Search
You have no alerts.

    489 Results in the "Hausa Novels" category


    • Mijin Kwaila by Bilyn Abdul Thumbnail

      MIJIN ‘KWAILA ����‍♀ sabon salo daga labarin zahra adam ishaq “-chapter one-“ Ahankali yake tafiya da motar sakamakon yanda ya iske saitin bakin makarantar yaran yacika yakuma batse da dandazon yaran da’aka riga aka taso daga makaranta,ya d’anja gajeren tsoki lokaci guda yana kallon tsadadden agogon dake hannunshi ya taka burki kamar yanda sauran masu ababen hawa y’an uwanshi sukaja nasu burkin sakamakon dakatar…

    • MALEEKA MALIK Thumbnail

      💦MALIKA MALIK💦..!* (Sai na rama..) By Janafty 1 Free Fage KATSINA Adaidai kan Titin akwai yan Sanda wadanda suke patrole awajen,Suna tsatsaye ne Gefe kuma ga motocinsu guda biyu akallah yan sanda zasu kai su Biyar kowannesu, sanye da uniform dinsu bakake,da ganin kayan jikinsu basai ka tambayesu ba,zaka gane dukansu inspector ne,domin basu da kowani Rank ajikin kakin nasu,dukkansu fuskarsu sanye da Hula…

    • Maleeka Malik Cover
      by Nadmin MASU ƁUKATAR A TALLATA MUSU HAJOJINSU ZA SU IYA TUNTUƁARMU TA LAMBOBIN 07045308523 MUN GODE 1 Adaidai kan Titin akwai yan Sanda wadanda suke patrole awajen,Suna tsatsaye ne Gefe kuma ga motocinsu guda biyu akallah yan sanda zasu kai su Biyar kowannesu, sanye da uniform dinsu bakake,da ganin kayan jikinsu basai ka tambayesu ba,zaka gane dukansu inspector ne,domin basu da kowani Rank ajikin kakin…
    • MAKAUNIYAR KADDARA Thumbnail

      MAKAUNIYAR ƘADDARA😭 Da sunan ALLAH mai rahama mai jinƙai. Ya UBANGIJIN al’arshi ka bani ikon rubuta abin zai amfani al’ummar MANZON ALLAH. Ka tsare harshena da alƙalamina rubuta abinda zai cutar da ni da duk wanda zai karanta littafin nan. Ka bani ikon rubuta abinda zai amfaneni duniya da lahira ni da masu karatun. Ina mai farin cikin sake dawowa a wannan karon tare…

    • Blog

      MAITAFIYA

      MAITAFIYA Thumbnail

      By Zahra Tabiu Tsokaci Wata irin gaba ce tsakanin talaka da mai kudi. Mai kudi yana yiwa talaka kallon nesa-nesa, irinka irin wahala, Allah nagode maka ba ni ba ne. Yakan kara yi masa kallon na fi ka, da gumina na nema kai ma sakacinka da mutuwar zuciya ya hana ka ka samu…ka da ka roke ni don baka nan lokacin da na nema! …

    • MAI IDO A TSAKAR KA Thumbnail

      MAI IDO A TSAKAR KA (DUNIYA) GAWURTATTU UKU BADI’AT IBRAHIM MRS BUKHARI B4B ( GIDAN ƘAMSHI) ƊANƊANO! ƊANƊANO!! ƊANƊANO!!! 1 DAMATURU Hadarine gagarumin gaske a garin namu na Damaturu, misalin ƙarfe huɗun yamma ne, amman yanayin duhun garin in ka kalla, zakayi tunanin asubane, ga wata sassanyar iska dake busawa tare da ƙananun yayyafin afumangai da aka soma yanzu. Jama’a sai gudu suke yi,…

    • Kura a Rumbu – Chapter Two Cover
      by Maryam Farouk (Ummu Maheer) *MASU ƁUKATAR A TALLATA MUSU HAJOJINSU ZA SU IYA TUNTUƁARMU TA LAMBOBIN 07045308523 MUN GODE* Washe gari daƙyar na yakice bacci nayi shirin makaranta, ina gama karatu Bilal ya kirani har gurin ƙarfe ɗaya muna hira kafin ya barni na kwanta dama ga gajiyar dana kwaso a makaranta jiyan na ɗora data girki sannan dana dawo gidan ma ban zauna ba na tarar anyi fenti a ɗakina gaba ɗaya an hargitsamun kaya seda na gyara su sannan na kwanta. Shaf na manta da munyi faɗa da Hansa'u jiya na zauna jiran zuwanta…
    • Kura a Rumbu – Chapter Twenty-two Cover
      by Maryam Farouk (Ummu Maheer) "Dagaske ne Anty, masu ƙwacen mashin ne suka bige shi; waɗan da suka kai shi asibitin ma na san ɗaya daga cikin su tare muka fara Maitama Sule" Mu'azzam ya faɗa jin Anty Labiba ta dage akan ƙarya kawai Bilal ya shirga ba wani abu daya same shi. Zuwan ta kenan ta tarar suna jimamin abun, Na kira Abba na gaya masa an masa takwara sannan na ƙara da faɗa masa dalilin da ya saka Bilal be duba mu ba har na bawa Bilal ɗin waya suka gaisa da Abban ya sake bashi haƙuri. Bayan mun gama wayar ne ya fito yake…
    • Kura a Rumbu – Chapter Twenty-three Cover
      by Maryam Farouk (Ummu Maheer) Se bayan sallar isha'i Bilal ya shigo gidan lokacin ina wanka saboda kitso da lallen da bamu gama da wuri ba se lokacin. Leda na ga ni da kuma ƙaramin kwalin biscuit a ajiye, sai bayan da na shafa mai na saka kaya kafinna nufi falo muka gamu a bakin ƙofa yana shirin shigiwa dan haka na juya. "Ga shi nan na suna ne se ki bawa waɗan da za su zo da safe" ya faɗa yana nuna mun kayan daya ajiye ɗin. "Har yanzu baka ce komai ba na ɗauka ma ai ka manta gobe ne sunan" na mayar masa da amsa ina kallon sa, se…
    • Kura a Rumbu – Chapter Twenty-six Cover
      by Maryam Farouk (Ummu Maheer) Ko ba'a faɗa mun ba na san da wahala idan jini na bai hau ba, daƙyar na lallaɓa Al'amin ya yi shiru na goya shi kafin na fita samawa Bilal abin da zai ci. Bamu da komai da zai ciyu da safe ban da taliya. Ita na yi jollof da sauran miyar da ta rage na dafa masa baƙin shayi. Ya ringa kallon abincin kamar wanda na aje wa mugun abu kafin cikin faɗa faɗa ya shiga tambayar babu nama a gidan ne da zan dafa masa tsurar taliya ko me? Haka na koma na ɗebo masa naman ina ajiyewa ya sake balbale ni da wata…
    • Kura a Rumbu – Chapter Twenty-seven Cover
      by Maryam Farouk (Ummu Maheer) Na ɗauka da wasa Mama take yi sai washe gari da safe bayan mun yi wanka na koma rage baccin da ban yi ba cikin dare saboda Kukan Al'amin ban jima da kwanciya ba Zainab ta tashe ni akan Mama tana kira na. A falon Abba na same ta, muka sake gaisawa sai Abba ya ce "Mamanku ta ce mijin ki yayi tafiya ko?" Ba tare da na kalle shi ba na amsa haɗi da gyaɗa masa kai dan haka kawai kuma kunyar Abban na ke ji yanzu, ni dai jiki na bai bani aka Baba Jummai bata basu labarin abin da ya faru ba yanda kuma suka mun…
    • Kura a Rumbu – Chapter Twenty-one Cover
      by Maryam Farouk (Ummu Maheer) Ina ɗaki, hayaniyar yan dubiya duk ta cika mun kunne, tun da Anty Amina ta tambaye ni abinda za'a dafa da rana na nuna mata shinkafa da mai wanda su kaɗai suka suka rage mana a gidan, ina ganin Hajja ta shiga kitchen ɗin na fito na barsu. Ta biyo ni ɗaki tana tambaya ta sauran kayan girki nace mata iya abinda muke dashi kenan, zata yi magana Anty Aminan ta jata waje shikenan nayi zamana a ɗakin ban sake fita ba suma kuma babu wadda ta sake leƙa ni. Da yaron yana gurin su ma aka maido mun dashi…
    Note
    error: Content is protected !!