Search
You have no alerts.

    489 Results in the "Hausa Novels" category


    • by Sadi Sakhna .........."zaki iya ki daure kinji,ki daure zaki iya,kin kusa saura kaɗan ,daure daure ga nan kan ina hangoshi" Nurse ɗin take fada,wacce ta haɗa gumi sharkaf saboda firgici. "Nafara gajiya nurse,karfina duk ya ƙare!" Share gumin tayi a karo na ba adadi kafin ta kalli wata wacce take gefenta,da alama tafi waccar ɗin matsayi,dan kayansu ma ba iri ɗaya bane. ""Ke maza hanzarta ki ƙira doctor yanzunnan,kice ana neman sa da gaggawa a labor room 24" "Toh ranki ya daɗe" Ta faɗa tareda zubawa dagudu.…
    • by Sadi Sakhna Ƙwana uku baya............ ________________"Ina jinka ZULUNGUM ya kake ganin za'ayi toh yanxun,nidai duk yanda zakayi kayi,kawai so nake ayi mata kisan wulaƙanci,saita ƙwammaci bata shigo rayuwar mijina ba. Duk wata mace data rabeshi banda maƙiyiya sai ita,zan iya komai kuma domin rabashi da ita. JABEER JAAN(JJ) nawane ni kaɗai a faɗin duniyar nan,ƙaddarar sa ce ya zauna dani ni kaɗai,duk da kuwa bana haihuwa,yanda bazanga ƙwaina ba a duniya,shima bazai taba ganin nasa ba har ya bar duniyar nan,…
    • by Sadi Sakhna Saida taje daff da inda su Hajiya Zeena suke tsaye ta riƙe kanta tareda fara layin ƙaryah. Lylah ce ta kulada ita tace. "Lubna kema kuwa lafiya,naga sai layi kikeyi?" "Uhm kaina ne nake jinsa kaman zai fashe,bana jin daɗinsa ko kaɗan" "Toh ta tafi gida mana,dama waye ya riƙeta,ni nayi mamaki ma danaga tazo wajennan" Hajiya Zeena ta faɗa tana binta da harara. Itama ta wata fuskar ramawa tayi,tareda yimusu sallama tabar wajen,shikuwa uban gayyar dama yayi fushi da ita jiya. Dan haka ko kallon ta bayyi…
    • by Sadi Sakhna Ƙarar jiniyar motar asibiti ce tafara amsa kuwwa a gidan,wanda hakan ne ya shaida alamar shigowa da gawar Hafsa tareda jaririn yaronta cikin gidan. Bayan motar asibitin ta shigo sai kuma motocin su Jabeer suma suka biyo bayanta. Kowanne idan kaga fuskarsa kasan mutuwar ta shigeshi,yanda suke fitowa daga motar jiki a sanyaye. Sashenta aka nufa da ita domin yi mata sallah a ɗakinta,duk abinda ake Lubna bata fito ba,bare tazo wajen yin suturar. Sai bayan an tafi da ita kafin tafito da jumbulelen hijabi a…
    • by Sadi Sakhna "Ke Madeena zoki rakani gidan Hajiya ladi,na daɗe banje ba,kullum cikin samun abin tashin hankali muke" "Kai ummah Binciken semina fah nakeyi,maleeka ta rakaki mana" Haɗe girar ƙasa da sama tayi,tasani sarai babu wani bincike da takeyi,dan tana jin ƙarar game ɗin candy crush a wayar tata,Kawai dai dan kar tajene su haɗu da Al'ameen a gidan,Babban ɗan Hajiya ladi wanda suke son haɗata dashi,shi yana so,amma madeena kam kwata kwata bayyi mata ba. "Banason shashanci dallah sanjo kayanki kizo mu…
    • by Sadi Sakhna "Saki kuma ummah?" "Eh saki haka nace,ko baka jiba kurmane kai nasake maimaita maka,ka rubuta sakinta ka bata tabar gidannan,bana sonta a cikin gidannan" Yawu ya haɗiya mai nauyi kafin yakai hannunsa zuwa kan takardar,tambayoyine suka fara kwaranya a cikin ƙwaƙwalwarsa,meyasa sai shine,meyasa komai shikaɗai zai dunga faruwa dashi? Daga ya fita cikin wanann ifila'in sai kuma yasake shiga wani. Koyaushe shidai bazai daina fita daga chaƙwakiyar mata oho. Biro ya ɗauka tareda takardar baya ya dawo daga…
    • by Sadi Sakhna _________________________ GEMBU babban garine dayake Tsibirin MAMBILA a Sardauna local government dake jihar Taraba a nigeria. Shine gari na karshe daga nan sai a shiga ƙasar camaroo,hakan nw yasa ya zamo gari mai tarin ƙabilu da kuma tarun yaruka,kama daga irin su Bummi wanda sune manyan ƙabilun garin,sanann kuma akwai Mbubo, Ngebu,Fulani. Wannan sune mafiya yawan mutane da ake samu a yankin,saikuma sauran mutane kaman su Igobo,Hausa,da yaruba,dama wasu daga cikin ƙasar camaroo,wanda mafiyansu…
    • by Sadi Sakhna Hasashen sa kuwa bai tafi a banza ba,dan Hajiya zeenah tanajin an fara gangara ta mulmulawa toro ashar. "Kai kuwa wanne ɗan rashin arziƙine,kashe mu zakayi bayan ka karbi kudi,wannan wane irin wajene na kawo kaina ni zeenatu,akan wata biyan buƙata ta duniyah. Juya juya damu na fasa zuwa garin waje saikace hanyar aljanu" Juyowa toro yayi yana dariyah,tareda ƙarewa mutanen cikin motar kallo kafin yace. "Ai hajiya tunda har muka ɗau hanya tofa sai munkaita casss,kuma banda abinki hawa ɗaya fah muka…
    • by Sadi Sakhna Buɗe ido tayi ta kalleta a wani ɗaki mai rufin zana,saidai yanayin zanar wata kalace daban mai ƙarfi da kuma adon rawaya rawaya. Abinda ya farune yafara tariyowa cikin ranta. Kama daga fitowarta daga gida neman wacce zatayi mata maganin lubna,harma da kuma shigowarta wata duniya sabuwa da tayi. Zabura tayi ta miƙe tareda ya mutsa fuska,jikinta yayi tsamin kaman anyi mata dukan tsiyah. Tambaya tafarayi a cikin ranta,akan nan ɗin inane,batakai ga samun amsar tambayar ta ba,kokuma son tunowa yaushe ta…
    • by Sadi Sakhna Har suka fito daga cikin gidan su bombin babu wanda yacewa wani komai,saboda ɗumbin abin mamakin da suka gani. Magana suka ji a gefensu,suna waigawa suka ga ashe saurayin daya rakosu gidanne,yana jingine a bakin motar tasu. "Sannunku da fitowa,na tabbatar masu samu amsar abinda kukaje nemaba" "Taya kasan hakan,ko shiyasa ka tsaya kana jiran mufito,kenan kasan inda take?" "Eh to nasani bankuma sani ba,kunsan ance ba'a aikin banza,zan nuna muku hanyar dazaku bi ku sameta dai. Amma daman batun ku tsaya cikin…
    • by Sadi Sakhna Kwanaki sunzo sun tafi,a ƙallah Daneji ta samu shekara guda babu kaɗan gidan malam Ahmadu,kuma har yanzu babu wata matsala data fito tsakanin ta da mijinta,ko kuma kishiyarta. Tana binta ta sau da ƙafa,itama kuma tana kyautata mata a matsayinta na babba. Tun bayan watanta uku a gidan Malam Ahmadu yafara zaton samun ɗa,amma ganin shuru shuru yasa shi dole ya bar zancen. Daga lokacin yafara zaton wataƙila wata matsala ce daga gareshi. Hakanne yasa ya nunka kulawar dayake basu fiyeda a lokacin baya,domin…
    • by Sadi Sakhna Hannu tasa ta karbi jaririyar tareda mannata a jikinta,wata irin tsagwaron ƙaunar yarinyar ne ya jiyarci tsakiyar zuciyarta,tareda muradin kareta a ta kowacce fuska. Idanuwanta ta sauƙe akan jar fuskar jinjirar,wadda yake ɗauke da ƙankanin kyau mai tafiyar da duk mai kallonta. Hancinta babu makawa kowa yakalleta yaga na ubantane,sai bakinta kuma data biyo irin na mahaifiyar ta ɗan ƙarami,motsashi take a hankali tana neman inda zataji abincinta ya isa gareta,wanda hakan yasa ainihin Cute feature…
    Note
    error: Content is protected !!