489 Results in the "Hausa Novels" category
-
Story
Bakar Ayah
.”zaki iya ki daure kinji,ki daure zaki iya,kin kusa saura kaɗan ,daure daure ga nan kan ina hangoshi” Nurse ɗin take fada,wacce ta haɗa gumi sharkaf saboda firgici. “Nafara gajiya nurse,karfina duk ya ƙare!” Share gumin tayi a karo na ba adadi kafin ta kalli wata wacce take gefenta,da alama tafi waccar ɗin matsayi,dan kayansu ma ba iri ɗaya bane. “”Ke maza hanzarta ki…-
1.6 K • Sep 17, '25
-
1.9 K • Sep 17, '25
-
2.0 K • Sep 17, '25
-
-
HALIMA Cike da haushin Dr Salman na koma gida ranar Juma'ar, haka nan ya san banda mu zasuyi meeting ɗin amma ba'a gaya mana ba saida muka rigada muka je tukunna sannan babu damar tafiya haka mukayi zaman banza har sha biyu kafin muka tashi. Dama-dama da na ji na samu nayi clearance ɗina kafin na wuce gida. Bayan sallahr magriba Anty Labiba tace mu shirya muje gidan Uncle Mudassir yaronsa na biyu Khalil ya faɗi ɗazu da safe ya samu karaya, muna shirin fita Mama ta kirata tana tambayarta yaushe zamuje…-
247.6 K • Completed
-
-
Sai dana tabbatar ya fice daga building ɗin gaba ɗaya kafin na fita daga office ɗin ina kalle-kalle kamar mara gaskiya, ganin babu kowa ya saka na shige Elevator da sauri, a reception na haɗu da Juwairiyya ta kalleni fuska ba yabo ba fallasa kafin tace "Ina kika tafi tun ɗazu?" Wucewa nayi ba tareda na bata amsa ba ta sake cewa "Dr Sulaiman yana neman ki?" Na amsa da "Toh" ba tareda na tsaya ba na fita. A can kan hanya ya tarar dani, fuska ba annuri ya sauke glass yana kallona kafin ya ce "Get in".…-
247.6 K • Completed
-
-
Chapter
Kura a Rumbu – Chapter Sixty
Ranar da Bilal ya kwana bakwai a Asibiti aka sallame shi sai Hajja wacce tun zuwan Fadila jikinta ya sake rikicewa sauƙin data fara samu komai yaja baya bata da aiki sai kuka da Allah ya isa ga Ahlan da tace ya yaudaresu ya auri autarta yaje yana azabtar mata da ita. Ganin jikin Bilal yayi sauƙi sai abinda ba za'a rasa ba ya saka aka sallameshi bayan likita ya ja masa kunne sosai akan kulawa da lafiyarsa. Sosai Zulaiha ke tsaye a kansa tana kulawa dashi, yanda Bilal yayi wani sanyi ƙalau lokaci ɗaya…-
247.6 K • Completed
-
-
Chapter
Kura a Rumbu – Chapter Forty
Tunda yaga babur ɗin Kawu Sani a ƙofar gidan gabansa ya shiga faɗuwa domin ya san abinda akw ɓoyewa ya rigada ya bayyana. Sai dai kuma shima yana buƙatar hakan ko dan ya samu a wuce gurin Zulaiha ta tare amma kuma ya san da wahala su kwasheta da daɗi da Hajja. Tun daga tsakar gida yake jiyo maganganun Hajjan tamkar zata ari baki tsabar masifar da take zazzagawa, yana ɗaga labule suka haɗa ido kallon data jefa masa sai da yaji yan cikin sa sun juya, ta ce "Yawwa gara da kazo, dama Bilal idan har ni…-
247.6 K • Completed
-
-
Chapter
Kura a Rumbu – Chapter Fifty-six
Kwana uku Jalilah tayi a Kano ta wuce Abuja bayan ta bar alhakin sauke kayan da suka fara isowa a hannun Bilal. A tsakanin kwanakin har rama yayi; duk wanda ya sanshi kallo ɗaya zakayi masa ka fahimci yana cikin damuwa matuƙa, duk in da yake tunani zai buga lissafi ya fita abu ya gagara, idan ya haɗo nan sai can ya rushe ga Alhaji Lawan ya taso shi a gaba da zancen kuɗinsa dan tuni ya kwashe kayansa ya bar gidan kamar yanda ya ce har Ahlan mamallakin gida na asali ya saka an sake gyara ko ina sai jiran…-
247.6 K • Completed
-
-
Chapter
Kura a Rumbu – Chapter Forty-one
A yayinda muke shirin kammala wannan littafi, idan kin san kina karantawa ba tareda kin siya ba kiyi ƙoƙari ki sauke nauyi domin babu lallai in yafe haƙƙina. Account details suna sama 🙏🏽🙏🏽 A hankali na buɗe ido na jin saukar abu mai sanyi a goshi na, ganin na buɗe idon ya saka Mama janye hannunta, ganin da tayi ina shirin sake komawa baccin ya saka ta ce "Da dai kin tashi haka nan kuma ki ƙarfafa jikinki tunda dai zazzaɓin ya sauka". Na yunƙura na zauna ina cije baki saboda kaina daya…-
247.6 K • Completed
-
-
BILAL Yana kwance a gida Hajja ta kirashi wai ya kawo musu kayan miyan da za'ayi tuwon ɗaurin auren Fadila da za'a ɗaura a gobe Juma'a. Da yake a tsini suke yayi mata laifi shiyasa bai musa ba ya tashi ya tafi kasuwar Yankaba ya yiwo musu cefanen ya tafi ya kai. Zagayewa yayi yaje ya samu Kawu Ɗayyabu, Yayan Hajja ne da suke uba ɗaya da yake mutum ne mara ɗaukar raini shiyasa duk rashin mutunchin Hajjan take shakkarsa ko da wasa kuma bata bari wani abu ya gilma a tsakaninsu shi Bilal ɗin yaje ya samu…-
247.6 K • Completed
-
-
Chapter
Kura a Rumbu – Chapter Forty-two
A yayinda muke shirin kammala wannan littafi idan har kin san kina karantawa ba tareda kin siya ba kiyi ƙoƙari ki sauke nauyi domin babu lallai in yafe haƙƙina 🙏🏽🙏🏽 Cike da ƙaguwa da zancen ya ce "Yanzu dai Umma wanne ake so a ciki? Lefen ko kuma kuɗin za'a bayar ko ayi mata kayan yanda tace?" "To ai ni ba na ce ba, kaga ita Nuratu dai kayan tace tana so to ita ya kamata ka tambaya itama kaji wanne tafi so" ta bashi amsa sai ya girgiza kai ya ce "Ai na gaya miki yanda mukayi da ita, dama…-
247.6 K • Completed
-
-
HALIMA Yanda naga rana haka naga dare, sai naji ashe ma jiya baccin daɗi nayi yaune nake ganin asalin baƙin dare. Sai da aka idar da sallar asuba kafin na samu bacci ya fizgeni, sai dai ban wani yi nisa ba na farka sakamakon kiran suna na da nake ta ji anayi. Na tashi zaune daƙyar ina matse ido haɗi da dafe gefen kaina da nake ji kamar zai faɗo saboda ciwo. Mama na tsaye ta ce "Hala kin manta abinda Abbanku ya faɗa miki shiyasa kika shantake kina bacci har ƙarfe tara". Gabana ya yanke ya faɗi,…-
247.6 K • Completed
-
-
Kafin na kai ga buɗewa Mu'azzam ya ɓalle murfin motar ya fita da sauri, gefe suka matsa, ina kallon su amma ban san mai ya cewa Bilal ɗin ba na dai ga ya kama baki da hannu biyu cikin alamar ninkuwar tashin hankalin da ya fito dashi akan fuskarsa kafin Mu'azzam ɗin ya nufo mota shi kuma ya biyo shi sai dai bai ko sake kallon sa ba ya shiga motar ya tayar. Na waiwaya ina kallon Bilal da ya bi motar da kallo cikin tashin hankali kafin na rufe ido na hoton ganin da na musu tar tamkar a lokacin abun yake…-
247.6 K • Completed
-
-
ALHAMDULILLAH Mun gama biki lafiya nagode da fatan Alkhairi. "Dan girman Allah Anty Amina kiyi mun wannan alfarmar, wlh nayi duk dabarata amma taƙi saurarona, idan naje gidan bata fitowa haka idan na kira wayarta bata amsawa. Ɗazu da safe suka zo ba dan na kulle gidan ta ciki ba ma da tuni sun kwashe kaya. Ke shaida ce ina son Halima duk abinda kuma ya faru sharrin shaiɗan ne da kuma Hajja amma wlh ba a son raina bane" ya faɗa bayan da ya tsayar da Anty Amina a ƙofar gida. Kallonsa ta ringayi har ya…-
247.6 K • Completed
-
- Previous 1 … 11 12 13 … 31 Next
