Search
You have no alerts.

    489 Results in the "Hausa Novels" category


    • Kura a Rumbu – Chapter Eight Cover
      by Maryam Farouk (Ummu Maheer) "Sannu Halims, kin tashi" Bilal ya faɗa yana nufo ni se dai shigowar Anty Labiba ɗakin ta katse masa hanzari se ya ja gefe yana shafa kansa ita kuma ta balla masa harara kafin ta nufo ni ta kamani ganin ina ƙoƙarin tashi zaune. "Sannu" ta faɗa tana gyara mun ɗankwali na daya zame. Bilal ne ya fita ya kira wo likita suka dawo ɗakin tare da Abba. Bin su kawai nakeyi da kallo har likitan ya gama dubani yace babu komai jiki na ya dai dai ta amma a barni na sake hutawa. Abba yayi mana sallama akan ze je…
    • Kura a Rumbu – Chapter Nine Cover
      by Maryam Farouk (Ummu Maheer) Ina ji wayata na ƙara na san kuma Bilal ne amma naƙi amsawa, Allah ya sani har raina naji haushin anin da ya mun. Wane irin tozarci ne lefe a leda? Idan bashi da kuɗin akwati ya ara mana ko kuma ya bar lefen gaba ɗaya tun da ni dama ban saka rai da zeyi mun ba. Shine kuma saboda rainin hankali har yana cewa ze bani mamaki da irin lefen da ze mun aiko ga mamaki nan ya bar mun abin faɗa a cikin dangi da unguwa. Kusan minti talatin ina kuka ina jiyo hayaniya sama sama daga falo, Anty Labiba ce ta tasa…
    • Kura a Rumbu – Chapter Ten Cover
      by Maryam Farouk (Ummu Maheer) Ɗaki na koma dan bazan iya karyawa ni kaɗai ba na fara sabawa tun da mukayi aure da Bilal bamu taɓa raba kwano ba, yanzu bama na jin cin abincin raina duk babu daɗi. Tun ina sauraron jin ya buɗe ƙofa ya fito har bacci ya kwashe ni a kishingiɗen da nake. Ban farka ba se da naji ana ƙwala kiran sallar azahar, nasha mamakin irin baccin da nayi. Se da sake watsa ruwa saboda jiki na da naji duk ya ɗaure sannan nayi alwala na fito ina jina fayau ciki na a rarake. Sallar na farayi sannan na gyara…
    • Kura a Rumbu – Chapter Two Cover
      by Maryam Farouk (Ummu Maheer) *MASU ƁUKATAR A TALLATA MUSU HAJOJINSU ZA SU IYA TUNTUƁARMU TA LAMBOBIN 07045308523 MUN GODE* Washe gari daƙyar na yakice bacci nayi shirin makaranta, ina gama karatu Bilal ya kirani har gurin ƙarfe ɗaya muna hira kafin ya barni na kwanta dama ga gajiyar dana kwaso a makaranta jiyan na ɗora data girki sannan dana dawo gidan ma ban zauna ba na tarar anyi fenti a ɗakina gaba ɗaya an hargitsamun kaya seda na gyara su sannan na kwanta. Shaf na manta da munyi faɗa da Hansa'u jiya na zauna jiran zuwanta…
    • Kura a Rumbu – Chapter Three Cover
      by Maryam Farouk (Ummu Maheer) *MASU ƁUKATAR A TALLATA MUSU HAJOJINSU ZA SU IYA TUNTUƁARMU TA LAMBOBIN 07045308523 MUN GODE* Ranar ina idar da sallar isha'i nayi bacci saboda ɓacin rai seda na farka da asuba sannan naga missed calls ɗin Bilal guda biyu ya kirani tun ƙarfe tara na dare. Duk yanda nake cike da haushin abinda yamun jiya amma haka nan zuciyar dake sonsa ta angiza ni nabi kiran nasa. Murya ƙasa ƙasa muka gaisa ya shaida mun yana masallaci idanya fita ze kirani. Ko yasan ina fushi dashi ne se gashi bayan ya fito…
    • Kura a Rumbu – Chapter Four Cover
      by Maryam Farouk (Ummu Maheer) *MASU ƁUKATAR A TALLATA MUSU HAJOJINSU ZA SU IYA TUNTUƁARMU TA LAMBOBIN 07045308523 MUN GODE* Ban yarda da gaske Bilal yake da yace ze turo saka rana ba se ranar Juma'a da Baba Salahu yazo gidan mu bayan sun gama maganar da za suyi da Abba yasa aka kirani. Seda muka gaisa kafin cikin tsare gida kasancewar sa me ɗan zafi ya kalle ni yace "Ranar lahadi idan Allah ya kaimu iyayen yaron da yake neman ki suka ce zasu zo saka rana, ina fatan da sanin ki?". Duk se na duburburce, abun yazo mun a ba zata domin…
    • Kura a Rumbu – Chapter Five Cover
      by Maryam Farouk (Ummu Maheer) A motar Nasir na ganshi, ya kame a ciki yanda kasan tasa. A raina nace kuɗi dai ze yi wa Bilal kyau dan kalarsu aka masa. Yanayin surarsa da irin kayan da yake sakawa ba zaka kalli gidansu kace daga nan ya fito ba. Yana son gayu, sau tari na kan raya a raina nan yake kashe kuɗin sa gurin siyan sutura da takalma haɗi da agogo masu tsada duk abin da samari sa'anninsa suke yayi zaka ganshi dashi hakan kuma yana burge ni duk da ba wadata ce dashi ba amma ba yanda za'a yi ka ganshi ka raina shi. A gaban…
    • Kura a Rumbu – Chapter Six Cover
      by Maryam Farouk (Ummu Maheer) Duk nazarin na ban hango abin da take ganin na rashin dai dai ba. Rashin yi mun kyauta ne aibun sa ko kuwa rashin kammala ginin da be yi ba da kuma zancen lefe? A cikin ukun sune abin da nake ganin Anty Labiban take emphasizing se dai ni a ganin ta wannan ai ba komai bane ba. Bilal nake so ba abun hannunsa ba. Iya kar ƙoƙari yana yi gurin ganin ya kammala in da ze ajiye ni kuma ba a ɗaura auren nan an ga be yi mun lefe ba balle su ce wani abu. Ni duk wani lefe da wasu bidi'o'i basa gabana duk da dai ba…
    • Kura a Rumbu – Chapter Thirteen Cover
      by Maryam Farouk (Ummu Maheer) Kasaƙe nayi ina kallon sa har ya fice daga kitchen ɗin lokaci ɗaya jiki na yayi sanyi lanƙwas kamar an watsa mun ruwan sanyi. A hankali na ajiye bowl ɗin hannu na na dafe drawer baya na da hannu biyu jin jiri na neman ɗiba ta. "Sam wannan ba Bilal bane, ba halin sa bane akwai wani abu da yake damun sa tabbas" abin da na furta a fili kenan cikin son ƙarfafawa kaina guiwa da kuma bawa kaina tabbacin ba cikin sani Bilal yayi mun wannan tozarcin ba. Nafi minti biyar kafin na tattara ƙarfin daya rage…
    • Kura a Rumbu – Chapter Fourteen Cover
      by Maryam Farouk (Ummu Maheer) Afuwan kun jini shiru. Wadanda suke cikin comment section group na bayar da uzuri. A ɗarare na ƙarasa yinin cike da taraddadin yanda zamu kwashe da Bilal idan mun koma gida. Se da akayi magriba ya turo mun text a waya in fito mu tafi. Jikina ya sake yin sanyi, haka nayi sallama da Hajja da sauran yan gidan su tana ta mun godiyar abin arziƙi da tace an kawo musu daga gidan mu cikin azumi ga kuma turmin atamfa dana kai mata dama yanzu kuma na kaiwa mejegon itama Atamfa da wani lace cikin ɗinkunan biki da…
    • Kura a Rumbu – Chapter Fifteen Cover
      by Maryam Farouk (Ummu Maheer) Ban tanka masa ba na shiga tattare kayan dake ajiye dana gama kuma na wuce ɗakina na kwanta, nayi mamakin ganin ya biyo ni, nayi lamo a kan gado ina sauraren sa har ya gama uzure uzurensa na bacci kafin ya kwanta a baya na tare da jana jikin sa yana cewa "Nasan ba bacci kike yi ba juyo na baki barka da sallah" nayi masa banza duk yanda yake ya mutsani da son se na biye masa na dake daya gaji ya sake ni ina jin sa yana tsaki har baccin gaske ya ɗauke ni. Washe gari nayi zaton ze cigaba da fushin amma naga…
    • Kura a Rumbu – Chapter Sixteen Cover
      by Maryam Farouk (Ummu Maheer) *Nayi kuskuren rubutu a page 13, ajizanci ne, abinda ke raina daban abinda alƙalamina ya rubuta daban. Ina fatan zaku mun uzuri* Na ringa juya zancen Farisa a raina bayan ta tafi har sanda Bilal ya dawo sau biyu ina buɗe baki da niyyar tambayar sa gaskiyar abin da ta faɗa mun se na kasa daga ƙarshe na tattara zancen na watsar har ina ganin baike na dana yarda da maganar tata har na saka a raina. Ta ya ma haka zata yuwu? Kawai dai haɗa guri ne irin na Farisa amma kuma idan tayi ƙarya ta ƙulla abu…
    Note
    error: Content is protected !!