496 Results in the "Hausa Novels" category
-
Chapter
Bakar Ayah – Chapter Twenty-nine
A hankali take bude idanuwanta wanda sukayi mata nauyi tamkar anɗora mata dutsi akai. Saurin yunƙurawa tayi zata tashi,amma saitaji jikinta tamkar an ɗaɗɗauresu da wasu boyayyun zarurruka. Ɗakin haskene dashi amma bana hasken rana ba ko kuma fitila,sai na tsabar farin fentin cikin ɗakin. Alamar motsi tafaraji a kanta,a hankali take daga kannata harta sauƙeshi akan fankar datake wainawa tana bawa ɗakin wadatacciyar iska. Baki tasake cikeda mamaki ,dan tunda take bata taba kallon waje mai irin haka… -
Chapter
Bakar Ayah – Chapter Thirty
Sauri take tayi cikin duhun dare,da alama fitsarine ya kamata sosai. Tazo daidai hanyar shiga banɗakin taga alamar wulagawar mutum a sashen goje. Ƙiftawa ido tayi tasake ƙiftawa,dan zaton ko aljani tagani,saidai kuma ta kawar ta hakan a ranta ta wuce banɗakin. Bayan tafito harta nufi ɗakinsu saikuma tashi alamar motsi a sashen kumadu. "To waye ne yashige sashen goje,shekara biyu kenan yadaina kawo mata,tunda kowa yasan babu abinda zai iya yi musu,to waye kuma a sashennasa?" Harzata shiga ɗakin kuma… -
Chapter
Bakar Ayah – Chapter Thirty-one
"Uhm karki ce mai yasa na tambayeki,amma menene haka kike nema a wajen wannan yarinyar,abinfah ya wuce yanda kike zato. Bayan bacewarta daga garinnan komai yafara tafiyah normal,saidai kuma mahaifiyar ta inna Danejo bata manta da batan ƴar ta ba,dakuma mummunan zagin da ake binta dashi. Hakanne yasa abin yafara damunta da kaɗan kaɗan,ga kuma dama ciki mai wahalarwa. Ba a tashi sanin mai ya faru ba har saida tazo haihuwa matsala ta tashi gadan gadan. A nanne mlm Ahmadu ya kaita asibiti amma tagagara… -
Chapter
Bakar Ayah – Chapter Thirty-two
Hamma Hajiya zeenah tayi tareda kallon muruje wanda yakai karshen labarin dayake basun. Kuɗi ta ciro daga cikin purse ɗinta ta miƙamasa tareda yimasa godiyah. "Mun gode da wannan labarin daka bamu,koba komai yanzu munsan mai yake wakana,mu bari mutafi gida,yamma tayi bazamu hau cikin jejin yanzu ba" Zaro ido muruje yayi tareda cewa. "Hajiyah wai har yanzu baki haƙura da zuwa wajenta ba,bazan tambayi mai kike nema ba a wajenta,nagode ni bari na tafi" Fita muruje yayi daga cikin motar yakama… -
Chapter
Bakar Ayah – Chapter One
.........."zaki iya ki daure kinji,ki daure zaki iya,kin kusa saura kaɗan ,daure daure ga nan kan ina hangoshi" Nurse ɗin take fada,wacce ta haɗa gumi sharkaf saboda firgici. "Nafara gajiya nurse,karfina duk ya ƙare!" Share gumin tayi a karo na ba adadi kafin ta kalli wata wacce take gefenta,da alama tafi waccar ɗin matsayi,dan kayansu ma ba iri ɗaya bane. ""Ke maza hanzarta ki ƙira doctor yanzunnan,kice ana neman sa da gaggawa a labor room 24" "Toh ranki ya daɗe" Ta faɗa tareda zubawa dagudu.… -
Chapter
Bakar Ayah – Chapter Two
Ƙwana uku baya............ ________________"Ina jinka ZULUNGUM ya kake ganin za'ayi toh yanxun,nidai duk yanda zakayi kayi,kawai so nake ayi mata kisan wulaƙanci,saita ƙwammaci bata shigo rayuwar mijina ba. Duk wata mace data rabeshi banda maƙiyiya sai ita,zan iya komai kuma domin rabashi da ita. JABEER JAAN(JJ) nawane ni kaɗai a faɗin duniyar nan,ƙaddarar sa ce ya zauna dani ni kaɗai,duk da kuwa bana haihuwa,yanda bazanga ƙwaina ba a duniya,shima bazai taba ganin nasa ba har ya bar duniyar nan,… -
Chapter
Bakar Ayah – Chapter Three
Saida taje daff da inda su Hajiya Zeena suke tsaye ta riƙe kanta tareda fara layin ƙaryah. Lylah ce ta kulada ita tace. "Lubna kema kuwa lafiya,naga sai layi kikeyi?" "Uhm kaina ne nake jinsa kaman zai fashe,bana jin daɗinsa ko kaɗan" "Toh ta tafi gida mana,dama waye ya riƙeta,ni nayi mamaki ma danaga tazo wajennan" Hajiya Zeena ta faɗa tana binta da harara. Itama ta wata fuskar ramawa tayi,tareda yimusu sallama tabar wajen,shikuwa uban gayyar dama yayi fushi da ita jiya. Dan haka ko kallon ta bayyi… -
Chapter
Bakar Ayah – Chapter Four
Ƙarar jiniyar motar asibiti ce tafara amsa kuwwa a gidan,wanda hakan ne ya shaida alamar shigowa da gawar Hafsa tareda jaririn yaronta cikin gidan. Bayan motar asibitin ta shigo sai kuma motocin su Jabeer suma suka biyo bayanta. Kowanne idan kaga fuskarsa kasan mutuwar ta shigeshi,yanda suke fitowa daga motar jiki a sanyaye. Sashenta aka nufa da ita domin yi mata sallah a ɗakinta,duk abinda ake Lubna bata fito ba,bare tazo wajen yin suturar. Sai bayan an tafi da ita kafin tafito da jumbulelen hijabi a… -
Chapter
Bakar Ayah – Chapter Five
"Ke Madeena zoki rakani gidan Hajiya ladi,na daɗe banje ba,kullum cikin samun abin tashin hankali muke" "Kai ummah Binciken semina fah nakeyi,maleeka ta rakaki mana" Haɗe girar ƙasa da sama tayi,tasani sarai babu wani bincike da takeyi,dan tana jin ƙarar game ɗin candy crush a wayar tata,Kawai dai dan kar tajene su haɗu da Al'ameen a gidan,Babban ɗan Hajiya ladi wanda suke son haɗata dashi,shi yana so,amma madeena kam kwata kwata bayyi mata ba. "Banason shashanci dallah sanjo kayanki kizo mu… -
Chapter
Bakar Ayah – Chapter Six
"Saki kuma ummah?" "Eh saki haka nace,ko baka jiba kurmane kai nasake maimaita maka,ka rubuta sakinta ka bata tabar gidannan,bana sonta a cikin gidannan" Yawu ya haɗiya mai nauyi kafin yakai hannunsa zuwa kan takardar,tambayoyine suka fara kwaranya a cikin ƙwaƙwalwarsa,meyasa sai shine,meyasa komai shikaɗai zai dunga faruwa dashi? Daga ya fita cikin wanann ifila'in sai kuma yasake shiga wani. Koyaushe shidai bazai daina fita daga chaƙwakiyar mata oho. Biro ya ɗauka tareda takardar baya ya dawo daga… -
Chapter
Bakar Ayah – Chapter Seven
_________________________ GEMBU babban garine dayake Tsibirin MAMBILA a Sardauna local government dake jihar Taraba a nigeria. Shine gari na karshe daga nan sai a shiga ƙasar camaroo,hakan nw yasa ya zamo gari mai tarin ƙabilu da kuma tarun yaruka,kama daga irin su Bummi wanda sune manyan ƙabilun garin,sanann kuma akwai Mbubo, Ngebu,Fulani. Wannan sune mafiya yawan mutane da ake samu a yankin,saikuma sauran mutane kaman su Igobo,Hausa,da yaruba,dama wasu daga cikin ƙasar camaroo,wanda mafiyansu… -
Chapter
Bakar Ayah – Chapter Eight
Hasashen sa kuwa bai tafi a banza ba,dan Hajiya zeenah tanajin an fara gangara ta mulmulawa toro ashar. "Kai kuwa wanne ɗan rashin arziƙine,kashe mu zakayi bayan ka karbi kudi,wannan wane irin wajene na kawo kaina ni zeenatu,akan wata biyan buƙata ta duniyah. Juya juya damu na fasa zuwa garin waje saikace hanyar aljanu" Juyowa toro yayi yana dariyah,tareda ƙarewa mutanen cikin motar kallo kafin yace. "Ai hajiya tunda har muka ɗau hanya tofa sai munkaita casss,kuma banda abinki hawa ɗaya fah muka… - Previous 1 … 10 11 12 … 30 Next
