Search
You have no alerts.

    489 Results in the "Hausa Novels" category


    • Kura a Rumbu – Chapter Twenty-five Cover
      by Maryam Farouk (Ummu Maheer) Ina zaune a falon har Baba Jummai ta gama haɗa kayan ta tana kukan da nake ji kamar na tashi na shaƙe mata wuya idan ya so ta yi mai dalili. Ni da ta ke neman ta kashewa aure ai ni ce da kuka ba ita ba, akan na ce ta tafi tun da ita ta janyo ni ma aka ce na tafin shi ne ta fasa kuka wai na mata rashin kunya tana ƙoƙarin kare mun mutunchi na watsa mata ƙasa a ido. Ta shi na yi na goya Al'amin bayan da ta fito da jakar ta daga ɗaki ina kallon ta na ce "Kuma wlh karki gayawa kowa abin da ya faru, kawai…
    • Kura a Rumbu – Chapter Twenty-eight Cover
      by Maryam Farouk (Ummu Maheer) Washe gari da wuri na fara haɗa kayan mu dan komawa gidan Anty Labiba duk da jirgin dare su Mama zasu bi amma da wuri nake so na tafi can ɗin dan ko rakiya ba zan tsaya yi musu ba. Gaba ɗaya raina babu daɗi na tashi, na ɗauka Bilal zai sake kira na daga baya ko kuma da asuba amma shiru. Ina zuge akwatin kaya na Zainab ta shigo ta ce mun na zo na yi baƙi, na ɗora mayafin doguwar rigar yadin jiki na ina ƙoƙarin kawar da ɓacin ran dake kwance akan fuskata na fita falon. Turus na yi a bakin ƙofa…
    • Kura a Rumbu – Chapter Twenty Cover
      by Maryam Farouk (Ummu Maheer) Washe gari har azahar banga Bilal kuma babu wani daga dangin sa se yan uwana da suke ta kaikawo a gurin. A ƙa'ida da safe za'a sallame mu tunda na cike awanni shida na ƙa'ida amma da likita ya shigo duba mu ya ɗauki yaron se yace akwai alamun jundice a tare dashi dan haka ba zasu sallame mu a lokacin ba se mun ƙara 12 hours under observation idan abun is not severe da zamu iya tafiya gida tohm. Nan da nan hankali na ya tashi saboda yanda nake jin labarin jundice ance yana kashe jarirai, shaiɗan da…
    • Kura a Rumbu – Chapter Twelve Cover
      by Maryam Farouk (Ummu Maheer) "Idan har izini na kike nema ban yarda ba, ko da yake ai kin saba yin gaban kanki. Kiyi duk yanda kika so Halima lokacin ki ne dama kika samu". Abinda Bilal ya gaya mun kenan bayan dana same shi akan maganar posting ɗina zuwa garin Bauchi. Duk yanda kuma naso da ya zauna muyi magana ta fahimta yaƙi, ƙarshe ma barin mun part ɗin yayi gaba ɗaya ya tafi can part ɗin sa da falon kaɗai muke amfani dashi ina jin sa a daren ya gyara ɗakin tun da dama da hado da komai a ciki ya dawo ya ɗauki bedsheets da…
    • Kura a Rumbu – Chapter Three Cover
      by Maryam Farouk (Ummu Maheer) *MASU ƁUKATAR A TALLATA MUSU HAJOJINSU ZA SU IYA TUNTUƁARMU TA LAMBOBIN 07045308523 MUN GODE* Ranar ina idar da sallar isha'i nayi bacci saboda ɓacin rai seda na farka da asuba sannan naga missed calls ɗin Bilal guda biyu ya kirani tun ƙarfe tara na dare. Duk yanda nake cike da haushin abinda yamun jiya amma haka nan zuciyar dake sonsa ta angiza ni nabi kiran nasa. Murya ƙasa ƙasa muka gaisa ya shaida mun yana masallaci idanya fita ze kirani. Ko yasan ina fushi dashi ne se gashi bayan ya fito…
    • Kura a Rumbu – Chapter Thirty-two Cover
      by Maryam Farouk (Ummu Maheer) *Barkanmu da Sallah yan uwa* 🙏🏽 Sai da na fita kofar asibitin kafin na tsaya ina raba ido, ina zan nufa ne ma? Gida zan tafi ko kuwa gari zan shiga cigiyar inda Bilal ya tafi? Na kai hannu na share laimar da naji akan fuskata wadda ban tantance hawaye bane ko zufa kafin na shiga tare abin hawa, gidanmu na wuce, ban ko karɓi canji ba bayan na sauka na shige gidan a bakin ƙofa na zauna kamar wata zararriya na fasa kukan da ya saka Mama ta fito daga falo kamar zata hantsila da Sharifa a hannunta ta…
    • Kura a Rumbu – Chapter Thirty-three Cover
      by Maryam Farouk (Ummu Maheer) Banji komai dangane zaman da ya ce Hajja zatayi ba dukda nasan ba jituwa mukeyi da ita ba amma kuma abinda yake so ne kuma wanda zai faranta masa ni kuma burina a koda yaushe kenan. Har ya fita ya kirani a waya yace na shirya gashi nan dawowa zamu fita tare, da nace masa Al'amin fa kar lokacin tashin su yayi bana nan sai ya ce ai ba jimawa zamuyi ba dan haka nayi maza na canza kayana na shirya Sharifa ina jin horn ɗin mota na fita. Raina fes na kame a gaban mota ina jin wani farinciki na ratsani. Na…
    • Kura a Rumbu – Chapter Thirty-six Cover
      by Maryam Farouk (Ummu Maheer) Ƙaddara da kwaɗayi haɗi da son zuciya irin nasa ya janyo masa faɗawa tarkon nadama. Dukda dai tsohon halin sa ne, a baya lokacin samartaka ya kan kwatanta domin rage zafi kamar yanda hakan yake ɗabi'ar dayawan Samari a wannan zamanin. Sun ɗauki hakan a matsayin wayo ko dabara a ganin su ai basu aikata Zina a zahiri ba sai dai suna mantawa da hanin ubangiji da yace kada a kusanci Zina ba wai kada a aikatata ba Aa kwata kwata kada a kusanci duk wani abu da yake da jiɓi da ita. Da yawan su sun ɗauki…
    • Kura a Rumbu – Chapter Thirty-seven Cover
      by Maryam Farouk (Ummu Maheer) HALIMA Sati na biyu a Asibiti kafin aka sallameni zuwa lokacin kuma Alhamdulillah na samu sauƙi sosai ko in ce nayi matuƙar ƙoƙarin gurin yakice damuwar dake raina ko dan in samu na bar gadon Asibitin domin a zahiri basu da maganin matsalata kamar yanda kullum Dr yake nanata mun ni zan yiwa kaina maganin matsalata in cire koma menene na saka a raina yake neman halakani. Zama yayi ya mun karatun Yaya da ƙanwa kamar yanda ya ce, "Ki dubi yanda hankalin iyayenki da yan uwanki duk ya tashi saboda ke, ki…
    • Kura a Rumbu – Chapter Thirty-one Cover
      by Maryam Farouk (Ummu Maheer) Nayi mamakin yanda Bilal bai musa ba lokacin da nayi masa maganar service. Nayi sa'a a lokacin ana dab da fara registration dama, ranar da aka buɗe kuwa banyi wasa ba na je na yi a matsayin mara aure saboda ko da na gaya masan ya ce toh nayi zaton zai je ya fitar da certificate of marriage da domicile letter waɗanda zan buƙata amma har ranar ta zo bai ce mun komai ba nima kuma banyi masa magana ba dan ina gudun kada ya canza ra'ayi. Posting ya fito aka kaini, ban wani damu ba tunda ba nesa bane nasan…
    • Kura a Rumbu – Chapter Thirty-nine Cover
      by Maryam Farouk (Ummu Maheer) Ko da ya koma gida daƙyar tunanin yanda Hajja zata karɓi zancen auren daya ɗaura ba tareda saninta ba ya danne waswasin da zuciyarsa ta dasa masa akan Zulaiha. Wayarsa ma kashewa ya sakeyi bayan daya shiga gida bai kuma kunnata ba sai washe gari gurin ƙarfe goma bayan daya shirya zuwa gidan Hajjan in da daga can kuma yake so ya biya gurin Halima. A tsakar gida ya tarar da Hajja tareda Fadila suna duba kayan da kallo ɗaya ya musu ya fahimci daga gurin Jalilah suka fito dan yanzu ta lalata Hajjan da…
    • Kura a Rumbu – Chapter Thirty-four Cover
      by Maryam Farouk (Ummu Maheer) Kwanaki biyu da suka biyo baya nayi su ne cikin taimakon ubangiji domin a kowacce daƙiƙa ji nakeyi tamkar numfashi na zai iya yankewa. Babu abinda yake shiga cikina banda ruwa da paracetamol da nake ta banka saboda azababben ciwon da kaina kama, ikon Allah kaɗai yake riƙe dani akan ƙafafuna hatta yaran ma game game kawai nake musu duk abinda hannu ya kai nake haɗawa na basu su ci. Nayi kuka har hawayena sun ƙafe ya zama sai na zuci nakeyi, a duk sanda na tuna abinda naji kuma na gani dangane da…
    Note
    error: Content is protected !!