Search
You have no alerts.

    489 Results in the "Hausa Novels" category


    • Kura a Rumbu – Chapter Thirty Cover
      by Maryam Farouk (Ummu Maheer) Watan Al'amin goma sha takwas na yaye shi a kuma watan na samu wani cikin wanda ko kusa Bilal bai yi maraba da samuwar sa ba. "Wai dama bakiyi komai na tsarin Iyali ba? Ni na zata hankalin ki zai baki da kiyi ba sai an tuna miki ba, kina kallon yanda abubuwa duke tafiya kuma kawai zaki kama ki wani sake yin ciki. To ni dai gaskiya ban so haka ba" Abun da ya faɗa kenan lokacin da na shaida masa ina da cikin. Gaba ɗaya sai na rasa yanda zan fassara maganganun sa. Fassara ta kai tsaye dai na san yana nufin…
    • Kura a Rumbu – Chapter Thirty-one Cover
      by Maryam Farouk (Ummu Maheer) Nayi mamakin yanda Bilal bai musa ba lokacin da nayi masa maganar service. Nayi sa'a a lokacin ana dab da fara registration dama, ranar da aka buɗe kuwa banyi wasa ba na je na yi a matsayin mara aure saboda ko da na gaya masan ya ce toh nayi zaton zai je ya fitar da certificate of marriage da domicile letter waɗanda zan buƙata amma har ranar ta zo bai ce mun komai ba nima kuma banyi masa magana ba dan ina gudun kada ya canza ra'ayi. Posting ya fito aka kaini, ban wani damu ba tunda ba nesa bane nasan…
    • Kura a Rumbu – Chapter Thirty-two Cover
      by Maryam Farouk (Ummu Maheer) *Barkanmu da Sallah yan uwa* 🙏🏽 Sai da na fita kofar asibitin kafin na tsaya ina raba ido, ina zan nufa ne ma? Gida zan tafi ko kuwa gari zan shiga cigiyar inda Bilal ya tafi? Na kai hannu na share laimar da naji akan fuskata wadda ban tantance hawaye bane ko zufa kafin na shiga tare abin hawa, gidanmu na wuce, ban ko karɓi canji ba bayan na sauka na shige gidan a bakin ƙofa na zauna kamar wata zararriya na fasa kukan da ya saka Mama ta fito daga falo kamar zata hantsila da Sharifa a hannunta ta…
    • Kura a Rumbu – Chapter Thirty-three Cover
      by Maryam Farouk (Ummu Maheer) Banji komai dangane zaman da ya ce Hajja zatayi ba dukda nasan ba jituwa mukeyi da ita ba amma kuma abinda yake so ne kuma wanda zai faranta masa ni kuma burina a koda yaushe kenan. Har ya fita ya kirani a waya yace na shirya gashi nan dawowa zamu fita tare, da nace masa Al'amin fa kar lokacin tashin su yayi bana nan sai ya ce ai ba jimawa zamuyi ba dan haka nayi maza na canza kayana na shirya Sharifa ina jin horn ɗin mota na fita. Raina fes na kame a gaban mota ina jin wani farinciki na ratsani. Na…
    • Kura a Rumbu – Chapter Thirty-four Cover
      by Maryam Farouk (Ummu Maheer) Kwanaki biyu da suka biyo baya nayi su ne cikin taimakon ubangiji domin a kowacce daƙiƙa ji nakeyi tamkar numfashi na zai iya yankewa. Babu abinda yake shiga cikina banda ruwa da paracetamol da nake ta banka saboda azababben ciwon da kaina kama, ikon Allah kaɗai yake riƙe dani akan ƙafafuna hatta yaran ma game game kawai nake musu duk abinda hannu ya kai nake haɗawa na basu su ci. Nayi kuka har hawayena sun ƙafe ya zama sai na zuci nakeyi, a duk sanda na tuna abinda naji kuma na gani dangane da…
    • Kura a Rumbu – Chapter Thirty-five Cover
      by Maryam Farouk (Ummu Maheer) Amirah ta ɗaga Sharifa data saka kuka daidai lokacin da Mama ta fito daga kitchen lokacin kuma Al'amin shima ya shigo Suraj na biye dashi da akwatin mu. "Ku kuma daga ina haka da sassafe?" Mama ta tambaya, Suraj ya ajiye kayan yana cewa "Tareda Babansu suke" ya juya ya fita sai Amirah tace "Yaya Haliman tana ciki itama". Tsaye Mama tayi kafin tace "Toh lafiya dai?" "Gaskiya ba lafiya ba kinga fa jefar da Sharifa tayi ta wuce ina mata magana ko saurarona ma batayi ba" Amirah ta amsa mata. Jumm tayi tana…
    • Kura a Rumbu – Chapter Four Cover
      by Maryam Farouk (Ummu Maheer) *MASU ƁUKATAR A TALLATA MUSU HAJOJINSU ZA SU IYA TUNTUƁARMU TA LAMBOBIN 07045308523 MUN GODE* Ban yarda da gaske Bilal yake da yace ze turo saka rana ba se ranar Juma'a da Baba Salahu yazo gidan mu bayan sun gama maganar da za suyi da Abba yasa aka kirani. Seda muka gaisa kafin cikin tsare gida kasancewar sa me ɗan zafi ya kalle ni yace "Ranar lahadi idan Allah ya kaimu iyayen yaron da yake neman ki suka ce zasu zo saka rana, ina fatan da sanin ki?". Duk se na duburburce, abun yazo mun a ba zata domin…
    • Kura a Rumbu – Chapter Five Cover
      by Maryam Farouk (Ummu Maheer) A motar Nasir na ganshi, ya kame a ciki yanda kasan tasa. A raina nace kuɗi dai ze yi wa Bilal kyau dan kalarsu aka masa. Yanayin surarsa da irin kayan da yake sakawa ba zaka kalli gidansu kace daga nan ya fito ba. Yana son gayu, sau tari na kan raya a raina nan yake kashe kuɗin sa gurin siyan sutura da takalma haɗi da agogo masu tsada duk abin da samari sa'anninsa suke yayi zaka ganshi dashi hakan kuma yana burge ni duk da ba wadata ce dashi ba amma ba yanda za'a yi ka ganshi ka raina shi. A gaban…
    • Kura a Rumbu – Chapter Six Cover
      by Maryam Farouk (Ummu Maheer) Duk nazarin na ban hango abin da take ganin na rashin dai dai ba. Rashin yi mun kyauta ne aibun sa ko kuwa rashin kammala ginin da be yi ba da kuma zancen lefe? A cikin ukun sune abin da nake ganin Anty Labiban take emphasizing se dai ni a ganin ta wannan ai ba komai bane ba. Bilal nake so ba abun hannunsa ba. Iya kar ƙoƙari yana yi gurin ganin ya kammala in da ze ajiye ni kuma ba a ɗaura auren nan an ga be yi mun lefe ba balle su ce wani abu. Ni duk wani lefe da wasu bidi'o'i basa gabana duk da dai ba…
    • Kura a Rumbu – Chapter Seven Cover
      by Maryam Farouk (Ummu Maheer) Na fi minti goma tsaye a ƙofar gidan mu ni ban shiga ba kuma ban bar gurin ba. Maganganun da mu kayi da Bilal ne suke mun amsa kuwwa a kunnuwa na da ƙwaƙwalwata bana kin ko wanne sauti dake zagaye dani banda muryar sa. "Ba ni da kuɗin da zan ƙarasa gini Halima, ba kuma ni da sararin da zan kama haya a yanzu. Abu biyu ya rage, ko dai iyayen ki su ɗaga auren mu ko kuma mu haƙura gaba ɗaya, ƙila a gaba idan muna da rabon kasancewa tare se muyi aure. Ina son ki Halima amma bani da halin mallakar ki a…
    • Kura a Rumbu – Chapter Eight Cover
      by Maryam Farouk (Ummu Maheer) "Sannu Halims, kin tashi" Bilal ya faɗa yana nufo ni se dai shigowar Anty Labiba ɗakin ta katse masa hanzari se ya ja gefe yana shafa kansa ita kuma ta balla masa harara kafin ta nufo ni ta kamani ganin ina ƙoƙarin tashi zaune. "Sannu" ta faɗa tana gyara mun ɗankwali na daya zame. Bilal ne ya fita ya kira wo likita suka dawo ɗakin tare da Abba. Bin su kawai nakeyi da kallo har likitan ya gama dubani yace babu komai jiki na ya dai dai ta amma a barni na sake hutawa. Abba yayi mana sallama akan ze je…
    • Kura a Rumbu – Chapter Nine Cover
      by Maryam Farouk (Ummu Maheer) Ina ji wayata na ƙara na san kuma Bilal ne amma naƙi amsawa, Allah ya sani har raina naji haushin anin da ya mun. Wane irin tozarci ne lefe a leda? Idan bashi da kuɗin akwati ya ara mana ko kuma ya bar lefen gaba ɗaya tun da ni dama ban saka rai da zeyi mun ba. Shine kuma saboda rainin hankali har yana cewa ze bani mamaki da irin lefen da ze mun aiko ga mamaki nan ya bar mun abin faɗa a cikin dangi da unguwa. Kusan minti talatin ina kuka ina jiyo hayaniya sama sama daga falo, Anty Labiba ce ta tasa…
    Note
    error: Content is protected !!