed
-
-
Chapter
Kura a Rumbu – Chapter Eighteen
Haka rayuwa taci gaba da gangarawa; yau fari gobe baƙi. A yanzu da nake lissafa watannin aure na goma sha biyar da Bilal shekara ɗaya da wata uku kenan, tabbas a zaman da mukayi nayi karatu da yawa tattare da halayen sa waɗanda a baya ban san su ba. Babban abinda na fara naƙalta da Bilal shine mutum ne me son abinsa. Tabbas Bilal nada son abin sa kuma ya kan iya rufe ido ya cima koma wanene mutunci har idan ya shiga gonar sa, idan yayi wani abun se na shiga mamakin ta yanda har muka shafe tsayin…-
247.6 K • Completed
-
- Previous 1 … 14 15 16 … 29 Next
