Search
You have no alerts.

    492 Results in the "Hausa Novels" category


    • by Sadi Sakhna Har suka fito daga cikin gidan su bombin babu wanda yacewa wani komai,saboda ɗumbin abin mamakin da suka gani. Magana suka ji a gefensu,suna waigawa suka ga ashe saurayin daya rakosu gidanne,yana jingine a bakin motar tasu. "Sannunku da fitowa,na tabbatar masu samu amsar abinda kukaje nemaba" "Taya kasan hakan,ko shiyasa ka tsaya kana jiran mufito,kenan kasan inda take?" "Eh to nasani bankuma sani ba,kunsan ance ba'a aikin banza,zan nuna muku hanyar dazaku bi ku sameta dai. Amma daman batun ku tsaya cikin…
    • by Sadi Sakhna Kwanaki sunzo sun tafi,a ƙallah Daneji ta samu shekara guda babu kaɗan gidan malam Ahmadu,kuma har yanzu babu wata matsala data fito tsakanin ta da mijinta,ko kuma kishiyarta. Tana binta ta sau da ƙafa,itama kuma tana kyautata mata a matsayinta na babba. Tun bayan watanta uku a gidan Malam Ahmadu yafara zaton samun ɗa,amma ganin shuru shuru yasa shi dole ya bar zancen. Daga lokacin yafara zaton wataƙila wata matsala ce daga gareshi. Hakanne yasa ya nunka kulawar dayake basu fiyeda a lokacin baya,domin…
    • by Sadi Sakhna Hannu tasa ta karbi jaririyar tareda mannata a jikinta,wata irin tsagwaron ƙaunar yarinyar ne ya jiyarci tsakiyar zuciyarta,tareda muradin kareta a ta kowacce fuska. Idanuwanta ta sauƙe akan jar fuskar jinjirar,wadda yake ɗauke da ƙankanin kyau mai tafiyar da duk mai kallonta. Hancinta babu makawa kowa yakalleta yaga na ubantane,sai bakinta kuma data biyo irin na mahaifiyar ta ɗan ƙarami,motsashi take a hankali tana neman inda zataji abincinta ya isa gareta,wanda hakan yasa ainihin Cute feature…
    • by Sadi Sakhna Babu 'bata lokaci daneji ta shirya domin su tafi asibitin,har sannan Bombee na hannun mahaifinta,motsi kaɗan idan tayi ya leƙata,gani yake tamkar ƙwai ne a hannunsa,zai iya fashewa a kowanne lokaci. Ƙosawa yayi darashin shiryawar tata da sauri,dukkuwa da yanda take iya ƙoƙarinta wajen yin saurin,gani yake kaman jinkirinta a lokacin wani abun zai iya faruwa. Fitowa sukayi daga ɗakin tareda yiwa Inna laari sallama kana suka kama hanyar asibitin a mashin ɗinsa. Yana tafiyah yana waiwayen ƴar…
    • Story

      Bakar Ayah

      by Sadi Sakhna .”zaki iya ki daure kinji,ki daure zaki iya,kin kusa saura kaɗan ,daure daure ga nan kan ina hangoshi” Nurse ɗin take fada,wacce ta haɗa gumi sharkaf saboda firgici. “Nafara gajiya nurse,karfina duk ya ƙare!” Share gumin tayi a karo na ba adadi kafin ta kalli wata wacce take gefenta,da alama tafi waccar ɗin matsayi,dan kayansu ma ba iri ɗaya bane. “”Ke maza hanzarta ki…
    • Kura a Rumbu – Chapter Fifty-nine Cover
      by Maryam Farouk (Ummu Maheer) Sai dana tabbatar ya fice daga building ɗin gaba ɗaya kafin na fita daga office ɗin ina kalle-kalle kamar mara gaskiya, ganin babu kowa ya saka na shige Elevator da sauri, a reception na haɗu da Juwairiyya ta kalleni fuska ba yabo ba fallasa kafin tace "Ina kika tafi tun ɗazu?" Wucewa nayi ba tareda na bata amsa ba ta sake cewa "Dr Sulaiman yana neman ki?" Na amsa da "Toh" ba tareda na tsaya ba na fita. A can kan hanya ya tarar dani, fuska ba annuri ya sauke glass yana kallona kafin ya ce "Get in".…
    • Kura a Rumbu – Chapter Sixty Cover
      by Maryam Farouk (Ummu Maheer) Ranar da Bilal ya kwana bakwai a Asibiti aka sallame shi sai Hajja wacce tun zuwan Fadila jikinta ya sake rikicewa sauƙin data fara samu komai yaja baya bata da aiki sai kuka da Allah ya isa ga Ahlan da tace ya yaudaresu ya auri autarta yaje yana azabtar mata da ita. Ganin jikin Bilal yayi sauƙi sai abinda ba za'a rasa ba ya saka aka sallameshi bayan likita ya ja masa kunne sosai akan kulawa da lafiyarsa. Sosai Zulaiha ke tsaye a kansa tana kulawa dashi, yanda Bilal yayi wani sanyi ƙalau lokaci ɗaya…
    • Kura a Rumbu – Chapter Fifty-eight Cover
      by Maryam Farouk (Ummu Maheer) HALIMA Cike da haushin Dr Salman na koma gida ranar Juma'ar, haka nan ya san banda mu zasuyi meeting ɗin amma ba'a gaya mana ba saida muka rigada muka je tukunna sannan babu damar tafiya haka mukayi zaman banza har sha biyu kafin muka tashi. Dama-dama da na ji na samu nayi clearance ɗina kafin na wuce gida. Bayan sallahr magriba Anty Labiba tace mu shirya muje gidan Uncle Mudassir yaronsa na biyu Khalil ya faɗi ɗazu da safe ya samu karaya, muna shirin fita Mama ta kirata tana tambayarta yaushe zamuje…
    • Kura a Rumbu – Chapter Forty-three Cover
      by Maryam Farouk (Ummu Maheer) HALIMA Yanda naga rana haka naga dare, sai naji ashe ma jiya baccin daɗi nayi yaune nake ganin asalin baƙin dare. Sai da aka idar da sallar asuba kafin na samu bacci ya fizgeni, sai dai ban wani yi nisa ba na farka sakamakon kiran suna na da nake ta ji anayi. Na tashi zaune daƙyar ina matse ido haɗi da dafe gefen kaina da nake ji kamar zai faɗo saboda ciwo. Mama na tsaye ta ce "Hala kin manta abinda Abbanku ya faɗa miki shiyasa kika shantake kina bacci har ƙarfe tara". Gabana ya yanke ya faɗi,…
    • Kura a Rumbu – Chapter Forty-four Cover
      by Maryam Farouk (Ummu Maheer) Kafin na kai ga buɗewa Mu'azzam ya ɓalle murfin motar ya fita da sauri, gefe suka matsa, ina kallon su amma ban san mai ya cewa Bilal ɗin ba na dai ga ya kama baki da hannu biyu cikin alamar ninkuwar tashin hankalin da ya fito dashi akan fuskarsa kafin Mu'azzam ɗin ya nufo mota shi kuma ya biyo shi sai dai bai ko sake kallon sa ba ya shiga motar ya tayar. Na waiwaya ina kallon Bilal da ya bi motar da kallo cikin tashin hankali kafin na rufe ido na hoton ganin da na musu tar tamkar a lokacin abun yake…
    • Kura a Rumbu – Chapter Forty-five Cover
      by Maryam Farouk (Ummu Maheer) ALHAMDULILLAH Mun gama biki lafiya nagode da fatan Alkhairi. "Dan girman Allah Anty Amina kiyi mun wannan alfarmar, wlh nayi duk dabarata amma taƙi saurarona, idan naje gidan bata fitowa haka idan na kira wayarta bata amsawa. Ɗazu da safe suka zo ba dan na kulle gidan ta ciki ba ma da tuni sun kwashe kaya. Ke shaida ce ina son Halima duk abinda kuma ya faru sharrin shaiɗan ne da kuma Hajja amma wlh ba a son raina bane" ya faɗa bayan da ya tsayar da Anty Amina a ƙofar gida. Kallonsa ta ringayi har ya…
    • Kura a Rumbu – Chapter Forty-six Cover
      by Maryam Farouk (Ummu Maheer) "Kar kice haka mana Halima. Ke da na san ki jaruma shine zaki bari daga sama wata ta zo ta ƙwace miki miji kuma ki sakar mata? Haba mana dan Allah karki bani kunya. Na san abinda ya aikata miki dole kiji zafi ba ke ba hatta Hajja dake goyon bayansa a ko da yaushe a wannan karon tana adawa da auren nan dan wlh ba dan mun tausheta ba rantsuwa tayi akan sai ya saki yarinyar ba zata tare ba. Mu muka yi ta bata haƙuri saboda a ganina bai kamata ace a gyara ɓarna da ɓarna ba, ubangiji ya rigada ya ƙaddara…
    Note
    error: Content is protected !!