Search
You have no alerts.

    489 Results in the "Hausa Novels" category


    • Kura a Rumbu – Chapter Thirty-five Cover
      by Maryam Farouk (Ummu Maheer) Amirah ta ɗaga Sharifa data saka kuka daidai lokacin da Mama ta fito daga kitchen lokacin kuma Al'amin shima ya shigo Suraj na biye dashi da akwatin mu. "Ku kuma daga ina haka da sassafe?" Mama ta tambaya, Suraj ya ajiye kayan yana cewa "Tareda Babansu suke" ya juya ya fita sai Amirah tace "Yaya Haliman tana ciki itama". Tsaye Mama tayi kafin tace "Toh lafiya dai?" "Gaskiya ba lafiya ba kinga fa jefar da Sharifa tayi ta wuce ina mata magana ko saurarona ma batayi ba" Amirah ta amsa mata. Jumm tayi tana…
    • Kura a Rumbu – Chapter Thirty-eight Cover
      by Maryam Farouk (Ummu Maheer) Madallah da mutane masu karamci. Nagode ƙwarai dagaske, ina lafiya wani aiki ne ya ɗauke ni tsayin kwanaki amma Alhamdulillah mun kammala na kuma gode ƙwarai da haƙurinku ina fatan har mu kammala babu wani uzuri da zai sake gifta mana 🙏🏽🙏🏽🙏🏽 *KURA A RUMBU littafin kuɗi ne 800, yake mai jira nayi posting ki fitar kiji tsoron Allah dakw da wacce take jira ki turo ta karanta a bati ku guji haƙƙin komai ƙanƙantarsa. Duk wacce ta shirya sauke nauyi ta tura mun kuɗi na a asususun…
    • Kura a Rumbu – Chapter Thirty Cover
      by Maryam Farouk (Ummu Maheer) Watan Al'amin goma sha takwas na yaye shi a kuma watan na samu wani cikin wanda ko kusa Bilal bai yi maraba da samuwar sa ba. "Wai dama bakiyi komai na tsarin Iyali ba? Ni na zata hankalin ki zai baki da kiyi ba sai an tuna miki ba, kina kallon yanda abubuwa duke tafiya kuma kawai zaki kama ki wani sake yin ciki. To ni dai gaskiya ban so haka ba" Abun da ya faɗa kenan lokacin da na shaida masa ina da cikin. Gaba ɗaya sai na rasa yanda zan fassara maganganun sa. Fassara ta kai tsaye dai na san yana nufin…
    • Kura a Rumbu – Chapter Thirteen Cover
      by Maryam Farouk (Ummu Maheer) Kasaƙe nayi ina kallon sa har ya fice daga kitchen ɗin lokaci ɗaya jiki na yayi sanyi lanƙwas kamar an watsa mun ruwan sanyi. A hankali na ajiye bowl ɗin hannu na na dafe drawer baya na da hannu biyu jin jiri na neman ɗiba ta. "Sam wannan ba Bilal bane, ba halin sa bane akwai wani abu da yake damun sa tabbas" abin da na furta a fili kenan cikin son ƙarfafawa kaina guiwa da kuma bawa kaina tabbacin ba cikin sani Bilal yayi mun wannan tozarcin ba. Nafi minti biyar kafin na tattara ƙarfin daya rage…
    • Kura a Rumbu – Chapter Ten Cover
      by Maryam Farouk (Ummu Maheer) Ɗaki na koma dan bazan iya karyawa ni kaɗai ba na fara sabawa tun da mukayi aure da Bilal bamu taɓa raba kwano ba, yanzu bama na jin cin abincin raina duk babu daɗi. Tun ina sauraron jin ya buɗe ƙofa ya fito har bacci ya kwashe ni a kishingiɗen da nake. Ban farka ba se da naji ana ƙwala kiran sallar azahar, nasha mamakin irin baccin da nayi. Se da sake watsa ruwa saboda jiki na da naji duk ya ɗaure sannan nayi alwala na fito ina jina fayau ciki na a rarake. Sallar na farayi sannan na gyara…
    • Kura a Rumbu – Chapter Sixty Cover
      by Maryam Farouk (Ummu Maheer) Ranar da Bilal ya kwana bakwai a Asibiti aka sallame shi sai Hajja wacce tun zuwan Fadila jikinta ya sake rikicewa sauƙin data fara samu komai yaja baya bata da aiki sai kuka da Allah ya isa ga Ahlan da tace ya yaudaresu ya auri autarta yaje yana azabtar mata da ita. Ganin jikin Bilal yayi sauƙi sai abinda ba za'a rasa ba ya saka aka sallameshi bayan likita ya ja masa kunne sosai akan kulawa da lafiyarsa. Sosai Zulaiha ke tsaye a kansa tana kulawa dashi, yanda Bilal yayi wani sanyi ƙalau lokaci ɗaya…
    • Kura a Rumbu – Chapter Sixteen Cover
      by Maryam Farouk (Ummu Maheer) *Nayi kuskuren rubutu a page 13, ajizanci ne, abinda ke raina daban abinda alƙalamina ya rubuta daban. Ina fatan zaku mun uzuri* Na ringa juya zancen Farisa a raina bayan ta tafi har sanda Bilal ya dawo sau biyu ina buɗe baki da niyyar tambayar sa gaskiyar abin da ta faɗa mun se na kasa daga ƙarshe na tattara zancen na watsar har ina ganin baike na dana yarda da maganar tata har na saka a raina. Ta ya ma haka zata yuwu? Kawai dai haɗa guri ne irin na Farisa amma kuma idan tayi ƙarya ta ƙulla abu…
    • Kura a Rumbu – Chapter Six Cover
      by Maryam Farouk (Ummu Maheer) Duk nazarin na ban hango abin da take ganin na rashin dai dai ba. Rashin yi mun kyauta ne aibun sa ko kuwa rashin kammala ginin da be yi ba da kuma zancen lefe? A cikin ukun sune abin da nake ganin Anty Labiban take emphasizing se dai ni a ganin ta wannan ai ba komai bane ba. Bilal nake so ba abun hannunsa ba. Iya kar ƙoƙari yana yi gurin ganin ya kammala in da ze ajiye ni kuma ba a ɗaura auren nan an ga be yi mun lefe ba balle su ce wani abu. Ni duk wani lefe da wasu bidi'o'i basa gabana duk da dai ba…
    • Kura a Rumbu – Chapter Seventeen Cover
      by Maryam Farouk (Ummu Maheer) Be ko saurari tayin abincin da na masa ba ya fice daga gidan bayan yayi wanka yana sake jaddada mun Fadila ta bar gidan kafin ya dawo, bayan fitar sa na shiga gyara falon da tayi mun kaca kaca da shi dan tun shigowar Bilal ɗin ta koma ɗaki na in da na sauketa. Na tabbatar taji banbamin da yakeyi tun da ba a hankali yayi maganar da ze fita ba, na ɗauka daya fitan zata tuntuɓe ni da zancen amma shiru se ma dawowa falo da tayi zata sake tarwatsa gurin na dakatar da ita ta hanyar ce mata ba nisa yayi ba…
    • Kura a Rumbu – Chapter Seven Cover
      by Maryam Farouk (Ummu Maheer) Na fi minti goma tsaye a ƙofar gidan mu ni ban shiga ba kuma ban bar gurin ba. Maganganun da mu kayi da Bilal ne suke mun amsa kuwwa a kunnuwa na da ƙwaƙwalwata bana kin ko wanne sauti dake zagaye dani banda muryar sa. "Ba ni da kuɗin da zan ƙarasa gini Halima, ba kuma ni da sararin da zan kama haya a yanzu. Abu biyu ya rage, ko dai iyayen ki su ɗaga auren mu ko kuma mu haƙura gaba ɗaya, ƙila a gaba idan muna da rabon kasancewa tare se muyi aure. Ina son ki Halima amma bani da halin mallakar ki a…
    • Kura a Rumbu – Chapter One Cover
      by Maryam Farouk (Ummu Maheer) "Malam idan kaje ƊAN ALJANNAH zan sauka" na faɗa ina nunowa me Adaidaitan da muke ciki saitin in da ze ajiye ni, bayan daya gama daidaita parking na sauka ba tareda na kalli Hansa'u data kalli ɗaya ɓangaren ba nace "Da ace kuturwa Allah yayi ni se inji haushi dan kince ba zaki tayani aiki ba, dake ko babu ke bazan rasa wanda zasu rufamun asiri ba" na faɗa ina miƙawa me Adaidaita ɗari biyar. Bata tankamun ba na juya ba tareda na amsa tambayar da me mashin ɗin yake mun ba akan iya kuɗi na ze ɗauka…
    • Kura a Rumbu – Chapter Nineteen Cover
      by Maryam Farouk (Ummu Maheer) Ba zan iya cewa ga ta yanda muka fita daga gidan ba ni dai kawai na san munje gidan mu; muna sauka daga Adaidaita sahu Amirah ta sake ni na dafe gini saboda jirin dake kokawar kayar dani ita kuma ta tura ƙofar get ta shiga tana rushewa da kuka tamkar wadda tazo isar da saƙon mutuwa. Daƙyar na cira ƙafata na rufa mata baya ina yi ina dakatawa saboda ciwon marar dake taso mun, na dafe ƙofar shiga falon na tsaya ina kallon mazauna ciki da suka rufu kan Amiran cikin tashin hankali suna tambayar ta ba'asin…
    Note
    error: Content is protected !!