489 Results in the "Hausa Novels" category
-
Chapter
Kura a Rumbu – Chapter Fifteen
Ban tanka masa ba na shiga tattare kayan dake ajiye dana gama kuma na wuce ɗakina na kwanta, nayi mamakin ganin ya biyo ni, nayi lamo a kan gado ina sauraren sa har ya gama uzure uzurensa na bacci kafin ya kwanta a baya na tare da jana jikin sa yana cewa "Nasan ba bacci kike yi ba juyo na baki barka da sallah" nayi masa banza duk yanda yake ya mutsani da son se na biye masa na dake daya gaji ya sake ni ina jin sa yana tsaki har baccin gaske ya ɗauke ni. Washe gari nayi zaton ze cigaba da fushin amma naga…-
247.6 K • Completed
-
-
Chapter
Kura a Rumbu – Chapter Sixteen
*Nayi kuskuren rubutu a page 13, ajizanci ne, abinda ke raina daban abinda alƙalamina ya rubuta daban. Ina fatan zaku mun uzuri* Na ringa juya zancen Farisa a raina bayan ta tafi har sanda Bilal ya dawo sau biyu ina buɗe baki da niyyar tambayar sa gaskiyar abin da ta faɗa mun se na kasa daga ƙarshe na tattara zancen na watsar har ina ganin baike na dana yarda da maganar tata har na saka a raina. Ta ya ma haka zata yuwu? Kawai dai haɗa guri ne irin na Farisa amma kuma idan tayi ƙarya ta ƙulla abu…-
247.6 K • Completed
-
-
Chapter
Kura a Rumbu – Chapter Seventeen
Be ko saurari tayin abincin da na masa ba ya fice daga gidan bayan yayi wanka yana sake jaddada mun Fadila ta bar gidan kafin ya dawo, bayan fitar sa na shiga gyara falon da tayi mun kaca kaca da shi dan tun shigowar Bilal ɗin ta koma ɗaki na in da na sauketa. Na tabbatar taji banbamin da yakeyi tun da ba a hankali yayi maganar da ze fita ba, na ɗauka daya fitan zata tuntuɓe ni da zancen amma shiru se ma dawowa falo da tayi zata sake tarwatsa gurin na dakatar da ita ta hanyar ce mata ba nisa yayi ba…-
247.6 K • Completed
-
-
Chapter
Kura a Rumbu – Chapter Eighteen
Haka rayuwa taci gaba da gangarawa; yau fari gobe baƙi. A yanzu da nake lissafa watannin aure na goma sha biyar da Bilal shekara ɗaya da wata uku kenan, tabbas a zaman da mukayi nayi karatu da yawa tattare da halayen sa waɗanda a baya ban san su ba. Babban abinda na fara naƙalta da Bilal shine mutum ne me son abinsa. Tabbas Bilal nada son abin sa kuma ya kan iya rufe ido ya cima koma wanene mutunci har idan ya shiga gonar sa, idan yayi wani abun se na shiga mamakin ta yanda har muka shafe tsayin…-
247.6 K • Completed
-
-
Chapter
Kura a Rumbu – Chapter Nineteen
Ba zan iya cewa ga ta yanda muka fita daga gidan ba ni dai kawai na san munje gidan mu; muna sauka daga Adaidaita sahu Amirah ta sake ni na dafe gini saboda jirin dake kokawar kayar dani ita kuma ta tura ƙofar get ta shiga tana rushewa da kuka tamkar wadda tazo isar da saƙon mutuwa. Daƙyar na cira ƙafata na rufa mata baya ina yi ina dakatawa saboda ciwon marar dake taso mun, na dafe ƙofar shiga falon na tsaya ina kallon mazauna ciki da suka rufu kan Amiran cikin tashin hankali suna tambayar ta ba'asin…-
247.6 K • Completed
-
-
A ƙaramar akwati na zuba mana duk abun da na san zamu buƙata a yinin, Baba Jummai ta goya Al'amin tana tsaye tana jiran na yafa gyale na da na ajiye a gefe. Zama na yi a gefen gado ina rarraba ido kamar wadda ta yiwa sarki ƙarya, ta kalle ni ta ce "Ya kuma kika zauna? Tun da dai an kaiwa maƙwaftan nan abinci se ki tashi mu tafi kuma su ce zasu shigo yinin suna". "Baba ban gayawa Bilal ba" na faɗa ba tare da na kalle ta ba, "Naga abinda ya ishe ni ni Hasana, yanzu gidan ku ɗin da zaki tafi shine kike…-
247.6 K • Completed
-
-
Ko ba'a faɗa mun ba na san da wahala idan jini na bai hau ba, daƙyar na lallaɓa Al'amin ya yi shiru na goya shi kafin na fita samawa Bilal abin da zai ci. Bamu da komai da zai ciyu da safe ban da taliya. Ita na yi jollof da sauran miyar da ta rage na dafa masa baƙin shayi. Ya ringa kallon abincin kamar wanda na aje wa mugun abu kafin cikin faɗa faɗa ya shiga tambayar babu nama a gidan ne da zan dafa masa tsurar taliya ko me? Haka na koma na ɗebo masa naman ina ajiyewa ya sake balbale ni da wata…-
247.6 K • Completed
-
-
Washe gari da wuri na fara haɗa kayan mu dan komawa gidan Anty Labiba duk da jirgin dare su Mama zasu bi amma da wuri nake so na tafi can ɗin dan ko rakiya ba zan tsaya yi musu ba. Gaba ɗaya raina babu daɗi na tashi, na ɗauka Bilal zai sake kira na daga baya ko kuma da asuba amma shiru. Ina zuge akwatin kaya na Zainab ta shigo ta ce mun na zo na yi baƙi, na ɗora mayafin doguwar rigar yadin jiki na ina ƙoƙarin kawar da ɓacin ran dake kwance akan fuskata na fita falon. Turus na yi a bakin ƙofa…-
247.6 K • Completed
-
-
Chapter
Kura a Rumbu – Chapter Thirty
Watan Al'amin goma sha takwas na yaye shi a kuma watan na samu wani cikin wanda ko kusa Bilal bai yi maraba da samuwar sa ba. "Wai dama bakiyi komai na tsarin Iyali ba? Ni na zata hankalin ki zai baki da kiyi ba sai an tuna miki ba, kina kallon yanda abubuwa duke tafiya kuma kawai zaki kama ki wani sake yin ciki. To ni dai gaskiya ban so haka ba" Abun da ya faɗa kenan lokacin da na shaida masa ina da cikin. Gaba ɗaya sai na rasa yanda zan fassara maganganun sa. Fassara ta kai tsaye dai na san yana nufin…-
247.6 K • Completed
-
-
Nayi mamakin yanda Bilal bai musa ba lokacin da nayi masa maganar service. Nayi sa'a a lokacin ana dab da fara registration dama, ranar da aka buɗe kuwa banyi wasa ba na je na yi a matsayin mara aure saboda ko da na gaya masan ya ce toh nayi zaton zai je ya fitar da certificate of marriage da domicile letter waɗanda zan buƙata amma har ranar ta zo bai ce mun komai ba nima kuma banyi masa magana ba dan ina gudun kada ya canza ra'ayi. Posting ya fito aka kaini, ban wani damu ba tunda ba nesa bane nasan…-
247.6 K • Completed
-
-
*Barkanmu da Sallah yan uwa* 🙏🏽 Sai da na fita kofar asibitin kafin na tsaya ina raba ido, ina zan nufa ne ma? Gida zan tafi ko kuwa gari zan shiga cigiyar inda Bilal ya tafi? Na kai hannu na share laimar da naji akan fuskata wadda ban tantance hawaye bane ko zufa kafin na shiga tare abin hawa, gidanmu na wuce, ban ko karɓi canji ba bayan na sauka na shige gidan a bakin ƙofa na zauna kamar wata zararriya na fasa kukan da ya saka Mama ta fito daga falo kamar zata hantsila da Sharifa a hannunta ta…-
247.6 K • Completed
-
-
Banji komai dangane zaman da ya ce Hajja zatayi ba dukda nasan ba jituwa mukeyi da ita ba amma kuma abinda yake so ne kuma wanda zai faranta masa ni kuma burina a koda yaushe kenan. Har ya fita ya kirani a waya yace na shirya gashi nan dawowa zamu fita tare, da nace masa Al'amin fa kar lokacin tashin su yayi bana nan sai ya ce ai ba jimawa zamuyi ba dan haka nayi maza na canza kayana na shirya Sharifa ina jin horn ɗin mota na fita. Raina fes na kame a gaban mota ina jin wani farinciki na ratsani. Na…-
247.6 K • Completed
-
- Previous 1 … 13 14 15 … 30 Next
