489 Results in the "Hausa Novels" category
-
Chapter
Kura a Rumbu – Chapter Nine
Ina ji wayata na ƙara na san kuma Bilal ne amma naƙi amsawa, Allah ya sani har raina naji haushin anin da ya mun. Wane irin tozarci ne lefe a leda? Idan bashi da kuɗin akwati ya ara mana ko kuma ya bar lefen gaba ɗaya tun da ni dama ban saka rai da zeyi mun ba. Shine kuma saboda rainin hankali har yana cewa ze bani mamaki da irin lefen da ze mun aiko ga mamaki nan ya bar mun abin faɗa a cikin dangi da unguwa. Kusan minti talatin ina kuka ina jiyo hayaniya sama sama daga falo, Anty Labiba ce ta tasa…-
247.6 K • Completed
-
-
Chapter
Kura a Rumbu – Chapter Fourteen
Afuwan kun jini shiru. Wadanda suke cikin comment section group na bayar da uzuri. A ɗarare na ƙarasa yinin cike da taraddadin yanda zamu kwashe da Bilal idan mun koma gida. Se da akayi magriba ya turo mun text a waya in fito mu tafi. Jikina ya sake yin sanyi, haka nayi sallama da Hajja da sauran yan gidan su tana ta mun godiyar abin arziƙi da tace an kawo musu daga gidan mu cikin azumi ga kuma turmin atamfa dana kai mata dama yanzu kuma na kaiwa mejegon itama Atamfa da wani lace cikin ɗinkunan biki da…-
247.6 K • Completed
-
-
Chapter
Kura a Rumbu – Chapter Four
*MASU ƁUKATAR A TALLATA MUSU HAJOJINSU ZA SU IYA TUNTUƁARMU TA LAMBOBIN 07045308523 MUN GODE* Ban yarda da gaske Bilal yake da yace ze turo saka rana ba se ranar Juma'a da Baba Salahu yazo gidan mu bayan sun gama maganar da za suyi da Abba yasa aka kirani. Seda muka gaisa kafin cikin tsare gida kasancewar sa me ɗan zafi ya kalle ni yace "Ranar lahadi idan Allah ya kaimu iyayen yaron da yake neman ki suka ce zasu zo saka rana, ina fatan da sanin ki?". Duk se na duburburce, abun yazo mun a ba zata domin…-
247.6 K • Completed
-
-
Chapter
Kura a Rumbu – Chapter Forty-two
A yayinda muke shirin kammala wannan littafi idan har kin san kina karantawa ba tareda kin siya ba kiyi ƙoƙari ki sauke nauyi domin babu lallai in yafe haƙƙina 🙏🏽🙏🏽 Cike da ƙaguwa da zancen ya ce "Yanzu dai Umma wanne ake so a ciki? Lefen ko kuma kuɗin za'a bayar ko ayi mata kayan yanda tace?" "To ai ni ba na ce ba, kaga ita Nuratu dai kayan tace tana so to ita ya kamata ka tambaya itama kaji wanne tafi so" ta bashi amsa sai ya girgiza kai ya ce "Ai na gaya miki yanda mukayi da ita, dama…-
247.6 K • Completed
-
-
HALIMA Yanda naga rana haka naga dare, sai naji ashe ma jiya baccin daɗi nayi yaune nake ganin asalin baƙin dare. Sai da aka idar da sallar asuba kafin na samu bacci ya fizgeni, sai dai ban wani yi nisa ba na farka sakamakon kiran suna na da nake ta ji anayi. Na tashi zaune daƙyar ina matse ido haɗi da dafe gefen kaina da nake ji kamar zai faɗo saboda ciwo. Mama na tsaye ta ce "Hala kin manta abinda Abbanku ya faɗa miki shiyasa kika shantake kina bacci har ƙarfe tara". Gabana ya yanke ya faɗi,…-
247.6 K • Completed
-
-
Chapter
Kura a Rumbu – Chapter Forty-six
"Kar kice haka mana Halima. Ke da na san ki jaruma shine zaki bari daga sama wata ta zo ta ƙwace miki miji kuma ki sakar mata? Haba mana dan Allah karki bani kunya. Na san abinda ya aikata miki dole kiji zafi ba ke ba hatta Hajja dake goyon bayansa a ko da yaushe a wannan karon tana adawa da auren nan dan wlh ba dan mun tausheta ba rantsuwa tayi akan sai ya saki yarinyar ba zata tare ba. Mu muka yi ta bata haƙuri saboda a ganina bai kamata ace a gyara ɓarna da ɓarna ba, ubangiji ya rigada ya ƙaddara…-
247.6 K • Completed
-
-
"Ashe baka da mutunchi kai mutumin banza ne ban sani ba? Ban taɓa zaton haka kake ba, ashe abinda kake aikatawa kenan a bayan idon mu kana can kana zubar mana da mutunchi kana tozarta kanka; matan banza kake bi Bilal?" Ya dafe in da ta mare shi ba tareda ya bari sun haɗa ido ba ya ce "Ni wlh ba wasu mata da nake bi Hajja sharri kawai suka mun". Wani marin ta sake kai masa ya goce ta ce "Yanzu kake da bakin kare kanka kenan? Ni zaka kalla ka ce sharri ake maka saboda ka raina ni mai ya sa a gabansa baka…-
247.6 K • Completed
-
-
Chapter
Kura a Rumbu – Chapter Forty-one
A yayinda muke shirin kammala wannan littafi, idan kin san kina karantawa ba tareda kin siya ba kiyi ƙoƙari ki sauke nauyi domin babu lallai in yafe haƙƙina. Account details suna sama 🙏🏽🙏🏽 A hankali na buɗe ido na jin saukar abu mai sanyi a goshi na, ganin na buɗe idon ya saka Mama janye hannunta, ganin da tayi ina shirin sake komawa baccin ya saka ta ce "Da dai kin tashi haka nan kuma ki ƙarfafa jikinki tunda dai zazzaɓin ya sauka". Na yunƙura na zauna ina cije baki saboda kaina daya…-
247.6 K • Completed
-
-
Kafin mu gana gane me ya faru Mu'azzam ya shigo ɗakin babu kuma ɓata lokaci ya zare belt ɗin jikinsa ya shiga dukan Bilal yanda ka san Allah ya aiko shi. Gefe na ja da sauri cikin tashin hankali na ɗora hannu biyu a ka na fasa ihu ina kiran sunan Mu'azzam ɗin, abin takaici Nasir da yake namiji daya kamata ko murɗe Mu'azzam ɗin yayi ya ƙwace bulalar idan ma yana tsoron kaiwa Bilal ɗin agaji ya haɗa da shi wai sai ya tsaya daga gefe yana ce masa ya bari. Bilal kuwa kamar mace haka ya shiga birgima…-
247.6 K • Completed
-
-
Kafin na kai ga buɗewa Mu'azzam ya ɓalle murfin motar ya fita da sauri, gefe suka matsa, ina kallon su amma ban san mai ya cewa Bilal ɗin ba na dai ga ya kama baki da hannu biyu cikin alamar ninkuwar tashin hankalin da ya fito dashi akan fuskarsa kafin Mu'azzam ɗin ya nufo mota shi kuma ya biyo shi sai dai bai ko sake kallon sa ba ya shiga motar ya tayar. Na waiwaya ina kallon Bilal da ya bi motar da kallo cikin tashin hankali kafin na rufe ido na hoton ganin da na musu tar tamkar a lokacin abun yake…-
247.6 K • Completed
-
-
ALHAMDULILLAH Mun gama biki lafiya nagode da fatan Alkhairi. "Dan girman Allah Anty Amina kiyi mun wannan alfarmar, wlh nayi duk dabarata amma taƙi saurarona, idan naje gidan bata fitowa haka idan na kira wayarta bata amsawa. Ɗazu da safe suka zo ba dan na kulle gidan ta ciki ba ma da tuni sun kwashe kaya. Ke shaida ce ina son Halima duk abinda kuma ya faru sharrin shaiɗan ne da kuma Hajja amma wlh ba a son raina bane" ya faɗa bayan da ya tsayar da Anty Amina a ƙofar gida. Kallonsa ta ringayi har ya…-
247.6 K • Completed
-
-
Abinda ya fi tsaya mun a rai yanda duk sanda zamuyi magana sai ya ce ya san ina son sa, kenan shi baya so na kuma yana ɗaukata wawuya saboda ina sonsa dole na jure duk wani abu da zan fuskanta daga gare shi ko me? "Dan Allah karki ce Aa Halims ki taimaka mu haɗu kada ki bari mahassada suyi galaba akanmu" ya sake faɗa cikin marairaice kamar zai fashe mun da kuka. Cikin dakiyar da na aro na azawa kaina na ce "Ka sameni a gidan Anty Labiba bayan Magriba" "Gidan Anty Labiba kuma?" Ya faɗa kamar a ɗan…-
247.6 K • Completed
-
- Previous 1 … 13 14 15 … 30 Next
